Downloaded From https://tknovels.com.ng *TYPING* 📲 *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *MARUBUCIYAR* 👇 SANADIN HOTO HASSANA DA HUSSAINA CIN AMANAR RUHI BAHAGON LAYI GARKUWA BIYU *DA KUMA*👇 BAHAGON LAYI (SABON SALO) *BABI NA D'AYA DA NA BIYU* WATTPAD:Hassana3333 ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ 🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION* ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ______________________________________ *~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~* _____________________________________ https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ *BISIMILAHIR RAHMANIR RAHEEM* DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI,TSIRA DA AMINCI SU K'ARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD (S A W)DA ALAYEN SA DA SAHABBANSA,DA MASU BIN SA HAR IZUWA RANAR SAKAMAKO. MASOYA GA HASSANA D'AN LARABAWA TA DAWO DA WANI SALON NA DABAN,BAYAN KAMMALA LITTAFIN *(GARKUWA BIYU)* DA NAYI,BA WANI SALO BANE ILLA CIGABAN LITTAFIN BAHAGON LAYI,WANDA A YANZU A KAYI MASA LAK'ABI DA BAHAGON LAYI *(SABON SALO)* GA DUK WANDA YA KARANTA BAHAGON LAYI YA GA IN DA MATAN LAYIN SUKA BAJE KOLIN SU,KUN GA YADDA YA NISHAD'ANTAR DAKU YA FAD'AKAR DAKU,TO WANNAN MA DA YARDAR ALLAH ZAI K'AYATAR DAKU,FATANA KU BIBIYESHI DOMIN KUGA ABIN DA YAKE D'AUKE DASHI,KUMA INA FATAN ZAKU FUSKANCI SAK'ON DA YAKE D'AUKE DA SHI,NA GODE MASOYA NA. *FITOWA TA FARKO (GIDAN MALAM ARABI)* "An gayu!An gayu!!An gayu!!!" Kiran da Malam Arabi ke ta k'wallawa matarsa kenan da k'arfi cikin d'aga murya,daga can ta amsa sannan ta fito daga d'akin ta zuwa tsakar Gidan da yake a hargitse da kaya ko ina a watse,ya dubeta yaga yadda jikinta yayi butu butu da k'ura,amma duk da hakan jagirar nan rad'au a fuskarta ta ta kalli gabas,tuk'ek'iya da ita kamar an zana ta da D'an yatsa,fuskar nan na maik'o ta lafta basilin (mai gurguwa)ga kwalli masha Allah ta rambad'a kamar wadda zata tafi tallan ganda,ta yi d'aurin ture kaga tsiya abinta cokalele a gaban goshi ,tazo gabansa ta tsaya tana karkad'a masa idanu wai ita fari take yi,ya dubeta daga sama har k'asa ya tuntsire da dariya har da rik'e ciki. Ta tsaya tana kallonsa yana ta dariya,da dai taga dariyar tak'i k'arewa sai ta juya a fusace tayi hanyar band'akin tsakar Gidan ko takalmi babu a k'afarta,taje in da ta ajiye tsintsiyar kwakwarta ta d'akko ta zaro sili d'aya ta nufoshi,ta na zuwa ta mik'a masa tsinken ta na rik'e k'ugu da Hannu d'aya ta na girgiza jiki,ya bita da kallo kana ya fara k'unshe dariyarsa,yayi mata alamar tambaya da hannunsa me zai yi da tsinken? Cikin k'ufula tace. "Ka karb'a ka cire abin da kake wa dariya a jikina kawai Malam" Babu b'ata lokaci ya amshi tsinken wata dariyar na k'ara zuwar masa,kamar gaske yace. "Rufe idanuwanki An gayu na,yanzu za kiga abin da zan cire miki kuwa,Wanda ya sani dariya" Ta rufe idanuwan babu musu ta na jiran ganin abin da zai yi ,duk da uwar kwalliyar da ta zauna ta b'ata lokaci tayi domin ya yaba amma Dan wulak'anci yake mata dariya,Malam Arabi ya matsa dab da ita ya d'aga tsinken ya zurkud'a mata a hanci,tayi baya da sauri saboda rad'ad'i ta na kurma ihu,amma sai da ya samu nasarar Ciro wani dank'areren curarren tasono da ya cike mata hanci. Ta bud'e idanu a razane tana kallonsa,cikin masifa tace. "Malam wai kasheni kake so kayi da man?daga baka tsinke ka cire abin da kake wa dariya a jikina sai ka Burma min shi a hanci?to bak'inciki kake da hancina Dan kaga nawa yafi naka tsayi ko? Malam Arabi ya d'ago mata tsinken mai d'auke da tasono yana nuna mata,ta yatsina fuska ta na murgud'a baki tace. " menene wannan kuma?" Yayi murmushi ya ce. "Abin da na cire a jikinki ne da yake sakani dariya,ke yanzu Dan girman Allah nan fa wai kwalliya kika yi ko?hanci fal tasono da majina,wai Dan Allah An gayu yaushe zaki nutsu ki koma tsaf kamar sauran mata ne?ke sai son kwalliyar amma sam baki iya ba,mu nan malamai da kika ganmu babu abin da muke so irin muga matayen mu sunyi tsaf dasu, saboda muna shiga cikin matayen Aljanu mu na ganin yadda suke d'aukar wanka,amma ni kullum nazo gida sai dai tasono ya amsa min sallama ta,kai Allah dai ya kyauta halinki An gayu." Ta k'yalk'yale da dariya ta na dukan cinya sannan ta dubeshi tace. "Au wai daman abin da kake wa dariya kenan?to ai ni ina sane na barshi,domin wata k'awata ce ta bani wani Sirri, tace min akwai fa'ida ga mata wad'anda suke barin tasono a hancinsu har mazajen su su gani,wai wani Sirri ne na daban Malam" Malam Arabi ya rik'e hab'a yana shafa gemunsa cikin takaici ya ce. "Ita kuwa wannan K'awar taki a wane Gidan mahaukatan take?" An gayu ta zaro idanu tace. " Gidan mahaukata kuma Malam?billahillazi mai hankali ce malam , ragas take" Ya harare ta yana zabga tsaki. "Wallahi k'arya ne An gayu!duk in da ta fito daga yankin mahaukata take,a rasa da abin da za a birge miji sai tasono? Wannan wane irin hauka ne?" Ta D'an yi shiru,sai kuma can ta tuna abin da yace yanzu,kawai sai ta kwashe da dariya,ya kalleta sosai yace. " Dariyar me kike?" Ta na dariyar bata daina ba ta ce. "Malam ji nayi kace kuna ganin yadda matan Aljanu suke d'aukar wanka da kwalliya,shine nace mai zai hana ka kaini su koya min nima na dinga yi maka,idan kuma ba zaka kaini ba sai naje Habiban Babalalo ta rakani na San ba zata rasa sanin wajen ba ko?" Ya k'ara Dank'ara mata harara yana tsaki yace. " Wato dai tunda kika jiyo gulmar abin da ya faru tsakanina da shegiyar matar nan kika sa min ido ko?to ai na gode wa Allah da cikin k'ank'anin lokaci Allah yayi min sakayya,kuma duk da haka ban hak'ura ba,ke nake so ki d'auko min fansar keta min haddi da tayi ta cijeni a al'aura ta saboda ita tsinanniya ce,kinga dai yanzu yau zamu koma layin da zama,to ina so ki shiga jikinta a hankali har ku saba sosai domin ki d'auko min fansa,yanzun nan me kura zai zo ya fara d'ibar kayan mu ya kai BAHAGON LAYIN,Gidan da K'asimu ya tashi nan na kama mana tunda me gidannan ya uzzura min na tashi zai yi bikin D'an sa ya sakashi a cikin gidannan" An gayu Tayi shewa ta ce. "Aikuwa angama Malam,bari na shiga na k'arasa fitowa da y'an komatsai na" Ya girgiza kai yana sab'a malum malum d'insa da take rinjayarsa,daga waje yaji ana rafka sallama da fad'in masu kura sun iso don d'iban kaya,da hanzari ya fice ya shigo dasu ,suka fara jidar kaya ana lodawa a kura domin tafiya a tare a BAHAGON LAYI. ************* Ta na durk'ushe gaban mahaifiyar Sunusi tana ta rafka kuka da hawaye da majina shab'e shab'e,har dai Inna ta gaji da jin kukan ta d'ago ta kalleta fuskarta cike da jimami tace. "Yanzu Harira ba zaki daina wannan kukan haka ba?kiyi hak'uri muyi zaman mu anan mana,kinga dai Zamanki ke da Amina gida d'aya ba zai yiwu ba,saboda ba zaku zauna lafiya ba Harira na san halinki,ita kuma Amina ba hak'uri ne da ita ba,ke yanzu ma ban da abin ki yadda gidan yake k'arami ina zai sa ka ki ? Ta d'ago ta na kuka sosai ta fara magana. " Wallahi inna na gyara hali na zamu zauna lafiya k'alau ni da Amarya Amina,kuma ni ko wannan k'aramin d'akin da muke ajiye shirgi na yadda zan zauna a ciki,kuma babu wata rigima da za ki ji ta b'ullo,nayi miki alk'awari in sha Allah ...... Inna ta girgiza kai za tayi magana Sunusi ya shigo da sallama. Comments share vote pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️ *TYPING* 📲 *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *MARUBUCIYAR* 👇 SANADIN HOTO HASSANA DA HUSSAINA CIN AMANAR RUHI BAHAGON LAYI GARKUWA BIYU *DA KUMA*👇 BAHAGON LAYI (SABON SALO) *BABI NA UKU DA NA HUD'U* WATTPAD:Hassana3333 ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ 🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION* ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ______________________________________ *~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~* _____________________________________ https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ ****Inna ta amsa masa sallamar,sannan ya shigo ya nemi waje ya zauna kansa a sunkuye ya gaida Inna,ta amsa tana kallon sa,ya waiwaya ya dubi Harira da ke gurshek'en kuka tana wage baki,ga wawulon bakinta ya dad'a fad'i ya wani wargaje,ya d'auke kansa ya maida kallonsa kan Inna ya gyara zama yace. "Inna Lafiya wannan ta zo ta saki a gaba tana kuka?" Inna ta sauke numfashi tace. "Wallahi ni dai D'annan na rasa ya zan yi da Harira,gabad'aya ta d'aga hankalin ta akan tana son komawa gidanta su zauna da Amaryar ka tare,duk yadda naso na nuna mata gara zaman ta a gidan nan tak'i ganewa,tun abin baya damuna har tausayin ta ya fara ratsani akan Nadamar da tayi" Da sauri Sunusi ya d'ago ya zabgawa Harira wata shegiyar harara,Sannan ya mai da kallon sa kan Inna fuskarsa babu walwala yace. "Wai shin Inna ba mun gama magana tun shekaran jiya akan hakan ba?a yanzu Harira bata da gurbi a cikin gidana,Lafiya k'alau nake zaune da Amina tsawon sati biyu da Auren mu kenan,amma wallahi Inna da zarar Harira ta koma gidan nan na san ba zata bari a zauna lafiya ba,gara tayi zaman ta a nan zai fi kwanciyar Hankali kawai" Harira ta mik'e a gigice ta k'ara fasa kuka da k'arfi har ta razana su,bata yi wata wata ba ta afka jikin inna da k'arfi tana ihu,har ta bugawa inna gingimemen kanta a baki,Inna ta tunkud'e Harira da k'arfi saboda yadda taji dadashin bakinta ya d'auki zugi,ragowar Hak'oran k'asa sun daki dadashin sama,Harira ta fad'o k'asa kan cinyar Sunusi,da sauri ya ingijeta yana sakin tsaki ya maida hankalin sa kan inna da ta rik'e bakinta tana zazzare ido saboda azabar da ta ratsa bakinta,hankalin Sunusi a tashe yace. "Sannu Inna,Allah yasa dai bata ji miki ciwo ba?ta kafa miki wannan k'aton kan nata me kama da duro" Da kyar Inna ta iya magana idanu a warwaje. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,Harira D'an ragowar bakin nawa na tsufa za ki k'arasa min?me yasa ba kya aiki da hankali da lura ne?yanzu jikina tamkar na yara yake fa,bai kamata ki rufto min a ka ba,gashi nan za ki rub'a min D'an ragowar bakina na taunar goro" Sunusi cikin b'acin rai ya fara magana. "To Inna ke ma dai gashi nan a gabanki ta gwada miki halinta na Akuyoyi,so take yadda bakinta ya zama duk gib'i ke ma ta k'arasa miki hak'oran k'asa,muguwa azzaluma kawai,Wallahi ni Inna ba don kin takura ba da tun a wancan lokacin na sake ta,gabad'aya zama da ita ya fice min a raina Inna" Harira ta kuma d'ora Hannu a ka ta zunduma ihu,yayin da Inna ta dubi Sunusi tace. "Kul!kar na sake jin maganar saki a bakin ka,kai da Harira mutu ka raba takalmin kaza,kaga dai Harira marainiya ce tilas kayi hak'uri da ita da halayen ta,ni dai ina tausayin marayan mutum ka sani, kayi wa Allah Sunusi ka yafe mata ka bata dama ta k'arshe,ka mai da ita wancan gidan tunda tayi alk'awarin gyara halin ta,insha Allahu za ku zauna lafiya da juna" Sunusi ba don ya so ba ya girgiza kai yace. "Shikenan Inna ba zan k'etare umarnin ki ba,na hak'ura zan mayar da ita can d'in ,amma sai nan da kwana biyu saboda ina so mu tattauna maganar da Amarya Amina" Harira ta fara share hawaye tana b'angala dariya cike da murna,Sunusi ya dank'ara mata Harara,yayin da Inna tayi murmushi cike da farinciki ta dubi Sunusi tace. "Yawwa D'an albarka aikuwa Na gode,kuma nayi murna da ka amince da magana ta,Allah Yayi maka albarka,kuma ina so bayan ta koma ka sa rana ka kaita Asibiti a saka mata hak'oran roba Sunusi,ba dad'i tai ta zama baki duk wawulo,idan aka dubeta a ka dubeni sai a zaci shekarun mu d'aya fa" Dariya Harira ta saka, suka waiwaya suna kallonta cike da mamaki,Inna ke tambayarta . "Lafiyar ki Harira kike dariya? Harira ta kuma fashewa da dariya tace. " Wallahi Inna wani Abu na tuno, lokacin da azzalumin D'an sandan nan yake jibgar mu da kulki ya za ci ni tsohuwa ce,har da ce min wai Dan kutumar ubana tsofai tsofai da ni amma ina shiga cikin yara ,kai gaskiya wannan ofisan bai da imani ko kad'an,da yayi wani tsalle ya dira kan k'afar Habiba ji kike b'ararassss!ya karya ta" Inna tayi dariya tana girgiza kai,shi kam Sunusi mugun tsaki ya ja yana k'ara jin tsanar Harira a zuciyar sa. **************** Da daddare misalin k'arfe Tara na dare Sununsi zaune a falo kan kujera,yayin da Amina take zaune a k'asa tana matsa masa k'afafuwan sa,zuciyar sa tana ta bugawa yana so yayi mata zancen amma yana jin tsoro matuk'a,amma hakan ya daure yayi gyaran murya yana murmushi yace. "Amarya ba kya laifi ko kin kashe D'an masu gida" Amina ta washe baki tayi fari da idanuwanta,ya dinga morewa kallonta jibgegiya da ita a gabansa jikinta duk tsoka,duk in da ya duma Hannu yaji abubuwa sun cika masa Hannu lumus!ba irin Harira k'ek'asasshiya da ko naman kirki babu a jikin ta ba,sai k'ashi da jijiyoyi rad'a rad'a. Can ya Numfasa yace . "Amarya magana nake so muyi ni da ke,dafatan zaki bani had'in kai ki fuskance ni,sannan ki tayani yiwa mahaifiyata Biyayya" Tayi k'asa da idanuwanta cikin kunya tana murmushi,ya kalli saman idanunta sun sha eye shadow malam abin gwanin Sha'awa,ta kuma d'ago idanuwan ta sauke su a kansa ta na cigaba da mammatsa masa k'afafuwansa da hannuwanta masu cike da nama,sannan ta kalmashe murya tace. "Kar ka samu damuwa,kai fa tamkar Sarki ne!ni kuma jakadiyar ka,kaga kuwa duk abin da ka umarce ni shi zan aikata babu musu" Sunusi yaji kansa ya kubura suntum,daman yana da irin wannan darajar bai tab'a sani ba,?Ashe shi cikakken Namiji ne amma Harira take mayar da shi Aljihun baya?Sosai ya kwaye baki yana dariyar murna yace. "Amma naji dad'in batun ki Amaryata,hakan ya nuna min darajata a wajen ki ta kai k'ololuwa kenan,to babu laifi Allah Yayi miki Albarka,daman ba wata magana ba ce illa d'azu da naje gaida Inna shine take min wata magana,wai tana so Harira ta dawo gidan nan ku zauna tare domin ku had'a kanku,hakan ne yafi cancanta a kan na barta can gidan,to ni kuma sai nace wa Innan ta jira sai na nemi shawarar ki tukun, duk abinda kika ce da shi za'a yi amfani,saboda bana son abin da zai zo yana d'aga miki hankali muna zaman mu lafiya,kuma na san Halin Harira ba kirki ne da ita ba kwata kwata,tun kafin ki zama matata ma rikici ya had'aku kunci uwar sabada a gefen hanya bare yanzu kun zama kishiyoyi,duk da Inna mahaifiyata ce ban isa na k'etare umarnin ta ba,amma dai ina son naji abin da za ki ce akan hakan tukun" Tunda ya fara magana k'irjin Amina ke bugawa,tabbas bata son zama da Harira guri guda,saboda ita dai bata da hak'uri ba zata jure iskancin Harira ba,kuma tana da saurin Hannu,Abu kad'an take kai duka,ga Harira da tsokana,tabbas kuwa idan tace zata yi mata iskancin da ta sa ba wataran za ta nakasa Harira ko ma a d'auki gawarta,amma in dai ta sauya halinta to za su zauna lafiya,domin babu abin da yafi zaman lafiya da kwanciyar hakali dad'i. Duk da tunanin da ya gallabi zuciyar Amina bata bari Sunusi ya gane ba,kawai sai tayi murmushi cikin Siyasa da kissa ta fara magana. "Haba Mijina!yanzu har Innar mu ta yanke hukunci amma ka ce wai sai kayi shawara da ni?hakan ai bai dace ba,saboda darajar Inna a wajenka ta ninka tawa sau ba adadi,kuma ko babu komai ai Yaya Harira zuwa nayi na sameta,ba zan hanata dawowa gidan ta ba,k'arewa ma ni zan kwashe kayana na mayar wancan k'aramin d'akin kawai domin ta dawo d'akin ta,idan yaso ragowar kayana sai a mayar da su gida har Allah ya hore maka ka Gina naka gidan,fatan dai ayi mana addu'a Allah ya bamu zaman lafiya da juna" Da sauri Sunusi ya tare ta yana girgiza kai. "Ba zai yiwu ki koma k'aramin d'aki ba Amina,sai dai ita ta zauna a can,daman ba wasu kayan kirki take da su ba illa kwarab'ab'b'en gadon ta da sari duk ya cinye shi,sai wata shegiyar tabarma da take shifid'awa masu kitso,ke za ki cigaba da zama a nan d'akin,ita kuma ta dawo wancan d'in,kuma Na gode da had'in kan da kika bani Amina,tabbas yanzu na san nayi dace da mace ta gari mai farantawa Miji, Allah Yayi miki Albarka" Amina tayi murmushi ta amsa da "Ameen". Sunusi Yayi mik'a yana Hamma,ta d'ago ta kalleshi tace. " Wai har ka fara jin bacci ne?" Sunusi ya ce "Eh wallahi bacci nake ji dan a gajiye nake,yau kwangilar wani bulo muka yi masu yawa duk jikina ciwo yake min na gaji" Amina ta mik'e da hanzari ta kamo hannunsa tace. "Ai banga ta zama ba Mijina yana tare da gajiya,muje d'aki nayi maka tausa ko gajiyar za ta warware" Sunusi ya mik'e yana murna da zumud'i yau za a yi masa tausa,yasan ba k'aramin dad'i zaiji ba yadda hannuwan Amina suke cike da nama,abin da Harira bata tab'a yi masa ba,ya san ma ko tayin ba dad'i zaiji ba sai dai ma k'asusuwan hannunta su soke masa jiki,Amina ta rungumoshi gefen jikinta,sai ga Sunusi Yayi D'an tsurut a Hammatar Amina saboda ta ninkashi sau uku a k'iba,suka shige d'akin su cike da son juna da farinciki. Comments Share Vote Pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️ *TYPING* 📲 *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *MARUBUCIYAR* 👇 SANADIN HOTO HASSANA DA HUSSAINA CIN AMANAR RUHI BAHAGON LAYI GARKUWA BIYU *DA KUMA*👇 BAHAGON LAYI (SABON SALO) *BABI NA BIYAR DA NA SHIDA* WATTPAD:Hassana3333 ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ 🖊️ *PEN WRITERS ASSOCIATION* ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ______________________________________ *~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~* _____________________________________ https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/ *** Washegarin ranar Habiba Zaune a tsakar gidan ta bayan fitar Babalalo wajen sana'ar Askin sa,wake ne a gabanta tana tsince mara kyau za ta surfa ta kai Markad'e,tun jiya Babalalo yake fad'amata cewar yana Sha'awar yaci Kulele,ita kam a dole zata yi saboda bata son sa,in dai ta ci b'ata mata ciki yake yi tai ta tusa cikinta ya kumbura suntum,wani zubin sai ta jik'a y'ar jar kanwa ta sha tukun take samun salama,Sallamar da taji daga soro yasa ta d'ago kanta ta na Amsawa. Wadda tayi Sallamar ta shigo tana taku a hankali,da sauri Habiba ta washe baki cike da murna tana fad'in. "Lallai yau ashe ina da Babbar Bak'uwa,yaushe rabon ki da gidannan Rauda?. Rauda ta yamutsa fuska ta ja wata kujera Y'ar tsuguno da ke kusa da Habiba ta zauna,Sannan ta sauke Numfashi ta Harari Habiba tana hura hanci tace. " Hmmmmm! Ai Habiba baki da kirki ko kad'an,gabad'aya kin manta da ni ma a rayuwarki kina ta sabgogin ki,wai shin ina gida na ina gidanki Habiba?tsiran mu layi d'aya ne fa,Amma kin d'auke k'afa daga gidana kwata kwata kin daina nema na ". Habiba tayi Ajiyar zuciya ta ajiye waken Hannunta a k'asa ta dubi Rauda fuska cike da jimami tace. " Hmmm!ke dai bari kawai Rauda,ina cikin tsaka mai wuya ne wallahi,tun bayan da Abubuwa marasa dad'i suka faru damu duk nayi sanyi,fita ma in Ba ta zama dole ba ba yin ta nake ba,Layin namu duk ya tarwatse,Oga Harira an samfata wata unguwa ta daban,Saratu tana gida Malam me almajirai na dila ta,K'asimu ya d'auke Zahra'u sun koma wata Unguwar ta daban,daga ni sai Shafa'atu fa yanzu,ita d'in ma ba ganinta nake ba saboda takunkumin da Babalalo ya sa ka min,wallahi Rauda bani da kwanciyar hankali duk a k'untace nake ji na" Rauda tayi murmushi tana sauke mayafin ta daga kanta zuwa kafad'ar ta,sannan ta dubi Habiba tace. "Ai Lokacin da abin nan ya faru nayi takaici Habiba,sosai naji Haushi fa,kuma ba Haushin kowa naji ba sai haushin ku,ban da ku mahaukata ne ku zauna wani shirgegen k'ato ya dinga laftarku ku wajen hud'u,ba kwa wawuso k'afafun Arne ku nanashi da k'asa,ai sarkin yawa yafi sarkin k'arfi Habiba,gaskiya kun bani mamaki,duk shaid'ancin ku amma ku ka zauna wani D'an iska ya dillik'e ku a banza a wofi,ai wallahi da ina cikin ku lokacin da kunga aiki da cikawa". Habiba ta sauke tagumi ta dubi Rauda ta girgiza kai tace. " Hmmm! zance kawai kike Rauda,in ba haka ba waye ya isa ya ja da Hukuma?ai Hukuma ta shallake tunanin kowa" Da sauri Rauda ta manna mata harara ta katseta da cewa. "Za ki sa na dannawa Hukumar zagi me sifirin,ai ko shi D'an sandan Yayi muku hukunci ne ba bisa k'a'idar aikinsa ba,kuna matan Aure d'ima d'ima amma ya keta muku haddin Aure yayi muku hawan k'awara? Habiba ta D'an yi dariya tace. " wane irin Hawan k'awara kuma Rauda?sai kace wad'anda yayi wa fyad'e". "To menene bambancin?" Rauda ta katseta da tambaya,sannan ta cigaba da cewa. " Ai bambancin kad'an ne Habiba,mutumin da aka ce har tsalle ya dinga yi yana tumami a ruwan cikin ku yana cafar nonuwan K'irjinku". Habiba ta zaro idanu tana dafe k'irji cike da tsoro,cikin rawar baki tace. "Inji wane tsinannen mak'aryacin Rauda?a ina kika samo wannan labarin k'anzon kuregen? Rauda ta tab'e baki tace. " Yo zancen duniya yana b'uya ne?ni ma a gari naji". Habiba ta girgiza kai tace. "Kai mutane an yi tantagaryar munafukai kuma magulmata,wallahi hannuwansa basu kai jikin mu ba,na san dai lokacin da ya gama kirb'ar mu ya sa hannunsa yana ta tunkud'o k'eyar mu waje,ban da haka bai tab'a jikin mu ba wallahi". Rauda ta D'an rage murya kad'an tace da Habiba. " Wai kuma da gaske mijin Amaryar ne ya kirawo D'an sandan aka tarfa ku cikin gidan sa? Habiba ta ce. "Hmmm!shine wallahi Rauda,bak'in matsiyaci ba"ta fad'a fuska cike da jimami. Rauda ta ce. " Kuma har yanzu suna layin nan basu tashi ba ko?naji an ce gini yake ba za su jima ba za su tashi. Habiba ta tab'e baki tace. "Suna nan har yanzu bak'ak'en munafukai,ai kin san damunar bana tayi gyara,ginin da ya fara ne ya rushe ya dawo baya,shine har yanzu basu tashi ba" Rauda ta numfasa tace. "Ya kamata kafin su bar layin nan ku d'auki fansar abin da yayi muku,wallahi idan baku rama ba kun yi asara duniya da lahira,ai rama cuta ga macuci ibada ne,ya kamata ki nemi Saratu da Harira da Shafa'atu ku had'a kai ku d'auki fansa,duk da dai ba Saratu a cikin ku lokacin da abin ya faru, amma na san zata taya ku yin yak'in,sai ta wakilci Zahra'u kawai" Habiba tayi kasak'e cikin tunani,zuciyarta na kai kawo,ta k'urawa Rauda ido tace. "Ta ya ya kike tunanin Hakan za ta faru Rauda?nifa Yanzu tsoron duniya nake ji domin ta koya min hankali,amma kuma kina zuwa da wannan shawarar naji ta kwanta min,yanzu me kike tunanin ya kamata ayi?" Rauda tayi murmushi ta matso jikin Habiba sosai ta kai bakin ta kunnen Habiban tayi mata rad'a,Habiba ta d'ago ta kalli Rauda bayan ta gama jin maganar ta,suka kwashe da dariya suka d'aga Hannu suka tafa……! Rauda ta tsagaita da dariyarta ta dubi Habiba tace. " Ke na manta muna ta zance ban yi miki jaje ba,Ashe Shagon Babalalo na Aski ne ya k'one,wai gobara da tsakar dare ko? ni sai jiya Shafi'u yake fad'amin,dalilin zuwana kenan ma" Habiba tayi murmushi tace. "Ai ba jaje ya kamata ki taya ni ba,Murna ya kamata ki taya ni Rauda" Rauda ta zaro idanu tace. "Murna kuma?asara ta samu mijinki amma kice a tayaki murna Habiba?ke kuwa wace irin zuciya ce da ke da kike murna da samuwar asara akan mijinki?" Habiba tayi shewa tana buga cinya tace. "Yo murna mana Rauda,Ai Babalalo mugunta ya so shirya min yayo min kishiya,can danginsa munafukai aka bashi wata tsomalalliyar Yarinya me zubin y'an ruwa,har fa ya ta da ginin filinsa kad'an ya rage ya kammala wannan ibtila'in ya same shi,gurin Neman abincin sa ya k'one k'urmus,yanzu tilas haka yayi gwanjon gidan da ya fara ginawa ya siyar ya samu kud'in da ya gyara shagon sa,kinga ai yanzu tilas ya hak'ura da Auren da ya jajibowa kansa ko?tunda babu y'an matsabbai a hannunsa da zaiyi hidimar auren da su,in kuma ba kan Uwatar zai siyar yayi hidimar Auren ba". Rauda ta tuntsire da dariya kamar za ta kifa,sannan tace. " Amma Habiba baki da mutunci wallahi,kuma fa da Babalalo zai siyar da kan Babarsa da ya samu kud'i,don naga kan nata har rinjayar jikinta yake saboda girma". Habiba ma ta shek'e da dariya ta ce. "Yo baki ga shi ma Babalalon gadon k'aton kai yayi ba,kwanaki da muka zabga karo ya buga min kansa wallahi na zaci dutsen Dala ne ya rufto min,sai da na kwan uku ina jinyar ciwon kai,ai Allah yayi musu baiwar gingimemen kai,ni da Atiringim". Suka kuma kwashewa da dariya suna tafawa,a dai dai lokacin suka ji ana zabga sallama a soro,Habiba ta Amsa da fad'in "wanene?" " Bak'uwa ce"Aka amsa daga soron. "To shigo Bak'uwa" inji Rauda kenan. Ta shigo tana murmushi, duk suka bi ta da kallo basu shaidata ba,banda kallon fuskarta babu abin da suke yi,tasha kwalliya hoda fururu,ga jambaki bak'i ta lafta tamkar wata Y'ar daba,d'aurin nan cokoko dashi a gaban goshi,Habiba ta matsa mata ta zauna kusa da ita kan tabarmar da take zaune,bayan sun gaisa ne Bak'uwar ta dubi Habiba da murmushi ta ce. "Na san baki shaidani ba ko?Ni sunana An gayu,jiya muka tare a layin nan gidan da aka tashi,ni matar Malam Arabi ce,kuma na shigo mu gaisa ne mu saba da juna a matsayin mu na mak'ota a yanzu". Ambatar sunan Malam Arabi da tayi yasa k'irjin Habiba bugawa da k'arfi,har abada ba zata manta da wannan matsiyacin mutumin ba,duk lokacin da ta tuna shi sai ta hango azabar da ya ganawa bakinta da lab'b'anta😂…….! Comments Share Vote Pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA BAKWAI DA NA TAKWAS* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ ***Habiba ta yank'are hak'ora zuciya a jagule tana zuba yak'e tace. "Ayyo! Ni kam da yake ban tab'a ganinki ba shiyasa ban shaida ki ba,na kan ji Labarin ki dai a wurin yara,kece mai sai da k'osai da safe ko? An gayu tace. " Eh wallahi kuwa,k'osai da awara duk ina toyawa da safe,haka nan ina siyar da gasarar kunu,dafatan kuma za ku zamo d'aya daga cikin kontoma na ku dinga siya" Habiba ta rik'e baki tace. "Kontoma kuma?menene kuma kontoma? Rauda da ba ta saka musu baki ba sai lokacin ta kwashe da dariya ta dubi Habiba tace. " Ke ina jin dai Costomer za ta ce ko?" An gayu ta buga cinya ta k'yalk'yale da dariya da k'arfi,sannan tace. "Ai kuwa kamar kin sani K'awata,Kastoma nake nufi" Habiba kam dariya tayi,daga ganin wannan matar shuda ce bata da cikakken saiti,domin zama tayi ta dinga zuba musu zance soki burutsu,idan tayi wata maganar sai ta dubi Rauda tace "Hakane ko K'awata?" Ita kam Rauda sai biye mata take suna shan Shafta da kwasar dariya,domin ta fahimci An gayu irin matan nanne masu shegen surutun tsiya,komai ya fito bakin su fad'a suke yi babu tantancewa. Habiba dai takaici ya ishe ta,An gayu tak'i tashi ta tafi gashi basu gama hirar su da Rauda ba,karad'in ta kawai ake ji tana buga zance,sai da ta kusan awa d'aya sannan wani yaro ya shigo yana fad'in "Wai An gayu ta zo in ji Malam Arabi" Aikuwa da hanzari ta mik'e ta shuri silifas d'in ta tana fad'in. "Bari naje na amsa kiran maigida,yanzu zan dawo,K'awata ai zan kuma tarar da ke ko?" Habiba ta zaro idanu ta fakaici idanun An gayu ta laftawa Rauda Harara,Rauda ta gane abin da take nufi shiyasa tayi murmushi tace. "Ah ah ba lallai ki sameni ba K'awata,wataran za mu sake had'uwa ai,ni ma bani da nisa tsiran mu layi d'aya ne,ina layin makarantar Daren da mijinki yake koyarwa" Nan An gayu tace Aikuwa za ta kaiwa Rauda ziyara,suka yi sallama ta fice da sauri,suka bita da kallo Rauda na dariya sai Habiba da take sakin tsaki tana hararan Rauda. Rauda tana dariya tace. "Wai ni me nayi miki ne kika isheni da harara?ni fa bani na sa mijinta ya jibgeki yayi miki ganda ba balle kice" Habiba ta sake sakin tsaki ta tofar da yawu tace. "Wai ke Rauda baki lura da wani curarren tasono da koriyar majina a hancin matar nan ba,an ya kuwa kanta babu motsi,babba da ita babu gyara ki dinga fitowa haka ana kallonki,ni wallahi duk ta tayar min da zuciya ma kamar nayi Amai" "Kika sani ko mura take yi?" Rauda ta fad'a tana tuntsira dariya. Habiba tace. "Kin manta Uwar mura take yi,ko in ce miki frinji ne a kanta k'arewa mura,to ko muran take yi ma ba za ta dinga gyara hancinta ba?ni wannan da abinci nake ci ai ta haramta min wallahi,kuma wai a haka ance miji na kira ta zabari k'afa ta tafi,taf! Wannan miji zai yi kyakkyawan gani,ke daga ganin matar nan kin san ladan noma ce,k'ila Noma malam Arabin yayi wa gyatumin ta aka bashi ladan ta daga k'auye,wannan aba haka babu fasali" Rauda ta keb'e baki tace. "Karfa ki manta kin saba da zama da k'azamai Habiba,babbar aminiyar ki Harira ma ai k'azama ce ta bugawa a jarida wallahi,kuma koma ladan nomar ce ba shi yaga zai iya ba" Habiba ta kama girgiza kai da Hannu ta na cewa. "Lala lala al mandudu kalas!billahillazi huwar rahmanu duk k'azantar Harira ba zaki ganta da tasono da mijina a hancin ta ba,ita dai kawai k'asanta ne bata gyarawa yake d'oyi da wari,sai kuma d'oyin hammata,kuma kwanakin baya kan abubuwan nan su faru har turaren tsuguno da miski ta siya gun zahra'u,kinga kuwa ai ta d'akko hanyar gyara ko…!? Rauda za ta yi magana kenan wayarta ta soma k'ara,ta bud'e Jakarta ta fito da ita ta na dubawa,Ashe yayarta ce ke sanar da ita sun zo bata nan suna k'ofar gida,nan Rauda tace su jirata gata nan zuwa,domin bata yi nisa ba tana kusa. Tana kashe wayar ta fara k'ok'arin mik'ewa tana gyara mayafin kanta,ta dubi Habiba tace. " Habiba bari na wuce gida,yaya Abida ce suka zo bana nan,ni ban ma san da zuwan su ba wallahi,k'ila yayen D'an ta Imamu ta kawo min Dan jiya mun yi waya da Umman mu tace min an yaye shi yau za a kawo min shi,to ban ma yi zaton da Uwar D'an za a zo ba" Habiba ta sauke numfashi tana mik'ewa tsaye ita ma,sannan ta dubi Rauda tace. "Wai ni kuwa Rauda ya kuka k'are da wannan tsinannen mutumin mijin Abida?haka kawai ya zamar da ita k'aramar bazawara haihuwa d'aya,amma dai kun maka D'an iska a kotu ko? Rauda ta ce. " Aikam dai yana nan yana zabga nadamar abin da yayi,kullum yana sintiri akan ta dawo gidan sa ita kuma ta k'i komawa,Yaya Abida ta sha wahalar wannan mutumin,kullum fa sai ya sha giyarsa yake zuwa ya tanana mata jikinta kamar wani d'anyen nama,hmmm…bari na wuce Habiba hirar ba zata k'are ba,in muka kuma had'uwa ma k'arasa " Rauda ta fad'a tana yin gaba. Habiba ta bita har Soro tana yi mata rakiya,suka yi sallama,Rauda ta wuce ita kuma ta juyo cikin gida ta fara k'ok'arin wanke waken kulelen da za ta yi. ************** Amina Zaune a tsakar gidan Shafa'atu ,ta tasa Shafa'atun a gaba da d'irmemen cikin ta haihuwa ko yau ko gobe ta zabga tagumi,a hankali shafa ta gyara zamanta kan tabarmar da take kai ta yatsune fuska,tana D'an jin ciwo kad'an kad'an kamar me nak'uda,sai da ciwon ya lafa ta d'ago ta dubi Amina tace. "Wai ni me yake Faruwa ne Amina?duk na ganki ba yadda na saba ganin ki ba,ko dai har kin fara shan gashi hannun Sunusin ne?waya gayamiki barno gabas take?kina murna wai ke kinyi Aure zaki sha soyayya ko?an fad'a miki mazan yanzu mutuncine da su? tattatun y'an iska ne fa wallahi,a waje soyayya kamar za a cinyeki,da zarar kin shiga kin zama nama,kinga duk k'ibar nan ta ki ko,idan miji ya minnira miki wani takaicin sai kin dawo kamar falwaya saboda rama" Amina ta sauke numfashi ta dubi Shafa'atu tace. "Ni fa Anty Shafa babu abin da ya shiga tsakanina da mijina kike ta wannan subad'ad'in,muna zaman mu lafiya wallahi,domin idan dad'i da soyayya suka yi mana yawa har goyani yake yi" "Ya Goya wa?" Shafa ta ambata tana zabura har k'ugunta na amsawa,sannan ta cigaba da magana cikin zare idon mamaki. "Wai Sunusin ne yake goyaki Amina?Sunusin da na sani me baya kamar allon mayya ta k'ak'a bayan sa zai d'auke ki kina da girman buhun kwaki uku?sake zance dai Amina" Amina ta b'ata rai ta d'aure fuska jin maganar Shafa'atu, nan da nan Shafa'atu ta shiga taitayin ta ganin yadda fuskar Amina ta d'aure,kar taje ta haye tsohon cikin ta ta saka ta haihuwar da bata shirya ba 😂. Cikin k'ufula Amina tace. "Ina ganin mutuncinki Anty Shafa, don haka kar ki sake cin mutuncin mijina gaskiya,nazo ne na fad'a miki damuwata saboda naga kin fi kusa da ni a halin yanzu,idan kuma ba zaki saurareni ba ne na k'ara gaba" Shafa'atu ta yi saurin tare ta da cewa. "Haba haba K'anwata,kiyi hak'uri wallahi zan saurare ki,menene yake faruwa da ya sanya ki a damuwa?" Amina ta yi ajiyar zuciya, ta k'urawa Shafa'atu idanu tace. "Wani tashin hankali ne yake Neman tunkara ta ina zaune lafiya,jiya Sunusi yake fad'a min wai Harira zata dawo gidan da nake mu cigaba da zama tare,to kin dai san Halin Harira,kin ma fini sani tunda tare na ganku,Kuma nima kin san kamar zawayi nake bani da hak'uri,shine nazo ki bani shawarar yadda zan zauna da ita,don gaskiya ba zan d'auki rainin wayonta ba,ban auri mijinta ba ma ban d'auka ba balle yanzu? idan tace zata kawon iskanci za mu ci uwar sabada ne ni da ita …… Wani irin zaro ido Shafa'atu ta yi,cikin ta ya fara k'ululu,Harira zata dawo?tabbas za a sha drama,musamman da jiya Kamilu yake bata labarin wai Malam Arabi ma ya dawo layin su gidan da su Zahra'u suka tashi,tabbas BAHAGON LAYI zai k'ara shiga chakwakiya kenan …….! Comment Share Vote pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA TARA DA NA GOMA* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ *Kar ku manta idan kun zo karatu ku fara yin fitsari saboda kar a samu matsala ya kufce kuyi a wando kamar wancan karon🤣🤭sannan a tanadi (Jar Kanwa) saboda ciwon cikin dariya*🤣🤣😆🤪🤪 "Wai da gaske kike yi Amina?da gaske Harira zata dawo layin nan da zama?" Shafa'atu ta ambata a tsorace. Amina ta cigaba da kallon ta cikin mamaki,ganin yadda duk ta firgice,ko menene abin tsoro a wannan maganar oho!dan haka ta k'ank'ance idanu tace. "Ya naga wai duk kin firgice ne?maganar da nayi ce ta firgitaki ko dawowar Harirar?" Nan da nan shafa'atu ta waske tana Sosa k'eya da cewa. "Ah ah wallahi babu komai Amina,kawai ina tayaki kishi ne,bana son Harira ta dawo ta takura miki Dan shegiyar kanta ce wannan matar" Amina ta tab'e baki ta D'an harari Shafa'atu tace. "Fad'i gaskiya dai,ko dai kike taya ta kishi tunda k'awarki ce?yo ni wata Harira ta isa ta takura min a gidan mijina?wadda nanan masai ma tafi min daraja a kanta,ai wallahi ta dawo mu zuba a gani,shege ka fasa,Idan ta kwantar da kanta muyi zaman lafiya,idan ta zo da akasin hakan kullum zata dinga cin na Akuya ne a hannu na,domin ba saurara mata zan yi ba" Shafa'atu ta rik'e hab'a tana girgiza kai tace. "Ah ah kar ki fad'i haka Amina,ta ya ya zan taya Harira kishi Dan a cutar da ke?kar fa ki manta ke K'anwar mijina ce,ita kuwa ba dangin iya ba na Baba sai had'uwar layi kawai,kinga kuwa ba zan tab'a barin ki Dan na bita ba,kuma insha Allahu ma lafiya k'alau zaku zauna,Harira ai taga ishara,bayan dahuwar ganda da kika yi mata ga dahuwar ragadada da yallab'ai me tiyagas yayi mata,ko in ce yayi mana,kinga kuwa dole ta hankalta ku zauna lafiya" Amina ta mik'e tsaye tana sab'a mayafin ta tace. "Atoh dai wannan ya rage na ta,ni dai a shirye nake tsaf da makaman ya k'i na,haka nan na tanadi nukiliya Wanda zan tarwatsa duniyar ta muddin tace zata yi ya k'i da ni,amma in ta zo da zaman lafiya ta yiwa kanta k'iyamullaili" Shafa'atu ta amsa da cewa. "In sha Allahu ma da zaman lafiyar za ta zo,ina da yak'inin hakan" sannan ta zarce da cewa. "Wai gida zaki koma ne naga kin mik'e?" Amina tace. "Eh gida zan koma,zan yi wa Sunusi wanki ne?" "Wanki kuma?yanzu har wanki kike wa Sunusin?cewar Shafa'atu cikin mamaki. Amina ta jijjiga kai tare da cewa. " k'warai kuwa,to ba mijina ba ne?ai babu abin da na zan masa ba,kamata yayi na share masa hawayen sa da suka dad'e suna zuba a dalilin rashin samun mace ta gari" Shafa'atu tayi murmushin yak'e tace. "Tabbas haka ne kuwa,Dan kuwa Harira ko D'an tofi bata tab'a wankewa Sunusi ba,wai bata ga yadda za a yi ta wanke kayan gardi me d'auke da guntun kashi ba" Takaici ya kama Amina,ta saki tsaki tana cewa. "Don Allah ni daina yi min maganar wannan dabbar,danni Harira bambancin ta da dabbobi kad'an ne,jaka jahila kawai" Shafa'atu tayi muk'us ganin Amina ta fusata kar ta huce a kanta,daga nan suka yi Sallama Amina ta wuce gidan ta tana cewa Shafa'atu "Allah ya raba lafiya,sai mun ji kyakkyawan labari don da alamun nak'uda kike yi" ta bar shafa'atu da bin ta da kallo tana hango yadda zaman Harira da Amina zai yiwu a muhalli d'aya,tashin balagar D'an tsako kenan….! ****************** Da Sallamar ta ta shigo tsakar gidan,daga can cikin d'aki ta ji ana amsa mata,Dan haka ta d'aga labulen rumfar ta shiga tana k'ara wata sallamar. Umman Saratu da ke zaune a tsakiyar Rumfar ta sake amsawa tana fad'in. "Maraba lale da Hajiya Maimuna, sannu da zuwa" Hajiya Maimuna ta nemi gefen Umman Saratu ta zauna tana kallon k'afarta da aka shafe ta da garin magani,cikin tausayawa ta amsa da . "Yawwa Fatsima sannun ki,ya kika k'ara ji da k'afar ta ki?" Umman Saratu ta ce . "Sai godiyar Allah,ga k'afa nan muna lallab'awa tak'i takuwa,kullum Malam yana hanyar k'auyuka karb'o min magnguna,ban da rubutun da kullum yake min ina sha,to kin san an ce ciwo farat d'aya yake shiga,sauk'i kam sai a hankali" Cikin jimami da tausayawa Hajiya Maimuna tace. "Tabbas hakane Fatsima,to Allah ya mayar kaffara ya baki lafiya,Allah ya yaye miki wannan ciwon k'afa" "Ameen Ya Allah" Umman Saratu ta amsa,sannan ta zarce da cewa. "Baki ga Malam d'in a zaure ba ko?ai baya nan sun tafi wani gida yin saukar alk'ur'ani,sabon gida ne shine me gidan ya gayyace su shi da almajiran sa domin ayi karatu a gidan" Hajiya Maimuna ta gyara zaman ta tace. "Aikuwa dai ban ganshi ba,sai dai wasu almajiran da suke karatu,yaushe Baba Laminde tazo daga k'auye Fatsima?na ganta a tsakar gida kan tabarma kamar tana bacci" Umman Saratu tayi kasak'e,sai can ta dubi Hajiya Maimuna tace. "Baba Laminde kuma?a gidan nan? " Eh mana Baba Laminde dai ta k'auye,ba ita ce kwance kan tabarma a tsakargida tana bacci k'uda na bin bakin ta ba?" Girgiza kai Umman Saratu tayi,cikin takaici tace. "Ni rabo na da Baba Laminde tazo garin nan ai an jima,Saratu ce fa take bacci,kama tayi miki da Baba Laminden ne?" A zabure Hajiya Maimuna ta dafe k'irji tana fad'in. "Wace Saratun?kina nufin Saratunki ce ta mommole ta zama tsohuwa haka?bata da lafiya ne?ko dai cutar k'yanda take? Ta jero tambayoyi cikin gigita. Umman Saratu ta girgiza kai cike da damuwa tace. " Yo ban da abin ki Hajiya Maimuna manyan mutane suna k'yanda ne?k'yanda ai sai yara,lafiyarta k'alau kawai duniya ce take ladaftar da ita,tak'i zaman Aure sai iskanci iri iri takewa mijin,shi kuma ya gaji ya sako ta,gashi nan har iddarta ta cika amma ya k'i ya maida ita d'akin ta " Hankalin Hajiya Maimuna a tashe tace. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, wallahi bani da wannan labarin Fatsima,da yake na jima bana gari ina Maiduguri ziyarar y'an uwa,amma banji dad'in wannan magana ba,me yasa kuka bari Saratu take cikin wannan yanayin,na rantse da Allah na zaci Baba Laminde ta k'auye ce,tana yarinyar ta da ita amma duk tsufa ya sakko mata,nifa kamar har furfura na gani a gefen kanta,daman an ce tashin hankali yana kawo furfura Ashe da gaske ne?" Umman Saratu tayi murmushi tace. "Haba dai furfura?tatar Koko ta gama yi min,ina ji k'ullun ne ya shafe ta kika ga kamar furfura,ni kaina da bana tausayin ta saboda ta b'ata mana rai,amma yanzu har na fara tausaya mata wallahi, haka kawai ma fa tana kwance sai kiji tana ihu kamar mahaukaciya,dukan da ta sha a hannun mahaukaci yana dawo mata a k'wak'walwar kanta" "Wane mahaukaci kuma?" Cewar Hajiya Maimuna. Nan Umman Saratu ta kwashe labarin komai ta fad'awa Hajiya Maimuna, takaici kamar ya kashe ta Dan Haushi,ga kuma dariyar da ke cinta,Umma bata kammala rufe baki ba suka jiyo ihun Saratu daga tsakar gida tana zambarwa tana fad'in. "Ku zo ku cece ni Mahaukaci zai kashe ni,Salisu kana ina ne?ka taimaken jijjib'in mijina,D'an lukutina abin alfaharina,inna fatahna laka fathan mubina,na shiga uku mahaukaci zai kashe ni" A zabure Hajiya Maimuna ta mik'e tana Neman wajen b'uya,domin ihun ya gigita ta,bata san lokacin da ta take k'afar Umman Saratu ba,umman ta zuba wani mahaukacin ihu saboda azaba,ihun ya k'ara razana Hajiya Maimuna ta kifa akan cinyar Umman Saratun,da azaba ta ishi Umma kawai sai tasa bakin ta ta dank'o wata Tsoka da ke gefen wuyan Hajiya Maimuna dai dai k'eyar ta,ta sakar mata cizo a wajen. Hajiya Maimuna ta zabga ihu,a dai dai lokacin da Saratu ta fad'o d'akin da gudu tana ihu. Comments Share Vote pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA GOMA SHA D'AYA DA NA GOMA SHA BIYU* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ ***Hajiya Maimuna ta ruk'unk'ume Umman Saratu jikinta na rawa tana ganin kamar kanta Saratu za ta yo,k'eyarta na zugi da rad'ad'i sakamakon hak'oran Umma da suka kaiwa naman k'eyar ziyarar bazata😂,ita kam Saratun tana shigowa zata nufo su cikin k'arfin hali Ummanta ta saki naman k'eyar Hajiya Maimuna ta kwaye murya ta daka mata tsawa da k'arfi tana zazzare idanuwa. "Ke Saratu !Dan ubanki dakata nan kar ki k'araso nan,shiga taitayin ki ki dawo nutsuwarki kafin ki sa na kirawo Malam yanzun nan yayi min maganin iskancinki". Chak! Saratu ta tsaya jikinta na rawa tana k'ik'k'ifta idanuwa, ta daina ihu da surutan da take yi,Umman ta k'ara dubanta tace . "Nemi waje ki zauna a nan in da kike kuma ki nutsu". Aikuwa sai Saratu ta zame ta zauna a inda take tsaye,sai kallon Hajiya Maimuna take yi wadda tayi ragajeje kwance a cinyar Umma,gabad'aya gab'ob'inta sun sage ta kasa mik'ewa tsabar matsanancin tsoron da ya rud'a ta,sai lokacin Umman Saratu ta dubi Hajiya Maimuna ta D'an yamutsa fuska cike da takaici ta ce. "Don girman Allah Maimuna ki d'agani,ina fama da jinyar k'afafuwana amma duk kin taushe min su" A hankali Hajiya Maimuna ta ja jiki ta d'aga Umman Saratun,ta koma gefe ta rakub'e tana satar kallon Saratu k'irjinta na tsananin bugawa tana sauke numfashi,gabad'aya a tsorace take,Dan ita tunanin ta Saratun Haukacewa tayi ta shigo za ta lode su,sai da ta gama mayar da Numfashin tsoro da jigata sannan ta dubi Umma tace. "Kiyi hak'uri Umman Saratu,domin ni ban san ma lokacin da na haye kan k'afafun ki ba wallahi,na tsorata da ihun da take zabgawa ne k'warai da gaske,amma dai gaskiya ya kamata a kai ta asibiti a duba k'wak'walwar kanta,kar fa wata matsalar ta samu daga haka,wannan ai ba k'aramar sukutar masifa ba ce". Umma ta sauke numfashi ta dubi Hajiya Maimuna ta ce. "Ni ma nayi wannan tunanin,amma da na fad'awa Malam sai yace min wai babu asibitin da za a kaita, tsabar iskanci ne kawai take ji da shi shiyasa take mana wannan ihun,rannan fa da tana yi kinga dukan da yayi mata?ni gashi ba k'afafu ba balle na tashi na k'wace ta,sai da yayi mata lilis,kuma yace duk randa ta kuma wannan ihun da surutai wai zai sa gardawan almajiransa su d'aga ta sama ya Zane ta ciki da bai, ni kam mamaki ne ma ya kamani da jin lafazin sa,shiyasa na dube shi nace da shi. " Malam da girmanta za a sa gardawa su d'aga ta a zaneta" Sai ya ce min wai in bari ta sake yi d'in a gabansa zan ga aiki da cikawa,to in tak'aice miki labari muddin yana nan yanzu bata yi,amma da zarar taga ya fita zata addabeni da ihu da surutai,hakan yasa na tabbatar da maganar Malam cewa Saratu iskanci ne abin na ta,don taga ni ban da k'afar da zan tashi na luguiguita mata jikinta ne kawai". Hajiya Maimuna ta ja ajiyar zuciya ta kalli Saratu da ke rakub'e jikin bango sai zare ido take,fuska duk ta yamushe kamar ta Akuya,kamar ta da Baba Laminden k'auye ta k'ara fitowa rad'au,ta girgiza kai a Zuciyar ta ta na ce wa. "Amma kin cuce ni fad'uwar gaban da kika sakani Saratu,ba Dan ina jin tausayin ki ba har gaban abada ba zan yafe miki ba" A fili kuma sai ta dubi Umman Saratun ta ce. "Lallai kam bata kyauta ba in dai haka ne,amma ina ganin damuwa ce tayi mata yawa fa,ya kamata a nemi Salisu a bashi hak'uri a daidaita su ta koma d'akin ta,zamanta haka kara zube babu fa'ida,tabbas Saratu tayi ba dai dai ba amma ayi mata Afuwa,na tabbatar ba zata sake aikata irin hakan ba in sha Allahu ,saboda bala'in da ta gani kad'ai ya isheta ishara a rayuwa" Umman Saratu ta ce. "Hmmm!yaushe rabon wani Salisu da gidan nan,sai fa yayi wata d'aya bai zo ba,sannan kuma ko yazo a waje yake tsayawa su gaisa da malam ya wuce,baya shigowa gidan nan ko don ma kar yaga Saratun, ai Salisu yayi fushi sosai kan abin da ya faru,Kuma ni banga laifinsa ba,tunda a gabansa har uwar sa take ambatowa ta zaga,tana ambatar ta iya me ido d'aya,kinga kuwa duk d'a na halak ba zai jure cin mutuncin iyayensa ba Hajiya Maimuna". Hajiya Maimuna ta girgiza kai cike da takaici ta ce. "Tabbas haka ne,ban da abin Saratu ma iyan da tuni ta riga ta mutu menene na ambatota?Allah dai kawai ya kyauta,abin da ya faru ya riga ya faru,sai a guji gaba kawai,yanzu dai zan samu nayi kiran Salisun gidana tunda mutumina ne,lokacin da yayi almajiranci a gidana yayi aikin wanke wanke da shara da wanki,har yanzu kuma yana ganin mutuncina yana zuwa ya gaisheni,Yanzu ma Dan nasan bana gari ne shiyasa baya zuwa,amma zan sa a kirawo min shi ko na kirashi a waya mu tattauna akan batun in sha Allah,kuma za a samu mafita da yardar Allah" Umman Saratu ta ji dad'i Sosai da maganar Hajiya Maimuna, ta dinga yi mata godiya,domin ita kanta ta gaji da zaman Saratun tare da ita,burinta ta koma gidan mijinta. ****************** Har soro ta rako shi ta na tafiya da k'yar,sai da suka zo soron k'arshe sannan ya tsaya ya waiwayo yana duban ta cike da tausayawa a fuskar sa,yayi murmushi ya ce. "Sannu kinji ,Allah ya raba lafiya,koma ciki ki huta don ni fa bana son naga kina Aiki da yawa,tausayin ki nake ji Zahra'u na" Zahra'u tayi murmushi tana langab'e wa ta kalli K'asimu ta ce. "Haba maigida,kullum fa naje awo likitocin suna fad'a mana mu dinga motsa jikin mu,idan nak'uda ta zo mana za mu samu sauk'in haihuwa,kuma ba za mu yi doguwar nak'uda ba,shiyasa kaga bana son zama na jab'e,nafi son in ganni a tsaye ina aiki ko wani abin" Ya D'an matsa kusa da ita ya d'aga rigar yana k'arewa cikinta kallo,Wanda yayi tirtsetse kamar y'ay'a biyu ne a ciki,shafa cikin yayi yana washe baki ya ce. "Allah yasa ki haifo min mace in sa mata suna Zahra'u, ko domin riritani da kike yi kamar wani k'wai" Zahra'u tayi Y'ar dariya,sannan ta rik'o hannun sa ta ce. "Ina so in anjima yarinyar mak'otan nan Nana zata rakani nan bayan layi gidan kitso,kaina duk ya dameni so nake ayi min kitso,kasan kuma tun dawowar mu unguwar nan Atika ce take min,ita kuma kwana Ashirin da Auren ta kenan,na rasa wata budurwar da zata dinga zuwa tana yi min,shine Nana tace min akwai wata mai yin kitso a bayan layin nan kuma ta iya,sai dai ita matar Aure ce bata zuwa gidan mutum tayi masa sai dai mutum ya taka yaje da k'afafuwan sa" Sai da K'asimu ya kammala sauraronta sannan ya sauke ajiyar zuciya, ya kalleta ya ce. "Kina ambatar gidan kitso sai da na tuna da BAHAGON LAYIN mu da muka taso,ni dai ba don an rasa mai kitso ba babu dalilin da zai sa na k'ara barinki zuwa gidan wani kitso,matattarar y'an iskan mata da gulmace gulmace,wace irin gwagwarmaya ce ba a sha gidan Harira mai kitso ba?abubuwa da yawa sun faru wad'anda ko tuna su bana son yi,sai da Harira ta wargaza layin nan sannan hankalin ta ya kwanta,shiyasa naji dad'in Auren da Sunusi yayi,har na bashi gudummawa mai Tsoka, sai yanzu zai san yayi Aure,domin da ba Aure yake ba wasan yara kawai yake da shirme" Zahra'u ta jijjiga kai tana sauke numfashi, tabbas sun shuka tsiya a BAHAGON LAYI ,har bata son tunawa da abubuwan da suka faru,musamman dukan da suka sha a hannun ofisa,wannan rana ba zata tab'a mantawa da ita ba,shiyasa tun da suka bar BAHAGON LAYI suka dawo wannan unguwar bata tab'a sha'awar shige shigen mak'ota ba,kuma ita ma kulle k'ofarta take yi bata bari a shigo mata in dai ba yara ba,suma d'in ba ko yaushe ba,Yarinya d'aya ce ta san sun yi Sabo sosai,kuma tana aikenta cefane ko siyo wani abin,ita ce( Nana),yanzu babu Ruwan ta da rayuwa irin ta BAHAGON LAYI, ba zata sake biyewa irin su Harira su Habiba su kaita su baro ba,domin ba don tayi sa'a mijinta yana sonta ba da tuni sun gurgud'e mata Aure, yanzu ga Saratu can gidan iyayen ta,tana girbar abin da ta shuka. K'asimu ne ya dawo da ita daga tunanin da ta afka,ta hanyar rik'o hannayen ta,ta sauke ajiyar zuciya ta dubeshi ta ce. "Ni kaina bana son zuwa gidan kitson mijina, duk da dai ba kowane gidan kitso ne zai kasance irin na Harira ba,kuma in sha Allahu zan tsare maka kaina da mutuncina,har naje na dawo babu abin da zai faru" Ya ji dad'in maganarta,ya shafa kumatun ta yana murmushi ya ce. "Yawwa y'ar Albarka, haka nake son ji,don Allah ki kula min da kanki,kinga dai tsohon ciki gare ki,ni ina ganin ma zuwa zan yi na koyo yadda ake kitson,sai na dinga yi miki a gida ba sai kin fita ba ko?" Zahra'u ta shek'e da dariya,K'asimu na taya ta dariyar,daga nan suka yi sallama ya fita zuwa kasuwa,ita kuma ta juya ta shige cikin gida tana takawa da k'yar saboda yadda cikinta yayi girma haihuwa yau ko gobe. *************** Salisu zaune a shagon Babalalo,shi kuma Babalalon yana yi masa aski,suna D'an tab'a hira kan yadda shagon askin ya k'one,lokaci guda Salisu yaji wayar sa na k'ara alamar kira,Hannu ya saka cikin aljihun sa ya zaro ta,yana dubawa sai yaga sunan uwar d'akin sa ce wato Hajiya Maimuna….. Da hanzari ya d'aga wayar ya kai kunnen sa ya rafka sallama cike da girmamawa. Comments Share Vote pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA GOMA SHA UKU DA NA GOMA SHA HUD'U* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ ***Kamar yana gaban ta haka ya D'an russuna yana gaishe ta cike da girmamawa,saboda ganin k'imarta da girmanta da yake,yayin da Babalalo ya koma gefe yana jiran ya kammala wayar ya cigaba da yi masa askin. Bayan gaisuwar da ta shiga tsakanin Hajiya Maimuna da Salisu, sai Hajiyar ta sanyaya murya cike da kyautatawa tana fad'in. "Kwana biyu ka guje ni Salisu,yaushe rabon da na sanyaka cikin idanuwana?dafatan dai ba wani laifi nayi maka ba?" Ya D'an yi murmushi yana Sosa gefen kansa da aka aske ya ce. "Ayi hak'uri Hajiya,wallahi yanzu ne ban cika shigowa unguwar ba ma kwata kwata,abubuwa sun min yawa bana samun isasshen lokaci,amma kwanaki da na shigo har gidan naki na zo na ganshi a rufe da kwad'o alamar bakya nan" Hajiya Maimuna tace. "K'warai kuwa an yi haka,bana nan naje Maiduguri ne lokacin ziyarar y'an uwa, don ban jima da dawowa garin nan ba ma" Salisu cikin murmushi yace. "Ayya!to Hajiya ya aka baro mutanen gidan?dafatan kowa yana lafiya dai?" Hajiya Maimuna ta ce. "Lafiya k'alau Malam Salisu, mutanen gida duk sun ce a gaisheku ma,yawwa daman ina son ganinka ne,shine nace bari na kira lambarka,don Allah ka samu lokaci kazo domin ina son zamu tattauna wata magana mai muhimmanci ni da kai" Ya gyad'a kai yana amsawa da cewa. "To babu damuwa Hajiya,insha Allahu zuwa gobe zan samu lokaci na b'ullo,Allah dai yasa lafiya?" Hajiya ta D'an yi dariya tace. "Lafiya lau, insha Allah kuma alkairi ne kiran kar ka samu damuwa,kuma ina nan ina zuba idanu sai na ganka d'in" Salisu ya amsa yana k'ara tabbatar mata in Allah ya yarda zai zo goben,daga nan suka yi sallama da juna ya kashe wayar. Sai lokacin Babalalo ya matso yana cewa. "Ni duk ka tsayar da ni man inji na yana tafiya a banza Salisu,gaskiya sai ka k'ara min kud'in askin nan naka" Salisu ya kwashe da dariya ya mayar da wayarsa aljihu sannan ya dubi Babalalo yana fad'in. "Kai fa Babalalo yanzu na lura son kud'in ka yayi maka yawa gabad'aya,ba kuma komai ya sa hakan ba sai don kana son ka k'ara Aure ko?" Babalalo ya sauke numfashi ya girgiza kai,yayin da ya cigaba da yiwa Salisu aski,a hankali yace. "Wane Aure Salisu? Bayan komai ya rushe, gobarar nan da ta sameni ta tsayar da komai,duk da k'addara ce amma gaskiya har yanzu ban gama farfad'owa daga k'uncin da na shiga ba,a shirye nake tsaf zan angonce wannan k'addara ta afka min,ga Sunusi nan har ya riga ni farke Amaryar sa a Leda ya barni da hamma " Salisu ya Kuma tuntsirewa da dariya yana fad'in. "An yi maganin mai zumud'i,na san yanzu ran Habiban ka k'al maganar Auren ka ta kwanta ko? dan wannan mata tunda tayi aljanun k'arya akan kishi na sallamawa kishin ta" Babalalo ya saki tsaki yana fad'in. "Kamar ka sani kuwa,ni sai naga ma kamar murna take yi da ibtila'in da ya sameni fa,Amma idan ta san wata ai bata san wata ba,idan tayi nasara wancan karon wannan karon kam tayi kad'an da yardar Allah" Salisu yace. "Wani abin za ka sake yi mata ne Babalalo?" Babalalo ya share maganar Salisu bai bashi amsa ba,ya sako wani zancen yana cewa. "Wai ni kam yaushe zaka dawo da Saratu d'akin ta ne ?gaskiya ya kamata ka yi hak'uri haka Salisu,ai ta horu da yawa matar nan,nifa labarin da ya iskeni tunda ka saketa cikin tumakai take kwana,an ce har ta so ta fara zaucewa,gashi har iddarta ta cika baka yi wani motsi ba,ya dace dai ka hanzarta a sake d'aura muku Aure ta dawo ku cigaba da zaman ku,zaman ka haka babu mace bashi da wani amfani balle fa'ida,aure rufin asiri ne da cikar kamalar mutum Salisu" Nan da nan Salisu ya canja fuska,domin babu abin da ya tsana irin ayi masa maganar Saratu,domin har yanzu bak'incikin ta bai goge a idanuwan sa ba,menene amfanin zama da mace irin Saratu wadda ta zama tamkar balama sak'andama?wani zubin ko rufe idanu yayi sai ya hango lokacin da Mahaukacin nan yake jibgarta babu kaya a jikinta,tana birgima nonuwa na rawa da tsalle,take sai yaji ya k'ara tsanarta,ko son ganin fuskar ta baya son yi,shi gabad'aya ma ji yayi baya son yin wani Auren,ganinsa duk matar da zai aura ita ma wannan akuyancin zata zo ta dinga yi masa a cikin gidan sa. Ganin Salisu yayi shiru ya b'ata rai sai Babalalo shi ma yayi shiru ya shiga taitayinsa,domin ya fahimci kwata kwata Salisun baya son ayi masa maganar Saratun, yanzu sai ya daina walwala ya shiga kumbure kumbure yana hura lukutin kumatunsa,a haka ya kammala masa askin sa yana zak'ulo masa wasu hirarrakin na daban. ************** Lokaci guda motar akori kuran ta tsaya a bahagon layi daidai k'ofar gidan Sunusi,Inna da Harira suka fito daga gaban motar,Harira tabi filin layin da kallo tana washe baki tana jin matsananciyar murya a zuciyarta,ashe da rabon za ta dawo layin ta cigaba da zama ba ta tafi kenan ba?. Direba ya fito yana ta k'ok'arin sassaukewa Harira kayanta,kwanuka da tukwane sai katifa da tabarma da kuma abin da ba za a rasa ba ragowar tsummokaranta,duk kayan dai a tsiya ce basu da wani yawa. A lokacin ne Sunusi ya fito daga gidan jin tsayuwar motar,kwata kwata baya jin dad'in dawowar Harira gidan ,amma saboda kar Inna ta fahimta sai ya dinga murmushin yak'e yana musu sannu da zuwa amma a fakaice sai zabgawa Harira mummunar harara yake yi. Da shi da direban suka dinga kwasar kayan suna shiga dasu cikin gidan har suka kammala,Sunusi ya biya direba kud'in mota ya tafi,shi kuma suka shige cikin gidan tare da Harira da Inna. Tarba ta mutunci Amina tayi musu,sai faman sannu take zabga musu,har falonta ta kaisu ta kawo musu ruwa,Inna dai ta sha amma Harira kam ko kallon ruwan bata yi ba,sai kallon Amina take yi tana ganin yadda ta k'ara hab'akewa ta zundume ta zama wata k'atotuwa kamar tifa,sai ta ganta wata y'ar tsurut kamar b'era a gaban zaki,amma wai duk da hakan Aminar in zata bud'e baki tayi magana sai ta dinga zabga mata (Yaya Harira) . Inna da kanta ta had'asu tayi musu nasihar zama lafiya da juna da samun kwanciyar hankali,sannan ta umarci Sunusi yayi adalci a tsakanin su banda wariya,hakanan tayi wa Harira fad'a akan ta ja girmanta banda fitina,ita kuma Amina ta girmama Harira tunda ita ce uwargida,sannan Inna ta nemi cewar idan da mai magana to bisimilla yayi k'ofa a bud'e take. Sunusi da Amina suka ce basu da magana,amma Harira uwar zirgilli karaf ta d'aga hannu tace tana da magana. Inna ta dubeta tace "To muna sauraren ki Harira" Harira ta gyara zama tana kaikaicewa tace. "Ni dai Inna daman maganarda zanyi ita ce, gaskiya ayi wa wannan dank'areriyar matar magana kar ta sake ce min Yaya Harira,ta kirani da Harira ta kawai,kalleta fa shirgegiya kamar buhun kwaki,wani ma ya kalleta sai ya zaci kakar babana ce,ni dai bana son wata Yaya ta daina gayamin kawai" Inna tayi murmushi tace. "Ban da abinki Harira girma fa ta baki a matsayin ki na uwargida,kuma kowa ya kalleku ai yasan kin girmi Amina,garun jiki ne kawai da Allah ya huwace mata,amma Amina ai yarinya ce kin fita shekaru nesa ba kusa ba" Sai lokacin Sunusi yayi magana cikin fushi da b'acin rai ya ce. "To Inna ba gara ma Aminar ba,ita fa kalleta duk a tsotse uwa Akuyar mayu,ai tafi ma kama da tsofaffin na rantse da Allah,wani idan ya dubeta ma ba sai ya za ci ta bawa shekaru sittin baya ba,daman ga bakin duk babu hak'ora" Amina dai shiru tayi kanta a k'asa,a zuciyarta tana cewa. "Au Harira bata nutsu ba kenan?lallai kam za ta koya mata hankali ta nutsar da ita,domin ba zata d'auki renin hankali da iskanci ba,tilas ta mik'e tsaye dan ta nunawa Harira ita d'in ba kanwar lasa ba ce" Nan dai Inna ta cigaba da yi musu nasiha,musamman Harira ita aka fi ambata saboda ita ce mai matsala,daga nan kuma Inna ta taya Harira shigar da kayan ta cikin akurkin d'akin da aka bata,wanda Harirar ta sha alwashin sai ta san yadda ta fitar da Amina daga gidan domin ta koma d'akinta na Asali da yardar Allah.....! Comments Share Vote pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA GOMA SHA BIYAR DA NA GOMA SHA SHIDA* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ *AYI DARIYA KAD'AN BA MAI YAWA BA* 😂 ***Zahra'u ta shirya tsaf a lokacin da Nana ta shigo domin rakata gidan kitso,suka fito ta kulle gidan suka tafi tana takawa a hankali Nana tana rik'e da jakarta,suna tafe suna d'an tab'a hira kad'an kad'an har suka k'arasa,tun daga k'ofar shiga gidan suke jin hayaniya da tashin muryoyi kamar ana fad'a da kokawa,a haka suka shiga gidan Nana a gaba Zahra'un K'asimu tana biye da ita a baya har suka shiga tsakar gidan,sai rafka sallama suke amma babu wanda ya amsa musu,sun tarar da mata kusan uku a tsaitsaye rik'e da k'ugu sai faman sababi suke, ga kuma Tarasulu me kitso a gefe ta rik'e hab'a fuskarta cike da damuwa tana sauraran matan da ke tsaye kowacce ta cakari k'ugu,su Zahra'u suka tsaya cike da mamaki da tsoro suna duban d'aya daga cikin matan da ta d'aga wata y'ar roba da wani kwab'ab'b'en abu bak'ik'k'irin a ciki tana nunawa Tarasulu me kitso tana ce wa. "Na rantse da Allah Tarasulu yau sai munyi maganin Munafuka,daga yau Gimbiya ba zata sake zuwa gidan nan tayi gulmarmu ba,yau har gidanta zamu dira mu ci ubanta mu dirje bakin munafuka,kinga wannan abun kashin awaki ne da gishiri muka kwab'a, da shi za mu je mu dirje bakin munafuka,daga yau idan an ce tazo gidan nan ta k'ara yin gulmar mu ba zata sake yi ba" D'ayar tayi shewa ta ce. "K'warai kuwa Jummai,wallahi yau ko sama da k'asa za ta had'e ba zamu saurarawa Gimbiya ba,in dai gulma da munafunci ne aikinta to za ta yi ritaya daga yau idan muka dirje bakinta da kashin awaki,gidan nan ma sai ya gagareta shigowa balle ta zo tayi gulmar mu" Tarasulu ta sauke numfashi a tsorace tana d'aga hannuwa tana rok'on su da cewa "Don girman Allah ku rufa min asiri Jummai,yanzu duk in da akaje cewa za a yi a gidana aka had'a wannan ruguntsumin,ni kuma ba don kuyi fushi na fad'a muku abin da Gimbiya ta fad'a a kanku ba,don Allah kar ku tada wata husuma ,kar kuje gidanta kuyi hak'uri maganar ta mutu anan" ta juya tana duban d'aya matar da ke gefenta ta rik'o hannunta tana ce wa. " Saude ki saka baki ki basu hak'uri dan naga Jummai da K'udisiyya sun d'auki zafi akan lamarin,ta k'ak'a za su ce wai sai sunje sun dirje bakin Gimbiya da kashin awaki?kuma har gidanta dan neman tashin hankali" Saude ta fizge hannunta tana sakin tsaki sannan ta ce . "Ai na su kad'an kika ji,su iya kashin awaki ne kawai makamin su,ni nan da kika ganni da askata nake tafe,wadda zan wa Gimbiya k'aton bille da ita" Dafe k'irji Tarasulu tayi cike da zaro idanuwa ta ce "Bille kuma Saude? wane irin bille kuma?don zatin Allah kuyi hak'uri" Saude ta ce "k'warai kuwa bille zan taya mata,ba a gabanki ta zo tana cewa wai billen mahaifina ya zanu ba?daga ganinsa rannan ya zo gidana duba Salim an masa kaciya tai ta kallon fuskarsa tana dariya,shine dan wulak'anci tazo gidan nan tana gulma wai da alamun da gatari aka yiwa mahaifina bille saboda ya zanu,to ni kuma yau za ta gani,dan wallahi bayan su Jummai sun dirje mata baki sai nasa sun danne min ita na tsaga fuskarta nayi mata bille irin na fuskar uban na wa" Gabad'ayan su suka kwashe da dariya,yayin da Tarasulu me kitso take basu hak'uri kamar ta tsuguna musu,amma suka yi banza da ita suka juya a fusace za su fita su nufi gidan Gimbiya, Zahra'u da Nana suka matsa a tsorace ganin tamkar wad'annan