Reading UWA KO YA by HAYATU BABA ZUBAIRU Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)


WHATSAPP NO:
07039625239


*💟💟UWA KO 'YA💟💟*




*written by:*
*FAREEDAH GURKU💚*


*Edited by:ANEELURV😍*




```Dedicated to my lovely MOM😍```




*Page 1▶2*










"Feenerh come on kitashi ko zakiyi late",
"Ohhh mommy ki dan barni mana iyi barci koda na minti daya ne",
"Feenerh rana fa ya fito,kuma kinsan halin daddyki",
"Mom ,the sun is out and I know that but am not a plant you know,I don't need to photosynthesise kuma kibar dad kinsan shima baya son Ina wahalat din kaina",
"Whatever feenerh , nidai kitashi",
"Okay mom,natashi".
Feenerh da mamanta kenan , kullum ana jayayya da safe.
Feenerh dai asalin sunnanta safiya zubair ne. Ita kadai ce a wurin Mr and Mrs zubair ,babanta attajiri ne kuma hamshakin business man kuma baya wasa da aikinsa.
Mamanta kuma is soft hearted . kuma tanada kirki sosai and she loves her daughter very much.
Feenerh dai is a very beautiful girl,ebony in complexion kuma tanada ilimi sosai saboda iyayenta basa wasa da karatunta.
Ta kammala karatunta na primary dana secondary a lafia. Anan suke zama DA iyayenta a G.R.A.
Sannan she came out with an excellent results, presently tana federal university Wanda ke lafia in her first year.
~back to reality~
"Feenerh nace ki tashi".
Feenerh ta tashi da kyar ta shiga bathroom, tayi brush sannan tayi wanka tafara shirin zuwa skul while mommynta ta wuce tana cewa"haka za'ayi skul din feenerh ,da wannan sleeping sickness din naki".
Bayan feenerh tagama shirin sai tafito yin breakfast, dama already maid dinsu ta soya mata omelette da toasted bread,sannan ta hada mata tea.
Bayan tagama breakfast, tafito direbar ta ya kaita skul,tana shiga Auditorium friend dinta Kadija taxo ta hugging dinta tana cewa"my dear friend, kamar kullum kin yi late",
"Khadija kibari kawai ,yawan baccina na soratar dani",
"Anyway ,yanzu mth111 zai shigo sai musamu waje mu zauna",
"Ohhhh my God ,khadija kinsan yanda na hating mth",
"Nasani ,amma kinsan baki dawani zabi,zakiyi shi na two semester",
"Toh, Allah ya bamu sa'a",
"Ameen".
"Yauwa khadija, after this lecture kizo muje ki rakani gurin technologist Musa",
"Hmmmm, feenerh kenan kedai da wannan Musa nan naki",
"Yes,kinsan ina sonsa sosai,amma na tabbata shi baya sona",
"Toh in banda ke feenerh , waze iya resisting epitome of beauty kamar ki",
"Musa",
Khadija tamata dariya sannan tace "toh feenerh ki fita harkarsa mama, tunda he is not interested in you",
" kema kinsan bazan iya ba,because he is the first man that ever catches my heart,bazan iya barinsa ba".
Suna kan maganan ne,lecturer dinsu yashigo sannan suka closing chapter din.






*Tnx for reading....*


*FAREEDAH😘*


*💟💟UWA KO 'YA💟💟*




*written by:*
*FAREEDAH GURKU*


*Edited by:ANEELURV😍*






Dedicated to my lovely mom😍








*Pg 3 ▶ 4*


Bayan lecture,feenerh da khadija suka wuce zuwa physics lab wajen Musa. Sun isa kofar office ďinsa khadija tace, "gaskiya feenerh an an zan tsaya saboda kinsan banason in shiga private conversation ďinku",
"Kai khadija ,meye kuma so private akan abinda zan faďa masa bayan wanda kika sani",
"Nidai baran shiga ba",
"Toh ,shikenan".
Feenerh ta shiga da sallama,
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikum sallam", Musa ya amsa.
"Good morning sir",
"Morning feenerh,yakike",
"Am fine sir".
