Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [3/3, 16:54] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo


*......FANSAR RAI.......*



_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_



*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]


_*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*_


*PAGE ONE*

Kotun cike take mak'il da jama'a kowa ya nutsu ana sauraren shara'ar da akeyi ana jinjina ma hukuncin da alk'ali yake yankewa, wata shari'ar tabaka tausayi wata kuma tabaka haushi, saidai babu yadda zakayi, me karanta k'ara ne yacigaba da karantawa inda yace shara'a ta biyar wadda take ta karshe a wannan ranar itace shara'ar jawahir wadda ake zargi da laifin kisa ta kashe mutane d'aid'aya har bakwai tsawon watanni goma da suka shud'e inda dangin wad'anda takashe suke k'ararta sukeso abi masu rayukan 'yan uwansu, ana ta zaman k'arar ammah har yau ba'a samu aka kammala ba idan Jawahir tana kusa anaso a gurfanar da ita a gaban kotu.

Wasu yan sanda ne guda biyu suka tafo da wata yarinya wadda bazaka gaza shekaru ashirin da biyu ba hannunta da kafafunta duk an d'auresu da kaca, dakyar take tafiya suna biye da ita a baya har aka isa da ita a daidai wajen da aka tanadar mata dan tatsaya,
Alk'ali d'agowa yayi daga rubutun da yake yakalli yar matashiyar yarinyar yaduk'a yacigaba da rubutun.
Me karanto k'ara ne yace kotu tana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara da lauyan masu k'ara.

D'aya daga cikin lauyoyin da suke zaune kujerar gaba ne yamik'e yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a sunana Barr Musa Bello (MB) nine lauyan 'yan uwan wad'anda aka kashe.
Jinjina kai Alk'ali yayi nan me gabatar da k'ara yace kotu tana buk'atar ganin lauyan wadda ake k'ara.
Shuru Kotun yayi nan aka sake maimaitawa sai chan d'aya daga cikin lauyoyin yamik'e yace Allah yagafarta malam lauyan wadda ake k'ara Allah ya yi mashi cikawa wata biyu kenan da suka wuce.
Gabad'aya kotun surutu tad'auka nan Alk'ali yad'ago yace ya rasu?
Me karanto k'ara ne cike da rud'ewa yace Allah yagafarta malam Barr Muhsin ne kuma wanchan Lauya d'in da yafara tsaya mata idan ban manceba shima mutuwa yayi toh ya akayi duka lauyoyin nata har biyu suka rasu?
Shuru Alk'ali yayi sai chan yace wannan baya cikin hurumin mu tunda bamu isa muhana mutum tafiya ba idan lokacinshi ya yi, saidai kotu tana so taga wanda zai tsaya ma wadda ake k'ara inkuma bata da lauya toh hukunci zai hau kanta kamar yadda kotu tazartas zata mata d'aurin rai da rai ko akasheta, inkuma ita zata iya kare kanta toh kotu naso tafito tayi mata bayani yadda akayi mutane dai d'aya har bakwai suka rasa rayuwarsu ta hanya d'aya.
Yarinyar duk'ewa tayi k'asa cike da tashin hankali tafara rusa kuka inda gabad'aya kotun takacame da surutu, Alk'ali teburin da yake a gabanshi yabuga nan kotu tayi tsit.
Yan rubuce rubuce yayi sannan yad'ago yace wadda ake k'ara tana da abinda zata ce, ko zata iya kare kanta?
D'agowa tayi daga duk'iyar da tayi tana mecigaba da kuka.
Yan sandan da suke tsaye kusa da ita ne suka daka mata tsawa sukace tayi ma mutane shuru.
K'ok'arin had'iye kukanta tayi nan me karanto shara'a yasake cewa wadda ake k'ara ko zaki iya kare kanki?
Jikinta gabad'aya rawa yake nan tasa hannu tadafe kanta lokaci guda tasulale k'asa a sume.
Me karanta k'ara ne yace Subhanallahi ta suma,
Alk'ali d'agowa yayi yakalleta sannan yace zamu d'aga wannan k'arar zuwa sati biyu masu zuwa lokacin muna sa ran wadda ake k'ara ta dawo cikin hayyacinta yanzu aje da ita abata kulawar da tadace sannan za a cigaba da tsaronta a gidan yari (prison) kamar yadda akeyi,, bubbuga table yayi nan wasu yan sanda ukku mata sukazo suka d'auketa suka fita da ita.



Tunda aka fara shara'ar gabad'aya hankalinshi yatattara yana kallon yadda komai yake tafiya musamman ma shara'ar yarinyar da ake zargi da kisan mutane har bakwai,,bubbuga table da Alk'ali yayi yasa duk suka mik'e gabad'aya nan alk'ali yatafi, mutumin dake sanye da riga irin ta lauyoyi komawa yayi yazauna tare da kallon nakusa da shi yace Barrister junaid me kake tunani agame da wannan shara'ar da ake ta wannan yarinyar kana tunanin itace tayi wannan kisan?
Murmushi Wanda aka kira da barrister junaid yayi yace inba ita ba wa kake tunani ai itace Barrister.
Girgiza kai yayi yace sam batamin kama da wadda zata iya aikatawa ba.
Da mamaki yake kallonshi yace me kake nufi da hakan?
Cikin nuna rashin damuwa yace inaso intsaya mata a matsayin lauyanta.
Zumbur Barr Junaid yamik'e tsaye yace Barrister Faruk ka san abinda kake fad'a kuwa? Na tabbata dan kana sabon Lauya a court d'innan bakasan halin da ake cikiba game da wannan shara'ar wannan yarinyar da kake gani itace takashe mutane bakwai sannan lauyoyinta biyu da suka tsaya mata duk ta kashesu, daga ciki har da Barr Muhsin da aka maidoka madadinshi itace tayi silar barinshi duniya dan haka kar kasaka kanka aciki domin shara'arta me had'ari ce,

Shuru yayi kamar me tunani sai chan yajuyo yakalli Barr Junaid yace bazan gasgatar da hakaba har sai na gane ma idanu na.
Jinjina kai Barr Junaid yayi yace gane ma idanunka daidai yake da rasa rayuwarka kamar yadda su Barr Muhsin suka rasa tasu rayuwar a dalilin nema suceceta dan wannan yarinyar bana tunani mutum ce hatta cikin gidan yari d'in duk wanda yasaki yata6a lafiyarta to bai kwana da rai dan sau biyu ana fiddo mata biyu da suke a rufe sun mutu a binciken da akayi angane cewa sun tak'uleta fad'a ne a ranar washe gari ba'a tashi dasuba saisa yanzu aka ware mata d'akinta ita kad'ai, shawarar da zan baka kar kajawo ma kanka abinda zai hanaka kwanciyar hankali kabarta kawai akasheta.
Barr Faruk murmushi yayi yace har yanzu banji wata kwakkwarar hujjaba da zata sa ingazaba dan haka ina nan akan bakana.
Mik'ewa Barr junaid yayi yace har yanzu na lura baka fahimci inda zance na yanufa ba.
Barr Faruk ma mik'ewa yayi yana murmushi yace na fahimceka kar kadamu zamu iya tafiya.
D'aukar kayansu sukayi suka juya suka fita daga court d'in lokacin babu kowa ciki sai su biyu suka rage.


Barr Faruk bayan ya koma office d'inshi zama yayi yana so yayi aiki saidai shara'ar yarinyar nan ta tsaya mashi a rai kasa aiwatar da komai yayi cikin ranshi yace taya za'ace yarinya k'arama ce take kisa? Anya kuwa ba sharri aka ja mataba? Mik'ewa yayi tsaye yace wannan yarinyar kwata-kwata batayi kama da wadda zatayi wannan aika aikan ba dan fuskarta kawai zaka kalla kagane hakan,,,wayarshi yad'auko yayi kira daga chan 6angaren ana d'agawa ko sallama baiyiba yace kazo office d'ina yanzu kasameni,,yana fad'in haka kashe wayar yayi tare da komawa yazauna yana juyawa bisa kujerar da yake zaune.