matan za su bangaje su,yayin da Tarasulu ta bisu tana rik'o su da basu hak'uri su kam ko sauraranta basu yi ba suka fice ,k'irjin Zahra'u na tsananin bugawa ta dubi Nana suka had'a ido,a zuciyar ta tana fad'in "Yau na sake shigowa wani cakwalin bala'in,wai shin kowane gidan kitso sai an samu irin wannan tarangahumar ne?" **************** A daren ranar da Harira ta dawo Amina da kanta ta umarci Sunusi da ya tafi d'akin Harirar ya kwana,domin a lissafinta ranar Harirar ce ke da miji,takaici ya ishi Sunusi kamar yayi kuka,kwata kwata baya son ya matsa daga inda Amina take saboda tsabar shagwab'ashin da tayi,in dai za su yi bacci sai ta san yadda tayi ta mammatsa masa jikinsa tayi masa tausa mai kyau saboda ta san aikin da yake yi na bulo akwai tarin gajiyar da ake kwasa,idan kuma ta kammala tausar haka take lankafeshi a zundumemen k'irjinta yasha baccinsa har da minshari da yawun bacci,duk inda ya kai hancinsa jikin Amina sak'o da lungu sai dai ya kwashi k'anshin Humra y'ar gaske,har cusa kansa yake tsakanin hammatar ta dan ya shak'i k'amshi me tafiya da hankalinsa,amma hammatar Harira fa?ni da (summun bukumun😂),Iya laushi da taushin da yake ji a luk'ek'en k'irjin Amina ko katifa albarka,har baya son Asuba tayi ya mik'e yin sallah saboda ya san lokacin dad'insa ya k'are,birgimar da yake yi da dadumar abubuwa son ransa yana cika hannunsa da su ya k'are,tilas haka yake mik'ewa ba don ransa yaso ba,to kuma wai yau d'in Aminar da kanta take umartarsa da ya tafi wajen Harira su kwana tare,ya san kwanan azaba kawai zaiyi,yadda ya saba da kwanciya cikin k'amshi ba zai iya kwana cikin d'oyi da samami ba,shi fa ko kallon fuskar Harira yanzu baya son yi,musamman idan ta wage masa baki da sunan murmushi sai yaji d'umbun takaici ya kama shi,ba k'aramin muni take a idanuwansa ba dalilin rashin hak'oran bakinta. Da yaga ba zai iya yiwa Amina musu ba tilas haka ya hak'ura ya fito daga d'akinta,amma ya gwammace yayi shimfid'a a tsakar gida ya kwanta da ya shiga d'akin da Harira take,sai da ya fuskanci Amina ta fara bacci sannan ya lallab'a ya koma ya d'auko bargo da matashi ya shimfid'a a tsakar gidan daga gefe ya kwanta,ya cukuikuye a cikin malum malum d'in da ke jikinsa ya lullub'a saboda gudun kar saurayen da ke tsakar gidan suyi masa illa,bai jima da kwanciya ba kam nan da nan bacci yayi awon gaba da shi ya fara sauke numfashi. Ita kam Harira duk abinda yake yi tana sane,bak'inciki duk ya cika ranta ta kasa bacci,ba k'aramin takura tayi a d'akin ba saboda k'aramine babu fad'i sosai balle tsawo,ga ta ita masha Allah tana da tsawo kamar samfalwa,ko ya ya ta mik'e k'afafuwanta sai su tokare babu alawus,ga d'akin duk ramukan kiyashi da cinnaka,ta kasa bacci amma daga in da take tana jiyo munsharin Amina tun daga d'akinta me kama da munsharin rago,takaici na k'ara cin zuciyarta tana jajantawa Saratu a zuciyarta,na tsawon lokacin da ta d'auka tana fama da minsharin da Salisu yake yi,to wai daman mutum yanayinsa yanayin munsharinsa kenan?idan kai lukuti ne haka munsharinka ma zai zama d'an lukuti?to amma ya aka yi Sunusi ba shi da k'iba amma shi ma yake ta kwarara munshari?kuma a lokacin baya baya yi,to ko dai zama da Amina ne yasa ya koyi munsharin shiyasa yanzu yake ta sakin abinsa?ita ta kasa bacci amma su sai baccin su suke shak'a sun barta da susar wuya da cinya?tabbas dole ta d'auki matakin farko ba zaiyiwu su suna sharar bacci ita tana cikin wahala da azaba ba,tilas ta d'an sammusu yanayin da take ciki ko suma sa d'and'ana. Zumbur ta mik'e ta k'aro hasken fitilar da ke gefenta tana dariyar mugunta,a hankali ta tashi tsaye ta nufi kwandon wanke wankenta da ke gefenta,ludayi ta zura hannu ta d'akko sannan ta nufi gefe in da ramukan cinnaku da kiyasai suke,babu tsoro haka tasa hannu tana tsintar cinnakun tana zubawa cikin ludayin da sauri sauri,sai da ta zuba kusan guda goma sha biyu sannan ta mik'e tana salallab'awa ta fito daga d'akin,wani farinciki ya tsirga mata da ta hangi k'ofar falon Amina a bud'e,tsallake Sunusi tayi ta nufi d'akin Aminar ta d'aga labulen ta shiga cikin d'auke numfashi da tafiya a hankali dan kar ta farka,saboda k'arfin hali irin na Harira har k'uryar d'aki ta shiga da ludayinta a hannu cinnaku fal a ciki,nan ta tarar da Amina tayi him a gado sai kwasar bacci take duk ta cika gadon, Harira ta k'unshe dariya a zuciyar ta tace"Wannan matar da saniya ce za a kwashi nama,musamman a samu wani gidan su yankata da babbar sallah a matsayin layya,wuuuuu gaskiya da anci nama mai yawa kuwa,iya cinyarta d'aya ta isa ayi dambun nama a cika fanteka da shi" Lallab'awa tayi ta isa inda Aminar take,baki a bud'e hanci a bud'e sai gurnanin munshari take, tana zuwa ta d'ebi cinnaku tasa mata d'aya kan hanci ,d'aya kan leb'en k'asa,d'aya a kumatu,d'aya a goshi,ganin Amina ta fara mutsu mutsu da sauri Harira tayi hanyar fita daga d'akin ta fito,tana zuwa tsakar gidan ta matsa kusa da Sunusi ta d'aga babbar rigar da ya lullub'a a hankali,dai dai k'eyarsa ta samu ta watsa masa ragowar cinnakun ,da sauri kuma tayi wuf ta shige cikin d'akinta tana rufe bakinta dan kar dariyar da ke cinta ta kufce har a jiyota. Ko cikakken minti uku bata yi da komawa d'akinta ba taji motsin Sunusi ya faraa buge buge da karkad'e malum malum sai zabga salati da hailala yake,matsawa tayi a hankali ta k'aramar tagar da ke d'akin tana lek'en tsakar gidan, sai ta hangi Sunusi a tsaye sai zare idanuwa yake yana susai k'eya,can kuma sai ga Amina ta fito da sauri zuwa tsakar gidan sab'atar sab'atar da ita,rigar baccinta iya gwiwa ta cika ta tayi dam,Harira ta rufe baki dariya na cinta,a zuciyar ta cewa take "Wannan ina ma iyayen ta ba Amina suka sa mata ba,don tafi dacewa a kirata da Maman Sumbi" A tsorace Sunusi ya juya ya dubi Amina,zaiyi magana kenan Aminar ta riga shi sai susar hanci da kumatu take " Me gida k'aik'ayi nake ji da wata irin azaba a fuskata,an ya kuwa ba cinnaka ne ya cijeni ba?" K'irjin Sunusi ya buga damm,ya matsa kusa da Aminar yana cewa " Nima yanzu na farka a gigice bakiji yadda k'eyata da bayana suke min zugi ba,kamar wanda kunama ta d'alla a.... Kafin Sunusi ya k'arasa maganarsa Amina ta zabura ta kai hannu ta daki goshinta tana sosawa,azaba ta ishe ta kamar ta mutu,idan ta sosa kunci sai ta sosa goshi,leb'en bakinta na k'asa kuwa ya kumbura yayi suntum jajawur da shi,ji take kamar ta tsinkeshi ta yar da shi don azaba,shi kam Sunusi k'eyarsa wani irin bird'in bird'in tayi kamar wanda ya k'one, sun rasa menene ya cije su da suke jin wannan azaba haka,safa da marwa kawai suke a tsakar gida kowa na fama da kansa, Harira na lab'e cikinta kamar ya fashe dan dariyar da ke cinta,tana kallo Sunusi yana ta fatali da kayan jikinsa,ya yar da malum malum,ya cire jallabiyyar jikinsa ma ya yar,hatta singleti sai da ya cire ya watsar,ya kama gajeran wandon zai cire Amina ta rik'e masa hannu a gigice da kumburarriyar fuskar ta ta ce "Mai gida a tsakar gida muke fa kar kayi tsirara" Sunusi ya fizge hannunsa ya kai bayansa yana susa idanu jajir,shi kad'ai ya san azabar da yake ji. Harira taji ina ma da zata sakawa Amina cinnakun a cikin rigar baccinta ta saka mata, kan zunduma zunduman nonuwanta,ta tabbatar da Amina ma sai tayi tunb'ur yadda Sunusi yayi,aikuwa da ta sha kallo ashe,ya za a ga Amina a tub'e?ina ruwan banu lukutuna 😂. Da taga suna ta safara a tsakar gida hakan yasa ta d'aga labulen d'akinta ta fito da fitila a hannunta,sai mik'a da hammar k'arya take kamar wadda ta farka daga barci,juyowa suka yi suna dubanta yayin da ta k'arasa garesu tana fad'in. "Wai lafiya nake ta jin motsinku da magana a tsakar gidan nan?me yake faruwa ne?" tana magana tana haska fuskar Amina da fitilar hannunta,ta wani zabura kamar zata yar da fitilar tana fad'in. "Kai ! an sukuta me ya sameki haka a fuskarki da leb'enki?kinga goshinki kuwa?uwa na wata yarinya Samiha da nake wa kitso lokacin baya, dan ita ma Allah yayi mata baiwar k'aton goshi wallahi" Amina tayi mata banza ta cigaba da safa da marwa dan azabar da takeji kan fuskarta ta isheta,bata da lokacin tasayawa kula wata Harira mara kan gado,Harira ta juya ta dubi Sunusi da ya lafe jikin bango sai gurza bayansa yake a jikin bangon yana cije baki idanuwa k'ulu k'ulu kamar su fad'o k'asa,saura kad'an wandon jikinsa ya fad'i k'asa dan mazarin da jikinsa yake yi,Harira ta k'unshe dariya tana fad'in. "Wai Sunusi me ya sameku ne?ko dai gamo kuka yi da aljanu da tsakar daren nan..... Wuf taga Sunusi ya daka tsalle zuwa gaban Amina har da d'an ihunsa yana fad'in " wihuhuuuu Amina dan Allah sosa min bayana da k'eya ta" Harira ta matsa ta haska bayan Sunusi da fitilar hannunta,ta zaro idanu cikin mamaki ta ce . "Sunusi ai wannan cizon cinnaka ne,subuhanallahi aikuwa in dai kuna son ku daina jin azaba to sai kun aikata wani abu tukunna" Da sauri Amina ta ce " To dan Allah me za mu yi mu daina jin zafi,wallahi ji nake kamar na cire fuskata na yar na huta dan azabar da nake ji" Harira ta maze kamar gaske ta ce. "Rikodar d'akin ki kawai zaki d'akko in saka muku disco,ku taka rawar amada 😂 ko etigi 😂 ko sabada😂 na rantse da kunyi zaku nemi azabar da kuke ji ku rasa" Wani mugun takaici ne ya kama Sunusi,ga azabar da suke ji ga rainin hankalin da Harira ke musu, bai san lokacin da ya d'ago a fusace ya gaurawa Harira mari me shegen zafi ba,fitilar hannunta ta fad'i,ta wage baki za ta saka ihu kenan Sunusi ya k'ara dunk'ule hannu ya kaiwa rub'ab'b'en dadashin bakinta naushi,sai ga Harira kwance riris ta fad'i tana birgima da shura k'afafu.....🤣 Comments Share Vote Pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA*✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA GOMA SHA BAKWAI DA NA GOMA SHA TAKWAS* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ *ASLM FATAN KUN WUNI LAFIYA HARYANZU DAI MUNA KARA TALLATA MUKU SABUWAR CHANNEL DIN DA ZATA RINKA KAWO MUKU LITTATTAFAI KALA DABAN² DAN ALLAH KU DANNA MANA SUBSCRIBE* DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ *K'awayen An gayu da Saratu ku fito yau fejin naku ne* 😂😂😂😂 ***Sallama ta ringa rafkawa tun daga k'ofar shiga gidan har ta dangana ga tsakar gidan,a nan ta ci burki tana sake d'aga murya tana kwad'a sallama da zazzak'ar muryarta,Hauwa da ke cikin ktcheen ta lek'o tana amsawa,bin matar da ke tsaye tayi da kallo cikin rashin sani,ta k'urawa fuskarta idanu sosai bakinta a sake, An gayu ta washe bakinta wanda ta rambad'a Jan jambaki me suna (Kan ta kile), Hauwa ta k'arasa fitowa daga ktcheen idanuwanta akan An gayu,kafin kuma ta bud'e baki cikin rashin sanayya tayi magana. "Baiwar Allah sannu da zuwa,amma ban shaida ki ba ko wani gidan kike nema?" Hauwa ta tambayi An gayu. Sake washe baki An gayu tayi ta sosa kanta sannan ta ce. "Ah ah nan gidan dai na zo,ni bak'uwa ce wajenki na zo". Mamaki ya kama Hauwa dan ita dai bata santa ba,ko mai kama da ita ma bata tab'a gani ba,wata irin mace a hargitse babu gyara,amma dan kar ta ce ta wulak'anta ta shiyasa ta d'an yi murmushi ta ce. "To babu laifi sannu da zuwa,shigo daga ciki sai mu gaisa". Tana fad'in hakan ta wuce falonta,yayin da An gayu ta bita jiki na rawa har hard'ewa take yi. Bayan sun zauna a kujerun da suka kewaye falon sai suka gaisa,An gayu sai kalle kalle take yi sosai falon ya birgeta,ita kuwa Hauwa babu abin da take kallo sai koriyar majinar da ta cika hancin An gayu,wani irin k'yank'yami take ji domin ko a hancin yaro ta tsani ganin majina balle a hancin babban mutum,har gara taga bayan gida akan taga majina,haka dai ta daure ta kawar da kai ta yi magana. "Baiwar Allah ina sauraronki,kiyi min bayani daga ina?domin ban shaidaki ba gaskiya". An gayu ta gyara zama ta dubi Hauwa tana murmushi ta ce. "Ni dai Suna na An gayu matar Babban malamin nan wato Malam Arabi,na tabbatar kin san shi domin kaf unguwar nan babu malami kamar sa,mun dawo layin nan da zama ne shine nace bari na shigo muga juna domin mu k'ulla zumunci tsakani na da ke a matsayin mu na mak'otan juna" Hauwa ta bud'e baki zata bawa An gayu amsa sai aka d'aga labulen falon aka shigo da sallama,da sauri Hauwa ta mik'e tana amsa sallamar tare da yi masa sannu da zuwa,Idrees ya amsa sannan ya dubi sashin da An gayu take ya d'an kalleta,wani irin yammmm ya ji a jikinsa sakamakon karo da curarren tasono da koriyar majina da yayi,da sauri ya d'auke kansa yayi hanyar cikin d'aki da hanzari ko amsa gaisuwar da An gayu take masa baiyi ba,Hauwa ta dubi An gayu tace mata. "D'an jirani ina zuwa" Tayi hanyar d'akin domin bin mai gida Idrees. Tana shiga ya juyo fuska a d'aure ya dubeta,a fusace ya tambaye ta. "Ke ! meye wannan abun na ci karo da shi a falo?" Hauwa ta rasa me yake nufi,dan bata gane hausar ba,shiyasa ta dubeshi cikin alamun tambaya ta ce. "Wane abu fa hubby?ban gane tambayar ba". Ya hayayyak'o mata. "Kan ban tsinke ki da mari ba shege nake,ina tambayarki kina tambaya ta dan kin raina min hankali?" Jikin Hauwa ya soma rawa saboda ta san jarabar Idrees,ba k'aramin aikinsa bane ya dalle ta da mari,gashi dai d'an tsurut da shi sai shegen zafin hannu,dan k'annensa ma har wani kirari suke masa da (me hannun kunama)dan idan ya mareka sai kaji kamar kunama ce ta d'alle ka a kumatu,sassauta murya tayi jikinta na tsuma ta ce. "Don Allah kayi hak'uri Hubby,wallahi ban gane abun da kake nufi ba ne shiyasa,amma ina neman afuwarka". Ganin yadda ta marairaice sai yayi tsaki ya d'an sassauto ya dubeta ya ce. "Wannan matar mara kyan fasali nake tambayarki,wacece ita?kuma daga ina take?wajen wa ta zo?" Ya jero mata tambayoyi idanuwansa a kanta. Hauwa cikin inda inda ta fara yi masa bayanin An gayu,bata ma kammala ba taga Idrees ya mik'e a sukwane yana muzurai,bai tsaya bin ta kanta ba kawai ya nufi falon da sauri,k'irjin Hauwa ya bada rasss! a hankali ta juya ta bishi falon jikinta sai rawa yake. Idrees na fitowa ya tarar da An gayu har da kashingid'a kan kujera tana lumshe idanu taji laushin (kushin),ya kwaye murya ya daka mata wata razananniyar tsawar da ta firgita ta,sai ga An gayu ta bud'e idanu a gigice tare da fad'owa k'asa daga kan kujerar rigijibbb! "Ke ! me ya kawo ki gidan nan dan ubanki?" An gayu ta razana sosai ,bata san lokacin da ta d'aga hannu sama bakinta na rawa ba ta ce. "K'arar kwana....! Idrees ya k'ara tamke fuska yana nuna ta da yatsa ya ce. "Idan k'arar kwana bata kawo ki ba k'ila rabon wahala ne ya kawo ki,baki da labarin na hana shigowa gidan nan ne?ko baki da labarin duk wanda ya shigo gidan nan baya fita k'alau sai ya karb'i kid'an janaral?to bari kiji in fad'a miki kin kawo kanki in da zaki karb'i tsarabar kulki da tiyagas". An gayu ta d'ora hannu aka ta rafka ihu had'e da salati,cikin kuka ta ce. "Ranka shi dad'e dan Allah kayi hak'uri,wallahi ni zumunci ne ya kawoni ba gulma ko kinibibi ba,don Allah kayi min rai in sha Allahu ba zan sake shigowa ba" ta juya tana kuka tana kallon Hauwa tana rok'onta akan ta bawa Idrees hak'uri,Hauwa tayi shiru domin ta san idan tayi magana bala'in kanta zai dawo,sai dai sosai An gayu ta bata tausayi ganin kukan da take sharb'a,sai shab'une take fuskar tayi dama dama da hawaye da majina,hakan ya k'ara fusata Idrees ya cigaba da masifa da hargowa. "Ke dalla malama rufe mana baki,in dai jumurinku bibiyar gidajen al'umma za ku jima kuna cin na akuya kuwa,y'an iskan mata magulmata munafukai,wutarku daban take ko a lahira matsiyata,wallahi ba don ina ganin mutuncin mijinki ba da sai na sa ammiki fiye da abin da na sa aka yiwa tinkiyoyin baya,sai na sa an zagargazaki fiye da inda bakya zato,k'azamar banza k'azamar wofi cikon benci cikon lissafi,tashi ki kwashi tsalolin k'afafuwanki masu kaushi da faso ki fice min daga gida tunda ba da gadon gyatuminki aka had'a aka kama hayar gidan ba" A gigice An gayu ta mik'e har zanin jikinta na niyyar salub'ewa ya fad'i k'asa,garin ta ja zanin sai ya hard'eta ta wuntsila ta kifa a k'asa,tsawa Idrees ya sake sakar mata wadda ta yamutsa mata y'ay'an hanjinta sai ga wata k'atuwar tusa ta fito b'urrrrrr.....b'urrrrr...b'urrrrrr...... wani azababben d'oyi ne ya daki hancin Idrees ya zabura yana toshe hanci cikin zare idanu ya ce. "Kutumar uban can,ke dan kan uwarki anan zaki mana rihi? Ya juya kan Hauwa da itama ta toshe hancinta saboda d'oyin da ya cika falon har mak'ak'i take ji a mak'oshin ta, daka mata tsawa yayi ya ce. "Ke shiga d'aki ki mik'o min wayar cajar nan da alamun matar nan sai jikinta yayi tsami za ta ..... Kafin ma ya k'arasa wuf An gayu ta mik'e da hanzari tana ta ta ta ta fice daga falon,ga tusar kuma tak'i tsayawa tana tafe tana sakin abarta b'urrrrrrrr ! A haka a daddafe ta samu ta fice daga gidan zuciyarta kamar ta fad'o k'asa saboda tsoro,ta bar Idrees yana ta bala'i da masifa,har kuma ya juya kan Hauwa yana sauke mata na ta fad'an,wai wallahi dole sai ta wanke kujerar da An gayu ta zauna da kafet d'in da ta taka na tsakiyar falon,sannan yace ta je ta d'auko air preshner ta feshe gidan gabad'aya da shi,ita dai Hauwa tsit tayi saboda tana tsoron ta tanka ya lafta mata hannunsa me cike da murd'ad'd'un jijiyoyi ya safa mata kumatu. *************** Tunda Salisu yayi wa Hajiya Maimuna waya akan gashi nan ya tawo zuwa gidanta take ta d'oki,nan da nan ta tura gidan malam me almajirai aka yi mata kiran Saratu,domin tana son ta had'a su waje d'aya ne tayi musu nasiha,haka nan ta taushi Salisun domin ya mayar da Saratu d'akinta su cigaba da zaman aure. Haka Saratu ta tawo tsolai tsolai da ita babu wanka balle wata kwalliya,dan idan ma tayi kwalliyar ba kyau take ba saboda tsabar rama da lalacewar da tayi,har wani doro me kama da k'usumbi ne ya fito mata,ita ma Hajiya Maimuna bata ce Saratun ta gyara jikinta ba,saboda tafi son Salisun ya ga yadda Saratun ta koma k'ila hakan zai sa yaji tausayin ta yafi mai da hankali akan ya mayar da ita d'akin ta, Saratu ta shige falon Hajiya Maimuna ta zauna ta takure,ga carbinta a hannu tana ja,burinta kawai tayi ido biyu da Salisu ko zai tausayawa halin da take ciki,domin ba k'aramar wahala take sha zamanta cikin gidansu ba,rayuwarta ta zama tamkar ta akuyoyin cikin gidan tunda cikinsu take rayuwa. Hajiya Maimuna ta fito daga band'aki kenan rik'e da buta a hannunta taji sallamar Salisu,ajiye butar tayi a gefe ta fara washe baki cike da murna take amsa sallamar sa,shigowa yayi shi ma cikin fara'a sosai,Hajiya Maimuna ta rik'e hab'a cike da mamaki take fad'in. " Tubarkallah ma sha Allah Salisu haka ka k'ara yin shirgegiyar k'iba?ko dan dai na jima ban ganka ba ne?" Salisu yayi y'ar dariya yana fad'in " Wallahi kwanciyar hankali kawai na samu Hajajju,ina shan sharafina yadda nake so shiyasa na k'ara wata k'ibar akan ta da" Dariya Hajiya Maimuna tayi tana girgiza kai,sannan ta ce. "To babu laifi Allah ya k'ara wadata,shiga ciki bari na zo mu gaisa mu tattaunar maganar da na kirawo ka akanta ko?" Salisu ya jinjina kai ya wuce tink'is tink'is zuwa falon mazaunansa sai rawa suke,Hajiya Maimuna kuma ta nufi ktcheen domin ta d'akko masa ruwan sha. Da sallamarsa ya shiga falon duk da baiyi tunanin zai tarar da wani mutum a ciki ba,saboda kamata yayi duk in da za ka shiga ya kasance kayi sallama,ga mamakinsa kuma sai ya tarar da tsamurarriyar tsohuwa a zaune ta takure da carbi a hannunta tana ja,cikin barkwanci ya nufe ta yana murmushi da fad'in. "ah ah ! Goggo Laminde saukar yaushe?ashe kina ciki?aikuwa ko jiya munyi waya da Malam amma bai shaida min kin zo ba,ai da tuni na zo na kwashi gaisuwa" Gaban Saratu ya yanke ya fad'i,ita kuwa wace irin lalacewa tayi da kowa yake kwatantata da Baba Laminde?Baba Laminden da a k'iyasi ta ba wa shekaru saba'in baya,idan kowa ma bai shaidata ba ai bai kamata Salisu ya kasa shaidata ba,wani hawaye mai zafi ya tawo mata,ta sunkuyar da kai tana sharewa. Shi kam Salisu matsawa yayi sosai gabanta ya tsuguna yana y'ar dariya yana kallon carbin hannun ta,sannan ya kuma ce wa. "Dad'i na da ke y'ar tsohuwar nan akwai ibada,to salatin da kike ne ya saki kuka ko me?ni dai kar a manta dani a sakani a addu'a,domin akwai albarka a cikin bakin nagartattun tsofaffi irinku". Lokacin ne Hajiya Maimuna ta shigo falon rik'e da ruwa a hannunta,Salisu ya juya yana murmushi ya kalleta ya ce. "Hajajju ashe Goggo Laminde ta zo bani da labari,ai da kin fad'a min da na tsaya nayi mata tsarabar goro me kyau,dan kuwa na wuce ta wajen masu siyar da shi naga daushen goro mai kyau da gani zaiyi dad'i" Ajiye ruwan Hajiya Maimuna tayi ta samu gefe ta zauna,ta mayar da hankali kan Salisu tana fad'in. "Ikon Allah! kaima Salisu baka shaida wannan ko wacece ba kenan ?har kake tunanin Baba Laminde ce?" Salisu cikin mamaki ya ce. "Au wai ba ita ba ce?wallahi ni na zaci ita ce,to daman tana da wata k'anwa ne mai kama da ita? Murmushin takaici Hajiya Maimuna tayi,sannan ta ce. "Abin da nake so kazo ka ganewa idanuwanka kenan Salisu,wannan dai da kake gabanta ba Baba Laminde ba ce,ni ma da na dawo daga mai duguri ganin farko da nayi mata na za ci Baba Laminden ce,sai da aka sanar da ni wai ashe Saratu ce ta koma haka" Kan Salisu ya toshe ya rasa ma wace Saratun ake nufi,kallon Hajiya Maimuna yake kawai da mici micin idanuwansa da suka shige loko,Hajiya Maimuna ta jijjiga kai cikin tabbatarwa ta ce masa. "Wannan dai da kake gani ba kowa ba ce face Saratu matarka" Sai ga Salisu yana niyyar mik'ewa a gigice,nauyin da jikinsa yayi masa ne ya hana shi mik'ewa ya koma jab'ar yayi zaman y'an bori yana zungura kai .😂 Comments Share Vote Pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA GOMA SHA TARA DA NA ASHIRIN* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ *AYI HAK'URI RASHIN JINA KWANA BIYU,HIDINDIMU SUNYI YAWA GA KUMA MAKARANTA,A DINGA YI MIN UZURI MASOYA* 👏🥰 ***Hajiya Maimuna ta zubawa Salisu idanu ganin yadda yayi jab'ar sai zungura k'eya yake yana zare idanuwa yana kallon Saratu wadda kanta ke sunkuye idanuwanta na zubar da hawaye,da k'yar Salisu ya iya bud'e baki cikin k'arfin hali ya ambaci sunan Saratu,d'agowa tayi ta kalleshi tana shesshek'ar kuka,ya tsurawa fuskarta idanu wadda ta zama kamar ta yamushasshen b'era irin ya takure d'innan zai shuka b'arna,Salisu bai san lokacin da ya tuntsire da wata mahaukaciyar dariya ba har da rik'e ciki,dariya yake bil hak'k'i har da hawaye,Hajiya Maimuna ta bishi da kallo ganin har da kwanciya a gaban Saratun yana birgimar dariya,idan yayi dariya ta isheshi sai ya d'ago ya kalli fuskar Saratu ya ce "Saratu" Idan ta d'ago ta kalleshi tana kuka sai yaga fuskar ta koma masa tamkar ta zomo ba b'era ba,sai ya kuma kwashewa da dariya,wannan dariya ita ta kuma raunata zuciyar Saratu ta sake fashewa da matsanancin kuka,ita kam Hajiya Maimuna suguri tayi tana kallon Salisu cike da mamaki. Sai da taga dariyar ta sa tayi yawa sannan ta dakatar da shi da fad'in. "Haba Salisu da girmanka za ka zauna kana dariya har da birgima?maimakon ka tausayawa halin da take ciki na bala'i da masifa sai ka zauna ka dinga shek'a mata dariya?" Salisu ya tsagaita da dariyar tare da goge hawayen da ya ratso masa,ya dubi Hajiya Maimuna ya ce. "Wato a rayuwa mutum ya gama shuka shakiyancinsa Hajiya,akwai ranar da Allah zai kama shi,dubi dai yadda wannan baiwar Allah ta zama sai kace mai lalurar k'anjamau" Hajiya Maimuna ta ce "Hmmmm ! kai dai bari kawai Malam Salisu,in fad'a maka fa ranar da na ganta na zaci lalurar k'yanda take,ni shaf ma na manta da cewar yara ne suke wannan ciwon sai da mahaifiyarta ta ankarar da ni" Hajiya Maimuna ta d'an yi shiru tana numfasawa cike da tausayi da alhinin halin da Saratu take ciki,Sannan ta d'ago kanta ta sake kallon Salisu tana marairaice fuska domin dai ya amince da abinda za ta fad'a masa. "Akan wannan dalilin ne yasa nace bari na kirawo ka mu tattauna,ka dubi girman Allah da darajar karatun Alk'ur'ani mai girma wanda mahaifin yarinyar nan ya koyar da kai tun kana yaro har ka girma a wajen sa,ka dubi raunin da mace take da shi,ka dubi sauyawar kamanni da wahalhalun da wannan baiwar Allah take ciki,haka nan ka dubi fushin da mahaifinta yake da ita,da ma wasu abubuwan da dama,duk su za ka duba ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi kayi hak'uri da duk wasu abubuwa da suka faru a baya,a sasanta domin ka mayar da matarka d'akin ka Malam Salisu" A gigice ya zuba wa Hajiya Maimuna idanuwa zuciyarsa na tafasa,idan da abinda ya tsana bai wuce ace ya mayar da Saratu gidansa ba,shi kad'ai ya san wahala da k'angin da ya shiga a dalilin zama da ita,da wata ce tayi masa wannan zancen ba Hajiya Maimuna ba zai iya bajeta a wajen nan take,take ransa yayi mugun b'aci yayi kicin kicin da fuska kamar ba shine me tuntsira dariya har da birgima a yanzu ba.. Lura da sauyawar da fuskarsa tayi sai Hajiya Maimuna taji gabanta ya fad'i,amma duk da hakan bata sare ba,ganin Salisun yayi shiru bai ce komai ba sai numfarfashi yake,ya cika ya batse dammm! k'iris yake jira yace tushhhh! domin ya fashe,Sai ta k'ara gyara zama ta dubi Saratu da ke ta sharar hawaye,tausayin ta ya sake kama zuciyar ta,ta sake mayar da kallonta zuwa kan Salisu da b'ata ran da yayi ya saka kumatunsa huruwa kamar an kwab'a (Alkubus), Hajiya Maimuna bata tab'a lura da manyan (Tayani muni)da ke fuskar Salisu ba sai a ranar,Daurewa tayi ta sanyaya murya ta cigaba da magana domin dai ta samu nasara. "Na san cewa a zamanka da Saratu kai take cuta,kuma daman dul lokacin da kaji ana bawa mutum hak'uri to tabbas an cuce shi ne,kuma kar ka manta masu iya magana sun ce (Babba juji) . Hakan ya sa kaine babba tilas sai kayi hak'uri da zamantakewar da za ka yi kai da iyalinka,duk abubuwan da suka faru tsakanin ku naji labarinsu kuma na tausaya maka domin kasha wahala tabbas,kuma kayi hak'uri,amma ina so ka k'ara hak'urin Salisu,duk wanda yayi hak'uri zai ga riba a rayuwar sa,don Allah da Manzon sa ( S A W) ka taimaka ka mayar da komai ba komai ba kayi hak'uri ku sasanta domin ta koma d'akinta,zaman ku a haka ba shi da wani amfani ko fa'ida,aure shine cikar mutuntakar mutum a rayuwa". Sauke Numfashi Salisu yayi idanuwansa har sun sauya kala,maganganun Hajiya Maimuna sun shiga jikinsa,sai dai abubuwan da Saratu tayi masa suna dawowa cikin k'wak'walwarsa,raini iya raini da aibantawa da kushe halittarsa babu wanda Saratu bata k'ware akai ba,ballantana a zo kan raina mahaifiyarsa da tayi,kai tsaye take ambatar ta ta zageta duk da kasancewar bata raye tana cikin k'abarinta,amma duk da hakan idan fitsarar ta ta motsa ambatota take da (Iya me ido d'aya) saboda kawai idon ta guda d'aya hallararre ne ya samu matsala,bayan wad'annan abubuwan ga shegen lek'e da ta k'ware a kai,tsayawa da maza suna hira tana wage baki kuwa har bai san adadin da tayi ba,dan akwai ranar da ya tab'a tarfa ta a soro daga ita sai d'aurin k'irji,sai wani yalolon mayafi da ta yafa,tana tsaye ta kirawo me siyar da kifi (Sukumbiya) suna ciniki,sai shakiyanci suke suna tuntsira dariya,da ya bata kifin har da cewa wai yayi k'ank'anta,gara ya duba ya nemo mata zundumeme me kama da cinyar mijinta,shi kuma me kifin sai dariya yake suna ta shakiyanci dai saboda rashin tsoron Allah da kamun kai. Hajiya Maimuna ganin yayi shiru bai ce komai ba ta san tunanin abubuwan da suka faru yake,hakan ya sa ta k'ara yin magana kafin ma ya tanka. "Salisu idan har za ka dinga tuna abubuwan da suka faru a baya to zuciyarka ba zata yi sanyi ba,za ta dinga ciwo ne kawai a banza,ka manta baya da abubuwan da duk suka faru,ka fuskanci gaba tare da addu'ar komai ya zama kaffara a d'ora sabuwar rayuwa,ina tabbatar maka Saratu in dai ba ta amsa sunan Jaka ko Jahila bane babu ta yadda za'a yi ta maimaita rayuwa irin ta baya,domin taga ishara ta d'and'ana rayuwa ta wahala da tozarta duk da a gaban iyayenta take,ta gasu iya gasuwa,na tabbatar rayuwar da ta d'and'ana ta hankalta,ba zata sake aikata wani abu mummuna a zaman aurenta ba,kuma kafin ma na kirawo ka sai da na zaunar da ita muka yi magana,wallahi Saratu tayi nadama sosai akan dukkan abin da ta aikata, ta wahala sosai,baka ga yadda ta koma bane kamar k'warangwal? to tsabar wahala da yunwa ne,domin Malam me almajirai baya bata abinci ta ci ta k'oshi,a yanzu da Saratu za ta matso kusa da kai tayi magana uban d'oyin da bakinta yake sai ya gigita ka,yunwa ce ta rarake mata ciki ta assasa mata miki cikin cikinta,numfashin kansa azabar wari yake,ya kamata a duba domin a fitar da ita daga wannan k'angi haka ta horu da yawa" Salisu ya kalli k'aton tumbinsa da ke jikinsa,gashi an ce Saratu tana d'oyin baki,idan ya mayar da ita d'oyin bakin na ta ya k'ara kumbura masa ciki ya zaiyi kenan? Wata lukutar ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi ya dubi Hajiya Maimuna ya fara magana. "Hajajju naji dukkannin bayanan da kika yi,kuma ke d'in a matsayin mahaifiya na d'auke ki tunda babu abinda baki yi min ba,wallahi a da na rufe babin Saratu a rayuwata domin zamana da ita na tagayyara matuk'a da gaske,duk da kince kar na tuna baya,a tun farko daman ita Saratu ba kalata take so ba,dan dai babu yadda za ta yi da mahaifinta ne da ya zab'a mata ni a matsayin mijin aure,kuma taje ta had'u da shakiyyan mak'ota suka dinga zuga ta suna d'ora ta kan bak'ar turba,tarbiyyarta ta lalace,babu irin nasiha da ban baki da bana yi mata amma tak'i saurarata,shiyasa na gaji da halinta har ta kaimu ga rabuwa,to amma Hajiya ni ba zan iya yi miki musu ba,zan mayar da Saratu d'akinta mu cigaba da zama,amma bisa wasu sharad'ai da zan kafa mata idan ta amince da su " Kafin Hajiya Maimuna tace komai Saratu ta zabura cike da tsananin murna ta rarrafa gun Salisu,cikin hawaye ta fara magana d'oyin bakinta na dukan k'ofofin hancin Salisu,nan da nan ya matsa da sauri yana kawar da kai. "Wallahi,wallahi,wallahi,na rantse maka da k'udura da irada ko me kake so zanyi Yaya Salisu" "Kambu!" Salisu ya ambata a ransa,lallai Saratu ta luguiguita tunda yau har ya samu canjin suna,yau shi Saratu ta kirawo da (Yaya Salisu) Saratun da ta sanya masa suna kala kala a baya na cin mutunci da muzanci,sunaye kala kala,irinsu d'an lukuti🤣 d'an sukuti 😂 dindimijijjib'i 😂 😂k'olo 🤣gardi 😂 basamude🤣 da dai sauran su. ************** Yana zaune a tsakar gida kan tabarma da wata zungureriyar bulala a hannunsa,a gefe ga man ja da man shanu sai shafawa bulalar yake yi tayi jajur da ita, A guje An gayu ta shigo gidan ko sallama babu,bata san lokacin da tayi fatali da robar manjan da ke gabansa ba man ya b'are a k'asa,tuntub'e ta ci da k'afafun Malam Arabi tana niyyar kifawa da hanzari ta mik'e tana rik'e zani tayi band'aki da gudu ta fad'a tana nishi. A gigice Malam Arabi ya mik'e tsaye yana zare idanuwa cike da tsoron da yaji,ya dinga waige waige domin yaga abin da ya razana masa matarsa haka,a hankali ya dinga tafiya salaf salaf har ya isa soro ya lek'a waje ko zai ga wani abun amma bai ga komai ba,juyowa yayi ya dawo cikin gidan yana sauke numfashi,yana shigowa ya jiyo muryar An gayu daga band'aki tana k'wala masa kira. "Malam...Malam kawo min ruwa a buta zan yi tsarki" Tsaki ya ja sannan cikin fad'a ya d'aga murya ya ce. "Wai ke baki san babu kyau magana a bayan gida ba?idan mutanen na mu suka wurgoki waje ke kika sani babu ruwana,kuma dan wulak'anci ma me ya sa zaki shiga bayan gida babu ruwa?" Yana jiyo muryar An gayu tana ce wa. "Yo Malam baka ga yadda na shigo gidan a (tiri sittin ba) baka san bala'in da ya koroni ba ne,ni ka mik'o min ruwa in yi tsarki ko kuma na fito a haka kayi min tsarkin da kanka" Wata muguwar harara Malam Arabi ya bankawa k'ofar band'akin,ya nufi in da buta take ya zuba ruwa sai sababi yake. "Allah ya tsareni da wanke miki gayad'i An gayu,na jikina ma dan ya zame min dole ne na wanke shiyasa" A haka ya d'auki butar yaje ya kai mata ya d'an bud'e k'ofar ya zura mata butar yana toshe hanci saboda warin da ya bugo shi. Can jimawa An gayu ta fito tana sauke wahalallen numfashi,Malam Arabi da ke tsaye ya dubeta cike da takaici,musamman da yaji ta ce masa. "Malam ashe kashi bala'i ne,aradu shingin kad'an nayi a buje na" Hararta yayi ya ce. "Tsakani da Allah An gayu kin firgitani,kina matar Malam ki shigo gida da gudu babu sallama?me ya firgitaki haka daga shigarki mak'ota ki fito? Allah yasa dai baki yi musu halin ki na tusa ba,domin ke dai mazaunanki ba iya rik'e rihi suke ba,ga maganin basir nan na jik'a nayi nayi da ke ki d'auka ki sha amma kin k'i,wani lokacin takaicin ki kamar ya sakani kuka wallahi,ke ki d'ura min takaici a makaranta ma ban tsira ba,shakiyyan d'alibai sai tsula iskanci suke,duk wadda tayi laifi da an doketa sai ta fad'i tana shure shure wai aljanu,to duk za su ci ubansu ga sabuwar bulala nan na siyo na shafeta da manja,babu munafukar yarinyar da zan saurarawa,duk wadda ta kuma yi mana aljanu jikinta zan tsamama mata" An gayu ta nemi waje ta zauna tana zare idanu,sannan ta ce wa Malam Arabi " Hmmmm ! mai gida yau ni naga abinda ya isheni,daman akwai maza ma masu aljanu ne? gidan da na shiga fa ina jin mai gidan Aljanu ne da shi,kaga yadda ya dinga zambarwa yana zare min idanu kamar tsohon kwarto kuwa?shine fa ya hautsina min ciki da ihunsa har ban san lokacin da na tako a guje ina sakin tusa ba,kai Allah buwayi gagara misali ban tab'a ganin tijararren mutum irin wannan mutumi ba,matsiyaci fuska duk jijiyoyi,Allah ya isa tsakanina da shi gantalalle mara mutunci,domin ba k'aramin d'aukar hakkina yayi ba" Malam Arabi ya matso ya zauna kusa da An gayu cikin mamaki ya ke fad'in. "Wai wanene haka?me ya faru ne?" An gayu ta kaikaice ta fara bashi labarin abin da ya faru,sai ga Malam Arabi na muguwar dariya har da rik'e ciki,fad'i ya ke. "Maganinki kenan uwar gantali da cusa kai....! Comments Share Vote Pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA ASHIRIN DA D'AYA DA NA ASHIRIN DA BIYU* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ *SAK'ON FATAN ALKAIRI DA BANGAJIYA GA MARUBUTAN DA SUKA HALARCI TARON MARUBUTA NA (BAKANDAMIYA)ALLAH YA CIGABA DA BAWA MARUBUTA NASARA,ALLAH YA K'ARA MUSU BASIRA DA HAZAK'AR KAWO LABARAI WAD'ANDA ZA A K'ARU DA SU,ALLAH YA NUNA MANA WATA SHEKARAR DA RAI DA LAFIYA* 🥰👏 ***Washe gari misalin k'arfe tara na safe,Habiba Zaune a tsakar gida kan tabarma sai hamma take,kana ganinta kasan yunwa take ji,Babalalo ne ya shigo da bak'ar leda a hannunsa yana sallama,da sauri ta amsa tana kallon ledar hannunsa sai tand'ar baki take tana zare ido,mik'a mata ledar yayi sannan ya shige cikin falo kai tsaye,da sauri ta karb'a jikinta na rawa,yunwa take ji sosai gashi ranar basu tashi da komai ba da za ta dafa,shiyasa tace Babalalo ya taimaka ya siyo mata shayi can k'asan layin su,mik'ewa tayi ta nufi ktcheen d'in ta ta d'auko k'atuwar mod'a da zata juye shayin,sai faranti da ta d'auko a zatonta cikin ledar har da indomie,dan kuwa kafin ya fita tana ta had'ashi da Allah akan ya siyo mata indomie marmarinta take. Sai da ta dawo ta hakimce kan tabarma jikinta har rawa yake,burinta taji indomie ta baje a bakinta,yayin da zata kora da shayi had'in kauri,tana bud'e ledar ta ci karo da farar leda da aka d'aure Koko a ciki,sai wata takarda da ta warware taga K'osai mai zafi a ciki yayi jajur da shi,wani bak'inciki ne ya daki zuciyarta take ta b'ata fuska,babu abinda ta tsana irin Koko,amma shine Babalalo dan wulak'anci ya siyo mata shi,d'aukar ledar tayi ta juye kokon a mod'ar da ta d'akko,sannan ta figi mod'ar ta fad'a cikin falon tana buntsura baki da hura hanci. Babalalo ta tarar ya jona k'arfen guga yana goge kayansa da zai saka ya fita,taji kamar ta juye masa Kokon a gadon bayansa,daurewa tayi cikin nunk'ufurci tayi magana tana rik'e k'ugu da hannu d'aya. "Gaskiya ni Babalalo ka gama da ni,sai da ka bari na gama sa rai zanci indomie kawai sai ka had'ani da koko?" Ya cigaba da gugar sa ko kallonta baiyi ba,sai dai ya bata amsa da cewa. "Gani nayi kinfi dacewa da Kokon shiyasa na had'aki da shi" Ranta ya b'aci da jin maganarsa,cikin hargowa ta ce. "Wallahi kaima kasan k'arya ka fad'a,ko a gidan ubana shayi nake sha ba Koko ba" Tana direwa ya amsa da ce wa. "To yanzu ai ba a gidan ubanki kike ba,gidan aure kike,kuma dole kiyi hak'uri da abinda ya samu,sannan ina umartarki da ki kauce a kaina idan ba haka ba na juyo billahillazi sai na b'arar da ke" Habiba ta harari k'eyarsa ta kauce da sauri,dan ta san idan tijararsa ta motsa wulak'ancinsa yawa ne da shi,fita tayi daga falon da Kokon a hannunta,ban da yunwar da take ji sosai babu yadda za a yi tasha wannan Kokon,dan dai bata da ko kobo ne da shayi za ta siyo da kanta,har gara a bata kunu da a bata Koko,kunu kam da kanta ma tana damawa amma ta tsani Koko,zama tayi ta fara kurb'ar Kokon tana had'awa da k'osan. Can ta jiyo muryar Babalalo yana tsaki da sakin maganganu,ta kasa kunne sai taji yana fad'in. "In dai Koko ne kin had'u da shi,ni zaki kawowa tantiranci wai bakya shan Koko,ni yanzu ma tunda na samu a layin nan ana siyarwa ai na huta da siyan gero ko siyo shayi,Kokon naira ashirin k'osan talatin ya isa in siyo miki ki karya da shi" Habiba tayi shiru ranta duk a b'ace,tunani take wane gida ne a layin ake sayar da Koko?sai can ta tuna da matar malam Arabi wato An gayu,dire mod'ar Kokon tayi da hanzari ta mik'e ta fad'a falon a gigice,Zabura Babalalo yayi yana cillar da dutsen gugar saboda yadda ta dira a gabansa ta tsorata shi, "Ke lafiya?wannan wane irin wulak'anci ne zaki tsoratani?da kin sa na k'one fa?" inji Babalalo. Cikin zare ido Habiba take tambayar sa. "Don Allah a ina ka siyo wannan Kokon da K'osai?" Tsaki yayi yana d'aga dutsen da ya wurgar,sannan ya ce mata. "Daman abinda za ki ce min kenan kika firgitani?ke dai naga randa za ki yi hankali Habiba, to nan mak'ota ne da suka tare matar malam Arabi ke siyarwa" Wani bala'in tashin hankali ne ya ruftowa Habiba,take idanuwanta suka hasko mata curarren tasonon da ke hancin An gayu da koriyar majina shar,wani azababben amai ne ya yunk'uro mata ta dafe kai,take ta fara shek'a shi a kan gogaggun kayan da Babalalo ya goge zai saka domin ya fita. Tsalle Babalalo yayi gefe guda yana dafe kai cikin matuk'ar takaici yasa k'afa ya haure Habiba da ke shek'a amai ya gara kanta da garu,cikin bala'in b'acin rai ya ke sababi. "Kan uban can kayyasa! idan ba sai kin wanke min kayana ba shege uwata ta haifeni,in wanke kayan in goge amma kiyi min amai akai dan wulak'anci?kin tashi ko sai na saka k'afa nayi ball da ke?" Habiba da k'yar ta mik'e jikinta na rawa sosai,ta kwashi kayan ta fice har lokacin zuciyarta tashi take yi,Babalalo ya bita tsakar gidan ya saka ta a gaba sai tijara yake mata har ta wanke masa kayansa fes yana tsaye a kanta. ************ A gefe guda kam Harira cike take da takaicin abin da Sunusi yayi mata,kuma a ranta ta d'au alwashin bashi ya d'auka domin sai ta fanshe,tunda sanin kansa ne ba'a tab'a ta ta k'yale,babu abin da ke d'aga mata hankali irin yadda kowa idan ya tashi dukanta bakinta yake hari,an maida bakinta wajen gwada k'wanji,ko wane shege da me lukutin hannu da me siririn hannu duk k'ashi da sun d'aga hannu su sauke mata shi a dadashinta,aikuwa ta daina ragawa kowa,duk d'an iskan da yayi mata sai ta rama. Tana zaune tana wannan tunane -tunanen har ta hango hanyar ramuwa,murmushi ya sub'uce mata,ta k'ara gyara zama tana janyo wata leda mai cike da kayan miya da Innan Sunusi ta harhad'o mata,kayan kad'i ne irin su Kuka da kub'ewa har da su waken miya da gyad'ar miya,tana cikin lalubawa ta ci karo da abin da take son gani wato (Kalkashi) . Tun a lokacin ta fara dariya saboda ta san muguntar da zata had'awa Sunusi zai ji jiki,ta san ba zai jima ba zai shigo,kofi ta d'auko ta jik'a wannan kalkashi me mugun yauk'i,tsayawa tayi a bakin tagar k'aramin d'akinta tana lek'a tsakar gidan,tana kallo Amina ta fito daga d'akinta da d'aurin zani a k'irjinta,ga kuma bokiti da kwandon wanka da alamun band'aki zata shiga tayi wanka,akan idanunta Amina ta bud'e rijiya ta saka guga ta janyo ruwa ta cika bokitin taf,sannan ta d'auki ruwan ta shige band'aki domin yin wanka. Amina bata jima da fara wanka sosai ba Harira tana nan tsaye ta jiyo muryar Sunusi daga soro kamar yana waya,da wani irin sauri ta fito domin aiwatar da nufinta dan kar ta rasa damar,k'ofar d'akin Amina taje ta juye wannan ruwan Kalkashi me mugun yauk'i,ta sa tsintsiya ta damalmala wajen,motsin Sunusi yasa tayi hanzarin komawa d'akinta tana k'unshe dariya,saboda ta san babu inda Sunusin zai nufa idan ya shigo sai d'akin Amina. Sunusi kam bayan ya gama wayarsa sai ya fad'o tsakar gidan da sallamar sa,cikin farinciki kuma ya nufi k'ofar d'akin Amina yana runtse idanuwan sa wai shi bai yarda ba lumshe ido yake🤣 Cikin jin shauk'in soyayya kuma ya d'aga murya ya fara rairowa Amina wani baitin wak'a da Umar m sharif yayi. *Ina kike masoyiya?* *Na duba gabas ban ganki ba* *Na duba arewa ban ganki ba* *Na duba kudu ban ganki ba* *Na duba yamma ban ganki ba* Sai kuma ya juya kan wak'ar Nazifi asnanic cikin wak'ar sa ta. *Amina Amina y'ar auta Amina tauraruwar mata* Yana yi yana tafiya a hankali idanuwa a runtse da nufin Aminar ta fito ta tarbeshi,ko domin tayi masa masauki a lafcecen k'irjinta mai cike da abubuwa,Ita kanta Aminar jin muryarsa yana rairo mata baitoci tuni shauk'i ya kamata,nan da nan ta zundumi ragowar ruwan bokitin ta shek'a a jikinta ta figi zani ta d'aura da nufin fitowa domin tarbar mai gida Sunusi. Shi kam Sunusi Angon Amina baiyi aune ba idanuwa a rufe kansa tsaye ya tunkari k'ofar d'akin Amina,shi dai da wani mugun santsi ya kwashe shi sai ji yayi kamar an d'aga shi sama an nunawa Allah shi an fyad'a shi da k'asa,wani gigitaccen ihu ya saki domin ba k'arya dandamalin k'eyarsa ya bugu ainun,ihunsa ne ya saka Amina cillar da bokitin hannunta ta fito da gudu daga band'aki a gigice tana sab'ar sab'ar daga ita sai d'aurin k'irji,ganin Sunusi yayi balance a k'asa bata san lokacin da ta kwaso sauri ba hankali a tashe,dab da zata iso gareshi domin ta d'aga shi ita ma santsi ya kwashe ta,kamar wadda akayi wurgi da ita sai gata akan ruwan cikin Sunusi rigijib,Sunusi ya k'walla wata razananniyar k'ara yana jin kamar zai kasayar da kayan da ke cikinsa,zaman y'an borin da Amina tayi akan cikin Sunusi sai ta kasa mik'ewa jikinta yayi mata nauyi,shi kuma Sunusi ya kasa ture ta sai ihu yake yana fad'in a taimake shi gingimari ta danne masa ciki😂,haka Amina ta dinga k'ok'arin zamewa daga kan ruwan cikin Sunusi da k'yar,ta dinga turo mazaunanta saitin fuskarsa tana niyyar mik'ewa,da dai azaba ta ishi Sunusi yaji kamar zai mutu ai sai ya samu tsakiyar d'uwainiyar Amina ya kafa kaifafan hak'oransa ya dinga cizgo tsokar wajen,Amina taji sukutar azaba ba shiri tayi wani zillo ta fad'o k'asa timmmm ta wargaje har zaninta na kwancewa 😂Shi kam Sunusi numfashin azaba da wahala kawai yake saukewa yana jin kamar k'eyarsa ba a jikinsa take ba,ga cikinsa na kartawa dalilin ziyarar da ya samu na d'uwaiwukan Amina😂 . Gogar ta ku Harira kuwa na lab'e jikin tagar d'akin ta tana kwasar dariya kamar wata zararriya🤣🤣🤣. Comments Share Vote pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA ASHIRIN DA UKU DA NA ASHIRIN DA HUD'U* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ *WANNAN FEJI SADAUKARWA NE GA MALAM ARABI NA ANGAYU😂DON ALLAH KAR KUYI MASA DARIYA SOSAI🤣NIMA KAD'AN NAYI* 🤭 ***Sai da aka d'auki tsawon lokaci kafin Sunusi ya dawo dai dai,kwata-kwata kuma kunnensa bai jiyo masa dariyar da Harira ke shek'awa ba,amma ita Amina tana jiyo Harira,hakan yasa ta gane duk abin da ya faru to da saka hannun Hariran a ciki,gyad'a kai kawai tayi tana ji a zuciyarta bankin da take tara Harira a ciki ya kusa cika,duk ranar da ya cika kuwa to tabbas Harira zata ga rayuwa,domin dai sai tayi dana sanin zuwa duniya. Bayan Sunusi ya gama mayar da numfashin wahala sai yake tambayar Amina dalilin santsin da ya kwasheshi,nan Amina ta shiga bashi hak'uri ta d'auki laifin ta d'orawa kanta,tace masa ta d'auko ledar kayan kad'in da inna ta bata ne shine kalkashi ya zube,to kuma ta wanke gurin ashe bata sani ba bai fita ba,har ya zo ya taka ya zame ya fad'i,nan ta shiga bashi hak'uri tana karkashe idanu,sai ga Sunusi ya rud'e jikinsa ya fara mazari,musamman da Aminar ta janyo shi jikinta ta kai hannu kan k'eyarsa da ta lunkuma tana mulmulawa,sosai k'eyar ta kumbura tayi zungureriya da ita,haka Amina ta dinga mulmulawa tana masa sannu,Sunusi ya kai siririn hannunsa kan murguza murguzan mazaunan Amina yana lailayawa da fad'in. "Ni ma kiyi hak'uri Aminata,azaba ce ta isheni har ban san lokacin da hak'orana suka kaiwa d'uwainiyarki ziyara ba" Murmushi Amina tayi ,ta mik'e tsaye da k'yar.Sannan ta taimakawa Sunusi ma ya mik'e,ta rungumeshi a gefen jikinta tana fad'in. "Ai ni baka laifi a wajena mijina,muje d'aki ma in tausa maka jikinka tare da mulmule maka k'eyar nan ko kumburin zai sace" Dad'i ya ishi Sunusi,nan da nan ya sake lafewa a hammatar Amina kamar wani tsuntsu,suka shige cikin d'aki suka bar Harira tsaye a bakin taga sakato da baki tana bin su da kallo. Wato hak'anta bai cimma ruwa ba kenan?ita da taso Sunusi ya fusata ya lodi Amina ko ya zazzage ta,shine suka tura mata aniyarta suka b'ige da soyayya?lallaikam sun d'au bashi,domin in dai tana da rai da lafiya ba zata bari su sakata su wala ba,tana ji a ranta duk wani hali na matsi da ta shiga Amina ce sanadiyya,haka nan ita ce sanadiyyar rasa hak'oranta take zaune da wawulo,wawulon da yake ja mata raini gun Sunusi,dan ko yau da safe da zai fita da ta biyo shi tana tambayarsa kud'in cefane kau da kai yayi,har da yi mata gargad'in in zata yi masa magana ta daina kallonsa,domin wawulon bakinta na firgitashi yana jin kamar zata had'iye shi,ire-iren wad'annan abubuwan suke k'ara bak'anta ranta,kuma ta d'auki alwashin ko zata yi yawo tsirara sai ta san yadda ta kori Amina daga wannan gidan. *Tofah! lallai Hajiya Harira kin d'ebo ta da zafi* 😳😂 ************ "Don Allah da gaske kake?" Zahra'u ta fad'a tana kallon fuskar K'asimu cike da mamaki,Yayi Murmushi da fad'in. "Wallahi kuwa da gaske fa,d'azun nan Salisun ya kirani a waya yake fad'a min wai an dai dai ta komai Saratu za ta koma d'akin ta" Zahra'u ta sauke numfashi ta ce. "Amma dai ba'a bahagon layi za su sake zama ba ko?" K'asimu ya d'an sosa kunnensa da ke masa k'aik'ayi ya ce. "Kamar kin sani kuwa tambayar da na fara yi masa kenan,sai yace min wai ya yanke shawarar su cigaba da zama a BAHAGON LAYIN,ta haka ne kawai zai gane idan Saratun tuban gaskiya tayi ko na k'arya" Zahra'u ta ce, "Tabbas kuwa yayi gaskiya,to Allah dai ya tak'aita,dan wannan layin ya zama bom,ni dai Allah ya taimakeni da na bar cikinsa na samu ingatacciyar rayuwa" K'asimu yayi dariya yana rik'e hannunta sannan ya ce. "Wai ni kuwa kina ta cewa zaki bani labarin abin da ya faru ranar da kika je kitso amma ban samu zama ba,me yafaru ne kika dawo ba tare da an miki kitson ba?" Zahrau tayi ajiyar zuciya tana kyab'e baki ta ce. "Hmmmm ! Ranar nan naga tijara da d'umamar yanayi,wai duk wani gidan kitso daman haka yake tattara y'an iskan mata magulmata?ni tun da uwata ta haifeni ban tab'a ganin inda aka yi brush da damammen kashin awaki da gishiri ba sai a GIDAN KITSO". K'asimu ya zaro idanuwa yana son jin cikakken bayani,nan Zahra'u ta fayyace masa komai na abin da idanuwanta suka gane mata,K'asimu ya dinga dariya har idanuwan sa na hango masa yadda aka turmushe Gimbiya aka yi mata brush da kashin awaki 🤣. Sai da yayi dariyarsa ta isheshi sosai,sannan ya tsaya yana sauraren bayanin da Zahra'u ke masa. "Ni da mai gida shawarar da na yanke,tunda nayi irin wannan zaman mara alfanu da zubewar mutunci a baya,me zai sa in sake ziyartar wannan gidan kitso domin in tattara wad'annan matan in basu labarin zaman mu a bahagon layi da abin da ya same mu daga k'arshe,in yaso in musu nasiha ko zasu fad'aka su gyara suma?saboda ni dai hankalina ya tashi da abin da na gani wallahi" K'asimu yayi kasak'e yana jinjina zancen,sai can kuma yayi gyaran murya ya ce. "To hakan ma wani abu ne me kyau,idan har kaga wani na aikata ba dai dai ba hakki ne akan ka kayi masa nasiha a matsayinka na d'an uwansa musulmi,to sai dai kuma in da gizo ke sak'ar su mata fa ba cikakken hankaline da su ba,kar aje garin neman gira a rasa ido,kinga tsohon ciki ne da ke,ina tsoron kije ki fad'a musu gaskiya ki musu nasiha a samu kuskuren fahimta su had'u su suburbud'aki,idan ba a gurje miki baki da kashin awaki ba ai kinga a saki ki haifo abinda ke cikinki ta baki 😂 kinga me gari ya waya kenan?"an b'ata goma d'aya bata gyaru ba". Murmushi Zahra'u tayi da fad'in. "Babu wani abu da zai faru sai alkairi,Allah zai dubi niyyata ta alkairi ya bani nasara akan k'udurin zuciyata,ina kishin in ga y'an uwana mata suna wannan rayuwar ta tumasanci wallahi,tunda na d'and'ana irinta babu komai cikinta face wulak'anta kai da zubewar mutunci had'i da sab'awa Allah,don haka ni dai idan har kayi min izini zan yi wannan jihadin,kuma ina da yak'inin in sha Allahu Allah zai bani nasara akan niyyata". K'asimu yaji dad'in bayanan da Zahra'u tayi,hakan ya sa ya runtse hannuwanta cikin nasa idanuwansa a kanta yana murmushi ya ce. "Na yi miki izini Uwar gidana,Allah yayi miki jagoranci akan niyyarki ta alkairi". ************* *‫*فصل ف الحيض‬ (Fasali a cikin Haila) Wannan shine darasin da Malam Arabi yake biyawa d'alibansa da suka kasance sun fara zama y'ammata,a cikin littafi (Ahalari),ya zage sosai yana ta jera musu bayanai ta yadda za su fahimta,hatta wankan hailar sai da ya koya musu tare da bayanin wadda ta saba da wadda ta fara, to da yake karatun ya shafi wani b'angare na kunya duk da dai babu kunya a cikin addini,sai d'aliban suke ta sunkuyar da kai suna dariya k'asa- k'asa. Tun Malam Arabi bai gane dariyar da suke ba har dai da ya fad'i wata kalma sai yaji an shek'e da wata y'ar iskar dariya,a fusace ya d'ago kansa yana kallonsu sai duk suka sunkuyar da kai k'asa,sosai ransa ya b'aci ya mik'e tsaye yana muzurai ya dube su ya ce. "Wace Shakiyyiyar ce take min dariya a aji?". Tsit suka yi babu wacce tayi magana,ya d'ago bulalar hannunsa zambad'ed'iya ya nuna su da ita cikin fushi ya sake ce wa. "Ba magana nake da ku ba?nace wace shakiyyiyar ce take min dariya a cikin aji?Za ku fito min da ita ne ko sai na had'aku nayi muku wankan jego?Kun san dai ni ba'a yi min had'in kan tunkiya ko?gara tun wuri ku fito min da ita a cikin ku kafin in tsamama muku jikin ku" Wasu da yawa daga cikinsu sai da gabansu ya fad'i jin Malam Arabi ya ambaci wankan jego,duk lokacin da ya ambaci wannan kalmar to fa ya shirya tsiya ne,domin wankan jego na nufin ya rufe mace da duka ko ta ina baya ji baya gani,hakan ya sa hankalin su ya tashi sosai,sai dai kuma suna tsoron su tona wadda tayi dariyar,saboda Azara'u ba k'aramar masifaffiya ba ce,duk wanda ya tona ta idan aka tashi daga makaranta za ta iya tare mutum a lungun (kaci uwaka) ta jibgi banza,shiyasa kaf ajin tsoranta ake yi. Ganin sunyi shiru sai Malam Arabi ya jijjiga kai ya nuna wata d'aliba mara yawan magana,saliha ce sosai,yace da ita "Ke Salama mik'e tsaye" ,A rud'e Salama ta mik'e jikinta na rawa sosai,ya kalleta yace mata. "Duk ajin nan da ke kad'ai na yarda zaki fad'a min gaskiya,dan na lura sauran y'an ajin duk taron munafukai ne,bud'e bakin ki ki fad'a min wacece tayi dariya ina karatu?" Salama tayi tsuru -tsuru ,musamman da suka had'a ido da Azara'u ta dank'ara mata harara alamun kar ta sake ta fad'a,idan ba haka ba ta san sauran,ganin tayi shiru sai Malam Arabi ya ce. "Ashe dai kema kin zama munafukar ko?to babu shakka kuwa yau zan miki wankan jego na hak'ik'a idan baki bud'e baki kin fad'a min gaskiya ba". Babu yadda Salama ta iya,haka ta bud'e bakinta yana rawa tayi magana. "Malam Azara'u Lawan ce tayi dariya" Gabad'aya y'an ajin sai da suka kalli Salama a tsorace,ita kuwa mai ya kaita tonawa Azara'u masifa asiri?lallai yau jikin Salama zai yi tsami kenan,ita kam Azara'u jijjiga kawai tana hango yadda zata shak'e Amina ta lodeta,yayin da Malam Arabi ya bawa Salama umarnin zama,sannan ya kalli Azara'u ya bata umarnin ta mik'e tsaye,da k'yar ta mik'e sai wani ciccin magani take tana botsaro baki gaba da jijjiga jiki,ya k'are mata kallo tsaf sannan ya tanka. "Ke ga fitsararriya ko?ina karatu a aji kina dariya,idan ubanki ne yake koya miki karatun za ki yi dariya ne?" Cikin rashin kunya Azara'u ta ce. "Ni gaskiya malam ka daina ambato mahaifina dan kuwa yana k'abari a kwance,dariya kuma ai ita tazo da kanta bani na gayyato ta ba,akan me zan koreta ta koma na k'i yi?" Wani takaici ya kama Malam Arabi,cikin matuk'ar fushi ya ce. "Ni zaki kawowa tijara da d'ibar albarka?ko nayi miki kama da sa'an wasanki,to dan ubanki fito nan ko in zo nan in miki wal mukalifatu,domin naga d'umaninatu (nutsuwa) bata wadace ki ba" Kawar da kai tayi tana shan k'amshi,kafin kuma ta fara takowa tana tafiya cikin izza da tak'ama,har ta takewa wata daga cikin y'an ajin hannun ta da ke k'asa. "Wash ! shine abin da Shukra ta fad'a tana yarfe hannu fuskarta a b'ace dalilin azabar da ta rasa yatsun hannunta,cikin jin zafi ta dubi Azara'u da tayi gaba ta ce. "Azara'u baki lura bane kin take min hannu?" A fusace Azara'u ta juyo ta gallawa Shukra harara,cikin masifa ta ce. "Na taka d'in ko kina da matakin da zaki d'auka ne?" Shukra ta sunkuyar da kai k'asa a tsorace bata ce komai ba,Azara'u ta saki mugun tsaki sannan ta juya ta nufi Malam Arabi da ke tsaye yana kallon iskancin da take,tana zuwa ta tsaya masa k'erere a ka bata tsuguna ba,ajin yayi tsit kowa ya zubawa Malam Arabi da Azara'u idanu ana jiran ganin abin da zai faru. Malam Arabi ya shammaci Azara'u ya d'aga lafceciyar bulalarsa da ya shafe ta da manja ya zumbud'a mata a gadon baya,wata zambarwa tayi ta durk'ushe k'asa ba tare da ta shirya ba,sosa bayanta ta shiga yi idanuwa a waje ta kalleshi ta ce. "Kai kai kai ! me nayi maka za ka dake ni?" Malam Arabi ya ce. "Ban sani ba mara kunya fitaararriya,saboda baki da ladabi da biyayya ni zaki zo ki tsayawa k'erere a ka?to yau zan sauke miki tashen balagar da yake damun ki dan gidanku" D'aga bulalar yayi zai sake zumbud'a mata,wuf ta mik'e a gigice ta rik'e bulalar jikinta na rawa,cike da fitsara take dubansa ta ce. "Na rantse da girman Allah ka sake dukana za ka ga abin da zai faru" Takaici ya sake kama Malam Arabi,yayi yayi ya fizge bulalar amma Azara'u ta rik'e gam tak'i saki,hakan ya fusata shi ya d'aga hannu ya dalla mata wani gigitaccen mari da ya saka Azara'u sakin k'atuwar k'ara da ta firgita y'an ajin,take kuma ta fad'i kwance a k'asa tana shure -shure da bige-bige tana sakin wani irin yare,alamar dai Aljanu ta tayar. A tsorace y'an ajin duk suka mik'e tsaye,Malam Arabi ya daka musu tsawa akan kowacce ta nemi waje ta zauna,jikin su na rawa duk suka koma loko suka takure suna kallon Azara'u da ke iface -iface da birgima. Malam Arabi kallonta yayi ya nad'e hannun rigar sa yana fad'in " Ni zaki kawowa iskanci da an dakeki ki fad'i kina birgimar k'arya wai ke Aljanu,da ke da Aljanun kun ci bantan ubanku,kuma yanzun nan zanyi maganin tak'adirancin ku" D'aga bulalarsa yayi iya k'arfinsa ya zulawa Azara'u a k'irji saitin nonuwanta,ta saki wata irin k'ara da zambarwa,ya sake d'agawa ya nufi bayanta dai dai mazaunata ya tsula mata,nan ma wata irin mik'a tayi ta saki bahaguwar k'ara,haka Malam Arabi ya dinga lodar Azara'u,kuma babu in da yake duka sai k'irjinta da mazaunanta. Idanuwansa sun rufe wajen tafkarta har bai ankara da sanda tayi zambarwa ta mik'e ba,kawai ji yayi kamar wanda aka d'aga sama cak,sai kuma yaji an yi wurgi da shi😂 bai tashi tsintar kansa ba sai a tsakiyar d'alibai 🤣 durum ya ji shi ya sauka akan muk'amuk'in wata d'aliba,yayin da gabad'aya d'aliban suka razana suka dare suna ihun tsoro,ita kam d'alibar da ya danne wani azababben ihu ta saki jin tamkar mak'ogoron ta zai cire😂Malam Arabi yayi ragajeje kan mak'oshinta,da k'yar ta samu ta ingije shi musamman da ta samu ta gallara masa mintsini. Ita kam Azara'u da ke tsaye nufoshi tayi gadan -gadan,hankalinsa a tashe ya fara matsawa yana zazzaro idanuwa,d'alibai suka kwasa da gudu suka fice daga ajin suna ihu da kiran sauran ragowar malaman,Malam Arabi dai tsintar kansa kawai yayi a hannun Azara'u ta shak'o wuyansa😂 bata yi wata -wata ba ta samu rungumemen kansa ta garashi da garu,azabar da ta ratsa tsakiyar kan malam Arabi har bai san lokacin da wata lukutar Atishawa ta fito masa ba,ji kuke (ekichifffffff 🤣),a loko Azara'u ta matse shi,yayin da yatsun ta guda biyu suka matse mak'wallaton da ke wuyan sa ta shak'e shi 😂 ,kakari yake sosai idanuwa a warwaje yana fad'in "Ya Subahanallah...Innalillahi salasa....inna atuni minal tona tone....😂" Malam Arabi ya hango lahira,cikinsa ya hargitse,sai ga wata irin gudawa(zawayi) mai shegen d'oyi ta zubo yarrrrrrrrr a wando 😂😂😂. Comments Share Vote Pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA ASHIRIN DA BIYAR DA NA ASHIRIN DA SHIDA* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ #SANARWA👇 *NI D'IN MAI YAWAN SABGOGI CE DA UZURURRUKA,HAKAN YA SA KWANA BIYU KUKA JI NI SHIRU,AYI MIN AFUWA👏 KUMA IN SHA ALLAHU ZAN TAK'AITA LABARIN DAN MUYI SAURIN KAMMALAWA KAFIN RAMADAN,GODIYA NAKE MASOYA* 🤝🥰 ***Saura kad'an numfashinsa ya bar gangar jikinsa tsabar shak'ar da ya ji.Shigowar ragowar malaman makarantar cikin ajin da sauri shine ya ceto malam Arabi daga hannun Azara'u. Da k'yar malamai guda uku suka k'wak'ule hannun Azara'u daga wuyan malam Arabi,tana ta fizge - fizge da ihu da kururuwa,ragowar d'alibai suna tsaye daga wajen ajin kowacce idanuwa a warwaje cike da matsanancin tsoro,fad'uwa k'asa Azara'u tayi tana shure - shure da wasu irin maganganu,wai wallahi ba za su yarda ba tunda malam Arabi ya dakar musu Nono da d'uwainiya,sai sun d'auki fansa. Shi kam gogan yana jin an raba hannun Azara'u da wauyansa sufa yayi ya silale a jikin malam Jibrin sai mirgina kai yake,da k'yar yake iya magana yana fad'in. "Malam Jibrin duba min wuya na akwai mak'wallato kuwa?ko dai ta gutsire min shi?" Takaici kamar ya kashe malam Jibrin saboda haushin malam Arabi,tunkud'e shi yayi daga jikinsa ya fara masifa cikin rawar baki har ba'a fahimtar abin da yake fad'a,da yake yana da saurin magana da in ina,shiyasa ma d'alibai har suna suka saka masa wai ( Malam Abirbireshan😆). Cikin masifa malam Jibrin ke fad'in. "Allah ya sa beli ta cire maka ba mak'wallato ba,Arabi baka jin magana wallahi,kwanaki har meeting muka yi a kanka akan wannan muguwar d'abi'ar ta ka ta dukan mata a jiki,har doka mun kafa maka akan duk dukan da zakayi kar ya wuce yin sa a hannu,ba'a ko'ina ake dukan mace ba,amma dan taurin kai ka k'i ka daina,har wani alfahari kake da fad'in zaka yiwa d'aliba wankan jego,wannan ba k'aramin iskanci ba ne da batsa,haihuwa suka yi da za ka dinga fad'in za ka yi musu wankan jego?ko kai unguwar zoma ne?haka kawai kana zubar mana da k'imar makaranta ba gaira ba dalili,saboda tsabar iskanci ka rasa in da zaka dinga dukan mace sai a k'irji da mazaunai,wannan d'abi'ar malamin k'warai ce?to wallahi ba zamu lamunci wannan ba,dole mu d'auki mummunan mataki a kan ka" Malam Arabi yayi k'us sai zare idanuwa yake,wandon sa taf da zawayi duk d'oyi ya cika wajen😂,hannunsa bisa wuyansa sai murzawa yake. Ragowar Malaman tuni suka janye Azara'u gefe suna tofa mata addu'o'i,har Allah yasa komai ya lafa ta fara dawowa nutsuwar ta,sai sharb'a gumi take,d'alibai suna ganin ta mik'e zaune kowacce ta d'iba da gudu suka ranta ana kare,kowacce tayi hanyar gidan gyatumin ta,Azara'u na waiwayowa suka had'a ido da malam Arabi,wata uwar harara ta zabga masa,da sauri ya d'auke idanuwansa ya juya mata k'eya cikinsa na k'ara karta masa tsabar tsoro,kuma kamar wanda aka d'aurewa k'afafu gabad'aya ya kasa mik'ewa tsaye,ko yana gudun kar gudawar ta zubo ne oho! Malam Zulyadaini ne ya fita yaje babban ajin y'ammata ya samo d'alibai guda biyu wad'anda ya umarcesu su raka Azara'u har gida,haka suka rik'eta duk da su ma a tsorace suke,suka fita da ita domin raka ta gidan. Suna fita nan fa malamai suka rufar wa malam Arabi da fad'a kamar su cinye shi,Malam Tukur shugaban makarantar fad'i ya ke. "Mun gaji da halinka wallahi,duk yadda muke ji a bakin d'alibai cewar kai d'an iska ne ban tab'a yarda ba,amma yau na yarda da maganar su,kwanaki nan Malam Jibrin yake fad'a min cewar ranar da Batula Kabiru ta tayar da aljanu kai ne me k'ok'arin danne ta,yace min yana lura da kai banda latse mata k'irji babu abin da kake yi,ban yarda da maganarsa ba saboda ina ganin kamar kuna y'ar tsama ne shine zai maka sharri,haka nan ranar da Bushira ta zo makaranta tana ciwon kai suka bugar da ita ta dinga ihu tana birgima ina kallonka har da rawar jiki ka fito daga ajinka tsabar tsugudidi ka nufi ajin da take,akan idanuwana ka saka hannayen ka ka danne mata mazaunai wai dan ta daina birgima,nan na k'ara tabbatar da cewar tabbas kai d'an iska ne lamba d'aya,yanzu kuma kazo kana dukan d'alibarka a k'irji da bayanta,saboda haka kayi na farko,kayi na biyu,yanzu kayi na uku,wallahi duk randa kayi na hud'u sai ka bar makarantar nan,kuma sannan sai mun had'a ka da hukuma domin a gyara maka zama" Kunya ta ishi malam Arabi kamar ya nutse,ashe duk abin da yake yi malamai da d'alibai na lura da shi kenan,tabbas amma yayi asara,haka suka sanya shi a gaba da fad'a da tijara,idan wannan yayi ya gama sai wani ya kama,har dai daga k'arshe Malam Jibrin yayi magana a fusace cikin in ina. "Ttttt tashi ka kka bamu guri,jajj ja'iri fitsararre,kakkka cika mu da d'oyi dad da samami,d'annnnnn iska kawai" Mik'ewa malam Arabi yayi da k'yar cike da kunya kansa a sunkuye,dukkan su suka toshe hanci suna hararasa,haka ya dinga jan k'afafu a hankali saboda yadda zawayin yake biyo k'afafuwan sa,har ya fice daga ajin ya nufi gida. ************** Isar sa gida ya tarar har Angayu ta fara bacci,shigewa yayi cikin d'akin girki yana karafniyar duba ruwan zafin da zai wanke jikinsa,motsin da Angayu taji ya sa ta farka a firgice tana tambayar . "Wanene anan ne?" Shiru yayi mata ya cigaba da dube-duben sa,ta sake d'aga murya tana da k'arfi ta sake ce wa. "Wai ba magana nake ba?nace wanene a nan yake min bud'e-bud'e?" Da k'arfi malam Arabi ya d'aga murya a fusace ya ce. "Ban sani ba,ki fito idanunki ya gane miki mana,mtswwww ,aikin b'ur in ji tusa kawai" Da hanzari Angayu ta wartsake jin muryar mai gida,ta kalli agogo tana mamakin har yaushe ya shigo?bata san ta fara gyangyad'i ba ,tashi tayi ta fito tsakar gidan tana hamma da mik'a,a lokacin shi ma ya fito daga d'akin girkin yana tsaye a tsakar gida ya tala k'afafu ya cakari k'ugu,jikinsa duk ya dameshi zawayi kaca- kaca,dubansa tayi tana sosa k'eya ta ce. "Yi hak'uri malam ni ban ma ji shigowarka ba,gyangya..... "Kina baccin asara daman ai ba zaki ji shigowata ba,ni dalla malama zo ki bani ruwan zafi zanyi amafani da shi" ya katseta cikin sababi da kumfar baki. Sai lokacin Angayu taji wani bala'in d'oyi ya cika tsakar gidan,toshe hanci tayi tana fad'in. "Malam wai baka ji wani mugun wari na tasowa ba?ko dai mushen bunsuru aka yar mana a soro yake wannan warin?" Cikin k'ufula malam Arabi ya ce. "Mushen alade ne ba na bunsuru ba,ban da ina cikin wani yanayi tsaf idan na naushi bakinki sai ganda ta fi shi kyan gani,tsabar wulak'anci nace ki bani ruwan zafi kin tsaya yi min suratakai?yanzu da kika tsaya min a ka kina susar kwarkwata zaki bani ruwan zafin ne ko kuwa?" Ita dai Angayu mamakin uwar jarabar da malam Arabi yake zubawa take,lafiya lau ya fita amma ya dawo mata da tijara,koma wa cikin d'aki tayi ta d'auko fitila dan ta haska ta d'ora masa ruwan zafin,tana isowa dab da shi wani arnen wari me juya kwanya ya buge ta,haske shi tayi taga yadda yake gumi sai k'walala idanuwa yake,hannayensa rik'e da wandon jikinsa,k'asa ta haska sosai sai taga bakin wandon jikinsa sai d'iga yake yi duk ya b'ata wajen da kashi,sakin fitilar tayi a k'asa tayi baya da sauri tana d'ora hannu aka cikin kwaroroto ta ce. "Malam me zan gani haka? kashi kayi a wando?" Da yake malam Arabi cikin b'acin rai yake,ga Angayu na k'ara bak'anta masa,bai ma san lokacin da ya ce mata " Ah ah ba kashi nayi ba,Tirmizi nayi" . "Kan ubancan kayyasa" Angayu ta ambata da sauri,sannan ta d'ora da ce wa. "Daga tambaya sai ka ambaci sunan ubana,to ko ba komai dai shi Tirmizin da ka ambata ya fika daraja tunda kuwa ya ci sunan mai rawaito hadisai,kai kuwa ko a majamu'ul bahraini banga in da sunan Arabi ya samu fitowa ba,ruwan zafi ne kuma ba zan d'ora ba tunda abin na ka cin mutunci ne" Tana fad'in hakan ta koma ta shige d'akinta,ta bar malam Arabi yana ta jaraba da masifa,da jarabar ta ishe ta sai ta mai da shi mahaukaci ta dinga tuntsira masa dariya tana mak'e murya har da raira masa wak'a,wai " Arabi me kashin wando" . Da haushi ya k'ume shi tilas ya janyo bokiti ya fara d'iban ruwa a rijiya domin wanke jikinsa da ya dame shi da k'aik'ayi,cikin d'aga murya kuma yayi magana yadda Angayu za ta jishi,ya mayar mata da raddin ce wa. "In dai kashin wando ne Uwarki ma da tana yarinya ai tayi 🤣. ********** Misalin k'arfe tara da rabi na daren,Sunusi da Amina zaune a k'ofar d'akin Aminar suna shan iska,sai hira suke yi cike da nishad'i da soyayya,Amina na yankewa Sunusi farce shi kuma yana haska mata da fitilar wayar sa. Ita kam Harira tana daga gefe zaune ita ma a k'ofar akurkin d'akinta,sai wak'e- wak'en habaici take amma sun mata banza sun nuna ma basu san da ita a wajen ba sai hirarsu suke suna tuntsira dariya,hakan ya sake b'atawa Harira rai sosai. A tsorace dukkansu suka d'ago jin an fad'o tsakar gidan da gudu,Kamilu ne yana haki duk ya had'a uban gumi sharkaf,Amina da Sunusi suka mik'e da hanzari suna tambayar sa "Lafiya?" A rud'e ya ce musu. "Ku taimaka mu kai Shafa'atu asibiti,gata can sai nak'uda take ta wahala sosai har k'arfinta ya k'are" Harira ce ta fara zabura da gudu tayi hanyar waje tana fad'in "Wayyo k'awata ashe an zo wajen" kafin ma su farga tuni har ta fice ta nufi gidan. Amina ce ta d'auko hijabinta ta sanya,duk suka fito har Sunusin suka nufi gidan Shafa'atun,Amina ta dubi Kamilu tana fad'in. "Yaya Kamilu ai da ka sani Umma kayi wa waya ta tawo,kaga duk cikin mu yaran mata ne babu wadda ta san kan yadda ake haihuwa" Shi dai Kamilu da yake a rud'e yake bai ce komai ba,sai Sunusi ne ya ce "Gaskiya dai kam haka ne,bari muga yanayin halin da take ciki in ma asibitin ne kawai sai a samo d'an sahu mu wuce" A dai dai lokacin suka shiga gidan,suka tarar da Shafa'atu sai juya kai take azaba ta ishe ta,ga Harira tsugune a gabanta sai zabga mata sannu take yi,Harira na ganinsu karaf ta mik'e ta dubi Kamilu ta ce. " Yawwa Kamilu ai tana dab da haihuwa ma,a samo garwashi wani turare zan mata yanzu za ta haihu da kanta in sha Allahu,ni ma da na zauna a gidan Iya ne naga yadda take wa masu nak'uda,da an kirata tayi musu turaren suke haihuwa" Da yake Kamilun a rud'e yake kuma mafita yake nema nan da nan ya yarda da batun Harira,da sauri ya d'auki abin da zai samo garwashin ya fice can bakin layinsu wajen masu tsire domin ya samo,Sunusi ya bi shi a baya yana jinjina batun Harira,shi dai zuciyarsa bata amince ba da dai asibitin aka tafi zai fi... Suna fita Harira ta shige ktcheen d'in Shafa tana dube-dube,har ta ci karo da abin da take so wato BARKONO, d'ebowa tayi a hannunta sannan ta fito,Amina rik'e da Shafa'atu sai sannu take mata tana tausaya mata,lokacin ne su Kamilu suka dawo da garwashin sun samo,Harira ta karb'a tace su fita waje su jira,Kamilu ya kama hannun Sunusi suka yi waje,Ita kam Harira shiga da garwashin tayi har falon Shafa,Sannan ta dubi Amina ta ce. "Hajajju makkatu rik'e ta zaki yi sosai fa" Amina duk ta d'auka abin arzik'i ne ta sake rik'e Shafa gam, Harira ta fakaici idanuwan su ta watsa wannan Borkono a cikin garwashin,tana zubawa ta dubi Amina ta ce. "Aiki ya same ki an sukuta,ni bari naje daga tsakar gida maza ki cigaba da rik'eta" tana fad'in hakan da sauri ta fice saboda yadda hayak'i me mugun yaji ya fara turnuk'e d'akin,k'ofa ta ja ta kulle su ta waje tana dariyar mugunta,Harira fad'i take a zuciyarta . "Dole ma yau ki rame Amina 😂 dan Wallahi ba zan bud'e ku ba sai kinyi tari kin rame wannan k'ibar ta zube dan wahala" Kafin wani lokaci tarin Amina da Shafa ya fara yawa,wani irin lukutin tari Amina take kamar ta shid'e tana ihun Harira ta bud'e su,amma Harira dariya kawai take shek'awa 😂. *Gaskiya Harira ke azzaluma ce* 🤣🤣🤣🤣 Coments share vote pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI DA NA ASHIRIN DA TAKWAS* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ *KUYI HAK'URI ZAN TAK'AITA LABARIN SABODA GABATOWAR WATAN RAMADAN,GA ABUBUWA SUN MIN YAW BANI DA LOKACI KO KAD'AN* 👏 *** Wata irin lukutar atishawa da tari kawai Amina ke saki,yayin da Shafa me nak'uda ke cikin wani yanayi na azaba da wahala,ga bala'in ciwo ga kuma hayak'in barkono,ita kanta Harira da ke tsakar gidan hayak'in ya dameta ta fara tari da atishawa,amma bak'ar zuciya da mugun nufi da ke d'awainiya da ita ba zai sa ta fasa k'udurinta ba. Tun daga waje Kamilu da Sunusi suke jiyo wani irin yaji da hayak'i,har su ma suka fara tari kad'an kad'an suna rufe baki,kamar kuma daga sama Sunusi yake jiyo muryar Amina na ihu da kururuwa,hakan yasa da hanzari ya juya ya shige cikin gidan har da d'an gudunsa,shi ma Kamilu ya rufa masa baya. Harira suka iske tsaye a tsakar gida tana d'an tari tare da shek'a dariya,sam bata lura da shigowarsu ba sai da taji tari a bayanta sannan ta waiwaya a firgice tana zare idanuwa,wani irin mugun tari ne ya sark'afe Kamilu da Sunusi ,cikin k'arfin hali Kamilu yake tambayar Harira cewar. "Wannan wane irin yaji ne?daga ina yake tasowa?" Shikam Sunusi k'ofar d'akin da su Amina suke ya nufa yana kacaniyar bud'ewa,saboda ihun ta da yake jiyowa da atishawa da kakkauran tarin da take yi,Harira ta zabura tana dakatar da shi daga k'ok'arin bud'e k'ofar tana fad'in. "Kar fa ka bud'e k'ofar nan,turaren nak'uda nake wa Shafa kuma na san yanzu zata haihu" Wata muguwar harara Sunusi ya lafta mata yana k'ok'arin cigaba da bud'e k'ofar ,sannan ya ce. "Turaren nak'uda ko turaren mutuwa?muguwa azzaluma haka kawai ki kulle su a d'aki ki bula musu hayak'i ke kin fito daga ciki,me ya sa ke baki zauna ciki ba?idan Shafa'atu ce me nak'udar ita Amina nak'uda take yi da za ki kulleta a d'aki tare da me nak'uda?" Dai dai lokacin ya bud'e d'akin yana shirin shiga,Kamilu ma ya ja k'afa suka afka d'akin yayin da wani mugun yaji da hayak'i ya bulesu,suka fara jero atishawa ba k'ak'k'autawa tafi guda saba'in 🤣. Harira kam tab'e baki tayi tana fad'in. "Ni me zai kaini rik'e me nak'uda ta b'allani a banza,ita dai Aminar da take y'ar sukuta ita ce mai k'arfin rik'e me nak'uda amma ba ni ba,kuma ko ba komai idan taji azabar turaren barkono ita ma ta kasayar da gayad'in da ya cika mata wannan k'aton tumbin na ta" Juyawa tayi da hanzari ta fice daga gidan ta koma gidanta tana dariya,saboda ta san muddin Sunusi ya fito daga d'akin zai iya bajeta ba tare da ta ankara ba😂. Cancakar Kamilu ya ciccib'o Shafa'atu da tayi balance a k'asa ko'ina na jikinta ya saki tsabar wahala,uban gumi take sharb'awa wahala ma ta sa ta daina atishawar,sai wata muguwar rama da tayi har wani gantso ne na musamman ya fito mata,babu abinda a ke gani a fuskarta sai hak'ora kacarrrrr da su,kumatunta sun lotse sun burma ciki tsabar wahalar nak'uda da turaren barkono,haka Kamilu ya ciccib'o abar sa ya fito da ita tsakar gida ya shimfid'eta,da sauri kuma ya d'ebi ruwa yaje ya zubawa garwashin da ke hayak'i domin ya kashe shi. Shi kam b'angaren Sunusi kacaniyar d'aga Amina yake yi amma ya kasa,jikinta ya sake mugun nauyi duk ya saki ta jibge kamar buhun kwaki,fuskarta tayi jajawur kamar wainar fulawar da ta sha manja😂ko kuma k'osan Angayu 🤣 da k'yar ya iya kamota suka fito tsakar gida su ma. A daidata sahu Kamilu ya fita ya nemo har k'ofar gida,ya ciccib'i Shafa'atu da ke k'ok'arin suma don tafiya asibiti,da shi da Shafa'atun da Amina suka shiga baya,yayin da Sunusi ya mak'ale a gaba kusa da me tuk'i,nan da nan suka bar BAHAGON LAYI suka nufi asibiti dan ceton ran Shafa'atu da ke cikin matuk'ar wahala da azaba,Amina kam zuciyarta bak'ik'k'irin har hango irin babbar fansar da za ta d'auka kan Harira ta ke. Basu jima da zuwa asibitin ba Allah ya sauki Shafa'atu lafiya. *************** Washe gari ne bayan Zahra'u ta kammala aikace-aikacen gidanta tare da taimakon Nana,sai tayi shiri domin zuwa gidan kitso don aiwatar da k'udrinta bisa sahhalewar mijinta K'asimu,duk da yadda take jin jikinta yayi nauyi kamar wadda zata haihu a lokacin hakan bai sa ta hak'ura da zuwan ba,Nanan dai ta sake d'auka domin yi mata rakiya,nan da nan sai gasu a gidan kitson ba tare da b'ata lokaci ba. Babbar sa'a tayi,domin kuwa a ranar ma dukkan su suna gidan kitson har ma da Gimbiyar da aka yi wa tambarin gulma da munafurci,suna tsaye cirko-cirko sun saka Gimbiyar a tsakiya tana sharar hawaye ana mayar da yadda aka yi,sai balok'ok'o da masifa suke yi kamar za su daki Gimbiyar,bakin K'udusiyya har kumfa yake yi wajen kallon Gimbiya tana dungure mata kai da fad'in. "Munafuka algunguma,idan kere na yawo zabo na yawo ai dole wataran za su had'u,ranar da muka je gurzar bakinki ai guduwa kika yi muka nemeki muka rasa,to yau gashi mun tarfaki a dandalin da kike zuwa ki sauke kwandon gulmarki,to albishinki,ki ce goro,ranar farko da guzurin kashin awaki muka tawo ki kasa muka yi asarar sa,to yau tattaki muka yi muka samo kashin alade da shi zamu gurje bakin munafuka,dan haka jummai ku tala min ita ku danne min matsiyaciya ku ga aiki da cikawa" Wani irin gigitaccen ihu Gimbiya ta saki tana basu hak'uri a sanda suke k'ok'arin dannetan,gabad'aya ta gigice dan bata san wane irin hali zata shiga ba muddin kashin alade ya ziyarci bakinta🤣,haka mai kitso ke ta faman basu hak'uri amma suka ce idan bata yi shiru ba wallahi za su had'a da ita,ganin da gaske sun danne Gimbiya da kokawa suna shirin loda mata kashin aladen da suka ce a bakinta hakan ya sa me kitso ta bud'e murya ta kwarara ihun neman taimako,a dai dai lokacin da Zahra'u da Nana suka kawo kai cikin tsakar gidan. Bayan sallamar da Zahra'u tayi sai ta daka musu wata gigitacciyar tsawa tana basu umarnin su d'aga Gimbiya,cikin mamaki suka tsaya cak suna kallonta,y'ar k'arama da ita a gabansu da tsohon ciki da alamun ma duk sun girmeta,fuska a d'aure ta k'araso gabansu tana fad'in "Ku d'aga ta" Sai kuwa suka bi umarnin Zahra'un suka d'aga Gimbiya wadda ke ta faman shure-shure da ihun neman taimako,tana jin sun d'aga ta kuwa tayi wuf ta mik'e da sauri zanin jikinta na yararin fitsarin da ta saki na tsoro,neman hanyar fita take yi kawai daga gidan dan ta tsira,sai da Zahra'u ta daka mata tsawa akan ta nutsu,sannan ta tsaya jikinta sai rawa yake yi tana zare idanuwa. Dukkansu kallon Zahra'un suke yi suna son jin dalilin da ya sa ta dakatar da su daga aikata k'udurinsu,gyaran murya Zahra'u tayi sannan ta janyo wata kujera da ke gefe ta zauna dan ba zata iya jure tsayuwa ba,ta umarce su da su ma su zauna,sai gashi kuwa sun zauna sun zuba mata idanuwa,su kansu mamakin kansu suke yi saboda sun san babu mai gaya musu suji,ko mazajen su hak'uri suke da su,amma y'ar ficiciya a gabansu ta zo tana basu umarni kuma suka bi,ita kam Zahra'u bata yi mamakin bin umarninta da suka yi ba,tasan wannan tasirin addu'a ne,kafin ta tunkaresu sai da ta rok'i Allah sosai akan ya bata nasara a kansu,tana da burin zama tsani wajen shiriyar su kamar yadda Allah ya shiryeta a baya,kuma Allah ya ga zuciyarta shiyasa ya fara bata nasarar,domin tun a fari ta hango za ta cimma nasara da yardar Allah. Sai da ta ga sun nutsu sosai idanuwansu a kanta sannan ta ce da su. "Ni suna na Zahra'u,kuma ni y'ar uwarku ce musulma,na zo gareku ne domin nayi muku nasiha akan tsoron Allah,sannan kuma na baku wani labari wanda nake fatan ya zame muku izina wajen hango abin da kuke aikatawa ba dai dai ba ne" Shiru suka yi har lokacin idanuwansu a kanta.Nan Zahra'u ta fara jero bayanai cike da nutsuwa take fad'a musu illolin abin da suke aikatawa,ayoyi da hadisai ta dinga janyo musu tana kafa musu hujja da su,tayi rantsuwar cewar ta san dukkansu babu wadda ta tambayi mijinta kafin ta fito wannan yawon barbad'ar,to su sani cewar dukkansu suna cikin fushin Allah tare da tsinuwar mala'ikun rahama,ta koma kan me kitson ita ma ta dinga yi mata nasiha da wa'azi,ta fito mata da laifinta akan cewar ta fi kowa laifi ita da take tara matan aure a gidanta ana gulmace-gulmace,haka nan ta dawo kan Gimbiya tayi mata nasiha mai tsoratarwa akan hanin da manzon Allah (S A W) yayi akan (GIBA) wato cin naman mutane idan basa nan,babu kyau munafurci ko kad'an,duk mai gulma da munafurci ranar lahira ba shi da rabo mai kyau a wajen Allah. Daga nan ne ta gangaro kan cewar ita ma ta d'and'ana irin rayuwar da suke yi a baya wadda babu alfanu a cikinta sai zubar da mutunci,ta kwashe labarinsu kaf na BAHAGON LAYI ta basu,sannan ta cigaba da yi musu nasiha akan su gyara halayyarsu su san mutuncin kansu. Dukkansu babu wacce bata yi hawayen nadama da danasani ba,sun ji matuk'ar tsoro da kalaman da Zahra'u ta fad'a musu,zuciyarsu ta girgiza,nadama ta rufe su,sai gasu suna hawaye da neman yafiyar ubangiji akan abin da suke aikatawa,kuma suka yi wa Zahra'u alk'awarin sun daina da yardar ubangiji,kowacce za ta cigaba da zama gidan mijinta bisa doron yadda shari'a ta shimfid'a,sun daina yawace-yawacen da suke yi,haka nan Gimbiya ma ta ce ta daina gulma da munafurci,ita ma me kitso tayi nadama ta ce in sha Allahu ta daina tara mata a gidanta ana gulma da munafunce-munafunce. Zahra'u taji matuk'ar dad'i a ruhinta ganin ta silarta matan duk sun yi nadama,a gaban idanunta kowacce ta tashi ta tafi gidan ta,ita ma tayi sallama da me yin kitson ta kamo hannun Nana suka dawo gida zuciyarta k'al cike da farinciki da murna. A yammacin ranar ne kuma ita ma Allah ya sauketa lafiya ta samu jaririn ta namiji,ba tare da wata doguwar nak'uda mai wahalarwa ba. ************* To kuma dai a yammacin ne Allah yayi dawowar Saratu cikin BAHAGON LAYIN a karo na biyu,wadda ta tawo da niyyar zaman aure na hak'ik'a da yi wa miji biyayya bakin iyawarta,babu ko d'iso a ranta na sha'awar maimai ta rayuwa irin ta baya,da gaske ta dawo da k'arfinta wajen mayar da hankalinta kacokam kan rayuwar aurenta,ko ta samu ta gyara laifuffukanta na baya. Harira tun da taji labarin dawowar Saratu take zakwad'i da murna,nan da nan ta jany o gyale ta fito daga gida dan ta je ta ganewa idanuwanta abokiyar shan mirinda 😂 daman Amina ma bata nan tana gidan mai jego Shafa'atu,tun safe ta fita,dalilin da yasa ita kuma tak'i zuwa gidan Shafa'atun taji labarin dangin Shafa sun ce sai sun ci ubanta tun da tayi mata turaren barkono ta wahalar da ita wajen nak'uda,hakan yasa tak'i shiga saboda kar suyi mata( walmukalifatu😆)ta bari ne sai ranar suna ta sake shiga ta san tunda taron suna ne babu mai tab'a ta. Da hanzarinta ta shige gidan Saratu tana kwad'a sallama da ambatar "oyoyo kina ina ne abokiyar shan mirinda?" Saratu da ke zaune a gaban Hajiya maimuna tana k'ara yi mata nasiha,jin muryar Harira sai da gabanta ya fad'i,kwata kwata bata son wata alak'a ta sake shiga tsakaninta da Harira,domin a baya ma duk ita ce musababbin b'ata musu rayuwa,Harira na shigowa bakinta a washe ta tsuguna tana gaida Hajiya maimuna,sannan ta gaida Saratu a zatonta wata goggon Saratun ce saboda yadda taga sunyi kama sai dai wannan tsohuwa ce,gabad'aya tunaninta bai bata cewar Saratun ba ce😆 sai da ta gama gaishesu sannan ta cigaba da k'wala kiran Saratun tana fad'in "Amarya ko lab'ewa kikayi a d'aki ne?fito man na ganki an dad'e ba'a had'u ba k'awar shan mirinda" Hajiya maimuna ce cikin d'aure fuska ta dubi Harira ta ce. "Alamu sun nuna min kece Harira duk da ban tab'a ganinki ba,to k'awar shan mirindar da kike kira ai gata a gabanki,da alamun kema baki shaidata ba kenan a karon farko ko?saboda lalacewar da tayi,kuma ke ce musababbi,to bari kiji na fad'amiki,Saratu ta dawo gidan mijinta ne dan tayi zaman aure na hak'ik'a ba yawon barbad'a ba,kin san Allah idan baki fita daga harkarta ba to Kuliya manta sabo ne zai raba mu da ke,daga yau kar na k'ara ganin lagutsattsiyar k'afarki cikin gidan nan dan ubanki,shegiya gafalalliya mara tunani da hankali,duk shakiyancin da kika yi a baya kika ga darasi har yanzu baki yi hankali ba,ke wace irin mace ce?to ahir d'inki ki fita harkar Saratu idan ba haka ba ba k'aramin shiri muka yi a kanki ba,Salisu ma kad'ai ya isa ya ci ubanki wallahi" Takaici ya ishi Harira,haka kawai kowa sai a dinga d'ora mata laifi?to kuwa wallahi hakan ba zata sab'u ba bindiga a ruwa,dole ta d'auki mataki akan hakan. Korar kare Hajiya Maimuna tayi wa Harira,haka ta tashi ta fita k'afafu a sanyaye,ita da take ta murna Saratu ta dawo domin ta samu su had'a kai da Saratun da Habiba suyi shawarar yadda zata fitar da Amina daga gidanta,sannan kuma su d'auki fansar yadda Idrees ya wulak'anta su,to amma ga wankin hula yana neman kai ta tsakar dare. Tana komawa gida ta tarar da Amina ta dawo,tana durk'ushe tana wankewa Sunusi kayansa,dan tsokana irin ta Harira kawai sai ta nufi gaban Amina ta sa k'afa ta shure bokitin ya fad'i kumfar ta zube,A fusace Amina ta d'ago daman a cike take da Harirar,dundumemen hannunta ta fitar ta faskawa Harira mari me shiga kwanya😂 wani azababben zafi ya mamaye Harira tun daga kai har zuwa k'afafu,zaro idanuwa tayi tana cukumar Amina dan k'arfin hali irin na Harira wai ba zata yarda ba,Amina ta ce mata "Idan dai ba so kike na tsige miki ragowar hak'oran da ke bakinki ba to dan jakar ubanki ki sake ni" Harira ta fara kokawa da Amina tana fad'in "Ba zan sakeki ba dan .....uwarki,akan me zaki d'auki hannunki me kama da k'irgi ki lafta min a fuska?wallahi ba zan yarda ba sai na rama" Nan da nan kokawa ta rincab'e a tsakanin su,daman Amina damar da take son samu kenan,gashi tayi sa'a gidan babu kowa babu me k'watar Harira,nan da nan ta fara kilar Harira nata kai mata naushi,Harira ta fara jin azaba tayi kukan kura ta tura kanta cikin hammatar Amina ta sa gefen bakinta da yake da ragowar hak'ora ta cafko fatar hammatar tana cizga 😆 Amina kuwa hannunta ta mak'e ta kaiwa kumatun Harira naushi,sai ga Harira na gurnani tana neman fito da kanta daga hammatar Amina 😂 azaba ta ishi Harira ta d'aga hannunta ta kaiwa k'irjin Amina duka,nonuwan Amina suka d'auki zugi kamar ta saki fitsari,ai bata san lokacin da tayi wurgi da Harira ba,Harira bata sauka a ko'ina ba sai kan murfin rijiya,murfin ya goce sai ga Harira tsundummmmmm cikin rijiya 😳😂😆 Dai dai lokacin da Sunusi ya rangad'a sallama ya shigo gidan,akan idanuwan sa Amina ta cilla Harira cikin rijiya...😂 Comment share vote pls *BY HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️ *BAHAGON LAYI* (SABON SALO) *TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️ HASSANA D'AN LARABAWA *BABI NA ASHIRIN DA TARA DA NA TALATIN* PEN WRITERS ASSOCIATION ✍️ *BARKAN MU DA SALLAH Y'AN UWA MUSULMI NA DUNIYA,ALLAH YA MAIMAITA MANA YA KARB'I IBADUNMU* 😍 ***Sunusi ya d'ora hannu aka ya rafka salati da k'arfin murya yana zare idanuwa kamar mage a kwali, da wani irin hanzari kuma ya d'ebi k'afafuwan sa zuwa gindin rijiyar kamar ya kifa,yana lek'a kansa ciki idanuwansa suka gane masa Harira saman ruwa sai facal -facal take ,ta rasa yadda zata yi. Juyowa yayi yana duban Amina fuskarsa d'auke da mad'aukakin tashin hankali,ga mamakinsa sai yaga Aminar ta juyar da kai alamar ko a jikinta ma abinda ya faru,sai ma tsugunawa da tayi tana tattara kayan da take wankewa wad'anda suka zube a k'asa.Sunusi bai san lokacin da ya daka wa Aminar wata razananniyar tsawa da ta saka ta d'agowa a firgice ba,cikin b'acin rai yake kallon ta yana magana. "Wai Aminatu anya kina da hankali kuwa?ko baki ga abin da kika aikata ba ne?an fad'a miki kishi Hauka ne da zaki d'auki Harira ki cillata cikin rijiya?yanzu har kishin da ke k'irjinki ya kai tunzira zuciyarki wajen aikata kisan kai Amina?" Sai lokacin gaban Amina yayi wata irin fad'uwa jin maganar kisan kai,a zahiri dukkan wani laifi Harira ce me dakonsa,amma idan silar fad'awar Harira rijiya y janyo ajalinta babu wanda zai dubi baya ya hango laifin Harirar,illa ita da za a yi ta yamad'id'i da ita cewar ta kashe kishiyarta saboda kishi,gidajen redio da talabijin da y'an jaridu su samu abin yi,dumiya tayi mata tofin ala tsine duk da cewar ita ke da gaskiyar,kowa ya tsaneta ,daga nan ta k'are rayuwar ta a gidan yari cikin takaici da bak'in ciki,to me gari ya waya kenan?. Bata san lokacin da wasu hawaye suka ratso idanuwanta ba ,cike da tsoro ta matsa kusa da Sunusi da ke gindin rijiyar ta kamo hannunsa jikinta na mugu mugun rawa,cikin saurin baki ta soma magana tana hawaye. "Wallahi ni ba da gayya nayi hakan ba,ita ce tazo ta kamani da kokawa,ni kuma na tunkud'e ta ban san cewa rijiyar zata fad'a ba,don Allah ka taimaka kayi hanzarin ciro ta kar ta mutu ta rataya a wuya na in shiga uku in lalace". Duk da takaicin da ya kume k'irjin Sunusi hakan bai sa yak'i jin tausayin Amina ba,domin ya san itan tana son ayi zaman lafiya,Harira ce ta cika fitina har bai san yadda zai yi da ita ba,shi kansa ta gama addabarsa darajar Inna kawai take ci da kuma maraicinta da yake duba wa. Yana nan tsaye ya rasa abinyi sai Amina da ke kuka.Lek'a kansa ya sake yi cikin rijiyar,gani yayi Harira ta daina motsi gabad'aya da alamun ko suma tayi,da wani irin hanzari ya ture Amina daga gefensa yana salati yayi hanyar fita waje domin neman mafitar yadda za a ciro Harira daga rijiya. ************ Kimanin kwana biyar da faruwar lamarin bayan an tsamo Harira daga rijiya,wadda taci bak'ar wahala duk ta gwaggwabje jikinta ya k'warzane,bakinta ya sake karkacewa daman ba hak'ora. Kwance take lamo cikin akurkun d'akinta,zaune ta tashi tana amsa sallamar Habiba da ta shigo cikin d'akin,Habiba ta k'araso da sauri fuskarta cike da jimami da tausayawa take kallon Harira ganin duk ta fita daga hayyacinta,zama tayi kusa da Harirar tana fad'in. "Sannu Harira ashe haka wannan abu ya faru?Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ,sannu kinji Allah ya mayar kaffara" Harira ta yatsina fuska ta dubi Habiba da lomammen bakinta ta ce. "Hmmmm! ni me zaki ce dani Habiba?wannan ibtila'i ya faru dani amma kika sa zuwa akan kari ki dubani har yau kwana biyar,anya kuwa aminci da zaman tare yace haka Habiba?" Habiba tayi ajiyar zuciya ta sauke mayafinta kan kafad'a tanai wa Harira nuni da k'asusuwan wuyanta sannan ta ce. "Ni ma idan kika dubeni tsaf daga sama har k'asa Harira bana cikin wata nutsuwa da kwanciyar hankali,a halin da ake ciki fa yau saura kwana shida rakkin a d'aurawa Babalalo aure Harira" Harira ta gwalalo idanu tana dafe k'irji ta ce. "Abin ya zo kanki kenan Habiba?to shi Babalalon dan uwatar da wane kud'in zaiyi auren?ko ba naji ance kwanaki azal ta fad'a masa yayi gobara ba?kai gaskiya Habiba maza ba k'ananun jarababbu bane,ban da toshewar basira wannan bala'in ya same shi amma ba zai iya hak'ura da auren ba?" Habiba ta fara matsar hawaye zuciyarta cike da k'unci take kuka tana fad'in. "Ni Harira kwata kwata ba auren ne yafi d'aga min hankali ba ma yanzu,yadda auren ya zamo auren cin amana shine yafi damuna,gabad'aya na rasa in da zan tsoma raina naji sanyi Harira" "Kamar ya ya auren cin Amana Habiba? Harira ta tambaya cike da mamakin jin kalaman da suka fito daga bakin aminiyarta Habiban Babalalo. Habiba ta fyace majina da gefen mayafinta hawaye na sharara ta ce. "Ai kin san k'awata Rauda ta bayan layi ko? wadda mijinta abokin Babalalo ne,to wallahi in tak'aice miki labari da Rauda da mijinta sune suka nanawa Babalalo Yayar Raudan,wata bazawara ce har da d'anta wai ita Abida,yanzu fa har an gama komai saura kwana shida a d'aura auren,wai duk yadda nake da Rauda shine taci amanata bayan har da had'in bakinta wajen tunzirani dan na cuzgunawa mijina,ashe munafuka tana can tana had'a min bomb d'in da zai tashi da ni,yanzu a yadda ake Babalalo ya sauya min baki ga wulak'ancin da yake min ba,kuma yace muddin nayi wani yunk'uri wallahi saki uku zai min,iyayena kuma sun ce min idan na kashe aurena to baza su karb'eni ba sai dai na shiga duniya,ni yanzu gabad'aya abin duniya ya isheni Harira,ina nadamar abubuwan da suka faru a baya,shiyasa nace bari na shigo na dubaki sannan na baki labarin abubuwan da suke faruwa dani,ya kamata mu gyara halinmu Harira mu zauna da kowa lafiya dan kyautata rayuwar auren mu,ki duba kiga yadda Zahra'u da K'asimu rayuwarsu ta canja suna zamansu lafiya,sannan ki juya ki kalli rayuwar Saratu da Salisu ta dawo suna zaune lafiya suna cin soyayyarsu har tayi kyan gani cikin kwana biyar,ga Shafa'atu da Kamilu su ma suna d'iga tasu soyayyar,yanzu ni da ke ya rage Harira,mu ma ya kamata rayuwarmu ta daidaita da mazajenmu da abokan zamanmu,kiyi hak'uri tunda Amina tana son ku zauna lafiya ki bata had'in kai ku cigaba da zama,na tabbatar har yanzu Sunusi yana sonki duk da halayenki marasa kyawu Harira,nima nayi alk'awarin zama da kishiyar da za a kawo min lafiya in sha Allahu,abin da nake dubawa mutuwa bata sallama Harira,kar muje mu mutu muna masu sab'awa Allah a lahira mu shiga wuta,ki duba yadda kika tsallake rijiya da baya,da kin mutu lokacin da kika fad'a rijiya me kika tanada da zaki fad'awa Allah Harira?ni dai na rok'e ki mu ajiye duk wani iskanci da muke ji da shi mubi hanyar Allah muyi bautar aure" Sai da Habiba ta kammala jawabinta tsaf sannan Harira tayi kabbara kamar gaske. "Allahu Akbar! me karatu na gaba,Habiba kenan,ke yanzu kina nufin duk wad'anda suka cuceni in k'yalesu kenan ba tare da na d'auki fansa ba?" Habiba ta girgiza kai ta ce. "Harira babu wanda ya cutar da ke,kece kika cuci kanki da kanki,kuma ina mai baki shawarar ki ajiye makamanki ki fuskanci rayuwa ta zahiri tun lokaci bai k'ure miki ba" Harira tayi shewa,Habiba ta bita da kallo.Sai da ta gama shewarta sannan ta dubi Habiba tana tamke fuska ta ce. "Billahillazi Habiba ko zan shiryu sai na d'auki fansa akan mutane guda biyu,kinga Amina ko,yadda ta azabtar da ni cikin ruwa ni kuma sai na azbtar da ita cikin wuta,daman kuma ita ce sanadiyyar rasa hak'orana,to yadda ta rabani da hak'orana na rantse da Allah sai na rabata da kunnuwanta domin sai na cizge su,duk da dai bayan an ciro ni daga rijiya na dawo hayyacina tazo har gabana ta tsuguna tana kuka ta bani hak'uri,na nuna mata kamar na hak'ura amma abinda bata sani ba shine na k'ullace ta a raina,kuma sai na d'auki fansa babu ragayya" Ta sauke numfashi yayin da ta dasa aya akan maganar,ita dai Habiba kallonta kawai take,Harira ta gyara zama ta cigaba da magana. "Sai mutum na biyu wato wancan matsiyacin takurarren mutumin,Idrees yake ko wa? shima har yanzu yana nan a raina yadda ya sabauta ni ni ma sai na sabautashi daga shi har tsinanniyar matarsa,alk'awari nayi kafin su bar layin nan kuma sai na cika aikina" "To ai kuwa kin makara Harira"cewar Habiba kenan kafin ta cigaba da cewa. "Yau kwana biyu kenan da tashin Idrees da Hauwa daga layin nan,kuma babu wanda ya san unguwar da suka koma,dan kuwa ko sallama baiyi da mak'ota ba wayar gari akayi aka ga sun tashi basa nan" Harira ta zabura tana fad'in " Kan ubancan ! wai da gaske kike Habiba ko dai wasa kike?" Habiba ta ce. "Wallahi da gaske nake miki,ke bama Idrees da matarsa ba hatta Malam Arabi da bai jima da dawowa layin ba to shima jiya jiyan nan ya tashi ya bar unguwar,dan shi a yadda naji ma wai k'auyensu ya koma,kin san yayi abin kunya ashe y'ammata yake latsewa a makarantar daren da yake koyarwa,shine aka ganeshi malamai suka yi masa fata fata da korar kare,duk unguwa ta d'auka ba damar ya fita sai yaran unguwa su dinga yi masa d'an kira suna tsokanarsa,nadama ta isheshi ya rasa yadda zai yi,ba shiri shima jiya suka had'a komatsen su shi da matarsa Angayu suka arce daga BAHAGON LAYIN nan zuwa k'auyen su" Bala'in takaici ne ya cika zuciyar Harira,bata damu da tashin Malam Arabi daga layin ba domin bata da case da shi,amma tabbas tashin su Idrees ya mugun tsaya mata a zuciya,matuk'a gaya taci burin d'aukar fansa,amma in dai ba bangon duniya suka tafi ba tana ji a ranta koma me zai faru sai ta nemo in da suke dan gabatar da k'udurin zuciyarta. Duk yadda Habiba ke bata baki Harira k'in ji tayi,mahaukaciyar k'wak'walwarta da muguwar zuciyarta suna ta kitsa mata sharri,har dai Habiba ta gaji tayi fushi tace ta k'yaleta taje ta aikata duk abin da tayi niyya,tunda dai ta fita hakkinta ta gaya mata gaskiya amma tak'i d'auka,ta tashi tayi tafiyarta ta bar Harira na k'ulle k'ullen sharri a zuciyarta. ************ Kwanaki suka shud'e abubuwa da yawa sun faru,ciki kuwa har da k'arin auren da Babalalo yayi,amma bai had'a su gida d'aya da Habiba ba,sai ya ware wa Amarya Abida gidanta daban suke shan sharafin soyayyah,yayin da Habiba tayi nadama sosai akan rayuwar da tayi a baya,ta nemi afuwar Babalalo shi kuma bai yi k'asa a gwiwa ba wajen yafe mata ,ganin tayi nadama da gaske,suka cigaba da zamansu lafiya da kwanciyar hankali,idan yayi kwana biyu a gidan Habiba sai yaje gidan Amarya yayi kwana biyu. B'angaren Saratu( Baba laminde😆) da nata gwarzon wato Salisu (d'an lukuti 😂) ,suma suna zaune lafiya ana cin soyayyah da tsinke,tuni Saratu ta murmure ta soma mulka k'iba ita ma,har Salisu na tsokanarta da y'ar lukuta ta d'an lukuti 😅,Zaman su gwanin sha'awa babu raini sai girmama juna,tuni ya ajiye zancen k'arin auren da zaiyi a gefe ganin babu abin da ya nema ya rasa gurin Saratu,tana masa ladabi da biyayya dai dai gwargwado. Shafa'atu ma zaman lafiya ne ya cigaba da wanzuwa a tsakanin ta da mijinta Kamilu da babyn da ta haifa,tuni kuma ta fita daga harkar Harira ita ma,musamman da ta ankara da cewar ba son gaskiya Harirar ke mata ba,tunda taso kasheta da turaren Barkono a yayin da take cikin halin nak'uda,tuni Harira ta fice mata daga rai,ta mayar da hankalinta wajen biyayyar aure da rainon babyn da ta haifa. Zahra'u kuwa ko a can baya mace ce me kyautatawa miji,domin bata raina K'asimu ba,a yanzun ma ta saka d'amba da sake d'amarar kyautata masa da rainon babyn da ta haifa ita ma,zaman su lafiya da kwanciyar hankali babu hargowa. Idrees da Malam Arabi kuwa tun da suka arce daga BAHAGON LAYI babu wanda ya sake jin d'uriyar su 😂. ************** Harira zaune a d'akinta taji sallamar Amina ta shigo,ta amsa tana gyara zama,Amina ta k'araso tana fad'in. "Sannu da hutawa Yaya Harira" Harira ta amsa fuska cike da fara'a kamar gaske,Amina ta cigaba da cewa. "Akwai aikin da zan yi miki ne yanzu? Girgiza kai Harira tayi ta ce. "Ah ah babu abin da zakiyi min" "To bari naje na d'an kwanta kafin azahar tayi,jikina ke min ciwo nasan idan na samu hutu zai warware" cewar Amina kenan yayin da ta nufi k'ofar fita dan tafiya d'akinta. Tana fita Harira ta kwashe da dariyar mugunta tana fad'in " zaki huta a k'iyama kam dan yau sai naga bayanki matsiyaciya,kin d'auka washe miki bakin da nake yi da gaske sonki nake ko?to ai duk duniya bani da mak'iyiyar da ta kai ki,shegiya y'ar iska ,lukutar banza sukutar wofi". Sai da ta bari Amina tayi minti arba'in da fita sannan ta mik'e,janyo galan d'in man k'uli tayi da kasko ta fito tsakargida ta nufi d'akin girki,har a ktcheen d'in tana jiyo munsharin da Amina ke saki alamar ta samu bacci mai nauyi,hakan yasa tayi dariyar mugunta,tana hango yadda zata toya hallitar Amina da man k'uli soyayye. Wuta ta had'a ta d'ora man,har da yanka albasa a ciki kamar wadda zata toya man da za a ci wake da shinkafa,tana tsaye har man yayi toyu albasar tayi jajir da ita,saukewa tayi a hankali sannan ta fito daga ktcheen d'in ta nufi tagar d'akin Amina da ke tsakar gidan,a hankali ta lek'a tagar sai ta hango Aminar tayi shirim a gado sai kwasar bacci da munshari take duk ta cika gadon,Harira tayi murmushin mugunta a zuciyarta ta ce. "Bak'ar arniya ji be ta kamar an kayar da wani bijimin sa,wannan baccin sai da ki farka ki ganki cikin k'abari,kuma in sha Allahu idan walakiri ya zo miki sai ya fara gaggab'e miki hak'ora kamar yadda kika gaggab'e min" Koma wa ktcheen d'in tayi ta sa tsumma ta d'auko uban man k'ulin da ta soya wanda yafi kwalba uku,dan so take tayi wa Amina wanka da shi tun daga guntun kanta zuwa gundumemiyar gangar jikinta har k'afafuwanta,yadda tayi balance a gado tana zuwa shek'a mata kawai zata yi. A hankali take tako wa har ta fito daga ktcheen d'in,wata k'usa da ke gefen ktcheen d'in ce ta ja hannun rigar Harira,bata yi aune ba kawai sai ji tayi kamar an fincikota tayo baya ta zame,kan ta ankara tayi k'asa gabad'aya toyayyen man da ke hannunta ya shek'o mata a ilahirin jikinta 😳 ,wani irin masifaffen ihun azaba da Harira ta saki sai da karad'e ilahirin unguwar ma ba layin ba. A gigice Amina ta farka tana dirowa daga gado tayo hanyar waje a firgice saboda ba k'aramar razana tayi ba jin ihun Harira da ya farkar da ita,tana fito wa tayi arba da Harira tana wata irin birgima cikin fitar hayyaci fatar jikin ta na salub'ewa,Amina ta d'ora hannu a ka ta zunduma ihun neman taimako,yayin da tayi waje a gigice kanta ko d'ankwali babu tana ihun a zo a taimaka musu. Kafin ka ce me gidan ya cika tab da mutane ma masaka tsinke,har Sunusi an masa waya ya tawo da hanzari,babu kuma wanda zai iya tab'a jikin Harira saboda jagwalewar da yayi sakamakon birgimar da take yi,gabad'aya ko ina na jikinta ya soye da man k'uli,tun tana ihun azaba har ta sume a wajen. Tilas motar asibiti aka kirawo ta kwashi Harira aka nufi asibiti da ita,duk k'ek'ashewar zuciyarka idan ka dubi Harira sai ka ji tausayinta saboda ta soyu ba da wasa ba,k'awayenta na BAHAGON LAYI kuka suka dinga yi da hawayen su saboda tausayin ibtila'in da afkawa Harirar. Kimanin sati biyu da k'onewarta amma jiki yak'i dad'i,kullum k'una k'ara jagwalewa take,idan ana mata dreesing kaf asibitin cika shi da ihu da kururuwa take dan azaba,babu mai iya dosarta saboda tsananin d'oyin da jikinta yake yi,tabbas Harira a wannan lokaci taga azabar duniya,shiyasa idan zaka gina ramin mugunta ka gina shi kad'an,domin idan baka yi wasa ba kai za ka afka a cikin sa. Ranar da jikin Harirar yak'i dad'i da bakinta ta dinga rok'on Sunusi akan ya kirawo mata dukkan k'awayen ta na BAHAGON LAYI,ba tare da b'ata lokaci ba dukkan su suka hallara har da mazajen su,Zahra'u da K'asimu,Habiba da Babalalo,Saratu da Salisu,Shafa'atu da Kamilu,sai Mijinta Sunusi da kishiyarta Amina,cikin jin jiki Harira ke kuka tana neman afuwar kowa,a lokacin ne kuma ta fallasa kanta ta gaya musu cewar reshe ne ya juye da mujiya,domin Amina ta so ta k'ona sai sharrin ya dawo kanta,shi daman sharri kuma d'an aike ne,wataran kanka zai dawo. Ba k'aramin mamaki dukkansu suka yi ba,Harira ta dinga wani irin kuka tana neman afuwa,nan kowa yace ya yafe mata ko dan ta samu sassauci,tun a duniya ma kenan tana shan wannan bak'ar azabar ina ga an je lahira? Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe! 😭 Bayan sun tafi likitoci suka shigo domin yi mata dressing,ana cikin yi mata tana wannan ihun da zabure zabure Allah ya karb'i ranta,Harira ta mutu cikin wani irin yanayi mara dad'i,Allah kasa mu cika da kyau da imani 👏Allah ka tsarkake mana zukatanmu ka k'ara mana imani da biyayya a gareka ya Allah! 👏 Mutuwar Harira ta girgiza mutane da dama,duk da halayenta marasa kyau sai dai anyi kukan sabo,kuma an yi mata addu'a sosai,ana mata fatan samun rahamar Allah tunda ta nemi afuwar wad'anda ta zalinta kuma sun yafe mata,kuma mijinta ma ya yafe mata,tsakanin bawa da ubangijinsa kuma ba a shiga. Rayuwa ta cigaba da tafiya tana mik'awa,mutuwar Harira ta k'ara nutsar da zukatan k'awayen ta,suka k'ara laushi da mik'a wuya zuwa ga Allah. *K'ARSHE*....! Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! INA GODIYA GAREKA SARKI ALLAH,ALLAH KA K'ARA TSIRA DA AMINCI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S A W) DA ALAYENSA DA SAHABBANSA. NA GODEWA ALLAH DA YA BANI LAFIYA DA DAMAR KAMMALA WANNAN LITTAFI,GODIYA GAREKU MASOYA MASU BIBIYATA TARE DA FATAN ALKAIRI,NAGODE SOSAI HASSANA D'AN LARABAWA TAKU CE😍SAI KUMA MUN HAD'E A SABON LITTAFINA MAI CIKE DA WANI IRIN DARASI DA RAYUWA TA ZAHIRI MAI TSAYAWA A ZUCIYA,KAMAR KULLUM SHI MA SALON SA NA DABAN NE, *(HAYATUL K'ADRI)* YA ZO DA WANI IRIN SALO DA RAYUWAR DA IDAN AKA BIBIYE SHI TABBAS ZA A K'ARU FIYE DA K'ARUWAR DA AKA YI A BAYA,SHIN MASOYA KUN SHIRYA KUWA...? IDAN KUN SHIRYA TO NIMA NA SHIRYA,KUYI HIMMA KU BIBIYENI NI HASSANA D'AN LARABAWA DA YARDAR ALLAH 😘 NAGODE! 👍👍👍 BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️ Downloaded From https://tknovels.com.ng