Reading TRIPLETS BOOK 2 by Star Lady Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya karya tan da gaske, dan haka ba musu tabi bayan sa, tana turo baki.

Allah sarki Akila baiwar Allah mai kaunar yan uwan ta, taso su fahimci Juna da Aafia amma abun bai samu ba, Aafia akoi ta da ji da kai, da nuna isa da izza.

Kai tsaye gida Akil ya kai ta da motar sa, kuma da kan sa ya tuka, sai dai ko da suka je gate ɗin gidan, shi bai shiga ba, a kofar gida ya sauƙe ta, ya juya kan motar sa zuwa gida.

Cikin gida ta wuce tana rakuɓe rakuɓe, tana addu'ar Allah yasa daddyn Jelly baya palo, dan idan ya kalle ta da kayan jikin tan nan akoi matsala ba kaɗan ba.

Tayi Sa'a kuwa daddy baya palon, cikin sauri ta wuce ta haye sama ta nufi bedroom nasu.Tana shiga ta cire kayan jikin ta ta faɗa toilet dan yin wanka.

Bayan tayi wanka ta fito, ta shirya cikin atamfa riga da skit kayan sun kama ta sosai, ta ɗauki after dress ta ɗaura saman kayan nata, ta fito palon kasa hannun ta riƙe da maganin da Rufee ta bata, dan ta zubawa Aunty a abinci, taci cikin jikin ta ya zube.

Shiru palon kasan babu kowa, ga kuma abinci saman table an geresu, sauri sauri ta nufi table ɗin, kulan miya ta buɗe ta zuba maganin a ciki tare da gauraya miyar sannan ta rufe, tana tunanin anya idan su Abbi suka ci maganain nan ba zai musu illa ba kuwa, gashi kuma bata da wata hanya da zata sa Aunty taci maganain nan dole dai sai dai ta zuba a kulan miyar gaba ɗaya, shiyasa ta zuba, kuma ta dawo tana danasani kar su Abbi suci maganin ya zamo musu illah.

Tayi nisa cikin tunanin da take, sai ji tayi Aunty nace mata "Aafia lafiya?" Yar firgigit tayi irin na marasa gaskiya.
Ganin Aunty ne yasa taja dogon tsaki tare da wuce wa, ta bar wajen, ta koma saman sofa ta zauna, Aunty kuwa baiwar Allah bata kawo komai a ran taba, tayi tunanin ma ko yinwa Aafia take ji ne yasa tazo wajen table ɗin, shiyasa ma ta tambaye ta ko lafiya.

Dai dai lokacin daddyn Jelly ya shigo palon shirye cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ɗinkin full jompa, yayi kyau sosai, ɗan zaman sa a gidan har ya fara murmurewa.

Har kasa Aunty ta tsuguna ta gaishe shi, da fara'a ya amsa tare da ce mata "Zan fita kila yaya ya rigani dawowa, idan ya dawo ki sanar da shi na fita, ganin gari shine abun da ya shigo dani part naku" cikin girmamawa Aunty ta amsa masa da to, ita kuwa Aafia ko ajikin ta kamar bata gan shi ba, sai faman tura baki take, wucewa yayi ya fice daga palon, dan tun da suka nuna masa basa son shi a gidan ya daina shiga harkan su, idan sun masa magana fine ya amsa, idan kuma basu masa magana ba shima baya kula su, dan baya son raini ko kaɗan, ko part nasu bai cika shigowa ba, sai dai idan Abbi yana nan, sai ya shigo palo suyi hira, Abbi na fita shima zai fice ya koma part na shi, wato ɓangaren Irfan kenan.

Bayan daddy ya fitane Aunty ta duɓi Aafia tace "Aafia me yasa zaku rinƙa yiwa kanin mahaifin ku haka? Babu kyau abun da kuke yi fa, ya kamata ku gyara kuyiwa kan ku faɗa domin baku san me gobe zata haifar ba, kuma kuna sane da tashin hankali da bawan Allah nan yake ciki, kamata yayi ku jashi a jiki dan ku ɗebe masa kewar rashin Jalila a tattare da shi, sannan kuma shima fa a matsayin mahaifi yake a gare ku ida.... Bata kai karshen maganar ba Aafia ta daga mata tsawa "Ke dallah kima mutane shiru, ina ruwan ki da rayuwar mu? Ba dai kanin mahaifin mu bane? Ai ba kanin tsohon ki bane, to dan haka ki shiga hankalin ki, ina buga miki last warning da babban murya, idan kika sake shiga harkana, wlh sai na miki illa, wawuya kawai yar datti!!" rai a matukar ɓace Aunty tace "Ke Aafia ina son ki shiga hankalin ki, ya issheki haka nan, ya isheki cin mutunci na a gidan nan in kyaleki, na gaji, wlh idan kika sake faɗa min wata maganar banza idan ranki yayi dubu sai na ɓata miki shi"