Ba'afi minti goma ba nan aka fara knocking, umurni yabada aka bud'e k'ofar.
Wani mutun ne sanye da rigarshi ta lauyers yashigo d'an gajerene baida tsawo sosai tsayawa yayi daga wajen yace Barrister gani.
Barr Faruk nuni yayi mashi da kujerar da take opposite d'inshi alamun yazo yazauna.
Bai musaba yazo yazauna yana kallon Barr Faruk dan jin abinda zaice.
Shima kallonshi yayi nad'an lokaci sannan Ahankali cikin muryarshi me sanyi yace Barr Bilal wani taimako nakeso kayi min.
Wanda aka kira da barr bilal murmushi yayi yace toh Oga wane irin taimako ko aiki ne kakeso inyi maka.
Shuru yayi na d'an lokaci sannan yace so nake kaje kasamo min duk wani information game da yarinyar nan da ake shara'a da ita a court.
Cikin rashin fahimta yace Oga wace yarinya kenan?
Barr Faruk d'an yatsine fuska yayi sannan yace wadda ake zargi da laifin kisa.
Zumbur Barr Bilal yamik'e tsaye a tsorace yake kallon Barr Faruk yace Oga kar kafara haka na tabbata dan baka dad'e da zuwaba saisa bakasan halin da ake cikiba duk lauyan da yayi k'ok'arin tsaya mata zai iya rasa rayuwarshi karufa ma kanka asiri kar kajefa kanka cikin abinda zai zame maka matsala.
Cikin nuna rashin damuwa yace ban damu da hakan ba dan inaso inyi bincike sosai akan haka Indai har nagane batada laifi a ciki ni zan tsaya mata a shara'ar nan ban damu da inrayu ko inmutu ba fatana shine inkasance a bayan gaskiya akowane lokaci.
Cikin kid'ima yace ammah Oga gaskiya.....Katseshi Barr Faruk yayi yace ba shi natambayeka ba kaje kawai kayi abinda nasanya ka.
Cikin sanyin jiki yace toh zanyi insha Allahu zuwa gobe zanzo maka da duk wasu bayanan da suka dace.
'D'aga kai yayi alamun toh, sannan yace zaka iya tafiya.
juyawa Barr Bilal yayi cikin sanyin jiki yafita.

Barr Faruk duba agogon hannunshi yayi sannan yamik'e yad'auki suit d'inshi yasaka yadad'e idanunshi da bak'in glass sannan yad'auki key d'in motarshi yafita cike da tak'ama yake taku

Wani lauyer ne yabiyo bayanshi da wasu takardu a hannunshi yana cewa 'Dallabai ga rohoton da muka samu game da case d'in Alhaji Salisu da yake so katsaya mashi akan k'arar da yashigar a court akan wani gida dayake so ak'watar mashi na wani matashi da yace ya siyar mashi da gidan ammah bai tashi daga gidan ba,,,,tafiya yake yana binshi yana kora mashi bayani har saida yakai aya sannan Barr Faruk yajuyo yakalleshi ta cikin glass d'inshi yace kaje kafad'a mashi yacanza lauyer dan ni bazan iya d'aure ma k'arya gindi ba na gama bincike akan case d'inshi banga wani k'amshin gaskiya akan cewa gidan mallakinshi bane,,,yana fad'in haka yajuya yashige motarshi
yabar court d'in.

A nutse yake tuk'i inda kid'i me dad'i yake tashi a cikin motar ahaka har ya isa G.R.A a gaban wani tank'amemen gida yayi horn, megadi dasauri yazo yabud'e mashi gate yacinna kan motarshi a wajen da aka tanada dan ajiye motoci yaje yai parking sannan yafito hannunshi rik'e da briefcase d'inshi yashiga cikin babban gidan hayaniyar da yajiyo ne a main parlor yasa direct yawuce part d'inshi,
Yana shiga ajiye yar briefcase d'inshi yayi yacire kayanshi yafad'a toilet dan yayo wanka.

