Reading Yafi dare duhu by Umar Dalha Funtua Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sauka ya tafi part dinshi, kawai he's thinking about new comer
dinsu, yaga daya shiga dakin masu aikin ko juyawa batayi ba balle ta kalleshi,
hakan ba karamin bata mashi rai yayi ba.
"I will give you special treatment...." Ya fada yana kwanciya.
The following day, Maryam ta tashi taji jikinta babu dadi saboda kwanciya kasan
katifa, daman kan katifan baba rabi taji, tun da sassafe su murja suka shiga
kitchen ita kuma zama tayi jikinta duk ciwo
"For how long...." Ta fadawa kanta Tana ragumi, Yanzu kuma taji yanayin ya Chanza
mata kan da don before Tana Jin dadin tsohon gidan da take da baba rabi kan nan
gidan especially data lura mutanen gidan are rude. Ahankali ta shiga bathroom tayi
alwallah ta fito tayi sallah, bayan ta idar ta fito falo lokacin gari ya fara
wayewa kadan2, Tana tafiya ahankali ta shiga kitchen, gaisawa sukayi da su sannan
ta samu stool ta zauna tare day in tagumi, Tana kallon yanda suke hada breakfast
cikin gaggawa. Karfe 6 daidai binto ta kalle sauran Tana cewa
"Bari inje in wanke mashi kewaye kar a samu matsala..." Ta fada Tana barin dakin,
Don daman kullum da karfe shiga suhail yasa dokan su dinga wanke mashi bathroom,
hakan yasa suka rana atsakanin su amma Banda baba rabi. Da sauri binto ta Isa part
din suhail, yana zaune da pure white jallabiya hannunshi rike da counter, idanuwa
shi lumshe sai bakinshi dake motsi ahankali, Ana bude Kofan ya bude idanuwa
ahankali, binto ya gani, da sauri ta durkusa ta gaidashi, bai amsa ba ya daure
fuska, ahankali ta mike Don she's not expecting him to answer Don bai taba amsa
gaisuwansu su ba saboda he feels he's far above them, hanyan bedroom dinshi tabi ya
daga mata hannu alaman ta tsaya, chak ta tsaya kanta kasa,
"Je ki Kara sabuwar zuwa nan..." Ya fada kaman baison magana Don in Baka kasa kunne
ba bazaka ji abinda yake cewa ba, da sauri ta juya ta koma, har lokacin gari bai
gama wayewa duka ba, ba kowa compound din balle wani yasan abunda ke faruwa. Binto
na bude Kofan kitchen Maryam ta Dan daga weak eyes dinta ta kalleta, Dan murmushi
binto ta sakar mata sannan tace
"Yace kije..." Tayi directing maganar ta ga Maryam, Maryam kallon ta ta tsaya yi
for a while sannan ta nuna kanta tace
"Ni?.."
"Eh...yace kije...." Ta sake fada mata, Maryam ji tayi gabanta na mugun faduwa
saboda bayan tsana Tana tsoron shi,
"Waye?..." Ta fada Don ta tabbatar da Mai kiranta
"Suhail ...." Binto Ta amsa mata
"Ina....ya...ke...." Ta fada cikin slant,
"Zo in nuna maki...." Binto ta sake fada mata, ahankali ta diro daga kan stool da
take zaune ta biyo ta, sai da suka isa falo binto ta juyo ta kalleta Sannan tace
"Da kin saka hijab kan Kayan baccin ki...." Ta fada mata, Don Kayan bacci ta saka
Mai Riga da wando cotton,
"Tou...." Ta amsa mata sannan ta koma ta dauko hijab cikin wayanda aka saya mata ta
saka ta fito, har bakin flat din suhail binto ta rakata sannan ta koma ta barta nan
tsaye, juyawa Maryam tayi Tana kallon compound din don ganin in da mutane taga
wayam yake. Suhail kam har ya fara zama in patient Don har ya mike ya kuma zama,
sai baya kaman minti biyar sannan Maryam ta bude, gabanta sai faduwa kawai yake,
lokacin suhail ya Dora kafa daya kan daya yana girgiza su ahankali, Tana shigowa ta
tsaya daga Dan nesa dashi kanta kasa, ahankali ya daga Kai ya fara kallon daga
beautiful feet dinta
zuwa kayanta then fuskan ta, da gani she's frightened Don daman bata Saba da tashin
hankali ba, kura mata Ido yayi amma yaga ko kadan bat daga Kai ba balle ta
gaisheshi kaman yanda su murja ke ke durkusawa sun gaida shi, relaxing yayi yana
kallon ta while ita kuma Maryam gabanta na dukan uku2 saboda tsoro, sun fi minute
biyu a haka yaga bata da alaman gaida shi, afusace ya mike ya je inda take tsaye ya
rike bayan wuyan ta ya dukar daita in a forceful manner, Dan Kara Maryam ta saki
Tana fashewa da kuka Don ko a wurin dad dinta haka take, she easily crys,
"Dan ubanki baki iya gaisuwa ba!!" Ya daka mata tsawa, kuka ta cigaba dayi bata
amsa mashi ba, cikin ranta Tana yau dad dinta wani banza yake zagi,
"Wato ke tashin jos kou?... You don't have respect...now kneel...." Ya sake daka
mata tsawa, da sauri ta tashi daga durkushen da take tayi kneeling Tana kuka
hannunta rike da bayan wuyanta,
"Zo nan..." Ya fada mata in an irritating way, mikewa tayi niyyan yi Don zuwa yayi
sauri cewa
"Koma kiyi kneeling then crawl to me..." Yayi commanding dinta, da sauri ta sake
kneeling Tana rarrafawa zuwa gabanshi, har lokacin hannunta bayan wuyanta sai kuka
take, sai da tazo daf dashi ta dakata, kura mata Ido yayi for just a second sannan
yace
"Kin San ni?..." Ya daka mata tsawa, da sauri ta girgiza mashi Kai,
"For your information nine suhail...wannan tsohon daya kawoki gidan nan is not the
boss...ni né boss...you do what I ask you to do ...Don in na so ko abinci bazaki
samu gidan nan ba....." Ya fada sounding very rude and harsh, ahankali Maryam ta
daga wet face dinta ta kalleshi cikin ranta Tana cewa
"You will pay for this...." Ta fada cikin ranta, the next thing nataji shine Mari
"Don't ever look at me again..." Ya fada cikin tsiwa, ihu Maryam ta farayi Jin face
dinta on fire, hannu tasa ta rike cheek dinta Tana hawaye
"Daddy....." Ta Kira cikin kuka,
"Me kika ce?.." Ya tambayeta Don bai taba Jin murya ta ba amma sai tayi share shi
ta cigaba da kuka,
" close your mouth..." Bai idaba tayi saurin hadiye kuka Tana sauke ajiyan zuciya,
"From now henceforth ke zaki dinga wanke bathroom Dina....ke zaki dinga gyara gado
na...inshort ke zaki kula da part Dina kuma I I see any dirt you are in
trouble...am I clear?!!!" Da sauri ta daga mashi Kai Tana sauke ajiyan zuciya,
"Kije ki fara da bathroom Dina....and make sure you fix ruwan wanka na..." Ya fada
yana relaxing..." Mikewa tayi daga gabanshi ta Kama one door dake wurin, nan ta
tarda bedroom dinshi, Tana ganin bi kusa ta fashe da kuka sosai, yau ta godewa
Allah ita ke komai na dakinta da bata San yanda zatayi ba, tana kuka ta bude Kofan
bathroom dinshi, gani tayi bathroom dinshi is nothing compared to hers Don ita har
da jacuzzi cikin nata, batayi wasting time ba t wanke mashi kaman yanda takewa nata
cikin ranta Tana tunanin abinda zatayi mashi ta huce Don tunda take baa taba sata
kuka da duka ba sai yau wai har mari. Cikin few minutes ta gama ta fito ta dawo
bedroom, gadon shi ta gyara dukda bai watse sosai ba, bayan ta gama ta tsaya ta
kasa fitowa saboda tsoro, har garin ya ida wayewa bata fito ba, suhail né ya gaji
da zama ya mike ya shiga bedroom din, nan ya ganta tsaye jikin bango, gadon ya
kalla yana cewa

"Stupid gal ko iya gyara gadon bata iya ba...sai iya kallon maza...idiot..." Ya
fada yana shiga bathroom, Maryam sake Sabon kuka tayi dataji abinda yake cewa, Tana
ganin ya shiga bathroom ta fito falo da gudu ta wuce waje har lokacin bata bar kuka
ba. Lokacin security sun fito likewise Salman, yana daga Kai ya hangi Maryam ta
fito daga part din suhail Tana kuka ta shiga part din hajiya, tunda yake ganin su
murja suna fita daga part din suhail bai taba Jin abinda yaji yau ba, ji yayi he's
heart is beating so fast,ahankali ya zame ya zauna yana tunanin me yayi mata take
kuka. Maryam na shiga ta wuce bedroom dinsu, Sabon kuka ta fara, Tana kiran daddy
dinta, murja ce ta shigo dakin ta zauna bakin katifan da take kwance Tana kuka,
"Yar uwa kiyi hakuri...karkiyi kuka Don in alhaji yazo ya ganki cikin damuwa ya
tambayeki dalili kika fada mashi ..tou wahalal ki sai ta ninka haka...Don haka ki
bar kuka kinji kou...." Ahankali Maryam ta daga mata Kai Kai Tana goge face dinta.
"Ki taso muje muci abinci...." Murja Ta fada Mata , ahankali Maryam ta kalli agogon
dake jikin bangon dakin taga it's just 7:20am, ahankali ta girgiza mata,
"Zamu ajiye maki naki...." Murja Ta fada mata sannan ta mike ta bar dakin, komawa
Maryam tayi ta kwanta Tana tunanin Suhail da irin kalaman dake fita daga bakinshi,
bata taba ganin Wanda ta gani yayi mata kyau kaman shi ba likewise bata taba ganin
Wanda ta ga munin halin shi kaman shi ba, yanda yake magana cikin command ta tuna
dukda she's angry bata San lokacin da murmushi ya zomata ba, Don gani take inda ita
yar wata matsiyaciya ce da bakin ciki ya kashe ta amma thank Allah she's among the
rich young ladies kaman yanda dad dinta yake fada mata, Tana tuna at times in tayi
ba daidai ba sai yace
"Baby the person who is worth billions of dollars shouldn't behave like such...."
Takanyi murmushi in ya fadi hakan and she do reply da
"Dad am I really worth billions of dollars?.." Shima sai yayi dariya yace
"in kinyi hankali zan fada maki ko ke wacece....". Idanuwa ta lumshe Tana tunanin
if Tana iya zaman gidan, tasan ko kadan she's not the lazy type Don dad dinta baiyi
training dinta tobe lazy ba
"The boss shouldn't be lazy..." Shine abinda yake fada mata duk sanda ta nuna
gajiyawanta kan wasu abubuwan,
"Always be strong in any situation you find yourself..." Ta tuna maganar dad dinta
kafin tazo Nigeria, tunani tayi ko ya San da halin suhail kafin tazo gidan
"No way...." Ta fadawa kanta Don ta San her dad will do anything to make her happy
and not the other way round. Tunawa tayi da alhaji Ismail, ji take kaman Ta fada
mashi abinda suhail yayi mata just in a day a gidan sai kuma ta tuna da maganar
murja, ko kadan batason abinda zai taba mata lafiya jikinta,
"Let's see your game....then it will be my turn..." Ta fadawa kanta sounding firm
and strong. Cikin tunani bacci yayi gaba daita.

Suhail na shiga bathroom yaga bata hada mashi ruwan wanka ba, a fusace ya fito amma
sai yaga bayanta har ta fita daga part dinshi, kawai sai ya saki dariya
"Idiot..." Ya furta under his breath sannan ya koma ya hadawa kanshi ruwan wanka ya
shiga cikin bathtub tare da sakin ajiyan zuciya.

Bayan alhaji yayi breakfast ya kalli agogon hannunshi, karfe 9 da yan minutes,
kallon hajiya yayi ya kalli wayanshi, babu abinda yake bukata Yanzu kaman yaji ya
Maryam ta kwana a gidanshi, duk sanda ya tuna alkawarin daya daukawar dad dinta sai
gabanshi ya fadi Don wani irin nauyin alamarin yakeji, ji yake Ina ma yana iya
fadawa family dinshi ko ita wacece Don anyi treating dinta like a princess that she
is amma babu daman haka, yasan ko special attention ya bata Yanzu zai sa hajiya ta
zargeshi, Dan ajiyan zuciya ya saki tare dacewa
"My hajiya I think zan saka wannan yarinyan a islamiyya..." Irin kallon da hajiya
tayi mashi yasa yayi shuru,
"Hana alhaji...do you mean dadewa zatayi gidan nan da har zaka sata islamiyya?...
Gaskiya ni shawarata is a kaita wurin wasu family sai ka dinga tallafa mata har
tayi aure...amma ni gaskiya I don't feel comfortable with her around..." Ta fada
babu wasa, daure face alhaji yayi ya fara cewa
"Hajiya kin San I have given you too much hand da Yanzu kike son maidani mijin
hajiya?"" Baki hajiya ta bude zatayi magana alhaji ya daga mat hannu tare dacewa
"Let me finish..." Ya fada tare da sauke hannunshi sannan yacigaba dacewa
"From now henceforth I don't want you making commands....in kuma Dan kishiya kike
wannan abun sai in auro so that hankalinki ya kwanta..." Bai idaba hajiya tq Dora
hannu bisa kai
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!!!...alhaji..." Still daga mata hannu yayi tayi
saurin yin shuru hawaye na taruwa eyes dinta
"I want you to know ba tsoron ki né yasa ban Kara aure ba da zaki hanani taimakawa
family Dina saboda kishi...if I want sai in jero uku bayanki amma bani da wannan
raayin..but if you continue like this I might change my mind..." Ya fada yana
kallon yanda tears ke rolling daga idanuwanta
"Am sorry...ban karawa..." Ta fada gabanta na dukan uku uku Sannan Tana tunanin why
alhaji ke mata harsh words saboda wannan yarinyan, Don har ta gane bayason ta soki
maganar ta, hannu yasa ya goge mata face yana cewa
"Stop shedding those expensive tears..." Sai da ya tabbatar ta goge face dinta ta
dawo mind dinta sannan ya mike yana cewa
"Bari in aiki Salman ya shiga cikin gari ya nema mata good islamiyya..." Ya fada
yana kokarin barin dakin, ahankali itama ta mike Tana cewa
"Nima Bari inje part Dina..."
"Ok..in na gama da Salman am coming to your part..." Ya fada mata Don abinda yake
so kenan Don yana son ya shiga part dinta yaga Maryam and how she is. Tare suka
fita compound ita tayi part dinta shi kuma ya yiwa Salman alaman ya zo da hannunshi
sannan ya koma ciki, da sauri Salman ya taho ya bi bayanshi, bayan sun zauna alhaji
yace
"Ka dauki mota kaje wannan islamiyya na modibbo kayi wa shugaban makarantan
magana...just tell him ni na aikoka kan maganar wannan yarinyan...zasu Baka
uniforms ka kawo...sannan pls ka tabbatar kana kaita kullum kana maidota..."
"Ok sir ..." Salman ya fada mashi sannan ya tashi ya fita, cikin ranshi ya jidadi
da Maryam ba gida zata zauna ba balle suhail ya takura mata. Sai da ya fita shima
alhaji ya fita ya shiga part din hajiya, sai da ya tabbatar hajiya bata downstairs
sannan ya leka kitchen yaga binto Tana aiki Don mostly cikin aiki suke saboda kowa
da irin kalan abincin da zaici especially suhail Don har time table yayi masu na
abincin shi sannan yakan Chanza ta after some weeks. Gaidashi binto tayi ya amsa
sannan ya tambayi inda Maryam take, nan binto ta shaida mashi Tana bacci, agogon
hannunshi ya kalla yaga few minutes to ten,
"Ina ta kwana?.." Shine tambayan da alhaji yayi mata,
"Dakin mu..." T amsa mashi kanta kasa, daure fuska yayi sanna yace
"Ima sauran yanuwnki?"
"Suna sama suna gyaran wurin hajiya..."
"Shikenan in kin gama ki shiga dakin dake kusa da naku ki gyara...in kin gama ki
maida jikkanta dakin..sannan duk abinda dakin ke bukata ki fadawa Salman ya
fadamin..."
"Tou..." Ta amsa mashi cikin ladabi. Wucewa yayi upstairs ya tarda hajiya kwance
while su murja na aiki, yana shiga sukayi saurin fita daga dakin. After kaman minti
talatin ya koma part dinshi hajiya na biye dashi.

Sai karfe goma da rabi Suhail ya shiga part din mom dinshi, upstairs ya hau ya gan
mom dinshi bata nan yasan Tana part din dad dinshi, downstairs ya dawo ya wuce kan
dining ya hakimce yana jiran breakfast, suna ganin shi kan dining sukayi saurin
fara jera mashi breakfast dinshi kan dining sai da suka gama murja tazo serving
dinshi ya daga mata hannu alaman ta dakata, tsayawa tayi Tana jiran next command
dinshi Don tasan ba da kaishi zai zuba abincin ba.
"-–-11222222222222Kirawo Dayan...." Ya fada mata atakaice, murja ta gane abinda
yake nufi, da sauri ta bar wajen while binto da asabe suka kalli juna.
Daki murja ta shiga har lokacin Maryam Tana bacci saboda kukan data sha, ahankali
murja ta Dan bugi shoulder dinta, cikin kasala Maryam ta bude idanuwanta,
"Yace kije...." Murja Ta fada mata, da sauri Maryam ta wace idanuwa Tana cewa
"Waye..again..." Ta fada gabanta na faduwa,
"Suhail..." Ta amsa mata,
"Na...shiga....uku..." Ta furta kaman zatayi kuka, nan take ta hada Kai da gwaiwa
gabanta na Kara dukan uku2,
"Ki taso..baya son jira, Ta fada mata, jiki ba kwari ta daga Kanta da idanuwan ta
da suka kada sukayi ja, kaman Mai maye ta biyo murja har lokacin Tana sanye da
Kayan bacci da hijab, duk ta susuce suna fita falo ta hangi suhail dake zaune kan
dining fuskan daure kaman bai taba dariya ba, daga Kai yayi suka hada Ido ya Kara
murtuke fuska haka nan yanajin wani Abu game daita dake sashi ji kaman ya dinga
dukanta, so he thinks. Yanda ta Saba tafiyan ta ta taka ta karaso inda yake zaune,
kusa dashi tazo ta tsaya, daga inda yake zaune yana ganin yanda jikinta ke rawa,
"Save me..." Yayi commanding dinta, jikinta na rawa ta isa kan dining din ta bude
abincin, hannunta sai rawa kawai yake, daga Kai yayi ya kalli sauran yan aikin
sukayi saurin watsewa, jikinta na rawa ta fara zuba Irish potatoes, rabi cikin
plate rabi kan dining, suhail harde hannuwanshi kan kirjinshi yayi yana kallon ikon
Allah, Kwai ta zuba mashi sama Tana kyarma, hannu tasa zata dauki flask da ruwan
tea ke ciki kamshi ya bugi hancin shi, dukda ta dade bata yi amfani da perfumes
dinta ba she doesn't smell bad saboda ya Kama mata jiki already, ruwan tea ta zuba
cikin cup Dan kadan kaman yanda ta Saba Shan nata, madara ta bude ta fara zubawa
cikin ruwan, sai data cika Dan karamin ruwan da madara ya koma Kama custard sannan
ta tura gabanshi, suhail zama kawai yayi yana kallon abun mamaki tea kaman koko,
saida ta gama ta mike tsaye, ahankali yayi mata hannu alaman tazo, Dan Matso kusa
dashi tayi sannan ya kalli tea da dankali dake kan dining yace
"Daman haka matsiyata suke...nasu dukiya na mutum banza,... Dan ubanki kin taba
ganin tea haka?..." Ya daka mata tsawa, jikinta na rawa ta girgiza mashi Kai dukda
ita paste takeyi da tea dinta ta dinga lashewa ahankali kaman Tana Shan ice cream,
lumshe idanuwa tayi Tana sauraron abinda yake cewa
"When am talk about to you look at me...." Ya daka mata tsawa, da sauri ta bude red
eyes dinta
"Nace haka ake tea?..." Ya sake tambayan ta cikin fada, da sauri ta sake girgiza
mashi Kai, tsaya kallon tender hands dinta data rike cikin juna yayi sannan ya
maida idanuwashi kan face dinta yana cewa
"Kin San ba haka ake tea ba shine kika hadamin haka Dan ubanki?... Wato tunda bana
ubanki ko uwarki bane even if it's wasted babu komai kou?.. Tou tunda na lira ke
yar raini hankali ce special treatment zan baki gidan nan...and now kin kwace
wannan Irish din kin cinye..." Ya fada yana nuna mata na kan dining, hannunta na
rawa ta saka ta fara daukan daya tana kaiwa bakinta, rike mata hannu yayi, cikin
second daya ya saki hannun saboda abinda yaji, ha shocking sannan hannunta kaman
cotton wool dukda bai taba hannun mata yasan ba haka hannunsu suke ba,
"Park all and eat..." Ya umarce ta, da sauri ta kwace duka ta Kai bakinta, Dan
karamin bakinta ta bude ta fara turawa cikin bakinta, shuru suhail yayi yana kallon
ta, Abu guda saya da bai gane ba shine at this moment he don't mean what he's doing
to her amma kuma he enjoys watching her,
"Get out..." Ya daka mata tsawa, da sauri ta bar wajen, direct bathroom ta wuce ta
saki abincin cikin sink Tana fashewa da kuka, she can't just believe yau tayi kuka
sau biyu because of same person. Bakinta ta wanke ta dawo dakin ta zauna bakin
katifan, wayanta ta dauka tayi dailing number dad dinta, ringing ya dingayi amma
baiyi piçking ba, bayan kaman minti biyu sai ya message cewa yana meeting that he
will get back to her, tasan ba lallai bane ya kirata a wannan ranar Don mostly
excuse da yake bata kenan.

Salman ya dawo da Kaya cikin Leda ya bawa alhaji, lokacin still suna tare da
hajiya, nan yake fada mata Kayan islamiyya Fatima ne, batace komai ba taja bakinta
ta tsuke.

Har karfe biyu Maryam bataci komai ba, wanka tayi ta Sam gown ta koma ta kwanta.
Alhaji bai samu kadaici ba sai da zashi sallan zuhr, sai lokacin ya dauki wayanshi
ya Kira Maryam yana tafiya, Tana piçking ya gane something is wrong
"Daughter meke damunki?.." Shine tambayan da yayi mata,
"Babu...komai..." Ta amsa mashi muryan ta narawa sannan hawaye na forming
idanuwanta,
"No..ya zakice babu abinda ke damunki while you sound dull...pls daughter ki fada
min..." Ya daka yana tafiya ahankali,
"No...just missing my daddy...." Tana kaiwa nan sai ta fashe da kuka
"And baba rabi...." Tayi adding,
"Am so sorry daughter...zansa a maido baba rabi nan ba da dadewa ba...have you
eaten?.." Ya tambayeta, sai lokacin ta tuna da ko ruwa bata sha ba yau, shuru tayi
babu response
"Daughter kinci abinci?.." Ya sake tambayanta,
"No...Yanzu...zan...ci..." Ta fada mashi,
"Daughter pls kar ki zauna da yunwa...and duk abinda kikeson ci just contact me
directly kinji kou?..."
"Yes sir..."
"Nasa an gyara maki dakin kusa da Wanda kika kwana...ki koma chan..sannan duk
abinda kikeso ki sa ayi maki...don't stress yourself...hope am understood?..."
"Yes sir..."
"Yes ma'am..." Shima ya fada cikin zolaya, San murmushi ta saki sannan ya kashe
wayan, relaxing Maryam tayi Tana tuna irin kirkin alhaji Ismail,
"He's so caring..." Ta dada under her breath, ahankali ta mike ta fito falo tare da
shiga kitchen,
"Baki ci abinci ba har na rana y kusa dahuwa..." Binto ta fada mata, murmushi kawai
ta sakar mata sannan ta bude fridge, yourght ta gani ta Fiddo,
"Tab ki maida shi..kika sha tou kin shawowa kanki..." Bata nemi Jin ko na waye ba
ta maida ta ajiye, cabbage da asabe ke yankawa ta deba ta wanke, ta fara ci haka
nan, kallon ta kawai suka tsaya yi
"Bazaki ci abincin da aka ajiye maki ba?.." Binto ta tambayeta, ahankali ta girgiza
mata ki Tana Kai cabbage bakinta.

Karfe hudu baba rabi ta dawo gidan, suhail dake zaune compound harara ya bita dashi
batare saya amsa gaisuwanta ba. Maryam Tana ganinta taji wani irin dadi Don har
hugging dinta tayi saboda farin ciki. Nikam nace baba rabi bata iya Hana Suhail yin
what suhail do best.


One love❤
8❤
Wulakanci dodone...





® zuwairat (ummumaryam)




0⃣8⃣



Dearies dont forget to be voting ohhh, wai NA CUCE ta have over 220k views amma ko
20k vote ban samu ba😥😥😢😢, ni inyi wahala amma you can't take just a second kuyi
voting 😭😭😭. Nidai Yanzu iya voting dinku iya samun new post 😾.
Suhail fita yayi daga gida Don daman yana zuwa football field da su sadeeq ranar
Sunday, a chan aliyu ke ta bayanshi Ina bakuwar gidansu, baki ya tabe sannan yace
"Inside my trousers..." Ya amsa mashi yana Shan bottle water, tsoki aliyu yaja tare
da juyawa suhail baya, gabanshi suhail ya zaga sannan ya daga gaban gajeran wandon
daya saka yace
"Kalli she's in side..." Banza aliyu yayi dashi.
"Ni dai pls kar kayi maltreating wannan yarinyan, she looks nice...." Yusuf ya fada
mashi, suhail dake sanye da jessy na bacelona ya rufe marfin ruwan ya ajiye cikin
bag daya taho dashi sannan ya tsaya kaman Mai tunanin wani abu, Kawai sai ya saki
dariya, kallon shi sukayi ya fara cewa
"Allah wannan yarinyan muguwar yar rainin wayauce...wai ta hada min tea sai ta tuka
min madara kaman tuwo...can you believe that?.." Ya fada fuskan shi dauke da
murmushin da in ba friends din ba babu Mai ganinta, dariya sukayi Banda aliyu
"Maybe haka ta Saba hada tea..." Inji sadeeq, baki suhail ya tabe tare dacewa
"Babu wani...kawai rainin hankali né...wallahi ni dai haka nan I feel like in
kamata in dinga duka...Allah what I feel for her banajin shi kan sauran yan
aikin...." Ya fada Fuskanshi babu walwala,
"Wai yar aiki ce?.." Aliyu ya tambayeshi
"Yes...to me..."ya amsa mashi atakaice,
"Amma seriously ka bar zaluntar wannan yarinyan...there's something about her...she
look unique...Allah nidai yarinyan nan tayi min...if I have chance Ina iya
aurenta..." Inji Yusuf, suhail kura mashi Ido yayi sannan ya kauda Kai without
saying a word,Dan murmushi ya Kara saki yana cewa
"Allah dukda she's annoying ta iya ban dariya...yau da safe da gudu ta bar part
Dina...." Ya fada wearing a killer smile,
"Me tayi a part Dinka?... Kar dai ka zama Dan iska..." Yusuf ya fada sounding
surprised,
"Allah forbid...ko ina Dan iska ai duk wannan gidan babu mate Dina...dukkan su are
under me..."
"Enough about her..." Duk maganar da suhail keyi yana batawa aliyu rai amma yayi
shuru kaman bai damu ba, kawai he has his plans
"Ni daga nan gidanku zani..." Inji aliyu,
"You're welcome..." Suhail ya fada mashi.


Da yamma alhaji ya shiga part din hajiya da Kaya cikin Leda, lokacin Maryam Tana
dakin da aka ware mata tayi kwance Tana kallon ceiling idanuwanta lumshe amma ba
bacci take ba, bude kofa da akayi yasa ta bude eyes, murja tagani
"Alhaji yace kizo..." Ta fada mata, da sauri ta mike Don tamkar dad dinta ta dauke
shi, falo ta tarda shi tare da hajiya, ahankali ta durkusa ta gaidasu Don duk ranar
bata gan hajiya ba, alhaji kura mata Ido yayi yaga ta Chanza in just an instance.
Alhaji né kawai ya amsa gaisuwanta while hajiya Tana kallon alhaji domin taga irin
kallon da yake mata
"Daughter meke damunki?..." Dan murmushin karfin Hali ta saki tare dacewa
"Babu...komai...." Ta amsa mashi kanta kasa,
"Daughter tell me meke damunki...ai ba haka kike jiya ba..." Ya fada kaman yana
magana da yarshi ta cikinshi Amman hajiya babu abinda take sai kallon su sannan
deep down she's boiling,
"Nothing sir..." Ta amsa mashi still, Leda dake kusa dashi ya mika mata,
"Ga Kayan islamiyya...zaki fara daga gobe..." Ya shaida Mata, ahankali ta taka ta
dauki ledan,
"Na...go..de..." Ta fada sannan bar su nan, alhaji shuru yayi yana tunanin abinda
ya sameta Don she was lively kafin ya kawota nan gidan, alhaji mikewa yayi ya fita
daga falon hajiya ta raka shi har bakin gate dayake a kasa zai fita kasancewan da
akwai majilisa da suke zama nan unguwan duk ranar lahadi. Hajiya na komawa ciki
alhaji ya dauki waya ya Kira

Please Login or Register in order to submit comment