Reading Sanadin Accident by FASMA Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [8/15, 5:13 PM] A A Dboy: SANADIN ACCIDENT
🌟 *STAR WRITER'S ASS* πŸŒŸβœ¨πŸ–Š
( _Home of spΓ©cial &extraordinary writers_ )

BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM ....
Godiya ta tabbata ga Allah (SWT)me kowa me komi ..
yanda na fara rubuta littafinan Allah ka bani ikon k'areshi lafiya ...tsira da
amincin Allah su k'ara tabbata ga Annabin mu (SAW) da sahabbasa da alayensan ...
Allahouma Salli Ala Sayyidina Mohammadin was Salim...
Ban yarda wani ko wata ya canza min littafina ba inhar bada izinina ba dan kotuce
zata rabani da shi dan haka akiyayeπŸ™

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

Ina mik'a gaisuwata ga yan kungiyar mu *STAR Writer's Ass ..* Allah ya k'ara had'a
kanmu.love you All❀

01__02

Tafe take tana rusa kuka kamar wanda aka ce parent d'inta sun rasu ..hannunta d'aya
ta kare fuskarta da shi d'ayan hannun kuwa tana rike da wani fashen2 tulu koda na
matso kusa da ita na k'are mata kallo senaga yarinyace qarama fara wacce baza tafi
11ans(11years)duda karanci shekarunta aman bai hana kyan ta fitowa ba tanada
hancinta zarot ..bakinta dan madedeci pink ga magana masha Allah amma fa kayan
jikintaa dakon2 dasu bakyan gani duk sun kod'e sun cicire ...riga da zanen da
d'an kwalin duk daban2 tayi daurin nan irin namu na yan kauye wato ta zaro jelar
dan kwalin ta gaban rigarta .....ganin irin shigar yasa nayi zaton tallaka wane
amma me..😳 ganin gidan data take shirin shiga yasa nayi mamaki dan kaf kauyen
manga gidan daya kaishi ba dan shafe da sumunti gidan yake kuma an kewayeshi da
katanga sab'anin sauran gidajen da kusan duka buka ne...

Ta jima tsaye baki kofar gidan ta kasa shiga se tayi kamar zata shiga se kuma ta
dawo baya tayi haka yafi sau ukku daga karshe tayi shahada ta shige ganin haka
nima na mara mata baya ..

Wata bakar mata nagani zaune bisa kujerar nan tayani tsegumi se girgiza kafa take
tayi d'aurin d'an kwali ture kaga tsiyar nan ..

D'an nesa da ita yarinyar nan naga ta durkusa se kame2 take ta kasa magana ga
hawaye na tsiyaya bisa ''joue''(cheek) d'inta ...

Matar ta kalleta tace wai miyene kin wanizo kin sani gaba kamar ni d'in bakuwar
ganin kice.....ina kuma ruwa dakikaje d'iba ne eee ta fad'i cikin tsawa..

Seda ta firgita yarinyar har tayi baya ta fad'i ragwaf baki na karkarwa tace kiyi
hakuri Inna Murza wly mun d'ebo ruwan nida su Ma'u kawai sega su Murtala sunzo fice
wa gani suna gigin tseda mu ne . da muka ki tsayawa se kawai suka biyo a guje ina
cikin gudu nayi tuntub'e nafad'i tulun ya fashe kuma ma harda ciwo naji ta bud'e
gwiwarta idan taji ciwon..tana nuna mata

A maimakon taji tausayi yarinyar se wani uban ashar ta abka tace yoni ina ruwana
dajin ciwonki .kuma kice de kin tafi wajen karuwan cin ki da samarinki de.. walahi
baki isa tulun nawa zafi fasa sanan wani bani hakuri ... to walahi se kin biyani ko
jikin ki ya fanshe ki yanzu nan dan bazan dauki asara ba....
Cigaba da kukan take tana bata hakuri amma ina Murza ita neman ma bugi
take ..muciya naga ta d'auko tayi kanta .nanfa ta dinga jibgar yarinyar tun kana
jin ihun ta har muryar ta dishe bata barta ba seda ta sumar da ita tayi jifa da
muciyar taja kafafun yarintar takaita tsakiyar rana tayi shigewarta daki se mita da
zagin yarinyar take ...

