Downloaded From https://tknovels.com.ng    DANDANO DAGA LITTAFIN 💥RUMBUN QAYA💥 ZAFAFA BIYAR 2023 ©®HAFSAT Rano    ***Tana tsaye gaban coat din sa dake rataye a jikin hanger da yake makaleta kullum yazo office din, waige-wage take tana son yin sauri ta dauki key din, sai da ta tabbatar da babu motsin kowa tayi saurin saka hannu a aljihun rigar ta jawo key din ta damke a hannun ta. "What are you doing..." Ya fada yana tsaye daga bayan ta Saura kiris glasses din idon ta ya fadi kasa, tayi saurin tare shi da dayan hannun ta juyo tana kallon sa. Takowa ya shiga yi har zuwa gabanta yana kare mata kallo tun daga sama har k'asa, kafin ya maida kallon sa zuwa wajen coat din tashi dake sakale. "Me kike yi anan?" Yace muryar sa a d'an shake yana kallon fuskarta, kanta ta sunkuyar kasa sosai ya cigaba da kallon ta a nutse kafin yace "Are you trying to steal something?" Zaro idanun ta, tayi da sauri ta hau girgiza kai "Then tell me, me kike min a wajen rigana?" "Am..am... Dama nazo na kawo maka wanchan report din da na hada ne, so sai na tarar kana restroom shine na ajiye a saman table shine sai naga kamar wani abu a saman rigar shine nazo zan duba na cire maka." Dan jim yayi yana kallon ta, kafin ya ja siririn tsaki ya nufi wajen zaman sa ya zauna. "Show it to me." Yace yana jan mouse ya dora hannun sa akai. Fakar idon sa tayi ta tura key din a cikin aljihun jacket din dake jikin ta sannan ta karaso ta dauki report din ta bud'e ta fara masa bayani. Danne dannen sa yake har ta gama sai da yaji tayi shiru sannan ya dago ya dan kalle ta "Ina jinki." "That's all." Tace "Shikenan abinda kika iya samu?" Gid'a kanta tayi kad'an "Come here." Yace yana maida kansa ya cigaba da abinda yake, gefen sa ta matsa ta tsaya daga dan baya "Result din nake son gani, show it to me." "Ok!" Tace ta dan runkwafo kad'an ta shiga nuna masa. Kamshin turaren ta ne ya shige masa chan cikin hancin sa ya haifar masa da mixed feeling, dan muskuta jikin sa yayi yadda ba zata gane ba amma still yana jin kamar sake matso shi yayi. "It's ok!" Yace da dan karfi "Just go, ki tura min ta email zan duba anjima." "Ok...Thank you" Tace dauki report din zata fita "Wait..."  Yace ta juyo ta tsaya "Ki bawa Kamal shayi na ya kawo min." "Ok sir." "Sannan...karki kara saka turare me karfi idan zaki zo aiki." "Na'am?" "You heard me right! You may leave." "Ok." Tace da saurin ta, ta fice hadda dan gudun ta   Tana fita ya saka hannu ya hau janye necktie din wuyan sa yana mikewa tsaye, ya isa gaban dan madaidacin fridge din sa ya dauki ruwa me sanyi ya hau sha "May I come in?" Ya turo kansa ya rike kofar ba tare da ya shigo ba "Kana da matsala, kayi ta tsaiwa a wajen." Yace yana dire robar ruwan ya shiga takawa zuwa seat din sa ya zauna. Shigowa yayi ya rufe kofar ya samu waje ya zauna shima yana murmushi "Ya akayi?" Yace yana duban sa "Akwai babban labari..." "Kamar na me fa?" "Barrister Nasir Matawalle is out!" "What!!!? Ya fada yana mikewa "Da gaske ko da wasa?" "Allah kuwa, naji labari daga majiya me karfi ya fito earlier last week, but zancen dai be fito sosai ba dan kamar yaran sa ne basa so a sani saboda suna so ya samu kulawa ta musamman ne." "Alhamdulillah!" Ya fada a hankali yana maida kansa baya ya jingina da jikin kujerar yana lumshe idon sa. "Me ya kamata ayi yanzu?" Kamal yace ganin yayi shiru, bud'e idanun sa yayi ya zauna sosai yace "Time zamu samu muje mu ganshi, inaso na ganshi dan shi kadai yasan abinda ya samu Mom, shi ne kawai zai taimaka min na cika buri na." "Kana ganin bud'e case din ba zai zama matsala ba? Kasan fa Daddy baya so, sannan sau nawa kana zuwa prison dan ganin sa amma yaki, kana ganin zai saurare ka yanzu bayan da be saurare ka ba?." "I don't know... " Yace yana tuna jelar zuwa prison din da ya dinga yi dan duk ya samu ganin shi amma fafur yaki yarda su yi wata doguwar magana. "Toh yanzu dai menene abun yi?" "Zuwa zamuyi mu ganshi din, ba kuma zamu hakura ba har sai ya hakura ya ganmu munyi magana, he's my only hope." Shiru ya danyi sai ya dora "Gaba daya rayuwata na yi ta ne akan jiran wannan ranar, that's what keeps me going, ba zan taba hutawa ba har sai na san abinda ya samu Mommy, wannan alkawari na ne, sai na bi kadin mahaifiyata, ko da hakan na nufin..." "Shikenan, shikenan. You have my support, Allah ya bayyana Mama gaskiya." "Amin thank you." Yace yana hasaso abinda zai faru kuma, ajiyar zuciya ya sauke ya sake tashi da nufin dauko key din nan ya bawa Kamal. ***Tana fita daga office din nasa ta dauki handbag dinta akan table ta zare rigar saman ta ajiye ta fita da saurin ta, a titi ta tsaya ta kira wayar tana kokarin tsaida me napep "Hello..." Tace tana fadawa cikin napep din bayan ya tsaya "Eh na dauko, ina hanya ma." Magana akayi daga dayan bangaren tace; "Ok tam.." ta kashe wayar tana sake duba key din ta tabbatar yana ciki. Tafiya kad'an suka isa unguwar, ta bashi kudin sa ta sauko ta karasa gidan a kafa.   Ciki ta shiga bayan an bud'e mata kofar tangamemen gidan da kaf unguwar babu me girman sa, yau ne karo na biyu da ta zo gidan amma sai take ganin kamar yau ne karon farko. A hankali take tafiya tana karewa gidan kallo har ta isa main part din. Tana zuwa daidai kofar ta bud'e da kanta, ta saka kanta ciki bakin ta dauke da sallama.    Tana hakimce a saman daya daga cikin kujerun falon rike da door remote din dan ita ta bud'e mata kofar dan ta hango ta tun sanda ta shigo gidan. "Rayhana..." Ta kira sunan ta tana sakar mata murmushi, murmushin ta maida mata itama ta gaishe ta a nutse sannan ta sa hannu ta ciro key din ta mika mata "Good! Kin taimaka min sosai kamar yadda nima na taimake ki, kin saka alkhairi da alkhairi nagode sosai." "Ba komai Aunty!" Tace tana murmushin jin dadi "Me zaki sha a kawo miki?" "Ba komai, komawa zan kar ya gane na fita." "Ok! Zan kiraki kinji?" "Ok." Ta mike tana rataya jakarta tayi hanyar fita "Kin ga jirani mu fita dake dan nima wajen hanyar taku zanyi." "Ok nagode." Tace ta koma ta zauna ita kuma ta tashi ta shiga ciki bayan ta dora wayarta a saman hannun kujerar da Batul din ke zaune. Tana zaune wayar tayi yar kara alamun shigowar sako, kallon wayar tayi sai ta dauke kanta kawai tana cigaba da more kallon dankararren falon. Wani sakon ne ya sake shigowa a wannan karon sai ta kasa dauke idon ta akai ta shiga karanta sakon da yake yawo a saman wayar _"An gama hajjaju, an zuba poison din, wuyarta Aryan yasha tea din nan, sai dai wani ba dai shi ba, tunda mun samu key din sai kiyi kokarin kwashe duk wani abu da ya tanada as evidence, ita kuma yarinyar ita za'a kama da case din poison din, kinga shikenan mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya!!"_ Wani irin sarawa kanta yayi cikin yanayin tashin hankali ta mike tsaye "_Na shiga uku!"_ Ta furta tana dafe kirjin ta. _" Amfani dani tayi kenan? Karya tayi min tasa na dauko mata key din? Duk abinda ta fada min akan sa kenan karya take?."_ "Shayi? Wayyo innalillahi." Ta fada gabanta na faduwa _"Ya Allah!!!"_ Da sauri ta juya har da dan gudu-gudu ta fice daga falon. Tana fita Hajiya Zeenat ta fito, mamakin rashin ganin ta ya kamata ta shiga kiran sunan ta, waya ta dauka ta kira gate ta tambaya aka ce mata yanzu ta fito ta fita "Ok... Ta huta" Ta dauki wayoyin nata ta watsa su a handbag dinta ta shiga kwalawa mai aikinta Harira kira   ****Yadda take gudu zaka dauka mahaukaciya ce sabuwar kamu, kamar zata fada duk napep din da tazo haka ta dinga bin su idan ta tsaida su basu tsaya ba, a karshe ta samu wani ta fada tana haki. Suna isa ta ciro kudi bata duba ko nawa bane ta cilla masa ta shiga building din a guje. Bata san in da take jefa kafarta ba har ta isa reception din, baki daya ma'aikatan wajen duk suna tsaitsaye sun yi cirko-cirko, kallon ta suka shiga yi irin kallon tuhumar nan, jikinta ne ya hau rawa tayi saurin haurawa sama zuwa office din sa. Kofar sa a bud'e take sabanin yadda take a rufe a kowanne lokaci, maganganu ne ke fitowa daga ciki wanda ta gaza fuskantar daya daga ciki, ji tayi kamar an dode mata jin ta, burin ta kawai ta isa ciki ta tabbatar da be sha shayin nan ba, kowa yasan Aryan da masifar son hadin shayi me na'a na'a da sauran nau'ikan kayan kamshi. Duk da rashin yardar sa da kowa amma ya kan sha shayin wanda ya yarda ta hada masa ita kadai, shi ma sai da Kamal ya tabbatar masa da babu wata matsala sannan ya amince. Idanun ta ne suka sauka akan Kamal dake dauke da tsantsar tashin hankali shinfide a saman fuskar shi, ji tayi tamkar an sassare mata guiwowin ta, ta zube a wajen tana fashewa da kuka. "Na shiga uku." Kawai bakin ta ke furtawa kawai, sai taji an saka hannu an tura kofar office din, shiru ya biyo bayan hakan sai shashekar kukan ta dake tashi hade da garar A.C da aka kureta sosai har take fitar da sound me dan karfi. Tirkashi!!! Guda daga cikin LABARAN zafafa na wannan karon. Karku sake a baku labari, kiyi sauri ki mallaki naki dan samun damar damawa a cikin wadannan dadadan Labaran masu fadakarwa gami da wa'azantar wa uwa uba rantsatsiyar soyayyar zukata biyu me shiga birnin zuciya *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +22799643131 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *RUMBUN QAYA*              Free Page 2 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 ***A tsaye yake ya rike karfen jikin stairs din yana amsa waya, wayar da yake me matukar muhimmaci ce daga yadda yake magana. Idanun sa ya daga sanda yaji an bud'e kofa. Adam ne, dauke kallon sa yayi zuwa wani shashen na daban yana kokarin katse wayar "Zan kiraka back." Yace ya katse yana juyawa da nufin hayewa saman. "Aryan..." Ya kira sunan sa yana tahowa, tsayawa yayi da hawan ya juyo yana masa kallon neman karin bayani "Ashe kana ciki baka fita ba." "Ya akayi?" Yace a gajarce cikin yanayin rashin son maganar tasu tayi tsayi "Nothing much, kawai dai maganar Daddy zan tuna maka, dan naga kamar ka manta ne ko kuma kana kokarin shashantar da maganar, ina jiran ka ajiye aikin ka bani wajen, dan da alama babu abinda zaka iya da irin wannan zuciyar taka." Kallon rainin wayo yayi masa, yaja tsaki kawai ya juya da sassarfa ya haye saman, murmushi Adam yayi yana janye hannun sa ya hade su waje daya. "Karamin dan air." Sai ya juya yana bouncing shima ya bar wajen.    A harabar gidan suka hadu, daidai lokacin ta fito daga motar fuskar ta dauke da annuri, tsayawa yayi ta karaso ya karbi handbag dinta yana murmushi "Mom sai yanzu? Har ina shirin fita." "Bari kawai, yau nayi babban kamu, duk da dama da wannan plan din na fita, and it was a success gaskiya, muje ciki." "Sai Mommy ta, mu je toh." Tayi gaba ya bita a baya yana mata hirar maganar da yayi ma Aryan yanzu, da kin amsa ma san da yayi "For now ka bar wannan maganar, mu bi komai a sannu dan na samo bakin zaren." "Wai kina nufin na bar masa matsayin MD din?" "Kwarai, ka cigaba da bin sa a hakan, saura kiris ya rage." "Oh shit! Mom yaron nan fa yana kokarin kai ni karshe ne, ni dai ayi duk yadda za'a yi na gaji da bin sa kamar wani uba na." "Kai dai ka zuba ido, ka kyale min komai." "Shikenan Mom, I trust you ai." "Yawwa My boy, yanzu kaje in da zaka idan ka dawo sai muyi maganar, ka biya office din Daddyn naku kaga ko yana da bukatar wani abu." "Shikenan, sai na dawo." Ya ajiye mata jakar a gefen bedside ya fita. Zama tayi ta ciro wayar ta, ta shiga number Hajiya Maryam wadda itace Co-ordinator ta NYSC Kano, maganar minti uku sukayi ta fada mata bukatar ta, take tace ta tura mata NYSC number din yarinyar cikin kankanin lokaci akayi komai, ta sauya mata zuwa company su. Tashi tayi bayan ta gama ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta sauya shigar ta zuwa wata shigar ta alfarma sannan ta fito babban falon tana kwala kiran Harira.     ***Wanka tayi bayan sun gama jimamin abinda ya faru da ita da su Adda Maimuna da Amina, magungunan ta, tasha sannan ta haye gado ta kwanta, cikin kankanin lokaci kuwa tayi bacci har da mafarkin matar da suka hadu wadda tayi masifar shiga ranta farat daya, ta burge ta matuka yadda ta jata a jiki cike da kulawa. Wajen la'asar ta tashi shima sai da Amina ta tashe ta dan yin sallah. Kasala ce ta rufe ta bayan ta tashi, tayi sallar da k'yar ta dan ci abinci sai kuma tunanin gida ya dawo mata, tayi kewar su dukka sosai, kamar ta fasa bautar kasar ta koma wajen Dadan ta tayi zaman ta haka take ji, dan ma gidan Adda Maimunan akwai dadin zama musamman aka zauna bayan magriba ayi ta hira wani lokacin sai akai sha biyu ana hira ana ciye -ciye, shiyasa take dan jin dama-dama. Dada ta kira bayan magriba sai dai bata fada mata bige ta da motar tayi ba dan tada hankalin ta zatayi tace dole dole sai ta taho shiyasa sai tayi kum suka gama wayar cike da kewar juna.    Kwana biyu da haduwar su da Hajiya Zeenat sai ga kiranta, tayi mamakin yadda ta samu number ta dan bata karba ba ranar amma sai bata kawo komai ba, ta duba ta sannan ta sake jaddada mata ta shigo goben ta karbi posting letter din tata kasancewar gobe sukayi dama Monday. Godiya ta sake yi mata cike da jin dadi sukayi sallama.  Washegari ta shirya cikin doguwar bakar abaya ta yafa medium veil tayi kyau sosai haka itama Amina ta shirya dan ita zata rakata suka fito titi suka samu napep suka masa kwatance kamar yadda yake a rubuce,kai tsaye yace "Ko dai gidan Alhaji Mukaddas?" Kallon juna sukayi ita da Amina kafin tace "Eh sunan dai matar da zamu gani Hajiya Zeenatu Mukaddas, gashi a jikin katin." "Ai sanannan gida ne wannan." "Alhaji Mukaddas wai me kudin nan da ake fadan sa?" Amina tace bayan sun shiga sun zauna "Eh shi fa." Me napep yace. Jinjina kai sukayi dukka suka ja bakin su sukayi shiru. Har gaban tangamemen gate din gidan ya kai su, kansa tsaye kuwa dan ba wannan ne karon farko da ya taba zuwa ba, duk azumi ana rabon kayan abinci kuma ya sha samu shi ma, dan ba wani nisa ne dasu sosai ba. Sakowa sukayi dukkan su idonsu akan gidan da ya cika da kyau da tsari, girman gate din ma kadai abun kallo ne. "Kin tabbata nan ne Raihana?" "Eh bari na kirata, amma dai ina kyautata zaton nan ne." "Toh kirata muji." Tace tana cigaba da kallon gidan. Kiran wayar tayi no answer, ta sake gwadawa a karo na biyu kafin ta daga tace mata suna waje, ok tace mata sannan ta katse wayar ta kira gate din tace a shigo da ita, suna tsaye aka bud'e karamar kofar shiga gidan, wani buzu ya leko kansa a rufe yace su shigo, a sanyaye suka shiga duk jikin su ya mutu saboda mamaki, har balcony din ya rakasu sannan yace su shiga, suna dosar kofar ta bud'e da kanta suka shiga da sallama wani masifaffan sanyi me hade da wani irin feshin raba ya bige su, wani irin tsam sukayi suna wurgurga ido a tsakiyar tamfatsetsen falon dake cike da manyan kujeru na alfarma "Raihana.." ta sake kiran sunan ta, tana sakkowa daga stairs din dake tsakiyar falon, murmushi ne a fuskar ta har ta karasa saukowa. Da sauri suka gaishe ta, ta amsa musu a sake tana nuna musu wajen zama. "Ya jikin naki?" Ta tambaye ta bayan sun gaisa tana cigaba da kallon su fuskar ta a sake sosai "Na samu sauki." "Alhamdulillah, sai zuwa ganin Baba kenan." Dariya suka sa dukka ta jawo wata drawer a jikin centre table din ta ciro envelop ta mika mata "Ga posting letter din ki as I promised!" Dadi ne ya kamata ta karba tana godiya sosai, ta bud'e sannan ta mikawa Amina ta karba itama ta gani, a sannan ne aka kawo musu snacks da juice da ruwa tace su ci tana zuwa. Zagewa sukayi suka ci Amina har ta daukar wani buns ta saka a tissue ta tura a jaka suka saka dariya "Mom!" Ya turo kofar yana kiran ta. Riga da wando ne a jikin sa, sai takalmi sau ciki, kansa rufe da pcap ya jona airpod a kunnen sa fari. Tsayawa yayi chak yana kallon su, kafin ya karaso ciki sosai still idanun sa na kansu yazo ya zauna a daya daga cikin kujerun falon. "Ina wuni?" Suka hada baki wajen gaishe shi "Lafiya Lou, wajen Mom kuka zo." "Eh suka amsa." "Adam ka dawo?" Tace tana fitowa daga hanyar dakin ta na kasa "Eh shigowa ta kenan, naga kin yi baki beauties dasu." "Raihana ce da sister din ta, ni ban ma tambayi sunan ki ba Yan mata." "Amina." "Yawwa Aminatu ce ashe tsohuwa." "Raihana... What a name! itace kuka bige ranar da driver?" "Eh itace." "Wow!" Yace yana taba gemun sa yana wani irin kallo k'asa k'asa, yana ayyana wani abu a ransa. *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +22799643131 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *RUMBUN QAYA*              Free Page 3 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 _____________ _*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_ _*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._ _*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._ _*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_. _*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._ _*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._ _*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_ _*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._ _*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._ *_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._* ****Yana tsaye a jikin gate din suka fito rike da yar madaidaiciyar leda, tasowa yayi ya tare su a hanyar yana sakin fuskar sa "Yan mata kun fito?" Yace idanun sa akan Raihana da tayi kicin-kicin da fuska dan har ga Allah yanayin kallon sa yayi mata kama da na shaidanun maza, da ka ta amsa sai Amina ce ta bud'e baki ta ce masa eh, ya jera dasu har zuwa gate din kafin yayi musu tayin motar sa, noke kafada tayi da sauri ta rike hannun Amina sannan tace "Mun gode." Daga haka sukayi waje da dan saurin su, dage kafadarsa yayi ya saki guntun murmushi da ya tuna a wajen su zatayi aiki har na tsawon shekara daya. Juyawa yayi da shirin komawa ciki yaji horn din motar Aryan, fasa shiga yayi ya tsaya rataye da hannuwn sa har ya shigo cikin gidan ya samu gefe yayi parking sannan ya fito da dan saurin sa, mantuwa yayi dan har ya kusa zuwa office ya tuna shine dalilin dawowar sa. Sarai ya ga Adam a compound din ya kuma san ganin shigowar sa ya hana shi shiga ciki amma sai yayi kamar be ganshi ba, yayi wucewar sa da dan saurin sa, bin bayan sa yayi suka shiga a kusan tare a lokacin tana zaune bayan fitar su Raihana tana amsa waya tana dariya cikin jin dadi, ganin Aryan a lokacin yasa ta yin saurin katse wayar tana fata da addu'ar Allah yasa be hadu da su Raihana da suke fita yanzu ba, dan ta tabbata idan yasan akwai wata alaka tsakanin su ba zai taba accepting dinta ba. "Son me ka dawo yi?" Tace tana mikewa tsaye cikin yanayin rashin gaskiya "Akwai abinda zan yi." Yace a gajarce yana hayewa saman da dan saurin sa, kallon Adam tayi da yake tsaye daga baya tace "Ya hadu da su Raihana ne?" Girgiza mata kai yayi "Basu hadu ba, dan su ta gaba suka bi shi kuwa ta baya yake shigowa." "Ok." Tace daidai lokacin ya dawo ya sake wuce su ya fice cike da sassarfa. Tsaki taja me tsawo bayan ya fita, bata son ganin sa tamkar yadda yaki jinin ganin ta, ta sani kuma tana da yakinin da za'a bashi damar kashe mutum daya a duniyar nan toh tabbas da itace kai tsaye, sai dai be sani ba, tsanar da tayi masa har ta ninninka wadda yake mata, dan ita baki daya rayuwar ta da tsanar sa ta ginu, fiye da yadda ta tsani mahaifiyar sa, shikuwa a baya ya sota, so me tsanani har baya iya bacci ba tare da ya ganta ba, ya mata irin son da d'a yake wa mahaifiyar sa ko ma fiye da hakan. ***Washegari ta tashi cikin shirin zuwa wajen aiki, ta shirya cikin shigar doguwar rigar atamfa A shape  me gajeran hannu sannan ta dora NYSC jacket dinta a sama ta yi rolling mayafi medium akanta sannan ta dora pcap din a sama. Jakar ta, ta dauka ta tura takardar da sauran abinda zata bukata ta fito falon ta samu Adda Maimuna zaune tare da Abban su Amina, ta durkusa ta gaishe su sannan tace zata tafi, kudi ya dauko ya bata sannan ya saka mata albarka.   Har gaban gate din me napep ya kai ta, ta sauka ta karasa wajen masu gadin dake zazzaune a kan benci ta gaishe su sannan ya fada musu abinda ya kawo ta, ciki suka ce ta shiga ta hau sama tayi godiya ta wuce ciki. A reception ta samu wata mata zaune tana shigar da abu cikin desktop, matsawa tayi ta gaishe ta sannan tace mata sabuwar corper ce ita, takardar ta karba ta duba sannan tace ta hau sama office din oga Kamal, godiya tayi ta wuce zuwa saman tana dubawa har ta kawo office din nasa, Knocking ta yi akofar kad'an ta jira aka ce ta shigo sannan ta tura kofar bakin ta dauke da sallama, yana tsaye yana duba wasu takardu tare da head supervisors na company suna magana akan sells din da kowanne gidan mai ya kawo a satin gaba daya, shigowar ta yasa su tsayawa ta karaso ta dan russuna ta gaishe su kafin ta fadi abinda ya kawo ta ya rigata cikin sigar tsokana yace "Corper we!" Murmushi tayi ya nuna mata wajen zama yace ta zauna ta basu minti biyu, ta zauna suka cigaba da dubawa har suka gama, sannan ya tafi shi kuma ya zauna a kujerar sa sannan yace ta taso, ta taso tazo ta zauna ta gaishe shi ya amsa a sake da tambayar camp, ta amsa itama tana murmushi "Ok welcome to Mukaddas and sons." Yace yana mika mata hannu ta bashi posting letter din tata "Thank you." Tace ta mika masa cike da girmawa ya duba ya saka hannu a wajen da ya kamata ya saka sannan yace "Bari na bawa Oga kwata-kwata ya saka hannu anan, bani minti biyu." Ya mike kenan aka dan yi knocking sau daya kafin ya turo kofar ya shigo kansa tsaye "Ina stamp din office dina?" Yace yana shigowa "Gashi nan dazu aka kawo, sai kuma Faisal ya shigo zan kawo maka kenan, dama yanzu office din ka zanzo we have a new corper." "I don't think muna bukata, reject her." Yace ba tare da ya kalli ko in da take ba, ya dauki stamp box din ya juya zai fice "Wait please , we need her saboda field din da ta karanta." "Regardless! Just reject her please wahalar corpers din nan yawa ne da ita." Yayi ficewar sa kawai, wata kwalla ce ta ciciko a idanun Raihana, ta tsani wulakanci a rayuwar ta, sai kace wadda tazo neman aljanna zaa wulakanta ta haka. Dawowa Kamal yayi ya zauna yana girgiza kai "What a tough guy! Sorry please don't be offended, I'm coming." Ya tashi ya fita da sauri, share kwallar tayi da bayan hannun ta, tana jin duk shaukin da take dashi na zama a wajen na gushewa.    A zaune ya same shi yana latsa computer as if nothing happens, ajiye masa takardar yayi a gaban sa yace "Please sign and stamp here, idan kuma ban kai nayi making decision anan ba sai na sani." Dagowa yayi ya tsaya da abinda yake ya kalle shi, sannan ya kalli takardar kad'an kafin yace "Me yasa kake so mu dauke ta?" "Haka kawai nake so, coz naga zatayi amfani, computer science ta karanta." Be ce komai ba, yaja takardar gaban sa ya dauki biro yayi signing a wajen da ya kamata yayi sannan yayi stamp ya tura masa yana maida kansa ya cigaba da abinda yake yi. Dauka Kamal yayi ya fice shima be ce komai ba, bayan sa yabi da kallo ya girgiza kai karon farko da yaga me irin sunan ta _"Raihana."_  ya furta a chan kasan makoshin sa, wani memory me matukar muhimmaci a rayuwar sa ya shiga yi masa yawo aka, ko suna wacce duniya a yanzu? Allahu a'alam.   ***Zuciyar ta a chunkushe ta bar office din, sam bata ji dadin abinda ogan yayi mata ba, ko ba komai mutum ba abun wulakanci bane ba. Tana tafiya a kafa ta kusa karasawa titi wayarta tayi kara, ta kalli screen din ganin me kiranta ya sakata dauka da dan sauri ta daidaita muryar ta sannan ta gaishe ta "Ok gani nan." Tace cike da zumudita tura wayar a jakarta sannan ta tare napep tace ya kai ta KURMAWA.  Motar ta, ta hango an yi parking dinta a chan gefe, ta sauka ta karasa ta danyi knocking, sauke glass din tayi tace ta shigo, ta zagaya dayan bangaren ta shiga, driver ya tashi motar suka nufi cikin prison din. Jikin ta gaba daya yayi sanyi tunda taga an shigo ciki, a waje ta hangi mutane a layi masu son samun shiga ciki domin ganin yan uwan su, sai an fara baka takarda ka shigar da sunan Ka sannan ku samu shiga ciki shima sai ku zazzauna a wasu kujeru kuna jira har a zo kanku sannan ku shiga ciki bayan an baku tag kun makala a wuyan ku. Su kuwa kai tsaye suka wuce duk wannan layin har ciki sukayi parking, manyan gandurobobin ne suka fito suka tare su, suka dinga kwasar gaisuwa ita dai Raihana sai kallo take yi, ciki suka shiga kai tsaye zuwa wani office suka zauna sai gashi an kawo mata tag din an ce ta taso, cike da zumudi ta mike suka fita, ta hade hannun ta waje daya saboda yadda suke mata wani iri. Wani dan daki aka ce ta shiga ta zauna ta jira, ta na zaune akayi sallama ta juyo da sauri, bata san sanda ta fashe da kuka ba,ta tashi ta rungume shi cikin kuka "Abby na." "Uwata... Kece da kanki? Ke kadai? Masha Allah Alhamdulillah." "Toh ya isa haka na, bar kukan ki zauna muyi magana, ya isa haka." Yace yana shafa bayan ta, shiru tayi ta zauna tana kallon sa cike da tausayawa "Abby ina wuni?" "Lafiya lou Raihanata, kece kika zo ganin abbinki da kanki?" Gid'a masa kai tayi "Basa so su zo dani kwata-kwata bansan me yasa ba." "Basa so kiyi kuka ne, amma kullum suka zo sai sun nuna min hotonki sannan sai sun yi ta min hirarki." "Abby yaushe zaka fito?" "Saura kiris kinji? Ki cigaba da min addu'a, sannan ki rike min mutuncin ki a duk in da kika samu kanki, sannan duk runtsi karki ci amanar wadanda suka aminta dake, ki zama me riko da gaskiya da amana duk runtsi." "In sha Allah Abby, zan zama me bin maganar KU." "Allah yayi miki albarka kinji? Allah ya baki sa'a a duk abinda kika saka a gaba dake da Yan uwanki, ki musu biyayya domin su ne iyayenki a yanzu da nan gaba ma." "In sha Allah." Tace tana cigaba da kukan da ta dan tsagaita da, sun dan dau lokaci suna hira har sai da yayi mamakin dalilin da ya saka aka barsu suka dade haka, amma be kawo tunanin komai ba, suka sha hirar su sannan tayi masa sallama cike da kewar sa, ta koma office din farkon nan jikin ta a sanyaye. Kayan provision ta gani a zube ana maganar su, ta shigo "Yawwa Raihana, gashi nan za'a bawa Abban ki, tunda zuwan bagatatan ne baki zo masa da komai ba." "Nagode sosai Anty, Allah ya saka da Alkhairi." "Amin Amin, officer bari mu koma, thank you so much, sai ka jini." "Ba komai Hajiya, dan Allah a mika mana gaisuwa wajen Alhaji, muna shan abin arziki sosai sai dai fatan Allah ya kara girma da arziki." "Ba komai." Tace suka fito ya rako su har mota suka shiga, sai da yaga tafiyar su sannan ya koma ciki. Sanda suka hau titi sosai ne Hajiya Zeenat ta riko hannun Raihana, ta saukar da kanta k'asa cikin yanayin damuwa tace "Ina cikin damuwa Raihana, damuwa me tsanani." "Allah ya yaye miki damuwar ki Anty." Tace cike da tausayin matar me tsananin kirki da karamci "Kina so ki san matsalar da nake ciki Raihana?" Gid'a mata kai tayi da sauri "Ko da yake be kamata na dora miki nauyin damuwa ta ba, ke yarinya ce, amma inaso kiyi hakuri da taka tsantsan da halin Aryan." "Aryan?" Tace tana kallon ta "Eh Aryan, ina kyautata zaton kin hadu dashi yau a office da kike je." "Shine oga?" Tace da sauri "Shine, yana da zafin rai da wani irin hali, shine kadai damuwa ta a yanzu, ina kaunar sa tamkar yadda nake kaunar raina, sai dai..." Sai tayi shiru kamar me tunani "Shikenan Raihana, zamuyi magana wani lokacin kinji?" "Tam." Tace a kasalance abinda yayi mata dazu ya dawo mata, lallai yana da babbar matsala idan har zai iya saka mace kamar Hajiya Zeenat a cikin irin damuwar da ta hanga a cikin idon ta. A hanya suka sauke ta, tayi godiya ta tsaya jiran abun hawa, sai ga kiran Hamman ta, da sauri ta daga tana dan matsawa baya daga titin. "Kina ina?" Dadah tayi maganar tana jin an daga "Daadah na, yanzu nake neman abun hawa zan tafi gida, yau ce ranar farko da na fara zuwa in da akayi posting dina." "Shikenan, ki kula da kanki kina zuwa ki kirani kinji?" "Tom." tace muryar ta a sake ba tare da tayi tunanin komai ba. *LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA* *DAUDAR GORA Billyn abdul* *KI KULANI hafsat xoxo* *A RUBUCE TAKE Huguma* *RUMBUN K'AYA Hafsat rano* *IDON NERA Mamuh ghee* _LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_ _KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_ _TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_ _TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_ _TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_ _TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_ _ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171 SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 09033181070 IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA 09166221261 *ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA* +22799643131 Books biyar  1250CFA Books hudu  1050CFA Books uku  850CFA Books biyu  650CFA Bookk daya  450CFA KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* *RUMBUN QAYA*              Free Page 4 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 _____________ _*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_ _*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._ _*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._ _*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_. _*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._ _*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._ _*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_ _*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._ _*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._ *_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._*. ••••••• Daga kansa yayi ya kalli kofar da akayi knocking kafin yace “Yes!” Turowa yayi ya shigo fuskar sa ba yabo ba fallasa,yanayin sa Aryan ya kalla kafin yace “Akwai matsala ne?” Girgiza masa kai yayi kafin ya zauna, sannan yace “A ah, maganar da na saba dai kullum ita ta kawo ni yanzu ma, dan Allah ka rage zafi Aryan." Bata fuska yayi yana duban Kamal din yace "Me kuma nayi?" "Yadda kayi ma yarinyar nan dazu, ba dadi." "Ni ba abinda nayi mata, iya gaskiya ta kawai na fada corpers din nan basa da wani amfani." "But ai be kamata ka fada a fuskar ta ba." "Toh naji, wai ka santa ne?" "A ah me ka gani?" "Yadda kazo ka titse ni mana akan ta." "Ni dai kawai ka yarda bakayi daidai ba, mata suna da rauni sosai, hakan zai iya effecting dinta." "I don't believe you, they are very cunning, sun iya shedding crocodile tears." "Banda Raihana." Yace yana murmushi "Raihana?" "Yes! Baka ga sunan ta a jikin takardar ta ba?" "Ban karanta ba ai." "Amma kayi signing?" "Ina da wani option ne?" "You are not nice wallahi, ai shikenan. Nace ta fara zuwa gobe sai ta dinga zuwa sau uku a sati,ta zauna a cash office muga abinda zata iya." "Cash office? Why not reception? Ko su zauna dasu Zainab." "A ah, karatun ta ya wuce haka nan, taje dai cash office din su yi aiki tare da su abdulhakeem." Mikewa yayi ya dauki rigar sa da ya sakale a jikin kujerar da yake zaune ya dora ta a saman t-shirt din dake jikin sa, ya kwashi wayoyin sa ya zuba su a aljihu sannan ya kalli Kamal din da ya mike tsaye shima yana daukar wani file a saman desk din Aryan din yace "Zan je naga Ya Nabeela." "Kaga da ba dan wannan aikin da yake gaba na ba, da munje dan na kwana biyu ban shiga ba, nayi missing daddad'an girkin ta "Muje mana, ba dadewa zan ba nima muna da meeting da shareholders da karfe biyu, so har ma dawo ma." "Ok toh bari na dauko wayata a office." "Ka sameni a parking lot." Yace yana yin gaba, suka fito a jere shi yayi k'asa shi kuma Kamal ya koma office dinsa ya dauko wayar sa ya rufo. A harabar wajen ya same shi tare da Malam Musa suna magana akan sabbin motocin da suka siyo na mai wanda zasu iso anjima, gobe yake saka ran dawowar Daddy shiyasa ma zai yi duk kokarin sa wajen ganin ya kammala duk ayyukan da ya tafi ya bari. Hango Adam yayi ya fito daga dayan block din da yake kallon nasa, ya nufo su ya sakashi katse maganar da yake niyyar yi ta hanyar cewa "Bari na dawo Malam Musa zamuyi magana." Ya nufi motar sa, Kamal da ya fuskanci dalilin da ya sashi barin wajen yayi saurin bin bayan sa ya shiga motar, yaja suka bar wajen. "Malam Musa biyo ni office." Adam yace ya juya ganin sun watse ba tare da sun bari ma ya karaso ba, bin bayan sa Malam Musa yayi ciki yana ayyana abinda Adam din zai tambaye shi wanda ya saba tambaya a duk sanda ya gansu tare da Muhammadun suna wata magana. ***Wayar sa ya dago da tayi kara ya daga ganin Ya Nabila ce, sukayi magana ya ajiye yana maida hankalin sa akan tukin da yake yi. Kamal ne ya karya shirun da yayi ta hanyar sako maganar Adam "Menene matsalar sa wai?" Yace yana duban Aryan din da kansa yake kallon titi cikin yanayin da zai yi wuya ka iya tantance abinda yake ransa "Matsalar sa ta wuce ni?" "Allah ya kyauta, yaushe Daddy zai dawo?" "Gobe in sha Allah, bansan ko daga goben zan sake shigowa office din ba a cikin week din, dan nima inaso na danyi wani aiki a office dina." "Ka daure dai ka shigo please, shi kansa Daddy yanzu baya iya dadewa a company dole dai kai ne kasan dai ba za'a sakar ma Adam komai ba ko?" "Kana mamakin hakan? Daddy yana ta shirye-shiryen bashi share me tsoka a company din." "Are you serious?" Dage kafadarsa yayi irin I don't care din nan sannan yace "I'm serious, abinda suke ta planning kenan." "Then me ka shirya?" "Ban shirya komai ba, na gaji ma baki daya ta zuwa company wallahi, na matsu ayi a gama na cike wa'adin da daddy ya daukar min nayi gaba, be damen ba wajen nan ko kad'an, buri na daya ne kuma ka sanshi, so bana bukatar wata dukiya ko wani fame, su suke ta wahalar da kansu I'm willing to give everything in dai zan samu cikar buri na." Murza saman goshin sa Kamal yayi cikin yanayin damuwa yace "Nasan yadda kake ji, ka sani kowanne tsanani yana tare da sauki, in sha Allah komai zai wuce kamar baa yi ba, zaka dawo rayuwar ka tamkar yadda kake a baya, in sha Allah." "In sha Allah, amma bana tunanin hakan Kamal,karka manta ina fama da PTSD (Post Traumatic Stress Disorder )." "Na sani, amma zaka samu sauki in sha Allah, mu cigaba da addu'a sannan ka cigaba da ganin therapist dinka kana shan dukkan magungunan ka, zai wuce." "In sha Allah!" Yace daidai lokacin suka karaso gidan, yayi horn megadi ya bud'e musu suka shiga ciki. Amna ce a gaba Amaani na bayan ta cikin rige-rigen zuwa yi masa oyoyo, sune kananan yaran Ya Nabeela sai yayyane su biyu Affan da Hadiyya. Daga su yayi sama a tare cikin tsananin kaunar su, ya rungume su a jikin sa yana dariyar da ba zaka taba ganin yayi ta ba in dai ba yana tare da su ba. Sai da ya gama daga su sama sannan Kamal ya dauki Amaani shi kuma ya dauki Amna suka shiga ciki suna musu surutu. Hadiyya da Affan na zaune sun saka Ya Nabeelan a tsakiya suka shigo, tashi sukayi su ma suka zo wajen su suka yi hugging dinsa sannan suka zauna duk suka mamuke masa. "Ku barshi ya zauna mana sosai Affan, kun bi kun dabaibaye shi kamar yau kuka fara ganin sa, sannun ku da zuwa kanina." Ta karashe tana kallon Kamal "Sannu da gida Babbar Yaya." "Sannu Kamal, ya gida ya aiki?" "Alhamdulillah wallahi." "Masha Allah." "Small mom ina wuni?" "A ah gama da yaranka, sai mu gaisa." Tace cikin sigar tsokana, murmushi yayi ya gyara zaman sa sosai yana daidai ta su suma sannan ya gaishe ta, ta amsa tana masa murmushi me dauke da kaunar da tausayi a lokaci daya, murmushin shima yake ta tashi ta kawo musu abinci sannan ta kora su Amna dakin su ta saka musu kallo ta dawo suka sake gaisawa sosai suka dan taba hira, ta dauko wasu takardu na maman su ta bashi ya bud'e ya dudduba sannan ya mikawa Kamal shima ya duba. Daga nan suka tashi sukayi mata sallama yaran suka rakosu har mota tare da ita, ya dauko musu chocolates dinsu a baya da ya manta da ita ya basu sannan suka koma office dan lokacin meeting din nasa ya kusa dan sai da suka kara sauri idan ba haka ba da ya makara. ***Tana fesa turare ta gama shiryawa Amina ta shigo, ta zauna tana kallon yadda tayi kyau cikin shigar riga da skirt na atamfa orange and mint green ta yafa orange veil wanda yayi matukar haska ta kasancewar ta fara sosai, tana son gayu a rayuwar ta duk da komai nata very simple ne amma tasan marching colours sosai shiyasa Amina take jinjina mata dan da gaske yar gayu ce ta bugawa a jarida, koman ta very unique and classy haka take yin sa. Tafa mata hannu tayi a saman fuskarta "Meena wannan kallon fa?" "Kin ganki kuwa Adda Raiha? Wallahi kayan sun miki kyau sosai, kar kije office kisa guys su dinga karo fa." "Look at you, me wannan shigar yayi da har za'a yi karo, ni tsoron zuwa ma nake wallahi, boss din bashi da kirki ko kad'an, irin masu wulakancin nan ne kinsan masu kudi dangin mala'u." "Allah? Wulakanci sukayi miki?" "Bari kawai, dan tsabar wulakanci wai fa a gaban ido na yace wai ayi rejecting dina, hadda cewa wai corpers basu da wani amfani." Dariya Amina ta fashe da ita ganin yadda Raihanan take tsuke fuska tana bada labarin "Kice kin hadu da mara m, toh ya akayi kuma suka karbe ki?" "Oga Kamal ne yaje ya same shi a office ko me suka ce oho, sai gashi ya dawo da takardar tawa anyi signing da stamp a jiki." "Ok Allah sarki, shi me kirki ne Kamal din." "A ah sosai wallahi, baki ga yadda ya dinga bani hakuri ba wallahi, har fa kuka nayi saboda takaici." "Ai da haushi wallahi, sai kiyi takatsantsan dashi sosai, Allah ma yasa ba shine zai dinga baki monthly clearance ba." "Da na kad'e har ganye na wallahi." "Allah ma yasa dai ba shi din bane ba, dan ma dai an ce ba ma wani zuwa PPA din mutane suka ba." "Ameen, idan ka hadu da supervisor me kirki ba, bari kiga na tafi yau farko kar nayi late nayi laifi." "Sai kin dawo, ni sai rana nake da lectures ba ma lallai naje ba gaskiya." "Ok." Tace ta zura takalmin ta suka fito a tare, taje tayi ma Adda Maimuna sallama sannan ta tafi. Kasancewar safiya ce bata wani sha wahalar abun hawa ba, nan da nan sai gasu a gaban wajen, ta sauka ta biya ta shiga takawa zuwa ciki. Gaisawa sukayi da masu gadin wajen dan sun gane ta zuwan da tayi, ta wuce ciki kanta tsaye. Babu cikar ababen hawa a harabar wajen hakan ya tabbatar mata da ba'a gama zuwa ba ko kuma ma dai tana cikin farkon wanda suka fara zuwa a yau din. Cikin reception din ta shiga ta tarar da wani namiji shi kadai yana zaune gaban computer, matsawa tayi suka gaisa tayi introducing kanta yace ta hau sama ta jira zuwan Oga Kamal, saman ta hau babu kowa sai Zainab tana gyara tarkacen da yake kan desk dinta. Itama gaisawa sukayi ta bata wajen zama tana dan satar kallon ta dan jiya da tazo bata nan sun fita da su Samuel. Tana nan zaune har aka dinga zuwa da kad'an kad'an, sai gashi wajen ya cika still dai tana zaune tana bin kowa da kallo tana jiran zuwan Kamal wanda take ganin kamar ba zai zo ba. "Sir Aryan is here." Taji Zainab din ta fada daidai lokacin ta wani kamshin turare me sanyi da dadin kamshi a mamaye ilahirin wajen da suke. Takun tafiyar sa ce ta fara isowa in da suke bayan kamshin sa da ya gama karade wajen baki daya. Manyan kaya ne a jikin sa sabanin jiya da yake sanye da suit ash grey colour. Fuskar sa dinke kamar yadda yake a kullum sai dai shi hakan ya riga ya zame masa wani shashen na daga cikin shashen rayuwar sa, idan ya saki jiki yana walwala sai abinda ya faru a baya ya shiga dawowa yana masa yawo a tsakanin zuciya da kunnuwan sa. "Welcome sir." Kawai kake ji tana tashi a wajen kusan dukkan su sun mike tsaye cikin girmamawa. Kallon sa take yi tun daga shigowar sa, har sanda ya tsaya gaban wani desk yayi signing jikin wata na'ura da ke daukar finger print din duk wanda ya shigo office a ranar da time din da ya shigo. Baki daya ya hada ya amsa gaisuwar da suke masa ya wuce kansa tsaye zuwa office dinsa dake daga dan wani corridor da ya hada da wani babban falon saukar baki. Ajiyar zuciya ta sauke bayan wucewar sa. Tashi tayi ta sake matsawa wajen Zainab ta tambaye ta yaushe Sir Kamal zai zo? Tana rufe bakin sa sai gashi ya shigo da saurin sa, da ita suka fara hada ido ya sakar mata murmushi ya karasa wajen attendance din yayi suka gaggaisa da kowa sannan ya karaso wajen da take a tsaye dan bata koma ta zauna ba kuma. "Goodmorning sir." "Morning corper, follow me." Yayi hanyar office din da oga at the top din yayi, bin sa tayi a baya kamar munafuka suka isa kofar ya fara yin knocking kad'an sannan ya murd'a ya shiga sannan yace ta shigo. *LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA* *DAUDAR GORA Billyn abdul* *KI KULANI hafsat xoxo* *A RUBUCE TAKE Huguma* *RUMBUN K'AYA Hafsat rano* *IDON NERA Mamuh ghee* _LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_ _KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_ _TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_ _TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_ _TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_ _TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_ _ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171 SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 09033181070 IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA 09166221261 *ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA* +22799643131 Books biyar  1250CFA Books hudu  1050CFA Books uku  850CFA Books biyu  650CFA Bookk daya  450CFA KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* *RUMBUN QAYA*              Free Page 5 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 _____________ _*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_ _*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._ _*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._ _*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_. _*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._ _*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._ _*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_ _*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._ _*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._ *_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._*. ••••••• Bata yi saurin shiga ciki sosai ba saboda bata san abinda zata tarar ba, bayan sa ya hanga da dukkan alamu yana tattare abubuwan da suke saman table din nasa ne, kamshin sa kamar dazun ya cika ilahirin office din. Juyowa yayi jin shigowar Kamal din sai kuma ya zagaya ya zauna a kujerar sa yana duban Kamal din da ya karaso sannan ya mika masa hannu sukayi musabiha "Yau na makara." "Nima yanzu na shigo." Yace yana daukar biro a saman table din "Raihana, shigo mana." Kamal yace yana waigowa. Dagowa yayi da kansa Jin sunan da Kamal din ya ambata idanun su suka sarke, saurin kauda kallon sa yayi ya maida kan Kamal cikin son karin bayani "Aryan ga Raihana, dama nace maka yau zata fara zuwa." "Yayi." Yace yana dora biron akan wata takarda take gaban sa ya shiga signing "Akwai wani abu da zaka ce mata?" "Babu, tayi aikin ta yadda ya kamata kawai, and abide by our rules." "Ok, Raihana wannan shine MD na company din nan." "Goodmorning Sir." "Morning." Yace a gajarce "Zakiyi aiki a cash office zaki taimaka wajen shigar da records na duk sales da akayi a ranar,kamar yadda nace zaki dinga zuwa Monday, Tuesday and Wednesday." "Ok sir, in sha Allah." "Shikenan,ki jirani a waje zan zo na kaiki office din ki, duk wata matsala idan ta shige miki gaba akan aiki kizo nan office din kiyi masa complain " Da sauri Aryan ya dago ya kalle shi, sai kuma ya saukar da kansa kasa ya cigaba da abinda yake yi. Godiya tayi ta fice da sauri dan jin ta take Baki daya ta takura da wajen, ga wani kallo da yayi mata da wasu irin idanuwan sa da suka sake dasa mata tsoron sa sosai. Tana fita Kamal ya mike shima, "Bari naje oga, sai an zo shan shayi " "Me yasa kace tazo nan bayan ga su abdulhakeem nan ga ka, me zan mata?" "Ka manta kai ne still incharge na wannan bangaren? Suma su Abdulhakeem din wajen wa suke zuwa?" "Kana takura min wallahi." "Kwana nawa ne wai tayi ta gama ta tafi?" "Idan ka fita ka tura min Zainab." Yace yana cigaba da abinda yake yi, girgiza kai Kamal yayi ya fice yana murmushi k'asa k'asa, yasan ba karamin daga mishi kafa Aryan yake yi ba, be cika ja da duk abinda zai ce ba duk kuwa da halin sa, tasu tazo daya ya riga ya gama sanin lagon sa da yadda zai bi dashi, shiyasa ko Ya Nabeela wani lokacin sai ta nemi taimakon sa akan abinda ya shafi Aryan din. Mutum uku ne a office din Maza biyu mace daya amma ba bahaushiya bace ba, wani empty seat hade da desk dinsa ya nuna mata yace ta zauna sannan yayi introducing dinta wajen sauran sannan ya fita. Gaishe su ta sake yi tana karewa office din kallo da yayi mata kyau sosai, da tuni tana kauye a gaban board tana koyawa yara karatu, nan kuwa ga AC ga ba wata hayaniya sam, ba zata gaji da daina gode wa Hajiya Zeenat ba dan ta taimake ta sosai. Ranar bata yi wani aiki ba dan bata gama gane kan abubuwan ba, Abdulhakeem ne ma ya dinga nuna mata wasu abubuwan har lokacin tafiyar ta gida yayi, ta musu sallama ta fito. Tana tafiya a harabar company tana kokarin fita waje ya hango ta yana kofar office dinsa, saurin tahowa yayi ya sameta tana daf da kaiwa gate "Raihana." Ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunan ta, tsayawa tayi ta juyowa, ya karaso fuskar sa a sake. "Ashe kin fara zuwa amma ko ki neme ni." Yace kamar irin sun dade da sanin juna din nan. Murmushi tayi masa wanda ya tsaya iya saman leben ta shima saboda tunowa da shi din waye a wajen Hajiya Zeenat, dan sam yanayin sa be mata ba tun ranar, yayi kalar yan iska daga yanayin kallon sa da yadda yake mata magana yana wurwurga idanun sa a ilahirin jikinta "Ina wuni?" Tace tana jin ta a takure da mutanen da suke wucewa suna kallon su a tsaye "Lafiya lou, zo muje kiga office dina, idan yafi miki sai ki dawo department dinmu, dan zama karkashin Aryan sai wanda ya shirya." "No wanchan din ma yayi nagode, bari na tafi." "Okh, muje na ajiye ki, tunda ranan kinki yau dai ba zaki ki ba." "A ah nagode, zan tafi da kaina." "Please let me drop you, kamar wani dodo, ke fa yanzu abokiyar aikin mu ce." "Haka ne, kawai bana shiga motar namiji ne, an hanani a gida kayi hakuri." "Ohh ohh okh!" Ya hau kid'a kansa kamar kadangare, sai kuma yace "Hakan ma normal ne, sai gobe toh." Ya juya ya barta a tsaye, juyawar tayi itama ta karasa fita daga cikin wajen. ***Waya ta samu Adda Maimuna tana yi ko da ta shiga gidan, zama tayi ta jira ta gama sai ta fuskanci da Dadan ta suke waya, tana jin sanda Addah Maimunan tace gata ma ta dawo, sai ta miko mata wayar tace "Dadah ce." Karba tayi da murnar ta tace "Dadah na on nialli e jam jam." "Jam nalli, no mbadda? "Jam tan, Alhamdulillah." "Yanzu har Raihana ta girman da zata fara boye mana abinda yake faruwa da ita?" "Dadah?" "Yaushe mota ta bige ki Raihana? Kuma har ki kasa fada min ko Hamman ki? Ashe kin girma har haka?" "Dadah ba haka bane ba fa, bana so ki damu ne, kuma ba wani ciwo naji ba, dan kurjewa nayi sai hakan ma kuma ya zama alkhairi." "Kin dai girma Raihana, ai shikenan, ki kula da kanki dan Allah." "In sha Allah Dadah nah, ina Babbo? Da Hamma Hydar da Hamma Lamido?" "Bakya kiran su a waya ne?" "A ah ina kiran su, kawai wai dai." "Suna lafiya duk sun fice sai ni kwal a gidan." "Allah sarki Dadah na, dole kiyi missing dina wallahi." "Ke ai naga kamar baki ma damu ba, duk wannan kawa zucin gidan tunda kika taho nan shikenan, bansan me Maimunatu take baki ba da har kika manta mu haka." "Kai ina, ai ban manta ku ba wallahi, kullum da daddare sai na tuno gida." "Ba wani nan." "Allah kuwan da gaske." "Toh yayi, kije ki huta naji an ce yanzu kika dawo, saura kuma ki dinga wasa da cikin ki yadda kika saba rashin son cin abincin nan." "In sha Allah Dadah, shikenan zan kira anjima idan su Hamma na sun dawo." "Haa nannde wonnde." "Haa gonngo." Tashi tayi ta kaiwa Addah Maimuna wayar ta dan ta tashi ta shiga ciki, sannan ta wuce dakin su ta cire kayan jikin ta, ta dan kwanta kafin anjima ta tashi tayi wani abun dan sai da ta fara lekawa ta kitchen taga an gama komai dama dai tasan da wuri ake gama girkin rana a gidan saboda yara yan makaranta da ake kai musu. ***Washegari ta sake shiryawa kamar jiya sai dai yau ta dan makara, a gaggauce ta shirya ko breakfast bata tsaya tayi ba, ta tafi. Tana zuwa ta ajiye jakar ta kenan Zainab ta shigo office dinsu tace tazo in ji oga, yadda tayi maganar fuskar ta a hade ba walwala, yasa Raihana ta zata wani laifin tayi, sai dai bata gane wanne ogan ake nufi ba sai da taga sun nufi hanyar office din oga kwata -kwatan, sai a sannan jikin ta ya saki dan bata son duk wani abu da zai hada ta dashi, wani irin kwarjini yake mata. Siririn medicated glass ne sanye a idon sa yana kallon computer, shigowar su ya saka shi dagowa ya kalle su kad'an sannan ya cigaba da abinda yake yi "Sir gata." "Ok you can go." Yace dai ya jawo drawer dake jikin table dinsa ya shiga dubo abu, juyawa Zainab tayi cikin yanayin da ya saka Raihana a tunani, sai ta lura tamkar zata bangaje ta sanda take juyawa amma kuma sai tayi saurin dauke tunanin hakan tayi mata uzuri kila haka yanayin ta yake ko kuma dai bata lura ba. "Ina kwana?" Tace daga in da take tsaye ta hade hannayen ta, ta damke su waje daya. "Kina lafiya?" Yace mata bayan ya ciro abinda yake so ya ciro din "Alhamdulillah." Ta amsa tsoron da take ji yana raguwa jin ya tambaye ta tana lafiya, sai kuma fuskar sa da take a dan sake ba kamar ranar ba, hakan ya bata kwarin guiwar sake matsowa ciki sosai dan da daga dan baya baya ta tsaya "Aiki nake so kiyi min, ki dauki wannan takardar kije ki shigar da duk wani information a cikin system din, kin iya excel?" "Eh na iya sir." "Ok, ki yi shi kamar yadda yake anan sai ki tura min komai ta wannan email din da yake k'asa , duk abinda baki gane ba kizo ki tambaye ni, I need it zuwa 12." "Ok sir." Ta dauki takardar ta juya ta fita. Zaman ta kenan ta kunna system din wayar Abdulhakeem tayi kara, ya daga taji sanda yake cewa ok sir, ya katse sannan yace "Oga Aryan yana kiran ki." "Ni kuma? Yanzu na dawo fa." "Toh dai yana kiran ki." Yace yana dariya ganin yadda ta zaro ido "Ni wallahi bana son zuwa." Ta fada tana mikewa, bata ma san ta fada ba sai da taji Abdul din na mata dariya "Hala dai oga yana miki kwarjini, muma duk kusan hakan ce amma wallahi he's very very nice." "I don't think so." Tayi gaba tana jin suna mata dariya shi da dayan da bata gama rike sunan sa ba. A kofar ta tsaya kamar ba zata shiga ba, ta dan juyo sai taga Zainab tana kallon ta, juyar da kanta tayi ta kwankwasa sannan ta tura kofar, babu kowa a ciki, sallama tayi a hankali jin shiru ya sakata juyowa da nufin komawa, sai gashi yana kokarin shigowa, saurin ja baya tayi dan kansa tsaye ya shigo saura kiris su yi karo, kamar be lura da abinda ya kusan faruwa ba ya wuce ya zauna. "Sir gani." "Na ganki ai." Sai da ya gama ja mata aji a yadda ta lura sannan yace "A cikin rules dinmu, babu fashi sai ta zama dole , shima sai ka rubuto email na dalilin rashin zuwan ka, sannan kullum idan kazo sai ka dauki attendance na time din da kazo da kuma time din da ka tafi." "Ok sir." "Zo ki saka hannun ki anan yayi capturing." Ya nuna mata wata na'ura akan desk dinsa, zuwa tayi ta dora thumb din ta, amma sai yaki dauka, be kalle ta ba yana jin dai tana ta sakawa tana cirewa. "Come to my office." Taji yace a waya kawai, sai kuma aka shigo. "Sir gani." "Zo ki rike hannun ta yadda zai yi capturing naga kamar bata iya ba." Yace ya mike ya fice daga office din, wani abu ne ya tokare mata wuya, ta tsaya kawai Zainab din ta matso da nufin kama hannun ta, saurin hanawa tayi tace "Zan iya da kai na." Wani kallo Zainab din tayi mata sai kawai tayi tsaki ta juya ta fice. Gefen rigar ta, ta saka ta goge hannun sosai sannan tayi bismillah ta saka, sai gashi yayi, ta cire ta saka dayan hannun shima ya dauka. Murmushi tayi dan a rayuwar ta, ta tsani ace bata iya abu ba, duk yadda zatayi taga ta iya kuwa sai ta koya. Daga shi har Zainab din ta lura yan rainin hankali ne, itace secretary dinsa daga gani shiyasa komai sai yace ita. Tana tsaye ya dawo ciki rike da tarin wasu takardun, ya kalli na'urar ganin tayi sai ya dauke kansa daga kai yace mata shikenan, thank you tace masa tayi gaba cike da jin haushin yadda yake abubuwan sa, gashi daga gani yana da son aiki dan ko da yaushe cikin yin sa yake yi kamar wani agogo. ****Karfe sha daya da mintuna hamsin ta gama aikin da ya sakata, ta tattare dukka ta tura masa sannan ta tura copy din a nata email din. Kafarta ta dan mike da tayi mata tsami saboda zama ga bayan ta da ya gaji dan kusan awoyin ta uku chur a zaune tana aikin, bata so ya sake kiran ta kuma shiyasa tayi iya kokarin ta, ta yi masa aikin daidai yadda tasan zai yaba, yau gaba daya bata ga Kamal ba, kamar ma be zo office din ba, dan tabbas da yazo zata ganshi ko taji wucewar sa. A gaggauce ya fito bayan ya karasa tattare dukkan aikin da yasan Daddy zai gani idan ya shigo, karfe daya da rabi jirgin su zai sauka, gashi yace masa lallai ya je ya dauko shi, duk da hakan yana cikin sharudan Daddyn amma sam baya so, musamman tafiya da zata hada shi da Adam waje daya, sannan idan yaje din abinda zai gani ba zai masa dadi ba, amma haka zai hakura dan yasan duk hanyar da zasu bi su hanashi aiwatar da abinda yake niyya zasuyi ne, dan haka ne ma ba zai basu kofar hakan ba. Waya suke da Kamal yana kokarin fita daga cikin building din, a daidai lokacin itama take kokarin fita dan dama sha biyu tayi zata dinga tafiya dan ba zata iya wunin da suke yi ba, an ce sai 4 suke tashi amma gaskiya ita tafiyar ta zatayi. Bata ganshi ba kawai tafiyar ta take yi, shima kuma wayar da yake ta dauke hankalin sa baki daya, yana yi masa bayanin abubuwan da zai karasa idan ya shigo shi daga airport ba zai dawo office din ba sai gobe. Driver daddy ne zai dauke su zuwa airport din, Adam tuni ya fito yana zaune a gaban motar yana latsa wayar sa, daga kansa yayi da niyyar ganin ko Aryan din ya fito sai ya hange ta tana tafiya hanyar gate, da gaske yarinyar tayi masifar yi masa, kuma duk yadda zai yi sai yayi ko ta hanyar amfani da Mom dinsa ne ganin ta bashi dama, ba aure bane shi yanzu a gaban sa ba duk da ya isa ace daga shi har Aryan din sun yi aure, amma tabbas yana jin zai iya auren ta ko dan ma Daddy ya sake yarda dashi tunda an ce cikar kamalar mutum itace aure. Balle murfin motar yayi ya fito, fitowar sa ita ta ankarar da Aryan ya kalli wajen da ya nufa. "Ina zata?" Ya tambayi kansa da kansa. Wani kallo yaga Adam din yana mata duk da baya jin abinda yake cewa, yanayin yadda ta nuna tamkar ta kosa da maganar da yake mata, sai a sannan ne yayi mata kallo sosai, har yaso ketara kallon da shari'ah ta yarje ma mutum, tsaki ya samu kansa da ja, baya son Adam yana shiga duk wata harka da ta dangance shi, sannan bazai taba yarda mutum irin Adam yayi mu'amula da ita ba, duk da ba wai ya santa bane ba, amma dai tunda a karkashin office dinsa take toh dole zai yi protecting dinta daga mutane irin Adam, shaidanun zamani. Motar ya bud'e ya shiga sannan yace wa driver ya karasa wajen da Adam din suke tsaye, suna isa ya bud'e murfin kofar sannan yace "Raihana, come in." Kallon sa tayi, yanayin fuskar sa da take a gimtse babu ko fara'ah daya, yanayin sa yayi mata kama da na wanda yake cikin tsananin bacin rai, ji tayi kamar ta juya ta zura da gudu dan yadda yake kallon ta "Bata shiga motar strangers, ko pretty?" Adam yace yana mata murmushi, hakan ya sake kular da Aryan ya kuma tabbatar da zargin sa akan Adam din "Kuna bata mana lokaci, I said get in malama." Ya yi maganar a dan zafafe Gefen mayafin ta ta damke da hannun ta, idanun ta suka ciciko, ya dauke kansa tamkar be gani ba, a hankali ta saka kafarta cikin motar, ta zauna daga karshen kujerar sosai sannan ta sauke kanta k'asa. Wani murmushi Adam yayi kawai, be ce komai ba, ya bud'e gaban motar ya zauna sannan driver yaja suka bar wajen. Shiru ne ya biyo bayan hakan a cikin motar, baka jin motsin komai tamkar babu kowa a ciki, hannu Adam yasa ya kunna Bluetooth din motar yayi connecting da wayar sa, hakan ya dauke shirun da sukayi ya maye gurbin sa da wakokin kudancin Nigeria. Daidai wani round about Aryan yace su tsaye, driver ya faka sukayi shiru, bayan mintuna biyar Kamal ya karaso a motar sa, yayi parking a bayan su sannan yace yazo, shi da Shahida kanwar sa da hajiyar su ne, daga asibiti suke abinda ya hanashi shigowa yau kenan sun kai Hajiya taga likita, bud'e kofar yayi sannan yace ta fito, ta fito a sanyaye suka nufi motar Kamal din, har kasa ya durkusa ya gaida Hajiyan ta amsa sannan ta saka musu albarka, suka gaisa da Kamal sannan yace ta shiga motar, shiga tayi ta zauna a gefen hajiyar ta gaishe ta. Shi kuma ya juya ya koma motar su, suka bar wajen. LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA* *DAUDAR GORA Billyn abdul* *KI KULANI hafsat xoxo* *A RUBUCE TAKE Huguma* *RUMBUN K'AYA Hafsat rano* *IDON NERA Mamuh ghee* _LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_ _KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_ _TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_ _TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_ _TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_ _TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_ _ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_ ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171 SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 09033181070 IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA 09166221261 *ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA* +22799643131 Books biyar  1250CFA Books hudu  1050CFA Books uku  850CFA Books biyu  650CFA Bookk daya  450CFA KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* RUMBUN QAYA*              Page 6 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 _____________ _*MAAB LUXURY HOME!!* Sabuwar duniyar hamshakan mata da ƴaƴan gata.💞_ _*GIDAN* ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida._ _*SABUWAR DUNIYAR* Amare da uwargidan data amsa sunanta ƴar gaban goshi._ _*MAAB LUXURY HOME* wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar hankalin duk wani mai kallo_. _*SUNYI FICE* Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari, a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya._ _*A GAREMU* ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin dubun da sukafi dubu._ _*MAAB LUXURY HOME* sun takaita mana dukkan wahalar nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu_ _*MAAB LUXURY HOME.* Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini._ _*INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._ *_Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️⛹🏼‍♀️._*. •••••Suna isa airport din daidai lokacin jirgin ya sauka, tun kafin ma Aryan ya samu damar fita Adam ya fice daga motar cikin yanayin bacin ran abinda Aryan din yayi masa, sai dai tunda ya nufi wajen da Daddyn yake ya saki fuskar sa kamar babu abinda ya faru, ya kuma tabbatar da idan Daddyn ya fito dashi zai fara arba kafin Aryan din ya kuma san hakan me zai kara zama a gareshi.   Hango fitowar su yasa shi nufar su da farin cikin sa, tare Daddyn yake cikin tagawar manyan abokan kasuwancin sa. Cike da tsananin girmamawa da kankan da kai ya tare su da gaisuwa har da durkusawa chan kasa, wanda hakan yake kara Samar masa fada a zuciyar Daddy dan shi mutum ne me matukar son girmamawa da sanin ya kamata. Shiyasa a ko da yaushe suke samun matsala da Aryan dan shi duk irin wadannan abubuwan be iya su ba sam. Kamar yanzu ma sai gashiya nufo su yana tafe yana amsa waya sai dai yana cike da wani irin haiba da kwarjini da kowanne lokaci yake samun galaba akan Adam din da duk kudure-kuduren sa. Ganin sun hango shi sun ya saka shi katse wayar da suke da Ya Nabila ya nufe su cikin tafiyar sa. Idanu duk suka zuba masa har Adam din hakan ya sakashi jin ya takura sosai, ya dan rissina kad'an ya gaishe su suka amsa babu yabo babu fallasa, hakan ya dan bata ran daddy ganin irin tarbar da sukayi wa Adam ba irin ta Aryan din ya samu ba, hakan kuma baya rasa nasaba da shi yadda Adam din yazo musu fuskar sa a sake cikin iya mu'amula da mutane.   A wajen shiga mota Daddy suka rabu da sauran, Adam ya karbi key din driver da ya kawo su ya shiga wajen tukawa yana jaddada shine zai kai Daddy gida, dariya sukayi shi da Daddyn dan shi komai Adam din yayi yana burge shi sosai yasan duk abinda zai ya faraanta ran Daddyn, a dole ba dan Aryan yaso ba, ya shiga gaba gefen sa ya zauna shi kuma Daddy ya hakimce a baya yana cigaba da nazarin halayen Aryan din duk da ba wai yau ne karo na farko da ya fara fuskantar hakan daga gare shi ba, amma kuma a yau sai yaga ya sauya masa sosai ya nuna matukar yanayin damuwa a tattare dashi, yasan damuwar sa bata raba dayan biyu akan abinda ya kwallafa rai ne yake ganin idan be cimma ba tamkar bashi da wani amfani a duniyar ma baki daya, dalilin sa kenan na sake komawa karatu a karo na uku yayi karatun da yake da yakinin samun cikar burin sa ta wannan hanyar, sai dai katse shi da Daddyn yayi ya kuma gindaya masa sharuda masu yawan gaske ciki har da dawowa yayi aiki a karkashin company sa wanda hakan yayi matukar takure shi, sai dai a duk wani abu da Daddyn zai saka shi ko ya gindaya masa baya taba iya ketare shi, shi din me matukar biyayya ne a gareshi ko da kuwa babu wata alama da take nuna soyayyar sa ga mahaifin nasa dan har kwanan gobe yana cikin mutanen da yake zargi wajen salwantar da rayuwar mahaifiyar sa, me tsananin so da kaunar sa.      Shiyasa komai ya tsaya masa chak dan yana rayuwa ne kawai a karkashin ikon sa ba wai dan yana so ba, sai dan cika umarnin Allah da Yace lallai ya zama wajibi 'yaya su yiwa iyayen su biyayya akan duk abinda be sabawa Allah ba.    Hirar dake wakana tsakanin Daddyn da Adam din yake sauraro cike da kulawa Daddyn yake saurare shi yana kuma amsa masa daidai kamar yana hira da abokan sa makusanta. Aryan ya kan yi mamaki idan yaga yadda Daddyn ya sake da Adam ya bashi dukkan yarda fiye da kowa a duniyar nan, yayi matukar yarda dashi har ta kai baya ganin iyawar kowa sai ta Adam din. Duk da dai shi Aryan zai iya rantsewa da wayon sa ba zai iya tuna wata hira doguwa da ta hada shi da Daddyn ba, dan baya jin akwai wani abu da zasu iya tattaunawa akai idan har ba maganar mahaifiyar sa bace ba, tun da kuma yaki zancen yace masa baya so, tun daga sannan ya bar shi, be kuma sake tada masa maganar ba ko da wasa, shiyasa duk abinda yazo masa dashi toh kawai yake cewa ya aiwatar ba tare da wani dogon nazari ba, shiyasa magana a tsananin su bata tsawo kwata-kwata. "Muhammad." Dan waigo da kansa yayi bayan motar hade da amsawa a lokaci guda "Na'am?" "Akwai wata matsala ne?" _"matsala?"_ ya tambayi kan sa, dan ya manta rabon da yaji irin wannan tambayar daga bakin Daddyn, ai shi a kullum a cikin matsala yake sai dai babu wanda ya damu ya fuskance shi ciki kuwa hadda Ya Nabila da yake ganin kamar tafi yarda da uzurin da Daddyn ya bayar shi yasa a kullum take dakushe shi a duk yunkurin da zai yi. Duk a zuci yake wannan tunanin a cikin yan dakikun da basu gaza sha biyar ba, a fili sai ya hau girgiza kansa kafin ya ce "Babu wata matsala." "Ka gane kuwa abinda nake nufi? Maganar company nake yi, ina fatan daga bangaren ka babu wata matsala dan shi Adam yana bani details da duk abinda ya faru a rana which I'm very impressed." _ohh."_ Ya raya a ransa, ashe ba tasa matsalar yake nufi ba, ta aikin da ya saka shi ce._   Dan murmushi yayi kad'an me ciwo wanda ya tsaya iyakar leben sa sannan yace; "Alhamdulillah,babu wata matsala." "Good, sai ku cigaba da kulawa da komai,dan zan kwana biyu gaskiya ban shigo company ba, domin Dr. Mubarak yace ina bukatar hutu dan haka zan huta sosai." "Allah ya kara sauki Daddy, babu wata matsala ni da Aryan zamu tsaya tsayin daka wajen ganin komai ya tafi yadda ya kamata." "Bana jin ka Adam, nasan zaka iya." "Shima zai iya Daddy, duk da dai sabo ne a system din amma naga kwazon sa,gaba daya da baka nan din nan yayi dedicating dukkan energy dinsa wajen aiki." "Ok." Daddy yace a gajarce ya daga wayar sa da take kara. Kallon Aryan din Adam yayi a fakaice yayi dariya kad'an, ko dagowa Aryan be ba bare ya kalli bangaren da Adam din yake tunda ya fara maganar har ya dire ta. Shi da ya riga yasan duk wani motives din Adam din babu wani abu da zai yi ko ya yabe shi har yayi masa dadi tunda ya riga yasan karya yake yi, ba kuma wai har zuciyar sa yake ba, tsabar makirci ne. Yana jin Daddyn na jinjina masa bayan ya gama wayar amma yayi kum yaki cewa komai, shi dai burin sa kawai a isa gida ya samu ya zame dan ko cikin gidan baya son shiga musamman da yasan dukkan su zasu hadu waje daya dole Hajiya Zeenat zatayi wani abun da Daddyn zai iya ganin bakin sa, shiyasa baya taba yarda zama inuwa daya ta hadasu tun bayan da yayi wayo ya kara sanin ciwon kansa, ya gano irin bakin fentin da take goga masa a duk sanda ta ganshi tare da Daddyn. Daga baya ya tsaya Adam ya dauki suitcase din Daddy yayi gaba, juyowa daddy yayi ganin yana tsaye yace "Muje ciki." Babu yadda ya iya, haka yabi shi a baya har suka dangana da cikin gidan. Hajiya Zeenat na tsaye a falon cikin matukar ado ta sha kwalliya irin wadda take ciki a kowanne lokaci musamman idan Daddyn yana gari, da sauri ta karaso ta tare shi, ta jingina kad'an da jikin sa jikin farin ciki da murnar ganin sa. "Sannu da hanya Your excellency." "Sannun mu Hajiya, kuna lafiya?" Yace yana zama, tayi saurin zama a kubin sa ta lankwashe murya cikin kissa da kisisina ta shiga gaishe shi, hannun ta, ta kai saman kansa ta zare masa hular kansa. "Wanka ko abinci Alhaji?" Waigowa yayi yaga Aryan din a tsaye amma ya basu baya "Muhammad." "Na'am." Ya juyo suka hada ido da Hajiya Zeenat yayi saurin dauke kansa daga gallon ta, ya bawa daddy dukka attention dinsa "Kaje kawai zan neme ka da daddare." Da sauri yayi gaba dan dama jira yake yayi saurin hanyar fita, murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, ta cigaba da shafa kan Daddyn zuwa gemun sa tana lankwasa jikinta cikin salon ta da tasan yana tafiya da Daddyn sosai. Shi kadai yake ta jan tsaki har ya fice daga gidan a kafa dan be dauko mota ba, kuma baya bukatar daukar motar kowa a gidan duk da ga motocin nan amma shi a komai yafi son nasa, gidan sa ya nufa wanda ya kasance mallakin mahaifiyar sa, shine asalin gidan su da suka fara zama anan ne kuma duk wani tarihin rayuwar sa yake, anan yake samun nutsuwa sannan anan ne hankalin sa ya kan tashi idan har memory din abinda ya faru a baya zai dawo masa. Babu kowa a gidan dan ko haya be yarda ya saka ba, sai Baba Me gadi da iyalinsa da suke zaune a bq suna kuma kula da gidan har yanzu sosai. Baya kwana biyu be ziyarci gidan ba, anan yake duk wani shiri da tanadin sa anan kuma yake ajiye duk wani abu me muhimmanci a wajen sa. Knocking yayi a gate din sanda me napep ya sauke shi, Baba me gadi ya leko ganin shine yayi saurin bud'e masa kofar ya shigo. "Sannu da zuwa." "Sannu da aiki Baba." "Yawwa, ban tsammaci zuwan ka a wannan lokacin ba, Allah yasa ba wani abu ne ya faru ba naganka a kafa." "A ah ba komai, motar na office zan dan huta ne anjima sai na fita, Malam Rabi'u zai kawo motar anjima kad'an idan yazo ya ajiye ta kawai inaga zan dan samu bacci." "Ok a fito lafiya." Yace masa, gaba yayi shi kuma ya koma bakin aikin sa cike da tausayin Aryan din. A falon ya yada zango ya kwanta rigingine yana kallon saman pop din falon, shi kadai yasan abinda yake ji a zuciya da gangar jikin sa, da abinda yake masa yawo a cikin kwakwalwar sa, baya iya controlling fushin sa wanda yana cikin abubuwan da ke matukar takura shi, abu kad'an sai ya hau yayi ta kunci wanda yake sake kashe masa kwarin guiwar sa, sai dai a duk fushin da zai yi baya taba nadamar fushi akan cin amanar sa, baya kaunar cin amana haka kuma baya yafewa duk wanda yaci amanarsa, shiyasa har gobe ya kasa hakura da abinda sukayi masa, yake kuma kaffa kaffa da duk wanda yasan zai iya cutar dashi. _Me Adam yake nema a wajen yarinyar nan?_ Abinda ya faru dazun ya fado masa, yayi tsai yana tunani ko zai iya gano wani abu,duk da yasan maitar Adam din akan mata amma kuma wannan karon yaga abu mabanbanci a tattare da kallon da Adam din yake mata. Toh amma menene nasa? Me yasa zai shiga tsakani? _Saboda a karkashin office dinka take, shiyasa kayi hakan._ Zuciyar sa ta tuna masa dalilin sa _Toh amma kuma idan itama ta amince da Adam din fa?_ Wata zuciyar daban ta sake tunasar dashi, tsaki yaja ya mike yana wurgi da pillow da yake kan kujerar yayi hanyar bedroom, ba zai taba yarda har wata shakuwa ta shiga tsakanin ta da Adam ba, idan kuma haka ne sai dai ta koma aiki a karkashin office din Adam din dan shi ba zai iya zama da duk wanda yake zaune inuwa daya da Adam din ba. Wannan dalilin shi ya bar wa kansa, da hakan ya samu bacci ya dauke shi, wanda be farka ba sai kusan karfe uku, a kasalance ya watsa ruwa hade da alwala yazo yayi sallah sannan ya dora kansa a gefen gadon cikin yanayin rashin karfin jiki. Ya dau kusan minti talatin a haka yana jin wayar sa tana neman agaji sai da ya ji tana neman takura shi sannan ya mike ya dauke ta a gefen bedside, ya duba call log din yaga kiran Ya Nabila ne sai Kamal wanda dama yasan a cikin su ne duk kiran da ake masan, be bi kiran ba sai da ya fara zuwa kitchen ya samar wa kansa shayi ya hado a cup ya dawo dakin ya zauna sannan ya bi kiran nasu. Tare sukayi sallar la'asar da Baba maigadi sannan ya dawo ciki ya bud'e safe dinsa, in da yake ajiye duk wani muhimmin abun sa ya jawo takardun da ya saka a karshe ya sake duba su, suna dauke da sa hannun mutane hudu ne Wanda yake dauke da yarjejeniya da aka kulla ta cikin aminci da yarda da juna, wajen da Ammin sa ta saka hannu ya kurawa ido, a hankali kwalla ta biyo gefen idon sa, yayi saurin saka hannu ya share, sannan ya cigaba da nakaltar saka hannun da yake kusa da na Daddy. *_Nasir Matawalle._* Ya furta a chan kasan makoshin, yana nan yana jiran fitowar sa, duk da rashin bashi dama da yayi akan duk abubuwan da yaje masa da su amma ba zai taba gajiya ko karaya ba, zai jira shi har zuwa lokacin da zai gaji da nacin sa, ya bashi abinda ya dade yana jira. Sannan ya kai shi yaga mutane mafi soyuwa a gareshi idan ka cire Ammin sa da Ya Nabila. Ajiye komai yayi ya rufe ya maida key din inda yake, sannan ya sauya shigar sa zuwa kananan kaya, ya bar gidan zuwa wajen Kamal da yake jiran sa a shoprite tun dazu. *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank. Shaidar biya tanan👇🏻 09033181070 *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 RUMBUN QAYA*              Page 7 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 ____________ Tunda ta koma gida take tunanin abinda ya faru tsakanin Adam din da Oga Aryan, bata san dalilin sa na yi mata hakan ba, sai taga rashin dacewar abinda ya aikatawa Adam din, ita a ko da yaushe a mai zafin gaske take kallon sa, dan yanayin sa baki daya ya gama nuna hakan, bata son mutum da ya cika zafi sosai a koman sa, dan ita bata ga abinda akayi da har zai yi irin wannan acting din ba. Muskutawa tayi daga kwanciyar da tayi,kamshin turaren sa na cigaba da shigar mata hanci sosai, bata san yadda akayi kamshin ya manne mata haka ba, tashi tayi ta cire kayan ta watsa su laundry basket ta zura boubou, ta koma ta sake lafewa a gadon. Gida take son komawa, tana so ta ji ta jikin Dadan ta dan ita din me masifar son jiki ce, ko zama kayi kusa da ita sai ta ra'bi jikin ka tamkar mage. Har la'asar likis tana ta juye-juye kasancewar bata sallah, ga Amina bata gidan bata dawo daga school ba balle ta rage mata zaman kadaitar. Bayan la'asar ta mike da k'yar, ta shiga toilet ta chanja pad ta gyara kanta sannan ta fito, tazo ta dau wayarta a saman mirror ta zauna kiran Babbo Sadeeq, shi kadai ne basu fiya waya sosai ba saboda duk ciki ya fisu commitment saboda yanayin aikin sa da baya bashi cikakken time, dama Hamma Hydar ne best friend dinta sannan Lamido. Tana fara ringing yayi rejecting tasan dama ba zai daga ba, haka suke mata basa taba daga wayarta sai dai su kirata, kiran ne ya shigo ta d'aga da yar murnar ta "Babbo nah." "Na'am, kanwata kina lafiya?" "Lafiya Lou, sai missing dinku da nake Babbo." "Shiyasa naji muryar ki haka?" "A ah bana dan jin dadi ne." "Me yake damun ki? Kinje asibiti? Kin sha magani?" Duk a jere yayi mata tambayar cike da kilawa "A ah, stress ne kawai kaina ne yake dan ciwo kad'an amma nasha magani ma." "Ciwon kan nan wai ba zai hakura bane ba ya kyale ki? Ko dai zuwa zamuyi ayi scan din?" "A ah da sauki, kwana biyu baya damuna sosai ma, ina shan magunguna na dukka, kawai ni gida nake son dawowa." Murmushi yayi me sauti, kafin yace "Ke fa kika dinga murna zaki tafi ki barmu, yanzu kuma?" "Allah na gaji, boss din wajen aikin namu bashi da kirki ko kad'an, yayi ta shan kunu." "Duk rashin kirkin sa dai kar ya yarda ya batawa kanwata, dan wallahi ranar Kano ba zata dauke mu ba, ki fada musu yayyanki maza ne kuma ke yar gwal ce baa taba ki, ba'a bata miki rai." "Kaiii Babbo." "I'm serious fa, gwara su sani, ba bautar k'asa ba ko bautar duniya ce ba zamu bari wani kato chan ya bata mana ran Princess ba." "Su ma ba zasu fara ba ai." "Yawwa better, yanzu dai nasan maganin boredom din nan da yake damun ki, zan sa miki wani abu kije ki dan yi shopping abinda kike bukata kinji?" "Yaayy, you are the best Babbo, nagode Allah ya kara budi, ya kawo mata ta kari." "Amin Amin, very soon in sha Allah, bari na koma aiki, sai anjima ki kula da kanki." "In sha Allah, bye." Da karfin ta, ta mike dan tuni karsashin ta ya dawo, duk halin da take ciki in dai tayi magana da daya daga cikin su toh in sha Allah sai sun san yadda zasuyi su faran ta mata, bata san yawan son da suke mata ba, dan tunda tayi wayo ta gane zasu iya komai da taba kowa akanta, ko dan ita kadai ce mace? Kuma karamar su? Kuma yanayin rayuwar da suke shiga? Ta fada mahaifiyar ta da karacin shekaru amma basu taba barin ta, tayi kukan rashi ba. Dadah kakarta ce wadda ta haifi mahaifiyar ta, amma ita take mata role din uwa da kuma role din kaka a lokaci daya,tana matukar kaunar su da dukkan rayuwar ta, domin sune Raihana, sune gatan ta, sune koman ta, zata bar duk wani abun da basa so bari na har abada, zata kuma so abinda suke so ko d hakan na nufin ajalinta. Dawowar Amina ya kara sata warewa ta manta da komai, suka shiga hirar su irin ta daidai da shekarun su, har zuwa sanda kowa ya aje hakarkarin sa domin samun hutu daga kwarafniyar da aka sha na ranar. Fresh ta tashi ta shirya a tsanake bayan sun gama ayyukan gidan, ba ta zuwa aiki yau dan haka ma tana yin breakfast ta koma gado ta kwanta Amina kuma ta tafi school, sai kusan sha biyu ta tashi shima kiran wayarta akayi ya sakata tashin ba wai dan taso ba. Miss called din Hajiya ZEENAT ta gani sai wata bakuwar special number da bata san ta waye ba, rabon da sukayi magana da Hajiya Zeenat din tun ranar da taje gidan karbar posting letter. Mikewa tayi da nufin zuwa toilet ta wanko fuskarta ta bi kiran sai ga kiran ya sake shigowa da wannan special number din, dagowa tayi dan duk a tunanin ta Hajiya Zeenatun ce, sai taji muryar wanda bata yi zato ko tsammani ba. "Ina kika ajiye paper din da na baki jiya?" Kawai abinda ya fara fada kenan ba gaisuwa ko sallama, yanayin yadda yayi maganar kamar wanda akayi wa dole yayi kiran, kafin ma ta bashi amsa ya sake watso mata tambayar cikin muryar sa da ta shiga ciki sosai ta shake. "Nasa ta akan table sir, good afternoon." "Ban ganta ba, dole ki dinga summiting komai idan kin san zaki yi fashi." Ya fada a hasale "Ba fashi nayi ba sir, yau Thursday dama Sir Kamal yace Monday - Wednesday zan dinga zuwa." "I'm waiting for you, kizo ki bani ita." Ya kashe wayar, tsaye tayi da waya a hannu kamar wadda aka dasa, sha biyu har da yan mintuna be tashi cewa tazo ba sai yanzu? Wanne irin abu me wannan? Ranta ya sosu sosai, tayi kamar kar taje dan tafi minti goma a tsaye tana tunanin kin zuwa din kuma ta kashe wayar tunda abin nasa kamar hadda rainin wayo, da tasan ma irin sa zata samu a wajen da ta gwammace ta karbi teaching dinta ko a kauyan ne yafi mata sau dubu. Tana shiryawa tana tsaki haka ta shirya ta fito ta samu Addah Maimuna a falo ta fada mata yadda sukayi, ta tayata jajantawa sosai dan yau ba karamar rana ake a gari ba, kuma sha biyu ranar ta kwalle sosai ace ka fito haka kawai ba tare da ka shiryi hakan ba. Ta dan sha wahalar samun napep dan suma idan azahar tayi sai kaga duk sun rage zirga-zirga, da k'yar ta samu wani shima a hanya ya sauke ta, ta taka a kafa har zuwa office din. A galabaice ta shiga ga yunwar da take ji a ranar da ta dake ta. Kai tsaye office din su ta fara zuwa ta dudduba ko ina bata ga takardar ba, ta tambayi Abdulhakeem shima ya tayata dubawa babu. Sai ta fito ta nufi office dinsa dan tasan dama ta kai masa dan tayi mamakin ma rashin ganin da yace be yi ba. Knocking tayi a kofar ta dan tsaya jim shiru, ta sake kwankwasawa sai ga Zainab ta taso, dama tana kallon ta tun shigowar ta "Oga ya fita fa." "Ya fita? Yanzu fa ya kirani yace nazo." "Toh ya fita dai, sai ki jirashi." Ta juya ta koma wajen zaman ta, ranta idan yayi dubu ya gama baci, bata san wulakanci a rayuwar ta wallahi, shi kuma taga alamun haka yake, kamar ma abinda yafi enjoying kenan a rayuwar sa, lallai dole Hajiya Zeenat ta shiga damuwa, dan zama da mutum da irin halin sa sai me tsananin hakuri. Office din su ta koma tana ta kunci, ta zauna bata sake kula kowa ba, ta ciro wayarta tana dannawa sai ga Oga Kamal ya shigo. Da mamaki yake kallon ta dan yasan yau ba ranar zuwan ta bace ba, zai yi magana ta riga shi "Oga ne ya kira ni yace nazo wai be ga takardar da ya bani jiya ba." "Aryan din?" Yace cike da tsananin mamaki "Eh." Ta gid'a kanta "Abun da mamaki, takardar fa tana wajena na bashi dazu, sai dai ko kafin na bashi ya kira kin kenan, maimakon kuma ya sake kira yace ki zauna ya ganta." "Hmm." Tace kawai "Shikenan tunda kinzo ma, zo na nuna miki wani waje" Tashi tayi tabi bayan shi, zuwa wata kofa da take kallon office dinsu, bud'e kofar yayi da key suka shiga ciki, ga mamakin ta sai taga kitchen din madaidaici, dauke da coffee machine, microwave da sauran kayan kitchen dangin su cups da spoon, yar madaidaiciyar kettle me dauke da kananan cups irin ta su Hamman ta ce ta ja hankalin ta, ta matsa wajen ta dauka tana kallo "Waye yake shan irin shayin nan." "Mune nan, ni da Aryan, dalilin ma dai samar da kitchen din kenan, dan gwara ni ma, Aryan baya wasa da shayin nan, ya zamar masa addiction wallahi." "Kamar su Hamma na,suma kullum cikin sha suke, tun ban iya ba har na koya dafa musu, nima kuma na koyi sha." "Kin iya dagawa?" Yace cike da murna dan dama suna tunanin yadda za'a yi "Na iya sosai, har majlisa suke kaiwa ayi tasha wallahi." "Shikenan wallahi, dama muna neman me dafa mana yadda aikin zai dinga tafiya sosai, ta kwana gidan sauki." "Amma sai dai na dafa maka kai kadai, banda shi." Ta bata fuska kad'an ita a lallai haushin Aryan take ji, dama kuma ita bata iya rufa rufa ba, idan ka bata mata sai ta nuna amma bata da riko ko tsananin fushi "Tuba muke, ai yanzu dole muyi miki biyayya, shima ba zai kara ba." "Allah ko abinci banci ba, daga bacci na tashi kawai naga kira wai nazo, dama ya fada min da ya ganta, amma haka na dauko kafa ga rana wallahi kamar zan narke." "It's not hygienic ko zauna a kitchen kuna gulmata." Kofar dama a bud'e take shiyasa ma basu ji shigowar sa ba sam, kusan subucewa kofin yayi daga hannun ta dan bata zata zai shigo a time din ba, kuma bata ma san dalilin da yasa ta ke fadawa Kamal din ba, ko dan taga kamar ya sake da ita kuma yana kokarin jan ta jiki? Ji tayi kamar Hamma Haydar take fadawa wallahi shaf ta manta ma da waye shi da alakar sa da wanda take masa maganar tasa. "Ba gulma bace ba, gaskiya ce ai Aryan, da sai ka kira kace ta zauna kawai." "Menene yayi saura da ba'a saka ba?" Ya share maganar ya sako tambayar, "Komai an saka, har kuma an samu wadda zata kula da bangaren." "Wace? Kasan dai i don't trust anyone." "Raihana ce." "Who?" Yace kamar be gane wacce yake nufi ba "Gata nan a gaban ka." "No, a samu wata dai.." "Why?" "We will talk about that later." "Raihana please ki jirani a office ina zuwa." Kamal yace cikin rashin jin dadin abinda Aryan din yake wa yarinyar, ya rasa dalilin sa kuma ai ba haka yake wa su Zainab ba, ba kuma itace corper ta farko da aka fara kawo musu ba. Ajiye cup din tayi ta raba ta gefen su ta fice ranta babu dadi. Tana fita Kamal ya tura kofar ya dawo wajen sa "Why are you like this dan Allah? Why are you soo mean to her? Me tayi maka?" "Babu abinda tayi, aiki tazo ba gulma ba naga, me yasa zata zauna taana fada maka laifi na." "Tsakani da Allah baka kyauta ba, ka kira ta kace tazo, bayan kasan ka samu paper din." "Bayan na kiratan ba." "Then you should have call her again kace ka ganta." "I forgot." "Anya? Anya kuwa?" "Me?" "Ban gane maka ba kwata-kwata." "Ba zaka taba ganewa ba kuma ba." Ya bud'e kofar yayi ficewar sa. ***Ko da ta fito daga kitchen din bata tsaya ko ina ba, tayi ficewar ta dan ba zata iya zama ba, yayi masifar bata mata rai yau din nan, me ya dauki kansa? Me yake ji dashi? Ta manta shaf da kiran da Hajiya Zeenat tayi mata kuma duk shi ya rikitata,sai da taji wayar ta na kara ta tuna tana ciro ta taga Hajiya Zeenat din ce. "Dan Allah Anty kiyi hakuri wallahi mantawa nayi ban kira ba." "Ba komai 'yata, nasan ba zaki da gangan ba, ya aiki?" "Lafiya Lou, ina wuni?" "Lafiya alhamdulillah, dama kira nayi naji babu wata matsala ko? Ina nufin bangaren Aryan kinsan halin nasa sai hakuri." Kamar me jiran kiris, kawai sai ta ji hawaye na sakko mata, ta share su cikin muryar kuka tace "He's very rude Allah Anty, ya tsaneni bansan me nayi masa ba." "Subhanallah, me ya faru?" "Bansan me nayi masa ba, komai nayi ban iya ba, a gabana sai yayi ta fadamin magana, ni wallahi na gaji." "Nasan zai aikata fiye da haka, amma dan girman Allah kiyi hakuri, kiyi hakuri a madadin sa, kiyi hakuri." Jikin ta ne yayi sanyi jin yadda Hajiyan take bata hakuri, har sai da taji nauyi da kunya, taji dama bata fada mata ba. "Ya wuce in sha Allah, ba zan sake damuwa ba ma duk abinda zai yi mun saboda ke Anty." "Nagode sosai Raihana, nagode." "Ba komai." "Akwai wata alfarma da nake nema a wajenki Raihana, wani taimako nake so kiyi min dan hakan ne kadai zai taimaka Aryan ya rage wannan halin nasa, taimakon sa zanyi amma baya so kowa ya taimaka masa, yana da yar matsala ne wadda ba kowa ne ya sani ba, kuma baya shan magani ko kad'an, duk da bani da hujjar hakan saboda ya toshe duk wata hanya da zamu gane amma ni nasan baya sha din, akwai in da yake boye su, tun wuri gwara a shawo kan matsalar kafin abun yazo yafi karfin mu, tunda bani da wata shaida shiyasa na kasa yin komai akai, dan ko nayi yunkurin fadawa Alhaji sai na kasa saboda zai bukaci shaida, shiyasa nake so ki taimaka min mu ceto shi daga fadawa cikin wahala. Dan Allah Raihana " "Bana jin akwai abinda zaki nema a wajena na kasa yi miki in sha Allah, zanyi komai dan ganin kinyi farin ciki." "Nagode sosai Raihana, nagode zan neme ki idan an kwana biyu, zaki ji abinda ya kamata kiyi ta nan bangaren ki." "Shikenan, Allah ya rufa asiri, nagode." "Amin nice da godiya." Dariya suka kwashe da bayan ta ajiye wayar, "Wawuyar yarinyar halin ta sak na mahaifiyar ta, dama ai barewa bata gudu danta yayi rarrafe." "Yaro be san wuta ba sai ya taka ai Hajjaju, ke din duniya ce in dai ta wannan fannin ne." Dariya suka kara yi a tare. "Da alamu tarihi ne zai maimaita kansa." *RUMBUN K'AYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +22799643131 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 RUMBUN QAYA*              Page 8 ©️®️ *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F9Fgin7INwl2MLGe0vpoEh 🌹 KUDI KE KIRA 🌹Don Neman Karin Bayani a Tuntubi Wannan number.. 🔥 09112842587 🌹Ko kun San akwai Wasu 6oyayyun damar Maki Wanda tun waccan shekarar data gabata mutane suke cin moriyar su..??? 🌹 An shirya wannan program din don canza Tsarin kasuwancin matasa da Mata Zuwa kusuwancin zamani 🌹 Inda za'a koyar da Mata sanaoi iri daban-daban 🌹Kamar yadda Sunan Shirin yake wato KUDI KE KIRA... tabbas za'a koya muku yaya ake Kiran kudi su zo kuma su zauna har su dinga Kiran 'yan uwan su...Ta hanyar koyar daku hanyoyin Neman su da kuma yadda za'a dinga kashe su 🌹 Business sai da Traffic is a game of Numbers Dole Sai da jama'a...shin ta yaya ake Nemo jama'ar? Right Target audience sune jama'ar ku 🌹 Kullum kuna sana'a Babu customers..?? To Albishirin ku za'a koyar daku building contacts yadda zaku Kawo mutane what's app din ku...Hatta yadda Zaku hada file na contacts Gain Yana cikin Abinda za'a koyar a wannan Training din.. 🌹 Cikin abubuwan da za'a koyar na sanaoi kadan daga ciki sune...Skin Care products, graphics, digital marketing, Gyaran jiki na sudan da chad, turaren wuta,na daki,na tsugunno,na tsinke,humra,body lotion, cream,izal,airfreshner, oils perfumes, wardrobe Balls, Sabulun wanka, Sabulun wanki,hypo,etc 🌹 Program din zai kasance cikin yare guda biyu wato Hausa da Turanci za'a kammala Shirin cikin Kwanaki goma in Sha Allah Stay Turn 🌹Bayan kammala Training din 🌹Zaki Sami certificate na shaidar kammala kyauta 🌹Ba Sai kina da Data ba...kina yin Register kungiya Zata baki Data kyauta har ki kammala Training din 🌹Zasu yi Miki website design kyauta 🌹Zasu koyar dake Kasuwanci Kyauta irin Wanda kika zaba 🌹Zasu yi Miki Logo na company ki kyauta 🌹 Goggle my business account kyauta 🌹Tallata muku kayan ku a yanar gizo kyauta 🌹Zaku Sami Product guda daya Kyauta da kungiyoyin suka tanadar Muku don Gyaran jiki da magance matsalolin Infection da saukar da niima ( Maganin Herbal ne 100%Natural ) 🌹 Yiwa Business din ku CAC Register kyauta 🌹 Yadda zaku Sami Rancen Kudi,ko nawa mutum ke bukata ku juya kuyi business ku maidawa kungiya kudin ta ( da yawa suna da ideas na business amma Babu Jari..don haka wannan babbar dama ce ayi amfani da ita don dogaro da Kai) 🌹 Kadan Kenan daga cikin Abinda program din ya kunsa mu kasance cikin group don samun Sauran bayanan Masu yawan gaske 💲ayi Sharing Link din don sauran Mata su amfana da wannan Shirin _________•••••••••••••••• ***A gajiye likis ta koma gida, ga uwar yunwa ga ranta da yake a chunkushe, ko abincin kirki kasa ci tayi duk da yunwar da take ji ta zauna shiru tana bitar abinda ya faru dazun. Wajen la'asar ta tashi ta je dakin Adda Maimuna ta tambaye ta abinda za'a dafa da daddare duk da ba ko yaushe ne take shiga kitchen din ba amma in dai tana nan, tana taimakawa sosai ayi duk aikin da za'a yi da ita, ba zata zauna ta lafe komai sai dai ayi mata ba, irin wannan zaman gundurar masu gidan kake yi shiyasa take shiga ayi duk abinda za'a yi da ita, ta lura kuma hakan na faranta ran Addan shiyasa ma take sake dagewa wajen ganin ta zauna lafiya dasu a dan zaman da zatayi. Tuwo tayi miyar kubewa daf da magriba ta gama ta gyara kitchen din tas, sannan ta dora indomie dan bata jin cin tuwon kawai gashi kuma tana jin yunwa tunda da rana bata wani ci abincin ba. Tana cikin cin indomie din Oga Kamal ya kirata, ta daga da yakinin dalilin da ya saka shi kiran nata. Hakuri ya bata akan abinda ya faru dazun ya kuma yi kokarin nuna mata sam hakan ba halin Aryan din bane ba, shi kansa be san dalilin da ya saka yayi acting haka toward her ba,amma sam tsakanin sa da ma'aikatan ba haka bane ba. Ta dai ji shi ne ba wai dan ta yarda ba, dan ita bata ga duk abinda ya fada din ba,tunda dai ita be mata ba. Tattare wajen tayi ta kai plate din kitchen ta dauraye shi sannan ta dawo falon ta samu su Muhammad suna kallon ball ta zauna kawai dan idan ta koma dakin ma babu abinda zatayi, ga Amina yau ba ta dawo ba ta tsaye gidan Anty Saliha babbar yayarsu watakila ma ta kwana a chan. ***Rashin neman sa da Daddy be yi ba jiyan sai ya zata ya manta ya cigaba da sabgogin gaban sa, yana raba kafa yaje nasa office din yaje na gida, baya shigowa gidan sai dare sosai kuma dan baya son abin magana, haka kuma da safe da wuri yake ficewa ya wuce gidan sa ya karasa shiryawa a chan daga nan ya tafi aiki, haka yakeyi a kwana biyun sai dai yau yana shigowa sai ga Daddy a falon k'asa shi da Adam da tarin takardu a gabansu daga gani wani muhimmin aikin sukayi tunda har suka kai wannan lokacin, ji yayi kamar ya juya amma babu hali dan sun riga sun ganshi. Karasowa yayi ciki ya durkusa ya gaida Daddyn wanda ya amsa masa idanun sa na kan wata takarda sannan yace ya zauna. Kallon juna sukayi shi da Adam kafin ya zauna yana zubawa takardun ido yana son fuskantar dalilin zaman nasu. "Kai da nace ka sameni da daddare shikenan sai kayi batan dabo? Yau kwana uku." Shafa saman sumar kansa yayi, ya dan yi yak'e kad'an "Ya tabbata a gidan dai kake kwana, ni ne dai baka son haduwa da, sai ka shigo late ka fice da safe ko?" "Ba haka bane ba." "Toh Ya ya ne? Har yanzu maganar nan ce Muhd? Ba zaka hakura ba ko?" Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, dan be zaci Daddy zai dauko wannan maganar ba a irin wannan lokacin, be taba kawo hakan ba da ya gwammace ya fasa shigowar da ya gansu, ko yayi wata karyar da zai samu ya zille. "Ya kamata ka sani, ban amince kayi wani abu akai ba, na fada maka ba tun yau ba, ka bar wannan maganar kawai amma na lura kamar baka ji, abinda ya riga ya wuce ya wuce, tsaurara bincike ba zai taba haifar d'a me ido ba." "Dan haka bana so, ka bar maganar nan na fada maka, ka barta tunda ba akan ka aka fara mutuwa ba, ba kuma zai zama na karshe ba, kana gani nayi iyakar kokari na akan case din, kuma an tabbatar da kanta ta kashe kanta, binciken Yan sanda, likitoci da duk kwararru akan fannin ya tabbatar da haka, akan kishi? Toh me kake so nayi kuma akai? Ko ban iya ba kaine ka iya?" Kansa a k'asa zuciyar sa na wani irin harbawa, lokaci daya yanayin sa ya sauya, ya dinga jin wani irin tashin hankali na bijiro masa, maganganun da ya tsani ji a rayuwar sa, ace wai ta kashe kanta da kanta, wanne marar tunani ne zai yarda da hakan? Ta ya ya kishi zai saka ta kashe kanta? memory din abinda ya faru ne ya shiga dawo masa filla filla. Muryar ta radau tana neman taimako, cikin tsananin wahala da galabaita. Sunan sa da take kwalawa ya shiga yi masa amsa kuwwa, tamkar a lokacin take kiran sa, tamkar a lokacin komai yake faruwa, idanun sa ya runtse, ya hango ta kwance a cikin jini, cikin tsananin jinin da be taba ganin irin sa ba, Ammin sa a kwance, an mata yanka irin wanda ake wa rago! Jikin sa ne ya hau rawa sosai, gumi ya shiga keto masa, Adam ne ya fara lura da halin da yake ciki, yayi saurin ankarar da Daddy dan tun sanda ya fara masa magaar be ko kalle shi ba, zabura yayi cikin tsananin tashin ya watsar da takardun hannun sa, sukayi kan Aryan din suna kwalla kiran sunan sa. "Kira Dr, kira likitan sa Adam, innalillahi." Wayar sa ya ciro da sauri ya shiga dialing number likitan da yake duba shi, ringing daya ya dauka dan har yana shirin kwanciya ma dan be dade da shiga gida ba. Suna tsaye akan sa suna kokarin bashi taimakon gwaggawa Dr ya karaso, ya taimaka musu aka karasa saka masa nebuliser dan dama gashi asthmatic toh da irin hakan ta faru sai numfashin ya soma yin sama. Kusan minti talatin zuwa awa daya sannan ya fara samun daidaituwar numfashin sa dama kan sa. Rufe idon sa yayi ruf, yana jin maganganun su akan sa da yake masa wani irin ciwo. Har kusan ukun na dare suna tare a dakin sa harda Hajiya Zeenat, dan nan aka maidashi, yana jin yanayin damuwar da Daddyn yake ciki fiye da duk wata damuwa da ya taba shiga akan ciwon nasa, me yasa yanzu ya nuna damuwar sa sosai? Me ya sauya daga sanin da yayi wa Daddyn na rashin kulawa da damuwa da abinda ya shafe shi? Be san dalilin nuna masa soyayyar ba, bayan be same ta a lokacin da yake da matukar bukata ba, a lokacin da ya chanchanci a jashi a jiki a nuna masa soyayya, sai yanzu? Da ya girma ya mallaki hankalin kansa? Baya bukatar wannan soyayyar, baya bukatar kulawar zai iya kula da kansa tamkar yadda yayi a baya. Suna fita daga dakin ya tashi da k'yar dan jikin sa baki daya babu kwari ya fice daga dakin ya sakko k'asa, ya isa dakin masu gadi ya taso daya daga cikin ma'aikatan gidan yace ya kaishi gidan sa, a daren nan da komai haka suka tafi. Suna isa ya ce masa ya zauna ya karasa kwana anan kawai ya shige ciki yana jin kamar ana daddatsa masa cikin jikin sa saboda wani irin mugun sanyi me hade da zazzafan zazzabi da ya rafke shi a lokaci daya. Gabannin asubah zazzabin ya dan sake shi kad'an, ya tashi da k'yar dan dama ba baccin yake ba. Alwala yayi yana fitowa daddy na kiran wayar sa, be daga ba dan yasan kila dakin sa yaje duba shi da asubah yaga baya nan shine dalilin kiran, bashi da wani bayanin da zai bawa Daddy bama shi da karfin jiki da na zuciyar da zai iya magana dashi, musamman da ya zama duk abinda ya fada ba zai iya ce masa a ah ba. Raka'atanil fajr yayi ya zauna a saman daddumar har zuwa lokaci ya tashi yayi subh sannan ya koma ya sake kudundunewa a cikin blanket. Bacci ne ya dauke shi me karfi cikin yanayin da shi kadai yasan abinda yake ji. RUMBUN QAYA*              Page 9 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 ****Karfe tara ya farka daga nannauyan baccin da ya dauke shi, bashi karfin zuciya da na gangar jiki amma hakan ya tashi da k'yar, yayi wanka ya shirya sannan ya kira Kamal yace yazo ya dauke shi dan baya jin zai iya driving. Ba'a dau lokaci ba sai gashi ya iso, ya fito yana tafiya wadda ya sa Kamal din karasowa da dan sauri yana kallon fuskar sa "Are you ok ?" Gid'a masa kai yayi, ya wuce shi zuwa wajen motar, bin sa yayi cike da mamakin karfin hali irin nasa. Bud'e masa motar yayi ya zauna a hankali sannan ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar gidan. A hanya be ce masa uffan ba, kansa jingine da jikin kujerar ya rufe idon sa ruf dan ma baya so Kamal din ya ishe shi da tambaya, he's so weak dan hatta heartbeat dinsa ya sauya. "Aryan!" "Um." Yace ba tare da ya bud'e idon ba "Baka jin dadi, let go back please." "Haka nace maka? Na gaji ne kawai." "Gajiya? Me kayi da safen nan da zai saka ka gajiya,?" "Ba sai ka sani ba." "Ai saboda babu shi din ne ma, sanin da nayi maka baka kwana a gidan nan idan har ba wani abu bane ya faru ba, kai da Daddy ne ko? Dan nasan baka saka damuwar Adam a ranka balle har ta dame Ka." "Kamal please, let talk about it some other time." "Ok, be strong please." Yace masa cike da tausayawa, kafin ya maida kansa kan titin ya cigaba da tukin sa ransa duk babu dadi.    Ko da suka isa company be fito daga motar ba, har sai da ya dauki wasu yan dakiku saboda yadda yake jin kansa na juya masa, da k'yar ya cije ya zuro kafar sa ya fito dan yayi ma kansa alkawarin ba zai taba bari hakan yayi affecting dinsa ba, amma kuma daga yadda yake ji yasan yana gaf da breaking alkawarin da yayi ma kansa nan kusa. Jerawa sukayi zuwa cikin building din Kamal na biye dashi a kusa kusa dan tsoron yanayin da Aryan din yake ciki. Har sai da ya kaishi office dinsa ya tabbatar ya zauna sannan ya wuce nasa da niyyar kiran Dr ya samu bayanin abinda ya faru dan yasan ta yadda zai iya kulawa da Aryan din. Be taba jin da gaske Aryan yana bukatar mace a tattare dashi ba sai yau, yana bukatar macen da zata zamar masa tamkar bangon da zai jingina dashi, tabbas zai rage abubuwa da yawa yasan, sai dai wacece zata iya zama da Aryan din da halin sa? Da ciwon sa? Da damuwar sa? Da shariyar sa? Wacece zata jure duk wannan? Dole sai dai wadda take tsananin so da kaunar sa fisabillillah, ba wai dan wani abun duniya ko fame ba, wadda take jin da gaske yana da bukatar a jashi a jiki, a nuna masa tsantsar soyayya, irin wadda ya rasa, wadda zatayi masa soyayyar uwa da danta, tayi masa soyayyar miji da mata. Tunanin sa ne ya katse sanda yaji Dr Ma'aruf din ya daga wayar, suka gaisa ya tambaye shi abinda ya samu Aryan din, yasan waye Kamal a wajen Aryan din shiyasa be boye masa komai ba, har ma da abinda ya kasa fadawa Daddyn, wanda ya sake tsoratar da Kamal din sosai.    System ce a gaban sa yana rike da mouse yana scrolling sai dai har ga Allah be san abinda yake dubawa ba, ga tarin bayanai nan da duk wani abu da yake da bukata a ranar amma ya kasa aiwatar da komai, lekowa Kamal yayi ganin sa a haka ya sashi zuwa office din su ya tarar da Raihana tana zaune babu abinda take dan babu aiki sosai a ranar saboda rashin zuwan Aryan din da wuri, dole sai ya gama dubawa idan ma akwai aikin zai aiko mata dashi ta mail ko ya kirata tazo ta karba. Gaishe shi sukayi dukka a karo na biyu sannan yace ta taso ta dan dafa musu shayin nasu. Ok tace ya fita ita kuma ta wuce kitchen din. Akwai komai da zata bukata nan da nan ta hada abinda zata hada ta dora, ta tsaya a kitchen din har ta gama sannan ta dauka zuwa office din Kamal din, tayi Knocking kad'an a kofar sannan ta tura, waya yake ya kalle ta sannan ya kalli kayan hannun ta "Kai mana office din Aryan please, thank you." Yace bayan ya dan zare wayar daga kunnen sa yayi maganar sannan ya cigaba da wayar, bata so ba dan ita bata ma san ya shigo yau ba duk da tasan babu abinda zai hanashi shigowar amma rashin jin duriyar sa yasa ta sakankancewa da be zo din ba. Tana kokarin karasawa office din nasa zainab ta taso da sauri ta tare ta "Oga yace baya bukatar kowa a office din sa yau." "Oga Kamal ne yace na kai masa." "Bani na kai masa da kai na." Wani kallo Raihana tayi mata,ta rasa dalilin takura mata da yarinyar tayi, gashi ita kuma sam ba'a nuna mata iko da gadara, wanda taga alamun dabiar Zainab din ce, murmushi tayi mata kad'an sannan tace "Karki damu bari na mika masa." Tayi wucewar ta, ta barta a tsaye a wajen cike da mamakin yarinyar.    Kan sa ya dora a saman table din bayan ya dan ture system din, sai da ta shigo sannan ya dago, tayi saurin janye idon ta daka kallon sa ganin yadda nasa suka kad'a sosai, kallon kayan hannun ta yayi har ta karaso ta dora su saman dan madaidacin table din dake gaban couch din. "Good morning Sir." "Menene wannan?" Yace bayan a amsa gaisuwar a ciki ciki dan ita bata ma ji ba "Sir Kamal ne yace a kawo nan." Juyar da kansa yayi gefe da yaji kamar ya makale masa, sannan ya sake dawo dashi tunanin taimaka masa ya fado masa "Have a seat." Ya nuna mata wajen zama, dan jim tayi kafin tazo ta zauna a daaya daga cikin kujerun biyu dake gaban table din nasa ta dayan side din, turo mata system din yayi gaban ta, sannan a hankali yace "Ki duba min wannan." Kallon screen din tayi, sai taga same aiki ne da wanda ya saka ta kwanaki . "In kin gama dubawa ga mails dinsu nan kasa sai ki tura." "Ok." Tace ta shiga aikin, yanayin maganar sa tayi mata kama da ta mara lafiya sosai, dan babu wannan zafin a maganar haka kuma babu nacaccen kamshin nan nasa da kullum yake mamaye baki daya ilahirin building din. Kamar ta bud'e baki ta tambaye shi ko akwai matsala ne? Dan tana jin sautin numfashin sa na fidda wata yar kara, sannan tana jin kamar jawo numfashin yake ta karfin gaske. Amma kuma tace masa me? Tasan yanayin sa zai iya bata amsar da zata gwammace dama bata yi tambayar ba. Wayar sa dake saman table din ce ta dinga kara amma yayi biris kamar bashi ake kira ba, so take ta dago taga yanayin da yake ciki amma sai ta kasa dan cike dake da shakkar sa. Tura kofar ya sakata kallon kofar, sai dai ganin wanda ya shigo ya saka gabanta faduwa, fuskar sa ce ta washe ganin ta, ya karaso yana maida kallon sa kan Aryan din da shigowar sa ta saka shi yunkurin mikewa amma kasancewar bashi da karfin jiki sai ya kasa. "Me ya kawo ka?" Yace muryar sa a shake wadda take kara tabbatarwa da Adam weakness dinsa, shafa saman kansa yayi yaja kujerar dake gefen ta Raihanan ya zauna sannan yace "Baka duba wayar kane? Daddy yana ta kiranka tun asubah, shi ya turo ni, na duba masa kai." "Tunda ka ganni sai ka tafi ko" "No ai ban gama ba,zai kira yanzu sai na hada ku." Yace yana zaro wayar sa da ta soma ringing ma tun kafin ya dire maganar, dagawa yayi "Eh daddy yana office, eh toh gashi nan dai bari na bashi." Ya cire wayar ya mika masa, wani kallo Aryan din yayi masa kafin ya karbi wayar ya saka handfree ya dorata a saman table din "Aryan kana jina?" "Ina kwana?" Yadda yayi maganar ya saka Raihana kokarin mikewa ta bar musu office din dan ita bata gane yadda abubuwan suke ba. "Seat down!" Yace mata yana zare idon sa akanta, komawa tayi ta zauna ta sunkuyar da kanta. Yadda yake maganar da yadda yake amsawa wanda aka kira da Daddy ne ya daure mata kai, shi kowa haka yake masa kenan? Har mahaifin sa ma? "Yan mata aiki ake yi ne?" Adam ya fada yana karyar da kansa hade da wani irin kallo, kallon da yake hana mata sakat idan yayi mata shi dan ta tsani a rayuwar ta yawaan kallo musamman irin wannan da kana gani zaka tabbatar da abinda mutum yake nufi. "Umm." Ta bashi amsa tana sake kankan da kanta dan ita gaba daya zaman wajen ya ishe ta. Wayar sa Aryan din ya garo masa bayan ya gama maganar, ya dauka yana mikewa "Babu kyau wulakanta mahaifa dai, baka ga yadda hankalin sa ya tashi ba, amma kamar ko a jikin ka." Uffan be ce masa ba, yayi masa wani banzan kallo kawai ya ja siririn tsaki, dama kuma Adam din yasan ba zai tanka masa ba, kuma dama be yi don ya tanka masan ba, yayi ne duk dan saboda aikin da suke kokarin dora Raihana akai ne, shiyasa ba karamin dadi yaji ba ganin ta zaune a office din Aryan din,hakan ya sake tabbatar musu da aikin su zai tafi yadda ya kamata.   Rankwafowa yayi ta saman kujerar da Raihanan ke zaune, ya dora kansa daidai saitin kunnen ta a hankali yace "Ki kula dashi sosai, kinsan yana da matsalar kwakwalwa." Daga kanta tayi da sauri ta kalle shi, ya kashe mata ido daya sannan yayi murmushi. "Get out!" Aryan yace a zafafe, daidai lokacin Kamal ya shigo office din, da saurin sa ya karaso ganin har Aryan din ya mike tsaye, ya kalli Adam din sannan ya kalli Raihana dake zaune da system din Aryan din a gabanta "Sannu da zuwa Malam Kamal, yau na kawo muku ziyara gashi har zan tafi, sai mun sake haduwa ko?" Yayi gaba ya bud'e kofar hade da banko ta a lokaci daya. Dafe kai Aryan yayi da yake jin kamar ya cire shi yayi wurgi dashi ya huta tsananin ciwon da yake masa. "Calm down please." Kamal yace yana matsawa gefen sa "Raihana, please excuse us kinji?" Tashi tayi da sauri ta fice sum-sum-sum dan dama hanya take nema. "Na gaji Kamal, na gaji wallahi, Adam yana so ya kai ni bango, yana so ya kai ni karshe." "Dan Allah ka kwantar da hankalin ka, yau ne karo na farko da ya fara irin haka? Kasan shi kasan abinda zai iya, kasan kuma komai akan dalilin da yasa yake maka hakan, ya riga yasan weakness dinka, dashi yake amfani wajen bata maka rai." Dafa jikin table din yayi da hannu daaya, dayan kuma ya rike kansa ya shiga jujjuya shi, yana ganin a karshe sai Adam ya haukata shi sannan zai kyale shi. Dafo shi Kamal yayi yace "You need some rest Aryan, baka da lafiya." Zame hannun yayi ya zauna yana sakin kan a hankali "Me yasa kake punishing kanka haka ne wai? Me yasa ? You are sick tun daga yanayin maganar ka har facial expression dinka ya nuna, amma ka dage sai kayi aiki? Akan me?" "Bani shayin chan please, mu bar maganar nan haka nan Kamal." Matsawa yayi ya zubo masa shayin a cup ya mika kasa, ya kafa kansa ya shiga sha a hankali dan zafin na ratsa makoshin sa wanda yake a matukar bushe. Shanye wa yayi tas ya sake kara masa shima ya shanye, sannan ya dan dora kansa a saman table din ya kulle idanun sa. Babu yadda Kamal ya iya face ya fita ya barshi, ya je ya dauki wayar shi ya kira Ya Nabeela yace ta shigo office din, cikin kankanin lokaci sai gata tazo a cikin yanayi, ta same shi kamar ma bacci yake a zaune dan har ta shigo be dago ba, sai da ta taba shi sannan ya tashi. Dole ta tilasta masa bin ta, ta dauke shi daga office din zuwa gidan ta, sannan ta kira Dr Ma'aruf din tun a hanya yace zai same su a gidan. RUMBUN QAYA*              Page 10 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023🔥🔥🔥🔥🔥 ****Tunda taga fitarsu ta lallaba ta gudu itama, dan dama hanyar tafiya take nema, bata san me ya hada su da Adam ba amma tabbas ta fuskanci yana cikin damuwa matuka, sai dai yadda yake abubuwan nasa ne sam basuyi mata ba. Bata cika son mutum me zafi ba, ko dan bata taso taga irin hakan ba? Hamman ta dukka basu da zafi ko kuma ita ce basa yi wa? Napep ta samu ya kaita makarantar su Amina dan sun yi daga nan zasu hadu su wuce ta rakata kasuwa, bata taba zuwa kasuwa ba tunda take a rayuwar ta, shiyasa take cike da daukin zuwa ta siyo wa yan gidan su abubuwa da first allawee dinta. Da weekend dukkan su zasu zo har Dadan ta, daga nan suje aga Abby wanda daga wannan zuwan sai kuma fitowar sa, shiyasa take cike da murna dan ji take kamar ta jawo ranar saboda tsabagen zumudi. A gate suka hadu da Aminan ta gama lectures har ta fito ma, dan haka ko sauka daga napep din batayi ba, ta shigo kawai suka tafi. Siyayya tayi sosai tunda kudin nata har da wanda Hamma Hydar ya bata ta hade ta sai musu abubuwa ta siya ma Adda Maimuna har ma da Aminan. A gajiye suka dawo dan saboda tsabar wahala ji tayi kamar kafarta zata tsinke, bata san haka wahalar kasuwar take ba sai da ta dandana, amma idan ta kalli abubuwan da ta siyo sai taji dadi ya kamata. Wanka tayi hade da alwala sannan suka zauna zaman cin abinci, shinkafa da wake da salad favourite abincin ta kenan. Da suka gama ta dauko kayan ta nunawa Adda Maimuna sannan ta bata nata da na Hidaya yar autar ta, aikuwa taji dadi sosai tayi ta godiya hakan ya yi mata dadi sosai. ***Yana zaune a falon Ya Nabilan tunda suka dawo be ce mata komai ba, kansa na saman pillow rabin jikin sa na saman kujerar sai wayar sa dake ajiye daga gefen hannun sa, abinci ta zubo masa a plate daga saman dinning ta kawo masa hade da ruwa sannan ta zauna a gefen sa. Tashi yayi ya daidaita zaman sa ya kalle ta sai yayi mata murmushi kad'an ganin yadda duk ta shiga damuwa. "I'm fine fa." "When last kaci abinci?" Sama ya kalla kamar me nazari, kafin ya daga mata yan ya tsun sa, yayi mata alamar biyu "Two days ago?" Ta zaro ido, gid'a mata kai yayi "Allah Aryan kana da matsala, so kake ka kashe kanka? Kwana biyu baka ci komai ba? Akan me?" "Abinci fa kika ce, nasha tea ai, ko yau ma sai da nasha." "Tea, tea, tea! Dama tea din na kirki ne me hadin madara da sauran su, ruwa ne fa kawai sai gayyayyaki, me zai maka dan Allah?" "Yana taimakawa sosai." "Kayi sauri kaci kafin ya huce." Tace tana mikewa ta barshi a wajen, yasan ranta ne yake a bace shiyasa ma yayi kokarin daidaita kansa dan ta samu natsuwa. Sai ma yaje ya samu Kamal yaji akan dalilin da zai sakashi kiranta, kaamar dai shi din har yanzu baby ne, yasan kuma halin rikicewar ta, gashi duk yanzu tabi ta damu kanta akan abinda da ya bashi some hours ma shikenan zai wuce kamar yadda sauran suka wuce tunda ya riga yasan ba yau aka fara ba ai. Abincin ya soma ci a hankali duk da bashi da appetite sam amma kuma hakan zai ci ko dan hankalin ta ya kwanta. Chinese rice ce da chicken breast sai lemon kwakwa me matsakaicin sanyi saboda yanayin sa baya shan duk wani abu me sanyi sosai. Sai da yaci fiye da rabi sannan ya ture ya dauki tissue ya goge bakin sa ya koma ya sake kwantar da kansa a jikin kujerar. Fitowa tayi dan dama bashi lokaci tayi yaci abincin dan in ta zauna ya dinga kawo kabali da baadi kenan har sai ya haramtawa kansa cin abincin kwata kwata. Magungunan sa ta dauko ta mika masa ya karba yasha, tun bayan da Dr Ma'aruf yayi masa allurar nan ya samu natsuwa sosai, kansa da yake masa azababen ciwon nan ma ya rage sosai ya samu kwarin jikin sa, allurar ta riga ta zamar masa kamar masifa dan shi yanzu inhaler ma ba yi masa take sosai ba. "Aryan?" Ta kira sunan sa tana tattara hankalin ta waje daya, dan gyara zaman sa yayi dan ya fuskanci magana me muhimmanci zatayi masa ganin yadda ta kira shi da yadda fuskar ta, ta nuna "Aure ne ya kamace ka a wannan yanayin, be kamata ka zauna haka ba." "Aure kuma?" Yace yana tashi zaune sosai "Yes aure, kana bukatar mace Aryan, kana bukatar life partner wadda zata tallafi rayuwar ka,." Bata fuskar sa yayi nan da nan, kamar wanda akayi ma wata magana mara dadi "Mun yi magana da Kamal, tabbas abinda ya kamace ka kenan, domin ba lallai ne mu kasance da kai a kowanne lokaci ba, Aryan ko zama da yunwar nan da kake matar ka ba zata taba barin ka haka ba, zaka samu nutsuwa hankalin ka zai kwanta." "Kun gaji dani?" Yace yana tashi tsaye "Bamu gaji da kai ba, amma duk yadda zamu yi maka ba kamar matar ka ba, aure yana cike da tarin ni'imomi da ba zaka gane su ba sai ka shiga cikin sa." "Bani da wadda zan aura, I don't trust just anyone, ba zan iya ba." "Zaka iya, just give it a try, zaka gode mana." "Ya Nabila, bana son kowa a tare dani,bana son zama da kowa, kune dama kawai tunda kuma kun gaji dani shikenan, i will take care of my self, ba sai an taimaka min ba." "Don't get me wrong, ni iya gaskiya ta nake fada maka, dole dole akwai abubuwan da ba zamu iya maka ba, sai dai matar Ka." Shiru yayi kirjin sa na bugawa da sauri, menene a cikin auren idan ba tarin nadama ba? Ta ina ma shi zai fara neman mata? Yace mata me kuma? Ba wannan ne shi yanzu a gaban sa ba. "Kana jina kuwa?" "Eh, kiyi hakuri ba yanzu ba, ba zan iya ba, naje na auri yar mutane na shiga hakkin ta." "Shikenan, amma ka bud'e zuciyar ka, may be sai kaga an samu wata ta samu ta shiga zuciyar taka, shikenan ma ba zaka san sanda zaka zo mana da maganar ba." "Hmm." Yace ya koma ya zaune, bata sake ce masa komai ba ta kyale shi dan ta lura ba zai fuskance ta a wannan lokacin ba. Yana gidan har yaranta suka dawo daga school, dan dama su ya zauna zaman jira da tuni ya tafi ya shiga wata sabgar, burin sa kawai ya koma office dinsa ya cigaba da aiwatar da abubuwan da ya fara wanda sam Daddy baya so shiyasa ma yake ta dakushe shi. ***A daidai kofar wani gida dake da karancin hadada har ma da karancin gidaje yayi parking. Fitowa tace ya je ya dawo ba tare da ya shigo ba, a duk sanda suka zo gidan ko cikin harabar gidan bata yarda ya shiga da ita da kafarta take takawa zuwa ciki duk kuwa da gidan ya kasance mallakin ta ne. Sai da taga tafiyar sa sannan ta juya ta shiga gidan. Yana tsaye a compound din yana dakon zuwan ta, sai gata ta shigo, su biyu ne tak suke da mukullin gidan dan hatta Adam bata yarda ya san da zaman wajen ba, dan tasan ba zai taba lamutar abinda take aikawata a wajen ba,amma kuma ya zatayi? Dole ta nemawa kanta biyan bukata dan babu wani abun arziki da take samu ta wannan bangaren. Ta dade a cikin harkar kuma bata taba jin dar ko dana sanin kasancewar ta akai ba. "Hajjaju kin karaso." Yace yana tahowa suka hadu a hanya, saurayi ne wanda a shekarun sa ba zai haura Adam dinta ba, idan ma zai haura din be fi da kad'an ba. Harkar computer ce ta hada su daga nan ta siye shi da wasu mahaukatan kudade har zuwa yanzu da suke rayuwa tamkar mata da miji a gefe daya kuma yana mata aikin da take so. Shiyasa Aryan yake a tafin hannun ta domin duk wani motsin sa tana sane dashi duk da akwai abubuwan da ta kasa samu a wajen nasa har yanzu. Babban burin ta shine samun faifan video din wanda take tunanin yana hannun sa, amma kuma idan ta zurfafa tunani sai taga ai da yana wajen sa da tuni ba maganar ake yi ba, dukkan su a yanzu sun yi taraiyane akan samun disk din wanda yake determining nasarar dayan su akan daya. "Na karaso, hope baka dade kana jirana ba handsome." Tace tana masa kallon kasa kasa. Irin na tsofaffin yan duniyar nan wanda suke san duniya take kad'a musu gangar shedanci a tsakiyar kansu "No ba yawa,ban fi 20mint ba." "Duk da haka ba zan so hadadden saurayi ya zauna zaman jira na har na 20min ba." Dariya ya kwashe da ita, ta mika masa hannun ta ya rike zuwa cikin gidan. "Me yasa baka shigo parlor ba,ka zauna a waje." "Jiranki nake, ba zan iya shigowa na barki ba." Murmushi ta saki me taushi sannan ta jefar da jakarta gefe hade da mayafin ta, ta zauna tana kashe masa ido. "Ya labari Hajiyata, ina fatan dai komai yana tafiya daidai?" "Ba zaka fara kwantar da tarzomar da ta taso ba? Kafin wannan maganar?" Dariya yayi, itama tayi dariya yace "Shawara ce dani akai Hajiya." Hannun ta, ta kai saman bakin sa da sauri "Ban hana ka ce min Hajiya ba?" "Tuba nake ranki ya dade." "Ina jinka toh." "Ina ganin duk wani communication da zai wanzu tsakanin ki da yarinyar nan ya zama call ne, banda text message kiran kawai sannan ki dinga recording call din, ni kuma zan san yadda zan nayi editing komai." "Shisa nake kara sansa, kasan deal." "Kinga baki bar wani sign ba da har zai iya zama hujja akan mu Hajiya, auw ranki ya dade." Ya kama baki da sauri yana dariya "Naji. Zan kuma yi amma dai for now dai mu shiga ciki, hakuri na ya kare." Tace tana mikewa "Ok muje." Yace yana murmushi suke shiga daga ciki. Allah ya kyauta ***Kasancewar Thursday yau ya sakata kin tashi da wuri dan ba zuwa zatayi aikin ba, a kaida CDS ya kamata taje wanda ake yi duk ranar Thursday, toh amma bata jin fitar kwata-kwata dan sai wannan satin tayi submiting takardar a road safety akayi mata signing. Tana jin Amina na tashin ta bayan ta shirya taki tashi haka ta hakura ta tafi ta barta, ta kara shigewa bargo dan akwai dan sanyi sanyi a garin. Kiran wayar Dadah ce ta farkar da ita, ta daga cike da zumudin ta. Nan da nan ta wartsake daga baccin jin suna hanya bayan da sai asabar zasu zo, suna Kaduna dama tun jiya yau dan haka tasan kamar yanzu zasu iso Kanon. Dadi kamar zai kasheta,ta shiga wanka a gurguje tazo ta ta hau gyaran dakin nasu, ta gyara ta wanke bandakin tas sannan ta hau shiryawa ta manta ma da wani batun breakfast, kaya tasa masu kyau sosai wanda tasan Dadah zata ganta fes da ita, dan kayan ma sababbi ne ta dinka su. Zuwa tayi ta fadawa Adda Maimuna suka hadu da Muhammad ya shiga tsokanar ta tana ramawa. Dakin ta dawo ta dauki wayar ta, ta dinga kallon lokaci ta kasa zama waje daya ko kad'an. Shigowar kira wayar ta yasa ta saurin zabura ta dauki wayar. "Hajiya Zeenat?!" Ta furta a hankali kafin ta daga wayar "Hello, aunty ina wuni?" "Raihana ta, kin manta dani ko?" "A ah Aunty." "Toh kina lafiya? Ya aikin ya komai da komai? "Lafiya lou alhamdulillah." "Babu wata matsala ko?" "Babu komai Aunty." "Toh Masha Allah, wani taimako zaki min dan Allah idan ban takura miki ba." "Ba komai Anty, me za'a yi?" "Nasan kince min yau bakya zuwa aiki ko?" "Eh bana zuwa, banje yau ba ma." "Taimaka min ki shirya, zan turo miki address kije ki duba min Aryan." "Na'am?" Tace tana zaro ido "Eh ki taimaka min, Aryan bashi da lafiya kwana biyu kenan, gashi duk yadda zamuyi akan sa mun kasa wallahi, Adam yace min ya sake dake har yana saki aiki a office dinsa, kiyi min wañnan taimakon dan Allah kije ki gano min shi, sannan ki dafa masa shayin nan da aka ce kin iya dafa masa, Kamal ya fada min komai, ki taimaka min dan Allah." Shiru tayi tamkar ruwa ya cinye ta, ita da take jiran Dadan ta yaushe kuma zata fita daga gida, suzo bata nan kuma sai tace tana ina kenan?kuma taje tace masa me? Bayan tasan halin sa sarai, kuma gidan shi da waye? Bata gane ba "Zaki iya min wannan taimakon Raihana?" "Zanyi." Tace kai tsaye dan bata jin zata taba iya kin duk wani abu da ta nema a wajen ta "Nagode nagode miki, Allah yayi miki albarka kinji? Ya baki miji na gari wanda zai kula dake." "Amin." "Karki damu, idan kinje gidan akwai mutane ba shi kadai bane, akwai maigadin gidan da matar sa su zaki samu kinji?" Ajiyar zuciya ta sauke, bata tunanin Hajiya Zeenat zata taba cutar da ita ko tayi abinda zai cutar da ita, dan haka zuciyar ta daya ta yafa mayafin ta, ta dauki yar madaidaiciyar jakarta ta saka waya da kudin napep sannan ta fito 🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 _ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_ _DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_ _MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_ +227 90 16 59 91 *Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na* Maryam sani 0022419171 ACCESS bank Ku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number* 09166221261 Litattafan dai sune kamar haka RUMBUN KAYA Hafsat rano A RUBUCE TAKE Huguma IDON NERA Mamuhghee KI KULANI Hafsat xoxo DAUD'AR GORA Billynabdul *Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥 *RQ*       Page 11 Hafsat Rano ***** Tana tsaye bakin titi suna magana da Hajiya Zeenat din motar ta tsaya a gefen ta, sauke glass din yayi nan take ta gane shi, driver da ya bige ta ne. Bud'e kofar bayan tayi ta shiga cike da taraddadin abinda zata tara. Ta rasa dalilin da yasa take wasu abubuwan duk da ba haka tarbiyyar ta take ba. Tasan kuma tabbas idan Dadah suka samu labari ranta zai iya mummunan baci, shiyasa ma taki sanar dasu komai akan Hajiya Zeenat din dan su sam basu da yarda tun abinda ya faru da Abbyn ta wanda an rasa wanda zai iya bata labarin ainahin abinda ma ya faru har ya samu kansa a prison tsawon wannan lokacin. Jikin ta ne yayi sanyi sosai ganin sun iso cikin layin gidan sannan ya rage tafiya sosai ta tabbatar a daf suke. Gefen wani gida yayi parking wanda yafi mata kama da kango sannan ya zuro wata leda me kyau yar madaidaiciya bayan yace "Wanchan bakin gate din shine gidan, ga wannan Hajiya ce tace na baki." Hannu tasa ta karbi ledar bata ko duba ba,tayi godiya ta fita shi kuma ya juya. Kallon gidan take gabanta na faduwa amma haka ta daure dan har cikin zuciyar ta, tana son sanin halin da yake ciki duk kuwa da ba wai tana shiri dashi bane, tana dai jinsa tamkar Hamman ta ne kuma zata iya yin komai dan ganin an san halin da yake ciki. _"Kiyi hankali dashi dan ba kalou yake ba."_ Muryar Adam a sanda yake mata maganar ta shiga yi mata amsa kuwwa. Damke ledar hannun ta tayi sosai ta durfafi gidan kirjin ta na wani irin lugudan duka. Knocking tayi a kofar a dan tsorace ta tsaya daga baya tana jira a bud'e. Baba maigadi na cikin dan karamin dakin dake wajen gate din ya fito da dan saurin sa a tunanin sa ko Aryan din ne ya fita yana ciki ko kuma Kamal ne yazo. Bud'e kofar yayi ya kalleta da alamun tambaya kafin yace "Kece kike kwankwasawa?" "Eh nice Baba, ina wuni?" Ta dan russuna ta gaishe shi "Lafiya lou alhamdulillah, bismillah." Ya matsa mata ta shigo sannan ya tura kofar "Wajen me daki na kike zo?" "A ah." Ta gid'a masa kanta tana tuno abinda Hajiya Zeenat din tace mata. "Aryan yana ciki?" "Na'am?" Yace da mamakin sa "Eh Ya Nabila ce ta aiko ni da sako na kawo masa, bansan ko ya fita ba amma " "A ah be fita ba, yana ciki kamar ma dai bacci yake yi." "Ok." Tace tana kokarin boye yanayin da take ciki na tsoro "Muje ciki." Ya nuna mata hanya, gaba yayi ta bishi a baya a hankali har zuwa kofar part din, ja tayi ta tsaya dan bata san ta in da zata fara. "Bismillah yana ciki." Shiru tayi tana nazari, ta shiga ciki bayan tana da yakinin shi kadai ne a cikin, hakan kuwa daidai ne? Kar tayi abinda zai zubda mata mutunci fa. "Amm Baba dan Allah a cikin gidan ba Yara?" "Eh akwai Amma sun je islamiyya, sai dai suna gab da dawowa." "Toh Baba bari na jirasu sai suyi min jaroranci, bana son shiga ciki ni kadai." "Toh... Bismillah muje na kaiki wajen iyalina, sai ki zauna ki jira su." Godiya tayi, suka juya zuwa hanyar bq, ya kaita wajen matar sa Hajara ta zauna. Minti goma da zaman ta yaran suka dawo, daya daga ciki tasa a gaban suka koma part din ta tura kofar da take a bud'e suka shiga ciki. Babu motsi ko alamun akwai mutum a ciki sai rigar sa dake ajiye a saman kujera hade da wayoyin sa da mukullin mota. Kamar munafuka ta shiga sallama tana dan daga kafarta kad'an tana mayarwa. Yana kwance akan gadon sa, daga gefe daya system dinsa ce a kunne da take nuna masa baki daya part din nasa. Aiki yake akan kara tabbatar da tsaron gidan sosai musamman da yake saka ran fitowar Barrister nan ba da jimawa ba. Kwanan sa biyu be fita office ba domin da gaske yana da bukatar hutu sai dai a gidan ma ba wani hutun kirki yayi ba, dan yan ayyukan sa ya tattare ya dira a kansu yana cigaba da bincike da nemo duk masu hannu a abinda ya faru a wanchan lokacin. Iska ya furzar me zafin gaske, ya tashi zaune yana bada hankalin sa akan system din. Tunanin sa ne ya tsaya chak ya zuba ma allon computer ido cike da mamakin abinda yake gani. Da sauri ya mike, jikin sa daga shi sai armless da 3-quarter, tun a falo ya zare kayan jikin nasa bayan ya dawo daga salla. Yanayin yadda take tafiya tamkar mara gaskiya ya sakashi yin hanyar waje da sauri. Juya bayan ta, tayi tana kallon yaron da ya rako ta shima ita yake kallo, tunanin ta kawai ya gama bata tayi tafiyar ta dan bata ga alamun yana gidan ba, idan ma yana nan toh baccin yake dan babu motsin komai. "Ya sunan ka?" Ta tambayi yaron "Habu." "Ok...Mu tafi kawai inaga bayanan." "Toh." _"Idan kuma yana nan, amma yana cikin matsala fa?"_ Wata zuciyar ta tambaye ta, tsoron ta ne ya dadu, ta juyo da nufin yin hanyar da ta gani da ta nunaa alamun daki ne a wajen ,sai ta ganshi a tsaye yana kallon ta, kallo me cike da tsantsar tuhuma. Ledar hannun tace ta zame, ta fadi a wajen apple din dake ciki ya tarwatse a kasan tiles din. "You!" Ya nuna ta da hannun sa, kafin ya shiga takowa zuwa in da take durkushe tana kokarin tattare apple din da ya zube. "Me kike anan? Me ya kawo ki nan? Taya akayi kika zo nan?" "Na'aa amm." "Me kike a gidan nan?" Mikewa tayi tsaye bayan ta gama tattare apple din, ta daidaita nutsuwar ta dan kar ta bar masa wani shakku. "Zuwa nayi na duba ka sir." "Ki duba ni? Ban gane ba." "I heard baka jin dadi, kuma kwana biyu baka zuwa aiki shine na tambaya aka ce baka da lafiya ne, shine nayi amfani da address din naje gida, daga nan aka ce in zo nan kana nan." "Unbelievable!" Yace yana kallon ta "Shikenan dan bani da lafiya sai kizo ki duba ni? Ke ba mace bace ba? Ya dace kizo ki duba ni kina mace?" "Um um, ai sai da naje cikin gidan shine aka saka habu ya rako ni." Kallon Habun yayi sannan ya maida kallon sa kanta "Shikenan duk wanda bashi da lafiya a office haka zaki bisu gida ki duba su? Kowa ba mace ba namiji?" Da sauri ta daga kanta "Eh." "Ina iyayen ki?" Yace yana bata ransa "Mamana ta mutu tun ina yar karama." Wani abu yaji tun daga kansa har zuwa kafar sa. Fuskar sa dake daure ta fara washewa zuwa kalar tausayi, tausayin rayuwar da tayi cikin rashin uwa wadda ta kasance jigo, tabbas rashin iyaye musamman mahaifiya babban tashin hankali ne, da akwai uwa babu yadda za'a yi ta aikata abinda ta aikata a yanzu, tazo ta duba shi har gida, daga haka kuma za'a iya samun matsala idan ta hadu da mara tsoron Allah. "Allah ya gafarta mata." Yace a chan kasan makoshin sa, kafin yace "Ki zauna ina zuwa." Zama tayi ya juya ciki, dan sai lokacin ya tuna da shigar dake jikin sa. Jallabiya ya dora akan armless din, sannan ya dawo falon ya tarar da ita a zaune tana wasa da hannun ta, habu na gefen ta yana karewa falon kallo dan ba shigowa suke ba. Zama yayi a kujerar dake facing dinta, ya dan kalle ta kad'an sannan yace "Karki kara zuwa gidan kowa da sunan duba shi, wannan ba tarbiyya bace ba, duk abinda ya faru ki kira a waya ki duba mutum." Gid'a masa kai tayi, ya girgiza kansa har lokacin mamakin ta be barshi ba. "Zaki iya tafiya, nagode." Tashi tayi tsaye, ta sake kallon sa sannan ta dauki ledar apple din, ya kalli ledar sannan ya kalle ta "Wannan ba nawa bane ba?" "Na'am?" "Eh ba kayan dubiya bane ba?" "Oh eh shine." Ta mika masa tana yake. Karba yayi ya ajiye a gefe, ita kuma ta sake masa sallama sannan taja hannun Habun suka fito. Kamar ta kurma ihu haka ta dinga ji, tabbas tayi abun zubda mutunci dan ta kasa gamsar dashi dalilin zuwan ta wanda kuma.dama bata dashi, Hajiya Zeenat tace kar ta ambaci sunan ta idan taje shiyasa tayi wannan karyar amma duk da haka karyar bata hau ba sam, gashi a karshe yana mata kallon marar kamun kai. Tsaki ta jashi yafi kala dari, tana ji wayar ta na ringing amma ta kasa dagawa saboda bacin rai. Bayan fitar su, ya mike rike da ledar ya kai kitchen sannan ya haye sama cike da mamakin ta. ***Duk abinda ya faru tun farkon shigowar ta gidan har tafiyar ta akan idon su akayi. Plan dinsu yayi aiki domin dama hanyar da zasu saka camera din a gidan suke nema sai gashi da kansa ya nemi ta bashi ledar apple din. Dukkan su ya basu mamakin yadda har ya tsaya ya saurare ta, tabbas Raihana itace kadai zata iya yi musu aikin domin tana da wani tasiri akan Aryan din. Da ace wani ya kama ya shigo gidan ko a cikin ma'aikatan ne ba zai taba aminta da bayanin su ba, rashin yardar sa yayi yawan da hakan ke basu cikas akan aikin su. Sai gashi har yana zama yayi magana da ita duk da zafi da tsaurin sa. Tunda sun samu abinda suke so sai zuwa next plan din, shine samo key din, wanda bata jin a yanzu zai musu wahala. "Hajiya ikon Allah!" Yace yana kishigida a kujerar da yake kai "Kaga yadda komai ya tafi ko? Na fada maka yarinyar nan asset ce." "Bata da wayo sam, sannan sak halin ubanta, da wannan zuciyar tasu suke saka kansu a wahala." "Wallahi kuwa." "Mum ni fa son ta nake wallahi, yadda kuma naga yaron chan na kallon ta bana so, I'm jealous kar naje ya fada son ta." "Kar ma ka fara wallahi, babu wannan maganar na fada maka tun farko." "Gaskiya ni son ta nake Allah da gaske." "Kar mu fara haka da kai Adam, so kake ka Latata mana aiki?" "Toh a cire ta daga aikin mana, she's too young for all this, ni a barni da Aryan din me ma yasa ne sai an dinga bin sa ta bayan kasa." "Lallai baka da hankali wallahi, toh ban amince ba, ban yarje maka soyayya da ita ba." "Kana ji kuwa Barrister?" "Ina ji Hajiya, Adam ka bar wannan maganar dan ba me yiwuwa bace ba, bata mana plan kawai kake son yi, karshe dukkan mu a watsa mu prison." Mikewa yayi tsaye ransa a bace ya fice daga wajen, baki sake Hajiya Zeenat ta bishi da kallo, ya zai mata haka? Bayan ta gama tsara komai. "Karki damu Hajiya, ba komai duk shirme ne, ba zamu barshi ya dauko mana abin magana ba, yayi kad'an ya bata mana plan." Kanta ta dafe da sauri, tasan taurin kan Adam da kafiyar sa, tasan kuma da gaske yake tunda ya furta, dan haka ya zama dole ta dau mataki kafin komai ya kwabe mata. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 _ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_ _DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_ _MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_ +227 90 16 59 91 *Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na* Maryam sani 0022419171 ACCESS bank Ku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number* 09166221261 Litattafan dai sune kamar haka RUMBUN KAYA Hafsat rano A RUBUCE TAKE Huguma IDON NERA Mamuhghee KI KULANI Hafsat xoxo DAUD'AR GORA Billynabdul *Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥 *RQ*       Page 12 Hafsat Rano ***A kofar gidan ta tsaya ta zaro wayarta ta shiga wajen message ta rubutawa Hajiya Zeenat sako. _"Na dawo, kuma ya samu sauki."_ Sai ta kashe wayar gaba daya dan bata so ta kirata kwata kwata idan suna tare da yan gidan su. Da sallamar ta, ta shiga gidan da daukin ganin su, ga mamakin ta sai ta tarar basu karaso ba. "Wai basu karaso ba Adda?" Ta tambayi Addan tana zama a gefen ta "Eh wallahi, bakuyi waya ba?" "A ah bamuyi ba, bari na kira su "Ok kira su muji." Wayar ta kunna ta kira amma har ta gama ringing ba'a daga ba, dukkansu tabi da kira amma duk basa dagawa, hankalin ta ne ya soma tashi tunda dai babu yadda za'a yi dukkan su ace basu ga kiranta ba. Mikewa tsaye tayi cike da zulumin abinda ya faru ko yake faruwa. Ita kanta Addan jikinta yayi sanyi ganin sai cigaba da kiran Raihana take amma ba ta ma shiga daga baya. Baki daya hankalin su ya gama tashi kusan awa guda kenan da dawowar ta amma duk da haka basu karaso ba, ba kuma su kirata ba. Sam ta kasa zaune ta kasa tsaye haka ta dinga zagaye zuwa chan ta soma kuka dan gaba daya jikinta ya gama bata ba kalaou ba. ***A kofar gidan Lamido yayi parking cikin yanayin gajiya da tafiyar dukkansu suka fito Dadah da jikin ta ya gama laushi sosai saboda tsabar gajiya ta zuro kafafun ta a hankali Hydar ya cicibo intisar da take baccin wahala. Shi da Dadah da intisar din ne a baya sai Lamido da Sadeeq a gaba bayan sun chanja tukin saboda wahala. Awar su kusan biyu a cikin hold up ashe masu manyan motoci ne suke zanga-zanga akan an kashe musu dan uwa, shine suka rufe hanyar gaba daya suka hana kowa bi sai zagaye ta wasu kauyukan suka dinga yi abinda ya saka su dadewar kenan. Sun ga kiran Raihanan sun kuma san tana cike da zulumi amma sanda duk suka ga kiran nata babu service a in da suke balle su iya kiranta. Tana tsakar gidan tsaye taji alamun tsaiwar mota, da mugun gudu ta kwasa tayo waje, bata san sanda ta rungume Lamido ba kasancewar shine a hanya cikin kuka kuka dariya dariya. Tausayi ta basu a lokaci daya duk da sun san zata aikata dama, ta bi su duk ta rungume taki daina kukan da k'yar ta kyale su ta kama hannun Dadah suka soma shiga cikin gidan. "Raihata kukan na menene kuma?" Dadah tace ganin still hawayen take, ita kadai tasan yanayin da zuciyar ta ta shiga dan saura kiris ta buga saboda tsabar tsoro. Kin musu magana tayi har aka shiga suka zauna a falon Adda Maimunan da ta taso ta riko mahaifiyar ta. "Sannun ku da hanya Dadah." Tace ta taimaka mata ta zauna Raihanan ta zauna itama a kujerar ta nanuke mata "Sannun ku Maimunatu,kun ganmu sai yanzu ko?" "Eh wallahi, gaba daya hankalin mu ya gama tashi." "Ku bari kawai, hanya ce tayi mana matsala wallahi, amma alhamdulillah tunda an iso lafiya." "Alhamdulillah kam." "Ina wuni Addah?" Yan mazan suka hada baki wajen gaishe ta. "Lafiya lou ya hanya?" "Alhamdulillah." "Menene wai?" Hydar yace yana kallon fuskar Raihana da tayi kicin-kicin ita a dole fushi take dasu. "Tunda dai gamu mun iso ba shikenan ba?" Lamido yace yana dariya "Ku kyale min kanwata, kusan ta da saka damuwa a ranta, nasan ta tsorata ne, toh gamu mun zo shikenan ko?" Daga mishi kai tayi sai hawaye shar-shar "Naji tsoro sosai." Tace da muryar kuka "Babu abinda zai faru damu kinji? Sai Abby ya fito mun yi rayuwar mu, mun aura miki best husband da zai kular mana dake" "Kai Hammaaa." Tace tana kunshe fuskar ta a jikin Dadah. "Kaga jaira taji maganar aure har ta murmushi." Sai aka kwashe da dariya gaba daya. Abinci da ruwa da lemuka aka kawo musu sannan aka kaiwa Dadah nata daki Raihana da Adda Maimuna suka bita ciki aka bar su Lamido da Muhammad din Adda Maimuna a falon suka fara sallah sannan suka ci abincin. ***Tsaki yaja a karo na ba adadi, sau biyu kenan yana kiran Kamal a waya amma yayi biris dashi. Tashi yayi bayan ya ture system din dake gaban sa ya nufi office din Kamal din da kansa. Yana zaune yana aiki kansa ya dau zafi sosai dan ya manta ma shaf da kiran da Aryan din yayi masa sai gashi ya shigo. Fuskar sa ya kalla ya tuno da abinda yace masa, ya tuntsure da dariya yana mikewa tsaye "Yanzu tsakani da Allah fa jiran ka fa nake." "Bata zo ba fa Aryan, beside kai da kanka kace baka son nata, a gaban ta, kuma yau Friday bata zuwa aiki kasan." "Call her toh mana.." "Allah ni ba zan iya kiranta ba, ka kirata da kanka amma ai da kunya nace tazo ta dafa maka tea." "Ba zaka kirata ba? Ni bani da number ta." "Waye ya kirata ranar nan? Beside ma ga number ta wajena bari na baka." "You have problem." "Ai gaskiya ne,da kunya ai." "Karka kira ta din." Ya juya ya barshi yana yi masa dariya. Dariya sosai Kamal ya dinga yi bayan fitar sa, yayi saurin karasa abinda yake ya bishi office din. Ya same shi yana ta jan tsaki fuskar sa a hade shi a lallai Kamal din ya bata masa rai. "Bari nasa Zainab ta dafa maka, amma dai kana da bukatar ka shiga daga ciki wallahi, dan rashin yardar ka dole abubuwa da yawa ba kowa zaka yarda yayi maka ba." "Sai ka sani dole nayi ai, dama ina ta so nayi maka magana, shine kaje kuka hada kai da Ya Nabila ko?" "A ah hira ce tsakanin ya da kanin ta." "Munafurci dai,kasan yanzu duk zata bi tasa abun a ranta" "Ai gaskiya ne." Chanja zancen yayi zuwa wani daban "Yarinyar nan ma dole ta zabi ko zuwa duk satin ko naki signing wannan watan." "Wacce yarinya?" "Oho." "Wai Raihana? A ah idan baka mata signing ba ma ni sai nayi mata, tunda dai batayi laifin komai ba, laifin ta daya da bata zo ta dafawa katon gwauro shayi ba." Wani kallo Aryan yayi masa, be sake magana ba ya ja system dinsa ya shiga motsa mouse din dan ya lura Kamal din so yake ya kure shi, shi be ma san yadda akayi har ya biye masa haka ba 🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 _ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_ _DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_ _MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_ +227 90 16 59 91 *Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na* Maryam sani 0022419171 ACCESS bank Ku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number* 09166221261 Litattafan dai sune kamar haka RUMBUN KAYA Hafsat rano A RUBUCE TAKE Huguma IDON NERA Mamuhghee KI KULANI Hafsat xoxo DAUD'AR GORA Billynabdul *Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥 *RQ*       Page 13 Hafsat Rano    Da weekend suka shirya gaba dayan su a karo na farko suka nufi prison din. Hajiya Zeenat na kwance akan tafkeken gadon ta kira ya shigo wayarta, sai data fara kallon number kafin ta daga da dan sauri dan bata wasa da duk wani information akan sa "Hajiya barka da safiya." "Barka dai Malam Salihu, ya aiki?" "Alhamdulillah, kina da labarin zuwan iyalan Barrister kuwa?" Wani irin wantsalawa tayi daga kwanciyar da tayi cikin yanayin tashin hankali tace "Iyalai kamar ya? Ban gane ba." "Toh dai gasu nan baki dayan su, mahaifiyar sa, da Yayan dukkan su." "Kan balai! Yaushe har suka shigo garin amma bani da labari?' "Toh gaskiya sai dai ki bincika, nima mamakin ganin su yasa ni kiran ki, bayan kuma naga baki sanar dani zuwan nasu ba." "Ka kyauta, ka sake ajiye min account details dinka ta whatspp, ko da yake, bana harkalla da account, zan aiko driver da cash sai kasha ruwa." "Godiya nake Hajjaju, bari na koma na bibiyar miki yadda ake ciki." "Toh sai na jika Salihu." Mikewa tayi tsaye ta hau safa da marwa a tsakanin dakin nata, ko da wasa bata ji zuwan nasu ba kamar yadda take bibiye da duk wani motsin su. Wayar ta, ta dauka da sauri ta yi dialing number sa. Ta cigaba da zagayen har zuwa sanda ya daga daf da katse "Ya akayi baka fada min zuwan su ba?" "Kano suka zo?' "Auw baka sani ba?" "Ban sani ba wallahi, Kaduna mukayi dasu zasu biki bansan me ya kawo su nan ba kuma, ko Raihana suka zo dubawa?" "Itace ma." Tace tana zame dankwalin kanta, idan ta bud'e baki ta fada musu komai fa? Tabbas tana fadan sunan ta da bayanin zasu gane, shikenan komai zai koma baya kenan. "Yanzu menene abun yi?" Yace jin tayi shiru "Ka kira Hydar kaji yaushe ne dawowar su, a cikin satin nan nake da bukatar key din nan, idan yayi dadewar duniya sati biyu,kai ba ma zan iya jira ba." "Shikenan, zan kira." Kashe wayar tayi da sauri ta sake kiran Salihu, yana daga tsaye a dakin da suke zaune suna jiran fitowar Abbyn, dukkan su cike suke da zumudi musamman da suka samu wani dadadan labari da ya saka su kusan sumewa dan dadi, signal yayi wa Lamido kafin ya matsa daga wajen ya daga wayar "Me yake faruwa Salihu?" "Babu abinda yake faruwa Hajjaju, kamar ma ba zasu samu ganin sa ba gaskiya" Ajiyar zuciya ta sauke da karfi hankalin ta,na dan kwanciya "Shikenan, ka kirani duk abinda ake ciki." "An gama hajjaju." Komawa yayi ciki, ya sake kallon Lamido da shima shi yake kallo, yayi masa alama da hannu ya jingina masa kai kawai.   A hankali ya zuro kafafun sa a karo na farko bayan shekaru masu yawan gaske, kansa ya d'aga kad'an ya kalli sararin samaniya sannan ya sauke a hankali yana cigaba da shak'ar iskar yanci, bayan tsawon lokacin da ya dauka a rufe. _"babu abinda yafi yanci dadi."_ ya furta a kan labban sa    Idanun su na kan kofar kyam ko kiftawa basayi, cikin yanayin farin ciki suke dukkannin su, hannun Raihana na sarke da na Haydar ta kasa nutsuwa ko kadan. Ita ce ta fara gano shi sanda ya fito, ta kwace a guje suka rufa mata baya, idonsa a kanta har ta karaso ta rungume shi kafin ta fashe da wani irin kukan na farin ciki. "Abby...". Suka kira sunan sa a kusan tare cikin yanayin nuna tsantsar farin ciki, jinjina kansa kawai yake ya kasa furta kalma daya saboda tsabar farin cikin da yake ciki, da k'yar Raihana ta cikashi tana share hawayen dake kwance a fuskarta tana had'awa da dariya. "Alhamdulillah Ya Allah." Ya furta bayan ya rungume yan mazan daya bayan daya banda Lamido dake tsaye hannun sa zube a cikin aljihun sa, fuskar sa a sake sai dai yanayin sa be sakashi furta kowacce kalma ba sai jinjina kansa da yake kawai. Kokarin dukawa yake ya gaida Dadah tayi saurin hanashi tana rufe fuskar ta da mayafin ta. Girma sosai ya kamashi duk kuwa da askin da yayi fuskar sa tayi fayau yayi matukar ramewa. Dukkan gandurobobin suka zagaye su cike da farin ciki, shi kansa Abby be san wanne irin yanayi yake ciki ba, tun bayan da ya samu labarin fitar sa a jiya da daddare, wanda ya rasa dalili tunda babu wanda ya sanar dashi dalilin sauyin lokacin da aka samu, shi dai kawai an ce ya shirya yau zai fita daga gidan, hakan kawai ya sani shikenan babu kuma wani bayani da ya biyo baya amma tabbas yasan akwai dalili me girman gaske, da har zai saka a chanja komai cikin dan kankanin lokaci.    Dukkan abinda ya kamata ayi an gama, haka suka rako shi har mota suna daga masa hannu, a hankali ya saka hannu ya share hawayen da ya biyo gefen kuncin sa a boye dan kar ma su gani, ya daga musu hannun suka fita daga harabar wajen. Idanun sa akan titi tunda suka fara tafiya yana mamakin sauye-sauyen da ya gani, yana tuna ganin sa na karshe sanda suka tabbatar sun tura shi prison bayan bashi da shakikai aminai sama dasu.idanun sa ya runtse ranar ta shiga dawo masa akan sa. ****KURMAWA PRISON,KANO.    Karar motar prison din ce ta sasu dagowa suka bi ta da kallo har zuwa sanda ta isa gate din, gandurobobin dake kula da kofar suka tashi da sauri daya daga cikin ya bud'e gate din motar ta saka kanta a ciki, a hankali gate din ya rufe ruf bayan shigar motar. Kallon ta yayi itama a lokacin ta kalle shi sukayi wa juna murmushi "Munyi nasara!" Tace cikin yanayin da yake nuna tsantsar farin cikin ta    "Yes we won!" Yace yana mika mata hannu. Kallon hannu tayi kad'an sai kuma ta zuge zip din jakarta ta ciro envelop me fadi ta dora masa a saman hannun sa "Na cika alkawari." Gid'a kansa yayi cikin yanayin jin dadi yace "Of course." Sai ya tura envelope din a aljihu ya murd'a handle din motar yana kokarin fita "Sai yaushe Barrister?" Tace tana dan karyar da kanta "Sai sanda kika neme ni Hajjaju, for now dai aci duniya da tsinke." Dariya ta kwashe da ita sosai yana tayata kafin ta ware yan yatsun hannun ta, ta kada su tana girgiza kanta "Sai ka ji ni." "Ok..." Yace ya karasa fita daga motar.  Motar sa ya nufa da take dayan side din. Ta zuba masa ido tana kallon sa ya shiga motar  ya kunna ta, yayi horn sannan ya bar wajen. Ajiyar zuciya ta sauke sannan  ta daga waya ta kira driver ta da yake tsaye daga chan gefe tace "Mu tafi." "Ok Ma."  Ya karaso da sauri ya kunna motar suka bar wajen suma.    Kallon daidaikun motocin dake kai kawo a tsakanin titunan garin take har suka kusa isa gida, wayar tace tayi yar kara ta ciro ta, murmushi ya subce mata, a yangace ta daga tana kara ta a kunne kafin ta dan yi baya yadda zata fi jin dadin amsa wayar "Kin kusa karasowa?" Aka fada daga cikin wayar bayan ta yi masa bayanin nasarar su. "Yes muna daf da shigowa, ya kayi da mutanen?" "Nasa aje a tashe su yanzu, sai dai kin karaso zaki ji komai." "Ok..." Tace tana zare wayar. Ba yau ne karo na farko da ta fara samun nasara a duk abinda tasa a gaba ba, haka nan take jin ta sakayau tamkar ta cire wani gagarumin abu daga birnin zuciyar ta, tayi fatali dashi, a yanzu ne zata mike kafarta sosai taci duniyar ta da tsinke! Babu wanda ya taba shiga gonar ta face ta saka kafa tayi fatali dashi daga cikin rayuwar ta, koma duniyar baki daya. Shi yafi komai sauki a wajenta. Barrister NASIR MATAWALLE! Kayi kad'an kace zaka tozartani, ta ja tsaki tayi cilli da wayar akan kujerar. "Abby na!" Muryar Raihana ta dawo dashi daga tunanin bakar ranar, ranar da ya fara kwanan bakin ciki, ranar da yayi kwanan tsaye saboda kwarkwasar da ta cika dakin da aka kira shi da nasa. Ido ya zuba mata dan bata da maraba da mahaifiyar ta zamanin kuruciyar ta, hatta dimple din da take dashi irin nata ne sak. Murmushi yayi mata yana riko hannun ta yana tunawa da rikon da yayi mata na karshe a wanchan lokacin "Raihana." Jinjina kai tayi dan dama tunanin da ya tafi ya sakata yi masa magana dan ta hangi damuwa shinfide a fuskar sa. Daidai lokacin suka isa asibitin Al-ihsan dake titin karkasara,tun suna hanya Babbo Sadeeq ya kira Dr Karaye a waya yace gasu nan, kafin ma su isa shi ya rigasu suna zuwa aka karbi Abby aka bashi gado domin a bashi kulawa ta musamman. Da Magriba Hydar ya maida Dadah da Raihana gidan Addah Maimuna ba dan sun so ba, Raihana har da kukan ta akan ba zata tafi ba. Kayan jikinta ta rage ta shiga wanka dan zafi take ji sosai, tana fitowa Hajiya Zeenat na kiran ta, taga kiran dazu ma amma bata daga ba dan tana tare da yan gidan su kuma tsaf zasu gano ta tunda sun san ita ba wai wasu kawaye ne da ita ba. Abinda ya faru da taje ne ya fado mata,sai kunya ta sake kamata, kamar ta bud'e kasa ta shige dan gani take shikenan a marar kamun kai zai dauke ta. Sake kira tayi dan yau baki daya ba'a nutsuwar ta take ba duk da Salihu yace mata ba'a barsu ma sun gansh ba amma dai tana son duk yadda za'a yi Monday Raihana ta dauko mata key din nan daga nan kuma duk ma abinda yaran suke shiryawa da sauki tunda ta samu abinda take nema a hannun ta. "Wai ba kiran ki ake bane Raihana?" "Dadah wata bakuwar number ce, idan ma na daga shiru akeyi." "Ko dai saurayi kikayi da bakya so mu sani ba. Amma ina ji dazu ma ana ta kiran ki." "A ah ai duk number ce fa." "Toh ai shikenan, idan ma hakan ne ai zamu sani ko ba dade ko ba jima." Wayar ta dauka tayi waje tana wa Dadan dariya, sai da ta zagaya bayan dakunan sannan ta bi kiran aikuwa ko ringing bata ji ba sai ji tayi an daga. "Ina kika shiga daughter ina ta kiran ki." "Ina tare da yan gidan mu ne Anty, ba zasu yarda ba idan suka ji muna waya hanani zasuyi." "Akan me?" "Ba komai, haka kawai suke ." "Toh tunda haka ne karki bari su san muna magana kinji? Ba zan kara kiranki ba sai Monday, nagode da taimakon da kikayi min ranar gashi har Aryan ya koma bakin aikin sa, nagode miki kwarai, Allah yayi miki albarka." "Amin." Tace cike da jin dadi, a duk taraiyar su da Hajiya Zeenat din babu abinda tafi jin dadi sama da albarkar da take saka mata, sai taji kamar mahaifiyar tace take shi mata albarka a duk lokacin da tayi wani abu. Sallama sukayi soyayayr matar na sake ninkuwa a ranta, dan samun kishiyar uwa me kaunar dan mijin ta kamar yadda take kaunar Aryan duk kuwa da baudadden halin sa sai an tona. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 _ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_ _DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_ _MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_ +227 90 16 59 91 *Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na* Maryam sani 0022419171 ACCESS bank Ku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number* 09166221261 Litattafan dai sune kamar haka RUMBUN KAYA Hafsat rano A RUBUCE TAKE Huguma IDON NERA Mamuhghee KI KULANI Hafsat xoxo DAUD'AR GORA Billynabdul *Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥 *RQ*       Page 14 Hafsat Rano Da duku-duku suka tashi ita da Amina suka shirya breakfast din da za'a kaiwa Abby a asibiti, daga nan sai ta wuce wajen aiki ta dau excuse ta dawo asibitin dan tana son zama kusa da Abbyn ta. Wajen karfe bakwai suka fita tare da Muhammad ya sauke ta ya dawo gida ita kuma ta shiga asibitin ta tarar da Abbyn nata yana bacci Hamma Hydar ne kawai a dakin Lamido yaje jigawa wani aiki da Abbyn yayi masa, Dadah da Babbo Sadeeq sun koma Adamawa saboda aikin da ya taso masa. Tana zaune har lokacin tafiyar ta yayi sai ga Lamido ya shigo rike da wata jaka ya ajiye a gefen gadon daidai lokacin da Abbyn ya farka dan tunda yayi sallar asubah yake bacci. Ganin Raihanan a zaune ya sakashi jin dadi, Hamma Haydar ya taimaka masa yayi brush ita kuma ta bashi abinci sannan tace zata je ta dawo. Tare suka fito da Hamman Haydar din ya kaita har office din sannan ya wuce gida ya shirya. Gobe suke san wucewa Adamawa dan Abbyn yace baya son cigaba da zama a Kanon har sun siya ticket din jirgi dan ba zai iya doguwar tafiya ba, amma basu sanar wa Raihanan ba dan sun san dole za'a yi rikici da ita. Attendance ta dauka ta zauna bayan sun gaisa da mutanen dake reception din banda Zainab da ta daina mata magana tun ranar da abin nan ya faru, ita ta manta ma shaf da anyi haka wallahi, sai data ga tayi mata magana taki amsawa ta tuna. Tun daga ranar ta fita sabgar ta itama zatayi mata sallama dai ruwan ta, ta amsa ruwan ta, taki amsawa wannan duk be shafe ta ba. Kira ne ya shigo wayar ta, tana kokarin clearing kan table dinta, tabi wayar da kallo da mamakin dalilin kiran nata a wannan lokacin, hada ido sukayi da Abdulhakeem sai kawai ta d'aga. "Ina kwana Anty?" "Lafiya lou Raihana, kina lafiya?" "Lafiya Lou." "Har kinzo office din ne?" "Eh nazo ban dade ba." "Yawwa, Masha Allah , Aryan ya shigo?" "Ban sani ba wallahi..." "Oga Aryan ya shigo?" Ta dan janye wayar ta tambayi Abdulhakeem, girgiza mata kai yayi alamar a ah "Be shigo ba wai." "Toh shikenan, naji alamar kina cikin mutane, ko zaki dan matsa gefe?" "Toh." Tace tayi hanyar fita daga office din nasu, ta nufi kitchen din dan tasan nan ne kadai za'a samu ba kowa. "Yawwa kina jina? Akan matsalar nan ta Aryan ce, kinsan nace miki muna zargin duk magungunan sa baya sha ko? Toh shine likitan sa yazo kin ganshi zaune ma, da zaki taimaka ki samo min key din gidan nan nashi, akwai in da yake ajiye su tabbas kuma a gidan ne, dole mu san halin da yake ciki dan ciwon idan yayi worst har haukacewa anayi Raihana." Sai ta fashe da kuka sosai, kukan da ya sake karyar mata da zuciya cike da tausayawa tace "Aina key din yake?" "Aljihun suit dinsa, yau ita zai saka saboda yana da meeting da shareholders, anan zaki samu idan kin dauko ki zarto gidan kawai ki kawo min da sauri, karki bari ya san bakya nan dan zai iya zargin komai." "Ok,zan kawo in sha Allah." "Tunda kin shigo sai ki karasa ladan ki, ki dafa mana shayi." Kamal yace yana daga kofar kitchen din, zare wayar tayi daga kunnen ta, sannan ta gaishe shi. "Lafiya lou, naje office dinku ai Abdul yace kin fito, ashe ma kina dayan office din naki" Murmushi tayi kawai, ya ja mata kofar ita kuma ta shiga fiddo da kayan da zata bukata. A makare ya shigo office din dan haka yana zuwa akan aiki ya dira, ya shiga duba abubuwan da yayi ragowa kafin meeting din nasu da yake karfe biyu. Tunowa yayi da wani aiki da be karasa ba, sai ya jawo landline din dake saman desk din nasa ya shiga kiran office din su. Abdulhakeem ne ya daga ya tambaye shi ko tazo,tana kitchen yace masa sai yace shi yazo, ya ajiye wayar ya dauko takardar daidai lokacin Abdulhakeem din ya shigo ya bashi takardar yace ya kai mata yana son result in less than an hour. Karba yayi ya fita shi kuma ya cigaba da abinda yake yi.    ***Tana tsaye gaban coat din sa dake rataye a jikin hanger da yake makaleta kullum yazo office din, waige-wage take tana son yin sauri ta dauki key din, sai da ta tabbatar da babu motsin kowa tayi saurin saka hannu a aljihun rigar ta jawo key din ta damke a hannun ta. "What are you doing..." Ya fada yana tsaye daga bayan ta Saura kiris glasses din idon ta ya fadi kasa, tayi saurin tare shi da dayan hannun ta juyo tana kallon sa. Takowa ya shiga yi har zuwa gabanta yana kare mata kallo tun daga sama har k'asa, kafin ya maida kallon sa zuwa wajen coat din tashi dake sakale. "Me kike yi anan?" Yace muryar sa a d'an shake yana kallon fuskarta, kanta ta sunkuyar kasa sosai ya cigaba da kallon ta a nutse kafin yace "Are you trying to steal something?" Zaro idanun ta, tayi da sauri ta hau girgiza kai "Then tell me, me kike min a wajen rigana?" "Am..am... Dama nazo na kawo maka wanchan report din da na hada ne, so sai na tarar kana restroom shine na ajiye a saman table shine sai naga kamar wani abu a saman rigar shine nazo zan duba na cire maka." Dan jim yayi yana kallon ta, kafin ya ja siririn tsaki ya nufi wajen zaman sa ya zauna. "Show it to me." Yace yana jan mouse ya dora hannun sa akai. Fakar idon sa tayi ta tura key din a cikin aljihun jacket din dake jikin ta sannan ta karaso ta dauki report din ta bud'e ta fara masa bayani. Danne dannen sa yake har ta gama sai da yaji tayi shiru sannan ya dago ya dan kalle ta "Ina jinki." "That's all." Tace "Shikenan abinda kika iya samu?" Gid'a kanta tayi kad'an "Come here." Yace yana maida kansa ya cigaba da abinda yake, gefen sa ta matsa ta tsaya daga dan baya "Result din nake son gani, show it to me." "Ok!" Tace ta dan runkwafo kad'an ta shiga nuna masa. Kamshin turaren ta ne ya shige masa chan cikin hancin sa ya haifar masa da mixed feeling, dan muskuta jikin sa yayi yadda ba zata gane ba amma still yana jin kamar sake matso shi tayi. "It's ok!" Yace da dan karfi "Just go, ki tura min ta email zan duba anjima." "Ok...Thank you" Tace dauki report din zata fita "Wait..."  Yace ta juyo ta tsaya "Ki bawa Kamal shayi na ya kawo min." "Ok sir." "Sannan...karki kara saka turare me karfi idan zaki zo aiki." "Na'am?" "You heard me right! You may leave." "Ok."  Tace da saurin ta, ta fice hadda dan gudun ta   Tana fita ya saka hannu ya hau janye necktie din wuyan sa yana mikewa tsaye, ya isa gaban dan madaidacin fridge din sa ya dauki ruwa me sanyi ya hau sha "May I come in?"   Ya turo kansa ya rike kofar ba tare da ya shigo ba "Kana da matsala, kayi ta tsaiwa a wajen." Yace yana dire robar ruwan ya shiga takawa zuwa seat din sa ya zauna. Shigowa yayi ya rufe kofar ya samu waje ya zauna shima yana murmushi "Ya akayi?"  Yace yana duban sa "Akwai babban labari..." "Kamar na me fa?" "Barrister Nasir Matawalle is out!" "What!!!? Ya fada yana mikewa "Da gaske ko da wasa?" "Allah kuwa, naji labari daga majiya me karfi ya fito last week ending, but zancen dai be fito sosai ba dan kamar yaran sa ne basa so a sani saboda suna so ya samu kulawa ta musamman ne." "Alhamdulillah!" Ya fada a hankali yana maida kansa baya ya jingina da jikin kujerar yana lumshe idon sa. "Me ya kamata ayi yanzu?" Kamal yace ganin yayi shiru, bud'e idanun sa yayi ya zauna sosai yace "Time zamu samu muje mu ganshi, inaso na ganshi dan shi kadai yasan abinda ya samu Mom, shi ne kawai zai taimaka min na cika buri na." "Kana ganin bud'e case din ba zai zama matsala ba? Kasan fa Daddy baya so, sannan sau nawa kana zuwa prison dan ganin sa amma yaki, kana ganin zai saurare ka yanzu bayan da be saurare ka ba?." "I don't know... " Yace yana tuna jelar zuwa prison din da ya dinga yi dan duk ya samu ganin shi amma fafur yaki yarda su yi wata doguwar magana. "Toh yanzu dai menene abun yi?" "Zuwa zamuyi mu ganshi din, ba kuma zamu hakura ba har sai ya hakura ya ganmu munyi magana, he's my only hope." Shiru ya danyi sai ya dora "Gaba daya rayuwata na yi ta ne akan jiran wannan ranar, that's what keeps me going, ba zan taba hutawa ba har sai na san abinda ya samu Mommy, wannan alkawari na ne, sai na bi kadin mahaifiyata, ko da hakan na nufin..." "Shikenan, shikenan.  You have my support, Allah ya bayyana mana gaskiya." "Amin! Thank you." Yace yana hasaso abinda zai faru kuma, ajiyar zuciya ya sauke ya sake tashi da nufin dauko key din nan ya bawa Kamal. ***Tana fita daga office din nasa ta dauki handbag dinta akan table ta zare rigar saman ta ajiye ta fita da saurin ta, a titi ta tsaya ta kira wayar tana kokarin tsaida me napep "Hello..." Tace tana fadawa cikin napep din bayan ya tsaya "Eh na dauko, ina hanya ma." Magana akayi daga dayan bangaren tace; "Ok tam.." ta kashe wayar tana sake duba key din ta tabbatar yana ciki. Tafiya kad'an suka isa unguwar, ta bashi kudin sa ta sauko ta karasa gidan a kafa.   Ciki ta shiga bayan an bud'e mata kofar tangamemen gidan da kaf unguwar babu me girman sa, yau ne karo na biyu da ta zo gidan amma sai take ganin kamar yau ne karon farko. A hankali take tafiya tana karewa gidan kallo har ta isa main part din. Tana zuwa daidai kofar ta bud'e da kanta, ta saka kanta ciki bakin ta dauke da sallama.    Tana hakimce a saman daya daga cikin kujerun falon rike da door remote din dan ita ta bud'e mata kofar dan ta hango ta tun sanda ta shigo gidan. "Rayhana..." Ta kira sunan ta tana sakar mata murmushi, murmushin ta maida mata itama ta gaishe ta a nutse sannan ta sa hannu ta ciro key din ta mika mata "Good! Kin taimaka min sosai kamar yadda nima na taimake ki, kin saka alkhairi da alkhairi nagode sosai." "Ba komai Aunty!" Tace tana murmushin jin dadi "Me zaki sha a kawo miki?" "Ba komai, komawa zan kar ya gane na fita." "Ok! Zan kiraki kinji?" "Ok." Ta mike tana rataya jakarta tayi hanyar fita "Kin ga jirani mu fita dake dan nima wajen hanyar taku zanyi." "Ok nagode." Tace ta koma ta zauna ita kuma ta tashi ta shiga ciki bayan ta dora wayarta a saman hannun kujerar da Batul din ke zaune. Tana zaune wayar tayi yar kara alamun shigowar sako, kallon wayar tayi sai ta dauke kanta kawai tana cigaba da more kallon dankararren falon. Wani sakon ne ya sake shigowa a wannan karon sai ta kasa dauke idon ta akai ta shiga karanta sakon da yake yawo a saman wayar _"An gama hajjaju, an zuba poison din, wuyarta Aryan yasha tea din nan, sai dai wani ba dai shi ba, tunda mun samu key din sai kiyi kokarin kwashe duk wani abu da ya tanada as evidence, ita kuma yarinyar ita za'a kama da case din poison din, kinga shikenan mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya!!"_ Wani irin sarawa kanta yayi cikin yanayin tashin hankali ta mike tsaye "_Na shiga uku!"_ Ta furta tana dafe kirjin ta. _" Amfani dani tayi kenan? Karya tayi min tasa na dauko mata key din? Duk abinda ta fada min akan sa kenan karya take?."_  "Shayi? Wayyo innalillahi." Ta fada gabanta na faduwa _"Ya Allah!!!"_      Da sauri ta juya har da dan gudu-gudu ta fice daga falon. Tana fita Hajiya Zeenat ta fito, mamakin rashin ganin ta ya kamata ta shiga kiran sunan ta, waya ta dauka ta kira gate ta tambaya aka ce mata yanzu ta fito ta fita "Ok... Ta huta" Ta dauki wayoyin nata ta watsa su a handbag dinta ta shiga kwalawa mai aikinta Harira kira   ****Yadda take gudu zaka dauka mahaukaciya ce sabuwar kamu, kamar zata fada duk napep din da tazo haka ta dinga bin su idan ta tsaida su basu tsaya ba, a karshe ta samu wani ta fada tana haki. Suna isa ta ciro kudi bata duba ko nawa bane ta cilla masa ta shiga building din a guje. Bata san in da take jefa kafarta ba har ta isa reception din, baki daya ma'aikatan wajen duk suna tsaitsaye sun yi cirko-cirko, kallon ta suka shiga yi irin kallon tuhumar nan, jikinta ne ya hau rawa tayi saurin haurawa sama zuwa office din sa. Kofar sa a bud'e take sabanin yadda take a rufe a kowanne lokaci, maganganu ne ke fitowa daga ciki wanda ta gaza fuskantar daya daga ciki, ji tayi kamar an dode mata jin ta, burin ta kawai ta isa ciki ta tabbatar da be sha shayin nan ba, kowa yasan Aryan da masifar son hadin shayi me na'a na'a da sauran nau'ikan kayan kamshi. Duk da rashin yardar sa da kowa amma ya kan sha shayin wanda ya yarda ta hada masa ita kadai, shi ma sai da Kamal ya tabbatar masa da babu wata matsala sannan ya amince. Idanun ta ne suka sauka akan Kamal dake dauke da tsantsar tashin hankali shinfide a saman fuskar shi, ji tayi tamkar an sassare mata guiwowin ta, ta zube a wajen tana fashewa da kuka. "Na shiga uku." Kawai bakin ta ke furtawa. Ji tayi an saka hannu an tura kofar office din, shiru ya biyo bayan hakan sai shashekar kukan ta dake tashi hade da garar A.C da aka kureta sosai har take fitar da sound me dan karfi. Durkusawa yayi a gabanta ya toge hannun akan cinyar sa. Kamshin turaren sa ne ya doki kofofin hancin ta, tayi saurin dago jajaye idanun ta da suka yi matukar rinewa saboda kuka. Ganin sa a durkushe a gaban ta ya sakata zabura. "Me ya faru?" Yace yana zuba mata ido muryar sa a matukar dashe saboda tsabar bacin ran da yake ciki. Mikewa tayi tsaye, ya saka hannu ya jawo ta da dan karfi har sai da tayi yar kara, ya kalli hannun nata ya dauke kansa yana girgiza mata kai. "Menene?" Ya sake maimaitawa har lokacin idanun sa dake matukar shanye na kanta ya zuba mata su. Girgiza kai ta hau yi da sauri da sauri, zatayi magana kenan Kamal yayi saurin katse ta "Ga key din Aryan, ashe nan ya fada." Dago idanun sa yayi, ya kalli hannun Kamal din da yake rike da key din da suke ta nema tun bayan fitar ta, mikewa yayi daga durkuson da yayi ya karbi key din yana kallo, sai kuma ya damke shi sosai yana sauke ajiyar zuciya "Jeki Raihana, jeki jirani a office dina." Kamal yace yana takowa gabanta, kasa mikewa tayi sai kukan da take yi har da shasheka. Sake maimaitawa yayi ta dafa da k'yar ta tashi, ta bud'e kofar ta fito ta nufi kitchen din da sauri dan a chan ta bar shayin tun bayan ta gama, ta kuma tuna da yace ta bawa Kamal ya kawo mishi bata bashi ba dan hankalin ta yayi gaba. A ajiye ta ganshi sai dai ba yadda ta barshi ba, tana kalla ta san an taba. Sauri sauri ta juye shi a sink ta wanke kayan. A tsaye ta samu Kamal din yana kaiwa da komowa, jin ta shigo ya saka shi saurin kallon kofar. Kanta a k'asa sosai ta karaso ciki ta samu waje ta zauna. Kofar ya rufe sannan ya dawo ya zauna yana duban ta "Ina key din?" Yace mata kai tsaye, shar-shar-shar hawaye ya shiga biyowa kuncin ta, tissue ya mika mata da sauri "Yanzu ba lokacin kuka bane ba, yana ina key din?" "Hajiya Zeenat ce tasa na dauko mata." Kad'an ya rage be fado daga kujerar da yake kai ba, yadda yayi wata irin zabura saboda tsananin mamakin abinda tace. *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *RQ*       Page 15 Hafsat Rano •••••• A tsaye ta samu Kamal din yana kaiwa da komowa, jin ta shigo ya saka shi saurin kallon kofar. Kanta a k'asa sosai ta karaso ciki ta samu waje ta zauna. Kofar ya rufe sannan ya dawo ya zauna yana duban ta "Ina key din?" Yace mata kai tsaye, shar-shar-shar hawaye ya shiga biyowa kuncin ta, tissue ya mika mata da sauri "Yanzu ba lokacin kuka bane ba, yana ina key din?" "Hajiya Zeenat ce tasa na dauko mata." Kad'an ya rage be fado daga kujerar da yake kai ba, yadda yayi wata irin zabura saboda tsananin mamakin abinda tace. Fashewa ta sake yi da wani irin kuka, ya mike tsaye yana mata wani irin kallo, kafin ya nuna ta da hannun sa "Dama kece spy din?" Girgiza masa kai ta hau yi da sauri "Wallahi yaudara ta tayi, bansan me yasa tayi amfani dani, amma wallahi bani da burin cutar da kowa." Yadda take kuka sosai ya sakashi samun waje ya zauna, a kalla zai bata damar jin ta bakin ta kafin ya yanke mata hukunci, dan yasan wallahi in dai har Aryan ya gano tana da alaka da Hajiya Zeenat shikenan an gama, ba ita ba kuma, duk wani da yasan yayi wata alaka ko mu'amula da ita babu shi babu su. "Sai kiyi min bayanin komai, sannan karki yi mun karya." Bayan hannun ta, tasa ta goge hawayen da yaki tsayawa sannan a hankali ta soma bashi labarin haduwar su da Hajiya Zeenat da duk abinda ya faru, da fara aikin da tayi dasu har zuwa gidan Aryan din da tasa ta taje, da kuma sakata daukar key din duk a tunanin ta taimakon Aryan din zatayi. "Bayan na bata key din ta shiga ciki, anan na gane amfani tayi dani, suna maganar sunyi poisoning tea dinsa..." "Poison!!!" "Haka na gani an turo mata message, abinda ya saka ni tahowa a yanayin nan kenan, bansan abinda suke shiryawa ba kenan, wallahi ban sani ba." Mikewa tsaye yayi dan zaman ma ya gagareshi, wajen kofar ya koma ya bud'e ya leka ya tabbatar babu kowa a wajen sannan ya maida ita ya rufe ya dawo ya tsaya yana zagaye a dakin "You have indeed dodged a bullet, da Aryan yasha shayin nan fa?" Yace da muryar sa da take nuna yanayin tashin hankalin da yake ciki da wannan labarin Girgiza kai tayi har lokacin hawayen yake tsayawa sam "She used you Raihana, tayi amfani dake ta samu abinda take so, a karshe ta dora miki blame din kamar yadda tayi a baya, da ace Aryan yasha tea din nan, da ba maganar da ake yi yanzu ba kenan, saboda ba zaki taba fita ba, ba zaki fita ba sam." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allahuma ajirni fi musibati..." "Kin gama magana Rayhan, tunda kika ambaci Allah. Sai dai akwai babbar matsala." Kallon sa tayi da alamar tambaya ya dora "Yadda na san Hajiya Zeenat, bata taba barin abinda ta saka a gaba, sannan kin riga kin shigo circle din, dole dole ki san me yake faruwa, sai dai, dole a yanzu ki cigaba da bin ta a yadda kuke da, karki kuskura ko da wasa ki nuna mata kinsan shirin ta. Hakan shine kadai kwanciyar hankalin ki, kuma hakan shine zai taimaka mana mu kara sanin duk wani shirin ta." "Wayyo Allah nah, wallahi ni tsoro nake ji." "Me kike so ayi?" "Garin mu nake son komawa, bana son cigaba da zama anan, tsoro nake ji dan Allah." "Service din fa?" "Innalillahi." "We have to do this together Raihana, ki taimaki rayuwar Aryan, dan Allah ki taimaka mana..." Sai ya dora "Na chanja key din nan bayan na samu leakage na son daukar, amma bansan wa zata saka ya dauka mata ba, saboda yadda Aryan yake kaffa-kaffa dashi zai yi wuya a yi dauka, ashe tayi amfani dake ne, saboda bayan Ya Nabeela dani babu wani da Aryan yayi saurin trusting sama dake, bansan me yasa ba, amma ko ma menene kina da babban tasiri a gare shi, dole zaki taimaka muyi aikin nan tare in har kina son ceto rayuwar sa, labarin sa yana cika da abun tausayi da tashin hankali wanda idan kika ji ke da kanki zaki yarda da yana bukatar taimako." Kukan ta ne ya rinjayi maganar da take son yi, bata son tashin hankali ko kad'an dan bata taso a cikin sa ba, bata taba sanin akwai irin wannan rayuwar ba sai yau, ta kan yi tunani sosai akan dalilin da ya saka Abbyn ta zaman prison amma kuma bata samun gamsashiyar amsa a wajen wanda ya kamata su sanar mata. Duk da tana da yakinin sharri akayi masa, dan ta tabbata Abbyn ta baya cikin mutane marasa kirki sai dai kaddara da ta riga fata. Sai dai a yau ta sake tabbatar da akwai tarin mutane masu bakar zuciya a doran kasar nan, masu halin Hajiya Zeenat wanda zasu iya yin komai akan cikar burin sa. Tun farkon haduwar ta shirya komai, ta dora ta akan tsarin ta da abinda take so, dalilin ta kenan na kawota aiki a wajen. Duk cikin plan din ta ne. Ya zatayi yanzu? A yanzu lokacin farin ciki ne a gare su na fitowar Abbyn su, ba zata so tayi wani abu ko tazo da wani abun da zai saka yan uwanta a tashin hankali ba, sun mata dukkan gata, sun fifita bukatar kansu akan tata, dole tayi kokarin ganin ta danne damuwar ta zuwa lokacin da Abbyn ta zai warware baki daya.   Kiran wayarta da akayi ne ya katse mata tunanin da take, ta share hawayen sannan ta daidai ta muryar ta sannan ta d'aga "Hamma na." "Me ya faru? Baki da lafiya ne?" Yace mata dan duk yadda taso ta daidaita muryar ta sai ya gano ta "Cikina ne yake ciwo." Tayi karya dan tasan idan tace mishi babu komai ba yarda zai yi ba "Subhanallah, bari nazo na dauke ki, ki nemi excuse a wajen aikin dan Abby yace gobe tare zamu tafi dake, idan kikayi sati daya sai ki dawo." Kallon Kamal tayi shima ita yake kallo kuma yana dan jiyo muryar Hydar din, gid'a mata kai yayi alamar eh "Ok tam, sai kazo Hamma." Ta zare wayar "Yayanki ne?" "Eh." Tace a sanyaye "Shikenan, ina ganin hakan zai taimaka miki ki samu hutu sosai, next week sai ki dawo idan Allah ya kaimu, zan ma Aryan magana." "Nagode." "Ba komai, kiyi kokarin boye damuwar kar ki yarda ta gane." "I will try." "Yawwa, Adam yazo neman ki dazu, abinda ya faru kenan har kika ga Aryan a cikin yanayin da yake ciki, muna cikin neman key din ya shigo yana neman ki, abinda ya bata ran Aryan kenan har suka dan samu matsala. Akwai wata alaka tsakanin ki da Adam din ne?" "A ah, babu komai." "Ok ki kula sosai." "In sha Allah." ***Duk da kasancewar mukullin a hannun sa amma ya kasa nutsuwa da abinda ya faru a dan lokacin, ya akayi ma key din ya fada kasan table din sa bayan tunda yazo be ciro shi ba. Menene matsalar ta da har zata zo tana rusa musu kuka haka bayan babu wanda yasan dalilin fitar ta daga office din cikin gaggawa. Tun ranar da ta sanar dashi mahaifiyar ta, ta rasu yaji tausayin ta ya tsarga masa, ya hasaso kalar rayuwar da 'ya mace zatayi ba tare da uwa wadda ta kasance jigo ba. Tabbas akwai abinda yake damun ta, dan har tayi yunkurin sanar dashi sai Kamal ya katse ta, ta hanyar maganar key din. Ya kamata su nemi ba'asin dalilin kukan nata wanda yayi kama da na wanda ya shiga mummunan tashin hankali. Da farko ya dauka akan key din ne wanda tashin farko ita ya zarga dan yana dubawa da yaga babu ya tuna sanda ya ganta a tsaye a gaban rigar sa, sai kuma ya aika a kirata aka ce masa bata nan, dalilin da ya daga hankalin sa kenan, sai kuma zuwan Adam da ya sake dagula masa lissafi baki daya. Drawer ya bud'e a jikin table dinsa ya ajiye key din, sannan ya rufe. Ya tashi ya fita zuwa wajen Kamal domin akwai abubuwan da yake da bukatar sani. Tana kokarin fitowa daga office din yana shigowa, saura kiris tayi karo dashi tayi saurin yin baya. Tsayawa yayi ya toge a jikin kofar yana kallon ta, kanta a k'asa saboda tsabar nauyi da kunyar sa da take ji. Kamal ne ya tako zuwa wajen yace "Ina ganin ya kamata mu fara shiryawa meeting din ganin saura lokaci kad'an." "I'm not attending, kayi representing dina." "Why?" Ya saka masa ido "Fita zan yi, zanje naga Dr Ma'aruf." "Ok ok"  Sai ya juya wajen Rayhana "Sai next week kenan?" Kamal yace ganin duk ta takura gashi Aryan din ya babbake kofar kuma ba zata iya bud'e baki tace masa ya matsa ba "Next week?" Aryan ya tambaya "Yes zata dan je gida ne, bata jin dadi so ta nemi permission nace ta huta this week." "Me yake damunki?"   Yayi directing tambayar kanta, duburburcewa tayi dan a tsorace take gani take zai gano abinda tayi ko kuma ma ya sani. "Let her go please Aryan, Raihana jeki Allah ya kara sauki." Kallon sa yayi kamar zai magana, sai kuma ya fasa ya dan matsa mata daga hanyar tayi saurin wucewa. Tabe baki yayi ya juya ya bar Kamal din a tsaye, be san yaushe ya fara damuwa da abubuwan da basu shafe shi ba har ya bada kulawar sa kamar haka. Key din kawai ya dauka da jacket dinsa, ya jawo office din ya koma ya bawa Kamal mukullin sannan ya tafi. ***Tunda ta fito daga office din Aryan din zuwa fitowar ta daga na Kamal ta lura da wani irin kallo da yan office din suke mata, ita kanta tasan tayi abun a kalleta sai kuma yanzu take tuno a yadda ta shigo wajen dole ta zama abun kallo kuma topic of discussion. Tazo daidai wajen da Zainab suke zaune tare da wata Cynthia sai kuwa Zainab din ta taso ta tare ta "Menene matsalar ki ne wai ke?" "Attention seeker ce kawai."    Cynthia tace itama tana tasowa. Kurar dake kan Raihana tafi karfin ta bata lokaci wajen kula su dan ta lura so suke su kular da ita. Kin maganar da tayi musu ne ya sake tunzura su, suka shiga fada mata maganganu tayi biris kamar bata ji ba, ta wuce office dinsu ta dauki abinda zata dauka ta fito lokacin Hamma Haydar ya karaso yana chan gate dan haka ne ma ta sake banza dasu kar su sake bata mata lokaci har Aryan ya san abinda ya faru.    Jiki a sanyaye ta isa wajen motar ta bud'e ta shiga tana sauke ajiyar zuciya. Cike da kulawa yake duban ta kafin ya sa hannu a saman kanta ya taba. "Tun yaushe ne baki da lafiya? Gashi har jikin ki yayi zafi." "Dazu ne Hamma, muje inaso na kwanta." "Asibiti zamu wuce ai, ba gida ba." "Asibitin da Abby yake?" "Eh nan zamu." "Ok." Tace. Matsowa yayi ya kwantar mata da kujerar yadda zata ji dadi ya gyara mata kanta sosai sannan ya tada motar suka bar wajen. * *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *RQ*     16 Hafsat Rano ***Duba lokaci Kamal yayi ya tuna karfe biyu suke da meeting din, akwai sauran kusa awa daya. Yana bukatar yayi abinda zai yi kafin lokacin. Computer ya jawo ya shiga ya tura musu da email na shifting time din meeting din zuwa karfe uku. A gurguje yayi komai be jira reply din su ba, ya kashe computer din ya dauki key din ya fita da sauri. Fitar su dukka a lokaci kusan daya ya sake saka su Zainab a kundin tunanin abinda yake faruwa. Da farko Aryan sai kuma Raihana yanzu kuma Kamal kuma dukkan su basa cikin yanayi me dadi. Maganganun suke cigaba da tattaunawa har zuwa lunch time sannan kowa ya tashi don neman abinda zai sakawa cikin sa, masu sallah kuma suka tafi yin sallah kafin cin abincin.    Da hannu daya yake driver dayan kuma yana kokarin kiran Aryan din ya tabbatar da in da abinda yake da wajen da yake a lokacin, be d'aga ba dan haka ne ma ya cigaba da kiran nasa har ya iso kofar gidan, amma ta baya. Ajiye motar yayi a wajen sannan ya zagayo gate din yana katse kiran ya tura wayar a aljihu kawai ya kwankwasa. Baba maigadi ne ya taso yazo ya bud'e yana ganin shine ya fadada fara'ar fuskar sa suka gaisa ya shiga ciki sannan yace "Zakuyi baki anjima kad'an Baba, ku dan je kauye na kwana biyu zan kira ka a waya sai ku dawo, ga kudin mota da na dan abinda za'a bukata." Ya ciro kudi ya mika masa "Lafiya dai ko?" "Lafiyar za'a ce Baba, amma dai kuyi tafiyar ku dan idan suka zo suka nemi abinda suke nema basu samu ba, zasu iya huce haushin akanku." "Toh Allah ya rufa asiri, ku kula dan Allah Kamalu, ku kula sosai da kanku dan Allah." "In sha Allahu Baba,ku taya mu da addu'a." "In sha Allahu." "Yawwa Baba, ku hanzarta dan Allah, karku bata lokaci dan nasan daf suke da zuwa." Da sauri ya juya ciki ya samu Hajara na wanki,ajiyewa tayi suka dau dan abinda zasu dauka suka fito.   Direct chan cikin bedroom din Aryan din ya shiga ta hanyar amfani da key din, wajen Safe din ya nufa da dan saurin sa, ya bud'e ta hanyar saka security code din ya tattaro dukka abin da yake ciki ya fito dasu hade da wani dan karamin flash ya tura shi a cikin wandon sa sannan ya ajiye wani empty disk hade da wasu tarin takardu yayi sealing dinsu a wata babbar envelope ya maida ya rufe ba tare da ya rufe ruf ba. Jakar da ya shigo da ita ya zuge ya saka komai sannan ya goya ta ya nufi kitchen dan samun ruwa duk yanayin komai a gurguje ne yana amfani da lokaci. Ledar dake saman island din kitchen din ce ta dauki hankalin sa, ya bud'e ganin Apple a ciki sai ya girgiza kansa dan da alama ya kwana biyu a wajen Aryan din ma ya manta dashi, jawo jedar yayi, ya kwashe su daga ciki ya zuba a wata container sannan ya saka a fridge ya rufe ya dauki pack din da niyyar sakawa a dustbin sai yaji kamar abu a jiki. Hannu yasa ya taba sai yaji dan karamin abu, dubawa yayi sai ga wata yar karamar camera a jiki an saka ta daga chan kasan yadda ba zaka taba gane akwai ta ba, ba ma kowa be zai san camera bace ba ,shima dan aikin sa ne, aikin da ko Aryan be san shi da shi ba, aikin da ya dau tsawon lokaci yana yin sa duk dan cimma wata manufa. Cire ta yayi daga jiki yana girgiza kansa, tabbas Hajiya Zeenat ce ta saka, kuma tabbas Raihana ce tazo da ita dan babu wani mahaluki da ya shigo gidan bayan Aryan, sannan apple baya cikin fruits din da Aryan din yake so balle har ya siya. Tambarin da yake jikin dan kwalin ya zubawa ido, sai ya ciro wayar sa ya dauka a hoto sannan ya shiga dudduba ko ina a gidan ko akwai wasu cameras din sai dai be gani ba. Ko ruwan da yayi niyyar sha be sha ba,dan ya sake bata lokaci sosai dan delay din da ya samu. Karar mota yaji da karfi sai kuma yaji alamun ana kokarin shigowa gate din gidan, kofar baya da take a cikin kitchen din bayan wata babbar drawer wadda zaka rantse kawai drawer ce a wajen amma kana bud'e ta zaka ga kofa a wajen ya nufa, ya bud'e ya shiga sannan ya rufe daidai lokacin da suka shigo falon. Suna da kowanne key na gidan dama, na dakin sa ne kawai basu dashi samun sa a yanzu shi ya basu kwarin guiwar shigowa a lokacin. Sun riga sun san lokacin da Aryan yake zuwa gidan shiyasa suka zo a wannan lokacin. Su hudu ne karti majiya karfi, a zahiri Kamal zai iya kiranyan sanda a yanzu ganin sun shigo gidan amma kuma sanin wacece Hajiya Zeenat ya hanashi dan ita din me karfin fada aji ce, waya kawai zatayi a fitar dasu, shiyasa gwara su bi komai a hankali suyi mata kamun da ko ubanta ne shugaban kasa ba zai iya fitar da ita ba. Agogon hannun sa ya taba wanda ya kasance smart watch sannan ya karasa ficewa daga gidan. Suna zaune a harabar gidan akan fararen kujerun nan,hannun ta rike da glass cup fuskar cike da annuri dan tana da yakinin zuwa yanzu Aryan ya gama, kuma ta samu abinda yake tunkaho yake mata barazana dashi. Faifan CD da yake dauke da komai, wanda tayi tunanin ta shafe shi daga doron kasa, ta hanyar batar da shi da kuma batar da mamallakin sa. Bata san yadda akayi Aryan din yake da shi ba, dan iya binciken ta bata samu amsar ba. Dagowa yayi daga dukufa da yayi akan system din ya juyo mata gabanta yana pointing hannun sa akai "Waye wannan?" Kallon screen din tayi kad'an kafin tace "Kamal ne." Wani abu ne ya fado mata, ta sake juyo da system din da sauri ta zubawa video din ido "Me yake yi a gidan?" "Ya cire camera din Hajiya." "Oh shit! Me yasa yaron nan yake shiga gona ta ne???" Tace tana dire cup din hannun ta "Kyale shi kikayi Hajiya." "Ba tashi nake ba yanzu, ka rabu dashi zan dawo kansa ne, ta uban gidan sa nake yi kuma ina jiran kyakkyawan labari." "Amma shirun yayi yawa, da wani abu ya faru da tuni kin karbi wayoyi ba ma waya ba." "Eh toh! Hakan ne kuma. Bari..." Ta dauki wayar ta, ta shiga call log tayi dialing number. "Ya naji shiru?" Tace yana dagawa "An samu matsala!" "Whaaat! Matsala? Ban santa ba, ban taba samun ta ba tunda nazo duniya, ban gane me kake nufi ba." "Kiyi hakuri Hajiya, Aryan be sha tea din nan ba, Oga Adam ne yazo ya dagula komai." "Adam! Adam? Ban gane ba." "Zuwa yayi a daidai lokacin da ya kamata ace ya nemi tea din, yazo ya hargitsa komai suka dan samo sabani da oga." "Ina ita Raihanan?" "Ta tafi, dan sanda naga oga Adam ya shigo har an fara samun sabani sai na fice, yanzu na dawo ba oga Kamal, ba oga Aryan itama kuma bata nan." Kit ta kashe wayar tana mikewa tsaye, ya za'a yi mata haka? Yaushe ta fara shirya abu yana watsewa haka? "Me ya faru?" "Babu nasara." Murmushi yayi ya maida kansa ya cigaba da abinda yake yi. Tana tsaye bacin rai ya cikata wata wayar ta sake shigo mata, a sukwane ta dauka dan idan aka samu wata matsalar yanzu kuma shikenan. "Ya akayi Gaza?" "Mun dauko kayan nan Hajjaju." Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta zauna sharaf tana sharce gumi. ***Abby na zaune ya jingina bayan sa da pillow, Lamido na ta wajen kafarsa ya dora kafar Abbyn akan tasa kafar yana matsa masa a hankali. Rayhana na kwance a carpet bayan tasha magani ta lulluba har kusan kanta dan a tsorace take sosai da abinda ya faru wanda yayi effecting dinta har ya saukar mata da zazzabi me zafin gaske. "Uwata?" Abby ya kira ta ganin ta juyar da bayan ta, tana rufe idon ta. Juyowa tayi ta dan yaye rufar ta sama tana marairace fuskar ta "Kasan nan akwai sanyi gashi kina zazzabi, tashi Haydar ku tafi, sai ku fito da wuri idan Allah ya kaimu." "Abby anan zan kwana." Tace kamar zatayi kuka "A ah uwata, kije dai gida ki huta kiyi wanka da ruwan zafi kinji." "Bata fa ci abinci ba ma kamar Abby." Lamido yace yana kallon ta "Hamma fa naci." "Kad'an ba, kuje Hydar ka samar mata abinda take so ko a hanya ne, sannan ka tabbata taci idan ba haka ba kuka zo gobe sai dai su yi mata alluran gaskiya." "Gaskiya dai kuwa." Abby yace shima. Tashi tayi da k'yar kamar zatayi kuka, ta saka Hijab dinta suka fito tana jin kamar iska zata dauke ta saboda rashin kuzari. Suna fita Lamido ya mike ya dauko jakar da ya shigo da ita da safe ya zaro abubuwan da suke ciki ya mikawa Abby "Sun cika komai Abby." "Masha Allah." Ya karba ya duba, sannan yace "Ya kukayi da Salihu?" "Be sanar da ita ba tukunna, dama jiran abinda zaka ce muke, ya dai barta a matsayin bamu ma samu ganin ka ba, yadda ba zata bibiyi kowa ba." "Sai ya sanar da ita yanzu ai, ina son haduwa da wanda ya taimaka fitowa ta duk da sun ki fada min saboda ya hana, amma ko waye yana cikin harkallar wanchan lokacin, zan dawo dawowa ta musamman, ba kuma zan yi bacci ba har sai na tabbatar da na tura Zeenatu gidan kaso!" "Abby kana bukata hutu sosai yanzu." " Kai yarone Lamido, ba zaka gane rayuwakan mutanen da suka shiga masifa ta dalilin ta ba, ba zaka gane komai ba, abinda na sanar maka kawai ka sani baka san komai ba." "Ni zan daukar maka fansa Abby, ka kwantar da hankalin ka da kaina zan daure Hajiya Zeenat har sai an rasa igiya a garin nan!" "Nasan zaka iya, dan ban haifi rago ba, sai dai nine kadai nasan lagon ta, ni kadai take tsoro a duk duniyar nan, dan haka a yanzu ne zata fara girbi!" "Kira Salihun!" Wayar ya ciro ya shiga kiran sa, ya saka wayar a handfree "Hello!" "Hello sir, barka da wannan lokacin." "Barka dai Salihu, lokaci yayi na cikar aikin mu tare, sai ka sanar da ita." "Ok an gama sir." Yana kashe wayar ya yi dialing number Hajiya Zeenat, a lokacin tana zaune kusa da Daddy tana murza masa hannun sa a hankali yana shan mixed fruit. Kamar ba zata dauki wayar ba saboda bata san abinda zai katse ta, sai kuma ta dauka din dan tana da abubuwan da bata son missing. Ganin Salihu ne yake kira ya sakata saurin janye hannun ta daga na cikin Daddyn ya kalle ta. "Lafiya?" Yace yana kokarin kallon wayar. "Salihu ne." Tace tana daga wayar sannan ta sakata a handfree "Hajiya akwai babbar matsala." "Hanzarta fada min." Kasa yayi da muryar sa sosai, kamar me rada sannan yace "Yau Barrister MATAWALLE ya shaki iskar yanci!" Cup din dake hannun Daddy ne yayi wata irin faduwa ya tarwatse a wajen, kafin ya mike tsaye cikin tashin hankali suka hada baki shi da Hajiya Zeenat din wajen cewa "WHATTTT!!!!" *RUMBUN QAYA *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥777 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *RQ*       Page 17 Hafsat Rano •••••• "Me kake fada min Salihu? Yaushe ya fito? Yaushe akayi haka duk ban sani ba." Karbe wayar Daddy yayi "Kana jina Salihu? Yi min bayani dalla-dallah ina sauraron ka." "Har yanzu ban samu dalilin fitar sa ba, amma tabbas ya fito, na kuma yi kokarin ganin na binciki lamarin sai dai ban samu dama ba, idan kuma na cigaba da kokarin bincikawa Zan samu matsala da Oga, dan da alama umarni ne daga chan sama." "Daga sama? Gwamna ko shugaban kasa?Wa ya damu dashi har haka da zai fitar dashi, waye wannan ya shammace mu? Waye shi? Hajiya Zeenat tace "Ban sani ba Hajiya, bari na koma bakin aiki kar oga ya lura bana nan." Jefar da wayar tayi bayan daddy ya miko mata. Ta cigaba da zagaye tana son figuring ainhin abinda yake faruwa. Babu wanda ya iya zama a tsakanin su saboda rud'ewa, dukkansu sun yi matukar shiga tashin hankali da gigita, shi Daddy har ya kusan d'ara Hajiya Zeenat a shiga yanayin tsoro da firgici ya dinga kai wa da komowa yana kokarin kiraye kiraye waye sai dai duk in da ya kira sai ya samu same labarin da Salihu ya bashi. Shugaban prison din baki daya ya yanke shawarar kira dan shima yaron sa ne kuma be kamata ace an yi irin wannan abun ya kasa sanar masa ba sai dai wayar sa ma a kashe. Daidai lokacin waani abu ya taso ya daki gefen kirjin Daddyn ya rike shi yana yin kasa rike da kirjin . Hajiya Zeenat da take ta waya ta lura da halin da Daddyn ya shiga amma tayi kamar bata gani ba dan ba tashi take ba dan haka ne ma ta cigaba da kokarin ganin ta samu information akan case din ko ya ya ne, domin tabbas an mata shigar sauri kuma ko waye yana da kusanci sosai da ita da har ya san duk moves din ta. Wayar da ta kira ta karshe ce ta tabbatar mata da komai zai soma budewa ne a wannan gabar, duk wani kulli da suka haka rami suke binne zai zama an tono shi ne. Duk kokarin ta na ganin ta batar da duk wani shaida a doran ya tashi a banza. "An chanja shugaban wajen ne." Shine abinda wayar da tayi a karshe ya tabbatar mata. Iska ta shak'a me zafin gaske ta fezar, ta rik'e kanta tana kokarin saka bayanin a mazaunin tunani. A dan takin da be wuce sati biyu ba, ta shiga prison din kuma ta samu tabbacin komai normal. Babu yadda za'a yi har a chanja shugaban wajen a wannan dan lokacin kuma ya aiwatar da wannan babban aikin da zai zama babban dalilin da zai tarwatse koman da ta gina. Dole wani yaci amanar ta "Ina ba zai yiwu ba!" Ta furta da karfi "Zeenatu. Zeenatu." Daddy ya shiga kwala mata kira jin abun na neman fin karfin sa, hannun sa na dafe da kirjin sa, matsowa tayi ta tsaya daga kansa a tsaye tana masa wani mugun kallo "Me kika bani nasha?" Yace da k'yar muryar sa na sarkewa ganin yadda take kallon sa "Abinda ya dace da kai." Tari ya soma yi da karfi, ta dauki wayarta tayi kira, minti kad'an wasu kartin maza suka shigo dauke da wata katuwar jaka, lokacin ganin Daddyn ya soma disashewa, takardun dukkan kadarorin sa suka fito dasu, ta karba ta ajiye a gaban Daddyn, daya daga ciki ya kama hannun sa, ya danna akan paper bayan ya dora shi akan stamp, sannan suka tilasta masa yayi signing wasu daga cikin takardun amma wasu ya kasa, zuwa lokacin abinda yake ji ya riga ya rinjaye shi har idanun sa sun rufe ruf. Kafarta tasa ta bugi kujerar cikin tsananin bacin rai. Ta riga ta shirya wannan plan din sai kuma labarin fitowar MATAWALLE ya rusa mata kusan rabin plan din, gashi bata samu ya gama saka hannu a dukka takardun ba, wanda suka kasance mallakin Aryan da Nabeela "Ku haura min dashi dakin sama." Tace tana kallon takardun ranta a bace. Ciccibar sa sukayi suka haura dashi zuwa dakin sa, suka kwantar dashi sannan suke rufe shi da blanket suka kashe wutar dakin suka fito. Sakowa sukayi ta basu umarni sannan suka fita. Sune sababbin masu kula da gidan daga yanzu, bata kuma yarda su bar kowa ya shigo gidan ba. Dakin ta, ta shiga rike da takardun ta daga wajen da ta ajiye na Aryan din da ko bude su batayi ba ta hade su, su kadai zata rike yanzu a matsayin makami, sannan samun da tayi wa disk din nan shine a yanzu garkuwar ta, dan ta tabbata Matawalle bashi da wani copy dan haka ne ma tasan bashi da wani abu da zai rike hujja akan ta. Shiryawa tayi cikin rantsatsiyar shiga, ta bulbula designer perfumes masu matukar tsada da kamshi sannan ta yafa dan mayafi a gefen kafadarta ta fito, a daren nan zata yi maganin Matawalle dan ko da ace ya fito va zata taba bashi damar da zai iya tabuka komai ba. Na farko yanzu girma ya kamashi, haka bashi da wani matsayi a hukumance dan a gabanta aka kwace license dinsa tun a wanchan lokacin. Ba ma wannan ba, yar sa mafi soyuwa a gareshi tana a tafin hannun ta ne, dan haka kome ma yake shiryawa da wanda ya saka aka fitar dashi daidai take dasu. Sai da ta shiga mota ta zauna sosai sannan ta kira shi a waya, dama yasan da plan din haduwar su a daren yau din amma kuma tana so kafin ta karaso ya nemo mata in da Matawalle yake da abinda yake yi a lokacin. Tamkar babu wani abu da ya faru, haka ta nuna dan a tunanin ta, tafi karfin dukkansu musamman da tasan ta kama abubuwa masu muhimmaci a garesu. ***Yau baki daya baya jin dadin jikin sa, tun da ya gama da wajen Dr Ma'aruf ya wuce gidan Ya Nabeela daga nan yayi kwanciyar sa dan ko ta kan wayar sa be bi ba shiyasa ma be ga kiran Kamal ba. Tun da akayi bikin Ya Nabeela bayan an dan kwana biyu ya tattaro ya dawo gidan dan kusan rabin rayuwar sa ta baya a tsakanin gidan ta da gidan su yayi ta, tun suna tsohon gida har suka dawo wannan da suke ciki mijinta yayi masa daki a gidan shikenan ya samu lasisin zama musamman duk sanda rashin lafiyar sa zata tashi dole tana kusa dashi tana kula dashi. Alwala ya shiga yayi a toilet din dakin da ya zama yanzu na baki idan sun zo sai kuma shi idan yaji bukatar zuwan. Lokacin la'asar ta dan gota yazo yayi sallar sannan ya shiga ciki. Suna zaune ita da Mijinta Dr Farouk lecturer ne a Federal University dake Dutse suna hira Aryan din ya shigo bayan yayi musu sallama daga kofar sun amsa. "Ka tashi kenan." Ya Nabeela tace tana kallon sa, "Eh bansan ya akayi nayi bacci haka ba." "Maganin ne." "Barka da warhaka Yaya Farouk." Hannu ya mika masa suka gaisa "Barka dai Aryan, ashe kana ciki." "Eh na shigo dazu." "Toh ya jikin?" "Alhamdulillah, ciwon kan ne dai yake dan takura min amma Alhamdulillah." "Toh Allah ya kara sauki, ka kula sosai ka kuma dinga ragewa kanka wasu abubuwan ba komai ake cewa dole dole sai an yi ba." "In sha Allah." "Gwara dai ka gaya masa zai fi ji, kuma kayi masa maganar aure dan zaman a haka ba zai yiwu ba." Ta wuce kitchen bayan ta gama maganar. Murmushi Dr Farouk yayi dan yasan yadda Aryan din yake idan aka dauko maganar aure "Rabu da yayar nan taka bata son zaman lafiya." Murmushi yayi kad'an ta fito rike da flask ta ajiye a saman dinning sannan tace ya taso yaci abinci. Tashi yayi yaje ya zauna ya zuba abincin kad'an ya dan chachakala ya tashi, nan ma sai da tayi maganar baya son cin abinci shi dai be ce mata komai ba, yayi musu sallama ya tafi. Har ya tafi ya tuna be dau wayar sa ba, ya dawo ya dauka anan yaga missed calls din Kamal rututu kamar ruwa, mamakin dalilin kiran ya tsaya yi sai kuma ya bi kiran yana rage gudun motar. "Ina ka shiga man?" "Ina gidan Ya Nabeela wallahi, bacci nayi bayan nasha magani." "Ok yanzu kana ina?" "Gani a hanya." "Ok kazo gida please, akwai magana." "Ok,i'm on my way." Ajiye wayar sukayi ya juya akalar motar zuwa gidan Kamal din. A kofar gida ya hange shi tsaye da alama shi yake tsaiwar jira. Parking yayi suka shiga ciki. "Madam fa?" Yace jin gidan shiru "Taje gidan su, da magriba sai mu je ka rakani na dauko su." "Ok." Yace ya zauna, ruwa da lemo Kamal yaje ya kawo masa sannan ya dauko jakar nan ya zauna yana dora ta a saman centre table "Wannan fa?" "Documents din nan ne, na cikin safe." "Anan?" "Eh, Hajiya Zeenat ta kai musu ziyara dazu." Ajiye ruwan hannun sa yayi da yayi niyyar sha, ya jawo jakar da sauri ya hau budewa. Sai da ya fito da komai ya tabbatar komai daidai sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya "Me ya faru? Ya akayi suka je gidan?" "A coincidence, kasan mun yi zanje har ka bani key din, ina shiga sai gasu." "Lallai tana da gut, da ranar Allah?" "Kana mamaki? Kafi kowa sanin wacece ita, da abinda zata iya aikatawa" "Then sai akayi yaya?" "I changed everything, na bar musu fake papers and the disk too." Zura masa ido Aryan yayi cikin rashin gamsuwa da bayanin sai dai ya yabawa kokarin Kamal din amma kuma be ji cewa ya gamsu coincidence bane, taya yayi planning komai within short time haka? "Are you sure?" Ya tambaya yana kara jawo papers din ya duba "Yes, it was a narrow escape." "Amma...it looks like a plan or something!." "How?" "Da farko dalilin zuwan su, ba zata taba samun gut din zuwa ba idan bata rike wani abu ba, na biyu yadda kayi saurin chanja komai a dan lokacin." Kallon sa Kamal din yayi, yana yabawa kaifin basirar Aryan din da saurin gano abu, amma dai dole a hakan zai barshi, dan ba zai iya fada masa abinda ya faru ba saboda Raihana, ba zai tona mata asiri ba dan yasan waye Aryan akan rashin yardar sa. Murmushi yayi ya dafa kafadar sa "Chill bro, koma menene mu gode Allah tunda bata samu nasara ba, she's after cd din nan while empty ne bata san komai yana kan flash ba, secondly Barrister Matawalle ya fito, wannan ba start bane me kyau ba?" "Oh yes!" "Yawwa, don't think hard akai, koma menene dai in sha Allah zamuyi nasara." "In sha Allah." Yace a sanyaye ya dan jingana da kujerar yana hasaso daga wannan sai wannan baki daya rayuwar. Daga sanda Hajiya Zeenat ta gane fake CD ne daga lokacin komai zai fara. "Kana bukatar driver Aryan." "Driver?" "Eh, saboda tsaro ba dan tsoro ba." "Bani da say ai, duk abinda ka tsara shi za'ayi dan yanzu kai ne ogan." Dariya Kamal ya kwashe da, shima Aryan din sai yayi murmushi dan ya sake tabbatar da babu wani a yanzu sama da Kamal din a gareshi. Tashi Kamal din yayi ya shiga ciki, ya sauya shigar sa zuwa ta fita. Tunanin Raihana ne ya fadowa Aryan wanda a dazu baccin ranar da yayi hadda mafarkin sanda tana kukan nan yayi, sosai kukan nata ya tsaya masa a rai be kuma san dalili ba, ya dai ji kawai yana tausayin ta ne sosai. Da kallo yabi Kamal bayan ya fito yana tunanin ya tambaye shi ne ko ya share? Yanke shawarar tambayar tasa kawai yayi ya dan mike zaune daga kishingidar da yayi yace "Yarinyar nan dazu ta fada maka matsalar ta?" "Wa fa?" Kamal yace kamar be gane wa yake nufi ba "Corper." "Oh Rayhan, Allah sarki bata jin dadi ne." "Ok." "I'm impressed." Kamal yace yana murmushi "With what?" "Wannan ne karo na biyu da naga ka damu sosai da abinda ya shafi wani, na farkon ma akanta ne, ga na biyu, did you have any feel..." Ai da sauri Aryan ya kai masa bugu abinda yasa maganar ta katse "Don't even start." Yace yana yin kicin kicin da fuska "Baka barni na dire magana ta ba ai." "Bana son ji, kuma ba zan sake tambayar ka ba, kawai dama naga yarinya ce, plus tace min ta rasa mamanta tun tana karama, and I know how it feels ka rasa iyayenka at younger age, shine kawai nothing more, shima ba zan sake tambaya ba." "Ikon Alalh." Kamal yace yana dariya "Why all this explanation? Daga magana? Ni na dade ban ji kayi irin wannan long sentence din ba wallahi, menene a ciki toh? Kai ma fa mutum ne me jini a jika, handsome guy son kowa kin wadda ta rasa." "Sai kayi, zaka je daukar Madam din ne ko na wuce gida?" "Zanje mana, an gaya maka zan iya kwana ni kadai a gidan nan? Nah ba zan iya ba, sai na rungume matata tsam tsam sannan." "Dan iska" Aryan yace ya fice ya barshi yana kyal kyala masa dariya *RUMBUN QAYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *RQ*       Page 18 Hafsat Rano ••••••Kokarin motsa ko da karamin dan yatsan sa Daddy yake amma ya gaza, gashi yana jin duk wani motsi amma ya kasa juya jikin sa. Kenan tsawon wannan lokacin Hajiya Zeenat ba san shi take ba? Ko kuma a yanzu ne ta sauya? Baki daya ya kasa tunanin abinda yake faruwa a dan gajeran lokacin. _"Tunda har ka iya biyewa mace ka bata da duk wani makusancin ka, toh tabbas dama irin wannan ranar ta nadama ta na nan zuwa."_ Wata murya daga chan bayan kansa tayi kokarin tunasar dashi abinda ya faru a lokacin baya. Hawaye ne ya shiga sakkowa yana biyowa ta gefen kuncin sa, bayan ya gama tabbatar da shikenan tasa ta kare, watakila haka zai karasa rayuwar sa har mutuwa tazo ta riskeshi. Kaico! Rayuwar cin amana bata dauke da komai sa tsantsar tashin hankali. Yinkurin ya cigaba da yi har ma da na kokarin yin magana Amma sam muryar sa taki fitowa kwata-kwata, so yake ma ko ihu ne yayi ko wani zai jiyo shi, ko yayi sa'a Aryan ya shigo yazo ya taimake shi. Wayar sa ya hanga ta gefen idon sa tana haske alamar shigowar kira amma ba zai iya kaiwa gareta ba, ballantana ya iya dauka. A gajiya Aryan ya shigo gidan dan sun dade a gidan Kaamal bayan sun dauko matar sa, sai suka zauna zaman tattaunawa abubuwan da suke tunkaro su, basu ankara da dare yaja haka ba sosai sai da Khadija tayi wa Kamal flashing sannan suke duba lokaci yayi saurin yi masa sallama amma maimakon ya barshi ya taho shi kadai sai yace Khadijan ta dauko Hijab dinta aka shigo da motar Aryan din ciki sannan suka kaishi har gida a motar Kamal din. Sam be yarda da tafiyar a sa lokacin nan ba dan yana tsoron abinda Hajiya Zeenat zata aikata tunda har ta kai ga batun poison duk da ba wai yau ne karo na farko da tayi attempting hakan ba, Allah ne dai be bata sa'a ba. Amma dai duk tsiyar ta ba zata taba yi masa komai a cikin gidan ba sai dai a waje yadda ba zata taba zama abar zargi ba. Stairs din ya kama ya soma hawa cikin yanayin kasala rike da suit din sa, duhu gidan yayi masa sosai duk da dama duk an kashe kwayayen dake bada haske a ilahirin falon zuwa saman an maida shi me dan gaske kad'an amma duk da haka sai yaga kamar ko ina baki ne kirin, ga wani irin shiru da ya dade be ji gidan ya dauka ba. Cigaba da hawa yayi zuciyar sa ta kasa nutsuwa da yanayin da yake jin sa, tabbas akwai abinda ya faru ko yake shirin faruwa, abinda ya dauka kenan dan a duk sanda yaji irin wannan toh yasan tabbas akwai wani abu da Hajiya Zeenat take kullawa. Dafe kirjin sa yayi da hannu daya jin yayi masa nauyi, ya shiga karanta la'ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin har ya kai kofar dakin sa, ya saka key din sa da yake tafiya da shi ko ina ya bud'e ya shiga sannan ya saka key din ya sake rufewa ya kunna hasken dakin. Ko ina a gyara yake tsaf tsaf kamar dakin mace, da kansa yake gyara komai dan yana da komai na gyara a ciki be yarda kowa ya shigar masa ba duk kuwa da ba wani abun amfani yake ajiyewa a dakin ba. Wajen shoe rack dinsa ya nufa ya dan duka ya hau zare takalmin kafarsa hade da socks din ya ajiye takalmin a ma'adanar sa sannan ya wuce wajen dan madaidacin laundry basket ya jefa socks din sannan ya fada saman gado yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. ****Duk yadda suka bincika sun kasa samun bayanin komai akan fitowar MATAWALLE, da kuma whereabout dinsa, kanta ya soma daukar zafi amma duk da haka ba zata ka raya ba, a wannan karon ya shirya mata sosai amma abinda be sani ba shine itama a shirye take. Da wani mugun bacci ta shigo gidan dan haka ne ma bedroom ta wuce kai tsaye ta fada sai bacci. Su kuwa dama sallar asubah kawai sukayi, suka hau shiryawa kafin takwas sun isa airport takwas da wasu yan mintoci suka d'aga daga garin Kano da niyyar dawowa a cikin babban shirin da zai rusa Hajiya Zeenat har ma da Alhaji Mukaddas a cewaar Aby dan har shi babu wanda zai ragawa, duk wani ma da ya zama tsatso ko dan uwan Daddyn babu sassauci ko kyautawawa a tsakanin su. Bacci bilhaki Hajiya Zeenat take kamar wadda tasha wani abu dan sai da rana ta daga sosai sannan ta tashi tana mika. Wanka ta farayi dan a rayuwar ta bata wasa da kula da kanta da jikinta wanda tun a zamanin baya ya kasance jari da tsanin da ta kai har wannan matakin. Ta kan yi wasa da sallah har ma tayi mirsisi wani lokacin taki yi amma bata taba wasa da gyara kanta da fatarta. A shirye ta fito da nufin zuwa dakin Daddy sai ta tarar da Adam ya kwance yana bacci akan kujerar falon,matsawa tayi ta taba shi ya farka a rikice idanun sa sun yi wani irin ja sosai. "Adam?" Tace tana dan ja baya saboda bud'e bakin sa da yayi wani irin wari ya bige ta "Giya Adam?" Tace tana waro ido, dan luu yayi da ya yi kokarin mikewa jiri ya kwashe shi ya koma jagaf yayi baya. "Wanne irin iskanci ne wannan? Yaushe ka fara shan giya ban sani? Yaushe?" "Maaa... Bafa giya bace." "Uban kace, tunda an gaya maka bansan warin ta ba." Tace da karfi tana tura shi baya "Please stop shouting! ki daina bana so kina min ihu da sanyin safiyar nan." "Adam!!!" "Sai kuma kiyi." Sai ya kama hannun kujerar ya mike yana cigaba da tangadi, yayi hanyar dakin Aryan kamar zai murd'a sai kuma ya fasa ya nufi nasa ya shige gami da banko kofar. "Na shiga uku, sai dai komai yazo karshe wannan masifun zasu fara kunno kai?" Bud'e kofar dakin Aryan din da taji anyi ya sakata kallon wajen da sauri, a shirye yake tsaf cikin shigar kamala kufta da hula sai kamshin turare ke tashi me matukar dadin kamshi, be ko kalli shashen da take ba kamar dai yadda ita take masa kallo me cike da tsana, tana kokarin hada yanayin nutsuwar sa da ta Adam wanda dama tun a zamanin kuruciya ba ma yanayin su daya ba. "ARYAN!" Ta kwala kiran sa ganin yana neman barin falon. Chak ya tsaya sai dai be juyo ba dan idan akwai abinda ya tsana ya biyo bayan kallon fuskar ta. "Daddyn ku yayi tafiya a daren jiya, zai kuma dan kwana biyu, ya bar sakon duk wani abu da ya shafi office ka sanar wa dan uwanka..." Wani irin juyowa yayi da shi kansa be san yayi ba, ya wurga mata wani banzan kallo kafin ya kad'a kansa ya soma kokarin barin wajen, sai da ya kai kofar fita sannan yace "Karki kara kokarin tsaida ni ki bata min lokaci akan shirmen ki." Dariya ta kwashe da, ya girgiza kansa kawai ya karasa ficewa. "Lallai wuyan ka yayi kauri." Tace tana bubbuga hannun ta da yake cike da bangles na zallar gold. Fasa zuwa duba Daddyn tayi dan tana bukatar sanin in da aka kwana da maganar Matawalle sannan kuma ta magance matsalar Adam da yake shirin bata mata komai bayan da take kokarin maida duk wani business akan sunan sa. Bayan Aryan din tabi suka hadu a compound din gidan yana tsaye jikin motar Daddyn suna magana da Kamal yayi kamar be san ta fito ba, ta girgiza kai ta shige motar ta suka fice daga gidan. Wayar ya tura a aljihun gaban rigar sa ya taka zuwa gate din, ya samu maigadi a zaune jigum. Zama yayi a gefen sa yayi saurin mikewa cike da girmamawa ya gaida Aryan din, hannu ya mika masa suka yi musabiha sannan yace ya dawo ya zauna. "Waye ya kawo wadanchan mutanen?" Ya nuna manyan securities din dake kaiwa da komowa a harabar gidan rike da bindigu kowannen su fuskar sa a tamke zaka rantse basu taba dariya ba "Hajiya ce ta kawo su." "Aikin me suke?" "Kula da shige da ficen gidan, kamar dai hakan ne." Tabe baki Aryan yayi yana cigaba da kallon su, suna ta safa da marwa tamkar mayunwatan zakuna. "Ok thank you" Yace ya mike ya isa wajen su, suka zubo masa ido kamar zasu cinye shi. "Ku gaya wa wadda ta ajiye ku, ko irin ku dubu zata ajiye kewaye da ita sai ta sha k'asa." "Ok sir!" Suka hada baki wajen fada, tsaki yaja ya juya ya barsu a tsaye suka bishi da kallo. Kamal ne ya karaso tare da wani da ya jawo motar Aryan din, a waje suka parker ya fice yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa "Idan kace 5min toh sai ya zama 20min, sam baka abu a exact time din." Aryan yace yana mikawa Kamal din hannu, dariya yayi ya juya wajen matashin da yake tsaye rike da key din motar Aryan din yace "Aryan ga Habeeb, sabon driver ka." Kallon wanda aka kira da driver Aryan yayi, ya ganshi tsaf dashi babu wata wahala a tattare dashi sai ma yanayin yan boko. "Amma be yi kama da driver ba." "Gaskiya ne, be yi kama ba saboda dai dan makaranta ne, ya samu matsala da karantun sa ne har akayi withdrawing dinsa, so kasan yanayin rayuwar dole sai an rayu, plus shi yake kula da mahaifiyar sa, ga aiki yayi wuya shine na kirashi a daren jiya ya kuma tabbatar min zai iya, nasan shi nasan gidan su kuma na yaba dashi shiyasa ma na nemo shi." "Allah sarki." "Karka damu, yaro ne me hankali." "Ok RUMBUN QAYA*🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 *RQ*       Page 19 Hafsat Rano https://arewabooks.com/u/hafsatrano *****Gaba ya bud'e ya fada ba tare da yace komai ba, dan tsaye Kamal yayi kamar zai ce masa ya koma baya amma sai ya kyale dan kar ya matsa sosai yasan halin Aryan sarai zai iya saka wani abu a ransa. Motar sa ya koma ya shiga, ya fara jira Habeeb din ya fara wucewa gaba sannan ya bisu a baya. A gate din company ya tsaya dan yana da dan wajen da zai je kafin ya shigo, wayar sa ya dauka ya kira Aryan din yace masa zai dan je ya dawo sannan ya juya ya bar wajen. Titin babu kowa dan ko motsin tsuntsaye babu saboda tsabar shirun shi, wajen ya kasance baya biyuwa saboda tsabar tsaron da yake wajen. Tun daga farkon titin suke tsayawa suna maida duk wani da yazo giftawa ta wajen tun mutane basu gane ba har suka gane kowa ya daina bi saboda tsoro. Sai kayi tafiya me nisa a kan titin sannan zaka iso gate din wajen, wanda shima yake zagaye da matakan tsaro. A guje wani rike da wata irin mahaukaciyar bindiga ya taso, yazo ya hau bud'e masa gate din da saurin gaske. Ciki ya shiga bayan ya dan daga masa hannu ya samu wajen yayi parking ya fito da sassarfa. Gari guda ne a cikin wajen domin kuwa waje ne me girman gaske, sannan ga matasa maza da mata wanda a kalla shekarun su ba zasu haura ishirin da biyar ba suna kaiwa da komowa a cikin wajen da ya kasance a kebence dan ba zaka taba tunanin wajen yana existing ba. Kowannen su rike yake da bindigu manyan gaske sai dai suna ta walwala a tsakanin su tamkar babu wani abu da yake faruwa Kai tsaye office dinsa ya wuce wanda aka rubuta daga saman office din da babban baki LIEUTENANT KAMAL HASSAN SARKI (DSS) Sergeants ne a kofar office din sukayi saurin bud'e masa, ya shiga ya zauna akan kujerar sa sannan ya fito da takardun Aryan din dukka ya baje su akan table din ya hau dubawa a tsanake. Knocking aka fara yi kad'an kafin ya bada izinin shigowa. Captain Mausul ne "Welcome sir." Yace yana sara masa. "Thank you, ya ake ciki?" "Ni da team dina mun samu nasarar kama wannan kasurgumin kidnapper din da ya addabi mutanen Batsari da kewayenta, mun yi ta bibiyar sa tun daga jos har zuwa sanda ya shigo Kano, but sai muka rasa shi kuma, jiya da safe ina kokarin shiga wanka na samu kira daga wajen Lawal, an samu signal na wayar sa a tasha, we quickly set-up a team muka bishi daga Kano har Katsina,anan ne mukayi arresting dinsa yana kokarin shiga garin na Katsina da tarin bullets." Dagowa yayi ya bar abinda yake yi ya dube shi "Well-done!" Ya hau tafa masa "You did a good job!" Ya daga masa hannu alamar jinjinawa "Thank you sir." Yace yana murmushi "Yanzu yana ina?" "Yana cell sir, ga duk bayanin abinda muka samu a gidansa da muka je." "Ka ajiye min, zan shigo da daddare sai mu duba komai, kwana goma na basu suyi duk binciken da zasuyi su gama, mu tur." "Ok sir." "Yanzu ina sauri ne, abubuwan sun fara sauya salo dan haka ne ma nake ganin kai ne zaka jagoranci wannan tafiyar a matsayin team captain din, dan na tabbatar zaka iya." "Ok sir!" "Ga record din komai, name, address and phone number, da duk finding dina yana ciki." "An gama sir." "Yawwa, thank you." Fita yayi ya barshi a ciki, ya karasa abinda zai yi sannan ya fito ya nufi office din ogan sa, ya dan dade a ciki kafin ya fito ya tafi ba tare da ya koma office din nasa ba. A mota ya bar wayar sa da yake amfani da ita a gari dan dama ka'idar aikin kenan dan a kashe ma take sai da ya fito gaba daya daga lungun sannan ya kunna ta. Kamar Aryan yana jira sai ga kiran sa ya shigo "Wai kana ina ne?" "Gani nan na taho." "Me ya samu wayarka a kashe?" "A aljihu na turata, ashe na danne power button din ban sani ba." "Ok sai ka karaso." Yace ya kashe wayar. Ajiye wayar yayi ya jawo dashboard dinsa ya d'aga wasu tarkace ya tura I'd card din sa. ***Kamar wadda ta shekara rabon ta da gida haka taji, wato dai da gaske kowa ya bar gida, gida ya barsh. Ji tayi baki daya ta tsani Kano da duk mutanen da suke cikin ta. Dama zata koma baya da sai ta goge haduwar su da Hajiya Zeenat shikenan da bata shiga wannan masifar ba, da kuma bata hadu da Aryan da Kamal ba. Baki ne suka dinga tuttulowa gidan nasu zuwa yiwa Abby barka da fitowa dan haka sai gidan ya zama ya cika sosai. Dakin ta, ta gudu taje ta kwanta dan har lokacin jikinta be gama yi mata daidai ba, gashi da ta zauna sai tunanin abinda ya faru ya shiga dawo mata. Dadah ce ta biyo ta dakin ganin ta baro falon kuma duk sai taga bata yarda da yanayin Raihanan ba. Zama tayi a gefen gadon tana duban ta. "Lafiya?" Tace mata dan fuskarta ta nuna ba lafiyar ba. "Zazzabi nake yi,Amma nasha magani." "Tun yaushe? Ko dai akwai wata damuwar bayan ta zazzabin Raihana?" Girgiza mata kai tayi, dan bata san ta in da zata fara yi mata bayanin abinda ya faru ba, musamman a yanzu da duk suke cikin farin ciki mara misaltuwa. "Ba komai Dadah na, da na sake hutawa shikenan." "Kayya, babu karyar da zaki yi min na yarda dake Raihanatu, ki sanar dani damuwar ki, na sanki kamar yunwar cikina dan haka kar nake kallon ki." Zamewa tayi daga kwanciyar da tayi da nufin zama sosai sai wayar ta, ta hau ringing, kurawa number dake kira ido tayi dan bata taba kawo kiran nasa ba. "Ko dai sabon saurayi kikayi a Kanon Raihana?" Dadah tace tana rike baki, da sauri tace " A ah wallahi, ni banyi komai ba." "Toh waye yake kiranki? Kika zubawa waya ido kuma baki dauka ba? Ko fada kukayi da saurayin?" "Kai Dadah kinji ki, ni wallahi ba wani saurayi, kawata ce ma take kira na." "Kawa? Yaushe kikayi kawar bamu da labari." "Shikenan bani da kawa a duniyar nan Dadah?" "Baki da ita gaskia, sai abokan arziki." "Ni me aka maida ni a gidan nan ne? Dole ma nayi sabuwar kawa." "Oho, kamar gaske. Idan kin gama wayar ki fito cikin mutane bana son kina darere kanki ke kadai." "Tohm." Tace ta rakata da ido har ta fice. Wayar ta riga ta katse, haka kawai sai taji babu dadin rashin dagawar da batayi ba. Jujjuya wayar ta dinga yi a tunanin ta zai sake kira amma shiru, yunkurawa tayi ta tashi tayi hanyar fita sai ga kiran ya sake shigowa, da sauri ta dawo baya ta rufe kofar kar Dadah ta dawo tayi wata maganar da zai ji, sannan ta daga tayi sallama a hankali chan kasa. Maimakon ya amsa sallamar sai yayi shiru ya fara tunanin dalilin da yasa shi kiran ta "Ya jikin naki?" Ya tattaro kalmar da k'yar ya fada yana ciccijewa "Ina wuni?" Ta gaishe shi a maimakon amsa tambayar da yayi mata "Lafiya, sai anjima." Kit ya kashe wayar, saroro tayi da waya a hannu cike da madaukakin mamakin sa, wannan wacce irin waya ce? Dariya abin ma yaso bata ganin yadda yayi maganar kamar wanda aka saka a gaba akayi masa dole ya kirata, saukin ta ma shine ya kira da ita ta kira yayi mata haka da tasha dan banzan kunya. Samun kanta tayi da dariya sosai daga karshe da ta gama tunanin abun, sam bata taba ganin irin sa ba, wai sai anjima, shikenan? Ta dauka ma wani abun ya rasa a office ya kira ta, bata ga amfanin kiran nata ba gaba daya. Toh ko dai kira yayi kawai ya duba ta tunda har yace mata ya jiki a farko. Ajiye wayar tayi kawai a dakin ta fice dan idan ta zauna tunanin son gano dalilin kiran nasa zata iya kaiwa dare a dakin bata fito ba. ****Dukkan wani kokari da Yaron Hajiya Zeenat zai yi mata akan Matawalle ya gaza, tun tana ganin abun wasa ne sai kuma jikinta ya fara bata lallai ya shirya mata, shirin da kuma ta gaza gane in da ya dosa, tasan shirun sa ba alkhairi bane a gareta, dan a sanin da tayi masa tasan tabbas da tuni ya neme ta ya kirata ya tabbatar mata da fitowar sa, dan ko a karshen zuwa ganin sa da tayi a prison ta lura da wata halayya daban da ta Matawallen da ta sani dan har ta dinga tunanin dalilin shi na share ta da kin yarda ya biye mata ba kamar a baya ba, idan taje ganin sa ya kan jaddada mata sai ya kaita k'asa in dai yana numfashi a doran k'asa. Raihana ce ta fado mata, tabbas ita kadai ce a yanzu zata zame mata garkuwa da kuma tsani wajen samun lagon mahaifin ta, da ita zatayi amfani ta sake kaishi kasa wanda zai fi masa ciwo fiye da kaiwar da tayi masa a shekarun baya dan wannan sai yafi jin zafin ace yar cikin sa ce zata aikata masa hakan. Wannan tunanin ya dan bata hope har ta kara samun kwarin guiwa sosai duk kuwa da chan kasan zuciyar ta, tana cike da tsoron abinda zai biyo baya idan komai a fallasa, amma duk da hakan ba zata karaya ba, dan ita din ba raguwar mace bace ba, tun zamanin kuruciya kuwa ballantana yanzu da ta kai matakin kuloluwa a matakan nasarar da ta tsarawa kanta cimmawa a tsawon rayuwarta. Gida ta koma kawai dan tun fitar safen da tayi bata komo ba, sai dai tayi matukar tsurewa ganin Adam har lokacin yana gidan a dakin sa yana ta sharar baccin asara. Wani wawan duka ta kai masa a gadon baya wanda hatta takalmin kafarsa be samu cirewa ba dashi ya kwanta ruf da ciki ya dage kafafun sama. Dabiar da ya fara kenan chan baya ta shiga ta fita ta samu nasarar hanashi tun Daddyn be farga ba, sai yanzu da kusan komai yazo hannu shine zai dawo ruwa kenan, ya barta da komai ta ina zata fara bayan ba aikin ta bane ba, wa zai cigaba da kula da komai kenan? Idan haka ne karshe fa kenan sai dai komai ya dawo karkashin Aryan abinda ba kuma zata taba amincewa ba dan duk wata dukiya da Daddyn ya tara kusan tare da ita aka tarata dan ita ta taimaka masa matuka har ya kawo wannan matakin da yake kai shine kuma dan rashin alkawari har ya maida komai da sunan yaransa biyu ita da Adam sun tashi a tutar babu. Bata da plan din yiwa daddy komai dan ta gama sakankancewa zai damka wa Adam kusan komai, rana daya ta ji shi yana waya da lauyan sa, daga ranar komai ya chanja ta shiga neman rayuwar sa tun kafin ya nemi ta ta. Soshe soshe Adam din ya hau yi wajen da ta dake shi, ya tashi yana kumbura fuska ya wuce toilet ya wanko fuskar sa da bakin sa ya dawo ya tarar da ita a tsaye tana jiran sa "Yanzu tun da na fita kake baccin asara Adam? Ina chan ina kokarin gina maka rayuwa amma shine zaka zo ka kwanta office din ma ka daina zuwa kenan Aryan ya mallake komai." "Ni bana son komai idan har ba zan samu Raihana ba." "Raihana kuma? Wai dama wannan maganar bata mutu ba?" "Wallahi bata mutu ba, kuma son ta nake auren ta zan." "Tirkashi, akan hakan kake son maida kanka wani na daban?" "Lallai baka da hankali ma wallahi, idan ma zaka hakura tun wuri gwara ka hakura, mahaifin ta ko mutuwa zakayi ka dawo ba zai baka yarsa ba wallahi,." "Akan me yasa ba zai bani ba?* "Saboda baka san waye uban nata ba ai shiyasa zaka tsaya tambaya, toh yar Barrister Matawalle ce, ina fatan yanzu zaka saita hankalin ka waje daya ka dawo hayyacin ka, kasan in da yake maka ciwo." Fuuu ta fice tana bambamin fada. Shiru yayi bayan ya fita, tabbas ya san waye Matawalle a wajen mahaifiyar sa, sannan yasan duk wata harkalla da ta ke tsakanin su, babban abinda yake damuwan sa shine yadda yaga Aryan ya damu matuka da al'amarin yarinyar, tunda ko last akan ta sukayi fada sosai ya kuma hangi wani abu a chan cikin idon Aryan din. "Ba zai yiwu ba, sai dai dukkan mu, muyi biyu babu wallahi." Yace yana yin hanyar barin dakin. Dakin Hajiya Zeenat ya nufa ya tarar bata ciki sai wayar ta, dama abinda yazo nema kenan, da sauri ya bud'e wayar ya shiga wajen audios din dukkan wayar da sukayi da Raihana, yayi copying komai akan wayarsa sannan ya ajiye mata wayar ya juya ya bar dakin. Da wannan zai yi amfani yasa Aryan ya tsane ta, tsanar ta har abadah, shikenan kowa ya rasa dan zuciyar sa ba zata iya daukar nasarar Aryan din ba. ***Daddy na kwance har ya bata jikin sa da fitsari dan gaba daya ranar babu wanda ya leko shi, motsin bud'e kofar yaji sai kuma haske ya gauraye dakin. Takowa tayi zuwa gaban sa tana toshe hancin ta da hannun ta. "Menene haka?" Tace tana ja baya ganin kayan jikin sa a jike jagwab, hawaye ne ya biyo gefen fuskar sa tana kallo, ya motsa idon sa. "Ni zaka ci amana Alhaji? Ni Zeenatu da na sadaukar da rayuwata da komai na akan ka ni kayi tunanin yaudara ko? Har kasa a fito da Matawalle ba tare da sani na ba, saboda kana son farantawa wanda ba zai taba yafe maka ba, duk da abinda kayi yanzu Matawalle ba zai taba yafewa mutum irin ka ba, macuci maha'inci irin ka, da kayi hakuri mun cigaba da yadda muka faro, domin nice daidai da kai, amma sai ka ci amanata bayan ka manta wacece Zeenatu, ba'a taba cin amaanata a zauna lafiya, dan haka sai ka cigaba da zama a haka har zuwa sanda na gama cika buri na,idan zuwa lokacin ka karasa kuma shikenan." Kokarin motsawa yayi amma ya kasa, gashi yana so yayi mata magana amma sam bakin sa ya kasa, be san me tayi masa haka ba, amma ko ma menene Yana bukatar taimakon gaggawa, dan wani irin nauyi da jikin nasa yayi masa ga wani irin ciwo da idanun sa suke masa tamkar zasu daina gani. A yau yayi nadamar biye wa mace irin Zeenat, ta raba shi da yayansa masu so da kaunar sa, ta nisantasu dashi ya zama na basa iya neman sa face shi ya neme su, da kansa kuma ya kafa musu wannan sharadin a lokacin da yake jin su tamkar wasu nauyi a gareshi. Da ace be hana su, yasan da tuni sun neme shi tun a jiyan, yanzu be san ranar fitar sa daga nan ba,watakila haka zai karasa RAYUWAR sa a wajen ba tare da ya nemi yafiya da afuwar su ba, musamman ARYAN! Ignore all the typos, I'm super busy wallahi. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ *RQ*       Page 20 ****A gurguje Adam ya watsa ruwa ya fito ya tarar da Hajiya Zeenat a zaune tare da wata mata, wuce su yayi bayan ya gaishe ta a gajarce suka bishi da kallo Hajiya Zeenat na cike da mamakin in da kuma ya nufa. Office ya wuce kai tsaye ya duba parking lot yaga motar Aryan sai yayi murmushi ya wuce bangaren sa kawai yana sake nanata abinda yake shiryawa a cikin kansa. Aryan na zaune a office ya gama duba wasu takardu Kamal ya shigo kamar yadda ya saba ya fara zuro kansa sannan ya shigo yana dariya. "Wai ina kaje?" "Sabuwar budurwar da nayi ce ta kirani, shine fa na amsa kira kar tayi fushi dani." "Sabuwar budurwa kuma?" "Eh karaye zan je, kai ba ka tsaye wasa ba, ta biyu nake shirin yi ka zauna dai." "Lallai wahala bata ishe ka ba,mace daya ma ya aka kare bare har biyu? Akan me yasa ma zaka kara aure." "Sunna." "Yen yen, dama haka kuke fakewa ai, ku tara matan suyi ta neman ranku." "Hahaha, ko su dinga yar rige-rigen kyautata mana ba." "Ba wani nan." "Yanzu kai kenan mijin mace daya ne." "Ko rabi ba,dayar ma ba dani ba, kai ni bana son wannan zancen please, akwai tarin ayyuka masu yawa suna jiran ka." "Yanzu zan hau kansu ai." "Yauwa jeka toh." "A ah ai yau a office din ka zanyi aikin, bari na kwaso komai na dawo." Kallon sa Aryan yayi, yana fita ya tashi yasa key a kofar ya dawo ya zauna yana murmushi. Baki daya yan office din sun dauka Raihana ta tafi kenan, ganin kwana biyu bata zo ba tun ma ranar dai da abin nan ya faru, sosai hakan yayi wa Zainab dadi dan a kwana biyun nan ko yaushe ita Aryan yake kira kamar dai da kafin zuwan Raihanan. Ta fito zata tafi gida kenan Adam ya tsaida ta, ta tsaya tana dan waige-wage, kafin ta dan matsa sosai yadda ba za'a gano ta ba. "Me yasa Raihana bata zuwa?" "Ya tambaya dan yana ta lura da shige da ficen wajen amma be ga wucewarta ba ko kad'an "Inaga ta chanja wani wajen, tun ranar da abin nan ya faru bata sake zuwa ba." "Damn it!" Ya bugi gefen gini sannan yace taje. ***Zaman Raihana a gidan su ya kara sata sakankancewa sosai har ta manta da sabgar Hajiya Zeenat da kowa ma, sosai Abbyn ta yake samun kulawa ta musamman dan bayan masu zuwa jaje sun zo sun gama wani sabon gida suka tattara suka koma me dauke da part hudu wanda Hamman ta suka dade suna ginawa dan sun yi alkawarin a tare zasu zauna gida daya har Abby. Bata san dalilin komawar su gidan a wannan lokacin ba dan ba'a gama ma sauran part din ba nasun dai kawai akayi sauri aka karasa. Ko yaushe Abby yana falon sa a zaune yana kallon news ko kuma ka same shi yana karatun alqur'ani me girma. Ko yaushe suna tare da Tafeeda dan shine yake kula da Abbyn da koman sa musamman da ya kasance su Hamma Haydar da Babbo Sadeeq suna fita aiki kuma suna kai yamma likis kafin su dawo wani lokacin har dare ma. Da sallamar ta, ta shiga falon bayan an amsa mata an bata izinin shigowa. Lamido ne zaune a gefen Abbyn sai wata jaka a gefen shi wadda ta nuna da alama lokacin aka rufe ta. "Uwata ce?" Abby yace yana dan mikewa daga kishingidar da yayi, "Eh." Ta gid'a kanta tana zama a daidai saitin kafarsa. "Abby barka da gida." "Barka dai, ya gidan?" "Lafiya lou Abby, gobe zan koma Kano." "Jibi, jibin nan?" "Umm." "Kaji Lamido, ba za'a yi wani abun ba akai?" "Anyi Abby, shine ma har aka samu kanon." "Toh ka tabbatar babu wata matsala ko?" "Babu in sha Allah, ko akwai kanwata?" Ya kalle ta "Babu Hamma." Tace tana murmushi "Shikenan, Allah yayi muku albarka, sai ka shirya mata tafiyar Lamido." "In sha Allah." "Ki kula sosai kinji? Dan Allah Raihana karki wasa da rayuwarki da tarbiyyar da kika samu, karki ga babu idon mu akanki, muna sane da komai." Shiru tayi kanta a k'asa, har ya gama mata nasihar, tayi godiya ta tashi ta fita wajen Dadah. ***Tafiyar rana zatayi dan haka ne ma ta karasa shiryawa a tsanake, bata son komawa har ga Allah amma kuma ya zatayi? Haka ta karasa hada abinda zata bukata sannan tayi wanka ta shirya. Babbo Sadeeq ne ya kaita airport dan Abby dama yace ya haramta mata tafiyar mota. A boye ta share hawayenta ba kamar wacchan tafiyar da take cike da dauki ba. ***Saukar ta a Kano yayi daidai da shigowar kiran Hajiya Zeenat, ta kikkirata a chan amma duk sanda tazo missed calls dinta take gani kawai kuma bata bi dan bata gama nutsuwa da abinda Kamal yake son tayi ba gashi be kirata ba kwata-kwata bare ta gaya masa abinda yake faruwa. Daga baya kuma kawai sai ta kashe wayar ta tura ta a drawer bata kuma sake kunna ta ba sai yau da zata taho shima dan tasan dole Dadah zata kira kafin su tashi sannan ta kira ta bayan sun sauka. Tsoron da take ji ne taji gaba daya ya dawo mata sabo. Kin dagawa tayi har ta katse sai tayi saurin kiran Kamal din tasan abinda ya kamata tayi. A lokacin suna tare da a gidan Aryan din kiran ya shigo, yayi murmured kad'an sannan ya daga yana mikawa Aryan din takardar hannun sa "Raihanatu." Dagowa Aryan yayi da dan sauri jin sunan da ya kira, Kamal na ankare dashi kawai sai ya bar wajen yayi hanyar fita baya yana amsa gaisuwar da take masa. "Na dawo yanzu." "Masha Allah , ya hanya?" "Alhamdulillah, lafiya lou." "Good, kin baro kowa lafiya dai ko." "Eh lafiya Lou." "Toh madallah." "Hajiya Zeenat ce take ta kirana a waya, bansan me zan ce mata ba." "Dagawa zaki kamar babu abinda ya faru". "Zan iya?" "Sosai, ki daga kafin ta fara saka shakku akanki." "Idan kuma ta sani wani abun fa?" "Karki damu, yadda kuka fara a baya haka zaku dora, kina jina? You have to be strong babu abinda zai faru nayi miki alkawari, trust me." "Ok." Tace a sanyaye "Yawwa, call her back karki ji komai, kawai dai duk yadda taso kuyi maganar family dinki karki bata fuska." "Ok." Ta sake cewa a sanyaye. Katse kiran yayi hango Aryan yana nufo wajen ta cikin glass, hannun sa rike da ball yazo ya wuce Kamal din ya bud'e kofar da zata kaika bayan gidan. Short ne a jikin sa da rigar sa da alama zai motsa jikin sa ne. Bin bayan sa Kamal yayi yana tattare hannun long sleeve din rigar sa "Raihana ta dawo." Yace masa yana durkushe yana gyara igiyar takalmin kafarsa. Be dago ba kawai yace ok ya daga ball din suka soma buga basketball. ***Bata bi kiran ba sai da ta karasa gida ta zauna bayan sun gaisa da Adda Maimuna sannan ta kira Hajiya Zeenat din gabanta na dukan uku uku. Rejecting kiran tayi ta biyo kiran nan take. "Idon ki kenan Raihana?" "Kiyi hakuri Aunty, na danyi rashin lafiya ne." "Ashsh, amma shine babu labari, ranar daga shiga in fito sai na neme ki na rasa ba wani bayani, ko akwai wani abu da ya faru ne?" "A ah, kira na oga Aryan yayi ya gane bana office din shine nayi saurin komawa." "Ok, toh ya jikin naki? Kin warware dai ko?" "Alhamdulillah, na samu sauki gobe zan koma aiki ma in sha Allahu." "Toh madallah, Allah ya kara sauki." "Amin ya Allah, nagode." "Zaki iya zuwa gobe? Ina son ganin ki." "Na'am?" "Eh ko akwai in da zaki je?" "Eh amma zan gani idan na dawo da wuri." "Toh ba damuwa,sai ki kirani." "Ok tam." Baya tayi ta kwanta ta ajiye wayar a gefen ta, anya? Anya ba zata sanarwa ko Hamma Haydar bane ba? Zata fara dai tuntubar Kamal ya gaya mata gaskiyar komai kar ya sakata a matsala da karancin shekarun ta. ***Da sassafe Habib ya iso gidan ya tsaye a waje har sai da Aryan din ya gama shiryawa ya fito sannan ya ganshi zaune tare da Baba me gadi, tashi yayi da sauri ya gaida shi ya karbi jakar hannun sa ya saka a mota ya bud'e masa bayan motar amma sai yaki ya wuce ya zauna a gaba yana kin kallon sa. Rufe kofar yayi ya zagayo ya zauna sannan yace "Sir da ka daure ka zauna a bayan" "Anan nake son zama Habeeb." "Please sir, bana so oga Kamal yaga kamar bana aiki na yadda ya kamata." "Menene aikin naka?" Ya tambaye shi "Driver." Dan shiru Aryan din yayi kamar ba zai koma ba, sai kuma ya bud'e kofar ya koma bayan ya shiga ya rufe ba tare da ya sake cewa komai ba. Gidan Ya Nabeela suka fara zuwa, tun daren jiya ta kira shi akan maganar daddy, hankalin ta ya kasa kwanciya dan duk wanda tasan suna harkar tafiye tafiye da Daddyn suna gari babu inda suka je, sannan duk rashin shirin da yake dasu musamman ma Aryan baya taba yin wata tafiya be sanar dasu ba, sannan wayar sa a kashe kuma maigadi yace be ga fitar sa ba dan tazo jiyan gidan lokacin Hajiya Zeenat tana sama sai wasu mutane da bata nutsu dasu ba da ta gani a gidan dan har ita kanta sai da suka tsaida ita da tambayar wajen wanda zata. Ko baccin kirki bata samu tayi jiyan nan ba kwata-kwata, shiyasa ta kira Aryan din shine yace mata zaizo da safe. A zaune ya sameta tayi jigum tana zaune ko kayan baccin jikinta bata cire ba sai Hijab data dora akai ta sallami yan makaranta ta dawo ta zauna a falon tana cigaba da gwada kiran wayar Daddyn ko zata samu ta shiga. Tasowa tayi da sauri ta tare shi "Aryan daddy ba kalou ba wallahi, ni ban yarda da matar nan ba,jiya da naje yanayin yadda take kaffa-kaffa da saman Daddyn na ji ban amince ba, dan Allah kayi wani abu akai, kar taje ta cutar da shi." Hannun ta ya kama ya rike suka zauna ya zama tamkar shine wan itace kanwar saboda yadda duk ta rikice. "Ya Nabeela, me yasa zaki damu kanki haka? Bayan kinfi kowa sanin Daddy ya zabi matar chan akan mu, duk abinda ya faru a yanzu be kamata ki damu ba, dan hakki ne ya fara bibiyar su idan ma wani abun ne ya same shi." "Aryan! Kasan me kake fada kuwa? Daddy fa akace mahaifin mu." "Na sani, ki kwantar da hankalin ki dan Allah, damuwarki matsala ce a gareni fiye da duk abinda zai same shi, amma zan bincika saboda ke, zan gano menene matsalar, amma saboda ke." "Naji, ka shiga dakin sa ka dubo da kanka, ban yadda da ita ba wallahi, she's hiding something matar nan bata tsoron ALLAH." "Zanyi, amma sai na gama da office" "Na yarda, ina jiranka dan Allah." "Ok, ki kwantar da hankalin ki, babu komai in sha Allah." "Tohm shikenan." "Bari naje, zamuyi waya anjima." "Ok." Maganganun Ya Nabeelan ya dinga tattaunawa da zuciyar sa har suka iso company, yana zuro kafarsa suka hada ido da Adam a tsaye cikin fence yana kallon saitin sa, tahowa yayi wajen sa kai tsaye ya ganshi sarai anma sai yayi kamar be ganshi ba ya shiga barin wajen yayi hanyar nasu building din. Daga kafa yayi ganin zai shige ya cimmasa ya tsaida shi. "Aryan please dan tsaye, tambayar ka zan,." "Menene?" "Dan Allah Raihana ta daina zuwa ne?" Kamar wanda ya sokawa mashi haka yaji, yayi masa wani kallon lallai ma ka raina mun hankali sannan yayi shigewar sa. Tsaki Adam yaja ya juya yana kunkuni. Kanshi tsaye ya wuce office dinsu ko wajen yin attendance be je ba, ya samu desk dinta empty ba kowa,juyawa yayi ya wuce office din sa kawai ransa a bace dan idan akwai abinda yaki jini shine Adam ya tsaida shi da shirmen sa, musamman yanzu da maganar wata daban take hada su ba abinda ya saba hada su a baya ba. Haka kurum a duk sanda irin haka ta faru yake kasa controling fushin sa, ya kasa zama sam a office din ya fito ya leka office din Kamal shima be zo ba, agogon hannun sa ya kalla yaga karfe tara har da rabi ta dan gota ma. Tasowa Zainab tayi daga wajen zaman ta cikin yauki da yanga tazo ta tsaya a gabansa tana murmushi "Akwai abinda kake bukata ne sir?" "Babu komai, idan corper din nan tazo kice tazo ta sameni a office." Sai ya juya ya koma office din ya barta a tsaye mamakin sa na neman kai ta kasa, akan Raihanan ya kasa nutsuwa tunda ya shigo haka ko kuma wani abun tayi da ya kasa hakura ya jira ta shigo. A sanyaye ta koma wajen zaman ta, ta zauna tana ko zama sai ga Raihanan ta shigo sanye da black abaya tayi rolling da mayafi mustard colour wanda yayi masifar karbar farar fatar ta. Wani kululun abu ne ya tokare Zainab a makogwaro ta yi saurin dauke kanta ganin tana bi suna gaisawa da mutane, ko da tazo kanta tayi mata sallama kamar yadda ta saba ta wuce office dinsu ta bar Zainab da wani irin sanyayyan kamshin ta da ya cika mata hanci. Tana sane taki fada mata sakon Aryan din dan zuciyar ta zata iya bugawa idan ta cigaba da ganin Aryan din yana kula Raihanan. Bayan mintuna kamar ashirin da zuwan ta, tana zaune kawai dan bata san aikin da zatayi ba Kamal kuma har lokacin be shigo ba bare ta tambaya shi, Aryan kuwa ko giyar wake tasha ba zata tunkare shi ba dan a dar dar take dashi gani take kamar zai gano abinda tayi. Kanta ta dora a saman desk din kawai ta kulle idon ta, ta kunna suratul bakara ta makala earpiece dan ta gaji da kallon wayar. A kanta ya tsaya yana nakaltar yanayin ta, amma sam bata san ya shigo ba, dan ko alamun an tsaya a kanta bata ji ba, a hankali kad'an kad'an take motsa bakin ta, tana bin kira'ar shuraim kuma har lokacin bata bud'e idon ta ba. Dan rankwafowa yayi a daidai saman kanta ya sa hannu ya zare earpiece din daga jikin wayar ta dago da sauri idanun su suka sarke da juna. Diriricewa tayi dan bata tsammaci ganin sa a wajen ba dan ba kasafai yake shigowa ba, waigawa tayi taga babu kowa ashe a office din su abdulhakeem duk sun fita sai ita kadai sai shi da yake tsaye a gabanta rike da earpiece din. Ji tayi baki daya office din yayi mata wani irin fadi da girman gaske, daidaita nutsuwar ta tayi ganin ko gezau be ba yana kallon ta kamar be san me yake ba. "Ina kwana?" Ta tattaro jarumta ta gaishe shi ganin yaki cewa komai "Follow me." Yace kawai ya juya ya fice daga office din rike da earpiece din nata a hannun shi. _ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1  _*IDON NERA*_     Mamuhgee 2  _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata     Billyn Abdul 3  _*RUMBUN QAYA*_      Hafsat Rano 4  _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata     Hafsat Miss Xoxo 5   _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata     Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ RQ*       Page 21 ***Tashi tayi jiki a sanyaye ta bishi, su Zainab suka bita da kallo kamar zasu cinye ta. Sai da ta fara knocking a kofar dan ya riga ya shige sannan ta tura kofar ta shiga kanta a k'asa sosai tana tsoron hada ido dashi. Tana jin idanun sa akanta sanda ta shigo har ta karaso ta tsaya a gaban table din. "Goodmorning sir." Ta maimaita gaishe shi jin yaki cewa komai "Zainab bata fada miki ina kiranki ba?" Girgiza kai tayi "Bata fada min ba." Waya ya jawo gabansa yayi kira "Come please." Yace kawai ya ajiye wayar. Cikin siritar da murya ta shigo tana gwalli tazo ta tsaya ta gefen kujerar sa "Sir gani." "Nace idan tazo ki turo min ita kamar ko?" "Na'am?" "Yes! Me yasa baki fada mata ba?" Kallon bangaren da Raihanan take tsaye tayi,sannan tace "Na fada mata sanda ta shigo, amma bata ji ba cox bata min magana ko nayi mata ni." "Innalillahi!" Tace tana kallon Zainab din "Eh a gabana kika gaisa da kowa kika ki kulani, ina ta miki magana kikayi biris kika wuce office na dauka ma kinji ne kawai ba zaki amsa bane ba." "Ikon Allah!" Kawai tace ba tare da tace komai ba kuma, abin ya tsallake tunanin ta gaba daya ma, shiyasa ta kasa cewa komai tana jiran gogan da ya kirawo ta yayi magana "Excuse us please." Ya cewa Zainab kawai ba tare da ya ce komai akan abinda tace din ba, sai data fara dan dukar da kai alamun respect sannan ta juya ta fita. "Zauna." Ya nuna mata kujera, zama tayi a darare tana jiran abinda zai ce "Ya jikin naki?" Yace yana kokarin bud'e computer sa "Na samu sauki." "Ok good, aiki zan saka ki, amma anan zaki zauna kiyi shi." "Ok sir." Takarda ya turo mata gabanta yace ta duba kafin ya gama shigar da komai, ta dauka ta fara dubawa shi kuma ya cigaba da abinda yake yana jin nutsuwa sosai na saukar masa. ***Yau baki daya Kamal be shigo office din ba, ya dai kira Aryan din ya sanar dashi ba zai shigo ba shiyasa ma aikin ya rinchabe ma Aryan din dole ya rarrabawa su Abdulhakeem aikin Raihana kuma na taya shi da wani anan office din nasa. Yanayin yadda aikin ya dauki zafi sosai ya saka sam basu gane lokaci ya ja sosai ba dan har azahar na neman kufce musu. Sallah yace suje suyi dukka sannan suyi lunch daga nan sai suzo su kara ko away daya be sannan kowa ya tafi. Tunda Raihana tazo office din basu taba dadewa irin ta yau ba, gashi ta kasa ce masa zata tafi dan ya tsare ko ina motsi kad'an zai ce ta duba masa abu kaza wanda kuma ko ta duba daga baya sai ya sake dubawa dan ba wai tasan kan aikin bane dukka, musamman harka ta kudi da lissafi yana da rikitarwa sosai. Ta idar da sallar kenan tana zaune tana tunanin ko ta gudu sai tunanin kiran da Hajiya Zeenat take mata ya shigo mata, ta manta shaf tace zata kirata idan zata zo gashi bata fadawa Kamal din ba ma bare ya gaya mata abinda zatayi. Wayar ta, ta dauka tayi masa text message ta ajiye tana jiran reply dinsa akan zuwan. "Call her kice zaki taho yanzu."     Yayi mata reply a take, tana duba message din ta kira number Hajiya Zeenat din, tace mata zata zo yanzu, toh tace mata duk da bata gidan amma ta lissafa zata iya zuwa kafin ta karasa ta jirata ko ma suyi daidai dan bata so damar yau din ta kufce mata.   Tashi tayi daga wajen sallar ta gyara mayafin ta sannan ta komo office din ta ganshi ya dora akan aikin ba ko hutawa, sau daya tak ya kalle ta sanda ta shigo ya cigaba da abinda yake yi, daga in da take ta tsaya tace masa zata tafi. Banza yayi Mata kamar ba dashi take magana ba, wanda a zahiri ya ji ta sarai sai dai haka kawai yaji maganar ta, ta dan bata mishi rai haka kawai kuma. Sai da ta kara maimaitawa sannan yace "Go." A bacin rai duk da be dago ba amma taji yanayin yadda yayi sounding, juyawa tayi kawai tayi ficewarta ya bi bayan ta, da kallo nan take sai yaji aikin ya fice daga kansa. Lunch din da yayi musu order dukkan su ma'aikatan ya kalla, kowa ya dau nasa sai nata kawai da nashi a wajen a ajiye. Ajiye pen din hannun sa yayi ya ji ba zai iya cigaba da rubutun ba, ya rufe komai ya tashi ya hau tattare kayan sa.   Tana tafe suna waya da Kamal yana gaya mata abinda yake so tayi masa a cikin gidan, har ta karaso gate ta dagawa masu gadin hannu dan har sun saba sannan ta fita. A daidai lokacin shima Aryan ya fito Habeeb dake zaune karkashin wata bishiya yayi saurin sanarwa Kamal fitowar Aryan din dan sun san dole idan ya ganta zai iya cewa su rage mata hanya kuma hakan zai bata musu shirin su. Da sauri Kamal yace mata ta samu wani wajen ta dan labe ta jira wucewar motar Aryan din. Da sauri ta shige wani dan lungu ta labe. Daga ganin yadda ya fito neman ta yake yi, yadda yake rarraba idanun sa a tsakanin wajen ya tabbatar musu da hakan, wajen sa Habeeb ya karaso bayan ya jawo motar "Baka ga wata yanzu ta fita ba?" "Ai da yake yallabai bacci ne ya dan dauke ni naji sanyin kasan bishiya, inaga ta fita ban lura ba sam." "Ok, muje." Ya bud'e masa motar ya shiga. Ta na nan a labe suka zo suka wuce sannan ta fito ta karasa titi ta samu abun hawa ta fada masa in da zai kaita.   Tun kafin ta karasa Hajiya Zeenat tayi waya tace a barta ta shiga, dan haka kai tsaye ta wuce in da tasan zata same ta. Falon tsit babu motsin kowa, dan zama tayi kad'an tana sake karewa falon kallo, sai ga kiran Kamal. "Kinga kafar bene?" "Eh." Tace tana kallon stairs din "Yawwa, tashi ki hau karki kashe wayar." Tashi tayi a tsorace ta kama matattakalar ta fara hawa cike da tsoro, babu abinda kirjinta yake sai dukan uku-uku. Shi yake directing dinta har taje kofar, tasa hannu ta murd'a da nufin budewa amma sai ta jita a rufe "A rufe take da key." "Gosh!" Ya hau kama goshin sa yana murzawa "Kinsan me zaki? Saka bakin ki a jikin kofar ki kira sunan Daddy." "Ok." Tace, ta dan makala kanta a hankali tace "Daddy." Shiru babu wani motsi, ta sake maimaitawa a karo na biyu, sai taji kamar motsi kamar gurnani, sake fadan sunan tayi, sosai taji sautin numfashin babban mutum me cike da wahalarwa. "Akwai mutum a ciki Sir, wallahi akwai mutum." Ta fada a rude tana yin baya "Calm down Raihana, don't panic please, maza ki koma falon kaza ki jirata, suna daf da shigowa gidan kiyi sauri." "Ok." Tace da sauri ta yi hanyar sauka daga saman, ta dinga hadawa da bibiyu ta sauka ta zauna tana dafe kirjin ta "Daddyn Aryan ne kenan a ciki?" Wani hawaye ne ya biyo mata ya sauko tayi saurin share shi jin alamun ana shigowa, tayi matukar kokari wajen daidai ta kanta sanda Hajiya Zeenat ta karaso ciki fuskar ta a sake da fara'ah "Yau ga yata da ta gujeni." Zamewa tayi daga kujerar ta zauna akan carpet sannan ta hau gaishe ta "Tashi ki hau kujera mana, tashi tashi sai kace wata bakuwa Raihana?" "Nan ma yayi Anty." "Toh ai shikenan, ya gida ya mutanen gidan?" "Duk lafiya lou." "Masha Allah , ya labarin Abban ki kuwa? Kin sake zuwa kin duba shi?" "Ai ya fito ma." "Kai haba? Ah Masha Allah, yaushe? Shine amma baki fada min ba." "Last week ne Anty, sannan bani da lafiya." "Ok haka ne, toh sai na shirya ai naje na gaishe shi ko?" "Ai baya nan Anty,baya kasar." "Ah lafiya dai ko?" "Da sauki toh." "Ayya toh Allah ya bashi lafiya, yana dawowa ki sanar dani zanje na duba shi nayi masa barka da arziki." "Ok tam in sha Allah."   Wayar tace tayi kara, message ne daga Kamal _"maza ki fice Aryan yana hanyar zuwa."_ Yunkurawa tayi da sauri "Hajiya zan tafi, Addah tana kirana." "Toh, toh shikenan sai munyi waya ko? Wajen aikin naki ba dai wata matsala ko?" "Babu komai Anty, nagode."    Sauri ta dinga yi tana waige har ta fita daga unguwar baki daya, har ta samu napep ta shige. Bayan wajen mintuna ashirin da tafiyar ta sannan Aryan ya iso. Da k'yar ya iya bari Habeeb yayi parking a harabar gidan ya balle murfin motar ya shiga ciki a sukwane. Yanayin yadda ya shigo gidan ya saka Hajiya Zeenat mikewa tsaye, "Lafiya?" Ta tare shi tana tambayar sa, wuce ta yayi ya fara hayewa saman da sauri da sauri. Bin bayan sa tayi da sauri tana kiran sunan sa. Kai tsaye dakin daddy ya nufa, yana zuwa ya tura kofar da karfi. Babu kowa a ciki sai dakin da yake a gyare ko ina. "Menene wai Aryan?" "Ina Daddy?" Yace yana zare mata ido cikin matukar bacin Rai. "Mtsw! Taja tsaki, "Dalilin da zaka shigo gidan a haka? Baka san yayi tafiya bane ko me? Me kake nufi kenan da abinda kayi yanzu?" "Ina kika kaishi? Yana ina?" "Ban sani ba, tunda baka yarda ba ai gidan ba bakon ka bane ba, ka shiga ka bincika. Mtsw!" Ta juya ta barshi a tsaye a wajen. Dafe kansa yayi da hannu biyu da yake masa wani irin bugawa ya shiga bi dakunan daya bayan daya yana dubawa har da lekawa kasan gado. Text message din da aka tura masa ya sake dubawa yana son sake tabbatar da abinda yake kunshe a sakon _"Kayi sauri kaje mahaifin ka yana rufe a dakinsa, suna kokarin chanja masa dakin dan haka sai kayi sauri."_ Abinda ya taso shi kenan afujajan duk da be san waye yayi amsa message din ba, waye yake kokarin wasa da hankalin sa? Ya tambayi kansa. Kiran Ya Nabeela a karo na kusan biyar ya shigo, dagawa yayi yana yarfe hannun sa ya zauna a gefen gadon Daddyn ya dafe kansa sannan ya daga "Ya ake ciki Aryan?" "Bata ciki ya Nabeela." "Na shiga uku, yanzu ya zamuyi?" Idon sa ne ya sauka akan yar karamar wayar Daddyn da ta kusa shigewa kasa gado, hannu yasa ya dauka ya ganta a kashe alamun charging ya kare "Na ga karamar wayar sa Ya Nabeela." Ya mike da sauri yana rike da wayar, "Sake duba dakin sosai Aryan, babu wani abu kuma?" Duddubawa ya hau yi amma be ga komai ba, fitowa yayi ya fice da wayar daga gidan. Asalin office dinsa ya nufa ya kira Kamal yace su hadu a can, yana zuwa Kamal din ma na zuwa kamar wanda yake a kusa, abinda yake faruwa da tunanin da Ya Nabila tayi har zuwa text message din da aka tura masa ya nuna ma Kamal din, shiru yayi kamar me nazari wajen mintuna biyar kafin yace "It's time da ya kamata muje muga Barrister Matawalle!" "Yaushe?" "Zan yi kokarin nema mana ganin shi ta wajen wanda ya sanar min da labarin fitowar sa, ina ganin kar mu wuce kwana biyu bamu neme shi ba, sannan maganar Daddy ka bar komai a wajena." "I trust you with my life Kamal, ka sani kai kadai na yarda dashi." "Ba zaka taba dana sanin taraiya dani ba Aryan, I promise you that." "Shikenan. Allah yasa." "Amin, muje mu kwantar wa Ya Nabeela hankali, in sha Allah ba abinda zai faru." "Ok Allah yasa." "Amin." ***Washegari ya tashi da wani irin ciwon kai sosai, dan dama tun dare yake jin alamar sa, haka ya daure ya shirya ya fito office. Kamal yau ya riga shi zuwa saboda rashin shigowar da be yi ba jiya, wanda aikin Aryan din ne gaba daya ya hana shi shigowa, a yanzu haka yasan komai akan daddy har in da suke kaishi, kuma shine da kanshi yayi wa Aryan din text message bayan ya aikawa Hajiya Zeenat nata akan tayi gaggawar dauke Daddyn daga gidan. Dan hatta gidan da ta maida shi suna kallon ta, tabbas karshen ta ne yazo dan haka cikin kankanin lokaci zasu kammala komai su damke ta, bayan sun samu dukkan hujjoji akanta. "Ya labarin zuwa gidan Alhaji Nasir din?" Aryan yace bayan ya shigo office din nasu sun gaisa "Gobe in sha Allahu zamu je mu ganshi." "Ya amince?" "Ko be amince ba, zuwa zamuyi dan idan ya ganmu ma dole ya amince, disk din wajensa shine kawai abinda muke jira dan shine yake dauke da komai da ya faru ranar, babban dalilin da ya kaishi prison Kenan, amma duk da haka be yarda ya bada shi ba tsawon lokacin." "Ina fatan komai zai zo karshe Kamal, na gaji wallahi, inaso nayi rayuwa kamar kowa, amma na kasa, idan ba gani nayi an daure Hajiya Zeenat ba hankali na ba zai taba dawowa jiki na ba." "Lokacin yazo ai." "Allah yasa." "In sha Allah, Amin." "Bari na je naga Ya Nabeela, kamar bata jin dadi tun ranar ." "Allah sarki, ka duba ta please, aiki ne dani da munje." "A ah yi aikin ka, jiya nima haka nayi nawa." "Na sani kam,sai ka dawo." Kofar ya ja masa ya fita, ko office dinsa be shiga ba ya sauko kasa. A reception din k'asa suka hadu da ita ta shigo, dauke kai yayi kamar be ganta ba, yana ji tana gaishe shi yyi biris kamar be ji ba, ya wuce kawai kansa tsaye. Tabe bakin ta, tayi kawai yau abin ya motsa, kaamar me aljanu jiya yana ta kula ta amma yau yayi kamar be san ta ba. Sarai ya ji sanda ta gaishe shi, haka kawai yaji yana fushi da ita tun jiya da ta matsa ana aikin nan sai ta tafi, shiyasa yayi kamar be ganta ba yay wucewar sa, sai dai kasan zuciyar sa na karanta masa rashin kyautawar sa. Adam na tsaye tun bayan da ta shige be bar wajen ba, magana yayi mata ta masa banza hakan ya kona masa rai, ganin Aryan yasa shi tunawa da abinda yayi niyya. Tarar shi yayi yana shirin shiga motar sa yace "Na raina wayon ka Malam, kana ganin kamar kana da wayo,amma ina, kana tare da mutanen mu amma baka sani ba, lallai na raina wayon ka." Yana rike da hannun motar be shiga ba yana jin shi amma be tanka ba, sai da ya kai karshe sannan yace "Kune baku da aikin yi da har kuke bibiya ta, dan haka wahala ce bata ishe ku ba." Ya shige ya zauna ya banko kofar, gaban motar Adam ya bud'e da sauri ya zauna yana dariyar shakiyanci "Da kana da wayo da sai ka tambaya su waye hakan? Ba wai ka share maganar ba, bayan nasan waye kai, hankalin ka ba zai taba kwanciya ba har sai ka gano waye." "Malam ka fitar min daga mota kafin na kira securities." "Please ka fita." Habeeb yace "Shut up, ba da kai nake ba, da ubangidan ka nake yaro, ka bari mu yi dashi. Kai kuma...". Ya juyo kan Aryan "Check your WHATSAPP!" Yana fadan haka ya fice daga motar gami da banko masa kofar. *RUMBUN QAYA* ©®_Hafsat Rano_ Page 22 ****Sautin bugun zuciyar sa ne ya sauya bayan fitar Adam din, ya runtse ido sosai tsoro na shigar sa, tsoron maganganun Adam din wanda yake da yakinin tabbas akwai wanda yake taimaka musun kamar yadda yace, amma waye? Ba zai iya dubawa ba dan yasan zuciyar sa zatayi bugawa ma baki daya musamman idan ya samu wanda yayi matukar yadda dashi da laifin. "Ya Allah!" Ya furta a hankali yana sake chusa wayar sosai a cikin aljihun rigar sa yana son dauke hankalin sa wajen hakura da ganin abinda zuciya da gangar jikinsa basu amince masa da gani ba. "Please oga karka daka ta, tashi dan Allah." "Ba komai Habeeb, muje kawai." "Ok ." Ya tada motar suka fita. Tana zaune a office din suna hira da Abdulhakeem wanda ta kura fiye da rabin hankalin sa na kan wayar hannun sa, chatting yake da alama dan yanayin yadda yake amsa mata wata maganar zaka tabbatar da ya kasa hankalin nasa waje da yawa. Shiru tayi masa ta dauki wayarta itama kawai ta hau dannawa ko ta rage zaman dan babu abinda zatayi har Oga Kamal ta tambaya yace ya bari Aryan ya dawo. Tayi mamakin da be yi mata maganar abinda ya faru jiya ba, gashi tana son sanin halin da Daddyn yake ciki dan kusan kwanan zaune jiya tayi tana tunanin abinda ta ji, tabbas nishin mutum ne me cike da wahalarwa, tana rufe idon ta shi take hasasowa hakan ya hana ta samun isheshan bacci sosai. Wayar tace tayi kara ganin Hamma Hydar ne yake kira yasa ta dauka da sauri. "Hamma na." "Na'am kanwata, gani a garin naku." "Kano?" "Eh shigowa ta kenan." "Laaa, shine baka fada min ba?" "Wallahi zuwan urgent ne, Abby ya taso ni, kina ina yanzu?" "Office." "Ok, zan kiraki ki jirani zanzo na dauke ki." "Ok Hamma, sai kazo." Tana cikin wayar taga fitar Abdul sai ya kasance babu kowa a office din, Zainab ce ta shigo rike da wani file ta dire mata a gabanta, takardu ne a ciki fal ta daga kai ta kalle ta "Menene wannan?" "Aiki ne, idan kin gama wasu na jiranki, dan na lura zaman dumama seat kawai kike yi, ko da yake kin samu masu daure miki gindi, farar kalar ke kwasar su da alama." "Ke a matsayin ki na waye da zaki sakani aiki?" "Hehe." Ta kwashe da dariya "Wato kina da baki ashe, a gaban Oga sai ki dinga yin kamar tsohuwar munafuka, da haka kika yi amfani kenan wajen tura kanki gareshi, sai ayi mu gani ai, aiki kuma shine ya saki bani ba, dan ni bani da lokacin batawa akanki, idan zakiyi gashi nan, idan ba zaki ba ki barshi, idan ya dawo ya sake dole ai." "Har shi ma bashi da hurumin sakani aiki dole, nasan rights dina dan haka ba zan ba, idan yazo sai ki fada masa nace ba zan ba, ke da suke biyan albashi sai kiyi." Kusan mutuwar tsaye Zainab tayi, bata dauka yarinyar na da gut haka ba, ganin ta take kamar doluwa a kullum, aikin Cynthia ne ba wani Aryan da ya sata, kawai neman rigima suke da Raihanan sai gashi ta nuna mata itama eh ce, juyawa tayi ta fita ba tare da ta sake magana ba, bayan kwafar da tayi kawai kuma bata dauki file din ba. Tashi Raihana tayi rik'e da file din, ta bi bayanta ta dire mata akan table tayi juyowarta tana sabani "Gani jaka, ba zan ba wallahi." Tayi zaman ta, ta ma kunno kallo a wayarta ta dora akan table din tana kalla. Ta dade tana kallon har ta gaji ta koma game daga nan ta kashe wayar ganin rana tayi har lokacin tafiyar ta yayi, Hamma Haydar ta kira yace mata ta jirashi wani abu ne ya tsaida shi amma yana nan zuwa karta tafi. Jugum tayi a zaune dan wasu har sun soma tafiyar da kad'an kad'an har kowa ya yaye sai ita kadai sai Kamal da yake cikin office dinsa ya dukufa akan aikin da yake yi. Wani kiran Hydar din ne ya sake shigowa, sai dai wannan karon da sauri yace;. "Raihana, ya sunan wanda kike PPA a wajen su." "Oga Aryan ne, da Oga Kamal." "Wai da gaske?" "Eh sune, Ka sansu ne?" "Kwarai kuwa, sai dai nazo zamuyi magana kawai." "Dan Allah Hamma gaya min, menene?" "Wallahi labarin me tsawo ne Raihana, amma ki bari nazo." "Toh sai kazo." Ta ajiye wayar cike da zulumi da tunanin yadda akayi ya sansu. ****Zuwan sa gidan Ya Nabeela ya hana shi aiwatar da abinda zuciyar sa take fada masa, kashe wayar tasa yayi gaba daya bayan ya karbi key dinsa a wajen Habeeb yace yaje kawai yayi zaman sa a gidan dan wani irin tsoro ne ya dinga shigar sa, tsoron abinda zai taarar. Har bayan azahar yana gidan sai a lokacin yaji nutsuwar tafiya yayi mata sallama yana sake danne zuciyar sa da ganin abinda zai tashi hankalin sa. Tuki yake a hankali ya ma sauka chan gefen titin dan ma kar ya hana masu sauri sai yan napep da suke ta daga masa hannu suna masa horn be kula su ba, da haka har ya kai office din ya samu gefe daya yayi parking ya ciro wayar ya kunna da niyyar kiran Kamal yaji ko yana office har lokacin dan haka babu mota a harabar wajen ko daya. Message din hoton da ya fito a saman notification bar din wayar ya dauki hankalin sa, hannun sa na wani irin rawa ya danna kan hoton wanda ya dauke shi direct zuwa kan chat din Adam din. Idon sa ne ya soma yi masa dishi-dishi kafin ya bud'e masa tar ya gani, hoton tane a zaune tare da Hajiya Zeenat, a cikin falon gidan su sanda take mika mata key din nan. Da sauri da sauri ya shiga bud'e sauran hotunan wanda duk itace a jiki suna magana da Hajiya Zeenat ko kuma tana murmushi. Audios din ya bud'e yana girgiza kansa da wani irin yanayi. Muryar tace ta bayyana tar a ciki tana shaidawa Hajiya Zeenat ta dauko key din, da sauri ya katse ya shiga wani, sai dai baya iya dire su har karshe yake kashewa ya kunna wani. "Why Raihana? Why?" Ya fada da karfi yana balle murfin motar, ya fito ya nufi cikin building din da wani irin sauri. Tashi tayi daga zaman da tayi da nufin fitowa ta sauko kasa kawa ta jira Hamma Haydar din dan saman yayi mata shiru sosai dan bata ma yi tunanin akwai mutum ba. A hanya sukayi kicibis tayi wani irin mugun ja baya amma duk da haka sai da jikinsu ya hadu kanta ya bugu da gefen kafadarta. Ture tayi da iyakar karfin sa, tayi baya kamar zata fadi tayi saurin dafe bangon dake wajen. "Me yasa? Me yasa zaki ci amanata?" Yace yana matso ta Zaro ido tayi dan sai da yayi magana ta lura da yanayin da yake ciki "Why Raihana?" Karo na farko da ya taba fadar sunan ta kenan, amma a yanayin da yake nuna tsantsar tsana da kiyayya "Me nayi?" "Baki sani ba?" Girgiza kai tayi, ya cije lips dinsa na kasa da karfi yana wurga hannun sa baya, sai kuma ya sake matsowa ya bud'e wayar sa ya nuna mata hoton "Wannan ma baki sani ba?" "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun." "Tell me, shima baki sani ba? Ko photoshop ne? Idan kince baki sani ba, wannan ma ba voice dinki bace ba?" Ya danna audio din "Na sani, na sani, amma zan maka bayani." "Bana so! I don't want to hear anything from you, babu abinda zaki ce min, i hate you! bana son sake ganin ki a gabana, just goooo." "Dan Allah zan yi maka bayani, wallahi amfani tayi dani, she used me wallahi, ban aikata abinda kake tunani ba, dan Allah." "Allah bana son ji, ki tafi kawai and don't ever show your face again." "Please..." Ta hade hannayen ta waje daya tana kuka Juyawa yayi da sauri ya shige office din dake kusa da wajen, wanda bashi da maraba da hadadden falon gida. Kuka ta durkusa a wajen tanayi, kamar ranta zai fita, duk abinda ake Kamal yana sama be sani ba, Hydar ne ya kirata yace yazo, amma jin muryar ta yasa shi katse kiran kawai ya shigo office din kansa tsaye dan ko magana ta kasa. A kofa ya tarar da ita tana gursheken kuka, ya dago ta yana tambayar abinda ya faru, a cikin kuka take masa bayani wanda ya kasa fuskantar komai, sai dai ya fuskanci da Aryan ne. "Ina Aryan din?" Yace,da hannu ta nuna masa office din, yace su shiga, tayi gaba yana biye da ita, yana son tabbatar da abinda yake zargi. A baya ya tsaye sanda suka karasa ba tare da ya shiga ciki ba. a Sanyaye ta turo kofar ta shigo, ta hange shi tsaye ya bada bayan sa yana kallon window hannun sa rike da curtains din, takowa ta shiga yi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, zuciyar ta na wani irin harbawa irin wanda bata taba ji ba. Motsin ta ya sashi juyowa kafin ya saki curtains din ya zuba mata ido cikin yanayin da yake nuna tsantsar bacin ransa. Ji tayi tamkar ba zata iya karasawa ba, kamar ta zube a wajen kawai tayi ta rusa ihu saboda tsananin tsoron da yake shigar ta. Da jan kafa ta karasa gaban nasa tayi saurin dukawa k'asa idanun ta na cigaba da zubda hawaye, hawayen bakin cikin abinda yake zargin ta dashi, ko da yake ta aikata din a baya duk kuwa da a rashin sani ne, amma bata taba zaton abun zai dawo musu a wannan lokacin ba "Me ya kawo ki?" Yace cikin dashashiyar muryar sa dake fidda amon sautin yadda ransa ya kai matuka a baci. Shi mutum ne mara yarda sam, rayuwar sa ta baya ta sashi rashin yarda da kowa da ma komai, Ya Nabila kadai ya aminta da ita, ita kadai ya yarda ba zata cutar dashi ba, sai Kamal sai kuma zuwan ta rayuwar shi, ya yarda da ita fiye da yadda ya yarda da kan sa, har ya kan ji nutsuwa a duk lokacin da yake tare da ita, amma kuma... "Dan Allah kayi hakuri." Tace cikin shashekar kuka, girgiza kansa yayi yana dauke kansa daga kallon ta dan ma kar zuciyar sa tayi masa rawa akan hukuncin da ya yanke, kar tayi rinjaye akan sa har ta sakashi karya alkawarin da yayi ma kansa na rashin kyale duk wanda ya ha'ince shi. "Ki tashi ki fita daga nan wajen, I don't want to see you ever again." "Please ka saurare ni, dan Allah ka bari kaji abinda zan fada maka." Durkusawa yayi a gaban ta kafar sa daya ya choge ta yana duban ta idanun sa sun yi mugun kadawa "I hate mutane masu fuska biyu RAIHANA , haka nan bana sake yarda da wanda yaci amanata, ki tashi ki fita bana son ganin ki, get out of my life!!" "Dan Allah..." "I said get out!" Ya fada da karfi bayan ya mike tsaye, hannun sa na mata nuni da kofar, rud'ewa tayi kasancewar yau ne karo na farko da aka fara mata irin wannan tsawar, juyawa yayi ya sake bata baya yana jin yadda take kuka sosai, kukan da yake jin tamkar ana daddatsa masa jikin sa, kamar ana zuba masa garwashi a cikin kokon kansa. Juyawa tayi da sauri harda dan gudun ta, ta fice daga wajen tana rusa kukan sosai, runtse idon sa yayi ya bud'e kansa da yake masa wani irin ciwo ya rik'e ya shiga matsawa a hankali zuwa kujerar dake gefe ya zauna yana tallafe kan nasa "Sai kayi nadamar abinda kayi Aryan, sai kayi nadama a lokacin da bata da amfani." Dagowa yayi da sauri ya kalli kofar, matashin saurayin da a kalla zasuyi kusan sa'a ne a tsaye yana duban sa, fuskar sa ce ta shiga dawo masa zuwa wani lokaci me tsawo, kamar sa ce tun a lokacin be chanja ba, ba kuma yana tunanin ko da zata chanja din ya kasa ganeshi, tare aka hada su aka tarwatsa musu rayuwar su, aka raba su da mutane masu muhimmaci a rayuwar su "Haydar?" Yace yana tashi tsaye da sauri "Sai kayi nadamar abinda kayi ma kanwata Raihana, kana nan da zuciyar ka da rashin yafiyar ka, kanwata bata chanchanci mutum irin ka, kamar yadda ka rasa mu a baya, haka zaka sake rasa mu a wannan lokacin. Sai ya juya ya buga masa kofar da karfi "Kanwata? Raihana? Raihana Nasir? BARRISTER NASIR MATAWALLE?" Duk a lokaci daya sunayen suka shiga amsa kuwwa a saman kansa "Ya salam!!" Yace da sauri yabi bayan sa, da gudun gaske ya dinga sauka daga stairs din yana hada bibiyu, harabar ya fito babu ko mota daya sai tasa, gaba yayi zuwa wajen masu gadi suka ce yanzu mota ta fita, gate din ya fita ya dinga waige-wage sai dai ko kurar su be gani ba, bare ya san in da suke nufa *TUNA BAYA* SHEKARU MASU YAWA DA SUKA SHUDE SUKA HAIFAR DA TARIN ABUBUWA MASU YAWAN GASKE, RAYUWAR GIDAN NASIR MATAWALLE DA AMININ SA IBRAHIM MUKADDAS.🖍️🖍️🖍️🖍️ MUN SHIRYA???? MU HADU A AREWA BOOKS😎😎😎 ZAFAFA BIYAR.....× 2023 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥🔥🔥🔥🔥💥🔥💥🔥🔥💥🔥🔥💥💥💥💥💥🔥💥🔥🔥🔥🔥 INA MAABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR WRITERS? WANNAN KARON MA MUN SAKE DAWO MUKU DA ZAFAFAN LITATTAFAN MU, MASU DAUKE DA ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA KU GARZAYO. ZAFAFAN NA KU SUN SAKE TAHOWA DA WASU ZAFAFAN LITTATTAFAN MASU DIMBIN DARUSSA NA MATAKAN ILMANTARWA RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM... SAFIYYAH HUGUMA A RUBUCE TAKE (KADDARATA)♥️ HAFSAT RANO (RUMBUN QAYA)🥰 MAMUH GEE (IDON NERA)🤩 NANA HAFSATU KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYA)😘 BILLYN ABDULL DAUDAR GORA (CIKI KA SHATA)💗 DUKA DUKA WADANNAN LITTATTAFAN ZASU ZO MUKU NE CIKIN FARA SHI MAI RAHUSA KAMAR KO DA YAUSHE. DUKA BIYAR DIN AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYU 1200 GUDA HUDU AKAN NAIRA DUBU DAYA 1k GUDA UKU AKAN 800 GUDA BIYU AKAN 600 GUDA DAYA AKAN 400 DADIN DADAWA, MUNA TALLATA HAJOJIN KU AKAN FARASHI ME SAUKIN GASKE! SANNAN GA BIYAN BUKATA HANYOYIN DA ZAKU IYA TUNTUBAR MU DOMIN ZAMA CIKIN SAHUN FARKO NA WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR SUNE; MASU BIYA TA BANKI ZAKU BIYA A WANNAN ACCOUNT DIN BANK: ACCESS BANK ACCOUNT NAME: MARYAM SANI ACCOUNT NUMBER; 0022419171 SAI A TURA EVIDENCE OF PAYMENT HADE DA ACCOUNT NAME TA WHATSAPP TA WANNAN NUMBER; 09033181070 IDAN KUMA KATIN WAYA NE NA MTN SEKU TURO KATIN VTU/SHARE AND SELL KO NUMBER KATIN HADE DA SHEDAR SA TA WHATSAPP ZUWA: 09166221261 FARASHIN LITTTAFAN ZAFAFA BIYAR NA CHANJAWA DA ZARAR AN KAMMALA SU. SAI KU YI SAURI KU GARZAYA DOMIN A DAMA DAKU A WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR 2023🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥 KU GARZAYO A SAKE DAMAWA DA KU A WANNAN SABUBAR TAFIYAR MAI DAUKE DA SALO NA BAN MAMAKI. KAR KU BARI AYI BABU KU. DOMIN ZAFAFA BIYAR NA KU NE. 😘🤩 [05/01, 21:53] Billyn Abdul 2: 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR MAZAUNA K'ASAR NIJER?*🤏🏾 *TO KU MARMATSO KUSA TA SAMU!!*🇳🇪🇳🇪 *MUN SAURARI KOKENKU MUN KUMA AMSA* *Zafafa biyar dinku sun samo muku hanyar biyan naku kudin karanta litattafan zafafa har guda biyar din* *ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE* +22799643131 *LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA* *DAUDAR GORA Billyn abdul* *KI KULANI hafsat xoxo* *A RUBUCE TAKE Huguma* *RUMBUN K'AYA Hafsat rano* *IDON NERA Mamuh ghee* *KUDIN LITATTAFAN ZAI KAMA KAMAR HAKA* Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA *MUNA GODIYA DA SOYAYYARKU GAREMU AL'UMMAR NIJER,MUNA MUKU FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA BISA ZABIN ZAFAFA BIYAR*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *RQ* 23 *TUNA BAYA* ****Gidaje guda biyu a jere da juna iri daya sak, hatta fentin jikin gidan da na gate din iri daya ne komai da komai. Daga cikin gidajen biyu akwai wata kofa da tayi linking gidajen biyu wanda baka da bukatar fitowa ainahin gate din idan zaka shiga daga wannan gidan zuwa wannan. Fiye rabin rayuwar su a tare suke yin ta shiyasa zaka samesu a kowanne lokaci a taren idan basa gidan wannan toh suna dayan anan suke komai. Nasir da Ibrahim Aminan juna ne tun daga zamanin kuruciya har kawo girman su har kawo yanzu da sukayi aure har suka samu zuria suna yadda suke babu wani abu da ya taba shiga tsakanin su. Asalin mahaifin su Nasir dan Zamfara ne sai aiki ya kawo shi kano in da suka hadu da mahaifin Ibrahim suka zama abokai ta in da abokantar yaran ta samo asali kenan. Tun daga primary suke tare sai da aka zo university sannan suka rabu in da Nasir ya karanci bangaren law shi kuma Ibrahim ya karanci mass communication. A university din suka hadu da matan su, kawaye ne su uku suma duk da banbancin jahohin da suka fito amma sun zama kawaye sosai. Khadija, Aisha da Zeenatu. Khadija itace yar kano sai Aisha daga Adamawa sai Zeenatu da ta kasance yar kogi state. Duk weekend a gidan su Khadija suke zama sun yi mugun sabon da babu wadda take boye wa wani sirri saboda shakuwa. A haka suka kammala karatun su lokacin har su Ibrahim sun fara business ba tare da sun jira aikin gwamnati ba dan sun kusan shekara uku da gama karatun kafin su Khadija su gama, Nasir dai yana dan zuwa chamber shima ba kowanne lokaci ba, saboda haka basu wani damu da dole sai sun samu aiki ba, suka fara business dinsu cikin ikon Allah komai ya soma bunkasa. Kiwon kifi suka fara Allah ya saka musu albarka a hankali sai suka yi expanding dinsa zuwa babban gidan gona cikin shekara daya komai ya kankama dan ba karamin samu suke da harkar ba, daga nan ne suka fara shawarar aure, tunda already suna da yan matan nasu a hannu. Ibrahim ya auri Khadija shi kuma Nasir ya auri Aisha wanda aka daura auren a Yola Adamawa tunda ita chan ne garin su. Duk shagalin bikin nan da Zeenatu akayi shi musamman da ta kasance babbar kawa kuma aminiya ga amaren dan haka ne ma ya kasance kusan itace akan komai har aka kai amaren gidajen su da suke a manne da juna. Rayuwa ta cigaba da garawa a hankali lokaci zuwa lokaci Zeenat ta kan kawo musu ziyara musamman idan ta shigo Kano wanda take sakewa tamkar a gidan ta ne saboda babu wani shamaki a tsakanin su saboda yadda suka yarda da junan su, duk sanda tazo suna jin dadi sosai dan ba karamin kirki ne da ita ba haka kuma ta saba sosai da nasir da Ibrahim dama tun a school. Aisha ce ta fara haihuwa ta haifi Namiji wanda nan take Nasir yayi masa huduba da sunan Ibrahim wanda suke ce masa Lamido. Bayan lokaci kadan itama Khadija ta haihu amma sai ta haifi mace ita, aka saka mata Nabeela. Rayuwar su gwanin sha'awa suka cigaba da rainon yaran su har shekara biyu sannan suka sake samun wani cikin a kusan lokaci daya amma wannan karon Khadija ta riga Aisha. *Mafarin Matsalar su* Watarana da azumi bayan sun yi sahur nakuda ta tasar wa Khadija, nan da nan suka dunguma zuwa asibiti aka bar Aisha da yaran a gida. Wajen azahar ta haihu ta haifi dan ta namiji, Zeenat a lokacin tana gari dan ta dawo Kano saboda ta fara masters a lokacin dan haka tana jin suna asibiti ta shirya ta tafi tana chan akayi haihuwar itace ma ta fara kira ta fadawa Aisha, nan da nan sai gata nan ta taho ita da Lamido da Nabeela. Daga nan aka sallamo su suka yo gida. A tsakanin gidajen biyu Zeenatu take zama, daga wannan gidan ta koma wannan har ranar suna in da sukayi anko su uku hadda ita, akayi suna gagarumi saboda ko a lokacin business dinsu ya sake bunkasa sosai har sun fara harkar man fetur. Bayan an gama suna mutane sun watse Khadija ta shiga wanka, ta bar Zeenat da Aisha a dakin. Ta dade a ciki sosai tana fitowa ta tarar basa nan dukkansu, ta dauka suna falo sai kawai ta hau shiryawa ta gama sannan ta fito falon. Basa falon babu kuma jaririn sai ta dauki waya ta kira Aisha. "Ashe kun shiga ciki." "Eh wallahi, ai kina shiga wanka na dawo na dan gyara gidan, na bar Zeenat dai ko itama bata nan?" "Eh bata nan." "Ok kira ta." "Gata ma ta shigo." Khadija tace idonta akan hannun Zeenat din ganin ita kadai ba jariri "Kin fito sister?" "Eh, na zata kuna falo sai naga bakwa nan, waye ya dau Ahmad?" "Ahmad? Baya dakin?" Tace tana kallon ta. Wani irin faduwa gaban Khadija yayi, ta juya da sauri zuwa dakin Zeenat ta mara mata baya. Abun daukar sa ne kawai a gadon babu komai, jikinta ne ya hau rawa cikin tsananin tashin hankali suka shiga dubawa, lungu da sako har da leka kasan gado amma babu jinjiri babu dalilin sa. Kanwar Khadija Habiba ce ta shigo daga waje dan suna chan dakin dake compound din basu san me ake ba. "Habiba kun dau Ahmad ne?" "A ah." Tace, hannu Khadija ta dora aka ta fara kuka, "Na shiga uku." Da sauri suka yo waje suka shiga gidan Aisha, tana gyarawa Nabila riga kenan bayan tayi musu wanka ita da Lamido suka shigo a birkice wai basu ga Ahmad ba, nan fa hankalin ta ya tashi itama suka yo waje gaba daya cikin tsananin tashin hankali. Wasa wasa ya tabbata an sace jaririn! Duk irin binciken da za'a yi an yi, babu jariri babu dalilin sa kuma babu wanda yasan sanda aka fita dashi daga gidan. Iyakar tashin hankali iyalan biyu sun shiga, an kai report din police station amma babu wani labari, haka suka zauna jigum-jigum yadda suka ga rana haka suka ga dare babu wanda ya runtsa. Tsawon lokaci ana saka ran zaa samu wani abu game da batan Ahmad Amma shiru har suka fitar da rai, Zeenat ko wanne lokaci tana tare da Khadija tana kwantar mata da hankali har Aisha ta haihu babu wani taron suna ko wani abu da akayi dan duk basa cikin nutsuwar su, ta sake haifar danta Namiji aka saka masa Abubakar Sadeeq. Rayuwar iyalan biyu ta sauya sosai tun bayan batan Ahmad, wanda har lokacin Khadija ta kasa hakura kullum cikin kuka take sosai dan ma Zeenat da Aisha suna kwantar mata da hankali sosai Amma duk da haka abun ya riga ya bar mata gibi me girma a rayuwar ta wanda zata dade bata cike shi ba. A hankali rayuwa ta cigaba da turawa yaran suna dada wayo sosai kuma suna kara shakuwa da juna, dan ko yaushe suna tare da juna a gida daya. Bayan wani lokaci suka sake samun wani cikin, tsoron Mommy (Khadija) ya dadu sosai tun bayan da ta gane tana da ciki, dole ta matsawa Daddy (Ibrahim)suka saka CCTV a kowanne sako da lungu na gidan sannan aka kawo megadi dan har lokacin bata amince cewa babu saka hannun na gida a dauke mata d'a ba, dan dai bata san wa zata ce ba dan dukka mutanen da suka yi ragowa a gidan a lokacin na jikinta ne makusanta. Ita ta fara haihuwa wannan karon ma, ta haifo dan ta namiji kyakkyawan gaske, ta rungume shi tana hawaye sosai tana tuno Ahmad, babu wanda yazo asibitin daga ita sai Ammy (Aisha). yaran suna gida tare da me aikin su da kanwar Mommy Habiba. Babu wanda ya san da labarin haihuwar sai yan gidan su har sai da aka kwana sannan ta kira Zeenat ta fada mata, ta nuna rashin jin dadin ta da ba'a fada mata tun jiya ba. Muhammad Aryan shine sunan jaririn, wanda baki daya dawainiyar sa Zeenat ta dauke saboda yadda take tsananin son shi. Yaro ne me shiga rai sosai da abun sha'awa, ada Sadeeq ne nata amma ana haifo Aryan ta tattara ta watsa Sadeeq a dustbin tayi sabo, suka dinga tsokanar ta tana dariya. Ko da Ammy ta haifi Hydar still dai Aryan din shine nata, dan duk wani kudi da zata samu toh Aryan ne, duk wani abu da yake so shi take masa, duk wani abu da ta gani nasa ne. Watarana suna zaune su uku suna hira sai Ammy tace mata yaushe zatayi aure wai? Lokaci yana tafiya gasu duk da yaran su ya kamata ta yi aure saboda shekarun sun fara tafiya. Murmushi kawai tayi tace ta kusa lokaci kawai take jira suka barta a haka da addu'ar Allah ya kawo lokacin kawai. Tun daga lokacin ta dauke kafarta daga gidan nasu, sai dai a waya kawai suke magana sai rana daya ta kirasu wai an daura mata aure a garin su. Dukkan su basu ji dadi ba ace har tayi aure sai bayan an daura zata sanar dasu amma sai ta nuna musu itama baa son ranta bane ba, dole sukayi mata uzuri amma a kasan zuciyar Mummy sam sai taji bata gamsu ba. *DAWOWA LABARI* Da sauri ya dawo cikin building din yana hawowa suka hadu da Kamal kunnen sa sakale da waya yana magana, rike hannun sa yayi yanayin Aryan din yasa shi katse wayar yana duban sa "Na kwafsa Kamal." "Da kayi me?" Yace yana duban sa "It's a long story, kasan gidan su Raihana please?" "Raihana kuma? Gidan su? Me ya faru?" "Ka sani? No wait ka sani Kamal, ranar nace kayi dropping dinta, please take me, inaso naga Hydar." "Wai me ya faru? Ka fada min naji tukunna." "Muje zan fada maka a hanya." Ya shiga jansa,binsa yayi yana cewa "An yanka ta tashi, Barrister yace mu dakata da zuwa." "Mu dakata? Akan me? Ba zai gan mu ba Kenan?" "Be dai ce ba, amma yace a dakata dai." "Zanje kuwa, kuma zai ganni. Na gaji da wannan jeka ka dawo din, dole ma ya ganni." "Toh yanzu fada min, menene ya faru? Me ya hada ka da Raihanan." "Shiga mota please." Ya bud'e masa kofar gaba da kansa, shi kuma ya shiga baya Habeeb ya tada motar "Kasan Raihana yar gidan Barrister Matawalle ce Kamal?" Juyowa yayi bayan "Na sani." "What? Ka sani Kamal? Baka fada min ba amma." "Ban dade da sani ba nima, kamar yadda ka sani yanzu, kuma ina shirin fada maka dama." "Shit!" Ya daki kujerar da Kamal din yake kai ta baya "Ouch, Aryan karya min baya zakayi ne?" "Ban sani ba, Adam yayi fooling dina, he sent me some audios da pictures da suke nuna Raihana tana ma Hajiya Zeenat aiki ne." "Yes? Sai kayi me?" "Na kore ta." "Kaji matsalar ka, kaji matsalar ka. Habeeb please drop me here, ba dani zaa ji ba gaskiya, me yasa zaka yarda da maganar Adam without proper investigation, me yasa ba zaka bata damar kare kanta ba? Me yasa kowa ba zai dinga wasa da hankalin ka ba, abu kad'an zai bata maka rai ka yanke hukunci, me yasa zaka damu yanzu? Ka yarda bata aikata bane shine zaka je ka ganta ko kuma dan ka gane yar gidan Barrister Matawalle ce shine zaka je? Wanne a ciki.?" "I don't know, I just want to see her, sannan naji her own side of the story." "Ba zata saurare ka, ko zata saurara sai na hanata, kuma nasan komai da ya faru, Raihana saved your life sau ba adadi, duk abinda tayi saboda taimakon ka tayi, kasan wace Hajiya Zeenat, kasan wayon ta, tayi amfani da innocent mind din yarinyar ta sata abu da niyyar wai taimakon ka zatayi, duk abinda tayi saboda kai tayi, idan zaka tuna ranar da tazo tana kuka, a ranar ta gane Hajiya Zeenat amfani take da ita, sannan ta gano tasa anyi poisoning tea din ka, hakan yasata cikin tashin hankali har sai da ta kwanta ciwo, she saved you a ranar har ta zubar da tea din ba tare da kasha ba, nasan duk wannan saboda ta fada min tun a ranar, tsoron yadda zaka yi reacting yasa naki sanar da kai." "Habeeb sauke ni anan." Kamal yace ransa a bace. Parking Habeeb yayi da sauri Kamal ya bud'e kofar ya fita shima Aryan ya fita ya tare shi "Nayi laifi, na ji kuma ban kyauta ba I'm very sorry." "Ni bani kayi ma laifi ba, fisabillillah tunda yarinyar nan tazo Aryan kake mata abubuwa, menene laifin ta?" "I'm sorry." "Ita zaka bawa hakuri bani ba, gashi kila dalilin da yasa Barrister yace ba zai ganmu ba, kasan yadda Raihana take a wajen yan uwanta? Ka sani? Suna sonta fiye da yadda suke son kansu." "Na fisu son ta wallahi." Ya fada kansa tsaye, wani kallon Kamal yayi masa kamar be ji me yace ba, ya girgiza kunnen sa yana sake duban sa "Me kace?" "Yes, I love her Kamal, tun bata san kanta ba." Kafadar Aryan din Kamal ya daka ya bud'e masa kofar motar yace "Let's go, idan muka je bata saurare ka ba, ba ruwana dan muna zuwa zan juyo, kasan yadda zaka yi." "Just take me, zan ga Hydar, I need to talk to him kafin Raihanan." "Wai corper?" Kamal yace yana dariya, bugo shi Aryan yayi daga bayan yayi murmushi kawai ZAFAFA BIYAR.....× 2023 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥🔥🔥🔥🔥💥🔥💥🔥🔥💥🔥🔥💥💥💥💥💥🔥💥🔥🔥🔥🔥 INA MAABOTA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR WRITERS? WANNAN KARON MA MUN SAKE DAWO MUKU DA ZAFAFAN LITATTAFAN MU, MASU DAUKE DA ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA KU GARZAYO. ZAFAFAN NA KU SUN SAKE TAHOWA DA WASU ZAFAFAN LITTATTAFAN MASU DIMBIN DARUSSA NA MATAKAN ILMANTARWA RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM... SAFIYYAH HUGUMA A RUBUCE TAKE (KADDARATA)♥️ HAFSAT RANO (RUMBUN QAYA)🥰 MAMUH GEE (IDON NERA)🤩 NANA HAFSATU KI KULA NI (MALLAKIN ZUCIYA)😘 BILLYN ABDULL DAUDAR GORA (CIKI KA SHATA)💗 DUKA DUKA WADANNAN LITTATTAFAN ZASU ZO MUKU NE CIKIN FARA SHI MAI RAHUSA KAMAR KO DA YAUSHE. DUKA BIYAR DIN AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYU 1200 GUDA HUDU AKAN NAIRA DUBU DAYA 1k GUDA UKU AKAN 800 GUDA BIYU AKAN 600 GUDA DAYA AKAN 400 DADIN DADAWA, MUNA TALLATA HAJOJIN KU AKAN FARASHI ME SAUKIN GASKE! SANNAN GA BIYAN BUKATA HANYOYIN DA ZAKU IYA TUNTUBAR MU DOMIN ZAMA CIKIN SAHUN FARKO NA WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR SUNE; MASU BIYA TA BANKI ZAKU BIYA A WANNAN ACCOUNT DIN BANK: ACCESS BANK ACCOUNT NAME: MARYAM SANI ACCOUNT NUMBER; 0022419171 SAI A TURA EVIDENCE OF PAYMENT HADE DA ACCOUNT NAME TA WHATSAPP TA WANNAN NUMBER;  09033181070 IDAN KUMA KATIN WAYA NE NA MTN SEKU TURO KATIN VTU/SHARE AND SELL KO NUMBER KATIN HADE DA SHEDAR SA TA WHATSAPP ZUWA: 09166221261 FARASHIN LITTTAFAN ZAFAFA BIYAR NA CHANJAWA DA ZARAR AN KAMMALA SU. SAI KU YI SAURI KU GARZAYA DOMIN A DAMA DAKU A WANNAN SABUWAR TAFIYAR SABUWAR SHEKARAR 2023🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥 KU GARZAYO A SAKE DAMAWA DA KU A WANNAN SABUBAR TAFIYAR MAI DAUKE DA SALO NA BAN MAMAKI. KAR KU BARI AYI BABU KU. DOMIN ZAFAFA BIYAR NA KU NE. 😘🤩 [05/01, 21:53] Billyn Abdul 2: 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR MAZAUNA K'ASAR NIJER?*🤏🏾 *TO KU MARMATSO KUSA TA SAMU!!*🇳🇪🇳🇪 *MUN SAURARI KOKENKU MUN KUMA AMSA* *Zafafa biyar dinku sun samo muku hanyar biyan naku kudin karanta litattafan zafafa har guda biyar din* *ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE* +22799643131 *LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA* *DAUDAR GORA Billyn abdul* *KI KULANI hafsat xoxo* *A RUBUCE TAKE Huguma* *RUMBUN K'AYA Hafsat rano* *IDON NERA Mamuh ghee* *KUDIN LITATTAFAN ZAI KAMA KAMAR HAKA* Books biyar  1250CFA Books hudu  1050CFA Books uku  850CFA Books biyu  650CFA Bookk daya  450CFA *MUNA GODIYA DA SOYAYYARKU GAREMU AL'UMMAR NIJER,MUNA MUKU FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA BISA ZABIN ZAFAFA BIYAR*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *RQ* 24 ****Kamal ne yake yiwa Habeeb kwatance har suka karaso kofar gidan Adda maimuna, Kamal ya juyo yace “Munzo, amma ban ga alamar suna nan ba.” “Call her please.” Aryan yace yana langwabe kai “I can’t gaskia, ai da kunya wallahi.” “Please please, ka taimaka.” “Sai kace please oga Kamal.” “Please Oga Kamal.” Ya fada da sauri “Ok let me call her, ba dan halin ka ba.” Ya Ciro waya yayi dialing number raihana, lokacin suna zaune a wani park ta gama bawa hydar labarin komai, fada yake mata sosai bayan da Ya gama jin komai din, be san zata iya saka kanta a irin wannan abun haka ba da tun farko basu barta tazo kanon ba. Abinda ya kawo shi kanon kenan a ranar dan Abby ya samu labarin in da take aiki da kuma labarin taraiyar su da hajiya zeenat har prison da ta rakata ganjn shi shiyasa yace lallai hydar yazo Ya dawo masa da ita, sannan kuma yace ya fasa ganin su Aryan din domin Abby yayi matukar fushi da daddyn su Aryan, baya jin zai iya yafe masa ballantana har wani abu ya sake hadasu, ba zai so taraiyar Aryan da raihanar sa ba, dan ba zai iya taba daukar yarsa Ya bawa dan gidan Mukaddas ba. Ba zai taba ba! “Gobe zamu wuce tare, kin daina zuwa sai karshen wata ni zan dinga kawo ki da kaina Kina clearance.” Bata ce komai ba, wayarta ta dauki kara “Waye?” Yace yana mika mata hannu, bashi wayar tayi Ya daga ya sakata handfree “Raihana gamu a kofar gidan ku.” Kamal yace shima wayar a handfree din take “Ba ita bace ba, yayanta ne.” “Ok Oga Barka da rana ya gida’?” “Lafiya lou, please dama zan wuce da raihana gida, idan yaso zata dinga zuwa karshen wata tana clearance.” Da sauri Aryan ya karbi wayar “Hydar please kuna Ina? Inason ganin ka dan Allah.” “Na riga na wuce.” “Please nasan baka wuce ba, nasan kana nan ka fada min inda kuke, zanzo Yanzu muyi magana dan Allah.” Kallon raihana yayi da itama shi take kallo sannan yace “Skypark.” “Gamu nan toh.” Yace yana katse wayar “Me yasa baya so ku hadu?” Kamal yace “Saboda fushin abinda ya faru tsakanin Daddy da Alhaji Nasir ya shafe mu.” “Me yasa kake son ganin shi toh?bayan ya nuna baya so.” “Muje dai please, kar mu bata lokaci ya gaji su tafi .” “Ok, muje Habeeb.” “Ok.” Ya tada motar A cikin sabon wajen sukayi parking, Kamal ya kara kiran raihana sannan ya bawa aryan bayan an daga yace wa hydar sun shigo wajen, in da zasu same su ya kwatanta musu. “Kaje kai kadai Aryan, zamu jiraka anan.” “Ba zakayi mata magana ba?” “Wa, nace mata me? Kai zaka gyara mess din ka da kanka.” “Ni? Ni fa Hydar nake son gani ma, not her.” Yace yana yatsine fuska “Haka kace?” “Yes, ni ba abinda zan ce mata, salon ta raina ni. Noo I can’t.” “Ikon Allah, Yanzu yanzu fa ka gama cewa you love her, ko ka manta?” “Yea I love her, tun tana yar babyn ta nake nufi ba fa Yanzu ba.” “Ok, a kyale ta.” Kamal yace yana gyara zama a motar Ya dauke kansa “A kyale.” Shima aryan din yace yayi gaba. Murmushin mugunta Kamal yayi, dole sai ya kure Aryan a wannan lokacin yaga karshe miskilanci. Text ya shiga ya rubutawa raihana “Karki kula aryan kanwata, ina parking lot come and meet me.” “Ok.” Tayi masa reply ya sake yin murnushi kawai dan ya riga ya san halin Aryan. Daga chan nesa ya hango su, raihana na facing din ta side din da yake hydar kuma ya bashi baya, sai da yazo daf dasu sannan ya lura sosai da yadda idanun raihanan suka dan tashi alamun taci kuka, kallon ta yake yana tuna shekarun baya tana yar karama suyi ta goya ta shi da hydar har suna fada akan wanda ya riga, tafi son Aryan dan haka ne ma kusan kowanne lokaci tana manne dashi yana fama da ita. Murmushi ne ya subce masa, a duk memory din rayuwar su ta baya wannan sune memory masu dadi a gare shi, kafin komai yazo ya tarwatse ya zama babu wani sauran haske a rayuwar sa sai bakin duhu da ya mamaye ko ina. Dagowa tayi da niyyar kallon wasu saurayi da budurwa dake gefen su sai ta ganshi a tsaye daga kusa dasu yana kallon ta. Saurin dauke idon ta tayi zuwa wani wajen tasa hannu a idon tana jin kamar wani abu ne ya fada mata a idon bayan tuno irin ihun da ya gama yi mata dazu dazun nan. Mikewa tayi tsaye hydar ya kalle ta da alamar tambaya “Zan je toilet ne Hamma, ga bakon naka nan yazo.” Sai ta bar wajen ba tare da ta ko kalli bangaren da Aryan din yake ba _“Get out of my life, bana son sakè ganin ki.”_ Kalaman da ya gama jifanta dasu suka shiga dawo masa a kansa. Kenan abinda take nufi da bako tana nufin ta fita daga rayuwar tasa har ma ta shafe babin sa kenan ko me? “Bismillah.” Hydar yace yana nuna masa wajen zaman da raihana ta tashi. Zuwa yayi ya zauna kamar wanda kwai ya fashe wa a ciki saboda rashin kuzari. Kwarjini sosai yaji hydar din yayi masa musamman bayan abinda ya faru ya kuma tabbatar raihana ta sanar masa da komai. Hannun sa ya zaro daga aljihun rigar sa da ya zube su ciki ya mikawa hydar din suka gaisa. “Hope kana lafiya, ko da yake from all indications kana lafiya din, well menene maganar da zamuyi saboda ina sauri ne, yau nake son barin kano ko mai dare.” Ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa yana maganar “I want to know Dama yadda kuke, ya bayan rabuwa!” “We moved on Aryan, tun bayan abinda ya faru muka dauki kaddara muka cigaba da rayuwa, duk kuwa da Daddy yaso rayuwar mu ta katse mu ta gayyara, sai dai bamu mutu ba, mun yi rayuwa me inganci duk kuwa da wahalar da muka sha din.” “Menene banbancin mu Hydar? Karka manta a gaban idona aka raba mahaifiyata da ranta, a gaban ido na aka tarwatsa ma wadanda suka fi kowa kusanci dani rayuwa, ka dauka nayi wata rayuwar jin dadi ne bayan haka? Ko ka dauka na manta daku? Allah ne shaida ta, rana bata taba fitowa ta fadi ban tunaku ba, ban kuma yi missing dinku ba.” “Kasan rayuwar da mukayi kuwa aryan? Ka sani? Kasan rayuwa babu uba babu uwa, ku zakuyi wa kanku komai, Atleast ka tsira da mahaifi Aryan, mu fa? Kayi karatu me kyau cikin rayuwa me kyau baka rasa komai ba, mu fa? Kasan da ya akayi muka zo har nan? Mu muka dauki nauyin kanmu da kanmu.” “Bani da banbanci da rayuwar da kukayi Hydar, duk abinda Ya faru ni ne na dauki consequences din.” “Hmm, ya wuce Aryan, ina ganin dawo da abinda Ya faru ba zai wani amfani ba, mu bar shi kawai.” Sai Ya mike tsaye “Raihana yarinya ce karama wadda bata san komai ba, bata komai akn abinda ya faru ba, dan haka nake rokon ka, stay out of her life dan Allah Aryan, ka rubuta mata clearance letter din ta complete har na last month, ka fada min nawa ne zan biya, ba sai ta sakè zuwa Office din ku ba.” Wani irin kallo Aryan yake masa, shi zai biya kudi? Shi? Akan raihana? “Kudi Hydar?” “Yes, nawa zan biya?” Hannun sa ya dunkule ya runtse idon sa ba tare da yace komai ba saboda tsananin bacin ran da yaji ya taso masa. Gid'a kai Hydar yayi "Well,idan sai kayi tunani ne toh, ga complementary card dina nan, just call me sai muyi magana.” Yana fadan haka ya soma tafiya yana barin wajen, ya bar Aryan cikin yanayin da ya kasa tantance a wacce duniya yake, tabbas yasan an cutar dasu cuta mafi girma, amma be dauka hakan zata shafe shi ba, shi menene nashi? Laifi na Daddy ne taya hakan zai shafi dangantakarsu. Kamar wanda aka dasa a wajen haka ya cigaba da tsaiwa har sai da Kamal ya gaji da jiransa dan a gabansa hydar din ya fito suka tafi da raihana sannan ya bishi ciki ya same shi cikin wani irin yanayi. ***TUBA BAYA* Zeenat ta dade tun daga lokacin bata ziyarce su ba, sun kuma yi kokarin zuwa su ganta amma sai ta dinga yi musu hanya hanya har suka hakura suka kyale ta kawai. Kwatsam sai mahaifin Mummy ya rasu, wanda ya tilasta mata zuwa yiwa mummyn gaisuwa, anan ne suka dinga yi mata fada akan share su da tayi tunda tayi aure ta dai basu hakuri kuma tace sun rabu da mijin, talaka ne gashi dan giya ne idan yasha sai yazo ya kamata da duka haka dai Allah ya taimake ta ya saketa. Sun mata murna sosai sun kuma tausaya mata rayuwar da ta shiga, ko da tazo zata koma garin su sai suka ce ta zauna ta dan kwana biyu ta sake hutawa sosai, ba musu kuwa tayi zaman ta dan dama chan hanya take nema. A lokacin arziki ya kara bunkasa sun gyara gidajen an dora bene komai an chanja shi kamar ba gidajen nasu ba na da. Duk abinda suke yi idanun Zeenat yana kai wani abun kusan ma tare da ita ake yi dan wata yar uwar mummy ta taba yi mata complain akan yadda suka sakar wa Zeenat din musamman ita mummy tunda ita Ammy bata da hayaniya sosai shiyasa Zeenat tafi shigewa Mummy sosai dan tafi fuska tafi kuma sakewa sosai da ita. Zaman ta a gidan ya kara mata kusanci sosai da Aryan dan ba karamin son ta yake ba, komai ita take yi masa ko yaushe yana wajenta tana dawainiya dashi haka yasa ita kuma mommy ta sake sakankancewa da ita dan dama an ce me d’a wawa, dan tunda ta rasa ahmad ta dauki son duniya ta dorawa Aryan din. Tafiyar ta ta karshe ita ta fara bawa Mummy shakkun akan zeenat, daidai lokacin da aka raba musu gadonsu tazo tana fada mata washegari ta shirya tace ta tafi okene zata kwana biyu kafin ta leko su, da farko bata kawo komai ba sai bayan tafiyar zeenat din da ta shiga dakin da take kwana sai taga wata takarda akan bedside drawer, hankalin ta ne Ya kai wajen ta sa hannu ta dauka ta warware sai taga takardar chèque ce a tsakiyar dayar takardar wadda ta fito daga hannun Daddy. “Kudi?” Tace tana sakè son tabbatarwa “Me zai hada Daddy da bawa zeenat kudi, kudi masu yawan gaske kuma be sanar da ita ba?" Ta tambayi kanta, rike takardar tayi a hannu ya fito a lokacin Daddy yana sama yana kallo ta same shi tare da Aryan da yake jingine dashi suna Kallon tare ta mika masa takardar tana kallon yanayin fuskar sa. "Ta mecece?" Yace yana warware ta "Duba ka gani." Dagowa yayi bayan ya gama dubawa ya mika mata yana maida hankalin sa kan TV cikin halin ko in kula yace "Me ya faru da wannan din?" "Me ya faru Daddy? Kudi ne naga ka turawa Zeenat har haka, kuma babu sani na at least ko wani abu ne ya faru ya kamata na sani." "Ke da kawarki? Menene dan na taimaka mata tana cikin halin neman taimako?" "Babu komai, amma a kalla na sani ba wai sai dai na gani ba." "Kishi dai irin naku na mata, ni ban ga abinda nayi ba." Ya mike yana daga Aryan "Let's go my boy, mummy tana bukatar hutawa ." Ya janye dansa suka fice suka barta a tsaye tsananin mamaki na neman kashe ta. Yau Ibrahim ne yake bata irin wannan amsar? Lallai akwai matsala. Mayafin ta, ta dauka ta sauko ta shiga gidan su Lamido, ta samu Ammy da yaran tana koya musu homework, yanayin mummyn da ta gani tasa tace su shiga ciki. "Menene ya faru sister?" "Akwai babbar matsala sister, nayi kuskure me girma." "Na me fa? Wai me ya faru fada min dan Allah duk hankali na ya tashi." "Kalli." Ta mika mata cheque din tana yin tagumi. Zaro ido Ammy tayi "Ban gane ba." "Zeenat ce ta karbi kudi a wajen Ibrahim, babu wanda ya sanar dani a cikin su, ni ba yawan kudin ne damuwa ta ba, yadda za'a boye min bayan duk cikin su babu wanda nake boyewa komai na." "Tabbas biri yayi kama da mutum, dazu da asubah Nasir yake ce min zamuyi magana akan Zeenat dani dake dashi idan ya dawo, tabbas akwai abinda ya faru, amma yanzu da abinda Zeenat zata saka mana kenan?" "Kin gani, mutum! Shiyasa aka ce karka taba yarda da mutum." "Gaskiya bata kyauta ba, da sai ta fada miki ma idan ni ba zata sanar dani ba." "Ni duk jikina yayi sanyi wallahi, tun farko laifi na ne, da na sakar mata gida na bayan duk fadan da akayi min, ke ai kinga kin fini hankali." "Ba haka bane ba, akwai yarda me karfi tsakaninmu uku, kema kin sani yanayi na ne kawai da naki ba daya ba, amma nima in dai Zeenat ce bana jin dar ko wani tunani akanta wallahi. Kawai dai ta zabe ki ne akai na." "Still duk da haka Aisha munyi shirme, a zamanin nan da yarda tayi karanci ka bar mutum babba baligi a cikin gidan ka bayan babu wata alaka ta jini a tsakani, wanda a yanzu ko yar uwarka ce ciki daya wallahi shaidan zai iya tasiri a wajen bare kawa, nayi kuskure sosai kuma na sabawa dokokin Allah." "Kuskure ne dukka mun tiga mun yi, yanzu kiranta za'a yi muji dalilin ta kila ko nauyin fada miki take kar kiga ta tambaye shi." "Babu yar wannan a tsakanin mu ai, bansan kuma yaushe ta fara ba." "Kirata muji." Kiran Zeenat din tayi amma har ta gama ringing bata daga ba, ta sake kira a karo na biyu amma still no answer daga karshe ba sai ta kashe wayar baki daya. Abinda ya daure kan su kenan har jikinsu ya sake sanyi. Bayan kwana biyu da abun babu wani shiri tsakanin Daddy da Mummy dan fushi take sosai dashi amma sai taga kamar ma be damu ba, sabgar gabansa kawai yake daga shi sai yayansa, hakan ya kara saka mata tsoro sosai a zuciyar ta, ta rasa in da zata saka kanta taji dadi. Zuwa tayi ta samu Abby a gida ta kai masa karar Daddyn yace su je gidan su sameshi dan shima kwana biyu basa wani zama sosai kamar akwai abinda ya dauke masa hankali. Yana ganin su tare yasan abinda ya kawo su, lokacin ma waya yake yana ta shewar sa, sai ya katse bayan yace mata zan sake kiranki. Sannan yace "Aboki bamu zauna ba kwana biyu, ga abu ya taso mana bakatatan gobe zaka rakani kogi state." "Kogi?" Yace zargin sa na tabbatuwa kafin yace "Magana nazo muyi ni." "Nasan maganar da zakayi, ai na ganku tare nasan kara ta aka kai, toh bari na saukaka muku maganar, Maman Nabila gobe in Allah ya yarda zaa daura min aure da Zeenat!" *RQ*                    25 Ji da ganin Mummy ne ya dauke na wasu mintuna, sai taji kamar mafarki take tana fatan ta farka daga mummunan mafarkin. Jiri na ya kusan dibar ta, tayi saurin kama hannun kujera ta rike kam, shi kuwa Abby ya rasa me zai ce saboda tsabar takaici da bacin rai. Duk maganar da yayi masa akan yadda suke rayuwa da Zeenat be dauka ba ashe, shine har da aure? "Aure kuma aboki? Ban fuskance ka ba." "Aure dai da ka sani, kasan komai kaga ya faru Allah ya riga ya kaddara zai faru, a kalla ita amaryar ma ai ba bare bace, itama yar uwa ce kaga shikenan sai a zauna lafiya." Kukan bakin cikin Mummy ta fashe da, ta juya ta fice da sauri. Zama Abby yayi yana duban daddy "Menene matsalar? Yanzu ace ta haka zaka sanar da matarka zakayi mata kishiya? Anya Ibrahim? Anya ka dauko hanya me kyau kuwa a shaanin auren nan?" "Toh ai kamawa tayi, dama yau nake shirin fada mata tunda sai a karshen satin nan fa muka yanke shawarar auren ma" "Amma yanzu kun kyauta Kenan? Ana barin halak dan kunya fa." "Toh ai ba laifi mukayi ba, kai fa da kanka kace soyayyar da muke bata dace ba, shine mukayi deciding muyi aure kawai ba shikenan ba?" "Still dai baka kyauta ba, sai ka sameta ka rarrasheta ka bata hakuri, dan ba'a kyauta mata ba." "Haba dai, a wannan gabar ai ba zan nuna mata lako lako ba bare ta botsare, ka bari sai an daura gobe yawwa, sai na dawo nayi rarrashi." "Baka kyauta ba gaskiya." "Toh ya za'a yi ne wai Barrister? Haka Allah ya tsara ya kaddara, bawa ai baya taba gujewa KADDARAR sa, kuma da sauki ba fa wata ce chan ta daban ba, Zeenat ce kasan dai yadda alakar su take, kuma ni ban ma ga abin damuwa ba in dai da gaske ake kawancen." "Me ta baka kasha wai? Maganganun ka sunyi kama da na wadda akayi brainwashing, maganar Khadija fa mukeyi fa, Khadijan ka ba wata ba, why are you trying to make it looks like kamar bakayi laifi ba." "Ai banyi bane ba Abokina, babu laifi a raya sunnar ma'aiki." "Shikenan, ni dai babu wani kogi state da zanje gaskiya, dan nasan na sake na bika wallahi Nima fushin sai ya shafe ni." "Wa zai rakani toh? Dole ango ai sai ya tafi da wani, kasan al'adarsu ba irin tamu bace ba." "Ba in da zani, ka kira zanna ya rakaka dan shima irin wannan tunanin ne dashi." "Alaka ta da Zanna daban taka daban, please ka shirya dan na riga na siya mana tikiti, sai tafiya kawai hatta kayan da zamu saka na dinka mana yana cikin closet dina." "Allah ba in da zani, har sai ka bawa Maman Aryan hakuri sannan idan sun amince sai muje." "A wannan kurarren lokacin yaushe ma har ta sauko ta hakura ta amince? " "Sai a d'aga har sai ta amince din." "Tab! Haba wa, ai idan kaga an daga goben nan ko? Toh mutuwa daya a cikin mu yayi. Kasan yadda ire iren matan nan nasu suka iya caring kuwa? Wai wai wai, soyayya alaji, wallahi kamar zasu kwanta maka saboda tsabar love da biyayya." "Allah ya kyauta, bari na je." Ya mike ya fice ya bar daddyn akan bakansa.    Tun Mummy tana kuka da hawaye har ya koma ya kafe sai ajiyar zuciya da take saukewa, ita kanta Ammy tayi kukan ba dan kad'an ba dan duk abinda ya shafi daya daga cikin su toh dukkan su ne, musamman irin wannan auren cin amanar, bayan babu irin hidimar da mummyn batayi dasu ba tun ma a zamanin makaranta da kuma bayan auren, komai ta samu nasu ne su uku ta yarda dasu fiye da yadda ta yarda da yan uwanta na jini ma, sai gashi irin sakayyyar da Zeenat din zata saka mata kenan. Abby ne yake ta kokarin basu baki da kwantar musu da hankali dan yasan ba'a kyauta musu ba, duk kuwa da shi namiji ne amma a kalla yasan abinda ya kamata da wannan be dace ba. Ita Ammy har shi take fushi da tunda dai ai ance Abokin barawo barawo ne, kuma ba zai yiwu ace tun farkon alakar Daddyn da Zeenat ace be san komai ba, amma yayi shiru har sai da abu ya riga ya kwabe kafin yace zai yi magana dasu ashe ma already su sun riga sun gama yanke hukuncin abinda zasuyi. Babu irin kiran da batayi wa Zeenat din ba amma bata shiga da alamu ma ta sakasu a black list ta yadda ko sun kira ba zata shiga ba, ta riga ta shirya musu ko ma menene wato babu gudu babu ja da baya.    Da daddare daddy na gaban mirror a dan corridor din dake gaban toilet yana shaving fuskar sa Mummy ta shigo wajen, ta jikin mirror ya kalle ta sai ya cigaba da abinda yake yana yana dan jujjuya kansa cike da nishadi kamar be san ta shigo ba. Wasu kaya ta zuba a cikin watching machine ta juya ba tare da tayi masa magana ba. Dakatar da ita yayi ya tako gabanta taki kallon fuskar sa "Na manta dazu ban fada miki ba, idan an daura auren daga chan zamu wuce honeymoon na wata daya, idan mun dawo zata zauna a k'asa sai ke kiyi amfani da sama. Please sai a kwashe komai zan turo masu gyara da interior designers suzo su hada mata kasan, naso kowa ta zauna ita kadai amma tace tafi so ku zauna tare, kinsan abunku da na kawaye."   Kad'a kanta tayi kawai tayi gaba ba tare da tace masa uffan ba, dan ta lura so yake zuciyar ta, tayi bindiga ta fashe ta mutu bashi da asara. Daki ta koma tayi kuka, tayi kuka kamar ranta zai fita, sannan taje ta wanko fuskar ta, ta kuduri aniyar ko me zai yi ba zata taba tanka masa ba, zata zauna ta rungumi yayanta ta kula dasu amma ita dashi shikenan, yaje ta barshi da Allah idan ya cutar da ita.   Sati uku da daura auren suka tattaro suka dawo, sati ukun nan ya zamar wa ahalin gidan tamkar wasu shekaru, babu wata walwala a gidajen biyu dan dukkansu abun ya taba su hatta yaran Aryan da Hydar ne kawai suke shaanin su amma kowa baya cikin walwala. Nabila da Lamido sun fi shiga yanayin sosai saboda sun riga sun girma sun san damuwar iyayen su. Ranar da zasu taho Kanon suka fara biyawa ta Kaduna ta dauko Adam, dan dama ta riga ta fada masa zata dauko Adam daga hannun kanwar ta, be musa ba dan a yanzu kaf duniya babu wadda yake so sama da Zeenat din dan shi ji yake kamar sai yanzu ne ma yayi aure dan wani irin kulawa da take bashi kamar zata maida shi ciki uwa uba ga soyayyar da take nuna masa a fili babu wata kunya ko noke-noke.    Kamar babu kowa a gidan da suka shigo dan Mummy tana sama a dakin ta yaran kuma suna wajen Ammy sai ya zama gidan yayi tsit. A falo suka baje manne da juna bayan sun ajiye kayan su. Adam na zaune a gefe yana buga game a sabuwar tablet dinsa da Daddyn ya siya masa. Sakkowa mummy tayi ta gansu kawai dan ko sanin ranar zasu dawo ma batayi ba. Tun daga ranar komai ya sake chanjawa! *Dawowa LABARI* ****Tunda suka dau hanya babu wanda yayi magana da dan uwansa, har suka iso office din. Balle murfin motar Aryan yayi Ya fita da sauri Kamal ya mara masa baya. Kai tsaye office dinsa Ya nufa duk da sauri yake komai ya bude ya shiga, Ya jawo drawer da yake ajiye takardun ya fito dasu daga tsayen da yake duk ya bisu da stamp da signing ya bar wajen date da sunan ta blank ya tattare su ya zuba a envelope sannan ya fito. Kamal ne ya tsaida shi ganin zai sakè fita “Wai me ya faru? Baka fada min komai ba.” “Ni hydar zai duba yace zai biya kudi kamal? Ni zai biya kudi akan raihana? Ni?” “Comman, na tabbatar ba abinda ya fada yake nufi ba har zuciyar sa, bacin rai ne kawai. Beside ko waye dole yayi abinda hydar yayi.” “Na tafi takanas na ganshi, thinking shine zai fi kowa fahimta ta, but me yayi? Yana fada min na kyale masa kanwarsa. Did I say I’m keeping her? Ba maganar tace ta kaini ba ni, Amma yana nuna kamar ni din mugu ne, ko ina nufin kanwar sa da sharri. Problems din dake kai na sun ishe ni, ba zan karawa kai na wasu ba kuma. Tunda sun zabi hakan fine, tunda ban mutu da ba, Yanzu ma ba zan mutu ba.” “Calm down, ka bari zan neme shi muyi magana, shima barrister Nasir na sake aika masa da sako, hopefully zai amince ya bamu goyon bayan da muke nema." "Don't please, ka kyale su kawai." Ya juya ya soma sauka daga stairs din, girgiza kai Kamal yayi kawai, yana ganin lokaci yayi kawai da zasu aiwatar da abinda suka tsara, sai ya ciro wayarsa ya yi kira, suka danyi magana kad'an sannan ya katse yana sauka shima.    Gidan sa ya wuce yana shiga ya jefar da envelope din a saman kujera ya shiga ciki, ya fara watsa ruwa sannan ya sauya kayansa zuwa kanana marasa nauyi, fuskar sa a hade take babu walwala ko kad'an domin a chunkushe yake jin sa amma dole sai ya aiwatar da abinda yayi niyya dan yafi karfin abinda Hydar yake jefan shi dashi. Fitowa yayi rike da wayar sa hannu daya rike da envelope din ya dan kalli time yaga biyar ta wuce ya tabbatar yanzu ta koma gida. Tun a office suka rabu da Habeeb shiyasa yanzu ya kasance shi zai tuka kansa. Sai da ya fara biyawa ta wani waje har magriba sannan ya dauki hanyar gidan nasu da suka je dazu. Lokacin masallacin unguwar suke sallah dan haka ya zamto babu mutane a waje duk suna ciki, a kofar gidan yayi parking ya zaro wayar sa ya kalli lokaci sannan ya dan jingina jikin motar yana karewa layin kallo. Muhammad ne ya dawo daga masallaci ya ganshi a tsaye a kofar gidan su. Sallama yayi masa ya amsa ya mika masa hannu suka gaisa kafin yace "Please wajen Raihana nazo." "Ok, ina zuwa." Ya shiga ciki ya barshi. Hannun sa ya zube a aljihu yana kallon kofar gidan fuskar sa a hade tsaf. Mintuna kad'an Muhammad ya dawo "Oga ko zaka kirata a waya? Tace bata expecting kowa." "Sorry bani da number ta ne, amma please kace mata Aryan ne." "Ok." Ya sake juyawa ciki. Jujjuyawa ya dinga yi a tsakanin wajen tsawon lokaci muhammad din be dawo ba, ita kuma bata fito ba. Ransa ne ya dan sosu, ya sake kallon agogon da yake daure a tsintsiyar hannun sa yaga a kalla ya kusan shafe mintuna ashirin a tsaye a wajen. Sallama akayi masa ya waigo da sauri, ganin babban mutum yasa ya dan russuna ya gaishe shi. "Sai dai ban shaida ka ba." Baban su Amina yace yana kallon sa "Eh dama ogan Raihana ne a wajen aiki, na kawo mata wasu papers ne." "Ah toh bismillah, shigo ciki mana ka tsaya a waje? Shigo shigo." Yayi masa jagoranci zuwa ciki, ya bud'e kofar falon sa da yake ajiye bakin sa yace ya shiga shi kuma ya shiga ciki.   Be zauna ba, ya tsaya daga farkon falon yana jiran shigowar ta, hankalin sa na kan kofar dan idan be aiwatar da abinda yayi niyya a yau ba toh tabbas sai ya kasa runtsawa. Yana tsayen yaji ana bud'e kofa, kafin sallamar ta, ta biyo baya amma a chan ciki. Amsawa yyi shima ciki cikin ta karasa shigowa sanye da dogon Hijab har k'asa kanta na kallon kasa sosai ta shige ciki ta tsaya itama daga dan nesa sosai dashi.   Envelope din ya bud'e ya ciro takardun ya ajiye a saman kujerar da take tsaye gefenta, "Babu bukatar sake dawowa duk wata kina karbar clearance saboda bani da wannan lokaci. Wajen suna da date blank yake dan haka sai ki cike da kanki." Wani abu ne ya sake taba ta, a tunanin ta Aryan yazo ya bata hakuri ne, yazo ya janye kalaman da ya faffada mata dazu, sannan ya kaskantar da kansa ya nemi afuwarta kuma yaji ta bakin ta, sai dai tsananin mamakin sa ya hanata cewa komai, ta dinga kokarin hadiye wani kukan bakin ciki da yake taso mata, tun da ta dawo ta kasa hada kayanta, ta kasa yin komai saboda yadda zuciyar ta, take a chunkushe. Akwai tarin bakin ciki a zarge ga da cin amana bayan kasan ba hakan ka aikata kai tsaye ba, sannan a hanaka kare kanka ballantana a samu yi maka uzuri, sannan ayi maka kora irin ta Wanda bashi da wani amfani. Duk wannan be isheshi ba, shine sai ya biyo ta har gida ya dora a in da ya tsaya? Lallai.    Gefen Hijab dinta ta kama ta rufe fuskar ta dashi kawai tayi hanyar barin dakin dan idan ta cigaba da zama kukan bakin cikin da take ta dannewa sai ya fito. Da wani irin sauri ya riko ta, Hijab dinta yayi niyyar rikewa Amma sai ya samu kansa da damko hannun ta, wanda yaji tamkar an jona masa shocking sabida yadda yaji. Tsayawa tayi chak ta kasa yin gaba, shi kuma ya kasa sakin hannun ta, saboda wani irin bugawa da kirjin sa ya shiga yi tamkar zai hudo. Kusan minti daya yana rike da hannun ta, yaki saki sai sheshekar kukan ce take tashi. Kokarin kwace hannun ta hau yi,sai a lokacin ya tuna yayi saurin cikata yana kallon nasa hannun. "Subhanallah." Ya furta a a hankali ya dafe kansa. "I'm sorry." Ya samu kansa da furtawa sai dai kamar iya saman leban sa maganar ta tsaya dan ko motsawa batayi daga wajen da take tsaye ba, bare yayi tunanin taji abinda yace "Kiyi hakuri." Ya sake furtawa wannan karon da dan karfi. Kamar mashi haka taji maganar tasa ta shige ta, kukan da take ta soma ragewa a hankali tana jan ajiyar zuciya.    Zuciyar sa ce ta dinga kokarin ingiza shi, ya dinga jin tamkar yaje ya rungume ta, tayi kukan a kirjinsa akan zafin da yake ji duk lokacin da sautin kukan nata ya shiga zuciyar sa. Gwara ya tafi, kar yaje ya karawa kansa zunubi bayan na rik'e mata hannun da yayi.   Gefen ta ya rabo yazo daidai saitin ta, a hankali yace "Na tafi." Sai ya bud'e kofar ya fice ya barta a tsaye a wajen cikin wani irin yanayi.     ***Ya dade a kofar gidan be tada motar ba, har sai da bugun zuciyar sa ya daidaita, sannan ya kunna motar ya bar unguwar cike da wasu irin tunani da suka cika masa kwanyarsa har yake jin kamar zasu fito waje. Gida ya wuce cike da son dauke hankalin sa daga kan abinda ya faru ya maye su da tunanin halin da Daddy yake ciki duk kuwa da Kamal yace zai duba, ya kamata suyi abinda ya kamata dan a yanzu ya kara samun tabbacin akwai babban al'amarin da yake faruwa da Daddyn.    Hajiya Zeenat bata nan, tana chan gidan da suka kai Daddy ta samu wani nurse ta sakashi duba Daddyn dan tana so ya dan yi regaining energy dinsa saboda ta samu damar da zai karasa mata abinda ya fara. Suna zaune a falo yana cigaba da aikin da yake mata sai sako ya shigo wayar ta, budewa tayi ba tare da ta bada dukkan attention dinta ba, sai dai abinda yake kunshe a sakon ya sakata mikewa tsaye ta dafe kirjin ta "Na shiga uku." Tace tana kokarin yadda wayar, video dinta ne da akansa ta salwantar da rayuwar mutane biyu, ta tura daya gidan yari, video da ta tabbatar sai da ya bata bat a doran k'asar nan amma kuma ta yaya? Waye yake dashi da har zai turo mata shi a irin wannan lokacin, babu abinda yafi tsorata ta, irin abinda yake rubuce a karshen sakon, abinda ya kara saka ta a matukar rudani, waye? Waye wannan? Wayar ya dauka da ta yar ya bud'e sakon sannn yayi kokarin daukar number ya hau duba ta, sai dai babu wani bayani da ya samu akan number din duk da ya riga dama yasan ba lallai a samu komai akan sako irin wannan ba.   "Me nake dauke dashi? Me na samo a wajen Aryan kenan?" Tace a birkice. Gida ta nufa a matukar rikice, taje ta bud'e in da ta ajiye takardun nan ta fito da komai sannan ta sake fitowa ta dawo in da yake. Ta bashi ya karba ya hau dubawa sannan yasa cd din a cikin computer "Babu komai a ciki Hajjaju. Empty disk ne." "Na shiga uku." "Sannan..." Sai ta durkusa a wajen "Baki daya takardun nan fake ne, ba sune originals din ba, sannan takardun properties din Alhaji ma duk fake din ne." "Shikenan, na gama, na gama." Ta zare dankwalin kanta ta dora hannu aka ta fara ihu, sai kuma ta tuno da wani abu, tayi wajen da daddy yake kwance da sauri ta kama jijjigashi "Ashe tsawon lokacin da muka dauka yaudara ta kake? Cuta ta kake ban sani ba? Wallahi sai na ga bayanka, sai na karar da duk dangin ka, ba zan je kasa ni kadai ba, idan ma mutuwa ce sai dai mu mutu tare, bakin azzalumi." Wayar ta, ta fara kashewa d sauri sannan ta saka shi ya kira gardawan nan suka zo suka dauke mata Daddy, suka saka shi a mota suka dau hanyar barin garin. *RQ*      26 *TUNA BAYA*     Rayuwar gidan baki daya ta gama sauyawa, babu sauran mutuntawa da soyayya tsakani daddy da Mum dinsu Aryan, baki daya Zeenat ta chanja komai ita ce a gaba a komai duk abinda ya taso ita daddy yake sawa a gaba. A hankali ta dinga kokarin raba tsakanin sa da yaran sa ya zamto Adam ne kawai a gaban sa idan yana gidan suna tare tamkar shine kadai d’a a gidan. A gabansa tana kokarin jan Aryan a gaba duk abinda yayi amma sai ta kushe tana nuna tamkar bashi da wani wayo ko hankali kamar Adam hakan kuma ba karamin tasiri yake ba. Rabin rayuwar su sai ta zama tana gidan ammy dan duk wanda Daddy yake gida toh sai yayi ta musu fada yana kyarar su, Aryan da karacin shekaru be gane ba da farko Amma daga baya sai ya soma fuskanta. Dama miskili ne tun da aka haife shi, hakan sai ya kara taimakawa wajen sake janye kansa daga sabgar daddyn dan da yayi abu kadan sai ya hau shi da masifa wani lokacin har da bugu, hakan ya saka shi shima yake rayuwar sa a gidan ammy din musamman Yanzu da ta haifa musu kanwa mace sai ya zama na yana chan a ko yaushe yana dawainiya da ita shi da hydar har kwana a gidan yake yi. Rayuwar mummy gaba daya ta chanja ta lalace ga hawan jini da ya sako ta a gaba dan tunda Daddy yayi aure ta koma kamar mujiya a cikin gidan. Zeenat kamar zata bangaje ta duk sanda suka hadu ko kuma tayi ta mata habaici da bakar magana amma a gaban Daddy sai ta chanja ta juya zance tace Mummyn taki karbar ta ko hakura zasuyi? Saboda ita bata son damuwar mummyn, hakan da take fada ne yake sake tunzura shi Ya samu mummyn ya cimata mutunci yace tana da bakin kishi haka zatayi kuka ta gode Allah.    Watarana da azumi bayan Daddy da Abbyn sun tafi Umrah, da daddare gidan yayi shiru yaran sun yi bacci a gidan Ammy sai mummy ta sakko da nufin daukar abu a kasan. Motsi ta dinga ji a hankali yana fitowa daga dakin Zeenat din wanda yayi mata kama da na wani abu, da sanda ta karasa kofar dakin duk da babu ishasshen haske ita ma da wayar ta take haskawa ta karasa kofar dakin amma ga mamakin ta sai taga kofar a bude. Abinda ta gani yayi masifar daga mata hankali, zeenat ce haihuwar uwarta tare da wani abokin su Daddyn suna aikata alfasha sun manta basu rufe kofar ba. Kafar ta ce ta dauki rawa ta rasa me zatayi kawai sai ta danna wayarta ta hau daukar su video saboda ta samu hujjar da zata kawo karshen zaman zeenat din a cikin gidan wanda dama ta dade tana zargin ta amma bata taba da shaida amma Yanzu ta tabbatar idan  daddy ya gani ba zai karyata ta ba. Dan short clip ta dauka wanda zai zama evidence sannan ta juya da nufin barin wajen sai ji tayi ta buge da kujera, tayi kara saboda zafi sai ta tuna da abinda tayi, sai tayi sauri ta juya ta bar wajen amma duk da haka sun riga sun ganta.   Dakin ta, ta koma tana haki cike da tsoro, dan tabbas zasu iya ganin ta, rasa abinda zatayi tayi kawai sai ta shiga whatspp din Abby ta tura masa video din sannan ta goge na wayarta ta ajiye wayar ta zauna ta zabga tagumi, ta dade a haka kafin ta hakura ta kwanta a tsorace   Tana kwance cikin bacci sai taji kamar ana taba ta, ta ware idonta da sauri ganin mutum a saman gadon idon sa a rufe amma jikin sa babu ko kaya ya rankwafo kanta, yinkurin tashi tayi ya danne ta da karfi ya toshe mata baki, Zeenat da take tsaye a bayan su ta karasa daukar video din sannan Ya daga ta suka shiga jawota daga kan gadon suka buga ta da bango tayi wata irin kara sukayi saurin toshe bakin ta. Kokarin tashi take ta gudu amma sam sun hanata, suka dinga bugun ta ta kai da ko ina tun tana kuka har ta soma shidewa numfashin ta yana neman daukewa dan tuni jini ya fara zuba ta kanta da bakin ta da hancin ta, ganjn tana daf da daina motsi sai sukayi amfani da wukar suka dirza mata a wuyanta.    Aryan da ya fito cikin magagin bacci yana kiran Mummy ya iso kofar dakin nata kenan daidai lokacin suna dirza mata wukar a makogwaron ta, sandarewa yayi a wajen zai kwalla kara aka yi saurin rufe masa baki da ido sannan yaji an janye shi da sauri.    Tashin Abby kenan bayan an kira sallar asubah, ya dauki wayarsa zai haska sai yaga alamun sako daga Mummy, fasa tashi yayi ya bude sakon sai dai abinda ya gani yayi mugun daga masa hankali “Help me, sun san na gansu bansan me zasu iya aikata min ba.” Da gudu ya duro daga gadon, yayo waje ya shiga gidan su Aryan din, ya wuce kai tsaye saman cike da tsoron abinda zai gani. “Innalillahi wa inna Ilaihi Raji’un.” Ya furta da karfi kafin yayi kanta yana kwala mata kira, ganin bata motsi ya sashi tallafo ta jikin shi    Karar jiniya ce ta cika layin kafin su soma shigowa gidan da karfin su, Abby na rik'e da gawar suka shigo dakin suka zagaye shi "You are under arrest." Ogan ciki yace yana rike da ankwa "Ban gane ba?" "Zaka gane a station, arrest him!" ****Firgigit Aryan ya farka daga baccin da yake me cike da mafarkai, a ko da yaushe idan ya kwanta sai yayi mafarkin abinda ya faru hakan ba karamin maida shi baya yake ba, shiyasa ba kasafai ya fiye samun cikakken bacci ba. Tun bayan da ya dawo daga gidan su Raihanan yayi kwanciyar sa bayan ya kashe wayar sa kar ma Kamal ko Ya Nabeela su kira shi, ta fara masa koarafin zuwa gidan su Mummy su gaishe su amma ya zame dan be yi niyya ba idan sun matsu suna son ganin su suzo in da suke amma shi babu in da zai je. Wayar sa ya lalubo a gefen sa ya kunna ta ya duba lokaci sannan ya sake kashe ta ya mike a hankali ya sakko ya nufi toilet ya dauro alwala yazo ya haye saman dadduma ya shiga kai wa Allah kukan sa kamar kowanne lokaci.    Tunda Kamal ya kirashi yaji wayar a kashe yasan kashe ta yayi, Raihana ya kira a lokacin tana kwance lamo bayan tafiyar Aryan din tana kuka k'asa-k'asa ta kasa tashi ta hada kayan nata ma sai Amina ce ta tayata. Bayan tafin hannun ta, tasa ta goge hawayen sannan ta daga wayar tayi sallama a hankali "Ba dai kuka kike har yanzu ba kanwata?" Shiru tayi tana jin wani sabon kukan na sake taso mata "Please ki daina kar kanki yayi ciwo, nasan Aryan yazo ko?" "Eh,yazo." "Ok, hope ba wani abu ya sake fada miki ba." "A ah, ba komai." "Ok, ki kwantar da hankalin ki. Duk abinda ya fada ba har zuciyar sa bane ba, ba da gaske yake ba wallahi." "Ok." "Yawwa, ki cigaba da normal activities dinki, sannan ki taya mu da addu'a, idan komai ya lafa seat dinki yana nan yana jiran ki a sabon office din ki." "SABON office?" "Yes, kujerar oga Aryan, ko bakya so?" Murmushi ta samu kanta da yi, dan tasan Kamal so yake kawai ya kwantar mata da hankali amma ita kuwa me zata koma yi har da zama a office dinsa? Dama ita ba permanent ma'aikaciya bace ba, kuma dama clearance din karshen wata take so toh tunda ya riga ya bata ba shikenan ba? Sai yaje ya karata da bakar zuciyar sa. "Da gaske nake miki, zamu zo kafa da kafa har Adamawa mu zo biko mu dauko ki." "A ah ni ba zan dawo ba." "Zaki dawo ne, baki ma san sanda zaki biyo mu ba, dan muka tashi zuwa a shiryen mu zamu zo." "Shikenan, zamu gani." "Zamu gani kam, Allah dai ya nuna mana, ki yi blocking number Hajiya Zeenat daga wayar ki, sannan ki samu hutu sosai idan kin koma karki yarda ki yi stressing kanki da tunani." "In sha Allah, thank you so much. Kana da kirki sosai." "Aryan yafi ni kirki fa." "Um um, wallahi kafi shi. he's not nice sam." "Shikenan, zamu gani dai." Murmushi tayi ta mike zaune sannan sukayi sallama. Ji tayi ta samu dan kwarin guiwa bayan sun yi maganar. Hannunta ta kalla ta tuno sanda ya rike ta, da wani abun da taji ya taho tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin hannun nata, damke hannun tayi ta lumshe idon ta wani abu na tsirga mata. Da safe suka bar Kano cike da tunanin abubuwan da zasu kasance bayan tafiyar ta.    Abby na sane da komai shiyasa ya tura Hydar ya taho da ita dan baya son duk abinda zai faru ya zama tana nan. Sun riga sun gama shirya komai shiyasa ma yace ba sai Kamal da Aryan sun zo ba, dan ya shirya bada abinda suke bukata din dama a wannan lokacin, ya kuma shirya yakar Hajiya Zeenat din ta kowacce siga. A yanzu ba kamar wanchan lokacin bane, dan ya gama tattara duk wasu bayanai a kanta, hadda wanda bata taba tunani ba. *******Da wani irin sauri yake fitowa daga Office din, kunnensa daya makale da waya dayan kuma bindiga ce irin AK47 din nan, sun riga sun shirya tsaf dama tunda already sun san abinda zata aikata bayan ta samu sakon. A jere ya same su dukkan su cikin shiri suna jiran umarnin sa. Kamewa sukayi dukkan su sanda ya iso in da suke, sannan ya basu umarnin shiga mota su dau hanya. Tun rana matawalle yake kano tare da Lamido da shima yake a shirye cikin shigar kayan nasu na dss shima. A wata mararraba suka hadu, suka dauke su kamal ya gaisa da Matawalle sannan ya gaida Lamido cikin girmamawa. "Kuna sane da location dinta ko?" Lamido yace yana duba agogon hannun sa "Yanzu haka tana daf da shiga kaduna, zata je su hadu da Barista.” “Good.” Wayar da suke amfani da ita wajen communicating Kamal ya saka a kunne, ya bada umarnin rufe hanyar shiga baki daya sannan ya ajiye wayar. Drivern ta ne yake tuka motar sai body guard din nan daya a gefe sai ita da Salim a kujerar tsakayi, sai Daddy a kujerar baya an shinfide shi, duk da tashin hankalin da take ciki hakan be saka ta nuna karaya ba, burin ta ta isa kaduna ta samu mafaka sannan tayi amfani da Daddyn wajen tilastawa Aryan ya mallaka mata duk abinda yake hannun sa sannan zata bar musu uban su Ya shaki numfashi. A daf da shiga kadunan suka hangi hold up me tsawon gaske, tsaki taja dan tasan zasu dan bata lokaci sai kawai ta kwantar da kujerar ta jinginar da kanta a jiki ta rufe idon ta. A hankali suka dinga ja motocin na matsawa da kadan kadan har suka kusan zuwa daf da wajen dan suna iya hango gaban sai dai alamu sun nuna kamar yan sanda ne suka tsaida hanyar suna searching. Shiru driver nan yayi be ce komai ba duk kuwa da yaga abinda yake faruwa Ya kuma hango Wasu irin manyan na’urori daga chan gaba da suka tabbatar masa da trackers ne. “Park!.” Aka daka musu tsawa dai lokacin da suka karaso daidai wajen da sai sun bude maka gate din da suka saka sannan zaka wuce. Sai a lokacin duk hankalin su ya dawo jikin su suka farga da abinda yake faruwa. “It’s a trap hajiya.” Salim yace yana kokarin bude murfin motar bayan sun yi parking a gefe nan da nan aka saki hanyar kowa ya wuce. “You are under arrest!” Aka kama hannun hajiya zeenat da tayi mutuwar zaune saboda tsananin gigita aka saka mata ankwa, sannan aka sakawa Salim da bodyguard din nan Amma banda driver da ya koma gefen su ya tsaya. Motar su Kamal ce ta karaso da wani irin gudu dan ba karamin gudu sukayi ba da suka iso a daidai lokacin, tun kafin motar ta gama tsayawa suka diro cikin kwarewar aiki. Abby ne ya fito daga motar a hankali ya tsaya a gaban ta, akan kafafunsa ba tare da ya jingina da komai ba. Tsayawar da yayi tayi daidai da tsayawar bugun zuciyar hajiya zeenat, tayi luu kamar zata fadi wata cikin su ta buga mata wani abu kamar sanda a gefen kafadarta, saurin Mikewa tayi sai ta fashe da kuka “Wallahi karya suke mjn, wallahi cuta ta zasuyi, me nayi da zaa min irin wannan kamun wulakacin? Me nayi? Mara lafiya zan kai asibiti, mijina ne zan kaishi asibiti shikenan sai a wulakanta ni?” “Abinda kika aikata ne zaki fara girba daga yanzu, nayi miki alkawarin sai naga down fall din ki zeenatu, baki sani ba duk abinda kike a tafin hannu na kike, wannan da kike gani! Ya nuna Salim da shine yake mata duk kokarin da yake mata yace “Daga baya mu yake wa aiki.” “Salim?” Tace, ankwar hannun sa aka cire masa ya matsa yana bubbuge hannun sa. “Kabir da kika saka yake bibiyar rayuwar iyali na duk da bana tare dasu, dss ne!” “Salihu da kika dinga bribing sanda ina prison, aiki yake mana.” “Kinsan mutane nawa ne yanzu zasuyi shari’ah dake?” Sai yayi murnushi me taushi sannan yace "Ina Ahmad?" "Dan Allah karku saurari komai daga bakin wannan mutuncin, mugu ne shine ya kashe min kawata Khadija, shine ya yi Sanadiyyar mutuwar matar sa Aisha, shine yanzu zaizo yana maganar banza, dan Allah karku saurare shi wallahi karya yake mun." "Abby, ina ganin mu bar wajen nan kawai." Lamido yace “Ok, muje Lamido.” "Take her, and lock her up kafin Muzo." "Ok sir." Suka sara masa. A mota aka tura ta,ta fara musu ihu da hargowa macen dazu ta dan sassama bakin ta har ya soma jini sannan suka samu tayi shiru. Kamal da wasu yaran sa su biyu sun wuce da Daddy asibiti tun karasowa su, su kuma sauran Yaran Kamal din sune suka wuce da Hajiya zeenat a daren suka juyo kano. Abby kuma da Lamido suka tsaya a kaduna kafin safiya su dawo Kanon dan Abby yace ba zai iya komawa ba ya gaji. Direct AKTH suka nufa dashi, Kamal ya kira Aryan yace yazo asibitin Malam yanzu ya same shi, da sauri ya fito ya nufi asibitin yana fatan ya isa kafin wani abun ya samu Daddyn. A hanya yayi ma Ya Nabeela waya ya sanar da ita an samu Daddy amma be san komai akai ba sai ya karasa zai kirata. Be ma san an kama Hajiya Zeenat ba dan Kamal be ce masa komai akai ba. A emergency unit yake dan haka kai tsaye chan ya nufa ya tarar da securities a kofar dakin da Daddyn yake sun tsare wajen rike da bindigun su, tsayawa yayi daga waje ya sake kiran Kamal dan sam be gane abinda yake faruwa ba. Daga dakin Kamal ya fito sanye da uniform dinsa, idanun sa sun yi matukar kadawa kamar wanda ya sha wani abu ko wani abu ya fada masa a ido saboda abinda yake ji, dan zai iya rantsewa yafi kowa cutuwa da wannan abun da ya faru. Da kallo Aryan ya bishi sanda ya nufo shi, yana son gasgata abinda yake gani din, shin Kamal ne da gaske ko dai idanun sa ne? Tunanin abinda ya faru chan baya ya shiga dawo masa, sanda ya fara haduwa da Kamal a kofar gate din makarantar su ta secondary, sanye da wata riga fara da dogon wando yana rike da waya a kunnen sa. "Aryan?" Ya kira sunan sa dalilin da ya saka shi tsayawa chak da mamakin ya akayi ya sanshi. "Ka sanni?" Yace da mamakin sa, gid'a masa kai yayi alamar eh sannan yace "KAMAL ne da kukayi Montessori tare." Shiru Aryan yayi yana son tonowa amma ya kasa, fuskar sa ya sake kalla sai yaga kamar ya sanshi amma ya manta "Ka manta ni Aryan? Ko da yake ni senior dinka ne ko a lokacin, ka manta sanda kake zama kai daya a karkashin wata bishiya nazo na same ka na tayaka zama? Har ma ka sanar dani damuwar ka, ka tuna?" "Na tuna." Yace a sanyaye "Boarding school na tafi, amma tun daga lokacin ban manta ka ba, ina tuno ka da damuwar ka, dalilin da yasa na zo ganin ka, na gama secondary school zan tafi karatu." "Allah sarki, nagode sosai." "Zan dawo, zan kuma taimaka ma in sha Allah." "Ok." Yace ya daga masa hannu, ya nufi mota lokacin driver yana tsaye yana jiran sa. Bayan nan be sake ganin sa ba, sai bayan shekara hudu, a lokacin ya dawo rayuwar sa,tun daga lokacin ya zama garkuwar sa, yake kare shi da dukkan iyawar sa. Ko da wasa Aryan be taba kawo shi a wannan layin ba, ya kan yi mamaki sosai idan Kamal din yayi wasu intelligence abubuwan, amma be taba hasaso shi a wannan yanayin ba. A gabansa ya tsaya ya karkada masa hannun sa ganin hankalin sa ya tafi tunani "Kamal?" Ya nuna shi da hannu sannan ya kalle shi tun daga sama har k'asa "Ka kara da Sir Kamal a gaba." Yayi murmushi. Girgiza kai Aryan yayi, sannan yace "Babu wanda yake zaune dani da gaskiya kenan? Kowa sai ya boye min ainahin waye shi?" "Karka fara, please." Kamal yace "Why? Me yasa?" "Kawai, kar muje nan, akwai abubuwan da suke gabanmu yanzu, dan haka ba yanzu bane lokacin." "Kasan yadda ake ji? After all this years? You pretend to be under me,it's like bansan ka ba, bansan komai akan ka ba, who are you?" "Aryan, is this the right time?" " I don't know, ban sani ba." Ya matsa baya "Please kar kayi complicating komai, yanzu ba lokacin fushi bane ba, Daddy yana bukatar ka a yanzu, kayi hakuri zan maka bayanin komai." "It's ok, bana son ji please." Sai ya juya kawai yayi ficewar sa, kwala masa kira Kamal ya shiga yi amma kamar be ji ba ya karasa sauka daga wajen ya shiga motar sa. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ *RQ*         27 ****Murza gefen goshin sa yayi ya juya kawai ya koma ciki dan yana so ya tabbatar da lafiyar Daddyn. Ya Nabeela ce ta karaso da maigidan ta, ta tarar da Daddyn ana kan yi masa gwaje-gwaje domin gano ainahin matsalar sa, domin akwai wasu allurai da Hajiya Zeenat tasa aka dinga yi masa a spinal cord dinsa wanda zai yi wuya idan basu yi effecting dinsa ba. Hankalin ta yayi matukar tashi da taga halin da Daddyn yake ciki, ta dinga kuka suna rarrashin ta dole ta dawo reception ta zauna saboda ta kasa yin shiru kwata-kwata. Babu kowa a ciki da ya rage sai Kamal wanda yake tsaye a kofar cikin jin zafin abinda Hajiya Zeenat ta aikata. Waje  ya fito bayan kiran Lamido ya shigo wayar sa, ya daga daga chan kofa sukayi magana sannan ya koma ciki suka cigaba da tsaiwa da jiran tsammani.    Driving Aryan yake amma ya kasa controlling fushin sa, sosai ya zama baya ganin gaban sa saboda yadda yake ji tamkar zuciyar sa zata yi bindiga, me yasa kowa sai ya dinga boye masa komai akan me? Zai iya rantsewa a yanzu be san waye Kamal ba, be kuma san komai a kanshi ba duk kuwa da tsawon lokacin da suka dauka a tare suna tare da juna. A dan lokacin da be gaza kwana uku ba ya zama heartbroke, daga wajen mutane masu matukar muhimmaci a wajen sa, duk kuwa da ya gano komai da sukayi sun yi shi saboda farin cikin sa amma me yasa sai an boye masa? Me yasa yake zama na karshe da zai san komai akan abinda ya shafe shi? Gefe ya samu yayi parking ya dora kansa a saman steering motar kawai dan ya tabbatar idan ya cigaba da tukin zai iya yi wa kansa mummunar illah. Ya dade a haka har sai da wani me wucewa ya zo ya kwankwasa masa glass din motar, ya dago ya kalle shi sai ya tuno a in da yake wanda shaf ya manta ma. Kunna motar yayi kawai ya bar wajen ya juya zuwa asibitin dan be wani yi nisa da chan din ba. A reception ya hadu da su Ya Nabeela taci kuka ta koshi kawai sai ya zauna a gefen ta ya rike hannun ta a cikin nasa ya sunkuyar da kansa. A gefen sa Kamal ya zauna ya dora hannun sa a saman kafadar Aryan din, dagowa yayi suka had'a ido sai ya juyar da kansa ba tare da yace komai ba. Shima Kamal din be masa magana ba dan ya san ba zai saurare shi ba. Cigaba da zama sukayi har zuwa sanda Dr ya fito suka tashi gaaba daya suka isa wajen sa, bayani yayi musu akan zasu maidashi ICU sannan ya wuce su kuma duk jikin su ya kara sanyi sosai.    Gida suka fara lallaba Ya Nabeela ta tafi saboda dare yayi sosai ya zama sai Kamal din da Aryan kadai har aka gama duk processing komai Kamal ya biya Bill din duk Aryan na kallon sa amma yaki masa magana shima kuma ya share shi kansa tsaye yake abubuwan sa dan ya riga yasan waye Aryan duk abinda zai kallon sa kawai zai, ya kuma san abun da ya tsana a shareshi idan ya nuna yayi fushi ka nuna sam baka san yanayi ba yafi saurin sakkowa. Wasu allurai likitan yace a siyo a pharmacy Kamal yasa hannu zai karba Aryan ya karbe yana bata fuska "Zan iya kula dashi." Dariya ce ta kwacewa Kamal ya fizge takardar sannan yace "I can do it too, kai I'm already doing it ma." "Ya isa hakan toh, I will take over." "Waya saka?" "Ni na saka kaina." "Kana magana da hukuma ne please, so ka gyara maganar ka kaga yaran chan jiran umarni suke kawai." Tsaki Aryan yaja kawai ya barshi a wajen yana masa dariya. Daya daga cikin yaran ya bawa takardar ya samo allurar a pharmacy ya kawo sannan ya kaiwa likitan. Sosai Aryan ya cika fam da abinda Kamal din yake masa, amma ya kyale shi dan ya lura so yake ya tike shi kamar yadda Adam yake masa a ko da yaushe.      Tare suka jera suka tafi masallaci da asubah dan a zaune suka kwana, sukayi sallar suka sake jerowa suka dawo sai a lokacin Kamal yace "Zanje gida na dawo, sannan inaso ka san Hajiya Zeenat ta shiga hannu, sai ka shirya shari'ah da ita."    Da sauri Aryan ya kalle shi,amma sai yayi tafiyar sa ya barshi a tsaye cike da mamakin Kamal din. Bin sa yayi da sauri ya sha gabansa yana kallon sa "Yaushe? Me ya faru? Ya akayi duk hakan ta kasance?" "Sai naje naga Madam naga yadda ta kwana tukunna, kasan me iyali gashi na barta ita kadai kuma ba wani Jin dadi take ba, mayi magana dai yanzu sauri nake." "Please kamal, tell me everything dan Allah." "Ka daina fushin kenan?" "Dan Allah!" "Labari ne me tsawo, amma from abinda ka gani a jikina zaka gane cewa duk plan ne, kuma a karshe munyi nasara, yanzu sai kayi taking over daga nan, da mun tura ta kotu aiki ya koma hannun ka. Sannan, barrister Matawalle yana tare da mu, duk da yana yi ne ba dan mu din ba shima saboda tasu matsalar amma a kalla mun samu strong evidence na videon ta da yake wajen sa wanda shine mafarin komai, kuma shine zai yi linking duk wani abun da ta aikata tare da me taimaka mata." "Huhh!" Ya sauke ajiyar zuciya cikin wani irin yanayi ya rungume Kamal din kwalla na taruwa a idon sa. Kwallar shima Kamal ya goge a boye sannan ya bubbuga bayan Aryan din yace "Over to you Barrister ARYAN!" Bud'e masa kofar Aryan yayi ya shiga motar ya zauna sannan ya rankwafo jikin window yace "I owe you Kamal. Bansan yadda zan saka maka duk abinda kayi min ba, you are more than a friend Kamal, bayan abinda ya faru da su Mummy na daina trusting duk wani friendships, na daina yarda da kowa da komai saboda ban taba ganin irin amintar su ba. Sannan abinda ya faru tsakanin Daddy da Barrister Matawalle ya kara tabbatar min da babu abokan gaskiya a duniyar nan. Amma banda irin ka Kamal, kai na daban ne." "Kana mantawa baka saka sir a farkon sunan, ko kana so ka kwana a guard room ne?" "Sorry Sir.' ya matsa baya ya sara masa sukayi dariya a tare "Kaje ciki, zanje an dawo, we have alot to talk about akan case din, kafin na yi maka handing over na dukkan evidence din plus wanda na karba a wajen ka." "Ok Sir, duk yadda kace haka za'a yi." "Duk abinda nace? Kayi alkawari?" "Eh nayi, anything." "Ok, ka kira Raihana a waya." "Me? Noo I can't me yasa Zan kirata?" "Yanzu kace anything, so dole kayi." "Please banda wannan, zanyi komai amma banda wannan." "Hadda shi, call her and apologies again." "Not now gaskiya, I'm sorry." "Ok! Bari naje, ka koma ciki." "Ok." Ya matsa daga jikin motar suka ja yana kallo har suka fita daga gate din sannan ya juya ciki yana jin sa wani irin sakayau kamar wanda kaya ta makalewa a makogwaro ya samu nasarar zare ta.    ****Da farko Hajiya Zeenat ta dauki abun wasa dan tayi tunanin normal yan sanda ne suka kamota sai data ganta a office din DSS sannan jikinta ya soma rawa tasan tabbas ba wasa a lamarin su. Bata taba hasaso wannan ranar ba, bata kuma taba tunanin duniya zata juya mata baya haka ba, komai da take yi a cikin tsari da plan take yin sa abinda ya saka take nasara a duk abinda tasa a gaba, sai dai wannan karon ta gama tabbatarwa karyar ta kare bata da kowa dan hatta wadanda take tunanin suna tare da ita ashe duk karya ne. Sun yi outsmarting dinta sunyi wasa da brain dinta kamar dai yadda ta dinga yi da tasu a baya. Laifukan ta masu girma ne idan har zasu taru akanta toh tabbas tasan hukuncin da ya dace da ita shine na kisa, mutum daya ne take da yakinin be juya mata baya ba har zuwa karshe sai dai ta tabbatar daga zarar ya samu labarin kamata shikenan zai cikawa wandon sa iska. SAN Mandawari wanda duk wata nasarar ta da taimakon sa ne dan hatta shari'ar abby shine ya tsaya mata har sukayi nasarar tura shi gidan yari.    Tana durkushe a k'asan dakin da aka ajiye ta ita kadai. Babu haske ko kad'an gashi an karbe komai nata an saka wayarta ana monitoring duk wata wayar da zata shigo daga daren zuwa wayewar garin yau. Budo kofar da aka yi ne ya bawa haske damar shigowa cikin dakin ta yinkura da sauri daidai lokacin da suka shigo su uku, Kamal ne a gaba sai Lamido sannan Abby a karshe, a gaban ta ya tsaya kamar jiya ta daga kan ta da k'yar ta kalle shi shima ita yake kallo, yana ganin lokacin da ta sauya masa rayuwa a saman fuskar ta, lokacin da suka kala masa sharrin kisa. ***Karar motar Yan sanda ce ta fara isowa kafin su hauro saman su shigo dakin su zagaye shi, kalmar da ogan cikin ya furta a lokacin da yake ce masa "you are under arrest." Ita tafi komai tsaya masa a lokacin ya kasa tantancewa abinda suke nufi da kalmar sai da yaga wani yazo ya damki hannun sa ya zura masa ankwa sannan abun ya shiga dawo masa a kansa.    Sakkowa sukayi dashi bayan sun dan gama dudduba dakin suka bar wasu cikin yan sandan a dakin hade da likitan da ya karaso a lokacin. Zeenat na zaune a falon ta hada kai da guiwa tana ta rusa kuka tamkar ranta zai fita, Nabeela na daga jikin kujera itama tana kuka sai Aryan da yake kiran mummyn sa a rikice yake gaba daya. Ammy ce ta shigo jin hayaniya a gidan ta tarar da mummunan tashin hankali a take ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya amma Abby yana kallo haka suka fice dashi suka saka shi a mota. Cikin kankanin lokaci labari ya soma zagaye gari anacewa aminin miji yaci amanar mijin bayan yayi tafiya, ya haike wa matar sa bayan nan kuma ya kashe ta har lahira.     Runtse idon sa yayi yana jin kamar a lokacin komai yake faruwa, yana jin da zai iya komar da hannun agogo baya da sai ya goge sanin da yayi wa Daddy iyakar rayuwar sa, amma duk da haka ba zai manta abinda yayi masa ba, ba kuma zai taba yafe masa ba har duniya ta nade.   Da niyyar yi mata magana Abby ya shigo amma sai ya fasa saboda baya ko son ganin fuskar ta, juyawa yayi ya bar Kamal da Lamido a dakin daga baya Lamido ya fita jim kadan wasu mata kedaru suka shigo, suka gaishe da Kamal din sannan ya basu umarnin su dan sassamata yayi ficewar sa. Jibgarta suka fara yi sukayi mata likis dan sai da suka farfasa mata jikinta sosai fatar nan me laushi da sheki tayi dud'um nan da nan ta sauya fasali da halitta ta koma kamar ba ita bace Hajiya Zeenat yar gayu me aji da tarin kudi. ***Adam na kwance a gida yana baccin asara bayan ya tabbatar da ya gama hada Aryan da Raihana ya kuma tabbatar zuwa lokacin Aryan ya yi mata korar kare shikenan hankalin sa ya kwanta ya samu damar shekar baccin sa hankali kwance duk da kuwa yana son yarinyar amma haka zai hakura bashi da asara tunda Aryan dai be same mu. Wayar sa ce ta farkar dashi ya daga yana jan tsakin katse masa baccin da yake yi amma abinda yaji a cikin wayar sa sashi wartsakewa nan da nan ya diro dga gadon ya hau neman dogon wandon sa da ya jefar tun a hanya da daddare. Da k'yar ya zura ya fito hankalin sa tashe da mummunan labarin da ya samu na zuwan DSS companyn su suka kuma yi awon gaba da wasu daga cikin securities din dake zaune a gate sannan suka hada da Abdulhakeem da wani abdullahi da yake a office din Adam din. A hanya kafin ya karasa office din ya sake samun labarin da ya sake rikita shi ya sashi chanja alakar motar tasa daga zuwa office din zuwa nearest police station dan tuni labari ya warwatsu a social media an kama Hajiya Zeenat Mukaddas bisa zargin yinkurin kashe mijinta, Alhaji Ibrahim Mukaddas,salwantar da rayukan wasu mutane da kuma wasu manyan laifukan da ta aikata wanda take da daurin gindi daga chan sama. Duk in da Adam yake tunanin zai sameta yaje amma sai ya tarar bata nan, haka ya wuni cur yana zagaye karshe ya hakura da ya gano tabbas daga saman ne aka kama dan be kawo DSS bane ba, kuma ko da ace ya sani bashi da hanyar tunkarar wajen domin bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane ba.     ****Matsawa Daddyn ya dan soma yi ya dan daga dan yatsan sa kafin ya bud'e idanun sa a hankali, da sauri likitocin suka rufa a kanshi dan dama suna cikin dakin harda Dr Mahfouz da ya iso da safe, sun yi kokari sosai wajen samun daidaituwar numfashin shi saboda irin shak'ar da Zeenat tayi masa bayan ya riga ya gama zama so weak saboda ajiye shi da tayi babu ruwa babu abinci, sun yi kokari sosai wajen samun daidatun amma kuma ya sake komawa wani baccin me matukar nauyi wanda suke tunanin zai yi wahalar gaske ya farka a nan kusa duk kuwa da yana numfashi amma idan har ya kai wasu hours be farka ba, toh tabbas ya shiga coma sai dai wani ikon Allah kuma.    Dr Mahfouz ne ya samu karfin guiwar yi musu bayani nan da nan Ya Nabeela ta rushe da kuka Aryan kuwa shiru yayi kawai ba tare da yace uffan ba, sai Kamal da yayi kokarin samun karin bayani daga bakin Dr Mahfouz din sannan ya yi kokarin kwantar musu da hankali. "Zan iya ganin shi?" Aryan yace yana kallon Dr Mahfouz "Zaka iya, muje." Bin bayan sa yayi suka shiga dakin dake cike da wasu irin na'urori manya manya, daga kofa ya hangi Daddyn a kwance sambal tamkar bashi ba, dan har wani irin dashewa fatar jikin sa tayi kasancewar babu riga a jikin sa an kakkafa masa wasu irin na'urori da suke nuna duk abinda yake fafuwa a jikin nasa. "Zai tashi Dr?" "Muna fatan hakan Aryan, amma... Yana bukatar addu'ar ku." "Ok, Allah ya bashi lafiya." "Amin ya Allah, in sha Allah komai zai wuce, abinda ya faru shine ta dade tana cutar da shi baa sani ba, akwai wata kwaya da take bashi a ruwa ko lemo da take kashe jikin mutum slowly, shi ta dinga bashi tsawon lokaci sai yanzu damage din ya nuna, so amma muna iya kar kokarin mu akai sannan ko ma sai kun hada da addu'a sosai, we are monitoring his kidneys yanzu haka and we are hoping ya zama babu abinda ya faru dasu." "Allah yasa." "Amin Amin." Shiru sukayi na dan wasu sakanni, sannan Aryan din ya juya ya fita cikin karyewar zuciya. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥 *_SAK'ON ZAFAFA BIYAR GA AL'UMMAR K'ASAR NIJER_*🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 _ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR JAMA'AR NIJER_ _DIMBIN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI A GAREKU_ _MUN FIDDA TALLA MUN BADA NUMBER DA ZAKU TUNTUBA,TO AMMA WANCAN NUMBER DA ZAKU TUNTUBA BA'A SAMUNTA,A HALIN YANZU GA SABUWAR NUMBER DA ZAKU TUNTUBA DON TURA KATI KU SAMU DAMAR SHIGA GROUP NA ZAFAFANKU BIYAR_ +227 90 16 59 91 *Yan jamhuriyyarmu nigeria kuma😂🇳🇬🇳🇬,zaku ci gaba da pyment ne ta account dinmu na* Maryam sani 0022419171 ACCESS bank Ku tura shaidar biya ga +234 903 318 1070 *Katin waya ko VTU zaku tura ta wannan number* 09166221261 Litattafan dai sune kamar haka RUMBUN KAYA Hafsat rano A RUBUCE TAKE Huguma IDON NERA Mamuhghee KI KULANI Hafsat xoxo DAUD'AR GORA Billynabdul *Muna godiya da zabin zafafa biyar*🤝🤝🤝🔥🔥🔥🔥 *RQ*      28 ****Kwana daya tak da faruwar abun Daddy ya dawo a hargitsa, tuni Hajiya Zeenat ta riga ta juya masa labarin abinda ya faru wanda ya samu komai a baibai. Yadda yake jin tsanar Abby da abinda ya aikata masa me girma ne, musamman video da Hajiya Zeenat din ta aika masa tun a chan din. Be taba tunanin zai ci amanar sa haka ba, dan a duniya ya yarda dashi fiye da yadda ya yarda kansa. Labarin da Hajiya Zeenat ta shirya shine dai yake cigaba da yawo a gare hakan ya kara tunzura daddy yaci alwashin sai ya ga bayan Abby ko da kuwa zai karar da duk abinda ya mallaka. Barrister Mandawari shine ya shiga shari'ar a lokacin kuma yana da sama sosai dan haka shine ya sauya komai na abinda ya faru ya maida shi kan Abby din wanda dama ya dade yana envying nasa da duk nasarar sa. Babu wata hanya da suka barwa Abby da zai kare kansa, haka yana ji yana gani suka tura shi prison ba tare da ya aikata komai ba. ***Zaune Ammy take ta hada kanta da guiwa tana kuka sosai, tun bayan da aka karkare shari'ar kuma aka tisa keyar shi zuwa prison ta saddakar da rayuwar ta da ta yaranta ta shiga cikin babbar matsala. Zagaye suke da ita dukkan su, Lamido na tsaye daga saman kanta kasancewar shine babba, Sadiq na durkushe a gabanta sai Haidar da yake rike da hannun karamar kanwar su Raihanawadda take kuka itama ganinAmmyn na kuka ba tare da tasan abinda yake faruwa ba.   Banko gate din gidan aka yi da mugun karfi, duk suka mike a firgice, kafin su farga har sun shigo ciki, suka shiga watsi da kayansu suna watso musu su waje, dukkan su kukan suka saka da kyar suka kyale su, suka dauki abinda zasu dauka suka fito daga gidan, su kuma suka saka padlock suke datse suka tafi bayan sun watso musu da ragowar kayan nasu waje. A daidai lokacin motar da Hajiya Zeenat ke ciki ya shigo layin, tayi murmushi ganin su a kofar gidan tsaye cirko-cirko, dan dama sun yi magana da Daddy tasan kuma zai aikata komai a yadda yake jin tsana da kiyayyar su a lokacin. Lamido ne ya durkusa ya dauki Raihana da hannun days, dayan hannun nasa ya rike jakar yan kayan su da suka samu suka dauka. Sauran abubuwan na hannun Sadiq da Haidar da ya rike hannun Ammyn suka soma takawa cikin yinkurin barin layin ba tare da sun lura da ita ba ma. Tana hangen su, har suka fice gaba daya daga layin dake dauke da tsirarun mutane suna kai kawo. "Wannan shine sakamakon duk wanda yace zai ja da Zeenatu!" Tace tana murmushi. Yanzu rayuwar zata dawo sabuwa taci karen ta babu babbaka tayi rayuwa me inganci. Gate din gidan aka bud'e driver ya saka motar ciki ya samu gefe daya yayi parking sannan ya fito da sauri ya bud'e mata kofar, ta fito a hankali ta shiga takawa zuwa balcony din da zai sadaka da cikin gidan.      Kuka Aryan yake sosai yana kiran mummyn sa, Nabila na rik'e dashi tana rarrashin sa amma sam yaki yin shiru, yau kwana wajen arba'in kenan da rasuwar Mummyn, amma ya kasa hakura, babu irin lallashin da ba'a yi masa ba amma kullum sai yayi kuka saboda shakuwar da suka yi da mahaifiyar sa. Da kallo Zeenat ta bisu cikin zuciyar ta,ta ayyana sune kadai suka rage mata a yanzu, sune kadai matsalar ta. Siririn tsaki taja a ciki -ciki, dole zata bi komai a sannu kafin tayi maganin su. Karasowa tayi da nufin rike hannun aryan din ya fizge da sauri yana matsawa baya. "Don't touch me!" Ya fada da karfi yana sake yin baya da sauri "Aryan nice fa? Aunt Zeenat come here my boy." Tace tana sake matsowa, cigaba da matsawa yayi yana mata kallon tsana kafin ya juya da gudu ya haye sama. Kallon Nabila tayi wadda itama ita take kallo tace "Ina Adam?" Ta zame jakar hannun ta tana jan tsaki "Yana falon Mummy yana kallon cartoon." "Ok." Tace tana zama a cikin jerin manya manyan kujerun dake zagaye a falon. "Jeki kawo min ruwa." Juyawa tayi zuwa kitchen ta dauko ruwa da cup ta kawo mata, ta ajiye,. "Kije ki dubo yaron nan, dan wannan bakar zuciyar tasa zata iya sakashi aikata komai,yaro karami da shegiyar zuciya kamar fir'auna, sai kace akan sa aka fara mutuwa. Mtsw!" Taja tsaki tana balle murfin ruwan Bata ce koma ba, dan ita dama ba me yawan magana bace ba, ta juya tana kokarin kama staircase din sai ta dakatar da ita "Ki turo min Adam." "Toh." Tace ta cigaba da hawa a hankali zuciyar ta na mata zafi.    A bedroom din Mummy ta same shi, ya kwanta lamo a saman gadon ta yana kuka k'asa -kasa, da sauri ta karasa ta dagoshi ta rungume shi suka sake fashewa da kukan a tare, Sun dade a haka kafin ta cika shi ta shiga share masa hawayen dake bin fuskar sa "Ka daina kuka kaji? Idan kana kuka kanka zai yi ciwo." "Ni Mummy!" "Zata dawo ne, very soon kaji? Amma sai ka daina kuka ka daina yiwa Anty Zeenat rashin kunya." "Bana son ta, I hate her. Muguwa ce sosai ita ta dauke min mummy ta." "Shsshh!" Ta rufe masa baki da sauri tana kallon kofar da ta bari a bud'e,tashi tayi da sauri ta rufo ta sannan tace "Don't say that again kaji? Ka daina fada kar Daddy yaji." "Na daina." Yace yana kwanciya a jikin ta. "Good boy." Tace tana share kwallar da ta zubo mata. Tunowa tayi da sakon Kiran Adam ta mike da sauri ta fita, taje ta same shi yayi kacha-kacha da falon ya zubar da ledojin munch-it da caprison ko ina. "Anty Zeenat na kiran ka." "Ta dawo?" Yace yana tashi daga riginginen da yayi yana kallo "Tana falon k'asa." Fita yayi ta jawo karamin dustbin ta kwashe komai da ya zubar sannan ta share wajen tas ta goge. Muryar Daddyn su taji a falon sa na sama, tayi saurin komawa bedroom din Mummy ta rike hannun Aryan ta dawo dashi dakin sa, sannan ta rufe dakin Mummy din ta sauko kasa. Fada Daddyn ya hau ta dashi ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, bata san takamaimai laifin da tayi masa ba,sai da ya gama banbamin tana durkushe sannan ya hau kwala wa Aryan kira, kin sakkowa yayi yasa key a kofar dakin nasa yana jin Daddyn yayi ta kiransa har ya hakura ya kyale shi. ***Gida Aryan ya koma da safe bayan Ya Nabeela tazo asibitin da nufin ya shirya. Dakin sa ya shiga da ya watsa ruwa ya sauya kayan sa ya fito ya tarar da Adam yana jiransa a falo. "Me yake faruwa?" Ya tambaya yana kallon Aryan din da yanayin sa "Baka sani ba?" "Eh ban sani ba, nake so ka sanar dani." "Da yake ka ajiye ni ne ko? Toh ban sani ba." "Please Aryan, ba fada nake so ba, just tell me, me yake faruwa ina Mom dita?" "Ban sani ba, dan bani da lokacin batawa, kawai dai mu hadu a kotu, koma me yake faruwa idan kaje chan zakaji." Wucewa yayi da nufin sauka Adam din ya riko shi da sauri "Aryan dan ALLAH! Help me." "Me kake so nace maka Adam?" "Me ya faru?" "Kamar yadda ka samu labari haka ne,kuma DSS ne sukayi kamen bayan hakan bansan komai akai ba, ina tare da daddy a asibiti." "Bashi da lafiya?" Ya fada cike da tashin hankali "Eh." Kawai yace cike da kosawa,ya karasa sauka. Da sauri Adam din yabi shi suka sauka a tare yana shiga mota shima ya shiga tasa yabi bayan Aryan din. ***Raihana na zaune tare da Daadah tana gyara mata kanta, suna yar hirar su, hankalin ta baki daya yana kan hirar da suke yi bata ji ringing din da wayarta take yi ba har sai da Hydar da ya shigo lokacin yace "Ba wayarki bace ba?" Sai lokacin ta ankara ta tashi da sauri ta dauki wayar sai dai sunan da ta gani akan screen din wayar ya saka ta jin kamar an sare mata kafarta, tayi sakale da wayar a hannu ta saci wajen da Hydar yake tsaye yana kallon ta "Aryan ne?" Yace yana kafe da ido Daga masa kai tayi alamar eh "Share shi please, me zai ce miki?" "A ah Aliyu, barta ta daga, ki daga mana kiji mai zai ce." Daadah tace "Daadah me zai ce mata? Mutumin da ya yi mata kora irin ta kare, kinji tsawar da yake mata ne? Idan tana da hankali ai ba zata dauki wayar sa ba." "Duk naji wannan, a kalla dai taji me zai ce mata ko?" "Ko me zai ce ma dai, muna nan akan bakan mu gaskiya, babu wata alaka da zata sake hada mu dasu, babu." "Toh wai Hydar duk hakilon nan da kake, shi Aryan din yace yana son Raihana ne?" "Ke Raihana yace yana son ki ne?" Girgiza kai tayi tace " A ah." "A ah toh, ba abinda kake tunani bane ba, maza kirashi kiji dalilin kiran nasa." Juyawa kawai Hydar yayi ya fice be sake cewa komai ba. "Kinsan zuciya irin ta Hydar." "Daadah wai dama Hamma Hydar yasan Aryan ne?" "Hmm.. ya sanshi Raihana." "Ok,wai menene yake faruwa? Naji tun ranar yana ta jaddada babu alaka a tsakaninmu dashi, kuma naji suna maganar da Abby ma har naji ya dau zafi sosai akai." "Labarin na da tsawo Raihata, amma je kira shi kiji me yake faruwa sai ki dawo na baki labarin komai, be kamata a bar ki a duhu ma musamman tunda yanzu kema kin shiga cikin abun." "Bari muga ko zai sake kira Daadah, ko mistake yayi dama ba kiran zai ba." "Wa yace miki? Kira shi dan Allah wallahi tausayi yake bani." "Kai Daadah, kamar kin sanshi?" "Jeki dai ki kirashi kizo." "Ok." Tace ta wuce dakin ta. Ta samu gefen gado ta zauna sannan ta shiga kan number Aryan din kirjinta na bugawa kamar zai fito, wani abu me kama da tsoro take ji musamman sanda wayar ta fara ringing sai taji kamar da bugun zuciyar ta yake tafiya. "Hello." Yace cikin husky voice dinsa wanda yasa ta yin tsam "Helloooooooo Raihanaaa?" Yace yana tashi daga wajen da yake zaune, har cikin kwanyar kanta taji yadda ya kira sunan nata, karo na farko kenan da ya taba fadan sunan ta amma sai taji sunan yayi sounding wani iri kamar ba nata ba "Helloooo." Ya sake maimaitawa "Hello." Tace a gajarce "Kina jina?" "Umm." "Ok, kina lafiya?" "Lafiya Lou." "Ok, sai anjima." "Sai anjima?" Tace a ranta cike da mamakin sa, "Ok." Tace a sanyaye "I'm sorry, bye." Ya kashe wayar, hankalin sa gaba daya yana wajen Dr da ya fito daga dakin Daddy shiyasa ya amsa wayar a gajarce, ya kirata ne ya sake bata hakuri kamar yadda Kamal yace kuma zuciyar sa ta amince da kiran dan haka kawai ya samu kansa da son ji daga gare ta, sai dai kuma bata daga wayar ba har ta katse lokacin kuma ya shiga wata sabgar sanda kuma ta kira yayi busy. Wayar ya tura a aljihun dogon wandon sa ya koma ciki yana shafa sumar gashin kansa Adam na tsaye ya dafe kansa tun bayan da ya ga halin da Daddy yake ciki jikin sa yayi sanyi sosai. ***Da daddare Kamal ya shigo asibitin, dan gaba daya be shigo ba ranar yana kan case din Hajiya Zeenat din in da suka gama tattare dukka bayanin wajenta da fari bata yarda ba amma daga baya da ta ji uwar bari sannan ta bud'e baki wasu abubuwan ma babu dadin ji dan ba karamin basu mamaki tayi ba dan wasu abubuwan ma basu san ta aikata su ba sai da tasha matsa sannan ta bud'e baki. Abu daya ne Abby ya dage ta fada musu in da Ahmad yake ko in da ta kaishi amma ta kafe akan bata san komai akai ba,dan tun bayan lokacin bata sake samun labarin sa ba, bata kuma sake ganin mutumin da ta ajiywa shi ba a lokacin da ta dauke shi, burin ta kawai a lokacin ta salwantar dashi kawai yadda zata fi samun saukin mallake daddy da duk dukiyar sa idan ya zama bashi da d'a namiji a matsayin magaji. Hannun Aryan ya kama bayan ya fito daga dakin Daddyn suka fito waje, suka samu gefen bishiya suka tsaya ya kwashe masa duk yadda akayi ya sanar dashi sannan yace “Zaka ji ni shiru na kwana biyu, ina da yakinin zakayi abinda Ya dace wajen ganin mun yi nasara.” “Karka ce min tafiya zakayi ka barni?” “Kamar dai haka ne, ba zan dawo ba kuma har sai ka nemo ni.” “Ban gane ba!?” “Zaka gane idan aikin ya biyo ta kaina.” “Kamal please waye kai? Kana sani tunani wallahi.” “Na lawyer bane ba kai? Find out please. And please be fast about it dan zan zauna zaman jiran ka ne.” “Ba zaka fada min ba?” “Yes! Na riga na gama part dina.” “Ok. I will find out.” “Please do, cox I’m eager.” “Ok, stay safe please. Ko ina zaka make sure to stay healthy. I will look for you kamar yadda kace in sha Allah.” “That’s my friend. Allah ya bawa Daddy lafiya Ya kuma baka nasara.” “In sha Allah Captain!” Ya tsara masa Sannan ya kame suka kwashe da dariya “Did you call her? Ka kirata?” “Wa? Ban kira ba bani ma da wannan lokacin ni.” “Ok let me find out.” Ya zaro wayar sa. Da sauri Aryan ya warce yana hararar sa “Me kake shirin yi?” “Kiran kanwata zan yi naji ko ka kira ka sakè bata hakuri.” “Akan me wai? Ka damu da ita sosai ni da ko tuno sunan ta ma banayi.” “Ikon Allah. Waye ya gama mana wakar I love her ranar?” “Ni ne, amma ai ba love na love nake nufi ba, na addinin muslunci.” “Hard guy.” Ya dake shi a chest sannan yace “please ka dan bude zuciyar nan taka haka nan mana, Atleast we are one step toward victory.” “We still have alot Kamal, kama hajiya zeenat kamar dai eye opener ne, we have to find out ina Ammy take? Ina Ahmad?” “Sannan sulhu sakanin daddy da Alhaji Matawalle.” Kamal yace “Anya? Haka zai yiwu?” “Gashi nan dai. Muyi addua sosai akai. Dan inaso mu kulla alaka me karfi bayan wannan ma, ko da yake kamar fa an ce min raihana tana da saurayi ko? Shaf na manta nake ta wannan abun.” Ya dan bubbugi kansa alamar yayi kuskure. Yanayin fuskar Aryan din ce ta sauya nan da nan, ya yi kicin da fuska ya hade rai kmar bashi ne yanzu suke magana normal ba. “Kasan ashe wai akwai wani guy da yake ciki, ta fada min sam na manta amma dai babu wani official magana akai gaskia.” “Toh ni menene nawa da zaka din ga fada min? Ina ruwana?” “Oh na manta ba ruwan ka, bari na wuce gobe da safe zan zo na dauke ka mu je Office dina.” “Ba zan je ba.” “Me yayi zafi ?” Ya fada yana kokarin hana kansa dariya “Ba komai , kaje bari na koma ciki sai anjima.” “Ok sai anjima. Ma yi waya.” “Oho.” Aryan yace yana juyawa Ya bar Kamal a wajen dariya na neman kashe shi *RQ*       29 ****Da sassafe Kamal yazo daukar Aryan ya same shi tare da Adam a asibitin. Adam tun da yazo yaki tafiya babu wanda yake ma wani magana a cikin su amma kuma duk abinda ake bukata da sauri yake tashi yayi. Kallon sa Aryan yayi yasan tafiya zai kuma shi sam zuciyar sa bata yarda da zaman Adam din a wajen shi kadai ba duk da ya nuna damuwar sa amma ba zai iya tantance gaskiyar sa ba "Kana ganin mu tafi mu bar Adam anan? Shi kadai?" "Yes akwai jamian mu a wajen duk da ba gane su zai ba, zasu kula da Daddyn har ka dawo." "Ok, muje." Suka fice Adam din yana kallon su ba tare da sun masa sallama ba. Shiru ne ya biyo baya tun da suka dauki hanyar babu wanda yayi magana a cikin su har suka kusa zuwa, sosai yanayin Kamal ya koma irin very serious din nan da suka isa gate din cike da mamakin sa Aryan yake kallon komai har suka shiga cikin harabar wajen yayi parking da sauri wasu matasa maza suka karaso suka bud'e masa kofar sannan suka gaishe shi irin tasu gaisuwa. "Sir Indabawa ya shigo?" "Yes, anan ya kwana ma." "Ok... Aryan show them your I'd card." Hannu yasa a jikinsa ya dudduba be ji shi ba "Yana mota ko office." "Ohh..." "Zamuyi searching dinsa ne sir?" "Oh yes, kuyi tunda haka dokar tace." "Ok, zamuyi searching dinka idan ba zaka damu ba." Kallon Kamal yayi ya gid'a masa kai "Haka dokar take Aryan, next time don't forget your I'd card ." Kamal yace yana kallon sa "It's ok, bismillah." Duba shi sukayi da yar karamar na'urar su suka tabbatar babu wani makami ko wani abu a jikin sa sannan suka ce babu matsala. "Are you for real?" Aryan yace suna tafiya ganin yadda ake saluting Kamal din yana babbasarwa. "Kai ne kadai ka raina ni ai." Ya bige shi a kafad'a Office dinsa suka isa, ya daga kai ya karanta sunan da yake rubuce a saman office din sannan a hankali ya furta "You are unbelievable." Ciki suka shiga ya nuna masa wajen zama sannan ya zauna a kujerar sa ya hau tattare abubuwan da yake son mikawa su ga Aryan din, sai da ya hade su waje daya tsaf sannan ya taso ya dawo kusa da Aryan din ya mika masa "Na gama part dina, yanzu saura naka part din, I trust you." "I will take over in sha Allah." "Good, ina nan ina jiran ka." "Wai da gaske kake? Tafiya zakayi?" "Yes da gaske mana, baka so kasan waye ainahin Kamal din naka?" "Is there anything da ya kamata na sani? Bayan wannan abun da na gani?" "Akwai da yawa ma." "Ok, let see." "Yawwa, lets go an meet Indabawa, daga nan sai kaga Hajiya Zeenat din." "Bana son ganin ta, mu hadu a court kawai." "In kace haka, shikenan." "Yaushe zaku mika ta kotu?" "Yanzu maganar da zan oga kenan, sai ya saka hannu sannan. Dole kuma za'a bata damar daukar lawyer." "Ok. Allah ya bamu sa'a." "Amin dan saurayi." "Zaka fara ko?" "Kayi zuciya mana idan baka so na dinga tsokanar Ka." "Toh yanzu wannan aikin da yake gaba na zanji ko da wanne?" "Da dukka mana." "I can't concentrate ai." "Shine ma zaka fi samun concentration din ai,guy kasan falalar dake tattare da nisa'u kuwa?" "Ban sani ba, bana ma so na sani, muje dan Allah." "A ah wait! nine oga anan ai, kaga hungry boys din can na waje, da nace tak zasu zo su sabe min kai sama." Dariya Aryan yayi yace "In ka fasa." "Naji tausayin ka ne, kar nayi ma me rabo asarar handsome guy kamar ka, shiyasa kawai." "Naji, muje dan Allah, a duk serious abu sai ka kawo wasa." "Na fada maka, kai kadai ka raina ni wallahi, amma ba komai." "Naji, lets go oga kwata-kwata." "Muje." Yace yana mikewa suka fita daga office din. Sun dade sosai a office din Indabawan suna magana dan har azahar basu bar wajen ba ana sukayi sallah sannan suka fito. Kan Aryan yayi masifar daukar charge dan yana bukatar yayi zama sosai ya duba dukkan shaidun da suke hannun sa, dan ya lura akwai abubuwan da basu gama bayyana ba Wanda suke bukatar nutsuwa sosai kafin su soma shari'ar. A gidan sa Kamal ya sauke shi amma sai yaki shigowa, har Aryan din ya soma tafiya ganin Kamal din be fito daga motar ba ya sashi dawowa baya "Ba zaka shigo ba?" "Eh, tafiya zan." "Muje mana mu karasa duba abubuwan nan sai mu fito anjima." "A ah, ka ajiye su kawai ka fito na sauke ka a office." "It's not safe ai na bar komai anan, ina ganin muje kawai na kai su gidan Ya Nabeela sai mu wuce office din." "Ok, hakan ma yayi." Fasa shiga gidan yayi suka koma tare ya kaishi gidan Ya Nabeela ya bata takardun da komai yace ta ajiye sannan suka fito a tare ta nufi asibiti wajen Daddy su kuma suka wuce office din.   ***Kamar yadda suka dauki kwanaki basu shigo office din ba, haka suka tarar da ayyuka masu tarin yawa.     Zainab ce ta yi knocking sannan ta turo kofar ta shigo tana yauki da rangwada ta gaishe shi a ladafce ya amsa kansa akan aikin da yake yi ba tare da ya dago ba. "Hope babu wata matsala sir, kwana biyu baku shigo office ba." "Babu, akwai wani abu ne?" "No babu komai,zuwa nayi dai naji." "As you can see I'm very busy, so please..." "I can help you." Ta tare shi "It's ok, zan iya. Zaki iya tafiya " Tsayawa tayi tana wasa da hannun ta, ba tare da ta fitan ba, so take ta tambaye shi Raihana amma tana shakku, dagowa yayi jin bata fita ba ya kalle ta, tayi saurin cewa "Sir Raihana fa? Ta daina zuwa ne?" "Zainab please go out." Yace mata politely yana kokarin hana kansa yi mata wulakanci "Ok sir, kayi aiki lafiya, idan kana bukatar wani abu ina waje." Shiru yayi mata haushin nacin ta na tike shi, juyawa tayi ta fita ya ja tsaki da karfi. Ta fara isar shi da shegen iyayin ta.     Akan aikin suka dukufa suna kokarin resolving komai sune har bayan magriba suna office din. Sallah suka fito yi da mamakin sa, sai yaga Zainab a zaune babu kowa sai ita. kallon juna sukayi shi da Kamal da ya fito daga office dinsa shima sannan ya kalle ta. "Baki tafi ba wai?" Kamal yace da mamaki "Eh, akwai wani aiki da nake karasawa ne." "Ko wanne aiki ne ba za'a barshi sai gobe ba Zainab?" "Aikin me muhimmanci ne Sir, shiyasa." "Still dai, gashi har duhu ya soma yi, ki jira idan zamu fita kawai sai muyi dropping dinki a gida dan samun napep idan dare ya fara yana wahala" "Ok sir, nagode." Tace fuskar ta dauke da murmushin jin dadi, ta saci kallon bangaren da Aryan yake taga ya bata fuska "Muje kar mu rasa jam'i." Yace kawai ba tare da ya saka musu baki a maganar tasu ba.   Tana zaune kamar mayya suka dawo daga sallar, ko motsawa batayi daga wajen ba kar ma su tafi bata sani ba dan ta samu opportunity me kyau da ba zatayi wasa dashi ba,shiyasa ko sallar bata tashi tayi ba tana zaune har suka dawo kowa ya shige office dinsa. Wajen minti talatin sannan Kamal ya fito ya shiga office din Aryan din yace su wuce. "Kuje kawai zan taho idan na gama." "A ah, motar ka fa tana asibiti, muje kawai ka ajiye mu a gida ka tafi da motar tawa ma hadu gobe idan Allah ya kaimu." "Kaga akwai abubuwan da ban karasa ba, musamman harkar shigar da lissafin nan, kwana biyu na samu saukin sa." "Amfanin Raihana kenan, da tana nan da tuni tayi." "Zaka fara, shikenan muje kawai." "Kai kuma baka san gaskiya, ka tsaya kallon ruwa dai, kwado yayi maka kafa." "Wai dan Allah me yasa kake min haka? Ni menene nawa tsakani na da yarinyar nan ne wai? Aiki take kamar kowa nothing more." "Kaga duk zagaye-zagayen ka ba zai maka ba, ni dai ba bako bane bare kace zaka ninke ni bai bai, nasan komai har kiran ta da kayi." "Ya Allah, ita tace na kirata?" "Ni na sani, kana wasa da aikin detectives ne?" "Aikin munafukai dai, na ji na kirata kuma saboda kai ne, babu kuma wata doguwar magana da ta hada mu, bayan gaisawa, hakuri kuma na riga na bata sannan na bata abinda take so na monthly clearance din ta, me ya rage kuma?" "Call her, kace ta dawo you need her." "Wa? Ina ba dai ni ba." "Ba in da ego dinka zai kaika, man accept your defeat kawai dan wallahi nasan kana son yarinyar nan, ban taba ganin kayi ma wani irin abinda kayi mata ba, amma ki fadin ka ya hana ka gane." "Ya Allah, yanzu me ya kawo duk maganar nan? Soyayya CE irin ta yarinta, irin ta yaya da kanwar sa, babu wani abu kuma,." "Shikenan, zaka ce na fada maka kila a lokacin da bashi da amfani." "Let's go please." "Yes muje, dayar girlfriend din taka tana jiranka kar ta gaji da jira." Fasa abinda Aryan din yake shirin yi yayi, ya tsaya yana kallon Kamal din "Girlfriend kuma?" "Zaka ce baka gane duk moves din ta ba?" "Ya Allah, me ka maida ni me wai Kamal? Huh?" "Oho, muje madam dita tana jirana kar hakurin ta ya kare." "Kana da matsala." Yayi gaba kawai Kamal din ya bishi a baya yana murmushi,duk taurin kansa da ki fadin sa ba zai hana shi fada masa ba, da bakin sa ya furta yana son ta, kila lokacin a rikice yake ne, yayi subutar baki amma dai ko ma menene ya riga ya furta, kuma yaga komai a idon sa, kuma yana da yakinin sune zasu dawo da alakar Abby da Daddy da ta dade da watsewa, hakan yake fata shiyasa kuma ba zai taba hutawa ba sai yaga hakan ya tabbata.    Kamal ne yake driving din, Aryan na gefen sa, ita kuma tana baya daga side din Aryan din, dadi kamar zai kasheta yau gata ga shi a mota suna tafiya. Babu me magana a ciki sai radio da Kamal ya kunna kawai a kalla zata rage shirun motar. Direct gidan sa ya fara kai su, Aryan ya dube shi da sauri "Baka sauke Zainab ba?" "Ai nine a hanya oga, ka sauke ta a gida." Bud'e kofar yayi ya fito da sauri ya tare Kamal din "Ya zakayi min haka?" "Me nayi kuma?" "Ni ba zan iya kaita gida ba, ta sauka ta hau napep daga nan." "Kasan dai ba'a fiye samu ba anan." "Toh ka san yadda zakayi da ita ni zan hau napep din kawai." "A ah Aryan, ka taimaka dan Allah, mace ce fa." "Ita bata da kamun kai ne da zata zauna tana jira maza su kaita gida?" "Taimaka dai toh, kar Madam ta leko ta ganta ma ni na shiga uku." "Ka gama dani wallahi." Ya bud'e motar ya shiga, tayi saurin bud'e kofar bayan ta dawo gaba ta zauna. "Sai da safe." Kamal yace ya daga musu hannu yana boye dariyar sa "Ina ne unguwar?" "Naibawa." Be ce komai ba, ya maida hankalin sa akan tukin, tana ta satar kallon sa amma ya hade fuskar sa tamau sai uban sharara gudu yake kamar zasu tashi sama. "Sir hope ban takura maka ba." "Mm." Yace a gajarce "Ok thank you so much, nagode sosai." "Ok." Shiru tayi jin yadda ya amsa mata, duk sai tasha jinin jikinta bata sake magana ba, sai da aka zo sannan tace yayi, yayi parking ta sauka tana kokarin yi masa godiya ya fizgi motar kawai. ***Da farko Aryan ya dauka wasa Kamal yake masa da yace zai yi tafiya kuma yana so ya nemo shi, be dauki maganar tasa da gaske ba sam wallahi, dan be yi tunanin akwai in da Kamal din zai wani je ba. Kwana biyu kenan yana neman wayarsa amma a kashe take, sannan yaje har gidan sa shima baya nan dan gidan ma a datse yake har da padlock a gate din. Abubuwan ne suka tarar masa sosai sukayi masa mugan yawa, ga kula da daddy, ga aikin companyn su da yanzu babu wani tsayayye a wajen sannan ga nasa aikin da ya fara a office dinsa, yana ta kokarin tattare dukkan bayanan kafin ranar da za'a soma shiga kotun amma gani yake komai ya dagule masa musamman matsalar Daddy da rashin wanda zai tsayawa companyn nasu wanda dama shi da Kamal suke karfin aikin toh duk su biyun basa samun shiga ma bare su san ya ake ciki. Haka yake fama tsakanin asibiti da offices din duk ya sauya tamkar bashi ba, yana kuma kara jinjinawa Kamal namijin kokarin sa. He's very strong kuma very hardworking dan sai yanzu ya kara tabbatar wa. Kokari sosai ya dinga yi ganin yayi copying dinsa dan bazai yarda ya bashi kunya ba, zai yi abinda zai yaba yasan taraiyarsu tayi matukar amfani. ***KURA LGA*    Tana zaune a dakin bayan ta gama tattare shi ta gyara yar katifar tata da Malam Audi ya siyo mata bayan iftila'in kofar da ya same su kwanakin baya da ya cinye kusan komai na gidan har da kayan ta da take ta boyo da ajiyar su tsawon lokaci tana fatan watarana suyi mata amfani.   Dago labulen dakin akayi, Atika ce dauke da langa ta shigo ta ajiye a gefen katifar ta gaida ta sannan ta juya ta fita. Jim kad'an sai ga Zuwaira itama da samira a rufe tazo ta ajiye daga gefen wadda Atikan ta ajiye itama ta gaishe ta sannan ta fita. Wannan al'adar su mutanen karkara ce basu da matsala ta rowar abinci duk kuwa da basu da kaloli na abincicikan amma kuma suna dafa shi yadda ya kamata dan haka kuma ko bako akayi yazo ba'a san da zuwan sa ba zaka samu da abincin da za'a bashi ya ci. Tsawon zaman ta dasu basu taba fashin bata abinci ba kuma dukkansu haka suke jere mata abincin ko tace yayi yawa sai sun kawo dole sai dai taci ta rage amma dole ne kowa ta aiko mata idan ta gama daga na safe har na dare abincin har yawa yake mata amma babu fashi, sun dauke ta tamkar itace ta haifi majajen su duk wani girmamawa suna mata suna kuma mutumta ta sosai basu taba yin abinda zai bata mata rai ba. Aminene ce ta shigo daga karshe ita ma da nata kwanon ta ajiye sannan tace "Yau su zuwai sun riga innarmu sauke tukunya kenan, toh na kulin mu zaki fara shi Inna." "Na kulin mu dai, ai shine farko." Atika dake kofar dakin ta dago labulen ta fada "Inna namu zaki fara, yau nice nayi girkin kici kiji dadi." "Toh aminene, duk zanci ai na kowa, naji girkin Aminatuwa ko da dadi?" "Wallahi da dadi Inna, taliya ce yar murji wallahi." Atika ce ta kwashe da dariya "Yo har wani birgewa ce a dafa taliya yar murji?" "Ina laifi ko Inna?" "Ba laifi kam." "Inna da dai tuwo tayi ko shinkafa da miya ko dafaduka, amma taliya da manja ina wani wahala?" "Duk da haka dai nayi kokari, ke da kika dafa ranar nan ai chabewa tayi." "Ai ranar ne kawai shima dan an dan samu akasi ne." "Toh yanxu dai duk kunyi kokari, ku kara zage dantse kafin bad'i a mika ku gidan majajenku." Da sauri suka tashi suka fice cike da kunyar maganar Innan, murmushin tayi itama kawai dan tasan dama maganin musun nasu da anyi maganar aure sai su gudu. Abincin ta jawo gabanta ta bud'e sannan ta tashi ta wanko hannun ta ta dawo ta zauna tayi bismillah ta soma ci a hankali.   *RQ*      Page 30 ****Yana tsaye gaban mirror yana feshe jikinsa da turare yana dan duba gefen wuyan sa da yake ganin kamar ya fada sosai a yan kwanakin nan saboda rashin nutsuwa. Adam ne ya turo kofar ya shigo kamar me jan kafa sai dai yanayin sa ya nuna alamun yasha wani abun. Wani kallo Aryan ya bishi dashi har ya karaso ya tsaya daga gefen sa yana yage baki yayi wata doguwar hamma idanun sa da suka yi mugun kadawa sukayi ja ya zube su akan Aryan din. Saurin ja baya yayi jin warin giya sannan ya zaro ido cike da mamakin Adam din yace "Giya Adam?" "Manta da wannan, alfarma nazo nema a wajenki." "Alfarma?" Gid'a kan sa yayi "Kwarai, ka taimaka ka kaini naje naga Mom please, ka yi mun wannan alfarmar kwaya daya tak, nayi maka alkawarin baka wani bayani me matukar amfani a gareka." Murmushi Aryan yayi kawai, yayi masa kallon mara hankali sannan yace "Yanzu Adam akwai wani taimako da kake ganin zaka iya yi min kuma ba amince maka?" "Ka gane? Ka ajiye duk wannan aside muyi magana ta fahimta nayi alkawarin taimaka maka amma ina son sanin in da uwata take mana, haba mana ka tausaya mun ita kadai gareni." "Kai kana da ita ma, ni fa? Ina tawa? Wannan abinda kake nema a wajena ba hurumin ka bane ba, ka jira mu hadu a kotu kawai." "Ba zaka dai taimaka min ba kenan ko?" "Ba zan iya ba , babu wani abu wai shi taimako tsakani na dakai." "Shikenan, shikenan zamu gani." "Babu abinda zamu gani sai alkhairi. Na riga nayi latti already kazo kuma ka kara sani yin wani,." "Shikenan, ba damuwa zamu gamu ne." Jakar sa Aryan ya dauka ya saba a kafad'a ya nuna masa hanya alamar ya fita, yayi kwafa sannan ya fita shi kuma ya rufe kofar sa ya jefa key din a cikin aljihun sa yayi gaba da saurin sa dan abinda yake gaban sa yau yayi yawa gashi har lokacin na neman kubuce masa. ***Ana i gobe zatayi monthly clearance dinta ta shigo Kanon ita da Hamma Hydar. Gidan Addah Maimuna ta wuce shi kuma ya shiga sabgar gaban sa saboda dama akwai abinda yake da niyyar yi a Kanon gashi kuma dama Abby yace dole duk karshen wata su dinga rakota shi da Bobbo Sadeeq wanda dai yake available a lokacin. Kayan ta kawai ta ajiye suka fito tare da Amina ta rakata cafe tayi printing schedule dinta sannan tayi photocopy na clearance letter din ta hade su waje daya sannan suka dawo gida. Sake gwada dialing number Oga Kamal tayi amma still a kashe, tun kwana uku da suka wuce take kiran shi amma bata shiga a kashe, da farko ta dauko ko bashi da charge ne ko wani abun dai haka sai ta share kawai, amma ganin ta cigaba da kiran kuma still a kashen sai taji duk babu dadi, taga missed calls dinsa a ranar amma ko sanda taga missed calls din bayan wajen awa biyu da kiranta ne dan tana chan falo tare da Abbyn ta ranar ya dawo daga tafiyar da sukayi shi da Lamido da bata san ina ba, shiyasa ta makale masa ta ki barin sa hatta abinci tare suka ci. Dalilin da yasa ta damu ta cigaba da kiran nasa taji ko lafiya amma shiru. Yanke shawarar kawai ta biya gobe ta office din ta duba shi daga I'd card dinta yana chan ta barshi idan yaso sai ta dauka daga nan ta wuce kumbotson. Da wannan shawarar ta kwanta ta kuma tashi ta shirya cikin NYSC khaki dinta da suka sha guga ta saka wani farin sneakers me adon stones ta bar jacket din a bud'e ba tare da ta saka buttons din ba sa saboda ta dan matse ta, tayi rolling da white medium veil da ya kara haske farar fatarta sannan ta fito. Sune zaune dukkan su a falon lokacin karfe tara daidai Muhammad ya kura mata ido yana kallon ta cike da yabawa sai dai be yi magana ba, Amina ce ta hau yi mata tafi dan yau ne karon farko da taga tayi complete dressing din dan last month da taje clearance din bata san "Kin ganki kuwa Adda Raihana, wow." "Kai Aminatu banda sharri." "Dan Allah Mama batayi kyau ba." "Tayi mana, amma wannan mayafin be yi karami ba Raihana?" "A ah be yi ba Mama, haka ake sawa fa." Amina tace da sauri "Ko da yake jacket din da tsawon ta kuma." Adda Maimunan tace "Yawwa, Allah muma ya nuna mana sanda zamu saka kayan nan wai za'a ga yanga." "Sai kace kyau zasuyi miki." Muhammad yace yana hararar ya "Ai dama ko kowa zai ce nayi kyau ai banda kai Hamma, amma wallahi ni na san zan yi kyau." "Tafi chan, wata mummuna dake." Dariya suka kwashe dukka, ta zumburi baki tana hararar sa ta gefe, ita dai Raihana dariya kawai take yi "Adda na tafi, zan fara biyawa ta office dinmu na dauki I'd card dina sai na wuce,." "Toh sai kin dawo Raihana." "Muje na sauke ki kanwata." "Nagode Hamma." Gwalo Amina tayi masa ya jefa mata pillow da yake kan kujerar ta chafe tana dariya "Zan dawo zan kamaki ne yarinya. Da kanki kamar goriba a wajen." "Irin kanmu daya." Tace ta gudu da sauri ta shige ciki. Girgiza kai kawai yayi, yabi bayan Raihana da tuni ta fita yana jin sa ontop of za world. Da sauri ya karasa ya bud'e mata motar ta shiga ta zauna sannan ya dawo wajen zaman driver ya shiga ya zauna yana shak'ar kamshin turaren me sanyin kamshi. Kusan minti biyu suka dauka ya kasa tada motar dan wani irin feeling ne yaji yana shigar sa akanta, karo na farko da yaji wani abu ya darsu a ransa game da ita. Sai da ya daidaita nutsuwar sa sannan ya kunna motar bayan ya sakar mata murmushi, ya saita radio din motar ya kamo cool FM ya dan rage volume din sannan suka bar layin.     Duk da saurin da Aryan yake yi sai da ya makara sosai, bacci ne be yi da wuri ba jiya yana wani bincike shiyasa ya makara gashi akwai meeting din da zasuyi anjima da directocin companyn su dake wasu states din sannan zasu je su duba Daddy da jikinsa dan sai jiya suka samu labarin abinda ya faru daga bakin Aryan din dan duk kiran da suka yi masa bayan labarin ya bazu be dauka ba, dan bashi da nutsuwar da zai iya yi musu magana a lokacin. Har ya hau sama ya zauna a office ya manta da important files din na cikin mota, tsaki ya dan ja kad'an ya tashi da sauri ya sake fitowa ya sakko kasan daidai lokacin da motar Muhammad ta shigo compound din tayi parking a opposite motar sa. Da farko be lura da wadda ke cikin motar ba, sai bayan ya bud'e tasa motar ya dauki abinda zai dauka ya fito kawai idanun sa suka hango masa ita a gaban motar tana magana da wani handsome saurayi suna ta faman zabga murmushi. Wani das yaji gaban sa ya fadi, maganganun  da Kamal ya fada masa suka shiga yi masa bita aka _"Tana da saurayi."_   yaji muryar Kamal din kamar tayi masa rada a kunnen sa. Tsayawa yayi chak yana kallon su ya ma manta shaf da abinda ya kawo shi wajen, Muhammad ne ya fito da sauri ya zagayo ya bud'e mata kofar sannan ya ware hannuwan sa alamun bismillah sukayi dariya a tare, muryar ta, ta shiga cikin kansa sanda tace "Kana da abin dariya Hamma." "Honey?" Kunnen sa kawai yaji tace ba Hamma ba, ji yayi kamar ya karasa ya same su ya faffalla musu mari a wajen da suke tsaye. Daga masa hannu tayi yayi reverse ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya tana jin kamar be dace ace tazo ba, kamar bata da zuciya ita kuwa? Korar kare fa Aryan yayi mata Amma shine ta zo? Wata zuciyar ce tace mata ai bashi kika zo gani ba, kuma Kamal yayi miki halacci babu laifi dan kin tabbatar da lafiyar sa. Da wannan shawarar ta amince ta nufi building din kanta tsaye duk kuwa da wani abu me kamar tsoro tsoro yana neman dakushe ta. Bayanta yabi kawai ganin ta wuce ba tare da ta lura dashi ba. Tana shiga su Zainab suka yo mata cha da ido, ta gaishe su normal kamar babu komai sannan ta yi hanyar office dinsu dan ta fara daukar I'd card din nata kar ta manta. Babu kowa a office din nasu ta bud'e drawer ta, ta hau duba I'd card din a in da take zaton ta ajiye shi, sai dai baya nan ta sake dubawa sosai tana cikin dubawa Abdulhakeem ya shigo suka gaisa sannan ta tambaye shi ko sun ga I'd card din ta "Kamar yana wajen oga Aryan gaskiya, saboda ranar Abdallah ya ganshi sai ya dauka ya kai masa." "Innalillahi, ai da kun ajiye min a wajen KU." "Ai yazo ma, kije kawai ki karba a wajen sa" "Ba karbar bace ba ai, ta ina ma zan fara shiga office dinsa?" "Ba zaki iya zuwa ki karba ba wai?" "Gaskia, gashi LGI dinmu idan babu I'd card din nan ba zai maka clearance ba" "Ba dai Tanko bani ba? Shine LGI din naku ko?" "Shine." "Wai, ai kuwa idan kina son kanki da arziki kije ki karba gaskiya, in ba haka ba zaki samu matsala." "Toh ka taimaka ka karbo min dan Allah, zanje na gaishe da Oga KAMAL idan na fito sai na karba na tafi." "Oga Kamal ai yayi tafiya, baya nan wallahi." "Haba dai? Ina ta neman wayar sa bata shiga." "Wallahi baya nan kuwa.' "Toh ko baya k'asar ne?" "Eh toh, watakila dai, babu wanda yasan ina yaje a cikin mu gaskiya." "Toh da sauki ai, dama na dauka ko ba lafiya ne naga ina ta kiran sa switch off, tunda tafiya yayi toh alhamdulillah, yanzu ka taimaka ka karbo min I'd card din ina jiranka dan Allah." "Ok bari naje." "Yawwa nagode." Ta zauna sosai shi kuma ya fita. Aryan na zaune yaji an kwankwasa yayi saurin kallon kofar a tunanin sa itace, come in yace yana sauke kansa sai kuma ya sake dagowa jin Abdulhakeem ne "Ya akayi?" "Sir dama sister Raihana ce tace nazo na karbar mata I'd card dinta." "Wacece?" Ya fada kamar be gane ba "Wannan corper din sir." "Kace tazo ta karba da kanta." Ya maida kansa kan aikin da yake yi. Juyawa Abdulhakeem din yayi ya sameta a office din ya fada mata abinda Aryan din yace "Na shiga uku, dan Allah yanzu be baka ba? Wallahi bana son zuwa." "Wai laifi kika yi masa ne hala?" "Ba komai, ba zaka gane ba." "Gwara kije da kanki, ba zai bayar ba wallahi." "Kai innalillahi." Ta mike jiki a sanyaye ta fito. Da sauri Zainab ta tashi ta tare ta. "Karki shiga office din Oga Aryan." "Akan me?" "Saboda yace kar wanda ya shiga yana busy ne." "Ni kuma shi yake kirana, please karki bata min lokaci ina sauri ne." "Bakar mayya." Zainab din tace taja wani irin dogon tsaki. Sarai ta jita amma sai ta kyale ta kawai ta barta tsaye da bakin ciki. Kamar kirjinta zai fado haka ta sa hannu ta kwankwasa a hankali sannan ta tura bakin ta dauke da sallama tayi kokarin daidaita kanta da nutsuwar ta. Ta kasan idon sa ya hange ta, ta shigo ya yi kamar be ji shigowar ta ba, ya dai amsa sallamar tata a ciki ciki yanda ba zata ji ba. A bud'e ta bar kofar ta tsaya daga wajen kofar ba tare da ta shigo ciki ba tace " I'd card dina da na manta nazo dauka." Yadda tayi maganar a dunkule ya sashi daina abinda yake ya dago idanun su, suka sarke da juna, ita ta fara janye nata da sauri ta dauke kanta gefe. "Close the door please." Juyawa tayi ta rufe kofar amma ba ruf ba, ta cigaba da tsayawa a jikin kofar fuskar ta ba fara'a. "Baki iya gaisuwa ba?" _"Eh ban iya ba."_ Ta fada a cikin zuciyar ta, Amma a fili sai ta fuske kamar bata ji me yace ba. "Me kika ce kika zo dauka?" "Identity Card." "Shine zaki aiko min wani? Ba zaki zo da kanki ba.?" "sauri nake ne." Kallon ta yake tunda suka soma maganar amma ita sam gefe take kallo. Mamakin ta yake sosai kenan fushi take dashi shine ta aiko wani ba zata iya zuwa ba, ko da yake shi yace mata baya son sake ganin ta, kila shiyasa ta aiko din amma kuma ganin da yayi mata a yanzu yasa shi karyata kansa da kansa da abinda yace din a lokacin, tabbas ba har zuciyar sa bane ba, a yanzu da yake cikin irin wannan yanayin yana bukatar ta, amma ta yaya zai fara gaya mata hakan? Taya zai yi sakata ta yafe masa abinda ya fada a bacin rai ta dawo su cigaba da aikin? He need her more than ever, ya tabbatar aikin zai fi tafiya masa daidai idan tana kusa dashi.    Mikewa yayi daga wajen da yake zaune, ya shiga takowa zuwa gaban ta, ya tsaya daga gefen da ta karkatar ta fuskar ta, kin kallon sa tayi kemaimai ta maida kan dayan side din ya sake biyo ta. "Fushi kike dani?" Ya samu kansa da tambayar ta. Kin amsawa tayi ya sake maimaitawa "I'm sorry toh." "Sir please zan makara, Kumbutso zan tafi clearance." Ta fada kanta tsaye tana jin wani sabon confidence musamman da ta jiyo sautin tausasawa a kalaman sa. "Please kiyi hakuri, nasan na bata miki rai amma kiyi hakuri." "Please sir zan makara." Kofar ya kalla sannan ya kalle ta, ya matsa jikin kofar kawai taji ya murda key, ya zare key din daga jiki ya juya ya koma wajen zaman sa ya zauna ya barta a tsaye a wajen cikin tsananin mamakin sa. *RQ*     Page 31 ***Cigaba da tsaiwa tayi a wajen shi kuma ya cigaba da abinda yake yi kamar babu mutum a wajen. Sosai ta shak'a ta cika ta hau ranta yayi mugun baci. Gaba daya ta gama lura da Aryan mugun dan rainin hankali ne. Abinda yayi niyya shi yake yi, kuma shi zaka yi masa magana ya share ka amma shi be yarda yayi maka kaki amsa masa ba. Cigaba da tsaiwar tayi har kusan goma da rabi ganin bashi da niyyar bata yasa ta bud'e baki tace "Sir zan makara dan Allah." "Hello." Ya daga waya ba tare da ya amsa mata ba. Wasu hawayen bakin ciki ne suka shiga sakko mata ta juyar da fuskarta ta goge su zuciyar ta na tafarfasa. Ya dan jima yana amsa wayar yana satar kallon ta kad'an kad'an har ya gama. Ya mike rike da wayar sa a hannu sai wallet din sa da I'd card din nata yake ciki. "Idan kin gama tsaiwar muje." Yace sanda ya isa gaban kofar ya bud'e yayi waje. Wani takaici ne ya sake turnike ta, tabi bayan sa a sanyaye. A reception ya tsaya suna magana da Zainab tazo ta gota su kawai ta fice daga wajen. Tsayawa da maganar da yake yayi, sai ya sauke kansa ya karasa yi mata bayanin da yake mata sannan yabi bayan Raihanan. Har ta fita gate din yayi saurin kunna motar shi yabi bayan ta, ya tarar da ita tana tsaye gefen titin da alama napep take jira. A gabanta yayi parking ya sauke glass din sannan yace mata "Shigo muje." Dauke kanta tayi daga kallon bangaren sa, ta saka hannu ta tsaida napep. Da sauri ya balle murfin motar ya fito ya saka hannu ya tare "Oga rabu da ita tare muke." Yace ma me napep din, dariya ya kwashe da yace "Gaskiya ne oga, ai na gane yaren." "Hajjaju kar kiyi saki reshe fa, irin yallabai wahalar samu suke duk sai ire-iren mu ne suka rage." Banzan kallo tayi masa, ya sake fashewa da dariya ya tada napep dinsa ya wuce yana dagawa Aryan din hannu "Kina sake bata lokaci ne." Yace mata yana nuna mata hanyar motar, hawayen da ya zubo mata ta share ba tare da tayi magana ba, ta wuce ta bud'e motar ta shiga saboda makarar da tayi. Shigowa yayi ya daura seat belt ganin tana hawaye ya ciro tissue daga saman gaban motar ya dora mata akan cinyar ta sannan ya tada motar. Tafiya suke tamkar kurame babu wanda yayi magana da dan uwan sa, kanta na kallon window tunda suka soma tafiyar shi kuma nasa na kallon hanya. Hamma Hydar ne ya kirata ta d'aga. "Kina ina? Gani a kofar wajen naku." "Yanzu nake tahowa hamma." "Yanzu? Ya akayi haka?" "Eh nayi mantuwa ne shine abinda yasa." "Ok, sai kun karaso ina jiranki." "Ok tam." "Hydar ne?" Ya tambaya "Umm." "Ok." Ya cigaba da abinda yake yi. Sake juyar da kanta ta cigaba da yi har suka karaso garin na Kumbutso. "Kinyi printing out schedule dinki?" Ya tambaya suna isowa daidai wani cafe "Umm." Ta sake bashi amsa a takaice. Be sake magana ba ya shiga kwanar da zata kaisu wajen, tayi mamakin ganin yasan wajen tunda ba wai ya tambaye ta bane ba. Motar Hamman ta, ta hango a karkashin wata bishiya. "Ya isa nan." Tace dan bata so ya karasa wajen Hamman. Banza yayi mata ya cigaba da tafiya har sai da yaje daidai gefen motar da Haydar din ke ciki shi da wani abokin sa sannan yayi parking ya kashe motar. Ranta a bace ta kama kofar zata fita ya ciro I'd card din ya dora mata a kan kafarta sannan ya bud'e kofar ya fita. Fitowa Hydar yayi dan tun daga shigowar su harabar wajen har zuwa parking din da yayi a kusa dasu yana kallon su. Da sauri ta wuce dan taga irin kallon da Hamma Hydar din yake mata. Hannu Aryan ya bashi sukayi musabiha sannan yace "Dama tare kuke?" Daga mishi kai yayi "Yes, ko nayi laifi ne?" "Kayi, ba hurumin ka bane kawo kanwata wajen nan, akan me ma zata shiga motar ka?" "Point of correction, kanwar mu dai." "Ko?" "Yes, kai ma ka sani ai, yadda take kanwarka nima tawa ce." "Da kenan banda yanzu, dan Allah Aryan don't drag Raihana into this, she's innocent shiyasa duk abinda yake faruwa ma bata sani ba, bama son duk abinda zai bata mata rai please dan Allah ka fita daga rayuwar ta." "Me kake tsoro?" "Komai ma, duk abinda zai faru ya tsaya iya tsakanin mu, amma banda ita." "Don't be selfish mana Hydar, menene laifi na dan Allah?" "Kai ma ka sani, mu bar wannan maganar tunda ba shine ya kawo mu ba, maganar kanwata ne kuma ina fatan zaka ja baya daga gareta." Murmushi yayi me taushi sannan yace "Hydar kenan, kana kara zugani ne wallahi, ina kuma wani tunani akan hakan, kuma zanyi trying luck dina, kaga karshe sai na zama sirikin ka kenan." "Allah ya kiyaye, kamar bamu da tunani ko hankali?" "Ya zakayi da innocent heart din ta toh? Idan tayi falling mun?" "Ba ma zai taba yiwuwa ba, never mu sake wata alaka tsakanin mu, ba ni ba, ko Abby ba zai yarda ba wallahi, bare Lamido da Sadeeq, it's over kawai tunda ka samu abinda kake so daga wajen Abby shikenan, babu sauran wata alaka tsakanin mu." Murmushi kawai yayi, duk kuwa da maganar ta dake shi sosai, amma sai ya nuna be ji komai ba. "Hamma yace wai na makara ba zai min clearance din ba sai anjima." Ta karaso wajen nasu tana fada, abinda ya hana Aryan fadar abinda yayi niyya sai ya juya akalar maganar zuwa wajen ta "Muje zai barki." Yace yana kallon ta, kallon Hamma Hydar tayi taga shima ita yake kallo, sai kawai ta juya Aryan din yabi bayanta. A kofar shiga wajen ta tsaya yazo ya wuce ta, tabi bayan sa. "Wa nake gani?" "Ni ne Oga." "Lallai yau nayi babban kamo, oga kai ne a tsangayar tamu haka da tsakar rana?" LGI Tanko yace yana mikewa, ya bashi kujera ya zauna sannan suka gaisa "Kwana biyu oga, Ka buya." "Wallahi abubuwan ne suka yi yawa Oga T, ya aiki ya fama da students." "Alhamdulillah wallahi, gamu nan muna lallabawa, tunda kunki saka mu a harkar mai." "Haba Oga ai ku manya ne." "A ah ina fa, yara dai." "My wife to be na kawo clearance Oga." "Are you serious, tana ina? Kace dai bana oga zai motsa, dama inaga kaf class din mu kaine kadai ka rage." Murmushi Aryan yayi kawai, ya waigo wajen da Raihana take tsaye kamar munafuka yace ta matso "Madam sannu da zuwa, bismillah zauna mana.". Yace yana nuna mata kujerar da take kallon ta Aryan din. Kalmar Madam din ce tayi mugun daure mata kai, yanzu yanzu fa ta shigo ya kora ta, shine yanzu har da bata seat da kiran ta madam, me Aryan din yace masa hala? "Ina takardun naki." "Gasu sir." Ta mika masa kanta a k'asa. Karba yayi ya ajiye yace tasa hannun ta tayi thumbprint, tasa yayi yace shikenan. "An gama?" "Eh shikenan oga, har an gama." "Ok, godiya nake oga, sai mun shigo wani watan in sha Allah." Ya mike tsaye "Allah ya kaimu, idan an saka bikin saura ka manta kaki sanar min, ko da yake nine me baka auren ma tunda dai amaryar tamu ce." "In sha Allah. Thank you so much sir, a huta lafiya.' "Yawwa, ku gaida gida." "Aure zaiyi kenan?" Ta raya a ranta. Tabe baki tayi suke fito daga wajen. A wajen motar suka samu su Hydar a tsaye suna jiransu "Har anyi?" Hydar yace mata QTace tayi saurin bud'e motar su ta fada baya dan ma kar Aryan din yace ta shiga motar sa "Zan wuce Hydar, sai yaushe?" "Ba rana." Ya fada yayi saurin shiga mota "Sai gani na uku, watakila a kano watakila kuma idan na zo har gidan wajen Abby." "Muje khalifa." Kawai yace dan sarai ya lura Aryan din so yake ya rama abinda yayi masa ranar nan. Matsawa gefe Aryan yayi suka tada motar suka bar wajen yana kallon su. A nutse ya karasa wajen tasa motar ya shiga shima ya bar wajen. Suna gaban sa yana bayan su har suka shigo Kano, hanyar bypass suka dauka shi kuma yayi naibawa saboda yana so ya shiga asibitin Malam. Yana gate din asibitin Ya Nabeela ta kirashi tace masa Daddy ya farka ya kara sauri ya isa, ya same shi idon sa a bud'e sai dai baya magana. Tunda Aryan ya shigo yake hawaye, yana ta kokarin yin magana amma ya kasa. Ganin ya matsa sosai yasa Aryan kiran Dr ya fito waje ya bar su a ciki. Ya hangi tsantsar nadama da dana sanin a idon Daddyn wanda dama abinda yayi ta gudar masa kenan, abin takaici hatta yan uwansa sai da Hajiya Zeenat ta raba shi dasu, su kuma dangin Mommy sukayi fushi dasu babu ruwansu da yaran tsakanin su sai ta kure tun wani zuwa da sukayi ganin su Aryan din Daddyn yayi musu cin mutunci tas sai suka bar masa yaransa shiyasa suka zama basu da kowa sai kansu su suke komai da kansu. Abinda Hydar ya kasa fuskanta kenan, da su da sukayi rayuwa tare da mahaifin su dasu da sukayi rayuwa babu, basu da wani banbanci domin babu wani amfani da zasu iya nunawa da ya amfanar musu sai ma rayuwar kunci da ya sanya su duk ta dalilin biyewa mace da kaidin ta. ***Fada sosai Hydar ya rufe Raihana dashi tunda suka dauki hanya yake ta banbamin masifa, ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, tun farko ma akan me yasa zata je office din har kuma ta yarda ta shigo motar Aryan din tun daga cikin gari har kumbotso. "Abinda kike aikatawa kenan da babu idon mu kenan." Ya karkare yana juyowa bayan. Kuka take dan zata iya rantsewa irin wannan fadan be taba hada ta da Hamman ta ba, duk da zafin zuciyar da yake da ita amma baya mata, basa taba mata fada duk abinda zatayi sai dai idan batayi daidai ba suyi mata ta sigar lallami amma sai gashi yau Hamman ta har buga dashboard yake saboda tsabar masifa. "Abinda kike aikatawa kenan ko? Ina tambayar ki." "Haba Hydar, yi mata a hankali mana,." "Ba zaka gane ba Khalifa, bana son alakar ta da Aryan ko kadan, ba ta yadda za'a yi mu zura ido tarihi ya maimaita kansa, ina ba zai yiwu ba gaskiya." "Na sani, amma menene amfanin fadan haka? Na tabbata a ba yadda zatayi ta shiga motar sa, ina ganin duk abinda zatayi kawai ku dinga tsayawa kuna shige mata gaba saboda gudun faruwar irin haka." "Munayi ai, me ya kawo ni Kano a wannan lokacin idan ba dalilin ta ba, sai da fa nace ta jirani zan zo na kaita da safe tace zata iya zuwa da kanta, mukayi da ita zamu hadu a chan sai mu taho tare saboda wannan fitar da mukayi da sasassafe, amma kana gani har mukaje bata zo ba." "Kayi hakuri dan Allah Hamma, wallahi I'd card dina na manta a office din shine naje karba be bani ba yace muje, wallahi har gate muka zo dashi na tsaida me napep ya hana shi daukata." "Ahaap, ai na fada maka ba lallai idan laifin ta bane ba, kazo kana ta fada haka." "Toh naji, wannan ya zama na karshe da hakan zata faru." "In sha Allah ba zan sake ba." Jikin sa ne kuma yayi sanyi, duk sai yaji babu dadi fadan da yayi mata "Ya isa toh kukan haka, ya isa." Share hawayen take kokarin yi amma yaki tsayawa, babu abinda yafi ciwo ace wanda be saba maka fada ba yayi maka rana daya, yafi komai kona rai. Kwana biyu tsakani suka koma Adamawa sai kuma wani karshen watan. Suna zuwa Hydar ya kwashe komai ya sanarwa Abby abinda yake faruwa tun farkon haduwar sa da Aryan har zuwa wannan karon, ran Abby ne ya baci ya kirawo Raihanan tana daki a kwance ta samu sakon kiran nasa, ta dauka ma wani abun ne sai dai tana zuwa Abbyn ya hau fada, ya dinga mata fada musamman akan shiga motar Aryan din da tayi. Sosai jikin ta ya dinga rawa tana durkushe yana fadan "Ya kyautu yau kiyi alaka da mutanen da suka tura mahaifin ki prison tun kina yar karama uhm? Ya dace kuwa?" Girgiza kai tayi da sauri dan ko ta bud'e bakin ta ma ba zata iya magana ba sai dai kuka ya biyo "Toh bana so, abinda ya faru ya riga ya faru kuma ko a yanzu sun girbi abinda suka shuka, duk da shi Muhd bashi da laifi ko kad'an amma babu wata alaka tsakanin iyalinsa da nawa, kowa yaji da kansa bana so." "In sha Allah ba zan sake ba." "Yawwa, Allah yayi miki albarka." "Amin." Tace ta tashi fuskar ta a dukunkune ta fice. Tana shiga falo Daadah ta rikota, kawai ta sake fashewa da kuka da karfi. "Na shiga uku ni salamaatu, me ya faru?" "Laifi tayi Dadah, ta shiga motar Aryan har ya kaita clearance." "Duk akan wannan maganar ce bata mutu ba ni Hajara? Akan me zaku matsa wa yarinya ne wai? Menene laifin ta, soyayya suke yi? Yau ace ma idan soyayya suke yi menene a ciki? Baku yarda da kaddara bane ko me? Eh? Ko zaku ja da hukuncin Allah? Idan ma haka ba, wai Aliyu idan Raihana bata samu saurayi me sonta ba, shin kune zaku aure ta ne wai? Ko zama zatayi tayi a gida kuna kallon ta eh?" "Baki fuskanta bane Daadah, bafa hanata kula kowa akayi ba, Aryan din ne dai, tayaya Abby zai dauki Raihana ya kaita gidan nan tayi rayuwa?" "Sai me toh? Dan tayi." "Kayya, Dadah karki manta fa abinda ya faru, karki manta." "Ban manta ba sarai, kuma bana daga cikin marasa yarda da kaddara, dan haka ba zan hana abinda Allah ya yi ba, kuma na tambaye ta ko Yaron nan yace yana son ta, tace a ah be ce ba, menene abun tada jijiyoyin wuya fisabillillah?" "Haka tace? Wallahi ni dashi yace min yana sonta, ido da ido kuma ba wai a waya ba." Saurin zabura Raihana tayi, ta kalli Hydar da sauri shima kuma ita yake kallo "Kwarai da gaske, kuma ko da be furta ba ai action dinsa ya fada, ni namiji ne duk nasan irin wannan abubuwan." "Na shiga uku." Tace da sauri ta ruga ta shiga dakin ta, hannun ta a saman kirjinta saboda yadda ya buga da karfi. "Yanzu dai sai ku bar yarinya ta sarara dan Allah, tunda da alamu duk ma abinda kuke tunani da zato ita bata ma sani ba, amma kunzo kuna mata fada akan me?" "Daadah please ki gane mana." "Naki na gane din, kai ba kwanan nan aka je aka tambayo maka aure ba, duk ba auren zakuyi ba kuma ma rana daya? A bar min yarinya ya shaki iskar yanci dan Allah, idan ba haka ba wallahi zamu saka kafar wando daya da duk wanda zai takura mata. Ba ku kuka tura ta Kanon ba, da kunsan da haka?" "Allah ya huci zuciyar ki toh." "Amin, ka gayawa Abban naku nace bana so, atoh." Dakin tabi Raihanan shi kuma ya kada kansa kawai ya fice. *RQ* 32 ***A kwance ta sameta tana kuka,ta zauna gefen ta "Kina so kanki yayi ciwo ne? Toh ki daina kukan nan haka, babu ne takura miki a gidan nan, idan ma soyayya kuke ai ba haramun bane ba." "Ni ba soyayya muke ba Dadah, ni bana son shi ya fiye masifa da fada." "Toh ba shikenan ba? Tunda kinsan haka sai daina kukan haka nan, suma duk neman rigima ce tasu, ai ba haramun bane ba, kuma kowa ba da KADDARAR sa ba ?" "Duk yasa kowa yana mun fada, Abby na ma be taba min fada ba sai yau, ga Hamma na Hydar shima tun a kano yake ta min fada, nima duk abinda basa so bana son shi." "Toh ai shikenan, sai ki tashi kije ki wanko fuskar nan, kizo mu fita yau chan gida zamu,sai dare zamu dawo naga me dafa musu abinci kuma." "Dadah fushi kikayi dasu?" "Eh mana, akan me zasu takura miki akan abinda ke ba shine ma a ranki ba? Bar su munyi fushi sai sun zo biko." "Waye zai kaimu toh?" "Ba zamu hau motar kowa ba, gwara ma Sadeeq idan yana nan,shi babu ruwan sa da wannan fi'ilin nasu, kira shi ma idan yana kusa yazo ya kaimu yau chan zamu wuni ki shiga cikin yan uwanki kuyi hirar zumunci ba ko da yaushe kina kunshe a daka ba daga ke sai basawan yayyan ki wanda basa son gaskiya, ko wa zai ganki yace yana so suna kaf kaf dake? Yadda suke manyan tuzurai haka suke so ki zauna kema saboda rashin gaskiya" "Kai Daadah,yau su Hamma sun tsokanawa kansu." "Dama fa a wuya nake dasu Allah, dole fa sai kin fita wani zai gani ya kyasa, ko a dangi ko a gari, amma duk inda zaki suna biye dake wannan ai kamar ma kashe kasuwa ne." Dariya ta fashe da, Dadah tayi tsut da fuska dan ita har zuciyar ta da gaske take, dole a sake sabon zama lokaci yana tafiya su bar yarinya ta sarara. "Bafa wasa nake ba kike dariya, da gaske nake kuma wannan karon dole a sake lissafi, ni da zai yiwu duk a hade ku dasu a sha biki wallahi." "Ashe kin gaji da gani na Daadah na?" "Yo ko na gaji dake ko ban gaji dake ba Raihanatu ke fa 'ya mace ce, gidan wani zaki kuma dole." "Ai shikenan tunda neman head kike dani, dama kin daina so na kwata-kwata." "Soyayyar ce ta jawo ai, dan haka ki tsaida hankalin ki waje daya kina jina? Ki bawa masu son ki dama ku daidaita, babu wanda lokaci yake jira su bar ganin kina da wannan jar kalar namiji da kin wuce lokacin ki zai daina ta taki." "Wannan maganar dai a barta sai next time Dadah, bari na wanko fuskar mu tafi." "Kyaji dashi, yi sauri kafin azahar tayi su shigo neman abinci, sun ga tsiya yau. Shima Abban naku aure ya dace dashi,sai na koma nima cikin yan uwana." "Ai ko aure Abby zai ba in da zaki Dadah, nan ne gidan ki,." "Sai dai ki tafi dani naki gidan idan an miki auren ke, amma ba zan zauna ba." "Ni ai muna jone Dadah, kafata kafarki ba wani da zai raba mu." "Karya, irin ku ne da an kaiku sai aji luf an samu gidan miji anyi shiru, wata tara a ishemu da kukan jinjiri." "Bari na dai wanko fuskar tawa Dadah." Tace da sauri ta shige toilet din dan ta lura yau Daadan a sama take neman rikici take da kowa. Fita tayi ta ja mata kofar tana sababi. ***Adam na tsaye a jikin stairs yana jiran fitowar Aryan sai gashi ya fito da dan saurin sa. "Lafiya?" "Yes, naji kana waya yau za'a kai mom kotu, so nake naji gaskiyar maganar." "Eh yanzu haka ma chan zani, kotun dake Normansland." "Why are you doing this?" "Wai tambaya ta kake?" "Yes, menene yasa kake son ganin bayana." "Bayan ka? Ina bayan? Kasan me kake cewa kuwa? Who are you by the way ma?" "Ba ta kai nake ba dan Allah Adam, kazo kotu sai kaji duk charges din da yake kanta, sai kasan irin maganar da zakayi." "Ba zaka taba succeeding ba in sha Allahu, heartless human being." Murmushi kawai Aryan yayi ya wuce ya bar shi a wajen, yasan ba a hayyacin sa yake ba, shiyasa ma ba zai biye masa ba, dan yana da abun yi, daga kotun wani kauye zai wuce wanda ya samu labarin Hajiya Zeenat din ta taba kai wa wani mutum ziyara garin. Shi zai je ya gani dan yana da yakinin akwai wani abu da ya sani game da ita. ***Sune tsaye a gaban kotun aka shigo da ita, tayi masifar sauyawa tamkar ba ita ba, hayaniya ce ta kaure a cikin kotun kowa yana kokarin tofa albarkacin bakin sa, masu daukar hoto na dauka a boye. Alkaliyar da zata saurari karar ce tayi calling attention din mutane aka samu wajen yayi shiru, sannan aka soma sauraran karar ta bakin lauyan gwamnati tare da Aryan. Bayan an karanto mata dukkan laifukan ta, ta kuma musanta, sai justice Fatima ta bada umarnin aike wa da ita gidan dan kande sannan an d'age sauraran karar zuwa sati biyu masu zuwa in da za'a dawo a fara gabatar da shaidu. Da sauri Adam ya mike daga in da yake tsaye yayi wajen ta, akayi saurin tare shi ya hau ihu yana zagin Aryan aka samu aka fitar dashi daga kotun sannan itama aka fice da ita ta kofar baya. Aryan na tsaye tare da wasu manyan barrister message ne ya shigo wayar, tun kafin ya bude yasan waye ya turo message din dan tun jiya ya fara aike masa da sakon akan shari'ar yana kuma kokarin kara masa kwarin guiwa akan abinda yake gaban shi, dan shine ma ya tura masa address din mutumin da kauyan da yake zaune kuma zai je ya ganshi dan so suke a sati biyun nan su karasa tattara duk shaidar da suke bukata "I'm proud of you.KM." Murmushi yayi kawai ya kashe wayar ya maida ita aljihu, sannan sukayi sallama ya fito daga cikin kotun. Habeeb ya hanga tsaye jikin motar sa, ya karasa yana duban shi da mamaki "Barka da rana Sir." "Ina ka shiga wai Habeeb?" "Na danyi tafiya ne. Amma na dawo yanzu zamu cigaba in sha Allah." "Ya akayi kasan ina nan?" Ya tambaye shi da mamaki sosai "Oga Kamal ne ya sanar dani." "Kaima cikin su kake ko?" "Na'am?" "I know, dama tun farko ban yarda ba, nasan akwai wani abu dole, baka yi mun kama da driver ba, lallai Kamal, akwai tarin abubuwa game dashi da ban sani ba." "Haka aikin yake sir, mu cigaba da tafiya a yadda muka faro, dan Hajiya Zeenat ba ita kadai bace a wannan tafiyar ba, tana da support kuma suna kokarin duk yadda zasuyi su dakile ka, muna cigaba da bincike a kansu amma dai for now kana bukatar tsaro." "Allah ya kyauta, muje toh." Ya mika masa key din, ya bud'e masa kofar ya zauna sannan ya zagaya shima ya zauna a mazaunin driver sannan ya kunna motar. ***A rana irin ta yau tarihi ya maimaita kansa, kamar yadda a irin wannan ranar Hajiya Zeenat take cike da murnar tura Abby prison sai gashi a yau an nufi gate din da ita. Hankalin ta ne ya tashi ta shiga tuno makamanciyar ranar. Goron dutse prison aka kai ta ita, ana zuwa aka tura ta prison 1 (welcoming prison) In da ake ajiye duk wanda ya shigo prison din a ranar kafin gobe a rarraba kowa prison din da ya dace da shi. Abby na zaune yana kallon komai da yake faruwa ta cikin wayar sa, duk da akwai sauran zama a shari'ar amma ko a yanzu hakan burin sa ya cika, idan komai ya dawo normal zai yi kokarin sake nesanta kansa da wani abu da zai iya hada su da Alhaji Mukaddas, baya ko bukatar ganin sa shiyasa ma ko zuwa be yi ya duba shi ba, haka ranar da aka kama Hajiya Zeenat din be ko bi ta kansa ba bare ya nemi ganin sa duk kuwa da ya samu labarin yana cikin matukar wahala. Lamido ne ya shigo ya zaune a gefen sa, ya kalle shi sannan ya ajiye wayar "Kaga komai Abby?" "Na gani, ko a yanzu buri na ya gama cika, matsala daya ce nake tsoron ta, Aliyu ya bani labarin alakar kanwarku da Aryan, ni kuma gaskiya ba zan amince ba, ba zan yadda ba, babu wata sauran alaka tsakaninmu da mutanen nan,." "Hydar din ya fada min nima, kuma in sha Allah babu abinda zai faru, Raihana yarinya ce me biyayya ba zata taba son abinda bama so ba." "In sha Allahu, ya isa hakan alakar da akayi a baya ta rashin sani ta wadatar,." "In sha Allah." "Yaushe zaka tafi wajen aikin ne?" "Karshen satin nan zan tafi, ina dan karasa hada abubuwan da zan bukata a chan ne." "Ok Allah ya taimaka ya bada sa'a, dama case din nan da kuke kai ya hana ayi muku transfer din tuntuni." "Eh shine yasa." "Ok, Allah yayi riko da hannayen ku, ya taimaka muku ya tsare ku a duk in da kuke." "Amin Abby." "Sai a fara maganar saka rana, zaman ya isa haka nan, ni ba mace kuma babu, dan haka dole ayi abinda ya dace." Sosa kansa yayi "In sha Allah." "Madallah. Bari na dan shiga ciki na kishingida ko zan dan samu bacci kafin la'asar, idan Sadeeq ya dawo kace inason ganin shi." "Ok a huta lafiya." "Allah yasa." *** *RQ* Page 33 ©️Hafsat Rano ***Tafiya kilometres hamsin da hudu ta kaisu garin na Rano, karon farko da Aryan ya taba zuwa garin duk da yana samun labarin cigaban da suka samu sosai ta fannoni daban daban musamman bangaren ilimin zamani da kuma kasuwanci da yan garin suka rike na man petrol, gas da kerosene. Sun kafu sosai akan harkar kuma suna samun arziki sosai dan tun daga kofar garin zaka tabbatar da hakan ganin tsarin gine-gine masu matukar kyau da suka zagaye garin ga wasu manyan duwatsu da suke karawa garin kyau da tsari. Akwai abokan Daddy sosai da suke harkar m ai a garin wasu suna haduwa idan an tashi taro ko kuma wani abun ya hada. Rage gudun motar Habeeb yayi sanda suka karaso kofar asibitin garin yayi parking bisa umarnin Aryan din sannan. Da kansa ya fito ya samu wasu mutane a zaune ya gaishe su sannan ya tambaye su in da zasu bi su je layin gidan sarki. Kwatance sukayi masa yadda zai gane yayi musu godiya ya koma mota ya nunawa Habeeb in da zasuyi, suka daga musu hannu suka wuce. Kasancewar karamin gari kowa ya san kowa basu wani sha wahalar gano gidan ba, maimaita sunan mutumin Aryan yayi, yayi daidai da sunan mahaifin Kamal, amma duk da haka be kawo komai ba, ya dauka kawai coincidence ne sunan yazo daya. A kofar gidan sukayi parking ya kalli layin me dan fadi ya hango wani dattijo a zaune a kan wata tabarma gaban wani dan karamin masallaci tare da wasu a zaune a gaban sa kamar suna daukar karatu, bayan su babu kowa a layin sai yan wasu yara suna wasan taya suma daga wani gefen. "Mu karasa wajen mutanen chan Habeeb." "Ok." Yace ya kashe motar suka fito suka nufi masallacin. Zuwan su wajen ya saka dattijon katse karatun da yake na littafin sunanin nabiy da yake karantar da manyan unguwar duk bayan sallar la'asar har zuwa magriba sannan suyi karatun alkurani me girma bayan magriba din zuwa Isha, daga nan sai su hadu suci tuwon dare har zuwa karfe taran dare sai kowa ya shige gida sai kuma asubah idan da rai da lafiya. Durkusawa sukayi har k'asa suka gaishe su dukka, suka amsa a sake sannan ya tambaye su daga ina dan be gane su ba. "Daga kano muke, munzo wajen Malam Hassan sarki ne, daga chan titi aka kwatanto mana wanchan gidan." "Ni ne nan Hassan sarki, sannun ku da zuwa." Kallon juna sukayi shi da Habeeb sai Aryan yayi murmushi ya kara gaishe shi sannan yace magana ce take tafe dasu. Tashi yayi bayan ya nemi afuwar wanda suke tare yace su taso su biyo shi, suka nufi gidan da suka yi parking. A jikin motar Habeeb ya tsaya shi kuma Aryan yabi bayansa zuwa cikin zauren gidan, me dauke da wani dan madaidacin daki. "Bismillah shigo." Yace masa bayan ya shiga ya zauna, shiga Aryan yayi ya zauna a ladafce sannan ya shiga yi masa bayanin dalilin zuwansa, "Yanzu haka an soma shari'ar tata, kuma ana bukatar samun hujjojin da zasu bada damar yanke mata hukunci." Ya karkare yana duban Malam Hassan din "Tabbas lokaci yayi da azzulumar matar nan zata girbi duk abinda ta shuka, naji dadi matuka kuma zan bada gudunmawa ta dari bisa dari, zan zo har kotun na bada shaidar duk abinda ya faru ranar, amma kafin nan inaso na sanar da kai yadda komai ya kasance. Gyara zama Aryan yayi cikin zakuwar son jin labarin duk da kuwa baya duniya a sanda abun ya faru amma ya samu labari daga baya, kuma yasan yana daga cikin abin da har Mummy ta koma ga Allah be bar zuciyar ta ba, ta kan tuna tayi kuka sosai dan ba karamin tashin hankali bane a raba ka da dan ka tun yana jinjiri. _"Kana jina yaro? Watarana bayan Magriba daf da ishai na fito daga gida ina kokarin karasawa masallaci a lokacin ni ne ladanin masallacin ni ke kiran sallah, a daidai wata kwalbati dake da dan tazara da masallacin na ji kamar kukan jinjiri, matsawa nayi domin tabbatarwa cikin tsananin mamaki na ga jariri babu ko riga a jikin sa sai pampers ya cure waje daya yana kuka sosai, waigawa nayi da tunanin zan ga wani amma babu kowa kasancewar layin babu mutane ba kuma kasafai aka fiya bin sa ba idan dare saboda masu kwacen waya da yan iska. Ni kaina a lokacin saurin da nake yasa ni yankewa nabi ta lungun saboda yafi kusa da masallacin akan ta chan titi. Jaririn ne ya cigaba da kuka na juya da nufin tafiya ta amma sai naji chak na tsaya, ba zan iya ba, rashin tausayi na be kai haka ba, dawowa nayi na duka nasa hannu na dauko shi ya kara chanyarewa da kuka, hawaye ne suka biyo gefen kunci na, na share ina rike shi kam kam kar ya sullube dan ba iya daukar jarirai nayi ba ko haihuwa akayi a gidana bana iya dauka har sai sunyi kwari. Lungun na sake bi da nufin na shiga cikin mutane sosai sannan na nemi taimakon su mu mika jaririn gidan mai gari ina shigowa wani dan lungu sai na hadu da wasu maza su biyu suna tsaye a dan wani lungu. Ina zuwa daidai in da suke tsaye dan da fari ban ma lura dasu ba, sai da na matso daf naji kuma sun min magana sannan na ankare."Malam Hassan barka da wannan lokaci." Gudan yace min yana kallon na. Amsawa nayi ina kallon yanayin suturar da take jikin su ta rashin d'a da wata uwar suma da suka tara akan nasu babu kyawun gani. Kallon hannu na sukayi nayi saurin cewa "jariri ne aka yar dashi a cikin kwata, ko su waye suka yar dashi basuyi adalci ba, basu kyauta ba kuma basu da imani, gidan me gari zan mika shi nasan in sha Allah za'a iya samun iyayen sa in da anan kusa suke." Babu wanda ya ce uffan a cikin su, sai cigaba da kallon na da sukayi , ganin haka kawai yasa nA juya da nufin yin tafiyar ta,sai ji nayi an fisgoni kamar wani karamin yaro, nayi baya kamar zan fadi suka shataloni sannan suka shaka min wani abu me warin gaske, Allah ne ya kiyaye ban yada jinjirin hannu na ba. Tun daga nan na rasa hankali na, bansan ina nake ba. Tsawon awoyi na dauka a hakan kafin na farfado na ganni a wani daki me duhun gaske. Kukan karamin jariri ne ya karade dakin a hankali sai haske ya maye gurbin duhun da ya mamaye dakin. Matata Rabi na hango a zaune a kuryar dakin rike da jaririn sai lokacin na tuna abinda ya faru, na yinkura da sauri zan mike naji an daure min kafa ta da hannu na. Rabi? na kira sunan ta, kanta a kasa tana kuka bata san na farfado ba sai da nayi magana ta dago a zabura. "malam." Tace cikin muryar kuka, "me muke anan Rabi?" Na tambaye ta ina kallon jaririn hannun nata da har lokacin kuka yake. "Wasu maza ne suka je har gida suka dauko mu ni, suka kawo ni nan sannan suka ce wai kashe mu zasuyi." Subhanallah, me mukayi musu." Ban sani ba, amma koma menene Malam akan jaririn nan ne, naji suna maganar kashe shi zasuyi ma, wallahi Malam inason shi, lokaci daya son shi ya shiga zuciya ta, dan Allah kar mu bari su kashe shi, ina son shi." Menene alakar su da jaririn toh? Tabbas shine dalilin da yasa su kawo mu nan, kuma ina kyautata zaton akwai wani abu da suke boyewa." Jin ana taba kofar ya saka mu yin shiru, samarin nan ne tare da wata mace wadda sai daga baya na gane wacece, itace Hajiya Zeenatu Mukaddas, itace kuma ta sace jaririn ta sa aka jefar dashi, mu kuma muka tsince shi, bamu taba haihuwa ba tsawon lokacin nan, dalilin da yace muka gudu da jaririn kenan muka raine shi, bayan mun gudun da safe a hanyar barin garin muka samu labarin batan dan gidan Alhaji Ibrahim Mukaddas, tabbas a lokacin mun so juyawa mu maida musu dansu, amma bamu samu dama ba saboda biyo mu da sukayi suka kuma yi yinkurin sake kwace shi, mun riga mun san idan har muka barsu suka tafi dashi kashe shi zasuyi, shine muka roke su, su bar mana shi da alkawarin ba zamu bari ya san su waye iyayen sa ba, zamuyi nisa da garin kano ba zamu sake waiwayowa ba. Kaji abinda ya faru a lokacin muka bar gari muka tafi chan Kaduna muka soma sabuwar rayuwa, muka raini jariri har ya kai munzalin saurayi daga nan muka tattaro muka dawo Kano mahaifar mu, daga nan ne kuma muka sanar dashi komai game da rayuwar sa, sannan muka bashi damar neman iyayen sa da kansa saboda a lokacin ya kai matakin da babu wanda zai iya takashi. Yanzu haka a cikin Kanon yake zaune da matar sa tunda da ma daga bayan dawowar mu nan gidan dan uwana ya koma da zama a chan kanon saboda makaranta."_ Hannu Aryan yasa ya goge hawayen da suka biyo gefen kuncin sa, ya dago kansa ya kalli mutumin yayi masa murmushi "Yanzu yana ina?" "Ya tafi umrah shi da mai dakin shi, amma a cikin satin nan muke saka ran zasu dawo in sha Allah." "Allah ya dawo dasu lafiya, ba zan iya fasalta yanayin farin cikin da na tsinci kai na a ciki ba, Baba." "Allah sarki, wasu mutanen ne basu da imani sam, mutane irin su Zeenatu zasu iya komai akan cikar burin su, dan ko da muka yi alkawarin yin nisa bata daina bibiyar mu ba, ta dinga tsoratar damu tana jaddada mana in dai muka karya alkawari sai taga bayan mu, na kuma tabbatar da zata aikata duk abinda tace." "Karshen ta yazo Baba, in sha Allah da duk masu taimaka mata, fatan dai zaka daure ka shigo ranar domin bada shaidar ka, sannan ina fatan zaku zo tare da dan uwana,." "In sha Allah, nayi maka wannan alkawarin." "Shikenan Baba, nagode sosai Allah ya kara girma." "Amin ya Allah." "Toh zamu koma Baba." "Har zaku koma?" "Eh in sha allah." "Toh madallah, ga number waya ta idan yaso sai ka bani taka, ma yi magana kafin ranar idan akwai bukatar hakan." "Yawwa Baba, hakan yayi nagode." Exchanging number sukayi, Aryan ya ciro kudi a envelope ya ajiye masa, da fari kin karba yayi yace ba zai karba ba, sai da ya matsa masa sosai sannan ya karba yayi godiya duk da yanayin sa be nuna yana da bukatar wani abu ba, tsaf yake kana gani kasan yana cikin rayuwa me kyau da hutu. A mota ya samu Habeeb ya kwantar da kujerar ya kwanta idon sa a rufe. Sallama yayi masa ya tashi dan dama idon sa biyu, ya zauna daidai sannan ya kunna motar, Malam Hassan na tsaye yana kallon su har suka bar layin. A garin karfi magriba ta riske su, suka tsaya suka yi sallar sannan suka cigaba da tafiya. Asibiti suka wuce direct Aryan yace masa yaje kawai idan ya gama zai tafi, watakila kuma ya kwana ma. Sallama sukayi ya bashi key din ya shiga ciki. Daddy na zaune an dan saka masa pillow daga bayan sa, sai wuyan sa dake makale da neck pillow ya jingina yana kallon kowa na dakin, abinci ya gama ci wani dan uwanshi da yazo ya bashi Ya Nabeela ta tashi ta shiga toilet din cikin dakin ta wanko cup tazo ta hada masa tea tana gama bashi Aryan ya turo kofar ya shigo. Mamakin ganin Daddyn a zaune ya saka shi karasowa ciki da hanzari. "Daddy?" Ya zauna a kujerar dake gaban gadon yana masa kallon tausayi. Be amsa ba sai motsi da yayi da idon sa a hankali yayi masa murmushi. Waigawa yayi wajen da Ya Nabeela take zaune yace *Yaushe ya tashi?" "Yau da safe." "Baki fada min ba amma?" "Nasan ka shiga busy, bana so nayi distracting dinka,gashi yanzu kazo ka gani, sai dai maganar ce har yanzu bata dawo ba, da tafiya amma doctor yace a hankali zai dawo normal tunda har yana cin abinci ma." "Alhamdulillah." Ya furta yana maida kallon sa kan Daddyn "Ya jikin? Allah ya kara sauki." "Ya maganar da mukayi ranar Aryan?" "Eh yanzu ne right time din, sai a fita dashi dama Dr Mahfouz yace a tsaya a ga progress din, kuma alhamdulillah akwai, amma idan aka je chan din za'a samu karin kulawa in sha Allah." "Ok, hakan yayi, sai a tafi da Baba Rabi'u da Uncle Mamman." "Eh, in sha Allah. Amma ke zaki kira su kuyi maganar." "Ai Baba Rabi'un yana nan yau masallaci ya tafi, idan ya shigo yanzu sai muyi maganar." "Ok good, wannan abun da ya faru kinga ya dawo musu da closeness dinsu da daddy." "Sosai, da mu ma kanmu." Shiru yayi yana tunanin ya fada musu ko ya bari tukunna, yadda zuciyar sa ta cika da son sanar musu baya jin zai iya rikewa. " Ahmad yana raye." Ya fada yana kallon bangaren Daddyn da yake kallon sa shima "Da gaske?* Ya Nabeela tace tana mikewa tsaye "Kwarai da gaske, a binciken da mukayi mun gano yana raye, kuma yau na je har in da yake wajen mutumin da ya rike shi, na kuma roke shi akan su bayyana a kotun." "Allah sarki Mummy." Ya Nabeela tace ta fashe da kuka, ta tuno masifa da tashin hankalin da mahaifiyar su ta shiga a lokacin akan batan Ahmad din. Kukan daddy yake shima ya motsa bakin sa a hankali yace "Yana ina yanzu, ka kaini wajen sa?" Da sauri suka kalle shi a tare, duk da maganar bata fito sosai ba amma tabbas magana yayi, girgiza kansa yayi hawayen na cigaba da sakkowa daga idon sa, yayi nadamar rusa gidan sa, da farin cikin sa da farin cikin matar sa me tsananin so da kaunar sa, yaci amanar aminin sa sannan ya ci amanar yayan sa. Kukan da yake na dauke da manufofi masu yawan gaske, yana sane yaki magana saboda bashi da karfin zuciyar da zai iya bud'e baki yayi musu magana, yace musu me toh? Kuyi hakuri ko me? "Daddy me kace? Magana kayi daddy?" Suka rufa akansa suna tambayar sa "Eh, magana nayi." "Alhamdulillah!" Suka hada baki wajen fada. "Kira doctor Aryan." Ya Nabeela tace tana murmushi hade da dariyar farin ciki. "Baki fushi dani ba Nabeela?" Ya tambaya bayan Aryan din ya fita duk da yasan dama ko a da din bata taba ketare maganar sa ba, bata kuma taba nuna masa ba daidai yake yi ba, hasalima a kullum nuna masa take yayi daidai saboda tsananin biyayyar ta. Da sauri ta hau girgiza kanta tana share hawayen fuskar ta "Babu abinda kayi min daddy, da zan yi fushi dakai." "Allah yayi muku albark." "Amin Daddy." Shigowar Dr da Aryan yasa ta matsawa baya ta basu waje, ta dauki wayarta ta fita waje dan kiran Mijinta ta sanar dashi daddy ya dawo daidai. Kallon Aryan Daddyn yake tayi yana so yasa idanun sa a cikin nasa amma sam Aryan din yaki kallon sa, har Dr ya gama abinda zai ya fita Aryan din yabi bayan sa jim kadan ya dawo ciki ya tsaya daga saitin kafafun Daddyn yace "Yau aka fara shari'ar Hajiya Zeenat, an dage sauraron karar zuwa sati biyu, ina fatan ban yi laifi ba, ina kuma fatan zaka saka min albarka sannan kayi min fatan nasara." "Allah ya taimaka ya baka sa'a, ina jiran bincike yazo kaina, domin nima me laifi ne Aryan, nayi muku laifi ku da mahaifiyar ku." Kin kallon sa Aryan yayi dan yadda zuciyar sa ta karye da maganganun Daddyn zai iya fashewa da kuka, amma baya so ko kad'an yaji d'ar wajen tabbatar da gaskiya,duk da deep down baya fatan wani abu ya shafi Daddyn amma kuma ya zai yi? Idan har kotu ta kama shi da laifi dole ta hukuntashi daidai da laifin da ya aikata. _*RQ*_                   Page 34 _*©®HRano*_   ***Turo kofar akayi aka shigo, Adam ne ya karaso da sauri ganin idon Daddyn a bud'e, kujerar da Aryan ya tashi daga kai ya zauna yana kallon Daddyn cike da farin ciki. Juyawa Aryan yayi ya fice ya rufe musu kofar dan baya son ganin abinda zai bata masa rai, duk da ya yarda da soyayyar da Adam din yake wa Daddyn ganin yadda ya damu sosai akan rashin lafiyar. Be san wani a matsayin uba ba, face Daddyn kuma shine kadai gatan sa. Shi ma Daddyn yana yi masa soyayya irin ta d'a ne da mahaifi yana jin shi sosai. "Ya ka fito?" Ya Nabeela tace tana mikewa daga wajen da take zaune "Adam ne yazo." "Ban ga shigewar sa ba kuma, ko lokacin muna waya da Daddyn su Amna ne." "Eh may be, bari na wuce idan Baba Rabi'un ya dawo sai kuyi maganar, zan yi kokarin fara processing tafiyar ina hadawa da sauran aikin." "Ok, nima tafiya zan naga dare ya fara, yace zai biyo sai mu tafi." "Ok, Baba Rabi'un shi kadai zai kwana yau?" "Eh ina jin tunda jikin da sauki. Kaje gida ka huta, kayi bacci sosai please." "Baccin ne ma baya yiwuwa ai, akwai ayyuka a gabana masu yawa." "Still dai, ka huta yau dai, kayi tafiya kana bukatar hutu." "Zan gwada." "Yawwa, ya labarin Kamal?" "Muna magana a chat,yana sane ya kyale ni sanda nake matukar bukatar sa." "Yayi min daidai ai, da ace kana da matarka ba zaka yi wani missing dinsa sosai ba, yanzu haka da yadda ka gajin nan kana komawa za'a tare ka a kula mun da kai." "Zan gudu, sai gobe." "Baka son gaskiya dai." Tasa dariya "Inaso mana, kawai maganar kara min pressure zatayi, amma dai I'm planning something, hoping yayi muku yadda kuke so." "Akan wannan maganar?" "Eh." Ya daga mata kansa "Good, haka muke son ji, Allah ya bada sa'a ya taimaka." "Amin, goodnight." "Goodnight,." Ta daga masa ya fice cikin takun sa me cike da nutsuwa. "Allah ya tallafi rayuwar ka Aryan ya hada ka da abokiyar zama me son ka." Ta daga hannu tayi addu'a sannan ta koma ciki. •••••••Raihana bata tashi tunawa da sakon Hamma Muhd ba sai da safe bayan tayi breakfast ma tana kitchen tana wanke kwanukan da aka bata abun ya fado mata, da sauri ta dauraye hannun ta, ta goge da kitchen towel ta dauki wayar ta bud'e whatsapp din ta shiga kan chat din nasa. Saura kasan wayar da subce daga hannun ta, ta fadi kasa saboda abinda ta karanta. _"Ni kuma? Soyayya?" Ta furta tana sake kallon tsararren sakon wanda ya tsaro da kalaman kokarin kafa kai. Ko kad'an bata ji son sa a zuciyar ta ba, hasalima baya cikin jerin mazajen da take jin zata iya zaman aure dasu kwata-kwata, ya tsaya dai a iya yan uwantakar amma ita dai a'ah, bata shirya ba sai ta kara wayo da hankali. Rasa me zata ce masa tayi, ba zata iya ce masa a ah kai tsaye ba, babu dadi duk tsiya wanda yace yana son Ka yafi makiyinka ai, ba kuma zata iya amsa goron gayyatar soyayyar tasa ba, dan ita gaba daya ba abinda ma yake gabanta ba kenan, Kar taje tana zaman zaman ta a hada bikin ta da na su Hamman ta, tafi so ta fara rakashewa a bikin su daidai gwargwado kafin a fara maganar ta. Jin ta take har lokacin yar karamar yarinya ce ita, bata isa aure ba, dan bata san ta yadda zata fara kula da garjejen saurayi ace ita zata masa kusan komai ita din da ba'a wani dade sosai da su Hamman ta suka daina goya ta ba. Fita tayi daga kan chat din sai tayi nazarin me zata ce sannan zatayi masa reply kar tayi a take ta kwafsa. Cikin chat din Aryan ta shiga kamar munafuka dan dama tunda ta tashi take son budewa amma ta kasa. Murmushi tayi ta tura masa hi a kasan hello din da yace mata, sannan ta dora da waye? A gaban sakon. Tana sane tayi hakan ta ajiye wayar tana murmushi ta cigaba da aikin da take yi. Sai da ta gama tas ta gyara kitchen din ta fito ta koma daki ta zauna a saman gadon ta sannan ta sake shiga whatspp din. Blue tick din da ta gani akan chat din Aryan yasa ta tabbatar ya karanta sakon ta, typing taga yanayi ta yi baya ta kwanta akan pillow tana jiran amsar sa. "Ghost ne!" Ya yi reply ya sauka a take ya kira wayar ta. Wani irin harbawa zuciyar ta, tayi da karfi ganin shine yake kira, ta rasa dalilin da yasa take jin hakan game dashi da duk wani abu da ya shafe shi. Kamar ba zata daga ba, amma kuma bata da wannan karfin zuciyar, sakata tayi a kunnen ta bayan ta daga tace hello. Ajiyar zuciya ya sauke me dan karfi, ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi sannan yace "Baki da number na?" "Na'am, mmm.. eh bani dashi." "Oh okh, baki saving bane ba?" "Eh." "Ok, do it now, please." "Why?" "Just. Kiyi saving bana so na kira mutum ko nayi masa magana yace be gane ba." "Ok zanyi." "Good, how was your night?" Gwalalo ido tayi waje, how was your night Yake tambayar ta? Lallai "Alhamdulillah." Tace "Masha Allah, me kike yi yanzu?" "Ba komai, just laying down." "Can i join you?" Ya fada kamar me rada, kame wa tayi a wajen cike da mamakin sa. Ta jishi sarai amma sai ta nuna bata ji me yace ba. "Na'am?" "Baki ji ba?" "Umm, banji ba." "Ok, yaushe zaki dawo, we need you here,." "Ka manta? Kaine kace na tafi,baka son sake gani na, you hate me!" "Shhhhh!!!" Ya dakatar da ita da karfi "Please Raihaana." Yayi lowering voice dinsa sosai sannan yace " Duk abinda na fada ba har zuciya na bane, and I said I'm sorry, I'm sorry kiyi hakuri." Bata ce komai ba, "Kinji? I'm sorry, kuma nayi regretting duk abinda nace." "Ok." Tace da k'yar "Kin hakura? Kin yafe min?" "Umm." "Serious?" "Umm..." "Thank you so much, nagode." "Uhum." "Are you coming back?" "A ah." "Pleasee dan Allah ki dawo, Kamal ya tafi, kema kin tafi I'm so lonely, please come back." "Hamma na ba zasu yarda ba." "Why? Me nayi musu ne har haka?" "Ban sani ba nima." "Shikenan, bari nayi clearing abubuwan da suke gabana, zanzo har nan din, sai muyi magana naji, menene laifi na." "Okh." "Na gaji, aiki yayi min yawa kwanan nan bana samun enough sleep." "Ayya sannu, it's not easy." "Thank you, bari na shirya na fita, sai anjima." "Ok sai anjima." Suka ajiye wayar a tare. Wani fresh Aryan yaji akan sa kamar an janye masa wani abu me nauyi da ya tokare shi. Nine kuwa? Ya tambayi kansa da kansa. Be zata zai iya wannan long conversation din da ita ba, sai gashi yayi, har yana jin kamar su dawwama a haka suna magana. Murmusawa yayi ya tashi daga zaman ya tattare takardun sa sannan ya fada toilet dan yin wanka. Yana wankan yana tunanin abinda ya faru, shi kadai kawai sai yayi murmushi, ya gama ya fito daure da towel ya shirya a tsanake cikin shigar suit baka yasa bakin takalmin sau ciki sannan ya dauki abinda zai dauka ya watsa su a brief case dinsa hade da notepad dinsa ya fito. A falo ya ajiye komai ya shiga kitchen ya samar wa kansa tea ya dawo falon ya zauna yana sha yana kallon TV har zuwa lokacin da Habeeb ya karaso ya mike ya maida cup din kitchen ya dauraye shi sannan ya fito yana jin sa sakayau. Kansa da a kullum yake masa nauyi yau sai yaji kamar an cire masa ciwon an maye masa gurbi da wani irin mixed feeling me tafiya hade da farin cikin zuciya. Tunda suka gama wayar take blushing, wani yanayi wanda bata taba jin irin sa ba take ji a yanzu. Muryar sa me cike da amo ta haddassr mata da wata irin kasala. Chusa kansa tayi a cikin filon tana murmushi k'asa k'asa, a haka Dadah ta shigo ta same ta. Tashi tayi zaune ta tankwashe kafarta tana kallon ta "Na zata bacci kike ai da naji shiru." "A ah, waya nake." "Ok, yanzu mamanku Maimunatu ta kirani da wani labari." Gaban Raihann ne ya fadi cike da tsoro tace "Wani abun ne ya faru?" Girgiza kai Daadah tayi "Babu komai, sai alkhairi. Wai Muhammadu ne ya sameta da maganar ki,." "Ni kuma Dadah?" "Akwai wata a dakin ne da muke magana bayan ke? Kaji min shiririta." "Toh ai Daadah maganar ce naji ta banbarakwai." "Kinci gidan ku, ace ana sonki kice maganar ce banbarakwai." "Ni dai gaskiya Daadah bana son shi." Tafa hannu tayi ta hau salallami "Menene laifin shi Raihana? Menene aibun sa? Yaro saurayi kyakkyawan gaske, me jini a jika, gashi dan dangi gashi kuma dan uwanki, me kike nema?" "Allah ni Daadah son shi kawai ne bana yi, son yan uwantaka nake masa." "Tirkashi, haka zaki mana Raihana? Har ina murna na sanar da yayyanki? Suma kuma murnar suke gasu chan a falo." "Allah ni Dadah bana son shi, Allah kuwa." "Toh wa kike so?fada min sai naji ai." "Ni ba wanda nake so." "Kinci gidan ku,ko aljanune dake ni jikar mutum hudu,eh?" "Ba komai fa Daadah, na zata zaki fuskance ni, ni kawai bana son kowa ne, zaizo ne soon, amma banda Hamman gidan su Amina." "Toh ni dai babu ruwana, kiyi tunani sosai sannan ki duba abinda zai faranta mana rai, idan kuma akwai wanda kike so ne ki fada min ni zan wuce miki gaba, amma idan har babu toh fa ba ruwana." "Shikenan zan fada miki shi, amma yanzu ki hana su Hamma maganar toh, yanzu sai su dauka su fadawa Abby." "Ki dai yi kokarin bashi dama ku fahimci juna." "Toh Dadaah,zan bashi dama." "Yawwa haka nake son ji, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Sai ta mike "Bari na samesu nace su bar maganar zuwa sanda kuka daidai ta kanku, amma dai zaa bashi damar zuwa wajenki, idan Allah yayi zaa yi dashi toh, idan kuma Allah be yi ba shikenan." "Ok tam." Tace dan so take a bar maganar haka nan shiyasa ta amsa mata da yadda take so. Tana fita ta kulle kofarta ta koma ta kwanta rigingine tana kallon saman dakin. Daga chan bangaren hankalin Muhd duk ya tashi, gashi ta duba message dinsa amma babu reply gashi yayi ta kiranta dazu yana jin user busy duk sai ya kasa nutsuwa, yaje ya sanar da Adda Maimuna shine ita kuma ta kira dadah dan ba karamin farin ciki ta shiga da labarin ba, dan dama tana ta fargabar wadda Muhd din zai dauko, sai gashi ta kwana gidan sauki. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ __**RQ**__                Page 35 ®️®️ Rano ***Tsawon sati biyun nan Aryan be zauna ba, shine daga nan yayi chan har ya samu ya kammala processing tafiyar Daddyn sannan ya tabbatar duk evidence din da zasu gabatar a kotu yana hannu. Sau daya sukayi waya da Malam Hassan ya kara rokar sa ya kuma amsa masa da zasu zo in sha Allah.     Yana tsaye a gaban table dinsa bayan ya gama tattare hannun rigar sa zuwa sama yana jiran shigowar Zainab kafin ya shiga ya dauro alwala ganin lokacin sallah yayi. Knocking ta fara yi ya bata izinin shigowa ta shigo ta gaishe shi sannan ta ajiye takardun a saman table din ta saci kallon sa ta gefe tana jin wani shaukin soyayyar sa na sake kamata. "Komai ya cika? Babu wata matsala?" "Eh sir, babu." "Ok good, sannu da kokari." "Thank you sir, akwai abinda kake bukata ne sir." "No babu, sallah zan na fita akwai in da zanje, zaki iya tafiya thank you." "Ok, Allah ya bada sa'a." "Amin." Yace ya shige toilet din bayan ya tabbatar ta fita ta rufe masa kofar. Alwala yayi ya fito ya samu dan karamin towel ya goge ruwan hannun sa da fuskar sa, sannan ya maida hannun ya saka links din ya kashe komai ya fito rike da wayar sa. A reception din ya tsaya ya dan duba abinda zai duba sannan ya leka office din su Abdulhakeem ya tarar dasu suna aiki ya kalli empty desk dinta ya kad'a kansa ya fito ya fice gaba daya daga cikin building din. ****Adam na zaune a office din shima ya hango fitowar Aryan din, waya ya dauka ya yi kira ya sanar dasu ya fito yanzu sannan ya kashe, tunda ya daure damarar ganin bayan sa toh shima zai yi nasa kokarin wajen ganin bayan Aryan din ya kuma taimaki mahaifiyar sa, a da ya kasa tunanin abinda ya kamata yayi ya taimaka mata sai da ya samu kira jiya akan maganar sannan ya zaburo,ya kuma kuduri aniyar sai ya hana shi aiwatar da komai.   Driving yake hankalin sa na kan titin gaba daya zuciyar sa ta lula zuwa kundin tunani har be san ana bin sa ba. Wayar sa dake a silent sanda yana aiki ya maida ita shaf ya manta be cire ba tana ta faman ringing a gefen sa amma be ji ba, he was so focused akan abinda yake yi har ya kusa karasawa asibitin, sai ya tuna wata allura da ya kamata ya siya ya manta gashi an ce masa sai yaje wellcare sannan zai samu. Yana daidai wani U-turn ya tuna sai kawai ya juya motar ya koma. Juyawar sukayi suka cigaba da bin sa cikin dabara. Sai da ya isa wellcare din sannan ya dauki wayar ganin tarin missed calls din Habeeb yasa shi shan jinin jikin sa, ya waiga bayan sa da sauri amma be ga kowa ba. Da sauri ya shige cikin wellcare din sannan ya danna kiran Habeeb din. "Kana jina? Ka jira mu a cikin wellcare din karka fito please, suna following dinka tun daga company luckily baka shiga wata hanya da babu mutane ba." "Su waye su?" "Idan nazo zamuyi magana, oga Kamal yace please karka fita, zai mana wuya mu iya tracing naka yanzu ma dan ka dauki wayar ne har muka ga location dinka." "Ok, sai kinzo." Ya katse wayar ya shiga ciki ya nufi bangaren magunguna yana dubawa. Biyo shi ciki sukayi, biyu suka zauna a mota. Kamar masu siyan abu haka sukayi pretending suna dubawa har suka kawo saitin da yake suna kallon sa suna monitoring din sa. Sarai ya lura da yadda suke bibiyar sa a cikin wajen. Glass din da ya ciro a aljihun sa ya saka me dauke da camera da Kamal ya bashi yayi amfani wajen capturing abinda yake faruwa duk da ba komai ba amma yayi sa'ar samun hoton fuskar daya daga ciki.    Cikin casual dress Habeeb suka shigo su ma wajen su uku, kunnen sa dake makale da Bluetooth ya taba yace "Kana ina?" "Wajen pharmacy, ina tunanin sun shigo ciki, "Ok, ka shiga wani dan corridor haka muga" "Okh." Yace ya juya ya hangi wani dogon corridor ya nufi wajen ya shiga, suna ganin ya shiga wajen suka rufa masa baya a daidai lokacin su Habeeb suma sun shigo. Su biyu suka yi wajen da Aryan din yake daya kuma ya tafi wajen receptionist din ya nemi office din manager ya nuna masa. Suna shiga lungun su Habeeb suka dirar musu, suka yi arresting dinsu a take.   Tare wanda ya shiga wajen manager suka fito bayan yayi masa bayanin abinda ya kawo su wajen, godiya manager yayi musu suka fito har wajen da motar su take, suka tura su a ciki sannan Habeeb ya mikawa Aryan wata yar karamar na'ura ya shige motar.   Tsaye kawai Aryan yayi cike da mamakin abinda ya faru just now, wato akwai mutanen da zasu iya goyan bayan duk zaluncin da hajiya Zeenat tayi kenan, har suyi kokarin taimaka mata da karfi da aljihun su. mutum daya ya rage DSS su kama shine SAN Mandawari shi kuma tun kama Hajiya Zeenat ya bi dare ya fice daga k'asar amma suna dakon dawowar sa wanda tabbas akwai saka hannun sa a harin nan da aka kaiwa Aryan din kuma shine mutumin da yake taimakawa Hajiya Zeenat din wanda suke da alaka me karfi tun da. Shine yayi shari'ar Abby kuma shine ya tabbatar da an tura shi prison. ***Kotun ta cika makil fiye da zaman farko, Adam na gaba dan da wuri ya iso kotun dan tun kafin a bud'e ma ya iso ya zauna a mota duk abin duniya yayi masa zafi. Tun da aka kama yaran nan da suka tura su tare Aryan yake cikin zulumi duk da kamasu ba bashi da direct alaka dashi sai na wanda suka tura shi, amma kuma idan har suka shiga hannu toh fa shima bincike zai iya zuwa ta kansa. Duk da ba lallai nasa yayi wani tasiri ba saboda su din manyan masu aikata laifi ne a k'asar kuma suna da daurin kafa shiyasa a sau da yawan lokuta Hajiya Zeenat din take having way din ta, wannan karon ne dai aka mamaye ta bayan ta gama sakankancewa itace da nasara domin ta samu duk wata hujja tasu a hannu not knowing that sunyi outsmarting dinta a matsayin su na yara matasa masu ji da zarra.   Shigowar judge din ya saka wurin ya dau shiru daidai lokacin aka shigo da Hajiya zeenat ta saka gefen mayafin ta, ta rufe fiye da rabin fuskar ta. Aryan na zaune tsakankanin manyan lawyers tare da Barrister Awais da yake leading din su.   Shi ya fara mikewa ya gabatar da kansa ga kotu sannan lawyer da yake kare Hajiya Zeenat din ya mike shima yayi introducing kansa sannan su Aryan da Barrister Hakim da Barrister Fatima suma suka gabatar da kansu. Cikin shari'ar aka shiga kai tsaye ba tare da bata lokaci ba, Judge din ta sake karanto tarin laifukan da ake tuhumar Hajiya Zeenat din dasu wanda suka hada da zargin salwantar da rayuwar Hajiya Khadija Mukaddas, Hajiya Aysha Matawalle, satar yaro jinjiri Ahmad tun yana zanin goyo sannan tayi yinkurin kashe mijinta Alhaji Mukaddas wanda yake kwance a asibiti yanzu haka da kuma sauran laifukan. Barrister Awais ne ya sake mikewa a isa gaban wajen da take tsaye saboda yana da bukatar ta amsa masa wasu tambayoyi. "Sannu Hajiya Zeenatu, akwai wasu yan tambayoyi ba masu yawa ba, da nake so ki amsa min." Idon ta akan Aryan da yake zaune daidai saitin ta yana facing dinta dan shi kadai kawai take gani a wajen. "Kina jina? Da farko dai kotu zata so sanin alakar ki da wadannan mutanen, Aisha da kuma Hajiya Khadija." "Kawaye na ne da muke tare tun makaranta." "Wani abu na rashin jituwa ya taba faruwa tsakaninku? Ko sun yi miki wani abu da ya bata miki rai har kika ji bari ki salwantar da rayuwar su?" "Objection My lord." Barrister Sule yace yana mikewa "Me kamata Barrister Awais ya dinga jinginawa mata kalmar kisa kai tsaye ba, tunda har yanzu zargi ne ba'a tabbatar da gaskiyar ba." "Barrister Awais ya kiyaye." "Ok, my lord." Komawa Barrister Sule yayi ya zauna ya yi folding hannun sa. "Muna son sanin me ya faru ranar bakwai ga watan October, da daddare wajen asubah, a lokacin da aka samu gawar Hajiya Khadija a kwance cikin jini." "Bansan komai akai ba, kamar yadda aka samu gawar ta haka nima na ganta,." "Hmm." "Abinda ya faru a ranar 7 ga watan October da misalin karfe biyar na asubah an samu gawar Hajiya Khadija a kwance a cikin jini, wanda barrister nasir Matawalle ya samu gawar tata bayan ta tura masa wani sako da misalin karfe biyun dare, in da be tashi samun sakon ba sai da asubah saboda ko a lokacin da ta tura masa sakon dare yayi, ga abinda sakon ya kunsa ya mai girma me shari'a."   Ya mikawa daya daga cikin na zaune gaban wajen sannan shi kuma ya mika mata, ta karba ta gani sannan ta ajiye a gefe "Kotu na sauraran ka Barrister Awais." "Bayan Hajiya Khadija ta kama Hajiya Zeenat da abokin aikin nata sai tayi yinkurin daukar hoto a lokacin ne suka lura da ita, sannan suka biyo ta har cikin daki suka kashe ta." "Objection My lord, ya za'a yi barrister Awais ya dinga jingina mata laifin kisa kai tsaye? Hakan yayi muni sosai, ina rokon da ya janye kalaman sa ya kuma tausasa lafuzan sa." "Ko kana da shaidar abinda ka fada barrister?" Tace tana kallon sa "Kwarai da gaske, ina da shaidu guda biyu, na farko shine d'an marigayiya Hajiya Khadija wanda duk da karancin shekarun sa a lokacin yana iya tuna abinda ya faru akansa, na biyu shine shaidar da aka samu a cikin CCTV camera din dake hanyar shiga dakin marigayiyar wanda ya dauki hoton hajiya Zeenat da abokin harkar ta wanda bamu iya ganin fuskar sa ba a lokacin da suke shiga cikin dakin." "Kotu tana bukatar ganin shaidun a gabanta." Aryan ne ya mike ya isa gaban wajen ya sake yin gaisuwa sannan ya gabatar da kansa a matsayin shaida duk kuwa da ba lallai shaidar tasa tayi tasiri ba sosai duba da karancin shekarun da yake dashi a lokacin da kuma kasancewar sa cikin lawyers masu kara. Yana maganar kirjin sa yana harbawa sosai saboda yadda a duk lokacin da ya tuna memory din yake shiga matukar tashin hankali, da kyar ya karasa maganar ya koma wajen zaman sa ya zauna dafe da kirjin sa. Ruwa Barrister Hakim ya bashi Yasha sannan ya dan samu daidatuwa. Shiru ne na dan sakannni ya bayan komawa wajen zaman Aryan din, sannan aka cigaba da sauraron karar. Sosai barrister Awais yayi kokari wajen bada hujjoji kwarara kafin ya gangaro laifi na biyu wanda yake akan batan ahmad ne. Hankalin Aryan gaba daya yana ga kofar yana lokaci zuwa lokaci yana kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, fatan sa shine Allah yasa su karaso a daidai lokacin da ake bukatar su.   Ta kofar dake chan gefe Barrister Nasir matawalle suka shigo tare da Lamido sun samu delay na flight dinsu ne abinda yasa suka makara. Waje suka samu suka zauna a nutse aka cigaba da shariar.    ***Tun da suka tashi Daddy yake faman rokon su akan su barshi yaje kotun amma suka ki, Har nurse din da ke duty yayi ma magana da ta shigo amma tace yayi hakuri Dr yazo. Hankalin sa baki daya yana wajen yana son sanin yadda zata kasance sannan yana so yaji komai game da hajiya zeenat duk da ya gano Wasu abubuwa masu yawa game da ita wanda sai lately ya gano dalilin da yasa shi shiga ya tsaya tsayin daka ya samu aka fitar da Abby, shine ya bada evidence din da ya wanke Abbyn sannan ya tsaya tsayin daka har aka fitar dashi da taimakon Kamal. Duk da ya san babu wani abu da zai fada masa ya yafe masa laifukan sa gare shi, amma duk da haka yana ganin yayi abun da ya dace, ko da ba zai yafe masa ba. Baba Rabi'u ne yazo gaban sa ya tsaya sannan yace "Nayi magana da Dr sun yi discharging dinka, yanzu sai muje chan kotun saboda nasan hankalin ka Yana wajen." "Nagode sosai Rabi'u, nagode." Yace cike da jin dadi. Sabuwar wheelchair din da Aryan ya siyo jiya ya jawo ya taimakawa Daddyn ya zauna akai tinda har lokacin baya tsayawa sosai akan kafarsa, dalilin da zasu fitar dashi kenan ma saboda ta wajen spine dinsa ne yake ciwo sosai. Tura shi yayi suka fito a hankali har zuwa wajen motar sa in da driver yake jiran su. Tare suka taimaka masa suka saka shi a motar sannan suka bar asibitin.    Abby suna zama shima Daddy aka shigo dashi ta same kofar da Abbyn suka shigo, karon farko suka hadu da juna bayan lokaci me tsawo, kallon sa Abby yayi kallo me cike da tsana da ki sannan ya dauke kansa da sauri ba tare da yaji ko dar din tausayin halin da yake ciki ba, dan shima sanda ya shiga matsala be tausaya masa ba, hasalima shi ya kara kokarin kara masa matsalar sannan ya kori iyalin sa ya kwace duk wata dukiya da suka mallaka a tare ya maida ita tasa. Jikin Daddyn ne yayi sanyi ganin abbin da kuma yanayin da ya ganshi yasan ko mutuwa yake yana farfadowa saboda tsananin azaba ba zai kula Shi ba. A bayan su Baba Rabi'u ya ajiye Daddyn sannan ya zauna a gefen sa suka cigaba da sauraron shari'ar duk da kusan rabin hankalin Daddyn baya tare dashi musamman ganin Hajiya Zeenat da abubuwan da ake faduwa a kanta wanda be taba tunani ko hasashen zata aikata ba.   Kara kallon lokaci Aryan yayi, Barrister Awais ya matso wajensa ya rada masa magana ya gid'a masa kai kawai zuciyar sa fal tsoro da zulumi. Daga waje me tsaron kofar ya shigo ya sanar wa da judge din karasowar shaidar da ake jira. Hakan yasa gaban Aryan yayi mummunar faduwa cike da tsoro yake kallon kofar haka ma daddy da Ya Nabeela da take dayan bangaren a zaune ita da Dr Farouk mijinta. Kofar ce ta bud'e, Malam Hassan sarki ne a gaba cikin shigar babbar riga shadda fara da kula jaddara wanda ya kasance shigar sa a kowanne lokaci. Wanda yake take masa baya ne yasa Aryan mikewa tsaye daga wajen zaman sa yana kallon Kamal din wanda shi kuma ko kad'an be kalli wajen da yake ba, hankalin sa yana kan Hajiya Zeenat fuskar sa a dinke tsaf babu alamun fara'a ko dariya. He looks very serious dan Aryan be taba ganin sa a irin wannan yanayin ba. Ganin Malam Hassan yasa Hajiya Zeenat tayi suman tsaye, taji kamar numfashin ta zai dauke ya bar gangar jikinta dan ko kad'an fuskar sa bata bace mata ba, duk da babu irin neman da batayi masa ba wasu shekaru baya amma bata same shi be. "Ya mai girma me shari'a, wannan shine mutumin da Zeenatu ta dauki jinjiri ta bashi bayan ta raba shi da mahaifiyar sa tun yana tsumma." "Kotu zata so taji abinda ya faru daga bakin ka." "Sunana Malam Hassan sarki, dan asalin garin Rano dake jihar Kano, ni ne mutumin da na tsinci jariri a cikin kwalabati a unguwar Tudun yola." "Kotu na sauraran ka." Justice Fatima tace tana rubutu "Abinda ya faru shine..." Ya shiga bada labarin abinda ya faru tun daga farko har karshe, sannan ya dora da "Wannan shine yaron da na tsinta a cikin ramin an yar dashi, shine kuma na raineshi har ya kai wannan munzalin." Ya nuna Kamal da yayi wani irin murmushi me ciwo ya rissinar da kansa alamar girmamawa ga me shari'ar. Ba Aryan kadai ba, Hatta Daddy, Ya Nabeela , Hajiya Zeenat , Abby, Lamido da sauran mutanen kotun sai da suka shiga mutukar mamaki. "Kamal?" Aryan ya furta yana kallonss _"You have to fiind me, look for me daga nan zaka waye ni."_. Abinda yake nufi kenan da yace ya neme shi dama? Kenan all this while, duk tsawon lokacin nan yana tare da brother dinsa ne, one and only brother din da yake dashi kaf duniya. Tunda yake da Kamal be taba yin abinda yasan zai bata mishi ba, be taba yin wani abu da zai cutar dashi ba, duk abinda zai yi yana yi ne saboda yayi protecting dinsa, ya kula dashi da rayuwar sa dan yafi kowa Zama dashi da karfafa masa guiwa. Hannu Kamal din ya d'aga masa ganin yadda yake kallon sa babu ko kifatawa. "An dage sauraron karar zuwa sha biyu ga watan maris me zuwa, kotu na bada umarnin a cigaba da tsare wadda ake tuhuma har zuwa ranar da za'a dawo kotu." Abinda kawai Aryan yaji kenan dan gaba daya hankalin sa baya kan shari'ar ya lula zuwa duniyar tunanin rayuwar su da Kamal tsawon lokaci. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ _*RQ*_      Page 36 ****A hankali mutanen da ke cikin kotun suka dinga ficewa har ya rage saura Aryan, Ya Nabeela Kamal, Daddy da Malam Hassan. Takowa Kamal yayi a hankali zuwa gaban Aryan, ya kashe masa ido daya yana murmushi. "Chill broh." Yace ganin Aryan din ya kasa ko da kwakkwaran motsi. Bin sa yake da ido kawai ya karasa gaban Daddy ya durkusa akan kafafunsa idanun sa na taruwa da kwalla kamar yadda na Daddyn suke cike da kwalla amma ta farin ciki. "K...a..mal?" Ya Kira sunan sa, sai kuma ya hau girgiza kai "Ahmad, Ahmad sunan ka." Hannun Daddyn Kamal ya rike yana durkushen ya girgiza masa kai "Karka takura kanka Daddy, kaga baka da lafiya." "Alhamdulillah!" Ya furta yana goge hawayen da ke bin fuskar sa, sannan ya daga kai ya kalli Malam Hassan da yake tsaye yana kallon su yayi masa nuni da hannu alamar ya matso, matsowa yayi sai Kamal ya mike ya karasa wajen Ya Nabeela. Da sauri kamar me jiran zuwan sa ta rungume shi tana fashewa da kukan da take ta rikewa,kukan farin cikin samun Kamal din a matsayin dan uwan su. Ashe shiyasa be taba barin su ba, ya tsaya sosai a rayuwar su musamman Aryan yayi masa duk gatan da wa ya kamata yayi wa kanin sa. ya shanye bacin ran halin Aryan din duk dan ya cimma wannan burin nasa. Tun farkon ganin sa taji ya shiga zuciyar ta, har ta kan jishi tamkar aryan din a gareta. Sakin sa tayi ta kai masa duka a bayan sa ya goce yana dariya sosai. "All this while ka sani Kamal? Amma Ka boye mana.?" Tace tana kuka me hade da dariyar farin ciki "Ayi min afuwa big sis, ina ta jiran right time ne, gashi kuma yazo yanzu." Ya hade hannayen sa waje daya alamar tayi masa afuwa. "Shikenan, dole na na hakura ma ai,farin cikin da nake ci, amma dai akwai sauran aiki, ga kanin ka chan yayi poster go and check on him please, dan kai kadai kasan kansa." "Troublesome guy kenan, nasan yadda zan yi handling nasa, bari kiga" Yace yana barin wajen ya nufi wajen Aryan din dake tsaye yana kallon su kamar ma baya gane abinda yake faruwa a wajen. Taping bayan sa Kamal yayi yana karasawa ya ratayo kafadarsa sannan yace "Won't you say anything Oga Aryan?" "Are you for real?" Ya nuna shi da hannun sa "Ofcouse, or did you need a DNA test to prove it?" "Noo." Ya girgiza kai da sauri "Ok... Tell me ya kake ji?" "Me yasa kayi min haka?" "Me nayi? Mr complainer." Ya ture shi yana hararar sa "Me yasa ba zaka fada min ba,all this while ashe kai ne, tsawon lokacin nan Ka sani ka boye min, I was so shocked Kamal, bansan wane irin abu ke min yawo akai ba." "Baka murna ne Aryan?" "Ina yi, sosai fiye da yadda kake tunani, like bansan wanne irin abu nake ji ba kawai, kamar mafarki nake, Kamal a matsayin Yaya na? Uwa daya uba daya? Nooo." "Yes, ba mafarki bane ba, same thing naji sanda na fara haduwa da kai, daddy, ya Nabeela. But bani da option than to hide it, idan nazo claiming zama Ahmad Hajiya Zeenat will never allow me to be close to you, zata san yadda zatayi ta bata ni wajen Daddy, wasu kuma zasu ce saboda dukiyar Daddy ne ba gaskiya nake ba, sai tasa ayi mun korar kare, so dole nayi hakuri, and watched you  tsawon lokacin nan feeling like ku din responsibility dina ne, I have to guard and protect you. Shiyasa nayi dedicating dukka komai na, just to be close to you and achieve this, gashi kuma nayi." "Oh Ya Allah! Ka shammace ni wallahi, Alhamdulillah. Alhamdulillah." "Won't you give me a hug?" Ya matso da hannun sa da ya bud'e. Ture shi Aryan yayi sukayi dariya a tare "Kana da matsala, deep down nasan yadda kake ji, amma you can't show it, haka zaka yi winning heart din Raihanan?" "Oh Ya Allah, ka dawo fa, shikenan na shiga uku." "Na dawo amma ba a Kamal ba, a matsayin Ahmad na dawo, kuma dole ne kabi duk umarni na, I'm your boss ka sani." "Na sani sir, kai ne ogan dama, shiyasa nake tuna maka office dinka yana jiran ka, lil bro need a break." "Baka isa ba, nayi yaya da aiki na?' "Please please, I'm tired wallahi." "Then tafiya Adamawa ta kama ka, kaje ka dawo da ita." "Wa?" "Babyn ka mana, a kalla zata rage ma loneliness din, sannan ta taya Ka aikin." "Daddy yana magana." Yace yayi gaba da sauri, dariya Kamal yayi yabi bayan sa, suka karasa wajen su Daddyn, Kamal ya rike saman Wchair din ya shiga tura Daddyn a hankali suka fito daga cikin kotun. A harabar suka hadu da Abby da Lamido jikin wata mota tsaye suna magana da wani lawyer, Lamido ne ya taho wajen su ya mikawa Kamal hannu suka gaisa sannan ya bawa Aryan hannu ya gaida Daddyn da Baba Rabi'u. "Congratulations Lt Kamal, I'm so happy for you." "Thank you sir, nagode for all your support." "Karka damu." "Aryan kula da Daddyn bari mu gaisa da Barrister." "Kuje tare, zan kula dashi." Baba Rabi'u yace "Ok." Suka bi Lamidon zuwa wajen da Abbyn yake tsaye. Har k'asa suka russuna suka gaishe shi ya amsa kadaran kadahan sannan yayi wa Kamal din murna, ya shige mota be kalli wajen da Aryan yake ba balle kuma su Daddy dake gefe suna kallon su. "Nasir yayi fushi da yawa." Baba Rabi'u yace "Ya chanchanci yayi fushi Rabi'u, baa kyauta masa ba, kuma an cutar dashi da yaran sa." "Kaima Yaya ai hakan ne, iya cuta kai ma an maka." "Still dai, amma shi be yi min ba, amma nifa, ban masa uzuri ba, na yarda da abinda aka fada min akansa bayan nafi kowa sanin waye Nasir, shi ko irin kule-kulen yan mata be yi ba, amma duk na manta na rufe ido na, na bi rudin shedaniyar mace ta kaini ta baro ni, ta raba ni da matata, ta raba ni da d'ana sannan ta raba ni da Yan uwana." "Allah ya kyauta, ka bar damun kanka kaga condition dinka, idan ka kara samun sauki sai kaje ka bashi hakuri har gida, Allah ma muna masa laifi ya yafe." "Haka ne kam, Allah ya yafe mana baki daya." "Amin ya Allah." "Malam Hassan dan Allah muje gida, a chan sai mu karasa maganar da zamuyi, dan Allah." "Ba damuwa Alhaji, amma me zai hana mu bari ka kara samun sauki, da an fadawa Kamalu zai kawo ni har gidan." "Um um, muyi dai yanzun, bamu san me zai faru gobe ba, dan Allah ka amince." "Ban ki ba dama Alhaji, dama na duba yanayin jikin naka ne, amma ba damuwa muje." "Yawwa Nagode kwarai." "Babu komai Alhaji, yanzu ai mun riga mun zama daya." "Haka ne." Mota suka shiga suka bar su Aryan din zasu biyo bayan su. Motar Kamal ya Nabeela ta shiga shi kuma Aryan ya shiga tasa yabi bayan su daga karshe. Gida suka wuce direct gidan yana nan a gyare tunda dama akwai masu aiki dake kaiwa da komowa a gidan. A falon k'asa suka zauna saboda daddy aka sake sabuwar gaisuwa tsakanin Daddy da Alhaji Hassan sannan aka dora akan maganar.  Har la'asar suna tare anan aka jere musu abinci suka ci sukayi sallah sannan Malam Hassan yace zai tafi amma daddy yace sam ba in da zashi sai gobe saboda yamma yayi, yayi yayi ya bar shi ya tafi amma yaki fafur dole ba yadda yaso ya hakura.   A gidan baki daya suka kwana, har Ya Nabeela ma da yaran ta, suna zaune ana cin abincin dare Adam ya shigo fuskar nan tasa babu walwala, ya shige su ya haye sama ba tare da yacewa kowa komai ba. Girgiza kai Ya Nabeela tayi Aryan ya kalle ta yace "Ehen?" "I feel bad for him." "Kai Ya Nabeela , tausayin ki yayi yawa wallahi." "No da gaske, be yi sa'ar mahaifiya ba." "Ni dai I don't feel anything for him, bana jin komai kuma ba zan taba ji ba." "Kai dashi dama baa shiri." "Babyna tana Kira." Kamal yace yana mikewa daga table din, tsaki Aryan yaja a hankali ya harare shi "Yaushe zata zo?" "Kinsan kwana biyu kenan da dawowar mu, so na barta a gidan su ne ta kwana biyu, amma bari muga ko gobe sai naje na dauka ta, dan nima na fara missing dinta." "Gaskiya ne, shiyasa kake burge ni, kamata yayi mu hada kanmu a waje daya gaba dayan mu wallahi, saboda mu rufe gaf din da muka rasa a childhood." "Wallahi Ya nabee, dama zaa yi hakan." "Dr ne matsalar kawai, ba zai yarda ba." "Eh gaskiya, but zamu iya samun area daya mu gina gida, nasan zai iya yarda da hakan." "Yes zan gwada convincing dinsa." "Kinga idan bana nan my wife ba zatayi zaman kadaita ba, ga kanin ta nan ta aike shi sannan ga big sis incase of emergency." "Wai ba zaka ajiye aikin ba? Ka dawo gida?" "Ba yanzu ba, akwai abubuwan da nake son nayi achieving." "Ok, best of luck kanina, Allah ya baka sa'a." "Amin, kinga ta kara kira, bari na daga kar nayi laifi." "Oya, Mr Romeo." Tunda suka fara maganar Aryan be saka musu baki ba, abincin sa yake ci hankali kwance kamar ma baya wajen. Sai da yaji sun kai karshe sannan ya ture plate din da yake gabansa, ya dauki tissue ya goge bakin sa ya mike rike da toothpick a hannun sa ya kalli Ya Nabeelan "Zan hau sama." "Ok, zaka watsa ruwa ne?" "No akwai abinda zan yi, zan sakko idan na gama." "Ok, bari naje na duba su Amna, nasa su suyi bacci." "Ok a shafa min kansu." "In sha Allah." Staircase din ya kama ya haye ya wuce bedroom dinsa yana shiga ya saka key dan baya so Kamal ya biyo shi bare yaga abinda zai. Kwanciya yayi rigingine ya jawo wayar sa dake jikin socket ya kunna ta ya shiga wajen contact dinsa yayi dialing number ta, gaba daya tsawon kwanakin nan tunanin ta yake sosai, komai yake sai ta dinga fado masa, kin kiranta yayi ko chat din yaga iyakar yadda zai iya daurewa. Abinda ya faru yanzu a dining yasa shi jin ba zai iya cigaba da pretending ba, dole ya kirata yaji lafiyar ta, sannan yaji yadda za'a yi ta dawo kawai domin hankalin sa ba zai taba dawowa daidai ba idan ba dawowa tayi ba. Ringing wayar tayi tayi har ta gama ta katse ba'a daga ba, sake kira yayi a karo na biyu duk da missed calls daya kawai yake yiwa mutum idan be daga ba shikenan amma sai gashi ya samu kansa da kira a karo na biyu hoping ta daga yaji zazzakar muryar ta me taushi da dadin sauraro.    Wayar Daadah ta jawo daga cikin blanket din da ta rufa mata bayan baccin ya dauke ta, wunin ranar a kwance tayi shi dauke da zazzabi me zafin gaske, wanda take yin shi dama lokaci zuwa lokaci. Tun yarintar ta dama haka take zazzabin ta me zafi sosai gashi har yanzu bata daina ba. Kamar baby haka take narke musu a duk sanda bata da lafiya suyi ta fama da ita dukkan su tarewa suka akanta suna bata duk kulawar da take bukata. Fitar Babbo Sadeeq kenan bayan bacci ya dauke ta saboda allurar da yayi mata Daadah na gyara mata kwanciyar kiran farko ya shigo, bata daga ba har ta katse da aka sake kira ne tace bari ta dauka taji waye. "Salamu Alaykum." Tayi sallama bayan ta daga, zaro wayar yayi daga kunnen sa da sauri ya duba number sosai ya tabbatar ita ya kira sannan ya maida wayar kunnen sa ya amsa sallama a hankali "Bata jin dadi ne yau da zazzabi ta wuni sai yanzu ta samu bacci, sai dai ka kira anjima idan ta tashi." "Ina wuni?" Ya gaishe ta dan bata bari sun gaisa ba ta hau yi masa bayani "Lafiya Lou, wa za'a ce mata ya kira?" "Aryan za'a ce mata Mama." "Toh toh, na gane. Shikenan zan fada mata." "Nagode Mama, Allah ya kara sauki." "Amin an gode." Ta ajiye wayar    Akan kirjin sa ya dora wayar bayan ta kashe, duk sai yaji hankalin sa ya tashi da aka ce masa bata da lafiya. Knocking aka yi a kofar, ya kalli kofar jiki a sanyaye ya mike, yasan ma waye yake knocking din yana budewa yayi baya ya matsa masa ya shigo. "Me ya faru?" Kamal ya fada yana kallon yanayin sa "Na gaji ne kawai, kai na kamar zai bursting." "Kana shan maganin ka kuwa? When last kaga Dr Mahfouz." "Umm... Kusan month kenan." "Drugs din naka sun ma kare kenan." "Abubuwa ne suka sha min kai wallahi, ba time kwata -kwata." "Amma lafiyar ka comes first, don't joke with it." "Tam, zanje da safe." "Good." Ya zauna a gefen gadon Aryan din yana karewa dakin kallo "Me kake nema?" Ware hannu Kamal yayi ya fada saman gadon yana kallon sama "Hoton mummy zaka bani please kanina." "A nawa?" "Ko nawa, zan siya saboda na mallake shi." Ya fada sounding so down idanun sa ma sun nuna yanayin da ya shiga. Takowa Aryan yayi ya zauna a gefen sa sai Kamal din ya mike yana kallonsa "Kayi hakuri, kowanne bawa da tasa KADDARAR. Imanin mumini baya taba cika har sai ya yarda da kaddara me kyau ko mara kyau." "Haka ne, thank you." "Bari na dauko maka album din, har na ranar sunanka akwai, mummy ta ajiye komai, tana sonka so me yawa." "Allah sarki, how i wish? Amma alhamdulillah hakan ma nagode Allah coz Ya bani iyaye masu matukar so da kaunata, masu riko da addini da amfani dashi, masu son duk wani farin ciki na a saman nasu.  Dole nayi Wa Allah godiya dan da Yaso sai ya barni a hannun baragurbin iyaye wanda zasu watsa min tarbiyya ta." "Alhamdulillah. Alhamdulillah." "Kasan me?" Aryan yace yana mikewa tsaye, "A ah." "You are my role model." "Wow! Da gaske?" "Da gaske, duk abinda nake kai nake kallo, you are just like a father figure to me." "Masha Allah, amma kake min rashin kunya." "Ahh, sanda ina boss dinka ne fa, amma na daina yanzu." "Yaro yaji tsoron hukuma, kaga tsaf zan saka a rufe min kai sai bayan Raihana tayi aure an kaita dakin ta." Fasa daukar album din yayi ya dago yana kallonsa "Why? So kake lallai sai ka kure ni ko?" "Yes, so nake kayi zuciya coz ina tabbatar maka idan Ka tsaya kallon ruwa kwado sai yayi maka kafa, which ba zan so hakan ta faru ba, please Aryan kayi abinda ya dace, kai ne yanzu kawai zaka iya dawo da rayuwar baya me cike da farin ciki." "Ta yaya zan fara? Bayan kana gani irin tarbar da na samu a wajen Barr. Nasir." "Ka kama zuciyar su mana, Raihana itace zuciyar ahalin nan, build your relationship with her, hakan dole zai saka su hakura coz farin cikin ta yana saman komai a wajen su." "Zan iya Kana gani?" "Why not? Don't you love her ne?" Shiru Aryan yayi yana jin yadda heart beat dinsa ya sauya lokaci daya "Please kayi abinda ya dace, dan Allah don't make a mistake da zai saka ka rasata." "But already kace tana da saurayi, no na ganshi ma da ido na ya kawo ta office ranar,har ta kirashi da Honey." Ya karashe muryar sa na nuna bacin ransa. Dariya sosai Kamal ya kwashe da, ya dinga tafa hannun sa yana dariya kafin ya tsagaita "Kaga ni ko?" "Menene na dariyar toh." "Baka ji yadda kayi sounding bane ba, man Ka tsaya watsa wallahi, ba ruwana." "Na kirata ma yanzu, sai wata babbar mata ta dauka tace min tana bacci bata da lafiya." "Ayya, shisa na shigo na ganka so down kenan?" "Ban sani ba." Ya ajiye masa album din a gabansa yana bata rai "Kasan me za'a yi, tafiya zamuyi kawai muje Yolan nan, zama ba namu bane ba, baa bori da sanyin jiki kar muje honey yayi mana shigar sauri." "Kana da matsala wallahi, shiyasa bana son fada maka abu sai kayi ta mocking dina." "Sorry oga Aryan, wasa nake maka amma dai zan siya mana ticket mu je , muyi dubiya sannan mu yada jam'iyar mu, yadda ka hadun nan da wuri zata fola amma sai ka aje girman head ka bud'e baki." "Ya Allah!" "Nan kuka gudo kuka bar ni?" Ya Nabeela da ta turo kofar ta shigo tace "Yanzu nake shirin zuwa wajen ki." Aryan yace "Nima hakan." "Album zamu kalla?" Ta karaso tana kallon hannun Kamal, gid'a mata kai yayi ya matsa mata gefen sa ta zauna Aryan ya zagayo ya zauna a dayan side din suka sakata a tsakiya suka shiga kallon album din a tare. _*RQ*_      Page 37 ***Wajen sha biyu da rabi bayan Ya Nabeela ta tafi, Kamal kuma ya fita falo yana waya da Khadija ya zama sai Aryan kawai wanda yayi shirin kwanciya ya saka kayan bacci ya kwanta a gadon hannun sa rike da wayar sa da yake ta faman jujjuya ta zuciyar sa na raya masa ya kirata. Baya so ya kira ya katse mata bacci ko matar dazu ta kara dagawa amma kuma yana son sanin ya jikin nata. Bin shawarar zuciyar sa kawai yayi ya kira ya saka wayar a handfree sannan ya dora ta akan chest dinsa. Cikin bacci Raihana taji ana kiran ta,zazzabin ya dan sake ta har ta tashi tayi sallolin da suka tsere mata ta dan sha yoghurt shine ta sake komawa. Cikin muryar bacci ta daga wayar tace hello, sai da yaja numfashi sosai ya sauke sannan yace "Bacci kike?" "Um um, na tashi." Ta amsa tana dan bud'e idonta kad'an. "Ya jikin naki?" "Da sauki." "I called you dazu, Mama ta dauka tace baki jin dadi." "Ok Daadah ce, da sauki alhamdulillah." "Sannu, Allah ya kara sauki." "Amin. Nagode." Shiru ne ya biyo baya, be san me zai kuma ce mata ba,amma kuma baya son ya katse wayar, "Sai da safe?" Tace jin yayi shiru "A ah, karki kashe please, ko ba zaki ce komai ba ki barta kawai." "Ok." Tace a sanyaye dan yadda take jin jikinta so weak bata da energy din da zata yi doguwar magana. Kusan minti goma wayar na kunne sun yi shiru suna sauraron bugun zuciyar juna. Turo kofar Kamal yayi ya shigo yana cewaa "Sai da safe babyna, bari na kwanta kar na makara." Dago kai Aryan yayi ya kalle shi yaga sanda yayi mata blowing kiss ta wayar sannan ya kashe wayar yana murmushi "Oh bakayi bacci ba wai?" Yace yana kunna hasken dakin sosai "Umm ban yi ba." "Ok bari na watsa ruwa na kwanta,babyna tana gaishe ka." "Naji." Dariya Kamal yayi ya wuce toilet "Oga Kamal ne?" Tace jin muryar sa "Eh shine." "Ya dawo ashe, ina ta kiran wayar sa switch off." "Ok, eh sunje umrah ne, shiyasa." "Ok zan kirashi mu gaisa, yana da kirki." "Nifa, bani da kirki?" "Umm." Tace tana turo baki, da sauri yace "Bani da kirki?" "Toh kai ne ai." "La'ila, shaidar da zaki min kenan." "Oga Kamal dai yafi ka." "Toh ni da wannan me kafar kamar mirkin lema, waye yafi kirki.?" "Wa?" "Ban san shi ba, wani da ya kawo ki office ranar." "Oh, Hamma Muhd?" Tace tana murmushi "Shi,Hamman ki ne?" "Eh, dan gidan Adda Maimunan mu ne, gidan da nake zaune a Kano." "Oh okh, na gane." "Ka ganshi ne?" "Eh na ganshi, kina masa murmushi." "Okh, bamu ganka ba." _"Ina zaku ganni kuna cikin soyayya."_ yace a ransa, a fili sai yace "Ni na ganku ai." "Waya kake?" Kamal yace yana fitowa daure da towel cike da mamaki "Umm, waya nake." "Da wa? A wannan tsohon daren?" "Ina ruwan Ka? Kai ma ba yanzu ka gama wayar ba." "Ni ai matata ce, kai fa? Bari naga sunan." Ya nufo shi, tashi zaune Aryan yayi da sauri yana hararar sa "Corper ce, shikenan." "Corper? Innalillahi wallahi yaron nan sam baka hadu ba, Raihana ce wai? Bani wayar." Ya fuzge yana dariya "Kanwata ashe kece?" "Sir barka da dare." "Barka dai, ya gida ya kwana biyu?" "Lafiya lou wallahi, nazo aka ce min kayi tafiya." "Eh wallahi, sorry ban fada miki ba, ya gidan?" "Lafiya lou." "Me yake ce miki da wannan tsohon daren?" "Ba komai." Tace tana murmushi "Karki yarda wallahi, haka kawai ya hanaki bacci shi ba wani abu zai fada miki ba." Dariya tayi k'asa k'asa, sannan tace "Toh sai da safe." "A ah karki kashe, bansan ko be gama fadar abinda zai fada ba, gashi sai da safe." Ya mika wa Aryan din wayar ya karba yana yin hanyar fita daga dakin. "Da kayi zaman ka ma, ni bacci na zan ba Jin abinda zaka ce zanyi ba." "Kana da matsala wallahi." Ya fice gaba daya, falo ya je ya zauna yana duba wayar sai yaga ashe ta kashe ma, tsaki yaja ya kwanta ya dora kansa a saman hannun kujerar ya cigaba da juya wayar, ko haushi taji dan yace mata corper? Dialing number ya sake yi amma sai yaji switch off, ya mike yana kashe tasa wayar ya koma dakin. Har Kamal ya kwanta ya rage hasken dakin, pillow ya dauka ya nufi kan sofa ya kwanta. "Har ka gama wayar?" "Bayan ka kore ta, ta kashe ai." "Toh akan me zaka hana yar mutane bacci, kai ba kalaman soyayya kake karanta mata ba, sai umm da a ah kawai." Juya bayan sa Aryan yayi dan ya cigaba da sauraron Kamal din tsaf zai tashi ya bar masa dakin. "Goodnight." Yace masa kawai ya ja duvet ya rufe har kansa. Dariya Kamal yayi ya ce "Sai da safe angon corper." ****Da safe Raihana ta tashi da karfin jiki, kafin ta gama shiryawa ta fito falo har Hamma Hydar ya shigo ganin ta, yana tsaye suna magana sai ga Babbo Sadeeq tare da Lamido, ganin jikin nata da sauki yasa su jin dadi suka mata sallama kowa ya wuce office. Dakin Daadah ta shiga bayan ta dan chachakali breakfast ta sameta tana yin sallar walaha, ta zauna ta jira ta idar ta juyo tana kallon ta "Nazo dazu kina ta bacci ai, ya jikin naki?" "Da sauki sosai." "Allah ya kara sauki, kinci abinci?" "Eh nasha tea." "Magungunan ki fa?" "Nasha suma." "Toh yayi kyau." Shiru tayi tana nazarin ta tambayi Dadahn ko kar ta tambaya, tana jin kunyar tambayar amma bata da wata kawa da ta wuce Daadahn dole ita zata tambaya. "Umm..Daadah." "Na'am?" "Misali, idan mutum yana kiranka yana nuna ya damu da kai amma be ce yana son ka, me yake nufi?" "Eh toh, kinsan kowa da yadda yake nuna soyayyar sa, amma dai duk wanda ya damu da kai toh alamu ne ko da be furta ba." "Ok." "Me ya faru?" "Dama Aryan ne..." "Kin tuna min ma, ya kiraki kina bacci." "Eh ya fada min." "Ok, ya sake kira kenan." "Eh." "Toh abinda nake so dake, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, sannan kiyi addu'a, saboda mahaifin ku ya dau zafi akan maganar da duk ta shafi gidan nan, amma kiyi addu'a nima zan tayaki, bamu san abinda Allah ya tsara ba." "In sha Allah." "Yawwa, karki tada hankalin ki, duk kuma abinda iyayenki suka zartar a kanki in dai be sabawa shari'ar musulunci ba toh kiyi musu biyayya." "In sha Allah Daadah, nagode." "Ah Lallai Raihanatu tayi hankali." "Kai Daadah." "Ja'ira, ashe kina son auren." "Innalillahi, shiyasa fa sai da k'yar na iya tambayar ki,nasan tsokana ta zaki." "A ah, murna nake dai, yarinya ta girma ta isa aure." "Shikenan na kad'e har ganye na." Ta tashi ta fice da sauri.     Missed calls din Muhd ta gani rututu ko da ta koma dakin ta, har yanzu bata yi masa reply din sakon sa ba, gashi sai sabani suke idan ya kira bata kusa, tausayi ya soma bata a kalla ko ba ta karbi tayin soyayyar sa ba ya kamata ta daga wayar sa taji. Kiransa tayi ringing daya ya daga kamar me jira "Alhamdulillah." Ya sauke ajiyar zuciya "Raihana wannan hukuncin yayi min tsauri." "Hamma ina kwana?" "Lafiya ba lou ba, kin sani tunani, nayi message no answer, kira no answer. Menene laifi na." "Kayi hakuri Hamma, bana jin dadi ne, amma na samu sauki." "Subhanallah, me ya same ki? Ban sani ba ai wallahi, sannu Allah ya kara sauki." "Amin zazzabi ne kawai ma kuma na samu sauki." "Kin tabbata?" "Eh." "Ok, Allah ya kara sauki. Zan shigo Yolan gobe in sha Allah." "Na'am?" Tace tana zaro ido "Eh, ko kar nazo?" "A ah ban ce ba." "Kiyi min addu'a, zanzo na ganki muyi magana face to face." "Toh, Allah ya kawo ka." "Amin nagode, please zan kiraki anjima karki ki picking dan Allah." "In sha Allah " "Nagode, sai na kira, I lov..." Kit ta kashe wayar ta jefar da ita gefe, ranta ne ya dagule musamman zuwan da yace zai yi, bata so yazo ya sake damalmala komai, tasan yadda ran Abby yake a bace yanzu zai iya yanke kowanne hukunci ma. Bata son shi ko na digo ba kuma zata iya son shi ba, bata tsane Shi ba amma dai, kawai be mata ba, musamman yadda yake magana ba, ba aji ba komai. Flight mode ta saka wayar dan ma kar ya sake kiranta. ***A tsakiyar falon suka hadu dukkan su dan yi breakfask saboda daddy ba zai iya zaman dinning ba. Ba zasu iya tuna when last sukayi irin wannan zaman ba. Aryan ne ya fito a karshe yana gyara links dinsa, ya karaso ya zauna a gefen Ya Nabeela sannan ya gaida Baba Hassan cikin girmamawa sannan ya juya ya gaisar da Daddy sannan ya Nabeela. Adam ne ya fito fuskar sa a hade yazo zai wuce shi daddy ya kira shi, dawowa yayi ya tsaya daga jikin kujera ba tare da ya russuna ba "Ba ka gan mu bane Adam?" "Sauri nake zan fita." "Kayi breakfast ne?" "Na koshi." "Yaushe zaka yi parking din?" Aryan yace yana kallonsa, duk sai suka dawo da kallon su kan Aryan din da yayi magana, yi yayi kamar be san suna kallon shi ba, ya dauki Irish Potato ya tura a bakin sa yana jiran amsar Adam din. Wani kallo yayi masa kafin yace "Idan kayi hakuri gobe zan tashi ai." "Good, ina jiranka." Juyawa yayi bayan yaja tsaki da karfi ya bar wajen. Kallon Aryan Daddy yayi irin kallon neman karin bayanin nan "Ni nace masa ya tashi." "Amma me yasa? Da Ka kyale shi ai tunda ba shine yayi laifin ba." Ya Nabeela tace, gid'a kai Daddy yayi shima yace "Ka kyale shi Aryan, be san ko ina ba sai nan, haka be san kowa ba sai mu, mune family dinsa mu kadai ya sani." "Ba zan iya cigaba da ganin sa ba, idan zai cigaba da zama anan ni zan koma wanchan gidan." Ya ajiye fork din ya mike, gefen rigar sa Kamal ya ja yaki kallon sa, mikewa yayi shima kawai yace "Ka kwantar da hankalin ka, zamuyi maganar please." "Me yasa zai cigaba da zama? Kasan me yake planing? Mahaifiyar sa ce fa ake magana, dole zai ga rashin kyautawar mu, kuma zai yi kokarin taimaka mata, ba zai yiwu muna tufka yana warwarewa ba." Ya fada a hasale, rike shi Kamal yayi yana girgiza masa kai "Karka sake daga muryar ka Aryan, waye yayi magana anan? Mahaifin mu ne sai Ya Nabeela, me yasa kake saurin hawa haka? Komai idan aka bishi ta hankali ai zaa fi cimma shi." "Fushi yake dani Kamal." Daddy yace muryar sa na rawa "Wannan ba daidai bane ba, baka kyauta ba kuma." Kamal yace Sakin hannun sa Aryan yayi yana matsawa nesa dashi, kirjinsa da yake harbawa da sauri da sauri ya dafe, ya runtse idon shi. Be san me ya hau kansa haka ba. "Are you ok?" Ya Nabeela ta riko shi tana kallon fuskar sa, girgiza mata kai yayi yana rike da kirjin sa "Kana shan maganin ka kuwa?" "Baya sha." "Zauna." Tace ta yi saurin dauko ruwa ta zo ta bashi, ya karba ya kafa kai ya shanye tas, sannan ya dafe kansa da hannun sa biyu. Malam Hassan ne ya taso daga in da yake zaune, yazo wajen Aryan din ya dafa shi, ya dago suka hada ido "Kar ka bari zuciya ta debe ka,ka aikata abinda zaka zo kana dana sani, su iyaye daraja ce dasu, kuma wajibi ne yin biyayya a garesu, kuma dole kayi hakuri dasu a duk yanayin da ka same su." "Bansan me ya hau kaina ba Baba, ban sani ba." "Na gane yanayin da kake ciki, amma dole ka sani baka da hujjar da zaka kare kanka ko a gaban Allah, iyaye sun wuce in da kake tunani." "Kuyi hakuri dan Allah, hakan ba zata kara faruwa ba." "Wannan itace tarbiyya, karka damu ka nemi gafarar mahaifin Ka sannan ka roki Allah ya yafe maka, ka zama me biyayya da danne zuciya, ka yawaita azkar zaka samu nutsuwar zuciya" "In sha allah." "Tashi muje ka karya, ka kuma nemi yafiyar mahaifin ka,komai ya wuce ku fara sabuwar rayuwa, domin kai ma Allah ya baka ya baka 'yaya masu jin kanka."    Falon me yayi shiru sosai sai karar AC kawai dake tashi a wajen, breakfast din ake amma kowa ransa babu dadi, Aryan dai jujjuya chokalin kawai yake ba tare da yaci komai ba. Dago idanun sa yayi da suka kad'a sosai ya kalli Daddyn "Dan Allah daddy kayi hakuri ka yafe min." "Na yafe maka Aryan, duk abinda kayi min kana sani da wanda baka sani ba, na yafe maka, nima ka yafe min halin da na jefa ka a ciki, dan Allah, kai yaro ne me biyayya, kuma ban taba saka ka ko na hanaka abu kayi ba, baka taba ketare umarni na ba, duk kuwa da tarin abubuwan ki da nayi maka." "Allah yayi muku albarka gaba daya." Hawaye Ya Nabeela ta goge a fakaice, wannan ranar na cikin ranakun da take burin gani a rayuwar ta, sai gashi ta gani yau, Aryan da Daddy sun shirya. "Ni baka bani hakuri ba." Kamal yace cikin sigar tsokana, dariya akayi dukka banda Aryan din, da ya mike yace zai ya hau sama, ya haye suka bishi da kallo dukka. _*RQ*_      Page 38 ***Tashi Ya Nabeela tayi ta kwashe kayan wajen da taimakon househelp suka kaisu kitchen, sama ta haura itama dan duba su Amna dan sun tashi tun safe sunyi breakfast dinsu sai tasa suka koma saboda an saba tashin wuri saboda school. Su uku ya rage a falon Malam Hassan yace wa Daddy zai tafi, duk da Daddyn be so ba amma dole ya barshi ya tafi amma da sharadin zai dawo nan kusa ya sake duba jikin Daddyn kafin su tafi. Shi ma kuma Daddyn zai zo har ranon da ya kara samun karfin jiki. Driver daddy ya kirawo yace ya shirya mota, dan da Kamal ne zai maida shi sai kuma Daddyn yace driver ya maida shi yana so zasu dan tattauna da Kamal din. Baba Rabi'u ne ya karaso ya kira Daddyn Kamal ya bud'e masa kofar tunda dole sai ta ciki za'a iya budewa idan basu yan gidan ba. Yana shigowa suka gaisa da Malam Hassan a sake sannan suka dingumo suka yo waje don rakashi, da waya Kamal ya kira Aryan yace yazo Baba zai tafi sai gashi ya sakko ya same su a compound din. Hannun sa zube a aljihun sa ya tsaya yana kallon su, daddy ya fito da Debit card dinsa karamin ya bawa Habu driver yace su fara tsayawa yayi ma Baban siyayya kafin su wuce. Godiya sosai. Malam Hassan yayi, ya zauna a gaban motar Kamal ya gyara masa rigar sa da ta dan fito sannan ya rufe masa kofar "Allah ya kiyaye hanya Baba, cikin satin nan zamu shigo in sha Allah." "Allah ya kawo ku,sai anjima Alhaji, nagode da karamci." "Ni ne da godiya, zan zo har gida ma in sha Allah." "Allah ya kiyaye hanya." "Amin Aryan, ka tabbata kaje kaga likita kaji?" "In sha Allah zanje." "Allah ya kara sauki." "Amin." Suka hada baki suka fada. Sai da suka ga fitar su daga gidan sannan suka juya suka koma cikin gidan. Saman Arya  ya haye, Kamal kuma ya zauna tare da Daddyn da Baba Rabi'u a falon k'asa. "Kaga dan uwanka ko Kamal?" "Daddy ayi hakuri dan Allah." "Ai ba laifi yayi min ba, ni tausayin sa nake kawai, yaushe zai yi farin ciki shima?" "Ya kusa daddy, in sha Allah kwanan nan zaka ga sauyi." "Ta yaya Kenan?" "Dama akwai maganar da nake son sanar dakai daddy." "Ina jinka." "Aryan yana son yar gidan Barrister Matawalle." "Raihana?" "Eh ita." "Tirkashi, a wannan yanayin da ake ciki? Kana ganin Nasir zai taba amincewa?" "Toh, shine dai ba zamu ce ba, amma dai zamu gwada. Shine kawai hanyar da za'a bi wajen dawo da tsohuwar alakar da take tsakanin ku Daddy." "Kayya, ban ki ta taku ba Kamal, amma Nasir yayi fushi, fushi me munin gaske, bana jin Nasir zai iya daukar yar sa ya bawa d'ana, abu me me kamar wuya,." "In sha Allah zai yarda." "Toh, shikenan amma dai, shikenan dai toh bari mu gani, ka bani number sa ina so na fara kiran shi ma dai, kafin naje har gida." "Ok." "Amma sai nake ganin kamar ya tsawwala, Allah muna masa laifi ya yafe mana, me yasa ba zai zama cikin masu yafiya ba?" Baba Rabi'u yace "Rabi'u ba zaka gane yanayin ba, ni bana ganin laifin Nasir, ko nine abinda zan yi Kenan, karshen rashin kyautawa an masa,." "Amma ai da sai yayi hakuri ko? Tunda dai yanzu kusan komai ya wuce." "Ba zai taba wucewa ba ai, tabon nan yana nan a zuciyar s, dan haka ni dai bana ganin laifin sa, idan ya amince ya yafe min ya kuma bawa Aryan Raihana toh, idan yaki sai Aryan yayi hakuri ya nemi wata." "In sha Allah ma zai hakura, in sha Allah." "Toh Allah yasa." "Bari muje muga Dr Mahfouz Daddy." "Ok, ya aikin naka?" "Ina hutu ne, karshen next month Zan koma watakila kuma ayi min transfer ma." "Toh Allah yasa muji alkhairi, da zaka bar aikin ka dawo ku cigaba da kula da companyn nan naku, Aryan kadai ba zai iya ba." "Yanayin aikin namu ne daddy, amma zan duba in sha Allah." "Yawwa, Allah ya baku sa'a, ya taimake ku baki daya yayi muku albarka." "Amin ya ALLAH."    Saman ya hau ya samu Aryan yace ya taso suje wajen Dr Mahfouz, be ce komai ba ya chanja kayansa zuwa jeans da shirt sannan suka fito tare. Kamal din ne yake driving Aryan na gefen sa, yaki cewa komai har suka karasa, suka same shi a office sukayi magana sannan ya kara rubuta wasu drugs din ya basu suka fito suka siya a pharmacy sannan suka dawo gidan. Suna dawowa gidan ya sha magungunan ya kwanta saboda wani irin azababen ciwon kai da yake, wanda yake da alaka da abinda ya faru dazu. Yayi regretting duk abubuwan da yayi, zafin zuciyar shi tayi yawan da yake kasa controlling dinta mafi yawan lokuta, sai yayi abu yazo yayi ta regretting. Dole sai yayi kokarin rage fushin sa idan yana son Jin dadin rayuwar sa. Fita Kamal yayi ya ja masa kofar ya nufi gidan su Khadija don dauko ta. ****Kamar yadda Muhd yace zai zo ranar, sai gashi ya iso da yamma. Raihana na daki Daadah tazo kiranta, dama tun jiya da ta kashe wayarta bata sake kunnawa ba. Ta dauka da wasa yake da yace zai zo, ashe da gaske yake. Kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu haka taji, ta bud'e wardrobe dinta ta dauko wani zumbulelen Hijab dinta tun na islamiyya ta zura sannan ta fito. Yana zaune a falon an kawo masa ruwa da abinci Dadah na gefen sa a kujerar sai Hamma Hydar da yake zaune a dayar kujerar suna magana. Da kallo ya bita ta kamar tsohon maye, ta turo baki ta hade rai ta zauna ta gaishe shi ya amsa yana kallon yanayin dake fuskar ta "Yasu Mama da Amina?" Tace kamar dole "Lafiya Lou, sun ce a gaishe ki, Amina taso biyo ni toh amma jibi zasu fara exams shiyasa." "Ok, Allah ya bada sa'a." "Har yanzu bakya jin dadi ne?" Hamma Hydar yace ganin yadda take magana. "Kasan sai a hankali dama jikin zai ware." Daadah tayi saurin kareta "Kin shanye dose din magungunan ki?" "Eh na shanye." "Nasan halin ki dakin magani, karki min karya." "Allah Hamma na shanye. Ko Dadah?" "Ta shanye." "Ya karfin jikin?" Muhd yace "Alhamdulillah." "Allah ya baki lafiya." "Amin." Sai ta mike "Karatu nake Daadah, bari na karasa." "Toh." Tace bayan ta gano ta tsaf zaman ne ba zata iya ba.   Tana shiga dakin ta cire Hijab din tana jan tsaki, bata son naci a rayuwar ta, menene na zuwa kuma? Kenan dadewa ma zai yi tunda yake maganar da zasu zo da Amina Amma jibi tana da exams, gaskiya zai takura mata zai shiga rayuwar ta da yawa. Cigaba tayi da kwanciya a dakin kawai dan ko fita bata son yi.   Falon Abby Hydar yaja Muhd domin ya gaishe shi, Abbyn na zaune suka shigo Muhd yayi saurin zubewa a k'asa ya gaida Abbyn ya amsa a sake sannan ya tambaye shi mutanen gida. "Duk kowa lafiya Abby, suna gaishe ku." "Madallah, sannu da hanya." "Nagode Daddy." Yace a ladafce. Wayar Abbyn ce kira ya shigo, Hydar ya dauko masa ya mika masa ya daga bayan ya kalli number "Assalamu alaikum." Daddy yayi sallama daga dayan bangaren. Wani irin dauke wuta Abby yayi, ya sake kallon number sannan ya saka wayar a handfree yana matsar da ita daga kunnen sa "Barka da rana Alhaji Nasir." "Da wa nake magana?" "Ibrahim ne Nasir, baka dau muryar ba?" "Wanne Ibrahim din?" Dan jim daddy yayi cikin yanayin ba dadi yace "Ibrahim Mukaddas." "Ok, ina sauraron ka." "Ya gida ya aiki?" "Kasan bana aiki ai, gida lafiya Lou." "Na kira ne na baka hakuri akan abinda ya faru..." "Muje Muhd." Hydar yace yana mikewa suka fita "Abinda ya faru ai ya riga ya faru, babu amfanin dawo dashi." Abby ya amsa bayan ya tari numfashin sa "Haka ne, amma dai ka daure ka saurare ni,nasan ban kyauta maka ba..." "Ina ganin da zamu jingine wannan maganar, kowa ya fuskanci rayuwar sa da yafi, gaskiya bana son dawowa da abinda ya wuce." "Na sani, na sani amma dan girma Allah ka saurare ni, akwai maganganu masu tarin yawa da nake so mu tattauna, sannan ka fuskance ni." "Ni ka fuskance ni sanda nake cikin matukar bukatar taimakon ka? Ka dubi halin da zan shiga da wanda iyali na zasu shiga? Ka tuna wannan? Ka kore su ka kwace musu muhalli sannan ka hau kan dukiya ta ka zauna daram." "Ko sisi ban taba maka a kudin ka ba, wallahi duk abinda Ka mallaka a lokacin yana nan, ya ninka kansa saboda kasuwancin da nake maka dashi." "Menene amfanin su, a lokacin da suke bukatar su me yasa baka neme su ka basu ba? Kasan wahalar rayuwar da suka sha? Kasan yadda akayi suka so nan?" "Ban kyauta ba, na sani wallahi ban kyauta ba, Dan girman Allah Nasir kayi hakuri ka yafe min, dan Allah." "Ba zan iya ba, ba zan taba yafewa duk wanda suka jefa rayuwata da ta iyalina a bakin kunci ba." "Ka saurare ni dan Allah." "Karka sake kirana dan Allah, ka rike girman ka na rik'e nawa, mun riga mun manyanta yanzu rayuwar yaranmu ce a gaban mu." Sai ya kashe wayar kawai yana kaiwa karshe. Dama dai Daddy yasan zaa yi haka, ko ma fiye da haka dan yasan iya karshen bata masa yayi, ya kuma cutar dasu. Baba Rabi'u dake kusa dashi a zaune ya girgiza kai kawai "Ina ganin ka barshi ya sake warwarewa." "Ba zan warware ba , kafin tafiyar nan zan aika yaran nan da komai da nasan nasa ne, bansan me Allah zai yi ba achan, ko rai zai yi halin sa, kar na mutu da hakkin sa." "In sha Allahu ma babu abinda zai faru, ka tura su din hakan ma shawara ce." "Abinda za'a yi kenan." "Toh maganar yaran fa? Wa zai shiga masa gaba?" "Rabi'u kana ganin Nasir zai saurare ni da maganar auren Yara? Ai a yadda ransa yake a bacen nan ba zan iya masa maganar ba." "Shikenan, Allah yasa muji alkhairi." "Toh Amin ya ALLAH."     ***Kwana biyu da zuwan Muhd duk in da Raihana tasan zata hadu dashi bata zuwa, zaman da take a falo ma ta daina sam ko yaushe tana daki idan akayi mata magana sai tace kawai tafi son zaman hakan ne. Hydar ne ya sanarwa da Abby dalilin zuwan Muhd din da izinin fara magana da Raihanan da yake nema a take Abby yace ya amince masa farin ciki fal zuciyar sa dan dama baya son wata magana ta taso akan Raihanan dan ba zai iya chanja alkawarin da yayi ma kansa ba. Har daki Hydar yazo ya sameta da maganar yace ta zo Muhd din yana falo zasuyi magana. Kamar wadda aka watsawa tafashshen ruwan zafi haka taji maganar. Ranta duk ba dadi ta sake zunbudo Hijab din ta fito babu kowa a falon, juyawa tayi ta nufin komawa Hydar ya kwala mata kira daga waje. Fitowa tayi yace taje falon su Muhd din yana chan yana jiranta. Zumburar baki tayi ba tare da ta bari ya gani ba, ta nufi shashen nasu fuskar ta a turbune tana cika tana batsewa haka kawai take jin wata irin tsanar shi na shigar ta, bata son naci gashi nema yake ta karfi da yaji sai yasa an mata dole.   Yana zaune ta shigo ya mike yana karyar da kai murmushi kwance a fuskar sa. "Alhamdulillah, tunda na samu Hydar ya fito min dake, wai Raihana gudu na kike ne?" "A ah." Tace a kufule "Toh bismillah, zauna magana zamuyi, kinsan fa dan ke nazo garin nan amma kike ta share ni." "Ni ba share ka nake ba, kawai bana jin dadi ne." "Wai har yanzu zazzabin be tafi ba?" "Umm." "Toh ko zamu koma asibiti." "Bobbo Sadeeq ne yake bani magani." "Oh na tuna fa Sadeeq likita ne, toh bari na masa magana ko?" "AI zan masa da kai na." "Ok, sannu, zamu iya maganar yanzu? Saboda gobe nake so na koma na bar aiki a gabana." "Kai na ke ciwo bana son yawan magana." "Toh, yanzu ya za'a yi?" "Nima ban sani ba." Shiru yayi duk sai yaji babu dadin yadda take amsa masa, wanda ta nuna masa clearly bata raayin sa, gashi shi kuma da gasken gaske yake son ta, har yana jin idan ya rasata zai iya shiga babbar matsala. Be zata abun zai zama haka ba, ganin yadda suka saba ta sake dasu sosai ya dauka da ya kawo kokon barar sa zata amsa. Toh ko dai tana da wanda take so ne? Ya tambayi kansa. Toh amma idan akwai ai Hydar zai fada masa. Toh ko dai be mata bane ba? "Raihana ko dai ban miki bane ba??" _"Eh."_ tace a zuciyar ta, amma a zahiri sai taki magana kawai ta cigaba da wasa da gefen Hijab dinta. "Ciwon kan ne?" "Umm." "Ok shikenan, ki koma ciki amma ki bar wayarki a kunne dan Allah, zan kiraki." "Toh." Ta tashi tayi ficewar ta,ba tare da taji komai ba, ko rashin kyautawar ta. Tana zuwa daki ta zare Hijab din tana jan siririn tsaki. _*RQ*_       Page 39 ***Kansa da ya kwanta luf ya kalla a cikin mirror sannan ya dauko designer perfume dinsa ya feshe jikinsa dashi. Kananan kaya ne a jikin sa brown chinos da riga long sleeve wadda ta dan matse shi kad'an. Ya gama saka two set na kayan sa a cikin suitcase dinsa. Turo kofar Kamal yayi ya shigo bayan ya dan kwankwasa. Dawowar sa kenan da ajiye Ya Nabeela da Khadija a gidan Ya Nabeelan ya gama shiryawa shima har ya karbi duk takardun da Daddyn ya bashi su kaiwa Matawallen. "Kar muyi missing flight muje ko?" Yace daga jikin kofar, "Ok." Aryan yace ya dauki wayoyin sa ya makala airdrop a hannun sa sannan ya shiga jan suitcase din tasa ya fito ya rufe kofar. A k'asa ya tarar da Daddy tare da Kamal a tsaye suna magana, ajiye kayan yayi a gefe ya karasa ya durkusa a gaban Daddyn ya gaishe shi "Har an fito?" "Eh." "Ok, Allah ya kiyaye hanya, Kamal ka dai ji me na fada maka ko? Akan wannan maganar." "Eh Daddy, in sha Allah zamuyi abinda kace." "Ok, sai kun dawo, Allah ya kiyaye." "Amin Daddy." Suka hada baki a tare.  Fita sukayi aka saka kayan nasu a booth sannan driver yaja suka nufi airport. Suna zuwa basu samu delay ba suka tashi sai Adamawa-yola. Duk abin nan Aryan be san daddy yasan da maganar shi da Raihana ba, be san Kamal ya gaya masa ba kawai a zuwan zasu je kai sakon Daddyn ne. Maganar da Daddyn yakewa Kamal din kenan dan yace kar su matsa idan yaki amincewa dasu suyi hakuri dan shi babu abinda zai iya.   Suna sauka a airport Kamal ya kira Lamido yace sun sauka, dama ya sanar dashi zuwan su tunda dama suna communicating, address din ya turo musu saboda lokacin yayi nisa baya kusa, sannan ya kira Raihana ya gaya mata akwai baki zasu zo amma sai yaji wayarta a kashe. Baya so ya kira daddy dan yasan yadda yake ciki dasu ita kuwa dadah wayar ta sai kayi ta kira bata dauka ba bata ma san anayi ba. Tunowa da yayi Muhd yazo kuma yana nan yasa ya kirashi ya sanar dashi baki zasu zo ya sauke su a falon baki kafin ya karaso, sannan ya tura wa Kamal din number Muhd din yace su kirashi idan sun karasa. Kasancewar zuwan su kenan na farko garin yasa suka dan samu delay kafin su isa, dan sai da suka fara neman hotel wanda yafi kusa da unguwar su Raihanan suka ajiye kayan su, suka huta ma sannan kowannen su ya sauya shigar sa zuwa manyan kaya fararen shadda rika da wando. Rigar Aryan irin 3quarter din nan ce me gajeran hannu, haka yake son rigunan sa mafi yawancin lokuta shi kuma kamal nasa tazarce ne har kasa ya fito a magidanci sosai me aure while Aryan kana ganin sa kaga matashin saurayi. "Dan Allah Aryan don't mess up, kaga dai abinda ya kawo mu, ba wai iya sakon Daddy bane kawai, munzo yada jam'iya ne, kayi abinda ya dace dan Allah." "Ni ai ban iya komai ba kasan." "Bance ba, kawai dai nasan halin ka ne, kar kaje kayi ma yarinyar mutane dunkum itama tayi shiru a rasa me magana." "Wai me ka maida ni ne?" "Me tsoron mata." "Hmm, toh ai shikenan." "Ko na rubuta maka abinda zaka ce idan kaje a waya? Sai ka faki idonta ka dinga karato Mata." Wata dariya ce ta tasowa Aryan din, gaba daya Kamal ya gama maida shi wani bita chan, shine har sai an rubuta masa abinda zai ce din? Dariyar da ya dade beyi irinta ba ya dinga kyalkyalawa, Kamal ya tsaya yana kallon sa da mamakin sa. "Allah ka ma maida ni wani iri, yanzu har sai na rubuta min abinda zan ce?" Dariya Kamal din yayi shima sai lokacin maganar ta bashi dariya "Toh ai kaine wallahi, nasan halin ka." "Hmm, toh muje dai, na matsu na ganta wallahi." "That's my guy, haka nake son ji, be romantic." "Muje toh, Mr Romeo." "Sunana kenan, ko kace laila majnun, yaro ba zaka gane ba ne, aure yayi wallahi." "Nifa kanin ka ne, don't spoil me." "Zaka ce na fada maka, muje." Ya dauki wayar sa dake saman gadon suka fito. Uber sukayi har unguwar tasu, sannan suka duba house number din suka tsaya a daidai date din gidan. Number da Lamido ya turawa Kamal ya kira Muhd yana ganin kiran ya fito waje ya same su, da kallo Aryan ya bishi dan be manta fuskar sa ba, sallama yayi musu suka bashi hannu suka gaisa sannan yace su shigo. "Wannan gayen shi na gani ranar fa ya kawo ta office." Ya fadawa Kamal k'asa k'asa. "Da alama a gidan yake shima." "Ok." Yace yayi shiru suka bishi ya bud'e musu kofar falon suka shiga sannan yace yana zuwa. Suna zaune ya dawo da bottle water da cup ya ajiye musu sannan suka sake gaisawa "Lamidon yana hanya ya kusa karasowa." "Ok mun gode, Alhaji yana gida?" "A ah, ya fita dazu." "Ok, Raihana fa?" "Tana nan." "Ok. Mun gode." Fita yayi ya bar su, kusan mintuna biyu da zuwan su Lamido ya karaso gidan. Sauri ma yayi sosai dan wani aiki yake gashi da nisa yake. Falon ya wuce direct ya same su, dan sun yi waya da Muhd yace sun karaso. Gaisawa sukayi da tambayar aiki tsakanin sa da Kamal sannan suka gaisa da Aryan. "Abubuwa biyu ne suka kawo mu Sir, na farko sakon me gidanmu ne yace a kawo wa barrister wasu takardu gasu nan." Ya daga envelope din, "Sai kuma magana ta biyu wadda na fara maka maganar a waya, maganar Aryan ce dama, munzo neman izinin a bamu damar ganin Raihana" "Ok,Masha Allah, abinda ya kamata muyi kenan bayan wannan case din, ina da niyyar ganin family dinmu sun hadu sun dawo kamar yadda muke a dah, yanzu kalli Aryan ni dashi kamar strangers haka ma Abby da Alhajinku. Dole muyi wani abu a matsayin mu na manya, duk abinda ya faru ya faru ne bisa kuskure,kuma bawa baya taba wuce kaddarar sa." "Naji dadi sosai daka fahimce mu sir, Allah ya bar zumunci, aikin yanzu na mu ne mu karasa shi dan dama mune muka fara shi, daddy bashi da matsala so yake ma Abbyn ya yafe masa laifukansa, ko ya samu ya karasa rayuwar sa cikin kwanciyar hankali." "Ka bar komai a hannu na, duk da nasan abu ne me matukar wuya amma dole zamuyi nasara a karshe." "Godiya muke Sir, Allah ya kara girma." "Yanzu mu shiga gidan ku gaisa da Daadah, sai muci abinci mu fita akwai wani abu da nake son nuna maka." "Ok sir." "Muje Aryan." "Ok." Suka bi kofar dake cikin falon wadda kai tsaye zata kaika cikin gidan. A main falon suka zauna ya shiga ciki ya kira Dadah yace tazo su gaisa da baki, ta fito tana tambayar su waye. Sai da suka gaishe ta sannan Kamal yayi mata bayanin su, aikuwa nan da nan ta hau murna. Ta tashi tace musu tana zuwa ta nufi dakin Raihana. Fitowar ta kenan daga wanka ta gama busar da dogon gashin kanta da hand dryer tana daure shi waje daya Daadah ta shigo. "Wai ke lafiyar ki kalou kwana biyun nan baki da walwala bakya sakewa ko yaushe kina daki, bayan mun riga munyi magana nace kiyi addu'a." "Hamma Muhd ne bana son gani, kuma kinga tunda yana gidan be kamata na dinga fita any how ba, kinsan ni da jin zafi bana son saka kaya masu kauri takura nake wallahi" "Toh yanzu sai ki tashi ki zura ko doguwar riga ce muje ki gaida baki a falo." "Baki akayi? Su waye?" "Idan kika fito zaki gansu." "Ok, bari na saka doguwar riga." Ta bud'e closet din ta, ta ciro wata doguwar ta zura ta dora mayafin rigar akanta da ta tufke jelar ta sakko ta bayan ta. "Ki dan kara fesa turaren ko?" "Nasa roll on fa Daadah, wannan wanne baki ne haka da har za'a ce nasa turare." "Zaki gani ai,maza fesa wanchan din chan sannan ki dan murza powder da lipstick." "Toh, ko dai Hamma Muhd ne yace kizo ki fito masa dani." "Kinji ki, maza dan Allah ni kin barni tsaye." Powder ta shafa kad'an tunda ita dama ba ma'abociyar powder bace ba, ta saka lipstick kadan ta murza lips din nata sannan tace "Yayi?" "Saura kwalli, bakwa san saka kwalli yaran yanzu, ido firkai firkai " "Kai Daadah." Ta dauki kwallin ta saka. Kallon ta Daadah tayi "Ya kunnen ba dan kunne?" "Daadah wai zance zani? Nifa dan kunne takura min yake." "Saka dai, ko kanana ne, mace sai da kwalliya." Bud'e wajen da take ajiye su tayi ta dauko ta saka. "Ko ke fa, muje toh." Tasa ta gaba suka fito. Dan corridor ne ya raba falon da dakin Raihanan. Dariya take suna magana da Dadah tana tsokanar ta kawai taga mutum a zaune, shine yake facing direct ta inda zasu fito sai Kamal da Lamido da dayar kujerar. Wani irin shock tayi, ta tsaya chak ta kasa karasawa saboda tsabar rud'ewa. Kasa k'asa yake kallonta, kallon da yasa taji kamar na bige mata guiwar ta, taji kamar ta juya saboda tsabar yanayin da ta shiga. "Raihana, karaso mana kika tsaya anan." Kamal yace yana mata murmushi. Da k'yar ta iya maida masa murmushin ta karaso ta zauna kusa da Daadah ta manne mata kamar zata shige jikinta ta gaishe shi. "Lafiya lou, ya gida ya kwana biyu?" "Lafiya lou sir, ina wuni Sir?" "Lafiya lou."  Aryan yace yana kallon centre table din dake gaban sa. Ganin ta gaba daya ya sauya masa lissafi, ga wani irin nauyin Dadah da take wajen kuma yasan kowa yaga irin kallon da yayi mata. "Mikewa Lamido yayi yace "Oga muje ko, Raihana ki kai mana abinci falon baki yanzu." "Ok." Tace ta mike da sauri tayi hanyar kitchen har tana hardewa. "Ba yau zaku koma ba amma ko?" "Eh sai sun ga Abby." "Ok, shima ya fita ne ya shiga gari, kila sai magriba zai shigo." "Ok Allah ya dawo dashi lafiya." "Amin." Ta amsa suka fita ita kuma ta bi Raihana kitchen din da sauri "A tsaye ta ganta jikin fridge bata taba komai a kitchen din ba, shigowar dadah tasa ta motsa ta kalleta tayi murmushi "Lallai dole yarinyar nan kiki dan uwanki,." "Kai Dadah, wai dama sune suka zo amma baki fada min ba, wallahi naji kunya." "Toh ba gashi kin gani ba, ni kuma naga abinda nake son tabbatarwa." "Nifa babu wani abu fa, ni ba ruwana wallahi." "Munafuka,ni zaki wa karya? Ban ga abinda ya faru bane ba? Maza wuce ki kai musu abincin kizo muyi magana." "Kai shikenan na shiga uku." Tace tana dora kayan akan wani babban tray sannan tasa plate uku da spoons ta dauka ta fita ta bi ta kofar da suka shigo din. Sallama ta fara yi a hankali ya amsa ta shigo kirjinta na faduwa. A tsaye yake dama tun shigowar su bayan su Kamal sun ce masa zasu dan je su dawo. Shigowa tayi tana kallon kasa, saura kad'an ta zubar da kayan hannun ta yayi saurin tarewa yana kokarin saka idanun sa a cikin nata da take ta kokarin boyewa. Sakar masa tray din tayi ya ajiye shi a tsakiyar falon. Juyawa tayi ta nufin barin dakin yayi saurin tare gabanta ya hanata fita. "In...a...wuni?" "Ai mun gaisa." Yace idon sa a kanta. "Gani a gidanku, nazo takanas na baki hakuri akan laifin da nayi miki." "Ai nace na hakura." "Ban yarda ba, me yasa kike avoiding idona." "Ni kawai, ba komai." "Oya, look at me." Dagowa tayi kamar munafuka ta kalle shi, tayi saurin maida kanta k'asa. "Please ki kalle ni... Yadda nake kallon ki." "Ba zan iya ba." "Are you shy?" Da ka ta amsa da eh ta juyar da kanta. Murmushi yayi me taushi sannan yace "Wannan gashin ki ne?" Da sauri ta juyo ta manta ma shaf bata rufe gashin ba ta baya, ta hau tura shi a cikin dan kwalin. "Rowa ake min? Idan kana neman aure ai ya halatta a barka ka kalla ko sau daya ne." "Aure?" Tace tana dagowa "Umm, aure. Ko ba zaki aure ni ba?." Bagatatan maganar tazo mata, dan haka bata ma san me zata ce ba, kamar wadda ruwa ya cinye haka ta yi tsit ko kwakkwaran motsi ta kasa yi. Tana jin idanun sa akanta. "Please, kice wani abu, will you marry me?" Hadiye yawu tayi da ya tsaya mata, ta daure tace "A ah." "Me yasa? Bakya so na?" "Nima ban sani ba?" "Ni na sani, amsar kuma yes ce." "La'ila,haka nace?" "Action dinki ne yace." "Karfin hali." Tace a zuciyar ta, haka kawai mutum kai tsaye be ce yana son ta ba, babu wata magana a tsakani sai yace ta aure shi? Haka akeyi dama?" "Zamuyi maganar a waya, karki kashe wayarki yau i will call you, zo ki zuba min abinci yunwa nake ji, sannan zan samu tea din nan?" Duk yana tafiya yake maganar ya karasa gaban tray din ya zauna ya barta a tsaye a wajen. Sai da ya kara maimaita abinda yace sannan ta karaso ta durkusa ta dauki plate ta soma zuba masa abincin cike da mamakin gut din sa. Tana ta zubawa yana kallon ta sai da ta cika sosai sannan ta ajiye masa a gaban sa ta saka spoon zata mike ya hanata "Wannan abincin ina zan kaishi? Ko tare zamu ci?" "A ah, ni naci abinci." "Toh ni ina naga cikin da zanci wannan abincin?" "Gashi nan." "Rage toh, idan ba haka ba sai dai ki zauna muci tare, ina ci ina kallon beautiful face dinki kinga bansan sanda zanci da yawa ba." "Na shige su." Tace a ranta, wai me yake damun Aryan din ne yau. Dauka ta sake yi ta rage ta ajiye masa a hankali yace "Wannan soft hands din naki, i can't wait to touch it again." Ai bata san sanda ta mike zumbur ba, tayi hanyar barin dakin da sauri, murmushi yayi ya dan daga muryar sa "Please ki kawo min tea din." Karasa ficewa tayi, tana fita ta dafe kirjinta da hannunta da yake wani irin harbawa, sai kuma ta samu kanta da yin murmushi. Salon sa daban ne a komai, maganar sa me sanyi da aji ta dinga yi mata yawo a cikin kunne. Kitchen din ta koma ta dauko kayan dafa shayin dan basa taba rabo dasu ta dora ta tsaya a kitchen din ta jira ya gama ta zubo a kettle din ta dauro cups uku zata fito daga kitchen din Muhd ya shigo ya tsare ta ransa a bace. "Waye wannan da yazo?" Ya tambaye ta yana kallon kayan hannun ta "Oga Kamal ne da Aryan, na wajen da nake PPA dina." "Amma sune har sai sun biyo ki har nan? Me suka zo yi toh?" "Waje na suka zo? Wajen Hamma Lamido suka zo ai, sun san juna tun da Baban su abokin Abby ne." "Wanda ya zalunci Abby ya tarwatsa muku rayuwa shine har zaku kawo su cikin gidan nan har kina dafa musu tea zaki kai musu?" "Hamma, ni menene nawa? Sani fa akayi." "Still dai, a gabana baban su ya kira Abby ya kuma ce ba zai taba yafe masa ba, amma me zai kawo yaransa gidan nan just two days da maganar, tun farko ma be kamata ku tarbe su ba." "Wannan dai toh Hamma Lamido zaka fadawa tunda shi yace suzo, ya kuma san abinda yake faruwa da Daddyn yace su zo din." Ta wuce shi zata fita yayi saurin tare kofar "Ba sai kinje kin kai masa ba, bani na kai." "Please Hamma ka matsa na wuce." "Why? Saboda kina son shi ko me?" "Zan wuce please." "Sai kin fara sanar dani amsata, kwana nawa ina binki kina min hanya hanya, akan ki na bar aiki na nazo garin nan, duk baki gani ba, amma wasu daban da suka wulakanta mahaifinki kin saurare su har kina dafa musu shayi, sai ki sanar dani nasan matsayata." "Me yasa kake irin wannan maganar?" "Kin fi kowa sani, kinsan komai tunda ke ai ba yarinya bace ba." "Me yake faruwa ne anan?" Daadah da tazo wucewa ta dan jiyo su ta karaso da sauri "Ya tare hanyar wai ba zan wuce ba, ni bansan me nayi ba." "Daadah shayi ne ta dafawa bakin chan, shine nace ta bani na kai musu da kai na ba sai taje ba." "Me yasa ba zan je ba? Me yasa zai hanani zuwa?" "Saboda gaba nake dake."   Yace cikin bacin rai da kishi dan gaba daya ya kasa controling kishin sa, dan ya dan saurari wasu maganganun da yaji Aryan din yanayi, abinda ya tunzura shi kenan ya biyo ta. "Bashi ya mika musu toh ke Raihana, bashi kiyi hakuri." Akan deep freezer din kitchen din ta dire masa, ta fice daga kitchen din da sauri. Bin ta Daadah tayi shima ya fice daga kitchen din ba tare da ya dauki kayan ba, ya nufi falon da Aryan din yake ciki. _*RQ*_       Page 40 ***Babu sallama ba komai ya fada ciki,fuskar sa a tamke. Dagowa Aryan yayi jin an shigo ganin wanda ya shigo yasa shi cigaba da abinda yake ba tare da ya bada wani attention din sa ba, tunda shi sam guy din be masa ba dama tun farko. "Malam magana nazo muyi." Yace ganin Aryan din ya share shi "Pardon?" Ya fada yana tsayawa da danna wayar da yake yi ya kalle shi a kaikaice "Naji duk abinda kace da duk take taken ka ma, Raihana tawa ce ni zan aureta, tunda gida be koshi ba, ba za'a bawa dawa ba." Kamar be ji abinda yace ba, dan idan ya motsa sanadin maganar Muhd din toh wajen nan ya motsa. wani kululun abu ne ya tsayawa Muhd din na wulakancin Aryan din,. "Lallai ma, Malam magana fa nake maka." "Oh haba? Ban ji abinda kace ba ko zaka iya maimaitawa." "In maimaita?" "Yes please, ina jinka." Ya zare airdrop din kunnen sa ya juyo yana bashi attention dinsa "Wasa kake wallahi,na maimaita kamar bani da abun yi? Na tabbatar kaji abinda nace kawai dai ka nuna..." "Hello baku kusa ba?" Ya d'aga wayar sa kamar ba magana Muhd din yake masa ba, "Ok, ni zan wuce ma hadu a chan." "No sai mu dawo ko bayan magriba ne, ko ka dawo kai kadai." "Ok." Ya katse wayar yana mikewa, ya dan kalli gefen da Muhd din yake a tsaye yace "Sai anjima Malam, ka dan shiga da kayan ciki." Ya fice ya barshi da tarin bakin ciki, tunda yake ba'a taba ci masa mutunci irin yadda Aryan din yayi masa ba. Rasa me ma zai yi yayi, ya dinga zagaye a dakin yana jin kamar ya bishi ya shako shi ko dai yayi masa wani abun da zai ji haushi sosai. Kafa yasa ya daki kujerar dake kusa dashi ya juya ya koma cikin gidan.    Kuka Raihana ta fashewa da Dadah, kukan bakin cikin abinda yayi mata. Iyakar kureta yayi ya kaita karshe. Ba haka ake ba, bata taba jin inda ake soyayya dole ba, tunda ta nuna masa bata so me yasa ba zai hakura ba, har zai wani zo ya sakata a gaba kamar wani ubanta. Hakan da yayi ya kara mata tsana da haushin shi a zuciyar ta. "Kiyi shiru haka na, kinsan zuciyar yan maza da kishi, kishi ne yake dawainiya dashi." "Toh fisabillillah amma ya dace ya saka ni a gaba yana titsiye ni? Naga ai ba'a dole ko?" "Ba'a yi, kiyi masa uzuri da ciwo kana son mutum yana shareka sai kaga wani yazo an kula shi, ko waye kuma dole yaji haushi, kawai kowa da yadda yake nuna fushin shi ne akan kishi, ni tausayi ma yake ban, son masu wani akwai wahala wallahi, be yi sa'a ba sam." "Baki ga yadda yake min fada ba Dadah?" "Na gani, menene toh? Hakuri zakiyi." Wasu hawayen ne suka sake biyo fuskar ta, har ga Allah taso kaiwa Aryan tea din nan, duk da tana jin nauyi da kunyar sa, tasan a yadda Muhd din yake cikin fushi da k'yar idan ba zuwa zai ya gaggaya masa magana, tasan kuma fushin Aryan zai yi yin zuciya ya tafi ma gaba daya. Dalilin kukan ta kenan, da k'yar Dadah bata baki tayi shiru sannan taje ta wanko fuskarta ta dawo dakin ta bud'e bedside drawer dinta ta ciro wayarta ta kunna ta, fita Dadan tayi ta ja mata kofar. Wani tunani ne yazo mata ta tashi ta fita, ta shiga kitchen din sai taga kayan tea din a ajiye akan freezer din, babu alamun an taba su daga yadda ta ajiye su. Falon chan ta nufa tayi sallama jin shiru baa amsa ba yasa ta tura kofar ta shiga, baya nan da dukkan alamu ma tafiya tayi, da sauri ta juya ta koma cikin gidan tana kwalawa Dadah kira. Dakin ta, ta shiga ta samu Hamma Muhd din a zaune idonsa ya yi ja sosai suna magana da Dadah, juyawa tayi da sauri ta koma dakin ta, ta shiga number sa tayi dialing. Alwala zai yi yana nannade hannun rigar sa kenan wayar sa tayi kara, daga in da yake tsaye ya leka wayar yaga me kiran. Ganin itace ya sakashi tsayawa da abinda yake yi, ya mika hannu ya dauki wayar sannan ya zauna a gefen gadon ya d'aga. “Hello.” “Hi, ka tafi?” “Yes,na tafi. Baki kawo min tea din ba.” “Nazo naga baka nan.” “Kinyi latti, amma zan dawo anjima. Ki ajiye min idan nazo sai ki bani nasha.” “Ok.” Tace tana sauke ajiyar zuciya jin muryar sa tar alamun babu abinda ya faru tsakanin sa da Muhd, amma kuma me yasa ya tafi haka kawai ba sallama? “Don’t think hard, wani abu ne urgent ya taso min Shiyasa ana tafi.” Yace jin tayi shiru yasan kuma dole tunanin da take kenan, idan ba haka ba ma yasan da wuya ta kirashi. “Sai anjima tom, sai ka dawo.” “Ok see you then.” Ya ajiye wayar, dan sosa kansa yayi yana son figuring abun baki daya, dama tun farkon ganin muhd yasan son raihana yake, ya kuma sakè tabbatarwa yau, sai dai be sani ba, mutual relationship ne ko one side? Sannan menene stage din da suke kai, baya son yayi abu da ka Shiyasa be biye masa ba duk da yayi masifar mata masa rai amma ya danne dan ba a irin sa yake bata energy da yawon bakin sa ba, ko Adam sai yayi masa abu sau nawa amma sai yaga damar kallon sa ma, ko ya bashi amsar da zata dade tana sosa masa rai. “I need to find out ko ma menene.”    Tafiyar da Aryan yayi yasa Kamal ma yace zai wuce kawai zasu dawo idan Abbyn ya dawo da magriba, sauke shi Lamido yayi a kofar hotel din sannan ya juya ya tafi gida. Knocking yayi a kofar Aryan yazo ya bude dan yasan shine , matsa masa yayi ya shiga yana kallon shi daga shi sai gajeran wando babu ko riga a jikin sa, shiryawa yake Kamal din ya dawo Shiyasa. “Fita zakayi ne?” Yace yana kare masa kallo “A ah, ruwa na dan watsa kaji garin zafi da na dawo alamun zaa iya yin ruwa.” “Eh akwai hadari da alama.” “Kun dade, ina kuka yi ne?” “Aikin mu ne, baa ji.” “Oh okh.” “Me yasa ka dawo wai? Nayi mamaki da kace zaka dawo.” “Aikin mu ne, baa ji.” Ya kwaikwayi same amsar da Kamal din ya bashi ya fada. “Haha, kana da matsala. Please fada min menene?” “Gayen nan ne, wanda ka kira shi da muka karasa gidan, yazo yana faffada min maganganu, ban ma dai saurare shi ba, ganin zai bata min rai ya tunzura ni yasa na taho kawai.” “Muhd, munyi maganar sa da Lamido. Cousin dinsu ne kuma saboda raihana yazo gidan takanas daga kano. Infact har Abby ma yasan da maganar kuma yana supporting dinsa sosai da hydar ma.” “I know, dole kayi mentioning hydar a karshe. It’s like kamar yafi kowa daukar zafi akai, da ni ma yake fushin naga alama.” “Eh gaskia. Shima irin ka ne da Zafin zuciya sannan abinda ya faru a office da kana ma raihana fada da Ya gani ya sake lalata komai.” “Yes na tuna, har yana cewa sai nayi nadamar abinda nayi mata. Amma ai na bata hakuri ta hakura ma. Shi menene Nasa?” “Gani yake baka dace da ita ba ko? Kamar zaka wahalar musu da kanwa.” “Hmm. Zan bashi mamaki. Shi zan fara kira nace yazo ya rakamu asibiti idan nayi ma kanwar tasa ciki.” “Hahaha! Kai ko? Baka fa da m wallahi aryan.” “Toh Allah ya zafafa da yawa. Ni kuma da gaske nake ba wasa nake ba, yadda mukayi ta rigima a kanta da yarinta shi yake so mu dora, ya manta ko da din nike winning, cox ni take zaba akanshi.” “Match made in heaven kenan.” “I’m serious, ni da shi ne.” “Ba kara? Soon to be in-law dinka ne fa.” “Lamido ba? Da sadeeq amma hydar sam. Su karata shi da dan iskan yaron chan da Ya gama gaggaya min magana.” “Yanzu dai haushin Muhd takwaran ka, zaka huce shi akan hydar.” “Duk su karata.” “Yanzu duk ba wannan ba, yadda zaa shawo kan Abby ya amince kawai ake nema, Lamido yace kafin mu koma anjima zai fara masa maganar, idan yaso sai muje masa muma da maganar.” “Ok. Go ahead dinsa kawai nake nema. Shi yasa nake bin komai a sannu saboda hakan shine daidai.” “In sha Allahu komai zai zama normal. Ka fara babbar magana ai dole ayi abinda Ya dace.” “Kar ayi ma.” Yace yana murmushi. Shi kansa maganar tashi ta bashi dariya. *****Fada sosai Abby yake wa Lamido, ta in da yake shiga bata nan yake fita ba. Tun da ya same shi da maganar zuwan nasu da kuma maganar raihana ya saka masa full stop dan baya son zancen ma. Da kyar aka samu yayi shiru da fadan ya zauna yana huci. “Kira min ita maza, idan bata da hankali ni Ina dashi. Idan kuma zaku nuna min iyakata ne toh.” “Ba haka bane Abby. Suna son junan su ne wallahi, mu kuma farin cikin ta muke nema.” “Kana nufin na dauke ta na kaita gidan nan? Kana da hankali kuwa Lamido? Ko dai girman ne kawai na hankali!?” “A ah, Allah ya huci zuciyar ka. Kayi hakuri.” “Sa waya ka kirata tazo maza ta same ni, akan wannan maganar zan yi mummunan sabawa kowa wallahi, har kai din kuwa.” “Ayi hakuri Abby. Kanwata Kizo Abby na son ganin ki.” “Tunda ita shashasha ce bata da hankali. Mutumin da ya wulakanta ku, Ya kore ku daga gida Ya kwace muku komai , shine dan rashin hankali zaka dauki kanwar ka, ka kaita gidan tayi rayuwar aure. Lallai kuwa sannun ka.” Shigowa tayi kamar Munafuka ta zauna daga bakin kofar ta gaida abbyn ya amsa a ciki ciki sannan yace “So nake ki fitar da miji, idan kuma babu kowa ni zan zaba miki mijin. Sati daya kuma yayi yawa na daura miki aure. Daki saka ni bacin rai gwara Kiyi na dan lokaci ne.” “Abby dan Allah kayi hakuri,wallahi ni ba wanda nake so.” “Karya ne, ba yaron nan Aryan kike so ba? Kin dauka ban sani ba? Bayan ni dake munyi magana na gaya miki bana so amma baki ji ba, shine kika cigaba da kulashi har yayan ki yana da bakin zuwa yayi min maganar bayan duk abinda Ya faru dashi ne akayi komai.” “Abby dan Allah kayi hakuri.” Ta fada muryar ta na rawa dan har ta soma kuka. “Naji, wa kike so toh?” “Ba kowa.” “Har Aryan din?” Shiru tayi, ya kara maimaitawa Amma batayi magana ba sai kuka da take yi “Kira min Muhd maza yazo yanzu.” Tashi yayj zai fita abbyn yace “Baka da number shi ne? Ka kirashi mana.” Dawowa yayi ya zauna ya kira muhd din yace yazo. Ko minti daya baa yi ba sai gashi. Ya durkusa ya gaida Abbyn “Kana son raihana?” “Naam?” Ya d’ago da sauri “Da gaske kake kana sonta zaka aurerà kuma?” “Eh Abby.” “Shikenan, zan kira Alhaji Kabir din muyi magana, na baka raihana nan da sati daya zaa daura muku aure.” *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ _*RQ*_      Page 41 Wani irin k'amewa Lamido yayi saboda yadda maganar ta bige shi, aure kuma? Aure a sati daya? Juyawa yayi da sauri ya kalli wajen da Raihanan take zaune, ta chusa kanta a tsakanin kafafunta, tana kuka sosai duk da ba'a jin sautin kukan nata. Sake maida da kallon sa kan Abbyn yayi sai ya hangi tsananin tashin hankali da damuwa cike a idon sa. Yanayin sa ya nuna irin na wanda yake tsoron wani abu wanda ya sha matukar wahalar sa. Sauke kansa kasa yayi dan be kuma san me zai ce ba. "Ku tashi ku bani waje." Yace yana zama cikin kujerun falon. Muhd ne ya fara ficewa da sauri, sai Lamido da ya kama hannun Raihana ya mikar da ita dan ko motsi ta kasa yi. Suka fita a tare Abbyn ya bishi da kallo. Me yasa soyayya zatayi masa haka? Me yasa a duk fadin duniyan nan zata rasa wanda zata so sai dan gidan mutumin da yake jin baya burin zama inuwa daya dashi balle har wani abu ya hada su. Mutumin da ya ruguza masa rayuwa ya lalata komai. Ya gwammace yayi mata auren yasan dole dole zata hakura ta zauna wataran tunda shi ma Muhd din bashi da makusa ko kad'an, sannan a kalla shi na gida ne. Duk da a k'asan zuciyar sa yana cike ds tausayin ta amma kuma ba zai bari ta cutar da kanta ba, dama musulunci shi ya bawa damar zaba mata miji a yanzu, dan haka zai yi iyakar kokarin sa wajen ganin be barta ta cutar da kanta ba.   Dadah na zaune suka shigo, ta mike da sauri dan dama tunda taji kiran nan tasan na lafiya ba. "Menene ya faru?" "Hmm, ita da Abby ne." "Laifin me tayi masa?" "Maganar Aryan ce dai, yace ba zai bashi ba, har ma ya sanar da Muhd ya shirya sati me zuwa za'a daura musu hannu." Salati Daadah ta rakfa tana rike Raihanan da take kuka wiwi. "Anya wannan hukuncin kuwa? Anya Ibrahim?" "Sai hakuri, nasan ba lallai ya sakko ba tunda yayi wannan hawan." "Kowa yasan ba'a kyauta masa ba, kuma yana da duk right din da zai yi fushi, amma ya za'a yi da hukuncin Allah? Rabo ba kisa yake fa, wallahi har lahira." "Bari na je masallaci, naji ana kiran sallah." Ya juya ya fita. Rike da hannun Raihanan suka wuce dakin ta, tana zuwa ta kwanta a gadon ruf sa ciki tana cigaba da gursheken kuka. "Wallahi Daadah bana son shi, wallahi bana son shi ko kad'an zan mutu idan aka daura min aure dashi." "Rufe bakin ki, kiyi shiru. Zan tursasa Lamido lallai ya hanashi abinda yake niyya, idan kuma yaki ni nasan ta in da Zan bullo masa, itama Maimunan zan kirata zan ce ta bawa Muhd hakuri, yayi hakuri dan ba'a aure haka, ba zai yiwu ba." "Dan Allah dadah karki bari yayi min auren dole, wallahi bana son shi." "Daina kukan toh, ba sati daya yace ba? Barni da su." Share hawayen take kokarin yi amma sam yaki tsayawa, da ta share sai wani ya hau zubowa. ***Ana kiran sallar magriba suka shigo unguwar, basu karaso gidan ba suka tsaya a masallacin kan layin suka fara yin sallah sannan suka nufi gidan. A kofar gidan suka tsaya kamal ya kira Lamido yace masa sun karaso Amma be daga ba, suna nan a tsaye sai gasu sun dawo daga masjid din tare da Abby, da Babbo Sadeeq da shima dawowar sa kenan ya tsaya sallar. Abby be lura dasu ba ya shige gidan sai Lamido da Sadeeq suka karaso wajen su, suka gaisa da Sadeeq din sannan Lamido yace su shigo gidan. Duk da yana cike da tsoro da taraddadin irin karbar da Abbyn zai musu amma kuma ba zai ce kar su shigo ba, dole dai zasu shigo din su ganshi tunda suna tafe da sakon Daddyn.    Ya zauna kenan yana son kiran mijin Adda Maimunan sai gasu sun shigo da sallama Lamidon na jagorantar su, suka zube a tsakiyar falon nasa cikin girmamawa suka gaishe shi. Ajiye wayar yayi ya fasa kiran ya amsa gaisuwar tasu babu yabo babu fallasa. Kamal ne ya dan sake russunawa ya mika masa envelope din da Daddyn ya basu sannan yace "Daddy ne yace mu kawo maka wannan sakon, jibi zasu tashi idan ya dawo in sha Allahu zaizo takanas har gida kuyi magana." "Menene a ciki?" "Sako ne dai, yace idan Ka duba zaka gani." "Ok, karbi Lamido, ka mika min shi cikin daki ka saka shi kasan drawer." "Ko na bud'e maka ka gani?" "A ah, kayi abinda nace kawai." "Ok." Ya tashi ya shiga ya kai masa ya saka a inda yace sannan ya dawo. Still dai Kamal din ne ya sake yin magana akan abinda ya kawo su na biyu, Abbyn na jinsa sarai sai da ya gama sannan yace "Sai dai kuyi hakuri Raihanan dai na riga nayi mata miji, sati daya ya rage a daura auren. Sai kuma me yake tafe daku?" Shiru sukayi gaba daya tamkar ruwa ya cinye su, Aryan da ya rasa a wacce duniyar yake saboda yadda yaji tana juyawa dashi ga wani irin abu da ya zo nan da nan ya tokare masa makoshi. Zufa ce ta shiga karyo masa ta ko ina da wani irin faduwar gaba. "Akwai wani abun ne kuma?" "Babu komai Alhaji, mun gode Allah ya kara girma." "Amin, na shiga ciki idan kun gama ku gaida gida." Ya mike yayi shigewar sa ya bar su a wajen. "Muje falon chan muyi magana Kamal." Lamido yace bayan tashin Abbyn. Aryan ne ya fara mikewa ya fice da sauri, sai suka bi bayan sa suma. Zuciyar sa ce tayi zafin gaske, irin wadda bata taba yi masa ba, ga wani irin ciwo da take masa irin wanda yake fama a duk lokacin da ya tuna ya rasa abu me muhimmanci a rayuwar sa. Niyyar sa kawai ya fice daga gidan, ya bar garin ma baki daya a daren dan a yadda yake ji komai zai iya faruwa. Amma sai Kamal yayi saurin tare shi, yace su tsaya suyi maganar dan Allah. Be iya bud'e baki ya amsa ba, sai bin su kawai da yayi ciki wanda ya tabbatar sai dai ya zauna kawai ba dan zai gane abinda suke cewa ba. A tsaye ya tsaya bayan duk sun zauna Lamido ya kira Sadeeq a waya yace ya zo sannan yace da Aryan din ya zauna dan Allah. Be magana ba yaje ya zauna ya dafe kansa kawai. Sadeeq din ne ya shigo ya zauna a gefen Kamal yana kallon Lamidon "Me yake faruwa ne? Yanzu nake samun labari a cikin gida wajen Daadah, ga Raihana chan kuka kawai take wallahi." Da sauri Aryan ya dago, dan be yi tunani ace masa tana kuka ba, ya dauka ma abinda ya faru da izinin ta ne, ko kuma da yardar ta. Kenan auren dole zai mata? Saboda kawai laifin da Shi bashi ne ya aikata ba, idan aka duba ma yana cikin wanda abun ya shafa. "Wallahi Sadeeq issue din ne babba ne, kasan haka kawai Abby baya fushi kuma ko yayi ma baya lasting, amma akan maganar nan wallahi baka ga ni kaina yadda yayi min kacha-kacha ba, sannan ya yanke hukuncin nan." "Subhanallah, abun yayi tsamari gaskiya, ni wallahi kasan rashin zaman da banayi ba komai nake sani ba, amma yanzu ya za'a yi? Baka ganin mu sake samun sa dai da maganar" "A yanzu dai ba zai yarda ba wallahi." "Ina ganin mu bari zuwa da safe,ko?" Kamal yace "Eh hakan dole za'a yi, amma please Aryan ka kwantar da hankalin ka, in sha Allah komai zai wuce, shaanin aure dole ne sai anyi irin wannan." "No ba komai." Yace kamar har zuciyar sa haka ne, nan kuwa abinda yake ji yayi tsanani sosai. "Oga bari mu wuce, zamuyi waya kawai." A tare suka tashi zasu fita, Lamido ya tsayar dasu ta hanyar kiran Aryan. "Please ina zuwa." Tsayawa sukayi, ya bi kofar cikin gidan ya shiga ciki, ya wuce kai tsaye dakin Raihana. Har a sannan bata daina kuka ba, ita kadai tasan abinda take ji idan har ta tuna aure za'a mata auren ma na dole, da k'yar tayo alwala tayi sallar magriba shine take zaune har lokacin akan sallamar tana cigaba da kukan bakin ciki. Tsayawa yayi daga kofar yana kallon ta, kallo me cike da tausayawa, baya son duk abinda zai bata mata rai, yana jin kamar idan suka sakata kuka be rike kalaman karshe da Ammy ta fada masa ba, akan yan uwansa da kula dasu, shiyasa be taba bari tayi kuka dashi ba, ba ya jin kuma zai iya zuba ido ta cigaba da zubar da hawayen. "Taso." Yace mata, sai a lokacin tasan yana tsaye a wajen. Dagowa tayi tana kallon sa yayi mata alamar ta tashi, ta mike da k'yar, ta karaso wajen da yake tsaye. "Please ki daina kukan nan kinji?" "Hamma Abby baya so na." "Yana sanki mana, duk abinda yake yi a yanzu saboda son naki ne." "Toh ni bana son Hamma Muhd, wallahi bana son shi." "Aryan kike so?" Da sauri ta daga mishi kanta "Toh kiyi shiru ki daina kukan nan kar kanki yayi ciwo." Goge hawayen tayi da bayan tafin hannun ta, sannan yace "Zo muje." Bin sa tayi har waje, ya bud'e motar sa yace mata ta zauna sannan ya koma ciki ya samu Kamal da Sadeeq suna magana Aryan kuma yana tsaye kawai hannayen sa zube a cikin aljihun sa. Kana gani kasan yana cikin yanayi amma kuma he calmness dinsa yana nan a tattare dashi. Kiran sa Lamido yayi yace Kamal ya jirasu dan Allah, yace toh suka fito tare ya kaishi har gaban motar tashi sannan ya bud'e masa mazaunin driver. Kamshin turaren sa ne ya fara sanar da ita yazo wajen ta dago da sauri sai a lokacin ya gane abinda Lamidon yake nufi. Motar ya shiga ya zauna ya karkato da jikin sa yana facing dinta sosai. Wani irin chakudadden yanayi ya shiga zagayawa a tsakanin su, kukan ta na fita kasa kasa, kukan da ya sake haddasa masa wani irin yanayi a zuciya da gangar jikin sa. Hannun sa ya mika ya kamo nata ya sakasu a cikin nasa, kukan ta ne ya tsaya chak kamar an dauke ruwa. Motsa bakin sa yayi a hankali cikin muryar sa da tayi wani irin dashewa yace "Please ki daina kuka, kina hurting dina, my heart is burning, tana min ciwo kamar zata fado." Bata cigaba da kukan ba sai ajiyar zuciya da take saki a hankali har sai da ta daina gaba daya, har lokacin hannun ta na cikin nasa yana kallon ta. sai da ya tabbatar da tayi shiru gaaba daya sannan yace "Bansan me yasa Abby baya so na ba, banyi laifin komai wallahi, I'm innocent, dan Allah yayi hakuri, I can't take it, ba zan iya jure rasa ki ba, I love you raihana, I love you so much ban taba son wata ba sai ke. Please karki bari na rasaki." Kuka tasa masa, abinda take ta so da burin ji daga bakin sa, yace yana sonta, sai gashi ya fada a yanayin da ita kanta bata san me zatayi ba. "Oh Ya Allah." Ya dan daki steering motar, hannun sa ya bude kamar zai jawota jikinsa sai kuma ya dunkule hannun yana girgiza kansa. "Kina so nayi hugging dinki? Please ki daina kukan nan bana son nayi abinda ya sabawa Shari'a, please ki daina dan Allah." "Na daina." "Yawwa, promise me ba zaki kara kukan nan ba." "Bazan kara ba." "Good girl, mu barwa Allah komai." "Are you ok?" Tace jin yadda yake numfashi har yana making sound "I can't say, already ina da tabo a heart dina raihana, my heart is so weak right now wanda bansan me zai faru ba, I don't know ko zan iya." "Zaka iya." Tace tana goge kwallar da ta zubo mata "I went through alot, may be time din da heart din zata daina bugawa ne yayi, I don't know." "Ka daina fadan hakan dan Allah." "Tom na daina, kema kiyi min alkawarin ba zaki kara kuka ba, idan kika cigaba da kuka zuciya ta zata cigaba da zama weak." "Ba zan sake ba." "Thank you so much." "Komawa zakayi?" "In sha Allah, gobe zan koma." "Dan Allah karka tafi." Kallon ta yayi, ba zai iya zama ba bayan yasan chanja raayin Abbyn ba abu ne me sauki ba. "Ki shiga gida toh, i will call you idan na koma." Bude gate din akayi, muhd ne ya leko kamar me neman wani abu, wani tunani ne ya fadowa Aryan, ya kalle ta da sauri "Don't tell me wannan sullutun Abby zai bawa." "Umm, shine." "Me? No ina ba zai yiwu ba, wannan din?" "Eh Hamma muhd ne." "I think bani da wani option da ya wuce na sace ki kawai, da dai a bawa wannan dan iskan yaron wallahi gwara na gudu dake." "Dan Allah kayi hakuri." "BA zaki bini ba?" "A ah, kawai dai." "Wasa nake miki, ki shiga gida kar Abby yayi fada." "Ok tom, sai da safe." "Sai da safe." Yana kallon ta har ta shige cikin gidan, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ciro wayar sa ya kira Kamal yace su tafi. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ _*RQ*_      42 ****Tunda suka koma hotel din Aryan be ce komai akan abinda ya faru ba, kashe wayar sa kawai yayi ya kwanta akan sofa bayan ya rage kayan jikin sa. Duk maganar da sukayi da Raihana kawai karfin hali ne shi kadai yasin abinda yake Ji. Dole yaje yaga Dr Mahfouz gobe in sha Allah. "Aryan?" Kamal ya kirashi ganin ya juya bayansa gashi bashi da tabbacin idan bacci yake ko idon sa biyu. Be amsa ba duk da yaji amma ba zai iya amsawa ba dan baya son maganar kawai. "Aryan kana jina? Please Let's talk mana." "Bana son maganar please." "Na sani, amma yana da muhimmanci muyi maganar." "Kasan me? Babu amfanin maganar, ya riga yayi making mind dinsa. A duk abinda yake faruwar nan nine nake daukar blaim din, ni ke biyan dukkan mistakes din su, no one cares about yadda nake ji." "Ba haka bane ba, duk abinda ya faru ya faru ne for a reason, don't let abinda ya faru yanzu yayi weighing naka down." "It's ok, ba komai kawai. Goodnight." "Shit, you are hurting your self, kasan condition naka so be kamata kana rike abu haka a ranka ba." Mikewa yayi kawai dan maganar Kamal din sake tunzura zuciyar sa take,ya isa wajen kayan sa ya ciro farar jallabiya ya zura, ya fice kawai daga dakin. Kasa ya sauka ya zagaya chan baya ya zauna a wata kujera yana kallon yanayin wajen. Daga sama ta hango sakkowar sa, ta biyo shi bayan da dan saurin ta. Ta zauna a gefen sa tana satar kallon fuskar sa da take a dinke. "Hi." Kallon ta yayi kad'an, ya dauke kansa da sauri yana dan matsawa dan sake bayar da tazara a tsakanin su. "Handsome saurayi kamar ka, be chanchanci zama anan ba, all alone." "Who are you?" Ya tambaya yana tsare ta da ido "AYUSH, and you?" "Please kije bana son doguwar magana." "Menene matsalar ka? Zan iya taimaka maka." Wani banzan kallo yayi mata ya sake juyar da kansa daga gareta. Tasowa tayi ta dawo dayan side din inda face dinsa take kallo ta tallafi fuskar ta tana kallon sa. Mikewa yayi kawai ya soma barin wajen, ta mike itama da sauri tabi bayan sa, suka haura saman a tare har kofar room dinsu. Ganin tana biye dashi yasa shi jan tsaki ya tsaya ya juyo yana facing dinta "Karki kuskura ki biyo bayana wallahi." "Toh ka saurare ni mana, ko ka bani number ka muyi magana." "Ba zan iya ba." Ya murd'a kofar ya shiga tayi kamar zata bi bayan sa yayi saurin banging kofar yana jan tsaki. Kamal da yake zaune yana waya ya bishi da kallo. "Kai da wa kuma?" "Wata stupid yarinya ce, ta dauka ma kowa irin ta ne. Nonsense." "Babe zamuyi magana." Ya katse wayar yana kallon shi ya zauna ya dafe kansa da hannu biyu "Da zan iya barin garin nan a yanzu da na bari wallahi." "But ba shine solution ba, ba zai yiwu mu kyale Barr yayi amfani da ego dinsa ya cutar da ku ba, abinda mukayi magana da Sadeeq da Lamido kenan,duk abinda ma zamuyi sai munyi kawai." "I don't think it will work, so ba zan takura masa ba, yar sa ce yana da right din yayi abinda yaga dama." "Kai kuma fa?" "Waye ya damu dani kuma?" "Ni mana,Daddy ,Ya Nabee. "Ok." "Ok?" "Me zance toh?" "Shikenan kawai." "Zan kwanta, but please karka yi min magana." "Naji, ba zan ba, sai da safe." ***Akan hannun ta, tayi bacci rike da waya tana jiran kiran sa, da asubah ta farka da sauri tana duba wayar amma sai taga be kira ba. Tashi tayi a sanyaye ta shiga toilet ta yo alwala ta fito, ta fara raka'atanil fajr sannan tayi sallar asubah ta roki Allah ya sassautar da zuciyar Abbyn nata. Tana zaune a wajen har gari yayi haske, ta tashi ta hau saman gadon ta kwanta lamo ta dora kanta akan pillow. Wajen bakwai da rabi Hydar yayi mata knocking, ta tashi ta bud'e masa ya kalli rinannun idanun ta wanda suka jeme saboda kuka, yi yayi kamar be gani ba yace "Kizo Muhd zai tafi." "Na'am?" "Eh, kizo kuyi sallama kafin ya dawo." "Kayi hakuri Hamma Hydar, amma ba zan iya zuwa ba." Ta juya ta koma ta kwanta ta barshi a tsaye baki hangame cikin tsananin mamakin ta, tunda suke bata taba masa musu ba, ko ya sakata abu taki yi sai yau, kasa magana yayi ya juya ya ja mata kofar kawai dan idan ma yayi maganar bata da amfani. Tunda har ta furta masa ba zata ba, toh ba zata din ba kuwa.   Muhd na tsaye yana jiran fitowar ta sai ga Hydar din ya fito shi kadai "Muje na sauke ka, bata tashi ba." "Oh ok, dadah ni zan wuce." Ya juya wajen Daadah da take zaune a falon, "Allah ya tsare, ya kiyaye hanya." Tace kawai dan a cike take dasu dukkan su, shiyasa ma taki sakar musu fuska musamman Hydar da ya zake sosai akan maganar. Fita sukayi sai ta tashi ta shiga ciki, idan sun san wata ai basu san wata ba, Muhd jikan tane kamar Raihanan, amma tunda tace bata so sai a bata zabin ta tunda dai bashi da wani aibu ya ma fi Muhd din nagarta ta kowacce fuska.    ***Akan hanyar su ta zuwa airport Kamal sukayi waya da Lamido, Aryan dai be san me suke tattaunawa ba shi dai kawai burin sa ya ganshi a Kano,kunnen sa a toshe yake ma gaba daya yana sauraron karatun alkurani,sai da suka shiga ciki sannan ya kashe. Suna zuwa basu dade ba suka tashi, ya sake maida karatun ya kwantar da kansa a jikin kujerar har suka iso. Sauri sauri ta dinga yi tun a cikin jirgin ta ganshi amma yana dan nesa da ita, shiyasa da aka fito tayi sauri ta biyo su ta same su a wajen shiga mota. Shi Aryan be gane ta ba ma kwata-kwata suka gaisa da su ya fada motar sai Kamal ne ya tsaya ya saurare ta, ya bata abinda ta tambaya sannan shima ya shiga motar. "Kayi kasuwa mutumi na." Yace yana dariya "Kana da matsala." "I'm serious, yarinyar nan kai ta biyo, har na bata number dinka ma, irin yaran nan ne ajeboters wanda basu san wani abu wahala ba ko kunya, idan sun ga namiji yayi musu kawai suna magana ne." "Lallai aiki ya gansu, Allah ya sauwake." "Amin, kaga shikenan ka samu replacement." "She's too cheap." "Wa din?" "Ita yarinyar." "Gashi nan kuwa tana kiran ka." Kallon wayar yayi da sauri sai ya tuna a kashe take ma tun jiya, kunnawa yayi ya kira Dr Mahfouz yace zai shigo yanzu. A asibitin aka ajiye shi, Kamal yace zai shigo yace a ah ya wuce ciki shi kuma ya wuce gidan Ya Nabeela. ***Yau kwanan Daddy uku da tafiya, washegarin da suka dawo shi kuma ya tafi, basu fada masa abinda ya faru a chan din ba sun dai ce masa ya karbi sakon. Ya dan ji dadi yana kuma fatan ya duba sakon a lokacin da ya dace.    Suna zaune a office din Aryan din Kamal na shigar da wasu ayyuka a cikin computer Aryan kuma yana signing wasu takardu Zainab ta kwankwasa ta shigo rike da takardu ta ajiye su, tun da suka dawo daga yolan aiki kawai Aryan yake yana so a lallai sai yayi keeping kansa busy saboda ya dauke hankalin sa daga abinda yake shirin faruwa. Hakan bata yiwuwa dan duk abinda yake tunanin kara kusanto shi yake ga wani irin fargaba da tsoron rasa abu me matukar muhimmaci a gare shi. Be kara tabbatar da yana son ta da gaske haka ba sai da kwanakin nan suke ta karatowa. Be kirata ba tun maganar da sukayi ranar yaki bari kuma itama ta kirashi dan baya so ya taka dokar Allah tunda akwai maganar aure a tsakanin ta da wani. Amma fa ba karamin dauriya yake yi ba, dauriyar da take neman kaishi k'asa sosai.   Gefen kirjinsa ya dafe yana cikin aikin ya tsaya chak da komai ya yi shiru yana jin yadda gudun zuciyar ya karu sosai. Dagowa Kamal yayi ya dube shi ya ture system din da sauri yana tashi tsaye "Are you ok?" Ya dafa shi "Bani ruwa please." "Ok." Ya dauko masa ruwa me dan rangwamen sanyi ya bud'e masa ya mika masa ya karba yasha kad'an sai yaji kamar an kara masa gudun bugun zuciyar. Saurin ajiye ruwan yayi yayi baya akan kujerar yana runtse idon sa "Ya Allah, bari na kira Dr Mahfouz." "No ba sai ka kirashi ba, zai daina haka yake min." "Haka yake ma? Tun yaushe?" "Zai daina fa, don't worry." "Ba maganar zai daina bane ba, bari kaga." Ya zaro wayar sa ya kira Dr Mahfouz, suka gaisa yake tambayar sa jikin Aryan din "Naso bashi gado amma yaki wallahi, amma abinda yake rikewa a ransa yayi yawa, he is holding alot hakan kuma yana kara damage din, last da yazo nayi masa bp it was high, na bashi drugs nace idan yaji any slight change ya dawo ko ya kirani nazo gidan." "Ya salam, wallahi be fada min komai ba, yanzu haka abun yana neman worst." Yace yana kallon yadda yake numfashi da k'yar "Subhanallahi, gani nan zanzo yanzu." "Ko mu hadu a gida na?" "Ok hakan yayi." "Thank you Dr, sai kazo." Ya ajiye wayar ya zagaya wajen Aryan din "Tashi muje please." "Kaima kamar mace, zai tsaya ba. Haka yake yi amma zai tsaya." "Allah baka isa ba." Tashi yayi kawai dan baya son su cigaba da musu, ya yi gaba Kamal din ya bishi rike da wayoyin su. Khadija na zaune suka shigo ta tashi tana kallon su, gaisawa sukayi da Aryan din ta shiga daki ta dauko mayafin ta sannan ta dawo falon. Karasowa Dr Mahfouz yayi Kamal ya shigo dashi falon yana shigowa ya kalli Aryan din ya girgiza kai "Ok kana da matsala wallahi, akwai wanda yake wasa da lafiyar sa irin ka kuwa?" "I'm fine fa." "Yes gashi nan, look at you daga ranar da kazo office zuwa yau, haba mana." Murmushi kawai yayi, Dr Mahfouz ya ciro abun auna BP ya gwada ya zaro ido da sauri yana kallon Kamal "You see, BP dinsa ya kara high sosai, a wannan stage din mutum zai iya collapsing." "Hmm, me ya kamata ayi yanzu kenan?" "Abinda dai baya so din shi za'a yi, dole ya kwanta coz yana bukatar hutu." "No Dr, dan Allah karka kwantar dani a gida." "Wallahi sai ka kwanta, bari kaji ma." Kamal yace kai tsaye, dariya ma ya bawa Aryan din ya murmusa kad'an be sake magana ba, an ce fadan da yafi karfin ka sai ka maida shi wasa kawai. ****Ana saura kwana biyu kamar yadda Abby ya tsara, dadah ta fito janye da akwatin ta katuwa da ta lodawa kaya, Hydar na zaune a falon yana breakfast ta fito ya mike tsaye da sauri "Daadah wannan kayan fa?" "Gidan ku zan bar muku." "Kije ina?" "In da naga dama, ina ruwan ka?" "Wasa kike Amma ko?" "Da yake ni sa'ar kace da zan maka wasa ko?" "Me ya faru? Munyi laifi ne?" "Akan me zan cigaba da zama daku? Tunda kun girma kun isa kuyi wa kanku hukunci abinda kuka ga dama. Bani da amfanin zama AI." "Me yake faruwa?" Lamido yace suna shigowa shi da Sadeeq "Tafiya zanyi, na bar muku gidanku tunda abun haka ne,." "Me mukayi Daadah? Dan Allah kiyi hakuri " "Ba zan hakura ba, gwara na tafi ai duk kun gama mallakar hankalin ku ya ci ace ma kun ajiye Yaya bibiyu ko uku ma" "Dan Allah kiyi hakuri, ki zauna muyi magana dan Allah." "Kasan bani da amfani a gidan nan, tunda har za'a yanke shawara ba za'a sanar dani ba,na zuba ido amma babu wanda ma yake yin maganar." "Wai maganar Raihana ce Daadah?" "Fisabillillah haka zaku zuba ido a cutar da yarinyar nan, marainiyar Allah, ina tausayin ku? Ina son da kuke mata? Yarinya a dan kankanin lokaci duk ta fige ta lalace." "Wallahi Dadah Abby hana mu maganar, wallahi ko da wasa kaje masa da maganar sai kaga bacin ransa, nayi iyakar kokarin ganin ya fuskance ni amma yaki fahimta ta." "Toh ai shikenan, sai ayi duk abinda aka ga dama, ni zama na ya kare, Allah ya bada sa'a ya taimaka." "Dan Allah kiyi hakuri, ki zauna ayi maganar nan dan Allah." "Kasan Allah Lamido, ba zan zauna ba, in dai ba za'a fasa auren nan ba ko a bata wanda take so ba toh zama na ya kare." "Hydar yiwa Abby magana." "Akwai munafuki sama da Hydar? Uwar me zaka amfana idan ka assasa abinda bata so?" "Kai Daadah." "Karya nayi? Ba duk kaine ka assasa ba." "Ku bani waje na tafi dan Allah, kuna bata min lokaci." Rike jakar Sadeeq yayi, Hydar kuma ya tafi bangaren Abbyn ya kirawo shi. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ _*RQ*_     Page 43 ***Tare suka dawo da Abbyn ya shigo falon ya durkusa har ya gaishe ta, ta amsa babu yabo babu fallasa sannan yace "Dan Allah Hajiya kiyi hakuri." "Ni ai ba laifi akayi min ba sam, abinda kake ganin daidai ne ka zartar akan yar ka, bani da wani iko akai na hana balle a nemi shawara ta." "Subhanallah, kiyi hakuri Hajiya wallahi ba haka bane ba, abubuwan ne suka zo a baibai, amma ba anyi hakan bane domin a bata miki rai, yaran nan gaba daya dani kaina a karkashin ikon ki muke, kece mahaifiyar su kuma kece mahaifin su, dan Allah kiyi hakuri Hajiya." "A ah, babu komai fa, tunda har an riga an yanke hukunci magana ta kare, zan tafi zamana ya kare a gidan nan, Allah ya bada zaman lafiya" "A ah Hajiya, ba za'a yi haka ba, dan Allah kiyi hakuri." "Toh..." "Yanzu me kike so ayi Hajiya?" "Ka saurari yarka, kaji damuwar ta, kaji abinda take so sannan idan be sabawa shari'ar musulunci ba kayi mata, Raihana yarinya ce karama wadda ba zata dorar da rayuwa tare da soyayyar uwa ba, ta girma a karkashin kulawa ta data yan uwanta gasu nan, bata taba bijire musu ko yi raina su ba, bata taba batawa kowa rai ba, yarinya ce me cike da walwala da farin ciki, akan me za'a dakushe ta? Akan me za'a bata mata rayuwa ta hanyar yi mata auren dole, kunsan illar sa kuwa? Kunsan abinda zai jawo? Me yasa ba zaku yarda da kaddara ba, KU zama masu hakuri? Allah ma muna masa laifi amma ya yafe mana, me yasa abinda ya faru ba zai wuce ba? Rayuwar gaba daya nawa ce? Sannan duk abinda ya faru ya faru ne tsakanin ku, ku iyayen yaran nan, menene nasu su? Me yasa abun zai shafe su? Me yasa ba zakuyi kokarin gina sabuwar rayuwa ba? Bansan dalilin ka na zafafa wa har haka ba, nasan an bata maka, an zalunce mu ciki har dani, wanda har yanzu bansan shin da gaske Aisha ta rasu ba, ko tana wacce duniyar? Bamu ga gawarta ba duk da mun samu tabbacin tana cikin motar da tayi hatsari, me yasa ni ba zan rike abun ba? Me yasa ba zamu fawwwalawa Allah komai ba? Mu zama masu karbar kaddara a duk yadda tazo mana, sai mu hau fushi muce mu sam ba zamu zama masu yafiya ba? Rayuwa zata yiwu a haka? Muna so kuma muma Allah ya yafe mana zunuban da muke aikatawa, bayan mun kasa zama masu yafiya da jin kai ga sauran mutanen da kaddara ta hada mu dasu. Ni dai nasan ban isa nasa dole ayi ba, ko na hana ayi ba, shawara ce dai a matsayi na na babba, ga Raihana nan, zabi ya rage naku, ku zaba mata rayuwa me inganci ko ku dakushe ta, ta hanyar tursasata tabi abinda bata so." "Ayi hakuri Hajiya, ayi hakuri." Abby yace maganganun sun yi mugun shigar sa. Juyawa tayi kawai ta bar musu falon ta koma ciki. Abby ne ya fara fita ya koma part dinsa, ya bar su a zaune cikin wani irin yanayi.    Direct wajen da ya ajiye envelope din da Daddyn ya aiko masa yaje, ya bud'e ya dauko dan tun ranar be bude ba, ya zauna a gefen gadon sa ya bud'e a hankali bayan ya zura medicated glass dinsa. Takardun filaye ne da gidajen da ya mallaka tun a wanchan lokacin, sai kuma takardar share din da yake dashi a company Mukaddas oil and gas. Duk bayanan da ya kamata ya samu suna ciki. Ajiye su yayi a gefe ya sake fito da wasu takardun wanda suke dauke da bayanin health condition din Aryan, wanda suka kasance na shekarun baya a lokacin da ya shiga matsalar PTSD at a very young age. Ajiye su yayi suma a gefe bayan ya gama dubawa cike da tausayawa. Wani dan karamin flash ya fado daga ciki. Ya dauka ya jawo system dinsa ya jona a ciki. Maganar Daddyn ce cikin muryar dake nuna jikin sa babu dadi yake rokon Abbyn ya yafe masa sannan ya taimaka ya bawa Aryan Raihana, yasan be kamata ya tambayi alfarma a wajen sa ba, kuma shi kansa Aryan din be san ya nemar masa alfarmar ba, amma idan yaga da takura shikenan babu komai. Ajiye flash din yayi bayan yayi copying maganar akan system dinsa sannan ya dauko takardar karshen. Wadda take kunshe da bayanan dalilin fitar Abbyn daga prison wacce ke dauke da sa hannun Daddyn. Jikinsa ne yayi wani irin sanyi sosai, hankalin sa ya tashi, yanzu idan wani abu ya samu Daddyn ya zaiyi? Me yasa be danne zuciyar sa ya saurare shi ba? Me yasa shi be rama sharri da alkhairi ba, ya nuna masa ya fishi ko a wajen Allah. Amma sai ya biye wa dokin zuciya ya aikata abinda sam ba halin sa bane, gashi har yana neman ya gurbata rayuwar yarsa kwaya daya tilo saboda wani dalili nasa na daban. Tashi yayi ya hau zagaye a tsakiyar dakin yana tuna maganar da sukayi da Alhaji Kabir akan maganar auren. Be goyi baya ba sam dan dai Abbyn ya matsa ne ya amince saboda kar yaga kamar ya ki yarsa. Amma daga shi har Adda Maimunan basu zama masu son kai ba, sun kuma nusar da Muhd yayi hakuri amma ya nuna musu shi dai ya amince. Tausayin Raihanan suke ji dan su ba zasu iya aikatawa Amina hakan ba. Zagayen ya cigaba da yi cikin son neman mafita, gashi saura kwana biyu kachal ta ina zai fara? Ya dade yana sakawa da warwarewa kafin ya tsaida shawara guda wadda yake ganin itace zata zama maslaha ga kowa da kowa. Alhaji Kabir ya fara kira, ya sanar dashi komai ya kuma basu hakuri, be damu ba, duk da yasan Muhd zai ji babu dadi amma yasan zai hakura a karshe tunda shi namiji ne. Ganin ya sauke wannan ya sa ya kira Lamido a waya yace suzo dukkan su part dinsa yana son ganin su, dama suna tare basu riga sun tashi ma daga falon ba dan ko aiki babu wanda cikin su yayi yunkurin tafiya saboda daga Daadah har Raihanan sun rufe kofar dakunan su sun shige ciki suna kuma tsoron wani abu ya same su. Part din Abbyn suka nufa suka same shi a falo yana zaune yana jiran isowar su, zama sukayi ya kalle su daya bayan daya sannan yace "Na yi tunani na kuma yanke shawarar bawa Raihana zabin zuciyar ta, zan kuma cika alkawari kamar yadda na dauka sai dai na dawo da daurin auren gobe ba sai jibi ba, inaso Lamido ka kira Kamal ka sanar masa, idan mutum daya ne ma ya samu zuwa ya wadatar, idan ba'a samu me zuwa ba, ni nan zan zamar masa wakili sai kawun ku ya yi waliccin uwata. Idan yaso ku dauke ta ku kai ma mijinta ita, ni kuma sai ku fara nemar min visa domin zan bi bayan aboki na." Wanan karon har Hydar maganar tayiwa dadi, suka yi murmushi dukkan su sannan suka ce alhamdulillah. A take Lamido ya fita daga falon ya kira number Kamal a lokacin yana tare da Aryan din da ake kara masa drip jikin nasa ya sake rikicewa sosai fiye da dah dan ma yana da masifar karfin hali da dauriya. Ba dan sun nuna masa dole dole ba da babu abinda zai sa ya yarda ya kwanta wanda kuma yake da matukar bukatar hutun. "Lamido ne yake kira." Yace yana nunawa Aryan din wayar, juyar da kansa yayi Kamal ya d'aga suka gaisa sannan ya tambaye shi idan suna tare da Aryan ne, ya amsa da eh sanann yace ya dan fita waje zasuyi magana. Chan compound din gidan ya fita sannan sukayi maganar, wani irin dadi ne ya lullube Kamal din, ya dawo dakin da Aryan din yake ya tarar dashi kamar me bacci, be fada masa ba dan dama plan dinsu kenan shi da Lamido. Zama yayi a gefen gadon ya hau duba available flight da zasu yolan gobe, yaci sa'a ya samu na safe amma da yar tsada, haka ya siya musu sannan ya dauki key din motar sa ya fita. Yana driving din suna waya da Baba (Malam Hassan) ya sanar dashi abinda yake faruwa sannan ya kira Ya Nabeela ya sanar da ita itama, lokacin tana hanyar zuwa gidan Kamal din saura kiris ta saki steering motar saboda murna. Rokon ta yayi kar ta fadawa Aryan din surprise zasuyi masa kawai.    Su uku suka shirya, Malam Hassan, Dr Farouk mijin Ya Nabeela sai wani cousin din Daddy. Da sassafe driver ya kaisu airport ko tashi Aryan din ma be yi ba suka lula sai Adamawar yola. Duk abin nan dake faruwa Daadah bata sani ba haka ma Raihana, suna dai tare Daadan na bata baki dan ta lura kaamar abinda tace be shige su ba, ganin yadda suka cigaba da sabgar gabansu a ranar. Dangin Ammyn ne suka zo gidan bayan Daadah ta sanar dasu, duk sun dauka ma Raihana sun daidaita kansu da Muhd din ne ashe ba haka bane ba, sai da suka zo sai duk jikin su yayi sanyi haka dai aka cigaba da zama a gidan kamar ba aure za'a yi ba.    Hydar ne yaje ya taho dasu daga airport din suna sauka, ya kawo su gidan suka hadu da Daddy a falon sa suka zauna har lokacin ya kusan karasawa sannan suka dunguma zuwa masallacin. Asabar ce sai kuma tazo da daurin aure da yawa, sai da aka fara na wadanda suka riga su sannan aka shiga daura auren Raihana Nasir Matawalle da angon ta Muhammad Ibrahim Mukaddas bisa sadakin dubu dari da Kamal ya bayar. Kasancewar anyi daurin aure da yawa ya saka ma ba zaka gane wannan mutanen wannan bane haka ma wannan, haka aka gama aka watse suka dawo gidan cikin farin ciki da annashuwa. Matan gidan na zaune aka shigo musu da alawa da goro. "Kar dai zargi na ya tabbata auren nan aka daura yau?" "Eh Dadah, an daura auren Raihana da angon ta Muhammadu." Lamido yace yana murmushi. "Yanzu har da kai Lamido?" "Muje ciki zan miki bayani Daadah." "Me zaka fada min?" "Muje dai, sirri ne." Da k'yar ta bishi cikin ya sanar da ita abinda ya faru, sai kuma ta hau murna tana saka musu albarka, ta juya zata je ta sanar da Raihana ya hanata "Angon yana chan kwance babu lafiya, karki fada mata dan Allah suprise za'a mata." "Akan me? Yarinya na chan na ciwon so Allah ya share mata hawayen ta za'a ce ba za'a fada Mata ba." "Dan Allah Dadah, dan Allah." "Gobe da safe zasu wuce da Kamal, sauran da suka zo dai yau zasu koma." "Haka da wuri? Me yasa ba za'a bari muyi biki ba." "Kai Dadah, da fa bakuyi niyyar bikin ba dama." "Wannan ai auren soyayya ne, wanchan kuma na dole, kai Allah ma yaso na jima ina gyara Raihana, da irin wannan auren bagatatan haka za'a kaita dakin miji ba wani gyara." "Wannan maganar ku ce Dadah, bari na koma waje." "Allah dai yayi maka albarka kaji, bari naje na sata tayi wanka ta ci abinci dan wannan ramar da tayi ma Allah yasa kar kasusuwan su ciji mijin." Dariya ya kwashe da ita, ya barta a ciki yayi waje, ta fito ta nufi dakin Raihanan ta same ta tare da wata kanwar Ammy da tazo ta fada mata an daura auren. Tsabar kukan tayi ta gaji ya ma ki zuwa, ta hakura kawai duk yadda sukayi da ita. Sata taje tayi wanka Dadah tayi babu musu taje tayi ta saka kaya ta zauna da kudaddiyar fuskar ta da ko mai bata saka mata ba bare ta samu arzikin powder. Abinci aka kawo mata taaci kad'an ta koma ta kwanta tana tunanin rayuwar da zata shiga da yadda abubuwan suka faru a dan kankanin lokaci. Tabbas Muhd ba zai taba jin dadin zama dashi ba, tayi biyayya ta aure shi amma ba zata taba son sa ba, har abadah gangar jikinta kawai ya aura.   A ranar Malam Hassan, Dr Farouk da kanin Daddy suka dawo wajen karfe taran dare, shi Kamal sai gobe zasu taho tare da Hydar dan Lamido ranar zai koma bakin aiki Sadeeq kuma yana da abubuwan yi a clinic.   Da duku-duku Daadah ta sakata ta hau shiryawa, tana shiryawar tana kuka sosai har wani jan numfashi take saboda kuka, har ga Allah Dadah taso ta fada mata da ainahin wanda aka daura amma Lamido ya hanata dole ta hakura amma tana matukar tausayin Raihanan ganin har zazzabi ya kamata ga jijiyoyin kanta da suka fito sukayi rado rado saboda kuka. Part din Abby aka rakata ta same shi a bedroom dinsa ya kira sunan ta, ya shiga yi mata nasiha me ratsa zuciya sannan ya rufe da saka mata albarka. Fitowa sukayi zasu tafi airport din wajen sha biyu, mota suka shishiga ita da Daadah ta kwanta a jikinta tana cigaba da kuka k'asa k'asa. Sai da suka zo airport din sannan kukan ta ya karu sosai, ta rik'e Dadah da itama kuka take dan bata taba kawo rabuwa da Raihanan a wannan lokacin haka katsaham ba. Da k'yar aka banbareta daga jikin Dadah Lamido ya rike Dadah ita kuma Hydar ya riketa suka nufi cikin wajen, sai da suka ga shigar su sannan Kamal yazo yayi musu sallama yace sauran kayan Raihanan zasu turo driver ya daukar mata idan an gama hadawa.Daga chan bayan su Kamal ya zauna hakan yasa Raihana bata ganshi ba, ta dora kanta akan kafadar Hydar din bayan ta daina kukan sai ajiyar zuciya da take saukewa a jere.    Ko da suka iso Kanon ma ba mota daya suka shiga ba, driver ne yazo ya dauke su shi kuma Kamal yayi Uber ya bi bayan su, suna sauka ya Aryan wanda yaga missed calls dinsa tun a chan amma be kira shi ba saboda baya so ma ya samu wani clue akan abinda yake faruwa. Yana kishingide a bayan mota kiran Kamal ya shigo wayar tasa. Ya kirashi na dama ya sanar dashi ya tafi gidan sa idan ya dawo sai ya dawo be daga ba,kawai sai ya kira driver Daddy yace ya zo ya dauke shi ya kaishi. Toh suna saukar ne ma Kamal din ya kira ya tambaye shi yana ina dan yaji karar hanya yace ya tafi gidansa, ok kawai Kamal yace ya kashe ya kira driver da ya dauki su Raihanan yace ya kaisu chan gidan Aryan din. Kasancewar daga inda Aryan din yake yafi kusa da gidan akan daga airport din  yasa ya riga su zuwa. Har ciki driver ya shigar da motar bayan Baba me gadi ya bud'e masa tunda already ya riga dama yasan motar gidan. Suna shiga Kamal yazo shima a Uber ya sauka ya sallama shi.   Aryan ya riga ya shige ciki amma kofar a bud'e take be rufe ta da key ba kawai murd'awa zaka yi ka shiga. Kofar driver ya nunawa Hydar din ya ce su shiga, ya murd'a kofar rike da hannun Raihanan suka shiga. Kayan Aryan din ne zube akan kujerar wanda ya cire yana shigowa ya wuce toilet ya sakarwa kansa ruwa ko zai rage nauyin da yake ji musamman idan ya tuna daga gobe shikenan bashi da sauran hope. Kasancewar ya kuna ruwa ya hanashi jin shigowar su kwata kwata. "Ina zuwa kanwata, ki zauna yanzu zan dawo kinji?" "Dan Allah Hamma karka barni anan, dan Allah." "Ai ba tafiya zan ba, waje zan je na sallami wanda ya kawo mu." "Toh dan Allah karka dade." Tace tana share kwallar da ta sakko mata. "Ba zan dade ba." Yace ya fito ya ja mata kofar ya nufi wajen Kamal da ke zaune tare da Baba mai gadi suna magana. __*RQ*__      44 ***Hydar na fita ta kalli falon sosai da sauri ta mike tsaye domin ta tabbatar da ba wai idon ta ne yake mata gizo ba. Fitowar sa kenan daga toilet din, hannun sa daya yana goge sumar kansa da dan karamin towel sai bathrobe dake daure a jikin sa, sai da ya tsane ruwan kan nasa sannan ya cire bathrobe din da towel din ya wurga su a laundry basket ya zura short trouser ya shafa mild oil perfume. Kwanciya yake so yayi ya dan yi bacci dan har lokacin jikin nasa is weak, dan haka ma be tsaya saka wata riga ba ya fada saman gadon. Yana kwanciya sai ya tuna da wayar sa a falon kuma yana so ya duba ta sannan ya kashe dan kar ma a kira shi. Mikewa yayi ya zura bedside slippers dinsa ya nufi falon kansa tsaya sanin shi kadai ne a gidan. Tana tsaye tana son gasgata in da take tana kuma son gano dalilin da ya kawo ta gidan ya fito. Da karfi ta kwalla kara ganin mutum daga shi sai gajeran wando ya fito, karar da tayi ce ta bashi tsoro dan ko da wasa be yi tunanin ganin ta ba. Juyawa tayi da sauri ta bashi baya tana runtse idon ta kam-kam. Tsayawa yayi chak daga in da yake yana son tantance me yake faruwa? Tunanin zuwan da tayi a wanchan lokacin ya fado masa, me take yi anan? Ya tambayi kansa. Tunowa da yayi da yanayin da yake ciki yasa shi juyawa da sauri zai koma ciki, sai kuma wani tunani ya fado masa, taku daya biyu yayi ya juyo ya shiga takowa zuwa wajen da take tsaye ta juyar da bayan ta ta runtse idonta jikin ta na rawa sosai. A daidai saitin bayanta ya tsaya, har tana jin hucin numfashin sa a saitin wuyanta.  Wayar sa ce tayi kara alamun shigowar sako, hannu yasa ya dauki wayar dake daidai saitin sa ya bud'e sakon ya karanta _"She's your wife man, taka ce halak malak. Sender Babban wa uba."_. Yasa emoji din wink a karshe. Wani irin murmushi ne ya subcewa Aryan, be san lokacin da ya dire wayar ba, sai ji kawai tayi ya rungume ta baya baya da karfi. So tight da har tana iya jin ragowar danshin dake jikin sa "Na shiga uku." Ta furta jikin ta na cigaba da rawa sosai, "Alhamdulillah zaki ce." Ya rada mata a kunnen ta a hankali. Har cikin kwakwalwarta maganar ta shigar mata, ta haifar mata da wani irin yanayi me wahalar fassarawa. Juyo da ita yayi gaba daya suna facing din juna, idon ta a rufe yake har lokacin ya tsurawa fuskar ta ido da tayi fayau daga ranar da ya ganta.  Hannu ya kai ya shafa saman idon nata, yace "Bud'e idon ki please." Girgiza kai tayi da sauri tana sake runtse idon ta "Pleaseeeee kinji? Wani abu nake son gani." "Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan na Hamma Hydar zai kawo ni ba." Ta fada muryar ta na rawa gashi ya rik'e ta kam kuma very close da jikin sa. "Hydar ne ya kawo ki?" Yace cike da mamaki, da kai ta amsa masa, sai yayi murmushi kawai ya tauna kasan lips dinsa ya tallafo fuskar ta "Batan hanya yayi kenan, yanzu ya za'a yi? Ni kuma gaskiya kinzo kenan." "Dan Allah dan Allah kayi hakuri." "Um um, ba zan iya ba gaskiya, sai dai idan zaki bud'e idon ki." "Toh kaje kasa kaya." "Zafi nake ji, idan kika bud'e kad'an naji zan je nasa amma." Shiru tayi ya cigaba da kallon ta zuciyar sa cike da farin ciki kal kamar ya zuba ruwa a k'asa yasha haka yake ji. A hankali ta dan bud'e idon kad'an ta kalle shi, dama shi ita yake kallo, idon ta ne ya shiga cikin nasa ya wani narke mata su, da sauri ta maida idon ta kulle kirjinta na wani irin fat fat. Dariya yayi kad'an ya sake matso da ita jikinsa gaba daya, ya kai bakin sa saman forehead dinta ya sakar mata light kiss sannan a kai bakinsa kunnen ta yace "Tsoron kallon mijinki kike ji?" Kalmar mijin ta shiga kunnen ta zuwa brain dinta amma sai ta kasa gane ma'anar abinda yake nufi ma baki daya. "Ok zauna ina zuwa." Yace yana sakin ta, sai kuma ya dawo da sauri yace "Muje tare kar naje na fito naga bakya nan" Ya kama hannun ta suka shiga ciki har lokacin taki yarda ta bud'e idon ta, gaba daya ta kasa nutsuwa ta kuma kasa fahimtar ma abinda yake faruwa gaba daya, shi kuwa a nutsen sa yake komai. Ba tare da ya nuna tsantsar mamakin sa ba, yanayin sa kenan. Bedroom dinsa ya shiga da ita ya zaunar da ita a gefen gadon ya wuce wajen kayan sa ya dauki jallabiya ya zura sannan ya dawo in da take zaune ya zauna a kusa da ita sosai yace ta bud'e idon ta. Budewa tayi a hankali amma taki kallon sa tana dan zamewa kad'an ta matsa daga zaman da yayi kusa da ita sosai. Sake matsowa yayi ya kama hannun ta ya juyo da fuskar ta bangaren sa ya cigaba da kallon zagayayyar fuskarta zuwa dan karamin lips. Gaba daya kallon da yake mata ya hanata sakat, gashi da ta dauke kai sai ya juyo da kan nata. "Please ki bari nayi ta kallon ki, kamar mafarki haka nake ji, how come? Ya akayi hakan ta faru?" "Oya bani labari, yaushe Abby ya chanja mind dinsa? Tausayi na yaji ko?" "Nima ban sani ba, bansan nan zamu zo ba." "Ok wait, bari na dauko wayata na kira kamal, shi zai fada mana komai. Just wait for me yanzu zan dawo kinji?" Duk yadda ya kware a iya boye mamakin sa ko damuwar sa ya gaza a yanzu, jin sa yake kamar a saman gajimare saboda tsabar farin ciki. Falon ya koma ya dauki wayar sa ya kira Kamal din. Dagawa yayi ya kwashe da dariya "Ango kasha kamshi." Yace yana kokarin rage dariyar tasa "Please kun saka mu a duhu, muna bukatar bayani." "Muma compound din gidan ai, bari mu shigo ciki." "Ok, kai da waye?" "Ni da surukinka, bari mu shigo." "Ok." Yace ya sauke wayar ya isa kofar falon ya bud'e ta, suka karaso Kamal na kallon shi ya sake kwashewa da dariya "Kasan kuwa angwaye akwai saka jallabiya wallahi, ko me yasa?" Yace cikin sigar tsokana suka yi dariya dukkan su har Aryan din, sannan ya matsa musu suka shigo. Zama sukayi, Hydar ya mika masa hannu suka gaisa sannan Kamal din ya soma yi masa bayanin duk abinda ya farun da kuma yadda akayi da zuwan da sukayi ya kare da "Gata nan mun kawo maka ita, sai ku daina ciwon love din ku mike aiki na jiranku." "Saboda mune agogo sarakan aiki ko?" "Emana, kaga ba shikenan sai ayi mata new seat a office dinka ba." "Ni duk ba wannan ba, wato duk kun sani har Ya Nabeela amma babu wanda ya fada min." "Toh Mr korafi, ai ka fara godiya kafin korafin." "Surprising naku muka yi ai." Hydar yace yana murmushi "Mun gode amma kad'an." "Wallahi idan ban sa ta fito mun tafi ba, babu fa wata wahalar da kayi ta aure ba lefe ba komai kawai aka kawo maka mata amma ba godiya ba komai?" "Ba komai duk zan yi mata duk abubuwan da ya kamata ne fiye da wanda ake ma kowa ma. Godiya kuma Daadah kawai zan shikenan." "You are not serious, a gaban Hydar din?" "Shima ya sani ai, yasan gaskiya." "You are not nice." Kamal ya dauki pillow ya jefa masa ya chafe suka sa dariya gaba daya, kallon Hydar kawai Aryan yake amma ya shirya masa rashin m, dole ne ma ya rama abinda yayi masa ta cikin ruwan sanyi. "Yanzu sai maganar biki, ya kamata ayi biki kamar yadda ake ma kowa ko?" "A bari hada da na suna nan da wata tara." Ya basar bayan ya fada kaamar ba shine yayi magana ba, wani pillow Kamal ya sake jefa masa ya mike tsaye cike da mamakin Aryan din "Muje Hydar." Yace sai kuma ya kalli Aryan din da shima ya mike tsaye "Gida zaku koma saboda a fara gyaran nan din ko?" "Ok hakan yayi, amma ba yau ba." "Idan kun ga dama karma ku koma, shima a hada da na sunan nan da wata taran ayi." "Eh hakan ma dai duk shawara ce." Ya fada yana dariya. "Gobe ma rana ce wallahi, kirawo ta Hydar zai mata sallama." "Komawa zai?" "Eh amma sai gobe ko?" "Eh in sha Allah." "Ai zaku sake haduwa, idan kace mata sallama yanzu zaka rikita min ita ne." Kama baki Kamal yayi wanda shi no a jikin sa maganar sa kawai yayi kuma tsakanin sa da Allah har a zuciyar sa haka ne. "Wai dan Allah Aryan yaushe bakin ka ya bud'e haka?" "Daga sanda kayi min aure." "Wato ni na jawo ko? Na karba maka mata yarinya me hankali amma da abinda zaka saka min kenan?" "Sorry sir." Ya fada yana dariya "Oga Hydar please ka bari sai gobe dan Allah." "Ok ba damuwa, zan shigo kafin na wuce." "Yawwa thank you." "Inaga kai ma fitowa zakayi kawai mu duba office din chan dan naga ka warke garau, sako kayan ka kawai mu wuce akwai ayyuka masu yawa, kasan kuma next week zan tafi." Kamal ya tsokane shi yana son Jin abinda zai ce "Tab wallahi ba zan je ba." Yace ya juya ya bar su a tsaye kawai suna dariya. Fita sukayi suka rufe kofar ya dawo ya saka key a kofar dan kar ma su dawo sannan ya nufi dakin cike da karsashin sa. Tana zaune a in da ya barta, ta kara jawo mayafin ta sosai ya sakko saman fuskar ta ya rufe fiye da rabin fuskar. Wuce ta yayi ya nufi wajen kayan sa, ya zare jallabiyar ya maida ita inda ya dauko ta dan duk ta takure shi, ya dauko wani wando ash colour da rigar sa masu laushi,wandon ya kai masa wajen guiwar sa sai rigar da take armless ya saka ya dawo wajen ta ya janye mayafin da ta rufe fuskar ya cire shi gaba daya ya ajiye shi akan bedside sannan ya jawota jikinsa ya sakata a tsakiyar kafafun sa ya dora kansa a saman kafardar ta yana shakar kamshin jikinta. "Naje munyi magana da Kamal yanzu, kina so kiji me muka ce?" Da sauri ta daga kanta sama alamar eh dan gaba daya ya na neman rikita mata tunani, hannun ta na cikin nasa yana murzawa a hankali ga shi ya dora kansa a jikinta duk maganar da zai yi direct cikin kunnen ta take zuwa. Yanayin yadda yake maganar so deep ma kawai ya isa ya rikitar da ita. Kamar bashi ba, kamar wani ne na daban aka chanja shi ba ainahin Aryan din da ta sani ba, gaba gadi kawai yake koman sa tun farko baya tsaya nuku nuku ko magana ce zai fade ta kawai ko ba zata maka dadi ba shi ba ruwan sa. "Abby yaji tausayi na ya bani ke, halak malak, naji dadi na gode wa Allah, daga ranar zuwa yau jini na ya hau yafi sau dubu, na rasa me ma zanyi, idan na tuna wannan sahoramin Abby zai bawa ya hanani sai naji duk babu dadi, nasan na fishi chanchantar ki, na fishi bukatar ki kuma na fishi son ki..." "Tun kina baby, tiny little baby nake son ki Raihana, tun bansan menene son ba ma, ashe ban sani ba matata ce aka haifa min." "Zan sha ruwa." Tace da sauri tana jin yadda yake shinshina wuyan ta yana saukar mata da wani irin numfashi me dumi a saman wuyan nata "Um um." Yace dan ya gano su take ta gudu, ya sake matse ta sosai a jikinsa ya saka hannayen sa ya makaleta ta yadda duk motsin da zatayi a jikin sa zatayi. "Zanje toilet." Ta sake fada cikin neman hanyar tserewa "Pleaseeee ki barni, na dade ina mafarkin wannan ranar, ki barni naji dumin jikinki, kiji nawa please." "Allah toilet nake son zuwa." "Ok, muje na rakaki." Zaro ido tayi da sauri, toilet din zai rakata? "Tashi muje toh." Ya dan cikata yana bata damar mikewa. Kasa tashi tayi dan har gwara su cigaba da zama a hakan da ya rakata toilet din "Um um na fasa zuwa." "Bakya so na raka ki?" "A ah na fasa ne kawai." "Ok, na fasa raka ki din, jeki ina jiranki, amma idan kika dade zan shigo." Kallon sa tayi ya daga mata kai "Na fasa da gaske, jeki." "Ok." Tace ta mike ya nuna mata toilet din da hannun sa. Kasancewar babu Hijab babu mayafi a jikin ta yasa ta kasa tafiya. Baya yayi shi kuma yana kallon ta yana jiran yaga abinda zatayi. Mayafin da ya cire mata ta saka hannu zata dauka yayi saurin daukewa yana tsare ta da idanun sa masu kashe mata jiki. "Haka zaki je, ko na rakaki." Sakin mayafin tayi ta wuce a hankali ya bita da kallo yana sakin murmushi. Tana karasawa toilet din tayi saurin shigewa ta saka lock din jikin kofar ta dafa kirjin ta da yake harbawa da karfi. Wayar sa ya dauka zai kira Kamal yayi masa maganar abinci dan yasan zata ji yunwa sai yaga missed calls din Ya Nabeela,fasa kiran Kamal din yayi ya kirata tana dagawa ta fara gud'a. Murmushi kawai ya dinga yi suka gaisa tayi masa Allah sanya alkhairi sannan tace zata turo driver ya kawo musu abinci zata shigo gobe, godiya yayi mata ya kashe wayar gaba daya tunda dama abinda zai tambayi Kamal din kenan. Dan kishingida yayi sai ya tuna tace zata sha ruwa, sai ya tashi ya dauko mata ya ajiye ya sake komawa yana jiran fitowar, kusan minti goma da shigar ta amma shiru kuma shi be ji alamar motsin ruwa ba. Mikewa yayi ya karasa jikin kofar toilet din ya kwankwasa kad'an. Tace tana tsaye gaban mirror tana kallon idanun ta da sukayi wani irin kodewa saboda kuka, fuskarta kuma tayi wani jaja jaja itama abin ka da farar fata. Sake knocking yayi sannan yace "Zan shigo fa." Bata dauka da gaske yake ba, dan tasan kofar a rufe take shiyasa taki amsa masa, sai da taji kamar ana murd'a kofar kafin ta yi aune har ya bud'e ya shigo. Hannun ta kawai ya kama ya fito da ita, dan dama yasan babu abinda take yi a ciki. Kan gadon ya maida ita ta zauna sannan ya mika mata ruwan ka karba tasha kadan ya rufe ya ajiye. Fita yayi ya barta a dakin ta dauki mayafin da sauri ta sake yafawa, ta takura sosai da rashin sa dan riga da skirt ne a jikinta rigar kuma fitted ce wadda ta dan kamata musamman ta sama. Tana zaune ya shigo rike da basket me kyau an rufe shi da wani farin kyale me kyau. Dire shi yayi akan carpet din dake gaban gadon ya zauna ya mika mata hannun sa yace ta taso. “Nakoshi” wani kallo yayi mata ya bude basket din yana kallon abinda aka rubuta a jikin farin kyallen. HML Aryan and Raihana. Murmushi yayi me dan sauti ya sauke warmers din masu kyau ya bude ya zuba abincin ba da yawa ba ya rufe ya dauki plate din ya dora shi a saman drawer sannan ya kama hannun ta ya gyara mata zama ya zauna yana facing dinta yace ta ci abincin ko ya bata. Duk da tana jin yunwa ga kamshin abincin da yake shigar ta amma kunyar sa ba zata barta ta iya ci ba, ganin ya tsare ta da ido yasa ta ci kadan tace ta koshi, be ce komai ba, ya karbi plate din ya ajiye ya duba duba time yaga lokacin sallar azahar tayi, yace ta yi alwala ya sakè ficewa daga dakin ya hau sama. Tashi tayi taje tayi alwalar tazo ta matsar da kayan ta  tada sallah. Turo kofar ya yi sai yaga tana sallah sai kawai ya ja mata kofar ya fita sukayi jam’i tare da babà maigadi yayi amsa Allah sanya alkhaiiri sannan ya dawo ciki. Motsin sa taji tayi saurin sakè gyara mayafin jikinta ta kame waje daya. Shigowa yayi suka hada ido ya sakar mata murmushi ta sunkuyar da kanta ya karaso ya zauna a gefen ta "Kinsan siesta?" Ya tambaye ta, girgiza kanta tayi "Ok, bari ki gani." Yace yana mikewa, ya dan karo karfin AC dakin sannan ya kashe hasken dakin ya saki curtains din da suke bud'e. Rigar jikinsa ya zare ya ajiye a saman sofa ya karaso wajen da take tsoro duk ya gama cikata ya kama mayafin ya zare shi ya je ya saka shi a wardrobe din sa ya rufe ya dawo ya mikar da ita. "Zo muyi siesta, nasan kwana biyu bakya wani baccin kirki." "Bana jin bacci" Tace tana zaro ido, da tsakar ranar nan ace tazo ta kwanta, akan me? "Allah sai kin kwanta, hutawa zamuyi." "Wallahi wallahi bana jin bacci, rana ce fa?" "Siesta kenan, bakiyi boarding school ba?" "Ban yi ba." "Shiyasa toh, zaki chanja wannan atamfar? Na baki kayana kisa?" "Um um, ni zan je falo idan ka gama sai na dawo." Tayi hanyar fita, da sauri ya riko ta, ya sakata a jikinsa gaba daya ya jata zuwa saman gadon, ya kwantar da ita ya kwanta a gefen ta ya saka hannunsa yayi mata rumfa dasu ta yadda ba zata iya ko motsi ba. Zatayi magana ya saka hannun sa a saman bakin ta "Shssh, don't say anything, ba abinda zan miki so nake kawai naji heartbeat dinki." Ya dora kansa a saman chest dinta. "Na shiga uku." Ta furta da dan karfi ganin yadda ya dora kansa a saman kirjinta ya rufe idon sa. Dago kansa yayi yana kallon ta "Relax please, kinji yadda heart din ki take gudu? Menene ? Tsoro na kike ji?" Gid'a masa kai tayi da sauri, ya matso da fuskar sa daidai tata a hankali yace "Babu abinda zan miki fa, heartbeat dinki kawai nake ji. dan Allah ki kwantar da hankalin ki kinji?" Sake gid'a masa kai tayi yace "Good girl." Rufe idon ta tayi shi kuma ya cigaba da kallon fuskar tata zuwa lips din nata da yake ta fuzgarshi, yana son ya ji shima yadda ake ji. _**RQ**_       PAGE 45 ***Babban dan yatsan sa ya saka a hankali ya shafa lips din nata a hankali in a stylish way, bud'e idon tayi da sauri tana kokarin tashi. Girgiza mata kai yayi ya matse ta sosai yana hadiye wayun bakin sa a hankali. Maida idonta tayi ta rufe hakan ya bashi damar yi mata light kiss akan lips din nata. Yana jin sanda ta matso da dan karfi yayi murmushi kawai yana jin zuciyar sa wasai. Bacci ne ya dauke shi da karfin gaske, domin hatta bugun zuciyar ya daidaita a lokacin, dama akwai alluran da Dr Mahfouz yayi masa masu saka bacci shiyasa yana kwanciya baccin ya dauke shi. Bud'e idon tayi ta lallaba a hankali da k'yar ta zare jikinta, bata jin bacci bata ma ga dalilin da zatayi bacci a irin wannan lokacin ba da bata gama tantance me yake faruwa da ita ba. Sadaf sadaf ta bud'e dakin ta fice zuwa falon ta samu kujera ta zauna akai ta shiga kundin tunanin abubuwan da suke faruwa da kuma yadda akayi suka faru haka cikin kankanin lokaci. Wayar ta da take ajiye tun dazun akan kujerar ta dauka ta fara da kiran Hamma Hydar tunda dai shine ya kawo ta domin ta tabbatar daga bakin sa. Lokacin yana gidan Adda Maimuna tare da Muhd da ya shiga tashin hankali sosai saboda abinda ya faru dan Alhaji Kabir be sanar dashi komai ba sai jiya bayan an daura auren saboda yadda zai fi karbar KADDARAR sa a yadda tazo masa ba tare da yace zai tada hankali ba. Duk da hakan kuwa sai da hankalin sa ya tashi domin har ya dauki hutu a wajen aikin sa sannan yana ta kiran abokan sa na nesa yana sanar dasu bayan invitation card din da ya buga saboda na kusa duk kuwa da a kurarren lokaci komai ya faru. Shiri yake sosai cike da doki da farin ciki amma sai ya samu labarin yadda abun ya kasance. Ya masifar shiga shock da damuwa me tsanani domin yaga samu yaga rashi gashi ya kwallafa rai akan ta har kwanciya ciwo yayi daga jiyan zuwa yau duk ya zama wani iri abun tausayi. Sosai iyayen sa suka tausaya masa dan basu dauka abun zai taba shi hakan ba. Shine da Hydar yazo ya same shi ya kara bashi hakuri ya kuma nuna masa komai mukaddari ne daga Allah. Toh suna cikin maganar ne Raihanan ta kirashi sai yaki dagawa saboda baya so ya kara sosa ran Muhd din. Ganin be daga ba yasa ta juya akalar kiran zuwa Lamido. Shi ya d'aga ya kuma sanar da ita komai har abinda Aryan din be gaya mata ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta share yar kwallar da ta zubo mata. Yadda komai ya kasance ne yake bata mamaki gashi dai ta zama matar aure a wani irin yanayi da ba zata iya tantance shi ba. Tabbas tana son Aryan dan bata san tana son shi har hakan ba sai da maganar ta da Muhd ta taso. Amma duk da hakan bata so irin wannan auren ba, babu lefe babu kayan daki babu komai ko lalle babu a hannun ta haka nan take kamar ba amarya ba. Ajiye wayar tayi ta sauko daga kan kujerar ta kwantar da kanta a jikin ta shiga tunanin yadda rayuwar zata kasance mata, ya zaman su zai kasance da Aryan din duk da taga sabon Aryan akan wanda ta sani a office a yau, amma kuma zama ne na dindindin, magana ake ta har abadah. Tana cikin tunanin bacci ya dauke ta itama.   Shi ya fara tashi ana kiran sallar la'asar lokacin, yayi salati bayan ya bud'e idon sa, mikewa yayi da sauri ganin bata dakin, sai yaji kamar dama chan mafarki yake yi. Fitowa yayi falon ya hange ta daga chan ta dora kanta a jikin kujerar. Ajiyar zuciya ya sauke ya karasa ya zagaye daidai saitin in da fuskar ta take, ya durkusa a gabanta yana kallon innocent face dinta, bacci take tsakanin ta da Allah amma kuma kana gani kasan bata ji dadin baccin ba kwata-kwata domin akan hannun ta ta dora kan nata wanda ya tabbatar zuwa lokacin hannun ya gama yin tsami. Kallon falon yayi, sai ya tashi ya dauko t-pillow ya ajiye daga saitin bayan ta, ya kai hannun sa a hankali ya zare kan nata daga kan hannun ya gyara mata kwanciyar yana fatan kar ta tashi. Bata tashin ba sai motsawa da tayi kad'an ta jan numfashi ta cigaba da baccin. Komawa ciki yayi ya fada toilet da sauri jin ana kokarin tada sallar. Wanka yayi a gurguje ya dauro alwala ya fito, be tsaya komai ba ya zura jallabiyar sa ta dazu ya fesa turare ya fita zuwa masallacin. Bayan sun idar da sallar ya dawo ciki ya zauna a gabanta ya tankwashe kafarsa yana kallon ta. Kamar mafarki haka yake ji, amma kuma gaske ne komai ya faru ya wuce bayan da ya gama cire rai da komai ma ya barwa Allah zabin sa. Sai gashi Ya yi masa abinda be taba tunani ba. Sunkoyowa yayi daidai fuskar ta yayi mata peck a kumatu anan idanun sa suka gane masa cleavage dinta,tsayawa yayi chak yaja numfashi da dan karfi ganin fararen boobs dinta da suka cika sosai. Damke hannuwansa yayi ya hade su waje daya kwakwalwar sa ta shiga chaji zuciyar sa kuma na masa bitar da yake ji kamar ya kai hannun sa. Daurewa yayi ya cije saboda baya son ya zake har ta samu damar yin tunanin ko jikinta yake so, sai dai ya kasa dauke idon sa daga kai har sake durkosowa yayi sosai yana more kallon su abinda be taba gani ba, hasaso yadda zasu zama a fili idan babu wani shamaki da ya tare shi. Motsi tayi alamun zata farka yayi saurin gyara zaman sa. A hankali ta bud'e idonta sai ta ga mutum a gabanta a zaune dirshen kamar me gadin ta, da sauri brain dinta tayi mata rewinding abinda ya faru, kunya ce ta kamata ta kasa motsawa bare ta yinkurin tashi zaune ganin yadda yake zaune a gabanta kamar me daukar karatu gashi kuma saman rigar ta ya bud'e sosai har ana kirjinta. Murmushi ya sakar mata ya mika mata hannun sa ta kama ya taimaka mata ta tashi zaune tana kin kallon sa.   "Kin tashi?" "Umm." "Toh ya baccin?" "Lafiya lou." Tace muryar ta kalar tausayi "Shine kika gudo kika barni ko?" "Wayata nazo dauka." "Ok, tashi toh kiyi sallah, la'asar ta wuce sosai." "Tom." Tace ta mike a hankali, tashi yayi shima suka jera zuwa bedroom din kamar tace ba sai yaje ba amma ta kasa magana. Toilet din ta shige shi kuma ya jawo akwatin kayan ta, ya bud'e mata, ya daddaga ya dauko mata wata doguwar riga me zip ta gaba da yake ganin zata fi dadi da yanayin weather din hade da Hijab ya ajiye mata a gefen gado, ya rufe ya fita domin ya dan mata warming abincin dazun dan ba wani ci tayi ba kuma baya so ta zauna da yunwa. Ganin kayan a saman gadon yasa ta dauka ta koma toilet din ta chanja dan dama sun takure ta kayan. Sallah ta tayar tana sallar ya dawo dauke da abincin a plate da exoctic me sanyi da cup ya ajiye mata ya ja mata kofar dan ya lura nauyin sa take ji.  Falon ya koma ya dauki wayarta ya kwanta ya bud'e gallery ya shiga kallon pictures dinta da na yan gidan su ita kuma ganin be dawo ba, yasa ta sauki abinci taci fiye da rabi dan dama yunwa take ji tasha juice din shima. Ji tayi ta samu nutsuwa sosai dama da yunwa a jikinta. Tunanin kwashe kayan tayi ta dauki tray din ta bude kofar a hankali ta fito. Lokacin ya haye sama dauko notepad dinsa shiyasa bata ganshi ba. Kitchen din ta shiga ta ajiye tray din sannan ta cire janye hannun Hijab din nata ta tattare dattin dake kan plate din abincin guda biyu ta kwashe ta zuba a ledar dustbin sannan ta saka su a sink ta wanke su ta ajiye a gefe, sauran warmers din dake da abinci a ciki ta dora su kan dinning din sannan ta dauki hadin salad din ta sakashi fridge. Ya dan dade a tsaye yana kallon bayanta, dan tana shigowa ya sakko kasan yaji motsin ta a kitchen din sai ya taho ya ganta yana gyara kayan. Takowa ya shiga yi a hankali sai da yazo daf da ita sannan ta ankare da farko ma tsorata tayi ganin shine yasa ta maze. "Wa ya fada miki amarya tana aiki?" Ya lakace mata hanci yana murmushi. "Baba Hajara zata shigo ta wannan kofar idan zatayi gyaran wajen, yanzu ma nasan Baba mai gadi ne ya sanar da ita kina nan shiyasa bata shigo ba, kinsan gidan ango da amarya ba'a zuwa karka bata musu budget." "Na'am?" "Ehen, kinci abincin?" "Um naci." "Good girl, wannan Hijab din bakya jin zafi?" Yace yana mata nuni da Hijab din jikinta. Gida masa kai tayi da sauri. "I don't like it." Ya kama zare mata shi, ya cire shi ya ajiye a saman dinning din ya sa hannu ya daga ta sama ya dora ta akan dinning din. Yadda ya daga tan batare da tayi aune ba yasa ta zaro ido a tsorace. Tsayawa yayi a gabanta yana kallon jelar gashin da take a daure. Sumar kan nata ya shafa me sulbi da laushi irin ta Fulani, bata taba saka mata relaxer ba tun da take, amma zaka rantse ta saka ne saboda yadda take a kwance ko tashi batayi. Kamar dan kauye haka yake kallon gashin nata cike da yabawa, komai yayi masa yadda yake so, yasan ba wayon sa bane ba, ba kuma chanchantar sa bace yasa Allah ya bashi domin sai yau ya kara tabbatar da Raihanan ta hadu ta ko ina, body structure, gashi farar fatar da kuma kyakkyawar fuskar ta me dauke da beautiful eyes irin na Ammyn ta. "I love everything about you, everything." Yace yana kama zip din gaban rigar ya rik'e, ya dan ja kad'an ya dauko zuwa daidai saman tudun abubuwan nata yadda zai iya hangen su ta hakan ma. Da farko ta zata dukka zai sauke amma sai taga ya barshi kad'an yana murmushi. ****Gaba daya Raihana ta kasa gane kan Aryan, kamar zai maida ita cikin sa haka yake duk da be mata wani abu bayan runguma da dan peck ba amma kuma ko kallon idon sa bata iya yi saboda yadda suke ciki sosai suke haifar mata da wani irin yanayi. Tare sukayi sallar magriba da isha sannan yace mata tazo su koma saman saboda chan ne main bedroom dinsa, marairace masa tayi tace zata kwana ita anan din duk kuwa da tasan akwai tsoro sosai, be ko tsaya jin me take cewa ba ya kama hannun ta, suka fito ya haura saman da ita ya kaita har dakin nasa ya dawo ya dauki wayoyin su ya kashe hasken kasan ya haye saman. Tana zaune in da ya barta duk tsoro ya cikata, ya shigo ya ajiye komai akan bedside ya zauna a gefen ta ya kunna wayar sa dake a kashe saboda yana son kiran Kamal da Ya Nabeela. Kamal din ya fara kira be dauka ba lokacin ya tsaya masallaci suna magana da wani neighbor dinsa ya bar wayar ya gida. Sai ya kira Ya Nabeela wadda dama tun dazu take neman wayar sa a kashe ta daga sukayi maganar yana son kaya tace masa sai suje gobe yace toh sannan sukayi sallama. *__*RQ__*       Page 46 **** "Kina da alwala?" Yace yana rike hannun ta cikin nasa. Da kai ta amsa masa yace ta tashi suyi raka'a biyu su godewa Allah. A take wani novel da ta karanta ya fado mata da irin hakan ta faru abinda ya biyo baya. Kasa boye tsoron ta tayi har sai da ya dakata da kokarin shinfida sallar da yake ya zuba mata ido. "Raihana?" Ya kira sunan ta yana dawowa wajen da take tsaye. "Menene? Me yasa duk kike a tsorace?" "Ba..ba komai." Tace ba wai dan babu koman ba. "Please ki kwantar da hankalin ki, ki saki jikinki dan Allah." "Tohm." Tace da sauri "Me kike tunani?" "Ni ba komai." "Tom, koma menene kike tunani ki daina, ki nutsu sallah kawai zamuyi mu godewa Allah, sai ki bani labarin abinda ya faru bayan na dawo, shikenan sai muyi bacci." "Tom." Ta sake cewa tana jin tsoron na raguwa zuwa kaso tamanin duk kuwa da tasan zai iya fada mata kawai dan ta nutsu amma kuma sai taji ta dan samu nutsuwa ko da babu yawa, saboda muryar sa da yayi maganar bata nuna da wasa yake ba. Daga gefen damar sa ta tsaya sukayi raka'a biyu sannan yayi musu addu'a sosai har sai da ya fara bata mamakin yadda yake zubo addu'oi babu kakkautawa wanda ya haifar mata da wata irin nutsuwa a tattare da ita.    Bayan sun gama ta ninke abun sallar ta ajiye su a wajen da taga yana ajiye su sannan ta tsaya daga tsaye ba tare da ta cire Hijab din ba bata kuma zauna ba. Be lura da ita ba dan yana idar wa toilet ya nufa yaje ya wanko bakin sa da mouth freshner me kamshin mint bayan yayi brush sannan ya watsa ma jikin sa ruwa dan ba karamin jin zafi ne dashi ba shiyasa idan zafi yazo baya gajiya da watsa ruwa, ba kuma ya taba kwanciya da riga a jikin sa haka zai kure AC ya baje haka ka'idar sa take tun da ma. Yanzun ma hakan ce ta faru bayan ya watsa ruwan ya fito daure da towel din ta yi saurin janye idon ta daga kallon sa dan ta lura ko kifi ba zai nuna masa son ruwa ba. Taune leben sa na sama yayi ya nufo ta gadan gadan kamar wanda zai cike jikin ta, sai kuma ya tsaya a daidai gabanta ya yarfa mata ruwan hannun sa a fuska. "Matsoraciya, jeki yi wanka kizo mu kwanta." "Nayi dazu ai." "Yen yen,dirty girl, na dazu ai ya yi expire." "Allah be ba, ni bana son nayi yanzu." "Kina so nayi miki?" Ya kakantar da muryar sa ya fada kamar rada. "A ah, zanyi da kaina." Tace da sauri tana kokarin barin wajen "No bari dai nayi miki,karki sha wahala." Yace yana riko da jikinsa, rikon da yasa ta jin wannan abun da take ji a duk sanda suka samu body contact. "Wallahi tallahi zanyi da kaina,." "Muje toh kiyi na gani, na tabbatar kin iya din." "Na shiga uku, dan Allah kayi hakuri." "Ba zan hakura ba, komai sai ace na hakura ni yanzu dai bazan hakura ba, muje kawai." Ya rike ta gam ya nufi hanyar toilet din da ita, kwalla ce ta fara sakko mata daga idon ta, ga wani tsoro da ya mamaye ta, ya bud'e toilet din ya shigar da ita, ya tura kofar da kafarsa. Rufe idon ta kawai tayi kam ya juyo da ita tana facing dinsa sosai, ya kama zip din rigar tata ya shiga ja a hankali yana kallon fuskar ta da ta soma hawaye. Sai da ya kawo zip din kusan kasan kirjin ta sannan ya tsaya chak yana kallon halittar Allah,a cike suke taf gasu farare ta saka musu white bra me adon lace a jikin saman. "Beautiful." Ya furta cikin muryar sa da ta soma shigewa ciki sosai saboda wani yanayi da ya shiga lokaci daya. Hannu ta saka zata ja rigar sama yayi saurin rike hannun nata abunda ya ja rigar ta subce daga hannun sa tayi k'asa gaba daya. Kicin-kicin kwatar hannun ta, ya hanata ta hanyar rike hannayen nata duk biyun sannan yace. "Idan baki nutsu ba zaki jawo na karya alkawarin da nayi,." "Dan Allah kayi h..." Bata karasa ba yayi mata wata irin runguma da karfin gaske, jikinsu ya hadu waje daya a tare suka ji wani irin abu kamar electric shocking, bakin ta ya laluba ya hade shi da nasa waje daya ya shiga kissing dinta da sauri da sauri. Kusan minti biyar ya dauka a haka yana jin tamkar notikan kansa na kukkuncewa, ya damtse idon sa sanann ya hau girgiza kansa. A hankali ya saketa tayi saurin daukar rigar ta hau kare jikin ta da yake rawa kamar mazari. Wajen shower din ya nufa ya kunna ruwan sanyi ya sakar wa kansa hade da sauke ajiyar zuciya da karfi. Fita tayi da dan gudun ta, ta yi saurin zura rigar ta koma jikin gadon ta tsaya kafarta sai wani irin rawa take kamar mazari. Fitowa yayi daure da wani sabon towel din idanun sa da suka dan yi ja ya zuba mata jikinsa yayi masifar weak a hankali ya motsa bakin sa yace "Je kiyi wankan." Wuce shi tayi ta shiga toilet din, shi kuma ya fice daga dakin ya sauka k'asa gaba daya. Da sanda ta fito da ta ga baya nan tayi saurin daukar rigar da ta cire ta mayar ta haye gadon ta dukunkune waje daya ta rufe idon ta. Ya Dade a kasan be dawo ba ya zauna zaman duba wani abu a system dinsa yana yi yana shan black tea ga wani irin dum da kansa yayi masa, abinda ya hanashi shigowa dakin kenan har sai da ta gaji da kallon hanya ta hakura tayi bacci a sake da tunanin ba zai dawo ba watakila. Ta dade da baccin ma sannan ya hauro saman ya shigo dakin ya hange ta kwance ta rungume pillown sa a jikinta rigar ta tattare har wajen cinyar ta a waje tana bacci cikin kwanciyar hankali wanda ma baki daya ta manta a in da take. Kashe hasken dakin yayi ya dan haska da flashlight din wayar sa ya karaso ya hawo gadon ya kwanta a gefen ta yana kallon fuskarta. Ta rame sosai ba kamar sanda tana zuwa aiki ba, sai dai ta kara haske sosai sannan tana dauke da wannan innocent look din da ya fara gani a tattare da ita ranar da ta kawo request letter dinta, da yanayin yadda tayi a lokacin da yace Kamal yayi rejecting dinta kawai. Murmushi yayi ya kai hannu ya gyara mata gashin ta da ya dan tattashi ya sakko saman goshin ta sai ya ji kamar zufa take yi, karo karfin AC yayi dan dama itace ta rage ya kwanta rigingine yana kallon saman dakin domin sam babu bacci a idon sa har lokacin. Ya dade sosai a kwance ganin yadda ta ke ta juye-juye yayi tunanin ko sanyin dakin ne yayi mata yawa kuma, sai ya mike ya jawo standing fan ya jona a jikin socket ya kunna ta daga dan nesa da gadon ya rage AC zuwa low sannan ya kwanta yana jawo ta jikinsa gaba daya ya rungume ta tsam tsam. Ita ta fara tashi da asubah ta ganta kwance jikinsa rigar jikin ta a bud'e zip din har k'asa. Da sauri ta jawo ta ta gyara ta tashi ta zauna a daidai lokacin ya bud'e idonsa ya ganta zaune a gefen sa, ya mata murmushi bayan yayi salati ta mayar masa tana sunkuyar da kanta a kunyace. Tashi yayi ya zauna ya jingina da pillow kusa da ita. "An kira sallah?" Yace mata ta daga kai sai ya hau sakkowa a hankali daga gadon sannan ya fita daga dakin bayan ya kunna mata hasken dakin. Ajiyar zuciya ta sauke ta mike zuwa toilet ta yo alwala hade da brush sannan tazo ta shinfida sallaya ya shigo yana gyara hannun jallabiyar sa fara kansa sanye da tashi kafiya naci yayi shirin zuwa masjid sai kamshi yake, ka'idar sa ce in dai zai je masallaci sai ya fesa turare ko da kuwa ba wanka yayi ba, shiyasa kullum cikin kamshi yake hakan kuma da yake sunna ce me kyau domin ba zai je masallaci ya cutar da wani ba. "Ok na zata komawa kikayi, naje masjid toh." "Ok." Tace a hankali ya juya ya fita ita kuma ta kabbara sallarta. Ko da ya dawo sai ya tsaya wajen Baba maigadi yayi masa maganar gyaran gidan da yake so ayi, so samu a gama magana da masu aiki su fara aikin ko zuwa jibi ne. Maganar ta zaunar dashi sosai dan har ta gyara dakin ta fesa air freshener da ta gani a kayan toilet din. Toilet din ta shiga ta fara wankewa ya shigo, tsayawa yayi cike da mamakin ta, haka ake dama? Kamar wadda aka turo aiki daga zuwa sai ta fara aiki. Toilet din ya bita ya sameta tana wankewa ya dago ta, ta hanyar riko waist dinta ya mikar da ita tsaye yana hararar ta. "Waya saki?" "Ba kowa." "So kike Hydar yace na bawa kanwar sa aiki ko?" "Wanke toilet din?" "Ehen, matsa kiga na wanke." Ya matsar da ita gefe ya dauki abun wankewar ya shiga wankewa. Kana gani kasan be iya ba, be saba ba da ma dai shara ce yanayin ta sosai dan baya ma jira ayi masa, toilet ne dai yake sawa a wanke masa. Tana tsaye ya yi abinda zai yi yace ya gama ya jawo ta suka fito ya rufe toilet din lokacin kusan bakwai da rabi. Kwanciya yayi yace tazo su kwanta taki ta fice ta barshi a dakin, alarm yasa zuwa karfe tara saboda yana so ya je office yaga wani aiki, sannan zasu hadu da Barrister Awais ma akan maganar case din nan. Kitchen ta wuce kai tsaye bayan ta sakko ta tarar da Baba Hajara matar Baba me gadi a kitchen din tana goge goge kofar bayan kuma a bud'e da alama ta nan din ta shigo. Gaisawa sukayi a sake don ta gane ta, ta amsa tana mata sannu da aiki. Tayata zatayi ta hanata tace ta barshi, maimakon ta tafi sai ta tsaya a kitchen din suna yar hira kad'an kad'an har ta gama ta shigo falon zata gyara ita kuma Raihanan ta wuce dakin k'asan da suka fara zama ta saka key a kofar ta fada wanka, ta gama ta fito ta shirya cikin wata riga da skirt din atamfar ta sea green da orange dinkin fitted sannan ta warware gashin kanta ta taje shi ta saka masa mai ya kwanta, ta daura dankwalin normal dauri sannan ta ciro orange veil ta dora akai ta fito kafarta ta sanye da flat shoe. Baba Hajara ta gama aikin har ta fita sai ta zauna a falon rike da wayar ta, data kunna ta tana son kiran Daadah. Bayan sun gama wayar harda yar kwallar ta sai taji ana knocking. Ta tashi tana gyara mayafin jikinta sannan ta karasa ta bud'e. Baba me gadi ne ta gaishe shi a mutunci sannan ta karbi basket din hannun sa ta shigo dashi ciki. Breakfast ne daga gidan ya Nabeela sai ta kai kitchen ta dauko basket din jiya da aka wanke kayan ciki ta mika masa ya bawa driver da ya kawo ita kuma ta dawo ta samu plate ta zuba pepper soup din da chips ta hada da tea ta zauna a kitchen din taci sannan ta dawo falon. A shirye ya fito cikin shigar navy blue yadin filtex. Kansa sanye da hula dark and navy blue sai takalmin kafarsa sau ciki shima navy blue. Shigar tayi masifar karbar sa sai walwali yake fuskar sa a sake ya karaso falon idon sa akanta. A kusa da ita daf ya zauna har kafadar shi na gogar tata, kamshin turaren sa na Hugo Boss ya hadu da nata turaren black oud ya bada wani kamshi me sanyin dadi. "Good morning my wife." Yace yana dan ture kafadarta da tasa, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa dan bata jure kallon idon sa ta gaishe shi ya amsa sannan ya dora da korafin kin tayashi baccin kuma ta barshi har zai makara. Murmushi kawai ta sanar dashi an kawo breakfast yana kitchen sai ya kama hannun ta suka nufi kitchen din ya haye kan dinning din ya nuna mata alamar ta basu breakfast din. Zuba masa tayi daidai daidai Kar ma yace yayi yawa sannan ta dauko mug zata hada masa tea yace karta hada dashi ta ajiye yace tazo suci. Girgiza masa kai tayi tace taci yace be yarda ba sai da ta nuna masa plate da cup din dan dama saboda hakan taki wanke su sannan ya kyale ta, ta wanke su a sink ta ajiye yana kallon ta yana cin abincin sa hankali kwance sai da ya gama tas tana wajen sink din kamar me neman abu, ta bayan ta ya zagayo ya ajiye plate din sannan ya dora kansa a saman kafadarta ya shaki kamshin jikinta "Ki rage kunyar nan dan tayi yawa." "Kinga ba dan kin saka turare me kamshi ba, kin saka kuma wannan fitted rigar da kin rakani office." "Zan chanja Allah." Tace da sauri dan har ta hasaso ya barta ita kadai a gidan nan duk da akwai mutane a bq amma ba ai ba zuwa wajen su zatayi ba. "Yi sauri toh, ina jiranki a falo." Ya saketa ta juya da sauri ya bi bayan ta da kallo yana ayyana abubuwa da yawa a cikin kansa. He can't wait. Kad'a kansa yayi ya koma falon yana zaune suna waya da Kamal yana tsokanar sa ta fito tasa black abaya da medium veil, kallon sama da kasa yayi mata ya gamsu da shigar sannan ya dauke idonsa daga kanta ya karasa bawa Kamal din amsa sannan ya katse wayar yana mikewa. Hannun sa cikin nata suka fito compound din gidan in da motar sa take ya bud'e mata ta shiga sannan ya zagaya ya shiga shima ya kunna motar, da sauri Baba maigadi ya bud'e musu kofar yana daga musu hannu suka fita daga gidan. Babu wanda yasan da labarin auren a office din dan haka ne ma ko da suka shigo hannun sa cikin nata ya saka kowa mamaki, musamman su Zainab da mutuwar zaune kawai sukayi ita da Cynthia. Be ko kalle su ba ya wuce kai tsaye office dinsa hannun sa har lokacin yana cikin nata, ita duk kunya ta cikata sanin cewa basu san me ya faru ba amma kuma shi ko a jikin sa ya shige office din yana shiga ya nuna mata kujerar sa yace ta zauna ya zare hular kansa ya ajiye ya dauki wayarsa ya kira reception din, Cynthia ce ta daga dan Zainab ta masifar rud'ewa tsoron abinda ta gani da abinda take tunani ya hanata komawa ma ta zauna a wajen zaman ta. Duk dadewar da tayi tana aiki a company saboda Aryan din ne, wani irin son sa take tun ganin farko da tayi masa a lokacin suna jamia da ya zo wajen wani lecturer dinsu tun daga lokacin take bibiyar sa har sai da ta samu nasarar fara aiki dasu kuma tayi kokari sosai ta shiga jikin sa dan kafin zuwa Raihana yana sakewa da ita ko da babu yawa hakan kuma ya fiye mata komai sai gashi cikin kankanin lokaci rayuwar ta na neman dagulewa akan karamar yarinyar da bata shige sa'ar kanwar kanwar ta ba. Umarni ya bayar akan kar wanda ya shigo masa office sannan ya katse Cynthia da ta daga wayar ta kama baki tana kallon Zainab din "Oga yace kar wanda ya shigo masa office." "Na shiga uku." "Akwai matsala fa zee, yarinyar nan dai ta gama siye zuciyar sa wallahi, hannun su fa hade da juna suka shiigo babu ko kunyar idon mutane duk da babu wanda yasan alakar dake tsakanin su, ya bani kunya sosai wallahi." Ita dai zee bata da bakin magana ita kadai tasan abinda take ji dan ta tabbatar babu yadda za'a yi Aryan ya riko hannun yarinyar haka babu wani dalili. Ita kanta ta sha gwada shi da shigar da bata dace ba amma be taba ganewa ba ma dan sai ta shiga office din su gama magana be ko daga kai ya kalle ta ba. "Yarinyar nan Allah sa oga ba auren ta yayi ba." "Haba aure? Haka ake auren zee?" "Nasan abinda yasa nace haka." "Toh, zamuji ko ma menene." Tace tana komawa seat dinta dan ta lura kamar Zainab din bata cikin hayyacin ta. **RQ**          *__47__* ***System din tasa ya kunna yana daga tsayen ya hau duba abinda yake son dubawar. Tana zaune a kujerar sa tana satar kallon sa, yadda yaci serious sosai yana aikin be san tana kallon nasa ba. Dagowa yayi bayan yaga duk bayanin da yake son gani din karaf ya kamata tana kallon sa, wata irin kunya ce ta lullube ta, tayi saurin sunkuyar da kanta yayi murmushi yana takowa wajenta. "Kina bukatar wani abun ne?" Yace yana dafa saman kujerar da take zaune. Girgiza masa kai tayi alamar a ah "Kallon mijinki kawai kike yi? Kinga handsome guy ko?" "Ni a'ah, aikin fa nake son ganin." "Ba wani, kina satar kallona fa tun dazu na ganki." "Ni ba haka bane ba." Tace tana yunkurin mikewa. Hannu yasa ya maida ita baya ta zauna a kujerar yayi mata rumfa yana kallon cikin idon ta "Ina zaki?" "Office dinmu zanje, abu zan duba." "Baki da wani office da ya wuce nan ai,." Ya nuna kujerar da take kai yana sake matsota. Dauke kanta tayi ganin yadda ya zo daf da ita kamshin oil turaren ta na touch yana shigar masa hanci. Saman hancin nata ya ciza kad'an yace "Battery na ne yayi low, shine nake son nayi charge saboda yadda aikin zai tafi sosai." "Na'am?" Tace cikin rashin gane abinda yake nufi da b3. "Bari kiga." Yace yana mikar da ita tsaye, ya jawota jikinsa sosai tayi saurin kulle idon ta,saman lips dinta yayi kissing a hankali yana cigaba da kallon kyakkyawar fuskar ta zuwa lips din nata da shine abu na biyu da ke jan hankalin sa a jikinta. Bakin nasa ya kai kan nata ya soma kissing dinta gently, da sauri ta rik'e wuyan rigar sa jin yadda abun ya shiga kanta har zuwa kwakwalwarta ya chakude da wani irin mixed feeling. Rik'e shin da tayi ya bashi damar yin yadda yake so da ita domin ya samu full support din da yake so ya cigaba da kissing din nata yana wasa da harshen sa a cikin bakin ta cikin wani irin salo da shi kansa be san ya iya shi ba. Knocking akayi a kofar yana ji amma be fasa abinda yake yi din ba, sai da aka kuma kwankwasawa sannan ya cikata yana jan tsaki da dan karfi. Yasan Kamal ne kadai zai iya zuwa bayan ya bada sakon kar wanda yazo masa office. Kallon gaban rigar sa yayi ya kalle ta sai yayi murmushi kawai ya kama hannun ta ya bud'e kofar da take cikin office din, dan karamin daki ne dauke da couch da fridge sai toilet a ciki. Ya sha kwana a ciki idan yana son karasa wani aikin. Suits dinsa ne guda biyar ya rataye jikin wata hanger. Zaunar da ita yayi a gefen couch din, ya zare rigar jikin sa ya ajiye a gefen ta ya dauki silk long sleeve black ya dora akan wandon yadin sannan ya fito ya karasa gaban kofar ya bud'e yana matsa masa hanyar. "Shiru inaa ta knocking, wannan dressing din fa?" "Wanne zan amsa?" "Dukka." Yace yana shigowa ciki "Kai da aka kawo maka amarya menene na fitowa aiki haka?" "Akwai abinda dole sai nazo, maganar kayan da zasu karaso gobe ban saka hannu ba bare a fitar da kudin, sannan akan case din nan, zamu hadu da Barr. Awais shima." "Ok, nima kuma tafiya zan." "Please ka ajiye aikin nan, kazo mu zauna anan kawai." "Toh haka ake ajiye aiki kai tsaye? Aiki ma irin namu me sarkakiyar tsiya, ko zan bar aiki sai an bi matakai masu yawa." "Haka ne, yanzu yaushe zaka wuce?" "Next week zan tafi in sha Allah." "Ok, Allah ya kaimu." "Ya kanwar tawa? Hope dai babu wata matsala." "Eh babu." "Man, karka je ka wahalar da yarinyar mutane ba, yawwa." "Ni me zanyi?" "Na sanka ne, yanzu sai kayi abu kai tsaye, dan yanayin ka na jiyan nan ni kadai ina zaune na dinga tunowa." "Hmm. Ni yanzu bayan an min auren har zaman auren za'a koya min?" "Emana, karka wahalar ma mutane da yar su." "Ina Haydar?" "Be kirani ba, kila ba da wuri zai wuce ba, ko kuma ya fasa, kaima naji Ya Nabeela ta kira sweetheart tace ta shirya zata zo ta dauke ta su tafi gidan naku." "Tana nan ai." "Wa din?" "Wadda zasu je wajen nata." Dariya Kamal ya kwashe da ita, ya nuna Aryan da hannu yana sake kyalkyalawa. "Abinda ya faru da rigar ka kenan?" "Ban sani ba, kaga ni yanzu aiki na ya tsaya gashi da wuri nake son mu tafi." "No wonder naga mutuniyar ka hankalin ta a tashe, kamar ma kuka tayi,." "Wa?" "Z..." Da sauri Aryan ya tare shi "Forget it, yanzu zan cigaba da aiki, sai anjima?" "Wanne aikin a ciki? Na office ko na..." "Na abinda yazo kanka." Dariya kawai Kamal yake sosai, har ya fita cike da mamakin Aryan din. Murmushi ya samu kansa da yi ya koma wajen wayarsa ya dauka ya kira Ya Nabeela yace mata kar suje gidan zasu zo tare anjima kad'an. Bar ta yayi a ciki ya karasa aikin da yazo yi dan ya lura idan ya biye mata ba zai aikin ba. Cikin minti talatin ya kammala ya rufe komai ya kashe computer ya bita ciki. Ya sameta a zaune tana danna wayarta tana ganin shi ta mike tsaye. Kofar ya rufe ya shigo ciki ya wuce wajen kayan nasa ya dauki wandon suit ya hau zare na jikin sa zai cire. Saurin dauke kanta tayi daga bangaren sa, yana sane yayi mata haka dan yaga yadda zatayi, ta kuwa bashi dariya ganin yadda ta kauda kai da sauri. Cirewa yayi ya saka na suit din ya ninke wanda ya cire din kamar yadda yaga ta ninke masa rigar ya hada su waje daya.   Tare suka sake fitowa wannan karon ma sai da ya rike hannun ta duk da zillewar da ta dinga yi dan har ga Allah kunya take ji sosai. Office din Kamal ya nufa da ita ya tura bayan ya kwankwasa suka shiga. Waya Kamal din yake amsawa yana jikin window yana kallon harabar wajen. Shigowar su ta sashi juyowa yayi sallama da wayar. Gaishe shi Raihana tayi ya amsa fuskar sa dauke da murmushin farin ciki sannan ya dora da "Ya bakunta? Hope babu wata matsala." "Babu." Tace a kunyace. "Zamu wuce, na kira ya Nabeela nace zamu zo gidan nata, ka kira Madam sai mu biya mu dauke ta mu wuce tare ko?" "Wa zai shiga motar newly weds? A barmun baby na zan kawo ta anjima tunda dai nasan kuna chan har dare." "Kana da matsala wallahi." "Naji, kanwata sai mun karaso." "Ok tam." Tace ta zame hannun ta a hankali daga cikin na Aryan din. Be ce komai ba, ya juya ta bishi a baya suka fito daga office din zuwa reception. Kara bin su yan office din sukayi da kallo Aryan din na lura dasu, bashi da lokacin tsayawa ya bata da ya basu amsar kus kus kus din da yaji suna yi. Zee rufe fuskar ta tayi da mayafin ta, ta dunkufar da kanta akan desk kuka na sake taso mata dan ta tabbatar da abinda take tunani ne ya faru. Suna fita ta dauki wayarta ta shiga toilet ta danna number Adam, ya dade yana neman hadin kanta akam office din nasu amma saboda Aryan taki bashi irin bayanan da yake nema amma yanzu a shirye take da tayi komai.   Yana zaune a falon Alhaji Nasara wanda gama wayar su kenan da SAN Mandawari wanda ya bashi wani tabbaci akan case din Hajiya Zeenat din zuwa ranar da za'a sake zama wanda ya rige saura kwanaki kad'an. Mikewa Adam din yayi ya dan yi excusing kansa zuwa waje sannan ya d'aga wayar Zainab din da mamakin dalilin kiran shi da tayi. Da wani ne ya kirashi a lokacin bazai daga ba amma ganin itace ya kuma tabbatar maganar da ta shafi Aryan din ce yasa ya fito ya daga dan kar koma menene ta chanja shawara idan be daga ba. "Ya akayi?" Yace kai tsaye babu ko sallama bayan ya daga wayar "Magana nake so muyi." "Ina sauraron ki." "Oga Aryan yayi aure ne?" "Aure?" Yace da sauri "Eh, kamar hakan ne. Kwana biyu baya zuwa office sai yau suka zo tare da yarinyar nan Raihana, hannun sa cikin nata suka kuma shiga office dinsa." "Come again please, ban gane ba." "Abinda nake tunani kenan, na tabbatar idan babu wani dalili babu abinda zai saka shi rike hannun ta a cikin mutane haka." "Toh ke haka ake daura aure babu wanda yaji." "Please ka dai bincika, ka taimaka min wallahi son da nake masa zan iya mutuwa idan ban same shi ba, wallahi duk zaman nan da nake zaman jiran sa nake wallahi." Wani shu'umin murmushi Adam yayi, ta zo gidan sauki domin dama hanya yake nema da zai rusa Aryan din, idan har zai samu taimakon yarinyar komai zai zo masa da sauki "Yanzu ina wani abu, zan neme ki anjima mu hadu face to face muyi magana, before then zan kokari na bincika naji gaskiyar batun." "Ok nagode." Ta katse wayar ta dauraye fuskarta ta fito tana jin zuciyar ta na kekakashewa, cike da tsanar Raihanan. ***Da hannu daya yake driving dayan kuma yana rike da nata a saman cinyarsa yana murzawa a hankali. Tunda suka shigo motar be yi magana ba, har suka karaso gidan Ya Nabeela ya kashe motar sannan ya juyo ya kalle ta bayan ya sakar mata hannu "Nan gidan sister na ne, my only sister da take tamkar uwa a gareni, ki saki jikinki kinji? Zanje na dawo sai mu tafi." "Ok." Tace sannan ya bud'e motar ta fita shima ya fito suka nufi cikin gidan. Su Amna ne suka fito da gudu suka d'ane shi cike da murnar ganin sa dan kwana biyi be shigo gidan nasu ba. Daga su yayi daidai yana dariya kafin ya kama hannun su, su karasa shiga cikin falon da Ya Nabeelan take zaune tana rubuta list na kayan Raihanan da zasu siya. Ajiye pen din tayi ta rungume Raihanan a jikin tana mata sannu da zuwa. A kunyace ta amsa ta gaishe ta tana dan russunawa ta amsa a sake tana kallon nutsuwa da kyawun Raihanan wanda bata da maraba da Ammy a wanchan lokacin dan hatta murmushin ta irin nata ne. Dole kanin ta ya shiga yanayi sanda yayi tunanin ta rasa ta dan ma dai Aryan din da taurin zuciya yake idan wani ne sai abun yafi hakan. Zama tayi a k'asan carpet da sauri Ya Nabeelan ta daga ta, ta zaunar da ita a saman kujerar sannan ta kalli Aryan da ya nuna kamar ta share shi tayi dariya. "Yau ni ake sharewa?" "Ba dole ba, kanwata tazo ai sai abinda ka gani." "Ai shikenan, tafiya ma zan, sai anjima zan dawo." "Ok, amma ita anan zaka barta gaba daya sai bayan kwana biyu." Da sauri ya kalli Ya Nabeelan, ta gid'a masa kai alamar abinda yaji hakan take nufi. Sauke kansa k'asa yayi kawai ba tare da yace komai ba "Idan ka gama ka wuce gida kawai ma, zan neme ka idan mun gama muma. Ba gobe ba ba jibi ba, sai kaji mu kawai." "Ok." Yace ya mike kasan zuciyar sa na fada masa yace a ah, amma kuma yasan ko giyar wake yasha ba zai taba iya cewa Ya Nabeela a ah ba, duk abinda ta tsara hakan za'a yi dole. Har ya kai kofa tace "Ka bawa Malam Bala kayan ta ya kawo nan please, anjima zamu fita tare kuma." "Ok." Yace a sanyaye ya bud'e kofar ya fice. Yanayin sa ya nuna mata sam ba haka yaso ba, kawai ba zai mata musu bane ba, tausayin sa taji amma kuma ba zata bari tausayin yayi tasiri ba, zata yi abinda ya dace domin shi namiji ne, tasan duk sumi sumi din namiji a wannan bangaren bashi da kunya. Ita kuma Raihana tamkar kanwarta ciki daya daya haka take jin ta, dan haka dole tayi mata abinda take ganin zata kara kima da daraja a idon Aryan din duk da tasan bashi da matsala amma kuma dai hakan shine daidai. _*RQ*_ 48 ****Tashi Ya Nabeela tayi bayan fitar Aryan din tace Raihanan ta taso ta nuna mata dakin ta. Tashi tayi ta bi bayan ta zuwa wani madaidacin daki me kyau da ya sha gyara na musamman saboda zuwan nata, hade yake da dan karamin toilet a ciki sai wardrobe a jikin bango me guda biyu. "Dakin mijinki ne, anan zaki yi zaman ki har sai mun gama abinda ya kamata muyi, ki saki jikinki dani dan Allah, ni yar ki ce dan dai ba zaki iya tuna lokacin ba, baki da wayo shiyasa." "Nagode Anty." Tace cike da jin dadin karamcin ta. Ta taimaka mata sosai dan ba karamin tsoron yanayin Aryan din take ba wanda yake abubuwan nasa babu ko digon nauyi bare kunya. Fita ya Nabeela tayi tace mata tana zuwa, ta zauna a gefen gadon kamshin turaren sa da ya riga ya kama dakin taji yana shigar mata hanci. ***Ransa a dagule ya fito daga gidan, gaba daya sai yaji kamar an zare masa dukkan kuzarin sa, ba hakan yaso ba duk kuwa da dama be niyyar wuce iyakar da ya gindaya wa kansa ba, amma kuma shi an katse shi gaskiya. A dan lokacin nan yake son ta saba dashi ta saki jikinta domin har yanzu akwai tsoron sa a tattare da ita. Shi be ga amfanin zaman ta wajen Ya Nabeelan ba tunda dai an riga an daura shi baya bukatar komai a bar shi da matar sa zai san yadda zai yi. Main house dinsu ya wuce kai tsaye dan yaji tukin ma duk ya fice masa a rai kuma zai shiga gari sosai gwara kawai yaje ya dauki Driver su fita. Gidan shiru kasancewar babu kowa sai masu aiki dake kaiwa da komowa a cikin gidan suna gudanar da aikin su. Niyyar sa yau ya dawo gidan tare da Raihana amma sai gashi Ya Nabeela tayi masa shigar sauri ba zai kuma iya ja da hukuncin ta ba. Kamal ne ya fado masa ya dauki waya ya kirashi dan yana da yakinin da saka hannun sa a wannan decision din da Ya Nabeela ta yanke domin yaga alama gaba daya sun hade masa kai suna acting kamar wasu iyayen sa, da sauki idan Ya Nabeela ce kawai amma banda Kamal da shi har yanzu a matsayin aboki yafi jin sa kuma dan uwa fiye da wai wa da ya girme shi. Parking yayi a kofar gidan nasu daidai lokacin da Kamal din ya daga wayar yana kokarin fita daga office domin yaje gida ya dauki Khadija ya kaita gidan Ya Nabeela. "Tare da kai aka hada baki aka karbe min mata?" Yace kai tsaye ko sallama be bari Kamal din ya amsa ba. "Karbe mata kuma? Ban gane ba." "Baka san shirin Ya Nabeela na rike min mata ba? Daga zuwa sai tace wai tazo kenan sai an neme ni." "Hahaha... Tsakani da Allah fa? Haka Ya Nabeelan tace?" "Ka rantse baka sani ba?" "No Allah ban sani ba, bamu yi maganar da ita ba wallahi, amma me yasa zata karbe ta, ko dai taga rawar kan ka tayi yawa ne?" "Oho, nima ban sani ba." "Wannan tsarin yayi min dadi, bari na karasa gidan naji kanun labarin." "Wai ni har nawa ka biya min sadakin nan ne? Naga alama dan kun karbo min aure juya ni zaku dinga yi." "Gaskiya sai abinda ka gani kawai, kayi biyayya mu baka mata kaki mu barka da hamma wallahi. Ga koshi ga kwanan yunwa. Kaga sai ka bada himma sosai wajen aikin office ka daina zama distracted har rigar ka na baci." Kit Aryan din ya kashe wayar yana jan tsaki, cike da takaicin maganganun Kamal din. Horn ya danna a gate din da karfin gaske, maigadin ya taso da gudu ya zo ya bud'e gate din, shiga ya shiga a guje ya samu gefe yayi parking, sannan ya fito. Yahya ne ya tashi da sauri ya karasa wajen sa. Cilla masa key din yayi ya chafe yace fita zamuyi, sannan ya juya ya shige cikin gidan. Dakin sa ya wuce kai ya cire kayan jikin sa ya sauya zuwa wasu daban ya saka socks da sau ciki sannan ya fito ya samu Yahya ya fito da motar da yasan Aryan din na nufi daga rumfa ya kawota tsakiya. Gaba ya bud'e gefen Yahyan ya zauna hannun sa rike da wasu files. "Ina zamu oga?" Yace yana saita motar akan babban titin "Chamber." Yace a gajarce ya cigaba da duba takardun har suka karaso chamber din su Barr Awais din. Sauka yayi yace ya maida motar inuwa ya jirashi ya shiga ciki. Suna zazzaune a wani round table Aryan din ya shigo, ya samu waje ya zauna suka gaisa sannan Barr Awais ya turo masa file din gabansa yace "This is a sad news." "Me ya faru Barr.?" Yaja takardar gaban sa yana dubawa "Menene ma be faru ba? Mutanen nan ta karfi da yaji suna kokarin sauya dokar nan, ko nace ba sauya ta zasuyi ba, kawai bata aiki ne akan masu arziki." "Ban gane ba?" "Duba a hankali." Yace yana mikewa tsaye. Ran Aryan din ne ya baci sosai bayan ya gama karantawa, ya mike shima yana kallon Barr. Awais din. "Me suke nufi?" "Zasu bada belinta a zaman da za'a yi next." "Innalillahi, haka k'asar tamu ta zama? Kisa fa ta aikata,duk shaidu sun bayyana, me yasa zasu sauya komai?" "Wallahi tallahi, at first da na samu labarin ban yarda ba, sai gashi na samu waya daga Barr namadina ya kuma tabbatar min da zargin da ake yi, yanzu haka kotu ta hana hukumar DSS kama Justice Mandawari duk da dama ya fice daga k'asar tunda aka kama Hajiya Zeenat. Ashe shiri yake yi sosai akai, domin gaba daya saman tasu ce, yana da manya sosai a k'asar nan. Anya wasu alkalan zasu gama da duniya lafiya kuwa? Sune suke Sawa ayi mana kudin goro gaba daya." Shafa kansa Aryan yayi da ya daure masa tamau saboda abinda yake shirin faruwar wanda be taba kawowa ba, yace "Yanzu menene abun yi?" "Dole zamu jira zaman da za'a yi jibi, anan zamu tabbatar da gaskiyar abinda yake yawo akan maganar." "Ya Allah!" Ya zauna a hankali ya dafe kansa, me yake shirin faruwa? Dafa shi Barr Awais yayi ya tsaya a gabansa ya dago yana duban sa "Menene alakar Alhajin ku da Adam?" "Adam? Babu wata alaka face ta auren mahaifiyar sa da Daddyn yayi." "Ok, ya shigar da kara kotu ne, yana bukatar kotu ta bi masa hakkin sa a matsayin sa na d'a wajen Alhajin." "Wannan maganar banza ce." "Yana da support sosai, dan haka ne ma nake tunanin akwai wani gagarumin abu da mu bamu sani ba, alakar Hajiya Zeenat da Alhaji. Am sorry to say amma akwai abinda mu bamu sani ba." "Na gaji wallahi, na gaji da duk wannan abubuwan dake faruwa. Inaga zan yi nisa da kowa na bud'e sabon shafin rayuwata. A sanda nake tunanin komai ya wuce a lokacin wani sabon al'amarin yake budewa." "Ba zaka ce haka ba, dole sai anyi hakuri sannan za'a kai gaci, sannan muna bukatar tabbatar da gaskiya domin a samu yiwa kowa adalci. Sai dai ina da yakinin a yanzu muna da bukatar support din Alhaji, domin a bayanin da na binciko, akwai wani babban al'amari da yayi matukar bani mamaki." "Menene?" "Tabbas Hajiya Aisha matar Barrister Nasir tana nan da rai, kuma tana wani waje a killace wanda nake kyautata zaton Alhaji yana da masaniyar komai." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun." "But bincike na ne ya sanar dani hakan, bani da tabbacin gaskiyar maganar, ina tunanin Hajiya Zeenat tasan abinda ya faru." "Ta sani, dan duk abubuwan da ya aikata tana da masaniya itace dai bata bari yasan nata." "Yanzu me ya kamata muyi?" "I don't know, ban sani ba wallahi. Kaina ya kulle gaba daya." "We have to figure out abinda ya kamata if not duk effort dinku zai tashi a waste." "Ya ma tashi." Ya mike dan be kuma sai me zai ce ba "We have to wait zuwa ranar muga abinda zai faru, idan yaso sai muga action din da ya kamata mu dauka." Barr auwal ya fada yana kallon Aryan din. Be ce komai ba, ya juya kawai ya fice daga wajen. Yana fita suka saka dariya gaba dayan su Barr Awais ya dauki waya ya yi kira sannan ya ajiye yana murmushi. ***Bayan motar ya bud'e ya shige dan gaba daya ya rasa me yake shirin faruwa dashi, wacce irin rayuwa mutanen mu suke yi? Tabbas be yarda da maganar Barr Awais ba, dan duk wani abu ma da yake faruwa dole da saka hannun sa. Shikenan babu wanda zakayi trusting a duniyar nan kowa ya lalace ya zama mutumin banza? Gidan sa ya ce Yahya ya kaishi dan ko magana baya son yi sosai, da k'yar ma ya iya bud'e baki ya amsa masa da in da zai kaishin ganin ya nufi main house din su dashi. Suna isa ya balle murfin motar ya fice ya shiga ciki ko bi takan Baba me gadi da ke masa magana be yi ba, be ma jishi ba kwata kwata saboda yadda hankalin sa baya tare dashi. Be san yadda Kamal zai ji ba, abinda yayi sacrificing dukkan time dinsa akai, cikin dan kankanin lokaci wasu mutane marasa daraja sun lalata komai. Saukin ta daya gaskiyar waye shi ta bayyana ga mutanen da ya kamata su sani din, amma bayan wannan babu wata nasara. Shiyasa tun farko Aryan be so aka yi ta daga zaman nan ba, domin yasan yadda k'asar take ya kuma san mugun connection din Hajiya zeenatun zata iya komai, tunda ta riga ta bar hannun DSS ta koma hannun kotu in da suke da damar yin abinda suke so domin alkalan nan ba kirki ne dasu ba. Kasa zama yayi ya dinga zagaye a dakin cikin yanayin bacin rai me tsanani. Ji yake kamar ya juyar da rayuwar sa ya chanja ta zuwa wani bangare na daban ba wanna din ba, ya manta kowa da komai ya fara rayuwar sa sabuwa ba tare da kowa a tattare dashi ba. Karar wayar sa ta dawo dashi cikin hayyacin sa, ya kalli me kiran Kamal ne, yana kallo ta gama burarin ta, ta katse sai kawai ya duka ya kashe wayar baki daya ya juya ya bar dakin. ***Fita sukayi bayan Kamal ya kawo Khadija gidan ya tafi. Ya Nabeela tace su fito suka nufi wani hadadden beauty spa and salon da tayi ma Raihanan booking jiya da daddare. Me wajen kawarta ce shiyasa ma suka karbi Raihanan duk da ana booking ne kusan wata guda kafin nan in dai bridal treatment ake so. Cike da kwarewa receptionist din ta karbe su ta basu wajen zama sannan tayi waya aka kawo musu ice tea kafin ta zo kansu. Kallon wajen Raihana take cike da burgewa kad'an kad'an suna hira har aka ce su taso aka shiga dasu ciki Ya Nabeela kuma ta nufi office din kawarta da tazo saboda Ya Nabeelan amma ba ko yaushe take shigowa ba ma. Cike da kwarewa aka shiga wanke musu kafa dukan su daga ciki kuma ana shirya kayan da za'a soma mata gyaran jikin na alfarma irin na manyan mata yan kwalisa. Ita aka fara gamawa wankin kafar aka ce ta taso, kafar tayi wani irin kyau da taushi ta dinga kallon kafar kamar ba tata ba saboda yadda tayi kyau kwarai. Ciki aka shiga da ita wadda zata mata gyaran jikin ta soma aikin ta bayan ta sauya kayan ta zuwa rigar da ake amfani da ita idan zaa ma mutum gyaran. Sai la'asar likis sannan suka gama da wajen dan ma dai akwai ma'aikata itama Ya Nabeela an gyara kai da kafa haka ma Khadijan Kamal. Wani irin kyau fatar Raihanan ta fara tun a yau din kuma a kalla zasuyi kwana biyar zuwa sati daya suna zuwa ta tabbatar idan aka yi kwanakin nan ita kanta ba zata gane kanta ba. Har suka isa gida Khadija na ta koda ta Ya Nabeela na dariya suna zuwa sallar magriba sukayi suka ci abinci. Sosai Raihana ta sake da Khadijan dan tana da sakin fuska da wasa da dariya sosai a dakin da aka bawa Raihanan suka zauna suna hira har Kamal yazo daukar ta. Duk sai taji babu dadi kamar kar ta tafi haka dai ta rakota falon in da Kamal da Ya Nabeela suke maganar Aryan din da kiran da Kamal yayi masa be d'aga ba daga baya kuma wayar tasa a kashe "Na zata ma zai dawo wallahi." "Ai yana jin nauyin ki, da dai nine marainin wayon sa. Amma bansan me yasa ya kashe waya ba gaskiya, haka kawai baya kashe waya sai dai idan akwai yar matsala." "Ko fushi yake na dauke masa matar sa?" "Anya? Zan dai biya ta gidan na same shi idan yana chan." "Ok." Tace a sanyaye. Gaishe shi Raihana tayi sannan ta yi wa Khadijan sai da safe ta juya ciki. Duk sai taji ta kasa nutsuwa da ta ji suna maganar ya kashe wayar sa kuma shiru be dawo ba duk da Ya Nabeelan ce tace kar ya dawo amma ai da wasa take masa. **RQ**     49 ***Kwantawa tayi lamo akan gadon cikin tunanin ko lafiya? Juye juye ta dinga yi har Ya Nabeela tayi knocking ta shigo ta sameta a kwance ta tashi zaune bayan ta shigo. "Kin gwada kiran Aryan kuwa?" Tace tana zama a gefen gadon. Girgiza kai tayi tace "A ah." "Call him please, na fara jin babu dadi, ko maida ke zanyi? Wai so nake yadda akayi auren nan urgent a kalla ki samu gatan da kowa ta samu, amma idan hakan zai takura masa gwara ki koma, bana son abinda zai taba lafiyar sa an samu ya fara warewa" Shiru Raihana tayi bata san me zata ce ba tunda har lokacin nauyin Ya Nabeelan take ji sosai. "Kira shi kinji? Bari naje naji shigowar Daddyn su Amna xan dawo." "Ok tam." Tace a sanyaye ya Nabeelan ta fita ita kuma ta dauki wayar ta, ta yi dialing number tasa. Kunna wayar sa kenan bayan ya tashi da k'yar daga wajen da yake zaune tun da ya idar da sallar isha. Ji yayi yana son kiran ta a kalla zai dan ji saukin abinda yake ji din a zuciya da ruhin sa. Sai ga kiranta ya shigo a daidai lokacin. Kallon number yayi kafin ya daga cike da mamakin co-incidence din da aka samu dan har ya hau kan number tata zai kira kiran ta ya shigo masa. Mikewa yayi sakale da wayar a kunnen sa ya koma saman gadon ya kwanta rigingine yana jin tayi sallama ya amsa a chan k'asan makoshin sa. Shiru ya biyo bayan amsa sallamar tasa saboda rashin sanin abinda zata ce masa, muryar kadai ta isa ta tababtar mata ba lafiya ba. "Ya Nabeela ce tace na kiraka dama." "Ok." Yace ya sake yin shiru. Sai ta rasa me zata ce masa kuma. Tana jin yadda yake sauki numfashi da dan karfi dan tana jin sound din sa. Kusan minti biyar suna a haka sai kudin ta ya kare. Kiran ya biyo a take ta d'aga jikin ta a sanyaye. "Raihanaaa." Ya kira sunan ta cikin jan sunan. Har cikin kwakwalwarta taji yadda ya kiratan. "Kina so na?" "Na'am?" "Tell me, kina so na? Zaki zauna dani duk tsanani duk runtsi? Ba zaki gujeni ba?" "Menene ya faru?" "Just answer me please, did you love me?" Hadiye yawu tayi jin yadda ya tsare ta, muryar sa kuma a chunkushe alamun ba da wasa yake ba. Sake maimaitawa yayi a karo na uku ta tashi tsaye tana tattaro kalaman bakin ta da take jin sun mata nauyi tace "Yes, ina sonka. Amma me ya faru? Me ya same ka?." Wata irin ajiyar zuciya ya sauke me karfi sannan ya k'ara gyara kwanciyar sa ya dora wayar a saman kirjin sa a hankali yace "Nagode sosai, babu abinda ya faru inaso kawai na sani ne." "Ok, but muryar ka..." Katse ta yayi yace "Missing dinki nake, inaso na ganki. Nazo?" "Eh kazo." Tace zuciyar ta na wani irin harbawa da sauri. "Ok, I'm coming right away." "Ok." Tace a sanyaye suka ajiye wayar. Sai ta kasa tashi daga in da take zaune kirjinta na cigaba da dukan uku uku, yanzu idan yazo ya zatayi dashi? Daga jin yadda yake magana rigima kawai yake nema,kar Ya Nabeela tace ma so take ta tafi, amma kuma ya zatayi masa? Ba zata iya hanashi zuwan ba dan tana son ganin shi ta kuma san halin da yake ciki.    Dawowa Ya Nabeela tayi dakin ta tambaye ta sunyi waya? Eh tace mata amma sai ta kasa fada mata yace zaizo yanzu. Sai da safe tayi mata ta ja mata kofar ta nufi part din Dr Farouk saboda lokacin kusan goman dare.   Da kansa yake driving din duk da jikin sa babu kwari sosai amma kuma yasan idan ya ganta zai samu wani kaso daga cikin energy din nasa, duk da yasan Ya Nabeela zata masa tsiya amma kuma bashi da wani option idan ba zuwan ba, yana so ya rik'e ta a jikinsa yana shak'ar kamshin jikinta me dadi da yake saka shi manta dukkan damuwar sa. A waje yayi parking motar ba tare da ya shigo ba, ya kwankwasa kad'an gate man din ya leko ya ganshi sannan ya bud'e masa da sauri. Haske sosai a harabar gidan ba zaka ce daren yayi har haka ba. Suka gaisa ya zaro wayar sa ya kira Raihanan ya ji tana ina. Sai da kirjin ta ya buga da karfi da taga kiran nasa wanda ta tabbatar da ya karaso kenan. Dagawa tayi jiki a sanyaye yace tana ina, ta fada masa tana dakin sa. Murmushi yayi da ya tuna da kofar baya ta dakin da yake amfani da ita idan baya son shiga cikin gidan. Ce mata yayi ta bud'e masa back door din, ta tashi ta bud'e masa ya shigo ya maida kofar ya rufe. Taku daya tayi da nufin komawa tsakiyar dakin ya riko ta da sauri ya sakata a jikinsa yana sauke nannauyar ajiyar zuciya. Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke itama dan ba karamin nutsuwa take ji ba a duk lokacin da ya rungume ta a jikin sa. Hancin sa ya kai saman wuyan ta ya shiga shinshinawa a hankali kamshin da jikin ta ke fitarwa na gyaran jikin da akayi mata ya shiga fizgar shi. Hadadden kamshi ne me aji da sanyin dadi wanda be taba jin irin sa ba. "I love this scent!" Yace yana kara kai kansa sosai ya zura a jikin wuyan nata wanda take jin hakan tamkar tafiyar tsutsa. Kankame shi tayi yayi murmushi yana raba jikinsa da nata ya zaunar da ita sannan ya durkusa a gabanta ya rike hannun ta. "Wani abu zai faru dani wanda ni kaina bansan menene ba, abu daya na sani shine, sai na cika alkawarin da nayi wa kaina, ko da kuwa hakan na nufin katsewar numfashi na. Ina fatan zaki zauna dani duk runtsi duk wuya, ba zaki gujeni ba." gid'a masa kai tayi idon ta na cicikowa da kwalla. Hannu ya kai ya share mata saman idon yana girgiza mata kai "Karki zubar da hawayen ki akan abinda be chanchanci zubar su ba, zan yi komai da kaina ba tare da kowa ba, kuma sai na tabbatar da duk wanda yake da hannu ya fuskanci hukunci me tsanani." "Su waye menene suka yi maka?" "Karki damu, just pray for me." "Tom, please karka saka kanka a wani abun dan Allah." "Ba abinda zai faru kinji? Na miki alkawari amma karki sanarwa kowa, sirri ne tsakanin mata da miji." "In sha Allah." Tace a sanyaye. Mikewa yayi daga gabanta ya zauna a gefen ta yana jawo ta jikin sa. Ya lumshe idon sa yana jin saukin abinda yake ji a ransa na bacin rai. Abinda ya rasa a baya da har ya bari bacin ransu yayi masa mummunan tasiri a rayuwar sa. Amma banda yanzu da yake jin yana da abu me muhimmanci da zai yi protecting, yana kuma da burin tara family nasa na kansa. Yayi musu irin tarbiyyar da yake so. Su rayu cikin so da kaunar junan su. Ba zai kyale duk wanda ya shiga gonar sa ba a wannan karon, idan har ya tabbatar da Barr Awais amanar su suka ci, sai yayi maganin su da duk wanda suke yiwa aiki, zai aje rigar hukuma ya saka wadda ta dace dasu zai kuma yi amfani da abinda Hajiya Zeenat din take ji da takama dashi wato dukiya wajen yakar ta.     Baya yayi dasu suka kwanta akan dan madaidacin gadon da yafi kama da na mutum daya, ya kara jawota sosai jikinsa har kusan rabin ta na saman sa. Hannun sa ya kai saman gashin ta yana shafawa a hankali, yana sauraron heart beat dinta take tafiya kusan daidai na nasa bugun zuciyar. "Inason babies Raihana." Da sauri ta yinkura zata tashi ya matse ta yana murmushi "Ba yanzu nace ba, kawai nace inason yara ne, da yawa da yawa kinga mu bamu da yawa, ina sha'awar naga mutum da yara masu yawa." "Ni ba ruwana." Tace tana turo baki. "Da ruwanki, kece zaki bani dukka kuma." "Ka tashi ka tafi kar Ya Nabeela ta dawo." "Um um ba in da zani, idan tazo ma shikenan kinga" "Dan Allah ni dai ka tafi." "Kora ta kike?" "Eh." Tace tana tashi zaune. "Ba in da zani, ai daki na ne nan din." "Yanzu ai ya zama nawa." "Aro dai aka baki." "Toh ka tashi ka tafi." Ta ture shi ganin yana matsowa gareta. "Kinaso in tafi?" "Eh." "Ok zan tafi, amma har yanzu b3 na a low yake, dazu ma 30% kawai yayi kuma ya zuke nan da nan, yanzu 50 nake so yayi kawai sai na tafi." "Toh ba sai ka saka charjin ba, ai akwai wuta." . Tace pretending bata gane me yake nufi ba. Murmushi yayi yana mata wani kallo me dauke da ma'anoni. Bakin ta da yake maganar ya bawa attention dinsa sosai. Kunya taji ta rufe fuskarta da sauri ganin yadda yake kallon ta. "Kinga yanzu ma ya koma 0, anya ba bari zanyi yayi 100% ba kawai?" Mikewa tayi ta hau yunkurin sauka daga gadon cike da dana sanin cewa yazo, ita wai ta tausaya masa ne amma ashe ba haka bane ba. Riko ta yayi ya dawo da ita kan gadon ya yi mata rumfa da jikinsa ya dora mata baki daya nauyin sa. "Kin yarda in samu full charge din?" Girgiza masa kai tayi alamar a'ah da sauri tana matso kwallar jin yadda ya danne ya hanata kwakkwaran motsi. "Dan Allah kayi hakuri." "Dan Allah kiyi hakuri." Ya ciji lips dinta na k'asa ya kwaikwayi muryar ta. Runtse idonta tayi ganin ya saka kansa a jikinta yana bin jikin nata da wani irin salon kiss. Jikinta ne ya dauki rawa ta rikice tsoro ya shigeta tayi kokarin ture shi amma ta kasa kwata kwata, numfashin sa yake sauke mata yana cigaba da abinda yake matan yana kuma saka idon sa a nata yana kallon reaction dinta. Hannun sa ya shiga zagaya a jikin nata zuwa saman cikin ta da yasa hannu ya yaye rigar t-shirt din dake jikinta ya zura hannun zuwa in da batayi tsammani ko tunani ba. "Wayyo Daadah." Ta furta da dan karfi jin yadda ya kaiwa b***b dinta riko, saurin hade bakin ta da nashi yayi waje daya ya cigaba da yawo da hannun nasa a saman kirjinta yana mata kamar tafiyar hawainiya. Sosai ta rude jikin ta ya hau rawa ta rasa in da zata saka kanta sai jujjuya kanta take saboda abinda yake mata ba karamin rudata yayi ba. Romancing dinta ya shiga yi sosai yana cigaba da kissing din bakinta cikin salon da ya sata fashe masa da kuka. Kukan tane ya ankarar dashi abinda yake aikatawar, da kuma abinda yake shirin zarmewa idan har ya biye wa mahaukacin feeling din da ya taso masa a lokacin. Cikata yayi ya dagata ya kwanta a gefen ta yana maida ajiyar zuciya ya jawota jikinsa ya manne ta yana lumshe idon sa da yake jin kamar kansa zai fashe saboda yadda ya yi masa nauyi. Be san me ya hau kansa ba, duk da abinda yayi din ba haramun ya aikata ba amma ba yanzu bane right time din. Dan light romance yaso sai gashi ya zarme da yawa har yana neman wuce gona da iri. Zafi sosai bakinta yake mata da saman kirjinta, haka ya saka ta kuka k'asa k'asa yana jinta ya hanata tashi duk da attempt din da tayi na son tashin. Bacci ne ya soma fusgarshi bayan wasu mintuna ya sake kankame ta yana jin baccin sosai na rinjayar sa. Tashi tayi ganin yayi bacci ta zubawa fuskar sa ido zaka rantse ba zai aikata abinda ya aikata a yanzun ba, innocent face gareshi da wani irin shariya wanda zaka dauka irin su rike hannun mace ba zasu iya ba bare har su iya hada jiki da ita. Ita gaba daya ma tsoro ya bata dan yadda ya sauya mata lokaci daya. Saukowa tayi daga gadon ta dan harare shi kad'an tana cije bakin ta da lips din suka dan yi ja kad'an ta wuce toilet tana gyara rigar jikinta da ya maida mata ita sama.   _**RQ**_ Page 50 ***Wajen karfe uku da rabi na dare ya farka daga baccin da ya dauke shi. Kansa ne yayi masa wani irin nauyi har zuwa idanun sa. Shi kadai ne a saman gadon tana k'asa ta shinfida sallaya ta kudundune a cikin Hijab dinta tana bacci. A hankali ya zuro kafafun sa ya sakko ya dagata daga k'asan zai maida ita sama ta bud'e idon ta da sauri dan ba wani bacci me nauyi tayi ba. Be lura da ita ba, ya ajiyeta a gadon ta yi saurin maida idonta ta rufe tana jinsa ya zare mata Hijab din jikinta sannan ya tashi ya nufi toilet din. Wanka ya fara yi sannan ya dauro alwala ya fito ya haye sallayar da ta tashi daga kai ya shiga raya daren cikin neman taimakon Allah a abinda yake shirin yi. Karfe hudu da rabi akayi kiran farko ya dauko wayarsa ya bud'e application din alqur'ani me girma ya kunna ya dan rage volume din ya jinginar da kansa a jikin gadon yana sauraron karatun yana shiga chan cikin zuciyar sa yana saukar masa da nutsuwa. Yana zaune har aka yi kiran sallar, ya duba time din yaga biyar da kwata. Sai ya mike tsaye yana gyara zaman rigar jikin sa. Ya kalle ta tana bacci hankalin ta kwance. Sai ya sunkuyo kanta yayi kissing dinta a saman goshin ta a hankali sannan ya bud'e kofar ya fita daga dakin. A gate suka hadu da Dr Farouk ya kalle shi da mamaki dan be yi tunanin a gidan ya kwana ba duk da yaga motar sa amma be kawo yana nan ba, Sai dai yana ganin shi yasan dalilin da ya kawo shi dan shi kansa sai da yayi wa Ya Nabeela fadan akan me zata dauko masa mata ta ajiye ta dai kawo excuse dinta amma shi sam be gamsu ba, dan be ga amfanin zaman ba. Ganin da yayi wa Aryan din a yanzu ya bashi dariya ganin yadda ya Nabeela ta hakikance jiya akan maganar ashe Aryan din na cikin gidan ma a lokacin. Lallai shaanin maza sai a barsu kawai. Gaishe shi yayi ya amsa yana tsokanar sa yayi murmushi kawai dan yasan bazai fadawa Ya Nabeelan ba. Tare suka je masallacin sukayi sallar sannan Aryan din ya tafi shi kuma ya shiga ciki yana murmushi shi kadai. Ganin yadda yake ta faman smiling yasa Ya Nabeela tambayar sa dalilin Murmushin sa amma sai yace mata sirri ne ba zai fada mata ba, sai an kwana biyu idan ma zata ji abinda ya faru. Tasan halin shi sarai ko me zatace ba fa zai fada matan ba tunda yayi niyya shiyasa sai ta kyale shi ta nufi dakin Raihanan taga ta tashi. Ta riga ta tashi tana ma toilet sanda Ya Nabeelan tayi Knocking a kofar sai kuma taji alamun ruwa sai ta juya kawai tasan ta riga ta tashi. Yana fita tana tashi ta shiga toilet din dan yin alwala tayo alwalar tazo tayi sallah bayan ta idar ta zauna tana azkar tunanin abinda ya faru tsakanin su na dawo mata a kwakwalwa. Bakin ta, ta dan shafa sai taji ya saki ba kamar jiyan ba. Samun kanta tayi da yin murmushi kawai ta chusa kafarta a tsakankanin cinyoyinta kunyar abinda yayi matan na kamata. Zai yi wuya ta iya kallon sa face to face a yanzu dan jiyan nan sosai ya wuce gona da iri da wasu irin salo da kwanyar ta, ta gagara dauka sam. Sake dawowa Ya Nabeela tayi dakin ta tashi taje ta bud'e mata ta shigo ta zauna Raihanan ta gaishe ta, ta amsa a sake tana tambayar ta bakunta. Amsawa tayi a kunyace ta dan zauna a dakin har garin yayi sha sannan ta tashi zata fita Raihana tace ko akwai aikin da za'a yi? Girgiza mata kai tayi tace "Akwai masu aiki karki wahalar da kanki, idan kin gama sha'awa zata shigo ta gyara miki dakin." "Zan iya gyarawa ma Anty." "Ban saki ba, kar ace ina wahalar da amarya." Tace tana dariya murmushi Raihanan tayi itama "Kinsan halin mutanen naki, jiya ma munsha fama da Daddyn su Amna wai akan me zan dawo dake, haka Kamal ma yayi ta mita suji kuma yanzu na barki da aiki ai sai kiji an aiko min da sammaci." "A ah dai Anty." "Ahaap, baki san halin su ba ai, sun iya son kansu." "Me zaki ci breakfast, ko da yake ma nasan me ya kamata na baki." Ta juya ta fita ita kuma Raihanan ta hau zare zanin gadon da duk ya yayyamutse kamar an yi dambe a kansa. ***Bacci ne a idon sa dan haka yana isa gidan tubewa kawai yayi ya haye gadon ya kwanta. Ba shi ya farka ba sai kusan sha daya, shima knocking ne ya tashi shi ya mike da k'yar muryar sa a chunkushe yace waye "Bud'e ka gani mana." Adam yace da full confidence. Muryar sa Aryan yaji, yayi tsaye cikin tunanin abinda ya kawo shi a lokacin bayan sai da ya tabbatar ya kwashe kayan sa tas daga gidan. Sake knocking yayi da dan karfi, Aryan din dake tsaye ransa ya soma baci ya isa kofar ya bud'e yana kallon sa. Kallon sama da k'asa Adam din yayi masa sai kuma ya bushe da dariya yana rik'e baki "Ina matar? Ko ba aure kayi bane ba? Naji ance kayi auren boye." "Me ya kawo ka?" Yace a fusace fuskar sa na sauyawa nan da nan zuwa bacin rai "Relax." Yace yana wara hannun sa. "kamar yadda kake da iko da gidan nan haka nake dashi, so karka daga min murya please. Zuwa nayi na maka murnar aure a matsayi na, na dan uwanka. Sai kuma nagan ka a haka." "Kana tunanin wai kana da waje a gidan nan Adam?" "Yes ofcouse, baka sani ba? Ko da yake ba zaka sani ba nasan. Kamar yadda kake da iko da right da gidan nan haka nake dashi nima." Tabe baki Aryan yayi yace "Ok yayi, zaka iya bani waje ko?" Ya kama kofar zai rufe Adam din ya rik'e da sauri "Ina matar wai? Ko dai ka kasa... Nooo don't tell me baka da wannan energy din, nooo." Sai ya rufe bakin sa da sauri yana dariya. Rufe kofar Aryan kawai yayi ba tare da yace komai ba. Yana jin dariyar Adam din cikin izgilanci ya wuce toilet ya sakarwa kansa shower ruwan ya dinga shiga simar kansa yana ratsa shi sosai. Ya dade a haka kafin ya dawo daidai sannan ya fito ya hau shiryawa a tsanake tamkar wani abu be faru ba. Shigar kananan kaya yayi masu kyau da aji ya saka sandal ya fito ya fice daga gidan yana jin hayaniyar Adam din kamar ba shi kadai bane a gidan ba ko kuma waya yake. Gidan Kamal ya wuce kai tsaye ya kirashi yana hanyar yace zai karaso. Lokacin Khadija na tayashi had'a kaya domin tafiyar tasa ta dawo yau saboda wayar da ya samu daga chan sama dole a yau zai wuce dama hutun nasa yaso yayi yawa dan dai shugaban su mutumin sa ne sosai. Zuwan Aryan din yasa ya bar ta, ta karasa hada kayan ya dawo falon wajen Aryan din da zuwan nasa haka urgent ya bashi mamaki. Sai dai a yadda ya ganshi a nutse tsaf ya samu kwanciyar hankali sosai har yayi masa maganar tafiyar sa da ta taso wanda da yaso sai yaje zai gaya masa amma ganin komai normal yasa kawai ya sanar dashi. Aryan din be nuna komai ba yayi masa addu'ar nasara sannan suka dan taba hira har suka gangaro kan shari'ar da za'a zauna gobe wanda Kamal din yaso yana nan za'a yi. Sam Aryan be fada masa abinda yake shirin faruwa ba, ya barshi kawai a goben suke saka ran za'a gama komai. Har bayan azahar suna tare a gidan Kamal din, sai da Habeeb yazo daukar Kamal din sannan Aryan yayi masa sallama ya tafi. Company ya wuce duk da yau ba ranar aiki bace ba, ya bud'e office dinsa ya shiga ya rufe ta ciki, ya dade sosai har kusan tara yana wajen sannan ya fito ya wuce gidan sa dan ba zai koma main house din ba yasan Adam yana chan. Shiryawa yayi ya saka kayan sa da yasan zai bukata a booth din motar sa, wajen sha daya ya fito ya nufi main house din ya ajiye motar tasa ya dauki kayan ya saka a motar Daddy sannan yasa Yahya ya kaishi gidan Ya Nabeela. Kiran ta yayi suna daf da gidan ta kalli wayar ta kalli Ya Nabeela da ta shigo suna maganar abubuwan da take da bukata duk da tana jin nauyi da kunyar ta amma haka ta dan dake ta fada mata, sun so tsayawa yau ma bayan sun baro wajen gyara jikin amma babu lokaci tunda kuma suka dawo Ya Nabeelan ta sake fita tare da Dr Farouk din sai past 10 suka dawo abinda ya sa suke maganar a lokacin kenan. Da wuri Ya Nabeelan zasu tafi Lagos da safe tare da Dr Farouk din zata rakashi wani taro shiyasa kuma bata so a sake bata lokaci. Sake kira yayi a tunanin sa ko tayi bacci jin bata daga ba sai tasa wayar a silent ta tura masa text suna tare da Ya Nabeelan. Bayan kusan 30min ya Nabeelan tayi mata sallama ta tafi ganin dare yayi sosai. Fitar ta da minti biyar taji yana kwankwasa kofar, sai da tayi wani irin jan numfashi kafin ta tashi ta bud'e masa ya shigo ciki. Kofar da Ya Nabeelan tabi ta fita ya nufa ya murda key sannan ya dawo cikin dakin. Gaishe shi tayi a hankali maimakon ya amsa sai ya zauna ya jawota ta zauna a saman cinyar sa. "Ya Nabeela tasa duk sauro ya gama cinye miki kafar miji." Yace yana zuro hannun sa ya zagayo dasu ta cikin ta ya hade su waje daya. "Ka dade sosai?" "Umm, kusan 40min." "Da ka tafi gida." "Me yasa?" "Dare yayi ai toh." "Na sani ai, ke nake so na gani." "Sai Ka tafi?" "Sai na kwana dai, dare yayi ma gashi da wuri zan fita, kinyi min addu'ar da nace kiyi min?" "Um nayi." "Good girl, ki cigaba kinji?" "Tam." "Me zan samu?" Yace yana mata wani shu'umin kallo, irin kallon da in dai yayi mata shi toh fa shikenan. Wasa da yan yatsun ta da suka sha gyara dazu ta hau yi ya kalli hannun da suka kasance dogaye zara zara ya rik'e su yana shafa fatar hannun da yaji tana wani irin sulbi da taushi. Gefen wuyan ta ya shafo a hankali ya yi baya da jikinsa suka fada saman gadon yana rik'e da ita. Batayi yunkurin tashi ba dan tasan ba zai taba bata dama ba, sannan a k'asan zuciyar ta tana son abinda yake wakana a tsakanin nasu sai dai ba zata nuna ba saboda kunya irin ta mace wadda shi namiji babu ruwansa da wani abu wai shi kunya musamman sababbin auren nan. Yau ya lura duk karantun da ya biya mata jiya ta dauka dan har wani bashi support take yi duk da tana cike da tsoro amma ganin ko kama hanyar abinda bata so din ma bayayi yasa ta saki jikinta sosai har ya samu damar yin yadda yaso da ita. Burin sa kenan dama, ta saki jiki dashi ko babu yawa domin yasan a duk ranar da me gaba daya ta faru akwai aiki babba. Kamar jiya yau ma da asubah ya tafi sai dai basu hadu da Dr Farouk ba dan ko jiya yaji nauyi da kunyar sa sosai shiyasa ya fito yau da wuri akan sanda yake fitowa ya kuma chanja masallaci ba wanda Dr Farouk din yake zuwa ba. Daga nan ya wuce main house dinsu wanda daga chan ne zai karasa shirin sa kafin lokacin da za'a shiga court din yayi. Sanda ya koma Adam baya gidan, be san ko be kwana a gidan ba ko kuma ya fita da wuri bane saboda shari'ar oho, shirin sa kawai yake a tsanake ba tare da ya saka kayan su na lauyoyi ba, dan ba shi da plan din halartar zaman kwata kwata. Bayan ya gama shiryawa ya dauki motar Daddyn wanda ta jima ba'a hau ta ba, ya fice daga gidan. **RM**     Page 51 ***Daga chan nesa da harabar wajen yayi parking din motar ya kwantar da kansa a saman sitiyarin kunnen sa dake makale da airpod yana sauraron duk abinda yake faruwa a kotun baki daya. Kusan mintuna arbain aka shafe tsakanin su Barr. Awais da lawyer me kareta, kafin Justice Fatima ta dan bukaci zuwa hutun minti goma sha biyar. A tsakanin minti goma sha biyar din nan ya sake tabbatar da abinda ya kuduri niyyar yi a yau din dan haka ne ma ya kara shiri sosai ya matso da motar kusa da kofar fitowa daga kotun ya samu k'asan bishiya yayi parking sannan ya maida kansa ya dora akan sitiyarin. Kasancewar tinted glass ne  motar yasa ba ka ganin na ciki, sannan kuma pcap ce a kansa da ta sakko saman fuskarsa sosai. Abinda ya yi tunani shine ya faru bayan an dawo hutun da aka tafi. Murmushi yayi me ciwo sanda yaji justice Fatiman tana jaddada rashin tabbacin hujjojin da su barrister Awais din suka gabatar sannan a take ta bada belin Hajiya Zeenat din sannan tace za'a cigaba da sauraron shari'ar bisa wasu sharudda da ta gindaya. Be gama ji ba, ya zare airpod din ya wurga shi cikin dan wani box dan baya bukatar karasa jin komai, bayan abinda yaji din ya kuma san dama abinda zai faru kenan.. Duk da kwararan hujjoji da suka tabbatar da komai amma suka chanjaa komai suka nuna kamar ma shaidun ba gaskiya bane ba, anyi amfani da fasahar zamani wajen tabbatar dasu. Yanayin sa da yadda yake a nutsen sa ba zaka gane yadda yake cikin tsananin bacin rai ba. Wayar sa ce ta dan yi kara kadan alamun shigowar kira, a very low volume ya sakata sai vibration din saboda baya son wani distraction. Dagawa yayi muryar sa a chunkushe saboda tsabar yadda wani abu me girma yazo ya chunkushe masa a makoshin. "Ok." Kawai yace bayan wanda yayi kiran ya gama maganar sa. Ya katse wayar ya kashe ta gaba daya ya bud'e dashboard din motar ya sakata sannan ya gyara zaman sa sosai. Yana zaune ya soma jin hayaniya alamun an fara fitowa daga cikin wajen. Tun zuwan sa dama yaga motar Adam yasan kuma yana ciki sai gashi sun fito tare da wani mutum suna magana suna dariya ya rakashi har gaban motar sa da driver sa yake zaune yana jiran sa. Adam din ne ya bud'e masa ya shiga ya zauna sannan ya rufe masa suka fice daga wajen. Ciki ya koma suka kara daukar lokaci sosai kafin su fito tare da Hajiya Zeenat din da su Barrister Awais da Adam din suna magana. Har wajen motar suka rakota Aryan yayi saurin cire lock din Adam ya bud'e mata bayan ta shiga ta zauna sannan ya rufe mata yace zai biyo bayan su a motar sa. Ok kawai tace masa dan a wani irin matukar gajiya take ga wani duhu da tayi duk da a prison din ma a VIP take amma still dai babu wani sauki. Ba karamin mahaukatan kudi suka fitar akan case din nan ba, wanda dama kowa ya sani a k'asar nan idan har kaga ya zauna ka dade a prison toh fa baka da gata ne ko galihu. Dan jinginar da kanta tayi a jikin kujerar Aryan na hangen ta, ta mirror ya kara kure mata AC motar wadda yasan tayi missing sosai hakan yasa jikinta kara saki sosai ya danna lock din motar ya take ta sosai ya dauki hanyar barin garin da ita baki daya. Da farko Adam na biye da motar da Hajiya Zeenat din take ciki har aka zo wata danja ta saida su. Waya aka kirashi ya d'aga daga nan Aryan ya bace masa kwata-kwata. Be kawo komai ba, ya chanja hanya dan da gidan zai je amma kuma kiran wayar da ya samu ya sakashi kyale zuwa gidan ya koma baya. Sai yamma likis sannan ya gama dasu ya dauko hanyar gidan, hold up ne ya rike shi sosai saboda yan siyasar da suka cika garin. Da k'yar ya samu ya yanke ya isa gidan bayan magriba sosai. Falon ya shiga kai tsaye da tunanin ganin ta sai dai yadda falon yake dim an kashe duk wani bulb me haske alamun babu kowa a gidan. Kunna hasken yayi ya nufi bedroom din Hajiya Zeenat din ya murd'a amma sai ya jishi a rufe. Mamaki ne ya kama shi, ya nufi hanyar kitchen yana kwalawa cook din gidan kira wadda yasan tana dadewa a part din nasu kafin ta wuce bq. Shiru bata amsa ba har ya karasa kitchen din ya tarar babu kowa alamun ta dade da kammala aikin ta, ta wuce bq. A kaida idan ace Hajiya Zeenat na nan ya kamata yaga mutane sun kusan cika gidan musamman kawayen ta amma ko a gate be ga alamar ta dawo gidan ba. Da sauri yayi hanyar waje ya fito compound din ya shiga kwalawa gate man din kira da karfi. Yana toilet yana uzurin sa ya jiyo kiran Adam din ya fito a guje dan ko karasa saka wando be yi ba, sai a wajen. "Sannu da dawowa ranka ya dade." Yace gaba daya ya manta ma shine ya budewa Adam din ya shigo. "Hajiya bata dawo bane ko ta fita?" "Hajiya, wacce Hajiyar?" "Ban sani ba." Ya daka masa tsawa "Gaskiyar Allah Hajiya bata dawo gidan nan ba." "Ina driver Daddy?" "Yaje ganin gida,tun tafiyar Alhaji ya tafi gida shima yaga iyalin sa." "Waye ya hau Babbar motar Daddyn a dazu?" "Motar sa? Anya? Gaskiya dama bata gidan nan tun kwanaki aka fita da ita." "Damn it!" Ya dunkule hannun sa kamar zai nashi gateman din sai kuma ya fasa, ya juya da sauri ya koma cikin gidan ya dauki key din motar sa da ya ajiye a saman kujerar ya sake fitowa yace ya bud'e masa gate ya sake ficewa daga gidan a haukace yana kokarin kiraye kiraye waya.    ***Abby na zaune a falon sa bayan fitar Sadeeq, Raihana ta kira shi. Tun da aka kaita basu yi magana ba sai yau da ta kira shin yana sane kuma be kirata ba ita kuma nauyin sa ya hana ta kiran shi. Murmushi yayi ya d'aga wayar tata yana jin soyayyar yar tasa tilo a cikin ransa. A kunyace ta gaishe shi ya amsa zuciyar sa fes sannan ya tambaye ta ko akwai wata matsaala. Girgiza kai tayi kamar tana gaban sa sannan tace babu, ya saka mata albarka sosai tayi masa godiya sukayi sallama. Dawowar su kenan daga wajen gyaran jiki tare da Khadija yau Ya Nabeela bata je ba tana da baki a gidan dangin Dr Farouk shiyasa ta hada su kawai da driver tace ya kaisu. Khadijan na falo ta shigo daki ta kara duba wayarta ko Aryan din ya kirata amma be kira ba, gashi ta gwada wayarsa a kashe tun rana. Komawa tayi falon ta zauna suka cigaba da hira da Khadija Amna na zaune a cinyar ta tana wasa da wayar tata har magriba tayi suka tashi don yin sallar magriba.    Ya Nabeela ce ta shigo dakin tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana istigfari. Zama tayi a gefen gadon ita kuma ta gyara zaman ta tana duban ta. "Wai kuwa kunyi magana yau da Aryan?" Tace cike da kulawa dan rashin zuwan nasa ya fara damunta sosai "Wayar sa a kashe take." "Toh, yau ma? Dan sake gwadawa ko lafiya. Na kirashi dazu ma switch off. Bakin da nayi ne suka sa na sha'afa wallahi." Daukar wayar tayi ta yi dialing switch off har lokacin, karbar wayar Ya Nabeela tayi ta kira Kamal sai dai har ta gama ringing be dauka ba. Tashi tayi taje ta dauko wayar ta, ta kira chan main house Malam Yahya yace mata ya fita tun sassafe. Duk da tasan Aryan ba wai karamin yaro bane da za'a yi ta neman sa amma kuma sam hankalin ta ya kasa kwanciya, tana jin kamar ba kalou ba yawan shirun nasa. Ganin yadda Ya Nabeelan ta damu sosai yasa Raihana sanar da ita yazo jiya da daddare wanda ita a tunanin ta ko tun ranar nan be sake zuwa ba. Hankalin ta ne ya dan kwanta tayi mata sallama ta tafi. Shiru shiru tana saka ran zaizo amma har ukun dare babu labarin sa. Da k'yar bacci ya dauke ta cikin tunanin abinda ya hanashi zuwa da abinda ya saka shi kashe wayar. Gashi yana ta rokon ta da kar ta barshi duk runtsi duk wuya. Kauye ne sosai wanda ya amsa sunan sa kauyen kayau a shekaru biyu baya da suka shige, babu wani jin dadi ko more rayuwa a wajen sai dai kawai ana rayuwa ne gaba gadi ba tare da sun san wani abu wai shi cigaba ba, ballantana su samu arzikin more wasu cikin alfanun gwamnatin. Aryan ne mutum na farko da ya fara shigowa cikin su sannan yayi musu abinda basu taba tunani ko tsammani ba. Duk da bashi da wata alaka ta kusa ko ta nesa dasu illa iyakar wata mai-aiki da suka taba yi bayan mutuwar mummy din wadda ta kula da Aryan din ta damu da damuwar sa sosai a karshe Hajiya Zeenat ta kore ta saboda yadda take saka ido sosai akan sa. Duk da ya dade rabon sa da zuwa amma ya kan yi musu aike ta lokaci zuwa lokaci sai gashi a yau yazo da uzurin sa da yake ganin anan ne kawai zai samu abinda yake so. Na farko shine Hajiya Zeenat tayi confessing dukka laifukanta da bakin ta sannan ya samu in da Ammy take, daga nan ne zai yi duk abinda zai yi ganin ta karbi hukunci daidai da ita, tunda sun bi duk matakan da ya kamata su bi wajen ganin anyi adalci amma ya gagara. Waigawa yayi baya sanda ya karaso kofar gidan da k'yar saboda lalacewar hanya da rashin bin ta da mota ba tayi. Baccin Hajiya Zeenat take har a lokacin irin baccin da ake cin karfin mutum ba tare da ya shirya ba. Parking yayi sosai sanda suka fito daga gidan jin tsayuyar mota. Sun riga sun san da zuwan sa dama chan dan haka ma yana zuwa suka fito. Hannu ya mika musu maimakon su bashi hannun sai suka dan duka cike da girmamawa suka gaishe shi ya amsa a sake yana jin nauyin yadda suke masan. Bashi da niyya ko cutar da Hajiya Zeenat amma kuma yana ganin wannan itace hanya mafi sauki wajen samun cikar burin sa, zai barta tayi rayuwa a cikin irin mutanen da take ganin har abadah su din kaskantattu ne a wajenta sannan ya tabbatar bata samu kofar sanin komai akai ba. Wayar ta dake tare da ita dama ya zare ta tun a hanya ya cire SIM card din ya jefa shi wani ruwa da suka gani a hanya. Mata biyu ne suka fito bayan sun gama gaisawa da Aryan din wanda ya kasance gidansu ne kadai a gaba daya rukunin main cikin garin sai kayi yar tafiya me nisa kafin ka shiga. Dalilin shi yasa suka dawo wannan gidan nasu saboda idanun mutane. Matan nan ne suka rirrike Hajiya Zeenat wadda har lokacin take shakar bacci suka shiga da ita cikin gidan zuwa wani daki da ya yi matukar lalacewa babu komai a cikin sa sai wata lalatacciyar tabarma da ta gama jin jiki sosai. Zaunar da ita sukayi amma sai ta bingire daga zaunen tana kiran sunan Aryan din cikin sumbatu. Sai da ya gama komai sannan ya sake dauko hanya a daren ya juyo Kanon. ***Da duku-duku ko gama tashi basuyi ba Adam ya fara bubbuga musu gate kamar zai karya shi, a firgice maigadin ya fito haka ma Dr Farouk. Shigowa yayi gidan bayan ya je gidan Aryan din ya tarar baya nan ya kira wayarsa a kashe kuma. "Lafiya Adam?" Dr Farouk yace yana kallon shi ganin yadda yake a hargitsa "Ina dan iskan yaron nan." "Wa? Ban gane ba?" "Aryan, yana ina ya fito ya gaya min in da ya kai min uwata, bana son rashin mutunci." "Yaushe Hajiyan ta fito?" Ya Nabeela tace tana karasowa wajen sanye da Hijab akan doguwar rigar baccin ta "Duk abinda yaron nan yake kece kike daure masa gindi, idan banda rashin mutunci bayan rufe ta da yasa akayi a prison har dadewa haka jiya court ta bada belin ta amma bata koma gida ba, wayarta a kashe haka ma tasa a kashe, ban kuma ganshi a zaman ba sam, ina ya kaita?" "Yanzu belin Hajiyar aka bayar Adam? Bayan laifin da ake tuhumar ta dashi?" "Malam ba ruwanka da wannan maganar, kaja girman ka." "Lallai Adam, toh Aryan baya nan kuma na tabbatar babu in da Aryan zai kai ta sai dai idan wani wajen taje." "Zai dawo ne, koma ina yaje ina nan ina jiran sa wallahi, yayi kad'an." Ya juya fuu ya fice. Cikin jimamin abinda yake faruwa suka koma ciki. Hankalin Ya Nabeela a tashe ta kira Kamal tana komawa cikin ta sanar dashi abinda yake faruwa. Yayi matukar mamaki da kaduwa jin court ta bata belin Hajiya Zeenat din wanda yake kyautata zaton duk cikin shirun su ne yasa akayi masa transfer a daidai wannan lokacin. Dakin Raihanan ta shiga ta samu ta tashi suka gaisa ta tambaye ta ko Aryan din ya kira. Dare sosai ya shigo ya wuce office dinsa kai tsaye ya shiga ya kwanta saboda yadda kansa yake masa wani irin sarawa. Be tashi farkawa ba sai wajen shida da rabi ya tashi da salati a bakin sa yayi saurin shiga toilet yayo alwala yazo yayi sallah ya roki gafarar Allah delay din da ya samu wajen tashi sannan ya koma saman gadon ya zauna yana tunanin abinda ya kamata yayi next. Kusan minti arbain ya dauka yana chaja brain dinsa kafin ya tsaya a matsaya daya ya tashi ya fito ya rufe ya nufi gidan sa yana cigaba da jin kan nasa na kara daure masa amma ya daure. Wanka ya farayi a tsanake ya shirya ya dawo falon ya ajiye tab dinsa da zai fita da ita da wayoyin sa da suka a kashe ya wuce kitchen ya samarwa kansa tea da short bread ya dawo falon ya zauna yana kurba a hankalin zafin na ratsa mokoshin sa zuwa lungs dinsa. Sai da ya gama sannan ya dauki wayar da yasan zaa neme shi ya kunna ta. Kamar jira Kamal yake kiran sa ya shigo. Cikin calmness dinsa ya d'aga wayar yana sakata a handfree dan baya jin zai iya riketa a kunne sa sannan airpod dinsa na mota bare yayi connecting. "Aryan? Kana ina?" "Oga sir, kai da kake officer, kawai tracing dina zakayi sai dai naga ka turo mota an yi min daukar kaza." "Joke apart, kana ina? Me ya faru da baka sanar da ni ba?" "Nothing much, kawai abinda kaji labari shi ya faru." "Are you serious? Amma shine ba zaka kira ka sanar dani ba?" "Naga babu amfanin hakan ne kawai, beside maganar ma bata min rai take." "Naji, yanzu ina Hajiya Zeenat?" "I don't know, ban sani b." "Adam yaje ya samu Ya Nabeela yana wasu maganganu, hankalin ta ya tashi sosai, ka sanar dani idan akwai wani abu." "Babu komai, zan je yanzu gidan. Please ka kirata kace ta bani matata dan Allah." "Muna maganar serious kana wata magana daban, please Aryan ka sanar dashi idan akwai abinda ya kamata na sani din." "Babu fa, karka damu shirmen sa kawai ne." "You are not telling the truth, zan gano da kai na." Yace ya kashe wayar. Tabe baki Aryan din yayi ya mike yana kakkabe jikinsa kamar wanda abu ya hau masa. Ya kwashi sauran gadgets din nasa yayi waje. **RQ**      Page 52 ****Tun da Adam ya tafi Ya Nabeela take tsaye tana kaiwa da komowa, tana jiran jin yadda Kamal sukayi da Aryan akan maganar domin tasan halin Aryan idan har suka yi kokarin danne shari'ar nan toh fa zai dauki doka a hannun sa ne wanda ba zata taba so ya shiga matsalaa ba. Kiran Kamal ne ya shigo tayi wajen wayar da sauri ta daga "Ya akayi Kamal? Ka same shi?" "Eh na same shi, munyi magana amma kinsan taurin kan Aryan, be bani damar ma da zamuyi magana sosai ba, dan haka yanzu ma ina hanyar office zan kiraki da na samu kan labarin in sha Allah, karki damu babu abinda zai faru shima yace yana hanyar zuwa gidan." "Nan zai zo? Gwara yazo ai ni zan masa maganar, ni ko visa za'a yiwa Aryan ne ya dauki matar sa su tafi? Wallahi bana son tashin hankali kwata-kwata." "Babu abinda zai faru fa, karki damu gaskiya ce zatayi halin ta, nasan waye Aryan nasan kuma ba zai yi abinda yasan zai bata shi ba" "Toh shikenan, bari ya karaso naji ko ni zai fada min abinda yake faruwa." "Ok, yadda kukayi let me know." "I will! kaima sai ka sanar dani." "In sha Allah." Ajiye wayar tayi Dr Farouk ya kalle ta sai ya mika mata hannun sa yace tazo ta zauna, zama tayi a gefen sa jikin ta duk a sanyaye kalou. "Calm down Maman Aryan, kinsan fa halin yaron naki, da kin bashi matar sa ma da duk hakan bata faru ba, ko da rike shin nan honeymoon kawai kika tura shi shikenan fa." "Ai wallahi ban san za'a yi haka ba, da ban fara ba ma wallahi, wai ni dai muyi biki a kai lefe da komai nake so ayi, ashe yace bari ya samu wani aikin yayi." "Toh wai kin yarda da maganar Adam ne? Kila ma Hajiyan wani wajen ta tafi ta huta " "Hmm, nasan waye Aryan, tsaf zai aikata wani abu wallahi. Dama Daddy ke hanashi dani wasu abubuwan, sai Kamal kuma. Toh babu ni babu daddy Kamal din ma ya tafi, kana ganin zai bari abinda ya dade yana tanadi ya salwanta a kankanin lokaci?" "Gashi nan naji an shigo da mota." Mikewa tayi da sauri tayi compound din dan ba zata bari ma ya shigo ciki ba saboda yadda ta matsu. Parking yayi ya hangi fitowar ta tana kallon side din da yake. Murmushi yayi kad'an yasan halin rikicewar ta, ya sake tattaro calmness dinsa ya balle murfin motar ya fito ya nufe ta hannun sa zube a cikin aljihun wandon sa. Fuskar sa ta ke kallo tana son gano wani abun amma sam ya hana mata duk wani clue da zata iya gani a tattare dashi. He looks so calm da ya hana mata gano ainahin abinda yake sussukar zuciyar shi. Tafiyar sa ta maida hankali har ya karaso ya tsaya a gabanta cikin sigar zolaya yace "Ya Nabeela yau tara ta kika fito yi haka?" "Me yake faruwa? Fada min maza maza." "Aina fa?" "Gama da case din Hajiya, abinda Adam yazo yana magana akai gaskiya ne?" "Ohh, Kamal ya fada min dazu, kawai shirmen sa ne dan Allah karki biye masa, matar da ta iya tserewa hukunci daga hukuma ni ne zan iya dauke ta? Na kaita ina ma toh?" "Are you telling me the truth?" Ta kalle kwayar idon sa. "Ku shigo ciki Maman Aryan, wannan tsarewa tun a waje." Dr Farouk yace yana tsaye jikin kofar shiga ciki. Juyawa tayi ta shiga ciki Aryan din ya bi bayanta. Ko zama bata yi ba ta sake watso masa tambayar, ya gid'a mata kai yace "Bansan komai akai ba." Wata katotuwar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zauna. "Barka da gida Dr?" "Barka dai kanina, ya angonci?" Murmushi Aryan yayi tunowar da yayi ya ganshi ranar ya kuma san da biyu ya tambaye shi angoncin dan a karshen muryar sa ta nuna sigar tsokana. "Ango kasha kamshi, gashi dai wannan yayar taka ta hanaka matar ka, bansan me take nufi damu ba, idan kuma sai mun kai kara wajen Daddy ne toh." "Ko zaku kai sai na gama shirya kanwata, shima Daddyn ba zai ce komai ba." "A ah, zai fada fa, ai ba haka ake ba, ke haka aka miki da aka aura miki ni?" "Aka aura maka ni dai." Tace tana dariya "A ah dai, kin ga handsome guy kika nace kika ce idan bani ba sai rijiya." "Ahaap, ai kullum aka tashi maganar haka kake cewa, bayan kowa yasan ba haka bane ba." "Haka ne ai ko Aryan?" "Haka ne." Yace yana murmushin jin dadin yanayin rayuwar su. Dr simple mutum ne me raha da iya tafi da iyali ba tare da cin mutunci ba. Zaman su lafiya lou babu wata matsala. Hakan yana bashi sha'awa wani lokacin shi kadai sai yayi ta hasashen dama hakan ce ta kasance tsakanin su daddy. "Aryan?" Ya Nabeela ta kira sunan sa jin ana magana be ce komai ba. Ya tafi duniyar tunanin har be ji tambayar da Dr Farouk din ya sake jeho masa ba. "Dr ne yake maka magana,." "Sorry sir, banji bane ba wallahi, na tafi wani tunani." "Cewa nayi yanzu shikenan haka zaka zuba ido a hanaka matar ka, ko dan kewayowa ai yakamata ka dinga yi." Shiru yayi yana dariya kasa k'asa, be san yaa Nabeela ta riga tasan da zuwam da yayi ba, wanda ta zata shine kawai. "Duk yadda akayi Dr ni bani da matsala." "Auw haka kace?" "Wai me ya faru ne? Ko dai Aryan kana dan lekowa ne?" "Ba ya lekowa, kanina ba haka yake ba." "Anya?" "Toh yaushe yazo? Kin hana shi kince kar yazo." "Toh shikenan." "Shiga ku gaisa Aryan, karka biye ta yayar nan taka kaje ka sake kafa gwamnatin ka." "Kai kake zuga shi ko?" "Laifi nayi?" "Emana, nace fa sai ne neme shi." "Sai kisa a toshe kofar baya." Dr yace yana mikewa "Na'am?" "No bance wani Abu ba, muje ki tayani shiryawa na wuce office kar na makara." "Ok, Aryan ga hanya ne, sai anjima." Tace tana mikewa tabi bayan Dr da yake dariya. Dan jim yayi a zaune kafin ya mike ya nufi dakin da take. Kansa tsaye ba tare da neman excuse ko knocking ba, ya murd'a kofar ya tura kansa ciki. Wanka tayi ta fito tana zaune tana shafa lotion din jergens a fatar jikin ta da tayi wani irin sulbi da kyau. Big size pink tpwel ne daure a jikin ta wanda ya sakko sosai ya rufe bayanta zuwa saman sangalalin kafarta. Bata kawo shigowar kowa a lokacin ba dan manta bata murza key din bayan fitar Ya Nabeelan ba. Dakin a share yake tas tas sai kamshin turarukan da Ya Nabeela ta hado mata ke tashi a dakin hade da kamshin room freshener din da moping mist sai ya bada wani irin kamshi me sanyin dadi. Farko da taji an murd'a kofar ta dauka Ya nabeela ce duk da bata shigowa kai tsaye kuma ba zata so ya ganta haka ba da kunya amma bata yi yunkurin tashi ba saboda ta riga tasan kafin tace ta tashi ta riga ta shigo dan haka gwara ta zauna a haka da ta tashi kuma ta shigo sai kunyar tafi haka. Kamshin turaren sa ne ya fara iso mata kafin shi din da kansa ya bayyana a tsakiyar dakin kasancewar dakin bashi da wani girma. Matsananciyar kunya ce ta rufe ta, ta sunkuyar da kanta ta gagara ko da kwakkwaran motsi ne. Be tanka ba, be kuma matsa daga in da yake a tsaye ba yana kallon ta yana nakaltar yanayin da ta shiga. Tun daga saman kanta zuwa yan yatsun kafafuwanta ya bi da kallo kafin ya ajiye idon sa akan gashin kanta da yake a bud'e kuma a sake ba tare da ta saka ribbon ta kama shi ba. Kusan mintuna uku ya dauka yana tsaye a wajen da yake kafin ya tattaro kansa yace "Tashi kisa kayan ki." Kasa tashin tayi dan tasan idan ta tashi toh kunyar sai tafi ma ta yanzu. "Tashi kisa kayan ki ko nazo na saka miki da kai na." Ya sake fada mata cikin muryar sa da take nuna gaskiyar abinda zai iya aikatawa din. Kamar ta rushe da kuka haka ta tashi tana kara jan towel din duk da ya ma.sauka sosai ta cigaba da jan jikinta tana matse shi har ta karasa wajen da kayan nata suke, ta bud'e wardrobe din hakan ya bashi damar ganin bayan nata sosai. Taune k'asan lips dinsa yayi ya kad'a kai ya karasa wajen da ta tashi ya zauna yana daukar lotion din nata ya hau duba jikin container din. Ganin kamar hankalin sa baya kanta tayi saurin daukar kayan zata shiga toilet, ya dakatar da ita ba tare da ya kalle ta ba, ya cigaba da duba abinda yake dubawar. Fasa shiga toilet din tayi duk da ba haka taso ba, ta dauki doguwar rigar da ita kadai take jin zata iya sakawa ba tare da ta kara kunyata ba, ta doro ta a saman towel din, tana kokarin zura kan rigar taji an rik'e rigar kam. Kicin-kicin sakawa ta hau yi ya hanata duk wani yunkurin ta, ya saka hannu ya fincike rigar daga kanta ya ya rungume ta a jikinsa. Saura kiris ta saki towel din saboda yadda ta shiga shock, sai taji ya tayata rike shi saboda kar ya saukan abinda ya bata mamaki ta kalli fuskar sa ya dan harare ta kad'an sannan yace "Idan na sake towel din nan ya fadi ai na kad'e har ganye na, dan haka ki kara rike shi gam, so kawai nake naji wani abu." Yace yana kashe mata gira. Barin kallon sa tayi dan ta gane abinda yake nufi tayi gajeran murmushi ba tare da ta bari ya gani ba. Sai da yayi kamar minti biyu sannan ya saketa yana matsawa baya "Kiyi sauri kisa rigar." Da sauri ta rarumi rigar ta sake dorata akan towel din sannan ta zare shi ta kasa. "Zonan." Wajen da yake zaune ta je, ya nuna masa gefen sa da hannu yace ta zauna, ta zauna tana sadda kanta k'asa. Gashin ta da yake har lokacin a yadda yaken ya kai hannu ya gyara mata shi yayi baya sosai, sannan ya tallafo fuskar ta da hannun sa suka kalli juna. "Magana nazo muyi Raihana." Yace yana kara saka idon sa cikin nata ya kuma hanata dauke natan saboda ya kara samun tasiri akan ta da abinda zai fada matan,da kuma labarin da yake so ta bashi. "Labari nake so ki bani." "Labarin Ammy." Yanayin ta ne ya sauya a lokaci daya, ya hangi wani irin abu me girma a cikin kwayar idon ta, wanda ya karasa kashe sauran kuzarin da yake dashi da karsashin sa, hade da wani irin matsananciyar soyayyar ta me zafin gaske dake shigaar sa tana huda shi. Lips dinta da suka yi fresh ya kalla, ya sunkuyar da kansa yayi kissing dinsu kad'an sannan ya gid'a masa kanta yana damke hannun ta a cikin nasa dukka biyun yana son tabbatar da ta ta samu nutsuwar da yake bukata daga gareta. Motsa bakin ta, tayi tana son fara magana tana kuma tunanin ta yadda zata fara. "Come here." Yace yana bud'e mata hannun sa, bata ki ba, ta shigo jikin nasa lamo kirjinsa ya hadu da nata ya haifar masa da wani yar. Da sauri ya dago ta ya zuba wa wajen kallo ya tabbatar da abinda yake son tabbatarwar. Murmushi ya yi me taushi ya sake rungumota yana son jin su sosai a jikin shi duk da hakan zai iya sanya shi wuce gona da iri amma zai yi takatsantsan har ya samu abinda yake son samun. ***TUNA BAYA ****Alhamdulillah.. Jamaaa sai bayan azumi ko?👏😊😁 Allah ya kawo mu wata me alfarma, Allah ya sa muyi azumi lafiya mu gama lafiya, ya sa muna cikin bayin da za'a yanta idan Allah ya kaimu. Ina barar adduoin ku dan Allah musamman akan ido, ina fatan zaku sakani cikin addu'ar ku a wannan azumin dan yana cikin abinda ya ke kawo mana tsaiko a kowanne lokaci. Ayi hakuri naso gama book din a Yan kwanakin nan amma hakan yaci tura sakamakon ido da ya matsa min sosai kuma bana so na gajarce labarin.Wanda na batawa ko zafafa suka batawa dan Allah a yafi juna, Allah ya kaimu da rai da lafiya kamar yau ne idan muna da rai da lafiya *RQ*     ** _53_** _Hafsat Rano_ ***TUNA BAYA Kokarin daidai ta kanta Ammy tayi ganin bata da kowa da komai a yanzu sai Allah sai yaran ta dake biye da ita wadda gaba daya kulawarsu take karkashin ta. Idan ta nuna karaya dole suma zasu karaya har a samu matsala wadda ba zata so ba. Tashar Kano line suka nufa duk da bata da wani ishashen kudi a hannun ta dan babu wani abu da suka bar ta, ta dauka sai yan abinda ba za'a rasa ba. Motar Kaduna suka samu suka hau Lamido rike da Raihana da ta kwanta lamo a jikin sa sai Babbo Sadeeq da Hamma Hydar a gefen sa sai Ammy din. Bayan gaba daya ta siye musu dan idan aka ce za'a karo mutum daya zasu takura saboda haka nan da nan motar ta cike suka dauki hanyar barin Kano zuciyar ta a chunkushe da tayi mata wani irin nauyi. Bata neme dangin Abby ba sam dan su ma basu neme su ba tunda aka fara case din kuwa dan dama ba wani shiri suke sosai saboda babu idanun mahaifan su, tasan babu wani abu da zasu iya yi mata shiyasa ma ta yanke shawarar zuwa nata dangin kafin ta san abinda ya kamata tayi. Tunda suka dauki hanyar babu wanda yayi kwakkwaran motsi a cikin yaran har Raihana da ba wani wayo ne da ita sosai ba, sau daya tace ruwa wani bawan Allah dake gaba ya miko mata gorar ruwan dake hannun sa Lamido ya karba ya bata tasha ya maida masa yace su barshi ko zata bukata,godiya Ammi tayi daga nan basu sake magana ba har bacci ya dauke Raihanan a jikin Lamido, Hamma Hydar kuma ya kwanto jikin Ammy shima yayi baccin ya rage sai Babbo Sadeeq da Lamido kawai. "Ina zamu Ammy?" Lamido ya furta k'asa-kasa yana kallon sashen da Ammyn take. "Gidan Adda Fatima zamu Ibrahim." "Ok." Yace ya sake yin shiru yana kallon hanyar yana tuna cin kashin da akayi musu wajen fitar dasu daga gidan. ***Shigar dare sukayi wa garin na Kaduna saboda yanayin tafiyar lokacin da suka taso ma yamma ce dan haka basu isa da wuri ba gashi sai da suka tsaya a hanya sau biyu ma abinda ya kara delay din kenan. A gajiya suke tikis Raihana ta tashi Ammy ta karbe ta daga wajen Lamido suka samu motor da zata kaisu unguwar su Adda Fatiman wadda ta kasance kanwa a wajen Daadah kuma wadda suka fi shakuwa sosai da Ammyn a kaf yan uwan su. Kasancewar ta san da zuwan su Ammy ta sanar da ita yasa tuni ta saka an gyara musu dakin da zasu zauna ana jiran isowar su. Jiki a sanyaye suka shiga gidan ga gajiya da wata irin yunwa da suka kwaso Raihana sai dan kuka take saboda wahala. Da fara'a ta tarbe su suka gaisa ta dauki Raihana ta rike ta cike da tausayin Ammyn da yaran. Abinci yaran suka fara ci ita kuma Ammy ta yi alwala ta hau ramakon sallolin da suka wuce ta, bayan ta idar sun gama cin abincin tasa Lamido ya jasu sukayi alwala sukayi sallar suma sannan suka kwanta. Abincin Adda Fatima ta ce taci, duk da bata da appetite amma haka ta dan ci kad'an saboda karfin jikinta sannan suka koma dayan dakin ta shiga bata labarin komai tana kuka sosai. Sosai Adda Fatiman ta tausaya mata dan sai data zubar mata da kwalla sai dare sosai suka kwanta duk da babu wani baccin kirki da ammin zata iya yi a lokacin. Juye juye ta dinga yi ta saka wannan da kwance cikin son samun mafita ganin ba zai yiwu ba yasa ta mike ta kara dauro alwala tazo ta hau sallah domin kai wa Allah kukan ta. ***Kwanan su uku a gidan Adda Fatima suka hau shirye shiryen tafiya Adamawa domin Dadah tace ta taho gida zaman anan ba zai yiwu ba ga yara, dama itama tana da niyyar tafiyar a kwana daya ma dan dai addan ta hanata ne shiyasa ta hakura ta zauna din amma yanzu da Dadah tayi magana dole ta hakura ta barsu su tafin itama zata fi sakewa a gidan su kafin ta san abinda ya kamata tayi. Da asussubah suka dauki hanyar Adamawa saboda su samu su isa da wuri dan babu dadi tafiyar dare ga yara. Zuwan su Adamawa ya dan rage wa Ammy abubuwa da yawa musamman na daga nauyin da take ji a kirjin ta da ya zo ya tokare ta ko ruwa ta hadiya sai taji zafi, Dadah ta tsaya mata sosai da ban baki da shawarwari sannan ta dauke mata duk dawainiyar yaran sai dai kawai ta zauna shiru tana tunanin yadda rayuwa ta sauya musu lokaci daya tayi tafiyar yaji da farin cikin su ya tarwatse ya barsu da tarin bakin ciki irin wanda yake da nauyi da wahalarwa. Ta ina zata fara ne? Haka zata hakura ta zuba ido ta bar Mijinta a irin wannan halin? Gashi bata da komai bare tace zatayi wani hubbasa wanda take ganin ko zatayi din ma ba zata iya karawa da Alhaji Ibrahim Mukaddas ba. Bata da zabi illa ta koma Kano ta je ta same shi, ta nemarwa mijinta gafara ta hanyar tunasar dashi dah da rayuwar su ta baya, wala Allah ya iya sauraron ta ya farfado daga ramin da ya shiga. Ire-iren wadannan tunanin take yi a ko da yaushe har tafiya ta soma mikawa. Basu da wani arziki dan ita kanta Dadah ma fama take da kanta dan ma mace ce me neman na kanta da kokari sosai. Dalilin da ya hanata waiwayen Kanon kenan ta maida rayuwar ta kachokam wajen kula da yaran ta da suke bukatar ta, babu batun maganar makaranta a yanzu saboda bata da kudin da zata iya sakasu a irin makarantar da suke yi a chan sai aka saka su islamiyya suka fara zuwa kafin komai ya daidaita. Watan abby hudu da rufewa aka bada damar zuwa a ganshi dan ko barin ganin shi ba’a yi ba tun lokacin nan. Cikin tsananin farin ciki ammy ta hau shirye shiryen tafiya ganinsa sannan ta samu ta je taga Alhaji Mukaddas ta roke shi. Lamido yaso zuwa amma tace su yi zaman su ita kadai zata je wanda ba haka yaso ba dan yana so yaje yaga Abbyn amma kuma dole ya hakura dan raihana ma rigima zatayi idan suka tafi. Ita kadai ta shirya ta dauki hanya bayan ta dan masa siyayyar abubuwan da zata kai masa ta isa kanon ta sauka gidan wata yar uwar abbyn da suke shiri ta kwana sannan ta nufi prison din da safiyar asabar din domin ta samu ganin sa. Ta dade sosai a layi tana jira har layi yazo kanta aka bude mata ta shiga ciki aka bata tag ta saka a wuyanta sannan suka shiga ciki sosai har zuwa wani dan madaidacin daki me dauke da dogon benci. Zama tayi tana kallon wajen a hankali jikin ta a sanyaye tana cike da zulumin ganin sa. Tare da wani ganduroba suka shigo yana sanye da dark blue uniform na yan prison yayi wata irin rama da baki tamkar bashi ba. Da sauri ta mike tsaye hawaye na zubowa a idon ta, ya dan yi murmushi kadan cike da farin cikin ganin ta ya girgiza mata kai alamar kar tayi kuka sannan ya zauna itama ya ce ta zauna ta zauna tana cigaba da kallon sa. “Ya yarana?” Yace tana zama dama kuma tasan su zai fara tambaya “Suna Adamawa.” “Adamawa?” “Umm, chan muka koma ai.” “Me yasa!?” “Ba komai, kana lafiya?” “Toh, kamar yadda kika gani dai, Alhamdulillah ala kulli halin.” “Baka cin abinci ne?” “Abinci Aisha?” Yace sai yayi wani irin murmushi kawai da yasan maanar sa shi kadai “Kuna lafiya? Babu wata matsala dai? Me yasa kuka koma adamawa?” “Lafiya lou.” Ta share wasu hawayen da suka sake sakko masa, bata son sanar dashi an kore su ne ta sake tashar masa da hankali amma ta ga alamar ba zai kyale tambayar ba “IBRAHIM ne ya tashe ku?” “Mu ne kawai muka tafi.” “Karya ne, ban yarda ba.” “Me yasa?” tace tana kokarin boye damuwar da take ciki. Girgiza kansa yayi sannan yace “Nasan babi dalilin da zai saku tafiya, me yasa zai min haka? Me yasa?” Ya furta cike da bacin rai “Ban sani ba nima.” Shiru yayi be ce komai ba, sai wani irin harbawa da zuciyar sa take yi cikin tsananin bacin rai ya hadiya wani abu be ce komai ba, dan bashi da abinda zai ce din dama kuma dan a halin da yake ciki babu abinda zai iya yi. “Karka damu dan Allah, muna nan lafiya suma yaran saboda nisan da kuma bana so suzo su tashi hankalin su shiyasa ban zo dasu ba, amma suna lafiya dukka.” “Shikenan, ba komai. Akwai wata bakar jakata ina fatan kun dauke ta, akwai debit cards dina a jikin wata wallet dina sannan akwai dayar wayar nan tawa a ciki itama, zai muku amfani.” “Basu barmu mun gama daukar komai ba, amma yanzu zanje gidan zan duba na gani.” “Lokacin ki ya cika hajiya.” Ganduroban dake zaune a dakin yace yana mikewa tsaye. Kallon Abbyn tayi idonta na sake ciccikowa ta kalli kayan da tazo dashi tace masa gashi, gid'a kansa yayi ta mika masa kudin dake hannun ta da nufin bashi ganduroban yayi saurin fizgewa yana kalle kalle. "Ba'a ce miki banda kudi ba? Idan ma zaki bayar dole mu zaki bawa." Yace yana muzurai gami da chusa kudin cikin aljihun sa, sannan ya nuna mata kofar fita da hannu "Sai anjima." Da wani irin sauri ta fice saboda kukan da ya taso mata gaba daya bata kuma son yi a gaban Abbyn. ***Abun hawa ta tsayar bayan ta fito daga prison din ya dauke ta zuwa unguwar tasu, duk da bata da tabbacin samun abinda taje nema din amma kuma dole zata gwada sa'ar ta dan suna bukatar kudin sosai. A gaban gate din gidan nasu ya ajiye ta, ta bashi kudin sa ta sauka tana kallon katoton padlock din da aka makala a jikin kofar. Matsawa tayi gaban dayan gidan ta saka hannu ta kwankwasa gate din tana daidaita kanta saboda gaba daya zuciyar ta tayi masifar yin weak kamar zata zube a wajen haka take ji. Gateman din ne ya leko ta dan opening din wajen kafin ya saki abun ya juya zuwa wajen su Hajiya zeenat da Daddy dake shirin fita ya duka cikin girmawa yace “Hajiyan gidan chan ce tazo.” “Hajiya? Ban gane ba?” “Makotan dake dayan gidan da suka tashi kwanaki.” “Aisha?” Daddy yace yana kallon Hajiya Zeenat “Shigo da ita Moses.” “Ok.” Yace ya juya da sauri. “Me ya kawo ta?” “Bari tazo muji.” Tace tana murmushi Yana gaba ammy na biye dashi a baya suka nufo su, idon su a kanta da yadda tayi wata irin rama da baki, murmushi hajiya zeenat tayi tana da yakinin zuwa yanzu Ammyn ta gama tantance wacece ita. “Kawata kece da tsakar rana haka?” Motsa bakin ta, tayi ba tare da tayi magana ba dan ji tayi bakin yayi mata nauyi sosai. “Muje ciki ko?” Daddy yace yana yin gaba. “Muje Kawata.” Tace tana mata murmushi. Bin bayan ta ammy tayi cike da zulumi da tsoro dan ta gama tabbatar da rashin imanin Zeenatu ya wuce duk yadda take tunani *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ RQ 54 ****Bata zauna ba ko da suka shiga dan hankalin ta be gama kwanciya da yanayin da Zeenatun ta nuna ba. “Ki zauna mana kawata, kamar wata baku wa.” “Ba zama nazo yi ba, abu nazo dauka a gidan mu da kuka kwace saboda tsantsar zalunci.” “Da yaushe ya zama gidan ku Aisha?” Daddy yace yana dariya “Kafi kowa sani ai, saboda tsabar zalunci da rashin tsoron Allah kuka kwace.” “Be sanar dake daidai ba, babu biyar dinsa a gidan nan saboda haka ba mallakin sa bane ba, sai dai ba zan hana ki daukar ahinda zaki dauka ba, kuje tare madam ta dauki abinda zata dauka kizo mu tafi kar mu makara.” Yace yana kallon Hajiya Zeenat da tayi kamar bata falon tunda suka fara magana, tana kuma sane tana so ammyn ta gane babu wani abu da yayi saura tsakanin su da Daddyn idan ba tazo da niyyar rokon sa ne. Dama kuma abinda tazo da niyyar kenan sai dai furucin Daddy ya wargaza duk shirin ta na neman wa mai gidan nata sassauci a wajen sa. Aryan ne ya sakko daga sama, ganin ammyn yasa shi yin saurin tahowa wajenta, itama shi take kallo sai taga ya rame ya lalace yaron gaba daya, da sauri ta bude masa hannun ta ya shige jikin ta sai ya fashe da kuka. Tsananin tausayin sa ya kamata fiye da tausayin nata yaran da aka raba da mahaifin su, su a kalla suna da ita amma shi kuwa fa? Babu tabaccin Zeenat zata barshi ya samu kusanci da mahaifin nasa sannan kuma ga rashin uwa wadda ta kasance jigo a rayuwar yayanta. Ran Hajiya zeenat ne ya baci, ta kalli fuskar Daddy taga kamar ta sauya mata, sai tayi saurin matsawa ta kama hannun Aryan din tana fadada murmushin fuskar ta “Menene my boy? Me kake so eh?” Kwace hannun sa yayi da karfi yana matsawa sosai daga jikin ta “Karki sakè taba ni, bana son ki ni mom dina nake so, ammy dan Allah ki tafi dani.” “Baka da hankali ne Aryan?” Daddy yace “Calm down alhaji na, he’s just a kid, kuma kasan sai a hankali aisha ce kawai take son wasa da hankalin sa, idan ba haka ba ai Ya hakura ko?” “Kiji tsoron Allah Zeenatu, ki sani zaki mutu sannan zaki koma ga Allah a lokacin zaki girbi duk abinda kika shuka.” “Da nayi me?” “Ya isa haka please, kuje please ta dauki abinda zata dauka ta wuce, Aryan wuce sama kafin na saba maka.” “Zakayi nadama sosai IBRAHIM, nadamar da bata da amfani kuma.” Shiru yayi be ce komai ba, ta juya tayi hanyar fita daga falon kwalla na sake taruwa a idanun ta. Tana jin ihun kukan Aryan din Amma babu yadda zata iya. A compound din ta tsaya zeenat din ta fito, bata kalle ta ba, kawai tabi bayanta suka fita daga gidan zuwa tsohon gidan nasu, ta bude kofar ta matsa mata hanya ta shiga, yadda suka fita suka bar gidan haka suka tarar dashi sai uwar kurar da yayi, bedroom din Abby ta nufa kai tsaye tana danne abinda yake taso mata na rauni sosai. Wajen da tasan ya ajiye jakar ta bude ta dauko ta bude ta, ta tabbatar da komai yana ciki sannan ta dauki duk abinda take tunanin zasuyi amfani dashi sai ta koma bedroom dinta nan ma ta dauki abinda zata dauka din ta gama ta fito ta nufi hanyar barin gidan. “Baki ji ba, sai na fara bincika me kika dauka sannan zaki tafi.” “A wanne dalili kenan?” Ta ja ta tsaya cike da mamakin ta “Wai kina nufin har yanzu bakiyi laushi ba aisha? Na fa ciku wasa ya kamata ace kin saduda , kin gane ni din ba ta wasa bace ba, idan kuma kina so kibi khadija in da ta tafi sai ki sanar dani, abu me mafi sauki a gareni na sa a kaddamar miki, duk wani abu da zai bani matsala kawar dashi nake ya kamata ki sani, dan haka idan kina son kanki da arziki kar na sakè ganin kafarki anan, ki koma chan kiyi rayuwar ki da yaranki.” “Idan raina a hannun ki yake Zeenat karki barni na bar nan wajen ba tare da kin kashe ni ba, har wani tinkaho kike da abinda kika aikata kenan.” “Hmm, kar dai ki cika baki wallahi, shawara na baki saboda har yanzu ke din kawata ce, amma idan kika ce zaki shiga gonata, toh tabbas zakiyi dana sani mara amfani.” “Idan kuma na samu hujjar da zan rusa miki duk shirin ki, ina fatan zaki iya wanke kanki tamkar yadda kikayi a Yanzu.” Wani irin murmushi tayi, ta kada kanta kadan sannan tace “Mu zuba dan halak ka fasa, sai dai ina me baki shawarar karki kuskura ki bari na wai wayo ki,ki tsaya a in da na ajiye ki karki tsallake limit dinki.” “Bana bukatar shawarar ki.” Sai ta juya ta fice daga gidan. Shiru zeenat tayi bayan fitar ta, ta tabbatar akwai dalilin furucin ammyn, dan haka ba zatayi kasa a guiwa ba, sai ta binciko abinda ta taka. Wayarta ta daga cikin yanayin bacin rai ta danna kira, ta tsaya tana jijjiga kafa da dan sauri sauri tana jiran a daga wayar. Yana dagawa tace “Follow her.” Sai ta katse kiran ta maida wayar handbag dinta ta fito tana daidaita kanta ta koma cikin gidan ta samu Daddy a tsaye jikin motar suna magana da Moses, bude mata kofar Driver yayi ta zauna sannan daddy ya shiga shima yana tambayar ta ina ammyn. “Ta tafi.” Kawai tace masa bata sakè cewa komai ba, be kuma tambaya ba shima suka fita daga gidan. *****Zuciyar ammyn a chunkushe ta tari abun hawa, gidan da ta sauka ta nufa tace me napep din ya jirata, kayanta kawai ta dauka amma sai tayi mantuwa ta bar jakar da ta dauko a dakin Abbyn suka dauki hanyar tasha dan bata jin zata sake kwana a kano. Tayi nisa sosai a tunani har me napep din ya dauke hanyar da suke kai bata lura ba, sai da yayi tafiya sosai da ita sannan ta Ankara, tayi saurin tambayar sa in da zai kaita, juyowa yayi da nufin bata amsa ya fesa mata wani abu a fuska wanda yayi sanadiyyar gushewar hankalin ta. ****A hankali Aryan yake murza hannun ta kadan kadan yana kallon dan bakin ta karami da yake magana, shirun da tayi ya saka shi jawota jikin sa ya rungume ta tsam tsam duk da nauyin da yake ji a zuciyar sa amma dole ya dake domin yana da bukatar nutsuwarsa. Ta dade lafe a jikin sa tana sauke ajiyar zuciya a jere har ta samu bugun zuciyar ta ya daidaita ta samu nutsuwa sosai. D’ago kanta yayi daga jikin nasa ya tallafi fuskar tata da hannun sa biyu, a hankali ya motsa bakin sa cikin muryar sa da ta shige ciki sosai yace “Zan dawo da daddare kinji? Sai mu karasa maganar for now ki huta sosai, karki stressing kanki kwata-kwata.” Gida masa kai tayi a hankali ya yi mata perk a gefen kumatunta Sannan ya dan ja mata hanci kadan sukayi murmushi a tare “Me Ya Nabee take bawa kumatun nan naki? Kamar bread irin bugun katon nan saboda laushi.” Dariya ta kyalkyale da ita, ya tsaya yana kallon ta cike da zallar kaunar ta me chakude da tausayin ta sosai. “Dariya tana miki kyau sosai, ni Kinga ban iya ba.” “Tafi maka kyau ai, tunda dama baka yi so idan kayi sai kayi kyau.” “Really?” “Umm.” “Tam zan dinga yi miki, ke kadai kawai kinji?” “Banda Zainab?” “Zainab?” Yace “Umm ta Office.” “Ohh..” sai yayi dariya kadan “Ke da ita toh,sai a raba 50/50.” Turo baki tayi ta juyar da kanta da jikin ta gaba daya daga kallon side din da yake, murmushi yayi yana jin wani dadi a ransa,ya juyo da ita gaba daya zuwa jikinsa ya matse ta a hankali ya dora habar sa a saman gashin ta dake fitar da wani irin kamshi me ratsa zuciya. Ya dade a haka tana manne dashi tana jin heartbeat dinsa kafin ya dan saketa kadan jin wayar sa na kara alamun kira, ciro wayar yayi ta dan yunkura zata tashi ya hanata ya daga wayar yana makala a kunne. “Daddy barka da rana.” Yace a nutse “Alhamdulillah.” Ya furta sai ya dora “Ya jikin?” “Allah ya kara sauki, eh in sha Allah ina kan kokarin, duk yadda ake ciki zan sanar in sha Allah, komai lafiya lou. Ok a huta lafiya.” Sai ya katse wayar ya tura ta aljihun gaban rigar sa “Yaushe Ya nabeela zata gama shirya min ke?” Ya watso mata tambayar ba tare da ta shirya ba, bata amsa ba sai dan murmushi da tayi. “Zan fada mata tayi sauri, dan tafiya zamuyi zamu bi su Daddy Ina bukatar na huta sosai, nauyin dake kaina da zuciya ta yayi sauki, ina so na bar komai behind me for sometime, wanda nake fatan komai ya daidaita kafin dawowar mu, just pray for me kinji? Akwai abinda nake son achieving idan Allah ya tabbatar ba ni kadai ba, mutane da yawa zasu samu farin ciki wanda nake da yakinin samun wanzuwar wani shashe na daga farin cikin da muka rasa a baya.” “Allah ya bada sa’ah ya tabbatar da alkhaiiri.” “Amin My wife.” Daga shi tayi ya mike hannayen sa zube cikin aljihun sa, ya dan sake kallon ta sannan ya nufi hanyar da ya saba shigowa don baya son komawa ta falon su hadu da Ya nabeela tayi masa tsiya. Yana fita ta yi baya ta kwanta a saman gadon wani irin mixed feeling na bijiro mata, koman sa burgeta yake, nutsuwar sa da yadda yake a kame ga wani irin charisma shi yafi komai birgeta a tattare dashi. Yadda yake treating dinta yafi komai tafiya da ita. Wayar ta , ta dauka ta kira Dadah suka yi hira sosai, sannan ta kira Abbyn ta da su Hamma hydar, dukkan su tambayar ta suke ko akwai wata matsala amma sai tace a ah, suna gama wayar duk suka turo mata kudi a tare kamar hadin baki, wai ko zata bukaci wani abun, murmushi tayi cikin farin ciki da yadda yan uwanta suke kokarin ganin sun faranta mata, da kokarin ganin bata yi lacking komai ba tun kuwa da ta taso. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETED)_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2K duk biyar_ *_ZAFAFA BIYAR 2023_*🔥🔥🔥 _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din👇*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta👇 _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin👇 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR🔥🔥 MUNGODE🙏🙏❤️ **RQ ** *_55_* *******Hannun sa daya na kan sitiyari dayan na rike da wayar sa yana neman number Hydar, kiran sa yayi ya dora wayar a gefen sa ya gyara zaman AirPod din dake makale a kunnen sa. Line busy yaji alamun waya yake har zai katse sai kuma yaji ya dauka “Yallabai barka da rana.” Hydar yace cikin rashin sanin dalilin kiran aryan din “Barka dai, ya gida ya family?” “Alhamdulillah. Komai lafiya.” “Masha Allah, please wata yar tambaya nake da ita idan ba damuwa.” “Ba damuwa, go ahead.” “Akan maganar ammy ne…” “Ok… ina jin ka.” “Yaushe ne ganin ku na karshe da ita, sannan me ya faru a lokacin?” “Umm, bari na dan fito daga office zan kiraka minti biyu.” “Ok ba damuwa.” Yace yana tsaida kansa akan titin daidai lokacin da ya shigo cikin layin nasu. Parking yayi a gaban gate din me gadi ya fito zai bude masa gate din yace ya barshi ya dan yi baya da kujerar da yake kai ya zura hannu ya dauko system dinsa a bayan motar ya kunna ta, a daidai lokacin kiran Hydar ya shigo, ya daga yana bada dukkan attention dinsa gareshi, domin akwai wani abu da yake son karasa tattarawa wanda zai tabbatar masa da abinda ya gano. “Kana jina?” “Eh ina jinka.” Yace masa “Ok…” *TUNA BAYA* ****Tafiya sukayi da nisa sosai kafin ya isa gidan da zai kai ta, bisa umarnin Hajiya zeenat din, a lokacin ammy bata cikin hayyacin ta bacci take sosai me nauyin gaske don sai da suka sauya mata abun hawa daga napep din suka saka ta a mota duk bata sani ba. Kwana uku tsakani ta farfado cikin wani irin yanayi ga wani azababben ciwo da kanta yake yi mata dan da farko kasa gane in da take tayi da abinda yake faruwa, sai daga baya abinda ya faru ya shiga dawo mata, a zabure ta mike da nufin guduwa amma sai taji ta a daddaure, motsi taji a kofar dakin da yake ta karancin haske kasancewar magriba ce, hasken touchlight ne ya dalle mata ido tayi saurin kawar da kanta, kautar ta hasken yayi zuwa wani shashen sannan ta samu damar ganin shi duk da ba tar ba saboda haske tan da yayi. “Kin farfado kenan, lallai maganin nan akwai mugun karfi na gaske.” “Ina ne nan?” Tace muryar ta na rawa saboda gano abinda yake faruwa da tayi “Nan? Baki san ina ne ba ko? Gidan yankan kai ne.” “Innalillahi wa inna ilahi, Raihana yarana.” “Tab ai ke da ganin su, sai dai a lahira idan kuna da rabon ganawa.” “Dan Allah dan girman Allah Kiyi min rai, wallahi yarana basu da kowa sai ni, mahaifin su yana kurkuku dan Allah ku kyale ni na tafi.” “Tabb, ai kin shigo kenan wallahi. Idan kin ga kin fita daga gidan nan sai dai idan gawar ki ce.” Sai ya juya zai yayi hanyar fita, magiya take masa tana kuka amma yayi biris kamar be ji ba, ya kai kofar kenan tace “Toh dan Allah zanyi sallah.” “Ba dai anan ba.” Yace sannan yayi ficewar sa. Kukan ta ne ya karu, tabbas akwai matsala gagaruma idan har ta cigaba da zama a wajen, ya rayuwar yaran ta zata kasance? Dole tayi wani yinkurin ganin ta bar wajen. Duhu ya mamaye dakin sosai alamun dare ya fara turawa, babu motsin kowa da komai kamar ma ita kadai ce take zaune a wajen, motsa hannun ta, tayi kokarin yi ko zata iya kwance daurin dake jikin nata amma ta gaza, bata hakura ba ta cigaba da gwadawa duk da bata da yakinin zata iya din. Motsi tajiyo daga nesa kamar suna musu, maganar na tunkaro ta har suka iso kofar dakin sannan suka shigo a kusan tare. Matashin nan ne na dazu tare da wani babba dan zai yi kusan saan su Abby ko ya dara su, bata san musun me sukeyi ba kafin su shigo ta dai ji yana cewa _”Dole a barta tayi sallah, idan hajiyan tazo kace nine nace.”_ Anan ta fuskanci akan dalilin musun nasu, shi matashin yace ba zatayi ba shine shi kuma yace a ah, da kansa ya karaso ya kwance ta sannan yace ta taso, ta mike da kyar kamar zata fadi dan yadda jikinta yake a sakè kamar zata fadi saboda emptiness din da take ji a tattare da ita hade da wata irin yunwa wadda damuwar da take ciki ta hana ta tasiri a gareta. Waje suka fito ya samu wata babbar tasa ya zubo mata ruwa ya bata, sai da ta kafa kai ta fara sha sosai har ta kusan shayewa ma saboda tsabar ishirwar da take ji, karo mata yayi tayi alwala bayan ta dan kama ruwa sannan ta koma cikin dakin dan a yanayin wajen da yadda bata jin motsin komai sai kukan tsintsaye ko hanya suka bude mata suka ce ta tafi ba zata iya ba, wani irin waje ne me matukar abun tsoro, tayi mamaki kwarai yadda suka iya zama a wajen sai dai duba da yadda baban yake furta kalmomin sa ya tabbatar mata da bafulatani ne irin na rugar nan wanda suka iya rayuwa a jeji daga su sai dabbobin su. Dankwalin ta, ta cire ta zauna a zaune ta kabbara sallar dan bata jin zata iya yi a tsaye saboda yadda take jin jiri na dibar ta. Ta dade tana jero sallolin kafin ta idar ta kalli kwanon da ya ajiye mata a gefen ta, tana sallar. Jawo shi tayi ta bude sai taga shinkafa ce da mai da yaji, cikin sauri sauri ta hau ci saboda tsabar galabaita batayi tunanin komai ba dan ta riga ta lissafa ba zata yarda ta zauna a gidan nan ba dan haka dole tana bukatar kuzari sosai yadda zata iya tsere musu idan ta samu damar tserewar. Tas ta cinye bata rage komai ba, ta yi hamdala ta gyara dankwalin nata sosai ta kwanta lamo a kasan wajen tana ji aka rufo ta, ta waje tayi shiru tunanin halin da yaran suke ciki musamman raihana da ta kasance karama, bata da alamun yin bacci har dare ya tsala sosai sai kukan sauro da yake tashi kamar ana kada ganga, tashi tayi tunda da alwalar ta, ta cigaba da sallolin ta a tsaye dan dama dazu da rashin kuzari ya hanata yi a tsayen. Har gari yayi sha bata runtsa ba, bata kuma ji motsin kowa ba sai chan zuwa lokacin da rana ta daga sosai sannan taji ana bude kofar. Matashin nan ne ya shigo dauke da kwanon abinci ya dire mata fuskar sa a rufe da bakin abu dama kuma ba gane shi tayi jiya ba saboda babu isahshen hasken da zata iya tantance shi. Fita yayi tayi shiru bata da niyyar daukar abincin bare taci. Sakè rufe ta, taji yayi ya bar wajen chan bayan kusan awa guda taji an sakè bude ta, Yanzu bata d’ago ba tana a zaune a yadda take sai da taji muryar sa ta d’ago suka hada ido. “Yi maza ki taso, karki bata lokaci har tazo ta same ki anan, zan bude miki hanya kiyi gabas zaki ga wata doguwar hanyar yar siririya kiyi ta binta zata fitar dake har titi, karki tsaya dan daf suke da isowa nan.” A gigice ta mike tayi hanyar fita suka fita a tare ya fito da ita har waje ta bayan gidan sannan ya nuna mata hanyar da zata bi, zata tsaya yi masa godiya yace tayi sauri. Gudu ta shiga yi na fitar hankali baji ba gani tana gudu tana addua da karfi, ta sha wahala sosai dan sai da taji kamar kafafun ta ba ajikinta suke ba, amma ta daure ta cigaba da gudun har fara hango titin me dauke da motoci yan tsirari, murna ta hau yi ta kara daga kafarta sosai tana jin a ranta ta kubuta har ta karaso titin kanta tsaye ta fada kan kwaltar ba tare da ta duba ko taji karar motar da take shararo gudu na musamman. Shi kansa be lura da ita ba, dan ba hanya ce ta wuce war mutane a kafa ba, dan baya tunanin akwai wani kauye a kusa da wajen saboda hatsarin sa, highway ce dan haka a full speed yake tafiya abinda ya hanashi samun damar taka birki har yayi wani irin tafiyar yaji da ita, ta kwalla kara karar da ta ankarar dashi abinda ya faru. ****Nannauyar ajiyar zuciya Hydar ya sauke kafin yace “Labarin mutuwar ammmy shine abinda ya taba faruwa damu wanda ya samu a cikin matsanancin tashin hankali, mun sha wahala matuka kafin rayuwar mu ta dawo daidai, munyi kuka tamkar idanun mu zasu rufe saboda azaba, amma Ya zamuyi? Haka Allah ya tsara, abin tashin hankalin shine rashin ganin gawar ta, yafi komai daga mana hankali.” “Allah ya gafarta mata zububanta, Allah yasa muyi kyakkyawan karshe.” Aryan yace muryar sa a ciki “Amin.” “Gobe Friday, zaka iya shigowa kano? Nayi maka booking flight din yamma, idan ka bar Office ka shigo akwai abinda nake son nuna maka.” “Ok, ba damuwa zan yi kokari nazo.” “Nagode sosai, Nagode da bani lokacin ka.” “Babu bukatar godiya,kai dai ka kula min da kanwata, shine kawai.” “Ko? Zan duba yiwuwar hakan toh.” “Karka manta dai, kanwar maza ce.” “Haka kace dai.” “Haka ne ma, bari na koma Office na bar ayyuka.” “Ok, sai ka shigo.” Suka ajiya wayar. Hoton dake kan system din ya sake budewa sosai, ya kara kallon sa sannan ya fita ya bude dayan, ya tabbatar da dukkan information din daya ne kafin ya kashe system din ya maida ita back seat din ya d’ago kujerar daidai sannan ya kashe AC motar ya kashe motar ya fito rike da wayar sa ta office a hannu dan da suna magana da hydar kiran zainab ya shigo sai dai be daga ba. Kofar jikin gate din ya tura ya shiga gidan ya hangi motar Adam a parking area ya wuce ciki ya shiga falon. Babu kowa kamar ko da yaushe sai tv dake a kunne tana ta fama ita kadai, kashe ta yayi ya kunna hasken falon wanda yake da a kashe sannan ya haura saman zuwa bedroom dinsa. A falon saman ya tarar da Adam yana waya yana daga muryar cikin tashin hankali dan da gaske karamar magana tana neman zama babba babu labarin Hajiya zeenat babu dalilin ta wanda babu wanda yake zargi illa Aryan gashi ya rasa yadda zai masa ya gano wani. Wuce shi Aryan yayi kamar be ganshi ba yayi saurin shan gabansa yana katse wayar. Wani kallo Aryan din ya watsa masa kafin ya giciye shi ya saka key zai bude dakin kasa Adam din ya rike kofar yana tare shi “Ina ka kai min uwata?” “Uwarka? Wacece kuma haka?” “Baka sani ba? Ko da yake ba zaka sani ba tunda ba wai ka wani san dadin iyaye bane ko kuma kasan shakuwar dake tsakanin uwa da danta.” Kamar an soke shi da mashi haka Aryan yaji maganar, tayi masifar taba shi amma sai ya dake ya fuske tamkar be ji me Adam din yace ba, ya sa hannu ya fincike hannun sa ya hankade shi baya ya shige dakin gami da banko kofar yana jin Adam din na dura duren ashar ya dafe kansa ya jingina da kofar kirjinsa na wani irin harbawa. Ya dan dade a tsaye a wajen kafin ya karasa gaban side drawers dinsa ya ciro maganin sa ya dauki ruwa yasha sannan ya rage rigar jikinsa ya kwanta a saman gadon ya jawo wayarsa ya kunno karatun alkurani me girma yana saurara a hankali nutsuwa na shigar sa tana ratsa shi har ya samu ya dawo daidai. Kusan awar shi daya a kwance ba bacci yake ba kawai yana sakawa da warware abinda yake shiri yi ne a cikin yan kwanakin nan, yana kuma fatan ya samu nasara. Yunwa ce ta soma nukurkusarsa, baya son sakè haduwa da Adam bare har ya biye masa su yi musayar magana Shiyasa ya dade a kwancen ma. A tunanin sa ya tafi dan haka ya dauki jallabiyar sa me gajeran hannu ya zura akan farar singlet dinsa ya sakko kasan zuwa dinning area, ya samu an jere abincin akan dinning din sai dai babu plate. Kitchen din ya nufa ya bude wajen da plates din suke ya dauko zai fito Kamal ya kirashi sai ya tsaya rike da plate din a jikin sink ya daga wayar. “Ina ka shiga ne wai?” Kamal yace yana fitowa daga meeting din da sukayi, a gajiya yake tikis dan ya matsu da kiran Aryan din ne ma Shiyasa amma da kashe wayar zai kawai ya koma ya kwanta dan kusan kwana uku kenan basa samun isashen bacci akan wani case da sukeyi “Na dan kwanta ne, Yanzu kuma na sakko zan yi lunch .” “Ok, kunyi magana da Ya nabeela ?” “Eh munyi, kasan ta. Komai ma abun damuwa me a wajen ta.” “Dole ne ai, ni kaina na damu din, kawai dan ni namiji ne. Please Aryan Karki yi wani abu, akwai shirin da nake akan case din nan, amma for now don’t make any move.” “Ok.” Yace a gajarce “Good.” “Em akwai abinda nake so dama na fada maka.” “Ok, ina ji.” “I think na gano in da Ammy take.” “Wait what!? Are you serious?” “Yeah, ba kace I should take over ba, so na gano in da take, kuma na gama planning yadda zamu je mu ganta, ni da hydar.” “Ku jira ni, zan shigo Sunday sai muje.” “Saturday zamu je, zai shigo kano gobe sai muje Saturday.” “Noo ku jira ni.” “Why? Ba zan iya yi ni kadai ba? Dole sai kazo?” “Zaka iya, but Inaso nazo nima.” “Wannan karon dai just allow me please.” “Aryan?” “Pleaseee.” “Ok,ok. Shikenan.” “Yauwa, Atleast nayi wani abu, Inaso raihana ta kara sakin jiki dani, idan hakan ta faru zata kara yarda dani. Zata yarda ni ma I’m a good person, ba Halin mu daya da daddy ba.” “Naji naji, don’t change the topic. Na gaji tikis zan je na huta, zamuyi magana anjima.” “Ok.” Yace ya katse wayar. Da sauri Adam dake makale a jikin kofar kitchen din ya bar wajen yana wani irin murmushi. _**RQ_** 56 ****Katse wayar yayi ya fito zuwa dining ya zauna gami da jawo warmers din ya bud'e ya zuba abincin dan madaidaci ya yi bismillah ya shiga ci a hankali yana danna wayarsa da yake kokarin tura mata sako. Yaci ba laifi dan ba wani breakfast yayi sosai ba ya ture plate din yana mikewa, ya koma tsakiyar falon ya zauna a cikin kujerun falon da ya dade be yi irin zaman ba. ***A firgice ta farka daga baccin da take, ta kwala sunan Aryan dan dama da sunan nasa baccin yaci karfin ta. Ladi ce ta shigo da saurin, ta zura mata ido tana kallon ta kafin ta kurma uban ihu bayan ta lura da in da take. Tashi tayi tana yunkurin kakkabe jikinta saboda wani irin mugun kyankyamin wajen da take da yadda dakin yayi mugun datti. "Ahe kin farka." Ladi tace tana matsowa kusa da ita, da sauri Hajiya Zeenat ta daka mata tsawa tana kallon ta cikin yanayin kyankyamin tace "Karki kuskura ki matso kusa dani." "Aradun Allah sai na matso ki, mune yanzu dangin ki tare damu zakiyi rayuwa." "Inji uban wa, na rantse da Allah kika sake matso ni sai nasa anyi maganin ki." "Tab lallai, baki san ma wacece ni ba." Kallon banza Hajiya Zeenat tayi mata, ta yi hanyar fita daga dakin a fusace, dariya ladi tasa tana gyara daurin zanin ta, ta bita da kallo dan tasan ko kusa bata isa ta zura kafarta waje daga dakin ba. A tsorace ta juyo dakin gami banko kyauren da ya kusa karyewa jikinta na rawa tace "Menene a waje?" "Jeki ki gani mana, aradun Allah sai ta cinye ki tas har kashin ki." "Dan Allah menene? Kamar kura na gani." "Ba kamar ba, itace wallahi. Kuma an riga na sanar da ita da kin fito tayi kalaci dake." "Na shiga uku, abinda yaron nan zai min Kenan?" "Ke kika san shi, kinga tafiya ta gashi nan garin buga kyauren kin kusan balla shi, idan ya karasa ballewa aradun Allah har cikin dakin nan sai ta shigo ta shinshina ki kuma." Da sauri Hajiya Zeenat ta damke ta ganin zata fita ta barta ita kadai, wani kallo Ladi tayi mata me cike da izgili tace "Ke da kika ce kar na matso ki, uban mi yasa zaki rike ni?" "Kiyi min rai, wallahi zan baki kudi, idan har kika taimake ni duk wata matsalar ki ta kau, sai kin zama abun kwatance a garin nan amma dan Allah ki barni na tafi, ba zan iya rayuwa anan ba." "Mu da muke rayuwa a wajen uban mi ya cinye mu?" "Dan Allah ni dai, kinji kanwata dan Allah." "Alkuran ko me zaki bani ba zan taimaka miki ba. Kuma kika sake rike ni idan zan fita sai na kira kurar nan ta shigo, zan bawa lantis tuwon dawa ta kawo miki da ruwan randa me sonyi, idan kin ci, cikinki, idan baki ci ba ma dai cikin ki." Sai ta juya ta fita gami da barin kofar a bud'e. Da sauri Hajiya Zeenat ta mayar da kyauren ta rufe cikin tsananin tashin hankali, lallai Aryan ya shirya tozarta ta, dama tasan halin yaron shegen taurin kai da kafiya, amma bata taba tunanin zai mata wannan azabar ba. In da ta tashi ta koma ta zauna cikin tsananin tsoro hankalin ta na kan kofar tana jin gunjin kurar da take a sake tana shawagin ta kamar yadda akuya ke yawo a tsakar gida. Taba kyauren akayi ta tsorata sai ga ladidi ta shigo da wata mummunar langa da ruwa a Kofin silba ta dire mata a gabanta tana kallon ta. "Taimako na zakiyi dan Allah, zan baki kudi da duk wani jin dadin duniya, waya kawai zaki samo min dan Allah." "Bamu da netiwok a garin nan ai, sai an je chan hayi ake samu ayi waya, su waye ma masu wayar a kaf garin nan? Basu fi mutum hudu ba." "Na shiga uku, Aryan!!!" "Inna Ladi tace idan kin cinye ki taba kyauren nan zan zo na dauki langar." "Ki zauna anan toh dan Allah karki tafi." "Chab, so kike taci ubana Kenan." "Toh ya sunan kauyan nan?" "Oho nima ban sani ba." "Shegu marasa iya magana." Hajiya Zeenat tace k'asa k'asa cikin bacin rai, juyawa Landis tayi ta fice tana kada kugu. Zame dankwalin kanta Hajiya Zeenat tayi dan wani irin tururin zafi ne ke fitowa daga cikin jikin ta. Da dan kwalin ta dinga kokarin firfita ta dan ja kwanon kad'an ta bud'e tuwon da sauri ta rufe ganin wata irin miya tsululu kamar an wanke kai, kwalla ce ta taru a idonta, lallai Aryan ya gama cutar ta, cuta me tsananin gaske, ba kuma zata kyale shi ba wallahi sai ta nuna masa ita uwar dakin sa ce a rashin mutunci. Tun da magribar fari sauro ya fara gud'a acikin kunnuwan Hajiya Zeenat, ta shiga aikin kore su amma ko gezau kamar ma kara turosu ake yi ga wani irin shegen kuka da suke kamar zasu ci babu sannan ga kukan da cikin ta yake yi dan daga prison take dole tana tare da yunwa. Bata yi tunanin yin sallah ba ko kad'an dan bata bukatar abinda zai fitar da ita waje. Ladi ce ta dawo dakin dauke da yar karamar touchlight ta haska. "Kiritta ce ko musulma?" "Ban..." Da ban sani ba zata ce, sai kuma ta tuna, ta ja tsaki cikin kunar Tai tace "Ina zanyi alwalar?" "Taso muje, ni shaf na manta ma ashe kina sallah, da naji baki magana ba na dauka kiritta ce." "Amma ai kinsan ni mace ce ko?" "Taso kafin K'adari ya dawo da kurar nan, sun dan fita shawagi sai kiyi da jiki." Da sauri Hajiya Zeenat ta mike tabi bayanta dan dama fitsari take ji, sai data fara tabbatar da babu kurar sannan ta yarda ta fito ta rakata kofar bayin da babu ko rufi sai dan zagaye shi da wanda idan kana tsaye tsaf za'a hango ka. Gefe ta samu tayi fitsarin dan babu yadda zatayi, ta fito tayi alwalar sannan ta koma ciki. Wata tsohuwar darduma ladi ta kawo mata tace ta barshi zata shinfida dankwalin ta, juyawa tayi da kayarta ta bar mata touchlight din ta yi sallar sharp sharp ta idar ta zauna jigum sai taji motsi alamun wanda aka ce ya fita da kurar ya dawo, kara nutsuwa tayi ta dauki ruwan a ba yadda zatayi tasha kad'an ta ajiye. Kayan abincin da Aryan yasa a siyo mata Buba ya kawo dama abinda ya fitar dashi tun rana kenan, maimakon akai dakin da take sai Ladi tace akai mata dakin ta dan so take sai ta koya mata hankali sannan zata kyale ta, katifar dai da maganin sauro ta bawa ladidi ta kai mata ta shinfida mata da sabon bedsheet dan karami sai pure water leda biyar. Ta dan ji dama dama da aka kawo karamar katifar da ruwa da maganin sauro, sai dai kuma taji babu dadi dan alamu sun nuna bata da shirin tafiya yanzu kenan. ***Kamar yadda Aryan suka tsara da Hydar haka akayi daga office ya wuce airport kai tsaye yana zuwa suka taso zuwa Kano. Yana sauka ya wuce gidan Adda Maimuna bayan ya kira Muhammad ya sanar dashi zuwan sa. Sai da ya isa gidan ya huta sannan ya kira Aryan yace masa ya sauka. Gashi nan zai zo ya dauke shi yace masa sannan suka ajiye wayar. Muhammad da suke zaune tare ya kalle shi cikin son Karin bayani yace "Kamar dan rainin hankalin nan ko?" "Wai Aryan?" "Eh shi, guy din nan ko? Hmm amma ba komai haka Allah ya kaddara." "Toh ya za'a yi da abinda Allah ya kaddara?" "Haka ne, amma ni sam be yi mun ba, bai kuma dace da Raihana ba, sai uban girman kai da nuna shi ya isa." "Calm down bro, komai ya wuce please a daina tuna baya, Allah zai musanya maka da mafi alkhairi ." "It's hard ai, kawai kai dai ayi sha'ani." "Na sani, ayi hakuri dai." "Wai ko tsoron sa kake ne?" "Tsoro? Me yasa zanji tsoron sa?" Yace a dan hasale dan dama akwai shi da saurin tunzura kamar Aryan din "Naga kana goyon bayan sa ne." "Yanzu shi yake auren kanwata, ko ina so ko bana so I have to respect the fact that mijin tane." "Ok ok, naji shikenan?" Mikewa Hydar yayi dan har ga Allah Muhammad din ya bashi haushi sosai. "Na fita ba lallai na dawo yau ba, zan samu hotel na zauna kawai." "Saboda nayi magana?" "Yes, bana so a zarge ni da abinda bashi bane ba." Sai ya fita, ya bar Muhammad din a tsaye. Biyo shi yayi ya tarar dashi a waje yana jiran Aryan din ya tsaya gefensa yana kallon yanayin fuskar sa, zai yi magana Aryan din ya shigo layin. Fasa maganar yayi yaji duk ransa ya baci ganin Aryan din sai kawai ya juya ya koma ciki. Aryan na ankare dashi dan yana shigowa layin dashi ya fara ankarewa. Parking yayi a gaban Hydar din ya sauke glass din. Bud'e kofar side din me zaman banza Hydar yayi ya shiga ya mika masa hannu suka gaisa sannan Aryan din ya ja suka bar wajen. Gidan ya Nabeela ya wuce dasu kai tsaye don yana so yaga Raihana dan ko da yace zai koma jiyan be koma ba sun dai yi waya da daddaren dan har sai da yaga ta fara hamma sannan yace ta kwanta suka ajiye wayar ya shiga wani aikin. Tana falon ya Nabeelan suna hira tana tsefewa Amal kanta suka shigo da sallamar su, wani yar taji tun daga kanta zuwa kafafunta amma sai ta kasa dagowa ta kalli kofar duk da tana jin idanun sa akanta yana takowa cikin falon Hydar na biye dashi a baya. Riga ce me gajeren hannun a jikinta da dogon skirt sai Chantilly Cap da ta rufe gashin kanta. Maganar Hydar yasa ta dago da sauri dan bata yi zato ko tsammanin ganin sa ba. Fuskarta ce ta fadada da fara'ah "Hamma na?" "Umm kanwata, sai gani." "Sannu da zuwa." Ya Nabeela tace tana murmushi "Yawwa sister, sannu da gida." "Yawwa, ya hanya anzo lafiya?" "Lafiya lou, mun same ku lafiya?" "Alhamdulillah wallahi." "Hamma ina wuni?" Tace a kunyace tana satar kallon Aryan da yake kokarin zama kan kujerar da take. "Lafiya lou." "Ya Nabeela... Ya gida?" "Lafiya lou, Aryan." "How are you?" Yace muryar sa k'asa-kasa yadda ita kadai zataji. Sunna kanta kasa tayi ba tare ta amsa ba. Murmushi yayi kawai dan dama yasan ba zata amsa ba. Mai aikin Ya Nabeela ce ta kawo musu juice da ruwa Hydar na lura da yadda Raihana duk ta takura. Mikewa tayi zata bar falon ya tsaida ita. "Raihana, banga kin gaida Aryan ba." Diriricewa tayi, shi kuwa gogan ya coge yana kallon yadda zatayi. "Um um... Dama." "Ta gaishe ni, kasan gaisuwar couples sai ka kura kunne sosai zaka iya ji." Aryan ya fada yana yin baya akan kujerar. Kallon sa tayi da sauri ya kashe mata ido daya tayi saurin dauke kanta tana murmushi "Umm lallai, abun na masoya na Kenan". Ya Nabeela tace tana dariya. "Yunwa nake jiiii." Yace yana kallon Raihanan kamar itace me gidan. "Kanwata kawo wa mijinki da yayanki abinci." "Yanzu naga cin abinci a gidan Adda Maimuna wallahi." "Ka ci dai ko babu yawa ai." "Toh ya Nabeela." Yace yana murmushi Kitchen din Raihana ta wuce ta hado musu abincin akan tray ta dawo falon, ta tarar Ya Nabeela ta tashi Hamma Hydar yana tsaye a jikin console yana waya sai Aryan din a zaune. A kasan rug din ta ajiye daidai saitin gaban sa. Ta yunkura zata tashi ya kamo hannun ta yana kokarin saka idanun sa cikin nata. Kin kallon sa tayi ya shiga murza hannun a hankali a hankali yana kashe mata ido daya. "Zuba min." "Ok." Tace ta durkusa ta shiga zuba abincin a hankali, zamowa yayi ya zauna ya rike hannun ganin tana ta cika plate din dan ba wata yunwa da yake ji kawai so yake kar ta tafi. Dawowa Hydar yayi wajen ya zauna a k'asan ta dauki wani plate din zata zuba masa Aryan yace ta barshi suci tare dan shima ba wani ci zai ba. Tashi tayi ta basu wajen suka ci abincin sannan ya Nabeela ta dawo suka cigaba da hira har kusan magriba sannan suka tafi. Direct main house suka tafi tare dan so yake ya sanar dashi komai tun daga kan binciken sa da kuma abinda suke shirin yi a goben dan yaga karar Hydar din ma sosai da be tambaye shi ba. Bayan sun yi sallah suka zauna a dakin Aryan din ya bud'e masa komai, ba karamin mamaki da kaduwa Hydar ya shiga ba, dan sai da ya zubar da hawaye, idan abinda suke tunani ya zama gaskiya wanne irin farin ciki Abby zai? Dadah, Raihana,Lamido da Sadeeq? Ji yayi gabaki daya ya kagu yaga goben tayi, dan baya jin ma zai iya runtsawa. Da asubah bayan sun dawo daga masjid wani tunani ya zo wa Aryan, wayar sa ya dauka ya kira Ya Nabeela yace zasu je wani waje da Raihana da Hydar idan ba damuwa. Toh tace kawai bata kuma bi baasin ina za an ba tunda dai matar sa ce. Dakin Raihanan ta wuce ta same ta tace ta shirya Aryan zaizo da Hydar zasuje unguwa. Da murnar ta, ta hau shiryawa dan yace zuwa bakwai yake so su tafi. Tana shiryawa yayi mata text message yace ta dau spare kaya two set, mamakin in da zasu yasa ta kusan makara da shiryawa a gurguje ta karasa ta sha tea da biscuits saboda yayi wuri sosai ta iya cin abinci me nauyi. Zuwa sukayi ta fita lokacin ma Ya Nabeela ta koma bacci sunyi sallama. A shirye shima Adam suka fito suka rufa musu baya, office Aryan ya fara zuwa ya fito ya dawo kujerar baya kusa da Raihanan Malam Yahya driver ya shiga mazaunin sa yaja motar suka dau hanya. **RQ** 57 ***Dan satar kallon sa tayi ganin ya dawo bayan, gaba daya attention din sa yana kan wayar dake hannun sa. Kauda kanta tayi zuwa windown ta zurawa tagar ido cikin tunanin in da zasu haka kuma har da hamma hydar. Kamar ba shi ba ma dan tunda suka shigo motar be yi magana ba, bare kuma Aryan din da dama shi ba gwanin magana bane ba. Ya dau kusan mintuna sha biyar akan wayar tasa kafin ya kashe ta ya ajiye ta a gefe sannan yace “Kunyi magana da Lamido ne?” “Eh munyi, yace be samu flight din safe ba sai dai na 12pm.” “Ok, Kamal ma yace yana hanya duk da nace masa noo, Ya dage sai yazo. tafiya ce me dan tsawo, inaga sai dai ma su same mu a gida kawai idan abinda muke so ya tabbata muna zuwa in sha Allah zamu juyo ai.” “I hope so, amma dai inaga so dai suke ayi komai suna nan, ban zata Lamido zai samu time haka ba.” “Dole ne ai, idan ka duba muhimmancin abinda za’a yi din.” “Haka ne, Sadeeq dai ban sanar dashi ba, kasan Shima he’s always busy a hospital plus nasan yana da wani surgery da zai yi yau a private hospital dinsu bana so na raba masa hankali.” “Yeah it’s good da ka kyale shi, mu ma mun isa ai.” Sai ya juyo da kallon sa kan raihana da tayi tsam tana son fuskantar abinda suke cewa din amma ta gaza gane komai. “My wife.” Yace yana dan jan jikin sa kadan zuwa bangaren ta sannan ya kwanto da kansa gefenta. “Umm.” Tace a hankali ya sa hannu ya dauki wayarta dake saman cinyarta ya kunna, hoton ta ne akan wallpaper din sanye da khakhi na Nysc tayi murmushi me kyau da ya kara fito da ainahin kyawunta sosai. “Corper.” Yayi dariya da ya tuna sunan da yake fada mata. Murmushi tayi itama ya ajiye wayar a inda ya dauka Maimakon ya tashi zaune sosai sai ya dora kansa a saman cinyar tata ya kulle idon sa. “Jiya banyi bacci sosai ba. Bacci nake ji sosai.” “Me yasa?” “Ina ta tunani, kaina kamar zai fashe na saka wannan na warware.” “Ok, ayya.” Shiru yayi idon sa a kullen amma ba bacci yake ba, kasa nutsuwa tayi har sai da ta furta “Ina zamu?” Bude idon yayi ya zuba mata su akan fuskar ta, tayi saurin janye idonta ganin yadda kallon nasa yayi tasiri akanta. “Siyar dake za muyi,Hydar nawa ma akayi cinikin kan ta?” “Wa fa?” Hydar yace yana waigowa bayan dan ba jin hirar su yake ba. Da hannu Aryan ya nuna masa raihana sai hydar yasa dariya “Kan kanwata ai me daraja ne, ba zai siyu ba.” Tashi zaune Aryan yayi jin wayar sa tayi vibrating, dubawa yayi sannan yace “Malam Yahya duba side mirror akwai masu bin mu ko?” Kallon side mirror Malam Yahya yayi sannan ya kalli rear mirror ya gida kansa. “Na lura kamar ana bin mu tun dazu, ganin yadda suke kokarin bin bayan mu sai da kafa ba tare da sun zo sun wuce mu ba duk kuwa da yanayin tafiyar da muke a hankali.” Murmushi Aryan yayi, hydar ya waigo yana bukatar karin bayani “Nasan suna bin mu, Adam ne tare da yaran Hajiya Zeenat.” “Ka sani?” Gida kai Aryan yayi, “Yaji convo dinmu da Kamal, na ganshi ta jikin window din kitchen sanda yake eavesdropping ma conversation dinmu, shisa na bashi damar yaji komai dan nasan dama abinda zai yi kenan, zai biyo mu not knowing zai fadama trap ne.” “Woaw! I’m impressed.” Hydar yace yana murmushi, be san Aryan din yana da basira haka ba, dan wani kallo yake masa duk da yaga kokarin sa sosai ko akan case din Abby Amma be dauka haka yake ba. He act calmly kamar ba wani abu bane ba ma. Menene trap din? Menene kuma plan din da Ya shirya? “Malam Yahya muje kawai, ka lura sosai da moves din su, hydar watch from your side,” “Ok.” Hydar yace yana kallon mirror side din shi ya kara tabbatar da, da gaske bin sun suke. A nutse suke tafiyar duk kuwa da doguwar tafiya ce, yana cikin plan din Aryan din dan ya riga yayi calculating hour nawa zasuyi covering akan speed din da suke kai. Wani messege din ne ya sake shigo masa, ya kalli wayar sannan yace “Taka motar nan malam yahya.” Take motar malam yahya yayi suma sai suka taka tasu, abinda ya bawa raihana matukar tsoro, tayi saurin riko shi tana matsowa jikin sa sosai. Riko ta yayi ya sakata a jikinsa ta makalkale shi. Hannun ta ya kama ya saka cikin nasa ya damke yana mata dariya. Idan kana neman kwararre a tuki ka samu malam yahya ka gama, dalilin da yasa Aryan ya zabi tafiyar tare dashi kenan dan yasan dama hakan zata faru. Kokarin bace ma su Adam din suke amma suma sun rike wuta gashi dama hanyar ba kowa sai yan motoci jefi jefi. Daf da zasu shiga garin ne wajen wani karkacewa da titin yayi Aryan yace malam yahya ya dauke hanya, abinda ya jawo suka bace wa su Adam, wani irin ihu Adam yayi kamar zai damki kan sitiyarin ya buga jikin dashboard cikin bacin rai yace driver ya sauka daga titin ya gangara kasa. Gangarawa suka yi ya hau duddubawa dan basu ga alamun hanya a wajen ba, sai wannan dai titin guda daya tal da suke kai. Tafiya suka soma yi a cikin garin har suka iso garshen dan titin da babu kwalta akansa, parking sukayi daga chan gefe sannan suka fito, a kaida machine ake hawa daga nan sai a shigar da kai garin amma sai Aryan yace su taka a kafa har su karasa dan baya so raihana ta hau bayan machine din, “Idan da nisa nake ganin gwara mu hau Aryan. “ “Daga nan zuwa gidan malam yakubu akwai nisa?” “Malam Yakubu wanne?” “Wani farin bafulatini, ya zauna a cikin gari kafin ya tattaro ya dawo gida.” “Oh na gane, gidan Baffan Kudu yake nufi, da yar tafiya gaskia musamman Yanzu da tsuka tayi yabanya hanyoyin sun zama masu wahala dan idan ba kwakwaran sanin wajen kayi ba sai ka bata.” “Ai ban ma san wajen ba, zuwan mu na farko kenan.” “Ina ganin mu hau kawai su kaimu Aryan.” Hydar yace “Ok, baba kai sai ka dauketa.” Yace yana nuna wani dattijo a cikin masu baburan. Girgiza kai hydar yayi, ya d’ane bayan machine dinsa. Taimaka mata yayi ta hau ya karbi jakarta ya saka a tsakiyar machine din tsakanin ta da baban sannan yace su yi gaba sai wanda zai hau yabi bayan su maana tana gaba yana bayanta kenan. Shi dai hydar be ce komai ba, burin sa kawai su isa, jikinsa yayi masifar sanyi ga wani irin tsoro, tsoron kar su tarar da labari mara dadi ko ace ba nan bane, duk da Aryan ya tabbatar masa da mutumin shine ya dauki ammyn kuma shine Hajiya zeenat take zuwa gani a lokacin. ***Babban gida ne da ya amsa sunan babban gidA, baki daya kauyen babu gida me girma da tarin mutane irin sa ba. Malam Yakubu shine Yanzu a matsayin babba a ahalin gidan kuma shine ya tatttara yanuwansa dukka ya hade kansu bayan ya tattaro ya dawo a lokacin da ake harin rayuwar sa. A duk safiyar duniya bayan sun dawo daga dubo gonar su su kan zauna a kofar gidan a shinfida babbar tabarma su zauna su sha fara ko kunu da gaya ko koko duk dai abinda ya sauwaka kafin kananan ciki su wuce zuwa aikin gonar na ranar zuwa dagawar rana su sake tattaro wa su dawo gida suci abinci tare. Babban abinda mutane da yawa basu gane ba shine cin abinci tare yana matukar kawo shakuwa tsakanin yan uwa, miji da mata da sauran su. Babban Dalilin da yasa suke da matukar hadin kai kenan suna kuma girmama Malam Yakubu a matsayin sa na babba suna kuma mutunta duk wani abu da ya jibance shi. Karar shigowar mashinan ya sa suka maida hankali wajen ganin su waye suka zo? Ganin baki ne yasa suka ajiye abinda suke a gefe. Gaban malam Yakubu ne ya fadi, daidai lokacin da raihana take sauka daga machine din, bata da maraba da Ammy sam, nan take ya gane su waye da kuma abinda ya kawo su. “Sani matsar da kayan nan gefe, sannun ku da hanya.” “Yawwa.” Suka amsa a tare sannan suka zauna a gefen tabarmar bayan sauran duk sun tashi, gefe Raihana ta samu ta tsuguna ya cigaba da satar kallon ta ganin tsananin kamar tasu. Gaishe shi sukayi sannan aka gaisa da sauran yan uwan sai malam Yakubu yace duk su koma bakin aikin su, su basu waje. Ba musu kowa yayi nasa waje ya rage sai su kadai. “Yan samari ban gane daga ina ba.” “Daga kano muke.” “Toh toh Masha Allah, me ke tafe daku.” “Munzo akan maganar mahaifiyar mu ne dama.” Aryan yace “Madallah, jini na karya ba, tun da kuka nufo mu nake kallon fuskar innar yara da wannan Baiwar Allar, kamar ta baci matuka. Ya gida ya hanya?” “Alhamdulillah.” “Anzo lafiya dai ko?” “Alhmadulillah.” “Toh Madallah, me kuke son sani game da mahaifiyar taku?” Ya tambaya “Munzo ne muji idan tana raye, muna so mu ganta.” “Menene sunan mahaifiyar taku?” “Aisha Nasir.” “Madallah, tana nan da ranta kuma a yanzu haka ma tana cikin gidan nan.” Ya nuna gidan nasu da hannu. “Alhamdulillah! Suka hada baki wajen fada. Kallon rashin sani da fahimtar abinda yake wakana raihana take musu dan Itafa bata fuskanci komai ba. “Zamu iya ganin ta ?” “Sosai, me zai hana? Sai dai wani hanzari ba gudu ba…” Duk sai suka tsaya suna kallon sa cikin tarradin abinda zai fada “Mahaifiyar ku na raya kuma cikin koshin lafiya, sai dai ta gamu da wani iftilai a shekarun baya in da mota ta kade ta har ta kai kan ta yayi mugun buguwar da ta manta komai da kowa da ita karan kanta. Bata san wacece ita ba bare tasan komai akan rayuwar ta. Anyi mata magani a lokacin daidai gwargwado sai dai duk lokacin da mukayi mata maganar gida da dangin ta takan birkice mana tamkar ana saka guduma ko karfe ana buga mata kanta. Haka zatayi kwana da kwanaki tana ciwo na fitar hayyaci, da muka gano haka sai muka daina yi mata maganar, tun daga lokacin shikenan ta samu sauki, muka cigaba da rayuwar mu tamkar babu abinda ya faru.” Shiru sukayi kamar ruwa ya cinye su, sai raihana da ta saka kuka a durkushen da take. “Yanzu menene abun yi?” Aryan yayi ta maza ya tambaya “Sati biyu da suka wuce na samu wani babban malami munyi maganar, domin tabbas ba kalou ba, anan ne yake tabbatar min ko dai anyi mata sihirin da aka raba ta da gida da danginta ne aka kuma saka mata tsanar su da tsanar waiwayar gida tunda bata shiga yanayin sai idan an mata maganar, dole sai anyi mata maganin sihiri idan har akwai shi toh sai an cire shi sannan zata iya dawowa daidai ta iya waiwayar danginta.” “Ya Allahu!” “Minti daya bari na daga waya.” Aryan yace yana tashi ya matsa gefe shi kuma malam yakubu Ya cigaba da yiwa su hydar bayani. Kamal ne ya kirashi sukayi magana sama-sama sannan ya kashe, sakon ne ya sake shigo masa ya duba sai yaga yace sun samu shigowar garin gasu a inda ma sukayi parking din motar su. Komawa yayi ya zauna kusa da hydar sannnan yace masa “Sun shigo suna wajen motarmu.” Kallon sa Hydar yayi da idanun sa da suka dan chanja kala, gida masa kai Aryan yayi sannan ya kalli malam yakubu “Baba dan Allah toh ko zaa shiga da ita ciki? Idan yaso ko maganar ce kar ayi mata tunda nasan ba gane ta zatayi ba.” “Abinda zan ce kenan, taso yan mata muje ciki, ya sunan ki.” “Raihana.” Jerawa sukayi tare da Aryan din har kofar gidan “Please karki yi kuka, komai zai wuce zamu san yadda za’a yi,just be strong kinji? For me.” Gida masa kai tayi, ya tsaya daga kofar ita kuma tabi bayan Baba Yakubu zuwa cikin gidan kirjinta na dukan uku uku. _*_*RQ_** 58 *****A tsaye take a gefen dakin ta, ba kasafai ta fiye fitowa a irin wannan lokacin ba, ta kan zauna a daki a mafiya yawan lokutan musamman idan gidan ya zama babu yaran duk sun fice. Yau tunda ta tashi gabanta ke faduwa kamar wani babban al’amari yana shirin faruwa da ita. Randar dake gefen dakin nata ta bude ta zuba ruwa a buta ta zagaya bayi domin kama ruwa sannan ta dan wasa kafarta ta dauke hankalin ta kuma daga tunanin dake bijiro mata. Fitowar ta kenan tana tattakowa a hankali zuwa kofar dakin nata tana kallon yanayin yadda rana ta bude kwal kamar irin azahar din nan sosai. Sallama taji ta Malam Yakubu yana shigowa cikin gidan, lullubin dake kanta ta ja ta gyara zuwa saman kafadarta sannan ta amsa masa jin kulin ta Ya shigo kai tsaye, a bayansa muryar mace taji da batayi mata kama da ta yan matan gidan ba. Amsa sallamar tayi tana sakè matsawa daidai kofar dakin nata kamar zata shiga. Kanta ne yayi wani irin sarawa tayi azamar dafe shi tana jin jiri na neman kai ta kasa. Da sauri cikin daga murya tace “Dan Allah karta karaso nan, dan Allah ta tafi bana son ganin ta.” “Wacece ?” Malam yakubu yace yana nazarin yanayin da ta shiga ganin raihanan “Ban santa ba, dan Allah ta tafi bana son ganin ta.” Ta sake maimaitawa tana yinkurin juyawa ta shige dakin nata. Kukan raihana ne ya karu, ta durkusa a bakin simintin kofar dakin tana sakè fashe wa da kukan. “Tashi tashi, ba kuka zakiyi ba. Abinda nake son ku gani kenan dama, nasan za’a yi hakan, amma ba wai yin kanta bane ba, an riga an raba ta da kowa nata ne, an saka mata wani ciwo me Zafin gaske akan duk abinda ya danganci gida.” “Zata warke?” Ta tambaye shi cikin muryar kuka “Sosai ma, ai maganin ne yazo, in sha Allahu karshen abun kenan.” “Mike muje shashen Asiya ki zauna kinji? Yaran gidan sun tafi makaranta ne amma daf suke da shigowa.” Tashi tayi tana kallon dakin da ammyn ta shige, babu ko Motsin ta gashi tana son shiga taga Halin da take ciki amma babu dama sam, dole ta hakura ta bishi zuwa bangaren Asiya din, ta zauna a gefen dan karamin gadon dakin na kaba taje ta debo mata ruwa a randa ta kawo mata sannan suka gaisa a mutunce. ****Daga chan jikin wata bishiya Aryan ya tsaya yana magana da Kamal a waya, yana sanar dashi abinda yake faruwa, da zuwan su Adam din da duk information din da ya samu daga wajen yaron da yake tare da Adam din. Ganin Malam Yakubun ya fito yasa Aryan katse wayar ya dawo wajen domin jin yadda akayi da suka shiga “Abinda dai na sanar daku din shine ya faru, dole sai anyi maganin sannan za’a samu waraka gaba daya.” “Yanzu ta zamuyi? Barin ta anan yana cike da babban hatsari tunda suka gano tana nan din domin a Yanzu haka suna cikin garin nan ma already, nasan jiran fitowar mu suke kila suyi attacking dinmu, ba zai yiwu mu dauke ta mu tafi da ita va?” Girgiza kai Malam Yakubu yayi, sannan yace “Bana tunanin hakn zai yiwu gaskia, baka ga halin da ta shiga ba ne ganin yarinyar nan, ina tsoron ma kada ciwon nata ya tashi dan baki daya yanayin ta Ya sauya, toh ta yaya kake ganij zata yarda tayi tafiya tare daku?” Dafe kai Hydar yayi da ya zama kamar ruwa a cinye shi a wajen saboda fargaba da tashin hankali, da kyar ya iya bude baki yace “Ina ganin ni da kanwata ne bata so ta gani, hakan ba zai shafi Aryan ba nake gani ko?” “Eh toh, bansan wanne irin Aiki akayi ba, amma idan gaba daya ne bana jin har shi din ma zata amince, sai dai mu gwada, bana kuma son mu kara dagula al’amarin ne.” “Gaskiya ne.” Aryan yace yana dora hannun sa a saman kafadar hydar, wai yau shine yake kokarin kwantar ma wani hankali. Wani messege din ne ya kara shigowa wayar sa, dama abinda yake jira kenan, dan matsawa yayi kadan sannan ya bude _”Oga suna planning shigowa ciki yanzu, muna tare da thugs ne kuma an basu umarnin daukar Madam ko Hajiyar da kuka zo gani.”_ “Adam!” Aryan ya furta a hankali yana kallon hanyar, baya son mutanen wajen su shiga Matsala saboda su, dan rayuwa suke me dadi da inganci ba irin tasu ba me cike da tashin hankali da tsantsar cin amana. Matsawa yayi wajen hydar yace ya taso suyi magana, Ya sanar dashi abinda yaron yace sannan ya dora “Menene abun yi? Bana so mu zamar ma bayin Allah nan matsala, dan na tabbatar a yadda Adam yakeji zai iya zasu aikata komai.” “Akwai matsala, Ammy ba zata yarda ta bimu ba, kana ganin muka barta anan zasu barta ne?” “Ba zai yiwu mu barta ba, dole zamu sake taking risk din kawai. Zan shiga a matsayin likita da zan duba ta, idan ta amince sai mu ce zaa kaita asibiti ne, daga nan sai muyi kokarin fitar da ita daga garin.” “Ayi hakan, Allah yasa ta amince.” “Amin.” “Malam dan Allah ina zamu samu mota?” “Anan? Eh toh, akwai nan makocin mu Isah da yake haya zuwa cikin gari, dazu naga ya dawo ko hutawa yake? Sai dai idan shi zaa yiwa magana.” “Ayi masan dan Allah. Ba zai yiwu mu bar mahaifiyar mu anan ba domin rayuwar ta na cikin hadari sosai, ina ganin zamu sakè gwada saar mu ne kawai, na gwada shiga din a matsayin likita ko zata amince.” “Toh Bismillah, muje ciki, kai kuma ko zaka yi sallama gidan chan muji ko Isan zai sake fita.” “Yawwa ayi hakan, bamu da time.” Aryan yace a dan gaggauce Ciki suka shiga zuwa dakin nata, tana kwanci kanta na jujjuya mata kamar zai fashe ga wani jiri wanda a kwancen ma yin sa take yi suka shigo. “Innar yara jikin ne?” Malam Yakubu yace yana da jikin labile “Eh malam, kai ne kamar zai fashe. Don Allah a samo min magani.” “Tashi ga likita nan yazo, abokin Hamisu ne nan na makota, tashi ya duba ki idan zai yiwu sai ya rubuta maganin idan ba zai yiwu ba sai mun bishi Asibitin su chan cikin gari.” “Toh.” Tace tana mikewa zaune, suka hada ido da Aryan din ai da sauri ta kwala kara, fita yayi shima da sauri har yana cin tuntube da kofar. Asiya ce suka fito tare da Raihana da sauri, ganin aryan yasa raihana yin wajen sa ita kuma Asiya ta shiga dakin Ammyn. “Menene? Me ya same ta?” Ta hada tambayar waje daya tana kallon sa hankali a tashe “Calm down kinji? Babu komai muna son ganin mun fitar da ita daga nan ne, but hakan ba zai yiwu ba sai bata ganin mu dukka, sai munyi hakuri mun bi komai a sannu, zo muje naga ko Hydar ya samu motar, idan yaso sai su, su dauke ta kawai mubi bayan su. Time yana kara kurewa.” Hannun ta ya kama suka fito wajen suka tarar da Hydar da Isan a tsaye ana magana har ya jawo motar ma, “Dama mota na shigowa nan?” “Eh Amma ta chan baya ne, sai anyi zagaye idan mutum ba a garin yake ba, ba zai gane ba.” “Haka ne, saura babura guda uku dan Allah, dan ba zai yiwu mu koma wajen motar mu ba.” “A cikin gidan nan ma ba zaa rasa babura ba, kaga biyu nan nasu Awaisu, bari na zagaya baya na kirawo shi sai Isuhu ya dauko nasa shima.” Isan yace yana barin wajen da sauri dan ya hasaso zai samu kudi sosai a wajen su, shi dama kuma mayen kudi ne kowa yasan shi. malam yakubu ne ya fito Aryan ya fada masa abinda ya tsara kawai, hakan kuwa akayi, suka hau suka bar wajen sannan aka fito da ita tare da Asiya da Matar kawu Liman na gidan sai malam yakubun a gaba. Ba hanyar da su Aryan din suka shigo ba tanan suka bi ba, hanya ce sosai babba kuma sai dai zagaye ne. Wayar sa ya dauka ya kira Adam domin baya so ma yaje musu wajen da yan iskan da ya dauko ya sake tayar musu da hankali duk da su din ma ba baya ba, mafarauta ne a garin idan ka cire gidan su Malam Yakubun da yan tsirarin gidajen. “Kar ka wahalar da kanka shiga cikin dan mu tuni mun wuce,kuma wallahi wallahi idan wani abu ya faru,sai na nuna maka na fika sanin duniya na rantse da Allah.” “Kai karamin dan iska ne, idan ka isa ka tsaya a in da kake, kaga yadda zan sa karnuka su yagalgalaka na rantse da Allah, kuma Yanzu ma ba hakura nayi ba, zan biyo bayan ku idan har zaka dauke min mahaifiya babu abinda ba zan iya aikata maka ba.” “Idan ka fasa Adam, kasan daidai nake da kai, dan haka duk abinda zakayi kayi, mahaukaci kawai. Sai nayi maganin ka.” Ya katse wayar ya maida ta aljihun gaban rigar sa. Bayan motar suke bi har suka fita daga lungunan suka hau main titin, wani abokin sanaar Isan suka hadu dashi zai koma gida isa ya tsaida shi ya dauki su Aryan din a motar sa su kuma su Isuhu suka koma bayan Aryan din ya basu kudade masu kauri suna ta godiya. Aryan ya riga yasan Adam sai sun biyo bayan su, ya kuma san a lokacin daf Kamal yake da shigowa tare da yaran sa, hakan ya bashi relief duk da yasan dole sai ya koma ya tabbatar da basa garin kamar yadda yace masa Amma yana da yakinin ba zai yi musu komai ba ko dan gargadin da yayi masa kuma yasan tabbas Hajiya zeenat na wajen sa dole zai bi a hankali tunda Yanzu be samu abinda yake so din ba. A kofar shiga babban garin suka hadu da su Kamal, a waya sukayi magana dan basu tsaya ba saboda jikin Ammyn ya rikice suka ce su hadu a asibitin garin domin suna da bukatar chapke Adam da yaran nasa dan haka suka bi hanyar da su Aryan din suka baro su kuma suka shiga cikin garin. Direct babban asibitin garin suka nufa wanda yake a matsayin zone 1 saboda haka yake da duk manyan kayan aiki da manyan likitoci da suke shigowa daga chan cikin gari suna komawa kullum. Yanzu ma akwai likita saboda haka suna zuwa aka karbe ta aka duba ta sannan aka rubuta mata maganguna ciki har da na matsanancin ciwon kan. Sanda suka gama da asibitin sannan yamma tayi sosai, ba zai yiwu su dau hanyar barin garin ba duba da yanayin nisa garin, Malam Yakubu ne ya nema musu alfarma sauka a gidan bak’i, gidan da wani me kudi a garin Alhaji Ahmad ya gina saboda bakin sa idan sun zo anan yake saukar su. Mukullin ya basu dan a lokacin ma babu kowa a gidan. Chan dakunan ciki aka kai Ammy saboda ma karsu hadu aka ce mata zasu kwana anan ne zuwa gobe su wuce gida, bata kawo komai ba kuma kan nata yayi sauki musamman ga asiya a tare da ita sai ta ware. Daki biyu bayan na ammyn aka bawa su Aryan,Aikuwa ya shafawa idon sa toka yace shi da matar sa zasu zauna hydar shi kadai dan a lokacin kamal sun wuce dasu Adam da suka labe suka kama su a hanya. Lamido kuma ya tsaya kawai a kano dan yasan ko yazo zai sake complicating abun ne tunda ga halin da Ammyn take ciki. Wuce wa yayi kawai rijiyar lemo gidan wani babban malamin sunna da yake maganin ire iren wadannan matsalolin ya same shi ya sanar dashi komai, suka shirya zasu tafi gobe tare daga nan ya wuce hotel ya kwana. Lawan ne ya maida su Malam Yakubu gida tare da matar Kawu Liman isa kuma ya zauna suka fita tare da Aryan samo musu abinda zasu ci, suka samu wani restaurant karami suka siyo abinci da gurasa sai tsire da soft drinks da ruwa. Malam Isan ne ya mikawa su Ammyn sannan shima aka bashi nasa hade da kudade masu kauri sannan yayi musu sallama ya tafi akan zai dawo da safe ya dauki Aryan din suje ya dauko motar sa. Ledar da akayi ma hydar daban Aryan ya mika masa sannan yace “Sai da safe Yaya.” Da sauri Hydar ya riko shi suka saka dariya a tare, yanayin shekarun baya ya dawo musu a lokacin “Dan wulakanci bari na zakayi?” “Me zanyi? Zan kwana da kai ne?” “Kafi karfi na, sai da safe.” Hydar yace yana sakin shi. Murmushi kaawai Aryan din yayi yana jin wani closeness da hydar din kamar a shekarun baya, ya wuce dakin da Raihanan take ciki. A chan gefen katifar dake malale a kasan dakin Ya hango ta, ta kwanta l’amo kana gani kasan ta gaji sosai. Ajiye ledar yayi a kan carpet din dakin ya karasa gareta gami da dagota ya jawota jikin sa yana kallon kumburarrun idanun ta da suka daga saboda kuka. Da yasan abinda zasu tarar kenan da be zo da ita ba, shi a tunanin sa suna zuwa komai lafiya tafiya kawai zasuyi, amma sai aka kuma samu akasi. “Ina ammyn?” “Tana dakin ta, ta samu sauki ma ta ware fa, aikin sihiri ne amma in sha Allah komai yazo karshe kinji?” Gida masa kai tayi, ya share mata fuskar da gefen hannun sa sannan yace ta wanko hannunta tazo suci abinci. Toilet din dake cikin dakin ta shiga ta wanke hannun ta dawo suka zauna Ya bude musu abincin suka fara ci a hankali. Gurasar suka fi ci da naman sannan suka sha juice din ta matsar da ragowar gefe ta koma gefen katifar bayan ta kara wanke hannun ta. Rigar jikinsa ya zare ya makale ta jikin kujera ya bar singlet yazo ya zauna a kusa da ita. **RQ**_ **59** A hankali yake shafa gashin kanta har ya samu bacci ya dauke ta. Sosai closeness dinsu ya haifar masa da wani irin yanayi me wahalar fassarawa. Zame jikinsa yayi a hankali ya wuce toilet din ya sakar ma kansa ruwa me sanyi ya dinga ratsa sumar kansa zuwa saman kafadarsa. Kansa a chunkushe yake matukar a yan kwanakin nan, sosai ya tsorata da al'amarin Hajiya zeenatu ganin halin da Ammyn take ciki, be taba tunanin akwai irin wannan kullin ba sai a yanzu, rashin imani ne tsantsa a rabaka da kowa naka domin samun biyan bukatar duniya. Da ruwan a jikinsa ya fito ya zauna akan kujerar dake gefe yana kallon fuskarta, yanayin yadda take fidda numfashi kadai ya tabbatar masa da bata wani jin dadin baccin. Tsaki yaja ya mike bayan ya dan share jikinsa da dankwalin ta sannan ya baza ji a saman kujerar ya zura boxer dinsa ya karasa wajen da take kwance. Rigar jikinta doguwa ce ta atamfa, ya tabbatar ba zata iya cin dadin kwanciya da rigar ba ganin yadda yanayin garin yake da dan zafi duk kuwa da akwai solar da fan tanayi amma garin a chunkushe yake babu iska tana kadawa sosai. A hankali ya juyar da ita ya kama zip din rigar ta baya ya shiga zare mata shi ya kawo mata zuwa kasan cibiyar ta sannan ya juyo da ita. Saurin janye idonsa yayi daga kallon saman kirjinta da yake a bayyane bayan ya janye rigar. Numfashi yaja da dan karfi sannan ya fezar da iska me zafi yana sakin ajiyar zuciya. Ya kai kololuwa a hakuri yana kuma tunanin hakurin nasa gaf yake da karewa, ba dan baya so ya takura mata ba, duba da yadda ta galabaita yau da babu abinda zai hanashi karban hakkin sa a yanzu, sai dai yana da tausayi sosai, ba zai iya kara mata wata damuwar ba, ya kara wahalar da ita ga damuwar Ammy da take ciki kuma. Juyi tayi ba tare da tasan wainar da ake toyawa ba, taji sanda yake zare mata rigar amma bata kawo wani abu ba, duk a tunanin ta ma mafarki take yi shiyasa ta cigaba da baccin ta hankali a kwance. Gefen ta ya kwanta sannan a hankali ya jawo ta zuwa jikinsa ya manna kirjinta a jikin sa, abinda ya janyo wani irin shock ya furta "Subhanallah!" Da dan karfi sai kuma ya samu kansa da yiwa kansa dariya, ya murmusa kad'an sannan ya sake matseta yana jaddada kansa ita din halilin sa ce. Yanayin yadda ya rik'e tan da kuma dan zafin da jikin tan yayi yasa taji ta takura har ta dan sake yinkurin juyawa amma sai ta jita a jikin mutum. Da farki ta manta a inda take kwata kwata, tunanin ta tana gidan Ya Nabeela kwance a gadonta tana bacci, jin ta jikin mutum yasa ta yin saurin yinkurin mikewa amma sai ya hanata, ya sake matse ta kam kam yana chusa kansa a jikin kirjin nata ya shiga sakar mata numfashin sa me zafi. Numfashin tane ya kusan daukewa take kuma sai kwakwalwarta ta shiga hasaso mata a yanayin da yake ciki. Hannun ta, ta kai ta taba kasan rigar ta, taji ta a zame sai tayi saurin kai hannu sama, daga ita sai bra daga sama. "Na shiga uku." Tace a ciki ciki kirjinta na bugawa da sauri. Yi yayi tamkar be ji ta ba, ya cigaba da chusa kan nasa hade da sakar mata zazzafan kiss a tsakanin wajen ga numfashin sa da yake hura mata. "Bacci nakeyi fa." Tace muryar ta a karye amma sam yaki dagowa bare ya nuna yaji me take cewa bare har ya iya amsa mata, maimakon haka ma sai ya sa hannun sa ta bayan ta ya shiga kokarin balle maballin bra din yadda zai samu full access da wajen. Kicin-kicin ballewa yake tana kokarin hanashi amma sai da ya samu ya balle su, sannan ya zare ta da dan karfi ya ajiye ta a gefe, da sauri tayi ruf da ciki tana manne jikinta da katifar dukka, dariya ta bashi sosai yadda tayi, amma sai ya kanne dan yanzu ba wai abinda yake gabansa ba kenan, so yake ya rage zafi ko yaya ne. Hargitso ta yayi gaba daya da hannu daya, ya dora gaba daya jikinsa akanta yayi mata rumfa ta yadda babu yadda zata iya hanashi abinda yayi niyya. Daidai saitin fuskar ta, ya kai tashi fuskar har numfashin su na sarkewa waje daya, ya shiga bin fuskar tata a hankali yana zagaye ta har ya kawo kan lips dinta. Kulle idonta tayi da sauri ya kai bakinsa kan nata ya shiga kissing dinta a hankali, duk da idon ta a rufe yake kokarin kare chest dinta take da hannun ta yana jin ta, ya kyale ta sai da ya gama kissing din bakin nata ta sakankance sai jin hannun sa tayi a saman kirjinta yana zagaya su ko ina, jikinta ne ya hau rawa ta shiga kokarin ture hannu tana masa magiya, amma yaki ya cigaba da abinda yake kansa tsaye, sai da ya ga dama dan kansa sannan ya kyale ta, zuwa lokacin gaba daya jikinta rawa yake yi, shi kuwa dama be ma san abinda yake ji ba, da be yi karfin halin kyale ta ba, da babu abinda zai hanashi aikata aika aikar, shiyasa ya hakura ba dan yana so ba. Toilet ya shige ita kuma ta yi saurin maida rigar ta, cike da mamakin Aryan din tamkar bashi ba. Tana kwance ta kulle idon ta, ta kudundune ya fito daga toilet din ya karaso gabanta idonsa ya dan tashi kad'an yayi ja, yace taje tayi wanka, yi tayi kamar bacci take ya sake maimaitawa sannan yace "Zan ciccibe ki na kaiki fa." Da sauri ta tashi, sai dai bata jin zata iya sakawa jikin ta ruwa a lokacin dan zazzabi zazzabi take ji, sai kawai taje ta kama ruwa ta dawo ta tarar har ya kwanta ta rakube a gefen shi ta kwanta kamar zata fada k'asa dan tayi masifar tsorata dashi. Mirginowa yayi ya jawota jikinsa a hankali muryar sa a ciki sosai yace "Ba zaki koma gidan Ya Nabeela ba, nayi kara ai, bana so a samu matsala." Bata ce komai ba, dan bata da amsar da zata bashi saboda maganar tafi karfin ta. Sai ta kulle idonta tana jin shi yana gyara mata kwanciyar sosai a jikinsa bata ce komai ma. A haka suka karasa daren bata san lokacin da yayi bacci ba. Ita ta fara tashi ta wuce tayi alwala tana fitowa ta ganshi a zaune yana kallon wayar sa, mikewa yayi ya isa toilet din ita kuma ta gyara tasa Hijab dinta zata tada sallar ya fito yaje ta jirashi. Kayansa ya mayar yazo ya jasu sallar sannan ya fita ya barta a dakin zuwa wajen Hydar. Hankalin ta gaba daya yana wajen Ammy ji take kamar taje ta ganta amma babu hali haka ta hakura ta zauna lamo sai ga kiran Lamido ta daga da sauri tana dagawa ta saka mishi kuka, dama neman wanda zatayi ma take yi sai gashi ya kira, kwantar mata da hankali yayi ya ce yana hanya zaizo tare da me maganin sannan ta dan samu relief. ***Wajen Hydar ya je ya kwankwasa masa sannan ya shiga, suka gaisa ya zauna. "Ina kanwar tawa?" Hydar ya tambaya yana kallon sa "Na cinye ta!" "Haba ka isa? Ai kanwata ba zata cinyu ba sam." "Wait and see, Lamidon sun tashi?" "Eh wayar sa ce ma ta tashe ni, sun dauko hanya." "Good, Allah yasa Isa ya kawo mana motar yanzu, Kamal ma nasan zai dawo in sha Allah yau zamu juya." "In sha Allah!" Kwankwasa kofar akayi, Aryan ya tashi ya bud'e, me gadin dake kula da gidan ne, hannu ya bashi sukayi musabiha sannan yace "Wai Isa ya karaso, suna waje tare da Malam Yahya." "Yawwa Masha Allah, dama yanzu muke maganar." "Ai naga mutumin ba baya ba, he's very hard working." "Yeah sosai, bari na je wajen sa." "Ok zan fito yanzu nima." Tare suka fito da maigadin suka tarar da Isan a waje tare da Malam Yakubu da Awaisu, key din motar ya karba bayan sun gaisa sannan yace su shigo ciki, ya kaisu dakin Hydar sannan Malam Yakubu ya kira Asiya yace zai shigo ta fadawa Innar Yara. Wajen Maalm Yahya Aryan ya karasa suka zauna ya tambaye shi yadda akayi jiyan bayan su Adam din sun zo wajen motar, guduwa yayi ashe ya buya be fito ba sai bayan magriba bayan ya tabbatar sun tafi. Shiru kawai Aryan yayi yana tunanin abinda ya kamata yayi next for now yasan ya gama da babin Adam da duk iskancin sa Wajen sha biyun rana Lamido suka karaso tare da malamin, lokacin duk sun shirya sun yi wanka suna jiran zuwan nasa, Kamal yace ba zai samu zuwa ba saboda a jiyan suka bar Kano tare da su Adam dan haka duk yadda ake ciki suyi waya kawai. Raihana na jin malamin yazo ta hau murna, zata fita ma Aryan ya riketa yana mata wani irin kallo, sunkuyar da kanta tayi k'asa cike kunyar sa, yana sane yake mata hakan dan ya lura gaba daya taki yarda ta hada ido dashi tun abinda ya faru jiyan "Ina zaki fita haka babu ko mayafi?" "Hamma Lamido zanje na gani." "Ba shi kadai bane ba, ko so kike a kalle min mata?" Komawa tayi ta zauna yayi murmushi ya fice. Gaisawa sukayi da Lamido da malamin me cike da kamala. Malam Yakubu ne ya jagorance shi zuwa in da Ammyn take, sukayi sallama bayan sun gyara jikinsu sun rufe sannan suka shiga, hannun sa dauke da Babbar jarka cike da ruwan addu'a, yana shiga Ammy ta mike zata gudu yayi saurin tura kofar yana murmushi "Bakaken shaidanu ne wallahi Malam, kaga sun ganni zasu gudu, suna matukar tsoron ayar Allah, domin kona su take kurmus, wannan ruwan da kake gani, ruwan addu'a ne da aka karance masa ayoyin alkurani me girma, idan ana zuba musu tamkar ana sheka musu tafasashen mai ne, amma in sha Allahu an zo in da za'a samu waraka, da yardar Allah zata samu sauki." "Allahu yasa." "A kujerar Malamin ya zauna sannan ya umarci Ammyn ta zauna, Asiya da duk ta tsorata tayi tsuru tsuru kamar za'a ce kyet ta gudu, amma haka ta daure ta zauna daga gefen amma sai Ammyn taki, cikin daga murya ya daka mata tsawa. "Zauna!!!" Da sauri ta zauna tana kin yarda su had'a idanu kwata kwata saboda tsabar tsoron sa da take nan take. Fita waje Malam Yahya yayi, ya matso yace ta mike kafa, ta mike a tsorace, sannan yace Asiya ta gyara mata Hijabin ta baya goshin ta ya bayyana, gyara mata tayi,yayi bismillah ya dibi ruwan ya zuba mata a saman kanta zuwa saman fuskar ta. Wani irin razanannen kara da ta saki sai da gaba daya gidan ya dauka, da sauri Aryan ya koma dakin da Raihana take, domin tana bukatar shi a lokacin. Cigaba da zuba mata ruwan yayi tana ihu da kururuwa kafin su fara magana daya bayan daya, tun yana irga su nawa ne a kanta har ya fara sarewa, ba karamin wahala tasha ba, domin duk abinda aka hada da bakaken shaidanu akwai matukar wahalarwa domin suna da masifar taurin kai, ba dukka ya samu suka fita ba a lokacin, sai dai yaci karfin su sosai, kuma ya karya lagon su ya kona da dama a cikin su, abu daya yafi tsaya masa a rai, inda suka tabbatar masa sai da aka yanka musu jinjiri sabon haihuwa akan aikin nata. Shekaru da dama suna tare da ita, sun hanata sakat sun saka mata ciwo, sun sakata manta kowa da komai da ya jibance ta, sannan sun dora mata ciwon kai me tsananin gaske. A hankali ta soma dawowa hayyacin ta, ya kira sunan ta na asali Aishatu,ta amsa masa da k'yar dan ko ina a jikinta ciwo yake mata, fita yayi ya barsu ita da Asiya ta sauya kayan ta, ta kwanta zazzabi me zafi na rufe ta. A cikin zulumi ya samu su Lamido da Hydar a waje, sai ga Aryan ya fito tare da Raihana sanye da Hijab, kallon ta malamin yayi sannan yace "Wannan ce Raihanan?" Gida masa kai tayi Lamido yace eh itace "Ki dinga azkar kinji? Akwai aiki babba akan mahaifiyar ku, dole sai kun dage da addu'a kar a dinga yin tufka ana yin warwara, suzo suna shafar yayanta, domin yanzu matsafa turke suke yi a jikin uwa,sai suje suna shafar yayanta suna wucewa." "In sha Allahu Malam, yanzu ya jikin nata." "Alhamdulillah, amma dole ne sai mun dage, sai munyi addu'ar nan kullum a kalla mu dauki wata guda munayi, domin ba karamin aiki akayi akanta ba, baiwar Allah an cutar da ita, sun zuba mata kaya sosai a jikin ta, domin duk wanda nace ya fita sai yace kayansa yake kwashewa, zan dauka sun tafi sai na sake zuba ruwan sai na gane makalewa yayi." "Wanne irin Kaya Malam?" "Cututtuka ne, idan kaji sun ce kaya toh sun saka ma mutum cuta, idan kuka tambayi wadanda ke tare da ita zasu gaya muku abubuwan dake faruwa da ita wanda duk su suke saka mata." "Mun gode Malam, yanzu muna so mu tafi da ita, amma muna tsoron kar ta rikice mana." "Babu matsala, tare zamu tafi baki daya ai, in sha Allahu babu abinda zai faru, domin ko a yanzu fa anci karfin su, sai dai nasan naci irin nasu, zai yi wuya su hakura a Zama daya, sai an kusan kone su kurmus sannan zasu hakura." "Mun gode Allah ya saka da Alkhairi " "Amin Amin, zan dan shiga gari wajen wani tsohon aboki na, idan kun gama shiryawa sai ku kirana nazo mu wuce." "Toh Malam, muma yanzu zamu fara shiri dama abinda ya zaunar damu kenan." "Ba laifi hakan, Malam Ibrahim sai ka kirani idan kun gama." "Toh Malam, muje na sauke ko toh." "A ah, je kaga mahaifiyar ka, ni zan iya karasawa da kaina ba wani nisa bane ba." "Isa yana waje ai, ga Malam Yahya sai su sauke ga Malam." Aryan yace yana bin bayan sa, yasa Isa ya tafi kaishi tare da Malam Yakubu da suka kulla sabuwar alaka da Malamin. Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Lamido, Hydar da Raihana. Kowa na tsoro da shakkar zuwa wajen Ammyn, duk da shi Lamido be ga yadda tayi ba, amma kuma yana cike da zulumi, sai dai a matsayinsa na babba shine zai shige gaba, sai kawai ya kama hannun Raihana suka nufi dakin Hydar da Aryan suka taka musu baya. Tana kwance Asiya ta lullube ta da zani suka shiga, taji shigowar su amma bata dago ba, bata kuma yi komai ba sai dai bata kalle su. Hawaye Lamido ya sharea boye da ya tabbatar da Ammyn tasu ce, ta chanja sosai kamar ba ita ba. An zalunce su zalunci mafi girma, be taba jin da gaske yana son ganin bayan Hajiya Zeenat irin yau, ko zaman prison din da Abby yayi be kai zaluncin da akayi ma Ammyn ba. Hannu tasa ta yafito Raihana dake faman kuka wiwi, ta shiga jan jikinta da sauri zuwa wajen Ammyn, ta fada jikin ta sannan ta fashe da wani irin kuka me cin rai. ***Kun jini shiru jiya glasses dina ne ya karye sai da na sake wani. In sha Allahu zamu koma posting din safe zuwa Monday. For now dai ku dinga expecting dina around magriba zuwa Isha. Nagode! **RQ**_ Page 60 ****Kuka wiwi suke daga ita Har ammyn, su kansu yan mazan dauriya ce kawai da taurin zuciya irin tasu ta maza amma dukkan in su jikin su yayi wani irin sanyi. Mikewa Aryan yayi, zai fita Lamido ya dakatar dashi. “Please karka tashi.” “Wai abu zan duba a waje ne.” “No ka zauna, dukkan mu daya ne kuma na tabbatar ammyn na cike da farin cikin ganin ka.” Zama yayi ya fasa tashin amma duk nauyi ya cika shi ga kuma kukan da raihana take yana taba shi sosai. Tashi tayi zaune da kyar dan har lokacin jikinta babu gwari, kokarin kokawa suka dinga yi da malam dan haka duk jikinta ciwo yake mata sosai. Matsawa Lamido da hydar sukayi gabanta bayan ta zauna sai ta yafito Aryan da hannun ta “Zo d’ana.” Wani abu ya daki aryan, a lokaci daya tunanin mummyn sa ya dawo masa. Sai yaji yana jin tausayin kansa da kansa, domin yasan shi tasa mahaifiyar ba zata taba dawowa ba. Matsawa yayi kamar yadda su Hydar din sukayi gabanta, duk ta shafa kansa tana murmushi. Kamar Aryan sak da na Khadija, babu in da ya barta a kamanni da dabiun ma sai dan abinda ba zaa rasa ba. Ko na a gayawa ammy shi din waye ba, tasan jinin aminiyarta ne, ballantana kamannin sa sune tun na kuruciya be chanja mata ba, sai dan abinda ba zaa rasa ba. Shi Ya fara zame wa da wayo da wayo ya bar musu dakin sai kuma asiya ta biyo bayan sa itama yanin suna da bukatar gamawa da mahaifiyar su. Sadeeq ne babu da Abby, wanda duk cikin su babu wanda yasan wainar da ake soyawa, sai kuma uwa uba Dadah da ba’a san kalar farin cikin da zata shiga ba. Da laasar sakaliya suka baro garin bayan Aryan fa hydar sun yiwa malam yakubu da isa harda asiya e sha tara na arziki, sannan Aryan ya basu complimentary card dinsa yace suzo Har gida su same shi. Sunyi ta godiya a haka suka rabu da niyyar idan ammyn ta warke sumul zasu dawo dukkanin su, zuwa na musamman wajen malam yakubun asan ahinda ya kamata ayi masa dashi da ahalin sa. Mutanen gidan basu ji dadin tafiyar ammyn a haka ba, tunda mafi akasarin su basa nan, Wasu sun tafi suna chan kauyan su kanwar malam yakubun yaran kuma sun tafi makarantar islamiyya. Hydar, Aryan da Malam Yahya mota daya suka hau kamar yadda suka zo, raihana ta gudu motar Lamido, ita da ammy da malam a motar. Tana lura da ammyn duk bata da sukuni shi kansa malam din ya lura ya kuma san dalilin hakan shiyasa yace kar su saurareta su tafi kawai idan sun isa lafiya sai a sakè yi mata adduar. Haka akayi kuwa, dare suka shigo Kano Aryan yace su wuce gidan su amma sai Lamido yace a ah, a kaita gidan adda maimuna, shiru aryan din yayi yana nazari, duk da kanwarta ce adda maimuna Amma be kamata akai ta gidan a yanayin nan ba. Magana yayi ma hydar idan ma gidan su ne Lamidon baya so aje toh akwai gidan sa dan Allah akai ta chan zaifi. Magana hydar din yayi ma Lamidon Ya tunasar dashi fa ba dan Aryan din ba da basu san ina ammyn take ba. Sai kuma abin ya dawo masa yace toh sannan aka wuce gidan Aryan din dake kusa da tsohon gidan su wanda yake har yanzu. Baba maigadi na zaune a gate yaji tsayuwar motoci, duk da kwana biyu ma Aryan din ya rabu da zuwa gidan yana chan main house din Amma yayi tunanin shine, lekowa yyai ganin motar yasa shi saurin janye gate din suka shiga sannan Lamido ma ya shigo da tasa yana karewa gidan kallo. Shi da Hydar suka taimakawa ammyn suka shiga da ita ciki Aryan ya kaisu bedroom din sa dake kasa suka zaunar da ita dan jirin ne ya sake dawowa. Sallah suka fita suka yi tare da Malam sannan suka dawo ciki Lamidon da malam Suka shiga dakin ita kuma raihana ta fito. Sai a lokacin suka hada ido da Aryan da yayi zuru zuru a kwana dayan nan kachal duk ya sauya, irin kallon da tayi masa taga ya rame shima shi yayi mata dan sai yaga har ta fishi ramewa ma ga wani abu me kama da tsoro dan kare a idon ta. Da hannu yayi mata alamar tazo gareshi, ta saci kallon falon babu kowa sai su biyu dan hydar ma ya shiga cikin dakin. A hankali ta isa wajen da yake tsaye daga jikin kafar bene kusa da wani dan corridor. Hannun ta yaja zuwa cikin wajen yana kokarin saka kwasar idon sa a cikin tata “Menene?” Yace mata cikin muryar tausaya wa. Kamar me jiran kiris sai hawaye shar shar shar suka soma zuba, jan ta yayi ya bude dayan bedroom din suka shiga ciki sannan ya rufe kofar ya jingina a jikin ta yana jawota gaba daya jikinsa. A hankali suka saki ajiyar zuciya dukkan su. “Please ki daina kuka,idan kina kuka bana jin dadi, zata samu sauki zata warke, amma sai kin zama strong, idan ba haka ba gidan Ya nabeela zan maidake har sai an gama komai.” “Na daina.” Tace da sauri tana goge fuskar tata da bayan hannun ta. “Good girl.” Yace yana murmushi. Murmushin da maida masa itama sai kuma wayar sa tayi ringing. Rike ta yayi da hannu daya ya saka dayan hannun ya jawo wayar daga aljihun wandon sa. Zainab ce take kiran sa, ya kwana biyu rabon da ya shiga office, dazu yaga kiran abdulhakeem be bi ba, yanzu ga na zee. Dagawa yayi yana sakata a handfree “Hello sir.” Muryar ta cike da yauki da rangwada ta fito daga cikin wayar tasa. Gaban raihana ne ya fadi, ya dan kalle ta kadan jin yadda ta motsa sosai. “Ina jinki.” “Ya gida ya aiki sir?” “Alhamdulillah, ya akayi? Naga kiran abdulhakeem dazu yanzu kuma ga kiranki, hope komai lafiya?” “Lafiya lou sir, wasu files ne dama da ake da bukatar kayi signing, sai kuma meeting din da za’a yi tun last week Monday muke ta daga shi, sun yi magana suna so a sake fixing musu wata ranar.” “Zan shigo Office din gobe, duk abinda ya kamata sai ayi.” “Ok sir, ka huta lafi…” Kit ya kashe kiran sannan yace “Zainab ce.” Bata ce komai ba, ta zare jikinta a hankali ya kalle ta “Zanje na duba ammy.” “Um um, ki zauna ki jirani anan, idan malam ya gama ma Dr Mahfouz ne zaizo ya bata magani, tana bukatar Hutu tayi bacci sosai, so ki barta ta huta kinji? Yanzu zanje na dawo.” “Toh zanje falo na zauna, bana son zama anan.” Rike hannun ta yayi zuwa gaban gadon, ya zauna sannan ta dora ta saman cin yarsa domin ya lura rigima take ji, yi tayi kamar zata tashi ya rike ta sosai yayi kissing lips dinta na kasa. Shiru tayi ta nutsu kamar ba ita ba, murmushi yayi kawai ya zaunar da ita a gefen sa sannan ya tashi “Yanzu zan dawo just wait for me.” Da kai ta amsa masa, ya fita ita kuma ta kwanta lamo akan gadon komai na dawo mata daki-daki. Be jima ba sai gashi ya dawo, kamar wanka yayi dan ya sauya kayan jikinsa zuwa marasa nauyi, dama a takure yake tun a chan din shiyasa ya hau saman ya chanja bayan ya watsa ruwa a gaggauce, sannan ya fita ya karbo abincin da Ya nabeela ta aiko dashi wanda yayi mata waya tun suna hanya. A dinning ya ajiye sannan ya dawo dakin sai kuma ya kara fita da sauri ganin hydar na kiran sa a waya. Malam ne zai tafi suka raka shi waje Lamido yace zai maida shi yaki yace zai tafi da kansa gobe sai suzo tare da ammyn su kawo ta domin akwai Aiki sosai akan ta. Godiya sukayi masa ya tafi suka dawo ciki Aryan yace ma hydar akwai abinci a dinning idan akwai me bukata. Ammyn ya dibarwa Lamido ya bata taci kadan sai ga Dr Mahfouz ya karaso, ya duba ta sannan ya bata magunguna yayi mata alluran da zasu taimaka mata ta huta sosai sannan yace a barta ta huta zuwa safiya. Jawo mata kofar akayi suka dawo falo raihana kuma ta koma dakin da Aryan din ya kaita dazu ta zauna sai ta rasa me zatayi ma. Tashi Aryan yayi ya je dinning ya dauki plate ya zuba mata abincin sannan ya nufi dakin hydar na satar kallon sa kasan ransa kuma yana cike da jin dadi da farin cikin kanwarsa ta samu wanda yake sonta yake kulawa da ita. ****Tana kwance gaban katifar duk abin duniya ya dame ta, sau biyu tana yinkurin guduwa amma da ta zura kafarta take cin karo da kurar nan, abun mamaki yake bata yadda mutum zai yi rayuwa da kura babu abinda ya shafe su kuma. Ruwan pure water da take sha ta kalla, saura uku ya rage, bata san ko zaa sake kawo mata ba, ko kuma haka zata cigaba da zama. Turo kyauren akayi, Ladi ce dauke da abun kari tuwon dawo miyar kuka kamar kullum, shine abincin ba’a taba fashi ko a chanja ba tun da tazo, ta farko bata iya ci sai da taga uwar bari yunwa zata kasheta ta soma dan tsakura shima ba da yawa ba, gashi minti kadan Ladi take bata idan bata ci ba tazo ta kwashe kayanta tayi gaba. Shiyasa ana kawo wa in dai tasan zata ci take yin sauri ta dauka dan ta gama gane rashin mutuncin Ladi kadan daga aikin ta, ta zauna da yunwa, ruwan ma sai kadan ta bata ta shanye sauran tayi magana kuma taci zata chuna mata kura a dole ta hakura take kankan da kai a gabanta duk kuwa da bata san wacece ita da kalar abinda zata iya aikatawa ba, Amma babu komai da zarar ta fita daga wajen zatayi maganin yar iskar matar dan sai ta batar da ita daga doran kasa kamar yadda ta batar da sauran da suka yi yinkurin shiga rayuwar ta. “Tashi ki yi maza idan kina da niyyar cin abincin kici, ki bani kwanon idan baki da niyya kuma nayi gaba da kayana dan ba ajiye ni kikayi da zan dinga dafa miki abinci kina wulakanci ba.” “Yanzu Dan Allah ba zaki barni na tafi ba?” Kallon ta Ladi tayi, kamar ba zatayi magana ba, sai kuma ta matso ta zauna a gefen katifar daf da hajiya zeenat din, kamar tace ta matsa amma sai ta daure dan idan tayi magana tata ce zatayi zafi. “Kina so ki bar nan?” Tace tana sunce gefen zanin ta, “Ina so sosai wallahi, ki taimaka min na rantse da Allah sai na inganna rayuwar ki, na daga darajar ki zuwa daraja mafi girma a duk garin nan.” “Toh Madallah, zaki bar nan amma sai na samu abinda nake so, idan kin yi hadin kai toh, idan bakiyi ba na rantse da Allah barki zan gaki ga kurar nan.” “Zanyi koma me kika ce,wallahi zanyi nayi alkawari.” “Tah! Ba naje na dawo.” Ta mike tana yashe baki, ta girgiza kai ta fice da sauri. Dakin Lawwali dake daura da zauren gidan ta nufa tana kwalamar kira, kafin ta karasa ya fito da sauri “Ya akayi?” “Matar nan ce mukayi magana, ina ganin abinda alhaji yace ayi Yanzu ne daidai lokacin, taji uwar bari dole zata fadi gaskia akan komai.” “Allah ko? Bari na dauko abinda ya bani, mun yi waya dashi ma jiya yace zai dan yi tafiya, zamu iya fara aikin muga.” “Dauko maza, maganin dan iska karen maguzawa, ka daure ta a wuya sai ka shigo da ita, idan tasan wata ai bata san wata ba.” “Hajiya Ladi ikon Allah, duk an buga dake an barki, me maganin yan iskan gari dana jeji, ke kadai gayya kin tare nan kin tare nan. Manya manya maganin kanana kanana.” Ya hau yi mata kirari yana dariya “Kai dai yi da jiki, na matsu naga idon yar iska. So nake ko banza ta danyi zawo a jikinta, shegiyar mata me zubin karu wai.” “Haka kika tsaneta wai Hajjaju.” “Kasan ni bana son rashin mutunci, duk kawaicin yaron nan sai da ta kure shi.” “Wallahi, bari na dauko.” Ya juya dakin ita kuma ta koma tsakar gidan ta jirashi tana cije lebe irin na mugunta. Dauke da camerar ya dawo ya mika mata yace ta rike masa, ya karasa gaban kurar da suka gada wajen mahaifin su ya sunto ta, ya makala mata abu a wuya da baki sannan ya ja ta suka nufi dakin da Hajiya zeenat din take ciki😂 Ladi ce ta gaba dan haka bata ga abinda yake bayanta ba sai da taji gurnanin da take ji a waje yana matso ta har ta tabbatar a dakin ne, idonta ne suka hasko mata kurar muraran dinta a tsakiyar dakin harshen ta a waje tana kallon hajiya zeenat din. **RQ** 61 ***Kwanon dake kan kafarta ta yi jifa dashi saboda tsabar kidimewa. "Na shiga uku, dan girman Allah ku fita da ita." Tace cikin k'araji "Hegiya ashe kinsan girman Allah." Ladi tace tana kwashewa da dariya, "Matso ciki Lawwali, tasan ba da wasa muka zo ba. Kwarankwatsa dubu idan baki sanar mana da duk abubuwan da kika dinga aikatawa ba sai kurar nan ta gwaigwayi kafarki." Ta jawo hannun Lawwali ta turo shi zuwa wajen da Hajiya Zeenat din ta makale idanun ta sun fito waje cikin tsananin tsoro. A dan zaman da tayi da Ladi ta fuskanci mace ce jajirtacciya mara tsoro kuma, duk hargagin da take mata be sa taji tsoro ko karaya ba, burin ta kawai tagan ta a masifa. "Na roke ke ki girman Allah ki kyale ni, na miki alkawari duk abinda kike so a duniyar nan zan miki Shi wallahi." "Na sha gaya miki babu abinda zaki iya bani,matsiyaciya ma irin ki, me rayuwa a cikin kudin haram da jinin mutane." "Zaki gaya mana ko sai na sako miki ita?" Lawwali yace yana zama so serious sannan yayi kamar zai saki kurar da take ta faman fitar da harshen ta "Zan fada!" Tace da sauri "Taji uwar bari, yar tasha. Zauna ki nutsu ki fara tun daga farko, kuma wallahi kikayi mana karya sai kin yabawa aya zakin ta." "Zan fadi komai wallahi, amma kafin nan waye ya saku kamani? Aryan ne ko?" "Tun yaushe nake gaya miki bamu wani san Aryanu ba, kin ga alamun wai mutane tunda kika zo wajen nan?" "A ah." "Toh mu ma aljanu mun gaji da shegen halin ki ne shine muka ga dacewar dauko ki mu kawo ki nan, tunda kin zama annoba cikin al'umma." "Aljanu?" Tace tsoron nata yana ninninka na da sau dubu "Kwarai, dan haka kiyi da jiki ki fada mana komai da bakin ki, duk da mun sani amma ta bakin naki muke son ji, kuma na rantse da girman me dukka kika yi karya sai kurar nan ta gwaigwayi kafarki." "Na rantse zan fada,wannan wacce jaraba ce? Babu me nema na ne?" "Ko sun neme ki ba samun ki zasuyi ba, alkadarin ki ne ya karya, sai ma kin soma ganin sakayya." "Wannan masifa dame tayi kama?" "Da uwarki tayi, do Allah Lawwali idan ba zata sanar damu ba mika mata lanto ta dan gutsiri kaurin shegiya." "Zanyi." Tace ta zauna sannan ta nutsu sosai ya mikawa Ladi camerar ya nuna mata yadda zata rike aikuwa ta shiga daukar ta tana bayani tiryan tiryan tun daga farko har karshe, sosai Ladi ta yi masifar firgita da matar tsoro ya kamata dan bata taba ganin tsantsar zalunci irin wannan ba, amma sai ta dake kamar bata ji komai ba ta boye yanayin da ta shiga har suka samu duk bayanan da suke so. Lallai Hajiya Zeenat abar tsoro ce, domin samun mara Imani kamar ta zai yi yuwa duk da akwai su sosai amma kuma bata dauka ana irin wannan masifar ba. Ta cuce su ta bata musu rayuwa da lokaci sosai. Jikin ta yayi sanyi kalou ta fice daga dakin bayan tasa Lawwali daure kurar a daidai kofar dakin Hajiya Zeenat din da sau kusan uku suna shuna ta yi balain tsorata. Tagumi Ladi ta zabga sai kuma wasu hawayen tausayin Aryan da ahalin su ya saukar mata, da tasan irin wannan kalar rashin adalcin akayi musu da bata bari ko ruwa Hajiya Zeenat din tasha a gidan ba, lallai ma yana da karfin zuciyar da har ya iya kulawa da ita anan din ma. Zame fuskarta tayi real fuskarta ta fito, itace dai mai aikin gidan nasu wanda Hajiya Zeenat ta kora saboda yadda take kula da Aryan din,ashe bayan tafiyar ta abubuwan sun sake lalacewa sosai. Abinda suka dauka Lawwali ya turawa Aryan ta WhatsApp domin dama abinda Aryan din yake so kenan. ***Tura kofar yayi da hannu daya da babu abincin a hannun sa ya shiga da sallama. Tashi tayi zaune tana amsa sallamar sannan tana kokarin gyara rigar jikinta da ta dan ya mutse. Akan bedside drawer ya ajiye dan karamin tray din yana kallon fuskarta da yanayin walwalar ta. "Tashi kici abinci." Yace yana zama a gefen. Zaman ta gyara sannan ta dauki tray din ta sauke shi k'asa ta zauna a gabansa tana kallon kayan ba tare da ta taba ba. Zamowa yayi ya zauna a kusa da ita ya bud'e ya saka mata fork yace taci. Bata ce komai ba ta dauki fork din ta soma cin stir fry spaghetti da minced meat me dan karen dadi. Ganin ta fara ci ya sashi komawa saman gadon ya dauki wayarsa ya kira Ya Nabeela. "Yanzu nake shirin kiran ka." Tace tana zaune tare da Dr Farouk yana dinner a tsakiyar falon su "Nima abubuwan ne suka yi min yawa na manta, thanks for the food." "Nasan dama kun gaji sosai dole,kira zanyi nace ina kanwata wai? Shiru an dauke min ita ba wani bayani dai?" Kallon shashen da take zaune yayi sai yayi murmushi kad'an mara sauti, Ya Nabeela ba abokiyar maganar sa bace irin wannan amma da sai ya bata amsa. Abu daya kawai ya sani shine ta dawo kenan, yan kwanaki kawai zasu kara su fice daga k'asar gaba daya sai kuma an gansu. Dstriya Kawai tayi jin yaki magana ta kuma tabbatar da ba zai yin ba dan tasan halin sa, dama kuma Dr ya fada mata an ga Aryan din a passport office yaje renewing sannan yace zai kawo Raihanan itama, wani abokin sa a passport office din ne ya gaya masa tun last two weeks ma. Sallama sukayi bayan ta tambayi jikin Ammyn sannan tace zata shigo gidan gobe tare da Khadija Matar Kamal su dubata sannan su taya Raihana zama. Ajiye wayar yayi ya dan leka plate din sai yaga taci sosai, dadi yaji domin baya son yanayin da yake ganin tan. Mikewa tayi a hankali zata dauke plate din ya hanata ta hanyar rigata dauka. "Allow me please, your majesty!" Yace yana sakar mata tsadadden murmushin nan nasa. Murmushin ta samu kanta da yi domin taji dadin yadda yayi maganar. Dauka yayi ya fita ita kuma ta yafa mayafin ta, ta fito zuwa dakin da Ammyn take ta tarar tana baccin ta a nutse. A gabanta ta durkusa tana kallon fuskar ta hawaye na bin fuskar, bata san wanne irin godiya zatayi ma Aryan din ba, soyayyar sa da matsayin sa ya karu sosai a wajenta har tana jin zata iya zama dashi a kowanne irin hali. Ya dan dau lokaci a dakin tana jin kamar tayi kwanciyar ta a bayan Ammyn amma kuma sai ta tuna zai bukace a kusa dashi tunda ita Ammyn bacci take kuma ba lallai ta farka ba kwata kwata ma sai zuwa safiya, tasan kuma Hamma Hydar da Hamma Lamido zasu dinga dubata sai kawai ta tashi bayan tayi mata addu'a ta jawo kofar ta fito ta koma dakin. Babu kowa a ciki,yaga lokacin da ta shiga dakin Ammyn shiyasa kawai ya haye sama bayan ya samu sakon Lawwali ya hau kan aikin kawai a gaggauce. Shiru shiru be dawo ba, ta tashi tayi shafai da wutri sannan ta zauna tana yiwa Ammyn ta addu'a ta dade a zaunen sai gashi ya shigo, babu haske ko kad'an a corridor din alamun sun kwanta su Hamman ta, sai hasken dakin kawai yayi tunanin ma ko bata dawo dakin ba tana wajen Ammyn amma ga mamakin sa sai ya ganta a zaune akan abun sallah. Mikewa tayi ta nannade abun sallar ta ajiye ya karaso cikin dakin ya tsaya a gabanta. Hijab din jikinta tayi niyyar cirewa amma sai ta fasa tayi tsaye tana jiran me zaice. "Baki bacci ba? Na zata fa kina wajen Ammy." "Yanzu na dawo." Tace dan kar ya gane zaman jiran sa take yi har ta gaji. "Zaki koma ne?" "Eh." Tace kamar da gaske take. Sai ya langabe kai "Ba zaki tayani kwana ba?" "Um um, wajen Ammy zanje ni." Tace tana kewaye shi zata wuce. Riko ta yayi yana kokarin hana kansa yi mata dariya domin ya riga ya gano ta tun daga yadda ta amsa masa da farko. "Wajen Ammy zani." "Wajen Ammy zani." Ya kwaikwayi muryar ta yana murmushi. "Muje ki tayani wani aiki a daki na, idan muka gama sai ki dawo wajen Ammyn ko?" D'aga masa kai tayi sannan tace "Zan dawo ko?" "Emana, me zaki zauna kiyi a chan? Zaki dawo ai dole." "Ok." Tace a tunanin ta da gaske yake da yace zata dawo din, rashin rigar jikin sa ya hanata sakewa dashi har taji tana son komawa dakin Ammyn. Saman suka haye hannun sa a jikin nata zuwa bedroom din nasa da yake shi kadai a bud'e a saman. Murd'a kofar yayi ya dan yi baya ya bud'e hannayen sa yace "Ladies first." Shiga tayi a nutse ya bi bayanta gami da rufe kofar hade da danna lock dinta yadda babu me iya bud'e ta sai shi, dama security door ce tunda duk abubuwan sa a dakin suke. Kallon yadda dakin yake a hargitse ya ajiye riga chan takalmi chan ga shi ya barbaza takardu a saman gadon sai system dinsa dake a kunne jone da wayar sa. Wuce ta yayi zuwa gaban gadon ya hau tattara kayan dake kai. Sauran kayan ta hau kwashe masa tana tayashi suka kwashe komai suka saka shi a muhallin sa yayi sauran sai computer kawai da wasu papers. Gadon ya haye yace tazo ta gani ta matsa gaban gadon ta tsaya tana leka system din. Dagowa yayi ya kalle ta yayi murmushi kawai yace "Zauna anan." Zama tayi tana kallon jikin system din ya cigaba da jujjuya mouse din ba tare da ta gane abinda yake ba, be dau lokaci yana yi ba ya tattara ya rufe ya dauki system din ya dora ta akan reading table dinsa ya jona ta jikin socket ya wuce toilet. Fitsari yayi ya sake wanke bakin sa da mouth wash sannan ya fito ya tarar da ita tsaye tana jiran ya fito ya bud'e mata ta tafi. Towel ya dauka ya goge fuskar sa tana tsayen ya dauki body spray ya fesawa jikinsa sannan yace ba tare da ya kalle ta ba "Cire Hijab din mana bakya jin zafi ne?" "Ai wai tafiya zan dama." Murmushi yayi gami da taune lips din k'asa ya girgiza kansa kawai yazo ya wuce ta ya kashe hasken dakin gaba daya. Kirjinta ne ya buga ta hau wara ido tana waigawa. Takowa yayi har inda take tsaye sannan ya riko ta gaba daya jikin sa ya zare mata Hijab din dake jikin ta ya jefa shi kan sofa, ya d'aga ta chak ya nufi kan gadon nasa da ita. "Taf..fiya fa zanyi." Tace cikin in da in da, ya dire ta a saman gadon sannan ya dora mata dukkan nauyin sa yana jin har sai da tayi yar Kara "Me yasa kike da tsoro ? Umm?" "Tsoro? Ni ba tsoro nake ji fa, tafiya zan." "Ba wani, ina ganin yadda idanun ki suke shigewa da tsoro, me nayi?" "Ba komai." "Ba wani, tsoro na kike ji bayan ni babu abinda nayi miki, infact nine ma ake wahalarwa da rayuwa dan an ganni bawan Allah babu ruwana." "Me nayi maka?" "Gashi nan, kinsan dai ai ba haka miji da mata suke rayuwa ba ko? Kina ji kina gani Ya Nabeela ta hanani ke, kamar ma dadi kike ji har wata kiba kikayi ta musamman." Ya taba saman wuyan ta zuwa saman kirjinta. "Ni Allah ba ruwana, yanzu fa wajen Ammy zanje." "Um um ni ba in da zaki. Anan zamu kwana Hydar suna k'asan babu abinda zai faru." "Toh d'aga ni." "Ina da nauyi ne?" Gid'a masa kai tayi "Haka zaki dinga daukata." Da sauri ta kalle shi, dan hasken da ya hasko daga corridor din wajen window ya bata damar ganin fuskar sa. Daga mata gira yayi sannan yace "Gwara ma ki saba da nauyin." Shiru tayi bata ce komai ba, ya dan sassauta yadda ya danne tan sannan ya mirgana gefen ta ya jawota ta dawo saman jikinsa gaba daya, yasa hannayen sa ya zagayo su ta saman bayan ta ya riketa da kyau. "Ke baki da wani nauyi, a haka zamuyi bacci. Goodnight." Yace yana rufe idon sa. Kwantar da kanta tayi a saman kirjinsa lamo tana sauraron heartbeat dinsa da take fita da dan sauri, dago kanta tayi daga kai da sauri da niyyar yi masa magana bakin sa da dama yake daidai saitin kan nata ya hadu da nata, cikin wani irin salo ya kama lips din nata ya shiga kissing dinta da sauri da sauri. Gwalalo ido tayi ganin yadda ya soma birkicewa, ya shiga hautsinata ta ko ina yana cigaba da kissing din nata, hannun sa dake jikinta ya shiga zazza gayawa a jikin ta yana bin ko ina da ko ina. Sosai ta kara tsorata domin yanayin sa na yau har ya fiye mata na kullum, da zafi zafi yake komai ya kuma k'asa tafiyar da ita a hankali kansa tsaye kawai domin da gaske ya kai karshe a hakuri, dama irin su ka kalle su kawai amma idan suka birkice maka zaka dauka basu bane ba. Cikin salon da yake mata da yafi karfin hankali da tunanin ta, taji shi sama sama yana kokarin aikata abinda kwakwalwa da gangar jikinta ba zasu iya dauka ba. Kuka ta fashe masa da karfi fiye da wanda take yi a dazun. Be ji ta ba kwata-kwata, ko da ma yaji ta toh ba zai iya fasa abinda zuciyar sa ke ingiza shi ba, duk kuwa da ya riga yayi ma kansa alkawarin har sai komai ya daidaita, amma ya k'asa, ya gaza hakurin. Muryar sa a matukar shake taji kamar yana karanto addu'ar da manzon Rahma ya koyar damu, anan hankalin ta yayi masifar tashi, ta tuna Ammy, Lamido d Hamma Hydar duk suna gidan, tabbas za'a yi abin kunya idan ta miye ma Aryan, amma kuma ya zatayi? Idan ta ki tabbas zata kware shi, amma kuma ba zata iya ba, hankalin ta ba zai iya daukar azabar da take ji ba, kuma ba zata iya daukar matsanciyar kunyar da zasu shiga ba. Daidai saitin kunnen sa ta shiga gaya masa "Ammy nah, dan Allah! kayi hakuri. Dan Allah zan mutu wallahi dan Allah, Wayyo hamma na." Sunan Ammyn ne ya shiga kunnen sa sosai, sai kuma tunanin suna cikin gidan ya fado masa. A wani irin yanayi ya zame jikin sa da sauri, ya mike kamar zai fadi ya nufi toilet ya sakar ma kansa ruwa idanun sa a rufe. Tashi tayi da sauri ta hau lalubar kayanta da yayi mata watsi dasu, da k'yar ta gano rigar tata a k'asan gadon ta saka, gaba daya jikinta wani irin ciwo yake mata da zafi. Bakin ta har wani zum yake saboda a zaba, tana jin karar ruwan a toilet din sai dai babu motsin sa ko kad'an, tasan ba abu bane me sauki a garesa ba, musamman tunda ta riga ya saka rai sosai.amma ya zatayi? Sakkowa tayi idon ta ya sauka akan wayar sa ta dauka ta dan haska tayi wajen kofar fita amma still ba zata iya budewa ba, hakura tayi ta dawo ta zauna akan sofar tana jiran ya fito. Ya dade sosai a ciki har sai da yaji ya dawo daidai sannan ya dauro alwala ya fito daure da towel, ya wuce ya dauki jallabiyar sa ya saka sannan ya dauki sallaya ya shinfida ya tada sallah. Tana zaune har ta gaji ganin bashi da niyyar tsayawa, sai kawai ta koma saman gadon ta kwanta tana curewa waje daya tana leka shi, har ta gaji bacci ya dauke ta. Ya dade akan abun sallar sannan ya nannade ya ajiye yazo daidai saitin kanta yana kallon ta cike da tausayawa. Allah ya rufa asiri da an yi abun kunya, shi kansa ba zai so hakan ta faru ba, yafi so daga shi sai ita yadda zai kula da ita sosai. Be san me ya hau kansa ba har ya kasa controlling kansa ya tafi haka da karfin sa. Kissing saman goshin ta yayi, ta sauke ajiyar zuciya a wahale, ya dan gyara mata kwanciyar ta shiga gadon sosai dan da a gefe take, sannan ya kwanta a dayan side din yana kallon innocent fuskarta. **RQ** 62 ***Da safen wuri Ya nabeela suka zo gidan ita da Khadija, lokacin raihana ko tashi ma batayi ba sai aryan din tare da su hydar a falo suna zaune suna magana. Ammyn ma bata tashi ba har lokacin baccin take yi. Zuwan su ne yasa ta tashi bayan yazo ya dan taba ta kadan ta tashi da sauri, murmushi ya sakar mata yana nuna mata agogon hannun sa dake nuna lokaci, sosai tayi mamaki dan bata dauka zata iya bacci har haka ba. A kunyace ta sakko ta wuce toilet din dakin shi kuma ya sakko kasa suka bishi da kallo Ya nabeela ta harare shi a wasance tace “Wai ina kanwata ne?” “Bacci take yi sai yanzu ta tashi.” Yace yana zama a gefen Hydar bayan ya zare hannayen sa dake zube a cikin aljihun dogon wandon shaddar sa da farar shirt da ta dan kamashi. “Ga breakfast chan toh na kawo muku, sai ku tashi nasan baku ci komai ba.” “Kamar kuwa Anty Kinsan yunwa muke ji.” Hydar yace yana dariya “Ya kukayi da Sadeeq din?” Aryan ya tambaya “Sun dauko hanya ai ma ai, babu available flight yau dole sai dai subi mota, Dadah ma nake tausayawa zaman motar dan kwana biyu tana complain din kafa sosai.” “Allah sarki, Allah ya Kawo su lafiya. Sai suke ji labari me dadi.” “Wallahi Anty, Alhamdulillah!” “Ina mutanen gidan ne?” Ammy tace tana budo kofar dakin da take bayan ta farka kusan mintuna goma kenan. Tashi sukayi dukkan su, suka karasa wajenta Lamido ya riko ta ganin kamar har yanzu da jiri a tare da ita, dakin ya maida ita suka shiga dukka shi kuma aryan ya dauki jakar Kayan raihana da Ya nabeela ta kawo mata ya haye saman. Wanka tayi tana tsaye tana tunanin kayan da zata saka bayan ta maida na jikinsa duk sai taji ta takura, ba zata iya zama da kayan ba dan ita a kaidar ta bata maimaita Kayan da ta saka sai an wanke. Turo kofar yayj ya dire jakar a tsakiyar dakin sannan yace “Ammy ta tashi, ki shirya ki sakko su Khadija suna jiran ki.” Da kai ta amsa ya juya ya jawo mata kofar ita kuma ta dauki kayan ta saka a gaggauce kin ammyn ta farka. Kasan ta sakko ta tarar da Ya nabeela da Khadija a falon bayan sun fito daga dakin duk sai taji kunya ta kamata ganin yadda suke kallon ta musamman Ya nabeela da take mata kallon tsaf kamar me shirin gano wani abu. A daddafe ta karaso tsakiyar falon tayi saurin dukawa kasa ta gaida Ya nabeelan da sauri tace “Tashi tashi daga kasa, ba’a zaman kasa musamman tiles din nan me shegen sanyi, yanzu sai sanyi ya shiga mutum.” Tashi tayi ta zauna a gefen Khadija suka gaisa sannan ta nufi dakin da ammyn take. Tana zaune Hydar na bata tea ta shiga, ta kalle ta kadan sai kuma ta cigaba da shan tea din har Raihanan ta karaso ciki ta zauna a gefen Ammyn suka sakata a tsakiya ita da hydar. Cup din ya mika mata sannan ya mike “Karasa bata sai tayi wanka time yana tafiya.” “Ok.” Tace ta shiga bata tea din tana sha a hankali tana ta kallon raihanan amma bata ce komai ba. Sai da ta gama bata tsaf sannan ta shiga toilet din ta hada mata ruwan wanka tazo ta taimaka mata ta kaita har toilet din ta nuna mata yadda zatayi sannan ta fito ta hau gyara dakin , ta gama ta fito mata da kayan da zata saka hade da Hijab sannan ta zauna ta jira ta fito ta kuma taimaka mata ta shirya sannan tace ta zauna tana zuwa. Wajen su Ya nabeela ta dawo Ya nabeela tace zata raka Khadija asibiti daga nan zata dauko su amna daga school amma zasu dawo da yamma. Sallama sukayi mata suka tafi dama ba kowa yan mazan sun shiga ciki shiryawa za’a kaita rijiyar lemo gidan malamin nan, shi kuma Aryan zai je Office yaga abinda ya kamata yayi kafin su dawo. A tare suka shirya suka fito harabar gidan aryan ya dauki karamar motar sa su kuma Malam Yahya ya dauke su suka wuce Rijiyar lemon shi kuma ya wuce Office. ****Kayan jikinsa yake so ya sauya zuwa na gida sannan yaje yaga abinda yake faruwa. Dukkan ranakun nan a cikin busy yake akn wani babban case da yake da yakinin zai kara daga darajar sa dan kuwa da kasan zuciyar sa yana jin zai iya barin aikin nasa nan kusa wanda yasan hakan bata yiwuwa a yanayin aikin nasu sai ka taka wani mataki. Familyn sa na bukatar sa a yanzu fiye da ko da yaushe, daga Baban nasa har Daddy suna bukatar Hutu a Halin yanzu domin dukkannin su girma ya kamasu sannan yasa aryan kadai ba zai iya cigaba da kula da companies din nasu shi daya ba, abubuwan zasuyi masa wahala at least Shima yana bukatar ya huta sosai ya fuskanci rayuwar sa da ta iyalin sa. Apartment dinsa ya koma ya shirya cikin kananan kaya marasa nauyi saboda yadda garin ya hade yake neman zubda ruwa. Direct in da aka ajiye Adam din da yaran sa ya wuce da knsa. Khadija ya kira yana driving ya saka wayar a jikin motar har ya isa suna waya sai da yayi parking sannan sukayi sallama ya fito ya kulle motar. Dakin da yasa aka ajiye su Adam ya wuce yana zuwa aka bude masa kofar ya shiga. Babu wadattacen haske a dakin amma yana iya hango Adam din a kwance a kasa gabansa da wani kwanon abinci. Shi kadai ne a dakin sauran yaran an maida su sashen masu kula da masu manyan laifuka domin an kamasu da laifin kidnapping, shigo da manyan makamai da amfani dasu wajen cutar al’umma. Ya daku sosai yayi likis dan dama yace kada su raga masa ko kadan domin yaron ya riga ya kaishi karshe shiyasa yasa suka masa liks ya zama ko mikewa baya iya yi sai jan ciki da yake yake karasawa dan gaban pit din dake hade da dakin idan zai yi bukata. Zarnin d dakin yake yi ya hana Kamal daurewa ya yayi saurin ficewa zuwa Office dinsa ya zauna ya rufe kofar sannan ya jona system dinsa mail din aryan ya shigo masa. Be duba mailbox dinsa ba tun kwana biyu saboda yayi busy dan haka ne yasa be san Aryan din ya turo masa ba, budewa yayi yana relaxing sosai akan kujerar sa ya shiga duba documents din zuwa video da yake attached da write up din. Yanayin yadda ya shigo Office din ya saka kowa shan jinin jikin sa, a daure tamau fuskar sa take be ko tsaya yayi attendance ba yayi wucewar sa Office ya bude ya shiga. Uwar iyayi zee tana zaune ta mike ta dauki files din dake ajiye a desk dinta ta nufi Office din duk kuwa da kallon kar ki je din da chomzy ta aikata mata amma tayi tafiyar ta bayan ta gyara jikinta. Knocking ta yi tana kara daidai ta fuskar ta, ya dago yana kallon kofar yasan babu me zuwa duk kuwa da yanayin da ya shigo sai zainab, yarinyar ta sakè da yawa zai yi maganin ta kuwa dan ya dawo aikin sosai kafin tafiyar tasu. Sakè kwankwasawa tayi a zafafe yace “Waye!!!” “Zainab ce Sir.” “Na neme ki?” “Mmm dama sir files din nan ne da mukayi magana jiya.” “Na saka ki kawo mjn ne?” “No sir na dauka zaka…” “Kije sai na neme ki da kaina.” Kamar an buge mata guiwa haka taji, ta waiga reception din taga duk ita suke kallo, gashi tasan ko basu ji abinda suka ce ba zasu gane korar da yayi, kamar kasa ta tsage ta shige ciki haka taji, ta rasa ma ya zatayi, tunowa da tayi da toilet a chan gaba sai kawai ta wuce, taji sanda chomzy da Ali da Fadila suka kwashe da dariya, ta kuma san ita suke wa dariyar.kuka ta fashe dashi a toilet din kukan takaici, ga wata zazzafar soyayya da take masa amma ya kasa ganewa. Sai da tayi kukan ta gama ta wanko fuskar ta fito ta koma Seat din ta, ta bude jakar ta, ta shafa powder da janbaki sannan ta rataya jakar ta fice ba tare da ta ce ma kowa komai ba. 10mint da tafiyar ta ya kira reception din Ali ya daga yace ya karbi file a wajen Zainab ya kawo mishi office. “Ta fita sir.” “Ta fita!? Ina taje?” “Bamu sani ba, ta fita dai cikin fushi.” “Check her table ka kawo min files din.” “Ok sir.” Ya ajiye wayar. Bama ta da hankali, idan kuwa haka zatayi zai iya bata suspension taje chan tayi ta haukanta. ****Ba kamar karon farko da akayi ma ammyn addua ba, wannan karon abun ya dasu zafi sosai domin ashe duk suna nan babu wanda ya tafi, dama malam din yayi tunanin hakan shiyasa wannan karon yaki raga musu sam, ya dinga ragargazar su da ruwan addua da ayoyin Allah suna gunjin kuka sosai, sai da ya tabbatar yayi musu babbar illah, sannan ya nemi su fice su barta bari na har abadah. “Ina zamu? Ka riga ka kone mu.” “Ku koma chan wajen wadda ta turo ku.” Ya basu amsa yana Kara daga ruwan zai sakè shekawa, ihu suka saka sai kuma ammyn ta hau attishawa ba kakkautawa tana wata irin mimmikewa tsawon lokaci tana a haka kafin a hankali ta shiga sauke ajiye zuciya. Duk yadda raihana taso boye kukanta, ta kasa kuka take sosai kamar zata shide, kukan tausayin zaluncin da akayi ma ammyn. Kallon ta hydar yayi yace ko zata je waje? Malamin yace a barta itama akwai bukata a duba ta, haka akayi kuwa itama aka yi mata amma ita babu komai. “Kina azkar ko?” Ya tambaye ta. “Inayi malam.” “Masha Allah, ki cigaba Karki daina, azkar tsari ne sosai amma sai wanda ya gane, ita kanta mahaifiyar ku da bata addua da abin sai yafi haka, domin so akayi a haukata ta, ta shiga duniya karshe ta mutu irin wannan mutuwa ta wulakanta, amma karfin addua da azkar din da take ya sa ta tsallake wasu tuggun, dan haka ku dage da azkar kamar yadda manzon Allah SAW ya koyar damu, in sha Allahu babu wani mutum ko aljan da zai samu damar cutar daku.” “In sha Allahu Malam, mun gode sosai Allah ya saka da Alkhaiiri.” “Amin ya Allah, zaku cigaba da kawota yanzu duk Asabar da lahadi muna cigaba da yi har sai mun samu ta samu lafiya gaba daya.” “In sha Allah, mun gode.” Sallama sukayi ma malam din suka shigo mota da ammyn da tayi shiru bata ce komai ba sai kanta da ta rike da yake mata wani irin ciwo. Dafa mata kan raihana tayi ta shiga yi mata addua tana tofa mata, sai kuma ta jawo kanta ta dora a saman cinyar ta, ta cigaba da matsa mata kan a hankali. ***RQ*** **63** *****Har suka isa gida babu wanda ya sake daga maganar da Malam din yayi, dukkannin su kowa da abinda yake sakawa a ransa. Sau daya Hydar yayi magana bayan ya daga wayar Babbo daga nan kowa yayi shiru. Daki Raihana ta wuce da ita suna zuwa ta kwanta saboda ciwon kan a hankali kuma sai bacci ya soma daukar ta, gyara mata kwanciyar yadda zata ji dadi raihana tayi sannan ta dan karo mata ac dakin ganin tana zufa ta goshi sannan ta jawo mata kofar dakin ta dawo falon. Shirun da taji yasa ta gane sun fice daga gidan sai ta fara tunanin abinda ya kamata tayi musamman dasu Dadah zasu zo ya kamata tayi girki ba sai Ya nabeela ta kawo ba. Kitchen din ta wuce ta duba abinda zata bukata babu kayan miya sai kayan abincin a store kawai. Mayafin ta, ta yafa ta fito zuwa bq sai taga malam Yahya tare da baba maigadin yana ganin ta fito ya taso da sauri. “Hajjaju Kina bukatar wani abu ne?” “Eh malam Yahya, wai da cefene nake so ayi mana.” “Sai naje ai, me ake bukata?” “Kayan miya.” “Toh ba damuwa, zaa samo hajjaju.” Kudin da ta dauka ta mika masa yace “A ah Oga zai bada kudin ai, kiran sa kawai zan.” “Toh,Nagode.” Ta juya zuwa bq su gaisa da Hajara shi kuma ya dauki mota ya fita. Sai da ya isa kasuwar sannan ya kira Aryan din ya sanar dashi yazo cefene. “Wa yace ayi cefene?” “Hajiya ce, ta bada kudin ma nace ta barshi zan gaya maka.” “Ok, ka siya duk abubuwan da muka saba siya, zan tura maka kudin sai a siya.” “Ok gani ma a kasuwar.” “Ok! Bari na saka maka.” Ya ajiye wayar ya tura masa kudin ya siyi komai da komai har abubuwan da raihanan bata ma san suna existing ba ya kai mata. Mamaki ne ya kusan kashe ta ganin uban kaya kamar zasu dawwama a gidan. Ta riga ta dafa white rice tuni dama sai kawai ta hada kayan miyan da chicken tayi stew ta hada musu hadin salad 🥗 me salad cream ,baked beans da egg. Ta gama ta dora su akan dinning sannan ta sake komawa ta duba Ammy still tana bacci. Dawowa falon tayi ta zauna shiru har aka kira laasar sannan ta tashi ta yi alwala tazo ta yi sallah a falon tana idarwa sai gasu Ya nabeela sun dawo. Dadi taji domin zaman dama ya isheta shiru ita kadai. Abinci ta kawo musu suka ci suna hira itama sai a lokacin ta dan ci kadan sannan ta koma kitchen din ta dora ruwa ta dafa spaghetti dan ba lallai kuma rice din ta ishi kowa da kowa ba, ta dora kenan Ammy ta tashi sai ta tafi wajenta ta barwa khadija ta karasa mata. A zaune ta samu ammyn tayi wanka tana gyara daurin dan kwalin kanta, mamaki Ya kama raihanan ta karasa da sauri wajenta ta tabbatar da abinda idanun ta suke gani. “Menene kike kallo na haka auta?” “Ammy? Kin sanni? Kin ganini dama?” “Kaji min yarinya, ni kike tambaya ko na gane ki? Tabbin jam.” “Wayyo dadi, wallahi ammy na zata kin manta ni, dan Allah ammyna kin tuna ni?” “Ikon Allah, kin taba ganin uwar da ta haifi da ta manta shi? Duk girman da zakiyi auta ba zan manta ki ba, duk kuwa da shekarun da yawa amma ke din dai kece.” Rungume ta tayi tana kyalkyalewa da dariya, sai kuma ta d’ago cikin tsananin farin ciki tace “Sannu Ammy, kan naki Ya daina ciwo?” “Um da sauki, sai a hankali. Ina yayannaki, banga Abubakar ba, Allah yasa yana raye.” “Kowa yana nan ammy, Abby, Dadah, babbo da su Hamma na, duk suna nan, su Dadah ma daf suke da karaso wa.” “Masha Allah, ashe ina da rabon sake ganin su dama?” “Kwarai da gaske, al’amarin Allah!” “Lallai kuwa al’amarin Allah, Alhamdulillah Allah shine abun godiya.” “Wallhi ammy.” “Ina Aryan? Ina Nabeela?” “Shi ya fita, Ya nabeela tana falo.” “Tashi muje falon toh.” Ta mike tsaye, rike hannun ta Raihana tayi har sun kai kofa sai kuma ta tsaya “Auta, nan gidan waye?” Kallon ta Raihana tayi da sauri, sai kuma tace “Gidan Ya Aryan ne.” “Duk da sauye sauyen da gidan ya samu, be chanja min ba ko kadan daga yadda na sanshi.” Sai idon ta ya cicciko gaba daya. “Muje kiga su Ya nabeela .” Tace tana jan hannun nata, suka fito falon. Da sauri Ya nabeela ta taso ta tare ammyn a hanya ta karaso da ita falon suka zauna tana kallon ta “Nabeela ta, kece kika sauya haka?” “Nice ammy.” “Masha Allah, Allah abun godiya.” “Ina wuni ammy? Ya jikin kuma?” “Alhmadulillah, an gode wa Allah. Sannun ku da kokari Kunji? Allah ya saka da allhairi.” “Amin Ammy.” “Ina maigidan naki ina yaran?” “Duk lafiya kalou, yaran sun tafi islamiyya.” “Masha Allah, Allah Ya raya su. Zan ga jikokina ashe, Masha Allah.” Yadda ammyn take furucin kasan zuciyar ta a karye take, dauriya ce kawai amma ji take kamar ta fashe da kuka, musamman idan ta kalli yadda Raihanan ta, ta girma sosai, ba a gaban idon ta ba, sai dai a yadda ta ga yanayin su dukka suna cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali. Hakn ya sakata kwantar da hankalin ta. Abinci Raihana ta zuba mata taci, tana cin su Hydar suka shigo tare da Dadah, Abby da Babbo Sadeeq, Adda maimuna da Muhammad da Amina. Nan fa falon Ya kaure da murna Dadah ta rungume Ammyn a jikinta suka fashe da kuka me cin rai, Abby kuwa kamar an dasa shi a wajen idanun yaran da kasantuwar Dadah a wajen ya hanashi zuwa ya rungume matar tashi, sai kallon ta kawai yake, tana nan da kurciyar ta da kyan jikinta da ya santa dashi, sai da suka nutsu sannan sai Dadah ta tuno da Abby yana falon. Sai kuma duk kunya ta kamata, suka shige daki baki daya har su Ya nabeela suka bar ammyn a falo tare da Abbyn. “Aisha!” Ya kira sunan ta cikin wani yanayi na son gasgata abinda yake gani din. “Naam.” “Ashe rai kan ga rai? Ya Allahu ya rahmanu, nayi bakin ciki nayi kuka da na samu labarin babu ke, nayi tunanin yadda rayuwar yaran nan zata kasance babu mu dukkan mu, sai Allah ya nuna mana ikon sa, na gane ba wayon mu ko dabarar mu bace, komai da kowa yana karkashin kulawa da ikon Azza wa zalla.” “Haka ne, ni kaina nayi mamaki yadda yaran suka zama. Alhamdulillah!” “Alhamdulillah, Allah ya duba mu, yayi mana abinda bamu taba zato ba, duk kuwa da zaluncin da akayi mana. Wannan kadai be isa mutum ishara ba?” “Ya isa!” “Ya bayan rabuwa?” “Alhamdulillah! Abinda kawai zan iya cewa kenan.” “Toh Alhamdulillah! Alhamdulillah!” Yace yana murmushi. Murmushi tayi itama, ta kasa misalta abinda take ji a zuciyar ta! ***Ya dade sosai a Office din sai da ya tabbatar ya kusan gama komai sannan ya raba sabbin mukamai wadanda yake tunanin zasu iya kula da company idan baya nan. Yaso ya saka zainab dan tasan Aiki sosai amma kuma yana so ya fara nuna mata matsayin sa domin be yi sanyin da har zata fice tayi tafiyar ta haka kawai ba. Wake ya fito rike da takardar ya tara su a dakin da suke yin meeting baki dayan su sannan ya shiga yi musu bayanin sabbin mukaman na rikon kwarya daya bayan daya, sai da ya gama dasu sannan ya bar office din ya wuce side din da Adam yake kula dashi nan ma yayi irin abinda yayi a dayan sannan ya bar office din gaba daya. Office dinsa ya wuce ya shigar da abubuwan da zai shigar ya gama ya fito sai ga kiran Lawwali. Parking yayi a gefen hanya ya daga wayar da sauri amma sai yaji muryar sa a dan tashe “Ya akayi Lawan?” “Akwai matsala alhaji, matar nan ce take ta hauka da ife ife wallahi, tamkar ma ta zare ne ko menene wallahi bamu sani ba mun samu mun dai rufe ta a daki amma muna ji yadda take hauka tsaf zata iya balle kofar.” “Subhanallahi! Me ya sameta?” “Wallhi Allah bamu sani ba, bayan mun dauki maganar nan ta jiya bata ko nemi fitowa ba saboda tsoro, yau dai Ladi ta je ta kai mata abin kari da safe har sunyi magana ma, dazu kuma kawai ina kwance dakin zaure naji wani irin ihu, na taso da gudu na shigo gidan kawai sai ganin ta nayi suna kokawa da Ladi har ta shake Ladin tana kakari.” “Yanzu zaku iya kula da ita zuwa safiya? Zaku iya?” “Toh wallhi abun ne akwai tsoro, ina jin yanzu haka yadda take kokarin bude kofar, idan muka bari ta bude zata fice ne.” “Kuma kuna ganin ba pretending take ba?” “Naam?” “Oh sorry, kuna ganin ba karya take ba?” Idan lafiya lafiya, bata isa taja da Ladi ba.” “Toh kuyi kokarin kula da ita, zan yi kokari na shigo gobe da safe in sha Allah, tunda mun samu abinda muke so cigaba da rike tan ma babu wani amfani.” “Toh shikenan, Allah ya kaimu.” “Amin, idan wani abu ya taso ka sanar dani kuma. “ “In sha Allah, Nagode.” “Nima Nagode.” Be tashi motar ba yayi shiru yana tunanin abinda yake faruwa, ganin ba zai samu amsar tunanin sa ba yasa shi hakura ya tada motar ya dauki hanyar main house dinsu. A waje yayi parking ya dan abu kawai zai dauka ya wuce, ya kashe motar ya fito ya nufi gate din, kafin ya karasa yaji alamun taku a bayan sa, 🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹 **RQ** Page 64 ***Juyowa yayi da sauri sai ji yayi an kwala masa abu akan sa, kara yayi wadda ta jawo hankalin gateman din yayi saurin fitowa a daidai lokacin da wanda ya kwala masa abun ya ruga da mugun gudu, bin sa gateman din yayj amma kfin ya cimmasa ya haye wani machine suka bar layin, da gudu ya dawo wajen da Aryan din yake rike da kan nasa da yake fidda jini sosai,rike shi yayi da sauri ganin jira na neman kayar dashi ya shiga dashi cikin gidan da gaggawa, tasowa su Bob sukayi da gudu suka tare su, suka taimaka masa aka saka shi a mota Malam yahya da Bob suka dauke shi zuwa asibiti dan tuni har idanun sa sun rufe ruf. Asibitin da suka saba zuwa suka je suna zuwa drs suka karbe shi direct suka wuce dashi theater room aaka shiga kokarin tsaida jinin sannan aga yanayin wound din da yake kan. Sosai suka same shi domin sun fasa masa kan mummunar fasawa kuma ya zubda jini sosai ba kadan ba, dressing wajen akyi masa bayan an masa alluran rage Zafin ciwon sannan aka tura shi zuwa dakin da za’a kwantar dashi. Sanda suka zo asibitin Dr Mahfouz baya nan yaje duba ammy, dawowar sa asibitinn kenan ya tarar da abinda Ya faru da Aryan din, zuwa yayi ya duba shi duk da har lokacin be farfado ba sannan ya fito ya koma gefe ya kira Kamal dan sanar dashi abinda yake faruwa tunda Alhaji baya gari. Ganin kiran Dr Mahfouz yasa Kamal ya dakata d abinda yake yi domin yasa magana ce me muhimman ci zai yi masa. Da sallama ya daga wayar suka gaisa a mutunce sannan yace “Sir kana gari ne ko kana wajen aiki?” “Ina wajen Aiki Dr, akwai abinda ake bukata ne?” “Eh toh, dama Aryan ne!” Tsaye ya mike chak cikin yanayin tsoro yace “Me ya samu Aryan din?” “I think thugs ne suka yi masa rauni akai, wanda yayi sanadiyyar sun ji masa deep wound a kan masa…” Da sauri ya katse “Yaushe? Aina? Garin yaya? Subhanallahi!” “Yanzu aka fito dashi an samu nasarar tsaida jinin kuma he’s stable now, but akwai bukatar ayi masa scan domin mu gano how deep ciwon yake.” “Yanzu kenan abun ya faru? Waye ya kawo shi asibitin?” “Daga gida ne kamar, naga driver da wani, but su chan gidan nasa I don’t think sun san me yake faruwa, cox daga chan nake na duba Hajiya Aisha, and banji wani magana akai ba.” “Basu sani ba, ya Allah! Shikenan Nagode Dr, za’a zo daga gidan yanzu, duk abinda ya kamata ayi kawai, zan shigo gobe in sha Allah.” “Ok ba damuwa.” Zagaye dakin Kamal ya dinga yi hankali a tashe, ya ma rasa abinda zai yi, wa zai kira wa zai gayawa? Baya so hankalin raihana ya tashi amma dole ne a sanar da Ita, amma ba yau ba, sai dai zuwa safiya Kila ya farfado lokacin. Lamido ya yanke shawarar kira kawai, lokaci suna tare dukkan su a falon suna hirar yaushe gamo, Dadah da Raihana suna daki suna hirar su suma Amma rabin hankalin raihanan na wajen Aryan musamman da taji shirun yayi yawa, lokaci lokaci tana duba wayar ta tana ganin time. Ganin dai shiru jiran ba zai yiwu ba sai ta fito da niyyar kawo ma su Ammy ruwa ta shiga kitchen ta kira shi amma no answer, dauko ruwan tayi da juice ta fito a daidai lokacin abby na cewa zai tafi hotel ya kwana ba zai kwana a gidan nan ba, Lamido ma yana cewa shima daga chan zai wuce da asuba zai koma wajen aiki,ajiye ruwan tayi ta koma kitchen din ta dauko cups Kamal ya kira Lamido, suka gaisa sannan ya sanar dashi abinda yake faruwa, “Subhanallahi, yaushe hakan ta faru? Yanzu ina Aryan din?” Tsayawa tayi chak bata karasa kitchen din ba jin an ambaci sunan Aryan, “Ok ok, Yanzu zamu je in sha Allah, Allah ya bashi lafiya.” Ji tayi kafarta na neman janta zuwa kasa, da sauri ta dafe kitchen din tsoro na shigar ta, menene ya same shi? “Wai wasu wanda ba’a san su waye bane suka kwala masa abu a Kansa,Yanzu haka yana asibiti ma.” “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, toh Subhanallahi, abinda ya samu Aryan din kenan? Allah sarki Shiyasa shiru be dawo ba ina taso na tambaya .” Ammy tace cike da alhini. “Yaron nan yana bani tausyai, wallahi yasha wahala sosai ya kamata ace zuwa Yanzu ya huta.” “Hutun ya zo ma Abby in sha Allah! Sadeeq, Hydar ku tashi muje.” “Nima dole zanje ai, muje tare.” Abby ya mike dan be ga zaman me zaiyi ha kuma. “Ku duba shi dan Allah, Allah dai yasa ba Wani serious abu bane.” “Toh Amin, amma yadda naji muryar Kamal.” “Dan Allah Hamma Nima zan je.” Raihana da ta fada kamar wadda aka tunkudo basu ji zuwan ta ba sam sai maganar ta. “Auta ki barsu suje kinji.” “A ah Ammy,mace da mijinta a hanata zuwa ganin shi? Dauko hijab dinki.” Kallon Ammy tayi itama sai ta kalle ta, sai kuma Wasu ahubuwan suka shiga dawo mata a dan zaman da tayi dasu na kwana biyu, babu wanda ma ya tabo maganar auren raihanan tunda suka zauna. Kasa magana tayi har raihana taje ta dauko Hijab dinta tabi bayansu da sauri Dadah ta biyo bayanta tana bata baki. Suna fita ammy ta kalli Dadah “Dama auta an mata aure Dadah!” “Eh, an mata wallahi, babu wanda yayi miki magana r ko? Abubuwa ne da yawa sai a rasa abinda ma zaa fada, sai a hankali komai zai dawo daidai.” “Ikon Allah, lallai shekaru sun ja.” “Kwarai d gaske, sai dai muyi fatan gamawa lafiya.” “Tafiya zamuyi Dadah, gwara na koma gidan Maimuna akan na zauna anan, ashe nan din gidan su ne, jaira dana tambaye ta sai cewa tayi gidan sa ne?” “Toh zata ce miki an min aure ne ammy?” “A ah, da Amma ai sai ta bani haske, mu jira su dawo gaskiya gwara na koma chan, ba zan kara kwana anan ba.” “Toh mu jira su din, Allah yasa yaron kalou yake, yaro me hankali da nutsuwa kai.” “In sha Allah zai samu lafiya.” ****Kuka take a boye a motar Hydar na jinta tunda shine a kusa da ita, tabo ta yayi ta kalle shi Ya girgiza mata kai, cikin kasa da murya yace “Ki daina kuka.” Share hawayen tayi da bayan hannun ta Amma still wani yana sakè zubowa, tsoron ta daya kar wani abu ya same shi, bata san yadda zatayi da rayuwar ta ba. Ko da suka isa asibitin tsoronta karuwa yayi har sai suka shiga dakin da yake, drip ne a hannun sa yana kwance sambal sai dan jinin da ya bata masa jikin rigar sa kadan sai ciwon dake kansa. A baya ta tsaya tana cigaba da kukan har suka gama duba shi suka fita zuwa wajen Dr. Karasawa tayi gaban kujerar dake gaban gadon ta zauna tana kallon fuskar sa da tayi ja sosai, hannun ta tasa ta gyara masa hannun da drip din yake jiki yadda zai dinga shiga sosai kamar ya dan taba shi, sannan ta goge masa gefen bakin sa tana cigaba da hawayen. Tana zaune suka dawo dakin ta tashi ta matsa gefe Dr Mahfouz ya sake duba shi sannan yace zai tashi zuwa safiya Amma dole sai an zauna an kula dashi da duk moves dinsa kafin safiyar idan an ga wani unusual abu a kira nurse. “Tunda ga amarya ma ai nasan zata kula dashi sosai.” Ya kara she maganar da sigar tsokana tana kallon raihanan “Ko Hydar ya zauna.” Lamido yace, “No a bar matar sa, zata kula dashi ai.” Abby yace yana matsawa wajen kofa, “Toh amarya sai d safe, ki kula dashi sosai please, duk da dai nasan va ma sai an fada va.” “Muma tafiyar zamuyi, sai da safe Kanwata, Allah ya bashi lafiya.” Lamido yace sannan ya fita, sallama Abby sukayi mata da Hamma hydar Abby yace tasa Key a kofar karta barta a bude sannan suka tafi. Locking kofar tayi ta dawo ta zauna a gabansa tana kallon sa, ta dade a zaune sai ta mike ta shiga toilet din dake jikin dakin tayo alwala ta hau kan dan madaidacin carpet din dake dakin ta dora dan kwalin ta akai ta tada sallah, isha tayi sannan tayi shafai da wutri tayi masa addua sosai sannan ta zauna jigum tana kallon sa daga in da take zaunen. Yadda taga rana haka ta kusan ganin daren domin ko bacci barawo be iya sace ta ba, sau biyu yana motsa wa idan ta rike hannun sa sai ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da baccin. Daf da za’a kira asubah ta sakè yo alwala tazo tayi raka’atanul fajri sannan ta hau saman sofa din ta dan kwanta tana facing din gadon nasa. Da safe gateman ya fito sai yaga karamar waya a kasa, hannu yasa Ya dauka ya kunna ta, sai wani tunani yazo masa, ko dai wayar wanda ya kwala wa Aryan abu ne? Ciki ya koma ya dauki wayar sa ya kira Kamal lokacin har ya dauko hanya ma, ya sanar dashi abinda ya cinta, ajiye ta yace yayi sannan sukayi sallama. Wajen bakwai da rabi Ya nabeela ta iso hankalin ta a tashe, sai a lokacin Kamal ya fada mata aikuwa tasha kuka tun kafin ta karaso tana zuwa ta rungume Raihana kafin ta karasa tana kallon yadda ya sauya a lokaci daya “Ba zai yiwu ba, kuzo ku bar kasar nan raihana, rayuwar shi suke nema gwara ku tafi, zan kira Daddyyanzu,nasan Ya samu sauki sosai gwara ya dawo kawai, ayi muku Emergency Visa ku tafi, wannan masifar har ina?” “Su waye suka yi masa hakan ?” “Ban sani ba Raihana, amma Kamal yana hanya, zai kuma binciko ko su waye, kuma sai sun fuskanci hukunci. Amma tabbas ba zaku zauna ba, gwara ku tafi kafin su kassara shi, gashi da naci da kafiya idan ba tafiya yayi ba Shima ba hakura zai ba.” “Allah ya bashi lafiya.” “Amin Amin, Dr din sun shigo?” “Wata nurse ta shigo da asubah, tace Dr Mahfouz zai shigo anjima kadan.” “Ok.” Ta zauna akan sofa din tana ciro wayar ta dan kiran Daddy din. . * *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾😂😂😂 ***RQ*** 65 ***Ta jikin tagar dakin Ladi ta zura kanta ta leka, tana tsaye a tsakiyar dakin duk ta yaga kayan jikinta kanta a barbaje tana ta jansa da karfi sai ta cizge shi, gwalalo ido Ladi tayi cikin tsoro ta juya ta samu Lawwali a dakin zaure zaune yayi tsuru dan baya jin zasu samu damar yin bacci a ranar. “Gashin kanta take cizgewa fa.” Tace masa tana rike hab’a cikin alajabi “Akwai matsala ,Allah yasa ba abinda ta dade tana aikatawa bane ba ya dawo kanta.” “Shi din ne ma, karshen shegiya ne yazo, mummunan karshe dan daga gani haukan nata babban ne, Allah yasa ba na yawo bane tsirara Innalillah.” “Yanzu ya zamuyi? Na kira shi dai yace zai shigo da safe.” Kafin ta bada amsa sai ihun balle kofar suka ji, sannan suka ji har ta fito tsakar gidan. Kusan gware sukayi da Ladi da Lawwali wajen fita daga gidan gaba daya, dan sun tabbatar ta zo ta cimmasu zata iya lahanta su. Suna fita ta karaso zauren a guje tana ife ife, tayo waje duk da duhun da garin yayi, ta yi gaba kawai tana tafe tana ihu da surutai tana jan gashin kanta, kusan minti goma suna labe jikin wata danga, sai da suka ji shiru suka fito zuwa lokacin tayi nisa ma, dan kamar iska haka suke kada ta, hanyar suka dan bi Lawwali na haska musu touch light dinsa amma babu alamun ta, dawowa sukayi kawai suka koma cikin gidan suka kulle cike da tsoron kar ta dawo musu cikin dare. Gajeren bacci suka yi a daren ranar da sun ji motsi sai su fito. Da gari yayi shaa suka dan sake fita neman ta tare da Malam sani Amma babu wani alamun ta ko in da tayi, dan ko sahun kafafunta babu a hanyar sam. “Ko dauke ta sukayi?” Ladi tace “Wa ya sani ne,lallai sharri dan aike ne, kuma komai daren dadewa sai ya dawo duk kuwa in da ka aike shi, ji sakayyar Allah.” “Yanzu menene abun yi?” “Mu jira zuwan sa, duk abinda ma ya kamata ayi idan yazo din sai ayi.” “Toh, Allah yasa ma ta tafi kenan, shegiyar mata jiya da ta shake ni wallahi na hango lahira, kai nasha azaba ba kadan ba.” “Ai karfi ne dasu.” “Naga alama.” Juyawa sukayi suka koma gidan suna tattauna abinda ya farun. *****Tashi tayi ta fita bayan sun yi magana da Daddy, tayi dana sanin fada masa abinda ya faru da Aryan din dan ya rikice sosai sai da ta kwantar da hankalin sa sannan ya hakura yace ta hada shi da Mahfouz din, a office ta same shi yana dora labcoat dinsa akan kayan sa, zai taho dakin Aryan din. Gaisawa sukayi ya tambaye ta me jiki sannan tace “Daddy ne zakuyi magana , bari na kirashi.” “Ok.” Ya zauna akan kujerar sa ta kira Daddy din ta bashi sukayi magana,yayi masa bayanin abinda ya faru. “Muna tunanin going for MRI or CT scan muga ko akwai internal injury ko bleeding.” Ya karkare bayanin “Wanne zaifi?” “CT scan is faster that MRI, but za dai mu duba tare da colleagues dina muga abinda zaifi.” “Please just do the needful Dr, zan fara ganin yadda za’a yi processing komai within a week, sai su wuce, na dade dama Ina binsa yazo ya samu doctors anan musamman akan severe headache din nan nasa.” “In sha Allah zamuyi iya kokarin mu kafin su wuce din.” “Nagode Dr, thank you very much.” “You are welcome sir.” “He’s so worried, naji a muryar sa.” Yace ma Ya Nabeela yana mika mata wayar “Nayi regretting sanar dashi nima.” “No dole ne ai, but in sha Allah ba wani serious case bane da zai fi karfin mu, dan dai yana so su tafi din ne kawai, but anan ma we can handle it.” “Dama da akwai plan din tafiyar tasu, suje ya huta sosai abubuwan sun yi yawa.” “Haka ne, nasha fada masa nima yana bukatar hutu, ko maganin sa baya samu yana sha yadda ya kamata, Shiyasa har bugun ma ya samu tasiri sosai akan sa.” “Yanzu tunda yana da mata dole ta sashi ya sha ko baya so.” “Yes zata sashi, bari na ga Dr Fredrick sai mu shigo dakin nasa.” “Ok Dr, mun gode.” Ta tashi ta fita. Ammy da Dadah sun karaso asibitin sun duba shi sai suka fito waje suka zauna duk da dakin babba ne kuma vip ne, zuwa Ya nabeela tayi suka gaisa suka yi mata ya mai jiki sannan ta shiga dakin. Raihana na zaune a gabansa, hannun sa cikin nata ya rike ta kam tun dazu tana so ta tashi amma bata so ta zare hannun sai ta hakura kawai ta zauna a gaban gadon tana gadin sa. Ya nabeela na shigowa tayi saurin cewa “Ya rike min hannun ya hanani tashi.” “Me Ya faru Raihana? Kunya ta kike ji ko? Karki ji komai Aryan yana bukatar kulawar ki fiye da kowa a yanzu, take good care of your husband kinji? don’t be shy.” Nodding kanta tayi tana sakè yin kasa da kanta “Tafiya zakuyi, za’a yi masa scan aga komai daga nan zaku bi daddy New Zealand.” “Ok.” Tace a hankali “Bari naje wajen su Ammy.” Juyawa tayi suka yi kichibis da su Dr Mahfouz, ta matsa musu hanyar suka shigo ta fice ita kuma “Madam ya patient dina?” Dr Mahfouz ya tambaye ta yana kallon drip din hannun Aryan din “Alhamdulillah,ina kwana?” “Lafiya lou, wanne ne drip na nawa da aka saka masa.” “Uku, tace idan ya kare ba zaa saka wani ba.” “Ok.” Ya taba gefen wuyan Aryan din “He looks stable akan jiya, I hope he regain his consciousness very soon.” “In sha Allah.” “Dr Ahmad me kake gani?” “I think we should go for the CT scan din.” “Ok, Madam wannan shine Dr ahmad, head neurologist na kano gaba daya, zamu yi ma oga scan na kai saboda mu san iya in da ya samu injury, ba wai wani babban abu bane as baya ma daukar wani babban time,.” “Ok, Allah ya bada sa’ah, ya bashi lafiya.” “Amjn ya Allah, zasu zo su tafi dashi.” “Ok, mun gode Dr.” “Yawwa.” Suka fita, ta dawo wajen zaman ta. Ta sakè rike hannun nasa tana kallon sa a marairaice, hawaye ne taji yana zubo mata ta yi saurin share wa bata so wani ya shigo ya ganta, Amma har ga Allah zuciyar ta a kusa take, ji take kamar ta zauna tayi ta kuka, daga wannan sai wannan su kenan? Shigowa nurses din da zasu tafi da Aryan din sukayi, tayi saurin mikewa tana goge fuskar ta, suka dora shi akan gadon da zasu tura shi suka fita dashi. Da sauri ta shige toilet ta rufe ta shiga rera kuka yadda ba zaa ji ta ba. Ammy ce ta biyo ta cikin jin bata fito ba, bata dakin ta karasa kofar toilet din ta kwankwasa “Auta?” “Umm!” “Ok Kina ciki.” “Umm.” Ta sakè cewa dan bata so tayi magana ammyn ta gane kuka take. Fuskar ta, tayi saurin wankewa sannan ta fito tana goge fuskar. Kallo daya ammy tayi mata tasan kuka tayi “Addua zaki masa auta, ba kuka ba.” Ai kmar wadda take jiran kiris sai ta sakè rushewa da kukan ta fada jikin ammyn, a kalla yanzu itama kamar sauran masu iyaye ne, zata yi kuka a jikin mahaifiyar ta har ta rarrasheta. “Ya isa toh, kar kizo ciwo Ya kamaki kema, ki kwantar da hankalin ki kinji? Zai samu sauki in sha Allah.” “Babu abinda zai same shi ko Ammy? Ya sha wahala sosai wallahi, shine kuma ya gano in da kike yayi risking life dinshi for my happiness, bana so wani abu ya same shi.” “Babu abinda zai same shi, amma sai kin daina kuka, kin zama strong kinji? Kiyi masa Addua.” Gid’a kanta tayi, ammyn ta share mata hawayen ta sata sakè wanko fuskar ta goge ta sannan suka fito wajen da su Ya nabeela da Dadah suke zaune. ****Ba karamin gudu yayi ba, har Allah ya sa ya iso lafiya, shi kansa be san ya iya taka mota haka ba sai ranar, sanda ya iso an shiga dashi scan din, gaisawa sukayi da kowa Ya nabeela ta taso suka shiga ciki ganin yadda idanun sa suka yi ja babu walwala ko kadan a tattare dashi “Kamal, ka ganka kuwa?” “Na gaji ne Ya nabeela, hakuri na Ya kare, an kaini karshe wallahi.” “Na sani, but dole mu zama strong, for Aryan, yana bukatar mu a wannan lokacin.” “An samu wayar daya daga cikin yan iskan, tana mota na zan wuce station zan duba ta, duk ma wanda yake da hannu akai wallahi ba zan kyale shi ba, idan akwai abu da ake bukata call me please.” “Ok, best of luck Kanina, babu labarin Hajiya?” “Babu, and I don’t care tana Ina ma yanzu, I hope ko a ina take tana cikin bakar wahala.” “Amin, Allah yasa.” “Bari naje, call me please.” “Khadija fa?” “Bata ma san ma shigo ba, zan kirata idan na natsu.” “Ok, sai ka dawo.” Bayan kamar minti talatin aka dawo dashi dakin nasa, lokacin ammy da Dadah sun je gida saboda kan Ammyn dake mata ciwo, Ya nabeela ce sai khadija da tazo bayan Kamal ya kirata ya fada mata, akwai matar Kanin Daddy dai da tazo duba shi ta kawo abincj bata ma jira an fito dashi ba ta tafi, su kuwa dama dangin maman su ba damuwa sukayi da sabgar su ba dan babu ruwan su dasu. Shiga dakin sukayi suka zauna tare da Raihanan duk sukayi jigum har kusan azahar sannan ya fara motsawa yana son farkawa. Kansa Ya nabeela ta tsaya tana dan kiran sunan sa a hankali wanda yake jin kiran a chan cikin kansa da karfin gaske. Yanayin yadda yake motsawar kana gani ba na dade bane ba, yasa Raihanan fita da sauri ta kira nurse din, ita kuma taje ta kira Dr ahmad suka shigo a tare, fita sukayi suka rufo musu kofar hankali a tashe dan yanayin sa ya tsorata su sosai, kusan mintuna biyar sai ga Dr Mahfouz shima yazo ya shiga ciki, sai chan kuma suka fito ya karasa wajen su Ya nabeelan “Yana fama da severe headache ne wanda dama munyi tunanin zaa iya samun hakan, amma in sha Allah ba wata babbar matsala bace ba, amma dole sai da mukayi masa allurar baccin domin yana da bukatar ya cigaba da baccin dan tashin nasa zai iya zamar masa matsala musamman ciwon kan nasa.” “Zai samu sauki ko Dr?” “Kwarai kuwa, zai samu in sha Allah, Kiyi masa addua.” “Me scan din yace Dr.” “Babu wani abu aside ciwon kan nan gaskia, wanda yake da wahalar wa sosai musamman dama ciwon sa ne, but for better result muna tunanin yin MRI.” “Ok, mun gode Dr.” “Ba damuwa, madam karki damu fa, ango zai samu lafiya” Kasa raihana tayi da kanta ya wuce yana murmushi. Baba ne yazo, Baban Kamal tare da matarsa da kannen sa su biyu daga rano, ciki aka shigar dasu suka duba Aryan din sannan suka dawo wajen. ****Daga chan Office din nasu main house din suka wuce tare da yaran sa su biyu, da normal police masu black uniform,wajen da abun ya faru suka dudduba sannan sukayi ma gateman tambayoyi ya amsa sannan suka wuce wajen gyaran wayar da suka bayar domin wayar da ta fadi ta dauke dan haka taki kunnnuwa, akwai yaron da yake musu irin wannan aikin dan haka da kansa Kamal yaje wajen ya karba sannan suka sakè komawa Office aka saka wayar a computer suka dauke komai na cikin ta har call log sannan suka bar wayar a kunne suna monitoring call din da zai shigo ko text message. Call log din Kamal ya shiga yana duba numbers din da akayi kiran da wadda sukayi magana last wadda itace number da aka fi kira a ranar gaba daya. Tura number yayj ya bada umarnin a duba masa me number, da adress da komai. Within 5min aka turo masa komai akan contact din. Tashi yayi yana kallon number da Address din cikin tsananin mamaki, tunani ko hasashen sa be taba kawo mishi ba, dan haka ne ma sai da ya sake dubawa sosai ya tabbatar da hakan ne babu mistake. Cikin shigar da suke idan zasu fita operation suka fita, zuciyar sa na faman wani irin tafasa yana jin kamar ya bude chest dinsa ta ya zare ta ya huta da tsananin bacin ran da yake ciki. * *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 **RQ** Page 66 ***A daidai kofar gidan motar tasu ta tsaya, yaran suke sauka da sauri suka shiga gidan. “Lafiya?” Matar tace da sauri tana kallon su. “Ina Zainab??” “Zainab? Bata nan ta fita wajen aiki.” “Ok, zamuyi searching gidan.” “Akn me? Me tayi muku?” Id card dinsa ya zaro ya nuna mata, sannan suka shiga duba gidan suka tabbatar bata nan, suka fito suka samu Kamal yana tsaye ya bada bayan sa “Tana Office sir.” “Ok, muje.” Suka shiga motar suka dauki hanyar Office din. Tana tsaye tare dashi a compound din company suna magana kasa-kasa, a tunanin su sun samu abinda suke sun gama duk da kasan zuciyar ta na nadamar biye masa da amsar tayin sa da tayi, wanda Adam ya dade yana binta akan ta amince amma taki, sai gashi jiya ta yarda ta amsa wa wanda bata sanshi ba, bata taba sanin sa ma a rayuwar ta ba sai da abu iri daya ya hada su, suka yi taraiya wajen cimma burin su. Shigowar motar dss din da yadda tayi parking a gaban su ya saka su niyyar fita a Dari, sai dai kafin su farga har sun d’uro sun saka su a tsakiya cikin wani yanayi. Kamal din ne karshen sakkowa ya kalle ta a matukar bacin rai yana kallon wanda suke taren da dama chan hasashen sa ya zama gaskia bayan ya samu waya daga Office din su akan an kama yaran da suka yi aika aikar har ma sun ambaci sunan mutane biyu. Zainab da Muhammad “Arrest them !” Kafin ya rufe baki an damke su, aka kuma tura su a motar da ta kasance baka kirin sannan suka fice daga cikin wajen da duk ma’aikatan suka firfito kallon abinda yake faruwa. ***** Ita kadai ce a dakin ta idar da sallar la’asar tana zaune akan sallaya tana azkar taga ya dan motsa kadan, mikewa tayi da sauri domin tana tsoron yayi irin abinda yayi dazu, cigaba da motsin yayi a hankali har zuwa sauran sassan jikin nasa sai dai idanun sa har lokacin a rufe suke. Tana tsaye a kansa tana tofa masa Addua ya cigaba da rage yadda yake matse fuskar zuwa kan a hankali ya dinga bude idanun sa har ya bude su tas a kanta, yadda ta rankwafo a kansa ya bashi damar ganin ta sosai ya kurawa bakin ta dake karanta adduar a hankali ido kafin ya shiga nazarin abinda yake faruwa dashi. Da sauri ya kai hannun sa Ya rike kan da yaji ya sara masa yace “Ouch!” “Sannu, Kan yana maka ciwo sosai? Na kira Dr?” Ta mike yayi saurin riko ta da hannun da babu cannula “Me nake yi anan?” Yace muryar sa chan ciki “Bigewa kayi, bari na kira Dr Mahfouz.” “Um um karki tafi pleaseee.” Yace yana yin kalar tausayi, Sai ta tsaya tana kallon sa “Kiran sa zanyi nace ka farka.” “Zauna.” Ya nuna mata gefen sa, a kujerar ta zauna ya juyo da kansa a hankali yana kallon ta “Tell me, menene ya same ni? I can’t remember anything.” “Wasu bata gari ne suka kwala maka karfe akan ka, anan.” Ta nuna wajen ciwon, hannu ya kai wajen da sauri yace “Ouchhhh.” Da sauri ta rike hannun nasa “Da ciwo? Sannu.” Duk ta rikice, kasa yayi da idon sa yana kallon yadda ta damu sosai, sai yaga ma kamar har ramewa tayi. “Naje na kira shi?” “Umm kira shi.” Yace ganin yadda ta damu sosai, fita tayi yabi bayanta da kallo, sai kuma ya dora hannu a wajen ciwon ya sake tabawa a hankali yana tuna abinda ya faru a ranar. Dr Mahfouz ne suka shigo tare da wani Nurse namiji, yana ganin shi ya soma dariya “Ah lallai amarya ta iya kula, banyi expecting ganin ka haka ba.” “Lallai kam.” “Ya kan? Akwai wata Matsala ko wani yanayi da kake ji?” “Akwai, kan yayi nauyi sosai sannan yana ciwo.” “Dole ne wannan, sai a hankali.” “Ok.” “Bashi drugs din Abba,bari nayi ma madam magana a samu abinci a baka kaci, zaka kara samun energy zuwa dare in sha Allahu.” “Kwana nawa nayi anan?” “Kwana daya ne” “Ok, zan iya rama sallolin da suka tsere min ko?” “Yes zaka iya, ko a yadda kake ma a kwancen, idan kuma zaka iya zama ne toh, but banda a tsaye cox ba’a so ka bawa kan wahala.” “Ok thank you.” “You are welcome.” Ya Nabeela ce suka shigo tare da Khadija, farin ciki fal fuskar Ya nabeela ta karaso gaban sa tana murmushi “Alhamdulillah kanina.” “Ya nabee kin ganki kuwa?kuka kikayi?” “Menene ma ba zan yi ba? Na damu sosai.” “Kin zata tafiya zan yi ko?” “Silly boy, bana son wannan maganar, ya jikin naka?” “Na samu sauki ai, baki ga alama ba?” “Nasan dai karfin halin ka, da iya pretending dinka,Allah ya kara sauki.” “Ya jikin Allah ya kara sauki.” Khadija tace “Da sauki, thank you matar Yaya.” “Mu shigo?” Dr Farouk tare da su Amna yace bayan sun turo kofar “Ashe kuna kusa ma, kace baku fito ba.” “Tsokanar ki muke, kanina. Sannu ya jikin?” “Alhamdulillah, da sauki.” “Allah ya kara sauki.” “Me Raihana take a waje ne?” Ya nabeela tace tana kallon khadija bayan ta gaida Dr Farouk din “Na ganta kuwa a zaune, kun zo kun cika dakin ku bar mutum da matar sa.” “Kunya ce da ita kasan, zuwa zamuyi mu fita mu bar su, kanina muna falon sai anjima zamu wuce.” “Ok.” Ya juyar da kansa gefe. Fita sukayi Ya nabeela tace Raihana ta shiga ta zauna da shi ko zai bukaci wani abu. Duk a kunyace take haka ta koma ciki da sallamar ta, be juyo ba ta zauna a kujerar, kan nasa ne yake masa wani irin ciwo shiyasa yaki juyowa kar ta ga halin da yake ciki. Sai da ya dan lafa masa sannan ya juyo suka hada ido “Zanyi sallah.” “Tom, ko zaka fara cin abinci?” “Um um, zan fara sallar.” “Jikin ka yayi weak, ka fara cin abincin please sai kayi sallar.” “Ok, bani kadan.” Kadan ta zubo masa bayan ta zuba masa fav tea dinsa ta kawo masa ya fara shan shayin saboda cikin sa ya dan warware sannan yaci abincin kadan yace ya koshi. Toilet din ta shiga ta dauko wani dan karamin bawo ta zubo ruwan a bucket ta kawo dakin dan ko da ya yunkura zai tashi jiri ne ya kwashe sh, taimaka masa tayi yayi alwalar daga zaunen yayi dukka sallolin dake kansa sannan ya koma ya kwanta ta gyara masa pillow. Gefen sa ya nuna mata, ta zauna ba musu ta zauna ya dawo da kansa saman cinyar ta sannan ya hade hannun su waje daya ya rufe idon sa yana jin kamar ana tsira masa allura akan nasa. ***Bayan isha su Ya nabeela suka musu sallama suka tafi, suka biya suka ajiye khadija dan kamal yace zai yi dare. Bacci Aryan din yake raihanan na kusa dashi dan hanata tashi yayi ko da su Ya nabeelan suka shigo sallama tana kusa dashi knsa na kan kafarta kuma ko motsawa be yi ba bare ya bata damar tashi. Kayayyakin da ke ajiye a dakin ta gama gyarawa ta dan tattare wajen duk da babu datti an zo anyi sharar yamma amma kuma tana bukatar taga wajen neat, Hamma Hydar ya dawo da yamma yayi musu sallama shi da Babbo sadeeq saboda zasu koma wajen aiki Abby dai yana nan da Dadah da Ammy saboda zuwa wajen malam sannan sun fara neman gidan da zasu zauna zuwa a gama maganin saboda ba zai yiwu suyi ta zaman gidan adda maimuna ba, gidan Aryan kuwa dama tun a ranar suka kwashe kayan su. Tana zaune jigum ita kadai tana dan duba wayar ta akayi knocking a kofar ta zata ma Dr ne ta dan gyara mayafin ta da ya dan yi baya sannan tace a shigo. Kamal ne, waya yake amsawa ,shigowar ya saka shi katse wayar yayi sallama ta amsa ya yi mata murmushi “Sannu da zuwa.” “Yawwa, sannu ya mai jikin?” Yace yana karasawa wajen gadon yaja kujerar ya zauna “Da sauki.” “Sai Yanzu zaka zo ka ganni?” Aryan yace yana bude idon sa “Ashe kana jin mu.” “Maganar kace ta tashi ni.” “Nazo dazu kana bacci, sai na wuce Office.” “Agogo sarkin Aiki.” “Aikin dole ne, ya jikin naka?” “Da sauki, as you can see.” “Allah ya kara sauki.” “Me kayi a Office din?” “Arresting suspects din da suka yi maka wannan illar?” “Are you for real!?” “Ka zata wasa nake? I’m serious Yanzu haka suna hannu, dan ma yanzu ba anan nake ba, but nayi handing over case din wajen wanda nasan bazai musu ta dadi ba.” “Lallai, kayi kokari.” “Ba zaka tambayi su waye ba?” “Mts! Na gaji ne kawai, ko ma waye dai ba shikenan ba? I’m alive wannan kadai Ya isa.” “Be isa ba, ran ka suka nema, idan kuma da abun yazo da tsautsayi fa?” “Be ma zo ba.” “Still dai, you have to be very careful, Yanzu ba kai kadai bane ba, bamu sani ba ma ko akwai unborn nan tafe.” Da sauri ya kalli raihana, tayi maza ta kauda kanta, murmushi yayi kawai “Nayi mamaki matuka da na ga wadanda suka saka yaran, “Su waye?” “Muhammad da zainab.” “Muhammad? Zainab?” Ya maimaita sunan yana son tuno su waye ma haka? “Zainab ta Office suka hada kai da Muhammad, cousin din Raihana.” Yayi kasa da murya da zai fadi cousin din, da sauri raihana ta dago dan taji, suka hada ido da Aryan din da Shima ita ya kalla don be so taji ba, amma yanayin ta ya nuna ta jin. . * *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 **RQ** *67* “Hamma Muhammad?” Tace tana zaro ido “Yes Raihana, shi da Zainab. Ba shi kadai ba.” “Innalillah.” Tace a kidime, dan bata taba kawo Hamma Muhammad da irin wannan halin ba. “It’s ok, ba komai.” Aryan yace ganin yadda raihanan ta rude “It’s not,dole sai an musu hukunci daidai dasu, kuma ba wai a hannuna ma case din yake ba, dan haka kar ma kace komai.” Kamal yace yana mikewa daga zaunen. Dr Mahfouz ne ya shigo aryan din na shirin yin magana “Ashe ka shigo.” “Na shigo Dr, Barka da dare.” Ya mika masa hannu. “Barka dai, Aiki?” “Alhamdulillah, ya akaji da patient?” “Baka ga patient din nawa bane ba? Kamar bashi ba da yake madam tana kusa.” “Na gani fa, Shiyasa Nima zan yi nawa waje tawa madam din nima tana jirana.” “Ah ya kamata.” Ya fada suka saka dariya, murmushi kawai Aryan yayi hankalin sa na kan raihana da ta nuna kamar ma bata jin abin da suke cewa. “Akwai security sosai a asibitin nan ko?” “Ba laifi gaskia, wani abun ne?” “No ba komai.” “Ya jikin naka?” “Alhamdulillah, please ka cire min drip din nan ya ishe ni wallhi.” “Yayi half ai, bari mu cire ka huta zuwa safiya sai a maidashi.” “Ba za’a hakura ba?” “Ai kana bukatar shi.” “Ok, zan iya wanka?” “Yes of course, zaka iya sosai, in dai kana jin karfin jikij naka zaka iya tashi, but sai ka kula wajen kan kar ka jika shi...” “Ko da yake, ga amarya ma she can help you.” Ya karashe yana dariya. Taji wannan dai, amma sai ta fuske tayi kamar bata ji ba, ta hau dudduba abubuwan cikin ledar gabanta. “Shikenan, idan akwai wani abu just call the nurses, sai da safe.” “Ok, sai da safe.” Aryan yace “Let me walk you to the door.” Kamal yace suka jera tare, dan dama akwai maganar da yake son tambayar sa amma baya so yayi a gaban aryan din. Suna fita yace “Come here.” Ta kowa tayi zuwa gabansa, nauyi da kunyar abinda Muhd yayi ya hanata kallon sa. Ya sani sarai abun sai ya dameta, shi kuma ko kadan be ji komai ba, domin a yanzu baya jin akwai wani abu da zai faru dashi da zai bashi mamaki, komai aka ce mutum zai aikata toh fa zai aikata shi ne. Yunkurawa yayi ya zauna ta gyara masa pillow ya jingina sosai, sannan yace ta zauna a kusa dashi akan gadon, zama tayi ya dora kanta a saman kafadarshi yace “Kar kiji komai akan abinda Kamal yace, babu wani new abu a wajena akan halin mutanen duniyar nan, kowa zai iya komai akan selfish interest dinsa, so ki manta komai kinji? So nake mu manta da komai da kowa mu fara sabuwar rayuwar mu, away from everything.” “Duniyar nan kamar rumbu ne da kayan abinci, sai dai an cika shi da kayoyi wanda zaka sha wuya kafin ka kai kasan har ka mori wannan kayan, duk in da kasa kafarka k’aya ce zata soke ka..” “Haka ne.” Tace a sanyaye tana jan kukan da yake ta neman cin karfinta “So ki daina damuwa, na daina nima from the moment da nasan ina dake, I have someone in my life that needs me, tun daga lokacin na watsar da komai.” “Yanzu ya kake ji? Kan ya daina ciwo.” “Alhamdulillah. But it feels so heavy, kamar an dora wani babban dutse akan” “Sannu, Allah ya kara sauki.” “Amin. Zaki taimaka min? Nayi wankan?” “Um.” Ta gid’a kanta. “Thank you.” Yace yana murmushi Tashi tayi ta sauka daga gadon ta nufi toilet din. Wayar sa ce tayi yar kara kdan saboda baya son karar. “Na wuce sai da safe.” Kamal yace yana dagawa “Ok, night.” Ya kashe ya ajiye, sai ma ya kashe ta gaba daya ya sakata kasan pillow. Ruwan ta hada me dan dumi sannan ta fito “Saka key a kofar kamal ba zai dawo ba.” “Ok.” Tace ta je ta saka key din sannan ta dawo. Da hannu ya nuna mata botir din rigar, ta matso ta taimaka masa ta bude su sannan ta zare masa rigar. “Thank you.” “Zaki ya sauka.” “Um um ba zan iya ba.” Yace mata a shagwabe ta kalle shi da sauri ya sake marairace fuska, hannun sa ta rike ta taimaka masa ya sakko a hankali, suka nufi toilet din yana dan cijewa saboda kan nasa da yayi masa kamar zai fado. A toilet din ma kin yi komai yayi, komai tace sai yace ba zai iya ba, haka da daure ta cije tana gogocewa daga kallon sa yana kokarin sakata dole sai ta kalle shin, haka aka gama suke fito yace ta kashe ac dakin saboda ji yayi yana jin sanyi, da sauri ta kashe ta bashi duvet ya rufa, ya dan dauki some minutes sannan ya dawo daidai, ya saka wasu kayan sannan ya zauna akan carpet din yayi sallah a zaune. Yana sallar ta koma toilet din ta gyara shi sannan tayo alwalar tazo ta dauki doguwar rigarta ta saka ta cire na jikinta da suke jike ta kai toilet din, duk in da tayi yana kallon ta har tazo tayi sallar a gefen sa ta idar. Matsowa yayi ya dora knsa a saman cinyar ta, ya rufe idon sa yana jin babu dadi jikin sa. Sun dade a haka shiru babu wanda yayi magana, kowa da abinda yake tunani, ta kasa cire abinda ya farun a ranta, ya adda maimuna zata ji idan taji abun da ya faru? Kowa yasan Dss basu dagawa kowa kafa dan haka tasan dole zasu sha wahala sosai, bata tausaya masa ba ko kadan, saboda abinda yayi ma Aryan din ya chanchanci hukunci me tsauri. “Tunanin me kike?” Yace yana kallon fuskar ta yana daga kwancen, ya dan dade da bude idon sa yaga tana tunani. “Emm, ba komai.” “Menene date din yau?” “30th.” “Yaushe zaki je clearance?” “On 2nd.” “Ok Allah ya kaimu.” “Amin ya Allah.” “Abinci?” “Umm, zanci kadan.” “Ok.” Kallon kansa tayi, yaji dadin kwanciyar bata so tace ya tashi, “Na tashi ko?” “Un.” Tace tana murmushi “Dan kara ko 5min ne sai ki bani abinci.” “Toh.” Tace ta zauna suka sakè yin shiru, yana rike da hannun ta daya yana wasa dashi, sai da aka kusan mintuna biyar din sannan ya tashi a hankali ya jingina da kujarar ta tashi ta je ta zuba masa abincin tazo ta zauna a gabansa ta tankwashe kafarta ta shiga bashi abincin a hankali. Yaci sosai har tayi mamaki, sannan ta kwashe plate din ta je ta ajiye ta dawo tace ya koma gadon. “Um um, nan ya ishe mu. Bani pillow kiga.” “A kasa?” “Um, carpet din ai yana da girma, kuma yana da laushi.” “A ah ni dai, please ka koma saman, ba zaka ji dadin kwanciya anan ba.” “Kiyi hakuri ki barni anan,pleasee.” Tsayawa tayi shiru, bashi da alamar tasowar “Miko min pillow din kizo mu kwanta.” Zuwa tayi ta dauko ta kawo masa, ya kwanta a hankali sannan ya mika mata hannu, ta tako ta zauna a gefen sa tana jin kamar be kamata ya kwanta a kasan ba. “Oya kwanta.” Yace yana kulle idon sa. Hijab din jikinta da tayi sallah ta zare ta dora a saman kujerar sannan ta kwanta a gefensa, hannu ya saka ya matso da ita sosai jikinsa ya maida idon sa ya rufe saboda baya son buden idon sosai. Cikin bacci taji alamun yana ta jujjuya wa, bude idon ta, tayi da yayi mata nauyi saboda baccin dake kanta ta kalle shi sai taga ya hada zufa sosai ya rike kan yana jujjuya shi. “Subhanallahi, ciwo yake yi? Sannu.” Ta tashi da sauri tana rike shi. “Kai na zai cire Raihanaa.” “Ba zai cire ba, bari na kira su, sannu, ba zai cire ba.” Ta ce tana mikewa da sauri har ta soma kuka. “No Karki kirasu, bani maganin a cikin drawer din chan, nasha.” Ya fada da kyar. Wajen su drawer ta yi da sauri ta dauko maganin, ta dauko ruwa ta kawo masa ta ballo ta bashi yasha, still yana rike da kan nasa. Tana durkushe a gaban sa har ya soma lafawa a hankali yana fitar da gumi sosai. “Kana jin zafi ne?” Da ido ya amsa mata ta karo ac ta dawo gabansa ta durkusa tana jera masa sannu. Bayan ya lafa gaba daya ta taimaka masa ya koma gadon ta dan rufa masa duvet a kafarsa zuwa cinyar sa, bacci ya dauke shi nan take. Haka suka karasa daren wajen shida na safe nurse din da zata tafi ta shigo ta duba shi ta mayar masa da drip din sannan tace idan ya tashi ga maganin da zai sha sannan ta fita. Sallah tayi dan ta dan makara sannan ta gyara dakin dan kafin masu sharar su zo ta share idan suka zo moping kawai suke su wanke toilet. ***Gaba daya hankalin Adda Maimuna da na abban su Aminan Ya tashi matuka, musamman da suka samu labarin tafiya da Muhd din a bakin wani abokin sa da suke a tare a lokacin yana daga gefe sai dai shi, duk kiran da zasuyi sunyi amma shiru baa san su waye suka tafi dasu ba. Yanke shawarar sanar da Ammy sukayi da Dadah a kalla idan aka sanar da Lamido zai iya yin wani kokarin tunda an ce SS ne suka dauke shi. Tun jiyan jikin ammyn ba wani dadi sosai shiyasa ko fitowa batayi daga dakin ba, tana kwance kawai dama karfin hali ne kawai amma tana jin jiki ba laifi. Dakin da suke kwana Adda Maimunan ta shigo jiki a mace ta zauna ta gaida Dadah sannan ta duba jikin ammyn. “Ya akayi Maimunatu? Na ganki haka jiki a mace.” “Wallahi Dadah, wai muhd ne jiya Wasu da ake zargin yan sanda ne na farin kaya suka zo suka tafi dashi, toh tun jiyan muke saurare amma shiru gashi har an kwana.” “Innalillah, yaushe? Me yayi musu?” “Wallhi Dadah muma bamu sani ba.” “Kai Subhanallahi, toh! Allah yasa ba wani babban abun bane ba.” Ammy tace tana mikewa daga kwanciyar da tayi “Toh Allah yasa, amma su DSS ai basa kwansu sai da zakara, dole akwai dalili, amma dai, bari na kira Lamido naji, ko zai iya wani abu akai duk da ba lallai ba Kinsan suna da tsari.” Dadah tace. Shiru sukayi gaba daya ta dauki waya ta kira Lamido sannan ta saka a handfree “Tsohuwa me ran karfe, daga tahowa ta har kin fara missing dina ne?” “Toh ba dole ba, miji baya kusa. Ya hanya ka koma kalou?” “Alhamdulillah wallahi, ya jikin ammyn?” “Da sauki Alhamdulillah.” “Allah ya kara sauki, na kira jiya da daddare inaga kunyi bacci time din.” “Watakila kam. Yar Matsala ce aka samu, muhd kanin ka ne aka ce jamian tsaro na farin kaya…” “Sun tafi dashi ko? Na sani Dadah.” “Toh! Me ya faru?” Tashi yayi daga in da yake zaune ya fita sannan yace “An kama shi ne da laifin abinda ya faru da Aryan.” “Naam!?” “Akwai yarinyar da suke tare a Office din su Aryan din, to kamar tana son Aryan din ne, shine sukayi irin abun nan da ake cewa tunda bamu samu ba kowa ma ya rasa, Allah ma ya takaita abun ya zo da dan sauki babu asarar rai.” “Turkashi! Shi muhdun?” “Wallahi, toh kinga ai babu abun cewa, zasu bincika shi idan har bashi da laifi zasu sallame shi, amma idan har yana da laifi toh fa dole zasu hukunta shi.” “Ashsha, abu beyi dadi ba, shikenan, sai anjima.” “Yawwa, zan kira idan ammyn ta tashi.” Duk sunji komai babu bukatar maimaitawa, adda maimuna har ta soma kuka dan bata taba tunanin zai aikata hakan ba, har son da yake ma raihanan ya kai yayi risking life dinsa haka? Kunya da nauyin ammyn ya rufe ta lokaci daya, mijin yarka aso a salwantar wa da rayuwa. “Yayi wauta sosai yaron nan, na tabbatar yarinyar da aka ce ita taja raayin sa, wannan wacce irin Kaddara ce haka?” “Be kyautawa kansa ba, ya kuma cuci kansa.” “Um um, karki cika magana kije Kiyi masa baki, addua zakiyi masa, tsautsayi da Kaddara dai.” Ammy tace “Sa kai ne da dorawa kai, idan ba haka akan da aka fara hana aure? Shi bashi da tawakkali? Eh?” “Ya isa dai, duk ma me zaki ce a yanzu cikin bacin rai ne, ki sawa zuciyar ki sallama.” “Dadah ya zanyi? Laifi ne fa babba ya aikata, Yanzu da wanne idon zamu kalli mijin Raihanan? Ita kanta da wanne ido zata kalle shi ace dan uwanka na neman ran mijinka?” “Abun da ya riga ya faru dai ya faru, yanzu addua zamuyi Allah ya fitar dashi kawai, amma kuskure an riga an tafka shi.” Dadah tace ganin yadda Adda Maimunan ta shiga damuwa Tashi tayi ta fita ta samu Baban su Aminan ta fada masa abinda yake faruwa, shima ya kadu sosai da laifin da aka ce muhd din ya aikata, be kuma taba hasaso zai iya aikatawa din ba. Ya dauka komai ya wuce Ashe abun yana ransa, ya biye ma dokin zuciya ta kaishi ta baro shi. *****Har su Ya nabeela suka zo da wata cousin din Mummyn su be tashi ba, gida Raihana tace zata je ta dan dawo ta bar su Ya nabeelan a tare dashi. Gidan sa ta fara zuwa ta dauko masa yan kayan sa ta dauki nata hade da khakhi dinta saboda clearance din gobe, sannan ta wuce gidan Adda maimuna. Kunya da nauyinta ya hana adda maimuna yadda su hada ido, ita bata ma sun san maganar ba sai da ta shiga daki wajen ammy sannan take fada mata, abinda ma ya hanasu zuwa yau da wuri kenan suna tunanin idon ta zasu kalli Aryan din “Yace ba komai Ammy, ni kaina baki ji yadda naji ba, na dauka zai yi fushi sosai amma ko kdan be damu ba.” “Amma ai duk da haka sai yaji babu dadi, a hari ranka fa? Mutum ya kai makura a kinka fa kenan.” “Nima haka na gani. Kuma wallahi Sir Kamal ba zai kyale ba, yanayin sa kadai ya nuna ba sassauci, sai hakuri Kinsan yanayin aikin nan nasu, ba ruwan su da alaka ko waye kai.” “Shine dama matsalar, sai hakuri kam.” “Tafiya zan.” “Toh, kamar naji an gama abinci tun dazu an kasa kai muku, ki tafi dashi idan Dada zata sai kuje tare, yau kam bana jin dadin jikina amma zan yi magana da Aryan din.” “Ok tam, Allah ya kara sauki.” “Amin.” Tare suka tafi da Dadahn suka tarar da Abby a chan Aryan din ya tashi yana yin breakfast, ta kasan ido ya kalle ta, ta ajiye kayan hannun ta, ta durkusa ta gaida abbyn ya amsa sannan ya gaida Dadah shima sannan yayi musu sallama ya tafi. Duba shi Dadah tayi ta dawo falon ta zauna tare da wannan matar sai Ya nabeela ta mikawa raihana cup din da plate tace “Karasa aikin ki.” A kunyace ta karba ta fita ita kuma ta zauna a in da ya Nabeelan ta tashi “Shine kika tafi kika barni?” Yace yana kallon ta “Gida naje na dauko mana kayan mu.” “Wait, wai zama zamuyi tayi anan ne?” “A ah amma naga babu kayan kuma babu dadi maimaitawa shiyasa.” “Uhm, da kin bari na tashi sannan kika tafi, ina ta neman ki.” “Toh gani na dawo ai.” Tace tana murmushi “Tam sannu da dawowa.” “Kan ya daina ciwo?” “Um kadan, ya fara amma da ya ganki sai ya daina.” “Da gaske?” “Da gaske.” “Umm, ammy na duba ka, da Adda maimuna, ammyn bata dan jin dadi ne shiyasa bata zo ba.” “Ba komai, tayi kokari ma ai da tazo.” “Dr Mahfouz yazo?” “Yazo, yace tafiya zamuyi in ji daddy ko?” “Naam?” “Yes, ki fara shiri idan muka tafi sai an ganmu.” Shiru tayi akayi sallama aka shigo, suka gaisa ta duba mai jiki sannan ta fita. Tana fita Hajiya zeenat ta fado masa. Da sauri ya dafe kansa “Subhanallahi, nayi babbar mantuwa. Ina wayata?” “Gata.” Ta mika masa ya karba da sauri, call log ya shiga ya tarar da missed calls din Lawwali sun fi 50, salati yayi a ransa yayi saurin kiran sa yana saka wayar a kunnen sa “Lawan? Kana jina!?” “Eh Alhaji, ina jinka.” “Afwan ka kira ni Ashe, wallahi wani dan accident na hadu dashi muna gama waya a daren, akayi admitting dina sai yanzu na samu kaina.” “Subhanallahi, Shiyasa nayi ta kira shiru, Ya jikin?” “Alhamdulillah, Ya ake ciki?” “Wallahi tallahi an samu matsala, tun a daren wallahi ta fice.” “Ta fita?” “Wallahi, babu irin duban da bamuyi mata ba, amma wallahi babu ko duriyar ta.” “Toh! Innalillah.” “Wallahi ranka ya dade, sama ko kasa mun rasa ta.” “Zan kiraka.” Yace sannan ya kashe ya yi saurin dialing number sa *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETE )_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2k duk biyar_ *BATCH F *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 IDAN AN GAMA SU DOCUMENTS DINSU DUK DAYA 400 NE GUDA BIYAR DIN 2k *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 **RQ** 68 ***Har ta gama ringing be daga ba, ya sakè kira no answer, sai ya ajiye wayar yana shafa kansa a hankali, ya kamata ya damu da in da take ko kuwa? Ya tambayi kansa, sai wata zuciyar tace kawai ya share ta, bata chanchanci damuwar sa ba, idan ma karya tayi dole zata dawo, idan ta dawo yana da karfin hujjar da zai iya tura ta gidan yari na har abadah. Be kira Lawwalin ba, dan ya gama yanke be kamata yayi wasting time dinsa akanta ba kuma, sai kawai ya cigaba da sabgar gabansa. Washegari ce ranar da za’a yi masa MRI kamar yadda Dr Mahfouz yace, ranar kuma Raihana taje clearance ta gaya ma LGI dinsu akan tafiyar da zatayi, yace ta rubuta letter zuwa ga co-ordinator din ta state, ta zauna ta rubuta yasa hannu sannan yace ta kai chan headquarter su dake gwarzo road. Daga kumbotson ta wuce taje ta kai ta dade tana jiran wanda zata bawa an ce ya fita gashi bata so ta tafi, hakan ya dauke ta lokaci me tsawo. Da laasar ta dawo asibitin babu kowa sai Ya nabeela Ammy sun zo da Adda Maimuna har sun tafi sai Abby ma yazo da safe zai wuce Adamawa. Wani kallo yake mata da ta shigo irin kallon kasa kasan nan, tana sanye da nysc khakhi dinta da white medium hijab sai jacket din da ta dora akan white shirt din ta bar botir din kasan a bude saboda ta sakè sosai. Gaishe da Ya nabeela tayi sannan ta dauki Amna da tazo da su yau kasancewar friday ne da wuri suke baro school, ta zauna akan kujerar tana yin kasa da kanta “Ba zaki kula ni ba?” “Laa wai baki masa magana ba? Tun dazu Aryan yake ta faman kallon hanya fa.” “Bata da gaskiya shiyasa ta ki magana.” “A ah, kunya ta take ji, kanwata me kunya ce.” “Me nayi?” Tace tana kallon sa Kayan dake jikinta ya nuna da bakin sa, sarai ta gane me yake nufi amma sai taki cewa komai, har Ya nabeela ta fita ta jawo musu kofar. “A haka kika je?” Yace yana zuba mata shanyayyun idanun sa dake nuna gajiyawar sa. “Kalli fa, me sukayi?” “Babu yar afterdress da naga matan aure na sakawa?” “LGI dinmu baya yarda asa kayan da ma khaki ba, shiyasa kuma jacket din babba ce sannan Hijab din ma…” “So yake ya dinga kalle matan mutane ko? Sai naje na tsone masa ido.” Dariya tasa ya cije baki “Dariya ma kike?” “Um um, ba ita nake ba, ya jikin?” “Da sauki…” “Anyi scan din?” “Um anyi, sai jiran result.” “Ok. Allah yasa muga alkhaiiri.” “Amin ya Allah.” “Oya tashi kici abinci amma ki fara chanja kayan nan kafin wannan Dr me katon kai ya shigo yana yashe miki baki.” “Dr Mahfouz?” “Shi.” Yace yana hararar ta. Gum tayi bata sakè magana ta, tasa key a kofar sannan ta chanja kayan a gefe yana kallon ta duk da kunyar da take ji haka ta daure, sannan ta zuba abincin tace zata je wajen Ya nabeela ta ci, hanata yayi yace ta zauna taci a gabansa yaga iya wanda zataci, zuwa tayi ta cire key din da tasa a kofar sannan ta dawo ta zauna a kujerar gaban nasa ta shiga cin abincin a hankali. ****Kwana biyu tsakani suka shiga shirye shiryen tafiyar, daddy ya matsa dan so yake su taho bayan two days zai dawo ya koma kan business dinsa dan ya samu sauki sosai yanzu kamar bashi ba. Shirye shirye Ya nabeela take musu da taimakon Kamal da khadija ita ta taimaka ma raihana ta hada abinda zata bukata sannan ta hada ma Aryan din nasa tunda Asibitin sun rike shi sai ranar da zasu tafi sannan direct daga chan airport zasu kaishi. Ana gobe zasu tafi Ammy ta tare a gidan da suka samu saboda zuwa wajen malam sannan tana ganin likitan kwakwalwa a asibitin nasarawa, sau biyu Malam yazo shi da Isa da Awais da Asiya suka sake duba ammyn sannan yace zasu dawo idan ta samu gidan nata. Dukkan su sunzo suna nan Lamido, Hamma Hydar da Babbo Sadeeq sun taho ma Dadah da abubuwan da zata bukata, tare suka dawo da Abby da yaje yayi kwana uku. Daga gida take bayan ta gama hada komai waje daya an saka a mota ta iso gidan nasu, dan madaidacin gida ne me kyau da aka kawata shi da furnitures masu kyau da tsada. A falo duk suka baje ana hira ana rawa cikin jin dadi da farin ciki Ya Nabeela ta kirata tace zata zo ta dauke ta akwai in da zata kaita, da kwatance tazo gidan ta shigo tayi musu Allah ya sanya alkhaiiri duk da taso su zauna a gidan su na asali amma tasan ba zasu yarda ba shiyasa ba batayi ma Aryan maganar ba musamman da yake fama shima da kansa Amma da ya san abinda ake ciki ba lallai ya bari ba saboda tsawon lokacin nan ya ajiye gidan ne saboda su. Tare suka fito da raihana tace zata dawo da ita, ita raihana bata san ina zasu ba sai da taga sun dauki hanyar saloon din nan da ta taba kaita. “Dan Allah kanwata wata alfarma nake nema.” Tace sanda suka iso daidai saloon din tayi parking tana kallon raihanan da ita ma ita take kallo da alamun go ahead “Aryan ba zai iya dorar da wata rayuwa me dadi ba, dukkanin rayuwar sa a fadi tashi yayi ta daga wannan sai wannan, ke kanki nasan kin lura da hakan a dan zaman ki dashi, dan Allah Raihana ki taimaki maraicin sa ki zamar masa sanyi zuciya da na idaniya, a yanzu gaba daya hankalin Aryan yana gareki, Kiyi yadda zakiyi dan Allah Kisa ya manta komai da ya faru, nasan zaki iya domin yana sonki har bansan adadin yawan son ba.” “In sha Allah zanyi iya kar kokarina Ya nabeela.” “Yawwa, Nagode sosai, Allah ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba. Ki taske sosai ki kama mijinki a hannu, karki tsaya wannan kunyar dan Allah, Yanzu ba lokacin da bane ba, ki nunawa mijinki soyayya shine cikakkiyar wayewa, akwai wani e-book da nake dashi, zan tura miki ta whatspp ki daure ki duba ki karanta kinji? Zaki amfana sosai game da rayuwar aure a zaman ance, domin maza yanzu basa son kunbiya kumbuyar nan, sai kin taske kin dage sannan ki hada da addua zaki ga komai yana tafiyar miki yadda Kike so.” “In sha Allah, Nagode Ya nabeela.” “Karki damu, ki dauke ni a matsayin babbar yayar ki mace ba wai Yayar Aryan ba, ni dama na dauke ki ne a matsayin kanwa mace da bani da Ita, mu hade kanmu karki dinga jin nauyi ko kunya ta. Duk abinda ya shige miki duhu ki sanar dani in sha Allah zan warware miki komai.” Godiya tayi mata suka fito suka shiga saloon din, tasa a gyara mata gashin ta sannan a wanke mata kafar ta aka gama suka fito ta kaita wani clothing store ta zabar mata hadaddun sexy kaya masu kyau da tsada na yan gayu sannan suka wuce gidan ta hada su cikin kayanta hade da wani hadadden gel a most have for every married woman wallah(wanda ba’a fadan sunan sa sai an biya 😜😅)lol. Daga nan gidan su ammyn ta maida ta, lokacin magriba ta kusa ta ajiye ta kawai ta wuce gida. Kamal na tare da Aryan ta fada masa dama a wajen ammyn ta zata kwana yau shiyasa bata koma asibitin ba, tayi sallar magriba sannan ta zubo tuwon Dadah me dadi taci ta zauna aka dasa zaman hira tana manne da Ammyn kamar zata shige jikinta. Sallar ishai ce ta sakè tashin su akayi sallah sannan aka zo aka sake zama Dadah ta tambayi Lamido akan case din Muhammad be ce komai va saboda ba hurumin sa bane ba kuma aikin sa be bashi dama ba amma yasan sai an ladaftar dasu idan ma zaa kyale su tunda Aryan din Allah ya takaita babu wani abu da ya faru. ***Yana tare da Kamal amma rabin hankalin sa na ga tunanin Raihanan, ya rasa dalilin da yasa yake jin ta sosai a yan kwanakin nan ko tafiya tayi sai yayi ta tunani ya gaza sukuni har sai ta dawo, ya samu saukin fushin nan nasa sosai dan ya lura kamar yanzu ma babu abinda yake tunzura shi shiyasa yayi zeroing mind dinsa daga tunanin duk wani abu da zai hana mishi farin ciki. Shi yasa ko maganar zainab da muhd bata wani dad’a shi da kasa ba dan ko da Ammy suka zo masa da maganar kin bari yayi tayi tsawo yace babu komai ya wuce, shi da Kamal din ma zai yadda da sakin su yasa akyi suje su karata da halin su. “Nasan be kamata nayi maka maganar nan ba, kuma nasan be kamata nayi bincike akai ba, amma har yanzu babu labarin Hajiya zeenat fa.” Yace yana son karanta wani abu a fuskar Aryan din wanda zai zame masa cikar aikin da yake akai. Dage kafada Aryan yayi, ya sa hannu a gefensa ya dauki envelope din dake ajiye da yasa Hashim kawo masa ya mikawa kamal din “Nine na dauke ta na kaita wani kauye, sannan nayi amfani da hakan na samu enough evidence din da duk balain su basu isa su wanke ta ba.” “Wait what? Ka dauke ta?” “Yes of course.” “Kana da hankali kuwa Aryan? Kana son saka kanka a matsala ne ko me? Kasan irin neman da ake mata Yanzu haka? Sannan kasan dama kaine prime suspect nasu?” “I don’t care, na samu abinda nake so ai, kuma ta riga ma ta gudu, bansan ina take currently ba, but duk abinda na samu yana cikin envelope din nan.” “Baka bi hanya me kyau ba ta samu information din.” Yace yana ajiye envelope din a gefen Aryan din A dan kufule Aryan din yace “What ever, na dai samu.” “I can’t use it, ba zan iya amfani dashi ba gaskia.” “Ok fine, don’t use it. It’s your choice after all. Ni dai ka sani nayi abinda zanyi, kana tunanin idan kabi right way din zaka samu abinda kake so?” “Idan kuma tayi denying fa, lawyer ta yace an matsa mata ne ko an firgita ta. Duk abinda ta fada din zasu ce ta fada ne under duress, kana tunanin alkali zai karbi shaidar?” “I don’t care anymore kamal, ya karba ko kar ya karba. All I know shine nayi abinda nake ganin shine daidai, duk wanda be yarda ba ban damu ba.” Yace a hasale ganin kamar Kamal din yana son nuna masa abinda yayi ya tashi a tutar babu. “Iya gaskiya ta na fada maka, wannan shine abinda ya kamata ka sani before putting your self in to this mess.” “Then leave me with my mess, ka barni nayi duk abinda naga dama, it’s my life and my choice.” Sai ya dafe kansa da yaji ya sara masa, ya runtse idonsa ransa na masifar baci. Turowa da condition din nasa Kamal yayi, sai kuma yaji nadamar abinda ya farun ya tashi da sauri ya rike hannun Aryan din “Are you ok?” Yace yana leka fuskar sa. Be yi magana ba sai rike kan da yake yana runtse idon sa. “Let me call the Dr .” Ya juya ya fita, suka dawo tare da Dr din ya duba shi sannan yace “A daina dawo masa da duk abinda zai bata mishi rai, jinin sa zai iya sake hawa ko yaushe, bama so mu dora shi akan drug na bp din Shiyasa ma tun farko bamu fara ba, please a kiyaye.” “In sha Allahu dr, za’a kiyaye.” Fita yayi ya ja musu kofar, da kallo kamal ya bishi yana jin rashin kyautawa abinda yayi. “I’m sorry.” Yace yana daga tsaye “It’s ok, I’m sorry for acting rude.” “No nine me laifi, ba haka ya kamata nayi ba, in sha Allah zan duba zan kuma san me yakamata, I will handle da case.” “Thank you.” Yace yana juya kansa zuwa dayan side din. Wayar sa ce tayi kara, yana ji yaki juyowa har sai da Kamal din ya duba sannan yace masa “Raihana ce.” Hannu yasa ya karba ya daga shi kuma Kamal din ya fita. Da safe suka tashi kamar babu abinda ya faru, da kansa yaje toilet yayi alwala hade da wanka yazo ya saka kayansa sannan yayi sallah. Ya nabeela ce ta fara zuwa dauke da breakfast, zuwan ta yasa Kamal tafiya gida yayi wanka sannan suka dawo tare da Khadija itama dauke da breakfast din, tare suka ci dukkan su a dakin sannan Ya nabeela da khadija suka hau kwashe kayan dakin suna hade su waje daya, komawa yayi kan gadon ya dauki wayar sa ya kirata lokacin ta fito daga wanka tana shafa mai, gaishe shi tayi ya amsa yana tambayar ta su Ammy sannan yace mata malam Yahya zaizo ya dauke ta. Sallama sukayi ta karasa shiryawa a gaggauce ta dan sha tea da cake Malam Yahya yazo ya dauke su dukkan su ita da Dada da Ammy su kuma yan mazan suka hau mota daya tare da Abby. Suna zuwa sun gama shiryawa har sun kai kaya mota Kamal yaje yayi clearing komai an yi discharging nasa. Motar Ya nabeela suka shiga Kamal din ya tuka su khadija na gaba Aryan da Ya nabeela na baya suka nufi airport din dan sai sun fara zuwa Abuja sannan zasu tashi ta chan. Karfe goma jirgi zai tashi dan haka sanda suka je tara ma har da rabi a gaggauce sukayi komai, raihana ta rungume Ammy sai kuka. Duk sai ta basu tausayi, Abby ne ya korata ta dole tabi Aryan din tare da Kamal da zai wuce Abujan shima. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETE )_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2k duk biyar_ *BATCH F *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 IDAN AN GAMA SU DOCUMENTS DINSU DUK DAYA 400 NE GUDA BIYAR DIN 2k *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 **RQ** **71** **** Karo na biyar kenan tana taka Qaya a kafarta, tayi tafiya sosai bata san ashe nausawa take kara yi ba, babu ruwa babu abinci, duk kafar ta, ta yayyanke saboda azabar da tasha. Tayi dana sanin fitowa daga gidan da ta zauna duk ma abinda zasuyi mata suyi mata. Bata san yadda akayi ta fito ba, gashi babu ko takalmi bare dankwali a kanta. Ta kasa tuna komai da ya faru har ta samu ta fito din gashi nata san yadda zatayi ta koma ba. “Bani da mara ba da mahaukaciya.” Tace tana kallon kayan jikinta da sukayi wani irin baki da daudar datti. Cigaba da tafiya tayi sai gata ta iso wani dan karamin gari. Safiya ce yara sun fito waje suna wasa, suna ganin ta suka mike da sauri suka fara ihun ga mahaukaciya ga mahaukaciya. Nan da nan aka taru ana kallon ta, wannan wacce iriyar rana ce a gareta? Yara ne fa suke yi mata ihun mahaukaciya. Duwatsu taga sun tsuguna sun dauka, da farko bata gane me zasuyi ba, sai da daya daga cikin yaran ya saita ta, ya jefe ta da dutsen a daidai goshin ta. “Kai kai, kuna da hankali kuwa?” Wani Babba da ya fito daga cikin gidan yace, da gudu suka watse ita kuma ta rike kan da ya soma jini. “Sannu Baiwar Allah.” Yace daga dan nesa nesa dan batayi masa kama da me hankali ba. “Yawwa, aina nake nan?” “Kina kauyen Yalwa ne, daga ina ke kuwa Baiwar Allah.” “Nima ban sani ba.” Tace jin gaba daya ta kasa tuna daga ina take ma. “Lafiya Ilu?” “Wallahi babà wata Baiwar Allah ce, yaran nan na wasa suka jefa da dutse.” “Subhanallahi, maza kira iliya me kemis yazo ya duba ta.” “Bana so, ku kyale ni. Sanda shegun yayan suka baibaye ni uban wa ya hana ku zuaa ku hana su, sai da suka ji min rauni sannan zaku nuna kun damu, dan baku san ni wacece ba.” “Toh, Baiwar Allah daga taimako?” “Bana so, duk kuma sai nayi maganin ku.” Tayi gaba fuu ta wuce su tana rike da wajen da yake jinin, mamaki ne Ya kusan kashe su. “Allah ya baki lafiya.” Ilu yace yana komawa cikin gidan. A wani kududdufi ta tsaya ta wanke fuskar ta bayan ta zagaya bayan garin, sannan tasha ruwan da bashi da kyau kwata-kwata, ta cigaba da tafiya a wahalce. Chan ta soma hango titi daga dan nisa, tayi saurin daga kafarta ta hau sauri sauri cike da murnan ta, ta karasa titin ta tsaya tana waige-waige. Motoci ne suke wucewa a guje saboda yanayin hanyar babbar hanya ce highway baa wani tsayawa. “Ina ma zance idan na samu motar?” Ta tambayi kanta tana kokarin tunowa amma sam ta kasa. Ji tayi kamar ana ingiza ta, ana tura ta sai kawai ta hau kan titin kanta tsaye ba tare da tunanin komai ba balle ta duba masu wucewa. Wani irin karar taka birki me karfin gaske ya shiga kunnen ta, kafin ta ji anyi sama da ita an watsa ta gefen titin, gaba daya jin ta da ganin ta ya dauke dip, ta sume a take. Be tsaya ba me motar, ya kara gudun motar sa ganin kamar ta mutu, Arne ne dama ba musulmi ba, kuma be san yadda zai da ita ba idan ya tsaya masifa zata zamar masa, ganin babu kowa a bayansa kawai ya take motar sa ya gudu. Tana kwance a gefen titin cikin jini, wata motar yan sanda tazo wucewa, da farko basu ganta ba, sai da suka dan gota ta sannan suka lura ta cikin mirror, baya suka dawo suka tsaya suka fita da sauri. “Wani ne ya bige ta ya gudu.” Daya yace “Ya Salam, bleeding take ta baki da hanci, mu taimaka mata.” Daukar ta sukayi, suka sakata a motar su, suka dauki hanya sai cikin Kano, suna zuwa suka wuce Emergency unit da ita, aka karbe ta aka shiga duba ta. Bayan likitocin sun duba ta, suka gano ta samu karaya biyu a hannu sai kafarta daya da motar tayi crushing kafar k’ashin ya dagargaje sosai. Hoton ta aka dauka sannan aka saka a social media dan gaba daya ma ta sauya kama numfashi kawai take yi amma ba karamin bugawa tayi ba. ****Ya nabeela na kwance bayan sun gama magana da Aryan a waya, ta shiga Facebook din ta zata duba newsfeed kawai sai ta ci karo da hoton da ya daga mata hankali ya sata mikewa da gudu tana kokarin jefar da wayar “Na shiga uku, Hajiya?” Tace tana dafe kirjinta, rasa me zatayi tayi, ta juya nan ta juya chan sai ta dauki wayar ta kira Kamal, yana compound din gidan su yana zaune da computer a gaba kiran ya shigo, a rikice tayi masa sallama ya amsa yana dan matsar da system din “Ya akayi Ya nabeela?” “Hoton Hajiya na gani, Yanzu a fb wai ana neman dangin ta, tana Akth.” “What?” Ya mike tsaye da sauri “Bari na tura maka ka gani, Itace wallahi.” “Calm down, ki kwantar da hankali, zan duba Yanzu.” “Ok, ka duba na tura ma a whatspp.” “Ok.” Yace suka ajiye wayar, ya shiga whatspp din ya bude hoton, itace kuwa, sosai ya shiga shock, me ya faru da ita bayan ta gudu? Aryan? Noo ba zai yi mata komai ba. Ya jaddada sai kuma ya kasa hakuri, ya shiga kiran Aryan din duk da yace ba zai taba damun sa da duk wata magana da ta shafi nan ba tunda baya nan. Shirin fita suke zuwa asibitin Raihana ta riga shi shiryawa dan wuni a kwance yayi shi sai da kyar ya tashi da yaga 5 din ta kusa. Yana daura belt kiran ya shigo, yasan idan ba Ya nabeela ba toh Kamal ne dan su kadai ya kira da number din sai yan gidan su Raihana wanda su kuma yanzu basu dade da gama wayar da ita ba. “Ya Kamal ne.” Tace tana mika masa wayar, maimakon ya karba kawai sai ya hada da hannun ta ya rike da wayar ya jawo ta sannan ya amsa wayar “Kana jina?” “Eh.” “Baka samu wani labari akan Hajiya zeenat ba?” “Na zata mun rufe wannan babin.” “It’s very important ne.” “Ok, ban samu ba. Har na taho babu wani bayani, ta gudu bayan ta musu pretending tana hauka, which nasan karya take.” “We can’t say exactly abinda ya faru dai.” “Akwai wani information ne?” “A ah, babu.” Ya rufe masa “Oh okh.” “Later.” “Ok.” Ya katse wayar “Kinyi kyau?” Yace yana kallon ta da murmushi, shigar da tayi ta palazzo da riga ta dora babbar jacket akai sannan tayi rolling medium veil yayi mata kyau ainun “Umm.” Tace tana murmushi. Peck yayi mata a kuncin ta, ya karasa gyara belt din shima ya dora rigar sanyin akai da katoton takalmin sa, suka fita hannun sa rike da nata. Uber sukayi zuwa asibitin wanda Daddy tuni ya isa yana jiran su. Suna shiga suka hange shi a zaune a reception, yayi haske sosai yayi fresh kamar bashi ba, ya samu lafiya sosai “Welcome son.” Ya rungume shi yana jin soyayyar dan nasa na kara shigar shi, tunda ya samu lafiya yaje saudiyya yayi dawafi ya samu saukin abinda yake ji akan yaran nasa, wata irin soyayyar su yake ji da tausayin su musamman Aryan da ya kusan fin kowa shan wahala. “Sannun ku da hanya.” Yace bakin sa yaki rufuwa saboda tsabar murna r ganin su, da kuma yadda yaga Aryan din ba haka yayi tunani ba. “Daddy ina wuni?” Tace tana zame wa “Tashi da sauri yata, maza tashi.” A kunyace ta mike “Sannun ku da hanya, kunzo lafiya?” “Lafiya lou Alhamdulillah.” “Masha Allah.” “Daddy barka da rana.” “How are you Aryan?” “I’m good, ya karfin jukin?” “As you can see, babu wani abu da yake damuna yanzu, na samu lafiya Alhamdulillah.” “Masha Allah, Allah ya kara sauki.” Suka hada baki da raihana suka fada “Amin, ya kake ji yanzu?” “Da sauki.” “Good, akwai excellent Dr anan, zasu duba ka sosai.” “Thank you Daddy, Allah ya kara girma.” “Amin.” Zama sukayi, duk sai suka kasa sakewa, Daddyn na lura da yadda Aryan yaki sakin jiki sam dashi, duk sai yaji babu dadi, duk da shine ya jawo Amma still babu dadi, ace kai da yaran ka kamar Wasu strangers, yayi dana sani har ba adadi, kuma ya nemi gafarar Allah akan abinda ya aikata yana kuma fatan duk su yafe masa har Aminin sa, yana kwadayin su dawo yadda suke duk da ba abu bane me sauki ba. Time din appointment din ne ya cika, aka nuna masa dakin Dr din ya shiga kai tsaye. Daddy da raihana zaune duk ta takura, waya yake ta faman yi tana jin shi har ya gama sannan ya kalle ta “Nagode sosai yata, Allah yayi muku albarka baki dayan ku kinji?” “Amin Daddy, mun gode.” “Sai na samu kyakkyawan labarin dawowar aisha, naji dadi matuka kuma na samu saukin abinda nake ji, a kalla zaku yi rayuwa kuma kamar kowa, tare da uwa da uba. Amma Aryan fa? Ya raga jigon rayuwar sa, yadda Aryan yayi rayuwa dashi da marayan da ya rasa uwa da uba bashi da maraba, da rai na da lafiya ta amma bani da wani amfani a gare shi, na kuntata masa, dan Allah kiyi min alfarma ‘yata.” “Daddy…!” Tace tana zamowa daga zaman da tayi saboda yadda ta kasa sukuni gashi yana yi mata wasu irin maganganu da suka sake sakata jin nauyin sa “Alfarma zaki min dan Allah raihana, ki taimaki rayuwar Aryan ki tallafe shi, Kisa ya manta duk wani bakin ciki da ya kunsa a baya, na tabbatar idan ya samu kulawa zai manta komai, yayi raywa kamar kowa.” “In sha Allahu daddy, in sha Allahu zanyi iya kar iyawata, in sha Allahu.” “Nasan zaki iya, karki ji nauyi ne, dan ni ma tamkar mahaifin ki nake, duk abinda Kike bukata ki kirani a waya ki sanar dani kinji?” “Nagode Daddy Allah ya kara girma.” “Amin ya Allah, Allah yayi muku albarka, ya baku zuri’ah dayyiba.” Kasa amsawa tayi saboda nauyin adduar a wajenta, sai yayi yake kawai ta amsa a ranta tana me cike da tausayin daddy da Aryan din ka gaba daya. Admitting dinsa akayi duk da ba wai yana cikin wahala sosai bane, amma suna bukatar rike shi na kwana daya suyi duk binciken da zasuyi kafin su dora shi akan magungunan da zasu raba shi da ciwon kan da yake damun shi. ***Tare da Dr Farouk suka je asibitin, a matsayin yan uwan Hajiya zeenat din tunda tuni mutane da yawa suka gane ta aka fara kananun magangunu a garin. Bata farfado ba har sanda suka je, aka tabbatar da dangantakar su sannan aka bar su suka ganta, sukayi settling dukka bills din sannan suka fito suka zauna. “Bata da dangi ne?” “Tana dasu amma ba yan kano bane ba, ta rabu dasu tunda ta auri daddy, yadda ta raba shi da nasa familyn haka itama ta watsar da nata.” “Yanzu ya za’a yi? Tana bukatar wani a kusa da ita.” “Ban san ya za’a yi ba.” “Ko ke zaki jinyar ne?” Yace cikin sigar tsokana “Ni kuma?” Tace da sauri tana kallon shi “Yes, ke din mana, ko ba zaki iya ba?” “Ba zan iya ba.” Tace a sanyaye “Wasa nake miki… Kinsan me?” “Um um.” Ta girgiza kanta “Kina da zuciya me kyau, kinyi kokari idan wata ce ko zata rube anan ba zata taba damuwa ba,kinyi kikari sosai.” “Bansan me yasa ba, bana iya daukar zafi akan duk abinda mutum zai mun, gashi ta bata min karshen batawa, tayi ahinda be kamata na kalle ta ba din, amma sai na kasa. Na barta da Allah duk cutar war da tayi mana.” “Allah yayi miki albarka.” Yace yana jin dadi sosai. ***Wata tsohuwa aka samo mata a chan kasan unguwar su, ta biya ta kudi ta kwana ranar da Hajiya zeenat din, duk da babu abinda zaa mata dan har lokacin bata farfado ba, amma a kalla Ana bukatar wani a kusa, gida suka koma da daddare sai da safe zata dawo taji abinda Dr din zai je dan suna tunanin da kyar kafarta zata sakè moruwa da kyar idan ba yanke ta za’a yi ba. ****Da safe suka sake dawowa ita da Dr Farouk din kafin Kamal ya karaso dan ya taho yana hanya, Ya dan tsaya ne akan case din Adam wanda aka shigar dasu court za’a yanke musu hukuncin su. A Asibitin ya samu su Ya Nabeela ,zuwan sa yasa Dr Farouk tafiya ya bar su dan dama dan kar ya barta ita kadai ne. Zama sukayi ta fada masa komai abinda ya faru jiya, sannan suka shiga dakin da take. Suna shiga tana farkawa da wani irin ihu me karfin gaske, wanda sai da ya tsorata su, da gudu nurses din suka shigo suka tarar har ta fara fizge fizge tana jan kanta da hannun da babu karayar tana gunjin kuka. Danne ta sukayi amma sai da ta kusan zubar dasu, sai da sukayi da gaske sannan suka iya danne ta, akayi ma allurar bacci. “Da kyar idan bata samu matsala a kan ta ba.” Nurse din tace ma dayar da suke tare “Bari nayi ma Dr Ammar magana.” Suka juya suka fita da sauri **RQ ** 72 ***Drs din ne suka shigo su biyu, da nurse din guda biyu mata, ihun da take ya kara tabbatar musu da zargin su, aka Dr din ya duba ta, yace a barta akan allurar baccin saboda karayar da take jikin ta sannan suka fita. Fita Ya nabeela sukayi da Kamal suna magana a tsakanin su, duk jikij Ya nabeela a sanayaye yake, duk abinda mutum yayi koman daren dadewa sai ya dawo kansa, Yanzu wa zai ce hajiya zeenat mace yar gayu da kwalisa ce haka? Rayuwar ta juya mata baya a lokacin da tafi bukatar ta. Sunyi iya yin su, sun mata abinda zasu iyayi mata har akayi mata aikin hannun amma kafar yayi damage, dan har infection ya shiga dan haka dole aka shiga aiki aka yanke ta, ga karaya ga hauka, abun ya hadar mata a lokaci daya, kuma irin haukan nan me me hawa da sauka, me saka surutai amma sarai tana gane kowa da komai. Ta sha bakar azaba bayan an fito da ita daga aikin guntule kafar,Amma ya nabeela ce kawai take tausaya mata. Chan asalin kauyansu aka aika, aka samo wata a cikin danginsu aka bata kudi ta cigaba da zama da ita dan baba tace ba zata iya ba. ****Kwana biyu Daddy ya kara bayan zuwan su, da ya tabbatar babu wata matsala ya tattaro ya dawo gida. Shigowar safe yayi, direct daga airport driver ya wuce dashi gidan su Raihana. Dadah bata nan taje gidan adda maimuna akan maganar muhd sai ammy kadai a falon tana zaune ta idar da sallar walaha Abby ya shiga ciki yana so ya dan huta. Knocking akayi a gate din, ta kalli lokaci taga tara da yan mintuna. “Lallai Dadah tayi sauri.” Tace tana mikewa, jikinta sanye da hijab da ta idar da sallar ta fita zuwa gate din ta bude sai ta yi sak dan bata taba tunanin ganin shi ba. Da sauri ta maida kofar ta rufe ba tare da tace komai ba, ta koma ciki ta sanarwa Abby sannan ta shige dakin ta. Shi ya fito ya tarar dashi tsaye jikin gate din, ya shigar dashi cikin shima cike da mamakin ganin nasa. “Kar dai isowar ka kenan?” “Eh, Yanzu na sauka. Daga airport direct nan na taho.” “Wai Masha Allah. Sannu da hanya, malam yahya ne ya kawo ka ko?.” “Yawwa, eh shine, yasan gidan. Ya bayan saduwa?” “Alhamdulillah wallahi, Ya karfin jikin?” “Na samu sauki Alhamdulillah, na dan tsaya na sakè hutawa ne.” “Allah ya kara sauki.” “Amin, sai naga aisha kamar bata gane ni ba.” “Hmm, ta gane ka mana. Zata manta ka ne?” “A ah.” “Ta gane sarai, bari nayi mata magana.” Ya tashi ya shiga ciki, shi kuma daddy ya cigaba da kallon falon da gidan gaba daya, su da suka tarwatsa wa rayuwa sai gashi Yanzu sune rayuwar su a hade, tare da yaran su kuma. Shi tashi rayuwar be san yadda zai kirata a yanzu ba, kawai gashi nan ne dai. A zaune Abby ya same ta, tana ninke wasu kayan Dadah da aka wanke. “IBRAHIM ne fa Ammy.” “Na ganshi ai.” Tace tana basarwa. “Kizo ku gaisa.” Sakin kayan hannun ta tayi, ta kalli Abbyn sannan tace idanun ta na kawo ruwa “Mutumin da ya wulakanta ni, ya raba ni da mijina da Yayana da dangi na gaba daya, yaki tausaya min a matsayi na na mace, ya manta karfin alaka ya bare matarsa ta wulakanta ni, shi kake cewa naje na gaisar?” Zama yayi a kusa da ita, ya riko hannun ta. “Na sani, nasan duk wannan. Na kuma fi ki daukar zafi a lokacin da na dawo, amma ya zamuyi da kaddarar mu? Ta hakan zamu sakawa Allah tarin ni’imomin da yayi mana? Ko bama wa Allah laifi ya kuma yafe mana? Ba wannan ba ma, yaran sa. Karki manta dawainiyar su gare mu. Ko dan Aryan da Kamal, IBRAHIM ya Chanchanci second chance, shi kansa fa ba wai dadin rayuwar yaji ba, dan Allah Kiyi hakuri Kizo muje, ki bashi damar neman gafarar ki tun kafin lokaci ya kure masa, domin idan mun ga yau ba lallai muga gobe ba.” Hawayen da take rikewa ne ya zubo, ba zata iya musu da Abby ba, bata saba ba bata iya ba. “Daure Maman Raihana,nasan ki da hakuri da yafiya.” “Itama Zeenatun zaka ce na yafe mata ne?” “Lala, wannan ko ni kika ce kin yafe mata wallahi sai mun yi sharia, duk da ko a yanzu duniya ta koya mata hankali. Amma da sauran ta. Domin wata shariar sai a lahira.” “Na zata zaka ce.” “Ban isa ba.” Yace yana murmushi. Tashi tayi yayi gaba ta bishi a baya. Ta wuce kitchen ta dauka ruwa da juice sugar free ta doro a plate ta kawo falon. “Sannu da zuwa.” Tace bayan ta ajiye sannan ta zauna a gefen Abbyn “Sannun mu, ina wuni?” “Lafiya lou, an dawo lafiya?” “Alhamdulillah, ya yara?” “Lafiya lo.” “Sai kaji labarin dawowar aisha, ko basu sanar da kai ba.” Abby yace yana son kawo zancen da zai yi tsawo “Na sani, nayi matukar farin ciki.” Mikewa ammy tayi zata koma ciki, da sauri Daddy ya dan zamo saura kiris ya zube a kasa “Ina neman alfarmar ki yafe min duk abinda nayi muku abaya, dan Allah ba dan ni ba.” “Allah ya yafe mana baki daya.” Tace ta wuce ciki. Bin ta da sauri Abby yayi, suka shiga dakin sannan yace “Haba ammyn yara, haba Aishatu.” “Me nayi kuma?” “Yadda kika amsa ne, sam be ji dadi ba. Kuma da kin dan kara zama.” “Ba muharrami na bane da zan zauna muyi ta musayar wayu ai, kaga kuma Yanzu akwai surkuta a tsakani.” “Aisha!!” “Gaskiya fa.” “Allah ya shirya min ke.” Ya fita yana murmushi. Yasan duk abin nan tana yi ne kawai domin ran ta a bace yake, dan yasan tafi jin haushin abinda Daddyn yayi mata akan na hajiya zeenat. Saboda ita dama chan tasan zata aikata fiye da haka, amma me yasa daddy zai wulakanta su, ya ajiye duk alakar nan ya rufe idon sa ya kore su. Duk a kunyace Daddyn yake, ya kasa sakewa sam tunda suka shiga ciki, kwata kwata be ji haushin abinda Ammyn tayi ba, ya chanchanci fiye da hakan, dan yayi musu abinda yafi haka. Dawowar Abbyn ta dan sa ya sake har suka shiga hirar rayuwa da sauran abubuwa, wanda ya dauke su lokaci me tsawo,har Dadah ta dawo suka gaisa ta shiga ciki, ta samu ammy tana ta faman fushi akan zuwan Daddyn, baki ta bata ta dan kwantar mata da hankali sannan tace ta taimaka su hada musu abincj musamman tunda daga tafiya yake kuma doguwar tafiya. Kitchen din suka shiga ta baya, daidai lokacin me taya ammyn Aiki tazo, sai ta koma ciki ta barta da Dadan tana guiding dinta suka dafa abincin me dan karan dadi. Duk da yasan ya kamata ace Ya tafi ko dan gajiyar da ya kwaso, amma Ya kasa tafiya. Idan yaje gidan ma be san me zai yi ba, dan gaba daya gidan yayi masa baki yanzu. “Kasan abinda ya faru da zeenatu kuwa?” Girgiza kai daddy yayi “Me Ya same ta?” “Kamal be sanar da kai ba ko nabeela kenan.” “Gaskia.” “Ai tsautsayi ta hadu dashi, ko nace Kaddara. Mota ta bige ta kuma me motar ya gudu, in ta kaice maka labari Yanzu haka ma an yanke kafar, sai dai suna zargin kamar Har da ciwon hauka yana damun ta. Ni dai ban je na ganta ba, haka dai na samu labari.” “Abinda ya chanchanta gareta kenan, ni bani da wani information akan ta da rayuwar ta tun bayan da na tafi, tun da zamu wuce na rubuta takardar saki na bawa Kamal nace ya bata, idan ta fito daga prison din dan na tabbatar sai ta fito, daga nan bamu sake maganar ta da kowa ba, dan sun san bana so.” “Ta fito din kam, sai dai tun ranar da aka fito din baa sake sanin in da take ba, Ana zargin kamar dauke ta akayi, sai gashi kuma yan sanda sun kawo ta a karye cikin mawuyacin hali. “Abinda ya dace da ita kenan Barr. Matar nan ta cutar da rayuka da yawa, tabbas nasan a karshe mutuwar wulakanci zatayi.” “Kaje ka ganta.” “Zanje, ko dan naga yadda rayuwa ta maida ita. Amma tare da kai zamu da hajiya aisha.” “Aisha zata kuwa?” “Zata, kasan ta da saukin kai.” “Yanzu ai tayi tauri.” Yace yana dariya “Rayuwa ce ta maida ita hakan.” Shigowar da tayi yasa su yin shiru, ta ajiye musu flasks din abincin. Sannan ta sakè fita. Tare suka ci abincin, wanda rabon daddy da yaci abincj me yawa irin haka ya manta, sai yaji kamar an dawo rayuwar su ta baya ne, babu abinda ya faru. “Allah ya jikanki Khadija. Allah yasa kina aljanna.” Yace a sanyaye, “Amin ya Allah.” Sai da akayi sallar azahar sannan ya fito ya tafi, ba a san ransa ba, ya wuce gidan nasu da babu kowa a yanzu sai masu aiki saboda kula da gidan, wanka yayi yana komawa dan ko wayar sa be kunna ba sai ya huta sosai. Kwanciya yayi ya dan yi bacci zuwa laasar sai ya tashi. Kafin ya tashi Ya nabeela da yaran da khadijan Kamal sun iso gidan, suka yi zaman su a falo dan sun san bacci yake yi. Suna zaune bayan an idar da laasar sai gashi ya fito, cike da mamaki yake kallon su, su amna suka tafi da gudu suka rungume shi ya daga su sama yana dariya. “Maimakon ku tashe ni.” Yace yana karaso wa falon rike da yaran “Munsan hutawa kake, kuma ba sauri muke ba.” “Lallai kun kyauta. Sannun ku da zuwa.” “Ina wuni?” Khadija ta gaishe shi a tsugune “Lafiya lou ‘yata. Kuna lafiya?” “Alhamdulillah.” “Daddy barka da yamma.” Ya nabeela tace tana murmushin jin dadin yadda Daddyn ya chanja “Barka dai Nabeela, kuna lafiya?” “Alhamdulillah wallahi, ya karfin jiki? Allah ya sa kaffara ne.” “Kalle ni fa, ke kin ga alamun ciwo? Ai na warke sarai wallahi. Alhamdulillah.” “Allah ya kara sauk.” Suka hada baki da Khadija suka fada “Amin, Allah yayi muku albarka.” “Dr yace yana maka sannu da zuwa Daddy.” “Likita bokan turai, Nagode masa.” “‘Yata kuna lafiya dai ko? Babu wata matsala?” “Babu komai Daddy.” “Toh Masha Allah, haka nake son ji” “Miko min wayata a ciki Nabeela, nasan an kikkira ni.” Tashi tayi ta dauko masa wayar sannan ta dauko kayan abincin da suka dafo masa ta kawo tsakiyar falon. Kamal ya fara kira sannan ya kira Aryan sai brothers dinsa da abokan hurda wanda yaga sakon su. Har dare su Ya nabeela na gidan sun tattauna maganar hajiya zeenat da Adam ma daga nan yace zai je ya ganta gobe daga nan ya wuce company. ****Washegari Khadija da Ya nabeela suka tafi garin su Kamal, wuni Ya nabeela tayi ta juyo in da ita kuma Khadijan zatayi musu kwana biyu daga nan taje gidan su itama tayi kwana biyu sai ta bi kamal din domin zai kwana biyu kafin ya dawo wanda yake saka ran dawowar sa ce gaba daya. Yana so ya dawo da babansa cikin kanon ma kusa dashi sannan ga Daddy ma yana so ya dawo su cigaba da rayuwa tare su cigaba da gina company su. ****Tana cikin tsananin azaba lokacin da Daddyn ya karaso, kuka take wiwi tana jin kamar a karasa guntule kafar a huta saboda ciwon da take mata na balai, a nutse take yau ba kamar kullum ba, abun ya dan sake ta dan dama zuwa yake yana tafiya. Sarai ta gane shi sanda ya shigo, sai ta rude ta fara kokarin mikewa, da sauri aka rirrikete akakwantar da ita saboda ba zai yiwu ta tashi a haka ba, ga hannu a nannade ga kafa a nannade da wanne zata iya? Karaso wa yayi ciki har gaban gadon ta da yake dakin mutane da yawa ne duk kowa ya basu hankalin sa yana kallon su. A tsaye ya tsaya daga gefen gadon yana kallon yadda ta koma cikin dan kankanin lokaci Allah ya chanja mata kamannin ta baki daya. Bubbuga kanta ta hau yi a jikin karfen gadon ya girgiza kai yace “Ya jikin nata!?” “Da sauki toh, an gode Allah.” Be ce Allah ya kara sauki ba, ya zura hannun sa a aljihu ya ciro envelope guda biyu ya ajiye mata a gefen gadon yana kallon yadda take kallon sa amma ta masa magana, ya lura kamar bata iya magana ma gaba daya sai dai yunkurin yi din. “Allah yayi miki abinda kikayi ma Bayin Allah da yawa zeenatu, ni IBRAHIM na sakè ki saki uku,ga takardar nan Allah ya sa wannan shine silar shiryuwarki idan zaki shiryu, dan bana jin zaki taba shiryiwa a rayuwar ki.” Wanda suke gefen gadon suka yi saurin toshe baki cike da mamakin mutumin, ace mace na wannan mawuyacin Halin amma ka saketa har saki uku? Lallai maza mugaye ne. Yana jin kananun maganganun da suka soma tashi a dakin, da ihun da ta saka amma yayi biris, ya fice da sauri yana jin zuciyar sa fes kamar an zare masa babban nauyi da ya to kare zuciyar. “Lallai maza sai a bar su, Yanzu saboda ta gamu da wannan kaddarar shine zai guje ta?” “Ai haka Halin maza yake, sai dai Allah ya bi mata hakkin ta.” Maganganu dai kala kala hadda nurses din ma da akan idon su abin ya faru. Matar dake kula da ita ce ganin maganganun sun yi yawa tace “Idan kunsan abubuwan da ta aikata, bana jin zaku iya cigaba da zama da ita a dakin nan, wannan matar da kuke gani, tayi abinda zaa kirashi da karshen zalunci, samun muguwa azzalumar mace irin zeenatu sai an tona, dan haka kar kuyi saurin yanke ma mutum hukunci, abinda alhaji Ya aikata shine daidai.” Tsit kake ji babu wanda ya sake magana, sai yan kananu dake tashi kasa kasa, sai kuma aka koma tunanin irin abin da tayi har haka amma dai babu amsa. **RQ** Page 73 ***Duk abinda ya kamata ayi masa an yi masa ya kuma samu sauki sosai, kamar bashi ba dan sakayau yake jin sa sosai. Kwana uku suka kara bayan tafiyar daddy duk wasu tests da ya kamata ayi masa an masa na kai da na jiki gaba daya ba. Ranar da akayi discharging dinsu suka koma hotel din da suka sauka. Tana da lura da yanayin sa, he’s so happy and eager ranar. Wanka ta yi ta shirya kanta cikin riga zuwa guiwa da wandon palazzo mustard ta kama gashin kanta da new ribbon bayan ta wanke shi tas da shampoo da conditioner masu dadin kamshi, sannan tasa head band akan yellow tayi kyau kamar wata yar baby. Daga kasa ya hawo bayan ya sake kara musu kwanakin zama a hotel din zuwa sati daya. A shirya ta sameta ya tsaya jikkn kofar ya kasa karasowa yana mata wani irin kallo. A yan kwanakin nan da ya zauna da ita a hospital din ya sake shakuwa sosai da ita, ya kara karantar kyawawan halayenta da nutsuwar ta. Komai a nutse take kuma duk abinda yake so da Ya nuna alamu zata tashi tayi masa. “Sanyiiiii.” Tace tana jan maganar a shagwabe ganin ya bar musu kofar a bude “Ohh! “ yace da sauri ya saki kofar ya shigo. “I was carried away by your beauty.” Yace yana murmushi, murmushin tayi itama ya tsaya a gabanta yana kallon gashin kanta da yake ta sheke da kyalli. “Kin yi kyau.” “Um thank you.” “Me zamuyi Yanzu?” Yace yana kallon ta “Wanka, abinci.” “Bacci fa?” Yace yana kashe mata ido “Um um, ni yunwa nakeji.” “Toh toh, let’s eat.” Yace yana mika mata hannu. Mikewa tayi suka karasa wajen abincin da sukayo order sa da suna dawowa, chips da peppersoup din kayan ciki suka ci da fresh milk ya dinga zuba mata tun tana masa kara har tace ta koshi. Tissue yasa ya goge mata bakin sannan yayi kissing lips din nata a hankali. “I love you.” Yace yana kama hannun ta, ta runtse idonta a hankali ta bude shi “Thank you for everything.” Ya dora “Kafin kizo rayuwata, bansan wacce irin rayuwa nake ba, my life has no meaning, bana jin dadin komai da kowa, I hate everything wallahi.” “Amma yanzu ina ji na fresh and new, am in love.” “Um really?.” “Sosai, baki ga alama ba?” “Na gani.” “Ehen, did you love me too?” “Umm.” Tace a kunyace “Say it please!” “Nace um fa.” “Fada zaki naji.” “Kaje kayi wanka.” “Um um, sai kin fada min. Idan ba haka ba…” sai ya kanne mata ido. “I… love… you.!” Tace a tsinke Tayi saurin saka kanta acikin cinyoyinta tana dariya. Hannun ta ya rike ya d’ago kanta yana mata dariya “Kamar yak’i?” “Ni kunyar ka nake ji.” “Zaki daina ne.” Yace yana cije lips din sa ya mike yana tattare rigar sa, ya cire ta ya ajiye ya wuce toilet daga shi sai boxers. Tashi tayi ta gyara wajen, tsoro na dan shigar ta saboda taga yanayin Aryan din tasan babu abinda zai saka ya daga mata kafa, tsoro ne fal zuciyar ta tana tuna wahalar da tasha ranar. “Ko nayi amfani da intim din nan da Ya nabeela ta bani?” Tace a zuciyar ta, tana tsoro sosai gashi ta taba karantawa a wani littafi may be idan tayi amfani dashi ta samu dan sauki. Bude chan kasan akwatin ta tayi, ta dauko tana duba jikin kwalin wajen da aka rubuta natural gel, ta dan dudduba ta karanta instruction din, alamun zai fito taji, tayi saurin boyewa ta rufe akwatin tana mikewa. Sanye da bathing robe ya fito, ya tsaya gaban mirror yana kallon kansa, yana hango ta ta cikin mirror din tana ta kumbuya kumbuya, duk ta tsargu gani take kamar zai gane abinda tayi. Be kulata ba, ya shafa mai ya dauki pjs masu taushi da nauyi ya saka a jikinsa sannan ya feshe jikinsa da turarurruka masu kamshi. A gefen gadon ta zauna rike da karamin alkurani izu biyu,karasowa yayi ya zauna a kusa da ita, ya gyara mata dan kwalin kanta da ya dan zame baya, a zuci take karantawa amma kuma ta kasa concentrating saboda kusancin dake tsakanin su, paji daya ta kai ta rufe ta ajiye. “Har kin gama?” Yace yana kallon ta “Um.” “Ok, banji kira’ar taki ba ai, anjima da asuba zaki biya min naji, nasan ma kin fini iyawa.” “A ah dai, nasan ka fini.” “Zamu ji dai, sai muyi musaffa. Izunki nawa?” “Nayi sauka, a hadda kuma izu na goma, ban dade da farawa ba.” “Masha Allah, ashe malama ce.” Murmushi tayi me sauti. “Mu kwanta ko?” Yace yana kama hannun ta. Da sauri ta mike jin yadda cikin ta ya kada lokaci daya “Zan je toilet.” “Muje na rakaki.” “Um um da kai na zanje.” “Tohm ina jiran ki.” Yace kai tsaye yana haye wa gadon, ya lulluba da blanket ya zama saura fuskar sa kawai. Jiki a sanyaye ta wuce toilet din, tayi fitsari sannan tayi brush, sai ta tsaya tana jin kamar kar ta fito ko ta fito ta tarar yayi bacci. Da kyar ta daure ta fito ta tarar ya rage hasken dakin sai yar kadan da zata iya gani, wajen kayansu taje ta rasa me zata dauka ma, duk ta rikice. “Kina neman wani abu ne?” Yace yana daga kwancen yana kallon ta sarai “Um! Na ganshi ma.” “Oya let’s sleep.” “Ni kamar ma akan sofa zan kwana.” Tace tana yin hanyar wajen sofa din. “Ok, zata ishemu ai.” Ya tashi daga gadon ya sakko. “Na shige su.” Tace tana dafe kirjin ta. Cim mata yayi a wajen ya rikota zuwa jikinsa “Tsoro na Kike ji?” Yace yana kallon fuskar ta. Gid’a masa kai tayi sai yayi murmushi “Menene abun tsoron? Comman karki badani mana.” “Ni wallahi tsoro nake ji.” “Comman, babu abinda zai faru kinji? Please allow me to show you how much you mean to me.” “Ki tausaya ma bawan Allah, maraya.” “Wayo zaka min.” “Ba wani wayo, gaskiya ce. Kinga ni maraya ne.” “Um.” “Oya muje mu kwanta, na gaji sosai.” Ba a san ranta ba, ta bishi suka kwanta din. Ya jawota jikinsa gaba daya, sannan ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe idon sa. ***Idan tace tafi shan wahala yau batayi karya ba, tasha wahala fiye da wadda tasha a baya, dan gaba daya rikice mata Aryan din yayi, tun tana neman agaji har ta hakura ta cigaba da jan numfashi. Babu irin maganganun da be fada mata ba kuwa, tun tana fuskanta har ta daina ganewa, daga ganjn alamun sa shi kansa yafi samun abinda yake so a yau din, dan a wanchan lokaci shima wahalar yasha kamar ita, kuma be samu zuwa in da ya kamata ya je din ba sai a yau. A gefenta ya kwanta yana maida numfashi yana jin yadda take jan kukan cikin dashewar murya, lalubo ta yayi ya jawota jikinsa ya matse ta yana cigaba da sauke numfashi. Sai da ya samu nutsuwa sannan ya shiga lallashin ta, tana kara volume cike da haushin sa. “I’m very very sorry. Dan Allah Kiyi hakuri ki daina kukan.” Banza tayi masa ta cigaba da kukan ta kawai, a maka laifi a isheka da turanci, sam bata ma fuskantar turancin a yanzu. _”Duk yaya nabeela ce ta jawo min.”_ tace a ranta tana ayyana abinda ya farun da abinda Ya nabeelan ta bata, dan ta dan yi amfani dashi da ta tafi toilet din. Da ta sani bata yi amfani dashi ba, dan shine ya kara taimakawa wajen rikita Aryan din har yayi loosing control dinsa ya dinga zuba mata turanci kamar sarkin engila. “Kinsan ina sonki ko? Ba zan yi abinda zan cutar dake ba.” Kautar da kanta tayi gefe yana goge hawayen, ya juyo da ita tana kallon sa, sannan yayi kissing bakin ta yace “I love you so much.” Gumin saman goshin ta ya goge mata da hannun sa, sannan ya share mata hawayen saman fuskar ta. “Kinga kowa fa ma da haka ya girma, kuma next time i promise you va zaki ji haka ba, yanzu ma dan an yi me gaba dayan ne.” “Next time?” Tace tana kallon shi, daga mata kai yayi yana murmushi “Next next next next time. Next time din to infinity, baya karewa.” “Tab!” Tace tana turo baki “Toh ki daina kuka, ba big deal bane ba, shikenan fa an kashe boss din.” “Ni ka daina.” Tace tana kai masa duka a saman chest din sa “Beat me, punch me idan zai sa ki daina kuka.” Yace yana tura hannun nata jikin sa sosai. Dainawa tayi tana hararar sa, yayi murmushi kawai dan shi dariya take bashi sosai, ga wani irin happiness da yake ji. Da kyar ya lallabata tayi shiru, ya taimaka mata zuwa toilet sukayi wankan a tare tana tutture shi amma yayi biris, so yake yayi enjoying zaman nasu kar yazo yana cizon yatsa. ***Washegari ya tashi fresh, fuskar sa kamar gonar auduga saboda farin ciki, bata taba sanin yana da faraa irin haka ba, tare suka yi wankan safe suka shirya a tare duk da tana nokewa Amma ya hana mata hanyar da zata samu ma bare ta zuke, idan ta dan yi kamar zata ki, sai ya hade rai ya nuna sam be ma fuskanci abinda take son yin ba, dole kanwar naki yasa ta hakura take biye masa, dan hatta shafa mai shine ya shafa mata tana kunya tana komai, amma haka ta hakura. Sai da ya dan ci ladan wanka da shiryawar sa sannan sukayi breakfast suka yi shirin fita suka fice dan su zaga gari saboda akwai saukin sanyin yau. Sky tower suka fara zuwa, sukayi hoto daga nan suka wuce memorial museum din Auckland, nan ma hotunan sukayi masu kyau suka karasa zoo suka ga dabbobi wanda ma basu taba gani ba. Daga nan suka wuce Le bistro des gourmets restaurant sukayi dinner a chan. Sai after 10 suka dawo gida, suna dawowa kwanciya kawai sukayi bayan sun yi isha, da Shafa’i da wutri. Gaba daya satin a fita suka karar dashi, wani zubin da wuri wani lokacin da yamma ko dare, sun zaga garin sosai sosai dan an dan fara shiga summer lokacin shiyasa basu sha wahalar sanyin nan ba. Basu wani siya kaya ba sun bari sai zasu koma gida. Maka suka wuce daga nan direct suka sauka a jidda daga nan suka wuce Riyadh sukayi kwana biyu sannan suka tafi makka don yin umrah. Misalta irin farin cikin da raihana take ciki ma karya ne, kusan kullum sai sun yi waya da yan gidan su da Ya nabeela hadda khadija, ita take tambaya ka abubuwa da yawa da suka shige mata jiki dan ta lura Aryan da gaske yake yi, tun tana tsoro har ta fara daurewa duk da ba wai ta daina jin zafin bane ba, abun ka da rashin sabo amma ta ware sosai. Sau biyu ta yi amfani da natural gel din nan na ya nabeela bata kara ba, dan ta lura yafi tunzura Aryan din, ajiye shi zatayi sai an kwana biyu kawai. Satin su biyu a saudiyya, sun yi ibada sosai raihana ta roki Allah abubuwa da dama ciki har da soyayyar Aryan a gareta, ya kara sonta fiye da duk wata ‘ya mace a duniya (ba laifi bane idan ka roki Allah mijinka ya soka ko a sujjadar sallah ne, kuma adduar na da matukar tasiri sosai) ta roki abubuwa da dama ta rokawa iyayen ta da kowa ma. Daga saudiyyan da dawowa zasuyi saboda service din da take yi amma daddy yace su karasa Dubai su sakè hutawa kar su dawo yanzu zai yi magana da co-ordinator din ta state din gaba daya, so yake sai sun huta sosai sannan su dawo zuwa lokacin komai ya dawo normal, shiyasa ma babu wanda yayi ma Aryan din maganar hajiya zeenat wadda take cikin tsananin azabar ciwo da nadama mara amfani, ga ciwon ta na hauka da yake kara karfi musamman tun zuwan da Ammy sukayi da Abby suka ganta a asibitin ta sakè rikicewa. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETE )_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2k duk biyar_ *BATCH F *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 IDAN AN GAMA SU DOCUMENTS DINSU DUK DAYA 400 NE GUDA BIYAR DIN 2k *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 ***RQ*** Hafsat Rano 74 ***Babu kalar gatan da Aryan be nunawa Raihana ba, tun tana nokewa har ta sakè dashi dan kansa tsaye yake mata abu duk ma yadda zata ji ba ruwan sa, dama burin sa ya cire mata kunyar sa da take ji kuma yayi nasarar dan saura kadan ya rage wadda ta zamar mata jiki. Yana kwance yana danna wayarsa, game yake yi dan tunda suka zo babu wani abu da ya danganci Office da yayi, sau biyu dai yana tambayar Daddy akai sai yace a bar maganar so yake ya nutsu waje daya. Saboda haka ya tartara komai ya watsar yayi focucing akan bbyn sa. Akan ruwan cikin sa ta dora kanta, tana sanye da kajeran wando iya cinya da half vest da suka kamata sosai, a wani mall da suka je ya kwaso mata kayan shikenan take saka su tun bata saba ba har ta saba ma. “Me kake yi?” Tace tana leka wayar, da sauri ya kautar yana rufe screen din karta gani “Chatting nake da wata new babe da na samo jiya.” Da sauri ta daga shi, ta yi kamar zata warci wayar ya hanata yana mikewa zaune. Jikinsa ta fada ta hau kokawar kwatar wayar ya daga ta sama yana mata dariya ganin yadda ta hakikance “Sai na gani.” Tace tana cigaba da kokarin karba shi kuma ya ki bari hannun ta ma ya kai wajen duk da daddanne shin da tayi. Ajiye wayar yayi a gefe ya kama hannun ta biyu ya rike kam, yana kallon yadda take haki a dole sai ta karba. Dariya take bashi sosai musamman yadda ta hakikance kamar idan ya barta da gaske zata iya kwatar. “Ba zaki ga min chat ba ehe, wata fine babe ce wow.” Turbune fuska tayi, ta kwace hannun ta, ta sauka daga gadon. Da sauri ya rikota ya jawota jikinsa gaba daya suka fada saman gado, kwace wa tayi ta karfi saboda ya bada karfin sa gaba daya ta mike. Tashi yayi shima yana mata dariya ta hada rai ta tsaya daga jikin drawer tana kin kallon side din da yake yana mata dariya “Wasa nake fa.” Yace yana nufo ta, sauri tayi zata bar wajen ya rikota yana cigaba da dariya “Kin fiya rigima wallahi. Babu fa komai game nake kinga?” Ya haska mata wayar, ta dan kalla kadan ta dauke kai tana turo baki. Jawota yayi ya sata a jikinsa yana rungume ta “Madam rigima.” “Ba kai ne ba.” Tace tana dan bubbuga kafarta a shagwabe “Me nayi? Daga wasa? Wacece ma ta isa nayi chatting da Ita, ina tare da matata da tafi kowa kyau a duniya.” “Ummm, sweet mouth.” Tace tana dariya “I’m serious fa, akwai wadda ta fiki ne?” “Babu.” Tace tana dariya “Ehen, daga ke an rufe kofa ba kari.” “Dadin bakin maza ne kawai, wait wai yaushe ka iya irin wannan kam kalaman na hausa ne?” “Browsing nayi.” Yace yana mintsininta. Dariya ta kwashe da “I see, dan nasan da baka iya ba.” “Baki san zaka iya komai ba?you can do anything for love.” “Gaskiya ne.” Dariya suka saka a tare, ya sa hannu a shafa cikinta wajen cibiyar ta da yake a waje, sigar jikinta ta tashi, ta rike hannun sa da sauri “Allow me to enjoy my self, allow me to enjoy my self.” Ya hau waka yana jujjuya hannun nasa a jikinta cikin wani irin salo. Ji tayi kamar zata fadi, ta rukunkume shi tana dariya jin kamar tafiyar tsutsa yake mata. Hannun nata ya gyara mata sosai ta yadda kirjinta zai gogi nasa wanda dama su suke tsole masa ido tuntuni. ****Ana I gobe zasu dawo, raihana na wanka Aryan kuma ya gama shiryawa suna magana da Kamal akan dawowar tasu da time din da zasu iso Nigeria, fita zasuyi akwai abinda yake son siya mata da ya bari sai yau. Yana gama wayar ta fito ta goge jikinta ta shirya a gauggauce saboda makarar da tayi da kyar ta tashi sai da ya yi ta jan duvet din wani irin bacci take ji me shegen dadi “Yanzu zan shirya.” Tace a gaggauce tana daukar kayan da zata saka, bakar abaya da black jeans sai undies dinta sai shoe and bag “Kina bukatar taimako na!?” “No I can manage.” Tace ta fara zura kayan da sauri “Kiyi a hankali, I can wait.” “Naga time ya tafi ne, baccin ne wallahi da kyar na tashi.” “Na gani ai, yanzu dai ki shirya a hankali kinji? Bari na sauka na dawo.” “Ok.” Tace ya fita, ta karasa zura rigar ta dan Shafa powder da lipstick kadan sannan ta yafa medium veil din abayar. Wayarta ta dauka ta saka a jaka da dan karamin oil perf dinta sai kudin da ya bata jiya da daddare da bata san me zatayi dasu ba ma. Har ta gama shiryawa be dawo ba, sai ta zauna ta ciro wayar tata,ta duba whatspp group dinsu na service taga an fara maganar passing out dinsu har zaa soma rehearsal weekend, cds group din su ta duba nan ma taga information akan final clearance da duk abubuwan da ya kamata su yi. Shigowar sa yasa ta kashe ta maida wayar jaka sannan suka fita hannun sa sarke da nata suka samu cab zuwa Gold and Diamond Park. Sakin baki tayi ganin katafaren wajen da yake cike da manya manyan golds masu girma da kyau. _“Gold and Diamond Park, one of the best place for gold and Diamond shopping in Dubai.”_ Ta karanta abinda yake rubuce a saman. “Ciki zamu shiga?” Tace “Yes, ciki zamu shiga.” Still hannun sa na rike da nata suka shiga ciki, yana tafiya yana duba wayar sa har suka karaso EMAAR. Da kanta kofar ta bude musu suka shiga ciki. Wani katafen shago ne gashi da tsawo iya ganin ka, ita dai raihana kusan yar kauye ta zama dan duk fitar da sukayi a dubai har yau bata gama ganin abubuwa masu kyau da daukar hankali ba. Wani farin balarabe ne ya taso da sauri ya tare su, suka gaisa da Aryan cikin harshen turanci sannan ya nuna masa payment slip dinsa dake cikin wayar, ya san da zuwan su daman dan tun kwana uku suka gama komai ta email sai yau yace su zo su karba. Wani kabattacen waje ma dauke da kujeru da table ya kaisu, ya tambaye su idan suna da bukatar wani abu, Aryan yace no thank you. Excusing kansa yayi ya fita, suka kalli juna da Aryan din duk ta kasa gane abinda yake faruwa, murmushi yayi mata kawai be ce komai ba. Mutumin ne ya sake shigowa bayan yayi musu sallama dauke da wasu boxes masu kyau. Akan table din ya ajiye sannan ya shiga bude shi daya bayan daya. Na farkon da ya bude customized diamond ring ne guda biyu daya an saka R daya A a saman dan stone din. Yayi kyau sosai sai shining yake yi. Mikama Aryan din yayi ya kalla ya ajiye a gabansa sannan ya bude dayan da yake dauke da customized sarka da dan kunne me dauke da A & R. Karba yayi ya gani sannan aka bude sauran da su kuma normal Diamond Necklace me da Earings sai wasu yan kananun box guda dauke da earring dan karami na yara. “Thank you so much, sunyi kyau sosai Alhamdulillah.” “Masha Allah, thank you for your patronage, kamar kace idan kika zo zaku duba golds din ko?” “Yes, madam zata duba wanda yayi mata.” “Ok, Bismillah.” Yace yana nuna musu hanyar. Ya kwashe diamonds suka fito ya bawa wani matashi yayi musu parkaging sannan suka wuce yace ta duba duk wanda yayi mata, rasa me zata ce tayi, ta kasa zaba kuma tayi ta zagaya idan taga kudin da yake jiki sai tayi gaba da sauri, dan duk sun yi masifar tsada, yana biye da ita ganin ta kasa zaba yasa shi zuwa Ya duba mata ya dauka wani me kyau ya mika suka auna, aka fada masa kudin yace ok. Mutuwar tsaye tayi da taji kudin amma shi kamar be san me ake yi ba, suka cire kudin aka hada musu kayan gaba daya suka fito suka nufi gida. Kasancewar basu dade sosai a shop din ba yasa yau bata wani gaji ba, zama tayi a kan sofa din bayan ta sha soya milk da ta ke masifar so tunda suka zo kasar. “Wai dadi take miki ne?” Yace yana zama a kusa da ita yana warware hannun rigar sa da yayo alwala. “Wallahi dadi, har cikin kaina nake ji.” “Lallai, let’s pray toh.” “Uhum uhum, ni sai ta anjima zan yi.” “Look at you, Comman taso muyi sallah.” “Allah ni bacci nake ji, kuma yunwa nake ji.” Fasa tashi yayi yana kallon ta, can biyu ta shanye fa na soya milk din sannan taci chicken wings suna shigo wa. “Wait… are you ok?” “Um, me nayi?” “What’s all this yunwa yunwa?” “Nima ban sani ba, ji nake kawai ina jin yunwa.” “Shisa like adding weight ai, look at your…” ya nuna chest dinta, da suka cika sosai har ta saman rigar ana ganin su. “Nima fa na gani. Ko kumbura nake?” Yace tana zaro ido “Anya?” “Kalli fa?” Tace tana nuna masa. Da sauri ya tashi dan baya son ya bata alwalar sa yace “Bari nayi sallah sai na gani.” Dariya tayi, ta gano sarai dalilin sa. Tashi tayi taje tayo alwalar tazo ta bishi a raaka ta biyu sukayi sallar. Bayan sun idar sun yi addua sai ya juyo yana kallon ta “Bari na gani sosai Yanzu.” Da sauri ta matsa baya “Anki wayon.” “Please mana, so nake na gani ko babu wata matsala.” Ya zama so serious kamar da gaske yake “Allah?” Tace tsoro na kamata “Da gaske, come here let me see.” Matsowa tayi kusa dashi Ya cire mata hijab din yana mata kallon tsaf, ba iya kirjinta ba, hatta waist dinta da fuskar ta sun yi kiba sosai,fuskar ya fara shafawa kafin ya sakko da hannun sa zuwa chest din nata kamar me dubawa da gasken, ganin yana ta jujjuya hannun yana sakè saka shi ciki sosai yasa ta dan ture shi “Wait, ina dubawa ne sosai.” “Tohm, kayi sauri.” “Inaga sai an zare zip din ma, bari kiga.” Ya kama zip din rigar dake jikinta, ta baya ya sauke shi sama, ta nutsu tana jira sai jin hannuwansa tayi ta bayan nata ya zuro su, ya shiga wasa da kirjin nata cikin salon shi da yake rikita dukka tunanin ta. ****Yau ma shi ya fara tashi ya shirya ya hada musu sauran kayan nasu waje daya, sannan ya tashe ta ganin idan ya dakata baccin ta zasu iya missing flight, da kyar ya dagata ya kaita har toilet din sai da taji ruwa a jikinta sannan ta wartsake ya fito ya barta tayi wankan bayan ya gama nazarin wani irin haske da fatar ta tayi kamar babu jini a jikinta. Wajen shiryawar ma sai da ya taimaka mata, tana gamawa da dira akan abinci ta soma ci yana ta lura da ita yana kara tabbatar da signs din da ya duba jiya a google bayan tayi bacci ya na kuma da yakinin hakn ne ma dan duk signs din da akace babu wanda bata yi. Saura kiris su yi mssing flight dinsu dan sune karshe daga su ai rufe jirgin ya tashi, tana langwabe kanta a jikinsa yana dan mammatsa mata hannun ta dake cikin nasa tayi baccin, dan gyara ta yayi yadda zata ji dadi. Ta Adis ababa suka bi daga nan suka taho Nigeria suka sauka da azahar wajen sha biyu. Sun dan dade a ciki wajen clearance da sauran abubuwa sannan suka fito Aryan na rike da matarshi, tun da suka sauka take masa shagwaba ita jikinta ciwo yake haka dai yake ta lallaba ta kamar kwai dan baya son abinda zai taba ta. Hamma hydar, Ammy da Dadah ne suka zo tarar su a gidan su raihanan, daddy baya nan yaje garin su, Ya nabeela da Kamal suna asibiti Khadija zata haihu. Da gudun gaske raihana ta kwasa ta yi wajen su, ta dane Dadah wadda tafi missing akan kowa. “Jama’a kuga raihana ta zama yar lukuta.” Dadah tace tana dariya “Cika min uwata ke, karki karya ta.” Ammy tace tana dariyar itama. Karasowa Aryan yayi Ya gaida ammyn a ladafce cike da nauyi da kunyar ta. Mamakin yadda suka chanja gaba dayan su, suke musamman raihana da tayi wani irin fresh da fari. Kallo daya Dadah tayi mata ta gane abinda yake tattare da ita, ta rike ta kuwa cikin farin ciki suka nufi motar da suka zo. *_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_* *ZAFAFA BIYAR BACTH A* 1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350 *(Bilyn Abdul)* 2.. _KAI MIN HALACCI_ 350 *(Miss xoxo)* 3.. _BURI DAYA_ 350 *(Mamu gee)* 4... _DAURIN BOYE_ 350 *(Huguma)* 5... _SAUYIN KADDARA_ 350 *(Hafsat Rano)* _Duka biyar 1500_ *___________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH B_* 1... _DAURIN GORO_ 350 *(Hafsat Rano)* 2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350 *(Huguma)* 3... _QAUNAR MU_ 350 *(Mamu gee)* 4... _IGIYAR ZATO_ 350 *(Miss xoxo)* 5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH C_* 1... _MIN QALB_ 350 *(Mamu gee)* 2... _SARAN ƁOYE_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _KIBIYAR AJALI_. 350 *(Miss xoxo)* 4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH D_* 1... _ALKIBLA_ 350 *(Huguma)* 2... _DALAAL_ 350 *(Miss xoxo)* 3... _UBAYD MALEEK_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350 *(Hafsat Rano)* 5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350 *(Bilyn Abdull)* _Duk biyar 1500_ *____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH E_* 1... _SO DA ZUCIYA_ 350 *(Mss xoxo)* 2... _TAKUN SAAKA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 3... _HALIN GIRMA_ 350 *(Hafsat Rano)* 4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350 *(Huguma)* 5... _DEEN MARSHALL_ 350 *(Mamu gee)* _Duk biyar 1500_ *______________________________* *_ZAFAFA BIYAR BACTH F_* 1... _BAKAR INUWA_ 350 *(Bilyn Abdull)* 2... _RAYUWAR MACE_ 350 *(Hafsat Rano)* 3... _NOOR ALB_ 350 *(Mamu gee)* 4... _MASARAUTA_ 350 *(Mss xoxo)* 5... _KUFAN WUTA_ 350 *(Huguma)* _Duk biyar 1500_ *_____________________________* *_ZAFAFA BIYAR BATCH G (COMPLETE )_* 1... _FARHATAL QALB_ *(mss xoxo)* 400 2... _GURBIN IDO_ *(Huguma)* 400 3... _SANADIN LABARINA_ *(Hafsat Rano)* 400 4... _INAYAH_ *(Mamu gee)* 400 5... _BABU SO_ *(Bilyn Abdull)* 400 _Kuɗinsu a yanzu 2k duk biyar_ *BATCH F *RUMBUN QAYA🔥 *DAUDAR GORA*🔥 *IDON NERA*🔥 *A RUBUCE TAKE*🔥 *KI KULANI*🔥 *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊 *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 IDAN AN GAMA SU DOCUMENTS DINSU DUK DAYA 400 NE GUDA BIYAR DIN 2k *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta* +227 90 16 59 91 Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!* *Thanks for choosing us*🔥 ***RQ*** Hafsat Rano page 75 Last Page😭 ***Direct asibitin suka wuce, suna zuwa ana fito da Babyn. Raihana ce a gaba wajen riga karbar ta daga hannun gwaggon Khadijan, a rayuwar ta tana balain son yara musamman tunda ta taso Itace karama babu wani yaro da take gani ko ta dauka. Kwakume yar tayi a jikinta wadda tayi mata kama da Aryan dinta sosai zaka rantse da Allah shine ya Haiti babyn. “Raihana bawa kowa ya dau babyn mana.” Ammy tace gani ta rike ta hana kowa, bata ma Ankara ashe rike bbyn tayi ba sai da ammyn tayi magana, a kunyace ta mika ma su Ya nabeela ita, ita kuma ta mikawa ammyn suka daddauka suna mata addua. Aryan yana tare da Kamal dan tun a gate din Asibitin suka hadu ya dawo daga siyo wata allurar (RhoGham) a waje da ake ma duk masu negative Rhesus (Rh negative )na jini wadda aka son ayi ta around 26-28weeks of pregnancy sannan a sake yi within 72hours idan mace ta haihu idan aka tabbatar da babyn Rh positive ne. Da farko asibitin sun zata suna da ita sai da suka duba suka ga basu da ita sannan suka ce yaje ya siyo ta shine abinda ya fitar dashi din har akayi haihuwar baya wajen. Rike da hannun juna suna magana suka karasa ciki, suka wuce wajen nurses din suka basu sannan suka dawo wajen da su Ya nabeelan suke. Ya nabeela ce ta fara hango su, tayi saurin karasawa ta rungume Aryan din, wanda yake ta faman murmushin jin dadin ganin ta “Maman Aryan ni fa?” Kamal yace yana dariya “Matsa nan wa yake ta kai naga boy dina.” “Boy? Wannan sangamemen magidancin katon ne boy?” “Ko shekara nawa Aryan zai a wajena boy ne.” “Hum hmm, lallai zaa sha kunya kuwa kwanan nan, dan nasan kin kusa jin kukan babies.” Yace yana dariya sosai. Shi dai Aryan be ce komai ba, sai hararar Kamal din kawai yake suka karasa wajen da sauran suke ya russuna har kasa ya gaida gwaggon khadija Sannan ya sake gaida su Ammy a karo na biyu. Bbyn aka mika musu yayi saurin karbeta ya riga Kamal din yana kallon kyakkyawar fuskar ta. Lekowa Kamal yayi sai ya rike baki “Kaga kama ko?” Ya nabeela tace “Exactly fa.” “Jini malam.” Yace yana murmushi. “Wannan mommy na ce, ni zan mata huduba.” “Kaine ma babanta ai.” Kamal yace yana dariya Waje aryan din ya samu yayi mata huduba nan take da sunan Nana Khadija, ta zama yar khadija jikar khadija kuma khadija. Sai a sannan ya mikawa Kamal din ita yana cewa “Ba dan halin ka ba.” “Nagode.” Ya karbeta yana kallon fuskar ta. Waigawa Aryan yayi yana neman in da raihana ta shige, bata wajen tunda suka karaso. “Tana ciki wajen mejego.” Sosa keyar sa yayi a kunyace ya bar wajen ya matsa wajen kamal da yake ta kallon babyn. Sai Ya tuna misscarrige din da khadijan tayi a wanchan lokacin, suka shiga yanayi saboda yadda suka kwallafa rai akan babyn, sai gashi Allah ya sake basu. Ya nabeela ya bawa bbyn tace su shiga da ita ciki khadijan ta ganta itama dan bata ganta ba. Cikin dakin suka shiga tare da Aryan, raihana na zaune a gabanta suna magana ita kuma tana kwance ta dan sha wahala sosai ta zubar da jini shiyasa suka dan riketa a cikin ma. Tashi raihana tayi da sauri da suka shigo ta dan buge da kujerar da take kai, da sauri Aryan ya riko ta ganin kamar zata fadi. “Wow… haka kake dama?” Kamal yace yana zama a kujerar da raihanan ta tashi. “Faduwa fa ta kusa yi, Allah Ya Rufa asiri idan ta fadi za’a iya samun matsala.” “Ko? Haka ne kuma gaskia, sannu kanwata ki dinga kula kinji?” “In sha Allahu, ina wuni?” “Lafiya lou, an dawo lafiya?” “Alhamdulillah, an samu karuwa, Allah Ya raya.” “Amin kunyi ‘ya, gata nan dan wayo sai ta kwaso mijinki.” “Ta kyauta ai.” “Ai shikenan.” “Sannu.” Yace ma khadijan yana rike da hannun raihanan, suka gaisa sannan suka juya suka fito suka bar musu dakin dan suna da bukatar kebewa. Suna fitowa ya tsare ta kofar “Let’s go home please.” “Ba’a sallame su ba fa, mu dan jira.” Tace tana satar kallon bangaren da su Ammy suke amma duk basa kallon su wani wajen daban suke kallo “No tafiya zamuyi, kin gaji kina bukatar hutawa.” “I can manage Allah, please mu jira a sallame su.” “A ah, muyi gaba zasu taho daga baya, after wannan long journey din Kina bukatar ki huta sosai, ba ki kara wata gajiyar ba.” “Kai fa? Baka kaji ba?@ “Ni I’m a man.” “Please.” “Noo. Muje kiyi musu sallama.” Marairace fuska tayi, yaki kallon ta yayi gaba, bin sa tayi kamar zata fashe da kuka, bata so ta tafi har ga Allah, wajen su ammyn ya isa yayi musu sallama sannan suka yi gaba shi da Ya nabeela suna magana. Tana karasowa Ammy tace “Ai gwara kuje ku huta, wannan uwar tafiyar haka.” “Ni nafi so mu tafi daku, na dade fa bana nan.” “Kaji min yarinya, kin tashi kin bi mijinki ko sai na buge ki?” “Dadah! Nice fa? Raihanan ki.” “Idan ba zaki bi umarnin mijinki ba, tsaf zan ajiye komai na dumama miki jikinki ehe.” “Kowa baya so na.” Tace wani kuka na taso mata, haka kawai taji kukan kuma ba gaira ba dalili. Basu goya mata baya ba, haka ta tashi suka bita da kallo tana matse kwalla saboda takaici. A jikin mota ta tarar dasu shi da Ya nabeela suna magana, kin kallon ta yayi data karaso dan tunda ta nufo su ya lura kuka tayi. “Sai mun shigo gidan kanwata.” Ya nabeela tace tana matsawa daga jikin motar, shine ya bude mata da kansa ta shiga gaban motar sannan ya zagaya ya bude wajen driver ya shiga ya zauna “Naga kamar an chanja motar nan.” “Itace dai, gyra tasha kasan ni da ita akwai amana.” “Ah gaskia ne. Tayi kyau kuma sosai.” “Nagode, sai mun shigo.” “Ok.” Ya yi ma motar key suka fita daga asibitin. Tunda suka dauki hanyar gidan babu me magana a cikin su, kowa yayi dip shi rigimar tace baya so gashi yana driving baya son raba hankalin sa, ita kuma haushin ta yaki kulata bare tayi masa darun nata. Cika tayi fam ta hau kamar flour wa, ga wani irin rauni da zuciyar ta tayi kamar ta zauna tayi ta zunduma ihu, ta zama so emotional kwanakin nan abu be kai ya kawo ba sai tayi masa kuka, ga saurin fushi wanda da ba haka take ba. “Me zaki ci?” Ya tambaye ta hankalin sa na bisa titi be kallo side din ta ba “Babu komai.” Tace a gajarce. Be sakè magana ba, ya dauki hanyar gidan su kai tsaye, wanda yake so yaga irin gyaran da akayi masa da Ya nabeela tace masa maganar. Tun daga kan layin ya tabbatar da an gyara gidan dan har fenti akayi masa me kyau da tsada. Ita raihana ma bata gane gidan ba sai data ga yayi horn a gate din gidan sannan ta gano. Da sauri Baba maigadi yazo ya bude yana ganin aryan din ya cika da murna da farin ciki, yayi saurin wangale gate din suka shiga harabar gidan da aka kusan sauya mata fasali aka kawata ta da wasu manyan flowers masu girma da kyau. “Sannu da zuwa ranka ya dade.” Baba me gadi da ya karaso yace yana dan dukawa “Baba, barka da gida.” Ya kashe motar ya fito sannan ya mika masa hannu suka yi musabiha, sannan suka sakè gaisawa. Suna gaisawar raihana ta wuce su zuwa ciki bayan tace masa ina wuni a gajarce. Tana shiga ta cire veil din sannan ta zare rigar jikinta ta watsar dukka a falon saman kujera ta wuce ciki da sauri ta shiga toilet ta kunna ma kanta shower, ta saka kuka. A falon ya zauna ya mike kafarsa da tayi masa wani irin nauyi, gajiyar da yake ciki ya duba ya auna da tata yasan definitely ta fishi gajiya gashi baya son wani abu ya faru da ita shiyasa yake kaf kaf da ita har zuwa sanda abinda yake zargin zai tabbata, ya lura sarai da yadda hanata zaman ya bata mata rai ya kuma yi mata uzuri dan ba halin ta bane ba, duk cikin signs din ne dan haka zai lallaba ta a hakan har Allah ya kawo karshen. Jin shiru shiru bata fito ba yasa shi mikewa yabi bayan ta zuwa saman ya hau yana kiran sunan ta, shiru babu alamun tana saman sai ya sauko zuwa bedroom din kasa ya tura kofar ya shiga. A chan saman gadon ya hange ta, tayi dai-dai a saman gadon ta kure ac dakin tana baccin ta hankali kwance. Towel ne kawai a jikinta wanda ya bayyana ilahirin cinyoyinta farare tas. Girgiza kai yayi ya karasa ya gyara mata towel din, sannan ya ja mata kofar ya fita zuwa sama, bayan ya dan lalleka yaga gyaran da akayi ma gidan wanda bashi da maraba da sabo, hatta furnitures da komai an zuba, kayan kitchen da kayan abinci dankare a store. Yana shiga dakin su na saman ya tarar da akwatunan raihanan dozen cif, guda shida golden sai shidan kuma Blue black. Wuce su yayi ya watsa ruwan shima sannan ya zauna ya dauki wayar sa yayi musu Order abinci daga Albaik Restaurant, ya zura slippers ya fita ya samu Baba megadi ya fada masa zaa yi musu delivery ya karba sai ya ajiye ta kofar baya na kitchen din. Ciki ya koma zuwa dakin da take, ya rufe kofar ya saki curtains din ya haye gadon gami da jawo ta jikinsa ya rungume ta, dan shima baccin zai dan yi ko babu yawa. ***Ita ta fara tashi ta zare jikinta wajen laasar, tana mikewa ya farka sai ta kauda kanta da sauri ita a lallai fushi take dashi, dariya ta bashi ya murmushi kawai yana dan kulle idonsa bacci ya sake shi sosai. Fitar ta yasa shi bude idon yabi kofar da kallo, sai ya mike ya shiga toilet din yayo alwala yazo yayi sallah a dakin dan an idar a masallaci, sannan ya fito falon ya tarar da ita, ta saka doguwar riga tana cin abinci, gefen ta ya zauna ta dan matsa ya sake matsowa ta sake matsawa sai ya karbe abincin ya ajiye ya jawota jikinsa. Shar shar shar sai hawaye, “Na banu.” Yace kasa-kasa “Fushi kike dani?” Daga masa kai tayi, ya sa hannun sa ya share mata hawayen fuskar “Ya isa toh, ba zan sake ba. So nake ki huta sosai. Kinga har baccin ki, kika samu kikayi.” “Ni nafi son wajen su Ammy, na dade fa ban gansu ba.” “Ai zaki je, tunda mun dawo sai kin gaji da zuwa ma.” “Ni yau nake so.” “Toh shikenan, anjima da daddare sai muje ko?” “Eh.” Ta gida masa kai “Good girl.” “Bani abincin toh.” “Glut…” da sauri ta kalle shi, sai ya rufe bakin sa ya girgiza kai “Wasa nake ba ke ba, bari na baki a baki Hajiya ta.” Dauko plate din yayi, ya shiga bata a baki tana ci a hankali, ta gama ya bata juice me dan sanyi tasha da ruwa sannan ya zuba nasa shima yaci. ***Da wayo da wayo suka fasa zuwa gidan yau kamar yadda yayi mata alkawari, daddy da Abby ma sai waya sukayi musu suka gaishe su kafin su shigo gobe. Basu san abinda ake shirya musu a gidan ba, basu kuma san yadda komai ya kusan dawo daida ba duk da har yanzu Daddy na ta faman bin Abby akan ya dawo company su cigaba da harkar su tare Amma sam yaki, shi kuma yaki hakura sai mutane yake tura masa amma fafur yaki. Dawowar su Aryan din nan yasa Daddyn yanke shawarar tura ma Abbyn su, su rokar masa shi wala Allah idan su ne ya amince. Apart from wannan komai tare sukeyi ko yaushe kuma suna tare a gida ko a SABUWAR majlisar su da suke zama a kofar gidan Abbyn da daddare suci abinci suyi hira. Yau rana ce ta musamman ga ahalin biyu, ga haihuwar matar kamal ga dan kwarya kwaryan bikin da Daddyn ya shirya ma su raihanan a matsayin murnar auren su da ba’a samu anyi ba, sannan da dawowar familyn nasu waje daya. Casual dress dinsu suka saka shi riga shirt da wando sai pcap da ya dora saboda ranar da ake kwallawa, ita kuma tasa normal doguwar rigar atamfa ta yafa medium veil sai shoe and bag. Da gidan su Aryan din suka fara daga nan sai su wuce gidan ammyn in da zai barta a chan har dare sannan yazo su tafi gidan Kamal su sakè ganin babyn, da shirin kwanan ta a gidan su ta taho ba tare da ya sani ba shi sam, suna zuwa gidan su sai suka tarar da Ammy, Daddy, Abby, Dadah, Kamal, Lamido, Sadeeq, hydar, Ya Nabeela a gidan suna jiran isowar su. Dadi kamar zai kashe raihana, ta rasa in da zata saka kanta saboda farin ciki, a babban falon suka taru dukkanin su, akayi ma Mommy addua sannan Abby ya fara magana akan hadin kansu da yarda da juna, ya gama Daddy ma yayi nasa ammy dai tace ba sai tace komai ba, daga nan ne kuma su matan suka shiga ciki suka bar mazan a falo in da suka zauna zaman cin abinci masu rai da lafiya, ana ci ana hira tsakanin iayyen biyu sai suma mazan suna nasu daga gefe, maganar auren Hydar da Lamido suke tattaunawa wanda har an saka date shi sadeeq tasa bata kasar tana Jordan tana karatu amma ta kusa kammalawa shisa aka daga nasa zuwa sanda zata dawo. Dama shi ba gwanin magana bane sosai he’s cool bashi da hayaniya ko kadan. Hydar ne dama me magana ma a cikin su dan Lamido ma kusan hakan yake, sai ya zama kamal da hydar ne kawai ke rike da wajen su sauran sai eh da a ah sai yar magana wadda bata cika wani tsawo ba. Har dare dukkanin su suna tare, hakan ya kara shakuwa sosai tsakanin su, wanda suka yanke zaa dinga irin zaman haka duk karshen wata aji uzurin juna da damuwar juna. Da aka zo zaa watse daddy yace yana da magana, anan ya sake bijirowa da Abby da hydar tayin dawowa su cigaba da Aiki tare, tunda shi Lamido aikin sa babba ne haka ma babbo sadeeq likita ne a babban asibiti sai dai idan yana da bukatar transfer wanda bashi da ma raayi chan ya saba chan zai zauna dama kuma Dadah ta kusa tattarawa ta koma gida shikenan bashi da matsala tunda akwai Dadan su. Idanun yaran ya hana Abby sakè rejecting offer din Daddyn amma har ga Allah be so ba, yaso ace ya barshi kawai hakan ma ya ishe shi, amma idan yaki sai yaran su ga kamar be yafe abinda ya faru bane ba. “Shikenan Allah ya kauda fitina a tsakani.” “Alhamdulillah, naji dadi sosai aminina. Nagode sosai.” “Hydar fa?” “Eh toh, gashi nan a zaune, dama shi Yarinyar da zai aura yar kanwar ammyn su ce, amina. Idan yaga zai tattaro ya dawo nan din gaba daya saboda karatunta ma toh, idan kuma ya zabi chan ba zamuyi masa dole ba.” “Zai dawo ma.” Aryan yace kai tsaye kamar shi aka tambaya “Waye Ya amsa ne wai?” Daddy yace yana kallon su “Aryan ne.” “Barshi daddy, ya ari baki na ya ci min albasa,Allah ya tabbatar mana da allhairi.” “Toh Amin Amin.” Su Abby ne suka fara tafiya tare da Hydar da Babbo Sadeeq , Lamido kuma ya dauki ammy da dadah. Raihana kamar tace zata bisu amma sai ta daure, ta buya ta share kwallarta. A Yanzu ne yake da bukatar zama tare da yan uwanta da iyayenta. A tare irin zaman da suka rasa a baya, amma bata so ta nuna damuwar ta a fili ga Daddy ga Ya nabeela. Dole ta shanye suka yi musu sallama suka tafi. Duk da dare ya fara yi sai da suka je gidan Kamal din, suka ajiye shi sannan suka sakè ganin baby sannan suka tafi. Dakin da akwatunan suke ya jata, kadan ya rage ta sangame saboda tsabar mamaki, zaunar da ita yayi ya shiga bude mata su daya bayan daya tana kalla, tun tana zaune har ta mike ta sake zaunawa ta rasa ina zata saka kanta saboda tsabar farin ciki Kwana hudu da fara azumi ta soma laulayi na sosai, wanda har sai da ta kwanta a asibiti aka sa mata drip saboda galabaitar da take yi wajen amai. *****Bayan Wani Lokaci🤪 Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Allah, komai yayi farko dama zai yi karshe, sannan duk nisan jifa kasa zai fado. Rayuwa ta sauya sosai a familyn Nasir Matawalle da amini shakikin sa IBRAHIM Mukaddas, kamar yadda suke a shekarun baya hakan ma yanzu suke , sun sake dinkewa koman su tare su ke yi, sannan yaran su sun zama yan uwan juna tamkar yadda suke a dah, kowa Ya dauki uzurin kowa ya dora a bisa kansa, duk abinda ya shafi daya ya shafi dukkansu. Suna matukar girmama juna da kaunar junan su. Hydar, Lamido da sadeeq duk sun yi auren su, suna zaune lafiya da matayansu gwanin shaawa basu wata Matsala haka kamal da matar shi. Haka uwar gayya Ya nabeela da nata familyn itama. Abby da ammyn sun dawo kusa da Daddy ga gida ga gida kamar yadda suke a da, tsohon gidan su raihanan kuma wanda yake jikin gidan su na yanzu Kamal ne da Hydar aka gyara musu shi aka fitar ma kowa da part dinsa daban da gate dinsa suke zaune, hakan ya kara shakuwar su ya kuma dawo da tsohuwar abota tsakanin hydar da Aryan dan kullum suna tare a gida ko a Office. A bangaren Adam, ya fito bayan daddy ya yi magana da Lamido akan akan case din an kuma duba laifin nasa an hukuntashi daidai da laifin sa sannan ya biya tara wadda Daddyn ne ya biya. Haka shima Muhammad akayi da Zainab aka kaisu court aka yanke musu hukuncin su daidai da laifin da suka aikata. Ita kuwa me gayya me aiki, uwar mugaye da tsinannu duniya ta gamu da daidai da abinda ta aikata domin sai da aka sake mata aikin kafar aka sakè yanke ta har zuwa cinya Ya zama baki daya bata da kafa kwata kwata, ga haukan da ya sake mata karfi sosai daga Akth din dawanau aka wuce da ita aka bata daki ita kadai saboda yadda take fizgar gashin kanta da yadda take yaga kayan da duk aka saka mata tana surutai tana tonawa kanta asiirin abinta ta aikata a baya, sau daya Aryan suka je da raihana suka ganta Raihana sai da tayi kuka shi kuwa Aryan ko gezau zuciyar shi ta riga ta bushe. Shi dai tunda burin sa ya cika dan hatta barrister din nan da sukayi aiki tare da Hajiya zeenat din sai da aka kamo shi aka yanke masa hukunci daidai dashi. Zuwan Aryan ya sake rikitata, ta dinga kiran sunan sa tana cizgar gashin kanta, daga ranar aka hana kowa ma zuwa ganin ta. ******Tana tsaye a jikin sink din kitchen tana wanke bowl din cereal din Hanan, suka shigo ya doro ta a saman kafadar sa tana ta yi masa gwaranci. Dogon wando cotton ne a jikin sa babu ko riga suka shigo kitchen din ya dora Hanan a saman cabinet din kitchen din ya riko kugun raihanan ya juyo da ita suka saka dariya a tare “Kai da yarinyar ka kun fiye rigima wallahi, ina zaman zama na kun sani Aiki.” “Ya zaki damu? Umm?” “Bada sadakar ku zanyi na huta kawai.” “Ke Babyna, Yanzu zaki iya bada mu sadaka? Kalle mu fa, innocent babies dinki.” “Ga shi nan ai, face dinka ne da ita. Ku narke ma mutum ido ko be niyyar abu ba yayi muku.” “Eh Munji, Yanzu dai a bamu abincin mu, idan kuma muka ga dama muce a mana wani daban.” “Allah ya baku hakuri, tasha friso din yanzu dai.” “Nifa me zaki bani?” “Ko zaka sha oat?” “Um um, ni sai dai ki bani wannan.” Ya nuna kirjin ta, “Kana da matsala.” Tayi saurin daukar gwangwanin friso din da bowl din ta zame ta barshi a tsaye yana mata dariya. Daukar yar su yayi suka koma falo still yana dariya a hankali. Ta fito ta ajiye masa bowl din a gabansa tasa spoon tace “Gashi nan.” “Mun gode Mamin mu.” Ya kwaikwayi karamar murya ya fada, murmushi tayi ya mayar mata, tayi hanyar bedroom dinsu tana cigaba da murmushin Alhamdulillah!!! Dukkan godiya ta tabbata da Allah ubangiji, da ya bani ikon kammala wannan littafin wanda ya ja ni har zuwa in da ban yi zato ko tsammani ba, ina rokon dukkannin wanda na batawa da ya yafe min, ina kuma fatan kun amfana da wani Darasi a ciki komai kankantar sa Duk abinda kuka gani na kuskure ku dauke shi a matsayin ajizanci na dan Adam. Allah ya shirya mana zuri’ah ya raba mu da sharrin masu sharri, ya hada mu da masu son mu na gaskiya ya yafe mana zunuban mu. Sai watarana idan allah ya Kaddara saduwar mu. Nagode Nagode Nagode. Zafafa biyar na matukar godiya. Na yafe ma duk wanda Ya bata min. Ma’assalam. Rano😍 Downloaded From https://tknovels.com.ng