Reading UWA KO UKUBA COMPLT BY M SHAKUR Chapter 42 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Asmeey ohh Allah kenan yarinya har tayi ciki abinta."

Around 6 Mama itama ta iso itama batazo da yara ba sabida school Asmeey bata wani rungumeta ba

"kaman yanda tama Ammi ba bawai she hates Mama bane kawai tasan Mama yar fadan Mom ce so she s kind of scared of Mama sabida Mom, Gwaggo tace  saura nafara jin zancen gidan nan awani waje sa idawa an diro, Mama tai banza da Gwaggo tanabin gidan da kallo tace  gida ya chanza gabaki daya kaman kasan waje na kirga motoci sunfi akirga sababbi a tsakar gidan Mamie tace  an gode Allah sulalewa Asmeey tayi ta kwashe abubuwanta tawuce sama mijinta by 9 zai sauka akano na dare around 7 zata sauko tamasa girki, da magrib taje tai salla sannan tafito tashiga saukowa kasa a dinning taga Mamie na magana da Mama tazo wajen tadan tsaya Mamie ta kalleta tace  Yaya akayi Asma u? Kin magana Asmeey tayi Mama tace  uhnn nidai na wuce takoma kitchen da sauri Asmeey tazo kusada Mamie kanta akasa tashiga wasa da hannunta Mamie tace  ina jinki ahankali Asmeey tace  uhmmm& ..Mamie& .d& .dama so nake nai girki sarai Mamie tagane sotake tama mijinta girki dudda Mamie tama Hamadi abinci da dama yanzu hakama akwai some a wuta amman sai anatse tace  zaki iya? Gyadama Mamie kai tayi Mamie tace  tom muje kiyi sai atayaki rage ayyuka me zaki dafamai? Ahankali tace  taliya Mamie tace  okay shiga kitchen din sukayi Mama na soya kifi a pan, kifin Asmeey takalla ga kamshin na dukan hancinta kawia taji cikinta ya hatsine, tun aman brush na safe yau batai wani ba she was very happy hartana cewa ta warke sai yanzu hannunta tadaura abaki tai wani kakarin amai da sauri daga Mamie har Mama suka kalleta Mamie tace  you see ba tashiga bude mata kofan backyard dasauri tafita kafin takai wajen grass ma tafara amai ba kakkautawa duka abincin da Asmeey taci yau taketa murna ya zauna saida ta amayar, Mama takashe gas tafito tana kallon ikon Allah itama tana mata sannu Mamie na bubbuga mata baya tace  sannu, yau baki amai ba inata murna amman kalli yanzu fitowa Gwaggo tayi dan ta window tajisu cikeda fada yace  mema yakaita kitchen din iyye? Ke wai bazaki rufama kanki asiri ki lallaba wannan cikin naki me mugun laulayi ba! Faduwa gaban Mama yayi cikinta har wani kyarma yake no wonder taga yarinya tai fara kal kaman zata koma zabiya tayi kyau jikina ne dai babu ashe ciki ne da ita, wankewa mata fuska Mamie tayi Asmeey ta kuskure baki ta mike tace  bari na wanke aman chan Mamie tace  nasaki? Oya zagaya ki koma compound ki shiga ciki kiwuce sama Gwaggo tace  barta sotake ta fiffige kamin Hamadi ya iso Ammi data fito tace  ba shuwaka ne idan zuciyanta na tashi taci yanamin aiki lokacin Mamie tace  banda shuwaka shine kawai abinda ban shuka agarden ba nama manta, Ammi ko zaki dan tayani kaita daki ba karfi jikin nata dasauri Ammi takama Asmeey suka zagaya suka shigo sukai sama har dakinsu Ammi ta kaita ta kwantar da ita ta zauna gefen gadon tace  sannu kinji haka ciki yake Allah saukeki lpy, the journey is not easy hawaye ne yataru a idanunta ahankali tace  Ammi nagaji da wahala, inaso nayi girki amman koyaya naji kamshi sai cikina ya rikice dariya Ammi tayi tace  hakanan zaki saba kuma yanzu kika fara kuwa zaki saba ne sabida na farko ne saisa kikejin wani iri ahankali Asmeey tace  Ammi ina Mom? Dan shiru Ammi tayi tana kallonta Allahu Akbar she just pity this girl yabda takeson mahaifiyarta, murmushi tayi tace  tana Abuja za a maidata Chief Judge na Bauchi taje tai paper work murmushi Asmeey tayi cikeda jin dadi tace  finally! Mom tadade tanason that position I am so happy wlh Allah sa albarka ahankali Ammi tace  Ameen bari naje ta tashi tafito gama soya kifin Mama tayi jikinta har kyarma yake"