"Okay, meya kawoki",
"Bakomai ,dama nace barin shigo ne mugaisa",
"Nagode kwarai feenerh,gaskiya kina 'ko'karin zuwa gaisuwa",
"Bakomai sir".
"Yawwa feenerh inada magana da'ke, I hope dai baki da lectures yanzu",
"A'a babu sai 'karfe biyu (2pm)",
"Okay toh ki zauna".
Feenerh ta zauna,zuciyar ta na bugu saboda tana ganin kamar daga 'karshe yafara gano cewa tana sonsa.
"Feenerh , nasan 'kila bazaki yarda da abinda zan faďi maki ba",
"Ba damuwa sir ,kafaďi inaji"
********************************
Musa yayi murmushi , sai ya kara fito da dimples dinsa. Atakaice dai Musa kyakyawa ne,fari kuma yanada tsawo. Yatashi a gida ne mai yawa,yanada kanne maza da Mata kuma babansa yana 'ko'korin yaga sunyi karatu.
Musa ya kammala karatunsa na primary a lafia sai ya tafi Keffi yayi secondary sannan ya karanta physics a state university dake Keffi, yanzu kuma yana aiki a laboratory a federal university dake lafia. Amma tunda ya hadu da feenerh shine gaba daya hankalinsa ya karkato ya koma kanta, duk lokacin da tayi murmushi sai ta tuno mashi da wata special girl data ta'ba kasancewa a rayuwarshi,Kumar tana burgeshi sosai shiyasa ya deciding yau zai faďa Mata abinda ke ranshi,gaskiya yanason ya faďa mata komai.
"Feenerh ,tunda na hadu dake my mind have not been at rest,saboda duk lokacin da kikazo gaidani inason in fada maki amma Ina tunanin bazaki amince dani ba kuma inason mu kulla kyakyawan zumunci a tsakanin mu".
****************************
Feenerh bata yarda da abinda Musa ke faďi , yanxu dama Musa na sharing thesame feelings da it's,lallai dama tasani da ta faďi masa gaskiya tuntuni,da bata wahalar da kanta ba. Wow ,yau kam tana cikin farin cikin da baya misaltuwa.
"Sir yanzu dagaske ,Kai kake faďin duka wannan",
"Eh nine feenerh ,kuma ki daina kirana sir,sunana Musa",
"Toh sir,A'a Musa".
Musa yayi murmushi sannan yace,"feenerh kenan, yanzu kiban numbanki saboda mu dinga communicating",
"Badamuwa ,zanbaka number na ,da Facebook username dina,da kuma handle dina a Instagram",
"Duka ni kaďai feenerh".
Tayi murmushi sannan tace"eh ,murna nake sosai saboda mafarkina yafara zamanto gaskiya".






*tnx for reading*


*FAREEDAH😍*


*💟💟UWA KO 'YA💟💟*


*written by:*
*FAREEDAH GURKU*


*Edited by:ANEELURV😍*




*Dedicated to my lovely mom*












Pg 5▶6




"Mafarki kuma feenerh , wani mafarki",
"Hmmmm,it's a long story amma gaskiya itace na daďe ina sonka amma bansan taya zan bullo maka ba ,saboda gani nake kamar abin kunya ne ace nina fara cema Ina sonka".
"A'a feenerh ba abun kunya bane in namace tace ma namiji tanason shi,kuma ba abun kaskantawa bane",
"Toh nagode Musa ,naji daďin waýenan kalmomin da ka faďi min"
Musa yayi murmushi sannan yace "bakomai you deserve everything",
"Toh ni zan koma saboda kawata na jira na awaje ,ga wannan paper na rubuta information din aciki",
Feenerh ta sallame shi sannan tafito tana mai murmushi sosai.
"I hope dai komai yatafi daidai feenerh ,wannan irin murmushi fa" kawarta khadija tace,
"Kibari kawai khadija,Ina cikin wani farin ciki ne yanzu",
"Ko zan iya sanin dalilin",
"Musa yace yanasona,yace yanasona"! Tafaďi tana Salle.
