Reading Abban Sojoji Takun Karshe 2&3 complete by Boss Bature Chapter 65 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai abunda ƙarfi ko dukiya basa iya siyawa mutun,duk da ana siyan soyayya da kuɗi,Amma bakowace zuciya bace zaka iya mallakarta cikin sauƙi ba,kuma hada ƙarin shi bai ta6a soyayyaba,balle yasan yarda zai baiyanata,"

Jinjina kai Hajiya Azeema tayi"Allah sarki Sehrish,wlh na tausaya mata baiwar Allah,banji daɗin abunda ya faru ba,Yanzu ya zamuyi?wlh duk na ƙagu da insan a wani hali take,Ga Abusufyan ma,Naji kince Ya fita ba'a san inda yake ba,"ta ƙarasa maganar tana kallon Mommy,Duk sun shiga damuwa,
  "Tun ɗazu suka fita nemansu,Amma har yanzu shiru babu wani labari,yanzu sai dai muyi ta jiran tsammani"acewar Mommy,


Kafin Hajiya azeema ta ƙara cewa wani abu,Jahad ta kwankwaso ƙopar dakin,
  "Wanene"
"Ni ce Aunty azeema,"kallon juna sukayi ita da Mommy kafin tace"Shigo daga ciki,"
Da sallama abakinta ta shiga ɗakin,cikin girmamawa Jahad ta gaishe su,Suka amsa mata,
  "Ina neman sehrish ne,Na bincika ko'ina banganta ba,Nayi tunanin ko tazo wurinki ne,"
  Jin wannan maganar yasa hankalinsu ya tashi,shiru su kayi na wani lokaci batare da sun amsa mata ba,
  ƙoƙarin juyawa tayi zata bar ɗakin,Da sauri Mommy tace"Zonan,Jahad ce ko Hosana?"
Cikin sanyin murya tace"Jahad ce,".
  Azeema tace"Baki bambantasu ne,Ae wannan duk tafisu natsuwa,Hosana kuma tafi su jiki,har ƴan kumatu gareta,kuma ita sam bata da natsuwa,ta cika ƙiriniya,"
Murmushi Mommy tayi tare da cewa"masha Allah,Juliet ɗin Junaid ce kenan,ae ko jiya sai da yayi mun maganarta,"
cike da mamaki Jahad ta ɗanyi murmushi,jin tace Junaid yayi mata maganarta,bayan ita ko son kallonta baiyi,
  "Amma Oummanku tasan cewa Sehrish bata nan"?hajiya azeema ce tayi mata tambayar,
  Girgiza kai tayi"a'a bata sani ba,Nima Yanzu nake ji wurin Amrish,tace tun da safe bata ganta ba,"
  Jinjina kai hajiya azeema ta ɗanyi kafin tace"Shikenan,koda ace Oummanku ta tambayeki game da sehrish,ki sanar da ita cewa Sun fita ita da babban yayanku,zasu dawo in sha Allah,"
  "Shikenan,zan sanar da ita hakan,"

Gyaran murya Mommy tayi mata,ɗagowa Jahad tayi cike da jin kunyarta take kallonta,
  "Munyi magana da Junaid,Na bashi shawara akan yazo wurinki kuyi magana,nasan zaki taimaka mashi sosai,"
  Ƙayataccen murmushi Jahad,ta saki daƙyar ta iya cewa"in sha Allah Mommy,"tana kai ƙarshen maganar ta fuce da sauri,murmushi suka saki gaba ɗayansu,daga bisani kuma suka cigaba da tattaunawarsu,

A 6angarensu Omar kuwa,Yinin ranar suna wajen neman Sgr,duk wani wuri da suke tunanin zasu same shi sunje basu gansu ba,lamarin ya fara bashi tsoro,

Har wuraren ƙarfe Goma na dare babu wani Labari me daɗi,duk sun shiga matsananciyar damuwa,ga Abusufyan yaƙi dawowa cikin gidan,Abu kuwa tunda Jahad ta sanar da ita cewa Sehrish sun fita tare da babban yayansu,bata wani sanya damuwa aranta ba,don tasan cewa duk inda take tana cikin ƙoshin lafiya,Tun da ba ita kaɗai bace,duk da ta ɗan damu ganin har goma tayi Basu dawo ba,

