bokin ka "Nura harda yara uku kai ko auran baka yi ba na zaɓa maka HAMEEDA a matsayin mata don har ansa rana nan da wata biyu masu zuwa"
Ya ce wacece kuma haka? Bansanta ba"Ammi" kallon shi tai ta ce ɗiyar mama mai wanke wanke mana ita ce ba ka sani ba bana son raini fa...
Ganin ran "Ammi na son ɓaci ya ce bansan sunan ta ba sai yau, Ammi Ni gaskiya bani santa"
"Hameeda tunda ƴan uwan mahaifin ki ne suka amshi kudin sa ranar kiyi hakuri' kada ki jazamin abin magana a cikin dangin ubanki"!
Kuka ne take yi ta ce" mama wallahi wannan mutumin ɗan iska ne Ni bana san shi nasan ko na aure shi wallahi wuya zan sha a hannun shi".
Mama ta ce"yanzu hameeda mijin da zaki aura kike kira ɗan iska, bari kiji ko ɗan guguwa ne wallahi sai kin aure shi don bazaki jamin zaki wajan ƴan uwan mahaifin ki ba tun da sun ansa sai ki hakura ki karbi kaddarki"!
Kuka ne ya ci karfin ta tunda ganan ta daina zuwa aiki kusan sati Uku kenan bata jeba, wani babban gida ne ya sai ma su "mama wanda kudin shi miliyan biyar ya zuba mata ƴan aiki ga ac ya ce su koma can hameeda ta ce ai ba a titi kagan mu ba balle kace muna bara"
Mama ce ta bashi hakuri' ya ce ai bakomi yarinya yace mama fita tai ta basu ɗakin shiru ba mai magana illa zuciyar kowa da ke bugawa kamar zata fito waje yace baki iya gaisuwa bane?
Watsa mai harara tai ta ce ba akoyamin ba........ Hmmmm kin san dai hukunci na wallahi ko anan sai na maki ba ruwa na!
Tashi tai tsaye tace in kafasa, ba sunan ka Sadeeq ba,
Ni kike ce ma haka wallahi to a satin nan za aɗaura auran mu ki tare a gida na naga ta tsiya haka dai aka gama fira inda aka maido biki asabar mai zuwa nan ne ta yarda "Sadeeq zai iya komi ta lura baya faɗa ya canza"
Hankalin ta tai ya ƙara tashi ganin an kawo lefe akwati set Biyar, ba abinda ya bata mamaki illa ɗayan saitin duk kayan barci ne wasu ma na iskanci ne ya sa mata da tagani tsaki tai don ba Yadda zata tai...
Yau ya kama labara suna da ƙyauyawa shiri akai mata wanda tai matukar ƙyau ba kaɗan ba ko gun ƙyauyawan sai wani rungumar ta yake haka tai aka tashi......ranar Alhamis Arabia night doguwar riga ce baka tasa yasa farar jallabiya "Nura ne ke driving suna baya ya ce wa kika sa ma jan baki salan ai ta kallon ki komi?"
Ta ce oho maza nasa mawa sugani mana, badan kai ba wallahi'' ya ce har da rantsuwa kike ba dan niba"
Ehhhh bakin ya kama ya shanye janbakin haka tai akai Arabia night ba wata walwala ranar juma'a ne aka Daura auren *ABUBAKAR SADEEQ MUNIR DA AMARYAR SA HAMEEDA MUHAMMAD* kan sadaki dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan
Tana jin daurin auren sai kuka" mama tana ta lallashin ta kada ƴan uwa su gane halin da ake ciki karfe 8:00pm aka dau amarya zuwa gidan ta
Contue
Alhamdulillah ala kulli halin zaku ji Ni kwana biyu shiru hakan ya faru sakamakon banda lafiya, amma nagode da addu'ar ku a gareni
Bismillahir rahamanir rahim
Page 36/42
Tun da ƴan kai amarya su katafi take kuka wannan gida ita kaɗai tsoro ne ya kamata shin yanzu ya zata yi ko ta koma gun mama ne? Wannan tunanin da tai zuciyar ta taba aman na gyalen ta ta yafa ta fito har ta fito get ɗin farko sai ga motar shi na zuwa tsayawa tai don ganin waye zai fito ganin ta da ya yi anan ba karamin mamaki ya bashi ba parking ya yi ya fito do so in da take yai ya ce ina zaki ne yanzu daddaran nan?
Harararn shi tai ta ce Ni gidan mu zan koma, bazan zauna da kai ba wallahi..
Dariya ya yi sosai ganin yana dariya tasan rainin hankali ne ya ke mata ya ce" wai kina da hankali kuwa daga kawo ki yau sai ki gudu?"
Ehhhh mai zai hana gidan mu na ce zani ba wai yawo ba!
Kallon ta ya yi tare da faɗin yanzu idan ki ka tafi ƴan uwan ki za su ce sakin na yi, kija ma "mama" zagi haba ki dunga aiki da hankali ya rungumo ta muje ciki shine abinda ya faɗa....
Palon su ka sauke zango yana manne da jikin ta,wani ƙamshi ke tashi a jikin ta jin sa ya ke kamar ya cinye ta ya ce ta shi mu yi sallah mu gode ma Allah ko?
Kallon ƙasan ido tai mashi ya ce " ko baki jina ne?"
A'a ina ji ni bana sallah to..... Ya ce" baki sallah mai ya same ki da ranki da lafiyar ki zaki ce bazaki sallah!
Ta ce" a'a banda lafiya ciki na ke ciwo kuma idan ciki na na ciwo bana yi ni"........ Ya ce dallah tashi muyi sallah bana san shirme fa..
Dariya ta samai ta ce" wai waya ce maka idan ana haila ana sallah ne?"
Kan shi ne ya ɗaure ya za'a ce amarya tazo da wannan abu ranar ta zai ..... Gaskiya shi ba a kyauta mahi ba😂😂😂😂😂😂😂
Tunanin da taga ya faɗa ne ta hura mai iska a kunne, firgit ya ya dawo hankalin shi fulat ya ɗauko ya juya masu kajin suka ci tare da korawa da lemo mai sanyi, basu cinye ba aka sa sauran cikin firis....
Bayan sati daya da bikin nasu Ranar Lahadi tai tsarki, tana cikin sallar la'asar ya dawo ya iske ta tana sallah a zuciyar sa ya ce yau akwai cin uwar sabada kenan 🤣 zama ya yi ta sallame ta mai sannu da zuwa ya aiki..
Alhamdulillah ya amsa ma