Reading TRIPLETS BOOK 2 by Star Lady Chapter 56 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka kama shi sun san waye suka kama ba? To sun gane waye suka kama ne ta hanyar wani ɗan ta'addan da ya zo yana dukan shi a fuskarsa, sai wanna fake face ɗin nasa ta goce, shine suna cire face ɗin suka ga ainahin face nasa, to wannan da suka yanka babban yaron James ɗin ne, shine suka sanya mashi fake face ɗin James ɗin dan su tayar mana da hankali, amma su sun san ba za su iya kashe James kai tsaye ba, saboda muna kewaye da su, lokacin da nake bincike ne na samu daman gane cewa sun gane James, amma batun sanyawa baban yaron sa fake face na san, wannan kuma sai da na zo nan na sani".

Abin da ya faru lokacin da Lion ya ga video ta hanyar camerar da ya sanya wa Tyrone a gaban botirin rigarsa, da yake yana ƙage da aikin alokacin, bai tantance cewa e ba James bane, sai da ya shiga mota yana zuwa ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo masa yanayin jikin wannan da kuma na James ɗin, a nan ne sai ya gane ba ɗaya bane, abin ka kuma da baban soja cikin kankanin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta tariyo mashi mutanen dake a wajen, a nan ne ya fahimci wanda yake zaune a ɗayar kujerar da ogansu ke zama tabbas shine James, daga yana yin jikinsa ya gane, alluran barci suka mashi sanna suka rufe mashi fuska da mask, da Lion ya shigo wajen kuma, kallo ɗaya ya yi mashi ya gane tabbas shi ɗin ne, shiyasa ma ya harbe shi a hannu dan kada su harbe shi su, wannan shine abin da ya faru!!

Ba karamin daɗi Tga ya ji ba, har wani nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe, haka sojijin suka ɗauke su zuwa cikin motar.

Kamar yadda Lion ya tuƙo motar ya zo haka ya tuƙata ya bar wajen tare da su Tga da James dake kwance rai a hannun Allah, ya sha harbin bindiga sau biyu, hannu da kuma kirji, haka suka tafi suka bar sojojinsu suna karisa sauran aikin.

Kai tsaye gida ya nufa da su, yana parking motar a parking space na gidan ya fito a zafafe tare da buɗe gidan baya na motar ya saɓi James a kafaɗarsa zuwa cikin gida, har lokacin akwai wannan mask ɗin a fuskar James ɗin. Jini sai tsiyaya yake yi, duk in da suka wuce sai jini ya zuba haka ya wuce da shi ɗaya daga cikin ɗakunan kasa.

Saman bed mai shinfiɗe da farin bed sheet tas ya kwantar da shi tare da sanya hannunsa ya tsage rigar James ɗin daga farko har ya direta.

Kamar yasan hakan zata faru ya taho da wasu kayan aikinsa, da yake dama su basu wani cika rabuwa da A box da sauran kananan tafi da gidan ka na kula da lafiya ba.

Cikin zafin nama yake takowa ya fito daga ɗakin izuwa nasa ɗakin. A box da sauran kayan aiki ya ɗauko ya nufo waje, daidai Palon saman suka yi karo da Imran lokacin kuma karfe 11 rana ta yi.

Daga ganin yadda Lion yake Imran ya san ba lafiya ba, dan haka sai ya yi saurin bin bayansa. Lokacin da Lion ya dawo ɗakin da James ke kwance, ya tarar da Tga da kuma Tyrone, sojan dake a bakin gate ne ya taimaka masu zuwa cikin gida, shi Tga ma kwata-kwata baya iya tafiya, gara Tyrone da yake kafa ɗaya aka harba yana iya jan kafar tasa.

Kokarin cire bullet ɗin jikin James Lion ya fara yi, su kuma suna kwance a gefen James ɗin, shi kuma Imran da ya shigo da ya ga meke faruwa ai sai ya fara ruwan hawaye, da sauri ya kariso wajen gadon, da farko bai gane cewa James bane, sai da ya matso kusa sosai, saboda duk sun saɓa mashi kamanni, fuskar tasa ta suntuma sosai, idan ba ka yi mashi farin sani ba, ba zaka taɓa gane cewa shi ɗin bane, yan ta'addan nan sun zalunce shi sosai.

Sosai Lion yake aiki babu kama hannun yaro dan cewa rayuwar ɗan uwansa, yana yi yana haɗa zufa, da sauri Imran ya kara gudun Ac dake a ɗakin, amma duk a banza, domin kuwa bai dai na zufar ba, kamar ma kara mashi ake yi, ganin haka yasa Imran ya wuce bedroom nasa ya ɗauro alwala ba ɓata lokaci ya fara gabatar da sallar nafila yana rokar Allah da ya bawa James lafiya, ya tashi kafaɗunsa.

Sai wuraren karfe 1 Lion ya samu ya iya kammalawa da James, ya yi nasarar cire bullet ɗin, sannan ya mashi dressing na wajen, sai barci James yake yi domin alluran da suka mashi tana da karfi sosai da sosai wata kila zai iya kai wa dare kafin ya farka.

LION

Bayan ya kammala ne ya nufi su Tga da nufi ya yi Tga dressing ɗin wajen tun da shi babu bullet ɗin a jikinsa, shi kuma Tyrone ya cire mashi bullet ɗin, amma duk azaban da Tga ya ke a ciki, bai hana shi ya ce lallai shi baya son a duba shi ayi treatment ɗin shi a Nigeria ba, saboda wai Nigeria me suke da shi da har za'a duba mashi lafiyarsa a nan, shi baya son kasar ma gaba ɗaya, shi tunda ba wani ciwo sosai ya ji ba zai iya tafiya a jirgi kawai a mai da shi Usa daddy ya je ya duba shi, Lion bai wani damu ba, dan dama baya son matsi sosai, dama ganin gidan yake yi ta yi mashi karama, da kaɗan tafi palon kasarsu na Usa, shi ji yake yi ma da kyar yake numfashin a gidan, duk girmanta amma wai ta yi karami, so da suka zo ɗan jiya kawai ji ya yi kamar sun toshe mashi iskan da yake shaƙa, dama ga zafi, hakan yasa ya ce to su wuce amai sa su, ba musu kuma suka ce to, cikin kankanin lokaci aka yi masu komai, amma kafin su tafi an cire wa Tyrone Bullet ɗin kafarsa, sannan Lion ya ɗan gyara masu wajen suka tafi, shi Lion ba zai yi wu su tafi da wuri haka ba saboda James jikinsa ya yi tsakani sosai, sai ya ɗan sami lafiya.

Yau sai misalin karfe 3 Lion ya samu ya yi sallar azahar, saboda busy da ya yi yawa. Bayan ya yi wanka ya yi sallah ne ya zauna saman bed nasa yana tunanin yadda zai yi da James.

A wanna hali Imran ya shigo ya same shi, sannu ya yi mashi tare da tambayar ya jikin James, jinjina mashi kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba.

Gefensa Imran ɗin ya zauna yana faɗin "Lion dan Allah ba dan ni ba, kada ka yi wa James hukunci mai tsanani, ni nasan ba haka kawai ya shiga wannan ta'addancin ba, akwai dai dalili, kai ma fa kasan James yana da zuciya mai kyau, ka tausaya mana".

Shiru ya yi na tsawon mintoci kamar 10 haka kafin ya fara magana gently. "Prof James ba ɗan ta'adda bane, kamar yadda ka ɗauka, amma dole zan hukunta shi, dole ya karɓi hukunci mai tsanani domin ya yi mani laifi, ya sayar mana da rayuwarsa".

Zaro ido Imran ya yi yana faɗin "Ban gane ba, dan Allah ka yi mani baya ni dallah dallah".

Na san kowa a ƙage ya ke dan jin cikakken bayani akan James da wannan sarkakiya, to ni *PRINCESS TEEMA* bari na warware maku cikin kwanciyar hankali, maza ku biyo ni.

JAMES dai ba ɗan ta'adda bane kamar yadda kuka ji Lion ya faɗa, abin da ya faru shi ne ku saurara ku ji, ya shiga ƙungiyar ta'addancin kala-kala, haka zalika ya kashe mutane kala-kala, sai dai duk mutanen banza yake kashe wa ba na kirki ba, alokacin da Lion yake bincike akan wani mutumi da James ɗin ya kashe ne wadda Lion yake yiwa kallo mutumin kirki, to alokacin ya fara fahimtar cewa duk mutanen da James yake kashe wa na banza ne ba na kirki ba, hakan yasa ya dakata da bincin ina James ɗin ma yake tukunnan, sai ya fara binciken waye James ɗin mai gaba ɗaya? Waye yake saka shi wannan aiki, a nan ne ya gane cewa James shi ne (DOA) DETECTORATE OPERATIONS ARIF na CIA gaba ɗaya, CIA kuma wata katafaren hukumar Row ce ta kasa da kasa, James ya shiga ne tun yana makaranta, da farko ya shiga ne dan kuɗi, daga baya ya koma kishin kasa, sannan ya zo ya shiga cikin manya-manyan yan ta'adda na duniya, domin ya rinƙa kashe su, to lokacin da ya fara sanin daɗin rayuwa ya fara jin tsananin kaunar yan uwansa, yana jin ba zai iya rabuwa da su ba, alokacin ne ya fara ƙoƙarin neman ta ina zai fita CIA, babbar matsalar shine idan aka shiga ba'a fita, domin kafin ka shiga sai ka sa hannu akan ka sayar masu da rayuwarka, idan ka amince da hakan to za su yi maka tiyata su dasa maka wani abin mai kama chemical kakar kuma bom haka yake, da na ura yake aiki, idan kayi wargi kaɗan mai sarrafa nauran zai iya fasa ka, abin da kuma yasa suke yin hakan domin idan yan ta'addan sun kama nasu idan ya ji wuya ya yi ƙokarin tonawa hukumar tasu asiri hakan zai sa su danna wanann abin su tarwatsa mutun ya mutu har lahira, dan kada ya fitar da sirrin hukumar har a iya far musu a gane ina suke, shine amfanin wannan makami mai kama da bom ɗin, ana danna na'uran zata fashe kamar bom ta kashe mutun, ko wani ɗan cikin CIA yana da ita a kirjinsa, shiyasa Lion ya ce kada su Tga su bari a sanyawa James Camera, domin ana sanya mashi CIA da su gani, su kashe shi dan kada ya tonawa hukumar asiri, kamar aljanu haka suke, sai ka zauna a tare da su baka san su bane, idan suka ga James acikin wannan hali to suna iya danna wannan naura abin da suka sanya mashi a kirjinsa ya tarwatsa shi kamar bom ya mutu, haka yasa Lion ya ce Tyrone ya harbi wajen da wanan abin yake, suna harbi wajen abin zai ɗauke daga jikin na'uran CIA kamar network, yana ɗauke wa kuma James ya tsallake layi ɗaya, shine Tyrone ya kasa yin harbin, yanzu babban tashin hankali shine tayaya za'ayi James ya fita daga cikin CIA (ROW)?, domin TRIPLETS ba za su yarda da sayarda ransa da ya yi ba, hakan ma yasa yake ɓoyewa Lion kada ya sani, shiyasa yake yi masu basaja dan kada su gane, ya ci bakar wuya kafin ya zama DOA ya sayar da ransa ya rinƙa shiga cikin kungiyoyin yan ta'addan, kuma abin da yasa da sun bashi contract na kashe wani zai yi sauri ya aiwatar da aiki, dan dama dukka yan ta'addan ne kashe su yake son yi, ya yi aiki tukuru dan tsabtace kasarsa kamar wani baban soja, ya wahala iya wahala, yanzu baraza ɗaya ta rage shine fita daga CIA, babbar matsalar ma Allah ne kaɗai ya san ina da ina suke sakawa mutun wasu abubuwa a jikinsa na tarwatsa sa, lokacin da Lion ya gane hakan ya ji haushi sosai kuma ya kiduri niyar hukunta James ɗin hukunci mai tsanani ta yadda gobe ko hauka yake yi ba zai sayar da rayuwarsa ba, idan aikin cetan kasa yake son yi ya shiga hukumar soja mana, ko siyasa. Batu akan wayan nan sojoji guda biyu da ya kama ya yi masu hukinci a ranar da Lion ya turo a tarwatsa kungiyar su kuma, suma duk gurɓatattune dan ya san su a wata dabar da ya taɓa shiga ya kashe mataimakin mai wannan dabar, shiyasa duk kunguyar dabar da ya shiga suke bala'in ji da shi, dan ya samu kwararren training kamar soja, har mamaki suke yi yadda idan ya kalli abu sau ɗaya zai iya rufe ido ya sa bindiga ya saita abin ya harba, a takaice dai JAMES ya fi Tga ma a samun cikakken horo, shiyasa yake iya dukan Tga ɗin, James jarumin gwarzon namijine sosai, har ya kusa kamo Lion a manya-manyan ayyuka domin cetar kasarsu, dan shima Lion kafin ya taka matsayin da ya taka sai da ya yi ayyuka fin haka.

