Reading MAKTOUB By HAWWA MUH'D USMAN Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng 💠💠💠💠💠
©®2020.




*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




Bʏ.
*HAWWA MUH'D USMAN.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
*IG:REALSMASHER898.*
*TWITTER:JEEDDAHMU898.*
*Wattpad link:* https://my.w.tt/NV64fA4cR6


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.*

*Aʟʜᴀᴍᴅᴜʟɪʟʟᴀʜ ᴀʟᴀᴀ ᴋᴜʟʟɪ ʜᴀʟɪɴ! Aʟʟ ᴛʜᴀɴᴋs ʙᴇ ᴛᴏ ᴀʟᴍɪɢʜᴛʏ ᴀʟʟᴀʜ,ᴛʜᴇ ʟᴏʀᴅ ᴏғ
ᴀʟʟ ᴄʀᴇᴀᴛᴜʀᴇs,ᴍᴀʏ ᴀʟʟᴀʜ's ᴘᴇᴀᴄᴇ ᴀɴᴅ ʙʟᴇssɪɴɢs ʙᴇ ᴜᴘᴏɴ ᴛᴏ ᴛʜᴇ ɢʀᴇᴀᴛ ᴀᴍʙᴀssᴀᴅᴏʀ
ᴘʀᴏᴘʜᴇᴛ ᴍᴜʜᴀᴍᴍᴀᴅ (ᴘ.ʙ.ᴜ.ʜ) ᴡɪᴛʜ ʜɪs ғᴀᴍɪʟʏ ᴀɴᴅ ʜɪs ᴄᴏᴍᴘᴀɴɪᴏɴs ᴀs ᴡᴇʟʟ.*

*ⅅⅈՏℂℒⅈℳℰℛ:Aɴʏ ʀᴇsᴇᴍʙʟᴀɴᴄᴇ ᴛᴏ ᴀᴄᴛᴜᴀʟ ᴘᴇʀsᴏɴ ʟɪᴠɪɴɢ/ᴅᴇᴀᴅ/ʀᴇᴀʟɪᴛʏ ɪs ᴘᴜʀᴇʟʏ
ᴄᴏɪɴᴄɪᴅᴇɴᴛᴀʟ.*


🆓 Pᴀɢᴇ..

»1⃣
1⃣ :#Tʜᴇ ᴍᴇssᴀɢᴇ

K'arar shigowar kiran waya shi ne musababbin da ya sata jan wani irin siriri
kuma malalacin tsaki,a yangance kamar ba ta son d'auka ta kai hannu ta bud'e
had'ad'd'iyar handbag d'inta made in Gucci company dake rataye jikin shoulder
d'inta,yayin da kyakykyawa,kewayayyiyar farar fuskarta mai d'auke da k'aramin
baki,dogon hanci had'e da manyan idanunta da suke cikin rainbow sunglasses suka
fara bayyanar da damuwa,ta gefe ta d'an saci kallon y'ar uwarta da suke tafiya tare
tana d'ane baki kamar za tayi kuka,kyawawa ne dukansu maa sha Allah,but da
kyakykyawan kallo guda za kayi saurin gane mai rainbow glasses d'in ta zarta y'ar
uwartan dake gefenta nesa ba kusa ba,but duk wanda yayi sa'ar kallonsu tabbas zai
so ace ya k'ara,hannayensu rik'e cikin na juna suke tafiya,yanayin yadda suka fito
suna hira da dariya gwanin kyau da burgewa,yayin da hakan zai yi saurin bayyana
maka irin shak'uwar dake tsakaninsu,dan yanayin da suke ciki ba k'aramin dad'i yake
musu ba,tab'e baki ta d'anyi bata bari sister d'intan ta fahimci yanayin b'acin rai
da take ciki ba tayi saurin mayar da wayar silent ta tura a jaka,a hankali suka ci
gaba da tafiya mai kama da yanga cikin tsakiyar babban compound d'in gidan wanda
shuke-shuke suka k'awata,sanye suke da irin gowns d'innan masu zubin babbar
riga,komai nasu iri d'aya ne a colour kawai ne aka samu bambanci,likewise their
handbags and shoes suma duka haka,daf suna k'arasowa bakin wani brand new toyota
landcruiser prado dake parke a carline wani kiran ya sake shigowa,kamar baza ta
amsa ba haka ta sake fito da wayar ta zuba mata idanunta da had'ad'd'en sunglasses
d'inta ya mamaye,a hankali d'ayar budurwar dake gefenta ta waiwayo a wani mugun
yangance ta kalleta kad'an ta cikin glasses dake sanye a fuskarta mai launin
pink,colour d'in rigar dake jikinta,fara ce itama sai dai bata kai d'ayar
ba,because ita farin nata kamar ya so yayi yawa dan yadda jikinta yake kamar ka