Damuwace ta ishi Abba,A ƙarshe ya yanke shawarar sanarma Ammi halin da suke ciki,wata'ƙil ta taimaka wurin shawo masu kan Abusufyan,A lokacin tana kishingiɗe saman gadonta,Abba yayi sallama daga waje,Amsa mashi sallamar tayi,A nutse ya tura ƙopar ɗakin ya shiga,cike da girmamawa ya samu wuri daga ƙasa ya zauna tare da lanƙwashe kafafunshi,cikin sanyin murya ya gaisar da ita,miƙewa daga zaune ammi tayi yayin da idanuwanta ke akan fuskarshi,tayi mamakin ganin jirwayen hawaye,
  Hankali aɗan tashe tace"Hossein!Lafiyarka kuwa?Hawayen menene akan fuskarka"kamar jira yakeyi tayi magana,nan take ya fashe mata da kuka kamar ƙaramin yaro,duk tabi ta ruɗe,
  "Ka faɗamun meya faru ne?Ka tasani gaba kana yi mun kuka,idan wani abu ke damunka bazaka fadamun ba!"
  Cikin shessheƙar kuka ya soma magana"Abubuwa ne sunyi mun yawa ammi,daga wannan sai wannan na rasa yadda zanyi da rayuwata"
  "Ka natsu ka sanar dani meke damunka,"daƙyar ya samu ya tsagaita da yin kukan,a tsanake ya kwashe duk abunda ya faru ya sanar da ita,

Jinjina kai ammi tayi yayin da idanuwanta ke akanshi sai da yakai ƙarshen maganarshi tukunna tace"Gaskiya banji daɗin wannan abun da kuka aikata ba,nayi masu auren yarjejeniya batare da kun sanar dani ba,sam bakuyi tunani ba wlh,Haba hossein da hankalinka da tunaninka...."ta ɗan dakata da yin maganar tana kallonshi,sosai hawaye ke zuba akan fuskarshi,
  "Dama dole kuga ba daidai ba,kuskure ne tun farko kun riga da kun tabka,Ni yanzu bansan ya zanyi ba,tunda baku yi shawara dani ba lokacin da kuka shirya yi masu auren,bani da abunda zan iyayi maku.... "Tunkan takai ƙarshen maganar,Abba ya zukunna agabanta ya ruƙe hannayenta,"Duk duniya bani da mai sharemun hawayena in bake ba,Dan Allah ki taimaka mun Ammina,ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata"
  Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,tafin hannunta ta sanya tana share mashi hawayenshi,
  "Shikenan,kadaina kukan ya isa haka,idan ba so kake nima in fara kukan ba,"
  Da sauri yace"nadaina ammina,bazan ƙara ba,"
  Jinjina kai ta ɗanyi kafin tace"abun da ciwo,banji daɗin abunda Rafayet ya aikata ba,Yanzu in mahaifiyar yarinyar nan taji ya kuke tunanin zata ɗauki abun?sam bakuyi tunani ba,Shi kuma Abusufyan baikyauta ba abunda yayi maka,Zai dawo ya same ni ne,Sannan inaso ka kwantar da hankalinka,ni nasan cewa duk inda rafayet yake a halin yanzu yana tare da yarinyar,koba komai ita ƴar uwarshice,Jinin dake yawo ajikinta shike yawo ajikinshi,zai bata kyakkyawar kulawa,tunfarko kuskuren da kukayi na tursasa mashi akan ya saketa shine duk yajawo wannan abun,da ace kun bi a hankali da duk baza azo ana danasani ba,"ta ƙarasa maganar tare da nuna mashi gefenta alamar yazo ya zauna,

Miƙewa Abba yayi tare da komawa gefen ammi ya zauna,kwantar da kanshi yayi asaman kafaɗarta,Wani irin ciwon kaine ke damunshi,

"Kayi hakuri da duk abunda ya faru,banason kana sanya damuwa aranka,in sha Allah komai zai tafi daidai,zan tayaku da addu'a akan Allah Ya bayyanar dasu"sosai ammi tashiga tausarshi,tana kwantar mashi da hankali,
  "Ka kwanta ka huta,zanyi kokarin jaraba kiran layinshi,"
  "To ammi,"ya amsa mata,kafin ya gyara kwanciyarshi A saman gadonta,

Miƙewa ammi tayi gaban drawer taje tare da kai hannu ta ɗauki wayarta,Layin Abusufyan ta kira,Cikin sa'a wayar ta soma ringing,yana ɗaga kiran ta kara wayar a kunnanta tunkafin yayi magana tayi saurin cewa"Duk inda kake kadawo gida yanzun nan,ina son ganinka aɗakina,Umarni nake baka,"tana kai ƙarshen maganarta batare da ta jira amsarshi ba,Ta katse kiran,

Safa da marwa ta shiga yi aɗakin tana jiran zuwanshi,kusan minti goma sha biyar da yin wayar,Motar Abusufyan ta kunno kai cikin gidan,bayan yayi parking ɗinta ya fito jiki babu ƙwari ya nufi cikin gidan,Yana shiga babban falon gidan Ya taras da mutanan gidan,bai bi takan kowa ba Ya wuce ɗakin Ammi,da sallama abakinshi Ya shiga ɗakin,

Tunda ya shigo ammi ta kafe shi da ido tana kallonshi,yaji jiki ba ƙadan ba,
  Daƙyar ya iya gaisar da ita"ina yini ammi,"bata amsa mashi ba,Sai nuna mashi wuri tayi saman sofa ɗin dake dakin,Ya zauna yana faman sauke ajiyar zuciya,sai daga baya ya lura da Abba dake kwance ya rufe idanuwanshi,
  "Meya haɗaka da ɗan uwanka'?tayi tambayar tamkar batasan komai ba dangane da abunda ya faru,a ruɗe yace"Wani abu yace nayi mashi"?
  "Kafi kowa sani ae,meyasa Abusufyan kafiye son zuciya ne?Sam baka da kara duk irin halaccin da hossein yayi ma ƴa'ƴanka tunkafin yasan cewa jininka ne su,abunda kayi mashi sam bai dace ba,kuma abunda Rafayet Ya aikata ma ƴar wurinka,Ni banga laifinshi ba,Nafi ganin laifinku ku da kuka shirya auren yarjejeniyar,In har kayi niyyar bashi auran ƴarka don me zaka tursasa mashi akan ya saketa?Gashi yanzu kun jefa rayuwar yarinyar cikin hatsari.....'tunkan takai ƙarshen maganar,Abusufyan yace"Dama nasani,ba sona kikeyi ba,Shiyasa har kike goya mashi ba,yanzu duk girman laifin da rafayet ya aikata baki ga laifinshi ba,Saboda shi jinin Hossein ne,dama can kinfi sonshi ae......'
Bai ƙarasa maganarba,Sakamakon tsawar da Abba ya daka mashi,a lokacin ya miƙe daga zaune ya sauko da kafarshi ƙasan gadon,
  "Dama abunda kake tunani kenan!?Meyasa Abusufyan?Wlh idan ka biyewa zuciyarka Zata kaika ta baroka ne,dani dakai duk abu ɗaya ne awurin ammi,baikamata ka furta mata haka ba,ni a tunani na ƴa'ƴana naka ne,Ƴa'ƴanka nawa ne,Ban ta6a tunanin ina da bambanci dakai ba,wlh nafika jin raɗaɗin abunda Rafayet ya aikatama Sehrish,Yinin yau ko ruwa bansa abakina ba saboda damuwar halin da suke ciki...."hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi,
  Maganganun Abusufyan sunyi matuƙar ƙona mashi rai,musamman ammi,tayi mamakin yarda harya iya furta mashi hakan,Son ƴa'ƴa ya rufe mashi ido har yake ganin tamkar ba'ayi mashi adalci,
  "Ammi dan Allah ki ƙyaleshi kada kice komai,kibarshi kawai ya tafi,Abusufyan yanzu baya acikin hayyacinshi,komai ya fito bakinshi zai iya faɗa mana,"
 Ranta a6ace tace "Banji daɗin kalamanka ba Abusufyan,ban ta6a tunanin zaka iya furta mun haka ba,kada ka manta dakai dashi dukanku ni na haifeku,kuma banta6a nuna banbanci atsakaninku ba,Abu ɗaya danasani shine Hossein yafika sauƙin kai,Zan iya cewa duk cikinku babu wanda yakaishi haƙuri,yana yi mun biyayya sosai,aduk lokacin dana shiga wani hali hossein shi nake fara gani,yana faranta mun rai sosai ba kamar kai ba.....'daƙyar takai karshen maganar,idanuwanta sun cika tab da kwalla,hankalin Abusufyan ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin ammi na shirin zubar da hawayenta kanshi,sai ma lokacin ya farga don baisan ya furta mata maganar ba,ranshi ne ya 6aci sosai,idanuwanshi sun rufe,