daidai wayanta na ringing Ammi ce kadai a kitchen din tace  bari nai waya da yaran nan suke kirana

Ammi tace  agaidasu ficewa Mama tayi ta kofar baya tai backyard din tama bar wajen duka tana

"rejecting call na Nana tashiga kiran Mom ta zaga chan hanyan dazai bullo dakai asalin compound yanda babu wanda zai ganta tashiga kiran Mom, is as if Mom has been waiting for her call yana ringing ta daga tace  ke Maman Aya kinsan meke faruwa kuwa? Da zafi zafinsa nakira na baki update dan ijiyan zuciya Mom tasauke cikeda gadara tace  ina jinki dan juyawa Mama tayi tai kalle kalle dan kara tabbatarwa babu wanda yabiyota tace  kin kosan Asmeey nada ciki! ? Wani durum news din yadaki kan Mom, wallahi wallahi to some extend bata tabajin dar na yaron nan zai kwanta mata da diyaba sabida she believe abubuwan data gayama yarinyar nan ko Asmeey na hauka bazata yarda tabudema mahaukacin nan kafafu ba, yanzu Asmeey ta tsallake tsinuwanta ta aminta da mahaukacin nan kutumar uba, Asmeey bata tsoronta kuma? Kasa yarda Mom tayi tasan Baba forced the girl a aure she can stay ba yanda zatayi but budema yaron kafa after everything she told her is very impossible, no she don t think ciki Asmeey ke dashi, tace  anya Maman Nana!? Anya Asmeey nada ciki ? Dasauri Maman Nana tace  na rantse miki da girman Allah ciki ne da Asmeey kumama irin cikin nan dakaman tana shigowa ta sameshi ayanda take laulayi da kyarne idan bata cikin wata na uku to duka duka bikin nasu ai wata uku ne da yan kwanaki"

"yanzu, that means ana musu auren basu wani bata lokaci ba sukai tarayya! ."

EPISODE

Jikin Mom harwani kyarma da zabura yake sabida bacinrai tama kasa magana ita Asmeey zata watsama

"kasa a idanu? Ita Asmeey zara yarda ta amincewa mahaukacin nan bayan duk abubuwan data gayamata? Asmeey dares sleep with that imbecile? Mama cikin exaggerating abu tace  ciki dai dakika sani shi Asmeey ke da shi sai uban laulayi ta  katse wayan tayi da sauri jin sahun tafiya tajuyo afirgice,"

"Mamie tagani Mamie tahada rai sosai, murmushi Mama tayi tace  Mamie kece wlh nida su Nana ne kinsan yara ba kunya ko shakka dan enough is enough strictly Mamie tace  idan gulman yarana kikazo yi Maimuna ki tattara inaki inaki yanzun nan nasaka amaidake airport kinemi jirgin Gombe kitafi dasauri Mama tace  laaa Mamie? Meya faru? Wannan maganan fa maiya kawota? Cikin tsananin bacin rai Mamie tace  kul Maimuna karki rainamin wayau ni ba tsaran wasanki bane, danayi aure dawuri zan iya haihuwarki wlh da kadan kika darama Mustapa na ashekaru! Nasan dawa kikai waya, I know duka abubuwan dakikayi tun a Bauchi nasan ke kika sanar da ita zancen auren in the first place, daga zuwanki harkin kirata kina sanar da ita zancen cikin Asma u, cikin shege tayi dakika kai gulma? Koko an gayamiki cikin baida uba ne? Ke uwace kin haifa yara mata bazaki daina wannan halin haddasana ba? Da ace dan alkhairi kika bada sanarwan cikin nan bazanji haushi ba amman kinfi kowa sanin waye Salima wani fitinan kikazo shiryamin agida? Ko ko so kike kada ayi bikin yarana lafiya iyye? Sunnar da kanta kasa Mama tayi kunyan duniya yagama lullubeta, Mamie tace  Allah yakaimu gobe da safe ki tattara kibarmin gida nagaji da halinki zumunci ba dole bane inhar abin yakai ga haddasa bala i da fitina, daga zuwanki kin"

"farakai gulman yarana har kina lissafin sanda yarinya tai ciki, yar cikinki fa shame on you Maimuna!"

"Shame on you! Mamie tajuya zata tafi dasauri Mama tariketa tace  dan Allah ki yakuri Mamie, wallahi"

"na rantse miki da Allah badan haddasa bala i kowani abun na gayamata ba cikin fushi Mamie tace  amman kinsan waye Salima? Baki tausayin yar yarinyar nan dake fama da laulayi tarasa inda zatasa kanta taji dadi? Haba Maimuna ke mace ce kin haifa fa kinada yara mata, kema u were once in Asmeey s shoe kowa yasan ya cikin farko yake, banda haka shi d a nakowa ne, baki tausayin Asma u? Idan matar nan tazo tamata jina jina fa? Mezakice? Kinada alhaki da kamasho a zunubin, U are a mother u should protect Asmeey at all cost not expose her to mutum kaman Salima, kibarmin gida I am very serious nagaji da munafuncinki Maimuna nagaji, bikin nayafe miki kitafi, ban bukatar ki wlh har abada ran Mamie yayi tsananin baci is not like ta tsani Mom but kawai tasan matan ta tsani yarta taji zancen cikin nan she can do the unthinkable, saita iya kashe yarinyar nan, tunda har tabata maganin bera she can kill Asmeey har lahira tsaf, Allah kadai yasan mata dalilin dayasa ta tsani yarta and now look at wat this witch munafukar is doing, sumazo ayi bikin Alhamdulillah an gama komi na Asmeey tare zasu koma DC yanzu, Mama na bata hakuri tawuce tashiga kitchen Ammi tabi Mamie da kallo da ranta yake a bace"

danta jisu ita daman tasan tunda har Mama tafita munafinci zatayi.

Sanda Mamie ta shigo kitchen ta tambaya ina Mama cemata tayi tafita tayi waya da yara taga Mamie

tabita abaya cus Mamie tasan hali.

Chan saiga Mama tashigo duk hankalinta tashe takalli Ammi dan yanzu harga Allah tafi damuwa da

"fushin su Mamie cus yanzu sune masu kudi ga Hamadi bai riga yabasu komi ba su har yanzu yaron nan zai iya yabasu miliyan goma goma fa itada Ammi kuma yabasu kujeran makka dasauri tace  wlh Ammi ba gulma bace kawai hira ne ina shiri da Salima kowa yasani tace na barmata gidanta so take ta bata zumunci Ammi tace  zumunci or not ba huruminki bane ki sanar da Salima zancen cikin Asmeey ba kibar diyarta ta sanar da ita ko mijin diyarta ko ita Mamie ko Abba ko Baba koni banda hurumin gaya mata balle ke mesa kike haka ne? Daga zuwanki da yamman nan harkin fara halin, idan an girma asan an"

girma .

Cikeda rashin jin dadi Mama tace  dan Allah kiyakuri hakan bazai kara faruwa ba Ammi kawai tawuce

abinta.

Duka yayyins tundaga kan Ya Mustapa down to Hameed dukansu na airport sunzo daukan Hamad tun

8:30 dan 9 jirginsu zai sauka but andan sami delay sai 10 suka sauka kafin yafito 10:35 sabida immagration.

"Ahankali yake tafiya yana sanye dawani long pant black mai bala in kyau, ya sanya wata Rapl Lauren polo"

"shirt fara sai kuma wani jacket na sanyi haka leather black asama dayake a bude yana goye da bagpack dinsa abaya na laptop sai LV box nasa guda daya tak yana gungurawa yana tafiya anatse dayake darene ba glasses a idanunsa yawani kara kyau fatarsa na kyalli sosai, yana sheki gashin kansa da gemunsa sun kara yawa cus all this while baitaba aski agarin ba, sai yawani kara girma wlh looking damn matured sama da Hameed ma and looking very rich yana sanye dawani Rolex wristwatch a hannunsa, kagansa saika kara kallonsa sabida yanda yayi kyau dukansu kallonsa suke babu motsi, shi baima lurada su ba"

"kaman ba Hamad ba, Faisal yace  Hamad ne yawani kara balaga haka? Hameed yace  yafini girma"

yanzu Innalillahi yaci abincin turawa Ya Abdullahi yace  kai my brother is looking very expensive wallahi

Tubarkallah Hameed yakasa daurewa kaman wani mace yayi ihu Hamadi dasauri Hamad ya tsaya ya waigo ya gansu Hameed yataho da gudu baiyi wata wataba yawani rungume dan uwansa Awani irin kunyace Hamad ya sauke kansa duk yaji kunya su Faisal suka taho suka rungumesa duka yace  Welldone da dirkama Yar Mutane ciki ka gudu kasan waje ka barmu da raino ciki kaman zai kasheta koma me kasamata acikin nan akwai fitina kaman kai Ya Abdullahi yace  Hamadi when did you even sleep with

that girl harka mata ciki ni dannan ?.

EPISODE

Turesu Hamad yashigayi sukaki sakinsa kaman zaiyi kuka yadago kansa looking for who to rescue him

"daga hannunsu akunyace yace  Yayaaa ahankali Ya Mustapa yashiga zuwa anatse, Ya Abdullahi yace  wlh Ya Doctor karka shiga maganan nan, yanda maganan nan ya tsayamin a wuya, he must explain o Faisal yace  munafukin yaro yadinga buga coitus yana tumurmusan yar mutane babu wanda yasani saidai ya tafi ya barmana result of good knacking! Sannu sharp shooter Hamadi fizge kansa Hamad yayi da sauri yawani fada jikin Ya Mustapa ya rungumesa asanyaye kunya kaman zai kashesa, ahankali yace  ina yini Yaya biyosa zasuyi, Ya Mustapa ya daka musu tsawa yace  leave this boy alone me haka kukeyi an airport? Zanci muku mutunci fa Kyalesa duk sukayi kowa na kwafa, Hameed yaja jakansa Ya Mustapa yace  let s go dagowa Hamadi yayi suka shiga tafiya yana gefen Ya Mustapa yaki yarda ya kalli any one of them kunya kaman zai kashesa wlh shi yasan daman ya shiga uku yadawo yanda sukasan Asmeey is pregnant dinnan, kowa yasan meyayi yanzu, suna zuwa waje motan Ya Mustapa yayi dayaga na dane har yanzu mesa bai chanza mota ba yadai shiga yayi shiru Faisal da Abdullahi suka shiga mota daya Hameed shima ya shiga motan Ya Mustapa, gida suka wuce sukai parking Hamadi yafito wani sanyin dadi da peace yaji jama a home is just home kawai and home is where the heart belongs and no place like home, gidansu yafimai hadadden gidansa a DC sau miliyan, labule Mamie tadaga hangota Hamad yayi sai kawai yashiga sauri yawuce Mamie na bude kofa yana kaiwa wajen kaman wani dan yaro yace  Mamie "

"yawani hugging Mamie Mamie ta kankamesa sosai tace  Hamadi! Kainake gani haka? Kaine ta kankamesa, Gwaggo ta taso tace  wai ke kadaine mai yaron nan sakin Hamad Mamie tayi Gwaggo tazo zata rungumesa kaman matsoraci yadan koma baya Mamie ta girgizamai kai hakan yasa ya tsaya da kyar ta rungumesa tace  Hamadi yadawo yadawo Hamad yadan koma baya ta sakesa Abba dake falo yace  kubarsa ya shigo mana ahankali suka matsa ya shigo kansa akasa yaga Ammi da Mama yace  ina yini ku atare sukace  sannu da zuwa Hamad yayi hanya Mama sai kallonsa take to karya aka musu ne ance suna kasarwaje tareda Asmeey gasa shi kadai yadawo, tadai hadiye maganan ganin ko kallon inda take Mamie batayi, ahankali Hamadi yawuce wajen Abba daya mike yana masa murmushi zai duka ya gaida Abba abba kawia ya rungumesa cikeda so yace  ahlan wa sahlan marhaba dasu lale ya hanya Hamadi "

sakinsa Abba yayi anatse yace  Alhamdulillah suka zauna aka shigo aka zazzauna Mamie da Ammi da

Mmaa suka shiga fito da abinci Hamad yadan saci kallon ko ina a falon saikuma yakalli su Mamie dake

"fitowa daga kitchen harda dan kara lekawa kowa yana luradashi, Ijiye abincin sukayi Mamie tawuce sama dakinsu ta shiga wanda tasan Asmeey tai bacci yanda tasha uban aman nan kuma yau excitement yasa batai baccin rana ba kwata kwata allah sa ta iya tashi, tana kwance akan gado sanye da atampan jikinta ko wankan dare batayiba balle chanza kaya Mamie tadan bubbugata tace  Asmeey, Asmeey amman ko gezau batayiba Mamie ta girgiza kai tace  Allah sarki ciki kenan, yammatana anyi ciki kalli yanda bacci ya shigeta bargo kawai Mamie taja tarufa mata tabude kofa tafito tashiga saukowa Hamad yakalli benen da sauri kowa na lurada shi, Mamie tadan kalli Hamad daya maida kansa kasa da sauri tace  yau gabaki daya batai baccin rana ba, nayi nayi ta tashi taki anatse Ya Mustapa yace  gwara dakika barta Mamie tashinsu a bacci is not good yana samusu migraine and other ciwo dan boyayyen ijiyan zuciya Hamad yasauke yashigacin abincin da tsakura yake but yaci still cus yayi missing abincin Mamie, yanaso yatashi yatafi sama amman yasan yana tashi yayyinsa will eat him raw Abba yayi gyaran murya yace  Doctor sha biyu tayi a tashi kowa yaje gida wajen iyalinsa, Hamadi jekai wanka kahuta mikewa yayyin sukayi Hamadi ma haka sukai sallama suka wuce Hamadi yawuce sama Hameed natayasa daukan jakansa har sama zuwa gaban dakinsa yawuce dakinsa ya shige shikuma Hamad ahankali yasa hannu yabude dakinsu gabansa kawai sai faduwa yake ya shiga ciki Asmeey yagani kwance agado maida kofan yayi yarufe without making a sound yasa key, yajuyo yakalleta tana sanye dawani brown atampa mai red pattern yamata kyau sosai kanta babu dankwali amman tayi kyau, kitsonta sunyi kyau sosai she s deeply asleep tana sauke ijiyan zuciya ahankali, gently yashiga wucewa har zuwa gaban gadon ya tsaya yana kallonta kafin ahankali ya zauna yamika hannunsa daya yakama hannunta kafin gently yakai dayan hannunsa yadaura saman cikinta murya chan ciki yace  Assalamu Alaykum Habibty and my little one, why are u making Momma sleep too much? Momma couldn t even wait for Abee because of you? Haka zamuyi? Uhm little baby ? Yayi shiru yana murmushi sai kawai yahau kallon fuskan Asmeey wani irin tausayi da sonta na shigansa duk namijin da bazai tausayama matarsa mai ciki ba baida imani, the way Asmeey was happy akan dawowansa to finds her sleeping yanzu just shows the journey na bringing human into this world is not easy, u have no control about rayuwanka from d day kayi ciki har zuwa haihuwa da sanda zaka aurar da yaro, murya chan kasa feeling very greatful to Allah daya basa ciki, and thankful to Asmeey for being the source of this blessing yace  thank you for doing this journey for me Husnahhh ta rame sosai but he promise he will take care of her harsai tasami lafiya jikinta yadawo bazai kara bari tai komi ita kadai ba, he will show her this pregnancy banbancin kawai shine ajikinta ne but this journey is so for both of them, he will be her support and her strength, he will be he comfort and peace, he will gives her the entire world if needed sef, cus he extremely love matarsa and loves"

their child datake dauke dashi.

Har wajen biyun dare yana zaune awajen just watching her sleep and turns yana rike da hannunta still

"sannan yatashi ahankali yawuce bayi yana kallon basket nasu babu kayan wanki ko daya bayi yashiga yaga ta jika under wears nata guda uku a karamin bowl kafin yayi wanka ya wanke mata ya shanya mata a igiya sannan yayi wanka, yafito yaciro jallabiya yasa she told him about batason turare sai baisa ba yadawo ya shimfida dadduma yahau salla har asubahi yazo gadon yakara rufamata bargo da kyau"

sannan tawuce yafita yatafi mosque.

Wuraren 5:30 Asmeey ta tashi firgigit ta zauna tabi dakin da kallo akwati data gani kwance abude da

"bagpack din Ya Hamad da takalmin data siyamai na Nike a gefe, dakin smells him yasa ta tashi tsaye da gudu tawuce bayi tabude bashi ciki ko kula da panties din batayi ba tafito tai kasa ba kowa tayi Kitchen ba Mamie ta hayo sama dakin Mamie tayi da sauri tai knocking Mamie tace  shigo dasauri tashiga Mamie na kallonta tasan ko salla batayiba ahankali tace  Mamie Yaya yadawo? Murmushi Mamie tayi tace  eh anyi anyi kitashi kinki wani murmushi Asmeey tayi tarufe fuskanta, Mamie tace  yana masallaci maza jeki wanka kici gayu kafin mijinki yadawo daga masallaci gyadama Mamie kai tayi tana wani irin murmushi tajuya tafita she seems so excited Mamie tabita da murmushi sunason junansu sosai Alhamdulillah, dasauri ta shiga bayi murmushi tayi Allah sarki harya wanke mata pants bata ijiye pant but this days omo yanke mata fara suke saisa take jikawa saita nemo leda tasa a hannu take wankin, brush tayi as usual saida tayi lafiyayyen amai sannan tai wanka bata using sabulu sabida ta tsani kamshin but yau saida tayi tana rike numfashi tadauro alwala tafito salla tafarayi sannan ta shirya cikin wani riga da skirt na lace maroon and black ya zauna a jikinta sosai, light makeup tayi ta daura dan kwali takawo wani maroon veil ta yafa tayi bala in kyau hadken fatanta yafito, ta gyara gadon tsaf sannan tabude kofa tafito ahankali Gwaggo na falo tace  ke gasan kyau zakije ne? Hararan Gwaggo tayi tace  ina ruwanki dani mutum sai sa ido Gwaggo tace  kaniyarki au sabida mijinki yadawo zamu fara fada ko yar adam ajiza hanyar kitchentayi ba Mamie kadai ha har Ammi da Mama saida suka kalleta Mamie tace  wuce falo girki ake kafin kifara mana amai akunyace tajuya tana murmushi Mamie tai murmushi wajen window Asmeey tawuce tadan daga labule takosa yadawo Gwaggo tace  wai me kike lekawa a window ne ? Dasauri Asmeey takalli Gwaggo kaman ta maketa ta tashi tabar wajen tadawo ta zauna bayan kusan 10min takara tashi taje wajen window tadaga Mamie na hangota daga kitchen daidai Hamad shi kadai yana bude gate yana shigowa dawani irin gudu Asmeey tasaki window tayi kofa tabude tafito ko kulle kofan batayiba ta tsaya chak tana kallon Hamad da shima ya tsaya chak yana kallonta cikeda wani"

"mahaukacin so,"

"Asmeey gani tayi Hamad ya chanza mata gabaki daya kaman ba mijinta ba he looks too classy, expensive"

"kaman yaran masu kudin da aka haifesu kasan wajen nan, kirjinta nawani irin racing yana bugawa kaman yau tafara ganinsa takasa motsi, ahankali Hamad yawani daga mata hannu yabude su alamun oyoyo, yanda kayan cikin Asmeey ke gudu tanajin wani super love for her man batasan sanda ta kwasa da gudun da bata tabayin kalansa arayuwanta ba, she just wants to hug her man, tawani fashe da emotional kuka dake dauke da murmushi da hawaye ko slippers bata saka ba, see tama manta tanada ciki gudu kawai take, batai wata wata ba tawani tsalleta ta fada jikinsa Hamad yawani kankameta shima tana kulle kafafunta abayansa daidai Baba na bude gate Hameed biyedashi abaya dawani irin sauri Abba yakoma waje har yana buge Hameed da ya hangosu shima yana kokarin rufe gate din kawai sukaga Hamad yawani daga Asmeey sama kaman yar yarinya yawaniyi juyi da ita Asmeey na washe all her 32teeth tana kallonsa tana dariya mai dauke da hawaye, Abba yarufe gate da gudu yakalli Hameed dake murmushi sosai kaman solobiyo yace  shi dan Uwanka baisan ciki gareta ba yake dagata sama haka yake juyi da ita ? Hameed nawani murmushi kaman lusarin Wawa yace  Abba wannan juyin shi ake kira da juyin love! Abba wlh inason soyayya Abba, Hamadi ya iya soyayya! Abba dan bude kofan nadan kara"

kallo! Takalmi Abba yadaga kafa yacire zai kwadamai Hameed ya kwasa da gudu yana dariya sosai.

YAU INA HANGO KALAN CIN GINDIN DA ZA AYI ASMEEY DA HAMADI

EPISODE

"Sosai Hamad yake wani juyi da ita tana dariya mai fitoda hawaye, yanaji kaman ya cinyeta kawai yahuta"

"kafin yadan sauko da ita daidai fuskansa yana kallon kwayan idanunta zaiyi magana tawani rigasa kara rungumesa ta wuyansa ta kankamesa sosai, Hamad yayi lamo da fuskansa a kirjinta yanajin yanda boobs nata suka kara girma sosai, her hugs are communicating to his soul, telling him just how much matarsa missed him, murya chan kasa yace  I ve missed you, it feels like nayi forever ban ganki ba dan sakinsa tayi tadago da fuskanta ta kallesa irin mijinane da gaske ba gizo idanunta kemin ba yadawo, dawani irin sauri yakai bakinsa zai daura kan nata zaro idanu tayi tana kallon cikin compound din sai shima yadan saketa cus wlh he genuinely got carried away dabata kalli cikin gidan ba dayayi kissing nata, ahankali yace  let s go inside gently yasauketa kasa zata wuce taji yakama hannunta

Please Login or Register in order to submit comment