tab'a jini ya fito,tana da madaidaitan idanu,hanci da k'aramin bakinta da ya zauna
saman fuskarta,a hankali tana ci gaba da kallonta da wani irin sanyayyan murya ta
furta "O'ohhh.! Sweetheart why didn't u pick?" Tab'e baki wacce aka kira sweetheart
tayi ba tare da ta kalleta ba tayi k'ayataccen murmushi cikin sanyayye kuma
romantic voice d'inta ta furta "Kada ki wani damu habibtiiy,guy d'in da nake baki
labarinsa ne,ni na tambayesa inda ya samu number na,wai ya d'auka number ne a
wayar.." Sai tayi shiru bata k'arasa ba saboda haushin da taji maganar ya
bata,murmushi d'ayar ta sake yi tace "No sweetheart as u know wulak'anci babu
kyau,har kina fad'amin hakan all the time nayi,ki d'auka ki ji mene ne zai fad'a."
Fuskarta da damuwa ta d'ago kamar a fusace tana b'ata rai tace "Haba mana na fad'a
miki ba na son damuwa ne,shi ya cika takuri yayi ta kiran mutum,bai san lokacin da
kake free ba" dariya mai sanye da pink d'in kayan tayi tana sakin hannunta,a
hankali ta dawo gabanta ta tsaya tana zare glasses d'in dake sanye fuskarta,daf ta
bud'e baki za tayi magana daga can nesa da su suka jiyo wani murya mai cike da
kwarjini ya furta *"ISMAT!"* Yanayin da aka yi kiran kamar da fad'a.

Saurin runtse idanuwa tayi tana yarfe hannu kamar ta ci chilli powder,a fili
k'asa² ta furta "Huh! Ya rabb! When Yaah *BARRAQ* zai daina min titsiye idan zan
fita?" Da sauri sai ta zare glasses d'in dake fuskarta ta juyo tana had'iye
saliva's very hardly,fuskarta k'unshe da wani irin munafukin murmushin tsoro tana
langab'ar da kai tace "Yes!" Saurayi ne matashi kyakykyawan gaske,wanda ya had'a
qualities da duk wata d'iya mace za tayi fatan kasancewa tare da
shi,Ilimi,hutu,class,naira,uwa uba kyau,yayin da da kyakykyawan kallo guda za ayi
saurin gane tsananin kama ta jini da suke yi da wacce ya kira ISMAT,tun da ya tsaya
gurin yayi shiru yana kallonsu na wani lokaci kafin ya rik'e waistband yace "Ina za
kuje yanzu da yamma?" In'ina ta fara saboda yadda ya tsare ta da idanu,ganin duk ta
rikice ta kasa tsayawa guri d'aya tayi masa bayani da sauri d'ayar ta matso tana
rik'e arm d'insa tace "Huh! Ya Barraq ba za mu b'ata ba,za mu dawo yanzun and.."
Kallon hannunsa yayi dai² inda ta rik'e ya kalleta yana had'e rai,da sauri ta sake
shi tana matsawa side ta d'aga masa hannu tace "Sorry" yace "Uhn!" Bai sake cewa da
ita komai ba,ya mayar da hankalinsa kan Ismat dake k'ifi² da ido yana sake had'e
rai yace "Tambayarki nake ina za kuje?" Ta d'ago tana matse k'afafu kamar mai jin
fitsari tace "Umhn! Dama!" Tsawa ya buga mata yace "Za kiyi magana ko sai na mare
ki?" Da sauri cikin firgici ta runtse idanu jikinta yana tsananta rawa ta k'ank'ame
d'ayar,k'wafa yayi a fusace yana zare idanunsa yace "Yawon banza za ki koya?"
Quickly ta girgiza kai za tayi magana cikin hayaniya yace "Zo ki wuce ciki,idan
kika kuskura kika sa k'afar ki wajen gidan nan kuma sai na..." Bai k'arasa ba daga
bayansa yaji ance "Za kayi mata me?" Da sauri ya juya ya kalli bayansa jiyo muryar
mahaifiyarsa dake tambaya,Ismat dake mak'ale a bayan d'ayar budurwar tana jin
maganar mahaifiyarsu hurriedly ta fito ta nufi kyakykyawar matar dake tsaye tana
k'arewa Barraq kallo,tana zuwa ta fad'a jikinta ta saki kuka,cikin wani irin
takaici Barraq ya bisu da kallo yana fad'in "Mom ban san me yasa ba kya so nayi
magana ba,wasu lokutan fa yaran nan baki san ina ne suke zuwa ba,freedom d'in da
ake basu idan yayi yawa za'a samu matsala Mom,idan yanzun kina nan babu tabbas ki
kai gobe,me yasa Mom? Ina da hak'k'in kulawa da tarbiyyar Ismat because i'm her
elder brother besides Daddy ba mazauni bane,but sai kina nuna mata hakan kamar
takurata nake yi,idan wani abu ya samu rayuwarta mu duka ya samu,dan Allah Mom ki
bari,idan kina bata support za kisa ta raina ni,baza ta tab'a ganin girma na
ba,sannan a ko ina ne nayi mata magana za ta iya bad'e min idanu da k'asa tayi min
rashin kunya,hakan ba wani abu bane sai don kina nuna mata rashin muhimmancin da
nake da shi a cikin rayuwarta,ki sani Mom ba iyaye kad'ai suke da alhakin kulawa da
tarbiyyar y'ay'ansu ba,mu da muke y'an uwa muma muna da namu hak'k'in.. Please Mom
ya kamata ki ba ni wannan damar a matsayin Yayanta na dunga bincika
al'amuranta,idan ya dace suje shi kenan,ba zan hana ba.!" Yadda ya k'are maganar
muryansa a k'asa kamar zai fasa kuka idan tace ba haka ba yasa ta kasa cewa komai
da farko,Ismat kam da kanta ke jikin Mom lokaci d'aya taji jikinta yayi wani irin
sanyi da kalamansa,though a times tana yiwa maganarsa kallon bai² but tabbas a
yanzun ta fahimci ya fisu gaskiya har Mom d'in da take mahaifiyarsu,d'ago fuskarta
tayi a hankali daga jikin Mom tana sauke ajiyar zuciya,Mom da ta zubawa Barraq
idanu ta kasa magana tayi k'wafa a d'an fusace tace "Kai dai Barraq always idanunka
na kan yaran nan,da sun fito kace su koma ina dalili? Duka inda kake zuwa na tab'a
cewa ina so na sani?" K'asa yayi da kai with elegance yace "But Mom itafa mace ce"
a fusace Mom tace "Ko mene ne,thought tarbiyya d'aya muka ba ku,me yasa za ka dunga
zargin y'ar uwarka eh?" Yace "Mom ba haka bane ki fahimce ni" za tayi magana Ismat
tayi saurin rik'o arm d'inta cikin sanyayyar muryarta tace "No Mom! Na fahimci
abunda Yah Barraq yake nufi and ya fimu gaskiya!" Mom tayi saurin kallon Ismat sai
dai bata ce komai ba,d'ayar budurwar dake gefe ne tun d'azun tana kallonsu jin
abunda Ismat ta fad'a da wuri tayi kicin²,quickly kafin Ismat ta sake yin magana
cikin sheshshek'ar kuka tana matso hawaye ta fara fad'in "No Mom! Duk abunda yake
faruwa kawai dama Yaah Barraq yana son cewa nice mai laifi,ina son koyawa y'ar
uwarsa yawo,da ba haka take ba,ko fita ba ta yi sai yanzun da nake zaune da ita,ni
dama ba tun wannan lokacin na fahimci ba ya son zamana a nan ba!" Saurin kallonta
Mom tayi tace "Haba *BADRIYAH* waye ya fad'a miki haka?" Barraq dake kallonsu ya
tab'e baki because shi ya san abunda ta fad'a haka yake babu k'arya sai dai shi bai
fito fili ya yi magana ba,Badriyah cikin sheshshek'ar kuka tace "Tun ba yanzun ba
dama na gane nufinsa,kawai yak'i fitowa ne ya fad'a,amman ai Allah yana gani idan
na kai Ismat wani wajen da bai dace ba ko nace tayi wani abun da yake inappropriate
saboda ta lalata tarbiyyar ta,Allah ya saka muku duka idan na cutar da ita,but kuyi
hak'uri yanzun na gane zamana a nan ba shi da wani amfani,Mom ke da Ismat kad'ai
kuke so na but Yaah Barraq baya son hakan,kayi hak'uri kaima in Allah ya yarda zan
tafi na bar muku gidan ku,nima ba a son raina nake zaune muku a gida ba ai.." Tana
gama fad'ar haka bata jira wani yayi magana a cikinsu ba ta juya da gudu² ta wuce
cikin babban simplex apartment d'in tana kuka,Mom da duk bata ji dad'in abunda ya
faru ba ta waiwaya ta kalli Barraq bata ce masa komai ba sai k'wafa kad'ai da
tayi,hurriedly ta juya tana kwala kiran Badriyah then a gurguje suka bi bayanta.

Kusan a tare suka shigo cikin parlor ita da Ismat suna kiran Badriyah but har
sannan bata amsa ba,dai² lokacin da suke jin sheshshek'ar kukanta da takun
takalminta a tare suka kallo direction da sautin yake fita,suna d'aga kai suka
hangota tana saukowa daga saman wani irin rantsatstsen staircases da ya bada style
mai jan hankali d'auke da trolley sai share hawaye take yi tana k'arawa,jikin Ismat
banda tsuma babu abunda yake tayi saurin kallon Mom hawaye suna taruwa a idonta
tace "Please Mom kada ki bari ta tafi,kice ta zauna please!" Mom cikin wani irin
mutuwar jiki ta kad'a mata kai,a hankali ta fara tafiya wajen staircases tana
kallon Badriyah,tana gama sakkowa Mom ta rik'e hannunta,muryarta a k'asa irin na
mai rarrashi tace "Haba habibtiiy,yanzun saboda Barraq za ki tafi ki barmu,mu duka
ai muna son ki,me zai sa kiyi fushi? Yanzun har akwai abunda zai yi miki ki iya
tafiya ki bar sweetheart d'in ki da ni? Kinga kuka take yi itama saboda kince za ki
tafi,u know ba za ta ji dad'i ba idan kika barta,please just be patience kada kice
za ki tafi a wannan lokacin kin ji?" Kai ta girgiza da sauri tana share hawaye
cikin muryar kuka tace "Please Mom allow me to go,ba zan iya ci gaba da zaunawa
ba,Yaah BARRAQ yana min wannan kallon" Mom ta kad'a kai tana sake rik'ota tace "No
habibtiiy ki zauna kinji zanyi magana da Barraq d'in,ba zai sake ba idan Allah ya
so!" A hankali Ismat ta k'araso saboda rashin kuzari tana rik'e trolley d'in
hannunta muryarta tana rawa tace "Please habibtiiy don't go,idan kin tafi binki zan
yi bazan zauna ba nima" Badriyah tana girgiza mata kai tace "No sweetheart ki
zauna,ai ke gidan ku ne,nima zan koma gida ne,bazan iya zaunawa ba Yaah Barraq yana
cewa ina koya miki wasu halin" Ismat ta kad'a kai tana share hawaye tace "Please
habibtiiy kada ki tafi,Mom za ta yiwa Yaah Barraq magana zai bari,Mom kice ta bar
tafiyan" Mom ta kad'a kai tace "Yeah! Zan yi magana da shi kin ji,ba zai kuma ba
habibtiiy" kamar Badriyah ba ta so sai ta rausayar da kai tace "Okay!" Tana fad'an
haka Ismat tayi saurin cewa "Za ki zauna d'in?" Ta kad'a mata kai cike da
sakarci,Ismat tayi saurin rungume ta tana sakin murmushi tace "Thank u habibtiiy"
ta bata wani deep peck a cheek d'inta guda,murmushi suka yi tare Mom dake kallonsu
tayi murmushi itama then suka koma sama mayar da kayan tafiyar,Mom kam suna barin
gurin ta dawo tsakiyar rantsatstsen parlor ta da yaji alatu,ko ba'a fad'a ba tsarin
gidan kansa kad'ai mutum ya kalla daga compound zuwa ginin gidan dole yayi saurin
gane lallai mamallakinsa ba k'aramin attajiri bane,wayarta data yasar bisan coach
k'irar company'n apple IPhone 11 Pro ta d'auka,in less than two minutes ta kai
wayar kunne,cike da bayar da umarni ta furta "Yanzun ka zo ka same ni a parlor"
tana fad'a ta katse kiran.

Barraq dake kwance saman lafiyayyen royal bed d'insa da yaji white beddings
tun bayan da ya shigo yayi shiru yana tunanin kiran da Mom take masa,quickly ya
tashi ya fito daga bedroom d'in,a parlor ya sameta ta hakimce,though ba wai tana da
irin girman jiki ba,but yanayin zaman da tayi shi zai sa ace hakan,yadda take had'e
rai tun kafin ya k'araso da ya kalleta sau d'aya yaji gabansa ya fad'i but haka ya
daure ya k'araso yana satar kallonta ya zauna kad'an saman wani kujeran da fad'in
"here i'm Mom" waiwayawa tayi ta kallesa tana kad'a kai then ta fara fad'in "yanzun
Barraq me yasa za kayi haka? Kana son girma amma kai sam baka san yaya ne za ka
same shi ba,shin idan za ka yiwa Ismat fad'an abunda take yi bai dace ba,ya kamata
ka dunga nunawa a fili kana zargin da sa hannun Badriyah?" Sunkuyar da kai yayi
saboda ya san gaskiya ta fad'a but shi yana yi ne ko Badriyah za taji haushi ta
daina jan Ismat yawo mara dalili,silently kamar ba ya son maganar yace "I'm sorry
Mom" muryarta a sanyaye tace "Daga yau ba na son haka,idan za ka yiwa Ismat fad'a
saboda wani abu da tayi ba dai² ba ka had'a su duka,because Badriyah is ur cousin
sis,abunda zai faru da Ismat kaji rashin dad'i itama idan ya faru baza ka ji dad'i
ba,please ka bari ka ga bata ji dad'i ba,kuma ko waye aka yiwa haka ba zai ji dad'i
ba,ku zauna lafiya dan Allah ba na son rigima,kai ne babba ka kama girmanka please"
a hankali ya kad'a kai ya furta "In Allah ya amince Mom ba za'a sake ba" tace
"better" ya jima a zaune bai sake cewa komai ba,da aka jima Mom ta kalleshi tace
"Tashi kaje Allah kiyaye" yayi ajiyar zuciya yace "Thank u Mom" ta rakashi da idanu
har ya shige room d'insa dake nan kusa da staircases.


Suna shiga bedroom d'in kai tsaye Ismat ta wuce closet da trolley d'in
Badriyah,while ita kuma ta haye saman bed tana kallon Ismat dake k'ok'arin shirya
mata kayanta cikin closet kamar yadda na ta suke,tana daga saman bed a zaune ta
fara yiwa Ismat maganar fitar da za suyi aka samu matsala,Ismat dake tsaye wajen
lafiyayyen reach-in closet d'insu ta tab'e baki,then a hankaki ta waiwayo tana
kallonta tace "Habibtiiy na fasa zuwa ni dai" hurriedly Badriyah ta d'ago kai tace
"Saboda Yaah Barraq ya yi magana ko kuwa saboda me?" Murmushi Ismat tayi kad'an ta
kad'a mata kai,Badriyah ta tab'e baki tace "Okay!" Daga haka bata sake magana ba ta
bud'e jakarta da ta yasar gefe ta ciro phone d'inta,tunda tayi shiru ta fara
clicking wayar bata sake ko tari ba ta fad'a dandalin sada zumunta. Sanda Ismat ta
gama shirya kayan a hankali ta dawo kusa da ita ta zauna,tana kallonta taga
fuskarta a had'e da sauri ta rik'o hannunta tana fad'in "Habibtiiy what's up?
What's happened?" Badriyah data d'ago kyakyawar doguwar fuskarta ta zubawa Ismat
idanu,kamar ba za tayi magana ba da farko ta tab'e baki tace "What's it?" Ismat
dake kallonta tace "To wannan had'e fuskar da kike yi fa?" Murmushin yak'e tayi
lokaci d'aya ta sake had'e rai tana kautar da fuskarta gefe tayi k'wafa,Ismat tayi
ajiyar zuciya ta kwanta tana kallonta ba tare da ta ce komai ba,da aka jima
Badriyah ta gaji da kallon da Ismat take mata ta d'ago idanunta tana b'ata fuska
tace "Wai me kike kallo?" Murmushi Ismat tayi tace "Kawai ina kallon yadda kika yi
ne duk fa wallahi ba kiyi kyau ba,don Allah ki saki fuskar ki" siririn tsaki
Badriyah tayi za ta tashi kenan daga gurin ring d'in wayar Ismat ya dakatar da
ita,a hankali ta juya ta kalli jakar dake kusa da ita ta sake kallon Ismat tana
had'e rai,ganin har lokacin bata daina kallonta ba a fusace tace "Ur phone miss
look" tab'e baki Ismat tayi tana juyar da fuskarta zuwa kallon wani gurin tace "Ke
rabu da su,idan sun gaji za su daina kira" tab'e baki itama Badriyah tayi daga haka
sai bata sake magana ba,sai da taga mai kiran ba shi da niyyar dainawa a hankali ta
ajiye nata wayar ta d'auko na Ismat data rufe idanu kamar mai bacci,ta d'an saci
kallonta ganin number ne ke kiran babu suna then tayi amswering tana furta "Hello!"
Daga can side d'in da aka kira da yake a free tasa wayar,cikin wani irin
shak'urarren murya mai cike da sanyi aka amsa "Hi! How are u and how was today?"
Saurin bud'e idanu Ismat tayi tayo kan Badriyah with intention of ta kwace phone
d'inta,Badriyah tayi saurin janye hannunta tana kallon Ismat ta furta
"Alhamdulillah! Da waye nake magana please?" Ismat taga Badriyah ba ta da niyyar
bata wayar ta dad'in rai tana had'e rai tace "Habibtiiy ki bani phone d'ina
mana,mene haka kin d'auki naki kuma kin rik'e min nawa?" A hankali Badriyah ta zuba
mata ido while tana cewa "Na tambaya waye babu amsa" murmushi aka yi mai sauti then
yace "Oh! Sorry dear,kina tare da *FAWAD!"* Ta kad'a kai tana lumshe idanu saboda
sanyin da muryar mai maganar yake tattare da shi,lokaci d'aya ta ji baza ta iya yi
masa rashin kunya ba,a nutse tace "Uhn! Who are u looking for please?" Ya sake yin
murmushi yace "mai wayar nake nema,and na kira na bada hak'uri ne please,if na
takuraki yanzun my first call was not intentional,i'm just looking for my
brother,aka samu matsala nayi missing 1 digit nayi kiran line,please kiyi hak'uri
it won't happen again!" Badriyah tana lumshe idanu tace "Uhn! No problem" yace "But
zan iya tambayar wani abu kuma?" Ta kad'a kai kamar tana gabansa tace "What's it?"
Yana sassauta murya yace "Ur name please?" Kai tsaye ba tare da ta yi tunani ba
tace *"ISMAT!"* yayi murmushinsa mai kyau yace "Nice name" kafin Badriyah ta sake
yin magana da sauri Ismat dake gefe tace "Mene ne haka kuma habibtiiy,why didn't u
tell him ur's? Kawai sai ki kama ki fad'a masa suna na ni da ban sansa ba?"