Abin da ya faru aka maka shi a Nigeria kuma da har Lion yake jinjina wa yan Nigeria shine, bayan ya kammala kashe gaba ɗaya dabar su dake a Spain ya biyo sahu dan ya karisa wayen dake a Nigeria, ba gaba ɗaya wayen dake a Nigeria bane yan Nigeria, no akwai turawa yan uwansu a ciki, wayan da suke haɗe da baban fatan mu, su dai sun ɓuya ne a cikin wannan gidan suna bawa bakaken fata umarnin da su kashe ko kada su kashe, to ya biyo ne ya shiga cikincin dan ya kashe su, ya yi amfani da ogansu dake dabar Usa wadda bai kashe shi ba, kuma dama bai kashe shi bane ya bar shi, ya ɗaure shi a asalin office nasu na ROW dake a karkashin kasa a Usa, dayawa daga cikinku zaku iya tuna wannan office ɗin, in da ya hukunta wayan nan sojojin, to ya bar wannan ogan nasu na dabar da ya yi ɓaɗɗa kama a ciki ne saboda ya cigaba da gaya mashi ina sauran yan ta'addan suke, shiyasa ya yi aiki sosai ya shiga jikin ogan nasu ya so shi sosai ta yadda baya ɓoye mashi komai, ya mai da shi babban yaronsa, to da wannan dama yake amfani yana mashi wayo yana kashe yan daban, wata sain haka kawai zai kashe wasu daga cikinsu idan ogan ya tambaye me yasa ya kashe su, sai ya ce ai ya gano su yan leken asiri ne wata kungiyar ta'addancin ne, hakan yasa ya zama ko ya kashe wani a cikin su ba'a tambayarsa dalili, kuma hakan ne yasa ya zama makusancin su saboda a tunaninsu yana da baiwa yana kama masu yan leken asiri, babu san yana yi masu kisan mummuƙe bane.

Yana shigowa Nigeria da kallo ɗaya yan daban Nigeria suka yi mashi suka kama shi, suka ce lallai ba ɗan ta'adda bane wannan, ya gaya masu waye ya turo shi, daga karkashin wace hukuma yake, wannan shine abin da ya sa Lion ya jinjinawa kaifi kwakwalwa ta yan Nigeria, yan kasashe da dama basu iya gane cewa James ba ɗan ta'adda bane, babba ne a cikin hukumar CIA, amma yan Nigeria da kallo ɗaya sun yi ram da shi, abin ya sa Lion ya jinjinawa Nigerians. Shi kuma wanda yan ta'addan nan suka yiwa yanka rago, ba kowa bane fa ce shine DIA babban mataimakin James ɗin ne awajen aiki, lokacin Lion ya gane hakan ya yi farinciki ganin James ba ɗan ta'adda bane, so kuskuren da James ya yi a wajen shine yadda ya shiga cikin yan ta'addan tsundum, kuskure na biyu kuma ɓoye masu da yake yi, kuskure na uku kuma sayar da rayuwarsa da ya yi. Duk guje gujen da yake yi yana yi ne dan kada TRIPLETS nasa su gane ne, saboda yasan ba za su taɓa yarda da hakan ba, kuma yanzu ma ba za su yarda da hakan ba, ya yi aiki sosai wadda ko General ba zai gwada mashi aiki ba, wannan dalili yasa Lion ce wa Tga James ya fi karfin sa, abin da ya yi abune mai kyau amma Lion ba zai taɓa yarda da hukumar CIA ba domin a yanzu haka James ba mallakin su bane, mallakin CIA ne domin ya riga da ya sayar masu da kansa. BABBAR MAGANA, A TAKAICE WANNAN SHINE WANENE JAMES DA KUMA HALIN DA YAKE CIKI A YANZU, KO BAN ZURFAFA BAYANI BA ZAKU IYA FAHIMTAR INA AKA DOSA!! MU KOMA CIKIN LABARINKU.

Story

Shiru ya yi na tsawon mintoci kamar 10 haka kafin ya fara magana gently. "Prof James ba ɗan ta'adda bane, kamar yadda ka ɗauka, amma dole zan hukunta shi, dole ya karɓi hukunci mai tsanani domin ya yi mani laifi" Zaro ido Imran ya yi yana faɗin "Ban gane ba dan Allah ka yi mani baya ni dallah dallah". Shiru ya yi, ya ɗan jima a haka kafin ya bawa Imran labari sama-sama kamar yadda dai na gaya maku waye James ɗin.

Ba ƙaramin daɗi Imran ya ji ba, sai dai kuma idan ya tuna cewa Lion ya ce sai ya yi mashi hukunci mai tsanani na sai da kansa wa CIA da ya yi, sai gaba ɗaya ya ji kuma jikinsa ya mutu, baban damuwar ma ba su san iya kar abubuwan da CIA suka sanyawa James ɗin ajikinsa ba, sai dai Lion yana bincike akan me da me suka yi mashi, dan ya san ta yaya za su iya samu su fitar da shi daga hukumar.

(Ni kuma na haɗa kayana zuwa wajen RIMSHA wata kila kafin na dawo su Lion sun ɗan gama jira)

🔥RIMSHA🔥

Sai zumuɗi take yi yau ta je school, fuskarta har wani kyalli yake yi saboda tsantsan farincikin dake a tattare da ita. Karfe 2 na rana daidai ta dawo, Akil ne ya je ya ɗauko ta, duk da busyn nan da yake a ciki, hakan bai hana shi kula da amanar da Imran ya bashi ba, ko da ya ɗauko ta bai tafi ba, ya tsaya yana kallonta har ta shiga part ɗin Imran, sannan ya juya kan motarsa dan suje su san yadda za'a kai kuɗin karɓar Aafia da Rufee, da farko yan ta'addan sun ce da daddare za'a kai kuɗin, daga baya kuma suka sake fasawa wai da rana za'a kawo, hakan yasa ya ce to shi zai kai ya karɓo A'afia ɗin. Kada ku mance Jinin Umaiya basa taɓuwa ta daɗi

Ko menene a jinin Umaiya oho? Waye ma ita ɗin? Mu je dai zuwa akwai labari agaba.

Rimsha tana shiga cikin palon yaya Imran ta tarar da Akila, a lokacin ta gama yi musu girki ta yi wanka.

Tana ganin Rimsha da sauri ta zo ta rumgumeta tana faɗin "Welcome my dear" ita ma Rimsha rungumarta ta yi tana mata oyoyo tare da tambayarta ya gida, nan ta ce mata ai ita ma karfe 12 ta dawo daga school, shine ta ce bari ta yi masu girkin abin da ta iya dafawa wato shinkafa da miyar steew, ita ma Umaisha yanzu da Akil ya fahimci me yake faruwa tsakaninta da Ammie sai idan zai fita, sai su fita tare ya kawo Part ɗin Imran ya ce ta zauna kada ta koma Part nasu sai ya dawo, abin da ya sa kuma bai kai ta gidan saba, saboda babu kowa kuma yanzu yana busy ba zama yake yi ba, ita kaɗai a gidan zata ji tsoro sosai, ya ce sai ya gama abin da yake yi, ma'ana kenan sai sun gama da case ɗin Aafia, zai mai data gidan nasa kafin su koma Madina, hakan yasa yake barinta suna zama a tare gaba ɗaya a part ɗin Imran ɗin tun da shi baya nan.

Wanka Rimsha ta fara shiga kafin komai, ko da ta je yin wanka sai faman shafa sunan Lion take yi, ita kaɗai kamar zautatciya sai murmushin take yi a toilet, har wani lumshe ido take yi kamar shine yake shafa mata wajen, abin da ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai shine yadda akayi sunan yake matsawa zuwa saman tula-tulan da kyau a nata ganin, bata san cewa asali ma akan su ta yi zanen ba, lokacin dai basu girma bane suna kanana, sai take ganin kamar baa kansu bane, abin da bata sani ba shine, kullun breast ɗin nata kara cikowa suke yi, wajen da ta yi rubutun yanzu duk ya ciko sosai, shiyasa take ganin kamar rubutun na matsawa ne.

Bayan ta yi wanka ta ɗauro alwala ta fito ɗaure da towel a kirjinta, sai santin dark black curly hair ta Akila da Umaisha suke yi, ga shi jiya sun sha gyara gashin har wani kyalli yake yi, kunshintan nan ba'a magana.

Shiryawa ta yi tsab cikin Pakistan wando fari rigar blue gyalen ma blue, ba karamin kyau ta yi ba, sai ta saje da indiyawa abinta, simple make up ta ɗan yi tare da feshe jikinta da perfume ta zo ta yi sallah.

Bayan ta idar ne Akila ta ce suje su ci abinci, to ta amsa da shi dan dama tana jin yunwa sosai, 1k ɗin da Akil ya bata dan sayan abu a school, bata sayi komai ba, ta dawo da shi a jakarta, dan bata saba ba, abin da ta saba shine tafiya da abinci daga gida, kuma yau saboda zumuɗi bata ɗauki abincin ba, duk kuɗin da daddynta yake da shi bai koya masu saye sayen abin da ake sayarwa a shop na cikin school nasu ba, hakan yasa yanzu ko ba'a basu kuɗi ba sun saba, duk wani kayan cima su biscuit, chocolate, har ice cream, yogurt duk daga gidan mun ɗin su ke shirya ma su a lunch box ɗin su, KUMA HAKAN YA FI SHINE DAIDAI, KADA A SABA BAWA YARO KUƊI, KODA BISCUIT ƊIN NE ARINƘA SAYA MASHI SAI ANA SANYA MASHI A BOX ƊIN NASA, DOMIN BAKA DA TABBACIN ZAKA RAYU DA YARONKA HAR YA KAI MUNZALIN YIN HANKALI, TO YA DAI KAMATA DUK ABIN DA YAKE SO ASAYA A BASHI, KADA A RINƘA BASHI KUƊIN KAI TSAYE!!!

Suna ƙokarin fita daga cikin ɗakin ne wayar Rimsha ya fara kara, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa, kamar ba zata ɗauki wayar ba, sai kuma ta koma ta je ta ɗauka, new number ta gani, zubawa number ido ta yi tana mamakin ita dai tasan cewa Yaya Ahmad da Aunty Akila ce kawai ke da number wayarta, ko Imran bata da number wayarsa, tana ta tunane tunane har wayar ta katse, yana katsewa sai ga saƙo ya shigo, Ki kunna data, shine kawai abin da aka rubuta a saƙon.

Cike da tsoro ta kunna data, tana kunnawa video call yana shigowa tare da wani sakon a WhatsApp, sakon ta fara karantawa da wannan number kuma. Yaya Imran ne ki ɗauki kiran, a wajen heartbeat na karɓin number ki, shi abin da ta gani a WhatsApp ɗin. Bata san time da murmushi ya suɓuce mata ba, da har ta tsorata sosai.

Picking na video call ɗin ta yi tana murmushi, wani irin muguwar kaɗuwar gaba ta ji lokacin da dara-dara sleeping eyes nata suka sauƙa akan Lion ba yaya Imran ba, yana zaune a gefen gadonsa yana ɗan latsa wayarsa, kansa na a kasa, da alama abu mai muhimmanci yake yi, da alama kuma bai san Imran ya sa mashi camera ba, har wani shocked ta ji jikinta ya yi, ta kasa motsawa, yau ga shi nan a gabanta ba face mask, kamar a mafarki, sai faman lumshe dara-dara blue eyes nasa yake yi, kamar mai jin barci, wayan nan zara zaran eyelashes ɗin nasa, da ya lumshe ido sai ki gansu kamar ya sanya na kari sabo tsawon su.

Hannu tasa ta toshe bakinta tana bin jikinshi da kallo shi kuma Imran yana bin fuskar ta da kallo, yana jin matsanancin farinciki yau ya sakata farinciki, zuba mata ido kawai ya yi yana kallon yadda take bin Lion da kallo, da wayan nan dara daran sleeping eyes ɗin nata, kwata-kwata bata kawo a ranta cewa Imran ɗin yana kallonta ba, dan kunga ya juya mata cameran.

Ganin ta yi shiru tana kallon waya ba wani motsi ne yasa Akila ta zo ta leƙa wayar tana faɗin "Me kike kallo kika natsu haka kodai....." Bata karisa maganar ba ta ɗauke wuta sakamakon sauƙa da idon ta ya yi akan Lion, ita kuma Umaisha tuni ta yi waje tun lokacin da Akila ta ce su tafi cin abin, sai tayi gaba.

Suna tsaka da kallonsa basu ankaraba sai gani suka yi ya ɗago wannan fusataccen fuskar nasa, kai tsaye kuma sai kan Imran ya sauƙe idanunsa, yadda kasan su yake kallo saboda saitin cameran yake kallo, razana tasa Rimsha ta saki wayar tata ta faɗi kasa, ba ita kaɗai ba har ta AKILA kwarjininsa ya razanata sosai da sosai, da kyar ta iya jan numfashi tare da haɗiyar wata wahalallen yawu ta ce "Rimsha aiki na gaban ki, wlh dole ki suma ashe haka yake

Please Login or Register in order to submit comment