Saukowa yayi daga saman kujerar,Ya zuƙunna saman guiwowinshi agabanta,
Cikin sanyin murya ya soma magana"dan Allah ammi kiyi haƙuri,banaso nayi silar da hawayenki zasu fita,hakan zai ƙara jefa rayuwata cikin matsala,na tuba bazan ƙara ba,Komai kikeso wlh shi zanyi,yaya hossein...."ya ambaci sunanshi tare da mayar da idanuwanshi kanshi"Kayi haƙuri da abunda nace yayana nakaina,nasan kalamaina sun 6ata maka rai,zuciyata ce sam batayi mun daɗi,Nafi kowa sanin yadda kakeson Jini na..."duk yabi ya ruɗe,
    "Ka tashi ka koma ka zauna,inason magana daku,"miƙewa yayi jiki na rawa ya koma saman kujerar ya zauna,gwanin ban tausayi ammi ke kallonsu,
  "Kada ku bari son ya'ya yayi silar da zaku raba kanku,bana fatan hakan ya faru,Ban goyi bayan abunda Rafayet Ya aikata ma ƴar wurinka ba,Kuma ban goyi bayan kowannanku ba,dakai dashi,duk abunda ya faru Laifinku ne,Tunda ku kuka haɗa aurennasu,Sannan kuma kuka soma ƙoƙarin tursasa mashi akan ya sake ta,wanda silar hakan ne yasa shi Rafayet ɗin yayi mata aika aikar da yayi,maimakon daya nuna yana son Ya tafi da ita ku ƙyaleshi yayi rayuwarshi da matarshi,amma sai kuka matsa lamba akan ya saketa bacin kuma kunfi kowa sanin halinshi,Wannan shine kuskuren da kuka aikata......"
  Shiru ta ɗanyi tana kallon kowannansu,gaba ɗaya sun natsu suna sauraronta,cigaba da magana tayi"Abusufyan amadadin Rafayet ina mai baka haƙuri,tabbas ya cutar da ƴar wurinka,Abunda yayi sam bai kyauta ba bai sa hankali ba,Amma inaso ka sani,Duk yayi wannan ne saboda tsananin son da yake yi mata,Yana gudun ku rabashi da ita ne shiyasa ya yanke shawara ya aiwatar da hakan,A tunanin shi in yayi mata hakan ba zaku iya raba shi da ita ba,Sai dai kash ya tabka babban kuskure,Ya kusanceta a lokacin da yake cikin fushi,shi kanshi yanzu nasan yayi danasanin abunda ya aikata mata fiye da tunaninku,kuma duk yacce kuka kaiga jin ɗacin abunda ya aikata mata wlh baku kaishi ba,Yafi ku jin raɗaɗin abunda yayi mata acikin zuciyarshi,da ace da son ranshi yayi mata wlh bazai gudu da ita ba,Anan zai bar maku ita,Ya tafi yabar kasar,Ya zakuyi dashi?tayi tambayar tana kallonsu,duk jikinsu yayi sanyi,
  "Duk inda yake yanzu nasan cewa yana tare da ita,Kuma zai gyara 6arnar da yayi ne,Sannan inaso ku kwantar da hankalinku,in sha Allah zasu bayyana ne,kuma kudaina tunanin cewa ko ta rasa ranta ne,tana araye bi'iznillah,kuma zata ji sauƙi ta dawo kamar yadda take ada"sosai ammi tayi masu nasiha,duk ta kashe masu jikinsu,
  A ƙarshe tace"idan har Allah yasa Rafayet ya dawo da yarinyar nan,zan zaunar dasu agaban kowa zan tambayi ra'ayinsu,idan har duka suka amince zasu rayu da junansu,To bana so wani daga cikin ku ya ƙara tada maganar saki,Idan kuma har ita jikar tawa ta nuna cewa batason shi,Zanyi adalci atsakaninsu in raba auransu,'

Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke,Abusufyan yace"In sha Allah,nima bazan ƙara tursasa mashi akan ya sake ta ba,"
Abba kuma yace"Duk hukuncin da kika yanke masu dai dai ne,mungode sosai da irin nasihar da kikayi mana,kuma in sha Allah,ba zaki ƙara jin kanmu ba,"
  "Allah yayi maku Albarka,Allah ya ƙara hada kan zuri'armu,"
Atare suka amsa mata da Ameen,
"Amma ammi,bansan ya zanyi da zainab ba"acewar Abusufyan
  "Kada ka damu,idan ta tambayeka akan Yarinyar,ka sanar da ita komai game da auran yarinyar,amma bance ka faɗa mata ainihin abunda ya faru ba game da abunda rafayet ya aikata mata,Idan kace mata Mijinta ya tafi da ita,Bazata damu ba,"
  Jinjina kai yayi"shikenan nagode sosai,Zan sanar da ita hakan,
    "Yanzu yakamata mu mayar da hankali wurin neman inda ya tafi da ita,",'
  "Zamuyi kokarin yin hakan,Yanzu haka Omar tun safe suke gararin nemansu acikin garin nan,Amma har yanzu shiru bamu ji daga gare shi ba,"Abba ne yayi magar,
  "Allah ya taimaka,zasu bayyana ne nasan zai dawo da ita ne"daga haka ta basu iznin tafiya,Miƙewa sukayi atare har sun kusa fita daga ɗakin,Ammi ta kuma kiran Abusufyan Dakatawa yayi tare da juyowa ya dawo wurinta,
  Dafa kafadarshi tayi"game da abunda ka yiwa yayanka,Ya tsaya mashi arai,yaji zafin abun har hawaye saida ya zubar akanka,sam banji daɗi ba daka buge mashi hannunshi don yana ƙoƙarin dakatar dakai,kafi kowa sanin yadda Hossein ke tsananin sonka,yafi kowa son ganin farin cikinka,Bai kamata kayi silar shigarshi cikin damuwa ba,Idan kukayi hakuri komai mai wucewa ne,Wata rana sai dai muji ana ɗaura auren jikokinku,". 
  Murmushi Abusufyan yayi,cike da jin kunya ya sunnar dakanshi ƙasa,
  'Koda yake naji ƙishin ƙishin wurin azeema cewa kanaso ka maida auranku da Zainab,dagaske ne'?
  Hannu yasa tare da shafa ƙeyarshi,
Murmushi ammi tasaki"Allah yasa ina da rabon sake ganin wasu Ƴa'ƴan na Abusufyan,"ƙasa kasa ya amsa mata da Amin,
  Hannu tasa ta ɗan bugi kafaɗarshi"rasa kunya,wayace maka ana amsawa,da ace yayanka ne,Cikin zuciyarshi zai amsa mun,"dariya sosai Abusufyan yayi,
   ɗaure fuska ammi tayi"Nama tuna fushi nake dakai,Ni banji daɗin maganar da kayi ba,nacewa wai nafison Yayanka akanka,kasan irin yadda nake jinka acikin zuciyata"?tayi tambayar tana kallonshi,duk tana yin wannan ne don ta faranta mashi ranshi,ko hankalinshi ya kwanta yadaina sanya damuwa aranshi,
  "Kiyi hakuri mommyna,bazan ƙara ba,nima nace ne kawai,ba don ina nufin haka ba,bana jin daɗin zuciyata ne shiyasa harna furta hakan batare dana tauna maganarba,"
  Shafa sumar kanshi tayi"Allah yayi maka albarka,dan Allah ka sanyaya zuciyarka,Allah ya baka hakuri da juriyar cinye wannan jarabawar,'
  "Ameen ameen Ammina,"rungumeta yayi sosai ajikinshi,Yaji daɗin kalamanta,Daga bisani yayi mata sallama Ya futo daga ɗakin,

Yana kokarin shiga bedroom ɗinshi,Muryar Abu ta katse mashi hanzarinshi,
  "Abban Jahad,"har sai da gabanshi ya fadi,A sukwane ya juyo yana kallonta,
  Jikinta na sanye da hijabi dogo,
Murmushin yaƙe yayi mata tare da cewa"Na'am Oummu Sehrish,"
  Murmushi itama ta sakar mashi,
Matsawa tayi kusa dashi"shiru har yanzu,Yayan sehrish bai dawo da ita ba ko"?tayi tambayar fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa,
  "Waya faɗa maki haka"
"Jahad ce ta sanar dani ɗazu,To naji shiru har yanzu basu dawo ba,duk nashiga damuwa,Gashi tabar wayarta agida,inason nasan a wani hali take ciki,"
  Bai bata amsa ba,sai da ya fara buɗe dakin ya nuna mata hanya"Mu shiga daga ciki,inason magana dake,"
Shiga ciki abu tayi yabi bayanta,Gefen gadonshi ya nuna mata"ki zauna,"
  Girgiza kai tayi"a'a,muyi maganar daga tsaye,inaso in koma ɗakine,
  "Ki kwantar da hankalinki,Ƴarki ko ince ƴarmu tana cikin ƙoshin Lafiya,Tana atare da yayanta kamar yadda Jahad ta sanar dake,
  Aruɗe abu tace"Dare fa yayi sosai,duk inda suka je ya isa ace yanzu sunyi tunanin dawowa gida,"
  "Shiyasa nace ki zauna muyi magana,akwai abunda nakeso in sanar dake,"jin haka yasa abu ta samu wuri ta zauna,tana kallonshi,daga can gefenta ya zauna suna fuskantar juna,
  "Nayi maki laifi bansanar dake ba,"
Cike da mamaki tace"Laifi kuma,na me kenan,"?
Daƙyar ya daure yace"naso na sanar dake amma halin da muka shiga a kwanakin baya yasa ban samu lokaci munyi magana dake ba",
Kasa kunne abu tayi tana sauraronshi,har ta ƙosa ya gaya mata,
  "Ina sauraronka,Ka sanar dani kawai,"
  "Sehrish tana da aure,"
Gabanta ne ya faɗi rass,A ruɗe ta maimaita abunda yace"Sehrish tana da aure?tun yaushe"?
  "Ina tunanin ya wuce wata hutu da yin aurenta,Ita da babban yayansu,Nasan kin gane shi,"
Abun yayi matuƙar bata mamaki,sai lokacin ta tuna da ranar nan da sehrish tayi jinya har ta kwana ɗakinshi,abun ya tsaya mata aranta ashe mijinta ne shi,zurfin tunani ta shiga,Abusufyan kuwa zuba mata ido yayi yana kallonta cike da fargabar amsar da zata bashi,
  Can yaga ta ɗan saki murmushin gefen fuska,
  "Ashe ina da suruki bansani ba,shine ba'a sanar dani bako"?tayi maganar tana harararshi,
  Ba ƙaramin daɗi abusufyan yaji ba,duk da halin da yake ciki,
  "am sorry,nasan nayi laifi amma yanzu na goge laifina tunda na sanar dake komai,"
"Hakane,naji dadi sosai,saboda na yaba da kyawun halinshi,Yana girmamani sosai"
  Kallonta kawai Abusufyan yake yi,acikin ranshi yace"da ace kinsan meya aikata ma ƴarki,da yanzu ba wannan zancen ake yi ba"a fili kuma yace"Ae abun alfahari ne shi,Mutumin kirki,yana da kyakkyawar zuciya,"
  "Yanzu kenan shiya tafi da ita,amma baka faɗamun inda suka je ba,kuma yaushe zasu dawo,"ba don yaso ba,Ya shiga shirga mata ƙarya,
  "Sun tafi kaduna ne,wani aiki ne yakai shi,Shine ya tafi da ita,Amma bai sanar dani lokacin da zasu dawo ba,"
  Jinjina kai Abu tayi"Allah ya dawo dasu lafiya,Har hankalina ya kwanta yanzu,Dama Hosana ta addabeni da tambayar ina Rishi ɗinsu take ne,Kaga yanzu na samu amsar da zan fada mata idan ta ƙara tambayata,"ta ƙarasa maganar tare da mikewa tsaye,
  Tashi yayi shima"mu je na rakaki ɗakin,Inaso na gansu,"
  "Kunya nake jifa,idan wani yaganmu atare fa?Kuma yanzu nasan sunyi bacci ma,"
  "Koda sunyi bacci nidai inason ganinsu,"duk yadda taso ta hanashi bin ta sai da yabita,Lokacin da suka shiga ɗakin A kwance ya samu jahad da hosana suna ta sharar bacci,tamkar ya fashe da kuka haka yaji,Saboda tunawa da halin da ƴar uwarsu take ciki,Yasan tana cikin mawuyacin hali,da ace sunsan halin da take ciki da baza suyi wannan baccin ba,Allah sarki,

Ya jima aɗakin yana kallonsu,Kafin yayi ma abu sallama Ya koma ɗakinshi,

Aranar kowa yayi bacci banda waɗannan mutanan,Abba,Abusufyan,Omar,Da duk wanda Yaji abunda ya faru da Sehrish,Baccinsu ragagge ne,sun shiga damuwa sosai,

*Boss Bature*

Tun da sanyin safiyar,Wayar Mommy dake ajiye saman side drawer ta soma Ringing,can cikin bacci ta dinga jin ringing ɗin wayar,daƙyar ta iya buɗe idanuwanta saboda baccin da ke fusgarta,Mikewa tayi daga zaune,batasamu Abba acikin ɗakin ba tun da suka fita sallar asuba shida Junaid bai kaiga dawowa ba,

Hannu takai tare da ɗaukar wayar,ta duba sunan mai kiran nata,Dr Harriet ce,ɗaya daga cikin aminnanta wanda ke zaune a Nigeria,tayi mamakin ganin kiranta a irin wannan lokacin,don sun jima basu yi waya ba,

Picking call ɗin tayi kafin ta kara wayar a kunnanta,Cikin harshen spanish suka soma magana
  "Ina fata ban katse maki baccinki ba,"?
  "Kusan haka,ina fata kina cikin ƙoshin lafiya"?
  Lafiya lou,kwana dayawa kin manta dani,Miji daɗi ko?Zaman Nigeria ya kar6eki,shiyasa har kika manta da mutane "acewar Dr harriet tayi maganar muryarta da sautin dariya,
  "Me yafi raina,Ga mijina Ga ƴa'ƴana atare dani,bani da sauran damuwa,"ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da murmushi,
  "Shiyasa kika manta dani kenan,Wai yaushe kika dawo Nigeria ne,baki sanar dani ba,nifa duk tunani na kina America ne ashe kin dawo daga yajin da kikayi,"
  Dariya Mommy ta ɗanyi kafin tace"Najima da dawowa,naso na sanar dake,mun shiga cikin wani hali ne na rayuwa,Amma yanzu Alhamdulillah,In na samu time zanzo,"
  "Oh sai ma kin samu time tukunna zaki zo,gaskiya ban yarda ba kizo kawai yanzu,Inason ganinki,Immediately pls,Wani taimako zakiyi mun,"
  Cike da mamaki tace"To fa!Wani irin taimako kenan"?
  "Kedai kawai kizo pls,I will be waiting for u,rashin zuwanki zai iya haddasa mun matsala,"tana kai ƙarshen maganarta,bata jira amsar da Mommy zata bata ba,Da sauri ta kashe kiran,
  Abun ya ɗaurewa Mommy kai,bata yi niyyar zuwa ba,amma yanayin yadda harriet tayi maganarne yasa ta mike da sauri ta shiga toilet,Shaf shaf Ta fito daga wanka,ta zura doguwar riga ajikinta,Ta ɗauki mayafi ta yafa akanta,

  Handbag ɗinta ta ɗauko,Sai da ta fara tura wayar cikin jakar,tukunna ta fito daga bedroom ɗin,bata samu kowa a babban falon ba,kaitsaye ta nufi hanyar fita daga falon da sauri da sauri,

  Da gudun gaske motarsu ta fuce daga cikin gidan,Wani sergeant ne ke yin driving ɗinta,Kaitsaye suka nufi estate ɗin da harriet take zaune,bayan yayi parking ɗin motar,ya fito tare da zagayawa ya buɗe mata mota ta fito daga ciki,

Da sauri ta nufi ƙopar da zata sadaka da cikin gidan,A bakin ƙopar ta tsaya tare da sanya hannunta taja door bell ɗin ƙopar,Yayi sauti,,

Ko minti ɗaya batayi ba a tsaye,taji an buɗe ƙopar,babbar mace ce fara tass baturiyar asali,a shekaru zata haura arba'in,tana da jiki,Ƙwayar idonta green colour ce,jikinta na sanye da riga da wando sun tsuke jikinta sosai dakyar take motsi acikinsu,Gashin kanta Ja ne sosai,Ta ɗaureshi da ribbom.
  Lokaci guda suka sakarwa juna murmushi,
  "You're highly welcome,Am really glad to see u,"Ta ƙarasa maganar,Tare da rungume mommy ajikinta,
   "I really missed u,Bamu kyautawa juna ba tsawon lokaci babu wanda ya nemi wani acikinmu sai kace ba abokan juna ba,"Mommy ce tayi maganar bayan sun raba jikinsu,
  Ruƙo hannunta Harriet tayi tajata izuwa cikin gidan"lets get in",
  Katafaren palour ne ya haɗu sosai,yaji komai na buƙata acikinsa,
  Nuna mata wuri harriet tayi"have a seat,". 
  Girgiza kai Mommy tayi"Nifa hankalina ba akwance yake ba,kince kinason gani na,ki fara faɗamun menene kafin in zauna "
  Murmushi harriet tayi"Jiya nayi baƙo,Na ban mamaki kuwa,"
  Zuba mata ido mommy tayi,
"Idan kinason ganin kowanene,mu shiga ciki,"tayi maganar tana yi mata nuni da upstairs,

  Gaba tayi mommy tabi bayanta har suka hau saman stairs ɗin,A ƙopar wani bedroom Harriet ta tsaya"Go in,"
  Sallama mommy tayi tare da sanya hannu ta tura ƙopar ɗakin ta shiga daga ciki,Ya haɗu bedroom ɗin sosai,Aljannar duniya ce,

