Downloaded From https://tknovels.com.ng [12/29, 2:19 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIO* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 1* Bismillahir-Rahmanir-Rahim NIGER STATE *Abayi close* fitacce ne kuma sananiyar unguwa a cikin garin na *Minna*, unguwace dake dauke da nau'ikan mutane kala kala ƙabilu dabam dabam musulmai,cristain, talakawa, masu matskaicin ƙarfi,da ma manya masu hannu da shuni, hakan yasa unguwar ke cakuɗe da gidaje maya da ƙanana. Misalin karfe biyu na sulisin dare, ruwa ake tsugawa kamar da bakin kwarya, ko ina ya dau sanyi bakajin ƙarar komai sai na yadda ruwa ke sauka a saman kwanukan gidajen mutane da mugun karfi haɗi da walkiya tare da razananiyar tsawa mai firgita mai sauraro tare da wani iska mai ƙarfi dake kadawa jefi jefi, hakan yasa gaba ɗaya garin ya ɗauki wani irin sanyi mai ratsa jiki. A ɗaya daga cikin gidajen talakawan dake unguwar, kwance *AL AMEEN* yake cikin ɗan madaidaicin ɗakin shi dake zauren gidansu a kan yar madaidaiciyar katifar shi, kuɗundune yake cikin bargo idanun shi a lumshe, a kallo ɗaya zaka dauka barci yake, sai dai ko kaɗan ba haka bane, yadda yake sauke numfashi a wahale da yadda zufa ke karyo masa duk da matsanancin sanyi da iskar dake kaɗawa a garin ne zai tabbatar maka ba lafiya yake ba. Cike da tsananin azabar ciwo ya buɗe rinannun idanun shi ya sauke akan wani jaka dake rataye jikin hangar dake manne a bangon ɗakin, so yake ya miƙe ya isa ga jakar domin ya dauki magungunan shi da ya musu kyakyawar buya a cikin jakar , sai dai inaa! Bazai iya ba domin Ko kwakwaran motsi baya Iya yi balle har akai ga batun miƙewa tsaye, idan kuwa yace zaiyi wani motsi mai karfi a halin da yake ciki, komai zai Iya faruwa da shi ciki harda rasa numfashin shi. Ci gaba yayi da kallon jakar, ji yake da yana da dama da ya kira jakar daga kwancen da yake, sai dai shi kanshi yasan hakan ba abune mai yuwuwa ba, A hankali ya mayar da idanun shi ya lumshe, cike da tsananin azabar ciwon maran da ke neman hallaka shi, ya riga ya sani a duk sanda za'a wayi gari cikin irin wannan weather ko makamancin sa, to kuwa shi a ranar bashi da sauran lafiya, yau kimanin shekara hudu kenan yana fama da wannan lalurar, tun daga lokacin da yakai munzilin balaga, lokacin yana da shekaru sha takwas a duniya ya fara fuskantar wannan matsalar, tafi tafi abu ya fara ƙamari wanda har sai da ya danganta kanshi da likitaba tare da sanin kowa ba, shi ƙadai yake gwagwarmaya da faɗi tashin shi ba tare da kowa ya sani ba, ciki harda mahaifiyar shi wacce duk duniya bashi da kamar ta. Cikin karfi hali irin nashi na jarumin namiji ya shiga, ambaton Allah a zuciyar shi domin ya kawo mishi ɗaukin gaggawa, yayin da ya kai duka hannayenshi biyu ya dafe marar shi dake mishi wani irin matsanancin ciwo tare da daurewa kamar jijiyoyin gurin zasu tsinke. Kimanin awa ɗaya da rabi ya dauka ba tare da bakin shi ya gaza da ambaton ALLAH ba, a hankali cikin hukucin ubangiji ya ji komai na lafa mishi. A hankali ya miƙe hannunshi ɗaya dafe da marar shi, yana tangaɗi ya isa gaban jakan da maganin shi ke ciki, hannu ya saka can kasar jakar tare da dauko sacet din magani, guda data ya ɓalla ya maida sacet din, komawa yayi bakin katifar shi ya zauna tare da jawo jug din dake gefe cike da ruwa babu bata lokaci ya afa maganin ya kora da ruwa, ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa ya kwanta rigingine yana sauke numfashi. *Washe gari* ********** 6 Am dai dai Alarm ɗin agogon dake ajiye akan bed side drowan dake kusa da gadonta ya fara ƙara yana girgiza, a hankali ta buɗe kyawawan idanunta tare da miƙa hannu ta kashe alarm ɗin, kusan minti biyar ta kwashe a kwance kafin ta yaye bargon da ke lullube a jikinta ta miƙe zaune tana tattare dogon gashin kanta daya barbaje ta ɗaure shi a baya, yunkurawa tayi ta miƙe akan kafafunta, mika tayi tare da dogon hamma baki bude tana furta "in Jesus name" cikin zazzakar muryarta, kayan bacci ne riga da wando masu kauri a jikinta saboda yanayin da ake ciki yau na sanyi a garin, cike da kasala ta fara takawa a hankali Kamar wacce bata da laka a jiki ta nufi wani ɗan ƙofa ta buɗe ta shige. Kusan minti 30 ta kwashe, sannan ta fito daure da dan ficilin tawel iyakarsa cinyoyinta, jikinta da gashin kanta na ɗigan ruwa, gaban mirron dake shake da kayan shafa na mata da turaruka ta tsaya, hand dryer ta kunna ta fara busar da gashin kanta bayan ta gaba ta shafe shi da mayukan gyaran gashin kusan kala uku masu kyau da tsada take ya dau kwalli da sheki, taje shi tayi kafin ta tattare shi tayi parking din shi a gefen kai. Body lotion dinta mai kamshi da tsada ta shafa, tare da turarukan ta na jiki, fuskarta ta gyara batayi wani dogon kwalliya ba hoda kawai ta shafa da lip gloss sai maskara data karama Zara zaran lashes dinta. Gaban makeken wadrob mai kofa shida dake dakin ta tsaya Wanda set ne da gadon da mirron dake dakin, kofan farko ta bude, inner wears ne shake a wurin kalakala kamar za'a bude kantin sayar da su, pant da vest da sock ta dauka ta maida kofar ta rufe, kofar dake kusa da na farko ta bude, school uniform dinta ne a goge a ninke kusan kala goma, ɗaya ta Zara tare da madai kofar ta rufe cikin Sauri ta shirya cikin farin riga mai dogon hannu tare da skirt sky blue damamme iyakarsa cinyanta, tayi stokin,farin sock ta Sanya dogo ta dauki wani farin both a cikin jerin takalmanta dake cikin abin jera takalma sunfi a kirga ta saka a kafarta, agogon ta dauka a cikin wani dirowa ta daura a hannuta, daga haka bata kara komai ba ta sunkuci gabjejen school bag dinta ta fice daga dakin. Sauri sauri take saukowa daga kan stairs ta iso wawakeken falon dake kasa, a share yake tsab sai tashin kamshi yake babu abin da ke tashi sai sautin TV dake kunne a tsahar eagle TV wani babban pastor na wa'azi cikin karadi da tsoratarwa, da alama ma,aikatan gidan masu alhakin kula da tsabtar falon har sunyi aikin su, bata bi takan TV ba ta ajiye jakanta akan daya daga cikin kujerun dake kewaye da falo ta fice. Hanyar dining Wanda ke kusa da makeken kitchen din gidan Wanda shine general kitchen na gidan a nan ake duk wani girki ta nufa, abin mamaki a shirye tsab ta tarad da dining din shake da warmers kala kala ga flask da kayan tea da sauran su. Bata bata lokaci ba gurin Jan daya daga cikin kujerun dining din ta zauna tana mai duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, motsin da taji daga stairs ne yasa tayi saurin daga kanta ta kalli hanyar gurin, kamar yadda tayi tsammani iyayen nata ne biyu mom and papa ke saukowa cikin shirin su ta tafiya aiki hannayen su sarke cikin na juna , mom sanye cikin dogon rigar less kanta babu dankwali, gashin dokin data kara a kanta a bayyane, papa kuma sanye cikin suit ash da kagansu kaga tsofafi masoya ya boko. A tare suka sakar mata murmushi, itama babu bata lokaci kyakyawar fuskarta ta yalwatu da farin cikkin ganin iyayen nata. Mikewa tayi tun kafin su ƙaraso tanufe su , jikin papa ta fara faɗawa ta bashi kyakkywan runguma tana cewa "gud morning my papa" shima zagayeta yayi da hannayen shi yana ɗan bubuga bayanta yake cewa "morning dear how ar U how was ur n9t." Ta amsa mai da "fyn papa." Sannan ta sake shi ta dawo jikin mom dake kallon su tana ta sakin murmushi, itama gaisawar sukayi kamar yadda sukayi da papa, kafin duk suka dunguma suka karasa kan dining. Suna zama kuku ya futo daga kitchen da alamar dama tsaye yake yana jiran fitowar su, cike da girmamawa ya gaishesu, kafin ya shiga serving dinsu, abinci ne lafiyayyu akayi shi kusan kala bakwai kai da gani kasan a kwai almubazzaranci a lamarin. Kusan duk a tare suka miƙe ba tare da sun ci abin kirki ba, Jakarta ta dauko a falo bayan ta shiga kitchen ta cikashi da chocolate da sauran kayan kwalama nau,i nau,i suka dunguma zuwa compound din gidan, ma,aikatan gidan ne suka Shiga kwasar gaisuwa, da sauri drivan dake kaita school ya fito da mota, duk da school din nasu ba wani nisa gare shi ba cikin anguwa ne amma kullum a mota ake kaita a dawo da ita tsabar gata. Mom ce ta kalli driven cikin harshen nasara ta ce "Peter ka barshi kawai yau ni zan yi dropping dinta tunda ina da aikin safe, kai kuma in sun tashi sai kaje ka dauko ta." A ladabce ya amsa da "yes maa." Sallama suka kara yi da papa ya sunbace ta a kumatu bayan ya sake hugging dinta a hankali yake gaya mata ta kula mishi da kanta cikin shagwaba take amsawa a sangarce. Daga cikin gidan zuwa school din kwata kwata tafiyar 15 minute sukayi har cikin school mom taso shigar da ita amma ta nuna bata so saboda gudun bacin ranta yasa mom ajiyeta a get, suna daga ma juna hannu har motar mom ya bace ma ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sunkuci Jakarta ta goya, saida ta yi tsayuwar minti biyar a bakin get din ganin babu Wanda ya ganta yasa ta juya cikin sauri sauri gudu gudu ta bar bakin get din, dai dai zata shiga wata kwana dake bayan katangar school din taji ance " *JOY JAMES* " da ƙarfi, koda bata juya ba tasan me wannan muryar hakan yasa ta juyo ido huɗu sukayi da juna ta maka mai harara tare da kallon gargaɗi kafin ta juya ta runtuma da gudu, "Joy!! Joy!!" Haka David ya dinga kwala mata kira amma a banza dan bata juyo ba balle ta tsaya, ƙwafa David yayi kafin ya kinkimi jakar shi ya shige cikin school din. ********* *AL AMEEN* kiran sallan Assalatun farko a kunnen shi saboda sabon da yayi da tashin asuba ko a wani iri hali yake idan har asuba tayi ko da kiran sallah ko babu zai farka, babu laifi yaji sauki sosai amma duk da hakan ciwon bawai ya gama sakin sa bane, lallaɓawa yayi ya mike yana yamutsa fuska alamar ciwo, ya dauki butar shi guda ɗaya dake ɗakin ƙofa ya nufa ya zare sakata tare da buɗe wa, wani sanyi ne ya doke shi wanda yasa yayi saurin rintse ido, danne zuciyar shi yayi ya zuro ƙafafun shi waje, a haka yana mammatse jikin shi ya nufi cikin gidan, tsakar gidan madaidaici ne mai dauke da daki babba guda daya ciki da falo, sai makewayi da madafi dake daga gefe. Ƙofar ɗakin Ummi ya nufa kamar kullum duk asubar duniya shi yake tashin su, sai da yaji Ummi tayi gyaran murya alamar tana farke, sannan ya lallaɓa ya nufi toilet, ruwa ya kama, ya fito ya daura alwala da sauri sauri ya koma ɗaki yana rawar ɗari, ranar kasa fita sallar asuba yayi yana ji yana gani aka tada sallah a masallacin kusa da gidan su amma bazai iya fita ba domin yana tsoron abin da zaije ya dawo bugu da ƙari kuma dama ba wai ya gama wartsakewa bane, komawa yayi ya kwanta bayan ya idar da sallah, a maimakon tilawar alƙur,ani daya saba yi kullum bayan sallar asuba har gari yayi haske, dalili kuwa, saboda jiya bawai ya samu isasshen barci bane. Ummi sai da tayi sallarta ta idar kafin ta ƙarasa kan karamin gadon dake uwar ɗakin ta, a tausahe ta kai hannu tana tsashin *FATIMA* Dake barcinta hankali kwance, ware ido fatima tayi akan Ummi, ganin ta buɗe ido yasa Ummi cewa "'ki tashi gari yayi haske, koda ba sallah zakiyi ba ki dauro alwala kizo kiyi arkar ɗinki." tashi tayi tana cewa "to Ummi" ganin ta tsahi yasa ummi komawa taci gaba da azkar ɗinta. Alwala Fatima ta dauro ta zo ta zauna ta gabatar da azkar da addu'ointa kamar yadda ummu ta sabar mata koda kuwa tana jini ne bata yarda ta barta ta zauna haka kara zube ba . Bayan ta idar miƙewa tayi taje gaban ummi ta tsuguna tace "ina kwana ummi." sai da ummi ta shafa adduar da take yi sannan ta juyo ta kalli fatima tace "lafiya ƙalau fatima, fatan kin tashi lafiya." ta amasa da "lafiya ƙalau ummi." "To alhamdulillah, maza ki tashi kije ki gaida yayan ki sai kizo ki amshi kuɗi ki sayo gawayi asaka ruwan wanka a dama kunu." "to ummi" fatima ta amsa tana miƙewa Ɗakin dake zauren gidan ta nufa, tafi matukar mamakin jin yau bata jiyo sautin zazzaƙar muryar yayanata ba, haka dai ta daure tayi sallama abakin ƙofar da mamakinta shiru taji ba amsa kusan sau uku tana sallama taji shiru abinda ba kasafai ya cika faruwa ba, hannu tasa ta dan turo ƙofar dakin ta leƙa don duk atunaninta baya ciki ne, ga mamakinta ta hango shi kwance kan gadon shi ya ƙudundune waje ɗaya cike da mamaki ta juyo ta dawo cikin gidan, ganin yanayinta yasa ummi tambayarta lafiya, cikin dan damuwa tace "ummi me yasa mu yayana yau yake barcin bayan asuba ko bashi da lafiya ne." kallonta ummi tayi kafin tace ""barci kuma? cikin sigar tamaya gyada mata kai fatima tayi ta ƙara da cewa "na leƙa ɗakin shi na ganshi kwance ƙudundune cikin bargo" ɗan jim ummi tayi ita kanta ta cika da mamaki can kuma tace "eh to wata ƙila baiji daɗi bane, bari naje na duba shi ki dauki dari biyu cikin pos ki siyo gawayi ki hura wuta." Bayan tafiyar fatima tashi ummi tayi taje ta duba Al'ameen, kamar yaddz FATIMA ta fada haka ta same shi, cike da alhini ta ja mishi kofar ta koma cikin gida. Ko da Fatima ta dawo kitchen ta shige ta hura wuta dakyar ya kama saida ta ɓata lokaci kasancewar gawayin yayi sanyi, tana gamawa ta haɗa wanke wanke, koda ta gama ta samu ruwan baiyi wani zafi ba haka ta zauna tana fofitawa har ummi ta gama lazuminta ta fito ta same ta, ganin haka yasa ummi cewa "har yanzu baki Shiga wankan ba Bintz kinsan yayanayin makarantar Ku basu da sauki idan aka makara fa" "Wlh ummi gawayin ne jikakke wutan baici sosai." Bude ruwan ummi tayi ganin zai isheta wanna idan ta juye duka yasa tace "je ki dauko bakitin wanka ki juye duka kije kiyi in kin tafi ni da yayanki sai musa muma muyi tunda mu babu Indi zamuje" Bayan ta juye ruwan, ruwan kunu ummi tasa gani har bakwai ta gota, da kanta ta zauna tana fifita wutan, koda Fatima ta fito wanka ɗaki ta wuce ta ciro kayan makaranta cikin sif a goge tsab, da sauri sauri ta fara shiryawa, cikin farin Riga mai dogon hannu da skirt sky blue sai dai nata dogo ne ya sauka har kaurinta kasancewarta musulma ta daura dankwali tare da madaidaicin hijabi daya rife mata kirjinta, Jakarta ta dauko ta fito tsakar gidan bayan ta saka takalmi da safa, nan ta tarar ummi ta gama dama kunun koko, ganinta yasa ummi cewa yawaa Binta miko robar siga da ledan kulikuli in baki naki ki karya ki tafi, ajiye jakar tayi ta koma ɗaki dauko sugar da kulin ta fito tana zare ido ganin yadda lokaci yaja. A gurguje tasha kunun bata ma shanye ba saboda da zafi ta ajiye saura ta sunkuci Jakarta, ummi tace "ki dauki nera hamsin a pos." Da Sauri ta shige dakin ta dauko tana fitowa tsakar gida *JOY* na kwada Sallama cikin gurbatacciyar hausarta, dai dai time ɗin kuma Al'ameen ya fito daga dakin shi sanye da singlet fari da dogon wando a jikinshi,turuss joy tayi gabanta na wani irin dokawa da mugun karfi take jikinta ya dau rawa lokacin da idanun Al'ameen ya sarke cikin nata..... More comment more typing Me buƙatar shiga group ya tuntuɓeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:19 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 2* Turusss Joy tayi gabata na wani irin dokawa, take jikinta ya ɗauki rawa lokacin da idanunta ya sarƙe cikin na Al'ameen, wani irin mugun kallo ya shiga jifanta da shi kallon gargaɗi da tsantsagwaron tsana wanda ita kaɗai ke ganin hakan , ta rasa dalili a duk lokacin da idanunta zai haɗu dana yayan Fatima ta kan rasa nutsuwarta, ta kan shiga firgici, da tashin hankali kwarjini yake mata kamar zaki, yanzu ma gani ta yi duk ya cika wajen, zata iya rantsuwa da yesu almasihu bata taɓa ganin murmushi a fuskarshi ba. Cikin rawar muryar ta ce " good morning Yaya Elameen." Bata yi zaton zai amsa ba don bai cika amsa mata gaisuwa ba, sai dai ga mamakin ta dauke kai yayi daga kallonta ya ce "morning." tare da rabawa ta gefenta ya shige toilet ya turo ƙofa garam. Daga ita har Fatima da Ummi da kallo suka bishi, bata san ta lula tunani ba sai da ta tsinkayi muryar Ummi na cewa "A'a Joy kece, baki tafi abinki ba kika tsaya biyoma Fatima salon ki ƙara makara, oya maza Ku tafi kar ku tsaya wasa Allah ya tsare." Sallama suka ma Ummi suka fice jikin Joy a sanyaye ko martanin murmushin da Fatima ke sakar mata bata iya mayar mata ba. Da kallo Ummi ta bisu a ranta ta rasa wannan wani irin haɗuwar jini ne tsakanin Fatima da Joy, ba yadda bata yi ba don ta raba wannan alakar tun abin baiyi nisa ba, amma ina!!! abin ya ci tura tayi dukan tayi faɗan ta daure fuskar amma duk a banza karshe dole ta hakura ta fawwalawa Allah bayan ta gane tsakanin Joy da Fatima hadin Allah ne. Motsin fitowar Al'ameen daga toilet ne ya dawo da ita hayyacinta, da kallo ta bishi har ya ajiye butar dake hannun shi, ranshi gaba ɗaya a jagule, ga ciwon daya kwana dashi yanzu kuma ga bacin ran ganin arniyar yarinyar nan mai fistari a tsaye a gidan su, tsugunawa yayi a gabanta cike da ladabi yace "Ina kwana Ummi." Amsa mishi tayi cike da kulawa tana nazartar yanayin shi, kwarai ta hango rashin nutsuwa a tattare da shi ga idanun shi ya dan fada, "Tabbas a kwai abin da ke damunshi don banza bata kai zomo kasuwa" ta fada a ranta, mikewa yayi bayan sun gama gaisawa ya nufi hanyar Zaure, murmushi tayi ta Riga ta sani dama bazai taba fada mata damuwarshi ba ita ta haife shi tafi kowa sanin zurfin cikin shi. Har ya kai bakin Zaure ya ji tace "*AMINTACCE*." Sunan da take Kiran shi da shi kenan a wasu lokutan, zai Iya rantsuwa tunda ya mallaki hankalin kanshi bai taba ji Ummi ta kira sunanshi ba yayan Fatima tafi kiran shi sau da yawa, cak ya tsaya tare da juyowa, kallon juna sukayi cikin ido da sauri ya sauke kan shi ƙasa, a sanyaye tace "Meke damunka." Bai yi mamaki ba don yasan yadda Ummi tasan shi ciki da bai duk yadda taga sauyi a tare da shi sai ta gane. Ba tare da ya dago kanshi ba ya ce "Ba koma Ummi jiya da zazzabin mura na kwana da ciwon kai amma Alhamdulillah zuwa yanzu ya sauka na ji sauki dan nasha maganin tun cikin daren." Cikin da nazarin yanayin shi ta ce "Ka tabbata." Ya gyada kai tare da ce wa "Eh Ummi." Ta ce "Allah ya kara sauki." Ya amsa da "Amin Ummi." "Kazo ka juye ruwa kayi wanka zaka ji karfin jikinka sai ka sha kunu ka kara shan maganin." "Toh Ummi."ya ce tare da juyawa ya nufi inda botikin wanka yake ranshi duk a ɓace. ********* Suna fitowa Fatima riko hannunta tare da maka mata harara cikin harshen nasara Wanda shine yaren da Joy ta fi iyawa ta ce "why Bestie me yasa kike son saka kanki cikin damuwa ne sabo da ni." Kallonta Joy tayi ta sakar mata murmushi Wanda har sai da dimple dinta ya loza, cikin jin haushi Fatima ta ce "OK dariya ma na bakin ko." Fari ta mata da idanu ba tare da ta amsa ba hakan ya ƙara hassala Fatima, take ta hade rai kamar bata taɓa dariya ba sake hannun Joy tayi ta kama hanya zata wuce ta barta, ganin haka yasa Joy saurin shan gabanta rike kunnayenta tayi cikin marairaice fuska ta ce "sorry my Teetee." Jin sunan da ta kira ne yasa Fatima kwashewa da dariya tare da kai mata dundun wasa, itama dariyar ta kwashe da shi, tana kaucema dundun Fatima, sai da suka natsa, Fatima ta ce "kin san dai mun makara, sai ki shirya amsan punishment." Ba tare da wani damuwa ba ta ce "Ai na shirya." Fatima ta ce "OK I see." Da haka suka kama hanyar school hannunsu rike dana juna suna fira suna kwasar dariya cike da nishadi hankali kwance, duk da ita Joy tsoron al'ameen bawai ya gama sakin ta bane, da ka gansu zaka hango yadda suke tsananin kaunar juna. Kamar yadda suka tsammata kuwa sun tarar ana kama late comer a bakin get ana musu bulala, sosai Fatima taji babu dadi a ranta dama abin sa take gujewa Joy kenan, amma ta lura ita Joy din babu alamar damuwa ko nadama a fuskarta. Koda suka Isa class har teachern da zai dauke su first period ya shiga class kasancewar sa ba mai tsauri ba yasa excuse kawai suka dauka ya basu izini suka shiga ciki. Suna shiga idanun Joy ya sauka akan na David daya zubo musu ido yana kallo yana gyada kai, harara ta maka mai tare da dauke kai daga kallon shi, sit din su suka nufa Wanda yake a layin gaba suka zauna su biyu, dama bibbiyu ake zama a kowane sit. Haka sukai ta daukan karatu cike da himma da kwazo don dukan su ba baya ba wajen kokari, wannan malamin ya shiga wannan ya fita har har zuwa break time, Joy ta fito musu da su chocolate da biscuit din da ta zuba a jaka suka zauna a class suna ci suna hiran karatu, sai jin tsayuwar mutum sukayi a kansu, kusan tare suka dago suka kalle shi, harara ya fara watsama Fatima wanda itama bata yi kasa a gwuiwa ba wajen ramawa kafin cikin wani yare wanda Fatima bata ji ya fara ce wa "dama nasan gidan su wannan matsiyaciyar zakije kuma ki rubuta ki ajiye daga wannan karan kinyi na farko kinyi na karshe don sai na gayawa papa halin da kike ciki a makarantar nan kin san kuma abin da zai biyo baya, wannan ai zubar mana da Kimar family kike yi." A harzuke ta ce da harshen turanci don shi tayi ji fiye da yaren su da David ke mata magana da shi "David ka fita harkata babu ruwanka dani kayi harkan ka nayi nawa a cikin makarantar nan." Ya ce "bazan fita a harkar taki ba, kiyi abin da zakiyi." Kwafa tayi ta ce "to ka ci gaba da shiga zan yi maganin ka." "Ni dai ne zan yi maganin ki, wawiya kawai Mara kishin kanta da addininta." Yana gama fadin haka ya juya ya fice daga class din, joy taji zafin zagin ta da yayi hakan yasa a zafafe ta mike zata bishi don ta rama, da sauri Fatima ta rikota tana bata hakuri, batasan takamaimai abin da suka faɗa ba tunda da yare ne amma ta fahimci a kanta ne suke wannan cacar bakin, kamar yadda ta bangarenta Joy ke fuskantar barazana da kiyayya a wajen yayanta, haka take fuskantar kiyayya da kyamata daga wajen duk wani ahlin Joy uwa uba iyayenta. David dan uwan Joy ne cousin dinta ne, mahaifiyar shi kanwar papa ne uwa daya uba daya. Rarrashinta Fatima ta shiga yi tana bata hakuri, da kyar ta hakura ta koma ta zauna don Joy akwai zafin zuciya idan ta fusata, basu fita ko ina ba har aka dawo break aka ci gaba da lesson, har kuma akayi closing bata daina hararan David tana kwafa ba, Fatima dai sai aikin rarrashi take kasancewar tasan halin kayarta. Tare suka fito daga cikin school din kamar yadda suka saba hannun sakale da juna, sarai Joy taga driventa peter yazo daukarta amma ta yi fuska ko kallon inda yake bata yi ba saboda tana so ta jera da Fatima ,sau da yawa takance Fatima tazo su Shiga mota su sauke ta amsa ƙememe take ƙi saboda gargadin ummi. Peter bai damu ba don Inda sabo ya saba da hakan, rana daddaya ne idan yazo daukan ta take yarda ta bishi. A hanyar su sai da Fatima ta san yadda ta yi, ta mantar da Joy ɓacin ran da take ciki na David, sai gata tana dariya har da kyakyatawa. Wani me sai da yalo ne ya zo wucewa yana talla a bairo, har sun gifta shi Fatima ta ce "laaa Joy bari na sai ma yayana yalo." Kafin Joy ta amsata har ta juya ta isa gare shi, hamsin din da ummi ta bata ta mika mishi ya bata na hamsin. Dawowa Inda Joy take tsaye tana jiranta tayi cike da farin ciki ta ce "nasan yayana zaiji dadi sosai don yana son yalo kamar me." Taɓe baki Joy tayi tare da cewa "Wanna yayan naki dabe dariya bashi da fara'a ko dan murmushi ni ban taba gani yayi ba kullum yayita yiwa mutane muzurai, shine zaiyi wani farin ciki don kin sai mai yalo, ni fa shi yasa yaya ko kani basa burgeni." Wani kallo Fatima ta mata kafin ta ce "waya gaya miki yayana baya dariya, waya gaya yayana baya fara'a ina jin duk unguwar nan babu wanda ya kai yayana iya murmushi." Joy ta ce "Au haka ne fa."ta fadi maganar cikin sigar tsokana, fon ita bata yarda ba gani tke yi fatina wasa take yi, Fatima ta ce "koma me zaki ce kice, kuma da kike cewa yaya ko ƙani bass burgeki wlh don bakin hadu da irin yayana bane, ganin kamar fa da gaske take yi, yasa Joy cewa "wai da gaake kike yi ko wasa." murmushi Fatima ta yi tana girgiza kai, nan kuma ta shiga ba Joy labarin yayanta yadda yake kula da ita yadda yake sonta da yadda baya kaunar bacin ranta, tun Joy na jinta sama sama har kuma labarin ya fara shigar ta, nutsuwa tayi ya maida dukkan hankalinta tana sauraren Fatima a ranta tana mamakin abubuwan da fatima tace al'ameen nayi, ji tayi a ranta koda so ɗaya ne zata so taga murmushinsa,a haka suka iso kwanan gidan su Fatima Wanda sai an wuce shi kafin a isa na su joy, ji tayi bata son su ru don bata gaji da jin labarin ba, har kofar gida ta raka fatima sannan suka yi sallama ta kama hanyar nasu gidan. Tana tafe tana murmushi ita kaɗai tana tuna labarin yayan Fatima, da haka ta ƙarasa nasu katafaren gidan, knocking tayi, jiki na bari me gari ya bude mata yana mata sannu da dawowa, bata da wulakanci da girman kai ko kadan ita dai barta da tabara da shagwaba, hakan yasa ta sakar mai murmushi tana amsawa ta sa kai ta nufi entrance din gidan. Fuskarta cike da murmushi ta turo ƙofar falon ta shiga, a bakin ƙofa ta taka birki murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya sauka akan mom da David da ke zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta da wani David da alwashin daya dauka yau a kanta, ganin iron kallon da mom ke jifanta da shi yasa taji gabanta ya fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku David ya gama dani...... Me bukatar Shiva group ya tuntubeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 3* Fuskarta cike murmushi ta tura ƙofar falon ta shiga, ta na kwalama Mom kira, a bakin ƙofa ta taka birki murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya sauka akan Mom da David da ke zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta da wani David da alwashin daya dauka yau a kanta, ganin irin kallon da Mom ke jifanta da shi yasa taji gabanta ya fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku David ya gama dani. Sai da ta hadiyi miyau mukut! Kafin ta kirkiro murmushin dole ta sakar musu , cike da fargaba ta nufi Mom don ta rungumeta kamar yadda Mom d'in ta sabar mata, hankad'e ta Mom tayi saura kad'an ta fad'i Allah ya taimaketa ta dafa kujera, cikin tsananin bacin rai ta ce "kar ki kuskura ki ta'ba ni Joy!!!" Ta karashe maganar a kausashe. A razane ta sauke manyan idanunta da lokaci d'aya suka tara kwalla a fuskar Mom, cikin karaji Mom taci gaba da ce wa "kije na yafe musu ke,tunda sun fini a ajenki kije kqai tunda ke kince baza kiji magana ba."daga haka ta mike a fusace ta bar falon ba tare da kara kallon gefen da Joy take ba. Lumshe manyan idanunta zuciyarta na wani irin tsinkewa, hakan da tayi ne yaba hawayen dake kwance a idanunta daman zubawo, minti biyu ta dauka a haka kafin ta waresu akan David dake kallonta yana sakin murmushin mugunta. Gaban shi ne ya fad'i ganin yadda lokacin d'aya manyan fararen idanunta suka rine zuwa launin jaa, take yaji wani shakkarta da tsoronta ya kama shi duk da kuwa ya girme mata don ya bata kusan shekara daya a haihuwa. Bai gama fita daga wannan yanayin ba ya tsinkayi muryarta a kunnayenshi, a kausashe ta ce "David!!! Burin ka ya cika yau ka hadani da iyayena ko, nasan kaji dadi ranka yayi maka fari ko? To ka rubuta ka ajiye na rantse da wanda ya busa min rai da numfashi sai kayi nadamar wannan abin da ka aikata." Mikewa tayi ta kama hanyar hawa upstairs. Ji yayi duk ya muzanta ida ta wuce bai mayar mata da martani ba zata ga kamar ya tsorata da furucinta ne haka yasa ya danne zuciyar shi tare da ce wa "Joy James." Da karfi, dakatawa tayi tare da juyowa suka hada idanu, takowa yayi ya iso gabanta ya tsaya, kamar zai fadi wani magana, sai kawai ya barke da wani mahaukacin dariya mai ban haushi, wani irin yawun takaici Joy ke hadiya a jejjere, ganin kuka na shirin kwace mata yasa ta juya a guje ta karkare hayewa saman bata zame ko ina ba sai dakinta kan gado ta fada tare da fashewa da kuka da iya karfinta. Mom koda ta shiga dakin ta kasa zama tayi safa da marwa kawai ta shiga yi ta kai gwouro ta kai mari, hankalinta a matukar tashe, girgiza kai tayi a bayyane cikin irin yaren da David yama Joy magana d'azu a school ta shiga ce wa " meke shirin faruwa da ni ne ni Alice, kardai asirin da na rufe tsayin shekaru goma sha biyar ke shirin tonuwa, tabbas ya kusa tonuwa." Bango ta kai ma duka kafin kamar zararriya ta ce "Ina!!! Ba zan taba bari hakan ya faru ba indai na haifu cikin pastor Samuel da Mrs Deborah." Da sauri ta rarumi wayarta ta danna ma wani lamba kira, ringing wayar keyi amma ba'a daga sake kira tayi still ba,a daga ba jife tayi da wayar a kan gado tare da zama da'bas tana tafa hannaye, can wayar ta dake kan gado daga bayanta ya fara ringing da sauri ta raruma don duk a tunanin wanda take ne ya biyo bayan kiran, ganin sunan me kiran ne yasa gabanta yankewa ya fadi, *Dr Hassan* ta ambaci sunan a bayyane tana zare ido lallai bata ga ta zama ba wai an saci san barawo. Tafi awa d'aya tana kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta hargitsa suman kanta ko takalmin school bata jire ba jakar ma jifa da shi tayi da shi can gurin kofar toilet, jinta take yi wani iri ji takeyi kamar ta aikata baban zunubi tunda take da Mom bata taba koda dungurinta bane, bata taba fushi mai tsanani da ita haka ba duk kuwa iya girman laifin da zata mata, amma yau ita ce Mom ke hankadewa lallai ta san ba karamin fushi Mom ta yi da ita ba, bata ga laifin Mom ba domin tun ba yau ba ta riga ta san yadda Mom ta kasance mace mai kishin addininta, tana tsananin kyamar addinin musulci, bata shan inuwa daya da musulmi, tana kyamarsu kamar me, ji tayi baza ta iya jurar fushin Mom, hakan yasa ta mike dakyar ta nufi dakinta. ******* KANO STATE *Dr Hassan special hospital Amenity word room number 5* Wani farin dattijo ne me kimanin shekaru 65 a duniya ke kishingide akan gadon marasa lafiyar dake madaidaicin haddadden dakin wanda kwata kwata baiyi kama da dakin asibiti ba, hannun shi sakale da karin ruwa, saman roofing dakin fuskar shi ke fuskanta idanunshi a lumshe, idan ba ka kula da yadda yake motsa bakin shi a hankali da kuma yadda yake danna caunter dake sakale a daya hannun shi da babu Karin ruwa ba zaka dauka barci ya ke yi. Daga gaban gadon wata dattijuwar mata ce zaune a kan daya daga cikin kujeru biyu dake dakin, a kalla zata kai shekaru hamshin da haihuwa amma tsabar hutu jin dadi jin iya kula da kai da yadda naira suka zauna zaka dauka batafi 38 to 40 ba, kallon dattijon mutumin nan take yi fuskarta cike da matsanancin damuwa, hannunta plate ne mai dauke da tuwon almaka da miyar alayyahu da nama, kasa ta yi da muryar a karo na barkatai cikin sanyi ta ce "Alhaji ka tashi kaci abincin mana gashi na zuba maka tun dazu yana hucewa." Bude lumsassun idanunahi yayi kafin a hankali ya ce "bana jin yunwa bazan ci ba." Shiru ta yi tana ci gaba da kallon shi tana tuna rabon shi da abinci tunda asuba da Dr yasa shi yasha tea lokacin da za'a daura mishi drip, kallon agogon dake manne a bangon dakin tayi karfe biyar harda mintuna biyu, ajiyar zuciya ta sauke, cikin son jaraba sa'arta ta sake ce wa "alhaji kayi hakuri ka tashi ka ci abincin nan, lafiya bazai samu ba idan har haka cin abinci." Wannan karan bai bude idanunnashi daya mayar ya lumshe ba kuma bai amsa ta ba, sai ci gaba da yayi da motsa bakin shi alamar yana ci gaba da lazumin shi, ganin haka yasa ta cigaba da yi mai magiya, jin ta dame shi yasa ya bude idanu tare da daka mata tsawa "keee! Nace bazan ci ba dole ne wai." Ta ke alhini da tausayin dake kan fuskarta ya bace bat lokaci daya bacin rai da bakin ciki suka maye gurbin su, ranta ya kai kololuwar baci , a hassale ta ce "wai har sai yaushe ne zaka cire wannan damuwar daga ranka? sai yaushe ne zaka dangana ka fawwalawa Allah lamuranka?, yau fa kimanin shekara goma sha biyar kenan, sai yaushe ne, iyeee alhaji na ce wai yaushe ne?" Ta karshe maganar cikin karaji tare da fashewa da kuka. Bude lumsassun idanun shi yayi ya kalleta kika take yi bil hakki, guntun murmushin karfin hali ya saki, cikin muryar shi ta marasa lafiya ya ce " ya isa haka Lubabatu kina son kisan sai yaushe ne ko?" Da sauri ta gyada kai tana sharar kwallah, idanun shi ya saka cikin nata kafin yace a kausashe "sai ranar da asirin wad'anda suka kashe ta ita da abinda ta haifa Tonu...." Yau ba yawa kuma ba editing🙏 Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 4* Mom na kallo har kiran Dr Hassan ya katse bata iya d'agawa, gaba d'aya a tsorace ta ke, banda zufa babu abin da ke tsatsafo mata, ajiye wayar ta yi a gefen bed ta rafka tagumi da hannu bibbiyu, wayarta ce ta sake d'aukar ringing kallon wayar ta yi bata d'auka ba don duk daukarta Dr Hassan ne again sai dai ganin me kira yasa ta zabura ta mi'ke, hannu na rawa ta yi received, tun kafin ta kai ga cewa komai ta ji ya kece da wata irin mahaukaciyar dariya wanda sai da ta tsorata, kusan minti uku ya kwashe sai da yayi mai isar sa kafin lokaci d'aya gimtse fuska. Jin yayi shiru yasa Mom cikin rawar baki ta shiga kokarin yi ma shi bayani, wani tsawa ya daka mata Wanda saura kadan ta saki wayar, cikin amon sautinsa mara dad'in ji ya fara magana cikin irin yaren su ba ibo "kin yi sake! Kin yi sake! Na ce kin yi sa ke Alice, tabbas abin da kike 'boyewa tsayin shekaru sha biyar zai bayyana matukar baki raba alakar *jini da jini* ba." Kan Mom ya kulle take ta 'kara tsorata jin ya ce asirin data binne tsayin shekaru zai bayyana, bata gane me yake nufi da Kalmar *jini da jini* ba, sanin hakan da yayi ne yasa ya ce "kiyi gaggawan raba Joy da ra'bar wadan nan ahlin musulman idan kuma ba haka ba." Sai kawai ya kara kecewa da dariya kit ya kashe wayar ba tare daya mata cikakken baya ni ba ya barta tana zare ido. Hakan yasa da sauri ta sake dialing number shi, daga wa yayi bai bata damar yin magana ya ce, "babu taimakon da zan miki idan har baki rabata da wadannan ahlil ba, dama na gaya miki tun farko ai karkiyi sake, idan kuma kika yi sake tabbas jini da jini ba karya bane." Daga haka ya sake kashe wayar bayan ya kwashe da dariya kamar mahaukaci. lallai bata ga ta zama ba, dole ta yi duk yadda zata yi domin taraba Joy da wadan nan tsinannun talakawan musulman, tana son jin cikakken bayani tana son sanin me Kalmar jini da jini yake nufi dan baza ta yi sake wani dan kankanin abu ya bata mata aikinta na kimani shekaru goma sha biyar ba. Saga da marwa ta tashi yana yi tare da tunanin me ya kamata ta yi, wasl zai taimaka mata, cak ta tsaya lokacin da kwkwalwa ya hasaso mata mafita. Kamar zararra haka ta rarumi wayarta ta fara dialing lambar Papa. Daidai nan kuma Joy ta karaso dakin, tana tangad'i kamar yar maye tsabar bata cikin hayyacinta, motsinta yasa Mom saurin dagowa ta kalli kofar, gabanta ne ya fadi ganin yadda Joy ta fita hayyacinta idanunta sukayi luhu luhu cikin kasa da awa daya, kwarai rauninta yaso ya bayyana a lokacin, saboda ba karamin so take ma Joy ba, a duniya Joy ce kadararta Joy ce arzikinta Joy ce rufin asirinta, dakewa ta yi ta dauke kai daga kallonta ta mayar kan wayarta, Halin da joy ke ciki yasa bata kula da yanayin yadda Mom din ke rude ba, zubewa ta yi akan gwuiwowinta daga bakin kofar don tana jin tsoron karasawa kusa da Mom, ta hade hannayenta alamar roko sannan ta sake fashewa da kuka Wanda dama cikin sa take, ba ta ce ko mai ba sai kuka da takeyi ba saurarawa. Kiran waya Mom keyi amma gaba daya hankalinta na kan Joy, kukanta na matukar ta'ba mata zuciya, har ta fara daina fahimtar abin da take yi, zuciyarta ce ke azalzalarta akan ta rungume Joy ta jawota jikinta ta rarrasheta ta hanata kuka, sai da ta yi da gaske ta yakice wannan tunanin daga ranta, dan idan yayi wasa ta bari rauninta ya bayyana ta bazan ta comma burinta na taba Joy da Fatima cikin sauki ba, juyowa tayi a fusace ta kalli Joy cikin tsawa ta ce "ki fita ki bani waje Joy bana son ganin ki." Joy data kara tsorata da lamarin Mom ta dago murya na rawa ta ce "I'm sor!!!" Kafin ta karkare fadin abin da zata fad'a Mom ta sake daka mata tsawar data fi na dazu " I said get out from here." Ta karashe maganar tare da yiyowa kanta kamar idanu waje, da gudu ta fice daga d'akin tana rizgar kuka. ********** Ko da Fatima ta isa gida, a daki ta samu Ummi, ta dan kishingid'a akan darduma da alama sallah tayi ta idar, Sallamar ta yasa Ummi da barci ya fara kwasarta ta bude idanu, ganin haka yasa Fatima cire takalmi ta karasa shiga dakin ta na cewa "Ummi sannu da gida." "Yawwa Fatima kin dawo." "Eh Ummi Allah ya dawo dani." "Maza ki debi ruwa ki dauraye jikinki ki kimtsa ga abincin ki nan a kitchen ki dauka. Bayan Fatima ta fito wanka dakin ta shiga ta kimtsa jikinta ta canza pad, wardrobe ta bude ta dauki kayan da zata saka, har ta ciro Riga da zani sai idanunta ya sauka akan wani Riga da siket na kanti da take da shi na gwanjo, ta Dade ma rabonta da sakawa, haka nan ranar taji tana sha,awar saka kayan, cirowa ta yi ta shirya cikin su, kayan sun mata kyau sai dai sun kamata tsam dai dai jikinta sabanin da da suka mata dan yawa yanzu har skirt din ya d'angale mata don iyakarsa 'kaurinta, amma dai sun bala'in yi mata kyua. Abincinta ta dauka ta ci , ganin Ummi ta samu barci yasa ta yi kwanciyarta a daki, tare da Ciro wani story book data amsa hannun Joy ta fara karantawa, tana fara karatun itama barci ya kwashe ta nan ta yada book din ta tintsire. Kiran sallar la'sar ne ya farkar da Ummi, ta shi ta yi ta fito tsakar gida dan ta dauro alwala ta na cikin zuba ruwa a buta Al'ameen ya shigo cikin gidan, shima kiran sallar ne ya tada shi ya shigo don ya daura alwala ya lallaba ya tafi masallaci, "Sannu Ummi." Cewar Al'meen kallon shi Ummi ta yi lokacin ta zuba ruwa ta tsuguna daga bakin makwarari zata fara alwala ta ce "yawwa yayan Fatima ya jikin." "Da sauki Ummi." Ya ce yana shigewa makewayi, koda ya fito Ummi ta idar da alwala ta shige daki don ba Iya kama ruwa yayi ba, sake diban wani ruwa yayi a drum ya tsuguna ya yi alwala, sannan ya fice zuwa masallacin kusa da gidan jin ana haramar tada sallah. Sai da Ummi ta idar da sallar ta tashi Fatima, akan taje ta wura wuta ta daura ruwan tuwo tunda yau alhamis basu da islamiya. Bayan Al'meen sun idar da sallah fitowa yayi daga masallaci, kallon yanayin garin yayi, ko'ina shar haka kawai yaji yana sha'awar yad'an zazzaga, Abokin shi Aliyu ne ya fad'o mai a rai murmushi yayi a fili ya ce "dan duniya nasan yana gida yanzu, bari na mike kafa na kai mishi ziyarar bazata." Kallon jikin shi yayi, ganin, kananan kaya ne a jikinshi wandon jins ruwan kasa da T shirt fari mai layilayi bakin, bai ciki son fita da kananan kaya ba, amma ganin rigar bai matse shi ba yasa ya kama hanyar unguwar su Aliyu a kafa kasancewar basu da nisa unguwa daya ne a tsakanin su. Stadium junction nan ne unguwar su Ali, a kofar gidan ya tsaya ya aika aka mishi sallama da shi, Aliyu ya fito yana waige waige, daga bayan shi yaji an ce "Aliyu timekeeper." Da sauri Ali ya juyo jin muryar da bai zata ba, a d'okace ya nufe shi ya na fadin" A'a ustaz! ustaz! ustaz! ustaz!!!! namu." Hannu Al'meen ya bashi suka kashe suna dariya, Al'ameen ya ce "Babban timekeeper babban timekeeper" suka sake kwashewa da dariya. Sunaye ne da suke kiran junan su tun a makaranta, hakan yasa koda aka gama karatun aka rabu ba'a bari ba, haka suke kiran junan su dama sunan makaranta ya gaji haka, hakan dabi'a ce ta dalibai duk Inda aka had'u komi tswon zamani kuma duk komin munin suna haka za'a kira juna, Ali ya ce "gaskiya ka shammaceni ustaz ban taba zaton kai ba ne." Al'meen ya ce "Ai baka da mutunci Ali, baka da kirki baka zumunci." Ali ya ce "Wai talle ne zai ma Audi gori ba gara ni ba ma ina kira a waya a kai a kai kuma ko last time na haduwar mu ni naje gidanku ko ka manta ne na tuna maka." "A'a fa Ali ka dai sake tunawa." Cewar Al'ameen, haka dai bayan sun gama yar musu as ka gaisa da tambayar ahalin juna daga na suka nemi waje suka zauna kan dakalin kofar gidan su Ali suka shiga hira suna kwasan dariya. Al'ameen bashi da aboki sama da Ali don shi ba mai yawan kwashe kwashe bane , tare suka yi makarantar primary nan IBB Inda bayan sun gama suka wuce maitunbi secondary school tun jss 1 ajin su daya har suka kammla gasu kuma yan unguwar kusan daya, hatta iyayensu sun san da zaman juna, yanzu da aka gama secondary kowa ya kama gaban shi shine zumuncin yayi wuya duk da suna tare a waya Bini Bini saduwace dai sai a hankali. Fira ce ta barke sosai, Aliyu ya siya musu awaran waken auya da pure water suka ci, sun sha fira sosai suna ba juna labarin makarnata da karatu, shi shi Aliyu direct university ya tafi yanzu haka FUTmin yake zuwa yana 200 level yana karanta languages, inda Al'ameen ke juwa JEFLA yana karantar bangaren Islamic low shima yana year 2 ne kamar dai Aliyu, sun Dade suna hira kafin Al'ameen ya mike yace zai wuce ganin biyar da Rabi ake nema. Taka mishi Ali yayi suna tafe suna ci gaba da hira, sunzo dai dai get din stadium wasu yan mata su uku suka fito daga cikin wajen kowaccenau cikin matsatsen JC kai ba dankwali daya da jakar baya goye a bayan ta dayar kuma hannunta kwallo ne suna tafe tana buga shi fa titi tana cabewa, da ka musu kallo daya zaka san yayan arna ne. Tsaki Al'ameen yayi tare da dauke kanshi a zuciya yana ambaton Allah da neman tsari daga shaidan, kallon shi Aliyu yayi ya ce "Ustaz namu har yanzu kanan nan da tsantsenin ka akan irin wadan nan matan." Al'meen yace "To ina amfanin wannan Abu haka don suna yayan arna sai su rika yawo haka suna fidda tsiraicin su, kamar wasu awaki, ya kamata gamnati ta dauki mataki don naga abin masgaba yake kara yi." Aliyu ya ce "waya gaya maka a zamanin yanzu yayan arna ne kawai suke irin wannan dressing, yanzu ai abin babu arna babu musulmai, don idan kaga wata yar musulman sai ka zubar da hawayen takaici yanzu haka wadan nan ma in ka bibiya musulmai ne." Da sauri Al'ameen ya ce "kai haba Allah ya sauwake, wadannan yayan arna ne babu hasken musulumci ko kadan a tare da su." Kafin Aliyu ya kai ga amsa musa suka jiyo muryar d'aya daga cikin yan matan bahaushiya rass tana cewa "Aisha, maryam pls Ku jirani na sai ruwa." Dariya Ali yayi yana cewa "you see ustaz me na gaya maka." Takaici da bakin ciki ya hana Al'meen amsawa, Aliyu ya ce "Hmmm alamarin yanzu duk sai a hankali fa kalli wasu ma." Ya Nuna mishi wasu yan mata dake sanye da atamfa amma ya matukar matsesu kamar in suka yi kwakwaran nishi zai barke, girgiza kai Al'meen yayi cikin takaici da wannan yanayin suka rabu da Aliyu ya kama hanyar gida. ***** Tunda Joy ta bar dakin Mom ta komawa dakin ta kan bed ta fada yana kuka ga ba ci ba sha, har kusan karfe biyar na yamma hakan ya saukar mata da zazzafan zazzabi mai hade da ciwon kai kafin shidda na gamma ta gama fita hayyacinci dkyar take sauke numfashi, Abu ne da bai taba faruwa da it's ba run tasowarta jinshi take yi sabo a gareta ,bata saba da hakan ba a kullum tsakanin vta Mom kulawace na musamman da Nina kauna haka ma Papa shiyasa duk ta wahala ta kasa sukuni...... Share pls kuma a dan ringa taba comment ko babu yawa, ta hakan ne zan gane kuma bite dani ko A'a Me bukatar shiga group a tuntubeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:30 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 5* Da takaicin wad'annan y'an matan Al'ameen ya kamo hanyar gida, daf magriba ya iso k'ofar gidan su, ganin ana shirye shiryen yin salla yasa bai shiga ba ya nufi masallaci, koda suka idar bai tashi ba zama yayi a cikin masallacin yana addu'o'i tare da neman Allah ya kareshi daga sharrin ta'bar'barewar zamani, bai fito daga masallacin ba sai da aka idar da isha'i, daga nan kuma bai zame ko ina ba sai gida. A tsakar gida ya samu Ummi zaune kan shimfidar babbar tabarma, tana sauraren labarai a redio kasancewar mace mai yawan sauraren labarai, zama yayi a gefen tabarmar bayan Ummi ta amsa mishi Sallama, "Ummi sannu da gida." Ya fad'a yana gyara zaman shi da kyau, "Yawwa yayan Fatima ka dawo dama yanzu nake zancen ka a zuciya, ashe kana tafe." "Eh Ummi na tsaya na yi sallah ne gaba d'aya." Ummi ta ce "yayi kyau. ya karfin jikin." Ya ce "Alhamdulillah Ummi naji sauki sosai, da nayi sallar la'asar ma na kaima Aliyu ziyara ne." Ta ce "Allah sarki Aliyu yaron kirki makaranta ya boye shi, yana lafiya." "Yana lafiya Ummi yace yana gaisheki sosai, " "Allah sarki Aliyu d'an gidana ina amsawa ." Murmushi Al'ameen ya yi tuna tsakanin Aliyu da Ummi. Fatima Ummi ta kwalawa kira, daga can kuryar d'aki ta amsa tana tasowa daga kwancen da take har zuwa lokacin riga da skirt din nan ne a jikinta, ji ta yi Ummi na ce wa "Ki zo ki kawowa yayanki tuwon shi ga shi ya shigo." Jin haka yasa da d'aukinta ta koma d'aki ta d'auko ledar yalon data siya mai d'azu a hanyar makaranta ba ta samu ta ba shi ba, ta fito fuskarta washe da fara'a, tana ji dadi zata farantawa yayanta, hankalin shi na kan daddana yar wayar shi buttus, ya tsinci muryar Fatima na cewa "Yaya sannu da dawowa." 'Dagowa ya yi yana amsa mata da "Yawwa Fatima ya gi." Sauran zance ya ma'kale lokacin da ya sauke idananun shi a kanta, ran shi ne ya baci ganin shigar dake cikin ta, ta ke ya had'e rai yana binta da wani irin kallon da yasa gabanta fara dokawa. Lokaci daya fara'ar dake fuskarta ya juye zuwa tsorata, ta ke ta fara ja da baya, bata kaunar ganin wannan fuskar na yayanta, firgitata yake yi, ya kan mata irin wannan kallon ne a duk sanda ta yi wani abu ba dai dai ba, tunda ta ke da shi bai taba d'aga hannu ya duke ta ba, sai dai ya kan ladabtar da ita da hanyoyin data gwammace gara ya faffala mata mari akan su. Ummi bata san meke faruwa ba hankalinta na kan rediyonta tana kokarin canza channel ta tsinin ci muryar Al'ameen cikin kaushi ya na cewa "Zo nan Fatima." Ya karashe maganar yana nuna mata gaban shi. Bata iya mishi musu run tasowarta, hakan yasa ta shiga matsawa a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, nesa kaɗan da inda yake nuna mata ta tsuguna, ta re da duƙar da kanta kasa, a banza ma wani lokacin bata iya haɗa ido da shi balle yana cikin iri wannan yanayin. Ummi dai da ido ta bisu su bata tanka ba a ranta tana kunfi kusa. Ciki muryar shi mai dauke da amon bacin rai ya fara cewa "Fatima wannan wacce irin shiga ce kika yi haka kina yar musulmai," tsuru tsuru ta yi tana zare ido, cigaba yayi da cewa "Ashe ba na hana ki saka kayan da zasu bayyana surar jikinki ba, ina duk tarin suturunki na mutunci da nake dinka miki? Shiru tayi ba amsa ya cigaba "Ok na gane tarayyarki da yar arna abin yayi 'kamari har kin fara kwaikwayon dabi'u da shigarta ko?." Tuni Fatima ta fara girgiza kai tana kuma jin abin da me fitowa daga bakin yayanta, "ina tambayarki baki bani amsa ba kina kuka, nace tarrayyarki da yar arna abin yayi kamari har kin fara dauka dabi'unta ko, to wlh ba a nan gidan ba, kuma zan yi wa tufkar hanci, tunda ke naga alamar bakin jin magana, don bazan zuba ido ke kadai yar uwata da nake da ita a duniya ta lalace ba, zan dauki kwakkwaran mataki akan ki dake da ita wannan yar arnan, domin hakkinane na kula da tarbiyarki." Ya kai minti ashirin yana mata fad'a ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba haushi da takaicin daya kwaso na yan matan da ya gani a hanya, da kuam haushin kawancen ta da yar arna da yake ji, duk Sai da ya sauke mata su, kafin ya tsagaita yana kallonta yana huci. Zuwa lokacin kuka Fatima keyi kamar ranta zai fita, daga yadda take jin amaon sautinsa tasan ba karamin baci ran shi yayi ba,ko daman bashi hakuri bata samu ba, jin yayi shiru yasa cikin shessheka ta ce "Yaya ka yi hakuri walla..." Dakatar da ita yayi da cewa "rufe min baki mutuniyar kawai, kuma ki bace min da gani." Dasauri ta tashi tana toshe bakin ta saboda sabon kukan da ke shirin kwace mata, ta kai bakin kofa ya d'aga muryar ya ce "kuma ki ciro kayan ki kawo mi yanzu yanzu." Ajiyar zuciya Ummi ta sauke, bata ce komai ba, a ranta Sai hamdala take da tasbihi ma ubangijinta tasan ko yau ta fadi ta mutu Fatima baza ta tagayyara ba in dai har da Al'ameen a gefenta, kallon shi tayi shima ita yake kallo, kallon tuhuma, saukar da kai kasa yayi cikin taushin muryar ba irin wanda yama Fatima magana da shi ba ya ce "Ummi kinga abinda nake gaya miki, kinga abin da nake so ki hango amma kin kasa hangowa Ummi tararryar Fatima da yar arnan nan wlh na tabbata babu alkhairi a cikin sa, Sai sharri Ummi ki buba wannan lamari dan Allah." Murmushi Ummi ta yi a ranta ta ce "yaro yaro ne kuma duk abinda babba ya hango akace yaro ko ya hau rima bazai hango ba." Jin Ummi bata ce komai ba sai bin shi da kallo da take yi yasa ya mike ya nufi haryar zaure ran shi duk ajagule. ********* Joy na barin dakin Mom dakinta ta koma, ta fada kan bed ta cigaba da kuka har zuwa lokacin ko takalmin makaranta bata cire ba bare uniform haka ta wuni a daki ba ci ba sha, har wurin karfe biyar na yamma hakan kuwa ya saukar mata da zazzafan zazzabi mai hade da ciwon kai, kafin shidda na yamma ta gama fita hayyacinci dakyar take sauke numfashi ko idanunta bata iya budewa. Abu ne da bai taba faruwa da ita ba tun tasowar ta, jin shi take yi sabo a gareta ,bata saba da hakan ba a kullum tsakanin ta da Mom kulawa ce na musamman da nuna kauna duk girman laifin da zata yi cikin rarrashi ta ke nusar da ita, haka ma Papa shiyasa ta ke ganin abin da girma. A bangaren Mom kuwa rudanin da take ciki ya shallake tunaninta, hakan yasa bata bi ta kan Joy ba. Karfe shida da rabi dai dai motocin Papa suka yi parking a counpound din gidan, fitowa yayi bayan daya daga cikin escort biyu dake biye da shi ya bude mishi kofa, fitowa yayi jacket din suit din shi a kafad'a hannushi rike da briefcase din shi, entrance din gidan ya nufa zuciyar shi cike da bege da kewar iyalan shi, ma'aikatan gidan sai kwasan gaisuwa suke yana amsa musu da fara'a, Koda ya shiga main parlour babu kowa bai damu ba, upstairs ya haura yana kiran sunan baby kamar yadda yake kiran Joy, yayi mamakin da har ya 'karasa hawa saman ya isa babban kayataccen falon daya fi na kasan kyau da kayatuwa, baiga ta fito da gudu ta tare shi ba kamar yadda ta saba, to ko dai bata gidan ne? Ya jefawa kanshi tambaya. Bai samu wannan amsar ba Mom ta fito daga dakinta, sakar ma juna murmushi suka yi wanda ita nata iyakarsa la'b'ba, bud'e mata hannayenshi yayi ta fad'a jikinshi suka rungume juna cike da soyayya,cike da kissa take mai sannu da dawowa yana amsa mata da zuciya d'aya cike da kulawa, amsar jakarshi da jacket din shi ta yi ta kama hannunshi zuwa dakin shi. Wanka ta taya shi yayi, ya shirya cikin kayan zaman gida, zama yayi a falon wanda ke hade da bedroom din shi, yana amsa called, fita Mom tayi ta dawo dauke da ruwa da lemon five alive a tray, zuba mishi ta yi ta mika mishi amsa yayi yana murmushi ya ce "thank you Sweetie." Itama murmushin ta yi ta zauna a gefen shi ta maida idanunta kan TV duk da kallo kawai ta ke yi hankalinta baya gurin, sama da minti talatin Papa ya kwashe yana waya da wani tsohon abokin kasuwancin shi wanda suke shirye shiryen had'akar Samar da wani kamfanin sarrafa 'karafina a Lagos. Ko da ya ajiye phone din Mom bata kula ba, muryar shi ta tsinta yana cewa "Hala baby bata nan ne?" Ta amsa mai da "tana nan, tana dakin ta." Murmushi ya yi ya ce "yau mulki take ji baza tazo ta ma Papa welcome back ba kenan, bari to ni naje na ganta." Daga haka ya mike ya fice daga dakin. Tun kan ya karasa dakin yake ce wa "baby where are u, I'm back, your Papa is back." Yana maganar yana murda handle din dakin nata,yana shiga idanun shi ya sauka a kan ta , zaro ido yayi kafin ya karasa da sauri ya haura kan bed din ya shiga jijjgata yana kiran sunan ta, da kyar ta bude idon ta da suka kumbura, murya a shake ta ce "Mom ki yafe Mom kiyi hakuri." Bai jita ba saboda shakewar da muryarta ya yi, a gigice ya ciro waya ya dannawa Dr dake duba su waya, jin yadda Papa ke gigice yasa, ya ce ya bashi fifteen minute gashi nan zuwa. Yana ajiye wayan ya shiga kwala ma Mom kira, bata ji ba saboda tazarar dake tsakanin dakunan, kuma gashi ko ina a kulle, ganin zai bata lokaci yasa yayi amfani da telephone din dake dakin joy ya kira lambar dakin shi da shi. Mom dake zaune ganin kira ta wayar tafi da gidanka abin ya bata mamaki, ta shi ta yi ta dauka, jin yadda Papa ke magana a rude yasa taji gaban ta ya fadi da gudu ta kwasa zuwa dakin Joy.......... Kuyi hakuri da jina shiru kwana biyu🙏 yawan comment yawan tsayin page😬 Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:31 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 6* *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* Yadda Mom ta hango Joy a hannu Papa tana kakkafewa yasa ta 'karasa da gudu, a rud'e take tambayar shi me ya same ta, cikin wani irin yanayin yace "Alice I don't no nima haka na shigo yanzu na same ta." "Jesus!!!" Mom ta ce lokacin da ta d'aura hannunta a goshin joy jin yadda ya dau zafi radau, "Mu kaita asibiti honey karmu rasata." Ta fada tana shirin fashewa da kuka, "Na kira Dr solo ya ce yana zuwa yanzu." Papa ya amsa mata, gyada kai ta yi tana share hawaye. Wayar Papa ne ya dauki ruri, ganin Dr ke kira yasa ya daga da sauri, yana cewa "ka iso ne Dr." Dan dakatawa yayi kafin ya daura da "OK ka karaso da sauri Dr ka hawo sama tana dakinta." Cikin kankanin lokaci Dr Solomon ya karaso dakin Joy yana d'auke da jakar kayan aikin shi, ganin yanayin da take ciki yasa ya nemi da su Papa su bashi guri, da kyar suka fita suka tsaya a bakin kofar dakin, Mom rungume jikin Papa tana kuka shi kuma sai bubbuga bayan ta yake yi idanu jajur, Minti talatin Dr Solomon ya kwashe akan Joy, ya gano damuwace da yawan kukan da tayi ya haifar mata da zazzabi da ciwon kai mai tsanani sai ulsanta daya ta shi saboda rashin ci da sha, take ya bata duk taimakon daya da ce, ya mata allurai tare da daura mata drip, barcin wahala ne ya kwasheta kasancewar a cikin alluran da ya mata har da na barci, sai da komai ya daidaita sannan ya fito. Da sauri suka yiyo kanshi suna rige rigen jero mashi tambaya, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya shiga yi musu bayanin abinda ya gano yana damunta, cikin kwantar da murya ya daura da cewa "kuyi hakuri yanzu dai komai zai dai dai ta don na bata duk taimakon daya dace na daura mata drip na mata allurai, yanzu haka barci ya dauketa saboda alluran da na mata masu karfi ne kuma akwai na barci a ciki zaku iya shiga shiga ku ganta." Tare suka koma dakin da Dr , zama kusa da kanta Papa yayi ya kamo daya hannunta da babu canula ya rike yana binta da kallon zallar kauna da tausayawa, Mom kuwa ta wurin kafafunta ta zauna ta zuba mata idanunta mai dauke da danshin hawaye ganin yadda ta rame ta kara haske a cikin yini guda. Gyaran murya Dr yayi duk suka kalle shi ya ce "Mr and Mrs James ni zan koma hospital dan na bar aiki sosai na taho nan, amma zuwa safe zan dawo na sake dubata na kuma kawo magungunan da zata sha, sannan ruwan da na daura mata zai Kare nan da sha biyu na dare, za kuma ta iya farkawa nan da hudun asuba idan ta ta farka Ku tabbatar ta ci abinci kafin na iso." Godiya suka mishi Papa ya rako shi har parking lot na gidan, tare da mai alkawarin kafin ya isa gidan zaiji alert kudin siyan magunguna dana shan mai, shima godiya ya shiga yi, don yasan yau account din shi zai kwana da nauyi. Kusan a kanta suka kwana suna bata kulawa, cikinsu babu wanda yayi barcin kirki, sha biyu ruwan ya kare kamar yadda Dr ya fad'a, Mom ce ta cire mata, bata farka four kamar yadda Dr ya ce ba sai gurin six na safe har sun fara damuwa suna tunanin kiran Dr ta farka. Dishi dishi ta fara gani, kafin a hankali komai ya daidaita, tar ta ware idanunta akan mahaifinta wanda zuwa lokacin shi kadai ne a dakin, da sauri ya karasa kusa da ita ya kamo hannunta yana mata sannu, kura ma shi ido tayi tana kokarin son tunano abin da ya faru, Dai dai time din Mom ta turo kofar dakin ta shigo, motsin kofar yasa ta maids idanunta gurin, idanunta ne ya sauka cikin na Mom, take abin da ya faru ya dawo mata tsab, shesshekan kuka ta fara, ganin haka yasa Mom karasawa da sauri ta kama daya hannunta, girgiza mata kai ta shiga yi, alamar kar tayi kuka, a hankali ta bude baki hawaye na bin gefen fuskarta ta ce "Mom ki yi hakuri ki yafe min." Hannu Mom tasa tana share mata haware, kafin ta ce "Ya isa haka daughter ki daina kuka, kinga baki da lafiya." "Bazan daina kuka ba har sai kin yafe min Mom, bazan iya jurar fushin ki ba." Dauke kai Mom tayi cikin dan bata fuska ta ce "zan hakura amma sai kin mini alkawari babu ke babu wannan yarinyar." Ba tare da tunanin komai ba don a lokacin mafita da sassauci kawai take nema ta ce "Na yi miki alkawari Mom daga yau babu ni babu ita har abada." Murmushin farin ciki da nasara ne ya kwacewa Mom ta rungumeta tana ce wa "nagode daughter ina son ki ina tsananin kaunarki." Dariya ta saki mai sauti cike da jin dadi ta ce "I luv u 2 my Dear Mom." Gyaran muryar da Papa yayi ne yasa Mom sake Joy, kallon tuhumar da yake mata yasa ta yin murmushi, da ido ta mai alamar yayi shiru zata mai bayanin komai anjima, bai ki ta tata ba, kawai yaja bakin shi ya tsuke. Tea Mom ta hada mata, papa ya taimaka mata ta zauna, da kanshi ya ringa bata tana sha har ta shanye, abinci mai saukin nauyi mom ta shiga kitchen da kanta ta samar mata, ganin yadda Mom ta sake da ita yasa ta kwantar da Hankalinta ta ci abincin sosai, kan kace koba sai gata ta gyagyije, da kanta tayi wanka ta shirya, cikin riga pink mai hannun singlet da wando legis fari, Karfe takwas Dr Solomon ya iso ganin yadda patient din shi ta gyagyije yaji dadi sosai, magungunata ya bata ya musu sallama ya tafi. ********* Sai da taci kuka ta koshi kafin ta mike jiki ba kwari ta kwabe kayan ta canza zuwa dogon rigar atamfa, ta dauke dan madaidaicin hijabi ta sanya, ninke wadancen kayan tayi ta kwaso ta fito dakin, ganin baya tsakar gidan yasa ta nufi hanyar zaure, sallama tayi da yar siririyar murya, amsa mata yayi tare da bata izinin shigowa, a bakin kafifar shi ta same shi zaune, har zuwa lokacin fuskarshi a hade babu rahma, daga nisa ta tsuguna, cikin sanyin murya ta ce "Yaya kayi hakuri bazan sake ba." Ta karashe tana mika misha kayan, bai amshi kayan ba kuwa bai amsa mata ba, ganin haka yasa ta sake cewa "Yaya dan Allah da manzonsa ka yafe min, wlh tsautsayine na yi maka alkawarin bazan sake ba" sai kawai ta fara shesshekar kuka. Rintse idanu yayi, jin kukarta yake kamar saukar ruwan zafi a zuciyar shi, yana jin Fatima a zuciyar shi fiye da tunani me tunani, yana mata so irin wanda kafin a same shi tsakanin yan uwa sai an tona, kukanta yakan yi saurin raunata zuciyar shi, matsayi uku yake takawa a rayuwarta UBA, DAN UWA, da kuma ABOKI, sun budi ido ne daga shi har ita basu san kowa ba sai junansu sai kuma Umminsu, hakan yasa suke ma juna wani irin so Mara iyaka, tunda ya fara girma ya fahimci basu da wani gata sai Allah sai Ummi mahaifiyarsu da take tsaye a Kansu dare da rana, ya kudiri aniyar zame mata gata, yadda yake maraicin rashin mahaifi ko wani tsayayyen dan uwa ita bazai taba bari tayi shi ba matukar yana numfashi, a komai nata yana tsaye da kafafun shi, ita macece mai raunice abar tausayi da riritawa. Dakyar ya bude baki ya ce mata ya "ya isa haka Fatima na hakura share hawayenki." Hijabin jikinta tasa ta share fuskarta da shi, gaban shi ya nuna mata yace "ajiye kayan a nan." Babu musu ta ajiye, numfashi ya sauke kafin a tausaahe ya shiga yi mata nasiha akan kula da mutuncinta matsayinta na diya mace, sosai ta nutsu tana sauraren shi sai da ya dauke lokaci mai tsawo kafin ya dasa aya. Godiya tayi kafin ta mike ta je kitchen ta dauko mai tuwon shi har zuwa lokacin Ummi na tsakar gidan tana sauraren shirin tsalle daya a radio. Ajiye tuwon tayi a gaban shi tare da ledar yalon da ke damke a hannunta tun dazu, murmushi yayi ganin yalo, ya dago ya kalleta itama sai ta sakar mai murmushi, ya ce "Nagode yar gidan Yaya Ameen" dariya ta saka cike da jin dadin yabawan da yayi da kyautarta, wani dadi yaji ganinta cikin farin ciki sai ya tsinci kanshi da yiwa marigayin mahaifinsu addua wanda har yau ko a hoto Ummi bata taba nuna musu shi ko wani nashi ba, kawai abinda suka sani ya rasu da dadewa. "Yaya sai da safe." Muryarta ya katsemai tunani, ya ce "har zaki tafi baza ki zauna muyi hira ba, ko barci kike ji da wuri haka?" Ta girgiza kai, ya ce "kinci naki tuwon ne ko?" Ta ce "A'a yanzu idan na shiga zanci." "Wanko hannu kizo muci tare." Ta amsa da "to Yaya" tare da shiga cikin gidan danta wanko hannu kamar yadda ya umarceta. Cike da nishadi suka ci tuwonsu cikin kwarya daya suna wasa da dariya, a karshe ya saka katon loma, kukan shagwaba ta saka tana dire kafa, cinyewa yayi ya kara kai hannu da sauri ta dauke kwanan ta cinye guntun daya bar mata, tana tura baki, yana mata dariya da gwalo kamar bashi ne dazu ya rufeta da fada ba, bayan ta kwashe kwanukan wanko hannu tayi ta dawo, nan shiga bata labaran ban dariya yana cin yalo yana yabawa ita kuma dadi kamar ya kasheta, daga karshe ya saurari haddarta. Ummi na tsakar gida tana saurarensu, tsakanin Al'ameen da Fatima sai Allah,ko ita data haifesu bata ce ga tsakanin subab, a haka bata san sanda ta fara gyengyadi ba. Ba su suka ta shi ba sai gurin goma da rabi, shima ganin tana ta hamma yasa ya ce taje ta kwanta, koda ta shigo gida ta samu Ummi tayi barci radio a kunne tashin ta ta yi, suka wuce daki bayan sunyi alwalan kwanciya. Washegarikamar kullum ta gudanar da aiyukanta na safe tayi shirin makaranta, tana ta zuba idon ganin Joy sai dai shiru shiru har ta gama ta fito gida ta kama hanya, yana ta tunanin ko zasu hadu a hanyar amma shiru har ta isa bakin get, bata kara shiga damuwa ba sai da ta isa class ta tarad babu joy babu me kama da ita, haka ta zauna jiki a sanyaye tana tunanin mekefaruwa ne yau, iya Sanin ta Joy bata fashin makaranta, can sa'insar daya shiga tsakanin joy da David ya fado mata, take gaban ta ya yanke ya fadi rassss.......... Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lamabar 09116099486 [12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *BY* *AYSHA NALADO* *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* *LITTAFI NA ƊAYA* *PAGE 7* *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* Ranar haka Fatima ta wuni a school babu walwala, sboda rashin zuwan Joy, gaba ɗaya jin school ɗin take yi babu daɗi a haka har suka yi closing, jiki a sanyaye ta kamo hanyar gida cike da tunanin abin da ya hana joy zuwa school, fatan ta Allah yasa dai lafiya. A kulle ta iske gida alamar babu kowa, sai lokacin ta tuna Ummi ta ce mata zata dan fita idan ta dawo ta karɓi key a maƙota. Gidan da ke kallon gidan su ta shiga, shima dai kamar nasun ne, na y'ay'an mallam shehu, sai dai yafi nasu girma da yalwar ɗakuna, sallama ta yi a ƙofar ɗakin Maman Amira kamar yadda suke kiran matar gidan, Amira ce ta fito daga ɗakin tana amsa sallamar, ganin Fatima yasa ta fad'ad'a fara'ar fuskarta, budurwace yar kimanin shekara goma sha bakwai, sanye da wandon uniform dinta na girls day, ta cire rigar ta bar farin singlet da alamar itama dawowarta kenan. Murmushi Fatima ta sakar mata tare da cewa "Yaya Amira ina wuni." Cikin sakin fuska ta amsa da "Ina gajiya Fatima kin dawo ya school." Fatima ta ce "Alhmdllh." "Shigo mana tana ciki." Amira ta faɗa tana kauce mata a hanya, "A'a dama Ummi ce idan na dawo na karbi key gurin Mama." "Ok bari na karbo miki." Ta koma ciki ba jimawa ta fito da key din ta mikawa Fatima, amsa tayi ta fice, bayan tayi godiya, da kallo Amira ta bi ta fuskarta dauke da murmushi a fili ta ce "kamar su daya sak! komai nasu iri daya hatta murmushin, ya Allah ka mallakamin Yaya Ameen kasa ya zama majibancin rayuwata, jin Mama kwala mata kira yasa ta amsa tare da komawa dakin da sauri. Ta tarar da gidan tsab kamar kullum, dakinsu ta bud'e ta shiga ta canza kayan jikinta, ganin Ummi bata nan yasa bata tsaya watsa ruwa ba, don idan tana nan bata yarda ta ci abinci sai ta watsa ruwa tayi sallah. Kitchen ta bude ta dauko Kular abincinta, shinkafa ce garau garau da yaji, a nan tsakar gida ta zauna ta ci abincin, tana gama ci ta mike ta kai kular kitchen, tana fitowa Al'ameen na shigowa bakin shi dauke da sallama, amsa mishi tayi tana mishi sannu da zuwa, murmushi ya sakar mata yana amsawa. Idanunshi duk sun zurma kafafunta shi futufutu, takardun hannun shi ya ajiye kan windon d'akin Ummi, ya ja kujerar ummi yar tsuguno ya zauna yana ce wa "Fatima bani ruwa a buta." Da sauri ta dauki buta ta kai mishi bayan ta zuba ruwa, kafafunshi ya shiga wankewa, Fatima dake tsaye daga gefe ta ce "Yaya tracking kayi ne?" Ya ce "Eh kuma A'a kusan dai haka." Ya karashe maganar yana miƙewa don ya riga ya gama dauraye kafar nashi. Kofar dakin Ummi ya nufa, ganin haka yasa Fatima ta ce "Bata nan Yaya." Juyowa yayi ya kalleta a mamakance ya ce "Bata nan, ina taje?" "Wlh ban sani ba ta dai ce min zata dan fita da safe kafin na tafi school." Gyada ka yayi bai, kara cewa komai ba ya nufi dakin shi, Fatima kuma ta nufi kitchen ta dauki abincin shi tabi bayan shi da shi. Abincin ya ci ya koshi, bayan ya gama yasha ruwan sama, kishingid'a yayi a katifar shi ya lumshe idanu, da ace shi wani dan gata ne da kwanciya zaiyi ya huce gajiyar daya kwaso na tafiya, amma yasan haka ba Abu ne mai yuwuwa ba, idan ya kwanta wa zai basu su ci,wa zai kula da mahaifiyar shi da kanwar shi, wa zai dauki dawainiyar rayuwar su, wa zai biya musu bukatunsu na yau da kullum???, "Babu." Ya ba kan shi amsa a bayyane, shine gatan su da shi suka dogora da Allah suka dogora, tunanin yadda yasha gwgwarmayar zuwa da dawowa school yau ya shiga yi, zai Iya cewa daga zuwan har dawowar kusan da kafa yayi saboda halin babu, duk abin da ya roro ba ta kan shi yake yi ba, ta Ummi da Fatima yake yi, sune a gaban shi, da wannan tunanin ya yunkura ya mike ya canja kayan jikin shi ya fice daga dakin. Cikin gidan ya shiga ya ma Fatima sallama sannan ya fice, daga gidan, direct unguwar Sayako ya nufa gidan Alhaji bala baka shot, in da yake zuwa daukar keke napep, ya na fatan Allah yasa akwai keken a kasa, cikin sa'a ya samu har biyu a kasa, take aka bashi wani form yayi singing, singing din da kulli yaumin idan zai yi sai gaban shi ya fadi ya rasa dalili, amma haka yake daurewa domin bashi da wata hanyar da zai samu kudi a saukeke sai wannan, yana dan tana sana'ar hannu, amma aikin nashi ne ba ko wani lokaci yake samu ba, haka ya dauki keke daya ya kama aiki da bismillah. Tafiyar Al'ameen babu dadewa Ummi ta dawo,dauke da buhun bakko, Fatima ta tare ta ta amsar mata kayan, tana mata sannu da dawowa "yawwa Fatima sannu da gida," ta karashe maganar tana zama a kan kujera, " matso da bakkon nan Fatima mu gani." Matso mata da shi gabanta tayi, kwancewa tayi ta shiga fito da kullin ledodi a kasa buhun kuma ta fito da doya manya guda uku, kallon Fatima da tayi kasake tana kallonta tayi ta ce "kwashe wannan ki kai mana kitchen wannan kuma ta fada tana nuna mata ledodin gabanta ki bud'e robar da muke ajiye kayan abinci ki sassakasu ciki shinkaface da wake, Fatima da mamakin Ummi ya gama kasheta tace "Ummi kasuwa kika je? Ita kanta bata san sanda tambayar ya subuto mata ba ganin dai tunda suke Ummi bata tana zuwa kasuwa ba komai yayanta ke kawowa, komai za'a siya shi yake siyowa dagowa Ummi tayi ta kalleta kafin ta ce "ba kasuwa naje ba." "To ina kike je waya baki wadan nan kayan abincin?" Ta fada a zuciyarta a zahiri kuma ta ce "Oh ai na dauka can kika je na ganki da kayan abinci." Ummi bata amsata ba, sai ci gaba da kokarin kwance ledan shambo da tarugu da take yi ta juye a kwando. Cefane Ummi ta dawo da shi ba na wasa ba , harda su mai da maggi da busasshen kifi, sai da suka gama Adanawa tsab ta kalli Fatima ta ce "ba na son yayanki yayanki ya san da maganar kayan abinci nan ko da wasa." "To Ummi amm....." "Kinji abunda na fada ko baki ji ba." Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "naji Ummi insha Allah bazai ji ba." Murmushi Ummi tayi ta ce "yawwa fateetee ngd,." Fateeteen data fada yasa Joy ta fado mata a rai, cike da dan damuwa ta ce "Ummi yau joy bata zo school." Ummi ta ce "Allah sarki kila ta samu wani uzurine yau din." Fatima ta ce "ummi Joy fa bata fashin makaranta, ni dai ina ji a jikina kamar bata lafiya, tun dazu da na tuno ta gaba na ke faduwa." Ummi ta ce "Assha! To kiyi ta addua, koma menene Allah ya takaita." "Amin Ummi" Fatima ta amsa yana mikewa zuwa kitchen dan ta hada wutar sanwar dare. Karfe Tara dai dai Al'ameen ya maida keke nape gidan Alhaji bala baka shot, kamar yadda yayi singing sanda zai dauka haka yayi singing da ya mayar bayan alhajin da kan shi ya duba lafiyar keken, yaga babu wata matsala, 3k Al'ameen ya bashi cikin cinikin dubu hudu da dari biyu da yayi, amsa yayi yana washe baki sabanin da da fuskarshi yake murtuk yana jiran yaji da wannne ya dawo dan yanzu kafin shi mutum biyu da suka dawo da kekuna har yanzu gasu nan ana kes, daya ya samu accident gefen keken ya lotsa dayan kuma dubu biyu yakawo sabanin dubu uku da yake a ka'ida idan mutum yayi fitar rana zuwa taran dare zai kawo. Sallama yayi musu ya tafi bayan yabar alhaji bala na ta bala'i a biya shi ko ya hada su da polie don shi akan kudi babu sani babu sabo ne. Sai gurin goma saura ya iso gida, a tsakar gida tarad da su, Fatima ta tare shi tare da karbar ledan biredin daya siya musu a hanya. Ummi ya tsuguna ya gaisar kamar yadda ya saba kullum, ta amsa mishi tana "Alhmdllh yayan Fatima jiki yayi warware dama tunda na dawo Fatima ta ce ka fita aiki nace to jiki ya yi dauki kenan." Murmushi yayi ya ce "eh ummi wlh jiki Alhmdllh." Nan ya zauna Fatima takawo mishi abincin ya ci suna ta hira, gefe daya kuma iska na kadawa hadari na haduwu, Sai gurin sha daya saura Ummi ta ce su ta shi haka gobe da makaranta, dari takwas din daya rage mai a aljihu ya kwaso duka ya mikawa Ummi, ya ce "Ummi ga wannan ki rike a hannunki a sai wani abin." Kallon shi tayi tana murmushi ta ce "A'a Amintacce ka bar shi kaima ka rike a hannunka kayi hidimar makaranta ni akwai kudi a hannuna kuma a kwai abincin da zamu ci gobe ka fini bukatarsu, Allah yayi albarka." Tana gama fadin haka ta mike ta shiga daki ta turo kofarta don karma ya tsareta da magiya, Iska da hadarin daya taso gada gadan ne yasa shi sauri ta shi yayi hanyar dakin shi, gaban shi na dokawa wanda shi kadai yasan dalilin haka. Kamar jira ake yi su ta shi a tsakar gidan, take ruwa ya kece da wani irin karfi mai ban mamaki, kudundunewa yayi cikin bargo bayan ya lafta kaya masu nauyi a jikin shi, kwance yake kawai yana jiran tsammani, amma zuciyar shi cike take fall da tsoro, fatan shi daya kar ciwon shi ya tashi, shiru yayi a kwance yana sauraren sautin ruwa da haka barci barawo ya kwashe shi ba tare da sanin shi kasancewar dama a matukar gajiye yake. Kusan raba dare akayi ana tsuga ruwa, can cikin barcin shi ya fara jin sauyi a jikin shi, ji yayi wani irin sanyi na ratsa kasusuwan jikin shi, babu abin da yake bukata a lokacin sai dumi, duk da kasancewar a cikin bargo yake a kudundune, dumi yake bukata ba irin dumin bargo ba, sannu a hankali tsigar jikin shi ya fara tashi, kafin daga bisani wani irin feeling ya lullubeshi, rasa Inda zai saka kanshi yasa ya cusa duka hannayenshi cikin wandon shi, ya matse abin shi dake ta mishi wani irin honkoro, yana ambaton innalillahi wainnailai rajiun a zuciya, magani yake son sha , amma har yanzu abin bai kai matakin da Dr ya ce idan ya kai ya hadiyi maganin ba, kuma baya fata ya kai stage din, sai dai fatan shi bata karbu ba, dan cikin abinda baifi minti biyu ba maran shi tayi wani irin kullewan da yasa babu shiri ya yaye bargon ya mike ya nufi jakar nan, ya zaro sachet din maganin shi balla yayi ya jefa a baki kafin ya bi da ruwan buta ya koma ya kwanta yana nunfarfashi. Da asuba da karfin shi ya tashi ba kamar wancen ranar ba kasancewar bai bari ciwon ya shige shi sosai ba ya sha magani, kamar kullum saida ya kwankwasa masu Ummi kofa kafin ya wuce masallaci, koda ya dawo zama yayi ya gabatar da azkar da sauran addu'o'inshi Inda ya roki Allah ya kawo mishi dauki game da wannan matsalar da kullum kara gaba take yi a gare shi, bayan ya gama kuma ya daura da karatun alkur'ani mai tsarki cikin daddadar sautin kira'ar shi wanda ya karade ko ina na gidan hatta da gidajen makota na kusa, Amira tana daga tsakar gidan su ta na aikace aikacenta tana sauraren shi zuciyarta gari tass. Seven fourty Fatima ta gama shirinta na schools, sai dai yau ma kamar jiya har ta fito gida babu Joy babu labarinta, jiki a sabule ta k'arasa class, tana fatan Allah yasa ta cimmata a can , sai dai nan ma wayam, haka ta isa sit din su ta zauna jiki a mace. Yau kan damuwar data shiga yafi na jiya haka kawai jikinta ke bata ba lafiya ba, ta kudiri aniyar zata tambayi David ta ji ko mekefaruwa tun da shi dan uwanta ne bazai rasa sani ba. Da aka buga break time, ta yi sauri ta isa sit din David da har ya mike yana goya jaka da harshen nasara ta ce "Sannu David." Wani banzar kallo ya mata ya dauke, bata damu ba ita dai fatan ta taji halin da Joy ke ciki ta sake ce ma shi "me yasa Joy bata zo school ba kwana biyu." Share ta yayi kamar bada shi take magana ba bata yi zuciya ba ta sake cewa "ko bata da lafiya ne dan Allah ka gaya min na damun sosai da rashin ganinta?" D'agowa yayi wannan karon ya ce "ha'ahh! Wai ke mayya ce ne? To nima ban sani ba kije gidan su ki duba."daga haka ya fice ya barta tsaye a wurin. Haka Fatima ta koma gida cikin wani irin yanayi, tana isa kuwa labarin yau ma Joy batta zo school ba ta fara ba ummi da yadda sumayi da David, tausarta Ummi ta yi akan kar ta damu in sha Allah joy tana lafiya ai lafiya ke buya, ta dai ji ne kawai amma ba wai hankali ta ya kwanta ba. Ranar har Yaya Ameen sai da ya fahimci tana cikin damuwa daya dawo da daddare, shima cikin damuwar yake amma ya danne nashi, koda ya tambayeta damuwarta kin fada ta yi sai hawaye da ta shiga zubarwa sharr! Ummi na jin su bata saka baki ba, don abin na Fatima ya fara wuce makadi da rawa, har kullum bata gajiya da mamakin irin shakuwa da kaunar dake tsakanin Joy da Fatima. Da kyar Al'ameen ya lallabata ta sanar mashi da damuwar tata, tabe baki bayan ya gama sauraranta, shi bai ga abin damuwa akan wannan ba, hakan yasa bai bama damuwar tata mahimmanci ba, sai ma canza akalar hirar tasu da yayi. Washegari daya kama friday ma bata sake zani ba still Joy bata je school ba, zuwa yanzu kuwa ta gama yanke shawaran bin abinda zuciyarta keta azalzalanta akai wato zuwa gidan su Joy ............... Me buƙatar shiga group ya tuntuɓeni ta wannan lambar 09116099486 [12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *PAGE 8* ASSALAMU ALAIKUM KUYI HAƘURI DA JI NA SHIRU DA KUKA YI KWANA BIYU, HAKAN YA FARU NE SABODA WANI DALILI MAI ƘARFI , AMMA YANZU NA DAWO INSHA ALLAH ZAMU ƊORA DAGA INDA MUKA TSAYA, FATAN DAI BAKU MANTA LABARIN AL'AMEEN DA JOY BA KUCI GABA DA BIBIYA AKWAI FAƊAKARWA, WA'AZANTARWA RIKICIN KABILANCI, TARE DA ZAZZAFAN SOYAYYA MAI TAƁA ZUCIYA. A bangaren Joy kam jinye take yi hankali kwance, daga Mom har Papa wani irin so da kulawa suke nuna mata na musamman, sai dai kamar yadda Fatima ta shiga damuwa saboda rashin ganin ta, haka itama ta shiga matsanancin damuwa saboda rashin ganin Fatima, hakan yasa ranar Friday ta shirya don zuwa school amma ƙememe Mom ta hana ta zuwa ta ce ta bari sai Monday badan ta so ba ta haƙura saboda kar Mom ta zargi wani abu, ta bari idan ta wuce aiki sai ta saci jiki ta je gidansu koda Ummi ne ta gani, da wannan shawarar ta koma ɗaki ta cire uniform ta yi shirin zuwa gidan su Fatima, sai dai ga mamakin ta ranar Mom ƙememe taƙi fita ko bakin get har wurin sha ɗayar rana, kamar tasan abin da take ƙullawa, gajiya tayi ta miƙe taje ɗakin ta, a kwance ta sameta bata da alamar fita, zama ta yi a bikin bed ta ce "Mom yau baza ki je aiki ba ne." kallon ta tayi kafin ta amsa da "Yes daughter yau na ɗauki excuse zan huta sai on Monday." har ranta bata ji daɗin wannan lamari ba don ta sani in dai ba yau ba to bata da damar fita daga gidan sai ran monday, ita kuma bata jin zata iya jurewa har zuwa ranar ba tare da ta saka Fatima a idanunta ba, haka ta bar ɗakin Mom jiki a sanyaye, ranar haka ta wuni sukuku duk ranta babu daɗi. Kamar yadda Fatima ta ƙudiri aniyar zuwa gidansu Joy yau, bata yi ƙasa a gwiwa ba, la'asar nayi tayi shirinta na hadda, cikin dogon zumbulelen hijabi ta ruwan toka, ko jiran Ummi ta shafa addu'a suyi sallama da kyau bata yi haka bata biya gidan su Amira su jera da yara gidan kamar yadda suka saba jerawa ba ta wuce. Direct haryar gidan ta kama tana sauri don kar ta ci karo da idon sani.Sai da ta tsaya a gaban tangamemen get ɗin gidan sannan gabanta ya fara faɗuwa take wani irin tsoro ya shige ta, tsoron mahaifiyar Joy , sau ɗaya rak ta taɓa ganin matar wata rana an tashe su school, tun daga irin kallo ɗaya data mata tsoronta ya ɗarsu a ranta, sai dai bata jin duk da haka zata iya komawa batare da ta san halin da Joy ke ciki ba don ta tabbata baza ta iya rintswaba idan hakan ta kasance. Ta fi minti goma kafin ta daure ta miƙa hannu tayi knocking ɗin ƙaramin kofar get ɗin a hankali, bata zata za'a jiyota ba balle har a buɗe mata sai dai ga mamakinta taga an buɗe get ɗin wani baba iyamuri da ko zo in kasheka da hausa bai sani ba ya leƙo. Suna haɗa ido gaban ta ya faɗi amma ganin ya sakar mata murmushi, yasa taji hankalinta ya ɗan ƙwanta, cikin harshen nasara daya caƙude da yaren igbo ya ce "My daughter who ar u looking." da sauri itama cikin harshe da ya mata magana ta ce "I'm looking 4 Joy, ni ƙawarta ce naga kwana biyu bata zo school bane shi ne nazo in dubata ko lafiya." ɗan jim ya yi kafin ya ce "kom in." tare da buɗe mata ƙaramin get ɗin, jiki a saɓule ta bi bayanshi gabanta na dakan uku uku. Gurin zama ya nuna mata daga gefe, ya ce ta jira shi ya na zuwa yama Joy ɗin magana, idan ya shiga wa za'a ce mata, ta ce "Fatima Husain." "Ok." ya amsa mata tare da ficewa. Farfajiyar gidan Fatima ta shiga bi da kallo, bata taɓa shigowa gidan ba sai yau, take ta ji ta raina kanta, ashe girman gidan da tsaruwar shi daga waje duk shafan mai ne akan cikin, baƙauyiya tukuf ta koma tana bin ko'ina da kallo baki sake , tare da tunanin wani irin dukiya mahaifin Joy ke da shi haka, manyan motocin dake fake a parking lot ta ringa kallo tana al'ajabin yanzu duk wannan na mutum guda ne. Get man direct entarance ɗin first plat na gidan ya nufa, tare da danna doorbell, dai dai lokacin Mom na zaune a main falon tana cin cake, tasowarta kenan daga barci yunwa ya korota ƙasa, ɗaya daga cikin hause maid na gidan waɗanda ke da zarafin shiga cikin part ɗin, ta kira ta ce ta duba wayake knock,dubowa tayi ta dawo ta sanar mata get man ne, umarni shigowa ta bashi, ya shigo ya zube a gabanta ya kwashi gaisuwa duk da ya girme mata nesa ba kusa ba don zai Iya haifarta ma, cike da fariya ta amsa, ya ce "Wata ce ta zo neman Joy yar school din su ce, ta ce sunan ta Fatima Husain wai taga kwana biyu batta zo school ba shine ta zo ta gani ko tana lafiya." Bata rai tayi tare da hade girar sama da ta kasa, ko bata tambaya ba tasan wannan tsinanniyar Muslim girl din ne dake shirin warware mata aiki, wato har abin bai tsaya Iya school ba shine har gida zata biyo ta, aiko zata ci ubanta yau sai ta gwammace kida da karatu a fusace ta mike ba tare da bi ta kan get man ba ta fice daga plat din, bayanta ya biyo da sauri yana tambayarta ko lafiya, Bata saurare shi ba, ta wuce kamar kububuwaa'aikan gidan tuni kowa ya shiga taitayin shi suka bits da kallo, a zaune ta tarar da Fatima in da get man yace ta zauna ta shagala da ka kallon flawers bata san karasowar Mom ba sai dai ta ji saukar gigitacen mari a kumatunta, a firgice ta mike tsaye, tare da sauke idanunta akan mahaifiyar Joy take gabanta ya yanke ya fadi, firgici da tsoro suna bayyana karara a fuskarta, shakar wuyar hijabinta Mom tayi cikin zare ido ta ce "Me ya kawo ki gidan na, Me kike nema a gidan nan,menene tsakanin ki da yata, abin naki har ya wuce school shine kika biyota har gida ko, ina da labarin komai akan gurbata mata tarbiya da kike yi da canza mata akida, to ina miki warning da babbar murya daga yau sai yau na miki tsakani da Joy babu ke babu ita, ba a gida ba, ba a makaranta ba, ki rabu da ita kar ki sake kulata idan kuma ba haka ba na miki alkawarin sai na batar dake a garin na daga ke har zuri'ar Ku gaba daya." Daga haka ta shiga janta keee kamar kayan wanki ta nufi get da ita. Hayaniyar Mom yasa Joy dake kwance a dakin ta cike da damuwan rashin damun famar zuwa gafan su Fatima saurin mikewal ta daga labulen window tare da lekawa idanunta ya saka a kan Mom rike da wuyan Fatima tana ja, gabanta ne ya yanke ya fadi, da wani irin mugun gudu ta nufo downstairs tana tsallakewa bibiyu ba tare da ta kula ba, tun daga bakin kofar part din ta shiga ce wa "Stop Mom Stop Stop please." Amma ina bata jita ba, ta bude get din tare da hankada Fatima wacce tuni ta fice a hayyacinta Wuyan hijabinta ya yage ya zame kasa, dankwalinta ya fadi kasa gashin kanta ya bayyana waje. Wani irin hankada ta mata mai mugun karfi da biyu niyarta ta tura ta bige da palwayan dake kofar gidan irin na kasan nan, sai dai kawai tajita caraf jikin mutum, wanda ya diro kamar daga sama, dai dai time din Joy ta iso wajen su a guje tare da rike hannun Mom tana kuka..... [12/29, 2:33 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *PAGE 9* Gaba ɗaya Fatima ta gama sadaƙarwa ta bugu da falwayan nan dan har ta rintse ido, sai dai babu zato ko tsammani ta jita a jikin mutum, turarensa ne ya tabbatar mata da cewa shi ne, take ta ƙamƙameshi tare da fashewa da wani irin kuka mai ƙarfi. Rintse idanu Al'ameen yayi zuciyar shi na tafarfasa, zai iya jurar komai amma banda taɓa tilon kanwar shi, zai iya yin fito na fito da ko waye akanta, ita kaɗai ce wacce zai iya bugu ƙirji ya nunawa duniya a matsayin ƴar uwarshi. Lokacin da ta fito daga gida tana shan kwanan gidan su Joy yana ɓullowa bata ganshi ba amma shi ya hango bayan, kamar ya kwala mata ƙira sai wata zuciyar ta raya mishi cewa ba ita bace, tunda yasan ba nan bane hanyar haddarsu wata ƙila daya daga cikin yaran maƙota ne da suke zuwa hadda ɗaya, sai dai shigan sa gida ya tabbatar masa da ita ɗin ce, don gaba daya ya tarar da yaran makotan nasu a tsakar gida wai sun biyo mata su tafi hadda, yana ji Ummi ta amsa musu da Fatima ta riga ta wuce bata biya musu bane" Gabanshi ya faɗi, ke nan ita ɗin ce ina zata je??? ya jefawa kanshi tambaya, tsoro ne ya shige shi lokacin da zuciyar shi ta raya ma shi wani mugun tunani, ta ke ya kawar da shi ya na girgiza kai, kasa kwanciya hankalin shi yayi hakan yasa ya biyo bayanta da sassarfa ba tare da ko Ummi ya sanar wa mekefaruwa ba, kwata kwata bai kawo gidan su Joy aka ba, sai dai ganin ya shanye kwanar ya shiga wata bai ganta ya fara zargin ko can ta je, take hirarsu ta jiya da dare ya dawo mai, tabbas yadda yaga ta damu da rashin ganin Joy yasan zata iya zuwa gidansu don ta duba lafiyarta, take ya kama hanyar gidan cike da yaƙinin ganinta sai dai yana isowa Mom na hankaɗo ta waje kamar wata barauniya. Sautin kukanta ne ya tilasta ma shi buɗe idanun shi waɗan da suka rine kamar gauta saboda ɓacin rai ya sauke su a kan get ɗin gidan, daidai lokacin da Mom ke banko ƙarami ƙofar bayan tayi nasaran tura Joy ciki dakyar. Hannu ya saka ya janyo hijabinta ya rufe mata kanta dake buɗe, a hankali kuma ya shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi ba tare da ya iya buɗe baki ya furta mata koda kalma ɗaya ba. A hankali sautin kukanta ya fara raguwa, daga bisani kuma ya dauke gaba ɗaya, sai shessheƙa da ajiyar zuciya, ganin ta ɗan samu nutsuwa, ya raba ta da jikinshi tare da kama hannunta suka bar ƙofar gidan ba tare da ya ƙara yi ma gidan kallo ɗaya ba. A bangaren Fatima mari da hankadar da Mom ta mata bai daga mata hankali ba, kamar yadda kalamanta suka daga mata hankali, tana jin Joy a jikin jinin jikinta da bargonta, jinta take yi kamar wata bangaren na jikinta, kwatankwacin yadda take jin Yaya Ameen haka ta ke jin Joy a zuciyar ta, shin me yasa Mom take son raba su, ta karashe tunanin sabbin hawaye na silalowa daga idanuwanta. A haka suke iso ƙofar gidan su ba tare da Al'ameen ya iya buɗe baki ya ce mata ƙala ba, domin ran shi a maruƙar ɓace ya ke idan ya ce zai yi magana a lokacin bazai faɗi alkhairi ba. A zaure ya dakatar da ita, ya shiga ciki ba jimawa sai gashi da dayan hijabin haddanta a hannunta shi, buta ya dauko ya bata ta wanke fuskarta, sannan ya bata hijabin ta saka, ya sake jan hannunta, bai tsaya da ita ko ina ba sai haddarsu, hakuri ya baiwa malamin su akan lattin da ta yi, sannan ya juya ya tafi ba tare da ya kalli Inda take ba, sai lokacin shirun na shi ya fara daga mata hankali, ta san sarai shirun nan na yayanta ba alkhairi bane akwai abin a yake shiryawa, magantuwan shi yafi alkhairi sau da yawa fiye da shirun shi. ********* A bangaren Joy dakyar Mom ta samu ta turata cikin gidan ta maida get ta rufe, zubewa ta yi a wajen ta fashe da wani irin kuka, cikin kukan take cewa "why Mom me yasa zaki yi mata haka, me yasa kika koreta Mom, me yasa kika daketa." Mom dake wani irin huci ta dago ta watsawa ma'aikan gidan da suka yi cirko -cirko suna kallonsu wani mugun kallo take duk suka dare kowa ya kama gaban shi, tsugunawa ta yi gaban Joy a tausashe ta riko hannayenta ta ce "Ki daina kuma daughter ban yi haka don na bata miki rai ba nayi ne dan kare martabarki data addininmu, na mata haka ne saboda ta rabu dake don ke ba sa'ar kawancenta bane," katseta ta yi da cewa "Amma ai na miki alkawarin ni da kaina zan rabu da ita, me yasa zaki wulakantata." Mom ta ce "To naji kiyi hakuri ki share hawayen ki, kinga baki da isasshen lafiya." Mikewa ta yi ba tare da ta kula Mom ba ta wuceta fuuu ta shige plat din su haurawa sama ta yi ta fada dakinta ta bugo kofa ta murza key. Nan ta silale bakin kofar ta ci gaba da rera kukanta ji take kamar ta yi tsunstuwa ta ganta a gaban Fatima, me zata ce mata da wani ido zata kalle ta, uwa uba Yayanta shin da wani baki zata fahimtar da su ce wa bata laifi. Biyo bayanta Mom ta yi ta tura kofar dakin ta ji shi a rufe, knocking ta shi ga yi tana kiran sunanta, tana ji taki tankawa, babu irin magiyar da Mom bata mata ba, karshe dole ta kyale ta, gajiya ta yi da kukan ta mike ta shi ga toilet ta wanke fuska ta dawo kan bed dinta ta kwanta, wuraren karfe goman dare ta jiyo muryar Papa a bakin kofarta yana kiran sunanta, ta shi tayi ta bude tare da fadawa jikin sa ta fashe da sabon kuka, rarrashinata ya shiga yi, cikin sigar nasiha ya ce "Akan me zata damu kanta dan kawai wata Muslim kanwar ta tazo Mom dinta ta ce bata nan, ai wannan ba abin damuwa bane Mom tayi haka ne don ta kareta daga sharrin terrorism. Daga yanayin kalaman shi ta fahimci bai san ainahin abin da ya faru ba, kawai karya da gaskiya da son rai Mom ta sanar mishi. Shi ya lallabta har ta dan sake ta samu ta ci abinci. A haka weekend days suka tafi duk bata cikin walwala, duk da irin kokarin da Papa yayi na fitar da ita shopping da wuraren shakatawa a ranar Sunday ya kashe mata makudan kukade hakan bai rage ta da komai ba, Allah Allah ta dinga yi gayi ya waye ta je school ta hadu da Fatima ta bata hakuri, washegari kuwa 6am ya gama komai har ta da breakfast ranar bata jira su Mom ba, daki ta bisu ta yi musu sallama direbanta ya wuce da ita. ********* Har akaci ranakun karshen mako aka sid'e Yaya Ameen bai ce komai game da abin da ya faru ba, Fatima ta yi ta zuba ido ko zai mata fada amma bai yi ba kuma bai canza mata a komai ba sannan bai gaya Ummi abin da ya faru ba, ganin haka yasa ta dan saki jiki, safiyar litinin cike da wani irin shauki da zakuwa ta gama shirin makaranta, duk da a ɓangare ɗaya zuciyarta cike take da fargaba amma hakan bai hata ta sauri ba, tsab ta shirya da wuri tana cikin sallama da Ummi dake zaune a tsakar gida Yayanta ya shigo, da fara'a ta kalleshi ta ce "Yaya barka da safiya." Duk da kuwa sun gaisa ɗazu bayan asuba, kallon ta yayi ya na jin wani irin a zuciyar shi game da hukuncin daya yanke ganin yadda take cike da farin ciki, dakewa yayi ya ce "Ya ce Fatima ki je ki cire uniform din jikinki daga yau na cireki daga challenge international school, zan canza miki wata makaranta." Wani irin zaro ido Fatima ta yi ta sauke a fuskar shi, hankaɗinta a tashe gabanta na wani irin dokawa, Ummi ma da sauri ta dago ka ta kalle shi, suka hada ido yayi saurin dauke kai, daga kallon da take mishi, kafin ta ce wani Abu yayi saurin cewa "ki yi hakuri Ummi hakan shine abin da zaifi mana kwanciyar hankali baki ɗaya." Ta san ɗanta yana da kaifin hankali da zurfin tunani bata jin zai aikata abin da ba dai dai ba, amma duk da haka zata so sanin dalilin shi, kallon Fatima da tuni hawaye sun game wanke mata fuska tayi ta ce "Binta bamu guri, koma ɗaki ki cire uniform ɗin kamar yadda ya fada." Da gudu ta wuce tana fashewa da kukan da tun ɗazu take kokawar rikewa, da kallo duk suka rakata har ta kule. Dawo da kallon ta kan shi ta yi, tare da yin gyaran murya, zama yayi a gefenta a tausahe ya ce "Ummi kiyi hakuri da hukuncin dana yanke ba tare da neman shawarar ki ba." Dakatar da shi yayi da cewa "Ba wannan nake son ji ba shin menene dalilinka na canja mata makaranta, duk da nasan makarantar kuɗi ne ya fi ƙarfin mu amma ai ba mu muke biya mata ba." Ya ce "Ummi dalili na mai karfi ne kuma shine kwanciyar hankalin ta da nawa da kema baki gaba daya." Tsare shi tayi da ido ganin yana son mata kwana kwana ta ce a dake cikin yananyi na rashin wasa "Dalilin naka na ke son ji ko bankai matsayin da zan sani ba ne?" "Ki yi hakuri Ummi." Ya fada ganin kamar ta dau zafi, kafin ya kwashe komai akan abin da ya faru ranar ya sanar mata, ya daura da cewa "Ummi tarayyar mu da su ta ko,ina bai kyautu ba, na yanke shawaran canzawa Fatima makaranta saboda rage karfin alakar dake tsakanin su, na san idan ba ta hakan ba babu ta yadda zamu Iya rabasu." Shiru Ummi ta yi labarin ya girgiza ta kuma ya bakanta mata, sai dai ita abin da ta dade da hangen a alakar Fatima da Joy ba kowa ne zai iya hango shi ba, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Amintacce wannan lamari baiyi dadi ba, sai dai har kullum ina kara sanar maka tsakanin yaran nan akwai wani boyayyen sirri wanda ni kaina bansan shi ba, mu bi komai a sannu don ina ji a jikina wata rana wannan alakar tasu zata fitar dani daga kangin rayuwar kadaicin da nake ciki na tsawon shekara da shekaru, duk da mafarki ba gaskiya bane, ba abin yadda bane ni naga hakan a cikin mafarkina yafi sai shurin masaki, Allah ya sani da fari nafi mahaifiyar Joy kiyayar tarayyarsu, kuma kai shaida ne babu ta yadda banyi don na raba su ba, sai dai daga baya na fahimci cewa tsakanin su hadin Allah ne, bazan hanaka canzawa kanwarka makaranta ba idan kaga hakan yafi maka kwanciyar hankali shi kenan." A ajiyar zuciya ya sauke dama fatan shi Allah yasa kar Ummi ta ki amincewa da hukuncin shi. Zamu dinga tsallaken rana daya idan nayi posting yau bazan yi gobe na sai jibi insha Allah. Ga me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar. 09116099486 [12/29, 2:33 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY*🌀🌀 *PAGE 10* Miƙewa yayi daga gaban Ummi ba tare ya sake cewa komai ba ya bi bayan Fatima, bata falo dama baiyi tsammanin ganinta a nan ba, bed room ya nufa kai tsaye , a kwance ya same ta kan gado tana ta risgan kuka , jin motsin shigowar mutum yasa tayi sauri ta juya baya ta fuskanci bango, yadda mai shigowan bazai iya ganin fuskarta ba ta yi tsit! kamar mai bacci. Daga bakin ƙofar ɗakin ya tsaya ya rungume hannayen shi a ƙirji yana ƙare mata kallo yana jin wani rauni na son ziyartar zuciyar shi, dakewa yayi ya ce "Fatima kuka kike yi???" Da sauri ta girgiza kai, wasu sabbin hawaye na sake wanke mata fuska. Ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da cewa "Kiyi haƙuri Fatima idan hukunci na yayi tsauri da yawa a gareki, amma ki sani bazan iya jurar ganin ana wulakanta ki ba, ya zama dole ki yanke alaƙa tsakanin ki da yarinyar nan tunda iyayen ta itama basa so, bamu da ƙarfin ja da su ta kowanne fanni, shiyasa na yanke hukuncin canja miki makaranta, duk da nasan zakiji babu daɗi, kiyi haƙuri ni mai kare martabarki ne a koda yaushe." yana gama faɗin haka ya juya ya fice don bazai iya jurar ci gaba da ganin kukanta ba. Ummi na zaune yazo ya wuceta yayi haryar ɗakin shi, kiran sunan shi tayi ya juyo ta ce "ka zo ka dauki kununka ka tafi da shi gaba ɗaya." dawowa yayi ya ɗauka ya wuce . ajiye kunun yayi ba tare da sha ba ya zuba tagumi ya faɗa komar tunani, sosai yayi nazari akan huƙuncin shi bai ga wani cutuwa a ciki ba, kuma hankalin shi ya kwanta da hakan ɗari bisa ɗari, dama shi bai taɓa kaunar alakar su ba , saboda Ummi kawai yake danne zuciyar shi. Sai dai zai iya kokatin shi wajen ganin ya duke mata duk wata damuwa bazai barta ta shi ga damuwa a dalilin hakan ba alkawari ya daukarwa kansa. ******* Tunda Joy ta shi ga class idanunta na kan kofa, jira kawai take yi taga b'ullowar Fatima amma shiru, har malamin da ke daukar su first period ya shigo, sai lokacin ta ji haushin kanta na k'in biya mata su taho tare da tayi, duk da ta gwada yin hakan sai dai kunyar Yaya Ameen da Ummi bazai barta ta iya zuwa gidan ba, da wani ido zata kalle su, har gara Ummi akan Yaya Ameen da dama can ya lafiyar kura. Sanin da tayi mata gwanar latti ce yasa bata d'aga hankalinta sosai ba, sai dai ganin malamin yaci double period dinsa ya fice wani ya shigo ta tabbatar Fatima bata zo school yau ba, kasa kwanciya hankalin ta yayi gaba d'aya ta daina fahimtar darasin da suke yi, me ya hana Fatima zuwa school?, ta jefawa kanta tambaya. Kar dai ace bata da lafiya, kar dai ace sanadin abin da Mom ta mata wani matsala ya same ta, take taji zazzabi na shirin saukar mata, ta riga ta yi amannna cewar haka ne, gaba daya ranar rasa kanta aka yi a class karshe kwanciya tayi akan desk har akayi closing, da kudirin zuwa gidan su Fatima ta fito daga cikin school, dan ta san zuwa yanzu Yaya Ameen baya gida, sai dai tana fito wa ta tarar Mom ce yau da kanta tazo d'aukarta, babu yadda ta Iya haka ta kirkiro murmushi yak'e ta sakar mata, tare da bude motar ta shi ga suka tafi gida. Ranar haka ta wuni a kwance kamar ruwa duk bata cikin walwala, sai dai bata bari iyayenta sun fahimci halin da take ciki ba gudun daga musu hankali, da tsoron kar si fahimci ta samu da Fatima su kara karfafa mata tsaro da sanya mata ido. ******* Fatima kam kuka tayi sosai har sai da kanta ya fara ciwo, tana jin sandaYayanta ya yi sallama da Ummi ya fi ce daga gidan, bayan tafiyar sa Ummi ta kwala mata kira, murya a dashe ta amsa, tare da mikewa ta kwabe kayan makarntar ta canza na gida sanan ta fito, ta ce "Ummi gani." Kallonta Ummi ta yi ta ce "Kuka kikeyi Fatima akan hukuncin da yayanki ga yanke akanki," da sauri ta girgiza kai, ta ce "Ummi ba hukuncinsa na ke wa kuka ba," "to me kikewa kuka." Narai narai tayi da ido ba tare da ta iya ba Ummi amsa ba, ganin haka Ummi tasan bata da ta cewa , don haka ta Dora da cewa "Ni dai har kullum ina kara umartan ki,ki zama mai biyyayya a gare shi domin shine jagoran rayuwar ki ko bayan raina." Gyada kai ta yi, Ummi ta ce "Tunda kina gida yau ina so zan dan fita unguwa bazan dade ba zan dawo kiyi girkin rana akwai tsakin shinkafa kiyi dambu ki tsinki zogale a ice ki ki gyara." Sake gyada kai tayi. Ummi bata bi ta kanta ta mike ta shige daki ta shirya cikin shigarta na mutunci ta fice daga gidan, ta bar Fatima cike da tunanin Inda take yawan zuwa a y'an kwanakin nan. Bayan tafiyar Ummi zama tayi ta rafka tagumu tana saka da warwara, tayi nisa cikin tunani, ta ji an gaba ta firgigit ta yi ta dago, da Amira ta yi ido biyu, murmushin yak'e ta kirkiro ta sakar mata, Amira dake tsaye a kanta tana mamakin irin zurfin da tayi a tunani ta ce " Fatima tunanin me kike yi haka, tun dazu Ina ta sallama baki ji ba." Bata amsa tambayarta ba sai cewa ta yi " Anty Amira Ina kwana." Amira ta ce "lafiya kalau baki je school ba ne yau?" Ta ce "Eh bana jin dadi ne." "Allah sarki Allah ya sauwake, ai ga idanunki nan ma sun nuna." Murmushi kawai Fatima ta yi, Amira ta sa ke cewa "Ummi na ciki ne?" Fatima ta amsa da "A'a ta fita." Kasa kasa Amira ta yi da murya cikin rad'a ta ce "Yaya Al'ameen fa?" Kallon ta Fatima ta yi, cike da mamakin yin rad'ar tata ta amsa mata da s "Shima ya tafi school." Ajiyar zuciya Amira ta sauke wanda ya tilastawa Fatima sake kallonta, ganin tana kallonta yasa ta sakar mata Murmushi ta ce "Dauko tsintsiya na taya ki sharar gidan tun da baki jin dadi." Cike da mamaki Fatima ta ce "A'a Anty Amira ki barshi zan yi." Harara ta watsa mata, tare da wuceta ga mamakin Fatima ta ga Amira ta nufi wani dan lungu da suke ajiye kayayyaki irin su tsintsiya da sauran tarkace ta dauko tsintsiya da faka, ba tare da ta jira an nuna mata in da suke ba, da alamar ta Dade da Sanin ma'ajiyar su, ta ke ta shi ga sharar ta hankalin kwance, Fatima mikewa tayi ta koma falo ta bata fili, zuciyar ta cike da mamaki. Tas Amira ta share gidan ta jawo ruwa a rijiya ta cika drum, falo ta dawo ta samu Fatima kwance nan ta zauna ta shi ga jan ta da hira wanda duk rabin hirar akan Yayanta ne, duk da Fatima bata cikin yanayin mai dadi, ta sake da Amira sosai suka yi hiran Al'ameen wanda gaba daya Amira ce ta karkata akalar hirar cen, sai da ta taya ta hura wuta kafin ta mata sallama ta fi ce, ta ce idan Ummi ta dawo ta gaisar mata da ita. Sai bayan azahar Ummi ta dawo zuwa lokacin fatima tayi girkin ta kwashe , sai dai ko kadan ta kasa dandanawa, a kwance Ummi ta sameta a daki, sannu da zuwa tayi mata, ta kawo mata abinci ta koma ta kwanta, Ummi bata takura mata ba sanin tana bukatar space, sai ma janta da ta ringa yi a jiki tana mata hirarraki , hakan kuwa ya taimaka sosai wajen rage mata damuwa da tunani makomar kaancenta da Joy. Ranar Al'ameen bai dawo ba sai dare, daga school da ya tashi, gidan daya ke daukar keke ya nufa, ya dauki keke ranar wuni yayi yana aiki sai bayan isha'i ya maida keken daga nan kuma kai tsaye ya nufo gida bayan ya tsaya ya sai ma Fatima Apple sanin yadda take matukar son shi. Suna zaune tsakar gida bayan sun idar da sallar isha'i, suna dan ta6a hira yayi sallama, a tare suka amsa masa, Fatima ta mik'e kamar yadda ta saba kullum ta kar6i ledan hannun shi, fuskarta ya kalla ganin bata cikin walwala kamar yadda ya saba ganinta kullum ya ji babu dadi, a ran shi , duk da tayi kokarin boye hakan ta hanyar sakar mishi Murmushi kafin daga bisani ta ce "sannu da dawowa Yaya." Murmushi ya yi mata shima ya ce "yawwa yar gidan Yaya Ameen." Sunan da yake kiranta idan yana cikin nishadi, dawowa tayi ta zauna ya biyo bayanta ya zuba a tabarma ya gaida Ummi, cike da kulawa ta amsa shi tana mishi ya gajiya, ta kalli Fatima ta ce " Binta daukowa yayanki abincin shi a kitchen." Da sauri ya ce "A'a Ummi bari na watsa ruwa tukunna." Ya karashe maganar yana mikewa, ya nufi hanyar wajen drum don ya dibi ruwan wankan , da sauri Fatima ta riga shi isa ta dauki boket ta zuba mishi ruwan , kallonta yayi da Murmushi a fuskar shi ya ce "Nagode kanwata." Daki ya koma ya rage kaya hadi da dauko kwandon soson shi da sabulu, har zai shige toilets din ya tuna dagargadin likita akan wankan shi da ruwan sanyi saboda larurar shi, dakatawa ya yi ya ce "Ummi a kwai ruwan dumi ne?" Ta ce eh akwai a flas, kafin ma a umurceta ta mike ta dauko mashi flas din ya juye ruwan ya shige. 20 minute kacal ya kwashe ya fito sanye da jallabiya, dakin shi ya nufa ya shirya cikin kana nan kaya ya dawo, abincin shi Fatima ta dauko mai, ya kalleta ya ce "zauna muci tare." Ummi ta ce "yawwa kamar kasan yau ta ki cin abinci kwata kwata dama jira name ka dawo ba gaya maka." 6ata rai yayi ya ce "me yasa Fatima." Tayi narai narai da idanu, babu alamar wasa a sautinsa ya ce "oya let it." Ba musu ta dauko cokali ta saka suna ci, ganin tana wasa yasa ya Shiga bata da kanshi a baki, hakan ba sabon abu bane a wajensu dama, sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya dauko Apple dinta ya bata, nan ta ke ta shi ga fara'a tana godiya, ya ji dadin gani yadda ya sake take farin ciki,nan ta wanko ta ba ummi daya ta dauki biyu, tana ci yana janta da hira, labarai masu ban dariya har da su tasuniyar gizo, Ummi ma ta biye musu tana saka musu baki, kan kace koba Fatima ta wartsake duk wani damuwa dake damunta ya kama gabanshi, sai lokacin take tunawa da batun Amira, kallon Ummi tayi tana gatsar Apple ta ce "dazu Anty Amira ta shigo." Ga mamakinta gani tayi Ummi ta washe baki ta ce "Allah sarki Amira yarinyar kirki, kai yarinyar nan tana da hankali wallahi, na Dade banga budurwa mai natsuwa da hankalin ta ba." Fatima ta ce "Hmmm Ummi ita fa ta share gidan nan ta cika drum da ruwa, ta zauna ta tayani hira sosai, Ummi dama ta saba zuwa ne." Ummi ta ce " ta kan shigo jefi jefi cikin kwanakin nan idan kuna makaranta da yake ita suna hutu kafin su fara zana waec, tana shigowa idan babu kowa a gidan su ta kama mini aiyuka ta tayani hira har wankin kayana tana yi min, kuma ko na ce ta bari bata bari, yarinyar ba dai hankali ba. Haka Ummi ta yi ta yabon Amira Al'ameen na jin su, bai dai tanka ba,sai gurin sha daya sauran suka ta shi. Pls comment yan Amana, comment dinku shine karfin gwiwana wollah, idan kina comment zaku ringa samun update a kai a kai😬 [12/29, 2:34 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *PAGE 11* Yau kimanin mako biyu rabon Fatima da school, a cikin wad'anan y'an kwanakin Al'ameen ya yi kokari sosai wajen ganin bai bar barta ta shiga damuwa ba, ya zaunar da ita tare da sakawa ta daukar mai alkawarin akan baza ta sake zuwa gidan su Joy, kuma daga yau babu maganar kawance a tsakanin su ya kashe har abada, da farko ta shi ga damuwa amma daga bisani ganin yadda ya nunka kulawar shi a kanta yasa cikin kwana uku ta ware ta nuna komai ya wuce ta hakura, sai dai na ciki na ciki, kusan kullum sai ta shiga toilet ta sha kuka idan ta tuna da Joy, damuwarta d'aya har yau bata san halin da take ciki ba, kewar ta take ji kamar kamar me. A bangaren Joy ma kusan haka ne sai dai ma mu ce har gara Fatima. Sosai Mom ta saka mata matakan tsaro bata zuwa ko ina, daga school sai school, kuma shima ita take sauke ta da kanta idan an tashi ta biya ta dauko ta, duk wata kafa da zata bi ya sadata da Fatima Mom ta to she shi, ga Papa ya yi tafiya zuwa Japan tun last week dama shi ba cikakken mazauni bane da wuya yayi zaman sati biyu a k'asa ba tare da yayi tafiya ba saboda harkokin kasuwancin shi, iya damuwa ta shige shi har ta kai yanzu bata tsinana komai a class bata maida hankali kan karatu bata jan note ga shi suna daf da fara mid term test. Duk halin da take ciki Mom ta sani, tun cikin last week ta yi bincike ta gane Fatima ta bar school din, hakan ya mata dadi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don murna, da gangan ta hanata duk wata dama na fita ita kadai don kar ta samu damar zuwa gidan su Fatima, uwa uba kuma security da ta saka Papa ya zuba musu a bakin get, har guda hudu babu mai ikon shiga ko fita daga gidan sai da sanin Mom. A haka makonni suka sake shud'ewa, ana sauran 1 week su fara test, Joy ta rasa yadda zata yi, saga da marwa ta ringa yi a dakin ta, duk wani dabara da zata yi don ta bar gidan ta gwada babu sa'a , wani tunani ne ya fad'o mata a rai, ta ke wani farin ciki ya lullu6eta, da sauri ta dauko note book dinta da biro ta zauna a kan bed ta shiga rubutawa Fatima letter, kalamai ne kad'an na ban hakauri tare da nuna yadda take tsakanin kewa da kaunar ta, ta k'ara da batun fara test din su next week tare da rokonta akan ta daure ta yi mata replay, a kasan tayi drowning din hearts guda biyu daya cikin daya kasancewarta gwanar drowning take ya fito share kaar ba hannu ya zana ba, a ciki ta rubuta sunayen su, a kasan hearts din kuma ta rubuta friends forever cikin wani salo mai kyayatarwa. Ninkewa tayi ta bude Jakarta ta dauki kudi kimanin dubu goma, ta boye a cikin aljihun pencil wandonta ta sake rigarta mai hannu bes wanda ya kai mata gwiwa ta fice daga dakin, sai da ta fara leka Mom ganin ta maida hankali tana danna system yasa ta fice da sauri direct counpuond ta fito, ma'aika nata gaisheta, da fara'a take amsawa tare da kiran sunan kowannen su, hakan na musu dadi, suna son Miss Joy sosai kasancewarta mai fara'a da sakin fuska bata da wulakanci da izza ko kadan sabanin mahaifiyarta da take ji kamar ita ce ma mai dukiyar ba Papa ba. In da ta hango drivernta Peter zaune shida gardener na gidan ta nufa, da fara'arta, ganin ta yasa Peter tasowa da sauri ya tare ta bayan ya kwashi gaisuwa ya shiga tambayarta za'a fito da mota ne. Girgiza kai ta yi ta ce "Peter wani taimako nake nema a wajenka, idan babu damuwa zan dan aikeka nan babu nisa amma bana son Mom ta san da maganar." Washe baki yayi yana kallonta, saukin kanta na kara mata kima a wajen shi, ji yadda take mai maganar don zata aike shi kamar ba zamanta yake yi a gidan ba a yau idan ta ce ta sallame shi a aikin nan ya zaunu. A dan ladabce ya ce " ki aike ni duk Inda kike bukata daga nan har abuja ni driven ki ne, kuma na miki alkawain madam bazata san da wannan maganar ba." Cikin jin dadi ta ce "Ngd Peter," ya ce "never mind your Majesty." Waige waige ta danyi kafin ta fito da pepan daga aljihunta ta mika mishi. Ta ce "Wannan nake son ka kaiwa kawata Fatima, nasan kasanta ai?." Ya gyada kai cike da mamaki, don ranar a gaban idanunsu komai ya faru, ta ce "Kasan gidan su?" Dan Jim yayi alamar tunani, ya ce "eh kamar na sani ba gidansu na a wancen layin ba ne." Ta ce "yes." Tare da sake yi mai kwatance sai da ta tabbatar ya gane sosai, sannan ta Ciro dubu goman nan data dauko ta mika mishi, godiya ya shiga kwasa cike da farin ciki, ta ce "Pls ka kiyaye ka san me zaka fadawa Mom idan zaka fita, sannan ka tabbatar ka amso min replay daga gareta kar ka dawo kin ba tare da amsa ba, sannan ka tabbatar ita ka damkawa hannu da hannu kar ka ba kowa idan ba ita ba." Ya ce "Am gama your Majesty." Daga haka juyawa ta yi ta koma ciki, dakin ta ta haura ta dage labulayen window, tana kallon sanda Peter ya isa bakin get a moto, sai da securities din nan suka kira Mom ta yi magana da Peter ko mai ya gama mata oho ta dai ga an bude mishi get ya fice ajiyar zuciya ta sauke ta koma da baya ta zauna a bakin bed ta rafka tagumi. Peter bai yi dogon tafiya ba ya iso kofar gidan, tunda dama already ya san gidan don haka bai sha wani wahala ba, daga nisa kad'an ya faka motar shi ya karaso da kafa, babu kowa a wajen hakan yasa ya dan jingina yana jiran ya samu yaro ya aika kiranta, sai dai ya kai kusan minti 30 babu yaron da ya gifta gaba daya duk ya gama gajiya da tsayuwa, cikin wannan halin Al'ameen ya fito daga gida cikin shirin shi na tafiya masallaci, don gabatar da sallan la'asar da ake kira, da sauri Peter ya iso gare shi, ya mishi sallama a gurbace tare da mika mishi hannu, kollo daya Al'ameen ya gane Arne ne, hakan yasa ya ki amsa masa sallman da ya mai kuma ya ki bashi hannu, peter bai damu ba, a haka suka gaisa, Peter ya ce da gurbataccen hausan shi "bros pls a gidan kake." Kollon uku saura kwata al'ameen ya mishi kafin ya amsa da "yes." "Thank God!" Peter ya fada yana Ciro pepen daga aljihu, ya ce " Miss Joy ne ta aikoni na kawowa Fatima wannan takardan pls ko zaka iya yi min magana da ita." Ji Al'ameen yayi ran shi na tafasa, ya tsani duk wani Abu da zai tuni mishi da ko sunan yatinyar ne balle abin da ya shafe ta, kamar ya fatattaki Peter ya kora shi, sai dai wata zuciyar ta hane shi dakewa yayi ya ce " Sorry Fatima bata gida yanzu haka sai dai ko ka kawo a ajiye mata. Ni dan uwanta ne idan tadawo zan bata." Jim Peter yayi ga koshi ga kwanan yunwa, idan ya ba Al'ameen wasikar zai zama babu replay din da zai kai ma Joy, kuma sai da ta ringa jaddada mashi ya tabbatar ya tsaya ya amso mata amsa, dagowa yayi ya kalli Al'ameen dake binshi da ido ya ce "Miss ta ce kar na bawa kowa kuma na tabbatar na amso mata repley. " shiru Al'ameen yayi yana nazari kafin ya ce "I'm coming." Dakin shi ya koma yq samu pepa da biro ya rubuta THANK U ya linke ya fita ya mikawa Peter tare da cewa "ka bata wannan ka ce daga Fatima, kagaya mata cewa ka ba Fatima wasikar hand to hand." Amsa Peter yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya ce "ok ngd sai anjima." Al'ameen ya amsa da yawwa sai anjima. Babu yawa.🙏 [12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *PAGE 12* Al'ameen na tsaye har Peter ya shiga motar shi ya tayar ya bar layin, mayar da kallon shi yayi kan pepen da ya bashi , kamar zai bude, jin ana kokarin tayar da sallah yasa ya fasa bud'ewan, sakawa a aljihu ya wuce masallaci. Koda suka idar da sallah bai bi ta kan pepan ba, hasalima ya manta da shi, kai tsaye Sayako ya nufa gidan Alhaji Bala ko zai samu keke, don d'azu da safe ya je babu keke a k'asa. Cikin sa'a kuwa yana komawa ya samu, singning yayi ya dauka ya kama aiki. ******* A cikin y'an kwanaki kad'an Amira tayi namijin kokari wajen cusa kanta gurin Ummi, har ta kai yanzu da sun zauna hira Ummi bata da wani zance sai nata, a 6angaren Fatima ma babu laifi don tana kyautata mata sosai tare da jan ta a jiki, kun san kuma ita zuciya an halicceta ne da son mai kyautata mata. Sai dai fa har zuwa yanzu uban gayyar bai san da zamanta ba, iyakar ta da shi gaisuwa, shi ma a d'arare don bata sakin jiki idan yana waje ta dinga sunne-sunnen kai kenan, kunyar shi take ji matuka gaya, babu wata sanayya mai karfi a tsakanin su, hasalima duk sanda zasu gaisa da sunan d'aya daga cikin kannenta yake kiranta alamar bai tantance ta daga cikin su ba, bare har ya kai ga batun bata wani matsayi na musammam a zuciyar shi abinda ke matukar ci mata tuwo a kwarya. Yau a islamiyya bayan an tashi su ka ke6e da k'awarta aminiyarta Zainabu wacce ita ka'dai ce ta san halin da take ci game da soyayyar Al'ameen, haka duk abinda take wa Ummi ita ta bata shawarar yin hakan kasancewar ta fita wayau da sanin duniya. Cike da damuwa ta kalli Zainabu ta ce "Zainabu Ya zan yi Al'ameen ya so ni? ya zan yi ya kalle ni da kallon soyayya koda rabin rabin wanda nake masa ne? na kusa gazawa zuciyata ta kusa tarwatsewa da soyyayar sa, Babban b'akin cikina shine yadda har yanzu ya kasa tantance ni a tsakanin kannaina bare har na samu wani matsayi na musammam a wajensa, bazan yi ci gaba da jurewa ba Allah ya gani nayi Iya yina wajen kare martaba da mutuncina na d'iya wajen ganin ban zubar da kimata na fara furta mashi kalmar so ba, duk wani alama da zan mishi na ma shi ya kasa ganewa, ya zan yi Zainabu ki bani shawara zuciyata zata tarwatse ki taimakamin plsss zeee."ta karashe maganar tare da kama hannun Zainabu ta kamkame cikin nata da karfi. Cike da tausayawa Zainabu ta ce "Na fahimci halin da kike ciki kawata domin nima na taba tsintar kaina a irin wannan halin da kika shiga, dole zamu sake salo tunda munyi mashi ta baya bai fahimta ba, ya zama dole ya san da zamanki don baza mu tsaya kallon ruwa kwad'o ya man kafa ba." Nan suka shiga tsara next plan din su, wanda zasu fara aiwatarwa a ranar ba sai gobe ba. ******** Lokacin da Peter ya koma gida, Mom na main parlour, hakan yasa bai nemi Miss Joy ba bare ya samu ya bata sakon ta, har dare basu samu haduwa ba, Mom ta kasa ta tsare kamar ta fahimci tana aikata wani abu. Wajejen karfe taran dare ta kasa jurewa, dabara ne ya fado mata , da sauri ta dauki telephone din dakinta takira kitchen ta bada umarnin a kawo mata juice daki, babu jimawa daya daga cikin ma'aikatan gidan ta yi knocking, umarnin shigowa ta bata, bayan ta ajiye mata juice din zata wuce Joy ta kira ta, juyowa yayi cike da ladabi ta tsaya, ta ce mata, tana son ta bin ta kofar baya na kitchen ta je wajen Peter ta karbar mata sako,idan ta karbo ta boye sosai yadda Mom ba za ta gani ba ta hado da bottle water ta kawo mata. Haka ko aka yi, babu bata lokaci, maid din ta kawo mata, amsa ta yi ta mata godiya, sai da ta maida kofar ta saka lock saboda tsaro, sannan ta koma ta zauna ta shi ga warware pepen cikin wani irin yanayin mai wuyar fassaruwa, idanunta da hankali ta kacokam na kan shi pepan Har ta gama warwarewa. Wani irin yankewa gabanta yayi ya fadi lokacin da idanunta ya saka akan wani unique handwriting mai shegen kyau da kayatarwa, a fili ta furta abinda ke rubuce a jikin pepan THANK YOU. Sake kure rubutun tayi da idanu har zuwa lokacin gabanta bai daina faduwa ba, zuciyarta ta ne ya bata ba rubutun Fatima bane, to amma kuma rubutun yayi kama dana Fatima, sai dai yafi na Fatima kyau da kayatuwa, to idan ba rubutun Fatima bane na wanenen? AL'AMEEN, zuciyar ta ya bata amsa, take wani irin tsoro had'i da firgici ya ziyarce ta, zaro kyawawan idanunta tayi tare da sakin pepen ya fadi kasa. A dai dai wannan lokacin Al'ameen ya fito daga masallacin unguwarsu, dawowar shi kenan bayan ya mayar da keke ya tsaya yin sallah, yana isowa kofar gida ya tuna da letter Joy, dakatawa yayi a kofar gida kasancewar a kwai wutar NEPA ko Ina na wadace da haske, yasa ya lalubi dakalin dake Jikin gidan su Amira ya zauna tare da zaro latter a aljihu. A hankali ya warware linkin da aka yiwa pepen, shina kamar yadda ya faru da joy haka ya faru da shi ras ras! Gaban shi ya fadi,lokacin da idanun shi su ka sauka akan wani dan rubutu da kwata kwata bai wuce layi goma ba, babu abin da yafi daukar hankalin shi irin drowning din hearts din dake Kasan rubutun, samun kanshi yayi da kasa dauke idanun shi akan hearts din. Bai san Iya adadin lokacin daya dauka a haka ba, sai jin sallama yayi a gefen shi, firgigit yayi tare da saurin kallon side din da ya jiyo sallamar, Amira ce sanye da dogon hijabinta daya sha guga har kasa, tana tashin kamshi kamar wacce tayi wanka da turare, idanun su na sarke wa tayi kasa da kanta teke duk wani jarumta da karsashin ta ya tafi, jikinta ya d'an fara rawa. Kallon ta ya yi, ganin tayi shiru ya ce "Aysha ya akayi." (Kanwarta dake binta) wani bakin ciki ne ya ziyarceta take ta dake , cikin dan rawar murya ta ce "Amira ce ba Aysha ba ce." Ya ce "Ooh sorry Amiran Ummi ko?" Dan murmushi tayi cike da farin ciki, ya sake cewa " ya akayi ne?." Dan Jim ta yi kafin cikin dan. jin nauyin tsareta da yayi da idanu, ta kara yin k'asa da kanta ta ce" Yaya Ameen dan Allah dama nace idan babu damuwa zan kawo pass questions na waec and neco ka koya min saboda muna daf da fara exam kuma kuma ni ban samu yin karatu sosai ba." Ta kareshe maganar a d.arere. Shiru yayi yana jin wani irin kasala na saukar masa saboda karfin turaren da ke ta shi daga jikinta. Ganin yana shirin Shiga wani yanayin yasa ya ce da sauri " shikenan kike idan na saka lokaci zan neme ki." Daga haka ya mike ya shigo zauren gidan su da sauri ba tare da ya jira ita ta fara tashi ba....... Yau na je suna ban wuni gida ba amma dai ga alkawarin da na muku jiya na cika duk da babu yawa🙏 [12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *PAGE 13* Yana shiga zaure ya a daddafe ya bud'e d'akin shi ya fad'a, bakin katifa ya laluba ya zauna yana sauke numfashi a wahalce. Ya rab! Wannan wace irin masifa ce ke neman yi wa rayuwarsa karan tsaye. Meke shirin faruwa ne? Bai ta6a jin irin wannan yanayin ba don ya shaki wani abu makamancin turare, Ras! Gaban shi ya fad'i, kar dai ace maganar doctor ne ya tabbata, kar dai ace matakin ciwon shi ne ya k'ara daga stage two zuwa four kamar yadda doctor ya sanar ma shi ce wa hakan na iya faruwa a ko wani lokaci matukar bai d'auki matakin da ya da ce ba. Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ba ya fatan ace haka ne, sai dai kuma a kullum lamarin k'ara gaba ya ke. Shi mutum ne mai matuk'ar tsantseni da kiyaye addininsa hadi da dokokin ubangijinsa, tun da ya fahimci lalurar shi, ya kiyayi kanshi da mu'amalantar duk wata d'iya mace, matukar ba muharraman sa biyu ba. Fatima da Ummi. Yana tsoron wata rana ya kasa rike kan shi, yana tsoron wata rana ya kasa controlling kan shi, shin ina mafita? Ya yi zama kusan na awa biyu a d'aki yana sak'awa da kwancewa, batare da yasan lokaci ya ja haka ba, k'arshe ya yanke shawaran zai kai ma doctor ziyara gobe kamar yadda ya ce mashi matukar ya fahimci wani sauyi daga matakin ciwon nashi yayi hanzarin zuwa don a san matakin da za'a dauka a kai. Karar shigowar message wayar shi ya ankarar da shi nisan zangon da yayi cikin tunani, da sauri ya zabura ya mik'e tare da yiyowa cikin gida. Hankalin Ummi da Fatima ya ta shi kwarai ganin har goma ta gota Al'ameen bai dawo ba, abin da bai saba yi ba, sun shiga damuwa sosai da tunanin ko wani Abu ya same shi ne, ko ya yi hatsari ko makamancin haka, babu irin tunanin da bai zo masu ba a rai ba. Suna nan zaune jigum² kamar masu zaman makoki, ya yi sallama, da gudu Fatima ta mike ta fada jikin shi tare da sakin kukan da take ta son yi tun dazu Ummi na hana ta, Ummi kam wani wawan ajiyar zuciya ta sauke a ranta ta shiga jero hamdala ga Ubangiji. A dan rud'e ya ce "Subhanallahi! Yar gidan Yaya Ameen menene haka meya faru?" Cikin shagwa6a ta ce "Yaya me yasa baka dawo da wuri ba yau ka dade duk hankalin mu ya tashi.muna ta tunanin ko wani Abu ne ya same ka" Ya ce cikin kulawa "Ya isa haka kanwata share hawayenki babu abin da ya samu Yayanki wani dan uziri ne ya rike ni." Ta ce "To dan Allah yayana idan uziri ya sameke ka ringa sanar mana ko ta wayar yaya Amira ce, zan amso maka lambarta, tunda wayar Ummi ya lalace." Ya ce "To shikenan zan ringa gaya muku daga yau insha Allah." Ya karashe maganar yana share mata hawaye. Basu yi zaman tsakar gida ba ranar saboda yanayin da yake ciki kuma already dare yayi, abincin shi kawai ya karba ya koma d'aki, suma suka shige nasu dakin suka kwanta. Bayan ya ci abinci, ya mike ya canza kayan shi zuwa T-shirt da dogon wandon jeans ya nufo katifarsa zai haye, ji yayi ya taka abu kamar takarda, da sauri ya kai duban shi kasa, lettern Joy ne, samun kan shi yayi da faduwar gaba, wanda ya rasa musabbabinsa, tsurawa takardan ido yayi na sakanni kafin ya tsuguna ya dauka, hawaa katifarsa yayi ya kwanta, sannan ya sauke duban shi kan rubutun, a hankali ya fara karanta abinda wasikar ya kunsa. Kalaman sunyi matukar daukar hankalin shi, bai san sanda murmushi ya subuce mishi ba, karantawa yake yi yana sake maimaitawa a zuciyar shi, matuka gaya abin ya kayatar da shi, sai dai bai wani basu mahimmanci ba saboda Sanin daga hannun wanda suka fito, ajiyewa yayi da nufin ya kwanta, sai dai zuciyar shi taki bashi wannan damar, ta ci gaba da kwadaita mishi son kallon kayataccen drowning din jiki, da kyar ya dake yayi fatali da bukatarta ya samu yayi wurgi da pepan ya rintse ido, take kuma damuwar matsalan ciwon shi ya dawo ma shi, ranar rana dare ya yi bai san sanda barci yayi a won gaba da shi ba. Washegari, da wurwuri ya shirya ya fice daga gidan bayan yayi sallama da su Ummi akan ya tafi school, sai dai yana fita ya dauki hanyar, S Alto special hospital, duk da sammakon da yayi sai da ya tarar da layi, zama ya yi a waiting area har layi ya iso kan shi, a hankali ya tura office din doctor ya shiga, kamar kullum kyakyawan matashin likitan wanda a kalla zai kai shekara talatin da takwas da haihuwa ya dago ya zubawa Al'ameen idanun shi dake sanye da farin glass kur kamar zai cinye shi da idanu, hannun da Al'ameen ya mika mishi ya dawo da shi hayyacinsa, hannun ya mika mishi sukayi musabaha, tare da nuna ma mishi wajen zama, zama Al'ameen ya yi a kujerar dake facing din *Dr Abdul Hafiz S Alto* Dr da har lokacin idanun shi na kan Al'ameen ya ce " Muhammadul-Ameen Husain ko?" Al'ameen ya gyada kai yana murmushi, Dr ya ce "Sai yau ka waiwayeni ko? To ya jikin naka, dama nasan zaka dawo ai domin wannan matakin daka za6a ba mai bullewa bane." Al'ameen Ya ce " Kayi hakuri Dr ba laifi na bane na gayaka tun farko a kwai nauyi a kaina bazan Iya hada taura biyu ba, jiki kuma sai godiyar ubangiji." Gyada Dr ya ce ya ce "well! yanzu meke tafe da kai?" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kwashe abin da yaji jiya game da shakar kamshin turaren Amira da ya yi, ya d'aura da "Na ji tsoro sosai Dr kar ace matakin ciwon nan ya kara karfi a jikina kamar yadda ka fada zai iya faruwa, Dr I can't hold my self idan abin ya fi haka, bazan Iya ba I'm so scare." Dr dake kallon shi tun dazu ya ce "Then ka yi AURE mana Al'ameen shekarun ka sun kai ai, U ar 25 years by now." Da sauri Al'ameen ya dago ya zuba mishi idanu, Dr ya daura da "Tun a baya na sha fada ma ka dat is d only solution of ur prlm. Duk wani tablet ko injection da zan baka,bazai taba zama total solution a gareka ba, sai ma ya janyo maka wata illar ta dabam, halittanka ne a hakan, wanda ya hade maka da lalura, a halin yanzu abin ya taka mataki na gaba ajikin ka, wanda idan ka bari ya kuma karawa gaba daga haka, to tabbas komai zai Iya faruwa ina tabbatar maka da bazaka iya controlling kanka ba." Kamar zaiyi kuka ya ce "Dr ka taimaka min bazan Iya rike mace a halin da nake ciki a yanzu ba, bani da wannan karfin a kwai nauyi a kaina ni maraya ne."kallon shi Dr S Alto yakeyi cike da nazari, "pls Dr dan Allah ka taimaka min." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce , "Naji zan taimaka maka amma kafin nan, kamar kullum yauma ina son sanin who ar u Muhammadul-Ameen." Kallon shi cikin ido Al'ameen yayi ya e "Bazan gaji da gaya maka cewa ni mayara bane. Bayan hakan bansan komai a kaina ba." Dr ya gyada kai cike da nazari ya ce " For now ka koma ka ci gaba da amfani da wannan tablet din, idan abin yayi tsamari dole akwai wani injection da zan maka, wanda kuma yin shi is very risk ga lafiyar mazan takar ka, idan akayi either a dace kokuma a ta6e." Godiya Al'ameen yayi mishi gwiwa a sage ya mike ya nufi barin office din, har ya kama handle Dr S Alto ya kira sunan shi, jiyowa ya kalle shi ba tare da ya amsa ba, Dr yaci gaba da cewa "Kayi tunani sosai akan shawarata AURE shine magananin matsalar ka, kaje duk abin da ka yanke ta waiwayeni." Murmushin yayi ya fice ba tare da ya amsa ba. Da kallo Dr Abdul Hafiz S Alto ya bi bayan shi har ya kule, ajiyar zuciya ya sauke zuciyar shi cike da wani irin yanayin mai wuyar fahimta, ganin yana shirin shiga wani yanayi yasa ya ba next patient damar shigowa don ci gaba da aikin shi. Cike da wani irin damuwa ya fito daga asibitin, tafe yake akan hanya amma kwata kwata baya cikin natsuwar sa jefa kafa yake yi kawai duk inda ya samu ba tare da ya ankare ba, kamar wani karatu haka ya rin ga maimaita Kalmar AURE a zuciyar shi, gaba daya kalaman Dr sun rikita shi har yana neman rasa nutsuwar sa, shin ta ina zai fara jajibo aure a halin yanzu? Shin wa ma zai aura, da wani ido zai Iya fuskantar Ummi ya gaya mata zai yi aure bayan bata da masaniya akan larurar shi, kai ina impossible, yana bukatar shawarata, lallai yana bukatar shawarata da gaggawa, wa zai fadawa matsalar shi ya bashi shawara, Aliyu! Aliyu ne ya fado mai a rai, a fili ya furta "Yesss! Aliyu ne." Daga nan direct gidan su Aliyu ya nufa, ba tare da sanin yana gidan ko baya nan ba. ******** Joy kwana tayi rungume da takardan da AL'AMEEN ya bayar aka kawo mata a matsayin Fatima ce ta bayar, wani irin magadisu ne a cikin takardan dake janta kamar magnet, ta rasa dalili ta rasa dan mafari, sai kawai ta dangata hakan da kasancewar takardar ya fito daga hannu Fatima ne. Ta ki yarda ta baiwar zuciyar ta damar cewa rubutun Al'ameen ne bana Fatima ba, hasalima duk sanda tayi wanan hasashen gabanta faduwa yake yi......... Wallahi Ku ringa comment ko kuma sai na bari labari ya dakko dadi Ku nemi sama da kasa Ku rasa, kun san dai halin , hayyaratata in ji me mata tara😬 Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar amma in kinsman idan kin shigo baza ki ringa comment ba karki fara yi min magana 09116099486 [12/29, 2:35 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *PAGE 14* Ban yi Editing ba🙏 Daga hospital kai tsaye Al'ameen gidan su Aliyu ya nufa, yaro ya samu ya aika cikin gidan kiran shi, sannan ya lalubi dakalin kofar gidan ya zauna, babu jimawa yaron ya dawo ya ce "Wai an ce Aliyu baya nan yayi tafiya." Jim Al'ameen yayi, kafin ya amsawa yaron da "Ok nagode." Agogon hannun shi ya kalla, sha biyu saura, ya san kafin ma ya isa school yanzu an gama lecture yau, kuma baya jin zai iya fita aiki a halin da yake ciki yanzu don haka kawai ya kamo hanyar gida. Kamar yadda ya zama wa Amira jiki cikin yan kwanankin nan kusan kullum sai ta shiga gidansu Al'ameen , yau ma cike da zakuwa ta shiga fuskarta dauke da madaukakin farin ciki. Jiya da dare dakyar barci ya dauke ta saboda farin cikin Yaya Ameen ya amince zai ringa koya mata karatu, ko babu komai zata samu lokaci ta ke6e da shi, zata samu wani dama wanda kuma ta daukar wa kanta alkawari iya wuya zata yi amfani da shi, zata yi kokarin fahimtar da shi halin da zuciyar ta ke ciki game da shi, ta hanyar kissa irin ta diya mace idan ta kama zata iya kauda zara ta kauda wata ta bude baki ta furta mashi kalmar so, domin kuwa ita kadai ta san irin azabtuwar da zuciyar ta ke yi akan shi. Tana tsaka da jan ruwa a rijiya, ta cire hijabinta ta rataye a igiyar shanya, kasancewar gidan su biyu ne ita da Fatima Ummi bata nan, ya shigo bakin shi dauke da siririyar sallama, gabanta ne yayi wani irin faduwa jikinta ta bi da kallo sanye take da riga da skirt na atamfa dinkin zamani abinka da budurwa ta yi das da ita kanta babu adiko kananan kitsonta a bayyane, wani irin kunya ne ya lullubeta, ga shi ta riga ta zura guga a rijiya,ji tayi kamar ta saki gugan sai dai ta daure ta, dukar da kanta kasa tare da amsa mashi sallamar da yayi cikin dan rawar murya, kallo daya ya yi mata da dauke kanshi, yana amsa gaisuwar da ta mishi da " Lafiya." Ya wuce ta zuwa dakin Ummi, Fatima na kwance ta na game da wayar Amira, ta ji sallama, amsawa tayi da sauri tana mikewa zaune, ya shigo akan wayar hannunta idanun shi suka sauka, zama yayi akan kujera daya tal dake falon 2 sitter, cike dan in'ina ta ce "Yaya sannu da dawowa." Bai amsa mata ba sa cewa da yayi "Wayar wa ye a hannunki." Ta ce "Na Anty Amira ne." Ya ce "Ki kai mata abinta ki ce na ce ta rufe gashin ta." Da to ta amsa tare da mikewa ta fice, wayam ta Tatar da tsakar gidan babu Amira babu mai kama da ita, da mamaki ta shiga kiran sunanta amma shiru, hakan ya tabbatar ma Fatima bata cikin gidan. Dawoqa tayi da wayar a hannu ta ce "Yaya ban ganta a tsakar gida ba ganin ta wuce." Ba tare da wani damuwa ko daukar lamarin da muhimmanci na ya ce "Ki kai mata gidansu, kuma kar na kuma ganin ki da wayar wani, idan lokacin ki rike wata yayi ni dakaina zan siyo miki." Ta amsa da "To Yaya." Tana zura hijabinta a jiki, har ta kai bakin kofa ya ce "Ummi fa? Ko ta kwanta ne." Juyowa tayi a sanyaye ta ce bata nan da mamaki a fuskarsa ya ce "Ba ta nan?." Ta ce "Eh." "Ina ta je." Ta ce "Bata fada min ba." Ya ce "ya ce ok je ki kai wayar ki dawo." Ta amsa da to ta fi ce. Da sallama Fatima ta shiga gidansu Amira, da sauri Amira da ke zaune a tsakar gida ta rafka tagumi ta mike tsaye, Fatima ta karaso ta ce "Anty Amira sai kika wuce babu sanarwa, Yaya ya ce na kawo miki wayar ki kuma ya ce na gaya miki ki ringa daura dankwali." Wani irin zaro ido da tayi sai da abin ya ba Fatima dariya, ta ce "Da gaske haka ya ce Fatima?" Fatima na mata dariya ta ce "Wallahi haka ya ce." Amira ta ce "Na shiga uku." Ba tare da tasan ta furta ba duk ta bi ta ruda kanta, Fatima cikin dariya ta ce "Wallahi ke babbar matsoraciya Anty Amira." Ta ce " Hmmm! Baza ki gane bane Fatima, wallahi naji kunya sosai yadda Yaya Ameen ya tarar da ni daga ni sai Riga da skirt babu ko dan kwali wallahi kamar na nutse a kasa saboda kunya, sai naga ma kamar ya harareni" Sa ke kwashewa da dariya Fatima ta yi ta ce "Bari na je na gayawa Yayana wagga batu." Da sauri ta juya zata fi ce, Amira tayi wuf ta rikota, cikin yanayin tsoro ta ce "Dan girman Allah Fatima kar ki gaya mishi." Fatima ta ce "To sakeni Anty Amira bazan fada ba." Ta ce. "Ki rantse." Sai da Fatima ta mata rantsuwa sannan ta saketa tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta yi gudu, cike da al'ajabi Fatima ta fito gidan ta shige nasu, koda ta koma Al'ameen ya fice data dakin su alamar ya tafi nasa ganin haka ta gane baya son hayaniya don tafi kowa fahimtar shi, bata nemi shi ba ta shiga kitchen ta daura musu sanwar rana kamar yadda Ummi ta bar mata sallahu. ********* Karfe biyar dai dai Dr Abdul Hafiz S Alto ya danna hancin motar shi cikin kyayataccen compound din gidan sa dake unguwar Brighter, bayan parking kai tsaye ya nufi asalin cikin gidan, da sallama dauke a bakin shi, da sauri yan yaran da ke zaune a falo suka kwaso da gudu suna ga Daddy ga Daddy, Daddy oyoyoo Daddy oyoyoo, suka rungume shi, jin hayaniyar su ya fito da matar gidan daga kitchen, matashiya ce mai kimanin shekaru 28 zuwa 30 fara tass da ita kyakkyawa, da fara'a ta karaso ta na mishi sannu sa zuwa, tare da dan runguma,yana murmushi, ya amsa mata da "Uwar gida ran gida, yaya gida ya yara." Ta ce "Gida da yara lafiya kalau sai hamdala." Zame hannun shi yayi daga cikin na karamin yaron shi ke kimanin shekaru biyu, ya ce "Aboki bari na watsa ruwa na dawo ko." Yaron ya gyada kai yana murmushi, daga nan yayi dakin shi, matar shi ta rufa mishi baya, ruwan wanka ta hada mishi kafin ta dawo ta taya shi rage kaya ya shige toilet don ya watsa ruwa. Minti goma ya kwashe kafin ya fito sanye da rigar wanka, bata dakin bai damu ba don yasan kila tana wani uzirin ne, shiryawa ya shiga yi cikin kananan kaya, yana gama shiryawa ta shigo da sauri ta, tana ganin haka tace "Oh shirt! Kayi hakuri wallahi Ina kitchen ne ban gama hada dinner ba shi yasa na barka." Murmushi yayi yace "Babu komai ai na gama." Ta ce "Nasan halinka yanzu zaka baza kaci abinci ba ka riga kaci abinci a hospital, amma duk da haka bari na kawo naka dan abin tabawa." Fita ta yi jim kadan ta shigo dauke da tray da jug cake ne da pineapple juice da ta hada mishi da kanta ta jawo center table ta daura mishi, godiya ya mata ya zauna ya shiga ci, ita kuma ta bashi hakuri ta sake ficewa kitchen, bayan ya gama ya dauki tissue ya goge baki, mikewa yayi daga gaban table din, ya koma bakin bed ya zauna, wayar shi ya dauka, ya lalubo wata international number da yayi serving da suna Hayatudden Aboki. Sai da ya kalli agogon bangon dakin ganin biyar da arba'in, ya tabbatar inda zaiyi kiran yanzu dare ne a wajen su amma haka ya daure ya yi dialling, lambar yayi ringing sosai kamar baza a daga ba can kuma lucky yaji anyi picking, daga can bangaren aka yi sallama da wata irin nutsattsatsiyar murya, kafin a daura da "He'll Aboki." Murmushi Dr Abdul yayi kafin ya amsa sallamar ya daura da cewa "Hi Aboki." Kamar yadda Abokin nashi ya fada, duk murmushi suka yi, kafin su shiga gaisawa da tambayar lafiyar juna, bayan sun gama suka dan taba hira irin ta amintattun abokai, daga nan kuma, Barrister Hayatudden ya ce "How about d boy, ya sake zuwa." Dr Abdul ya ce "Yes ya sake dazu shi yasa ma na kiraka." Cike da wani irin karsashi Barrister Hayat ya ce "Me ya kawo shi? Me ya ce maka? Yaya matakin ciwon shi zuwa yanzu? Ya fada maka shi wanene? Su waye iyayensa." Dr Abdul ya ce "Easy mana aboki, wadannan irin tambayoyi haka a jere, koda yake ba wani Abu bane tunda da cikakken lawya me zaman kansa nake magana." Barrister Hayat ya katse shi da cewa "All, aboki, duka tambayoyin nake bukatar amsarsu daga gareka."............ Ayi hakuri da wannan, yau bani da naji sosai🙏 masu comment ngd sosai na gani kuma na yaba much luv 2 u ppl all INA yinku irin totally. Da iya masu comment kadai fa nake yi atoh! Ga masu bukatar shiga group. 09116099486 [12/29, 2:36 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 15* Dr S Alto ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya ya ce "Bai gaya mani komai game da ahlin shi ba, still yau ma ce min yayi shi maraya ne kamar yadda ya saba fada, game da matakin ciwon shi kuwa, yanzu abin ya kai mataki na hudu a gaskiya yana cikin hatsari ." Barrister Hayat cikin sanyin jiki ya ce "Aboki lokaci yayi da zan dawo 9ja koda kuwa ban gama cike wa'adina a nan ba, ya zama dole na san ko wanene shi, jikina yana bani cewa mafarkina yana gaf da tabbata." Dr S Alto ya ce "Aboki ban katsi hanzarin ka ba, sai dai ina mai kara baka hakuri, kayi hakuri ka zauna ka kammala aikin da ya kaika, kar muyi biyu babu." A dan harzuke Barrister Hayat ya ce "me kake so ka gaya min, wani irin biyu babu, kafin kowa sani na Abdul idan da wanda zai karfafa min gwiwa akan lamarin nan baren ka ne, amma sai naga kamar baka dauki lamarin da muhimmanci ba." Dr ya ce "Ba haka bane Hayat, so nake mubi komai a hankali, ka tuna fa har yanzu, tsammani kawai muke bamu da tabbaci, kuma har yanzu idanunsu ba wai ya dauke akan ka bane, kana dawowa Nigeria ba tare da wa'adin ka ya cika ba, zasu saka maka ayar tambaya duk wani motsin ka zai kasance a kan idanun su, kayi hakuri ka zauna nayi maka alkawari kafin nan da shekaru biyun da suka rage maka ka dawo kasarka zan tabbatar na gama duk wani bincike daya kamata." Ajiyar zuciya B Hayat ya sauke, a sanyaye ya ce "Na yarda da kai Aboki, a duniya bayan y'an uwana bani da wanda ya fi ka, na san zaka iya, na damka maka amanar rayuwata ka kulamin da ita." Dr ya ce "in sha Allah na maka alkwari bazan baka kunya ba." Daga haka ba su yi wani hira ba, suka yi sallama zuciyoyin kowannen su a jagule musamman Barrister Hayat wanda maganar ta yi mishi fami a zuciya. *********** *JOY* Zaune ta ke a kyayataccen garden din gidan su, yammaci ne mai cike da ni'ima kasancewar garin yau kwata kwata basu ga kyallin rana ba saboda ruwan da aka kwana ana tsugawa daren jiya kamar da bakin kwarya. Books ne a gabanta da yawa, ta kwaso domin tayi karatu saboda gabatowar lokacin fara mid term test wanda ya kasance na third term ne, wato na canza aji, d'aya daga cikin books din na rike a hannunta tana dubawa, a zahiri idan ka ganta zaka dauka a gaske karatun takeyi amma a badini kwata kwata hankalinta baya kan karatun, tunani ne fal zuciyar ta, kallo daya zaka fahimci bata cikin walwala ko kad'an, yau kimanin kwana biyar kenan data aikawa Fatima letter, amma har satin ya kare bata je school ba, gashi on Monday zasu fara mid term test, bata yi aune ba sai kawai ta ji hawaye na zuba daga idanunta yana diga kan book din da take kallo, Ta na matuk'ar kewar Fatima ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gidan su, ta ke ta shiga tunano yadda suke gudanar da rayuwarsu a baya, yadda suke nunawa juna tsatanin kauna da kulawa babu kyamata kyashi ko hassada tsakanin su da juna soyayya ce gangariya daga indallahi' ta tuna ranar data fara haduwa da Fatima, farkon shigowar su SS1, wata rana suna zaune a class aka kawo musu new comer Fatima Husain, kallo daya suka yi wa juna a tare suna sakarwa juna murmushi kamar dama sun san juna, lokacin da class Master su yaba Fatima umarnin ta je ta samu sit ta zauna direct ta nufo kujerarta duk da cewa ga sauran empty sit nan a class din da yawa kuma ga musulmai nan yan'uwa ta a ajin, babu musu ko gaddama ta matsa mata ta zauna, ranar ko kalmar A bata shiga tsakanin su ba, sai satar kallon juna da suke yi kamar wasu munafukai, idan suka had'a idanu su sakar wa juna murmushi, tun daga ranar farko da suka fara haduwa zuciyoyin su ya sark'e da soyayyar juna, sun kai kusan kwana uku a haka kullum idan Fatima ta zo sit d'inta ta ke zama suyi ta kallo juna, maganar farko data fara shiga tskanin su a rana ta hud'u maths teacher ya shigo ya yi musu lesson bayan sun gama ya bada class work kowaccensu ta dauko notebook d'inta ta fara solving, Fatima ta gama nata kamar yadda suka saba satar kallon juna ta juya ta saci kallon na Joy, zaro ido tayi ganin yadda ta yi solving wrongly, sai dai ta rasa yadda zata gaya mata, ta zauna tana ta sak'e sak'e , har lokacin data mik'e zata je tayi submit, har ta fita daga sit d'in ta ji an riko hannunta, juyowa tayi suka kalli juna cikin ido, cikin inda inda Fatima ta ce "please can I see ur calculation." "Why not." Ta amsa mata da murmushi tare da mik'a mata, bata ce mata komai ba ta shiga gyara mata inda ta yi kuskuren tana gamawa ba tare da ta kalleta ba ta mik'a mata tare da cewa "ki yi hakuri da shisshigina." Sai lokacin ta kula da kuskuren data tafka, murmushi tayi tare da ce mata "Thanks" Itama ta sakar murmushi ba tare da ta amsa ba. Tuna wannan yasa Joy sakin murmushi ba tare da ta san tana yi ba, still ga hawaye a idanunta, Hannu ta saka a aljihun wandonta ta zaro letter n nan na Al'ameen, daya zame mata kamar wani gold duk inda zata je yana tare da ita da shi take kwana rungume a jikinta duk daren duniya, ta warware pepan tana kallo, sai dai har yau bata sauya zani ba a duk sanda zata daura idanu a jikin rubutun gabanta sai ya fad'i, ba tare da tasan dalilin hakan ba, tana kallo tana ci gaba da hawaye ta ce a bayyane "I missed u a lot my Teetee." ba ta san isowar Mom ba sai jin muryar ta tayi akanta, ta na ce wa "Joy what's wrong wit U? me ya same ki, kukan me kike yi." Da sauri ta shiga goge hawayenta at same time tana kokarin boye letter n cikin inda-inda ta ce "Nothing Mom, abune ya fad'a min a idanu." Mom da ta gama karantar rashin gaskiya k'arara a fuskarta ta shammaceta ta fusge letter n, a bayyane ta karanta abinda ke ciki "THANK YOU." A razane ta kalli Joy data zaro manyan idanunta cike da fargaba ta watsa mata, k'ank'ance ido Mom tayi cike da tashin hankali ta ce "Menene wannan Joy?" Ta ce "Babu komai Mom." Mom ta ce " Wannan letter daga ina." Cikin inda-inda ta ce "Ya dade sosai Mom a cikin textbook dina, yanzu dana dauko su ina dubawa shine na gani." Mom ta ce "To naji wannan kukan kuma na menene shi?" Ta ce "Ba kuka na ke yi ba Mom abune ya fada min a ido." Ko kadan Mom bata yarda da batun ta ba, hakan yasa ba tare da wani dogon nazari ba ta daga letter n ta kekketa shi. Rintse ido Joy ta yi don ji tayi kamar zuciyar ta Mom ke ketawa, lura da haka yasa Mom yin gutsi gusti da shi yadda koda ta tattara pieces din baza ta gane komai ba. Tana gamawa ta ce ki tashi muje ciki kiyi yan shirye shirye, tafiyar gaggawa ta kamani gobe da sassafe zamu bi jirgi zuwa Oshogbo . Cike da mamakin me zai kai su Oshogbo tana tsaka da shirin fara mid term test hankali ta she ta ce "Mom Oshogbo kuma." Mom Ta ce "Yes of course." "Ba sai hutun karshen shekara Mike zuwa ba? Kuma next week Monday zamu fara text." Mom ta ce "dat is not my prlm." Cikin shesshekar kuka tace "Gaskiya Mom ni bazan je ba." Wani mugun kallon ta watsa mata tare da saka mata wata uwar tsawa da gufu ta mike tayi cikin gida tana kuka. ********* Tsawon sati guda Al'ameen bai cewa Amira komai game da batun karatun su ba, iya damuwa ta shiga damuwa gashi tana jin kunyar sake tunkarar shi da maganar, yau a islamiyya, ta zayyane wa Zainabu halin da take ciki, Zainabu ta ce "Ko dai ya mata ne?" Amira ta ce "bana tunanin haka." Numfashi Zainabu ta sauke ta ce "Fatima zaki aika ta tuna masa idan ma mantuwa yayi sai ya tuna." Amira ta ce "nima tunanin da nake yi kenan k'awata.sai dai nake ga kar yaga kamar na cika gajen hakuri." Zainabu ta ce "Bana ganin zai ce haka a yadda kike dan bani labarin halayensa, ni nama fi zargin mantawa yayi." Amira ta ce " to shikenan yau zan mata gamana sai mu ji mai zai ce, amma wallahi ni kunyar sa nake."Tsaki zainabu tayi ta ce "wannan kunyar naki wallahi shi zai kasheki Amira." "Hmmmm wallahi kawa dan dai baki san shi a zahiri bane, kamar zaki haka ya ke da kwarjini bashi da wasa baya daukar wargi at all."............. Ga masu bukatar shiga group 09116099486 [12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 *PAGE 16* Da gudu ta k'arasa d'akinta ta fad'a kan bed d'inta tana sakin wani irin numfashi mai zafi, can kuma sai ga hawaye shaaa! kamar an bud'e famfo, wani irin tafarfasa zuciyar ta ke mata. Yanzu shikenan Mom ta yaga mata wasikarta, shikenan Mom ta rabata da letter n ta, ji take kamar wani part na jikinta aka yaga mata ba fallen takarda ba, tana jin son latter n nan sosai a ranta shi kadai me debe mata kewar Teeteenta. Ranta ya matukar baci da abin da Mom ta mata yau, tun da take bata ta6a ja'inja da ita ba amma wannan karon ta lashi takobin ko zata yanka ta baza ta bi ta Oshogbo ba suna tsaka da shirin fara text, Ai ba dole ba ne sai anyi tafiyar da ita, zabura tayi ta mi'ke tare da d'auko wayar ta dake yashe kan madubi, bata damu da waya ba don sai tayi sati bata ta6a wayar ba musamman idan Papa yana gari, idan baya nan dai dama kullum da safe zai kiranta ya ji lafiyarta ko ita ta kira shi. Lambar Papa da tayi saving da My blood ta laluba ta dannawa kira, lucky ringing biyu ya d'aga, ta na jin muryar shi ya ce "He'll my lovely princess my Joy." Ta daddage ta fashe da wani irin kuka mai k'arfin gaske, kamar yadda ta tsammata a rud'e ya shiga tambayar ta "Menene ? Mekefaruwa ? waya ta6aki? Kina ina ne yanzu? Ina Mom dinki?" Babu d'aya data amsa sai ma k'ara sautin kukanta da tayi, aikuwa Papa dake zaune a office d'in abokin shi Mr Jack dake kasar Canada ya mike tsaye, ya shiga safa da marwa yana mata magiyar ta yi shiru ta daina kuka haka, sai da ta bari ta gama rud'ashi sannan cikin wani irin shagwabebben muryar mai hade da shesshek'a ta ce "Papa Mom ne." Wani irin kankance idanu yayi don bai ta6a tsammanin Mom ce ta saka mishi tilon yar shi irin wannan kukan ba, tausasa murya yayi dan kar ya kara daga mata hankali ya ce "Mom din ki kuma? Me tayi miki." Sai da ta gama jan majina ta ce "Ta ce wai gobe in shirya muje Oshogbo kuma On Monday zamu fara test." Cikin danne bacin ranshi ya ce "Ki ce mata bazan kije ba." "Na ce mata ta ce wai ban isa ba." Zazaafar huci ya fesar ya ce j "Ok haka ta ce, To ki kwantar da hankalin ki ni nace baza ki je ba, yanzu dai ki share min hawayen ki bari na kira Mom din naki muyi magana." Ta amsa da "Toh Papa." Tana share hawaye. Bayan ficewar Joy daga garden da wani irin mugun harara Mom ta raka bayanta, a bayyane ta ce "Ya zama dole mu tafi Oshogbo tare gobe goben nan kamar yadda bokanta ya umarta bazan yi sakacin da aikina na shekara goma sha biyar zai lalace ba, zan Iya kawar da duk wanda ya ce zai min shamaki da wannan burina kowaye, Ta karashe maganar tana huci kamar kububuwa. Daga haka kuma tabi bayan fuuuu Joy, sai dai kuma kafin kai ga karasawa dakin Joy wayar ta ya dauki ruri, ganin lambar Papa yasa gabanta faduwa kar dai ace yarinyar nan ta kira Mr James ne, shaf ta manta da hakan da kwace phone din ta, dakewa tayi ta daga cikin kissa ta ce"He'll My O..... Kafin ta kai ga karashe maganar ta ya dakatar da ita ta hanyar ce wa "Alice!!!!!" A tsawa ce. Diriricewa ta yi don tsawar ya shigeta, don bata ta6a tsammanin hakan ba,Rabon da ya mata irin wannan tsawar tun kafin su dawo Niger state da zama, kafin ta dawo hayyacinta ya rude da fada akan me zata saka mishi d'iya kuka Akan me zata tilasta ui. Abinda bata so, sai da ya.mata tatass ba tare da ya bata damar amsawa ba ya daura da kuma "Ban amince miki ki fita ko bakin get da ita ba, ki je duk inda zaki je na lamince miki amma ban amince ki tafi min da Y'ata ba wannan umarni nake baki, idan kuma kika ki ji." Ya yi kwata! Bai jira cewar ta ya katse kiran, ya sake kiran Joy ya ci gaba da rarrashinta. Daskarewa Mom tayi a tsaye a inda take, tana zazzaro idanu hankalinta a kololuwar tashe, kar dai a ce aikin da ta sha bakar wuya aka yi mata akan Mr James lalace, tashin hankali wacce ba'a saka mata rana, hannu na rawa ta lalubi lambar bokonta Kubal. ta danna mishi kira, cikin sa'a ya daga muryar na rawa ta shiga kwashe abin daya faru tana zayyana mai, tsawa ya faka mata shima , a kausashe ya ce "Na gaya miki matukar baza ki rabata da wad'an nan ahlin ba ba kiga komai ba, duk wani abu da kika binne ina mai tabbatar miki sai ya tonu." Hankali ta she Ta ce "Na rabata da su Kubal duk wani tsaro da takumkumi na saka mata, na shata babbar layi a tsakanin su." Dariya ya kece da shi mai ban tsoro lokaci daya ya gimtse sannan ya daura da "Wannan bai isa ya raba alakar jini da jini ba, kizo da ita garemu kizo da ita garemu kizo da ita garemu zamu rabasu rabuwa ta har abada." Ta ce "Mr James ya hana kubal. ka taimakeni bana son na rasa aurena ba tare da ba samu ci kar burina ba, ka taimakeni da kai kadai na dogara, tsoro nake ji kar Mr James ya rabu da ni." Boka Kubal ya a tswace ce "ki taho ke kadai da gaggawa, zamu canza kalar aikin namu, ki taho da gaggawa." Ka fin ta bashi amsa tuni ya yanke kiran. A gurin ta zube ta daura hannu akai, ta san idan har asirin data ma Mr James tsohon shekara sha biyar ne ya karye kashinta ya bushe tabbass kashinta ya bushe, bata ga ta zama ba, idan ba haka ba ta tabbata zata kare rayuwarta a prison madadin ta zama daya daga cikin matan da suka yi ficce suka shahara a duniya kamar yadda take buri, zabura tayi kamar zautacciya ta bar gurin a guje, dakin ta ta shiga ta fara hada kayanta. Ranar daga ita har Joy basu samu barci mai kyau ba, Joy kukan bakin cikin rabata da letter n ta, ta kwana yi, yayinda Mom tsananin tashin hankali ya hanata rintsawa. ******** Kamar yadda suka tsara da Zainabu hakan ce ta kasance, washe gari kamar yadda ta saba ta shiga wajen Ummi bayan ta tabbatar Al'ameen ya fita, a tsakar gida ta samu Fatima na wanke wanke Ummi na daki, dakin ta nifa ta durkusa har kasa ta gaida Ummi cike da lababi,cikin fara'a Ummi ta amsa tana saka mata albarka daga haka ya fito ta saka hannu tana taya Fatima dauraya suna hira, cikin hiran Amira ta ce "Wai ni kam Fatima Yaya Ameen na nan kuwa." Fatima ta ce "Yana nan mana yanzu bai dade da fita ba." Amira ta ce "Ikon Allah wallahi na kwana biyu ban gansa bane, duk zato na yayi tafiya ne ." Fatima ta ce "A'a yana nan wallahi." Shiru Amira ta dan yi can kuma ta ce "To kodai ya manta ne?" Fatima ta kalleta cikin rashin fahimta ta ce "Ban gane ba Anty Amira." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wallahi rannan nan mama ta saka na tambaye, wai ko na kawa past question na waec ya dinga koyamin kafin namu jarabawar ya kara so, ya amsa min da to zai ne me ni idan ya shirya amma na ji shi har yanzu shiri shi yasa nayi yunanin ko yayi tafiya ne, Ashe yana nan, shine nake tunanin ko ya manta ne." Fatima ta ce "abin ya kai kwana nawa yanzu." "Ummm! Ina ga yafi sati fa." Cewar Amira, "kai anya kuwa! Yayana bai cika mantuwa haka ba, amma dai ki kara tuna ma shi kiji, zai Iya yuwuwa mantawar yayi" marairai ce murya Amira ta yi ta ce "Fatima dan Allah ki taimake ni ki tuna mishi yau idan ya dawo." "To me zan ce ma shi?" "Ki ce Yaya Anty Amira ta ce wai ya maganar da kuka yi ran nan na karatu. Haka kawai zaki ce masa nasan zai tuna." Fatima ta ce "to shikenan in sha Allah idan ya dawo yau zan dasa masa." Haka ko akayi a ranar da dare bayan Al'ameen ya dawo suna zaune a tsakar gida kamar yadda suka saba, Fatima ta ce "Yawwa Yaya Anty Amira ta ce wai na tuna maka ya maganar da kuka yi ran nan na karatu, wai har yanzu ta ji shiru daga gareka." Dan ya mutsa fuska yayi, jin abinda Fatima ke fada, sarai yana sane da ita shareware yayi don shi a halin yanzu yana tsoron kebewa da wata mace wacce ba muharramarsa ba, bai manta da abin daya faru ranar da tazo tambayarsa ba, common turarenta na neman zamar masa masifa. Ummi kam jin an ambaci Amira, tuni ta maido hankalinta Kansu ta ce "Binta me ya samu Amiran?" Fatima ta ce "A'a Ummi babu komai, ta aikoni wajen Yaya ne akan maganar da suka yi da shi, wai ta tambaye shi zai koya mata karatun jarabawan su dake gabatowa, ya e mata to zai neme ta amma yau kusan sati bata ji daga gareshi ba, shine ta ce idan ya dawo na tuna masa." Kallon Al'ameen Ummi tayi dai dai shima ya kallota suka hada idanu, da sauri ya sauke kai. Ta ce "Yayan Fatima idan da hali ka koya mata dan Allah, Amira yarinyar kirki ce." Shiru yayi kadan kafin ya amsa da "Toh Ummi." Sannan ya dago ya kalli Fatima ya ce "Fatima ki CE mata gobe idan na dawo da daddare tazo sai mu fara karatun." Yana kallon Ummi ta gefen ido yadda fuskarta ta yalwatu da fara'a. Fatima ma taji dadi don ba karya tana son Amira kamar dai Ummi. ******* Washegari Sunday da sassafe Mom ta fito da trolley dinta, cikin shirinta na tafiya, sai da ta daidaita komai batta driven da zai kaita airport yana zaune a mota yana jiranta sannan ta nufi dakin Joy, tura kofar tayi da karfi, taga ya bude, bata zaci a bude kofar ya ke ba, shiga ta yi, a kwance ta sameta idanunta a rintse kamar mai barci sai dai ba barcin take yi ba, hasalima jin motsin mom din ne ya saka ta rintse idanu, tsayawa a kanta Mom ta yi ta kare mata kallo, sai da tayi mai isarta, sannan ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce "Daughter zan wu ce." Sai lokacin Joy ta bude kumburarrun idanunta amma bata ce komai ba, Mom ta sake cewa "Ba yan school ban lamunce miki zuwa ko ina ba, zuwa anjima Madame Esther zata zo ta zauna dake kafin na dawo." Daga haka ta juya ta fice Joy ta rakata da kallo. Bani da isasshen lahiya banyi editing🙏 Ga masu bukatar shiga group Ku tuntubeni. 9116099486 [12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 17* Tana tsaye jikin windon d'akita tana kallo har motar Mom ya bar compound d'in gidan, ko kad'an bata ji wani damuwa ko alamar kewa a zuciyarta game da tafiyar Mom ba , sabanin hakan sai ma wani irin sanyi da farin ciki ta ji yana huda zuciyarta, wani tsalle ta daka tare da fad'awa kan tattausar katifarta, yau jin ta take yi kamar sakakkiyar tsuntsuwa, rasa irin murnar da zata yi yasa ta ci gaba da jumping akan bed d'in tana tambul da adungure, sai da ta ji ta fara gajiya ta dakata tana sauke numfashi, bayan ta dan huta daga tsalle tsallen murnanta, ta mik'e ta fad'a toilet ta shek'a wanka, tana yi tana wake wakenta alamar cikin farin ciki take, gaban mirror ta tsaya daure da mini tawul, tana kallon fuskarta, Zum6ura baki tayi ta kwa6e fuska, bayyane ta ce "Ji duk yadda nayi baki kamar bani ba, duk Mom ta gama ramar dani da jidalinta." Kwafa ta yi ta harari mirron kamar dai Mom d'in na cikin madubin ne, kallon kayan kwalliyar dake shake kan mirron tayi sai kuma ta saki murmushi ta ce "Bari nayi wa My Teemah kwalliya." Kujera ta ja ta zauna, cikin gwanancewa ta shiga fesa kwalliya a kwakkwayar doguwar fuskarta. Bata cika yin makeup ba, shi yasa duk sanda tayi yake zama special a fuskarta, lallausar gashinta ta tattara tayi paking din shi gefe ta zubo da jelar ta gaba har kafad'unta, ta yi kyau sosai matuk'a gaya kamar wata y'ar tsanar roba. Mik'ewa tayi ta isa gaban wardrobe din ta ta wangale kofofin shi, tsayawa tayi tana kallon kayyayyakin ciki, kaya ne shake a ciki ba na wasa ba, wasu ma batta taba sakawa ba sai dai duk kanana ne babu wani na mutunci a ciki, idanuta ne sauke akan wani kaya da Papa ya taba kawo mata daga America lokacin da yayi wani tafiya, kaya ne masu matukar kyau da tsada irin ta yayan masu jajayen kunnuwa, bata taba sakawa tunda ya bata ta jera su a sif, zarowa ta yi ta warware kayan. Straight skirt ne mai dauke da dogon tsagu ta baya red colour da riga karami mai hannun bes White colour mai V neck a gaban rigar an rubuta JOY cikin wani irin design mai kayatarwa ya sha stone sai walwali yake, sai dan karamin jaket kalar skirt din, iyakar shi kasan boobs yana da igiya daga kasa da za'a d'aure ta gaban. A tsanake ta shirya cikin kayan tsab! Duk da kasancewarta bera dan yanzu take shiga sha biyar hakan bai hana kyakkyawan surarta kayatuwa cikin shigar ba, siririyace sosai sai tsayi, sai dai akwaita da faffadan gudu, hakan yasa take da shape kayatacce, idan ka dauke hakan babu wani abu jan hankali a jikinta, dan y'an boobs dinta basu fi girman lemon tsami ba samsam basu da girma shiyasa bata fara saka bra ba. Takalmi half cover ta saka fari ta daura agogo a tsinstiyar hannunta, daga haka ta fito daga d'akin ta da sauri har tana had'awa da d'an gudu, direct get ta nufa ko tsayawa ta yi breakfasts ta kasa, sai dai tana isowa, d'aya daga cikin security d'in dake bakin get, ya ce "Miss kiyi hakuri madam ta ce kar a bari ki fita, in dai ba school zakije ba." Bata san lokacin da ta kwaso wani irin mugun kallo ta watsa mashi ba, take ta fusata kasancewarta dama gwanar saurin fushi babu wuya ta hassala sai sai tana da saurin sauka. A tsiwace cike da gadara ta ce "Na ce Ku bud'e min get zan fita." K'asa yayi da kai ya ce "I'm sorry Miss sai dai Ki kira madam ki sanar mata." A tsawace ta ce "Bazan kirata ba! kuma ina umartanka da ka bud'e min get kokuma yanzu wallahi a bakin aikin ka." Tsorata yayi ganin yadda ta ke huci yar karamar yarinya da masifa kamar wata babba, shikam bazai so abinda zai raba shi da wannan aikin daya samu mai maik'o ba, jiki na rawa ya shiga bata hakuri, ko kallon banza bai isheta ba, dsauri ya bud'e mata karamin kofar yana mata a dawo lafiya tana fita ya lalubi lamabr Mom don ya sanar mata, sai dai wayar tak'i shiga kasancewar jirgin su ya riga ya lula. Sai da ta fito gida sannan, ta ji wani tsoro na shirin kamata sabanin da da take cikin farin ciki, da wani ido zata kalli Fatima, da Ummi, uwa uba Yaya Al.......kasa karasa tunanin tayi don bata fatan hakan takasance fatan ta Allah yasa zuwa yanzu baya gida, duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta yi, karfe goma har ta gota, ta tabbata zuwa yanzu ya fita, dakewa tayi ta ci gaba da tafiya. Tana kusantar gidan gabanta na faduwa, duk taku daya karfin bugun zuciyarta na karuwa, sanda ta fara hango gidan ji tayi kamar ta koma saboda yadda zuciyar ta ke luguden daka kamar zai fado kasa, ita kanta baza ta ce ga dalili ba, ta san dai ba tsoron Fatima ta ke yi ba, haka Ummi akwai kyakkyawar alaka ta mutunci a tsakanin su, dakewa tayi ta karasa kofar gidan, babu kowa a layin kasancewar shi karamin layi. A hankali ta tura kofar gidan ta shiga da sand'a kamar barauniya, a haka ta wuce kofar dakin Al'ameen ta isa kofar shiga cikin gida, la6ewa ta yi jikin bango ta kasa shiga, can ta jiyo muryar kamar na Fatima tana magana hakan yasa ta leka kanta a hankali. Al'ameen na tsaye a bakin kofar dakin shi cikin shirin shi na fita ya na makala links a hannun rigar shi, ya ji an turo kofar gidan, shiru shiru ba'a shigo ba, ba, a koma ba hakan yasa ya dago kai ya kallo waje ta raga ragar net door din dakin shi, mamaki ne ya kusa kashe shi lokacin da idanunshi ya sauka a kanta tana tafiya cikin sand'a kamar wacce ta shigo sata, kwafa yayi a ranshi lallai yarinyar nan, uwar me ta zo yi gidan su bayan irin wulakancin da sukayi wa Fatima, kamar zai dakatar da ita sai kuma ya dakata yaga Iya rashin kunyar ta, yana kallo ta la6e a jikin bango ta lek'a kai cikin gidan. Shiru shiru bata d'ago ba hakan yasa Al'ameen yin gyaran muryar daga bayanta, kiriss! Ya rage ta saki fitsari lokacin da sautin muryar shi ya ratsa dodon kunnenta, da sauri ta d'ago kai ta zubawa kofar dakin shi idanu batta hango shi saboda duhun net amma shi yana iya ganinta. Bud'e net door d'in yayi ya fito fuskar shi a had'e kamar hadarin gabas, Sai lokacin ya samu damar ganinta da kyau, wani irin wulakantaccen kallo ya shiga wurga mata ganin irin dressing d'in dake jikinta a rayuwarshi ya tsani yaga mace da shigar banza koda kuwa arniya. Shesshekar kukanta da ya ji yasa ya kai kallon shi ga fuskarta, zaraf idaunsu ya sarke dana juna, a tare zuciyoyinsu ya yi wani irin girgiza, bude baki ta yi da nufin yin magana, da sauri ya daura hannunta shi akan leben shi ya ce mata "Shiiiii!!!." Tsit! tayi tare da hadiye shesshekanta tana wurwurga manyan idanunta da suka kada saboda tsorata. Ya sake yi mata alamar ta zo ta fice da hannu, baya son ya yi magana ne don yasan su Ummi na tsakar gida zasu jiyo su. Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta fara takowa, ta gaban shi ta bi ta fice daga zauren, minti biyar ya dauka kafin bayanta yabi bayanta, tunanin shi zuwa lokacin ta dan yi nisa da gidan, sai dai ga mamakin shi yana fitowa, ya tarar da ita durkushe a kofar gidan tana sharar kwalla, ranshi yaji yayi mugun baci, wato bata tafi ba kenan don rainin hankali, a hasale ya daka mata tsawa " keeee!" A zarane ta dago ta watsa mai idanunta da suka fara sauya launi, take ya ji duk wani karsashinsa ya tafi, kasancewar sa dakkaken namiji mai dakakkiyar zuciya yasa ya dake ya ce "Me ya kawo ki gidanmu." Shiru ba amsa sai sabbin hawaye dake sake shatata akan dakalin fuskarta, ya ce "Ok na gane yau ma kin biyota har gida ne ki sake ci mata mutunci kamar yadda rannan kuka ci mata matunci a gidan Ku keda mahaifiyar ki ko?" Da sauri ta shiga girgiza kai cikin shirin fashewa da kuka, ya ce "Kul! Kar ki min kuka a nan. Kuma ki bud'e kunnuwar ki da kyau ki saurereni, daga yau sai yau idan na sake ganin wadan nan kazaman kafafunta naki a gidan nan, hmmmm! Sai na lahira ya ciki jin dadi. Oya kafin in bude idanuna ki 6ace daga kofar gidan nan, daga yau babu ke babu Fatima har abada." Rushewa ta yi da kukan da take ta kokarin rikewa tun dazu, cikin magagi ta ce "Pls Yaya Alemin karka raba ni da Fatima wallahi ba laifi na bane laifin Mom dina ne idan ka raba mu, zan shiga tasananin damuwa ku yi hakuri da abinda ya faru rannan Ku yafe min." Ya ce "Ok baza ki tafi ba ko? Ina zuwa." Ya fad'a yana shirin juyawa zuwa cikin Zaure, caraf ya ji ta riko kafafun shi, wani irin shock ya ji a jikin shi wanda tunda yake bai taba jin irin shi ba, hakan yasa yayi wani irin fusgar k'afunshi da mugun karfi, har saida Joy ta fad'i tare da bige goshi da wani dutse............. Na gode da addu'o inku gareni, na j sauki sosai hannu ma da sauki alhmdllh ngd kwarai da kulawa. Me bukatar shiga group din joy ya tuntubeni ta wannan Layin. 09116099486. [12/29, 2:37 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 18* Yauma ba editing a tai ta hakuri🙏 Ba tare da ya kula da fad'uwar da tayi ba ya shige zaure da sauri ya bugo k'ofa. Zafin buguwar da taji yasa ta saki yar k'ara "Acchh!" da siririyar muryarta , hannu ta kai ta dafe goshinta dai dai gurin da ta bige, danshi da ta ji a wajen yasa ta dubawa da sauri, zaro ido tayi a tsorace ta ce "Jini! wayyo my Dad." Sai kuma ta fashe da kuka tana yarfa hannaye, rabon da jini ya fita a jikinta irin haka har ta manta, ji tayi ranta ya mugun baci da abinda Al'ameen ya mata sosai ta kullace shi, dama tun farko bata ta6a mishi kallon mai saukin kai ba, kallon wani irin murd'add'en mutum mugu mara fara'a take mishi, sai gashi yau ya tabbatar mata da hakan, mikewa tayi ta kakkab'e jikinta ta na hawaye ta kama hanyar barin kofar gidan. Duk abin da take yi yana tsaye daga cikin duhun zaure yana kallo, ji yayi zuciyar shi ya sosu, haka kurum kukanta ke ta6a mishi zuciya, irin abinda yake ji a duk sanda ya ji Fatima na kuka ya dinga ji, gaba d'aya tausayinta ya ji ya kama shi, idan ya barta ta fice haka, anya ya kyauta kuwa, Annbin Rahama ya hane mu rama sharri da sharri, ya gamsu da irin soyayyar da ta ke yiwa yar uwar shi kodan wannan ya kamata ya raga mata, da sauri ya fito ya biyo bayanta, lokacin har ta riga ta bar kwanar gidan, sunanta yake son ya kira amma ya kasa, sau uku yana gwada bude baki sai dai ya mayar ya rufe, hakan yasa ya k'arasa da dan gudu gudu ya isa gareta, jin karan gudu daga bayanta yasa ta juyowa da sauri har zuwa lokacin kuka take, daai dai nan shi kuma ya iso inda take, kasancewar tana cike da haushin sa yasa ko d'ar bata ji ba sai dai ta kasa kallon fuskar shi ko da gigin wasa, a gabanta ya tsaya sai kuma ya rasa me zai ce mata, samun kanshi yayi da zaro handkerchief daga aljihun shi ya mika mata, kin Karba tayi sai ta samu kanta da dan zumbura baki. Zaro ido yayi ganin abin da tayi, sai kuma ya samu kanshi da sakin murmushi wanda shi karan kanshi bai san ta su6uto ma shi ba, yarintarta yake gani karara idan tayi wani abin San Fatima yake ganinta. A hankali ya kai hannun shi fuskarta da nufin ya share mata hawayen, a razane ta dago idanunta ta karaf! Ya sauka cikin nashi, wani irin lamari ne wanda tunda take a rayuwarta bata taba tsintar kanta cikin shi ba ya afku da ita cikin abinda bai fi kiftawar ido ba, sakone na zuciya wanda ke shiga ba tare da neman shawaran mamallakinta ba bare izini. Samun kanta tayi da Kasa janye idanunta daga cikin nashi duk da irin duguden da zuciyarta keyi, shima bai dauke idanun shi ba a haka kuma bai fasa goge mata hawayen da yayi niyya ba. Murmushin daya Dakar mata ne ya fargar da ita yanayin da da ta shiga, da sauri ta kawar da fuskarta daga gareshi, tana jan numfashi da karfi don ji ta yi numfashinta na shirin daukewa, bata dawo hayyacinta ba ta tsinci muryar shi a kunnenta cikin shigar rarrashi yana cewa "I'm sorry! Ban yi don na cutar dake ba." Maimakon ta amsa mishi sai kawai ta juya da gudu gudu ta bar shi a tsaye rike da handkerchief. Ya fi minti goma yana bin inda ta bi da kallo, shi karan kan shi bazai ce ga abinda yake kallo ba, Me yasa ta wuce ta barshi ba tare da amsa mishi ba, ko dai bata hakura ba ne, "Ya ilahi!" Ya ambata a baiyane. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yayi amfani da dakakkiyar zuciyar shi wajen yi fatali da abinda raunatacciyar zuciyar shi ke shirin ingiza shi a kai. ******** Lokacin da Amira ta samu sakon Al'ameen, ruwa ne kawai bata zuba a kasa ta sha ba saboda farin ciki abin har saida da ya ba Fatima mamaki, duk da karancin Shekarunta sai da ta diga mata ayar tambaya. A daren ranar kuwa bata ko daga kafa ba tana idar da sallar isha sai gata dauke da tarin littafanta, Al'ameen din ma shigowar shi kenan daga masallaci yana dakin sa ko abinci bai kai ga ci ba. Yana jin sallamarta ya bata rai shi har ga Allah zata takura mashi. A gaban Ummi dake zaune a tsakar gida ta zube cike da girmamawa ta ce "Barka da dare Ummi."Fuska a sake Ummi ta ce "Yawwa Amira maraba, har kin shigo karatun ne?"Eh wallahi Ummi." "To madallah! Allah yayi jagora, shima Yayan Fatiman yanzu ya shigo gidan." "Allah sarki, to ko na koma in dawo anjima kafin ya gama kimtswa." "A'a yi zamanki yar nan idan ya ganki zaune zaifi maida hankali ya kimtsa da wuri."Ta amsa da "To Ummi."dadi fall ranta don dama ta dai fada ne kawai ba don ya kai zuci ba.Dan waige² tayi, kafin ta ce "Ummi Fatima bata nan ne.". "Tana daki ina ganin sallah take." Hira su ka shiga ta6awa da Ummi, a haka Fatima ta fito ta same su. Da fara'a ta ce "Laaa! Anty Amira har kin shigo." Ta ce "wallahi Fatima ba shigo." "To bari na sanarwa Yayan yana dakin shi." Duk yana jiyo su a ranshi ya ja karamin tsaki, ya rasa me yarinyar ta taka da suke rawan jiki da ita dhi shiga harga Allah bata kwanta mashi a rai ba. Sallamarta Fatima ya katse mai tunani, a dakile ya amsa mata don haushin Amira ya shafe ta, tura net door din tayi ta shiga, ta same shi zaune yana latsa waya, da zumudi a muryarta ta ce "Yaya Anty Amira ta zo karatu." bai dago yakalleta ba ya ce "Na sani, ki kwaso littafanki kema Ku jirani tare zaki dinga karatun." Ta amsa da " To Yaya." Yana jin ta tana gaya musu sakon shi. Said da ya kwashe minti sha biyar kafin ya taso. Ummi ya gaisar, kafin ya samu guri ya zauna, a sanyaye Amira ta ce "Ina yini Yaya Ameen." Sai lokacin ya kalli side din da take, ya amsa mata da "Lafiya." Ummi ta ce "Fatima kawo mishi abincin shi yaci tukunna kafin Ku fara karatun." Da sauri ya ce "A'a Ummi bari mu gama tukunna." Bata ce komai ba, ya kalli Fatima da Amira ya ce "Ku matso" Matsowa sukayi ya kunna fitilar wayar shi ya haska, ya dauki daya daga cikin papers na past question da Amira ta zo da shi ya bude ya dan dudduba sannan ya dan kalleta ya ce "Bismillah ko." Da kyar ta iya dagowa ta saci kallon shi, ta re da gyada kai. A tsanake cike da baiwa da basida ya shiga yi mata bayanin kowani question dalla dalla, duk da kasancewarta ba mai kaifaffan brain ba, tsaka tsakiya take, hakan bai hanata dan ganewa ba, wai damma ta fi maida hankali ta akan kallon kyakkyawar fuskar shi, tana sakin murmushi tare da kiyasto abubuwa da dama a ranta. Sai gurin goma saura ya dakata, tare da rufe paper ya dago ya kalleta ya ce "Zamu dakata a nan said Allah ya kaimu gobe, idan kina da tambaya kiyi akan abinda baki gane ba." Da sauri ta girgiza kai, ya ce "ok shike nan gobe idan muka karkare subject din ni zan miki tambayoyi tunda kince kin gane ko?" Ya karashe maganar da tambaya da sauri ta sake gyada ka ya ce "To sai da safe." Ba don ranta ya so ba ta amsa da "To sai da safe Yaya Ameen nagode sosai Allah ya saka mata da alkhaiti ya baka mata ta gari." Ummi da Fatima ne suka amshi, shi kuwa kasa amsawa yayi don jin addu'an yayi banbara kwai. Bayan tafiyar ta ya yi wa Ummi sallamarta tare da umarta Fatima ta kawo mishi abincin shi daki, daga haka ya wuce dakin shi....... *********** Tashin hankali wacce ba'a saka mata rana, a bangaren Joy ranar kusan yadda taga dare haka taga rana, duk da bata san so ba, zata iya kiran abinda take ji game da AL'AMEEN da zazzafan soyayya wanda tayi wa zuciyar ta daurin goro a farat daya... Wata sabuwa inji yan caca hmmmm! Joy ina raraki da, kinsan dai Mom kamar yunwar cikin ki, atoh ni dai babu ruwana, masoyan Joy Ku bata shawara. Pls kuyi ta manage da guntayen page insha Allah komai ya kusa dawo min normal muyi mu gama book din nan don ni na fara gajiya da shi saboda rashin comment dinku. yasin. Ga masu bukatar shiga group Ku tuntubeni kai tsaye 09116099486. [12/29, 2:38 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN 👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN 👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 19* Washegari Monday da shirin school ta tashi hakan ne ya d'an d'auke mata hankali daga tunanin Yaya Ameen data kwana yi, jiki a sanyaye ta gama shiryawa, sai kuma ta nema waje ta zauna ta rafka tagumi, ta yaya zata je ta zauna ta zana jarabawa ita kad'ai ba tare da Fatima ba? ta ina zata fara? Me zata rubuta? Ko dai ta je gidan su ne, wata zuciyar ta bata shawara, yayinda wata zuciyar ta hane ta da aikata hakan. A karshe hankalin ta yafi karkata akan ta bari idan sun yi closing ta je, Haka tayi ta zaman gawon shanu har na kusan 30 minutes ba tare da ta ankara ba. Ringing d'in wayar ta ne ya dawo da ita hayyacinta, da kyar ta mik'e ta isa ma'ajiyar wayar, sunan Mom ta gani yana yawo a fuskar wayar, gabanta ne ya yanke ya fad'i, tunda Mom ta wuce basu yi waya ba. Jiki a matukar sanyaye ta kara wayar a kunne ta ce "Gud morning Mom." Daga daya 6angaren Mom dake cikin matsananin tashin hankali ta ce "Morning." A dak'ile ta d'aura da "Thank u 4 what u did, nagode sosai kin nunwa duniya ban isa dake ba, na ce karki je ko ina amma sai da kika fita saboda ke mai kunnen k'ashi ne, to baki isa ba, kin yi karya, kin yi kad'an, ni na haifeki ba ke kika haifeni ba don haka baki isa ki juyani, kuma zan nuna miki." Cikin rawar murya ta ce "Kiyi hakuri Mom " Mom ta ce "No don't sorry me, sorry 4 ur self akwai ranar karbar result yana nan tafe. Kuma me kike yi a gida har yanzu, ko ba yaune kika ce zaku fara test ba?" A sanyaye ta ce "Yau ne." "To zaman me kike yi?" "Kiyi hakuri mom na shirya yanzu zan wuce." "Da kyau, ki fita waje driver na nan da zai kai ku kuma zai jira har ku tashi ya dauko ku, idan ki ga dama kar ki bishi,Duk abinda kika yi zan samu labari." Kit ta kashe wayar ta. Wayar ta bi da kallo kafin ta ce "Zai kai mu ni da wa?" Bata da mai bata wannan amsar hakan yasa ta saki ajiyar zuciya a bayyane ta ce "kiyi hakuri Mom ba yin kaina ba ne." Jiki a sanyaye ta jawo jakarta ta sakko downstairs, babu kowa a main parlour, ko kallon 6angaren dining bata yi ba don bata jin zata iya saka koda ruwa ne a cikin ta a halin yanzu. Tana fitowa compound idanunta ya sauka akan wata bak'uwar mota fake a gaban plat din Mom daf da kofa, bata gama mamakin su wanene a ciki ba aka bude kofar motar, David ne ya fito sanye da uniform d'in shi irin nata fuskarshi dauke da murmushin mugunta, kafin ta gama mamaki aka bud'e d'aya 6agaren mahaifiyar shi ce ta fito Mrs Esther fuskarta a had'e kamar hadarin gabas! cikin wani irin takun isa da tak'ama ta iso gaban Joy, kallon sama da k'asa ta mata kafin a gadarance ta nuna mata motar data fito, da hannu ta mata alamar ta shiga. Sai lokacin ta fahimci jam'in da Mom keyi d'azu wata ita da David za'a kai school tare me hakan ke nufa? Kar sai Mom Anty Esther ta fito ta zaua da ita kafin su dawo da kuma ta shiga ukunta. Sai da ta hadiyi wani busassshen yawu kafin, ta kimkimi jakarta jiki a sanyaye ta nufi motar ta bud'e baya ta shiga, David dake tsaye shima ya bud'e inda ya fito ya koma ya zauna, driver yayi ribas ya fice daga gidan. A rayuwarta tana matukar tsoron Anty Esther, macece masifaffiya ta karshe, uwa uba kuma bata kaunarta ko miskala zarratin, tun bata mallaki hankalin kanta ba ta fahimci hakan, ko kadan jininsu bai hadu ba. Bata san school ba sai da ta ji k'arar bud'e kofa David, dagowa tayi yana tsaye daga jikin windon suna had'a ido ya d'age mata gira tare da sakar mata murmushin keta ya ce "Muje ko." Harara ta watsa mai kafin ta 6alle murfin motar ta fito a fusace ta nufi cikin school ba tare data kula shi ba, tana jin shi yana biye da ita yana fito kasa-kasa. Ko a class kasa concentrating ta yi akan abin da ke gabanta, tana kallon sauran student na d'aukan notebooks din su suna dubawa kafin shigowar invigilator, amma ita ko kwakkwaran motsi ta kasa, har zuwa lokacin da aka shigo yi musu first paper wanda English ne, bayan suna babu abinda ta iya rubutawa a script dinta, ajiyewa tayi akan desk ta rafka tagumi, ta fada komar tunani, rintse idanu tayi take kyakkyawar fuskarsa ya shiga yi mata gizo, komai nashi na dawo nata dallah-dallah, especially moment din su na jiya a tare. Bata san iya adadin time din data kwashe ba sai sai ta ji ana cewa everybody submint, tana kallo aka d'auke script din ta ba tare da ta iya rubuta koda kalma d'aya ba. Koda suka fita break kasa fita tayi, kwanciya ta yi kan desk, duk da irin yunwar dake nukurkusarta. A haka har lokacin second paper yayi, shima dai kamarna farkon babu abinda ta tsinana, da ta kai hannu ma sai ta samu kanta da yin drowning din hearts da arrow ba tare da ta farga ba, a haka lokaci ya tafi, ta yi submit ba tare da ta goge ba. Kasancewar suna test sha biyu suka ta shi, ga mamakin ta David ta ga yazo ya tsaya akanta, a hasale ta ce "what?" Yayi murmushinsa dake kular da ita tare da cewa "Nothing, just let's go." Tsoron Anty Esther ne kawai yasa ta bi bayan shi suka wuce, kamar kuwa yadda Mom ta fad'a a bakin get suka tarar da driver'n daya kawo su yana jiran su, kai tsaye gida ya wuto da su ba tare da ta samu damar zuwa gidan su Fatima ba kamar yadda ta tsara. Cike da fargaba ta bi bayan David suka shiga plat din Mom, a hakimce ta tarar da Anty Esther a falo kafa daya kan daya, ta tara duk ma'aikata gidan a gabanta, ko me take gaya musu oho! A haka suka karasa ciki David dake gaba ya ce "Good afternoon Mama." Ta amsa da "Fine Son kun dawo." Ya ce "Yes Mama." Tare da neman waje gefenta ya zauna yayi balance kamar gidan uban shi. Idanunta ta dawo da shi kan Joy, ta shiga binta da wani shegen kallo mai cike da tsana. Jikinta ne ya d'an dauki rawa lokacin da sukayi hada idanu rasa abin yi yasa ta samu kanta da maimaita abin da ta ji David ya fada ita ma, a d'arare ta ce "Good afternoon Anty." Harara ta watsa mata kafin ta ce "Afternoon." A dakile daga haka bata kara ce mata komai ba sai tsarabar hahara. Ganin haka a sukwane ta kimkimi school bag din ta, ta haura dakinta. Tana shiga ta yi wurgi da jakar, ta fada gado ta fashe da kuka, wata zuciyar ce ta mata, "yanzu haka zaki zauna wannan matar ta yi ta mulkarki a cikin gidanku gidan mahaifinki. Impossible!" Zabura ta yi da nufin ta dauki wayarta ta kira Papa sai dai wayam babu wayar a ma'ajiyarta babu dalilinta, sake fashewa ta yi da sani sabon kukan, ko bata tambaya tasan Anty Esther ce ta daukar mata waya, dan kuwa babu mai ikon shigar mata daki cikin ma'aikan gidan matukar ba ita ta bukaci hakan. Zamewa tayi kasan tiles ta jingina da bed din ta tana matsar kwallah. Tsawar da Anty Esther ta daka mata aka ne, yasa ta mikewa a firgice, cike da masifa ta ce "Kukan uban me kike yi, iye nace kukan Uban me kike yi." Cikin son hadiye kukanta ta ce "Kiyi hakuri Anty." "Rufe min baki munafuka kin zo kin zauna kina kuka saboda tsabar sangarta da fitsara kamar wacce aka daka ko aka zaga, maza ki cire wadan nan kayan ki fito ki yi lunch." Tana tsaye a kanta ta cire uniform ta sauya na gida, daga haka ta tasata a gaba zuwa dining, dinning din shake da abinci kamar wanda mutum goma zasu ci saboda almubazzaranci. Uban abinci tayi serving dinta tuli wanda tasan ya mata yawa, ta tasata a gaba wau sai ta cinye shi, tana ci tana kuka ita kuma tana antayata zagi, "Yarinya duk anbi an sangarta ki, kina yiwa mutane fitsara iri iri, babu tarbiya, to ni nan zan gyara miki zama kafin Mom dinki ta dawo." Da kayar ta iya cin rabin abinci, ta shiga kakarin amai, ganin haka yasa Anty Esther kyaleta, tana sharar kwallah ta mike zata wuce daki, hanata tafiya Esther tayi ta sakata ta zauna ta mata massage. Ranar haka Joy ta wuni cikin wahala da zagi da tsamgwama daga wannan ta shiga wannan , ba ita ta samu kanta ba sai wajajen karfe goman dare, duk wannan wahalar da gajiyar da tayi tana samun hakarkarinta ta kasa tunanin Al'ameen ya mata sallama, Babu abin da yafi tsaya mata a rai irin kyakkyawar murmushi sa, ta tuna ranar da Fatima ke ce mata duk duniya babu wanda ya kai Yayanta iya murmushi, a she da gaske ne. Ta sake tuno daddadar muryar sa lokacin da yake ce mata "I'm sorry! Ban yi don na cutar dake ba." Murmushi ta yi tare da kai hannu ta shafi goshinta dai-dai gurin daya d'an kuje har yayi jini tana sahafawa tana murmushi, bata san iya tswon lokacin data kwashe a haka ba kafin barci barawo yayi gaba da ita... *********** Masu bukatar shiga group na joy su tuntube ni kai tsaye . 09116099486 [12/29, 2:38 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writers Association* *PAGE 20* Washegari wajajen bakwai da rabi na safe, Anty Esther ta fad'o mata dak'i, tana cikin barcinta mai dad'i wanda ya d'auke ta dakyar gabanin asuba cike begen Al'ameen ta ji an d'ad'a mata duka a cinya, a zabure ta farka zata zunduma ihu idanunta ya sauka akan Anty Esther, tuni ta ja bakinta ta tsuke tana zare ido. Harara Esther ta watsa mata ta d'aura da "Sannu isasshiya, karfe bakwai da rabi kina kwance ki na barci, wa kike jira ya tashe ki. Common get up, stupid girl!" Ta karashe maganar a tsawace tare da mi'ka hannu kamar zata kai mata mari. Da gudu ta mik'e ta fad'a toilet ta rufo kofar ta murza key, jingina tayi da kofar ta fashe da kuka k'asa-k'asa don kar Anty Esther ta jiyo ta, sai da ta yi mai isarta babu mai rarrashi ta samu tayi wankan dakyar, a d'arare ta turo kofa ta lek'o, ganin Anty Esther bata d'akin yasa ta k'arasa fitowa da sauri, sharp-sharp ta shirya cikin uniform dinta ta sakko downstairs dauke da makeken school bag d'in ta mai tayoyi. A dining ta tarar da David gaban shi shake da abincin kala-kala ya ci wannan ya ture ya janyo wannan, Harara ta watsa mishi a fakaice a ranta ta ce "Shege mayunwaci babu a hause anzo an samu na banza." Muryar Anty Esther ta jiyo daga hanyar kitchen tana tahowa,sai masifa take da hargagi da alama da kuku's take yi. Da sauri ta ja kujera ta zauna, cikin dan karkarwar jiki ta shiga kokarin had'a tea, David na kallon ta yana mata murmushin keta. Bata wani ci abin kirki ba ta mi'ke, ganin David ya gama don kar tayi laifi, du k da haka bata tsira ba sai da Anty Esther ta zage ta tas, wai tsabar iskanci ta zuba abinci ta barshi bata ci ba. Kuka take son yi amma babu dama, Tana kallo David ya kwaso kayan kwalama dangin su cake, ice cream, chocolate, ya tula a jaka, sannan su ka fita sabon driver'n Mom ya d'auke zuwa school. A cikin mota ta samu damar yin kukanta, kwantar da kanta a jikin kujera ta yi tana shesshekar kuka kasa-kasa, David dake gefenta ya kalleta yayi murmushi, cike da izgili ya ce "Yarinya ki kwantar da kai a gabana ki roke ni abin da kike so, zan taimaka miki." Harara ta watsa mishi ta dauke kai wani irin mugun haushin shi take ji. D'age kafad'a ya yi ya ce "kin huta." Yau ma kamar jiya babu abin da ta tsinana a school d'in har sukayi closing. Koda su ka koma gida yau ma bata huta ba, haka Anty Esther ta sakata a gaba kamar jiya, ko garden ta ki bari ta fita ta sha iska, wayarta take bukata ta kira Papa amma tsoro ya hana ta tambaya, tana ji a gabanta Anty Esther da Mom suka yi waya, amma Mom bata ce a bata ba, sai ma cewa ta yi wai a ci-gaba da tsareta kar a barta fita ko compound ne idan ba school zata je ba, kuma koda wasa kada a kuskura a bata waya, har sai ta dawo, daga nan kuma suka ci-gaba da wasu maganganu wanda tuni ta daina fahimtar komai saboda kukan da ya ci karfinta. Kamar jiya tana samun kanta tuni ta manta da duk halin da take ciki, ta tsunduma tafkin begen abinda zuciyar ta ke bege. ************** Bayan wasu kwanaki. Sosai Amira ta dage da zuwa daukar karatu wurin Al'ameen, sai dai hakan ba abinda ya kareta da shi sai wani irin mahaukacin kaunar shi, a duk sanda zasu zauna karatu zuciyarta sake narkewa take da soyayyar shi, haka zata yi ta kallon shi wani bin sai Fatima ta ta'ba ta zata yi firgigit ta dawo hayyacinta, zuwa yanzu Ummi ta soma fahimta wani abu game da Amiran sai dai ta bar abin a zuciyar ta a tunda hasahse ne kawai take bata da tabbas. Shi kam Yaya Ameen bai fahimci komai ba, saboda kwata babu wata aba wai soyayya a gaban shi, sai dai ya kan rasa wani irin kallo ne yarinyar ke yawan bin shi da shi haka. Ita kam a bangaren ta sosai lamarin ke damunta, duk wani salo da iyayi da zata yi don Al'ameen ya gane halin da take ciki ta yi amma a banza, hakan yasa ta sake tarar Zainabu da maganar, zee ta bata shawara kamar yadda ta saba, ta yi na'am da shawarar don a yanzu yadda take jin soyayyar shi, bata ki kowa ya sani ba don ta k'una bata tsoron kauri. Yau ma kamar kullum ta shigo gidan bayan sallar isha'i, kasancewar an wuni ruwan sama gari yayi sanyi, yasa Ummi basu zauna a tsakar gida kamar yadda suka saba ba, a falo ta same su gaba dayan su harda Al'ameen d'in da dawowar shi gidan kenan, ya mutsa fuska ya yi lokacin da ya ji sallmarta, baya jin dadin jikin shi tunda rana karfin halin kawai yake yi, ga wani sanyi-sanyi da yake ji yana shigar shi. gaban Ummi ta zube ta kwashi gaisuwa, sannan ta juyo bangaren sa, cikin wata irin narkakkiyar muryar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen." Ya amsa da "Lafiya kalau." Yana dauke kai daga gareta don take kamshin wannan mayataccen turaren nata na ran nan ya mashi sallama, dafe kanshi daya fara Sara mishi ya yi. Fatima ce ta gaisheta, ta amsa cike da kulawa kafin ta samu waje kusa da ita ta zauna, ta saitin shi yadda zata samu damar satar kallon shi hankali kwance. Ya fi minti uku a haka kafin ya dago, carat idanunsu ya sarke dana juna ba tare da ta ankara da zai dago ba, da sauri ta kawar da kanta don bazata iya jurar hada idanu da shi ba, muryar shi ne ya dawo da ita hayyacinta "Amm! Amira ki yi hakuri kike gida yau baza mu saka yin karatu ba, Bana jin dadin jikina." Jin haka yasa Ummi kallon shi da sauri, ta katse shi da cewa "A'a yayan Fatima baza ayi haka ba, tunda ta riga ta zo, ka koya mata ko kadan ne." Shiru ya dan yi kafin ya amsa da "To Ummi." Baya iya mata musu matukar akan abinda bai fi karfin shi ba ne. Mikewa yayi ya kalli Fatima ya ce "Ku muje dakin zaure taskar gida a kwai sanyi." Daga haka ya fice, Ummi ta so tsayar da shi suyi karatun a falonta ganin ya riga ya fice yasa ta kyale shi. Fatima ce a gaba Amira na biya da ita suka shiga dakin bayan ya amsa musu sallama, lumshe idanu Amira tayi lokacin data shaki daddadar kamshin turarensa da take maitar son ji kullum. Dakin tsab da shi a tsabtace kamar ba dakin saurayi ba. Cike da karfin hali da jarumta ya fara koyar da su, sai dai ko minti goma basu dauka ba ya fara neman fita hayycinsa, rintse idanu ya yi, yana jin yanayin shi na canjawa, gefe daya ga wani shu'umin kamshin turaren da yake shaka na neman hallaka shi. Babu shiri ya dakata, ya kalli Amira da kyar ya ce "Amira kije kawai gobe ki dawo, bana jin zan iya karatu yau, na so na koyar da ke kamar yadda Ummi ta saka ni amma bana jin zan iya." Cike da matsanancin tausayin shi ganin yadda idanun shi suka rine, ta ce "Toh Yaya, Allah ya saukawake." Da kai ya amsa mata don baya jin zai iya bude baki ya yi magana, a rude Fatima ta shiga jeromai sannu, da kai ya ke amsa mata, tuni idanunta ya ciki da kwalla, da hannu yayi musu alamar su tafi kawai, jiki duk a sanyaye suka mike, har sun kai kofa, cikin wata irin wahalalliyar murya ya kira sunan Fatima, duk dakatawa suka yi, ya ce "Kar ki gayawa Ummi halin da nake ciki bana son hankali ta ya tashin, kin ji ko. " ta gyada kai tana sharar kwalla, cikin shesheka ta ce "Yayana to kasha magani." Ya ce "zan sha yanzu nan." Ta amsa da "Toh ."suka fice. Da kyar Amira ta tafi gida ranar, barci kuwa kaurace mata ya yi juyi ta dinga yi, tana ji kamar ta koma ta kara duba shi duk da dare ya tsala, karshe dai ta lallaba tayi alwala ta yi nafila ta shiga nema mishi sauki a wajen Allah, tare da mika nata kokon baran. Kwanar wahala Al'ameen ya yi a wannan dare, tunda yake ciwon shi bai taba tashi da karfi irin na yau ba,ya sha maganin shi amma a banza, jarumta ce kawai ta hana shi sumewa a cikin daren nan..... *Jama'a masoya masu bibiyar littafin JOY, pls Ku kara hakuri da ni, wallahi kwana biyu nan nayi busy da yawa, amma insha Allah zuwa ranar Monday komai zai daidaita daga ranar zaku dinga samun update kullum, harda weekend bi iznillah na muku alkawari ni dai kawai comment dinku da addu'ar Ku nake bukata, sai kuma shearing fisabilillah* 🙏 [12/29, 2:39 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN *AyshaNalado*👉 ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writers Association* *PAGE 21* Kwanar wahala Al'ameen ya yi a wannan dare, tunda yake ciwon shi bai ta6a tashi da k'arfi irin na yau ba,ya sha maganin shi amma a banza, jarumta ce kawai ta hana shi sumewa a cikin daren nan, wani irin hank'oro had'i da jijjiga jikinsa ke yi masa, babu abin da yake muradi irin ya samu biyan bukata, rashin samun hakan ya haifar masa da mummunar zazzabi, tare da matsanancin ciwon mara, duk dauriya da jarumtar Al'ameen sai gashi yana zubar da hawaye yana mulmula a tsakar d'aki, tare da rok'on Allah ya d'auka ranshi ya huta. A 6angare d'aya kuma shaidaniyar zuciyar na masa zuga tare da bashi gurbatacciyar shawara akan ya ta shi kar ya yarda ya hallaka kanshi, ya samarwa kanshi sauki ta kowacce hanya, ta shiga zano mashi hanyoyin mafi sauki da zai bi ya samu cikar muradin gangar jikinsa. Dakyar da taimakon Allah wani wahalallen barci ya sure shi ba tare sa zato ko tsammani ba. Kimanin awa biyu ya kwashe yana barcin wahala, wani irin azababben murdawar da mararsa tayi ya tilasta masa farkawa a zabure, cikin fitar hayyaci da rufewar idanu ya rarumi sacet din maganin shi da ke yashe a gaban katifarsa, guda uku ya 6alla ya watsa a baki, daga kwancen da yake ya d'auki ledar ruwa ya kora. Komawa yayi ya kwanta lamo ya lumshe rinannun idanunsa yana sauke wani irin wahalallen numfashi mai fita tare da hucin zazzafar zazzabi, hannyen shi duka biyu dafe da mararsa. Jinsa yake kamar a duniya, kamar matacce kamar yarayye shi sai gashi na, sai dai duk da haka bakinsa bai yanke da ambaton Ubangiji ba. Wani haske ne ya mamaye idanunsa, da sauri ya rintse idanu saboda sun gaza daukar hasken, bayan wasu sakonni ya bud'e su a hankali har ya gama waresu, bai san tahowarta ba bai san ta ina ta shigo d'akin ba sai dai kawai ya ganta a agaban shi, sanye da fari kar d'in dogon riga mai sulbi da taushi. Fuskarta ya kurawa idano yana son gane ko wacece, amma ya kasa saboda rufe shin da tayi da farin mayafin rigarta kamar nikab, banda kwayoyin manyan sexy eyes din ta babu abin da yake iya gani, a gaban shi ta tsuguna, tare da sanya kwayar idanunta cikin na shi, a hankali da wani irin tattausar murya ta furta cikin rada "I Luv u Ameen, zan kareka da dukkan karfi da iyawata, ruhina da naka suna tare tun fil azal, zamu rayu a tare bakin rai bakin fama nice cikon farin cikin rayuwar ka kuma nima kaine farinciki na." Wani dakowa zuciyar shi ta shiga yi har ya kai ga kirjin shi na sama da kasa kamar mai shirin barin duniya, kallonta ta mayar kan kirjin, na wasu sakonni, a hankali ta dago hannunta masu dauke da Zara zaran faratuna ta daura akan kirjin shi ta shiga balle boturan rigar. Wurgi tayi da rigar bayan ta zame shi a jikinsa, faffadan kirjinsa ya bayyana mai dauke da tattausar kwantaccen bakin gashi. Kamar an kwato zancen daga bakin shi cikin rarrabewar harshe ya ce "Wa ce ce ke?" Murmushi ta saki a hankali ta ce "FARHAT." Bai yi aune ba ya ji ta fada jikin shi gaba daya tare da bashi wata irin runguma, wani irin karkarwa jikinsa ya shiga yi. Sark'ewa nunfashinsa ya fara yi lokacin da ya ji tattausar tafukan hannayenta a gadon bayan shi tana shawafa, wani irin karfi ya ji ya ziyarce shi, yunkura yayi ya yi wani juyi, ya mirginata kasan shi ya dawo samanta kamar mayunwacin zakin daya dade bai ci abincin ba, ya samu daga sama haka ya shiga yamutsarta, laushi hadi da taushin fatar ta tare sa wani irin mayataccen kamshin da jikinta ke fitarwa suka hadu suka kara zautar da shi, cikin zafi da fitar hayyaci ya ke bin duk wani sakon jikinta da wani irin romance wanda bai san yaushe ya koya har ya iya ba. Lokacin daya isa inda yake muradi, ihu ya takarkare ya yanka saboda jin shi a wata duniyar da gangar jikin shi ya dade yana muradi, da taimakonta ya samu satisfaction koro na farko a rayuwar shi. Cikin karkarwar jiki da gushewar hankali ya juye mata duk lalurarsa. Kwanciya yayi lamo a jikinta tare da kamkameta kamar zai maidata cikinsa, ya shiga maida wahaltaccen numfashi, jin shi yake sakayau kamar jariri sabuwar haihuwa. A lokacin ya farka daga nannauyan barcin daya kwashe shi bayan ya yi overdose! A hankali ya ware idanun shi, yana bin dakin da kallo, akan labbansa ya furta dream! Tabbas mafarki yayi, mafarki mai cike da rudani. Abin mamaki Normal ya farka babu wani ciwo a jikinta sai rashin kwarin jiki, don a lokacin ko dan yatsarsa akace ya daga bazai iyaba. Lamo ya kwanta brain din shi na sake tariyo masa mafarkinsa, me yasa baiga fuskarta ba, mai yasa duk irin abinda ya faru nadin fuskarta ko gezau bai yi ba, wacece ita. "FARHAT." Zuciyar shi ta bashi amsa, "FARHAT." Ya sake maimaitawa sunan a bayyane, wani irin damuwa yaji ya mamaye zuciyar shi, kar sai ace aljana ce ta Aureshi. Tabbas! Abin tayi kama da apmara ko tasuniyar gizo. kafin yayi aune ya ji ladan ya rangad'a kiran sallar farko. Ga al'adarsa ta yau da kullum, da anyi Kiran sallar farko yake tashi, yau ma bai bari shaidan yayi tasiri akansa ba, bakin shi ya samu da furta adduar tashi daga barci tare da Karin wasu addu'oin, wani karfi yaji ya shige shi, yunkura yayi ya mike zaune, rass! gaban shi ya fadi, ta yaya zai gusar da najasar jikinsa ba tare da Ummi ta sani ba yana matukar kunyarta baya so ta yi wani tunani akan shi, take duk karsashin daya ta shi da shi ya ji ya ragu. Jiki babu kwari ya mike tsaye, cike da kyankyamin jikin shi ya dauki buta da jallabiyarsa wankakke da short ya dauki kuma extra leda da zai saka short din jikinta idan ya cire, daga haka ya fice daga dakin zuwa cikin gida, ya saba buga ma su Ummi kofa kullum daya fito amma yau direct toilet ya wuce, cike da kyankyami da taka tsantsan ya kwabe short din jikin shi ya saka a Leda ya kulle, sannan ya cire riga. Duk sanyin da akeyi bai ji ba haka ya rintse idanu ya tsarkake jikin shi, a hankali cikin taka tsantsan don kar kwarafniyar shi ya farkar da Ummi ko Fatima. Jallabiyarsa ya sako baya ya kammala wankan, sai da ya gabatar da alwala a tsakar gida, ya mayar da butar shi da kayan shi daki, sannan ya tukarin dakin su Ummi, kamar ya kyale su ranar don gani yake kamar zasu iya gane wani Abu, dakewa yayi ya karasa bakin kofar ya bubbuga musu, sai da Ummi ta amsa sanna ya tafi masallaci. Koda suka idar da sallar subh, samun waje yayi a masallaci ya zauna yayi addu'oinsa tare da karatun alkurani, don ya tabbata idan yake gidan ya kebe tunani bazai bar shi yi ba, sai da gari ya fara haske sannan ya fito ya nufo gida. Sallamar shi ya fito da Fatima sake kitchen tana wura charcoal da sauri, cikin raunatacciyar murya ta ce "Yaya Ina kwana ya jikinka, tun dazu nake duba dakin ka baka dawo ba." Murmushi ya sakar mata tare da matsawa gabanta ya kama kumatunta ya dan ja da sigar wasa ya ce "Fatiman Yayanta." Dagowa ta yi ta kalleshi da idanunta da sukayi yi raurau da hawaye ta ce "Jiya dakyar na yi barci saboda tunanin halin da na barka ciki Yayana." Cike da so da kulawa ya ce "Na ji sauki sosai kanwata baki gani ba." Ta gyada kai hawayen daya taru a idanunta na sakkowa, ya ce "Kukan fa Bintan Ummi, oya share wahayenki," da Saudi ta share ya ce "then smile." Murmushi ne ya subuce mata, shima murmushi tayi ya ce "Da fatan baki gayawa Ummi ba." Ta girgiza kai alamar A'a ya ce " Yawwwwa! Gud gal! Ci gaba da aikin ki bari in gaisa da Ummi inzo in tayaki." Daga haka ya nufi dakin Ummi, a falo ya sameta karamin kur'ani ne a hannunta tana karanta suratul kahfi. Wuri ya sama ya zauna yana saurrenta wani natsuwa na huda zuciyar shi, sai da ta kai karshen surar tayi addu'arta ta shafa sannan ta juyo ta kalle shi da kulawa, murmushi dauke a fuskarta. A ladabce ya duka gabanta ya sunkuyar da kai, ya ce "Ummina ina kwana." Cike da alfahari da kasancewarsa d'a a gareta ta ce "Lafiya kalau alhmdllh Amintacce, da fatan kai ma haka." Bayan gaisuwa zama yayi su ka dan taba hirar duniya. kallon agogon yayi ganin bakwai da rabi ta yi, ya mike ya ce "Ummi bari na je na kimtsa yau ina da lecture safe." Ta ce "Allah ya taimaka, Allah ya yi albarka ." ya amsa da "Amin Ummi." Sannan ya fito, sharar tsakar gida ya tarar Fatima na yi, ya ce ta kawo ya karkare ta kama wani aikin kememe ta ki yarda wai ya je ya huta bashi da lafiya. Yana saka kai a kofar shiga zaure su ka zabga karo. Taga-taga ta yi zata fadi, da sauri ya rikota, Zazzare idanu Amira ta shiga yi cike da kunya, bata taba tunanin zata same shi tsaye haka akan kafafafun shi ba, saboda yadda ta barshi, tun asuba take son shigowa ta ganshi tana tunanin idan shigo, ta ce musu meya kawota, yanzu tana zaune ta ji mamanta zata yi aike wajen Ummi tayi caraf ta amsa ta ce bari ta kai. Sake ta yayi ta tsaya akan kafafunta ya ce "Ki dinga kula mana, ina kike kallo haka?."Cikin inda- inda ta ce "ina kwana Yaya Ameen, ya karfin jiki." Babu yabo babu fallasa ya amsa mata da "lafiya jiki Alhmdllh." Ya rabata ya shige dakinsa, yana shiga daga bakin kofa yaji ya taka Abu kamar takarda, kallon shi ya kai wajen, paper ne a nannade, da mamaki ya tsuguna ya dauka tare da budewa da sunan ta idanun shi ya fara tozali. Cike da dumbin mamaki ya furta "What!!! Amira!"......... Ga mai bukatar shiga group ya tuntunbeni kai tsaye. 09116099486. [12/29, 2:39 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiyi Writer's Association* *PAGE 22* Dunk'ule paper n ya yi bayan ya gama karanta abin da ya k'unsa, ya dafe goshi cike da takaici, ko kad'an bai ji wani karsashi ko shauk'i game da kalamanta ba, sai ma ganin tsananin wautarta da shirmenta da ya yi, dama he is wonder yadda ta ke yawan kallon shi ashe da dalili, guntun tsaki ya ja, ran shi duk ya 6aci, cike da takaici ya ce "Yara tun baku tafasa zaku k'one!" Wurgi ya yi da paper'n ya shiga kimtsa d'akinsa, tattara komai ya yi, ya shere d'akin tass! kamar yadda ya saba, wurin tattara shara ya sake cin karo da paper n kamar ya share da shi ya zubar sai kuma ya dauka ya warware ya linke, zai ajiye saboda evidence, gurin da tarin littfansa suke ya nufa, ya dauki wani babban textbook da yake saka paper's ya bud'e da nufin ajiye wa a ciki, karaf! ya bud'e dai-dai page d'in da ya ta6a ajiye letter n Joy, gaban shi ne ya yanke ya fad'i, kurawa latter n idanu ya yi, brain din shi na tuno masa abin da ya faru tsakanin su rannan' lokacin da take sand'a da za ta shiga gidansu, yadda ta firgice daga jin muryarsa kadai, yadda ta riko kafafunsa tana rokonsa, yadda ya fisge kafarsa da k'arfi ta fad'i ta fasa goshi, yadda ta mik'e tana hawaye ta kakka6e jikinta, ta tashi tana tafiya a slow, bin bayanta da ya yi, guduwan da ta yi ta barshi a tsaye rik'e da handkerchief, k'ak'k'arfar ajiyar zuciya ya sauk'e. Hakan na nufin bata yafe masa ba fa kenan, take jikin shi ya yi mugun sanyi, hakika ya cutar da ita, kuma he regret, zai yi kok'ari ya gyara kuskurensa. Latter n ya d'auka ya koma bakin mattress d'insa, ya warware yana bi da kallo tare da sake karantawa, yana maimaitawa, zuciyarsa na k'ara shiga matsanancin tausayin yarinyar kamar yadda ya fassara lamarin. Bai san adadin lokacin daya 6ata a haka ba, ya tsinkayi sallamar Fatima a k'ofar d'akin shi, da sauri ya linke wasikar, ya tura karkashin pillow, sannan ya bata izinin shigowa, kayan breakfast d'in shi ne ta kawo, guri ta samu ta ajiye, godiya ya mata, sannan ya tsareta su ka yi breakfast d'in tare. Yana ta so yayi mata zancen Joy zuciyar shi na hana shi, a haka su ka kammala, ta kwashe kayan ta mayar cikin gida shi kuma ya d'ibi ruwan wanka ya shiga. Har ya yi wanka ya shirya tunanin Joy ya ke, da kyar ya yakice ta a rai ya samu ya fita, school ya tafi daga can kuma bai dawo gida ba, ya ta fi harkar kekensa. Karfe takwas ya shigo gida, as usual su Ummi na tsakar gida, nan ya zauna su na shan iska, a nan ya ci abincin suna sauraren shirin kwarmato! A redion Ummi abin mamaki ranar Amira bata shigo karatu ba, Ummi ta ce "Wai ni kam yau banga Amira ba tun safe ko lafiya? " Fatima ta ce "Nima Ummi wallahi tun d'azu abin ke raina."Ummi ta ce "Allah dai yasa lafiya, da safe idan Allah ya kaimu sai Ki dubo mana ita." Al'ameen na jin su bai saka musu baki. Hira suka shiga yi, sai sha d'aya saura suka ta shi lokacin tuni Fatima ta yi barci. Shi ya kwashe tabarman bayan sun ta shi, sai da ya d'aura alwalar barci sannan ya nufi d'akinsa, shafa'i da wutiri ya gabatar, ya rage kayan jikinsa ya haye katifarsa, sai dai me! Tunanin yarinyar ne ya yi wa kwakwalwarsa kawanya, ya rasa me yasa ya damu da ita cikin y'an kwanakin nan, tun ranar da abin nan ya faru bai ta6a wayar gari ba ta fad'o masa a rai ba koda sau d'aya ne, tausayinta ya ke ji kamar me, sai dai ya alakanta hakan akan abin da ya gifta tsakanin su ran nan, hakan yasa ya daura damaran gyara kurensa, ya dauki tsawon lokaci kafin barci ya d'aukesa. Cikin barci yaji yanayin shi ya fara sauyawa, tun yana d'aurewa har sai da da ya kai ga bud'e idanu, "Allahumma ajirni fi musabati! Hasbunallahu wa ni'eemal wakeel!" Ya shiga maimaitawa, iya hasashe babu wani abu daya faru cikin abubuwan da ke tasar masa da ciwonsa, babu ruwan sama babu sanyi a garin hasalima zafi ake yi saboda kwallara ranar da akayi a yinin ranar, bai shaki wani abu makancin kamshi ba, bai ga wani sura ko wani abu da zai iya daga mashi hankali ba, to menene dalili? Jin abin na k'ara yawa yasa ya yi ta maza ya d'auko maganin sa ya 6alla sai dai ko gezau, sai ma ci gaba da hauhauwa da abin ya k'ara, hankalin sa ya ta shi mak'ura, abin da ya lura yanzu tab! 'Din ya daina mishi aiki ma, kardai maganar Dr Abdul ne ya tabbata. Tuni ya fara ficewa a hayyacinsa, sharkab ya had'a gumi, jikin shi na karkarwa tare da soma daukar zafi, gefe guda ga mararsa da yayi wani irin kumburi ya yi tauri had'i da k'ullewa, numfashi ma dakyar ya ke iya ja da saukewa. Cikin lalube da malelekuwar da yake yi, hannun shi ya sauka akan sachet din maganinsa, kamar jiya, wawura yayi ciki rufewar ido ya 6alli uku ya watsa a baki. Da farko kamar ya k'arawa ciwon karfi, don sai da ta kai shi ga fara mirgina a tsakar d'aki. Kimanin 15 minute ya kwashe a haka, kafin kuma ciwon ya fara lafawa, dakatawa ya yi da mirginan ya yi lamo yana sauke numfashi, a hankali komai ya tsaya cak! Kamar an yi ruwa an d'auke, kumburin maran ya sace, sai dai duk da haka jikinsa na nan da zafi rau, a haka wani wahalallen barci ya kwashe shi. Kiran farko ya farka as usual, Alhmdllh! Zuwa lokacin zazza6in ya sauka, babu wani alamar ciwo sai idanunsa ne kad'ai su ka nuna, zaune yayi a bakin katifarsa zuciyarsa cike da damuwa, sachet d'in maganin shi dake yashe a k'asa ya dauka ya tsurawa idanu yana kallo, tsakanin jiya da yau ya sa guda takwas, abin da ake shan d'aya d'aya, kuma ba kullum ba don da sai yayi sati biyu uku bai sha ba, hakan na nufin d'aya ya daina mishi aiki ke nan, tabbas akwai gagarumin matsala, dole ya koma wajen Dr Abdul, amma kafin nan yana bukatar shawara, yana bukatar shearing din matsalarsa da wani, wayar sa ya d'auka ba tare da la'akari da lokaci ba ya dan nawa Aliyu kira. Ringing biyu Aliyu ya daga, tare da sallama, Al'ameen bai taba kiransa a irin wannan lokacin ba, cikin dan tashin hankali ya ce "Ustaz lafiya, hankali ya ta shi da naga kiranka a irin wannan lokaci." Numfashi ya sauke kafin ya ce "Aliyu ina cikin damuwa." "Subhanallah! Me yake faruwa Ameen? Bai amsa mishi tambayar shi ba, ya daura mishi da wata "Yaushe zaka dawo? Maganar bata waya ba ce." Jim! Aliyu yayi kafin ya amsa da "Zan kai karshen wata, ka fa'di ka d'an daga damuwar ka abokina zaka ji sauki." Girgiza kai Al'ameen yayi kamar suna kallon juna ya ce "Sai dai ka dawon zan kira ka." Daga haka su ka yi sallama jikin Aliyu duk a mace, ya san halin Al'ameen ba tun yau ba, tun da ya bukaci su tattauna akan matsalarsa to ya tabbata babbar matsala ce, zai yi duk yadda zai yi ya samu ya koma gida a karshen watan don su zanta kuma zai taya shi da addu'a Allah ya kawo ma shi d'auki. Tun daga wannan rana kusan kullum sai ciwon shi ya ta shi, walau da sanyi ko babu, taimakon shi daya bai tab'a tasar masa da rana ba, sai dai wani lokacin tun da yamma zai fara jin alamun shi, da yaji haka ranar da wuri yake komawa gida da ya yi isha kuma yake shiga d'akin shi ya kulle. A bangare daya ga damuwar FARHAT zuwa yanzu kusan sau hudu yana yin mafarki da ita, tana maimaita masa kalamanta na ran nan, sai dai har zuwa yanzu bai yi nasarar ganin fuskarta ba duk irin kwakwanshi da son ganin hakan, lamarin yana matukar damun shi. Duk wannan matsanancin yanayin da ya shiga bai manta da Joy ba, sai dai idan bai samu sarari ba sai ta fado masa a rai, ya kan alakanta hakan da cutar da ita da ya yi ran nan kuma yana fatan ya samu damar da zai nemi yafiyarta. ***************** Kamar yadda Al'ameen ke cikin damuwa haka a bangaren Amira, zuwa yanzu ta daina zuwa daukar karatu kasancewar tuni sun fara exam, sai dai kusan kullum tana gidan, bata da aiki sai ajiye masa wasika, a mabanbantan wurare amma koda wasa, Al'ameen bai taba daga ido ya kalle ta ba balle ya nuna ya san da zamata, tuni ta fara rama a tsatsaye kasancewar so ne take masa mai girman gaske, abin na matukar damunta, ya haifar mata da damuwa da duk wani wanda yake makusancinta zai lura, baga iyayenta ba hatta da Ummi da Fatima sun fahimci tana cikin damuwa, sai dai banda Allah! da Zainabu babu wanda ya san halin da take ciki sai ko Al'ameen, wanda shi kuma damuwar gaban shi ta sha kan shi, kwata kwata bata gaban shi , don tun yana bude wasikun shirmenta acewarshi yana karantawa har ta kai ga ya dai na budewa idan ya gani sai da ya dauka ya ajiye ba tare da ya bude ba. *************** *JOY* Cikin abin da baifi wata daya ba soyayya ta gama ragargaza jini da bargon jikinta, i zuwa yanzu bata ji bata ganin komai sai Yayan Fatima, tun tana karyata zuciyar ta akan lamarin har ta yi surrender. Sai dai takan shiga matsanancin damuwa, hankalinta kan tashi a duk sanda ta hango k'urar dake tafe da lamarin, ta ko ina idan ta hanga ta hango babu sauki, baga Al'ameen ba baga Mom da sauran ahalinta ba, har Papa bata tunanin a wannan karon zai kalle ta da idon rahama, a duk sanda tayi irin wannan tunanin takanyi kokari ta yakice shi daga zuciyar ta amma ina! Abin ya ci tura, kullum sai Dada hauhawa ya ke kamar farashi. Gaba daya ta koma so silent, bata da aiki sai rubuce rubucen kalaman soyayya, sai ko kuka da ya zama mata kamar ibada, tuni ta yi rama ta dishe. kwarafniyar Anty Esther tuni sun daina gigitata, gani take hargagin Mom da anty Esther ya fiye mata sauki akan tashin hankalin dake tunkarota, zuciyar ta na daf da yi mata bore, sai dai ta lashi takobin ko zata mutu bazata ta6a bata dama ba, don tana ganin yin hakan tamkar tarwatsa rayuka ne, gara ita nata rauyuwar ya tarwatse. Tuni anty Esther ta bata wayarta, sai dai abin mamaki tunda ta karbu wayar Papa bai taba kiranta ba itama idan ta kira shi baya dagawa, idan ya daga ma da sun gaisa sama sama zai kashe gaba daya ya dena nuna mata kulawa kamar da. Bata wani dauki abin serious ba ta mishi uzuri don a ganinta aiyuka ne suke sha kan shi. A cikin wannan dan tsukin girgin su Mom ya yi dirar mikiya a 9ja, ko gezau bata yi, babu yabo babu fallasa a tare da ita, suka dunguma ita Anty Esther, David, zuwa airport don tarbota, babu wani karsashi ko kewa a ranta su ka iso, lokacin tuni jirgin ya sauka, da sauri Mom ta iso gareta tare da rungumeta, lamarin ya dan so ya daure mata kai, amma tuna yadda Mom dinta ke matukar kaunarta, ada kafin ta soma canzawa yasa ta saki jiki itama ta rungumeta, cikin kunnenta Mom ta rada mata "I missed u a lot daughter." "I missed u 2 my Mom." Ta amsa mata. "Ki yafe min abubuwan da suka yi ta faruwa a dan kwanakin nan, kuskurene." Hawaye ta ci ya ciki mata idananu, "take daskararriyar soyayya ta fara narkewa." Tsaki Anty Eshart ta za a bayyane, tare da kauda kai zuciyar ta na tafasa, murmushi Mom ta yi, ta saki joy ta rungume Eshart tana cewa "Oh! I'm Sorry my dear sister. Na yi kewarta sosai ne shiyasa." Daga haka ta rungume David da shima yake mata sannu da zuwa, hannunta sarke da na Joy suka shiga mota, Joy na kwance a jikinta har su ka iso gida. Duk da izza da dagawa irin na Mom, ma'ikatan gidan sunyi murna da dawowarta, daga yadda suka dinga zuwa kwasar gaisuwa kowanne baki har kunne zaka tabbatar da hakan, ko ba komai zasu rabu da masifar Esther. Ranar Joy na makale jikin Mom din ta, tana lelenta kamar yar five years abinda ta dade rabonta da gani daga Mom din hakan yasa ta saki jikinta sosai ta wuni da farin ciki, koda lokacin barci yayi har daki Mom ta rakata ta tayata shirin barci ta kwantar da ita ta kashe mata wuta sannan ta barta ba yan ta yi kissing forehead din ta tare da shafa kanta. Mom na fitowa daga d'akin Joy ta tarad da Esther tsaye tana Binta da wani irin kallo, hannunta Mom ta kama ta jata su ka bar wajen, d'akinta ta nufa da ita sunan shiga Esther ta fisge hannunta daga na Mom, tare da watsa mata wani lalatatcen kallo, ajiyar zuciya Mom ta sauke a tausashe ta ce "I'm sorry Esther. Ba abinda kike tunani ba ne." Cikin daga murya ta ce "Ta Yaya zan tabbatar da haka ba yan kina aikata sabanin abin da kika sanar min, na gani lokaci yayi da ya kamata ki cika alkawari." "Calm down Esther ki saurare ni." Daga mata hannu ta yi a zafafe ta ce "Bazan saurare ki ba, zan bar gidan nan don bazan zauna bakin ciki ya kashe niba." Daga haka ta tuya ta fice daga dakin fuuu! A fusace. Dabass Mom ta zauna tare da rafka tagumi. Washegari da duku duku safiya Anty Esther ta fito da jakar kayanta ta bar gidan. ********** *Al'ameen* Kwata kwata babu sauki a cikin lamuran sai ma kara tabarbarewa da abubuwa ke yi I zuwa yanzu tab! biyar yake sha kafin ya samu relief........ Ga mai bukatar shiga group. 09116099486. [12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 23* *AL'AMEEN* Kwata-kwata babu sauk'i a cikin lamuransa, sai ma kara ta6ar6arewa da abubuwa ke yi i zuwa yanzu tables biyar yake sha kafin ya samu relief, yana cikin matsanancin damuwa, tuni ya fara rama a tsaye. Ba Ummi ba hatta fatima sai da ta fahimci Yayanta na cikin damuwa, don gaba d'aya ya sauya mata, ko magana yanzu bai cika yi ba, haka firan dare, da ya dawo zai shiga d'aki ya kulle ya kwanta da safe ya fito da idanu jajur kamar gauta a kumbure idan ta tambaye shi ya ce babu komai, tuni duniyar ya fara mata zafi, take kewar aminiyarta ya dawo mata sabo fil dama shi ke dauke mata hankali akanta ba wai don ta manta da ita ba. Ummi kam damuwar da ta shiga ba'a magana, matsayinta na uwa lamarin ya shigeta matuk'a gaya, tsoranta Allah kar ace shaye shayen nan na zamani Al'ameen d'in ta ya fara, a duk sanda ta yi wannan tunanin, takan shiga kololuwar ta shin hankali, har ta zubar da hawaye, ta zauna da shi ba sau daya ba ba sau biyu ba cikin lalama da dabara ta naimi jin damuwarsa, amma ya ki fad'a mata, sai dai ya girgiza kai ya ce mata "Babu komai Ummi, kawai gajiyan aiki da karatu ne, sai mura da ta saka ni gaba a yan kwanakin nan ki taya ni da addu'a." Ba dan ta yarda ba, dole take hakura, ta san tunda ya nace a haka bazai fada mata ba ne, ta fi kowa sanin halin zurfin cikin shi tun yana dan kankanin yaro. Da misalin karfe takwas na dare ya shigo gida kamar yadda ya saba, sunan zaune jigum jigum a tsakar gida, duk yadda Ummi take da son sauraren redi'o yau rediyon nata a kashe yake carbi ne rike a hannunta tana ja, Fatima kam notebook din ta ne a gabanta data dauko zata yi karatu amma ta kasa, ta ajiye ta rafka tagumi. Kallo daya Ummi ta mishi ta kauda kai gefe, sai ga hawaye shaaa! Duk yadda taso ta kauce kar ya gani abin ya ci turo. Da sauri ya kara sa shigowa, zubewa yayi a gabanta hankali tashe, ya ce "Subhanallah! Ummi." Daga mai hannu ta yi ta ce "Karka kira sunana Al'ameen ni ba Umminka ba ce, ka tashi a gabana." Ta karashe maganar tare da fashewa da kuka mai karfi, Fatima da maganar Ummi ya dawo da ita hayyacinta, rarrafowa tayi ta fada jikin Ummi ta fashe da kuka itama, cikin kuka ta ke cewa "ki yi hakuri Ummi, ki yi hakuri ki yi shiru." Rungumeta Ummi ta yi su ka ci gaba da rera kukan a tare. Kololuwar tashin hankali Al'ameen ya shige shi, zuciyar sa tuni ta shiga wani irin tsalle kamar zata faso kirgi ta fito, rasa abin yi yasa shi fara zubar da zazzafar hawaye da , sai kawai ya rungume su gaba daya, cikin zubar hawaye da kunar rai ya ce "Ki yi hakuri mahaifiyata ki dena zubar da hawayenki a kaina, na tuba nabi Allah na bi ki." Kalmomin da ya dinga maimaitawa ke nan kamar karatu. Sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin Ummi ta tattare d'an jarumtarta ta danne zuciyarta, ta zame su daga jikinta ta dago ta kalle shi cikin ido ta ce "Al'ameen shaye shaye ka fara?"da wani irin sauri ya kalle ta yana girgiza kai, ta ce "Karya ka ke yi, idan ba haka ba kuma ka sanar dani damuwar ka, don na tabbata a kwai abin da ke damunki ji yadda ka koma gaba daya ka lalace cikin yan watanni, bazan jura ganin ka haka ba Aminullah." Shiru ya yi yana kallonta bazai iya yi mata karya ba, kuma bazai iya fitowa kai tsaye ya sanar da ita damuwar shi ba, duk da yasan bashi da kamar ta duk duniya, yana matukar jin nauyinta, kasa ya yi da kai ya ce "Ki yi hakuri Ummi, bazan iya yi miki karya ba, kuma bazan iya sanar miki damuwata ba, amma wallahi tallahi bana shaye shaye, ki taya ni da uddu'a Ummina." Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke ko babu komai ta samu saukin kaso ashirin cikin damuwarta kashi dari. Sai dai ko da wasa bata nuna a fuska ba, mikewa ta yi ba tare da ta kalli gefen da yake ba ta shige daki. Fatima ma mikewa ta yi zata bi bayanta, har lokacin kuka take yi, da wani irin raunatacciyar murya wanda basu san shi da shi ba ya kira sunan ta "Fatima." Dakatawa ta yi da tafiyar ta juyo tana kallon shi tana shesheka, girgiza mata kai ya yi tare da cewa "Shiiiiii!" Alamar ta yi shiru, sai kuma ya yi mata alamar ta zo da hannu, da sauri ta karasa gareshi ta fada jikin shi, ta sake fashewa da kukan da dama ba wai ta dai na ba ne. Rumgumeta ya yi, wani irin rauni na kara kaiwa zuciyarsa farmaki. A yau ya kara tabbatarwa, shine cikin farin cikin yar uwarsa tilo, da kuma mahaifiyarsa wacce itace komai na shi a rayuwa. Muryarta ne ya katse masa tunani, cikin shesheka take cewa "Yayana ka canza, yayana ka dawo kamar yadda ka ke da don Allah, da ni da Ummi muna cikin damuwa kai ne haske ka jagoran rayuwar mu." Bubbuga bayanta ya shiga yi, ba tare da ya iya bude baki ya amsa mata ba, sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin ya samu ta yi shiru, sai ajiyar zuciya da take saukewa jefi jefi. Dagota ya yi daga jikinsa ya shiga share mata hawaye, yana yi yana cewa "Kar ki sake yin kuka My luv na miki alkawarin zan dawo muku da farin cikin ku ke da Ummi. Al'ameen din Ku zai dawo Yaya Ameen din ki zai dawo kin ji ko." Ta gyada kai ya ce oya wuce kije ki kwanta, Babu musu ta wuce shi jiki a sanyaye, sai da yaga shigewarta daki sannan ya kwashe tabarman ya jingine, kamar mara laka haka ya nufi dakinsa. Ranar damuwa biyu ne ya hade masa, ga na azababbiyar ciwonsa gana tunanin halin da ahlinsa suka shiga a dalilin sa, bazai iya jurar ganin su cikin wannan yanayin ba, bazai iya jurar zafin zubar hawayen uwa ba, ya san wata kila Ummi ta na fushi da shi, dole ya tsayar da mafitar da yake ganin ita ce dai-dai. Ranar yadda yaga rana haka yaga dare. Da safe kamar yadda ya saba gudanar da komai haka ya gudanar, hankalinsa ya kara tashi lokacin da ya hada idanu da Ummi, bai taba ganinta cikin irin wannan kamar ba, gaba daya idanunta sun kumbura sun yi jajur, sai dai bata nuna masa wani sauyi a fuska ba, ya san ta kwana cikin damuwa, abin da ya fi daga mai hankali ganinta da ya yi kwance a dai-dai lokacin da kullum yake samunta zaune ta na lazumi tabbas! Bata da lafiya, kuma yasan shine sila, shikam ina zai kai girman sannan zunubin uwa tafi gaban wasa,zai iya sadaukar da komai domin ganin farin ciki ta, a koda ya tambayeta ko bata da lafiya ne, cewa ta yi kalau ta ke. Ko breakfast bai iya tsayawa yi ba, ya shirya afujajan ya nufi asibitin Dr Abdul Hafiz S Alto don a nan ne kadai yake ganin zai samu total solution. Lokacin da ya isa Dr bai iso ba, zama yayi a waiting area shi da sauran patient din da ke nan. Sun dauki almost gud 2 hours kafin Dr Abdul ya iso, tun daga nesa ya hango Al'ameen, boyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tuna wayar da su ka yi da Aboki, shekaran jiya. Sama sama ya amsa gaisuwar ma'aikata ya shiga office ya fara duba patient dinsa, gefe guda kuma zuciyarsa cike da fargabar da me yaron ke tafe fatansa Allah yasa ya zabi cancanta kar ya zabi son zuciya. Mutum bakwai ya gani kafin layi ya iso kan Al'ameen, tun da ya turo kofar office din Dr Abdul ya dago yana kallon shi, shima jemammun idanu shi na kan Dr din. Guri ya samu ya zauna a inda aka tanada don zama, da wani iron cool voice ya ce "Dr na dawo gareka ka taimaka ka yi mini wannan alluran da ka ce shine zabina." Rasss! Rasss! Haka gaban Dr Abdul ya yanke ya fadi, ya san za'a rina dama. Shiru ya yi yana kallon Al'ameen din ba tare da ya amsa shi ba, gajiya da zaman shirun ya saka Al'ameen sake cewa "Don Allah Dr ka taimakeni ina cikin matsanancin damuwa." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Wacce irin damuwa ce sannan data saka ka kake shirin kashe rayukar a tsaye." Ya ce "Duk abinda kaga ya koro bera daga rami har ya fada wuta to hakika yafi wutar zafi, ni dai don Allah ka taimake ni." "Ta yaya zan maka injection irin wannan mai hatsari alhalin ban san matakin ciwonka ba, kar ka boye min komai ka gaya min gaskiya mekefaruwa?" Tuni idanun Al'ameen suka kara kadawa, a raunace ya shiga labartawa Dr halin da yake ciki, ba tare da rage komai ba kamar yadda Dr ya roka. Tun kan ya kai kar she tuni Hankalin Dr ya ta shi, ranshi yayi mugun baci, bai taba sanin akwai mutane kidahumai ba a duniya sai yau. Cike da wani irin bacin rai ya katse shi ta hanyar jiran sunan shi a tsawace "Muhammad!!!! "........ 09116099486. [12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 24* Cike da wani irin bacin rai Dr ya katse shi ta hanyar kiran sunan shi a tsawace "Muhammad!!! Baka da hankali ashe, five tablets fa ka ce." Komawa ya yi zauna da6ass "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Ya furta tare da dafe forehead. Ganin yadda hankalin Dr Abdul ya ta shi yasa Al'ameen yin k'asa da kai, cikin sanyin murya ya ce "I ha6 no choice, dat is y" Dagowa Dr ya yi idanun shi har sun kad'a ya ce "Ni ka ke gayawa baka da za6i, shin! haka mu ka yi da kai?" Ya girgiza kai. "Then y ka yi hakan, kasan me ka aikata kuwa, hakan fa dai-dai yake da kashe kai." "I'm sorry Dr." D'aga ma shi hannu Dr ya yi , ya ce "Ka rike hakurin ka, ka tashi ka fice min daga office bana bukatar ganin ka, don babu abin da zan iya yi maka a halin yanzu." Jin haka yasa hankalinsa kara ta shi tuno yadda ya baro Ummi a kwance cikin ciwo ya yi, ya sake tuna irin damuwar da tilon kanwarsa ke ciki duk akan wannan matsalar, sannan ya zo in da yake ganin zai samu maslaha amma yana ji yana gani ana neman yi masa sakiyar da babu ruwa. A raunace ya ce "Dan girman Allah Dr ka tausayin min ka dubi maraicina, ka yi mini wannan alluran, na amince da duk abin da zai biyo baya." Kallon zautacce wanda bai san ciwon kan shi ba Dr ke mishi i zuwa yanzu, hakan yasa ya baiwar iska ajiyar shi ya ci gaba da duba tarin files din dake gabansa. Magiya da ro'ko Al'ameen ya shiga yiwa Dr amma yayi kamar bai san da zaman mutum a wajen ba, don ran shi a matukar 6ace yake danne zuciyarsa kawai ya yi don tunzira shi ta ce akan ya ta shi ya dinga sharara ma shi mari, amma yaga alamar yaron na neman kai shi bango. Magiyar duniya Al'ameen yayi wa Dr amma bai kalle shi ba, har k'asa ya duka ya riko kafafusa yana rokonsa, amma kamar da dutse yake, tuni zuciyarsa ta fara tunzira. Mik'ewa ya yi a fusace cikin tafasar zuciya da matsanancin bacin rai ya ce "Kar ka yi min mana so what!" Kalmar da ta doke kunnen Dr da ya sa ka shi dagowa da sauri a kalle shi. Cikin tsawa da rufewar idanu ya ci gaba da cewa "Wacce irin zuciya ce a kirjinka Dr? Shin baka da imani da tausayi ne baka san Allah da ma'aiki ba? To shike nan ka je ka rike taimakon na ka, gari da yawa maye baya ta6a cin kansa! Idan baka taimaka mini ba akwai dubban irin ka da zasu iya taimaka mini, duk duniya babu wanda na yarda ya san sirrina ciki da waje sai kai, na gaya maka abin da ke faruwa ban 6oye maka komai ba, na ce maka na amince da duk abin da zai biyo baya ba shike nan ba, ina ruwanka jikin ka ko jikina rayuwar ka ko nawa? So kake na fifita wani jin dad'i na rayuwana akan farin cikin mahaifiyata, to ka sani UK duniya babu wanda ya isa, bani da kamar ta itace komai nawa, kuma zan iya yin komai dan ganin farin cikin ta, dukan table ya yi da karfi har sai da wasu takardun dake kai su ka watse ya ce " Ni muhammadul-Ameen Idan na haifu dan halak na maka alkawarin baza ka sake ganin kafata a cikin asibitinkada zumar naiman taikamo a wajen ka ba." Daga haka ya juya a fice daga office din tare da buga koda da mugun karfi. Tun da Dr ya kafe shi da ido bai sauke ba har ya fice daga office din. Ya fi minti goma a haka, kafin ya sauke zazzafar huci, fuskar yaron yake sake kallo a idanunsa maganganun yaron ne ke sake repeating kan su a cikin kunnuwansa, "Ya Rabbi! Kaga niyyata ka dafa mini." Ya furta a bayyane wayar shi ya dauka ya yi dialing lambar Hayatuttdeen, kamar yadda ya tsammata kiran bai tafi ba, kife wayar ya yi akan table, shima ya kife kanshi tare da lumshe idanu..... *********** Da wani irin fushi hadi da bacin rai ya fito daga asibitin, jefa kafa yake yi duk in da ya samu, idanun shi a rufe, ikon Allah ne kawai ke rike da shi, bai san ina yake nufa ba, don zuciyarsa ce kawai ke jagorantarsa kwkwalwarsa kam ta dau zafi a lokacin da bazata iya tantance komai ba. Wani irin mugun horn ne hadi da taka burki suka ziyarceshi lokace daya, sai dai kafin ya yi aune tuni motar ta ture shi, duk da ba wani mugun turi bane don direban yayi iya kokarinsa wajen kaucewa hatsarin, sai da ya fadi kasa. Gigitacciyar kara ta saki a matukar razane. ba ta san yadda a ka yi ba, ta shiga komar tunanin shi kamar yadda ya zame mata ibada, kawai ta ji direbanta ya taka birki, a firgice ta dogo kafin tayi aune kamar kiftwar idanu taga motarta ya ture shi. Ita da direbanta rige rigen fita a mota suka shiga yi, kusan a tare suka isa inda yake, bata tabbatar shi din ba ne, don duk a tuninta gizon da ya saba mata ne, sai da ta fito daga mortar ta ganshi ra'ayil aini. Cikin rawar jiki Peter ya isa gare shi don ya taimaka mi shi ya mike, abin mamaki da daure kai dakatar sa shi yayi ta hanyar daga mishi hannu cikin karfin hali da jarumta ya dafa kasan titi ya mike tsaye, bai ji mugun rauni ba sai dan kujewa, sai dai ga dukkan alama ya bugu a kafafun shi ganin yadda tsayuwa ta so gagararsa da fari, amma yayi ta maza ya cije lips ya tsaya cak. Tuni ta fashe da wani irin kuka tare da karasawa garesa, a gabansa ta tsaya cikin kuka take cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri, Peter mu kai shi asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a jikinka." Riko hannun shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba daya ta rude bata cikin hayyacinta...... Ku yi manage pls. Masu comment nagode kwarai ina alfahari daku, jiya kun faranta min sosai dana bude data naga ruwan comment na shigowa group di na pls Ku ci gaba hakan shine karfin gwiwata ina sonku sosai masoya mabiya. [12/29, 2:41 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 25* Fashewa ta yi da wani irin kuka, da gudu ta k'arasa gare shi, a gaban shi ta tsaya cikin kuka da kid'ima ta ke cewa "Na shiga uku na lalace! Yaya Alamen ka yi hakuri, Peter mu kai shi asibiti, Yaya Alamen ka zo muje asibiti pls jini yana zuba a jikinka." Riko hannun shi ta yi ta soma kokarin jan shi, gaba d'aya ta rud'e bata cikin hayyacinta. Duk da yana cikin halin ciwo, sai da ya ji Yarrrr!!! A jikinsa lokacin da hannunta ya sauka a kan nasa, da sauri ya saka hannusa d'ayan ya 6an6are hannunta daga nasa. Jin haka yasa ta dago da jikakkun idanuta ta sauke a fuskar shi, karaf! Suka su ka sauka cikin na shi kaifaffun idanun da suke rine, tuni zuciyarta ta shiga wani irin dokawa da wani irin speed,wasu irin sinadarai masu kama da surkulle ke fitowa daga idanun shi suna shiga na ta direct ba tare da wani shamaki ba, kasa janye idanu ta yi daga cikin na shi, duk da irin kaifin da suka mata. Kayataccen murmushinsa ya sakar mata, ya girgiza mata kai, murya kasa-kasa ya ce "I'm ok' ba sai kin kai ni hospital ba thank yhu for Ur care." Daga haka ya juya ya ci gaba tafiya yana d'ingisa kafarsa ta hagu. Kamar a sume kuma ba a sume ba, haka ta dinga jin kanta, bata farga da ya bar wajen ba sai da ta tsinkayi muryar Peter yana cewa "Miss ar u ok." Firgigit ta yi ta kalle shi, ta sake kallon hanyar da al'ameen ya bi, ji ta yi wani kuka mai karfi ya taho mata from no where, da gudu ta wuce shi ta bude motarta ta fada tare sa fashewa da kuka. Jiki a matukar sanyaye Peter ya bude motar ya shiga mazauninsa, ya tada motar suka bar wajen, zuciyarsa cike da tausayin uwar dakinsa. ************* Karfin hali da jarumta ce kawai da kuma taimakon Allah suka karasa da shi gida, zuwa lokacin tuni kafar ta kumbura, baya son ya tadawa su Ummi hankali hakan yasa bai nufi cikin gida ba ya tsaya dakin shi. Karar taba kofar dakin ne ya jawo hankalin Fatima dake tsakar gida, da sauri ta leko don ganin ko waye tunda dai ta riga ta san yayanta ya fita, kuma muddin ya dawo sai ya shigo cikin gida kafin ya nufi dakinshi, sai dai ga mamakinta shi din ta gani tsaye idanun shi a rintse ya cike lips yana kici kicin soka key a jikin padlock. "Yayana." Ta furta tana karasawa gaban shi, sai lokacin idanunta suka kai ga kujewar dake gefen fuskar shi da gwiwar hannun shi da ke zubar jini, zaro idanu ta yi a rude ta ce "Subhanallahi! Yaya me ya sameka?" Kafin ya bata amsa ta hango kumburan da kafar shi ta hagu ta yi, "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na shiga uku!" Da sauri ya bude rinannun idanunsa jin zata yi masa kwarmato, cikin karfin hali ya yi mata alamar shiii! Da hannu, girgiza mishi kai ta yi tana hawaye sai kuma ta juya ta runtuma da gudu, "Ya Salam!" Ya furta akan labbanasa, ya fahimci gaba daya ta rude ne kuma yasan Ummi zata je ta gayawa, sam baiso ba sanin da ya yi Ummi bata jin dadi yau. Allah sarki uwa! A kwance take amma jin abin da Fatima ke fada tuni ta mike zaune, kafin Fatima ta kai aya, ta mike kan kafafunta, ta yo gaba, Fatima ta rufo mata baya. "Subhanallahi! Yayan Fatima me ya faru haka, innalillahi wa inna ilaihi rajiun!" Ta fada cikin tashin hankali ganin yadda kafar shi ta kumbura, "Fatima amshi makullin ki bude kofar." Fatima dake sharar kwalla ta amsa key a hannun Al'ameen ta bude kofar, dakyar ya iya daga kafa ya shiga ciki, Ummi da Fatima suka rufa masa baya, kwanciya yayi, don bazai iya zama ba, Ummi ta sake cewa "Ko dai asibiti zamu je Al'ameen?" Dakyar ya girgiza mata kai yana cike lips Cike da azaba, sannu suka shiga rige-rigen yi masa. Sake kallon kafar Ummi ta yi dakyau ta ce "Wannan kafar taka akwai targade, Yayan Fatima. Binta yi maza ki je gidan Mallam Surajo mai dori ko yana nan" Da gudu Fatima ta fice, Ummi kuma ta zauna tana yi masa sannu, daurewa kawai ta ke yi kar ta zubar da hawaye. Minti sha biyar Fatima ta yi sallama, Mallam Surajo biye da ita, fitowa Ummi ta yi a dakin suka gaisa sama-sama ta ce "Mallam yaro ne ya shigo yanzu da kafa a kumbure, shine nace ta kira ka ka duba ina ganin kamar targade ne." Ya ce "Assshha! To bari a duba, Allah kiyaye gaba." Daga haka ya shiga dakin Al'ameen din. Kamar yadda Ummi ta yi hasashe targaden ne kuwa. Babu bata lokaci Mallam Surajo ya hau aikinsa, duk da cewa kafar bata yi mugum tsami ba, Al'ameen yaji jiki, rintse idanu kawai yayi yana ambaton sunaye Allah. Ummi kasa tsahuwa ta yi a baki kofar jin hawaye na shirin zubo mata da sauri tayi cikin gida, Fatima kam kuka take wiwi ta aza hannu aka. Bayan wasu mintuna Mallam Surajo ya kammala aikinsa, fitowa yayi ya tarad da Fatima, ya ce "Yan mata ki gayawa innarku an gama." Ta amsa da to , ta shiga ciki, tare suka dawo da Ummi. "Mallam ashe har an kammala, to mungode Allah ya saka da alkhairi, ga wannan ayi hakuri." Cewar Ummi tana mai mika mishi naira dubun dake hannunta, amsa ya yi, ya ce "Nagode Hajiya, an kammala an daure kafar nan da kwana hudu zan zo a kwance, an ma yi sa'a baiyi tsami sosai ba ku ka kira ni, Allah ya bashi lafiya." Da "Amin ya Rabbi!." Ummi ta amsa mishi, suka yi sallama ya tafi. Jiki a sanyaye Ummi ta tura kofar dakin ta shiga, cikin hukuncin Ubangiji barci ya dauke shi, sai dai kallo daya zakasan barcin azaba ne, duk ya hada uban gumi. Labulen window ta dage ma shi don ya samu iska, daga haka ta fice daga dakin. Awa biyu ya kwashe yana barci kafin ya farka, zuwa lokacin zafin da bacin ran dake tattare da zuciyarsa game da abinda Dr Abdul ya yi masa ya ragu kaso hamsin cikin dari. Shiru ya yi yana tunanin abinda ya faru da shi yadda accident din ya afku da abinda ya biyo bayan afkuwarsa, bai san dalili ba sai ya samu Kansa da sakin tattausar murmurshi a fila ya furta "Matsociya." Sallamar Fatima ya katse ma shi tunani, ganin shi a farke yasa ta saurin karasowa cikin dakin, a gabashi ta zauna tare da cewa "Sannu Yayana ka farka ya jikin?" Murmushi ya yi mata a hankali ya ce "Alhmdllh kanwata." Mikewa ta yi tana cewa bari na gayawa "Ummi ka farka." Tare suka dawo da Ummi, gefen katifar shi ta zauna, cike da tausayawa ta ce "Amintacce ka farka, yaya jikin?" Ya ce "Ummina da sauki." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Garin yaya kaji ciwo haka?" Shiru ya dan yi kafin ya ce "Accident na samu mota ce ta kade ni, amma ba wani mugun kadewa ba kawai dai abin yazo da tsautsayi ne." Girgiza kai ta yi cike da alhini, ta ce "A ina ne?" "A cikin unguwa ne, na kamo anya ina dawowa gida." "Asshha!Ubangiji ya kara kiyayewa." Ranar Al'ameen a gida ya wuni Ummi da Fatima na jinyar shi ko kwakkwarar tari ya yi su yi ta rige -rigen tambayar shi lafiya me yake bukata, tausayinsu ya kara lullube zuciyarsa, ya kara tabbatarwa duk duniya bashi da kamar su. *********** *Amira* Yinin ranar haka ta yi cikin rashin walwala da faduwar gaba, kullum da tunanin shi ta ke wuni, sai dai yau duk sanda ta tuno shi sai gabanta ya yanke ya fadi, yau kimanin kwana uku kenan rabon da ta saka shi a idanunta, takan shiga gidan kullum kamar yadda ta saba sai dai ta lura kamar yana kaucewa haduwar su da gangan ne, yau kam tana jin idan bata saka shi a idanunta ba baza ta iya rintsawa, hakan ya sa ta shirya abin da zata fada a gida don a barta fitowa. Misalin karfe takwas na dare ta yi sallama a tsakar gidan, Fatima na wajen Al'ameen don haka Ummi kadai ta tarar a daki, zama ta yi a saman dardumar da ke shimfide a tsakar dakin, a mutunce kamar ko da yaushe ta ce "Barka da dare Ummi mun wuni lafiya." "Lafiya kalau Amira, ya dare ya exam." "Alhmdllh Ummi, an gode Allah." "To Allah ya dafa ya bada nasara." "Amin Ummi nagode." "Ya su Maman Amira, da sauyan yan uwa." "Duk suna nan kalau." "Ma sha Allah kya isar min da gaisuwa." Daga haka su ka zauna shiru na dan mintoci, Ummi ta yanke shirun ta hanyar cewa "Ya akayi ne Amira naga kamar ki na son yin magana." Kasa ta yi da kai ta ce "E Ummi dama wajen Fatima na zo kuma naga kamar bata nan." "Ayyo Fatima na wajen Yayanta, da yake dazu ya samu tsautsayi a kafa." Rass! Rass! Haka gabanta ya yanke ya fadi, bata san sanda ta dafe girji da sauri ba, cikin rudewa ta ce "Subhanllahi! Na shiga uku! Meya same shi, Allah yasa ba mummunar rauni ya ji ba?" Shaf ta mance da Ummi take magana. Ganin yadda Ummi ta zuba mata idanu yasa ta ji wani kunya ya lullu6eta, da sauri ta yi kasa da kai don gani ta yi kamar Ummi taga abinda ke zuciyarta, basarwa Ummi ta yi ta ce "Wallahi d'azu ne yana dawowa gida mota ta kade shi har ya samu targade a kafa, amma da sauki an gyara an daure kafar." Dakyar ta iya ce wa "Allah sarki! Ubangiji ya ba shi lafiya." Ummi ta amsa da "Amin." Daga haka shiru tayi zuciyar ta ya raunata ji take kamar ta zubar da kwalla amma ta daurw saboda a gaban Ummi take, ranar kasa sakin jiki ta yi suyi hira da Ummi kamar yadda su ka saba ta yi,duk da yadda Ummin ta dinga kokarin jan ta da hira, ita kanta Ummi ta fahimci tana cikin tashin hankali. Zaman mintuna ka dan ta kara ta mike ta na cewa, "Ummi bari na je." Ummi ta ce "Har zaki tafi, to shike nan Amira sai da safe, ki biya dakin Yayan Fatiman, Bintan tana can daga nan ma kya gaishe shi da jiki." "To Ummi nagode." Ta fada tana ficewa. Ta kusa minti biyar a bakin kofar dakin ta kasa shiga, dakyar ta yi ta maza ta yi sallama a hankali Kamar wata mai koyan magana, karfin jin da yake da shi yasa ya jiyo ta, Fatima kam bata ji, a kan labbansa ya amsa, haka kurum ya samu kan shi da da faduwar gaba. tsoron shi daya kar ace ta fesa wannan shu'umun turaren na ta. Minti biyu ta kuma kwashewa kafin ta sake yin wata sallamar ta karo na biyu, wannan karon da dan karfi, sai a lokacin Fatima ta ji, amsawa tayi , tare da ce wa "Anty Amira ce Bismillah! Shigo mana." Kamar wata munafuka haka ta bude kofar net din ta shigo, daga dan nisa da shi ta samu waje ta zauna, idanunta na kan kafafun shi dake daure, wani irin tausayi shi ne ya lullu6eta, ji take kamar ta zubar da hawaye, a sanyaye ta dago ta saci kallon fuskar shi, cikin sa'a su ka hada ido, da sauri ta dauke idanunta daga cikin na shi, ta mayar kan kujewar dake gefen fuskar shi, don baza ta iya jurar ci gaba da kallon kwayar idanun shi ba, a haka ta bude baki dakyar ta ce "Ina wuni Yaya Ameen, ya jiki, ashe abin da ya faru kenan Allah ya sauwake yasa kaffara ne." A jere ta yi gaisuwar ba tare da ta jira sai ya amsa ba. Kusan hada baki suka yi shida Fatima wajen amsa mata da "Amin ya Allah." Daga haka su ka gaisa da Fatima, tana kara tambayarta ya mai jikin, ta amsa mata da "Alhmdllh." Zaman shiru na yan sakanni ya gifta, Fatima ce ta katse shirun ta hanyar jan Amira da hirar islamiyya, kasa sakin jiki ta yi su yi hira kamar yadda su ka saba. Al'ameen na jin su, amma ya lumshe idanu kamar mai barci, a zuciyarsa kuwa hamdala ga Allah yake da bata feso wannan bakin turaren na ta ba. Hirar bai yi wani tsayi ba ta mike ta ce zata wuce, Fatima tace "Kai Anty Amira tun yanzu, ki dan kara zama mana yanzu fa 8:30 ta yi." Kin zaman ta yi don jin ta take duk a takure. Ba don Fatima ta so ba su ka yi sallama, sake satar kallon shi ta yi ganin idanu I a lumshe ta samu karewa kyakkyawar fuskarsa kallo, har da dan sakin ajiyar zuciya irin mutum ya samu relief din nan, sai da tayi ma'ishi sannan ta mike tana cewa "Fati ya samu barci in ya farka kya kara gaishe shi, sai da safe." Duk abin da take yana kallon ta ta kasan ido har ta fice daga dakin. Bayan tafiyarta Fatima kimtsa mi shi dakin ta yi ta kashe mishi wuta ta fice don duk a tunanin ta barcin gaske yake. Ya dade yana tunane-tunane kafin barci gasken ya yi awon gaba da shi, koda ummi ta zo sake duba shi itama ta tarar ya na barci ne, gyara mishi rufa tayi ta yi addua'a ta tofa mishi sannan ta fice ta kulle kofar gidan tunda yau me kullewar na kwance babu kafa. Daga nan itama ta wuce ta naimi makwanci asuba ta gari. ******** *JOY* Daga wurin da accident din nan ya faru direct gida su ka wuce don dama akan hanya komawa suke, ta je shopping ne. Har su ka iso gida kuka ta ke yi, Peter duk ya rude sai hakuri yake bata, zama tayi a mota dakyar ta samu ta tsaya da hawayenta, ta goge fuskarta sannan ta fito ta nufi Cikin gida, tuni kayan shopping dinta sun isa ciki, daki ta ta yi niyar shigewa ba tare da ta bari sun hadu da Mom ba, sai dai hakan bai su ba, don a main parlor ta tarad da Mom, a rude mom da yanzu take nuna mata wani irin soyayya mai karfi, ta tare ta ganin yadda manyan fararen idanunta su ka rune su ka kankance, sai dai tambayar duniya ta mata ba amsa data takura mata sai hawaye, a rude Mom ta sama aka kira mata Peter, a bakin shi take jin abinda ya faru, amma bai gaya mata cewa Al'ameen ba ne, ba tare da nuna alhini ko tausayi ba take tambayar ina wanda su ka bige din, nan ya kwashe yadda su ka yi da mutumin ya gaya mata, kuma ya tabbatar mata dan unguwar nan don ya san gidan su. Cike da jin haushi Mom ta ja tsaki ta ce "Mitsiyacin banza shi ya sani ai, ya yi wa kansa" daga haka ta ci gaba da rarrashin yarta. Wani irin yini ta yi ranar mai matukar azabtuwa ga ruhinta, a duk sanda ta tuno lamarin kukanta saboda fil yake komawa, hakan ya haifar mata da ciwon barin kai, sai dai ta yi ta dauriya bata bari Mom ta sani ba gudun kar ta saka mata ayar tambaya, dakyar da rarrashi ta iya tsakarar abinci haka ta wuni a kwace kamar ruwa. Bata gane lamarin ya girmama a gareta ba sai da dare ya yi, kememe barci ya kauracwa idanunta, don a duk sanda ta rintse idanu shi take gani,cikin raunika da yadda yake dingisa kafa cike da azaba, haka ta kusa raba dare tana hawaye, dakyar barci barawo ya saceta, sai dai ko awa biyu bata cika ba ta farka a firgice ta yi mafarki wai Al'ameen ya mutu, ta shi ta yi daga kwance ta zauna da duwawunta a tsakiyar gadon ta rafka tagumi tana ta tsiyayar hawaye ji take kamar ta yi tsuntsuwa ta je taga halin da yake ciki, ya zama dole gobe ta je ta duba ba shi idan ba haka ba hankali ta bazai taba kwanciya ba............. Gashi nan harda na jiya😬 Gamai bukatar shiga group ya tu tubeni kai tsaye. 09116099486. [12/29, 2:42 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ DAGA ALƘALAMIN👉 *AyshaNalado* ƘARƘASHIN JAGORANCIN👉 *Mikiya Writer's Association* *PAGE 26* No editing ayi ta hakuri🙏 Washegari haka Ummi da Fatima su ka tashi da hidamar Al'ameen, abin ma yazo musu da d'an sauk'i ne saboda shi d'in jarumi ne, bai sakar musu ragamar komai ba, yakan yi iya k'ok'arinsa, idan ya kasa sannan ya naimi taimako, yanzu ma Fatima ce ta yi sallama d'auke da abincin karin kumallon shi a hannu, ga mamakinta a tsaye ta same shi yana bin bango zai fito waje har ya kai bakin k'ofa. "Subhanallah! Yaya ina zaka je?" Murmushi ya sakar mata, ya ce "Na gaji da zaman d'aki ne k'anwata zan fita tsakar gida in sha iska." Kwa'be fuska ta yi ta ce "Shine baka kirani in taimaka maka ba, idan ka fama ciwon ka fa?." Ta karashe maganar tana k'ok'arin rik'e shi, ya ce "No Barshi Fatima zan iya, ki je ki shimfid'a mini tabarma a tsakar gida." Cike da mamakin karfin halinsa ta ce "To Yaya." Ta fi ce. Kici kicin shimfid'a tabarman da ta ke yi ne yasa Ummi dake kitchen lek'owa "A'a Fatima ya haka kuma?" Cewar Ummi sanin ba wai sun saba zaman tsakar gida da safe bane. "Yaya ne ya ce na shimfid'a mi shi zai fito yasha iska wai ya gaji da zaman d'aki." Kafin Ummi ta ce komai sai gashi ya shigo da bin bango da dabara ya ke lalla6awa, da sauri Ummi ta zo ta rik'e shi, ta na cewa "haba Amintacce, ai da ka yi magana sai a taimaka maka." Da murmushi ya ce "A'a Ummi zan iya ai." Ita dai bata yarda ba sai da ta rik'e har kan tabarman da Fatima ta gama shimfid'awa ya lalla6a ya zauna, yana rintse ido lamar yana jin azaba, cike da tausayawa Ummi ta ce "Sannu Yayan Fatima Allah ya sauwak'e, ka yi k'o'kari ma wallahi zaman da'ki babu dad'i ga namiji, zaman dak'i ai sai mata, Allah dai ya ta shi kafad'a yasa kaffara ne." Ya amsa da "Amin Ummi." Kayan tea Fatima ta jera a gaban shi da flask d'in ruwan zafi ta shiga had'a mi shi, kallon ta ya yi ya kalli Ummi ya ce "Ummi yau kuma tea zamu sha, babu kamun ne." Ta ce "A kwai naga baka da lafiya ne, kamar zaka fi son shayin shiyasa na bada kudi ta siyo buredi da sauran kayan hadin tunda shi kokon naga kayan fitsari ne." Yamutsa fuska ya yi alamar baiso ba, amma bai ce komai ba, sai kallon Fatima da ya yi ya ce "Sister ka d'an za ki hada shayin." Ganin yanayin shi yasa Ummi cewa "ko a dama maka kunun ne? Naga kamar baka son shayin." Baya son bata wahala , sai kawai ya ce "A'a Ummi ki barshi kawai zan sha." Kafin Ummi ta ce wani abu Aysha kanuwar Amira, ta yi sallama a tsakar gidan. A tare suka amsa mata, ummi ta ce "Aysha ke ce tafe." Ta ce "E ni ce, ina kwana ummi ya mai jiki. " "Alhmdllh da sauki." Juyawa ta yi bangaren Al'ameen shima ta gaishe shi tare da yi masa ya jiki, ya amsa da " Alhmdllh." Basket mai dan girma dauke da kuloli da flask ta fito da shi daga hijabinta, ta ajiye gaban Al'ameen tare da ce wa "Yaya Ameen wai gashi, in ji Anty Amira ta ce na kawo maka wai tana gaishe ka da jiki." Share Aysha ya yi kamar bai ji abinda ta ce ba, wani banbarakwai ya ke jin lamarin, amma yarinyar nan bata da hankali mai take tunanin Ummi da Maman Amira zasu zata idan suka ga haka. Ummi kam murmushi ta yi ta ce "Lallai an gaida Amira harda hidima haka ki ce mata Amintacce yana godiya." Fatima murmushi take yi a ranta tana lallai Anty Amira kin zurma da yawa Allah dai ya tabbatar da wannan lamarin. Sallama Aysha ta yi musu Ummi ta ce "Tsaya ki amshi tukwuici." Tana kwance habar zani da sauri Aysha ta yi hanyar waje ta na cewa "A'a Ummi wallahi ki barshi nagode." Yi ya yi kamar bai san an ajiye wani basket a gabansa ba, ya yi kicin kicin da rai, Ummi ta kalle shi, sai kawai ta yi murmushi, ta ce "Fatima bude abincin nan mu gani." Barin hada shayin ta matso ta fara cirowa kula guda biyu ne tuwo da miya, sai jug, babban kulan ta fara budewa kosai ne an yi shi manya manya jan suya gwanin sha'awa, ta bude karamin shi kuma farfesun kayan ciki ne a ciki da romo kadan sai turiri yake da kamshin kayan yaji jug din kuwa kunun tsamiya ne hadadde shima da zafin shi. Rike haba Ummi ta yi, ta ce "Umm! Lallai Amira, to angode Allah ya yi albarka." Kollonta ta kai kan shi ko kallon side din abincin bai yi ba, ta ce "Amintacce ga abin kari in ji Amira." Ya ce "Angode kuci kawai Ummi, Fatima mikomin shayin da kika hada."Ummi ta ce " Baza ayi haka ba Yayan Fatima, Binta dauko kofi da plate ki zubawa yayanki abinci." Mikewa tayi ta shiga kitchen ta dauko ta zo ta zuba mishi kunun da kosan zata zuba farfesun Ummi ta ce "Bar wannan Binta ya ci anjima." Ta amsa da "To ummi." Tare da mika mishi abincin gaban shi. Dakyar da takurar Ummi ya dauki kosai daya ya yi bismillah ya kai baki ya gutsira, babu laifi yaji dadin shi sosai bai san sanda ya tura guntun a baki ba, daga haka ya shiga ci yana kora kunun sai ga Mallam Aminu ya kar kunu da kosai tas. Ummi da ke mishi dariya a ranta ta ce "A kara ne?", yamutsa fuska ya yi ya ce "A'a Ummi Alhmdllh." Ummi da Fatima ne suka ci sauran ragowar kunu da kosan, farfesun kuwa Al'ameen aka ajiyewa da rana aka dumama mi shi ya sha. Makota na ta shigowa yi mi shi sannu da jiki baga mata da matasa tsararrakinsa ba har da dattijan unguwa, domin shi din mutumin mutane ne, yana da kirki da yawan gaisuwa, Maman Amira ma ta shigo haka kafatanin yan gidan gaba daya. ************* *JOY* Allah-Allah ta dinga yi gari ya waye ta je ta ga halin da Al'ameen ke ciki idan ba haka ba zuciyarta zata iya tarwatsewa, sai dai gaba daya Daren ranar ya mata nisa, dakyar ya iya jumirin jiran har bakwai da rabi ta yi. Duk da tarin ciwon kan da take fama da shi, hakan bai hanata tashi ba, cike da karfin hali ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando kanana as usual, sakkowa ta yi dining ko Mom bata jira ba ta yi breakfast din ta ita kadai duk da iya tea ne kawai ta iya sha. Dakin Mom ta nufa, ta tarar bata tashi ba, ji ta yi baza ta iya jira har sai lokacin da ta farka ba, hakan yasa ta zauna a bakin godon ta shiga dan bubbuga pillow, Mom ta bude idanu cike da barci ta kalleta, ganin yadda idanunta suke har zuwa yanzu a rine gashi sun kara kankancewa fiye da jiya, saboda kwanan da ta yi kuka yasa ta mikewa zaune cike da damuwa ta ce "Daughter, me yasame ki?" Ta kai hannu tana tattaba jikinta, rike hannunta ta yi ta ce "Babu komai Mom tun kukan jiya ne da na yi." "Amma Daughter ya kamata ace tunda kin yi barci kin farka idanunki su dawo daidai ba wai su kara rinewa ba." Shiru ta yi ta rasa me zata ce don kare kanta. "An ya kuwa lafiyar ki kalau, idan kina jin wani damuwa ki sanar min muje asibiti." Girgiza kai ta yi, ta ce "I'm ok" "Well!" Mom ta faa tana gyara kwanciya. Langwabe kai ta yi ta ce "Mom ina son zanje landmark bookshop na duba wani story book da nake nema, da ma wasu books din wadanda nake da su duk na gama karantasu." Tsare ta da idanu Mom ta yi na yan wasu sakannni tana nazartanta, Hankalinta bai kwanta mata da fitar ba, hakan yasa ta ce " Da sassafen nan haka? Ki barshi kawai ba sai kinje ba, ki fadi sunan book d'in zan saka a naimo miki." "Ok Mom Thank U." Ta fada tare da mikewa ta fice a dakin gudun kada kwallan daya ciki idanunta su zubo a gaban Mom. Sarai Mom ta ga yanayin da ta shiga hakan yasa ta kara gaskata zarginta akanta. Da gudu ta fada kan gadonta ta rushe da kuka, ya ya zata yi? Ina zata saka ranta ta ji sanyi? Wani hali Al'ameen yake ciki, shin kodai ya mutun ne da gaske kamar yadda ta gani a cikin mafarkinta, yin wannan tunanin yasakata mikewa zaune zumbur! Zuciyar ta ne ke Ingizata akan ta saci hanya ta tafi . Da sauri ta mike tsaye da nufin tafiyar , sai kuma tsoro ya kamata, idan asirinta ya Tonu Mom ta sani mai zai biyo baya, ta tuna sanda Mom ta juya mata baya lokacin da ta gane tana mu'ala da Fatima, ko kadan baza ta so su koma gidan jiya ba, don baza ta iya jura ba da wanne zata ji. Komowa ta yi dabass ta zauna a bakin bed ta ci gaba da kuka. Wani shawara ne ya fado ranta wanda ya sakata mikewa da sauri kamar an tsikareta, da sauri sauri gudu gudu ta dinga saukkowa stairs, tana fitowa direct boy quarters din gidan ta nufa, bangaren da wasu daga cikin ma'aikatan gidan suke kwana, a kofar dakin Peter ta tsaya ta shiga knocking, da sauri ya fito ko amsa gaisuwar da yake mata bata yi ba ta ce "Peter, ka taimakeni." Ta fada tana hade hannaye hawaye na bin kumatunta, rudewa Peter ya yi, cikin rawar bani ya ce "Miss me ki ke bukata kiyi hakuri ki daina kuka ko meye zan miki matsawar baifi karfina ba." Tunda ta fara zayyano ma shi bukatar ta na tana son ya je gidan su Fatima ya dubo mata wani hali Al'ameen ke ciki, ya ke bin ta da kallon tausayawa ji yake kamar ya zubar mata da kwallah wannan wacce irin jarabta ce, a raunace ya ce "ki yi hakuri Miss na miki alkawarin zan je na dubo miki shi, yanzu dana gama abinda nake yi." Haka suka rabu da Peter ta koma cikin gida tana jiran tsammani. Kamar yadda Peter ya yi mata Alkawari karfe goma sha daya a kofar gidan su Fatima ya mi shi, kasancewar gidan ana ta shiga da fice na masu zuwa gaisuwa bai sha wahala gurin sanin halin da Al'ameen ya ke ciki ba, shi kanshi ya tausayawa yaron da fargaban yadda zai sanarwa uwar dakinsa wannna bakin labarin ya koma gida, bai samu haduwa da ita ba a lokacin, sai wuraren karfe shiddan yamma suka hadu. Kallo daya ya mata ya sauke kai, gaba daya ta fice a hayyacinsa kamar ba Miss Joy daya sani ba, "I'm sorry Miss labarin babu dadin ji." Ya fada a sanyaye. Wani irin Kwalalo ido waje ta yi tare da safe kirji a razane ta ce "Ya mutu ko."