Reading TRIPLETS BOOK 2 by Star Lady Chapter 11 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri Rimsha ta karɓa wayar, jikinta har wani kerma yake wajen karɓan wayar.

Cike da zumuɗi ta fara gwada number mum. Sai da kirjin ta ya ba da wani dum-dum lokacin da kunnuwan ta suka ji layin mum a kashe.

Sake gwadawa ta yi, nan ma a kashe, kamar za ta yi kuka ta sanya number Jehan, shi ma a rufe, nata number ta sa ta gwada ƙira, shi ma a kashe, turo ɗan bakin nan nata tayi kafin ta gwada number daddynta duk da ta san tasa wayar a kashe take, saboda tun kafin ta bar gida, numbersa ba ta shiga.

Kamar a mafarki ta ji number daddy ta shiga, cikin sauri ta ciro wayar daga kunnanta don ta gani shin da gaske numbersa ta sanya da kyau, ko kuma akwai in da ta yi kuskure.

Tabbas da gaske ne babu wani kuskure number daddy ne. Sai dai wayar ta yi ringing har ta katse ba a ɗaga ba, Iya dai tana daga kwance ta zuba mata ido. Sake kira na biyu tayi, nan ma ba'a ɗaga ba, sai a karo na uku ne, aka ɗaga.

Cike da zumuɗi ta ce, "Hello daddy." Wani murya ta ji wanda da alama Hausa bai ishi mai wannan murya ba, "Hello waye ne?" Mai wannan murya ya tambaya, sake ciro wayar daga kunnenta ta yi don ta sake tabbatarwa da kanta number daddy ne.

Tabbas numbersa ne, sake mai da wayar kunnenta ta yi ta ce "Ina wuni?" Bai amsa gaisuwar ba sai cewa ya yi "Waye ne wai?" A ƙule ta ce "Kai ba musulmi ba ne?" Shi ma da alama ya ji haushin maganar nata, da ɗan karfi ya ce "Ban sani ba, ki kira ni kuma kina neman gaya min magana!" Ɗaure fuska ta yi ƙamar tana gaban shi ta ce "Ka bawa mai wayar wayarsa, ina son yin magana da shi" "Ke wai waye ke ne tukun nan ma?" Kamar za ta masa da faɗa, sai kuma ta tuna cewa daddynta take nema, dan haka sai ta ce "Dan Allah ka bawa mai wayar wayarsa, ni yarsa ce, magana na ke son na yi da shi ka taimaka" "Ke ni bani da wata ƴa, wannan waya kuma wayanane, dan haka kada ki sake kira" ranta ya ɓaci sosai, cike da jin haushi ta ce "Kai malam idan baka bawa mai waya wayar sa ba, wlh sai na saka an ɗaure ka dan kaga ina bin ka a hankali ko?" tofa ba karya jinin dake gudu a jikin Jehan shike gudu a jikin Rimsha, kada ku manta da hakan.

Jin ta ce za ta saka a ɗaure sa sai ya yi kasa da murya ya ce "Ni ban san mai wayar nan ba, wata ɗaya da ya wuce ne, na tsinci wayar kusa da wani gawa, na dawo daga gona zan koma gida lokacin, dan Allah ki rufamin asiri wlh ban san komai ba, wasu ne suka kashe shi".

Saboda tsabar shiga tashin hankali ya ta kasa tsayuwa a kan kafafun ta, zubewa ƙasa ta yi, ta zauna zaman dirshan, nan take hawaye masu bala'i zafi suka fara zarya a kan kuma tunta, cikin sauri Iya ta sauƙo kasa daga saman gadon, ganin Rimsha na hawaye ta tada mata da hankali.

"Bawan Allah a wani gari ka ke?" Rimsha ta faɗa cikin kuka, "A nan agadas nake" sakin wayar Rimsha ta yi, wayar ya faɗi kasa, kuka ta sa mai tsuma zuciyar mai sauraro, yanzu da man da gaske ne daddyna ya rasu, ta tambayi kanta, tambayar da ba ta da amsar shi.

Sosai Iya ta rinƙa bata baki tana bata hakuri tare sa tuna mata da yarda da kaddara. Rimsha tasha kuka har ta koshi, da kyar iya ta iya samo kan ta, har tayi shiru.

Bayan tayi shiru ne ta miƙe jiki ba kwari ta koma ɗakin Kausar dan kanta dake mata barazanar fashewa saboda tsananin ciwo tana son ta kwanta ta huta. Kausar da Ayla suna falo ba su san meke faruwa ba. Tana shiga ɗakin Kausar ta haye gado ta kwanta tana mai da numfashi tare da jan hanci. Tunanin irin rayuwar da suka yi da daddyn su ta fara yi, tana yi wasu siraran hawaye na biyo ta gefen idon ta zuwa kunnen ta. Allah sarki rayuwa kenan, yau gare ka gobe ga ɗan uwanka.

To masu karatu mu leƙo Washington DC wata kila kafin mu dawo Rimsha ta yi shiru.



💞💞Washington DC💞💞

Romeo

Zaune yake saman katafaren lallausan bed nasa, jikinsa na sanye da farin short da farar singlet, hakan ya bayyanar da kyakkyawar kakkarfar surar jikinsa, irin na jarumai sadaukan yaki. Ya ɗaure dark black curly hairsa a bayansa ya bar wannan guntu na gaban goshinsa mai kara fito da kyansa.

Ya zubawa system da ke gaban sa wayan nan dara daran blue eyes ɗin nasa, ya yi shiru ya dukufa aiki yake yi sosai a nutse, sai faman cizan lallausan red lips nasa yake, har wani ja sosai lips ɗin nasa ke karawa saboda ciza wa da yake yi.

"What CIA?!" Ya furta da ɗan karfi, kara zaro dara daran idon nasa ya yi, har sai da suka kara haske saboda zaro su da ya yi, kara cizan lips ɗin nasa ya yi da karfi, alamar abun da yake gani a cikin system ɗin ya ɗan ɗaga ma shi hankali, kuma ya bashi mamaki.

Wayarsa dake gefen sa ne ya fara ruri yana neman ɗauki. Sai da wayar ya kusa katsewa, sannan slowly ya mai da idon sa izuwa kan wayar, Dr Tyrion, shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, shiru ya ɗan yi bai ɗauka kiran ba, har wayar ta katse. Kira na biyu ne ya sake shigowa, alamar Dr fa a matse yake, shiru lion ya yi kamar mai tunani.

Kiran na gab da yanke wa ne, ya sa hannun sa a nitse ya ɗauki wayar tare da yin picking call ɗin, tun bai yi magana ba ya jiyo sautin kukan Michael ta cikin wayar, katse kiran ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya miƙe cikin sauri ba tare da ya kashe system nasa ba, ya nufi toilet.

A nutse ya yi wanka, sannan ya fito ya tsaya a gaban mirror, kamar yadda ya saba haka ya tsaya ya rinƙa shafe dark black curly hair nan nasa da mayukansa masu kyau da tsada.

Bayan ya gama da kai ne, ya shafe soft skin nasa da wadannan mayukan nasa masu bala'in kamshi da tsada tare da feshe jikinsa da wannan haɗaɗiyar perfume ɗin nan nasa mai bala'i fitinannen kamshi, sannan ya wuce dressing room nasa, sai tashin daddaɗar fitinannen kamshin yake.

Bayan wasu yan mintoci ya fito sanye da wandon jeans fari tas, da Turtle High T-shirt, kasancewar rigar ta kama shi sosai ta bi jikinsa, hakan ya bayyanar da kakkarfar surar jikinsa, damtsen hannun nan nasa kamar za su fashe saboda karfe da yake ɗagawa, ga breast nasa ɓul-ɓul, sai tashin kamshin yake, ya ɗauki wayarsa ya fito ya bar system nasa.