Bayan ya fito ya shirya kwanciya yayi saman makeken gadon dake cikin d'akin tare da maida idanunshi yalumshe.
Ta haka ne nasamu damar k'are mashi kallo Barr Faruk dogo ne yana da haske sosai saidai bazaka kirashi fari ba fuskarshi doguwace med'auke da dogon hanci bakinshi d'an madaidaici ne, idanuwanshi manya ne sosai sannan yana da saje sirri a fuskarshi wanda yataimaka wajen k'ara ma fuskar kyau, gashin kanshi kawai zaka kalla kagane cewa shi bafullatani ne na usul, saidai yanayinshi da ka gani zaka gane ba mutum bane me yawan son hayaniya ba, saurayine wanda shekarunshi bazasu gaza 29yrs ba.

Turo k'ofar da akayine yasa yabud'e lumsassun idanunshi ahankali yasafkesu a k'ofar wata mata ce tashigo cikin shiga ta alfarma tana kama da saurayin sosai saidai ita fara ce matar bazata wuce shekaru arba'in da bakwai ba, fuskarta d'auke da murmushi ta isa bakin gadon daga gefenshi tazauna tace Son ashe ka dawo?
Dan guntun murmushi yayi yace Eh Momcy ban dad'e da dawowa ba.
Shafa kanshi tayi tace kuma shine kakwanta? katashi muje kayi lunch nasan ka kwaso yunwa.
D'agowa yayi yakalleta yace Mom... sai kuma yayi shuru.
Murmushi tayi a karo nabiyu tace oh sorry su Hajiya Maijidda ce sukazo ita da Nasiba ya kamata ma kazo kugaisa.
Marairaicewa yayi cike da Shagwa6a yace Mom ina buk'atar hutu yanzu please kisa akawo min lunch d'ina a nan bana son hayaniya.
Matar tace shikenan Son yadda kakeso haka za'ayi bari inkawo maka ma dakaina.
Murmushi yayi yace thanks mom.
Tashi matar tayi tafita chan sai gata d'auke da tray tazo ta ajiye saman wani d'an center table tace son katashi kaci bari inturo Nasiba takawo maka drinks.
Saurin cewa yayi a'a Momcy please kar kituro min ita yau banason yawan surutu kuma kinsan da ta zo damuna zatayi.
Shikenan Son bari ni inje inkawo maka da kaina.
Baice komai ba yatashi yanufi inda ta ajiye mashi abincin yazauna yafara ci.

Bayan ya gama yad'auko System d'inshi yazauna yafara research aciki wayoyinshi ne da aka dinga kira yasa yad'auko su yakashe ganin zasu hanashi yin abinda yake son yi.


*WASHE GARI*

Tunda yaje wajen aiki files d'in da yagani kusan ukku a office d'inshi yasa ko kallonsu baiyiba yawuce yazauna ko minti goma da zama baiyiba secratry yashigo gaisheshi yayi sannan yawuce wajen da files d'in suke yad'auko yakawo mashi yace ranka yadad'e wannan daga gidan Alhaji k'asim ne suna gaiyatarka a matsayin lauyan da sukeso yatsaya masu akan gadonsu da dangin mamacin sukeso su cinye, sannan wannan kuma Alhaji Mamman ne ya aiko ya ce ya yi maka bayani duk wani abu da ake buk'ata suna ciki sannan wannan kuma na Alhaji Bashir ne ya..... D'aga mashi hannu da Barr Faruk yayi ne yasa yai shuru bai ida bayani ba.
Hannu yamik'a mashi yace bani na gidan Alhaji k'asim bai musaba yamik'a mashi yace Oga sauran fa?
Cike da k'osawa da maganar yace amaida masu ace na ce su samu wani lauyan.
Juyawa sectary yayi yafita da files d'in

Barr Faruk bud'e files d'in da ya amsa yayi yafara dubawa knocking d'in da akayi ne yasa yad'ago kai tare da cewa yes come in.
Barr Bilal ne yashigo hannunshi rik'e da wani file zuwa yayi yazauna yace sannu Oga.
Murmushi Barr Faruk yayi yace Yauwa Barrister ina fata dai ka samo min duk wani detail din da yadace.
Eh toh ansamu abinda yasauwak'a mik'a mashi file d'in yayi yace saidai duk k'ok'arin da nayi ban samu full information ba wajen masu kula da prison d'in.
Bud'e file d'in yayi yaduba yace Jawahir Muhammad Maikudi shine cikakken sunanta?
Eh shine sunanta d'iyar wani hamshak'in me kud'i ce saidai a yanzu mahaifin nata baya raye, ana zarginta da kashe mutane kusan bakwai ko ma sama da haka ta hanyoyi daban daban.
Jinjina kai yayi yace shikenan iyakar abinda kasamo game da ita? Gyara zamanshi yayi yace sannan abinda nak'ara sani shine itace tai silar mutuwar Barr Mubarak alokacin da yake k'ok'arin ganin ya tsaya mata kasancewar shi lauyan abokin mahaifinta ne sai yanemi yataimaka mata wajen fitar da ita ta hanyar k'aryata k'arar, a daren ranar da zai rasu ya je prison d'in ya gana da ita lokacin da yashiga ba'asan abinda yahad'a suba andai jiyo ta fasa k'ara nan ma'aikatan gidan yarin suka yi saurin zuwa dan gane ma idanunsu abinda yake faruwa ammah abinda yabasu mamaki shine ansameta ta shak'e mashi wuya tana kuka inda shi kuma yake k'ok'arin k'wace kanshi daga rik'on da tayi mashi dakyar aka samu aka 6an6areshi daga hannunta nan ma'aikatan suka fara bugunta inda shikuma aka fitar da shi ranshi duk a 6ace abinda aka kasa ganewa shine a matsayinshi na lauyanta minene yahad'a su fad'a?
Tafiyar da yayi washe gari sai jin labarin mutuwarshi akayi wanda aka rasa dalilin haka saidai an sameshi cikin jini.
Barr Faruk idanu yazuba mashi yana kallonshi.
Barr Bilal cigaba yayi da cewa tun daga lokacin aka dinga surutu ana cewa ko dai aljanace ko kuma wani yabud'e mata tafita taje takashe shi, koda dai ba'a tabbatar da hakan ba aduk binciken da akayi babu wata hujja da tanuna haka sai kuma Barr Muhsin babban lauya kuma lauyan da yakasance lauyan mahaifinta wanda bayan rasuwarshi aka kawoka a matsayin madadinshi........




_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_

_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_


_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_




_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/4, 16:05] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo


*......FANSAR RAI.......*



_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_



*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]


_*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*_




*PAGE TWO*

Barr Bilal cigaba yayi da cewa a lokacin da za'a yanke mata hukuncin kisa ne saboda batada lauya shine shikuma Barr Muhsin yafito yatsaya mata a matsayin lauyanta haka aka fara gabatar da shara'a sau biyu aka zauna kotu wannan zaman da za'ayi jiya shine zai kama na ukku toh shine wata biyu da suka wuce aka tsinci gawarshi a chan wani daji saidai ba'asan wanda yakashe shi ba.

Barr Faruk ajiye biron da take hannunshi yayi yace kuma ba'ayi bincike aka gano wanda yayi kisan ba?
Duk binciken da yadace anyi ammah ba'a samu komai ba agame da mutuwarshi, nidai gaskiya hankalina bai kwantaba akan yarinyar chan dan nima kaina ina tantama akan shara'arta kar kajefa kanka cikin halaka kabari kawai kotu tayanke mata hukuncin kisa kowa yahuta.

Girgiza kai yayi yace bazan bari ayanke mata hukuncin kisa ba har sai na tabbatar da itace me laifin dan gaskiya a irin shekarunta bana tunani zata iya irin wannan aika aikan.
Cikin sanyin jiki yace a'a Barrister kar kace haka.
Shuru Barr Faruk yayi yacigaba da duba file d'in da aka kawo nata sai chan yarufe yajuyo yakalli Barr Bilal yace Barr Bilal ina nan akan batuna na son intaimaka mata dan haka zanje inyi magana da Alk'ali kome kenan gobe bayan azuhur zan zo muje karakani a chan prison d'in...tun kan yarufe baki Barr Bilal yai zumbur yamik'e tsaye yace ni kuma Oga?
Kallonshi Barrister yayi yace Eh saboda inason samun wasu bayanai daga wajenta.
Barr Bilal kamar zaiyi kuka yace shikenan Allah yakaimu zanyi yadda kace.
Murmushi Barr Faruk yayi yace nagode sosai Barrister.
Batare da ya ce komai ba yajuya yafita.

Barr Faruk cigaba yayi da nazari akan file d'in Jawahir kafin daga bisani yatashi yabar office d'in.




A chan gidan yari duk inda kakalla matane suke ta faman aiki a gefe d'aya nahango Jawahir duk'e gaban wasu mata masu kula da su hannunsu rik'e da bulali magana suke mata akan tatashi tayi aiki ammah tak'i ko motsawa batayiba bare asa ran zata tashi.
D'aya daga cikin matan ne tad'aga bulala tashaud'a mata cikin fushi tace ke wace irin macece kullum ayi ta fama da ke akan kitashi kiyi aiki ammah kik'i.
Kokad'an jawahir bata motsaba bare asa ran zata tashi.
Su dukansu d'aga bulalen hannunsu sukayi suka dinga shaud'a mata ta ko'ina suke dukanta ammah ko kad'an bata motsaba kanta yana sunkuye k'asa ta runtse idanunta gam bugunta suke kamar sun samu jakka lokaci guda tasulale k'asa tafad'i saida suka ga bata iya motsi sannan suka barta nan mutum biyu yakamata suka tafi da ita d'akinta ana zuwa aka wurgata suka rufe k'ofar nan wajen tayi kwance idanuwanta a rufe gashin kanta duk ya baje mata fuska ahankali tad'ago hannunta tadafe kanta daga haka bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.

Ruwan sanyin da aka makaka mata a jiki ne yasa tayi saurin bud'e idanuwanta d'aya daga cikin masu tsaronsu ce abinci ta ajiye mata cikin wani d'an k'aramin kwano duka abincin bai wuce ayi loma biyar yak'are ba, a wulak'ance tace ga abincinki nan.
Tashi tayi zaune tana kallonta da idanuwanta da suke lumshewa saboda wahala har matar tajuya tatafi.
Maimakon taci abincin sai ma rarrafawa da tayi dakyar taje chan k'arshen ginin d'akin tad'age wani dutsi dan babba babba dayake ajiye cikin d'akin nata tad'auko wani d'an k'aramin littafi duk ya cumimiye me kama da diary tabud'e hannunta yana rawa tad'auko wata biro still dai hannunta yana rawa tafara rubutu chan kuma tarufe tamaida inda tad'auko tatashi tana tafiya tana rangaji takoma chan wajen da abincin yake tazauna d'aukowa tayi zata ci wata irin iska me karfi tataso a cikin d'akin k'ara jawahir tasaki nan tasulale tasume.




Barr Faruk zuwa yayi yasamu Alk'ali sukayi magana Alk'ali Jinjina ma maganar tashi yayi yace anya barrister zaka iya wannan aikin? Nifa yarinyar chan hankalina bai kwanta da itaba.
Murmushi Barr Faruk yayi yace Allah yagafarta malam hankalina ne bai kwanta da abinda ake zarginta akaiba nafiso inyi bincike intabbatar da gaskiya idan dai har nagano akwai sa hannunta a ciki toh zan janye daga tsaya mata.
Alk'ali yace toh shikenan tunda ka ce haka Allah ubangiji yataimaka.
Barr Faruk yace Ameen zanje insamu registrar muyi magana inyaso kafin azauna court a karo nagama ingama bincike akanta.
Jinjina kai Alk'ali yayi yace hakane.




Barr Faruk yana komawa gida a harabar gate d'in gidansu yaga wata irin dank'areriyar mota ko kallon motar baiyiba yazo zai wuce nan driver yai saurin fitowa yaje yalek'a ta window d'in motar daidai da Barr Faruk yayi horn dan abud'e mashi gate.
Juyowa yayi yakalli driver d'in da yace ranka yadad'e d'alla'bai ne yake son magana da kai.
'Bata fuska yayi yace wanene kuma haka?
Bud'e motar da akayi aka fitone yasa yajuya yakalli wanda yafito daga cikin motar Alhaji Mani yagani nan yak'ara had'e fuska har ya iso wajen daga saitin motar yatsaya sannu Barrister.
Batare da ya juyoba ya amsa da yauwa.
Alhaji Mani yace ina fata kaga sak'o na jiya dan ina ta Kiran wayarka inji daga gareka ammah baka d'auka.
Cikin nuna rashin damuwa yace Eh nagani kawai dai bazan iya tsaya makaba so yakamata kasamo wani lauyan.
Cikin d'aga murya yace haba Faruk meyasa zakayi min haka? Toh tsaya fad'i kud'in da kakeso inbiyaka kasan dai banda matsalar kud'i.
Wani irin kallo Barr Faruk yayi mashi kafin daga baya yaja motarshi yashige cikin gate d'in da megadi tuni ya bud'e mashi.
Alhaji Mani tsaye yayi yana bin motar da kallo cike da bak'in ciki da takaici Jinjina kai yayi tare da cize le6e yace tabbas bakasan wanene niba ammah zan fahimtar da kai,,,,juyawa yayi cikin 6acin rai yanufi wajen motarshi inda driver yai saurin binshi yaje yabud'e mashi k'ofa yashiga.



Washe gari bayan azuhur Barr Faruk yakira Bilal a waya yace yana son ganinshi a office d'inshi.

Bayan ya zo ne Barr Faruk yace yana so yarakashi gidan yari dan yagana da Jawahir.
Hankalin Bilal ba k'aramin tashi yayiba gabad'aya yanemi nutsuwarshi yarasa ji yake kamar yace bazaijeba saidai baya iya yi ma Ogan nashi musu dan haka saida yahad'e wani wahalallen miyau sannan ya amsa da toh.

Barr Faruk saida yagama wani aiki da yake sannan yakira shugaban gidan yarin sukayi magana akan zuwan da zaiyi yagana da Jawahir a matsayin shi na lauyanta meson kareta.
Bayan sun gama wayar yamik'e yace ma Bilal suje.

A cikin motar shi suka shiga suka kama hanyar prison na mata su dukansu shuru sukayi babu me magana kasancewar shi dama Barr Faruk ba me yawan magana bane, shi ko Bilal tsoro ne yataru yai mashi yawa ahaka har suka isa.

Suna isa daidai zasu shiga k'ofar Barr Faruk bai ko tsaya yi ma masu gadi magana ba yanemi yawuce su dukansu tasowa sukayi suna cewa malam Lafiya ina zakaje? Wa kake nema?
Batare da ya basu amsar tambayoyinsu ba yad'ago ID card d'inshi yanuna masu cikin sauri duk sukaja baya yawuce matan da suke zaune suna aiki nan duk suka zuba masu idanu suna kallonsu duk inda suka gifta binsu suke da ido wad'anda suke cikin Ceil ma haka suka dinga lek'osu k'ofa k'ofa suka dinga shiga duk inda aka nemi a tsaidasu Barr Faruk ID Card kawai yake nuna masu baya tsayawa dogon bayani da su, wasu ko basu tsaida su kasancewar sun san Barr Bilal ahaka har suka kai wajen wani d'aki inda me gadi na musamman akasa yana tsaron k'ofar inda daga gefen d'akinta d'akin wasu mata ne su ukku a ciki, Barr Bilal cike da tsoro yajuyo yakalli Barr Faruk yace Oga nan ne take.
Cikin nuna rashin damuwa yace toh muje girgiza kai yayi yace a'a zan jiraka a daidai nan kaje kadawo ganin yadda yatsorata yasa yace shikenan nan yawuce zai tafi megadin d'akin yayi saurin mik'ewa yanufo wajenshi yace malam wa kake nema?
ID Card din hannunshi yanuna mashi nan yai saurin bud'e mashi yana shirin shiga Megadin yace saidai ranka yadad'e...sai kuma yayi shuru Barr Faruk yana jin haka yaciro wayoyinshi daga cikin suit d'inshi yamik'a ma megadin sannan yawuce yashiga, tsaye yayi bakin karfunan k'ofar yana bin cikin da kallo wani d'an k'aramin kurkuku ne baida girma sosai kuma babu wadataccen haske a ciki Juyowa yayi yakalli me gadin yace ina buk'atar haske.
Megadi zuwa yayi yad'auko wata torch light me haske sosai yahaska d'akin nan Haske yagauraya a

Please Login or Register in order to submit comment