Slowly mommy ta sauke idanuwanta saman katafaren gadon,Mutun ta gani kwance saman gadon,lullu6e da white bedsheet,ba'a rufe fuskarba,Amma daga inda take bazata iya tantance fuskar wanene ba,kuma daga gani patient ne,Hannun mara lafiyar hada kanula ajiki,da alama Jini aka ƙara mashi,Ga kuma allurorin dake ajiye tare da magunguna gefen side drawer ɗin,

"Ki ƙarasa ciki mana,"harriet ce tayi mata maganar,tana ƙoƙarin ɗaga ƙafarta ta shiga daga ciki,Taji an buɗe kopar toilet ɗin ɗakin,da sauri takai idanuwanta akan mai fitowar,bakowa bane face SGR daga shi sai short ajikinshi,Rass yaji gabanshi ya faɗi lokacin da yayi arba da Mommynsu,Zuba mashi ido Tayi ƙuri tana kallonshi,mamaki ƙarara akan fuskarta,

Duk yasha jinin jikinshi,a ruɗe ya juya zai koma cikin toilet ɗin,Tayi saurin dakatar dashi"Rafayet!"a sukwane ya juyo,duk ya sauya tamkar bashi ba,Jiya zuwa yau har ƴar rama yayi,
  A hankali ya ambaci sunanta"Mommy"juyawa ta kuma yi tana kallon Sehrish dake kwance saman gadon sai da taga Sgr sannan ta gane cewa itace,
    "So u are here?meyasa baka sanar damu ba,gaba ɗaya ka tashi hankalinmu rafayet,Duk mun damu akan son sanin halin da kuke ciki'
  "Mommy,I ave no choice,Nasan babu wanda zai saurareni awannan lokacin shiyasa kawai na yanke shawarar in baro gidan da ita,Omar ma ya juyamun baya,"cikin sanyin murya yayi maganar,kana kallon fuskarshi zaka gane cewa Ba ƙaramin kuka yayi ba,idanuwan duk sun kumbura suntum,hatta la66ansa,Ga Sahun yakushin Sehrish nan a asaman kafaɗarshi da kuma damtsen hannunshi,duk da anyi dressing ɗin ciwukan '
   Shigowa ciki Harriet tayi tana kallon kowannansu,kafin ta soma magana"Jiya da suba Alexander ya kirani a waya ya sanar dani cewa Yana da patient zai kawota private hospital ɗina,Sai na bashi shawarar cewa Ya kawota gidana,tunda dama aikina ne,kuma dayawa masu irin matsalarta a cikin gidana nake dubasu,Gaskiya Yarinyar tasha baƙar wahala sosai,don nayi mamaki data kasance araye bata mutu ba,don ma Allah yasa munyi mata aiki cikin gaggawa batare da 6ata lokaci ba,Amma taji jiki sosai,ta zubda jini,don kusan leda biyu na Jini muka ƙara mata,Alex ne ya bata jininshi aka sanya mata,ni tun da nake duba patient irinta banta6a zubda kwallata ba,Sai akanta Mun sha kuka,daga ni harshi,yarinyar ce ga ƙananun shekaru......."cikin harshen spanish take maganar idanuwanta cike tab da kwalla,Mommy kuwa tuni ta fashe da kuka,dakyar ta iya matsawa gefen gadon da Sehrish take kwance ta sanya hannu ta yaye bedsheet din,Riga ce ajikinta blue colour dai dai guiwarta rigar ta tsaya,duk jikinta ya bushe,kamar matacciya haka take yin bacci,

Yatsun hannunta na kerma ta ɗaurasu asaman fuskar sehrish,tsananin tausayinta ne ya kamata,Juyawa tayi wurin da Sgr yake tsaye ya duƙar da kanshi kasa,duk jikinshi yayi sanyi,Ya karaya sosai,
  "Rafayet yanzu ka kyauta abunda ka aikata mata"?idanuwanta jawur take kallonshi,
  "What i neva expect from u,kai da kanka kake hukunta masu aikata laifi makamancin wannan amma yau kaida kanka kayiwa ƴar uwarka ta jininka,Why rafayet?ko laifi tayi maka ta cancanci wannan hukuncin?balle kuma batayi maka laifin komai ba!saboda kawai sun 6ata maka rai sai ka huce haushinka

Please Login or Register in order to submit comment