Reading Me and My Lion Part 5 by Autar Alheri Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng *🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹




Special and romantic love story 💋💓🫣



Writer by Autar Alheri ✍️




🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁

🌹🌹

🦁




Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭

Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze
cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️na haƙiƙa 💯




Book five
Chapter 81 & 82




"A perking space tasameshi yana magana da Captain sahib, tana Zuwa tashige jikinshi tahanyar kwanciya
saman ƙirjinshi tasaƙalo hanninshi, juyowa yayi yashafa kanta tare da dage mata gira ɗaya, aiko tasaki
murmushi tana ƙara shugewa jikinshi. Bece komaiba se umurnin dayabawa Captain sahib ɗin akan
abinda yasakashi kana yaja hannunta yasaka mota, Shima ya shiga mazaunin driver yaja sukabar gidan su
kaɗai batareda yaranshi ba....da kallon Captain sahib yabi motar harta ɓacewa ganinshi. Dafashi yaji anyi
koda yajuya yaga captain Usman ne ke masa dariya cikin barikanci yace "Captain yadai? Wannan
kallonfa? Ko baka taɓa ganin oga yayi driving bane? Humm, yasauke nunfashi kafin yace "bahaka bane
Usman kawai ina mamakin yadda akayi wannan abin wai dama ashe wannan yayinyar ƙanwar oga ce
Basu saniba daga ita harshi, kodai kawai basarwa ne oga yayi awancan lokacin? Domin nakasa manta
diramar da aka yi da ita a suleja. "Wlh ƙanwarshi ce Shima alokacin ganetaba shine yakawo wannan
damuwar kuma ai bama ita ƙanwaba matarshifa, cewar Captain Usman..ido Captain sahib yawaro cikin
mugun mamaki yace "matarshi dai yoshe suka yi Aurento? "Hum nimadai bansaniba amma Hakan Auta
fa'iz yagayamin. "Tab ɗijam kace madam ce gaskedai naga wannan shigewar datakeyiwa oga tayi yawa
kuma Shima yana biyeta, amma fa kam wannan rayuwa oga ƙarama sedai yayi renonta..dariya captain
Usman yayi cikin neman magana yaceto bara idan yazo katambeshi se muji..Duka Captain sahib yakai
masa cikin sauri yagoce yana dariya.



Tunda suka ɗauki hanya take maƙale ajikinshi tamkar wata mage, har suka ƙarasa school ɗin, "uhnm my
lion ni kabari riganka natafi dashi ciki. "Riga kuma my lushaa? Yatambaya yanaɗan waro manyan
idanuwanshi. "Eh mana ai idan katafi bazan ƙarajin ƙamshin jikinkaba shine nakeso kabani ita kaji,
tafaɗa cikeda taɓara...shiru yayi yana kallonta cike da nazari amma sam yakasa fahimtar komai, Hakan
yasa ya shiga cire rigar aikinshi kawai domin yabata yahuta, dama ƙananun kayane ajikinshi. "Nidai ba
wannan ba tacikin nakeso.."oh ya rabbi, kafin ya ajiye tasaman ya cire mata wadda yatakeso yabata..baki
tawashe bayan ta ƙarbi rigar ta rungumeta cikeda ɗauki tamkar shita runguma, tana lumshe lulu ayes
ɗinta, kafin tabuɗe tare da sakin murmushi tana faɗar "karka Daɗe please lion kaji..martanin murmushin
yamaida wata wanda yakusan zautarda ita, kafin jinjina kanshi alamar baze daɗeba kamar yadda
tace..ajiyar zuciya ta sauke kafin tabuɗe motar tafice shi kuma yatada motar zebar wurin amma hangota
tsaye tana kallonshi bata wuceba yasakashi tsayawa tare da juyowa ya dawo kusanta, glass ɗin motar
yasaukar Sekuma yaga duk Hakan bemishiba kawai Seya ɓalle marfin yafito cikin takonshi na ƙaƙƙafan
namiji kuma me class yanufeta. "What's happened my bigger sweet umm? "Nothing, tafaɗa tana ƙaƙaro
murmushi..ido yazuba mata nayan daƙiƙu kamin yasaka hannu yana janyota jikinshi. Aiko kamar jira
takeyi ka ƙwaƙumeshi sosai tana sauke nunfashi. Shima lumshe rikitattun idanuwanshi yayi yana shafa
bayanta kusan minti biyu suna Hakan mutane se kallonsu sukeyi ciki da birgewa domin dayawa kallon
yaya na ƙanwa yake musu.."please kije kisamu lecture ɗinki kinji dakin gama zanzo mukoma gida nabaki
babynki fara kinaso ko? Cikin sauri ta shiga daga Mishi kanta tana murmushi domin har wani yarr taji
ajikinta. Shima murmushin yayi yana ɗage gira ɗaya tare lumshe idonshi yaƙara buɗewa yana tsotsar red
lips ɗinshi yace "itama harta buƙaci ganinki my lushh kinji yadda take nemanki ko? Yafaɗa yana wani
taune lips ɗinshi...Dariya failusha tasaka kana tace Allah my lion Ina mugun san naga. Sekuma tayi
shiru."uhm hum kigame? Yatambaya cikeda kulawa.. murmushi taƙara saki kana tace "aa bara seka
dawo Sena gayama bye tafaɗa tana manna Mishi Kiss a ƙirji domin yayi mata tsayi sosai, tare da juyawa
cikin sauri tabi hanyar hold ɗinsu.. murmushin gefen baki shattima yayi yana shafa kwantacciyar sumar
fuskarshi kafin yajuya ya shiga motarshi yabar makarantar.




Su failusha kan Basu fitiba se ƙarfe 11, suna fitowa suka samu wani wuri suka zauna inda ba haya niya
itada wasu ƴammata, domin ita sam dudda iskar dake kaɗawa warinta takeji shi yasa ta toshe hancinta
da rigar lion ɗinta tana shaƙa sedai sam batayi mata yadda takesoba domin tafijin daɗin ƙamshin ajikin
lion ɗinta, Sunan zaune suna jiran 12 tayi suƙara shiga, kawai setaga motoci kiɗan uku sunyi perking
agabansu. Sojan dake cikine ya fito zuwa gabanta yatsaya kafin yace "assalamualaikum madam oga yace
kizo. Ahankali Failusha taɗago ta dubeshi Sekuma ta kalli motocin dudda cewer sune na lieutenant
musayyeer amma babu wadda yake hawa acikinsu, sedai kuma ɗaukin ganinshi yahanata bawa tunanin
mahimmanci Hakan yasa tamiƙe kawai tanufi motar da aka buɗe mata. Tabaya ta shiga kafin tarufe
motar tajiyo domin taga lion ɗinta, amma me tana jiyowa ana fesa mata wani abun afuska, kafin tayi
wani yunƙurin kawai tabaje awurin somammiya. Su kuwa suka ja motocinsu sukabar makarantar.



Misalin ƙarfe 1:00pm motar lieutenant musayyeer tashigo school ɗin, bayan yayi perking ya fiddo
wayarshi yana kiranta amma bata shiga wayar akashe, sosai yayi mamaki domin tun lokacinda yabata
waya bata taɓa kashe wayarta ba koda kuwa batada lpy ne seyanzu datasan ze lirata idan yazo zata
kashe? Yatambayi kanshi. Kafin yarife motar kawai yanufi office ɗin shugaban makarantar. Bayan sun
gaisa yace masa yanaso akira masa ƙanwarsa ne, sunanta Failusha ma'arub shattima. "To shikenan
ƴallaɓai bari anemota level nawa take ne? "1 tana karantar gynecologist ne? "To shikenan yanzu zatazo
in sha Allah cewar shugaban makarantar yana ficewa daga office ɗin...kusan minti 20 segashi yanadawo
yana faɗar "sorry ƴallaɓai nabarka kana jira wlh ƙawayenta sunce tun 11 tabar makarantarnan domin
wasu sojojine sukazo ɗaukarta..wata irin ɗagowa lieutenant musayyeer yayi yana kallon shugaban
makarantar arazane jin ance sojoji sukazo ɗaukarta to suwaye? Yatambayi kanshi kafin yace "soldiers
kuma? To waye keda zarrar yimin wannan kutsen? General Mutallab ne kawai ze iya Hakan ya shiga cikin
lamarin ahalina batarefa saniba kuma da kyakkyawar manufa. Yaƙara bawa kanshi wannan amsar kafin
yazaro wayarshi kawai ya shiga Kiran Mami, domin inda ace wani kawai akace ya ɗauke ta bazu tada
hankalinshiba domin ya san duka ƙanenshi zasu iya zuwa ɗaukarta koda besaniba amma sojoji to da
wacce manufar. Yana cikin wannan tunanin yaji Mami ta ɗaga wayar, beko bari tayi magana bana yace
"Mami lusha tadawo gida? "A'a babana batare kuka fitaba..ƙit ya kashe wayar Dr Noor yakirs yatambeshi
ko shine ya ɗaukota daga school ɗin, Shima Noor yace bashi bane, Hakama fawan maheer auta fa'iz
kowanne Seda yakira amma suna sheda masa Basu suka ɗauketa ba. Tashin hankali kenan wanda ba'a
saka Mishi rana wata irin zabura yayi tare da fatali da tebble ɗin dake gaban shugaban makarantar yana
faɗar "no impossible wlh waye yakeda wannan ƙarfin guywar na ɗaukarmin mata batareda saniba? Da
wacce manufar aka ɗauke ta sata? No no matar lieutenant musayyeer mahabub shattima tafi ƙarfin sata
wlh kai kan ahalin shattima sunfiƙarfin sata wlh Balle ƙanwata kuma matata nooo, yafaɗa da azabar ƙarfi
yana naushin iska. Atake jikin shugaban makarantar ya ɗauki karkarwa cikin mugun tsoro da rashin
hankali aranshi se famar addu'a yake yi duk wadda tazo bakinshi ganin yadda wannan gafjejen sojan
yabirkice musu lokaci ɗaya. Atake aka cika office ɗin shugaban makarantar da duka malamai ana jimami.
Dalibai kuwa duk sunacan basusan Mike faruwa ba se tsiraru daga cikinsu. Wata waya yazaro daga cikin
aljihun wandonshi yar ƙarama domin bata ita yake anfaniba, kunnata yayi ta ɗauki ƙara kafin ya maidata
aljihun wandonshi, aiko ba afi minti 3 ba da kunnata sukaji jiniyar manyan motocin sojojin Iran irinna
yaƙi Ɗinnan takaraɗe ilahirin makarantar, kafin suyi wani motsin kawai sukaga motocin nashigowa cikin
makaranta cikin azababben gudu tamkar zasu tsaga ƙasa, suna kama shigowa suka shiga diddora da
bindigunsu cikin hanzari tamkar waƴanda zasu yaƙi Hakan wasu daga cikinsu suka nufi office ɗin
shugaban makarantar domin anan location kenuna musu lieutenant musayyeer yake. Cikin ƙaƙanin
lokaci sukayiwa makarantar ƙawanya.



Shugaban makaranta da sauran malamai suna ganin wannan kwaratan sojojin masu kama da samu
dawan farko wanda, gasu ƙili minaddaɗi innahu ɗib'ɗib ɗib. Domin kuwa tamkar wanda basaji kuma
basa gani Hakan suke indai kasake kashiga hannunsu to ka kaɗai domin sedai uwarka ta haifi wani. Ai
atake jiki yaƙara ɗaukar rawa, masu kuka nayi masu sakin gudawa ajikinsu nayi domin ba wanda cikinshi
be hautsine ba acikinsu. Hakuri sukeson bashi amma babu dama domin ko bada haƙurin rahama ce.



Sauran ɗalibai kuwa dunacan labari ya riskesu hadda ƙanwar anty Marwa wato maiha...aiko tarushe da
kuka tana tsinewa wanda suka ɗauke Failusha domin ko fitowa atare suka fito abinda yabasu ƙamshin
turaren maiha sam beyiwa Failusha ba shiyasa Takoma can nesa dasu inda bazatajiba, ashe rabon
asacetane...tana nan tana kukanta akazo kiransu domin lieutenant musayyeer cewa yayi duka akira
Mishi yan department ɗinsu, Hakan aka tasasu agaba aka kai masa.



Kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke kanshi kafin yayi managa wata daga cikin ƙawayensu tace "wlh Allah mu
bangantaba tun da aka fito peper farko, atareda maiha suka fito..da sauri ya kallesu nason sanin wacece
maiha, sedai Basu gane yaren nashi ba domin yan miskilancin sun motsa babu ba'asin magana idan
kuma kako wargi kaga tsan tsagaryar rashin M..ganin taƙi magana ne yasa ya runtse idonshi kawai, aiko
wani so ya zabga mata mugun Marin Seda ta wutsila kafin yace "who is maiha? Yafaɗa cikin tsawa me
amon sauti Seda office ɗin ya ɗauke baki ɗaya. Ihu wannan yayinyar tasaki tare da fitsari lokaci ɗaya
tana nuna maiha. Aiko ma maida kallonshi gareta..maiha kam gabaki ɗaya tarikice inbanda kyarma babu
abinda jikinta keyi cikin tashin hakali tace "wlh Allah yaa shattima tareda ita muka fito sedai munrabu
sabida ƙamshin turarena ne bemataba tace zuciyarta ke tashi ita ita ƙamshin jikin yayanta takeso taji,
Shiyasa tayi nesa dani taje tazauna tare da ridda wata riga tana shaƙa, nikuwa danaga Hakan se kawai
nayi dariya natafi abina domin wlh banyi tunanin wani abinba ni na ɗauka kawai tsokanata ne take yi,
taƙarsa zancen tana rushewa da matsanancin kuka...ido shattima yaruntse da karfi sabida kalaman
maiha sunyi bala'in ƙara Zafafa masa rai, domin tun da tafaɗi sunshi kuma tafaɗi wannan zancen tabbas
sunyi Hakan da ita domin dagashi se ita suka san Hakan kosu mami basusan tanason ƙamshin jikinshiba..
toyanzu da suka dauketa ina zasu sama mata ƙamshin jikinsa? Yatambayi brain ɗinshi tambayar kuma da
batada amsa..."Ohh god, yafaɗa a hasale yana dukan iska, kafin ya kalli yaran nashi yace "you are the
head of this school, and their plan to improve.."okay Sir, suka haɗa baki wurin faɗa. shikuwa bejira
cewarsuba yafice daga office ɗin ahasale. Aikuwa nan take wuri yaƙare rufewa da koke koke daga
malaman har ɗaliban cikin tashin hakali da ruɗani...mota ya shiga tare da figarta aguje yabar makarantar
sedai tashi na fita ta Dr Noor da maheer nashigowa lokaci ɗaya, kuma suna gama shigowa wannan
soldiers ɗin narufe ƙofar get ɗin makantar....!
Autar alheri ✍️



*🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹




Special and romantic love story 💋💓🫣



Writer by Autar Alheri ✍️




🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁

🌹🌹

🦁




Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭

Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze
cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️na haƙiƙa 💯
Book five



Chapter 82 & 83




"Suna yin perking wannan sojojin suka zagaye motocinsu cikin tuhuma. Da mamaki duk suke kallon
sojojin kafin suka buɗe motocinsu suka fito, ai maiha naganin Noor tashiƙo wurinshi tana faɗar "Yaa
Noor wlh Bansan wanda suka sacetaba Nima Bansan za'a sacetaba dan Allah katemakemu. "Ya isa maiha
please kiyimin bayani yadda zan fahimta, yafaɗa cikin tashin hakali domin tun da suka fito sojojin dukaga
tsantsar kama da me gidansu a gun Yaa Noor suka canje domin wasu daga cikinsu sunsan ƙanen nashi a
picture., wani malamine ya shiga bawasu labarin duk abinda yafaru tun shigowar lieutenant musayyeer
har labarin ɓatan failusha dasukaji, domin sam maiha taƙi samun nutsuwama Balle tayi masa bayanin,
habawa ai tun kafin malamin yagama bayaninshi zufa ya fara wanke musu fuska tako ina domin sunsan
yau kam tashin hankali yasamu agidansu sabida lieutenant musayyeer be iya ɓacin raiba idan ranshi
yaɓace kuwa Seta shafa. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai suke maimaitawa kafin Yaa Noor yakoma
mota cikin tashin hakali yabi bayan yayan nashi, Shima maheer tashi motar ya shiga yabi bayansu..




Lieutenant musayyeer.




Kaitsaye gida yanufa kafin ya isa ne yajira mutallab awaya yagaya Mishi yabada umurnin shige da fice
agarin Abuja abaza sojoji tako ina domin ansace Angel ɗinshi..tab ɗijam wata muguwar ash Shar
mutallab yalailayo yaɗurawa sojojin dake tsaye awurin cikin bada umurni yagaya musu abinda yake
buƙatar ayi, aiko kafin kace me tuni garin Abuja ya ruɗe da wannan Sabon tashin hankalin, domin sojoji
sun bazu ta kowane lungu da saƙo ba'ashiga kuma ba'a fita kana ko zirga zirgar cikin gari zakayi anriƙa
bincikenka kenan tamkar wani ɓarawo....yana isa gidan yasamu Mami da Hajiya kaka jugun jugun domin
tuni labarin ya riskesu Hajiya kaka kam se kuka takeyi tana tsinewa ko suwaye suka sace Failusha.
"Mesunan mlm ya ake cikine? Ko anganta ne? Cewar Hajiya kaka tana ƙoƙarin miƙewa tabi bayanshi
ganin ko kallonsu beyiba ya haura Pert ɗinshi. Dasauri Mami tariƙeta tana faɗar"yi haƙuri mama in sha
Allah za'a ganta karki bishi a wannan halin da yake ciki domin baze saurarekiba..haka Hajiya kaka
Takoma ta zauna batareda tayi wata jayayya ba domin ita kanta tana hango wutar bala'in dake kwance
acikin idonshi.
Shi kuwa bemasan sunayiba bedroom ɗinshi yawuce tareda buɗe wata ƙofa dake jikin bangon ɗakin ya
shiga, ɗakine me ɗan girma aciki wanda babu komai acikinshi se manyan computer's da kujerun zama,
wata computer yanufa tareda buɗeta ya kunna, atake yasaka wasu nonbers yafara aiki cikin ƙwarewa,
aiko cikin ƙanƙanin lokaci yasamu abinda yakeso, location ɗin da contact ɗin failusha ke aiki, ido
yazubawa wurin kafin yace "what iyakar nasarawa kuma? Domin domin akan hanya dazata sadaka da
garin nasarawa state yaga location ɗin. Azabure yamiƙe tare da buɗe wata diriwa yabuɗe tare da zaro
bindiga ƙirar AK-47 guda biyu yatura cikin aljihun bayan wandonshi, tareda ɗaukar waya yakira mutallab.
Fitowa yayi cikin tafiyar ta ƙaƙƙarfan namijin Zaki yanufo general parlor tamkar ze tsaga ƙasar, kallo ɗaya
zaka mishi kasan cewar ranshi a mugun ɓace yake, kofar ficewa yanufa kicin sauri Mami tace "babana.
Cak yatsaya daga tafiyar batareda yafuceba yana sauraronta...tasowa tayi hartazo kusanshi kana tace
"dan Allah babana abi komai a hankali karka yanke hukunci cikin fishi dan Allah, kaje cikin amincin uban
giji Allah yaƙareku yakuma baku nasara Allah yabayyana daughter duk inda ta shiga aduniyar nan.
"Ameen y Allah, ya amsa akan lips ɗinshi kafin ya juyo yariƙe hannu Mami kawai batareda yace komaiba
Sekuma yajuya yafice daga gidan. Motocinshi na fita layinsu, motocinsu nashigowa layin su uku,
mutallab da zugar yaranshi, se maheer da Dr Noor, ganin ficewar lieutenant musayyeer yasa duk suna
marawa motocinshi baya, inda suka ɗauki hanyar barin Abuja zuwa garin nasarawa a inda location ke
nuna masa contact ɗin failusha.




Kidnappers




Wani ƙaramin gidane ne ɗauke da hawa ɗaya, gidane aka gina shi acikin wani ƙugurumin jeji dake jihar
Nassarawa, abakin ƙofar shiga gidan wasu giga gidan ƙarti ne majiya ƙarfi tamkar yan resiling, kowanne
jikin murɗe sunfi mutum 20, suna zagaye da gidan ɗauke da muggan makamai...acikin gidan kuwa
Failusha ce kwance acikin wani bedroom a some domin tun abinda suka shaƙa mata bata ƙara sanin inda
takeba., a parlor kuwa kusan ƙarti 6 ne kezagayen parlor duk bayan minti biyar sesun leƙata suka gani
idan ta farka.... ahankali tafara buɗe lulu ayes ɗinta dasuka mata wani irin nauyi, harta waresu duka,
kallon pop ɗakin datake kwance takeyi cikin mamaki kafin tamiƙe zaune da sauri tana dube dube, tabbas
nan wani wurin ne domin batasan ko ina bane gawani mugun ƙarni dataji ƙamshin tiraren ɗakin keyi,
yamutsa kyakkyawar fuskarta tayi kafin ta fara waigen jakarta tana neman rigar lion ɗinta, sedai fa
wayam ba komai babu jakar Balle wayarta kuma babu rigar lieutenant datake shaƙa, wani irin faɗuwa
taji gabanta yayi Hakan yasa tamiƙe cikin sauri tana yunƙurin ficewa daga bedroom ɗin, a kuma Dede
wannan lokacin ɗaya daga cikin gardawan nan yaleƙo waya manne ƙugunshi...da sauri failusha taja baya
tana watsa Mishi wani mugun kallo kafin tace "kaikuma fa daga ina? "Gata madam tafarka, yafaɗa cikin
muryar basawa me mugun buga zuciya sabida ƙarfinta, yana miƙawa Failusha wayar. Kikarɓa tayi tana
kallonshi a wulaƙance babu ko alamar tsoro atattare da ita balle wata fargaba. "Kikarɓa mana kin wani
zubamin ido kosena tashi kanki da bindigarnan, yafaɗa cikin tsawa. "Taƙi karɓa ne? Aka faɗa daga cikin
wayar.."yes madam. "Okay buɗe sipikar wayar. "Okay yafaɗa yana saka wayar spiker. "Welcome to new
life mrs lieutenant musayyeer mahabub shattima, ina tayaki shigowa komata kuma ina Miki albishir
dacewar a yau nice zan binneki daranki tamkar yadda kike alƙawarantamin nikuwa zan cika Miki, tafaɗa
cikin shaƙiyanci.. ƙanƙace ido failusha tayi kana tace "wacece ke? Aiko wannan matar taƙara shekewa da
dariya kafin yace "kishiyarki mana, wadda zata rusa tarihin kasan cewarki ke kaɗai acikin rayuwar
lieutenant musayyeer mahabub shattima, wadda zata wanke Mishi tinaninshi akan cewar ke kaɗai
acikinta, ina Fatar kin fahimta...gyara tsayuwa failusha tayi cike da ƙarfin hali domin wani irin tashi
zuciyarta keyi akan wannan ƙamshin datake shaƙa, kana tabuɗe baki cikin ko in kula tace "au haba? Dan
Allah da gaske? "Tantama kikeyine? To kibari nazo ananne Zaki fahimci inda kalamaina suka dosa domin
wlh sekin Rena kanki sekinyi nadamar zuwanki duniyama balle haɗa alaƙa da abin sona, cewar wannan
matar, kafin Failusha tayi magana takarajin muryar wata mace daban tana Dariya, itama takora mata
nata jawabin, Hakan kowacce Seda tayi mata magana duka su huɗu, kafin taƙarshen tace "mun
munanan zuwa gareki muƙare da matsalarki daga nan kuma lieutenant musayyeer mahabub shattima
yazama na har abada. Suna faɗar Hakan Sekuma suka sheƙe da wata irin dariya me cikeda
shaƙiyanci..suna cikin dariyar sukaji ta ɗauki tata itama tanayi hartafi tasu amshi suda keyi su duka huɗu,
kafin ta tsagaita tace "ina jiranku sekunzo gadangarun bariki, da nayi niyyar barin gidanga a yau ɗinnan
base gobeba amma yanzu ba inda zani zan zauna na jiraku, domin kucika alƙawarin dakuka ɗauka sedai
ina shawartarku da cewar karku makara domin idan kuka makara lion ɗina yarigaku zuwa bazaku
sameniba sedai muhaɗu a wani karon, kuma ina muku albashir da cewa kunshigo komarda bazaku iya
fitaba kushigo hatsabibin tsibirin da yafiku hatsabibanci ƙananun ƙwari, ina mugu jinjina da wannan
ƙarfin halin maraba da fara buga sabuwar wasa, so I'm waiting. Tana gama faɗar Hakan tabuɗe wata
ƙofar tashige dasauri domin tana tunanin toilet ne, aiko tana shiga ta fara kelaya wani irin amai tamkar
zata amayarda ƴan cikinta..sukuwa kallon kallo su kayi tsakaninsu kafin Hajiya Turai tace "tofa kunji
shegiyar yarinya me taurin kan tsiya.."Humm ai shi yasa nace muku doline semun ɗauketa daga gare shi
tukunnah samu samu abinda mukeso, yanzu gabaki ɗaya hankalinshi nakan neman ta, idan yayi nema
yagaji dole ze haƙura yakoma tunani babu dare babu rana to mu kuwa da wannan zamuyi anfani mu
janyoshi cikin komarmu, cewar mushaffa tana murmushi. Dasauri anty mubina tace wannan gaskiya, bar
shegiya bazamuje yanzuba domin kuwa lieutenant musayyeer be isa yagantaba a inda take tun da bata
cikin garin Abuja kana sun toshe duk wata kafa daze iya bibiyarsu. "Good ai dear Hakan yayi👍 suka haɗa
baki wurin faɗa suna shewa kafin suka lula duniyar iskancinsu.




