Downloaded From https://tknovels.com.ng LAUJE CIKIN NAƊI. NA ZAINAB FALALU (MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU Page 1 Cikin sanɗa ta tura ƙofar ɗakin, ganin ƙofar ta buɗe yasa ta sauke ajiyar zuciya me nauyi Seda ta waiwaiga taga ba motsin kowa tukun ta saka kanta kai tsaye cikin ɗakin Seda ta gama ƙare ma ɗakin kallo ta lumshe ido tana shaƙar mayen ƙamshin turaren da ko a bacci taji shi ta san na waye, tukun ta ƙarasa inda taga agogunan shi a jere Tas ta gama ƙare musu kallo, seda ta darje tukun ta ɗauki wanda suka fi ko wanne tsada a ciki, ta ɗaga rigar ta saƙa ta ɓoye su Motsin data ji ne ya sa bata kai ga taɓa sauran abubuwan ba ta fice da sauri Tana fitowa daga ɗakin ta hango shigowar shi gidan Da sassarfa ta kwasa tayi hanyar part ɗin su tana tallafe da agogunan data ɗakko tana jin yarda gaban ta ke dukan uku-uku a duk sanda tayi dafe La haula wala ƙuwata illa billah! yanzu inda ban ankare dake ba da shikenan kin min illa kin sa na yanke, ki sabauta ni haka kurum mumtaz Mumtaz da ake maganar domin ta tuni ta ƙule can cikin bedroom dan ko waiwayowa bata yi ba, ballanta na tasan me tayi Tana shiga ta banko ƙofar da ƙarfi sannan ta murɗa key Ta window taci gaba da leƙen ya Faruƙ dake tafe hankalin shin na ga wayar da yake, Kamar walƙiya yaga giftawar mutum da gudu amma hankalin shi be kai ga kowaye ba, waya ce me muhimmanci yake amsawa shiyasa be wani damu da ya san waye ɗin ba. Seda taga shigewar sa tukun ta sauke ajiyar zuciya tana komawa da baya ta zauna Ɗaga rigarta tayi ta ciro agogon, ƙare mishi kallo tayi sosai sannan tace "Daga gani zasuyi mugun tsada, Komi na ya Faruq me kyau ne wallahi, Jakar islamiyar ta tajanyo ta saka agogon tukun ta rufe ta maida sannan ta fito palon inda mama take Zama kusa da Mama tayi ta zabga tagumi ta kafe ta da ido Maman tana kallon ta tayi fuska kamar bata san da zaman ta a wajen ba taci gaba da yanke farcen ta tana magana da atine dake kitchen tana haɗa kayan shan ruwa, da yake yamma ta gabato ana gab da a kira sallar magriba. Murya a sanyaye Mumtaz tace "mama yau ba aikin da zan yi ne ni?" ko kallon ta bata yi ba ballanta na ta saka ran amsa mata Ganin ba amsa mata maman zatayi ba yasa ta miƙe jiki a sanyaye ta koma ɗaki tayi kwanciyar ta dama ba ƙaramin jin azumin yau take ba, ko gudun data yi ɗazu shima dan ya zama dole ne dan in har ta kuskura ta shiga hannun yaya faruƘ to tabbas se dai buzun ta dan tsaf se ya sauke mata waɗan nan yatsun nashi kamar itace bama biyar ɗin ba goman duka ze sauke mata Juyi tayi ta gyara kwanciyar ta, tayi shiru tana tunanin wannan muguwar halayyar ta ɗauke-ɗauke datake yi kan kice me hawaye suka cika idanun ta kamar zasu zubo, Da iyakacin ƙarfin ta tahanasu sauka ta maye gurbin su da murmushi, cikin zazzaƙar muryar ta me daɗin sauraro tace "Komi yana da lokaci, Allah ka yaye min wannan ɗauke-ɗauken da nake yi na ba gaira ba dalili' kiran sallar magriba ne ya fito da ita palon inda aka jera komi da komi na buɗa baki Dabino uku ta ɗauka ta taci tukun ta wuce toilet ɗin palon ta ɗauro alwala Seda ta gabatar da sallar magrib kafin ta ƙaraso ta zauna kamar yarda kowa da kowa ke zaune ana shan ruwa. Sama-sama ta tsakuri abincin, ita she ƙarshe zama kuma itace ta fara tashi Ba wanda ya kula ta, kusan haka ɗabi'ar ta take, bata fiya son cin abinci ba, tafi auki a kayan ƙwalama, shiyasa gata nan bata da wani auki na azo a gani. Gaba ɗaya gidan suka hallara a babbar harabar gidan inda anan yaya faruƙ yake jan su sallar asham in har yana gari Manyan su da yaran su, kowa na wajen amma banda mumtaz, sakina ce dake zaune kusa da mama kawai ta lura da rashin ta a wajen, A hankali tace "Mumtaz bata fito ba mama" Kafin maman ta buɗe baki suka ga tawowar ta da sauri Bawanda mumtaz ta kalla ta samu gefe ta shimfiɗa dardumar ta tabi sahu Tunda suka ɗago daga sujjada ta ƙella ido akan carbin dake aje a gaban umma babba ta rasa sukunin ta gaba ɗaya, Salla ake amma ita tunanin gaba ɗaya ya tafi ta inda zata ɗauke carbin Har aka sake komawa sujjada mumtaz bata ankare ba Can ƙasan zuciyar ta tace "bari a tafi sujjadar ƙarshe, ai nasan ya faruƙ jimawa yake, har in ɗauke shi ma ba lale ne a ɗago ba" Haka tayi ta fakon wannan carbi har aka kai sujjadar ƙarshe Cikin sanɗa ta janye jikin ta, ta matsa kusa da umma babba, cikin ƙwarewa a harkar ta saka yatsar ta ƴar manuniya ta janyo carbin, seda taji shi gaba ɗaya a hannun ta tukun ta juya a hankali bayan ta cusa shi a cikin rigarta tkun ta koma kan dardumar ta tayi sujjada kamar yarda taga kan kowa a ƙasa. Sosai Umma babba tayi mamakin rashin ganin carbin ta, har Aunty dake gefen ta take tambayar ta da "lafia umma babba?" Da mamaki tace "na rasa ina na wurga carbi na wlh, abun mamakin da shi na fito ba" Kyaɓe baki aunty tayi, bata sake cewa komi ba taci gaba da tasbihin ta tana ɗan dudduba wayar hannun ta sama-sama Itama umma babban shiru tayi, taci gaba da mamakin ta ita kaɗai a cikin ranta Ɗaya bayan ɗaya ahalin gidan suka rinƙa watsewa kowa na kama gaban shi, kowa ya kama hanyar part ɗin su Ya faruƙ na zaune be kai ga tashi ba, mumtaz na ɗago kai taga ya rage daga ita se ya faruƙ se kuma ya Tk dake waya tayi saurin miƙewa da sauri zata bar wajen Tsautsayi wannan carbin na umma babba data ɗauka ya faɗo Caraf akan idon ya faruƙ da ya kafe ta da kallon tuhuma yana kallon carbin yana kuma kallon ta at thesame time Wuri-wuri mumtaz tayi da idon ta tana kallon shi, gaba ɗaya rashin gaskiya ya bayyana a tattare da ita A hankali ta saka hannun ta ɗauke carbin sannan ta kwasa da gudu tayi hanyar part ɗin su, tana yi tana waiwayen shi ganin har lokacin be ɗauke idon shi a kanta ba. Seda ta ƙule ma ganin shi tukun ya kauda kan shi yana mamakin rashin nutsuwa sam na mumtaz kusan so biyu kenan yana kama ta da makamancin abubuwa shigen wannan Ƙwata ya ja tukun yace "zan saka miki ido kuwa" Tashi ya faruƙ yayi ya wuce ɗakin shi waya kare a kunnen shi yana sauraron saƙon da Abba babba ke bashi akan rabon kayan masarufi da za'ayi ma bayin Allah saboda alfarmar watan ramadana da ake ciki. Mumtaz na shiga part ɗin su ta wuce palon mama, Tana shiga ta iske yayun ta da suke uwa ɗaya uba ɗaya zaune a palon suna fira mama na daga gefe tana duba list ɗin sunayen ƴan'uwa da abokan arziƙi masu ƙaramin ƙarfi tana fidda list ɗin wanda ya kamata ayi ma kayan salah Ɗago kai mama tayi ta kalli mumtaz da alamun rashin gaskiya ya bayyana a gare ta Cike da kulawa mama tace "zo nan mumtaz" A tsorace tace "ina zuwa mama, futsari nake ji" ta yi hanyar ɗakin su da sauri tana ƙara damtse carbin hannun ta. Seda ta adana shi tukun ta fito ta zauna kusa da mama tace "gani" Kafe ta da kallo mama tayi tace "Anya akwai alamun gaskiya kuwa a tattare dake mumtaz, ƴan watannin nan sam na kasa gane ki, kwata-kwata baki da nutsuwa kullum in aka ganki a zabure kike, kodai basir ɗinki ya tashi ne mumtaz?" Shiru mumtaz tayi tana kallon, ya Ahmad da yake dariyar basir da mama tace Jiki a sanyaye ta girgiza kanta, sannn tace "be tashi ba mama" Sosai mama ta hauta da nasihar ita ƴa mace da nutsuwa aka santa, ba wai komi ta rinƙa yin shi a hauka-hauka ba Abinda mama bata sani ba shine duk maganar nan data ke ma mumtaz yana shiga ta kunnen dama ne ta fice ta kunnen hagu, hankalin ta gaba ɗaya na kan ɗayar wayar ya Ahmad da ya aje a hannun kujera Lissafin ta kawai yarda zata ɗauki wayar ba tare da an samu matsala ba, Ganin yarda mumtaz tayi shiru kamar tana sauraron abunda maman ke cewa yasa mama taci gaba da kawo mata misalai da sauran ƴammatan gidan da suke sa'annin ta Nuna mata take saboda tsabar rashin nutsuwar ta yasa ko saurayi yazo wajen ta baya sati uku ze kama gaban shi, tun suna zuwa har sun dena zuwa Murmushin ta me kyau mumtaz tayi, kallon mama tayi tace "Saboda haka kenan suka dena zuwa waje na mama?" Sosai mama ta buɗe ido akan ta, sannan tace "ai duk ɗa namiji yana sonbya samu mace nutsatstsiya me nutsuwa sosai, amma a yarda kike yin abubuwa haka ai dole saurayi ya gudu" Murmushi mumtaz tayi, bata sake cewa komi ba, sema kishingiɗa data yi tana jiran sa'ar ya Ahmad akan wayar data ƙwallafa rai akan ta. KAMAR YARDA NACE, IN SHA ALLAH NAN KUSA ZAN FARA SAKIN SHI, SABODA MASU TAMBAYA NA DAN ALLAH IN ƊAN GUTSIRA MUSU KAƊAN DAGA CIKIN LABARIN, TO GASHI NAN, INA MUKU FATAN ALKAIRI ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU (MRS SULAIMAN) WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg2 Tana a nan zaune jiran tsammani bacci yayi awon gaba da ita, har su ya Ahmad suka tashi bata sani ba Wajajen goma mama ta tashe ta tawuce ɗaki Da wannan wayar ta farka, tunda ta buɗe ido taga wayam sun tashi ranta ya ɗugunzuma ya ɓaci Haka tayi ta zumɓure-zumɓurenta ta haƙura ta shige ɗaki. WASHE GARI Ƙarfe takwas da rabi na safiya ƴammatan gidan suka fito kusan a tare Dukkan su sanye suke da blue dogayen hijabai Su shida ne kyawawa da su ma sha Allah Parcking lot suka wuce inda bala driver ke jiran su Kowa ya shiga mota banda najwa data waiga ba ta ga mumtaz ba Da sauri tace "Ina zuwa mlm bala, bari in taso kira mumtaz Bata jira cewar su ba ta juya da sauri har ta na haɗawa da ɗan gudu-gudu knocking ƙofar part ɗin su mumtaz da basu buɗe ba tayi cikin nutsuwa Cikin bacci Altine me aiki taji knocking ɗin, da sauri ta taso ta zo ta buɗe ƙofar A ladabce najwa ta gaishe da altine tukun ta shige ciki Direct ɗakin mumtaz ta wuce tana kiran sunan ta Mumtaz na tsaye gaban mirrow tana saka nata hijabin najwa ta shigo Ganin ta a tsaye yasa ta tsaya itama, tace "nasha baki tashi ba ai" Fuska a sake mumtaz tace "Tun asuba ban koma ba, sam na kasa komawa se yanzu da lokacin islamiya yayi nake jin baccin wallahi" Dariya najwa tayi tace "na saba jin wannan zancen naki malama, koya ya shiga mota fa, muje" Tana gama faɗin haka ta juya ta fice Jakar islamiyar ta dake ajiye gefe ta ɗauka, seda ta buɗe jakar ta ga ajiyar ta na nan tukun ta rufe ta sagala sannan ta janyo ƙofar Ɗakin mama ta leƙa taga bata tashi ba ta wuce bayan ta sallami altine Mumtaz tasan sarai jiran ta suke, tunda ta fito suka haɗa ido da hafsa taga yarda ta banko mata harara yasa ta koma tafiya ɗai ɗai kamar bazata taka ba, ba dan komi ba se dan ta sake ƙular da hafsa Daga ƙofar part ɗin su zuwa wajen parcking lot ɗin seda tayi mugun ɓata musu lokaci kafin ta ƙarasa, Da ka gani kasan da gangan take, tsabar neman magana ne Abunda bata sani ba shine, tunda ta fito ta fara tafiyar ta ya faruƙ ke kallon ta da mamaki a fuskar shi, sarai zaka ga zallar neman fitina da neman saka su suyi latti a fuskar ta Kasa cewa komi yayi yana jiran ganin gudun ruwan mumtaz ɗin har ta ƙarasa wajen motar inda suke jiranta Daga can ya hango yarda take murguɗa ƙaramin bakin ta, da dukkan alamu rashin kunya take ma hafsa dan tana gaba da ita a shekaru Seda ta gama murguɗe-murguɗen ta tukun ta buɗe baya kusa da najwa ta zauna, tukun bala driver yaja suka tafi. Seda ya faruƙ yaga fitar su tukun ya maida idon shi kan systerm ɗin shi dake ajiye akan stool ɗin gaban shi yana shigar da wasu bayanai. Suna shiga aji mumtaz ta kalli najwa dake ƙoƙarin zama a gaba tace "hour ɗaya kafin a tashi ki tashe ni dan Allah" Balla mata harara najwa tayi kafin tace "wai da gaske baccin zaki yi yau ma?" Seda mumtaz ta rama hararar da najwa tayi mata, kanta tsaye tace "kina da damuwa ne a ciki?" Banza najwa tayi da ita, dan ta san ba ƙaramin aikin mumtaz bane tasa su raba hali Ganin najwa ta juya yasa mumtaz sake maimaita mata tafa tashe ta kafin a tashi, tukun ta juya ta koma can baya ta zauana. Tun kafin a fara tafsir bacci me nauyi yayi awon gaba da ita, ba itace ta farka ba har seda aka tashi sannan najwa ta tashe ta suka fito Tunda suka fito mumtaz ke mata ƙorafin taƙi tashin ta Da dai najwa ta gaji da ƙorafin mumtaz tace "inda na tashe ki ina zaki je to?" Tsaki mumtaz taja, tukun tayi gaba inda anan bala driver ke ɗaukan su ta barta a nan Sosai mumtaz ta haɗe rai har suka kai gida, bata ce ma kowa uffan ba ta wuce part ɗin su duk ba haka ranta yaso ba. Bilkisu da hafsa na ganin wucewar mumtaz har wani rige rigen tambayar najwa suke da "me akayi ma warcan mara kunyar ne?" Murmushi kawai najwa tayi, bata basu amasa ba, itama ta ɗauki jakar ta tayi nasu part ɗin. Sosai rana ta take, kusan kowa na side ɗin shi yana bacci, dan azumin yau yana ƙwala jama'a Tunda mumtaz ta shiga part ɗin su ta tabbatar da kowa bacci yake bata yi ƙasa a gwiwa ba ta yi maza ta cire hijabin uniform ɗin ta tasauya wani, Jakar makarantar ta buɗe ta ɗauki wannan agogunan da ta ɗakko a ɗakin ya faruƙ ta saka a hand bag ɗin ta, se ƙaramar wayar ta nokia data saka a ciki, sam bata lura ba ko sisi a ciki ba, haka ta fice sauri-sauri tayi waje, ko ta kan mama dake bacci bata bi ba tayi waje tana waiwaye kamar warce za'a ce ma tak ta kwasa da gudu. Dai dai ya faruƙ ze tashi daga wajen da yake zaune yaga fitowar Mumtaz da sauri, tana yi tana waige, rashin gaskiya ƙuru-ƙuru a tattare da ita Shiru yayi yana kallon ta har ta fice ta ƙaramar ƙofar gate ɗin gidan, Cikin ɗaga murya malam ado yace "Sauka lafiya zankaɗaziya" Haka ya ke kiran Mumtaz tun tana ƙarama Cuno baki mumtaz tayi ta ƙarashe ficewa da sauri, dan kar tsautsayi yasa wani a gidan ya ganta. Ya faruƙ har ya juya ciki, amma zuciyar shi sam ta kasa nutsuwa, a rayuwar shi be cika shiga abinda ba ruwan shi ba, amma sam ya kasa nutsuwa da yarda yaga fitar mumtaz. Haka ya danne ya buɗe ƙofar ɗakin shi ya shige, Amma me?, kwata kwata ya kasa samun nutsuwar rai ganin ya kasa nutsuwa yasa ya juya ya fice da sauri yayi hanyar fita shima Wayam layin, ba alamun mutum ko ɗaya a layin, yanayin layin dama bana jama'a bane, da wahala kaga mutum tafe a ƙafa Haka ya gama wurwurga manyan idanun shi da suka zama na gado ya haƙura ya juya cikin gidan da niyar shima ya ɗan kishin giɗa zuwa yamma, lokacin ranar ta ɗan yi sanyi. Seda ya watsa ruwa tukun ya kwanta, amma sam ya kasa baccin da yayi niyar yi, al'amarin mumtaz na daɗa ɗaure mishi kai, shi ya san kaf yaran gidan nan babu warce ta kai nutsuwar ta, amma wannan dawowar da yayi yaga saɓanin haka daga gare ta Can daga ƙasan zuciyar shi tace "Ka sani ko dama lumbu lumbu take, dan ba'a shedar mutum" A sanyaye ya faruƙ yace "Haka ne, amma ya zama dole in saka mata ido, ba mamaki mugayen abokai tayi" Da wannan tunane tunane bacci yayi awon gaba da shi. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg3 Babbar kasuwar seye da sayarwa na diamond da gold na garin mumtaz ta nufa kai tsaye Seda suka isa tukun ta tuna da bata da ko sisin da zata ba me keken data ɗakko Nan fa ido ya raina fata, Me kekenapep ya kafe ya tsare, kai da fata besan wani zance ba in ba na kuɗin shi ba Mumtaz na tsaye ƙwale da idanu kamar zata fasa ihu akan tereren da me keken ke mata Murya ƙasa-ƙasa tace "Da Allah fa nake haɗa ka bawan Allah, wallahi ban san ba ko sisi a cikin jakar ba" Cike da hargowa ya yunƙuro kamar ze make ta, da sauri ta ja da baya tana ƙara danƙe jakar ta tamau A fusace yace "Wallahi tallahi in baki bani haƙƙi na ba se ba miki tsinannan duka a wajen nan, se in ga uban da ya tsaya miki" Fuska a ɗaure Mumtaz ta ɗaga mishi hannu tace "ah, dakata mlm, zagin ya tsaya kaina kar ya kai can, inda yanzu zaka ga waɗan da suka tsaya min da bakin ka ba ze ƙara furta ko da kalma ɗaya a wajen nan ba, kawai ka nutsu muyi sulhu tunda ni na kawo kaina" Ta ƙarashe maganar tana jujjuya manya idanun ta na gado. Da zafin nama me keken ya sakko yayo kan Mumtaz da ke tsaye Ƙiris ya hana ya sauke mata yatsun shi biyar a kumatun ta Allah ya kawo wani matashin saurayi da tunda suka fara dramar kuɗin yake kallon su Da sauri saurayin ya riƙe hannun me keken, fuska a sake yace "Haba kai kuwa, ya zaka daki mace kamar ba na miji ba?" A fusace ɗan keken ya ƙwace hannun shi, cike da kumfar baki yace "Banda tsabar wulaƙanci ɗakko yarinyar nan nayi, duk da zafin ranar nan da kuma ƙishirwa be sa na kwanta ba, na fito neman halali na amma dan ta raina min hankali se da na kawo ta zata ce min bata san babu kuɗi a jakar ta ba" Nunata yayi sannan yaci gaba "To wallahi ko waye ya tsaya mata yau ɗin nan se ta bani haƙƙi na, ko kuma na daki kuɗi na" Cikin nutsuwa saurayin ya waiga inda mumtaz ke tsaye tana wani karkaɗa jiki, Murmushi yayi, sannan ya waiga yace wa me keken "To nawa ne kuɗin naka?" Baki a bushe yace "Ɗari biyar ne". A aljihun rigar shi ya saka hannu ya ciro sabuwar dubu ɗaya ya miƙa mishi warce dubun yayi ya juya ya shiga keken shi yana mita Da sauri Mumtaz tace "Ɗari biyar ce haƙƙin ka malam, se ka kawo canjin na samu na komawa gida" Duk yarda me keken nan ke ɗaurewa seda maganar Mumtaz ta bashi dariya Shi kuma saurayin na gefe yayi folding hannuwan shi a ƙirji yana kallon Mumtaz cike da mamaki da kuma ban dariya Mumtaz kam har ga Allah da zuciya ɗaya tayu maganar, Daga bayan su suka tsinkayi muryar saurayin yace "Ki barshi ya tafi, ke se in maida ki gida a mota ta" yayi maganar yana nuna inda yayi parcking motar shi da hannu. Ko tsayawa me keken ya ƙarasa jin zancen beyi ba yayi gaba abun shi. Seda ya ɓace ma ganin mumtaz tukun ta waigo da fuskar ta inda saurayin ke tsaye yana kallon ta tun daga sama har ƙasa Tana juyowa idanun ta suka sauka a cikin nashi, Da sauri ta sauke kanta ƙasa tana wasa da hannun jakar ta dake cikin hijabi Murmushi ya sakar mata, Cike da ƙwarewa a magana yace "im khalid, and u?" Kanta a ƙasa kamar ba zata ce komi ba, Har ya fitar da ran jin wani abu daga gare ta, can dai tace "MUMTAZ" can ƙasan numfashin shi ya maimaita "mumtaz" Murmushi sosai ya sakar mata a wannan karon, sannan yace "unique name" murmushi itama tayi sannan tace "nagode". Tana gama faɗin nagoden tayi gaba Da sauri khalid ya bita a baya yace "Ah ya zaki tafi kuma ki barni bayan bamu gama magana ba?" Be jira cewar ta ba ya sake cewa "ina ma zaki je tukunna?" Yana mata wannan tambayar ta tsaya cak gaban na dukan uku-uku, sarai zaka ga hakan ga fuskar ta Kafe ta da kallon ƙurilla yayi yana jiran jin me zata ce Ganin bata da niyar cewa komi yasa yace "tunda ba zaki faɗa min ba, muje to na rakaki" Da sauri Mumtaz tace "na fasa, gida zan koma" Shiru khalid ya sake yi yana kallon ta Can yace "Muje na sauke ki to" Da sauri ta girgiza kanta tana yin gaba da sauri Haka khalid yayi ta binta yana roƙonta akan ta tsaya ya sauke ta amma firr mumtaz ta ƙi yarda Badan yaso ba ya sake tsaida mata ɗan keke Yana ji yana gani ta tafi, ko arzikin number wayar ta be samu ba. ****Duk a tunanin mama mumtaz sun dawo tana ɗakin su, Yau da yake a general kitchen za'ayi abincin buɗa baki yasa tun da akayi sallar azzahar matan gidan suka hallara a babban kitchen ɗin dake ta can ƙarshen makeken gidan dake ɗauke da ahalin gaba ɗaya ko wacce mace da ƴan aikin ta, se ɗaiɗai ku na daga cikin ƴaƴan gidan da suke ɗan taɓa wani abun a wajen. Cike da haɗin kai suke aiyukan su, Yawanci duka matan suna zazzaune akan kujeru suna basu order abubuwan da za'ayi Sun jima suna aikace-aikacen su suna taɓa fira sama-sama Ganin duka yaran gidan sun fito waje, mama ta kalla taga mumtaz ce kawai babu Atine ta ƙwala ma kira daga can in da suke Da sauri atine ta tawo tana amsawa Kallon ta mama tayi tace "Je ki taso min mumtaz, bacci ya isa haka" Da "to" atine ta amasa tukun ta wuce part ɗin maman kai tsaye Mumtaz na cire hijabi atine tayi sallama a ɗakin Da sauri mumtaz ta waiga tana kallon ta, Seda ta sauke ajiyar zuciya, duk a tunanin ta mama ce, tukun tace "ya akayi ne?" Atine tace "mama na kira" ta juya ta fita. Seda Mumtaz ta adana waɗan nan agogunan sannan ta gabatar da salla tukun ta fito zuwa kiran maman. A hanya kafin ta ƙarasa kitchen ɗin suka yi kiciɓus da yaya faruƙ da ya kafe ta da kallo tun fitowar ta daga part ɗin su Ita sam bata lura da shi ba seda ta kawo daf da shi Fuska a ɗaure bayan ta kawar da kai gefe tace a taƙaice "ina wuni" Be bi ta kan gaisuwar ta ba yace "After asham kizo ki same ni a ɗaki" Ko kallon ta be kuma yi ba ya wuce abun shi. Jin kalmar ta same shi a ɗaki ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, sosai tsoro da fargaba suka kamata Murya ƙasa-ƙasa tace "ko dai ya duba bega agogunan shi bane ni mumtaz"? Ta jima tsaye a wajen tana saƙa da warwara, can dai ta yanke hukuncin ƙin zuwa kamar yarda ya umarce ta. Ƙarasawa tayi inda su mama suke a ka ci gaba da aikin da ita. Wajen biyar da rabi na yamma suka kammala, su Mumtaz, Najwa, Bilkisu da Hafsat ke ta kwasan manyan kulolin suna kaiwa kan babban dinnig ɗin gidan suna jejjerawa, inda lokaci zuwa lokaci ake haɗuwa duka iyalan aci abinci Seda suka gama tas, tukun kowa ya koma part ɗin shi domin yin wanka kafin kiran sallah. SHARE PLS. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 p4 Ahalin gidan gaba ɗaya kowa da kowa ya hallara a babban ɗakin cin abincin da yake musamman sabida lokuta irin haka dama Cikin nutsuwa kowa ke cin abinci, baka jin motsin komi sai cokula, se kuma waya da wasu daga cikin ƴan mazan dake amsawa lokaci zuwa lokaci. Ba wani abincin kirki Mumtaz taci ba, Ƙaramin bowl ta ɗauka ta zuba pepper soup ɗin cat fish ɗan madedeci ta fakaici idanun kowa tukun ta fece zuwa part ɗin su, duk dan gudun kar su ƙara arangama da ya faruƙ Bata san yana lura da duk wani motsin ta ba, duk da a zahiri zaka ce besan da wanzuwar ta ba a wajen, amma kar yake kallon ta. Tana fitowa ta sauke ajiyar zuciya, a bayyane tace "Na sha a wannan karon, sallar ma a ɗaki zanyi ta tunda ba'ace dolen dolen mutum se yayi ta a cikin jam'i ba" Ta ƙarashe maganar haɗe da murguɗa baki. Ɗan karkatawa Abba ƙarami yayi saitin kunnen mama yace "Wani abun kika daka Mumtaz halan?" Saitin ƙofa mama ta kalla sannan tace "Ba abunda na saka ta, ƙila ta ƙoshi ne, kasan bata fiya zama taci abinci kamar yarda kowa keyi ba" Abba ƙarami ba sake cewa komi ba, sema ɗan yatsina fuska da yayi yana streaching wuyan shi da kwana biyu yake ɗan sagewa, kamar irin be kwanta da kyau ɗin nan ba. Ya faruƙ ne ya fara tashi, Sannan ɗaya bayan ɗaya ƴan samarin suka fara watsewa daga teburin cin abincin suna ficewa, Cike da isa Umma babba tace "Hafsa, ku tashi ku kwashe plates ɗin nan, uwayen son jiki" Ta ƙarashe maganar tana miƙewa haɗe da kara wayar ta dake ringing ga kunne Tas su Najwa suka gyara wajen kamar yarda suka shirya shi a ɗazu, kowa da abinda ya ɗauka yake yi, banda Hafsa dake ƙorafin bata ga Mumtaz ba, ai ba su kaɗai ya dace su rinƙa aikin ba Da yake ƙasa-ƙasa take ƙorafin ta yasa Umma babba bata jiyo ta ba, dan ita ta mammake mutum ba wahala yake mata ba Macece me son iyawa da kuma kamewa, bata ɗaukar raini balle shashanci, kuma bata fiya shiga sabgar mutane ba, in abu be shafe ta ba da wahala kuga ta saka baki, amma tana da mugun kishin zamantakewa, se ka zauna da ita sosai zaka fahimci hakan. Mama, aunty, umma ƙarama da mummy suma suka kama gaban su, kafin lokacin sallar isha yayi, ko wacce tayi part ɗin ta suka bar iyayen maza kawai a babban palon da tun bayan gama cin abincin suka koma cikin palon. Cike da kulawa Abba babba ya kalli Abba ƙarami yace "Ina lura da yanayin ka se streaching baya kake, badai ciwon bayan bane ya dawo?" Murmushi Abba ƙarami yayi, yana lumshe idanun shi dake nuna tsabar gajiya tukun yace "Ɗazun nan na fara jin alamun shi dai, amma ina tunanin gajiya ce, in nayi bacci zan warware in sha Allah" Da "Amin suka amsa dukan su Seda suka gabatar da sallar isha'i suka ɗora da asham kafin kowa ya kama gaban shi. Tunda ya faruƙ ya shiga ɗaki yaƙi cire riga saboda yana jiran Mumtaz Ɗabi'ar shi ce sam baya son zama da riga, komin sanyi kuwa Haka ya zauna tun yana kallon agogo har ya gaji da jiran ta Se a lokacin ya fara recalling befa ganta a wajen salla ba Ƙwata yaja tukun ya tashi ya cire rigar shi, List ɗin da Abba ƙarami ya bashi ɗazu ya janyo ya hau duddubawa yana fitar da wanda ya dace ya fitar ya bar wanda ya dace ya bari, Ba shine ya gama ba, se wajen sha biyu saura, tukun ya kishingiɗa. Tun da mama ta koma part ɗinta ta hau Mumtaz da faɗan rashin fitar ta salla da kuma tashi data yi bata tsaya an gyara wajen cin abincin da ita ba Marairaice murya Mumtaz tayi sannan tace "kaina ne ke fa ciwo shiyasa ban fita ba mama" Taɓe baki mama tayi, tace "Da dai ban san halin ki ba, in bakiyi sharar masallaci ba ai kya yi ta kasuwa" ta juya tayi ficewar zuwa palon Abbah ƙarami da shima shigowar shi kenan. Direct kitchen ɗin palon ta nufa, butar shayi ta ɗora akan gas bayan ta zuba kayan ƙamshi da ruwa Seda ya dahu tukun ta juye a ƙaramin flask golden colour tukun ta ɗora a tray ɗan madedeci bayan ta ɗora ƙananun cups biyu da kuma glass ɗin sugar akai, tukun ta fice zuwa palon Abba ƙarami Zaune yake ya kafa kai da gwiwa mama ta shiga, tana ganin a yanayin da yake seda gaban ta ya faɗi Jiki a sanyaye ta ƙarasa ciki, ajiye tray ɗin hannun ta tayi sannan ta zauna a kusa da shi Jiki a sanyaye ta ɗora hannun ta a kafaɗar shi, bata ce komi ba se ɗan shafa bayan shi data ke alamar rarrashi. A jejjere Abba ƙarami ke sauke ajiyar zuciya, sun ɗan jima a haka kafin ya ɗago idanun shi da suka yi jajir Kafin yace komi mama ta rigashi faɗin "Dukkan tsanani yana tare da sauƙi yallaɓai, tunda har warcan shawarar da na baka ba zatayi aiki ba, dole mu rungumi haƙuri sannan mu ƙara ƙaimi wajen kaima Allah kukan mu, shine yasan abunda muka sani da wanda bamu sani ba" Murya a sanyaye Abbah ƙarami yace "Maganar ki haka take, amma can ƙasan raina ina jin wani mugun yanayin da ke ƙoƙarin taɓa min zuciya, faɗuwar gaban da nake ji sam bata barina na aiwatar da komi cikin salama, amma ba komi ƙila dalilin hawan jinin nan ne yasa nake jin hakan" ya ƙarasa maganar yana ƙirƙirar murmushi. A hankali mama tace "shima ze iya sawa" Flask ɗin shayin ta janyo ta zuba mishi. Suna a haka Ahmad da mus'ab suka shigo a tare bakin su ɗauke da sallama Akan laɓɓa Abba ƙarami ya amsa musu yana jiran yaji me kuma suka zo da shi. "Mus'ab ne ya fara magana cikin inda inda "Abbah, dama akan maganar tafiya umarar ne, mun gama shiryawa ni da Ahmad gobe da yamma zamu wuce" Mama na gefe ta zuba musu idanu da mamaki sosai a fuskar ta Abba kuwa murmushin da yafi kuka ciwo yayi, yasan ze iya jin abunda yafi wannan ba daga bakin su, wannan zuwan ma da suka yi yasan ba da son ransu suka zo ba Duk da haka a matsayin shi na uba be kamata yayi musu shiru ba akan muguwar ɗabi'ar rashin shawarar da sam basayi da shi ko da mahaifiyar su ba Gyaran murya Abba ƙarami yayi yana ajiye mug ɗin hannun shi a kan table ɗin gaban shi Ɗaya bayan ɗaya yake kallon Ahmad da mus'ab da ke zaune kansu a ƙasa Ɓacin ranshi keson fitowa fili, amma ya danne ya kalle su ya ce "Yanzu kun kyauta akan wannn halin naku?" be jira cewar su ba ya ɗora da "A matsayina na mahaifin ku ai naci arizikin a sanar dani kafin ku aiwatar da komi zakuyi, dukkan ku ina lura da sabbin halayen da kuka tsiro da su, So har kunyi arzikin da zaku iya biyan ummara, kuma har kk biya se zaku tafi muke da arzikin ji ko?" Kansu a ƙasa suka haɗa baki wajen faɗin "a'a Abbah" Murmushi ya sake yi sannan yace "Yanzu nayi asarar kuɗin da na biya harda ku kenan?" caraf mus'ab yace "zaka iya sawa ayi refunding maka ai Abbah, mu mun riga da mun gama shiri" Shiru yayi ganin mama na gaf da fashewa da kuka a gaban su yasa Abbah ƙarami saurin faɗin "ku tashi kuje, Allah ya kaiku lafia" Kamar wa ɗanda suke kan ƙaya haka suka tashi har suna gwaren fita. Aikuwa suna fita hawayen mama suka ɓalle, sam ta kasa riƙe su tsabar yarda zuciyar ta ke mata zafi Abba bece komi ba, ya kamota ya rungume ta tsam a jikin shi yana shafa bayan ta alamar rarrashi. SHARE PLS ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 WALLAHI YAWAN SHARHIN KU YAWAN SAMUN UPDATE AKAI-AKAI 😎 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg5 Seda yaji mama na sauke ajiyar zuciya akai-akai tukun ya buɗe baki a hankali kuma cike da rarrashi yace "Kiyi haƙuri ina a kan umarnin hajiya ne, abu ɗaya na sani shine komi yana da lokaci" Kasa cewa komi mama tayi, sema ɗan zamewa data yi anan kan kujerar ta kwanta haɗe da lumshe idanun ta. shayin da Abba ƙ be ƙarashe sha ba kenan, shiru yayi yana ci gaba da tunane tunanen da suka aure shi tun shekarun baya. WASHE GARI Abba ƙ na zaune a ɗan madedecin palon shi na sama inda ba kowa ke shigar shi ba Hankalin shi da na mama ya tafi ga tafsirin da akeyi a sunnah tv, Baka jin motsin komi sena tv, se kuma air con da take aiki Kusan 1hr suna sauraron tafsirin kafin a gama Sama-sama suke ɗan taɓa hira, can Abba ƙ yace "Miƙo min warcan yawar" Tashi mama tayi ta ɗakko mishi duka wayoyin a inda ya aje ta kawo mishi Yana karɓa kai tsaye dialing no ɗin ya faruk yayi. Fitowar ya faruk daga wanka kenan yaji ringing ɗin wayar shi Ganin sunan Abba ƙ a kan screen ɗin wayar yana yawo yasa yayi saurin ɗagawa ya kara a kunne haɗe da sallama Abba ƙ najin ya ɗaga yace "In baka komi kazo ka same ni a palona" Cike da girmamawa ya faruk yace "To Abba" Yanayin zafin da ake tsugawa yasa ko mai be shafa ba, roll on kawai ya shafa se body spray, tukun ya saka kayan shi ya fice zuwa kiran da Abba ƙ yayi mishi Tunda ya fito daga ɓangaren su na samarin gidan Hafsata ta hangoshi ta windown ɗakin mama Kamar zata kifa wajen saurin juya tace "Umma, zo ki gani" Fuska a ɗaure Umma babba tace "me zan gani?" Da sauri hafsat ta sake cewa "ze shige wallahi" Da ɗan sauri umma babba ta ƙaraso jikin windown itama, akan idon ta ya faruk ya ƙarashe shigewa part ɗin Abba ƙ Ƙwata tayi ta koma ta zauna, fuskar ta ba yabo ba fallasa tace "Bani waya ta hafsat" Juyawa hafsat tayi ta ɗakko mata wayar, har ta miƙa mata ta tsaya tace "karki kira shi umma" Kallon ta umma Babba tayi tukun tace "wa kenan? Dariya Hafsat tayi, wani lokacin halin umma babba mamaki yake bata, wani lokacin kuma dariya Kafe tan da ido da umma b tayi yasa tace "na sha ya faruk zaki kira ai" Tsaki umma b tayi taci gaba da danna wayar hannun ta. Mumtaz na kwance taƙi tashi tayi komi wai azumin yau na bata wahala taji sallamar ya faruk A guje Mumtaz ta miƙe tayi hanyar ɗakin su, sam ta mance da yunwar data ce tana ji Tana shiga ta banko ƙofar da ƙarfi ta murɗa key tana maida numfashi da ƙyar Gaba ɗaya seda hankalin su sakina ya dawo kanta, har altine dake kitchen seda ta leƙo jin ƙarar ƙofar da aka buga Karkaɗa kai ya faruk yayi, can ƙasan zuciyar shi yace "Zanyi maganin ki, da gangan kenan kika ƙi zuwa kiran da nayi miki" Sama-sama ya amsa gaisuwar su sakina, tukun ya nufi stairs ɗin da ze sada shi da palon Abba ƙ. Ya jima sosai a wajen Abba ƙ kafin ya sakko, da ka ganshi kasan ranshi a mugun ɓace yake, amma in bakai mishi farin saniba ba lale ka fahimci hakan ba. yana shiga ɗaki ko zama beyi ba, wayar shi ya ɗauka da niyar kiran Ahmad Missed calls ɗin Umma b ya gani kusan biyar, Saka wayar yayi a aljihu ya juya ya sake fita zuwa part ɗin Umma b. Har bedroom ɗinta ya same ta, tana zaune riƙe da carbi a hannun ta tana ja yayi sallama ya shiga Zama yayi kan kujerar dake kallon gadon ta, Hafsat na zaune akan 1 seater dake kusa da window tana duba handout ɗinta, kai kace gaba ɗaya hankalin ta na ga handout ɗin, da yake ya faruk yasan halinta sarai, kuma yasan umma b babu ruwan ta duk maganar data ga damar faɗa zata faɗeta koda kuwa a gaban ƙannen shi ne Fuska a ɗaure yace "Tashi kiba mutane waje" Tasan sarai da ita yake, Da sauri ta hau tattare takardun ta tanayi tana zumɓure-zumɓure ta fice a ɗakin Seda yaga ta fita tukun yace "Umma gani" Juyawa tayi ta ajiye carbin hannunta ta fuskance shi da kyau, Seda tayi gyaran murya tukun tace "Tun last week nake jiran naga saƙon da kace amma shiru, banji daga gare ka ba" Murmushi ya faruk yayi, a ranshi yana faɗin "Taga shiga ta part ɗin Abba ƙ kenan" Kafin yayi magana ta ɗora da "Ni ba shiru na kira ka kayi min ba faruk, ko manzon Allah (SAW) yace uwa tana gaba da kowa" Cike da kulawa ya faruk yace "Haka maganar ki take umma, ban mnta da saƙon ba, zuwa anjima nake sa ran za'a kawo se a fitar ma da kowa na shi dana mutanen shi" Taɓe baki umma b tayi, kamar ba zata ce ƙara cewa komi ba, can dai tace "In dai kana son ganin farin ciki na, to tabbas a fara girmama ni kafin waɗan da ke wahalar da kai da sunan nuna kulawa" Shiru ya faruk yayi ya sunkuyar da kan shi ƙasa, yana jin maganar da umma b keyi wani iri Seda ta kai ƙarshen maganar ta tukun yace "Toh, mu kasance masu yawan kyautata zato umma" Da mamaki umma b tace "Fassara abinda kk nufi faruk" Murmushi ya sake yi, sannan yace "Umma kenan, bari inje kar in rasa jam'i" Kafin ta sake magana ya fice daga ɗakin ranshi a jagule. Aljihun shi ya laluba yaji ko da key ɗin motar shi a jiki Tsaki yaja jin be jishi ɗin ba, part ɗin su ya koma domin ya ɗakko, yana shiga su mus'ab na ƙoƙarin fita, Kauda kai gefe mus'ab yayi yace "barka da rana ya faruk" Ko kallon shi beyi ba, har ya tura ƙofar ɗakin shi ze shiga ya waiwayo yace "Ku kawo min passport ɗinku kai da Ahmad yanzun nan". Ya ƙarashe shigewa ɗakin. Ya faruk na shigewa suka kalli juna shi da Ahmad Murya ƙasa-ƙasa mus'ab yace "mu gudu wallahi" Tsaki Ahmad yayi yace "Ba inda zamu, mu kai mishi ya gani, nasan in yaga yaune tafiyar ze bamu kayan mu" Shiga ɗakunan su suka yi suka ɗakko passport ɗin su, Mus'ab na fitowa ya miƙa wa Ahmad na shi yace "ka kai ni bazan shiga ba" Ansa yayi ya haɗa da nashi, knocking ƙofar ɗakin yayi Seda ya bashi izini tukun ya shiga Tsaye yayi bayan ya miƙa mishi passport ɗin yana jira ya gama dubawa ya bashi Duk da ya faruk yasan me Ahmad ke jira hakan be hana shi faɗin "Tsayuwar me kake yi kuma?" Ido waje Ahmad yace "ya faruk baka date ɗin bane?" Kan gado ya wurga passports ɗin ya miƙe tsaye bayan ya ɗauki keys ɗin shi, da ido ya faruk ya nuna ma Ahmad ƙofar fita Ba musu ya juya sum-sum ya fice, ran shi baƙiƙƙirin Akan idon su ya faruk ya rufe ƙofar shi ya wurga keys ɗin shi a aljihun wandon shi yayi gaba abinshi ya barsu da ƙamshin shi me daɗin gaske. SHARE PLS ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg6 Rai a ɓace mus'ab yace "wannan ai mulkin kama karya ne wallahi, na gaji ƙarar shi zan kai wajen umma b wlh" yayi gaba a fusace ze fita Da sauri Ahmad ya damƙo shi, murya ƙasa-ƙasa yace "Baka da hankali mus'ab ya faruk ɗin ne zaka kai ƙarar shi? Malam ka dawo hankali ka" Banda huci babu abinda mus'ab keyi Hannun shi Ahmad ya kamo suka fito harabar gidan Suna fitowa suka yi kiciɓus da ya faruk zaune a kan boot ɗin motar shi waya kare a kunnen shi Kallo ɗaya yayi musu ya kauda kanshi gefe yaci gaba da wayar shi Har sun gota shi Ahmad ya sake yin ƙasa da murya yace "Ko dai muje mu bashi haƙuri ne?" Tsaki Mus'ab yaja yace "wallahi ba zanje ba, sedai kai kaje" Yana gama maganar yayi gaba fuuu kamar wanda ze tashi sama. Murmushi kawai ya faruk yayi, dan sarai yaji me mus'ab yace. Mus'ab ne ya fara shiga part ɗin su fuska a ɗaure yana wani ciccin magani Sakkowar mama da Abba ƙ kenan suka gan su a tsaye cirko-cirko kamar wasu zakaru Rai a ɓace mama tace "Lafia kukai mani tsaye a palo?" A fusace mus'ab yace "Gaskiya mama an fara saka mana ido a cikin gidan nan, kuma gaskiya ba zamu ɗauka ba" Ba mama kaɗai ba, hatta Abba ƙ dake tsaye seda yaji wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarce shi jin furucin rashin ɗa'a a karo na farko daga bakin ɗan nasu me kunya da tsananin biyayya gare su" Kafin Abba ƙ ya buɗe baki yayi magana mama ta rigashi faɗin "Mus'ab me kake nufi da an fara saka muku idanu? Mu iyayen ku ne ke saka muku idanu ko kuwa me kk nufi?" Ta ƙarashe maganar tana zaro mishi idanun ta da suka kaɗa suka yi jajir. Watsa hannayen shi yayi alamun oho ɗin nan, sannan yace "Ai ba se na ambaci suna ba mama, kawai dai ku dena ɗaure ma ya faruk ƙarƙashi yana mana abunda yaga dama bayan mun kauce mun bar mishi komi da ya dace ace mune akai" Cikin zafin nama mama ta sauke wa mus'ab wasu mahaukatan maruka a kumatun shi Mumtaz dake zaune itama mamaki ya gama kashe ta na jin abunda mus'ab ke faɗa, kamar ƙiftawar ido taga tafiyar marin nan, muguwar zabura tayi taja baya tana dafe kuncin ta kamar ita aka zabga wa marin, Ahmad kuya ja da baya yayi ganin yarda mus'ab ya samu tsarabar tagwayen maruka Ido jajir mus'ab ke kallon mama, har wani huci yake Abba ƙ kam dafe kanshi yayi ya samu gefen kujera ya zauna. Ganin kallon da mus'ab ke mata yasa ta matso kusa da shi, Cikin ƙaraji da kuma fushi tace "Kallon nan ba ze gamshe ni ba har se naji yatsun ka guda goma a fuskata tukun dan ubanka" Dunƙule hannu mus'ab yayi, kamar ze kai wa mama duka, ya fasa ya fice daga palon a fusace, a mugun firgice Ahmad yabi bayan shi Mumtaz kuwa ganin yarda komi ya birkice yasa tuni ta fara kuka tana wa mama ɗan kira Su mus'ab na fita mama ta juya da gudu ta koma sama Tana shiga palon Abba ƙ ta fashe da kuka tana dafe kanta da take ji yana juya mata Sunan Allah kawai take ambata jin yarda numfashin ta ke neman gagarar ta gaba ɗaya. A daddafe Abba ƙ ya bi bayan ta, shima riƙe da kanshi. A hankali altine ta koma da baya bayan ta sakayo ƙofar kitchen ɗin tana sauke ajiyar zuciya. Se wajen bayan la'asar mama ta sakko, da ka kalle ta kasan bata cikin nutsuwa, ƙarfin imaani ne kawai ke riƙe da ita Tsabar yarda ta sha kuka yasa muryar ta bata wani fita can sosai, Ɗakin su Mumtaz ta nufa, tana shiga ta iske ta kwance akan darduma bacci ya ɗauke ta Seda mama ta gama ƙare ma ɗakin kallo tukun ta taɓa mumtaz tana kiran sunan ta Seda tayi da gaske kafin mumtaz ta haƙura da baccin ta tashi zaune A muryar bacci tace "Wallahi ina jin azumin yau mama" Juyawa mama tayi zata fita tace "sannu uwar raki, ki taso ki taya Altine aiki bana jin daɗi" Ta ƙarashe ficewa. Seda Mumtaz ta sake ɓata lokaci kafin ta fito zuwa kitchen inda Altine ta fara aikin abincin buɗa baki. BAYAN AN SHA RUWA Wajajen tara da rabi na dare, ya faruk na kwance yana ƙara nazarin maganar da suka yi da mama da kuma Abba ƙ, abun na ƙara ɗaure mishi kai matuƙa Waigawa yayi inda ya watsa passport ɗin su Ahmad yayi yaga suna nan Daga can ƙasan ranshi yace "Ƙila sunyi trying ɗaukar abun su fa" A hankali ya sauka daga kan gadon shi ya nufi inda laptop ɗin shi ke ajiye Seda ya koma gefen gadon ya zauna tukun ya buɗe A hankali ya rinƙa kallon yarda mus'ab ke wani muzurai yana magana Shiru yayi ya kafa wa screen ɗin idanu yana tuna irin kunya da kuma biyayya na yaran, Seda ya gama kallo tas, kamar ance ya duba wasu vedios ɗin da CCTV CAMERAr shi ta ɗauka A hankali ya rinƙa scrolling yana kallo, Wata muguwar faɗuwar gaba ce ta same shi a take Hannun shi har rawa yake wajen maida vedion baya, me idanun shi zasu gani? Mumtaz ce a lokacin da ta shigo ɗakin shi ta ɗauki agogunan shi na diamond masu mugun tsada Tsayar da vedion yayi ya tashi da sauri ya nufi wajen safe ɗin shi Sanin ba me shigo mishi ɗaki ne yasa be wani damu da rufe shi ba Ilai kuwa, yana dubawa yaga babu waɗan nan agoguna da ya gani a hannun ta Da baya da baya ya koma ya zauna haɗe da maimaita sunan ubangiji A hankali ƙwaƙwalwar shi ke tuno mishi ganin ta da yayi tana abubuwa irin na marasa gaskiya Da ƙarfi ya runtse idanun shi yana hasasho kirkin Abba ƙ da kuma maman kanta, kusan kowa inuwar arzikin su yake sha a cikin gidan nan. A bayyane yace "Nata yafi muni akan nasu Mus'ab Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! ya Abba ƙ da mama zasu ji in suka ji wannan mummunan abun?" astagafirullah!" A wannan dare ya faruk ya jima be rintsa ba, gani yake kamar wasa kamar kuma a mafarki abunda ya gani Alwashi kala-kala ya ɗauka a wannan dare, har barci mara daɗi yayi awon gaba da shi. ALLAH YA ZAƁA MANA SHUWAGABANNI NA GARI. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 YAWAN COMMENTS, UPDATE AKAI-AKAI 😎 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg7 Kusan kwana biyu kenan ya faruk ke fakon mumtaz da duk wasu motsin ta So yake ko ta wani hali ya ritsata amma be samu zarafin yin hakan ba Mumtaz kam kamar ta so ta ɗago ya faruk, sam taƙi yarda ta fita balle har ya ritsata, ko da yaushe tana ɗaki kwance Da mama ta matsa akan zaman ɗakin data tsira, shine tayi ƙaryar ciwon kai ne ke damun ta Shiyasa mamar ta rabu da ita ba dan ta yarda ba. Zaune ya faruk yake a palon umma b yana dudduba tickets yana siya ma kowa Fitowar Umma b kenan daga side ɗin Abba b, da yake ita ke da girki shiyasa bata yi ma ya faruk titsiyan da ta saba mishi ba Tana fitowa yana gamawa, cikin nutsuwa ya ɗaga kanshi ya kalleta tukun yace "Barka da fitowa umma" Seda ta zauna tukun ta amsa da "yauwa, kana nan ashe, su hafsa sun kawo maka kayan buɗa baki ko?" Idon shi akan screen ɗin wayar shi ya amsa da "Nace a kai min ɗaki na" Taɓe baki umma b tayi, so take tayi magana amma tana ɗan jin shakkar yi Can dai ta daure tace "Halan kayi banbancin da ka saba yi? Da mamaki ya faruk ke kallon mahaifiyar shi, bece komi ba seda ya miƙe har ya kai ƙofar fita ya ɗan dakata yace "Gida uku na kasa ku umma, ko wani kashi ɗaya jirgi daban, be dace ace duka ahali ɗaya su haɗe a jirgi ɗaya ba, babban kuskure ne, Tunda har Allah ya hore yarda za'a rarraba ɗin ai gara a rarraba, ki duba na tura miki naki a wayar ki" Yana ƙarashe maganar ya fice yana jin ba daɗi sam a cikin ranshi na yarda umma b ke mishi. Yana shiga ɗaki bayan ya zauna, wayar shi ya ciro ya kira mama dake zaune gefen Abba ƙ tana yanka mishi apples a plate wayar ta tayi ringing Seda ta kammala tukun ta kira shi yana ɗagawa yace "Mama yau akwai kunun gyaɗar nan kuwa?" Murmushi mama tayi tana gyara zamanta kafin tace "So sorry yaro na, na mance shaf ba'a kawo maka ba" Kafin yace a ba mumtaz ta kawo mishi, mama tayi saurin faɗin "Bari mumtaz ta kawo maka yanzun nan" Godiya yayi mata suka aje wayar Number mumtaz mama tayi dialing, bugu biyu ta ɗaga tana wani shaƙe murya kamar me ciwon gaske, a tunanin ta wani aikin mamar zata saka ta Ilai kuwa mama tace "Ki duba kan dinnig flask ɗin yayan ku na nan ki ɗauka ki kai mishi yanzu" Da sauri mumtaz ta wuntsulo daga kan kujerar da take kwance tace "mama kuma kince nice zan kawo mishi?" Tsaki mama ta ja tace "in sakko inga baki kai mishi ba, zan baki mamaki ke da baki son a more ki sam" Ta tsinka wayar ta, tana ci gaba da mammatsa wa Abba ƙ ƙafar shi. Cikin marairaicewa mumtaz ta kalli sakina dake waya da saurayin tace "Dan Allah sakina ki kaima ya faruk kunun shi" Mumtaz bata gama rufe baki ba sakina tace "caɓ, wallahi ba zani ba, salon inje ya rinƙa mun kallon wulaƙancin nan da ya saba" Kamar mumtaz zatayi kuka tace "Baki fahimce shi bane, haka yake shi, ni wlh jiwa nake gani shiyasa nace ki kai mishi" Tsaki sakina ta sake yi, seda ta gyara kwanciyar ta tkun tace "Haka nan zaki daddafa ki kai malama, thank God ba'a gidan nan nake ba da za'a kwashi ƴan kallo dani" Ta maida wayar ta a kunne taci gaba sa firar ta. A zuciye mumtaz ta yayimi hijabin ta tasaka tukun ta ɗauki flask ɗin kamar shine me laifin, ƙiris ya hana shi suɓucewa daga hannun ta tasamu ta taro shi Tafi minti goma a tsaye tana jiran taga ko zata ga wani daga cikin yaran gidan ta bashi ya kai, haka nan ta gaji da tsayuwar ta tayi shahada kawai ta nufi ɗakin Ya faruk na zaune a gaban laptop ɗin shi, vedion mumtaz wanda ta ɗauki agogon nan ya kafa ma ido yana kallo, har yanzu ya kasa yarda da abun, se yake gani kamar ba nutsatstsiyar mumtaz ɗin da ya sani bace Knocking ɗin ƙofar da tayi ne yasa yayi maza yayi pausing vedion ya juyar da laptop ɗin zuwa ɗayan ɓangaren da ba lale wanda ze shigo ya gani ba Seda ya kimtsa tukun yace "Come in" A hankali mumtaz ta tura ƙofar kamar warce ƙwai ya fashe ma a ciki Tunda ta shigo ya kafe ta da manyan idanun shi yana kallon ta, Gaba ɗaya wani mugun tausayin Abba ƙ da mama ne suka lulluɓe shi, for the first time da yaji kamar ya fashe da kuka tun bayan ya mallaki hankalin shi. Tana sunkuyawa zata ajiye flask ɗin ya faruk yayi saurin tashi ya rufe ɗakin da key Tana ganin haka ta juyo a tsorace tana niyar kware baki ta kurma ihu Kamar yasan me take da shirin yi kuwa, manyan idanun shi ya zazzaro waje ya ɗora yatsar shi ɗaya a kan laɓɓan shi yace "shiii, kina fasa ihun nan zan sauya miki kamanni wlh" Ƙut mumtaz ta haɗiye ihun ta, taci gaba da rarraba nata manyan idanun Belt ɗin jikin shi ya zaro, tana ganin haka ta tsugunna ta dunƙule waje ɗaya tana ɓarin jiki Rufe ida ya faruk yayi ya zambaɗa mata ɗaya a jikin ta Kuma ya hana ta ihu Sosai mumtaz ta tsorata da yarda taga ya faruk ɗin, a iya tsawon rayuwar ta bata yaɓa gani ya ɗaga hannu ya daki wani a cikin gidan nan ba se yanzu, yanzun kuma a kanta Cikin tsananin tsoro mumtaz tace "Dan Allah ya faruk kayi haƙuri, wallahi mantawa nayi ranar da kace inzo in same ka ba da gangan naƙi zuwa ba" Bayan hannun shi yasa ya make bakin ta da ƙarfi, cikin fushi yace "Rufe min baki maƙaryaciya, bayan sata har ƙarya kika koya kenan?" Ƙwalalo manya idanun ta tayi waje, a lokaci ɗaya kuma kukan da take ya ɗauke ɗif Jiki a sanyaye ta sauke kanta ƙasa tana sauraron yarda gaban ta ke dukan uku-uku Sosai ya faruk ke kallo da nazartar yanayin ta, Farko yaso yazo mata da mugun zafi, amma haka nan yaji zuciyar shi bata aminta da hakan ba Unexpected muntaz taji murya ya faruk a kanta cikin nutsuwa yace "Bayan ni akwai wanda ya taɓa kamaki?" Shiru tayi bata ce komi ba, seda ya buɗe murya yayi kamar ze sake shauɗa mata belt ɗin tukun ta girgiza mishi kai da sauri Rai a ɓace yace "buɗe bakin ki kiyi min magana kamar yarda kika ji inayi" Kanta a ƙasa tace "a'a" Kallon ta kawai ya faruk yake, sam ya rasa ta ina ma ze fara, sosai yake jin ɗacin abun a ranshi Can dai ya daure yace "Me kika rasa da kika saka rayuwar ki a cikin wannan ƙazamar ɗabi'ar?" Bata ce komi ba se sheshshekar kuka da take Shima be buƙaci da yajin ba ya ɗora da "Yanzu kina ganin kinyi wa Abba ƙ da mama adalci kenan? kina ganin suka san wannan abun ba ze zama musu mugun tashin hankali ba? Ashe baki da tausayi? imanin ki ragagge ne? Baki jin kunyar Allah balle ace kunyar da zaki shiga duk ranar da aka kama ki?" Kuka kawai mumtaz take, maganganun ya faruk nayi mata raga raga da zuciya A tsawace yace "ki min shiru, wannn kukan munafurci ne ai, gaya min tun yauahe kika fara satar"? Kasa cewa komi tayi, banda aukin share hawaye Wata tambayar ya faruk ya sake wurgo mata "In kin saci kayan me kike da su?" Kanta a ƙasa tace "Ban taɓa ɗaukar ma kowa ba ai" Bayan hannun shi ya saka ya make mata baki tukun ya waigo mata da screen ɗin laptop ɗin shi yace "Wannan wacece?" Baki sake mumtaz ke kallon vedion kanta da kanta, da dai ta san ta kamu kawai se ta fashe da kuka me taɓa zuciya Cikin muryar kuka tace, "wallahi wannan shine karo na farko da na fara ɗauka, nasha ganin abubuwa zan ɗauka amma bana samun dama, kuma kaima yanzu zanje in ɗakko maka kayan ka" Da mamaki ya faruk ke kallon ta,jin tace "tasha gani abu amma bata samun ɗauka" "Da kika ɗauki wannan me zakiyi da shi da?" "bakomai" tace cikin kuka Da sauri ya faruk yace "Ƙarya kike, kodai kina da saurayin dake saka ki ɗauke-ɗauke?" Da sauri ta karkaɗa kanta, tana ci gaba da share hawayen ta da bayan hannun ta Shiru ya faruk yayi, can dai yace "tashi kije" Sosai tayi mamakin furucin shi Tsaye tayi taƙi fita, Da ƙarfi yace "I said get out!!" Da gudu ta fice tana ƙumshe kukan da ya tawo mata da mugun ƙarfi. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 pg8 Memakon ta wuce side ɗin su kai tsaye se ta wuce can back yard ɗin side ɗin su Suna ajiye kujeru haka a wajen dan hutawa wani lokacin Zama tayi dirshen a ƙasa ta haɗe kai da gwiwa Tunda ta shigo wajen mus'ab yaga shigowar ta, Ya jima yana kallon ta bece komi ba, sema faɗuwa da gaban shi ke yi tunda yaji sautin kukan ta A hankali ya taso daga inda yake ya matso kusa da ita Dafatan da yayi ne yayi matuƙar razana ta, ƙiris ya hana ta kurma ihu, Allah yasa yayi saurin yin magana Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke ta saka hannun tana share hawayen fuskar ta Sam taƙi yarda ta kalli mus'ab da ta san shima kallon ta yake Abubuwa take na irin wanda suke a tsarge ɗin nan Murya ƙasa-ƙasa mus'ab yace "me ke damun ki? waye ya saka ki kuka?" Muryar ta na rawa tace 'Bakowa ya mus'ab, kawai bana jin daɗin komi ne" A hankali, yarda ba lale tajishi ba ya ce "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Jin bece komi ba yasa tace "Kai me kake yi a ban ya mus'ab?" Ƙirƙirar murmushi yayi tukun yace "Zafi ne ya fito dani" Da sauri mumtaz ta ware manyan idanun ta da mamaki tace "Zafi fa kace? Air con ɗin ɗakin ka fa?" Shiru mus'ab yayi ya dafe kanshi, shi sam ya manta da wata aba wai air con, Sam baya jin daɗi ji yake kamar ana iza mishi wuta a zuciyar shi, azalzala kawai yake ji, sam ya rasa nutsuwa ko kaɗan Bugu da ƙari ga abunda ya faru ɗazu, wanda shi kanshi seda ya bar wajen tukun yake tuna rashin ɗa'ar da yayi" Still bece komi ɗin ba, Miƙewa yayi sannan yace "Ki rinƙa addu'a ne, kuma kar in sake ganin dan abu ya dameki ki rinƙa fitowa wajen nan da daddare, tashi ki wuce ciki" Tashi tayi ta wuce jiki a sanyaye, Seda mus'ab yadena hangen ta tukun ya koma ya zauna a wajen memakon ɗaki da yayi niyar tafiya Zabga tagumi yayi hannu bibbiyu yana maganar zuci da be san ta fito fili ba "Allah na roƙeka kasa ba abinda nake ji bane yake damun mumtaz, Allah ka tsayar a iyakacin kaina kar ka ɗora musu ya rabb, nima ka yaye min ya Allah". Sanda mumtaz ta shiga side ɗin su kowa ya kama gaban shi dan har an kashe wutar ko'ina Ɗaki ta wuce itama kai tsaye tunani kala-kala a cikin ranta Abunda ya bata mamaki shine, titsiyen da ya faruk yayi mata ya sa taji tsanar kayan kowa, amma tunda ta saka ƙafarta a side ɗin su taji damuwar ta ragun mata, tana ƙara jin kwaɗaituwar sake tattara duk wani abu da yazo gaban ta koda kuwa na Abba ne ko mama Murmushi tayi bayan ta sake yin ido biyu da agogunan ya faruk da sam ta gama ƙudirtar salwantar da su ta ko wani irin hali a goben nan A hankali ta saka hannu ta shafi laɓɓan ta inda tasha masga ɗazu Jin sun ɗan tasa kaɗan yasa ta murguɗa baki tace "Allah ya isa na". 2am Karo na kusan biyar kenan yana fitowa daga wanka, In ka kalli idon shi kamar an zazzago su tsabar azabar raɗaɗin da yake ji a cikin zuviyar shi A daddafe ya samu yayi sallar isha da se yanzu ya samu zarafin yin ta Tunda ya idar ya janyo biro da takardar da ya ajiye tun ɗazu Hannun shi na rawa idanun shu na zubar da rywa ya fara rubutu ..... Seda ya gama, ya ninke takardar tukun ya ajiye a gefe Jeans da riga ne a jikin shi, se baƙar jacket da ya ɗora akai Ya jima a tsaye kanshi jingine da bango kafin ya ɗauki takardar nan Seda ya kalli agogo yaga huɗu saura, lokacin da yawa wasu sun tashi sahur Fitowa yayi daga ɗakin ya wuce part ɗin su kai tsaye Knocking biyu yayi Altine ta buɗe mishi ya shiga Kallon stairs yayi yaga alamun mama bata sakko ba, dan ko hasken corridor ɗin ba'a kunna ba Ɗakin mumtaz ya ɗan ƙonƙosa, tashin ta kenan dama taji knocking ɗin, ta aza mama ce ma, shiyasa tayi saurin sakkowa ta buɗe ɗakin Tana buɗewa taga mus'ab tsaye a bakin ƙofar "lafia ya mus'ab?" Muryar shi a dishe yace "mama bata sakko bane?" Gyaɗa kai kawai tayi tana ci gaba da kallon shi Be sake cewa komi ba ya saka hannun shi a aljihun jacket ɗin shi ya ciro takardar ɗazu ya miƙa mata Hannu tasa ta karɓa Kafin ma ta nemi ƙarin bayani yace "Ki ba mama in ta fito, ni ba zan samu damar shigowa ba anjima, kice mata list ɗin data ce akawo mata ne" Yana gama faɗar haka ya juya ze fice Da sauri mumtaz tace "ya mus'ab" Waigowa yayi yana ya kalle ta da jajayen idanuwan shi Jiki a sanyaye tace "Baka da lafia ne?" Murmushi yayi mata tukun yace "lafia lau nake, kawai ban samu enough bacci bane" Yana gama faɗin haka ya ƙarasa ficewa. Anan kan mirrow ta ajiye takardar ta shige toilet. Wajen sha ɗaya da rabi na safe, Mama na zaune tana nuna ma Altine kayayyakin sallah da za'a kai gidan marayu tana haɗe su a babban kwali Dogon list ne a hannun ta na sunayen jama'a, sannu a hankali sukai ta fitar da na kowa, hatta altine an cire mata nata rabon Rabon yazo ya caɓe mata, ga shirin tafiya umara da zasuyi jibi shiyasa take so ta sallami kowa da kowa dan ta tafi cikin kwanciyar rai Mumtaz na zaune a gefe tana auna sarkar wuyan mama da tun fitowar ta take tsole mata idanu, ta tuna da takardar da mus'ab ya bata ɗazu da asubah, kamar ba zata tashi ba can dai tace "Akwai fa sauran ki mama, ɗazu ya mus'ab ya kawo wani list ɗin fa" Bata jira cewar mama ba tayi ɗaki. Hankalin ta na kab wayar da take daddanawa ta miƙa wa mama takardar har tana ƙoƙarin tsole mata idanu Daga mama har Altine sakato sukayi suna kallon Mumtaz da bata ma san me takeyi ba Rai a ɓace mama tace "Ki cire min idon se ki huta" Ɗago kanta tayi, memakon ta gane abinda tayi sema dariya datayi tace "Da abun yayi mana yawa ai mama, ga makanta ga kuma faɗa" Da sauri Altine ta sauke kanta ƙasa tana ƙunshe dariyar dake cinta Mumtaz kam ganin kallon da mama ke mata yasa tace "Allah baki haƙuri, ni wasa nake miki" ta aje mata takardar a table ɗin gaban ta. Seda mama ta gama da gaba ɗaya na hannun ta tukun ta ɗauki warda mumtaz ta ajiye mata Haka kurin taji gaban ta na dukan uku-uku A hankali ta warware, memakon taga sunaye ko gidauniyoyi se kawai taga an fara da "Dear mamana da kuma Abba na" Dummmm, haka gaban ta ya bata wani mugun sauti, ji tayi miyan bakin ta ya ɗauke, numfashin ta na ƙoƙarin fin ƙarfin ta Ido a waje take karanta takardar, gaba ɗaya hannun ta rawa yake Tana kaiwa ƙarshe ta hau nanata kalmar "innalillahi wa'inna ilaihirrahi'un! da ikacin ƙarfin ta Mumtaz da Altine sukayi kanta da gudu suna auna ma sunan ta kira Dai-dai shigowar Ahmad kenan ya iske su a haka Shima da sauri ya ƙarasa inda suke ƙoƙarin ganin sun tare mama bata kai ƙasa ba Amma inaa jikin ta ya riga da ya gama saki ba wani alamun numfashi a tattare da ita. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg 9-10 Ganin yarda Ahmad ke girgiza ta da ƙarfi yana kiran sunan ta yasa Mumtaz ficewa da gudu tana faɗin "Innalillahi mama bata numfashi, bala ka fito da mota". Cikin bacci ya faruk ke jiwo kururuwar ta, kasaƙe yayi dan yaji me take faɗi Jin muryoyi daban daban ciki harda na Umma ƙarama(kishiyar umma b) Yasa shi saurin miƙewa yana lalubar jallabiyar shi Da sauri ya fito, jin furucin Umma babba da tace "Wannan gawa ce ai, ba wani alamun rai a tattare da ita" A sukwane ya faruk ya ƙarasa palon sunyi cirko-cirko, mummy da umma b na faɗin ta mutu, Aunty da umma ƙarama na faɗin a tafi hospital dai. Gaba ɗaya ihun mumtaz yasa ba'a jin komi, seda ya faruk ya waiga ya daka mata tsawa tukun ta lafa da iface ifacen, Jiki a sanyaye Amal ta rungume ta itama tana ta ɗigar da hawaye Kutsawa wajen yayi gaban shi na dukan uku uku hannun shi ya saka a wuyan mama, jin da alamun numfashi a tattare da ita yasa ya cicciɓe ta yayi waje da gudu yana faɗin "Fito da mota Ahmad, tana numfashi" Ɗiii, haka suka biyo shi harabar gidan Kafin Ahmad ya ɗakko motar har bala driver ya fito da ita A bayan motar suka saka mama, Fuska a ɗaure umma babba tace "Ai kwa tafi da mace ko?" Ya faruk na ƙoƙarin shiga motar ya dakata tukun yace "Wani ya shiga muje to" Kafin umma ta gama rufe bakin ta Aunty tayi parcking kusa da motar ya faruk, tace "Faruk kuyi gaba, zamu biyo bayan ku" Jan murfin yayi ya rufe, bala yaja motar a sukwane suka fice. Seda suka fice aunty tace "Ku muje mana" Fuska a ɗaure umma babba tace "Kuje, ai ba'a bar gidan ba kowa ba ko?" Ba wanda yace mata uffan a cikin su, mummy ta buɗe front seat ta shiga, umma ƙarama kuma ta shiga baya suka ja suka tafi. Zaman dirshen mumtaz tayi a compound ɗin taci gaba da kukan ta, duk da ba sauti kamar na ɗazu Amal ce a gefen ta tana ta fama rarrashin ta, se sakina itama daci kukan har ta koma ajiyar zuciya. Umma B na ganin Altine ta koma part ɗin mama tace "Bari inje in saka Altine ta haɗa abubuwan da za'a iya buƙata a hospital ɗin, dan na san dawowar ta ba yanzu ba" Tana gama faɗin haka ta juya da sauri ta wuce sasan maman. Umma b na wucewa sakina ta taɓe baki, tana binta da harara gefen ido, dan har ga Allah ta san ranta fes ne da abinda ya faru ga mama. Mumtaz na nan zaune, Amal tayi-tayi da ita ta tashi amma taƙi Can dai kamar warce aka tsikara ta miƙe zumbur tabi bayan umma b da mugun sauri Ilai kuwa, tana shiga ta iske ta titsiye altine tana tambayar ta ainihin abinda ya faru, Altine nata inda-inda dan itama takamai mai bata san me uwar ɗakin nata ta gani ya gigitata ba, Sosai Mumtaz tasha kunu, ido cikin ido ta kalli Altine tace "Bani takardar" Ba musu ta miƙa mata ta juya ta bar wajen kanta a ƙasa. Sosai umma b ke kallon mumtaz da ta nuna kamar ma bata san da tsayuwar ta a wajen ba Seda ta ɗauki wayar ta tukun ta haura sama zuwa ɗakin mama. Kusan a tare da su Abba ƙ suka isa hospital ɗin, Ba wani ɓata lokaci akayi emergency da mama, duk da dai ta farfaɗo, amma sambatun da take yi ne ya ƙara rikitar da duk wani masoyin ta dake wajen Tunda Abba ƙ ya ƙaraso wajen yake tambayar me ya same ta a ruɗe A sanyaye ya faruk yace "Calm down Abba, kar ku zama ku biyu mana" Sam Abba ƙ ya kasa zama, kuma kowa a wajen yace be san musabbabin ciwon ba Suna a hakan Abba babba da uncle Abbas(mijin mummy) da kuma uncle ƙasim(mijin aunty suka shigo hospital ɗin Suma same tambaya da Abba ƙ yayi suka yi, amsa ɗaya ce ba wanda yasan me ya faru. A GIDA Tunda Mumtaz ta karanta takardar nan ta sake shiga mugun tashin hankali, Kukan kam tayi shi kamar ba gobe, tausayin iyayen ta kam ba'acewa komi, da ta tuna actions ɗin mama lokacin data gama karanta takardar hankalin ta ƙara tashi yake A sanyaye tace "Duk randa ta gane ni kuma sata na fara ƙila mutuwa zatayi" Ta sake rushewa da kuka me taɓa zuciya. HOSPITAL Dukkan su suna zaune dr ta fito daga ɗakin da mama ke a ciki, sam ba wani walwala a tattare da ita Cikin nuna damuwa tace "who is her husband" Kasa cewa komi Abba ƙ yayi, se idanu da ya fito da su waje, yana jiran yaji me zata ce Jin ba wanda yace mata uffan se ma idanu da suka bita da shi yasa taci gaba da maganar ta "patient ɗin ku taƙi yarda sam muyi mata allurar da zata samu bacci dan a samu ƙwaƙwalwarta ta huta, Jinin ta yayi mugun hawa, amma duk da hakan taƙi bari ayi mata abunda ya dace, so zaka iya zuwa kayi mata magana maybe ta tsaya a temaki rayuwar ta" Da sauri Abba ƙ ya tashi ya nufi ɗakin, drn kuma ta wuce office, a hankali ya faruk ya sakko daga inda yake ya tsallake kowa ya shiga ɗakin shima A rungume a ƙirjin Abba ƙ ya iske mama, ita kuka shi kuka babu wani me rarrashin wani a cikin su Daman abunda yayi tunani kenan shiyasa ya biyo bayan Abba ƙ ɗin Kanshi a ƙasa ya ƙarasa kusa da mama ya zauna, murya a tausashe ya ce "Mamana me yasame ki? nasan ke jaruma ce, kina tarban ko wani kalan ƙalubalen da ya riske ki, kece kika koyar dani dauriya da kuma fauwala ma ubangiji komi, amma wannan kukan da kike yasani cikin kokwanto da kuma fargaba me tarin yawa a cikin zuciya ta mamana" Shuru yayi yana haɗiyar zuciya, dan shima gaf yake da rasa jarumtar shi, Sakin Abba ƙ tayi ta juya inda ya faruk yake zaune kanshi a ƙasa Hannuwan shi ta ƙanƙame cikin nata, Cikin kuka tace "Yarona, Mus'ab ya gudu ya bar gida, yace yayi nisan da bazamu taɓa samun shi ba Wai ba ze iya ci gaba da zama a cikin gidan nan ba saboda muguwar azabar dake damun shi, yace tafiyar shi itace mafi alkairi gare shi, dan kuwa wata rana ze iya aikata mugun abun da Allah zeyi fushi da shi yace baya ƙaunar gani na ko Abban ku sam, in ya ganmu yana jin zafi me ciwo a cikin zuciyar shi" Kasa ƙarasa maganar tayi, kuka me tsanani yaci ƙarfin ta Ya faruk kam, banda maimaita kalmar "innalillahi wainna ilaihirraji'un" ba abunda yake Mamaki da kuma tsoro na neman lulluɓe shi, a iya sanin shi, tun yana ƙarami yasha kama mama na kuka a ɓoye, in ya dame ta da tambaya se tace mishi wani abunne ya faɗa mata a idanu, tun yana yarda har yazo ya fara wayo ya gane waskewa kawai take. A sanyaye ya faruk yace "Mamana ke kika koyar dani kalmar "innalillahi wainna ilaihirraji'un, kikace in har na tsinci kaina a cikin matsin zuciya in yawaita karanta "LA 'ILA HAILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN da kalmar HAZBINALLAHU WANI'IMAL WAKIL" Bema gama maganar ba mama ta hau maimaita la'ilahailla anta subhanaka inni kuntu minazzalimin da sauransu Gefe Abba ƙ yaja yana kallon ɗan ɗan'uwan nashi da kuma matar tashi Kafin wani lokaci mama ta hau sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanu alamun bacci nason ɗauke ta. SHARE PLS ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg11-12 Seda suka tabbatar da bacci ya ɗauke ta tukun suka fito daga ɗakin da niyar kirawo dr Suna fitowa Abba babba yayi saurin tarbar su da tambayar ya mamar take Ya faruk bece ma kowa komi ba, Abba ƙ ke basu amsa da "Ta saamu bacci" Direct office ɗin dr ya faruk ya nufa, Be jima da shiga ba suka fito a tare zuwa ɗakin da mama take, seda ya tsaya komi da yake da buƙata ya kammala kafin ya fito daga ɗakin, a lokacin su umma ƙ da mummy se aunty ne kawai a wajen, mazan sun fice massalaci sallar la'asar Fuska ba yabo ba fallasa yace "Tace zaku iyw shiga ai Umma ƙ" Da "to suka amsa duk fuska babu walwala. Allah-Allah ya faruk yake ya isa massalacin kafin liman yayi sallama, in be kai ga isa ba aka sallame tabbas shirin shi ba ze tafi a yarda ya tsara ba Jin ana zaman tahiyar ƙarshe yasa ya ɗan haɗa da ɗan gudu-gudu har ya samu ya ƙarasa, Daidai kuwa an sallame mutane an fara futowa Gefe ya tsaya daga can yana hango iyayen na shi suna tawowa inda yake Ganin Uncle Abbas ya tsaida Abba ƙ alamun magana zeyi yasa ya faruk ƙarasawa wajen da sauri Kanshi a ƙasa yayi musu sallama, sannan yace "Ina son magana da ku tun ɗazu, to abun nan da ya faru yasa kawai na yanke hukunci daga baya in komi ya lafa na sanar muku" Dukkan su kallon shi suke, suna jiran jin me zece Uncle Ƙasim yayi saurin cewa "Mu koma daga cikin mota mana, akwai jama'a a nan, bakuma musan me sauraron mu ba" Sunyi na'am da abinda uncle ƙasim ɗin yace, dukan su suka nufi parking lots inda ba hayaniyar mutane Abba babba yace "ihum, muna jin ka" Kan ya faruk a ƙasa hannuwan shi duka biyun ya maida su bayan shi yace "Akan tafiyar nan tawa ta zuwa china, to abun ya haɗe min biyu ne, su daga can aka samu clashing ɗin time, alhalin na gama budget ɗin se na dawo daga Turkey akan maganar kayan, har in huta kafin time ɗin tafiyar tawa china, to se jiya da daddare na samu email ɗin su akan dawo da date ɗin da suka yi a jibi, to ganin kar ayi asarar kayan yasa nayi replacing sunan mus'ab memakon sunan tunda shi yana da visar ƙasar, A taƙaice dai na kaishe airport wajen 2:30pm, itace maganar dama" Tunda ya faruk ya fara maganar Abba ƙ ke kallon shi da mugun mamaki, amma can ƙasan zuciyar shi yana jin wani sanyi na ratsa shi duk da dai yasan haɗa maganar yayi Kicin-kicin da fuska Abba babba yayi, ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, yace "Ba haka ya dace kayi ba ai, ga Tk ai yana gaba da mus'ab kuma nasan shima yana da visa ƙasar, shi ya kamata ka tura ba mus'ab ba" Kan ya faruk a ƙasa yace "Ayi min afuwa, nayi kuskure" Shafa kanshi uncle Abbas(Baban Tk) yayi yace "An maka afuwa, kaje abinka, Allah yayi muku albarka ya ƙara muku ƙaunar junan ku" Da "amin" suka amsa dukan su, dai-dai ze wuce ta saitin Abba ƙarami ya faruk yace a hankali yarda ba wanda zeji se shi "Ka duba inbox ɗin ka Abba". A wayance Abba ƙ ke karanta saƙon ya faruk inda yace "Abba, mu bar maganar a haka saboda mama, kasan mata ba sa raina abun gulma ko habaici" Murmushi Abba ƙ yayi ya maida wayar a gaban aljihun shi. Sanda ya faruk ya koma ciki har su umma ƙarama sun fito da niyar komawa gida saboda shirin buɗa baki, duk da dai ba wacce bata da me aiki a cikin su, bayan masu aiki ga kuma yara. Mummy ce ta amsa mishi da "Bata farka ba, zuwa bayan magrib mun dawo yamma tayi" Da "to" ya amsa musu, suka fice shi kuma ya koma ciki. Kallo ɗaya yayi wa mama ya gane sarai ba bacci take ba, Murya a sanyaye yace "Mamana" Seda ya maimaita so biyu tukun ta buɗe idon ta da yayi ja kamar gauta, Kujera ya ja ya zauna a gaban gadon, Hawayen da suka taru a idon ta suka gangaro ta gefen idon Shiru ya faruk yayi ya barta tayi me isarta, tkun yace "Mama, kinji kinji......." Tas ya kwashe maganar da ya faɗa ma iyayen shi maza ɗazu itama ya faɗa mata Sannn ya ɗora da "A bar maganar a haka mama, se muci gaba da addu'ar Allah ya karkato da hankalin shi gida, sannan kuma zan ci gaba da duba shi lungu da saƙo na cikin garin nan dama kewaye, ni dai babban buri na shine ki kwantar da hankalin ki mu samu jinin ki ya sauka, kar ki bari maƙiyan ki su yi nasara a kanki mamana" Shiru mama tayi, can ƙasan zuciyar ta tana maimaita kalmar "maƙiya" da ya faruk yace Can dai tayi murmushi, ta kai hannu ta shafa kanshi tace "Allah yayi maka albarka faruk, Allah ya baka mace tagari warce zata kular min da kai" Murmushi kawai yayi, bayan ya amsa a can ƙasan zuciyar shi Shiru ɗakin ya ɗauka, can mama tace "Ahmad fa?" Se a lokacin ya faruk ya tuna da wani Ahmad, in be mance ba tun da aka shigo da mama hospital ɗin be tsaya ba, kama gaban shi yayi, irin ko a jikin nan nashi. Da sauri ya faruk yace, "Na aike shi ne". Shigowar Abba ƙ ciki ne yasa ya faruk tashi yace "Bari inje gida in tawo da Mumtaz se ta zauna dake" Gyaɗa kai mama tayi, har ya kai ƙofa ya waigo yace "Da me da me zance ta ɗakko?" A hankali mama tace "Ta kawo min dogayen riguna marasa nauyi, se phone ɗina" "Okay" yace ya ja musu ƙofar ya fice". Altine kawai ya samu a tana kaikawo a ƙasan Gaisawa sukayi tana tambayar jikin maman, Sama-sama ya amsa mata, tukun yace "Mumtaz fa?" Kanta a ƙasa tace "Tana sama tun ɗazu" Ko rufe baki batayi ba ya haura saman A buɗe ya iske ƙofar, duk da a buɗe take be shiga ba seda yayi sallama tukun Tana kwance idanun nan nata a kumbure, jin muryar ya faruk yasa ta miƙe da sauri, duk a tunanin ta agogon shi ya biyo Sarai yaga tsoron haka a tattare da ita, fuska a ɗaure kamar be taɓa dariya ba yace "tashi ki haɗa wa mama kaya marasa nauyi, sannan kema ki ɗauki naki, five minutes na baki zan je in dawo" Har ya kai ƙofa ya waigo yace "Ina takardar da mus'ab ya baki?" Jiki a mace ta ɗaga pillow ta ɗakko takardar ta miƙa mishi. Seda ya karanta tas ya ninke ya saka a aljihu, tukun ya kalle ta ido cikin ido yace "wallahi, wallahi ko da wasa naji maganar nan a bakin wani se na baki mugun mamaki, nasan ko na tambaya ko ban tambaya ba kin karanta abinda yake a ciki" Yana gama faɗa ya juya ya fice. Kamar warda ta sa ana gadin shige da ficen shi Yana fitowa Amal tayi saurin isko shi tace "Ya faruk Umma babba na kira" Badan ranshi ya so ba ya juya zuwa sasan ummah b Fuska a sake tace "Wai me ya same ta ne faruk? Kanshi a ƙasa yace "Hawan jini ne wai" Riƙe baki tayi ta hau salati, "itako me yayi mata zafi haka?" Can dai ta taɓe baki tace "Mugun nunkufurci ne ze halaka ta wlh, mace sam baza ka taɓa jin cikin ta ba, sedai tayi ta barin abu yana damun ta a cikin rai, to Allah ya tsayar a kanta" Ya faruk bece uffan ba, seda ta ƙaraci ƙorafin ta dan kanta tayi shiru tukun ya sallame ta ya wuce. Mumtaz ta jima tana jiran shi a wajen motar shi, duk da ba wani fira suke da Amal ba, amma taji daɗin tsayawar ta a kusa da ita ko ba komai tsayuwar ba zata dame ta ba Suna tsaye a haka ya faruk ya iso, tun kafin ya iso ya danna remote boot ya buɗe, Jakar hannun kayan ta saka a ciki, Amal kuma ta saka basket ɗin abincin hannun ta Murya ƙasa-ƙasa Amal tace "Ya faruk dan Allah nima zani" "muje" kawai yace Front seat ta shiga, mumtaz ta shiga baya ya ja suka tafi. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg13-14 Sanda suka shiga ɗakin mama na zaune dattijuwar likitar na cire mata drip ɗin da aka saka mata Mumtaz da Amal suka gaishe ta a ladabce ta amsa musu da fara'a Can gefen da fridge yake suka ajiye kayan hannun su, kujera Amal taja ta zauna, Mumtaz kuma ta koma gefen mama Drn na gama cire mata ta juya ta fice, tukun ya faruk ya ƙaraso ciki Be wani jima ba yace wa Amal "ke muje" Sosai mama ke mishi addu'ar gamawa lafia, dan ya faruk mutum ne. Suna fita mama ta kalli Mumtaz da har yanzu idanun ta basu sauka da fushin da suka yi ba tace "Kunna min heater can in watsa ruwa, kayan nan sun min nauyi da yawa" Jiki a mace Mumtaz ta tashi, duk mama na lura da yanayin ta, ba se an faɗa mata ba dama daga ganin idanun ta kasan ba ƙaramin kuka ta sha ba Tana kunna heater ta koma ɗayan gadon da aka aje shi domin me jinya ta kwanta haɗe da lumshe idanu, tanajin shigar mama toilet ta sakko ta hau bincike gadon da mamar ta tashi Seda ta bincike ko'ina bata samu komi ba tukun ta koma ta zauna Koda mama ta fito tayi mamakin ganin yarda shimfiɗar gadon tayi, bata kawo komi a ranta ba ta waiga tace "Kakkaɓe min gadon kafin nayi sallolin da suka wuce ni" Seda ta fakaici idonta ta zumɓura baki kafin ta nufin gyara gadon. Suna shiga gida ana kiran sallar magrib Shigewa Amal tayi cikin gida seat ɗin baya ya faruk ya buɗe ya kwashe ledojin siyayyar da yayi tun shekaran jiya be kwashe ba Seda ya kwashe har ya ja baya ze rufe motar yaga wata ledar a ajiye a inda Mumtaz ta zauna ɗazu Haɗe ledojin yayi a hannu ɗaya sannan ya ɗauki warcan, be tsaya dubawa ba saboda kiran sallah da akayi, seda ya kai kayan ɗaki tukun ya ɗauro alwala ya fito Seda ya ratsa cikin cincirindon maza da mata dake danƙare a wajen ana ta rabon kayan buɗa baki, sam wasun su bama ta sallar suke ba, ta cikin su suke, a haka ya samu ya wuce da ƙyar TUSHEN SU! Alhj sule me awaki shararren attajirin ƙauye ne, mutum ne me dattako da sanin yakamata, a lokacin Iyaye sukayi shawara aka haɗa shi aure da matar shi ta farko wato Balki, sun kwashe tsawon shekaru Allah be basu rabon haihuwa ko ɗaya ba, Kusan shekarar su Goma sha bakwai da aure kafin Allah ya ba balki rabo, sosai sukayi murna suka ji daɗi da rabon da Allah ya basu Haka Balki tayi ta rainon cikin ta cike da kulawar ko wani ɓangare, Alhj sule ya kan fita kasuwannin kusa dana nesa a ranakun kasuwa ya seda dabbobin sa, haka yake raba jama'a zuwa ko wacce kasuwa a wannan lokacin. Hanun shi a buɗe yake sosai, shiyasa be samu matsala da yawanci waɗanda ya aza akan dukiyar shi ba A haka wata rana da dare naƙuda ta kama balki, Daman jiran ta ake, Inna(kishiyar maman Alhj sule) itace tsaye kan Balki har Allah ya sauke ta lafia ta haifo ɗanta namiji me kama da Alhj sule, Suna daga can waje suka jiyo guɗar inna har uku, nan fa akayi ta murna ana ma juna sam barka, dan balki ba ƙaramar wahala ta sha ba Tas aka gyare balki da ɗanta aka miƙa wa Alhj sule, anan yayi mishi huɗuba da suna "Aliyu"(Abba babba) so ɗaya Balki taba Aliyu nono, sedai aka tashi washegari da gawar ta, cikin dare jini ya ɓalle mata, kafin ayi wani yunƙuri rai yayi halin shi Sosai aka shiga tashin hankali, masu kuka sun yi kuka, Wasu kukan su duk akan jaririn data bari ne saboda tausayi Kar kuso kuga Alhj sule, shi kanshi ya shiga ɗimuwa ƙwarai, ya yabi kyawawan halayyar balki ƙwarai da gaske. Duk nonon da aka baiwa Aliyu baya kamawa, akwana biyu duk wanda ya kalle shi se ya tausaya mishi, dan yunwa sosai ta fara bayyanar mishi Kamar da wasa, ƙanwar balki me suna Abu na zaune tace a miƙo shi, Tana karɓan shi tayi bisimillah ta kafa mishi nono, aikuwa cikin hukuncin ubangiji Aliyu ya karɓa, Yana sha yana sauke ajiyar zuciya Tunda mahaifiyar Alhj sule ta ƙyallara ido taga an samu ya karɓa tace "a barmata shi ta shayar da shi" Abinda akayi kenan, A wannan dalili na shayar da shi datayi yasa mijin ta yayi fushi ya sake ta, haihuwar su ɗaya dama Haka ta tattara ta dawo, sosai rayuka suka ɓaci ta dalilin komen da ake so tayi Ganin abun yaƙi yiwuwa yasa aka haƙura Ko sati bata rufa ba da gama idda aka ɗaura auren ta da Alhj sule ta maye gurbin yayar ta balki. Cikin hukuncin ubangiji tana shiga ta samu ciki, Haka Abu ta rinƙa rainon Aliyu da kuma cikin ta duk a lokaci ɗaya, Wata tara cif ta haifo ɗanta me kama da Aliyu dak Lokacin data haihu Aliyu ya cika shekara ɗaya da wata huɗu a duniya, a ranar kuma ta cire shi daga nono. Yaron data haifa aka saka mishi sunaa "Abubakar". Bayan shekara uku ta sake haihuwar Abbas, sannan tayi ƙasim, ta rufe da Auta Aisha. Sosai suka haɗa kai suka rinƙa ba yaran su tarbiya, yara dama dole se da saka idon iyayen su Sam sauran yaran basu taɓa sanin cewa ba Innaa Abu ce ta haifi Aliyu ba seda suka girma kowa ya mallaki hankalin sa tukun. A lokacin innaa Abu na iyakacin ƙoƙarin ta wajen ganin sun haɗa kansu, Kana naka Allah na shi, Aliyu ne yaso ya fita zakka, Allah yayi shi mutum ne me zuciyar tsiya, ga saurin hannu, abu kaɗan ze ɗaga hannu ya kai wa Abubakar duka, shikuma be iya ramawa ba wai dan bashi da ƙarfin ba, seda koyar da su da innaa Abu keyi kullum akan bin na gaba da su Yawan doke-doken da Aliyu ke yi ne yasa wata rana Innaa Abu ta dake shi shima, tayi ta mishi faɗa daga baya ta ɗora da nasiha akan yaja ƙannen shi a jikin shi. Duk da haka dai ba wani jituwa me ƙarfi a tsakanin Aliyu(Abba babba) da Abubakar(Abba ƙarami). Anan ƙauyen sukayi makaranta muhammadiya da kuma primary da aka buɗe Duk a cikin su Abubakar yafi nuna son karatun zamani, sauran se sun ga dama zuwa wani lokacin Bayan sun gama primary, Alhj sule da kanshi ya ɗauki Aliyu da Abubakar ya kaisu makarantar gaba da primary, wanda sauran su basu kai ga gamawa ba A haka dai, yau daɗi gobe akasi hakan, har Allah yasa suka kammala, Aliyu ya tsunduma harkar kasuwanci irin na mahaifin su, inda shi Abubakar ya tafi makarantar gaba, anan ya fara karatun shi na jami'a a fannin kasuwanci yana gaf da gamawa, Abbas ya fara nashi karatun a fannin mass com daga baya ƙasim ma ya biyo shi, inda anjima da aurar da Aisha ga wani ɗan me garin garin da suke, inda shima ya ɗauke ta ya bar ƙauye da ita suka fito gari. A lokacin da Aliyu ya cika shekara 25 yayi aure, Ya auri matar shi me suna Nabila, iyayen ta na da rufin asiri daidai gwargwado, nan inda yake kasuwancin shi a nan ya kama gida suka zauna Abubakar kam seda ya gama degree, a lokacin ba kowa ke samun wannan damar ba, sanda ya gama ya samu aiki a wani babban company ana biyan shi sosai da sosai Lokacin shi ba nauyin kowa a kanshi, iyaye ne kuma Allah yayi musu rufin asirin da ba se sun dogara da kowa ba seda ya shekara uku da fara aiki, a shekaru ukun nan kaf haka ya rinƙa tara albashin shi, tunda ko gidan zama ma bashi akayi, ba shi da wani buƙata sedai abunda ba'a rasa ba To da waɗan nan kuɗi beyi shawara da kowa ba yaje ya siya wani mahaukacin fili me girman gaske, lokacin wajen daji ne ma ba gida ko ɗaya, sedai an yanyanka filayen, haka ya siya ya adana takardun shi, filin kuma yayi banza da shi yaci gaba da aikin shi, Duk sanda ya samu lokaci yakan kaima iyayen shi ziyara, kuma ya kai ma ɗan'uwan shi Aliyu ziyara haɗe da sha tara ta arziki Nan Nabila(umma babba) ta rinƙa ma ƙanwarta campaign a wajen Abubakar, shi kam tuni ya ƙyallara idanu akan ƙanwar aminin shi. SHARE PLS ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg 15-16 Duk sanda su Nabila(umma babba) zasu tare shi da zancen ƙawarta yakan basar da zancen ya nuna be gane inda suka dosa ba Ba yarda suka iya, dole suka rabu da shi. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yau fari gobe baƙi Duk asabar ɗin duniya Abubakar(Abba ƙarami) ke zuwa wajen Zahra'u, sosai suka fahimci juna sukayi sabo me wahalar mancewa Da yake yana da ƙafa a gidan, yayan ta aminin shi ne sosai yasa be wani sha wahala ba, kuma da Allah yayi cewa ita ɗin rabon shi ce. Bayan shekara biyu da kusan rabi da auren Aliyu(Abba babba) shima Abubakar aka ɗaura nashi, an yi shagali dai dai gwargwado a wannan lokaci, amarya ta tare a gidan ta da ya kama haya Zama ne na fahimata da kuma ƙaunar juna Takan leƙa Nabila wani lokacin, duk da ba wani fira ce ke shiga tsakanin su ba se dai harare harare daga ɓangaren Nabila Da dai zahra'u taga take taken ta se tasha maganin zama da ita, tsaf ta ɗauke ƙafar ta daga zuwa wajen ta, in ba dai abun murna ko Allah kyauta ne ya faru ba Wannan kenan. Tsakanin auren Abubakar da Abbas ba wani tazara, shima ya haɗu da matar shi me suna hauwa, a ranar bikin Abbas ɗin ne matar Aliyu wato Nabila ta haifo santalelen ɗanta me kama da baban shi sak, ranar data zagayo yaci suna Umar faruk, shine suke kiran shi da faruk, sosai Zahra'u ta ɗauki son duniya ta ɗora ma faruk, da ta ɗauke ƙafa daga gidan, amma haihuwar faruk yasa take zuwa a kai akai, Nabila tayi ta yada mata magana son ranta amma haka nan take basarwa dan son da take masa Cikin hukunci ubangiji haka buɗi yayi ta buɗe ma kowa a cikin su, Saboda nema haɗuwa ta fara musu wahala, a wannan ɗan tsukin ne, Aliyu ya sake rarimo wani auren na biyu Sosai hankalin Nabila ya tashi, ta shiga nan ta shiga can, to da yake duk abunda Allah ya ƙadarta se ya faru ba makawa, haka akai auren nan kamar ba za'ayi ba Haka itama ya kama mata gida daban, Sumayya macece me haƙuri da sanin ya kamata itama bata da matsala ko kaɗan. Lokacin da Aliyu ya ƙara aure faruk be wuce shekara biyu da rabi ba Haka sumayya ta ringa janshi a jiki, ganin hakan yasa Nabila ta hana ta gwammace gara ta rinƙa barin Zahra'u na ɗaukar shi akan ace kishiyarta ke ɗauka Wannan dama da ta samu ne yasa sukayi mugun shaƙuwa da faruk, inda bakin shi ya buɗe da kiran ta da "MAMA" Abubakar kuma yana ce mishi "Abba" Da faruk ya ƙara wayo ne yake banbance sunan iyayen da Abba babba da Abba ƙarami kishiyar mahaifiyar sa kuma ya laƙaba mata "Umma ƙarama" mahaifiyar shi kuma "Umma babba" Sosai sunayen nan suka yi wa Umma babba ciwo, tasha ta rinƙa mammake mishi baki, amma haka nan ta haƙura ta rabu da shi badan ta so ba. Abu kamar wasa har umma ƙarama tazo ta haihu amma mama shiru babu alamun ciki Sam basu saka wata damuwa a zukatan su ba, sun san Allah ne meyi, duk da habaicin da umma babba ke yawan yi mata a duk sanda suka haɗu a wani taro ko sha'ani bata taɓa saka abun a ranta ba balle ya dame ta. Ta ɓangaren matar uncle Abbas kam bata fiya shiga sabgar kowa ba, saboda take-taken umma babba data gani Sun ɗan fi zama da mama suyi fira ma, sukan ziyarci juna lokaci zuwa lokaci. Sosai rashin lafia ya kama Inna Abu, hankalin kowa ya tashi, Lokacin da Abba ƙarami yaje yaga halin data ke a ciki hankali a tashe ya ɗakko ta suka shigo asibitin cikin gari Sosai sirikan nata ke bata kulawa, babu warce ta rainata a cikin su, A cikin jinyar ne Inna Abu ta lura da sam sirikan nata ba wata jituwa a tsakanin su Batayi musu magana ba, seda gaba ɗaya ƴaƴan nata suka hallara tukun tace "Kuji tsoron Allah kuso junan ku da amana, kar ku bari asamu ɓaraka a tsakanin ku balle har na kusa da ku su gane su shigo da nasu son rai, ku sani duk abu ɗaya ne yayi ku, baku da banbancin komi a tsakanin ku, bana so ko so ɗaya wani daga cikin ku ya ɗarsa wani abu mara daɗi a cikin ranshi, ku zama tsintsiya maɗaurin ta ɗaya wanda ko ƙasa ta rufe min ido zanyi alfahari daku" Can ta fashe da kukan tausayin kanta da ma su yaran nata Sosai hankalin su ya tashi sukai ta banbaki har tayi shiru Ɗakin yayi tsit, maganar inna Abu ta katse shirun da "Abubakar, maganar filin nan da kayi min ɗazu nace ka ban lokaci, to na yanke shawarar ka gina ɗin kamar yarda ka fara faɗi, alabarshi se ku haɗe iyalan ku duka a waje ɗaya se fahimta ta sake shiga sosai a tsakanin su Ku kuma zumuncin ku na nan sema ƙarfi da ze ƙara" Tana rufe baki uncle ƙasim yace "Kar kice haka inna, ni anawa tunanin se inga zama a waje ɗayan nan ba shine zefi ba, kamar za'afi zumunci in kowa na muhallin shi" Da sauri Abba babba yace, "Yarda tace haka za'ayi ko muna so ko bama so, ballantana banga wani aibu a cikin maganar ta ba" Abba ƙarami bece komi ba, duk da shi ya fara kai wa mahaifiyar shi shawarar yin hakan, amma daga baya ya gane ya tafka babban kuskure, kuma tunda yanke shawarar hakan bashi da kuma bakin da ze iya hanawa. Ta ɓangaren uncle Abbas kam cewa yayi "bani da choice ni kam, dan ba lale ayi amfani da abinda kace ba" kKowa seda ya kalle shi jin furucin bakin shi, inna Abu tace "Ni dai ga abunda nace, kuma duk wanda yayi watsi da wannan maganar ban yafe ba" Tsit wajen yayi, kowa da abunda yake saƙawa a ranshi, in ka kalli fuskar Abba babba zaka ga kamar me murmushi. Abba ƙarami kam baka gane a wani yanayi yake a ciki ba, kanshi na ƙasa. Uncle ƙasam ne ma yace "Allah ya baki haƙuri, ai abun be kai ga haka ba hajiya Inna" ya ƙarashe maganar da barkwancin shi. ganin dare yayi ne kuma suna ta zama yasa tace "zaku iya tafiya dare yayi, Allah yayi muku albarka yasa duk ku gama da duniya lafia" Gaba ɗayan su suka amsa da amin, ɗaya bayan ɗaya suka yi mata sallama suka fice Abba ƙarami ne na ƙarshen fita, har ya kai ƙoma yaji inna Abu tace "zo nan Aliyu" Jiki a sanyaye ya dawo ya zauna still kanshi a ƙasa Kanshi ta dafa tace "Ka daure kayi hakuri da Aliyu, da sauran ƴan'uwan naka, sannan kaba zahra'u haƙuri itama, zaman ku a tare ze saka ni farin ciki, duk da bakayi magana ba nasan baka so hakan ba, amma kuyi haƙuri kuma na yafe muku gaba ɗayan ku, tashi kaje Allah ya sada mu da alkairin sa" Murmushi yayi jin zolayar da tayi mishi, Sanda ya fita duk sun kama kansu, shima ya haye babur ɗin shi ya tafi gida. WASHE GARI Wajen shida saura suka ji bugun gida, mama na kitchen tana dafa ruwan wanka ta shiga ɗaki ta taso Abba ƙarami Yana fita ya dawo yana salati duk yabi ya ruɗe Anan take jin rasuwar Inna Abu, Hankali ya tashi sosai, ko wanka basu samu yi ba suka ɗunguma suka tafi asibitin Sosai ahalin nan suka shiga damuwa, mota aka samo aka sakata, sannan wasu daga ciki suka shiga Sauran kuma suka samu wata motar suka bi bayan su zuwa ƙauyen su A nan aka sallace ta aka rakata zuwa gidan ta na gaskiya. Bayan bakwai kowa ya kama gaban shi yin harkokin sa. Tunda inna Abu ta rasu Abba ƙarami da maganar inna Abu yake kwana yake tashi Sam ya kasa samun sukuni a zuciyar shi Wata safiyar Asabar ce yana zaune suna ɗan taɓa hira sama-sama da mama, faruk na kwance a gefen ta yana bacci Abba ƙarami yace "Zahra'u bari in daure inje in duba filin nan inga ta ina zan fara" "Okay to, Allah ya kiyaye, ai gara kaje ka duba ɗin tun wuri". Da Abba ƙarami yaje wajen da ƙyar ya iya gane wajen, seda ya nemo me unguwar da kusan a hannun shi dama filin yake tukun ya gane Sosai Abba ƙarami yayi mamakin cikar wurin, gidaje ne a tsare reras manya-manya gabas da yamma kudu da arewa, Be bar wajen ba seda ya tabbatar da ya daidaita abunda ya dace. Tsayawa yayi tsayin daka aka fitar da zanen gidan cikin kwana kaɗan flat biyar aka zana, ko wanne duplex, Flat ɗin Abba babba anyi shi dan zaman mace biyu, a ido yafi ko wanne girma, sama ɗaki biyar, ko wacce biyu se na Abba ƙarami ɗaya Ƙasa kuma akayi ɗaki biyu, se babban kitchen da store Flat ɗin uncle Abbas da na uncle ƙasim na tsarin mace ɗaya kuma iri ɗaya, sama ɗaki biyu ƙasa biyu se kitchen da store Flat ɗin Abba ƙarami mama yaba wuƙa da nama ta faɗi yarda ta ke son ya kasance Aikuwa tayi tsarin da yafi na kowacce kyau da haɗuwa Dan ita hada palo tace ayi mata a sama, Sosai tsarin ɓangaren ta ya babban ta da na sauran. Gadan gadan aka fara gini, Alhamdulillah, da yake ya tara shiyasa nan da nan komi ke sauri A cikin shekara ɗaya gam aka kammala gidan, dai-dai lokacin uncle ƙasim shima ya samu mata Sanda Abba ƙarami yaje musu da maganar komawa sabon gida memakon yaga murna a fuskokin wasu daga cin ƴan'uwan nashi, se yaga saɓanin haka, tun daga nan jikin shi ya sake yin sanyi zuciyar shi ta karye dauriya kawai ya ara ya yafa ma kanshi. Yaso yayi furnishing gidan, wata zuciyar ta hana shi, Mama kawai ya ɗauka suka je ta zabi komi da ya dace da gidan suka siya aka wuce dasu can Sun riga kowa komawa, se uncle Abbas, Abba babba be dawo ba har seda uncle ƙasim ya riga shi shiga da sabuwar amarya, yana can yana fama da rikicin umma babba, ita allanbaran sedai ya barta a gidan hayan, dan ita wai zuciyar ta bata mutu ba da zata kwanta ƙanin ta yayi mata komi Ƙarshe dai seda abun ya ɗauki zafi sosai, dan har umma ƙarama ta koma da ƴar jinjirar ta da bata wuce watanni ba tukun umma babba ta dawo Tun da kuma ta saka ƙafarta a gidan ta hau danasanin ƙin dawowa da wuri da bata yi ba, a cewar ta "wannan aljnnar duniyar" Nan fa ƴan'uwa da abokan arziki akai ta zuwa taya su murna da saka albarka Tunda suka tare kowa ya shiga saiti, harta da umma b da ke da matsala ta nutsu ta dena shiga sabgar kowa, se kuma a lokacin ne take so ta kame girman ta Haka ta ɓangaren sauran, kowa harkar gaban shi yake Mazajen ma sun haɗa kai, komi da ya shafi cigaban su a tare suke shawartawa, se kuma albarkar haihuwa da aka fara samu akai akai Gaba ɗayan su sun riga mama hauhuwa, dan har seda matar uncle ƙasim ta haihu da kusan shekara kafin mama ta samu cikin mus'ab, lokacin faruk na da shekara goma sha biya a duniya. Randa mama ta haihun kuwa haka ya kafa ya tsare akan babyn, Sosai yake nuna mishi so da kulawa, kullum da safe kafin ya tafi school se ya leƙa ya gan shi, haka zalika in ya dawo se ya leƙa Gaba ɗaya ma kusan tarewa ne kawai beyi a sasan mama ba, umma b tayi faɗan tayi dukan har ta gaji ta haƙura. Shekarar mus'ab ɗaya da watannin mama ta sake haifo Ahmad, hmmmm ga arziki yaci uban na da ga kuma ƙaruwar ƴaƴa maza da ake ta samu ta ɓangaren su da Allah yafi rufa wa asiri Tun daga kan Ahmad shiru mama bata sake haihuwa ba, haka akai ta tafiya, yau daɗi gobe akasin hakan Umma b seda ta haifi yara shida cif sannn haihuwar ta tsaya Ya faruk, ya sabiha, ya maryam, ya fa'iza, se hafsa da auta Amal. Umma ƙarama tana da yara uku, ya fauza, ya khairi da auta fadil. Mummy na da biyu Ya Tk, da Aliyu(amir) Aunty na da uku, Abdul, muhammad da mahmud. Mama na da uku, mus'ab, Ahmad da auta mumtaz. WANNAN KENAN, IN DA WANI ABU KUMA KWAJI A GABA. CIGABAN LABARI. Ledojin da ya shigo da su ɗazu ya janyo ya bubbuɗe su yana ware kayan, sosai ɗinkunan suka yi kyau Seda ya gama tas ya matsar da su tukun ya janyo ledar ɗazu da ya gani a inda mumtaz ta zauna, yana buɗewa yaga agogunan shi guda biyu data ɗauka ne a ciki Shiru yayi ya kafe su da idanu kamar me nazarin wasu abubuwa, a hankali ya saka hannu ya ciro ƴar ƙaramar takardar da ke ciki ya buɗe idon shi suka kai ga ɗan gajeran rubutun dake ciki "Kayi haƙuri dan Allah kar ka faɗa wa mama ko Abba na" Iska me huci ya fesar bayan ya ajiye takardar a gefen shi, dunƙule hannun daman shi yayi da ƙarfi, dan zaka ga jijiyoyin hannun sun yi riɗu riɗu Cike da tsananin ɓacin rai yace "Who is behind this?"(waye me hannu a ciki?) Tabbas AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI" INA ME BADA HAƘURI NA JINA SHIRU DA KUKA YI NA KWANA BIYU, ABUBUWAN NE KASHI DA KASHI ❤️ INA MIƘO SAƘON GODIYATA GARE KU "LAUJE CIKIN NAƊI FANS" ADDU'O'IN KU MEANS ALOTS TO ME, ALLAH YA SAKA DA KHAIRAN ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 SHARE PLS. LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg17-18 A daren bayan sallar isha'i Abba ƙ da aminin shi yayan mamar suka turo ƙofar ɗakin suka shigo, a lokacin an maida wa mama drip tana ta bacci mumtaz kuma na kwance ita ba baccin take ba kuma ba wani abun take ba, kwance take tana saƙa da warwara Jiki a mace kamar ko da yaushe ta tashi zaune haɗe da amsa sallamar Abban nata da kuma aminin shi kuma kawun ta. Kanta a ƙasa ta gaishe su bayan ta sakko daga gadon zuwa gefen mama Har mumtaz ta zauna ta tuno da dattijuwar likitar tace ta kirata in Abba ƙ ɗin yazo Murya a sanyaye tace "Abbana, dr tace in kirata in kazo wai" Jin yarda take magana a sanyaye yasa Abba ƙ kafe ta da ido yana son ya gano mene matsalar ɗiyar tashi Jin ta sake maimaita tambayar a tunanin ta beji bane, Still idon shi a kanta yace "Je ki kirata" Gyara dogon hijabin ta tayi tukun ta fice zuwa office ɗin likitar. Tun sallamar farko da Abba ƙ sukayi mama ta farka, idon ta ne kawai bata buɗe ba jin yarda sukayi mata nauyi Ganin tana marmar da idanun yasa Abban matsowa kusa da ita ya zauna Bayan hannun shi ya ɗora a kan goshin ta jim kaɗan ya cire Murya ƙasa-ƙasa mama tace "temaka min in tashi zaune" Kara mata pillow yayi a bayan ta tukun ya jingina ta da bango A hankali ta buɗe idon ta a kan yayan nata da yayi shiru yana kallon yarda ƴar'uwar tashi ta koma Murmushin ƙarfin hali tayi tace "sannu da zuwa ya junaid" Shima matsowa yayi tukun ya amsa da "ya kika ƙara ji?" Kanta a ƙasa tace "Alhamdulillah" nan da nan idanun ta ya kawo ƙwalla, Abba ƙ na lura da ƙwallar ya fara tapping bayan hannun ta a hankali, ita tasan me yake nufi, cike da dauriya ta maida hawayen. Tayi knocking a bakin office ɗin yafi a ƙirga, jin shirun da yawa yasa ta murɗa handle ɗin duk a tunanin ta ba ze buɗe ba Aikuwa tana murɗawa ya buɗe, Leƙawa tayi ciki, ganin babu kowa yasa ta jayo ƙofar da niyar kullewa, amma sam zuciyar ta taƙi barin azalzalar da lokaci zuwa lokaci takan ji hakan Sam mumtaz kasa daurewa tayi seda ta biye wa azalzalar zuciyar ta taƙara shiga office ɗin Memakon data shiga ta yi abinda aka aiketa, Ina ta mance tunda ta ɗora idanun ta akan abin hannun data gani ajiye akan teburin likitar ta nufe shi kanta tsaye, jikin ta babu inda baya rawa tsabar luguden data ke ji a cikin zuciyar ta Tana kaiwa teburin ta dafe abun hannun nan dake ta walwali da ɗaukar idanu daga ganin shi kasan dutse ne me mugun daraja Tana ɗauka ta zira shi a aljihun doguwar rigar ta Seda ta tabbatar da taji shi a jikin ta tukun ta sauke ajiyar zuciya me nauyin gaske, bata sake kallon komi a wajen ba ta juya tafice da mugun sauri har tana harɗewa da ƙafafuwan ta. Mumtaz na fitowa daga office ɗin dattijuwar likitar na shawo kwana, Juyawar da mumtaz tayi yasa likitar bataga fuskar ta ba Kafin ta ƙaraso mumtaz ta yi gaba, Gaba kaɗan ta ƙara se ga Abba ƙ Fuska a ɗaure yace "daga kiran dr se kije ki shantake?" Da sauri ta sadda kanta a ƙasa, duk a tunanin ta ze gane abinda tayi a cikin ƙwayar idon ta, tace "Bata cikin office ɗin, shine na tsaya jiran ta, da naga bata dawo ba shine na tawo" "okay" kawai Abba ƙ yace ya juya suka koma ɗakin. Su Abba na shiga ɗakin likitar ta turo ƙofa itama Da fara'a sosai a fuskar ta suka gaisa da su Abba, sannan ta ƙarasa kusa da mama dake zaune Mumtaz kam ƙasa tayi da kanta tana ƙara jin faɗuwar gaban ta na daɗa tsananta, a hankali ta saka hannun ta cikin aljihu ta lalubo abin hannu taji yana nan Ajiyar zuciya ta sauke wanda yasa daga mama har likitar kallon ta. Murmushi likitar tayi, sannan tace "wannan ajiyar zuciyar fa ƴammata" Itama ƙaƙalo murmushin tayi, bata ce komi ba ta tashi ta shige toilet. Kallon ta Abba ƙ yayi yace "Yanzu mumtaz ke cemin kina son gani na" Gyara zaman glass ɗin fuakar ta tayi tukun tace "Eh, matar ka na son in sallame ta, ni kuma saboda yanayin jikin ta da na gani yasa nace ba yanzu ba, ta zauna ta ƙara jin sauƙi, da dai naga ta nace yasa nace in kazo ayi min magana" Kafin Abba ƙ yayi magana ya junaid yace "Kiji wata magana se kace ƙaramar yarinya fa" Murya a sanyaye mama tace "Ni fa saboda tafiya ta umara nace a sallame ni, a can ne zan kai ma ubangiji kuka na yarda ya kamata, kuma ko ba haka ba ai ina ganin dr Sanaa kuma ta san problems ɗina sosai" Kallon ta Abba ƙ yayi yace "Yaushe ne tafiyar to?" A gajerce mama tace "next tomorrow" Numfashi ya sauke a hankali tukun yace "Ki yi discharging ta kawai, na manta sam da zuwan namu can ma" Cike da fara'a likitan tace "yarda kuka ce ai, fatan mu a samu lafia ai" Kafin goma na dare Abba ƙ ya gama da bills ɗin tas Ankai komi mota, da kanshi ya kama matar shi ya riƙeta mumtaz na biye da su a baya Ya junaid ya musu sallama ya tafi. Seda Abba ya zaunar da mama a seat ɗin gaba kafin ya zagaya ya shiga Mumtaz kuma na baya, yaja motar suka fice Daidai gate mumtaz tayi ido biyu da khalid da suka taɓa haɗuwa a kasuwar seda gold Tsaf sun gane junan su, da sauri khalid ya sauke glass da niyar yima mumtaz magana, kafin ma ya gama saukewa ta kawar da kanta gefe, gaban ta naci gaba da bugawa haka kurin Ganin ta kauda kanta yasa da sauri ya gangara gefe yayi parcking, kafin ya ƙaraso motar su Abba yaja sunyi gaba Mumtaz na ganin sun wuce ta waigo da kanta tana kallon shi ido cikin ido, shima yayi tsaye ya kafe ta da nashi idanun har motar ta ɓace ma ganin shi. SHARE PLS ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg19-20 Jiki a mace yace "Tunda har Allah ya sake nuna min ke to tabbas zamu sake haɗuwa dake!" Still jiki a mace ya juya zuwa inda yayi parking ya shiga ya ƙarasa shiga ciki Office ɗin da mumtaz ta fito ɗazu naga ya sanya kai ciki, yana shiga ya iske dattijuwar nan tsaye tana dube dube ranta a mugun ɓace Sallama ya sake yi a karo na biyu tukun taji, bata waigo ba ta amsa Da mamaki khalid ya ƙarasa kusa da ita haɗe da faɗin "Lafia kuwa mami?" Ƙaramin tsaki taja, tana aje book ɗin ƙarshe data ɗaga tace "Hmm, bracelet ɗina na aje anan ɗazu da zanyi alwala, emergency call da na samu ne na mance ban ɗauka ba na fita, amma abun mamaki na duba sama ko ƙasa ban gani ba" Sanin muhimmancin abun a wajen Mami ne yasa shima ya zage yana taya ta nema, Aikuwa abun hannu yace ɗauke ni inda kk aje Abu kamar wasa seda mami ta koma har inda taje ɗazu amma babu shi ba alamun shi In ranta yayi dubu to ya ɓaci, sosai ta ɗauki abun hannun nan da muhimmaci ba wai dan tsananin tsadar shi ba, se dan daga hannun wacce ya fitone yasa tayi mugun ɗaukar shi da muhimmanci a rayuwar ta Kankace me idanun mami yayi jajir tsabar ɓacin rai, macece me sauƙin hali amma tana da mugun fushi in abu ya kaita maƙura Tsabar gajiyar da ta yi ne yasa ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun dake jere a office ɗin nata Hannun daman ta tasaka ta tallafe kuncin ta na dama, Shiru tayi tana sake nazari ko zata tuna ƙila ba anan ta ajiye shi ba Amma tsaf iya tunanin ta me hasasho mata komi ba Jiki a mace ta tashi bayan khalid ya haɗa mata hand bag ɗin ta da duk wani abu da ya san tana tafiya gida dashi Murya a tausashe khalid yace "Kiyi haƙuri mami, tunda kaf garin nan bracelet ɗin irin shi ne kaɗai baze yi wahalar ba, in ma ɗaukan shi akayi to ba ze wuce sedawa za'ayi ba, Se mu bada sanarwar kama duk wanda aka gani ya kaishi kasuwa" Ajiyar zuciya mami ta sauke, bayan ta gyara zaman ta a cikin motar tace "har na ɗanji sauƙi a raina, Allah ya dubeni yasa a ganshi da gaggawa, kafi kowa sanin yarda nasa shi a raina, infact ma a gaban ka goggo ta damƙa min shi gaf da Allah ze karɓi rayuwar ta" Sosai khalid ya kwantar mata da hankali, basu kai gida ba yayi ta making calls yana bada sanarwa akan abun hannun. Tunda Mumtaz ta shiga ɗaki take kallon abun hannun, sosai idanun ta suka cika da ƙwallar rashin sanin ta mecece Jiki a sanyaye tace "Kodai inje in maida?" Jitayi zuciyar ta na raɗa mata "banda abunki mumtaz in kika kaishi kasuwa ba ƙaramin kuɗi zaki samu ba, se kiyi ta hidimar ki ba se kin takura mama ko Abba da tambayar bani bani ba" Knocking ƙofar ɗakin da akayi ne ya katse mata tunani, da sauri ta mayar da shi cikin aljihun ta tukun taje ta buɗe ɗakin Altine ce tsaye a ƙofar, mumtaz na buɗewa tace "mama na kiran ki" Bayan ta tabi, ita tayi kitchen, mumtaz tayi can ƙaramin palon maman inda matar uncle junaid(yayan mama) tazo se wasu daga cikin ƴan'uwan su Gaishe su tayi kanta a ƙasa ta wuce inda mama ke kishingiɗe, manya manyan ledoji jube a gaban ta Seda ta zauna tukun tace "gani mama" Idon maman a rufe ta nuna wa mumtaz ledojin gaban ta tace "hijabai ne, ki ware naki, nima ki haɗa min nawa a cikin babbar akwatin nan da na haɗa kayan tafiyar mu" Da "to" ta amsa, da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai ta ɗauki ledojin tayi sama da su Seda ta gama haɗa wa mama nata tukun ta wuce da nata da se a yanzu ta harhaɗa kayan tafiyar ta, duk uban shelar da mamar tayi mata kusan sati kenan amma bata haɗan ba se yanzu. A daren duk suka koma gidajen su da adduar samun lafiya ga mama, wanda har yanzu babu wanda yasan sabab ɗin ciwon maman. Mumtaz na kwance wajen ƙarfe ɗaya da rabi na dare ta fara jin ƙarar kunna motacin gidan A mugun sukwane ta sakko daga kan gadon ta leƙa ta window Su umma b, mummy, da aunty ne, se Amal, hasfa, Bilkisu yarinyar ƙanwar umma babba ce, se najwa itama mummy ce ke riƙe da ita, da Amir ɗan gidan mummy se mahmud autan Aunty Da sauri mumtaz ta janyo wayar ta tayi dialing no ɗin Amal Bugu biyu Amal ta ɗaga tayi saurin yin ƙasa da murya dan kar hafsat dake kusa da ita taji ta faɗa wa umma b Mumtaz tace "Ina zakuje da tsohon daren nan? nasha tafiyar se daren gobe fa?" Murya ƙasa-ƙasa Amal tace "ɗazu naji umma b na cewa an raba tafiyar ne saboda jikin mama wai, so kune zaku tawo gobe" Daga can mumtaz ta taɓe baki, murya ciki-ciki tace "Ta daiyi munafurcin data saba yi" Daga can Amal tace "banji ba fa," sake taɓe baki mumtaz tayi tukun tace "se mun haɗu kawai" ta tsinka wayar ta Murmushi kawai Amal tayi, dan yanzu sam ta dena mamakin sauyin ƴar'uwar tata kuma ƙawarta Maida wayar tayi jaka ta juya ta shiga kusa da Bilkisu Mota biyu sukayi zuwa airpot, wajen huɗu saura jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasa me tsarki. WASHE GARI Mumtaz na ganin zuwan sakina ta bar mata sauran aikin da mama ta saka ta Ɗaki ta nufa hijabi ta ɗauka se wannan abun hannun da zuciyar ta ke ta azalzalar ta akan ta saida shi Ta ƙofar da Abba ƙ ke shigowa tabi cikin sanɗa dan kar Altine ko sakina suji motsinta take tafia Seda ta ɓulle zuwa gate tukun ta saki jikin ta tafara tafiya normal Abunda bata sani ba shine, ya faruk ya ba me gadi lasisin kiran shi a duk lokacin da ƴammatan gidan zasu fita, be ware sunan ta ba gudun zargi ko wani abun daban, se yace dukan su har da wanda ake riƙon su a gidan kuwa Yana ganin tunkarowar ta gate ɗin ya zaro wayar shi kuwa Tana ficewa ya danna ma ya faruk kira, murya a ƙasa yace "yallaɓai, yanzun nan hajiya mumtaz ta fita" "nagode" ya faruk yace ya tsinka wayar, yana gab da shigowa layin gidan ne daman, tunda gate man ya kira shi ya samu waje ya tsaya, be kashe motar ba yana zaune a ciki ya baza idanu yaga ta ina zata ɓullo Zaman kusan minti biyar yayi tukun ya hangota, In wani ne da be san ta ba ya ganta zece a nutse take tafiyar ta Amma shi da yayi mata farin sani kallo ɗaya yayi mata ya gane ba gaskiya tattare da ita A ɗan gaba da shi kaɗan ta samu kekenapep ta hau Beyi ƙasa a gwiwa ba ya bi bayan su a hankali, sosai gaban shi ke faɗuwa dan sam be yarda da fitar ta ba Haka zalika a dokar gidan ba'a aiken ƴaƴa mata ko nan da can hasalima basu hawa motocin haya balle a kai ga kekenapep, duk rintsi ana musu wannn alfarmar na kaisu duk inda suke so Sannu a hankali yake binsu har suka dangane da bakin babbar kasuwa A tsorace mumtaz tace "sauke ni a nan kawai mlm" Waigowa me keken yayi yace "bamu zo ba ai hajiya, kasuwa gold na ɗan gaba wannan babbar kasuwa ce ai" Dallaro mishi manyan idanun ta tayi tukun tace "na sani ai ɗan'iya, a nan naga damar sauka" Ta ciro ɗari biyar ta miƙa mishi sannan ta sauka. Ya faruk na ganin ta sauka yayi saurin ciro wayar shi ya danna mata kira Yana kallon sanda ta kalli wayar, memakon ta ɗauka sema murguɗa baki datayi, yana kallo tana motsa baki alamun magana take, maganar ma yasan be wuce rashin kunya ce Seda yayi mata kira uku bata ɗaga ba, kuma ta kasa shiga kasuwar sam Sosai zuciyar ta ke ingiza ta, amma wani sashi na zuciyar yana dakatar da ita Kome ta tuna oho, jikin ta har yana rawa ta tsaida wani me keken ta hau Ya faruk na ganin haka ya juya yabi bayan ta again Mugun mamaki ne ya sake kamashi ganin sun ɗauki hanyar gida A fili ya furta "bata da gaskiya, wani abun tayi niyar shukawa" Kafin a kai gate ɗin gidan ya sauke ta taƙarasa da ƙafa. Seda ya faruk ya bada tazara sosai kafin ya shiga gidan shima Direct side ɗin mamar ya nufa, seda ya duba ta da jiki tukun ya fito Sakina na zaune ana mata kitso yace "ina mumtaz" fuska a ɗaure tace "ƙila tana ɗaki" Kai tsaye ɗakin ya nufa, seda ya ƙwanƙwasa kafin ya shiga Zaune ya iske ta gaban mudubi comb a hannun ta ga gashin nan buzu-buzu kamar mahukaciya sabon kamu, ido sharɓe da hawaye Jin shigowar mutum yasa ta waiga da sauri tana tashi tsaye, ita duk a tunanin ta mamar ce ta dawo kamar yarda tace Ganin ya faruk ne yasa ta ja baya ta ɗauki hijabin ta zata saka Yasan sarai me take wa kuka, sam bata ƙaunar kitso tun tana ƙarama, Taɓe baki yayi sannan yayi ƙasa da murya yace "wajen ubanwa kika je ɗazu, me ya fitar dake?" Firgicin jin tambayar da yayi mata ne yasa ta saki comb ɗin hannun ta, ido a waje tace "wallahi ba inda naje fa" Cable ɗin wayar ta da ya gani a kan mudubi ya ɗauka, shima zaro mata nashi manyan idanun yayi yace "kin iya rantuwa akan ƙarya ko?, me kika je yi a kasuwa?" ya sake maimaita tambayar yana ɗaga cable ɗin kamar ze tsula mata Bata mance da haɗuwar su ta rannan ba, jiki na rawa tace "wallahi abu naje siya, kuma ban shiga kasuwar ba na dawo" Ƙara matsowa kusa da ita yayi, kamar ze shaƙeta yace "ƙarya kike, abun wani kika sata halan zaki je ki ɓatar da shi?" kasa magana tayi, se girgiza kai kawai tana sake ja da baya, murya na rawa tace wallahi ban ɗauki abun kowa ba" Jin muryar mama na kwala kiran sunan ta yasa ya shige toilet ɗin ɗakin da sauri, yana shiga tana turo ƙofar Tsaye tayi tana ƙare mata kallo ganin yarda take sharar hawaye wani na korar wani A mugun fusace tayi kanta da faɗa "Kitson kike ma wannan kukan mumtaz, saboda baki san darajar mutum be shine kika shanyata tun ɗazu tana jiran ki? To wallahi ko kukan jini zakiyi bazamu tafi dake a haka ba kai kamar na mahaukata, ni wlh dama gashin ze kakkaɓe uban kowa ma ya huta ni kaina na huta da ciwon kan da kike sakani duk sanda za'ayi miki kitso" Tsaye mumtaz tayi bata ko motsa ba, ganin mamar tayo kanta ta fice da gudu hada ɗan haɗawa da ihu Haka mama tayi ta sababi kamar zata ari maki saboda takaici. Ya faruk najin fitar su ya fito, ba komai ya sakashi ɓoyewa ba se sanin halin mama da yayi Tsab zata zargi da wani a bu a ƙasa, shi kuma be shiryawa tambayoyin ta ba Wayar mumtaz da ya gani akan mirrow ya ɗauka tas ya bincike wayar ko da zega wani abun, amma bega komi ba, haka ya maida ya ajiye Can ta ƙofar baya yabi ya fice ba tare da kowa ya lura da shi ba. Seda mumtaz tasha faska a wajen mama kafin me kitson nan ta gama. Ya faruk tunda ya shiga ɗaki yake saƙa da warwara, tun lokacin da ya kama mumtaz da fara ɗauke-ɗauke yake shawara da zuciyar shi, se yau yaji kwarin zuciya inda yayi alƙawarin zuwa bayan sallah in sun dawo daga umara ze faɗa ma iyayen nashi dan a tunanin shi shine babban mafita, gwara duk a aurar da su kowa ma ya huta. SHARE PLS ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 IN SHA ALLAH SE ZUWA BAYAN SALLAH ZAMU ƘARASA ALLAH YASA MU FARA AZUMIN MU GAMA A SA'A, UBANGIJI YASA MUNA DAGA CIKIN ƳANTATTUN BAYIN DA ZA'A ƳANTA YA RABBI YA ZAƁA MAMU SHUWAGABANNI NA ƘWARAI ALLAH YASA MU CIKA DA KYAU DA IMANI. LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg-26-27 Ko second goma beyi ba ya ɗauke kanshi yaci gaba da wayar shi kamar be ganta ba. Mumtaz kam tunda ta ja ta tsaya bata sake motsi ba seda taji maganar khalid daf da ita tukun ta dawo hayyacin ta Da mamaki khalid yake tambayar ta "Are u okay?" Ko kallon khalid bata tsaya yi ba ta ɗiba tayi ciki, ƙiris ya hana ta kwasa da gudu, tana kaiwa ƙofar ɗakin su jikin ta na ɗan rawa ta ciro katin ɗakin ta kara a jiki, yana buɗewa tayi wuf ta shige dan har seda ta ba Amal dake zaune tsoro Ido a waje Amal tace "Mumtaz ina kika je?" Banza da ita tayi, cire hijabin jikin ta tayi ta wuce toilet Gaf da zata shige toilet ɗin Amal ta sake cewa "Tunda bani da matsayin da zan tambaya ki bani amsa se ki tanaji amsar da zaki ba ya faruk da su Abba ƙ" Tana gama faɗin haka ta juya tayi kwanciyar ta mamakin mugayen halin mumtaz na daɗa cin ta a ciki Duk da mumtaz ta ɗanji tsoro da Amal ta ambaci su Abba, amma ji tayi zuciyar ta dake sam tsoron babu shi, Ƙaramin tsaki taja bayan ta watsar da komi hankalin ta gaba ɗaya ya ɗugunzuma ga agogon hannun khalid, tunani take na yarda zata raba shi da shi har ta shiga toilet tana saƙe-saƙen ta. Cikin farin ciki da zumuɗi khalid ya koma masauki, sedai murnar shi ta koma ciki, inda yayi ta kiran layin Mumtaz amma shiru bata shiga Ta ɓangaren mumtaz kuwa kashe wayar tayi, dan kar Abba ƙ ko ya faruk su nemeta. Sam kasa rintsawa ya faruk yayi a cikin wannan dare, da ya tuno fuskar khalid se gaban shi yayi mummunar faɗuwa Sam kwanciyar ma gagarar shi tayi ya tashi zaune, duk da sanyi air con dake ɗakin hakan be hanashi zufa ba Zazzafan huci ya fesar, cike da kokwanto ya furta "Allah yasa yarinyar nan bayan ɗauke ɗauke bata bin maza!" Shi kanshi seda ya runtse ido da ya faɗi kalmar "neman maza" da yace da sauri kuma ya koma faɗin "a'uzubillahi minashshaiɗanirrajim" A haka har dare ya raba yana saƙe saƙen abubuwa a ranshi. ****** Hafsa ce ɗaure da towel zaune a gefen gado tana shafa mai, kunnuwan ta gaba ɗaya ta miƙa wa najwa dake ta fama fallasa mata sirrin dake cikin zuciyar ta akan ya faruk Seda hafsa tagama jin komi daga bakin najwa tukun tace "Danƙari, lallai najwa zuciyar ki batai miki adalci ba wallahi, tunda muke dake kin taɓa ji ance ga budurwar ya faruk?" Bata jira cewar hafsa ba ta ɗora da "To wallahi na taɓa jin ance aljanar dare ta aure shi da daɗewa, dan haka ki shafa ma kanki lafia ki lallaɓa da ɗan sadik ɗin ki, in kuma baki ji ba kyaji da wulaƙancin shi ba ruwana" Murmushi Najwa tayi ta matso kusa da hafsa da har a fuskar ta zaga gane batayi na'am da maganar ba tace "Haba hafsa, ke da zaki bani shawarar yarda zan fara tunkarar shi amma ke ce ma sage ni, koma dai menene zaki fini sanin abinda yafi so tunda ciki ɗaya kuka fito dashi" Taɓe baki hafsa tayi kafin tace "To ko umma data haife shi ba zata iya tantance abinda ya faruk ya fi so ba wallahi, dama dai mamace ko kuma warcan data ɗakko ma kanta dala ba gammo(tana nufin mumtaz) ƙila ki samu wani abu da ze amfane ki" Shiru Najwa tayi tana sauraran hafsa, can Najwa tace "zan san yarda zanyi dai" Sake taɓe baki hafsa tayi, taci gaba da shafe+shafen ta Seda ta gama shiryawa tsaf tukun ta sake cewa "Yanzu ya zakiyi da sadik da ya mutu a kanki najwa?" Kai tsaye Najwa tace "haƙuri zeyi" Bilhaƙƙi da gaskiya hafsat ta fuskanci najwa tace "Ki bi a hankali najwa, karki fara da bawa sadik haƙuri baki damƙi dahir ba, wallahi tallahi zakizo kiyi danasani nan gaba" Tana gama faɗin haka ta ɗauki wayar ta da ƙaramar jakar hannun tace "mu wuce kar mu makara sallah". ****** Kamar kullum yauma mumtaz wajen ta daban ta zauna, gaba ɗaya ta rasa sukuni ta rasa me ke mata daɗi a cikin zuciya Hand bag ɗinta ta buɗe ta zaro wayar ta da tun jiya take a kashe ta kunna Few seconds ta gama booting, seda ta kalli wayar taga ashe data a kunne ne ma ta kashe wayar jiya Kamar jira khalid yake ta kunna wayar, nan calls ɗin shi sukai ta sintiri, mumtaz na kallon kiran tana ignoring Sam ta kasa samun courage ɗin amsa shi Sauka tayi da niyar kashe data, kafin ta kashe message ɗin shi ya fito a saman notification, "Dan Allah ki amsa mumtaz" Hakanan ta samu kanta da replying shi "muyi chat, i cn't answer ur call now" Cikin damuwa khalid ya ce "kina ina yanzu, ina so in ganki pls". Da ƙyar da jiɓin goshi mumtaz ta tura mishi live location ɗinta, ko minti shabiyar beyi ba ya ƙaraso, Abu na farko da mumtaz ta fara kai idonta kai shine hannun shi, Ganin babu agogon data ƙwallafa rai akai taji ranta ya ɓaci, ɗan sakin data yi wa fuskar ta ma ta koma ta ɗaure tamau Da ƙyar mumtaz ta ɗan fara sakin jiki da shi, suka fara fira sama-sama Cike da ƙwarewa khalid ya fara kafa gwamnatin soyayyar shi a zuciyar ta. Sosai khalid ya saki jiki ya fara bata labarin shi "Ni haifaffen ɗan kano ne, ɗa ɗaya tilo a wajen iyayen shi, babana tun ina secondry aji biyu ya rasu, ya barmu daga ni se mamina taci gaba da kula dani a yanzu haka ina aiki da A.S.K textile company" Da sauri Mumtaz tace "A S.K company fa kace"? Gyaɗa kanshi yayi kafin yace "kin san wani a wajen ne?" Murmushi kawai tayi, bata ce komi ba A.S.K, textile company na Abba ƙ ne, shine kampani na farko kuma mafi girma a dukkan sauran kampanonin shi guda takwas, shiyasa tayi mamaki jin a can yake aiki Jin bata ce komi ba shi ya ɗora da "Saura ke ranki shi daɗe" ya ƙarashe maganar yana murmshi kan mumtaz a ƙasa tace "nima ƴar kano ce, a sharaɗa phase 2, ina a 200lv a jami'ar bayaro ina karantar mass com" Daga nan tayi shiru taci gaba da wasa da yatsun ta. Girar shi biyu ya ɗaga haɗe da kallon yatsun ta datake wasa da su yace "ma sha Allah, sauran abu ɗaya ne banji na" Ɗan ɗagowa tayi kaɗan, tana sauraren shi yace "Ni na gaya miki nine tilo, nine ɗan fari nine kuma auta" The way ya ƙarashe maganar se ya baka dariya Ilai kuwa seda mumtaz ta ɗan dara, tukun tace "muna da yawa sosai a gidan mu, but a wajen Abba da mama nice ta uku, ina da yayu maza guda biyu, se ƙanwa mace ɗaya, mama tace bata wuce 6month ba ta rasu" Dariya khalid yayi yace 'kawai malama kice min kema autace" Murmushi kawai mumtaz tayi, tana ɗan waigawa gefe, akwai wani feeling datake ji a jikin ta in har ana kallon ta Ɗayan gefen ta sake waigawa caraf suka sake yin ido huɗu da ya faruk dake kallon ta ko ƙyaftawa babu, fuskar nan tashi a murtuke ba wani alamar sassauci Da sauri ta waiga ta dena kallon side ɗin da yake A ɗan tsorace, bama lale ka gane a tsoracen take ba tace "ehnmm, tun da mun gaisa ka tafi, nima zan tafi ne yanzu" Da kyau khalid ya kalleta, kafin yace "ke dawa kukazo ne nake ganin ki ke kaɗai?" Seda ta miƙe tsaye ta gyara hijabinta tukun tace "muna da yawa sosai, kusan duka gidan mu" Ganin tayi gaba da sauri ya sashi bin bayanta, A ɗan ƙage ta juyo tace "Kar ka biyoni pls, zamuyi waya kawai" Sototo khalid ya tsaya ganin yarda mood ɗin ta ya sauya gaba ɗaya Har ta ɓace wa ganin shi be motsa daga wajen ba. ***Ran ya faruk a ɓace ya ɗaga waya ya kira guy ɗin da yake sawa yana siyen mishi tickets duk sanda tafiya haka me yawa ta taso Sallamar shi kawai ya faruk ya amsa, ko ta kan gaisuwar da yake mishi be bi ba ya ɗora da "sagir dan Allah date ɗin komawa gida nake so a sauya ma wasu daga cikin yaran gida" Daga can ɓangaren wanda aka kira da sagir yace "to yallaɓai, yaushe za'a maida kuma da wa da wa?" Ya faruk yace "in har za'a samu jirgin zuwa anjima ma yayi, zan tura maka sunayen su yanzu" "okay sir". *****Mamace kaɗai zaune a masaukin su tana waya da yayan ta(baban sakina) mumtaz tayi knocking ƙofar Still wayar na a kunnen mama ta tashi ta buɗe mata ƙofar, Da sallama mumtaz ta ƙaraso ciki, tana shigowa ta cire hijabi ta haɗa da hular kanta tacire, agogon ɗakin ta kalla taga shida saura, ɗan tsaki taja ta zame a wajen ta kwanta, dai dai nan mama ta gama wayar, kallon mumtaz tayi ganin yarda tayi ɗai-ɗai kamar wata mara lafia tace "Ya dai? garin ko jikin?" Turo baki gaba tayi kafin tace "wallahi muguwar ƙishirwa nake ji mama, gashi yau lokacin baya gudu sam" Kallon agogo mama tayi, tukun tace "saura kaɗan ai" Kamar an zunguri mumtaz ta miƙe zaune tace "Mama Abayar dana ƙwallafa rai zan saka ranar idi ɗazu ina gyaran kayana ina buɗeta naga ta gefen ta a ƙone" mama tace "subhanallah, ko dai wajen guga ne aka ƙona?" Taɓe baki mumtaz tayi tukun tace "Abba nake jira yazo ya ban kuɗi na siya wata kawai" Cike da kulawa mama tace "ki duba acikin sauran mana ba zaki rasa wacce zaki saka ba ai" Kafin Mumtaz ta sake magana wayar mama dake gefe ta fara ringing Kallon screen ɗin wayar mumtaz tayi taga waye, sunan "YARONA" ta gani Taɓe baki tayi ta waiga sanin ya faruk ne me kiran, ita duk a tunanin ta ze faɗa wa mama ganin ta da yayi ɗazu tare da khalid Jin mama tace "To, yau kuma?" da ɗan ƙarfi yasa hankalin ta komawa ga mamar Can ta sake jin tace "Yau da jibin ai duk ɗaya ne, Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi, bari inyi sauri in gaya musu kuwa" Daga nan mama ta aje wayar, ta maida kallon ta ga mumtaz datayi saƙe tanajiran jin me mamar zata ce unexpected cikin ƴar dariya mamar tace "Yau me tafiya gida ce yarinya" Da sauri mumtaz ta sake zama da kyau, ido a ɗan waje tace "Ban gane ba mama?" Sanin yarda Mumtaz ke ƙaunar yin sallah a garin makka yasa mama ke danne dariyar ta, dan ta san sarai za'a kwasota da ita Ɗan taɓe baki mama tayi tukun tace "Tashi zakiyi ki samu su Amal da sauran ki faɗa musu yau zaku wuce gida, ku haɗa yanaku yanaku" Wani shegen ihu mumtaz ta buga wanda seda mama ta toshe kunnen ta da sauri Duka hannaye mumtaz ta aza ga ƙirjin ta, ido waje tace "Na shiga uku mama, waye yayi mana wannan muguwar muguntar dan Allah?" Bata gama rufe baki ba hawaye suka wanke mata fuska Kankace me mumtaz ta rushe da kuka me ƙarfi tun daga ƙasan zuciyar ta. Galala mama tayi tana kallon ta, gaba ɗaya dariyace ta kamata ganin yarda haiƙan take rusa kuka dan ance zasu tafi gida Jin kukan na neman wuce gona da iri gashi ba'a gaya ma sauran ba yasa mama faɗin "ke bana son shashanci, dama zama ne ya kawo ku ƙasar, ai dama dole ku koma" Cikin kuka mumtaz tace "Ai ba yau ne ranar tafiyar mu ba mama, kawai dan a ƙuntata mana ne wlh" Cin serious mama tayi tace "faruk yace mistake aka samu, amma yaune ainihin tafiyar ku ba washegarin sallah ba, ki tashi ki je ki gaya ma sauran" Banza mumtaZ tayi da mama taci gaba da rera kukan takaici Ganin time na tafiya yasa mama tashi da kanta ta saka hijabi ta nufi ɗakunan su Amal da su hafsa Dukan su zaka ga rashin jin daɗin maganar a fuskokin su, amma ba yarda suka iya, haka suka hau shiri a take Mama da kanta ta tsaya ta haɗa wa mumtaz nata kayan tukun ta koma nata ɗakin A nan zaune ta iske ta, idanuwan nan sunyi ƙulu-ƙulu sunyi ja Maman bata ce mata komi ba ta wuce toilet ta ɗauro alwala tukun ta fito Murya a dishe hawaye na ɗiga mumtaz tace "yanzu in na koma a wajen wa zan zauna mama?" Shiru mama tayi tana nazarin maganar Can tace "ki sauka wajen hajia sumayya(umma ƙarama), muma da anyi sallah in sha Allah da kwana biyu zamu dawo". Duk yunwar da mumtaz keji shayi kawai tasha da aka kira sallah, Sallar ma da ƙyar ta tashi tayi ta, naci kam tayi shi har ta haƙura tayi shiru. *****goma saura kwata ya faruk ya kira mama yace "Su fito ga motar da zata fita dasu nan tazo" Sanda mama ta je ɗakunan su duk sun shirya sunyi wanka sun sauya kaya, mumtaz ce kaɗai ke ta nunkufurci, tsabar nunkufurcin ko wankan batayi ba ita Haka mama ta haɗo kawunan su duka, suka fito Suna fitowa mama taga Ahmad zaune a gaban motar kanshi a ƙasa yana danna wayar shi Baki sake take kallon shi, rabon data saka shi a idanun ta tun ranar da zasuzo ƙasar nan, Da mamaki sosai tace "Wai Ahmad na ƙasar nan dama faruk?" Kallon mama yayi yace "nima se jiya na ganshi, nasha ma ni kaɗai ne ban ganshi ba" Hmm, kawai tace ta kawar da kanta daga kallon shi A dabatance ya faruk ya fakaici idon mama yayi wa Ahmad magana Abinda be sani ba shine ta ganshi sarai, basarwa kawai tayi A ciccije Ahmad ya fito ya gaishe da mama Tunda tace "lafia" bata ɗora ko kallama ɗaya a agaba ba ta juya tana ma su Amal da sauran magana. Kallo ɗaya ya fatur yayi wa mumtaz ya ɗauke kai, a ranshi yake cewa "Tafiyar ce bata so kenan?" Taɓe baki yayi, seda ya tabbatat da komi ya kammala tukun yace shiga motar Ƙam ƙam mumtaz ta riƙe mama tana kuka, Hafsa, Amal, bilkisu duk sun shiga mota, Mumtaz na manne da mama tana mata magana ƙasa-ƙasa cikin kuka, Najwa kuma ta tsaya se fama iyayi yake wa ya faruk da mamaki ya gama kashewa Cike da iyayi da sanabe najwa tace "ya fatur ka dai yanke mana jin daɗi ba shiri" ta gefen ido ya kalle ta bece komi ba Jin bece komi ɗin ba yasa najwa buɗe baki da shirin faɗo wata maganar, kafin ta kai ga furtawa ya faruk yace "Ke shiga mota, bana son rashin kunya" dai dai mumtaz ta baro jikin mama ta nufo motar akai abun akan idon ta, duk da yarda ranta ke a mugun ɓace hakan be hanata darawa ba Sum-sum kamar munafuka najwa ta shige mota tana wani haɗa rai kamar zata kai duka. Gaf da mumtaz zata shiga motar, ya faruk yayi ƙasa da murya yace "kici gaba da ballagazancin a can in kin koma, kuma ki jirayi ƙarasowa ta shasha". A ido mumtaz ke kallon ya faruk da bazaka taɓa cewa ya faɗi wani abun ba Ganin ta tsaya yasa balaraben direban motar ya ce "Time na tafiya fa" tukun ta shiga tana jin wani mugun nauyi na daɗa danne zuciyar ta, musamman akan kalaman da ya faruk ya furta mata a yanzu. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 SHARE PLS. LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg 28-29 Har suka shiga jirgi mumtaz nai wa maganar ya faruk fashin baƙi Da kanta ta tambayi kanta "wai bayan kallon ɓarauniya da yake min harda na ballagazanci ma ashe?" dafa goshin ta tayi ta hau furta "LA'ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN" Idonta a lumashe, laɓɓanta ne kawai ke motsi, Alhamdulillah, ko ba komai ta fara jin sauƙin nauyin kirjin ta. Seda jirgin su ya lula sararin samaniya, komi ya daidaita dan har hasken ciki an kashe Hafsat ta dafa kafaɗar najwa dake kujerar kusa da ita tace "me na gaya miki?, in har baki fita sabgar ya faruk ba to tabbas abinda yayi miki ɗazu kaɗan ne, ko baki faɗa ba nasan kinji haushi dan gashi nan ya nuna ƙuru-ƙuru a fuskar ki" Yaƙe najwa tayi sam bakin ta ya mutu murus, dan bata taɓa zaton hakan ba. Haka hafsa ta gama ban bakin ta har ta gaji tayi shiru. *****KHALID Tunda aka kira sallar magariba yake neman mumtaz be samu ba Duk ya bi ya damu ya susuce na rashin ji daga gareta A hankali ya taka har zuwa wajen da yake tunanin ganin ta, amma wajen wayam bata ba alamar ta Jiki a mace yayi typing mata "Call me as soon as u see this pls" Ƙura wa saƙon ido yayi kamar zega ta buɗe, haka nan ya ƙaraci tsayuwar shi ya haƙura, bayan ya bar masallaci seda ya jima sosai a bakin hotel ɗin da suka sauka, nan ma ya ƙaraci tsayuwar shi har ya gaji ya tafi. **** Ƙarfe huɗu da rabi na asuba jirgin su ya sauka, tun kafin su taso dama ya faruk ya sanar wa da bala driver yaje ya ɗakko su. Sanda suka shiga gida har an fito daga sallar asuba a masallatai, Allah ta temake su sunyi sahur a cikin jirgi Kowa na fitowa daga cikin motar ya nufi part ɗin su, Amal ce kawai bata kai ga tafiya ba tace wa mumtaz da tayi tsaye "muje part ɗin mu mana" Murya a dishe mumtaz tace "no, kije kawai" Da yake akwai gajiya sosai yasa Amal ko jan maganar batayi ba ta juya ta shige ta barta nan a tsaye jiki a mace ta waiga ta kalli ko ina na gidan, a hankali ta furta "tabbas mahaifa babban garkuwa ne ga ƴaƴan su" Tana nan a tsaye kusan minti sha biyar bata ga tsuntsu bata ga tarko taji muryar Abbah babba yace "waye nan a tsaye?" Kai tsaye tace "nice Abba b" Da mamaki yace "me kike jira baki shigo ciki ba?" Still jiki a mace ta waiga inda akwatinta yake ta janyo shi tukun tace "yanzu nake shirin shigowa" "to" kawai yace ya juya ciki. Tana ɗaga kai taga ya bar balcony ta juya ta fasa shiga can ta wuce part ɗin su kai tsaye Duk da bata da tabbacin ganin keyn ƙofar, haka ta ƙarasa wajen data san suna ajiye spare incase ko wani abun ze kama Da ƙyar ta ɗaga tukunyar flower dake aje ta gefen part ɗin, luckey enouhg kuwa taga makullin, ɗauka tayi ta nufi ƙofar palon kai tsaye ta buɗe Seda ta buɗe tukun ta koma ta janyo jakar kayanta sannan ta shige Da mamaki tabi palon da kallo ganin ba'a kashe wutar gidan ba, motsin data ji daga wajen ɗakin mama yasa ta ƙarashe firgicewa, Duk da tsoron data ke ji hakan besa ta fasa kurɗawa ciki ba Saɗaf-saɗaf, haka yake tafiya har ta ƙarasa inda tafi jin motsin Ga mamakin ta mutum ne a kwance kan doguwar kujerar ɗakin, ya kifa cikin shi kan kujerar, Idanun shi a rufe yana bacci Mumtaz na tozali da wanda ta gani ta ja da baya ta kurma uban ihu, hannun ta na karkawa bakin ta na rawa take nuna shi Jin ihun ta da mutumin yayi ne ya farkar da shi shima da sauri ya nufeta a mugun sukwane. HMMMMMMM! RASHIN SHARHI KE HANANI TYPING ME YAWA 🙄 AYI MANAGE DA WANGA 👆 ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 SHARE PLS. LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg30 A mugun sukwane ya nufi mumtaz ganin tana neman fita daga hayyacin ta Ƙam ya riƙeta a jikin shi, muryar shi ta irin wanda ya jima da fara bacci yace "Relax mumtaz, kar kisa a san da zamana a cikin gidan nan mana" Sam ta kasa riƙe kukan dake cinta, cikin kukan tace "Dama ya mus'ab kana nan?, ina kaje ina ka shige dan Allah, mama har kwanciya a asibiti tayi saboda tafiyar ka, hankalin duk wani masoyin ka ya tashi" Nan da nan idanun shi suka kaɗa sukayi jaajir tsabar fushi da yarda yake jin raɗaɗi a cikin ziciyar shi Kasa furta ko kalma ɗaya yayi, sema janta da yayi zuwa kan kujera ya zaunar da ita Ya kai kusan minti biyar yana haɗiyar zuciya kafin yace "Na sani mumtaz, ina tare da ku a koda yaushe, zamana a cikin ku babbar illace a gareki, Ahmad, mama da kuma Abba, na gano abinda be kamata na gano ba sam, naji abinda ya hanani zama a cikin jini na mumtaz, banso kika ganni ba a halin yanzu gudun kar kema kishiga matsala makamanciyar tawa" Shiru yayi yana sadda kanshi ƙasa Cike da mamaki da kuma kokwanto mumtaz ke kallon shi, ji take kamar bata gane yaren da yake, duk da yaren hausa ne Cike da tsoro tace "Ya mus'ab me kake nufi ne wai, nifa sam ban fahimce ka ba" Murya ƙasa-ƙasa yace "Bana so ki fahimta ne ai, abu ɗaya nake so dake shine, ki zama very vigilant a gidan nan, karki yarda da kowa sannan karki yarda da kowa a kusa da mama, Sannan ban san ko yaushe ne za'a tattara ku ba a kan maganar fitar da mazan aure, amma ko yaushe ne ki tabbatar da kin tsaya a kan ra'ayin ki, kada ki kuskura ki yarda da ra'ayin kowa, kuma duk yarda za'ayi kisa mama ta kori Altine daga gidan nan koda kuwa ta hanyar ƙulla mata sharri ne" Da sauri mus'ab yayi shiru yayi kasaƙe da kunnen shi, ko second goma beyi ba ya miƙe zumbur Mumtaz na ta binshi da kallon tsoro da tuhuma Har ya kai ƙofar kitchen ya dawo, be yarda yaci gaba da magana kamar ɗazu ba, saitin kunnen ta ya ranƙwafo yace "zan tafi badan naso ba, kar ki kuskura ki nuna ma koda mama ne in sun dawo cewa mun haɗu, amma kisa a ranki ina nan a tare da ku ako wani irin hali" Har ta buɗe baki zatayi magana yayi saurin rufe mata baki da hannun shi, sannn ya sake ƙasa da muryar shi yace "Kome kika furta a yanzu ze iya zama ajalina ko naki ko kuma na iyayen mu da sukai saura basu dawo ba, ki adana maganar ki har sanda muka sake haɗuwa, shima se Allah ya nufa" Kitchen ya nufa da saurin gaske, Shiru-shiru mumtaz na zaune tana jiran taga ya fito, tun tana kallon agogo har ta gaji ta yunƙura da ƙyar ta shiga kitchen ɗin, amma ga mamakin ta ba mus'ab ba dalilin shi, bakuma taga wata ƙwaƙƙwarar hanya da za'a ce mutum ya wuce ba Nan ma tsananin tsoro ya kamata, jikin ta har karkarwa yake wajen kunna wayar ta Allah-Allah take ta gama booting, tana gamawa tayi dialing numbar sakina(ɗiyar yayan mama) seda ta kusa tsinkewa tukun sakina ta amsa da "Barka da sauka mumtaz" Bata tsaya jin komi ba tace "Sakina dan Allah kizo yanzu ki ɗauke ni a gida, ba se kin shigo da motar ba, kawai ki kirani in kin ƙaraso" Tambayoyi ta fara jero mata, cikin zaƙuwa mumtaz tace "kedai ki zo zakiji komi pls" kit ta kashe wayar ta koma ta dunƙule waje ɗaya, tana jin wani mugun zazzaɓi na kamata. 20mins drive ne ya kawota sharaɗa phase2, dialing no ɗinta tayi Mumtaz na ganin call ɗin sakina ta tashi da sauri, akwatin data zo dashi shi ta sake ja ta fice, sam ta mance bata da rufe ƙofa, seda ta kusa gate ta tuna ta dawo da gudu ta rufe Gaf da da zata fita gate taga ya TK da wani friend ɗin shi sun shigo gidan Sama-sama ta gaishe su tayi gaba Haka abokin nan ya kafeta da ido kamar wani tsohon maye, dan seda ya Tk ya zungure shi da ƙafa kafin ya dawo daga lulawar da yayi Warda akeyi domin ita bama tasan yana yi ba, tayi waje abinta. Sakina na zaune cikin mota taga fitowar ta, fitowa tayi ta taya suka saka kayan Kafin sakina ta gama saka zakar hannun ta har mumtaz ya shiga motar Sanna itama ta zagayo ta shiga mazaunin driver taja suka tafi. Jin mumtaz ta mata shiru batace komi ba yasa tace "kin tsira ma waje ɗaya idanu bayan kin san jiran jin ki nake" Mumtaz tayi niyar suyi maganar, amma haka nan taji ranta be aminta da tayi zancen da sakina ba, Busashshen murmushi ta yi sannan tace "Dan kizo ki ɗauke ni fa kawai, amma bakomaai" Murmushi sakina tayi kafin tace "in tayi wari maji, yaushe kuka dawo?" "Ɗazu" tace ta maida idanuwanta ta lumshe. **** Biyu da rabi na rana umma babba ta sakko zuwa ɗakin ƴammatan ta dake ta baccin gajiya tun da suka dawo Tura ƙofar ɗakin tayi ta iskesu sunyi ɗai-ɗai, taso tashin su kome ta tuna? oho, ta juya ta fita zuwa kitchen inda masu aiki ke ta soye-soyen kayan flour Nan ta gama bada umarni umarnin yarda za'a shirya komi kafin ta koma bedroom ɗin ta. Kamar yarda ake ta hada-hada a sasan umma babba haka sauran sasan aunty da mummy ma, wasu daga cikin su ma har sun fara karɓan baƙin ƴan'uwansu da zasuyi sallah a nan. ***MAMA Tun da ta tashi take neman layin mumtaz amma shiru bata ɗauka, farko tayi tunanin ko baccin gajiya take, amma har bayan la'asar data sake neman ta shima shuru ba amsa Sauya akalar kiran tayi ga layin umma ƙarama, bugu biyu umma ƙ ta ɗaga, cike da fara'a da mutunta juna suka gaisa Can mama tace "Ehn, dan Allah hajiya sumayya mumtaz nike so ki ɗan haɗani da ita, ina ta kiranta bata picking" Da mamaki umma ƙ tace "Ah, wai mumtaz ta dawo ne itama?" Mama tace "tare suka dawo duka ai, nasha tana nan wajen ku" Umma ƙ tace "to banƙi ta taki ba, bari na dubota ko tana wajen su Amal, riƙe wayar" Da "to"maama ta amsa A kunnen ta taji umma ƙ na tambayar Amal inda mumtaz take Daga can ta jiyo Amal tace "ban sani ba umma ƙ" Umma ƙ tace "kamar ya baki sani ba?" Da ɗan ƙosawa tace "da muka dawo a waje muka barta, nace tazo muje tayi banza dani, daga nan ban san inda tayi ba" Umma ƙ na tsaye a ɗakin su Amal, umma b ta shigo jin maganar su, Ba yabo ba fallasa tace "hajiya sumayya lafia?" Mama na jiyo su daga can, kafin umma ƙ tabawa umma b amsa mama tace "ko tana part ɗina ne?" Umma ƙ tace "bari inje can to" Taɓe baki umma babba tayi ta juya tana faɗin "Gulmamammu kawai, shishshigi babu kwarjini" ta ƙarashe ficewa. Can ma wayam bata, nan ne fa hankalin mama ya fara tashi, farat ɗaya tafiyar mus'ab ta dawo mata kai Cike da zullumi tace "ko dai tana gidan Abbas ko ƙasim?" Kafin umma ƙ tayi magana, mama taga call ɗin mumtaz na shigowa, da sauri tace "gashi tana kirana bari naji". Seda taji daga wajen ta tukun hankalin ta ya kwanta, duk da tayi mata faɗan rashin gaya mata datayi. Da suka gama wayar ta kira umma ƙ ta gaya mata taje gidan ya junaid ne ashe. *****KHALID Daga yinin jiya zuwa na yau duk yabi ya susuce rashin ji daga wajen ta, msgs kam ya tura mata su kamar me Bashi da aiki se duba waya akai akai, Bayan sallar isha haka ya sake wankar ƙafa ya koma hotel ɗin da suka sauka, haka yasha zama kamar jiya amma bata da dalilin ta. Zuwan shi na jiya dana yau duk akan idon ya faruk, yasan khalid farin sani tunda a ƙarƙashin su yake aiki, Yasan yana da kirki, amma ba ze iya cewa ga hallayyar shi ba, a fili yace "Zanci gaba da sa maka ido naga dame kazo". Mumtaz na kwance a ɗakin data sauka, baka jin motsin kowa alamar dai dare ya ratsa Juyi kawai take tana farfasa maganganun da ya mus'ab yayi mata ɗazu, Gaba ɗaya kanta ya kulle ta rasa wani kalar tunani zata yi akan maganar, dama tacika damun kanta taji ya fara sassara mata, Haka ta tattara ta watsar da zancen, abu ɗaya ne ta ɗauka shine bazata bari kowa yaji ba har sanda ya dace Khalid ne ya faɗo mata a rai lokaci ɗaya, sam ta mance da babin shi daga jiya zuwa yau, se yanzu daya faɗo mata Wayarta dake gefe ta janyo, kunna data tayi ta hau whatsapp, kan kice me saƙonnin shi suka rinƙa antayowa Tsuru tayi ta kafe wayar da ido Seda suka gama shigowa tas tukun ta buɗe ta fara bin saƙonnin ɗaya bayan ɗaya tana dubawa A karon farko tun jiya da tayi murmushi, ita kanta bata san sanda hakan ta kasance ba Se tsintar kanta tayi da replying shi, ta rubuta "whats wrong"? akan saƙon shi da ya rubuta "ina cikin wani hali" da manyan baƙi. Khalid na ganin saƙon ta, hannun shi har rawa yake wajen danna mata kira Tana ɗaga wayar ta kara a kunne tayi shiru tana sauraren shi "Baki da wani excuse da zaki bani, kina ina?" Murmushi mumtaz tayi kafin tace "ina nan mana" Cikin zaƙuwa yace "meyesa ban ganki a masallaci ba? har hotel ɗin da kika sauka naje nasha jira amma banga ko me kama dake ba mumtaz" yaja sunan ta daga ƙarshe Zumɓuro baki tayi kamar yana ganin ta kafin tace "kai dai bari, Allah ne ya haɗamu da ɗan baƙin ciki yasa aka auno mu gida" Yarda tayi maganar dole ya baka dariya, seda khalid ya dara kafin yace "who was that person?" Seda ta taɓe baki again kafin tace "a dangi yake, ataiƙaice dai ina ƙasarmu ta gado" Duk da khalid beji daɗi ba, amma ya samu relief ko yayane, nan suka raba kusan daren gaba ɗaya suna fira, Abun mamaki sosai mumtaz ta saki jiki da shi se gashi tana neman kunci da damuwar data shiga sam ta raaa ta, ji tayi ma kamar kar ya kashe wayar su dauwama a haka. A ranar daga khalid har mumtaz baccin farin ciki sukayi da alƙawarin haɗuwa a ranar sallar da ze dawo da yamma, Saɓanin wasu ƴan tsirarai masu mugun nufi da suke kwana da yini wajen tarwatsa rayuwar bayin Allah da yawa wanda basu jiba basu gani ba, saboda tsabar son zuciya da rashin rabo!!!!. SHARE PLS ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg 31-32 BAYAN SALLAH DA KWANA BIYU Tun safe da umma b ta fito daga wajen Abba b ta samu su Amal a ɗaki, duk da sun tashi amma suna zazzaune Wayace a kunnen hafsa, while Amal kuma handouts ne a gaban ta tana dubawa Da sallama umma b ta shiga ɗakin, Stool ɗin gaban mudubi taja ta zauna, Sallama hafsa tayi da wanda suke wayar ta maido da hankalin ga umma b dake binsu da kallo Amal ma juyowa tayi gaba ɗaya sukai shiru suna kallon ta. Seda ta mula da kallon su tukun tace "Dake zan fara Amal, Amir da faisal wanne yafi gwaɓi a cikin su?" Bin ta da kallo Amal tayi, dan har ga Allah bata fahimci kalmar "gwaɓi" da umma tace ba Ɗan shirun da Amal tayi tana nazarin kalmar, umma ta sake maimaita tambayar tana kafe ta da idanu itama Da gaske Amal tace "wallahi ban gane me kike nufi ba umma Ƙafa ɗaya kan ɗaya umma ta ɗora sannan tace "Bari nayi maki dalla dalla, ina nufin Amir da faisal wanne yafi wani a cikin su?" Murmushi Amal tayi kafin tace "Amir ɗin dai umma" Karaf hafsat tace "billahillazi ƙarya take, ko motar da faisal ke zuwa gidannan zata siya ta Amir sau biyar umma" Murtike fuska Amal tayi, cike da tsiwa tace "ba ruwanki a cikin maganar nan wallahi" Da sauri Umma ta ɗaga masu hannu haɗe da faɗin "Ku dakata min" duka sukayi shiru suna kallon ta, idonta ta maida ga Amal sannan tace "na san kece zaki fi bani matsala, daga yau zuwa jibin da Abban ku yace zasu tara ku suji zaɓin ku na wanda kuke so, ina so ki fitar da wanda yafi rigar arziƙi a cikin su, kuma kar naga ba abinda nake so ba" Sadda kai ƙatsa Amal tayi jin abinda umman ke faɗa Cike da zumuɗi hafsat tace "umma wai maganar ta taso ne?" Seda ta ɗan taɓe baki tukun tace "Tunda me ƙumbar susa ya bada umarni ai dole a bi," Zaro ido Hafsat tayi ta ɗan sake matsowa kusa tayi ƙasa da murya tace "Umma, to harda ƴar gaban goshin nashi ko mu kaɗai?" Dariya umma b tayi sannan tace "hmmm, harda ita fa, da Bilkisu da Najwa ma" Baki buɗe hafsat tace "jakar uba, to da wa za'ayi kenan?" Wannan karon dariyar da umma b tayi tafi na ɗazu Seda ta dara sosai tukun tace "Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta" Da ga nan tayi gaba ta ja musu ƙofar. Umma na fita Amal ta kalli hafsat tace "Mugunta fitsarin faƙƙo ce dai ya hafsa, har wani murna kike saboda wani dalilin ku mara tushe" Kafin Amal ta rufe baki hafsat tayo kanta a mugun sukwane, dayake Amal ta san hali, dama tayi readyn fita, aikuwa tana yunƙurowa ta kwasa tayi waje da gudu Aikuwa hafsat kamar ta ari baki saboda masifa da take zazzagawa, seda ya fauza da basu jima da zuwa gidan ba ita da khairi suka shiga tsakanin su tukunna. Ya fauza da yake tana da faɗa sosai ta hau surfa musu bala'i, tace "kuna girma kuna cin ƙasa shirmen banza" A fakaice hafsat ta murguɗa mata baki ta juya tana gunaguni. Kamar yarda umma b ta zaunar da yaran ta tasanar da su saƙon Abba b, haka ma mummy, duk da Najwa ba ƴar cikin ta bace riƙonta take, hasali ma saboda son da take ma ƴa mace ne kuma Allah be bata ba yasa yayan ta ya bata Najwa halak malak tun daga yaye Najwa na kwance a kan doguwar kujera mummy ta sanar mata da umarnin su Abba jin Najwa bata ce komi yasa mummyn cewa "ya dai? ko akwai wani abunne?" Can ƙasan zuciyar ta na zigata ta ce ya faruk take so, amma wani sashi na zuciyar yana ƙwaɓar ta, murmushin dole ta ƙwaƙulo tukun tace "nothing mummy, kawai naji maganar ne daga sama" Shafa kanta tayi tace "mutuncin duka ƴa mace ɗakin mijin ta, tun da Allah yasa sadik na son ki kema kuma kina son shi ba shikenan ba?" Gyaɗa kai tayi, tana ƙara cire ya faruk daga cikin ranta dan har ga Allah bata son tayi auren da ita kaɗai ke so. ******MUMTAZ Kicin-kicin mumtaz tayi da fuska, jin me sakina ke gaya mata, bayan sun gama shirin tafia airport tarban Abba ƙ da mama "Gaskiya guy ɗinnan be iya zuwa ba, wai fisabilillahi baki gaya mishi fita zamuyi ba?" Sakina da ke ɗaura ɗankwali a gaban mudubi tace "shap na mance ban gaya mishi ba, ko muje ya sauke mu ne?" Da sauri mumtaz tace "no, bari nayi wa drivern ku magana, in kuma yana da abinda zeyi zan hau taxi" Sakina batace komi ba, looks like kamar da gangan ma tayi hakan. Mumtaz na fita ta iske an aiki drivern, Dama ba kowa a gidan, mama asiya taje unguwa, daga su se masu aik. Agogo ta kalla taga befi awa ɗaya ba su sauka, Wayarta ta ɗauka ta kira bolt, minti biyar da kiran shi ya ƙaraso, "na wuce" kawai tace wa sakina ta fice. Saboda traffic ɗin hanyar, seda suka kai kusan minti talatin kafin suka kai Daidai da zata shiga ciki call ɗin khalid ya shigo wayar ta Jin cewa tana airport ne yace ta jira shi yana ta wajen ze ƙaraso, taso ta hana shi zuwa amma ya kafe se yazo, rabuwa tayi da shi ya zo ɗin. Bata jima a tsaye ba yayi parking a gaban ta, Ganin da sauran time ɗin saukar su mama yasa ta buɗe gaba ta shiga Fuska cike da annuri khalid yace "Da za ki min buƙulun gaisar da su Abba ko?" Murmushi kawai tayi, can tace "yanzun ma ba ganin su zaka yi ba malam, suna sauka zan sauka kai kuma ka kama gaban ka" Gyara parking yayi da kyau, sannan ya waigo ya fuskance ta, ƙasa da murya yayi kafin yace "Gani nake kamar bakya so na mumtaz" Ɗago manyan idanuwan ta tayi ta kalle shi sau ɗaya ta kauda kai, sannan tace "mene dalilin ka?" "gashi kuwa bakya so na ga su Abba, ko gidan su sakina da ƙyar fa kika yarda naje" Kallon agogon wayar ta tayi taga time ɗin ya cika, Cike da nutsuwa tace "gobe ina gayyatar ka gidan mu to, Amma yau kam zanji kunya a Abba ya ganmu tare, in ma da babban wanmu suka dawo wata maganar ce daban" Marairaice fuska yayi, ba yarda ya iya dole ya haƙura, Fita yayi da niyar ya buɗe mata ƙofa, yana fita idonta na kaiwa ga agogon shi dake ajiye, wuf mumtaz tayi sama da shi, daidai ya buɗe mata ƙofar Cikin ƙwarewa ta saƙe agogon nan tayi ciki wajen tarban matafiya, shi kuma ya shiga motar shi ya tafi. LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg 31-32 BAYAN SALLAH DA KWANA BIYU Tun safe da umma b ta fito daga wajen Abba b ta samu su Amal a ɗaki, duk da sun tashi amma suna zazzaune Wayace a kunnen hafsa, while Amal kuma handouts ne a gaban ta tana dubawa Da sallama umma b ta shiga ɗakin, Stool ɗin gaban mudubi taja ta zauna, Sallama hafsa tayi da wanda suke wayar ta maido da hankalin ga umma b dake binsu da kallo Amal ma juyowa tayi gaba ɗaya sukai shiru suna kallon ta. Seda ta mula da kallon su tukun tace "Dake zan fara Amal, Amir da faisal wanne yafi gwaɓi a cikin su?" Bin ta da kallo Amal tayi, dan har ga Allah bata fahimci kalmar "gwaɓi" da umma tace ba Ɗan shirun da Amal tayi tana nazarin kalmar, umma ta sake maimaita tambayar tana kafe ta da idanu itama Da gaske Amal tace "wallahi ban gane me kike nufi ba umma Ƙafa ɗaya kan ɗaya umma ta ɗora sannan tace "Bari nayi maki dalla dalla, ina nufin Amir da faisal wanne yafi wani a cikin su?" Murmushi Amal tayi kafin tace "Amir ɗin dai umma" Karaf hafsat tace "billahillazi ƙarya take, ko motar da faisal ke zuwa gidannan zata siya ta Amir sau biyar umma" Murtike fuska Amal tayi, cike da tsiwa tace "ba ruwanki a cikin maganar nan wallahi" Da sauri Umma ta ɗaga masu hannu haɗe da faɗin "Ku dakata min" duka sukayi shiru suna kallon ta, idonta ta maida ga Amal sannan tace "na san kece zaki fi bani matsala, daga yau zuwa jibin da Abban ku yace zasu tara ku suji zaɓin ku na wanda kuke so, ina so ki fitar da wanda yafi rigar arziƙi a cikin su, kuma kar naga ba abinda nake so ba" Sadda kai ƙatsa Amal tayi jin abinda umman ke faɗa Cike da zumuɗi hafsat tace "umma wai maganar ta taso ne?" Seda ta ɗan taɓe baki tukun tace "Tunda me ƙumbar susa ya bada umarni ai dole a bi," Zaro ido Hafsat tayi ta ɗan sake matsowa kusa tayi ƙasa da murya tace "Umma, to harda ƴar gaban goshin nashi ko mu kaɗai?" Dariya umma b tayi sannan tace "hmmm, harda ita fa, da Bilkisu da Najwa ma" Baki buɗe hafsat tace "jakar uba, to da wa za'ayi kenan?" Wannan karon dariyar da umma b tayi tafi na ɗazu Seda ta dara sosai tukun tace "Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta" Da ga nan tayi gaba ta ja musu ƙofar. Umma na fita Amal ta kalli hafsat tace "Mugunta fitsarin faƙƙo ce dai ya hafsa, har wani murna kike saboda wani dalilin ku mara tushe" Kafin Amal ta rufe baki hafsat tayo kanta a mugun sukwane, dayake Amal ta san hali, dama tayi readyn fita, aikuwa tana yunƙurowa ta kwasa tayi waje da gudu Aikuwa hafsat kamar ta ari baki saboda masifa da take zazzagawa, seda ya fauza da basu jima da zuwa gidan ba ita da khairi suka shiga tsakanin su tukunna. Ya fauza da yake tana da faɗa sosai ta hau surfa musu bala'i, tace "kuna girma kuna cin ƙasa shirmen banza" A fakaice hafsat ta murguɗa mata baki ta juya tana gunaguni. Kamar yarda umma b ta zaunar da yaran ta tasanar da su saƙon Abba b, haka ma mummy, duk da Najwa ba ƴar cikin ta bace riƙonta take, hasali ma saboda son da take ma ƴa mace ne kuma Allah be bata ba yasa yayan ta ya bata Najwa halak malak tun daga yaye Najwa na kwance a kan doguwar kujera mummy ta sanar mata da umarnin su Abba jin Najwa bata ce komi yasa mummyn cewa "ya dai? ko akwai wani abunne?" Can ƙasan zuciyar ta na zigata ta ce ya faruk take so, amma wani sashi na zuciyar yana ƙwaɓar ta, murmushin dole ta ƙwaƙulo tukun tace "nothing mummy, kawai naji maganar ne daga sama" Shafa kanta tayi tace "mutuncin duka ƴa mace ɗakin mijin ta, tun da Allah yasa sadik na son ki kema kuma kina son shi ba shikenan ba?" Gyaɗa kai tayi, tana ƙara cire ya faruk daga cikin ranta dan har ga Allah bata son tayi auren da ita kaɗai ke so. ******MUMTAZ Kicin-kicin mumtaz tayi da fuska, jin me sakina ke gaya mata, bayan sun gama shirin tafia airport tarban Abba ƙ da mama "Gaskiya guy ɗinnan be iya zuwa ba, wai fisabilillahi baki gaya mishi fita zamuyi ba?" Sakina da ke ɗaura ɗankwali a gaban mudubi tace "shap na mance ban gaya mishi ba, ko muje ya sauke mu ne?" Da sauri mumtaz tace "no, bari nayi wa drivern ku magana, in kuma yana da abinda zeyi zan hau taxi" Sakina batace komi ba, looks like kamar da gangan ma tayi hakan. Mumtaz na fita ta iske an aiki drivern, Dama ba kowa a gidan, mama asiya taje unguwa, daga su se masu aik. Agogo ta kalla taga befi awa ɗaya ba su sauka, Wayarta ta ɗauka ta kira bolt, minti biyar da kiran shi ya ƙaraso, "na wuce" kawai tace wa sakina ta fice. Saboda traffic ɗin hanyar, seda suka kai kusan minti talatin kafin suka kai Daidai da zata shiga ciki call ɗin khalid ya shigo wayar ta Jin cewa tana airport ne yace ta jira shi yana ta wajen ze ƙaraso, taso ta hana shi zuwa amma ya kafe se yazo, rabuwa tayi da shi ya zo ɗin. Bata jima a tsaye ba yayi parking a gaban ta, Ganin da sauran time ɗin saukar su mama yasa ta buɗe gaba ta shiga Fuska cike da annuri khalid yace "Da za ki min buƙulun gaisar da su Abba ko?" Murmushi kawai tayi, can tace "yanzun ma ba ganin su zaka yi ba malam, suna sauka zan sauka kai kuma ka kama gaban ka" Gyara parking yayi da kyau, sannan ya waigo ya fuskance ta, ƙasa da murya yayi kafin yace "Gani nake kamar bakya so na mumtaz" Ɗago manyan idanuwan ta tayi ta kalle shi sau ɗaya ta kauda kai, sannan tace "mene dalilin ka?" "gashi kuwa bakya so na ga su Abba, ko gidan su sakina da ƙyar fa kika yarda naje" Kallon agogon wayar ta tayi taga time ɗin ya cika, Cike da nutsuwa tace "gobe ina gayyatar ka gidan mu to, Amma yau kam zanji kunya Abba ya ganmu tare, in ma da babban wanmu suka dawo wata maganar ce ta daban" Marairaice fuska yayi, ba yarda ya iya dole ya haƙura, Fita yayi da niyar ya buɗe mata ƙofa, yana fita idonta na kaiwa ga agogon shi dake ajiye, wuf mumtaz tayi sama da shi, daidai ya buɗe mata ƙofar Cikin ƙwarewa a harkar ta saƙe agogon nan, Sallama suka yi sannan tayi ciki wajen tarban matafiya, shi kuma ya shiga motar shi ya tafi. Mumtaz na shiga ta ga bala driver da sani driver zaune suna jiran ƙarasowar su Abban, Tacan gefen su ta zauna, sam basu lura da ita ba Bata jima da zama ba su mama suka fito Da gudu taje wajen iyayen nata, Abba ƙ se murmushi yake haka maman ma Ɗaya bayan ɗaya ta rungume iyayen nata tana musu sannu da zuwa Gasu bala a gefe suna ta aika gaisuwar su suma cike da girmamawa . Ganin mumtaz tare da su bala ne mama tayi tunanin tare suka zo. Abba ya miƙa wa bala no ɗin dake jikin tag ɗinsu na kaya yace "bala kai ka tawo mana da kayan, kai kuma sani muje" A yarda suka zo bala ne ya ɗakko motar da ze ɗauki su Abba, amma jin Abban yace balan ya tsaya ya ɗakko kayan su yasa sukayi sanjen mukulin motocin Hakan kuwa akayi, bala ya tsaya shi kuma sani ya jasu zuwa gida Abba da mama baya suka shiga, mumtaz ta shiga seat ɗin gaba, Gaba ɗaya murnar ganin iyayen nata yaƙi ɓoyuwa akan fuskar ta. Jingina da kujera mama tayi idon ta a rufe tanajin yarda Abba ke amsa calls akai-akai na gaisuwar sallah Mumtaz kam shiru tayi tana sauraron wani ɓangare na zuciyar ta for the first time yana ayyana mata tayi daidai kuwa ɗaukan agogon nan da tayi? Sosai bala ya shararo motar ganin yarda titin ba cinkoso, unexpected wani me keke napep ya gifta musu Da hanzari ya kai ƙafarshi kan burki, amma inaaa sam burki ya saki ya shafe gaba ɗaya A firgice suka haɗa baki shi da mumtaz wajen faɗin "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN" Wajen ƙoƙarin kauce wa me keken, motar ta ƙwace tayi kan shagunan mutane dake gefen hanyar gadan gadan A firgice Abba ke faɗin " ka taka burki mana," Shima sanin a firgice yake kokawa da sitiyari haɗe da faɗin "wallahi ba burki yallaɓai" mama kam salati kawai take, mumtaz tana ihu tana haɗawa da salati, Abba kam bakin shi ya ƙi dena faɗin "Kamar ya ba burki, kamar ya ba burki" can kuma se ya hau salati, haɗe da rungume mama ƙam a jikin shi ganin tsananin tashin hankalin da ta shiga Mutane dake waje suna kallon mugun tashin hankalin nan wasu na salati wasu na ihu, wanda motar ke tunkarar su kuma suna ta neman ceton kawunan su. ALLAH YA TSARKAKE MANA ZUCIYAR MU, YA RABAMU DA HASSADA DA KUMA AIKATA AIKIN DANASANI. KUYI HAƘURI DA WANNAN PLS, JIKI DA JINI. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 SHARE PLS. LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg 35-36 Ya faruk suna tafiya Abba b yace "Wasu a cikin ku su ragu aje wajen jana'izar sani, wasu se su tsaya" Uncle ƙasim yace "Tunda Drn yace suna buƙatar hutu sosai kamata yayi ace matan duka su koma gida, mu kuma har munje mu dawo basu farka ba nake tunani" Ta gefen ido Abba b ya saci kallon kusan kowa kafin yace "Hakan yayi" dukan su matan Abba ya ce su tashi su tafi, Cike da nutsuwa da sanin yakamata umma ƙarama ta matsa kusa da Abba b, seda tayi ƙasa da murya tukun tace "Ya kamata ace ko ni ko hajiya nabila(umma babba) wani ya tsaya a cikin mu fa" Kallon ta shima yayi kafin yace "ba'a buƙatar kowa inji likitan, gara ma kuje gida a shirya abinci dan nasan zuwa anjima hospital ɗin nan ze cika da jama'a," Umma babba nadaga gefe tana cika tana batsewa ganin yarda umma ƙ ke wani shishahigewa kamar itace babba. Ya maryam dake kusa da umma b tace "kalli mutuniyar umma, ita ala dole so take ta ƙwaci matsayin ki a idon kowa fa" Taɓe baki umma b tayi kafin tace "ai bata birgeni ba, kamata yayi ace itama ta kwanta se asan taji ciwon nasu sosai, amma wannan kwaɗifirin ba birgeni yake ba, shishshigi ba kwarjini" Amal dake tsaye a gefe tana jin abinda mahaifiyar su da kuma ƴan'uwan ta keyi, sosai takaici ya tokareta a wiya, ba'abin tayi magana ba su hayayyaƙo mata, Rai a ɓace tace "Ya sabrina tafiyar ko kuma zaman?" Dukan su suka kalle ta, cike da takaici umma b tace "ai fa, sabrina kin taɓo waƴanda tafi gani da mutunci akan mu, bari muyi kaffa-kaffa kar muji duka daga sama" Gefe Amal ta sake yi, bata ce komi ba sema ƙara ƙyamar irin halayar su datayi. Dukan ahalin sun mimmiƙe da niyar tafiya, wasu zasuyi gida wasu kuma zasu wuce janaizar sani kenan khalid ya iso wajen shi da wani abokin shi kamal Ganin manyan shi na wajen aiki tsaye a ta gefen emergency yasa shi fasa wucewa ciki ya nufi wajen su Cike da girmamawa ya mimmiƙa musu hannu Duk cikin su ba wanda ya sheda fuskar khalid se uncle Abbas Khalid yace "Halan kun kawo wani ne sir?" Uncle Abbas yace "megida da iyalan shi ne suka samu accident" Cike da jimami yayi Allah kyauta, suna nan tsaye ya hango sakina dake nufo inda suke Tana zuwa tace" sannun ku, ba'a bari a shiga wajen su fa" Da mamaki khalid yace " its seems kamar yallaɓai Abbas na da alaƙa da su mumtaz ko?" Murmushi sakina tayi kafin tace "Halan bata gaya maka ƙanin ubanta bane uwa ɗaya uba ɗaya?" Rungume hannun shi yaya a ƙirjin shi, idon shi a kanta yace "waye mahaifin ta a cikin su?" Jin kamar ana kallon ta yasa ta juya, ido huɗu suka haɗa da Amal dake musu kallon ƙurilla, Taɓe baki tayi tukun ta jiyo tace "Abubakar sule ƙaraye, shine mahaifin ta" Shiru khalid yayi yana tuna haɗuwar su a makka da kuma sanda yake gabatar mata da kanshi, Da kuma kallon data mishi da yace a ASK TXTL COMP, yake aiki Murmushi me ƙayatarwa ya saki kafin a ranshi yace "shine taƙi sanar dani". Ya ɗora da "Allah ya tashi kafaɗun su gaba ɗaya" Da "Amin sakina da kamal suka amsa" Sun ɗan jima, dan suna a nan kowa da kowa ya tafi, ya rage daga sakina se mama Asiya ne kawai zaune a wajen Suma basu ƙara daɗewa ba suka yi musu sallama da niyar zasu dawo zuwa jimawa. ****YA FARUK leda ɗaya kawai aka ɗiba bayan gwaje-gwajen da ya dace ayi ma wanda ze bada jini Cike da kulawa nurse ɗin tace "zaka iya kwanciya ka huta sir" "Thanks" kawai yace rufe idon shi yayi yama rasa wani kalar tunani zeyi a wannan marrar. Gado uku ne a ɗakin, amma ko wanne ɓangaren gado akwai labulen da ya sakaya gadon Gadon farko Abba ƙ ne akai, na tsakiya mumtaz, na can lungu kuma mama Dukan su bacci suke, a fuskokin su zaka ga tabbacin baccin ba na daɗi bane Abba ƙ an naɗe hannun shi na dama da bandeji, sannan ga drip an saka mishi While mama drip kawai aka saka mata Se mumtaz da ake wa ƙarin jini, saboda jinin data zubar, Zamu iyacewa tafi kowa jigata tunda ta side ɗinta komi ya faru Ga tsananin firgice da dukkan su suka shiga, in mukayi duba ga sani da ya riga mu gidan gaskiya, shi bako ƙwarzane a jikin shi, zuciyar shi ce ta buga farat ɗaya, ya zama sanadi da kuma lokaci. Bayan nurse ɗin ta gama saka wa mumtaz jinin ta fice haɗe da sakayo musu ƙofar. Ya faruk seda ya huta na kusan minti talatin kafin ya taso ya fito, sanda ya dawo bakin emergencyn ya iske ba kowa da ya sani Ciki ya shiga, cikin sa'a sega nurse ɗin data kaishi aka ɗiba jinin shi, da azama yace "excuse me" Waigowa tayi, fuskar ta da fara'a tace "laa, anya ka huta ɗin kuwa?" Shima fuskar shi ba yabo ba fallasa yace "Zan iya ganin su kuwa?" Da sauri tace "why not, duk da dai an sauya musu ɗaki, kuma bacci suke, amma zaka iya shiga" Gyaɗa kai yayi tukun yace "room number?" Kai tsaye tace "muje na kaika sir" ta ƙarashe maganar tana wani far-far da idanu A cikin zuciuyar shi yace "sakarya!" Tana gaba yana biye da ita a baya har suka kai bakin ƙofar tukun ta tsaya, tace "shine ɗakin sir" "nagode" ya sake cewa, Ganin bashi da niyar ƙyasata yasa ta juya gwiwa a sace tayi gaba. Ya faruk ya jima a bakin ƙofar tsaye, ya kasa samun ƙwarin gwiwar buɗewa ya shiga Tsananin tausayin ahalin ya gama mishi rugu-rugu a zuciya Fargabar shi ɗaya shine besan a wani yanayi ze shiga ya iske su ba Yana nan a tsayen, hannu ɗaya a jikin handle ɗin ƙofar hannu ɗaya kuma a aljihin rigar shaddar jikin shi Ƙasa-ƙasa ya fara jin kakarin Abba ƙ na tashi, har yayi kamar ya juya ya kira likitan ya fasa, da sauri ya murɗa ƙofar ya shiga a kiɗime Ga mamakin ya faruk, Mutum ne tsaye da rigar likitoci a jikin shi, gaba ɗaya ya aza nauyin shi a kan pilon da ya ɗora akan fuskar Abba ƙ Ga karaya a hannu ɗaya, ga rashin ƙarfi gaba ɗaya, duk da haka Abba ƙ na neman ƙwatar rayuwar shi a hannun wannan mutumin. Lukutar masifar da ya faruk yayi tozali da ita ba ƙaramin gigitashi tayi ba A firgice hankali a tashe ya faruk yayi kan wannan mutumi da gaba ɗaya fuskar shi da kuma hannayen shi dik a rufe suke Wata muguwar shaƙa da wawura ya kaimishi, duk da shaƙar da ya faruk yayi ma wannan mutumin besa ya ɗaga Abba ƙ ba Seda yaji azaba kamar ya faruk ze ƙwaƙule mishi maƙogoro tukun ya ɗaga Abba ya fara neman ceton kanshi Sosai tari ya sarƙe Abba ƙ bayan mugun ya sake shi Akan idon shi ya faruk ke kokawa da mutumin yana son ya cire mishi mask ɗin fuskar shi, Duk ƙwaƙwar shi na son ganin waye wannan mutumi haka ya haƙura, saboda mugun tokarin da ya kai mishi ta gefen cikin shi Akan idon Abba ƙ da mama da ƙarar kokawar su ya farkar da ita mutumin ya fece a guje Ya faruk na duƙe riƙe da gefen cikin shi na dama. Karkarwa kawai jikin Abba keyi, a ruɗe cikin tsananin tashin hankali yake furta "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, menayi musu ni Abubakar meyasa suke farautar rayuwata dana ahalina, suwaye waɗan nan, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" Yarda Abba ƙ ke magana ze tabbatar maka da ba a hankalin shi yake ba sam Yarda jikin shi ke rawa haka jikin mama ke rawa, ko motsin kirki ta kasa yi Ya faruk da zafin bugun da mutumin yayi mishi ya sauka ya miƙe, gaba ɗaya shima ruɗewa yayi, ya rasa kan wa zashi, kan mama ko kan Abba fa ya gama girgicewa da tsananin azabar da aka gana mishi Ganin mamar ta sakko da ƙyar tayo kansu yasa shima ya faruk ɗin ya nufi Abba fa ke neman cizge ruwan da aka sa mishi Da sauri ya faruk ya dafe Abba ƙ, kasa cewa komi yayi Abba ƙ kamar ƙaramin yaro haka ya ƙwaƙume ya faruk da shima ƙiris yake jira ya fasa kuka Dukda jarumtar Abba se gashi yana kuka kashirɓan a jikin ɗan ɗan'uwan sa Mama ma rashin madafar dafawa yasa ta matso, zama tayi kusa da Abban ta kutsa kanta kusa da inda Abba ƙ ya saka na shi a jikin ya faruk, itama ta fashe da kuka Haka ya faruk ya rungume su kamar shi ke sama da su Suke kukan amma yafi su jin raɗaɗin abun a cikin zuciya Ganin kukan nasu ya wuce ƙima yasa da ɗan ƙarfi yarda zasuji ya hau maimaita kalmar "HAZBIYALLAHU WA NI'IMAL WAKIL!!! LA'ILA HA'ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN!!" ALLAHUMMA LA SAHLA ILLA MA JA'ALTAHU SAHLAN, WA'ANTA TAJ'ALUL HAZNA IZA SHI'ITA SAHLAN!!!" Haka yayi ta jero musu waɗannan addu'oin, yakai ya dawo, har mama ta fara yi itama, can Abban ya ɗauka shima Cikin hukuncin ubangijin bayi jikin su ya dena rawa, zuciyoyin su suka yi sanyi hankulan su suka fara kwanciya Abba ƙ ya fara sakin faruk ya koma ya kwanta, sannan mama itama ta kifa kanta a jikin bango Ya faruk na ganin haka ya juya ya saka key a ƙofar sannan ya buɗe toilet ya shige ya kullo kan shi a ciki Yana shiga shima ya haɗe kanshi da bango ya fashe da kuka me taɓa zuciyar me sauraro. Duk suna jih shi, banda mumtaz da har yanzu bata san inda kanta yake ba Jin kukan ya faruk ba ƙaramin sake taɓa su yayi ba, amma ƙarfin kiran da suke ma ubangiji ya nasu hope da juriya Ya faruk seda ya kusa minti talatin a cikin toilet kafin ya fito Be yarda ya haɗa ido dasu Abba ba yayi hanyar fita daga ɗakin Da sauri mama tace "ina zaka ka barmu faruk?" Be waigo ba yace "yanzu zan dawo mama" Key ɗin ƙofar ya zare ya fita tukun ya rufo su ta waje Seda ya ƙarewa wajen da yake tsit kallo tukun ya nufi office ɗin likitan Shima ya ɓata lokaci sosai a wajen kafin ya fito, Ta can baya ya zagaya, wayar shi ya ciro yayi ƴan danne dannen shi tukun ya kara a kunnen, shima ya ɓata time yana waya kafin ya juyo ya dawo ɗakin Shigar shi kenan mumtaz ta farka a firgice tana sambatun kiran sunan Abba na mamana! Mamace a kanta duk da irin jirin da ke ɗibar ta, Abba kam ya kasa koda motsi daga inda yake Da sauri ya sake kulle ɗakin ya nufesu ganin mumtaz na neman dirowa daga kan gadon cikin gushewar hankali har tana neman hankaɗe mama da ba ƙarfi sam a jikin ta Da azama ya tallafe ta ya ɗaga ta cak ya mayar kan gadon Tukun yace "mama lallaɓa ki koma ki kwanta, bari na tare ta" Ba yarda ta iya haka ta daddafa ta koma nata gadon ta kwanta. Sosai mumtaz ke fizge-fizge tana sambatu Ganin tana neman fin ƙarfin shi ne yasa ya rungume ta a ƙirjin shi ya hau tofa mata ayatul kirsiyu da falaƙi da nasi. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 SHARE PLS LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg39-40 Sauke hannun Abba babba kenan daga kuncin ya faruk, goggo safiya na ƙarasowa baki sake hannu a saƙale Da mugun mamaki goggo safiya tace "me zan gani haka Ali?, me yayi zafi ka sauke mishi wannn marukan kamar wanda akaiwa turaren tsiya?" Cikin fushi Abba babba yace "ya safiya yaron nan yayi mana ɗiban albarka, banda bamu isa da shi ba ya za'ayi ace yaje ya aiwatar da abu ba tare da masaniyar mu ba? banda ya raina ma mutane hankali" Itama a ɗan fusace gaggo safiya tace "ɗiban albarkar me yayi?, ko me yayi be kamata ace da girman sa mutum ya zama magidanci ace kayi mishi haka ba sam ga yara ta ko'ina" Shiru Abba babba yayi yana maida numfashi, mutum ne shi me zuciyar tsiya, be raina abun fushi sam Uncle Abbas yayi saurin faɗin "Tunda haihuwar shi akayi ai befi ƙarfin hukunci ba" Tunda Abba ya sauke ma ya faruk marin be yarda ya ɗaga kanshi ba se yanzu da uncle Abbas yayi magana, Da jajayen idanuwa ya faruk ke kallon uncle Abbas wanda daga ganin yarda yake magana kasan harda zigar shi Abba b ya ɗauka Be yarda yace komi ba ya juya da niyar barin wajen, Taku ɗaya yayi ya jiyo muryar Abban ya sake faɗin "Au tafiya zakayi baka sanar wa mutane inda ka kaisu ba?" Murya a cunkushe ya faruk yace "Na kira wayoyin ku dukan ku a kashe, uncle Abbas kawai na samu kuma be ɗaga ba, shine nayi dropping muku hospital ɗin da na sauya musu" Be jira cewar su ba ya juya ya nufii ɗakin shi. Tunda akai marin hafsat ta kwasa da gudu tayi ciki, cike da kwaratsi hafsat ke ƙwala wa umma babba kira, faɗi take "umma, umma, fito kiji!" Cike da tsoro umma b ta fito daga ɗaki jin yarda take ƙwala mata kira Ido a waje umma b tace "lafia hafsa?" Cike da gulma hasfat tace "yanzun nan Abba ya wanke ya faruk da zafafan maruka yasin" Duk da taji kalmar marin banbaraƙwai, amma ga tunanin ta tasha ɗaya daga cikin wanɗa ke hospital ne ya margaya Fuska a ɗaure umma babba tace "mari fa kika ce, se kace faruk ɗin wani ƙaramin yaro ne?" Taɓe baki hafsat tayi kafin tace "aikuwa yasha su da zafin su kam, dama yarda naga Abba ya shigo gidan nan kamar da fushin kowa ya shigo". Juyawa cikin ɗaki umma b tayi, wayar ta da ke kan mudubi ta ɗauka tayi dialing nombar ya faruk Wayar nata ringing be ɗaga ba, Seda tayi mishi kira uku be ɗauka ba tukun ta aje wayar haɗe da faɗin "zuciyar gadon ta motsa kenan". Ta ɓangaren ya faruk kuwa yana shiga ɗakin shi ya shige wanka, yana wankan ne yaji kira nata shigowa, sauri-sauri yayi ya gama wanka duk a tunanin shi calls ɗin daga asibiti ne Yana fitowa yaga missed calls ɗin ummar har uku Be kira ta ba seda ya gama shiryawa tsaf tukun ya maida mata da kiran Umma b kamar daman jiran kiran nashi take ta ɗaga, kafin yace wani abu ta riga shi faɗin "meke faruwa ne faruk?" Cike da basarwa yace, "a ina umma?" Sakatoo umma b tayi da baki tana sauraron rainin hankalin ɗannata, cikin ko in kula ta maida mishi da "ohhh, hakane fa ba kai nayi niyar kira ba fa" Murmushi ya faruk yayi jin yarda ta ƙule nan da nan, kafin ta aje wayar ta sake faɗin "ayi jinyar kumatu lafia" Wannan karon he can't hold it seda ya dara, duk da raɗaɗin da zuciyar shi ke mishi kuwa Sosai ya faruk yayi nutsu cikin tunanin shi, gaba ɗaya ya rasa inda ze kama, ya kuma rasa da wa ze tattauna akan wannan matsalar Saƙon da'aka tura mishi a jiya ya buɗe ya sake karantawa "ya faruk kar ka bar su mama su kaɗai" A bayyane yace "waye wannan?" Can kuma ƙwaƙwalwar shi ta koma ga likitan ɗazu da ya danne Abba da pilo Gaba ɗaya kanshine ya hau hautsinawa yana juya mishi, alamar in mutum ya cika tunani. Zumbur ya faruk ya miƙe, still a bayyane yace "wallahi AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI, dole ma" Sanda ya fito harabar gidan ba mutane kamar ɗazu, dan har su Abba b da uncles ɗin shi duk basa wajen Ahmad ua hango can wani lungu zaune shi kaɗai ya haɗa kai da gwiwa Tsayawa sosai ya faruk yayi yana kallon shi, duk a tunanin shi wayace a hannun shi Ya kai kusan min biyu yana kallon shi kafin ya ƙarasa kusa da shi Sam Ahmad beji zuwan shi ba har seda ya faruk ya dafa kafaɗar shi tukun ya ɗago da sauri Zazzaro ido ya faruk yayi ganin yarda fuskar Ahmad tayi ruɗu-tuɗu tsabar kukan da ya sha Cike da fargaba ya faruk yace "me ya same ka Ahmad?" Murya na rawa Ahmad yace "ina son zuwa inga su Abba, amma sam na kasa ya faruk, zuciya ta na min ƙuna da zafi duk sanda na kusance su" sunkuyar da kai ya faruk yayi yana faɗin "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" yana tunowa da abinda mus'ab ya rubuta sak da da abinda Ahmad yace a takardar shi lokacin da ze bar gida Gaba ɗaya jikin shi yayi mugun sanyi, Bayan kalmar innalillahi da ya furta be sake cewa komi ba, Miƙewa yayi tukun ya kamo hannun shi ya miƙar da shi shima Janshi ya hau yi har bakin motar shi, se a sannan yace "shiga ka jirani" Ya juya yana amsa call ɗin dr jamal Yana cikin amsa call ɗin dr jamal ya fauza(babbar ƴar umma ƙarama) ta fito ɗauke da manyan kuloli Yana a inda yake tsaye ya buɗe mata booth ta saka na hannun ta, sannan fadil ma ya saka nashi. Kaf a gidan babu warda suke zama suyi magana ta fahimta kamar fauza, tasu tazo ɗaya tun suna yara Ya faruk na gama wayar ya dawo jikin motar inda ya fauza ke tsaye tana jiran shi Da ɗan damuwa a fuskar ta tace "ya faruk me yayi zafi wai ɗazu har Abba b ya mareka"? Hannu ya saka ya shafi kumatun shi kafin yace "nima dai nayi mamaki, daga na sauya ma su Abba ƙ hospital shikenan fa" har yayi niyar sanar da ita abinda ya faru, ɓangaren zuciyar shi ya gargaɗe shi, waskewa yayi da maganar yace "bari in dawo dai mayi magana" Da "to" ta amsa, ta shige ciki, shi kuma ya shige mota. Daga shi har Ahmad ba mece ma wani komi har suka isa asibitin Har yayi parking ya fito bega Ahmad nada niyar fitowa ba Kallon shi ya faruk yayi yace "fito" Jimm ya ɗanyi tukun ya fito jiki sam ba ƙwari Booth ya buɗe ya ɗauki kulolin da ya fauza ta saka Yana gaba Ahmad na binshi a baya Jiyake kamar yayi ta zunduma ihu tsabar zugin da ranshi ke mishi Amir dake zaune a ɗan harabar wajen ya hango su, da sauri ya taso yazo ya karɓi kular hannun shi yayi ciki da su Amir na shigewa Ahmad yayi saurin faɗin "ya faruk ɗan riƙe min, fitsari nake ji" Karɓa yayi tukun yaci gaba da tafiya zuwa ciki. Ba wani fitsari da Ahmad keji, kawai yakasa riƙe kanshi ne sam shiyasa yayi haka Ya faruk na shigewa, Ahmad ya zagaya ta bayan windows ɗin ɗakin, Laɓewa yayi ya rinƙa leƙen iyayen nashi dake zaune bama zaka taɓa cewa sunyi accident ɗazu ba, bama kamar mama ita ko ƙwarzane babu a jikin ta, Abban ma ƴar buguwace kawai a kafaɗa Cike da so da ƙauna yake kallon iyayen nashi, Abinda be sani ba tun da ya leƙo na farko mama taji ajikin ta ana kallon ta A wayence ta kalli windon, ganin Ahmad ne ke leƙen su hakan ba ƙaramin karyar mata da zuciya yayi ba. Kusa da mama ya faruk ya zauna, cike da kulawa yace "mamana ya jikin?" Murmushi mama tayi kafin tace "naji ƙarfi sosai yanzu, mumtaz ce har yanzu tun baccin daka tafi ka barta tanayi bata farka ba, Allah yasa dai kan yarinyar nan be taɓu ba" Da sauri goggo safiya tace "ah tuf da baƙin yawu, in sha Allah garas zata miƙe kamar yarda kuka miƙe kuma" Kowa seda ya murmusa wa yarda tayi maganar Tsam ta taso daga inda take ta matso kusa da ya faruk, ƙasa tayi da murya tace "waɗan nan masu kakin fa faruk?" Kai tsaye yace "saboda tsaron lafiyar su na aje su goggo" Taɓe baki tayi kafin tace "kamin daidai faruk, ni kaina ban gane ma wasu abunuwan ba wallahi, tunda na iso garin nan na fara gane-gane masu ban tsoro wallahi" Tsit wajen yayi jin abinda goggo safiya ke faɗi Cike da son jin me tagani ya faruk ya ce "me kika gani ne goggo?" Shiru tayi bata sake tanka kowa ba, daga baya ma miƙewa tsam tayi ta nufi gadon mumtaz dake mutsu mutsu. Se asannan mama tace ma faruk "In yasan ba ze shigo ba mene na zuwa yana leƙen mu?" Da sauri ya faruk ya kalli window ido biyu suka yi da Ahmad dake laɓe Da Ahmad yaga sun ganshi yayi saurin barin wajen yana jin azalzala acikin ranshi Murya ƙasa-ƙasa ya faruk yace "mama akwai matsala babba wallahi, ban san daga ina take ba, amma kowa ya kalli yarda abubuwan nan ke tafiya zaka san akwai wani abu a ƙasa," Murmushi me cin rai tayi sannan tace "Tabbas AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI FARUK, Amma mubi komi a hankali mu dage da addu'a Allah ze warware mana komi" Kafin ya faruk ya sake magana goggo safiya ta dawo tace "faruk zo ka kamamin mumtaz in saka ta fitsari kar ta jiƙe shimfiɗar" Dururu yayi, cikin ƙinƙina yace "ni kuma?, ah bari a kira nurse tazo ta tayaki dai" Goggo safiya tace "kai bana son shashanci, yo kafin nas ɗin tazo ai ta gama fitsare wajen" Murmushi mama tayi tace "muje na kama miki ita yaya safiya" suna shiga yayi wuf ya bar wajen ya nufi office ɗin dr jamal. *******KHALID Yinin ranar yayi shine cikin rashin sukunin maganar da sakina ta gaya mishi game da mumtaz wani ɓangaren na zuciyar shi yaso ya yarda, amma wani sashin ya gargaɗe shi da kar ya kuskura yayi sake na dafe da mumtaz Da ya zauna yayi tunani me kyau, yayi la'akari da irin yanayin rayuwar da akeyi a yanzu, hassada, baƙin ciki, da zallar zagon ƙasa da yayi ma al'ummma katutu yasa ya dawo daga rakiyar maganar sakina Dan tabbas a rayuwar nan wanda kafi kusanci da shi se ya cuceka, ko kuma ya nemi ganin bayan ka, kuma haka kurum siddan ragadan baka tare mishi komi ba, zallar hassada da tsananin baƙin ciki ya ginu a tsakani. Bayan wannan dogon tunanin da yayi ne yasamu sukuni a cikin ranshi Beyi fushi ko zuciya ba ya sake kiran sakina, da ƙyar da ɗan wulaƙanci ya samu ta gaya mishi asibitin da aka maida su Aikuwa beyi ƙasa a gwiwa ba yaja abokin shi kamal suka nufi hospital ɗin Sanda isa an shiga sallar isha, seda suka tsaya a masallaci sukayi kafin suka fito Suna fitowa suka sake haɗuwa da uncle Abbas shima da fitowar shi kenan, cike da girmamawa su khalid suka sake gaishe shi da tambayar masu jiki Uncle Abbas da kan shi yayi musu jagora zuwa ciki Inda Allah ya temakesu kenan, dan jami'an tsaron wajen bazasu taɓa barin su shiga ba saboda tsaro Direct ya wuce da su ciki Abba ƙ kam be sheda shi ba, duk da yayi mishi bayanin a cmpnyn shi yake aiki Ganin basu ga mumtaz a wajen ba yasa shi tambayar uncle Abbas "an sallami mumtaz ne sir?" Uncle Abbas yace "ohh, gadon ta na ciki, ai tafisu jin jiki kam, ku shiga" Suna shiga suka isketa zaune goggo safiya ta tasata a gaba tana cin abinci Kalid na yin sallama mumtaz ta ɗago kanta da sauri, a take agogon data ɗauka a cikin motar shi ya faɗo mata, da sauri ta sunkuyar da kai ganin yarda ya kafe ta da kallo Murya ciki-ciki mumtaz tace "goggo bani hijabina pls" Baki sake goggo safiya tace "Ah lallai kin fara dawowa hayyacin ki ƴannan da har kike neman hijabi" Ganin ba bata hijabin zatayi ba yasa taja ɗankwalin goggo safiyan dake ajiye a gefe ta yafa a jikin ta Hannu bibbiyu goggo safiya ta karɓi su kalid jin bayanin da kamal yayi mata Nan suka zauna suna ta fira kamar irin sun saba ɗinnan Ita kam komawa tayi ma tayi kwanciyar ta, sedai kaf firar da suke tana jin su. Kiran da uncle ƙasim yayi mata ne yasa ta tashi a wajen kamar dama jira kalid yake ta fita, matsawa yayi kusa da mumtaz data juya baya yace "ya jikin naki?" Ƙin amsawa tayi, in da ta waiga fuskar ta ya koma, ido huɗu suka yi Da sauri ta rufe nata tana jumɓuro baki gaba Murmushi kalid yayi kafin yace "nagode ma Allah da ya takaita abin nan a iya haka mumtaz, yanzu kam zan iya bacci me daɗi tunda na ganki na kuma ga yanayin jikin ki" "hmmm" kawai take cewa Cike da damuwa yace "ina wayar ki?" Se a sannan tayi magana tace "kamar an sace fa" Yace "toh bakomai, gobe in zanzo zan tawo miki da wata, amma yanzu ba wani nonba da zan same ki kafin safe?" Girgiɗa kai kawai tayi, Daidai nan goggo safiya ta dawo Basu sake wani jimawa ba sukayi mata sallama, bayan sun aje ma goggo safiya 20k agaban ta. Sun fita kenan ya faruk ya shigo hannun shi ɗauke da takarda, kusa da Abba ya zauna, miƙa mishi takardar yayi kafin yace "dan dai ka matsa ne Abba, amma da kun zauna kun sake warwarewa tukun" Cike da kulawa Abba yace "gara mu tafi gida tunda Allah yasa ba wani matsala, kuma na gaji da tambaye tambayen da ake min akan waɗan nan ƴan sandan da ka zuba, kuma hankalina baze taɓa kwanciya ba a nan" "Hakane Abba, amma waze zauna da mumtaz?" Se a sannan mama tace "Ya safiya zata zauna da ita mun gama wannan maganar, gwara muje gida a sauƙaƙa ma jama'a dake ta sintirin zuwa" Ba yarda ya iya, haka suka tattara suka koma gida aka bar mumtaz da goggo safia a asibitin. ****gaskiya ya kamata kije ki gaishe ta mami, wallahi taji jiki sosai Cike da zolaya mami tace "ohh khalid bako kunya?, in na dawo daga tafiyar da zanyi gobe zanje in gaishe ta, Amma dai zuwa gobe ka samu binta da azima suje su dubata(binta da azima ƙannen mamin ne) Se su sake tabbatarwa da gaske kake Cike da jin daɗi khalid yace "yauwa mami na, kin kawo shawara me kyau wlh" Haka suka yi ta firar su irin na uwa da ɗa, sun jima suna fira kafin mami ta sako maganar abun hannun ta data nema ta rasa "Wai khalid har yanzu shiru ba wani labari game da abun hannun nan?" "Mami, tunda kikaji har yanzu ba wanda ya kirani to wlh ba satar shi akayi ba, maybe ya faɗa wani wajen ne, ki sake dubawa dai" Taɓe baki mamin ta kafin tace "ko ɗazu seda na sake dubawa wallahi, ɓatan shi yayi min ciwo sosai" Da sauri khalid yace "mami ba akwai CCTV a office ɗin ba?" Mami tace "akwai mana" yace "ki duba to, ƙila kiga inda ya faɗa" Da ɗan murna mami tace "aikuwa danaji daɗi, sam na mance da wata CCTV a office ɗin' ya ɗan jima a wajen mamin kafin yayi mata sallama ya wuce ɗakin shi. *****wajajen ƙarfe biyu da rabi na dare, ya faruk na kwance sam bacci yaƙi zuwar mishi ya rasa mafita ga wannan matsalar da ke neman fin ƙarfin su Yaji ana ƙwanƙwasa ƙofar shi kaɗan kaɗan Nutsuwa yayi yaji da gaske nan bugawar ake Seda ya tabbatar da bugawan ake, da sauri ya zira riga haɗe da kallon agogon wayar shi lokacin da ya gani ne yasa shi jin faɗuwar gaba, haka ya dake ya matsa jikin ƙofar, a dake yace "waye?" Daga can akace "MUS'AB". NAGODE DA CALLS ALLAH YA BAR ZUMUNCI ❤️ ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 SHARE PLS. LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg 41-42 Babu inda jikin ya faruk baya rawa jin mugayen maganganun da mus'ab ke bashi labari, Cikin kuka mus'ab yace "shiyasa na yanke shawarar nisantar su gaba ɗaya, dan muddin ina kusa da su komi ze iya lalacewa". Sam ya faruk ya kasa magana, ajiyar zuciya kawai yake saukewa yana tuna yarda uncle Abbas ke gaggaya mishi magana akan sauya ma su Abba hospital da yayi Da ƙyar maganar ya faruk ke fita yace yace "Mus'ab zaka iya tunawa, bayan shi se wa?, baze taɓa zama cewa shi kaɗai ne ke wannan aika-aikar ba" Kan mus'ab a ƙasa, yaƙi yarda sam ya ɗago kanshi, ga alamar yana son cewa wani abu, amma sam yaƙi ya furta A zuciye ya faruk ya finciko shi, murya a murmurɗe yace "ka gaya min mus'ab, kar kaji shakkata, se kuma wa ka gani?" Ƙin cewa komi mus'ab yayi banda haɗiyar zuciya da yake ta faman yi Sun jima a haka, har wajen asuba tukun mus'ab yace "Zan tafi, tsayawa ta babbar matsala ce anan ya faruk" Ya faruk be hana shi ba, sema dafa kafaɗar shi da yayi yace "Ko shine silar zama ƙarshen numfashi na zan kare ahalin Abba ƙarami in sha Allah" Mus'ab be seke minti ɗaya a wajen shi ba ya fice. BAYAN SATI ƊAYA Sosai jikin mumtaz yayi sauƙi dan suna saka ran sallama a yau ko gobe A ɗan zaman asibitin da tayi wata soyayya suke zubawa ita da khalid da tuni yayi watsi da maganar sakina Ɗari bisa ɗari goggo safiya na goyon bayan hakan, itama ba ƙaramin son haɗin nasu take ba Zuwan aunties ɗin shi biyu haɗe da shatara na arziki suna zuwa dubata Wasa wasa, wani lokacin kafin khalid ya wuce asibitin se ya fara zuwa gaishe da mama har gida tukun yake wucewa can Mama tayi murna, ko ba komi ta yaba da hankalin shi, balle ma maganar da sukayi da Abba ƙ akan aurar da su na nan maƙale a ranta, dan ma wannan tsautsayin da ya faru ne akayi shiru da maganar, yanzu kam ta fara samun kwanciyar hankali. Tafiyar khalid kenan ya faruk ya tura ƙofar ɗakin ya shiga Da fara'a sosai goggo safiya ta tarbe shi, haɗe da faɗin "Oh kana nan faruk? tunda aka sallami iyayen ka mu kuma ka ɗauke mana ƙafa" Ɗan murmushi ya saki kafin yace "nima banji daɗi bane goggo, amma Alhamdulillah" Ta gefen ido mumtaz ke kallon shi, tabbas ko be ce baya jin daɗi ba zaka hango hakan, ramar da yayi ta nuna ƙarara a fuskar shi Jajanta mishi goggo safiya tayi kafin tace "To ga kayan marmari a miƙo maka?" Kallon tulin ledojin gaban su yayi yace "wannan shirgin fa"? Cike da jin daɗi goggo safiya tace "Hmm kaima dai ka faɗa, yarone mara ƙyashi wallahi, kullum in zezo baya zuwa hannu bibbiyu se kaga ya riƙo wani abun yazo da shi, Allah dai yasa hat cikin gida ba maƙeƙe bane ba" Idon ya faruk na kan wayar shi yace "wa kenan goggo?" Baki buɗe, tace "khalid sunan shi, kuma wallahi baka ga yarda yake kula da mumtaz ba, abin har birgeni yake" A hankali ya faruk ke furta sunan khalid, be sake cewa komi ba yaci gaba da danne dannen shi jin yayi shiru yasa goggo safiya tashi ta ɗauki komi bibbiyu ta aza akan plate ta tafi wanko mishi Tana fita ya kalli mumtaz data juya baya yace "Tunda har kin samu damar yin soyayya kina jinya kin warke kenan?, duk da na lura bayan halayyar ki har rashin gaisuwa ma kin iya" Bata ce komi ba, bakuma ta gaishe shin ba Suna a haka goggo safiya ta dawo, kusa da shi ta aje plate ɗin sannan ta kabbara sallar isha'i Ko kallon plate ɗin beyi ba ya fice daga ɗakin Direct office ɗin dr jamal ya nufa, ba wani ɓata lokaci ya karɓi takardar sallamar da yasa akayi ta dole. Ya jima a cikin mota yana amsa wayar mus'ab kafin ya koma ɗakin Goggo safiya na ganin shi tace "au nasha ka wuce ne ba ko sallama" Kujera ya ja ya zauna tukun yace "a'a, nayi waya ne, ku haɗa kaya ku same ni a mota an sallame ku" Sakato goggo safiya tayi tana kallon shi bako ƙiftawa, can tace "yo haka ake sallama da dare tsaka mutum ya gama sadaƙarwa kwana zeyi?" Murmushi ya faruk yayi kafin yace "To mene abun ɓata rai goggo, ai komin daɗin asibiti gida yafi shi ko? tunda naga kamar daɗin zama kuke ji" ya ƙarashe maganar yana kallon mumtaz ta gefen ido Be jira amsarta ba ya juya ya fice Aikuwa suna haɗa kaya goggo safiya na mita, wai khalid zezo yaga basa nan Mumtaz da se yanzu tayi magana tace "Rabu da shi goggo, zan kira shi a waya yanzu ma" Saboda yawan kayan su seda goggo safiya ta kira masu goge goge suka taya su ɗauka Suna zuwa wajen da yayi parking ya fito, ɗaya bayan ɗaya yake kallon kayan da suka jido Beyi wata-wata ba yace wa warda ta tayasu ɗakko kayan "kwashi wannan da wannan ki tafi dasu" Nan tayi ta zabga godiya, goggo safiya na gefe tana zuba ƙorafi. ƙofar baya ya buɗe mata ta shiga, sannan ya zagaya shima ya shiga Mumtaz na tsaye ita bata shiga ba, sanin waye ya faruk yasa ya zagaya ta shiga gaba Suna tafe yana ayyana abubuwa da yawa a ranshi, bin diddigin uncle Abbas da yake har yanzu ya kasa gane komi, gani yake kamar ma incle Abbas ɗin ya gane yana bin diddigin shi Dai dai wajen shagon da ake seda fura ya tsaya, sanin goggo safiya ta shaƙa da yawa yasa yace "Bari na karɓo miki fura goggo" be jira cewar ta ba ya fice a motar ya barsu a cikin raɓa. Tunda mumtaz ta shiga motar idon ta ya sauka ga zoben azurfar da ya faruk ya aje domin ya gwadata ya gani se kuma bandir ɗin ƴan dubu dubu guda uku dake gefen zoben Ba wani dogon tunani mumtaz ta saka hannu ta ɗauke zoben nan, sannan duk a bandir ɗaya ta zari goma goma a ciki ta saƙe a hijabin ta Be daɗe ba ya dawo, kallo ɗaya yayi ma wajen ya ga babu, abunda bata sani ba saboda ya gwada yaga ko ta dena halin ne yasa ya ajiye Bece komi ba yashiga yaja suka tafi. Goggo safiya na sauka ya waiga side ɗin mumtaz dake saurin sauka itama, fuska a ɗaure yace "bani abinda kika ɗauka a nan"! Duru duru tayi tana wani kauce-kauce, kunya da tsananin nadama na baibayeta Gani kawai yayi ta sauke kai ƙasa ta fashe da kuka haɗe da ciro zoben da kuma kuɗin Duk da yarda ranshi ke tafasa ganin yarda tayi yayi mugun ɗaga mishi hankali da kuma mamaki, Kasa ce mata komi yyi, da yaga bata da shirin sauka a motar yace "you can go, Allah ya shirye ki ya kuma rufa miki asiri" Jin yarda yayi maganar cikin sanyin rai da batayi zato ba yasa ta ɗago fuska da sauri tana kallon shi Kashe motar yayi, ya fice ya barta. Seda ya ɓace wa ganin ta tukun ta fito bayan ta share hawayen ta tas, tayi cikin sasan su inda take jin hayaniyar mutane sosai. ****Da asuba bayan sun dawo daga massallaci duk suna tsaye a harabar gidan Abba babba yace "Inajin zuwa gobe duka yaran su aiko da samarin nasu se asan abun yi ko?" Amsawa sukayi da "hakane" Tukun suka ɗora da firarrakin su na ƴan'uwa Sun ɗan jima sosai kafin kowa ya nufi sasan shi. Uncle Abbas na shiga nashi part ɗin ya iske duka nashi ahalin a dinning suna breakfast Amir ne ya fara gaishe shi kafin Najwa da Tk Shima kujera ya ja ya zauna, Mummy da kanta ta tashi ta fara haɗa mishi tea, tana haɗawa take faɗin "Yaudai firar nan ta jima" Seda ya kai mug ɗin bakin shi kafin yace "Aikam" yana tsaka da cin abincin ya kirayi sunan najwa da ke gaf da barin dining ɗin Kanta a ƙasa tace "na'am daddy" Kai tsaye yace "ki sanar ma wanda ke zuwa wajen ki yazo gobe muna son ganin shi" Duk da tasan da zancen amma hakan be hanata jin faɗuwar gaba ba, jiki a mace tace "to daddy" haɗe da barin wajen. Cike da jin daɗi mummy tace "abun ya taso kenan" Yace "ya taso fa, in sunyi daidai da ra'ayin mu ba za''a ɗauki wani dogon lokaci ba, kin san bama saka biki da nisa" Cike da jin daɗi mummy tace "hakane, Allah ya tabbatar mana da alkairi" Uncle Abbas na gama cin abinci ya tashi ya nufi palon shi, kasancewar asabar ce ba ranar aiki bace Tsum ya Tk ya miƙe shima yabi bayan sa Uncle Abbas na zama Tk ya shigo ya zauna kusa da uban nashi Fuska ba alamun rahma Ya Tk yace "Daddy, na kasa gane me kake nufi gaskiya, na gaya maka nifa ina son yarinyar nan, nace zanyi magana ka hanani da niyar kai zaka nemar min auren ta, kuma ga ƙishin-ƙishin ɗin da nake ji na daban, nifa gaskiya an saka ni a duhu" Murmushi uncle Abbas yayi tukun yace "Daɗi na da kai gajen haƙuri, akwai damar da nake jira ne TK, kuma nafika sanin muhimmancin mumtaz a gareka, just trust ur dad, haƙƙata ta kusan cimma ruwa soon!!! Kamar wasu sa'anni haka suka tafa suna kwashewa da dariya. Mus'ab na gama recording maganar yayi saving, har yayi niyar tura ma ya faruk ya fasa, ya koma yayi kwanciyar shi haɗe da rufe fuskar shi. 😊 Sorry for the late update, kunsan jiki da jini ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 SHARE PLS. LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg43-44 Da yamma lis, yau baƙi masu zuwa gaisuwar sallah da kuma dubiya duk sun ɗauke ƙafa Gidan an samu sauki mutane sosai Mama da goggo safiya na zaune a palon ƙasa suna firar kayan sha tara na arziki da aka kawo na saka ranar hafsa da bilkisu da kuma najwa Goggo safiya tace "naji Ƙassim yace yau da daddare za'a kawo na Amal itama" Mama tace "hakan Abban su ke gaya min kafin ya fita" Can goggo safiya ta sake cewa "mumtaz fa? ko har yanzu ta kasa tsaida zuciyar ta akan yaron kirki nan" Gyara zama mama tayi kafin tace "a dai gaban ki jiya muka titsiyeta ya safiya, na kasa gane kan yarinyar nan sam, ɗazu da safe da na sake mata magana ma fashe min da kuka tayi, Na rasa yarda zanyi ni kam" Da mamaki goggo safiya ta sake cewa "kuma fa naga kamar tana son yaron, nikam wallahi na yaba da hankalin shi sosai, duk yafi min samarin sauran kamala da nutsuwa" Ta waiga wajen da mumtaz ɗin ke zaune ɗazu taga bata nan Altine ta yafito tace "shiga kira min mumtaz" Altine na shiga ɗakin ta iske mumtaz tsaye gaban mudubi tana saka kwalli Ta cikin mudubin take kallon ta, fuska a ɗaure tace "lafia?" "ana kira" kawai tace ta juya A fili mumtaz tace "munafuka kwanan ki sun kusa ƙarewa a cikin gidan nan, ki gama raɓe-raɓen ki" Seda ta gama tas abunda take tukun ta fito Wannan karon harda umma ƙarama a palon Kusa da mama ta zauna haɗe da faɗin "gani hajiya mama" Yarda tayi maganar ya basu dariya, a da mumtaz akwai iya shege sosai, amma tunda ɗabi'ar sarface-sarface ta kamata ta sauya gaba ɗaya. Dundu mama ta sakar mata kafin tace "seda kika gama shanya mutane tukun zaki fito? Ya safiya ke kiran ki bani ba" ta juya sukaci gaba da magana da umma ƙarama Goggo safiya tace "shiru mumtaz banji kince komi ba, bana so kizo kina danasani daga baya" Shiru tayi bata ce komi ba, umma ƙarama tayi tsulum tace "Ya safayi shifa yaro ba'a mishi dole, in bata son wancan ta kawo wanda yafi kwanta mata mana" Taɓe baki mama tayi, badai ta saka musu baki ba Goggo safiya tace "haka maganar ki take sumayya, ni nagartar yaron kawai nake hangowa wallahi" Umma ƙ ta kalli mumtaz cike da kulawa tace " a cikin samarin naki wanne kk so tunda kamar baki gama aminta da shi khalid ɗin ba"? Kafin mumtaz tayi magana mama tace "ba se in akwai wasun ba, da bakin ta take korar su, nasha zaunar da ita ina nuna mata illar hakan amma yarinyar nan ta maidani wata gani can dai, to ga ranar maganata nan" Zumɓura baki mumtaz tayi, duk maganganun su sun isheta, Ga khalid ya jima da zuwa yana jiran ta, gashi su kuma sun titsiyeta a nan. Suna tsaka da surutun su megadi ya ƙwaɗa sallama a ƙofar palon Altine ce ta leƙa, ya faɗi saƙon ya juya Tana komawa ciki tace "Tunɗazu baƙon na jiran ki wai mumtaz" Salati goggo safiya ta saki haɗe da riƙe baki "yanzu fisabilillahi ajiye shi kikayi yana jira? to gaskiya baki kyauta ba tashi kije" Daman maganar su ta ishe ta, Da sauri tayi waje ta barsu da binta da kallo. Khalid na zaune a mota yaga fitowar ta, Ajiyar zuciya me sanyi ya sauke ganin ta fito fuskar ta a sake ba kamar jiya da yazo ba Da sauri ya fito ya tako zuwa wajen ta Fuska a washe yace "barka da fitowar sarauniyar kyawawa" Murmushin ta me kyau ta saki tana sunkuyar da kanta ƙatsa "muje ciki" tace, tana gaba yana binta a baya har palon baƙi. Da ƙyar da jiɓin goshi a ranar mumtaz ta yarje wa khalid turo manyan shi kamar yarda ya jima da nacin tambaya" Tsabar murnar maganar data yi yasa shi tashi ya fara juyi yana rawa yana mata waƙar "ta kusa zama tawa, ta kusa zama tawa" Ganin murnar da yake yasa yasata jin nutsuwa sosai a cikin ranta Tun tana ɓoye fuska tana dariya har ta dena ta koma yin ta a fili, Tsabar murna duk abinda aka jera mishi beci ba, time ɗin tafiyar shi ma beyi ba yayi mata sallama ya tafi cikin zumuɗi da zakwaɗin sanar wa mami. Tana komawa ciki kusan a tare sukace "har ya tafi?" Mama tayi caraf tace "ko kuma ta koreshi ba" Goggo safiya tace "Daɗina dake wani lokacin baki faɗin alkairi zahra'u," Murmushi mama tayi taci gaba da danna wayar hannun ta. Mumtaz ko a jikin ta, seda ta shiga ɗaki ta ciro hijabin jikin ta tukun ta dawo palon, kusa da goggo safiya ta koma ta zauna Ƙince ma kowa komi tayi, seda ta mula ta mulmule tukun tace "wallahi ji nake a raina dama ban amsa mishi ba" Ta gefen ido mama ke kallon ta, ba dai tace komi ba dan kar tayi tunanin ta matsu taji Goggo safiya ce ta gyara zama tukun tace "bana son iskanci mumtaz, duk kin bi kin saka mu a duhu, shin kin ce ya turo ne koko wani taɗin kike yi na daban?" Tura baki tayi gaba kafin tace "ai shine nace nayi danasanin cewa na yarda ya turo ɗin" Kusan a tare umma ƙarama da goggo safiya suka saki wata narkekiyar guɗa wanda seda yasa Altine dake baya shigowa da sauri Mama kam ajiye wayar hannun ta tayi, haka kurun taji gaban ta na faɗuwa ba gaira ba dalili. Tsabar haushi mumtaz barin wajen tayi Kallon yarda mama ke binsu da ido goggo safiya tayi Cike da murna tace "naga kamar kina wani basarwa zahra'u" Kafin mama tace komi umma babba ta shigo itama, duk dan saboda yaya safiyar suke yawan shiga sasan maman, duk da umma babba bada son ranta hakan ke kasancewa ba Waje ta samu ta zauna, fuska ba yabo ba fallasa ta gaishe da yaya safiyar, sauran ko sannun ku tace Jin ana kamar magana me muhimmanci ne yasa taƙi tashi ta tafi Kowa yasan bata jimawa in tazo, amma yau suka ga saɓanin hakan Murna nata cin goggo safiya, bata so ci gaba da murnar a gaban umma b ba Haka nan ta basar ta kalli mama data ci gaba da danna wayar ta tace "Kin dai gani in baki buɗe ido kin tsaya ma ƴarki ba to ke kika sani, yarinyar da ba ƴar fari bace balle ace zaka ɗanyi kawaicin wani abun, wasu ma da zasu aurar da na farin basuyi kawaici ba sam" Kowa yasan da umma b take, dan tana maganar tana kallonta ta wutsiyar ido Dan haka ki saki zuciyar ki kinuna ma ubangiji godiyar ki. Umma ƙarama ta amshe da "gaskiyar ki kuwa yaya safiya, Allah dai ya tabbatar mana da alkairin sa" Cike da shewa goggo safiya ta taɓa umma ƙ tace "na taɓa ki da alkairi mutuniyar kirki" Sosai umma babba ta ƙunsa, rai a ɓace ta miƙe tayi hanyar fita Har ta saka ƙafarta waje ta waigo tace "Duk wanda yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake, kuma wallahi ya safiya ki kama girman ki tun wuri" tana gama faɗan haka ta fice fuuuu kamar zata tashi sama. Umma babba na fita mama tace "kayya ya safiya ni kam bana son irin haka sam wlh" Banka mata harara tayi, tukun ta waiga saitin umma ƙarama tace "Bazata taɓa sauya ba ita, daga faɗin gaskiya kinga zata fara jero wa'azin nan nata " Murmushi umma ƙ tayi kafin tace "zaman lafia yafi komi daɗi ai ya safiya" Basar da su tayi taci gaba da murnar ta, harda faɗin "tafiya kam ba yanzu ba, se baba ya gani". ******Bayan isha, duka iyayen na nan suka tarbi masu kawo kayan Amal, aka tarbe su kamar yarda aka tarbi sauran, sosai aka daddara kafin suyi sallama suka tafi. Ta ɓangaren khalid kuwa yana barin wajen mumtaz gida ya nufa, duk da yasan mami bata nan, hakan be yana shi komawa gida ba, gaba ɗaya yama rasa me zeyi Waya ya ciro ya danna mata kira, amma har ta tsinke bata ɗaga ba Maida kiran yayi ga kiran ƙanwar mamin, da ya sanar mata itama tayi murna sosai, a zumuɗin ta har ta fara mishi lissafe-lissafen abinda za'ayi. A daidai lokacin da call ɗin khalid ya shiga wayar mami tana tsaka da kallon videon data zaƙulo na sanda mumtaz ta ɗaukin abin hannun ta Sosai abun ya bata mamaki, ta kalli videon yafi a ƙirga Sosai ta lula tunanin inda tasan yarinyar, daga baya ta gane sun taɓa kwanciya anan. Kwana biyu da mumtaz ta bashi dama aka saka musu ranar aure, bayan an gabata da komi na al'ada Zukatan mafia akasari basu so haɗin ba, to da yake aikin gama ya gamu ba yarda wasun suka iya dole suka haƙura da bin abun da addu'a. Ta ɓangaren mus'ab kam ya samu kwanciyar hankali jin har an tsaida magana da khalid ba da TK ba, sosai ya saamu nutsuwa. TK tunda aka saka ranar mumtaz aka haɗe da sauran hankalin shi yayi mugun tashi Takanas ya je ya sami uncle Abbas a guess hause ɗin shi ya tayar mishi da hankali Da ƙyar da lallami uncle Abbas ya lallaɓa TK haɗe da alƙwari me ƙarfin gaske na mallaka mishi mumtaz a cikin ƙanƙanin lokaci. ƘILA KU JINI ANJIMA ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg45-46 Yinin ranar umma b a sama take gaba ɗaya sam Abba babba baya shawara da ita a kan hidimar nan Alhalin nata yaran sunfi yawa a ciki waɗan da za'a auras Tunda ta baro ɗakin shi take yaɓa maganganu marasa daɗi wanda sam bema dace ace tayi su ba Amal da shigowar ta kenan daga school ta iske umma b a haka, cike da damuwa tace "Haba umma, dan Allah kicire wannan abun a ranki, wallahi in kika ga ramar da kikayi se ace ma jinya kika kwanta" Wata mahaukaciyar harara ta ballo mata Aikuwa gumm tayi da bakin ta dan tasan sauran zancen in taci gaba da magana. Shigowar ya faruk kenan daga tafiyar da yayi ta sati, jakar shi kawai ya aje ya shiga sasan nasu Nan shima ya taras da banbamin da umma b ke yi Tana ganin ya faruk tayi shiru ta bishi da kallo Sama-sama ya gaishe da umma ƙarama dake ta harkan gaban ta, tukun ya shige uwar ɗakan umma babba Tsam ta miƙe tabi bayan ɗan nata Ko gaisuwar shi bata amsa ba ta hau tambayar "ciwo kayi ne acan faruk?" Tashi zaune yayi tukun yace "aikuwa, zazzaɓin dare nayi" Zama a gefen gado tayi sannan tace "Allah yasa kaje an duba ka, yanzu haka maleria ce" Gyaɗa kai kawai yayi, Shiru ɗakin ya ɗauka, an ɗan jima kaɗan tukun ya faruk yace "Umma dan Allah ki rage yawan faɗan nan naki, wallahi bana jin daɗi ace sam ba'ajin sautin muryar kowa a gidan se taki, kuma in anji takin faɗa ne a koda yaushe umma" Taɓe baki tayi tana kallon shi sama da ƙasa sannan tace "Ai zanyi mugun mamaki innaji baka tanka ba, ayi tajin muryar tawa mana, shikenan akan gaskiya ta baza'a barni nayi magana ba?, to wallahi bazata saɓu ba, dole in naga abinda beyi min ba in tanka" Dafe gefen kanshi yayi tukunyace "ni ba haka nake nufi ba umma, akwai abunuwan da suna son a kawar musu da kai, ba komai bane ake tankawa, wallahi mu ƴaƴan ki bama jin daɗi sam, Baki ganin yarda umma ƙarama ke shanye abubuwa bama kamar akan Abba b, duk zuciya da fuahin Abba tasan yarda take mishi" Bata bari ya ƙarasa ba ta miƙe tsaye, idon ta a rufe ta nuna mishi ƙofa tace "Fita kafin zuciya ta ɗibeni nayi maka muguwar magana" Jiki a sanyaye ya miƙe, murya cike da damuwa yace "ban faɗi dan na ɓata maki rai ba umma, ki gafarceni, Allah ya huci zuciyar ki" Da ƙarfi tace "naji kullum haka kake faɗa, fitar min a ɗaki, kuma Allah ya kiyashe ni zama micijiya me kan mutum!!" cak ya tsaya ya kafe umman nashi da kallo jin maganar ƙarshe datayi Ganin ya kafe ta da ido tace "bari na maimaita kaji da kyau, cewa nayi Allah ya kiyashe ni zama micijiya me kan mutum!" Ta juya tayi shigewar ta ciki. Umma ƙarama na tsaye a wajen dining tana shirya kulolin abincin dare a kai Kunya sosai ta rufe ya faruk ganin ko kallon inda suke umman bata yi ba Jiki a sanyaya ya taka zuwa inda take Murya ƙasa-ƙasa yace "Dan Allah umma ƙ kiyi haƙuri, har yanzu na kasa gane kan umma sam" Murmushi tayi kafin tace "bakomai faruk, watarana zata gane ni ba mace me zafi bace, kowa da kalar nashi kishin zaka ga na wani yafi na wani zafi ne kawai" A ranshi yake faɗin "inama ace haka umman tashi ke da sauƙi hali kamar na umma ƙarama" Har umma ƙarama ta wuce be dawo daga ɗan guntun tunanin da ya tafi ba. Beyi niyar shiga part ɗin mama na a yanayin da yake a ciki, amma ganin motar khalid a gidan yasashi nufar sasan kai tsaye Mama ce zaune a palon tasha lulluɓi yayi sallama ya shiga Fuska cike da fara'a mama tace "oyoyo yarona" Murmushi yayi ya ƙarasa kusa da ita ya zauna, cike da zolaya yace "Fita zakiyi ne naga kin sha lulluɓi? daga gani ma sabon mayafi ne wannan" Dariya mama tayi tana kai mishi ranƙwashi, tace "Yaushe ka fara saka wa mutane ido ban sani ba?" daidai nan goggo safiya ta fito itama da nata lulluɓin ta samu waje ta zauna Kallon shi ya maida ga goggo safiya Be san sanda ya kwashe da dariya ba Ya hau raba kallon shi a tsakanin su Be kai ga sake maimaita tambayar shi ma khalid da kamal suka yi sallama duk sun sha shaddaji suna ta zuma ƙamshi Kansu a ƙasa suka ƙaraso ciki, fuska a sake goggo safiya ke musu maraba haɗe da nuna musu waje su zauna Shigowar su khalid yasa ya faruk gane lulluɓin me suka sha Yi yayi kamar ze bar palon ya dake ya basar Ɗaya bayan ɗaya ya miƙa musu hannu suka gaisa, tukun ya koma ya zauna Cike da girmamawa kai a ƙasa khalid da abokin shi kamal suka gaishe su Mama dai tunda tace 'lafia lau, ya mutan gidan" bata sake magana ba, haka zalika ya faruk wayar shi ma ya ciro yaci gaba da danne danne Goggo safiya ce kawai ke jansu da surutu Daga gefe kuma Altine tana ta ukin kai kawo tana jera musu abubuwan motsa baki. Cike da kulawa mama tace "Bisimillan ku fa, ya safiya muje ciki su samu suci" Da sauri khalid yace "a'a mama mun ƙoshi daga gida muke, zamu koma ne ma yanzu" Goggo safiya tace "ai ko ɗan lemon kwasha ko?" Murmushi dukan su sukayi Ɗan ɗaga murya mama tayi tace "Altine, zoki parckaging musu su tafi da shi" Hakan kuwa akayi, Altine ta naɗe komi da komi da suka tashi tafiya suka tafi da shi. Ta ƙofar da Abba ƙ ke shigowa mumtaz tabi ta fita jin sun bar palon Basu wani jima sosai ba suka ƙara gaba ita kuma ta dawo A tunanin ta ya faruk ya fita shine ta shigo ta palo Ido huɗu sukayi da shi Da sauri ta ɗauke kanta, ko gaishe shi bata yi ba ta shige ciki Yana ganin shigowar ta ya tashi ya fita Har mama na faɗin "ka fasa shan kunun ne faruk?" Yana tafiya yace "Zan sha, anjima zanyi wani aiki a palon Abba ƙ, a saka a flask" Goggo safiya tace "uban ƴan'iyayi" Dariya mama tayi tace "ai kuwa yarona bashi da wannan iyayin". Wajen goma saura na dare ya faruk ya gama tas abinda yake Farar jallabiya ya saka se gajeren wando a ciki Laptop da wayoyin shi ya ɗauka tukun ya kulle ɗakin ya wulla keys ɗin cikin aljihun jallabiyar A kan idon uncle Abbas ya faruk ya fito daga sasan mazan gidan Ƙara lafewa yayi yaga ina zeyi, dan yau a babban company yaji sanda Abba ƙarami ke waya yana faɗin wasu mahaukatan daloli da babban companyn ya kawo a iya watan kawai Shine yake ta bin diddigin yarda za'a fitar dasu ko shigo da su Ga mamakin shi yaga ya faruk ya shige part ɗin Abba ƙ memakon ya shiga mota ya fita Kuma a iya sanin shi yasan Abba ƙ ɗin baya cikin gidan So abin yayi confusing shi ƙwarai Haka ya gama tsayuwar shi bega shigowar Abba ƙ ba be kuma ga fitowar ya faruk ba Wayar shi dake ta vibrating tun ɗazu ya ɗaga ya kara a kunne tukun ya juya yayi ciki. Ya faruk na shiga sasan mama, sama yayi inda a nan suke komi da ya shifi dukiyar Abban Wani sirrin da ba kowa ne ya sani ba tunda aka gidan gidan shine a sasan Abban akwai gidan ƙasa a ciki Daga shi se mama se kuma ya faruk suka san da zaman gidan ƙasan nan In zaku tuna sanda Abba ƙarami ya fara gini be kawo kowa ba har seda aka kammala komi, so ba wanda yasan da zaman wannan wajen. Yana shiga palon ya matsar da ƙatuwar kantar dake manne a jikin bango, inda akayi decorating palon da ita To ta bayan kantar ne akwai ƙofar da zata sada ka da gidan ƙasan Ya shige ya aje kayan hannun shi tukun ya fito ya zauna a palon yana jiran akawo mishi kunun shi ya sha kafin ya koma ciki Be jima da zama ba mumtaz ta kawo mishi kunun, tana ajiye wa ta juya da sauri ta fita, ƙaramin tsaki yaja kafin yaja flask ɗin ya zuba, yana sha yana kallo har ya gama tukun ya sake komawa gidan ƙasan. shabiyu ta gota gidan yayi tsit baka jin motsin komi da kowa Mama na kwance ta rasa me ke mata daɗi sam ga bacci yaƙi zuwa ga kuma rashin daɗin zuciya Hijabi ta ɗora akan kayan baccin ta tafito ta nufi palon Abba ƙ Tana shiga ta juya kantar palon ta shige ƙasa Ya faruk na tsaka da aiki yaji takun tafiya, duk a tunanin shi Abba ne Sallamar data yi ne ya kawar mishi da shakku Kuerar kusa da shi taja ta zauna, bata ce komi ba Matsar da tarin takardun gaban shi yayi ya maida hankalin shi gare ta Yace "mama lafia? bakiyi bacci ba? "Na ƙasa bacci faruk, kawai bana jin daɗin jikina, nasan kuma kana nan kana aiki ga Abban ku be dawo ba, Me zan taya ka da shi?" Da yake ba sirrin lissafin su da bata sani ba, kafin ya faruk yayi wayo ma da ita da Abban suke abinsu. Tunda mus'ab yaji muryar mama ya kasa sukuni Zuciyar shi kawai ke azalzala mishi ya fito yaji ɗumin ta Daurewa iya daurewa yayi ta, amma sam ya kasa riƙe kanshi, ji yake kamar ana ingiza shi. Sosai suka duƙufa da aikin shi da maman, kamar daga sama taji an rungumeta ta baya yana faɗin "Nayi kewar ki mama!" Duk da ya faruk ya firgita, amma mama tafi shi shiga mugun ruɗu, tozalin da tayi da mus'ab ba ƙaramin gigitata yayi ba. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg47-48 Duk da daurewar da mama ke ƙoƙarin yi na kar ta yi kuka amma hakan ya gagara Tun da mus'ab ya fara bata kaɗan daga cikin dalilan da yasa ya koma tayuwa a nan Cikin kuka abinda mama ta fara tambayar shi shine Mus'ab a ina kake cin abinci to?" ya faruk najin yambayar da mama tayi wa mus'ab seda tsiga jikin shi ta tashi A ranshi yake faɗin "uwa daban ce!" Mus'ab sake shigewa jikin mama yayi sannan yace " da bakwa nan ina cin su biskit da su goldenmoon, amma kusan kullum dani ake girki a gidan" Jiki a sanyaye ya faruk yace "bama wannan ba, ya akayi kasan da wajen nan?" Da sauri mama ta gyaɗa kai, dan itama tana son jin wannan amsar Kai tsaye yace "a ranar dana fara jin mugun ƙullin da uncle Abbas suke ƙullawa shida waɗanda ban san ko suwaye ba naji yana maimaita "anya akwai gidan ƙasa kuwa a cikin gidan nan malam" Tunda naji haka na fara dube-dube, dan nima ina mamakin wani lokacin da na san Abba na cikin gidan nan, amma lokaci ɗaya inga ban ganshi ba yasa na yarda da hakan kuma na taɓa jin sanda Abba ke waya da ya faruk akan ya same shi a gidan ƙasa" Daga maman har ya faruk ɗi da rayuwar ki data Abbanmu dakuma Ahmad da mumtaz bbas ya kamani ina mishi laɓe shine y Na firgita sosai da naji abinda yn kafe shi da ido sukayi suna sauraren shi Ya ɗora da "A ranar da uncle Aace min, ya bani kwana ɗaya in ɓace a idon shi, inba haka ba ze salwantar ace, kuma mama bazan ɓoye miki ba, in har na kusance ki ko Abba ina jin wani mugun ƙunci da tsananin baƙin ciki a cikin zuciya ta wani lokacin inajin zuciyata na tunzura ni nazo na shaƙeku ko kuma in burma muku wuƙa Tsoron kar hakan ta kasance yasa nayi niyar nesanta kaina da ku Amma ina tunanin kar yazo ya aiwatar da abinda yace alhalin ku baku san da wace irin zuciya yake zaune daku ba Shine na rubuta wasiƙa na ba mumtaz ta baki, dalilina na yin haka shine uncle Abbas da ma wanda duk suke aiwatar da mugun nufin su zasuji na bar gidan Amma a baɗini shine ina nan gidan ƙasan." Karkaɗa kai ya faruk yayi yana mamakin hakan, can yace "a ina ka samu keys to?" murmushi Mus'ab yayi kafin yace "inda kake aje spare keys a nan na ɗauka" Sosai mama ke kuka, ko bakomai wani nauyi da ƙirjinta yayi mata tun lokacin data ga wasiƙar nan taji yana sauka a hankali, nutsuwa na ratsata Kuma ko da wasa batayi mamakin jin sunan uncle Abbas a masu neman ganin bayan su ba Tsoronta ɗaya shine bata san suwaye sauran muƙarraban shi ba. Murya a dishe mama tace "faruk ya kake gani zamuyi wajen sanar da Abba ƙ, ko ba komai yayi taka tsantsan da shi" Murmushi ya faruk yayi, sannan yace " bazamu gaya mishi ba mama, shari'a saɓanin hankali ce, zuba ido kawai zamuyi akan komi, sannan kar mu bari ko Abba ƙ yasan da zaman mus'ab a nan, in da hali ma shiryawa zeyi ya tafi can china ya wakilci Abban kamar yarda nace musu yana can dama gudun magana" kan mus'ab a ƙasa yace "Bazanje ba gaskiya ya faruk, wallahi ko kun saka ni na tafi nasan bazan iya aiwatar da komi ba Ni kaɗai nasan abinda nake ji a raina" Dafe ƙirji mama tayi tana kallon su kafin tace "kodai akwai sihiri a lamarin nan ni zahra'u"? Dan dai kawai ya faruk ya kwantar mata da hankali yace "haba dai, ba wani sihiri mama" Amma deep down him yasan baza'a rasa sihirin ba, Yana cikin wannan tunanin mumtaz ta faɗo mishi a rai, haka nan yaji mummunar faɗuwar gaban da har seda ya dafe zuciyar shi, Yace "In sha Allah nata ma sihirin ne" Mama da mus'ab suka kalle shi jin me yace Ganin kallon tambayar da mama ke masa yasa ya gane a bayyane yayi maganar ba'a zuci ba Ganin sunji yasa ya waske yace "ina nufin mu dage da addu'a, sannan zuwa da safe zanje wajen Alaramma Baffa ya bamu ayoyin karya sihiri mu gwada mu gani" Cikin kuka mama tace "bani da bakin gode maka faruk, Allah yayi maka albarka ya baka mace tagari warda zata zauna dakai da zuciya ɗaya" Lumshe ido yayi ya buɗe sannan yace "amin" a kan laɓɓan shi. Yanzu kullum mama da kanta take fakaitan ido ta kaimishi, ba dan kowa ba se dan itama ta saka ayar tambaya akan Altine Bata da tabbas dan zargi take, shiyasa ma ta kore ta ba, ta dai ci gaba da saka mata idanu. A ɗan tsukinne uncle Abbas ya tsiri tafiya duk da shirye2n biki da aka fara gadan-gadan, duk iya bin diddigi su sun kasa kama koda hujja ɗaya a tattare da shi Haka dai suka watsar da magana amma dai ba su rufe idanun su ba. BAYAN SATI ƊAYA Ya faruk ya shigo gidan kenan ya hango tawowar mumtaz ita da Amal Jira yayi har suka ƙaraso, gaishe shi sukayi har sun gota shi yace "mumtaz kizo ki same ni in kun dawo" Seda ta zumɓura baki kafin tace "to" Duk da ya gani besa ya tanka mata ba, dan yaga kamar da bikin nan ya sake ƙaratowa wani rawar kai ta ƙara, ƙwata kawai yayi ya wuce. Koda su ka dawo ƙin zuwa tayi, har seda ya ɗaga waya ya kira mama yace ta turo mishi ita Shima seda tagama nuƙu-nuƙun ta tukun taje Kallon ta yayi yace "Ki kiyayi ranar da zan miki fyaɗin ƴan kaɗanya wallahi, saboda kin raina mutane shiyasa kike abinda kk ga dama ko?" Bata ce komi ba, ta dai tsaya a saitin ƙofa, inta baci tayi waje. Ƴar ƙaramar farar roba ya miƙa mata, Karɓa tayi tana jujjuyata, Ko kallon ta beyi ba yace "gashi nan, kishi kafin ki kwanta, da safe ma kisha, sannan da daddre ki sha, sha uku zaki mishi" Ɗan kallon shi tayi tukun tace "to shi wannan ɗin mene?" Balla mata harara yayi kafin yace "maganin mutuwa ne" Ta san sarai baƙar magana yayi mata, Juyawa tayi da niyar tafiya taji ya ce "In kin sha domin kanki ne, dan ina jiye maki tsoron ranar da wancan wawan ze gane kina ɗauke-ɗauke, duk da dai bani da tabbacin baki taɓa yi mishi ba" Acikin zuciyar ta taji dirar kalaman ya faruk, duk da gaskiya ya faɗa amma se taji tayi mugun muzanta, da kuma ta tuna agogon khalid data ɗauka taji gaba ɗaya wani tsoro da farga sun lulluɓe ta Ganin ta tsaya tayi shiru ya faruk yace "fita kija min ƙofa ta malama" Seda ta harari gefe tukun taja ta fita rai a ɓace. Tana fita ya sauke ajiyar zuciya, a bayyane yace "Allah ka bata ikon sha". Mumtaz na shiga ɗaki ta aje robar akan mudubi taci gaba da harkokin gaban ta. Tunda bikin ya rage saura sati huɗu, kusa ko wani sasa basa zaune, aunty ce kawai take free, kuma ta ɗan fi shiri da mama akan sauran matan gidan Gaba ɗaya angwayen sun haɗe waje ɗaya sun san juna Wanda hafsa zata aura ya kawo shawarar su haɗe duka events ɗin waje ɗaya Yarda baza'a haɗa ma family gajiya ba Duk da hafsat taaso ta kawo gardama, amma ganin an rinjayeta yasa ta haƙura shima ba da son ranta ba Haka akayi ta shirye-shirye, wanda kaf komi da komi na amaren a hannu Abba ƙarami yake, ya ɗora ya faruk a kan komi da ya dace ayi WATA RANA DA DADDARE BAYAN ISHA Umma babba ta kira ya faruk yazo ya same ta a ɗaki Yana zuwa ya iske ƙannen shi duk sunzo, duk akan maganar bikin Zama yayi bayan ya gama amsa gaisuwar su, harda haɗawa da ƴar tsokanar shi "mata sarakan son biki". Ba yabo ba fallasa mama ta kalle shi tace "Faruk banji kace min komi ba game da hidimar nan" Cike da kulawa yace "kamar me umma?" "Kamar ka ɗebo kuɗi masu kauri ka bani tunda ragamar komi a hannun ka take" Shiru yayi, yama rasa amsar da ze bata ta sake cewa "magana nayi fa bakace komi ba" Tallafe gefen fuskar shi yayi sannan yace "ai maganar ce naga tafi ƙarfi na umma, amanace fa a hannun na kin fi kowa sani, kuma ni a halalin da nake samu daidai gwargwado na baki kusan 4m ki yi wani abun, ni kam ban gane ba gaskiya" Ɓata rai umma tayi tace "nasan ka bani 4m, amma babu wani abu da zasuyi min game da hidimar nan wallahi, ka mance bayan hafsa da Amal harda bilkisu a ciki? Ya faruk da maganar ta fara isarsa yace "na sani umma, duk abunda ya dace ayi wa yaran nan Abba ƙ yayi, ko cokali be barku kun siya ba to me kuma ya rage?" "hmmm" tace, sannan ta ɗora da "Duk baƙar wahalar da yake saka ka ai baka gani kullum cikin goyan bayan shi dana matar shi kake, inda bani na haifeka ba banjin ko kallo na ishe ka a cikin gidan nan ba" Ya maryam tayi karaf tace "haba umma, dan Allah kidena kawo ma zuciyar ki irin wannan abubuwan, be dace ba gaskiya" Tana gama faɗin haka ta bar ɗakin ita sam bata ƙaunar abinda umman keyi, abun na mugun ɓata mata rai Sakin baki tayi tana binta da kallo Ya sabiha da ita ce ke bin ya faruk itama tace "gaskiya ne umma, dan Allah ki rinƙa hanga abubuwa mana, in baki fahimci ya faruk ba waye ze fahimce shi, wallahi yana a tsaka ne, kuma abun alfaharin ki ne ace ɗanki nada amanar da har aka yarda dashi akan maƙuden kuɗaɗe har yake kula da su bako wani shakka, wallahi bama jin daɗin yarda har ita maman kike nuna mata abubuwa marasa daɗi" itama miƙewa tayi kafin ta fice tace "Amma in maganar mu ta ɓata maki rai ki yafe mana" ta fice. ya sabiha na fita, ya faruk ya miƙe shima, cikin ladabi yace "kiyi haƙuri, zan ƙaro miki 2m yanzu in sha Allah" shima ya fice Ɗakin su hafsat ya nufa dan yasan basu wuce can Yana shiga ya iske ya maryam na kuka ya sabiha na bata baki Shima zama yayi sannan yace "uwa uwace dole muyi haƙuri da ita a duk yarda take, sannan muriƙa tausasa kalaman mu a garesu domin dacewa gobe alƙiyama Nasan yarda kuke ji a ranku, to duk mu haɗu muyi haƙuri, muna haƙuri muna nusar da ita a hankula se muga ta sauya" yana gama faɗin haka ya miƙe ya fice. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg49-50 A haka zaka ga kamar umma b tayi laushi Hakance ke kasancewa duk sanda yaran suka mata gyara akan halin ta. Ya faruk be jima da fita ba yayi mata transfer sannan ya shirya ya bar gidan. Sati ɗaya kawai Ahmad da mus'ab sukayi suna sha addu'a nan suka fara jin canji sosai a jikin su Babbar alama kuwa itace yarda yanzu har Ahmad na iya kusan yini a palon mama in har bashi da wajen zuwa Ita da kanta taga canji sosai, wani lokacin ma har surutun shi ya dameta Ta ɓangaren mus'ab ma haka, da bakin shi yace "mama, kwana biyun nan ina jin zuciya ta na sauka, wani nauyi datayi min shima se sauka yakeyi" Murmushi mama tayi tukun tace "ai duk wanda ya riƙe Allah bashi ba taɓewa, shike yi shike sakawa kuma shi ke hanawa, Allah ya warware mana komi cikin sauƙi da salama" "Amin" yace ya ci gaba da aikin shigar da takardun da ya faruk ya bashi yayi tun shekaranjiya". Ta ɓangaren mumtaz kuwa tun da ya faruk ya bata nata maganin ƙin sha tayi, anan kan mudubi ta ajiye shi, Altine kuma data tashi shara ta haɗa da shi ta share Da ya faruk ya tambaye ta tasha maganin? eh kawai tace ta barshi a hakan. Wasa wasa biki nata matsowa, rayukan wasu fes wasu kuma gasunan dai Tun biki na saura wata ɗaya Ya sabiha ta kira umma babba a waya tace "umma su hafsat zasu iya tawowa zuwa jibi, me gyaran jikin na hanya itama" Cike da fara'a umma b tace "aikuwa anjima zan kira Bilkisu ta dawo" Ya sabiha tace "bata nan ne?" "eh, taje wajen mahaifin ta tun shekaranjiya" Cike da ɗan shakku ya sabiha tace "ehnn dama ina ta son in sanar da ke nayi wa mama da mummy magana subar Mumtaz da Najwa su biyo su hafsan suzo tare se ayi musu gyaran duka" Umma nadaga kishingiɗe dama suke wayar, jin abinda ya sabihan tace yasa ta miƙewa zaune Ƙanƙance ido tayi kamar tana ganin ta tace "ohh, seda kika aiwatar tukun kike sanar dan saboda ban isa dake ba?" Cikin rashin jin daɗi sabiha tace "ba haka bane umma, a matsayina na babba a cikin su be dace ace na kira ƴan ɗakin mu ba kawai na bar sauran alhalin dukan su rana ɗaya za'a aurar da su, kuma.." Bata bari ta ɗora ba ta dakatar da ita da sauri tace "Su da kike kumfar baki akansu kika san me iyayen su ke musu ba tare da sun haɗa da su Amal ɗin ba?" Shiru sabiha tayi tana danasanin sanar mata data yi, data sani tayi shiru sedai daga baya taji labarin dasu suka tafi Cikin fushi umma tace "ba magana nake miki ba kikayi banza dani?" Kasa cewa komi tayi sedai tace "kiyi haƙuri ban san bazakiji daɗin hakan ba" Tu zaburar farko da umma b tayi ta fara sababin ta mumtaz ke tsaye jikin ƙofa, Hannun ta riƙe da leda me ɗauke da sauyoyi na maganin sanyi da goggo safiya ta bata ta kai mata ita da mummy Tas ta gama jin me suke faɗa ita da ya sabihar kafin ta ƙwanƙwasa ƙofar A sama umma tace "waye? shigo" a tare Seda mumtaz ta taɓe baki kafin ta tura ƙofar bakin ta ɗauke da sallama ta shiga Umma na kallonta ta sake haɗa fuska Ɗan rissinawa tayi ta gaishe ta, Ta amsa ba yabo ba fallasa Mumtaz bata jira komi ba ta miƙa mata babbar ledar tace "gashi inji goggo safiya, wai ki tafasa da jar kanwa ki ba su Amal su rinƙa sha" A yatsine ta karɓi ledar ta leƙa sannan ta ɗago kai Har mumtaz ta kai ƙofa taji tace "Kuma tace maganin mene?" Ko waigowa mumtaz batayi ba tace "na sanyi" a taƙaice ta fice ta nufi sasan mummy(matar uncle Abbas) Seda tayi knocking me aiki tazo ta buɗe mata Tayi niyar taba me aikin saƙon, jin muryar mummyn tana tamvayar waye yasa ta ƙarasa shiga cikin palon Cike da fara'a mummy ke faɗin "Ah lallai ɓatan hanya kika ne ko?" Murmushi mumtaz tayi ta ɗan ɗosana mazaunan ta a bakin kujera tace "ina wuni mummy" Tace "lafia lau mumtaz" Bayan gaisuwan bata sake cewa komi ba ta miƙa mata ledar hannun ta tace "goggo safiya tace na kawo, a dafa Najwa ta rinƙa sha" Allah Allah take ta bar sasan saboda wani mayen kallo da Tk ke binta da shi Mummyn na ankare da rashin nutsuwar ta, a wayance ta kalli Tk da ido tace "meye haka?" Murmushi kawai yayi ya kashe mata ido ɗaya mumtaz na gama faɗin saƙon ta miƙe tace "se anjima mummy" Cike da fara'a mummy tace "shikenan tunda kinƙi zama, kice mata angode" Tana fita ya Tk yayi wuf ya biyo bayanta da sauri, ko maganar da mummy ke mishi be tsaya yaji ba yayi gaba Sauri kawai take zubawa ta bar wajen kar ya cin mata, Hakan be samu ba seda ya sha gaban ta cike da shaƙiyanci yace "ina fatan kema ana gyaramin ke yarda ya kamata?" Ɗaure fuska tamau tayi ta kewaye shi tayi gaba abinta, a ranta tana faɗin " Ɗan iska, Allah yayi min tsari da kai" Beyi yunƙurin binta ba ganin kallon da Ahmad ke mishi, duk da ya girmi Ahmad amma hakan be hana shi jin ɗan shakka ba, tunda yasan ba Allah acikin kalaman bakin shi. BAYAN KWANA BIYU Ya sabiha da su ya maryam da ƙyar suka shawo kan umma b ta yarda da maganar zuwan mumtaz da najwa. Randa ya dace su tafin, akai-akai da mumtaz ta shirya su tafi, ba abinda ya fito bakin ta se cewa tayi "Wallahi ko waye yazo kanta bw zata je ba, ita bata son gyaran jikin tunda be zama dole ba" Da bayan hannu goggo safiya ta make mata baki, kafin tace "dan kanki tunda kin raina kowa" Mama kam tunda tace "meyasa ba zaki je ba" tace mata "ka kurum" bata sake magana ba, tasan sarai tana da dalilin ƙin zuwan, in akai duba da tun randa sabiha tayi maganar bata musa ba. Haka Amal tayi nacin har tayi fushi ta rabu da ita, Da dai taƙi zuwan, haka zuka tattara sauran suka tafi. Ko da ya sabiha taga ba mumtaz a cikin su ta ɗauki waya ta kirata, bugun duniya taƙi ɗagawa daga baya ma kashe wayar tayi. BAYAN SATI BIYU, ANA SAURA SATI BIYU ƊAURIN AURE Kayan funitures suka iso tun daga turkey ya faruk yayi order bisa ga zaɓin ko wacce a cikin su manyan stores ɗin dake gidan aka buɗe aka shaƙare kayan duka a ciki tukun aka rufe Duka su biyar ɗin saiti ɗai-ɗai Abba b yayi musu, wanda yaga ze ƙara ma ƴarshi shikenan shidai yayi nashi A sanda akayi order kayan mama itama ta yi nata order har sun so sufi wanda akayi musu duka tsada, A ranar da akaje ganin gidajen amaren aka ga gidan mumtaz ɗaki uku ne, nan Mama tayi wa Abba magana ya bada wasu kuɗin aka siya saiti ɗaya. Kamar Najwa da Bilkisu su dama dangin mahaifin su sun masu ɗaya, sun tashi da bibbiyu kenan Ranar da za'a je jere raba tafiyar akayi Umma babba da aunty suka tafi na mumtaz tare da ƴan'uwan mama Mummy tabi wasu daga cikin ƴan'uwan umma b suka tafi na Amal Umma ƙarama tabi wasu suma daga cikin dangin umma b ɗin zuwa gidan hafsa Mama tabi zuwa na Bilkisu, inda kuma dangin mummy duka suka ɗunguwa zuwa ga Najwa. Ganin dukiyar da aka narka ma mumtaz a ɗan madedecin gidan ta hankalin umma babba yayi masifar tashi tunawa data yi bayan saitin da Abba ƙarami yayi musu, Abba babbar ƙananun saiti ya ƙara musu da shi Duk da tana basarwa, amma indai kayi mata farin sani zaka san bata cikin nutsuwar ta Gefe taja bayan ta fakaici idon mutane ta ɗaga waya ta kira ya sabiha tace "Duk yarda za'ayi kar ajera saitin da Abba babba yayi musu, a samo mota a kwashe su a maida store ɗin da aka siya zatayi ciko a zaɓo musu waɗan da suka fi wannan tsada" Cike da mamaki ya sabiha tace "saboda me umma?, har fa mun gama da gidan hafsat mun wuce na Amal" Cikin fushi umma b tace "haka nake so ayi sabiha, nan da awa ɗaya zan kira" Ba ta jira jin komi ba ta tsinka wayar. Haka suka haɗu aka ɓalle gadon aka loda su a mota sannan suka wuce gidan hafsa aka ciro nata suka kama hanyar store ɗin da aka siya kayan Tsabar gasa da umma ta saka a cikin ranta seda ta siya musu wanda yayi shige dana mumtaz tukun hankalin ta ya kwanta, amma fa aljihun ta ya girgiza. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg51-52 Gadan gadan shieye shirye sun fara kankama, Ta ɓangaren mumtaz taƙi yarda da duk wani gyaran jiki da mama Asiya tasa azo ayi mata Abu ɗaya ta yarda da shi shine turaren jiki da ake mata, shima dan tana son ƙamshi ne, irin haɗin nan ne mesaka jiki yayi laushi kamar fatar jariri Wannan bata fashin shi, ko ba'ace tayi ba takan ɗauka tayin Ana sauran kwana goma sakina ta haɗo yanata yanata ta dawo nan gidan, duk da ka kalle ta zaka san akwai abu a ranta Ganin vatayi nasara akan khalid ba yasa tun da ta iso da zaran sun keɓe se ta fara kusar kalid ɗin Jinta kawai mumtaz take, abinda bata sani ba khalid ɗin da bakin shi ya gaya mata tayi hankali da ita. Fitowar su daga ɗaki kenan suka iske ya faruk zaune kusa da mama Cike da damuwa mama ke faɗin "Memakon ka bari se bayan biki se ka tafi faruk? ko dai wani abunne baka sanar dani ba?" Murmushi yayi yace "ko ɗaya mama, nema ne kawai ze fitar dani" Shiru mama tayi, haka kurin take jin wani yanayi mara daɗi a tattare da ita. Sakina har ta kai ƙofa amma mumtaz bata tawo ba juyowata tayi tace "ko mun fasa ne?" Bata san me yasa jin wani iri ba jin ya faruk zeyi tafiya Jiki a sanyaye tace "bamu fasa ba ina zuwa" Da sauri ta haura sama, ɗakin da aka loda layan lefen ta tashiga Bubbuɗe akwatunan tayi ta rasa me zata ɗauka ma a ciki Shiru tayi ta zuba wa kayan ido kafin idanun ta sukai ga akwatin turaruka Bata yi la'akari da cewa turaren mata bane, haka ta ɗakko wata ƴar madedeciyar jaka ta kwashi kusan guda huɗu ta saka a ciki, se lip balm guda biyu Tusa jakar tayi a hijabi bayan ta rurrufe komi tukun ta sakko Bata iske kowa a palon ba se sakina data gama cika Da sauri mumtaz tace "sakina su ya faruk fa?" Seda tayi mata kallo ɗaya tukun tace "gashi a baya na" Tsaki mumtaz taja tayi waje da sauri Tana fita ta iske bala driver na saka jakar shi a mota Ƙarasawa tayi tace "Bala ya faruk fa?" Yanzun nan umma babba tayi kiran shi Jakar hannunta ta miƙa mishi tace "in ya fito ka bashi kace nace Allah ya tsare" Karɓa yayi ya aje a kujerar gaba sannan ya shiga ya kunna motar Sakina na ƙarasowa suka fice zuwa neman head ɗin da ze hau kayan da zata saka ranar kamu. Seda suka isa cikin airpot sannan bala ya miƙa ma ya faruk ledar da mumtaz ta bayar Da alamun tambaya a fuskar shi yace "na mene wannan?" Kai tsaye yace "Mumtaz tace a baka, kuma tace nace Allah ya tsare" Akaro na ba'adadi da yaji faɗuwar gaba, karɓa yayi be tsaya ya buɗe ba ya saka a jakar hannub shi yayi sallama da bala ya shige. Ta duka ɓangarorin kowa shiri yake ba ji ba gani Yau ya kama saura kwana biyar ɗaurin aure, yayin da zasu fara biki daga jibi Duka ƴammatan da suka tafi gidan ya sabiha sun dawo, ko wacce ka kalla zaka ga tana sheƙi da ƙamshin amarci Randa suka dawo da goggo safiya taga yarda suke sheƙi gunin ban sha'awa, aikuwa ta tasa mumtaz tayi ta caccakar ta tana dungure mata kai Ɗaya daga cikin dangin mahaifiyar mama tace "banda abinki ba wanda ze ganta yace ba tare akai musu gyaran ba" Da sauri ta gyaɗa kai tace "ƙarya haram, hasken fata daban sheƙin ta daban, in kika ga yarda suke sheƙi ba zaki ma fara haɗa su da wannan ba" Matan dake palon suna ta kakkare mumtaz, anayi ana dariya Gida sosai ya ɗau harama malam, saura kwana uku ɗaurin aure amma zakayi tunanin ranar ɗaurin auren ce. WASHE GARI Tunda safe wajen goma masu decoration ɗin wajen da za'ayi kamu suka iso Ɓangare ɗaya na gidan aka shirya, kayan gargajiya da ake kamu dasu aka danka gunun ban sha'awa Ta ɓangaren amaren kuwa akan gama sallar azzahar aka fara musu kwalliya Masu kwalliya mutum biyu aka kira dan asamu yin sauri Hafsat aka fara ma, se najwa, se bilkisu se Amal sannan akai ma mumtaz da seda aka kai ruwa rana kamar wacce za'aiwa auren ƙi Ta ɓangaren gidajen angwayen kuwa sun shirya tsab domin halartar taron kamun, wanda a al'ada suke zuwa su kama amarya. Mutum shida mami ta wakilta daga ɓangaren khalid Bayan la'asar kamal da wani abokin khalid suka je ɗakko su, mota biyu sukayo Sosai sukayi shiga ta alfarma ta kuma kece raini wajen biyar saura duka dangin angwayen suka iso, an jima da nisa wajen farawa Masu kiɗin ƙwarya da aka gayyata sun baje kolin su, mata na ta rausayawa Su kansu iyayen amaren ba daga baya ba, karma ku hango shigar da mama tayi, tuni wasu da dama suka fara raina tasu shigar alhalin suma ɗin ba daga baya ba Dangin angwayen ma zuwa suka gabatar da al'ada na feshe feshen turaruka da kuma sauran abubuwa Ana gab da kiran magariba aka tashi, na tafiya suka tafi, wanda kuma dama sunzo se bayan biki kowa ta kama inda ya dace ta zauna. Wajen sha biyu saura na dare da yake gidan biki ne, bama zaka taɓa cewa dare yayi haka ba, shewace shewace da guɗa da kuma hirarra ki ke tashi ta ko wani lungu da saƙo na gidan, uwa uba ga hasken fitulu ta ko'ina mumtaz ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Abba ƙ inda take kyautata zaton maman na nan tunda bata a ɗakin ta Fitowar mama daga wanka kenan taji bugun ƙofar Zuwa tayi ta buɗe, ganin mumtaz a tsaya yasa ta matsa ta bata hanya ta shigo, sannan ta maida ƙofar ta rufe Kan kujera ta wuce ta kwanta bata ce wa maman komi ba Maman ma bata ce ba taci gaba da abinda take Seda ta gama tas tukun ta mayar da hankalin ta ga mumtaz da har ta fara bacci anan kan kujerar Kafe ta da kallo mama tayi, ta jima tana kallon ta kafin ta tashi ta fito kitchen ta nufa, shayi ta haɗa sannan ta ɗauki cake gudu uku da su Altine keta parckaging rabon da za'ayi a gobe wajen walima Saman ta koma, a gefe ta aje shayin tukun ta fara tashin mumtaz "Tashi mumtaz daga ganin ki na san bakici komi ba, tashi kisha tea" Da ƙyar mama ta samu ta tashin, ko rabin kofin bata sha ba tace "mama ya ishe ni" Cike da lallami maman tace "daure ki shanye dai, ko ɗaya ne kici cake ɗin shima" Tusa mata shi tayi tayi har seda ta kusa shanye shi tukun ta rabu da ita, kafin daga baya tace "anan zaki kwana ne?" Gyaɗa kai tayi tace "Mutane sun cika ɗakin ba wajen kwanciya" Bata sake cewa komi ba ta juya tayi kwanciyar ta bacci yayi awon gaba da ita. Mama kam tun ranar da aka fara taruwa ta ƙarasa rasa sukuni gaba ɗaya, Maman sakina tasha ta titsiye ta tana tanbayar ta "lafiyar ta kalau kuwa" Amsa ɗaya ce kodayashe itace "lau" ko kuma tayi murmushi kawai Dan ko an titsiyeta ta faɗi meke damunta ba zata iya kwatantawa ba. Daga baya kawai take alƙanta abin ga kewar mumtaz da zata yi. Daga wannan saƙe-saƙen bata san sanda bacci itama yayi awon gaba da ita ba. WASHE GARI Biyar saura na yamma harabar gidannan a shaƙare take da ƴan'uwa da abokan arziki, wasu sun sha Abayoyi, wasu sun sha jalbab ɗinsu wasu kuma normal hijabai ne a jikin su, Wasun su da niƙab wasun su kuma haka nan SHAIKA ZAINAB MAHMUD ADAM na tsaka da fara muƙaddima amare suka fara shigowa, dukkannin su sunsha tsadaddun Abayoyin su, banda mumtaz da ta naɗe kanta da jar laffaya me tsaɗar gaske Ɗaya bayan ɗaya suka samu waje suka zauna a kujerun gaba-gaba Sosai shaika zainab mahmud Adam tayi shikekken wa'azi game da haƙƙin mace akan mijin ta sosai wa'azin ke shiga dukkan mahalukin dake wajen, bama amaren kaɗai ba, harda waɗan da sun jima a cikin auren dama wanda basu kai ga shiga ba Shaika zainab mahmud ta ɗau lokaci me tsayi kafin ta rufe Ɗaya daga cikin malaman da suka zo tare ta fara rero waƙa cikin harshen larabci, Tana tafi tana waƙen, wasu a ciki da suka iya suka hauyi suma Anata tafi ana waƙen gunin ban sha'awa. Note: waƙe ne da musulunci ya yarda dasu, don't come and attack me 😎 Sosai walimar tayi armashi, aka ƙaru sosai, waɗan da jikin su yayi sanyi saboda tsoratarwan datayi duk suka warware wajen waƙe da kaɗa kai. Shima gab da magriba aka watse, bayan an gabatar da hotuna, ciye ciye da shaye-shaye. WASHE GARI RANA BATA ƘARYA SEDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA!!! Tunbatsar da gidan yayi ba'acewa komi, mata ne ta ko'ina, Tsabar cikar gidan har seda ta kawo da an buɗe makeken gate ɗin gida Runfuna ne da kujeru ta ko'ina, karku mance biki ne na masu shi masu ƙubar susa Matane hawa hawa, waccen wace wannan, wannan wace wancan Kowa kaga fuskar shi zaka san yana cikin murna da farin ciki banda ƴan tsiraru daga ciki Ciki kuwa harda mumtaz da mama da har shi Abba ƙarami da faɗuwar gaba ta same shi a safiyar ɗaurin auren Haka zalika kalid, Daga wayewar gari zuwa yanzu ya ƙira mumtaz a waya yafi a ƙirga, kuma in ya kirata abu ɗaya yake tambayar ta shine "Ba wani abun dai ko" har ma ta gaji da amsashi. Sanda ya faruk ya tafi, se washegari ya buɗe jakar turarukan da mumtaz ta bayar a bashi seda abun yaso bashi dariya da yaga duk turarukan mata ne Ɗaya bayan ɗaya ya hau shinshinar turarukan, yanayi yana lumshe ido tsabar yarda sukayi masa daɗi Yana tsaka da jin daɗin shi zuciyar shi tace "Allah yasa ba satar su tayi ba dai" Nan da na mood ɗin shi ya sauya haɗe da jin wata mummunar faɗuwar gaba. HMMMMM. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg53-54 Tunda garin Allah ya waye mumtaz ke zauna a bedroom ɗin Abba ƙ Ita batayi wanka ba, ba ta kuma da niyar tashi tayin. Kusan tashi uku mama na shigowa ɗakin, a inda ta barta a nan take isketa, Har ita maman tayi wanka ta shirya duk mumtaz na nan zaune, ta muskata nan ta muskuta can A shigowa ta huɗu ne mama tace "Kalli agogo fa mumtaz, sauran duk sunyi shiga ta bibbiyu amma ke ko ɗayar bakiyi ba, ni shin gaya min gaskiya, kodai kina da wata damuwar ne da kika kasa gaya min"? Sadda kanta ƙasa tayi ta kasa cewa komi, se hawaye da suka fara tsere akan kumatun ta Jikin mama dama a sanyaye yake, nan da nan ganin hawayen ɗiyar tata yasa jikin ta ya sake yin sanyi Kayan dake hannunta ta aje sannan ta matsa kusa da ita A hankali ta janyota ta rungume ta, cike da tausayi da kuma ƙauna irin ta uwa ta fara shafa bayanta, a hankali tace "Ki gaya min ko dai kun samu matsala da khalid ɗin ne?" Tana cikin jikin ta ta karkaɗa kai, Maman ta sake cewa "To gaya min menene?" Cikin sheshekar kuka tace "Kawai bana jin daɗin jiki na, kuma gabana na yawan faɗuwa akai-akai" Murmushin yaƙe mama tayi ta ɗago da kanta daga jikin ta Sosai ta fuskance ta tukun tace "Wannan ba wani abu bane mumtaz, duk amarya a ranar auren ta takan fuskanci abubuwa makamancin waɗan nan da kike ji, daurewa ake da zaran an ɗaura auren zakiji kin dena ji" Mumtaz tace "Amma mama jiya a wajen walima seda na tambayi Amal ko itama tanajin hakan tace min a'a" Shiru mama tayi can tace "ai shine nace miki ya danganta, ta yuwu ita ba kalar naki take ji ba, wani daban take ji" Bata sake cewa komi ba, Seda maman ta sauya kaya tukun tace "Maza kije kiyo wanka, ga akwatin kayan ki nan, zan turo me kwalliyar zuwa palo se ki fito tayi maki" Ɓata fuska mumtaz tayi tace "yau ba zanyi kwalliya ba mama" Kai tsaye maman tace "zakiyi, zance ayi maki light one" ta juya ta fice tana amsa call. Gida ta ko'ina ba matsaka tsinke, kowa ka gani ya cike da murna da kuma fara'a Wasu sunyi group ana ta fira wasu kuma suna ta harkokin su Daga can gefe sautin waƙar gwanja ne ke tashi Duk da ba rawa ake ba amma daga gani kasan sautin na kaima kowa Ta ɓangaren amare kuwa ko wacce daga cikin su ta gaji da haɗuwa Babban palo aka ware musu su da ƙawayen su, Sakina ce keta tarbar ƙawayen mumtaz dabata fito ba haryanzu Sauƙinta ɗaya ma ƙawayen nasu ɗaya ne da Amal, amma ko wacce in tazo bataga mumtaz ba se ta tambaya Da dai Amal ta gaji da tambayoyin yasa ta janyo waya tayi dialing no ɗin mumtaz Ana tsaka da mata kwalliya call ɗin Amal ta shigo, Ganin an kusa gamawa yasa bata ɗaga ba dan dama tasan ƙorafi ne. Ta ɓangaren angwace ba'acewa komi, in ka kalli wannan sekace yafi sauran kyau, da ka kalli wani shima se kaga kamar yafi wancan kyau, Khalid na zaune kusa da kamal yana ɗaure igiyar takalmin ƙafar shi Waya kare a kunnen shi yana sauraren mami dake ƙorafin kar ya wuce wajen ɗaurin auren ba tare da sun biyo taga wankan shi ba Murmushi kawai yake zubawa, sannan yace 'na san yarda mamina ke sona da kuma son nayi aure tabbas zata so ta ganni for the last time a matsayin saurayi kafin na zama ango kokuma ince magidanci" Dariya da salati a tare mami ta hau yi kafin tace "naji ka dai zo in ganka" tana gama faɗin haka ta ajiye wayar taci gaba da saka ɗankunne a ɗayan kunnen. Khalid na aje wayar mami abokan shi suka hau tsokanar shi da mummys boy Shidai murmushi kawai ya ke ta faman yi yana jin azalzalar ayi a ɗaura auren nan ko ya samu nutsuwar zucia. ***** A mugun fusace uncle Abbas ya sauke ma Tk mari a duka kumatukan shi Cikin zafin rai yanuna shi da yatsa yace " Har kai ka isa ka nuna min ga yarda zanyi a al'amura na? tun jiya nake lallaɓa ka akan ka bari ina da shiri na amma ka ƙi ji, na faɗa na kuma faɗa mumtaz bata da wani miji da ya wuce kai a yau ɗin nan saboda ina da tabbaci daga majiya me ƙarfi, ohhh shine zakazo kana min barazana da zaka faɗi gaske cewa ni na saka ka danne Abubakar(Abba ƙarami) ka kashe shi, ko kuma ka sanar mu muka saka a tsinke wayar burkin motar shi?" Cikin zafin rai ya ƙara matsawa kusa da TK dake ja da baya ya ɗora da "to da kayi babban kuskure a rayuwar ka, kallo na kawai kake a matsayin mahaifi amma kai kanka kawar da kai ba wani abu me wahala bane a waje na, sakarai shasha" Still a cikin fushi ya juya gefen gadon ɗakin hotel da ya kama saboda cinkoson mata a cikin gida, ya janyo babbar farar leda me ɗauke da farar shadda aciki Wirga mishi ledar yayi kafin yace "kaje ka shirya, kuma karkayi wasa da turaren da na baka ka tabbatar da seka hango Abubakar(Abba ƙ) tukun zaka shafa a hannun ka, ka tabbatar da ko yaya ne hannun ka ya taɓa jikin sa kafin a ɗaura auren, daga nan ka gama naka se kaja gefe kayi kallo" Duk da ya TK yaji marin da uban nashi yayi mishi amma jin wannan bayanin ya wanke mishi zuciya, ko ba komi yanzu ze nuna ma ya faruk yafi kusanci da Abba ƙ da kuma duk wani abu da ya mallaka Seda TK ya ɗauki ledar tukun yace "sorry dad, nima ba da son raina nayi maganar ba" yana gama faɗin haka ya juya ya fice ranshi fess. KHALID Ɗaya da kusan rabi ya shiga cikin gidan nasu inda shima a cike yake danƙam da mutane Tunda ya shigo yaje gaishe gaishe Guɗa ta ko'ina se tashi take Mami nadaga can ta jiyo guɗar mutane, da sauri ta tawo dan ta san be wuce kalid ɗin ne ya shigo Tana zuwa kuwa ta rungume shi haɗe da fashewa da kukan murna da kuma tunowa da mahaifin shi Shi kanshi dauriyace kawai ya ara ya yafa ma kanshi, amma ƙiris da ya fashe da kukan Mami na rungume da shi ta rinƙa jeho mishi addu'oi mutanen kusa da ita suna amsawa Ta jima a haka, kafin kamal ya matso kusa da ita yace "mami time ya kusa wallahi, 2pm ne ɗaurin auren fa" Da ƙyar dai ya zame kanshi daga wajen ta suka ɗunguma zuwa babban masallacin dake manne a jikin gidan amaren. Fotowar mumtaz kenan taji ana ta guɗa a palon ƙasa, kamar ta fasa sakkowa take ji Badan calls ɗin da ƙawayen su keta auno mata ba da bazata sakko ba ISMAT ƴar ƙawar mama da bata jima da isowa ba, dataga alamun juyawa mumtaz zatayi yasa ta taro ta, galla mata harara tayi kafin tace "Halin ki sak da na yaya mardiya wallahi, kuyi ta abu kamar baku da gaskiya" Mumtaz bata ce komi ba, dan tasan musu da ISMAT ɗin Ummu ba riba shiyasa ta lafe a jikin ta suka fara takowa Tana sakkowa daidai nan taga mama ta rungume ya faruk da yasha galleliyar farar shaddar shi da ta amsa sunan ta Yarda yake sheƙi da walwali kwa rantse da Allah shine angon Sakato Mumtaz tayi tana kallon su Sam fara'ar fuskar mama taƙi ɓoyuwa, gefen kumatun shi ta mangara tukun tace "ka kyauta daka dawo yarona, a jiki na naji kamar wani abu da na rasa ya dawo" Dariya yayi yace "wallahi saboda ke na aje komi mamana nazo, daga tafiyata na gane baki so hakan ba, shiyasa ni kuma nace dole nayi suprising ki" Kafin mama ta sake magana ta hango mumtaz, da sauri ta kamo hannun ta Tsakiyar ita da ya faruk ta shiga sannan tace wa me hoto ya ɗauke su Haka camera man ɗin nan yayi ta kashe su da hotuna ISMAT kam wayar ta kunna itama tayi ta kashe su Tajuddeen(me hoton) yace "Hajiya ɗan fita a yi musu au biyu" Fita mama tayi, nan kuma tsakanin ya faruk da mumtaz aka tsaya kallon kallo Ko a jikin Tajuddeen ya matasa kusa da su sannan yace "yallabai matso kayi haka" ya nuna mishi ya dafa ta Ganin zasu ɓata mishi time yasa ya ɗauki hannun ya faruk da kanshi ya ɗora a kafaɗar mumtaz data ɗan sunkuyar da kanta Ganin da sauran space a tsakanin su yasa ISMAT matsowa da sauri ta tura mumtaz jikin ya faruk Da yake Tajuddeen mayen hoto ne tuni ya samu ya hashaska su, kai kace shine mijin Bayan ya gama ɗaukan su, ya faruk ya juya ya fice da sauri dan gaf ake da fara ɗaura auren Ɗago kan da Tajuddeen zeyi yace "Kai ban taɓa ganin angon da sukayi mugun dace da amaryar sa ba irin wannan" Daga mama har mumtaz seda suka ji wata faɗuwar gaba dajin furucin Tajuddeen me hoto Ganin ba wanda ya bashi amsa yace "next, se suwa za'a ɗauka" ISMAT na dariya tace "muje ta can" sannan taja mumtaz suka ƙarasa ficewa zuwa babban palon da amaren da kuma ƙawayen su suke. Tunda ya Tk ya iso wajen yake kutsawa ya samu ya dangane da cikin masallacin Duk inda ya saƙa be yarda Abba ƙ ya ɓace wa idanun shi ba Cunkoso ne sosai a wajen, amma haka ya kurkurɗa har ya dangane da gaba gaba inda wakila duka angwayen ke zaune Can ta gefe ya hango Abba babba da Abba ƙarami se kuma uncle junaid yayan mama Ta ɗayan ɓangaren uncle Abbas da uncle ƙasim se ya faruk a gefen su da kuma dr jamal a kusa da ya faruk Kusa da Abba ƙ ya matsa mutum ɗaya ne a tsakanin su, daga can uncle Abbas na kallon shi ganin ya dangane da Abban yasa shi lumshe idanun yana sauke ajiyar zuciya Cike da kula ya Tk ya sunkuyar da kanshi tukun ya zaro kwalbar turaren daga cikin aljihun shi, da ƙyar ya kwance ledar duk dai yana bi a hankali kar ya tama kayan shi Yana samu ya kwance ledar ya buɗe murfin shima da ƙyar tukun ya tsiyaya turaren a tafun hannun shi, ya riƙe kwalbar da ledar da kuma murfin a hannu ɗaya Tsabar mugunta seda ya wani runtse idanu tukun ya matsa a inda yake tunanin Abba ƙ ɗin na zaune, a wayance ya shafe wannan turare da ya zuba kaf a jikin uncle junaid, wanda a tunanin Tk a jikin Abba ƙ ya saka Buɗe idon da zeyi ya hango Abba ƙ ya matsa can wajen da liman ke sallah yana amsa waya A mugun tsorace ya ja baya, tsautsayi da baya wuce lokacin shi, aikuwa sauran turaren ya kife a jikin ya Tk Tsaf akan idon uncle Abbas da hankalin shi yafi na Tk tashi A mugun tsorace uncle Abbas ya miƙe tsaye, har uncle ƙasim na tambayar sha da "lafia?" Ko amsa be bashi ba, yafara ƙoƙarin cinma Tk dayayi mutuwar tsaye anan inda yake Kafin uncle Abbas ya ƙarasa wajen Tk ya fara jin juyawar kai da kuma ɗarsuwar abu a zuciya Ko tunani na biyu beyi ba ya matsa can kusa da Abba babba Abba Abba na ganin shi yace "ya akayi ne Tk?" Kanshi a ƙasa yace "Inaso ka nemar min auren sakina a hannun mahaifin ta uncle junaid Abba b" Da mamaki Abba b ke kallon shi, bama shi kaɗai ba har sauran dake gewaye a wajen ma sunyi mamaki Uncle junaid na gefe idon shi sun kaɗa sunyi jajir, ga wata muguwar azalzala da yake ji a cikin ranshi Uncle Abbas na ganin an tsaya saurarar Tk ya koma kawai ya zauna, dan yasan tunda tsautsayi yasa har turaren ya taɓa shi to ba makawa se an ɗaura auren Amma inda zaku duba kuga a wani irin yanayi zuciyar shi ke a ciki se kun firgita da mugun baƙin da zaku gani. Wasa-wasa magana ta zama babba, Uncle junaid da kanshi ya amsa da ya ba Tk auren sakina Ya faruk da gayya ya cire sadaki ya biya ma Tk Har aka ɗaura auren Tk da sakina mamaki be bar zukatan kusan kowa dake wajen ba Da gangan ya faruk yace a fara ɗaura na Tk dan ba'a san abinda ubangiji ya ɓoye a ciki ba Aikuwa nasun aka fara ɗaurawa, sannan aka ɗaura na hafsa se Bilkisu sannan Amal se najwa Kafin a ɗaura auren mumtaz ya faruk ya saɓar ya bar wajen cike da ƙunar zuciya da rashin sanin abun yi kuma. ALHAMDULILLAH aure ya ɗauru tsakanin khalid safwan da amaryar sa mumtaZ Abubakar Haka maroƙi yayi ta kururuwar faɗar sunayen angwayen da kuma amaren Khalid da suke tsaye ta can ya lumshe ido haɗe da godiya ga ubangiji jin anɗaura Jikin shi har rawa yake wajen ciro wayar shi yayi dialing no ɗin mumtaz. HMMMMM, AKAWAI FA LUKUTAR MASIFA JAMA'A!!!!!! ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg55-56 Mummy na cikin jama'a taga uncle Abbas ya shigo fuuuu kamar ze tashi sama gaisuwa da mutane ke masa ko kallo basu ishe shi ba yayi ciki Da mamaki mummy tabi bayan shi, sanda ta je har ya kulle ƙofar bedroom ɗin shi Tsaye tayi a bakin ƙofar tana so ta gano abunda ya ɓata wa mijin nata rai har haka A hankali ta fara kiran sunan shi tana ƙwanƙwasa ƙofar ya buɗe Cikin tsananin fushi da hargowa uncle Abbas yace "Wallahi da zaran kin ƙara taɓa ƙofar nan a bakin auren ki!!!" A mugun bazata mummy taji furucin Sakato tayi tana jin yarda bugun zuciyarta ya ƙaru daga jin furucin sa Da yake tasan halinn zuciyar shi, a ranta tace "yanzu haka abinda akayi mishi be taka kara ya karya ba yake wannan ɓacin ran," dawayewa tayi ta ja ƙafafuwanta ta bar wajen ta koma wajen mutanen ta. Tunda uncle Abbas ya kulle kanshi a ɗakin yake buga number malamin nasu, Busy kawai ake ce mishi, amma ya ƙi haƙura ya manne wuta, da ta tsinke ya maida wani, daga ƙarshe ma akace wayar akashe take. Wurgi yayi da wayar sannan ya dafe kanshi da hannu bibbiyu ya kifa goshin shi a jikin bango ya runtse idanu Da ƙarfi ya ce "no! bazeyuwu ba billahillazi, ba zan ɗauki asara ba ban kuma santa ba" the way yake magana da ƙarfi badan hayaniyar ƴan biki ba da babu abinda ze hana a ji shi. Ganin yana neman zarewa a ɗan ƙanƙanin lokaci yasa ya janyo drower gefen gado ya zaro kwalin sigari ya buɗe ya hau kunna musu wuta yana zuƙewa A ƙanƙanin lokaci ya zuƙe kwalin tas sannan ya fara samun ɗan sukuni a ranshi. Amare da ƙawayen su suna a nan anata shewa Amal ta shigo palon da gudu tana haki Kusan kowa kallon ta yake da mamaki Hafsat ce tayi tsalan tace "oh Allah ya kyauta miki kedai, kar ki manta kin dai zama matar aure tun ɗazu" Dariya da shewa sauran suka saka, banda mumtaz data kafe ta da ido Seda Amal ta zauna ta mayar da numfashin gudun data kwasa tace "Gulma da ɗumi ɗumin ta na kwaso yasin" Bata jira amsar su ba ta ɗora da "Ya TK shima ya angonce" Ido a waje Najwa tace "Amma ba ya Tkn da na sani ba ko?" Dariya sosai Amal keyi bayan ta kalli sakina dake ta wani taɓe baki irin ko'ajikin nan nata Cike da son tabbatar da gaskiyar zancen mumtaz tace "a ina aka bashi auren tunda dai naga alama kin koyo gulma kema" Dariyar ta kawai take kwasa, lukutar masifar data hango a fuskokin mutanen gidan kawai ya isheka sanin cewa AKWAI LAUJE A CIKIN NAƊI! Ganin Amal taƙi basu amsar tambayoyin su ne yasa suka shareta dan maganar dama batayi kama da warce za'a yarda da ita ba. A waje kuwa, ana gama ɗaurin aure uncle junaid ya bar wajen saboda yarda yake jin kan shi na jujjuyawa. TK kam ya shiga sahun angwaye bakin nan nashi har kunne yake gaisawa da mutane ana masa murna da sam barka. Wurin a hautsine yake bama ka iya gane inda kowa yake Ɗaurin aure ne ba na mutum ɗaya ko biyu ba Shiyasa cinciridon jama'ar yayi yawa. A haka dai aka rinƙa ragewa ana watsewa Duka angwayen ko wanne tawagar shi sun bishi zuwa reception da suka shirya Sam khalid beso tafiya ba, yaso se yaga fuskar amaryar tashi, bata samu amsa wayar shi ba, ga gidan kuma ba ze shigu ba a yanzu, haka nan ya shige mota kamal yaja suka nufi wajen reception. Ba abinda mama ke maimaitawa se kalmar "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" Da damuwa a fuskar tace "An dena irin wannan auren fa Abban mus'ab, ni a iya zuwa gidan nan da sakina keyi ban taɓa ganin wani abu ya haɗa ta da TK ba in ba gaisuwa ba, amma rana tsaka ace an ɗaura aure" Abba ƙ da shima haryanzu be fita daga mamakin al'amarin ba yace "To tunda mahaifin yarinya yaji ya gani ai mu bamu data cewa zahra'u, in kika ga yarda junaid ya amsa ma Tkn ma zaki sha mamaki wallahi, nasha Abbas zeyi magana shima naga yayi shiru daga baya ma ya bar masallacin gaba ɗaya Shi kuma junaid kafin na gama gaigaisawa da mutane na nemesa na rasa, kuma ya tashi ya kashe wayoyi gaba ɗaya" Ajiyar zuciya mama ta sauke sannan tace "Danƙari, tabbas akwai wani abu a ƙasa wallahi" Goge zufar goshin shi yayi kafin yace "Yanzu abinda nake so dake shine, ki san yarda za'ayi ita hajiya Asiyan kiyi mata magana ta fahinta kafin taji daga sama, daga nan se asan yarda za'a ɓullo wa sakinar itama" Jiki a mace mama tace "toh, bari naje" Ta hauro sama, shi kuma ya fice ta ƙofar sirrin sa. Mama na fitowa sukayi kiciɓus da hajiya Asiya data shigo a ruɗe Da sauri mama ta tarbeta, bata jira komi ba gudun jan hankalin mutane garesu taja ta zuwa bedroom ɗinta da ba kowa Suna shiga ta danna key a ƙofa, kafin mama tace komi hajiya asiya tace "Ga dukkan alamu kinji abinda na jiyo ko hajiya zahra?" Jiki a sanyaye mama ta kamata ta zaunar da ita a gefen gado tace "Ki nutsu muyi magana haj Asiya" Da sauri maman sakina tace "Da gaske ne kenan?" Cike da hikima mama tafara magana "Karki ɗaga hankalin ki akan abinda kika ji pls, Ya junaid ba ze taɓa cutar da ƴarshi ba, ki riƙe zuciyar ki har sanda zakiji daga bakin mijin ki, nasan zaki fi fahimtar zancen" Fashewa da kuka tayi tace "wannan wani irin ƙaddara ne, aure ba shiri ba sanin uwa balle ƴar, yanzu ya zanyi da sakina in taji wannan maganar bayan tana da wanda take so yake sonta, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Miƙewa da sauri mama tayi tace "ki zauna a nan kuma ki share hawayen nan, bari inje in tawo da sakinar" Ta fice da sauri har tana ɗan cin tuntuɓe. Tun bayan shigowar Amal a gujen nan sakina taja can gefe tana amsa call ɗin saurayin ta dake hanyar zuwa Matsawa kusa da ita Amal tayi, seda tayi ƙasa da murya tace "wayar nan da kikeyi fa ta saɓawa addini malama" Ta ja gefe kamar ba ita tayi maganar ba Seda sakina ta gama masa kwatancen gidan ta aje wayar kafin ta waiga inda Amal ke zaune tace "Me kikace uwar ƴan shishshigi?" Banza Amal tayi da ita, duk da taji me tace, amma tayi pretending kamar bata ji ba taci gaba da firar ta Ƙwata sakina tayi ta miƙe da niyar jan mumtaz zuwa sauya kaya mama ta faɗo ɗakin itama Sama-sama ta amsa gaisuwar su kafin ta wurga idon ta can inda sakina ke tsaye tana wa mumtaz magana Da hanzari mama ta ƙarasa can, hannun sakina kawai ta kamo ta janyota suka fito daga palon zuwa can sasan maman. Suna fita Amal ta saki guɗa haɗe da karkaɗa jiki tana juyi Kallon ta mumtaz tayi ta yafitota da hannu Amal na dariya ta matso kusa da mumtaz Kafin mumtaz tayi magana Amal tace "muje mu sauya kaya" Mumtaz ta gane me take nufi, ba musu suka fice daga palon Tacan bayan ɗakin ya faruk Amal taja mumtaz, ido cikin ido Amal ta kalle ta tace "kin san wa ya Tk ya aura?" Tsaki mumtaz taja kafin tace "wai wani ya Tkn kk magana akai?" Cike da gulma Amal tace "Ya Tk na nan gidan, to wallahi na shiga ɗakin umma babba naji tana waya da Abba b yana faɗa mata an ɗaura aure harda na ya Tk da sakinar uncle junaid" Ido waje mumtaz ta dafe ƙirji tace "jakar ubancan kayyasa!! Sakina fa kikace?" Rai fess Amal tace "Rass sakinar da kika sani, kuma daga majiya me ƙarfin gaske naji" Ai mumtaz bata gama tsayawa jin ta ba tayi hanyar sasan su da sauri kamar zata kifa Direct bedroom ɗin mama ta nufa, Murɗa ƙofar tayi tajita gam a rufe Ƙwanƙwasa tayi, daga ciki mama tace "waye?" "nice mama" Sakina ce ta buɗe ƙofar duk tabi ta firgice Mumtaz na shigowa tace "mama wai da gaske ya Tk an ɗaura mishi aure da sakina" Dakatar da ita mama take, saboda sun kasa gaya ma sakinar, amma ina seda ta kai ƙarshen tambayar ta kafin ta tsaya A mugun firgice sakina tace "wai wace sakinar kike nufi?" Shiru mumtaz tayi, ta nemi waje ta zauna ganin ɓallo ruwan datayi. A tsorace sakina ta kalli maman ta dake kuka sannan ta waiga ta kalli mama itama tayi zuru-zuru tace "Dan Allah da gaske ni sakinar ake nufi wai?" Yarda tayi magaanar mama taji wani mugun tausayi ya kamata, Kamota tayi ta zaunar da ita tukun ta runguneta sannan tace "ki kwantar da hankalin ki sakina, Dad ɗin ki kawai muke saurara muji tabbaci amma ba wani abun da zaki ɗaga hankalin ki bane akai" Da ƙarfi ta ture mama ta miƙe tsaye, cikin hargowa da rawar jiki tace "ku faɗa min gaskiya kafin zuciyata ta buga, da gaske ni sakinar ake nufi ko wata ce daban?" gyaɗa kai mama tayi sannan tace "ki nutsu abi komi a hankali sakina" Wage baki tayi ta kurma ihun da seda ya janyo hankulan mutanen dake zaune a palo. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR MAKIRCI KISHI DA ALJANA 👹 WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg57-58 A guje mama da mamar ta suka tare ta ganin zata buga kanta a ƙasa Kafin ta kai ƙasa suka tare ta Cikin kuka maman ta ke jijjiga ta tana kiran sunan ta Mumtaz dake tsaye jiki na ta kerma mama tace "kawo ruwa da sauri suma tayi" Gaba ɗaya mumtaz ta ruɗe ta manta sam akwai toilet a ɗakin ta buɗe ƙofa ta fice a ruɗe zuwa neman ruwa Buɗe ƙofar data yi ne ya ba wasu daga cikin ƴan'uwan maman shigowa ɗakin Ƙanwar mahaifiyar su maman ce tace "me ya same ta ne ni hassu, ina yanzun nan naga gilmawar ta?" Cike da kuka sa kuma ɓacin rai da ya fara bayyana a fuskar mum ɗin sakina ta waiga ta kalli matar tace "inna hassu wallahi in dai junaid yayi sanadiyar rayuwar ƴata sena maka shi a kotu, na san ba wanda ya isa ya gaya mishi yaji, amma ke tunda ƙanwar uwace a wajen shi ƙila yaji taki maganar" Bata ƙarasa ba inna hassu ta dakatar da ita cikin sauri tace "Kiyi ki kaini inda nake son zuwa kin tsaya kina ta mana jaye jayen lukutar masifa" Mama tayi caraf tace "ayi a hankali dan Allah, kunga akwai baƙin kunya a gidan" Inna hassu tace "ku faɗa min me junaidun yayi? Mama tace "aure ya ɗaura mata da ɗan gidan ƙanin megidana" Kusan gaba ɗaya ɗakin aka hau salati da tafa hannuwa Riƙe baki inna hassu tayi tace "shine wai abin ɗaga hankali harda suma?" Sakatoo mum ɗin sakina da mama sukayi suna kallon ta da mamaki mum ɗin sakina tace "aure fa ba shiri, babu jituwa ko wata sanayya tsakanin ta da yaro fa inna hassu" Ɗaya bayan ɗaya inna hassu tace kowa ya fita Kowa ya fita ya rage daga ita se mama se mum ɗin sakina, Se sakinar dake kwance ido rufe bayan ta farfaɗo daga suman wucin gadin data yi Inna hassu ta kalle su duka tace "waye ke da haƙƙin aurar da ƴarsa?" Ba wanda yace komi, da kanta ta ba kanta amsa tace "ina ubane ke da wannan haƙƙin"? Ta ɗora da "mujira shi muji hujjar shi ta yanke wannan hukuncin da yayi ba wai ku zauna ku ɗaga hankalin ku ba itama yarinyar ku ɗaga mata nata. Yanzu abunda za'ayi shine, ke Asiya kamo ƴarki mu tafi can gidan naku ayi komi a can gudun surutun mutane" Ba yarda suka iya haka mum ɗin ta kamo sakina da banda kuka babu abinda takeyi, duk uban kwalliyar da aka ɗauka ta caccaɓe da hawaye da majina, suka yi waje. Kun san gidan biki, nan aka koma maganar da yarda abun ya kasance. Mummy kam data ji batayi mamaki ba, dan ta san a halin mijin ta ze iya aikata komi ba tare da sanin ta ba Da Tkn ya shigo gidan ma rungume ta yayi yana murnar shima ya zama ango Zaunar da shi tayi ta tambaye shi ra'ayin shi ne ko kuwa na iyayen shi ne Da bakin shi yace mata ra'ayin shi ne, harda ƙarin cewa, daga tambayar baban ta yace kawai a ɗaura yanzu. a haka ya barta, ko ajikin ta taci gaba da sabgar jama'ar data gayyata. Tsegumi na can sasan umma babba tunda ita ta fara jin maganar auren Tayi-tayi taji wani abu game da auren a bakin ya faruk, amma yace mata be san komi ba akan lamarin. Inna hassu suna isa gidan suka iske uncle junaid baje yana bacci Da mamaki sakina da mum ɗinta suke kallob shi, Cikin kuka sakina tace "Gaskiya ba lafia ba mum, kalli a yarda dad ke bacci fa" Ita kanta hajiya Asiyan jiki a sanyaye ta matsa kusa da mijin ta, Ƙafar shi ta kama ta jire mishi takalmi sannan ta cire mai hular kanshi, da ƙyar suka haɗu su ukun suka cire mishi malum malum Inna hassu ta kalli haj Asiya tace "anya lafiar shi ƙalau kuwa?" Shiru hajiya asiya tayi, tama rasa wani kalar tunani zatayi. A gidan biki kuwa an ci gaba da shagali, masu janjanin magana nata yi, a haka ma wasu basu san da maganar ba ana ta sha'ani Wajen biyar da rabi na yamma masu ɗaukar amare suka fara isowa Kaf amaren sun bar palon da suke zaune, ko wacce ta koma sasan su Ya sabiha ta sasu Amal yin wanka kafin su Abba babba su ƙaraso Haka Najwa itama ƙanwar mummy ta haɗa mata ruwan wanka da yaji turaruka masu ƙamshi. Mumtaz kuwa tunda aka fitar da sakina jikin ta ya sake yin sanyi, ga azababbiyar faɗuwar gaban da ta ƙaru fiye da na baya Maman kanta dauriya kawai take wajen sallamar mutane dan kalli ɗaya zakai mata kasan duk a firgice take, bata da sukunin zuciya Mumtaz na nan kwance a kan gadon mama ta sake shigowa ɗakin cikin faɗan dabata san daga ina ba tace "yanzun ma se nace kiyi wankan ne?" Murya na rawa tace "a'a mama" Mayafin ta tafara cirewa sannan ta cire sauran kayan Ɗaya daga cikin akwatunan ta da ta haɗa ta buɗe, towel ta ɗauka sannan ta shige toilet tana share hawayen da suka sakko mata. Ta jima a ciki tana kuka kafin tayi wankan ta fito Mai kawai ta shafa, se kayan ƙamshi, amma ko kwalli babu a idon ta Wannan karon blue black ɗin atamfar me ratsin fari a jiki ta saka Masha Allah, sosai ta fito a cikin ɗinki tayi ɗass abinta shigar ta dace da kalar fatar ta ƙwarai. Buɗe jakar da ƴankunnaye ta ke aciki tayi har ta ɗauki ƴan kunne masu kyau zata saka ta fasa, ƙananun barima ta ɗauka ta manna a kunnen ta, har zata rufe jakar ta hango wannan ɗan abin hannun da ta sata ta, da sauri ta kai hannu ta ɗauke shi ta saka a hannun damanta, first time da ta saka abun hannun kenan, shiru tayi ta tsaya tana kallon yarda ya dace da hannun ta da kuma shigar data yi Haka kawai ta tsinci kanta da yin murmushi. Maida komi tayi ta rufe bayan ta cire sabon farin hijabi ƙar daga cikin kayan Sassauke akwatunan tayi ƙasa, tukun ta haye gefen gadon tayi kwanciyar ta. Gab da magariba su Abba b suka sallami ƴaƴan nasu bayan doguwar nasiha da suka sha Tun ana jiran uncle Abbas har suka gaji suka sallami yaran . Tabbas gida yana da daɗi, koda kai kaji kana son auren, amma ranar tafiya gidan miji se an ɗaure gaba ɗayan su kuka suke, kar ma kuzo kuga mumtaz, duk irin dauriya da kawar da kai irin na Abba ƙ, kasa daurewa yayi, be bari an gama ba ya bar palon Mama kam dama ko da aka kira ta ƙin zuwa tayi, da goggon safiya ta dameta se cewa tayi "ai ni na gama mata faɗa, duk abinda taga inayi tayi shi bazata taɓa taɓewa ba" Ba yarda goggo safiya ta iya, haka ta rabu da ita. Ya faruk na cikin RANGE ROVER shi ƴar yayi, gab da babban palon, Ko wacce an riƙota fuskar ta a rufe zuwa wajen motar Duk da ba da son ranshi ze kaisu gidajen nasu ba ya sakko yace "Iya su biyar ɗin zan ɗauka, ko wacce ta shiga wata motar" Goggo safiya tayu caraf tace, "a ina ka taɓa ji amare sun tafi ba ƴan rakiya?" Fuska ba yabo ba fallasa yace "bance kar kuje ba ai, ina nufin motar bazata ɗauke ku ku duka ba" Uncle ƙasim ya ƙaraso yace "su shiga mu gani" Hafsat ta fara shiga, se najwa, sannan bilkisu, se Amal, kujerar Bayan ta cika, uncle ƙasim ya rufe musu ƙofar sannan ya buɗe ƙofar gaba yace "zo ki shiga nan mumtaz" tana shiga yace "matsa" sannan yace "ya safiya shiga" ta shige tukun ya rufe ƙofar. Tun kafin dama a fito da amaren, ƙawar ko wacce tabi motocin angon ƙawar ta Haka dangi ma, wasu suce can zasu wasu suce nan zasu Haka angwayen suka kwashe su tas Tun farko sun san dama daga gida za'akai musu amaren nasu. Ya faruk ya daidaita motar akan titi tukun ya kalli goggo safiya yace "gidan wa za'afara zuwa"? Tana kallon hanya tace "a fara kai babba se ƙaramar ta zama ta ƙarshe" Mumtaz najin haka ta sake lafewa a jikin goggo safiya tana sauke ajiyar zuciya, tun jiya dama take roƙonta kar a fara kaita, kuma a al'adance in biki ya haɗe haka, ƙarama ake fara kaiwa sannan babba. Hakan kuwa akayi, hafsat naji na gani aka fara kaita, Sannan bilkisu Gidan najwa da Amal ba nisa tsakani, se anje gidan najwa kafin na Amal, Nan ma seda aka kai najwan tukun aka zagaya da Amal, rungume juna suka yi da mumtaz suna ta kuka, da ƙyar aka raba su tukun aka wuce da mumtaz Kukan da mumrtaz keyi a yanzu yafi na ɗazu Gaba ɗaya ya faruk na neman rasa nutsuwar shi A cikin zuciyar shi yake jin kukan ta Jiki a mace ya kai hannun shi jikin radion motar ya kunna karatun ALARAMMA AHMAD SULEIMAN wanda yake karanta suratul mulk Tun sautin kukan na tashi da ƙarfi har ya koma yayi ƙasa sosai Shi kanshi karatun ya saka shi nutsuwa ƙwarai Yarda suke tafiyar har yaso bawa goggo safiya mamaki Laƙaƙai laƙaƙai haka suke tafia, da na kalla da kyau naga a 40 yake tafiyar Kasa haƙuri goggo safiya tayi tace "wannan tafiya haka faruk, kamar baka so mu kai" Se a sannan ya farga da yarda yake tafiyar Duk haushin kanshi ya kama shi Sunyi nisa sosai goggo safiya tace "na mance, gidan sirikanta Za'a fara kaita kafin mu wuce gidan ta". Cike da ƙosawa ya faruk yace "mijin ya kaita da kanshi, ina da abun yi ni kam" Da sauri goggo safiya tace "wallahi baka isa ba, al'adar suce, kuma tunda har suka sanar mana to ba zamuyi ƙaranta ba, dole muje" Rai ɓace ya faruk yace, "nifa ban san gidan ba" Itama rai a ɓace tace "bari na kira yayi maka kwatance" Be sake cewa komi ba, se muryar kalid da yake saurar ta wayar goggon yana musu kwatance. Har ƙofar gidan suka je, a can suka iske mota biyu ɗauke da mutum uku-uku a ciki, ciki harda umma babba suna jiran ƙarasowar su. Suna zuwa suka ɗunguma zuwa ciki inda ahalin mami ke jiran ƙarasowar su Mami da kanta ta tarbi mumtaz da ƴan rakiyar ta har zuwa ciki Tana rungume da mumtaz data lafe ajikin mamin, itama ta taro bayan mami da hannun ta na dama ta riƙe ta A haka suka taka zuwa ciki, ana ta ɗaukar su hotuna, ga guɗa nata tashi ta ko wace kusurwa Da dai mumtaz taji ana ƙoƙarin yaye mata rufin fuskarta ta saka duka hannayenta ta riƙe hijabin ƙam Har seda mami ta aje ta a babban palon gidan, tukun ta kalli su umma babba tace, "marhabun ku zauna bari nazo" Hannun daman ta mumtaz tasa ta taɓo goggo safiya dake gefe, Ɗiyar ƙanwar mami nata ɗaukan hotunan ta, Khalid ya saka ta dama, seda ta ɗauka sosai duk da ba wani ganin fuskar ta ake ba tukun ta fice Ɗakin da sauran take takoma, sannan ta danna ma number khalid ɗin kira Yana ɗagawa tace "duba whatsapp yanzu zan antayo maka pic ɗin, dan ma taƙi bari muga fuskar ta" Cike da jin daɗi khalid yace "Thank you, yanzu kuwa zan duba" Babbar yayar mami da ke zaune kan dadduma tace "muga hotunan" Miƙa mata wayar tayi ta ce "gama gani kafin na zo" Aunty hajara(yayar mami) ta rinƙa duba pics ɗin da ƴar tata ta ɗauka Tana ta scrolling taci karo da hoton da mumtaz ta miƙa hannu ta taɓo goggo safiya Har ta wuce ta dawo da sauri, kafe hannun mumtaz da ido tayi tana kallon abun hannun ta, daidai nan mami ta shigo da sauri cike da annushuwa tace "ya hajara muje mana sun iso fa" Yafito mami da hannu tayi, tace "zo kiga, kodai idona ne kemin bishi-bishi?" Ɗan ranƙwafowa mami tayi ta amshi wayar ta kalli hoton Dariya tayi tace "amaryar ce ai, muje ki ganta a zahiri" Aunty hajara tace "ki kalli hannun ta, kamar abun hannun da inna ta baki ne" Dummmm, haka mami taji gaban ta ya faɗi yin tozali datayi da shi. Zooming hannun tayi da kyau, tana kallo ƙirjin ta na dukan uku-uku, Da sauri ta fice daga ɗakin ta nufi nata, itama aunty hajarar da sauri ta bita a baya tana ƙwala mata kira, Tana shiga ta janyo laptop ɗin ta ta hau binciko videon data yi mushi ajiya me kyau Tare da aunty hajara suka kalli ɗan gutun videon da fuskar mumtaz ce ɓaro ɓaro Tsayar da videon tayi, a tare suka nufi palon da aka sauke su Fuska ba yabo ba fallasa aunty hajara tayi musu sannu da zuwa ta tsallake su ta nufi mumtaz dake ƙudindine a hijabi Su goggo safiya sun sha duk a cikin al'adar su ne hakan Ido suka zuba wa aunty hajara data ɗaga hijabin mumtaz fuskarta ta bayyana ma kowa. BA LALE KU JINI GOBE BA, SHIYASA NAYI PAGES BIYU ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg59-60 Aunty hajara na buɗe fuskar mumtaz ta waiga ta kalli mami dake tsaye a bakin ƙofar palon hannayen ta harɗe a ƙirji Da ido tayi mata alamar itace Gyaɗa kai mami tayi ta juya ta fice Gaba ɗaya ranta a mugun ɓace, Fuska ba yabo ba fallasa aunty hajara tace "kuyi sallah se ku ci abinci muna zuwa" Goggo safiya tayi caraf tace "a'a tafiya mu kam zamuyi, anan zamu bar muku ita ko kuwa zamu dangane ta ga ɗakin ta?" Ɗan taɓe baki aunty hajara tayi kafin tace "ku jira ku wuce da ita muna zuwa" Gaba ɗayan su jikin su yayi sanyi ganin yarda fara'ar su ta ɗauke lokaci ƙanƙani ta koma yaƙe Farat ɗaya umma babba ta fara hasashen akwai matsala tsabar ƙwarewarta asa ido Suna nan a zaune babu wanda a cikin su yayi yunƙurin yin sallar balle har su taɓa kayan ciye-ciyen da aka jera musu Mumtaz kam kanta na a cikin hijabi, gaba ɗaya ta nemi nutsuwarta ta rasa, tsananin faɗuwar gaban datake ji ya zarce na ko wani lokaci gaba ɗaya ra kasa sukuni. Aunty hajara da wata ƙanwar su suka iske mami a a ɗaki ta haɗa goshin ta da bango Idon nan nata ya kaɗa yayi jajir Kallon su kawai tayi tama kasa cewa komi Amma kallo ɗaya zakai mata ka gane tana cikin tsananin ɓacin rai Dafa kafaɗar ta aunty hajara tayi tace "Meye mafita?" Cikin karayar zuciya tace "ban sani ba aunty hajara, gaba ɗaya tsanar yarinyar ta gama rufe ni, banji ko ta zauna da khalid zanso ta ba, kuma ba zan taɓa sakin jiki da ita a cikin zuri'ata ba" Gyaɗa kai aunty hajara tayi, tana ƙara jinjina wannan al"amari a cikin ranta Can mami ta sake faɗin "Ɗa ɗaya tilo da Allah ya bani nake saka ran samun zuriya me yawa daga tsatson shi kuma ya jarbce shi da auren ɓarauniya, wasu kalar ƴaƴa zata haifa mishi kenan ni ƴasu?" Ta fashe da kuka tana sake hango yarda mumtaz ta ɗauki abin hannun nan Cike da jimami aunty hajara tace "dole khalid ya san wa ya aura gaskia, kuma tun farko inda ansan haka halin ta yake bazamu tama yarda ya aure ta ba, kuma in kika kalli yarinyar bazaki taɓa cewa zata aikata ba" Zama mami tayi haɗe da dialing no ɗin khalid Ringing biyu ya ɗaga, Kafin yayi magana tace "kazo yanzun nan ka same ni" Har ya buɗe vaki yace "lafia mami?" yaji ta tsinka Da ɗan mamaki a fuskar shi ya kalli kamal yace "Muje, mami na kira na" Suna a mota dama, daga inda suke zuwa gidan ba wani tazara, cikin minti biyar suka ƙarasa ƙofar gidan Gab da ze shiga gidan ya faruk yayi mishi fitila Dawowa khalid yayi, saitin ƙofar ya tsaya, A hankali ya faruk ya sauke glass Cike da fara'a khalid ya miƙa mishi hannu suka gaisa, sannan ya faruk yace "In ka shiga kace musu muna jira fa suyi sauri" Still da fara'ar shi yace "yanzu kuwa, ai yakamata ace sun gama komi zuwa yanzu, ina zuwa" ya juya zuwa cikin gidan. Direct ɗakin mami ya nufa, yana shiga yagan su wani iri Da fara'ar shi ya shiga, amma ganin yanayin da mamin shi ke a ciki yasa jikin shi yin sanyi Jiki a mace ya samu waje ya zauna haɗe da faɗin "me ya faru mami?" Ganin shi da mami tayi yasa idanun ta sake cikowa da ƙwalla dan bata so yaji kalar ɓacin ran da take ji a yanzu, kuma abu ne da bazata taɓa iya ɓoye mishi ba sam Cikin ƙagara sa kuma tsoro da yafara kama shi yace "Dan Allah ku faɗa min meke faruwa, na fara jin tsoro wallahi" Kasa magana kowa yayi, se can mami tace "Ina zuwa" ta tashi ta fice Palon da aka aje su mumtaz ta nufa Ciki-ciki tayi sallama, tukun tace "zaku ɗan bani aron yarinyar ku pls" Rassa, haka mumtaz taji a ƙirjin ta, bama ita kaɗai ba har su goggo safiya seda suka ji maganar mami wani banbaraƙwai da ita, ba kara sam a maganar ta Jin kowa yayi shiru ne yasa umma babba tace "Tashi mana mumtaz" ta yunƙura ra kamota kamar da gaske Ganin umma babban zata taso mumtaz yasa mami tace "Da kin zauna hajiya, ita kaɗai muke son gani" Baki sake kowa ke bin mami da kallo, gaba ɗaya ta sauya ba kamar da suka shigo ba, yanzu har wani hare-hare take da kuma maganganu na gadara Cak mumtaz ta tsaya taƙi yarda ta bi mami, gaba ɗaya tsoro ya gama rufar mata Ba ganin fuskar ta take ba, amma ji take kamar ta san muryar kuma ta rasa a inda tasan muryar. Mami har ta kai ƙofa ta waigo jin mumtaz bata biyo ta ba Ganin haka yasa ta dawo da baya tace "wanda suka fi kusanci da ita mutum biyu suzo muje A fili umma babba tace "yau ko mun kawo kanmu gidan iko" Goggo safiya da itama zuciyar ta na gaf, kawai tana basarwa ne ta miƙe tace "muje to" Umma babba tayi tsalan tace "ai ba kyaje ke kaɗai ba yaya safiya, muje na rakaku nima" Suka saka mumtaz a tsakiya suka bi bayan mami da tayi gaba Har cikin bedroom ɗinta taja su Khalid na ganin mumtaz a tsakiyar su goggo safia ya miƙe tsaye, da fara'a yace " sannun ku gaggo, bisimillah ga waje" Ya tashi daga kujerar da yake umma b da goggo safiya suka zauna Ganin an bar mumtaz a tsaye yasa ya janyo mata kujerar gaban mudubi Ganin taƙi zaman, kuma a cikin iyayen nashi ba wanda yayi yunƙurin cewa ta zauna yasa ya rufe idon shi ya kama hannunta ya zaunar da ita, Sannan ya tsaya ta ɗan saitin ta, da gangan ya rinƙa taka mata ƙafa yana mata waiwayi. Jin shuru kowa ya kasa magana yasa goggo safiya faɗin "To mu kin ƙira mu bakuce komi ba ga lokaci na tafiya dare na daɗa yi" juyawa mami tayi ta kalli aunty hajara tayi mata signal da ido ta fara magana Gyaran murya aunty hajara tayi kafin tace " faruk da kai zan fara" Gyara tsayuwa yayi ya fuskance ta da kyau, dan wannan abun sabo ne a idon shi shikam Shiru ta ɗanyi sannan tace "ku gafarce ni akan abinda zan faɗi hajiya, amma gaskiya an ha'inci ɗanmu da ba'a sanar da shi cikekken halin ƴarku ba!" Duuuuuum, haka ƙirjin mumtaz dana khalid da goggo safiya kai harma dana umma babba ya bada wannan sautin a kusan tare Da sauri khalid ya kalli yayar baban nashi yace "Wannan wace irin magana ce aunty"? Goggo safiya ta ƙanƙance idanun ra tace "Me kike nufi da an ha'inci ɗanku??" Gyara zama sosai ta sake yi sannan tace "eh hakan dai nake nufi, an ha'inci ɗanmu, kun san sarai ƴarku na ɗan hali,baku faɗa mana ba, da akazo neman auren ta ai se ku faɗi ba wai ku ɓoye ba, daga baya se anyi abu ta yi halin a inda ze tonu azo ana kai ruwa rana, ana wallahi tallahi" Bama ta kai ƙarshe ba mumtaz ta buɗe fuskar ta tana bin kowa dake palon da kallo har idonta ya sauka akan mami da se a yanzu ta tuna da inda ta santa Goggo safiya da umma babba kuwa a kusan tare suka miƙe tsaye, salati suka hauyi haɗe da kallon aunty hajara da mugun mamaki da al'ajabi Rai a ɓace goggo safiya tace "wannan wani kalar sharri ne daga kawo yarinya? Umma babba tayi caraf tace "bayan sharri harda cin fuska ma wannan ai" Khalid kam jin mugun kalamin bakin auntyn nashi yasa shi ƙamewa a wajen, ido jajir yake kallon mamin shi da sauran, sam ya kasa cewa komi banda rawar leɓe dayake faman yi Jiki a mace mami ta kalli mumtaz da gaba ɗaya bata san a wani kalar yanayi take a ciki ba tace "Ya kike da suna, muga abun hannun ki" Gaba ɗaya kallo ya koma kan mumtaz datake ta muƙumuƙu da hannuwa a cikin hijabi Da sauri ɗayar ƙanwar mamin tace "zata cire ne fa" Tsabar zuciya yasa goggo safiya matsowa gaba mumtaz ta yaye hihabin ta, Aikuwa se gashi tana ƙoƙarin cire abun hannun Khalid na tozali dashi yayi baya baya kamar ze faɗi, Allah ya temakeshi bango yayi mishi waigi da ya sha ƙasa Finciko abin hannun goggo safiya tayi kafin tace "wannan abun kike nufi ko me?" Gyaɗa kai mami tayi, hannu ta miƙa da niyar karɓa ta fasa, can tace "Kaf ƙasar nan ciki da kewayen ta wannan abun hannun ne kawai, ba zaki taɓa samun kalar shi ba, kai ko irin shi banjin zaki samu ba Gaɗon shi naci daga wajen mahaifiya ta, itama daga wajen tata mahaifiyar ta gajeshi, Bama wannan ba, har sanda ƴarku ta saci abin nan ina da videon ta, maganar gaskiya inda na san wannan ce yarinyar da ɗana ze aura bazan taɓa bari ba, ba wai dan yana da muhimmanci a waje na ba, se dan ba zan taɓa bari na haɗa jini da jinin sata ba" Dafe ƙirji umma babba tayi A yayin da goggo safiya kuma ta saki abin hannun a ƙasa tana wa mami kallon tuhuma da kuma tsantsar rashin mutunci Idon mumtaz kam ya gama soyewa, bakin nan ya bushe tsabar rashin isheshshen miyau a bakinta Khalid kam gaba ɗaya ya lula tunanin maganar da sakina ta faɗa mishi akan mumtaz kwanakin baya. Ido jajiri goggo safiya ke kallon videon da mami ke nuna mata Umma babba ta gama yarda da sadaƙarwa, tunda har ga Allah bata yarda ba daga farko seda taga videon tukun Mumtaz na nan zaune idon ta a ƙasa tana kallon abun hannun da goggo safiya ta wurgar Jiki a sanyaye ta duƙa ta ɗauki abin hannun ta matsa har gaban mami ta tsugunna Se a sannan idanun ta suka kawo ruwa, murya na rawa tace "ki gafarce ni mami, kuma ki yafe min, sannan dan Allah ku bani dama ta biyu karki yanke hukunci cikin ɓacin rai, wallahi sata ba halina bane, haka nan na tsinci kaina da kwaɗaituwa da abun mutum in na gani" Wani mari me raɗaɗi goggo safiya ta yarfa mata da ya hanata ƙarasa maganar data faro Cikin tsananin fushi tace "Da gaske bayan wannan ma kin taɓa ɗaukar abun wasu mumtaz?" Kafin tace komi khalid shima cikin tsananin ɓacin rai yace "Munafuka halinta ne wallahi, ni kaina tamin sata amma na kasa yarda cewa itace saboda yardar dana mata, sannan banyi mamakin satar da kike ba tunda dama duk me bin maza bazaka taɓa rasa shi da ƴan ɗauke -ɗauke ba" Ido a waje kowa ke kallon khalid jin abinda yace Ita kanta mumtaz jin maganar khalid ba ƙaramin ƙaraa saka ta wani mawuyacin halin yayi ba Amma kalmar bin maza da yace yasata saurin faɗin "Kar kayi min sharri khalid, eh tabbas nasan ni na ɗauki agogon ka a airport, amma kar ka ƙara da abinda baka da tabbas akai" Kamar ze maketa ya matso, da sauri mami ta riƙe shi, yace "Tunda baki da kunya ai zaki faɗi hakan, kuma in kowa yayi maki ƙarya ina jin jinin ki SAKINA bazata munafurce ki ba"! Mumtaz tace "SAKINA"! Fashewa da kuka khalid yayi ya rungume mami da itama gata nan dai Cikin kuka yace "wallahi mami bayan sata har maza take bi, ƴa'uwar ta musamman takirani ta sanar dani amma ban yarda ba se yanzu, wallahi mami ba zan yarda da rufa-rufar da akayi min ba se na bi kadi na" Goggo safiya da umma babba kam basu da bakin magana tunda har mumtaz ta amsa da bakin ta Kunya kam ta gama saka su a cikin ta, dan ji suke ina ƙasa take su shige Jiki a mace umma babba tayi hanyar ƙofa ta fice, goggo safiya bata da wata mafita itama tabi bayan ta Suka bar mumtaz a ɗakin a tsugunne riƙe da ƙirji. Waigowar da khalid zeyi ya ganta durkushe, a mugun fusace yace "Ki tashi ki bisu kafin su bar gidan nan, dan wallahi bazaki kwana a gidan nan ba" Da sauri mami tace "kull kalid, bana son ka sake furta komi" Da ƙyar mumtaz ta lallaɓa ta miƙe itama ta fice Umma babba cikin ƙarfin hali tace ma sauran mutanen da suka zo tare su taso su tafi Goggo safiya kan waje tayi tana kuka kashirɓan. Ya faruk na hangota ya sakko ganin yarda ta fito a firgice ga kuma kuka Gaban mota ya buɗe mata ta shiga, kafin yace "Halan haka kika barota itama tana ta kukan ko?" Bawan Allah besan abinda ke faruwa ba 🥹 ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg61-62 Kukan goggo safiya yaso ba ya faruk dariya, Yarda ta aza hannuwan ta duka biyu a kanta ka rantse da Allah wata gagarumar mutuwa akayi mata Ganin bata da niyar magana ga kukan dake ƙara yawa yasa shi ficewa a motar, haɗi da hango su umma babba da fitowar su kenan. Ganin jikin umma b a sanyaye itama kamar warce ta yi kuka yace "lafiya dai ko umma" Murmushin takaici tayi tace "da sauki dai" Bata gama rufe baki ba suka ga fitowar mumtaz da gudu tayi hanyar titi Daga cikin mota goggo safiya ta hangota, a guje ta fito itama A ruɗe goggo safiya ke faɗin " ku bita kar tayi wani wajen, faruk ku bita, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! ku bita bata cikin hayyacin ta" Shima a kiɗime yace "wacece me akayi mata" Kwata kwata beyi tunanin mumtaz bace tayi wannan fecewar Umma babba ma a ɗan ruɗe tace "mun shiga uku, muntaz ce fa" Umma b bata kai ga rufe baki ba ya faruk ya kwasa da gudu yabi bayan ta. Kamal abokin khalid dake jiran shi a mota, jin ana a bita mumtaz ce, yayi saurin fitowa ya mara ma ya faruk baya a guje shima. Sauran matan da suka zo tare ɗaya daga cikin su ta kalli ɗaya tace "anya lafia kuwa, akwai dai wani abun a ƙasa nake ji, wannan baza'a ce kukan rabuwa da gida bane gaskiya. Da ƙyar ya faruk ya dafe mumtaz da saura ƙiris mota tabi ta kanta Da wani irin speed ya damƙo ta gam ya fincikota baya Allah yasa me motar ya ankare da yarda ta shiga titin ya taka birki da sauri Ganin fizge-fizgen da take ne yasa ya haɗeta da jikin shi, Shi kanshi jikin shi rawa yake dan ya sadaƙar da me motar nan ya take ta Da ɗan fushi-fushi ya fara mata faɗa yace "Da hankalin ki da komi zaki je ki kashe kanki, inace ke kika kawo mijin kika ce kina so ba dole akayi maki ba? to shine dan ankawo ki kuma bazaki zauna ba se kiyi ta wa mutane hauka?" Ƙanƙame shi tayi ta fashe da wani irin kuka me taɓa zuciya Shuru ya faruk yayi, shi be tafi ba shi kuma be sake ta ba Yarda ta ɓoye kanta a jikin shi yake jin yarda hawayen ta ke taɓa jikin shi yasa jikin shi sake yin sanyi ga matsanaiciyar faɗuwar gaban dake damun shi Tunda kamal ya hango ya faruk rungume da ita ya tsaya, Wayar shi ya ciro ya danna wa kalid kira Wayar tayi ta ringing be ɗaga ba, Shima jikin shi yayi la'asar be ma yarda ya ƙarasa wajen ba ya juya. Hangowa da ya faruk yayi Ganin kowa jiran su yake yasa ya cireta daga jikin shi ya kama hannun ta ya fara janta Tirjewa ta hau yi, taƙi yarda ta sake koda taku ɗaya ne Da mmaki ya faruk ke kallon ta, beyi niyar cewa komi ba jin yarda kanshi ke mugun sara mishi, duk saboda firgicin daya shiga Amma ganin tirjiyar da take yasa ya tsaya yace "Talk to me menene mumtaz?" Cikin kuka tace" na shiga uku ya faruk, wallahi ba da son raina nake sata ba, nima bana so, kuma wallahi bana bin maza" Kalmar farko ta sata data ce ba ƙaramin dukan zuciyar shi tayi ba Ya tsorata ainun, duk da besan me ya faru ba Dan ya kawar da kokwanton shi yace "Nasan ba da son ranki bane ai, nutsu kiyi min bayani yarda zan fahimce ki" Kasa cewa komi tayi taci gaba da kuka kamar ranta ze fita Jin taci gaba da kukan kuma taƙi cewa komi yasa ya jata zuwa inda su goggo safiya da kuma sauran mutanen suke Amma deep down him yasan akwai matsala, ko daga ganin yanayin fitowar umman shi da kuma goggo safiya da kukan ta yayi kala dana mumtaz. Yana ƙarasawa inda ya aje motar shi yace "nan gidan za'a barta ko kuma gidanta zamu?" Murya a dishe goggo safiya tace "ba wannan maganar ai, muje gida kawai kafin mu tara wa kanmu jama'a" Baki sake yace "kamar ya goggo, ban gane ba, kina nufin mu koma da ita gida wai?" Muryar ta bata fita sosai tace "eh muje" kafin ma ta gama rufe baki mumtaz tayi wuf ta shige mota Ƙin shiga mota ya faruk yayi, kusa da umma da ke ƙokarin bude front seat ta zauna ya matsa, da dan tsoro a fuskar shi yace "umma wai menene ke faruwa dan Allah" Taɓe baki umma b tayi sannan tace "ai yau kunya da ƙasƙanci babu kalar wanda bamu gani ba, ni wallahi ko maƙiyi na ba zanso ace an mishi kalar tozartar da ƴarnan tasa akayi mana ba" Tsabar faɗuwar gaban da yake ji sam ta hana shi magana, Kamar wanda beda lakka ya zagaya ya shiga motar A cikin zuciyar shi yake jin sautin kukan ta, be waiga ba, murya na rawa yace "Seda kika bari asirin ki ya tonu ko mumtaz"? Daga umma b har goggo safiya sakin baki sukayi suna raba kallon su a tsakanin su. Ba wanda ya sake cewa komi ya tayar sa mota yaja suka yi gaba Baki a sake kamal yabi motar da kallo, ganin sun tafi da mumtaz, Daga baya ya tuna ƙila gidan ta zasu kai ta kafin su wuce. ***UNCLE ABBAS Tun baccin daya kwashe shi bayan ɗaurin auren sakina, se da akayi sallar magariba ya farka Ganin shi kwance a gida yasa ya sauke ajiyar zuciya haɗe da hamdala, shi duk a tunanin shi mafarki yake Be kai ƙarshen tunanin da yake ba yaji muryar maman sakina bisa kanshi tace "Tunda har ka farka se kazo muji da sakina, gata can jikin ta ya ɗume da zazzaɓi" Da ƙyar ya miƙe zaune, dafe kanshi yayi kafin yace "Zazzaɓi kuma? ko daga gidan bikin ne ta kwaso shi?" Galla mishi harara haj Asiya tayi, ta cika kamar ta fashe dan takaici, tace "Hmm ka gama kewaya-kewayar ka, kana nuna kamar babu abinda ya faru alhalin kasan silar zazzaɓin nata" A ƙasan ranshi yace "da gaske ne kenan ba mafarki nake ba" Hular shi ya ɗauka, se waya sannan makullin mota ya miƙe Kai tsaye hanyar fita yayi, yana tafe yace "Ku jira ni, zanje na samu Abbas yanzun nan" Ƙwata hajiya Asiya tayi ta koma ta zauna ta zabga uban tagumi Fitowar inna hassu kenan daga sallar magrib, itama ta samu gefe ta zauna sannan tace "Fita yayi?" Haj Asiya tace "yaje warware abinda suka haɗa ne, ai kowa yaga abunnan yasan akwai wata a ƙasa, anyi auren so da ƙauna ma ya aka ƙare ballantana auren haɗi" Tana gama faɗin haka ta tashi tayi shigewar ta ɗaki. ****MAMA Tunda aka saka ƙafa aka tafi da mumtaz t shige ɗaki ta kulle kanta, haka nan take son tayi kuka ƙila Allah ya temake ta abinda ya tokare mata maƙogwaro ya wuce. Mama bata fito ɗakin ba seda tayi sallar isha sannan ta sakko akwai ƴan'uwan ta sosai a palon, ana ta fira da yaba ɗakuna Nan mama take ji har suka baro gidan mumtaz ba'akaita ba Ɗaya daga cikin ƴan'uwan maman tace "ƙila mijin ne ze kaita, dan da muka fito naga an rufe gidan ma" Kamar daga sama suka ga faɗowar mumtaz a firgice Dan har tsoro taso basu Ganin yarda kowa ya watso mata idanu, ga kuma palon da yayi tsit kamar ruwa ya cinye su yasa ta haura sama da gudu ta shige ɗakin mama ta danna key Shigowar goggo safiya a hautsine itama ya sake kaɗa hantar cikin mama, nan da nan cikin ta ya ƙulle taji kamar zata zagaya toilet A tsorace mama ta miƙe tsaye tace "Lafia yaya safiya?" Goggo safiya na zama tace "Se alkairi" Gulma kecin kowa dake palon, tambayiyi fal baki, amma sun kasa tambayar ta Zaman goggo safiya kenan ta miƙe tace "muje sama zahra'u" Kasa miƙewa mama tayi, karkarwar da jikin ta keyi kawai ze nuna maka ba ƙaramin tashin hankali take a ciki ba Cike da ƙarfin hali goggo safiya ta temaka mata suka haura saman. ***UMMA B Wallahi ka fitar da kanka acikin lamarin nan, Kuma ba zan zaman babbar banza ba tunda har a gaba na komi ya faru to wallahi babu abinda zan rage se na faɗa wa Abban ku, ai in har nayi shiru da maganar nan na ha'inci kowa. Kan faruk a ƙasa ya ce "naji ki sanarwa da Abban amma dan girman ubangiji bayan shi kar ki bari wani yaji maganar nan daga bakin ki umma" Taɓe baki tayi kafin tace "saboda ga munafuka ko?" Da sauri ya faruk ya ɗaga kanshi yace "subhanallah, Allah ya tsare ni da furta mugayen kalami a gareki umma, kawai dai alfarman hakan nake nema, duk wanda ka rufa ma asiri kaima Allah ze rufa maka a ranar da kaima kake da buƙata" Banza dashi tayi, can tace "buɗeni na fita" Jiki a mace ya saka hannun ya danna lock ɗin motar Har umma b ta saka ƙafarta waje ta waiga ta nuna shi da yatsa tace "wallahi kar naji kar kuma na gani, ko uffan bana so ka tofa" Gyaɗa kai kawai yayi, yana jin tsananin zafi da kuma suya da ƙirjin shi ke mishi. *****MAMA Kuka take me sauti, kuka irin na yaya zanyi, daga wannan se wannan Ta maimaita kalmar sata yafi a ƙirga Tayi kuka tayi kuka har muryarta na neman dishewa Goggo safiya na gefe, bata hanata kukan ba sam, Da barin shi a zuciya babbar matsala ce Mumtaz na daga gefe, itakam idanun ta a bushe suke Da rarrafe ta matso kusa da mama dake zaune dirshen ta mimmiƙar da ƙafafuwan ta a ƙasa Dafa ƙafar ta tayi tace "Mama dan girman Allah ki yafe min, bansan me ke damuna ba nima, tsoro nake ji mama wallahi tsoro nake ji!" Tana maganar jikin ta na rawa kamar mazari Cikin kuka mama ta janyo ƴarta ta rungume ƙam a ƙirjin ta Bata ce komi ba, amma rungumar data yi mata shine ke nuna komin Sunfi minti talatin a haka kafin mama tace "Baki kyauta min ba mumtaz, ni mahaifiyar ki ce, in baki sanar dani halinnda kike a ciki ba wa zaki faɗa ma? inda na sani ba zan taɓa bari ki tozarta ba mumtaz ba zan bari a kai ga haka ba" ta sake fashewa da kuka tace "Allah kana kallo kana gani kana ji ya Allah, bana nufar ɗan kowa da sharri ya ubangiji amma ga ɗiyata a daren amarcin ta an koro min ita saboda wani dalili na bayin ka masu son zuciya da son ganin bayana Ya Allah wannan tozarci ne a gareni da ɗiyata dama ahalina gaba ɗaya, Allah na kawo ƙarar kowa gareka, bani da sani sedaga abinda ka sanar dani ya ubangiji, ka shiga cikin lamarin nan da gaggawa, kabi mani haƙƙin tozarcin nan me muni da aka yi min ya ubangiji, Allah ƙarfi na ya ƙare haka zalika dabara ta taƙare" Kuka yaci ƙarfin ta, seda ta koka sosai kafin tace "Alhamdulillah ya rabbi, kayi mani kuma nagode da ni'imarka" Tunda mama ta fara addu'ar nan ya faruk ke tsaye, bata ganshi ba, amma mumtaz da goggo safiya sunga tsayuwar shi Shi kanshi neman maɓuya yake ya samu ya sauke nauyin da zuciyar shi ta ɗauka A hankali ya ƙaraahe shigowa ciki Kusa da mama ya zauna, se a sannan ta ganshi, da sauri ta saki mumtaz ta kama ya faruk tace "kaji ko? ita kuma sata takeyi, faruk ko iya haka aka barni ai na gama tozarta ko?" yatsun hannun shi ya saka ya goge mata hawayen fuskarta sannan yace "Allah baze taɓa barin iyalan Abba ƙ su tozarta ba mama, haka zalika Allah ba zeyi watsi da wannan roƙa da kika yi mashi ba, an zalunce ku kuma kin kai ƙara wajen wanda shi ya halicci ɓoyo, dan haka ki kwantar da hankalin ki mama, ƙaddara ce kuma ina da yaƙini zamu cinye ta nan kusa" Ajiyar zuciya take saukewa babu abinda take faɗa se "nagode faruk, naji sanyi a raina da na ganka" Waigawa wajen goggo safiya yayi da gaba ɗaya ta wani susuce a lokaci ƙanƙani yace "dole su Abba su san dawowar mumtaz, abinda nake son sani shine sakin ta yayi kokuwa cewa yayi ta dawo gida, dan mu san ya za'a tunkari su Abban da maganar" Murya a dishe tace "ban sani ba wallahi faruk" Mumtaz na lafe a jikin mama idonta a rufe, ya faruk yace "me mijin naki yace, saki ko ki koma gida?" Bata ko kalle shi ba tace "Bansani ba nima" Miƙewa tsaye yayi yace "bani number shi" Mumtaz tace "ban san inda wayar take ba" Da sauri goggo safiya ta buɗe jakar hannun ta ta ɗauko nokiar ta tace "nemo shi a nan, da kanshi ya saka ta" Amsa ya faruk yayi, direct sunan kalid ya nemo, kwashe no ɗin yayi a wayar shi sannan ya miƙa mata ya fice Yana fita mota ya faɗa, har yayi niyar kunna motar ya hango uncle Abbas na tahowa Cike da fara'a yaji yana faɗin " Kin kawo babban albishir wallahi, bari na koma gefe nayi gum muji ta ina maganar zata fasu Ina me tabbatar miki da in har Abubakar(Abba ƙarami) yaji wannan batu se zuciyar shi ta buga, daga nan kuma ai kin san sauran, shi kuma wancan shashashan a daren nan zan sa yazo ya sakar ma junaidu ƴarsa, in huta da tashi barazanar tunda ga babban kamu nan, yarda maganar zata fasu kowa yaji banjin akwai wanda ze sake zuwa neman auren ta ba, zanyi amfani da wannan damar ni in tausasa kaina se in nema wa Tk auren ta ba tare da anzargi komi ba" Lafewa ya faruk ya sake yi, duk dan ya jiyo wacece wannan ke magana da shi Kai tsaye zuciyar shi ta bashi da "umman kace, yo inba ita ba waye yasan da maganar" kan kace me zufa ta lulluɓe faruk da ya fara tsoron abinda ranshi ke gaya mishi. Kasa tada motar yayi yaja seat ɗin baya ya kwanta, yana ta farfasa maganar uncle Abbas dalla dalla. Gyaɗa kai yayi kafin yayi dialing no ɗin khalid, haka tayi ta ringing be ɗaga ba har ta katse Ya faruk be gaji ba ya sake danna mishi kira a karo na biyu Khalid na kwance a ɗakin mamin shi, abun duniya yayi mishi cak ya rasa meke damun shi Cike da tausayi mami tace "dole zaka je gobe ka ɗakko ta, amma tabbas zaka auri macen kirki wanda zata haifa mata nagartattun ƴaƴa Tana gama faɗin haka kiran ya faruk ya sake shigowa Mamin tace "ka daure ka amsa khalid, ko wani bawa fa da kalar tashi jarabawar" Idon shi a rufen yana daga kwance ya janyo wayar, ko number be duba ba ya ɗauka ya buɗe speaker, Daga can ya faruk yayi mishi sallama Da ƙyar kalid ya amsa jin muryar waye Ya faruk beyi fushi ba yace "Naji duk abinda ya faruk khalid, amma yanke hukunci a cikin fushi ba halin mumini na ƙwarai bane, komi yana buƙatar bincike kafin hukunci" Tsaki da ƙarfi khalid yaja sannan yace "malam ka faɗi abinda kayi niya ina da abunyi" Shiru faruk yayi, yana danne zuciyar shi sannan yace "okay, abinda yasa na kira ina so inji shin da wata manufa mumtaz ke zaune a gida? in ba wata manufa to zan dawo maka da ita yanzu dan munfi buƙatar sulhu akan wani abu daban" Da sauri khalid ya miƙe zaune yace "Dalla malam dakata, karma ka kuskura ka dawo da ita ku rubuta ku ajiye se Allah yayi mani sakayya akan ha'intata da akayi, kuma har abada bazan taɓa iya zama da mumtaz ba, NA SAKE TA, NA SAKE TA, NA SAKE TA!!!!!" Salati me ƙarfi mami ta saki haɗe da faɗin "Baka da hankali ne dan ubanka! ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg63-64 Cikin zafin nama ta kashe wayar, ta hau zazzaga mishi bala'i, cikin fushi tace "Maza-maza ka janye sakin nan nace maka" Ido jajir yace "mami wallahi ko na zauna da ita cutar ta zanyi, kuma bana so Allah ya kamani da laifin cutar da wani" Cikin kuka mami tace "su Baffan ka in suka ji abin zeyi muni, dama suna cewa na sangarta ka kalid, yanzu kuma suji labarin ko tarewa da yarinyar baka yi ba kayi mata sakin wulaƙanci, babu wanda zeyi la'akari da ɗan halinta" Da ƙayar yake iya buɗe idon shi tsabar nauyin da kanshi yayi mishi, ya fice a ɗakin Dafata aunty hajara tayi tace "Karki tilasta mishi, addu'ar ki yafi buƙata a yanzu, kuma tunda yace ko sub zauna ze iya cutar da ƴar mutane kinga ba zamu sa ya kai kanshi ga halaka ba, Da kaina zan kira su Baffan nayi musu bayani, gara ɓacin ran lokaci ɗaya akan na har abada" Da kalar wannan kalaman aunty hajara ta kwantar wa da mami hankali Gidan biki kam basu san me ke faruwa ba banda ƴan tsirari. YA FARUK Tunda khalid ya ɗaga wayar shi ya danna record saboda sheda Har ga Allah da ya faruk yaji kalmar kalid ta ƙarshe baze iya fasalta yarda yaji ba Daga sama kawai yaji kalmar beta tunanin hakan cikin sauƙi ba Ta wani ɓangaren kuma beji daɗi ba sam ko dan saboda bakin duniya Ya faruk na tsaka da wannan tunanin kiran Abba babba ya shigo mishi Ba ɓata lokaci ya ɗaga Kan yace komi Abba b yace " Kana ina?" Har yayi niyar cewa yana cikin gida ya fasa,yace "ina wajen dr jamal Abba" Jim kaɗan yayi yace " kaje gida ka ɗakko min Hajiya zahra'u da yaya safiya ku tawo da mumtaz ma" Da mamaki ya faruk yace "ina zan kawo su Abba?" Kai tsaye yace "guest house ɗin Abubakar, kayi maza karka ɓata min lokaci kaima" Huci me zafin gaske ya fesar daga bakin shi Number dr jamal ya kira, yana ɗagawa yace "Be farka ba?" Daga can dr jamal yayi dariya yace "ai na gaya maka se gobe kuma shi da ya buɗe idon shi" "good" ya faruk yace, sannan ya ɗora da "kar ka bari ya gane kaine pls, in da hali ka barshi a motar ya kwana da safen masan yarda zamuyi daga nan" Dr jamal yace "no baza'a barshi a mota ba, tun ɗazu nasa aka shigar da shi ciki, kawai sanda kake da buƙatar shi kayi min magana" Daga haka sukayi sallama. Seda ya sake ɓata time kafin ya fita ya shiga sasan mama, inda ya barsu anan ya iske su Suna ganin shi suka zubo mai ido Goggo safiya tace "Yace a maidata ko?" Basar da tambayar yayi yace "Abba b yace ku shirya na kaiku yana son ganin ku" Tafa hannu goggo safiya ta hau yi haɗe da faɗin "nasan dama tunda akayi komi a gaban uwarka bazata rufa ba se ta fesar ni safiya, nasha zamuyi rufa rufar mu a mayar da ita ba tare da kowa yaji ba" Murya a dishe mama tace "Ba magana bace da zata ɓoyu ba ya safiya, muje kawai komi ze faru da sanin ubangiji" Ƙwale mumtaz tayi kamar me shirin hawa bori Cike da tausayawa ya faruk yace "Tashi mana" Hawayen da take maƙalewa suka sakko murya na rawa tace "tsoro nake ji ya faruk" Da sauri ya runtse idon shi, be yarda ta gane halin dayake a ciki ba, Seda ya juya yace "keep on praying, nothing will happen kinji ko?" Taji shi ne amma bata yarda ba, har ji take a ranta inama tana da layar ɓata, ta ɓace kowa ma ya huta Mama ce kaɗai ta shiga ta ɗauki lulluɓi Tukun ta fito. Baƙi suna ta harkokin gaban su, dukda da ka kalli kowa zaka san akwai tambaya a bakin shi. Mumtaz na gaba mama da goggo safiya baya, Motar tayi tsit baka jin komi Mintuna ba su fi sha biyar ba suka isa guest house ɗin Abba ƙ Mumtaz na fitowa daga motar gaban ta ya hau lugude ganin motar Abban ta data Abba b, uncle ƙasim, ga kuma motar Ahmad a gefe Se ɗayar motar da bata san ko ta waye ba Da sauri ta koma bayan goggo safiya, murya na rawa tace "Na shiga uku, nan ma mutanen aka ƙara tara min" Gam goggo safiya ta riƙeta, ya faruk na gaba mama na biye da shi se su daga baya suka kutsa har cikin palon Dukan su ciki-ciki suka yi sallama inma bakaji da kyau ba balale ka gane sunyi ba kusan palon a cike yake, Abba b, uncle Ƙasim, Amir(me bima TK) Ahmad, Fadil se kuma ALHAJI SULE(Mahaifin su) kowa yayi zuguɗi ran kowa babu daɗi Kan mama a ƙasa ta gaishe da sirikin nata, goggo safiya ma ta gaishe shi Mumtaz bamata da courage ɗin gaisar da kowa, tunda ta lafe kusa da goggo safiya ko ɗaga kanta bata sake ba Waigawa Abba b yayi gaba ba Abba ƙarami a wajen Ya ciro waya ya danna mishi kiraz gab da zata tsinke ya ɗaga Abba babba yace "jiran ka muke" Ko minti ɗaya ba'ayi ba suka jiyo takun saukowar shi daga sama A fakaice mumtaz ta saci kallon Abban nata, sosai gaban ta ya faɗi ganin yarda idanun shi suka yi jajir, sun ɗan kuma tasa alamun wanda yayi kuka dai Yana sakkowa amma idanun shi na kan mumtaz Yana shigowa palon yayi kan mumtaz da bugu, duka yake kaimata tako ina Banda ihu da neman agaji babu abinda take Da sauri ya faruk yayi kan Abba ƙ yana riƙe shi, shima ya samu tsarabar nashi dukan Abba babba na daga zaune yake faɗin "ya isa Abubakar mana" Alhj sule faɗi yake "Abubakar kar ka sake taɓa ta, baka ji ina maka magana" Maganar mahaifin shi ce kawai ta dakatar da shi, yaso yayi mata lilis yarda bazata moru ba sam. Yana huci ya koma ya zauna. Gyaran murya Alhj sule yayi kafin ya buɗe taron da addu'a Nasiha ya fara yiwa mama da Abba ƙ akan muhimmancin haƙuri da kuma ɗaukar ƙaddara, seda ya tabbatar da nasihar ta shigesu kafin yace "Ba wani sauran dawo da maganar data wuce tunda munji komi, Faruku" ya nuno ya faruk da hannu "kace min ka kira shi mijin mumtaz ɗin ko?" Jinjina kai ya faruk yayi ya ciro wayar shi daga aljihu Kunna maganar da sukayi da khalid yayi, Tsit wajen ya sakeyi kowa najin abinda yake faɗa A ƙarshe da ya ce NA SAKETA, har sau uku Alhj sule yace, "Sake kiran shi ya tantance mana, saki nawa yake nufi" Da sauri uncle Abbas yace "Baba ai bama buƙatar ƙarin bayani, sau uku ya furta" Alhj sule yace "a kira shi dai, ta iya yuwuwa ɗaya yayi" Badan ya faruk yaso ba ya sake dialing no ɗin khalid Duk ringing ɗin data yi tana yi ne da faɗuwar gaban shi, bama shi kaɗai ba har uncle Abbas dake ganin ta leƙo ta koma mishi Gab da zata tsinke khalid ya ɗaga Murya ƙasa-ƙasa yace "ehen, inaji?" Seda ya faruk yayi gyaran murya kafin yace "na kira ne naji tabbacin saki nawa kayi wa mumtaz?" Shiru khalid yayi kamar baya kan layi, seda ya faruk yace "kana jina kuwa?" Kai tsaye khalid yace "uku gaba ɗaya" ɗif ya tsinka wayar. Seda wajen ya ɗau shirun mintoci kafin Abba ƙ yace "Good tunda haka kika zaɓar ma kanki, Allah shine shedata ban rageki da komi ba amma kika tashi kika saka kanki a abu mafi ƙasƙanci da har wanda be isa ba yake tozarta mana ahali, to wallahi ba zan zauna inuwa ɗaya dake ba," Da sauri mama ta ɗago kanta ta kalli Abba ƙ da mmaki da kuma tsoro, tasan mutum ne me haƙuri amma in yyi fushi a abu yakan kafe akai. Nan da nan uncle Abbas ya sauya fuska zuwa ta tausayi yace "Hannun ka ba ze taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ba, dole babu yarda zamuyi haka zamu haɗu mu rufa ma junan mu asiri Abubakar, tunda dai babu wata idda akanta ni ina nemar wa TK auren mumtaz" A firgice mama ta ɗago kanta, tana kallon uncle Abbas Haka zalika ya faruk da beyi expecting jin maganar a yanzu ba Karaf uncle ƙasim yace "Gaskiya be kamata ayi hakan ba Baba, karfa ku manta Tk na auren sakina ƴar gidan yayan zahra'u(mama kenan) Be kamata a haɗa mishi mata biyu ba a lokaci ɗaya kuma daɗin daɗawa ƴan'uwan juna, kunga anyi ba'ayi ba kenan, nan mun gyara zumuncin mu can kuma mun haɗa tsiya" Cikin hargowa uncle Abbas yace "to ai ba haramun bane ko malam" Ɗaga musu hannu alhj sule yayi yace "Duk ya isa akira min Tukur ɗin muji ta bakin shi Se asannan ya faruk ya sauke ajiyar zuciya, dan yasan ba yarda za'ayi a samu no ɗin Tk kuwa Kafin ma ayi dialing no ɗin mama tace "Baba ayi mun afuwa abani dama nayi magana" Tacan uncle Abbas na ta aiko mata da harara ta ɓangare ɗaya kuma yana ta danna wa Tk kira amma shiru bata shiga Alhj sule yace "ina jin ki zahra'u" Seda ta kalli Abba ƙ da ya zabga tagumi kanshi a ƙasa kafin tace "ina neman alfarmar ta farko kar ayi mana wannan haɗin ko dan saboda girman zumunci, duk da nasan ba haramun bane, Sannan alfarma ta biyu kuma, INA NEMAN WA YARONA FARUK AUREN MUMTAZ ƊIYAR ALHJ ABUBAKAR BISA WAKILCIN UNCLE ƊIN SA ƘASIM" Da sauri Abba ƙ ya ɗaga kanshi ya kalli mama, idanun shi na ciccikowa da hawaye Alhaj sule kam dariya yanayin yada mama tasa maganar ya bashi, banda kaɗa kai babu abinda yake Uncle ƙasim ma murnar shi na gaf da bayyana, a ranshi yake jinjinawa jarumta irin ta mama Mumtaz kam daskarewa tayi a wajen gaban ta na dukan tara-tara Yayin da goggo safiya ta kasa riƙe kukan ta sam Oga ya faruk kam lumshe ido yayi yana sauraren amsar da Alhj sule ze ba mama Haka Abba babba ma jira yake yaji me baban nasu zece Jin shurun da yayi yasa Abba babba faɗin "Ni ALIYU SULE NA BAMA ƊANKI FARUK AUREN ƳATA MUMTAZ Dariya me haɗe da kuka mama ta saka Da sauri ta janyo wayar ta tace "zan biya sadakin ɗana yanzu" Sosai taba wasu ɗariya Uncle ƙasim yace "zaki iya bayarwa" A take ta saka dubu ɗari biyu cif a asusun bankin uncle ƙasim Uncle ƙasim na faɗin "kuɗi sun shiga" uncle Abbas yayi fuuuu yafice daga palon Alhaji sule dake kallon iyalan nashi cike da jin daɗi yace "Tun da akwai shedu har sama da mutum shida a ɗaura shi a yanzu kawai" Abu kamar wasa ya zama gaske a take!!! Da ƙarfi ya Ahmad yace "Allahu akbar" Mama da ya faruk kusan a tare suka yi sujudushshukur, banada mumtaz data kasa ɗauke idonta ga kowa dake palon. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg65-66 Saɗaf-saɗaf Abba ƙarami ya tashi daga palon yayi sama, Tsabar sauri bema san a bibbiyu yake taka matakalar benen ba Yana shiga ɗaki ya kalli gabas ya kabbara sallah Nafila yayi ta godiya ga Allah, Acikin addu'o'in da yayi yake faɗin "ya Allah ban taɓa tsammanin wannan abu ba, ada munso hakan amma ganin waɗanda mukeyin dan su basu da ra'ayi, haka muka danne zuciyoyin mu muka haƙura, ashe akwai shirin da kayi mana Allah, Allah na gode maka, kacika mana burin mu nida nagartacciyar matata alokacin da muke tunanin an mana tozarci mafi muni a rayuwar mu, Allah ikon ka ne kuma yardar kane ya rabbi, kai kayi mana kuma mun gani, Allah ka ƙara tsira da aminci ga shugabanmu kuma masoyin ka annabi Muhammad" Haka Abba ƙ yayi ta wa ubangiji godiya da wannan sauyi da yayi musu a lokaci ƙanƙani. Mama na ɗagowa daga sujjadar datayi ta rungume ya faruk da shima ɗagowar shi kenan Jin yarda jikin shi ke rawa yasa tayi ƙasa da murya tace "Bi a hankali yarona, kar ka kunna kanka fa" Dariya yayi, a karo na farko da kunyar mama ta kamashi a kaf rayuwar shi Ƙeyar shi ta mangara sannan ta yunƙura ta tashi, har gaban Alhj sule taje ta tsugunna Gwiwowinta a ƙasa haka zalika kanta a ƙasa tace "Nagode Baba, Allah ya ƙara girma, arziki da wadata" Murmushi yayi yace "Amin, Allah kuma yasa ace gara da akayi, ya kaɓe sharri da fitina" Da "amin" ta amsa, sannan ta tashi. Uncle Abbas na fita dama uncle ƙasim yabi bayan shi da sauri ganin abinda yayi be kyauta ba, dan kamar raini ne ace mahaifin su na zaune dan ba'ai mishi abunda yake so ba se ya tashi ya fice Yana fita ya iske shi zaune a mota yana waya cike da tashin hankali a fuskar shi Uncle ƙasim na ƙarasawa wajen yayi saurin datse wayar yaci gaba da muzurai yana wani ɓata rai Jinjina kai kawai uncle ƙasim yayi sannan yace "Yanzu ka kyauta abinda kayi Abbas?, Ai ko baka ɗaga ma kowa ƙafa ba ka ɗaga wa Baba da shine silar zuwan ka duniya" Cikin hargowa uncle Abbas ya fara magana daidai kuma Abba babba da ya faruk sun sako Alhj sule a tsakiya zasu maida shi masaukin shi suka ji yana faɗin "Ai ɗaya bayan ɗaya zan same ku, banda toshewar basira irin taku ai wani kusancin yafi wani, kuma komin lalacewa kusanci na da Abubakar yafi kusanci shi da Aliyu" Cak Alhj sule ya tsaya jin wannan furuci da uncle Abbas yayi Kafin Alhj sule ya magantu, Abba ƙarami dake bayan su yace "ka tafka babban kuskure Abbas, akan abinda be taka kara ya karya ba kake wani tada jijiyoyin wuya haka? To bari kaji abinda baka sani ba, wanda kake cewa kafi kusanci dani akan shi, shi ya fara shan nonon mahaifiyar mu kafin mu musha, haihuwar shi ce kawai inna batayi ba, amma tundaga shayarwa zuwa raino, cin kashi da fitsarin shi duk itace Sannan kuma abinda yayi mahaifiyar Aliyu shi yayi inna in baka sani ba na sanar da kai Kuma wallahi inda inna zataji wannan furucin daga bakin ka tabbas da zaka ga mummunan fushin ta" Waigowa Alhj sule yayi yace "wannan bayanin ma ya ishe shi haka Abubakar, kuma har gobe ina alfahari da jinin Bilkisu da Zainab(Bilkisu itace mahaifiyar Abba babba, zainab kuma mahaifiyar su Abba ƙarami)" Shiru uncle Abbas yayi yana muzurai har su Abba suka bar wajen shi yana nan tsaye. Cike da fargaba mumtaz tace "mama haka ake ɗaurin auren wai?" Daga mama har goggo safiya kwashewa da dariya sukayi Goggo safiya tace "Kinga yardar ubangiji ko?" Gyaɗa kai mumtaz tayi hawaye na sakko mata tace "wallahi kashi na ya bushe in dai da gaske an ɗaura min aure da ya faruk" Sakin baki suka yi suna kallon ta, goggo safiya tayi ƙarfin halin cewa "Kamar ya mumtaz, mudai kiyi shiru kar ki janyo mana wata lukutar masifar bamu jima da fita a wata ba" Mama kan kafe mumtaz tayi da ido tana nazartar ta. Tsaki Ahmad yaja kafin yace "yo ya faruk befi wancan sakaran ba so ba adadi?" Cikin kuka mumtaz tace "To wallahi baku san halin ya faruk ba, ku rubuta ku aje kullum se ya narkeni tunda ba dena ɗauke-ɗauken nayi ba" Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi, harda shi kanshi ya faruk ɗin da dawowar shi kenan daga kai Alhj sule masauki yaji ma kunnen shi. Jiki a saɓule goggo safiya tace "Allah ze rabaki da ita in sha Allah, kema ki daure ki rinƙa kai zuciyar ki nesa dan Allah mumtaz" Shiru mumtaz tayi tana share hawayen fuskar ta, Amma tsoro na nan danƙare a zuciyar ta, bayan tsoro ga tsananin mamakin wai an ɗaura mata aure da ya faruk. Murya ƙasa-ƙasa goggo safia tace "Ni ba kowa nake ji ba se tijararriyar uwar faruk wallahi" Tagumi mama tayi kafin tace "babban damuwa ta da kikace a gaban ta akayi komi a can gidan" can ta nisa tace "mu bar ma Allah kawai, kuma ina fatan zuciyarta tayi sanyi ta karɓi abun da hannu bibbiyu". Ɗan komawa da baya ya faruk yayi, kamar zuwan shi kenan yayi sallama Da sauri mumtaz ta juya baya tana dafe ƙirji jin yarda gaban ta ya yanke ya faɗi Yana lura da actuons ɗinta, basarwa yayi yace "mama ku taso na maida ku gida" Kallon shi mama tayi cike da fara'a tace "su Abban naku fa?" Yace "Alhj ya tsaida su duka" Tashi tayi tace "ku muje to" Ita ta fara fita sannan goggo safiya, se Ahmad dasu fadil Mumtaz kuma ta tsaya neman warin takalimin ta da ya shige ƙarƙashin kujera Duk tabi ta ruɗe jin kowa ya fita se ya faruk da ya rage Daga inda yake tsaye yana hango takalmin, Daburcewar datayi ne ya bashi mamaki Dan ya sake tabbatar da ta ruɗen ne ya matso kusa da ita ya tsaya ta bayanta Da hannu ya zungureta, aikuwa a firgice ta juyo jikin ta na ɗan rawa Da baki ya nuna mata inda takalmin ya shige Da sauri ta janyo shi tayi hanyar fita har tana cin tuntuɓe da ƙafarshi Karkaɗa kai kawai yayi tukun ya bi ya kashe wutar gidan sannan yaja ƙofar ya rufe ya ƙarasa motar Ganin mama zaune a gaba yasa ya ɗab waiwaya baya, can ya hango mumtaz maƙure a gefe Be san sanda murmushi ya suɓuce mishi ba, Duk abinda yake ta gefen ido mama ke kallon shi, Farin cikin da take ji be misaltuwa dan rabon dataji irin haka ta mance. Motar tayi tsit baka jin motsin kowa, dukansu da saƙe-saƙen da suke Sun ɗanyi nisa kaɗan, jin shirun yayi yawa ya faruk ya kunna radio, rabi idon shi na titi rabi kuma yana kan radio Canza radion yayi da bluetooth sannan yayi searching waƙar Naziru "IN RABO YA TSARO DA KAI, KUMA ABUN YA TABBATA DA KAI, RABBI NE YACE SE DA KAI EM SE DA KAI KAWAI SEDA KAI...." har ƙarshe Cikin shauƙi da annushuwa yake bin waƙar duk da a hankali yake bi amma hakan be hana mama jin shi ba Murmushi sam yaƙi barin fuskar ta. Suna zuwa ƙofar gida yace "mama ba zan shiga ba nan zaku sauka akwai inda nake son zuwa" Agogon motar mama ta kalla tukun tace "its late fa faruk" Murnushi yayi tukun yace "Bazan jima ba ai" Ganin mumtaz na son riga kowa fita yasa shi saurin faɗin "Mumtaz tsaya ke ki wuce da wannan" yayi maganar yana wani faskewa Ranƙwashi goggo safiya ta kai mishi haɗe da faɗin "algungumi, kaji dashi dai" ta fice, mama ma na dariya ta fice Suna fita ya saka lock a motar Idin shi na kansu mama har suka shiga gate, sannan ya waigo ya kalle ta Daga sama har ƙasa yake kallon ta, itakam taƙi yarda ko sau ɗaya ta kalle shi, ta takure a waje ɗaya Seda ya gama kallon ta tas tukun yace "Da kin shiga gida ki tabbatar da kin cire waɗan nan kayan jikin naki, ki ɗauki naki na gida ki saka, ko da wasa kar in sake ganin ki da kayan da wancan guntun ya kawo" Mancewa ma tayi da tsoron ta saki baki tana kallon yarda ya faruk yasha mur yake bata umarni Hannu ya kai ya tsokale mata manyan idanunta da sauri ta rufe idon da hannu haɗe da faɗin "wayyo Allah" Murya ƙasa-ƙasa yace "nan gaba ƙwaƙulo daƙwa daƙwan idanuwan zanyi tunda baki iya amsa ni ba sedai ki kafe ni da idanu kamar ansoya tasoyu" Murza idon take, amma hakan be hanata zumɓuro mishi baki ba Murmushi yayi ya kauda idon shi tukun yace "jeki, shine saƙon dama" Ko ƙarasa rufe baki beba tayi wuf ta fice, ki waiwaye batayi ba, tana tafe tana faɗin "daɗin abun ma ai idanun ka sun fi nawa girma" Seda yaga ta shige tukun yaja motar yayi gaba. Wayar shi tayi ringing ya ɗaga yace "on my way" ya sauke yaci gaba da tuƙi. A parking lot na gidan dr jamal yayi parking, direct ciki ya shiga inda ya iske mus'ab da dr jamal na zaune ko wanne da yana ɗauke da mug me ɗauke da coffee a ciki Yana shiga toilet ɗin palon ya shiga ya ɗauro alwala sannan ya fito Anan palon ya kabbara sallar shi, Ya jima yana addu'ar neman sassauci daga wajen ubangiji akan umman shi, haɗe da godiyar kyautar da ya bashi a sanda ya riga da yacire rai gaba ɗaya Seda ya gama tukun ya dawo palon ya zaune haɗe da cire hular kanshi yana faɗin "wash" Cike da damuwa mus'ab yace "kun mayar da mumtaz ɗin ne?" Karkaɗa kai yayi haɗe da kallon dr jamal ya ce "guess what?" Girar shi biyu dr jamal ya ɗaga sannan yace "kasan im not a good a guessing abu, kawai mlm ka gaya mana" Murmushi ya faruk yayi yace "Da gaske nima yau ango ne" A mugun bazata suka ji maganar, sedai basu yarda ba Dr jamal tsaki yaja yace "karo na farko da naji kayi ƙarya kenan wallahi, Halan tsinko matar akeyi a bishiya?" Dariya kawai ya faruk keyi Mus'ab da yasan waye yayan nashi yace "Sunyi galaba akan mu ko mu mukayi ya faruk?" Tashi ya faruk yayi, ya zagaya ta side ɗin mus'ab yace " akoda yaushe Allah na bayan me gaskiya mus'ab, a yau Allah ya mallaka min mumtaz a matsayin matar aure" Da gudu mus'ab ya rungume ya faruk, tsabar murna da yarda yake ji ya hana shi magana, banda "Alhamdulillah, Alhamdulillah" babu abinda yake faɗa, dan ya san babban burin yayan nashi kenan, kuma babban burin iyayen shi. Tasowa dr jamal shima yayi baki buɗe yace "are u for real guy?" Gyaɗa kai ya faruk yayi, shauƙin abun na daɗa tasiri a ranshi. Ɗakin da Tk yake kwance suka nufa Yana nan a kwance kamar yarda suka aje shi Ya faruk yace "Ina ganin ba zamu bari se da safe ba, kawai mu fitar da shi tunda abun yazo da sauƙi" Mus'ab yace "hakane, ina ta ganin calls ɗin uncle Abbas harda na uncle junaid ma, amma ba wanda muka ɗaga daga baya ma kashe wayar muka yi" Murmushi ya faruk yayi yace "su ya shafa wannan, mu saka shi a mota mu maida shi" Su ukun suka cinciɓe shi sukayi waje da shi A bayan motar da mus'ab ke basaja da ita aka saka shi ya faruk ya shiga tashi motar, mus'ab da dr jamal suka shiga motar mus'ab ɗin suka fice kusan a tare. a inda suka ɗaukeshi nan suka koma, mus'ab ya ciro key ɗin motar TK ya buɗe, sannan suka kamo shi suka saka shi a motar shi Dr jamal yayi mishi allurar da zata dawo da shi hankalin shi cikin minti biyar, sannan suka bar wajen gaba ɗaya. ****** Tunda su mama suka shiga gida goggo safiya ke rafka guɗa a tsakar gida Irin guɗar nan me shiga kai har ƙwaƙwalwa Da kusan gudu mama ta shige sasan ta dan ta san jan maganane goggo safiyar ke ƙoƙarin yi Jama'ar gida jin guɗar taƙi ƙarewa yasa aka hau firfitowa, abinka dama da gida na a cike da ƴan biki Dangi su goggo safiyar ma tun kafin suji komi suka hau tayata da guɗar Umma babba na ɗaka tana ba su ya sabiha labarin abinda ya faru a gidan su kalid suka jiyo hayaniya gidan gaba ɗaya ya ƙaure da iface iface da guɗoɗi Su ya sabiha hankalin su a matuƙar tashe jin mummunan labari daga mahaifiyar tasu suka mimmiƙe, dan a yarda suke jiyowa kamar ma faɗa ne aje a wajen Ya maryam ce ta banko ɗakin da gudu, ta ƙanƙame umma babba tace "Allah mun gode maka, Allah ya kiyashe mu jin kunya duniya da lahira, ga goggo safiya can na faɗin an ɗaura auren ya faruk da mumtaz yanzu"! Wata wawiyar hankaɗa umma b tayi ma ya maryam har seda ta kusa wuntsilawa, a mugun firgice tace "Na shiga uku na Nabila, waye ke shirin ganin bayana"! Tayi hanyar fita da gudu! ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg67-68 Cikin zafin nama ya sabiha ta tare umma babba da gaba ɗaya idanun ta sun rufe tsabar tashin hankali Jiki na rawa ya sabiha tace "Dan girman Allah umma ki nutsu kar kije kiyi abinda zaki zo kina nadama daga baya" Ya maryam itama tace "ga gida bamu kaɗai ba, baka san waye ze tafi da kai a baki ba umma" Ya fa'iza kam na ganin umman zata fice tayi wuf ta fice ta rufe main ƙofar palon da key tayi gaba. Cikin tsananin fushi umma b tace "sakeni sabiha kafin kiji mugun furuci daga bakina wallahi" A hankali jiki a saɓule suka ja baya suka zuba mata ido Yarda ta fito da zafin ta tana zuwa ƙofar palon taja tajita a garƙame Kallon ƙofar tayi taga ta waje aka rufe Fuuu ta koma ciki, a yarda ta barsu a haka ta iske su, zazzare musu ido tayi ta hau nuna su da yatsa tace "ubanwaye a cikin ku yasa aka rufe ƙofar?" Kusan a tare sabiha da maryam suka sauke ajiyar zuciya, sanin aikin fa'iza ne Cikin tsawa umma tace "ba magana nake muku ba wai" Nan ma a tare suka haɗa baki wajen faɗin "bamu sani ba umma" Yaraf ta faɗa a kan kujera, tama rasa me zatayi, can ta zabura tace "Ku miƙo man wayata" Sanin zata nemi wayar yasa suka kasheta suka ɓoye" Kamar da gaske suka hau neman wayar Sama ko ƙasa ba'a ganta ba, duk suka yi tsuru-tsuru ganin kallon da umman ke musu Seda ta gama kallon su tsaf tukun tace "na gama gane rainin hankalin ku, to ku rubuta ku ajiye ba zan taɓa yarda da wannan abun da akayi man ba, dama sun mallake man ɗanne dan sun san abinda suka shirya ko?" Da sauri ya sabiha tace "karkice haka umma, dan girman Allah ki nutsu kar ki kawo wani abu can da be da alaƙa da wannan" Da ƙarfi umma b tace "ku dakata man dan ubanku, na lura kallon mahaukaciya kuke man a gidan nan, to bari kuji na jima da sanin faruk yana son mumtaz shiyasa tun wuri nayi ma tufkar hanci na gargaɗe shi, da yake munafuki ne shima se yayi man wasa da hankali ya nuna min bema san wacece mumtaz ba da har ze so ta ohhh shine yanzu dan su nuna min ban isa ba yasa aka tafi can aka gama ƙulle-ƙullen tukun zanji, banma ji daga matushiya me ƙarfi ba se a saƙar gari" Gefe da gefen ta sabiha da maryam suka zauna Cike da lallami suka fara nusar da umma b da gaba ɗaya ta gama haɗa zufa tsabar bala'i Ya sabiha tace "Umma kar muyi ma ubangiji shishshigi a cikin ikon sa fa, wallahi tsanani akan abunda akwai rabo yakan kai mutum ga kushewar sa fa" Wannan maganar da ya sabiha tayi ta sake tunzira umma b, Dole suka haƙura suka rabu da ita, haka tayi ta surfa bala'i a cikin ɗaki, su kuma suna gefe sun zuba wa sarautar Allah ido Amma fa sunyi babakere sun hanata fita ko nan da can. ****Da mamaki Tk ke kallon gari yarda yayi duhu Da sauri ya janyo wayar shi dake yashe a kusa da shi ya danna yaga har sha biyu na dare ta kusa Da mamaki yace "Ahh gari da sauran haske fa na tsaya a wajen nan, To bacci nayi ko me? Bashi da me bashi wannan amsar, Missed calls ɗin uncle Abbas dana uncle junaid har ma dana mummyn shi da ya gani tururu a wayar shi ƙara bashi mamaki Da sauri yayi dialing no ɗin uncle Abbas, Kamar jira yake, ringing ɗaya tayi ya ɗaga, cike da zafin rai uncle Abbas ya fara surfa mashi banbamin bala'i, shiru Tk yayi yana sauraron shi yana wani ɓata rai Daga can uncle Abbas yace "To gidan ubanwa kaje ka ajiye wayar ina ta neman ka, kai duk abinda aka haɗa da kai suka ba mutane matsala, kazo hotel ɗin da nake ka same ni yanzun nan shashashan banza" be jira cewar shi ba ya kashe wayar shi. A guje TK ya taka motar ya bar wajen, cikin ƙanƙanin lokaci ya isa hotel ɗin. Ƙwanƙwasa ƙofar yayi, ko cire hannun shi beyi daga ƙofar ba akace "shigo" Tura ƙofar yayi ya shiga, kanshi a ƙasa dan be san da wacce kuma uncle Abbas ɗin ze tarbe shi Still kanshi a ƙasa ya samu waje ya zauna, muryar uncle junaid da yaji ne ya sashi saurin ɗaga kanshi Fuska a ɗaure Tk ke kallon uncle junaid da sam shima babu alamun rahma a tattare da shi Ɓata rai Tk yayi yace "Banji me kace ba" Miƙewa tsaye uncle junaid yayi, cike da hargowa yace "Ka sakar min ƴa nace!" Dariyar gefen baki Tk yayi sannan yace "shine kiran dama?" Daga gefe uncle Abbas yace "Dole ka saketa yanzun nan kafin mu fuskanci matsalar dake shirin tunkaro mu" Cike da hargowa uncle junaid yace "ni kam yanzu na haƙura da komi, kawai ka saka ɗanka ya sakar man ƴa daga nan ku ƙarata can ku kuka sani, shekara da shekaru muna akan abu ɗaya, har yau ba nasara, da munga alamun nasara lokaci kaɗan kuma muga akasin haka, To ni na janye na fita a ciki tunda har abun na neman taɓa min gida" Daga can gefe umma ƙarama ta cire nose mask ɗin fuskar ta, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tace "Baka isa ba Junaid, tunda aka soma da kai to tabbas da kai za'a gama"!. Bani kaina ba har Tk da ke zaune seda ya miƙe ganin warce betaɓa zato ba, da mamaki ya nuna umma ƙarama yace "umma ƙ!" Gira ɗaya ta ɗaga mishi kafin ta miƙe tsaye, dariya tayi tace "kayi mamaki ko Tk?" Murmushi ta sake yi sannan tace "anmin shigar sauri ne da tuni nice mahaifiyar ka" Da ƙarfi uncle Abbas yace "Stop it sumayya" Cikin salo da ƙwarewa a bariki umma ƙarama ta juya kaɗa mishi idanu tayi kafin tace "We will come back to that my Abbas" Daga can inda ya faruk da mus'ab ke zaune suna sauraron su ta wayar Tk ɗin, Tsabar tashin hankali ya faruk kasa ci gaba yayi da saurare jin muryar umma ƙarama ƙurukuru cikin gang ɗin su uncle Abbas Sunan Allah kawai yake ambata dan tabbas ya shiga ruɗu, anan take maganar umma babba ta faɗo mishi inda take cewa "Allah ka rabani da zama mutum me kan maciji" A bayyane yace "La haula wala ƙuwata illa billah" Murmushi mus'ab yayi yace "Anjima ana ruwa ƙasa na shanyewa". Tk be gama fita a mamakin da ya shiga ba uncle junaid yace " Kai nake jira Tk, bani takardar ƴata kafin ran kowa ya ɓaci a wajen nan" Dariya Tk yayi ya hau tafa hannaye yana nuna su ɗaya bayan ɗaya, kafin yace "wallahi ba zan sake ta ba, babban kuskuren da kuka yi shine bari a ɗaura auren, oh kuna nufin in sake ta shikenan nayi biyu babu?" Kanne musu ido uncle Abbas yayi, sannan ya matsa kusa da Tk ya dafa kafaɗar shi yace "Baka yarda da baban ka ba kenan?" Shiru yayi ya hau hura hanci Cikin dabara uncle Abbas ya ɗora da "mu gata muke maka baka sani ba, taya za'ayi a baka auren mumtaz bayan kana auren ƴar ɗan'uwan mahaifiyar ta? Kai sakarai ne, kayi tunani akai" Shiru Tk yayi yana nazarin maganar uncle Abbas, can yace "Kasan faruk ba ze taɓa sakin yarinyar nan ba tunda ya samu ya dafe ta, balle na aure ta, kuma kowa yasan sarai yana sonta dama" Tsaki umma ƙarama tayi tace "Lallai da gaske sakaran ne kai, yanzu kai kana tunanin mahaifiyar faruk zata yarda ya zauna da yarinyar da aka saketa a ranar da aka kaita gidan miji ɗanta ya aura? Har yau kenan baka gama fahimtar wacece hajiya Nabila ba, macece da bata son wani aibu ko kaɗan ya shafi ƴaƴan ta, kuma kar ka mance a dalilin sata ne aka sako mumtaz har aka maye gurbi da ɗanta, daɗin daɗawa ma a gaban ta akayi case ɗin komi" Shiru Tk yayi, tabbas ya yarda da abinda umma ƙ kefaɗa, Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "na yarda in har faruk ya saki mumtaz to nima zan saki sakina" yana gama faɗin haka ya fice Zama suka yi gaba ɗaya kowa da saƙe-saƙen da yake a rai Umma ƙarama ta katse shirun da "mu sake haƙuri mugani, muka yi haƙurin shekaru ma balle yanzu na ɗan taƙin lokaci" Tsaki uncle junaid yayi yace "Baki san taurin kai da tsaurin ido irin na faruk ba wallahi, Shiyasa nayi mugun tsanar yaron nan" Murmushi uncle Abbas yayi yace "Dole daman sedai a ɓullo mashi ta bayan gida" Umma ƙarama tace "to ta yaya kenan"? Uncle Abbas yace "habaici zaki koma ki rinƙa saƙa mata a fakaice, tunda har mun san inda weakness ɗin ta yake, dole zata hasala tace zata yi mishi baki in be sake ta ba, shi kuma in ba wawa bane ai ba ze yarda ya ɓalɓance a banza a wofi ba, daga nan ze sake ta, kuma at the same time mun karya ƙwarin gwiwar iyayen da kuma ita kanta ƴar" Dariya suka kwashe da ita duka, umma ƙarama harda kwanciya a kafaɗar uncle Abbas tana wanu jinjina mashi. Tas plans ɗin da suka shirya a kunnen ya faruk da mus'ab, seda suka gama naɗar komi kafin suyi saving Dialing no ɗin dr jamal ya faruk yayi, yana ɗagawa yace "na gama ji aboki, saura abu na gaba kuma". KUN SAN YAU INA HUTU, AMMA HAKA NAN NA DAURE NAYI MAKU ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg69-70 Duk wata hanya da ya faruk yasan ze haɗu da umma b ya kauce mata A daren suka yi waya da ƴan'uwan shi suka ji dahir ɗin zancen auren a bakin shi, kuma suka sanar da shi jiran da umma b ke masa, Sosai suka taya shi murna, bama kamar ya sabiha datafi kowa sanin shi. ***MAMA Murnar data ke ciki bata musaltuwa, ƴan'uwan ta kaf da suke gidan kowa yaji abunda ya faru na auren mumtaz da ya faruk, Da mamaki da yawansu ke tambayar ya akai hakan ta kasance Kafin mama tayi magana goggo safiya tayi caraf tace "sauyin ubangiji mana, a daren tun kafin mu kai ga isa da ita mijin ya kira yace ya sake ta akan dalilin shi mara tushe, Aikuwa a cikin daren jiya iyayen ta suka ɗaura mata da wanda yafi shi komi" Al'ajabin maganar kowa yake, Sedai maganar data ke fitowa daga sasan umma babba daban da warce goggo safiya ke faɗa Yawanci da magana biyu a zuciya suka bar gidan. Tun a daren jiya da aka ɗaura auren ya faruk da mumtaz Abba babba ke neman umma babba a waya amma wayar a kashe Se kawai yayi la'akari da ƙila ta shiga ribibin mutane ne ya haƙura zuwa wayewar garin Allah besan tana can tana tafasa ba. Mutane na nesa nata shirye shiryen tafiya gidajen su ta ɓangaren mummy da aunty, tunda su acewar su sun gama nasu bikin. Mama kuwa a wannan safiyar tana tashi ta bada umarni a ɗora manyan tukwane a wuta Inna hassu da ta baro gidan uncle junaid tun a daren jiya tace "anya basuyi yawa ba zahra'u?" Murmushi mama tayi annushuwar fuskar ta na daɗa yalwatuwa tace "Basu yi ba inna, so nake akai gidan marayu sannan a raba wa almajirai " Gyaɗa kai inna hassu tayi, kafin tace "kice mu yanzu muka fara hidamar tamu" Mama tace "ƙwarai kuwa, sabon ango sabuwar hidima" Gaba ɗaya wajen suka saka dariya da guɗa A hankali Altine tayi ƙasa da murya tace wa ɗayar me aikin da suke aikin hidimar bikin tare tace "Rabon da naga baiwar Allah n nan a cikin farin ciki haka na mance wallahi, Ki kalle ta da kyau ki gani, tunda aka fara hidimar bikin nan bata a cikin walwala sam, amma daga jiya da daddare zuwa yanzu ko aljihun ki ze sheda da tana cikin murna" Dariya matar tayi ta dafe lalitar ta taji zam kuɗin ta na nan, sannan tace "kyauta me tsoka fa mun shata, mukam gaba ta kaimu wannan sauyin tunda ko ba komi mun sami alkairi" Suna aiki suna hirar su, ko irin su nuna gajiyar nan, amma daka gansu zaka san cikin nishaɗi da walwala suma suke aikin. ***** Sha ɗaya da kusan rabi na safe yaya faruk yayi parking a harabar gidan nasu Tunda ya tsaya be fito ba, yana ciki zaune yana ƙare wa jama'ar dake harabar gidan kallo ta cikin baƙin gilashin motar shi Seda ya gama kallon kowa tukun ya kwashi wayoyin shi dake ajiye a gefe sannan ya saka ƙafa ya fito Ma sha Allah! koni kallo ɗaya nayi mashi na tabbatar da lallai ya faruk ya zama ango da gaske Banda baza ƙanshi da sheƙi ba abinda yake Duk da faɗuwar gaban da yake ji hakan be hana shi murmushi ba ya fauza dake ta kai kawo a harabar gidan ita ta fara hango shi Ihu ta fasa tace "Angooooo" Aikuwa akayo mishi caaa Abokan wasa kowa na yagar shi, hatta da ƙannin shi yau basu barshi ba Ba abinda yake se aukin murmushi da saɓa babbar riga Ta window umma babba ke hango shi, ta ƙara ciki tayi fam ganin yarda yake wani zuba murmushi yana amsa addu'o'in da ake mishi. Da ƙyar ya kufce musu ya shige ciki wajen umma b Zaune a palo ya iske umma ƙarama da wasu daga cikin baƙi Be nuna komi a fuska ba yace "barka da safiya umma ƙarama" ya gaishe da sauran sannan ya shige ɗakin umma babba Tana tsaye jikin window dake kallon harabar gidan A ɗan ɗarare yayi sallama ya shigo ɗakin Ciki-ciki ta amsa, bata waigo ba bata kuma nuna tasan ya shigo ba Gefen kujera ya ɗosana ya zauna, kanshi a ƙasa yace "Ki yafe min umma na, wallahi tallahi ba'a tambayi ra'ayi na ba nima akan maganar" Jin rainin da yake ƙoƙarin kawo mata yasa ta waigo a fusace tace "Dakata faruk, yanzu na sake tabbatar wa da bani da wani matsayi me girma a wajen ka kai da mahaifin ka, Na sha komin lalacewa ta tunda har ni na tsugunna na haife ka za'a nemi shawarata koda kuwa ba zan yarda ba, nasan an fita haƙƙina an gaya min Amma abun haushin sedai naji a gari, har wasu su sami damar yi min gori da habaici" Tana faɗin haka ta hau share hawaye tana tuno da kalar habaicin da umma ƙarama ta yayyaɓa mata ɗazu da safe Gyaɗa kai ya faruk yayi, a ranshi yace "Tabbas sun gama sanin laggon ki umma na" Jin bece komi ba yasa taci gaba da faɗin "wai kamar ni ace ɗan da shi kaɗai ne ɗa namiji dana haifa ya ɓige da auren ɓarauniya, kai abin da ciwo wallahi" Jin ta ɗan fara ɗaga murya, ga kuma mutane dake ta kai kawo yasa ya miƙe a hankali ya sakaya ƙofar sannan ya dawo kusa da umman da ke ta sharar ƙwalla ya zauna Kama hannayen ta yayi sannan yayi ƙasa da murya cike da ladabi da kuma sanin haƙƙin mahaifiya yace "Ki yafe min kuma ki yafe wa Abba na umma, wallahi tallahi muna sonki kuma kina da daraja a waje na fiye da kowa a duniyar nan umma, kece kawai kika kasa fahimtar hakan" Muryar ta na rawa tace "Yanzu kai kaji ka amince da auren yarinyar nan? wallahi faruk karka so kaga wulaƙanci da cin kashin da mutanen can sukai mana saboda halin yarinyar nan Ganin bazasu ɗaukar wa kansu jidali bane yasa ya sauwaƙe mata amma kai se ka kwaso mana ita?" Nutsuwa sosai faruk yayi yace "umma ke da akace maki mumtaz na ɗauke-ɗauke ya kika ji zancen?" Ya kafe ta da ido yana jiran jin amsar ta. Shiru tayi can tace "gaskiya daga farko ban yarda ba" "good" ya faruk yace sannan ya sake cewa "Tsakanin ki da Allah kuma baki ɗarsa komi a cikin ranki ba, duba da ynayin yarda kuka bamu tarbiya daidai gwargwadon iyawar ku?" Gyaɗa kai tayi tukun tace "Da wannan dan wannan kuma" Murmushin gefen baki yayi ganin tun ba'aje ko ina ba matsalar shi ta kusa warwarewa. Gyara zama sosai yayi sannan yace "Umma in kika duba gatan da iyayen ta ke mata, dan ban manta ba har maganar kin taɓa yimin cewa gatan da suke mata yayi yawa, kar su saka mata girman kai a abubuwa, har kike cewa hakan yana da nasaba da ƙin kula samari da takeyi saboda tana ganin ta wadatu da komi ta fi ƙarfin su" Gyaɗa kai tayi tace "anyi haka" Sannan yace "To umma kina ganin wanda ya wadatu da wannan gatan shine har wani abu na wasu ze birgeta ta ɗauka?" Ajiyar zuciya ta sauke a wannan karon, taci gaba da sauraron shi Jin bata ce komi ba ya ɗora da " Tabbas in hakan da gaske ne to AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI umma" Shiru umma babba tayi tana nazarin maganar ɗan nata a karo na farko da taji wani abu me kama da tausayi tausayi na son kamata game da ahalin mama. Cikin ido ya faruk ya kalli mama yace "Kiyi nazarin maganata umma, in har baki gano komi ba to ina me tabbatar miki da a gaban ki zan saki mumtaz!." Yana gama faɗin haka ya miƙe yace "na barki lafiya umma" ya fice. Yana fitowa yaga juyawar umma ƙarama da gudu Karkaɗa kai kawai yayi a ranshi yana faɗin "Baƙar macijya me kan mutum". ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg71-72 Yaso ya shiga sasan mama amma ya kasa, dan yau sasan nata yafi na kowa cika, a yarda yake gani ma kamar sake yin wasu baƙin akai Mota ya koma ya zauna, so yake yaga mama ya shawarce ta kafin ya aiwatar da ƙudirin shi Wayar shi ya ciro yace "bari nagwada kira ƙila na same ta yanzu" Mumtaz na kwance taji wayar maman na ringing Calls ne ke ta shigowa na mutane daban daban Jin wayar ta sake ringing yasa taja tsaki a gajiye ta kara wayar a kunne ko saurarawa bata yi ba tace "Mamar fa na ƙasa tabar wayar a ɗaki" Tsit faruk yayi da yaji muryar ta, Can daga baya yace "Kuma bazaki iya kai mata ba?" Durumm haka taji saukar faɗuwar gaba Da sauri ta cire wayar a kunne ta kalli sunan dake kan screen ɗin Daga can ya faruk yace "kar ki kashe man waya, ki sauka ki kai mata ina jin ki" Zumɓura baki tayi kafin tace "wallahi akwai mutane da yawa, ni kuma kunyar sauka nake ji" Murmushin da iyakar shi kan laɓɓa yayi tukun yace "saboda an miki auren dole da wanda bakya so ko?" Dafe baki tayi da sauri tana baza idanu, Jin tayi banza da shi yace "Tunda baki da amsa ze ki kai mata" Badan taso ba ta sauko, Ta wayar ya faruk najin yarda abokan wasa ke warfarta suna tsokana, gummm yaji bakin ta dan beji taba ko mutum ɗaya amsa ba. Mama na cikin mutane mumtaz ta miƙa mata wayar Ansar wayar tayi haɗe da tambayar ta "waye" Zumɓuro baki tayi tace "yaron ki wai" Dariya ya faruk yayi jin abinda mumtaz tace. Tsinkayar muryar mama yayi tana faɗin "faruk ya akayi?" Barin wajen hayaniyar tayi tana sauraron shi, da mamaki mama tace "Banjin ta sha ba gaskiya, me yasa baka bani a hannu na ba? Riƙe wayar ina zuwa" Da sauri mama ta haura sama zuwa ɗakin ta inda mumtaz ke zaune Ya faruk naji tana tambayar ta "mumtaz ina maganin da faruk ya baki tun last month?" Kai tsaye tace "akan mirrow na ajiye shi, da nazo zan sha kuma bangan shi ba" Ajiyar zuciya mama ta sauke, jiki a sanyaye tace "bata sha ba faruk" Daga can ya faruk yace "ba abin damuwa bane mama, yanzu zan koma wajen Alaramman dama nayi waya da shi tun last week akan ya sake yin wani, nasan ƙila ya gama zuwa yanzu" Mama tace "rubutu ne ko me?" "Ba rubutu bane, ayoyin karya sihiri ne wanda ake yin shi da ganyen magarya, daga bayanin da nayi mashi ne ya gane abun akwai sihiri a ciki" Jiki a sanyaye mama tace "Allah yayi maka albarka faruk yasa ka gama da iyayen ka lafia, ya albarkaci auren ku da zuri'a managarciya me albarka" A hankali ya amsa da "amin" kafin ya ɗora da "ki kira Abba ƙaramin akan maganar kayan nasu, dan be dace ace su sake kwana anan ba" Murmushi mama tayi, tace "baka da matsala yaro na" Da haka su kayi sallama ta aje wayar. Kafin ya faruk ya tafi seda ya kira ya maryam ya sabiha da ya fa'iza yace "Ku lallaɓa ku saɓar wa umma babba ku tafi can gidana dake nasarawa, Ku cire komi da komi ayo waje dasu, nasa azo a kwashe su, za'ayi ma gidan sabon penti" Ɗan baya ta maryam taja ta rangaɗa guda haɗe da tafa hannaye Ganin zata jawo masu hankular jama'a yasa yayi saurin miƙa wa sabiha keys yaja motar ya fice. Yana a hanya call ɗin Abba babba ya shigo masa, da sauri ya ɗaga haɗe da sallama Abba babba yace "kasa an fara aikin ko kuwa shiririta kasa?" Seda ya ɗan rissinar da kai yace "yanzun nan muka gama waya da su har sun iso masu gyaran" Abban yace "yauwa to, ka kyauta" ya aje wayar. Seda mama ta je kiran da ake mata kafin ta dawo ɗakin ita da goggo safiya Zaunar da ita mama tayi ta mata tace "kayan da can suka kawo ya kamata a maida masu kar su sake kwana, nima a kwaso man furnitures ɗina" Goggo safiya tace "hnn na taɓaki da alkairi, ai ni tsabar farin ciki yasa na mance da wasu kayan su, gaskiya gara a maida musu, kira man ƙasim a wayar ki muji ya za'ayi" Ba ɓata lokaci mama ta danno wa uncle ƙasim kira Yana ɗauka ta miƙa mata. A take suka gama arranging mayar da komi dan acewar su babu abinda zasuyi da kayan su. Gaf da la'asar goggo safiya da matar uncle ƙasim se inna hassu da wata ƴar'uwar mamar suka kwashi akwatunan aka loda su a mota ɗaya, su kuma suka shiga mota ɗaya suka nufi gidan su khalid da su. Babu kowa a gidan se ƴan tsirarun mutane, ba zaka taɓa cewa anyi biki jiya a gidan ba Goggo safiya ce kan gaba, kwaɗa sallama tayi, sauran kuma suna ta shigo da akwatunan Aunty hajara ce ta amsa musu haɗe da fitowa, cak ta tsaya tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya Da sauri ta juya ta koma ciki, se gasu sun fito da ɗayar sister mamin Suna tsaye har aka gama shigo da akwatunan sannan goggo safiya tace "sannun ku bayin Allah, uwar kalid ɗin na ciki ne?" Sister mamin tayi saurin faɗin "ku ƙaraso daga ciki mana kuka tsaya a nan" Palon da aka tarbesu jiya a nan aka sake saukar su Sun kai kusan minti goma a zaune kafin mamin ta shigo fuskar nan tata a ɗaure Waje ta samu ta zauna, sama sama aka gaisa kafin goggo safiya tace "To bayin Allah, ga kaya nan dai mun dawo dasu, tunda aure beje ko ina ba akayi saki, shine muka yanke shawarar dawo muku da su Kunga an ɗan rage mashi asara ko yaya ne" Wani wawan kallo mami ta jefi goggo safiya da shi, bata yi magana ba har goggo safiya takai aya tukun aunty hajara tace "ai da kun bar mata kayan tunda har kun riga da kunyi jere, mu dama a al'adar mu in akayi sakin aure kayan ɗaki ya zama na miji, kuma kunga yarda wannan auren ya kasance, se ku koma da kayan kunga an raba asarar duka" Matar uncle ƙasim tace "tohh, wannan wace irin al'ada ce ta son banza da yawa haka?" Sister mami tayi wuf tace "kalar warce kuka ji yanzu" Da sauri inna hassu tace "ku tashi muje, naga kamar abin ze zama da cin mutunci" Miƙewar su kenan khalid ya shigo palon, kallo ɗaya zakayi mashi ka san ya zabge daga jiya zuwa yau ɗin nan Kanshi a sama yace "mami bani mukullin gidan, babu abinda zanyi da kayan nan, gara abari su kwashe" Sudai basu tsaya ba, ficewa sukayi gaba ɗayan su bama su tsaya jin amsar da mamin ke bashi ba. Aunty hajara da sistern mamin suka hau shi da faɗa, "sakarai in ba haka akayi musu ba kaike da aasara, duk uban kuɗin da aka kashe wajen hidimar bikin, ba se ka fanshe da kayan ba" Juyawa yayi ya fice haɗe da faɗin "nidai bana so". Ganin sun bar akwatunan yasa suka shigar da su palo suka hau bubbuɗewa Mami na daga gefe ta zabga uban tagumi tana kallon kayan a cikin ranta tace "basu taɓa komi ba ma ashe". Bayan sun koma gida mama taji abinda gidan su kalid ɗin suka ce, murmushi tayi tace "ku rabu da su, Allah ya rufa mana asiri kawai". ***Umma babba tunda ya faruk ya barmata assignment take tufka da warwara, har ma bata san time ya tafi haka ba Duk in ta ƙulla se taga warwarar daga ƙarshe ba aibu bace ba kuma abar ƙyama bace sannan kuma alamar tambaya ce me girman gaske. Da dai tayi tayi ta gaji, haƙura tayi ta miƙe haɗe da faɗin "Allah ka warware mana komi cikin sauƙi da salama, ka hanamu cutar da ɗan kowa albarka annabi muhammad" Kai jama'a tun kafin lauje ya warware daga cikin naɗi umma babba tayi la'asar fa Haka kawai take ji acikin jikin ta akwai wani ƙulli me girman gaske a lamarin. Sanda labari ya iske Amal cewa aure ya koma kan ya faruk tayi matuƙar shiga ruɗu bama ita kaɗai ba, harda sauran amaren da suma al'ajabi be barsu ba Duk wanda suka tambaya kanun zancen sedai yace "haka kawai khalid ɗin ya sake ta aka mayar da auren akan ya faruk" Abun mamaki sanda hafsat ta kira umma babba dan taji dalilin hakan, umma babba ta tsinci kanta da kasa faɗin komi game da mumtaz, abu ɗaya tace "Sauyin ubangiji ne kawai hafsa". Kusan hakan maganar take a kunnen kowa, takamaimai ka titsiye mutum kace meye dalilin da yasa aka mayar da auren mumtaz kan ya faruk,? Sedai suce "Ikon ubangiji ne". TO HAKA UBANGIJI YAKE ABUN SHI, IN YA RUFA MAKA ASIRI TO BABU WANI MAHALUKI DA YA ISA YA TONA SHI SHIYASA AKO DA YAUSHE MUKE ROƘON UBANGIJI DA YA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA, YA HANE MU AIKATA AIKIN DANASANI. Goma saura na dare su Abba babba suka tara matan su da kuma ƴaƴan su kaf dake ma'aura, da kuma wanda kenan cikin gidan banda wanda aka kai jiya, Mumtaz na raɓe jikin mama taƙi yarda ta buɗe ido sam tsabar tsoro da kuma abinda take tunanin ze kai ya kawo Ƙafa ɗaya kan ɗaya umma babba ta ɗora tana zaune a gefen Abban ta dama, umma ƙarama kuma na gefen shi ta hagu Mama na kusa da Abba ƙarami da shima zaka ga annurin fuskar shi ya daɗu, Uncle ƙasim ma aunty na kusa da shi. Unccle Abbas da shima da ƙyar ya yarda ayi zaman yana zaune kuaa da mummy Goggo safiya na daga gefe. Yaran duka suna zaune a ƙasa Ƴaƴan ta mata gaban su na ta faɗuwa dan sun san umma babba ba ƙaramin shiri tayi wa zaman ba Da addu'a Abba babba ya buɗe taron, sannan ya fara da ban haƙuri ga wanda suke tunanin ba'ayi musu daidai ba Nan Abban yayi nasiha me ratsa jiki kafin ya waiga ga umma babba yace "a matsayin ki na uwa nasan ban kyauta ba da ban baki damar ki ba, amma ina me baki haƙuri" Ido ɗaya umma ƙarama ta kashe wa uncle Abbas da gaba ɗaya hope ɗin su itace umma babba, botsarewar ta kawai suke jiran ji Amma ga mamakin su da Abban ya kai ƙarshen maganar shi, se ji sukayi umma babban tace "ai kai da kaya duk mallakar wuya ne, Allah ya bashi ikon riƙe ta da gaskiya da amana, ya tsole idon maƙiya" JAKAR UBAN CAN 😳 ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg73-74 Tsit palon yayi, wanɗanda kansu ke a ƙatsa duk suka ɗago tsabar yarda kunnuwan u suka kasa gasgata abinda suka ji Bama yaran kaɗai ba, kaf iyaye matan da mazan mamaki ne kwance a fuskokin su Mama kam sakin baki tayi bilhaƙƙi da gaskiya tana kallon umma babba da tai mirsisi da idanuwan ta Ƴaƴan umma babba kaf idanun su ciccikowa da ƙwalla sukayi jin irin bazatan da mahaifiyar tasu tayi musu Abba babba shi kanshi maganar umman tayi mugun bashi mamaki, ta wani fannin kuma a take yaji ƙimarta na daɗuwa a zuciyar shi, ko ba komai bata kunyata shi ba A hankali mama ta maida kanta ga ya faruk dake gefe yayi folding hannayen shi ga ƙirji A fakaice tayi mishi jinjina da hannun ta, dan ta san ba aikin kowa bane inba shi ba, duba da sanin kafaffen hali irin na umma babba. Mumtaz kam banda raba ido babu abinda take, dan ita har ga Allah bata yarda da abinda umma b tace ba Hajiya umma ƙarama kuwa ƙiri-ƙiri zaka hango rashin nutsuwa a tattare da ita, ga uwar zufa data ke ta fama gogewa a fakaice Goggo safiya ta gyara zama duk da itama mamakin ne kwance a fuskar ta tace "To se muyi wa ubangiji godiya, Nasan yarda nake cikin bazata haka kowa yake a nan" ta maida kallon ta ga umma babba da har yanzu ƙafarta ɗaya na kan ɗaya tace "Kin kyauta ƙwarai da gaske hajiya Nabila haka akeson babba ya kasance kullum cikin fahimta da fawwala ma ubangiji komi, wallahi dole mu faɗa kin mana bazata, Allah yayi riƙo da hannayen ku wajen riƙe amana" Da "Amin" kowa ya amsa, fuskar kowa da fara'a da annuri banda uncle Abbas da yayi mutuwar zaune tunda yaji furucin umma babba Ga Tk da ya gama ƙullin shi shima zaune, idanuwan nan kamar zasu faɗo ƙasa saboda muguwar hararar da yake aikawa ya faruk. Cike da farin ciki uncle ƙasim yace "magana ta ƙare anjima se a sada ta ga ɗakin mijin ta" Ba wanda ya ankare se ji sukayi Tk yace "wallahi da sake babu wanda kuma ya isa ya sake titsiye ni yace na saki matata alhalin warda ake jira aji ta botsare bata botsare ba" A firgice umma ƙarama ta dafe bakin ta, Uncle Abbas kuwa cikin zafin nama ya sauke ma Tk tagwayen maruka, cikin tsananin fushi me haɗe da tsoro yace "Baka da hankali ne Tk, iyayen ka na magana kana magana, kodai kaje kasha abinda ke maka saƙe-saƙe a cikin kai ne?" Umma ƙarama na ganin hankalin kowa ya koma kan Tk ta samu ta saɗaɗa ta bar palon ta nufi ɗakin ta. Abba babba da yafi kowa zafi shima yace "Ku rabu da shi, maimaita abinda kace Tukur" Ƙunƙuni ya hauyi, ya kasa magana Tsintsinkewa kawai zuciyar Uncle Abbas keyi, karon farko da tsoro me tsanani ya kamashi Tsawar da Abba babba ya daka mishi yasa shi faɗin "Ina nufin nima a anso min tawa matar tunda kowa ana maganar shi amma anyi shiru da tawa" A kusan tare umma ƙarama dake laɓe suka sauke ajiyar zuciya ita da uncle Abbas da ya silale ya koma ya zauna Sedai abinda basu sani ba shine ba ƙaramin yaro kaf a palon, maganar Tk ta farko abar tunanice a ƙwaƙwalwa Yarda umma babba ta zauna tana fasa maganar a kanta abun se ya baku mamaki Daga haka dai iyayen maza suka sallami kowa ya rage se su kaɗai se kuma goggo safiya. Ba ƙaramin mamaki umma babba ta shiga ba ganin yarda manyan ƴaƴan nata ke murna, masu raguwar zuciya daga cikin su harda kuka Nan ma zuciyarta ta sake yin sanyi A nan palonta ta barsu su duka ta shige bedroom Seda ta kulle ƙofar tukun t zauna tana sake fasa maganar da Tk yayi Can data gama fasata ta kuma ɗauko maganar da ya faruk yayi mata a ɗazu ta haɗa, se ta ga abun ya bata ma'ana ɗaya Ta jima sosai a zaune tana nazari har lokaci yaja bata sani ba, daga ƙarshe a bayyane tace "Tabbas AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI a maganar shi". Abba ƙarami ne ya amshi maganar Tk da niyar gobe Ze kira aminin nashi ya sanar mishi da zasu zo su ɗauki amarya sakina. Da wannan maganar ta Abba ƙarami aka rufe taron, bayan faɗa me zafi da Abba babba yayi masa. Umma ƙarama data shiga ɗaki waya ta ɗauka ta kira uncle junaid da shima jarabar maman sakina tasa ya kulle kanshi a ɗaki Jiki na rawa umma ƙarama tace "wallahi junaid asirin mu na gaf da tonuwa, nidai na kasa sukuni gaskiya ku kira malam kusa shi ya rufe mana bakin kowa gudun jin kunya" Shiru uncle junaid yayi kafin yace "Baya ɗaukar wayata daga jiya zuwa yau, tuntuni naso ya rufe min bakin sakina da mahaifiyar ta kafin mu samo bakin zaren" Dogon tsaki uncle junaid yaja sannan yace "duk wannan wawan ne da ya sako mana ɗanshi a tafiyar, wallahi ba dan ya sako sakaran ɗanshi ba da babu yarda za'ayi mu rinƙa shiga tashin hankalin da ze sa har a farga da yanayin da mutum ke a ciki ba" Still gaban ta na faɗuwa tace "kuyi magana da Abbas ɗin dai, shi ya kwatanta kiran shi, in ma be ɗauka ba dole aje a same shi a daren nan kar wanki hula ya kaimu inda bamuyi tsammani ba junaid" Daga can uncle junaid yace "Bari nayi trying shi". Ƙiri-ƙiri uncle Abbas na ganin call ɗin uncle junaid yaƙi ɗagawa, haka ya ƙaraci kiran shi har ya haƙura. A daren ranar bayan tashi daga zaman da akayi a palon Abba babba, ya faruk ya ɗauki maganin da ya amso daga wajen Alramma ya nufi sasan mama Ta can ƙofar baya ya shiga, har sama ya haura A palo ya iske maman da goggo safiya se inna hassu da su kaɗaine sukayi saura a ƴan biki Zama yayi suka gaisa da inna hassu, itace dama basu gaisa ba tukun ya matsa kusa da mama yayi ƙasa da murya yace "Mama na karɓo maganin tun ɗazu, ya kamata ta sha kar tayi wasa dashi kamar wancan" Hankali kwance mama tace "shiga tana ɗakin ta" Ɗan jimm yayi kaɗan kafin ya miƙe ya nufi ƙofar da zata sada shi da ɗakin nata. Mumtaz na kwance ta kifa cikinta akan gado, daga ita se ƙaramin baƙin wando da be wuce tsakiyar cinyar ta ba se vest fara ƙal da bata ƙarasa rufe mata cibiya ba Ga gashin ta da yasha gyaran biki ta baje shi, yarda take kwance haka gashin yabi lafiyar pilon shima, kusan rabi ya rufe mata gefen fuska, Wayar goggo safiya ce a hannunta, ta ƙuƙe se typing msg take Gaba ɗaya hankalin ta da nutsuwar ta yana kan wayar, baka jin ƙarar komi a ɗakin se na madannan wayar Ya faruk ya turo ƙofar ya shigo bakin shi ɗauke da sallamar da bata kai ga fitowa ba ta koma inda take Tunda ya shigo ya ƙame a wajen kamar wanda aka dasa Gaba ɗaya bugun zuciyar shi ya sauya daga yarda take, ta koma bugawa da sauri-sauri Yarda yake a tsayen nan babu wani abu dake motsi a jikin shi se idanuwan shi dake bin ko ina da ina na jikin ta da kallo. Seda ya gama ƙare mata kallo ya saɗaɗa a hankali yakai hannu ya fizge wayar dake hannun ta A firgice tace "wayyo Allah na" tana waigowa da sauri Tana ganin waye a tsaye ta miƙe a guje ta sauka daka kan gadon ta ɓoye a bayan abun saƙale jakunkuna ta tsaya Fat-fat haka ƙirjin ta ke duka Leƙo da kanta tayi taga ita yake kallo ko me, ga mamakin ta gaba ɗaya hankalin shi na kan screen ɗin wayar da ya fizge daga hannun ta Da sauri ta dafe ƙirji tunowa da tayi khalid fa take rubuta ma saƙo Aiko mancewa tayi da kayan data saka ta fito da sauri tayi wuf zata ƙarɓe wayar Cikin zafin nama ya damƙeta da hannun shi ɗaya sannan yaci gaba da karanta dogon saƙon data rubuta ma khalid ɗin Wutsil wutsil ta hau yi tana son ƙwacewa daga riƙon da yayi mata Seda ya gama karancewa tsaf tukun ya maido da idon shi kanta Jinjina kai yayi haɗe da ɗaga gira ɗaya yace "ohhh ashe har haddace number guntun can kikayi"? Zumɓura baki tayi sannan tace "Akwai no ɗin ai a wayar" Ɗalle mata maki yayi da ɗayan hannun sannan yace "dan akwai number a wayar shine ya baki damar yin magana da shi?" Banza tayi da shi Jin tayi shiru yasa ya sake matseta sannan yaja kumatun ta da ɗan ƙarfi yace "kin mance akwai auren wani a kanki ko?" Nan ma shiru tayi, tayi ƙwalƙwal da ido kamar me shirin yin kuka sannan tace "Haƙuri na bashi, kuma na gaya mishi ni ba fasiƙa bace, bayan sata babu wani abu danake wanda be dace ba" Nan da nan maganar datayi yasa yaji wani iri haɗe da tausayin ta na daɗa kamashi A hankali ya samu gefen gadonta ya zauna, sannan ya janyota ta zauna akan cinyar shi Seda ya ɗauki mintoci kafin yace "daga yau daga rana irin ta yau bana so na kuma jin kince kina sata Kuma kar na sake ganin ko da wasa kin sake ɗaukar waya da sunan zaki ma wani wawa da be cancanci sanin ki ba sam msg, ki rabu da kowa" Robar maganin da ya shigo da ita ya ɗakko, da kanshi ya buɗe murfin ya kai maganin bakin ta Gintse baki tayi taƙi buɗewa, Ware mata manyan idanun shi na gado yayi sannan yace "buɗe bakin ki kisha" Duk da ɓata ran da take haka ta buɗe ya tuttula mata shi, seda ya tabbatar da tasha ya kai adadin daya dace tukun yacire ya kulle Jiki a sanyaye yace "da izinin ubangiji kin bar ƙara sha'awar kayan kowa daga yau" Gaba ɗaya kunya ta rufeta Hannayen shi nata zagaye a bayan ta kusan mintoci kafin ya sake cewa "gaya min abun wa da wa kika ɗauka, kuma in kin ɗauka me kike yi da shi?" Shiru tayi kanta a ƙasa, duk a takure take jin kanta Seda ya sake maimaita tambayar tukun tace "Tsaya in saka kaya to" Buɗe idanun shi yayi sosai a kanta kafin yace "wannn su ba kaya bane?" Banza tayi da shi, ta miƙe daga jikin shi Shi kam be ma da energyn da ze iya hanata tashi, yana kallo ta ɗauki zumbuɗeɗen hijabi ta saka sannan ta koma kan stool ɗin gaban mudubi ta zauna Gyara zama yayi ya ɗan kishin giɗa a gefen gadon sannan yace "ina jin ki gaya min" Kanta a ƙasa tace "agogunan Abbana nafi ɗauka, se na wani malamin mu guda ɗaya, se agogon khalid da abun hannun mamanshi, se carbin umma babba, se kuma naka agogon" Tana gaba faɗa ta sadda kanta ƙasa Tashi zaune yayi yace "meyasa abun maza kawai kika fi ɗauka?" Jiki a sanyaye tace "nima ban sani ba" Gyaɗa kai yayi, a ƙasan ranshi yace "shima wannan akwai lauje cikin naɗi kenan" Bayan ɗan shirun da yayi, can yace "to me kike da su in kin ɗauka?" Still kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannun ta tace "Ba abinda nake da su, ajiyewa kawai nake" Bata gama maganar ba ta tashi daga inda take zaune ta buɗe wata jaka madedeciya ta miƙa mishi Ba musu ya karɓa, ya duba, a hankali tace "na baka naka, yanzu agogon khalid dana malamin mu se kuma na Abbana ne kawai a cikin nan" Hannu ya saka ya ciro carbin umma, kafin yace komi tayi sauri tace "se kuma carbin umma babba" Kallon carbin yayi yana tuna sanda ya ganshi ya faɗo daga jikin ta Gyaɗa kai yayi ya miƙa mata jakar "ungo ajie, zuwa gobe in nazo kawo maki maganin ki se in tafi da su" Gyaɗa kai tayi Ɗaukan maganin yayi ya nufi ƙofa, Jiki a sanyaye ta bi bayan shi da kallo, Kallo ne me ma'anoni da dama Gaf da ze fita ya waigo karaf suka haɗa ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa Murmushi yayi yace "Nafi wancan guntun kyau ko?". ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg75-76 Seda ya faruk ya jera kwana huɗu cif se bayan isha zezo da kanshi yabama mumtaz maganin ta A kwana huɗun nan shaƙuwar da ita kanta bata san ta yaya hakan ya faru ba ta shiga tsakanin su. ****BAYAN SATI ƊAYA Tsaf an gama gyaran gidan ya faruk inda mumtaz zata zauna Haɗaɗɗu kuma tsadaddun kayan ɗaki Abba ƙarami ya zuba wa mumtaz tunda yaji labarin abinda dangin khalid suka ce game da kayan Dan kanshi yace a rabu da su kar wanda ya sake binsu. Ƴan tsirarun dangin mama da kuma su ya sabiha ne suka je akayi jeren sabbin kayan da aka siya Duk wanda ka gani a gidan kasan ɗan'uwa ne duk wasu bare sun jima da tafiya. Da yamma wajen ƙarfe biyar saura ya faruk ya nufi gidan da a yanzu can mus'ab ke zama Da keys ɗin shi ya buɗe gidan ya shiga Seda ya ƙare wa dattijon dake ɗaure a tsakiyar palon kallo sannan ya zauna a kujerar dake kallon shi Da ƙyar dattijon ya ɗago kai ya kalli ya faruk sannan ya maida kanshi ƙasa Ya faruk bece mishi komi ba, sema wayar shi da kara a kunne, shirun da be wucw seconda yayi ba kafin yace "uncle ƙasim ka shigo layin ne?" Daga can yace "ina daidai gidan" Fitowar mus'ab daga cikin bedroom kenan ya faruk yace "bari na shigo da uncle ƙasim" zama mus'ab yayi yace "to" Anan waje uncle ƙasim yayi parking, tukun ya biyo bayan ya faruk tambayoyi fal bakin shi. Yana saka ƙafar shi a palon ya tsaya cak yana kallon mus'ab da ya tara ƙasumba a fuska Raba kallon shi yayi, ya kalli mus'ab da murmushi yaƙi barin fuskar shi, sannan ya kalli dattijon da yake a ɗaure a ƙasa tukun maida kallon shi ga ya faruk da yasha baƙin gilashi fuskar nan a murtuke. Ƙarasowa yayi a hankali idon shi a kan mus'ab yace "Mus'ab yaushe ka dawo?" Kai tsaye ya faruk yace "Ba inda yaje uncle, yana nan" Da mamaki uncle ƙasim ya maimaita "yana nan fa kace?" Be jira amsar su ba ya sake nuna mutumin dake ɗaure yace "shi kuma waye wannan kuka ɗaure shi haka?" ya faruk yace "calm down uncle ƙasim, dalilin zuwan ka nan kenan ai" Be sake cewa komi ba se waje da ya samu ya ɗosana ya zauna, dan ya faruk da mus'ab sun fara bashi tsoro. Gyaran murya ya faruk yayi ya fara bashi labarin komi A-Z, sannan ya nuna mutumin nan yace "shine tun shekarnjiya muka je na ɗakko bokan nasu na kawo shi nan. Duk yarda zuciyar uncle ƙasim take da dakiya se gashi zaune dirshen yana kuka da idanuwan shi Kuka harda majina jin kalar cin amanar da ɗan'uwan shi da kuma matar ɗan'uwan shi suka ƙulla Cikin su babu wanda ya lallashe shi, dan abin ayi kukane ga duk wanda yaji labarin cin amanar nan Uncle ƙasim yafi awa ɗaya kafin ya dawo normal, yayi shiru ya zabga tagumi yana kallon mutumin da ya shirya dukka tuggun Murya a dishe yace "all this while me yasa kuka bar abun a tsakanin ku baku fallasa maƙiyan Allah ba?" Haɗiye miyau me ɗaci ya faruk yayi sannan yace "Uncle ƙasim, in baka iya kama ɓarawo ba, to shi se ya kamaka" Ya faruk be gama rufe bakin shi ba wayar bokan tayi ringing a karo na ba adadi Kallon wayar sukayi dukkan su, sannan ya faruk yace "calls ɗin su ya fi ɗari uku daga shekaran jiya zuwa yanzu" Cike da ɓacin rai uncle Ƙasim yace "ba amfanin hakan, so nake kawai yanzu ku tashi muje gidan ayi wacce za'ayi kawai" Karkaɗa kai ya faruk yayi sannan yace, "akwai abinda ban ƙarasa ba, kuma yanzu zan kammala shi kafin mu dangane da gidan" Shiru kawai uncle ƙasim yayi, dan abun yafi ƙarfin kanshi gaba ɗaya. Juyawa saitin bokan ya faruk yayi, rufe ido yayi ya tsinka mashi mari me shiga jiki kafin yace "ka haddace abinda nace ka gaya musu ko na sake maimaita maka maƙiyin Allah?" Cikin rawar murya ta irin wanda yasha wiyar nan yace "wallahi na haddace ranka shi daɗe" Da kanshi ya janyo wayar bokan yayi dialing no ɗin uncle Abbas Tsit polon yayi, ringing ɗaya kamar dama suna a kan wayar uncle Abbas ya ɗaga, Daga jin muryar sa zaka san a kiɗime yake, "Haba malam, haba malam, ina ka shiga tsawon kwanakin nan muna neman ka amma baka amsa wayar mu?" Cikin ƙarfin hali bokan yace "Ina wani aiki ne, ba gashi na kira da kaina ba" Kamar me ƙinƙina uncle Abbas yace "dukan mu gamu a waje ɗaya, rikici na neman ɓarkewa a tsakanin mu, in hakan ta kasance asirin mu ya gama tonuwa malam" Buɗe mishi manyan idanuwan shi yayi, yayi mashi alama da ido Bokan yace "Kuna jina dukan ku?" a tare su ukun suka haɗa baki wajen faɗin "eh malam" ya ɗora da "abinda nake so da ku shine, ku tabbatar da ankai yarinyar nan komin dare ɗakin ta, rufe bakin kowa da kukace nayi, to nayi, kaita ɗakin ta shine rufar bakin kowa, daga nan ku bar min komi babu wanda ya isa yaga bayan ku, kuma takardun campanonin da nayi muku alƙawarin cewa da kanshi ze tabbatar da cewa ba mallakin sa bane shi kaɗai, akwai saka hannun jarin ku a ciki ze tabbata shima a daren gobe, amma sharaɗin shine ku kai yarinyar nan kafin goben" Yana gama faɗin haka ya faruk ya gintse wayar haɗe da tallaƙe ƙeyar maƙiyin Allah. Da ƙarfi uncle ƙasim yace "HAZBINALLAHU WANI'IMAL WAKIL"! Ya sake kaɗa kai yace "Mutum da dukiyar sa halalin sa gumin sa amma suke son ganin bayan shi". Tsuru tsuru sukayi gaba ɗayan su, maganar tarewar sakina sam uncle junaid beso ba, amma jin kalaman bokan nasu na ƙarshe yasa yaji ranshi yayi fari Uncle Abbas da umma ƙarama daman uncle junaid ne matsalar su Suna jin yace "Na yarda ta tare ɗin" umma ƙarama ta daka wani uban tsalle kamar ƙaramar yarinya ta rungume uncle Abbas da shima dariyar cin nasara da suke tunanin sun samu yake (WA'IYAZUBILLAH) A take umma ƙarama ta bar wajen ta nufi gida. Uncle junaid ma ya nufi nashi gidan da yazama kamar gidan mutuwa a ƴan kwana biyun nan. A yarda suka rabu dama uncle junaid ze kira Abba babba da kanshi ya sanar dashi tarewar sakinar a yau Aikuwa hakan ta kasance, ko gidan be kai ga shiga ba ya kira Abban A mutunce suka gaisa, yayi masa bayanin komi Abban yaso yaja maganar amma uncle junaid ya fahimtar da shi amfanin yin hakan tuntuni A take Abba babba ya yarda, sukayi sallama sannan ya kira Abba ƙarami ya sanar da shi, tukun ya kira uncle Abbas da dama call ɗin yake jira, Sannan ya kira uncle ƙasim suma da suke zaune suna jiran kiran Sanda uncle ƙasim ya yaga kiran Abba babba kuma yaji akan maganar da ya kira, abun ya sake bashi mamaki ainun. Murmushi ya faruk yayi jin komi na zuwan masu da sauƙi. ***TK Sanda uncle Abbas ya kira shi ya sanar da shi tarewa sakina a yau ɗin nan, haka yayi ta birgima yana murna kamar wani ƙaramin yaro A take uncle ƙasim yace "Yanzun nan zan sa azo ayi shara da goge goge tunda gidan sabo ne babu abinda yayi" Cike da zumuɗi Tk yace "To daddy" Kankace me maganar tarewar sakina ta baɗe sasan gidan gaba ɗaya Abba ƙarami da kanshi ya kira mama ya sanar da ita, har da faɗin "ki shirya ki tafi can gidan junaid ɗin" Jiki a sanyaye mama tace "to, Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi" Mumtaz da inna hassu na gefe, har rige-rigen tambayar ta suke Nan tace musu "yau ne sakina zata tare wai" Riƙe baki inna hassu tayi sannan tace "shine ko junaidu ya kirani yasan da ina nan ban koma ba" Mama tace "ai bata ɓaci ba, yanzun ma shiryawa zakiyi mu tafi tare" Mumtaz tayi karaf tace "mama nima zani dan Allah" Ɗaga hannu sama mama tayu tace "ba ruwana, ki tambayi faruk" Taɓe baki mumtaz tayi kamar gaske tace "to ara min wayar ki na kira shi" Da hannu ta nuna mata inda wayar take haɗe da miƙewa zuwa ta shirya Mumtaz na ganin mama ta shige ta maida wayar ta ajiye, haɗe da turo baki tace "wallahi ba zan kira ba kuma se naje, kullum in zakayi abu se ace se ka kira wani can" ALLAH KASA ANNABI YA CECE 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg77-78 Da gudu ta shige ɗakin ta, Bata jima da watsa ruwa ba dama, Rasa kayan da zata saka tayi, can idon ta ya kai ga baƙar Abaya Da sauri ta cirota haɗe da mayafin ta Roll on se ɗan body spray me daɗin ƙamshi ta fesa Sannan ta saka rigar Gashin ta da ke a wargaje ta haɗe shi ta saka ribbom ta ɗaure sannan tayi rolling da mayafin mudubi ta kalla, ganin yarda ta fito ras a kayan yasa ta wani kashe ma kanta ido ɗaya Har ta juya zata fita ta dawo da saurin ta zizara kwalli a idon ta, dan tasan sarai mama se tayi magana in taga idon ta fari ƙwal. Fitowar su kenan suka ga sisters ɗin mummy kusan su takwas sun shigo Cike da mutuntawa aka gaisa suka wuce. Miƙawa mumtaz key ɗin motar tayi sannan ta zagaya ta shiga gaba Inna hassu kuma ta shiga baya, mumtaz na mazaunin driver. Suna hawa titi mama ta kalle ta tace "Ba sauri muke ba mu kam, jamu a hankali wallahi" Dariya mumtaz tayi, tace "Hajiya mama" Daga can baya inna hassu tace "ah da gaskiyar ta wallahi, koni yarda naga kin fizgi motar seda na zabura" Haka sukayi ta wasa da dariya har suka kai gidan uncle junaid. Suna shiga gidan suka iske ana buga danbarwa da sakina akan shiryawa Kallo ɗaya mumtaz tayi ma sakina taji mugun tausayin ta ya kama ta gaba ɗaya a ƴan kwanakin nan da akayi ta wani koɗe ta rame kamar warda ta shekara tana jinya Jiki a sanyaye tace "ina kayan nata?" Ƙanwar mum ɗin sakinar ta miƙa wa mumtaz kayan, suka juya suka bar musu ɗakin. Sakaya ƙofar mumtaz tayi tukun ta matsa kusa da sakina da ko ƙarfin kirki bata da shi tsabar rashin cin abinci da ba tayi, Kusa da ita ta zauna, dafa ta tayi tace "Haba sakina kina cutar kanki da yawa, jifa yarda kika koma daga last week zuwa yau, Ki ɗauki ƙaddara ki fawwala ma Allah komi, ko wannen mu yana da tashi jarabawar" Cikin fushi sakina ta katse mumtaz tace "Kin faɗi haka ai bayan ke kin samu muradin ranki" Murmushi mumtaz tayi sannan tace "nasan baki san khalid ya sakeni ba a ranar da aka kaini gidan su" Duk da rashin ƙarfin jikin da bata ji hakan be hanata waigowa da sauri ba haɗe da faɗin "Haba dai?" Gyaɗa kai mumtaz tayi Can ƙasan zuciya sakina tace "Kaɗan kenan kika gani" A bayyane kuma tace "To garin yaya hakan ta kasance, me kikayi mishi to?" Taɓe baki mumtaz tayi sannan tace "shi ya san ma kanshi sakina" mamaki mumtaz keyi ganin yarda sakina kamar fara'a take da jin labarin sakin da akai mata Basarwa tayi taci gaba da bata baki akan muhimmancin bin iyaye, Haka kurum ta tsinci kanta da kasa gaya mata an maida auren ta kan yaya faruk. Biyar da rabi na yamma aka fito da sakina da, sam ba zaka iya tantance a wani yanayi take ciki ba Fuskar ta ba yabo ba fallasa, har cikin bedroom wajen maman ta aka kaita Saboda yarda kuka yaciyo ta kasa cewa komi tayi, su mama suka taso ta suka fito Motoci ne reras ba laifi, kusan guda shida, haka aka saka sakina idon nan nata ƙur tana bin kowa da kallo har motocin suka ɗaga Mumtaz ma na daga motar mama tana binsu a baya, wannan karon ita kaɗaice a motar. Masha Allah, gida se ƙamshi yake zubawa kamar gaske, haka aka wuce da sakina har cikin ɗaki aka zaunar da ita Su mama suka sakata a gaba da nasiha da rarrashi tukun sukai mata sallama suka fito. Ba su wani jima a gidan ba suka fito kowa ya kama gaban sa Suna tafe a hanya mama tayi shiru tana ta kallon titi Can ta nisa tace "wallahi sakina ta bani tausayi, Allah yasa dai ta sa ma kanta haƙuri da salama ta zauna har su samu su fahimci juna" "hmm" kawai mumtaz tace, taci gaba da tuƙin ta har suka je gida Suna shiga gida taga motar ya faruk a pake Duk a tunanin ta baya cikin motar, taje tayi parking a kusa da tashi Yana zaune yana waya da mus'ab amma hankalin shi gaba ɗaya yana gareta Mumtaz na parking mama ta fice tayi sasan mummy yi mata Allah sanya alkairin Tk Ya faruk na ganin mama ta fice ya sallami mus'ab yayi wuf ya fito Mumtaz bata ankare ba taji shi tsulum ya faɗo mata cikin mota, har seda ta ɗan firgita taja da baya Dalalo mata ido yayi yace "wa kika tambaya da zaki fita?" Sosa kai ta hau yi, tana inda inda tace "ai ban same ka bane, kuma naga da su mama zamu fita ai" Ɗage duka girar shi yayi, sanna yace "Shiyasa kika ƙi tambaya kenan?" Shiru tayi ta sunkuyar da kai ƙasa a hanakali tace "to kayi haƙuri" Murmushi yayi haɗe da faɗin "Ah lallai asalin mumtaz ɗin da na sani ta fara dawowa tunda har ana iya faɗin nayi haƙuri" Murmushi kawai tayi Ya sake cewa "muje ki raka ni wani waje" Taso yin gaddama, amma bata ga wannan fuskar ba. Motar shi suka koma daidai fitowar mama daga sasan mummy ta hango fitar su, murmushi tayi kawai ta wuce nata sasan. Suna tafe yana mata hira, tun tana basarwa har ta dawo tana bashi amsa Daidai ƙofar wani ɗan madedecin guda me kyau yayi parking Kallon shi tayi sannan tace "gidan wa ne nan?" Taɓe baki yayi yace "cewa akayi na kawo ki dan Allah, ki shiga minti goma na baki ki fito" Ƙin fita tayi dan bata san ina ne ba, Shima basarwa yayi yaja seat ɗin kujera baya yayi kwanciyar shi Can ya waigo yaga itama idonta a rufe, zungurin ta yayi da hannu Sannn yace "yarinya duk a cikin mintocin ki ne, ba ruwa na" Yana gama faɗin haka ya janyo wayar shi yayi dialing no ɗin Amal, bugu biyu ta ɗaga, cewa kawai yayi "Leƙo" ya aje wayar Mumtaz na zaune taga fitowar Amal da gudu tayo kan motar Da mugun mamaki mumtaz ta kalli ya faruk da ya basar tace "Innalillahi, wallahi ban yarda ai faɗa min ya kamata kayi" Bama ta jira me zece ba ta buɗe motar Wani ihu suka saka seda ya faruk yayi saurin toshe kunnuwan shi Cike da farin ciki suka rungume juna, ko ta kan ya faruk basu sake biba sukayi ciki rungume da juna. Karkaɗa kai kawai yayi yace "Bazasu taɓa girma ba yaran nan". ****Ango TK Ana idar da sallar isha'i ya nufi gidan amarya sakina Tana nan zaune inda aka barta, ba sallah ba salati, banda saƙa da warwarar mugun abu babu abinda take tun tafiyar waɗanda suka kawo ta A hankali ta tashi ta ƙarasa gaban mudubi ta tsaya, ƙare ma kanta kallo tayi daga sama har ƙasa, a fili tace "wallahi ba ajin ka bace ni Tk, ko ta halin ƙaƙa se na bar gidan nan ba tare da igiyar ka a kaina ba wannan alƙawari ne na ɗaukar ma kaina! ta dafa ƙirjin ta haɗe da gyaɗa kanta. KUYI HAƘURI NA JINA SHIRU, JIKI DA JINI 😊 ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 WANNAN PAGE ƊIN SADAUKAR WANE GA DUK WANI MAKARANCIN "LAUJE CIKIN NAƊI" ƘAUNAR KU TA DABAN CE A CIKIN RAINA ❤️ LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg79-80 Tana nan a tsaye taji shigowar shi cikin gidan, Rufe ko ina yayi sannan ya ƙaraso cikin ɗakin da take Tk na tura ƙofar ya tsaya cak yana bin sakina dake tsaye a gaban mudubi da ido Kamar maye haka ya hau lashe baki yana wani marmar da idanu. Ta cikin mudubin take hango shi, wani tsana da ƙyamar shi kawai ke taso mata bilhaƙƙi Ba sallama ba komi haka ya wuntsulo ciki, Cike da zumuɗi yace "a ƙarshe dai kin yarda an kawo min ke amaryata" Yana ƙoƙarin kai hannu jikin ta A fusace sakina ta jiyo ta bige hannun shi, cikin fusata tace "Kar ka kuskura ka sake kai hannun ka jiki na malam" Dariya Tk ya saka haɗe da shafa ƙeyar shi, koma da baya yayi ya zauna a gefen gado sannan yace "Halan iyayen ki basu ce maki gidan aure suka kawo ki ba?" Banza tayi da shi ta buga tsaki ta shige toilet Gyaɗa kai yayi haɗe da faɗin "gama ki fito, zaki gayan wanda kikayi ma tsaki yar gidan mugu" Tun yana saka ido yaga fitowar sakina daga toilet har ya koma ya fara kallon agogo Da dai yaga abin ya wuce gonabda iri ya miƙe haɗe da faɗin "ko kashin danƙo kike yi ai yaci ace kin gama shi" Tura ƙofar bayin yayi, Da mamaki yake kallon sakina da tayi zaman dirshen a ƙasa Ranƙwafowa yayi ya taɓata, da sauri ta buɗe ido haɗe da ja baya tace "miye haka?" Ɗaure fuska TK yayi yace "baki da hankali ne zaki fara bacci a cikin toilet? nan wajen bacci ne akace maki?" Banza tayi da shi ta juyar dankanta can Gyaɗa kai kawai yayi ya juya ya fice Ɗayan ɗakin ya shiga ya gama duk uzirorin sa sannan ya shiga kitchen ya ɗakko cups da kuma juice ya fito a palo ya tsaya ya saka sleeping pills a cup ɗaya sannan ya tsiyaya juice ɗin a ciki ya nufi ɗakin Daidai sakina ta gaji da zaman bayin ta fito Kallo ɗaya tayi masa ta watsar, Gefen gadon ta zauna haɗe da cire lulluɓin jikin ta Kamar wani mutumin kirki Tk ya matsa kusa da sakina, Cikin dabara ya fara magana,"ki fahimce ni mu nema wa kanmu mafita sakina, kin san nima ba son ki nake ba, kamar yarda akayi maki dole to nima dolen akayi mani, Abinda nake so dake shine, ki kwantar da hankalin ki muyi musu lamɓo kamar mun haƙura, daga nan zuwa sati ɗaya nasan sun gama sakin jiki da mun haƙura da juna, ni kuma daga wannan lokacin se in sake ki kije ki auri wanda kike so nima na auri wacce nake so" Kafe ta da kallo yayi yaga a wani yanayi ta tarbi maganar tasa Murmushi sakina tayi, tana jin sanyin nutsuwa na kama ta Cike da jin daɗi da fara'a tace "Da gaske kake Tk?" Gyaɗa kai yayi shima murmushi ɗauke da fuskar shi ganin yarda tayi saurin faɗawa tarkon shi Gyara zama tayi ta fuskance shi da kyau tace "To muyi ma juna alƙawari" Kai tsaye yace "alƙawarin me?" A ido ta kalle shi tace "babu wani abu da ze taɓa shiga tsakanin mu har mu rabu" Da sauri Tk yace "da me kike tunani?, ai ki saka a ranki yarda kike zaune a gidan ku haka zaki zauna a nan, ba wannan maganar ma" A take sakina ta ɗauki yarda ta aza wa maganar ta da Tk, Shiru tayi tana ta saƙe saƙen abubuwan da ya dace tayi bayan rabuwar ta da TK. Tashi yayi ya nufi ƙofa sannan ya waigo yace "nan ɗakin yayi maki ko can kike so? Taɓe baki tayi tace "it's okay nan" Har ya fice ya dawo ya ɗauki juice ɗin da ya watsa ma pills a ciki Fuska ba yabo ba fallasa tace "nasha ni ka aje ma ai?" A fakaice yayi murnushi ya yace "bari na kawo maki naki dai" "to" kawai tace ta gyara kwanciyar ta Tk na fitowa palo, ya nufi kitchen ya zubar da rabin wannan sannan ya sake ɗaukar me sanyi ya cikasa cup ɗin tukun ya koma ɗakin Ko kallon shi bata yi ba ta karɓa Kofin ta kai baki, har wani lumshe ido take tsabar yarda sanyin juice ɗin ya ratsa ta Tk na tsaye, seda ya ga ta kusa shan rabi tukun yace "mu kwana lafia" Ko tanka shi batayi ba ta ci gaba da sipping juice ɗin ta. *****Ya faruk Wasa-wasa sedai ya bar mumtaz a gidan Amal yace zuwa bayan magrib ze dawo Sam Amal kasa ɗauke ido tayi daga kallon mumtaz, saboda tsananin mamaki da kuma al'ajabin komi da yaƙi barin ta Faska mata duka a cinya mumtaz tayi tace "kar ki cinye ni malama, kallon ya isa haka" Amal na sosa cinyarta tace "wallahi ganin abun nan nake kamar a mafarki mumtaz, wai ya faruk ya zama mijin ki har kike masa yarda kika dama" Kai tsaye mumtaz tace "To Allah ya kashe ya bani, ya son ranki?" Ihu Amal ta saka tsabar ƙwaƙwalwar ta takasa riƙe jin daɗin da take a ciki Cike da azarɓaɓi tace "wallahi kunyi mugun dacewa mumtaz, se yanzu na tabbatar da baku wani dace da khalid ba sam, nifa na jima da zargin dama ya faruk na son ki wallahi" Taɓe baki mumtaz tayi tuno mata da sunan kalid da amal tayi, can tace "Haka Allah ke abin shi, dama kana naka ne Allah na nasa, kuma na Allah shine daidai akan namu" Ko sallar basu tashi sun yi ba, mijin Amal ya shigo palon haɗe da kiran sunan Amal Tashi Amal tayi ta fito zuwa palon, ya faruk ta gani zaune Sam kasa ɓoye murnar ta tayi, cike da ɗoki tace "oyoyo ya faruk" Murmushi ya faruk yayi yace "kuna lafia?" Da sauri ta juya ta nufi kitchen ta haɗo mishi abun motsa baki sannan ta dawo Ruwa kawai ya sha yace "kice ta fito mu tafi, akwai inda zani" Ɗan ɓata rai Amal tayi sannan tace "Dan Allah yaya" Be ma bari ta gama faɗin me zatace ba yace "no Amal, wani lokacin dai" Jiki a saɓule ta koma ɗakin da mumtaz ke zaune, tace "ki fito zaku wuce" Daga zaunen da take tace "ya dawo wai?" "eh" tace sannan ta ɗauki hijabin ta dake aje a gefe. Kan mumtaz a ƙasa ta gaishe da mijin Amal, ya faruk na ta satar kallon ta a fakaice har suka fita. **** Uku da rabi saura na dare Tk ya turo ɗakin da sakina ke ciki, wata muguwar dariya Tk ya saka Matsawa yayi ya ɗaga hannuwan ta Ya ɗanyi mata cakulkuli yaga ko motsawa batayi ba Sake ɓaɓɓaka wata dariyar yayi sannan yace "an gaya maki kowa sakarai ne irin ki, ai ko zan sake ki bazan bari ki tafi hakanan ba ya mori sadaki na ba" Hmmmm!! daga nana labari ya sauya, Tk dai ya saɓa alƙawarin da suka yi shi da sakina A daren ranar ya hakke ma sakina da sam bata cikin hankalin ta. Abun da Tk yayi ya wuce hankali sam, Kusan zamu kira abun da fyaɗe kai tsaye Tunda ya gama hankalin shi ya dawo jikin shi yabar ɗakin ya koma nashi ɗakin yayi kwanciyar shi nan da nan bacci yayi awon gaba da shi. Asubar fari sakina ta farka daga mugun baccin datayi, Jan ƙafarta na farko datayi ya tabbatar mata da ba haka ta kwanta ba Da ƙyar da dabara ta tashi zaune, alamomin data gani da kuma tsantsar azabar da take ji ya tabbatar mata da abinda Tk yayi mata Hankali a tashe ta samu ta lallaɓa ta sakko daga kan gadon, sam tsayuwa na neman gagarar ta Tana tsaye dafe da bango Tk ya buɗe ɗakin ya shigo Ido cikin ido sakina ke kallon shi Tsabar yarda take jin bushewar zuciya yasa idanuwan ta bushewa ƙamas Da ɗan sauri TK ya matsa kusa da ita Cike da duniyanci yace "ashe kin tashi amarsusu" Maganar shi ji tayi kamar ya daɓa mata wuƙa a ƙirji Yarda take jin zuciyar ta kamar ta shaƙe shi har se ya dena motsi Matsowa yayi daf da fuskar ta yace "kin ɗauka kowa ma wawa ne irin ke da ubanki?, Be jira cewar ta ba ya ɗora da "in ma zakiyi ɗammarar zama dani to kiyi, in ba haka ba ke zaki wahalar da kanki a banza a wofi?" Yana gama faɗin haka ya juya yayi ficewar shi ko duba da yanayin datake a ciki beyi ba ya balle ya temaka mata. Tk na fita sakina ta durƙushe a wajen ta fashe da kukan baƙin ciki Karkuce kuka na hankali, kuka take na fitar hankali da kuma tsanar duk wani wanda ya shafi Tk Cikin hargowar kuka tace "wallahi, tallahi sekayi mugun danasani na wannan aika aikar da kayi min". A ranar seda sakina tasha baƙar wahala kafin ta samu kanta. Ta can ɓangaren su mama kuwa ana ta shirye shiryen miƙa mumtaz gidan nata mijin A hankali kamar kuma da wasa gida ya fara cika kamar ba last week akayi biki ba Duk da gidan be kai ko tabin cikar wancan taron ba, amma ba laifi ƴan'uwa nata halartowa domin shedawa da idanuwan su Abun har yaso ba kowa mamaki Da safe wajajen sha ɗaya saura warce zata yi wa mumtaz kitson amarci ta iso Kun san dai gwanar taku basa shiri sam da kitso Seda mama tayi kamar zata maketa kafin a gama kitson Ana gamawa me ƙunshi tazo, ta yarfa mata shi a farar fatar nan, Masha Allah, ba'acewa komi. Ya faruk kam ya bar mus'ab da uncle ƙasim wajen tsare bokan su uncle Abbas, shi yana can shi da su ya sabiha da ya maryam wajen haɗo wa mumtaz kayan da zatayi fitar buɗar kai da umma babba da kanta ta shirya hakan a gobe kafin ango ya ɗauki amaryar sa su tafi. Sosai umma babba ta sanar da taron buɗar kan babban ɗanta a gobe Duk wata ƙawar ta da tai tasan da zaman taron a gobe Haka mama ba'a barta a baya ba, itama ta gayyaci ƙawayen ta sosai Wasa wasa, gida ya kacame da sabuwar hidima. Su umma ƙarama da sauran sun samu kwanciyar hankali tunda sukaji abinda bokan nasu ya sanar da su Haka itama umma ƙarama ta saki jiki sosai a ka shiga hidima da ita harda ƴaƴan ta ba'a barsu a baya ba. *****Khalid A fusace mami ta tura ƙofar ɗakin shi ta shiga Kamar koda yaushe yana kwance idon shi a rufe duk da ba bacci yake ba Bakar shi tayi a ƙafa ya buɗe idanun shi da suka kaɗa sukayi jajir Jiki a sanyaye ya tashi zaune yace "lafia mami?" Galla mishi harara mamin tayi tace "wallahi khalid na gaji da wannan halin da ka tsirar ma kanka, Tunda kaji labarin an aura ma yarinyar nan ɗan'uwan ta ka wanu susuce ka fita hayyacin ka, Ina kai ka sake ta da kanka ba wanda ya saka ka?" Shiru kalid bece komi ba kanshi a ƙasa Mamin ta ɗora da "wallahi na gaji to, ka dena fita sam, aikin ma ka dena zuwa, abinci se nayi da gaske kafin kaci saboda ka ɗora ma kanka wahalar banza data wofi Shiyasa tun farko nace karka sake ta, kawai dai zaka nemi warce zata haifa maka ƴaƴa na gari amma bance ka sake su ba, Dole ko ka ƙi, ko ka so kacire ta a ranka tunda har Allah yasa ta zama mallakin wani, kuma mu gode wa Allah ma ba seda aka fara tara ƴaƴa ba tukun muka san halin ta Gwara da aka sani tun wuri" Can kuma ta sausauta murya ta koma rarrashi. Tun ranar da mumtaz ta ɗauki wayar goggo safiya tayi mishi msg khalid ya rasa sukunin kanshi bayan ya karanta saƙon ya biyo da kira, a lokacin wayar na hannun ya faruk, nan kuwa ya karta mishi warning me zafin gaske da fayyace mishi abubuwa da yawan gaske a game da satar da mumtaz keyi Da yake yayi nisa bejin kira yasa yace "ai da bayani za'aimin tun farko na fahimta ba wai kaje ka aure min mata ba" Ya faruk be wani tsaya ya saurare shi ba ya kashe kiran haɗe da blocking number shi daga wayar goggo safiya. *****RANA BATA ƘARYA.. Tunda garin Allah ya waye masu decoration suka iso Gidan yana da girman gaske kamar yarda na faɗa a baya Shiyasa zeyi wahala in ana biki kuga sun fita wani waje da sunan kama hall. Ma sha Allah su ya sabiha sun tsaya tsayin daka wajen ganin komi ya kammalu Ba ƙarya an shirya wajen yayi kyau matuƙa Baloons ɗin da akayi kwalliyar wajen da su su kansu abun kallo ne Kala uku sukayi using, sky blue, baƙi se fari Haka kujerun wajen gaba ɗaya farare ne, se ɗan kwalliyar baƙi da sky blue a saman teburin Ko wani teburi da sunan wanda ya dace ya zauna a wajen Side ɗin abokan ya faruk daban abokanan umma babba daban sanan na mama daban Se wajen da ango da amarya zasu zauna shi kanshi wajen abun kallo ne, Sannan wajen da ƴan'uwa da abokan arziki da zasu zauna daga can gefe. Mumtaz kam bata gayyaci ko mutum ɗaya ba acewar ta ai biki ɗaya ne. Tun kafin azzahar me makeup ɗin da zata yi wa mumtaz ta iso, wannan karon babu wani cewa banaso, da kanta tace "ki tsatso ni infi kowa fita fa" Yarda tayi maganar seda taba kowa dariya a wajen Ita kanta seda ga baya taji kunyar abinda tace. Abun mamaki umma babba itama musaman ta sa aka kira mata me kwalliya har gida. Ta can ɓangaren yaya faruk shi zamu iyacewa taron shi ya fi na kowa, Tunda ba ɗaurin aure, shiyasa ya yi gayya sosai wannan karon Gaba ɗaya abokab shi wankan blue shadda sukayi se baƙin takalmi da baƙar hula Shikuma yayi wankan farar shadda ƙal da baƙar hula. Ma sha Allah, ku hango tsarin da kanku ku gani 😊 Biyar saura wajen ya ɗinke sosai da mutane, shigowar iyayen amarya da ango ake jira sannan shigowar amarya da angon. Mamace ta fara isowa bayan MC ya sanar da shigowar ta, tana a tsakiyar ƙawayen ta da ko wacce ka kalla zaka san nera ta zauna ba ƙarya Gaba ɗaya maman wankan blue black lace tayi ta amsa sunan shi. Seda suka sami waje suka zauna, sannan MC ya sanar da shigowar hajiya umma babba da nata tawagar Ba ƙarya itama itama a tsakiya suka sako ta, bakin nan nata kamar gonar audiga saboda fara'a Wankan ta itama yayi kyau ba ƙarya, inda ta saka farin lace me ratsin baƙi a jiki Itama ta samu waje ta zauna. Seda kowa da kowa ya nutsu ya zauna sannan MC yayi sanarwan shigowar ya faruk da mumtaz da har yanzu ya faruk ya kasa yarda cewa ita ce saboda yarda shigar fari da baƙi yayi mata masifar kyau Da gudu ya sabiha ta ƙaraso da sky blue ɗin net sharara ta rufa wa mumtaz akan goggoron ta, sannan tace "yes, zaku iya shiga Tunda suka fara takowa, wajen ya ruɗe da tafi, wasu na guɗa wasu suna sowa Mama kam ta kasa ɗauke idanun ta akan su, banda murmushi da hamdala babu abinda take Umma babba kam miƙewa tayi ta tarbosu har seda ta dangane dasu da gujerar su Tajuddeen me hoto na gaba gaba yana haske su ta ko wace kusurwa. (ƘANI NA YANA PICS ƊIN BIKI, SUNA, BIRTHDAY, DA KOMI MA, KUMA A KO WANI GARI 👉 😊 KUKE, A CIKIN FARASHI ME SAUKI DA RAHUSA, ZAKU IYA TUNTUƁAR SHI TA WANNAN NUMBER 09078408747, KU GWADA BABU DANASANI A CIKI ) ***TK Tun da rana da ya leƙa sakina ya aje mata abincin da yayi musu order yace mata "ki shirya anjima zamu je buɗar kan ya faruk da mumtaz" A mugun firgice da kuma mamaki ta ɗago, murya a dishe tace "wacce mumtaz ɗin kake nufi?" Har ya saka kanshi ze fice ya dawo yace "Mumtaz nawa kuke da su a dangin ku?" Ganin kamar bata fahimce shi ba ya tsaya yayi mata bayanin auren mumtaz da ya faruk dalla dallah sannan ya fice haɗe da faɗin "kar kuma ki ɓatan lokaci" yana ficewa sakina tayi jifa da ledar abincin haɗe da gwara kanta da jikin gado Cikin kuka take faɗin "ya za'ayi ma na ƙare akan TK mumtaz na auren faruk, Wallahi baze taɓa sakuwa ba"! Fuuu ta tashi ta fice daga ɗakin Bata tsaya ko ina ba se kitchen, sharɓeɓiyar wuƙa ta ɗakko ta fito, direct ɗakin Tk ta nufa ido rufe Tana shiga tayi kanshi, kwata kwata beyi aune da wuƙar dake hannun ta ba sedai jin shigarta yayi a cikin shi Wani wawan ihu ya fasa haɗe da faɗuwa wanwar. Hmmm ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg81 Cikin raɗaɗin sukar da tayi mishi yace "sakina wuƙa kika caka min fa" Ganin yarda jini ke bin jikin shi a lokaci ƙanƙani yasa ta firgice ta fice daga ɗakin da gudu tayi nata. A hankali ya fara matsawa inda ya aje wayar shi Amma da yayi motsi kaɗan zeji kamar wuƙar na sokar wani abu a cikin shi Yunƙurin da ya rinƙa yi wajen janyo wayar sa yasa jinin ƙara yawan fita Duhu duhu ya fara mamaye idon shi, amma duk da haka besa ya fasa yunƙurin kaiwa ga inda wayar shi ke ajiye ba Cikin yardar Allah ya samu ya ɗauki wayar amma sam baya iya kallon meke ciki saboda yarda duhu ya mamaye shi Shafa wayar yayi, ganin ba iya kiran ze ba, ya saketa a wajen a hankali ɗakin ya fara juya mishi. A inda ya yasar da wayar yaji kira ya shigo Duk da ba gani yake ba, kuma hankalin shi na gaf da gushewa ya janyo wayar Janyowar da yayi ya ɗauka ba tare da ya sani ba Muryar abokin shi yaji Cikin fitar numfashi Tk ya ce "Ta caka min wuƙa, kazo, kayi sauri kazo zan mutu" Daga can abokin Tk ke jin shi cikin mawiyacin hali A kiɗime yace "Guy me kake faɗa ne wai, ina waje fa, waye ya caka maka wuƙa, kana ina"? Duk a ruɗe yake zubo mishi tambayoyin haɗe da ƙoƙarin fitowa daga motar Daidai nan sakina ta fito a kiɗime tayi hanyar titi bako suturar arziki a jikin ta Juyawa yayi da niyar binta, ya fasa ya shiga gidan da ta barshi a buɗe da gudu haɗe da ƙwala kiran sunan "TK." Ɗakin sakina ya fara shiga, began shi ba, sannan ya leƙa ɗayan ɗakin da Tk ke kwance cikin jini baya numfashi A kiɗime yayi kan TK da be san a inda kan shi yake ba Sam be lura da jinin dake fitowaa ta cikin sa ba yayi kanshi ya rarime shi haɗe da jijjiga shi yana ambaton sunan shi Maida shi yayi ya aje da niyar kiran uncle Abbas a waya Se a sannan idon shi yakai ga wuƙar dake cikin shi A tsorace yaja da baya yana bin jinin dake a ƙasa da kallo Da ƙarfi yace 'inaaa, wallahi bazan taka sahun ɓarawo ba" yayi waje da gudu ya faɗa motar shi ya jaa. *****waje yayi waje fa, Fuskar kowa ka kalla kasan yana cikin annushuwa da farin ciki Da ɗan damuwa mummy ke kallon kowa, taga kowa da kowa harda amaren wancan satin da mazajen su amma bata ga TK da iyalin shi ba Waya ta ciro tayi dialing no ɗin shi, amma har ta katse be ɗaga ba A ranta tace "maybe suna hanya, ko wani abun ne ta tsaida su" Anyi bajinta a wannan taron ba ƙarya, duk da ba'awani shirya mishi ba, amma kai da ka gani zaka ce an jima ana shirin taron tsabar yarda komi ke tafiya akan tsari da tsaruwa. Bayan an gwangwaje, anci an sha, sannan akazo akayi cinikin fuskar amarya a tsakanin dangin mama da dangin umma babba Ƙwarai da gaske abun ya ƙawatar, dan an ta zabga ciniki cike da barkwanci har aka daidaita a kuɗi adadi masu nauyin gaske kafin aka buɗe fuskar amarya kowa ya ganta Tunda ya sabiha ta ɗaga net ɗin fuskar mumtaz bakin kowa be huta ba wajen faɗin "ma sha Allah, tubarakallah", shi kan shi ya faruk seda ya furta "Tsarki ya tabbata ga ubangijina me kashewa da kuma rayawa, tabbas wannan shi ake kira da sakin wawa"! Hakanan ya tsinci kanshi da murmusawa game da maganar da yayi ta "sakin wawa" Waigawa ya faruk yayi ta inda su ya sabiha ke zaune, yafito ta yayi da hannu Da sauri ta taso taje ya faruk yace "na gaji da hayaniyar nan fa, akwai kuma abinda zanyi kisa ya taƙaita abin pls" Gyaɗa kai tayi tukun ta sauka zuwa wajen MC dake ta ɓaɓatu yana kwasar nera. Biyar da kusan kwata abokan shi suka fara mishi sallama suna tafiya haɗe da mishi fatan alkairi da zama lafia. 😂 A taƙaice aka rufe komi duk da can na hango fuskokin LAUJE FANS ba haka suka so ba, dan basu gaji da gwangwajewa ba aka katse su LOL Su o'o da o'o kam kamar su fashe saboda haushi. Lalubo hannu mumtaz ya faruk yayi ya miƙar da ita tsaye tukun ya ja ta suka fice ta can bata hanyar da kowa ke fita ba Seda ya dangane ta da sasan mama tukun yace "zanje na dawo, ki shirya komin dare in sha Allah yau zamu wuce gidan mu" Sunkuyar da kai ƙasa tayi tana wasa da stones ɗin jikin kayan ta Murmushi ya faruk yayi, yatsar shi ƴar manuniya ya saka ya tallafo gemun ta ya ɗago da fuskar ta sama Ɗayan hannun yasa ya zunguri hancin ta sannan yace "ko baki shirya hakan ba?" Da sauri ta ƙwace fuskar ta ta sake yin ƙasa da kai, kunya duk tabi ta cika ta Daga can ta hango Amal nata nunosu tana kwasar dariya, tana nuna mata irin meye haka take yi Murguɗa mata baki mumtaz tayi, shi kuma ya faruk se yayi tunanin da shi take Folding hannayen shi yayi, still murmushi a fuskar shi yace "eyee harda murguɗa min baki ma kike?" Da sauri mumtaz ta dafe baki haɗe da zaro ido tace "Amal ce fa" ta nuna wajen da Amal ke tsaye Waigawa yayi daidainan Amal ta juya kamar ba ita ba Murmushi kawai yayi ya kaɗa kai, sannan yace "Ki taya ni addu'a akwai abinda zan aiwatar a cikin daren nan in sha Allah" Kafe shi da ido tayi can tace "me zakayi ya faruk?" Kallon ta kawai yake yama kasa ce mata komi Ta sake faɗin "gaba na yana faɗuwa tun ɗazu, bana son yarda nake ji ɗin nan" Kafe ta da kallo yayi, can ya basar yayi murmushi yace "kazar amarci zan je siyowa fa, wasa nake maki" Yana faɗin haka ta rufe fuska ta juya da gudu tayi ciki Murmushi kawai ya sake yi sannan yace "i have to do this for Abba ƙarami's sake, barin bara gurbi a cikin zuri'a shi kesa wasu taɓuwa" ya juya ya fice. Duk sha'anin nan da akayi umma ƙarama bata cikin gidan nan sam, Har abun ya ba ƴaƴan ta haushi, ganin kowa na nan amma ita bata nan, kuma bata ce ma kowa ga inda taje ba A wannan lokacin su suna can suna jiran lokacin da bokan su ya basu ya cika yarda zasu sami Abba ƙarami su titsiye shi akan maganar hannun jarin da suke da shi a cikin dukiyar sa. ***Tunda abokin Tk ya fice daga gidan saboda firgita da yayi ganin halin da Tkn ke ciki Beyi nisa ba ya dawo, ya sake komawa ciki Da ƙyar ya iya saka shi cikin mota yayi rushing zuwa asibiti Ganin halin da yake a ciki ne yasa suka ce ba zasu karɓe shi ba seda ƴansanda Hankalin abokin Tk a tashe ya hau kiran uncle Abbas a waya Haka wayar nan tayi ta ringing amma shiru be ɗaga ba A ruɗe ya maida akalar kiran ga ya faruk Ya faruk na zaune a cikin mota yana waya da mus'ab kiran abokin Tk ya shigo Seda ya faruk ya gama wayar shi, sannan ya amsa kiran A kiɗime yace "na kawo TK hospital sun ƙi karɓar shi" Hankali kwance ya faruk yace "nutsu kayi min magana mana, me ya samu TKn? sannan meyasa basu karɓe shi ba?" A ruɗe yake mishi bayani Ido waje ya faruk yace "ɗauke shi maza bari na tura maka address na hospital ɗin dr jamal, zan kira shi a waya yanzu" Seda ya faruk ya tura mishi sannan ya kira dr jamal, Daga nan shiru yayi da bakin shi be gaya ma kowa ba yaja motar shi ya fice. Sanda sakina ta fice daga gidan bayan aika-aikar da tayi Gida ta wuce direct A firgice ta afka ciki, babu kowa a palon se me aiki da ke kitchen Sakina bata tsaya ko ina ba ta ware ɗakin ta haɗe da rufo ƙofa harda murɗa key Jin motsin ƙofa da me aikin ta jiyo yasa ta leƙo, ganin bata ga kowa ba ta koma taci gaba da aikin ta. Se can wajen magrib mom ɗin sakina ta fito dan taga ko me aikin ta kammala tana son aikenta Da mamaki tabi palon da kallo ganin jini a ƙasa Da ƙarfi mom ɗin sakina ta ƙwala wa me aikin kira Jiki na rawa ta fito, rissinawa Idon ta akan jinin tace tace "meye wannan daga ina?" Matswa me aikin tayi, seda ta kalla da kyau sannan tace "jini ne hajiya" Kafin ta sake magana me aikin tace "kamar da ƙafa aka tako shi, naga har ta can wajen ma gashi can" ta nuna hanyar da tabi zuwa ɗakin sakina" Da mamaki mom ɗin sakina tabi takun jinin, har seda ya dangane ta ga ɗakin sakina Da sauri ta taɓa ƙofar Jin ƙofar a kulle kuma ta san bata rufe ɗakin ba yasa tace "waye a ciki?" Shiru ba amsa Juyawa tayi da sauri ta koma palon tace "waye ya shigo gidan nan?" "ina ciki ina aiki banji shigowar kowa ba hajiya" Fita mom ɗin sakina tayi waje har wajen gate ta ƙwala wa megadi kira ta tambaye shi, nan yake gaya mata yaga shigowar sakina a firgice ƙafarta duk jini. Da gudu ta koma ciki, Ƙofar ɗakin sakina ta tsaya a tsorace take ƙwanƙwasa ƙofar haɗe da kira sunan sakina Sakina najin ta amma tayi banza da ita Seda ta gaji da bugawa tukun sakinar tazo ta buɗe A kiɗime tace "me yasame ki?" ta hau dudduba jikin ta Ba wani wata wata ko ɓata lokaci sakina tace "Druging ɗina yayi sannan yayi amfani da ni ba a cikin hayyaci na ba" ta tsaya a nan Ido waje mom ɗinta tace "se akayi yaya?" "tsautsayi ya ɗebe ni na caka masa wuƙa" Da mugun ƙarfi uwar ta aza hannu bisa kai tace "na shiga uku na lalace ni asiya!!! wuƙa fa kika ce sakina? A guje ta fita ta koma ɗakin ta, jikin ta na rawa hannun na karkarwa ta janyo wayar ta, uncle junaid ta danna ma kira daidai lokacin suna tare dukkan su a inda suka saba haɗuwa Har wayar ta gama ringing be ɗauka ba Ta kira ya kai sau uku amma ba amsa, da gudu ta sake komawa ɗakin sakina da har yanzu tana a tsaye abin duniya ya ishe ta "ɗakko gyalen ki mu je" Daƙilewa tayi a tsorace tace "ina zamuje mom?" Falla mata mari tayi tace "dan ubanki har kina da bakin tambaya ta, to bari kiji wallahi in har kika bari akazo aka ritsaki anan to kashin ki ya bushe" Ba sake cewa komi ba banda fizgar ta datayi suka fice A guje mom Asiya taja mota suka bar gidan. *****Ya faruk na zaune a gaban Abba ƙarami call ɗin dr jamal ya shigo wayar shi, Ɗagawa yayi, daga can dr jamal yace "sun iso fa, case ɗin babba ne wallahi, wuƙar ta shiga cikin sosai fa" Murya can ƙasa ya faruk yace "ban fa sanar ma kowa ba a gidan, amma bari na gaya wa su Abba yanzu" Da haka suka yi sallama. ******Har aka fito da Tk daga theater ba uncle Abbas ba dalilin shi Hankali ya tashi ƙwarai da kowa yaji labarin abinda ya samu Tk, dama zargin da ake na sakina ce tayi hakan, dan labarin bata gidan ya baɗe ko ina, Ga mom ɗinta a gefe da take ta pretending kamar itama bata san inda sakinar take ba, alhalin ita ta kaita ta ɓoye ta. Wajen goma saura su Abba babba da ƙarami dama su goggo safiya, harda su mama da su mummyn Tk suka koma gida, aka bar Amir ya kwana da shi. Ta ɓangaren su uncle Abbas kuwa sun ƙagara lokacin ya cika, miƙewa tsaye umma ƙ tayi, gyara lulluɓin ta tayi sannan tace "zanyi gaba se kun iso, zuwa yanzu na san sun gama taron shirmen su" Gyaɗa kai sukayo duka, duk sun bi sun ƙagara Uncle junaid yace "nan da 30mins muna hanya muma" Da haka sukayi sallama. ***** Sanda suka shigo gida daga asibiti ba kowa a baƙi, duk wanda ka gani ɗan gida ne, kowa sasan shi ya nufa, ga gajiyar hidima ga kuma gajiyar tsayuwar hospital da sukayi Abba ƙarami na zaune a palon shi bayan yayi wanka ya kimtsa mama ta kawo mashi tea, Tana zaune a gefen shi suna firar abunda ya faru da Tk wayar shi tayi ringing Mama tafi kusa da wayar, yunƙurawa tayi ta ɗakko, sunan Abbas ta gani a rubuce Da sauri ta miƙa mishi haɗe da faɗin "ƙila se yanzu yaga calls ɗin da akayiyyi masa" Gyaɗa kai Abba ƙ yayi haɗe da kara wayar a kunne Duk a tunanin shi maganar Tk ze mishi, se yaji saɓanin haka Da mamaki Abba ƙ ke sauraron shi, can dai yace "ba matsala ku ƙaraso ina palo na" aje wayar yayi ya kalli mama yace "ki ɗauki mayafi su Abbas na shigowa" Babban hijabi ta ɗora akan kaya jikin ta sannan ta koma ta zauna. Kamar wasu mutanen kirki, uncle junaid da uncle Abbas sukayi sallama suka shigo, ɗauke da wasu files a hannun su Amsa sallamar sukayi Da fara'a Abba ƙarami yace "bisimillah ku zauna mana" Zama sukayi a kujerar dake kallon tasu Kafin suce komi ya faruk yayi sallama ya shigo Da sauri uncle Abbas ya kalli uncle junaid sannan suka kalli ya faruk dake murmushi kanshi tsaye ya ƙaraso ciki Basu gama mamakin ganin ya faruk ba se ga uncle ƙasim shima ya shigo goggo safiya biye da shi a baya Daga mama har Abba ƙ tsoro ne ya fara kamasu, ganin basu jima da rabuwa ba ai Baki sake su uncle Abbas ke kallon su Can suka jiyo ya faruk na faɗin "muna palon saman shi Abba babba" Miƙewa Abba ƙarami yayi yace "wai lafia?" Daidai shigowar Abba babba kenan shima ya ɗora da tashi tambayar "me ya faru kuma?" Uncle ƙasim yayi karaf yace "Ku zauna mana, tunda kuka ga haka ai da magana ne" A take uncle junaid ya fara jin tsintsinkewar zuciya se wani mutsu mutsu yake kamar me basir. Ɗaya bayan ɗaya sauran matan gidan ke shigowa harda manyan ƴaƴan Kowa ya shigo se yayi turus yabi kowa da kallo kafin ya zauna Ashe ya faruk ne yabi kowa da kowa ya tura mishi saƙon yana son magana da shi ta sirrin a palon Abba ƙarami misalin ƙarfe goma da rabi. Babu wanda yasan da an turawa ɗan'uwan shi saƙon, shiyasa duk wanda ya shigo se yayi mamaki Umma ƙarama ce kawai be turama ba, saboda itama yasan zata zo kodan shirin su. Kowa ya nutsu ya zauna, cikin faɗa Abba babba ya kalli ya faruk yace "kai bana son shashanci, meye haka ka wani tara mu anan kamar wasu sa'o'in ka?" Kafin ya faruk yace komi, uncle junaid ya miƙe haɗe da faɗin, "ina jin abun na family ne, nikam bari naje gobe na dawo muyi maganar data kawoni" Karaf uncle ƙasim yace "ta shafe ka mana, aikama ɗan gidane, zaka iya zama" Musu yaso yayi, amma amma ganin mus'ab ya ɗaga labule ya shigo haɗe da sallama yasa ya tsaya cak, kamar yarda zuciyar shi data uncle Abbas ma ta tsaya. INA MATUƘAR GODIYA DA ADDU'O'IN KU GAME DA ƁATAN ƘANWATA ALHAMDULILLAH, KUMA TA DAWO LAFIA MASU KIRA DA MASU TURO SAƘON JAJE DA ADDU'A ALLAH YA SAKA DA ALKAIRI, MATSAYIN KU NA DABAN NE, ALLAH YA BAR ZUƁUNCI ALLAH YA TSAREMU DA TSAREWAR SA ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD INA MATUƘAR KAUNAR KU ❤️ ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg82 Hannun Abba ƙ na karkarwa ya nusa mus'ab da ya bar ƙasumba sosai a fuskar shi yace "Mus'ab!" Cike da rauni mus'ab ya ƙaraso inda Abba ƙ yake ya rungume shi Kowa mamakin ganin mus'ab yake a wannan lokacin duk da sun san cewa baya ƙasar(in baku mance ba haka ya faruk ya faɗa ma kowa) Abba babba yace "saukar yaushe mus'ab?" Jin abinda Abba babba yace shine ya dawo da tunanin Abba ƙarami shima ya basar Shigowar mummy(matar uncle Abbas) kenan ta ga uncle Abbas zaune, Batayi tunanin komi ba ta ce "Dama kana nan nake ta faman kiran ka baka amsa min ba?" Kallon ta kawai yayi amma ya kasa ce mata komi Goggo safiya tace "ki zauna mana, ƙila wani abun ne ya tsare shi, tunda Allah ya taƙaita wahala ai da sauƙi" Taɓe baki mummy tayi kafin ta samu waje ta zauna. Ta gefe kuma uncle junaid se zungurin uncle Abbas yake da ƙafa, shima yana zungurinnshi Duk ya faruk da uncle ƙasim na lura da su. Cikin ƙagara Abba babba yace "wai meke faruwa? wannan gangankon namene?" Kai tsaye ya faruk yace "Na uncle Abbas da uncle junaid ne, se kuma umma ƙarama" Da mamaki kowa ke kallon ya faruk, har da su waɗanda aka ambata ɗin Cikin faɗa uncle Abbas yace "ohhh rainin da kayi wa kowa shine har ya fara gangarowa kaina nima?" Murmushi ya faruk yayi sannan yace "ku gafarce ni da abinda zan faɗa yanzu" Tsuru kowa yayi yana sauraron ya faruk da ya shafa ma idanun shi toka ya ɗora da "Abba ƙ ina neman alfarmar ka bar su uncle junaid da uncle Abbas gabatar maka da abinda ya kawo su kafin akai ga jin komi" Ɓata rai Abba ƙ yayi yace "meye haka kakeyi ne faruk?" Kafin ya faruk ya ce komi uncle ƙasim yace "ya kamata su faɗi abinda ya kawosu a gaban kowa da kowa a irin wannan lokacin" Nan ma kallon kowa ya koma gareshi. Cike da tsantsar rashin gaskiya uncle Abbas yace "me kuke nufi da hakan, ko kuna tunanin wani mugun abunne ya kawo mu?" Ba wanda yace mishi komi, Abba babba dai yabi kowa da kallo yana so ya tantance abinda ke shirin faruwa" Cike da rashin gaskiya ya hau buɗe files ɗin gaban shi, amma rawar da hannayen shi keyi sam yakasa samun sukunin iya riƙesu da kyau. Miƙewa tsaye mus'ab yayi, seda yayi ma kowa sallama kafin yace "A dena wani ɓoye ɓoye so muke su uncle Abbas su fayyace mana meyasa suke cin dunduniyar ahalin Abba ƙarami!" Mus'ab na gama faɗin haka aka hau kallon kallo Nan da nan zufa ta rufe su uncle Abbas duk da sanyin aircon dake aiki a palon Cikin ɓacin rai Abba ƙarami yace "baka da hankali ne mus'ab, waɗan nan ba iyayen ka bane kake faɗin irin wannan munanan maganganun akan su?" Shiru mus'ab yayi yana ci gabaa da haɗiyar zuciyar gado Uncle ƙasim da shima fuskar nan a cukune take yace "tunda ba zasu ce komi ba, bari mu kawo wanda zeyi ma kowa bayani" Abu ya fara ɓaci fa, zama na neman gagarar su uncle junaid gaba ɗaya Umma ƙarama kam saita ƙofa kawai take, dan ba zata taɓa tsayawa ta kunyata ba. Kafin kowa ya dawo daga duniyar mamakin da suka shiga uncle ƙasim ya shigo da Altine da idanun ta suka kumbura tsabar kukan data sha Wiƙi wiƙi su umma ƙarama sukayi Kunsa mara gaskiya ko a ruwa jiɓi yake. Tallaƙe ƙeyar ta yayi sannan yace "munafuka faɗa ma kowa abinda kika shuka kafin na fasa kanki" Cikin kuka Altine ta kalli mama da gaban ta banda dukan tara-tara babu abinda yake tace "ku yafe man hajiya, Wallahi duk abinda nayi maku ba da son raina bane, a bisa tirsasawar hajiya sumayya(umma ƙarama) ne da kuma waɗanda ban sani ba wallahi" Dafe ƙirji umma ƙarama tayi haɗe da faɗin "ku ji man wani sharri da tsohon daren nan, ina fatan ba dai ni sumayyar kike nufi ba??" Ido rufe Abba babba yace "dakata hajiya sumayya!" Tsit umma ƙarama tayi ta koma zaro idanu Altine taci gaba "wallahi da zuciya ɗaya na nemi aiki a gidan nan ba dan na cutar da kowa ba, wata rana ina ƙasa a kitchen mama tace na ɗan fara ɗora mata ruwa a kan gas kafin ta sakko, sega umma ƙarama ta shigo sasan ta iskoni har cikin kitchen tace min "kizo anjima da daddare ki same ni, akwai maganar da nake son yi da ke" tana gama faɗa min haka ta juya ta fice da sauri jin sakkowar mama daga sama. Ban kawo komi a raina ba naci gaba da aikina, amma can ƙasan raina murna nake ƙila wani abun zan samu daga wajen ta tunda ta saba min alkairi haka kurum. Da nagama aiki na, kusan kowa ya kwanta na tashi naje na sami umma ƙarama a ɗakin ta Maganar data fara min ba ƙaramin gigita ni tayi ba da naji tace aiki zan mata bakin raina a tsorace nace "wani kalar aiki ne haka hajiya?" Dariya tayi tace "ba wani aiki bane me yawa, hasali ma ba ze ɗauke ki minti biyar ba kin gama, amma fa se kin sa kanki" Kaina a ƙatsa nace "to hajiya, ina jinki" Wani ƙulli ta ɗakko a takarda ta miƙo min, murya ƙasa-ƙasa tace "so nake ki zuba shi a abincin Abba ƙarami, shikenan kin gama aikin ki, ba abinda ya rage sedai kija bakin ki kiyi shiru" A firgice na saki ƙullin a ƙasa na miƙe tsaye, jiki na yana rawa nace "bani ke girka mishi abinci ba umma ƙ, mama da kanta ke dafa mashi" Tsugunnawa tayi ta ɗauki ƙullin sannan tace "kin yi babban kuskure tunda har kikaji sirrin mu, kuma dole kiyi abinda nace ko kuma ki baƙunci lahira" Na tsorata matuƙa da naji haka, a taƙaice dai dole tasa na karɓi maganin nan da niyar in anjera wa Abba ƙ abinci a dining in fakaici ido na zuba mashi" ba yarda na iya haka na karɓa na fito hankali na a tashe" Shiru Altine tayi tana share hawayen ta, Kaf mutanen dake palon banda kallo-kallo babu abinda suke aika ma junan su, Umma babba kanta jin maganar take kamar a mafariki, dan bata taɓa tunanin hakan ba. Goggo safiya tayi karaf tace "ci gaba algunguma' Kan Altine a ƙasa ta cigaba "seda maganin yayi kusan wata a hannun na ban zuba ba, Kuma a lokacinne nayi yunƙurin barin aiki, amma ga mamaki na se ganin umma ƙ nayi ita da wani sun zo har cikin ɗakina sun min kakkausar gargaɗi akan duk inda naje se sun ga baya na Ba shiri washegari na samu sa'a na zuba mishi maganin a cikin abincin, Tsautsayi kuma a ranar Abba ƙarami be dawo ba, Mama da kanta tace mumtaz ta ɗauki abincin ta kaiwa masu gadi, Da naji haka shine nayi sauri na kwashe abincin na kai kitchen da niyar zan fakaici ido in zubar dan kar wani yaci ya cutu, kiran da mama tayi min kafin na zubar da abincin yasa har mumtaz ta shiga ta ɗiba taci Ganin babu wani abu da ya same ta yasa hankali na kwanciya, amma duk da haka ban bari wasu sunci ba na zubar da abincin. Daga wannan ban san komi ba, seda aka jima sannan na fara ganin sauye-sauye a cikin halayyar mumtaz da yasa na rinƙa bin diddigin ta dan nasan meke damun ta, amma bam samu komi ba" Tsit palon yayi baka jin motsin kowa sedai fitar numfashi na wasu yafi na wasu. Abba ƙarami zuguɗin yayi yana kallon umma ƙarama dabkanta ke sunkuye takasa haɗa ido da kowa har ƴaƴan ta da ke zaune hankalin su a mugun tashe. Kafin kowa ya samu zarafin magana Ahmad ya taso ƙeyar bokan da ya faruk ya kamo tuntuni Suna shigowa uncle Abbas ya miƙe tsaye da sauri haɗe da faɗin "na shiga uku" Abba babba yace "waye kuma shi wannan"? Kafin kowa yace komi bokan nasu yace "ni malamin hajiya sumayya da Abbas da kuma junaidu ne" Gaba ɗaya wajen suka hau faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!" Dafa ƙirji goggo safiya tayi tace "yau ko munga lukutar masifa a cikin gidan nan, kai jama'a ana zaton wuta a maƙera yauko gata mun ganta a masaƙa" Gyaɗa kai umma babba tayi sannan tace "humm danƙari!!" Fuska a ɗaure ya faruk yace "maƙiyin Allah, zauna ka gaya ma kowa abinda suka saka ka kayi wa bayin Allahn da basu jiba basu gani ba" Shima kanshi a ƙasa yace "Hajiya summaya itace ta haɗani da Abbas da junaidu inda suka kawo min aiki na suna so a dankwafar da cigaban Abba ƙarami, Dana buga ƙasata na gano cewa ba ta yarda za'ayi nayi kutse a lamuran shi sedai abi wata hanyar A take na fahimtar da su hakan, se suka ce min bari suyi shawara su dawo Ina zaune suka fita, basu jima ba suka dawo, se ɗaya daga cikin ƴan mazan yace "tunda har kace hakan ba ze yiwu ba, muna so ka kawar da hankalin ƴaƴan shi maza daga kan dukiyar shi, sannan ka saka musu rashin jituwa tsakanin su da iyayen, shi kuma Abba ƙarami a saka mishi halin ɓeraye gashi dai me arziƙi amma ya rinƙa sha'awar duk wani abu da ya gani a hannun abokan kasuwanci, haɗe da muguwar azalzalar zuciya, yaji in be ɗauka ba ze iya rasa ranshi. Shine na basu magani nace a saka mashi a binci, daga nan shikenan. Daga baya suka dawo min da zancen basuga yana komi ba, dan har gwada shi sunyi amma basu ga komi ba Dana bincika se na gano beci maganin ba, ɗaya daga cikin iyalan shine suka ci Danayi musu bayani se suka sauya wata shawarar na cewa a kawar da shi. nayi-nayi, amma Allah be ban sa'a ba, amma anci nasara da raba shi da ƴaƴan shi, Se kuma in zasuyi abu nakan duba musu na faɗa musu lokacin da yafi dacewa su aiwatar da abinda suke so, amma daga wannan wallahi babu wani abu da nayi, se wanda hajiya sumayya(umma ƙarama) ta dawo ita kaɗai ta nemi alfarmar in mallake mata Alhj junaid da kuna shi Alhj Abbas, akan duk wani abu datace mu suyi, to zasuyi shi kai tsaye ba tare da sun mata musu ba" Salati me ƙarfin gaske umma babba da goggo dafiya suka ɗauka Sunayi suna tafa hannuwa Mazan kam gaba ɗaya kansu na a ƙasa, bama kamar Abba ƙarami da gaba ɗaya rufe idon shi yayi ƙam yana jin ƙirjin shi na mishi nauyi. ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg83 A tsananin firgice mama ke kallon uncle junaid da kanshi ke ƙatsa, zufa tayi mishi sharkaf Kukan mummy ne ya dawo da kowa daga ɗimuwar da ya tafi Cikin kuka ta cukumi kwalar uncle Abbas tace "butulu maƙiyin Allah, dama zaman haƙuri nake da kai saboda baƙin mugun halin ka, wallahi ko ka sakeni ko ka tsammani sammaci daga kotu inda zanje in tona maka asiri wallahi" Duk zafin uncle Abbas kasa cewa komi yayi, jikin shi har wani rawa-rawa yake Tashi uncle ƙasim yayi ya shiga tsakanin su Da ƙyar aka ɓanɓare mummy daga jikin shi, ƙin zama tayi ta fice cikin kuka da nauyin zuciya. Haka mama, kukan da take ta dannewa ta kasa seda ta sake shi, still idon ta na kan uncle junaid da ya kasa kallon ta sam. Abba babba shima ya kasa cewa komi tsabar yarda abun ya dake shi har cikin ƙwaƙwalwa Gaba ɗaya wajen ma hautsinewa yayi, kukan ƴaƴan umma ƙarama gunin ban tausayi, Ya fa'iza faɗi take "umma ƙarama kin cucemu innalillahi wainna ilaihirraji'un". Kai tsaye ya faruk yace "Ku gafarce ni Abba, ni kam na riga da na gama haɗa komi da za'a maka su a kotu, suje can su girbi abinda suka shuka" Anan ya faruk ya sake fayyace musu kashe Abba ƙarami da suka sha kwatanta yi Allah baya basu nasara Da kuma irin ƙulle-ƙullen da suke shiryawa, har ma da auren Tk da sakina tayi, da shirin su na warwarewa a maida auren mumtaz kan Tkn, kaf har accident da Abba ƙ sukayi duk shirin su uncle Abbas ne. Nan ma waje ya sake kiɗemewa Basu ankare ba sedai ganin Abba ƙarami suka yi yana sassan ƙamewa idanun shi na kakkafewa gaba ɗaya kowa yayo kanshi banda umma ƙarama data fece, uncle junaid ma na ganin haka ya fece, uncle Abbas na zaune ba um ba un un se idanu A ruɗe uncle ƙasim yace Ahmad ɗakko mota bari mu sakko da shi Mama kam faɗi take "shikenan sun ƙarasa min shi, sun kashe min shi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" Ihun da mumtaz take ne ya raba hankalin ya faruk biyu, daga ƙarshe dai barin su Abba babba yayi da ɗaukar Abba ƙarami, shi kuma ya rungume mumtaz da itama ke neman fita daga hayyacin ta Hankali a tashe umma babba ke faɗin "riƙeta da kyau faruk kar ta illata kanta ayi biyu" Da ƙarfi ita da goggo safiya suka kama mama itama suka riƙe Cike da tausayi umma babba ke faɗin "Sannu hajiya zahra'u(mama) nutsu kar kema kiji wa kanki ciwo, Akwai baƙin ciki amma kar ki bari hankalin ki ya gushe ya bar jikin ki" Tana magana tana maimaita kalamar "hazbinallahu wani'imal wakil" da kusan kowa ke ambata a palon. Da mus'ab da uncle ƙasim ne suka ɗauki Abba ƙarami da gaba ɗaya baya numfashi Abba babba da kanshi ya karɓi key ɗin motar daga hannun Ahmad ganin yarda jikin shi shima yake rawa Seat ɗin baya aka buɗe, uncle ƙasim ya fara shiga se aka saka abba ƙarami aka miƙar da shi, kanshi na kan cinyar uncle ƙasim, Mus'ab da Ahmad suka shiga gidan gaba a matse, Abba babba ya figi motar da gudu suka fice. Cikin kuka mama ke faɗin "wannn wani iirin cin amana ne da yankar ƙauna, ƴan'uwan ka na jini su rinƙa maka maƙarƙashiya saboda abin duniya da duk barin shi zamuyi a nan mu tafi" Tana rungume jikin umma babba take wannan maganganun, Umma b faɗi take " ya isa haka, kiyi addu'a ne, surutun kar ya jawo miki wata matsala" Zabura mama tayi ta miƙe, gaban Tv stand taje ta ɗauki wayar ta, Sam bata yi la'akari da cewa dare ne ba ta danna wa inna hassu kira dake gidan uncle junaid Bugu biyu ta ɗaga, fashewa da kuka tayi tace "kizo inna hassu su ya junaid sub kasaarani sun kashe man miji bayan mugayen manufofin su da basuyi tasiri ba se a yau" Hankali a tashe inna hassu ta miƙe zaune tace "me kike nufi? Abubakar ɗinne ya mutu?" Sam hankalin mama baya jikin ta, "eh" kawai tace kafin ta aje wayar A kiɗime inna hassu ta fito palo ta nufi ɗakin mum Asiya da shigar ta kenan A firgice tace "yanzu aka kirani Abubakar(Abba ƙarami) ya rasu Salati mum asiya ta buga haɗe da dafa ƙirji Hankali a tashe tace "mun shiga uku, wannan wani irin masifa ne daga wannan se wancan" Da sauri ta rarumi hijabi ta ɗora akan kayan baccin ta tace "muje inna hassu, ai bamu ga ta zama ba" A tsohon daren nan suka nufi gidan Abba ƙarami. Da suka zo kuma suka ji saɓanin abinda mama tace, nan hankali yafi na ɗazu tashi Banda kuka babu abinda mum asiya keyi, Cikin tashin hankali take faɗin "shine yasa min ƴa a cikin masifa, wallahi tallahi ba zan yarda ba, sedai koma meye ya ƙare a kanshi shi kaɗai" Inna hassu kam ba baka se kunne, dan abin ya wuce da tunanin ta sam. Tuburewa mama tayi tace "se ta tafi hospital ɗin itama" Umma babba tace "ai dole ko mu hankalin mu ai ba kwanciya zeyi ba muna a nan". Goggo safiya, mama, umma babba, aunty(matar uncle ƙasim), inna hassu, su biyar umma babba ta kwashe su a mota bayan ya faruk ya gaya mata asibitin dr jamal aka kaishi Su umma babba na fita ya waiga inda su ya maryam sukayi cirko-cirko kowa hankalin shi a tashe yace "ku kula da gidan, bari na bi bayan su" Mumtaz na a jikin shi, seda ya zagaya ya saka ta a seat ɗin gaba sannan ya zagaya shima ya shiga yaja suka tafi Suna tafe tana ci gaba da kukan, Da ƙarfi ya taka burki yace "wallahi zan fasa zuwa dake in bakiyi shiru ba, haka zamu shiga cikin hospital ɗin kina rusa kuka?" Da sauri ta kaɗa kai dan taji tsoro da birkin da ya taka "To share hawayen ki, babu abinda ya same shi, shock ne kawai" Da bayan hannu ta shiga share hawayen ta, ta hau sauke ajiyar zuciya. Sanda su Abba suka isa har an tanaji streacher a wajen parking lot Suna isa ba awani ɓata time ba aka shiga da shi ciki. Nan suka tsaya cirko-cirko, basu kai minti talatin da isa ba motar umma babba ta iso Ita da kanta ta riƙe mama har suka ƙarasa wajen da su Abban ke tsaye duk sun kasa zama Cikin kuka mama tace "ya mutu ko?" Cike da tausayawa Abba babba yace "be mutu ba zahra'u, addu'a zamuyi masa Allah ya tashi kafaɗun sa" Kamata umma babba tayi tace "zauna a nan karki faɗi" Ba musu mama ta zauna haɗe da aza kanta a kafaɗar umma babba. Su ya faruk na isowa mumtaz ta ƙwace hannun ta daga cikin nashi ta nufi inda mama ke zaune, kusa da ita ta zauna itama ta ɗora kanta a jikin maman Daga can gefe ya faruk na tsaye yana kallon su Kan maman shi a kafaɗar umman shi, sannan kan mafi soyuwar matar shi a kafaɗar maman shi Besan lokacin da ya hau furta "Alhamdulillah" ba, haɗe da sake jin ƙaunar ta na ratsa jini da jijiyoyin jikin shi. Suna a nan zaune har wajen huɗu saura na asuba dr jamal ya fito, Cike da girmamawa ya gaishe da iyayen aminin nashi sannan yace "zaku iya tafia gida Abba, zuwa da safe se ku dawo, mun samu numfashin shi Alhamdulillah ya samu bacci kuma" Kai tsaye mama tace "zan tsaya ni kam, bazan iya komawa ba gaskiya" Jinjina kai Abba babba yayi sannn yace "ku muje gidan, ita seta tsaya" Hakan akayi kuwa kowa ya tafi, umma babba har ta miƙe ta dawo saitin mama tace "Me za'a tawo maki da shi da safen?" Murya a dishe tace "kaya marasa nauyi kawai" Umma babba ta sake cewa "abinci fa?" Shiru mama tayi can tace "anything" Snnan umma b ta miƙe haɗe da faɗin Allah ya bamu alkairi yasa kuma muji shi, tabi sahun sauran. Ya faruk da mumtaz suka saka mama a tsakiya Ahmad da mus'ab na tsaye suma Ya faruk yace "ki kwantar da hankalin ki mama, ki dena kukan in sha Allah komi yazo ƙarshe" Sake fashewa da kukan tayi tace "ya junaid fa faruk? ɗan'uwana ne fa in kowa zemin haka ban taɓa tsammanin hakan daga wajen shi ba, wai harda hajiya sumayya da nafi kusanci da ita akan kowa a cikin gidan nan" Ta ɗora da "kai innalillahi wainna ilaihirraji'un, Allah ya sani sub cutar dani da alhalina, sub cutar da zukatan da basu san komi ba se alkairi" kuka yaci ƙarfin ta takasa cigaba da maganar Nan dai suka haɗa baki dukan su suka rarrashe ta Kafin su rakata har ƙifar ɗakin da Abba ƙarami ke ciki Kallon ya faruk mus'ab yayi yace "ka ɗauke ta kawai kuje, ni da Ahmad muna nan" Murmushi ya faruk yayi, dafa kafaɗar su yayi yace "I trust u guys, nasan ba wani shege" Dariya Ahmad da mus'ab sukayi gane me ya faruk ke nufi da ba wani shege. daga nan ya wuce wajen dr jamal sukayi magana, kafin ya dawo yaja hannu mumtaz suka wuce. Titi tsit babu kowa saboda dare, haka ya faruk ya saki mota hankali kwance Memakon mumtaz taga sunyi hanyar gida se taga sun ɗauke wata hanyar daban har taso tayi magana ta fasa ta dai ci gaba da kallon hanya Nasarawa taga sun nufa, a take gaban ta ya faɗi tunowa anan ne gidan ya faruk ɗin yake Ta gefen ido yake kallon actions ɗinta, ganin ta dake itama ta basar yasa shima basarwa har kai makeken gate ɗin gidan nashi sannan ya danna horn Seda ya danna kusan sau uku tukun gate man ɗin yaji Leƙowa yayi, ya faruk ya sauke glass ya leƙo da kanshi ya ganshi, sannan ya koma da sauri ya tura gate ɗin ya shiga. Ba can wajen da aka tana da domin parking ya nufa ba, gaban ƙofar da ze sada ka da cikin gidan ya tsaya sannan ya kashe motar kwashe wayoyin shi yayi, sannan ya fito, da kanshi ya buɗe mata ƙofar itama ta fito ya riƙe hannun ta suka haura har ƙofar palon sannn ya saketa ya buɗe ƙofar tukun yace "bisimillah" Da ƙafar dama ta shiga haɗe da sallama duk da tasan babu kowa a ciki Ko wutar palon be kunna ba yaja ta zuwa bedroom A gaban mirrow ya aje wayoyin shi da mukulin mota sannan ya kunna heater Waigowa yayi ya ganta tsaye bata zauna ba A hankali yace "baki gaji ba kenan?" Zumɓura baki tayi ta zauna a gefen gadon da tunda ta shigo idon ta ke a kanshi A ranta tace "choice ɗina" Aircon ɗin ɗakin ya kunna, ya daidaita temperature ɗin ta sannan yace "ke zaki fara shiga ko in shiga?" Kallon shi tayi tace "ina?" Kai tsaye yace "wanka mana, ko haka kike kwanciya bakya wanka" yayi maganar da alamun tsokana A fakaice ta murguɗa baki, duk da ya ganta basarwa yayi ya shige toilet Be wuce minto sha biyar ba ya fito ɗaure da towel, ɗaya a jikin shi ɗaya a hannun shi yana goge sumar kanshi Da sauri mumtaz ta kauda kai haɗe da jin bugawar zuciya da ƙarfi Firt time da ta taɓa ganin ya faruk a haka, tun daga wannan kallo ɗayan bata yarda ta sake na biyu ba Yana a gaban mirriow tsaye yace "kije ki watsa kema mu samu mu kwanta kafin asuba tayi" Gajiyar dake jikin ta yasa ba wani musu ta nufi bayin itama Sosai tayi wanka da ruwan ɗumi, duk ɗaɗɗaurewar da jikin ta keyi taji ya fara sakewa a hankali Babban towel ta ɗauka ta ɗaura sannan ta mayar da hijabin ta tukun ta fito Sanda ta fito shi har ya hau gado ya kashe hasken ɗakin Hasken dake jikin aircon ke hasko mata shi Matsowa tayi gaban gadon, a hankali tace "ya faruk babu kayan sawa ne" Janyota kawai yayi, batayi aune ba taji ta faɗa gadon A gajiye ya faruk yace "nima haka na kwanta, babu kaya anan" Shiru tayi ta hau muzurai, can tace "bari na ɗakko wanda na cire na maida to" Banza yayi da ita, sema ƙokarin cire mata hijabi da yayi ya rufa musu bargo. Lamo mumtaz tayi tana jin yarda bugun zuciyoyin su suka ƙara sauri akan yarda suke bugawa Shi kanshi ya faruk da niyar baccin gajiya ya kwanta, amma tunda ya riƙe mumtaz a jikin shi yaji ya nemi baccin ya rasa. A hankali yake shafa kanta har bacci-bacci ya fara ɗaukan ta, Daga ƙarshe dai sabon al'amari ya kankama a wannan dare me ɗinbin tarihi da tsayawa a rai. ASUBAH TA GARI YA FARUK DA AMARYA MUMTAZ 😎 ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 LAUJE CIKIN NAƊI NA ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN) MARUBUCIYAR 👹 MAKIRCI KISHI DA ALJANA WANI HANIN GA ALLAH ƘADDARAR MU LAUJE CIKIN NAƊI WATTPAD@ZAINABFALALU8 Pg84 Tunda ya samu tayi bacci bayan doguwar rigimar da yasha Ya tashi yayi wanka ya fuskanci alƙibila yana me nuna godiyar shi a wajen ubangiji. Har aka kira sallar asuba yana nan zaune, bini bini ya leƙa mumtaz da ke baccin gajiya da rashin sabo Haka har aka kira sallar asubah ya canza kaya ya fita zuwa masallaci. Ya faruk na dawowa sallah ya tashi mumtaz itama Haka yayi ta fama da ita har ta samu ta kintsa ta gabatar da sallah A dudduƙe ta haye gado, ba wani ɓata lokaci bacci ya sake awon gaba da ita. Ya faruk yaso ya ɗan rintsa shima, amma tunowa da yayi akwai sauran ƙura a ƙasa yasa ya fasa, Wanka ya sake yi ya shirya, be tashi mumtaz ba ganin yarda baccin ya ke mata daɗi kawai ya fice. Kafin yaje asibitin seda ya je gida, Direct sasan umma babba ya nufa Kowa yana nan jigum jigum kamar anyi mutuwa a gidan Ɗakin umma b ya shiga a nan ya iske ƙannen shi, jiki a sanyaye suka hau gaishe shi Kiran ya maryam yayi gefe, Yace "umma fa?" "Tana wajen Abba b" "okay" kawai yace sannan ya ya ce "Ki shiga part ɗin mama ki duba ɗakin mumtaz ki ɗibo mata kayan da zata ɗan iya amfani da su" yana maganar yana wani basarwa ganin kallon da ya maryam ke masa murmushi tayi tace "to ai mun kai mata kaya tun shekaran jiya da mukayi jere, suna nan mun jere mata" A ranshi yace "kash, me yasa ban duba ba" Basarwa yayi yace "okay tanx" ya juya ya fice Yana fita suka saka ihu hale da shewa gaba ɗayan su yana jin su, murmushi yayi ya gyaɗa kai kawai yayi gaba. Sasan Abban ya nufa kai tsaye Yana shiga ya iske umma ƙarama zaune a ƙasa dirshen, idon nan nata ya kaɗa yai jajir Daga can ciki kuma yana jiyo muryar Abban nasa na tashi sama-sama Ko kallon umma ƙ beyi ba ya ƙarasa ƙofar haɗe da yin sallama be wani jima a tsaye ba Abban ya fito da shirin fita a jikin shi, umma babba na biye da shi a baya Kanshi a ƙasa ya gaishe da iyayen nashi, sannan yace "umma b me za'a kai hospital ɗin?" Cike da annushuwa tace "tun wajen 8 aka kai musu komi, nima da na kammala abinda nake zamu je" Tunda yaji haka yayi musu sallama ya fice. Abba babba na fitowa ya iske umma ƙarama zaune Cikin fushi yace "ohhh bakiji me nace maki ba ko?" Murya a dishe umma ƙarama tace "dan girman Allah ka tsaya ka saurare ni, wallahi sharrin zuciya ne da kuma makircin Abbas da junaid" Abba babba be bari ta ƙarasa ba yasa ƙafa ya tokareta da ƙarfi, zaro mata manyan idanun shi na gado yayi, ya nuna ta da yatsa yace "fita, ba zan taɓa sauraron ki ba wallahi, kuma ba zan taɓa hana hukuma aiki a kanki ba mara imani" Da rarrafe umma ƙarama ta bar sasan riƙe da gefen kafaɗar ta inda Abba ya tokareta. Ya faruk na fita be tsaya ko ina ba se wani resturant dake gaf da unguwar su chips and liver sauce ya siya sannan ya ƙarasa gidan Har lokacin mumtaz bata tashi ba, Motsin shi ne ma ya farkar da ita, se kuma yunwar dake ƙwaƙular ta Wanke baki kawai tayi ta hau kan abincin Seda tayi nak tukun ta ture. Cike da tsokana ya faruk yace "yau ma babu gaisuwa amaryar faruk?" Banza tayi da shi ta kauda kanta gefe Bugun duniyar nan yayi dan ta tanka mashi, amma mumtaz tayi banza, banda aikin zumɓure-zumɓure babu abinda take. Wajen sha ɗaya saura yace "tunda kinƙi kula ni bari nazo na fita" Da sauri mumtaz tace "indai hospital zaka koma zanje" Shima da sauri yace "a hakan kina ciccin maganin zaki bini?" Ƙara ɓata rai tayi, badai tace komi ba Murmushi ya faruk yayi yace "bama inda zaki bini yarinya, nan zaki zaman ki har sena dawo" Kafin mumtaz tayi magana kira ya shigo wayar ya faruk Ganin mus'ab ne me kiran yasa ya ɗaga da sauri haɗe da cewa "hope ba wata matsala?" Daga can ya mus'ab yace "to Abba ƙarami ne ke son bamu matsala, yanzu haka ma shine yasa na kira ka" Gyara zama ya faruk yayi haɗe da janyo mumtaz ta dawo jikin shi, sannan yace "Abban ya farka ne?" Seda mus'ab ya aje numfashin takaici kafin yace "tun cikin dare ya farka, kuma muke ta fama fa shi ba" Gyaɗa kai ya faruk yayi yace "ina hanya yanzu kawai" Ya aje wayar, gaba ɗaya mood ɗin shi na sauyawa, yasan sarai dama zasu sha fama da Abba ƙarami akan case ɗin nan A sanyaye mumtaz tace "Abba ya farka ne?" "ya farka, sannan yace "shirya ki same ni a mota" Gaba ɗaya bata wani jin ƙarfi, haka dai ta daure ta shiga ta watsa ruwa. Har ya faruk ya sauka ƙasa ya tuna da be gaya mata akwai kayan sawa ba ya dawo Daidai ta fito daga wankan, walldrop ya buɗe, se ga kayan ta jere Kallon shi tayi bata san sanda tace "kai yaushe ka ɗakko kayan"? Murmushi yayi yace "dama suna nan" Temaka mata yayi ta zaɓi wanda zata saka sannan yace "ina mota kiyi dauri ko in tafi in barki". Tunda suka doso wajen goggo safiya ke kallon yarda mumtaz ke tafiya tana yatsina fuska kamar warce ake ma dolen tafiya. Murmushi kawai tayi haɗe da kauda kai, can ƙasan ranta tace "kamar dan junan su akayi su". Umma babba, Goggo safiya da aunty ne kawai a wajen, se mama da zuwan su yasa ta fito palon ta bar wa ƴan mazan ciki. Cike da ladabi mumtaz ta rissina ta gaishe da umma babba da bakin ta yaƙi rufuwa saboda fara'a Cike da kulawa tace "tashi zo ki zauna a nan" Ba musu ta zauna a inda ta nuna matan sannan ta gaishe da aunty da goggo safiya, tukun ta gaishe da mama A ɗan kunyace ya faruk ya gaishe su, sannan yayi ciki shima. Yana shiga Abba ƙarami yace "yauwa zo nan faruk" ko gaisuwar da ya faruk ke masa be amsa ba yace "Bana so a sake tada maganar su Abbas, yanzu ƙasim da su mus'ab ke min maganar zaku shigar da ƙara a kan su, To ni ban yarda ba, munyi magana da zahra'u(mama) itama tace abar magana, fitar maganar ba mafita bace a garemu" Rai ɓace ya faruk yace "Haba Abba ƙ, laifin su ya kai a hukunta su, hukunci me tsananin gaske ma kuwa, be kamata a ɗaga masu ƙafa ba sam" Cike da ƙarfin hali Abba ƙarami yace"ku barsu da haƙƙi ma, ko shi kaɗai ya ishe su, amma bana son attention ɗin ƴan media sam" Mus'ab da Ahmad na gefe suna haɗiyar zuciya tsabar takaici da baƙin ciki. Tun jiya Abba babba shikam ya rasa tofa komi, Tsabar takaicin da yake a cikin zuciyar shi kasa haƙuri yayi seda ya sanarwa da mahaifin su maganar Jijjigar da maganar tayi masa ne yasa ya kasa haƙuri shima ya bugo sammako yazo asibitin Kafin kowa ya ƙaraso har ya gama ganawa da Abba ƙarami da mama ya koma. Gyara zama Abba babba yayi sannan yace "Kaine ya kulle, ban san me zan ce ba, zalinci dai an riga da anzalince ka, sannan kuma haƙuri abune me kyau, Allah ya ƙara mana haƙuri da tsoron sa, Allah kuma ya hanamu cutar da kowa saboda son abun duniya" Uncle ƙasim cikin ɗacin rai yace "Ai shikenan, bala'in dake a tsakanin su kawai ya ishe su" Ya faruk kam kasa cewa komi yayi, duk da daman yasan zesha fama da Abba ƙ kafin ya amince da maka su a kotu A cikin ranshi yace "in an san wata ai ba'a san wata ba wallahi" Ficewa yayi daga ɗakin rai ɓace Mama na hango shi ta yafito shi da hannu Duk da ya sassauta fuskar shi hakan besa ɓacin ranshi ɓacewa ba Mumtaz kanta kallon shi take tana so su haɗa ido taji meke damun sa. Kusa da mama ya zauna ya sadda kan shi ƙasa Jiki a sanyaye tace "nasan hukuncin ba daɗi ze maka ba yaro na, mu barsu da aniyar su, mukuma gode wa Allah da ya taƙaita mana abun, ko a haka aka tsaya Allah ya warware mana kaikaifen LAUJEN da ke CIKIN NAƊI" Bece komi ba sema sake jin wani tausayi da ƙaunar ta a cikin ranshi. Gyaɗa kai goggo safiya tayi itama tace "hakane abinda zahra'u tace faruk, koda amanar zumunci da suka ci aka barsu ya ishe su" Umma babba ta ɗora da "mugunta kuma ai fitsarin faƙƙo ce, suje can su ƙarata da matsalar dake a tsakanin su ma ta ishe su" Aunty tace "Allah yayi mana maganin abinda bamu iyawa" Haka suka haɗu sukai ta ba ya faruk baki da kalami masu daɗi har sanda su Abba babba da uncle ƙasim suka fito da niyar zuwa duba Tk dake kwance shima har yanzu. Gaf da azzahar aunty da umma babba suka wuce gida aka bar goggo safiya da mama se mumtaz da ke bacci tunda ta samu ta shiga ta gaida Abba ƙ ta bi lafiyar ɗayan gadon da mama ke kwana a kai ta kwanta Ba wanda ya tashe ta aka barta tayi baccin ta. ***Sosai ya faruk ya fuskanci mus'ab da Ahmad yace "Ku saurare ni da kyau kuji, tunda har su Abba suka yanke wannan shawarar to babu yarda za'ayi mu ja da su, abinda zamuyi yanzu shine, zan yi write up akan uncle Abbas da uncle junaid harma da umma ƙarama akan cin amanar da sukayi, mu yaɗa su a duniya" Tun ɗazu se yanzu mus'ab yayi murmushi, dan gaba ɗaya wannan tunanin bezo mashi ba sam Ahmad yace "yes, shiyasa nake alfahari da kai ya faruk" Murmushi ya faruk yayi sannan yace "zamu haɗa duka da pictures ɗin su, yarda har fita ma seta gagare su saboda kunya, sannan ko su Abba sunji zamuce bamu san yarda akayi ba" Dariyar farin ciki mus'ab da Ahmad suka saka haɗe da rungumar ya faruk dake ta murmushin jin daɗi shima. BAYAN SATI ƊAYA Khali na kwance yana ta scrolling a facebook yaci karo da dogon rubutu me ɗauke da hoton umma ƙarama da uncle Abbas da kuma uncle Junaid Ganin fuskokin su da kuma rubutun da akayi da manyan baƙi daga sama ya sa shi miƙewa zaune da sauri haɗe da ƙurama rubutun ido, inda ka rubutu "MACIYA AMANA UKU" Tiryan-tiryan khalid ya karanta labarin tas, inda babu wani abu da aka ɓoye akan irin cin amanar da sukayi, har da asirin da akayi wa Abba ƙarami na sata da be kamashi ba ya kama ƴarsa mace ɗaya tilo A sukwane khalid ya fito ya hau kiran sunan "mami" da ƙarfi Mami na zaune ita da aunty hajara suna firarsu sukaji mahaukacin kiran da kalid ke kwaɗa mata A firgice har suna rige*rigen fitowa Mami tace "lafia khalid" Fuska shaɓe-shaɓe da hawaye yace "mami na cuci kaina, na shiga uku, ni dama nasan mumtaz mutuniyar kirkice wallahi" Kallon kallo mami da aunty hajara sukayi kafin mamin tace "me yafaru kake kira ma kanka shiga uku?" Cikin kuka kamar wani ƙaramin yaro ya miƙa mata wayar Hannun ta har rawa yake wajen ƙoƙarin ƙarɓa Shiru tayi tabi wayar da kallo, bata san mutanen dake cikin hoton ba, amma content ɗin saman yaja hankalin su ita da aunty hajara har suka tsunduma cikin labarin Tun kan mami ta kai ƙarshe take furta "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!" Aunty hajara kanta jikin ta yayi sanyi tana tuno fuskar mumtaz Kukan da khalid keyi ya karyar musu da zuciya, se ga mami itama shaɓe shaɓe da hawayen nadama da danasani (SHIYASA BINCIKE YAKE DA KYAU KAFIN KA YANKE HUKUNCI KUMA GAGGAWA AIKIN SHEƊAN CE) Ranar haka khalid da mami suka yini cikin juyayi da danasani. Kamar yarda kalid yaga wannan rubutu game da su incle Abbas, haka ya karaɗe lungu da saƙo na ƙasar. Uncle ƙasim na gani yayi murmushi, a fili yace "Nasan ba kanwar lasa bane kai faruk, kayi ƙoƙari" Gaba ɗaya fita ta gagari uncle Abbas da uncle junaid, ga tsiyar dake tsakanin su data kunno kai me zafin gaske. Umma ƙarama kam tun sanda Abba babba ya bata tikitin sallama taƙi yarda ta sanarwa da iyayen ta abinda tayi Seda wannan rubutu me ɗauke da hotunan su ya bayyana aka san komi, Abin duniya suka taru sukai mata yawa, ga tsana daga wajen ƴaƴan cikin ta, ga kuma tsana daga nasu gidan, rana zafi inuwa ƙuna kenan. Abba ƙarami tun yana hospital yasa aka gyara mashi ɗaya daga cikin maka makan gidangen shi Kai tsaye yace "ya gama zama da kowa, nesa nesa tafi" Hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi wa mama ba, dan sanda ya sanar da ita kasa ɓoye murnar ta tayi seda ta rungume shi. Haka ya faruk yayi ta up and down har seda gidan ya shirin gidan ya kammala sannan aka sallami Abba ƙarami Direct sabon gidan suka wuce Seda aka kwana ɗaya tukun mama taje can gidan Ta kwasa abinda take so daga nan, ta rabar da wanda bata so. Duk da ƴan'uwan nasa basu ji daɗin huƙuncin da Abba ƙ ya yanke ba, amma hakan besa sun hana shi ba, sanin irin haƙurin da yayi da kuma ɗawainiyar da yake kan yi dan ba denawa yayi ba. BAYAN WATA TARA DA ƳAN KWANAKI Ya faruk na kwance waya kare a kunnen shi suna magana da mus'ab da ya fita shigo da wasu kaya na ɗaya daga cikin companyn Abba ƙ dashi ke managing yanzu a maimakon uncle Abbas Mumtaz na zaune akan darduma tayi zaman tahiya ga uban tirtsetsen cikin ta a gaba haihuwa yau ko gabe Ta gama karatun tahiyar tana so ta miƙe tsaye amma ta kasa, Ya faruk hankalin sa na can kan wayar da yake Hannun ta tafa alamar magana Shiru beji ba Sake tafa hannuwa tayi a karo na biyu sannan ya faruk ya farga da tafin nata Sallama sukayi da mus'ab ya taso ya matso kusa da ita yace "menene" Alama ta sake yi mishi da hannu, shiru ya faruk yayi ya bita da ido dan har ga Allah be fahimci me take nufi ba Da dai mumtaz taji kamar bayanta ze ɓalle tace "Ai se ka ɗaga ni tunda kasa na ɓata sallah ta" Kwashewa da dariya ya faruk yayi ganin yarda har idonta sun cika da ƙwalla Seda ya miƙar da ita tukun yace "yanzu dai in kin huta kiyi sallar a zaune tunda in kin yi sujjada baki iya ɗagowa ta daɗi" Banza tayi da shi ta wuce can gefen gado ta zauna tana maida numfashi. Kallon ta yayi cike da so da ƙauna haɗe da tausayawa yace "in sha Allah kin kusa sauke su ki huta kema, Allah yayi maki albarka matata!" Lumshe ido tayi, a koda yaushe ya faruk na sata jin nutsuwa a rayuwar ta Ko kallon shi tayi takan tsinci kanta cikin farin ciki haɗe da godiya wajen ubangiji cike da shauƙin so ta ɗora kanta a kafaɗar shi, shi kuma ya zagayo da hannun sa kan ƙaton cikin ta yana shafawa. A GURGUJE. Mom Asiya data samu ta anshi nata tikitin daga wajen incle junaid taje ta maka Tk a kotu tana nemar wa ƴarta saki Haka akaita tafka shari'a har Allah ya basu sa'a ta samu sakin, sedai ba'a jima da sakin ba cikin Tk ya bayyana a jikin sakina Hankalin sakina ba ƙaramin tashi yayi ba, haka sukai ta fama wajen ganin bayan cikin nan, amma da yake duk abinda Allah yayi niyar halitta babu makawa seyayi haka suka haƙura har ƴar Tk tazo duniya ba dan ransu yaso ba. ALHAMDULILLAH!!! DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TALIKAI NAGODE WA ALLAH DA YA NUNA MIN FARKO DA ƘARSHEN LITTAFIN "AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI" ALLAH UBANGIJI YASA MU AMFANA DA DARASIN DA KE CIKI, KUSKUREN CIKI YA YAFEMAN, YASA MUYI TARAYYA A LADAN! ❤️ GODIYA DA JINJINA TA MUSAMMAN GA MIJI NA ABIN ALFAHARI NA, ƘAUNAR KA TA DABAN CE A RAINA, ALLAH YA BAKA KARIYA ADUK INDA KAKE JINJINA GAREKU IYAYE NA, ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKAIRI. SANNAN INA MIƘO GAISUWA DA FATAN ALKAIRI GA DUK WANI MAKARANCIN LITTAFI NA 😊 MUSAMMAN ƳAN CIKIN GROUP ƊINA, ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA HAƊA MU A BOOK ƊINA NA GABA DA ALKAIRI ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲 30/5/2023 ZAINAB FALALU 08145225540 Downloaded From https://tknovels.com.ng