Badriyah ta kalleta tana matsar da wayar gefe tace "Wayar waye wannan?" Ismat tace
"Mine" Badriyah ta harareta tace "Shi ne zan fad'i nawa dan kin rainawa kanki
hankali?" Fawad dake sauraren conversion d'insu ta cikin wayar yayi murmushi yace
"Ohh! Ki bata hak'uri please,na ga mun yi laifi duka" Badriyah ta harari Ismat tana
sake kallon wayar dake hannunta k'iran IPhone 8 Plus tace "Rabu da ita kawai wata
irin mai duhun kai ce itan,but ni babu yadda za tayi da ni" Ismat tana kallon
Badriyah kamar za ta yi kuka tana nuna kanta tace "Ni kike cewa mai duhun kai?"
Badriyah dai bata sake tanka maganar Ismat ba sai sauraron abunda yake fad'a
take,Fawad ya sake yin dariya lokacin da Ismat ke fad'in haka yace "I'm really
sorry ma'am." Almost 30 minutes suka d'auka suna magana yana sake bawa Badriyah
sak'on ta bawa Ismat d'in hak'uri then suka ajiye wayar lokacin tana kallon Ismat
da taji haushi ta rufe idanu kamar mai bacci tace "Idan ba ki da duhun kai me yasa
kika bawa Yaah Barraq dama yake hana mu fita a gidan nan? Wai idan bamu samu
freedom yanzun ba sai wane lokaci ne? Nifa gaskiya ba na son zaunawa a gida,zama
guri d'aya tsautsayi inji kifi,so why bazan fita na sha iska ba tunda i gotta
chance?" Ajiyar zuciya Ismat tayi a hankali ta bud'e lumsassun idanunta tana kallon
Badriyah ta yada kai gefe ba dai tace komai ba,Badriyah tayi tsaki ganin Ismat ba
ta da niyyar yin magana tace "Ko yanzun abunda yasa ni ba zan fita ba raina ne a
b'ace da ko baza ki ba ni kam sai na je" still Ismat bata ce komai ba,sai tashi da
tayi ta nufi hanyar entrance za ta fita,sai da ta kusa door a hankali tace "Ni kam
na je wajen bhai!" Badriyah ta rakata da mugun kallo a masife tace "Allah raka taki
gona" murmushi Ismat tayi tana rik'e da handle na bedroom door d'in cikin zolaya
tana kallon yadda Badriyah tayi kicin² tace "Ko za kije ne mu tafi tare?" Badriyah
ta kyab'e fuska tana yi mata wani kallo tace "Huh! Allah tsare ni da zuwa
wajensa,yanzu kam ina zuwa ai ban san me zai yi min ba kuma" saurin fita Ismat tayi
tana cewa "kanku ake ji,but ni duk na kasa gane muku always fad'a ba kwa shiri"
Badriyah ta tab'e baki tace "Shi dai da bai so a zauna lafiya,mutum kullum fuska
kamar wanda ake aikawa sak'on mutuwa."

Ismat da ta fita tayi dariya tana tafiya cikin nutsuwarta,sanda take sakkowa da
taga babu kowa a parlor,tana gama tsallako staircases d'in ta wuce hanyar bedroom
d'insa,a bakin door d'in ta tsaya ta fara yin knocking,Barraq dake kwance yana
operating laptop ya d'ago kansa yana tambaya "Who's there" Ismat dake tsaye cikin
cool maganarta tace "It's me bhai" tab'e baki yayi yace "come in" a nutse ta murd'a
handle d'in ta tura k'ofar,yana adjusting kwanciyarsa daga rub da ciki ta shigo,ya
zuba mata tsumammun idanunsa har ta k'araso kusa da shi da sallama a bakinta,yana
sake kallonta bayan ya amsa yace "Ya aka yi?" Fuskar damuwa tayi wearing tace
"Bhai! Dama zuwa nayi na baka hak'uri,in Allah ya yarda ba zan sake yin abunda za
kayi fad'a ba" yana kallon yadda take matse yatsun hannunta yace "Gaskiyar da nake
fad'a shi ne nayi miki fad'a kou Ismat?" Saurin kad'a masa kai tayi idanunta suna
tara hawaye tace "A'a kawai na fad'a ne,but na sani gaskiya kake fad'a" ya kad'a
kai yana tab'e baki yace "Ok then?" Tayi shiru,komawa yayi ya kwanta yace "na ji
tafi ki ba ni wajen Allah kiyaye" still tayi ta kasa motsawa,ya d'ago a fusace yace
"Tafi mana,tsaiwar me kike yi min a kai kuma?" Ta d'ago kanta tana kallonsa hawaye
har sun fara sintiri saman fuskarta tace "Please bhai bazan sake cewa haka ba,kayi
hak'uri har abunda Mom tace please!" Idanunsa yayi saurin rufewa because a
rayuwarsa ya tsani yaga tana kuka,but abunda yake shirin yi yanzun ya san dole ne
ya fara koyan yadda zai jurewa ganin zubar hawayenta,a dak'ile bai yarda ya sake
kallonta ba yace "Uhn! Will u get out please my friend?" tana kallonsa tace "Toh"
da muryar tausayi,a sanyaye cike da wani irin mutuwar jiki ta juya ta fara tafiya
tana share hawaye,ya bita da kallo har ta je bakin k'ofa za ta fita yayi calling
sunanta out "Ismat!" Tayi saurin juyowa tana amsawa yace "Ina Badriyah?" Tace "Tana
can bedroom" yace "Kice tazo ina nemanta,ku taho tare" amsawa tayi da sauri ta
fita,sun jima sosai kafin su zo saboda Badriyah bata yarda Barraq yana kiranta
ba,har sai da Ismat d'in tayi mata rantsuwa sannan ta yarda ta biyota suka
taho,suna shigowa Ismat tayi sallama,ita kam Badriyah tana had'a rai tace "Ga ni
ance kana kira na!" Ya d'ago idanunsa ya zuba mata su saboda jin a yadda tayi
maganar da raini,inwardly yayi k'wafa yana saita yanayinsa yace "Yeah! I just want
to say sorry kan abunda ya faru d'azun" tayi saurin kallonsa taga ita yake kallo
shima sai tayi fuska tace "Uhn! Babu komai" yayi murmushin gefe a ransa yana wani
tunani yace "Shi kenan za ku iya tafiya" Ismat da ta ji dad'in abunda yayi da sauri
taje ta rungume shi tace "thank u bhai,i love u" yayi murmushi ya shafa kanta,ta
juya da sauri ta kalli Badriyah dake shirin fita tace "Habibtiiy why didn't u say
u're sorry too to bhai?" A fusace Badriyah dake tafiya ta juyo za tayi masifa suna
had'a ido da Barraq da ya kafeta da kallo,quickly ta lumshe idanunta tana jin yadda
gabanta yake fad'uwa saboda idanunsa ba k'aramin kwarjini suke yi mata ba,duk
iskancin da take ji da shi ko fitsara ta shirya yi masa a mafi yawan lokuta da sun
had'a ido da shi take jin ta kasa,muryarta tana rawa ta kasa sake kallonsa tace
"I'm sorry Yaah Barraq,nima bazan sake cewa komai ba" idanu suka zuba mata jin
abunda tace a k'arshe,Ismat ta fashe da wani irin dariya tana satar kallon Barraq
daya tab'e baki tace da Badriyah "Ba fa haka ake cewa ba,kice baza ki sake ba" da
sauri Badriyah ta kalli Ismat rai a b'ace but ta yi k'ok'arin dannewa,tana aike
mata sak'on harara k'asa² tace "Yeah! This is what i want to say ai hausar ne ya
gudu" lumshe idanu Barraq yayi ya juya because ya san baza ta tab'a fad'a dai² ba
duk da anyi mata gyara,ya riga ya san halayyarta na girman kai ba tun yanzun ba,ba
wai iya fad'a ne baza tayi ba kawai bata yi

Please Login or Register in order to submit comment