Miƙewa tsaye Aafia tayi tana faɗin "Eyee a lallai yar talakawa kin sha jar miya, har ni kike wa last warning kenan, to wlh baki isa ba, in dai ni Aafia na haifu sai kin bar gidan nan yau!!" guntun tsaki Aunty taja kafin tace "To sai me? Dan na bar gidan ku sai me? Mutuwa zan yi ne dan na bargidan, ko kuma a'a aljanna ce ba zan samu ba idan na bar gidan, ai wlh da zaman wannan gidan naku gara mutun ya tabbata a gidan uban sa, yan iskan yara mara sa hankali, marasa tarbiyya, ku daga gani wlh uwarku ba hausa fulani bace , dan wanna bakin halin naku bayyi kala da na mu ba, amma ni ina mai baku shawara wlh kubi duniya a sannu, idan ba haka ba, watara na sai kunyi nadamar zuwan ta, ku mata ne, baku san ina aure zai kai ku ba"

Rai a matukar ɓace Aafia ta nufi Aunty da niyar ta mare ta, cak Aunty ta riƙe hannun ta, yau fa hakurin mai hakuri ya kare, daman ance mai hakuri bai iya fushi ba, to wanna ma hake ne

Wanke ta da wawan mari Aunty tayi a fuska, tare da daka mata tsawa "Dan baki da hankali sai kiyi yunkurin saka hannun ki a jikin mahaifiyar ki, matar baban ki?!!" tashin hankali Aunty fa ta fusata.
Kokarin kwace hannun ta Aafia take daga riƙon da Aunty ta mata dan ta rama marin ta da aunty tayi, tureta aunty tayi ta faɗa sama sofa, sanna ta wuce da sauri ta haye sama abun ta, dan bata son tsayawa tayi faɗa da Aafia, yin hakan zubar da kai ne, sai dai kuma Aafia tana da burin hakan ko dan ta daki Aunty a ciki.

Da gudu Aafia ta miƙe tabi aunty sama, sai dai kafin ta iso Aunty ta shige bedroom nata tare da murzawa kofar ta key, haushi kamar Aafia ta fasa ihu, kafa tasa ta shuri kofar da karfi sannan tace "Zaki fito ai, wlh sai kin yabawa aya zaƙin ta a gidan nan" hayewa saman gadon ta aunty tayi abun ta, ta kwanta tana mai jin bakin cikin abun da yake faruwa a gidan nan, Aafia ta kureta, ta kai ta bango, taso suyi zaman lafiya amma abun ya faskara, ba yadda za tayi dole ta fito ta karɓawa kan ta yanci kawai dan ta samu zaman lafiya kuma ta samawa ɗan da zata haifa ko ƴa yancin kan su a gidan baban su.

Aafi kuwa palo ta koma tana ta surfa ruwan bala'i a kan aunty zata fito ta same ta, ba zata kyale taɓa.

A ɓangaren Umaisha kuma, da zazzaɓi mai zafi ta tashi tare da kuka, lokacin ana kiraye kirayen sallar mangariba, Akil baya nan, ya tafi kai Aafia gida bai kai ga dawowa ba, ya wuce masallaci daga nan.

Jin kukan Umaisha yasa Akila ta tashi ta nufi part ɗin Akil, lokacin Ammie ta bar palon ta koma bedroom nata, shi kuma Abba ya wuce masallaci.

Tana shiga bedroom ɗin ta haye saman gadon kusa da Umaisha tana faɗin "Umaisha lafiya? Me ya same ki kike kuka? Ko dai yaya Akil ya miki wani abu ne? Ko kina son komawa gida ne?" Kuka kawai Umaisha keyi, bata samu damar samun bakin magana ba "Dan Allah akila kiyi shiru kinji? Tun ɗazun fa nake ta murna ina jiran ki tashi daga barci muyi hira, tun da na dawo school yaya Akil ya sanar min ya ɗauko ki, kuma ke yanzu matar sace, sai murna nake tayi, ina fatan ki tashi daga barci muyi hira, amma shi ne kuma zaki tashi kina kuka? Dan Allah ki dai na kuka ki faɗa min, idan ma yaya Akil ne ya miki wani abun to yanzu zan kira yaya Imran a waya na faɗa masa, kuma zai rama miƙi, dan yaya Imran yana da adalci" nan ma Umaisha bata kula taba, ci-gaba da kukan ta tayi kawai, ita ka ɗai tasan me take ji a jikin ta, ganin haka yasa Akila ta sauƙo daga gadon, ta fice daga ɗakin da sauri, ta nufi bedroom ɗin Ammie.

Zaune bakin gado ta samu Ammie, da sauri ta tafi ta faɗa jikin ta tana faɗin "Ammie dan Allah kizo ki lallaɓa Umaisha tayi shiru, sai kuka take taki yin shiru, ban sane me ya same taba" guntun tsaki Ammie taja kafin tace "Kije kice mata, ta tashi ta tafi gidan su tun kafin nazo na same ta a wajen" zaro ido Akila tayi tare da turo baki tace "Haba Ammie yaya Akil fa yace matar sa ce, to ya za'ayi kuma ta tafi gida?" "Waye yace miki matar sace? Ba matar sa bace, shi ba ajin irin wayan nan yaran bane, ki tashi kije ki ce mata ta wuce ta tafi gida tun kafin nazo na karya ta, dan haushin suma nake ji gaba ɗaya" Kukan shagwaɓa Akila tasawa Ammie, tana ɗan bubbuga kafar ta a jikin gadon tana faɗin "Haba Ammie, to ai ko ba matar yaya Akil bane yar uwar mu ce, kinga kuwa zata iya zama a gidan nan" Jin Akila tace yar uwan suce yasa Hajiya ta miƙe a fusace ta fito ta nufi part ɗin Akil. Da sauri Akila ta miƙe tabi bayan ta

Kamar yadda Akila ta bar Umaisha haka Ammie ta shigo ta same ta, tsawa ta daka mata "Ke tashi ki wuce gidan uban ki, ban son munafurcin banza" shiru Umaisha tayi bata amsa mata ba, kukan ta kawai take.

A fusace Ammie ta haye saman gadon tare da yaye bargon da Umaisha ke lulluɓe, ta riƙon ta, ta miƙar da ita tsaye tana faɗin "To wuce a kai kaya ma sauki" kasa tsayuwa Umaisha tayi, Ammie na sake ta, ta zube a kan gadon tare da kara sautin kukan nata, daidai lokacin Akila ta shigo ɗakin, kamar zatayi kuka tace

"Ammie dan Allah kiyi hakuri ki barta kinji?" Ammie bata kula taba, sai ma kara mikar da Umaisha tayi, ta jata, sai kokarin faɗuwa kasa Umaisha take saboda jikin ta ba kwari, kuma ba zata iya taka kafar ta ba, saboda azaban da take ji, sai kukan wahala take abun gwanin ban tausayi.

Kai tsaye waje Ammie ta nufa da ita, tana jan ta kamar wata rago, sai kuka Akila take tana addu'ar Allah ya kawo yaya Akil ko Abba.

Ammie tana zuwa bakin kofar Palo, ta tura Umaisha waje tana faɗin "Kar na sake ganin kafar ki a gidan nan" tana turata ta tafi sai saman kirjin Akil ta faɗa, yanzu ya dawo daga masallaci yana kokarin shigowa kenan

Umaisha na kokarin sulalewa kasa daga kirjin nasa, yayi saurin riƙota yana kallon Ammie dake tsaye a bakin kofa tana kallon sa

Kasa tsayuwa Umaisha tayi dan kafar ta babu kwari, sai kerma jikin ta keyi, dawo da kallon sa kan fuskar Umaisha ɗin yayi, kasa kasa yace "I'm so so sorry" ya kai karshen maganar tare da ɗaukan ta cak, ya juya ya bar wajen, ya nufi motar sa da ita ba tare da yace da Ammie ko uppan ba, dan baya son jan magana da ita a kan Umaisha, yasan halinta sarai zata iya yi masa baki a kan hakan, ta raba shi da Umaisha, shiyasa baya son maganar Umaisha ta haɗa su

juyawa ita ma Ammie tayi ta koma cikin Palo, tana jan guntun tsaki, a tunanin ta Akil zai mai da Umaisha gida ne. Ita kuma Akila tana ɗakin Akil tana kukan ta.

Kai tsaye asibiti Akil ya wuce da Umaisha dan yaji jikin ta da zafi sosai, yan gwaje gwaje aka mata, sannan aka basu bagunguna, ya ɗauko ta suka dawo gida.

A palo ya samu Ammie da Akila suna zaune, Abba bai dawo ba, bai yiwa kowa magana ba, ya wuce ya nufi ɗakin sa, "Akil kazo ka ci abinci" cewar Ammie, a takaice yace "Bana ci, na ƙoshi" yayi maganar ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake ba, "Ka fitar da yarinyar nan daga gidan nan nace ko?" Ammie ta sake yi masa magana, shiru yayi bai tanka ba, ya wuce bedroom nasa.

Saman gado ya kwantar da Umaisha, wadda take fitar da numfashi da kyar saboda wahala, bargo yaja ya rufa mata sanna ya fice ya dawo palon

Kusa da Ammie ya zauna yana faɗin "Ammie me yasa yanzu baki son farinciki nane ne? Me na miki? So kike na mutu ne eh Ammie na?" Zaro ido tayi kafin tace "Haba Akil kasan me kake faɗe kuwa? Nice bana son ka? Idan ni bana son farincikin ka waye kake tunanin zai so farincikin ka?" Kallon Akila dake zaune tayi shiru tana tunani, tasha kuka ta koshi, dan ita a tunanin ta Ammie ta kori Umaisha ɗin ce

"Heartbeat tashi kije ɗaki bari muyi magana" Akil ya faɗa yana tsare Akila da ido, tun bai kai karshen maganar ba ta miƙe ta wuce bedroom nasa wajen Umaisha, dan bata da burin da ya wuce ta gan ta tare da yan uwan ta.

Dawo da kallon sa yayi kan Ammie cikin nitsuwa yace "Ammie na faɗa miki ina son matata, kuma ita ce farinciki na, me yasa baki son hakan? Me ta miƙi? Na san bai wuce kice abun da ya faru tsakanin ku da baban ta, da kuma su bappa Husaini bane, to ita me nata a ciki, kinga ai ita bata san komai ba, kuma da wuya ma idan ta san labarin abun da ya faru kafin a haife mu, dan Allah Ammie ina son kiyi min wannan alfarma, ki yafe wa family'n Abbana komai ya wuce kinji ko?" Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun ta yana kallon cikin idon ta "Akil, Akil, Akil, sau nawa na kira sunan ka?" Shiru yayi yana kallon ta

"Ba zaka bani amsa ba, nace sau nawa na kira sunan ka?" "Sau uku kika kirani Ammie" ya bata amsa, "To wlh ka fita ido na, karka sake min maganar su Hussaini a gidan nan, ita kuma yarinyar tun da kace ita kake so, kaje kai kasani da ita can, in dai family'n Abban kane da kan ka ma zaka guje su ba sai wani yace ka barsu ba" murmushi yayi kafin yace "Shikenan Ammie in dai kin yarda na zauna da ita shikenan ba damuwa ai" kawar da zancen tayi da cewa "To ka tashi ka ɗauko abinci ka kaci" to kawai ya amsa da shi tare da miƙewa ya nufi saman table ya ɗauki abinci kula ɗaya da plate ɗaya tare da spoon shima ɗaya, ya wuce bedroom na sa, binshi da kallo Ammie tayi, kasa kasa tace "Ba zan taɓa bari ka zauna da yarinyar nan ba, dan bana son ta, kuma bana kaunar iyayen ta, dole ka rabu da ita"

Da sallama ɗauke a bakin sa ya shiga cikin bedroom na sa, Akila na zaune saman gado tana rarrashin Umaisha dake ta faman kuka har lokacin.

"Heartbeat ɗauko min Yoghurt a Palo" turo baki Akila tayi kafin tace "Yaya Akil ba haka zaka ce ba, kace Heartbeat tashi ki fita min a ɗaki" murmushin yayi kafin yace "Ni na isa in ce ki fita min a ɗaki ne? Yoghurt fa kawai nace ki ɗauko min" "Yaya Akil yaushe ka fara shan Yoghurt ban sani ba? Kai da ko tea da madara baka sha saboda karni shine yau zakace na ɗauko maka Yoghurt, na sani ba wani Yoghurt kawai korata kake yi" ɗaga mata gera ɗaya yayi yana faɗin "To tun da kin gane me kika tsaya yi ware da wuri" dariya tayi tana faɗin "Ba damuwa yaya Imran ya kusa dawowa ai, idan ya dawo ba zan sake zuwa nan ba, kuma shi nasan ko ya auri Aunty jelly ba zai koreni a ɗakin saba" "oho dai tashi ki tafi" yayi maganar yana kokarin hawa saman gadon, bayan ya ajiye musu abincin su saman table dake cikin ɗakin,
Da sauri Akila ta diro kasa daga saman gadon tana faɗin "Aunty Umaisha Amarya sai da safe, yaya Akil mun ɓata da kai" shiru ya mata, dan bai son biye mata, so yake ta fita ta basu waje.

Tana fita ya sanya hannun sa ya tallaɓo Umaisha yana faɗin "Sorry tashi kici abinci kisha magani" cikin kuka tace "Na koshi" girgiza kai yayi yana faɗin "a'a ban yarda ba ki tashi kici" ba dan taso ba, haka ya miƙar da ita zaune ya rinƙa ɗura mata abinci tana ci dan dole

Bayan ta gama ya bata ruwa ta sha, sannan ya mai da ita ya kwanta, ya sauƙo ya wuce toilet dan yayi wanka yazo ya gabatar da sallar issha da bai samu yayi ba, sakamakon kai ta asibiti da yayi.

Bayan yayi Sallah ne ya haye gadon kusa da ita ya kwanta, yana faɗin "I'm sorry kinji?" Shiru ta masa ba tayi magana ba na ɗan lokacin kafin tace "Ka mai dani gida kada Abbi ya neme ni" juyo da kallon sa yayi kan fuskar ta "Already na kira bappa a waya na sanar masa da nazo na ɗauke ki daga school kina tare dani" mamaki ne ya kamata tace "Abbi na fa wanda ya haifeni" ya gane me take yiwa mamaki, wato ya za'ayi Abbi ya yerda ya ɗauke ta su tafi su kwana, bayan ba aure sukayi ba, shine abun ya kulle mata kai

"Eh Abbin maki fa, bakin san cewa ke matata bace ko?" Shiru ta zuba masa ido tana kallon sa "To ki rufe idon ki ya isa haka kallon nawa, karki haifa mana baby mai kama dani, zai fi kyau ki haifi mai kama dake, kiyi barci da safe zamuyi magana" ya kai karshen maganar tare da sanya hannun sa ya rufe mata ido, mamaki ya hana ta magana ta kwanta shiru, da haka barci ya ɗauke ta.

Shima shiru y kwanta har barci ya ɗauke sa. Ammi kuma tana can palo tanan saka yadda za tayi da Akil dan ya rabu da Umaisha, Akila kuwa tana fita ɗakin Akil nata ɗakin ta wuce dan taje ta kira daddyn Jelly dasu Abbi, yayan Imran, haka take, kafin tayi barci sai ta kira kowa daga cikin yan uwan ta, har da Abla sun sha hira sannan take barci.

Muleƙo Washington DC mu dawo

Yau ban haɗa muku page biyu bane, sakamakon bana jin daɗin jikina, shiyasa ban samu damar yi muku editing 2 page ba, amma In Sha Allah gobe zan biya

Karku manta idan Allah ya kai mu ranar Jumma'a da rai da lafiya, zan ɗauki hutu na ɗan wani lokaci, dan in ɗan huta in samu kwakwalwata tayi fresh, in ji daɗin zubo muku zafafan page's masu tashin kai, ina godiya sosai da sosai Allah ya bar zumunci 🥰

Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu .

💞💞TRIPLET'S💞💞






# BOOK 2📚📙✍️


💔💔Episode 5-6💔💔


💔RIMSHA💔


💞💞Washington DC💞💞

09:30am

A hankali yake sako kafar sa a saman benen yana tafiya kafar baya son taka kasa, jikin sa gaba ɗaya a mace, sai wani cizan lallausan laɓɓan sa yake, jikin sa na sanye da Ripped Jeans black color, da white Round neck t-shirt, kayan sun masa kyau sosai da sosai, kamar dan shi akayi su, kyawawan fararen kafafunsa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal fari tas kalar rigan sa, ya ɗaure wannan kyakkyawan dark black curly hair nasa a bayan, ya bar wanna ɗan guntu a gaban goshin sa, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshi yake, kamar anyi ɓarin turare.

Palon kasa shiru babu kowa kasan cewar already sun riga sun breakfast kowa ya kama harkan gaban sa, masu barci sun koma barci, masu fita sun fice yawon party da sauran su, dan basu da aiki da ya wuce wannan.

Jiki na kerman tsoro bodyguard dake cikin palon suka fara ɗaga masa gaisuwa ta hanyar ɗaga hannayen su, suna sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba, ya sa kai ya fice daga palon.

Already an jera motocin da zasu fita, shi kawai suke jira. Yana fitowa jibga jibgan sojojin sa suka fara sara masa, wucewa yayi kai tsaye ya nufi motar sa kirar Bugatti La voiture, da sauri wani jibgegen soja yazo ya buɗe masa motar, ya shiga ya zauna. A guje sauran sojojin suka haye saman bayan nasu motoncin.

A jere motocin suka tashi, suka fice daga gidan, tare da sakin jiniya, tamkar yaki zasu tafi. Kai tsaye white house suka nufa.

Kun dai san yadda white house yake ba sai na tsaya dogon bayani ba, ko ta ina sojoji ne kewaye a cikin gidan, hannayen su riƙe da manya manyan bindigu masu rai da lafiya, ga yan sanda ma ba'a barsu a baya ba, suna tsai tsaiye.

His excellency mr president yana cikin fadan shugaban kasa, kai tsaye wajen sa Romeo ya nufa yana taku irin na manyan jarumai sadaukan yaki, duk in da ya wuce sai sojojin wajen sun sara masa, jibga jibgan sojojin sa huɗu ne suka take masa baya har zuwa bakin kofar shiga cikin fadan, a daidai wajen suka dakata, shi kuma ya shige ciki.

Fadan shugaban ƙasa waje ne mai girman gaske, duniya ne guda, cikin fadan ɓangarori ne daban daban, sannan akoi ofisoshin da dama a ciki, kaɗan daga ciki, akoi office ɗin shi kan shi His excellency mr president, sai office na vice president, sai na secretary sa, da dai sauran su, sannan akoi manya manyan kujeru masu rai da lafiya, launin ja set nasu daban, haka zalika launin blue suma set nasu daban, akoi abubuwa da dama wadda faɗen su da baki ba zai yiwu ba, sai dai ku kawata su a ran ku, a takaice dai fadan shugaban ƙasa ya haɗu iya haɗu, domin tsayawa zayyana muku yadda cikin fadan yake zamu jima bamu gama ba, dan fadan dunaya ce guda.

Kusa da His excellency lion ya wuce yaje ya zauna, kallon sa cike da so da kauna His excellency yayi yace "My dear what is happening, naga kamar ranka a ɓace?" Ba sai na faɗa muku ba, kun dai san da turanci suke magana.
_Shiru lion yayi na yan sakanni kafin yace "kasan komai uncle ba sai na sake faɗa maka ba, Ina son a matsayin ka na president kayi magana da president na Spain, ina son a bincika min bayan James ya sauƙa daga jirgi ina ya nufa, shin ya hau wani jirgin ne ko kuma ya shiga cikin kasar ne, idan ya shiga cikin kasar wani gari yaje, uncle ina da ayyuka dayawa, ba zan iya zuwa Spain yanzu ba, kuma ina da tabbacin duk in da James yake yana cikin damuwa da tashin hankali, na kasa samun nitsuwa, ina jin har cikin zuciya ta, James na neman taimako na, a halin da nake ciki yanzu, ba zan iya fita daga Washington DC ba, saboda matsawa ta zai iya sanya mu rasa jigo na rayuwar mu, wato daddy, a situation ɗin da daddy yake yanzu, yin nisa da shi babban haɗari ne, da gara idan Michael yana da lafiya ma, zai iya ɗebe masa wasu matsaloli da kuma damuwa na rashin mu ni da James, amma ace babu ko ɗaya daga cikin mu, abune mai wuya a gare shi ya iya zama, jiya nayi tunanin zanje Spain da kai na, zuwa wayen gari na sake wani tunanin kuma, hakan ba mai yiwuwa bane, jiya ne kaɗai daddy bai ga James ba, ya damu sosai, yau da safe tun karfe 6 yazo bedroom na, wai sai na kira masa James a waya dan yayi mafarkin sa, da kyar na lallaɓa shi ya hakura, idan aka ci-gaba a haka, tofa akoi babban matsala, ka sani kuma ba sai na sake maimai ta maka ba" shiru His excellency ya ɗan yi kafin yace "Yes

Please Login or Register in order to submit comment