"Dagaske feenerh",
"Wallahi dagaske nake khadija ,dana shiga ne ya ambato min wannan maganan",
"Lallai kinci sa'a feenerh ,yanzu dai burinkin ya cika ,Musa yazama naki",
"Hakane kawata ,ki tayani murna",
"Toh amma khadija ,bakya ganin Musa yamiki babba ,kefa you are just 18(shekara goma sha takwas)",
"Babba fa kika ce khadija, nawa ne shekarun Musa ,shekarunsa fa 34 kuma ni haka nagani in a so",
"Toh ai da yayi auren wuri daya haifi irinki",
"Kinga bansan wannan wasan khadija,toh sai me in har ya isa ya haifeni ,nidai haka nakeson sa".
"Toh kiyi hakuri kawata, kuma gaskiya Musa baiyi fuskar shekarunsa ba",
"Yawwa haka nakeson ji kawata ,ki dinga supporting dina",
"Ako wani lokaci kawata" khadija ta amsata.
Sun koma Auditorium domin lectures ďin CHM111 , feenerh na bala'in son wannan course ďin kuma tana bashi dukkan hankalinta domin sauraron lectures ďin da kyau.
Karfe uku suka kare lectures na yay,feenerh da khadija suka wuce masallaci don yin sallar azahar ,bayan sun idar feenerh ta kira direbar ta ya zo ya ďauketa.
Suna jiran zuwan direbar sai ga Kira a wayan feenerh ,ta duba sai taga new number,
"Hello",
"Assalamu alaikum",
"Wa alaikum salam,dawa nake magana"
"Baki gane muryar ba",
Feenerh ta ďanyi tunani sannan tace
" Musa ?",
Yace,"eh nine",
"OK,bangane muryar da sauri ba,kayi hakuri",
"Ba damuwa feenerh ,dama nace ne barin in Kira saboda ki saving numban a waýanki".
"Toh shikenan ,nagode sosai",
"A'a nine da godiya saboda kin aminta dani batare da wani damuwa ba",
"Hakan tafaru ne saboda yadda kakeji nima haka nakeji a zuciyata",
"Ban taba zaton zaki amshi soyayyata ba feenerh ,nagode sosai",
"Ba damuwa",
"Toh shikenan ,sai anjima zan kira in kin koma gida",
"Toh bye".
Feenerh ta kashe wayar,khadija dake gefenta tace,
"Hmmm,feenerh kenan soyayya daďi".




*Tnx for reading*
*FAREEDAH😍*




Follow for more of my writeup...www.f-novels.blogspot.co.ke


*💟💟UWA KO 'YA💟💟*


*written by:*
*FAREEDAH*


*Edited by:ANEELURV😍*




*Dedicated to my lovely mom😍*




*page 7▶8*




Soyayyar Musa da feenerh yayi nisa saboda yanzu students ďaďďaya ne basu san dasu ba .
Suna chatting ta WhatsApp sannan kuma suna magana ta waya sosai, yau ma feenerh ba lectures saboda haka ta tafi office ďin Musa Don suyi hira.
"Feenerh ,ya karatu I hope dai komai na tafiya daidai"Musa ya tambayeta,
"Eh ,everything is fine (wato komai lafiya) kawai na missing ďinka ne nace bari inzo in ganka",
"Hmmm feenerh nima na missing ďinki , aiki ne yamana yawa kinsan kun kusa fara jarabawa",
"Wallahi fa, har ka tunomin da exams dinmu",
"Amma fa ki tabbata kina karatu sosai saboda ki passing exams ďinki , kinga tukkuna kike first year dinki kuma yakamata ace result ďin first year yayi kyau sosai",
"Eh Ina karatu sosai, sometimes nida khadija muna zuwa library karatu inbamu da lectures",
"Toh ki kokarta ,saboda niman ilmi nada kyau mussaman na ýa mace",
Musa ya faďi a raunane. Feenerh ta noticing kamar ya tuno wani abune saboda taga fuskarsa ya canza,
"Wani abu ne yafaru?",
"A'a bakomai , kidai kula da karatunki Sosa",
"Toh nagode da nasihar da kamin",
Feenerh suka cigaba da hirar su har lokacin next lectures ďinsu yayi sai ta sallameshi ta wuce class.
Tana shiga lecture room ,ta hadu da khadija a zaune tana karate.
"Kai kawata,karatun test ďin kenan ba wasa",
"Lallai feenerh ,wato kin mayar da test ďin wasa KO, kinsan yanzu zamu rubuta koh", feenerh tayi murmushi ,tasani amma dayake chm111 me, ba damuwa saboda best course ďinta ne kuma ta riga da tayi karatu a gida.
"Ba damuwa kawata ,zamu kokarta Allah kuma yaba mu Sa'a",
"Ameen kawata"khadija ta amsata.
Sun rubuta test ďin cikin kwanciyar hankali kuma test ďin yamusu simple sosai don haka suka gama da wuri suka fita don zuwa ýin sallah.
Kamar kullum , feenerh ta Kira direbar ta yazo ya ďaukesu ,daganan ta sauke khadija a gidansu sannan ta karaso gida.
"Mommy na dawo" feenerh ta tashiga gida tana kirarin mamanta ,
"Naam dear, sannu da dawowa ya makarantar",
"Lafiya kalau mommy",
"Yawwa feenerh inada magana dake ,so in kinci abinci , kin watsa ruwa ki sameni a da'kina",
"Toh shikenan mommy".
Feenerh ta tafi ta ajiye jaka sannan tafito zuwa dinning table Don taci abinci sannan ta watsa ruwa a jiki tayi sallar la'asar sai ta nufi dakin mamanta.
"Assalamu alaikum ",
"Wa alaikum salam" mamanta ta ansa,
"Mommy sannu da hutawa".
"Yawwa ýata ",
"Mommy wani magana zakimin ďazun DA kikace inzo dakinki",
Mommy tayi shiru sannan tace "ýata tunda kikasamu wannan admission ďin bamu zauna munyi magana ba, I have some words dana keso in miki so listen carefully",
"Ina jinki mommy",
" feenerh kinga ni dai ban kammala karatuna ba akamin aure , I was just 15 (wato shekara goma sha biyar) babana ya hadani da babanki Wanda shi yaron amininsa ne,alokacin gani suke kamar in har mace tayi karatu toh raini ne ga mijinta ko Kuma bai kamata ba,bansan daďin karatu ba,kuma bansan yanda university life take ba ,koda mukayi aure da babanki bai bari na kammala karatuna ba cewa yayi its too late amma still hakan baisa naji haushinsa ba saima Kara respecting ďinsa da nayi",
Feenerh tayi ajiyar numfashi sannan tace "mommy ,duk Wanda ya ganki in besani ba bezai taba cewa baki kammala karatu ba, saboda you are more educated than other educated women",
"Hakane feenerh, shiyasa nakeson mu tattauna dake akan wannan al'amari mai muhimmaci, jiya nida daddynki munyi magana akan makarantarki kuma we have reach a conclusion, muna sonki fito da miji nan da shekara daya!!!!".






*tnx for reading....*
*FAREEDAH©*


*💟💟UWA KO ÝA💟💟*


*written by:*
*FAREEDAH*


*Edited by :ANEELURV😍*


*Dedicated to my lovely mom😍*




*pg 9▶10*




*(bayan sati daya)*


Feenerh na zaune a mosque gefe daya hankalinta gaba daya baya jikinta.
Khadija tashigo tayi sallama amma feenerh bataji ba,ta ta'bata amma still bataji ba saida ta ta'bata da karfi sannan tace "keh!!!”.
Feenerh a razane ta juyo tana waige waige saitaga khadija a gefen ta sannan ta saukar da numfashinta ,
"Haba khadija ,ji yanda kika soratar dani",
"Lallai feenerh hankalinki ya dauku, irin wannan sai a sace ki ma bara ki sani ba",
"Haba dai ,sata kuma" feenerh tace,
"Wai shin meke damunki kwana biyu ne feenerh , ko a lectures room dazun ina miki magana amma duk hankalinki baya wurin,kodai akwai wata matsala ne kawata",
"A'a babu" feenerh ta faďi da sauri.
Koda khadija ta ďago cewa feenerh karya take faďi mata sai tace"yanzu feenerh har kawancen namu ya kai haka, ban ta'ba zaton akwai wani abu da zaki iya boyemin ba ,lallai so feenerh yanzu na zama stranger ko, thanks nina wuce", khadija tayi yunkurin tashi sai feenerh ta kamo hannunta, "kiyi hakuri kawata,wallahi banyi niyar bata miki rai ba am just confused shiyasa",
"I know feenerh ,shiyasa nace ki faďa min ,kinsan cewa a problem shared is a problem solved",
"Hakane khadija ,zauna kusa dani zan faďa miki komai",
"Toh ina sauraronki" khadija tace.
"Wato khadija ,wani magana ne mukayi da mommy last week shi yake dauke min hankali",
"Wani magana?,i hope dai bata gano kina soyayya da musa bane",
"A'a khadija ba wannan ba",
"Toh menene kawata",
"Khadija , mommy da daddy sun yanke hukuncin min aure nan da shekara biyu kuma sunce in fito da miji nan da shekara daya",
Khadija tayi salati sannan tace ,
"What feenerh ,this early",
"Wallahi fa khadija koni kaina am surprised ,kuma ni gaskiya i dont know what to do saboda banason ganin bacin ran iyayena",
"Hmmmm lallai feenerh wannan babban magana ne,toh yanzu ya batun makarantarki, bara su bari ki karasa ba",
"That's the aim dayasa sukace nan da shekara biyu ,saboda alokacin ina 400lv zanyi auren,kinga aina kammala ,sauran kuma a gidan mijina",
"Tohhhh, yanzu ya za'ayi",
"Shine nima bansani ba ,khadija am so confused",
"Kinsan me kawata , ki kwantar da hankalinki basunce nan da shekara daya ba",
"Eh" feenerh tace,
"Toh kinga ai nan da shekara daya soyayyarku da musa tayi nisa kuma zaki iya kai shi gida a matsayin mijin dazaki aura",
Feenerh tayi shiru na ďan wani lokaci sannan tace ,
"Kuma hakane fa kawata ,what you said is true , hakan za'ayi nagode sosai khadija",
"Bakomai feenerh, what are friends for",
"Hakane , a friend in need is a friend indeed".
Suna kan maganar ne ,course mate dinsu ruqayya tashigo mosque tayi masu sallama ,bayan sun amsata sai tace,"dama kuna nan nake ta nemanku",
"Meya faru" feenerh ta tambayeta,
"First semester results ne yafito sannan kuma an kori wasu malamai saboda wani laifi da sukayi , an placing information ďin a notice board dake lab",
Nan da nan zuciyar feenerh ya tashi ,ita bama ta results take ba malamai da akace an kora daga aiki ne yake damunta.
"Khadija tashi muje mu duba",
"Amma feenerh da wuri haka ,kodai kina doubting result dinki ne",
"A'a so nake inga wasu malamai aka kora",
Khadija tayi dariya sannan tace ,"lallai feenerh soyayya daďi",
Feenerh tayi murmushi sannan ta tashi tafito tasa takalmin tana jiran khadija tafito.
Suna zuwa notice board ďin ,bata ko duba result ba,idon ta na kan sunnayen lecturers ďin,"inna lillahi wa ina ilaihi raji'un"!!! ta faďi hawaye nafitowa a idanunta.






*Tnx for reading*
*©Fareedah*


*💟💟 UWA KO ÝA💟💟*


*written by:*
*FAREEDAH*


*Edited by :ANEELURV😍*




*dedicated to my lovely mom😍*




*pg 11▶12*




"Meya faru feenerh , an koreshi ne",
Feenerh ta kasa magana sai hawaye,
"Ki ansani mana feenerh" khadija tace,
"A'a khadija, ankara masa matsayi ne",
"Toh meyasa kike kuka",
"Bakya gani ne khadija , anbashi scholarship zuwa New York ya karasa karatunsa na masters acan",
Khadija tasaki numfashi sannan tace "Lallai feenerh , wallahi har kin tsoratani , sawa nayi ko an koreshi ,toh mena kuka ai wannan abin murna ce",
"A'a khadija ,musa zai tafi ya barni har na tsawon shekara ďaya , wallahi bazan iya rayuwa bashi kusa ba",
"Hmmm feenerh har soyayyar taku tayi karfi haka ,toh kisani dole zakiyi hakuri saboda yaje ya kare karatunsa kema kiyi naki karatun",
"Anya khadija zan iya kuwa",
"Ya zamanto miki dole , nidai bari in duba result ďina in kin gama kukan kya duba naki".
Feenerh ta rasa ya zatayi ,musa zai tafi ya barta yanzu ma kenan zuciyarta na mata zugi toh ya in ya tafi yaza tayi, ya Allah kasamin sanyi a zuciyata.
Khadija ce ta katse mata tunaninta,
"Keh munyi passing duka wallahi",
Feenerh tayi shiru tana kallonta sannan tace mata,"toh ai dama nasani",
"Taya kika sani",
"Saboda nina rubuta exams ďin",
"It's not funny feenerh",
"Toh naji ,yanzu muje kirakani office din musa",
"Dama nasani ai ,abinda ke zuciyarki kenan".
Sun kai office ďin sai khadija ta tsaya a waje as usual, feenerh naso ta bude kofar kenan sai taji a kulle yake, ta juyo tace ma khadija a kulle yake,
"Maybe ya fita ne, ki kirashi a waya mana",
"Yeah hakane, bari in trying numbanshi" .
Feenerh takira numban yayi ringing ba amsaba ,tasake kira har 5 missed call ba amsa ba ,
"Khadija ,no answer",
"Ki bar damuwa feenerh ,everything will be alright kinji",
"Toh muje".
Sun koma mosque suka zauna amma sam hankalin feenerh ba a kwance yake ba ,har lokacin sallah yayi.
Bayan sun idar da sallah kenan sai wayarta yafara ringing ,tana dubawa sai taga musa da sauri ta dauka,
"Hello dear",
"Hello *D* (wato darling) yakike",
"Lafiya kalau ,nakira numbanka amma baka picking ba",
"Eh wallahi *D* muna meeting ne shiyasa nasa shi a silent",
"Okay ina son muyi magana ne",
"Toh ki sameni a office, yanzu na dawo".
Ta kashe wayar sannan ta sanarwa khadija cewa zata tafi office ďin musa.
"Okay toh ina jiran ki a mosque".
Feenerh ta shiga office ďin ta same shi zaune tace ,"assalamu alaikum",
"Wa alaiki salam *D*" ya amsa muryarsa a sanyaye,
"Dear ya aiki",
"Lafiya, ya karatu",
"Kalau",
"Naji ance results ďinku yafito "
"Eh yafito",
"Toh i hope dai komai yayi kyau *D*",
"Eh",
"Tohhh *D* konayi laifi ne, naga harma 5 missed call",
"Eh, babban laifi ma",
"Hmmmm *D* kenan, toh menayi",
Feenerh ta ďanyi kitsitsina sannan tace ,"haba dear ,ya za'ayi ina jin irin wannan news ďin a notice board",
"Wani news kuma *D*",
"Kafini sani ai",
"A'a sai kin faďa",
"Maganar zuwanka states don karasa karatunka na masters acan",
"Ohhhh *D* wannan , am truly sorry, actually am on my knees, naso in faďi maki but i wanted to surprise you, bansan zasu manna a board ba ,am really sorry *D*".




*tnx for reading....*
*©Fareedah*


*💟💟 UWA KO ÝA💟💟*


*written by:*
*FAREEDAH GURKU💚*




*Edited by:ANEELURV😍*






*Dedicated to my lovely mom😍*






*pg 13▶14*








Akwana a tashi ,su feenerh sun fara jarabawa sannan kuma musa na shirye shiryen zuwa turai amma feenerh bataji ďadin abin ba ,gani take kamar in yatafi can mantawa zaiyi da ita sannan yasamu wata sabuwar budurwa.
*lectures hall*
Feenerh ke zaune a kujera bayan sun gama zana jarabawar yau wanda kuma itace ta karshe.
"Feenerh?" Kiran sunnan da khadija tayi ne ya fitar da ita daga tunaninta.
"Ohhh khadija har kin shigo",
"Eh na shigo amma ga dukkan alamu kin fara waýenan tunani tunaninki ko",
"Toh ya za'ayi kawata ,masoyina zai tafi ya barni kina ganin inada wani kwanciyar hankali ne",
"Tabbas feenerh in bakiyi a hankali ba ,tafiyar musa zai sa kiyi ciwo",
"Kawata ciwo ma bazata iya kwatanta abinda nakeji a raina ba, haba khadija taya zanyi long distance relationship kinsan wahalarsa kuwa",
"Aini ko nasan wahalarsa , ko kin manta ja'afar na uganda ,banafa ganinsa sai sau daya a shekara",
"Am sorry kawata wallahi na manta ne ,gaba daya wannan maganar ya dauke hankalina",
"Bakomai ,i understand".
"Toh yanzu ya za'ayi",
"Yanzu muje kisami musa ki masa maganar da kukayi da mommynki saboda ku sami mafita",
"Kuma fa gaskiyarki kawata ,kinga yanzu inya tafi bazai dawo ba sai nan da shekara ďaya",
"Hakane so lets go",
Suka kama hanya zuwa office ďin musa ,feenerh ta kwankwasa sannan tashiga.
"Assalamu alaikum",
"Wa alaiki salam *D*,
"Dear yakake, ya aiki",
"Toh aiki alhamdulillah *D*, yanzu ma nake tunanin kiranki a waya",
Feenerh tasamu wuri ta zauna.
"Toh gani nan, koda wani sa'ko ne",
"No kawai missing ďinki nayi",
"Koh",
"Eh *D* bansan ya zan iya shekara ďaya batare da ganinki ba,i feel like marrying you right now",
Gaban feenerh ya buga, kamar yasan zancen da tazo mashi dashi kenan.
"Dear inada wata magana dakai",
"Toh bismillah *D* inaji",
Feenerh ta zayyana masa yadda sukayi da nahaifiyyarta sannan ta faďa masa dokokin da suka bata.
"Lallai *D* iyayenki sunyi gaskiya , bakowwani namiji zai yadda ya auri wanda ta experiencing university life ba , nima saboda *muna tare da juna ne* shiyasa",
"Amma dear don't you think it's too early, nifa yanzu kwatakwata shekaruna nawa?",
"It's doesn't matter *D*,wasu na aure tun basu kai shekarunki ba",
"Toh yanzu dear mekake ganin zamuyi yanzu",
"Toh atakaice dai *D* biyyaya zamu musu ,tunda yanxu *mun aminta da juna* mezai hana infito gun iyayenki da neman auranki",
"Dagaske dear",
"Eh *D* dagaske nake ,amma kinsan bezai yiwu intafi yanzu ba,kibari inna dawo daga karatuna alokacin komai yayi daidai sai in turo magabata na zuwa ga iyayenki",
"Dear har kabani kunya", ta faďi kanta a kasa,
"Kunyar mekuma",
"Yadda kake wannan maganar a gabana",
"Ba abin kunya bane ,abin farin ciki ne because i can't wait inga kin zama matata",
"Nima haka dear",
Ahaka suka cigaba da hirar soyyayarsu har lokacin sallah yayi ,ta tashi ta wuce massallaci.
*Bayan sati ďaya*
A yau jirgin su musa zai tashi zuwa New York, feenerh koh sarkin kuka tayi har ta gaji .Ta rakoshi har zuwa airport saboda ta mashi sallama irin ta masoya".






*tnx for reading...*
*©Fareedah*.


*💟💟 UWA KO ÝA💟💟*


*written by:*
*FAREEDAH GURKU💚*




*Edited by:ANEELURV😍*




*Dedicated to my lovely mom😍*




*pg 15▶16*






Kira ya tayar da feenerh da daddare ,tamanta batasa wayar a silent ba.
"Hello", ta faďi muryarta a ciki,
"Hello *D*",
Nan da nan idon feenerh ya kwashe,
"Dear",
"Naam *D*, yakike*",
"Lafiya kalau , dear kun kai lafiya",
"Kalau *D*, kwana biyu ban kira ba saboda ban siya sabon sim bane, abubuwa sun min yawa",
"Bakomai dear, nayi missing ďinka sosai",
"Nima haka *D*, shiyasa nafara launching sim ďina da numban ki",
"Owww thanks dear",
"Toh *D* nasan bacci kikeyi ,gobe zan kira ki saboda muyi hira sosai",
"Toh shikenan dear, gud night i love you ,sweet dreams",
Feenerh ta kashe wayar tana murnushi ,atlast musa ya kirata yanzu zata samu kwanciyar hankali, she can't wait gobe yayi saboda su kara yin magana. Anan tayi bacci da wayar a manne da kirjinta .
"Feenerh!!!"
Feenerh ta bude ido da kyar sai taga mamanta a tsaye ,
"Oh mommy gud morning",
"Kema haka, wato daga sallar asuba sai kika koma bacci koh, saboda yanzu ba makaranta",
"Wallahi mommy bahaka bane, nagaji ne sosai shiyasa",
"Wani aiki kika yi har kika gaji",
Feenerh tayi shiru ,batason mommy tasan jiya tayi night call da musa",
"Mommy nayi karatu ne jiya shiyasa kinsan mun kusa dawowa school",
"Lallai toh kitashi saboda yau daddynki yace yana son magana dake kafin ya tafi wurin aiki",
"Allah mommy, toh gani nan zuwa yan zunan".
Feenerh ta sami daddynta a zaune a falo ya gama shirin zuwa gurin aiki ,
"Daddy ina kwana",
"Lafiya kalau safiya, antashi lafiya",
"Lafiya kalau daddy",
"Toh safiya, abinda yasa na aika mamanki ta kira shine akan maganan da kukayi da ita ,kin tuna",
"Eh na tuna daddy",
"Toh yawwa ,wani decision kika dauka akai",
"Daddy naji abinda kuka ce kuma na gamsu da dakkan kalamominku ,nan da shekara daya in sha allah zan fito da miji kamar yadda kuka kayyatamun",
"Yawwa safiya,ýar albarka kinga inkika yi hakan shi zai fiye miki saboda kowace mace gidan mijinta shine aljannarta",
"Toh daddy",
"Shikenan zaki iya tafiya yanzu",
"Toh daddy nagode".
Feenerh ta koma dakinta ,ta zauna shiru yanzu dai iyayenta da gaske suke son auran da ita ,kodai sun gaji da ita ne amma ai ita kaďai suke da ,baya yadda za'ace sun gaji da ita. Toh maybe shiya fiye mata alkhairi tunda ance abinda babba ya hango ,yaro koya hau saman tsauni baxai gani ba.
Kirar wayarta ne ya katse mata tunaninta tana dubawa sai taga kawarta ne khadija ,
"Hello khadija",
"Naam feenerh yakike",
"Kalau kalau babe ,ya hutu",
"Lallai muna nan muna shan hutu , ni duk na kosa ma mu koma",
"Nima haka kawata",
"Toh yanzu dai kina gida ne ",
"Eh ina nan",
"Toh gani nan zuwa ,i hope dai kin ajemana gist",
"Akwai gist kam sosai kawata",
"Toh gani nan zuwa",
"Sai kin shigo".








*tnx for reading....*
*©Fareedah*


*💟💟 UWA KO ÝA💟💟*




*written by:*
*FAREEDAH GURKU💚*






*Edited by :ANEELURV😍*






*Dedicated to my lovely mom😍*


*pg 19▶20*






Feenerh na zaune a falo tana kallo bayan wucewar khadija ,tasa AIT a dstv daidai ana jenifa's diary(best comedy ďinta) tana kallo tana dariyar yanda turancin jenifa yake ,wayar ta na ringing amma bataji ba saboda karar tv sai da aka kira na uku tukkuna taji vibration kusa da ita sannan tasan ana kiranta ta duba sai taga masoyinta ne wato musa.
"Hello dear",
"Hello *D*",
"How is you",
"Tohhh *D* wannan turancin kuma fa",
Feenerh tayi dariya,
"Turancin jenifa namaka",
"Ohhh wannan comedy ďin",
"Eh ,wallahi inason wannan comedy ďin",
"Lallai kam toh *D* ya dai",
"Kalau kalau dear",
" ina missing ďinki sosai *D*",
"Nima haka dear, kamar inyi tsunsu inzo wajenka",
"Allah sarki *D*",
"Tun dazu naketa jiran kiranka amma shiru",
"Eh kinsan lokacin mu ba daya bane,ina bacci ne shiyasa",
"Okay toh good morning",
Musa ya ďanyi dariya sannan yace,
"Morning *D*",
"Dazun khadija ta bar nan ,tacemin ja'afar zai dawo next week",
"Ohh har ya kammal kenan",
"Eh",
"Bawuya abun",
"Eh wallahi",
"Toh kinga nima nan bada jimawa ba zakiji nagama har ina hanyar dawowa",
"Dear ko kwana ďaya ka tafi yi zan missing ďinka balle har shekara ďaya",
"Toh *D* ai wahalarsa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment