Reading Abban Sojoji Takun Karshe 2&3 complete by Boss Bature Chapter 94 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soma cewa "Mom dama.....um......kuɗine...muke....so...awurin ki, ki bamu,"
tana jin haka ta fashe da dariya hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba jin yarda mommyn nasu ke 6a66aka dariya,
Ayaan yace "mom why are u laughing pls, don Allah ki tausaya mana mommy muna cikin wani hali ni da Jahan....' dakatawa tayi sannan ta soma magana anatse "Har nawa ne kuɗin"?
Jahan yace "80million,"
ɗan zaro ido tayi tare da cewa "har 80m? what are going to do with it?
Ayaan yace "mom dan Allah kada ki tambaye mu me zamuyi dasu, saboda ba zamu iya yi maki ƙarya ba, kawai ki taimaka ki ba mu,"
Murmushi ta ɗan saki tana kallonsu na wani lokacin kafin tace "Ni a wuri na miliyan tamanin tamkar naira tamanin take, naji zan taimaka na baku amma bi sa sharaɗi ɗaya"! Har sun fara sakin fara'a amma jin maganarta ta ƙarshe yasa su dakatawa da murna,
Jiki asanyaye Jahan yace "what mom"?
alexandra tace "Inaso ku sa ROMEO ya kira ni a waya, sannan ya kira ni da sunan mommynsa Kuma ya bani haƙura na bijire mun da yake yi, kiran yakasance video call ne, in har ku ka sa romeo ya amince ya kira ni awaya,i promise to give each one of u 50 50millions,' tayi maganar tare da jaddada musu,
Zaro ido suka yi gaba ɗayansu ga samu ga rashi, domin kuwa sunsan cewa Junaid bazai ta6a kiran mahaifiyarsu ba harya bata haƙuri kuma ya kirata da sunan mommynsu tabɗijancan,
gaba ɗaya sun tafi zurfin tunani suka ji tace "i will be waiting to hear from u guys," tana faɗin hakan ta kashe video call ɗin,
Hannu ayaan yasa ya rufe laptop din sannan ya kalli jahan wanda shima kallonsa yake yi yace "Yanzu ya zamuyi jahan? ga samu ga rashi ! duk da nasan junaid yana son mu sosai kuma yana yi mana biyayya zai iya yi mana komai amma banda wannan ALFARMAR,
zugudum su kayi cikin tsananin tashin hankali da kuma tunanin yarda zasu tunkari junaid da maganar! 😥

***********JAHAD***********"**

a hankali ta soma buɗe idanunta biji² ta dunga gani a idonta, daker take motsa su zata buɗe su, sai faman ambaton sunan Allah take yi a hankali,
lokacin da taƙarasa buɗe idanun nata mamaki ne ya kamata ganin ta kwance a wani ɗaki, komai na cikinsa fari ƙal a tsaftace, ga mutanen dake tsaye akanta farare fat hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, gaba ɗaya ranta ya bata cewa mutuwa tayi ne, saboda yanayin wurin da ta gani fari ga mutanen dake tsaye akanta farare, hawaye ne suka soma zubo mata a idanunta cikin kuka take cewa "Ya Allah kasa ba mutu nayi ba,nabar hussana aduniya wurin wancan fasiƙin mutumin, nashiga uku wa zai taimake ta acan, meyasa mutuwa bata ɗauke mu, mu biyu ba atare? Sai ta ɗauke ni nikaɗae tabar hussana a waccen duniyar mai cike da ruɗani," gaba ɗaya jahad ta fashe musu da kuka, Hankalin nurse ɗin dake tsaye da likitan ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin sauri su kayi kanta, ko da jahad tagansu sai ta ƙara sautin kukan tana cewa "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un,! dan Allah su wanene ku farare haka, ina hussana take,
zama nurse ɗin tayi daga gefenta sannan tace "Sannu da jiki ƴar uwata, ni ce nurse ɗin dake kula da ku, sunana Camila ke fa"?
