An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KARSHEN MADIGO ( Part 1 )
..
..
Vio Sani Hamza Funtua
..
..
Ofishin Dakta Sa’ad ya dau shirun dole tamkar ba
mutane a cikin shi, idan da ace za’a ajiye zomo a
cikin ofishin bana tunanin zai iya jiyo sautin
numfashin mutane biyun dake a ciki. Wasu
lokuta, shiru zaifi yawan surutu koda maganar
nada ma’ana, amma a wannan lokacin, kunnuwan
RUMASA’U a tsunke suke da son jin sakamakon
awon da akayi mata.
“Dakta Sa’ad, bana jin zan iya jure kallon ka ba
tare da kana magana ba. tsawan shekaru ashirin
ke nan rabon da Namiji ya burge ni bare na dau
mintuna uku ina kallon shi. Zan so ka sanar dani
sakamakon awon da kayi min”—Rumasa’u ta
fad’a bayan gajiya da tayi akan shirun dakta
Sa’ad.
Dakta Sa’ad ya gyara zaman gilashin dake a kan
karan hancin shi. Duk macen da take zaune a
wannan ofishin kuma taji kalaman da Rumasa’u
tace akan daktan lallai ba abinda zai hana ta
wanke Rumasa’u da mari. Duk inda Namiji yakai
a koluluwar had’a sinadaren da mace zata so
namiji to Dakta Sa’ad ya had’a su. Daktan ya
kara kallon takardar dake hannun shi tare da
sake maimaita karanta abinda ke ciki—kusan a
karo na hudu. Ya yi gyaran murya mai kamar tari
wanda yasa shi bude robar ruwan Swan ya sha.
“Kiyi hakuri Rumasa’u, lokuta da dama likitoci
kan kasa fitowa kai tsaye su fadiwa mara lafiya
cutar dake damun shi musamman idan cutar tayi
tsauri sosai, ba komai ke san hakan ba sai don
gudun kada su jefa kansu a halin da yafi na cutar
illatarwa.”
“Dakta tsaya kaji”—Rumasa’u ta dakatar da
daktan don sam ita ba wannan bane a gabanta.
Ta ci gaba da cewa, “Kana tsoron ko bayan ka
fadi min zan ruga a guje in bude tagar ofishin ka
in fad’a kasa? Duk da nasan ofishin naka nada
tsawan hawa uku? Ko kuwa zan koma gida in sha
guba ko in harbe kaina da bindiga? Ko kuma in
tsaya a tsakiyar titi mota tazo tabi ta kaina?”
Rumasa’u ta d’an tsahirta kamar tana jiran likitan
ya bata amsa, sai dai koda ya ce zai bata amsa
bazama ta tsaya sauraron shi har sai ta dire da
zancen ta, wannan tsayarwa ma tana son hutawa
ne.
“Ni ba yarinya bace ba a yanzu, shekaru goma
sha biyar da suka wuce idan ka yi min irin
wannan maganar shine zan yi shiru inbi abinda
kake so. Lokacin ko wace mace tana da ikon
Mallaka a kaina. Likita kasan kuwa mata nawa
suka rasa rayukan su a wannan lokacin?”
Daktan Sa’ad ya girgiza kai alamar a’a, Rumasa’u
ta ci gaba da cewa, “Idan ban manta ba, mata
uku ne suka rasa ransu, kawai a kokarin su na
ganin sun mallake ni. Dan haka Dakta, kai tsaye
nike so ka sanar dani sakamakon awon da kai
min”
Dakta sa’ad ya jinjina takardar da sakamakon ke
ciki, ya mikawa Rumasa’u, ta karba tana nazarin
rubutun dake a ciki. Zuwa wani dan lokaci ta
d’ago kai cikin sanyin jiki ta kalli daktan.
“Ni ba likita bace, abubuwan dana gane a ciki
kadan ne wad’an da koda na hada su basu banin
wata ma’ana ba, ko zaka iya fassara min abinda
ake nufi?
“Rumasa’u. a yanzu haka kina d’auke da cutar
STDs kamar HIV wanda kinsan babu wani
tabbataccen magani na warkewa din-din-din.
