Reading Yafi dare duhu by Umar Dalha Funtua Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalinki...insha Allah you will love my home kinji kou?.."Alhaji
ta gyada mashi Kai tare da goge hawayenta,
"Yanzu wane suna kikeson a dinga kiranki dashi..." Ya tambayeta, shuru tayi for a
while sannan tacel
"Anyone is okay " Ta amsa mashi in a cool tune,
"No..ya kamata ki zabi Wanda kikeso Don in fada masu shine sunan ki...Sannan duk
sanda aka kiraki ki San dake ake...so tell me wanne suna kikeso..." Ya sake
tambayanta,
"Choose for me..." Ta fada mashi kanta kasa
"No na baki dama... You choose...", shuru né ya Dan biyo baya Tana tuna sunaye data
sani, after like minti biyar tace
"Fa...ti...ma..." Ta fada voice dinta na rawa, Dan murmushi alhaji Ismail ya saki
tare dacewa
"Nice name Fatima...so always remember Fatima kinji kou?" Ahankali ta daga mashi
Kai, sadda Kai kasa tayi while pilot na aikinshi na tukin jirgi. Alhaji Ismail kura
mata Ido yayi for a while deep down yana ganin she's gentle compared to wasu yaran
zamani Don ko kadan babu rawan kai tattare daita, tunawa yayi da suhail sai ya Dan
saki murmushi kawai. Kafin su Isa Kano alhaji Ismail ya gama plan yanda abubuwan
zasu kasance. A aminu Kano airport pilot yayi landing tunda alhaji Mahmoud ya Sanar
dasu zuwan su, suna landing Maryam taji new alamari tattare daita Don it feel so
weird. Motan cikin airport ya samu ya kaisu daya daga cikin gidanjen dake cikin
garin Kano. Suna isa ya kalli Maryam tare dacewa
"Daughter relax kinji kou "?
"Tou..." Ta amsa mashi. Wayanshi ya dauka yayi dailing number Salman after ringing
biyu ya dauka tare da sallama, nan alhaji ke fada mashi ya kaiwa baba rabi waya
amma kar ya Bari kowa ya sani. Babu musu ya shiga cikin falo da sallama luckily ya
shiga babu kowa falo sai murja dake mopping kan stairs, nan ya tambayeta inda baba
rabi take Ta amsa mashi da Tana cikin kitchen. Nan ya shiga kitchen din ya kirata
waje, mikawa mata wayan yayi. Nan sukayi magana da alhaji Ismail, da Jin yanda suke
maganar kasan sirri suke Don ko Salman bai Jin abinda suke cewa, bayan sun gama ta
mikawa Salman wayan sannan ta fashe da kukan karya tare da shiga falon. Direct
upstairs ta nufa da hannuwanta bisa kanta sai rusa kuka kawai take su murja sai
binta suke a baya suna tambayanta abinda ke damu ta amma ko kadan bata basu amsa
sai hawan stairs take hannunta biyu gida kanta, lokacin suhail na kwance kan three
sitter sai latsa waya yake suna hira da mom dinshi Don mostly tare suke hira sai
indai yana tare dasu sadeeq amma in har his not with them tou his with his mother.
Ihun da suke ji ya doso su yasa hajiya dake zaune gaban mirror ta kalli suhail tare
dacewa
"Eyeballs kanajin abinda nakeji?.. Ko kunnena né?.." Ta fada Tana sauraron ihun
dake kussantosu, suhail daga manyan eyes dinshi yayi tare da cire ear phones dake
kunnen shi sannan yace
"Kaman someone is crying kou?" Ya tambayeta
"Yes..abinda nake ji kenan..." Bata rufe baki ba sukaji muryan baba rabi Tana
kiran
"Hajiya!... Hajiya!!.." On top of her voice, daura face hajiya tayi tayi tare
dacewa
"Wai waye hakan...kina haukane?" Ta fada a tsawace, cikin kuka baba rabi tace
"Hajiya nice...inna mu Ta rasu..." Ta fada cikin kuka kaman ba innan da
Ta dade da rasuwa ba, suhail mikewa yayi zaune tareda saka slippers yana kallon mom
dinshi,
"Ki shigo..." Inji Hajiya, ahankali Ta bude kofa ta shiga sai hada zufa take kaman
da gaske take, suhail kallon ta yayi from head to toes sannan yace
"Shi yasa kike mana ihu cikin gidan kaman zaki tada mana gidan?.. Sai kace kanki
farau rasuwa?... Annabi ma ya rasu anyi hakuri balle wata hagged old woman...after
all kina sonta me ya Hana ki zauna ki kula daita?... Rubbish..." Y fada tare da Jan
Dan guntun tsoki ya koma ya phi kwanciyan sa, kallon ta hajiya tayi sannan tace
"To ya zaayi...zaki tafi gida né ko daga kukan shikenan?.." Ta tambayeta In i don't
care manner, cikin kuka inna rabi tace
"Ai dole in tafi..." Bata idaba hajiya ta daga mata hannu
"I don't want long story..." Ta fada atakaice sannan ta kalli suhail before saying
"Eyeballs bata transport fare...", kaman bai so ya mike ya bude locker ya dauko
kudi kaman five thousand, ta tako zuwa inda take tsaye har zai bata sai ya maida
hannun baya yace
"Wai nawa né kudin zuwa garinku?.." Ya tambayeta kaman wata mate dinshi
"Dari bakwai ake kai mutum..." Ta amsa mashi
"Duka nawa kenan?..." Ya sake tambayanta
"Duhu daya da Dari hudu..." Kallon kudin hannunshi yayi ya zari dubu uku cikin
kudin ya mika mata dubu biyu ahankali baba rabi ta sa hannu Ta amsa daga hannunshi
tare dacewa
"Nagode...", duk mom dinshi Tana kallon shi
"Eyeballs give her all..." Ta fada mashi, kallon ta yayi tare dacewa
"Mommy why?... Ai the one I gave her is enough...she should manège it..." Ya fada
tare da maida sauran cikin locker daya dauko su in the first place. Mom dinshi bata
kada cewa komai ba ita kuma baba rabi ta fita. Dakinsu ta shiga ta hada yan kayanta
as instructed ta fita su murja suna biye daita sai sannu suke mat kaman da gaske.
Har bakin gate Suka raka ta sannan suka koma ciki Don hajiya bata yarda suna fita
sai indai ita ta alike su Don cewa take bata kawo su Don su dinga kallon garin Kano
ba ta kawo su né Don su dingayi mata aiki. Baba rabi na fita ta taka har bakin titi
ta samu a daidaita ta hau Ta fada mashi address da alhaji ya bata. Cikin minti
talatin baba rabi ta Isa gidan. Da sallama ta shiga ciki bayan Mai gadi ya bude
mata gate. Tana sallama bakin Kofan alhaji ya bude mata kofa, durkusawa tayi zata
gaida shi yayi saurin cewa
"Wai Dan Allah baba sau nawa nake fada maki ki daina durkusa min...." Da sauri ta
mike Don ko kadan bata son ran alhaji ya bace. Shiga tayi suka gaisa, sai lokacin
ta hangi wata kyakyawan yarinya dake zaune kan kujera with her head down, abinda ya
fara zo mata shine kilan aure alhaji ya Kara bayason hajiya ta sani, wani irin dadi
taji,
"Ki zauna mana..." Alhaji ya fada mata yana nuna mata wani kujera dake kusa Dana
Maryam, ahankali ta zauna sannan Maryam ta daga kanta ta kalli baba rabi tare da
gaidata cikin hausan ta da bai fita, da sauri baba rabi ta amsa mata Tana kallon
alhaji Ismail for a while sannan ta kauda kanta cikin tunani kala kala Dan gyaran
murya alhaji yayi sannan yace
"Baba wannan itace Fatima...." Ya fada mata ataikace,
"To...madalla...." Baba rabi ta amsa mashi Tana dauke da murmushi,
"Ya uwa,...inason ki zauna da ita zuwa nan da sati daya...ki kula daita tamkar
yanda zaki kula da suhail...sannan inason wannan ya zama Sirri tsakanin mu..."
"Ai alhaji komai ma zaa yi maka...." Ta amsa mashi, mikewa yayi tare da kallon
Maryam before saying
"Fatima zan wuce...."
"Ok..." Ta amsa mashi kanta kasa, cikin ranta sai tunanin Ina family dinshi suke
daya kawo ta nan gidan, kallon baba rabi yayi sannan yace
"Anjuma zan aiko Salman da abinci sannan zan bashi kudi sai ya kaiki kasuwa ki samo
mata atampopi da hijabai....sannan Dan Allah ki dinga tunatar daita in lokacin
sallah yayi...in kun shiga kasuwa a samu tailor a bashi Kayan ya dinka mata su..."
Ya fada yana kallon baba rabi,
"tou alhaji..." Ta amsa mashi. Fita yayi ya barsu nan. Maryam ji tayi kaman her
world have come to an end Don Jin ta take so lonely Don babu waya da zatayi
chatting da friends sannan babu wajen zuwa and the most annoying part shine gata a
Nigeria.
"Sannu yan nan" Inji baba rabi, daga eyes dinta tayi tace
"Yau...wa..." Baba rabi kura mata Ido tayi Tana sauraron yanda take magana, cikin
ranta Tana tunanin kilan ba yar kasar bace saboda yanda take amsa mata kaman ba
bahushiya ba. Ahankali Maryam ta mike tare da cewa
"Bacci..." Ta fada Tana yi mata alaman kwanciya da hannunta, murmushi baba rabi
tayi tare dacewa
"Bacci.. Zakiyi?.." Da sauri Maryam ta daga mata Kai
"Tou...amma ai baa bacci bayan sallan asar...ki Bari sai bayan sallan ishai..." Ta
fada mata ahankali, shuru Maryam tayi not knowing what to say, Don ita ji take babu
abinda take bukata kaman ta watsa ruwa ta Dan kwanta,
"Wanka....and hu...tawa....." Maryam ta fada mata,
"Tou...muje in hada maki ruwan wankan..." Ta fada mata Tana mikewa, ahankali Maryam
ta girgiza mata Kai tare dacewa
"Zan...yi...myself..." Dukda baba rabi bata San maanar myself ba ta gane inda ta
dosa
"Tou shikenan..amma dai kar kiyi bacci kinji kou?.."
"Tou..." Ta amsa mata, takawa tayi ta shiga corridor dake da dakunan bacci gida
biyu, dakin right hand side dinta ta nufa ta bude taga well dressed bed da. Bed
set, bata damu taga Yanda dayan dakin yake ba ta bude bathroom Don taga how neat
it is, luckily taga kaman baa taba amfani dashi ba, shiga tayi ta kunna tap Don
gani in da akwai ruwa, gani tayi every thing is okey, tunawa tayi babu sabulu babu
soso sannan babu towel amma she have no choice haka ta shiga ta sakarwa kanta ruwa
ta fito daure da dogowar rigarta dukda bai ko rufe mata jiki sosai ba amma haka ta
dawo daki ta kakkaba zanin gado ta jefa kanta kan gadon ko minti goma batayi ba
bacci yayi gaba daita.

Alhaji Ismail na fita ya Kira Salman yana ce mashi ya kawo mashi mota, ba tare da
bata lokaci ba Salman yazo ya dauki alhaji cikin ranshi yana tunanin ya akayi baya
airport bayan kuma daga abroad yake. Gida ya kaishi inda suhail dake kwance under
thatch sanye da singlet da Jean was surprised, yana ganinshi yayi saurin mikewa
zaune,
"Dad...harka dawo?.." Ya fada sounding so surprised, murmushi dad dinshi ya saki
tare dacewa
"Yes son...ho have you been?.."
"Alhamdullilah...." Suhail ya fada yana mikewa tsaye tare da Jan Jean dinshi dake
Neman kwallewa. Alhaji tsaya kallon shi yayi sannan yace
"Are you out of belt?.." Ya tambayeshi yana kallon yanda yake tafiya Jean din na
yawo waist dinshi
"No dad...kawai inason feeling free né...." Ya fAda sannan ya karasa ya amshi bag
dake hannun dad dinshi, hanyan part din alhaji sukayi, bayan sun shiga ciki suhail
ya kalli mom dinshi data shigo ciki sannan ya kalli alhaji yace
"Dad ya trip?.."
"Lafiya lau..."
"Dad ya Maryam...." Ya tambayeshi, kallon shi mom tayi before saying
"Who is Maryam"
"Ask him..." Inji alhaji, Dan Shafa Kai yayi sannan yace
"Dad yar boss mana...." Ya fada kaman wani Mai kunya
"She's fine..." Ya amsa mashi cikin ranshi yana this days zaka hadu daita, it
depends on you ka ja raayinta,
"Pls dad...." Ya bude baki zaiyi magana hajiya tace
"Pls eyeballs ka bar dad ya huta...he's just coming back..." Bai Kara cewa komai ba
ya juya ya basu wuri, nan hajiya ta dinga fada wai ya dawo bai fada mata he's on
his way ba, hakuri kawai ya bata yana kallon how glowing and beautiful she is.
After yayi wanka ya yaci abinci shima ba sosai ba Don hankalinshi na kan Maryam Don
yasan bataci Komi ba tunda babu wani Abu naci agidan. Hajiya na zaune kusa dashi ya
rasa excuse da zai bata ya fita ya bawa Salman kudi ya sayo mashi abinci, labari
take bashi amma he's so absent minded,
"Bari in aiki Salman...." Ya fada mata yana kokarin mikewa,
"Aiken me zakayi mashi...." Hannu yasa a aljihunshi ya Fiddo atm sannan yace
"So nake ya amso min kudi a bank...." Bata Kara cewa komai ba ya fita. Salman dake
zaune kusa da masu gadi suna hira ya hangi alhaji ya nufosu da sauri ya mike shima
ya nufeshi. Nan alhaji y mika mashi atm ya fada mashi ya amshi 100k yaje ya sayo
abinci Mai rai da lafiya tare da drinks yanda mutane biyu zasuci, sauran kudin ya
ajiye. Nan ya fada mashi address da zai Kai abincin.


Bayan kaman hour guda Salman ya isa gidan, bayan Mai gadi ya bude mashi ya shiga
ciki rike da manyan Leda guda biyu, door bell ya latsa few seconds later baba rabi
ta fito, he was surprise to see her, gaidata yayi in a respectful way sannan yace
ga sako daga alhaji, yana mika mata ledan yana leken dakin ko da akwai wata nan.
Kaman ya tambayeta amma yayi shuru ita kuma ta maida kofa ta rufe without caring
for the inquisitive look he's wearing. Bayan ta shiga dakin ta jera abincin kan
center carpet sannan ta shiga ciki nan ta hangi Maryam kwance daure da riganta Tana
bacci, kaman ta tashe ta sai kuma ta kyaleta.

Falo ta koma Tana zaman jiranta har magrib bata fito ba, komawa tayi this time ko
tunani batayi ba ta tadata daga bacci, a firgice ta farka Don gani yake it's the
end of the world Don tunda take baa taba tadata daga bacci ba, murmushi baba rabi
ta saki tare dacewa
"Dazun kinyi min alkawarin bazakiyi bacci ba...amma sai kika kwanta kou?.." Ta fada
sounding so friendly, cikin karfin Hali itama Maryam ta saki murmushi tare dacewa
"Yi...ha...kuri..." Ta fada cikin sanyinmurya,
"Ba komai...tashi kiyi sallah sai muci abinci..." Babu gardama ta mike daga kan
gadon sai hamma take Don ko kadan baccin bai isheta ba. Bathroom ta shiga ta cire
riganta ta maida sanna tayi alwallah. Fitowa tayi bata ga kowa ba, lokacin baba
rabi ta je tambayan Mai gadi Ina alkibla, bayan ya fada mata ta dawo ta tarda
Maryam falo with her eyes closed
"Kin fito Fatima?.." Ta tambayeta, Sam Maryam ta mance her new name is Fatima,
hakan yasa bata ko bude Ido ba har saida baba rabi ta Maimaita same question sanna
tayi saurin bude idonta.
"Eh..." Ta amsa mata ciin natsuwa, hijab baba rabi ta mika mata tare da nuna mata
kiblah sannan itama ta shiga ciki tayi alwallah. Bayan sun idar da sallah, baba
rabi ta kalleta, lokacin ta hada Kai da gwaiwa sai tunanin rayuwa take
"Matso muci abinci..." Ta fada mata, Maryam daga Kai tayi ta kalli abincin da aka
jera taga babu abinda zata iyaci sai lean meat da juice. Ahankali ta Matso kusa da
abincin suka faraci, bayan kaman minti biyu ta sha juice din, da sauri ta bata
fuska Wanda yasa baba rabi tambayanta
"Da...sugar..too much..." Ta fada mata, dariya baba rabi tayi Tana kallon ta cikin
so da Kauna Don Tana da shiga rai sosai, kaman ta tambayeta daga Ina take da bata
iya Hausa ba sai kuma tayi shuru
"Tou kici abincin..." Ahankali ta girgiza mata Kai. Duk yanda tayi magi ya Don
Maryam ta Kara cin abinci ki tayi. Haka dai ta Ci ta koshi ta mikawa Mai gadi
sauran ta dawo lokacin Ana kiran sallah ishai, da umarnin ta Maryam tayi sallah
isha sannan ta koma ta kwanta full of tunani daga baya bacci yayi gaba daita.




One love❤
[10/26, 8:57 PM] Jamila Muh'd: 5❤
Wulankaci dodone........




®zuwairat (ummumaryam)



0⃣5⃣



Pls masu yi min flashing su daina if you can't recharge and call me then don't
expect me to call you back. Sannan wasu zasu kiraka amma da nayi piçking ko magana
basuyi sai su katse, I may not pick unknown number again. So pls don't be offended.
Thanks



The following day bayan alhaji yayi breakfast yayi shirin office, sai sauri yake
saboda Maryam har hajiya taso ganewa something is wrong, ko suhail da ya raka shi
har bakin mota sai da yace
"Dad are you meeting the president today...." Ya tambayeshi cikin zolaya, banza
yayi dashi ya shiga cikin mota Salman yaja su suka bar gidan. Bayan sun Isa office
ya Kara mikawa Salman atm tare dacewa
"Ka koma bank ka amso 100k ...nawa na jiya suka rage?". Ya tambayeshi sounding
calm,
"95k.. Sir,,,," ya amsa mashi,
"Ok then...in ka amso 100k ka hada Dana hannunka zasu zama 195k kou?"
"Yes .." Ya amsa mashi kanshi kasa,
"Tou ka saya masu abincin breakfast ka Kai masu sai ka jira su gama ka kaisu kasuwa
zasuyi siyayya ..." Ciin respect ya amshi atm card din cikin ranshi yana tunanin
abubuwa kala kala Don yaji yana using plural that means ba baba rabi kadai bace
amma bai gan kowa sanda yaje ba, he lots of questions to ask amma waye shi da zaiyi
tambaya, kawai he's happy alhaji yayi trusting dinshi yana nuna mashi abunda ba
kowa ya sani ba, not even suhail. Da sauri ya fita yaje ba ka ya amshi kudin sannan
yaje breakfast joint ya sayo masu abinci Mai dadi ya Kama hanyan gidan yana tunanin
meke faruwa.
Yana Isa gidan maigadin gidan ya bude mashi kofa ya Kama hanyan parlor. Lokacin
Maryam na zaune tayi relaxing kan kujera idanuwanta lumshe Don yau bata samu bacci
yanda takeso ba saboda kiran sallan farko baba rabi ta tadata wai ta tashi tayi
sallan nafila kafin a akira asalatu, bayan sallan asuba bata koma ba Don Tana bakin
cikin a tadata daga bacci, hakan yasa ta hakura da baccin completely. Door bell da
akayi ringing yasa baba rabi dake zaune mikewa, bakin kofa taje ta bude taga Salman
tsaya rike da leathers gaisawa sukayi sannan ya mika mata ledan da sauran 180k yana
cewa
"Baba ha sako daga alhaji..." Ya fada still yau yana Dan Neman leka dakin amma bai
samu daman hakan ba saboda baba rabi ta tare Kofan da kyau,
"Tou madalla..." Baba rabi ta fada Tana Amsan ledan, har zata juya yace
"Alhaji yace zan kaiku kasuwa...." Ya fada mata in a respectful way,
"Tou..zaka shigo ka jira mu ko zata tsaya waje?.." Ta tambayeshi, kaman yace zai
shigo Don ganin the third party amma sai yace
"Bari in jira ku a mota..." Yana kaiwa nan ya juya ita kuma baba rabi ta maida
Kofan ta rufe.

Bayan sunci breakfast Wanda baba rabi ta cinye almost all saboda yanda Maryam bata
wanI damu da abinci sosai ba sannan all this new for babu vegetables yana damunta
Don she loves vegetables sosai. Baba rabi ta fara tattara wurin sai itama Maryam
ta taimaka mata, ko kadan baba rabi bata hanata ba, tare suka gyara wurin sannan
Maryam ta mike tare dacewa
"Bacci...zanyi..." Ta fadawa baba rabi,
"Aa diyata...babu zancen bacci...kasuwa zamu...Don haka ki shiryo kizo mu tafi...."
Ta in
Umarce ta, idanuwa Maryam ta lumshe sannan ta budesu ta kalli kanta from head to
toe Tana son fadawa baba rabi bata da wata shirin tunda tayi wanka kuma bata da
wasu Kayan amma ta rasa yanda zata fada mata, few seconds later sai cewa tayi
"gamawa..." Dariya baba rabi tayi sannan tace
"Ba gamawa zaki ce ba....na shirya zakice...." Ta fada Tana dariya, itama Maryam
Dan murmushi ta saki tare dacewa
"Na shir...ya...."
" tou shikenan...mu je..." Ta fada mata Don itam by da wata shi da zatayi kuk her
hijab is handy, da sauri Maryam ta shiga bedroom dinta ta dauko vail dinta ta daura
kan gashinta, Tana fitowa baba rabi ta umarce ta data yafa vail din, babu musu ta
yafa shi sannan suka fita.

Ana buda gate Salman ya maida dubanshi kan Kofan, then he meet the shock of his
life Wanda ya nuna karara a face dinshi, Maryam yake kallon, bai taba ganin
yarinyan data hada komai na kyau a face dinta ba kaman Maryam, tafiyan ta na abun
kallo né Don she walks majestically kaman wata saurauniya, har suka Isa bakin Kofan
bai sani ba, sai da suka bude mota ya San sun iso,
"Na shiga uku...." Ya fada under his breath, daga Kai yayi yana kallon ta ta mirror
lokacin ta shiga cikin motan,
"Who is this...." Ya tambayi kanshi cikin ranshi,
"Mutum ko aljana..." Ya sake tambayan kanshi,
"Ya rabbi save my job...." Ya fada cikin ranshi, ganin su shiga har sun rufe mota
yasa yaja motan sai kasuwa, amma kafin su Kai ya kusa buge mutum har sau uku har
saida baba rabi ta yi mashi magana kan ya kula da hanya sannan ya maida hankali Don
bai minti daya bai daga Kai ya kalleta ta mirror ba, ita kuma ko kadan bata damu ta
daga ki ta kalleshi ko wani abuba, ita kawai she's depressed. Lokacin da suka isa
kasuwa rana ta fito sosai Don irin morning sun din nan né Mai haske, parking lots
na kasuwan kwari Salman yayi parking, baba rabi fita tayi amma Maryam ko alaman
fita bata dashi, sai kallon ranar dake walkiya kawai take
"Ki fito mu tafi mana..." Taji baba rabi na fada mata, Kara kallon rana tayi sannan
ta nuna shi Tana cewa
"Ra...na....it's hot...." Ta fada ahankali, Salman kam mutuwan zaune yayi cikin
motan saboda muryan da yaji Mai kaman waka,
"Ya zakiyi...ai sai hakuri...ki fito mu tafi kafin ranan ya fara zafi...." Baba
rabi ta fada mata, with out choice ta fito daga cikin motan, da sauri shima Salman
ya fito yana cewa
"In taho in tayaku daukan Kayan?." Ya fadawa baba rabi,
"Da ka taimaka..." Ta amsa mashi, bayansu yabi yana tunanin wacece wannan duk da ya
San da gani wannan ta fi ajinshi amma he can't stop thinking,tunanin da baba rabi
tayi shima yayi wai kilan matar alhaji ce. Da sauri ya kauda wannan zancen still
yana tunanin
"Who is she?..".

Cikin wata shago suka shiga inda baba rabi ta kalli Maryam before saying
"Ki sayi atampopi da kike so..." Baba rabi ta fada mata, Maryam tsaya kallon shagon
tayi Tana kallon abinda ita da kawayenta suke Kira da weirdos clothes, amma gashi
itama zata saka,
"Ki...saya..." Ta fadawa baba rabi, duk mutanen cikin shagon juyawa sukayi suna
kallon ta,
"Ki zaba....ai ke alhaji yace ayiwa siyayya...Don haka ki saya...." Ta fada mata,
tsayuwan tayi bata ce komai ba, Salman na Jin shurun yayi yawa ya fada masu su kawo
atampopi da materials masu kyau, sai lokacin Maryam ta daga Kai ta kalleshi for one
to two seconds sannan ta kauda kanta, Kaya aka dauko Mai yawa aka ajiyesu gabansu,
kallon ta yayi sannan yace
"Select..." Ya fada mata ataikace, Kara kallon shi tayi sannan ta maida duban ta ga
tilin shadda, materials da atampopi dake gabansu, har ha Allah babu abinda take so
ciki amma she have no choice haka ta zabi 3 daga each sannan ta kalli Salman tace
"I want gowns...like the one am wearing..." Ta fada Tana kallon eyes dinshi without
anything, shikam ganin ta zufa mashi idanuwa yasa ya sadda Kai kasa Don bai am da
budurwa balle ya koyi kallon mace eyeballs to eyeballs.
"Ok..." Ya amsa mata sannan suka bar shagon da Kayan da suka shiga, suna kan hanya
alhaji ya Kira shi Don Jin halin da ake ciki, nan ya ke fada mashi komai shi kuma
alhaji yace, a tambayeta ta sayi duk abubuwan amfanin ta. Yawo sukayi a kausuwa
tare da siyan duk abinda take so, ba Dan Tana son abubuwan da take saye ba sai Don
bata da choice, nan cikin kasuwa suka mikawa wani tailor yayi mata dinkingowns Don
ba iya daura zani tayi ba. Man shafawan ta ta nema amma bata samu ba, kawai sai
tayi settling for so white exclusive cream da sabulun, a gajiye ta koma gida, Don
duk jikinta zafi kawai yake mata. Direct bathroom ta shiga ta sakar wa kanta shower
sannan ta dauki gown daya cikin wayanda suka saya ta saka, falo ta dawo ta bude
wayan da tasaya ta saka SIM card dinta ta jona charging.



Bayan sati biyu rayuwa ta sauyawa Maryam sosai Don har ita kanta ta Chanza, tayi
pimples saboda man da take shafawa Sam bai amsheta ba, sannan hasken ta ya rage
sosai, idanuwanta sun koma ciki Don duk kokarin kula daita da alhaji da baba rabi
sukeyiis to no avail saboda ba abinci takeci sosai ba, she feels so lonely sannan
bata fita koina, abun da ke Kara tada mata hankali shine dad dinta bai yarda ta
dinga kiranshi always ba, ya fake kan security. Amma ba laifi ta Saba da baba sosai
sannan babu laifi Hausa na Dan shiganta fiye da da kuma Yanzu sallanta kan lokaci.
Duk sanda ta koma gaban mirror ta kalli kanta sai ta fashe da kuka amma baba rabi
is always around for her. Kuma zaman datayi daita yasa ta fara gane traditions na
yan arewa saboda always suna kallon arewa24, sanna wakan Adam zango yana bata
nishadi sosai Don if she's in the mood har takawa take. Kullum sau uku Salman ke
kawo masu abinci amma iyakar shi bakin kofa, gurinshi ya Kara ganin wannan yarinyan
just for once but no chance gashi bai iya tambayan baba rabi izinin shiga palour.


A bangaren alhaji ya rasa abinda zai cewa matarshi kafin ya kawo Maryam cikin
gidanshi, kullum suna waya da alhaji Mahmoud, sannan ya fada mashi gaskiya alamari
and alhaji mahmoud is ok by he's decision. Yau Friday suna zaune da hajiya ya
kalleta wearing a smile sannan yace
"My hajiya I think tunda gobe weekend zanje katsina...na kwana biyu ban je ba..."
Ya fada mata, Dan bata fuska tayi before saying
"Kai Baka gajiyawa da zuwa wannan kauyan.." Ta fada sounding irritating, Dan
murmushi ya saki Don in da sabo ya Saba cos har kullum kauye take cewa katsina,
"Mutum ya taba gajiya da tushinshi?... Besides ni wurina it's as beautiful as
London..." Ya fada babu alaman fushi tattare dashi,
"Hmmm...Kai ka sani...amma dai gobe zaka dawo kou?" Ta tambayeshi kaman bata son
yayi tafiya, pointed nose dinta yaja before saying
"Why bazan kwana ba?.." Ya tambayeta sounding naughty kaman wani yaro, itama cikin
shagwaba tace
"Because zanyi missing Dinka....." Dariya yayi before saying
"Banason hajiyata tayi missing dina...so in naje gobe zan dawo goben insha
Allah ...."dariya hajiya tayi tare dayi mashi peck a goshi sannan tace
"Thank you my alhaji...".

Wace gari around 9am sadeeq, aliyu da Yusuf suka zo gidansu suhail, daman mostly
weekend suna organizing meeting dinsu na shegantaka a gidan daya daga cikinsu, yau
gidan su suhail suke, kowannen su yazo cikin motanshi da shiga ta

Please Login or Register in order to submit comment