............ 09116099486. [12/29, 2:42 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 27* Wani irin gwalalo idanu waje ta yi tare da dafe kirji a razane ta ce "Ya mutu ko?" Girgiza kai Peter ya yi ya amsa da "Bai mutu ba." "To mai ya same shi?" Ta fad'a cikin shirin fashewa da kuka, Shiru ya yi yana nazarin mai zai ce mata don ba k'aramin tausayin ta yake ji ba, baya so ya fad'a mata abin da zai tayar mata da hankali, muryarta ne ya katse mishi tunani "Na rok'e ka kada ka boye min komai Peter, sanin halin da yake ciki shine kwanciyar hankalina." Ba yadda zai yi hakan yasa ya yi k'asa da kai ya ce "Na samu labarin cewa sanadiyar kad'e shin da muka yi, ya samu targad'e a kafar shi ta hagu sannan......" Shesshekar kukanta ya saka shi dasa aya, da sauri ya dago yana kallon ta, dama yasan za'a rina, an saci zanin mahaukaciya. Cikin muryar rarrashi cike da girmamawa matsayinta na uwar dakinsa ya ce "I'm sorry Miss ki daina kuka zai samu sauk'i soon, naji labarin tun jiya an gyara kafar an d'aure." Cikin kuka ta ce "Saboda mai ka ke cewa kar na yi kuka, bayan nice sanadin raunatar shi? Me yasa bazan yi kuka ba? Kasan yadda na ke ji a zuciyata kuwa?" Ta fad'a tana ta6a saitin zuciyarta, kasa ya sake yi da kai, tare da cewa "I'm sorry Miss." Zuciyarsa gaba d'aya ta raunana, anya zarginsa bai zamo gaskiya ba kuwa? Ko dai uwar d'akinsa ta fad'a soyayya da wannan yaron ne, domin lamarin ya fi gaban tausayi kad'ai. Daurewa ya yi dago ya kalleta tare da jeho mata tambayar da ke kai kawo a ransa, "Miss Joy ar u in luv wit him?" Ya fad'a a d'arare. Tsittt! Kukan ta ya d'auke, ta zuba ma shi rinannun idanunta na yan sakanni, can kuma ta girgiza kai ta ce "Noooo! Babu wani abu makamancin haka a zuciyata game da shi, kuma kar ka sake yi min irin wannan tambayar." Daga haka kuma ta juya da sauri sauri gudu gudu ta bar gurin. Ajiyar zuciya ya sauke ya san ta fad'i son ran ta ne kawai amma shakka babu tana son yaron nan, shi daga ita har yaron tausayi suke ba shi, yasan wannan abu ne da ba zai ta6a yiwuwa ba ko a tastuniya balle a zahiri. Alice fa! jinin Alice da soyayya da musulmi tabbas akwai k'ura, shi dai zai saka su a addu'a shine k'adai taimakon da zai iya mu su. Ta d'auka sanin halin da yake ciki zai sama mata sauki a zuciya, amma ina! Babu wani sauki sai ma k'ara mata damuwa da tashin hankali da ya yi. kamar jiya daren ranar sai barci 6arawo ne ya sace ta bayan ta gama tsara yadda za ta yi gobe ta samu fita ta je ta gan shi ko a sace ne. ******** *AL'AMEEN* Kasancewar sa jarumi kuma sam ba shi da k'an jiki yasa nan da nan ya fara samun sauki, a Washegari rana ta uku da samun tsautsayin ya soma taka k'afarsa, tuni kumburin ya sa6e sai dan abin da baza a rasa ba. A ranar ma haka Amira ta sake had'o lafiyayyan karin kummalo ta aiko ma shi. Sam bai ji dad'i ba, a ganin shi ta cika zak'ewa, hakan yasa ya kuduri aniyar taka mata birki, yau kam bai ci abincin ba duk irin magiyar Ummi, ya fake da cewa shi ba cimarsa ba ne, shi kunun zai sha, kasancewar Ummi tasan hakan yasa bata tsaurara masa dole sai ya ci ba. Wainar shinkafa ce da miyar taushe yaji tantakwashi da man shanu, Ummi da Fatima ne kad'ai suka ci. Yau kam a d'aki ya yi zaman shi bai fito tsakar gida ba kasancewar akwai wutar nepa. Wuraren karfe goman rana Amira ta yi sallama tsakar gidan, direct cikin gida ta nufa don bata za ci yana d'aki ba, a kitchen ta samu Ummi, kamar kullum a mutunce ta gaisheta tare da tambayar mai jiki. Ummi ta amsa da "Mai jiki Alhmdllh yana samun sauki, sannu da hidima Allah ya saka da Alkhairi Allah ya yi Albarka." K'asa ta yi da kai tana d'an murmushi ta ce "Amin Ummi." D'aukar tsintsiya ta yi ta tattare hijabinta tana "Ummi bari na tattara gidan naga ba'a riga an share ba." Kallon ta Ummi ta yi ta ce "Kun gaisa da mai jikin ne?" Ta girgiza kai tare da cewa "A'a Ummi." Ummi ta ce "kije Ku gaisa yana d'akin shi." Ajiye tsintsiyar ta yi ta kama hanyar d'akin ,zuciyarta na dokawa da mugun gudu. A sanyaye ta yi sallama a bakin k'ofa. Ya amsa mata yana daga zaune a bakin katifarsa, duk a tunaninta zata tarar da Fatima a d'akin kamar ran nan sai dai ga mamakinta shi k'adai ne zaune a sanye da singlet da dogon wando, kallo daya ta yi masa ta yi saurin yin kasa da kai, take jikinta ya dauki rawa, kasa zama ta yi don gaba daya gani take ya cika dakin tsabar kwarjini. Shikam a tsanake yake kare mata kallo, Sam! Bata da makusa sai dai ita zuciya ba'ayi mata tilas. Ganin bata da niyyar yin magana gashi ta doje a bakin k'ofa ita ba ta koma ba ita ba ta k'arasa shigowa yasa ya yi gyaran murya. A diririce ta dago su ka had'a ido sai kawai ta zu6e gwiwowinta a k'asa a nan inda ta ke tsayen cikin dan rawar murya ta ce "Ina kwana Yaya Ameen ya karfin jiki." Maimakon ya amsa gaisuwarta sai ya cewa "Amm! Amira." Da sauri ta dago tare da amsawa da "Na'am." Ya ce "Na ga sa'kon ki nagode, sai dai ina rok'on ki daga yau kar ki sake wahalar da kanki wajen aiko min da wani abu ko yi min girki please bana buk'ata, wani irin tunani iyayenmu zasu yi idan suka ga haka, to dan Allah wannan ya zama na karshe, and maganar wasika shima daga yau na kashe please kar na sake gani bana so, sannan ina mai jan hankalinki da ki zama mace mai kamun kai domin mazan yanzu basu da tabbas wani zai iya yin amfani da wannan irin damar ya sabauta rayuwarki. Wani irin tafarfasa zuciyarta ya shiga yi, tun kafin ya dasa aya tuni hawaye sun gama wanke mata fuska. Meye laifinta don ta nuna masa soyayya, dama duk tsawon lokacin nan aikin banza take, Ashe kallon sakarya mara kamun kai yake mata, ji ta yi zuciyar ta ya dake duk wani tsoro da kwarjinin daya cika mata ido ya kau. Dagowa ta yi ta kalle shi, ta ce "Shin laifi ne don na nuna maka soyayya da kulawa, ka sani nima ba yin kaina bane kuma bani na daurawa kaina ba, don Allah na rokeka ka daina min kallon sakarya mara kamun ka wallahi ba haka na ke ba, sannan don Allah ka ta ya ni da addu'a Ubangijin daya sanya mini soyayyarka ya yaye min, na maka alkawarin daga yau bazan sake gwada maka wani abu makamancin soyayya ba, zan yi kokarina na taushi zuciyata, amma ka sani bazan daina sonka ba har karshen numfashina." Ta kai karshen maganar tare da fashewa da wani irin kuka wanda ya taso mata daga can k'asar zuciya, to she bakinta tayi da hijabinta saboda kar sautin kukanta ya fita har Ummi ta jiyo ta da sauri ta mike tare da ficewa daga dakin da gudu. Karo suka yi da Fatima a k'ofar d'akin, bata tsaya ba ta ra6a ta gefenta ta fice daga gidan. Kur!: ya kurawa hanyar da ta bi idanu, rana ta farko da wani abu mai kama da tausayi game da ita ya tsirgar ma shi a zuciya, me ya aikata kenan ya salam! Ya fad'a tare da dafe kai. ************ *JOY* Safa da marwa kawai take yi a d'akin ta ganin karfe ukun rana ya gota babu wata dama da ta samu na fita, babu irin tunaune da bata yi ba ciki har da da haura katanga, sai dai ta san ko cikin maye take bazata iya ketare katangar gidan ba. Cak ta tsaya lokacin da zuciyar ta ya hasko mata mafita "David." Ta fad'a a saman lab'b'anta, da sauri ta rarumi wayar ta, ta lallatsa tare da karawa a kunne. 🙈🙈🙈 kunya duk ta isheni na rasa da bakin da zan baku haƙuri ma yasin😬 😬😬 in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba🙏🙏🙏 Ku tayani da addu'a aljanun kiwar yin typing ne su ka kusa sauka a kaina😂😂😂 09116099486 [12/29, 2:43 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 28* "He'll who ix on d line" David ya fad'a bayan ya daga wayar, a sanyaye ta ce "David." Murmushi ya yi, sannan ya ce "So is u, ba gizo idanuna ke min ba dana ga call d'in ki a wayata." Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "David I need ur help." Wata irin shegiyar dariyar ya saki kafin ya ce "Big gal yau kuma a wajena ki ke naiman taimako? Any way ni d'an uwanki ne bazan 'ki taimaka miki ba, fad'i muji ko zan iya." Jim ta yi kafin ta ce "David fita nake son yi daga gida amma Mom ta hana ni." Ya ce "uhumm! To ni meye nawa a ciki? Me kike so na yi miki? Ko so ki ke yi zo na ce ma Mom dole ta barki fita, a beg obey ur mother." Kamar ta fashe da kuka tsabar takaici amma ta dake don mai nema baya fushi, ta ce "Ba haka nake nufi ba, so na ke kazo ka ce mata zamu fita tare zuwa wajen wani taro na school d'in mu nasan idan ta ji daga bakin ka zata barni." Shiru ya mata bai amsa ba, ganin haka yasa ta ce "please David ka taimake ni." Magiya ta dinga yi mai har da kuka. Ajiyar zuciya ya yi ya ce "To shikenan zan taimaka miki, amma a nawa?" Wani firin ciki ne ya ziyarceta jin ya ce zai taimaka mata, cike da jin dad'i ta shiga cewa "Thank u David, thank u very much."ganin kamar bata gane nufin shi ya yasa ya ce "Rike godiyar ki, ki fad'a min a nawa zan taimaka miki." "Ban gane ba?" Ta fad'a cikin rashin fahimta, "Ok ina nufin zaki biya ni ne ba a free zan taimaka miki ba." Ta ce "Ok nawa zan baka." Murmushin cin nasara ya saki, ya ce "Zaki bani 100k idan ya miki to, idan bai miki ba kuka shikenan." Ba tare da wani tunani ba tace "Na amince." Fiton murna ya saki ya ce "gud gal! Ki shirya gani nan zuwa." Daga haka ya katse kiran ya ta shi yana tsallen murna dama yana bukatar kudi abokinsa zai yi birthday ko babu komai ya samu na fita kunya tsuntsu daga sama gasasshe. A bangarenta ma hakan ne, don har ta fi shi farin cikin samun biyan bukata, sai dai bata da kuzarin yin tsalle-tsalle kamar shi. Zama ta yi bakin bed tana sauke ajiyar zuciya, finally yau zata gan shi, ji ta yi kaso goma cikin d'ari na nauyin da zuciyarta ya mata ya kau. Bayan 30 minute David ya iso tuni ta shirya cikin wani Straight gown 3 quarter yar kanti dark blue, ta gyare dogon gashinta da rabonki shi da cumb tun ranar da su ka yi accident, ta yi parking din shi a baya, mai kawai ta iya shafawa sai perfume, ba cin su ko lip gloss bata shafa ba. Direct dakin Mom David ya nufa, bayan sun gaisa ya ce "Mom Joy ta gama shiri kuwa?" Cikin rashin fahimta tace "Shirin me?" Ya ce "Na zuwa taron CRS official da zamu yi a school yau 4 to 6." Mom ta ce "Ai kuwa ta manta bata gaya min ba, dubo dakin ta ka kira min ita." Tana tsaye tsakar d'aki tana kiran tsammani ta jiyo knocking, da sauri ta bude , d'age mata gira ya yi ya ce "I hope kin shirya." Ta gyada kai ya ce "muje Mom na kira. Amma kafin nan in ji alert." Ta ce "Bani account number na yi maka transfer." Wayar ya karba ya saka mata, sai da ta yi mashi transfer 100k. Sannan su ka tafi dakin Mom. Kallon ta Mom ta yi ta ce "daughter dama kuna da irin wannan taro mai mahimmanci shine baki fad'a ba, yanzu da David bai biyi miki barka shikenan ko." "Sorry Mom wallahi Na manta ne." "Ok maza ki shirya ku tafi kar ku makara." "Ok Mom " ta fada tana mikewa, takalmi da wayarta kawai ta dauko a dakin ta ta dawo ta ta yi sallama da Mom suka fito. Waige-waige David ya fara yana naiman Peter, riko hannun shi ta yi ta ce "Da kafa zamu fita." D'age kafad'a ya yi alamar he don't care. Ba su sha wahalar fita ba, don kafin ma su iso Mom ta sanar wa security din ta. Suna dan yin nisa da gidan David ya kalle ta ya ce " To Miss yanzu sai ina." Ta ce "Gidan su Fatima Hussain." "Fatima Hussain!" Ya maimaita sunan cike da dimbin mamaki, juyowa ta yi ta kalle shi cikin ido ta ce "Yes ko kana da magana." Yadda ta tsare shi da manyan idanunta masu kwarjini yasa ya yi saurin d'age kafad'a tare da cewa "Nop! Zan je wani waje na dawo mu had'u a nan." Ta ce "OK ya yi." Gaba ya yi ya barta a tsaye har sai da taga k'ulewarsa. Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta kama tafiya. Cike da karsashi da shauk'in so dake d'ibarta ta dauki hanyar gidan, zuciyar ta na k'ara karfafa mata gwiwa. Sai dai ko da ta iso k'ofar gidan sai ta kasa shiga, tsayawa ta yi tana rarraba ido, sai lokacin wani tsoro da fargaba ya shigeta, ji take kamar ta juya ta runtuma da gudu, amma wani bangare na zuciyar ta na ingizata, kar fa ta shiga ya yi mata wani abin, cewar wani side na zuciyar ta, don warning din shi na ran nan har yau yana nan rad'am a kwakwalwarta. Ta fi karfin mintuna ashirin a haka tana karantar wasikar jaki, ita bata shiga ba ita bata wuce ba, kamar daga sama ta ga an bud'e k'ofar gidan, a daburce ta d'ago manyan idanunta da suke cike da tsoro ta kalli k'ofar don ganin mai fitowa. Al'ameen ne, ya lalla6a ya fito don ya sha iska , yana bude k'ofa ya ci karo da ita, rasa wani yanayi zuciyarsa ta shiga a lokacin da idanunsa suna sauka akan kyakkyawar fuskanta ya yi, farin ciki ne ko kuwa kewa ne oho, sai dai ko da wasa bai bari fuskarsa ta nuna ba, sai ma k'ara tamke ta da ya yi babu fara'a ko kadan, sannan ya zuba mata kaifaffun idanun shi. Numfashinta ne ya dauke na wucin gadi, lokacin da idanuwanta ya sark'e cikin na shi, baki ta ke son ta bud'e ta yi magana amma kamar wacce aka sakawa padlock. Sosai ya hango tsoratar da ta yi a cikin kwayar idanunta, yadda take rarraba idanu tana muymuy!! Da d'an bakinta ba bakaramin kyau ta yi mashi ba, tana d'aya daga cikin mutanen da ko wani irin yanayi suka shiga kyau ya ke musu. Jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa ya ce "You again? Ba nace miki kar na sake ganin k'afar ki a gidan nan ba, babu ke babu Fatima, ok baki jin magana ko?." Da sauri ta girgiza kai a raunace ya ce "Ba wajen Fatima nazo ba, wajen ka nazo." Had'e hannayenta ta yi take har ruwan hayawe sun cika mata idanu, ta ce "Na zo ne na sake baka hakuri akan abin da ya faru ran nan, ka yafe min for God sake, it all my fault." Ta k'arashe maganar tana kallon d'aurarren k'afar shi. Wani irin rauni gami da tsantar tausayinta ne suka shiga ratsa zuciyarsa, shiru ya yi yana kallonta, yana jin wani irin yanayi a zuciyarsa game da ita, kwatankwacin yadda yake ji a zuciyarsa game da tilon kanwarsa. Ganin bai amsata ba bai kuma daina binta da wani irin kallo mai kama da harara ba, yasa ruwan hawayen da take ta kokarin rike wa wanke mata fuska, ta san dama bazai kalleta da idon rahama ba, cikin muryar kuka ta ce "Nasan ni mai tarin laifuka ne a gare ka Yaya Alamein, zai yi wuya ka iya yafe min at once." Ta karsahe maganar cikin kuka da shessheka. Rintse idanu ya yi da karfi. Da tasan yadda kukanta ke tsisstinka jijiyoyin zuciyarsa da ko da wasa bata yi ba. Ita kam bata san abin da ke faruwa ba ganin yadda ya rintse idanu, yasa ta k'ara sautin kukanta wanda kukan da biyu ne, harda na yadda soyayya ke nukurkusarta. "Stop!!!" Ya fad'a a tsawace jin tana shirin tarwatsa masa kwakwalwa. Ta sauri ta had'iye kukanta, tana zare idanu, still hawaye bai bar zubo mata ba, kasa ya yi da murya ya ce "Is ok, na hakura ki dai na kuka, kinji." Yadda ya yi maganar a sanyaye cikin shigar rarrashi yasa ta yin shiru ta na kallon shi. Hannu ya saka aaljihunsa ya dauko farin handkerchief ya mik'a mata ya ce "Oya wipe ur tears." Wannan karon kasa ignoring ta yi duk da wannan time babu sassanyar murmushi nan a fuskarshi kamar wancen karon, sai ma sa6anin hakan. A hankali ta miƙa hannunta dake d'an karkarwa ta kar6a, sai kuma ta kasa goge hawayen ta rik'e hankin a hannun tana kallon shi, gyada mata kai ya yi ya ce "uhumm!. a hankali cike da shauki ta kai handkerchief d'in fuskarta, wani irin sassanyar kamshine ya ziyarci hancinta, a ta ke ta lumshe idanu tare da k'amk'ame handkerchief d'in gam ta na shakar shi. Duk abinda ta ke yi idanunsa na nan k'em akanta. Minti biyu ta kwashe a haka, kafin ta bud'e idanunta tare da sauke handkerchief d'in a fuskarta ta mik'a ma shi, had'i da cewa"Thank u." Bai san sanda sassanyar murmushi ya ku6uce masa ba, mi'ka hannu ya yi kar6a hankin ya mayar aljihu tare da "gud gal! Don't cry again kin ji" A sanyaye ta gyada kai tare da cewa "Ni zan wuce ina rok'on ka ka mika min gaisuwa wajen Fatima ka gaya mata ina kaunarta kuma ina tsananin kewarta." Tana fad'in haka ta juya ta kama tafiya. Gaba d'aya lakkan jikinsa sun mutu, so yake ya bud'e baki ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta amma kamar last time ya kasa kiran sunan, sai a zuciya yake ta maimaita Kalmar JOY. FARHAT ya fad'a akan la66ansa, tabbas d meaning of d word Joy in Arabic is FARHAT. Sai ya tsinci bakinsa da furta FARHAT da 'karfi, cak ta tsaya duk ta san ba ita yake 'kira ba, amma haka kawai ta ji k'iran ya ratsa har cikin kwakwalwarta. Ganin ta tsaya yasa ga sake furta FARHAT, a karo na biyu, dis time juyowa ta yi, don jikinta ya gama bata da ita yake, daga Inda take tsaye ta nuna kirjinta da hannu ta mashi alamar ita yake kira, kai ya gyada mata tare da cewa "Yes u FARHAT." FARHAT ta maimaita sunan a zuciyar ta, tana tsaye a in da take bata motsaba, ganin kamar bata da niyyar zuwa yasa shi fara d'ingisa a hankali yana nufarta, ganin haka yasa ta saurin takowa itama ta nufo shi, a gaban shi ta tsaya ta zuba mishi ido tana jiran ji daga gare shi. Ya kalleta ya sakar mata murmushin da ke shagaltar da ita, ya ce "Kin nemi yafiyata na yafe miki amma ni har yanzu baki ce kin yake min ba akan abin da na miki ran nan." Shiru ta yi tana son gano akan me yake magana, ganin kamar ta manta yasa a hankali ya kai hannun shi goshinta daidai inda ta k'uje ran nan ya ce "For dis." Sai lokacin ta gane me yake nufi, Karo na farko ta saki murmushi har fararen jerarrun hakwaranta suka bayyana. "Masha Allah, tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta." Ya fada a zuciyarsa, muryarta ne ya katse mai tunani cikin sanyi ta ce "Baka yi min komai ba Yaya Alamein, idan ma kayi min ni ban 'rike ka rai ba, I know it fault, duk wanda aka yi wa kanwar shi abinda Mom ta yi wa Fatima in dai yana da hankali zai iya daukar matakin da yafi wanda ka dauka, ka ce wa Fatima ta yi hakuri, kaima kayi hakuri." kallon ta kawai take yi cike da birgewa har ta dasa aya. Ta matukar birge shi kalamanta da hikimarta sak irin na Fatimarsa sai yake ganin kamar ma ita ce tabbas maganar Ummi gaskiya ne a cikin tarayyarasu akwai wani sirri wanda Allab daya haɗasu ya barwa kansa sani. A tausashe ya ce "Kina son ganin Fatima?" Bata iya bashi amsa ba sai gyada kai da ta yi da sauri, ya ce "Oya muje na kai ki wajenta." "Da gaske!" ta furta cikin wani irin farin ciki tare da zaro ido............ Harda na gobe🙈🙈🙈 09116099486 [12/29, 2:43 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 29* Murmushi ya yi tare da gyad'a mata mata kai alamar da gaske ya ke yi. "Oh my god!!! I'm so happy." Ta fad'a cike da mad'aukakin farin ciki, fuskarta dauke da yalwataccen murmushi. Kallon juna suke yi kowanne zuciyarsa fari 'kal, shima murmushin yake ganin yadda ya wanzar mata da farin ciki, cikin sigar zaulaya ya ce "Miss smiller! Wannan murnar duk na ganin Fatima ne?" Da sauri ta gyada kai, ya girgiza kai tare da ce wa"To Oya let's go to her." A hankali ya juya ya fara tafiya yana d'ingisa k'afarsa. Tsayawa ta yi tana karewa bayan shi kallo, ta na zayyana irin kyawun surar shi a ranta, sai da ta ga yana daf da shigewa zaure sannan ta bi bayan shi da sauri. Sallama ya yi a tsakar gidan, kusan a tare Fatima da Ummi suka amsa, Ummi na daga d'aki Fatima kuma na kitchen. Da sauri ta mik'e ta fito tana ce wa "Yayana har ka daw......" Sauran zancen ne ya mak'ale lokacin da idanunta suka yi arba da Joy tsaye a bayan Yayanta, cikin rawar murya ta ce "My Joyyyy!" Joy da tuni ta fara takowa wajenta ta ce "My Teetee!" Da gudu Fatima ta k'arasa gareta suka rungume juna, fashewa da kuka Fatima ta yi tana ce wa "My Joy ke ce da gaske ba mafarki nake yi ba kamar yadda na saba, mai yasa baki zo naima na ba, kika bar ni da tarin kewar ki." Joy da tuni itama hawaye ya wanke mata fuska, at d same time kuma tana murmushi, ta ce "I'm sorry My Teetee, ki yafe min, nima na yi kewar Fatima, I missed u my friend, I badly missed u." Tsabar farin ciki bata iya amsa mata ba, sai zame jikinta ta yi a nata da sauri ta isa wajen Al'ameen dake tsaye yana kallonsu, yana murmushi ta fad'a jikin shi ta rungume shi gam ta kwantar da kanta a kirjin shi, cikin shessheka take ce wa "Nagode Yayana, nagode nagode daka dawo min da walwata da farin cikina, yadda ka faranta min Allah ya faranta maka Yayana." Tsam! Ya saka hannu ya zagayeta, yana bubbuga bayanta, gaba d'aya zuciyarsa ta karye ji yake kamar tana melting, tausayin rayan gaba d'aya ya cika shi, ba dadan shi din jarumin namiji ba ne , da babu abin da zai hana ya zubar da hawaye. Tsayawa Joy ta yi tana kallonsu cike da sha'awa tana murmushi still hawaye na zubar mata. Daga bayanta taji an dafa kafad'arta, da sauri ta waiga, ganin Ummi yasa ta saurin fad'awa jikinta ta 'kamk'ameta. Ummi kam kasa jurewa ta yi sai da ta dauke kwallah a fakaice, murmushi farin ciki kwance a fuskarta, ta shiga shafa kanta alamar rarrashi. Dakyar Al'ameen ya raba Fatima da jikinsa, handkerchief d'in sa yasa ya shiga share mata hawaye, lokaci 'daya kuma yana ce mata cikin rad'a da rarrashi, "Ya isa haka k'anwata, ki yi shiru ko kuma na ce ma FARHAT ta wu ce abinta tunda ba ki son ganinta." Da sauri ta mak'e kafad'a tare da ce wa "inyiiiin!" Cikin sigar shgwa6a ya ce "Oya go to her." Ya k'arashe maganar tare da rik'e hannunta ya soma tafiya, gaban Joy da Ummi suka tsaya, a hankali ya ce "FARHAT!" D'agowa ta yi daga jikin Ummi ta kalle shi, murmushi ya sakar mata, tare da kamo hannunta ya had'a da na Fatima. A hankali ya saki hannayen ya juya ya bar tsakar gidan, Ummi ta kalli Fatima data kamkame hannun Joy gam kamar za'a kwace mata ita, ta ce "Yau kuka da mafarke mafarke da surutan cikin barci ya kare ko?" Zafo ido ta yi ta ce "Laaaa! Ummi ni?" Ummi ta ce "Ke fa, kusan kullum sai kin yi sambatun kiran sunan Joy cikin barci." Duk dariyar farin ciki suka saka, Fatima ta ja hannun Joy ta na ce wa "Friend mu je d'aki ki bani labarin school da bayan rabuwa." Joy ta amsa da "Sai dai na baki labarin irin yadda na yi missed d'in ki." D'akin Ummi suka shige basu tsaya a falo ba har bedroom Fatima ta ja ta. Ganin shigewar su yasa Ummi girgiza kai, lamarin Al'ameen sai shi, ta fad'a a ranta, d'akin shi ta nufa don tana son jin yadda aka yi ya had'u da Joy har ya kawo ta cikin gidan yau dan kan shi. A d'aki kam, hira ce ta 6arke tsakanin kawayen biyu. Bayan sun gama musu kowa na fad'in shi yafi missed d'in dan uwan shi, Fatima ta ce "Ya aka yi Ki ka had'u da yayana, ni farin ciki ma ya hana ni wannan tunanin sai yanzu." Ajiyar zuciya Joy ta sauke ta ce "Friend labarin da tsayi amma bari na takaita miki." Tiryan tiryan ta shiga bata labarin abin da ya faru da ita tun daga ranar da Fatima ta je gidan su, wasikar data aiko mata da replay din data bata zuwanta gidan haduwar ta da Al'ameen da abinda ya wakana, hatta bige shin da suka yi bata boye mata ba, zuwa yadda aka yi ta samu fitowa, sai dai koda wasa ta kasa fad'a mata yadda soyayar Al'ameen ya mata kamun kazar kuku. Mamaki gami da dum6in Al'ajabi ne ya cika Fatima jin wai motar Joy ce ta kad'e Al'ameen, lallai Yaya Ameen yana da kyakyawar zuciya ko da wasa bai fad'a musu cewa itace ta kad'e shi ba, kuma harga Allah bai rike ta a zuciya ba, don ko yan dubiya ne suka zo irin masu kumbar bakan nan idan suna tsinewa wanda ya bige shi yakan ce su bari babu komai shi ya yafe, kuma suma ba da gangan suka yi ba. Ranar Fatima da Joy kamar karsu rabu. Dakyar ta yadda Fatima ta rakata ganin karfe shidda ya gota,Fatima kuwa tsoron Mom ya riga ya gama cika ta, shi yasa ta dinga kora Joy akan ta tafi amma ba wai don ta gaji da ganinta ba, ita bata ki Joy ta dawo gidan su da zama ba su dinga kwana suna ta shi tare, Ummi na yi musu dariya suka ta fi, ta ce "Teetee mu je na k'ara gaisar da Yaya Alamein, ba tare da tunani kamaj ba Fatima ta ce "Ok muje." A kofar d'akin Fatima ta yi sallama, shiru babu amsa, hakan ya sa ta lek'a wayam baya ciki, dagowa ta yi ta kalli Joy ta ce "Ya fito." Kwa6e fuska ta yi ta ce "Ina ya je." Dariya Fatima ta yi ta rik'e ha6a tare da cewa "Iyeeee, wannan sabon salon fa." Sai lokacin ta fahimci mai ta yi, Itama dariyar ta yi ta ce, "Ina son ganin dat his cute face kafin na tafi.Teetee mu jira ya dawo sai na tafi." Zaro ido Fatima ta yi kafin ya ce wani abu sai gashi yana shigowa, fatima ta ce "Yawwa Yaya zo kaji." Da sauri joy ta kai hannu ta rufe mata baki, tana zare ido, bata yi zaton yana kusa ba, jingina ya yi da bango ya yi folding hannayesa a kirji ya ce "Menene sister gayamin, gulma na FARHAT ta yi ko." Girgiza kai Fatima ta yi, ya ce "To menene." Kallon Joy ta yi tana dariya da sauri ta girgiza mata kai, sai kawai ta ce "Yaya babu komai." D'age kafada ya yi ya ce "Ku kuka sani Ku bani hanya na shiga dakina." Kaucewa suka yi ya shige bayan sun yi sallama da Joy. Har inda suka yi da David zasu hadu Fatima ta rakata, a wurin suka tarar da shi shima isowar shi kenan, kallo Fatima ya yi yana murmushi ya ce "Fatima my classmate." Harara ta watsa mashij, ya kyalkyale da dariya ya ce "Yau ina cikin farin ciki don haka bazan kulaki ba, amma zamu jone, muje Joy time ya wuce sosai." Ya karashe maganar yana kallon agogon dake daure a hannun shi........... 09116099486. [12/29, 2:44 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 30* Ga link domin shiga group na Littafin *JOY* kai tsaye. https://chat.whatsapp.com/EhPtIfeNaTtCC2GS6SvOnW Tun daga wannan ranar k'awancen Fatima da Joy ya dawo d'anye sharrr!shak'uwa da soyayya da sukewa juna ya sake nunkuwa, abin har mamaki ya ke ba Al'ameen sai ka ce wasu tagwayen da su ka fito mahaifa d'aya. Kusan kullum sai Joy ta zo gidan su Fatima daga school ba tare sanin Mom ba, yanzu bata da wata matsala ko shamaki da yin hakan, dama can David ne matsalar kuma yanzu ta yi maganin shi ta hanyar sakar mishi kud'i, tunda ta fahimci halin shi, sai ta ci maganin zama da shi. Daga ita har Fatima yanzu hankalinsu a kwance ya ke sai walwalarsu suke kamar basu da sauran damuwa. A halin yanzu zaman Fatima a gida shi ya fi tayar musu da hankali, kullum cikin zulumin school d'in da Al'ameen zai kaita su ke yi. Joy har ta fi Fatima shiga damuwa da tashin hankali a kan hakan, zama suka yi suka yanke shawarar zasu same shi su bashi hakuri a kan ya barta ta ci gaba da zuwa tsohon school d'inta kar ya canja mata. Har daki suka same shi, karo na farko da Joy ta fara shiga d'akin shi, sosai ta yaba da kyawun d'akin duk da ba wasu abin azo a gani ne a ciki ba, yar katifarsa ce, sai karamin wardrobe na kayan shi, sai yar duruwar da yake zuba littafai, sai hanga dake sama ta bangon gabas d'in dakin,sai ko dan tarkacen da baza'a rasa ba, iyakarsu kenan sai dai ko ina tsab kamar ba d'akin namiji ba sai daddad'an kamshin room freshener ke tashi. Yana daga kishingide cikin damuwa, ya yi nisa cikin duniyar tunani, suka yi sallama sanye yake da singlet da short kasancewar a kwai zafi a garin ga babu wutar nefa, ga dai hadari d'ankare a sararin samniya, amma kuma rana ake kwallarawa kasancewar daminar na gaf da wucewa, ganin su yasa ya yi sauri ya ja bargon dake kan katifarsa ya rufe daga kwankwasosa zuwa k'asa, ya ta shi ya zauna da kyau fuskarsa babu walwala saboda yanayin damuwar da ya kwana ciki. Bakin katifarsa Fatima ta laluba ta zauna, Joy kuma ta zauna daga gefenta a k'asa, kallo d'aya ta mishi ta d'auke kai ganin shi sanye da singlet gaba d'aya surar mazantakarsa a bayyane ga wani kwantaccen bakin bashi luf a kirjinsa, duk sai ta ji wani iri a jikinta, hakan yasa har suka gama gaisawa bata iya d'ago kai ta sake yi masa kallo na biyu ba, sai da ta tsinci muryar Fatima na cewa; Yayana dama Joy ce ta ce na rakota tana son yin magana da kai. A zabure ta dago jin kullin sharin da Fatima ta mata, dai-dai lokacin ya mai da kaifaffun idanunsa kanta, carat idanuwansu ya sark'e da na juna, da wani irin sauri ta kawar da kai don ji ta yi gabanta ya yi wani irin fad'uwa, zuciyar ta kamar zata faso kirji ta fito, Fatima ta zungura da itama tsabar kwarjinin shi yasa ta kasa fadar bukatarsu kai tsaye. Dagowa Fatima ta yi ta kalleta, Suna hada ido ta watsa mata harara tare da yi mata kallon ya zaki mini haka, alamar ki fad'a ma shi, Fatima ta mata da ido, ta sake watsa mata harara tare da make kafad'a ta mata alamar ke ki fad'a. Duk abin da suke yana kallonsu, ganin suna neman 6ata masa lokaci yasa ya yi gyaran muryar duk d'ogowa suka yi suna kallon shi, idanunsa a kan Joy ya ce "Uhummm! FARHAT ina jin ki." Cikin inda-inda ta ce "Daa da dama! Mun zo ne, mu rok'e ka a kan ka yi hakuri kabar Fatima ta ci gaba da zuwa school, kar ka canja mata wani' ko Fatima ai haka ne ko?" Ta fada tana kallon Fatima da sauri Fatima ta girgiza kai ta ce "E, e, Yaya haka ne don Allah ka yi hakuri ka bar ni na ci gaba da zuwa can d'in." Duk da yanayin damuwar da yake ciki sai da suka so ba shi dariya; ji yadda suke abu kamar uban wani ya turosu, ba su suka gama tsara abinsu ba, ji adanun Fatima kamar wacce ta yi wa sarki k'arya, ita kuma kawar cin mushenta ji nata kwala-kwala kwalan idanun kamar fitulun mota. A zuciyarsa yake musu wannan tsiyar, dakewa ya yi ya ce, to shikenan na ji kuje sai na yi shawara, har suna had'a baki wurin cewa "To Yaya mun gode." Suna fitowa "ta zubawa Fatima dundu ta ce " Haka muka yi dake Teetee." Dariya Fatima ta saka ta ce, "To ni kasa fad'a na yi yasin kwarjini ya min." "To kema kenan ina ga ni, amma sai naga kamar bai dauki maganar mu da mahimmanci ba." Fatima ta ce "Wallahi kuwa, tunda kika ji ya ce haka, amma nasan abin da zamu yi da Ummi zamu hada shi nasan idan ta saka baki idan da yuwuwar ya bar ni zai bar ni." Da kyar Ummi ta amince musu zata mishi magana, sai da suka yi ta magiya da bambaki! A ranar kuwa daya dawo da dare ta tuntu6e shi da zance, kallon Fatima ya yi da ta yi saurin yin k'asa da kai ya jefe mata kallon tuhuma, Ummi ta ce "Amintacce kai na ke sauraro, idan da yuwuwar hakan don Allah ka barta ta koma can d'in su k'arata tunda sun kusa kammalawa." Jim ya d'an yi kafin ya ce "To Ummi shikenan, ta shirya zuwa Monday sai na rakata da kai na Allah yawa hakan shi ya fi alkhairi ya kad'e fitina." Ummi ta amsa da "Amin ya Allah." Fatima kam washe baki ta yi tana dariyar farin ciki, Al'ameen ya jefa mata hararar wasa, sake kyalkyalewa ta yi da dariya tare da cewa; Thank u Yayana Allah ya faranta maka kai ma." A tare suka amsa da Amin shi da Ummi. Ummi ta ce "Wai ni kam Yaran nan ko kun ji mini motsin Amiratuwana, yau idan ban yi karya ba kusan kwanan ta goma rabonta da gidan nan, Allah yasa dai lafiya." Fatima ce ta dago da sauri tare da cewa "Yawwa Ummi tun ranar Asabar a hadda Aysha ta ce min bata da lafiya wallahi na manta na gaya miki kwata kwata na sha'afa." Tafa hannanye Ummi ta shiga yi tare da sakin salati. "Haba Fatima, yanzu tun ranar Asabar aka gaya miki amira babu lafiya amma ki ce wai kin manta, Haba haba Fatima amana bai ce haka ba, Amira ai ta wuce haka a gareki, don komin lalacewar giwa ta fi karfin kwandon goro, wato yanzu kin samu Joy shikenan kin rabu da kowa ko? Gaskiya banji dadi ba baki Kyauta min ba, ai hausawa sun ce ka gaida mai gaisheka ko ba zai amsa ba." Haka Ummi ta yi ta mita tare da yi wa Fatima fad'a, can kuma ta ce "Amintacce duba min karfe nawa idan dare bai yi nisa ba yanzu zan shiga na dubo ta yarinyar kirki, ai ko iyayenta ma sai su zageni ba don Allah yasa mutanen arziki ba ne." Shikam Al'ameen shaf ya manta da batun wata Amira, zai iya cewa tun daga ranar da wannan maganar ya shiga tsakanin su bai kuma saka ta a ido ba, agogon ya duba kamar yadda Ummi ta umarta jin tana ta sake tambayar shi karfe nawa ya ce "Ummi goma da rabi ta gota nasan yanzu sun kulle kofar gida ki bari da safe." Badan ta so ba dole ta hakura, amma fa ranar Fatima taga fushin Ummi, itama duk ta yi laushi jikinta ya yi sanyi tabbas bata Kyauta ba, gaba daya cikin yan kwanakin nan Joy ta d'auke mata hankali ita ce kadai a rai da zuciyarta. ************ *AMIRA* Tun daga ranar da Al'ameen ya nuna baya da ra'ayinta ta shiga matsanancin damuwa, a ranar ta yi kuka kamar baza ta daina ba, har sai da ta kwanta zazza6i na kwana uku, tun da ta tashi daga wannan zazza6in gaba d'aya ta canza, a hankali aka fara rasa gane kanta, bata da aiki sai kuka sai tunani, kurmar karfi da yaji ta naimi komawa, don tana iya wayar gari ta wuni ta kwana ba tare da ta cewa kowa uffan ba, lamarin da ya fara d'aga hankalin ahlinta, wa'ec d'in da suka fara bada ita aka kark'are ba, sosai Maman Amira ta shiga damuwa duk a tunaninta iskokai ne suka shigeta, hakan yasa kullum cikin tofa mata addu'o'i take da amso mata taimako a wurin malamai, amma a banza lamarin sai dad'a gaba ya ke yi, wani irin rama da mugun haske ta yi cikin abin da bai fi wata guda ba, kusan sau uku suna zuwa asibiti ganin likita maganar daya ce kullum; damuwa ce ke damunta." tambayar duniyar nan ta k'i fad'awa kowa damuwar, sai dai ta ce ita babu wani damuwar da ke damunta, har kuka mahaifiyarta ta yi mata ta yi magiyar ta yi nasihar ta yi fad'an akan ta gaya mata matsalarta amma a banza, hakan yasa Maman ta k'ara gaskata zarginta na cewa; Iskokai ne suka shigeta. Da farar safiya Ummi ta yi wa gidan su Amira dirar mikiya, lokacin ko Al'ameen bai dawo daga masallaci ba, wasu masallatan ma ba'a idar da sallah ba, itama tana sallame nata ko tasbihi bata yi ba ta tashi, don jiya dakyar ta yi barci saboda damuwa da tunanin halin da Amiranta ke ciki, yarinyar kirki, babban abin da ya k'ara d'aga mata hankali bai wu ce mummunar mafarkin da ta yi a kan ciwon Amiran ba, kwarai ta tsorata da lamarin, don ita kanta tana tsoron mafarke mafarken da take yawan yi a cikin yan kwanakin nan. Tsakar gidan babu kowa, duk su na d'aki, a k'ofar d'akin Maman Amira ta yi sallama, Aysha ce ta fito tana amsawa, ganin Ummi yasa ta yi saurin risinawa ta gaisheta, ummi ta ce "Ina gajiya Aysha ya mai jiki." "Alhmdllh Ummi tana samun sauk'i." Kafin Ummi ta ce wani abu Maman amira ta fito daga d'akin sanye da hijabi hannunta r'ike da carbi, murmushi ta sakar wa Ummi tare da cewa "Maraba da Ummi ke ce da farar safiyar nan, ina kwananmu ya kwanan iyalai." Ummi ta ce "Ni ce Maman Amira, ya mai jiki, wallahi ban ji sai jiya da dare, da nake cewa yara nikam kwana biyu banga Amira ba, shine Fatima ke ce min wai bata da lafiya, wallahi hankalina ya ta shi, ba dadon dare ya yi ba da a daren zan shigo na duba ta, a addafe na yi barci jiya wallahi." Ta karashe maganar cike da alhini da tausayawa. Maman Amira ta yi murmushin karfin hali ta ce "Allah sarki Ummi Kiyi hakuri wallahi nima harda laifi na da ban aika miki ba lamarin ne da rikitarwa." Ta fad'a damuwa bayyana k'arara a fuskarta ta, hakan ya k'ara daga hankalin Ummi, "Ki shigo daga ciki gata nan." Maman Amira ta fad'a tana juyawa cikin d'akin da sauri tare da d'auke dan guntun hawayen da ya zubo mata ba tare da ta bari Ummi ta gani ba. Salati da sallallami Ummi ta saka a lokacin da ta yi arba da Amira kwance a kan gadon Mama tana barci, wanda sai gabanin asubahin nan ya dauketa cewar Mama "Na shiga uku ni Balkisu! Mai zan gani haka." Sai kuma ta fashe da kuka tana maimaita kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, allahumma ajirni fi musabati wa aklifni khairan minha!" Ganin tana neman fad'uwa yasa Mama saurin rikota tare da zaunar da ita a bakin gadon. Kuka Ummi ta yi sosai, Mama na rarrashinta cikin karfin hali da danne zuciya, bayan ta tsagaita ta dago ta kalli Mama tare da cewa "Hafsatu mai ke damunta haka?" Take Mama ta kwashe komai ta gaya mata ba tare da tare da rage ta da komai ba, itama dai aljanan ta fi baiwa karfi, don ko kusa babu wanda zai kawo wani tunani makamancin soyayya a cikin lamarin. Addu'a Ummi ta sauna ta dinga tofa mata har wuraren bakwai na safe, har zuwa time din bata farka ba, sallama Ummi ta musu a kan zata je gida ta dawo.......... Dan Allah Ku yi hakuri da jina shiru kwana biyu Mamana ce bata ji dadi ba, bana samun zama bare nayi typing dan Allah Ku sakata a addu'a. Ku ci gaba da hakuri da ni littafin Joy yanzu ya fara dadi, Ku dai Ku ci gaba da bibiya. Yan group d'ina *Joy Novel Fans* ina Godiya da addu'o'inku ga Mamana Allah ya amsa, Allah ya sake muku da alkhairi ina matukar Alfahari da ku. Kar a manta da comment and share pls🙏🙏🙏🙏🙏🙏 09116099486. [12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 31* No editing🙏 Ko da Ummi ta shiga gida da Al'ameen ta fara cin karo a tsakar gidan yana wanki, a kid'ime ta fara labarta masa rashin lafiyar Amira, ta k'are da, cewa; Wallahi Amintacce na tsorata da ganin yarinyar nan, hankalina ya tashi, da da k'arar kwana da sai dai na ji mutuwar ta." Ta kai karshen maganar tana matsar kwalla, sosai ya kid'ime da ganin hawaye na kwaranya a idanun ta. Ummi jaruma ce, abin da zai sakata zubar da hawaye haka lallai ya kai abin tausayi, rik'e hannunta ya yi ya kai ta falonta ya zaunar da ita, ya shiga bata baki a kan ta yi hakuri ta yi shiru cuta ba mutuwa ba ne, ta ce "Yayan Fatima dole na koka, kar kaso kaga Amira." Rarrashinta ya ci gaba da yi, har ya samu ta yi shiru, Fatima kam jikinta ne ya yi sanyi tun lokacin da ta ji Ummi na labartawa Yayanta halin da Amira ke ciki, hakan yasa ta lafe a kitchen ta kasa fitowa. Ranar yini Ummi ta yi zirga-zirga tsakanin gidanta da gidan Maman Amira, babu irin tambayar da Ummi bata mata ba a kan damuwarta amma kamar yadda ta saba ta k'i fad'a, da Ummi ta dame ta da tambaya, sai kawai ta fad'a jikinta ta rungumeta ta fashe da kuka, hakan ya k'ara sanyayar ma Ummi da gwiwa kwarai. Fatima ma ta shiga ta duba ta, sai da ta yi kwalla itama. Kamar yadda Al'ameen ya yi alkawarin ranar Monday zai kai Fatima makaranta hakan ko aka yi, ranar ita da aminiyarta sun yi farin ciki kamar babu gobe, dan kar Mom ta sani yasa Joy ta laftawa David kud'i, ai kam ji kake tsit! Mallam ya ci shirya. A bangaren ciwon Al'ameen, babu abin da ya canza, sai ma sake ta6ar6arewa da lamarin ya yi, kusan kullum a cikin damuwa ya ke, sai dai koda wasa bai bari Ummi da Fatima sun fahimta ba , don baya son abin da zai d'aga musu hankali, haka ya ci gaba da shan overdose d'in maganin shi, don a halin yanzu ba shi da wata mafitar data fi wannan, abin da ya fi d'aga hankalinsa a yanzu bai wuce yadda, ciwon ke yawan tayar mishi a kowani irin lokaci ba, babu dare babu rana babu safiya, hakan na nufin ya kai stage 5 kenan a jikinsa, hakan yasa ko ina zai ce maganinsa na tare da shi saboda tsaro. Sau biyu Ummi na kama shi yana kokarin shan maganin, hakan ya firgita shi, sai dai ya yi mamakin yadda bata tambaye shi na menene ba, itakam har ga Allah bata kawo komai a ranta ba don ta yadda da tarbiyar da ta yi ma shi d'ari bisa d'ari. Ana cikin wannan halin Aliyu ya dawo, A ranar ya kira Al'ameen ya sanar mi shi da shigowar shi Niger, kuma a ranar yana ajiye jaka a gidan ya yi wanka ya yi wa gidan su Al'ameen tsinke, don lamarin shi ya tsaya ma shi a rai a kulli yaumin da tunanin shi yake kwana yake tashi. Da yammaci ne misalin karfe biyar da rabi, Aliyu ya iso unguwar Abayi, bai tsaya an yi mai iso ba, ya yi sallama ya shiga don yana son gaisawa da Ummi, babu kowa a tsakar gidan Fatima na islamiyya, Ummi na d'aki. Sake rafka sallama ya yi, daga cikin daki Ummi ta amsa mashi, tare da mikewa ta fito tana cewa; Muryar wa nake ji haka kamar Ali gadanga." Ta karashe maganar tana rike ha6a lokacin data yi arba da shi, risinawa ya yi yana murmushi ya yi ya ce "E Ummi ni ne, Ina wuni." Cike da fara'a ta ce "ina gajiya Aliyu muatanen kano saukar yaushe?." Ba tare da ya mike ba ya amsa da "D'azu Ummi." Ta ce "Masha Allah shine barka zauna ka huta ba ka kamo hanya, to ya ka bari yan cen, fatan an iske mutanen gida lafiya." "Lafiya kalau Ummi duk suna gaishe ki." "To madallah! Ina amsawa, ina yawan samun sak’on gaisuwarka wajen Yayan Fatima, har ya ce zai had’a mu a waya Allah ba nufa ba." Ya ce “Allah sarki! Haka ne dama komai sai Allah ya so” "mik’e Aliyu ga kujera ka zauna, d’aki zafi sun dauke wutar su." Ta karashe maganar tana nuna mashi kujera y’ar tsuguno. Zama ya yi, itama ta d’auko tabarma ta shimfid’a ta zauna tana cewa; ga shi Fatima bata dawo makaranta ba da tsoro maka ruwan sanyi amma nasan tana hanya.” murmushi ya yi ya ce " Ba komai Ummi yanzu ma masha ruwa kafin na shigo." Hira suka shiga yi da Ummi cikin sakin jiki da sabo, da alamar a kwai shakuwa a tsakanin tun ba yanzu na, kusan rabin hirar ta Amira ce, Ummi ke mashi, duk da baisan yarinyar ba ya tausaya mata sosai, ya yi mata addu'a da fatan samun sauk'i. Fatima ce ta yi sallama ta shigo ganin Aliyu yasa ta sakin fara'a ta ce "Laaa! Yaya Aliyu Kaine a gidan namu yau." Murmushi ya saki a ransa yana mamakin girmanta ya ce " Ni ne Zahra, kin dawo ya makaranta?" "Alhmdllh Yaya ya su Umma da su Aziza, da sauran y’an uwa?" "Duk suna gida na baro su k'alau." "Madallah! A gaishe su." "Insha Allah zasu ji." "Maza ki ajiye jaka ki amso mi shi ruwan sanyi." Cewar Ummi bayan sun gama gaisawa da Fatima, jakarta ajiye a d'aki, ta amshi kud’in ta je ta siyo pure water mai sanyi a shago ta kawo, ajiye ma shi ta yi, ta ce "Ummi bari na dubo Anty Amira." "Yawwa Binta maza je ki, ni ma naso shiga da dazu sai ga Aliyu, amma idan na yi isha kafin na kwanta zan dubota nima." A zaure ta ci karo da Al'ameen, "Yayana oyoyoo." Ta fad'a tana amsar ledar hannunsa, godiya ya mata, tare su ka shigo cikin gidan, d'akin ummi ta kai ledar ta ajiye ta fice zuwa gidan su Amira. Cike da d'okin ganin juna, suka yi musabaha, "Timekeeper kanawan dabo, gaskiya kano ta kar6e ka abokina, kaga yadda ka yi wani k'ato." Cewar Al'ameen cikin sigar zaulaya, dariya Aliyu ya yi ya ce "Na gode da zagi, kana ga duk na kanjame sai kashin wuya kamar kai, ka ce wani na yi kato." "Allah ba sharri na ka yi dan gwa6i, me ye sirrin." "Kai dai ka sani ni babu wani gwa6in da na yi, kowa cewa ya ke ba rame na yi katon kai." Haka suka yi ta zaulayar juna, Ummi na yi musu dariya daga bisani suka fito kafar gida suka zauna a dakalin gidan su Amira dake kallon nasu. Jiki a sanyaye Aliyu ya dafa kafadar Al'ameen, juyowa ya yi suka kalli juna cikin ido, damuwa da tsantar so da kulawa Al'ameen ya hango kwance a kwayar idanun Aliyu, "Abokina mekefaruwa, ka rame Ustaz kamar ba kai ba ka taimake ni ka gaya mini halin da ka ke ciki." Ajiyar zuciya Al'ameen ya sauke, ya ce " Ina cikin matsanancin damuwa Aliyu! Damuwar da take neman ruguza mini rayuwa, ta hanani farin ciki da kaanciyar hankali dani da ahlina." Ya karashe maganar a sanyaye, agogon hannunshi ya kalla ganin lokacin sallah ya kusa ya ce , "maganar da yawa bari mu yi sallah tukun na." Kafin Aliyu ya amsa suka ji sallama a kansu, a tare suka mai sallamar jin muryar mace. Kallo d'aya ta ma shi zuciyar ta ya bata cewa shine, tabbas bata ta6a gaskata zantukan Amira ba sai yau da ta yi arba da shi, gaba daya duk wani karsashinta sai ya nemi arcewa ya barta, dakewa ta yi ta karfafa zuciyarta, tuna halin data baro Amira a ciki, duk da haka ta kasa kallon shi cikin ido , sai Aliyu ta kalla ta ce "Barkan mu da yamma." Kamar yadda shi take kallo take magana haka zalika shi ya amsa mata da cewa "Yawwa barkan ki dai." Ta ce "Sunana Zainabu, kaqar Amira, idan babu damuwa ina son yin magana da Al'ameen." Sai lokacin ya sake kai kallonsa gareta gabansa ne ya shiga faduwa jin ta ambaci Amira, kallon shi Aliyu ya yi, yana jira ya ji ta bakin shi, ganin bai tanka ba yasa ya ce "Bismillah! Yana saurarenki bari na baku wuri" ya fada yana kokarin mikewa, da sauri Zainabu ta ce "A'a ka zauna zan yi maganar a gabanka ka zama sheda don naga kamar kai abokin shi ne." Ya ce "Ya ce OK to shikenan." Shiru ta yi na yan sakanni kafin ta yi karfin halin d'agowa ta sauke kallon ta a kan shi shima ita yake kallo har lokacin ta ce, "Shin kasan cewa wannan ciwon da amira ke yi ciwon sonka ke ne? Kasan cewa idan ba ka kawo dauki gaggawa a gareta ba tabbas soyyarka zata zama ajalinta? Nasan duk baka sani ba, to yanzu na sanar maka, Wallahi Al'ameen idan ka rasa Amira ka yi asarar masoyiya, ka dubi girman Allah ka amshi soyayyar ta kodon ceton rai, wallahi muna gaf da rasata kuma idan ka bari hakan ta kasance sai munyi Sharia da kai a kotun Allah." Ta karashe maganar tare da fashewa da matsancin kuka, kasa tsaywa ta yi da gudu ta bar wajen ta shige gidan su Amira, Fatima da ta yi suman tsaye ne tun da ta kunnayenta suka jiyo mata maganganun Zainabu ta fito zata shige gida ne, ta karaso gaba su da sauri cikin kidima da rawar muryar ta ce "Ya Yaya da gaske ne ciwon soyayarka ne ya mai kwantar da Anty Amira? " Kallon ta yake yi kamar mutum mutumi ya kasa koda gyada kai ne, hawaye ne suka Shiga gudu a fuskarta, da sauri ta mike tana girgiza kai sani kuma ta juya da gudu ta shige gida tana kwala kiran sunan Ummi, sai lokacin ya Ankara da tashin ta "Fatimahhhh!" Ya kwala mata kira amma ina! Tuni ta shige "Innalillahi wa inna ilaihinr rajiun." Ya fada yana dafe kanshi dake Sara mishi kamar zai rabe biyu.......... 09116099486. [12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 32* Tana kaiwa dai dai tsakiyar zauren gidansu ta jiyo muryar shi cikin wani irin sauti kwala kiran sunanta, cak! Ta tsaya ta kasa ci gaba da gudun, sai dai kuma ta kasa dawowa gare shi, sai samun kanta tayi da durkushewa a zauren ta sake fashewa da wani irin kuka mara amon sauti, kukan tausayin Amira, dama ta dad'e tana zargin wani abu a tattare da Amira game da Yayanta sai dai bata ta6a tunanin lamarin har ya kai haka ba, take ranar da ta ga Amira ta fito daga d'akin Al'ameen tana kuka ya shiga dawo mata. A can kofar gida kuwa, dafa kafad'ar shi Aliyu ya yi, a hankali ya d'ago kaifafun idanunsa da lokaci guda su ka canza launi ya watsa ma shi,kallon cikin idanun juna su ka yi na y'an sakanni, Kafin Aliyu ya lumshe ido ya bud'e tare da cewa a sanyaye "It's time 4 prayer, muje masallaci." Bai amsa shi ba, don baya jin zai iya bud'e baki ya yi magana, mik'ewa ya yi jikinsa a matuk'ar sanyaye, su ka nufi masallacin kusa da gidan. Bayan sun idar da sallah, hannaye Al'ameen ya d'aga sama ya shiga kai kukan shi ga mahalici, ya dad'a yana kwararo addu'o'i har sai da kusan kowa ya watse a masallacin, bai sauke hannayensa ba. Aliyu na daga gefen shi yana amsawa da amin duk da ba jin abin da yake fad'a yake yi ba don a zuciya yake yi. A tare suka shafa addu'ar, shi ya fara mik'ewa ganin haka yasa Aliyu ya biyo bayan shi. Tafiya suke yi a jere sai dai babu wanda ya ce wa d'an uwansa kanzil, daurewa kawai Aliyu yake yi ya hana kansa magantuwa ganin halin da abokin nasa ke ciki, amma bakinsa fal! yake da tarin tambayoyi, Kansa gaba d'aya a k'ulle ya ke. Mazaunin su na da suka koma suka zauna, shiru ne ya gifta a tsakanin na wasu mintuna, Aliyu dauriyarsa ya k'are don gabansa fad'uwa kawai yake, har ya bud'e baki da nufin magantuwa, Ya tsinkayi muryar Al'ameen cikin wani irin amo mai nuni da cewar tabbas maganar da zai fad'a mai girma ce, ya ce"Aliyu! Banda Allah mahaliccina, bayan ni kaina da kuma likitan daya d'aurani a kan magani, Kai ne mutum na uku da na za6a kasan sirrina, hakan kuma zai faru ne saboda na yarda da kai, na dauke ka d'an uwa amini abokin kuka wanda hausawa kan ce ba'a boye masa mutuwa." Gyada kai Aliyu ya yi cike da gamsuwa da bayanansa, shiru Al'ameen ya yi na wani dan lokaci, kafin daga bisani ya sauke kakkarfar ajiyar zuciya a hankali ya bud'e baki tiryan-tiryan ya shiga bawa Aliyu labarin ciwonsa tun daga lokacin daya fara fuskantan matsalar har zuwa kan yanzu da larurar ke mataki na biyar a jikinsa. Dagowa Ali ya yi idanunsa jajur yace "Wacece Amira? Menene alakar ka da ita." Nan ma bai yi k'asa a gwiwa ba wajen zayyanewa Aliyu wacece Amira da alak'arsu tun daga farko har zuwa yau , ya daura da cewa "Aliyu ban sani ba cewa akan soyayyata ne ta ke wannan ciwon, ban yi zaton lamarin ya kai girman haka ba, abin da na sani kawai bana son ta." Shiru ne ya biyo baya, gaba d'aya jikin Aliyu ya yi la'asar, lamarin ya sosa ransa fiye da zaton mai zato, gaba d'aya tausayin Al'ameen da ahlinsa harma da Amira ya gama cika masa zuciya, a iya hasashensa babu wata mafita data wuce wacce Dr Abdul ya fad'a, to amma ta yaya hakan zai kasance. Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya d'ago ya ce "Abokina na tausaya maka kwarai, sai dai naga zallar wautarka, shin me yasa ka za6i ka kassara rayuwarka akan ka yi Aure, kula da Ummi da Fatima kadai bai isa hujja ba, ka gwammace ka mutu a tsaye a kan ka yara sunnar ma'aiki, wallahi na tabbata idan Ummi ta ji wannan maganar sai ta zubar da hawayen bakin ciki da takaici, kana fa da ilmin addini daidai gwargwado, kana da tabbacin zaka iya rike kanka har zuwa lokacin da ka yanke wa kan ka yin aure, kana da tabbacin kwayoyin maganin da kake sha zasu ci gaba da rike ka har zuwa lokacin da ka d'ibarwa kan ka?" Girgiza kai Al'ameen ya yi ya ce "Ba ni da tabbas abokina yanzu menene mafita." Aliyu ya ce "Da gaske ka dauke ni amini abokin shawara kamar yadda ka fada?" Gyada mashi kai Al'ameen ya yi ba tare da ya iya bud'e baki ya amsa shi ba, "To mafita shi ne ka jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya." " Kamar yaya?" Ya tambaya cikin rashin fahimtar inda maganar Aliyu ya nufa, kallon shi ciki ido ya yi ya ce "Ka Auri Amira." "Na auri Amira?" Ya maimaita maganar cikin sigar tambaya, Aliyu ya ce "E ." girgiza kai ya yi ya ce "Bazan iya ba zan dai taimaka mata ta wata hanyar." A harzuk'e Aliyu ya ce "Ya zama dole ka iya, dole ka auri yarinyar nan Ameen." "Akan me zan aureta ba bayan bana son ta, ita fa zuciya ba a yi mata tilas." Ya amsawa Aliyu shima a fusace, mikewa Aliyu ya yi ya ce "Na sani Ameen zuciya ba'ayi mata tilas, amma ka sani a wannan ga6ar ba maganar so ko kiyayya ake yi ba, magana ake ta ceton rai da rai " Yana gama fad'in haka ya juya ya kama tafiya ba tare da ya sake kallon Al'ameen ba. Da kallo Al'ameen ya bi shi, zuciyarsa na harbawa, shin ya tsayar da shi ne ko ya k'ale shi? Ya fi minti goma yana bin haryar sa Aliyu ya bi sa kallo, a zuciyarsa yana taraddadin mai Aliyu zai yi? Ya fi kowa sanin Aliyu, ya san dai tunda ya ce dole yana nufin dolen ne, sai dai komai zai faru ya faru, fatan shi dai kar Ummi ta ji wannan batu, Rass! Gabansa ya fad'i lokacin da ya tuno da Fatima, a hargitse ya mike, shaf! Ya manta cewa ta ji, ya tabbata ya zuwa yanzu Ummi ta san da maganar, da sauri ya nufi cikin gidansu, sai dai tuntu6en da ya yi da abu a zaure ya dakatar da shi, kafin ya gama tantance da mai ya yi tuntu6e shesshekar kukanta ya cika mishi kunne, "Fatima!!!" Ya ambata a tsorace, yana kokarin haska tocilar wayarsa, itan ce kuwa kamar yadda ya yi hasashe, da sauri ya d'ago ta yana cewa; Menenen Fatima me ya faru, ina Ummi?" A rud'e ya shiga jero mata wad'annan tambayoyin. jikinsa ta fad'a tare da sake rushewa da kuka, k'ofar d'akinsa ya bud'e ya ja hannunta a su ka shiga, ya mai da k'ofar net d'in ya rufe. Zaunar da ita a bakin kafitarsa ya yi ya tsuguna a gabanta, ya ce "Fatima Menene?" Cikin shessheka ta ce "Yayana Anty Amira, da gaske ne?" Gabansa ne ya fad'i, k'ura mata idanu ya yi, kafin ya ce "Kin fad'awa Ummi ne?" Ta girgiza kai. Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa; Kar ki gaya mata kin ji kanwata hankali ta zai tashi sosai." Gyad'a kai ta yi alamar to, sai kuma ta hade hannayenta alamar rok'o ta ce cikin kuka; Yaya dan Allah ka so ta, dan Allah ka tausaya mata ka kaunaceta wallahi tana son ka matsanancin soyayya Yaya ina tsoron kar mu rasata ta dalilinka, idan ka yi haka ka yi ceton rai, kuma na tabbata Ummi zata fi kowa farin ciki da hakan, idan kuma ta samu labarin ciwon Amira na da alaka da kai na tabbata zata fi kowa bakin ciki, Yayana don Allah karka ce A'a, ko dan ni da Ummi ka kaunaci Anty Amira baza ka yi nadama ba.." Hannayenta dake hade ya kama ya rike gam! da hannyensa yana jin maganganunta na ratsa kwakwalwarsa take idanunsa suna karasa rinewa, cikin matsanancin kuka ta ci gaba da cewa "Don Allah Yayana, don Allah pls kar ka ce A'a, ko dan ni da Ummi, ba baka da tam karmu muma bamu da ya kai." Kalaman data yi ta maimaitawa kenan idanunta a rufe tana hawaye har sai da ta ji ya ce "Is ok Fatima, is ok naji na Amince." Cak! Ta tsayar da sambatu da kukan da take yi ta dago ta kalle shi idanu jaga-jaga da hawaye ta ce a sanyaye "Da gaske Yayana." Ya gyada mata mata kai tare da sakar mata murmushin karfin hali. Fad'awa jikinsa tayi tana sakin dariya mai sauti hawayen farin ciki da kaunar tilon dan uwanta na kwaranya a idanunta, tallefe kanta ya yi shima yana jin kamar ya yi wahayen. Sun kusa minti goma a haka, tun tana shessheka har ta koma sauke ajiyar zuciya, jin ana shirin tayar da sallar isha'i yasa ya sake ta, ya kalleta ya ce, "Ina rokonki Fatima ki yara daren yau wajen taya ni neman za6in Allah, ni ma yau zan gabatar da istikhara akan lamarin kome ciki Allah zai dafa mana." Gyada kai ta yi ta ce "In sha Allah Yayana." Mikewa ya yi ya ce ki shiga gida nima zan ta fi masallaci. Koda ta shiga gida bata nunawa Ummi komai ba, alwala ta yi ta gabatar da sallar magriban da batta yi ba ta daura sa ishan da ake kira. Kamar yadda Al'ameen ya roketa ranar daga ita har shi kusan kwana suka yi a bisa sallaya suna kai kukan su ga Mahalicci. Washegari ************** Ajiyar zuciya Dr Abdul ya sauke bayan ya gama sauraren jawabin dan matashin yaron da bai gaza tsaran Al'ameen ba ya gama yi masa, sake kallon yaron ya yi da kyau, ya ce "Aliyu ko?" Gyada kai Aliyu ya yi, Dr ya sake cewa "Thank u Aliyu!" K'arara mamaki ya bayyana a fuskar Aliyu, shi da ya zo ban hakuri da neman taimako ana yi mishi godiya, goron ruwan faron dake kan table Dr Abdul ya dauka ya bude murfin ya kur6a kadan ya mai da murfin ya rufe, kallon Aliyu ya yi ya ce "Nasan kana mamakin dalilin da yasa na yi maka godiya ko." Aliyu ya gyada kai, Murmushi Dr ya yi yace "Saboda ka rage mini aiki, sam! Ban yi fushi da Al'ameen ba domin da baka zo ba ina daf da bin sahun shi, jira nake wa'adin dana d'aukar masa ya cika, sai ga shi kai ka fanshe shi, na jinjina maka lallia ka cika Amini na kwarai kuma ina da tabbacin zaka taimakeni a kan abin da na saka a gaba na alkhairi." Shiru ya yi kad'an kafin ya daure da " Aliyu na fi ka son na taimakama Al'ameen, amma na rasa irin taurin kan shi, sometimes na kan zauna ni kad'ai na dinga tunanin irin karfin hali da taurin zuciyar shi, ko da yake ance ma gaji ma fiyi, ada ni kad'ai na me gwagwarmayar nan yanzu gaka ka shigo ciki, don haka zamu had'a karfi da karfe! Yanzu dai abin da ya kamata mu yi, shine mu samu ya amince da maganar auren domin a yanzu shi ya fi komai mahimmanci, idan muka yi sanya, ina mai tabbatar maka daga nan zuwa ko wani irin lokaci zai iya haduwa da mummunan attack wanda idan ba'ayi da gaske ba zai iya shiga wani mummunan garari ko kuma ya rasa rayuwarsa ma baki d'aya." "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!" Shine Kalmar da Aliyu ya furta a baiyane cikin tsantsar tashin hankali, "Dr yanzu menene abin yi?" "Ka bi duk hanyar da zaka bi wajen ganin ka tirsasashi ya amince da batun auren yarinyar nan." Cikin tashin hankali ya ce "Zan yi Dr, zan tirsasashi ko zai amince' dole zai amince." "To shikenan Aliyu zan kar6i lamabarka saboda ina son sanin duk halin da ake ciki." Canjen lambar waya suka yi daga haka suka yi sallama Aliyu ya tafi. *************** Washegari ya kama asabar babu school, misalin karfe tara na safe Al'ameen ya shiga d'akin Ummi cikin shirin shi na tafiya wajen neman halalinsa ya sha kyau cikin wani yadi milk, dinkin karamin riga mai guntun hannu da wando babu hula akansa don ba abocin sakawa bane, duk suna falo Ummi ta maida hankali tana sauraren wa'azin Dr jabir mai hula a tashar Afrika TV 3, yayin da Fatima ke zaune daga can sak'on kujera, kallo daya zaka san tana tattare da damuwa, idanunta sun yi luhu luhu alamar rashin barci, sallamar sa ne ya dawo dasu duk hayyacinsu. Ummi ta ce cikin fara'a bayan ta amsa sallamarshi, "Amintacce har an fito." Murmushi ya yi ya ce "E Ummi na fito a yi mini addu'a." Ya karashe maganar yana rage tsawo a gabanta. Kan shi ta dafa ta ce "Ubangiji ya tsare gabanka sa bayanka ya yi maka albarka ya saka maka Albarka cikin neman ka ya jikan mahaifinka." Cikin wani irin yanayi ya amsa da "Amin Ummi." Tare da mikewa tsaye, ya kalli Fatima da itama shi take kallo ya ce "Kanwata muje ki min iso na shiga na dubo jikin Amira." Daga yadda fara'a ta fadada a fuskar Ummi ya tabbata ta ji dadin lamarin sai ya tsinci Kansas cikin farin ciki shima, Fatima kam wuf! Ta yi ta mike fuskarta dauke da madaukakin farin ciki........ Oum ummeetarh 09116090468 [12/29, 2:45 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 33* No editing 😤 Cike da zumud'i Fatima ta zura dogon hijabinta, bakinta washe kamar gonar auduga ta ce "Yayana muje." Ya gyada mata kai tare da k'ara yin sallama da Ummi suka fito. Tana gaba yana biye da ita har k'ofar gidan, a nan ya dakata ita kuma ta k'arasa ciki bakinta d'auke da sallama, a tsakar gida ta tarad da Maman Amira da Aysha da sauran k'annen Amira, Mama ta fara gaisarwa tare da tambayar mai jiki, sannan suka gaisa da Aysha wacce suke kusan sa'anni, sauran yaran suka gaisheta. Wuri ta samu ta zauna a dakali, ta kalli Mama ta ce "Mama Yaya Ameen ne yace na mashi iso yana son ya shigo ya duba Anty Amira da jiki." Mama ta ce "Assha! Aminullahi ne da neman iso dan zai shigo gidan nan, jeki maza ki ce ya shigo, ke kuma Aysha gayawa Amiran zuwan Aminullahi." Kusan a tare Fatima da Aysha suka amsa mata da to Mama. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bi bayan Fatima, da ta juya bayan ta isar masa da sa'kon Mama, Bakin sa dauke da cikakkiyar sallama ya saka kansa cikin dan madaidaicin tsakar gidan, dai dai lokacin Aysha ta fito daga d'akin Mama tana cewa; "Mama Anty Amira fa ta samu barci." "Barci kuma? ikon Allah! Yanzu fa na barota ido biyu." Cewar Mama tana kallon Fatima da ke tsaye tana jiran k'arasowar Al'ameen. Sallamarsa ne ya karad'e musu kunnuwa kusan a tare duk suka amsa, gefen Mama ya risina cike tsantsar ladabi da kamun kai ya ce "Mama ina kwana." Da fara'a ta amsa da "Ina gajiya Aminullahi, ya harkoki ya karatu." "Alhmdllh Mama ya jikin Amira." "Hmmm! Jiki da sauk'i Aminu sai hamdala." Ta fad'a muryarta cike da rauni. "Allah Ubangiji ya bata lafiya." "Amin ya rabbi, Mai jikin ma ta samu barci, idan ta farka zan sanar da ita zuwan ka." Ya amsa da " Ayya ba komai Mama, a gaisheta idan ta farka, idan na dawo da wuri zuwa dare zan sake shigowa in sha Allah." "To to!! Aminullahi Allah ya kaimu daren an gode sosai, Allah ya yi Albarka." Da Amin ya amsa tare da mik'ewa ya fice. Fatima ma bata dad'e ba ta yi musu sallama ta tafi tare da Alkawarin sake shigowa anjima. Kamar almara tana fitowa daga gidan ta yi kicibis da Joy. Da fara'a suka tari juna, Fatima ta ce "ya akayi kika fito da sassafen nan, yau Saturday." Murmushi ta yi kafin ta kai bakinta dai dai saitin kunne Fatima cikin rad'a ta ce "Na zo ganin Handsome Yayana ne, na yi masa godiya a kan, turaren da ya siya mana, yanzu zan koma kafin Mom ta nemi ni." Dariya Fatima ta yi, Idan da sabo ta sabo da jin ire iren sunayen nan kala kala daga bakin kawar tata da take kiran Al'ameen da su, sai dai bata ta6a daukarsu da wata manufa ba, ta bar hakan a matsayi kirkin da yake gwada mata shima, yana kula da ita sosai ya daukesu duk daya, sometimes har tsaraba yake musu a tare, tun bayan da hargitsin nan ya lafa ta lura da irin yadda Joy din ke matukar girmama lamarin da ya shafe shi, ko fira suke idan na shi ne ta fi maida hankali, kullum zancen ta Yaya Ameen kaza Yaya Ameen kaza, takan yi mamakin yadda lamarinsu ya juye daga kiyayya da kushe juna zuwa yabo da girmamawa hadi da tsantsar kulawa. "Umh! Wato shi kadai ki ka zo gani ko banda ni, to kin mak'aro yarinya ya fita." Narai narai ta yi da ido ta ce "Da gaske?" Cikin dariya Fatima ta ce "Ah swear!" "Ok bari na tafi, idan ya dawo ki fara Isar min da sakon godiya, kice nace turaren yana da kamshi wai tunda nake ban ta6a jin turaren mai dadinsa, kar ki sanarwa Ummi zuwana pls zan dawo may be gobe." Fatima ta ce "Oh naso kuwa na baki wani labari mai dadi, tunda kina sauri shikenan, kuma labarin ya shafi Yaya Ameen." A d'okance ta ce "Pls ki fara fad'a min Teetee ko Kad'an ne." "A'a ki tafi kawai bana son Mom ta miki fad'a, ranar Monday zan gaya miki a School." Riketa ta yi tamau ta ce "Ban yarda ba, sai kin fad'a min." "Ok to sake ni." Sake ta yi ta ce "Oyo tell me." Shammatar ta Fatima ta yi ta kwasa da gudu tana cewa; Sai Monday." A jigace ta yunk'ura ta mike zaune, lamarin da ya kusa zautar da Aysha tsabar mamaki, saboda rabon da ta iya mik'ewa ta zauna da kanta haka har sun manta, kullum sai dai a kwantar a tayar, bata damu da irin kallon da Aysha ke mata ba ta ce da muryarta wadda bata fita sosai saboda jigata "Da gaske ki ke Aysha Yaya Ameen ya shigo gidan nan duba jikina?" Aysha ta ce "Ya shigo mana Anty zan miki karya ne." Ga mamakinta wani Busasshen murmushi taga Amira ta saki wanda rabon da ta yi irinsa har sun manta sai kuma ga hawaye shar yana bin kumatunta,, murya ciki ciki ta ce " Tabbas ban yi farin ciki da wannan barcin da na yi ba, domin yayi mini shamaki da ganin rayuwata." "Anty mai Ki ka ce? "Ban ce komai ba Aysha." Gyada kai Aysha ta yi wani tunani na zuwar mata a kwakwalwa, da sauri ta d'ago ta kalli Amira ta ce "Yaya ina zargin wani abu, kar dai kice min soyayyace silar damuwarki?" Kura mata ido Amira ta yi, dai dai lokacin Zainabu ta yi sallama a k'ofar d'akin tare da kutso kai, gaban Aysha ta tsuguna tare da dafa kafadarta ta ce "Kwarai kuwa Aysha zarginki ingantacce ne, ranar wanka ba'a boyar cibiya." Ajiyar zuciya ta sauke, tiryan tiryan ta shiga labarta mata komai, tausayin Amira ya saka Aysha kuka kashir6an, cikin shessheka ta ce "Dama na dad'e ina zargin Anty Amira na son Yaya Ameen, amma ban ta6a tunanin shine matsalar larurarta ba, da tuni na bankad' sirrin kowa ya ji, dan bazan yarda na rasa yar uwata ba ina ji ina gani, amma ko yanzu bata 6aci ba." Ta kai karshen maganar tare da mikewa a fusace, riko hannunta Zainabu ta yi ta ce "kar ki yi haka Aysha abi komai a sannun." Komawa ta yi ta zauna tare da dafe kai ta ce "Gaskiya Yaya Ameen bashi da tausayi, ko dubata bai ta6a shigowa yi ba fa Anty Zainabu" "Kar kiga laifin shi Aysha bai san komai ba sai jiya." Nan ta kwashe yadda su ka yi da shi jiya ta fada mata. Ta daura da "Tun sa kika ga ya biyo baya ina ga akwai alamun nasara abin ba sai ya kai ga manya ba." "Allah yasa" Cewar Aysha. kamar almara ranar a zaune Amira ta wuni sa6anin kullum da take wuni kwance, sai gata harda dan cin abinci, Tsabar farin ciki Mama da gudu ta garzaya ta sanarwa Ummi don abokin kuka da shi ake dariya. Hamdala Ummi ta shiga yi, ranar da wannan zancen ta wuni duk wanda ya shigo gidan kuwa da maganar take fara taron shi. Cikin sa'a karfe shidda Al'ameen ya dawo, da wannan zancen Ummi ta tare shi fuskarta a washe, murmushi yak'e ya kirkiro ya yi tare da cewa "Alhmdllh kai na yi murna Allah ya kara mata lafiya." Jiki a sanyaye ya juya ya koma d'akinsa, kimtsawa ya yi, ya tafi masallaci, daga masallaci direct gidan su Amira ya nufa, a lokacin duhu ya fara. Sam ta ki yarda ta sake komawa barci tun bayan wanda ta yi da safe wanda ta yi mishi lakabi da barcin shamaki, tun karfe biyar take ta zuba idon ganin shi amma shiru, shidda ya yi da rabi ya wuce har magrib zuwa lokacin ta fara sarewa, silalewa ta yi ta kwanta ta lumshe idanu hawaye na bin kumatatunta. Kamar a mafarki ta tsinaka yi sallmarsa a cikin dodon kunnenta, kafin ta gama tantance a wani hali ta ke ta sake jiyo muryar Mama tana cewa "Tana d'akinsu, Aysha yi wa Aminullahi iso." Kur! Ta kurwa k'ofar dakin idanunta masu danshi ya yin da bugun zuciyarta ya tsananta.......... Haka so yake d'iba ya maida kai bawa🎶🎶🎶🎶 Allah sarki Amira. Y'an term d'in sannunku hwa 😬 [12/29, 2:46 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 34* Har ya k'arasa shigowa d'akin jikakkun idanunta na kafe a kan fuskar shi, ta kasa koda keftawa, gani take yi idan ta rintse ido ta bud'e zai 6acewa ganinta. Aysha ce ta bashi wajen zama kafin ta fice daga d'akin ta basu guri. Sai lokacin ya samu damar sauke idanunsa a kan ta, wani irin kwance-kwance gabansa ya yi ya fad'i, Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! ya ambata a zuciya. hankalinsa ya yi k'ololuwar ganin gaba d'aya yadda ta rame ta lalace, ta fice daga hayyacinta kamar na Amiran daya sani ba, take tausayinta ya yi wa zuciyarsa kawanya. Sassanyar Muryarta daya ratsa dodon kunnesa ya jawo hankalinsa, cikin maganarta 'kasa-k'asa irin ta majinyata take cewa; Yaya Ameen kaine da gaske! Ba gizo idanuna ke min ba, A she zan sake saka ka a idanuna kafin na amsa kiran mahaliccina, nagode sosai da ka zo gareni na yi farin ciki, nagode sosai." Ta karashe maganar tana sakin murmushi, hawayen soyayyarsa na kwaranyo mata ba tare da tasan da kwaranyarsu ba. Jikinsa ne ya yi sanyi kalau! Gefe guda kuma wani irin kunyarta ya ji ya lullu6e shi, sai ya samu kansa da kasa ci gaba da kallon idanunta. Lallai zuciyar so makauniya ce, duk irin abin da ya aika ta mata Sam! bata ga laifinsa ba, bata yi fushi ba, wata d'aya da kwanaki ta kwashe cur! Tana jinya saboda soyayyarsa, bai ta6a koda aikowa bane yace ace mata sannu, amma take mashi godiya don yau ya shigo dubiyar da bata kai zuci ba. Dakyar ya d'ago idanunsa da ke kyallin hawayen tausayinta ya sake kallota, da wani irin sassanyar murya ya ce " *Meerah* ya jikin ki." Kusan suman wucin gadi ta yi, don lokacin da tattausar murya shi ya ratsa kunnenta, cak bugun zuciyarta ya tsaya, kamar sabuwar makauniya haka ta kure fuskar shi da kallo ba tare da ta amsa mishi ba. Ganin haka yasa ya yi karfin halin sakar mata tattausar murmushi, abin da ya yi sanidiyar lumshewar idanunta a hankali ta sake budewa a kan shi, still murmushin na nan bai 6ace a fuskar ba, cikin k'asa k'asa da murya ya sake kira sunanta da cewa "My Meerah." Gudun wahayenta ne ya ninku, la66anta ne su ka kama rawa alamar tana son furta wani abu amma ta kasa, gyada mata kai ya yi ya ce "Yess My Meerah, do u lik d name? Bata iya amsa tambayar ba, sai kawai ta tsinci kanta da rintse idanu tare da furta "Ya Allah na roke ka, kar ka farkar dani daga wannan daddadar barcin da nake yi, Ya Allah ka dauwamar dani a cinkasa." Ta karashe maganar da fashewa da kukan da ita kanta bata san na mai zata kira shi ba. Bai san sanda ya isa gabanta ba, cike da tausayi ya shiga share mata hawaye, cikin rad'a ya ke cewa; It's reality Meerah ba mafarki bane, nine Ameen d'in ki a gabanki, bud'e idanunki ki kalleni." Samun kanta tayi da budewar kamar yadda ya umarta, suna hada idanu ta mika hannu ta kama nashi ta rike gam! Cikin kuka da fitar hayyaci ta ke cewa; Dan Allah Yaya Ameen kar ka barni, ka tsaya a tare dani ka dauwama a tare dani, kar ka gusa kusa dani na roke ka, yin hakan daidai yake da yankewar numfashi na, bazan iya rayuwa ba tare da kai ba, Ina son ka Ameen, ina son ka ina son ka, kaine rayuwata farin ciki na, idan babu kai a duniyar Amira zan zamo kamar mutum mutumi." Ta karashe da fashewa da wani irin kuka mai narka zuciyar mai sauraro. "Shiii! ya isa Meerah, ga Ameen a gabanki, na yi miki alkawarin zan rayu dake zan zamo maji6ancin rayuwarki insha Allah." Ya fad'a cikin wani irin amo wanda yake fitowa tun daga kasan zuciyarsa. Sun dad'e a haka hannun shi, cikin nata, dakyar ya lalla6a ya zare hannunsa tare da komawa mazauninsa ya zauna, yana ci gaba da gaya mata kamalai masu kwantar da hankali, sai ga Amira tana dariya kamar wayiya, kallonta yake cike da tausayi tare da kara tabbatar da cewa lallai shine farin cikinta. kiran isha'i ne ya tayar da shi, kafin nan sai da ya yi mata alkawarin shigowa da safe ya dubata kuma ya jaddada mata ta tabbatar ta ci abinci da yawa. Cikin kwana uku da faruwar haka sai ga Amira ta gyagije ta mike tsaye kan kafafunta, kamar ba itace a kwance rai a hannun Allah ba, lamarin da ya baiwa kowa matukar mamaki banda Aysha Fatima da Zainabu da su ka san abin da ke ciki. Al'ameen yana iya kokarinsa wajen ganin ya wanzar da farin ciki a gareta, kullum yakan shiga ya dubata suyi hiran hakan ya jefawa Mama zargin wani abu a zuciyar ta, Fatima kam kusan tafi kowa farin ciki don tsakanin ta da Allah har zuciyar ta take kaunar Anty Amira, ba don warning din da Al'ameen ya mata akan kar fa fadawa Ummi ba, da tuni ta fada, duk da haka takan yi su6utar baki wani bin. Yanzu damuwar Al'ameen bai wuce Aliyu ba, tun daga ranar da wannan abin ya faru basu sake haduwa ba ranar da damuwa yadda su ka rabu ya kwana, a zuciyar sa yaji bai kyauta ma shi ba, ya je gidan su sau biyu baya samun shi, kiran waya kam ya mishi ya fi sau shurin masaki amma baya d'agawa. ********* Tun da Joy taje gida take ta tunanin albishirin da Fatima ta ce , zata mata a kan Yaya Ameen, kasa juriya tayi don akan duk abin da ya shafe shi zuciyar ta azalzala take, babu yadda bata so ba ta samu hanyar fita ran Sunday zuwa gidan sai dai babu dama, don Mom tasata tayi a gaba tunda sassafe suke wuce church ranar acen suna kusa wuni, haka ta kwana da daukin wayewar garin Monday, sai dai cikin rashin sa'a ranar karatu ta yi musu zafi, kuma da aka yi closing Mom ce da kanta ta zo daukarta, ba don ta so ba ta bita suka wuce gida da kudirin koma menene gobe baza ta rabu da Teetee ba sai ta gaya mata...... [12/29, 2:46 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 35* Washegari tun six thirty ta gama shirin school saboda gand'oki, a gaggauce ta sauko dining, a shirye ta same shi tsab! Kamar yadda ta tsammata, sai dai tea da cake kadai ta iya sha shima kad'an, sake kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta yi, ganin bakwai saura yasa ta naima waje a parlour ta zauna tana kallon cartoon a tv duk da kallon kawai take amma hankalinta baya gurin, karfe bakwai dai-dai ta nufi upstairs, direct d'akin Mom ta nufa, tura kofar ta yi ta shiga ba tare da knocking ko excuse ba. Mom bata falo dama bata yi zaton ganinta a nan ba, kai tsaye ta nufi bedroom, muryar Mom da ya daki dodo kunnenta ne, ya dakatar da ita daga karasawa cikin d'akin. Cike da tabbatarwa ta ke cewa "Kar ki damu Esther bani da kowa a duniyar nan bayan ke, ke kad'ai ne iyayenmu suna haifemu tare mu biyu kuma a yanzu basa raye, ki sani ita d'in ba komai bace a gareni fa ce tsanin cikar burina, lokacin dana dibar mana na daf da k'aratowa, sai na tabbatar da ya mallaka mata komai nasa daidai da tsinke bai bari ba, zan kashe shi, sannan daga baya ita......" Sauran zancen ne ya mak'ale lokacin da idanunta suka sauka a kan Joy rik'e da k'ofa, da alamar ta ji me take cewa' Jikinta ne yaso daukar rawa, amma tuna wacece Joy yasa ta dake rainonta ce, ta fi kowa sanin halinta bata da shiga sabgar da bai shafeta ba. "Excuse me." Ta fad'a tare da sauke wayar daga kunnenta, sakar mata murmushi ta yi, cike da wayancewa ta ware mata hannayenta tare da cewa; "Come to me my dearest princess." Martanin murmushi ta mayar mata ta k'arasa ta fad'a jikinta suka jungume juna, "Morning my lovely Mom." Joy ta fad'a tana zare jikinta daga na Mom, rike hanayenta Mom ta yi ta na kallon ta cikin ido don son karantar yanayinta ta ce "Morning my Happiness, har kin shirya? "Yes Mom har ma na yi breakfast." "Auh! Shine babu jira ko gud." Dariya ta kyalkyale da shi, "I'm sorry Mom na tashi da yunwa ne." "Ok no prblm." Mikewa ta yi tana cewa; "Bye bye! Mom till I came back." "Ok princess nima yanzu zan shirya na tafi gidan antynki Esther, tana can tana rigima da Mr Moses wai sai ya sake ta, yanzu ma da ita nake waya kika shigo Esther bata jin magana lamarinta ya fara isa na." Ta karashe maganar tare da dafe kai cike da takaici, "Ki yi hakuri Mom ki ci gaba da abin da kike yi na alkhairi zaki samu lada." Tana gama fad'in haka ta fice, a parlour n k'asa ta dauk'i jakarta ta fito compound, already Peter na jiranta basu 6ata lokaci ba, ta shiga ya tukata zuwa school. Da biyu Mom ta fad'i wannan magana, don ta kauda hankalin joy daga zargi ne, hakan kuwa ya yi tasiri, da farko kalmar kisan da ta ji a cikin maganganun Mom sun saka ta a shakku, sai dai jin zancen Esther yasa ta yi watsi da lamarin don bata kaunar abin da zai had,a ta da tilon kanwar uwartata, tun a bedroom d'in Mom ta watsar da batun, ko kafin su isa school ta shafe babin batun a ranta. Shiganta aji da mintuna kad'an Fatima ta iso, kasancewar babu teacher a ajin yasa ta tashi da gudu ta tare ta suka rungume juna, dakyar suka saki juna suka k'arasa sit suka zauna, sauran student na masu dariya masu jin haushin kawancensu kuma na ta6e baki da zund'en su. "Teetee tell me about him, ki gaya min mana sai ja min rai kike yi." Dariya Fatima ta saka ta ce "Sai during break." Fushi Joy ta yi ta juya mata baya, magana Fatima ta dinga mata amma ta share da gaske fushi ta yi sosai don harda guntun kwallah ta share ba tare da sanin Fatin ba. Abin da ya ba Fatima mamaki da kuma dariya ana ringing bell, Joy ta kalleta tare da cewa; "Oya tell me." Dariya Fatima ke son yi, amma sanin halin Joy na saurin fushi yasa ta danne, ta yi abinta a ciki, narai-narai Fatima ta yi da ido ta koma kalar tausayi kafin ta ce "Zan gaya miki amma sai kin saki fuskarki, kinji my beautiful friend." Murmushi ta saki, Fatima na dariya ta ce "Ba irin wannan ba gaskiya, idan ba haka ba kuma bazan fad'a ba." Ga mamakinta sai ji ta yi Joy ta kyalkyale da dariya. Gimtse nata dariyar ta yi tana binta da kallon mamaki, gira Joy ta d'age ta ce "A kan Yaya Ameen komai zan iya yi domin nima a yanzu shine komai nawa." Rass gaban Fatima ya fad'i da sauri ta kauda tunanin da yazo mata zuciya, jin Joy din ta ci gaba da cewa; "Shine ya bani matsayin kanwa, ya zame mina Yaya dan uwa abin da na nake tsananin kewa shekara da shekaru, ina jinsa har cikin bangon zuciyata." Murmushi Fatima ta yi ta ce "Umm! Kaji masu yayyi muma Allah ya bamu." "Amin!" Joy ta amsa mata a gatsile. Fatima ta ce tana murmushi, "To albishirinki." "Goro fari kal!" Ta amsa mata, "kawo kunnenki kiji." Matso da kunnenta ta yi fuskarta a washe yau dai finally zata ji abin da Teetee ke ja mata rai a kai kwana da kwanaki, Fatima ta kama kunnen ta matsa da bakinta cikin rad'a ta ce "Yaya Ameen ya yi budurwa very soon zai yi Aure, zai auriAnty Amira....." 6at tattausar murmushin dake kwance a kan fuskarta ya ba ce within second, kamar saukar gudumar wuta haka kalaman Fatima suka daki zuciyarta take idanunta suka fara juyawa, wani irin dunkulallen abu ya tokare mata kirji, take numfashinta ya shiga sama da kasa kamar mai cutar Asthma. Jin shiru yasa Fatima kallon ta, a tsorace ta zaro idanu tare da furta "Na shiga uku." A bayyane "Joyyy!"ta kira sunanta da karfi tana jijjigata, suuu! Ta ta tafi zata fad'i, da sauri Fatima ta rikota cikin tashin hankali take kiran sunanta da karfi tana jijjigata, lamarin daya jawo hankalin yan tsirarun student d'in dake ajin, da gudu wasu suka yo kansu suna tambayar menene, ya yin da wasu suka tafi kiran class teacher d'in su. Wata cikin yan ajin ne tayi dabarar fasa pure water mai sanyi da ke hannunta ta shiga antaya mata daga kai zuwa fuskarta, wani irin ajiyar zuciya mai karfi ta shiga saukewa tana kokawa da numfashinta tare da kokarin hadiye kululun daya tokare mata wuya amma ina! Abin ya ci tura. Tuni Fatima ta dad'e da fara kuka, hannayenta bisa kai, ta ke cewa; "Na shigo uku! Joy dan Allah kar ki mutu ki barni, wasa nake yi miki." Ana cikin haka class teacher ya shigo bayan shi nurs na school d'in ne cikin uniform d'in su, d'auke da first aid box..... Kishin balbal😱 *********** A karo na babu adadi ya sake trying lambar, yana kallo har kiran ya katse kamar koda yaushe ba'a d'aga ba, text ya shiga rubuta ma shi na ban hakuri, tare da tabbatar mashi a kan lallai yana so su had'u a kwai story. Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke lokacin da ya gama duba sak'on, ya tabbatar ya zuwa yanzu abokin nasa ya yi laushi, zai jaraba sa'ar shi wata kila ya dace. Replay ya yi ma shi cewa; Zai shigo after magrib. Karfe bakwai da yan mintuna a k'ofar gidansu Ameen ta yi Aliyu, zama ya yi a kan dakalin wajen ya zaro waya da niyyar kiran shi, sai ga shi, babu yabo babu fallasa Aliyu ya ba shi hannu suka yi musabaha, zama ya yi kusa da shi yana murmushi, ya dafa kafad'ar shi ya ce "Timekeeper nawa, har yanzu kana nan da dabi'arka ta r'iko ko?" Ba tare da ya kalleta shi ba ya amsa da "E kamar yadda kaima dabi'arka ta kafiya bata canza ba haka nima." Murmushi ya sake yi ya ce "Baka ce min ya jikina ba." Dage kafad'a Aliyu ya yi ya ce "Naga ai ba ka damu da lafiyar taka ba bare aje yi maka ya jiki." Dariya ya yi ya ce "To naji baka tambayeni ya jikin My Meerah ba." "Wacece haka?" Aliyu ya tambaya, amsa mashi ya yi da cewa; Masoyiyata mana Amira wacce kake fushi da ni saboda ita." Sai lokacin Aliyu ya d'ago ya kalle shi. Ajiyar zuciya Ameen ya sauke a nan ya kwashe duk abin da ya faru bayan wucewar shi ran nan har zuwa yanzu. Ya daura da "Aliyu ina matukar tausayinta, na amince zan zama maji6ancinta zan rayu da ita koda a zuciyata babu d'igon soyayyarta." "Bare ma baza a rasa ba." Aliyu ya fad'a yana hararanshi, murmushi kawai ya yi ba tare da ya tanka ba, sun dad'e suna hira, sosai Aliyu ya nuna mishi jin dadinsa game da amicewarsa da Amira ya k'ara da nusar da shi alfanun hakan ga shi karankanshi, sai dai koda wasa bai sako zancen Dr Abdul ba, don so yake ya bi komai daki-daki. Tare suka yi isha'i bayan sun dawo daga masallaci ne, Aliyu ya shiga gida suka gaisa da Ummi, ya ce "Ummi ya mai jikin nan na kwanaki." Fara'ar fuskarta ce ta fadada ta ce "Hmmm! Aliyu mai jiki ta ji sauk'i sai hamdala, kar kaso ka ganta yanzu kamar ba ita ba." "Masha Allah, Ubangiji ya k'ara mata lafiya." "Amin Amin Aliyu nagode sosai." "To Ummi ni zan tafi a gayar da Fatima idan ta tashi." "To zata ji Aliyu a gaida mutan gida." Tare suka fito da Al'ameen don yi masa rakiya, "Aboki ya kamata ka kira Amira mu gaisa, ka gabatar dani a matsayin babban aboki tun yanzu." Harara Ameen ya watsa masa, ya ce "Dalla Mallam muje na raka ka, matata mai tsada ce ba'a ganinta haka a arha." Rik'e ha6a Aliyu ya yi ya ce Ya ce "Da bamu san asalin balbela ba da sai tace mana daga saudiya take." Had'e rai Ameen ya yi ya ce "Me kake nufi."dariya Aliyu ya yi ya ce "Naga dai bada wani yare na yi magana ba ko?" "Kai dai ka sani ja'iri." Haka suka yi ta raha suna wasa da dariya har ya rako shi bakin Babar titi a nan suka yi sallama kamar kar su rabu. Direct gidan su Amira Al'ameen ya nufa, ta sheka wanka da kwalliya tana jiran shi, jin sallamar shi yasa ka yin wuf ta mike, kallon da Mama ta watsa mata yasa ta yi saurin k'asa da kai, Aysha dake kallon abinda ke faruwa sai dariya take mata, hararar ta ta yi ta gefen ido tare da yin kwafa. Shiga falon ya yi ya zauna bayan ya risina ya gaisar da Mama, Aysha da sauran kannenta suka gaishe shi, da gefen ido ya saki kallon side d'in da take, jin idanunta na yawa a kan shi, gaba d'aya ta shagala da kallon shi, Mama jin kowa ya gaishe shi banda ita yasa ta kallonta, ganin yadda ta shagala yasa ta cewa "Amira." Ina sam bata ji ba, don ta yi nisa Sam bata jin kira, ganin haka yasa Mama sake kiran sunanta a karo na biyu a tsawace "Amira!!!!" Firgigit ta yi ta kalli Mama, wani irin kunya ce ta lullu6eta sai kawai ta tashi da gudu ta bar falon, tafa hannaye Mama ta shiga yi tana sallallami. Juyowa ta yi da zumar yiwa Al'ameen magana, sai dai wayam! babu shi babu mai kama da shi a falon sam babu wanda ya kula da sanda ya sudad'e ya fice, ai sai ta sake rafka salati tana rik'e haba take cewa; Aysha kin ga abin da na gani kuwa, dariya Aysha ta kyalkyale da shi, cike da nishad'i, "Ikon Allah, yaran zamani ka haifesu baka haifi halinsu ba ai kuwa banga ta zama ba ni hafsatu, wannan abin farin ciki har ina." ta fada tana mikewa tsaye............ Comment and share masoya Oum Ummeetarh 09116099486 [12/29, 2:47 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 36* A firgice Mom ta shigo cikin makaranta, tana gurin aiki kirata same ta daga principal na school d'in Joy babu lafiya, office d'in principal ta nufa bayan gaisuwa principal da kanta ta yi mata jagora zuwa d'an karamin clinic d'in makarantar in da Joy ke kwance tana hutawa, don koda nurses suka tambayeta cewa ta yi kanta ke ciwo maganin ciwon kai kawai suka bata na kwaya ta sha, daga nan kuma suka bata bed rest kafin a iyayenta su zo. Tun da ta kwanta idanunta ke lumshe, da gaske kanta ke yi mata ciwo, bayan ciwon da zuciyarta ke yi mata, har zuwa lokacin babu abin da ya ragu dangane da abin da take ji a zuciyarta,wannan kululun na nan tokare a kirjinta, babu abinda ke amsa kuwwa a kunnenta sai maganganun Fatima, babu yadda bata yi ba, don hawaye su zubo daga idanunta ko zata samu sassauci a zuciyarta amma abin ya faskara sai kukan zuciya take wanda irin wanda ke kara ma mutum kunci. Cikin wannan yanayin Mom da principal suka iso d'akin, sarai ta ji su amma ta kasa bude ido ta kallesu, tana ji d'aya daga cikin nurses d'in wajen na yima Mom bayanin cewa kanta ta ke ciwo kuma sun yi mata abin da ya kamata sun bata magunguna, godiya Mom ta yi musu, ta matsa gaban gadon tare da dafa kanta, kan da d'umi, ga jijiya nan a goshinta sun tashi alamar dai ciwon kan mai yawa ne, kallon principal Mom ta yi ta ce "Dama tana da larurar ciwon kai tun tana k'arama, ina ga shine ya tasar mata, amma kuma gaskiya ya dad'e bai tashi ba don tun tana da shekara bakwai muka fitar da ita kasar Mexico ta ga wani babban likitan kwakwalwa shikenan bai k'ara tashi ba sai yau." Cike da Alhini principal ta jajanta lamarin. "Zan tagi da ita gida sai na kira Dr ya sake dubata." Cewar Mom, "Ok ba damuwa hakan dama shine daidai." Matso da mota Mom ta yi har bakin clinic d'in, da taimakon nurses ta samu ta isa motar don da ta mike jiri ne ya ringa dibanta dole a ka suka rirrik'eta suka taimaka mata. Har a ka tashi Fatima kuka take yi, ta firgita sosai da yadda Joy ta yi, tunda suke tare bata ta6a ganin ta cikin yana yin makamancin wannan ba,ta yi nadamar fad'i mata wannan maganar yafi sau shurin masaki, sai dai taki baiwa zuciyarta damar gaskata zarginta na cewa Joy tana son Yaya Ameen ne, duk wani kofa da zai bata damar gasgata hakan ta toshe, har suka yi closing bata fahimci wani teacher da wani teacher bane suka shigo class d'in bare tasan me suka koyar, itama da nata kamashon ciwon kan ta koma gida, sa'arta d'aya Ummi bata nan, dama Yaya Ameen ta san baza ta same shi a gida ba daidai wannan lokacin sai da wani kwakkwaran dalili. Sallar azahar ta gabatar ko abinci bata iya ci ba, ta sha paracetamol ta hau gadon Ummi ta kwanta, babbar damuwarta rashin sanin halin da Joy ke ciki, gashi ko giyar wake tasha baza ta iya taka 'kafarta zuwa gidansu ba, haka ta yi kwanta cikin damuwa tana tunane tunane cikin sa'a barci ya yi awon gaba da ita mai cike da mafarkai barkatai. ********** Dr Solo ya kalli Mom bayan ya gama duba Joy ya yi mata duk abin da ya makata ciki harda alluran barci don ta samu hutun zuciya da kwakwalwa, ya ce "Ciwon kan ta ne ya yi kokarin ta shi dalilin wani yanayin tashin hankali da ta shiga, amma zuwa yanzu da sauk'i, sai dai a kiyaye shigarta cikin irin wannan yanayin, gudun samun matsala." Cike da damuwa Mom ta ce "ok Dr mungode kwarai." A ranta tana mamakin wani irin tashin hankali ne Joy ta shiga haka. Sallama Dr ya yi ma Mom ya tafi tare da alkwarin sake kira zuwa dare yaji halin da ake ciki. Tare suka five da Mom daga d'akin don yi mashi rakiya. Duk abin da Dr yake fada tana ji domin kuwa idanunta biyu, sai dai fitar su daga d'akin bai fi da minti biyar ba wani nannauyar barci ya yi a won gaba da ita. Awa bakwai cur! Ta kwashe tana barci, kafin ta farka lokacin karfe shidda daidai na yamma, a hankali ta bud'e idanunta da suka mata nauyi, ta ji sauk'i sosai don wasai take jin kanta babu d'igon ciwo, haka ma nauyin zuciyarta ya ragu kaso hamsin cikin d'ari, a hankali ta lalla6a ta mik'e zaune, tankwashe kafa a tsakiyar gadon tare da rafka tagumi da hannayenta bibbbiyu. Maganganun Fatima ne suka shiga dawo mata filla-filla, "Yaya Ameen ya yi budurwa very soon zai yi aure, zai auri Anty Amira." Kalmomin da su ka yi ta amsa kuwwa kenan a kunnenta suna neman rikitar mata da kwakwalwa, da sauri ta saka hannu ta toshe kunnenta da hannayenta tare da fashewa da kuka, take hawayen da take muradin fitarsu tuntuni suka samu hanya, a guje suka shiga wanke mata fuska. Kuka tayi sosai don a kalla ta kwashe kusan awa guda tana yi, a hankali ta ji kuncin dake zuciyarta na yayewa, ajiyar zuciya ta shiga saukewa akai akai hadi da shessheka, ita kanta baza ta ce ga dalilin kukan nata ba abin da ta sani kawai umarnin zuciyarta take bi, sam! Zuciyarta baza ta iya jurar jin Kalmar Yaya Ameen yana son wata mace ba, balle har a kai ga batun aure, tabbas a duniya tana ganin babu abin da yafi wannan tashin hankali a gareta, a halin yanzu ita kanta bata san meke damunta ba, bata kishi ba domin ita kadai ta tashi gaban iyayenta abin da ta sani kawai soyayya, shiyasa abin da ya faru da ita yau bata san da mai zata kwatantashi ba. Shigowar Mom ne ya katse tunaninta, da sauri Mom ta k'araso ganin ta a zaune, zama ta yi a kusa da ita ta kai hannu tana tatta6a goshinta zuwa wuyanta,salam! Babu zafi ajiyar zuciya ta sauke tare da godiya da abin bautarsu. Cike da kulawa tace "Princess ya jikin, yaya ki ke ji yanzu, ina ne ke yi ma ki ciwo?" "I'm fine Mom babu in da ke min ciwo, naji sauk'i." "Ok bari na kira miki Papanki ku gaisa tun dazu yake ta kira yana son yaji muryarki." Da d'unbin mamaki a fuskarta ta ce "Papa kuma?" "Yes Ur Papa." Zun6ura baki ta yi ta ce "Ya daina sona yanzu ai." Murmushi Mom ta yi ta ce "Who tell that, a duniya babu abin da Mr James yake kauna sama dake tillon y'arsa,ina tabbatar miki yafi kaunarki fiye da ni dana kawo ki duniya." Ta karashe maganar cike da d'aci a muryarta, amma sam Joy bata fahimci komai ba saboda kakanun shekaru, "Na sani Mom a da Papa yana sona amma cikin yan kwanakin nan ya canza min, abin ya dame ni amma na yi masa uzuri, nasan aiki ne ya sha kan shi." "Of course princess haka ne, jiya ya kammala duk aikin sa ya kaishi kasar Canada, yanzu hankalin sa gaba daya ya waiwayo kan little princess d'in shi, tun safe yake min waya yana neman ki,. Ta kai karshen maganar tana mika mata wayarta da ta yi dialling lambar Papa. Cike da shauk'in so irinta tsakanin da da mahaifi ta kara wayar a kunnenta tare da cewa; He'll My Papa." "My Joy My everting." Ya amsa mata cike da soyayya, sun Dade Suna waya ta yi mai korafi akan shareta da yake yi kwana biyu hakuri ya bata da cewa shima bai san mai ya same shi ba cikin kwanakin nan, sun dad'e Suna waya kafin su yi sallama. Mom ta amshi wayarta tana sakin wani shu'umin murmushi wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa....... Ko kunsan ma'anar murmushin Mom, ni da ban sani ba😢 Oum ummeetarh 09116099486 [12/29, 2:47 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 37* Mikiya Writer's Association No editing🙏 Washegari a sanyaye Fatima ta gama shirin school, gaba d'aya bata cikin walwala har sai da Ummi ta kula da yanayinta ta tambayeta ko bata da lafiya ne. Al'ameen dake wanki a tsakar gida lokacin da Ummi ke mata magana ya d'ago ya kalleta, tabbas shima ya hangi damuwa da rashin walwala a tare da ita, hakan yasa ya ce mata "Idan baza ki iya zuwa makarantar ba ki barshi kawai gobe Sai ki je" da sauri ta ce "A'a Yaya zan je." Ci gaba ya yi da wankinsa ba tare da ya sake cewa komai ba, sallama ta yi musu ta goya gakarta ta fice. Da sauri ya dauraye hannayensa ya bi bayanta, girgiza kai Ummi ta yi ba tare da tace komai ba, tasan dama bazai iya barin ta tafi ba sai yaji damuwarta, idan ba haka kuwa a cikin damuwar zai wuni. Kasancewar ya hada da sassarfa, ita kuma a sanyaye take tafiya yasa ya cimmata a zaure, jin k'arar taku ya sakata saurin juyowa ganin shi yasa ta shagwa6e fuska, a gabanta ya tsaya ya kafeta da ido sannan ya jeho mata tambayar "Meke damunki?" Take ruwan hawaye ya cika mata mata kaurin ido, "shiii!!!." Ya yi mata tare da daura yatsa a lips dinsa ya ce "Kar ki kuskura ki zubar da hawayen nan." Kokarin shanye hawayen ta shiga yi don cika umarnin shi, amma ina sai da su ka zubo. Ganin haka hankalinsa, ya k'ara tashi, riko hannayenta yayi ya ce "Kin samu wanda zaki sanarwa damuwarki wanda ya fini a duniya ko?" Da sauri ta girgiza kai, ya ce "Oya tell me meke damunki." Cikin shessheka ta ce "Yaya Joy ce." Wani irin yankewa gabanshi ya yi ya fad'i, "Joyyy?" Ya maimaita sunan cikin sigar tambaya, gyada mai kai ta sake yi, cikin tashin hankalin da yake kokarin boyewa ya ce "What happend to her?" "Bata da lafiya ne." Ba karamin jarumta ya yi da bai kai hannu ya dafe heart dinsa ba saboda wani irin fad'uwa da ya yi, cikin wani irin voice da saida Fatima ta d'ago da sauri ta kalle shi ya ce "Mekedamunta." Jim! Fatima ta yi zuciyarta ne ya so shiga rudani, kasancewar ta mai azabar wayo yasa ta yi gaggawar boye yanayinta ta ce "Ji ya ne school ta dinga yin wani abu haka kamar ta sums numfashinta ya dinga sizing idanunta ya juya har saida a ka bata bed rest, kafin Mom d'in ta tazo ta dauketa su ka wuce gida, ni yanzu bansan halin da take ciki ba tun jiya." A sanyaye ya ce "Addu'a zaki ta ya ta da shi na kuka ba Fatima, ki yi mata addu'a Allah ya bata lafiya." Ta gyada kai alamar to, ya ce "Share hawayenki." Babu musu ta share, naira dari ya ciro a aljihunsa ya cika mata tare da cewa; Maza ki wuce kar ki yi latti." Amsa ta yi da hannu biyu ta ce "Nagode Yayana." Tafiya take tana tariyo abin da ya faru yanzu cike da tarin mamaki, wani irin rauni hadi da damuwa ta hanga karara a tattare da shi, irin wanda ba kasaifai a ka fiye gani a tattare da shi na sai a kan abu mai mahimmanci a gare shi. Bayan tafiyar Fatima k'asa komawa ya yi yaci gaba da wankinsa, gaba daya jikinsa ya yi san yi kalau, gabansa kuwa har lokacin bai dena faduwa ba, dakinsa ya shigeta ya lalubi kafifarsa ya kwanta a hankali ya lumshe idanunsa da suka canja launi sabida damuwa. Ya dad'e a haka, ya rasa mai ke masa dad'i a lokacin ya rasa ina zai tsoma zuciyarsa ya ji san yi, tambayar da yake jehowa kansa shine "Meya sameta? Meya faru da ita? Meke damunta." Abinda ya yi ta maimaitawa a ran shi kenan, har bai san iya adadalin lokacin daya 6ata ba, kiran wayar shi ne ya dawo da shi hayyacinsa, Aliyu shine sunan daya bayyana akan fuskar wayar, a matukar sanyaye ya d'aga wayar, magana suka yi na mintuna uku zuwa hudu kafin ya sauke wayar, message ne ya shigo wayar, budewa ya yi, My Meerah ita ce ta yi masa sak'on sai da ya saki murmushi kafin ya bude sakon, kamar kullum sakon Barka da safiya ne da fatan ya ta shi lafiya hadi da zafafan kalaman soyayya, ya kan yi mamakin a ina ta koyi irin wad'an nan kalaman, Sam! Bata jin kunyar fad'a masa kalaman soyayya, ajiyar zuciya ya sauke ko babu komai suna burge shi kuma suna saka shi nishadi a duk lokacin da yake karantawa. Kwanciya ya ci gaba da yi sai da Ummi ta gaji ta biyo shi d'akin sannan ya samu damar mikewa ya je ya karkare wankin ya yi wanka ya shirya ya tafi school inda daga nan zai zarce wajen kasuwancinsa. ********** Da sauri Fatima ta karasa sit d'in su, dalilin hango Joy da ta yi zaune, zama ta yi ta shiga tatta6a goshinta zuwa wuyanya at d same time ta na tambayar ta na cewa; Friend ya jikin ki? Meya same ki jiya. Ina ke yi miki ciwo?" Rike hannun Fatima ta yi tana murmushi ta ce "I'm fine Teetee ki bari haka mana." Rau-rau da ido Fatima ta yi ta ce "Hankalina ya ta shi sosai jiya, ban yi zaton zaki zo school yau ba." Dan dariya ta yi ta ce "Matsoraciya naji sauki tun jiya." Daga haka bata sake bata dama sun yi magana akan abinda ya faru jiya ba sai ta canza akalar hirar da gaya mata cewa cikin Wannan month d'in Papanta zai dawo kuma sun dai-daita yanzu ya kula da ita kamar yadda yake yi da, da yake Fatima ta san komai game da tsakaninta da Papanta. ************ Da misalin karfe goma sha daya Maman Amira ta shirya ta shiga wajen Ummi, tun jiya a d'okance take da tazo ta labarta mata abin farincikin dake shirin wanzuwa a tsakanin su. Gyara zama Maman Amira ta yi bayan sun gama gaisawa da Ummi tare da tambayar lafiyar iyalai harma da d'an ta6a hira, tace "Wai nikam Ummin Fatima ko kin hangi abin da na hango?" Cike da rashin fahimta Ummi tace "Name kenan Maman Amira?" "A game da yaran nan Al'ameen da Amira, sai nake ganin kamar a kwai wata alak'a a tsakanin su." Dariya Ummi ta yi , tace "Maman Amira na dad'e da fahimtar hakan, sai dai rashin tabbaci yasa na bar maganar a zuciyata, don su y'ay'an yau ba'ayi musu katsalandan a irin wannan lamarin, nasan dai komai dad'ewa idan zargina gaskiya ne zasu bayyana kansu, to ashe kema kin kula." Mama da fara'ar fuskarta ta kara fad'ad'a tace "Hmmm na kula Ummi lamarin yaran zamani sai a barsu." Ummi tace "In dai haka be sai muce Alhmdllh! Don wannan abin farin ciki ne." "Kwarai Ummi Fatima zan iya cewa nafi kowa farin ciki da hakan." "A'a fa Maman Aysha, na fiki farin ciki domin kuwa amira diya ce yar albarka duk wacce ta sameta matsayin rusuka ta yi dace." Mama ta amsata da shima "Aminullahi haka." Sun dad'e suna raha kamar na masu shirin zama surukai ba kafin Maman Amira ta yi sallama da Ummi ta tafi............ Oum ummeetarh 09116099486 [12/29, 2:48 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 38* Mikiya Writer's Association. *NOTE* Jiya na yi mistake wajen saka number, instead of 37 na sake maimaita 36, so yanzu zamu je 38 da fatan kun fahimta👌 A kwana a tashi ba wuya, musamman a wannan zamanin da muke ciki ta karshen duniya yadda lokaci ke gudu kawai ya ishi bawa tsoron Allah. Tsakanin Al'ameen da Amira komai ya k'ara daidaita soyayya suke gudanarwa mai tsabta, kyautatawa tare da kulawa had'i da girmamawa sune manyan makaman da Amira ta yi amfani da shi wajen kafa kanta a zuciyar Al'ameen, bugu da k'ari yadda take nunawa Ummi da Fatima tsantsar soyayya da kulawa ya k'ara mata kima a idanunsa, wani babban matsayi na musamman ya ware mata a zuciyarsa, da fari ya k'arbi, soyayyar ta ne saboda Fatima sai kuma tausayinta da yake ji, sai dai da tafiya tayi fatiya rashe ya juye da mujiya, don a halin yanzu idan ya ce baya sonta to tabbas ya yi babban karya. Ya zuwa yanzu babu wanda ya kamata yasan da maganar soyayyar su da ya rage bai sani ba, kama daga dangi, makota, y‘an uwa, da abokan arziki, tuni kawunan Amira suka fara maganar cewa Al'ameen ya turo magabatansa idan da gaske yake, lamarin da ya yi masifar d'aga masa hankali, bashi da kud'in aure yanzu bai ajiye ba bai baiwa wani ajiya ba, hasalima d'akin da zai sakata kango ne bai kai ga k'ark'are ginawa ba. Cikin kwana biyu kacal da samun wannan sak'on duk ya gigice ya shiga damuwa, tabbas yana buk'atar mace a rayuwarsa, musamman a halin yanzu da ya kai gargarar da tablet d'in da yake sha sam! ya daina yi masa aiki, ko da kuwa zai shanye sachet biyu ne a take, k'arfi da ya ji ya koyi, istimna'i, (Biyawa kai bukata) wanda a duk lokacin da hakan ya kasance yakan kwana ne yana kuka tare da neman gafarar Ubangijinsa, sarai ya san abinda yake aikatawa sa6o ne babba haramun ne , kuma cuta ne ga lafiyarsa, sai dai shi hakan ya fiye masa a kan ya aikata zina, yana kyamar zina, haka yana tsananin tsoron aikatawa domin ya dad'e da sanin bashi ne, idan kaci sai ka biya, shiyasa yakan yi taka tsantsan wajen ke6ewarsa da Amira, saboda kasancewar ta ma'abociya son gayu da kamshi, a cikin yan kwanakin nan, hirasu ta waya ya fiye masa alkahiri bisa ga ace sun ke6e, domin a duk sanda hakan ta kansance ya kan shiga wahala da garari. Misalin karfe biyu na sulisin dare, zaune yake a bakin kafifarsa, ya rafka taguma da duka hannayensa biyu, idanunsa ya yi jajur, hankalinsa a tashe nadama da kaico kwance k'arara akan fuskarsa,ya tabbata idan mutuwa ta riskesa a wannan halin la shakka zai gamu da fishi da azabar Allah, take wani irin tsoron Allah ya dirar masa, zuciyarsa ce ta karye, take hawaye ya shiga kwaranya daga idanunsa, ya dad'e yana kuka, banda "Astagfirullah Allah na tuba Allah ka yafe mini." Babu abinda yake maimatawa a zuciyarsa, ganin zaman da yake yi da najasa a jikinsa bashi da amfani yasa ya tsagaita da kyar, ya mik'e yana layi tamkar wanda ya yi tatul, daga shi sai gajeran wando a jikinsa, sif ya bude ya dauki, wani wandon wankakke, ya kuma dauki babbar butarsa dake ajiye a gefe cike da ruwa ya fito, kamar yadda ya saba kullum cikin sand'a da taka tsantsan ya nufi toilet. Cikin takaitaccen lokaci ya tsarkake jikinsa ya fito sanye da wankakken wandonsa yayinda ya riko daya wandon da hannu hagu cike da kyamkyami, gabansa ne ya yi wani irin yankewa ya fad'i lokacin da idanunsa ya hadu dana Ummi da ke rike da buta wanda ta gama zuba ma ruwa a ciki yanzu yanzu, da sauri ya yi kasa da kansa gabansa na ci gaba da wani irin dokawa, take ya ji wani irin sanyi na kada shi, da yana da hali a lokacin da babu abin da zai hana yace kasa ta bud'e ya shige tsabar kunya. Kur! Ta kure shi da kallo zuciyar ta na tsinkewa, ba yaune karo na farko da ta ta6a kamashi yana wanka ba musamman ma a cikin yan kwanakin nan da abin a shi ke neman shallake tunaninta, sai dai basu ta6a yin gaba da gaba ba sai yau, ita kanta bata san yana tailet d'in ba da batta yarda ta fito alwalan ba, ta bari har sai ya gama ya shige d'aki. Yi tayi kamar bata gane komai ba, ta ce "A' a Amintacce hala kaima zafin nan ya dame ka, da sauri ya ce "E wallahi Ummi, na kasa barci sai da na fito na watsa ruwan sanyi." Tana nufar toilet d'in tace "Hmmm! Allah dai ya saukaka mana." Daga haka ta shige toilet, da sauri ya bar tsakar gidan. Ta dad'e a kan darduma tana kai kukanta gurin Allah tana hawaye, tun jiya da maganar cewa Al'ameen ya turo magabatansa ya risketa take cikin matsanancin tashin hankali, shin wa zai wakilci lamarin auren nan, shin wa zata nuna musu a matsayin dangin mahaifinsu, tabbas lokaci yayi da zata waiwayi wadancen azzaluman Ahlin, lamarin Al'ameen ya fara bata tsoro ita kanta zata so ya kasance da mace a kusa, domin dai ta riga ta gama fahimtar shi din mai tsananin bukata ne. Da safiya kasa hada ido ya yi da ita, duk da yadda ta yi iya kokarinta wajen ganin ta nuna mishi bata fahimci komai, shi yasan ta fahimta d'in domin dai ita ba yarinya bace duk da babu wanda zai ganta ya ce ita ta haife shi Indai ba wanda ya sani ba, haka jiki a sanyaye ya shirya ya fice daga gidan. School ya nufa don yana da lecture, karfe goma ya fito daga school, jikinsa duk a mace kansa ne ke masa matsanin ciwo kamar zai rabe biyu baya jin yana da kuzarin iya fita aiki yau, hakan yasa ya kira Aliyu ya ya ji ko yana gida, samun tabbacin yana gida yasa kai tsaye ya tari dan acaba ya nufi gidan su Aliyu. Ganin shi a sanyaye yasa Aliyu tarar shi da cewa; Lafiya Ameen mekefaruwa." Zama ya yi a kan kujera 2 sita dake d'akin Aliyu ya dafe kai, yana sauke numfashi. Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke, ya zauna kusa da shi, sun fi minti biyar a haka, Al'ameen bai ce komai ba shima Aliyu bai matsanta mashi ba, sai da ya gaji don kan shi ya dago idanun da suka kara rinewa ya kalli Aliyu. Ya ce "Aliyu ya zan yi? Nutsuwa Ali ya kara yi ya maida dukkan hankalinsa garesa, ya ci gaba da cewa; "Iyayen Amira sunce na turo, Aliyu bani da halin aure ban ajiye ba ban ba wani ajiya, kuma ina bukatar aure Aliyu ya zan yi? Murmushi mai sauti Aliyu ya yi a zuciyarsa ya ce anzo wajen. Wani irin kallo Al'ameen ya shiga bin Aliyu da shi ganin yana murmushin, ganin irin kallon da yake masa yasa ya dafa kafadar shi, ya ce " Abokina a kwai mafita." Tamkar wani soko ya ke bin Aliyu da kallo kafin ya ce "Akwai mafita kace Aboki?" Gyada kai Aliyu ya yi ya ce "kwarai kuwa a kwai mafita.".............. Oum ummeetarh 09116099486 [12/29, 2:48 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 39* Mikiya Writer's Association. "Menene mafitar?" Al'ameen ya tambaya idanunsa cikin na Aliyu. Nannauyar ajiyar zuciya Aliyu ya sauke, cike da kwarin gwiwa ya ce "Dr Abdul Hafiz ." Wani irin k'ank'ance ido Al'ameen ya yi, a hankali ya maimaita sunan da sigar tambaya "Dr Abdul Hafiz S Alto?" "Kwarai shi nake nufi." Aliyu ya fad'a shima yana kafe Al'ameen da ido. Bacin rai ne ya bayyana k'arara a fuskarsa take, a kausashe ya ce "Menene had'in ka da shi?" Dakewa Aliyu ya yi daman yasan hakan zai iya kasancewa, ba tare da shayin komai ba ya ce "Zumunci." Gyada kai Al'ameen ya yi, ya ce "Zumunci ko? Very gud." Daga haka ya mik'e bai kalli side d'in da Aliyu yake ba ya fice daga d'akin jiri na kwasarsa. Murmushi Aliyu ya saki a yayin da ya raka bayan shi, da kallo, taurin kan Al'ameen ya wuce tunanin mai tunani, idan ya riga ya kau da kai a kan mutum da wuya ya k'ara waiwayarsa ko shi waye, sai dai ya lashi takobi zai yi iya 'kokarinsa wajen ganin komai ya daidaita. ********* *JOY* Tun daga ranar da Fatima ta sanar da ita batun soyayyar Yaya Ameen da Amira, bata sake yarda wani hira makamancin wannan ya sake shiga tsananinsu ba domin ta san baza ta iya jurar ji ba, zuciyar ta baza ta iya d'auka ba. Haka suka ci gaba da harkokinsu ba tare da ta bari Fatima ta fahimci komai game da abin da ke lullu6e a zuciyarta ba, ta bi ta toshe duk hanyar da Fatima zata fahimci a kwai wani abu a zuciyarta game da Ameen, tun da ta fahimci kamar Fatin na zargin hakan, sai dai duk wani walwala da kuzarinta ya ragu, sam! ta daina tambayar Fatima game da Al'ameen kamar yadda take yi ada, idan ma Fatima ta dauko hirar shi, da dabara za ta dakatar da ita ta hanyar sako wani hirar dabam ta shashantar da wancen hakan ya saka zuciyar Fatima a wa si wasi a kan zarginta, har ta samu kwanciyar hankali, don ta yi imanin cewa; Joy baza ta ta6a boye mata wani sirri na rayuwarta ba, sai ta watsar da zargin da ta ke yi suka ci gaba da sabgarsu na yau da kullum babu wani sauyi. Joy kuwa kwantan 6auna ne kawai ta yi, don zuciyarta cike ta ke taf da kaunar Al'ameen, ita kad'ai ta san irin famar da take da zuciyarta, duk daren duniya sai ta sha kuka ta gode Allah, musamman da ta fahimci yadda ya ke kaunar Amira da kuma yadda itama Amiran ta mace a kaunar shi, ganin haka yasa ta gama sadak'arwa ta rasa Al'ameen domin dai da idanunta take ganin zallar soyayyar Amira a tattare da shi, hakan yasa take jin wani irin mahaukacin kishi da haushinta na babu gaira babu sabar, har yau ta kasa bata fuska su dinga ko da gaisuwar mutunci ne, ba yadda bata yi don ta tausasa zuciyarta a kan hakan ba abin ya gagara, Fatima da ke tsakanin su, sai ta bar hakan a kan cewa jininsu ne bai hadu ba. A duk sanda ta zo gidan ta yi rashin sa'a da katarin ganinsu a tare, ranar takan wuni ta kwana da mugun ciwon kai, bata ta6a zaton duk wadannan abubuwan da take ji shafar mai ba ne, sai yau da suke k'ule a uwar d'akin Ummi, Fatima na sanar da ita cewa iyayen Anty Amira sun ce Yaya Ameen ya turo magabatansa a zo ayi zancen aurensu. Kamar saukar gudumar wuta haka zancen ya daki zuciyarta, da sauri ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta da ya yi wani irin dokawa da mugun k'arfi, a dan gigice Fatima ta kalleta tare da cewa "Ar u ok." "yes I'm ok." Ta fad'a da sauri tana ya mutsa fuska jin gefen kanta ya fara sara mata, sannu Fatima ta shiga jero mata, ta gyada kai tare da mik'ewa tsaye, Fatima ta kalleta da mamaki ta ce "Ya dai friend ina zaki je ?." "Teetee I want 2 leave now." Ta fad'a cike da wani irin rauni a muryarta, mik'ewa Fatima ta yi ta riko hannayenta tana kallon cikin idanunta, cikin k'asa-k'asa da murya ta ce "Ki gaya min dan Allah, menene?" Tsura mata idanu ta yi, na yan sakanni take hawaye ya ciko a kwaurin idanunta, can kuma kamar an tsikareta ta fisge hannayenta da sauri ta fice daga d'akin tana sharar kwallah. Wani irin tafiya take yi tana layi kamar yar caburos, duk in da ta samu jefa kafarta kawai take yi ba tare sa kula ba, gaba daya idanunta sun kulle bata ko ganin gabanta, tuni hawaye ya gama wanke mata fuska cikin kankanin lokaci. Babu zato babu tsammani ta ji an ca6e hannunta, yana yin sauyin bugun zuciyarta da kuma kamshin turaren shi ya tabbatar mata da cewa shi ne, hannun shi da ke rike da nata ta kalla, kafin a hankali ta d'ago kai ta sauke idanunta a fuskar shi. Wani irin kallo yake binta da shi, mai dauke da ma'anoni daban-dabam, d'ago idanun da ta yi, ya ba shi damar sauke kwayoyin idanunsa a cikin nata, wani irin kallo suke bin juna da shi mai kama da kallon kuda, hawaye ne ke zurara a kumatunta, hawayen zallar so da kauna, yayinda shi kuma na shi idanun suka kara rinewa jajur, zakarar wuyar shi na motsawa yake alamar yana hadiyar wani abu wanda shi kad'ai yasan ko menene, dawowarsa kenan daga wajen Aliyu zai shiga gida ya ci karo da ita, ganin yana yin da take ciki yasa ya kasa bari ta wuce, domin da gani ba lafiya ba. Kamar an wuntsilota daga sama ta bayyana a gabansu, wani irin abu ta ke hanga kwance a idanuwansu su duka biyun wanda bata fatan ace gaskiya ne, shin ina ma mafarki take yi' cike da matsanancin tashin hankali, cikin rawar murya ta ce "Yaya Ameen." Sautin muryarta ya daki kunnuwansu baki d'aya, sai dai ko da wasa Al'ameen bai dauke idanusa daga fuskar Joy ba kuma bai saki hannayenta ba. Yayinda ita kuma ta d'ago manyan jik'akk'un idanunta ta sauke su a kan fuskar Amira dake tsaye tana binsu da kallo hankali tashe, suna had'a idanu ta ji wani irin k'ululun abu ya tokare mata makoshi, wani irin kuka ne ya taho mata daga can kasar zuciyar, da mugun k'arfi ta fisge hannunta daga rik'on da ya mata ta juya da gudu ta bar wajen. Ba shi da kuzarin tsayar da ita domin jin damuwarta, shi kan shi cikin matsanancin damuwa yake, Sai dai ganinta cikin damuwa ya so mantar da shi ta shi damuwar. "Yaya Ameen." Sautin muryarta a karo na biyu ya ratsa kunnuwarsa, a hankali ya dauke idanunsa daga hanyar da Joy ta bi, ya sauke a fuskarta, hawaye ya gani kwance a kwaurin idanunta, tsabar wutar kishi da tashin hankali kwance karara a idanunta. A halin da yake jin kansa bai san mai zaice mata ba, sai kawai ya samu kansa da cewa; Ban san menene ya saka ta kuka ba, bansan me yasa na damu da damuwarta ba abin da na sani kawai ina jinta a zuciyata misalin yadda nake jin Fatima a raina, bana son ganin hawayenta kamar yadda bana son ganin hawayen Fatima. Kasancewarta mai tsananin wayo, yasa ta yi murmushin yak'e wanda aka ce yafi kuka ciwo, tana share hawayenta da bayan hannu a fakaice ta ce " Wata kila hakan nada nasaba da yadda suna shaku da Fatima ne, tabbas nima ina kaunarta a raina kamar yadda nake kaunar Fatima." Tsura mata idanu ya yi, shin da gaske take abin da ta fada ya ke tambayar kansa, yayinda maganganunta suka maimaita Kansu d'aya bayan d'aya a kunnuwansa. Ganin haka yasa ta ra6a ta fice ta gefensa ba tare da ta sake kallonsa ba. ************ Ragwab! Fatima ta koma ta zauna a kan gadon Ummi, hankalinta a tashe, shin' me abinda Joy tayi yake nufi, wannan shine karo na biyu da shigen irin haka ya faru, kar dai ace zargin da ta dade da cirewa aranta ne ke shirin tabbatuwa, zumbur ta mik'e, ya zama dole ta tabbatar kafin ta zartar da wani hukunci da mugun sauri ta biyo bayanta, a zaure suka yi kicibus da Al'ameen, kallon tuhumar daya jefe mata yasa da sauri ta ce "Yayana ka had'u da Joy a waje." Girgiza mata kai kawai ya iya yi ya bude d'akinsa ya shige,yana tambayarta Ummi ta dawo? A sanyaye ta amsa mashi da "A'a Taya." Kafin ta juya jiki a sanyaye ta kima cikin gida zuciyar t ciek da tunani kala-kala. Sai da Joy ta kwashe kwana biyar bata je gidansu Fatima ba kuma bata je school ba, tana gida tana fama da mikin zuciyarta don sai da ta kwashe kwana biyu kwance tana fama da zazza6i da ciwon kai, lamarin da sai da Mom ta kira Dr solo ya daura mata drip kafin ta ji dama dama, wannan shurun na Joy ya saka Fatima a cikin matsanacin damuwar da ya kasa 6oyuwa a tattare da ita duk kuwa yadda ta so boyewar, Al'ameen ne ya fara lura, ritsata ya yi a d'akinsa ya tambayeta meke damunta, bata 6ata lokaci ba wajen sanar da shi damuwarta ba, san da ta ambaci Joy sai da gabansa ya fad'i, tun Daga ranar da abin nan ya faru da tunanin ta yake kwana yana tashi, taurin kai da dakiya ce kawai irin ta shi yasa bai bude baki ya tambayi Fatima ba, dakewa ya yi ya shiga bata baki a kan ta cire damuwa a ranta domin dai lafiya ita ke 6uya. Ranar Monday kamar wasa Fatima na shiga class ta tarad da ita, da gudu ta karasa ta rungumeta ya baya, ranar basu maida hankalin kan darusan da aka koyar ba, saboda yadda sukayi kewar juna, Fatima ta so ta tuhumeta a kan abin da yasa ran nan ta fice ta barta daga ta yi mata zancen Yaya Ameen da Amira sai kuma wani tunani ya fado mata ar rai wanda tilas ya sakata fasawa. ********** Ajiyar zuciya Zainabu ta sauke bayan ta gama sauraren jawabin Amira, kallon Amira tayi da ke kuka sha6e sha6e ta ce "kin tabbatar da abinda kike fada kuwa Amira." Cikin shessheaka ta ce "Tabbas na tabbar da idanuna na hango tsantsar soyayyar Arniyar yarinyar na kwance a cikin kayan idanunsa dan Allah Zainabu ki bani shawara ya zan yi wallahi zuciyata zata tarwatse."............ Afuwan masoya🙏 Oum Ummeetarh 09116099486 [12/29, 2:49 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 40* Mikiya Writer's Association *Masu facebook ku yi following wannan account ɗin domin samun damar cin giveaway ɗin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa* https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL Kwantar mata da hankali Zainabu ta yi, tare da ba ta shawara a kan ta yi kunnen uwar shegu da abin ta cire shi daga zuciyarta ta yi kamar bata fahimci komai ba tunda dai hasashe ta ke yi bata da tabbas a kan lamarin. Cikin kuka ta ce "Wallahi Zainabu da idona na gani ya rik'e hannayenta, suna bin juna da wani irin kallo, kollon da bai ta6a yi mini irin shi ba, irin kallon da nake fatan samu daga gare shi koda a mafarki ne. Ta6e baki Zainabu ta yi ya zuwa yanzu lamarin Amira ya fara bata haushi, cike da jin haushi, ta ce " Ke dai Wallahi an yi raguwar banza, yanzu haka ma fa ba abin da ki ke tunani ba ne shegen kishinki ne yasa ki ke ganin hakan, ta yaya Ustaz kamar Al'ameen zai tsaya soyayya da wata arniya mai fistari a tsaye, ai ruwa ba sa'an kwando ba ne, ni kam ko duk jikina kunne ne ban yarda ba." Murmushin takaici Amira ta yi, ta na kallon Zainabu a zuciyarta tana cewa; Hmm! Zainabu don dai ba ki san so ba ne shiyasa ki ke cewa haka, "Kallon fa?" Zainabu ta fad'a tana dan zaro mata ido had'i da d'an hararanta, girgiza kai ta yi tare da sakin murmushin yak'e wanda ya fi kuka ciwo. Amira ta dauk'i shawaran Zainabu don kuwa koda wasa bata yarda ta yima Al'ameen maganar Joy ba haka ma Fatima duk irin yadda abin ya tsaya mata a rai kuwa. A haka tafiya ta mik'a a ka kwashe satittika, har zuwa lokacin kuwa Al'ameen bai tura magabatansa wurin kawunnan Amira ba kamar yadda suna buk'ata kuma bai ce musu komai ba, ganin shirun nashi ya yi yawa yasa d'aya daga cikin k'annen marigayin mahaifin nata kiran Al'ameen har gida. Tare suka shirya da Aliyu suka tafi gidan nasa bayan sallar isha'i, d'aya daga cikin samarin gidan ya musu iso har falon kawu Basiru kamar yadda suke kiran shi, bayan gaisuwa aka gabatar musu da ruwa da abin motsa baki, sai da suka d'an ta6a hira da Aliyu kasancewar kawun mutum mai yawan magana sai dai mafad'aci ne na karshe, haka ma Alin shima magananne ne ba laifi idan ya samu waje. Al'ameen kam kansa na k'asa yana saurarensu gabansa na fad'uwa ya k'agu ya ji kiran me a ka yi masa. Sun dan d'auki lokaci a haka kafin kawu Basiru ya yi gyaran murya ya ce "Am! Aminullahi." D'agowa Al'ameen ya yi ya kalle shi tare da sake yin k'asa da kai cike da surukuta, "Abinda yasa na kira ka, mun ji shirunkaya yi waya, yau kimanin wata 3 da aka yi maka magana ka turo magabatan ka amma har yanzu shiru, to mun gaji da gafara sa kuma har yanzu bamu ga k'aho ba, domin dai yarinya cikin y'an uwanta wani ya ganta kuma ya nuna yana so , to kaga gida bai k'oshi ba ba'a kai waje ba, sai dai kasancewar mu ba k'ananun mutane bane yasa jiya muka zauna ni da y'an uwana, a kan maganar, yanzu dai an umarceni kasancewar nine k'arami a cikinsu suka wakiltani a kan na kira ka na shaida maka, an baka nan da sati d'aya idan har da gaske ka ke muji wani motsi idan kuma ba haka ba, to gaskiya komai zai iya faruwa, wannan shine mak'asudin kiran da na yi maka da fatan ka fahimce ni." Tun kafin kawu Basiru ya kai aya a maganarsa, tuni gumi ya tsatsafowa Al'ameen a gaban goshi, banda dukan uku-uku babu abin da zuciyarsa ke yi, sai Aliyu ne ya yi karfin halin amsawa kawu Basiru da cewa; Na'am kawu mun fahimta." Ya ce "Toh dama kiran ke nan idan kuna da abin fad'i kuma ku fad'i ina saurara." Aliyu ne ya sake amsawa da "A yi hakuri kawu, in sha Allah zaku ji mu kafin satin." Da haka suka yi sallama da kawu basiru, Aliyu ya ajiye masa naira dubu uku suka fito. Daga Alin har Al'ameen an rasa mai karfin halin cewa wani abu, har suka yi nisa da k'ofar gidan, shi Aliyu ganin halin tashin hankalin da abokinsa ya shiga ne ya sanyayar masa da jiki hakan ya tabbatar masa da akwai wata matsala, yayinda A bangaren Al'ameen yake hasaro irin tashin hankalin da Ummi ta shiga ranar da ya fara sanar mata da cewa; Iyayen Amira sun nemi ya turo, wannan na d'aya daga cikin abin da yasa har yau bai sake tayar da maganar ba, bawai don ya rasa naira dubu goman da za'a kai a matsayin kudin gaisuwar ba, kwarai ya hangi firgici da tashin hankali a cikin kwayar idanunta, wanda har ya kai ta ga son yin su6ul da baka a gabansa ta furta wasu kalamai da suka hana shi rintsawa a daren ranar. Aliyu ne ya katse shirun da cewa; Abokina ya kamata fa ka yi wani motsi a kan lamarin nan, ka dai ji abinda kawu ya fad'a, kar ka yi sakacin da zaka rasa Amira domin na lura kiris suke jira shi yasa suka yi maka wannan daurin talalar, duk da nasan kai ko da ta subuce makan ba damuwa zaka yi ba tun da ba wani sonta kake yi ba" Ajiyar zuciya ya sauke, da wani irin sanyin murya wanda Aliyu bai ta6a jin ya yi irinta ba ya ce "Aliyu ina son Amira, wallahi ina kaunarta ina fatan ta zame mini uwar y'ay'ana, sai dai ina jin tsoron wani abu, ina ji a jikina a kwai gagarumar matsala." "Wacce irin matsala? Aliyu ya jefa masa tambayar cikin dan tashin hankali, cike da wani irin k'unci ya ce " Dangin mahai...." Sai kuma ya yi shiru ya girgiza kai, Aliyu ya dafa kafadarsa ya ce "Dan girman Allah kar ka boye mini matsalarka abokina, idan kamin haka zaka saka zuciyata cikin zullumi." Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na yan sakanni, kamar bazai ce komai ba, can kuma ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, kafin ya kwashe komai ya fad'awa Aliyu, shi kan shi Aliyu abin ya so girgiza zuciyarsa, sai dai bai nuna hakan a fili ba, ya ce "Wannan ba hujja ba ce da zai ka kasa sake tunkararta da wannan maganar, Ameen ka sani anzo gabar da dole ne kusan su wanene ku." Wani irin kallo ya shiga bin Aliyu da shi kamar ranar ya soma ganin shi a duniya, domin ya sosa masa inda ya dad'e yana masa k'aik'ayi." Basu rabu ba sai da suka tsara yadda lamarin zai gudana. Bai iso gidan ba sai wajajen k'arfe goma da rabi, kamar yadda ya zata a tsakar gidan ya tarad da su, Fatima na kwance barci ya kwasheta yayinda Ummi ke kishingid'e tana sauraran redio, ta amsa masa sallama tana mik'ewa zaune, tare da gyara rik'on carbinta da gyangyadi yasa ya kusa subucewa daga hannunta. "Barka da gida Ummi." Ya fad'a yana zama a gefen tabarmar, dan tsira mashi ido ta yi ganin kamar yana tattare da damuwa kafin ta amsa masa da "Yawwa barka da dawowa Amintacce." Ganin irin kallon da take binsa da shi yasa ya yi saurin yin kasa da kai, gabansa na faduwa, ya ce "Fatima ta yi barci kenan." Ta amsa da "E ta yi da kyar bayan ta gama dakon jiran ka, kazo ka ji mata hadda." Murmushi ya yi idanunsa kan kanwar ta shi tare sa cewa; "Allah sarki yar uwata." Lamarin da ya saka Ummi sakin murmushi ba tare da ta sani ba. Bayan ya ci abinci ya fusakanci Ummi gabansa na wani irin dokawa yace "Ummi kawun Amira ya kirani d'azu a kan yana son ganina." Dakatawa ta yi da kokarin canza channel din da take kokarin yi ta zubawa fuskar shi manyan fararen idanunta masu cike da kwarjini........... Har kullum Afuwan shine abin da zan iya cewa gareku masoya🙏 *Pls a ta6a comment domin shi ke saka min karsashin yi muku typing ko da ban yi niyya ba* Oum ummeetarh. 09116099486 [12/29, 2:49 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 41* Mikiya Writers Association *Masu facebook ku yi following wannan account ɗin domin samun damar cin giveaway ɗin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa* https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL Bayan ya ci abinci ya fuskanci Ummi gabansa na wani irin dokawa yace "Ummi kawun Amira ya kirani d'azu a kan yana son ganina." Dakatawa ta yi da kokarin canza channel din da take yi ta zubawa fuskar shi manyan fararen idanunta masu cike da kwarjini, da sauri ya yi k'asa da nasa kan, tare da ci gaba da cewa; Ya bani nan da sati d'aya in turo magabatana idan har da gaske na ke yi, idan kuma na wuce hakan to za su aurad da ita ga wani dan uwanta wanda yake son ta." Har ya dasa aya bata iya dauke idanu daga kallon shi ba, yayinda shi kuma ko da wasa ya kasa d'agowa ya kalleta, Ajiyara zuciya ta sauke mai nauyin gaske, cikin sanyin murya ta ce, "Kar ka damu yayan Fatima in sha Allah, gobe zan je na samu yan uwan mahaifinku duk da sun min kyakkyawar kashedi a kan babu ni babu su kar na sake na sake ra6arsu yanzu lokaci ya yi da dole na neme su domin su sauke hakkin nauyin daya rataya a wuyansu." Ta karashe maganar cikin karyewar harshen, tare da sauri d'auke kwallar da ta ciko mata idanu. Hankali tashe ya d'ago ya kalleta, suna had'a ido ta yi saurin d'auke kai, don bata son ya fahimci kuka take yi, sai dai tun a yanayin sautin muryarta ya fahimci kukan ta ke yi, bata son ta ba shi damar da zai jeho mata wata tambaya hakan yasa ta mi'ke da sauri ta shige d'akinta ba tare da sake kallon gefen da yake ba. Gaba d'aya duk wani ga6a na jikinsa ya mutu, haka ya dinga sauke wani irin nunfashi mai hade da kunci, ya yi zama ya kusa na awa d'aya a tsakar gidan nan ba tare sa ko kwakkwaran mosti ya iya yi ba, shin dole sai sune zasu nema masa aure? Tun bai mallaki hanakalin kansa ba ya san cewa; Yan uwan mahaifinsu basa kaunarsu, a she dama dalilin da yasa Ummi bata yi musu zancensu kuma ta hane su da yin zancen su kenan, me yasa zasu ce kada su ra6e su shin su d'in ba jininsu ba ne, shin ita Ummi ina nata dangin suke? Tambayoyin da ya dinga kai komo kenan a cikin kwanyarsa, sai dai bashi da mai bashi amsarsu. Ya dade sosai a zaune kafin ya yi karfin halin mikewa ya tashi Fatima ta wuce daki shi ma ya nufi nasa dakin bayan ya nade tabarmar. Daren ranar ya jima kafin ya iya rintsawa, yayinda a bangaren Ummi yadda taga rana haka taga dare, ta yi kuka sosai bayan shigewarta d'aki, rayuwarta ce ta baya ya dinga dawo mata filla-filla, tabas ta yi rashin masoyi na hakika Al-hussain ya kaunaceta ya tallafeta ya nuna mata hakikanin soyayya duk da irin yadda gaba d'aya kafatanin danginsa su ke kin ta, kamar mujiya a cikin taron jama'a, sun yi mata korar wulakanci tana tsaka da alhinin rabuwa da masoyinta, sai dai dole haka zata sake tunkararsu a wannan ga6ar domin bata sa wadanda suka fisu bata san kowa ba sai su. Ta yi kuka sosai wanda rabonta da yin irin shi tun rasuwar marigayin mijinta, dakyar ta danne zuciyarta ta mike ta dauro alwala, a kan darduma ta karkare wayar gari ranar, Da safe haka ta wayi gari idanunta sun yi jajur sun kumbura, Fatima ta tsorata da ganinta, sai dai yadda ta tsare gida sai ta kasa tambayarta me ya same ta, hankalin Al'ameen ba karamin tashi ya yi da ganin ta ba, sai dai kamar yadda Fatima ta kasa tambayarta haka shima ya kasa,jiki babu kwari ya shirya ya fice daga gidan zuwa wajen harkokinsa. Karfe goma da rabi ta gama shirinta tsab cikin riga da zani na atamfa ta sanya hijab dinta gogagge mai matsakaicin tsayi, fes ta fito a matashiyar mace kyakkyawar gaske mai cike da haiba da kamala, sallama ta yi wa Fatima bayan ta bar mata sallahun abubuwan da zata gudanar a gidan kafin ta dawo. Tafiyar mintuna ashirin a cikin a daidata sahu ya isar da ita unguwar mak'era, a hankali ta dunfari babangidan mai dauke sa babbar k'ofa hadi da babban zaure. Family hause ne mai dauke da dakuna masu yawan gaske, kai tsaye ta nufi cikin gidan gabanta na fad'uwa sai dai ta dake, don babu alamun hakan a fuskarta. Kasancewar safiya ce yawancin matan gidan na tsakar gida kowacce na gudanar da sabgar gabanta, sallamar da ta yi ne ya janyo hankalin mafi aksarin jama'ar dake tsakar gidan. Kamar wata sabuwar halittta haka wasu daga cikin matan suka Shiga kallonta fuskokinsu dauke da tarin mamaki, yayinda bakin fuskoki a gare ta ke binta da kallon rashin sani. D'aya daga cikin matan ne ta kasa jurewa sai da ta maganta, cikin tu'ajjabi ta ce "Wa nake gani haka Lamar Balkisu? Na kusa da ita ce ta amsa da " Taya ni fada dai, ashe ba gizo bane. Tsaki d'aya daga cikin su ta ja tare sa cewa; Allah ya wadaran naka ya lalace, dai dai lokacin kuma d'aya daga cikin mazan gidan ya sawo kai jin kananun maganganu na tashi daga matayen nasu wadanda dama kullum basu rabo da hakan. Turus ya yi da farko lokacin da ya yi arba da ita, sai dai daga bisani ya wani irin hade rai kamar hadarin gabas, a kausashe cikin zare jajayen idanunsa ya ce "Meya kawo ki gidan nan Balkisu, Ashe ba mun yi miki kashedi sake rabar inuwarmu ba, shin ke mayya ce, to wallahi wallahi billahillazi la'ilaha illah huwa idan kika kara, minti biyu a cikin gidan nan sai na yi miki mummunar lahani. Wannan haniyar ta Yaya Al-hassan kamar yadda suke Kiran shi ita ta janyo hankalin kafatanin sauran muatane gidan dake dakunansu, suka Shiga firfitowa d'aya bayan d'aya. Gyaran muryar da aka yi daga bayansu yasa duk suka maida hankali gurin, sabanin Hassan fuskarshi washe ta ke da wani irin shu'umar murmushi, ............ Oum ummretarh 09116099486 [12/29, 2:50 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 42* Mikiya Writers Association *Masu facebook ku yi following wannan account ɗin domin samun damar cin giveaway ɗin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa* https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL "Ka barta Hassan, ka barta mu ji da me ta ke tafe." Yaya babba ya fad'a a gadarance, cike da umarni, Al-Hassan dake huci kamar kububuwa ya juya ya kalli inda sautin muryar d'an uwan nashi ke tashi, ya ce "Yaya ka yi hakuri ka barni in ci mata mutunci, in wulakantata, kamar yadda na yi mata alkawari duk ranar da na sake ganin kafarta a cikin gidan nan zan yi mata. " Ka bari na ce Hassan" cewar Yaya babba, bayan ya k'araso kusa da Al-hassan d'in, daga haka ya juya ya nufi falon shi ba tare da sake cewa komai ba, wani irin huci Al-hassan ya dinga furzarwa yana bin Ummi da wani irin wulakantaccen kallo mai dauke da tsantsar tsana, daga bisani ya juya ya bi bayan dan uwansa a fusace. Jiki babu kwari Ummi ta k'arasa madaidaicin falon mai d'auke da satin kujeru da k'aramar TV, guri ta nema ta zauna daga can gefe bayan tayi musu sallamar da cikinsu babu wanda ya amsa mata. Shiru ya ratsa falon na y'an wasu dak'ik'ai, Yaya babba ne ya katse shirun ta hanyar cewa; Ke muke saurare Balkisu me ya kawo ki garemu, bayan mun riga mun gaya miki babumu babu ke har abadan da'ima." Dagowa ta yi ta kalle shi idanunsa kem a kan ta, yana binta da wani irin mayen kallo kamar zai cinyeta da ido, da sauri ta d'auke kanta a zuciyarta tana neman tsari daga sharrin shi, domin bata manta waye Yaya babba duk da shekaru sun ja. Cike da fargaba da tsananin fad'uwar gaba, ta samo gabatar musu da abin da ke tafe da ita, tun kafin ta k'arasa Al-hassan dake binta da mugun harara ya daka mata tsawa, a kausashe ya ci gaba da cewa "Ban ta6a sanin ke dabba ba ce, a cikin dabbobin ma tunkiya marar hankali ba sai yau Balki! Kina nufin ni ko d'aya daga cikin ahlina ne za mujelup nemar wa shegun y'ay'anki aure? Lallai kwakwalwar kan ki iri d'aya ne sak dana jaka shiyasa ta baki wannan shawaran na ki tunkare mu da wannan maganar. To ki sani har gaban abada babu gamin mu da shegun y'ay'anki, y'ay'an zina tsintattun y'ay'an kwararo........ " Ya isa Hassan ya isashe haka!!!" Ummi ta fada da wani irin murya mai kaushin gaske, tuni idanunta sun juye sun yi jajur, ga hawaye da tuni ya gama wanke mata fuska, Mikewa tsaye ta yi ta ci gaba da cewa a tswace "Kada ka kuskura ka sake sheganta mini y'ay'a, kada ka kuskura na ce maka, y'ay'ana ba shegu ba ne ina ji a jikina y'ay'ana y'ay'an halak ne tsarkakku!!! Ta k'arashe maganar tana nuna shi da yatsa idonta kem! Cikin nasa babu alamar tsoro ko shakkarsa a ciki sai ma tsagwaron tsana a cikinsu. Mikewa ya yi a fusace ya iso gabanta yana cewa " Ni kike nunawa yatsa, ni kike yiwa ihu Balki! To na sake fad'a cewa y'ay'anki y'ay'an zina ne shegune me zaki yi??? Saukar miyan bakinta a fuskarta ya dakatar da shi daga hargagin da yake yi, a fusace ya daga hannu zai wanke mata fuska da mari, caraf! Yaya babba ya rike hannayensa ta baya, "koma ka zauna Hassan." Yaya babba ya ba shi umarni, bai zauna d'in ba sai kawai ya fice daga d'akin yana kwafa, zuciyarsa na tafarfasa Bayan fitar Hassan, Yaya babba ya maida kallonsa ga Ummi data durkushe a wajen tana kuka mai tsuma zuciya, shu'umar murmushi ya saki, kafin ya bita ya tsuguna shima , cikin kasa-kasa da murya kamar me rada, ya fara cewa "Duk da shekaru sun ja, kina nan a balkisunki kyakkyawar mace fara kal, d'anya sharaf mai dauke da tarin baiwarwaki, kwata kwata baki tsufa ba balki, har yanzu ina nan da kudirina a kan ki, ki amincemin koda sau d'aya ne na cimma muradina a kan ki ni kuma na miki alkawarin zan tsaya miki da ke da y'ay'anki har duniya ta nad'e muddin ina numfashi. An yi ta babu dad'i sosai a gidan, domin sun yi musayen maganganu a tsakanin su,Ummi ta kauda ido ta wanke Yaya babba tas ta kira shi da fasiki dan akuya, kasancewar Tana cikin bakin ciki da bacin an sheganta mata y'ay'a da Hassan ya yi. Sosai ran Yaya babba ya 6aci, Inda ya dauke mummunan kudiri akanta idea da shegun y'ay'anta, ita kuma ta kalli cikin idanunsa ta sanar masa ta Allah ba yasa ba da Allah ta dogara, da su nemarwa yayanta aure da kar su nemar musu duk daya a gareta Allah yana nan kuma bazai ta6a bari su wulakanta ba, a karshe haka Ummi ta kamo hanya gida, babu nasara sai tarin bakin ciki da ta k'unso tare da tayar mata da tsohon mikin da ta dad'e da lullu6eshi a can karkashin zuciyarta. Su hudu ne y'an uwan marigayi mijinta Al-husssain. Mata biyu maza uku Yaya Tanimu wanda suke kira da yaya babba kasancewar shine babba a cikin su, sai Hassan sai hussain da yake mijinta, sai mata biyu wadanda ke gidajen mazajensu kowacce ta tara nata iyalin. Kaddarace ta jeho ta cikin ahlinsu ba tare da ta san sanda ta giffa a gare ta ba, ta yi gwagwarmaya sosai a lokacin duk da karancin shekarunta, ta kowane bangare ta fuskanci kalubale rayuwa, duk don kasancewarta tsintacciya mara galihu, Mara gaba Mara baya wacce bata san inda ta dosa ba. Tanimu mutuncinta yake nema ido rufe yake so ya keta mata haddi tun kafin su yi aure da marigayi, ta dauka aurenta da dan uwansa zai sa, ya rabu da ita , sai dai hakan babu abinda ya rage a kan irin bibiyar da yake yi wa mutuncinta saboda rashin tsoron Allah har da igiyar aurenta, igiyar aurenma na dan uwansa, sai dai har mijinta ya kwanta dama bai samu galaba akanta ba hakan ya haifar mata da mummuna tsana da tsamgwama daga gareshi, zata iya cewa shine ya fara hura wutar kiyayya tsakanin sauran kannensa da marigayi wanda suka dauki karan tsana suka dora mata acewarsu itace silar mutuwar dan uwansu, yayinda kiri-kiri suka sheganta mata y'ay'a, y'ay'an da bata san daga ina suke ba, kawai ta bud'e ido ne ta ganta a tare da su. Ta dauka zuwa yanzu Tanimu ya saduda, tunda shekaru sunja, bata ta6a tunani ko hasashen cewa zai kuma tayar da wannan maganar ba, sai gashi yana sake baiyana mata har yau yana nan da muradin tarayya da ita, wa'iyazubilla. Ta yi kuka ta yi bakin cikin wannan lamarin don sai da ta kwashe kwana uku tana zazzabi a tsaye saboda jimamin wannan lamari, bata cewa Al'ameen komai a kan lamarin, haka shima bai ce mata ba, sai dai shirun shi ba yana nufin bai damu bane, daurewa kawai ya ke, kullum suna tare da Aliyu shine ya ke don karfafa masa gwiwa da bashi baki, a bangare daya kuma suna nan suna wani shiri shi da Dr Abdul wanda Al'ameen din bai san da shi ba, don tun ranar da Aliyun ya mishi maganar shi suka rabu baran-baran bai kuma ambaton sunan shi ba, wannan kuma umarnin Dr din ne. Da misalin karfe biyar na yamma yaro ya yi sallama, tsakar gidan Ummi ya sanar da ita wai wani mutum na sallama da ita a waje, a lokacin ita kadai ce a gidan Fatima na islamiyya Al'ameen kuma na gurin sana'arsa, cike da madaukakin mamaki, ta ce "Balkisu aka ce ka kira ko dai Fatima." Yaron ya tabbatar mata da Balkisu ake kira, har ta ce ya je ya ce wanene, sai kuma ta ce ya barshi, ya ce wa mutumin ya shigo daure ya kirata tana zuwa, ta dade zaune tana sake-sake , kamar ta fasa fitar don hankalinta bai kwanta ba sai dai ta dake ta mike ta sanya hijab dinta ta fitan........ Oum ummeetarh 09116099486 [12/29, 2:50 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 43* Mikiya Writers Association *Masu facebook ku yi following wannan account ɗin domin samun damar cin giveaway ɗin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa* https://www.facebook.com/naeemerh.suleiman?mibextid=ZbWKwL “A'uzu billahi minashshaidanir rajim” Ummi ta furta lokacin da ta yi arba da ba‘kar fuskar Tanimu a matsayin wanda ke sallama da ita. Dakatawa ta yi daga bakin k'ofa ta kasa k'arasowa cikin zauren, sai bin shi take yi da wani irin mugun kallo, mai cike da tsana tsaba. Zuciyarta cike take fal da tsoro, amma a zahiri sam babu alamar hakan a kan fuskarta. Shu'umar murmushinsa ya saki yana jan dogon gemunsa yana binta da wani kallo, irin ta gogaggun y'an duniya tare da ce mata "K'araso mana Balkisu mai gadon zinare, Alheri ne ke tafe sa ni, na canza shawara domin daren jiya na kasa barci kyakkyawar surarki ce ta dinga yi mini gizo zuciyata ta sake kwadaituwa da son tarawa da ke, yayinda gangar jikina ke sake fallasa mini muradinta na son yin nitso a kogon ni'imarki, shine na ji a raina gara na zo mu sasanta, idan hagu ta ki sai a koma dama ko na haka ba yar shilata." Ya karashe maganar yana fitar da wata sautin murmushi mai cike da zallar iskanci. Had'e girar sama da ta k'asa ta yi babu alamaun fara'a ko sassaci ko miskala zarratin a fuskarta, ta ce "Ta Allah ba taka ba mugu fasiki dan Akuya, da yardar Allah baza ka ta6a cin galaba a kaina ba, baza ka ta6a cimma mummunar nufinka a kaina ba har lokacina ya cika na bi bayan mijina, kuma ka fita kabar mini gidana bana bukatar taimakon daga wajenka ko wani naka, Allah da na rike zai kawo wanda zai tallafa mana." Takowa ya shiga yi gareta yana fadin "Haba mana balkisu, ya zaki yi mini haka, wannan harkar fa cudanni in cudeka ne, kan ki kawai zaki mallaka min na rana d'aya, ni kuma na jiyar take dad'in da babu wani namijin da ya ta6a jiyar take irinsa a duniya, tun daga kan kwaratanki har zuwa kan mataccen mjinki, iye yan mata kar ki yi mani rowa mana, nasan ai kema kina da muradi." Ya karashe maganar yana kokarin kai hannusa jikinta. Da sauri ta ja baya hankali tashe take fad'in "Tanimu kar ka ta6a ni, ka fitar mini daga gida ni ba fasika bace irinka." Dariya ya kece da shi, ya ce "to muje cikin gidan mana ai nasan babu kowa daga ni sai ke sai Allah, kinga sai na cika tsohon muradina a kan ki ko ta karfi ne." Yana maganar yana dariya. Jin hakan ya matukar daga mata hankali, take ta sake k'amk'ame hijabinta tana sake ja da baya, yayinda shi kuma ya ci gaba da biyota har suka shiga cikin gidan. Zuciyarta ta dinga bata shawarwari shin ta juya ta runtuma da gudu ne zuwa dakinta ta datse kofa ko kuma ta nemi makami ta illata shi ko kuma dai ihu zata yi mashi. Kamar ya shiga zuciyarta ya ga abinda take kitsawa sai ji ta yi yana cewa " Kina tunanin yi mini ihu ko? To bismillah, idan kika yi mini ihu na rantse miki da Allah k'aik'ayi ne zai koma kan mashek'iya don sai kin gwammace mutuwa da irin Sharrin da zan kulla miki." "Mugu azzalumi dan Akuya Allah ya fika." Murmushi ya yi ya ja gemunsa ya ce "Balkisu taurin kai! Ni wallahi ko a yanzu kika bani kan ki na minti ashirin na miki Alkawarin a yau zan je na nemawa dan ki aure kuma na tsaya masa babu wanda zai san shege ne balle ayi masa gori, ba sai munje da nisa ba a tsakar gidan nan ma sai mu yi mu ta shi don ni ba bakon zafi bane." Ya fad'a yana murmushi tare da bin tsakar gidan da kallo. Wannan kalle kallen daya tafi ne ya bata damar zarar wuka a jikin rufin din kitchen Inda suke ajiyewa, cikin zafin nama ta kai mishi yanka cike da shammata, da sauri ya saka hannu sa ya tare yankan hakan yaba wukar damar yankarsa a tafin hannu mugun yanka kuwa, take jini ya balle, razananniyar kara ya saki tare da rike hannun, tuni idanunsa sun kada sunyi jajur, rigar jikinsa tuni jini ya bata shi kaca-kaca. Ganin yadda mini ke zirara kamar an yanka karamin dabba yasa jikin Ummi ya fara karkarwa take ta sake wukar dake hannunta, don ta tsorata ainun, tunda ta taso ita mai taushin zuciya ce ko kiyashi bata kashewa da gangan balle ace wai yau ita ce ta yanki mutum da wuka haka jina na zuba, hakan ya tayar Maya da hankalin ainun. Bata yi aune ba taji ya shaki wuyar hijabinta tare da hed'e ta da bango kafin ya shiga wanka mata mari a fuskarta, karfi ya saka ya yage hijabinta jikinta ya damk'i wuyarta ya shake, a zuciye cikin zaro jajayen idanunsa yake cewa " Ni zaki jiwa ciwo! Ni za ki yi wa lahani! Wato don kinga ina bin ki ina da lalla6a ki ko, to bari na turmushe ki ta karfi da ya ji muga ta tsiya." Yana maganar ne cikin fitar hayyaci da tsananin fusata, yayinda ya shiga kokarin keta dogon rigar atamfar dake kijinta. Babu zato wani irin wawan naushi ya sauka a gefe fuskasa wanda sai da jini ya yi tsartuwa daga bakinsa ya famtsama a fuskar Ummi, babu shiri ya sake ta tare da tallafe gefen fuskarsa ya furzar da miyan bakinsa mai gauraye da jini, saiga hakora uku turame sun biyo. Kafin ya gama tantance meya faru, Al'ameen ya yi wa wuyarsa wata irin muguwar shaka, idanunsa a waje cikin tsananin fusata ya shiga dukansa ba tare da ya tsaya tantance wanene ba. Cikin yan dak'ikai ya hada mishi mi shi jini da majina, nan ya zube kasa warwas kamar gawar sababi, bai bar shi ba ya zauna a ruwan cikinsa ya ci gaba da duka yana fadin "Mahaifiyata, Uwata ita za ka yi wa fyad'e kai waye, wallahi wallahi, sai na kashe ka, ni Muhammadul-Ameen yau sai an kashe ka." Jin shirun Al'ameen ya yi yawa yasa Aliyu dake jiransa a kofar gidan ya miko masa sak'o, ya gaza hakuri ya kutso kai cikin gidan, tun daga Zaure ya fara jiyo sambatun Ameen hakan yasa ya k'arasa cikin gidan a guje, abinda ya tarar ne ya saka shi zare ido tare da runtumawa da gudu ya shiga kokarin bambare hannun Al'ameen a wuyar mutumin da yake duka kamar Allah ya aiko shiz sun yi kokawa sosai kafin ya samu nasarar daga shi daga kan mutumin. Jijjigashi Aliyu ya shiga yi , yana fad'in" Ameen menene haka ka dawo cikin hayyacin mana." Sam Al'ameen ba ya jinsa, sai yunkurin kwacewa ya ke daga rikon da Aliyu ya yi masa yana kokarin sake kaiwa Yaya babba cafka, ganin haka yasa Yaya babba mikewa a daddafe ya fece daga gidan ba tare da ya tsaya ko neman takalmansa ba. "Ka sake ni Aliyu, wallahi sai na kashe shi , bazan barshi ba, sai na raba shi da numfashin sa." A tsawace Aliyu yace "Ka nutsu Ameen, ka kalli halin da Ummi ke ciki." Jin haka yasa shi saurin juyawa gareta, a kwance take sharaf a kasa kamar bata numfashi, da wani irin sauri ya karasa gareta ya dagota yana jijjigata tare da kiran sunanta, da kyar ta bud'e idanunta dake lumshewa ta kalle shi a kan la66anta ta furta "Ka kula da Fatima Ameen na bar maka ita amana nasan za ka iya.... Bata karkareba idanunta suka lumshe numfashita ya dauke cak! " Ummi!!!!!!!! Ya ambata da Iya dukkan karar muryarsa.............. Kunfa rage comment mutanen Joy😬 Oum ummeertah 09116099486 [12/29, 2:51 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀 ~FARHAT~ *PAGE 44* Mikiya Writer's Association Cike da tsananin tashin hankali Al'ameen ke safa da marwa a bakin d'akin bada agajin gaggawa na karamar asibitin dake unguwarsu, in da suka yi gaggawar kai Ummi bayan sun fahimci suma ta yi ba mutuwa ba, tunda suka kai ta kimanin awa hudu a tsaye yake kamar mashi, a k'ofar d'akin sallar magriba da ishsha ne kadai ya kau da shi daga wajen, Fatima na zaune a kan d'aya daga cikin bencinan da a ka tanada domin zama, sai kuka take yi idanunta sun kumbura sun yi jajur, dawowarta daga hadda ta tarar da wannan tashin hankalin ko gida bata kai ga shiga ba ta ga an fito da Umminta a sume kamar gawa, hakan ya daga mata hankali, a guje ta kutsa kai cikin napep din da aka sanya Ummi ta kamkameta tana kuka, tun lokacin take rusar kuka har zuwa yanzu da ake neman karfe goman dare. Yau dai kam kasa rarrashinta Al'ameen ya yi, Aliyu da Maman Amira wacce ta biyo su asibitin daga baya ne suke kokarin bata baki idan suka ga kukan nata ya yi yawa. Likita ne ya fito daga d'akin , da sauri suka yi caaa! A kan shi kowanne na jeho mishi tambayar da ya zo bakinsa duk a game da Ummi, kallonsu ya yi cike da tausayawa ganin yadda hankalinsu ke tashe, murmushin kwantar da hankali ya sakar musu, ya daura da cewa "Ku yi hakuri yaran Ummi, Ummi tana lafiya, firgicine ta shiga shine ya haifar mata da daukewar numfashi ta yi, dogon suma, yanzu dai Alhmdllh mun bata taimakon da ya dace ta farfado tun dazu,sa dai mun yi mata allurar barci domin kwakwalwarta ta samu hutu, zuwa safiya in dan Allah ya kai mu zamu sallameta. Hamdala Aliyu da Maman Amira suka shiga jerowa, Al'ameen ku wa rintse idanu ya yi shima yana jero hamdala a zuciyarsa, wani irin farin ciki da kwanciyar hankali na maye gurbin fargaba da tashin hankalin da ke dankare a zuciyarsa. Yayinda Fatima ta rungume Mama ta na shessheka tun da dama cikin kuka take. Aliyu da Ameen ne suka kwana a asibitin, Mama da Fatima kuma suka tafi gida, bayan sun shiga sun duba Ummi, tana barci kamar yadda likita ya fada. Bayan tafiyarsu ne Al'ameen ya samu damar baiwa Aliyu labarin abin da ya sani game da abinda ya faru, yana ba shi labarin zuciyarsa na kara daukar zafi yana sake cin alwashi a kan kassara rayuwar koma waye wannan mutumin, shi kan shi Aliyu ran shi ya baci, zuciyarsa ta tashi har yaso yafi Ameen daukar zafi a kan lamarin, ko da wasa bai ta6a kawo hakan a ransa ba, ya ciji yatsa ya fi sau shurin masaki a kan rike Al'ameen da yayi har mutumin da ko sunan sa basu sani ba ya samu damar guduwa, karshe Ameen ne ya koma tausarsa. Washegari karfe goma a ka sallami Ummi, a lokacin Fatima da Amira ne ke tare da ita don Aliyu tun wuraren bakwai ya tafi gida da zummar kimtsawa ya dawo, Al'ameen ma ganin sun zo yasa ya tafi gida don yin wanka. Sosai makota da abokan arziki sukai ta shigowa yi wa Ummi sannu, yinin ranar bata samu kanta ba, kallo daya zaka san bata cikin walwala amma haka ta daure ta saki fuskarta ta dinga amsa gaisuwar yan dubiya. Ranar da matsanancin damuwa Al'ameen ya kwana, bai iya rintsawa ba, burinsa ya ji daga bakin Ummi 'shin wanene wannan mutumin, domin baya jin har duniya ta nade zai iya yafe mishi. Washe gari da safe ko da ya je gaisheta bata ce masa komai game da batun ba, haka ya shirya ya tafi makaranta jiki babu kwari, da yamma tare suka shigo gidan da Aliyu ya biyosa don ya sake gaida Ummi duk da jiya ma yazo, kuma mahaifiyarsa da matar kawunsa harma da kannensa sun zo suma a jiyan. A falonta suka same ta zaune a kan dadduma, carbi a hannunta tana lazumi, zama suka yi suna jiranta, itama ganin shgowarsu yasa ta yi sauri ta kai karshen lazumin, Aliyu ne ya fara gaisheta da jiki ta amsa cike da kulawa, Al'ameen ma ya sake gaisheta. Daga haka duk zama suka yi jugum-jugum daga yanayin fuskokinsu ta fahimci da magana a bakunansu, ajiyar zuciya ta sauke dama ta san ko ba jima ko ba dad'e wannan ranar zata zo, bata gama tunanin da take yi ba ta tsunkayi muryar Al'ameen yana cewa. "Ummi don Allah da manzonsa ki gaya mini wanene wannan mutumin? Kallonsa ta yi sai kuma ta yi shiru, ba tare da amsa shi ba, ganin haka yasa Aliyu kar6ewa da " Ummi don Allah ki daure ki sanar da shi, domin yana cikin matsanancin damuwa ni shaida ne, saboda ni amininsa ne, muna da kusancin da bazai iya boye min duk wani damuwarsa ba, nine na ba shi shawara a kan ya zo ya tambaye ki, shi kuma ya ya dauko ni don na taya shi rokon ki, Ummi don Allah ki fad'a masa menene hadin ki da shi." Ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu, ta ce "Dama ko baka tambayeni ba Yayan Fatima yau ne na yi niyar sanar maka su wanene ahlin Alhussain a gare ku da nima baki d'aya." Aliyu ya ce "Alhmdllh Ummi, Ameen ya dade yana tsumayen wannan ranar tsayin shekaru." Ya k'arashe maganar cike da tsantsar farin ciki kamar shine Ameen d'in. Murmushi Ummi ta yi tana sake jinjina amintar dake tsakanin Aliyu da Ameen, kamar dai Fatima da Joy. Fatima ce ta shigo d'akin daga hadda take, ganin yayyinta yasa fara'ar fuskarta k'ara fad'ad'a, ta gaishesu baki d'aya a ladabce, ta wuce uwar d'aka ta ajiye hijabinta da jakar haddarta ta fito zata wucesu, har ta kai bakin k'ofa, Ummi ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Fatima! Kema zo ki zauna." Bata musa ba ta dawo ta samu guri kusa da Yayanta ta zauna, zuciyarta na tsinkewa haka kurum take jin gabanta na fad'uwa. Mikewa Aliyu ya yi, da nufin tafiya gida don ya basu waje, Ummi ta dakatar da shi da cewa; Dawo ka zauna Aliyu, domin kuwa kaima d'ana ne, tamkar Al'ameen haka nake jin ka." Bud'e baki ya yi da nufin yi mata musu, sai dai ganin yadda ta tsare gida yasa ya kasa, sai dai bai koma ya zaunan ba kamar yadda ta umarceshi, idanunta ta watsa mishi, irin kallon da take yi wa Al'ameen idan tana son ladaftar da shi, babu shiru ya koma ya zauna. Sauke kai Ummi ta yi kasa ta yi shiru duk ido suka zuba mata falon ya dauki shiru na tsayin mintuna biyu, a hankali ta dago idanunta da suke cika taf da kwallah cikin wani irin murya mai sanyi wacce basu ta6a junta da irin shi ba ta fara cewa.............. Oum ummeertah 09116099486 Downloaded From https://tknovels.com.ng