Downloaded From https://tknovels.com.ng *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* _Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi!!! Godiya ta tabbata ga Allah, Ina mai Ƙara Jaddada Godiya ta Ga Allah da ya bani Rai da Lafiyar fara Rubuta wannan littafi Nawa Mai suna *DR SULTAN* Allah ka bani Ikon Kammala shi Lafiya, dani da Masu karatu, wannan Labarin Ƙirƙirarren labari ne, Ina roƙan Allah ya bani ikon gamashi cikin kwanciyar hankali da Salama Amin_ *WANNAN PAGE NA SADAUKAR DASHI GA AYIYA GENERATION ALLAH YA ƘARA MUNA DANƘON ZUMUNCI! ALLAH YA JIKAN AYIYA DA RAHAMA!! ALLAH YASA TA HUTA*😥 _The Beginning_ *Page 1-2* *Book1* _____Hayani ya ce ke tashi ta ko'ina Mutane kowa na Harkan gaban shi, Wani kyakkyawan Saurayi ne tsaye a gaban wani ƙaton shago suna saukar da kaya a moto, Jikin shi duk a jiƙe da Zufa, " Sannu da Aiki, Ya yi Murmushi tare da Faɗin "Yauwa Oga, Haka suka riƙa sauƙe kaya a mota suna shigar da su cikin Shago, Gama warshi ya yi dai dai da Kiran Sallah Maggariba, Alwalla Ya yi suka wuce Masallaci, Saida Akayi Isha'i suka dawo Shago, "Oga zan wuce gida Ya yi Maganar kai a sunkuye, "Har zaka tafi Maleek"? "Eh Oga"Toh ga wannan ko sai Allah ya kaimu gobe, "Oga Nagode Sosai, "Miye Na godiya Maleek Hakƙen kane fa, Murmushi mai ƙawatarwa Ya yi, tare da barin shagon, Kai tsaye ya nufi cikin garin cikin ƙanƙanen lokaci ya iso Unguwar su , daga can Nesa ya han geta tsaye, Sai faman Kalle kalle take, ganin shi tafe yasa ta ruga da gudun Gaske ta nufi inda yake, durƙu sawa yayi ƙasa tare da buɗe mata Hannu ta faɗa a ƙirjinshi ya rungumeta, "Ya Maleek! Tun ɗazu nake neman ka Ya Maleek ina Ƙwai da kwai na? Ya Maleek Ina Arake na? Ya Maleek ina.... Yayi saurin da katar da ita a hankali ya janyeta daga jikinsa, ya tsura wa kyakkyawar fuskantar ido, "Irin wannan tabbaya Haka Maryama ta!"? "Ya Maleek kaifa kace zaka siyo min, tayi maganar tana Turo ɗan ƙaramin bakinta mai launin pink color, Numfashi ya fesar cike da gaji, a hankali ya Buɗe lumsheshin idanuwansa da suka ƙara sakayi jajir saboda gajiya, "Kinje Islamiya"? Kai ta ɗaga Mishi, "Bazaki bani Amsa ba? A karo na biyu na sake ɗaga Mishi kai, "Shike nan tunda Baza kiyi magana ba ruwa da ke kwai da kwai Ma Bazan baki ba daman Kaka kawai na saya....tayi sauri rufe Mishi Baki da iya ƙarfinta da laulausar fatarta kaman ta jariri sabon haihuwa, dariya ta bashi sosai ya yi saurin gimtse ta, ƙoƙarin janye hannunta yake sam taƙi bashi dama, ƴar ƙaramar ƴarinƴa da Ida sai shegen ƙarfi, "Uhmm Uhmm ya fara ya jujjuya kai ita ko sai kallonshi take, "Bazato ba Tsammani yaga hawaye na zubo mata a kan kyakkyawar furkarta, janye hannunta tayi daga bakinsa tana ƙoƙarin barin wajen, da sauri ya riƙo hannuta tare da juyo da ita suna fuskantar juna, a karon farko ya saki Murmushi, "cikin sanyi Muryar ya soma faɗin, "Meye a bin kuka a nan"? Kina son Nima nayi Kuka"? a hankali ta girkiza kai almar A'a, "Toh ki Dena kuka bana so Kinji,hannunsa yasa yana share mata Hawayen, " Ya Maleek da gaske Kaka kawai kasaya wa kwai da kwai"? "A'a wasa nake ga wannan ke kadai na sayawa, wani irin daɗi taji, "Ya Maleek komai da komai ka saya min,"Ehh" Ya Maleek Nagode," hannuta ya riƙe suka wuce gida, Koda suka shigo zaune take a tsakiyar gida saman tabarma, da sauri ta saki hannun sa, ta zauna saman tabarma, "Kaka Kinga Abinda Ya Maleek ya kawo min Ni kadai bada keba,"Kaka Barka da dare, "Abdul Maleek Barka kadai an dawo lafiya,"Lafiya kau Kaka, "Madalla ya Kasuwa," Alhamdulillahi Kaka, "Allah ya taimaka, "Amin ya faɗa cike da gajiya, "Maryam tashi ki ɗauko masa Abinci sa, "Kaka bari na gama cikin kwai da kwai na, "Bana son shashanci maza tashi, "A'a Yayi saurin ka tsayeta Kaka ki barta kwai zan ɗauko da kaina, bai jira mi zata ce ba ya wuce cikin ɗin, "wai yaushe zaki girma Maryam, shekara Goma sha biyu har yanzu ba ki sa ciwon kan kiba"? dai dai lokacin ya dawo a hankali ya zauna gefen tabarmar ya fara cikin Abinci cikin natsuwa, lokaci lokaci yakan ɗago ya kalle ta har ya kammala cikin Abincin ya maida kwananan cikin, " Kaka Kinga sallamar da Oga ya bani yau dubu Biyar ne, "Kai Masha Allah, Allah ya ƙara buɗi Mai Albarka Abdul Maleek, "Amin Kaka A kwai Abinda kike Buƙata, "A'a Abdul Maleek Allah dai yayima Albarka, furkarshi dauƙe da Murmushi ya ce "Godiya nake Kaka" Idon Kin gama cikin kayan kwadayin ki ɗauƙo littafin ki muyi karatu kafin na wuce, "Abdul Maleek idon ka biye mata sai ka kwana a gidan nan bata kammala ba, " Ni Wallahi kin saka min Ido da yawa Kaka, tayi maganar cike da Shogoɓa, Aure ma zanyi na huta da wannan ɗumin Naki, lokacin ɗaya suka kwashe da dariya, "Ya Maleek ba kai kace zaka min Au.... "Kinga kina ɓata min lokacin, zumbur ta miƙe tare da barin wajen, " Allah ka shirya min ƴarin ƴar nan cewar Kaka, "Amin ya faɗa a hankali, "Yau Ni zan fara yin karatun idon magana sai ka ƙaramin, " wannan saurin Allah yasa kin iya a bin kwarai Kaka ta faɗa cike da zolaya, "Babu Ru wanki da Ni, tayi maganar tana ƙoƙarin zama, " Abdul Maleek ga wannan idon tayi kuskure ka zane ta, ƙarɓan balar ya yi ya na Murmushi, "Ni na san Ya Maleek bazai da ke ni ba, littafan boko ta fito dasu Nan tashiga yimai bayanin Abinda aka koya musu sosai yaji daɗin yadda take mai bayani komi dalla dalla ko wanne subject, harda Assignment ya nuna mata yadda Zatayi, tana gamawa ta fara karatun Alkur'ani cikin zazzaƙar Muryar ta mai sanyi, tunda ta fara karatun ya lumshe ido yana saurarenta harta kammala, ya ƙara magata, tunda suka fara karatun Kaka ta tsura musu ido tana kallon su, cike da Sona da kyauna, bayan sun kammala hira sukayi ƙaɗan, Maryam sai hamma take, "Kaka ni zan tafi Saida safe, "Toh Abdul Maleek Allah ya tashe mu lafiya, "Amin Kaka, cikin murya Bacci Maryam tace, "Ya Maleek Saida safe, Murmushi kawai ya sakan mata, sannan ya fice daga gidan, Kaka ta rufe gida, tadan yin kakkace kakkacen sanan suka wuce ɗakin, Suka kwanta, Nan take Bacci mai daɗi ya dauƙe su, ★★★ Yana barin gidan kai tsaye ya nufi ɗan ƙaramin ɗakinsa irin na samari, ya watsa ruwa yaji wani irin iska mai daɗi na shiga jikinsa, a hankali ya zauna saman katifarshi, karatu ya soma yi da ɗan rubuce rubuce bayan, yana gamawa ya fara karatun Alkur'ani na ɗan wani lokaci, Addu'a yayi sannan ya kwanta nan take bacci mai ɗaɗin gaske ya yi a won gaba shi cike da mafarkai masu ɗumbi da ɗi da rudarwa, ★★★ Washe gari Tunda Assuba ya farka Alwalla ya yi ya wuce Masallaci, bayan ya dawo ya yi karatun Alkur'ani sannan ya yi Wonka ya shirya, ya gyara ɗakinsa tsab kana fice daga gidan kai tsaye ya nufi gidan kaka.... "Maryam tashi kiyi Sallah karki bani na same a wajen, ko motsi batayi ba, "Wai ba magana nake ba, a hankali ta Buɗe Idanuwanta ta sauke su kan Kaka dake zaune a tsakiyar ɗakin, "Ga ruwan Zafi can cikin bokiti saura kuka ki tsaya shirita ta, A hankali ta fice daga ɗakin, tana gama Wonka ta fito a tsiyar gida ta duƙa tana Alwalla a hankali ta janye hular kanta nan take gashin ta dake kwance har gadon baya ya bayyana baƙi wul da shi sai sheƙi yake, tana kammala Alwalla ta wuce cikin ɗaki Kaka na Zaune tana juya mata Shayi ɗon yayi sanyi, bayan ta shirya ta saka Unifrom farar riga da Blue wondo sai hijabi fari ɗan ma dai daici sosai Unifrom ɗin sukayi mata kyau sun zauna Das a jikinta," Ta yi Sallah, a tsanake ta soma shan shayin , dai dai lokacin ya shigo gidan," Kaka Ina kwana"? "Abdul Maleek lafiya lau shigo Mana,a hankali ya shigo ɗakin ya zauna, "Ya Maleek ina kwana"? "Lafiya lau" "Ga Naka Abdul Maleek, "Nagode Kaka a tsanake ya soma cin abinci, lokaci ɗaya suka Kammala," Tashi mu tafi karmu makara, a hankali ta miƙe tare da ɗaukar jakar Makarantar ta, "Kaka zamu tafi, "Allah ya kiyaye Abdul Maleek Allah ya bada Sa'a, "Amin Sannan suka fice daga gidan, Tafiya suke a natse yana riƙe da hannunta Suna hira gwanin burgewa har suka iso makaranta," Toh ni zan tafiya kiyi karatu Kinji, "Toh Yaya me zaka seya min? ta ƙarasa maganar tana Murmushi, "duk abinda kike so, "Kasiyi irin na jiya, "Shikenan kiyi sauri karki makara, yana tsaye a wajen yana kallon harta shige Ajinsu, A hankali ya sauƙe Ajiyar zuciya, dai dai lokacin mai mashi ya aje wani Malami, "Malam tafiya ne "? Wacer ɗan Ajaɓa, "Ehh kasuwa zaka Kaini, "muje" yana hawa suka wuce, Suna isowa ya sallami mai mai Mashin ya wuce shago, "Oga ina kwana, "Lafiya lau Maleek" Nan ya shiga gaida mutan dake kewaye da shagon Abokan Ogan shi, yana shiga shagon ya fara kakkance Kakkance tare da fitar da Abu marar Amfani bayan ya gama ya share Shagon har zuwa gaban shago ko'ina tsab, Haka ya suka yini a kasuwa suna hadada da Mutane har zuwa Bayan Isha'i, sannan ya wuce gidan yauma kamar jiya da gudun Gaske ta iso wajen sa, ya rugumota, "Ya Maleek sannu da zuwa, "Yauwa kina Lafiya"? "Ya tsaraba na"? "Gashi nan" ya faɗa a ɗan fusace, "Rau rau da ido ganin ya ɓata rai, "Ya Maleek kayi haƙuri, "ALLAH Idon na sake kiyi Miki magana kika share Ni Bazan ƙara saya Miki wani Abuba, "Kayi Haƙuri Ya Maleek!!" Kama Hannuta yayi suka wuce cikin gida, Yauma kamar kullum zaune take a tsakiyar gida suka shiga Yayi Sallama ta Amsa Mishi, "Abdul Maleek Sannu da zuwa, "Yauwa Kaka ya gida, "Lafiya lau' " Tashi ki ɗauko Mishi Abinci, bayan ya kammala cikin Abinci sukayi karatu Sannan ya wuce gida, "Kaka kaman Wayar ki Na Ringing, tashi ki ɗauko tun bata tsinke ba, da sauri ta nufi ɗaƙi lokacin har kiran ya yenke tana dauƙar wayar wani kira ya sake shigowa, "Abba Abdullahi ne ɗaga wayar tayi, "Abba Barka da Dare, daga can ɓangaren aka Amsa da "Mamana Kina lafiya? Ina Mama? "Lafiya lau muke Abba, Abba yaushe zaka kaimu birni nida Kaka, "Abba ka maida mu Birnin tare da Ya Maleek Abba K..... "Ya isa haka Mamana Ina Mama"? "gata Abba, cikin Sanyi Murya Kaka ta kira sunansa,"Abdullahi Ya gida"? Ya Iya linka"? "Lafiya lau suke Mama ɗazu da Safe na kira baya zuwa, " Ehh ɗazu sabin din ya ɗauƙe, Dariya Maryam tayi,"Kaka service Ake cewa ba Sabin ba, duka ta ɗan kai mata tayi sauri kaucewa tana dariya, "Yauwa Mama gobe zan aiko da Direba ya kawo muku kayan Abinci ina fatan ba wata Matsala, "Ba komai Abdullahi Nagode sosai Allah ya yi maka Albarka," Amin Mama ki ƙara Haƙuri har yanzu Abubuwan sai Addu'a Nasara gane mike da mun Kubra, " Ba komi Abdullah Allah dai yayi maka Albarka tare da zuri'ar ka, " Ya su Nana "Lafiya lau suke, sun ɗan jima suna hira kafin nan sukayi Sallama, Tuni Maryam tayi Bacci, da kyar Kaka ta kaita ɗaki suka kwanta, Washe gari yau ta kasance Weekend ne, Zainab na zaune a tsakiyar gida tana Aiki zane zane nenta, sai faman Murmushi take, "Kaka Kinga na zana Ya Maleek, tayi Maganar tana nuna mara zanen da tayi," Dai dai lokacin Akayi sallama, "Kaka kaman muryar Direban Abba, "Aiko shine ji kice ya shigo, da sauri ta nufi wajen gidan," Kaka tace ka shigo, Binta yayi a baya har inda Kaka take zaune, "Mama ina kwana, "Lafiya lau Atiku ya Hanya"? "Lafiya lau Mama" suna gama gaisawa ya wuce waje ya shigo da kayan Abinci da yazo dasu, Maryam sai faman tsalle tsalle take tana jin daɗi, "Sannu da aiki Atiku ga ruwa ka sha ,"ba musu ya ƙarɓa ya sha tare da yi mata Godiya, "Ga wannan nan yace a baki 50k cike da farin ciki ta karɓi kuɗin tana mishi godiya, sallama ma yayi masu har ƙofar gida suka rakashi, sai lokacin Kaka ta samu daman kallon kayan, kayan Abinci ne kala kala da duk wani Abin buƙata yau da kullum, sai kayan saka kusan kala goma ita biyar zainab Biyar sai su sabulaiya da turarukka masu daɗin gaske, "Ya Allah kayi wa Abdullahi Albarka Allah ka kare a duk inda yake, ta ƙara sa maganar tana share hawayen da suka zubo mata,"Kaka kukan me kike? Murmushi ƙarfin hali tayi," Ba kuka nake ba Maryama, "Kaka me yasa duk Abba ya Aiko muna da kaya sai kiyin Kuka"? Nan take ya nayinta ya sauya, ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciya mai zafi.... ★★★★ "Ya Maleek Sannu da zuwa, Ya Maleek Abba na Birnin ya aiko muna da kaya, "Kiyin kyau Maryama ta Ya faɗa a hankali sun kuyar da kai ta yi, "Uhmm Maryama An girma Kunya kike ji"? Murmushi ya sakan mata da taune Lip ɗin sa na ƙasa ya ɗage mata gira ɗaya da Lumshe idanunsa ya buɗe a kan fuskarta ya danyi murmushi tare da tsurawa furkarta ido, " Ya Maleek kayan nan Abba ya aiko min su, "sun Miki kyau sosai, "Nagode, A karon karfo ya saki Murmushi murya. sanyaye ya ce," Maryama ta an girma? Murmushi ta yi ta ɗan marairaice fuska cike da kula ta ce," Ya Maleek bai kai ne ka ce na rage yin surutu ba"? Suka ha ɗa Ido a karo na biyu, da ƙarfin zuciya taso janye Idonta Amman bai bata daman hakan ba cike da ƙwarewa ya Lumshe idanunsa ya buɗe a tsakiyar kwayar idonta, tsabar lamarin yazo mata a bazata tai saurin Janje idota, wani irin kwarjini ya yi mata.... Cikin tattausar muryar sa mai cike da sanyi ya ce ,"Muje gida, a hankali ta sauke Numfashi tare nema duk kan natsuwar, tana gaba yana biye da ita har suka iso cikin gida, ganin Kaka bata tsakiyar gida suka wuce ɗaki, ya yi Sallama, ta basu izinin shiga, koda suka shigo tana zaune a saman tallausar carpet ɗakin na fitar da wani irin fitinannen khamshi mai daɗin gaske, Cikin sanyi Muryar yace," Ina wuni, "Lafiya lau Kaka, " Zauna mana, a hankali ya zauna tare da lonƙosa ƙafarshi,ta hagu, kwanukan Abinci dake gefenta ta aje Nishi a gaban sa, "Sannu da Aiki Kaka!" Murmushi ta sakan mai, "Ya Maleek Ni ba zaka min sannu da aiki ba, tare mukayi girkin, "kwaɓe fusaka yayi cike da zolaya ya ce,"ke ɗin"?.sai kuma yayi dariya mai sauti, da ce wa, " Maryama an girma!" hakannen yasa Kaka Murmushi, " Kaci abin cikin ka Abdul Maleek" kwaɓe fusaka Maryam ta yi tana turo baki gaba tana ce wa," Ai Bazan ƙara ta yaki aiki ba, A hankali ya buɗe kwanon abinci wani irin khamshi mai daɗi ya daki hanci sa, Wani irin sassanyan Nunfashi ya sauke tare da Lumshe idonsa, "Ya Rabb" tuwon shimkafa ne da miyar taushe taji nama da kifi, sai man shanu, nan take ɗakin ya gauraye da ƙamshi, a tsanake ya riƙa cin abinci har ya kammala, Juyowa ya yi ya watsa mata narkakkun Idanunshi sa da bata iya gano mike cikin su, turo baki tayi tare da sunkuyar da kai ta murguɗa baki, "Taso muyi karatu, ba musu ta dauko littafanta sukayi karatu kaman yadda suka saba, "Kaka Nagoge zan wuce gida, "Ji mana Abdul Maleek!" a hankali ya zauna, "Abdul Maleek ya batun karatunka"? Nunfashi ya ɗan fesar cikin sanyi Murya ya soma faɗin," Kaka kuɗin ne bai gama kammalawa ba! kaka Makarantar tana da tsada sosai, " Abdul Maleek idon ka biye wa sai ranar da ka tara kuɗin da zasu isheka ba zaki karatu yanzu ba! Komai a hankali aka farashi, baka san me Allah zai yi nan gaba ba, yanzu nawa ka tara"? Nannauyan Ajiyar zuciyar ya sauke, " Kaka! dubu Ashirin ne a hannun yanzu, "Abdul Maleek, kana nufin tsawon lokacin nan da ka dauƙa kana aiki iya abinda ka tara kenan?, Rau Rau ya yi ido Kaman zaiyi kuka, "A'a Kaka! "Toh ya akayi suka zama 20k"? "daman kwanaki koda na dawo da shago na tarar da An ɓalle ɗakina! "Subuhalillah" kai ya jingiya cikin ya nayin da muwa yace," Wallahi Kaka duk kudin da na tara sun kwashe!" Nannauyan Ajiyar zuciyar Kaka ta sauke, "shine baka gaya min ba"? "Kiyi haƙuri Kaka!", "Allah ya tsare gaba ɓarayi sunyi yawa a unguwar nan, cikin yana yin Natsuwar sa da ya zame mishi jiki, yace "Haka ne Kaka, Allah ya shirye su! "Amin" " Kayi ƙoƙarin Abdul Maleek kar shekarar nan ta ƙare baka shiga makaranta ba, In sha Allahu Kaka zanyi ƙoƙarin, "Allah ya taimaka idon ka tara ra gowar sai na cika ma, "Nagode Kaka cikin yana yin natsuwar sa da ƙasaitarsa ya kalli inda Maryam take zaune,ya Lumshe ido ya buɗe a kan fuskarta, cikin sanyi Murya ya ce,"Kaka Saida safe, "Allah ya tashe mu lafiya, "Amin" Kai tsaye ya nufi ɗakinsa, ya watsa ruwa, a hankali ya fara jin natsuwa na saukar masa, karatun Alkur'ani ya yi kana ya yi Addu'a ya kwanta nan take bacci ya yi awon gaba dashi, can cikin Bacci ya fara ganin wani gaske mai bala'i ƙarfi ya kewaye wani ka tafaren wajen, wasu muta ne sanye da Fararen kaya za gaye da wannan hasken, daga can gefe wasu kyakkyawan ƴan mata ne tsaye ko wacce furkarta ɗauke da murmushi, ɗaya daga cikin ƴan matan ta soma kiran sunanshi ciki wata irin zazzaƙar Muryar mai cike da natsuwa," Abdul M.....!" dai dai lokacin ya farka daga baccin da yake cikin wani irin ya nayi, wata irin Zufa ce me bala'in ɗumi ke sauƙo daga saman kanshi, cike da Razata da kaɗuwa, dafe kai ya yi dake junjuyawa, ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar mai ɗumi ya juya gefen hagu ya kwanta ta re da yin Addu'a ya sake juya hannu izuwa dama ya yi Addu'a... Sam bacci ya ƙi zuwa sai faman juyi yake cikin wani irin mummunan ya nayin da ke faruwa dashi duk lokacin da ya yi irin wannan markin da yake duk bayan shekara, karatun Alkur'ani ya riƙa cikin sassanyan murya mai cike da kasala.. cikin ikon Allah ya samu bacci ya yi awon gaba da shi......✍️✍️✍️ _More comments and share_ *Sadeeya Ka'oje ce*✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ .Bismillah........ ✍ https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* *Page 3-4* _______ Washe gari , gaba ki ɗaya yinin wannan Rana haka ya yini a kasalance, komai a hankali yake yinsa, zaune suke a tsakiyar gida, suna hira, Kaka ta kalleshi cikin sanyi Murya ta soma magana, "Abdul Maleek mike da munka"? cewar Kaka, " sassanyan Nunfashi ya sauke, " Ba komi Kaka, gaji ya kawai ke da muna, " Ka tattabar ba komi"? A karon farko ya saki Murmushi,"ALLAH Ba komai Kaka!, "Shikenan, "taso muyi karatu, ya faɗa yana kallon Maryam dake kwance, a hankali ta mike ta nufi daƙi ta dawo dauke da jakar Makarantar, nan suka soma yin karatu cikin natsuwa da kwanciyar hankali, kana ya yi musu sallama, bayan ta fiyar shi Kaka ta rufe gida kana suka wuce ɗaki suka kwanta, Washe gari ma haka ya tashi ba wani kuzahari, jikin sa ya musu sosai da mafarki, duk da ba wannan ne karo na farko da ya fa irin wannan mafarkin, tawon sati guda kenan yana fama da kasala, Kaka tayi tambatayar duniya ya ki ya faɗa mata, Bayan Isha'i kamar ko yau she tana tsaye a ƙafar gida, tana jiran da wowar shi, ta ɗau tsawon lokaci tsaye a ƙofar gida tana jiran da wowar shi, " Maryam wai miki ke a waje"? " Kaka Ya Maleek nake jira!" Ajiyar zuciya Kaka ta sauke, tare da faɗin Allah ya sa yaron nan lafiya yake? bai taɓa kai irin wannan lokaci ba, "Allah ka tsare shi a duk inda yake" Cikin tsananin da muwa Maryam ta shigo gida, " Kaka ya Maleek bai dawo ba har yanzu ta faɗa kaman Za tayi kuka, Murya na rawa tace" Kaka muje mu nemo shi Kaka!" Bata jira me Kaka zata ce ba ta wuce ɗakin ta ɗauko jiha bi da fitala, kana suka fice daga gidan hankali a tashe, saboda bai taɓa kar War haka ba, "Kaka ko zamuje Kasuwa ƙila yana can, Maryam ta faɗa a hankali, "Bana tunanin yana kasuwa wani lokacin idon Oga ya riƙe shi a kasuwa, yakan kirani da wayar Oganshiya ya sanar dani, " Kaka ƙila ya ƙira ba Network, "da wuya idon yana Kasuwa, ganin Maryam ta matsa sai sunje kasuwa,hakan ya sa suka wuce kasuwa, Nan mai shagon ya sanarda su tun bayan Isha'i ya wuce gida, cikin tsananin tashin hankali da dake tattare dasu, suka baro kasuwar,Nan suka ruƙa neman shi cikin Unguwa,duk sun san baya zuwa gidan koma ha salima ko aboki Baida idon ka ganshi tare da wani to Maryam ce, " Kaka ko zamuje ɗakin sa"? cewar Maryam, "Anya wuya yana ɗakinsa, "Kaka muje mu duba, Haka suka ɗunguwa zuwa ɗakinsa, iso warsu ya yi dai dai sakin wata irin ƙara mai razanarwa, nan take jikin Maryam ya soma ƙarƙarwa,"“Innalillahi wa innailaihi raji'un!! Abdul Maleek ta kira sunansa a rauna ce, da sauri ta nufi cikin ɗaƙin, tana kiran Sunanshi" Abdul Maleek! Abdul Maleek!! tsawa tayi cak, tuni Abdul Maleek ya suma babu a lamar Nunfashi atare dashi, Rungumeshi Kaka tayi tana kiran Sunanshi, cikin tsananin tashin hankali Kaka ta fashe da Kuka tana kiran Sunanshi.... A Ɓangaren Maryam tuni ta fita haiyacinta, jikin Kaka sai karkarwa da kyar ta tattaro ƙarfi ta, kana ta janye shi daga jikinta, ta zuba Nishi ruwa, ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, a hankali ya shiga karanto Addu'oi cikin ikon Allah hankalinsa ya fara dawowa jikinsa, a hankali ya ɗago da idanunsa da suka kaɗan sukayi jazir ya kalli Kaka ya yi ƙasa da kanshi, Murya a dishace ya ce "Kaka! zasu tafi dani sai kuma ya fashe da Kuka, A razaje Kaka ta ɗago ta kallesa Zuciyarta na bugawa da ƙarfi idanunta a kansa, "Suwa ye zasu tafi da kai Abdul Maleek!" su tafi da kai su kaika Ina?" Kai ya gyaɗa mata cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare dashi ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, Murya a dishace yace,"Kaka wlh tafiya zasuyi dani Kaka bana son rabuwa daku! "Kaka Ina Maryama ta!" Wani sabon Kuka Kaka ta fashe dashi tana girkiza kai" Abdul Maleek ba inda zasu kai ka, Abdul Maleek sam baya cikin Haiyacinsa sai sabbatu yake, Maryam dake baƙin ƙofa tana sauraren sabbatu da Abdul Maleek yake, ta durƙu she a wajen ta saki wanin irin marayan kuka, Kwallnshi kaka keyi cike da tausayawa ganin yadda ya takure a waje ɗaya yana sabbatu, cikin raunan'nanyar Murya Abdul Maleek yaci gaba da fadin "Kaka gasu nan zasu tafi dani, Wayyo Allah na!! nan Kaka ta shiga tafa Nishi Addu'oi, a hankali ya fara sauke Ajiyar zuciya, Nan take jikinsa ya sake, sai lokacin Maryam ta samu damar shigowa ɗakin, cikin tsananin tashin hankali ta kalli Kaka Murya a dishace ta ce,"Kaka don Allah karsu rabani da Ya Maleek! zujjuya kai ta farayi kaman zautacciya hawaye na bin fusakar ta cikin muryar Kuka ta soma kiran Sunansa, "Ya Maleek karka tafi ka barni don Allah Ya Maleek idon ka tafi ka barni mutu.... ta kasa ƙarasa maganar tayi sai kwai ta fashe da Kuka..... Kaka kam tunu jikinta Ya yi sanyi, Ajiyar nan ta sauke tare da fesar da Numfashi, cikin raunin Murya ta ce "Maryam ki dena kuka karki ta dashi daga bacci Kinga da kyar na samu ya koma Bacci, da sauri tasa hannayenta tana share hawayen, "Kaka na dena Kuka" murmushi ƙarfin hali Kaka tayi kana tace Yauwa " Yar Albarka!" haka suka kasance a dakin na ɗan wani lokaci, lokaci lokaci kaka na tofa mishi Addu'oi, shiko sai sauke Ajiyar zuciya yake, fusakar shi tayi fayau duk da bacci yake Amman tashin hankali da fargaba ke kwance a saman fusakar sa,, Wuraren 11:30 ya fara buɗe idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir bishi bishi yake gani cikin wani irin ya nayi ya danƙi hannu kaka cikin nasa bugun zuciyarshi na tsananta,a hankali ya fara buɗe idanunsa da sukayi masifar nauhi ya sauke su a kan Kaka dake riƙe da Hannu sa, Maryam ta ɗora nata a sama, cikin wata irin murya mai ciki da rauni yace "Kaka zansha ruwa!" da sauri Maryam ta janye hannunta ta ɗebo ruwa cikin robar fenta dake cikin ɗakin, "Gashi Kaka a hankali ya ɗari da kanshi Maryam ta saka Nishi ƙofin A baki haka ya riƙa zukar ruwan maƙoshin na bata wani irin sauti kwat kwat tas ya shanye ruwan, wata irin Zufa ce ta riƙa tsastafo mishi daga saman kai, ya sauƙe sassanyan Numfashi, Murya a dishace yace, " Nagane Maryama ta!."Abdul Maleek me kame ji Yanzu? Kaka ta tambataye shi cike da kulawa" Murmushi ƙarfin hali ya yi cike da ɗauriya, " Bana jin komi kak, " Ka tabbatar"? Kai ya gyada mata a lamar ehh, tashi muje gida ka kwana a can kaga dare yayi ba'a san me zai faru ba, "A'a Kaka ki bari kwai zan kwana a nan, Maryam kowa idanuta ne suka shiko da kwalla, cikin sanyi Abdul Maleek ya dafa kafaɗar Maryam, cikin sanyi Muryar mai cike da natsuwa," Maryama ta kiyi haƙuri ki Dena kuka Kinji kina son Nima nayi kuka!"? da sauri ta girkiza kai, "Yauwa" Kaka kam sai kallon su take, Ajiyar zuciya ta sauke tare da fesar da Numfashi ta kalli Abdul Maleek ɗin, " kasan baka da Lafiya me saya Baka je gida ba? A hankali Abdul Maleek ya tauna lip dinsa, cikin sanyi Muryar yace," Kaka wlh lafiya kau na baro kasuwa, ina shigowa Unguwar nan kaina ya yi mugun sarawa nan take zazzaɓi mai ƙarfi ya rufeni da kyar na iso ɗaki na tare da taimakon Kabiru" Kaka ko ido ta tsurawa Abdul Maleek kaman mai son gano wani Abu, A karon farko ya saki Murmushi...✍️✍️ *DR SULTAN* *( THE BEGINNING)* _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* *Page 5-6* _________ A karon farko ya saki Murmushi wanda ya fito daga ai nihin zuciyarshi, Nunfashi Kaka ta fesar tare da sauke Ajiyar zuciya, Kana tace "Maryam tashi mu tafi gida dare nayi, a hankali ta ɗago idanunta suka sarƙe da na Abdul Maleek daya wani irin zuba mata matattun idanunsa da suka sake can launi izuwa ja ko ƙittawa baiyi, cikin wani irin yanayi na tsananin kunyarsa da take a kwana nan, tayi sauri janye Idonta daga nasa, cikin sanyi Muryar mai dauke da kunya tace ," Ya Maleek Saida safe" jin Muryar Kaka ta faɗin," Abdul Maleek zamu tafi Allah ya ƙara sauƙi!, " Mu tafi Kaka" Jin Muryar Maryam ta ratsa dodon kunnesa ya yi sauri Lumshe idanunsa, tare da sauke sassanyan Numfashi, " Kaka bari nazo na raka ku, "A'a Abdul Maleek yi zaman ka kaida baka da Lafiya,"Kaka bana jin komi yanzu, "a'a Abdul Maleek" tana kai ƙarshe Maganar ta ja hannu Maryam suka fice daga dakin kai suka wuce gida.... A hankali ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, tare da fesar da Numfashi mai Zafi, nan abinda ya faru da shi ya riƙa dawo mishi a kwakwalwa, "Ya rabb" ka kareni daga wannan mummunan Al'amari, narar yabaki ɗaya bai runtsaba, haka ya kwana yana nafilfili tare da kai kukan sa ga Allah sai gab da Assuba mai mai daɗi yayi awon gaba da shi...... A ɓangaren Kaka ma ranar bata runtsa, Washegari tunda sassafe ta wuce gidan Liman, dai dai lokacin zai shiga gida dawowar shi kenan daga masallaci, "Mama ina kwana, ya faɗa cike da girmamawa, "Lafiya lau malam liman ya iyali," Alhamdulillahi Mama" "Mushiga daga ciki" yayi maganar tare da nuna mata ɗan ƙaramin ɗakin dake suka dasu, Bayan sun shiga sun zauna, Mama ta Kalli Malam liman, ta sauke sassanyan Nunfashi cikin sanyi Murya ta soma magana," Malam Liman batun Abdul Maleek ne, lamarin nashi sai ƙara tsauri yake, nan ta shiga bashi labarin abinda ya faru jiya, Ajiyar zuciya Malam Liman ya sauke tare da kallon Kaka da jikinta duk Ya yi sanyi, "Mama tabbas akwai wani babban Al'amari dake tattare da wannan yaro! Daga ɗayan Ɓangare kuma kwai masu son cutar dashi, jin haka yasa a tsorace ta zaro ido jin Abinda Malam liman ya faɗa" Malam liman wannan wane irin Al'amari ne?" " malam Liman Meye ma fita yanzu?" Kaka ta faɗa a rauna ce, "Mama mafita ɗaya ce ya dage da Addu'a saboda rayuwar shi tana cikin hatsari mudɗin miyagun mutanen nan sukayi nasara a kanshi, "Innalillahi! Allah ka tsare shi daga Sherri su..." "Amin ya Rabbi Mama ina Abdul Maleek ɗin yake? Nunfashi Kaka taja kana ta fesar, cikin tsananin damuwa da tashin hankali da take ciki Murya a dishace ta ce,"yana ɗakin sa, komi Malam Liman bai sake cewa ba, rubuta ya somayi a allo cike da natsuwa bayan ya kammala ya wonko da ruwan zam zam kana ya zuba su cikin gorar ruwa, " Yauwa Mama ga wannan ya riƙa sha yana shafe jikinsa, hannu biyu Kaka ta karɓi gorar ruwa cikin tsananin farin ciki ta shiga yi mai godiya, da sauri ya da katar da ita cikin girmamawa ya soma magana"Haba Mama miye abin godiya ai yiwa kaine, mahaifin ya Ron nan kafin Allah yayi mashi rasuwa munyi zaman mutunci dashi Allah dai ya tsare shi daga sharrin miya gun nan, "Amin ya rabbi Malam Liman" "Ke ma Allah ya biya ki Mama yadda ki kayi tsayin daka akan Abdul Maleek Allah ya ƙara Miki lafiya da nisan kwana!" "Amin Allah ya yi Albarka!" har ƙofar gida ya rakata kana ta wuce gida cike da ƙwarin Quiwa, tana gab da shiga gida Abdul Maleek ya iso fuskar shi ɗauke da murmushi kallo ɗaya zaka mishi ka fahimci akwai reshin isasshen bacci a tattare dashi, cikin sun kuyar da Kai da Muryar shi dake dishace har yanzu yace " Kaka ina kwana,"Abdul Maleek an tashi lafiya?" "Lafiya kau Kaka, " ya jiki?" haka ta riƙa jerin mai tambayoyi yana bata Amsa, kana suka wuce cikin gida, da guda Maryam ta ƙaraso wajen shi ta rugumeshi ya ɗanyi baya kaman zai faɗi, "Ke kiyi a hankali fa karki kada shi, cewar Kaka, Kai ta cuta cikin ƙirjinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi, cikin wani irin ya nayi mai cike da kasala ya fara janyeta daga jikinsa, " Ya Maleek! " Hakan yasa ya buɗe idanunsa cikin sauri ya janyeta daga jikinsa tare da matsawa gefe kallo ɗaya yayi mata ya kawar da kai gefe, maryam ta Lumshe ido ta buɗe akan fusakar sa, " Ya Maleek jiya bakayi bacci ba?" Juyawa ya yi ta re da kallon Kaka, cike da tsuke fuska yace, "Nayi!" Kallon Mamaki kaka ke masa, Wani irin kallo ya watsa mata cikin ɗaya girarsa ta sama," Kiyi sauri mu wuce makaranta, a Gurguje suka karya, kana Kaka ta bashi ruwan maganin ya sha ba tare da yasan na miye ba, saboda ya san kaka bazata cutar da shiba bayan ya sha ya shafe jikin sa, kana suka fice daga gidan, yana kaita makaranta, kana ya wuce kasuwa...... A hankali kwanaki sukaci gaba da shuɗewa, ya yin da Kaka taci gaba da ba Abdul Maleek rubutu da Malam Liman ke aiko mata duk safe, a ɓangaren Abdul Maleek da Maryam shaƙuwar su sai ƙara ƙarfi take..... tunu Su Maryam sun kammala jarabawar su, Ranar da ta karɓo sakamakon ta, Ranar kowa ya shaida saboda tsananin farin ciki da take ciki, Ƙasan cewar ta ƴarinƴa mai kwazo tun shigarta makarantar ita ke dauƙar na ɗaya a class ɗin su, duk da sunyi Hutu kullum dare sai sunyi karatu kaman yadda suka saba, a ɓangaren islamiya tana daya daga cikin yara masu kwazo da hazaƙa, tana daga da cikin wa ƴanda zasu sauke a shekarar nan.... *WAIWAYE ADON TAFIYA* Malam Aliyu Gwani shine cikakken sunan mijin Kaka, Babban Malami ne mai tarin ilimin Addini, daya taka muhimmiyar rawa a duniyar Musulunci, Kasan cewar ya yi gwagwarmaya Rayuwarsa ta neman ilimin lokacin ƙuruciyar shi a garin ƘARAYE ta jahar Kano , hakan yasa ake kiran sa Malam Gwani Ƙaraye, matar sa ɗaya A duniya Maryam (Kaka) wanda ta Kasance ƴar Gwoggon sa, Ƴaƴansu biyu Abdullahi shine Babba sai Ibrahim Mahaifin Maryam dun daga Ibrahim Kaka bata sake haihuba, haka suka ci gaba da renon yayan su cikin kwanciyar hankali Abdullah da Ibrahim sun taso cikin haɗin kai da tausayin juna da kyaunar junan su hakan yasa iyayayen ke tsakanin son su komai a tare suke, Haka kwanaki suka ci gaba da shuɗewa zuwa yanzu Abdullahi da Ibrahim sun zama samari, tuni sun kammala secondary school, har Abdullah ya tafi jami'a, Ibrahim kuma ya ci gaba da neman ilimin addini a wajen Mahaifinsu, ya Rayuwa ta yi ta tafiya cikin kwanciyar hankali, Abdullahi bayan ya kammala jami'a Malam Aliyu Gwani ya basu jari suyi kasuwanci cikin hukunci Allah kasuwancin su ya fara ha ɓaka ciki suka biyawa iyayen na su aikin hajji, Koda suka dawo sun gida musu guda dai dai da na masu kuɗin ƙauye, suna da kamfani da ke sarrafa shimkafa kan farashi mai sauƙi kamfanin su sanannen kamfanin ne saboda sauƙin kayans su, wanda suka saka wa *GWANI RICE LMD* Zuwan da Abdullahi yake a birni nan Allah ya haɗashi da Kubra Galadima mafinta babban Attajiri ne kuma sananne, itace ƴa ɗaya tilo a wajen sa, Kubra yarinƴa ce da tashi cikin gata, tun tana kara Mahaifiyarta Allah ya yi mata rasuwa wajen haihuwa, cikin ƙanƙanen lokaci Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, ba wani bata lokaci kayi buki taro ya tashi lafiya, Ranar su Kaka suka kai masu ziya a birnin sam basu samu tarɓar kwarai ba daga wajen Kubra daga karshe dai suka tattara kayan su suka dawo ƙauye, bayan Auren su da wata biyu Allah ya yiwa mahaifin Kabra Rasuwa, sun shiga tsakanin tashin hankali hakan ya haifar da zubewar ɗan ƙaramin cikin da take ɗauke da shi, saida ta yi jinya a Asbiti tsawon sati biyu, haka suka ci gaba da rayuwa, cikin kwanciyar hankali Azziki tana haɓaka, tsawon shekaru biyu kenan da Auren, zuwa yanzu Ibrahim ya zama cikekken Malamin Addini kaman Mahaifinsu, a dayan ɓangaren kuma babban Attajiri a ƙauye su, lokacin Hauwa'u ta kawo masu jiya ɗayar ƙanwar Kaka, Yarinya ce kyakkyawa ga natsuwa da kunya, soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninta da Ibrahim hakan ya yi wa Kaka daɗi Kasan cewar ƴar uwarci ce ta ko'ina, bada ɓata lokaci ba akayi bukin su, suka tattara kuka wuce Birni Kasan cewar gidan su a haɗe yake, a lokacin Kubra ta shiga da muwa da jin gida ɗaya zasu zauna da Ibrahim, tunda Hauwa'u ta tare a birni bata jituwa da Kubra kullum cikin hantarar Hauwa'u da zaginta taken da ita har Ibrahim ɗin ita a tunaninta dukiyar Abdullahi suke so, don bai taɓa gaya mata dukiyar su a haɗe take ba, saboda Ibrahim ba dukiyar ce a gabanshi ba, Hauwa'u da Ibrahim Rayuwar suke cikin tsananin farin ciki da kyaunar juna... Kubra tun barin da tayi bata koma samun ciki ba, lokacin da ta fahinci Hauwa'u ciki gare sosai hankalin ya tashi ƙiri ƙiri take nuna tsanar cikin, Abdullahi sam baya jin daɗin halaryar Kubra haka Ibrahim sukaci gaba da renon cikin su cikin kwanciyar hankali, har Allah ya sauketa Lafiya ta haifo Kyakkyawar ƴarta, murna wajen Abdullahi ba'a ko magana, narar suna yarinƴa ta ci sunan kaka Maryam, Kaka ta hana a saka mata laƙani, wani lokaci su kira Maryam ko Mamana, Maryam nada sheka ɗaya Allah ya yiwa Malam Gwani Rasuwa, ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, wannan lokaci Kaka tai kaman ta zare don ƙiɗima, Abdullahi shine ya zame musu Mahaifinsu bayan rasuwar malam Gwani ya kama mahaifiyar su ɗa danwan shi, suka haɗa kansu ba mai jin su sai Allah suna kyaunar junan su matuƙa da mutunta juna, komai zasuyi sai sun shawarci juna, bayan Kaka ta gama ta kaba ba yadda basuyi ta dawo birnin ba taƙi haka suka haƙura suka barta, lokacin lokacin sukan kai mata ziyara, itama takan kawo musu ziya, idon yazo har ta koma ba wani a bin ƙirƙi dake shiga tsakanin da Kubra, rayuwar suke cikin kwanciyar hankali, Ranar da aka yaye Maryam suka shiya zuwa ƙauye kai maryam wajen Yaye a hanƴar su ta dawowa sukayi hatsari nan take suka rasu, A lokacin ba ƙaramin tashin hankali Kaka ta shiga ganin gawarwakin su a bangaren Abdullahi har akayi jana'izar baya cikin Haiyacinsa, duk sanda Maryam take kukan yunwa haka zasu saka ta a gaba suna kuka, tana kukan reshin Nono suko suna kukan tausayi ta, hakan ya sa suka ɗauƙi son duniya suka ɗorawa Maryam, bayan wata biyu da rasuwar su Abdullahi yaso Mama ta dawo ɓangaren Ibrahim da zama taƙi haka ya ƙukura ya barta a kyauye. Maryam nada shekara Biyu da Rebi Kubra ta haihu murna wajen Kubra ba'a ko magana, Ranar suna Yaro yaci sunan Malam Aliyu suna kiransa Haydar, Maryam tana son Haydar sam Kubra bata son Maryam ta raɓeshi, duk yanda Abdullahi yake iya ƙoƙarin sa wajen nuna mata Maryam da Haydar duk ɗaya ne, sam taƙi ɗaukar haka, daga ƙarshe ma ta ƙarar tsanar Maryam saboda irin son da Abdullahi da Kaka sukale~~~~ mata... Bayan ƙura ta lafa aka raba gado Kaka da Abdullahi duk suka barwa Maryam, sai a lokacin Kubra tasan dukiyar su a, haɗe take, Haka Abdullahi yaci gaba da juya Dukiyar maryam tare da tashi, Rayuwa naci gaba da huɗewa, zuwa Kurba ƴaƴanta Ukku Haydar, Khalil, Hauwa'u, suna kiranta Nana, zuwa yanzu Abdullahi Baida kowa sai Kaka da iyalinsa..... Haka Kaka taci gaba da kula da Maryam cikin kwanciyar hankali, Abdullahi baya babbata Marayam da ƴaƴan sa, lokacin da ta cika shekara Ukku Abdullahi ya matsa su dawo birnin saboda karatun Maryam ba yadda Kaka ta iya suka tattara suka dawo Birnin badon ta soba, zuwanda ya zame mata damuwa, tunda Kaka da maryam suka dawo birnin da zama, Kurba na kullum cikin Habaice Habaice take tana faɗin, tunda an raba gado an ba kowa nashi zaman me suke a gidan, ko so suke suga bayan dukiyar Abdullahi, tun Kaka na haƙuru har takaiga yiwa Abdullahi magana ya jawa Kubra kunne, hakan ya janyo tashin hankali tsakanin Kubra da Abdullahi har ya haifar da saki tsakanin su, Ganin haka yasa Kaka ta yenke shawarar suka koma ƙauye tare da Maryam, ranar da zasu Tafi Abdullahi da Hawayen shi, a ganin sa kaman bai riƙe Amana ba, nan Kaka tashiga lallashinshi kan yayi haƙuri karatun birni da ƙauye duk inda mutum yayi bazai wuce Azzikinshi, tunda suma a ƙauye sukayi karatu har suka kai matsayin da suke a yanzu, sosai maganar Kaka ta shigeshi bayan sun koma ƙauye ya gyara musu gida da duk wani abun buƙata, saboda Kaka ba mai son kyale kyale ba ce, sam zaka ce tana ɗaya mai kudin, duk da hakan gidan ta na ɗaya daga cikin gidajen masu kyau a ƙauyen kayan Abinci duk wata yake turo mata.. haka suci gaba da rayuwa cikin kwanciyar da walwala... tuni an saka Maryam makaranta... Abdul Maleek yaro ne na tsastse dawowar ƙaunyen bada jimawa Allah ya yiwa mahaifiyar shi rasu, haka suka ci gaba da rayuwa tare da Mahaifinshi, a lokacin shekarar sa goma, zuwan da yake gidan Kaka ɗibar ruwa nan Allah ya haɗa jinin shi da Maryam, wata irin shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, Ranar da ba makaranta idon ya zo gidan su Maryam baya koma sai dare, Mahaifinshi ɗan kasuwa ne yana sayarda dabbobi, duk lokacin da zaiyi tafiya a gidan kaka yake Barin Abdulmalik Kasan cewar Baida ɗan Uwan a garin Kaka ce ta zame mishi dengi, haka suke rayuwa tare da Mahaifinshi cike da kyaunar juna, Mahaifin Abdulmalik mutumen girki ne. Abdulmalik na jss3 Allah yayi wa mahaifinsa rasuwa a can garin da yake zuwa kasuwanci, lokacin da labarin mutuwar ta riski kaka da Abdulmalik sun shiga tsakanin tashin hankali, haka yaci gaba da rayuwar shi cikin kulawar Kaka da ta ɗokeshi tamkar jikanta, ba yan rasuwar mahaifinsa ba yadda Kaka batayi ba a kan ya dawo gidanta da zama ya ƙi a cewar shi baya son barin gidan saboda mallakin Mahaifinshi ne, da taimakon Kaka Abdulmalik ya kammala Secondary, Abdulmalik yaro ne mai son neman na kasan ka, bayan ya kammala Secondary yaci gaba da neman aiki duk da bai rasa komi ba duk abinda yake buƙa Kaka nayi masa, hakan yasa ya nemi aiki a kasuwa nan Allah ya haɗa shi Oga Kabiru da yake fake masa shago da ɗan aikace aikace duk sati yake biyan shi dubu biyar.. Kasan cewar Abdul Maleek yaro ne mai natsuwa da Amana hakan yasa Oga Kabiru ke ƙaunarsa duk lokacin da yake zuwa birnin sayen kaya da Abdulmalik yake zuwa Kasan cewar bai yai karatu ba duk cikin yaran shi ba kaman Abdulmalik... Maryam ƴarinƴa ce kyakkyawa fara Masha Allah don tana kama da mahaifiyarta sosai maryam ƴarinƴa ce mai shegen wayo ga reshin tsoro ga tsiwa ga miskilanci akwai shaƙuwa sosai tsakinin Abdulmalik da Maryam... wannan kenan....🤗 Bayan Isha'i suna zaune a tsakiyar gida, Abdul Maleek ya shigo gida da guda Maryam ta nufi wajensa ta rungumesa, tana faɗin "Sannu da zuwa Ya Maleek!" Sassanyan Nunfashi ya sauke cike da gajiya yace "yauwa Maryama ta!" "Barka da dare Kaka, "Abdulmalik An dawo lafiya?" "Lafiya lau Kaka" yana gama cikin Abinci sukayi karatu, kana ya kalli Kaka cikin sanyi Muryar yace "Kaka gobe idon Allah ya kaimu zamuje Birni sayen kaya tare da Oga, Nunfashi Kaka ta ja kana ta fesar, murya a sanyaye tace "Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya!" "Amin Kaka" cikin raunin Murya Maryam tace "Ya Maleek idon ka tafi yaushe zaku dawo!" Ajiyar zuciya ya sauke kana yace," Ban sani ba" Maryama kaman Zatayi kuka," Ya Maleek zan bika, "A'a, kana ya yi musu sallama ya wuce gida.... Washegari tunda safe bayan sun karya yayi Kaka Sallama kana ya wuce kasuwa... Yana barin gidan Maryam ta fashe da Kuka tana kiran Ya Maleek...✍️✍️ *More comments and share* *Sadeeya Ka'oje ce* *DR SULTAN* *( THE BEGINNING)* _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ Tallah ! Tallah !! Tallah!!! Shahararriyar Marubuciyar nan Hafsat Muhammad Bature (Boss Bature) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *ABBAN SOJOJI* yau ta sake dawowa muku da sabon labari mai ɗauke da sabon salo na musamman *KURKUKUN ƘADDARA* labari ne mai kunshe da Butulci , tausayi , ban dariya , cin amana , soyayya mai shiga rai karna cika Ku da surutu, *KURKUKUN ƘADDARA* littafine mai ɗauke da Rudani da ban Al'ajabi kudai ku kasance da Alƙalamin *Boss Bature*💋💖 domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Number 08103884440 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *Page 7-8* _______Yana barin gidan ta fashe da kuka tana kiran," Ya Maleek!" da kyar Kaka ta lallashe tayi shiru, Abdulmalik bayan fitar dashi daga gidan Kai tsaye ya nufi Kasuwa ba wani jimawa motarsu ta ɗaga cike da kewar Maryam.... Yinin Ranar gabaki ɗaya Haka maryam cikin fushi, da Daddare haka taƙi cin Abinci, Saida kaka tayi mata zan ido kana ta ɗan ciki ƙaɗan, kwanan su Abdulmalik Ukku a birni suka dawo, Wuraren ƙarfe Shidda ya shigo gida, " Maraba da mutanen Kano, Kaka ta faɗa cikin tsananin farin ciki, dai dai lokacin Maryam ta shigo gida dawowar kenan daga Islamiya a guje ta nufi inda yake ta rungumeshi, "Ya Maleek sannu da zuwa!!" A hankali ya juyo da ita suna fuskantar juna, "Kina Lafiya?" da sauri ta ɗago ta kalleshi tare da sakin Murmushi Nan take ɗin dinta suka bayyana, A hankali ya motsa Lips ɗinsa hakan ya sa ko Kaka dake kusa dasu bati me ya faɗaba, " Maryama ta!" ta kira sunanta cikin kasalelliyar murya da ta sa Maryam sauri ɗagowa ta zuba mishi ido domin bata taɓa saninsa da irin wannan Muryaba, a hankali ta sake yin ƙasa ta kanta cikin tsananin kunya, yatsun hannunta ya sha jan lalle ya zubawa ido, ƙasa tayi da kanta tana ci gaba da wasa da yatsunta, a hankali Maryam ta Manyan idadunta ta kallesa, ya ɗaga mata gira tare da jan Numfashi ya fesar, Kaka dake gefe ta saki baki cike da Mamakin irin Kallon da suke wa juna, Abdulmalik har ga Allah ya manta da Kaka na Wajen, Ido a lumshe yaci gaba da kalli yatsun hannunta, Maryam tuni jikinta Yayi sanyi, Kaka sam ta gaza ɗauke ido a kansu, Murya can ƙasa ƙasa kaman mai raɗa yace "waya Miki lalle nan mai kyau!" Sassanyan Nunfashi ta fesar cikin sanyi Murya tace "Kaka!" kaka kam sai Raba ido take ta kalli Abdulmalik ta kalli Maryam, a hankali Maryam ta fara janye hannunta daga nashi, ciki wani irin yanayi da Baitaɓa rikar kanshi ya yi saurin janyo Hannuta yana ci gaba da kallon su, a hankali ya lumshe idanunsa nan take hawaye Masu matsifar sanyi suka zubo kan kyakkyawar fuskarsa, Maryam da Kaka cike da Mamaki suka zubawa fusakar ido ganin Hawaye kwance a saman fusakar shi, haka Maryam ta tsinci kanta da share mishi Hawayen, a hankali ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya, " Ya Allah ka jiƙan Ummina!" Ya faɗa can ƙasan maƙoshi, Murya a dishace Maryam tace ," Ya Maleek Kukan me Kake?" A karon farko ya saki Murmushi ƙarfin hali, cikin wani irin yanayi da bai iya jurewa, sun ɗau tsawon lokaci a haka ba tare da sun sake Magana ba. Mutsu mutsu ta fara tare da ƙoƙarin janye hannunta dake sarƙe da nashi, kansa ya ɗago ya kalleta da rikitattun idanunsa, Nan taga yadda idanunsa suka kaɗa sukayi jazir sun sake cika da tace da hawaye, Ƙoƙarin janye hannunta taci gaba da yi jiki a ya ɗago da kansa ya kalleta sai kuma ya Lumshe idon Hawayen da suka cika a idonsa suka zubo, a hankali yaja dogon Numfashi mai bala'in ɗumi da kyar ya tattaro da ƙarfisa, murya a dishace yace," ga wannan, ba tare da yadda sun haɗa ido ba, murya a dishace Maryam tace ," Ya Maleek baka son lalle na Dena!" ba tare da ya kalleta cikin sanyi Murya yace Ina s.... Karab Idanunsa suka sauka kan Kaka dake tsaye ta zuba musu ido, da sauri ya janye Idanunsa daga kallon Kaka, a hankali ya sunkuyar kai tare da shafa kanshi cikin sanɗa sanɗa ya yi ƙoƙarin ficewa daga gidan," Abdulmalik cak ya tsaya jin Muryar Kaka ," Ina zaka je? Cikin sanyi Muryar ya soma Magana," Gida zanje Kaka!" "Dawo Kaci abinci" a hankali ya sauke Ajiyar zuciya, kai a sunkuye ya dawo ya zauna a tsakiyar gida Kana kaka ta aje mishi abincin sa yaci, Kaka na janshi hira har ya kammala, dai dai lokacin Maryam ta iso riƙe da perpar," Ya Maleek duba ga ki waye wannan?" A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe akan takardar, da sauri ya runtse idanunsa, wani irin Amitattacen Nunfashi mai cike da yanayi na Musamman ya fesar da idanunsa suka kan Hoton da jikin takardar, "Ya Rabbi!!" Shine a binda ya iya furta, a hankali yaci gaba da kallon kyakkyawan Saurayin da ke cikin takardar, Kaka ma zajen take kallo, "Maryam waye kuma kika zana?" Wani irin sassanyan Nunfashi ta fesar," cikin sanyi Muryar tace,"Kaka Ya Maleek!! Ne" Wani irin lumshe idanunsa ya yi, wani irin kallo mai tafiya da dukan natsuwa yake binta dashi tun daga farko hoton har zuwa sama ina Aka rubuta YAYA ABDULMALIK da manƴan haruffa, hoton shine sak Maryam ta zana, zane na ɗaya daga cikin bawarda Allah ya yi Maryam, "Maryama ta!" Nina kika zata haka, ai zanen ya fini kyau, Harara ta zabga mishi, murmushi yayi tare da ƙarɓan zane yana Kallo, "Maryam ta! Allah zanen nan ya fini kyau!" da sauri Abdulmalik ya juya yana kallon Kaka," Kaka da zanen nan dani wa yafi kyau!"?yadda yayi maganar da kuma yadda ya marairaice abin yaba Kaka Dariya," fusakar Kaka ɗauke da murmushi tace ," Abdulmalik ai kafi zanen nan kyau kaifa kyakkyawa ne! Ma sha Allah!" Rau rau Maryam tayi da ido sai kun ta ta tsuke fuska kana tace ,"Ya Maleek kaifa kyakkyawa ne!" Abdulmalik a hankali ya tauna lips kana yace," Ki bani hoton nan na tafi dashi ɗakina" Harara ta dalla mishi ,"Allah Bazan Bazan ba daba, Saida na zana ma wani ta karasa maganar cike da tsiwa da murguɗa baki, Abdulmalik ya yi Murmushi, haka suka kasance cikin farin ciki zuwa bayan Isha'i bayan sunyi gama karatu suka ɗanyi hira kana ya wuce gida cike da gajiya... Yana isowa ya ɗan yi yi gyare-gyare a ɗakin.Abdulmalik Gwani ne a fanni tsabta kana ya yi Wonka ya kwanta nan take bacci gajiya ya yi awon gaba shi.... Washe gari ranar baije kasuwa ba wonki yayi musu kayanshi dana Kaka da Maryam, Maryam na tayashi gwanin burgewa, "Kinga ki Dena wankin Nan kar lallenki ya goge, "Ya Maleek idon ya goge Kaka zata min wani, haka suka ci gaba da wonki har suka kammala, ranar gabaki ɗaya a gidan kaka ya yini sai dare ya wuce gida tare da kayan shi da wonke Kaka sai saka mishi Albarka take..... A hankali Rayuwa taci gaba da tafi cikin kwanciyar hankali tuni su Maryam sun koma Makaranta, sosai ta maida hankali wajen karatun, duk abin ya shige mata duhu takan tuntuɓi Abdulmalik, hakan yasa komi ke zuwa mata da sauƙi, a ɓangaren islamiya ma ba'a barta a baya ba, Rayuwar suke cikin kwanciyar hankali da ƙaunar juna, zuwa yanzu Maryam Na gaba da cika shekara goma sha ukku a duniya, A Ɓangaren Abdullahi ma duk bayan wata ɗaya yakan aiko musu da kayan Abinci kaman yadda ya saba da duk wani abun buƙata, kusan kullum sai ya kira su, Abdulmalik da Abdullahi basu taɓa haduwa kasan cewar yana jimawa bai zo ƙauye ba saboda yanayin aikin sa, duk lokaci zaizo ko tunda safe yake zuwa haka zai zauna suyi hira da Kaka harzu zuwa lakacin da Maryam zata dawo daga Kamaranta, kana ya wuce Kano... “Kaka Abba ya Kira, kiran na gab da tsinkewa ta ɗaga, cikin sanyi Murya ta soma magana "Abba ina wuni ya gida Abba ina su Haydar"? daga can ɓangaren Abba ya sauke Ajiyar zuciya Kana," Mamana Lafiya lau suke, Ina Mama"? "Gata Abba" tayi Maganar ta re ɗorawa Kaka wayar a kunnen, "Abdullahi Ya gida"? ta faɗa cike da kewar ɗanta, " Lafiya lau Mama" cikin raɗa Maryam tace "Kaka ga ki gaya mishi na kusan sauka, ranar walima yazo dasu Haydar" Kaka ta talla mata Harara,nan take Maryam ta tsuke fuska tana turo baki, haka suka ci gaba da hira gwanin burgewa, Kana kaka ta mikawa Maryam waya nan ta sanar da shi abinda ta gayawa Kaka," Insha Allahu zamu zo tare, Kafin nan ma zamu shigo Ranar Assabar tare dasu, wani Irin daɗi Maryam taji, sun jima suna hira tana bashi labari Abdulmalik da yajima da sanin sunan sa a baki, Kafin nan sukayi Sallama, cikin wani irin ya nayi mai ɗauke da tsantsan farin ciki.tace , " Kaka Abba ya ce zasu zo ranar Assabar tare da su Haydar! Allah ya nuna Muna," Amin Kaka..." Washegari tunda da sassafe Abdulmalik na shigo ta bashi Labarin su Haydar zasu zo, "Ya Maleek karka je Kasu kaji," "saboda me?" "ka zauna gida muyi hira tare dasu Haydar" "Maryama ta! Idon na zauna a gida wazai min aiki na?" "Ya Maleek don Allah fa nace" " Shike nan zan zauna Amman idon suka jima basu zoba zan wuce kasuwa kin yadda" "Ehh Na yadda na san Abba da wuri zai yake zuwa duk lokacin da zai zo" "Nadai faɗa Miki" "Naji" ta faɗa cike da tsiwa tare da murguɗa baki" "Wannan bakin wata rana saina canye shi idon baki dena murguɗa shi ba" Kallonta Abdulmalik ya yi kana ya yi Murmushi a hankali ya ce ,"Maryama Sarkin tsiwa" A gurguje suka karaya ganin lokaci na tafiya, lokaci ɗaya suka kammala kana sukayi Kaka sallama kai tsaye suka wuce makaranta daga can ya wuce Kasuwa.... sai dare ya dawo, Yau take Assabar tunda sassafe Kaka ke aikin Abinci nan take gidan ya gauraye da ƙamshi mai daɗin gaske koda 8:30 tayi Kaka ta kammala komi tare da taimakon Maryam suka gyara gida tare da kunna turare mai matsifsr ƙamshi da saka natsuwa..... Wuraren 8:46 Abdulmalik ya shigo gidan, "Kaka ina kwana, " Lafiya lau Abdulmalik" " Kaka baƙin basu iso ba?" "Nunfashi Kaka taja kana ta fesar,"muma zaman jiran su muke Abdulmalik" "Gashi har 9 ta kusa ni zan waje kasuwa" wani irin Kallo Maryam ta watsa mishi" " Ai kam gaskiya ne ba'a san ranar zuwan su ba ga abincin kanan" " Nagode Kaka!" A tsanake ya soma cikin Abinci bayan ya kammala ya wuce, " Wai wannan fushi duk na miye haka cewar Kaka" turo ɗan ƙaramin bakinta tayi "Kaka ba Ya Maleek ba ne yaƙi tsayi ya ga su Haydar" Kaka tayi murmushi kana tace," to ai ba laifinshi bane sune basu iso da wuri ba kuma jiya Saida ya gaya Miki idon basu zo da wuri ba zai wuce kasuwa kike ce kin yadda to miye kuma abin ɓata rai" "Wallahi ba ruwa dashi bari ya dawo" dai dai lokacin sukaji tsayuwar mota a ƙofar gida, Kaka ta sauƙe sassanyan Nunfashi, can ƙasan maƙoshi tace "Alhamdulillahi Allah na gode ma da ka kawo su Lafiya" Cikin tsiwa Maryam tace Kaka wallahi sun iso" da sauri ta mike har tana batun faɗuwa, "Mamana kiyi a hankali karkiji ciwo!" A hankali ta Lumshe idanunta kana ta buɗe akan fusakarsa kyakkyawan dottijon dake tsaye a harabar gidan dogo ne fari sol da sauri Maryam ta iso wajensa tare da rungumeshi "Abba sannu da zuwa!" "Mamana! Kina lafiya!?" "Lafiya lau Abba!" A hankali ta janye jikinta daga nashi"Abba ina su Haydar!?" dai dai lokacin suka shiga cikin gida su Ukku sanye shedda mai matsifsr kyau da tsaya sosai kayan sukayi masu kyau, da sauri maryam ta iso wajensu ta rungumesu gabaƙi ɗaya tana faɗin ,"Ƴan ƙanne na! Mai ɗan girma cikin su ya harareta....... duka shekara nawa kika bamu? ya ƙara sa maganar cikin tsokana, " Koma dai nawa ne ai na girmeku...... A hankali ya nufi inda Kaka take zauna ya durƙusa har ƙasa cikin girmamawa ya gaishe ta,"Mun sameku lafiya Mama!" Cikin sanyi Murya tace ," Lafiya lau Alhamdulillahi" Haka suka zage Kaka gaba ki ɗayan su Kana suka Gaisheta, cikin tsananin farin cike ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana shafa kansa tare da sanya musu Albaka, "Malam Gwani ya Makaran?" "Lafiya lau Kaka" "Masha Allah ya maman ku?" "Kaka Momy bata da lafiya! komai bata iya yi sai masu Aiki sunyi mata" da sauri Kaka ta maida Kallonta ga Abdullahi, murya a dishace tace ,"Gaskiya ne abinda Malam Gwani ya faɗa? Kai a sunkuye yace ," Jikin da sauƙi sosai" " haba Abdullahi me saya tun lokacin baka sanar dani ba!" " ki gafar ceni Mama" "Ya jikin nata yanzu mike da munta kuma?" "Cikon sugar ne Mama" "Allah ya bata lafiya" ga baƙi ɗayasu suka Amsa da Amin, "kira min Ita mugaisa ba musu ya kira, Kaka tayi mata ya jiki basu wani jima sukayi Sallama Kasan cewar ba shaƙuwa a tsakanin su, dai dai lokacin Atiku Direba ya shigo gidan dauke da ledoji niki niki, cikin girmamawa ya gaida Kaka kana ya fice daga gidan, "Maryam tashi ku kai mishi abinci gaba ki ɗaya su suka miƙe zuwa kicin suka ɗauƙi Abinci kana suka kai mishi. Koda suka dawo Kaka ta jera masu Abinci haka suka zauna cikin Abicin cikin natsuwa da kwanciyar, sai sontin Abinci suke, Bayan suka gama cikin Abinci suka tattara kayan zuwa kiciin, Kaka da Abdullahi suka ci gaba da hira yaushe gama, nan yake faɗa mata irin ciki gaban da yake samu a kasuwanci su dukiyar Maryam ma sai haɓa ka take, Kaka ta yi farin ciki sosai da wannan maganar, A ɓangaren su Haydar kam sai wasar su suke, gwanin burgewa, Ranar dai haka suka kasance cikin tsantsan farin ciki, sai gab da maggariba sukayi Kaka Sallama kana suka wuce, cike da kewar zuna, Kaka ta haɗa masu kayan tsaraba irin na kyauye, lokacin da suka wuce Maryam Hadda kukanta, har ga Allah tana son Kasan cewar da ƴan Uwanta, Har bayan Isha'i fusakar a tsuke, Koda Abdulmalik ya shigo gida Kaka na ɗaki, ko inda yake Maryam bata kalla ba, "Cikin sanyi Murya ya kira sunanta "Maryama ta!" Miƙewa tayi tare da barin wajen, a hankali Abdulmalik ya sauke sassanyan Nunfashi tare da fesar da Numfashi, A karo na biyu ya sake kiran sunanta "Maryama ta! Maryama ta!! Maryama ta!!!" tuni ta shige ɗaki , durƙu sawa ya yi a wajen cikin zazzaƙar Muryar shi mai cike da natauwa ya soma rare mata wakar Umar M Sharif ( Maryama) wanda duk lokacin da tayi fushi ita yake rera mata, 🎶" Ina kike Masoyiya! na duba gabas ban ganki ba na duba Arewa ban ganki ba naje kudu ban ganki ba naje Yamma ban ganki ba! Ehya ya ya oh yah yah yaushe zaki yaushe zaki zo! Yaushe zaki zo Masoyiya!...... naga ƴan mata iri kyawo baza su fiki ba! Kalaman so kashi kashi banji salo irin naki ba kyan halinki ba'a faɗa baki hanya wuce gaba gata nan tafe🎶gata nan tafe gata nan tafe Masoyiya 🎶gata nan tafe tana zuwa!🎶 Maryama zo Maryama zo Maryama zo Masoyiya!!! 🎶 Kinza ma Ni nazama ke komi zanyi done Saida ke banci abinci inbabu ke Nagode Allah daya bani ke! Maryama Maryama ta iya kalliya Maryama mai kyau da dariya Maryama!!! Lala lalaye Maryama zo Maryama🎶💖💋 Yana mai ƙarshe baiti ta fito ɗakin a guje ta faɗa ƙirjinshi ya rungumeta da karfi Ya runtse idanunsa "Ya rabb" ya faɗa a ƙasan maƙoshi, Kanta ta manya a ƙirƙijinsa tare da sa hannuwanta duka biyu ta zagaye ƙugunshi tare sakin sassanyan Ajiyar zuciya, Runtse idanu sukayi lokaci ɗaya tare da sakin sassanyan Ajiyar zuciya, "Maryama ta!" Kin Dena fushin? a hankali ta gyaɗa maishi kai, a hankali ya janye ta daga jikinshi, lokaci ɗaya suka sakarwa junansu Murmushi. "Ya Maleek kana fida su Abba suka iso ta karasa maganar cike da Shogoɓa, "Ayya Maryama ta Allah bai kadda zamu haɗu ba! Amman Insha Allah wata rana zamu haɗe a tare!" "Abdulmalik an dawo cewar Kaka, "Ehh Kaka na dawo ya baƙi" "Lafiya lau yanzu mukayi waya har sun isa gida" "Masha Allah, Allah ya wutar da hajjiya Allah kuma ya basu ladan zumunci" "Amin ya rabbi Abdulmalik" ga abin cinka nan, tare suka ci da Maryama suna ci yana tsokanar ta har suka kammala, kana sukayi Karatu, nan Kaka ta kawo musu kayan marmari da Abba ya kawo musu, Abdulmalik yana ci yana. Lumshe ido Allah ya sani yana son kayan marmari, bayan sun gama shan kayan marmarin ya wuce gida..... A hankali Rayuwa taci gaba da shuɗewa , tuni su maryam sunyi sauka aka haɗa musu gagarumar walima kusan komi Abba ne ya ɗau nauyi komi ranar walima Malam Gwani da iyayen Maryam sunsha Addu'a, Ranar walima su Haydar kaɗai suka samu damar zuwa, Abdulmalik ya taka muhimmiyar rawa a wajen walimar, haka tare ya tashi lafiya, A ɓangaren kubra ko jikin tana sai ƙara tsauri yake, wani lokacin har gado aka bata Asbiti, gabaƙi ɗaya Abdullahi baya cikin Haiyacinsa, kullum sai kaka ta kira taji yakinta..... Haka dai kwanaki suka ci Baga da shuɗewa..zuwa yanzu Maryam ta fara girma, Kwance a take a tsakiyar gida sai juyi take,"Kaka ƙirjina ciwo yake har yanzu Kaka wlh gobe idon naje makaranta sai na rama, "Kiyi Haƙuri tunda tace ba da saninta ta buge ki ba, daman idon ana ƙidan degin hake abu kaɗan saiya taɓa wajen, nidai wlh Kaka saina rama itama gidan dengi take taji irin zafin da nakeji!" "Ohni Mairamu" cewar kaka shegen jini nin tsiya ginga tafiya ta, a hankali Kaka ta nufi ɗaƙi, dai dai ya Abdulmalik ya shigo, da sauri ta mike zaune tana faɗin "Maleek kalli Ubaidah ta ɓararmi da ƙidan dengi na tayi magana tana ƙoƙarin buɗe gaban rigarta da sauri ya dakarta ita ta hanƴar daga mata Hannu, "Ya Maleek duba ka gani wlh ciwo suke min da sauri ya runtse idanu wansa cikin wani irin yanayi da shi kanshi ba zai tantance wani iri ne ba " ya Salam" da sauri ta maida rigarta cikin tsiwa tace ," Ya Maleek zafi suke min!" "Ina Kaka?" "tana ɗaki" kai tsaye ya nufi ɗakin ya gaishe Maryam ta bishi da Harara, bayan sun gaisa tare suka dawo Tsakiyar gida suka zauna kana yaci Abinci, bayan ya gama ta kalli Kaka cikin sanyi Muryar yace "gobe zamuje Kano tare da oga" " TOH Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" Amin Kaka, dai dai lokacin wayar Kaka tayi Ringing a hankali ta ɗaya wayar "Abdullahi Ya gida lafiya? Ya nayi muryar a haka? Ya jikin Kubra? Daga can ban ɓangaren Abdullahi ya sauƙin Nannauyan Ajiyar zuciyar murya a dishace yace ," Kaka jikinne ya kara tashi sosai yanzu haka muna Asbiti, "Subuhalillah Allah Ubangiji ya bata lafiya "Amin" "Gobe ka aiko Direba yazo ya kaimu na ganata, "TOH Mama sai kushirya da wuri Allah ya kawo ku lafiya, " Amin ya rabbi, kana sukayi Sallama, kaka ta sauke Ajiyar zuciya kana ta fesar da Numfashi mai Zafi, "Abdulmalik gobe muna zamuje Kano matar baban Maryam ce ba lafiya yanzu haka suna Asbiti, "Allah ya bata lafiya Kaka yaushe zaku dawo kenan goben zamu dawo Insha Allahu, Nima ina tunani kwana ɗaya zamu kana mudawo, " TOH Allah ya dawo damu lafiya Amin Kaka" Maryam ha kawai gabanta ya riƙa faɗiwa, Murya a dishace tace "Kaka Nikam Bazan je ba,"saboda me? "Bakomi Kaka" "Aiko dole kije" Jiki a Mace Abdulmalik yayi musu sallama ya wuce gida, Nan Kaka tashi haɗa .musu kayan su, Washe gari tunda sassafe Abdulmalik ya shigo gidan tuni su kaka ma sun shirya direba kawai suke jira tare suka karya kana Abdulmalik ya yi musu Sallama ya wuce har ya kai baƙin ƙofa ya dawo "Kaka yau kike zaku dawo ko?" "in sha Allahu Abdulmalik yau ko gobe duk yadda hali ya yi bazamu jima ba kodon makarantar Maryam koda ka dawo baka gobe baku da woba zan a jema makulli kodon dafa abinci " Toh Kaka Allah ya tsare" "Amin" "Maryama ta! Bazaki min rakiya ba cikin mutuwar jiki saba ta san namiye ta rakashi har ƙofar gida har ya tafi ya kira sunan sa "Ya Maleek" a hankali ya juyu suna fusakar zuna da sauri ta faɗa jikinsa ta rungumeshi, "Ya Maleek Allah ya kaika Lafiya ya dawo dakai lafiya" "Amin ya Allah Maryama ta! Kinga bari na tafi lokacin na ƙarewa, " Ya Maleek Allah ya sadamu da Alheri! Nan take jikinsa ya yi sanyi, murya a dishace yace ," Amin" tana tsaye a wajen har ya ɓace mata kana ta wuce cikin gida, Jikin a mace ya wuce kasuwa tsawon Awa guda kenan da isawarshi sai yanzu Oga Kabiru ya iso Kana suka wuce..... Bayan tafiyar Abdulmalik baifi minti goma Atiku Direba ya iso kana suka wuce, tafiya suka hankali a kwance kar suka iso Kano kai tsaye ya wuce dasu Asbiti.... Isowar su ya yi dai da likata na sanarda Abdullahi rasuwa Kubra Haka kaka taji maganar kaman saukar Adaru nan take jikinta ya soma ƙarkarwa cikin wani irin mummunan yanayi da tashin hankalin murya rana ta kira "Abdullahi da gaske Kubra ta rasu Abdullahi da tunu ya baya cikin Haiyacinsa sam baiji me kaka ka faɗi ba, Maryam gabaƙi ɗaya a ruɗe take....... Nan take Kaka Abdullahi ya yenke jiki ya fadi a sume, Maryam ta kwalla wata irin ƙara mai razanarwa, tare da ƙamkame Kaka jikinta naci gaba da ƙarƙarwa........ *ABDULMALIK*😥 Tunda suka dauki hanyar suna tafiya ba abinda yake ji a zuciyarshi kamar kewar rabuwa da Maryam ya rasa abinda yasa bugun zuciyarshi take tsananta a kowani dakika na bugun agogo dake cikin motar,lokaci zuwa lokaci zufa ke tsatsafo masa yana gogewa ji yakeyi kamar tafiyar da zaiyi bazai dawo ba,wata zuciyar Kuma na raya masa sun rabu da Maryam kenan rabuwa ta har abada,addu'a yakeyi indan yaji irin wanan tunanin ya fado masa har suka Yi nisa sosai a tafiyar tasu. Bayan yayi addu'ar ya samu nutsuwa ba'a mintuna kalilan ba yaji kamar yanayin tafiyar motar ya chanza,bae samu cewa komai ba ya dinga sauraro a tsanake chan dae yaji kamar motar na kara wani irin kara, da sauri ya ce "Anya baza'a faka a duba motar nan ba kuwa dri......" Ko karasa abinda zaifada baiyi ba motar ta kwace a hannu driver ta shiga junjuyawa har zuwa jeji sosai yake son rike sitiyarin motar abin ya ci tura,Wani babban dutse motar ta daka da karfin tsiya ,a take bangaren da maleek yake qofar ta bude kamar wanda akayi wurgi dashi ya fada cikin dokar daji kansa ya bugi katon dutse nesa da inda hatsari ya afku. haka motar taci gaba da junjuyawa cikin hunkici Allah ya tsaya cak...... Bayan wani ɗan wani lokaci mutane suka taru a wajen tare da basu taimakon gaggawa, tuni labarin mutuwar ya kewaye garin ƙaraye cikin tsananin tashin hankali, daga daga cikin maƙotan Kaka ta kiranta kusan sau ukku gab da kiran zai tsinke Kaka ta daga murya a dishace tace"Iya! "Kaka ya mukaji da haƙuri Abdulmalik ashe lokacin Yayi! cikin tsananin tashin hankali da ruɗewa "Kaka tace wanne Abdulmalik!"Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!" Kasan cewar wayar a hand free take nan take Maryam ta yanke jiki ta faɗi.....✍️✍️✍️ *More comments and share* *Sadeeya Ka'oje ce✍️* *DR SULTAN* (A heart touching love story) *( THE BEGINNING)* _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ Tallah ! Tallah !! Tallah!!! Shahararriyar Marubuciyar nan Hafsat Muhammad Bature (Boss Bature) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *ABBAN SOJOJI* yau ta sake dawowa muku da sabon labari mai ɗauke da sabon salo na musamman *KURKUKUN ƘADDARA* labari ne mai kunshe da Butulci , tausayi , ban dariya , cin amana , soyayya mai shiga rai karna cika Ku da surutu, *KURKUKUN ƘADDARA* littafine mai ɗauke da Rudani da ban Al'ajabi kudai ku kasance da Alƙalamin *Boss Bature*💋💖 domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Number 08103884440 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *Page 9-10* ________ Nan take ta yenke jiki ta faɗi "Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n! Atiku Direba dake tsaye cikin ruɗu da tausayawa ya yi saurin ƙara so gaban Kaka, cikin tsananin tashin dake tattare re dashi murya a disashe ya soma magana ,"Mama suma tayi, Kaka tuni tayi suman zaune, "Doctor ku taimaka muna, da sauri Nurse suka ƙara so wajen tare da ɗaukar Maryam suka wuce da ita..... Cikin Wata irin dakakkiyar murya mai ɗauke da tarin raɗaɗi ta ƙuna tace," Abdulmalik ɗin ne ya rasu! Kallonta ta mayar ga Abdullahi dake zaune daɓas a ƙasa kaman wani yaro tare da wani likita Rungume da shi, dai dai lokacin wata nurse ta iso hannuta dauke da ruwan gora, Dr ya karɓa kana ya buɗe tare da yayyafawa Abdullahi ruwa dake kwance a jikinsa har so biyu sai a karo na Ukku ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, a hankali ya soma buɗe idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir ya sauke su akan Kaka, a hankali Abdullahi ya fara sakin Ajiyar zuciya kana ya shiga maimai ta Addu'oi sannu a hankali ya fara dawowa haiyacinsa A hankali ya sake ɗago da idanunsa ya kalli Kaka ya yi ƙasa da kansa cikin raunin Murya ,"Mama da gaske Kubra ta rasu!?" Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da Kaka, ta kallesa Zuciyarta na bugawa da matsifar ƙarfi murya a disashe tace ,"Abdulmalik ya rasu! jiki a mace Abdullahi ya fara janye jikinsa, "Mama kubra ta tarasu!" Kai Kaka ta gyada mishi cikin tsananin tashin da ruɗu ta fashe da kuka mai tsuma zuciya murya na rawa tace ," Abdulmalik ma ya rasu!!!"Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n" cikin ƙanƙanen Lokaci Asabiti ya cika da mutane kasan cewar ɗaya daga cikin nurse ɗin kwai ƴar Uwar Kubra, ko wannen su damuwa fal a fusakar sa, koda aka fito da gwar Kubra da kyar Abdullahi ya iya mata kallon karshe, kana ya fashe da sabon Kuka, kasa cewa komi ya yi kawai ya fashe da matsanancin kuka cikin raunin Murya yace," Allah ya jiƙan ki Kubra! Allah ya ƙarɓi baƙunci ki!, Kaka ma tuni hawaye sun cika tab a Idonta, wani irin tausayin ne ya ratsa duk kan mutanen da ke tsaye a wajen, anan Asibitin aka shiryata kana akayi mata sallah tare da kaita gidanta na gaskiya, Jana'izar da tasamu halattar dumbin jama'a yan uwa da abon Azziki.... *ƘARAYE* tuni an iso da gawarwakin wayan da sukayi Hatsarin nan take gari ya hargitse da koke koke, kasan cewar sunyi dameji sosai bata ɓata lokaci akayi jana'izar aka gaisu gidan su na gaskiya,..... *KANO* Murya a disashe Abdullahi yace " Kaka Mutafi gida ko!" Cikin raunin Murya Kaka tace ," Abdullahi Maryam tana wajen likitoci!"Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!" Cewar Abdullahi , *MARYAM* Likitoci ne suka duƙufa a kanta tare taimakon gaggawa koda wasa bata bata farfaɗo ba, ganin haka yasa suka ɗauko wata na'ura mai kama da iron suka fara dannan mata a ƙirji... haka suka ɗau tsawon lokaci Amman ina babu alamu rai a tare da ita.. haka likitoci suka kwace tsawon lokaci don ganin sun ceto rayuwarta, a karo na Barka tai suka sake danna mata na'urar a ƙirji ta ƙarfi, cikin ikon Allah Maryam taja wani dogon Numfashi sai kuma jikinta ya sake, a karo na biyu Dr ya sake danna mata na'urar,da ƙarfin gaske, ta sake jan wani Numfashi, still bata farfaɗo ba, Dr wata irin zufa ce ta riƙa tsastafo mishi, sauran Dr duk jikinsu ya yi sanyi, a hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe su a kan fuskarta Maryam, da kyar ya tattaro duk kan ƙarfinshi ya sake danna mata na'urar da karfi, taja dogon Numfashi tare da buɗe idanunta cikin raunin Murya tace," Ya Maleek!!!" Lokaci ɗaya likitoci suka sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar tare da fesar da Numfashi, Duk da bata cikin haiyacinta hakan bai sa ta Dena faɗin ," Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!! da duk wata Addu'a data zo mata a hankali ta ɗago da kanta ta kalli Lokacin dake tsaye a wajen, "Ina ya Maleek!!?" "Ina Kaka!!?" "Je ki kira ƴan Uwanta" cewar Dr, tare suka shigo Abdullahi da kaka da sauri suka nufi wajen Maryam, Murya a dishace Maryam tace ," Kaka da gaske ya Maleek ya yarasu!?" Jinjina kai Kaka tayi cike da tausayawa cikin raunin Murya tace," Ki Dena kuka Maryam kiyi mishi Addu'a Kinji!" Girgiza kai tayi tare da cije lips ɗin ta kana ta runtse idanunta cikin wani irin mummunan yanayi mai wuya tace. ," kaka shikenan na rasa Ya Maleek! Kaka shikenan Ya Maleek ya tafi ya barni? Wayyo!! Allah ya Maleek me yasa zaka min haka?" Sai kuka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, cikin wata irin raunan'nanyar murya taci gaba da kiran Ya Maleek!! a karo na Barka tai, Kallonta Kaka tayi cike da tausayawa yanin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi kaman zata fasa ƙirjinta......da sauri ta runtse idanunta da masifar karfi Zuciyarta naci gaba bugawa da ƙarfi.... Mutsu mutsu ta kaman wata zautacciya hawaye Masu bala'in zafi na zubo mata.. "Ya Maleek me yasa ka tafi ka Bar....ni kasa ƙarasa Maganar nan take ta fashe matsanancin kuka a take Numfashin ya sake ɗauke...... Likitoci suka sake duƙufa a kanta suka shiga bata taimakon gaggawa da kyar da bone suka samu ta farfaɗo still tana ci.gaba da surutai haka yasa Dr ya yi mata Allurar Bacci nan take bacci wahala yayi a won gaba ta da ita.... Ajiyar zuciya suka sauke," ɗaya daga cikin nurse ɗin yace halam," Mahaifiyarta ne?" ba wanda ya kulashi , Ina ga tunda ta samu Bacci a barta ta huta Insha Allahu idon ta farka zata samu natsuwa, Jiki a mace suka fice daga dakin ," Abdullahi Ya kamata kaje gida Kodan masuwa gaisuwa," TOH Mama!!" kana ya wuce tare da Atiku, sai lokacin ya samu damar duba wayar shi Kasan cewar a silent take miss call ne ba a daɗi koda suka iso gida mu tane cike tam, ɗaya ba yan ɗaya suka riƙa jajanta mishi sai wuraren 10 ya samu damar shiga gida, tuni su Haydar sunyi Bacci koda yaje daƙinsa kwance suke suna Bacci hankalin kwance..... Ɗakin sa ya wuce ya watsa ruka ya canza kaya kana ya wuce Asbiti, har yanzu Maryam bata farka ba. Sosai Kaka tayi Mamakin ganinsa,"Abdullahi Meya dawo da kai? " Mama kona zauna gida ba bacci zanyi ba!" ga wannan nasan baki ci komi ba!" Kaza ce da Youngaut mai sanyi," Abdullahi ka koma gida kasamu ka huta, kaji Kaka ta faɗa cikin tausayawa," da kyar Kaka ta shawo kanshi kana ya wuce gida cike da damuwa, Ranar dai Haka suka kwana a zauna cikin ƙunci da raɗaɗin zuciya, A ɓangaren Abdullahi ma haka ya kwana cikin wani irin yanayi na kewar matarshi..... Kiran farko na Assalatu a kunnen Maryam, a hankali ta fara buɗe idanunta da suyi bala'in hauyi ta sauke su kan Kaka dake zaune a wajen hannuta rike da tazzabaha idanunta a bushe alamar ko runtsawa bata yiba, Cikin wata irin raunan'nanyar murya tace ," Kaka!" Kallonta Kaka tayi cikin ƙarfi hali da danne damuwar ta tace," Na'am Maryam" ya yinda Zuciyarta ke ci gaba da bugawa da matsifar ƙarfi tace ," Ya Maleek!" cike tausaya Kaka tace ," Maryam kiyi haƙuri Kinji" kiyiwa Abdulmalik Addu'a kinji, Jinjina kai tayi tare da sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar, tashi muyi sallah Kinji kiyiwa Abdulmalik Addu'a!" tare da taimakon Kaka Maryam tayi Alwalla kana sukayi salla a tare bayan ta sallame sallah ta daga hannayen ta sama ta soma Addu'a tana Kuka, Kaka ma Hawaye ne taf a Idonta cikin dubara tasa hannuta ta goge Hawayen..... Wuraren karfe 8:30 Dr ya shigo, " Masha Allah jikin da sauƙi zaku iya zuwa gida, ƴan rubuce rubuce yayi kana ya miƙawa Kaka ,"Ga wannan a saya mata maganin zai taima kamata sosai Allah ya bata lafiya," Amin likita mun gode," ba komi Mama!" "Bari na kira Abdullahi Azo a ɗauke mu, nan Kaka ta nemi wayar ta rasa, cikin tsananin tashin ta fara neman waya a ɗakin ba wata ba madadinta, sai yanzu ta tuna tunda Iya ta kirata ta sanar da ita Amrasuwar Abdulmalik wayar ta faɗi Ƙasa bata koma binta kanta ba, tana tsaka da tunanin Atiku ya shiga hannusa dake da Basket mai matsifar kyau, " Mama ina kwana ya mai jiki," Cikin sanyi Murya Kaka tace ," Jiki Alhamdulillahi har an sallame mu" Mutafi gida kwai"ba tare da ɓata lokaci ba suka wuce gida,ƙofar gida cike tab da jama'a, ya yi parking Abdullahi ya nufi wajen su ," Ina Kwana Mama!" " Lafiya lau Abdullahi ya ƙarin Ha ƙuri" " Angode Allah, Mamana ya jiki!" Murya a disashe Maryam tace ," naji sauƙi Abba!" Nan Abokan Abdullahi suka shiga yiwa Kaka gaisuwa, kana suka wuce gida da gudu su Haydar suka sheƙo tare da Rungume Kaka da Maryam, Kaka ta kallesu cikin tsananin tausai yaro kenan, mutane ne cike cikin palon matan Abokan Abdullahi ne sai masu aiki, da ƴan uwan Kubra, cikin girmawa suka gaida kana Haydar yaza Hannuta suka wuce ɗakin su, nan suka tarar da a kwatin su, Wonka Kaka tayi, bayan ta fito Maryam ta shiga sosai taji daɗin jikinta koda fito a shirya musu Lafiyanyen Breakfast, Kaka kam ruwan tea kwai tasha, Maryam haka, Ranar dai Kaka suka yini har zuwa dare ba wata walwala a tare da su kawo da abinda ke damunsa, bayan Isha'i kowa ya watse ƴan gida dai aka bari, Abdullahi koda ya shigo yaran duk sunyi Bacci Hadda Maryam saboda cikin maganinta ta akwai na bacci ciki, Kaka ce kwai zauna ta saka yaran a gaba tana kallo, " Mama bakiyi bacci ba?" Abdullahi ya faɗa cikin sanyi Murya," Ajiyar zuciya Kaka ta sauke kana ta kalli Abdullahi, " Banyi ba Abdullahi"ya kamata kikwanta ki kuhuta," Abdullahi kona kwanta Bazan iya yin Bacci!" Abdullahi ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, " Mama wannan yaro dake zuwa gidan ki shine ya rasu!?" "Shine Abdullahi!" "Baida lafiya halam?" "Lafiya lau yake jiyama kafin mu ta so tare muke dashi, hatsarin mota sukayi nan Kaka ta shiga bashi labarin Abdulmalik tun farkon haɗuwarsu" " Ya Salam! Mama me yasa tun lokacin baki sanar dani ba na ɗauƙi nauhin karatun sa, Kaka ta sauke Ajiyar zuciya," Abdulmalik ba irin yaran nan ne masu matattar zuciya Abdulmalik yaro ne mai son neman na kasanta ba yadda banyi dashi akan ya bari na taima ka masa yaƙi!?" Abdullahi ya fesar da iska mai ɗumi kana yace " Allah ya gafar ta Nishi!" "Amin ya rabbi" "Saida safe Mama ya kama ki kwanta" Bayan tafiyar shi Kaka ta jima zauna kafin nan Bacci yayi a won gaba da ita...... ★★★★.......... *BAYAN SATI ƊAYA* Rayuwa ta juya musu izuwa kunci da baƙin ciki musamman Abdullahi, Kaka Maryam, cikin satin nan daya sunyi wani irin masiffen ramewa, kallo ɗaya zaka musu kasan kusa cikin tsananin damuwa musamman maryam gabaƙi ɗaya ta fita cikin Haiyacinta duk ta dawo Shuru Shuru.... Tuni mutane sun watse su Haydar tuni sun fahinci Mahaifiyar su bata cikin gida lokacin da suka matsa tambaya Abdullahi ya faɗa musu Mahaifiyarsu ta rasu basu wani shiga damuwa saboda yarinya dake damun su, Haydar ne ma ƴa dan shiga damuwa Kasan cewar ya ɗan fisu wayo, daga baya kuma ya saki jiki sukaci gaba da wasar su...... ★★★★★..... A hankali ya fara buɗe idanunsa cikin wani irin mummunan yanayi da kyar ya tattaro duk ƙarfin ya miƙe zaune ya jingina jikin dutse a hankali ya riƙa bin dajin da kallon ko'ina tsit sai kukan tsuntsaye dake tashi, da sauri ya dafe kanshi dake sarawa da matsifar ƙarfi,ƙoƙarin tashi tsaye yake gabaki ɗaya jikinsa ƙarkarwa yake, ga wani irin masiffen kishin ruwa da yake ji, cikin wani irin yanayi a fara tafiya yana faɗuwa kaman yaro mai koyon tafiya daga ƙarshe ya dawo rarraye haka ya riƙa rarrarehe batare da yasan ina yake tafiya ba a hankali ya fara jin kukan motoci a karon farko ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar ha ya riƙa rarrafe har ya iso saman titin cikin wani irin yanayi ya kiƙe tsaye yana tal gal tal gal kaman zai faɗi magana yake son yin ya kasa saboda masifar bushewa da maƙoshin yayi yana tsaye a waje wata mota ta wuce da masifar guda fuuuuuu. Ƙasan cewar ba ƙarfi a jikin sa wannan isar motar yayi sanadiyar faɗa warshi a' tsakiyar titi... Hakan yasa motar dake tafe ta taka burƙi da ƙarfi har motar na bada wani sauti tsuuuuuuu" direban ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar, mutumen dake zauna a bayan ya yi sauri safe kanshi yana faɗi" Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n!!! kana ya sake Ajiyar zuciya.... Motoci dake bayan su suka tsaya da ƙarfi, wasu kattan maza kusan guda huɗu suka diro daga cikin motar ko wannen su riƙe da bindiga da sauri suka nufi matar dake gaba, suka zagaye ta... "Doga duba ga yaron na yare!" Allah ya ƙarama lafiya mutafi kwai yanzu haka shirin miyagu ne! mutumen dake zaune bayan motar Ya yi Murmushi kana yace" duk Abinda ya faru da bawawa daga Allah ne! Koda mugaye ne Allah bazai bari su cutar damu Saboda da kyakkyawar niya muke, Dogo Direba ya sauke Ajiyar kana yace ," gaskiya ranka ya daɗe hankali bai kwanta ba shiyassa bana son mota ta ta zama itace gaba, "Dogo da gaba da baya da tsakiya duk Allah ne ke kare su!" Dogo Direba ya yi Murmushi kana ya buɗe motar gaban shi na faɗuwa, ɗaya daga cikin security ɗin yabi bayan shin da sauri dogo Direba ya dawo wajen mota ,"Ranka ya dade Yaron nan a sume yake.... Ɗaukoshi muje Asbiti, " Ranka ya Daɗe..... da sauri ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu jiki a mace ya koma suka tallabo suka saka shi cikin mota. Kana suka wuce da gudun Gaske...... Tafiya suke da gudun Gaske kicin cikin ƙanƙanen lokaci suka iso Kano kai tsaye suka wuce Asbiti. nan take aka soma basu Agajin gaggawa, kasan cewar tare yake da ƴan sanda yasa sukayi gaggawar amsar shi, nan take likitoci suka fara gudanar da aikin su tsawon awa huda kana aka wuce dashi ɗakin hudu, bayan ya biya su kudin su ya wuce gida tare danƙa Amanar a hannu litaka kana ya tattabar mai cewa zuwa Anjima zai dawo.... Suna barin Asabiti akai tsaye suka wuce Nasarawa tun kafin ya iso aka wangale mishi gate wani katafaren gidane mai matsifar kyau da ɗaukar ido gaba ki ɗaya motoci suka dannan han hancu nansu cikin farfajiyar gidan sukayi Parking, a parking space da sauri ƴan sanda suka nufo motar shi kana suka buɗe Mishi, kai tsaye suka wuce cikin gida, dai dai lokacin kwata Kyakkyawa mata fara sol doguwa mai matsifar kyau sanye take wani tsadadden lass doguwar riga ta zauna mata ɗas a jikin a hankali taci gaba da sauko saman bene ɗin fuskarta dauke da murmushi.....✍️✍️✍️✍️ *More comments and share pls* *Sadeeya Ka'oje ce* *DR SULTAN* (A heart touching love story) *( THE BEGINNING)* _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ Tallah ! Tallah !! Tallah!!! Shahararriyar Marubuciyar nan Hafsat Muhammad Bature (Boss Bature) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *ABBAN SOJOJI* yau ta sake dawowa muku da sabon labari mai ɗauke da sabon salo na musamman *KURKUKUN ƘADDARA* labari ne mai kunshe da Butulci , tausayi , ban dariya , cin amana , soyayya mai shiga rai karna cika Ku da surutu, *KURKUKUN ƘADDARA* littafine mai ɗauke da Rudani da ban Al'ajabi kudai ku kasance da Alƙalamin *Boss Bature*💋💖 domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Number 08103884440 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *Page 11-12* _______fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙara so wajen sa tare da Rungume sa. A hankali ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya. tare dai lafe a jikinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi, Lumshe ido tayi kana ta buɗe a kan kyakkyawar fuskansa, cikin Murya mai kama da raɗa tace ,"Sannu da zuwa Habibi!" A hankali ya Lumshe idon kana ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya, cikin sanyi Murya yace," Yauwa Habibity!"A karon karfo ta saki murshi Mai ƙawatarwa, kana tace "Ya hanya? Numfashi ya ja kana ya fesar, cike da gajiya yace ," Alhamdulillahi!" "muje ciki kawatsa ruwa" Kana suka wuce ɗaki rike da hannun juna, kallon ɗaya zaka musu ka fahimci tsantsan so da kyauna da shaƙuwa mai ƙarfi, Masha Allah wani haɗaɗɗen daki suka shigo mai matsifar kyau, cikin tsananin kewa ya rungumeta nan take suka faɗa duniya masoya, kana sukayi Wonka tare, bayan ya gama shiri ta kallesa," Habibi ina zuwa kuma?" A hankali ya sake Ajiyar zuciya kana yace ," Gidan Abdullahi zanje nayi Masa gaisuwa!" "Gaskiya kam ya kamata kaje karya yi fushi da kai, ya ɗanyi Murmushi," Abdullahi bazai yi fushi dani ba saboda yasan Uzurin da ya riƙe Ni! " Wannan Gaskiya ne Habibi ba mai shiga tsakanin ku" tare suka fito daga ɗakin kai tsaye suka wuce darning,da kanta da riƙa ciyar dashi Saida ya ƙoshi kana ya shiga bata ita ma gwanin burgewa, "Yauwa ki haɗa min Abici mai ɗan ruwa ruwa zai kai Asbiti, "Subuhalillah Habibi waye ba lafiya?" Nan ya bata labarin abinda ya faru ,"Ya Allah ya jikin nashi"? Numfashi ya fesar kana ya ce ," Alhamdulillahi zanje gidan Abdullahi daga can zan wuce Asbiti" "Allah ya tsaye!" ", Amin ya rabbi Habibity ya faɗa tare da manna mata Kiss a hankali ya Lumshe idon, har bakin mota ta rakashi cikin girmamawa security suka Gaisheta fuska a sake ta amsa musu. "Barka da fitowa ranka ya dade!" "Yauwa Dogo, security suka buɗe mishi mota kana yashi a tsake suka fike daga gidan, kai tsaye suka wuce GRA, Suna isowa mai gadi ya buɗe musu gate a tsanake Dogo ya danna hanci matar cikin gida, dai dai lokacin Abdullahi ya iso fuskar ɗauke da murmushi ƙarfin Hali, "Sannu da zuwa Abdullahi ya faɗa cikin sanyi Muryar, saukar yaushe?" Batare da ya bashi amsar tambayar shi yace, " Ya ƙarin haƙiri!?" "Alhamdulillahi mun gode Allah!" "Allah ya gafar ta mata! cikin raunin Murya Abdullahi yace," Amin!" Kana suka wuce cikin gida kai tsaye suka wuce ɗakin Kaka, "Mama!!" Abdullahi ya kira sunanta cikin girmamawa" Kaka dake kwance saman lallausar Katifa ta mike.murya a disashe tace ," Abdullahi ƙara so mana" Kai a sunkuye ya shigo ɗakin ,"Barka da war haka Mama!" "Yauwa Abdullahi" "Mama ga Nuraddeen can Palon yazo gai sheki" Kaka ta sauke Ajiyar zuciya kana tace ,"wannan Abokin ka da kake bani Labarin?" "Ehh Mama shi koda aka yi rasuwa yana india dawowar shi kenan daka India" "Masha Allah" Tare suka fito daga ɗakin fuskar Kaka ɗauke da murmushi har suka ƙarasa cikin palon Abdullahi mai matsifar kyau, Suna isowa Alhaji Nuraddeen ya durƙusa har ƙasa ya gaida Mama cike da girmamawa da sauri Kaka ta dakatar da ta hanyar daga ƙafaɗun sa Kana ta zaunar dashi saman Sopa masu matsifar laushi, Fuska a sake Nuraddeen ya soma gaida Kaka tare da jajanta mata rasuwar Kubra, " Allah ya jikanta da rahama Allah yasa ta huta !" Suka Amsa da "Amin" Kana Kaka tace ya Iyali? " Lafiya lau mama" Mama ai Matar ce wannan dake kawo Abin tunda akayi rasuwar" cewar Abdullahi, "Allah sarki Allah ya yi Albarka, Allah yasa a gama Lafiya!"cikin tsananin farin ciki da Addu'ar suka amsa da "Amin" "Naji gidan shiru ina yara halam?" "Ina suna ɗaki Abdullahi ya bashi amsa" Dai dai lokacin Nana ta shigo Palon fuska a tsuke hannunta riƙe da tap ta yara," Kaka Kinga Khalil ya goge min Gama ɗina" sai kuma ta fashe da Kuka," zo Nan Nuraddeen ya faɗa tare da riƙe hannunta kana ya zaunar da ita saman ƙafafunshi, " Ki Dena kuka Kinji ya faɗa tare da kai Hannusa yana share mata Hawaye, sai gasu sun fito ga baki ɗayan su, da sauri Haydar da khalil suka ƙara so wajen tare da rungumeshi cikin tsantsan farin suka soma faɗin," Oyoyo "Daddy sannu da zuwa!" a hankali Maryam ta zauna kuka da Kaka, "Daddy yaushe kazo?" Cewar Haydar, "Banjima da zuwa ba" Daddy Ina kaje kwana biyu mun Dena ganin ka? " Tafiya nayi yau ɗin nan ma na dawo!" "Daddy Ina Mommy?" "Tana gida tace na gaishe ku gaba ki ɗayan ku, kuma tace yaushe zaku kuzo mata weekend? "Daddy yau Monday ran Friday zamu zo Weekend" "Yauwa Allah ya kaimu" "Amin Daddy" A hankali Kaka ta cewa Maryam je kicewa Azumi ta haɗo mata ruwa, a hankali Maryam ta kike kana ta wuce Kicin, "Abdullahi wannan kuma wace?" a hankali ya fesar da Numfashi kana yace ƴar Ibrahim ce Ƙane na!" "Allah sarki kasan ban santa ba Allah ya jiƙansu da Rahama!" "Amin ya Allah" Dai dai lokacin Azumi ta iso hannunta dauke da tire mai matsifar kyau kayan drinks ne ƴa ƴan itatuwa masu sanyi, "Sannu da zuwa ranka ya daɗe cewar Azumi" "Yauwa ya aiki" "Alhamdulillahi yanka ya fade" kana ta wuce, sosai yasha kayan marmarin kana suka ci Baga da hira zuwa na dan wani lokaci, Lokacin cinda zai tafi ya ba Su Haydar kyautar 100k Azumi kuma 10k kana ya yi musu sallama, har bakin mota Abdullahi ya raka shi nan yake sanar dashi daga nan Asbiti ya nufa ,"waye ba Lafiya. Nuraddeen?" Nan ya sanar dashi abinda ya faru, cikin tsananin damuwa ," Abdullahi yace Allah ya bashi lafiya ," Amin" kana ya shiga Mota suka fice daga gidan kai tsaye suke wuce Asbiti, tare da likita suka wuce ɗakin da aka kwantar dashi har zuwa yanzu bai farka ba, kallon yaron yaro cike da tausayi a Ranshi yake faɗin wa wanne hali yan uwanshi suke cike oho.... "Ranka ya daɗe ga kuje ka zauna" cewar Dr, "Bazai farka yanzu ba kenan? "Ranka ya dade da wahala gaskiya Allurar Bacci ka mai saboda ya nayin jikin sa yana bukatar Hutu sosai!" "Okay ba dawuwa Allah ya tasheshi lafiya!" "Amin" "Yauwa ga katina koda za'a buƙaci wani abun bana kusa" a hankali Dr ya karɓi katin tana kallon da sauri ya aware manyan idanunsa yana kallon sunan dake jikin katin NURADDEEN MAI NERAH! Cikin tsananin Mamaki yaci gaba da kallonsa mutumen da sunanshi ya kewaye da duniya,tabbas shine" a hankali Alhaji Nuraddeen ya ɗago ya kallonsa," Shi kowa sam Baisan Maganar ta fito ba, ya miike tare da barin ɗakin kai tsaye suka wuce gida..... Nuraddeen da Abdullahi tare sukayi jam'iya Nuraddeen Mahaifinshi Babban Attajiri ne kuma dan Kasuwa ne a Kano Nuraddeen shi kadaine ɗanda suka haifa Nuraddeen yana Ss3 Allah ya yiwa Mahaifiyar shi rayuwa, farkon shigarshi jami'a Allah ya haɗashi da Abdullahi kasan cewar Course ɗinsu ɗaya wasa wasa shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su Nuraddeen yaro ne mai kirki da kyauta ga tausayi ga son taimako, yadda yake rayuwar shi da mutane sam ba Zaka dauka ɗan masu kuɗi bane rayuwar shi yake kaman kowa, shaƙuwar su tayi karfi sosai a makaranta ba wanda bai sannu ba baru wansu da ƴan mata karatun su suka saka a gaba, bayan sun kammala jami'a sukaci ga da zumunci su, Abdullahi baida wani Aboki a duniya kaman Nuraddeen haka shima Nuraddeen baida wani Aboki kaman Abdullahi duk abinda zasuyi sai sun shawarci junan su, Mahaifin Nuraddeen haka ya dauki Abdullahi kaman ɗan cikin sa, Mahaifin Nuraddeen mutum ne mai matsifar son yara, Haka Nuraddeen ma kusan halayen sa ɗaya da Mahaifinshi... Nuraddeen can waje yawacen ya wace shi ƙauyuka wajen taimakawa ta takkawa Allah ya haɗashi da Ummul khairi bafulatanar daji kyakkyawan da ita wasa wasa soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu ba bata lokaci Akayi Auren bayan Auren su ya saka ta Kamaranta yaƙi da jahilci cikin ƙanƙanen lokacin ta fara waye a bangaren ilimin Addini ma har gida malami ke zuwa koya mata karatu, bayan Aure su da shekara Biyu Allah ya yiwa Mahaifin Nuraddeen rasuwa, Nuraddeen ya gaji duk a binda ya mallaka, tsawon shekara goma sha biyar kenan da sukayi Aure, Allah bai taɓa basu haihuwa ba, likitoci sun tabbatar musu da duk lafiyar su lau lokaci ne kwai bai yi ba, tun abin na damusu har suka barwa Allah, hakan yasa shida Matar shi suke tsananin son yara, zuwa yanzu Nuraddeen baida kowa sai matarshi da Abdullahi da ya kasance tamkar dan uwanshi haka ya dauƙi ƴa ƴan Abdullahi tamkar ƴa ƴan cikin sa wani lokaci a gidan shi suke hudu ko weekend. Kubra har ta raru basa shiri da Ummul khairi, saboda ƙashi da hassada da tasawa kanta ganin yadda Ummul khairi ta ke sharhiliya da dukiyar mijinta tare da ƙanwarta Ummul Kulsum,duk da ta kasance ƴar Attajiri matar Attajiri, Abdullahi duk da ya kasance mai kudi Nuraddeen ya kereshi shi da komai..... Wannan kenan....👌🙌🤗 Gab da maggariba ya shigo gida Kai tsaye ya wuce masallaci dake cikin gidan Saida kayi Isha'i kana ya wuce cikin gida cikin tsastsan farin ciki ta rungumeshi tare da manna shi hot kiss a kumatu, "Sannu da zuwa Habibi ya mai jiki ina fatan yaji sauki?" Ya sauke Ajiyar zuciya kana yace jiki da sauki!" "Masha Allah, Allah ya tashi kafaɗunshi Allah kuma ya baka ladan taimako, "Amin Habibity!!" Tare suka ci Abinci kana suka wuce daki, sukayi Wonka a tare bayan suna gama shirin suka kwanta rungume da juna nan take bacci ya yi awon ya gaba su...... *BAYAN KWANA HUƊU* Zaune suka a Palo suna hira Kaka ta kalli Abdullahi cikin sanyi Murya tace "Abdullah ya kama mu koma gida! Kodan makarantar Maryam kusan kwanan mu goma sha ukku kenan" Abdullahi ya sake Nannauyan Ajiyar kana yace," Mama don Allah karon nan ki dawo nan da zama Ko dan yaran nan! Kafin na samu mai kula dasu.don Allah Mama," nan take Idanunsa suka shiko da kwalla, Su Haydar suka haɗa baki wajen faɗin "Kaka don Allah karki koma ƙauye! Murya a disashe Maryam tace " Kaka Nima Bazan iya zama ƙauye ba tunda Ya Maleek baya nan! Nan take maryam ta fashe da kuka,"shike nan ya isa ki Dena kuka nan zamu ci gaba da zama insha Allahu Kaka ta faɗa cikin sanyi Murya" tare da sharewa Maryam hawaye, " Nagode sosai mama Allah ya ƙara Miki lafiya da nisan kwana!" cewar Abdullahi, "Amman ya kamata mu naje ƙaraye ko don nayiwa maƙotana sallama" "shike nan mama ko yanzu zamu iya tafiya! " kaka Ni kam ba zanje ba cewar Maryam" Nan take Kaka ta shirya suka wuce tare da Abdullahi" *ƘARAYE* Suna isowa kai tsaye suka wuce gidan cike da kewar Abdulmalik da ke mata gizo a tsakiyar gida, isowar keda wuya Mutane Unguwar suka fara shigowa tare da yiwa Kaka Gaisuwar Abdulmalik da Kubra, nan take Mutuwar ta dawo mata sabuwa, cikin dauri ta shiga amsa musu tare da faɗa musu zasu koma birni da zama, kowa sai tambatayar Maryam yake, haka Kaka ta shiga rarraba kayan Abincinta ga duk wanda ya shigo gidan, kana ya shiga haɗa musu kayan su da duk wani Abin mafani aka saka a motar Hilux dasuka zo da ita, "Abdullahi sai batun gida ya za'ayi dashi kasan idon aka bashi ba kowa zai nakkashe miye shawarar ka," Mama ina ga kwai ki kyautar dashi ga duk wanda kikega dama, "Bana da sauran dengi a duniya kaman yadda kaima baka saura kowa a duniya. sai Ni, da iyayen Hauwa'u suna rare sune suka fi cancanta dana mallakawa gidan!" Abdullahi ya sauke Ajiyar zuciya kana yace Hakane Mama! Barinsa haka zai sa ya lalace ko bata garin su samu wajen aikata barna" "zan mallakawa Malam liman idon har ka amince, " Haba Mama miye saina wani Abince damu da gidan duk a ƙarƙashin ikon ki muke duk wanda kika ba banda matsala!" "Allah ya yi maka Albarka!" "Amin Mama" Bayan sun gama kwashe duk wani abinci mai mahimmanci suka wuce gidan Malam Liman, bayan ya fito suka gaisa kana ya yi mata gaisuwa, a hankali Kaka ta miƙa mai makullin gida, batare da yasan na miye ba karɓa, "Malam Liman zanmu koma Kano da zama Insha Allahu, wannan makullin gidan muna na mallaka mashi halak malak, cikin tsananin Mamaki Malam liman ya waro ido yana kallon Kaka, Murya na rawa tace ," Mama kin mallakamin gida, saiga waye shar a fuskar malam liman har ƙasa ya duƙa tare da yiwa Kaka godiya, Kaka tayi sauri dakar dashi," Haba Malam liman miye abin godiya anan, da sauri ya nufi cikin gida jim kaɗan suka dawo tare damatar shi, fusaka a sake ta ciga yiwa Kaka godiya.... Haka Kaka riƙa shiga gidan maƙota tana musu sallama, kana suka wuce cike da kewar ƴan uwa da abokan arziki...Sai bayan Isha'i suka iso gida cike da gajiya nan masu aiki suka fara shigar da kayan cikin gida, Kaka na shigowa Suka rungumeta gabaki ɗayan su suna mata Oyoyo kana suka wuce daƙi.... ★★★ yana shigo wa dakin yana farka da sauri ya nufi wajen sa, a hankali ya fara idanunsa suka kaɗa sukayi jazir cikin Wani irin mummunan yanayi ya soma magana murya a disashe yana faɗin ,"ruwa Maryama ta! Zan sha ruwa Kaka ƙishi nake ji!Alhaji Nuraddeen dake tsaye a wajen cikin tausawa yace ",Ruwa kake so? A hankali ya gyara kai, ruwa masu sanyi ya ɗauko cikin fridge a hankali ya fara murɗa wani ƙarfe dake jikin gado,, gadon ya fara ɗagowa kana ya zauna kusa dashi ya buɗe marfin gorar ruwa ya ɗora mishi a baki hannayenshi ya ɗoro saman gorar yana zukar ruwan da ƙarfi har kana iya jin sautin maƙoshinsa dake kwat kwat cike da tausayawa Alhaji Nuraddeen ke kallo sai, da sauri ya janye bakinsa tare faɗin," Ruwa Kaka ban kwoshi ba! a karo na biyu yasa ake dora mashi gorar ruwa ya shanye ta tsas kana ya sauke Nannauyan Ajiyar nan take Zufa ta riƙa tsastafo mishi, dai dai lokacin Dr ya shigo fusakar ɗauke da murmushi, " Masha Allah ya farka kenan?" " Ranka ya dade yaushe kashigo?" Alhaji Nuraddeen ya sauke Ajiyar zuciya mai ɗumu kana yace Ban jiba ina shigo yana farkawa ka" Nan Dr ya shiga dubashi ," Masha Allah komai ya yi dai dai Insha Allahu, zuwa gobe za'a iya sallamar shi!" A hankali ya ware mayan idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir ya sauke su akan Alhaji Nuraddeen dake zaune," murya a disashe yace ," Ina Kaka Ina Maryama ta!" Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi kana ya kwantar da hankalinka kaji Wanne gari kake,"Karaye!" Nan Alhaji Nuraddeen ya bashi labarin inda ya gansa a hankali abinda ya faru ya fara dawo mishi a kwakwalwa nan take ya fashe da Kuka mai tsuma zuciya, da kyar Alhaji Nuraddeen ya shawo kanshi ya Dena kuka ," Kana da Numbar iyayenka na sanar dasu nasan yanzu yana suna cikin tsashin hankali," Murya na rawa yace ," Iyayena sun rasu! bana da kowa sai Kaka da Maryam!" Cikin tsananin tausai Alhaji Nuraddeen ya kalleshi kana da Numbar Kaka kota Maryam!?"kabani na kirasu na sanar dasu Halinda kake ciki? A hankali ya gyara kai nan ya shiga faɗa mishin number kaka Kiran farko aka sanar dashi number aka take a karo na Barka tai yariƙa kiran Number a kashe daga karshe ya haƙura... "Number a kashe take, ko Kanada wata number," A'a!" "Zan yi Sallah! A karon farko Alhaji Nuraddeen ya saki Murmushi, " Kasan kwananka nawa a Asbitin nan kai ya gyaɗa a lamar a'a, yau kwanan ka Hudu" a Asibitin nan,, "Murya a disashe yace yau nawa ga wata?" Alhaji Nuraddeen ya faɗa mishin," Nan ya fahimci iya a daɗin kwanakin da ya rasa sallah Alhaji Nuraddeen ya taimaka masa zuwa toilet wanka yayi da duwa ɗumi kana ya yi Alwala ya fito sosai yaji daɗin jikin sa....kasan cewar baida karfi jiki da zaune ya yi Sallah tsawon lokaci ya dauka yana rama sallalolin da ake biyar shi, duk wani motsin sa akan idon Alhaji Nuraddeen sosai yaron ya burkeshi, Bayan ya gama sallah ya zuba mai Abici palpesu kayan ciki kana ya haɗa mishi tea mai ƙauri kana ya miƙa miƙa mishi," Kaci kasha magani ko Yarona!" da sauri ya ɗago ya kalleshi ya sakar mai murmushi, a tsanake ya soma cikin Abinci, sosai palpesu ya yi mishi daɗi, bayan ya gama cikin Abinci yasha magani nan take bacci ya yi awaon gaba dashi..... Saida Baccinsa ya yi nisa sosai kana ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce gida a gajiye, Washe gari tunda sassafe ya wuce Asbiti koda ya shigo dakin yana zaune a Dr na dubashi ," Ranka ya dade sannu da zuwa" yauwa ya mai jiki?" Alhamdulillah zaku iya tafiya gida yanzu," rubuce rubuce ya yi a takar da kana ya miƙa mishi, Murya a disashe yace "Ina kwana Baba!" A hankali ya sauke sassanyan Ajiyar zuciya, "Lafiya lau Yarona ya jiki?" A karon farko ya saki Murmushi kana yace ," Lafiya lau Baba!" Yauwa sha tea sai mu tafi gida ko, cikin tsananin farin ciki ya daga mishi kai, tea ya haɗa mishi mai kaura kana ya bashi a hankali ya riƙa sha yana Lumshe ido, bayan ya gama suka fice daga ɗakin tare da yiwa Dr godiya kai tsaye suka wuce Nasarawa, lokacin da suka iso gidan haka ya saki baki yana kallon gidan a rayuwarshi ta duniya bai taɓa ganin gida mai kyau irin wannan duk abinda yake a kan idon Alhaji Nuraddeen, koda suka shigo palon zaune take tana kallon,"Habi..... sai kuma yayi shiru ganin yaron dake tsaye, fuska a sake ya gaisheta, "gabaki ɗaya ta kasa ɗauke idonta akan shi, "Ummul khairi lafiya?" Tadanyi Murmushi kana tace ba komai shine marar lafiyan?" "Ehh shine an sallame shi" " Masha Allah ,Allah ya ƙara sauki" "Amin" Kaisa ɗakin ɓaki ya huta koda yake bari yayi breakfast" tare suka wuce darning shiko sai ɗari ɗari yake sam ya kasa sakin jikin sa abinci ma kaɗan ya ci, kana ta kaishi ɗadakin baƙi, mashi Allah dakin ne na Alfarma komi na ɗakin farii ne, " Kayi Wonka sannan ka kwanta ko zakaji daɗin jikin ka" cikin sanyi Murya yace ," Toh Mama! Nagode" tana fitan ya kalli dakin da kyau kana ya sauke sassanyan Nunfashi, ƙofor dake like a dakin ya kallon hakan ya tabbatar mai da toilet ne a hankali ya buɗe kofar ya yi Addu'a kana ya shiga Wonka ya yi da ruwan dumi ya fito nan ya tarar da kaya saman gado ciki da mamaki ya riƙa bin kayan da kallon,ƙananun kaya ne masu matsifar kyau da tsada bayan ya saka kayan ya kalli kanshi a madubi ganin yadda ya yi matsifar kyau," Ina kike Maryama ki ga wannan kyau! Yana jima yana kallon kanshi a madubi, can muka ya ɗan ya mutsa fuska ganin yadda ya rame, sanyi ɗakin ya sakar mai da matsananciyar kasala hana yasa ya kwanta saman katafaren kadon ya lunlube da laulausar blanket nan take bacci ya yi awon gaba da shi.....✍️✍️ _More comments and share_ *Sadeeya Ka'oje ce*💋💋 *DR SULTAN* _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 13-14* ___Bacci sosai ya yi sai gab da maggariba ya farka a gurguje ya yi Wonka ya rama sallalolin da bai samu damar yi ba, yana zauna saman sallah, aka buɗe ƙofar ɗakin a hankali ya ɗaga kansa tare da kallon ƙofar tsaye take fusakar ɗauke da murmushi," Ka farka kenan?" tun dazu nake kai da komowa," kai a sunkuye yace,"Mama! Barka da warhaka," Barka kadai Yarona! Ya ƙarfin jiki?" "Alhamdulillahi!" " taso muje Kaci abinci ko kafin aka kira sallah" "Cikin sanyi Murya yace ," Mama saina yi Sallah.maggariba" "Aa Yarona Ci yana gaba da Sallah don. Haka taso muje Kaci abinci," Kaman wani ƙaramin yaro taja hanunsa suka wuce Darning da kanta tayi sarcevig ɗinsa Kana ta tura mishi Plate ɗin a gaban sa, a tsanake ya soma cikin Abinci yana Lumshe ido," "Yauwa ko kaifa ba gashi kana gamawa ba ana kiran sallah" dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen ya shigo Palon fusakar ɗauke da murmushi ya kalli matar tashi ," Ya tashi ke nan?" Murmushi na kara faɗaɗa a fuskarshi tace ya tashi da kyar ya yadda zai ci Abin wai nabari sai anyi sallah," Raron nan naki inga shine limamin unguwar su ya faɗa cike da zolaya, lokacin ɗaya suka saki Murmushi," "Tashi muje masallaci ko? Kaman jira yake da sauri ya mike tare suka fice daga palon a hankali ta sauke sassanyan Ajiyar zuciya," Barka da warka Ranki ya daɗe" "Yauwa Ladidi ya aiki ," Alhamdulillahi" " ina fatan An kammala Abinci?" "Ehh Ranki ya daɗe" "Yauwa a jera komi saman Darning"tana kai ƙarshe Maganar ta wuce ɗakin, Sai bayan Isha'i suka shigo palon dai dai lokacin ta iso palon ," Sannun ku dazuwa" "Yauwa" "Mama ina wuni" "Lafiya lau Yarona" "An kammala abinci," "Nidai a kwoshe nake bana jin yunwa, aiko zanma ɗure a gidan ta faɗa cikin zolaya" ga baki danyan su suka wuce Darning Abinci su sukaci cikin. Kwanciyar hankali da natauwa, Bayan sun gama cikn Abinci Alhaji Nuraddeen ya kalleshi cikin sanyi Murya ya soma Magana,"gashi har yau bamu san sunanka ba!" a karon farko ya saki Murmushi tare da fesar da Numfash Kana yace ," Sunana Abdulmalik!" a hankali ta sauke Nannauyan Ajiyar kana ta fesar da iska," Kallonta Alhaji Nuraddeen ya yi kana yace ,"Lafiya?" "Ba komai fa!" "Are you sure!? Gira ɗaya ta daga mai tare da sakin Murmushi" "Ma sha Allah suna nan Uncle ɗina! In sha Allahu idon ka ƙara jin sauƙi sai ka koma gida ko, kar Kaka da Maryam su shiga damuwa," dai sauri ya gyada mai kai tare da faɗin Ni Ko yanzu ma zanje wajen su! "Mai sunan Uncle yanzu kam dare ya yi " ka bari ka huta nida kaina in sha Allah zan maida ka gida!"cikin tsastsan farin ciki ya yi mai godiya, "Kaje ka kwanta ko" a hankali ya mike Kai tsaye ya wuce ɗaki ya watsa ruwa Kana ya kwanta cike da kewar Maryam da Kaka da haka har Bacci ya yi a won gaba shi...... ★★★★★..........★★ Jikin Abdulmalik ya yi sauki sosai Alhamdulillah kwana huɗu kenan da samun sauƙin sa, tunda sassafe suka wuce Ƙaraye cike da zumuɗin ganin Maryam da Kaka, lokacin da suka iso da taimakon Abdulmalik Alhaji Nuraddeen ya iso gidan su Kaka, . lokacin da suka iso yara cike a ƙofar gida wasu na shiga sawu na fitowa masu shiga kowannen rike da kaya, cikin tsananin damuwa da tashin Abdulmalik ya fito daga Mota lokacin da yaron Unguwa sukayi ido huɗu dashi suka kwasa a guje tare da faɗin fetalwa ta shiga gari, nan take mutane suka fara guduwa, da farkon abin yaba wa Alhaji Nuraddeen dariya, nan take gari ya dauƙa da labarin bayyana Abdulmalik, haka mutane suka tsaya cirko cirko a ƙofar gidan Kaka, cikin tsananin tashin hankali da ruɗu Abdulmalik yariƙa binsu da kallo ɗaya ba dayan ɗaya, Alhaji Nuraddeen ya yi gyaran Murya cikin sanyi Murya ya soma magana ," wai mike faruwa?" Nan hankali kowa ya dawo kan Alhaji Nuraddeen," lokaci ɗaya mutanen dake wajen suka sauke Nannauyan Ajiyar zuciya," Abdulmalik daman kana yare?" Sai lokaci Alhaji Nuraddeen ya fahimci mike faruwa, Ayuba yaci gaba faɗin ai tsawon sati Ukku kenan da labarin mutuwarsu, Alhaji Nuraddeen ya sauke sassanyan Nunfashi kana yace," Abdulmalik bai mutu ba nan ya shiga basu labarin da Abdulmalik ɗin ya bashi har izuwa haɗu warsu, sosai Al'ajabi ya kama su da jin Labarin da Alhaji Nuraddeen ya basu, Sai lokacin Abdulmalik ya samu damar ya yi magana cikin raunin Murya ya soma magana," Ina Kaka da Maryama ta!?" dai lokacin Malam liman ya iso ƙafar gida da farko ya tsorata da ganin Abdulmalik tsaye, cikin ɗauriya ya ƙaraso wajen tare da ba Alhaji Nuraddeen hannu suka gaisa kana ya maida kallon da Abdulmalik. Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare dashi ya gaida malam Liman, Kana Alhaji Nuraddeen ya shiga yiwa Malam liman Abinda ke tafe da su da labarin abin ya faru, Cikin tsananin mamaki Malam Liman ya Kalli Abdulmalik cikin sanyi Murya ya soma tambayarshi ya jiki," Murya a dishace ya soma magana ," naji sauƙi!" "Allah ya ƙara sauƙin!" "Malam Liman ina Maryama da Kaka!" Nan Malam Liman ya shiga bashin labarin koma warsu Kaka birni, cikin tsananin tashin hankali jikinsa ya soma karkawa," sai kuma ya fashe da kuka mai tsuma zuciya jikin kowa a wajen ya yi sanyi, sanin irin shaƙuwar da ke tsakanin su,"Malam ya ɗora da cewa yanzu haka sun mallakamin gidan su, Alhaji Nuraddeen ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, cikin tausasa halshe yace ," yanzu kenan sun koma Kano da zama? Ko kana da Address ɗinsu ko number waya haka ,"wlh banda masaniya akan su, Number Mama bata shiga shima ɗan nata kuma banda wata masaniya akan sa halima rabona dashi tunda mahaifinsu ya rasu duk garin nan kuma ba wanda yake da masaniya a kansa, Saida yana kamfanin mai suna Gwa....... Bai kai ga karasa ba Abdulmalik ya yenke jiki ya faɗi a sume, cikin tsananin tashin suka dukufa akansa don ganin sun ceto rayuwar sa cikin aikon Allah ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya, "Nagode sosai Alhaji Nuraddeen ya faɗa cikin girmamawa in sha Allahu kuma daga yau kula da Abdulmalik ya rataya a kaina canzi gaba da kula dashi har ranar da Allah zai baiyanar da Kaka da Maryam ɗin.... Godiya sosai malam Liman ya yi sama ko ba komai Alhaji Nuraddeen ya kwanta masa a rai duk da bai naɗa musu koshi waye ba, a hankali Alhaji Nuraddeen ya kalli Abdulmalik kana yace ," Ko a wai abinda zaka ɗauka?" a hankali ya gyaɗa mishi kai, lokacin da zasu tafi Alhaji Nuraddeen ya ba malam Liman kusan 50k..... tare da Number wayarshi koda wani Abin ya taso.. Kai tsaye suka wuce dakin Abdulmalik cike da kewa ya riƙa bin dakin da kallo komai na yadda ya barshi, yana kuka ya soma kwasar kayanshi da takardun sa na makaranta da duk wani abu mai mahimmanci kana ya fito daga ɗakin jiki a mace ya nufi wajen mota ya shigar da kayan bayan Booth. a tsanake suka bar ƙofar gidan... Kai tsaye suka kama hanyar Kano tafiya suke a hankali.. Abdulmalik ido kawai ya runtse cikin wani irin yanayi mai Tsananin kai kuma ya juyuwa ya runtse ido tunowa da kalaman Maryam lokacin da zai tafi ," Ya Maleek Allah ya sada mu da Alheri!" Wannan kallama ta tsaya mishi a rai haka ya riƙa tubka da warware har suka iso gida.... Tamkar wanda aka zarmewa lakkar jiki Haka suka shigo cikin palon ," Habi......saikuma tayi shiru ganin Abdulmalik a tsaye ," Sannun ku da zuwa!" Jiki a Mace suka zauna Abdulmalik da dan kunshin kayan, " Lafiya dai?" Lokaci ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar," Alhaji Nuraddeen bai ɓoye mata komi ba ya sanar da ita bayanin da Malam liman ya yi mi shi, "Allah yasa hakan shine Alheri! "Amin" Alhaji Nuraddeen ya yi gyaran Murya cikin tausasa halshe ya soma magana ," Abdulmalik!" Cikin raunin Murya yace ," Na'am Baba!" " Wannan itace Matata sunanta Ummul khairi tsowon Shekara Goma sha biyar kenan da Auren mu Allah bai taɓa bamu Haihuwa!" daga yau ina son kadauƙi Ummul khairi a matsayin Mahaifiyarka, bana son ka a jeta a wani matsayin da bana Mahaifiya ba!" Ummul khairi ta sauke sassanyan Ajiyar zuciya, kana ta kalli Abdulmalik dake zaune jikinsa duk ya yi sanyi cikin sanyi Murya tace," Abdulmalik wannan shine mijina! Alhaji Nuraddeen Mai Nerah! Ina son daga yau ga ɗaukeshi a matsayin Mahaifinka! Gidan nan gidan Mahaifinka ne kayi duk abinda kake so, Ina fatan zaka ɗauke mu tamkar yadda muka ɗauke ka!" Cikin wani irin yanayi Abdulmalik ya gyaɗa kai dan damuwa ƙarara ta fusakar sa da cikin idanunsa cikin ƙarfin hali ya sakar mata murmushi, " Yauwa Uncle ɗina .Allah ya yi maka Albarka! cewar Alhaji Nuraddeen," Murya a disashe yace ," Amin!" "Wai da gaske sunan Uncle ɗin mu gareshi," Alhaji Nuraddeen ya gyaɗa mata kai," Yayan Mama ne Kuma yana bala'in so na!" Lokaci kafin ya rasu kullum a gidansa nake kwana" "Allah ya gafarta mishi tare suka Amsa da "Amin" "Wannan ai babban suna ne gaskiya Bazan iya kiran sunan Uncle kai tsaye ba" Shidai Abdulmalik sai kallon su yake, Cike da zumuɗi Alhaji Nuraddeen yace ," wanne suna zaki riƙa kiran sa?" Kai ta ɗan daga kaman mai tunani ," Uhmm Aryan! cike da zolaya Alhaji Nuraddeen yake ,"A'a bakin ta.dan turo cike da Shogoɓa da sauri Abdulmalik ya sunkuyar da kai, a karo na biyu ta sake cewa,"Affan! "a'a Abba! Ya girkiza mata Kai," Ayman! "A'a Aslam! A karo na Barka tai tariƙa faɗin sunaye," yana faɗin A'a," fuska a tsuke taci gaba da faɗin sunayen ," Allah na gaji!" kana taci gaba,"Muslim! Arif! Sultan!!" da sauri Alhaji Nuraddeen yace ," Yes wannan ya yi! SULTAN!! Allah sunan ya yi daɗi sosai kuma ya dace dashi," Abdulmalik ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe akan fusakarsu, "A hankali ta sauke sassanyan Nunfashi kana tace ," da gaske sunan ya yi!?" "Sosai ma" "Sultan! Sultan!! Sultan!!!" Abdulmalik da sauri ya juya yana Kallonta" a karon farko Alhaji Nuraddeen ya saki Murmushi, kana yace Mahaifiyar ka ta maidaka Sultan saboda sunan Uncle ɗin a gareka!" Ɗan Murmushi ya sanka masa da sadda kai a kamar jin kunya, shima ya yi Murmushi, shekarar ka Nawa? Kai a sunkuye yace ," Ashirin da Biyu!" "Masha na kai ga saurayi!" Tashi muje muje a binci ko? tare suka nufi darning sukaci Abinci cike da natsuwa, Bayan suna gama ya wuce ɗaki ya yi wanka kana ya kwanta cike da damuwar sabuwar rayuwa da ya tsinci kansa a ciki da wannan tunani bacci ya yi a won gaba dashi...... "Habibi gaskiya ya ron nan ya kwanta mi har ga Allah hakan nake jisan kaman ɗan da na haifa!" idanunsa ya lumshe tare da kwantar da ita a jikn nasa da kyau ya zame hular kanta yana shafa kanta dake cike da gashi dogo mai tsantsi, sunja tsawo lokaci a haka a hankali yaja musu lallausar Blanket ya rufe su dashi.... Washe garin wuraren karfe 10 security gidan suka shiko palon a kwataiya kusan set ɗaya kowanne cike maƙil da kaya... Anan tsakiyar Palon suka ajiye su... Cikin tsantsan farin Ummul khairi ta soma buɗe kayan tana kallon kaya ne kala kaya na maza shadda, ƙananan kaya jallabiyoyi kayan bacci, turarukka da muyun kan shafawa masu kyau da tsada ta takalma Kala kala e.t.c Abdulmalik kam haka ya saki baki yana kallon ikon Allah wai yau shike da kayan nan masu matsifar kyau da tsada... dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen ya shigo Palon fusakar ɗauke da murmushi kamr ko yaushe, cikin raunin Murya Yace ," Sannu da zuwa Baba ," Yauwa my Son! Zo kaga kayan ka idon akwai a binda baiyi ba sai a canza,"Baba Allah ya saka da Alh..... Alhaji Nuraddeen ya yi saurin da katar dashi," bana son gidoya ƙarɓi nan ya yi maganar tare da miƙa Mishi waya kwalin wuyar Samsung Galaxy S23 Ultra mai matsifar kyau da tsada sai ga hawaye shar a fuskar Abdulmalik," Lokacin ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar ," Sultan!! suka.kira sunan sa tare! A hankali ya ɗago da idanunsa da sukayi kaɗa sukayi jazir cikin wani irin yanayi ," Yace Na'am Baba miye na muka ya yi maganar tare da share mishi hawayen, Sultan ya sauke sassanyan Nunfashi," ashe bayan kaka zan sake haɗuwa da mutane masu kirki ya faɗa a zuciyar sa," Karna sake ganin hawayen nan kaji," kai ya gyaɗa mashi" je kaka wayar ka charge "Ta Baba har ya juya zai tafi Alhaji Nuraddeen ya dakatar shi," Bana son Baba nan da kake kirana ya faɗa cike da zolaya," A karon farko ya saki Murmushi har haƙora sa suka bayyana" Nima dai bana son Maman nan kaman wata tsohuwa lokaci ɗaya suka saki Murmushi," a nan cikin palon ya saka wayar charge, " Larai ina Abu kuzo ku shigar da kayan nan ɗaki ku jera moki yadda ya dace" "TOH Ranki ya daɗe" Ranar haka suka kwance cikin tsantsan farin ciki..... A ɓangaren su Maryam a hankali ta fara sakin jiki zuwa yanzu harta fara maida jikinta tuni an saka ta makarkatar su Haydar a jss3 saboda ƙoƙarinta haka kaka ta rungumu jikokinta tana kulada dasu tare da masu Aiki... A ɓangaren islamiya sosai ta maida hankali da karatun hadisai da harda, Abdullahi ma ya fara maida jikinsa kullum Kaka a gaba take sashi harsai yaci Abincin... a hankali shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakin kaka da jikokinta Rayuwar suke gwanin burgewa, Washe gari tunda sassafe Alhaji Nuraddeen suka wuce Asbiti wajen likita tare da saka Dr ya bincika mai lafiyar Sultan ko yana ɗauke da wata cuta, Alhamdulillah duk wasu kwaje kwaje da ya kamata ayi Mishi an kammala tsab bai dauke da kowacce cuta.... Nan ya ƙara jin son yaron A ranshi.. godiya sosai Alhaji Nuraddeen ya yi kana suka wuce gida.... Bayan sun iso gida ya kira Abdullahi ya sanardashi abinda ya faru tare da ɓoyemai wasu bayanai kan Abdulmalik ɗin kan Ainiyin sunanshi da garin da yake da kaka da Maryam da ya rasa, haka wai yaji yana kyaunar yaron shima,nan ya shiga taya shi murna sun jima suna waya kana sukayi Sallama.... Sannu a hankali shaƙuwa mai ƙarfi ta fara shiga tsakanin su zuwa yanzu Abdulmalik ya fara sauyawa sosai ya yi warin fari mai matsifar kyau da ɗaukar ido fatarshi har wani glowing take sumar kanshi ta kara cikowa da tsowo ga wani sheƙi da take... Wasa wasa Abdulmalik ya fara saba wanda sabon sunanshi Sultan da kowa ke kiransa a gidan hasalima ba wanda ya san Ainiyin sunansa na gaskiya, a Wani ɓangaren kuma duk lokacin da ya tuna da Maryama da Kaka har kuwa yake. Sosai facebook ke ɗebi Mishi kewa. haka suka ci gaba da rayuwar su cikin kwanciyar hankalinki, Yau ta kasan ce Assabar Tun safe Ummul khairi keta aiki abinci tare da masu aiki tuni gidan ya gauraye da kamshi, a hankali yake yaku har izuwa Darning erea a hankali ya ɗan juyo jin an jamai kujera tsaye yake fuskar sa ɗauke da murmushi ," Daddy Ina Kwana? A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe a kan kyakkyawar Fuskarsa,"lafiya lau" "Wai me Mommy ka ke girkawa haka niji gidan sai khamshi yake?" "Aiko haƙura Zakuyi da khamshin nan don ban dafa daku ba ta karasa maganar cike zoyala lokacin ɗaya suka saki Murmushi, " Laifin me muka aikata haka?" Dai dai lokacin kwata Kyakkyawar mata shigo," Fuskar cike da damuwa," sauri Mommy ta nufi wajen ta tana faɗin Kulsum lafiya sai kuma ta fashe da kuka lokaci ɗaya Alhaji Nuraddeen da Sultan suka miƙe tare da barin Darning suka nufi wajen su, cike da damuwa ," Mommy ta soma tambatayar ,"Kulsum lafiya mike faruwa? a hankali ta share hawayen murya a disashe tace ,"Anty wlh na gaji da walaƙanci da Dengin Marigayi suke min yau suksan sati guda kenan da suka sani a gaba wai saina bar musu gida tunda an raba gado na tashi na bar musu gida," Shine na ce banza tashi ba zan Ƴa ƴa na ke," Yauwa da safe koda na kaisu Meena islamiya na dawo sun rufe gida wai na tafi na bar musu gida, ba yadda banyi dasu akan subarni suka ƙi, ta ƙara sa maganar tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya," da kyar suka shawo kanta ta Dena kukan," Yanzu ina su Meena ɗin?" ,"Suna islamiya Anty," shikenan ki Dena kuka," je ɗaki ki watsa ruwa ki fito muyi Breakfast, " Anty Don Allah a karbo min ƴa ƴa na bana son su zauna tare su, zasu.. ya isa za'a karɓo su cewar Alhaji Nuraddeen," jiki a mace ta wuce ɗakin ta watsa ruwa koda ta fito Mommy ya aje mata kaya a saman gado bayan ta shirya ta fito Palo suka karya.... "Wacce islamiya suke" Madarasatu Norul Islam ta faɗa cikin sanyi Murya, shike nan zan tura Dogo ya dauko su, batun gida kuma ki bar musu gidan Yara muka canzi gaba da kula dasu,"mommy ta sauke sassanyan Nunfashi tare da kallon Mijin nata ,"Alhaji Allah ya.... "Ya isa" "Ya Nuraddeen nagode sosai itama ya yi sauri da Katar da ita, sanin halinsa na reshin son godiya idon ya aikata alheri.. dai dai lokacin Dogo Deribe ya shigo Palon, "Yau dogo su Meenah zaka ɗauƙo a islamiya Yaya bari na bishi mu tafi tare okay ba damuwa, tare suka fice daga palon.... "Daddy mun gama shirin Maryam tace bazata jeba karatun Hadda Zatayi, Abdullahi ya Kalli Maryam dake zauna,"Mamana tashi ki shirya mu tafi Kinji! Ke kadai za'a bari gida sai ran sunday zasu dawo, "Abba Malam yace idon ban iya sai ya zaneni!"ta ƙarasa maganar kaman Zatayi kuka," Shike nan" Abdullahi ya kalli Kaka," Kaka yace Mama zamu tafi," toh Abdullahi Allah ya Tsare," Amin Amma!" Har bakin kaka ta sakaru tare da Maryam, bayan tafiyar suka wuce cikin gida....✍️✍️✍️ _More comments and share_ *Sadeeya Ka'oje ce* ✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 15-16* _______Lokaci ɗaya su ka iso ta re da Dogo Deribe, ya na ga ma Parking su ka buɗe motar cikin tsananin farin ciki har wa ni tsalle su ke saboda mur na, dai lokacin Ummu Kulsum ta fi to cikin mota ta re da wa su kyawawan Yara gu da Ukku kusan kama su ɗaya Ummul Kulsum ga baki ɗayan su suka nufi palon, Sunyi nisa sosai da kallon tv Alhaji Nuraddeen ji kwai ya yi a rungumeshi a hankali ya juyo da fusakar karab Idanunsa suka sauka kan Abdullahi dake tsaye murmushi na ƙara faɗaɗa akan fuskarsa, Alhaji Nuraddeen ya sauke sassanyan murya tare rungume Abdullahi yana faɗin ,"Sannu da zuwa Aminina irin wannan bazata haka?" Bayan sun zauna Mommy ta kalli Abdullahi cike da girmamawa ta ce ,"Abban Haydar sannu da zuwa yasu Mama?" "Duk lafiya lau su ke tace a gaishe ki," ,"Amin ina mai sunan Mama!" "Tana gida ba yadda banyi da ita ta zo muje ta ce a'a saboda karatun Hadda da take!" "ma sha Allah!, Allah ya ƙara basira mai Albarka" "Ga ba ki ɗaya su ka Am sa da "Amin" "Ina yaron Nawa?" Abdullahi ya tambaya murmushi na ƙara faɗaɗa akan kyakkyawar fuskarsa," Cikin girmamawa Sultan ya ce ,"Abba Barka da zuwa" "Yauwa My boy ya gida" "Alhamdulillah Abba!" "Daddy waye wannan Haydar ya faɗa tare da nuna Sultan,"Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi tare faɗin ," Yayan kune Sultan! " Daddy ban taɓa ganin saba" "Ehh a school yake last Month ya dawo daga yanzu ku riƙa kiransa Ya Sultan! kaji" "Toh Daddy" "Yauwa my Boy!" "Meenah Zo non Mommy ta faɗa a hankali yariyan ta ƙara so wajen ta zauna ƴar kimanin shekara goma sha sha biyu, "Meya sameki?" cikin raunan'nanyar murya ta ce ,"Mommy kaina ke ciwo!," Cike da damuwa Mommy tace ,"Ayya sorry Mamana!" Shiko Sultan sai kallon yarinƴar yake, Yana mai jin. tsakanin son a Ranshi, ga baki ɗaya hankalin sa nan kansu, ,"kinci abinci?" A hankali ta gyaɗa kai, "Yauwa to je ɗaki ki watsa ruwa kizo na baki magani,"toh Mommy kana ta wuce ɗaki, Ummul Kulsum ta sake Nannauyan Ajiyar zuciya,"Anty dole Kanta Ya yi ciwo jiya a zauna kuma kwana reshin barci ne ya sakan mata ciwon kai nan, jiya tunda ƙannen magariyi suka zo gidan a suna faɗamin na tattara kayana na bar musu gida, tun a lokacin ta ke ta na kuka! haka muka kwana zaune" "Mommy ta fesar da Numfashi mai zafi, cikin tausasa halshe ta ce ,"Allah ya jiƙan Aminu sam basu hali!" "Ya isa hakan nan cewar Alhaji Nuraddeen,.. In sha Allahu daga yau wannan matsalar tazo ƙarshe!" "toh Allah ya sa hakan shine Alheri Mommy ta faɗa cikin wani irin yanayi," ga baki ɗayan su suka Amsa da Amin,.. Sai lokacin Sultan ya samu damar gaida Ummul Kulsum,"Ina kwana Mommy!" Lokaci ɗaya su ka juyo da Ummul khairi, ko waccen su furkarta ɗauke da murmushi," shima murmushin ya sakar musu," Ummul Kulsum haka kawai ta tsinci kanta da kallon Sultan.. "Wai bakiji yana gaishe ki ba da sauri Ummul Kulsum ta janye hannunta,"Kana ta ce ,"Lafiya lau!" su Haydar kam sai guje guje suka a Palon suna wasa, "Mommy nayi Wonka" "Yuwa Mamana muje na bakin maganin tare suke wuce ɗaki bayan ta bata bamagani ta Kwantar da ita tare da lulluɓeta da laulausar blanket nan take Barci ya yi won gaba da ita. Ranar dai haka suka yi cikin tsastsan farin karfe Abdullahi sai bayan isha'i ya wuce gida.. Sultan ma tunu ya wuce ɗakin sa tare da Haydar da Khalifa... "Anty wai Nikam ina kuka samo yaro nan?" cewar Ummul Kulsum,"Mommy bata ɓoye mata komi,"Kai gaskiya Anty ya Nuraddeen nada kirki Allah ya saka Mishi da Alheri, shiko Sultan Allah yasa ya zame muki ɗan Halak duk da dai naga bashi da matsala" "Amin ya rabbi!" Kinga Saida safe wlh Barci nake ji sosai jiya ga baki ɗaya ban runtsa ɓa" "Allah ya tashe mu tafiya lokaci ɗaya suka miƙe ko waccen su ta nufi ɗakinta, Ummul Kulsum koda ta shi Meenah na zaune a tsakiyar gado ta dafe kai, da sauri Ummul Kulsum ta nufi wajen ta zauna tare da Rungume ta kana ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar cikin raunin Murya tace," Mamana lafiya mike da munki?" Murya a disashe Meenah ta ce wannan mafarkin na sake yi! da sauri ta Ummul Kulsum ta waro manyan idanunta cikin raunin Murya ta ce ," Yau kuma?" Mamana! Kai ta gyaɗa mata, a hankali ta rumtse idanunta ta na mai jin wani irin Radaɗi a Zuciyarta, "Mami Yauwa cewa sukayi Zasu ta fi da.....Ya isa Mamana tayi saurin da katar da ita," idanunta duk a rufe take Maganar," Mamana Kodai baki Addu'a ba?" Mame Wlh nayi harda Alwalla nayi kafin na kwanta" a hankali ta riƙa shafa kanshi ita ko sai ƙara shigewa jikinta take, a hankali ta Kwantar da ita ta re da tofa mata Addu'oi, tana sauke Ajiyar zuciya, haka dai har Barci ya yi awaon gaba da ita.... a hankali ta gyara masu kwanciya kana ta kwanta cike da ruɗu da tashin hankali ta ɗau tsawon lokaci a haka sai faman juyi take, har wuraren karfe 2:20 kana wani Nannauyan Barci ya yi a won gaba da ita.. Washe gari bayan sun suyi sallah suka kowa Barci sai wuraren 12:10 suka farka, ta re su ka yi Breakfast ga ba ki ɗayan su, lokacin da suka gama Alhaji Nuraddeen ya mikawa Ummul Kulsum ATM dinsa, ga wannan a je a sewa su Meenah kayan sawa da duk Abinda ya dace gobe Monday zasu fara zuwa makarkata" yana kai ƙarshen Maganar ya bar Darning ɗin. Ya.. Ummu Kulsum da Mommy sai kallon kallon suke, "Anty a da ya bar kuɗin sa kwai muje a kwaso kayan su a gida."kedai kawai kiyi a binda ya ce," Bayan sallah Azzuhur suka wuce kasuwa ga baki ɗayan su Hadda Sultan... "Abdullahi!" "Na'am Mama!" "Zaman ka a haka bazai yiwu ba ya kama kasamu Mata kayi Aure! Kodan tarbiyyar ƴa ƴan ka, kagani sai ƙara tsufa nake ba komai zan i ya yi yanzu ba sanan ba'a bar masu Aiki da tarbiyyar su ba, Abdullahi ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya Kana yace ," Ina sha Allahu Mama zanyi ƙoƙari!" "Yauwa haka nake son ji Allah ya yi maka Albarka! Allah ku ma ya haɗa ka da mata da mata ta gari! "Amin Mama nagode sosai da Addu'a!" "Yaushe su Malam Gwani zasu dawo?" "Insha Allahu yau zasu dago gobe Monday Akwai makaranta" "Allah ya dawo dasu Lafiya" "Amin Mama!" "Ina Mamana ?" "Tana ɗaki tana Karatu" daga haka sukaci gaba da hira..... Sai bayan Isha'i suka dawo gida da kaya niƙi niƙi ko wanne su a gajiye haka suka zuɓe gabaki dayan su a Palo, dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen ya sauko daga sama bene fusakarsa dauke murmushi ya ƙara so cikin palon, cikin sanyi Murya ya ce ," Kun dawo ,"Ehh" "Yauwa A shiyama su Haydar zan maida su gida gobe Monday!" Nana kaman ta yi Kuka," Daddy Nidai bazan koma ba!" Alhaji Nuraddeen ko sai kallon ya yan nashi yake,"Kuyi haƙuri ku shirya muje gida kunji Ɗazu ma Abban ku ya kirani Mama Zatayi Magana daku tace Mishi kunje kasuwa!" "Daddy Amman Next Week ma zamu dawo" "Ba damuwa Allah ya kai mu!" "Amin" tare suka tattara kayan suka shigar dasu ɗakin Ummul Kulsum, bayan sun dawo gaba ki ɗayan su suka nufi Darning Abcin suka ci cikin kwanciyar hankali da natsuwa.... Ƙarfe 9:30 Su mommy suka raka su har bakin Mota tare da kayan tsara da ta haɗawa Kaka turame guda uku masu matsifar kyau da tsada da turare... cike da kewar Sultan da Ihsan, Arif, Meenah dan kwana dayan da sukayi har sun saba da juna musamman Sultan..... Suna barin gidan kai tsaye Alhaji Nuraddeen ya wuce dasu super market ya yi musu seyayya kayan sweet kala kala dasu ice cream kana suka wuce gida... Koda suka iso gida su Kaka na zaune a palon suna kallo, da gudu suka nufi wajen Kaka tare da rungumeta cikin tsananin kewar su ta ƙara rungume su tare da sha bayan su, dai dai lokacin Maryam ta shigo polon a hankali ta sauke sassanyan Nunfashi kana ta nufi inda suke cikin sanyi Murya ta gaida Alhaji Nuraddeen,"Yauwa Mamana ya karatu," Lafiya lau Daddy!" "Kuje ɗaki ko kwanta ko dare nayi" Bayan tafiyar su Kaka ta kalli Alhaji Nuraddeen ta ce ," Ya su Ummul khairi!" "Lafiya lau take Mama ta ce a gaishe ki ga wannan ta ce a kawo Miki!. Cikin tsastsan farin ciki Kaka ta karɓi Ledar tare da buɗewa wani irin sanyi yaji a ranta,"Allah ya yi muku Albarka! Allah ya baku zuri'a mai Albarka! gaba ki ɗayan su suka amsa da Amin hira sukayi danyi zuwa ƙarfe goma ya yi mu su sallama har bakin Mota Abba ya rakashi, bayan ya shiga Mota ya ɗan kalli Aminin nashi kan ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya," Abdullahi mike damun ka?" tun zuwa na gidan nan na fahimci kana cikin da muwa miye matsalar?" Abdullahi ya dago da kansa cikin wani irin yanayi ya ce," Ba komi Nuraddeen!" Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi gefen Baki kana ya ce ,"Abdullahi duk duniya bayan Mama banyi tunani akwai wanda ya fini sanin halinki ba!" Tabbas akwai abinda ka ke ɓoye min!" Abdullahi ya fesar da Numfashi kana ya ce ," Ba komai fa" "Uhmm Abdullahi kenan shike nan tunda ka ce ba komai yanzu na san yadda ka ɗauke Ni!" Nan take Jikin Abdullahi ya yi sanyi" cikin wani irin yanayi Alhaji Nuraddeen ya tada motar yana ƙoƙarin barin wajen Abdullahi ya yi saurin da katar dashi, "tsaya kaji zan faɗa ma!" a karo na Barka tai ya yi ƙoƙarin da katarshi amman ina tuni har ya kai baƙin gate, Abdullahi ya yi tsaye a bakin gate ya hana mai gadi ya ɓude Mishi gate... Shi ko Alhaji Nuraddeen sai hon ya ke, fuska a turmuƙe ya sauke Glass ɗin motar shi a fusace yace ,"Salihu Kaje a buɗe min gate na wuce dare na nayi, Abdullahi ya saki Murmushi kana ya nufi wajen mota tare da faɗin idon har kaga ka bar gidan to mun gama maganar da muke!" Wacce magana kuma? Gaga haka na fa ɓata min lokaci!" "Haba Habibin Ummul khairi! Haba Babibin Habibaty! Nan take Alhaji Nuraddeen ya saki Murmushi ta re da Lumshe idanunsa kana ya buɗe su akan fusakar Abdullahi" "Mugu ta wannan hanƴar ka ɓullo ko? ya ƙara sa maganar murmushi na ƙara faɗaɗa akan fuskarsa, Abdullahi ya sake sassanyan Nunfashi Kana ya kalli Alhaji Nuraddeen," Wlh Mama ce ta sani gaba akan maganar Aure!" "Kai Amman wallahi Mama ta yi dai dai to miye a bin tada hankalin a nan? Mama Gaskiya ta faɗa kodon tarbiyyar Yaran nan ya kamata ka yi Aure Mama ta tsufa yanzu tana buƙatar Hutu sanan masu Aiki ba zasu kulamar ya da yadda ya dace ba! duk da dai naga Mai Aikin tana da natsuwa Amman wallahi abu mafi muhimmanci shine kayi Aure! Abdullahi!" Abdullahi ya sauke Nannauyan Ajiyar kana ya ce ,"Nuraddeen ba na son na koma gidan jiya bana son na sake Auren mata mai irin halin Kubra Nuraddeen bana son Na Auro matar da zata sake rabani da Mama da Maryam! Duk lokacin da na buɗe idona na ganni a kusa da Mama na kan ji sanyi a raina, ba ma wannan ba Su Haydar sun saba sosai da Kaka yanzu bana son Abinda zai raba su! Ya ƙasara maganar cikin tsananin damuwa... Alhaji Nuraddeen ya sauke sassanyan Nunfashi kana ya ce, wannan gaskiya ne Abdullahi Nima bana fatan Abinda zai sake rabaka da Mama!. "tunda ta matsa ka yi Aure ya kama ka nemo Mata Abdullahi! Nuraddeen wlh tsoro nake ji!" Alhaji Nuraddeen ya ɗan yi shuru na ɗan wani lokaci kana ya ce ," Na baka shawara!" da sauri Abdullahi ya ɗaga kai,"Ina jinka Aminina! "Me zai hana ka Auri Ummul Kulsum ƙanwar Ummul khairi na tabbata zaka samu duk natsuwar da ka ke buƙata, Ummul Kulsum bata da matsala kusan halin su ɗaya da ƴar uwarta na tabbata idon ka Aure zakayi farin ciki har ƙarshe yayuwar ka! Tsawon shekara ɗaya kenan da rasuwar mijinta Aminu mutumin kirki ne, ƴaƴanta Ukku Amina, Ihsan, Arif na tabbata zata riƙa ma zuri'ar ka da Amana! na tabbata duk matar da zaka Aura ba lalle bane ka samu kaman Ummul Kulsum ba! Wannan shawara ce idon har ka Amince!" Abdullahi ya ɗan kalle shi sai kuma ya yi shiru," dare na yi fa zan wuce gida" Abdullahi ya sauke Ajiyar zuciya kana ya ce,"Kana ganin zata Amin ce dani!" "Me zai hana duk fa zaurawa ku ke ya faɗa cike da zolaya. "Allah yasa Ha kan shine Alheri! "Amin ka Amince kenan?" "Bazan ki zaɓin ka ba!" "Shike nan Allah ya yi muna zaɓi na Alheri! "Amin ya rabbi haka su ka ci gaba da tattaunawa sai warren 11:30 Alhaji Nuraddeen ya wu ce gida ci ke da ƙwarin Quiwa, ko da ya iso gida :12 har ta gota... Koda ya shigo ɗakin zaune ya sa meta sanye sa Kayan Barci sunyi matsifar yi ma ta Kyau ga wani fitinannen khamshi da ta ke, da Sauri ta faɗa jikinsa tare da rugumeshi," murya a shogoɓe ta soma magana," Habibi ina ka tsaya haka" a hankali ta ƙara lafewa a jikinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi, janye ya yi daga jikinsa suna fusakar juna hannayen sa ya ɗaga sama, ta san mi ya ke nufi a ta fara gwaɓe kayan jikinsa, "Haɗo min tea kafin na matsa ruwa, bai jira mi zata ce ba ya wu ce toilet ya yi Wonka da ruwan dumi, ya na fitowa dai dai lokacin ta shigo hannu dauƙe da Mug ɗin Black tea mai zafi sai tururi ya ke fitarwa saman Centre table ta aje Mug ɗin ,bayan ya gama shirinsa ya zauna suna fusakar juna,a hankali ya soma shan Black tea ɗin yana Lumshe ido, ita ko sai kallonshi take, a hankali ya aje Mug ɗin saman table, cikin tsokana ya ce "irin wannan kallo ha Habibity!" Kana ya yi gyaran Murya, Hankalin da natsuwarta ta maida a kan, "wani aikin lada na ke son ki ta yani ai watarwa wanda zai amfane nu ga baki ɗaya!" ta sauke sassanyan Nunfashi tare da faɗin," Allah ya sa wanda zan iya ne Habibi!" Nan ya taba labarin yadda su ka yi da Abdullah... A hankali ta sauke Ajiyar zuciya kana ta fesar da Numfashi," cikin tausasa halshe ta ce ," Haba Habibi ai da ni da Ummul Kulsum duk a ƙarƙashin ikon ka mu ke, zaɓin ka shine na mu, na amince da wannan haɗi, Allah ya ƙara danƙon zumunci, " Amin ya rabbi" "Sai ki san yad da zaki shawo kan ƙanwar ta mu, " Ina sha Allahu!" Mommy ko har Allah, Allah ta ke gari ya wa ye.. washe gari bayan su Meenah su wace Makaranta, Mommy ta wu ce ɗakin Mame, "Anty Ina kwana?" "Lafiya lau" Zama ta yi su na fuskarta ju na, Ummul Kulsum! Mommy ta kira sunanta ci kin sanyi Murya,. "Na'am Anty!" "Daman Baban Sultan ne ya zo min da wata Magana ji ya!" a takaice ta sanar da ita duk Abinda ya faru, Ummul Kulsum ta fesar da Numfashi,cikin wani irin yanayi tace ," Anty! Ba zanƙi zaɓin Yaya Nuraddeen ba! Na san ba zai zaɓin abinda zai cutar da Ni ba!" Mommy ta sauke sassanyan Murmushi,"kin Amin ce kenan?" cike da kunya ta gyaɗa kai" Masha Allahu, Allah ya tabbatar mu na da Alheri!" ★★★★★...... "Habibi kaga ikon Allah ko komi yazo da sauƙi ko?" Alhaji Nuraddeen ya yi Murmushi kana ya ce ,"Ai daman shi Alheri ha ka ya ke Allah dai ya tabbatar muna da Alheri!" "Amin Habibi" Nan take Alhaji Nuraddeen ya kira Abdullahi ya sanar da shi, cike da zolaya ya ce,"koda ma can kuna so juna? Naga Abin ya zo da sauƙi ha ka! An ya Abdullahi!" daga can ɓangaren Abdullahi ya ce ," Ba na son sa ido fa, "Ba wa ni sa ido gaskiya na faɗa" Anjima zan shigo muyi Magana da Mama!" "Okay Allah ya kai mu" "Amin" Kaman yadda Alhaji Nuraddeen ya faɗa wuraren ƙarfe Biyu ya wu ce gidan Abdullahi ya yi Kaka bayanin komi sosai Kaka ta yi Murna..," Allah ya sanya Alheri, "Amin Mama!" dai dai lokacin su Maryam su ka da wo da ga school da gudu su Haydar suka ƙara so cikin palon su na faɗin "sannu da Daddy! Daddy munga su Meenah da Ihsan da Arif a school ɗin mu!... Daddy Ina Ya Sultan?" "Ya na gida, "Daddy Muna gaida shi, "Wai waye Sultan ɗin nan tunda su ka dawo hirar sa su ke" cewar Kaka, Abdullahi ya yi saurin ce wa "Ɗan Nuraddeen ne Mama" ita ko Kaka a tunanin ɗan Uwan Nuraddeen tunda ta san bai taɓa haihuwa ba, "Allah sarki tunda su ka dawo kullum cikin hirar sa su ke, Murmushi su ka yi ga ba ki ɗayan su, Nuraddeen ya jima a gidan Kana ya yi musu sallama ya wu ce gida, Lokacin da ya isa gaida haka su Ihsan da Arif su ka faɗa mai sunga su Haydar a makaranta.... ★★★★........ Bayan Isha'i Abdullahi na zaune a ɗaki wayar shi ta fara Ringing a hankali ya ɗaya wayar ta re da Manta ta a Kunna," ka shirya ka zo gida na yanzu," Me Zanyi?" "Bana son Munafurci kaman ya me za ki yi, "Nuraddeen!!!.. "Yanzu don Allah da girman nawa zanje ta ɗi?" "Au Ashe kasan Abinda za ka yi" "Allah idon baka zo ba zan fa sa Ni daga yau ma na dawo Mahaifinka tunda Ni ne waliyin Ummul Kulsum! Ya ƙarasa maganar cike da zolaya,"Auw ta nan ka ɓullo!" "don Allah mu aje maganar wasa ya kamata kazo taɗi, "za ka rani idon nazo?" "Ina matsayin Yayan ta zan raka ka taɗi" "A matsayin Abokin Ango zaka rakani" Mommy na zaune ta na jin duk Abinda suke faɗi sai Murmushi ta ke, a hankali ta miƙe ta nufi ɗakin Ummul Kulsum dai dai lokacin ita ta fito da Wonka," Shi ke nan ma abu ya zo da sauƙi ki shirya Abdullahi na nan tafe" Da sauri ta waro manyan idanunta tana kallon Mommy," Anty wlh Kunyar sa na ke ji, "Kedai a ke ji Kinga tafiya ta, Koda ta tadawo dakin sun kammala waya,. Ba tare da tace Mishi komi ba ta buɗe durowa ta sauko wani tsadadden lass mai matsifar kyau tare da gyale color less ɗin da turare mai matsifar khamshi ta wuce ɗakin Ummul Kulsum, "ga wannan ki saka, ita ko duk kunya ce ta ce, Mommy ta taimaka ma ta ta shirya "Masha Allahu madarar kyau Mommy ta faɗa! a hankali ta sunkuyar kai.... ★★★★★★.......★★ Abdullahi suna gama wayar ya faɗa toilet ya yi Wonka kana ta fito ya shirya sanye da wata tsadaddiyar shedda sky Blue sosai kayan suka yi mishi kyau abinka da farin Mutum ga wani irin fitinannen khamshi da ya ke, a hankali ya fi to da ga ɗakin, dai dai lokacin kuma Kaka ta fito da ga cikin, da sauri Abdullahi ya sunkuyar da kai cike da kunya, kaka kasa ɗauƙe Idonta ta yi akansa saboda kyau da ya yi mata yau kamanninsa sak da na Mahaifinshi da dan uwanshi Ibrahim, a hankali ta sauke sassanyan Nunfashi, "Mama baki Barci ba?" "Yanzu nan zanci na zo ɗaukar Ruwa ne kasan Nana kullum dare saita farka shan ruwa" Bata tambaya ina zashi ba shi ko bai bai ga ya ma ta ba duk da ranta ya na bata ina zai tafi. Bayan ta fiyar Kaka ya fice daga palon Kai tsaye ya wuce gidan Nuraddeen lokacin da ya iso ya kira Nuraddeen ba jima ya fito Abdullahi sai wani ɗari ɗari ya ke ha kwai gidan ya zamo mishi kaman sabon zuwa, kai tsaye suka wuce palon baƙi Alhaji Nuraddeen sai murmushi ya ke,"Abokin irin wannan kyau ha ka Kodai A ɗaura Auren yanzu ka tafi da matarka, dai dai lokacin Mommy ta karaso da Ummul Kulsum da kanta ke sunkuye ga baki ɗaya a kunyace ta ke, Abdullahi ko ga baki ɗaya ya kasa ɗauke idanunsa kanta wani irin kallo yake binta dashi mai cike da ma'anoni "Sannu da zu wa Ango cewar Mommy bayan sun gama gai sa wa Mommy da Alhaji Nuraddeen su ka wuce, A hankali ya Abdullahi ya sauke sassanyan Nunfashi kana ,"Ya gida Kulsum!" A hankali ta Lumshe idanunta ta buɗe akan fusakarsa cikin sanyi Murya ta ce," Lafiya lau" "Ya su Mama!" "Alhamdulillahi" Bada ɓata lokaci ba ya sanar da ita abinda ke ta fe da shi, cikin Ikon Allah ko buƙatar shi ta karɓi hira suka sha sosai cike da so kaman waƴan da suka shekara a ta re. Wuraren karfe 10:30 ya yi mata sallama ta re da bata Number wayarshi, har bakin mota ta rakashi baiko bi ta kan Aminin nashi ba...🤣🤣 Bayan ta fiyar shi Ummu Kulsum ta sauke sassanyan Ajiyar zuciya tare da yi wa Allah godiya fuskarta ɗauke da murmushi ta wu ce ciki gida wuraren 11:10 ta kira shi tare da tambatayar ya iso lafiya nan fa suka barke da hira sun jima suna waya kana su ka yi sallama.. Ranar da haka su ka kwana cikin farin ciki.... Washe gari Abdullahi ya sha tsiya wajen Alhaji Nuraddeen 🤣 (Haba Abdullahi tun ba'a je ko'ina ba ina ga idon Anyi Aure zai manta da Nuraddeen 🤣🤣🤸) ★★★★★ A bunka da manya cikin ƙanƙanen lokaci suka fahimci juna duk wasu shirye shiryen Aure sun kammala Abinsu, lehe ma tuni ta haɗa abinda tare da Mommy gyara na Musamman Mommy ta yiwa ƙanwar ta ta A ɓangaren Alhaji Nuraddeen ba'a bashi a baya ba sosai ya gyara Aminin nasa... Ranar jumma'a kaka daura Aure gagarumin buki aka shirya na gani faɗa. Bayan Isha'i Amarya ta ta re ɗakinta... tarba ta Musamman Ummul Kulsum ta samu daga wajen Kaka... Washegari Abdullahi ya gabatar da ita a wajen ƴaƴansa, "wannan sun Nan Mama ga reta Maryam,zo nan mai sunan Mama!" Fuska a sake Maryam ta nufi wajenta,"Kina Lafiya?" Lafiya" "Abban Haydar yanzu kowa da Sunan Mama yake kiran ta ba sakayawa? Gaskiya Bazan yadda a riƙa kiran sunan Mama kai tsaye ba" ta yi maganar cikin gaskiya da gaskiya,"Kaka ko sai kallo su ta ke tana Murmushi har ga Allah Ummul Kulsum ta kwanta mata a rai, Abdullahi ya yi Murmushi kana ya ce "Mama ce ba ta son A kiranta da ko wanne suna!" Ummul Kulsum ta marairaice fuska kana ta ce,"Allah Ni kam ba zan "iya ba! Ni daga yau zan riƙa kiranta Sultana!!! Mama don Allah a yimin wannan Alfarma!" Fusakar Kaka ɗauke da murmushi ta ce," Ba komi Maman Haydar warin daɗi ta ji, Ranar dai ha ka suka kasance cikin tsantsan farin, Satin Ummul Kulsum biyu da tarewa Meenah da Arif suka dawo gidan da zama Haka sukaci ga ba da Rayuwa cikin kwanciyar hankali da so da kyaunar juna, ★★★★★★★.......... "Sultan Daddy ya ki ra sunansa cikin sanyi Murya, a hankali ya ɗago da kansa kana ,"Na'am Daddy!" Batun karatu tu ne? Mi ye burin ka? a hankali ya sauke sassanyan Nunfashi kana ya ce "Likita Daddy!" "Wow Ma sha Allah my Boy wacce ƙasa ka ke son ka yi karatu? " Daddy ko'ina ma zan iya ina takardun ka suke," Suna ɗaki Daddy je ka kawo min su, A hankali ya mike ya nufu ɗauki sa, jim kaɗan ya dawo riƙe da ta kardunsa cikin girmamawa ya miƙama Daddy takardun, ya na duba takardu ya na Murmushi, Ma sha Ɗan na wa ashe jarumi ne! Bayan ya maida ta kardun ya kalli Sultan kana ya ce," nan da sati biyu komi zai kammalu ka kasan ce cikin shiri... dai lokacin Mommy ta iso palon Fuskarta ɗauke da murmushi kaman ko yaushe, "Ni fa bana son ɗan uban cin nan da ake nunamin sai ku zauna kuna hira ba ni, ga ba ɗaya su su ka ya yi Murmushi, fuska a shogoɓe Sultan ya ce "Sorry Mommy!" "Na bi Sorry nan da gudu" "Batun karatun sa ne, "Mommy ta sauke Ajiyar zuciya kana ta ce ," Gaskiya ne Nima a bin na a raina" "In sha Allahu nan da sati biyu komi zai kammala yaron naki ya ce Likita ya ke son Zama! "Auww DR SULTAN!! Allah sunan ya yi daɗi!" "Allah ya tabbatar da Alheri" "Amin ya rabbi" ★★★★★★★.......... Bayan sati biyu kaman yadda Alhaji Nuraddeen ya faɗa tuni an Kammala duk wasu shirye shiryen ta fiyarsa washe gari wuraren 12 jirgin su ya ɗaga zuwa India ta re da Alhaji Nuraddeen.... Haka Mommy ta dawo gida cike da kewar Ɗanta da mijinta....satin Alhaji Nuraddeen ɗaya a India ya dawo gida... cike da kewar ɗan sa... Ranar da ya dawo tarba ta Musamman ya samu da ga wajen Habibity ɗin sa..... A hankali kwanaki suka ci gaba da shuɗewa tun bayan tafiyar Sultan kullum sai sunyi video call, A ɓangaren ka ratun sa kuma Alhamdulillah ko mi na tafiya yadda ya dace, duk wani Abin buƙata Alhaji Nuraddeen ya tanar da Mishi gida suku tun ya seya Mishi ɗaki biyu da palon kusa da Makarantar su ga maƙuddan kuɗi da ya zuba mishi a account. hakan ya sa ya maida hankalin sa sosai wajen karatu.... A ɓangaren Abdullahi komi Alhamdulillahi komi na tafiya yadda ya kamata Wata irin shaƙuwace mai ƙarfi ta shiga tsakanin Kaka da Ummul Kulsum Maryam wasa wasa ta saba da sabon sunanta gaba ki ɗaya kidan yanzu an Dena kiranta da Maryam harda Kaka.... Shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin Meenah da Sultana.... duk weekend su kan je gida Alhaji Nuraddeen wani lokacin hadda Sultana... Rayuwa taci gaba da tafiya, komai bisa tsari.., Lokaci na tafiya Rayuwa na ju yawa eh zuwa kwanaki - kwanaki na komawa makonni Makonni na juyuwa eh zuwa wattani Wattani na juyawa eh zuwa shekara Bayan tsowan shekara Takwas!!! "Mommy mun kammala shiri cewar wata kyakkyawar yarinya ƴar shekara bakwai, ta sake ce wa "Daddy mu yi sauri kar jirgin su Ya Sultan ya iso, Dai dai lokacin Alhaji Nuraddeen suka fito ta re da wani kyakkyawan Yaro dan shekara shidda kamanni su sak da yaron, "Ina Ihsan,"Daddy ta na waje" "Je daki ki kira Mommy da gudu yarin ƴar ta wu ce ɗaki ta na faman kiran "Mommy Daddy ya ce ki fito mu ta fi jirgin su Ya Sultan ya iso. "Mu tafi ta yi ta re suka fito daga ɗakin tuni Alhaji Nuraddeen sun fita waje Mommy na iso wa Security suka buɗe mata Mato a tsanake suka fice daga gidan kusan mota Ukku kai tsaye su ka wuce Airport, i sowar su ya yi dai da saukowar jirgin... Bayan mintu na Biyar mutane suka fara fitowa, mutum ukku ne suka sauko Sultan ya biyo bayan su, sanye da tailored suit sunyi matsifar yi masa kyau, tun bayan sakkowar sa ya hango iyayensu, don ha ka ya na saukowa ya nufo gurin su janye da trolly, da sauri Salma, Ihsan, Salim, suka isa gurinsa hannunsa ya buɗe su kowa suka shige ya rungumesu bayan ya janye su daga jikinsa ya isa gurin Daddy tamkar gaisuwar Indiawa su kayi Daddy ya buɗe Hannunsa shi kuma Sultan ya shige ya yi kwance a kirjinsa Kamar wani ƙaramin Yaro. Sun jima a haka sannan ya isa gurin Mommy ƙasa ya zuɓe a gabanta yana murmushi ita ko wa Hannuta ta ɗora a bisa kansa cike da farin ciki dai dai lokacin Abba Abdullahi ya iso fuskar ɗauke murmushi, Hannu ya miƙa Abba Abdullahi su gaisa kana ya ce ," An iso lafiya My Son? Cikin sanyi Muryar yace Lafiya kau Abba" kai tsaye suka nufi gun motocin su, a tsanake suka fice daga Airport ɗin," Wani farin ƙalle Salma ta saka ta rufewa Sultan Ido tana Murmushi haka suka ci gaba ta dafi ba tare da ya san ina suke nufa ba.... Har suka iso anan gama Parking Securitys su ka buɗe mu mota a hankali su ka fito daga motar Salma na riƙe da hannun sa, basu tsaya ko'ina ba a ƙofar gate, Ya Sultan Buɗe idonka " A hankali ya fara janye ƙallen daga saman fuskar sa har wani bishi bishi yake gani, cike da mamaki ya riƙa bin Gate ɗin da kallon ganin an kwawata shi da wani farin zare daga tsaki ana saka red ɗin zare anyi mishi Ado mai matsifar kyau a hankali Daddy ya fito da Almakashi mai matsifar kyau ɗan ma dai dai ci, "karɓi nan cewar Daddy jiki a mace ta ƙarba a hankali mommy ta ƙara so wajen ta ɗora Hannuta saman na Sultan kana Daddy ya ɗora nashi Abba ya ɗora nashi sai Salma Salim, Ihsan, a hankali Securitys suka fara ƙirga 1,2,3,!! Lokaci ɗaya suka yanka zaren cikin tsananin farin ciki, Mutane dake tsaye a wajen suka soma taɓi, A hankali Sultan ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar, Mai ga ɗi ya buɗe gate ɗin gana ki ɗaya, Daddy ya Kalli Sultan cikin sanyi Murya ya ce ," mu shiga ko, cikin wani ɗin yanayi ya tattaro da duk ƙarfisa suka wuce ciki a hankali ya ɗago da kansa yana kallon wajen karab Idanunsa suka sauka kan Rubutun da Saman ginar SULTAN PRIVATE HOSPITAL.....ciki wani irin yanayi mai cike da tsantsan farin Sultan ya rungume Daddy ta re da faɗin Thank you so much Daddy Allah ya ƙarama lafiya da nisan kwana Daddy!" a hankali ya share kallor da ta zuɓo mishi... a hankali Daddy ya janye shi daga jikin sa, kana suka soma za gaye Asbitin, lungu da sako Saida suka za gaya komai an ta nada sun ɗau tsawon lokaci suna zaga ye Asbitin kana su ka wuce gida.....✍️✍️✍️ _More comments and share_ _domin neman ƙarin bayani 👉08149979652_ *Sadiya Ka'oje ce* *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 30 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* Not editing!!! *Page 17-18* ________tun kafin su iso mai mai gadi ya wangale mu su gate a tsanake su ka shiga cikin farfajiyar gidan kana suka yi parking, gaba daya suka fito da sauri Security ya sa hannu ya dauƙo trolly ɗin, Sultan Murmushi ya yi,"Na gode ya furta a hankali, haka suka ɗunguma Palo cike da Annushuwa. suna shiga palon Daddy ya dubi Sultan,"My Son jeka ɗakin ka Ka yi Wonka ka huta in Anjima ka fito". Ya yi Murmushi," To Daddy ya nufi ɗakinsa da ke cikin Palon, da sauri Ihsan da trolly ɗin sa. Ɗakin ya ɗau sanyi A.c sai ƙamshi turaren ɗaki ne ke tashi, ya sha gyara sosai, ya ɗan ya dubi ta ," Sannu na gode ".ya furta a hankali. idonsa a lumshe, kuma duk sanda ya yi magana kumatunsa duka biyu su kan lotsa, sannan idonsa a lumshe ji dai kaman ƙafafuwan ta ba za su iya ɗaukar ta ba,don haka da sauri ta yi waje... Ya bi da kallo tare da taɓe baki.sannan ya tuɓe kayansa ya daura towel ya nufi toilet, ya jima a jiki yana cuɗa jikisa sanan ya ɗaura Alwalla ya fito, yana wani irin matsiffen ƙamshi ya yi da gashin jikinsa ya kwanta lib a tattausar fatarsa, ɗan ƙaramin towel ya jawo yana mai tsane tattausar sumar kansa mai tsantsi baƙi har wani sheƙi take... A hankali ya nufi gaban dressing Mirror ya tsaya ya fara kimtsawa cikin ya nayinsa natsuwarsa. Yana ƙamshi mai masifar daɗi Wata lallausar jallabiya ya saka mai gajeren hannu, ta yi cib da ɗan madaidaicin jikinsa, ya haye gado don yin Bacci gajiya... A Palo kuwa tuni su Mami sun iso, Sultana ko tunda suka iso gidan bugun zuciyar ke tsananta jikin ta duk ya yi sanyi, bayan sun gama ciki Abinci su wuce ɗakin,. Mommy ko suka ci gaba da hira, tare da Daddy, Abba..... Barci sosai ya yi, A hankali ya fara buɗe idanunsa da sukayi nauyi ya furzar da iska a hankali ya mike zauna ya jikin gida da gado kana ya yi miƙa, dai dai lokacin Wayar shi ta fara Ringing murmushi ɗauke da fuskarsa ya ɗaga wayar murya a sanyaye ya ce ,"Aziz, daga can ɓangaren Aziz ya sauke Ajiyar zuciya, kana ya ce,"Bayya! Daga nan ya juya halshe zuwa India cike da ƙorewa sun jima suna waya, kana su kayi sallama, a tsanake ya fi ce daga ɗakin fusakarsa dauke murmushi ya nufi palon ba kowa a cikin kai tsaye ya nufi Darning, Abinci ya fara ci cikin natsuwa... "Salamu Alaikum!" Cewar Meenah, Kansa ya ɗaga jin jin Muryar Meenah, cikin Sa'a Idonsa bai sauka a kan kowa ba sai kan na Sultana, ya ɗan zare Ido kamar zai yi magana, sasai kuma ya ɗauke kansa cike da miskilanci, ita ma da sauri ta janye hannunta jin bugun zuciyarta na tsananta da sauri ta nufi dakin Ihsan jikinta har karkarwa ya ke, Shima zuciyarsa ta cika da wasiwasin in da ya san mai irin fusakar, amma sai ya bar shi zuwa ko a ƙasashen da ya ziyarta ne To sai dai kuma ina su Mommy suka san ta?, Haka dai ya riƙa yiwa kansa tambayoyi gami da yarinyar har ta ƙule yade na hangen ta, sannan ya mai da maida dubansa gurin Meena da sauri ta sakan mata tattausar Murmushi, Dai dai lokacin su Daddy suka ƙara so palon ko wanne su fuskar sa ɗauke da murmushi, a hankali Sultan ya miƙe tare da barin Darning ɗin ya nufi wajen su Daddy, "My Son har ka tashi?" Murya a sanyaye ya ce ,"Eh Daddy, "Ga wannan!, ba tare da ya san miye ya karɓa kana ya buɗe Key ɗin ɗanƙareriyar Mota ya gani mai masifar Kyau da tsada, Ga baki dayan su suka hau tsalle murna, kamar su Aka yiwa kyautar motar, ya toshe kunnensa tare da cewa karku fasamin dodon kunne, ga baki daya suka rungumeshi suka faɗin "Congratulations Ya Dr Sultan!" Kowa a Palon sai murmushi yake, a hankali ya janye su daga jikin sa kana ya rungume Daddy ta re da farin,"Thank you so much Daddy! I love so much Daddy!" Daddy yace Love you too my Boy cikin tsantsan din ya sake lafewa a jikinsa kaman wani ƙaramin yaro, Gabaki ɗan su suka ɗunguma zuwa waje, mota ce mai masifar kyau da tsada, nan su Mommy suka ta ya shi murna, cike da farin ciki suka dawo Palo, "Wai Ina Sultana!" Cewar Daddy, "Daddy tana ɗakin Haydar ya bashi amsa, "Salma je ki kira ta, da gudu Salma ta wuce ɗakin tana kiran Anty Sultana Daddy ya na kiran ki" Sultana dake kwance ta yi rub da cike, cikin wani irin yanayi murya a Raunace ta ce,"banda lafiya kaina ke ciwo, da sauri Salma ta fice ɗaga ɗakin, tana Faɗin ," Daddy Anty Sultana ba lafiya kanta ke ciwo!" "Subuhalillah! Daddy ya faɗa cike da damuwa, "ta zo Sultan ya duba ta, Mommy ta yi Murmushi kana tace Ka manta ita ma Nurse ce!, ga baki daya palon suka yi Murmushi, Ihsan ta kalli Sultan, yanzu kuma sai take gani kamar ƙara masa kyau da kwarjini a kai, duk da dama can ta san shi ɗin mai kyau ne. Yarrr! har tsakiyar kanta haka ta ji lokacin da suka haɗa ido wata irin goguwar son sa ce ta sake mamaye Zuciyarta, don haka da sauri ƙasa da kanta, shiko ya taɓe baki... "Salma je ki kira Anty Sultana" "to Daddy". Koda ta shigo dakin zaune ta sameta idanunta a lumshe ya yayin da ta jingina jikin gado, ƙarasa wa Salma ta yi,cikin sanyi Murya ta ce ," Anty Sultana Daddy na kiran ki, a hankali Sultana ta buɗe idanunta dake Lumshe ta ce, "Ina zuwa" tare suka fito daga ɗakin Sultana na riƙe da hannun Salma, tunda suka ƙara so.falon Zuciyarta ta riƙa bugawa da ƙarfi gaske, cikin dauri ta iso tsakiyar Palon ta zauna still bugun zuciyar na tsananta... Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu marar musaltuwa ta ɗoro Hannuta dai dai wajen Zuciyarta ta na mai girgiza kanta, gaba ki ɗaya ta rasa natsuwarta. "Sultana jikin ne ?" Mami ta tambaya, Kasa cewa komai tayi, ta kasa ɗago da kanta, banda bugawa da Ƙarfi ba abinda Zuciyarta keyi.... A ɓangaren Sultan ma kusan hakan ta faru dashi, sosai bugun zuciyar sa ke tsananta, A hankali ya ɗago da kansa, da sauri ya yi gefe da kansa lokacin da idanunsa suka sauka kan Sultana da idanunta ke ƙasa a lumshe tana wasa da yatsun hannuta da suka shan jan lalle a hankali ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya cike da ruɗu..... Sultana! Ciwon kan ne har yanzu Daddy ya tambaya a hankali, Murmushi ƙarfin hali ta saki har Saida Dimple ɗinɗa suka lotsa, cikin raunin Murya ta ce," daina ciwo Daddy, "Ma sha Allah" "Sultana ga Sultan nan kun gaisa?" kai a sunkuye ta ce ,"A'a Daddy!" Cikin wata irin sanyayyar murya mai cike da rauni da tashin hankali ta kawar da kai gefe na kana ta ce "Sannu da zuwa" Kaman yadda ta kawar da gefe haka shima ya kawar da kaife cikin raunin da ruɗu dake tattare dashi ya ce,"Yauwa" Ido Daddy ya zuba musu kaman mai son gane wani Abu a tattare da su, kana ya ce, "Yauwa Sultan nan da sati biyu ka tabbatar an gama ɗaukar ma'aikata a Asibiti, Sultana ma tana ɗaya daga cikin Ma'aikatan da za'a dauka wata ukku kenan da ta kammala karatun ta Nurse ce yanzu Sultan kuwa cikin sauri zuciyarsa ya ciga ba da bugawa yana bada sautin dif-dif cikin wani Irin yanayi ya dafe saitin ƙahon zuciyarsa jin yanda yake bugawa da azabebben ƙarfi yana cigaba da bada sautin dif-dif rintse idanunsa yayi still hannunsa na dafe da saitin ƙahon zuciyarsa. A hankali Sultan ya sauke Nannauyan Numfashi tare ƙoƙarin dai dai natsuwar sa kana ya ce "in.sha Allahu Daddy" Ranar haka suka Abba da su Mami suka ya yi gidan cikin tsantsan farin, A ɓangaren Sultan da Sultana ga baki ɗaya jikin su a mace ya ke har bayan Isha'i kana suka musu sallama cike da tsantsan farin.... Bayan ta fiyar su Sultan ya wuce ɗaki jiki a mace ya yi Wonka kana ya shiryar cikin lallausar kan bacci masu matsifar kyau, cikin wani irin yanayi ya durƙusa ƙasan gado ya janyo wani ɗan madaidaicin A kwatin mai masifar kyau duk da ya yi ƙura hakan bai hana shekin A kwatin bayyana ba, ƙurar ya goge kana ya buɗe Akwatin bugun zuciyar sai tsananta ya ke, Hannunsa ko sai ƙawatarwa yake lokacin da ya buɗe Akwatin wani irin fitinannen khamshi mai masifar daɗi ya daki hanci sa a hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe akan zoben Azurfa mai matsifar kyau ta re da Abin hannu a an yimai Ado mai kyau a hankali ya zura zoben A ya tsarshi cib cib zoben ya yi masa, dai dai ya kuma Zuciyarsa ta yi Masifar tsinkewa har Zufa na tsastafo mishi saman goshi, da sauri ya janye zoben daga yatsar sa, ya sauke Nannauyan Numfashi mai zafi, a hankali idanunsa suka sauka kan wani hoto mai Black & write ga baki ɗaya hankalin sa na kan hoton, dai dai lokacin kuma wayar shi tayi ringing da saurin ya mai da hoton cikin Akwati kana ya turu ƙarƙashin gado, yana mai sauke Ajiyar zuciyar, wayar na gan da tsinkewa ya ɗaya, "Aziz ya kira sunansa a hankali basu jima ya kashe wayar, kana ya kwanta... ★★★★... Daddy kuwa a kwance ya tarar da Sultan idansa ba kallon silin ɗakin, sai dai ya yi zurfi a cikin tunani, don ko sallamar Daddy bai jiba har isa gefensa ya zauna, hannu ya sa ya dafa kafaɗarsa. Ajiyar zuciya ya saki mai ɗan ƙarfi, ya dubu Daddy, "Sultan tunani me kake yi har nayi sallama baka jiba?" A hankali ya ce Ba komi Daddy" Daddy ya ce ,"Da komi kam sai dai In ba za ka faɗa min ba, "Allah ba komi Daddy" kawai gajiya ce ke da muna" "Wannan takardun Asbitin ka ne duk wasu marin bayani na ciki Allah ya yata haka riƙo. Rau rau ya yi da ido kaman zai yi kuka!, "Daddy ban san da wanne Abu zan saka ma A duniya ba! Daddy ko Mahaifiyana iya Abun..... Alhaji Nuraddeen ya yi saurin da katar da shi ta hanyar rufe mishi baki, "kwanta ka huta good night my Boy ya faɗa tare da shafa kanan Sultan, A hankali ya miƙe tare da barin ɗakin, yana fita Sultan ya sauke sassanyan Nunfashi, tare da jan lallausar Katifa ya rufe jikin sa iya ƙirji kana ya haske ɗakin ya yi addu'a ba jima bacci ya yi a waon gaba dashi...... Washe gari, A hankali ya fara buɗe idanunsa tare da yin Addu'ar tashi daga barci. Hannunsa ya saya ya jawo wayar sa dake gefen Pillow ya sannan pawer karfe 5:8am, a hankali ya zuro siraran ƙafarun Farare sol toilet ɗin sa ya nufa yana shiga ya yi brush ya yi Wonka da ruwan ɗimu ta re da Alwalla kana ya fito, durowarsa ya buɗe wata lallausar jallabiya Milk color ya zura kana ya fesa turare ya fice daga ɗakin, tare suka wuce masallaci da Daddy Saida gari ya fara haske suka dawo gida kai tsaye ya wuce ɗakin laptop ɗin sa ya jawo ya fara sarrafata cike da ƙwarewa... Wuraren kafe goma suka yi Breakfast a tare cikin kwanciyar hankali, Ranar haka suka yini cikin farin ciki.... ★★★★★★★ Bayan sati biyu tuni a kammala duk wani shirye shiryen fara aiki A Asbitin, yau ta kasance Monday tunda safe ya shirya zuwa Office cike da ƙwarin Quiwa bayan sun kammala Breakfast ya fice daga palon, har bakin mota Su mommy suka rashi tare da yi mai fatan nasara.... " Anty Sultana gaski kinyi kyau sosai ban taɓa ganin Unifrom ɗin nan sunyi Miki kyau kamar yau, Meena na faɗa cike da zolaya, Harara Sultana ta dalla mata kana ta fice daga ɗakin Meena na biye da ita, "Abba zan wuce wajen Aiki!" "Ma sha Allah Mamana Allah yasa kin fara a Sa'a!" Fusakar ta ɗauke da murmushi tace ," Amin Abba na gode sosai, "kaka Mami zan su ce, "Allah ya bada Sa'a! "Amin" har bakin mota suka rakata cike da kwarewa ta ja motar ta ta fice daga gidan, kai tsaye ta nufi Asbitin.... kusan lokaci ɗaya suka iso. A hankali ya fito daga cikin motar, ba tare da ya lura da ita ba, ya yi gaba abinsa Cikin natsuwa ya fara taku yana ƙarasowa cikin farfajiyar Asbitin, A hankali take ta kowa, suna fuskantar juna, sosai ya zuba mata ido, ita ko tafiya take kai a sunkuye Hakan yasa bata san da mutum a gaban taba.. da sauri Sultan ya tsaya saboda warin matsiffen bugawa da Zuciyarsa take ganin ta yi dab da shi, A hankali ta ɗaga da kanta ganinta tsaye kusa da Namiji, ya sa taja da baya da sauri tare da tsuke fuska, a wani ɓangare kuma a ruɗe take saboda warin bugawa da Zuciyar take, Bai kula taba sai kauda kanshi da ya yi fege kaman bai ganta ba. Cike da tsiwa ta ce," miye na tsayawa a hanya" Da mamaki ya ɗan kalleta ta gefen idonsa, kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya, kai tsaye ya wuce Office ɗinsa ya fara aikin da ya kawoshi...✍️✍️ _More Comments and share_. _Domi neman ƙarin bayani ku tuntuɓi ta wannan Number👉 08149979652_ *Sadeeya Ka'oje ce*💋 *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 19-20* _____Da mamaki ya ɗan kalleta ta gefen idonsa, kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya, kai tsaye ya wuce Office ɗinsa ya fara aikin da ya kawoshi. Sultana da har yanzu ke ta faman jan tsakin takaici ta nufin cikin Asbitin, Nurse's sake tsake a wajen sai faman kwallonta suke cike da mamaki, Jidda tayi sauri riƙo hannuta, tana faɗin,"Daughter Lafiya?" da saurin Sultana ta juyo tana kallon Jidda fuska a tsuke ta ce, "Ba komi Mommy na!" salin halin kawar ta ta, yasa ta yi shiru, Jidda ƙawar Sultana ta re suka yi school of nursing. Kasan cewar tana da sunan haifiyar ya sa take Sultana take kiranta da Mommy. Sosai suke mutunci, "Daughter me a ka Miki Hlm?" Kafin Sultana ta samu damar bata Amsa sai gashi ya fito daga Office ɗinsa Dr Aryan ta biye da shi a baya, taku yake cike da natauwa irin ta zakaran Samari masuji da lokacin ƙuruciya da kwanciyar hankali har yanzu fusakar a tsuke take, ƙoƙarin janye idanunta take daga kallon nasa Karab idanunta suka sauka kan Sunan da ke rubuce a jikin rigarsa DR SULTAN da manyan Rubutu, Cikin suɓutar Halshe ta ce, "don yana Asbitin sa yasa zaiyi wa Mutane tsaye a tsakiyar Hanya" Karaf wannan Maganar ta sauka a hunnensa. ta gefensu ya raɓa ya barta da kamshin turaren sa mai sanyi da daɗin shaƙa. Ko kallon ida take baiyi ba, zaka fahimci da wahala ma ace yaji Abin da ta faɗa.taɓe baki ta yi tare da jan tsaki Jidda ko sai kallon ikon Allah ta ke, dai dai lokacin tawagar Nurse's suka i so wajen Jidda ta ce ina zuwa haka," Dr ne ke son ganinmu ga baki ɗaya, Sultana Uffan bata ce ba. Dan ita takaici yake bata... (Hmm Sultana kenan bari dai nayi shuru 🤣🤣🤸) Nan take kuwa, duk Nurse's suka fara haurawa sama suka shiga babban Hall ɗin nasu, maza gefe ɗaya Mata gefe ɗaya. Sultana da Jidda zaune a waje ɗaya, Cike da natsuwa da sanin darajar kansa ya gyara samansa saman Kujera Dr Aryan na zauna a gefensa, a hankali ya gyara microphone tare da hura Iska a hankali kana ya yi gyara murya," “Bismillahir Rahmanir Rahim!.. Sai kuma ya Lumshe idanunsa tare da sauke sassanyan Ajiyar zuciya cikin sanyi Muryar ya ci gaba da cewa. "Ina mai farin cikin wannan rana mai dinbin Tarihi a Rayuwata! duk yabo da godiya sun tabbatar da ga Allah ma ɗokakin sarki. Ina mai farin cikin zuwan ku Asbitin nan mai Albarka.daga nan yaci gaba da bayanai masu ɗinbin mahimmanci da zasu taimake su gaba ki ɗaya. Gaba ki ɗaya wajen ya yi shiru kowa ya maida hankalinsa ga Sultan dake magana, yan matan wajen ke jin ina a ce su mullake sa a matsayin mijin. Sultan ya sauke sanyayyar Ajiyar zuciy, Kana ya ce,"a kwai mai magana?" Nan wasu suka soma tambayoyi, Shiko yana basu Amsa cikin natsuwa, Kana ya mai da sauran kallonsa ga Dr Aryan dake gefensa cikin sanyi Muryar yace ,"A kwai mai magana a cikin ku?" Duk kan ninsu suka girkiza kai. Dr Aryan ya nuna Jidda tare da fadin ki rufe muna taro da Addu'a,da saurin Jidda ta sunkuyar da kai kaman bata ji me yace ba, tsawon mintu na Ukku, kana ya Kalli Sultana Kai ta juya tare da taɓe baki, "Sultana!Dr Aryan ya kira sunanta,a hankali ta ɗago da kai tana kallonsa dai dai lokacin na kansa, a tsanake ta mike tare da neman dukan natsuwarta ta amshi microphone ta fara Addu'a cikin zazzaƙar Muryar mai cike da natsuwa.. Kana aka tashi kowa ya wuce wajen aikin sa, Sultan kai tsaye office ɗin sa daya amsa sunan Office ya nufa, baka jin komi sai Dadɗan khamshi turaren dana Ac mai sanyi dake tashi, ya zauna saman lallausar kujerar yana sauke sassanyan Nunfashi, dai dai lokacin Dr Aryan ya shigo Office ɗin fuskarsa dauke da murmushi cikin sanyin murya ya ce,"Sir kwai wanda zaka duba yanzu ya yi maganar tare da aje mishi files a gaban sa, kana ya fice daga Office ɗin, files ɗin ya duba kana ya fice daga Office ɗin... ★★★ Bayan Awa Ukku, Fitowarsa kenan ɗakin theater a gajiye.yanda yake tafiya kwai zai tabbatar ma yanayin da yake ciki.tare da Doctors Biyu da suka tayasa Aiki, da Nurse Biyu rike da kayan Aiki.a dai dai lokacin suka ƙaraso Office ɗinsa hand gloves ɗin hannunsa ya cire kana ya jefa a tasar dake hannu Nurse. Hannu ya ɗaga musu alamar su daga ta daga anan a hankali ya tura ƙofar ya shige. Bayan mintuna goma Dr Aryan ya shigo Office ɗin, "Sannu da hutawa Sir ya faɗa cike da kulawa, "Sir ga wasu files" Kansa ya ɗaga masa fuska a ya mutse na Almar gajiya,kana ya ƙara sa kusa da Sultan ya aje mishi wasu files ya fara singing, a hankali Dr Aryan ya mike murmushi na ƙara faɗaɗa akan fuskarsa kana ya ce," Kwai mutun biyu da zaka Duba yanzu kafin kaje Hutun awa biyu,Da sauri Sultan ya ɗago yana kallon Dr Aryan fuska a marairaice kaman Zaiyi Kuka. Dr Aryan ya yi saurin sunkuyar da kai ƙasa yana haɗiye dauriyar dake neman kubce masa dan yasan shima da gaske Sultan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace,"Da gaske nake Sir, gama files nasu na kammala dubawa" "Aryan Please, wallahi na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi wata ƙofa. Murmushi Aryan yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice daga office ɗin zuwa nashi shima. Ɗan madaidaicin ɗakin dake cikin Office ɗinsa ya nufa dake ɗauke da kayan daɗi compiled, shima sai kamshi yake mai daɗi.kamar ba'a cikin asibiti ba. Kai tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan barci yake matuƙar ji. Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin sanye da rigar wanka Fara, sai hular wanka data kare gashinsa daga jiƙewa, da alama dai baya buƙatar jiƙawar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent ɗinne tun lokacin dazai shiga theatre room. Aziz ya kira, sai akai rashin sa'a ya samu wayarsa a busy. Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ɗayar ya ɗauka itama ya cireta a plane mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ɗin sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ƙofar. Rasa wanne zai farayi yayi. Ɗaga wayar? Kokuwa buɗe ƙofar?. “Sir" ya tsinkayi muryar Dr Aryan na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ɗin da Dr ɗin ya yi maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya buɗe masa ƙofaba, sai dai ya sake haɗe fuska alamar da gaske ya gaji baison takura. Yana buɗe ƙofar yace, “Aryan plea.....” Saurin katsesa Aryan yayi da faɗin, “Yi haƙuri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Sir ɗaya daga cikin Nurse ɗin nan ta yiwa Yaro Allura ta kare a jikinsa. “What?!” ya faɗa hankali tashe. Shima Aryan da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai. Juyawa cikin ɗakin ya yida sauri, yama manta da wata gajiyarsa. A Gurguje ya shiya ya fice daga ɗakin Dr Aryan zauna a Office ɗinsa tare suka fice daga Office ɗin, tun kafin su ƙaraso suke juyo Murya yaro na kuka, sauri sauri gugu gudu suka ƙasaso wajen, Sultana nabaki ɗaya a ruɗe take jikinta har karkarwa ya ke, Cikin tsananin tashin hankali da tsagwaron damuwa yace, " ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya kamata a ba mara lafiya kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?” ya ƙare maganar da ɗan raunin murya. Sultana da maganar Dr Sultan tai mata zafi ya buɗe baki zaiyi magana cikin ƙoƙarin danne fushinsa, amma sai Sultan ɗin ya kuma dakatar da ita ta hanyar faɗin, “Bana buƙatar jin komai please" yaron ko sai kuka yake kaman Ranshi zai fita, cikin dubara Sultan ya cire Allurar wajen harya kumbura, kana ya shika lallaɓa yaro har Saida yayi Barci ya bar wajen Sultana ta rakashi da Harara. Dai dai lokacin Jidda ta ƙara so wajen tana faɗin ,"Daughter Lafiya Sultana ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar kana,"tace ni da ɗan renin hankali,bai ko tsaya jin bahasi ba zai rufeni da faɗa ta ƙara sa maganar cike da tsiwa, "kimin baya Meya faru Daughter, "wai yaron nan ne fa ya ƙi tsayi nayi mishi Allura garin mutsu mutsun sa Allura ta kare a jikinsa, da sauri Jidda ta ware mayan idanunsa kana yace," nashiga ukku Ni Kuluwa!" "Haka kwai zai hauni da faɗa kaman wani ubana" "Daughter gaskiya ne Dr ya faɗa ki riƙa kula Allah ya tsare gaba" Ƙala Sultana bata ce mata ba. Kana sukaci gaba da aikin su. A bangaren Sultan yana komawa office yayi wonke hanneyensa sannan ya fada kan sofa ya zauna yana jin haushin abunda ya faru...gaba daya bacin ranshi sai ya karu fiyeda wanda yake ciki already...tunda yake bai taɓa ganin sangartacciyar yarinya kaman wannan yarinyar ba...maida kanshi ya lafe jikin kujera tareda lumshe ido.. a hankali ya mike yaci gaba da aikin da ke gabansa, Wuraren ƙarfe 5:40 ya kira Direba, bayan mintuna 20 ya iso, bayan ya kammala a binda yake ya fice daga Office ɗin kai tsaye ya wuce Parking space, dai dai lokacin Sultana ta iso wajen tattausan sumar ƙeyansa dake kwance lib-lib ta zubawa harara. Numfashi mai sanyi taja tare da shaƙa daddaɗan ƙamshin turarensa mai sanyi. Sai kuma tayi ƙasa da kwayar idanunta,baki ta ɗan tura sama ta da liƙa ƙeyarshi wani sabon harara tare da zan tsaki hankali ya ɗan juyo gefen damansa, jin inda sautin tsaki yake ɗan tashi ya kauda kai gefe kaman bai jita ba ya shige mota, motar na ɗagawa Jidda ta iso wajen tana faɗin ," Daughter tsaya ki rage min hanya, ba musu ta tsaya jidda ta shiga kana suka fice daga Asibiti, cikin mota kuwa Jidda sai labarin Sultan take,har suka iso gidan su, kana Sultana ta kalleta,"Allah kika ƙara min maganar Shi a mota zai dai na sauke ki a hanya, "haba Daughter Meya yayi zafi haka gama Insha Allahu da mota na zanjo daman ɗazu koda na fito aba'a wanke taba, "Nadai gaya Miki" yana kai ƙarshen Maganar ta wuce, a hankali Jidda ta sauke sassanyan Nunfashi kana ta nufi cikin gida... Tunda suka baro cikin Asbitin ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yayi shiru idanunsa dake da cikar baƙin gashi da gira a sama suna a lumshe. Sai faman juya zoben hannunsa dake a hannunsa na dama. Duk abinda ya keyi drivernsa na kula ta cikin mirror, Haka dai suka cigaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai. Gashi mahaukacin gudu yakai Tunda 6pm tayi kiran Mommy da Daddy ya fara shigowa a wayarsa, sai dai ko sau ɗaya bai amsa masu ba ya share, sai ma kwanciya daya gyara cikin lallausar kujerar motar ya cigaba da latse-latsen laptop ɗinsa har yanzu da takaicin Sultana a ransa. Ƙarfe 7:20 suka iso gida Tunkan su gama dai-daita parking idanunsu suka sauka akan Mommy da Ihsan dake ta faman kai kawo ta barandar saman bene. Sai dai ganin shigowar motocin tuni tabar wajen da alama zata fitone. Tare suka iso wajen harda su Salma da gudu suka rungumeta tare da faɗin,"Sannu dazuwa Ya Sultan" Ihsan ko wani irin kallo take binsa dashi, a hankali ya janye su daga jikinsa ya nufi wajen Mahaifinyarsa, "Sultan ya Aiki?" "Alhamdulillahi Mommy Ina Daddy?" "Yana masallaci" "Ya Sultan sannu da zuwa Ihsan ta faɗa cikin sanyi Muryar, "Lafiya" yaba Amsa, kana ya wuce cikin gida, yana zame baƙar jacket ɗin jinsa tunkan ya buɗe. Ya riƙeta a hannu ɗaya sannan ya ƙarasa ya murda handle ɗin ƙofar ya tura ya shiga. Fes ɗakin yake shima, yanata tashin ƙamshin fresheners data haɗe da turaren da yake amfani da shi. Jefa jacket ɗin yayi saman gadon ya ƙarasa gaban mirror yana ajiye wayoyin saman mirrorn. Zama yay a stool ɗin gaban madubin yanata faman yamutse fuska dan yunwa yakeji, sai da ya cire takalman ƙafarsa da safar, farar ƙafarsa dake fes ta bayyana kafin ya miƙe kansa tsaye ya nufi toilet Yana shiga aka fara knocking ƙofar falonsa, amma sai ya share ya cigaba da abinda yake a ciki. Anyi kusan sau uku sannan aka bari. Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe Milk color. Hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana tsane sumar kansa da kallo ɗaya zakai mata ka fahimci tana masifar lasar kuɗaɗe kodan ƙyawun da take dashi ga mai kallo a ido balle kuma wanda ya taɓa. “Sultan! Buɗe min ƙofa”. Ya tsinkayo muryar Mommy tana faɗa cikin yaren fulatanci da tun zuwansa gidan ta fahimci yanaji da ɗan buga ƙofar yanda tasan bazai takurasa ba. Gefe ya karyar da wuyansa yana yamutsa fuska da yarfar da hannayensa duka alamar shifa an takura masa. Fuskarsa cike da takaici yaje ya buɗe mata tare da juyowa a binsa batare da ya tsaya saurarenta ba. Ƴar dariya tayi abinta, dan ko ɗan hakan bai dametaba, tasan ya gajine matuƙa, shikuma idan ya gaji to lallai sannan baƙin ransa ke ƙara hauhawa, kowa kuma yimawa yakeyi har ita da Daddy. Ƙarasawa tai inda yake tsaye a gaban mirror yana cigaba da tsane kansa. Kama hannunsa tai ta zaunar, ta amshi towel ɗin ta cigaba da goge masa kan tana kallonsa ta cikin mirror fuskarta washe da murmushi. Shiko ya ciskule tasa kamar zai fasa ihu. Sai da ta tsane masa kan tas kafin tajawo hand dryer ta jona a jikin soket ta fara busar masa da shi. Ajiye dryer ɗin tayi da jan hancinsa tana faɗin, “Nasan wannan fushin bana komai bane sai yunwa da gajiya Taso kaje kaci abinci ka kwanta ka huta. "Mommy bari nayi sallalolin" ya faɗa fuska a tsuke, Mommy tai Murya kana ta fice daga ɗakin, Saida ya yi kana ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ya wuce palon duk suna zaune a palon, Daddy L "Ma sha Allah" "Taso muje kaji Abinci, karkamin Kuka, cewar Mommy,gabaki. Suka wuce Darning a tsanake suka soma cikin Abinci.... tun kafin ta iso mai gadi ya buɗe mata gate cike da kwarewa ta danna hanci motar cikin gida tana gama Parking ta fito, mai gadi na rufe gate wani yaro ya yi knoking, "Gashi a ba Sultana, ba musu ya karɓa ya nufi wajen Sultana dake ƙoƙarin shiga cikin gida, "Madam gashi akace a baki 🎁abinda ke hannunsa yamiƙamata Ido.Sultana tazaro waje, "Baba nifa?. "Eh ked'in, cewar Baba. Karɓa Sultana Tayi tabud'e, 💐filawa ce mai k'amshin tsiya aciki, saikuma turare mai masifar kyau da ƴar ƙaramar takarda ta zaro anrubuta. _for you! my Sweetheart_....✍️✍️ _More Comments and share_ *Sadeeya Ka'oje ce* ✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 21-22* _______tagaza gane wanene zai iya tura mata wannan sak'on?, tad'an shinshina fulawar, kamshi mai dad'i yadaki hancinta, harsaida ta shak'a ta lumshe idanunta, kamar tataɓa jin k'amshinan, to amma a ina?, wannan itace tambayar. Dai dai lokacin kuma Motar Haydar ta shigo gidan da wowarsu kenan daga school tare da Meena, Cikin mamaki duk suke kallon Sultana, "Anty Sultana waye ya aiko miki?. "Wlhy Haydar....ban saniba nima?. Haydar.... Yamaida kallonsa ga Baba Mai Gadi, "waye yakawo?. "Wata 'wani ɗan Saurayi ne. "Saurayi" Sultana ta faɗa a hankali. "Anty Sultana Kodai kinyi sabon Kamu ne?" cewar Meenah, "Bana son Iskanci fa kowaye ya yi a banza,tana ƙoƙarin jefarda jakar Haydar ya yi saurin da katar da ita,"A'a Anty Sultana bai kamata ki jefar da ita ba.taɓe baki tayi, Haydar da Meena sukayi Murmushi cikin gida suka nufa, "Maraba da mutanen Asbiti, cewar Mami. fuska a yamutse Sultana ta nufi wajen su, "Mami Wlh na gaji"Sultana kuwa jingina bayanta da jikin Kaka tayi tana sauke Ajiyar zuciya, "ina kika samo flowers kuma?" "Say zaa nayi kaka ta bata Amsa a takaice, bari Naje nayi sallah a hankali ta mike Kai tsaye ta wuce ɗakin ta jefar da jakar saman gado kana ta wuce toilet Wonka tayi da ruwan dumi tayi Alwalla ta fito a tsanake ta yi Sallah, bayan ta gama ta wuce palon suka ci Abinci. hira suka dan taɓa kana kowa ya wuce makwancinsa.... Washegari , Yau sama-sama Sultana ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon Baya alamar zuwan period ɗinta. Ita dama takan fara da ciwon Baya, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma normal sai shegen ƙwaɗayi kamar mai ciki. Tunda Kaka ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin daɗi, dan maimakon kwance saita isketa zaune ƙasa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Meena nata da Nana barcinsu a kan gadon . Ita ta fara tadawa kafin su Nana, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Sultana data maida kanta ta kife tsakanin ƙafafunta....... “Ke kuma lafiya?”. Da ƙyar Sultana ta ɗaga kai ta kalli Kaka, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti a mata allura sai ta daure tace, “Kaka lafiya lau, kawai gajiyace. Ɗan ƙura mata idanu Kaka tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa komaiba. Meena ce ta ƙaraso wajen Sultana ɗin ta durƙusa. “Anty Sultana ƙarya kikaima Kaka wlhy, daga gani baki da lafiya”. Yamutsa fuska Sultana tayi kaɗan tana maida ƙwallar data cika mata ido. “Baya na ke ciwo Meena nasan kuma period ɗinane zaizo zuwa gobe idan Allah ya kaimu ko anjima”. Nana dake fitowa daga bayi tace, “To miyasa kikaƙi faɗar gaskiya?”. Meena dake tsokanar Sultana tai saurin cewa, “Allura”. A tare suka kwashe da dariya ita da Nana Sultana kuma tai tsaki idonta cike da ƙwalla ta miƙe. Da ɗingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Meena ke mataba har yanzun. Bayan sun idar da salla Meena da Nana suka soma shiri zuwa School, Sultana kam saita koma saman gado ta kwanta. Babu jimawa barci ya yi gaba da ita. kaka da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan sun kammala breakfast, Su Meena suka wuce makaranta ga baki dayan su, "Wai Nikam ina Sultana Mami ta tambaya,"tana ɗaki ba Lafiya, cike da damuwa Mami ta ce," Subuhalillah Meya sameta ta faɗa tare da ƙoƙarin barin wajen, kai tsaye ta wuce ɗakin su Sultana, koda ta shigo Sultana sai faman juyi take tana damƙe da mara, "Sultana tashi maza ki shirya muje Asbiti, murya a disashe tace,"Anty naji sauƙi, dai dai lokacin kuma wayarta ta soma Ringing, "Kinga ana kiranki Jidda ce,Mami ta faɗa tare da ɗaga wayar, daga can ɓangaren Jidda ta ce,"Daughter Lafiya har yanzu Ban ganki ba?" cikin raunin Murya Sultana tace Mommy banda Lafiya!" "Mike damunki? Kinsha magani?" Kai Sultana ta girgiza mata kaman tana gabanta, "turomin Address ɗin gidan ku ganinan zuwa, suna gama wayar Mami ta tura mata Address ɗin, "tashi ki watsa ruwa kafin ta iso Mami ta taimaka mata zuwa toilet, tana fotowa da Wonka dai dai lokacin Mami ta shigo ɗakin riƙe da Cup din tea Mai kwauri, cikin ɗauriya ta kammala shirin, "karɓi Kisha, fuska a yamutse ta ce ,"Na ƙoshi Mami" "Ƙarbi maza Kisha" Ba yadda ta iya dole ta karba ta sha, kana suka fice ɗaga ɗakin, "Ya jiki Abba ta tambaye cikin kulawa, "Naji sauƙi Abba, dai dai lokacin Jidda ta shigo cikin palon cike girmamawa ta gaishesu, "Asbitin zaku je?" Mami ta tambaya,"Allah ya kiyaye,"Amin kana suka fice daga palon har bakin mota Mami da Kaka suka rakaru,tunda suka shiga cikin motar Sultana ta Kwantar da kai tare Lumshe idanunta,har suka iso Asbitin. A hankali suke takowa suna fuskantar juna. Sosai ya zuba mata ido sabida ya lura gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi alamun tsananin ciwo takeji gashi a hankali take taku. Ita kuwa Sultana, tafiya takeyi da kyer sabida azaban ciwo da bayan ta da mararta keyi. Kanta a sunkuye take tafiya, Jidda na biye da ita a baya. Ganin yayi ta wani irin sunkuyawa tasa hannunta duka biyu ta damƙe mararta dake matsifar ciwo. "Yauwa ga Dr Sultan na ma yanzu ya iso, muje ya duba ki ko?" hannu tasa ta matse mararta tare da cewa."Allah ya tsareni ya Dubani duk Doctors dake Asbitin nan A rasa wanda zai Dubani sai shi.ta ƙarasa maganar cikin yanayin muryar mara lafiya. "Sir ga marar lafiya nan"Jidda ta faɗa, Dai-dai lokacin kuma suka kutsa kansu cikin asibitin. Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, har ya shiga cikin wani ɗan corridor ya shiga wanda zai sadashi da Office dinshi ba tare daya ratsa ta cikin Reception ɗin su ba.. A Gurguje Jidda ta buɗe mata File ta wuce dashi Office ɗin Sultan. Jim kaɗan ta dawo. ta kama hannu Sultana,Da ƙarfi ta damƙi hannun Jidda Cikin tausayawa Jidda tace. "Sannu, in sha Allah bazamu jimaba za'a kiraki, dan na nemi al'farman sauran sun yadda.Kai kawai ta iya gyaɗa mata, sai taune lips ɗinta da takeyi. Suna isa office ɗin sa dai dai lokacin ya kira sunanta, batare da ta san waye ba ta nufi Office ɗin.Nurse namiji na ga banta.A haka suka shiga, Ajiyan zuciya taja a hankali sabida tsaruwa da kyau da tsabta da ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta, su sukasa ta son bin Office ɗin da kallo amman ina ciwo bazai bartaba... A hankali ta iso gaban table ɗin baƙin Glass dake gabanshi. Ɗaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table ɗin ta zauna. Ƙasa tayi da kanta cikin tarin ciwo da fargaba.Shiru tayi zaune bisa kujerar tayi ƙasa da kanta.Sultan ko kanshi bai ɗago ya kalli inda takeba.shiru Office ɗin sai sautin A.C da yake busawa, Kusan tsawon 2 minute suna a haka, cikin dakiya da rauni ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi, Ga mamakinta sai taga asalima hankalinshi baya kanta, baki ta ɗan taɓe, a hankali tace,"Wai daman nan Jidda ta kawo Ni?" Sultan duk abinda takeyi yana ganinta ta ƙasan ido.cikin sanyi Murya ta ce, Nifa Lafiya ta lau. Shiru bai kulataba har sawon wasu mintuna 3 har ta fara zaton ko bai jita bane. Da sauri ta ɗago kanta jin yayi mata magana, cikin wata zazzaƙar murya a takaice yace. "Suna?". Cikin fargaba ta tace."Sultana Abdullahi. Shine sunan da jidda ta buɗe mata file dashi. A hankali ya ɗan ɗago ƙwayan idanunshi ya kalleta. Kanta a sunkuye hannunta biyu duka na kan mararta cikin wani, irin yanayi take wanda yake nuni da tana cikin wahala... Sultana ya maimaita sunan a Zuciyarsa. A fili kuma kauda idonshi yayi daga kanta ya maida idanunshi kan files dake gabanshi, wanda sunanta ke rubuce akan na samanshi yaja da yatsu biyu.Tsiraran idanunshi ya lumshe sabida wani irin bugu da yakeji zuciyarshi nayi tun lokacin ya kasance kusa da ita har zuwa yanzun nan da take gabanshi a zaune. Rubuce-rubuce yayi a ciki file. Kanshi ya kuma ɗagowa ya kalleta a fizge da gefen idonshi, sunkuyar da kanshi yayi tare da cewa. "Meke damunki?". Murya a disashe da son danne kukan da ke son kabce mata tace."Baya da Marata. Kai ya ɗan jujjuya tare da kallon shekarunta dake rubuce a cikin File din, Yar shekara ashirin kuma da ƙorafin ciwon baya, cikin sanyi Murya yace. "Yaushe ya fara miki ciwo?". Hannu tasa ta share hwayenta a hankali tace. "Shekara Huɗu da suka wuce". "Meyasa bakije asibitiba tun lokacin?". Ya tambayeta. "Ina zuwa asibiti duk sanda ya tashi". "Kamar yaushe da yaushe yake tashi?". Ya jefo mata tambayar kamar yadda zuciyarshi ke harbawa da ƙarfin tsiya da kuma sauri-sauri, cikin ɗauriya tace," duk ƙarshen wata. Kawar da kanshi ya yi gefe kaman bai jita ba yaci gaba da Rubuce rubucensa. Saida ya gama ya tura mata file ɗin a gabanta, Jikinta na rawa tasa hannu ta ɗauki file ɗin, ta yunƙura zata tashine, ya basu damar samun kusanci da juna, da sauri ya rumtse idanunshi sabida wani irin matsiffen bugawa da zuciyarshi keyi. cikin zuciyarshi yake maimaita. "Innalillahi wa innailaihi rajiun." A hankali ya buɗe kyawar kyawan idanunshi jin bugun zuciyarshin ya fara yin ƙasa-ƙasa, ido ya zubawa mata ganin ta juya tana tafiya, wani abin al'ajabin a gareshi shine duk taku ɗaya da zatayi tana nesanta dashi sai yaji zuciyarshi na tsinkewa yana bada wani mugun bugun , yayinda bugun tsinkewanta kuwa yaketa dai-dai-ta, Cikin mamaki ya sunkiyar da kanshi yana kallon yadda takeyin taku, tana riƙe da mararta, taje gab bakin fofar fitane, Taji wani irin murɗa da kartan da mararta ya farane yasa ta sakin wani sauti mai cike da wuya. "Wayyo! Allah na, Wayyo Mami cikina Wayyoo Ka...." Da sauri Jidda ɗin nan yayi kanta tare da cewa."Sannu Sultana"a hankali jidda ta zaunar da ita kujerun ƙarfe dake gab da bakin ƙofar. Bata da zaɓin daya wuce ta zauna ɗin, domin gaba ɗaya ƙafafuwan ta rawa sukeyi alamun bazasu iya ɗaukar nauyinta ba ga duhun daya rufe mata ido. Sunkuyowa Jidda ɗin yayi ya amshi file kana tace. "Zauna bari inje Pharmacy in amso miki magungunan da alluran sai ayi miki". Kai kawai ta iya gyaɗa mata... da sauri Jidda ta bar wajen.bayan mintuna goma ta dawo tuni Sultana ta fara fita haiyacinta," kije ki mata Allurar, Jidda ta ware manyan idanuny," Sir Wallahi Bazan iya ba tsoron Allurar tsiyane da ita , Ta gefen idonshi ya ɗan kalli Sultana da keta durƙushe a wajen ɗaya. cikin bada murni ya ce ."Tazo". Da sauri Jidda ɗin ya juyo ya nufoshi, hannu yasa ya amshi allurar, kana ya ɗan kalleta a fakaice yace. "Zo nan". A hankali ta taso cikin sanyi takeyin taku tana matsoshi. A take kuma bugun zuciyarshin ya fara tsananta Taku biyu tayi ana uku yaji ƙirjinshi ya bar tsinkewar da yaketa yi ɗin, sai kuma bugun da yakeyi da sauri-saurin ne yaketa tsananta.da sauri ya dafe ƙirjinshi lokacin da ta iso gab dashi, cikin ranshi ya kuma cewa. "Ya Rabb" A zahiri kuwa, da kai ya nuna mata ta kuma matsowa, ba musu ta matso, yatsarshi ya jujjuya mata alamun ta juya mishi baya, still babu musu ta juya, a hankali ya murza kujerar da yake kanta, ya juyo ya fuskanci bayanta, dai-dai saman mazaunanta ta sama ta ɗan gefe kaɗan, ya saita, tsinin bakin allurar, cikin iyawa da gwarewa rumtse idanunta tayi da azaban ƙarfi sabida, wani zafi da taji yana ratsata, hannunshi yanada masifar zafine, Da ƙarfi tace. "Wach Allah na zafi-zaffi." Wani irin azaba taji lokacin daya fara sakar mata ruwan allurar a jikinta, babu zato babu sammani yaji tasa hannu damanta ta damƙe hannunshi dake mata alluran hannunta na hagu kuwa yarfashi take tare dasa kuka da sauti tace. "Wayyoo Allah na Zafi nake ji, bugun zuciyarsa ko tsananta yake, ya kusan hallakashi lokacin data riko hannunshi, da sauri ya tura mata ruwan kana ya zare Allurar da ƙarfi. Sannan ya miƙe tsaye, sabida muddin yana kusa da ita babu makawa wata ƙil zuciyarshi zata faso ƙirjinshi ta fito woje. Wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya bi gefen Jidda ɗin ya fice daga Office ɗin... da sauri Jidda ta riƙo hannuta suka fice ɗaga Office ɗin. Ta kaita ɗakin ta kwantar da ita nan take bacci ya yi awon gaba da ita... Sultan da sauri yake tafiya sabid iya yedda yake nesanta da ita iya yadda kirjinshi ke dai-dai ta bugawa, sai kuma tsinƙewa da zuciyarshi keyi... Bacci Sai Sultana ta yi sai ƙarfe Shidda ta farka, ba ɓata lokaci suka wuce gida, har gida Jidda ta kaita, sai lokaci ta tuna da wayar ashe cikin mota tabarta, Miss Call ɗin Mami da Kaka. Da Abba ba iyaka... lokacin da suka iso ƙofar gida Sultana ta kalli Jidda ta ce," me yasa zaki kai wajen Ɗan is..... "ya isa Sultana Jidda ta yi sauri dakatar da ita," to in ba iskanci ba zai sani a gaba yana mun tambayoyi, wannan sam bai dace da zama likita ba ɗan jarida yafi dace wa dashi... "Kai Nikam me Dr Sultan ya yi Miki kika tsaneshi haka, karfa ƙiyayyar da kike mai ta kowa so! Wata rana, " Allah Ubangijin ya tsare ni ko shine Autan maza a duniya Bazan zaɓa Auren sa ba!" (Ni dai nace Humm😅). Jidda ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciyar,kana tace,"Allah ya kyauta" Ƙala Sultana bata ce mata ba ta fice daga motar ta nufi cikin gida... Kai tsaye bathroom ta wuce, tabbas kuwa baƙon ya iso, Wonka tayi kana tayi al'wala dan ko bata salla bata zama babu al'wala. Tana fitowa ta kimtsa jikinta kana ta zura tattausan doguwar riga. Tana kokarin fitowa falo Meena na ƙoƙarin shigowa da sauri Meena ta zaro ido tare da cewa. "Yaushe kika dawo?". Hararanta ta ɗanyi tare da cewa. "Ban sani ba" Cikin tausayawa Meena tace. "Sorry Anty Sultana Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana tace. "Ya jikin naki Anty Sultana!" "Naji sauƙin" "Na dawo a guje fa, wannan Sultan ɗin hannunsa zafi. Zaro ido na mamaki Meena tayi tare da cewa. "Anty Sultana Shida kanshi ya miki?". Kai ta gyaɗa tare da cewa. "Eh". Cikin taɓe baki tace. "Lallai yau kin tashi da ƙafar dama, gashi kuwa naga har kin worke". Wucewa sukayi zuwa tsakiyar falon, cikin sauƙe numfashin Sultana tace. "Ba doleba Ko don mugutar da ya yi min dole na warke, Dariya Meena tayi tare da cewa. "Kinji allurar manyan likitocin da duniya keji dasu dai". Uhum kawai tace sannan suka fara cin abinci, sunaci suna hira. "Wai ina Mami da Kaka, "Barci suke, sai gab magriba kaka ta farka daga Barci ruwa ta watsa don taji daɗin jikinta... "Sultana ya jiki" "Lafiya lau Mami, tun ɗazu na dawo ai. su Khalil basu dawo ba har yanzu, "Mami Kinsan yau hadda suke sai 8 zasu dawo..." "Na manta Sam" A hankali Meena ta wuce ɗaki don yin Sallah, Sultan ta nufin ɗakin Kaka , koda ta shigo tana Sallah zama tayi tana karanta Askar a wayarta bayan ta kammala ta kunna Data tana chatting da Jidda dake tsokanarta.. Kaka ko bayan ta sallame sallah taci gaba da Addu'oi...har zuwa bayan Isha'i, ƙarfe 8:15 su Khalil suka dawo a gajiye,bayan sunyi Wonka suka ciki Abinci,kana kowa ya wuce ɗakin sa....., Sultan bai samu dawowa gida ba sai bayan magrib...haka kuwa ya shigo gidan rai a hade saboda tsabar gajia da yayi...driver na shigowa ya samu wuri yayi parking sanan ya bude motan ya fito saidai tun kafin ya zagaya ya bude mishi kofa mai Security yazo ya bude yana mishi sannu da zuwa, Sultan bai iya ce mishi komai ba sai hannu daya daga mishi kafin ya nufi cikin gida a yayi da fusakarsa zai baka daria sosai...ya lumshe idanunsa tareda dora kanshi shoulder din Mommy murya can kasa cikin yace"Mummy na gaji ta shafa kanshi fuskanta daukeda murmushi itama tace,"welcome back son..akwai gajiyan aiki koh"...ya ɗan tauna lips dinshi kana ya ce "Akwai gajia sosai Mommy.. "ina Salma da Salim?" "Sunyi Bacci tun ɗazu" je ka watsa ruwa kazo muci Abinci, jiki a mace ya wuce ɗakinsa ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin lallausar jallabiya yana zuba kamshi, ya fito palon ruwan tea kawai ya sha ya wuce ɗaki...... Haka Sultana ta kwana ranar cikin takaicin Sultan da jidda da duk ta tattara laifin a kan Jidda da ta kaita wajen Sultan ɗin, Bata da riko sam idan akai mata abu. amma sai gashi Jiya da yau Abun ya tsaya mata a rai da tarkacensa sun kasa barin ranta harma washe gari da shima dai haka ta yini babu walwala saboda jininin tana, Jidda tuni ta kama kanta don ko a Asibiti bata sakar mata fuska ba.... Washegari ya gama shirya kanshi cikin suit kaman ko yaushe ya nufi parlon Mummy don yin breakfast, A Gurguje ya yi Breakfast ya wuce Office. Cikin ƙanƙanen lokaci ya iso, bayan mintuna 5 Sultana ta iso kallon motarsa take tanan dalla mata Harara tare da jan tsaki.. kana ta wuce.... A hankali Rayuwa taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali. cikin ƙanƙanen lokacin Sunan Sultan ya kaɗe duniya saboda kwarewar Aikinsa. Kowa yasan Dr Sultan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana idon ma kaga yana doguwar magana Murmushi to a gida ne, Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar girman kaine bisa ga ɗaukakar da Allah ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Sultan sam ba haka baneba ko a nan Asbiti ƴan mata da dama sun nuna mai so. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. yanda yake gudanar da Rayuwarsa Allah ya ɗaukakashi a duniya a dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan Allah shine mai komai da kowa. A ɓangaren Sultana ma sosai ta maida hankali ga Aikin ta... A dayan ɓangaren kuma Al'ummar musulmai tana faman shirye shiryen Azumin watan Ramadan...yau Azumi sauran kwana biyu, Daddy tun Azumi saura sati ɗaya yake rabon kayan Azumi da mabuƙata, A ɓangaren Abba ba'a barshi baya ba.... Washe garin washe gari. Da daddare watan Ramadan ya bayyana. Haka yasa dukkan ɗauka cin Musliman duniya suka cika da farin ciki tare da yin niyan ɗaukar azumin watan Ramadan ɗin, kana kowa yana shirya bukatunsa dan miƙa su ga Ubangiji Mabuwayi...✍️ Ina ma kowa Barka da jumma'a 🥰💖 _More comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce* ✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 23-24* _____ Alhamdulillah an shiga watan azumin ramadan cikin rahamar Allah da yardarsa. Kowanne musulmi na ƙwarai yana cike da farin cikin shigar wannan wata mai tarin Albarka dake zuwa mana a cikin watanni goma sha biyu na shekara sau ɗaya kacal ya wuce. Randa aka kai azumi na goma Daddy ya gama shirya maganar Umrah da sukan kanje duk shekarar, tafiyar baifi saursa kwana uku ba Kaka ta kwanta Zazzɓi, hakan yasa Mami ta fasa tafiya, Amsar passport ɗinsu Daddy yayi musu komai su duka,.Haka kawai sai Sultana ta tsinta kanta da rashin jin ɗokin zuwan, duk da kuwa tana matuƙar son rayuwa a ƙasar saudia saboda karon nan da sultan Za'a tafi. Ranar Ta samu Kaka a ɓoye ta roƙeta akan ita bazata je ba karon nan, ita batason zuwa batajin daɗin jikinta. Harara Kaka ta watsa mata tana taɓe baki. Batare da tace mata Uffan ba a zancen ta ɗauke kanta ta maida ga karatun Alkur'ani da take karatu. “Kaka dan Allah Sultana ta faɗa cike da shagwaɓar data saba yima Kaka tana kwanciya mata a gefen kafaɗa. Ture mata kai Kaka tayi tana faɗin, “ da Allah jacan Dukfa take-takenku ina sane dasu. Yanzu bautar Allah ce ma baƙyason zuwa saboda Sultan zaije ko yaya? Baki Sultana ta sake kumburawa tana faɗin, "Kaka don Allah fa" Kuma Umrah babu fashi sai kinjeta. Dan Allah idan kunga juna ke da Sultan ku mutu Ni bansan me yaron nan ya tare Miki ba, haka ranar naji kina zaginsa don ya yi Miki Allura. Sultana bata sake tankawaba, dan ita ɗaya tasan damuwar da take ciki. Washe gari Jirgi su Sultan ya ɗaga tare da su Ihsan, Salma, Salim, Mommy,. Bayan shan ruwa suna zaune a Palo, Sultana na kwance saman cinyar Kaka Lafiyarki kuwa Sultana? Kina tafiya kamar hankalinki baya jikinki?”.Kaka dake zaune a falo tana duba ta faɗa tana kallonta. a hankali ta kiƙe saune ɗora kanta gefen kafaɗar Kaka ɗin. “Kaka kaina ke ciwo fa yau tunda safe,. Shiru Kaka tai kawai tana kallon Sultana, dan gaba ɗaya a kwanakin nan tana kula da ita kamar akwai abinda ke damunta. Ta zaunar da ita yafi a ƙirga tana tambayarta amma sai tace mata babu komai. Jin Kaka batace komaiba itama sai bata sakeyin magana ba, tama lumshe idonu kamar mai barci. Sun jima a haka, kafin Kakada taji Sultana ta mata nauyi a kafaɗa taɗan ɗago ta kalleta, numfashi take saukewa a hankali na barci. ta girgiza kai kawai da ɗagota a hankali ta gyara mata kwanciya a kujerar tare da ɗaura kanta saman cinyarta. Aiko kamar jira take saita sake gyara kwanciya da ƙyau a cinyar Kaka ɗin. "Mama lafiya take kuwa?” Abba ya ya faɗa yana ɗaura hannunsa saman goshin Sultana. Ɗago ido Kaka tai ta kallesa dai-dai ya janye hannun ya sake maidawa a gefen wuyan Sultana. “Lafiya lau take, barcine kawai”. Janye hannun ya yi yana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “To Alhamdulillah, "Abban Haydar har ka foto, Mami ta faɗa lokacin da ta fito daga Kicin tare Meena. "Zanje gidan Nuraddeen, Kanta ta jinjina masa cike da girmamawa, tare da masa addu'ar dawowa lafiya. "Amin ya amsa ya yi gaba. Harya kusa ficewa a falon sai kuma ya tsaya tare da juyowa. “Banji motsin su Arif ba, " Sunyi bacci tun ɗazu..... ★★★ Yau Azumi 15, yaune Kuma su Sultana zasu wace Umra. Kaka ta Zaunar da ita Kaka tayi tai mata doguwar nasiha akan wannan tafiya, tare da tunatar da ita manyan ibadu da idan taje zata maida hankali a kansu ba shashanci ba. Tsaf Sultana ta riƙe komai a ranta, tareda ƙarfafa ranta akan in sha Allah zata zama mai himma. Ƙarfe 10:40.jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Ta tafi cike da kewar Kaka da Mami da Jidda.. _____________________ *SAUDI'A* Cikin sa'a kuwa yana isa airport ɗin jirginsu na sauka.Lumshe idanu tayi tana karanto addu'oi da fatan cika alƙawarin da taima Kaka akan kama kanta. A hankali suka fito. Sanye take cikin Abaya mai masifar kyau, an ma rigar ado da duwatsu manya da ƙanana, sai veil da ta naɗa a kanta wanda ya sake fidda ƙuruciyarta da ƙyawun da Allah ya bata. Farar ƙafar ya haska tana sanye cikin Black ɗin takalmi da yayi masifar mata ƙyau. Sai ƙaramar jakarta itama dai Black ɗince. Kallon agogon dake ɗaure a hannunta tai lokacin da suke ƙoƙarin sakkowa daga jirgin, ta ɗan yamutse fuska tana sauke hannun a hankali da kai dubanta can ɗan nesa dasu. Wani irin bugawa ƙirjinta yayi saboda hango Sultan dake tsaye jikin mota sanye cikin Jallabiya ta masa ƙyau.sosai, ya ƙara ƙiba da ƙwarjini a idanun mai kallo kamar ba azumi ake ba, Sultan da ya yunƙuro saboda hango Daddy dake a gabansu da yayi yaja ya tsaya cak lokacin da idanunsa suka sauka akan Sultana ƙirjinsa ya yi matsifar bugawa , ya kasa motsi balle ɗauke ido daga kallonta har suka ƙaraso inda yake. Abba ko sai kallo su yake,"sultan ya ibada ya Abba ya faɗa tare da kallon sultan ɗin. sauƙe Nannauyan Ajiyar zuciya,ya kasa ɗauke idanun nasa daga kan Sultana da ta ɗauke kanta gefe tamkarma batasan da zamansa ba a wajen. "Alhamdulillahi Abba da ƙyar ya janye Idanunsa daga kallon Sultana. "Daddy sannu da zuwa, "Yauwa my Boy, Meena ta nufi wajen Sultan ta rungumesa tare da faɗin,"Ya Sultan ya ibada?, "Alhamdulillahi Aminatu!" wani irin tsam take ji a jikinta duk lokacin da ya kira ta da sunan, ɗaya bayan ɗaya ya riƙa rugumersu Haydar, kana suka shiga Mota, Sultan kam rabin hankalin na'a tuƙi ne rabi akan Sultana da a yanzuma ta ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. A haka suka iso gidan nasu a mai ƙyau da tsari da Daddy ya saya musu Saboda Aikin Ummra da yake zuwa duk shekara. Sai da ya Parking motar inda ta dace kafin su fita shi da Haydar ya buɗe musu Mota suka fito, Sultana a kuma ta buɗe da kanta ta fito tana kallon gidan ta yi da duk shekara suka sai sun tarar da An sabun tasa, zuciyarta har wani zallo take saboda ganin Sultan, duk yanda tai tunanin zata daure sai ganinsa ya canja dukan ƙudirin nata lokaci guda. Sai dai kamar yanda ya fiske itama haka tai ƙoƙarin fiskewar. dai dai lokacin kuma su Salma da Salim, suka iso wajen A guje tare da Rungume Sultana,"Anty Sultana oyoyo, suka faɗa tare cike da tsantsan farin ciki, "Anty Sultana I miss You! "Miss you too my baby's ta faɗa tare da shafa kumatun su, kana suka nufi wajen Abba,"Abba ina Mami da Kaka? Me yasa basu zo ba?, "Salma kaka ce ba lafiya shiyassa basu zoba" Marairaice fuska Salma ta yi tare da faɗin,"Allah ya bata lafiya Abba" "Amin Ummul Salma!" Ƙirjin Sultan ne ya yi matsifar bugawa.cikin wani irin yanayi ya lumshe idanusa kana ya buɗe akan fusakar Salma yana mai jin tsakanin Sonta a ransa. "Ya Haydar, Ya Khalil Ya Arif ya Hanya?" "Lafiya lau little Sis, Sunan da Sultan ke kiran wani lokacin.. Daddy ko kallon yayan nasa yake cike da so da kyauna... Sultan ne a gaba lokacin da zasu shiga gidan, cewar Daddy ya yi musu jagora shine mai gida suko baƙi ne Sultana ita ce ƙarshe tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki domin samun sassauci daga daga bugun zuciyar da takeji.. Falon tsaf yake ko ina a gyare, ga ƙamshi mai daɗi yana tashi da sanyin ac. cikin tsananin farin ciki Mommy ta musu sannu da zuwa, "Oyoyo Anty Sultana. Karan farko Sultana ta saki wani lallausan murmushi da har ya bayyana fararen haƙoranta waje, ta taho da wani irin ɗoki ta rungume Mommy, a hankali Sultana ta janye jikin, ,"Anty Yara ya jikin Mama!" "Alhamdulillahi Mommy taji sauƙi sosai, Gabaki ɗan su suka Rungume Mommy, "Arif Autan Abba ina Mami," Arif ya yi Murmushi kana yace ,"Lafiya lau take Mommy, Mommy ta maida kallon ta ga Ihsan kana tace,"Ihsan kai musu kayan su ɗaƙi," Mommy Nidai a ɗakin ki zan zauna Nana ta faɗa cike da shagoɓa,"TOH shike nan..," Mommy Nima a ɗakinki zan zauna, taso ki koma ɗakin Ihsan, Kafinma Mommy ta rufe baki cikin sauri tace, “A'a zan zauna anan tare da ke Mommy. da ga Mommy har Daddy kallonta sukai, amma saita ɗauke kanta tana ɓata fuska danma kar Mommy tace dole sai taje. Abba Shima har zai sake magana sai kuma ya fasa. Murmusawa Mommy tayi kawai tana ɗauke kanta batare da ta sake cema Sultana komai. Sultan Kafeta yayida idanu kamar mai nazarinta, sai kuma ya ɗauke kawai yana ƙaɗa kansa.. Har ɗaki Mommy ta wuce da Sultana. Kana ta dawo Palo, Daddy ya kalleta cike da zolaya yace ," Kinga ya yanki kin manta da ni ko?" Kai ta sunkuyar cike da kunya Sultan dake zaune a Palon, tuni su Meena sun wuce ɗaki tare da Ihsan.. "Ya hanya?" Mommy ta faɗa cikin girmamawa. "Alhamdulillahi" "Bari muyi sallah ko, "Toh sannan suka fice atare kai tsaye masallacin suka nufa cike da nutsuwa da kuma kamala suka gabatar da Sallah da karatun Alkur'an.. Bayan sallah la'asar suka wuce Kicin don haka kayan buɗe baki.Cikin ƙanƙanin lokaci dai suka haɗa duk aiyukan da zasu iya ajiyesu ba tare da sun samu matsalaba. Cikin ikon Allah shida da Rebi suka gama kan aikinsu. Sultana , ta jerasu a Foodflaks, Nan duk suka wuce ɗaki. Wanka sukayi, kana sukayi al'wala sannan suka fito falo. A nan suka samu su Daddy,Koda aka kira sallah ruwa da dabino kawai suka ɗanci, sannan suka gabatar da sallah magriba ,tare suka shigo gida, Ihsan ta kalli Sultan da gaba ɗaya hankalinsa akan Sultana yake. Haushine ya sake turniƙeta, murya a cinkushe tace, “Ya Sultan Barka da shan ruwa Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. "Lafiya" Nan suka shiga gaida iyayen nasu. Dai dai lokacin kuma Massage ya shigo a wayar Sultana, a hankali ta ɗaga wayar ta karanta massage ɗin, *Barka da shan ruwa Sweetheart, Allah ya ƙarɓi ibadar mu. daga NAS* taɓe baki tayi a hankali tace ɗan wahala kayi ka kagama, Cikin sanyi Murya Meena ta ce ,"Nas ne halam? Kai ta ɗaga mata.... A haka dai suka kammala buɗa bakin, yayinda kowa yaci komai. Duk da akwai gajiya tattare dasu haka suka wuce massallaci sukai isha'i da asham. Kafin su dawo kowa ya nema makwanci... Washe garima haka suke tafiyar da rayuwarsu. Cikin tsari da kuma samun damar hutu da ibada dan ribatar watan Ramadan ɗin. A hankali aka fara nisawa cikin watan Ramadan, kwanaki suna suka ci gaba da shuɗewa da kaɗan-kaɗan. Yau wunin azumi na 20 kenan. Da safe duk su Daddy sun wuce masallaci wajen tabsir, Sultan Ya dawo daga sallar Azahar ya shiga gida sai ya ji ƙanshin abinci. Abinci a watan Ramadan? Ya juya inda ya ke jin ƙaran sokali . Ta barraje a ƙasa tana cin jollof ɗin taliya da daffen kwai. Ɗago ido ta yi ta kalleshi hannunta ɗauke da sokali totse da abinci. Zuwa yai ya zauna bai ƙara cewa komai ba. Lokaci zuwa lokaci yana ɗaga ido ya kalleta. Shi mamakin yadda ta ke cin uban abincin nan da gani Zaiyi taji sosai ke. Ko za a matse shi ba zai iya cinye abincin nan. dai dai lokacin Kuma Meena ta shigo Palon riƙe da wayar Sultana,"Anty Sultana Jidda ta kira Video call," Ya Sultan Sannu da zuwa , " Lafiya lau ya bata amsa fuska a sake, a hankali mike tare da barin Palon, "Anty Sultana kiran zai katse fa, "idon na kammala zan kirata, haka ko akayi bayan ta kammala ta kirata bayan sun gaisa daga can ɓangaren Jidda tace,"Daughter wlh Asbitin nan ba daɗi Dr Sultan baya nan ke ma baki nan duk dai Dr Aryan na iya ƙoƙarinsa da Dr Nasir! Gaban Sultan ne ya yi mugun tsinkewa," Nasir kuma? "Daughter Lafiya kin san shi Hlm?" A'a ta faɗa da ɗan sauri. "Sabon Dr ne bayan ta fiyar ku da kwana biyu ya fara aiki a Asbitin nan.." Toh" daga suka ci gaba da hira, sun jima suna waya. Bayan sunyi sallama Sultana ta kira Mami Video call bayan sun gaida Mami ta miƙa ma Kaka wayar suka ci gaba da hiya cike da kewar Juna.... Ana idar da salla suka fito, kitchen suka nufa ita da Meena da Sultana Suka fara aikin buɗa baki sunayi suna kimtsa komai. Kafin shida ta cikama sun gama komai... Haka dai komai yaketa wakana cikin aminci da tsari. A wurin al'ummar Annabi kowa ya nitsu ya maida hankali kan ibada domin neman rabauta. Ƙarfe takwas dai-dai suka shiga kitchen dan yin aikin sahur. A kwana a tashi Babu wahala wajen Allah , dan gashi yau saura kwana biyu kacal sallah, kowanne yanki na musulmi suna cikin shirye-shiryen ta da yin bankwana da azumin watan ramadhan Yayinda su Sultana keta shirin dawowa suma a ranar sallah. Bayan Isha'i tana zauna a palon tana waya da Jidda Konciya tayi bisa 3 str tana kallo wayarta na hannunta. Tana ba Jidda Labarin NAS dake Turo mata massage duk safiyar Allah.. A haka bacci yayi awon gaba da ita. Can Cikin bacci take jin alamun kamar mutun na tsaye a kanta, cikin magagin baccin ta buɗe idonta. Gabann Tv ta ganshi ya kashe TV kana ya juyo ya kalleta a fizge yace. "Ba Aiki sai kallo da bacci". Jin haka yasa ta gyara kwanciyar tare da murguɗa baki. Shi kuma tuni ya wuce ɗikinsa... Can kuma ta miƙa ta nufi ɗaki ta ɗan kwanta kafin lokaci sallah tuhajju tayi.... Washegari Mommy ta tamusu ƙunshi jan lalle irin na larabawa.. Washegari haka suka niyi suna aiki tuƙuru .. Washe gari aka tashi da azumi na talatin. Allah cikin ikonshi aka kaishi lafiya.Watan Shawwal ya baiyana Ramadan ya tafi kuma sai mai nisan kwana, Ana idar da sallan isha'i da yawa suka fara ɗawafi.A nitse bisa tsari suke ɗawafin sunje ƙafa biyu ana uku sun isa dai-dai. Maƙama Ibrahim. Sultan ya juyo kanshi ya kalli gefen damanshi da sauri cikin tarin mamaki al'ajabin Fuskar mutumin da ya ga ya wulgawa a idonshisa. Zuciyarsa tayi mugun buguwa da ƙarfin gaske. A hankali ya dai dai ta natsuwarsa kana ya ci gaba da ɗawafi Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu. Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi. Zuciyarshi nike da mamaki.Haka yaci gaba da ɗawafin.Saida sukayi. Kana suka wuce gida gabaki ɗayan su. Washe gari da safiya.Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla.Manya da yara duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya. A gaggauce sukayi wonka kowa yayi shirin idi.ko waccesu sanye cikin Aba mai matsifar kyau, Ƙarfe tara saura kwata duk suka fito falo. Tuni lokacin kuma liman har ya fara huɗuba.Suna fita su mata sukayi gefen mata su kuwa maza sukayi gefen maza. Lokaci da aka kammala salla sosai Sultan ke baza ido ko zai sake ganin wancan mutumin amman ina.. (Shiko wannan waye?) Kai tsaye suka wuce gida, suka ci Abinci cikin kwanciyar hankali, "Kuyi sauri mu kammala ƙarfe 1:30 jirginmu zai ɗaga, cewar Daddy. Dai dai lokacin muka massage ya shigo a wayar Sultana.. *Aminci Allah ya tabbata a gareki yake farin ciki raina! Ina fatan kinyi Salla lafiya, Allah ya mai mai ta Muna, Allah kuma ya ƙarɓi ibadar mu. daga NAS!!.* A karon farko Sultana ta saki Murmushi lokacin da ta kammala karanta saƙon, a karo na farko ta maida mai da Amsa. *Amin Na gode!* (Haba Sultana daga ganin Sarkin fawa sai miya tai daɗi😉,) Nan suka soma shiri.karfe ɗaya dai dai suka wuce Airport..Bayan duk matafiya sun shiga, jirgin ƙasar Nigeria wanda zai sauƙa a kano.A hankali ya zauna. Ya Meena na gefenshi. Riƙe da hannunsa Kasan cewar yana kusa da window ne, ya ɗan juya yana kallon mutanen daketa hada-hadar nufar inda jiragan ƙasar su jihohinsu suke. Can cikin wasu ayarin mutane maza da mata ya hango wannan fuskar da ya gani. Sun nufi can ciki suna tafiya yankin da jiragen ƙasarsu. A hankali yake jin zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Hannu Meena ya damƙe sosai. Kana ya sauƙe Nannauyan Ajiyar kana, Cikin tarin mamaki ya bishi da kallo tabbas badon jirginsu ya fara ƙugin tashiba da ya fita yaje ya tabbatar da fuskar dattijon da yake hangowa. A haka dai suka ɓacewa ganinshi. Kana jirginsu ya ɗaga zuwa Kano..... ______________ *Najeriya* Ƙarfe 7:20 jirginsu ya sauƙa, a hankali suka fara fotowa kai tsaye wajen motocin suka nufa, A tsanake suka fice daga Airport. Mommy da taga a canza hanya zuwa gida ta Kalli Daddy,"Lafiya?" Kai kwai ya ɗaya mata. Abban tuni sun kama hanya gida.. Anguwace da bata da maraba da a cikin turai saboda rashin hayaniya da haɗuwarta. Ko ina ƙwanyar yake da wutar nepa tamkar rana. Dai dai lokacin kuma suka iso wani tantsamem gida mai matsifar kyau.Dogon building ne mai matukar kyau da tsaruwa...sannan yanada girman sosai kusan part biyu.. Mommy ta saki baki tana Kallo cike da mamaki, "Abban Sultan ina ne nan?" tayi maganar cike da damuwa, "Sabon gidan mu ne!" da sauri Mommy ta ware manyan idanunta ta kalli Daddy,"Sabon gida kuma?" Kai ya gyada mata, "Abban Sultan Amman Ai.... Ya isa. Mommy ta sauke sassanyan Nunfashi tare da faɗin,"shike nan, Tsarin ginin gidan tsarine, wanda ko a ƙasashen turawa na musamman ne, Ƙaton gidane sosai an ƙawatashi da shuke shuken ƴan ƴan itatuwa kala kala ga ƙasansu kuma, wasu tsirran fulawowi ne masu masifar kyau da sanyi masu collor's Pink da yellow. da wajen shan iska na musamman mai masifar kyau da ɗaukar hankali.. Salma da Salim ko sai tsalle tsalle suke a farfajiyar gidan, A ɓangaren Sultan ma sosai gidan ya masa kyau, kai tsaye suka wuce gidan cikin gida Cikin Part ɗin nasa kuwa, wani tamfatsetsen parlour ne mai kyan tsarin ƙasaitattun kujeru da labulaye da kayan wuta, komai na ciki farine. Numfashi Mommy ta sauƙe lokacin da ta gama ƙarewa gidan da lukkunan gidan kallo, (Hmm sabuwar duniya sabuwar rayuwa🥂🙌💃🥰 ) Ɗaki Ukku ne a cikin palon, ɗakin Salma da komai naci pink color ne ya yi Masifar kyau, sai ɗakin dake liƙe dashi ɗakin Salim komi blue da kayan wasan shi, daga gefe kuma ɗakin Ihsan ne,suka ƙarasa madaidaicin falon daya gama haɗuwa, yanata wani tattausan ƙamshi mai daɗin shaƙa da kwantar da zuciya. zuwa wata ƙofa dake a cikin falon. ɗaki ne mai matsifar da tsaruwa komai na cikin ɗafin fari ne ," Masha Allah shine Abinda Mommy ta furta. Sultan tsab ya ƙare wa ɗakin Kallo dai lokacin kuma idanunsa suka sauka kan wani makeken hotonsa dake manne yana sanye da Fararen kaya na likitoci da wata na'ura sarkafe a kafaɗarsa daga kasan hoton An rubuta *DR SULTAN*. a hankali suka fice daga ɗakin kai tsaye suka haura sama. Nan ma Wani haɗaɗɗen Palo ne da ɗaki Ukku. Ko'ina ya yi Masifar kyau... Sultan ya kalli Daddy cikin sanyi Murya yace ,"Daddy Allah ya ƙara Azziki mai Albarka, Allah ya ƙarama tsawon rai mai Albarka!" "Amin my Boy!" Sultan ya gargaɗi ƙannen nasa zuwa palon ƙasa.. aiki Mommy kaman jira take su bar wajen, ta wa Daddy kyakkyawar ruguma tare da manta mishi kiss. A hankali ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe a tsakiyar idanunta. Cikin tsantsan farin ciki Mommy tace ,"Na rasa dame zan saka ma Abban Sultan kamin komi A rayuwa, ka ilimarta dani! Ka ciyar dani! Ka suturtani ka min muhalli! Kamin gata! Abban Sultan, ina rokon Allah ya saka ma da gidan Aljana, Allah ya jikan iyayenmu Allah ya ƙarama Azziki mai Albarka ina roƙan Allah ya shayar da kai ruwan Aljana!" ta karasa maganar cikin raunin Murya, a karon farko a rayuwarta tun zaman da shi ya Amsa da "Amin!" A hankali ta sake lafewa a jikinsa tana shaƙar dadɗan khamshi mai daɗi. Ɗaukar yayi Cak zuwa ɗakinsa cike da so da kyau da kewar Juna suka faɗa duniyar ma'aurata.... ____________ Wannan littafi DR SULTAN na kuɗine, yana ɗaya daga TITAN'S OF TALENT WRITER'S, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana Zaku biya kudinku acikin wannan asusun na banki👇👇 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗..... ★★★....... Tunda suka fito daga Airport ɗin kai tsaye suka wuce gida, da mamaki ya Abba ya riƙa kallon gidan sa daka sauyawa fenti mai kyau, koda suka shiga cikin cikin gidan ko'ina tsab Motorsu na gama tsayawa Sultana bata tsaya sauraren masu tarar tasu ba ta shige sashensu da gudu tana ƙwalama Kaka kira. Da sauri Kaka dake ƙoƙarin fitowa taja baya dan kaɗan ya rage suci karo da Sultana Faɗawa jikinta tai ta ƙanƙameta tana faɗin, “Kaka, nayi kewarki ”.Kaka dake murmushi tasa hannu biyu ta rungumeta itama, sai da ta tabbatar sunji ɗumin juna kowa na sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗagota da ga jikin nata. “Sultana! Yaushe ne zakiyi hankali kisan kin girma ne?,"Kaka daga dawota har zamu fara faɗa ko Cike da shagwaɓa ta karasa maganar tare.da saka kanta a kafaɗar Kaka tana faɗin, “Kaka ni indai ina gabanki Ni ƙaramar yarince, nayi kewarki ne my Happyness. Ina Mami take?”. "Maraba da yan Saudiya, Mommy ta faɗa cike da farin ciki da gudu Meena, Nana,Khalil Arif Haydar suka rungumeta," Mami munyi Missing ɗinki," Nima nayi missing ɗinku. Bayan sun janye jijin daga na Mami suka nufi wajen Kaka tare da rungumeta gabaki ɗayan su, "Mami ta kalli Abba cikin Sanyi Murya tace,"An dawo lafiya? Allah ya karɓi ibada" "Amin ya rabbi,mun same ku Lafiya. "Alhamdulillahi" Kana suka wuce cikin palon tsawa cak da Daddy ya yi hin an sauya komi na palon i zuwa sabo ya kalli Mami,"Lafiya? " Mami ta yi Murmushi kana ta ce ," Aikin Abban Sultan ne bayan ta fiyar ku da kwana ɗaya ya Turo masu aiki komi na gidan nan an sauya shi izu sabo hadda ɗayan ɓangaren na Uncle Ibrahim..sai yanzu maganar Daddy ta faɗo mai ɗaya taɓa tambatayar yana da ra'ayin sabo gida nan gaba, ya ce mishi a'a ya fito son gidan nan tunda ba shike dai keda shiba... Waton da wannan damar ya yi amfani ko, ya faɗa a hankali. Nan suka shiga jagayen gida. Ko'ina Ma sha Allah gwanin burgewa. tarba ta Musamman suka samu daga wajen Mami, Abinci sunci Saida suka ture, suna zaune a palon suna hira, Mommy ta kira Mommy tayi mata sannu da zuwa, bayan sun gaida Mommy ta sanar da ita sabon gidan da suka koma, cikin tsananin Murna ta taya ƴar uwar Tata murna.jin jima suna waya, bayan sun gama wayar ta kira Daddy shima ta taya shi murna, Nan Mami ta sanar da Abba da kaka Abinda ke faruwa, suma sosai sukayi Murna, duk da Abba ya sanda komi Amman bai haya ya nuna tsantsan farin cikisa ba...sun jima a palon suna hira yaushe gamo. Bayan sallah la'asar suka wuce gidan Mommy banda Sultana da Kaka.... Sai bayan Isha'i suka dawo a gajiye ko wannensu ya wuce ɗakin sa... *SULTAN* Bayan ta fiyar su Mami, ya dawo ɗakinsa ya yi Wonka ya shirya, a hankali ya zauna gefen gado tare da ɗaukar wayarsa ya kira babban Aminsa, Aziz kusan sati ɗaya kenan yana kiran sa wayar sa a kashe.yanzu ma a kashe take, cike da takaici ya wulgar da wayar gefe gado kana ya kwanta tare da Lumshe idanunsa yana mai jin zuciyarsa na mai nauhi da haka bacci ya yi a won gaba shi...Yauma kamar duk shekara da yake irin wannan Mummunan mafarkin da yake duk bayan shekara hakan ne ya sake faruwa dashi, sai dai na wannan karon ya sha babban da saura.. wannan Dattijo da yaga A Umura shine ya gani a mafarkinsa tare da wata kyakkyawar mata yana zauna a ge fensu da wata matsifar budurwa fusakar da lullɓe da farin mayafi. A hankali yarinƴar ta fara janye matafiya, dai dai kuma wata mata sanye da baƙaƙen kaya ta shigo ɗakin da matsifar guda Hannuta riƙe da ƙaruwar yuƙa Idanuwanta sunyi Masifar ja, gadan gadan ta tunkari Sultan tana zazzare idanunta masu matsifar ban tsoro. da ƙarfi ta ɗaga yuƙar zata soka mishi dai dai lokacin ya farka daga baccin da yake cikin wani irin ya nayi, wata irin Zufa ce me bala'in ɗumi ke sauƙo daga saman kanshi, cike da Razata da kaɗuwa, dafe kai ya yi dake junjuyawa......✍️✍️ (To wata sabuwa inji yan caca, ni dai nayi nan🏃🤣) *Assalamu alaikum! Ina matuƙar godiya da Addu'oi ku, da masu kirana, damu min text nagode sosai Allah ya bar zumunci!! Don Allah kuma a ci gaba da haƙirin reshin samun Update a Kai a kai. Nagode sosai* _More comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce* 💋 *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 25-26* _________cikin wani irin yanayi mai tsanani ya miƙe zaune tare da dafe kanshi, yayi bala'in fita hayyacinsa saboda wahala ya kasa bari ya huta. Sai da yayi wujiga-wujiga da shi, daga ƙarshema ya yanke jiki ya faɗi. A take wasu hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa a fuska, ya shiga taunar lip ɗinsa ƙirjinsa na sake zafafa, dai dai kuma Daddy ya shigo Dakin da niyar ya faɗa mishi ya kamata ya leƙa Asibiti gobe. da ƙarfi yaja ya tsaya ganin Sultan kwance a ƙasa ga baki ɗaya baya cikin Haiyacinsa ba abinda ya faɗo masa a rai sai wannan mafarkin da Sultan yake duk shekara, kusan sau Ukku abun na faruwa a gabansa lokacin idon ya kai masa ziyara a India. Duk da Daddy yasan da yanayin na Sultan sai hankalinsa ya sake ƙololuwar tashi fiye da da can. Wannan al'amari na Sultan na bashi tsoro.. Allah shine yasan gaibu game da matsalar Sultan. To a yanzu gashi al'amarin nasa ya sake motsawa, duk da yakan jima baiyiba ma. Daddy ya nufi wajensa da sauri ya ɗora kansa Sultan samar cinƴarsa tare da shafa kanshi Cikin murya mai cike da lallashi ya kira sunansa ,"Sultan!".Duk da yana jinsa bai motsa ba, da ƙyar ya miƙa Zaune Daddy da kansa ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi sosai. Kafin ta dawo inda Sultan yake ke rungume da shi yanata faman lallashinsa da masa magana mai daɗin gaske, wadda ko ba'a faɗaba da alama tana tasiri ga Sultan ɗin. ★★★ Mommy ko jin shuru Daddy ya jima yasa ta biyo bayansa, a hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga,aiko da sauri na nufi wajensu ganin Halinda Sultan ɗin yake ciki.Zama tai kusa dasu itama, ta miƙa hannu ta riƙo na Sultan ɗin tana murmushin jin daɗin ganin ya nutsu, matsawa tai jikinsa sosai zata rungumesa kamar yanda Daddy yayi masa, sai ya ƙwace hannunsa ya miƙe zumbur Cike da Kasala. ya nufi toilet. Duk binsa da kallo sukai ita da Daddy, "Abban Sultan mike da munsa?" "Ina tunanin wannan mafarki ya sake yi, Juyowa tai idanunta cike da ƙwalla, muryarta na rawa tace, “Habiby! Anya kuwa bazamu nema masa magani ba, Daddy dake kallonta ya ɗanyi Murmushi yana nazarin maganarta, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya amsa mata. “Shawaranki mai ƙyaune Habibaty, Na jima ina tunani akan haka na tabbata akwai wani babban Al'amari dake tattare da ɗan naki. Kafin ta samu damar bama Daddy amsa Sultan ya fito daga toilet ɗaure da towel, dan duk zatonsa sun fita. Turus yaja ya tsaya yana kallonsu ya maida ƙifar toilet ya rufe, jingina yayi a jikinta ya lumshe idanu zuciyarsa na ƙara bugawa. Daddy ya Kalli Mommy," Kinga tashi mu tafi yaron naki kunyar fitowa haka yake a gaban mu. Badan Mommy taso hakanba ta yarda suka fita. A hankali ya buɗe kumburarrun idanunsa dake cike da barcin da baisan ranar yinsaba, ya sake lumshesu yana sauraren yanda Daddy ke lallaɓa Mommy akan su fita su bashi waje ya shirya, idan yaso saisu dawo daga baya. Sultan najin sun fita shima ya fito sai da ya leƙo ya tabbatar babu kowa sannan ya fito. Bai kalli ko inda Mirror ɗinsa yake ba balle ai tunanin shafa mai ya nufi wajen kayansa kawai. Dogon wando black mai taushi da farar t-shirt data kama jikinsa ya saka. Ya taka zuwa gaban gadon yana cije lips ɗinsa, A hankali ya sauke Nannauyan Numfashi, tare da dafe ƙirjinsa da ya yi masa nauhi."Ya Allah ya faɗa da ɗan ƙarfi. Har rige-rigen shigowa ɗakin Yanda sukagansa a kan gadon ya saka hankalinsu sake tashi, suka zagayesa da tambayoyin yaya akai? Yanda jikinsa ke rawa zufa na fito masa sai duk tausayinsa ya sake kamasu, Mommy tai saurin zama ɗaya gefensa tare da kwanciya a jikinsa tana hawaye. Zama Daddy ya yi a gefe suka saka Sultan ɗin a tsakiya, Daddy ya fara tofa mishi Addu'oi a hankali ya fara sauke Ajiyar zuciya.a hankali a hankali ya fara samun natsuwa, haka suka ci gaba da zama a ɗakin har Sultan ya yi barci..... Washegari A hankali ya buɗe idonsa wanda su ka ma sa nauyi saboda gajiya, ya rufesu saboda hasken da ya karaɗe ɗakin yaiwa idonsa ƙarfi. Ɗan wasu daƙiƙai ya ɗauka kafin ya sake buɗe idon a karo na biyu. Lokaci guda kuma mafarkin da yai ya dawo ma sa. Da sauri ya tashi zaune saboda tunowa da yai da abinda ya gani a mafarkin. Agogo ya duba ya ga ƙarfe goma na safe, kenan ya jima yana barci. Idan ya tuna da kyau to ba maganin bacci ya sha ba jiya. Ya shigo ɗaki, Wonka ya yi ya sanya jallabiya ya gabatar da sallar.Assuba Fitowar da zai yi bayan ya shirya cikin ƙananun kaya baƙar shirt da guntun wando baƙi na jeans ya haɗu da Ihsan tana haurawa sama. Ya Sultan ina kwana" Ta faɗa a hankali " lafiya" ya faɗa ba tareda ya kalleta ba. Ihsan ta bishi da ido tana haɗiye wani abu mai ɗaci da ya taso ma ta tun daga wuya. Wajen Daddy ya nufa my Boy" Dad ya faɗi lokacin da Sultan ke ƙoƙarin zama a ɗaya kujeran. Zuwa yai ya tsugunna a gaban Daddy Daddy ya shafa goshinsa ya ce "Allah ya ma ka albarka" Sultan ya amsa da Amin "Ya jikin na ka?" "I'm fine Daddy" "Allah ya ƙara sauƙi" "Amin Daddy". "Mommy Ina kwana" "Lafiya lau ya ƙarfin jik?" "Alhamdulillahi Mommy!". Tare sukayi Breakfast cikin kwanciyar hankali, ranar dai a gida ya yini har dare... Washegari cikin ikon Allah ya wayi gari da walwala kaman ba shine a ka sha fama da shi da Daddare ba. Wuraren ƙarfe huɗu ya leƙe Asbiti tarba ta musamman ya samu daga wajen yaran sa, A ɓangaren Aiki kuma Alhamdulillah komi na tafiya yadda ya dace sai bayan maggariba ya dawo gida.. Bayan Isha'i Sultana na zaune a ɗaki suna chatting da Jidda, kira ya shigo a wayarta. Kiran na gab da tsinkewa ta ɗaga ba tare da tayi magana ba, daga can ɓangaren ," Assalamu Alaikum ya yi maganar cikin wata irin zazzaƙar Muryar mai Amo,da sauri Sultana ta mike zaune tare da faɗin ,"Waye?" My Sweetheart kenan, abinda ka ke so ai duk wuya duk rintsi sai ka samu" "Chan ta matse ma ka" ta faɗi tareda kashe wayar. Ya sake kira ba ta ɗauka, "nace waye wai?" "NAS NE!!" "Sultana haƙiƙa Ƙaunar acikin Zuciyarta tamkar ta bo ne da yuƙa mai ƙarfi ta yishi gogewar warsa Abu ne mai matukar wahala ina ƙaunar ki! Bani da burin daƙushe Miki farin cikin ki koda na second ɗaya ni ki ɗauke cewa yanzu ne kika samu mahaɗin Rayuwarki bani da wani a buri a Rayuwa da wuce na hanki cikin farin ciki!!!" Jikin Sultana ya yi sanyi, sosai kalamansa suka ratsa Zuciyarta, A hankali a hankali NAS ya cigaba da kiran Sultana, tun tana ƙin ɗauka har ta koma idan ta ɗauka za ta surfa ma sa masifa, shi kam da gaske ya ke dan haka bai damuba duk abinda za ta ce ma sa shanyewa ya ke. Cinkin ƙanƙanen lokaci sai da ya san yadda ya ja hankalin Sultana har tana ɗan kulashi ta dena ma sa faɗa idan ya kira. A dayan ɓangaren kullum sai ya Turo mata massage na kalaman soyayya masu ratsa zuciya katin waya ma sai ta ture duk bayan kwana ukku sai ya Turo mata katin 5k... ( Haba Sultana😡😡) ★★★★ Isowar sa kenan cikin gidan a gajiye. Kai tsaye ɗakin sa. Jim ƙaɗan Ihsan ta shigo ɗakinsa Tana jin ƙaran ruwa a banɗaki lokacin da ta ajiye ma sa tea ɗin a ɗakin, kamar za ta fita sai kuma ta samu kujera ta zauna tana jiran sa. Kusan minti biyar sai ga shi ya fito ɗaure da towel. Ya na faman goge gashin sa da ɗan ƙaramin towel ya ganta ta ƙura ma sa ido. "What the fuck! Mi ki ke yi a ɗaki na" Ya daka ma ta tsawa Daburcewa ta yi ta fara kame-kame. "Get out" ya daka ma ta tsawa ba shiri ta fita da gudu dan ta san halin sa sarai. Sai da ya shirya cikin farar riga da wando baƙi three quater sannan ya buɗe laptop ɗin sa ya na duba wani aiki da Dr Nasir ya turo ma sa. Yana dubawa yana kuɓartea ɗin sa a hankali. Ba laifi Nasir yai ƙoƙari, da alama ya san aikin sa dan tunda ya fara ma sa aiki bai samu kuskure ɗaya cikin ayyukan da ya ke sa shi ba, sai dai da saura tunda dududu sayi Ukku kenan da Nasir ɗin ya fara ma sa aiki kenan. ★★★★ A hankali soyayyar NAS da Sultana ta fara nisa, domin har Meena da Jidda sunsan komi... Washe gari bayan ta dawo da wajen Aiki, tana ƙoƙarin shiga cikin gida mai gadi ya da katarda ita, "Madam gashi yamimama bag🛍 mai k'yau, ta amsa tana tafad'in namiye Baba?. "Wannan yaron ne ya sake da wowa, aiko da sauri Sultana ta nufi wajen tuni ya Ron ya ɓace, kai tsaye ta wuce ɗaki 🎁bud'ewa sukayi, flower🌹ce tanata k'amshi, sai zobe Azurfa mai masifar kyau da tsada Sultana tasauke ajiyar zuciya tareda tunanin sak'o makamancin wannan da aka taɓa bata wata ukku dasuka wuce , da ƴar ƙaramar takarda, *_kenafi ƙauna cikin matan duniya bani da buri sai muyo Auren dake!* Wannan shine kawai arubuce, Sultana ta maimaita baitikan yafi sau goma, to wanenen wannan?,Kodai ya NAS ne? Kai anya kuwa?. Saikuma turare mai masifar k'amshi, Sultana ta shinshina turaren talumshr idonta. Jitake tabbas tataɓajin wannan k'amshin, amma a ina?. Shine abin tambayar. Da sauri tatashi zuwa gurin ajiye muhimman abubuwanta ta aje su anan.. Koda Meena ta shigo ta bata labarin sosai Meena tayi mamaki,"Anty Sultana nifa ina zargin NAS ne ke turo Miki saƙon nan gaskiya, "Nima Meena nafi zargin Shine!" "Aiko Anty Sultana kiyi duk yadda Zakiyi ki gano ko waye. Suna cikin managar kiran Nas ya shigo," Yauwa Anty Sultana ki nuna mai sauƙonshi ya iso kin gode, Meena ta faɗa a hankali," mai Sultana ta gyaɗa mata, "Assalamu alaikum ta faɗa cikin sanyi Murya, " daga can ɓangaren Nas ya sauke sassanyan Nunfashi kana ya ce," Ina fatan saƙo Na ya samu ƙaɓuwa a wajenki?" da sauri Sultana ta waro manyan idanunta kaman tana a gabansa tace ," daman kaine?" Nas ya saki Murmushi mai sauti, Meena ga baki daya hankalin ta kan Sultana dake faman sakin Murmushi kaman gonar Auduga. "Allah ka shammateni Nas!" Ta faɗa cike da shagoɓa, sun jima suna waya cike da zallar Soyayya.... ★★★ "Anty Sultana Kinga Abinda nake faɗa Miki ko, "najina ina zargin shine" Cike zumuɗi Sultana ta kira Jidda ta sanar da ita komi. Sosai Jidda ta taya murya, tun daga wannan lokaci so da shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙara shiga tsakanin Nas da Sultana.... (Hmmm 🥱🥱) *Sultan* Ba ƙaramin kyau yai ba cikin shirin sa na Shuit . Ɗauke da briefcase ɗin sa fito.daga ɗakin sa cikin takunsa na girma da ƙasaita. Ƙai tsaye wajen dining ya je "Morning Ya Sultan" ya amsa tana ma sa murmushi Shima Salim da ke gefe ya ce " Good morning Ya Sultan" "Morning" ya faɗa a taƙaice. Tea ɗin da ke gaban Salma ya ɗan ƙurɓa ya ce " sai na dawo ko" ina gai da Mommy da Daddy idon sun fito.. Yana fita ya shiga matar sa kai tsaye ya wuce Office.. A hankali ta nufi kan step ɗin. Dai-dai lokacin kuma Sultan ya fito daga wani ɗaki ya nufi ƙasa, a hankali yake take steps din yayinda hankalinsa baki ɗaya yana kan file dayake kan hannunsa na dama yana duddubuwa da hannun hagunsa, bisa dukkan alamu. Abu mai mahimmanci ne yakeye karantawa. A dai-dai lokacin kuma Sultana ta iso bakin steps ɗin, cikin sauri take tafiya, da alamun sauri Da sauri take tattaka steps ɗin tanayi sama. Steps biyu ta taka ana uku, taji juyo da kanta da sauri dan jiyo muryar Jidda “Daugter sai yanzu?”. Ba tare da ta tsaya ba, kana bata kuma juyo kanta ba taci gaba da tafiya a haka, hannunta na kan da ƙarfe dake gefen steps ɗin."Dr Sultan na memanki, Cikin sauri ta kuma juyo kanta da dama bata gama juyashi ba cike da tsiwa tace. "Mezan masa?" “ oh ho miki Tun ɗazu.yake nemanki” Cikin yanayin tsoro ta ɗan zaro manyan udanunta tare da cewa. "Ba inda zanje "Kaman ya ba inda zaki je?" Haka taci gaba da haura saman steps ɗin ba tare da tana kallon gabanta ba. Wanda kuma dai-dai lokacin Sultan ma ya taka step na ƙarshen bazato ba tsammani taji tayi karo da mutu. Shi ma Sultan ba zato ba tsammani yaji kanta ya bugi ƙirjinsa yayinda hannunta ya bugi file ɗin dake hannunsa ya subce ya tafi ƙasa ta kardun suka watse gabi ɗaya Tagal-tagal Sultana tayi baya zata fadi yayin da shikuma Sultan da ƙyar ya tsaida kansa daga faduwar da zai yi. lokaci guda ta rumtse idanunta tare da sakin kara. Sultan cikin hanzari yakai hannu ya riƙota sai alokacin idanunsa suka sauƙa akan fuskarta ita. Sultana sassayan numfashi ta ssuƙe jin an riƙeta bata faɗiba yasa ta ɗago kan Idanunta ne suka sauƙa akan fuskar Sultan, lokaci ɗaya zuciyoyin suka buga da masifar ƙarfi, cikin wani irin yanayi Sultana ta yi ƙoƙarin janye hannuntata rumtse idonta wanda duhu mai tarin yawa ya mamaye mata , kana tayi baya baya zata faɗi, ƙafarta ta sule yasa takuma sakin wani Nannauyan Ajiyar zuciyar Gaba ɗaya ta sadakar,da faɗuwa, Jidda da tuni ta fara yi musu video da Snapchat tana Murmushi. Cikin zafin nama ya janyota da ƙarfi hakan yasa ta faɗa jikinsa. jinta a jikin mutum ne yasa tayi masa wata irin rugguma mai cike da razani dan gani take kamar dai har yanzu bata tsira ba. Kanta ta cusa cikin ƙirjinsa tana mai shaƙan dadɗan ƙamshinsa turarensa mai sanyi da saka natsuwa.. Sultan cikin tsoro da wani irin yanayi abu da yaji ya soƙi tsakiyar kansa har zuwa zuciyarsa yana mai jin baƙon al'amuri. a cikin jijiyoyin jikinsa da suka sa jikinsa sakin wani, ya ware hannunsa tare da rumtse idanunsa da masifan ƙarfi....✍️ More comments and share *Sadeeya Ka'oje ce* ✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 27-28* _____Cikin sauri Sultan ya janye hannunta daga jikinsa tare da matsawa gefe da sauri. Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da watsa mata kallon da yasa hantar cikinta kaɗawa. dai dai lokacin Dr Aryan ya fito daga ɗakin da sauri ya durƙusa kasa ya tattara takardun ya maidasu cikin File kana yamiƙawa Sultan, cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai ya ce, “Biyoni!”. Kaman wata soloɓiyo ta bi bayan sa har zuwa Office ɗin sa,.Ya na so ya ma ta faɗa, ya na so ya nuna ma ta ko shi waye, amma ba zai iya ba saboda ransa da ke a ɓace. Tsawon lokacin Sultana na tsaye a Office, ƙanta ta ɗago ta kalli Sultan dake zauna a saman lallausar kujerarsa yana danna laptop, "Nifa na gaji da tsayin nan" Ƙoƙarin fice wa ta yi daga Office ɗin,"Come Back" da sauri ta juyo ta kallesa kaman bashi ya yi maganar ba, a hankali ya mike ya nufi ƙofar fita, sai muka ya juyo ya kalleta," ki biyo da file ɗin can, ya faɗa a hankali, "A kwai aikin da Zanyi" Sultana ta ka tseshi daga kallon walaƙanci da yake jifanta dashi.. Shut up" Sultan ya katse Sultana da tsawa. Hannu Sultan ya kai zai ma ta mari sai kuma ya tsaya yana huci hannun na reto a sama " I'm warning you, ki kama matsayin ki ko kuma na nuna mi ki" Haɗiye miyaun da ya tokare ma ta maƙoshi ta yi lokacin da Sultan shi ma ya juya ya bar wajen. Ta gama sadakarwa Sultan marin ta zai yi. Har ta hango yadda fiskarta zai koma idan da marin ya sauka a fiskarta. "Aikin banza" ta faɗa sannan ta bar wajen. Da sauri Jidda ta bi bayanta tana kiran sunan ta. Ta shiga wani ɗaki amma kafin ƙofar ta rufe Jidda yai saurin sa hannu ya tare sannan ya shiga,"Daughter Lafiya?" "Nida ɗan renin hankalin can ma ya Kaini Office ɗin sa ya tsayar dani kaman wata kunki." Oh ni jidda Daughter wai mike tsakin ki da Dr Sultan?" "Mtsss Sultana taja tsaki "Daughter pls ki daina fushin nan mana, Allah ɗazu ba ƙaramin dacewa da juna kikayi ba. ta ƙara sa maganar tare da nunama Sultana video da tayi musu ɗazu, da sauri Sultana ta fisge wayar da niyar goge video Jidda yayi sauri saka wayar a key, "Allah Bazaki goge ba Daughter, wlh baki ga yadda mukayi matuƙar dacewa ba ina a ce ki Auresa!" Juyowa da saurin Sultana ta yi tana kallon Jidda ,"Allah ya kiyaye, Ni matar Nas ce da yarda Allah! "Nawa ba irin na kowa ba ne Batun nayi bayani ko jawabi akan sanda zuciyata take masa hakan ba Abu ne mai sauƙi ba na sai san ina son sa domin ya kasance na mummunan a rayuwata hakan yasa na kulle ƙofa daga kansa ba wani a gabansa kuma ba wani a bayansa! Jidda da ta tsura mata ido tana kallon ta kaman ta samu tv. Sultan Idanu ya zuba musu na wasu sakanni fuska a matuƙar ɗaure. Sai kuma ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. "Lallai Daughter kin kamu da Soyayyar Nas, to wai Daughter kintaɓa haɗuwa dashi, kai Sultana ta gyaɗa mata alamar A'a, Jidda ta sauƙe Nannauyan Ajiyar zuciya kana yace ,"Daughter Anya bakiyi kuskure ba? Yanzu duniya ta sauya Daughter Mutane ba Amana!" "Nas baya ɗaya daga cikin Mutanen da kike tunani" "Daughter ya kamata ki....." "Mommy ya isa pls! Bana son mu samu matsala" "Shiken Daughter Allah ya tabbatar muku da Alheri" Fuska a sake tace "Amin Mommy na koke fa" Jidda ta sauke Ajiyar zuciya. haka suka ci gaba da aiki a ranar har zuwa lokacin tashi kowa ya nufi gida.... Washe gari ta kasance Weekend ne Sultana basu tashiba sai around 9, wanka sukayi sannan mami takawo musu breakfast sukayi, Mami takallesu cikin soda k'aunar y'ay'an nata, tace, "kutashi Ku shirya kuje shoprite, To suka fad'a suna mik'ewa, Sultana tasaka wando da Riga sannan ta ɗaura After dress sunmata k'yau sosai, Meena na rik'eda ATM d'in Abba tare da Nana suka fice daga gidan. Tunda suka Isa shoprite d'in k'irjin Sultana ke bugu da sauri-sauri, addu'a tafara karantowa ahankali, basuwani ɓata lokaciba suka fara duba abinda suke buk'ata, Sultana ce rik'eda keken🛒tana zaɓa tana sakawa, Bugun zuciyarta ne yatsananta, waige-waige tafara, Dan lamarin yafara tsoratata, babu wani alamar abinda yashafi rayuwarta awajen, Dan haka ta dake tacigaba da duba abinda take buk'ata. Sanye yake cikin ƙananan kaya sun masa kyau sosai. Taku yakeyi cikin nuna shinfa jarumine mai wadataccen jini, kasaitarsa da kwarjini sun taka rawar gani wajen bayyana kwarjininsa, dasuka k'ara haska farar batar sa mai matuk'ar taushi da d'aukar idanu, k'asumba tad'an taru masa afuska, hakama kansa akwai Y'ar kwantacciyar suma, hakan yanada nasaba darashin lokacin kai, Dan aiki ya cakud'e masa sosai a ɗan kwanannan. Yana tafiyane kunnensa manne da waya, magana yakeyi ahankali kuma cikin nutsuwa, Wanda baisaniba saiya d'auka da matarsa ko budurwarsa yakeyin wayar, fuskarsa babu walwala, yanayi yana duba abinda yad'auka, saiya d'an karanta kafin yajuyo yasaka a keke. Wannan salo nasa yayi masifar tafiya da y'an Matan wajen, Dukda zuciyarta Na masifar harbawa hakan baisa tadamu da kallon waɗanda ke bayanta da gabantaba, anutse takai hannu zata d'auki wani turare , shima yakai hannu. Akan nata hannun yaɗora nashi, da sauri kowa yajanye danjin wani masifaffen shock daya jasu atare, lokaci ɗaya suka zubama juna idanu, burkitattun idanunsa masu girma da haske suka shige cikin Na Sultana manya masu yalwataccen gazar- gazard'in gashi. Da sauri Sultana ta janye idonta cikin nasa. Ahankali ya sauke ajiyar zuciya tareda jan tsaki afili, yacigaba da ɗaukar abinda yakeso. "Ya Sultana Meena ta kira sunansa cikin tsananin farin ciki, tare suka iso wajensa da Nana, ba kunya ta faɗa jikinsa ta rungumesa hannu bibbiyu ya sa shima ya rungumeta tare da Nana, yan matan dake tsaye a wajen ko waccenta ta tsuke fuska 🤣, A hankali ta janye jikinta, "Ya Sultan ina Mommy da su Salma," Murmushi ɗauke a fusakar yace ,"lafiya lau suke , " ya Sultan ina nan tafe Weekend ka gaya Mommy idon ka koma gida. Kai ya gyada mata, haka suci gaba da seyayyar su, Awajen biyan kud'i suka iske Sultana, Sultan ya miƙama Meena ATM ɗinsa, aiko da sauri ta miƙa ma su Aiki.. tare suka fito daga shoprite ɗin. Kowa ya nufi motarsa Meena da Nana na yiwa Sultan Bye bye... Ahaka suka k'arasa gida, suna shiga harabar gidan taci karo da motar Daddy, da sauri suka wuce cikin gida nan Palo suka tarar da su gabaki dayan suna hira," Daddy sannu da zuwa, suka faɗa a tare ,"yauwa my Daughter's, daman wajen ku nazo, Mommyn ku tace nazo na ɗaukeku kuyi Weekend a gida, wani irin farin ciki ne ya lulluɓe Meena da Nana," don haka kuje ku haɗo kayan ku," Daddy Nidai Bazan je ba! Sultana ta faɗa cike da Shogoɓa," wani irin kallo Abba ya watsa mata, nan take ta kama kanta, ,"Abba ga Atm ɗinka cewar Meena," Banji debit Alert ba har yanzu. "Abba ya Sultan ne ya biya muna" "Toh ma sha Allah, maza kuje ku haɗo kayan ku, da sauri suka wuce ɗakin , Sultana na kumbure kumbure, jim kaɗan suka fito, Kaka ta kalli Sultana cikin tsokana tace idon kunje ina gaida Sultan, wani irin kallo Sultana ya yi kaka tare da murguɗa mata baƙi... Har bakin Mota Mami ta raka ƴa ƴan nata, dai dai lokacin kuma Motar Haydar ta jigo. Yana gama Parking suka fito gabaki ɗayan su, "Daddy Abba Ina wunin ku, "lafiya lau Haydar,"Khalil ya kalli Sultana," Anty Sultana ina zuwa haka ?" Ya Khalil gidan Mommy zamu tafi Nana ta bashi amsa. "Allah ya tsare sai mun shigo" "Amin" "Ina Arif halam ko bada shi za'a je ba?" "Ya Haydar bacci yake kansa ke ciwo, Saida suka wuce sanna su Haydar suka wuce cikin gida. Tafiyar Mintuna Kaɗan sukayi suka isa gidan Daddy Hon yayi mai gadin ya taho da sauri ya buɗe musu tamfatsetsen gate din. Aɓangaren Sultan bayan ya dawo daga shoprite Side ɗinsa ya wuce, Ruwa ya watsa tare da sauya kayan jikinsa, wani tattausan riga da wondo blue mai taushi ya zira, tare da fesa turarensa mai masifar ƙamshi, System ɗinsa da wayarsa ya ɗauka kana ya fito, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sassanyar kamshi turarensa ya mamaye ko'ina A hankali yake taku wani irin masifeffen kyau yayi collor kayan jikinsa yayi matuƙar amsarsa farar fatarsa.kai tsaye ya nufi babban palon ya zauna, Cikin wani irin farin ciki Sultana ke bin ilahirin gidan da kallo ganin yanda flowes da shuke shuken kayan marmari suka zagaye gidan, Da sauri ta juyo da kallonta kan Meena tare da cewa. "masha Allah wai daman haka gidan yake da kyau? gaskiya yayi kyau sosai" ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta tare da shaƙar sassayan iskar dake haɗe da ƙamshi flawers,y "Anty Sultana yanzu kam kin Dena fushi ko? Kinga gida mai kyau?" "Wallahi Meena gidan nan ya yi kyau sosai komai kuma ya burgeni gawani irin ƙamshi da suke, ji yanda ilahirin gidan ke fitar da wani Daddaɗan ƙamshi,har Naji ina son yaruwa a gidan nan!" Meena Kam dariyar dake cinta take ƙunshewa, Tunda sukayi sallama su Salma da Salim dake falon suka taso da gudu suka rungume Sultana Meena gefe takoma tana kallonsu cikeda birgewa, saida suka gama murnarsu sannan suka lura da Meena da Nana , suma suka rungumesu tare da Nana. "Maraba da baƙi" cewar Mommy. Lokaci ɗaya suka juya suna kallonta karab Idanunta ya sauka kan Sultan zaune akan sofa, dagashi sai wando 3quter idonsa a wayarsa yana danne-danne. Rumtse ido Sultana tayi gabanta Na fad'uwa, bak'aramar firgita tayiba daganinsa haka, Dan damtsen hannunsa yamugun tsoratata, tai saurin kauda kanta daga kallonsa. Har yanzu idonsa nakan waya, tare suka wuce tsakiyar palon suka zauna. Kafeta tayayi da idon nasa, wannan yasakata gaza koda kallonsa, "Mommy Ina ihsan?" "Tana ɗaki bansa uban me take kitsawa a ɗakin, kullum tana ɗaki kaman wata Amarya. "Sultana kun gaisa da Sultan, cewar Mommy. Kai ta gyaɗa a lamar a a'a, bazaki gaida Ogan na Kiba?" "Mommy nan ai ba Asbiti ba ne" ta yi maganar tana kallon Sultan, Mommy tayi ya yi Murmushi kana tace," Oga oga ne a duk inda yake Sultana, Batasan sanda bakinta yasuɓuce tace kamarya? Banda waje na ?, tak'arashe maganar da murgud'a baki. Aransa yace akwaifa rashin kunya sosai awajen yarinyarnan.. Afili kuma saiya gallah mata harara. , harta samu kwarin guywar kallon cikin idonsa, amma kwarjinin dake taredashi yasakata saurin janye idon nata, Kuttt! Yafad'a yana binta da kallo, yana rasa mizaice, saikawai yaja ajiyar zuciya, dolenema yayi bincike akan yarinyarnan, danyasan wacece ita?, shifa mamaki take basa, saikace aljana, tunda yake babu macen data taɓa kallon tsakkiyar idonsa sai yarinyarnan, duk girman mace kwarjini yake mata takasa masa kallon minti2 ma, bare cikin idonsa, duk jidakan yarinya da isarta, inhar zatazo wajensa tace tana sonsa, kotazo suyi wata magana, wlhy inhar yadasa mata idonsannan na yan sakannnu kawai saikaga jikinta narawa, tashiga hankalinta daganin bakin Rijiya bawajen wasan makaho baneba. Amma yau ga yarinya k'arama, ta kalli tsakkiyar idonsa. Ya furzar da huci daga bakinsa, Wanda yasaka su Daddy kallonsa. "Sultana kuje sama kukai kayan a ɗakina. "Mommy yau a ɗakinki zamu kwana wajen Anty Sultana, Salma da Salim suka faɗa, "Salma a zaku takure a ɗakin ku barsu Kinji, ,"nan ta ke ta marairaice fuska kakam Zatayi Kuku, Mommy ki barsu zamu kwana a tare, "A'a sai dai Salma ta kwana tare da kuku, Nana taje ɗakin Ihsan su kwana tare, "Mommy Nifa". "Kaje ɗakin Ya Sultan ka kwana, dai dai lokacin kuma su Haydar suka iso da Khalil da Arif, "Yauwa ga Ya Arif nan ma yazo zamu kwana a tare.. Nan take palon ya ƙara hargitse wa da hayaniyar su, kafinan suka ci Abinci na musamman da Mommy ta girka musu. Sai bayan Isha'i Ihsan ta fito daga ɗakin fuska a tsuke, sama sama suka gaisa dasu Sultana, Ƙarfe 8:50 su Haydar suka wuce gida haka a bar Arif.. bayan ta fiyarsu Sultana ta wuce ɗakin Mommy tare da Meena, "Anty Sultana karku rufe ɗaki ina nan tafe, ,"sai kinzo... Suna shiga ɗakin Meena ta wuce toilet Wonka tayi ta fito ta saka kayan bacci ta kwanta nan take bacci ya Awon gaba da ita. Bayan tafiyarsu, Salma bata jima ba ya yi Awon gaba da ita, koda Sultan ya shiga palon tana kwance, kashe Tv ya yi kana ya ɗauke a hankali, kansan cewar bacci nata baryi nisa Sosai ba, ta buɗe idanunta a hankali, cikin muryar Barci tace ,"Ya Sultan kaini wajen Anty Sultana... Sultana Meena na fitowa daga toilet ɗin itama ta shiga Wonka tayi ta fito bayan tafito tashirya cikin wando dogo da Riga Na cartoon kalar Pink sunmata kyau.sosai, tana gaban mudubi tana tufk'e gashinta Dan bataso tayi barci dashi ahaka, yaturo k'ofar yashigo, da sauri Sultana tajuya tana kallonsa. 'Dauke yake da Salma a kafad'a, saɓanin d'azun yanzu yasaka doguwar jallabiya, Salim nabiye dashi abaya, da'ala shi baiyi barcinba. Ko kallonta baiyiba yad'orata a gadon Mommy, saida yagyara mata kwanciya sannan, sannan yamata addu'ar barci ya shafa mata, Salim yace Ya Sultan ni awajenka Jan kana. "Arif na can na jiran aka palon ɗakin ka Zaiyi barci. Taɓe baki Sultana tayi, Duk abinda takeyi ya Sultan Na kallonta ta k'asan idonsa, bakinsa yataɓe ya kauda kansa daga kallon nata. yafice abinsa, batareda ya nuna yamasan dawata hallita a d'akinba. Da uwar harara Sultana taraka bayansa harya fita. Yana fita ta kace wutan ɗakin ta kwana, nan take Barci ya ɗauke ta... _Washe gari_ Har 8:30am Sultana bata tashiba, tuni su Salma da Meena sun tabar ɗakin ita kad'ai taketa juye-juyenta ƙaton gadon Mommy Kowa ya hallara a dining har Daddy kasancewar weekend ne, Mommy takalli dukkan yaran babu Sultana da Sultan , Meena tashi kakira Yayan ku, kekuma Salma kira Anty Sultana. Da to suka amsa. Babu dad'ewa saiga ya Sultan sunfito shida Meena rike da Hannun juna har k'asa ya durk'usa ya gaida iyayen nasa, k'annensa suka gaisheshi. Yaja kujerar ya zauna, Sultana suka fito, da alama saida Salma tasha dagama wajen tashin Sultana, dan kayan barcinema ajikinta sai hijjab data d'ora iya ƙirji a saman kayan barcin, daka kalli idonta kasan yanzu tatashi a barci, saboda akwai ja acikinsu, gasukama sun k'ara zama manya, durk'usawa tayi tagaida Daddy, ya amsa cikin fara'a, "Mommy Ina kwana" "Lafiya lau Anty Yara" Daddy yace tashi kizauna d'iyata yanuna mata kujera d'aya data rage wadda take kusada ya Sultan . Jitayi tamkar tafasa ihu, amma babu damar hakan, dan Daddy kallon mahaifi take masa. Mommy ta haɗawa Daddy Abincisa dasu Salma da Salim. "Sultana tatashi ha had'a masa shima, bak'aramar kid'ima zancen Mommy yasakataba, Babu yanda zatayi tahad'a masa komai, yanata danna waya abinsa tamkar baisan mi'akeyi a dining d'inba, Kowa yagama zuba abincin Daddy yayi bismillah, kowa yayi aka fara break, Sultana dukata takura, sai juya cokalin takeyi, shiko a kwalar rigarsa, abincinsa yakeci hankali kwance, bayan sun kammala break fast Sultana tazare jikinta zuwa kicin taya masu aikin gidan Aiki Abinci.... Bayan La'asar, Sultana ta nufi gadin, tafiya take a hankali kai a sunkuye batare data san mike a gabanta ba. Kaɗowar iska da sassanyan ƙamshin turare mai daɗin gaske ya sakata tsayawa cak ƙirjinta na harbawa da ƙarfi. Fararen idanunta ta janye daga kan wayar tare da ɗago kanta gaba ɗaya, a kan mutumin dake kishingiɗe bisa wata lallausan kujera, yana Danna lap-top ƙirar kamfanin apple dake akan wani ƙaramin table Gefensa kaɗan wani ƙyaƙyƙyawan bowl ne fari na tangaran cike da ƴaƴan itatuwa masu in ganci. Duk da tana a gab da shi aikinsa yake hankali kwance baiko nuna alamar yasan da zuwanta ba. A hankali ta kawar da kanta gefe tana kallon gwaiba. Matsawa tayi a hankali, tsalle tayi da niyyar tsinkowa dan bishiyar na da tsayi sosai. tsalle ta kuma yi amman ta kasa ga dai hannunta na taɓawa sede baza ta iya tsinka ba. "Ki bar nan". Sassaanyar muryarsa mai sanyi ta daki kunenta. Ƙirjinta ne ya sake harbawa har tanaji kamar jininta daya tsinke na neman biyo hudojin gashin fatarta ya fito. Bata da niyyar cewa komai, gata tsaye tamkar an dasata ta gagara ɗaga ko ƙafa ɗaya tabar wajen duk da haka zuciyarta tafi buƙatar da tayi. Jin shiru ba'a amsa masa ba, ga tsaiwar mutum yanaji har yanzu a gabansa ya sashi ɗago manyan idanunsa masu haske ya sauke a kanta. Fuskarsa dake a kame da kwarjini ya sake tsumewa yana sassauta girman idanunsa tamkar mai son lumshesu.. A fisge, tamkar an jawo furucin daga bakin Sultana ta yamutsa fuskarta da ƙanƙance manyan fararen idanunta , "Ansa dokar shika nan ne?" Kamar yanda bai motsa daga yanda yake ba haka bai ce mata komai ba, bai kuma janye idanunsa a kanta ba har yanzu, tana matuƙar jin kaifi da tasirin idanunsa a dukkan ɓargon jikinta da jijiyoyi da gudanar jini. Harara ta balla masa ta ƙyaɓe fuska da raɓashi ta wuce, danji take ƙafafunta tamkar ba'a kansu take ba. Kai tsaye ta wuce cikin gida fuska a tsuke ta nufi ɗaki ta kwata cike da takaicin Sultan, da wannan takaici barci ya yi Awon gaba da ita, sai gab da maggariba ta farka, ruwa ta watsa tare da Alwalla kana ta fito, dai dai lokacin Meena na shigo ɗakin," Anty Sultana kinsha barci yau. Harara Sultana ta dalla mata, "yi haƙiri karki sauke barin nan a kaina, Saida suka Isha'i suka fito Palo.... Koda suka shigo palon Salim na kuka Miya faru kake kuka Salim?. Cikin kukan ya nuna Salma, ta Sultana ta maida kallonta kan Salma ita ma tana niyyar kukan. " Meki kamasa?" " Anty Sultana biscuit d'ina da yana Sultan ya bani shine ta kwace min." "Anty Sultana jiya tare mukaci nawa" Bata k'arasaba taji Salim ya fusge hannunsa anata yakwasa aguje. Juyowa tayi da sauri Dan ganin itama Salma tagudu. Kasa ya duk'e suka shige jikinsa, bataga fuskarsaba saboda sun kare, amma jin yanda kirjinta keta harbawa taji ajikinta shine, dak'yar tacira k'afa danufin Darning.. Tare sukaci Abincin, bayan sun gama Daddy ya kalli Sultan, "idon sun gama ka maida su gida gobe Monday, wani irin farin cikin Sultana taji.... ai da sauri ta wuce ɗaki ta haɗa kayanta ta fito Palon Meena da Nana har ga Allah basa son barin gidan, Lokaci da zasu tafi Daddy ya basu 200k su sa kati. da farko ƙin ƙarɓa Sukayi Saida Daddy ya yi musu jan ido kana suka ƙarɓa tare da yi masa Godiya. Har bakin mota suka raka su. Meena ce a gaba Sultana na zaune gefen Meena, har suka iso gida Sultana Ƙala bata ce ba, suko sai hirar su, suke gwanin burgewa.suna isa ƙofar gida Sultana ce farko fita. "Ya Sultana kazo muje cikin gida ka gaida Mami, Ya Sultan ni banma taɓa ganin kazo gidan nan ba,"Ameenatu! dare ya yi Zanyi na san duk sunyi Bacci next time zan shigo in sha Allahu. Ya Sultan.... Pls tayi maganar cike da Shogoɓa, kai ya gyaɗa mata alamar A'a, jiki a mace ta fife daga motar... Saida yaga shigar su cikin gida kana ya wuce... Waje gari, da safe Sultana ta wuce wajen Aiki... A hankali Rayuwa taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali. A ɓangaren Sultana da Nas Soyayyarsu suke Sha hankali kwance. Yau ta kasance Weekend, tunda safe Sultana ta wuce gidan su jidda Kaka ko yau tunda safe ta tashi da matsanancin ciwon kai. Bayan La'asar Mami ta bata maganin ciwon kai, tana sha bada jimawa barci ya yi a won gaba da ita... Sai ƙarfe Shidda Sultana ta dawo. Duk da takalman data gani na maza a ƙofar palon Daddy bata damu ba, sallama tayi kawai, kafimma su gama amsa mata ta shige dan duk zatonta Su Haydar a ciki, tunda tasan duk suna gidan. A shagwaɓe ta buɗe baki zatai magana. sai dai cin karo da fuskar da batai zato ko tsammanin gani ba ta sata waro manyan fararen idanunta waje cike da al'ajabi.....!"✍️ *Har yanzu dai muna cikin Book 1* _More comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce* ✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 29-30* ______Sultan dake zaune sanye da ƙanan kaya sun yi masa Kyau sosai, kallon nata yake cike da mamaki,, ya ɗauke kansa cike da shan ƙamshi kamarma irin bai ganta ba ɗin nan shi....... " Oyoyo Anty Sultana ”. Salma ta katse mata tunaninta. Juyawa tai inda Salam take, har yanzu mamakin ganin Sultan ɗin bai barta ba, Sosai mamaki ya kume Sultana, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta sake maida dubanta ga Sultan daya maida dukan hankalinsa kan wayarsa.. "Shigo mana Sultana" A hankali ta ƙara so cikin palon, "Daddy sannu da zuwa" "Yauwa yar Albarka" Kana ta zauna tare da su Salma. "Toh shi Sultan bazaki gaida hiba?" cewar Abba. Yanzun kam baki ta kumbura sosai, ta kalli Sultan ɗin da yayi tamkar baisan da zaman kowaba a palon ba tace, "ina wuni". Sarai yajita, amma sai ya share tamkar bejita ba, "Ya Sultan Anty Sultana ya gaisheka" Salma ta faɗa a hankali. Ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke a cikin nata. Karan farko da sukaima juna kallon ido cikin ido. Kusan lokaci guda kowanne gabansa ya faɗi. Sultana tai saurin fara janye nata da ƙoƙarin juyawa. Shima ɗan lumshe nasa yayi ya buɗe cikin muryarsa mai amo ɗin nan yace, "Lafiya lau" "Jeki kawo musu ruwa". A hankali ta miƙe ta nufi cikin tare da Salma, kayan drinks ta haɗo musu masu sanyi, wani irin Murmushi yayi , tare da miƙewa saboda wayarsa da aka kira, harar ƙofar da Sultan yabi ya fice ta gefen ido. Jim kaɗan mai gadi ya shigo, a bakin ƙofa ya tsaya, yana kiran ,"Sultana" Miƙewa ta yi ta nufin wajensa, tsaye ta tarar dashi rike da 🎁, "gashi" A hankali ta kai kallo da Sultan dake waya yana faɗin ,"Haba Aziz kasan irin da muwar da najiga reshin samunka a waya da nayi, taɓe baki Sultana tayi, tayi, yauma dai Flower ce mai masifar kyau da kamshi da yar takarda, *Zan Kasance cikin Son ki har Abada* *kalaman bakina sun gaza furta adadin yadda Zuciyata* take* kyaunarki kin zamo tamkar Numfashin da nake shaƙa kece rayuwarta ina Son ki Sosai wallahi ban san na linda zan shiga ba In don na rasa ki ba kece Abar be gena safe da yamma daga Nas* Wani irin sassanyan Nunfashi ta sauƙe lokacin da tagama karatun, tafiya take kai a sunkuye Karo sukayi, goshin Sultana ya bugu goshin Sultan, Da sauri tai baya saboda azaba. Shima bayan yaja kaɗan yana wani yamutsa fuska idonsa a kanta. Kasancewar Sultana bata taka ɗan step ɗin ƙofar falon Abba dai-dai ba lokacin da tai baya sai ta sake yo gaba zata faɗi. Sultan ya tabbatar idan ya barta ta faɗi zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta faɗo jikinsa. Sai kuma ta firgice saboda tsoratar da tai najinta kwance a ƙirjinsa, ta wage baki zata tsala ihu yayi sauri ɗora lallausan tafin hannunsa saman bakin nata ya rufe, Cikin tashin hankali Sultana ta fara mutsu-mutsun kwatar kanta, jikinta sai rawa ya ke yi. Shikuma yaƙi sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata faɗuwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu, cike dajin haushi ya daka mata tsawa, dan jiyayma kamar ya saketa ta faɗin ma yaga ƙarshen tsiwa. cigaba dayin mutsu-mutsunta nason ƙwacewa takeyi, tuni hawaye kuwa sun fara bimata kumatu, baya baya Sultana ta riƙa yi shiko yana biye da ita, Jin ya manneta da bango sai tashin hankalinta ya ƙaru, dan ta zata wani abun kuma zai aikata mata, ta kasa nutsuwa ta fahimci taimakonta yayi. hannayenta duka biyu ta saka tare da dukan ƙarfinta tana ƙoƙarin ture masa hannunsa daya rufe mata baki da shi. Ko gezau baiyiba, saima wani shegen kallo da yake binta da shi tamkar ya manta a inda suke, ga fuskarsa a matuƙar ɗaur, sai dai shima zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri. "Ash!!" ya faɗa da sauri yana janye hannunsa da ya toshe mata baki da shi, dan kuwa daddagewa tayi ta gasa masa cizo a tafin hannun. Yaja da baya yana yarfe hannun nasa da faɗin, "Witch girl" Sultana da har yanzu jikinta bai bar rawa ba ta galla masa harara tana share hawayenta. “Allah ya tsare da maita, Kuma wallahi ka sake gigin taɓani saina karye hanneyenka, danni ba ƴar iska baceba!”. " Waye ɗan iskan?"ya faɗa yana galla mata harara tare da cafkota, iya ƙarfinsa ya fisgota tayo baya ta sake faɗawa jikinsa. Mannata jikin bangon ya sakeyi, ya toshe mata baki da ɗayan hannunsa. kafin ya ɗago ɗayan hannun ya kalli inda ta cije sa, yamutse fuska yayi ganin yanda shatin haƙoranta suka fito masa Sultana hankalinta ya yi ƙololuwar tashi,ta rikice iyakar rikicewa yanzun kam, dan ta yarda a ranta da gaske Sultan son cutar da ita yake. Ƙilama abinda ya kawosa gidan kenan. Sake kaima ɗayan hannun cizo tayi. Yayi saurin janyewa , ba zato ba tsammani taji saukar lallausar labɓansa a bakinta. Shi kansa baisan yaya akai hakan ta faru ba, ya tsinci kansa ne kawai da haɗe bakin nasa da nata ya shiga kissing ɗinta. Atake wani matsananci tsoro ya sake lulluɓe Sultana yayin da jikinta yashiga rawa tamkar mazari. Wani irin masifaffen tsuma jikin Sultana keyi yayin da numfashinta ke fusga saboda tsananin tsoron Abinda Sultan ya aikata mata yasa ta sake ƙanƙamesa tamkar zata tsaga jikinsa. wani irin rungumeta yayi da masifar ƙarfi yana mai sakin Nannauyan Ajiyar zuciya Daƙyar ya iya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa da yake jin wani irin jiri na fizgarsa tare da sarawa, da sauri ya sake sunkuyar da kansa akan wuyanta kana ya sake rungumeta da ƙarfi baki ɗaya ya rasa wani irin yanayi yake ciki.. dai dai kuma a ka ɗauke wutar nepa. hakan yasa ta sake rungume Sultan da ƙarfi,Jin yadda take liƙewa a jikinsa ne, yasa shima ya saƙe yi mata wani irin rugguma tare da sauke Nannauyan numfashin yana shaƙan Daddaɗan ƙamshin jikinta. Itama sake rungumesa tayi cikin mawuyacin hali tana neman numfashi domin numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa gaba daya tsananin tsoro da tashin hankali ya bayyana asaman fuskarta, a tarihin rayuwar hakan bai taɓa faruwa da ita ba, Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da ficewar hayyaci Sultan ya sake rungumeta yana jin ɗumin jikinta. A hankali yasa Lallausan tafin hannunsa ya tallabo fuskarta tare buɗe manyan idanunsa da ƙyar dan har yanzu dishi-dushi yake gani, idanu ya tsirawa kan goshinta , yalwataccen sumar kanta da yasha gyara, kallonsa ya mayar kan fuskarta jin, yanda numfashinta ke fita da sauri sauri. Idanunsa ya mayar kan ƙirjinta da sauri ya lumshe idanun, a hankali ɗaura lips ɗinsa a kan kunnenta ya hura mata iska mai ɗumi..Wani irin dogon numfashi taja mai nauyi tare da fesar dashi da ƙarfi, cikin ƙanƙanen lokaci numfashinta ya soma dai-dai kana duk abinda ke faruwa idanunta na lumshe.. Sultan sannu ahankali ya fara dawowa hayyacinsa da nitsuwarsa. Sake lafewa Sultana tayi ajikinsa tare da lumshe Idanunta. lumshe idanunsa yayi jin jikinsa babu kuzari kona kaɗan, ji yake tamkar an zare masa lakar jikinsa cikin sanyi da rashin kuzari dake tare dashi. A hankali ya janyeta daga jikisa.Shiru bata motsaba, hakan yasa ya sake ɗan fizgo muryasa tare da faɗin."Sultana!" Karon farko A rayuwarsa da yafara kiran sunanta. Cikin raunatattiyar Murya yaci gaba da kiran Sunanta, "Sultana! Sultana!! Sultana!!!" Sultana har yanzu idanunta na lumshe take Jin sautin muryar Sultan na kiran sunanta kamar amafarki, Lumshe Idanunsa yayi akaro na barkatai tare da kai bakinsa cikin kunnenta kana cikin raunan'nanyar murya mai taushi yace.,"Sultana!!" Cikin tsananin tsoro Sultana ta janye jikinta, Cikin mawuyacin hali ya dafe kansa da hannunsa na hagu murya narawa yace." Astagfirullah wa,atubu ilaik Ya Allah!!" "Allah ya isa ban yafeba mugu kwai Azzalumi, Yanzun kam da kansa ma ya matsa ya bata hanya, da gudu tabar wajen kuwa tana kukanta har yanzun. Cike da takaicin kansa ya rumtse idanusa da ƙarfi, tare da ɗora hannunsa a goshi yana murzawa da abaton “Ya rabb!" gudu ta shiga palon ta nufi ɗakin su, tana shiga ɗaki ta lumshe Idanunta tare da manna bayanta da jikin ƙofa. Hawaye masu ɗumi suka zubo mata har zuwa yanzu jikinta baibar rawa ba, sai faman waige-waige take tamjar ance mata Sultan ɗin biyota yayi. Ta ƙanƙame jikinta lokacin da abinda ya farun ya sake dawo mata a rai, yanda gashin jikinta ke wani mimmiƙewa zai tabbatar maka da tsigar jikinta tashi takeyi. Da sauri ta saka hannu tana share hawayenta saboda jin tahowar mutum. ‘Na shiga uku ya biyo ni’ ta faɗa a fili zuciyarta na wani irin bugawa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito.. "Anty Sultana lafiya?" Duk da ganin Meena ce ba Sultan ba hakan bai hana Sultana sake rikicewa ba, ta shiga inda-inda jikinta na tsuma. "Ba Komai". da sauri ta share hawayenta ,"Ba komi Meena, "Anty Sultana kuka kike fa sannan kike ba komi?" "Kinga ya isa. Share waɗan nan hawayen idan baso, aiko kaman jira take da saurin Sultana tasake share hawayen, "gayamin me yafaru Anty Sultana!" Sultana bata ɓoyewa Meena komi ba, "Anty Sultana shi Ya Sultan ɗin da kansa ya yi haka?" Kai ta gyaɗa mata, Ƙasa Sultana ta zube tana kuka tamkar ranta zai fita, Ɗagota Meena tayi ta share mata hawayen tana murmushi, “Shikenan naji, kuma na miki alƙawarin babu maijin zancen nan a gidan nan kinji, toilet ta Wuce tare da cire kayan jikinta ta sakarwa kanta ruwan ɗumi Da ƙyar ta iya yin wankan ta fito bayan ta ɗaura alawalan tare da doguwar riga ta roba ta saka har zuwa lokacin jikinta na ƙamshin tularensa Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah... Har aka kira sallah Sultan bai dawo ba, kiran Sultan ɗin Daddy ya yi, nan ya sanar dashi ya wuce Asbiti an kawo wani Emacency, Sultana yana isa gida kai tsaye ya wuce ɗakinsa kayan jikinsa ya cire kai tsaye toilet ɗin sa dake cikin Bedroom ɗinsa ya nufa yana shiga ya sakarwa da kansa ruwan ɗumi batare daya cire boxer ba yana tsaye ruwan ɗumin ya cigaba da zuba akansa Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan ya kashe shower ɗin yana sauke numfashi a jajjere babu abinda ke yawo a idanunsa kamar lokacin daya rungumi Sultana ga wani Daddaɗan ƙamshinta da yake ji ajikinsa da ƙarfi ya Lumshe idanunsa. Kai kawai yake girgiza wa cike da tashin hankali mara misaltuwa daya rufe idanunsa babu abinda yake hange face yanayin da suka kasance, bayan ya gama wanka al'wala ya ɗaura tare da fitowa, ya sanya lallausar jallabiya, a hankali ya tattaro duk kan natsuwar kana ya kabbarta sallah. Har akayi Isha'i ya zauna a wajen, Babu abinda kema Sultan yawo a zuciya da ruhi sai kalaman Sultana. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da A.c dake aiki a dakin bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi. Kana ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake tariyo kalaman Sultana ,"Allah ya isa ban yafe ba! Mugu Azzalumi!!, ɗunbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin hakan,bayan Maryama ba wata ɗiya macce da ya taɓa runguma, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko ganinsu a lokacin bazai taɓa yarda da shi ba. Ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa da ƙarfin tsiya, ƙirjinsa na sake masa zafi. Mikewa tsaye ya yi tare da zaɓewa saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu, Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ƙara kusanto masa da hotonsa ne a zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai fuskar Sultana da ƙirjinta, sune kwai Abinda yake gani... Su Daddy sai bayan isha'i suka dawo gida. Bayan ta fiyarsu Meena ta shigo ɗakin riƙe da 🎁 ta mikama Sultana, jiki a mace ta ƙarɓa ,..... Washegari Duk yanda Sultana taso sakewa ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru tsakaninta da Sultan,..ranar dai haka ta yini cikin sanyin jiki....A ɓangaren Sultan ma ranar gabaki ɗaya a ɗaki ya yini sallah da cikin Abinci kwai ke fitar dashi.. Washe gari. Cikin sanyin jiki da damuwa Sultana ta shirya cikin Uniform ɗin ta da suka sha guka baki daya ta kasa sakewa da zaran ta tuna, Sultan sai tashiga da muwa..cikin dauriya ta nufi Asbitin...tana kaffa kaffa karsu haɗu da Sultan.... À ɓangaren Sultan ma tunda yashigo Asbiti ya wuce office ɗin su ya zauna cikin zullumi da damuwa. idanunsa alumshe duk abin duniya ya Ishesa. Haka dai Sultan ya yi Ni a Office har zuwa lokacin tashi ya wuce gida.. ★★★★ Yana isa gida ya Parking ya fita Kai tsaye sashensa ya wuce cikin mutuwar jiki ya kwanta ruf da ciki tare da lumshe idanunsa yayin da ƙwaƙwalwar sa ta shiga tariyo masa yanayin da suka kasance, sam Abin ya ƙi barin ransa, Miƙewa yayi cikin rashin sanin Abinda Zaiyi, ya zaiyi da wannan jarabar tun jiya yake fama da zaran ya rufe Idanunsa yanayin da suka kasance da Sultana ne yake gani. Batare daya shirya ba yaji hawaye Masu Zafi suna bin kuncinsa shi kansa baisan meyake so ba bai san meke faruwa dashi ba yakasa sanin yana yin da yake ciki ji yayi kawai yana kuka hawaye na bin kuncinsa yana sheshsheƙa. Nan take kuma zazzaɓi ya rufeshi lips ɗin sa suka shiga rawa.. A hankali Daddy ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, ganin Sultan kwance jikinsa na karkarwa ya nufi wajensa da sauri ya na kiran sunansa,"Sultan!! Me ke damun ka? Baka da Lafiya ne?" Sultan ko magana yake son yi Amman ya kasa, da kyar ya fisgo magana,," Daddy sanyi nake ji, Daddy ciki na ciwo kaman zai ɓalle!" da sauri Daddy ya lulluɓesa da blanket mai laushi..a hankali Daddy ya miƙe ya kashe A.c dakin kana ya gyara mishi kwanciya, kasan cewar lokacin Sallah ya yi ya wuce masallaci, ana gama Sallah ya wuce Asbitin Sultan dai dai lokacin Kuma Dr Aryan na ƙoƙarin barin Asbitin ganin motar Daddy yasa ya nufi wajensa da saurin ya gaida shi cikin girmamawa, bayan sun gaida Daddy ya yi mai bayanin Sultan ba lafiya, Tare suka wuce can gida, koda suka iso Ana kiran Sallah, Saida sukayi sallah kana Daddy ya yi mishi jakora zuwa ɗakin Sultan, yadda Daddy ya barsa kwance haka suka tarar dashi. Dr Aryan ya fara dubasa. gyaran murya Dr Aryan yayi tare da cewa,"ciwon Mara ke damunsa,"Daddy Dr Sultan na fama da matsananciyar Sha'awa!" Yanzu ma itace ta motsa" idan har aka bar shi da wannan sha'awar zai iya zame masa matsala zata iya jefashi acikin damuwa. Daddy ko sai kallon Dr Aryan yake. A hankali Daddy ya sauke Nannauyan Numfashi kana sannan ya ce,"Miye mafita yanzu?" "Mafita ɗaya ce yanzu Daddy kawai yayi ƙoƙari yayi aure”. Nannauyan Ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe tare da cewa. "In sha Allahu zamu yi ƙoƙarin mu" Magani Dr Aryan ya rubuta Mishi kana ya miƙama ,"ga wannan ya yi ƙoƙari yasha su kafin zuwa safe, a samu ruwan ɗumi a masa laimun tsami da zuma a bashi ya sha.. godiya sosai Daddy ya yiwa Dr Aryan har bakin mota ya rakashi..bayan ta fiyarshi Mommy ta kalli cike da damuwa tace ," mike damun sa?" "Je ki daɗo min Lipton da Lemun tsami ki saka zuma kaɗan" da sauri Mommy ta wuce Kicin, jim kaɗan ta dawo hannunta ɗauke da Mug sai tururi yake, Daddy ya ƙarɓa ya wuce ɗakin Sultan. da taimakon Daddy Sultan ya sha ruwan Lipton ɗin nan take Zufa ta riƙa tsastafo mishi, Atake yafara jin abinda ke damunsa na sauƙa kaɗan-kaɗan ahankali yaji lips ɗin sa ya daina rawan zamewa yayi ya kwanta akan gadon yana sakin Ajiyar zuciya.. ya kallesa ya yi Murmushi kana ya fice daga ɗakin. Sai wuraren ƙarfe ɗaya Sultan ya farki, da sauri ya nufi toilet ya watsa ruwa ya yi Alwala kana ya fito, Sallah Maggariba da Isha'i ya yi da bai samu damar ya ba. Washegari sosai ya ji sauƙi...wuraren ƙarfe Goma ya wuce Office, sai shidda ya dawo, haka suka ci gaba da wasan buya shida Sultana... Bayan Sati ɗaya, Bayan Isha'i Suna zaune a Palo Sultan na zaune kusa Mommy, Daddy ya yi gyaran Murya tare da kallon Sultan," My boy! Mun gama yanke shawara da nida Aminina, ya kuma mallakama Sultana halak malak don haka ku dai daita tsakinin ku" Tunda Daddy ya fara magana, gaban Sultan ke daɗuwa, Mommy ko sai murmushi take . "Ya Naji baka ce komi ba ?" "Duk yadda kace haka za'ayi Daddy" "Good haka neke son ji, mun riga da mun gama magana da Mahaifinta, ko wanne lokaci zaka iya zuwa, Allah ya tabbatar da Alheri," Amin Mommy ta faɗa cikin tsananin farin ciki... A ɓangaren Abba tuni ya sanar da su Mami da Kaka halin da ake ciki, sosai kuma sukayi farin ciki, musamman Kaka, saboda Sultan ya kwanta mata a rai sosai duk da bata taɓa ganin sa ba, Abba ya so A sanar da Sultana komi Amman kaka ta hana shi, a cewar a yiwa Sultana ba zata... Yau ta kasance Friend Tunda safe, Massege ɗin Nas ya tashi Sultana daga barci. *Aminci Allah ya tabbata a gare ki yake ma'abociyar kyau, da kuma kyawun sura burin zuciya ta kasance dake, duk wanda ya samu mace tamkar ya dace, kece mai ɗebin min kewa kece mai Shogoɓa Ni,kece farin ciki na, kin kasance komai a rayuwanah Sonki ya mamaye Zuciyarta cikikar burkina shine ki zamo uwar ya yana Sonki ya mamaye Zuciyarta ba zan iya rayuwa idon har ba keba ki riƙe min Alƙawari ki zamo jigo a rayuwata Good Morning my Hubby, I love you so much * Wani irn murmushi ta saki.tare da sumbatar wayar. *Kayar dani my Hubby Babu wani da zai kwace Zuciyata, domin Zuciyata ta kece har Abada Idanuwana kai kaidai suke kallo a matsayin Abokin rayuwata in son ka! Ina kyaunar ka da fatan ka tashi Lafiya Hubbyna i love you so much 💋* (Hmmm🤣🤣🤐) ★★★ tsananin mamaki ta kalli Mami da tuni ta bar wajen, Baƙo ta faɗa a hankali.. tsawon lokaci Sultana na zaune tana maimai ta kalmar baƙo a ranta,tana zaune a wajen har Abba ya fito," Wai zaman me kike anan,"firgit ta mike tsaye tare da barin Palon kai tsaye ta wuce palon Abba...✍️ ( Oh ni Halimatu ko ya za'a tarbi baƙo oh ho 🥲🤣🤣) _More Comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce*✍️ *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 31-32* _______Murya a sanyaye tai sallama a ƙofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya sakata tura kanta ciki da haushi. rashin amsa mata sallamar da ba'ayiba ne ya sakata ƙin kallon baƙon ma balle tasan wanene. murya a cinkushe batare data kallesa ba tace, "ina wuni". Sultan dake zaune yana dannar waya .ya ɗan ɗago kansa dan sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani yanzu da take ƙoƙarin fita. Cikin tsautsayi ta bigi Center table da ƙafa. baya tai taga-taga zata faɗi cikin sa'a yayi saurin saka mata ƙafa dan son kareta bisa tsautsayi ta faɗa saman cinyarsa.. Daddan turarensa ta Shaƙa tayi tai azamar ɗagowa cikin tashin hankali da tsantsar takaici. Idanunsu ne ya shige cikin na juna, cike da firgici Sultana ta sake waro masa idanunta da kware baki zatai ihu saboda harga Allah ta tsorata da ganinsa. Saurin saka tattausan hannunsa yayi ya rufe mata bakin , tare da sake manneta a jikinsa sosai shima a cikin ɗan firgice. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta ya sakeyi, jikinta ya hau ɓari tamkar mazari mutsu-mutsun ƙwace kanta tana kai masa duka a ƙirji.. "Oh my God!. Please calm dawn”. Ya faɗa yana janye hannayensa duka daga jikinta. Cikin rawar jiki hawaye na zirara ta miƙe, sake bigewa tai da kujera ƙafarta ta tuzguɗe ta sake yin gaba kuma zata kifa yayi saurin riƙo mata hannu ta sake dawowa jikin nasa. “Wayyo Kaka ɗan isk.........” ta wage baki da iya ƙarfinta zata faɗa yay azamar saka hannu ya sake toshe bakinta da manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba. da ƙarfi Sultana ta janye jikinta Sultana dake ja da baya tana ja da baya da kallonsa tace, “Ɗan iska kawai, Allah ya isa ban yafeba. Wallahi daga yau ka sake ƙoƙarin taɓamin koda hannu sai na illataka. A hankali ya nufi wajen Sultana dake durƙushe har yanzu tana kukan tashin hankalin, Handkherchief ya ciro a aljihunsa tare da tsugunawa gabanta, murya ƙasa-ƙasa yace, “ Stop crying!”. A razane Sultana da batasan da isowar tasaba ta ɗago danjin maganarsa gab da ita. Kamo hannunta yayi, da sauri ta dawo da dubanta garesa tare da fisgewa da ƙarfi. Sai dai ko gezau baiyiba balle tai tunanin ƙwacewar. “Kai wane irin......” Yatsansa ɗaya ya ɗaura akan baki. “Shii!" ya faɗa cikin katseta da zazzaro mata idanunsa sosai. Tai saurin rufe bakin kuwa. Dan wani irin shakkarsa da tsoronsa da bata taɓa fuskantaba daga gareshine ya shigeta yau ɗin. Ga wani irin kwarjini mai bala'in cika idanu da yayi mata. Batare da yayi magana ba ya saka mata handkherchief ɗin cikin tafin hannunta tare da matso da fuskarsa gab da tata cikin wata irin raunanniyar murya yace, " It okey" daga haka ya fice daga palon Ya tabbata idan ya cigaba da zama a falon to lallai zai iya aikata abinda shi kansa bazai yafema kansaba. da kyar Sultana ta tattaro da duk natsuwar Kana ta wuce gida tana sauke Ajiyar zuciya, Palo ta tarar da Abba da Mami da Kaka. Sai faman kallonta suke, Kaka ta ce ,"Ina mijin namu yake?" Shine ya wuce ko gaksuwa babu?" Ciki reshin fahinta Sultana tace ,"Miji Kuma?" "Mamana! Sultan shine mijin da zaki Aure" Sultana dake jin jiri na neman zubar da ita ƙasa ta faɗa tana mai dafe kanta,Da ƙyar ta iya kai hannu domin lalubar bango. Sai dai kuma ina bai kai ga bangonba wani duhu ya mamaye idanunta. a take ta zube ƙasa jikinta na karkarwa saboda wani bala'in sara mata da kanta yayi lokaci ɗaya, cikin tsananin tashin hankali suka nufi wajenta da sauri Abba ya zabura dan jin jikinta yayi sanyi ƙalau ya saki. Yayi saurin maida yatsunsa biyu wajen hancinta. tabbas bata numfashi’l ya ambata a zuciyarsa yana ɗagota gaba ɗayanta. Mami da Kaka duk sun ruɗe Cikin tashin hankali Kaka tace, "Abdullahi mike damunta "Ban saniba nima Mama, kinga miƙo ruwa dan bata numfashi" . da sauri Mami ta ɗakko masa ruwan , ya miƙa hannu ta tsiyaya masa. shafama Sultana yayi a fuska. sai dai ko motsi batayiba balle ai tunanun zata farko. Hankalin Abba ya sake tashi matuƙa. Ya ɗago idanunsa da sukai jajur ya kalli Mami dai dai lokacin Haydar da Khalil suka shigo palon, hankali a tashe suka nufi wajen Sultana dake kwance kaman babu a rai a cikinta, cikin raunin Murya Abba yace Haydar fito da mota, aiko da sauri ya ɗauke key mota ya wuce wajen jikinsa na karkarwa, Abba ya ɗauki Sultana suka wuce waje, Kaka ta bi bayansa da Mami kai tsaye suka wuce private hospital dake cikin Unguwar su, Tun isowarsu asibitin aka fara bama Sultana dake a sume taimakon gaggawa. tsawon lokaci bata farfaɗo ba Hakan sai ya sake ɗaga hankalinsu. musamman ma Kaka dake ta faman sharɓar hawaye. Cike da kulawa Abba ya zauna kusa da ita duk da kunyar ɗan fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ɗunbin kulawa da ladabi ya fara lallashinta da faɗa mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya nuna mata koda rasa Sultana sukayi su zama masu haƙuri da godema Allah . Dan lokacin da ya basu ita baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya karɓeta ya fisu bukatarta ne. Haka ya cigaba da mata nasiha harta samu nutsuwa tai shiru. Ya saka handkherchief ya share mata hawayen. Ana haka Doctor ya fito daga ɗakin da aka sanya Sultana. Ya buƙaci ganin ɗaya daga cikinsu cikin Abba da Kaka suka bisa Zuwa Office, A office ɗin likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa gasu Abba," Alhamdulillahi ta farfaɗo,.Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin ƙwaƙwalwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matuƙar buƙatar son ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ƙwaƙwalwar ta. . A duk kuma lokacin data shiga ƙunci ciwon na mata kuɗa a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da kuma addu'oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan lokaci batare data tsinci kanta a ciwon hauka ba. Duk da komai na Allah ne, babu wani bawa daya isa canja ƙaddarar wani bawa daga yanda tazo a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako kawai muke bata na dakatar da raɗaɗin a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi gaskiya, Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da Kaka ta kalli Abba cikin raunan'nanyar murya ta ce ," Abdullahi mike damun Sultana!!!? Naji likita na faɗin kwakwalwarta ta samu matsala yaushe hakan ya faru ban sani ba? Abdullahi mi kake ɓoyemin akan Maryama!!? A iya sanina Maryam lafiya kau aka haifeta bata da wata matsala!!" Abdullahi da gabaki ɗaya jikinsa ya yi sanyi, irin wannan rana yake gudu da tun lokacin da abin ya faru ya yiwa Kaka bayani da han bata baruba.. Abdullahi ya sauke Nannauyan Numfashi kana ya kalli Kaka cikin sanyi Murya mai cike da lallashi ya ce ," Mama ki gafarceni akan reshin faɗa Miki gaskiya da banyi ba, Mama shekara Takwas da suka wuce Sultana tana fama da wannan matsalar Sanaɗiyar Wannan yaron da ta rasa Abdulmalik dake ƙayare, saboda so da shaƙuwar dake tsakaninsu jin labarin mutuwarsa a bazata shine ya haifarda wannan matsalar!" Kaka ba baki ɗaya jikinta Ya yi sanyi, duk abinda aka ce mata ya faru da Sultana sanaɗiyar rashin Abdulmalik ba zayi musu ba, saboda tafi kusanshi dasu tafi kowa sanin irin shaƙuwar dake tsakinsu, cikin raunin Murya tace ,"Allah ya jikanka da Rahama Abdulmalik!! Allah yasa ka huta" "Amin Abba da Dr suka amsa mata. Abba da duk jikinsa yay sanyi godiya sosai sukaima Doctor Tare da tabbatar masa insha Allahu a wannan karon zasuyi abinda ya dace. Yaji daɗin hakan sosai. Ya sake ɗan musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Sultana. Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Ɗakin da aka Kwantar da Sultana suka shiga Sultana dake barci suka bar Kaka, sanin halinta koda Ance taje gida bazata yadda ba, hakan yasa suka wuce gida, koda suka iso gida Haydar Meena Khalil Nana duk suna zaune a Palon kallo ɗaya zaka musu ka fahimci suna cikin damuwa, lokacin da Abba ya shigo ya tabbatar musu Sultana tana cikin kwacin lafiya, hakan yasa suka wuce ɗaki.. ___________★★★ Sultan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan . Abinda ya aikatama Sultana. awannan dare haka ya kwana cikin mawuyacin hali saboda wani azabebben yanayi dake damunsa sai. Wajajen ƙarfe Huɗu wani irin bacci mai shegen daɗi ya ɗauke sa. Washe gari tunda safe Abba ya wuce Asbiti tare da Breakfast ɗin su, Alhamdulillahi koda ya shiko ɗaki jikinta da sauƙi sosai, Office ɗin Dr ya wuce, bai jima ba ya dawo. ya maida hankali ga Sultana da Kaka take lallaɓawa taci abinci amma sai shagwaɓa take ita ta ƙoshi. Ya ɗan murmusa tare da kamo hannunta cikin nashi. “Mamana daure kici ko kaɗanne kinji, inba hakaba fa kinsan Doctor yace allura zai miki, idan kuma kin fison allurar to sai a kirashi kawai”. Da sauri ta shiga girgiza kanta idanunta cike da ƙwalla. “Abba dan Allah a'a banaso”. "To ki daure kici abincin sai kisha magani ki kwanta ki huta. Kinga kince dama kanki na ciwo har yanzu, Doctor kuma yace kina buƙatar hutune sosai" Kanta ta sake jinjina masa. kaka da batace musu komaiba taci gaba da bata Abinci Batafi spoon huɗu ba su tace ta ƙoshi, kwanan Sultana Huɗu a Asbitin aka sallamesu... Alhamdulillah jikinta yayi ƙyau sosai, sai dai haɗarin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing mamory shine ya jefasu a cikin tsananin damuwa. a ɓangaren Sultana sam bata son mike faruwa ba, Lokacin da suka dawo Mami ta taimaka mata tayi Wonka, saboda Kaka ma na bukatar Hutu, taci abinci da magungunanta ta kwanta danta huta. Sosai Sultana ta yi barci Kiran sallar magriba ne ya saka Mami shigone ɗakin Sultana ta tadata. Da ƙyar ta samu ta tashi dan barcin nata yayi nisa sosai. Taimaka mata tayi tai alwala, Koda ta idar bata fitaba tai zamanta a ɗaki, sai da tai sallar isha'i da shafa'i da wutiri sannan ta ɗauƙi wayarta, miss call ɗin Nas ne da massages ɗin sa ba adadi, Sultana ta sauƙe Sassanyan Nunfashi, a hankali ta riƙa bin massages ɗin tana karantawa. "Anty Sultana ya ƙarfin jiki?" "Alhamdulillahi Meena" "Nas ya yi takira lokacin da kike Asbiti, Anty jidda ma ta kira ba adadi. "Allah sarki My Mommy nayi kewarta Sosai, bayan sun gama waya da Nas ta kira Jidda sun jima suna waya.. ____________★★★★ A ɓangaren Sultana kuwa tunda daga ranan da Abba yayi mata maganar aure ta watsar da maganar kasancewar Kaka da Mami ma basu sake yi mata maganar ba ita ma bata sake tada maganar ba hakan yasa bata ɗauki maganar da muhimmanci ba ita kuwa Kaka ko kullum cikin ya mata Addu'a take Sultan al'khairi ne agareta Allah ya tabbatar mata da al'khairi idan kuma ba al'khairi bane Allah ya zaɓa mata mafi al'khairi shima kuma Allah ya musanya masa da mafi al'khairi.... A ɓangaren Sultana kam Soyayyarsu suke Sha hankali kwance ita da Nas... Tsawon sati biyu kenan da zuwan Sultan wajen Sultana, tun lokacin ko bai sake sakata a ido ba, ka a Asbitin ba sake haɗuwa ba.. Sultana duk wata hanya da zata haɗa ta Sultan ta daƙileta... A hankali kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, yau sati ɗaya kenan da akayi sallah layya, haka suka gudanar da bukin sallar su cikin kwanciyar hankali. Ƙarfe Shidda suka tashi daga aiki, lokacin da suka fito jidda ta nufi Motarta ta wuce gida, Sultana ta nufi motar,ta tada motar taƙi tashi kusan minti 20 tana abu guda gabaki ɗaya a gajiye ta, wayar Abba ta kira ta sanar dashi, daga can ɓangaren Abba yace mata baya gida, Su Haydar ma basu dawo ba ga hadari kuma gari har yasoma duhu mamana nasan Abin hawa zai Miki wahala, bari naki Sultan idon bai wuce ba ya dawo dake gida, gaban Sultana ne yayi Masifar tsinkewa tana ƙoƙarin magana Abba ya kashe wayar, a hankali ta ɗaga kanta ta kalli sama hadari ta ko'ina yana batun haɗewa, A ɓangaren Sultan ko yana ƙoƙarin barin Office kiran Abba ya shigo, Cikin girmamawa ya gaida Abba," Yauwa Sultan ƙanwarkace motar ta taƙi tashi shine nake son ka maida da gida...Shiru Sultan yayi tun lokacin da Abba ta ambaci sunan Sultana ya nemi nutsuwarsa ya rasa sam baya. Son wata alaƙar da zai haɗa sa da ita..Jin yayi shiru Abba yace ,"Kana jina Sultan?" da sauri ya ce ,"Ehh Abba" "Yauwa na gode". "Ba komi Abba" A hankali ya sauke Nannauyan Numfashi kana ya nufi farfajiyar Asibiti, A natse ya nufi matarsa ya shiga Cak Sultana ta tsaya ganin motar Sultana tafe nanda nan ta nemi natsuwar ta ta rasa A hankali ya yi parking kusa da ita, buɗe bayan mota tayi ta shiga. lumshe idanu Sultan yayi ba tare da yaja motar ba. Sun kai kusan minti huɗuahaka ita batace komai ba, haka zalika shima baice komai, har a fara iska da ƙarfi, ɗago Idanunsa yayi dai-dai lokacin da itama Sultana ta ɗago Idanunta ta kalli madubin cikin motar, idanunsu ne suka sarƙafe cikin na juna. Cikin sanyi Muryar da bai san yana da ita ba,"Halam Ni direban ki ne ?" Jikinta har yarawa yake ta fito , gaban motar ta buɗe ta shiga dai-dai lokaci Ka ɓarke da ruwa kamar da bakin ƙorya, Suka.fice a guje .Tunda suka shiga motar babu wanda yace da ɗan Uwansa komai kowa da irin tunanin da yake Aransa kana ga abin hawa da suke giftawa da ɗan gudu kasancewar maghariba ta gabato gashi har yanzu ana tsula ruwa... jinginar da bayanta da jikin kujeran zuciyarta na bugawa. Suna cikin tafiyar aka wani walƙiya mai masifar haske , Atsorace tace.“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.Ta gefen ido ya kalleta Sultan ya Kalleta. Gudu Sultan yake sosai, Sultana ko duk ta tsorace,cikin Suɓutar halshe tace "Don ka rage gudu bana so!!" Ƙala Sultan baice mata ba. Ƙawar da kai gefe Sultana tayi tare da watsa masa Harara kana ta murguɗa baki, A hankali tace ,"Mugu kawai" Cikin Wata irin murya yace. "Idan kika sake tura min bakin nan, zan tsikeshi🤣" haka dai sukaci gaba da tafiya Suka cikin tafiya aka saki wata irin tsawa mai firgitarwa Cikin wani irin tsananin tsoro Sultana ta saki ƙara mai razanarwa tare da faɗawa jikin Sultan ta mishi wata irin Runguma Wani irin bugawa zuciyarsa keyi da masifar ƙarfe yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa ƙoƙarin taka burki yake amma ya gagara saboda yanda ta takure jikinta ajikinsa ta ƙamƙamesa, ta kife kanta afaffaɗan ƙirjinsa, . Wani irin masifaffen tsuma jikin Sultana keyi yayin da numfashinta ke fusga saboda tsananin tsoro Allah ya sani tana masifar tsoton tsawa hakan yasa ta sake ƙanƙamesa tamkar zata tsaga jikinsa ta shige ciki.cikin wani irin yanayi ya ya buɗe hannayensa ya rungumeta da azaban karfi tare da taka burkin motar da ƙarfi, Rungumeta yayi da masifar ƙarfe kana ya cusa kansa atsakanin kafaɗarta da wuyanta. Lokacin da aka kuma sakin wani irin tsawa, Atake zuciyarsu ya buga da mugun ƙarfi , Sultan wani irin rungumeta yayi da masifar ƙarfi yana mai sakin Nannauyan Numfashi. Sultana numfashi ta shiga saukewa akai-akai tare da sake manna kanta ajikin damtsen hannunsa. Ahankali ya juya ya kalli yanda rabin jikinta ke kansa cikin wata Sanyayyar murya, "Sultana!! Wannan shine karo na biyu arayuwarsa da ya taɓa kiran sunanta,"Sultana!! ƙara lafewa tayi a jikinsa, tana shaƙar dadɗan ƙamshinsa turarensa mai sanyi, Buɗe idanunsa yayi da kyar murya a sanyaye ya ce, "sauka a jikina!". Cike da tsoro da kuma sanyin jiki ta janye jikinta daga garesa kana ta sauƙe ajiyar zuciya... "Nidai tsoro nake ji, kayi sauri ka maidani gidan mu" Harara ya watsa mata kana ya cigaba da Driving ɗin sa batare daya tanka taba yana isa ƙofar gidansu yayi Parking cikin sauri ta buɗe motar ta fita da gudun Gaske, kai tsaye ya wuce gida saboda har yanzu ruwan basu ɗauke ba ....jiki a mace.. Sultan ya wuce gida.... ________★★★★ Bayan sati ɗaya, suna zaune a palon Abba ya killi Kaka cikin sanyin Murya yace ," Mama ya batun maganar Auren Sultana naji shuru, gashi Nuraddeen kullum sai ya yi min maganar, Kaka ta sauke Ajiyar zuciya kana tace ,"Nima maganar ta tsaya min rai, Saida kuma matsalar da Sultana ɗin ke mafa dashi, ya kama abita cikin lalama," Haka ne Mama!" Saboda matsalar yasa nake goyen baya ta Aure Sultan shine zai zame mata jigo a rayuwarta kasan cewar Likita! "Wannan gaskiya ne. Suna tsaka da Magana Sultana ya shigo Palon, "Mamana zonan" a hankali Sultana ta nufi wajen su ta zauna, Abba ya fesar da Numfashi mai ɗumi . Palon yayi shiru, kowa ya maida hankalinsa ga Abba yafara nasiha, sannan yaɗora da faɗ'in wannan zama yashafi ki Sultana, Batun Auren kine da Sultan ina maganar ta kwana ?" Cikin raunan'nanyar murya tace ,"Abba wlh banza Aurenshi ba! Abba wlh ɗan isk.....Abba ya yi sauri ɗakarta da ita ta, fashewa da kuka mai tsuma zuciya Sultana ta yi. "Abba wlh bana sonsa Abba ina da wanda nake so!!! ABBA ya dubeta rai Ɓace, waye ne zaɓin baki? Kuma yasa baki taɓa gabatar da shi ba ?"Kintaɓa yi masa magana? Wanene zaɓin naki? Kin taɓa sanar dani kinada wadda ki keso ne? Kai ya Sultana a ƙ'asa tana sauke numfashi da k'yar, saboda damuwar datake ciki, gawani Abu dayazo ya tokare mata mak'oshi saboda tashin hankalin, ta girkiza kai Shiru yayi bata komaiba.cewa ƙanana. Wannan ya k'ara hasala Abba, ya ce Sultana kabud'e baki kayi magana ta ɗ'ago idanunta jajur tazubasu kan Abba, Babu wanda ya lura da halinda yake ciki . Sai ganinta kawai sukai kwance ƙasa wanwar. A take falon ya sake rikicewa gaba ɗaya. Duk suka rufu a kanta ana zubama ta ruwa dan son aga ta farfaɗo. Sai dai kuma ko motsi batai ba balle suyi tunanin dacewa. Kaka ta aza Hannu saman kai tana faɗin ,"Shike nan ta mutu!!!"✍️ (Nima na aje biyo ina hawaye )😥 Yanzu Aka soma wasan kudai ku zance da Sadeeya Ka'oje don jin ya zata kaya!!!. _More comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce ✍️* *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 33-34* _______Hankali a tashe suka wuce da ita Asbiti, An musu ƙarɓar gaggawa saboda halin da Sultana take ciki. yanda suka ga likitocin na kai kawo ɗakin da aka saka Sultana hankalinsu ya daɗa tashi sosai. Duk kuma sanda wani ya fito suka tambaya baya basu amsar komai yake wucewa da sauri. Tun suna ɗaukar al'amarin ƙarami har suka fahimci yanada girma sosai, dan Doctors har huɗu sun ƙaru bayan na farko. Sai faman yin ƙus-ƙus kuma sukeyi a tsakaninsu...." Cikin ƙarfin hali Abba ya dubi Dr yana faɗin, "don idan yarinyar nan ta rasa ranta ne ya kamata ku sanar mana, dan kunata sake ɗaga mana hankali da rashin cewarku komai da kai kawon nan naku". Dr Sadiq ne ya tada kansa ƙasa cikin girmamawa yace, “Ai mana afuwa Ranka ya dade, ba muna ɓoye muku komai baneba. Kawai muna akan aikine shiyyasa, amma insha Allahu zakuji komai nanda ƴan mintuna kaɗan" Shiru wajen yayi babu wanda yace komai, sai dai a zukatansu sam basu gamsu da zancen Dr Sadiq ba. Kaka dake zaune a hankali ya jingina jikin kujera ta lumshe.ta faɗa duniya tunani. Tun da suka iso Asbitin har zuwa yanzun zuciyarta a ruɗani take. Motsin da taji a kusa da ita ne ya sakasa ta buɗe idanunta da ƙyar.Abba ne ta gani tsaye. "Mama muje gida ki huta ko" Duk da halin da take a ciki itama sai da tausayinsa ya kamata jin a yanda yayi magana. Tasan ƙarfin hali kawai ya keyi tun jiya akan al'amarin nan, amma shima a ruɗanin yake. Hannunsa ta kamo da ɗayan hannunta, ta Zaunar da shi. "Abdullahi inaji a jikina karon nan mutuwa Sultana Zatayi , a wannan karon zuciyata bazata iya ɗaukar wannan al'amarinba!!" Ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Shima sai ya ji hawaye na ziraro masa batare da ya shirya yin hakan ba. Dan zuciyarsa ta karye gaba ɗaya. Ya rungumeta a jikinsa sukayi mai isarsu kafin ya ɗagota yana kallon yanda take faman dafe kanta dake mugun sarawa. Haka sukaita hawaye har sai da baba Abba ya fahimci Kaka na neman rasa numfashin ta. Sake ruɗewa yayi ya shiga girgiza ta jikinsa na rawa. Yama rasa miya kamata yay mata, kiran sunanta kawai yake iya yi da iya ƙarfinsa. Mami ta ƙara so wajen su da saurin tare da rungume Kaka tana kiran Sunanta.... da saurin Abba ya kira Dr suka duba kaka Allurar Bacci akayi mata kana nan take bacci ya yi Awon gaba da ita.... Wuraren 12:40am Doctors ya buƙaci ganin wasu a cikin su Abba. suka shiga office ɗin, aka bar Kaka kawai a ɗakin. Dr Halima ta ɗanyi gyaran murya tana kallon sauran ƴan uwanta uku likitocin. Kawuna suka ɗaga mata alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta. Cike da girmamawa a garesu tace, “Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku damu ba”. Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da faɗin, “Maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi ƙarfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na'urori kafin a samu mafita. Muna Bukatar Babban likita da zai dubata, matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin hankalin musamman da ya kasance yana Aiki a Asbitin kansa dan haka munyi ƙoƙarin nemansa dan muji ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ɗaga wayar ba, sai dai mun kira ɗaya daga cikin ya ransa yanzu haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar tata dan shima babban likita ne”. Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka karɓa mata da “Allah yasa a dace” tare da musu godiya sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu'ar dacewa a cikin ransa... Mami ta kalli Abba Murya a raunace tace ,"Abban Haydar bazu kaita Asbiti n Sultan ba inaga haka zaifi" Murya a disashe Abba ya ce, saidai mu bari mu ga yadda hali Zaiyi!!" wasa Wasa har gari ya waye amma babu labarin likitan da ake tsumayen jira. Su kuma likitocin basuce musu komaiba. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum suna addu'oi a zukatansu har tsahon wani lokaci. lokacin sallar Azzuhur ne ya sake tadasu suka nufi massallaci, bayan an idar da salla suka sake fitowa suka sake zaman jiran tsammani. Mami ta kalli Abba cikin Sanyi Murya tace ,"Abba Haydar ya kamata Mama ta koma gida ta huta tana buƙatar hutu sosai, Abba ya sauke Nannauyan Numfashi kana yace," Na kira Haydar yazo ya kaita gida, yana rufe bakinsa Haydar na isowa, fuskarsa cike da damuwa ya gaida iyayen nasa,da kyar Abba da Mami suka shawo kan Kaka ta yadda suka wuce gida.... Bayan ta fiyarsu lokacin ɗaya Abba da Mami suka sauƙe Nannauyan Ajiyar zuciya, haka suka shafe tsawon Awa ɗaya zaune a wajen ba wani labari.... "Abban Haydar da zaman jiran tsammanin nan da muke da mun wuce Asbitin Sultan tunda duk private hospital ne. "Ina ga haka za'ayi tashi mu tafi" Abba na ƙoƙarin miƙewa zuwa office ɗin Doctor Halima, sai kuma ya hangota tana fitowa da ga office ɗin nata fuskarta ɗauke da murmushi. Kafin ya samu damar mata magana yaga ta nufi ƙofar fita da hanzarinta. Kamar zai bita sai kuma ya fasa, ya cigaba da tsaiwa a wajen yana jiran ganin ko zata dawo wajen su... Tsayuwar tasa tayi dai-dai da shigowarsa cike da takunsa na ƙarfi da lafiya, wanda idan baka saniba zaka iya ɗauka tsabar isa ce da izza ke ɗawainiya da shi. Amma sam ba haka baneba, halittar tasa ce kawai haka. Kansa duƙe yake sakamakon file ɗin Sultana da ke a hannunsa yana dubawa. ga wani irin ƙwarjininsa da cikar haiba, Kamar kullum sanye yake cikin suit, na yau ɗin sun kasance Black color, Dr Aryan na gefensa Doctor Halima na daga gefen damarsa, da alama bayani take masa akan matsalar. Sai Nurse Yusra dake ɗauke da jikkarsa a hannu, da Doctor Nasir da wasu likitoci biyu da Nurse guda biyu na biye da bayansa. Har suka zo suka gitta Abba bai ga fuskarsa da ƙyau ba, dan har lokacin kan nasa a sunkuye yake ga file ɗin. A dai-dai ƙofar ɗakin da Sultana ke ciki suka ja birki, su Abba da duk suka zuba nusu ido duk suka miƙe, sai dai kafin wani cikinsu yace wani abu. Ya tura ƙofar ɗakin ya shige har lokacin hankalinsa nakan file ɗin...... Daga shi sai Dr Halima da Dr Aryan suka shiga . A hankali ya ƙarasa gab da gadon da Sultana take kwance sannan ya ajiye file ɗin ya kai dubansa gareta, bai ganeta ba sam, saboda na'urar da aka saka mata mai taimakama numfashinta fita. Ya ɗan ranƙwafo kanta kaɗan ya kai hannu ya zare na'urar mai haɗe da oxygen. Ba ƙaramin bugawa zuciyarsa tayi ba da sauri ya janye Glass ɗin idonsa ya ƙare mata kallo. da sauri ya maida na'urar saboda ganin yanda ƙirjinta ke sama da ƙasa da sauri-sauri ga jikinta na karkarwa har gadon kansa na motsawa. Luuu ya ɗanyi da idanunsa ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta. murya a cinkushe ya dubi Doctor Halima a ɗan faɗace ya ke faɗin, “Anyi matuƙar sakaci da lafiyar yarinyar nan da har take neman shima matakin ƙarshe, A Rayuwarta 😥 (Allah ya baki lafiya Sultana)😥 Cikin ɗauriya yace ," Su waye suka kawo ta?" duk suna waje, Baice komaiba, ya dai sake kai dubansa ga Sultana, sai kuma yayi saurin ɗauke kansa batare da nasan dalilin yin hakan ba. Juyawa yayi zai fita. Doctor Halima tai saurin ɗaukar file ɗin da ya ajiye suka fita.... Kai tsaye ya wuce Babban Office ɗin ta aka tanada saboda manya baƙin lokitoci ake gaiyata aiki... komai tsab yake, dan tunda Dr Halima ta tabbatar da zuwan nasa ta saka aka sake tsaftace office ɗin duk da dama ƙa'ida kullum sai an share an goge. Gudun a girshe su... A hankali ya zauna sannan ya kunna Computer ɗin da ke a gaban sa . Yanda yayi matuƙar zuba idanunsa ga Computer ɗin zai tabbatar maka abunda yake yi a ciki yana da matuƙar muhimmanci. A haka Dr Halima ta turo ƙofar bayan tayi knocking ta shigo, Batare da ya ɗago ya kalleta ba yace, “Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ƙaramin Aiki yanzun, dan haka ku shiryata zuwa theatre room”. Ya miƙa mata file ɗin gabansa yana cigaba da faɗin, “Wannan mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta Kuma dole ɗaya da ga cikinsu ake buƙata kawai”. gyaɗa masa kai da faɗin “Okay sir”. Daga haka ta fice... Cikin girmamawa ta ƙarasa wajen su Abba Fuskarta ɗauke da murmushi tace, “Congratulations, mun samu nasara babban likitan da ganinsa ke da matuƙar wahala ya amshi gayyatarmu”. Cike da jin daɗi suka shiga faɗin "Alhamdulillah Allah mun gode maka!!" Da ga haka ta buƙaci magana da Abba Babu musu ya bita office. Bayani tai musu akan ƙa'idar saka hannu da Dr Sultan ya sanar mata, jikin Abba bar karkarwa yake ya ƙarɓi file ɗin ya saka hannu..... Bayan Abba saka hannun da Dr Sultan da wasu likitocin biyu sai Dr Halima ta uku suka shiga theatre room da Sultana da ko maƙiyinta ya ganta a wannan lokacin sai ya tausaya mata.... (Dr Sulta Allah yasa ayi aikin cikin nasara!!!💔🤲 Tsawon lokaci suka ɗauke a theater room ɗin Sai kusan ƙarfe takwas na dare dai-dai su Sultan suka fito, duk su Abba suka miƙe tsaye don son jin yaya ake ciki? Su Doctor Halima ne kawai suka tsaya musu bayani, dan Sultan yana ɗakin bai fito ba... A tare suka shiga faɗin Alhamdulillah Koba komai sunɗan sami kwanciyar hankali duk da ba cewa akai Sultana samu sauƙi ba, Su Dr Halima da suma fuskokinsu ke nuna alamar nutsuwar jin daɗin yanda aikin ya kasance suka sanar da su zasu iya tafiya gida. Dan Doctor yace babu wanda zai iya ganin Sultana a yanzu, hasalima ba'a buƙatar kowa a gareta. Duk da ba haka suka so ba sun gamsu da bayanin Doctor Sadiq... "Kulsum mu tafi gida ko zuwa anjima sai Mudawo.... Jiki a mace suka wuce gida ... ______★★★★★★_______ Abba ya kalli Kaka Ɗan Murmushin ƙarfin hali tai masa ta duƙar da kanta. Shima sai ya ɗan murmusa cike da jarumta ya kirayi sunanta a hankali. ɗagowa tai ta sake kallonsa. Muryarsa a sanyaye yace, " an kammala Aiki cikin Nasara Mama, ki Kwantar da hankali ki!!" inason mu ɗauƙi komai matsayin jarabawa, Ƙwallar da suka cika mata idanu haɗiye da ƙyar, ta maida kanta ƙasa dan karya gani tana faɗin, “Allah ya bata lafiya!!" “Amen ya rabbi” ya amsa mata shima. Shiru ɗakin yayi kowa na nazari a zuciyarsa,. Washe gari tunda safe Sultan ya iso Asbitin ko da yaje ɗakin da Sultana take har yanzu kwance take tana bacci cikin wani irin yanayi. tsowan mintuna goma Sultan na tsaye yana kallonta... A hankali ya sauke Nannauyan Ajiyar zuciya kana ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce gida... ★★★★★★★ sai Kusan ƙarfe Ukku na rana Sultana ta farfaɗo. Dr Sadiq dake tare da ita dan duty ɗin rans ne da shi yay saurin kiran Dr Sultan ya sanar dashi, Cikin ƙanƙanen lokaci ya shigo asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da baƙin Glasses da yay masifar sake fiddo masa ƙyawun fuskarsa da kwarjinin saTunda ya shigo asibitin baiyi magana da kowa ba. Ko gaidashi da Nurses suke da sauran ma'aikatan hannu kawai ya dinga ɗaga musu kansa a ƙasa ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ɗin.... Ɗakin da Sultana ke a kwance ya tura a hankali ya shiga da sallama ƙasa-ƙasa. Dr Sadiq da Nurses guda biyu dake a tare da shi suka amsa suna ɗagowa. Da girmamawa Nurses ɗin suka risina suna gaishesa. Batare da ya amsa musu ba suma ɗin ya ɗaga musu hannu kawai. Kafin ya miƙama Dr Sadiq hannun suka gaisa.. A hankali ya juya kansa zuwa ga sashen da kanta Sultana ya ke. Ya ɗan ranƙwafa kanta ƙaɗan ya janye wani igiyan na'uran dake a gefen kanta gab da kunne. Yanda ƙamshin turarensa ya buga mata hancine ya saka ƙirjinta harbawa. Buɗe idanun nata tayi da ƙyar saboda bala'in nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Sultan ya dubeta shima yana ƙoƙarin zare glasess ɗin idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ɗin dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara ganesa ba. Wani irin juyawa kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ƙarfe, zabura tayi, ta yunƙura zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, "Wayyooh kaina!’. Sultan da shima zuciyar tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ɗauke idanunsa daga kanta cike da basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba. Yanda jikinta ke wani irin ɗan karkarwa ga kanta data riƙe da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka Nurses ɗin nufarta da sauri tare da Dr Sadiq Sultan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana kallonsu ne ta ƙasan ido. Yanda duk suka so Sultana ta nutsu hakan ya gagara, dan ganin Sultan ɗin ya sake dawo mata da komai, “Live her.” ya faɗa a hankali tamkar ba shine yayi maganar ba. Baya Nurses ɗin suka ja domin cika umarninsa, amma tausayin Sultana fal ransu. Dr Sadiq ya yi ƙoƙarin riƙo hannun Sultana data riƙe kanta da shi gam ya keyi. A bazata yaji an riƙe masa hannun lokacin da yake gab da ɗorasa saman nata. Sosai mamaki ya kama Nurse's Sultan ya fiske abinsa tare da sake tsuke fuska tamkar ba shine ya aikata ba. Sai tura tattausan nasa hannun yayi ƙarƙashin kan Sultana da dogon gashinta ke a tsefe duk ya baje a saman filon. Da sauri ta sake buɗe idanunta, dan kusancin da suka samu gaba ɗayansu neman haifar da barazana yake a bugun Zucikatan su, cikin rawar ji kinta daya ƙaru ta sake buɗe baki zatai magana, sai dai kuma hakan kamar da wuya a gareta. Dan saɓanin yin maganar sai hawaye sharrrr!! Suka fara bin kumatunta. Yanda damshin ruwan hawayen nata suka sauka bisa fatar hannunsa ne ya sakashi lumshe idanu yana wani jan numfashi da sassarfa. Sai kuma a hankali ya janye hannun nasa daga cikin kanta dama jikinta gaba ɗaya ya ɗan matsa baya yana Lumshe ido.. idanu da ya zubama Sultana da jikinta ke Karkarwa a hankali, har zuwa yanzun kuma riƙe take da kan nata da duka hannayenta tana ɗan mirginashi bisa filon. Kusan mintuna biyu yana kallon nata, kamar yanda su Doctor Sadiq ke kallonsa a tsorace, kafin ya ɗauka file ɗin Sultana yaja da baya daga gaban gadon Ya shiga buɗe takardun dake a ciki file ɗin yana bin rubutun ciki daki-daki da nazari a nutse. Su Dr Halima duk sun rikice, sai dai sun kasa fahimtar wane taimako ya dace su bata ne. Dawowar da yayi gaban gadon riƙe da file ɗinne ya sakasu zuba masa idanu su duka. Ya ajiye file ɗin a saman drawer'n gefen gadon da take sannan yayi magana a ɗan kausashe yana kallon Sultana " ki nutsu" wani irin masifar zabura zata miƙe. Cikin sassarfa Dr Halima ta ƙaraso ta tareta. Da ƙyar ta iya dannata saman gadon ta kwantar, duk da hakan kuma fisge-fisge takeyi har yanzun. Batare da Sultan , razananniyar ƙara da ta amsa duka Word ɗin, Shiko yana tsaye ko gezau, duk da kuwa ƙarar tata jiyay tamkar zata tarwatse kansa. Lumshe idanu yayi ya buɗe a hankali, a hankali ya nufi wajen Sultana ya maida saman gadon, a kallo ɗaya zaka fahimci batama yin numfashi. Sai da yaja bargo ya lulluɓa mata sannan ya maida mata duka na'urorin da ke manne da kanta ɗazun. Juyawa yay yayima su Dr Sadiq alamar su fita. Suna gaba yana biye dasu riƙe da file ɗin Sultana... a ƙofar ɗakin ya tarar da Abba da Mami tsaye sunyi zugum, sosai Abba da Mami sukayi mamakin ganin sa, basuyi tunin shine Dr da aka gaiyata ba, "Abba mu tafi Office" kai tsaye suka wuce Officer...." "Sultan pls ina bukatar ganinta Sultana!!" Sultan da yake wani irin jin kunyarsu da nauyinsu ne yay musu rakkiya har ɗakin da Sultana ke kwance. Ba ƙaramin tashi hankalinsu yayiba ganin yanda aka jajjone kan Sultana da na'urori, Mami harda hawayenta. Basu wani jimaba suka fito. Office ɗin Sultan suka sake komawa. Inda ya sake musu bayanin komai dalla-dalla a nutse. “Abba Alhamdulillah ta farfaɗo, sai dai kuma.......” Sai yay shiru kuma. Cike da dauriya yace, “Sultan ! Sai dai me? Karkaji komai kai min bayani akan duk halin da Sultana take.. Abba tanama da ranta, sai dai dama bawai mun mata aikin ainahin matsalarta bane kamar yanda Dr tai maka bayani ɗazun kafin mu taɓata. Aikin da mukai mata zai bata taimakone kawai wajen hana ƙwaƙwalwarta goge komai da take barazanar yi, sannan zai sassauta mata raɗaɗin da takeji a duk lokacin da matsalar ta motsa, insha Allahu zai hana ta iya rasa hankalinta. Nayi tunanin aikin zai bata kariyar da zamu iya ɗaukar kamar watanni ai mata aikin gaba ɗaya, dan dole sai an fita da ita waje, a ƙasarnan bamu da isassun kayan aikin, hankalinsu nakan abinda ya dace suyi bane. To a yanzu dai matsalar dana fahimta dolene ai gaggawar yimata aikin koda nan da wata ɗaya ne insha Allahu, inba hakaba zata iya rasa hankalinta a koda yaushe”. Ɗan rumtse idanu Abba yayi ,cikin jarumta yace, “Shikenan Sultan , duk yanda kake ganin ya kamata akai kayi tunda aikinka ne, . Sosai suka gamsu da bayaninsa, wanda a take duk murmushi ya baibaiye fuskokinsu, suka shiga saka masa albarka da jera masa addu'oin fatan alkairi. Har wajen mota ya rakosu, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki, dan yau a asibitin zai sake kwana saboda Sultana zata iya farkowa a kowane irin lokaci wani Abokinsa dake India ya kira Yana buƙatar a aiko masa da wasu allurai ne masu matuƙar tsada da zaima Sultana amfani da su. Kuma yana buƙatar sune da gaggawa daga nan zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Bayan sun gama maganar Sultan ya yi mashi transfer na maƙuddan kuɗi........✍️ _More Comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce ✍️* *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 35-36* ________ Washe gari, Wuraren ƙarfe Huɗu sakon Sultan ya iso, kai tsaye ya wuce Airport ya karɓi saƙon Ya nufi ɗakin da Sultana take ya nufa. Dr Sadiq na biye da shi ɗauke da wata madaidaiciyar bag. A ciki ya samu Nurse ɗin data gama gogema Sultana jiki. Da girmamawa ta gaida shi, Dr Sadiq kuma ya ajiye bag ɗin ya fice. Matsawa yay gaban gadon lumsassun idanunsa akan Sultana da fuskarta tai wani irin fayau. ta ƙara haske sosai Ya kafe Laɓɓanta da sukayi wani irin jajur gwanin sha'awa, gashi taɗan tsuke bakin ya sake komawa ɗan mitsitsi, Ajiyar Zuciya sauƙe kana ya janye idanunsa daga kallonta, ’ ya gyara kujerar gefen gadon ya zauna tare da ɗaukar bag ɗin da Dr Sadiq ya ajiye ya buɗeta. Madaidaicin abu ya fiddo cikin kwali mai kama da kula, ya buɗesa sai ga ƙanƙara a sama tanata huci. a ƙasan ƙanƙarar ya zaro kwalaben alluran kusan guda guda bakwai ƴan ƙananu, zaune da ƙafafunsu. Sai da ya gama duba takardar dake a cikinsu kafin ya maidasu ciki ya fiddo ɗaya kawai. Miƙama Nurse ɗin dake a ɗakin yayi, murya a daƙile yace “Kiyi mata allurar nan yanzun nan”. Amsa tayi da girmamawa. A gabansa ta buɗe syringe ta kwashe ɗan ruwan allurar da ko ganinsa bama ayi sosai cikin syringe ɗin. Shine ya nuna mata a inda zatayi. Nan take wani irin mahaukacin zufa ya fara tsatstsafowa a kowacce ƙofar gashi ta jikin Sultana Kafeta da kallo Sultan dake zaune ƙafa kan ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji yayi. Yanda take wani irin mutsu-mutsu ya sakin wani tattausan murmushi daya ƙawata cikar haibarsa da kwarjinin Ya ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta yana jan ajiyar zuciya. Bayan Isha'i Su Abba suka zo gabaki ɗayan su, kamar ko yaushe basu duka aka bari suka shigaba. Abba ne kawai . Sai Kaka da Mami. Basu jima a asibitinba suka dawo gidan, cike da tausayin Sultana. Bayan ta tafiyar su bada jimawa Jidda ta iso, da kyar ta shawo kan Dr Sadiq ya barta ta ga Sultana, sosai Hankalin Jidda ya tashi ganin halin da Sultana take ciki... Bayan kwana Biyar, tsawon kwanakin nan Daddy bai san mike faruwa, Abba bai sanar dashi ba, Sultan ɗin ma bai gaya Mishi ba, Abba ya yi hakan ne saboda ya san halin Daddy yanzu sai yace sai an fitar da Sultana waje don nema mata lafiya..... Alhamdulillahi cikin hukuncin Allah Sultana ta farfaɗo. cikin hankalinta, sai dai ramar da tayi dolene ta baka tausayi, hancin nan ya sake tsaho. Haka ma ta ƙara haske idanun sun fita da ƙyau masha Allah . Ramarma sai ta sake fiddo mata da ƙyawun nata. Ba ƙaramin farin ciki ahalinta suka tsinci kansu ba. Dan tunda farar safiya aka fara tururuwar zuwa ganinta. Washe gari Sultan ya basu Umurnin sallamarta..dan insha Allahu ya tabbatar ta dawo cikin hayyacinta. Zata kuma lallaɓa jikin har lokacin da za'a fita da ita ai mata aiki a ƙwaƙwalwarta ɗin... Suna isowa gida Kaka ta sakata ta shiga wanka da ruwan data haɗa mata mai ɗumi. Yanda take jin jikinta wani irine yasata nutsuwa sosai tai wanka mai ƙyau, dan ta kwashe tsahon lokaci a ciki kafin ta fito, Abinci na musamman Kaka ta haɗa mata bayan ta gama ci ta bata maganinta kana ta kwanta nan take bacci ya yi a won gaba da ita.... Sai bayan la'asar Sultana ta tashi. Wanka ta sakeyi da ruwa mai zafi tai sallah. Su Mami sai nan nan suke da ita duk abinda take so shi aka mata, Hakan yasa jikinta keta ƙara warwarewa. Bata fita ko ina, ko yaushe tana ɗakin Kaka . Sai dai taci ta ƙoshi tasha magani tayi barci. Wani lokacin Meena da Nana kan shiga su tayata hira. Bayan sati ɗaya, Still Abba ya sake tunkar Kaka da maganar Auren Sultana... Sultana na toilet Nana ya shigo ɗakin Su,"Anty Sultana Abba na kiran ki. Da Sauri Sultana ta fito da wanka ta zura dogon hijjab akan zanin wanka ta fita kiran da Nana sake zuwa tai mata. Ta iske kowa ya hallara ita kawai ake jira, zuciyarta cike da mamakin taron ta ƙarasa garesu. Kusa da ƙafafun Kaka ta zauna tana gaishe da iyayen nata. Duk suka amsa mata da kulawa suna sake tambayarta ƙarfin jikinta. "Alhamdulillahi Naji sauƙi sosai!" A kusan tare suma sukace Alhamdulillah "Allah ƙara sauƙi, "Amin Abba" Abba ne ya buɗe taron da addu'a kamar yanda shari'a ta koyar da mu. Bayan sun kammala Kaka ta fara magana akan abinda ya tarasu. "Sultana! Har yanzu dai muna kan maganar Aurenki da Sultan, Wani irin faɗuwa gaban Sultana yayi, ta dubi Abba. Nan Kaka ta soma yi mata Natsiha cikin ruwan sanyi, ta yadda Abun zai zo musu da sauƙi.. Zuciyarta na wani irin harbawa ta sake duban su Abba Yanda duk suka zuba mata idanu cike da tashin hankali sai itama suka sake ɗaga nata hankali ƙololuwa. Saurin maida kanta ƙasa tai tanajin anya kuwa zata iya?. A take rauninta ya sake bayyana bisa fuska tamkar yanda suma duk suke a raunane zukatansu na rawa da barazanar son faso ƙirazansu su fito......... "Mamana ke muke saurare daure ki faɗa mana abinda ke a ranki kinji, Kuka Sultana ta fashe da shi, bakinta na sake rawa tace, “Abba Abbah ni Nas nake so!!!.. "Sultana Abba ya kira sunanta da ƙarfi. Bayan ta ɗan zabura kaɗan ta ƙara mannewa da jikin Kaka . Sai ɗan girgiza kanta take hawaye na zubo mata da sauri-sauri... Cikin sanyi Murya Mami tace ," Abban Haydar Abita a hankali kasan matsalar dake tare da ita" "Sultana ki kwantar da hankalinki kinji, cewar Mami, Kanta ta jinjina tana share hawayenta. Ta ɗago a hankali ta zubama su Abba dake kallonta idanun. Kowannensu a kallo ɗaya zaka fahimci roƙonta sukeyi da idanu ta zaɓesa. Hakanne ya sake saka zuciyarta sake raunana. Cikin rauni Murya tace Abba na Amince zan Au..... Sai kuma ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Fusakar su ɗauke da murmushi, suka shiga sanya mata Albarka... "tashi kije mun gama da ke. Ki kuma share waɗan nan hawayen ki kwantar da hankalinki, dan munsan abinda mukeyi”. Kai kawai ta jinjina mata tana miƙewa. Batare da ta sake duban inda su Abba suke zaune ba ta fice a falon jikinta duk a sanyaye. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take.. Sultana na zaune a ɗakin kaka tana sharɓar kuka, ahaka Kaka tashigo ta isketa. Da sauri tak'arasa gareta tajawota jikinta ta rungume, tana mai lallashinta. Kiyi hak'uri Sultana, nima bazan yarda a cutarmin dakeba, Sosai Kaka ta lallesheta tare da Kwantar mata da hankali... _______★★★★★_______ Sultan Komai yinsa yakeyi cikin wani yanayi, kokad'an babu alamar d'igon walwala tattare dashi, ga d'unbin kasala daya tashi da ita ayau, hakan tafarune saboda k'arancin barci dabai samuba a kwanan nan , saboda Feshin lafiyar Sultana, siririn tsaki tareda yaye towel d'in dake kugunsa bayan yasaka boxer, yad'an Mirza mai kad'an ajikinsa tareda feshe ko ina Na jikinsa da body spry d'insa mai dad'in k'amshi, yasaka farar vest sannan yasaka Shuit , yayi k'yau sosai, Wani turaren yakuma d'an fesawa kad'an, sannan yajawo takalmansa da safa yazauna kan sofa yana k'ok'arin sakawa. Knocking d'in k'ofarsa da akeyi yasakashi jan tsaki, da k'yar yabud'e baki yace ashigo. Ihsan ce d'aukeda tire Wanda aka shirya masa break d'insa. "Ina kwana Ya Sultan Cigaba yayi da saka takalmansa batareda yad'ago ya kalletaba. Taja table ta ajiye."Ina kwana" Yanzunma bai d'agoba ya amsa da lafiya. Duk atsorace take, jin alamar tana tsaye akansa yasakashi d'ago jajayen idanunsa yazuba mata, cikin daburcewa tace dama um..um.... Mommy ce tace akawo maka break fast naka, . Baice komaiba yamaida kansa yana k'ara gyara igiyar takalminsa. Da sauri Ihsan tabar d'akin, Koda yagama bai kalli abincinba, yak'arasa gaban madubi yad'auki agogonsa yasaka, sannan yad'auki jakkar lap-top nasa yanufi k'ofa. Sai kuma ya dawo, tareda jawo table d'in da Ihsan ta ajiye break fast d'in gaban sofa. Tea kawai yahad'a kad'an yasha, Dan bayajin cin komai ayanzun. Yana gamawa yamik'e yafice. Babu kowa afalon, yana ƙoƙarin haurawa Sama Mommy ta fito daga Kicin riƙe da Basket ɗinsu Salma da Salim, dai dai lokacin suka suka fito daga ɗakin su, riƙe da School bag ɗin su, "Ya Sultan Good Morning!" "Morning kun tashi lafiya?" "Lafiya lau Ya Sultan" "Ya Sultan jiya na ganka a mafarki kaida Anty Sultana kuna riƙe da baby tana kuka, kace Anty Sultana ta goya taƙi wai tagaji bayanta ciwo yake, shine kai kuma ka goya Baby! Ya Sultan ina son Baby tana da kyau sosai!" Tunda Salma ta fara magana Mommy ta kafeta da kallonta tana Murmushi, Sultan ya Lumshe idanunsa kana ya buɗe a kan fuskar Salma dake Murmushi har yanzu.... "Mommy Ina kwana?" "Lafiya lau Ya Babba!" Ina fatan kayi breakfast ɗin ka?" Kai ya gyaɗa mata. Kana yace "Ina Daddy?" " Ya tafi wani jana'iza wani Makwoƙocin mune ya rayu a tsuhuwar Unguwarmu."Ayya Allah ya jikan musulmi!" ",Amin" "Zan wuce Mommy! "Allah ya kiyaye,"Amin yana fita bada jimawa Su Salma suka wuce School... __________★★★★_________ Saida Kaka tayima Sultana jan ido sannan tad'an saki jikinta, Duk Wanda yaga halin da Sultana take ciki tun ajiya zai tabbatar batason aurenne?. Amma tasan yanda zata ɓulloma lamarin kodan ta kuɓtar da kanta.... Sultana wayarta ɗoka takoma can Ɗakin su ta rufe , Number Jidda takira, babu dad'ewa tad'aga. Tana d'agawa tasaki kuka, cikin mamaki Jidda tace Daughter! Lfyarki kuwa? Ko wanine yarasu?. 'a, Sultana tafad'a cikin shashshekar kuka. Tomiya faru?. Sultana Na kuka ta zayyanema Jidda komai, a mamakin Sultana saitaji Jidda ta daddage ta rangad'a gud'a. Da sauri Sultana ta janye wayar daga kunnenta, saida ta tabbatar Jidda tagama sannan tamaida wayar tana kuma rushewa da kuka," Mommy na wallahi bana son sa!, daga can ɓangaren Jidda ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciya kana tace ,"Ha ba Daughter Miye aibun Dr Sultan! Ni fa wallahi na jima ina fatan Allah yasa yazamo mijinki, baki yadda kuyi matuƙar dacewa ba!, " Mommy yanzu kema kina goyon bayan shi?," Sosai ma! Daughter" "Shikenan daga haka ta katse wayar tana share hawaye.. _________★★★ Sultan zaune agaban Daddy da Mommy, kansa ak'asa yana sauraren iyayen nasa. Abba yayi garan murya irintasu ta manya, idonsa akan Sultan d'in, cikin murmushi yace Sultan anzama Ango. Alhamdulillahi munje anyi maganar aurenka da mahaifinta Sun yanke mana ranar d'aurin aure nanda wata biyu , Sun yanke sadaki naira dubu 50k kacal, dan albarka ake nema acikin auren. Sultan yakuma yin k'asa da kansa, dama can shi mutumne mai kunya, Mommy tayi murmushi kana ce Allah ya nuna muna," Amin" cewar Daddy. ★★★★★ __________★★★★ Sultana na zaune ta saka waya a gaba tana magana tana kuka," Nas ya sanyi!! Nas yanzu haka an saka ranar Aure na!!..daga can ɓangaren Nas yake ya sauke Nannauyan Numfashi kana yace ,"Bazan iya jure reshin ki ba hawaye na baza iya wonke damuwar da Zuciya zata shiga ba hawayena sunyi ƙanƙanta matuƙa su hana rayuwata gangar jikina ban taɓa sonki ƙasa da yadda zan iya rayuwa batare da ke ba ina sonki Sultana!!!.. Soyayyarki a cikin jinina take, ban taɓa tunanin zan tsinci kaina a cikin wannan yanayi ba, zan kasance cikin sonki har Abada,kin koyamin soyayya,kin koyamin farin ciki,kin koyamin dariya, Amman kin manta baki koyamin yadda zan manta dake bayan kin rabu dani💔, ki talla fawa rayuwata data tsunduma akan tsakanin kyaunar ki, ki tausayawa Zuciyata da ta shagala akan tsakanin Soyayyarki, ki taimaki idanuna da sauraren zazzaƙar Muryar fusakar ki, ina sonki Sosai Sultana!!!!!." Wani irin matsanancin kuka Sultana ta fashe dashi Zuciyarta na mata zafi kaman zata fashe. Cikin shekarar kuka tace ," Nas Bazan iya butulcema iyayena ba, Nas mesa tun lokacin baka bayyanar da kan ka a wajen iyaye ba? Nas bana son fushin iyayena Nas Nima Kai banza iya zuje reshin kaba, Amman dole zanyi haƙuri!!! ta ƙara sa maganar cikin raunin Murya, _________★★★★_____ "Ya Sultan Daddy yace ka kaini wajen Anty Sultana, "my little sis, ki bari sai gobe na kaiku ku yini a can, nan take Salma ta ɓata fuska kaman Zatayi Kuku," Ya Sultan Nidai yanzu nake so!" "Ya Babba tun ɗazu ta isheni sai an kaita wajen Anty Sultana ta ga Baby, Sultan ya sunkuyar da kai ƙasa cike da Kunyar Mahaifiyar sa, " Jeki shirya da sauri Salma ta wuce ɗakin jim kaɗan ta dawo.." Ina Salim? "Ya yi bacci,haka suka wuce, tunda suka fita Salma ke mai mai yawa Sultan mafarki har suka iso gida, a farfajiyar gidan ya yi Parking kana ya kira Haydar bai ɗaga ba har kiran ya tsinke,Khalil ya kira bugu biyu ya ɗaya, nan take sai ga Khalil ya fito fuskarsa ɗauke da Murmushi,"Ya Sultana kazo a Sa'a ko ga Anty Sultana can ta birkice muna" gaban Sultan yay matsifar tsinkewa, Amman ko kaɗan bazakace ga yanayin da yake cikiba, tare suka wuce cikin gida. __________Sultana zaune a ɗakin tun bayar gama wayarta da Nas. ta ɗora hanunta saman kai ta riƙe. Cusashi tai a tsakanin cinyoyinta jikinta na wani irin tsuma. Ga kanta ya fara sara mata sama-sama. Duk yanda taso ta daure ta kasa. Dan haka cikin ƙarfin hali ta shiga laluben wanda ke a kusa da ita. dai dai lokacin kuma Meena ta shigo ɗakin Cikin sa'a ta damƙo hanun Hankali tashe Meena ta dubeta, sai kuma yanda taga jikinta na karkarwane ya sakata ambaton ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ da ƙarfi.da sauri Abba da Mami suka shigo ɗakin.. Sultana ta damƙi hannun Abba tana cigaba da jujjuya kanta da fisgar numfashi a wahalce. A hankali take magana wadda idan ba'a kusa da ita kakeba ma bazakajita da ƙyau ba. “Abba kaina, kaina zai fashe Abbah. Kamin addu'a kaina zai fashe, Innalillahi... Abbana zan mutu..". Bazaki mutuba Mamana kinji, daina magana kiyita addu'a a ranki insha Allah bari na kira Doctor kinji”. Ya ƙare maganar da saka ɗan yatsa ya ɗauke hawayen da suka tsatstsafo masa saman fatar ido. Meena da Mami ma hawaye sukeyi. Dai lokacin Khalil ya shigo ɗakin,"Abba ga Ya Sultan nan yazo tare da Salma, Abba ya sauke sassanyan Nunfashi tare faɗin ,"Alhamdulillahi!!... "Don Allah ayi a hankali kar a tashi da kaka daga Bacci. "In sha Allah Abba, tare suka fito da Sultana zuwa Palo. Tunda yay sallama Abba da Mami suka zuba masa idanu cike da jin daɗin isowarsa a kan lokacin da ya dace. Cikin girmamawa ya gaida su . Suma sun amsa masa da kulawa Meena harda ƴar tsokana. Kaɗan gefen bakinsa ya motsa alamar murmushi yana Lumshe ido. Abba ya nuna masa alamar ya zauna anan. Bai musaba ya zauna idanunsa akan Sultana da har yanzu take riƙe da kanta. Sai da yay mata kusan kallon minti ɗaya da wasu sakanni sannan ya ɗago. Ɗan kallonsu yayi sai kuma ya sake maida idanun nasa kan Sultana. Hannunsa da Sultana ta riƙo ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan tafin hanun nasa cikin nata tare da ɗorasa bisa kanta, “Abba ka riƙemin zai fashe”. A hankali Sultan ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye hannunsa data ɗora akanta ba ta danne da hannunta kuma. Salma gabaki ɗaya jijinta yay sanyi ganin Halinda Sultana take ciki. "Tunda ga Shi yazo mu barshi ya yi aikin sa ko, cewar Abba Janye idanunsa yay daga kallon da yakema Sultana, sai dai kafin ma ya ɗago su duk sun fice. Meena da Haydar kawai aka bari. Baice komaiba sai hannunsa da yay ƙoƙarin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake riƙesa da ƙyau tana faɗin, “Abba don Allah karka tafi ka barni, kaimin addu'a kaji Abba”. Sosai tausayinta ya sake lulluɓe su Meena . Sultan ya ɗan matsar da kansa kusa da nata kaɗan, a hankali yace, “Ki daina magana zan baki magani yanzu zai Dena ciwo Kinji, Sultana duk da bata cikin haiyacinta ta gane ba Muryar Abba ne, Hayda buɗe mota na ka ɗauke box a ciki, da sauri Haydar ya fice daga palon jim kaɗan ya dawo hannunsa rike da ɗan ƙaramin Akwati mai kyau , Kallon Haydar Sultan yayi, Please ko zaka iya haɗamin allurar nan?” kasan cewar shima a school of nursing yake karatu . “to ya Sultan" ya jawo box ɗin. Wata irin zabura Sultana da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa ƙafafunta jikinta na rawa. “Bana son allura, Abba! Abba! banason allura...” ta faɗa a wahale tana riƙe kanta da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube. Cikin zafin nama Sultan ya miƙe tsayen shima, hakan yasa Sultana faɗawa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin riƙota yayi shima yana faɗin, “ Please calm dawn!” Ina batama san yana faɗa ba, kanta kawai take jujjuyawa a ƙirjinsa da faɗin, “Banason allura, Abba banaso”. “Okay shike nan, kinga baza'ai mikiba, ya isa ki daina magana, tana sa miki ciwo kai”. Yay maganar da ɗaukarta gaba ɗayanta ya maida a kujerar zai kwantar. Sake ruƙunƙumesa tai, sautin muryarta na ƙara fita da ƙarfi wajen faɗin, “Abbah karka bari sumin allura dan Allah ” ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Meena da Haydar suka fice daga palon.... Sultana ta kanannaɗema jiki Sultan..........✍️ *Muna gab da kammala book 1 in sha Allahu* PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 _More comments and share pls_ *Sadeeya Ka'oje ce 💋* *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand* *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 37-38* ___________Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Sultana take sake tura kanta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akan dogon gashinta dake ta uban ƙamshi “Sultana ” ya faɗa a hankali yana kai bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba ya sake miƙewa da ita ɗauke a hannunsa. Zama ya farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ƙyau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe ɗin da Haydar ya ajiye ya ɗauka, ɗan guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ɗan fesar da huxi kaɗan da zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Sultana ya girgiza kansa, cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki ya kuma turata jikinsa da ƙyau tare da ranƙwafowa ya ɗaura bakinsa akan kunnenta. Wata irin sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata allurar batare da ta saniba. A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ƙarfi ta zabura tare da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na wani irin karkarwa. Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya faɗa a hankali cikin kunnen nata. idanunsa ƙyam akan Sultana dake ta juyi a jikinsa, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi. Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya. Tsawon mintuna biyar suna a haka, A hankali ya shimfiɗe Sultana a kujerar da ƙyau ya gyara mata kwanciya, kana ya fito daga palon Duk kallon Sultan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake faɗin, “Abba karku damu aikina ne ai. Insha Allahu zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya birkita, “Insha Allahu za'a kiyaye. Allah ya saka maka da alkairi, ita kuma Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne”. A tare suka amsa da amin, "Ni zan tafi, "A sauka Lafiya ina gaida Daddy ku, 20k Abba yaba Salma gashi kuma sai Ice cream, Abinka da yaro nan take ta karɓe kuɗin tana murna, suna tsaye a wajen har su motar Sultan ta fice daga gidan,.... Bayan wucewar Sultan duk suka shiga har falon yadda suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai, Kwanaki Ukku Sultana tayi tana jinyar kanta, amma Alhamdulillah da sauki, dantana samun kulawa daga Kaka da Mami, ___________★★★★____________ Yau tunda safe Sultana ta shirya zuwa wajen aiki kwanta huɗu kenan bata je ba.ta fito fes Abinta sai zuba kamshi take, Kai tsaye ta wuce Asbiti kusan lokaci ɗaya ta iso tare da Jidda, Gaban Sultana yafad'i lokacin da idonta ya sauka akan ya Sultan dake jingine jikin mota, sanye yake da Shuit Ash color, yayi masifar k'yau, tunda take yaune karon farko data ƙare mata kallo,Jidda tace woow wlhy Dr Sultan yahad'u Daughter kin more miji gaskiya! Allah nuna min ranar Auren ku!!" "Ba Amin ba!" Dariya Jidda tayi tana fad'in ," Ai tun tuni Allah ya ƙarɓi Addu'ar mu" Lumshe Idanunsa yayi tare da saurin dafe ƙirjinsa kana ya buɗe Idanunsa tare da Kallonsu ɗaya bayan ɗaya, har suka shige cikin Asbitin, daga can ɓangaren Aziz yace ," Bros baka jina? A hankali ya sauke Ajiyar zuciya kana ya fesar da Numfashi,"Ina jikin ka Bros!" Aziz yaci gaba da faɗin ," jikin Abie ya tsananta sosai Wallahi! Harta kai ga sai amma sa aiki a zuciya, Sultan ya sake Nannauyan Ajiyar zuciya tare da farin ,"Allah ya bashi lafiya!" "Amin Bros! Ya shirye shiryen Aure wai Ni kam har yanzu baka haɗani da matar tamu ba, Murmushi mai sauti Sultan ya yi tare da faɗin ,"zaka ganta idon lokacin ya yi, " Bros nifa Very Soon Zanyi Auren nan, cike da farin ciki Sultan yace ,"Allah ya nuna muna!" "Amin Bros Ina gaida Amarya kuma In sha Allahu Aure saura sati ɗaya zanzo, da ga haka sukaci gaba da yin waya, zuwa na ɗan wani lokaci kana ya wuce Office...... sai ƙarfe Shidda suka tashi, Sultana na ƙoƙarin shiga Motarta Jidda ta Kalleta cike da tsoka tace ," Daughter duk yadda namiji yake sonki karki taɓayin wasa da damarki har kici masa mutunci da rashin kunya, a duk lokacin da nakilli Dr Sultan nakan ga tsantsan Soyayyarki a cikin idanunsa wanda ke kika kasa ganewa, Sultana ta taɓe baki tare da faɗin,"Aure mafi daɗi da.kwanciyar hankali, babu kamar Auren wanda kake so yake sonka!!" Sultan dake bayan su yana sauraren duk a binda suke faɗi, kai kawai ya sunkuyar yaci gaba da tafiya har zuwa wajen motarsa ya shiga ya yi tafiyarsa... Jidda tuni ta yi mutuwar tsaye, Sultana ko a jikinta, haka ko wannen su ya shiga motarsa ya wuce gida... Sultana ya isa gida ta watsa ruwa tayi sallah, woyarta ta fara suwa tun kafin ta d'aga tasan waye ne dan sautin kiran kawai ke shaida mata Nas ne ke kiran ta haka yasa cikin shauk'i da k'aunar juna suka fara magana a waya cikin sanyin muryar da ko kana gefen ta a kan gadon bazaka ji abin da take fad'i ba, Ido ta lumshe cikin sauk'e ajiyar zuciya tace. "Hubbyna!" "Na'am." Yace mata tare da cewa. "Sultana kina sani d'imuwa soyayyarki tana cazamin kai da jinin jikina k'ok'olwata na cushe in banji muryar ki na awa 3 ba Sultana ki daure ki soni ko rabin yadda nake sonki." Ido ta kuma lumshe wa cikin hura mishi iska a kunne murya can k'asa maƙoshi tace " Hubbyna ka kontar da hankalin ka Sultana taka ce jiki da jini da duk wani motsina kana cikin raina ko bacci nake muyarka nake jiki a kunnuwata. A can Ɓangaren Nas kam k'ara sakewa yayi kan kujerar da yake konce gaba d'aya tsikar jikin shi yana mik'ewa lokaci d'aya kalaman ta suka sakar mai wani kasala da shauk'i k'aunar ta yakeji na ratsashi har cikin k'ahon zuciyarshi, yayin da ita kuwa Sultana take jin duk duniya ba yanayin da take so da jin dad'in shi kamar kasan cewa a haka suna musayan zantukan so masu sanyi, ji take matuk'ar babu Nas a rayuwarta toh gani take kamar ba nunfashi tare da ita. Haka sukaci gaba da soyewa kamar su shiga jikin juna, bayan ta gama wayar tayi salla Isha'i kana ta wuce Palo Abinci suka ci gabaki ɗayan su kana kowa ya wuce makwancinsa...... _*five Weeks Ago_* Kwanaki nata shurawa, bikinsu Sultan na ƙara matso gab. Sultana tanashan gyara wajen Mami da Kaka, Ga Mamie tatsaya akanta wajen koyamata girke-girke dazama da miji, Tayi k'yau harta gaji, Kaka ma Na koya mata dabarun zama da miji irinna zamaninsu, sosai Sultana take fahimtar komai daki-daki. Sati ɗaya kenan da dawowar Mommy daga Dubai wajen haɗo lefen Sultana. Yauma da kamar kullum Bayan Isha'i Mami ta saka Sultana a ɗaki Mami ta b'alle marfin wani roba sannan ta jijjiga tare da mik'ewa Sultana d'in cikin tsuke fuska tace. "Karb'a ki shanye yanzu ki bani robar." Kai Sultana d'in ta karya cikin kuka da gajiya da d'ure-d'uren da suke mata tace. "Ni dai amai nakeji dan Allah Mami a barni hakanan." Ba yadda ta iya dole ta karɓi gorar ta sha ye tas, Mami na fita Jidda da Meena suka shigo ɗakin, Jidda tace ,"Allah dai ya biya Mami yadda kike mishi mugunta haka zai rama kiji tsoron mutumin da baya magana inya tashi ramawa zaki yabbawa aya zakinta." kai Meena ta jinjina sannan tace . "Gaya mata dai Anty Jidda wallahi wata rana zakiyi nadama abinda kikewa Dr Sultan ," Haka suka rink'a tsokanar Sultana, Abba tuni ya kammala kayan ɗakin Sultana da duk wani Abin buƙata a ɓangaren Kaka duk wani Abin gargajiya ta seya Sultana... Washe gari Aka kai lefen Sultana, Set shidda, kowa nata yaba lefen Sultana, ba ƙaramar dukiya a ka barke ba, A ɓangaren Sultana kowa ba Abinda kecin zuciyar Sultana bai wuce Nas ba, musamman y'an uwanta keta shirye-shirye da Duk yadda tayi banza da maganar Auren sai da auren ya zama saura sati ɗaya sai jikinta yai sanyi. Haka kawai sai tsoro ya shigeta, Sultana ta fito tayi rasa sai wani shek'i take tamkar tarwad'a fatar jikinta komai nata yasha gyara sai wani k'amshin mai Daɗi take fiddawa ko wucewa tayi k'amshin ta sai ya ratsa wurin gashin kanta kuwa ba'a maganar gyaran d'aya sha, an gyareshi gyara na mussamman, *Sultan* Ƙarfe biyar ya nufi Airport, ya na isowa jirginsu na sauka, a hankali wani kyakkyawan Saurayi ya ke saukowa daga jirgin, tun bai gama saukowa ba Sultan ya nufi wajensa cikin tsananin farin ciki suka rungume juna..kai tsaye suka wuce Hotel,annan suka cigaba da shagalinsu, Sultana yau ta wayi wagi cike da mutuwar jiki, a hankali ta mike daga kwancen da take ta ɗauƙi wayar ta dake ringing ta ɗaga, cikin raunin murya mai haɗe da kuka tace. "Hubbyna nayi ma al'kawarin ni taka ce har Abadan bazan bari wani yayi nasarar rabamu ba, nayima alk'awarin zan adana maka kaina zan killace maka jikina ba wani mahaluk'in da zai zama hijabi a tsaka nin mu." Sai kuma tayi shiru tare da sheshshek'an kuka murya na rawa tace. "Sultan zai rayu cikin bak'in cikin rayuwa tunda har ya kasance a sanadin shi za,a rabamu , bazai sake samun farin ciki da konciyar hankali ba gidan shi zai zame mai tamkar kurkuku zai rayu cikin k'unci da bank'in da tashin hankali ta yadda shida kanshi zai sauwa k'amin, Sai kuma ta saki kuka mai tsuma zuciya, Nas Kuma lallashin ta yake cikin raunin murya yake cewa. "Kiyi hak'uri Sultana ki daina kuka ki sani har Abadan kina cikin raina bazan dena sonki ba, da ƙarfi aka bankaɗo ƙofar ɗakin, Abba Yayi mata wani irin kallo cikin tarin mamaki da jin zafi a ranshi murya can k'asa yace. "Mamana! duk wannan kukan kina yinshi ne dan zaki Auri Sultan? Mamana Ashe har yanzu kina kan bakarki?, "Abba wlh na tsaneshi Bana sonshi, Wata irin gigitcciyar ƙara ta saki da k'arfi tare da dafe fuskar ta jin wani irin zazzafan mari da Abba ya zuba mata cikin huci da zafin rai ya nunata da yatsa murya a hargitse yace. "Wallahi koda mutuwa zaki sai kin Auri Sultan ina ya so Aiki gawarki a gidan sa!" Kife kai Sultana tayi a bakin gado ta saki wani irin kuka mai cike da zafi a zuciya kuka mai cushe zuciya gaba d'aya jikin ta sai karkarwa yake, Abba ko har cikin ranshi yake jin tsanar Nas tunda a kan Nas ne Sultana take furta kalaman k'iyeyyar kan ɗan Aminshi da duk duniya Baida kaman sa, haka kuma yake jin zai iya yiwa Sultana ko wanne hukuncin matuk'ar zatayi wa Sultan d'in rashin mutunci, Sultana kuka take kamar zata had'iyi zuciya ta mutu, Mami yayi ta lallashin ta amman ina, Haka har dere yayi Kaka. kam ko ta kanta bata kuma biba dan inta tsaya kusa da ita tana jin tausayin Jikar tata, har dare Sultana tana kuka ne hannun ta dafe da kanta,ta kuma kifewa kan kago ta ci gaba da kukan da sautin shi baya fita dan muryar ta ta dashe, Meena da Nana duk taisayin Sultana ya cika su, Washe gari haka ta tashi jiki a mace, tun da sassafe gidan su yake cike tib da bak'in haka yasa Sultana ta takure kanta cikin d'aki akan gado kaman ba Amarya ba sam bata da walwala. Mami dake zaune a ɗaki tana shirin Kiran Sultan ya shigo a wayar ta, ta ɗaga a hankali tace ," Sultan ya dai?" daga can ɓangaren Sultan," Yace Mommy ɗazu na mata Atm ɗina ina wajen Bazan iya shigowa ba mutune sunyi yawa a gida," Mommy ta yi Murmushi tare da faɗin ,"lalle Ya tona ya girma,"Mommy ya kira sunanta cin Shogoɓa," Shike nan bari na ɗauƙo sai naba Salma ta kawo ma, Bayan ta kammala shirinta ta wuce ɗakin Sultan, a hankali ta buɗe ɗuwar madubi, karab Idanunta suka sauƙa kan A kwatin Azufar nan cike da mamaki ta riƙa kallon A kwatin, Atm ɗin ta ɗauka dake gefen Akwatin har takai baƙin ƙofa ta sake dawo wa, Haka kwai take jin son buɗe A kwatin, cikin wani irin yanayi da bata san namiye ba, ta soma buɗe Akwatin cikin Sa'a idanunta suka sauka kan hoton dake sama mai Black and write, da sauri ta wace manya idanunta tana kallon mutanen dake cikin hoton Zuciyata na bugawa da ƙarfi, cikin murya na na rawa ta soma faɗin,"Adda Sal......ma......✍️ Is sha Allahu gobe idon Allah Ya kaimu zan kammala Book 1 *DR SULTAN* (A heart touching love story) _💖Story And Written💖_ ⬇️ *Sadeeya Ka'oje* 💖‫💖الَح ْمُدِ لله سبحان الله الله أكبر‬ ﷽ Bismillah........ ✍ PAID BOOK Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 *💋TITAN'S OF TALENT💋* *Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa* *(T .O.T)* *Breathe in courage, breathe outfear, together we stand *Alkalaminmu abin alfaharn mu* https://chat.whatsapp.com/CuNxneQ0ONc6x9yn9a16Jj *The beginning* *Page 39-40* ____________"Adda Sal...Salma, dai dai lokacin a ka Turo ƙofar ɗakin, "Anty Ina key ɗin part ɗin Sultan? zamu saka kaya a ciki, ganin Mommy bata tanka ba yasa ta nufi wajenta ta sake cewa "Anty Lafiya? Sai kuma ta kai Idonta ga hoton da Mommy take riƙe da shi, Allah sarki Bappa da Nenne Allah ya gafarta muku, hawaye ta share cikin raunan'nanyar murya tace ,"Amin" "Amman Anty Me Hoton su Bappa yake a ɗakin Sultan?" "Ni ma ban sani ba" tsaye sukayi a ɗakin sunyi Zugum, kowa da abinda yake tsaƙawa a Ranshi, A ɓangaren Sultan ko zaune a mota yana jiran Atm ɗin sa shiru shiru har tsahon wani lokaci sai faman kiran Mommy yake aman ba'a ɗaga ba, hakan yasa ya nufi cikin gidan, batare da ya so hakan ba, tun da ya saka ƙafarshi a palon hankalin Mutane suka dawo kansa suna faɗin Maraba da Ango" cike tsakanin kunya ya nufi ɗakinsa, tsaye ya tarar da su sunyi cirko cirko, cike da tarin Mamaki ya riƙa binsu da kallon Musamman Mommy dake riƙe da Hoto, cikin ƙoƙarin danne abinda ke ranta tace ,"Sul.... Sultan na Barka a tsaye ko?" Makom ya bata Amsa, ya jefe mata tambaya ,"Mommy lafiya? mike damun ki?" A karo na farko ta saki Murmushin ƙarfin Hali Kana tace ,"Ba komi Sultan" Mami tace ta yi ƙarfin halin faɗin ,"Sultan ina kasan mutanen nan dake cikin hoton nan?" Nannauyan Ajiyar zuciya Sultan ya sauke kana yace ,"Mami Dengin Mahaifiya tace!!! " Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu dake tattare da su," Mami tace Degin Mahaifiyarka Sultan? Wace Mahaifiyarka a ciki?" cikin raunatattiyar Murya yace," Ummul Salma!!!" Nan take hawaye Masu matsifar Zafi suka zubo Mishi, Kallon kallon aka tsaya yi tsakanin Mommy da Mami, dai dai lokacin Kuma Daddy ya shigo ɗakin, "Ina fatan Lafiya? Daddy ya yi maganar yana kallon su, "Sultan yanzu kana nufin kai ɗan Adda Salma ne!!!" Cikin wani irin yanayi ya gyaɗa musu kai, A karo na Biyu Daddy ya sake tambatayar Lafiya? Mami ta sauke Nannauyan Numfashi kana yace ,"Abban Sultan! Sultan ɗan Adda Salma ne Sultan ɗan yar Uwar muce.*A DALILIN SO* Muka zamo Tamkar *JINI ƊAYA* Daddy ya sauke Nannauyan Numfashi kana yace,"Allah mai Iko!!, Zama sukayi Ga baki ɗayan su, cikin tarin Ruɗu dake tattare da Sultan yace ," Mommy ku fahimtar dani mike faruwa" Mommy ta sauke Nannauyan Ajiyar zuciya kana tace..... *WAI WAYE A DON TA FIYA* "Alhaji Abubakar Siddi shine sunan mahaifinmu, haifaffen garin dawakin tofa ne dake jahar Kano, Asalinmu Fulani ne, Mahaifinmu babban Attajiri mai darin dukiya da garken Shanaye da tumaki, Matarsa ɗaya a duniya Zainabu yar Gwoggon sa ce, Mu Ukku ne a wajen iyayen mu, Kuma duka mata Ummul Salma, Ummul Khairi, Ummul Kulsum, mun ta so cikin kyaunar Junan haka muke Rayuwar cikin kwanciyar hankali da kyaunar juna, wata rana Bappa ya fita da safe zaije masallaci, yaci karo da wani kyakkyawan Saurayi Mai Suna kwance a ƙofar gida cikin wani irin Mummunan yanayi Ya shigo dashi cikin gida tare da bashi taimakon gaggawa, kwanansa Ukku yana jinya, bayan yaji sauƙi Bappa ya bashi masauƙi a gidanmu saboda ya fahimci saurayin Bai san kowa a garin ba, sannu a hankali shaƙuwa mai ƙarfim ta shiga tsakanin Bappa da saurayin har kiwo yake ma Bappa, ana cikin haka Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin Adda Salma da Abduljalil, Allah ya azurta da wani sirrin ƙyau mai fita da kwarjini. ba wani ɓata lokaci Bappa ya ɗaura musu Aure, tare da basu muhalli zama, Rayuwar suke cikin so da kyaunar Juna, Adda Salma ta jima bata haihu, Auren su nada shekara Huɗu aka haifi Abdulmalik, lokacin Ni kuma nayi Auren Kulsum tana gidana, Abdulmalik nada shekara ukku Kulsum ta yi Auren, itama Saida ta shafe tsawon shekara Ukku sannan ta samu ciki, lokacin da cikin ta ya isa haihuwa, nazo ta zauna a wajen Amman Nenne yaƙi yadda haka yasa Kulsum ta koma gida anyi dai dai Adda Salma ma nada ciki, kusan lokaci ɗaya suka haihu da Adda Salma, Kulsum ta haifi ɗa na miji aman baizo da rai ba, tashiga tashin hankali sosai, saboda gorin da take sha a wajen dengin mijin da suke kiranta juya,ganin Halin da Kulsum ta shiga na tashin hankali yasa Adda Salma ta saudakar da yarta ga Kulsum ita ko karɓi ɗa najimin matacce a matsayin nata... Ranar Suna Yarinya taci Suna Aminatu, da sauri Daddy da Sultan suka maida Kallonsu ga Mommy dake ci gaba da faɗin, ba wanda ya san da maganar daga Ni dai Adda Salma da Kulsum ɗi, Lokaci kafin Kulsum ta koma ɗakin ta, Kowa yaga Aminatu sai yace kamanninsu sak da Adda Salma, duk lokacin da akayi magana Adda Salma takan nuna musu ai ba wani Abu bane don Aminatu tayi kama da ita tunda duk Jini ɗaya suke, hakan yasa muke samu tsanuwa a ranmu, bayan Kulsum tayi Arba'in ta koma gidan mijinta... Ranar Kulsum ta cika wata ɗaya da koma a rar faɗa ya caƙuɗe tsakin fulani da makiyaya in da akayiwa iyayenmu da yanzuwan mu kisan gilla... Washe garin bayan faɗan ya lafa muka wuce rugarmu,mun shiga tashin hankali sosai, ganin gawar Bappa da Nenne kawai muka ganin, ba irin neman da bayiwa Adda Salma da Abduljalil da Abdulmalik, lugu da saƙo na rugugarmu mun neme su mun rasa, daga ƙarshe muka haƙura da neman su, satin mu ɗaya a ruga muka dawo Kano cike da kewar Yar uwarmu da muke rasa....... Mommy ta ƙara sa maganar cikin raunin Murya. Wannan kenan🤗 ★★★★_________ Meena dake tsaye bakin ƙofa tana jin duk abinda Mommy take faɗin, nan take jikinta ya soma rawa, daman tare suka zo da Mamk tashi ta shiru shine ta biyo bayanta ashe da rabon taji me suke faɗi, cikin wani irin yanayi ta buɗe kofar ɗakin ta shiga tare da faɗa wa cikin Sultan ta rugumeshi tana kuka mai tsuma zuciya, Wata iriyar zuface ke tsastsafo mishi bisa goshinsa, Kamar an watsa mishi ruwa. Ya kamo lip ɗin shi na ƙasa yana taunewa. Zuwa yanzu gaba ɗaya jikinshi tsuma yakeyi ta ciki. Kanshi ne yakeji yana jujjuya mishi Da sauri ya ɗago kanshi tare da ware matsakaita kyawawan idanunshi, idanunshi sun cika tab da ƙwalla sai sheƙi sukeyi alamun suna iya zubda ƙollan a ko wanne lokacin. Ita Meena sai ƙara shigewa jikinsa take tana shaƙar dadɗan khamshi turarensa... "Allah mai iko Daddy ya faɗa ya faɗa cikin wata irin murya mai cike ruɗu.yanzu da Sultan da Meena uwa ɗaya uba ɗaya suke, kai Mommy ta gyaɗa mike, Murya a rauna ce Mami tace ," Na jima ina zargin Sultan nada alaƙa damu duk sanda na kallesa nakan kammanin ya Abduljalil A tattare dashi,wani lokaci kuma ya kanyi min kama da Adda Salma" Murya na rawa Mommy ta soma tambatayar,"Sultan ina Adda Salma da ya Abduljalil?" Cikin ƙoƙarin danne kukan dake son kubce Mishi yace ,"Ammie na da Abie duk sun rasu!" da gan ya soma basu labarin rasuwar da sukayi tare da Mahaifinshin kafin ya rasu, Mahaifiyashi kuma bazai iya tuna komi a kanta, ko da abin ya faru yana ɗan shekara Shidda. Lokaci ɗaya suka sauke Nannauyan Ajiyar zuciya,"Allah ya jikan su da rahama Allah yasa sun huta!" "Amin" A hankali Sultan ya janye Meena daga jikinsa ya share mata hawaye kana ya sakar mata Murmushi ƙarfin lahi, sai yanzu ya gane dalin da ɗasa yake Masifar kaunar Meena ace jini ɗaya suke.... Cikin tsananin so ɗan Uwan nata tace "Ya Sultan idon an daura Aure zan dawo gidanka da zama!!" Murmushi ya sakar mata, "Allah abin godiya! Ina son maganar nan ta tsaya iya tsakanin muna, bana son kowa yaji har sai ranar da ya ce, "In sha Allahu Daddy!" Yauwa a je aci gaba da shirye shiryen, Cikin mutuwar jiki Sultan ya fice daga ɗakin tare da Daddy. _____________★★★★ Haka a ci gaba da shirye shiryen Ta ko wanne Ɓangaren, yau jumma'a sun safe ake ta shiryen shiryen walima,. Tsab Sultana tai shiri da kayan da jidda ta kawo mata ɗakin Mami . Lass mai matsifar kyau da tsada sky blue da akaima ɗinkin riga da zani. Ya zauna mata ɗas a jiki tare da haskaka farar fatarta daketa ƙyalli. Ƴar ramar da tayi sai ta sake fiddo ainahin dogon hancinta da manyan idanunta masu matuƙar haske da cikar gashi. Turaren ta fesa tana zuba uban ƙamshi tamkar tayi wanka da turare. Gashi cakuɗasun da tayi sai ya bada wani irin shu'umin ƙamshi mai narkar da zuciyar mai shaƙa.Ta saka sarƙa da sauran kayan adon sannan ta ɗauki blue gyalen da aka haɗo mata da shi ta ɗora a kafaɗarta. ta zira flat shoes ɗinta suma blue. Tayi ƙyau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Su jidda ma tuni sun kammala shirin su tsab, Ana idar da sallar la'asar mafi yawan mutanen dake cikin gidan suka fice wajen walimar. Anguwar tayi tsit bakajin komai sai karatun alkur'ani, Alhamdulillahi, anyi taron walima an tashi lafiya, inda malamai suka yi wa'azi masu ratsa jiki ga ma'abocin saurare. Gaba ɗaya an gina sune akan zaman aure da kurakuran da muke tafkawa a cikinsa da hanyoyin magancesu, inda amarya da angonta sukasha addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya, Tunda aka tashi da walima jikin Sultana sai ya sake yin sanyi, Palon Abba ta nufa sallama, daga ciki suka amsa mata da bata iznin shiga. “amarya da kanta. Miya farune?”. mami ta faɗa tana murmushi. Kallon Kaka da batace komaiba Sultana tayi, sai kuma ta duƙar da kanta hawaye na cika mata ido. Mami tace, “Kinga zonan”. mamana! tai a hankali zuwa garesu, ta zauna a ƙasa jikin ƙafafun Kaka data cigaba da abinda takeyi tamkar batasan da shigowar Sultana ba. "Anty Sultana gobe War haka kina gidan ya Sultan! hawaye suka gangaro mata a kumatu, ta kwantar da kanta bisa cinyar Kaka tana jan ajiyar zuciya a jajjere. Dauriya kawai Kaka keyi dama, taja ɓoyayyen ajiyar zuciya da girgiza kanta tana kallon Sultana. “Ke kuma me ya sameki? "Kaka don Allah ya gaya Abba bana son Auren, A aura masa Meena ko Ihsan harda Jidda ma idon yana so!" Sosai abin ya basu dariya, cukuykuye ƙafafunta tana kukanta, "Kaka wallahi banaso Sultan!" Hawayen da tun ɗazun take haɗiyewa ne suka silalo saman kumatunta a hankali. Ta sake matso hawayen masu zafi tana jan ajiyar zuciyar da har jijiyoyin wuyanta saida suka miƙe “Haba Sultana kukan ya isa haka mana, ko an miki wani abune?”. Kanta ta girgiza tana sauke ajiyar zuciya a jajajjere. Hannu tasa ta share hawayenta, cikin rawar murya tace, “Mami wallahi bana son Auran, "Sultan ɗin ne baki so!!" kanta ta girgiza mata tana haɗiyar zuciya dajan numfashi. Mami ta sauke Nannauyan Numfashi tana girgiza kai, hannu ta ɗaura kan haɓarta ta ɗago fuskarta. “Kalleni Sultana”. A hankali ta ɗago manyan idanunta da launinsu ya koma Jaa, gashi sun kumburo saboda kukan data sha ta saukesu akan Mami ”. “Kukan ya isa haka kinji Mamana, kicire komai a ranki babu abinda zai faru sai alkairi, duk wani tsanar sa da kike ci zai koma Soyayya ki cire tsanar Sultan a zuciyarki, kiyi farinciki dan gobe ranarki ce idan Allah ya kaimu, fatanmu Allah ya sanya albarka a al'amarin ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, Allah yasa wannan haɗi ya zamewa family ɗinmu alkairi duniya da lahira”. faɗawa jikin Mami Sultana tayi tana kuka, sake fashewa da wani sabon kukan, “Mami Wallahi ina sonshi, idan baku auramin shiba mutuwa zanyi, wallahi saina kashe kaina idon ba'a autamin Nas ba, Mami wallahi Nas nake so....! Ta fashe da wani irin kuka tana zamewa zata faɗi ƙasa jikinta na rawa. Da wani irin kallo Kaka ta bita harta zube ƙasan yaraf, taɗanja jikinta baya tana jan tsaki zata raɓata ta wuce. Saurin tashi Sultana tai zaune ta riƙo hannunta. Kaka Wallahi inhar baku aura masa niba saina gudu na bar muku gida!. Mami da Meena da Jidda gabaki ɗaya jikinsu ya yi sanyi, basu taɓa tunanin ƙiyaryar da Sultana take wa Sultan takai haka ba. Run gumeta Mami tayi Cikin hikima da wayo Mami ta riƙa yi mata nasiha da ƙara ƙarfafa mata gwiwa harta daina kuka, cikin wani irin yanayi ta nufi ɗakinsu ta kwanta,cikin raunan'nanyar murya ta soma faɗin" Ya Allah ina mai ƙara roƙonka ka bani haƙuri da juriya tare da wadatar zuciya a kan dukkan a binda zanci karo dashi cikin rayuwata na jin daɗi ko a kasin hakan ka kuma bani ƙarfin Zuciya da zan iya tafiyar da ita akan hakan.... Ranar dai da kyar Sultana ta iya yin Bacci,.... Washegari Tun kiran sallar farko wasu daga jama'ar gidan da makusantansu suka tashi aka fara ƙaƙainiyar ɗaura abinci. kaka ta nufin Ɗakin su Sultana ta tada ta don tayi Wonkan lalle,a hankali ta buɗe ɗakinsu Sultana. Babu wanda ya tashi a cikinsu, dan mafi yawansu basuyi barici da wuriba, Kaka ta kunna fitilar ɗakin tana kiran sunan "Sultana ki tashi kiyi Wonkan lallen ki, Meena ce ta fara farkawa saboda bata da nauyin barci sam, ta tashi zaune da ƙyar tana murje idanunta, "Ina sultana?" "Kaka ƙila tana toilet? Bakin toilet ɗin Kaka ta nufa tana ƙoƙarin buɗewa taga ƙofar a buɗe, "bata ciki fa? Fita kaka tayi daga ɗakin, bakin ƙofa taci karo da Mami ," Kulsum kodai Sultana tana ɓangaren ki?" "A'a Mama bata can" Lungu da saƙo na gidan Mami da Kaka suka shiga namen Sultana, Sosai hankalin Abba ya tashi lokaci da Kaka take sanar dashi Sultana bata gida.... Yanzu kam dai kowa ya tabbatar Sultana bata gidan, Kamar wasa saiga ƙarfe 10:30 babu Sultana babu labarinta, kowa jikinsa ya yi sanyi.. Meena ta nufi ɗaki tana hawaye, a hankali ta zaune saman gado karab Idanunta suka sauwa kan takarda,.ta ɗauki ta kartada ta nufi wajen su Abba, Assalamu alaikum Abba!! Kuyi haƙuri da abinda zaku wayi gari da shi daga taskar kuskurena, wallahi Abba bana son Auran Sultan Nas zuciyata keso. Nasan babu wanda zan faɗamawa a cikinku ya fahimceni balle akai ga yarda, amma wallahi ina masifar son Nas fiye da yanda kuke zato da tsammani. Banason na wahalar daku wajen ɗauramin Aure da wanda bana so! Abba bana son na zama sanaɗiyar rugujewar zumunci ku kaida Daddy, ga Meena nan da Ihsan da Jidda duk wanda yake so A aura masa, Na muku alƙawarin idan komai ya lafa zan dawo gareku ku ɗaura mani aure da masoyina Nas. Na barku Lafiya!!!, Daga ɗiyarku Maryam Ibrahim Gwani...... Tsit palon yayi babu wanda ya iya ko ƙwaƙwaran motsi, Abba sai faman kaɗa kai yake "Wallahi ni dai ban yardaba, sai dai idan wani Azzalumi ne ya sacemin jikata". Kaka ta faɗa tana fashewa da kuka. Tashin hankali, 🙆 *SHIN WA SULTANA ZATA AURA??* *SHIN WANI HALI SULTAN ZAI SHI GA??* *SHI WAYE NAS??* *SHI WANNE IRIN MA FARKINE SULTAN YA KE DA MEENA??* *SHIN WANE IRIN RUƊANI NE KE TATTARE DA RAYUWAR SULTAN??* *SHIN YAUSHE SULTANA ZATA GANE ABDULMALIK SHINE SULTAN??* *SHI WANNE IRIN MATAKI ABBA ZAI ƊUAUKA A KAN SULTANA??* *SHI YAU SHE KAKA ZATA HAƊU DA ABDULMALIK??* *SHIN WANNE MUTUM NE SULTAN YA GANI A UMMURA?* Amsarku na a cikin Littafin DR SULTAN. A nan na kawo ƙarshen Book 1, sai mun haɗu a book 2 in sha Allahu Littafin *DR SULTAN* na kudine akan 300 kacal , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 1490318334 Sadiya Attahiru kaoje Access bank ,sai a turo shaidar biya ta wannan number 08149979652. Nagode🤗 Downloaded From https://tknovels.com.ng