Ba'ita ta farka ba se wajejan karfe biyu na rana shima sakamakon ruwan da Inna
Murza ta sheka mata...firgit ta tashi se wuki2 da ido take ....

Murza tace shegiya mai kama da aljana tashi ki fice kiwo sauran inkin tafi ki tsaya
yawon karuwancin naki dakika saba ...

sum2 ta d'au buta ta nufi rijiyar cikin gidan da niyar yin alwala tayi
sallah ..ashe ma akwai rijiya cikin gidan dan tsabar mugunta irin na Inna Murza
tace baza'a ja ruwan ba sede taje can cikin rijiyar garin ta d'auko mata..

Wata tsawa ta daka mata tace ke kina hauka ne uwar mi zakiyi min da butana iye..

Cike da tsoro tace Inna alwala zanyi inyi salla..

Shewa tayi tace gaji ladaniya to kokece tabarmar massalaci wacce kullum acikin
mosque d'in take baza kiyi sallar ba kamar wacce tafi kowa addini .....maza aje ki
fice..

Tace inna to bari nayi fitsari sena tafi ...

Shiga kiyishi hakanan base kin kama ruwan ban ...shasha kawai ..

Fitsarin da batayiba tace Inna abincina fa yunwa ake ji...

Iye i lalle wuyanki yayi kwari kai tsaye tace to ban dafa dake ba

Zata yi magana Murza tace.MAYSAM MAYSAM dige ki fita a idona in rufe tau..tayi
shigewarta d'aki

Bayanda MAYSAM d'in ta'iya dole ta d'au sandar kiwon ta kora shanun ta
fice....Allah yaso ta cikin shanun akwai masu shayar wa bayan taje idan take kiwon
se ta tatsi nonon tasha ta gama.cikin ta dan dama kullum hakace take faruwa idan
anbata abincin safe tofa da ranan batada kwanon tuwo idan kuwa bata bata na safe ba
to zata bata d'an tsakure da rana...
Bayan tagama sha tayi alwala tayi sallah
Wanan kenan...

Fasma ce✍
Wannan littafin daya daga cikin member din Page din nan ce duk comment din da kuka
yi xata na gani in ma gyara kuka mata xata dauka
[8/15, 5:15 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š
[8/15, 5:27 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

