Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹 Special and romantic love story 💋💓🫣 Writer by Autar Alheri ✍️ 🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁 🌹🌹 🦁 Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭 Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️🫂 na haƙiƙa 💯 بسم الله الرحمن الرحيم Book one Chapter 1 & 2 "Zaune suke acikin wani tanganemen parlor dukkan sun kewaye kujerin dake zagaye da dining tebble. Mutum kusan 6 de akai dattijuwa wadda bazata wuce shekaru 57 ba a duniya se megidanta dakuma yaransu duka maza su huɗu, kyawawa dasu tamkar ƴaƴan Larabawa Masha Allah ...Abinci sukeci hankali kwance bawanda ke wani ƙwaƙwaran motsi acikinsu. Kallon matar tayi akarona ba adadi kafin ta sake murmushi cikin soyayyar yaran nata tace "fawan wai duk wannan shiru shirun na minene abu kamar masu zaman makoki? Kodan son nagarine duk kuke wannan abin? Kafin fawan yabata amsa, Sena gafenshi yayi saurin cewa"yo ba dole mutum Yakama kanshi ba mami, idan kuma bahakan ba yasha horon sojoji. Dariya mahaifinsu yayi yaname faɗar "ah'ah da maheer Banda sharri ba'aninda SHATTIMA zemuku Indai bawani laifin kukayi masaba, yaƙarasa zancen cikin barkwanci acikin ahalin nashi. Cikin sauri wanda yake duka ƙarami acikinsu masuna Fa'iz yace "Allah Dady doline mutum Yakama kanshi koda bemaka komaiba idan yazubawa mutum waƴannan idanuwan nashi doline afirgita. Ɗagawa wanda inaga shine babba acikinsu yayi yana kallonsu fuskarshi ɗaukar da lallausan murmushi kafin yace "ga wanda aka tambaya ga masu bada amsa, kai fawan dukafa kai mami tayiwa tamba amma kowanne kamar jira yakeyi wurin bada amsa. Dariya duka iyayen nasu sukayi. Kana fawan yace "bazaka ganeba bane yaa Noor lamarin babban yayane Seda taka tsantsan. Aiko suka koma sakin dariyar sedai kafin wani yakomayin magana acikinsu sukaji sohirtaccen ƙamshi turarenshi namusu sallama yana sanar dasu zuwanshi. Aiko atake duk suka ƙara shan jinin jikinsu suna maida hankalinsu akan acin abinci dasukeyi. Takowa yashigayi zuwa inda yahango ahalin nashi zaune, ƙaƙƙarfan mutun ne cikakken namiji mejini ajika ma'abuci kyau da tsari irinna zaratan maza, farine tass dogo ingarman namiji mecikar zati. Kyakkyawa ne ajin farko domin duk kyawun ƙanenshi idan kaganshi zakace su ɗin munana ne, yanada manya kuma rikitattun idanuwanshi masu bala'in kaifi da saka mutum ya shiga taitayinshi, yanada dogon hanci wanda yayi dede da zubin kyakkyawar fuskarshi, idan aka gun suma kuwa bance komaiba domin yanada suma wadda bazata misiltuba sabida shi ɗin gargasa ne. namijin gaske ne kuma kwallon dan iska ne ga wanda ya shiga gonarshi, ba shida mutunci ko kaɗan agun miyagun mutane ko kuma ɓata gari, kana baya ɗaukar wargi agida ko awaje, tsayayyen mutun ne me martaba kima da bukatar ahalinshi, agaskiya duk yadda zan misilta muku wannan guy ɗin to yawuce nan, sedai ku wassafa kamanninshi dakansu, halayenshi kuwa aikinshine zenuna muku asalin wayarshi. Sanye yake cikin kayan aikinshi wato kakin soja green color sunyi bala'in zaunawa a mirɗaɗɗen jikinshi na ƙaƙƙarfan namiji, domin kamar danshi kawai akayisu, farin silver dake manne akan gaban aljihun rigarshi nayi, inda naga anrubuta *LIEUTENANT MUSAYYEER MAHABUB SHATTIMA* da manyan haruffa, Hakan yasa nagane kenan Sunanshi musayyeer ne, woww gaskiya guy ɗinnan nikaina yatafi da inana ba ƙarya 🫣 Ƙarasowa yayi dining ɗin cikin sassarfa yaduƙa dede fuskar maminshi yana manna mata kiss a goshi kuma adede lokacin ne ya motsi siraran lips ɗinshi yiwa dady shi barka da safiya acikin wani irin cool husky voice meshiga rai da ratsa zuciya....cike da so da birgewa Dady ke amsa mishi ta hanyar faɗar "yawwa barka dai babana, fatan katashi lpy? "Alhmdulillah Dady, yafaɗa yana me lumshe rikitattun idanuwanshi jin yadda mami keshafa sumar kanshi. "Good morning Yaa shattima, cewar fawan, maheer kuwa cewa yayi "barka da safiya yaa Sayyeer. Yayinda Fa'iz yace "good morning yayanmu, yaname riƙo hannun yayan nasu. Dukkansu amsa musu yayi fuska asake cike da son ƙanen nashi, kafin Noor yabashi hannu yana faɗar "good morning big bro. "Morning too bro, how is my baby's? "They are fine big bro, zasuzo ma anjima sukace. "Okay, kawai yace tare da fara shan coffee da mami ta ajiye mishi anutse, batareda fa'iz yasake mishi hannuba har ya gama shan coffee, kana yamiƙe yana yiwa iyayen nashi sallama yafice daga gidan riƙeda hannun Fa'iz besakeshiba seda yakaishi har inda dandazon motocinshi suke, yaranshi naganin fitowarshi sukazo cikin sauri suna sara mishi cike da girmamawa, kafin ɗaya yabuɗe mai motar dake tsakiyar motocin farakal parado girar GLK, shiga yayi yana kallon fa'iz dake manna mishi kiss a hannu, kana suma duk suka shiga sauran motocin tare da tadasu, suka harba su akan kwalta cikin azababben gudu kamar yadda sukeyi akoyoshe. Suma duka matasan dake cikin gidan miƙewa suka yi domin kowanne yanufi wurin aikinshi, Noor Dr ne, fawan kuma company Dadynsu yake aiki shida maheer, fa'iz kuwa yanzu yake school begama amma yace yayanshi zegada. Wannan kenan. Musayyeer shine babba suna kiranshida shattima kasan cewar yanada Sunan mahaifin dady kuma shine shattiman garinsu, Hakan yasa suke kiran musayyeer da Sunan. Sekuma Nuraddeen wato Noor Fawan shikebin Noor se fawan, dakuma maheer kafin autansu fa'iz. Dukkansu sunada aure amma Banda auta fa'iz dakuma babban yayansu. Noor yaranshi biyu mace da namiji, fawan kuwa ƴarshi ɗaya yayinda matar maheer takeda shigar ciki ayanzu. Kowannesu shine yanemo matar aurenshi ya aura amma Banda fawan daya auri yarinyar abokin Dady su wanda kuma Dady ne dakanshi tanemi wannan alfarman. Sunan matar Noor Marwanatu suna kiranta da Anty Marwa. Sunan matar fawan, safiyya, suna kiranta Anty sofi, sematar maheer ita kuwa sunanta jidda. Anty Marwa mace ce me Son mutane da kawaici, kuma ta fito gidan mutunci da sanin darajar ɗan Adam, amma fa batada kunya ko kaɗan wurin nunawa mijinta da soyayya. Anty sofi, mace ce me jiji dakai da isa, tana mugun son fawan amma shi kam auren biyayya yayi mata, sedai betaɓa bari tafahimci hakanba. Iyayenta basuda mutunci ko kaɗan watsatsune naƙashe kana basuda tarbiyya ma balle subawa ƴaƴansu, su uku suke agidansu akwai yayansu mubina wadda tagirmewa safiya sosai sekuma ƙanwar safiya wato zeemama domin Zainab ne sunanta amma zeemama suke kiranta. Jidda maheer kuwa, muguwar raguwa ce takarshe sedai ahakan mijinta na mugun sonta kuma itama tana sonshi sedai ragwanta kawai dake damunta. Masu karatu kubi komai ahankali yadda Zaku fahimta domin akwai abubuwan dasu iya bayyana agaba wanda bamu faɗesuba ayanzu. Bayan wani lokaci. Cikin isa da izza irinta ƙaƙƙarfan namiji kuma jami'in soja mejini ajika ya fito daga cikin tanganemen office ɗinshi tafiya yake yi cikin sassarfa yanufi dandazon motocinshi, kyakkyawan mutum ajikin farko domin fa baƙarya lieutenant musayyeer mahabub shattima handsome ne baƙarya. Cikin sauri yaranshi suka miƙe tare da sara mishi kafin suka buɗemai motar tsakiya ya shiga, kana su kuwa suka shiga cikin sauran helux ɗin dake zagaye da ita, kana suka harba kan kwalta cikin azababben gudu. Suna ɗaukar hanya yabuɗe baki tamkar wanda akayiwa dole yace "suleja zamu nufa Usman. "Okay Sir, cewar captain Usman kana suka ɗauki hanyar dazata sadasu da suleja. Tsugunne take gefen hanya tana tsintsar yayan goribarta data watse, yarinya ce ƙarama wadda bazata wuce shekaru 16 ba aduniya kyakkyawar budurwa me matuƙar birgewa da ɗaukar hankali, black beauty ce domin ba fara bace, tanada suma metarin yawa kuma me ɗaukar hankali, nagano Hakan ne ta hanyar ƙananun gargar dake kwance akan gashinta kasan cewar sanye take da milk hijab wanda yahanamin ganinta da kyau. Tana cikin tsintsar goribarta tamiƙe arazane tana faɗar kan ubancan, saka makon ruwan da akayimata wanka dasu na damana dake kwance agefen hanya. Ganin tayi motocin sunwuce tamkar basu wanzu a wurin ba, balle susan ta'asar dasuka yimata, Hakan yasa ta kwashe sauran goribar dake hannunta takwasa aguje tabi bayan motocin tana jifarsu da ƴaƴan goribar da iya ƙarfinta kuma tana zaginsu, ta hanyar ɗura musu ashar.....! Humm ME & MY LION yanzufa za'afara wasan 💃💃💃 Autar Alheri ✍️ *🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹 Special and romantic love story 💋💓🫣 Writer by Autar Alheri ✍️ 🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁 🌹🌹 🦁 Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭 Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️🫂 na haƙiƙa 💯 Book one Chapter 3 & 4 "Amma ko alamar sunsanda zamanta Basu nunaba har suka ɓullewa ganinta, bata haƙura tabisu har cikin gidan gonar da suka nufa....dukkansu sojojin sun fito tare da ƙamewa wuri ɗaya, shi kuwa ogan nasu yaziro kafarshi ɗaya, ɗayar kuma na cikin mota, da waya maƙale a kunnenshi. Dagudu taƙaraso gidan gonar tare da nufar inda ta hangesu tsaye, babu abinda mugun yimata ɗaci arai irin yadda suka jiƙa mata milk ɗin hijab ɗinta na islamiya. Waye ketuƙin wannan motar? Tafaɗa cikin wani irin sexy sound tana zuba musu lulu ayes ɗinta masu kama da na yar shaya. Dukkansu juyowa suka yi suna kallonta jin wannan sweet sound ɗin metafiya da imanin mutum, ganinta sukayi asatsaye tazuba musu ido tana ƙare musu kallo. Yarinyar kyakkyawa ce baƙarya Sedai black beauty ce amma tanada wani irin sohirtaccen kyau me ɗaukar hankalin me kallonta. Bawanda yace mata ƙaka sema ɗauke kansu dasukeyi daga kallonta. Cikin ƙufula tasaka hannu tare da dukan motar dake kusanta tana faɗar "wlh sekun fiddamin kowaye ke tuƙin wannan motar domin bazan yadda ba Hakan kawai yajiƙani dan rashin imani kuma kugudu kubarni dan rashin tausayi tunku gaku sojoji, Toni wlh baruwa dako suwayeku kawai kufitimin da wanda yajiƙani dan Sena rama. Cikin hasa da mamakin ƙarfin halin yarinyar Captain Usman yajiyo yana faɗar "kee barnan kafin natashi kanki da bindigarnan, yafaɗa cikin tsawa yana nunata da bidigar dake hannunshi...wani kallon bakada hankali tayi masa babu ɗigon tsoro ko ɗar aranta, domin ko karkarwar da jikinta keyi na sanyine bawai natsoroba sabida bata ƙaunar sanyi ko kaɗan ajikinta. Cikin tsiwa da rashin tsoro tace "au badai Zaku nunaminba kenan, tayi maganar tanabin ƙafar wanda ke cikin motar tsakiya da kallo, a kuma Dede wannan lokaci lieutenant musayyeer ya fito gabaki ɗaya daga cikin mitar dawayarshi akunne yafara takawa zuwa cikin cikin parlor.....Shi kuwa Caspian ganin renin hankalin yarinyar yayi yawane yasa yayi kanta cikin tsawa yake faɗar "dan ubanki munyi miki kamada sa'arkine? Yana faɗar Hakan yana kaima mata harbi daƙafa. Aiko cikin zafin nama tagoce tare da daka wani uban tsalle kamar wata kwaɗo segata ɗare ɗare ajikin lieutenant musayyeer shattima daya kusan ƙarasawa kofar parlor. Wani irin runtse ido yayi daƙarfi jin mutun yafaɗo mishi ajiki ajikin tamkar wani soso domin ko kaɗan batada wani nauyi. Ido duk sojojin dake wurin suka zaro cikin mugun tashin hankali da mamakinta, wasuna dafe kai wasu buɗe baki tamkar za su tsaga bakin sabida tsabar ruɗewa...shikuwa wani irin sanyi yaji yadsuke bayanshi saka makon jikinta datake cuɗawa aduka bayanshi tana goge masa ruwan da suka watsa mata. Wani irin fisgota yayi da hannu ɗaya taredayin jifa da Ita aƙasa, kana yajiyo yazuba mata wannan rikitattun idanuwan nashi masu firgita yan maza. Ganin Hakan yasasu Captain Usman dawowa cikin hayya cinsu cikin hanzari sukayo kanta domin suci ubanta kafin su aci nasu, domin wlh shattima kwallon ɗan iskane ze iya cin ubansu amadadin ita, Sedai kafin su ƙarasa sukaga yaɗagata cak da hannu ɗaya yayi cikin parlor da ita.."yayi kyau kinkai ƙarshen rashin kunya yau. Cewar wani soja. Cikin takaicinta ɗaya daga cikinsu yaƙara cewa "Allah yasa boss yayi raping ɗin shegiya taso jaza mana masifa koyanzu kuma nasan batsira mukayiba. Girgiza kai Captain Usman yayi kawai domin ya san abune me wahala lieutenant yayi raping ɗinta kamar yadda suke faɗa domin shi sam baya harkar mata, amma da yanayi shikanshi zeso ya ɓalla yar iska. Shi kuwa shattima yana shiga parlor yayi wani irin wulgata tamkar ya jefa kiyashi. Aiko ta tsandara ƙarar da seda gidan ya ɗauke saka makon mugun buguwar da ƙugunta yayi ajikin kujerar parlor. Tsallaketa yayi yashige wani bedroom dake cikin parlor yana shiga toilet yawuce domin wani irin ƙyanƙyamin kayan yakeji dudda kasan cewarsu kaya mafi yosuwa da daraja agareshi, cire su yayi doka har Short ɗin pajamas daje jikinshi. Yayi saura dagashi se Fatar jikinshi. Ataoroce nayo baya domin nikam bazan iya jurar kallon wannan mirɗaɗɗen sojanba🫣 bayan minti biyar ya fito ahakan yadda yake, kana yabuɗe widrop ya fiddo wando 3 kwata da ƙaramar riga duka farare ƙall yasanya. Acan parlor kuwa gabaki ɗaya wannan budurwar tafita hayya cinta sabida wani irin ƙugi da ƙugunta keyi kasusuwanta narabuwa da junansu sosai take kuka tana jan Allah ya isa domin ko motsin kirki takasayi. Unguwa uku Misali ƙarfe 7:30pm wata dattijuwar sohuwa ce ke tsaye abakin ƙofar gidanta se kuka take yi, gabaki ɗaya taɗagawa maƙotanta hankali, mlm Bello se haƙuri yake bata amma fir taƙi se ƙara tuburewa takeyi. Daga gefe ɗaya kuwa samarine kusan su shida ke tattauna yadda zasuje neman jikar tsohuwar domin sunsan yau tabbas idan ba'aga *FAILUSHA* ba sunsan babu sauran zama lafiya a unguwar...da ƙyar da siɗin goshi mlm Bello da matarshi suka lallaɓa Hajiya kaka ta shiga cikin gida da aƙawarin zasu Nemo mata failusha Aduk inda tashiga. Hakan suka zauna da Ita har kusan 11:00pm amma babu failusha babu dalilinta, wannan dalilin ne yasa hankalin Hajiya kaka yaƙara tashi, takira yayar failusha dake aure anan cikin suleja ɗin tasanar mata ɓatan ƙanwar tata. Cikin tashin hankali Anty fa'iqa tagaizayo zuwa idan Hajiya kaka itada mijinta, anan mijin nata yaƙara baza motane yadda sanarwa da ja'an tsaro zancen neman failusha, abu kamar wasa cibi na neman kaisu dare. Cikin karaya Anty fa'iqa tacewa Hajiya kaka "kaka wai kinsanarwa dady ne? "Nasanar mishi a ina inazanganshi tund kinzo yanzu ai seki kirashi. Gidan gona Tun da ya shiga bedroom ɗinshi beƙara fitowa ta se wuraren 2:30am. Yafitowa yayi sanyeda sleeping dress riga da wando masu santsi, se wani irin sihirtaccen ƙamshi yake bazawa memugun shiga jiki, riƙe yakeda laptop ahannunshi yana tafe yana aiki hankalinshi kwance, ga dukkan alamu ma yamanta da wata halitta acikin parlor. Sedai yana zama ya fara jiyo shashekar kuka ƙasa ƙasa murya ko fita batayi, atake yatinada abinda yafaru ɗazu. Cije lips ɗinshi naƙasa yayi cikin wani irin ɓacin ran abinda ƙaramar yarinya tayi mishi tabbas kowaye yaturota baƙaramin shiri yake dashi akanshi ba, yajima yana tinani acikin ranshi kafin yamiƙe ya shiga tako cike da izza da kurazari tamkar bijimin Zaki. Yana zuwa wurinda take, betsaya komai ba ya falla mata wani gigitaccen marinda seda ta mulmula sau kusan huɗu kafin tatsaya sabida ƙafar senter tebble data tareta. Takawa yakarayi ya cimma ta kana yadoƙo da zimmar tambayar ta, domin shi baya fara tambayar mutum seya fara sauke mishi maruka. Ganinta dayayi asomene yasa yamiƙe azuciya ya ɗauko ruwan faro masu bala'in sanyi yaɓalle marufin kawai ya shiga bulbula matasu atsakiyar kanta suna sauka ajikinta. Wani irin nunfashi taja tare da ƙoƙarin buɗe lulu ayes ɗinta ataoroce Sedai takasa Hakan sakamon wani arnen sanyi dataji yana shiga cikin ƙofofin gashin jikinta wanda yasa nomfashinta fara kokawar barin jikinta, bata gama kokawa da nomfashinta tafara wani irin kakari idonta na neman kafewa saka makon wata muguwar shaƙa da shattima yayi mata tare da falla mata mari lokaci ɗaya, cikin wani cool voice me firgita tsagera yace "uban waye yaturoki gareni? Waye shi baze iya tunkarana ba harse yaturomin mace? Macen ma jinjira irinki. Zaki gayamin wanda yaturoki kosena kashe anan naɓatar da gawarki. Yaƙarasa zancen yana karayin jifa da ita again. Afirgice taƙara farkawa domin tun sheƙar da yayi mata taƙara somewa. Cikin wani irin tashin hankali da tsoron ganin mutuwa afilin Allah, tabuɗe bakinta dake rawa muryarta ko fita batayi sabida tsabar gala baita, tace "MY LION, zokaceceni ahannun wanna sojan zekasheni sekuma tasake rushewa da kukan nadamar zuwanta makasarta. Shi kuwa azuciye yayi kanta, sedai tana ganin yanofota tamkar wani Zaki yasa taƙarayin ɗib tasome akaro na uku. Wani mugun tsaki yaja taredayin Ball da ita kana ya ɗauki laptop ɗinshi yakoma bedroom domin tabbatar idan yabi ta zuciya to kasheta kawai zeyi. Ashe gari Misalin ƙarfe 9:00am ya fito cikin wasu ƙananun kaya wanda suka yi bala'in karɓar Fatar jikinshi blue gens and jar t-shirt kayan baƙaramin kyau suka yi mishiba, tako yake yi cike da jamunta ya fito daga cikin gidan kai tsaye motocinshi yanufa da da waya a kunnenshi yana magana cikin harshen Turanci tamkar ba ɗan Nigeria ba, magana yake yi da abokinshi kuma aminin shi mutallab. Cikin sauri duka yaranshi suka taso suna sara mishi cike da girmamawa kafin Caspian sahib yabuɗe masa kofa ya shiga kana yarufe suma duk suka shiga nasu motocin sukabar gidan gonar cikin azababben gudu tamkar zasu tada ƙwallar kamar yadda suka saba... Captain Usman da Captain sahib kuwa tunanin yarinyar dake cikin gidan sukeyi sunsan tunda sukabar gidan gonar bazasu dawoba kana kuma ga yar mutane aciki, kuma basuda halin tambaya ko tunatar dashi domin basuga fuskaba, wata zuciyar natabayarsu to wai koya kasheta ne? Wata kuma na gaya musu sam shattima baze iya kashe maceba macen ma ƙaramar yarinya kamar wannan dudda kuwa yakeda baƙar zuciya. Suna cikin wannan tunanin sukaji sansanyar muryarshi yana faɗar "muce unguwa uku kawai sauri nakeyi mu koma Abuja dawuri.."okay Sir cewar captain Usman kana suka ɗauki hanyar unguwa uku dudda cewar sunsan dama can ne inda zasu nufa a suleja ɗin.....! 🌹ME & MY LION 🦁 Kofa sanwa ba'a ɗoraba balle ayi zancen fara girki💃💃💃 Autar Alheri ✍️ *🌹🦁🌹ME & MY LION🌹*🦁🌹 Special and romantic love story 💋💓🫣 Writer by Autar Alheri ✍️ 🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁🦁🦁 🌹🌹🌹🌹 🦁🦁🦁 🌹🌹 🦁 Oh'oh'ohhhh 🤭🤭🤭 Wannan kabcen tabbas zegigita duniyar makaranta littafen Hausa ze hautsina brain ɗinsu, kana ze cika zukatasu da shauƙi tareda begen reality love❤️🫂 na haƙiƙa 💯 Book one Chapter 5 & 6 "Hakan suka nufi unguwa uku kai tsaye., tafiyar minti 15 takaisu unguwa uku parking suka yi bakin wani madaidaicin gidan me shegen kyau da tsari, dirowa sojojin suka shigayi cikin hanzari suka nufi motarda ogansu ke ciki suka buɗemai. Shi kuwa tun tsayuwarsu mitar dake Parke bakin ƙofar gidan yake kallo yana tinanin abinda yakawo Noor gidan yanzu da sassafe. Fitowa yayi cikin takonshi na ƙaƙƙarfan namiji yanufi cikin gidan yana mamakin abinda yatara mutane ƙofar gidan kamar Hakan. Tun a tsoron gidan yafara jiyo ihun Hajiya kaka, kuka take yi sosai tana tsinewa mutanen da suka sace mata jikarta, domin jiya ko bacci batayiba kuma batabar kowa yayiba., ƙarasawa yayi cikin gidan anan yasamesu duka zaune tsakar gida se famar bawa Hajiya kaka baki sukeyi. Kuma shine dalilin zuwan Noor tunda sassafe sabida kiranda Anty fa'iqa tayi masa. Sallama yayi akan lips ɗinshi yanabin mutanen wurin da rikitattun idanuwanshi. Dasauri Noor yaɗago jin muryar yayan nashi yana "Yaa shattima kaima Sedai Hajiya kaka tatasoka? Kafin lieutenant musayyeer yayi magana. Hajiya kaka tayi wani zumbur tamiƙe tana faɗar "mesunan mlm Kaine? Yoshe kadawo? Wlh kadawo akan dede domin inason kanunawa koma waye yaɗaukemin jika cewar ba'a taɓa matar soja azauna lafiya, yanzu inbanda suke gantalalin mutane su ɗauke amarya alokacinda angonta yadawo, wlh dai wannan mutanen sun cucemu Allah ya isa tsakanina da koma waye yayimin wannan aika aika, taƙasara zancen tana fashewa da kuka. "Inakwana Yaa shattima. Cewar Anty fa'iqa. "Lpy qalau ya amsa mata cikin cool voice ɗinshi kafin yadubi Noor yana faɗar "miyake faruwa ne wai? "Wlh Yaa Sayyeer wai failusha ce aka ɗauke tinjiya har yanzu ba'agantaba shine duk Hajiya kaka ta daga hankalinta. "Eh naɗaga hankalin, yo badole naɗaga hankalinaba ai idan ba'agantaba shine mutun nafarko daze fara tuhumata, to wlh nidai kaji nagayama maisunan mlm kasaka anemimin jikata duk inda ta shiga aduniyarnan domin wlh Allah bazan yadda yawwa. Taƙasara zancen tana share hawayenta da gefen zanenta....idon lieutenant shattima yazuba mata yana kallon yadda take surfa tijara kafin yataɓe baki irin ko ajikinshi ɗinnan, kana ya kalli Anty fa'iqa yace "little sis turomin picture ɗinta natura anemota. "To yaya cewar Anty fa'iqa tana buɗe wayarta kana ta tura kishi picture ɗin failusha a WhatsApp. "Natura yaya... bece mata komaiba ya shiga Whatsapp ɗin kuma yana amsa wayar general, kana kana yiyi forwarding ɗin picture ɗin izuwa wayar Captain Usman, tare da tura gajeren saƙo kamar Hakan "Anemota yanzu duk inda ta shiga Usman. Daga Hakan yafita contact ɗin Usman kana yana cigaba da amsa wayarshi. Gefen Captain Usman kuwa koda yabuɗe yaga saƙon megidan nasu, ido yazaro arazane yana faɗar"anemota kuma kai ina, sekuma yasakawa megidan nasu kira, amma harta yanke ne dagaba, zesake kira kenan kira shi yashigo, cikin sauri yaɗaga yana faɗar "Sir wannan yarinyar da kace anemo ai itace muka bari agidan gona yanzu. "Whatt? Yafaɗa daƙarfi yana zaro rikitattun idanuwanshi kafin yajuya fuuuu yabar gidan, yanaji Noor da Hajiya kaka natam bayar shi lpy amma beko waigoba balle suyi tinanin ze amsa. Shi kuwa yana fitowa yafaɗa mota batareda yace komaiba, Hakan suka shiga tare da fisgar motocin aguje sukabar layin kaitsaye gidan gonar suka koma. Cikin takonshi na ƙaƙƙarfan namiji yanufi tare da nufar cikin parlor. Kwance yaganta tamkar ma tacciya domin babu inda ke motsi ajikinta, duƙawa yayi ya ɗaukota Sedai ganin yadda jikinta yasaki baƙaramin kayar masa da gaba yayiba sabida yasan tanada matsalar remonia gaya kuma takwana cikin azababben sanyi irin wannan. Hakan dai ya fito da ita domin ko a fuska baka isa kagane hankalinshi yaɗan tashi ba. Yana zuwa ya sakata motar da suka buɗemai kana yashiga wata daban sukaja motocin suka fice daga gidan gonar. "Musamu hospital mafi kuwa Captain Usman, yafaɗa tamkar bashine yayi maganarba. "Okay Sir, captain Usman yace kana yaɗauki

Chapter 1 of 3