Reading Bahagon Layi Sabon Salo by TARE DA ALK'ALAMIN Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng *TYPING* πŸ“²

*BAHAGON LAYI*

(SABON SALO)

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* πŸ‘‡

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
GARKUWA BIYU

*DA KUMA*πŸ‘‡

BAHAGON LAYI (SABON SALO)

*BABI NA D'AYA DA NA BIYU*

WATTPAD:Hassana3333


✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

πŸ–ŠοΈ
*PEN WRITERS ASSOCIATION*


✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️




______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*


_____________________________________


https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/



*BISIMILAHIR RAHMANIR RAHEEM*

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI,TSIRA DA AMINCI SU K'ARA TABBATA GA ANNABI
MUHAMMAD (S A W)DA ALAYEN SA DA SAHABBANSA,DA MASU BIN SA HAR IZUWA RANAR SAKAMAKO.

MASOYA GA HASSANA D'AN LARABAWA TA DAWO DA WANI SALON NA DABAN,BAYAN KAMMALA
LITTAFIN *(GARKUWA BIYU)* DA NAYI,BA WANI SALO BANE ILLA CIGABAN LITTAFIN BAHAGON
LAYI,WANDA A YANZU A KAYI MASA LAK'ABI DA BAHAGON LAYI *(SABON SALO)* GA DUK WANDA
YA KARANTA BAHAGON LAYI YA GA IN DA MATAN LAYIN SUKA BAJE KOLIN SU,KUN GA YADDA YA
NISHAD'ANTAR DAKU YA FAD'AKAR DAKU,TO WANNAN MA DA YARDAR ALLAH ZAI K'AYATAR
DAKU,FATANA KU BIBIYESHI DOMIN KUGA ABIN DA YAKE D'AUKE DASHI,KUMA INA FATAN ZAKU
FUSKANCI SAK'ON DA YAKE D'AUKE DA SHI,NA GODE MASOYA NA.




*FITOWA TA FARKO (GIDAN MALAM ARABI)*



"An gayu!An gayu!!An gayu!!!"

Kiran da Malam Arabi ke ta k'wallawa matarsa kenan da k'arfi cikin d'aga murya,daga
can ta amsa sannan ta fito daga d'akin ta zuwa tsakar Gidan da yake a hargitse da
kaya ko ina a watse,ya dubeta yaga yadda jikinta yayi butu butu da k'ura,amma duk
da hakan jagirar nan rad'au a fuskarta ta ta kalli gabas,tuk'ek'iya da ita kamar an
zana ta da D'an yatsa,fuskar nan na maik'o ta lafta basilin (mai gurguwa)ga kwalli
masha Allah ta rambad'a kamar wadda zata tafi tallan ganda,ta yi d'aurin ture kaga
tsiya abinta cokalele a gaban goshi ,tazo gabansa ta tsaya tana karkad'a masa idanu
wai ita fari take yi,ya dubeta daga sama har k'asa ya tuntsire da dariya har da
rik'e ciki.

Ta tsaya tana kallonsa yana ta dariya,da dai taga dariyar tak'i k'arewa sai ta juya
a fusace tayi hanyar band'akin tsakar Gidan ko takalmi babu a k'afarta,taje in da
ta ajiye tsintsiyar kwakwarta ta d'akko ta zaro sili d'aya ta nufoshi,ta na zuwa ta
mik'a masa tsinken ta na rik'e k'ugu da Hannu d'aya ta na girgiza jiki,ya bita da
kallo kana ya fara k'unshe dariyarsa,yayi mata alamar tambaya da hannunsa me zai yi
da tsinken?

Cikin k'ufula tace.

"Ka karb'a ka cire abin da kake wa dariya a jikina kawai Malam"

Babu b'ata lokaci ya amshi tsinken wata dariyar na k'ara zuwar masa,kamar gaske
yace.

"Rufe idanuwanki An gayu na,yanzu za kiga abin da zan cire miki kuwa,Wanda ya sani
dariya"

Ta rufe idanuwan babu musu ta na jiran ganin abin da zai yi ,duk da uwar kwalliyar
da ta zauna ta b'ata lokaci tayi domin ya yaba amma Dan wulak'anci yake mata
dariya,Malam Arabi ya matsa dab da ita ya d'aga tsinken ya zurkud'a mata a
hanci,tayi baya da sauri saboda rad'ad'i ta na kurma ihu,amma sai da ya samu
nasarar Ciro wani dank'areren curarren tasono da ya cike mata hanci.

Ta bud'e idanu a razane tana kallonsa,cikin masifa tace.

"Malam wai kasheni kake so kayi da man?daga baka tsinke ka cire abin da kake wa
dariya a jikina sai ka Burma min shi a hanci?to bak'inciki kake da hancina Dan kaga
nawa yafi naka tsayi ko?

Malam Arabi ya d'ago mata tsinken mai d'auke da tasono yana nuna mata,ta yatsina
fuska ta na murgud'a baki tace.

" menene wannan kuma?"

Yayi murmushi ya ce.
"Abin da na cire a jikinki ne da yake sakani dariya,ke yanzu Dan girman Allah nan
fa wai kwalliya kika yi ko?hanci fal tasono da majina,wai Dan Allah An gayu yaushe
zaki nutsu ki koma tsaf kamar sauran mata ne?ke sai son kwalliyar amma sam baki iya
ba,mu nan malamai da kika ganmu babu abin da muke so irin muga matayen mu sunyi
tsaf dasu, saboda muna shiga cikin matayen Aljanu mu na ganin yadda suke d'aukar
wanka,amma ni kullum nazo gida sai dai tasono ya amsa min sallama ta,kai Allah dai
ya kyauta halinki An gayu."

Ta k'yalk'yale da dariya ta na dukan cinya sannan ta dubeshi tace.

"Au wai daman abin da kake wa dariya kenan?to ai ni ina sane na barshi,domin wata
k'awata ce ta bani wani Sirri, tace min akwai fa'ida ga mata wad'anda suke barin
tasono a hancinsu har mazajen su su gani,wai wani Sirri ne na daban Malam"

Malam Arabi ya rik'e hab'a yana shafa gemunsa cikin takaici ya ce.

"Ita kuwa wannan K'awar taki a wane Gidan mahaukatan take?"

An gayu ta zaro idanu tace.

" Gidan mahaukata kuma Malam?billahillazi mai hankali ce malam , ragas take"

Ya harare ta yana zabga tsaki.

"Wallahi k'arya ne An gayu!duk in da ta fito daga yankin mahaukata take,a rasa da
abin da za a birge miji sai tasono? Wannan wane irin hauka ne?"

Ta D'an yi shiru,sai kuma can ta tuna abin da yace yanzu,kawai sai ta kwashe da
dariya,ya kalleta sosai yace.

" Dariyar me kike?"

Ta na dariyar bata daina ba ta ce.

"Malam ji nayi kace kuna ganin yadda matan Aljanu suke d'aukar wanka da
kwalliya,shine nace mai zai hana ka kaini su koya min nima na dinga yi maka,idan
kuma ba zaka kaini ba sai naje Habiban Babalalo ta rakani na San ba zata rasa sanin
wajen ba ko?"

Ya k'ara Dank'ara mata harara yana tsaki yace.

" Wato dai tunda kika jiyo gulmar abin da ya faru tsakanina da shegiyar matar nan
kika sa min ido ko?to ai na gode wa Allah da cikin k'ank'anin lokaci Allah yayi min
sakayya,kuma duk da haka ban hak'ura ba,ke nake so ki d'auko min fansar keta min
haddi da tayi ta cijeni a al'aura ta saboda ita tsinanniya ce,kinga dai yanzu yau
zamu koma layin da zama,to ina so ki shiga jikinta a hankali har ku saba sosai
domin ki d'auko min fansa,yanzun nan me kura zai zo ya fara d'ibar kayan mu ya kai
BAHAGON LAYIN,Gidan da K'asimu ya tashi nan na kama mana tunda me gidannan ya
uzzura min na tashi zai yi bikin D'an sa ya sakashi a cikin gidannan"

An gayu Tayi shewa ta ce.

"Aikuwa angama Malam,bari na shiga na k'arasa fitowa da y'an komatsai na"

Ya girgiza kai yana sab'a malum malum d'insa da take rinjayarsa,daga waje yaji ana
rafka sallama da fad'in masu kura sun iso don d'iban kaya,da hanzari ya fice ya
shigo dasu ,suka fara jidar kaya ana lodawa a kura domin tafiya a tare a BAHAGON
LAYI.
*************


Ta na durk'ushe gaban mahaifiyar Sunusi tana ta rafka kuka da hawaye da majina
shab'e shab'e,har dai Inna ta gaji da jin kukan ta d'ago ta kalleta fuskarta cike
da jimami tace.

"Yanzu Harira ba zaki daina wannan kukan haka ba?kiyi hak'uri muyi zaman mu anan
mana,kinga dai Zamanki ke da Amina gida d'aya ba zai yiwu ba,saboda ba zaku zauna
lafiya ba Harira na san halinki,ita kuma Amina ba hak'uri ne da ita ba,ke yanzu ma
ban da abin ki yadda gidan yake k'arami ina zai sa ka ki ?

Ta d'ago ta na kuka sosai ta fara magana.

" Wallahi inna na gyara hali na zamu zauna lafiya k'alau ni da Amarya Amina,kuma ni
ko wannan k'aramin d'akin da muke ajiye shirgi na yadda zan zauna a ciki,kuma babu
wata rigima da za ki ji ta b'ullo,nayi miki alk'awari in sha Allah ......

Inna ta girgiza kai za tayi magana Sunusi ya shigo da sallama.




Comments
share
vote
pls




*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️


*TYPING* πŸ“²

*BAHAGON LAYI*

(SABON SALO)

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* πŸ‘‡

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
GARKUWA BIYU

*DA KUMA*πŸ‘‡

BAHAGON LAYI (SABON SALO)


*BABI NA UKU DA NA HUD'U*


WATTPAD:Hassana3333


✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

πŸ–ŠοΈ
*PEN WRITERS ASSOCIATION*


✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️




______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*


_____________________________________


https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/




****Inna ta amsa masa sallamar,sannan ya shigo ya nemi waje ya zauna kansa a
sunkuye ya gaida Inna,ta amsa tana kallon sa,ya waiwaya ya dubi Harira da ke
gurshek'en kuka tana wage baki,ga wawulon bakinta ya dad'a fad'i ya wani wargaje,ya
d'auke kansa ya maida kallonsa kan Inna ya gyara zama yace.

"Inna Lafiya wannan ta zo ta saki a gaba tana kuka?"

Inna ta sauke numfashi tace.

"Wallahi ni dai D'annan na rasa ya zan yi da Harira,gabad'aya ta d'aga hankalin ta
akan tana son komawa gidanta su zauna da Amaryar ka tare,duk yadda naso na nuna
mata gara zaman ta a gidan nan tak'i ganewa,tun abin baya damuna har tausayin ta ya
fara ratsani akan Nadamar da tayi"

Da sauri Sunusi ya d'ago ya zabgawa Harira wata shegiyar harara,Sannan ya mai da
kallon sa kan Inna fuskarsa babu walwala yace.

"Wai shin Inna ba mun gama magana tun shekaran jiya akan hakan ba?a yanzu Harira
bata da gurbi a cikin gidana,Lafiya k'alau nake zaune da Amina tsawon sati biyu da
Auren mu kenan,amma wallahi Inna da zarar Harira ta koma gidan nan na san ba zata
bari a zauna lafiya ba,gara tayi zaman ta a nan zai fi kwanciyar Hankali kawai"
Harira ta mik'e a gigice ta k'ara fasa kuka da k'arfi har ta razana su,bata yi wata
wata ba ta afka jikin inna da k'arfi tana ihu,har ta bugawa inna gingimemen kanta a
baki,Inna ta tunkud'e Harira da k'arfi saboda yadda taji dadashin bakinta ya d'auki
zugi,ragowar Hak'oran k'asa sun daki dadashin sama,Harira ta fad'o k'asa kan cinyar
Sunusi,da sauri ya ingijeta yana sakin tsaki ya maida hankalin sa kan inna da ta
rik'e bakinta tana zazzare ido saboda azabar da ta ratsa bakinta,hankalin Sunusi a
tashe yace.

"Sannu Inna,Allah yasa dai bata ji miki ciwo ba?ta kafa miki wannan k'aton kan nata
me kama da duro"

Da kyar Inna ta iya magana idanu a warwaje.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,Harira D'an ragowar bakin nawa na tsufa za ki
k'arasa min?me yasa ba kya aiki da hankali da lura ne?yanzu jikina tamkar na yara
yake fa,bai kamata ki rufto min a ka ba,gashi nan za ki rub'a min D'an ragowar
bakina na taunar goro"

Sunusi cikin b'acin rai ya fara magana.

"To Inna ke ma dai gashi nan a gabanki ta gwada miki halinta na Akuyoyi,so take
yadda bakinta ya zama duk gib'i ke ma ta k'arasa miki hak'oran k'asa,muguwa
azzaluma kawai,Wallahi ni Inna ba don kin takura ba da tun a wancan lokacin na sake
ta,gabad'aya zama da ita ya fice min a raina Inna"

Harira ta kuma d'ora Hannu a ka ta zunduma ihu,yayin da Inna ta dubi Sunusi tace.

"Kul!kar na sake jin maganar saki a bakin ka,kai da Harira mutu ka raba takalmin
kaza,kaga dai Harira marainiya ce tilas kayi hak'uri da ita da halayen ta,ni dai
ina tausayin marayan mutum ka sani, kayi wa Allah Sunusi ka yafe mata ka bata dama
ta k'arshe,ka mai da ita wancan gidan tunda tayi alk'awarin gyara halin ta,insha
Allahu za ku zauna lafiya da juna"

Sunusi ba don ya so ba ya girgiza kai yace.

"Shikenan Inna ba zan k'etare umarnin ki ba,na hak'ura zan mayar da ita can
d'in ,amma sai nan da kwana biyu saboda ina so mu tattauna maganar da Amarya
Amina"

Harira ta fara share hawaye tana b'angala dariya cike da murna,Sunusi ya dank'ara
mata Harara,yayin da Inna tayi murmushi cike da farinciki ta dubi Sunusi tace.

"Yawwa D'an albarka aikuwa Na gode,kuma nayi murna da ka amince da magana ta,Allah
Yayi maka albarka,kuma ina so bayan ta koma ka sa rana ka kaita Asibiti a saka mata
hak'oran roba Sunusi,ba dad'i tai ta zama baki duk wawulo,idan aka dubeta a ka
dubeni sai a zaci shekarun mu d'aya fa"

Dariya Harira ta saka, suka waiwaya suna kallonta cike da mamaki,Inna ke tambayarta
.

"Lafiyar ki Harira kike dariya?

Harira ta kuma fashewa da dariya tace.

" Wallahi Inna wani Abu na tuno, lokacin da azzalumin D'an sandan nan yake jibgar
mu da kulki ya za ci ni tsohuwa ce,har da ce min wai Dan kutumar ubana tsofai
tsofai da ni amma ina shiga cikin yara ,kai gaskiya wannan ofisan bai da imani ko
kad'an,da yayi wani tsalle ya dira kan k'afar Habiba ji kike b'ararassss!ya karya
ta"

Inna tayi dariya tana girgiza kai,shi kam Sunusi mugun tsaki ya ja yana k'ara jin
tsanar Harira a zuciyar sa.




****************



Da daddare misalin k'arfe Tara na dare Sununsi zaune a falo kan kujera,yayin da
Amina take zaune a k'asa tana matsa masa k'afafuwan sa,zuciyar sa tana ta bugawa
yana so yayi mata zancen amma yana jin tsoro matuk'a,amma hakan ya daure yayi
gyaran murya yana murmushi yace.

"Amarya ba kya laifi ko kin kashe D'an masu gida"

Amina ta washe baki tayi fari da idanuwanta,ya dinga morewa kallonta jibgegiya da
ita a gabansa jikinta duk tsoka,duk in da ya duma Hannu yaji abubuwa sun cika masa
Hannu lumus!ba irin Harira k'ek'asasshiya da ko naman kirki babu a jikin ta ba,sai
k'ashi da jijiyoyi rad'a rad'a.

Can ya Numfasa yace .

"Amarya magana nake so muyi ni da ke,dafatan zaki bani had'in kai ki fuskance
ni,sannan ki tayani yiwa mahaifiyata Biyayya"

Tayi k'asa da idanuwanta cikin kunya tana murmushi,ya kalli saman idanunta sun sha
eye shadow malam abin gwanin Sha'awa,ta kuma d'ago idanuwan ta sauke su a kansa ta
na cigaba da mammatsa masa k'afafuwansa da hannuwanta masu cike da nama,sannan ta
kalmashe murya tace.

"Kar ka samu damuwa,kai fa tamkar Sarki ne!ni kuma jakadiyar ka,kaga kuwa duk abin
da ka umarce ni shi zan aikata babu musu"

Sunusi yaji kansa ya kubura suntum,daman yana da irin wannan darajar bai tab'a sani
ba,?Ashe shi cikakken Namiji ne amma Harira take mayar da shi Aljihun baya?Sosai ya
kwaye baki yana dariyar murna yace.

"Amma naji dad'in batun ki Amaryata,hakan ya nuna min darajata a wajen ki ta kai
k'ololuwa kenan,to babu laifi Allah Yayi miki Albarka,daman ba wata magana ba ce
illa d'azu da naje gaida Inna shine take min wata magana,wai tana so Harira ta dawo
gidan nan ku zauna tare domin ku had'a kanku,hakan ne yafi cancanta a kan na barta
can gidan,to ni kuma sai nace wa Innan ta jira sai na nemi shawarar ki tukun, duk
abinda kika ce da shi za'a yi amfani,saboda bana son abin da zai zo yana d'aga miki
hankali muna zaman mu lafiya,kuma na san Halin Harira ba kirki ne da ita ba kwata
kwata,tun kafin ki zama matata ma rikici ya had'aku kunci uwar sabada a gefen hanya
bare yanzu kun zama kishiyoyi,duk da Inna mahaifiyata ce ban isa na k'etare umarnin
ta ba,amma dai ina son naji abin da za ki ce akan hakan tukun"

Tunda ya fara magana k'irjin Amina ke bugawa,tabbas bata son zama da Harira guri
guda,saboda ita dai bata da hak'uri ba zata jure iskancin Harira ba,kuma tana da
saurin Hannu,Abu kad'an take kai duka,ga Harira da tsokana,tabbas kuwa idan tace
zata yi mata iskancin da ta sa ba wataran za ta nakasa Harira ko ma a d'auki
gawarta,amma in dai ta sauya halinta to za su zauna lafiya,domin babu abin da yafi
zaman lafiya da kwanciyar hakali dad'i.

Duk da tunanin da ya gallabi zuciyar Amina bata bari Sunusi ya gane ba,kawai sai
tayi murmushi cikin Siyasa da kissa ta fara magana.

"Haba Mijina!yanzu har Innar mu ta yanke hukunci amma ka ce wai sai kayi shawara da
ni?hakan ai bai dace ba,saboda darajar Inna a wajenka ta ninka tawa sau ba
adadi,kuma ko babu komai ai Yaya Harira zuwa nayi na sameta,ba zan hanata dawowa
gidan ta ba,k'arewa ma ni zan kwashe kayana na mayar wancan k'aramin d'akin kawai
domin ta dawo d'akin ta,idan yaso ragowar kayana sai a mayar da su gida har Allah
ya hore maka ka Gina naka gidan,fatan dai ayi mana addu'a Allah ya bamu zaman
lafiya da juna"

Da sauri Sunusi ya tare ta yana girgiza kai.

"Ba zai yiwu ki koma k'aramin d'aki ba Amina,sai dai ita ta zauna a can,daman ba
wasu kayan kirki take da su ba illa kwarab'ab'b'en gadon ta da sari duk ya cinye
shi,sai wata shegiyar tabarma da take shifid'awa masu kitso,ke za ki cigaba da zama
a nan d'akin,ita kuma ta dawo wancan d'in,kuma Na gode da had'in kan da kika bani
Amina,tabbas yanzu na san nayi dace da mace ta gari mai farantawa Miji, Allah Yayi
miki Albarka"

Amina tayi murmushi ta amsa da "Ameen".

Sunusi Yayi mik'a yana Hamma,ta d'ago ta kalleshi tace.

" Wai har ka fara jin bacci ne?"

Sunusi ya ce "Eh wallahi bacci nake ji dan a gajiye nake,yau kwangilar wani bulo
muka yi masu yawa duk jikina ciwo yake min na gaji"

Amina ta mik'e da hanzari ta kamo hannunsa tace.

"Ai banga ta zama ba Mijina yana tare da gajiya,muje d'aki nayi maka tausa ko
gajiyar za ta warware"

Sunusi ya mik'e yana murna da zumud'i yau za a yi masa tausa,yasan ba k'aramin
dad'i zaiji ba yadda hannuwan Amina suke cike da nama,abin da Harira bata tab'a yi
masa ba,ya san ma ko tayin ba dad'i zaiji ba sai dai ma k'asusuwan hannunta su soke
masa jiki,Amina ta rungumoshi gefen jikinta,sai ga Sunusi Yayi D'an tsurut a
Hammatar Amina saboda ta ninkashi sau uku a k'iba,suka shige d'akin su cike da son
juna da farinciki.




Comments
Share
Vote
Pls
*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️



*TYPING* πŸ“²

*BAHAGON LAYI*

(SABON SALO)

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* πŸ‘‡

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI
BAHAGON LAYI
GARKUWA BIYU

*DA KUMA*πŸ‘‡

BAHAGON LAYI (SABON SALO)


*BABI NA BIYAR DA NA SHIDA*


WATTPAD:Hassana3333


✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

πŸ–ŠοΈ
*PEN WRITERS ASSOCIATION*


✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️




______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________


https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/




*** Washegarin ranar Habiba Zaune a tsakar gidan ta bayan fitar Babalalo wajen
sana'ar Askin sa,wake ne a gabanta tana tsince mara kyau za ta surfa ta kai
Markad'e,tun jiya Babalalo yake fad'amata cewar yana Sha'awar yaci Kulele,ita kam
a dole zata yi saboda bata son sa,in dai ta ci b'ata mata ciki yake yi tai ta tusa
cikinta ya kumbura suntum,wani zubin sai ta jik'a y'ar jar kanwa ta sha tukun take
samun salama,Sallamar da taji daga soro yasa ta d'ago kanta ta na Amsawa.

Wadda tayi Sallamar ta shigo tana taku a hankali,da sauri Habiba ta
washe baki cike da murna tana fad'in.

"Lallai yau ashe ina da Babbar Bak'uwa,yaushe rabon ki da gidannan Rauda?.

Rauda ta yamutsa fuska ta ja wata kujera Y'ar tsuguno da ke kusa da Habiba ta
zauna,Sannan ta sauke Numfashi ta Harari Habiba tana hura hanci tace.

" Hmmmmm! Ai Habiba baki da kirki ko kad'an,gabad'aya kin manta da ni ma a
rayuwarki kina ta sabgogin ki,wai shin ina gida na ina gidanki Habiba?tsiran mu
layi d'aya ne fa,Amma kin d'auke k'afa daga gidana kwata kwata kin daina nema na ".

Habiba tayi Ajiyar zuciya ta ajiye waken Hannunta a k'asa ta dubi Rauda fuska cike
da jimami tace.

" Hmmm!ke dai bari kawai Rauda,ina cikin tsaka mai wuya ne wallahi,tun bayan da
Abubuwa marasa dad'i suka faru damu duk nayi sanyi,fita ma in Ba ta zama dole ba ba
yin ta nake ba,Layin namu duk ya tarwatse,Oga Harira an samfata wata unguwa ta
daban,Saratu tana gida Malam me almajirai na dila ta,K'asimu ya d'auke Zahra'u sun
koma wata Unguwar ta daban,daga ni sai Shafa'atu fa yanzu,ita d'in ma ba ganinta
nake ba saboda takunkumin da Babalalo ya sa ka min,wallahi Rauda bani da kwanciyar
hankali duk a k'untace nake ji na"

Rauda tayi murmushi tana sauke mayafin ta daga kanta zuwa kafad'ar ta,sannan ta
dubi Habiba tace.

"Ai Lokacin da abin nan ya faru nayi takaici Habiba,sosai naji Haushi fa,kuma ba
Haushin kowa naji ba sai haushin ku,ban da ku mahaukata ne ku zauna wani shirgegen
k'ato ya dinga laftarku ku wajen hud'u,ba kwa wawuso k'afafun Arne ku nanashi da
k'asa,ai sarkin yawa yafi sarkin k'arfi Habiba,gaskiya kun bani mamaki,duk
shaid'ancin ku amma ku ka zauna wani D'an iska ya dillik'e ku a banza a wofi,ai
wallahi da ina cikin ku lokacin da kunga aiki da cikawa".

Habiba ta sauke tagumi ta dubi Rauda ta girgiza kai tace.

" Hmmm! zance kawai kike Rauda,in ba haka ba waye ya isa ya ja da Hukuma?ai Hukuma
ta shallake tunanin kowa"

Da sauri Rauda ta manna mata harara ta katseta da cewa.

"Za ki sa na dannawa Hukumar zagi me sifirin,ai ko shi D'an sandan Yayi muku
hukunci ne ba bisa k'a'idar aikinsa ba,kuna matan Aure d'ima d'ima amma ya keta
muku haddin Aure yayi muku hawan k'awara?

Habiba ta D'an yi dariya tace.

" wane irin Hawan k'awara kuma Rauda?sai kace wad'anda yayi wa fyad'e".

"To menene bambancin?"

Rauda ta katseta da tambaya,sannan ta cigaba da cewa.

" Ai bambancin kad'an ne Habiba,mutumin da aka ce har tsalle ya dinga yi yana
tumami a ruwan cikin ku yana cafar nonuwan K'irjinku".

Habiba ta zaro idanu tana dafe k'irji cike da tsoro,cikin rawar baki tace.

"Inji wane tsinannen mak'aryacin Rauda?a ina kika samo wannan labarin k'anzon
kuregen?

Rauda ta tab'e baki tace.

" Yo zancen duniya yana b'uya ne?ni ma a gari naji".

Habiba ta girgiza kai tace.

"Kai mutane an yi tantagaryar munafukai kuma magulmata,wallahi hannuwansa basu kai
jikin mu ba,na san dai lokacin da ya gama kirb'ar mu ya sa hannunsa yana ta
tunkud'o k'eyar mu waje,ban da haka bai tab'a jikin mu ba wallahi".

Rauda ta D'an rage murya kad'an tace da Habiba.

" Wai kuma da gaske mijin Amaryar ne ya kirawo D'an sandan aka tarfa ku cikin gidan
sa?

Habiba ta ce.

"Hmmm!shine wallahi Rauda,bak'in matsiyaci ba"ta fad'a fuska cike da jimami.

Rauda ta ce.

" Kuma har yanzu suna layin nan basu tashi ba ko?naji an ce gini yake ba za su jima
ba za su tashi.

Habiba ta tab'e baki tace.

"Suna nan har yanzu bak'ak'en munafukai,ai kin san damunar bana tayi gyara,ginin da
ya fara ne ya rushe ya dawo baya,shine har yanzu basu tashi ba"

Rauda ta numfasa tace.

"Ya kamata kafin su bar layin nan ku d'auki fansar abin da yayi muku,wallahi idan
baku rama ba kun yi asara duniya da lahira,ai rama cuta ga macuci ibada ne,ya
kamata ki nemi Saratu da Harira da Shafa'atu ku had'a kai ku d'auki fansa,duk da
dai ba Saratu a cikin ku lokacin da abin ya faru, amma na san zata taya ku yin
yak'in,sai ta wakilci Zahra'u kawai"

Habiba tayi kasak'e cikin tunani,zuciyarta na kai kawo,ta k'urawa Rauda ido tace.

"Ta ya ya kike tunanin Hakan za ta faru Rauda?nifa Yanzu tsoron duniya nake ji
domin ta koya min hankali,amma kuma kina zuwa da wannan shawarar naji ta kwanta
min,yanzu me kike tunanin ya kamata ayi?"

Rauda tayi murmushi ta matso jikin Habiba sosai ta kai bakin ta kunnen Habiban tayi
mata rad'a,Habiba ta d'ago ta kalli Rauda bayan ta gama jin maganar ta,suka kwashe
da dariya suka d'aga Hannu suka tafa……!

Rauda ta tsagaita da dariyarta ta dubi Habiba tace.

" Ke na manta muna ta zance ban yi miki jaje ba,Ashe Shagon Babalalo na Aski ne ya
k'one,wai gobara da tsakar dare ko? ni sai jiya Shafi'u yake fad'amin,dalilin
zuwana kenan ma"

Habiba tayi murmushi tace.

"Ai ba jaje ya kamata ki taya ni ba,Murna ya kamata ki taya ni Rauda"

Rauda ta zaro idanu tace.

"Murna kuma?asara ta samu mijinki amma kice a tayaki murna Habiba?ke kuwa wace irin
zuciya ce da ke da kike murna da samuwar asara akan mijinki?"

Habiba tayi shewa tana buga cinya tace.

"Yo murna mana Rauda,Ai Babalalo mugunta ya so shirya min yayo min kishiya,can
danginsa munafukai aka bashi wata tsomalalliyar Yarinya me zubin y'an ruwa,har fa
ya ta da ginin filinsa kad'an ya rage ya kammala wannan ibtila'in ya same shi,gurin
Neman abincin sa ya k'one k'urmus,yanzu tilas haka yayi gwanjon gidan da ya fara
ginawa ya siyar ya samu kud'in da ya gyara shagon sa,kinga ai yanzu tilas ya
hak'ura da Auren da ya jajibowa kansa ko?tunda babu y'an matsabbai a hannunsa da
zaiyi hidimar auren da su,in kuma ba kan Uwatar zai siyar yayi hidimar Auren ba".

Rauda ta tuntsire da dariya kamar za ta kifa,sannan tace.

" Amma Habiba baki da mutunci wallahi,kuma fa da Babalalo zai siyar da kan Babarsa
da ya samu kud'i,don naga kan nata har rinjayar jikinta yake saboda girma".

Habiba ma ta shek'e da dariya ta ce.

"Yo baki ga shi ma Babalalon gadon k'aton kai yayi ba,kwanaki da muka zabga karo ya
buga min kansa wallahi na zaci dutsen Dala ne ya rufto min,sai da na kwan uku ina
jinyar ciwon kai,ai Allah yayi musu baiwar gingimemen kai,ni da Atiringim".

Suka kuma kwashewa da dariya suna tafawa,a dai dai lokacin suka ji ana zabga
sallama a soro,Habiba ta Amsa da fad'in "wanene?"

" Bak'uwa ce"Aka amsa daga soron.

"To shigo Bak'uwa" inji Rauda kenan.

Ta shigo tana murmushi, duk suka bi ta da kallo basu shaidata ba,banda kallon
fuskarta babu abin da suke yi,tasha kwalliya hoda fururu,ga jambaki bak'i ta lafta
tamkar wata Y'ar daba,d'aurin nan cokoko dashi a gaban goshi,Habiba ta matsa mata
ta zauna kusa da ita kan tabarmar da take zaune,bayan sun gaisa ne Bak'uwar ta dubi
Habiba da murmushi ta ce.

"Na san baki shaidani ba ko?Ni sunana An gayu,jiya muka tare a layin nan gidan da
aka tashi,ni matar Malam Arabi ce,kuma na shigo mu gaisa ne mu saba da juna a
matsayin mu na mak'ota a yanzu".

Ambatar sunan Malam Arabi da tayi yasa k'irjin Habiba bugawa da k'arfi,har abada ba
zata manta da wannan matsiyacin mutumin ba,duk lokacin da ta tuna shi sai ta hango
azabar da ya ganawa bakinta da lab'b'antaπŸ˜‚β€¦β€¦.!




Comments
Share
Vote
Pls




*BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️


*BAHAGON LAYI*

(SABON SALO)


*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️
HASSANA D'AN LARABAWA


*BABI NA BAKWAI DA NA

Please Login or Register in order to submit comment