Kodayaushe motoncinsa a shirye suke, duk lokacin da ya fito don su tafi wani waje, to tafiya kawai za su yi, yanzu ma yana fitowa kawai buɗe masa kofar motarsa wani jibgegen Baturen soja ya yi, fari ƙal da shi. Duka sojojin Romeo farare ne kal, masu kirar cikakkun mazaje, kallo ɗaya zaka musu, kasan sun shirya shiga fillin daga a ko wani lokaci, fuskokin suma kawai abun tsoro ne, ganin fuskarsu takan sa hantar manyan maza ya kaɗa, amma a haka, suna mutuwar tsoron fusataccen fuskar Romeo wato lion, duk da cewa kullun a kame suke suna nutse, idan suka gan shi ya fito, har wani damke kakin jikin su suke yi saboda kamewa da suke kara yi idan suka gan shi.

A jere motoncin nasu suka tashi suka miki titin zuwa bakin babban gate, jibga jibgan jaruman security da ke bakin gate ɗin ne, suka wangale musu katafaren gate ɗin gidan, amma kafin su isa babban gate sai da gate na biyu ya yi checking na motocin da wannan na'uran, sannan ya kira numbobin motocin gaba ɗaya ya shigar cikin babban na'uran Romeo dake ɗakin bincike dan already na'urorin a haɗe suke da juna tura sako kawai suke.

Da gudun gaske suka danna hancin motocin waje tare da sakin jiniya tamkar wayan da za su tafi filin yaƙi, kai tsaye hospital suka nufa. Duk wasu abin hawa dake kan hanya, tun jerin motoncin su Romeo bai iso wajen su ba, suke basu hanya dan jin jiniyar sun san jerin motoncin The General of the Army ne.

Suna shiga asibitin suna wuce parking space, kasancewar asibitin yana da girma sosai ya ɗauke gabaɗaya motoncinsu.

Suna parking a guje jibga-jibgan sojojin nan suka diro kasa daga saman bayan motoncinsu, ɗaya daga cikin sune ya buɗe kofar motar lion suka tsaya a bakin kofar motar suna jiran fitowar sa.

Yana sako kafar sa ɗaya waje, a sukawane suka ɗaga hannayen su dake sanye cikin black hand gloves su ka sara masa, ba su sauƙe hannayen su ba, har sai da ya fito ya nufi cikin hospital ɗin.

Sai ya wuce su sannan suke sauke hannayen nasu. Sojoji shida madaka karti ne suka take masa baya zuwa ciki.

Kai tsaye ɗakin da Michael ke kwance wato ɗaki na musamman ya nufa. Tun daga nesa yake ji yo kukan Michael, da ma kuma ya san za a yi hakan, dan ya san halin Michael da ragon ta.

Kwance Michael yake saman bed nasa, na majinyata sai kuka yake, hawaye sharaɓa sharaɓa a fuskarsa kamar ƙaramin yaro, ga shi idon nasa a runtse.

Gaban gadon lion ya je ya tsaya tare da riƙo hannun Michael ɗin, Michael jin an kama hannun sane yasa ya yi saurin waro brown eyes nasa.

Ganin Romeo ne yasa ya kara sautin kukan nasa, yana ƙara kankame hannun Romeo,

kallon jinin da aka kara masa Romeo ya yi kafin ya dawo da kallon sa kan fuskar Michael ɗin.

Gently in a cool voice ya ce "Michael whapped? Why are you crying?" Yun kurin tashi Michael ya yi, cikin sauri Romeo ya mai da shi yana girgiza masa kai alamar kada ya yi yunkurin tashi, kara sautin kukan sa ya yi.

Shafa lallausan dark brown hair sa Romeo ya fara yi alamar rarrashi, cikin kuka da shagwaɓaɓɓiyar murya ya ce "My lion zafi nake ji, jiki na ciwo yake min, ji nake kamar zan mutu, wayyo ka taimake ni".

Ikon Allah shi da ya je zai kashe kansa, an ceto rayuwarsa da kyar amma yake kukan zai mutu zafi yake ji, a taimake sa, lallai Michael tabbas ba laifin ka bane, laifin kwakwalwar kane da take nuna maka komai daidai ne.

Gently cike da kaunar Triplets nasa lion ya ce "Is okey My Tiger zai dai na yi maka zafi ka ji, ka yi shiru, just for a while minutes zafin zai tafi." Kuka sosai Michael yake yi kamar ba namiji ba, har da wani shassheka tare da jan hanci.

Romeo baya son ganin kukan nasa dan haka sai ya juyo ya ce da Dr Tyrion ya yi masa alluran barci. Jin lion ya ce a masa allura yasa ya kara sautin kukan nasa, dama kuma already kun san halin sa da rashin son allura.

Da kyar ya yarda aka ma shi allura, nan ma sai da lion ya karɓi alluran da kansa ya masa.

Bayan an kammala komai, Michael ya yi barci ne, Dr T wato Dr Tyrion ya dubi lion fuska ɗauke da murmushi ya fara magana, "Congratulations Sir." Zuba masa dara-daran kyawawan idanunnan nasa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Ci gaba da magana Dr ya yi "Abin da muƙa ɗauki tsawon shekaru muna fafutuka a kan shi, yau mun yi nasaran samun bakin zaren matsalar." Still Romeo bai yi magana ba, ya dai tsare Dr da ido yana jiran ya ji karshen maganar kawai.

"Yau mun yi nasaran samun bakin zaren matsalar Michael, kuma muna sa ran nan da yan kwana ki zuwa watanni zai iya samun sauƙi kwakwalwan sa za ta koma daidai, zai daina yin abubuwa kamar yaro, zai zama cikakken mutun, kuma duka hakan ta farune sakamon buguwa da kansa ya yi a sanadiyar accident da ya sa mu, amma fa a yan kwana kin nan sai kun kara hakuri da shi, dan zai birkice mu ku fiye da a baya, amma daga nan zamu yi nasara". Jin abin lion ya ke tamkar a mafarki, dan sun kwashe shekaru suna neman wa Michael magani, sun je hospital kala-kala, amma ba su yi nasara ba, dan ko wani likita cewa yake a haka a ka haife shi, dan haka babu wani magani, sun tambayi daddy sun lokacin da suka yi wayo, menene asalin abun da ya faru da Michael daddy ya ki faɗa musu sai dai ya ce musu shima bai sani ba.

To yau Allah ya yi Michael zai samu sauki, farinciki ya hana lion magana,. Kasan cewar shi baka taɓa gane farincikin sa ko bakin cikin sa, hakan yasa ba wanda ya gane cewa lion ya yi farinciki da samun saukin Michael.

Yau saboda murna lion ya jima sosai a hospital ɗin kafin ya koma gida. Yana zuwa gida, ya isko daddy a falo, nan fa daddy ya tsayar da shi, tare da sa masa kuka a kan ya har yanzu Michael bai dawo daga white house ba, kuma yana kiran layin James baya shiga. Da kyar lion ya samu ya lallaɓa daddy tare da yi masa alkawarin gobe Michael zai dawo, da kyar daddy ya yarda sannan ya wuce bedroom nasa.

Kai tsaye bedroom na James lion ya wuce, dan ya je ya yi wasu binciken na shi. Ya jima a ɗakin James yana yan bincike-binciken shi, kafin nan ya fito ya koma part nasa.

A gaban mirrorsa ya tsaya yana kallon fusataccen fuskarsa, sosai ya zubawa kansa ido kamar mai son gano wani abun, a hankali ya kai hannun sa yana shafa kyakkyawan fuskar sa, tunani yake sosai a kan James, tabbas James na bukatar taimako. Kamar wanda a ka tsikara ya ciro wayar sa daga aljihun sa tare da fitowa da sauri ya shige ɗakin binciken sa.

Ɗaki ne mai girman gaske, kasan ɗaki wani irin tiles ne mai kamar glass kana iya ganin fuskar ka jikin tiles ɗin, ga shi tsab tiles ɗin yake kamar kafa bai taɓa takawa ba. Bangon jikin ɗakin ta gabas, ma'ana ta wajen mahangar garin, glass ne a wajen maimakon gini kana tsaye daga cikin kana hangen cikin birnin Washington DC. Gaba ɗaya cikin ɗakin kewaye yake da haɗaɗɗun drawers masu kyau, wanda a ka ɗaura Manya-manyan na'urorin da kuma manya-manyan desktop computer a kansu, wadanda da ka gan su ka san ba aikin wasa ake da su ba, ga kuma wasu haɗaɗun chairs masu kyau da tsada, a kalla chairs ɗin nan za su kai 20 a cikin ɗakin, dan gaban kowani na'ura ko kuma desktop computer akoi wannan kyakkyawan chair ɗin a wajen. Komai na dakin a share a gyare tsaf kamar sababbin kaya a ka zuba, su kan su computers ɗin ba za ka taɓa cewa hannu ya taɓa taɓa su ba, saboda hasken da suke da shi ba datti ko kaɗan, wani daddaɗar kamshin tare da sanyin AC ke tashi a ɗakin wadda zai baka tabbacin mamallakin ɗakin nan mutunne mai mugun bala'i tsabta tare da son kamshi, dan komai nasa wani hadaɗɗe. Kamshi yake yi.

Um Masha Allah lion na mu duniyar tsabta da kamshi, kai dai in dai kamshi da tsabta ne to kai ne number 1 amma kar aje ta ɓangaren tausayi da horar da masu laifi dan a komai kai number 1 ne ba'a magana!!.

Saman wani haɗaɗen chair lion ya zauna, da kaga chair ka san na musamman ne, kamar yadda mamallakin ta yake na musamman, ɗaya tamkar da billion. Zama ya yi yana fuskantar wani makekiyar desktop computer mai bala'i kyau da tsada, mai girma sosai. Kunna computer ya yi, ya sanya hannun sa a kan screen ɗinta ya fara aiki.

Number James ya shiga cikin computer dan ya binciko a daidai ina aka soke layin James, kuma bayan an soke layin ya aka yi da ita.

Sosai ya nutsa cikin bincike ba ji ba gani, aiki yake tukuru babu kama hannun yaro. Duk da daddaɗar sanyin AC dake tashi a ɗakin, hakan bai hana zufa karyo masa daga gefe da gefen kunnensa ba, lokaci guda ya birkice kamar ba shi ba.

Zaro idon nan nasa ya yi yana kallon cikin computer, kamar wanda alluran sojansa ta motsa, nan take idon nan nasa suka canza launi zuwa ja, wasu siraran jijiyo ne suka bayyana daga goshinsa har zuwa wuyansa, sai huci yake fitarwa.

Ya jima a haka kafin nan ya furzar da iska mai bala'in zafi daga bakinsa tare da jan dogon numfashi ya sauƙe a hankali. Ci gaba da bincikensa ya yi na tsawon lokaci, duk yanayinsa ya canza, kamar ba shi ba, ya fito a asalin lion ɗinsa, duk wanda ya yi gigin tinkarar shi a yanzu za a iya ce masa mai kararren kwana, don halin da yake ciki a yanzu tsaf zai iya hallaka duk wanda ya tinkare shi, ganin shi a yanayin da yake ciki yanzu zai iya sanya mutun ya mutu ba tare da shiri ba.

Dakatawa ya yi da binciken nasa, ya miƙe a zafafe ya nufi bangrensa. Yana shiga bedroom nasa ya wuce toilet. Ruwa mai bala'in sanyi ya zuba wa kansa, don ya samu sauƙi, ya samu zuciyarsa ta ɗan sauka, ya huce, saboda ba ya son ya yi aiki cikin fishi da ɓacin rai, shi yasa ya yi hakan.

Bayan ya zuba ruwa ya fito ne, ya wuce dressing room ya shirya cikin pajama launin fara, sannan ya dawo saman lallausan gadonsa ya kwanta, ya jawo system nasa zai kunna hasken screen ɗin, sai kuma ya fasa, saboda har lokacin zuciyarsa na masa zafi, ba ya son yin aiki cikin ɓacin rai, don haka sai ya mayar da system ɗin saman bedside drawer ya kwanta tare da lumshe dara-daran idonsa yana tunanin James har barci ya yi awon gaba da shi.

After some day's, a yanzu Musharraf ya samu lafiya sosai, don yana iya taka kafarsa a hankali ya fito falon kasa, haka zalika shi ma, Michael ya samu sauƙin ciwokan da ya ji a sanadiyar hatsarin da ya yi, sai dai matsalar kwakwalwarsa ce, har yanzu da saura.

_Ni ma na tattare kayana na yi nan wannan dirama ba a nan ba._

Sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu


💞💞TRIPLET'S💞💞





🌹🌹Episode 15-16🌹🌹


After some day's, a yanzu Musharraf ya samu lafiya sosai, don yana iya taka kafarsa a hankali ya fito falon kasa, haka zalika shi ma Michael, ya samu sauƙin ciwukan da ya ji a sanadiyar accident ɗin da ya yi, sai dai matsalar kwakwalwarsa ce, har yanzu da saura ba ta warke ba.

Yau tun safe sosai helicopters ke shawagi a sararin samaniya, daga cikin Washington DC zuwa wajenta, kamar masu duba wani abin. Tun da daddy ya ji shawaginsu ya yi yawa ya san Romeo zai bar kasar ke nan, don da ma in dai ba fitar sirri zai yi ba kafin ya fita kasar sai an tashi helicopters sun yi ta kewaye cikin Washington DC, don tabbatar da tsaro, sai sun duba ko'ina. Idan sun tabbatar normal sannan private jet ɗin Romeo ya ɗaga, amma kafin ya ɗaga sai manya-manyan jiragen sojoji na kota-kwana biyu sun yi gaba, sannan nasa jet ɗin ya bi bayansu, sai wasu jiragen biyu su saka jet ɗinsa a tsakiya sai jirgin yaki ɗaya a bayan jet ɗin, don tabbatar da sun ba wa The General Of The Army kuma jika ga His excellency tsaro mai kyau, don ran Romeo daidai yake da ran zaratan sojoji 100 a cewarsu, don za a tara sojoji 100 ba za su iya aikin da shi kaɗai yake yi ba, kasancewar shi ba komai yake saka wa karfin dantse ba, akwai shi da aiki da kwakwalwa kamar agogo, manyan kasashe na duniya idan abin ya shige musu duhu sai sun nemi taimako daga wajensa, sannan kuma His Excellency yana bala'in kaunar sa fiye da tunanin mai tunani, duk cikin jikokinsa ya fi son lion, daga shi sai Michael yana matukar son su sosai. Ran Romeo babban abu ne mai matukar mahimmanci ba ga iya USA ba, har wajenta. Matukar Romeo zai fita Washington DC to fa sai an bincike ko'ina, har kasar da zai je, kafin ya dira cikin kasar sai helicopters sun tashi a cikin kasar ma, sun duba ko'ina da kyau.

Cikin taku irin na jaruman maza masu jini a jika, ya fito daga ɓangarensa, jikinsa na sanye da blue jeans mai bala'in kyau, sai Round neck T-shirt black color mai ratsin blue, a saman kayan nasa ya ɗora wannan jacket ɗin nasu, wato Puffer Jacket, ita ma black color, kalar rigarsa, kyawawan fararen kafafunsa na sanye da Hermes Birkenstock sandal, hannayensa na sanye cikin hand gloves baka, yayin da fuskarsa ke sanye da face mask baki, ya ɗaure dark black curly hair sa nan a baya, ya bar na gaban goshin kamar kullun. A yau fusatacciyar fuskar nan tasa ta fi ta koyaushe razana mai rai, domin yau fuskar tasa a ɗaure take tamau kamar wani hadari, har wani siraran jijiyo ne suka bayyana masa a goshinsa saboda ɗaure fuska sosai da ya yi, girarsa sun haɗe waje guda, saboda ɗaure fuska da ya yi, da ma gashin girar nasa ya kusa haɗewa saboda yawa, shi yasa da ya ɗaure fuska sai girar tasa ta haɗe, kwarjininsa ya kara bayyana sosai, tamkar wani zakin da ya yi shekara babu abinci, kallo ɗaya za ka masa ka san yau a fusace ya ke ainun.

Yana sako kafarsa ta saman benen zai sauƙo kasa, shi ma Musharraf yana sako tasa kafar zai hauro, bawan Allah bai san da cewa idan lion na saman staircase to ba wanda ya isa ya hau ba, har sai ya sauka, shi bai ma san waye lion ɗin ba, sunansa kawai yake ji.

Ga shi yau ran lion a matukar ɓace yake, don shi kaɗai ma sai wani huci yake, kamar ba lafiya ba, yana tafiya yana wani bubbuɗe kirjinsa, da ma kuma ga kirjin nasa a bubbuɗe.

A daidai tsakiyar staircase ɗin suka yi karo da Musharraf yana ɗan jan kafar sa a hankali yana ɗingisawa.

Wani mahaukacin mari lion ya sauƙe wa Musharraf a fuskarsa, wadda ya sanya shi yanke jiki ya zube kasa sumamme, kasancewar bene ne, hakan yasa ya gangara a sume ya sauka kasa, tsallakawa ta kansa lion ya yi, ya nufi hanyar fita daga cikin falon, don ma yana sauri ne shi yasa ya yi wa Musharraf mari ɗaya ya wuce.

"My lion where are you going?" Cewar daddy da ya fito daga ɗakin magungunansa da yake kasan benen, a hankali lion ya juyo da kallon sa kan daddy. Ganin fusatacciyar fuskarsa ba karamin razana daddy ya yi ba, ya sha jinin jikinsa don ya san halin ɗan nasa, kun san halin daddy da saurin birkicewa nan take ya ruɗe ya fara haɗa wa lion words yana in-ina. "My lion what is going on? What is happening? What is wrong with you?". Sai jero tambaya yake yi yana haɗe words, kuma ya yi maganar cike da tashin hankali.

Furzar da iska mai matikar zafi daga bakinsa lion ya yi, da kyar ya iya buɗe ɗan karamin bakinsa ya ce, "Zan je Spain ne dad, I need your prayer." Yana kai karshen maganar bai tsaya ya jira amsar da dad zai ba shi ba ya fice da sauri, don ba abin da zai hana shi dira cikin Spain yau, kuma bai son ganin tashin hankali da dad zai shiga, don ya san ba karamin tashin hankali zai shiga ba, ya san halinsa sarai, musamman ma Michael ba ya nan James ba ya nan, halin da zai shiga ba zai yi kyan gani ba, kuma ba tafiyar sirri zai yi ba ya zama dole daddy ya sani, ko bai faɗa masa ba, dole zai sani ko don jiragen dake shawagi a sama, shi yasa ma bai ɓoye masa ba, ya sanar da shi ga in da zai je kawai.

Yana fita daga falon ya nufi jerin gwanon motocinsa dake jere kamar kullun suna jiran tafiya kawai. Gidan nasu yau ya

Please Login or Register in order to submit comment