Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 22 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an d'aureshi idanunshi a rufe.
Wasu sabbin hawayen ne suka gangaro mata nan tsohuwar tajanye hannunta sannan tace wannan itace k'addararshi bazan ta'ba iya zuwa inceceshi ba, ke kuma ya kamata kafin gobe kiyi nadamar maganar da kika fad'a min idan har kinason cigaban rayuwarki inko ba haka ba kema kanki zaki mutu.

Matsowa tayi kusa da matar tana me cigaba da kuka tace bazan ta'ba nadama ba indai a kan kainane saidai zan iya Nadama indai har zaki ceci Faruk kije kiku'butar da shi.


Bushewa tsohuwar tayi da dariya sannan tace dakyau jawahir hakan ya yi miki kyau, saidai ni bazan ta'ba taimaka ma wanda kikeso intaimaka ba saboda ni bana taimako abu guda kawai nake kuma shi na iya shine *'DAUKAR FANSA*

Jawahir kasa cemata komai tayi nan taduk'ar da kanta tana me cigaba da kuka cike da tashin hankali.....


______

Gidan su Faruk mutane zuwa suke suna yi ma iyayenshi jaje dan gidan komawa yayi kamar gidan gaisuwa mutane sai shiga da ficce sukeyi inda suke addu'a Allah yabayyanar da shi.
Hatta limamin unguwar kullum sai ya zo anyi safka sannan ayi abincin sadaka a raba.
Iyayenshi duk sun fita hayyacinshi saboda tashin hankalin da suka shiga.


A ranar yau da takasance kwanan Faruk ukku baya gida, Dad d'inshi yana zaune a setting room shi kad'ai ya buga tagumi Barr Nas yazo gidan duk sallamar da yayi Dad baijiba saida yad'an buga k'ofa sannan yad'ago yakalleshi yace bismillah Nasir kashigo man.
Shiga yayi yazauna a k'asa suka gaisa bayan sun gaisa ne Dad yace Nasir kuna ta k'ok'ari gaskiya mungode sosai, a yanzu mudaina wahalar da kanmu wajen yawon nemanshi mucigaba da addu'a indai har yana raye Allah zai bayyana mana shi, saidai abinda nake zargi mutanen da suka ta'ba kirana waya sukace ingargad'eshi yacire hannunshi daga wani case ina tunanin sune suka sace min shi dan a ranar da akayi maganar a ranar ya'bata.

Cikin sanyin jiki Barr Nas yace Dad wane mutane ne? Me sukace maka?

Kwashe komai yayi yafad'a ma Barr Nas.
Mamaki yacikashi yace tabbas wad'annan mutanen akan case d'in Jawahir ne.

Eh tabbas hakan sukace wai yajanye akan case d'inta ammah wacece ita? Meyasa zasuyi min haka da sunbi ta lalama ai da na sashi ya janye.

Shuru Nasir yayi sai chan yace tabbas case d'in akwai rikitarwa a cikinshi saidai ita yarinyar tana a kan gaskiyarta wannan dalilin ne yasa Faruk yakeso yawanketa a idanun duniya daga zargin da akeyi mata, saidai a yanzu lokaci ya k'ure na tabbata a gobe idan har babu lauyan da zai tsaya mata kasheta za'ayi gashi Barr Faruk shine kad'ai zai iya tsaya mata.
Jinjina kai Dad yayi yace Allah yakyauta, Allah dai yabayyanar da shi a duk inda yake.
Barr Nas ya amsa da Ameen sannan yayi mashi sallama yatafi.



Nasiba saboda tashin hankalin da tashiga ko baccin kirki bata iyawa abinci ko ba'a magana sai Mummynta ta yi dagaske sannan take samu tana d'anci kullum cikin kuka take, Daddynta ko shareta yayi yafita batunta.

Yau ma kamar kullum Hajiya Maijidda ce tashigo da azuhur tasameta zaune saman darduma da alama sallah tagama saidai ta jingine jikinta a jikin gado tana hawaye, tsayawa Hajiya Maijidda tayi tana kallonta sai kuma chan tataka ta isa wajenta a saman gadon tazauna cikin lallashi tace haba Nasiba wai meyasa kikesa ma ranki damuwa addu'a fa yakamata kiyi mashi duk inda yake Allah zai bayyana mana shi.
Goge hawayen fuskarta tayi tare da gyara zamanta ta fuskanci mahaifiyartata sannan tace Mummy dan Allah taimako d'aya nakeso kiyi min.
Toh ina jinki wane irin taimako ne?

Saida takalli k'ofa sannan tace dan Allah kitaimaka min kibarni inje gidansu Faruk ingano Mom d'inshi na tabbata tana chan hankalinta a tashe, nima zuwana zai sa ind'anji sauk'in rad'ad'in da nakeji a raina.

Jimm tayi sannan tace Nasiba kinsan mahaifinki baya so ranshi 'baci zaiyi.


Kamar jira take tafashe da kuka tace Mummy kitaimaka min wajenki ne kawai nake jin dad'i kin san yadda nakeson Faruk hankalina bazai ta'ba kwanciya ba idan banje naji halin da ake cikiba yanzu.
Cikin sanyin jiki tace shikenan Nasiba tashi kije ammah kar kidad'e saboda kar Daddynki yadawo bakinan kinsan ba ke ba hatta ni kaina sai raina ya 'baci.
Murmushin jin dad'i tayi tace nagode sosai mummyna.
Shafa kanta tayi tace bakomai dota idan kinje kigaishe min da Hajiya Nuratu.
Toh insha Allahu zataji Mummy, nan tamik'e tashirya tafita tana Allah Allah kar suhad'u da Daddynta a lokacin da zata fitar da motarta sai gashi cikin ikon Allah har tatafi bai dawo ba.....










_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 19*

Washe gari ya kama ranar litinin tun da safe a gidan kaso akasa duk wani wanda za'aje kotu da shi yayi wanka yashirya, jawahir tunda tashirya zaune tayi tana tunanin halin da Faruk yashiga akanta ko kad'an fuskarta babu alamun fara'a dan jiya ko rintsawa bata samu tayiba, abinda zai ba mutum mamaki ita hankalinta bai tashi akan zaman kotun da za'ayi ba, bah wai kuma dan tana da tabbacin zata tsira ba dan tasa ma ranta dole cikin biyu ayi d'aya ko rayuwa ko mutuwa ko da ta ma fi bama ranta mutuwar dan tasan itace kawai makomarta.


Kamar yadda aka saba a duk ranar da za'a shiga kotu akan case d'in jawahir ana yin sanarwa a gidajen yad'a labarai saboda za'a iya cewa mafi yawa daga cikin mutanen da suke garin katsina sun san da case d'inta dan abinda ba'a ta'ba jin an aikata bane sai akanta, musamman ma da akasan manyan mutane ne masu hannu da shuni ake zarginta da kisansu, wannan dalilin ne yasa duk ranar da za'a shiga kotu akan case d'inta mutane dadama suke zuwa acika kotun mak'il, wasu ko ba komai yake kawosu ba sai dan suzo sugane ma idanunsu yarinyar da akace tana da k'arancin shekaru takeyin kisan.


Dad d'in Faruk da a yanzu ko baccin kirki baya samu yayi saboda 'bacewar d'anshi, yau ma tunda yadawo sallar asuba bai koma bacci ba Redionshi yajawo yakunna yana daga kwance saman doguwar kujera dan a yanzu ya fi sauraren Redio ko dan saboda yana tunanin a nan zai iya samun bayyanar d'anshi indai ma ansameshi a wani wajen, yana cikin sauraren labaran safiyar yau akan abubuwan da suka farune yaji ana sanarwa
"Gwamnatin jihar katsina zata bada tallafi ga wad'anda 'yan ta'adda suka shiga garuruwansu suka kashe masu 'yan uwa sannan suka kora masu dabbobi suka tafi da su, inda me girma gwamna yayi sanarwa zai taimaka masu da tallafi.

Sannan a cikin labaran na mu zakuji cewa a yau ne za'a yi zama na k'arshe a kotu akan case d'in Jawahir Muhammad Maikud'i wadda ake zargi da kashe kawunta da 'ya'yanshi wanda daga baya hukuma tagano hadda mijinta aciki sannan tasambad'a abokan mahaifinta suka ziyarci lahira inda dangin mamatan suke k'ararta akan suna so abi masu hak'k'in rayuwar 'yan uwansu, ko me ya jawo ma yarinyar yin kinsan? Wannan ne bamu saniba dan har yanzu ba'a samu wata k'wak'kwarar hujjaba guda d'aya da me laifin tabayar saidai jitajitan da mutane sukeyi, koma me kenan kukasance da mu da anjima acikin labaran mu dan jin yadda shari'ar ta kasance..

Haka kuma a cikin labaran namu zakuji cewa...
Dad tsaki yaja tare da kashe redion yakunna TV dan yakalli News tunda yakunna TV d'in kallo kawai yake ammah hankalinshi ba a wajen yakeba abinda yatsaya mashi a rai case d'in yarinyar da yaji ansanar musamman ma sunan da aka ambata Jawahir Muhammad Maikud'i tabbas zai iya cewa 'ya ce ga Marigayi Alhaji Muhammad Maikud'i inko ba haka ba toh sunan ya zo iri d'aya da nashi toh ammah shima ya san yana da d'iya guda d'aya bazai iya cewa ga sunanta ba, anya kuwa itace ba wata bace ta daban ba?
Toh ko dai itace Jawahir d'in da Faruk yatsaya mawa wadda saboda case d'in ake barazana a rayuwarshi, tabbas ko zaya iya zama itace dan zai iya tuna labarin da Faruk yabasu akan case d'in ya ce ana zarginta akan kisa.
Jinjina kai yayi yace tabbas itace wannan saboda ita aka d'auke min d'ana....haka yayi ta tunane tunane inda daga k'arshe yakasa kallon News d'in yakashe TV d'in yayi kwance yana tunanin halin da d'anshi yake ciki a yanzu ko da rai ko kuma babu rai.



_______
A chan 'bangaren Faruk yana kwance a saman gado ko runtsawa bai samu yayiba saboda tashin hankalin da yake ciki musamman akan shara'ar da za'a gabatar a yau ta jawahir, ko da daman ba samun wani baccin kirki yakeba saboda halin da yake ciki ga d'aurin da akayi mashi wai dan kar yagudu ahaka yake kwanciya.

Hatta sallah sai ya yi dagaske sannan suke barinshi yayi shima sai kusan mutum ukku sun tsareshi sannan.

******
Wajen k'arfe Taran safe aka fiddo wad'anda za'a yi shara'a akan case d'insu aka saka cikin mota aka nufi kotu inda motocin 'yansanda suka kasance gaba da bayan motarsu, tunda suka fara tafiya matan suka dinga bin titi da kallo masu farin ciki sunayi masu bak'in ciki nayi akan case d'insu dan kowa ya san makomarshi, jawahir ko jingine jikinta tayi a inda take zaune yanayinta kawai zaka kalla kagane tana cikin tashin hankali saidai abinda zai baka mamaki ba wai akan case d'inta tashiga tashin hankalinba ta shiga ne saboda halin da Barrister yashiga akanta, wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin sa hannu tagoge, a cikin zuciyarta tana addu'a Allah yasa ko bayan ranta Faruk yaku'buta daga sharrin mutanen nan, ahaka har suka isa HIGH COURT bata saniba saida aka bud'e aka fara fita sannan takusa da ita tata'bota tafito.....


********

Nasiba bayan ta gama sallar asuba da azkhar d'inta gari yana fara haske fitowa tayi dan tagaishe da iyayenta kamar yadda tasaba saidai da ka kalli fuskarta zakaga alamar bata runtsaba, hanyar part d'in mahaifinta tanufa tana isa a parlor taji muryarshi yana waya har zata d'age labulen tashiga sai kuma tafasa taja tatsaya dan yagama wayar abinda taji yana fad'a ne a wayar yad'aga mata hankali sosai saurin sa hannu tayi tatoshe bakinta tare da zaro idanu gabanta wani irin mummunan fad'uwa yayi tayi saurin ja da baya lokacin da taji yana cewa "Haba Alhaji Mansur ai kar kadamu tunda dai Faruk yana hannunmu nasan yarinyar nan ta shiga damuwa sosai saboda ba lauyanta,,, dariya yayi sannan yace ai ya kamata muma muje High court d'innan ayi shara'ar a gabanmu akasheta kowa yahuta kaga shikenan sai mucinye sauran dukiyar hankalinmu kwance.
Eh daman ka fad'a min kunyi magana da Barr M.B jiya toh shikenan koma menene sai mun had'u a kotun".

Saurin juyawa tayi dagudu tabar wajen tare da fashewa da kuka tana isa parlor taci karo da mahaifiyarta da tafito daga part d'inta, kallonta tayi tace lafiya Nasiba.

Jikinta tafad'a tare da k'ara sautin kukanta.

Kingani ko kedai bakijin magana yanzu haka wani laifin kikayi ma Daddyn naki ko? Na fad'a maki kicigaba da addu'a indai Faruk yana raye zaya dawo.
Cikin sheshek'ar kuka tabud'e baki tace Mummy...sai kuma tayi shuru.
Rik'ota Hajiya Maijidda tayi tace shikenan kiyi hak'uri muje inrakaki d'akinki kikwanta kafin agama had'a breakfast insa akawo maki.

Tana a jikin Mummyntata a haka sukaje tarakata har bedroom d'inta saida talallasheta tadaina kukan sannan tatafi.

Nasiba tana ganin ta fita mik'ewa tayi taje tarufe d'akinta tacigaba da kukan maganganun da taji mahaifinta yana yi a waya suna dawo mata, kanta tafara tambaya tana cewa kenan su Daddy sun san inda Faruk yake? Ammah akan me suke magana dukiyar wa zasu cinye?
Ko dai akwai gaskiya akan maganar da Faruk yafad'a akan Daddynta?

Saurin girgiza kai tayi tace a'a Daddyna ba haka yakeba kawai dai suna magana akan wani abun nadaman ammah kuma.....komawa tayi takwanta tare da dafe kanta da taji ya fara sara mata nan hawaye suka cigaba da ambaliya a fuskarta....


__________

Tunda aka shiga kotun waje aka samar masu su kusan hud'u ne suka zauna, mutane ne sosai a cikin kotun, ahankali ahankali ake zuwa lokaci guda kotun tacika mak'il da jama'a ana jiran k'arasowar alk'ali inda gabad'aya ciki da wajen kotun zagaye take da police, a gaba kuma lauyoyin masu k'ara da wad'anda ake k'ara ne zazzaune, goma saura minti biyar alk'ali yafito nan gabad'aya mutanen suka mik'e har saida yazauna sannan kowa yazauna.

Court Reporter ne yamik'e yayi sallama tare da yin addu'a bayan anshafa ne sannan yace a yau 2 ga watan Afurili (April) wanda yayi daidai da 7 ga watan Rajab......Shara'a ta farko da zata kasance a yau itacs Shari'ar Maimuna Ahmad wadda ake zargi da zuba ma mijinta guba a cikin abinci yaci yamutu daga k'arshe dangin mijin sukayi k'ararta bayan antabbatar masu da guba ce takasheshi, juyawa yayi yakalli Alk'ali yace Allah yagafarta malam wannan itace shari'ar tamu ta farko, jinjina kai Alk'ali yayi nan court reporter yaje yamik'a ma alk'ali file d'inta.


Dattijon Alk'alin gyara zaman farin glass d'inshi yayi a saman fuskarshi sannan yaduba file d'in ya d'au kusan minti biyar a duk'e sannan yad'ago kai yace kotu tana buk'atar ganin Maimuna ta bayyana a gabanta.

Jawahir da tunda taji za'a fara karanto k'ara taruntse idanunta dan a tunaninta shari'ar ta ce za'a fara'a bata bud'eba sai da taji ta kusa da ita ta fara kuka ahankali sannan tabud'e takalleta da alama itace Maimuna nan wasu police mata guda biyu sukazo suka jata suka tafi da ita wajen da aka tanadar ma me k'ara da wanda ake k'ara dan sutsaya.

Alk'ali d'agowa yayi yakalleta sannan yaduk'a yafara 'yan rubuce rubuce sai kuma yad'ago yace kotu tana buk'atar ganin lauyan me k'ara da na wadda ake k'ara.

'Daya daga cikin lauyoyin da suke zaune ne a layin gaba yamik'e yayi sallama sannan yace sunana Barr Mu'ammar nine lauyan da yake kare wadda ake k'ara sannan yakoma yazauna, Barr Junaid da yake zaune ya yi zugum bai ma san abinda ake tattaunawa ba saboda hankalinshi yana wajen abokinshi da ya'bata tsawon kwanaki hud'u, Barr Bilal ne yad'an zunguroshi da biron hannunshi sannan yadawo hayyacinshi saurin mik'ewa yayi yai sallama sannan yace sunana Barr Junaid nine lauyan da yake kare mek'ara.

'Dago kai Alk'ali yayi yakalleshi sannan yaduk'a yayi 'yan rubuce rubucenshi.

Yad'ago kai yace kotu tana so maimuna tabayyana mata gaskiya a game da kisan da ake zargin ta yi ma mijinta ta hanyar ciyar da shi guba.

Sheshek'ar kuka tafara yi saida megabatar da k'ara yamik'e yasake maimaita mata jawabin alk'ali sannan cikin inda inda tace bani bace nakashe shi dan lokacin da yamutu bana gidan.

Alk'ali ganin ta yi shuru bata sake cewa komai ba yasa yaduk'a yayi 'yan rubuce rubuce sannan yad'ago yace shin ko Lauyan wad'anda suke k'ara yana da shedar da zai bayyana ma kotu wadda zatasa tagamsu da cewa maimuna ce tayi kisan bayan a yanzu maimuna ta nuna ba itace tayi kisan ba.

Mik'ewa Barr Junaid yayi yace tabbas ina da ja ya maigirma mai shara'a inaso kotu taban dama ind'an yi wasu tambaboyi ga maimuna.
Kotu ta baka dama,,, cewar alk'ali.

Fitowa Barr Junaid yayi yanufi wajen da take tsaye yace malama maimuna shin ko zaki iya sanar da mu kina ina a lokacin da mijinki yamutu?
Inda inda tafara yi tace na je gidan 'yar uwata ranar ban gida nima saidai nadawo natarar da gawarshi.

Murmushi Barr Junaid yayi yace shikenan abinda kika sani?
'Daga kai tayi alamun eh.

Juyawa yayi yakalli alk'ali yace ya megirma me shara'a maimuna bata amsa laifinta ba saidai duk na kusa da ita sunsan cewa itace tayi kisan.

Lauyan wadda ake k'ara ce yayi saurin mik'ewa yace ya me girma me shara'a ya kamata a tsawatarwa lauyan wanda suke k'ara yagyara jawabanshi dan sunyi muni ga wadda ake k'ara.

'Dagowa Alk'ali yayi yakalli Barr Junaid yace kagyara bayaninka.

'Dan duk'ar da kai yayi cikin girmamawa yace na gode, sannan yad'ago yace ya megirma me shara'a inaso kotu taban dama ingabatar da shedu.
Kotu ta baka dama.

Godiya yayi yace malam zubairu me gadi da Talatu me aikin gidan sune sheda.

Alk'ali ne yace kotu tana buk'atar ganin Malam Zubairu me gadi gidan Sadik'u da Talatu me aiki sun gurfana a gabanta.

Su dukansu suka fito nan aka sa su sukayi rantsuwa akan zasu fad'i gaskiya sannan aka tambayesu suka bada shedar cewa babu inda taje a ranar tana gida inda 'yar aikin gidan tak'ara da cewa a gabanta ta ga me d'akintata ta fiddo wani abu cikin leda ta zuba a cikin abincin wanda yaci yamutu.


Maimuna na jin haka tafashe da kuka tace talatu sharri zaki ja min Allah ya isa ban yafeba, police d'in da suke bayanta tsaye ne suka daka mata tsawa tayi shuru, Barr Junaid cewa yayi sukoma suzauna sannan yamaida kallonshi ga alk'ali yace ya megirma me shara'a bayan wannan shedar ina da shedar report d'in da likita yabada na mutuwar mamacin inda ya rubuta ya ci guba sannan an d'auko abincin da yaci anduba anga akwai guba a ciki.

Alk'ali ajiye biron hannunshi yayi yace ina sheda?
Barr Junaid d'auko wata farar takardar yayi yaje yamik'a ma alk'ali yace ya me girma me shara'a wannan itace shedata sannan a cikin file d'in mamacin ma akwai shedar hakan, nan yaje yad'auko file d'in yakawo ma alk'ali yace jiya na amsoshi a asibiti.


Dubawa alk'ali yayi sannan yad'ago yakalli wadda ake k'ara yace shin ko kina da ja akan wannan shedun da aka samo?
Shuru tayi tana cigaba da kuka ganin haka yasa lauyanta yamik'e yace ina da ja ya megirma me shara'a abinda lauyan masu k'ara yafad'a ba gaskiya bane.

Cikin kuka tace tabbas hakane nice nakasheshi saboda bana sonshi iyayena ne suka aura min shi, wallahi nice nakashe shi.

Alk'ali yace kin tabbata kece?
'Daga kai tayi alamun Eh.

Duk'awa yayi yai 'yan rubuce rubuce sannan yad'ago yace Alhamdulillah kin amsa laifinki bayan duk bayanai sun nuna hakan dama, dan haka kotu zata yanke maki hukuncin zaman gidan kaso har k'arshen rayuwarki domin laifin da kika aikata na kashe mijinki wannan shine adalcin kawai da zamuyi.


Kuka tacigaba da yi cike da tashin hankali nan aka tafi da ita.


Jawahir wani irin tausayinta taji ganin yadda take kuka saidai me matar itace me laifi babu yadda za'ayi.

Haka me gabatar da k'ara yamik'e yasake bayani akan k'ara ta biyu aka fito aka fara yin shara'a.


Jawahir tana nan tsaye saida akayi ma mutane hud'u inda wasu aka yanke masu hukuncin kisa wasu kuma aka maidasu gidan yari, ita d'in kanta ta san dole cikin biyu za'ayi guda ko kisa ko yanke hukuncin k'arashe rayuwa a gidan kaso, wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata cikin zuciyarta tace Barr Faruk rayuwarka kawai nakeji ba wai abinda zai faru da ni ba, ina ma ace Ammi zata taimaka taku'butar da kai.



Ana gama wad'annan shari'o'in megabatar da k'ara yamik'e yace sai shari'ar da takasance ta k'arshe a wannan ranar itace shari'ar Jawahir Muhammad Maikud'i wadda ake zargi da yin kisa na mutane d'aid'aya har mutum bakwai, inda dangin mamatan suka shigar da k'ara,, sannan yaje yamik'a ma alk'ali file d'in,
kotun kacamewa tayi da surutu saida alk'ali yad'an buga tebirinshi sannan akayi tsit,


Duk'awa yayi yafara duba file d'in ya d'auki lokaci yana dubawa sannan yad'ago yace kotu tana buk'atar ganin Jawahir wadda ake k'ara ta bayyana a gabanta.

Police d'in matan nan ne guda biyu suka fito da ita tatsaya a wajen da ake tsayawa, me karanta k'ara yace ya me girma me shari'a wannan itace Jawahir.
'Dago kai alk'ali yayi yakalleta nan yashaidata sannan yacigaba da cewa kotu tana son ganin lauyan masu k'ara da na wadda ake k'ara.

Barr MB ne yamik'e yayi sallama sannan yace sunana Barr Mahamud Bello nine lauyan masu k'ara,, sannan yakoma yazauna.

Shuru babu wanda yasake mik'ewa daga cikin lauyoyin, Barr Junaid dafe kanshi yayi tare da runtse idanunshi saboda tsananin tashin hankalin rashin abokinshi dan shi kanshi shara'ar da sukayi ta maimuna ya san ya yi k'ok'ari sosai a yadda ya iya yinta saboda tashin hankalin da yake ciki.
Me gabatar da k'ara ganin babu wanda yamik'e daga cikinsu yasa yak'ara cewa kotu tana son ganin lauyan wadda ake k'ara.

Jawahir idanu tazuba ma lauyoyin lokaci guda tasafke idanunta k'asa dan ta san babu lauyanta a ciki.

Me gabatar da k'ara ne yasake maimaitawa nan Barr MB yamik'e yakalli alk'ali yace ya me girma ne shara'a lauyan wadda ake k'ara ya gudu saboda baida bayanan da zai kare wadda ake k'ara da su.
Karaf a kunnuwan Barr Junaid lokaci guda yamik'e a harzuk'e yace k'arya ne ya me girma me shara'a lauyanta ba guduwa yayi ba akwai dalili me k'arfi da yahana bayyanarshi, kallon Barr Mb yayi yace ya kamata kadinga gyara kalamanka sannan yakoma yazauna.

Barr MB d'an rissinawa yayi sannan yakoma shima yazauna.

Alk'ali da yake kallonsu bayan sun zauna ne yace shin ko akwai wanda lauyan wadda ake k'ara yawakilta a cikinku?
Su duka shuru sukayi nan yasake cewa ko akwai wanda zai kare wadda ake k'ara?
Nan ma shuru.

Dan haka yaduk'a yayi 'yan rubuce rubucenshi sannan yad'ago yakalli jawahir yace Malama Jawahir kamar dai yadda shari'ar tamu ta baya takasance tsawon shekara d'aya har yau kin kasa amsa laifukanki akan zargin da akeyi maki shin ko a yau zaki iya kare kanki kafin kotu tazartas da hukunci na k'arshe?

'Dago kanta tayi takalli alk'ali sannan tamaida idanunta ga d'unbin jama'ar da suke zaune wajen kowa idanunshi akanta suna jira suji abinda zata fad'a, karaf idanunta suka safka akan mutum biyu.
Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan murmushin mugunta suka sakar mata.
Idanu tazuba masu bata ko k'yaftawa musamman ma Alhaji Sufyan nan hawaye suka fara gangarowa daga cikin idanunta, tana ji kamar taje tashak'esu

Alk'ali sake maimaita mata tambayar yayi ammah bata ma san yana yi ba, saida police d'in wajen suka d'an ta'bota sannan tadawo hayyacinta.

Ganin bata ce komai ba yasa alk'ali yace shin ko Lauyan masu k'ara yana da k'wak'k'warar shaidar da zata ida bayyanar ma kotu cewa jawahir ce tayi kisan?

Mik'ewa Barr MB yayi yace tabbas ina da ita ya me girma me shara'a inaso kotu taban dama ind'anyi ma jawahir wasu 'yan tambayoyi.
Dama alk'ali yabashi nan yawuce yanufi inda jawahir take tsaye....



_____****______


Barr Faruk hankalinshi atashe yake a ranar duk k'ok'arin da yayi dan yakwance kanshi kasawa yayi yana nan zaune inda aka d'aureshi idanunshi suna a kan agogo har k'arfe tara da rabi tabuga, kallonsu yayi yaga suna zaune su biyu dan sauran ukkun basunan sun fita tare da ogansu gashi wad'anda sukafi rashin mutuncin ne suke zaune babu damar yarok'esu, runtse idanunshi yayi ahankali yace kiyi hak'uri Jawahir banda yadda zanyi in ceceki wannan itace k'addararki saidai ina maki fatan Allah yatseratar da ke,,, bud'e k'ofar da akayine yasa yai saurin bud'e idanunshi sai ganin d'aya daga cikinsune yashigo d'auke da takeaway, sauran yaji sunce ya dai bahbah wani abu aka kawo mana?
Zuwa yayi ya ajiye masu kowa takeaway guda yace wani aiki ne mukayi da oga yau mun samu kud'i sosai cikin kud'in ne yace ink'ara siyo mana breakfast tunda bamu k'oshiba, su dukansu dariya sukasa sukace dakyau, nan yakoma yazauna kusa da su, su kuma suka d'auka suka fara ci, Barr Faruk yana kallonsu suka ci abincinsu shi ko ba'ayi mashi ko tayi ba.
Faruk wasu irin hawaye ne masu gumi suka gangaro mashi saboda tsananin tausayin halin da Jawahir zata shiga yau, runtse idanunshi yayi yana cigaba da yi mata addu'a a cikin zuciyarshi.
Jin su yayi shuru dan haka yabud'e idanunshi sai gani yayi mutane biyu daga cikinsu sun hankad'e kai saman kujera suna bacci inda d'ayan yake zaune yana kallonshi.
Mamakine yakamashi cikin ranshi yace daga gama cin abinci sai bacci.

Bai ankaraba kawai sai gani yayi babu mutumin a wajen, mamakine ya ida kamashi yace ikon Allah ina mutumin nan yayi?

Murya ce yajiyo a bayanshi me firgitarwa wadda sautinta tacika d'akin gabad'aya yaji ance "barka da wannan lokacin Barr Faruk"
Yunk'urin waigawa yayi dan yaga me magana ammah yakasa saboda d'aurin da akayi mashi.

Ji yayi anbushe da wata irin mahaukaciyar dariya wadda tasa saida

Please Login or Register in order to submit comment