Lieutenant musayyeer
Basu tsaya ko inaba se a inda location ɗin kenuna Mishi, anan yayi perking motarshi domin shine ke
driving dakanshi yaranshi biyo shi kawai sukayi, buɗe motar yayi afusace ya fito, Hakan yasa duk dukayi
perking suna suka fito, dajine fallau filin Allah babu ko alamar ƙauye balle gida a wurin babu wani gu
inda za'ace aɓoye mutum awurin, amma kuma nan location ke nuna masa,. Dafe kanshi yayi cikin mugun
ɓacin rai yanabin wurin da kallo. Ahankali mutallab ya dafashi cikin rarrashi yace "my man miyasa Zamu
tsayanan? Shiru yayi tamakar bazeyi maganaba, Hakan yasa duk jikin ƙanenshi sanyi domin gabaki ɗaya
yanayinshi na tsoratasu, kowa yayi jugun anajiran jin mizece, cikin wani irin voice me firgita yan maza
yace "adede nan wurin location ɗin ke nunawa kuma gaya ba komai, yafaɗa cikin baƙin ciki tamkar
zuciyarshi zata fashe. Ai mutallab najin Hakan yacewa yaransu suduba wurin kozasu samu wata makama.
Anan kuwa suka bazama suna dube dube, kusan minti biyar Sega wani sojan yana faɗar"sir ga waya mu
samu riga dakuma jarkar mace..ai cikin sauri lieutenant musayyeer yajiyo tare da....!
Autar alheri ✍️




*🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹




Special and romantic love story 💋💓🫣



Writer by Autar Alheri ✍️




🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁🦁🦁

🌹🌹🌹🌹

🦁🦁🦁

🌹🌹

🦁




Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭

Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze
cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️na haƙiƙa 💯
Book five



Chapter 85 & 86




"Tareda zuba musu ido yana kallo, tabbas wannan kayanta ne wayarta jakarta dakuma rigarsa, runtse
idonshi da mala'in ƙarfi yana jin lokacinda maheer ke faɗar "ai wannan wayarta ce yaa mutallab. "Maza
kubazu daganan zuwa kilo mita 50 Gabas, yamma, kudu, arewa, kuduba idan zamu samu wani
inpomation, kuma war wanda ya dawo bada wani ƙwaƙwaran labariba. "Okay sir suka faɗa atare. Shi
kuwa wayarshi yaciro ya shiga Kiran wata nomber ana ɗagawa yace "anyi kidnapped ƙanwata mus'ab
anufo nasarawa da ita ina hanya Nima please..kafin yaƙarasa abinda yakeson faɗa Major mus'ab yace
"Bama seka riƙeniba lieutenant musayyeer Nima ƙanwata ce indai tana cikin Nigeria ko ina itace seta
bayyana biƙudiratillah. Yana gama faɗar Hakan ya yanke wayar....gefe ɗaya kuwa ganin lieutenant ya
ɗanyi nisa dasune yasa Noor matsawa kusan mutallab yace "Yaa mutallab please waccan makarantar da
yaa shattima yarufe dan Allah atemaki daliban dake ciki koba komai akwai ƴammata aciki kuma kaga
baby bata hannunsu kuma bada saninsu aka sacetaba..ido mutallab yawaro ganin dare yayi kuma shi
sam besan lieutenant yagarƙame makarantaba, "suwaye yasaka tsaronsu? "Wlh Nima bansaniba Yaya.
"Ina nufin sojojin ƙasar nan ne? "No sojojin ƙasar Iran ne. "Oh god wlh kuwa ba wanda ya isa yadakatar
dasu seshi, kuma wlh kai kasan kasani Noor ba wanda ya isa yasakashi sakin makarantar ayanzu duba da
yanayin da yake ciki, abu ɗaya zamuyi, baya nayi magana da shugaban makarantar. "Okay yaya
badamuwa, cewar Dr Noor ranshi duk ba daɗi. Gefe mutallab yakoma yakira shugaban makarantar tare
da bashi umurnin duka dalibai mata sukoma hostel sukwana kuma dalibai maza dake hostel sufito
subawa mata wuri su sukoma holds ɗin makantar sukwanta yanzu zesa akawo musu duk wani abin
buƙata kuma yakira iyayen yaran yasanar dasu karsu tada hankalinsu za'a buɗe makantar in sha Allah
dazaran lieutenant musayyeer yahuce...godiya sosai shugaban makarantar yayiwa general mutallab
kafin su kayi sallama. Cikin ƙanƙanin lokaci yabada umurnin kai duk wani abin buƙata a makarsntar kana
kuma atambesu duk abinda suke buƙata ayi musu..Seda yagama wayarne suma suka shiga motocinsu
suka nufi cikin garin nasarawa.



A gurguje
Yau kusan kwana uku kenan su lieutenant musayyeer suna bulayi acikin jihar Nassarawa da kewayenta
amma sam basuga kome kamada Failusha basu ganiba, tuni lieutenant musayyeer yafita hayyacinshi
domin acikin wannan kwanakin idan kaganshi zaka ɗauka jinyar shekaru yayi, yarame yayi wani iri dashi,
bayacin komai kuma baya bacci bayacewa kowa komai idan kaji yana magana to wayace yake yi akan
neman failusha gabaki ɗaya sun rasa gane kanshi. Wannan abin kuwa baƙaramin tada musu hankali
yayiba domin kuwa koba komai yanzu sunga tsintar soyayyar yarinyar a idonshi dakuma yanayinshi.
Kullun sesun lallaɓashi akan yaci wani abin amma yaƙi ruwa kawai yakesha se lemu idan general
mutallab da Major mus'ab sun Mishi dole tukunnah suda suke abo kananshi, suma su Dr Noor duk
sunrame sabida damuwar ganin halinda yayansu yake ciki gakuma ta ɓatan ƙanwar tasu. Kuma har
yanzu bawani labari agun wanda mutallab yatura domin yasanar dasu karsu dawo babu labarinta.



A gida kuwa ɗaya arikice daga mami har Hajiya kaka domin itace ke tankwasa Hajiya kaka akan tadena
kuka za'aganta, to itama yanzu kukan takeyi. Dady da fa'iz ma basu hutaba dudda cewer haryanzu sojoji
sunƙi barin mutane su sake agarin amma ahakan Seda yasako police ciki, kuma yaje dakanshi gidan
alƙalin alƙallai yasanar mishi abinda ke faruwa da ahalinshi. Wannan abu fa ya ɗau zafi dayawa domin
kuwa duk Nigeria acan cewar ansace yar gidan manya kamar Alhaji mahabub shattima, kuma ƙanwar
sojoji domin tawuce ƙanwar soja ɗaya kam a yadda gari yarikice..



Failusha



Tun ranar da suka kawota bata ƙara waya da waƴannan matanba kana kuma bata gansuba, sedai kullun
dasafe za'a kawo mata abinci, ba'aƙara kawowa Seda yamma, sedai a yadda suka bar nasafe ahakan zasu
ɗaukeshi domin Bataci, acikin kwanakin nan uku itama duk tafita hayyacinta kasan cewar batacin komai,
ga wani irin amai datakeyi a koyoshe saka makon ƙamshin datakeji aɗakin wanda take kira wari, domin
ita sam batada wata damuwa wadda tawuce wannan ƙamshin dakuma ƙamshin jikin yayanta
datakesonji gwani mukugun feeling harna tashin hankali dake neman hallakata, wanda tarasa kina miye,
harki takeyi wani lokacin tankar ƙwarin keshan nononta kuma suna yamutsa mata gindi, idan abin
yaciyota sedai tahaɗe kafafuwanta kawai tayita rusar kuka, wannan shine abinda yafurgita Failusha
bawai satar da aka Mataba, gashi kuma tayi alƙawarin bazata fita daga gidanba indai ba lion ɗinta ne
yazo yafitar da ita ba harse taga kosu waye keneman kutsowa rayuwarsu..



Yau tunda sukayi sallar azahar yahaɗe kanshi da guywa be ɗagoba kuma bemitsaba kusan awa ɗaya
domin har 3:30pm tawuce amma yana nan a yadda yake. Tasowa mutallab yayi ya dafashi tare da cewa
"please shattima kayi haƙuri dan Allah karage wannan tinanin wlh in sha Allah duk inda Failusha take
za'aganta, karkazo

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment