Reading Budurwan Sirri BY ZAINAB MUHAMMAD Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ranka shi dade,
**********
Ina zaune a cikin dakin da zirwanu ya kawo ni , nayi tagumi bana tunanin komai sai
na gida,
Yanzu a wani hali iyayena suke nasan dole su shiga wani irin hali izan har ya
kaasance basu ganni ba,
.
Nan take naji bana marmarin komai sai gida dun kuwa nima ina so na gansu ko
hankalina ya kwanta, sai de ba anan gizo ke sakar ba, aduk lokacin dana tuna cewa
ina da zukekiyar budurwa kamar haseena sai inji zanma iya yin shekaru hamsin muddin
zan zauna da haseena
.
Tunane tunane kala kala suna ta zuwanma kwakwalwata, ina cikin wannan hali ne sai
na fara jin wata zazzakar waka tana tashi daga bayan dakin danake, cikin zumudi na
nufi taga na bude don naga wacce keda wannan zazzakar muryar,
Wani kayataccen lambu ne yaiwa idanuna maraba acikin wannan lambu kuwa yan mata ne
su ashirin, suna rike da kayan kida sai kidi sukeyi, dukkan matan nan kyawawane na
gaban kwatance domin kuwa in ka dauke haseena har yau banga macen da ta kaisu kyawu
ba,
A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar
muryarta ne kawai yake tashi, ......
.
.
Kuyi hakuri da rashin post nawa akan lokaci rashin wadatuwan lokaci shi ya janyo
haka
,
Ni dinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks
BUDURWAN SIRRI
Marubuci:- Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 5
.
A tsakiyar wayannan yan mata wata mace ce ta lullube kanta da mayafi zazzakar
muryarta ne kawai yake tashi,
Zuciyata ce ke fisgata irin fisgar da ruwan kashe gobara yakeyi yayin fitowa daga
cikin bututun ruwan
.
Ni kaina ban san lokacin dana je na bude kofar dakina ba da nufin nayo waje naga ko
wacece wannan mai wakar, har na saka kafa na fita kuma sai nai wani tunani ,
Ayanda nake jin ana labarta min cewa nan duniyar aljanu ce , na tashi na nufi wajen
wayannan kyawawan matan, kila ma aljanu ne ban sani ba,
Wannan tunanin dana yi shi yasa na dawo da baya nai kwanciyata cikin dakina,
Dakyar na samu nasarar yin bacci sakamakon wannan zazzakar wakar dake tashi daga
waje, aduk lokacin dana runtse idanuwana domin nai bacci sai na wannan zazzakar
murya ya farkar dani,
Har takai da saida na samu wasu yanki na toshe kunnuwana da su sannan na dena jin
wannan waka
.
Washe gari na farka a gajiye na tashi na nufi dan wani kofa dana gani a cikin dakin
wanda tunanina ya bani cewa bayi ne, kama yadda na zata dun haka yake dun kuwaina
budewa na shiga na samu ruwa cikin wata randa na zinare batare da bata lokaci ba
nayi wanka da wannan ruwan sai de abun daya daure shine a duk lokacin dana debi
wannan ruwa sai naga ya karu
Har na iddar da wankan na fito daga bandakin na nufi kan gadona domin na saka kayan
dana cire ajje ,
Amma kayan sai sukace daukanmu inda ka ajje, na neme su sama da kasa na rasa, can
na bayan na gaji da nema sai na dawo kan gadon na zauna nayi tagumi, wani haske
naga dan kashe mani idanu, na kai dubana ga wajenda hasken ke fitowa sai naga ashe
ma a gefena ne, nakai hannu don ganin menene wannan yake wannan haske, cikin mamaki
sai gani nayi hannuna ya tabo wasu lallausan abu duk da ban ko menene ba sai na
daga abun sama toh anan ne aka samu mishkila abun ya kubuce daga hannuna ya fadi a
kasa ai yana faduwa sai naga ashe ma kayane riga da wando irin na sarautar mutanen
garin
Cikin tu'ajjibi na dauki kayan na sanyasu a jikina sannan na nufi wajen madubin
dayake dakin nayi mamaki ainun alokacin dana irin zunzurutun kyan danayi, kai
alokacin sai dana koda kaina nace ashema ni kyakkyawane haka,
,
Karar Kofan dakin ne ya katse ni, lokacin da ake kwankwasawa, na nufi kofan nabude
su ukune kamar yadda na fara ganinsu, har yanzu babu wani sauyi atare da su, yan
matan jiya ne daya daga cikinsu ta dubeni tace "ran ka ya dade gimbiyace ta turomu
mu tafi dakai wajenta don kuyi kalaci"
"Wacece kuma gimbiya" na tambaya
"Wacce ta kawo ka nan garin"
"Wai HASEENA ki ke nufi"
Na lura da cewa wannan kalma danayi na karshe yasa dukkansu sun tsorata duk da
bansan dalilinsu na tsoratan ba,
"Eh itace , amma yallabai kasani duk fadin kasarnan babu wadda yake kiran ta da
sunanta hatta mahaifinta ma, "
"Saboda me ba'a kiranta da sunanta"
"Wannan kuma wani sirrine na gidan sarauta"
Na jinjina kai sannan nace masu
"Toh muje "
Suka juya suka fara tafiya ni kuma na take masu baa
.
Mun danyi tafiya mai dan nisa sa wacce takaimu izuwa wani kayataccen lambu wanda ya
yalwatu da yayan itatuwa, su kansu bishiyoyin dake cikin lambun ababen sha'awane,
domin kuwa bishiyoyin dukkansu yana yinsu daya ne, tsayinsu da komai na su,
Furannin lambun kuwa sun kasance a duk bayan dakika daya suna dunkule wa waje guda,
Muka nufi wani waje daban a inda muka bi ta kan gada, wannan gadan de an kerashi ne
da zallar itace da igiyoyi aduk lokacin da muka taka gadan sai kaji wani kara na
tashi
.
Tun daga nisa na hango kyakkyawar fuskarnan nata sai sheki yakeyi, farace kyakkyawa
gata da dirarriyar jiki domin kuwa shape dinta na kwalbar cokacola ne,
Ta mallaki tsastsaikan fuska wadda ke dauke da dara daran idanu, wayanda jure
kallonsu, dan mitstsin bakinta wanda idan ka lura da kyau alokacin data ke magana
zakaga tamkar baya so ya bude,
.
Ayau tana sanye ne da irin kayan duniyanmu kuma irin na kasarmu, riga Atamfa da
sikert, abun ya bani mamaki ainun, ni danake zaton babu irin wannan kaya a wannan
garin, sai de dana tuna da abu guda sai nama dena mamaki
.
Ayau tafi kowanne lokaci kyau fuskarta sai sakin tausasan murmushi yake a gareni,
ai ban san lokacin dana kura mata idanu ko kiftawa bana yi ba,
Muka kariso wajen yan matan nan sukayi saurin russunawa akasa zasuyi magana kenan
ta dakatar da su ta hanyar daga masu hannu sannan ta sallamesu, sukai tafiyarsu
.
Ta dubeni tai wani murmushi wanda yake zuzuta wutar kaunarta a zzuciyata, "ka kwana
lafiya"
"Lafiya lau"
Ta riko hannuna , awannan lokacinma sai da naji shocking ya ziyarci kwakwalwata,
har nayi dan kara karami, ta jani muka karisa gindin wata bishiya, inda naga an
shimfide gaba dayan wajen da wani babbar tabarma, a tsakiyar ta barmar ga abubuwan
ci da sha nan birjik,
Takalmi na cire alokacin da nake shirin hawan tabarmar,
Wani laushine ya ziyarci tafin kafafuwana ,ko kadan wannan baiyi kama da tabarmar
dana sani ba mai uban gurza-gurza
Haseena ta zaunar dani itama ta zauna kusa dani yanda muna iya jin numfashin juna
"Shuraih tun da nake a duniya ban taba ganin dan Adam lokaci daya naji sonsa ba
saikai, hakan nema yasa yau dinnan zan fada maka sirrin dake tattare dani ina sonka
shuraih so ,kuma ina muradin zama abokiyyar zamarka na duniya da lahira,
Jina nake tamkar wanda akaiwa kyautar Aljanna domin kuwa a wannan lokaci na tabbata
babu wanda yakaini farin ciki
"Haseena kiyi sani cewa nima ina sonki , kuma babu abunda bazan ma don na
mallakeki, nasan cewa kina shakkun wannan gasa ta fidda gwani ne, toh ki sani
muddin akan ki ne sai de na mutu awannan gasa don kuwa bazan bari wani daban ya
sameki ba, ki kudurta a zuciyanki nine mijinki"
Hannu ta saka ta dauki wani tuffa ta mai gaza daya, har zata kai na biyu sai nayi
sauri na karbi tuffan daga hannunta ina mai yimata wani irin murmushi na zolaya,
sannan nima na gaza daidai wajen da ta gaza
Anan muka luluka izuwa duniyar soyayya domin kuwa hira muka shiga yi sosai yadda
take bani labarin garinsu, sosai naji dadin wannan lokaci
.
Muna tsaka da hiran ne wani lokacin izan ta fadi abun dariya sai mu dara , wata
kakkausar murya ce ta katse mu da fadin "BUDURWAN SIRRI bata bil'adama bace,
.
Dukkanmu muka juya don ganin mamallakin wannan murya,,,,,,
.
www.facebook.com/hausaebooks
BUDURWAN SIRRI
Gajeran labari
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks page
@shuraih 99%
Page 6
.
Gabjejen katone mai kirar mutanen farko yana da tsayi wanda na tabbata yayi ni Uku
a tsayi don sai dana daga wuyana sannan nai nasarar ganin Fuskarsa
a turbune fuskar yake babu alaman murmushi ko kadan a tare da shi, kwayan idanunsa
jane, gashin kasumba ya rufe mai baki yayin da ya hade da gashin gemunsa wanda ya
zura ma wani zobe ya kulle
.
Yana sanye da riga falmara mara hannu hakan yasa na samu nasarar ganin kwanjinshi,
gaba daya jikinsa a mummurde yake, ga jijiyoyin jikinsa sun tashi sunyi burdum
burdum kai kace igiyace
.
Hannunsa na dama yana rike da gashin gemunsa wanda ya rike daidai wajen da ya zura
zoben yana dan liliyawa ,fuskarsa na yatsinewa wanda shi a zatonsa murmushi yake,
Shi ba mummuna ba haka kuma shi ba kyakyawa ba, amma kallo daya kadai nai masa na
gane cewa wannan dakare ne, domin kuwa akuibin cinyoyinsa hagu da dama akwai wasu
takubba manya manya cikin kufensu , wayanda na tabbata in aka ce na daga daya
cikinsu bazan iyaba
.
Cikin firgita da tsoro na saki baki galala ina kallonshi har ya kariso garemu,
Abun daya daure mani kai shine sam babu alamun firgici a fuskar haseena
A zuciyata nace yo ta ina zata firgita bayan itama yar uwarsu ce, na sake maimaita
wannan suna da naji ya kira haseena da shi a cikin zuciyata BUDURWAN SIRRI
.
Yana tafiya takubban dake jikinsa suna dan kara sakamakon yadda yake tafiyar din
.
Ya kariso wajen da muke zaune
Neman waje yayi ya zauna sannan ya harde kafafuwa irin zaman da yayi sai ya tuna
mani da lokacin da nake makarantan Allo, fuska cikin fuska ya dubeni sannan ya
takarkare da mahaukacin dariya mai matukar amo, ba shiri na sanya yan yatsuna na
toshe kunnuwana sakamakon yadda naji dodon kunena na neman agaji
.
Sai da yayi dariya mai isarsa sannan ya dubi haseena yace
"Budurwan sirri, wai dama wannan dan tsakon ki ka je kika samo, ai nayi mai girma
ina laifin ki samo dai dani, "
Ya nuna ni da yatsa batare daya kalleni ba sannan yacigab da magana da muryansa mai
kama dana jaki
"Ina mai tabbatar maki da cewa nine zan aureki ,kuma nine nan zan lashe wannan gasa
wacce zamu kara wata mai zuwa ni da wannan dan kwaron "
.
Duk da cewa ina jin tsoron wannan basamuden aljani wanda bansan sunansa ba , ai
koda naji irin kalaman dayake furtawa ga haseena sai na fahimci cewa shine SALMAN,
nan take na nemi tsoron dana ke mai na rasa cikin kunan rai na daka masa tsawa
"Kai Aljan mutun bisa kanka, girman jiki bashi bane ke nuna cewa mutun yana da
karfi, to kayi sani nidin dai daka raina da yardar Allah sai na baka mamaki" ai sai
dana gama furta maganar sannan nayi nadamar furtawa
Domin kuwa alokacin fuskar aljani salman ta yamutse , yadda kasan an aiko masa da
sakon mutuwa,
.
Badon ina da dauriya ba da babu abunda zai hana ban tsiyayo fitsari ba kasancewar
irin kallon danaga yana yimin
Cikin kunan zuciya ya daga girjejen hannunsa mai kama da tabarya da nufin ya zabga
min mari, rufe idanuwa na nayi don kuwa nasan babu makawa zai aikata, ko kadan
banyi kokarin kare kaina ba ta hanyar rufe fuskata don nasan muddin hannunsa ya
taba jikina to take zan baje a kasa sumamme ko matacce
.
Cikin sauri haseena ta daka masa tsawa wanda ya sanya shi tsayawa cak tace "salman
izan ba kana son kaaga fushina bane toh ka gaggauta barin wajennan , in kuwa ba
haka toh zakayi daana sani wanda ba zai maka Amafani ba, "
cike nake da tsoro kamar ace kyat na ruga na dubeshi a yayin da ya dunqule hannunsa
ya naushi kasa , a hassale ya tashi sa'annan a dubeni yace "ka shirya nan da wata
daya bil'adama maza bisa kanka," yana gama fadin hakan sai naga manyan fuka fukai
guda biyu sun fito daga bayansa cikin kankanin lokaci ya tashi sama ya luluka cikin
gajimare
Na dawo da dubana ga haseena tambayoyi fal bakina
.
Murmushi tai min wanda shine ya mantar da ni dukkan wannan tambayoyi dana ke shirin
jera mata su
Tace "nasan ka tsorata da Al'amarin Salman amma karkadamu akwai wanda zan kaika
wajensa ya koyar dakai fada da kuma yaki"
.
"Toh" kawai bakina ya samu fadi a yayin da muka cigaba da hirarmu in ka ganmu sai
ka rantse mun yi shekaru da ita, na saki jiki sai zuba zance nake

******
.
Washe gari tunda sassafe wayannan yan mata uku suka sake zuwa kirana sai de yau
dukkansu sun canja kayan dake jikunsu irin kayan dana sanya jiya shi na sake sakawa
duk da ban san wanda yake kawo mani kayan ba hakan bai hanani sakawa ba
.
Wannan karon ba yalwataccen lambunnan muka nufa ba wani bangare ne daban wanda
kallo daya naiwa bangaren nagane cewa mutane ba su cika shiga wajen ba duba da
yadda naga wajen yayi kura, kuma yanan gizo gizo duk ya gauraye rufin wajen,
.
Muka iso bakin wata kofa mai kauri wacce aka sana'antata da zallan bakin karfe daya
daga cikin matannan ce ta ciro wata tsohuwar kubba daga jikinta ta zura a cikin dan
siririn ramin dake jikin kofan sannan ta murda
Dan karamin dakine mai dauke da kayan tarkace iri iri , a karshen bangon dakin muka
hango ta naayi mamaki kwarai da ganinta anan
.
Na kariso ni kadai a yayin da yan mata ukunnan suka tsaya a bakin kofan dakin rufe
kofar dakin sukai
Na budi baki zanyi magana haseena ta dora yatsanta a kan lebbana alamar nayi shiru
ta nufi wani kusurwan dakin daban wata tsohuwar tayan keken doki naga ta daga, ta
kama wani katako ta murda shi
.
Nan take jiri ya fara dibana sakamakon yadda naga dakin yana juyawa da sauri
haseena ta ruko hannuna sannan itama ta rike wani karfe , kafin kace kwabo sai
dakin ya runga juyawa dukkan tarkacen nan suka fara tashi sama suna haduwa da
junansu, baki kawai na saki ina kallon ikon rabbi, sai da gaba dayan tarkacennan
suka gama hadewa waje guda suka dunkule kaman dunkulin magi
.
Sai da suka gama dulkulewa tukunna sai kuma dunkulin ya fara fitarda yar karamar
kofa, kan kace kwabo har wannan dunkulin ya canja siffa izuwa na Kofa,
Babu abunda zai baka mamaki ma kaman yadda kofan ta kasance sai haske take tana
daukan idanu
.
Adai dai lokacinne dakin ya daina juyawa komai ya tsaya cak sai a sannan haseena ta
ce "wannan shine babul hajir, ta cikin wannan kofa zaka iya tafiya ko ina a doron
kasa, tun daga kan duniyarku har zuwa wasu duniyoyinma,"
.
Shiru kawai nayi na saki baki ina kallonta ni yanzu ma har na saba da abubuwan
mamakinsu koda na gani ma banayin mamaki sosai kamar yadda nake a baya
.
Ta ja hannuna wanda hakan yasa nima nabi bayanta bakin kofan muka zo muka tsaya ta
sanya lallausan hannunta ta bude kofan sai a sannan dukkan wani mamakina ya karu
domin kuwa babu komai a gaban kofan banda hazo daya ke gittawa lokaci lokaci, banga
alaman wani abun ba
.
Haseena ta jani muka shiga cikin kofan ai sai dukkanmu muka ji kamar mun fado daga
saman wani katon tsauni ne, saboda tsaban firgici kulle idanuwana nayi yayin da
muke fadawa kasa iska sai gittani yake ta ko ina hakan yasa na saki wata kara
.
Kamar daukewan wutan nepa sai mukaji mun fado a cikin wani rami, abun da ya kara
dauremin kai shine da kafafuwanmu muka fado kuma ko dan zogi banji kafata tayi min
ba
.
Haseena tai murmushi "tace haka ka iya ihu dama ban sani ba, ai kuwa sai ka tanadi
wani ihun da yafi wanda kayi a baya, domin kuwa yanzu ne za'afara ainahin tafiya"
cikin sigar zolaya ta fada
Na sosa keyana "ai ni kaina ban san lokacin da na saki ihun b....."
Wani kara ne ya katse mani maganata karan kuma daga kasan inda muke yake fitowa sai
a sannan na daga kaina na kalli sama
Gani nai tamkar mun fada cikin rijiya gaba dubu ne
Ban gama wannan tunanin ba kasan wajen ya wawake take muka fada ciki amma wannan
karon a tsaye muka fada kuma ahankali muke sauka kasa,
Cikin wani daji mai yawan guntayen bishiyu muka sauka , sosai yanayin dajin ya
burgeni dukkan wasu ganye na dajin jane maimakon kore mun danyi gajeriyar tafiya da
kafafunmu sannan muka riski wani Bukka irin na mutanen da shi kansa bukkan da
jajayen itace aka sana'anta shi, bakin bukkar muka tsaya sannan haseena tai
sallama, wata tsakurarriyar muryace ta amsa sallamar, daga bisani sai wani dattijon
Aljani ya fito daga bukkar yana sanye da dogon yar shara har kasa sam sam fuskarsa
bata nuna alamar tsufa ba ,zai yin kama da saurayi mai jini a jika
Har kasa ya zube yayi gaisuwa wajen haseena ta durkusa ta dagoshi tace "baba zaikid
nasan dai basai na maka bayanin abunda ya kawoni wajenka ba, amma duk da haka zan
sake maimaitawa, wannan shine Mijin nawa In Allah ya yarda ina so a cire masa
dukkan wani tsoro na jinsun mu kuma ka koya masa dukkan wasu dabaru da salon yaki,
nan da wata daya zan dawo na daukeshi"
Murmushi tsoho zaikid yayi "an gama ranki shi dade"
Ni dai na cika da mamaki ainun jin cewa wai ni za a cire ma tsoro sannan kuma wai
za a koya min yaki da dabarun fada
Haseena ta dubeni a lokacin da fuskarta .......

Kwana biyu kun jini shiru
Bani da lafiya ne shi isa
BUDURWAN SIRRI
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 7
.
Haseena ta dubeni a lokacin da yanayin fuskarta ya sauya , ta kankame hannuna sosai
tace" shuraih muddin muna son mu rayu har abada amatsayin mata da miji toh dolene
ka koyi wasu abubuwa na yaki, da kuma ka kuma cire tsoro a zuciyarka, ina matukar
sonka irin son da baki ba zai iya fasaltashi ba, hannu ba zai iya rubutashi ba ko
na dakika daya bana son rabuwa dakai, amma dole na na barka anan domin ka koyi
yadda zaka kare kanka daga sharrin Salman"
.
Har na budi baki zanyi magana sai ta sanya yatsanta a akan lebena alamar nayi shiru
ba musu nayi shirun duk da irin tarin tambayoyin dana ke shirin jefamata
Ta dan ja baya kadan sannan ta soma tafiya har tayi nisa idanunawana suna kanta ta
juyo muka hada idanu ta sakarmin murmushi daga haka ta cigaba da tafiyarta har ta
bacemin da gani ina nan tsaye a gun
.
Tsono zaikid ya dubeni da kyau yace "yaro shin meye sunanka"
"Shuraih" na bashi amsa batare dana kallesa ba haryanzu idanuwana na kan hanyar da
haseena ta bi
Tsoho zaikid ya sha gabana sannan ya turbune fuska yace "shuraih kake ko wa to bari
kaji Abunda kazo yi nan shi za kamai da hankalinka gareshi , domin kuwa in kai wasa
toh kana ji kana gani ta rabu da kai kenan"
Sosai hankalina ya tashi da maganganun wannan tsohon
Batare daya jira amsana ba ya juya ya shige cikin bukkarsa yana cemin" ka dai
shirya don kuwa daga gobe zamu fara atisaye "
....

Har magriba ta gabato banga alamar tsohon nan zai fito ba hakan ya sani ta shi na
kwankwasa kofan bukkar daga ciki muryan tsohon naji yace "ya akayi ne"
"Yun wa nake ji ,kuma gashi dare ya fara yi baka bani makwanci ba" na fada
Sautin dariyarsa naji alamar dariya yakeyi
"In tambayeka mana" ya fada
"Ina jinka "na bashi amsa
"A rana sau nawa kake cin abunci"
"Sau uku"
"Toh daga yau ka sanya a ranka kuma a jikinka baza ka sake cin abinci ba sai bayan
kwana daya,kuma ka sani baka da abunci sai yayan itace"
Sosai na girgiza da jin batun tsohonnan
"To shi kuma makwanci fa"
"A nan zaka runga kwana kuma ka tabbata asubar fari ka farka yanzu dai ga ruwa kayi
alwala kai sallah," ya jefo min wani batta na ruwa
Na karba nai alwala nai sallah daga nan na zube wajen durkushe duk da yanayin
wajen yana da kyau kuma ko kadan babu kwari ko wasu muggan dabbobi masu cutarwa a
cikin dajin domin kuwa tunda muka shigo dajin kawo izuwa yanzu bamuyi gamo da wani
abu mai rai ba
.
Haka na kwanta akasa kan ciyayin dajin masu tsananin laushi duk da ya kasance ina
rawar dari saboda sanyi da nake ji, bai hana bacci daukata
Ba
.
A fiirgice na farka sakamakon jin an kwara min ruwa da nayi waige waige na fara yi
don ganin mahalukin daya kwara min ruwa dan tsakurkurin tsohon ne dai a gabana ya
bata rai yana rike da wasu mayan mangala guda biyu
Ya ce"shin jiya ban sanar dakai cewa asuban farko taimaka a farke ba, shine ka
shagala har asuba ta biyu baka tashi ba"
Bai jira cewana ba ya jefo mani mangalolin nan masu dan karen nauyi da kyar na iya
cafe guda daga cikinsu
Yacigaba "maza maza ka tashi ka tafi wancan kogin yai nuni da hannunsa zuwa wani
gefe dabam, ka debo ruwa ka runga zubawa anan ya nuna mani wata katuwar rijiya
wadda tun zuwana wajen ban lura da ita ba
.
A kasale na tashi na rarumi mangalalolin na nufi inda ya nuna mani nayi tafiya mai
dan karen nisa kafin na iso bakin koramar na zauna kan daya daga cikin mangalolin
nan ina hutawa bayan nagama hutun ne na cika mangala daya da ruwa sannan na
kinkimeta da kyar da sidin goshi na dorata akaina irin nauyin danaji akaina yafi
kama da na Mota ko wani katon dutse a daddafe da kuma ikon Allah har nakai bakin
rijiyar na zuba ruwan na sake komawa rafin kai in takaice maku sai wajejen la'asar
na idda kai ashirin din daya ce na zuba, na samu waje na baje a kasa ina numfashi
sama sama alamar na jikkata naji karar budewan bukkar tsohon ya zo ya tsaya daidai
gabana sannan ya bushe da dariya yace "kai amma bil'adama da ragwanta suke yanzu
wai dan wannan aikin shine har da numfarfashi sai kace wanda yai aikin azo a gani,
maza ka mike tsaye"
A daddafe na mike tsaye don kuwa tun da nake a rayuwata ban taba yin wani aiki mai
wahala daya kai wannan ba
.
Yanzu kam da sauki tunda dai na dan rage nishin da nake tsoho zaikid ya shige cikin
bukkarsa yadan dau lokaci kafin ya fito rike da sanduna guda biyu, sandunan
dogayene sosai don kuwa sunyi tsayina biyu
Ya jefo mani guda daya duk yanda naso na cafe ta amma na gagara saboda irin saurin
zuwan da tayi sai gashi sandan ta wuce ni tamkar walkiya , ta sauka nisa dani tsoho
zaikid yayi murmushi "
Maza kaje ka daukota"
Ba musu na nufi wajen da sandar take ina zuwa na sanya hannuna da nufin na rabata
da kasa amma sai wani nauyi ya ziyarci hannuna ji nai tamkar na ina kokarin daga
katon dutsene na daddage na tara karfina har ina nishi na daga sandan daga kasa na
kafata tsaye , sai nishi nake haka na fara jan sandan a kasa har na kawota wajen
tsoho zaikid,
"Da alama wannan tayi ma nauyi toh bani ita ka amshi tawa"
Ya karfi wannan daya bani ya kuma mika mani nashi da sauri na karfa don dama ni
nasan kuskure yayi wanda ya kamata ya bani shike hannunsa , ai mugun nauyin danaji
shi yasa na saki sandar ta fadi a kasa don kuwa hartafi waccan dinma nauyi tsoho
zaikid yai kasake yana kallona kafin yace "muddin zaka runga yimasu irin wannan
daukan toh baza ka taba iya rike koda daya daga cikinsu ba"
"Yaya kake so na dauka toh"
"Kasanya a ranka cewa zaka iya , sannan kana nan ne kawai don BUDURWAN SIRRI, haka
kuma ka cire tunanin duniyarku daga ranka ka dauka tamkar a gidanka kake, sannan ka
tausasa zuciyarka, a natse zaka ji mamaki ainun don kuwa ba wannan sandan ba hatta
wancan tsaunin zaka iya yin gamo a dora maka shi"
Nai kasake ina kallonsa yayin da na kalli tsaunin daya ke nuna mani a zuciyana nace
"toh ko nine ILYA DAN MAI KARFI sai haka"
.
Na nufi sandan nayi tamkar yadda yafada na rufe idanuwana na shafi sandan da
hannuna na kama na daga cikin matukar mamaki sai naji tamkar na dau fallen takarda
don kuwa ko kadan sandan bata da nauyi yanzu na juya na dube shi yai mani murmushi
yace "shin yanzu ka yarda da magana ta"
"Shakka babu na yarda"
Daga nan ya fuskanceni yace "daga yau zamu fara darasin mu na koyan fada , da kuma
yadda zaka kare kanka,
.
Ya koyar dani abubuwa da dama a wannan rana don kuwa in ba sallah ba babu abunda
yake tsaida mu, da shike ina da saurin daukan abubuwa , har magariba tayi ya ce
mani "je kai sallah ka kwanta kuma gobe ka tabbatar kafin safiya ka gama diba
ruwanka nai godiya sannan nai wucewata izuwa inda na kwanta jiya
*******
Kwanaki suna ta wucewa tamkar yadda takarda ke zukar ruwan biro yau saura kwana
daya wata daya ta cika,
A cikin wayannan kwanakin na koyi a bubuwa da dama, dun kuwa ji nake babu wanda ba
zan iya tunkara ba yanzu batun tsoro kuwa babu ita ,
Tunda kuwa ni da kaina nake fada da manyan zakuna da kadoji kuma na kai su kar
.
Shi kansa tsoho zaikid yana mamaki ainun da saurin daukan fada na, kaman kullum
yauma muna filin koyon fadanmu ni da tsoho zaikid sai fafatawa muke in ka ganmu a
lokacin sai ka rantse wasu a bokan gaba ne domin kuwa kowannenmu burinsa shine yaga
ya cutar da dan uwansa, ni dai na dage sai kare hare haren tsoho zaikid nake wanda
shi kuma ya kufula ainun ganin sam bana kawo hari, sai da muka shafe wasu sa'o'I
kafin ya samu nasarar buguna da sanda akafa nan take kafana ta gurde amma saboda
juriya irin nawa sai na

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment