Reading LELEWAL Farin Wata by Fatima Muhammad Gurin Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [15/07, 6:25 pm] Diddi Walida: πŸŒ•πŸŒ•



πŸŒ•LELEWALπŸŒ•

πŸ¦‹FARIN WATAπŸ¦‹



πŸŒ•πŸŒ•



STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin.



MARUBUCIYAR:-

ZUHRAA

HAMRAH

IGIYAR RAYUWA

NOOR IMAAN and

RUWAN SAMA.



FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763



SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy
and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar
kauna.



JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not
perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a
wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta
hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku
masoyana. Na godeπŸ₯°πŸ™.
EXQUISITES WRITERS FORUM πŸ“

(Home of exquisite writers')



Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai.

β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”



1 1
.....
1️⃣



Gabad'aya tunaninta ya tafi ne ga wani shud'dd'en lokaci chan a rayuwarta, tayi zurfi sossai cikin tunani
har bata san ana kwala kiran sunanta ba seda aka ta'ba ta, firgigit tayi tana kallon wacce ta ta'batan,
cikin fad'a baaba lami tace "Anya kekam bilkisu ba aljannu bane a kanki? Mutum shi kad'ai se ya zauna
yayi zurfi cikin tunani ayi ta kira bazaki ji ba? Da kankantar shekarun kin nan wani irin tunani kikeyi
haka?" Murmushi da be kai zuci ba bilkisu tayi cikin sanyin murya irin nata tace "yi hakuri baaba" tsaki er
tsohuwar tayi tana ci gaba da mitanta ta nufi katifarta "nan kam ai kin fi kowa kwarewa eeh fannin bada
hakuri ba se ki je hajjiya yasmeen ke nemanki".



Cikin sanyin yanayi na rashin hayaniya bilkeesu ta mike wadda ita a ganinta hakan sauri ne take abinda
ke konawa masu gidan rai kenan musamman Yasmeen da sahla se su ce iskanci ne, fita tayi daga
'bangaren nasu na masu aiki ta nufi chan cikin gida dukda yadda zuciyarta ke luguden bugu sbd sanin se
ta sha zagi da fad'a kila harda rankwashi wurin Anty Yasmeen hakan be hanata tafiya cikin natsuwa ba,
da sallama ta tura kofan parlorn kasan.



Had'add'en parlor ne babba sossai me set d'in kujeru har uku kuma a hakan ba wadda ya takure wani
chan tsakiyar parlorn ta hango fahad da khalil suna buga PS kallo d'aya ta musu ta wuce ta nufi stairs da
ya kasance had'add'e shima ta haura kanta kasa har ta isa tsakiyar parlorn saman da shima yake yanayi
da parlorn kasan tsawa taji an daka mata a firgice ta d'aga kai ta zubawa sahla idanunta masu ruwan
zaiba da d'igon baki a kan farin na hagun.



Sahla da ta harzuka da kallon ta jefa mata trow pillow tana furta "dan uwarki parlorn na gidanku ne da
zaki shigowa mutane kai tsaye ba sallama ba gaisuwa?" Dukawa tayi tace "kiyi hakuri Anty sahla nayi
sallama sede baki ji bane ku......." a harzuke sahla tace "you are very stupid ni sa'ar uwarki ce ai da zaki
na min magana kina kallon tsakiyar kwayar idona" Shiru kuma tayi bata kara magana ba, sanin halinta na
baza ta sake magana ba kuma yasa sahla cigaba da aika mata zagi kala kala.



Ita ta rasa me tayiwa en gidan nan da suka tsaneta haka, duk cikin masu aikin gidan ba wadda suka tsana
kaman ita komai tayi bata burgesu, duk wahalansu da take sha ba me mata Sannu bare na gode,
maganan sahla ne ya katse mata tunaninta "kin 'bace min da gani ko se na mike na taka ruwan cikinki?"
Da sauri ta mike ta nufi d'akin Yasmeen, da sallama ta shiga sede Yasmeen dake zaune tana danna waya
ko d'agowa batayi ta kalleta ba bare ta sa ran amsar sallamanta.



"Anty Yasmeen gani" Shiru ta mata taci gaba da abinda takeyi seda ta shaaka don kanta tace "Don
ubanki bance kar na dawo na samu inner wears d'ina a toilet nan ba?" Hawaye ne cike tab da kwayar
idanunta wadda suka kara musu sheki, cikin rawar murya tace "Anty na ga sunyi stain ne and wannan
kaman sirrinki ne ke ya kamata ki...." bata karasa ba taji saukan rankwashi a kanta runtse idanunta tayi
wadda hakan ya baiwa hawayen ciki damar zuba.



"Wuce kije ki d'auka ki wanke min maza maza, har ke Kin isa ki gayamin abinda ya kamata nayi? Shegiya
me kama da aljannu da shegen turancin karyar da kika d'aurawa kai" cewar Yasmeen, da sauri ta wuce
hawayenta na kara yawa d'auko panties d'in tayi ta fito, daga nan saman ta bud'e wani kofa wadda ya
kasance stairs ne daga bakinshi har kasa ta gangara wurin tap da suka saba wanki da wanke wanke se
kuma irin girkin taro haka ruwa ta tara ta hau wankewa bayan ta shiga laundry room dake nan wurin ta
d'auko sabulu da omo.



Cikin tsantsan kyankyami da take dashi wadda ko ita kanta jininta da kyar take wankewa bare na wata,
cikin bakin ciki ta fashe da kuka, wani irin rayuwar rashin 'yancin kai ne wannan? Haka rayuwarta zata
kare? Cikin muryan kuka ta furta "Ammiee..... Abbiena me yasa kuka yi saurin tafiya kuka barni?" Se
kuka....



~~~~~~~~



Wayarshi kirar iPhone 11 pro max ce hannunshi yana kallon porn kaman yadda ya saba yayinda d'ayar
hannun ke rike da glass d'in wine me tsananin tsada sossai ya shagala da kallon wadda har be san an
shigo ba se ji yayi an fisge wayan, a Zafafe ya d'ago se suka had'a ido da wata had'add'iyar babe da yayi
d'azu wani kasalallen murmushi ya saki tare da janyo hannunta jikinshi yana shunshunata yace "hey hind
banyi zaton zaki zo ba ai".
Cikin karairaya irin na matan bariki ta sa hannu tana shafa wuyanshi zuwa kirjinshi da ya kasance naked
tace "na isa? Duk garin nan wace babe ce da ta isa ta amsa sunanta zata ji Kira irin naka na manyan
harka taki amsawa Ai babu shegiyar" wani irin dariya yayi ya kur'bi giyar hannunshi ya tsiyaya mata a
baki ta kuwa had'iye tana me shafashi nan take suka shagala suna yi suna kuma kallon sex video da
dama yake kallo. Allah ya shiryamu ya shirya mana zuriah.



~~~~~~~~~



A matukar gajiye ya bud'e motanshi kirar Hyundai Elantra ze shiga yaji ance "barrister Aayan" seda ya
runtse ido yayi kaman ze yi kuka da fuskanshi kan ya juyo ya Kalli abokinshi dake kiranshi "what again
shaheed?" Dariya shaheed ya fashe dashi yana nuna shi yace "ka ga fuskanka kuwa kaman irin baby da
uwa ta hana wasan kasa" had'e rai yayi yace "in ba ka da abin fad'a shaheed na wuce na gaji hutu nake
bukata" mika mishi file d'in hannunshi yayi yace "case d'in rape da kace zakayi handling d'in nan ne ka
san jibi za'a fara sauraran shari'ar ya kamata ka duba In kaje gida" kar'ba yayi ya had'a da blazer d'inshi
ya watsa sit d'in baya kan ya shiga motar ba tare da ya kuma tankawa shaheed ba ya ja ya fice don ya
san yace ze kara magana se ya kuma rikeshi da wani surutun.



Direct gidanshi ya nufa dake malamre nan jimeta dukda gida yake shirin shiga sede hankalinshi in yayi
dubu a tashe yake na tunanin abinda ze je ya tarar, mazajen aure na nufan gidanjesu ne cike da farin ciki
da jin daad'i sbd natsuwar da ako yaushe suke samu da iyalansu amma banda shi, ya gwammaci
rayuwarshi kan aure da wannan da yake ciki.



Da wannan tunani yayi horn a bakin ash iron gate d'inshi me gadi yazo da sauri ya bud'e mishi da adu'ar
shiga gida a bakinshi ya shiga yayi parking bayan ya d'an tsaya sun gaisa da me gadin, kallon inda
motanta yake yayi tana nan kenan bata fita ba, sit d'in Baya ya bud'e ya kwaso abubuwanshi ya nufi cikin
gidan da sallama a bakinshi ya tura kofan parlorn sede hautsatsiyar karni da ya tareshi ne yasa ya kasa
karasawa, tana zaune kaman kullum gaban extension wire hannunta rike da wayanta tana dannawa tana
dariya.



Kallon jikinta yayi tun kayan baccin da ya fita ya barta dashi wadda jiya ma dasu ta yini rintse idanunshi
yayi ya kuma bud'ewa sun kad'a sunyi ja ranshi a hautsine ya kalli tsakiyar parlorn komai d'ai d'ai ba
kimtsi ba komai cups ko ta Ina sbd bazata iya dafa abinci ba tana dannan waya ta gwammaci ta sha
wannan ta sha wanchan suma da kyar, wani irin bala'i ne wannan.
Be san sadda ya fara sana'ar tashi ba wato taunar Lips musamman In ranshi na a matukar 'bace,
idanunshi na kan 'yarsu kwaya d'aya sahar dake da 3 and half years tana bacci ita d'inma kayan baccinta
da ya sauya mata jiya ne jikinta kenan ba'a mata ko wankan safe ba, ga fuskanta duk jirwayen hawaye da
suka bushe alamun kuka ta sha har ta gode Allah uwar taki kulata.



In da sabo yaci ace ya saba da halin Zaheera, yana matukar bakin cikin ganin matar aurenshi a haka,
lumshe ido yayi ya kuma bud'ewa kan ya sa kafafunshi cikin parlorn direct kan sahar yayi ya d'auketa
suka haura sama ita kuwa zaheera ko motsinshi ma bata ji ba se murmushi take tana chatting, yana shiga
room d'inshi da niyyar kwantar da ita ta farka tana ganinshi ta saki murmushi tace "Daddy..." murmushi
shima ya kakalo yace "baby har kin tashi?" Kai ta gyad'a se ta marairaice tace "mi nyaman nyamdu
daddy"(zan ci abinci daddy) murmushi ya mata yace "toh first of all ayi wanka kan abinci right?" Kai ta
gyad'a.



Ya d'auketa zuwa toilet d'inshi dake wanke tas sbd kan yayi wankan safe yake wanke abinshi in ya fito ya
gyara gadonshi ya share d'aki ya fice in yaci sa'a normal ze dawo ya samu d'akin nashi kaman Yadda ya
bari but in har be ci sa'a ba jujun zaheera suka kawota d'akin toh fah kan ya dawo bola albarka.



wanka ya ma sahar ya fito da ita cikin towel seda ya shafa mata mai kan yaje room d'inta ya d'auko mata
riga da pant yazo ya sa mata se surutu take zuba mishi yana biye mata, a tare sukaje kitchen na saman
ya had'a mata tea me kauri tare da soya mata kwai guda biyu ya kawota parlor kan su zauna ma ta kusa
shanye tean sbd yunwar da take ji da kanshi yayi ta bata kwan har ta koshi, baki ta shangala mishi tana
buga ciki tace "daddy pim pim" yana murmushi yace "toh se d'ume?"(se mene) tace "a wannam
banchilili"(ayi mini banchilili).



Yace "toh ha mi yiwa minfu mi nyama se en wad'a"(to bara nayi wanka nima naci abinci se muyi) tsalle
ta fara ya mike ya barta nan ya wuce room d'inshi yayi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya tunaninshi
gabad'aya na ga kan matakin da ze d'auka kan zaheera, ga wannan yarinyar ba karamin shiga hakkinta
take ba, ba ma ita ba yanzu yadda ta barta a parlon da yunwa da komai tayi bacci da wani mugun ne ya
shigo ya sa'beta yayi gaba bama Zata sani ba fa tunda bama taji shigowanshi da d'aukan samha zuwa
haurowansu ba.



Ya gama yanke ze samu ummie da maganan zaheera for the last time tunda kullum hakuri ake bashi ace
kuruciyace zata dena, In taki sa mishi hannu wurin gyarata toh fa dole yayi wani aure don ba me aikin da
ze ajiye gidanshi, sahar kuma for now play class ze samu ya saka ta ko ba komai zata na cin abinci me
kyau in har me tsada ne.



Car key ya d'auko ya sauko sbd rashin ganin sahar sama tana nan tana wasanta da Teddy's d'inta tana
ganinshi ta kwala mishi kira wadda hakan ya sa zaheera farga da zuwanshi ta d'ago tana sosa kanta da ya
daskare sbd rashin gyara tace "au ashe ka dawo?" Be kalleta ba yace "uhmm" ta'be baki tayi ta maida
kanta kan wayarta shi kuwa hannun samha ya kama suka fice.



~~~~~~~~~~



Kaman daga sama taji muryan hajiya tana cewa "samun wurii, wato sbd Yasmeen ta sakaki wanke en
waennan kayan shine kike rusa wannan uban kuka? Wai me ya kawoki gidan nan ne In ba aikatau ba sbd
mutuwar zuciya irin na iyayenki, Toh kuwa sede kiyi kukan jini gama mata kije closet na akwai kayan
wankina cikin basket dama Adamu zan bawa amma tunda gaki Ai shikenan" cikin ladabi tace "Toh
hajiya" ta cigaba da wankin hawaye na kwaranya kan fuskanta, ba abinda yafi tsaya mata a rai irin yadda
suke cin mutuncin iyayenta da suke kwance a cikin kabarinsu ta san da Abbienta na nan ko Ammienta
babu wadda ze bari a turota aikatau gidan irin waennan mutane marasa tausayi sede ma ita ta saka ayi.



Hawayenta ta share ta mike taje ta shanya panties d'in Yasmeen daga nan ta kuma komawa saman zuwa
d'akin hajiya Allah ya taimaketa bata had'u da kowa ba ta d'auko basket d'in ta nufo kofar se tajishi a
kulle kuma murd'awa tayi da gaske dai an kulle kuma ba key jiki juyowa tayi tabi ta cikin parlorn anan ta
ga sahla rike da keys d'in tana juyawa bata ce mata komai ba ta sauka parlorn kasa anan ta ga hajiya na
zaune da wata bakuwa, bakuwar ta gaisar tayiwa hajiya sannu kan ta fice.



Babban abinda ya sa ta tsani bi ta nan sbd yaya Aadil ne part d'insu na nan daga inda yabi zuwa baya
hajiya kuma ta hana bin ta cikin kitchen da ko wani kaya In ba kayan da dama a cikin kitchen d'in suke
ba, aiko abinda ta tsani gani shi idanunta da kunnuwanta suka jiyo mata, had'a idanun da sukayi yasa
tayi saurin ta'awizi tana neman tsarin Allah da sharrinshi, iskanci a filin Allah.



Seda ya mata kiss kaman ze cinye bakin kan ya d'aga mata hannu tana godiya ta fice akan zasuyi waya,
kallon bayan Bilkeesu yayi tare da lashe baki yace "in har sunana Aadil Sadeeq Chubado se na koya miki
hankali, ba ni kike kyama ba?" Yayi wani irin dariya kan ya juya ya koma part d'inshi dama rako hindu
yayi bayan sun gama masha'arsu ya cika ta da kud'i.
Sarai ta jishi sede bata tanka ba se ma kara sauri da tayi zuwa backyard d'in nan ta sunkuya wankin
hajiya, tana cikin yi aka kira magrib bari tayi tayi alwala nan bakin pampon ta nufi part d'insu tana shiga
taga Indo cikin murna ta rungumeta tace "indo yaushe kika shigo ban ga wucewarki ba?" Itama indo
cikin farin cikin ganinta tace "ban jima sossai ba wuraren biyar haka" Bilkees tace "kila lokacin naje
d'auko kayan hajiya, sannu da zuwa ya mutanen gida?"



Tace "suna nan kalau" bilkeesu tace "bara nayi sallah se muje wurin wankina Ina yi muna hiran yaushe
gamo" sallaya ta shimfid'a ta tada sallah itama indo toilet d'insu ta fad'a tayi alwala ta fito ta tada nata
sallahn a gefen bilkeesu inda baaba lami ma na chan tanayi.



Bayan sun idar tana ninke sallaya indo ke tambayarta "banga su grace ba" Tace "suna kitchen da rana
ma seda muka kwasa da blessing ganin abinda en gidan nan ke min yasa su ma suke neman maidani
jaka" dariya indo tayi tana ajiye khimar d'inta Don ita yawo take ba wani khimar a gidan sa'banin
bilkeesu da seda hijabi take fita daga d'akinsu, tace "me ya had'aku?" Baaba lami da take ta lazaminta
bata tankasu ba se binsu da tayi da ido har suka fice Bilkeesu na cewa "wai fah kayan miya aka kawo
dayawa a lokacin ma gyaran d'akin Anty Yasmeen nake kuma ga na su khalil da ban gyara ba Sannan ga
wankin jibgin inner wears d'in Anty Yasmeen wai ta sameni wai hajiya tace In zo muyi gyaran kayan
miya".



Dariya sossai indo ke yi sbd yadda bilkisu ke kwaikwayar maganansu itama se murmushi take kaman
bata da wani damuwa Alhalin kasan ranta duhu ne baki kirin, indo tace "Toh me kika ce musu?" "Ke ma
Ai kin san abinda zance, cewa nayi bazanyi ba" wani dariyar indo ta fashe dashi tace "yanzu da da gaske
hajiyarce ta aikosu fah?" Ta'be baki tayi tace "na san karyarsu na kuma san ba aikosun zatayi ba".



Seda suka isa wurin wankin nata da hasken security light d'in gidan ya haska ko Ina tarwal kaman rana
kan indo tace "bara naje nayiwa hajiya sannu da gida ta san da dawowata" Kai kawai bilkeesu ta d'aga
mata yayinda ta ci gaba da wankinta, kaman daga sama taji ance "Ke" Da sauri ta d'ago a firgice ta matsa
jikin gini ta mannu tana kallonshi da idanunta dake kara sashi jin tsantsar kwad'ayi da sha'awarta.



"Ki je d'akina akwai plates da na ci abinci yanzu ki fiddo ban son kazanta" dakewa tayi don baza taje ba
sede hajiya ta kila ta yadda ta saba In ya aiketa d'akin shi taki zuwa, kallon wurin tayi ba kowa so quit se
ta fara ambaton Allah cikin dakiya tace "ba aikana ba kenan, as you can see wanki nake" matsota ya fara
a harzuke yace "kee!! Wai me kika d'au kanki ne? Ina sa'a dake da kullum zan sakaki aiki kice bazakiyi
ba? Kin kuwa san waye ni?" Hannunta ze rike ta fisge ta matsa tana cewa "Wallahi bazan je ba In ka ga
dama sa wuyana gabas ka yanka" a zafafe ya kuma nufota ihu ta kwala se ga baaba lami bayanta ta
riketa tana cewa "lafiya Alhaji Aadil?" Lip d'inshi na kasa ya taune yana aika mata sakon harara ya juya ya
fice.



Kuka ta fashe dashi tana furta "ya zanyi ne da rayuwata? Ya suke so nayi dan Allah?" Cike da tausayinta
baaba lami tace "Bilkisu na d'aukeku kaman 'ya'yan da na Haifa a cikina bazan ta'ba son wani
mummunan abu ya sameku ba musamman ke da Aadil ya sawa ido, bakya ganin kaman komawanki
gidanku shi yafi alkhairi?" wani irin murmushin takaici ta saki kan tace "hmmm baaba kina ganin akwai
banbanci tsakanin gidanmu da nan ne? Gani nake ma gwara nan zasu iya min in hakura amma chan fah?
Gwara duka da gallazawar hajiya akan na mama, gwara barazanar Aadil akan na shu'aib gwara hantara
da kyara irin na Yasmeen da sahla akan ummu hadiyya da Zainab gwara anan khalil da fahad suna bani
girma akan yasir da yassar, a nan ban ta'ba ganin mahaifinsu ba bare ya bada gudumawa kan abinda ake
min amma a chann......." kuka ne yaci karfinta wadda ya hanata karasawa......




*Amm a wannan Karon bazaku samu yadda kukeso ba sbd abubuwa da suka d'an min yawa maybe inyi
typing sau hud'u a sati maybe sau uku In na samu sarari kuma kullum In Shaa Allahu. Fatana dae kawai
shine inga ruwan comments*




πŸ–€GureenjoπŸ–€

[15/07, 6:26 pm] Diddi Walida: πŸŒ•πŸŒ•
πŸŒ•LELEWALπŸŒ•

πŸ¦‹FARIN WATAπŸ¦‹



πŸŒ•πŸŒ•



STORY AND WRITTEN BY:- Fatima Muhammad Gurin.



MARUBUCIYAR:-

ZUHRAA

HAMRAH

IGIYAR RAYUWA

NOOR IMAAN and

RUWAN SAMA.



FOLLOW ME ON WATTPAD @Gureenjoh6763



SADAUKARWA:- wannan littafin gabad'ayanta sadaukarwace gareku @68Billygaladanchi wato Anty billy
and my dearest sister haneefah Muhammad Gurin thanks for your Advices and support Allah ya bar
kauna.



JAN HANKALI:- Toh masoya na ga ni da sabon labari kaman yadda kuka dad'e kuna tsumayi, am not
perfect but I promise to give you all my best on this, akwai tufka da warwara masu matukar sarkakiya a
wannan labari. Kaara d'aya zuwa biyu nake bukata daga gareku please ku Nuna min jin daad'inku ta
hanyar comments and share ta yadda ze karad'e ko ina, wannan littafi kyauta ne domin jin daad'inku
masoyana. Na godeπŸ₯°πŸ™.




EXQUISITES WRITERS FORUM πŸ“
(Home of exquisite writers')



Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai.

β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”β€”



2
.........
2️⃣ 2



Dafa kafad'unta baaba tayi dukda kuwa tsawo da bilkees ta fita cike da tausayawa tace "Daga ranar da
na fara ganinki bilkeesu na san akwai murd'dd'iyar abu cikin rayuwarki, kwarai na kasance me matukar
tausaya miki Allah ya kawo miki mafita" rungume baaba kawai tayi tana me ci gaba da hawaye cikin
rawar murya tace "kwarai kuwa baaba rayuwata bata da wani abu face duhu me matukar sarkakiya
tabbas a Baya nayi farin ciki sede ya wanzu a rayuwata ne na lokaci kankani, na gode kwarai da
kulawarki watarana zan baki labarin bilkees.." tana kai nan ta d'ago ta share hawayenta tare da sakin
murmushi tace "baaba bara na karasa wankin nan kar dare ya min".



Da mamaki baaba ke kallonta kaman ba itace ke kuka yanzu ba, ta jinjinawa matukar dauriya da shanye
damuwa irin na bilkisu, ita ma murmushi tayi kan ta wuce, bata kai ga kulewa ba indo ta dawo kallonta
bilkees tayi tace "se yanzu? Ko wani aikin aka saki?" Girgiza kai tayi tace "na tsaya kallon dramar ya Aadil
da yayanshi ne" bilkees na me cigaba da wankinta tace "ya zo ne?" Indo tace "har ma yayi zuciya ya fice
kuma fah da 'yarshi yazo baki ga kyaunta ba" d'an kallonta bilkees tayi tace "zuciya kuma?" Indo na
tsoma hannunta cikin wankin Don tayata tace "eh kin san ya tsani halin Aadil na bin mata so yana
kokarin shigowane yaga wata karuwa da ta fita daga gidan nan shine fah yazo ya haushi da fad'a hajiya
kuma ta shiga ta kareshi Toh ko zama be yi ba ya fice".



Girgiza kai bilkees tayi tana cewa a zuciyarta 'ashe ba ni kad'ai bace na kyamaci wannan hali na ya Aadil'
a fili kuwa cewa tayi "oh watana uku a gidan nan amma Allah be yi na ga wannan yayan nasu ba" waro
ido indo tayi tana cewa "ashe fah baki ta'ba ganinshi ba duk ya fi su kyau da hankali har Anty Sumayya
da Anty Rufaida kuwa ga 'yarshi Masha Allah In kin ganta" murmushi bilkees tayi tana cewa "wata rana
zan ganshi Ai tunda Ina gidan".



Daga nan ta kauda hiran en gidan suka koma na kauyen su indo se labari take bata tana dariya, kusan
8pm suka gama wankin, bilkees na da tattare parlorn kasa inda anan suke cin abinci hakan ya sa indo
d'auka musu dinner d'insu ta wuce shiyarsu na masu aiki da ya kasance da d'akuna manya biyu kowanne
da kewaye an zagayeshi Sannan tsakiyar ya kasance kaman zaure da aka sa mishi tiles.



'Daki d'aya ya kasance su su uku indo, bilkees da baaba kowacce da katifanta kuma su ne masu share
share na cikin gida, se baaba lami dake girkin abincin gargajiya a duk sadda suke marmari ko Alhajinsu ya
dawo, d'ayar d'akin kuma na grace da blessing sune masu aikin duk wani abincin da ya shafi turawa.



Da sallama ta shiga parlorn Allah ya taimaketa sun haura Don chan take jin muryoyinsu suna hira, a
tsanake ta tattare parlorn tsab duk wasu kwanuka dake dining wadda suka ci abinci suka wargazar ta kai
kitchen ta goge dining d'in tare da share parlorn, a gajiye ta mike da ta gama aikin sbd bayanta da ya
kama lumshe ido tayi ta kuma bud'e komai normal se ta ja kofa ba tare da ta kashe wuta ba sbd su
Fahad da zasu sauko zuwa d'akinsu dake parlorn kasan In sun gama hira.



Seda tayi Alwala a tab kan ta wuce d'akinsu hira ta samu baaba nayi da indo yayinda abincinsu ke zaune
suna jiranta ba tare da tayi sallar da tayi Niyya ba tayi joining d'insu suka ci abincin, dake a ka'idarta In
tana cin abinci In ba ya kama dole ba bata ta'ba iya magana hakan ya sa sede ido take binsu dashi tana
gamawa kuwa ta mike ta kurkuro baki tazo tayi sallah tare da gabatar da shafa'i, kasancewar tana tashin
dare yasa batayi wutiri ba kan ta idar indo ta tattare inda suka ci abincin kwanukan se gobe in sun tashi
fita zasu fita dashi sbd tsoron sharrin mutan gidan.



Hamma ta saki tana kallon indo dake son fara janta da hira tace "ke wallahi bacci nake ji kaman me
bazan iya biyewa surutun kin nan ba" kwanciya tayi tana jin yadda indon ke mita bayan ta gama
adu'o'inta na bacci ta shafa tace "baaba se da safe" baaba da ita ma ta kwanta tace "Allah ya tashe mu
lafiya d'iyar albarka" sossai bilkees taji daad'in sunan se ta lumshe ido kawai tana tuno mahaifiyarta, a
lokaci d'aya tana dariyar indo sbd ganin ta kashe wuta itama ta kwanta sbd ba me biye mata ayi surutu
har da hawayenta, kan kace me bacci ya sureta sbd wahalan da ta sha na aiki.



~~~~~~~~



Abinda ya faru kuwa ta 'bangaren Aayan yana danna horn na shigowa gidan nasu yaga wata ta fito da
wani irin shiga na Allah wadai cikin takaici da jin haushi yake kallonta har ta fice, gaba yayo da motarshi
ya sauke glass yana kallon baba lawalli dake gaisheshi sama sama ya amsa ya d'aura da "wan chan
bakuwar hajiya ce?" Girgiza kai yayi yace "a'a Alhaji karami wurin Me gida Aadil ta zo" had'e rai yayi yace
"tun yaushe?" Me gadin yace "tun bayan la'asar ranka ya dad'e" lip d'inshi ya taune yana

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment