Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 17 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi yace hakane kuma bari inje inkawo maka ruwan dan na nan ciki basuda sanyi inyaso in nagamu da shi sai infad'a mashi.
'Daga kai kawai yayi dan baya ji a yanzu zai iya magana saboda tsananin tsoron da yashiga juyawa Nazir yayi yafita dan samo ma abokin nashi ruwa.

Yana fita Nas yana son yamik'e ammah yakasa jikinshi ssi rawa yake yana nan zaune sai ga Faruk ya fito yana fitowa cikin sauri yarufe d'alkin, jin motsin tafiya yasa yawurgo ma Nas key d'in yayi saurin juyawa tare da kanga wayarshi a kunne kamar yana waya.
Nas tura key d'in yayi a k'ark'ashin throw pillow d'in da Nazir ya ajiye key d'in daidai lokacin Nazir yashigo yana cewa na sa yanzu za'a kawo maka.
Ajiyar zuciya Nas yasafke ganin asirinsu bai tonuba.
Nazir kallon Faruk yayi da yajuya yana waya yace ashe ya dawo ai da nafita ban ganshiba.
Murmushi Nas yayi yace Eh kana fita yadawo kuma aka sake kiranshi waya shine yamatsa chan yana yi.

Nazir yace Allah sarki yanzu kuzo mukoma setting room na san sun ragu gashi fitarnan da nayi andameni infito inrufo d'akin.
Murmushi Nas yayi yace haba ba damuwa ai mu ba bak'i bane, daidai lokacin Faruk yajuyo yana murmushi yace bakomai ai yanzu ma zamu tafi dan daga wajen aiki ake min neman gaggawa.

Nazir yace tun yanzu maimakon kubari sai anjima.
Kar kadamu muma munso mubari sai da anjima dan dai kiran gaggawar da akayi min ammah zamu dawo wani lokacin.

'Dauko key d'in Nazir yayi yace toh shikenan sai mufita gabad'aya in mik'a masu key d'in inhuta.

Faruk yana lura da Nas da yake ta yi mashi kallon tuhuma ammah yak'i kulashi ahaka har suka fita.
Saida suka jirashi yafara mik'a key d'in wa Ummanshi sannan suka tafi yarakasu har wajen mota yayi masu godiya suka shiga suka tafi, suna fara tafiya Nas yajuyo yakalleshi yace wai ya dai Faruk sai alama nake ta tambaya kuma ka gane nufina ammah kashareni wallahi hankalina ya tashi sosai Allah ya taimaka guy d'in nan bai gane komai ba.

Murmushi Faruk yayi yace daman ya gane da kai zaka fi kwana ciki tunda abokinka ne.

Au haka ma kace ko?
"Toh me kakeso ince?

Yanzu dai fad'a min shin ka d'auko wayar ko kuwa hakanan kafito baka gantaba?

Murmushi yayi yace Eh toh banga wayar ba.

Kana nufin baka gantaba hakanan kafito?,, Nas yatambayeshi cike da mamaki.

Juyawa yayi yakalli taga sannan yace ina nufin ban gantaba a inda jawahir ta fad'a min saidai na ganta a wani wajen na daban.

Ajiyar zuciya Barr Nas yasafke yace Alhamdulillah na ji dad'in haka gaskiya Barrister kai d'in nadaban ne saisa ko a school nake jinjina maka dan k'walwarka tana ja sosai.

Juyowa Faruk yayi yakalleshi tare da fiddo wayar daga cikin aljihunshi yana murmushi yace tabbas ina farin ciki Nas ko ba komai wayar nan zata taimaka min wajen samun duk wani abu da nakeso, yanzu dai mu wuce gidana kasafkeni dan ko motsta bazan d'auko gidanka ba.

Kallonshi Nas yayi yace ban gane insafkeka ba malam, muje dai ind'auko su Madam inmaidasu gida inyaso kaga sai muwuce gidan naka ko ba haka ba?

Hakan ya yi abokina ai duk yadda kakeso haka za'ayi dan yau ba k'aramin taimako kayi min ba.

" yoh ba dolena intaimakeka ba tunda nima ka taimaka min wajen samo soyayyar madam a school"

Su dukansu dariya sukasa nan Faruk yagirgiza kai tare da juyawa yana cigaba da kallon taga.




Bayan sunyi sallar magrib a cikin anguwarsu Faruk sannan suka wuce gidanshi a parlor suka zauna Faruk yaso yakunna wayar ammah yajita a kashe alamun ba charge dan haka yatashi yajonata sunayin sallar isha'i Barr Nas yace shi zai wuce gida koma menene inyaso gobe zasu had'u.
Barr Faruk yace babu damuwa nan yarakashi har wajen mota yana tsokanarshi tashin hankalin da yaga ya shiga lokacin da yafito cikin d'akin.
Barr Nas yana dariya yace ka ma yi sa'a da bakaga na saki zawo ba dan wallahi har na hango makomata gaskiya na yi kasada dayawa Allah dai ne yacecemu.
Hakane Nas ni fa daman kai nafi ji ba kainaba dan banaso inja maka wani abu yasameka.

Hmm toh yanzu ya za'ayi idan zaka maida wayar?

Barr Faruk yace a'a bazan maidata ba tunda shima ba tashi bace idan nagama bincikena zansan yadda zanyi da ita.

Toh shikenan Barrister Allah dai yataimaka sai dai goben idan na shigo.
Toh Allah yakaimu.


Bayan tafiyarshi Faruk wanka yayi yashirya wajen k'arfe tara yacire wayar daga charge yafara bincika abubuwan da suke cikinta ya samu shaidu sosai dan hatta recordings ya samu na wayar da akayi har da wanda alamu yanuna anyi recording antura ma wani ya saurara, wata murya da yaji anyi waya da me ita saida yaji kamar ya san muryar ammah yakasa tantanceta.

Cikin contacts yashiga yafara binciken numbobin ciki nan yaci karo da number d'in da tad'aga mashi hankali saurin d'auko wayarshi yayi yasaka number d'in yayi dialing a nan ya ida tabbatarwa da tabbas number d'ince hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba, ajiye wayar yayi tare da dafe kanshi ji yayi komai ya tsaya mashi, chan kuma yamik'e yafara zagaye d'akin yana zuwa yana dawowa hannuwanshi suna a bayanshi ya rik'esu tunowa yafara yi da lokacin da jawahir take ce mashi zaka taimaka min kana nufin komai kusancinka da mutum idan har yana da hannu a ciki bazaka ta'ba barinshi ba?
Cize le'be yayi a hankali sannan yakoma yazauna yak'ara d'auko number yasake dubawa tabbas idanunshi ba gizo sukeyi mashi ba toh ammah me hakan yake nufi kenan shima akwai hannuwanshi acikin mutuwar mahaifan Jawahir? A'a kodai abokinshi ne kawai ammah baida hannu acikin mutuwarsu, toh ammah call recording d'in da naji fa tabbas akwai na muryarshi ya ji shi, sake kunno recording d'in yayi yasaurara muryarce yaji tana cewa Hello kana jina ya kamata kayi k'ok'ari wajen ganin ka samo mana file d'in filin nan dan da alama zaiyi kud'i sosai ni na san yadda za'ayi asiyar da shi batare da kowa ya ganeba dan nima kaga wannan filin da kabarmin gwamnati nasiyar mawa kuma ta siya da kud'ad'e masu tsoka.
Toh shikenan Alhaji koma me kenan nasan hanyar da zanbi insamo dan dama maganar da muka gama yi da Alhaji tanimu kenan dan shine jagoran komai, da ace akwai hanyar da zanbi da a yau d'innan sai naga bayan yarinyar nan kowa yahuta dan na san idan har tamutu dole abarmin gadonta gabad'aya tunda ni kad'ai ne d'an uwan mahaifinta,,, Cewar Alhaji Mu'azu.

Daga chan 'bangaren dariya akayi akace kaidai kabi komai a hankali ko da baka kasheta ba zaka iya yin amfani da damarka wajen ganin mun samo dukiyar Alhaji Muhammad, inyaso idan har mun gama samun yadda mukeso zaka iya kasheta saidai kuma idan har zaka rufe ma mutane baki dan kar ayi zargin wani abu kamar yadda mukayi bayan munsa ankashe Alhaji Muhammad da matarshi.

Dariya Alhaji Mu'azu yayi yace ai fiye da hakan ma zan iya sa wa ayi mata dan ni ban had'a komai da kud'iba abokina, yanzu dai zuwa anjima zan kiraka idan har nagama tattara bayanan filin inyaso sai muje musiyar da shi.

Yauwa mutumina kayi k'ok'arin haka sai na ji daga gareka.


Ana zuwa nan recording d'in yak'are.

Wani kuma yasake kunnowa nan ma yaji muryar mutumin yana cewa, Hello Alhaji Mu'azu ina jinka d'azu ka kirani bana kusa.
Eh Wallahi abokina cewa nayi ta samu fa a yanzu ga wani gida nan na Alhaji Muhammad da nagano yana da shi batare da sanin kowaba sai yanzu naga takardun gidan na je na ganshi kuma antabbatar min da nashine.
Daga chan 'bangaren dariya akayi akace lallai Alhaji Muhammadu wayonshi ya yi yawa watau yana da gida batare da sanin ka ba, toh bari zan zo inje muga gidan idan har yana da girma sosai ni zan sayeshi dan dama inaso mutashi da iyalina daga nan, kace abu ya zo gidan sauk'i ai wallahi mutuwar nan tashi dad'i tayi min dan ko bakomai munsan muma mun mori dukiyarshi.
Alhaji Mu'azu ma dariya yayi yace kaidai bari a yanzu gashinan ina ta facaka da kud'i yadda nakeso ba kamar lokacin da yake raye ba, ka san mutuwarshi ko kad'an bata d'aga min hankali ba sai waje d'aya lokacin da kabani layarnan insaka mashi a baki toh a nan ne nad'an tsorata dan ko da su Alhaji Mannir suka shigo gidan zasu kasheshi ban wani d'aga hankaliba dan na san zamuyi nasara.

Katseshi yayi yace a'a Alhaji Mu'azu kayi shuru kar ajiyo ka asirinmu yatonu agane mune muka kasheshi abar maganar kawai zan zo yanzun nan muje inga gidan dan ka san bana wasa da kud'i,,, su dukansu dariya sukayi.

Hakayayi ta kunno recording d'in me muryar yana saurare


________Yana gama sauraren recording d'in ajiyar zuciya yasafke tare da kwantar da kanshi saman gadon inda k'afafuwanshi suna a k'asa ahankali yace tabbas biri ya yi kama da mutum toh ammah ta wace hanya zanbi wajen ganin na kamasu da laifin da nake zarginsu, dan shi kad'ai ne yagane muryarshi bai gane muryoyin sauran da yaji ba saidai ya gane ta mutane biyar saboda sunansu da Alhaji Mu'azu yake ambata a cikin wayar saidai mutum biyu ne bai ganeba toh ammah su wanene? Shin suna raye ko su ma ankashesu? Kanshi ne yajefa ma tambayoyin.

Kasa runtsawa yayi dan kwatakwata daman bai sa ma ranshi yin bacci a lokacin ba nan yayi kwance yana ta 'yan tunane tunane tare da neman hanyar da zai 'bullo wajen ganin ya kamashi da laifin da yake zarginshi da shi, tashi yayi yad'auko wayarshi yana tura duk recording d'in da yake so masu alak'a da case d'in ya dad'e yana turawa dan suna da yawa sosai saida yaza'bi iya wanda yakeso, a cikin kunnuwanshi akayi kiran sallar asuba.


Wajen k'arfe goma yagama shirin shi yaje wajen aiki kasancewar litinin ce yana zaune yana aikinshi nan aka kirashi a waya dubawa yayi ganin private number ne yasa yashare baiyi picking ba wani kiran yasake shigowa a karo na biyu, tsaki yayi sannan yad'auko wayar zai kashe ta gabad'aya dan kar tahanashi yin aikinshi sai kuma yafasa yayi picking batare da yayi magana ba.
Daga chan 'bangaren akace Hello kana ji?
Shuru yayi yana sauraren muryar kamar ya ta'ba jinta k'ara jefo mashi tambaya akayi "wai ko ba Barr Faruk bane"
Saurin d'ago wayar yayi daga kunnenshi yadanna inda zatayi mashi recording d'in maganar sannan yace Hello ina ji.
Au daman kana ji shine zakayi shuru watau har rainin hankalinka ya kai ga haka,,, tsaki yaji anja sannan aka kashe wayar.

Bai damu da hakan ba ya ajiye wayar yacigaba da aikinshi.


Saida yatashi daga aiki sannan yaje yasamu Jawahir tana ganinshi murmushi tasakar mashi tace ina tayaka murna.
Shima murmushin yayi yace murnar me kenan?

"yanayinka da nagani ya sa na gane ka samo wayar"
Matsowa yayi kusa da ita yace Eh hakane na samo kuma duk na saurara saidai mafi yawansu sun mutu dan naji maganarsu da sunan su da aka kira acikin recording d'in.

Fara'ar da take fuskarta ce tagushe tace tabbas hakane duk sun mutu dan dama mutane takwas ne kuma a yanzu shidda daga cikinsu sun mutu, Yaya Aliyu baya cikinsu kawai dai Ammi ta d'auki fansar kasheta da yake da hannu a ciki da kuma niyarshi ta ganin bayana, Mijina Umar ma baya da hannu a ciki, su Abba da abokanshi ne.

Jinjina kai yayi yace na fahimci haka Jawahir saidai akwai wani taimako da nakeso kiyi min.
Taimako kuma? Wane irin taimako ne?,, tajefa mashi tambaya.
"Kar kidamu yanzu zan sanar da ke koma menene.....



_____________


Bayan kwana biyu Faruk yana kwance a d'akinshi Mom tashigo tasameshi zama tayi daga gefenshi tace ya dai Faruk ba dai tunani kake ba?
Murmushi yayi tare da tashi zaune yace No Momcy bacci natashi ne.
Ohk, ina fatan babu wata matsala.
Kallon Mom d'in tashi yayi cike da k'aunarta dan ya san bata son ganinshi cikin kowace irin matsala, girgiza kai yayi yace babu komai Momcy.
Yauwa haka nakeson ji da anjima idan zaka fita zan baka sak'o kabiya kakaima Hajiya Maijidda.

Da mamaki yake kallonta yace Hajiya Maijidda kuma?
Cikin nuna rashin damuwa tace Eh ita tunda kai bakayi da 'yarta wannan ba zai sa mu mudaina zumunci ba dan ka san matsayinta a wajena.
Murmushi yayi yace toh Ammi babu damuwa ai yanzu ma zan watsa ruwa infita sai ma kawai infara zuwa gidan.

Hmm ka ji da shi kana so kana kaiwa kasuwa nasan dai kana son ganin Nasiba ne.
Kallon mahaifiyar tashi kawai yake batare d ya ce komai ba.
Nan tamik'e tace idan kafito sai kasameni a part d'ina ka amshi sak'on.
Toh Mom.




Wajen k'arfe biyar ya isa gidansu Nasiba yana shigar da motarshi cikin gate d'in gidan daidai lokacin Nasiba tacinno kan tata motar, da mamaki take kallon motar Faruk cikin ranta taji wani irin sanyi har ta ayyana ko ya dawo gareta, murmushi tayi tace inko hakane zanyi farin ciki sosai, duba fuskarta tayi ta cikin mirror d'in motar taga fes take sannan tabud'e tafita.

Faruk yana yin parking zaune yayi cikin motar sai a lokacin yafara tunanin ta yadda zai iya shiga yakai ma Hajiyar Nasiba sak'o da tun chan baya baiyi tunanin haka ba ko da ya san hakan yana da nasaba da son ganin sanyin idaniyarshi da yakwana biyu baisakata a idanunshi ba, zaune yayi yana kallonta har tafito daga motar tajingine a jikin motar tana kallon tashi motar.

Ganin haka yasa yabud'e yafito hannunshi rik'e da sak'on Mom, tsayawa yayi yana kallonta shima da manyan idanuwanshi su dukansu kowa yana ayyana abu acikin zuciyarshi chan sai Faruk yataka yanufi wajen da take.
Har ya isa bata daina kallonshi ba, sallama yayi mata sai a lokacin tajanye idanunta daga kallonshi tasadda kanta k'asa sannan ta amsa mashi ahankali.
Murmushi yayi yana jin wani irin dad'i a ranshi, muryarta yaji ta gaisheshi, nan ya amsa, daga haka kuma duk sukayi shuru still dai idanunshi suna a kanta gani yayi ta d'an rame, ya shagala da kallonta ita kuma jira kawai take yafad'a mata ya dawo gareta bakinta d'auke da murmushi jin shuru har lokacin bai ce mata komai ba yasa tad'an d'ago tasaci kallonshi karaf suka had'a idanu.

Dabarbarcewa yayi yace am Nasiba daman Mom ce tabani sak'o inkawo ma Hajiya ban saniba ko tana ciki.
Saurin ida d'ago kai tayi takalleshi nan k'wallah tacika idanun cikin ranta tace ashe daman ba dawowa yayi gareni ba, ahakali tabud'e baki cikin murya me kama da ta kuka tace kashiga tana ciki.
Tsaye yayi yana kallonta shi kanshi baiji dad'in hakan ba ko bakomai ai ya kamata ace sun gaisa, cikin k'arfin hali yace Nasiba ina fatan kina lafiya?
'Daga mashi kai tayi alamun Eh.
Ajiyar zuciya yasafke yace ammah na ga kin d'an rame saisa nayi tunanin ko bakida lafiya.
Hawayen da suka taru cikin idanunta ne suka zubo, cikin zuciyarta tace lallai ma Faruk watau tambaya yake ko banda lafiya bayan ciwon da yabar min acikin zuciyata, girgiza kai tayi tace a'a kawai dai...sai kuma tayi shuru.
Kawai dai me?
Memakon tabashi amsa sai cewa tayi kaima naga ka d'an rame ko duk aikin ne?
K'ayataccen murmushin shi me tsada yasakar mata sannan yace ko d'aya lafiya ta lau saidai kece kad'ai damuwata.

Ji tayi kamar a mafarki yafad'a mata haka shi kanshi saida yaga tsantsan mamaki a tattare da fuskarta, saurin sa hannu tayi tagoge hawayen da suke fita tace anya Faruk hakane ba kawai ka fad'a min bane? Na tabbata da ace kana sona da bazaka ta'ba banzatar da ni ba.
No Nasiba ko d'aya ban banzatar da ke ba kawai dai banda yadda zanyi ne saboda Daddynki ammah ni ko a yanzu yajanye k'udurinshi..
Tarar numfashinshi tayi tace ammah dai Faruk wannan bai dace yazama hujjar da zaka iya hak'ura da ni ba kaidai kawai kace min ka daina sona, bayan ka dasa min ciwon da har yanzu ya kasa warkewa a cikin zuciyata.
K'ara matsowa yayi saitin fuskarta yace Nasiba da sannu zani dawo gareki kikwantar da hankalinki.
'Dan guntun murmushi tayi sannan tace wane lokaci ne wannan ko har sai na bar duniya?
Please kidaina wannan maganar bazaki mutu ba insha Allahu nan da 'yan kwanaki kad'an zan dawo gareki, kallon k'ofar gidansu yayi sannan yace kinga amsa inbaki kishigar ma Mummy da shi.
Wani irin dad'i taji akan maganarshi ko bakomai yanzu ta tabbatar Faruk zai dawo gareta, kasa 'boye farin cikinta tayi har saida yabayyana, tace dagaske kake Faruk?
Maido kallonshi yayi akan fuskarta sannan yace insha Allahu Nasiba dan bana ji zan iya cigaba da rayuwa batare da ke ba, nasan Daddynki yana nan bazan shiga gidan ku ba dan banso muhad'u dan Allah ki amsa kikai mata.

Kallon motocin da suke wajen tayi taga dukkansu suna nan dan haka ta san tabbas Daddy yana gida, bata musaba ta amshi ledar.
Murmushi yayi yace yauwa na gode, nan yajuya zai tafi, bud'e baki tayi kamar zatayi magana sai kuma tafasa.
Ja yayi yatsaya tare da juyowa yakalleta yace please Nasiba akwai wani d'an taimakon da nakeso kiyi min.
Murmushi tayi tace toh ba damuwa, menene kakeso ko ma menene kafad'a zanyi maka.
Rasa yadda zai ce mata yayi dan bayaso tazargi wani abu, ganin ya yi shuru yasa tace kai nake sauraro.
Am daman dan Allah Number d'in Alhaji Mansur nakeso kisamo min a wajen Daddynki ammah dan Allah kar kibari yagane ni zaki ba.
Murmushi tayi tace indai wannan ne kar kadamu zan samo maka.
Shima murmushin yasakar mata yace Nagode sosai My Wife to be sai na jiki.
Wayyo farin ciki tsantsa Nasiba tashiga batasan lokacin da tamaimaita kalmar ba, nan yajuya yafara tafiya, ji take kamar tatsaidashi ammah takasa.
Shi kanshi wani irin dad'i yake ji ko bakomai ya ba idanunshi abincin shi, ko da ya san ya yi k'ok'ari sosai wajen controlling kanshi bai nuna mata irin yadda yadamu sosai d'innan ba, ko da ya san k'asan zuciyarshi shi kanshi ciwone da baida magani indai ba ya ga anmallaka mashi Sanyin idaniyar shi ba.

Yana isa wajen motarshi har ya bud'e zai shiga yajuyo yakalleta yasakar mata lallausan murmushi itama maida mashi martani tayi sannan tanufi cikin gida.


Tana shiga dagudu tanufi hanyar part d'in Mummy tana k'wala mata kira, ja tayi tatsaya a parlor lokacin da tagansu zaune ita da Daddynta,
Daddyne yace Nasiba wannan irin kira haka me yafaru? Ko ta samu ne?
Murmushi tayi tace bakomai Daddy.
Yace ke dai fad'amin shalele ko ansamo mana wani sabon siriki?
Kunya ce takamata tayi saurin mik'a ma Hajiya Maijidda ledar da Faruk yabata tace Hajiyata ga sak'onki sannan tajuya dagudu tanufi part d'inta.

Ba Daddy ba hatta Hajiya maijidda saida tadara, duba ledar tayi ganin sak'on Hajiyar Faruk ne yasa tayi murmushi tace watau yau ta had'u da abin k'aunarta saisa tashiga farin ciki, har ta bud'e baki zata sanar da mijin nata dalilin farin cikin d'iyar tasu nan wayarshi tafara ruri, mik'ewa yayi yafita yana cewa ganinan zuwa.

Nasiba tana shiga d'akinta saman gadonta tafad'a tare da jawo pillow tarungume a k'irjinta fuskarta tana d'auke da k'ayataccen murmishin da tunda taga Faruk take fitar da shi, ahankali tace nagode faruk tabbas a yanzu na tabbatar zaka dawo gareni, lumshe idanunta tayi tare da k'ara matse pillown a k'irjinta tana jin farin cikin da rabon da taji irinshi tun lokacin da aka fasa baikonsu da Faruk...










_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 13*

...Nasiba ce zaune a parlon Daddynta da dare ita da iyayen nata suna kallo ammah ita duk hankalinta ba a wajen kallon yakeba tunani kawai take tana neman hanyar da zatabi tasamo number d'in Alhaji Mansur batare da Daddynta ya ganeba, a gefe d'aya kuma tambayar kanta take shin me yasa Faruk yake son tasamo mashi number d'in? Chan kuma a fili tace ko dai akan maganar aurenmu ne yakeso suyi magana.

Muryar Hajiyarta ce taji ta ce lafiya Nasiba kike magana ke kad'ai?
Murmushi tayi dan batasan maganar ta fito fili ba dan ma Allah ya taimaketa ahankali tayita, girgiza kai tayi tace a'a ba magana nakeba Mummy, juyawa tayi takalli Daddynta da hankalinshi yake a kan news d'in da yake kallo gyaran murya tayi tace am Daddy dan Allah ka ara min wayarka.
Juyowa yayi yakalleta yace Nasiba me zakiyi da ita ba dai wayarki babu credit ciki ba?
Girgiza kai tayi tana murmushi tace a'a Daddy Number d'in Yaya Maryam zan d'auka na yi loosing d'in contact d'inta.
Mummy ce tace ai dama sauk'i tunda number ce kikayi loosing ba taki wayar ba.
Turo baki tayi tace kai Mummy ni yaushe rabon da inyada waya anfi shekara biyu.
Daddy ne yamik'a mata wayarshi yace amsa rabu da ita shalele anfad'a mata da da yanzu d'aya ne bataga da bambanci ba.
Amsa Nasiba tayi tana dariya tace Allah Daddy ita Mummy da abu ya wuce sai tadinga tuno ma mutum
Kibarta Shalele na ma kusan canza maki sabuwar waya.
Mummy murmushi tayi tace oho dai na baku zuwa gobe ai sai anji ku indai Nasiba ce.


Fakar idanun iyayenta tayi tashiga cikin contact d'in Daddy tad'auki number d'in Alhaji Mansur sannan tamik'a ma mahaifin nata wayarshi.



Zama tayi na kusan mintuna biyar sanna tayi masu sallama tatashi takoma part d'inta cike da farin ciki, saida tahau saman gado sannan talalubo number d'in Faruk.




A chan 'bangaren Faruk bayan ya gama shirin shi na bacci yana kwance saman gadonshi yana tunanin abar k'aunarshi yana jin wani irin dad'i a ranshi akan had'uwarshi da ita, shi kanshi ya san yana son Nasiba sosai ya yi k'ok'ari sosai da har ya iya danne son nata a yau bai nuna mata ya yi missing d'inta ba, murmushi ne yasu'buce mashi lokacin da yatuno yadda suke nuna ma juna soyayya kafin wannan abun yafaru, lumshe idanunshi yayi ahankali sannan yace Nasiba kina raina a kowane lokaci, yadda kike missing d'ina nima haka nake naki, ina fata akwai lokacin da komai zai zo k'arshe muyi aure.....yana cikin haka wayarshi tafara ringing tashi yayi zaune tare da d'aukota saman bedside ganin Nasiba ce yasa yai murmushi tare da yin picking, daga chan 'bangaren tayi mashi sallama ya amsa nan kuma duk sukayi shuru sai chan kuma takauda shurun ta hanyar cewa ina fata ka koma gida lafiya?
Lafiya lau Nasiba.
Wani irin haushi taji ganin a yanzu wai Faruk ne yake kiranta da sunanta ko dai ya daina sonta ne? Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata cikin sanyin murya tace am daman na kira ne infad'a maka na samo number d'in.
Kai masha Allah na ji dad'i sosai Baby ina fata dai baki bari Daddy yagane ba?
'Dan guntun murmushi tayi cikin ranta tace wai kuma Baby dan na samo mashi abinda yake so, sai kuma chan tace uhm uhm bai gane ba.
Toh shikenan kituro min kinji?
Shuru tayi batace mashi komai ba, sake maimaita mata yayi nan ma shuru.

Ajiyar zuciya yasafke yace Nasiba kiyi hak'uri duk yadda kikeji nima kaina ina ji ba wai na daina sonki bane wallahi ina k'aunarki sosai saidai banda wani za'bi da zan iya hak'ura da case d'innan bayan alk'awali nayi akanshi kuma kema kinsan girman alk'awali.

Fashewa tayi da kuka tace ammah Faruk ka san ina sonka shine karabu da ni..
Katseta yayi yace kidaina cewa haka Nasiba wallahi ko d'aya ban rabu da ke akan son raina ba kuma har yanzu ina nan akan bakana zan dawo gareki a duk lokacin da muka gama shara'ar nan kikwantar da hankalinki kin ji ko?
Rage sautin kukanta tayi

Please Login or Register in order to submit comment