Jin tayi mata magana raɗau da hausa yasa jahad dawowa cikin hayyacinta sosai tana kallonta da mamaki, kana kallonta ka ga english woman, Cos majority na ma'aikatan asibin sgr daga u.s suke, wasu daga india, wasu kuma ƴan nan nigeria, akwai kwararrun likitoci da nurses acikin asibitin,
ƴunƙurawa jahad tayi zata tashi cikin sauri Camila tasa hannu tare da mayar da jahad kwance tace "Ana miki ƙarin jini ne, ko baki lura ba ne"? ta faɗi tana kallonta da murmushi a fuskarta,
ɗan juyawa jahad tayi ta kalli ledar ƙarin jinin da akeyi mata,
sassauta muryarta tayi sannan tace "sister dan Allah ina ne nan? Kuma waya kawo ni nan?
Murmushi Camila tayi sannan tace "nan asibiti ne, sannan yayanki ne ya kawo ki domin mu baki kyakkyawar kulawa!"
Cikin mamaki jahad tace "Yayana kuma? ae ni bani da kowa aduniyar nan ƴar uwata ce kawai hussana nasani, dan Allah tana ina"? tayi maganar tana jiran amsa,

duk tattaunawar da suke yi dr Emran na tsaye yana jin su , kafin Camila ta buɗe baki tace wani abu sai ga MARSHAL OMAR ya shigo ɗakin shida Major, gaisawa su kayi da dr emran, sannan ya matsa wurin da jahad ke kwance,
tsayawa yayi yana kallonta fuskarshi asake saboda ganin yarda ta wartsake alamar tasamu kyakkwar kulawa awurin Nurse ɗin,
Sam jahad bata lura da marshal omar ba dake atsaye har sai da ya ambaci sunanta "JAHAD,"
A razane ta wurga kwayar idonta akan shi, ganin Ya Omar ɗinsu yasa ta zabura zata tashi zaune da sauri Camila ta mayar da ita, duk tabi ta zazzare idonta tana nuna shi da hannu tana ambaton sunan shi cikin tsananin mamaki,
tashi Camila tayi taba Omar wuri donya zauna kusa da jahad saboda ta lura yarinyar nason magana dashi,
Zama Omar yayi saman chair ɗin dake facing medical bed ɗin da jahad ke kwance asama sannan yace "Ya jikin naki"? tana jin haka ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, hannunta tasa ta ruƙe hannunsa tana cewa "Ya Omar ina ka shiga tsawan kwanaki kabar mu, bakasan halin da muke ciki ba..........' tana magana muryarta na shasshaƙewa saboda kukan da take, sam Omar ya gaza cewa komai tuni idonsa sun cicciko da kwalla,
Jahad taci gaba da cewa "Ya Omar har yanzu nagaza yarda cewa kaine! dan Allah kayi mun magana taya akai haka tafaru ya omar, kuma ina hossana take? mutumin nan ya gudu da ita ya omar..........." kasa ƙarasa maganar tayi saboda hannunsa daya sanya ya rufe mata bakinta........................................



*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®️_* ✍️
──────────────29
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•
bin idanunta yayi da kallo itama tana kallon nashi hawaye ne cike taf da idonta, bai janye hannunsa daga bakinta ba har sai da ya tabbatar cewa ta samu natsuwa sannan ya zame hannunsa yace  "Jahad duk wani abu dake faruwa ni bansani ba,bani da masaniya akai,jiya ne aka turomin saƙo da privet number bansan ko wanene be,let me show the message,
Hannu yasa ya curo wayarsa daga trouser pocket ɗinsa kunna wayar yayi sannan ya shiga wurin messages ya buɗe saƙon ya nuna ma jahad don ta gani,
Zuba ma screen ɗin wayar tayi da ido tana karantawa kamar haka
_"Omar ka yi ganganci daka bar rayuwar yaran nan a hannun Laila, ina baka shawarar ka hanzarta zuwa ka ɗauko su, saboda naji cewa gobe goben nan za'a fitar dasu daga gidan_"
Janye wayar yayi sannan yace"lokacin da message ɗin ya shigo mun bana cikin natsuwa ta, saboda mun shiga tashin hankali,ƙanne na da aka tura aiki miyagu suka farmake su, mun samu nasarar ceto rayuwarsu kuma mun kama wasu daga cikin waɗanda suka farmake sun, yanzu haka da nake maki magana ɗaya daga cikinsu yana kwance a A&E ward, baisan inda kansa yake ba,saboda sai da suka banka mashi kayan miyagun ƙwayoyi sannan suka azabtar dashi, ba don Allah yasa an samu wani daga cikinsu ba yayi mana waya da shikenan ba'asan mai zai biyo baya ba,
  Shiru Omar ya ɗanyi na wani lokaci kafin yaci gaba da cewa "tun shekaran jiya da muka fita daga gida muna can wurin cetonsu,a asibitin nan aka kwantar da waɗanda suka raunata sosai daga cikinsu,gaba ɗayan mu babu wanda ya samu runtsawa adaren jiya saboda tashin hankalin kada mu rasa su,kuma a daren jiyan ne acikin asibitin nan saƙon ya shigo mun,duk nabi na rikice saboda narasa yarda zanyi, Major shine babban na hannun dama na, shi na kira na nuna mashi saƙon da aka turomin game daku, koda ya gani sai cewa yayi dama ya jima yana son ce mun wani abu, amma ba zai iya sanar dani ba saboda bayason shiga tsakanina da matar yayana, sai abun ya ɗaure mun kai jin abunda yace,a lokacin ban matsa masa ba akan son sanin wani abu ne yake son sanar dani ba,a time ɗin duk da halin da nake ciki burina kawai inzo in ganku, Major shine yace nabar masa komai a hannunsa kar na damu, sai a washe gari major ya sanar dani cewa mu shirya mu tafi, sannan kuma yaban wata number yace mu bi diddiginta, atare dashi muka fito mu biyu kawai muka miƙi hanya, da wayata nayi amfani wurin bindiddigin numbar daya bani har muka ƙaraso titin da dajin nan yake,mu ka shiga cikinsa kai tsaye, muna cikin tafiya naji an kwala mun kira ta waje "yalla6ai," cikin sauri na zuge glass ɗin motar don naga wanene, shine naga wani saurayi zuƙunne a ƙasa, ga ki kuma kwance a sume duk jini a goshin ki, hankali atashe na zabura zan fito daga cikin motar, kawai sai saurayin nan yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar acikin motarsa, gashi can ya miƙi hanyar da tayi dama don Allah ku ceto rayuwarta, " jin haka yasa gaba ɗaya na rikice, cikin sauri major yaja motar mu da gudun gaske muka bi motar wannan tsohon mutumin da gudun gaske har cikin gidan gonarsa, ina shiga najiyo kukan hossana hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, tuni na makance na afka ma ƙopar ɗakin gidan gonar na tarwatsa ta, ina shiga naga hossana a lokacin har yayi nasarar yage mata rigarta ya ruƙe ta a hannunsa, raina yayi mugun 6aci abunda ya hanani yin motsi a lokacin saboda bansan wane irin hukunci zan yanke masa ba,yanzu haka da nake baki labarin nan babu wannan tsohon a duniyar nan saboda na kashe shi,kuma na ɗauko hoton gawarsa don na nuna ma hossana,"
  Wani irin murmushi jahad ta saki har ta gaza rufe bakinta don murna,shima Omar ɗin murmushi yakeyi yana kallonta,

  Nasan dayawa za suyi mamakin yarda akai hakan ta kasance,abun da ya faru shine cikin sojojin dake gadin gidan general ishaq akwai wani matashi Abokin major ne, a lokacin da suka kawo su hussana da jahad gidan Omar ya shiga tare da su ciki , A nan major suka haɗe da wannan saurayin abokinsa ne tun suna yara ,sunan Shi Osman bayan sun gaisa Osman ke cewa "Abokina waɗancan yaran fa? dana ga ka shiga ciki dasu ƴa'yan wanene? ko dai ogan naku ne yayi aure matar ta haihuwa,
Dariya Major yayi tare da cewa "Wai dama Osman har yanzu kana nan da shegen sa idon nan naka? Haba no wonder shiyasa Allah yabarka a matsayin mai gadi, in banda abun ka ina ogan mu yakai shekarun da zai iya ajiye ƴa'ƴa kamar waɗancan? shima fa ba wani babba bane duka shekarunsa bazasu wuce 28 years, matsayi ne kawai Allah ya bashi," jin haka yasa osman ɗan zaro ido tare da cewa "ka ce ashe shima ɗan shila ne, amma dan Allah tun yaushe nake ta fama dakai ka taimaka ka sama mun aiki a ƙarƙashinsa amma ka ƙiya, kafi son kaita ganina a matsayin mai gadin gidan genar, kalli fa yarda na rame nayi baƙi, kai kuwa har wani tumbi kafara ajiyewa saboda jin daɗin rayuwa, wlh abota bata ce haka ba," ya faɗi yana tsuke fuska, dafa kafaɗarsa Major yayi tare da cewa "Ina sane da wannan Osman, kuma insha Allah zanyi ƙoƙari na sama maka gurbi a kusa dashi, mutumin kirki ne sosai yana da sauƙin kai kuma ina jin daɗin aikin dashi,yana kyautatamun domin kuwa kafin ƙarshen wata yayi ina samun ninkin ba ninkin abunda nake samu a albashina wurinsa," jinjina kai Osaman yayi zugudun yayi masa fuskar tausayi kafin yace "Kaji daɗi mutumina,ni dai zan jira naji daga wurinka don Allah karka manta kasa ma mun kusanci dashi, nima na dangwali arxiki,"
Major yace"baka da damuwa, yanzu ma haka ga wani aiki ka samu, waɗancan yaran da kake gani ogan mu yana sonsu sosai, bashi da alaƙar komai dasu hasalima a asibiti ya taimake su,ya kawo su nan ne domin su zauna tare da matar yayansa ishaq, to ni hakan bai kwanta mun araina ba, shi ne nakeso ka sanya mun ido akansu! ka zama tamkar ɗan leƙen asiri duk da nasan hakan ya sa6ama dokar aikin ku amma inaso kayimun wannan Osman,ka lura da duk wani motsinsu acikin gidan nan, so nake kayi aiki tamkar jami'in sirri! dalilin dayasa nayi hakan saboda bana son duk wani abu da zai cutar dasu don na lura da yadda ogan mu ke tsananin ƙaunar yaran,ni kuma bana son duk wani abu da zai 6ata masa rai, ta6a yaran nan tamkar ta6a masa zuciya ne," ya ƙarasa maganar yana kallon osaman da yayi kasaƙai, daga bisani yace "Na amince zanyi hakan, amma wlh ka sani duk ranar da asirina ya tonu, sunanka na ciki ! don ba zan shiga haɗari ni kaɗai ba,"
  dariya major yayi sannan yace"Ai ni babu wanda ya isa ya ta6ani muddin ina tare da Marshal, don haka kaima ka kwantar da hankalinka, ba abunda zai same ka face alkhairi,tunda ka amince zaka yi ɗin, inaso duk wani hali da suke ciki ka tabbatar da ka kira wayata ka sanar mun,"
  Osman ya amsa masa da "toh," daga nan su kayi sallama, a lokacin marshal Omar ya fito daga cikin gidan jikinsa asanyaye suka shiga cikin mota su ka tafi,
  tun daga wannan lokacin Osman ya zaman ɗan leƙen asiri duk wani hali da su hossana ke ciki yana sane dashi kaf, kuma duk rana yana kiran major ya sanar dashi halin da suke ciki, Major bai ta6a sanar da marshal Omar ba, saboda gudun karya shiga tsakanin shi da matar yayansa ishaq,kullum yana sanar da osman cewa yaci gaba da sa musu ido,
  Idan har masu karatu zasu iya tunawa akwai lokacin da Aunty babba tayima su hussana da jahad bugun mutuwar nan, har suka kaisu asibiti bayan sun dawo suka shige cikin gida ita da hafsat suka bar jahad tsaye gaban motar tana kuka saboda hossana na'a cikin motar kwance rai hannun Allah gashi bata iya ɗaukarta bare tashiga da ita cikin gidan, a lokacin idan zaku tuna akwai wani soja daya zo yana tambayarta meke faruwane, take ce masa ƴar uwartace acikin motar kwance bata lafiya kuma bazata iya ɗaukarta ba, sai sojan yace maza "Can i help," take ce masa eh, yasa hannu ya ɗauki hossana ya shigar mata da ita ciki, ya kwantar da ita saman doguwar kujera, yayin da jahad tabisu, to wannan sojan ba kowa bane face Osman abokin major ɗan leƙen asirinsa, ko lokacin da zai fita daga falon bayan ya kwantar da hossana sai da ya ɗan tsaya daga bakin ƙopar ya juyo yana kallon jahad dake zukunne saman guiwarta agaban hossana tana yi mata addu'a tana kuka, jinjina kansa yayi tare da fuce wa bayan yafita, ya ɗauko wayarsa tare da buga ma major kira, bayan ya ɗaga kiran yake sanar dashi abunda ke faruwa, nace wa shifa yana zargin cewa Matar ishaq tayima yaran mugun bugu har ma ɗaya daga cikinsu ta jigita sosai tamkar ba zata rayuwa,don haka ya hanzarta sanar da ogansu Omar yazo ya kwashi yaran tunkan ta kashe su, har lokacin major bai sanar da Omar ba game da wannan ma, saboda yana tunanin koya faɗi masa daker ya yarda kuma yasan makircin mata, abun zai iya dawowa kansa,

tun fa lokacin da su jahad da hossana ke wanki abayan gidan ita da jahad, Osman yake ganinsu sai yazo ya gifta ta wurinsu tamkar yana yin waya alhalin su yake kallo, har video yake yi masu yana turawa major donya gani," Major ya tsorata da ganin irin uƙubar da yaran suke sha,
Bayan wannan lokacin kuma sai salon ya canza, duk osman na zuba ido yana kallon ikon Allah yarda hafsat ke nuna ma yaran soyayya, aduk lokacin da hafsat ta fita dasu cikin motarta, sai osman ya bisu da machine ɗinsa dom yaga ina zata dasu, dashi suke yin yawo abayansu batare da sun sani ba, duk inda zasu osman na biye dasu a sirrince,
  daya kira Major ya sanar dashi abunda ke faru na cewa yaran fa yanzu suna samun kulawa sosai a wurin mutanen gidan, sai major yace mashi "Wannan salon da suka canza,alama ce dake nuni da cewa sun kusa salwantar da yaran,ina da tabbacin cewa so suke su zubar dasu kaci gaba dasa musu ido,daga yanzu banaso ko bacci ka dunga yi osman, saboda wannan lokacin ne mafi haɗari, aduk lokacin da maƙiyin ka ya canza maka salo na soyayya to kaji tsoransa halakar dakai zaiyi,"
Tun daga lokacin da Major ya sanar dashi haka, bawan Allah osman bai ƙara yin bacci ba, koda bashi ke akan duty ba, yana nan yana lura da shige da ficen da hafsat keyi dasu hossana,

A ranar da baba alamu zai tafi dasu hossana, akan idon osman Aunty babba ta fito tare dasu jahad da hossana,ta buɗe masu motar hafsat suka shiga, duk yana kallonsu, daga bisani kuma sai yaga hafsat tafito hannunta ɗauke da trolley hakan na nufin wani ne zaiyi balaguro, bayan hafsat ta shiga cikin motar taja motar tafito dasu daga cikin gidan, cikin sauri osman ya hau mashine ɗinsa da yake ajiyesa acikin gidan yabi bayansu a hankali yake tuƙa mashin ɗin don kar su ganshi, da hafsat ta tsayar da motar abakin titi tana jiran ƙarasowar baba alamu, sai osman ya dakata da tukin mashin ɗinsa, cikin sauri ya sauka tare da samun wuri ya cire rigar jikinsa ta kakin sojoji ya 6oyeta a ƙarƙashin wani benci dake agaban wani shago dake rufe, sannan ya tu6e wandon jikinsa ma, ya ajiyesa a ƙarkashin bencin bakomai yasa shi yin hakan ba face don karsu ganshi da kakin sojoji yana binsu, Asirin shi zaiyi saurin tonuwa ne,
   Sai daya rage daga shi sai farar shirt da gajeran wando ajikinsa a lokacin motar baba alamu taƙaraso,cikin sauri Osman ya zuƙunna agaban mashin ɗin tamkar ya samu matsala yana gyaransa, alhalin nan duk salon dabaru ne na jami'ae,
   yana gyaran mashin ɗin yana satar kallonsu, akan idonshi hafsat ta buɗe ma jahad da hossana mota suka fito sannan ta ɗauko masu trolley ɗinsu da food basket ɗinsu ta basu,bayan hafsat ta tafi, baba alamu ya amshi akwatin Su hossana da jahad ya wurga cikin boot ɗin motarsa, daga nan jahad da hossana suka shiga cikin motar, shima ya shiga tare da tashin motar suka tafi, cikin sauri Osman ya haye mashin ɗinsa tare da tashinsa yabi bayan motar baba alamu da gudun gaske amma bai bari ya ƙurewa motarsa ba kasancewar Motar baba alamu glass ɗin jikinta duk ya fashe, muddin osaman ya ƙurewa motar tofa zasu iya hango shi, hakan yasa ya basu tazara sosai, yana cikin tuƙin mashin ɗin ya ɗan jinkirta tare da zura hannu cikin aljihun wandonsa ya zaro wayarsa tare da bugama major kira, bayan ya ɗaga yake sanar dashi duk abunda ke faruwa,
Hankali tashe major yace "Osman kada ka bari ya kubce maka, kaci gaba da bin motarsa, sannan kabar wayarka a kunne zamu biyo diddigin layinka, mu zo inda kuke," bayan osman ya amsa masa, ya mayar da wayar, sannan ya ƙara ma mashin ɗinsa gudu, a lokacin da motar baba alamu tashiga dajin da gudun gaske, jahad na ƙoƙarin fitowa tana ihu bayan ta samu ta harba murfin motar ya buɗe, sai baba alamu ya girgiza motar da mugunta, ta faɗo ƙasa timmmm goshinta ya bugu, ta taso da gudu tana bin motar tana kiran sunan hossana daga bisani ta yanke jiki ta faɗi, adai-dai lokacin shi kuma osman ya ƙaraso ba komai yasa shi yin jinkiri ba fa ce wayar da yayi da major shiyasa bai ƙaraso akan lokaci ba har baba alamu ya kubce mashi,
ganin jahad da yayi yashe a ƙasa ta sume ga jini, ba ƙaramin razana yayi ba, cikin hanzari yayi wurgi da mashin ɗinsa ya nufe ta hankali atashe, ya zuƙunna gabanta yana faɗin "ke!ke!! tashi ki tashi dan Allah, kada ki mutu,"
Adai-dai lokacin kuma motarsu Marshal Omar ta faso cikin dajin ta hanyar tracking layin osman da sukayi yasa har suka ci nasarar cimma inda yake,
Osman na ganin motarsu Marshal yasan cewa sune aciki, a lokacin omar ya zuge glass ɗin motar a tsorace ganin jahad kwance duk jini a goshinta, harya harzuƙa zai fito daga cikin motar, cikin sauri Osman yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar, gashi can ya miƙi hanyar dama da ita, don Allah ku ceci rayuwarta," jin haka yasa Omar fasa fitowa daga cikin motar, cikin sauri major yaja motar da gudun gaske suka bi motar baba alamu a lokacin ya ɗanyi masu nisa, hayaƙin da bayan motar baba alamu ke fitarwa shine yasa suka gane hanyar da yabi,
suna isa basu tsaya buɗe kopar katakon gidan gonar ba, kai tsaye major yabi ta ƙopar atsiyace ya tarwatsa katakon gidan gonar suka shige,
Tamkar zaki haka omar ya fito daga cikin motar ya afkawa ɗakin da baba alamu ya shige da hossana,

*Wannan shine abunda ya faru taƙaice kenan*

"Ya omar ina hossana take ita'? Omar yace"hossana tana cikin ƙoshin lafiya, itama ƙarin jini akeyi mata, yanzu haka bacci take sha tana a kusa da ɗakin nan," ajiyar zuciya jahad ta saki kafin ta kuma cewa "ya omar kullum hossana saita ambaci sunanka, komai akayi sai tace "ya Omar fa," ita bata son rabuwa da yaya omar ɗinta,"
Murmushi Omar ya saki jin abunda jahad tace,
"Amma ya Omar ba zaka ƙara rabuwa damu ba ko? dan Allah kada ka haɗamu da kowa kabarmu kawai a wurin ka, kai kaɗai ke son mu," tayi maganar idonta akansa tana jiran amsar shi,
Omar yace "ko wancan time ɗin bada son raina nabar ku ba, jahad you're always in my mind ina jin ku araina,amma yanzu komai ya wuce just forget about the past, ku ƙaddara cewa wani abu bai ta6a faruwa da rayuwarku ba na ƙunci, saboda yaya omar ɗinku ya shirya maku kyakkyawar rayuwa ta jin daɗi da walwala, masarauta ce wadda ku kaɗai zaku mulketa sai yadda kuka ga dama zakuyi acikinta, hatta yaya omar ɗinku zai zama tamkar bawa agare ku,"
dariya kawai jahad ke faman tiƙa saboda murnar jin abunda omar ke cewa, hatta dr Emran da Camila dake tsaye murmushi kawai suke saki, shima major dake tsaye daga ƙopar ɗakin murmushi ne a fuskarsa, ƙarasa shigowa ciki yayi yana cewa "Sir idan ba damuwa inaso a bani muƙami acikin masarautar nan, zanso na zama sojan dake kula da princesss ɗin dake acikinta, bama ni kaɗai ba ga abokina osman nan shima yana roƙon gimbiya jahad da ta bashi damar zama ɗaya daga cikin masu kula dasu,"
Abun sai ya zama tamkar shirin wasan kwaikwayo gaba ɗayansu dariya ce a fuskarsu, hakan ba ƙaramin farantawa omar rai yayi ba ganin yadda jahad ke faman tiƙar dariya, sai yaji sanyi aransa sam ya gaza janye idonsa akanta,
Muryar Camila (kameela) ce ta katse su da cewa "Yalla6ai nima idan ba damuwa ina neman alfarmar zama ɗaya daga cikin masu yi ma gimbiya jahad hidima, ko da a matsayin jakadiya ne mafi kusanci dasu,"
Fashewa da dariya jahad ta ƙara yi daga kwancen da take har omar na cewa "Bi a sannu my baby, kada ki shaƙe,"
gaba ɗayansu sun natsu sai raha akeyi, suka ji Muryar hosana kamar daga sama tace"YA OMAR,"
Atare suka juya suna kallonta, tsaye take a bakin ƙopar ɗakin daker take buɗe idanunta tana kallonsu, hannu tasa ta murza idonta sannan ta ƙara buɗe su da kyau donta tabbatar da abunda idonta ke gane mata, tabbas kuwa shine wato yaya Omar ɗinta,
tsananin farin ciki ne yasa hossana ƙarasa shigewa ciki da gudun gaske tana isa inda

Please Login or Register in order to submit comment