03__04

```An karbo daga Anas dan maalik R A yace: Manzon Allah( S A W) yace''dukkan d'an
adam mai kuskure ne,mafi alkhairin masu kuskure sune wad'anda suke tuba(idan sun
aikata kuskuren kuma bazasu sake komawa ba)''
``

Bayan ta gama sallar nan ta zauna tana tunani rayuwarta ita bata san miyasa innarta
bata sonta batason dommi yasa ta tsaneta ba ...kullum da iri cin zarafin data ke
yimata sab'anin kowace UWA da take nunawa d'anta so da tattali ...ga kuma kalmar da
take tsaya mata cikin brain wato Karuwa '' tarasa mi kalmar take nufi so tari Murza
zatayi ta kiranta da sunan kuma ba damar tabbayarta ....tana nan har aka kira
sallar Asr ,,,bayan tayi sallah ta d'an ringesa kafin a d'an jima ta koma
gida...abunka da wanda ta gaji ga wahala da yunwa se kawai bacci me zurfi yayi awon
gaba da ita ...ba'ita ta farka ba se gab da magarib ,,,da sauri ta tashi ta kora
shanun ta kama hanyar gida tana addu'ar Allah yasa baba MUSA ya dawo ...

Tun daga nesa ta hango Murza a bakin kofar gida tana dube2 da alama jiran isowarta
take ,,,..
Dafe kirji tayi tace na shiga Ukku ni MAYSAM yanzu kuma ko wace azaba Murza zatayi
mun..Murza na hangota ta juya cikin gida ...

nan Maysam ta fara karkarwa tana matsar kollah ...

Bayan ta d'aure shanun ta shiga gidan ai kuwa tun a bakin zaure taji saukar dorina
a jikinta seda ta gantsare ta zube nan ta kama qafar ta tana bata hakuri .....

Hankad'ata tayi da qafa ta dinga zabga mata dorina tana fadin kaji shegiyar yarinya
kina son d'auko muna magana a gari wato kiwon ma se kin tsaya wurin
karuwanciki.....

Fad'i take wly inna ba'inda natafi bacci ne kwashe ni.....

Iye dan ubanki har kika samu lokacin bacci keda kika tafi kiwo kenan kice hakan
kika bar min dabbobi da kishi dan bakin ciki ko....

Tace a'a inna wly ...
Bata bari ta qarasa ba tayi ball da ita wani kara ta saki segata wanwas ta suma a
wurin dama sauran yanwa ga duka ai abin yayi yawa(gaskiya na tausaya miki Maysam
😭)...
Ana kiran isha'i ta kuma shekamata ruwa a firgice ta tashi se kuma ta saki wani
kuka me cin rai ...

Amaimakon taji tausayin ta se kawai naga tana kasa gyad'arta tana qirgawa .bayan ta
gama tace idan kin gama kukan munafuncin se kizo ki tafi dandanli kuma wly b'atan
daya kikayi jikinki ze fanshe ki..

Ta goge hawayen tace dan Allah ki temakamun da abinci yunwa nakeji ...

Kamar baza tace wani abuba se kuma tace ga zazafen safe can ki d'auka kice ..

Hannu baka hannu kwarya take loma dan ba wani yawane dashi ba amman de ta done wasu
kofofi cikin...ta d'au tiren tallar ta fita......

Wajejen goma na dare aka tashi a dandali ..itada kawarta Ma'u suka rako dayake
makota ne a hanya tace dan Allah Ma'u ina sonyi miki wata tambayya....

Ma'u tace ina jikin Allah yasa na sani....

Maysam tace wai mi kalmar karuwa ke nufi?

Waro ido Ma'u tayi dayake ta d'an girmeta kad'an tace kada ki bari wani a kauyen
nan yaji wannan kalmar a bakin ki ...
Miyasa don ni sunan da innata ta lakaba min kenan...

Ma'u tasa hannuta ta rufe mata baki tace kul kada kibari wani ya san da maganar nan
dan karuwa na nufin macen data bada kanta ga maza saboda kud'i wato ta meda yin
Zina sana'arta ...ita kuwa zina anyi hani dayinta ga dukka musulmi mumuni dan ko
kasanci da ita an hanemu bare yinta .......

Gyad'a kanta kawai tayi amma badan tagane duka abunda Ma'un ta fad'imata
ba ...ganin Ma'u ta shiga yanayin damuwa yasan itama tashiga koda bata gane ma'anar
kalmar ba amman tasan ba abu ne me kyau ake nufi da ita.....

Bawanda ya sake cewa komi har suka zo kofar gida Ma'u ta kalli Maysam cike da
tausayawa kawartata tace kiyi hakuri da abunda Murza take mike wata rana se
labari...nan sukayi sallama kawa ta fice gidansu....

Zaune ta tarar da Murza nan ta biqa mata kud'in da ragowar gyadar...seda ta lissafa
yafi sau ukku wai ko zataga b'ata amma taga sun cika cif2 ...ta harareta tare da
yi mata rankwashi a ka tace Allah ya soki da kinci na jaki....

Sum2 ta d'au buta tayi alwala ta shige wata yar bukka kusa da kitchen da alama
store ne dan ga kayan miya nan a ciki ..tattare wuri tayi ta kabarta sallah bayan
ta gama ta b'ingire nan bacci ya kwasheta.....

Kiran sallar farko akunnenta akayishi ta tashi ta sand'a tayi alwala ta koma
bukkarta tayi sallah...ta salamce kena. Murza ta shiga kwalla mata kira ko azkar na
safiyar bata samu damar yi ba ta fito a guje ta durkusa gaban ta tace ina kwana
Inna ..

Ya tsine fuska tayi tace da ban kwanaba kya ganin ..ni ba wannan na kira kiyi mun
ba maza 2 d'au tulu ki tafi rijiyar cikin gari ki d'auko ruwa sauran ki tsaya yin
abunda kika saba....

Tulu da guga ta d'auka amma me har ta kai kofa Murza tace dawo aje mun gugar inki
tafi can wani ya baki ki d'iba..
Haka ta fita a ranta tace da rijiya a gida amma ace se an tafi wani wuri d'aukan
ruwa ..dan kawai wai kada ruwan rijiyar ya kare...ko a ina ruwan rijiya ya tab'a
qafewa.....
Bata dawo gidan ba se bakwai ...

Murza ta kalleta tace issashiya se yanzu kika gama tumb'elen ki ko nan da cikin
gari ma sekinyi halin....

Batade ce komi ba ta sauye ruwan ta fara kiciniyar d'aura koko a ranta tace waye
ze tafi daukar ruwa da asubar fari kuma kinsan da hakan kika hanani d'aukan
goga ...bayan ta gama ta d'umama tuwo sannan ta share tsakar gidan tas ta had'a
kayan wanke2 tayi...

Ta zauna zaman jiran a bata kari amma Murza yi tayi ya bata san da halita a wurin
ba ta bud'e baki da niyar yin masifa ta tsinkayi sallamar Malam Musa d'up tayi
shiru ta fara washe baki tana laale Malam sannu da zuwa...

Da gudu Maysam ta rumgume shi tace sannu da zuwa Abba.....
Rumgume ta yayi shima ya shafa kanta yace yawwa yar Abba da fatan na same ku lafiya
..e tace ya jawo ta suka zauna bisa tabarma yace yar Abba mike damunki naga kinyi
wani irin a kwana biyunan da bana nan....
Kasa magana tayi se hawaye da take gogewa ...
Hankalinshi ya tashi yace yar Abba kiyi mini magana mana ...

Karaf Murza tace ayya ai rashin lafiya tayi massasara ke damunta ...jiyan nan na
kaita chemist aka bata magani gashi bata son cin abinci ko kad'an har balangon nake
sayo mata amman bata iyaci se na matsa mata....ga jikinta wuni take da zazzab'i
bata son ruwa ko kad'an ya tab'ata.shiyasa kaga jikinta da d'an datti...kuma kasan
marar lfy ba'a matsa mishi diyawa seda lallab'a ...yanzu haka dramar setayi break
ne muke nayi2 takici .....

Maysam batayi wani mamaki ba dan inda sabo ta saba da makircin Murza tayi fiye da
hakama ...

Malam Musa yace wayoo yar Abba ashe baki ji dad'i ba to Allah sawwake ya baki lfy..

Ameen tace da farar'arta dan ko ba komi zatayi hutun masifar Murza Kwana biyu...
Suna had'a ido Murza ta buga mata harara ...ta sadda kanta a ranta tace sede harara
dan yau ba wunin yunwa bare zuwa talla da kiwo...

Nan ya bude tsarabar daya kawo musu fruits iri2 nan Maysam ta bud'e sauran qofofin
cikinta ta dinga ci ba kyakyautawa...seda taji ba wuri tukon ta sarara...ga wasu
d'inki atamfa daya basu kala uku2 ,,,.nan ta ja ruwa a rijiya ta feso wankanta
wanda rabonta dashi tun bayan tafiyar Abbanta ..tasa kayanta ta fito tsaf da
ita .Murza kamar ta had'e rai dan takaici ...

Abinci rana ta d'aura musu abbanta na gefe se fira suke abunsu gwanin ban
sha'awa...dan kuttu Murza kasa zaman wurin tayi ta koma d'aki ..haka tayi musu
lunch tare sukaci ..

A kwana biyun nan da Abba ya dawo har wata yar kiba da haske ta qara dama gata da
tsapta masifar Murza ce ke sata zama da daud'a dan kuwa batada incin saka kaya masu
kyau inde har Malam Musa baya nan...
.
Tofa kuji makirci irin na Murza... ..

Love you all my fans ❀

Fasma ce✍
Ahmed Gumel
[8/15, 5:27 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š
[8/17, 1:08 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

05__06
```Daga Abdullahi dan Umar Allah ya yarda da shi yace:Manzon Allah (S A W)
yace''mutum bazai gushe ba yana tambayar muta ne(roqo) har sai yazo ranar qiyama
fuskarsa babu tsoka d'aya ta nama
,ruwayar Bukhari da Muslim ce_
```
Washe gari Maysam cike da farin ciki ta tashi tayi shirinta na zuwa school tasa
uniform d'inta ta fito tsaf da ita ...nan tsakar gida ta tarar da inna Murza da
kuma malam Musa suna breakfast ta zauna itama ta gama cikinta lokacin da zata tafi
Malam ya dari biyu na break ....ta ansa tanata godiya ...
Wani kallo Murza tayi mata sena ga ta gyad'a mata kai ta fice a gidan ...(ko kallon
miyake nufi oho)
Haka Murza tayi wunin aiki a ranar se tsaki da gungunai take ...
Ita kuwa Maysam a school d'inma principal hanata shiga aji yayi dan cewa yayi seta
zo da parent d'inta yaji mike hanata zowa akai2 ...
Da kyar ta samu ta shawo kanshi tana kuka ta d'an fad'i mishi abubuwa kad'an daga
rayuwarta ....
Nan ya tausaya mata tare alkawari tallafa mata tasamu ta gama primary tunda ma
yarinyar Allah yayita da kaifin ilimi dan danan ta haddace duk abunda aka koya
mata....
Qarfe biyu na rana suka sauko ta dawo gida Allah ya temaketa Malam yana gida nan ta
shari girkin lunch ...qarfe hudu kuma ta tafi islamiyya ....
Malam na fita sallar magrib Maysam na zaune tana biya karatunta se jin rankwashi
aka tayi ...koba'a fad'a ba tasan inna ce ...tana d'ago idonta kuwa taga Murza se
wani fuci take ta biko mata hannu tace ban ...
dari biyu naga Maysam ta fitar daga bag d'inta ta bata ...
Warcewa tayi tasake yi mata wani rankwashin tace nazata baki ganeba dana ganar dake
yanzu munafuka kawai ..
Itade ko A batace ba ta meda hankalinta kan abinda takeyi...a ranta kuwa kukan zuci
take ace kud'in break d'inma se an anshe ...
Bayan kwana biyar Malam Musa yayi shirin tafiya dayake kasuwoyin kauyika ya keci
shiya sama be cika zama a gida ba...
Kuka kuwa harda na banza Maysam tayi dan tasan tayi bye2 da jin dadi har seya
dawo ..
Nan ya rungumeta yana lallashi yace yar Abba kukan nan ya isa haka ...
Murza se wani washe baki take tace ai kasan bata san rabuwa da kaine ...
Maysam aranta tace dole inyi kuka dan nasan lokacin azabata da cin zarafi yayi..
Kudi ya fiddo ya bawa Murza sanna ya bawa Maysam kudin school dinta ..
Ya tafi ya barsu nan Maysam na ta d'aga mishi hannu...
Shigowar su keda wuya Murza tace munafuka annamimiya .. Kwace kud'in tayi tace
tundade ba school din zaki ba ..aiki ya dawo sabo..
Haka rayuwa tayi ta tafiya kulum da irin sabuwar muguntar da inna Murza take fito
mata dashi ..yau har zasu zana jarabawa shiga secondary Allah yasota Musa na gida
dan haka bata samu wata matsalaba ...bayan yan watanni resulta kuwa na fitowa Allah
ya temaketa taci fad'ar irin murnar datayi b'ata time ne ....
Inna Murza na gefe se wani murmushi mugunta takeyi a ranta tace e kuma kin gama
school daga haka..wannan d' inma dayaya na bari balle har na bari kishiga secondary
ee bazama ta sab'u ba....
Bayan kwana biyu da faruwar hakan suna zaune bayan sun gama abincin dare Murza tace
Malam dama ina son yimaka wata maganace game da karatun Maysam amma ina tsoron kace
nayi mata shishigi..
Malam yace haba Murza wani irin shishigi keda y'arki ki fad'i kawai ina
sauraronki..
Dam gaban Maysam ya bada ta kasa kunne tana jiran jin mi zata fad'i
Kalar tausayi tayi tace dama cewa nayi be kamata taci gaba da karatunta ba dan kaga
a al'adar garin nan yan mata basayin makaranta gabada primary kuma ka sani kowacce
a d'akin mijinta take jinin farko (menstrue)dan abun kunya da tsangwama ne idan har
yarinya ta farashi a gida..
Gaban Maysam cigaba da fat3 yayi tana jiran taji mi Malam ze fad'i..
D'an jim yayi yace nikaina abunda nake dubawa kenan dan d'azun nan Mai gari damuka
gama yin sallah bayan yayi min barka nasararta se kuma yace d'anshi Murtala yaga
y'ar wurina kuma yana so ..na de cemishi zanyi shawara da iyalina tukon..yakike
gani kenan
Wasu sirarrun hawayene suka zubowa Maysam tayi sauri ta gogesu a ranta tace aure
kuma..
Wani malolon bakin ciki ya tokare mata wuya aman seta cije tace kawai ka bashi
tunda Mai garin da kanshi ya nema kaga be dace ba ka hana d'anshi ko...ta kuma cewa
kaga jiya2 nan aka saka ranar qawarta Ma'u ..a ranta kuwa cewa tayi yanzu de
matsalar cigaban karatunta ce a gabana tunda nayi nasara daga baya kuma sena ji da
auren dan walahi bazan barta ta aurin d'an me gari ba .
Malam yace shikena Allah ya zab'a mafi alheri...
Kasa2 Murza tace ba Ameen ba..
Ya kalli Maysam yace y'ar Abba kinji duka abunda mukace in har bakya son Murtalan
ki fad'an bazan miki dole ba..
Kanta a kasa tace Abba zab'inku shine nawa kuma ai dama Uwaye ya dace su zab'awa
yar su budurwa miji .. Allah yayimana zab'i mafi alheri
Ameen y'ar Abba hakika ina alfahari dake Allah yayi miki albarka ..
Ameen tace ta shige d'aki dan wani kuka yazo mata..a ranta tace yanzu a rasa wanda
za'a had'ani dashi se marar mutunci nan meyiwa y'ay'an mutane fyad'e ..ta d'aga
hannu sama tace Allah gani gareka kayi mini zab'i na alheri ..tana kuka ta
shafa ..nan bacci ya kwasheta....
Tofa fans anya Murza zata bari ayi auren nan kuwa?
Ina sonku masoyana irin dayawan nan
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:08 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP
08064400100_ πŸ“šπŸ“š
[8/17, 1:10 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* πŸ’₯πŸš‘πŸŒΉπŸŒΉ

πŸ‡³πŸ‡ͺStory&Written
by
*FASMA* πŸ‡³πŸ‡ͺ

07__08
```Mazon Allah (SAW) yace''lallai mamaci anayi masa azaba saboda kukan masu rai''
Ruwayar Bukhari da Muslim ce```
Washe gari da matse nanci ciwo kai ta tashi saboda kikan datayi dayake babu school
tayi shara da wanke2 gidan tana kiciniyar d'ora break Malam da Murza suka fito da
alama tafiyar kasuwancin shi zashi bata san lokacin da hawaye suka zubo mata a
ranta tace yau kuma ko wata azabar zansha ....nan ya bawa Murza kud'in cefane ita
kuwa Maysam dari biyar ya bata tunda yanzu ba school ..ko fita daga gidan beyiba
Inna Murza ta kwace kud'i tayi shigewarta d'aki ashe Malam Musa ya gani dan yayi
mantuwa ya dawo ....bece komi ba ya d'auki abunda ya manta ya sake yiwa Murza
sallama sekuma yace Maysam ta biyoshi ze aiketa wani gu......Murza bata kawo komi a
ranta ba..
Bayan sun fita ya kalleta yace yar Abba ki zanki hakuri da Innarki wata rana se
labari ki qara hakuri da ita kinji ko...ina sane daduk abunda take miki dan qawarki
Ma'u tana sanar dani komi yayi zafi maganinshi Allah dan baze yuyu na dinga tafiya
dakene ba ..
Wani hawaye taji ya zubo mata magana ma kasayi tayi se gyad'a kai kawai ta
iya'yi ...
Share mata hawayen yayi ya rumgumeta yana lallashi har ta fasa kukan ..ya ciro dubu
biyu ya bata yace ki sayi duk abunda kike so kada ki bari innarki ta gani bare har
ta kwace miki kinji kuma daga yanzu zan ringa baki kud'in da zakina kashewa ...
To tace Abba na gode Allah ya kara bud'i ya bada sa'ar abunda aka tafi nema...
Sosai yaji dadi addu'ar yace ameen yar Abba Allah ya albarkaci rayuwarki....
Ameen tace ..
Nan ya tafi ya barta tana d'aga mishi hannu har ya bace ganinta...a bakin zaninta
ta kulle kudin ta koma gida...
Tana shiga taga inna da tulu a hannunta tasan mi hakan yake nufi dan haka da duka
da niyar karb'ar tulun ai kuwa ta daka mata duddu tace shegiya annamimiya har da
wani kukan munafurci dan Malan yayi zaton ina cin zarafin ki in bayanan ko.....
Itade batace mata komi ba ..
Dungura mata tulun tayi tace saura kitsaya inda kika saba tsayawa .....
Biyawa Ma'u tayi sukatafi tare ..a hanyarsu ta dawo ne suka gamu da Murtala shida
abokanan shashacin shi....
Nan suka taresu har sun tatare zanin su zasu arce Murtala yace wly in kuka gudu kun
jawowa kanku ..cak suka tsaya ...
Ya matso daf da Maysam yace matana ya kike ...kin san banso kina daukan ruwan nan
bara natayaki ..yayi niyar sauke tulu daga kanta nan taja baya da sauri ..ma'u tace
wai miye hakane kun wanizo kun tsare mu a hanya har kana wani kiranta da matarka
kota ina ma...
Daka mata tsawa yayi yace ke kuwa asuwa ...kinci darajar kece yarinyar da abokina
ze aura wly da yanzu na keta miki haddi...tsit kake ji Ma'u tayi...
Suka kwashe da wata arniyar dariya ya sake matsowa daf da Maysam wadda ita alokacin
tuni hawaye keta zuba....yace haba tawan nan yasa hannu ya share mata hawaye se
kuma yayi niyar rumgumeta wai azuwan lallashi ..
Efa nan ake yinta nan kokowa ta barke har rigarta ta cire daga gefen ai bata san
lokacin da yarda tulun anan ta arce a 60.....zasu mara mata baya Murtala yace a'a
ku barta ku muje idan zamu kawai ....
Seda ta isa kofar gidan su tukon ta tsaya duk jikinta karkarwa yake ...se kuma ta
sake fashewa da kuka ...ga abunda Murtala yaso yimata ga kuma tulun Inna ya fashe
wanda jiya2 nan ta sayeshi ta jima nan tsaya sannan ta shiga gidan se rarab'ewa
take..
Inna na ganinta ba tulu tayi dariyar mugunta dan ta fad'i gassasa yau....
Game hanunta tayi tace dan Allah inna kada ki dokeni walahi su Murtala ne nan ta
kwashe yanda sukayi ta fad'i mata..
Wani ashar tayi ta rarumo icce ta fara buga mata tace kicede yau asirinku ya tunu
keda shii wurin gudu kika barar mun da tulun ga sheda nan harda cirewar
riga ..dukan ta take baji ba gani ai kuwa dubu biyun da Malan ya bata ta fad'i kasa
..
Salati Murza ta shiga yi tace munafuka asirinki ya tunu ashe karuwancin naki me
degree ne harda dubu biyu ...nan ta dauke kudin ..ta d'ago fuskarta za zazzabga
mata mari ta kuma sa hannun a kwalmin idon ta dunga kyarkyarta saman idon har seda
taga jini yana fita tace shegiya me kama da mayu wata ran sena fidda miki idon nan
kowama ya huta ..sanan ta cigaba da duka har seda taga bata motsi tajata ta yar a
tsayar rana..lokacin kiwo nayi ta sheka mata ruwa ta tashi tace maza tashi ki fice
kiwo..
Tasan kotace zatayi sallah baza ta barta ba setace Inna abincin nafa?
Abinci fa ai kedashi se gobe kuma tunda yau kinyi kari ...
Haka ta fita gwani ban tausayi...
Haka rayuwa tayi ta tafiya wanda kullum se Murza ta caje Maysam inde harta
fita ...ga kuma takurar da Murtala ke mata kullum inde sa had'u to seya nemi tab'a
jikinta...shiyasama bayan anyi auren Ma'u ta sati ta gayawa Malan itama gwara asaka
nata auren dan saboda tsaro..
Haka kuwa akayi nan aka saka ranar goma ga sabon wata kenan nanda kwana goma...
Iya tashin hankali Murza tashiga dan ga dukka alamu auren nan ba fashi gashi kuma
da gani yarinyar zata huta idan ta auri d'an megari tunda ko kayen lefenta ya

Please Login or Register in order to submit comment