Sannan kina da cutar BMI a hausance cutar
nauyin jiki wanda illar cutar zata bayyana nan da
wani karamin lokaci. Haka zalika, sakamakon
awon ya nuna kina dauke da cutar sankarar
mahaifa da ciwon daji, ma’ana Cancer. Sai dai
babbar matsalar shine, kwakwalwarki ta fara
tabuwa sakamakon Mad’igon da kika dau shekaru
kina yi.”
Dakta Sa’ad yayi shiru ba tare da ya kara cewa
komai ba, ya sunkuyar da kanshi kasa, hawayen
takaici da tausayin Rumasa’u suka gangaro
mashi.
Cikin murya mai rawa-rawa Rumasa’u ta ce da
shi “Dakta kukan me kake yi?”
A hankali ya d’aga kai ya kalle ta, “Dole nai maki
kuka Rumasa’u, ina takaicin yadda mace yar
shekaru ashirin da biyar kamar ki rayuwarta zata
kare a haka”
Rumasa’u tai murmushi, “Dakta ke nan, na sosu
kwarai da jin irin cutukan da nike dauke da su,
wanda duka na same su ne a sanadin rayuwar da
nayi a baya. Na kuma gode kwarai dakta.”
Ta mike tsaye da alamar zata tafi, dakta Sa’ad
ya mike shima bayan ya share hawayen dake a
fuskar shi.
“Duk lokacin da kike bukatar wani taimako, kada
ki manta, ina nan zan kuma taimaka maki.”
Rumasa’u ta kara yin murmushi a karo na biyu,
“Na gode dakta, bazan kuma taba mancewa da
irin taimakon da kai min ba. Inaga ya kamata ka
huta hakanan, dan ba lallai bane ba ka sake gani
na.”
“Me yasa?”
Har Rumasa’u ta juya, kamar ta tuno da wani abu
kuma sai ta dawo, ta nemi waje a kusa da likitan
ta zauna, ta ciro Bindiga kirar “AK47” daga cikin
jakarta.
Dakta Sa’ad na ganin bindiga a hannun ta
hankalin shi ya tashi, ya ja baya nesa da ita,
yana tambayarta, “Rumasa’u ina kika samo
bindiga? Ki mayar da ita cikin jakar ki, meke
damun ki?”
A karo na uku Rumasa’u tai murmushi, ta mike
tsaye tana kallon dakta Sa’ad, ta sake sanya
hannu a cikin jakar ta ta ciro wani karfe da ake
kira “Silencer” da turanci wanda ake sawa a
karshen bindiga don kada tai kara idan an
harbata. Ta sanya ma bindigar, cikin yanayin
rashin tausayi ta saita Dakta Sa’ad.
Hankalin Dakta sa’ad ya dugunzuma, ya fad’i
kasa yana tuba da rokon Rumasa’u kada ta harbe
shi.
“Rumasa’u me kike nufin yi? Kada ki manta na
taimake ki a rayuwar ki, ina kallonki a matsayin
‘yata. Dukkan abubuwan da suka faru a baya
wallahi ba nufina bane, biya na ake, wanda idan
banyi ba kashe ni zasu yi.”
“Shi yasa yanzu zan kaika inda babu wanda zai
saka har kayi, inda babu wanda zai kara kashe
ka. Lokacin ka ya kare Dakta, zan fara kawo
KARSHEN MADIGO ta kanka.”
Dakta Sa’ad na magiya Rumasa’u ta danna
kunamar bindigar, harsashi ya fita ba tare da yin
kara ba ya sauka a kan Dakta, take kwakwalwar
shi tai fitar burgu daga saman kanshi tare da
harsashin suka tsaya cak a jikin bango. Jini ya
bata kan teburin da kujeru.
Rumasa’u ta mayar da bindigar ta a cikin jaka, ta
fita daga ofishin.KARSHEN MADIGO ( Part 2 )
..
..
..
Sadaukarwa ga Taron Ranar Marubuta Hausa ta
Duniya...
..
© Sani Hamza Funtua
..
INDA AKA TSAYA:-
Dakta Sa’ad na magiya Rumasa’u ta danna
kunamar bindigar, harsashi ya fita ba tare da yin
kara ba ya sauka a kan Dakta, take kwakwalwar
shi tai fitar burgu daga saman kanshi tare da
harsashin suka tsaya cak a jikin bango. Jini ya
bata kan teburin da kujeru.
Rumasa’u ta mayar da bindigar ta a cikin jaka, ta
fita daga ofishin.
.
CI GABA
Cikin nutsuwa taci gaba da tafiya bayan ta fito
daga ofishin, har ta fita daga cikin asibitin babu
wani wanda ya maida hankalin shi akan ta kowa
na harkokin gaban shi. Kai tsaye ta isa harabar
inda ake ajiye motoci ta shiga motar ta kirar
Highlander.
“Na fi son na rinka shiga motar da zan rinka
ganin tsakiyar rufin sauran motoci, yadda nike a
haka, so nike kullum in ganni a gidan sama mai
badawa ba wanda ke mika hannu ba”—Rumasa’u
take fadin haka wata rana da suke hira ita da
kawarta Zainab.
Tunda Rumasa’u ta tashi bata da wata kawa data
wuce Zainab, tare sukai wasan kasa har zuwa
girman su. Iyayen Zainab sun rasu a had’arin
mota wanda hakan yasa mahaifin Rumasa’u
Alhaji Baffajo rike Zainab a gidan shi tamkar yar
da ya haifa. Mahaifiyar Rumasa’u ta rasu lokacin
Rumasa’u nada shekaru Goma sha biyar—wannan
ma labari ne mai zuwa nan gaba.
A hankali take tafiya a kan titin da zai sadata da
gidanta dake a unguwar G.R.A, babu alamar
nadama a tare da ita akan kashe Dakta da tayi,.
Sai dai hawaye da ke gangarowadaga idanuwan
nata cikin kwanciyar hankali.
“Ina da cutuka kusan hudu a jiki na, nan da wani
karamin lokacin zai iya rasa rayuwata don duka
cutukan da nike dauke dasu ba masu magani
bane. Ya zama dole a gare ni na dau fansar
watsar min rayuwa da akai, ba zan taba mutuwa
ni kad’ai ba”. Hakan take sakawa a cikin zuciyar
tata. Har ta isa gida tana zubar da wannan
hawayen wanda bata san ko yaushe zasu tsaya
ba, ta dai san cewa hannuwanta bazasu taimaka
wajen tsayar da zubar su ba.
A gaban katafaren gidan ta mai hawa biyu ta
tsaya, tayi oda mai gadi ya bude kantamemen
gate d’in. ta shigar da motar tare da ajiyeta a
harabar da aka ware don ajiye motoci. Bayan ta
kashe motar, ta kuma cire dukkan abubuwan da
zata shiga cikin gida dasu. Ta fito ta rufe kofar
motar kana ta yunkura don shiga cikin gida.
“Yar Halak kinki ambato”, wata murya ta fad’a.
Rumasa’u ta juya don ganin mai wannan muryar,
har matar ta karasa inda Rumasa’u take
Rumasa’un bata gane ta ba. Matar wacce zan
iya cewa ta dau kira irin ta mawakiyar nan
“Cellidion” wajen Shaf, kyau kuwa wannan ba’a
magana don tsatson larabawa ce.
Yanayin salon tafiyar ta kadai zai tabbatar maka
da cewa wannan matar bata saba tafiya da
kafafuwanta ba, adon tayi kuwa ya isa ya fad’i
maka cewa lallai don ance maka itace d’iyar
Ambasadan kasar United Emirate a Nigeria
bazakai musu ba.
Matar mai kimanin shekaru talatin da biyar ta
tsaya gaban Rumasa’u, ta mika mata hannu,
Rumasa’u ta mika nata hannun don suyi
musabaha, sai dai Matar ba hakan take nufi ba,
domin tana jin hannun Rumasa’u a cikin nata tayi
saurin sunbatar hannun Rumasa’un.
“Na fara yarda daga zancen mutane akan ki yake
Rumasa’u”
“Ko me mutane ke cewa akai na?” Rumasa’au ta
tambaya ba tare da ta nuna alamar mamakin
ganin matar ba duk da cewa wannan ne karo na
farko da suka hadu.
Matar tayi murmushi, har yanzu hannun
Rumasa’u na a hannunta, ta murza hannun tare
da jin laushin fatar ta, cikin yanayin annashuwa
taja iska da siririn hancinta kamar mai son jin
wani kamshi dake fitowa daga nesa, ta ajiye
numfashin kana cikin lumshe idanu ta kalli
Rumasa’u.
“Baki sanni ba ko Rumasa’u”
“Nasha haduwa da ire iren ki dama wadan da
suka fiki, baki alamar hakan ba?”
“Kwarai na gani, rashin nuna damuwarki na
rashin sani na, ya tabbatar min da cewa zaki
zamo masoyiya ta hakika”
Ba tare da cewa komai ba, Rumasa’u ta juya tare
da nufar cikin gidan, Matar ta bi bayan ta. Suka
shiga cikin kantamemen gidan ba tare da
shamaki ba.
Duk inda ake neman cikar tsari na falo to
wannan ya wuce shi, ba sai na tsaya kamanta
yadda tsarin falon yake ba, amma ku dauka
kamar yadda matar gwamna zata tsara falonta to
haka wannan falon ma yake a tsare.
Kai tsaye Rumasa’u ta wuce inda Friza take, ta
bude ta ciro kalolin lemuka har guda biyu, a gefe
guda kuma akwai gwandon kofuna, ta ciri guda
biyu ta koma inda Matar take tsaye.
Suka zauna a saman kujera d’aya, Rumasa’u ta
zuba masu lemun suka sha cikin annashuwa.
“Sunana Nurul Huda, ni ce babbar ‘ya a wajen
Ambasadan kasar United Emirate a nan kasar
taku.”
“Ni kin san sunana, kinga basai na yi bayanin
kaina ba”
“Haka ne wannan, amma fa gaskiya kina da
kyau”
Rumasa’u ta kalli kanta ta jinjina kai tare da
yarda da cewar tabbas tana da kyau, badan
NurulHuda balarabiya bace da babu mahad’i a
tsakanin su, duk abinda Nuru take dashi
Rumasa’u ma nada shi.
Bayan sun gama shan lemun, Nuru ta bude
jakarta ta ciro bandir din kudi ‘yan dubu dubu har
bandir goma, milyan d’aya ke nan. Ta ajiye a
saman cinyar Rumasa’u. Rumasa’au ta dauki
bandir d’aya ta rinka jujjuya shi.
“Waya turo ki wajena?”
“Manajar ki ce, Hajiya Babba”
Rumasa’u ta jinjina kai. “Kema fa kina da kyau
Nuru, babu macen da zata kalleki bata lashe baki
ba, dubi zubin kirjinki, na dad’e banga mace irin
ki ba”
Nuru ta d’an yi murmushi tare da jin dadin
wannan wasawar da akai mata, hakan ya bata
kwarin guiwar kara matsawa daf da Rumasa’u, ta
rike hannuwanta tana wasa da yatsun ta.
“Kina da laushin fata, ga yatsunki abin kauna.
Babu wata rana da zanyi farin cikinta irin
wannan, wannan ne karo na farko da zan fara
wannan harkar”
Rumasa’u ta nuna alamar mamakinta a fili, ta
kara da tambaya, “Da gaske kike Nuru?”
“Wallahi kau”
“Amma mace kamar ki, me yasa kika zabi
wannan harkar?”
“Kawai na Tsani Maza”
Rumasa’u ta jinjina kai, kashi hamsin daga matan
dake Mad’igo kusan amsar su ke nan “Na tsani
Maza”, babu wacce zata tsani namiji face sai
wacce sha’awarta ta karkata ga yar uwarta
mace.
A cikin Zuciyar Rumasa’u tace “Yau kuma zaki
tsani Mata”
Kamar yadda saurayi da budurwa yan nanaye, ko
miji da mata suke fara tadowa junan su sha’awa,
haka ta kasance a tsakanin Rumasa’u da Nuru.
Sun dau lokaci a cikin falon suna shafar junan su
da yiwa juna “Kiss”, shaukin hakan ne yasa Nuru
ta fara fita daga hayyacin ta, ganin hakan yasa
Rumnasa’u ta d’aga Nuru cif kamar ta dauki bebi
ta wuce da ita cikin uwar d’aki.
A wannan yammacin sun farantawa junan su rai.
Misalin karfe biyar suka kimtsa tare da yin wanka
da canja kaya, a tare suka shiga cikin kitchen
suka had’a abinda zasu ci, suka koma kan
dinning, kowa na ba dayan a baki. Soyayya ta
rana d’aya ta kullu a tsakanin su.
Anyi yarjejeniya akan cewa Nuru zata kwana Uku
ne a wannan gidan akan farashin Milyan d’aya. A
kaf cikin sashen kasar da muke, babu wata mace
wacce take da babbar nasaba da sura irin
Rumasa’u, hakan yasa tafi kowace mace tsada a
harkar. Mata daga kasashen waje, wasu
larabawa, wasu turawa, wasu indiyawa wasu yan
cana, duk sukan shigo kasar don dai su yi
soyayya da Rumasa’u.
Hakan ya biyo bayan sihiri da kafin da Hajiya
Babba, manajar Rumasa’un tai mata, duk macen
data had’a idanu da Rumasa’u to ko nawa
Rumasa’un ta tambayar ba jayayya zata biya.
Misalin karfe tara na dare, soyayya ta kara tashi
a tsakanin Rumasa’u da Nuru, bayan sun dau
kusan awa d’aya suna abu daya, Rumasa’u ta
gaji, ta sauka daga saman gadon ta shiga toilet
tayi wanka. Bayan ta gama ta tsaya gaban
madubin dake a cikin kewayen ta kalli kanta da
irin kirar da take da shi.
Cikin nutsuwa ta karasa gaban madubu, ta sa
hannu daga sama ta ja madubin a gaban ta,
madubin ya baro da jikin bango, wanda ya bada
wata yar karamar kofa, Rumasa’u ta sa hannun
ta a cikin kofar ta ciro wata bindigar daban da
wacce ta kashe Dakta Sa’ad da ita.
Ta maida madubin ta jingina shi da bango kamar
babu yadda za’ai ya rabu da bangon. Ta sanya
doguwar riga kana ta fita daga kewayen.
Zaune a saman gado ta iske Nuru, Nuru tayi
saurin mikewa tsaye ganin bindiga a hannun
Rumasa’u, ta fara yin rawar jiki tana ja da baya
har ta kai karshen bango.
“Rumasa’u me nene hakan? Ya na ganki rike da
bindiga? Ko kudin dana baki sun maki kadan ne?
Just Tell me how much you want”
“Bana bukatar kudin ki Nuru, wad’an nan ma da
kika bani sun ishe ni, ina so ne kawai na hutar
dake daga bayar da kudin ki. Sannan tunda
wannan ne karo ne na farko da kika fara, nan
gaba bazaki yi da kowa ba, ko ba komai, zan
hana faruwar shigar wasu wannan harkar ta
sanadin ki.”
“Rumasa’u don Allah kiyi hakuri, kada ki kashe ni,
ina da abubuwan da nike so inyi da rayuwata”
“Nima haka Nuru, ina da buri da yawa, sai dai
nan da yan kwanki ko shekaru zan mutu. Kinga in
dai na rage irinku a duniya na ci riba. Sai mun
had’u a kiyama”
Tana rufe bakinta ta danna kunamar bindigar,
karar bidigar ya amsa amo a cikin d’akin. Take
Nuru ta zube kasa matatta. Rumasa’u ta dauki
wayar ta dake kan gado ta lalubo wata lamba.
“Ma’aikaci. Ga aiki na samar maka, kazo gidana,
amma kuzo da salataf mai yawa, sannan ko
alamar jini bana son gani. Zan ajiye maku kudi a
saman gado, in kun gama sai ka kira ni.”
Ta maida wayar ta aje, ta bude durowar kayanta
ta ciro kaya kala biyar ta sanya a cikin karamar
jakar tafiya, ta ajiye masu Ma’aikaci dubu dari
uku, ta saka sauran dari bakwan a cikin jakar ta
fita daga dakin.KARSHEN MADIGO KASHI NA UKU Sadaukarwa
ga Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya... ©
Sani Hamza Funtua INDA AKA TSAYA Ta maida
wayar ta aje, ta bude durowar kayanta ta ciro
kaya kala biyar ta sanya a cikin karamar jakar
tafiya, ta ajiye masu Ma’aikaci dubu dari uku, ta
saka sauran dari bakwan a cikin jakar ta fita
daga dakin. CI GABA... Wani yanayi da Rumasa’u
ke shi kullum shine nutsuwa, ko da ace gwamna
ne ta kashe bazaka taba ganin alamar damuwa
ko tsoro a tare da ita, sai ma dai yanayin fara’a
da takewa fuskarta ado dashi. Bayan ta fito daga
cikin gidan ta karasa inda motarta take, ta shiga
mai gadi ya tashi da saurin shi ya bude mata
“gate”, ta tsaya kusa da mai gadin ta sauke
gilashin kofar da take. “Ranki ya dade har zaki
fita ne?” mai gadin ya tambaya cikin girmamawa
da alamar wasa. Rumasa’u tai murmushi kana ta
amsa mashi da cewa, “Zan fita Baban Hafsat.
Ina su Hafsat d’in suke ne? Tunda na shigo banji
koda kukanta ba” Mai gadin ya nuna jin dadin shi
yadda Rumasa’u ta dauko zancen iyalan shi. “Ai
yau tana gidan kakarta, a can zata kwana”
“Hafsa ko rigima.” “Sha’anin yara ke nan, Muna
nan muna jira muga ‘ya’yanki wata rana” Wannan
maganar ta soki kahon zuciyar Rumasa’u, ta kalli
mai gadi ta jinjina kai kawai tana murmushi,
amma tunani yayi awon gaba da ita a lokaci
d’aya. Bayan ta nisa ta sake kallon mai gadin
cikin nutsuwa. “Baban Hafsa kana ganin ina da
sauran lokacin da zanyi aure har in haifi ‘ya’ya?”
“kwarai ma kuwa Ranki ya dade, ai tunda nike a
rayuwa ban taba ganin mace mai farin jini da son
mutane kamar ki ba. Yanayin yadda naga mata
na zarya, matan ma masu kud’i, wasu jinin
sarauta, wasu attajirai, wasu ma daga kasashen
waje suke zuwa wajen ki. Hajiya ai rayuwarki sai
dai muce Allah yasa kifi haka.” Rumasa’u ta
girgiza kai kawai, ta tsahirta kana ta ce, “Kasan
abinda ke kawo su wajena kuwa?” Mai gadi
yad’an dau karamin lokaci yana so ya gano
amsar wannan tambayar, ganin kada ya bata
lokaci yaja hirar ta katse yayi saurin cewa,
“Hajiya, ai a nawa tunanin, kina d’aya daga cikin
manyan mutane a kasar nan, duk da ban san a
ko wane fanni bane amma nasan ke oga ce. Kina
kuma kula da marasa karfi da marayu, dole ne a
rinka zuwa daga kasashe wajen bada tallafi...”
Rumasa’u ta katse shi da cewa, “Ba haka bane
ba, Ni matar Mata ce” Mai gadi ya d’an nuna
alamar rashin fahimtar wannan maganar ta
Rumasa’u. itama ta lura da wannan yanayin,
hakan yasa bata bari ya ce wani abu ba ta ci
gaba da magana. “Kada ka damu, nan gaba kdan
zaka fahimci abinda nike nufi. Baban Hafsa,
akwai Motar da wannan matar tazo da ita d’azu,
ka canja lamba da kuma fenti, ga makullinta na
mallaka maka ita.” Ta mikawa Mai gadi makullin
motar ya sa hannu ya karba, ya durkusa har
kasa yana godiya da Allah yashi albarka.
Rumasa’u ta amsa da ‘Amin’ ta ja motarta ta fita
daga cikin gidan. Mai gadi ya tsashi jiki na rawa
ya kulle gate d’in. ya rinka jujjuya makullin motar,
da gudun shi ya karasa inda motar take. Motar
kirar Lexus ce mai ruwan toka. “Ban taba
haduwa da macen dake da kirki kamar Rumasa’u
ba, duk da cewa bazata girme ni ba, amma ko na
girmeta baifi na bata shekara daya ko biyu ba.
Tunda na fara yi mata aikin gadi, ban taba siyan
abinci ko sutura ba daga ni har iyalina ita ke yi
mana. Kai wani lokaci ma har yan uwana dake
kauye sukan rika zuwa tana yi masu sha tara ta
arziki. Allah ya kara nisan kwana dai uwar
gijiyata”—mai gadi yaci gaba da jero addu’o’i tare
da sawa Rumasa’u albarka. Karfe goma da rabi
agogon motar Rumasa’u ya nuna, hankalinta na
kan titin amma zuciyarta ta tafi tunanin abin yi a
gaba, tunda ta baro gidan take tariyo
maganganun mai gadi, musamman maganar shi
akan suna nan suna jiran suga ‘yayanta. Tun da
take a rayuwarta tsawan shekaru talatin a yanzu,
sau daya bata taba zaunawa tai nazarin wai
samun d’a ba. Kafin mace ta haihu saita sadu da
namiji, ita kuma abinda bazata taba yi ba ke nan,
ta tsani Maza. Karar shigowar waya ya karade
cikin motar, hakan ne ya dawo da Rumasa’u cikin
hayyacinta. Tayi mamakin jin karar wayar don ta
manta da cewa ta taho da ita, wayar Nuru Huda
ce. Rumasa’u ta duba fuskar wayar tare da
karanta sunan mai kiran, “HAJIYA BABBA”—
sunan mai kiran. Har wayar ta karaci kukanta
bata amsa ba, a karo na biyu kiran ya kara
shigowa nan ma har ya tsinke bata dauka ba.
Bayan kamar minti daya sai karar alamar
shigowar sako ya daki kunnuwan Rumasa’u. Da
farko dai kamar bazata duba sakon ba, daga
bisani ta dauki wayar tare da bude sakon. “Nuru
ko dai har kun shiga duniyar kurame ne sai aiki
da jiki? Ina son ganin ki yanzu don Ambasada ya
kirani yace wai ya kiraki baki dauka ba.”
Rumasa’u ta fita daga akwatin sakon, ta duba
cikin lambobin da suka kira wayar amma ba’a
dauka ba, sunan “My Dad” ya bayyana kasa dana
Hajiya Babba. Da sauri Rumasa’u taja birki tare
da sauka daga saman titin, ta danna kan lambar
Ambasada ta tura mashi sako kamar haka. “Ka
hanzarta zuwa gidan Hajiya Babba don d’aukar
gawar ‘yarka.” Tana gama rubuta sakon ta rufe
wayar tare da cillar da ita nesa da titin. Da sauri
kuma ta dauki wayarta ta lalubo lambar
Ma’aikaci, bayan wayar ta shiga ya dauka.
“Ma’aikaci, ga canjin shawara. Har kun nad’eta
da salataf ne? Ma’aikaci ya amsa mata da “Har
mun gama yanzu muke shirin fita, an kuma
tsaftace ko ina ba alamar koda takun sawaye”
“To ku hanyarta warwareta. Sannan na baku
mintuna ashirin kacal kusan yadda zakuyi ku
saka gawar a cikin gidan Hajiya Babba,
musamman a cikin boot din motar ta. Hakan zata
yiyu?” “Kwarai ma kuwa Hajiya, ai ko bamu
iyawa, aljanu zasu iya. Ki bamu mintuna goma
kawai” Dan wannan ta kashe wayar, ta maida
kallonta ga motocin dake zuwa da komawa, ta
fara nazari akan rayuwarta kwatancin wadan nan
motoci. Wata rana dole man dake jikinta zai kare,
zata daina amfani. Kafin zuwan wannan ranar,
sai ta tsayar da numfashin sama da mutum
hamsin koma fiye, hakan ne kawai zai kwantar
mata da hankali. “Dole in kasance a gidan Hajiya
Babba, don kada zargi ya biyo baya, ba wai
burina a kaita kotu da hukuncin daurin rai da rai
ba. A’a, ina son Mutuwarta ta zamo a hannuna.
Wannan ne kadai zai sa in shafe HAJIYA MAI
DALA a doron kasa. Ko Hajiya Mai Dala tana ina
yanzu? Koma dai tana ina, labarin kama Hajiya
babba zaisa dole ta dawo kasar—don an kama
Abokiyar hamayyarta.”
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta