Downloaded From https://tknovels.com.ng *EL--HABEEB*💥 ©️Oum Hanan *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) Bismillahir Rahmanir Raheem. Da sunan ALLAH mai rahma mai jin k'ai tsira da amincin ALLAH su k'ara tabbata ga shugaban mu ANNABI MUHAMMAD sallallahu alaihi wa alihi wasallam. Yadda nafara wannan book din lafiya ALLAH ya bani ikon gamawa lafiya. Duk wanda yaci karo da wani gyara ko kuskure a cikin book din nan ya nemeni ta wannan number 09139964697 k'ofa a bud'e take nagode. Writer of *DANA SANI* *SURAYYAH* *NIDA YAH SAYYADINMU* *HAD'IN ALLAH* *D'AN BASAJA* *KAUTHAR* *DR SAIF* *KALLON KITSE* *WATA SOYAYYAH* No 1. Shimfid'a. Kwanciyar shi ya k'ara gyarawa a faffad'an gadon nashi wanda yaji tausasan shimfid'u na alfarma a karo na ba adadi yana k'ara k'ank'ame pillown dake rungume a k'irjinshi cikeda shauk'in samun nasarar dayayi a yau d'in nan zata bud'e masa fuskarta yagani, har wani tsuma yake yana sakin lallausar murmushi akan kyakkyawar fuskarshi tareda k'ara ware manyan manyan idanunshi dan yaji dad'in ganin fuskar tata saidai kash kafin takai ga bud'ewar kamar wanda aka mintsina yayi saurin tashi daga nannauyan barcin dayake zumbur ya tashi zaune yana wuwwurga idanunshi gefe da gefenshi dako ina na d'akin tamkar wanda yake neman wani abu. Kanshi ya dafe da duka hannaye biyun cikeda b'acin rai tareda rufe idanunshi gam yana sauke numfashi wannan masifa dame tai kama? ace sama da shekara biyar yana wannan mafarkin daya rasa ta inama zai fassara shi kullum ta ALLAH saidai idan bai kwanta ya rufe Ido da sunan yin barci ba ya zamar masa kamar k'aidah ne idan baiyiba bayajin dad'i abin ya zamar masa bala'i ya rasa ta inda zai b'ullowa al'amarin shin wannan yarinyar dake zuwa masa wacece ita? meye alak'arta dashi datake addabar rayuwarshi haka? a ina take? a ina zai ganta? matacciya ce ko rayyaya? meyasa take zuwa masa cikin barcinshi ta hanashi sukuni? tarin tambayoyin da har yagaji dayiwa kanshi su batare da har yanzu yasamu amsarsu ba to waye ma zai amsa masa su? bayan ba wanda yasan yanayin mafarkin, sosai yake k'ara hango kyawawan idanun yarinyar wanda su kadaine suka bayyana a fuskarta sai tudun dogon hancinta da shima ya kasa b'oyuwa ta cikin bak'in mayafin data rufe fuskar tata dashi. Wasu irin idanuwa ne farare k'al masu mugun kyau da shek'i ga wani k'yalli da cikin k'wayar idanun nata keyi kamar wadda hawaye suka fara tarar mata a ido, dad'in dad'awa kuma yanayin shape d'in idanun nata da bai tab'a ganin makamantan su ba saboda yadda ubangiji ya tsara mata su. A hankali ya bud'e idanunshi da launinsu ya d'an fara canzawa kad'an cikeda damuwa ya sauka daga kan gadon ya nufi wata k'ofa wadda nake kyautata zaton bathroom ne dama boxer ne kawai a jikinshi hakan yasa kai tsaye ya wuce ciki da alamu wanka zaiyi. Mintuna k'alilan ya fito daga bathroom d'in ya d'aure k'ugunshi da babban towel sai k'arami dake saman kanshi wanda yake goge sumar kanshi zuwa fuskarshi da cikin kunnuwan shi, wajen k'aton mirror dake cikin bedroom d'in ya nufa wanda yake shak'e taf da manya manyan turaruka masu masifar k'amshi da mayuka masu matuk'ar tsada sama sama ya shafa lotion ya taje lallausar sumar kanshi da zagayayyen gemunshi ya shafa musu mai sannan ya nufi wata k'atuwar clothed ta jikin bango wadda ta kusan mamaye duka bangon ya bud'e kayane gasu nan iya ganin mutum shaddoji ne voil, yadika, suits da sauran k'ananun kaya na kamfanunuwa kala kala da sukayi fice a duniya, jeans ya d'auko dark blue da riga body hook mara nauyi light blue ya shirya cikinsu sosai kayan sukayi mugun amsarshi wajen takalma yaje wanda suma gasu nan lodi lodi tamkar shagon siyar dasu farin boot ya d'auka ya zauna gefen tamfatsetsen gadon ya saka yaje wajen ajiyar agoguna ya d'auki wani bak'i k'irar kamfanin Gucci ya d'aura, wajen mirror yakoma ya feshe jikinshi da sanyayan turaruka masu matuk'ar k'amshi da sanyaya zuciya daga nan ya fice daga bedroom d'in bayan ya d'auki wayoyinshi. Kai tsaye cikin gidan ya nufa dan yasan Ummi nacan na jiranshi musamman yau daya d'anyi late ba kamar lokacin daya saba shiga gidan ba da safe. Da sallama ya shiga makeken falon wanda yaji kayan k'awa masu tsada tako ina sai k'yalli da walwali yake ga k'amshin turarukan wuta had'i da air freshener spray da aka k'ara dashi. Cikakkiyar dattijuwa mai cikar kamala na hango kan d'aya daga cikin kujerun falon tasha adonta cikin wani dakakken lace blue black da torch d'in pink na fulawoyi wuyanta da kunnenta zuwa hannayenta sunsha gwala gwalai sai faman walwali suke, kallo d'aya zakayi mata kaga tsantsar kamannin su da wannan saurayin daya shigo babu ta inda ya barota daga zaunen datake zaka iya ganin tsayin datake dashi kamar yadda shima yake dogo sosai har d'an rank'wafawa yayi daga sama. Tun shigowarshi falon fuskar matar ta washe da fara'a shima dolenshi ya d'an saki fuskar sakamakon da datake a d'inke ya had'e gabas da yamma, wajenta ya k'arasa ya tsuguna har k'asa yafara gaisheta cikin sakin fuska ta amsa masa tana shafa kanshi sai yaji duk tarin damuwar dayake ciki game da irin mafarkan dayake ta fara raguwa a hankali yace "Ummi zan fita ayi mana addu'a". "Breakfast d'in fa?". tace tana kallonshi tana k'ara nazarin yaron nata kamar yanada damuwa. Fuska kawai ya d'an yatsina yana girgiza kai yace "Banajin zan iya cin komai yanzu Ummi kawai zan fita zansamu abinda zanci acan". Sosai ta b'ata rai tace "Ban yardaba sam, halinka ne ban saniba? kokuwa yau ka fara fad'ar haka kuma har kaje ka dawo baka sawa cikinka komai ba? meyasa kake son yin wasa da cikinka ne mai babban suna?". Shagwab'e mata fuska yayi yana shirin yin magana ta dakatar dashi ta tashi tsaye tareda rik'o hannunshi batare datayi magana ba ta bayan kujerar datake sukabi suka nufi dinning area shidai yana biye da ita har suka k'arasa k'aton dinning table d'in daya gaji da had'uwa wanda aka cikashi da warmer's kala kala masu muguwar tsada da plates da cups duk masu kyau da sauran kayayyakin da ake ajiyewa a dinning d'aya daga cikin kujerun dinning d'in taja masa ya zauna da kanta tayi saving d'inshi ta tura masa plate d'in gabanshi da mug da aka had'a tea mai kauri wanda yaji kayan k'amshi da na'a na'a da sauran had'in da larabawa sukeyiwa shayi sai tashin k'amshi yake, fuska ya shasshake yana kallon Ummi ganin babu alamun wasa saman fuskarta sam yasa baima fara yin magana ba ya maida kallonshi kan abinda ke gabanshi dan dole zaici abincin nan jin cikinshi yake duk a wani cunkushe ba dad'i bai sha'awar sa masa komai sosai mafarkin nan yafara tsaya masa cikin ranshi yarasa kuma ta yadda zai b'ullowa al'amarin gashi bayaso kowa yasani. Kujera Ummi taja itama ta zauna kusa dashi tana fad'in "Saikace wani k'aramin yaro kullum sai anyi fama dakai wajen cin abinci kafi kowa sanin yadda kake matuk'ar shan wahala idan ulcer d'inka ta tashi amma bazaka dinga kiyayewa ba". "I'm sorry Ummi zanci fa". yayi maganar yana b'ata rai kamar mai shirin sakin kuka shifa hidimarshi ma tafi k'arfin shi dan haka yake ganin tsayawa ma cin abincin kamar b'ata lokaci ne shiyasa saiya kusan yini da yunwa a cikinshi sai coffee da ako yaushe yake d'irkawa cikinshi. Kan dole yafara tura abincin ganin yadda Ummi ta kasa ta tsare ba alamar ma zata bar wajen bare yayi sharp sharp ya tashi, bai wani ci dayawa ba ya ture mug da plate d'in daga gabanshi ya yagi tissue ya mik'e tsaye yana goge bakinshi da hannu d'aya d'ayan kuma yana k'ok'arin d'aukar wayoyinshi dake zube kan table d'in. "Oyaa koma ka zauna". cewar Ummi tana kallonshi. Sosai ya marairaice mata ya wani langab'e kai yace "Please Umminah I'm full wllhy ALLAH bansan ina zansa sauran ba kinji". ya k'are maganar yana d'an tura baki gaba. Kamar zatayi magana kuma saita fasa ta girgiza kai kawai tare da fad'in "To ai shikenan ALLAH ya kiyaye yabada sa'a". Murmushi yayi kad'an wanda ba lallai ma mutum ya fahimci murmushin yayi ba saboda yadda suka tsaya iya labb'anshi kawai cikeda jin dad'in addu'ar yace "Amin Amin Ummi thank you so much". ya k'arasa maganar yana sakar mata kiss a gefen kuncinta ya nufi k'ofar fita daga falon da kallo ta bishi har ya fice daga falon cikin zuciyarta tana k'ara bin yaron nata da kyawawan addu'oe. Tun fitowarshi harabar gidan bodyguard d'inshi suka fara d'iban gaisuwa hannu kawai ya d'aga musu ya shige dank'areriyar motarshi wadda dama already an riga an bud'e masa tun kafin ya k'araso. D'aya daga cikin motocin ne tafara fita bayan an bud'e k'aton gate d'in gidan sai wadda yake ciki ta take mata baya saikuma wata guda d'aya data biyo bayan wadda yake ciki suka shilla kan titin unguwar wanda yake kamar an shareshi saboda rashin mutane da motoci. Shi kad'aine a bayan motar ya lafe a bayan sit d'in idanunshi a lumshe ya lula can duniyar tunani kan irin mafarkin dayake tunani yake ya fad'awa Ummi ko Mujaheed babban amininshi kokuwa dai yayi shiru da bakinshi abin yana matuk'ar cimasa tuwo a k'warya yanaso ya samu mafita to ta ina mafitar zatazo masa ma? bai saniba yana rok'on ALLAH dai ya yaye masa dukkan wani duhu daya baibayeshi. *H. I .A GASHUA ENTERPRISES LIMITED* Sunan dana gani kenan manne daga gaban companyn bayan shigarsu wanda yadda aka rubuta sunan ma kad'ai abin kallo ne da yadda aka tsarashi. Har akayi parking a cikin harabar k'aton companyn wanda yayi mugun had'uwa yaji glasses tako ina ko cikinshi ba'a gani bai bud'e ido ba saida aka bud'e k'ofar motar sannan ya bud'e idonshi da suka d'anyi ja k'afafunshi yafara zurowa kafin gangar jikinshi ta biyo baya saida ya daidaita tsayuwarshi sannan ya shiga takawa cikin sauri da kazar kazar irin na mai wadatacciyar lafiya da ubangiji ya hore masa ita sauran suka rufa masa baya. Tunda ya shiga cikin companyn ma'aikata keta faman mik'o gaisuwa da hannu kawai yake amsawa batare dayace komi ba wanda sun riga da sun saba da yanayin amsa gaisuwar tashi dan haka ba wanda ya damu suka cigaba da ayyukan gabansu. Maryam Ibraheem Aleeyu (Ummee) Mrs Salees Mu'az 💝 *EL--HABEEB*💥 *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) ©️Oum Hanan. No 2. Daga inda zai hau lifter ta kaishi 2nd floor inda office d'inshi yake suka rabu dasu bayan sun bashi briefcase d'inshi. K'aton office ne mai girman gaske wanda aka k'awatashi da duk wasu nau'ikan kayan k'awa da akeyin ado dasu a office k'amshi kawai yake zubawa da k'yalli tako ina saboda gyaran dayasha, wani d'an k'aramin katako ne wanda shima akayi masa wani irin fenti mai kyau aka k'awatashi da tambarin sunanshi ajiki wato *HABEEB IBRAHEEM AHMAD GASHUA* daga k'asan sunan nashi aka rubuta matsayin shi a kamfanin wato _GENERAL MANAGER_. Had'add'iyar office chair d'inshi wadda take har yanzu a ledarta kamar yaune aka ajiyeta ya nufa ya zauna bayan yayi bismillah wanda ya zame masa k'aidah kullum sai yayi kafin ya zauna k'asa ya d'anyi da kanshi ya dafe goshinshi da hannu d'aya d'ayan kuma ya shiga d'an bubbuga table d'in da pen d'in daya d'auka bayan zamanshi kujerar ta shiga jujjuyawa dashi tarin ayyuka ne a gabanshi saboda shirye shiryen bud'e wani sabon company da babban kamfanin nasu zaiyi na sarrafa fata shiyasa a y'an kwanakin bashida tsugun koyaushe yana busy hakan nema ya k'ara rage masa tunanin yarinyar shi ta mafarki sai yau kuma da abin yadawo sabo fil. Knocking akayi daga bakin k'ofar "Yes coming". yace a hankali tamkar mai ciwon baki cikin daddad'an sound d'inshi da ubangiji ya azurta shi da ita batare daya bud'e idonshi ba koya daina jujjuyawa kan kujerar ba, wani kyakkyawan saurayi ne dogo ya matse cikin suit light blue da tarin files files a hannunshi ya shiga office d'in "Mazajeeeee". wannan saurayin ya fad'a yana zube tulin file's d'in bisa table tareda jan kujera ya zauna fuskarshi d'auke da fara'a, cak ya tsaya da juyawar dayake yaja siririn tsaki tareda bud'e idanunshi ya sakarwa wannan saurayin harara a hankali kamar mai tsoron yin magana yace "Matsalata dakai kenan hauka MJ ya zaka shigomin office ba sallama saikace ba musulmi ba". "Oh shiiit wllhy na sha'afa ne". Mujaheed yace yana d'an dukan goshinshi, idanunshi ya k'ara mayarwa ya rufe batare dayace komi ba murmushi MJ yayi yana kama kunnuwanshi da duka hannayenshi yace "Afwan abokina kaina bisa wuya salamu alaikum". zamanshi ya gyara yana amsa sallamar ya mik'awa MJ hannu kamar yadda shima ya mik'o masa alamun suyi musabaha, takardun MJ ya janyo gabanshi da nufin fara yimasa bayani saiyaga yayi relaxing kan kujerar ya d'aga kanshi sama yana kallon roofing office d'in wanda ya wadatu da fitilu masu kyau da tsari, ido kawai MJ ya k'ura masa yana nazarinshi alamu sun nuna abokin nashi kuma d'an uwanshi yana cikin damuwa zamanshi ya k'ara gyarawa yace "Hey Mr Gashua what's wrong with u? uhmm akwai matsala ne?". "Nothing". Habeeb Gashua yabashi amsa a yadda yake batare daya d'ago kaiba, kai MJ ya girgiza yana fad'in "No is possible kanada damuwa Gashua fad'amin menene?". "Nace babu komai MJ please ka k'yaleni haka mana". Wani d'an murmushi MJ yayi alamun bai yarda da maganar daya fad'a ba yace "Nikuma nace akwai wani abu ba yau nafara ganinka ba Gashua na sanka farin sani duk da dai dama kullum cikin k'unci da takurawa kanka kake amma tarayyarmu dakai da dad'ewar da mukayi da juna yasa a hakan nake iya gane farin cikinka da akasin hakan please tell me what's problem.......A fusace Habeeb ya d'ago kanshi har yana d'an dukan table d'in gabanshi yace "Nace maka ba komai ba komai har sau nawa kakeso in maimaita maka ne kurma ne kai ko makaho? zaka dameni ko maye ne kai ban saniba?". Dariya ma yaba MJ ya d'an dara tare da fad'in "Maye ne mana amma ban fara cin mutane ba wai kodai duk rashin mace a kusa dakai ne yake kawo hakan?". Harara ya dalla masa yaja wani dogon tsaki ya janyo takardun da MJ yazo dasu yana fad'in "Mahaukaci kawai". Dariya MJ ya k'yalk'yale da ita hakan ya k'ara fusata Habeeb a hasale yace "Zaka tsaya kayi min bayanin abinda ya kawoka kokuma dariyar zaka tsaya yi?". Gimtse dariyar yayi ya tattara nutsuwarshi suka shiga yin abinda ya baroshi daga nashi office d'in. Sun d'an d'auki lokaci a tare sannan MJ ya tashi ya tattara takardun zai koma dasu office d'inshi tsayawa yayi ya kalli Habeeb zai k'ara yimasa wani iya shegen yaga yaci serious ya tamke fuskar nan tam yaci d'aci tamkar wanda bai tab'a yin dariya ba murmushi kawai MJ yayi ya fice daga office d'in batare dayace komi ba kuma bawai dan murtukewar da Habeeb d'in yayi ba sai dan tarin ayyukan dake a gabanshi wanda yakeso ya kammala a yau idan ya tsaya kuma zai b'ata lokacin shi anan. Numfashi ya sauke tareda lumshe ido bayan fitar MJ yanajin tamkar ya kirashi ya fad'a masa damuwarshi ko zaiji sanyi a zuciyarshi idan ya fitar da abinda ke cikin ranshi bayaso lamarin nan ya shafi aikinshi gashi kuma abin ya fara worsted dannewar dayake yi ada tana neman gagara a yanzu. Tsayin mintuna kusan ashirin ya d'auka a haka daga bisani ya tashi ya nufi inda coffee machine yake ya zuba a mug yadawo tsakiyar office d'in inda aka k'awatashi da leather chair milk color kalar fentin office d'in da glass table a tsakiyarsu, bisa 2sitter ya zube ya shiga shan coffee'n duk kuwa da irin zafin dayake dashi haka ya dinga sha yana lumshe ido. A tak'aice dai a wannan yinin ranar ba wani abin kirki daya tsinana a office d'in har lokacin tashi yayi ya tafi gida. Flashback. GASHUA'S FAMILY. Tun asalin ahalin masu arzik'i ne wanda suka gaje shi tun iyaye da kakanni tun lokacin ma arzik'in na noma da kiwo ne da sauran nau'ikan abubuwa da mutanen da suka dogara dashi ta hanyar cin abincinsu. Malam Ahmad da inna Karime sune iyayen Ibraheem wanda shiya kasance d'a na uku a gurin iyayenshi akwai maza biyu kafin shi Sulaiman da Adam saikuma mata hud'u dake binshi dukansu dai su bakwai ALLAH ya azurta Malam Ahmad dasu sun tsaya tsayin daka wajen ganin sun basu cikakkiyar kulawa tarbiyya ilmin addini dana zamani sannan mazan duk wanda ya taso zai nuna masa kasuwanci dan haka suka taso masu neman na kansu ga kuma ilmin suna kan nema. Adam da Sulaiman tare sukayi aure lokaci d'aya dan dama tsiransu a haihuwa bawani mai yawa bane, Ibraheem kuwa saidaya dad'e sosai baiyi aure ba yanata bawa biro da takarda hakk'insu da neman kud'i har Malam Ahmad ya gaji dasa masa ido ya magantu ganin bashida alamar yi ko maganar ma bayayi dama kuma shi kad'ai ya rage a gidan sauran k'annen nashi mata duk sunyi aure, wata tafiya da zaiyi Dubai kan harkokin kasuwancin Malam Ahmad yace yana dawowa koya nemi yarinyar dazai aura kokuma shi ya nema masa cikin dangi da abokan arzik'i yace to insha ALLAH yana dawowa zai duba matar aure ashe matar auren ce ke kiranshi acan Dubai d'in dan yana zuwa kwananshi biyu ya had'u da wata yarinya balarabiya mai suna AFEEFAH mazauna k'asar Dubai d'in ALLAH ya d'ora masa masifar sonta lokaci d'aya yasha matuk'ar wahala kafin ma yasamu ganinta dan irin gidan nan ne masu mugun tsaro wancan ganin nata ma dayayi har yaji yana sonta sa'a yaci da kuma ubangiji daya rubuta itace matarshi kuma uwar y'ay'anshi. Gani d'aya tayi masa itama taji ya kwanta mata sosai cikin ranta duk ya fiye mata samarin larabawan nan dake kai mata hari kasancewar ta kyakkyawar gaske dama ance SO GAMON JINI. Ta guri d'aya suka samu mishkila a soyayyar tasu wato iyayen Afeefah musamman mahaifinta Habeeb Al-Hussain a ganinsu idan suka bari ya aureta zai tafi da ita k'asarshi ya rabasu da ita gashi dama yara biyu kawai ALLAH ya basu daga ita sai k'aninta Muhseen. Da k'yar da k'yar aka samu suka amince ya aureta amma sun kafa mashi sharad'in saidai yadawo Dubai d'in da zama gaba d'aya dan bazasu iya nisa da yarinyar su ba kai tsaye ya amince batare da wani dogon tunani ba saboda soyayya data rufe masa ido a lokacin burinshi kawai yaga ya mallaketa a matsayin matarshi, ALLAH ALLAH ya dinga yi ya kammala abinda ya kaishi yabaro k'asar yaje yasamu iyayenshi da maganar yana kammalawa kuwa ko kwana d'aya bai k'ara yi a k'asar ba ya dira 9ja cikeda zumud'in zaijewa da iyayenshi labari mai dad'i na samun matar aure. Bayan dawowar shi ya sanar dasu abinda ke tafe dashi yasamu matar aure balarabiya, Malam Ahmad bai wani ja da tsayi ba ya amince tareda sawa lamarin albarka amma koda yaji maganar Ibraheem ta k'arshe ta saidai yakoma can da zama gaba d'aya anan fa Malam Ahmad ya tubure yace sam bazai yiwuba bai amince ba idan har zai aureta to kuwa saidai su dawo Nigeria su zauna anan bawata k'asa da zaibi wata y'a mace hankalin Ibraheem ya tashi sosai ga waya da Afeefah ke masa akai akai tana k'ara jaddada masa irin son datake masa taji shiru kuma har yanzu bawani labari dan ALLAH karya gujeta ya taimaka yadawo gareta, hakan ba k'aramin k'ara d'aga hankalin Ibraheem yayi ba ya cigaba da bin Malam Ahmad da magiya da rok'on ya k'yaleshi har mutanen da Malam Ahmad d'in yake ganin mutuncinsu duk ya had'ashi dasu amma fur Malam Ahmad yak'i amincewa k'arshe dai da Ibraheem yaga haka saiya yanke shawarar tafiya batare da yardar mahaifin nashi ba dan haka ya tattara duk wasu muhimman abubuwan shi na harkar kasuwancin dayake yayi hayar wasu mutane daga nan suka tafi Dubai nema masa auren Afeefah. Ba b'ata lokaci kuwa akayi komai aka gama yayi k'ok'arin yin duk wasu al'adunsu wanda saida jarinshi ya girgiza saboda yadda tsarin neman auren nasu yake akwai kashe kud'i amma dayake SO ya rufe masa ido yasa duk baiji k'yashin yin komaiba kuma ko d'ar baiyiba wajen yinsu saboda ALLAH yayi masa lud'ufi cikin sana'ar shi arzik'inshi kuma a lokacin yafara hab'aka sosai kuma a yadda yakejin zuciyarshi koda bashida komai ma zaisan duk hanyar dazai bi yasamu abinda zai mallaki Afeefah dashi. Daga can kuma gida Nigeria Malam Ahmad da sauran ahalin gidan suna cikin damuwa da rashin jin dad'in abinda Ibraheem yayi Yaya Sulaiman da Yaya Adam sunso binshi Malam Ahmad ya hanasu yace su k'yaleshi kawai a yanzu koda sunje bazai sauraresu ba saboda giyar soyayya na d'ibanshi kuma bazai yimasa baki ba koya furta wata magana marar dad'i a kanshi ba. Maryam Ibraheem Aleeyu💝 *EL--HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 3. Yasani komai daren dad'ewa zai nemesu dan haka kullum cikin kwantarwa da mahaifiyarsu hankali yake saboda yadda ta d'aga hankalinta sosai gani take tamkar shikenan fa d'anta ya tafi kenan bazai k'ara waiwayar gida ba daga k'arshe tasawa zuciyarta dangana ta cigaba da binshi da addu'ar ALLAH ya kare mata shi a ko ina yake a matsayinsu na iyaye wanda ko yaya suka furta kalma mara dad'i a kanshi saita bishi ta nakasta rayuwar shi bai kamata suyiwa yaronsu mugun baki ba ya k'ara lalacewa. Sosai akasha shagalin bikin Ibraheem Ahmad Gashua da Afeefah Habeeb Al-Hussain naira tayi kuka kasancewar harkar ta masu arzik'i ce dan shima mahaifin Afeefah mai kud'i ne sosai. Bayan kwanakin da aka d'iba ana shan shagalin biki amarya ta tare a gidanta na wani abokin kasuwancin shi balarabe daya bashi aro kafin ya mallaki nashi plat house ne wanda aka b'ata lokaci wajen tsarashi kuma ya tsarun an k'ayatashi sosai. Nan fa aka shiga cin amarci kowa yana k'ok'arin farantawa d'an uwanshi rai da nuna irin tsantsar soyayyar da sukewa junansu Afeefah na shan kulawa da tarairaya tsabarsu a wajen Ibraheem duk abinda yasan zai faranta mata shiyake yi haka itama a nata b'angaren. Shekarar su d'aya da aure ALLAH ya bata ciki kuma har lokacin bai tab'a tunanin waiwayar gida ba kuma ko sau d'aya bai tab'a gwada koda kiran waya ba kawai matarshi yasa a gaba musamman data samu cikin nan sai kulawar ta ninka ta baya fiye da tsammanin mai karatu har zuwa lokacin da ALLAH ya sauketa lafiya ya azurtasu da samun k'aruwar d'a namiji wanda gaba d'aya zubinshi da kamannin shi na asalin jinin larabawan ne babu ta inda ya d'auko mahaifinshi komai na mahaifiyarshi ne. Fad'ar irin farin ciki da murnar da wannan ahali sukayi ma b'ata baki ne amma tabbas sunyi matuk'ar farin cikin zuwan jaririn duniya musamman Alhaji Ibraheem Gashua daya d'auki son duniya ya aza kan jaririn nan da ranar suna ta zagayo yaro yaci sunan mahaifin Afeefah wato *HABEEB* ba k'aramin dad'i Afeefah taji ba a lokacin saboda karar dayayi mata yasawa first born son d'insu sunan babanta ta rungume shi tana fad'a masa wasu kalmomi masu tsada na soyayya da nuna jin dad'i da godiya duk da larabci take maganar wanda yakejin yaren sosai a yanzu saboda zama da Afeefah, rungumeta ya k'ara yi sosai a jikinshi yana murmushi na jin dad'in ya faranta mata. Ta b'angaren Habeeb Al-Hussain ma wanda suke kira da Abi yaji dad'i k'warai da gaske na samun takwara dayayi tuni yaji yaron ya k'ara kwanta masa cikin ranshi tuni ya shiga yimasa kyaututtuka na alfarma abinka ga wad'anda sukaci suka tada kai da naira. Ba k'aramar dukiya aka salwantar ba wajen sunan yaron ga kyaututtuka dayake ta faman sha tako ina daga b'angaren kakannin shi na wajen uwa kowa son yaron yake da nuna masa k'auna. Afeefah ta cigaba da rainon yaronta cikin tsananin kulawa da taka tsantsan kan duk abinda zai cutar dashi ya taso cikin gata kowa ji dashi yake. Yarone daya taso da mugun k'ok'ari fikrah, zalak'a, da tarin baiwa suka fito k'uru k'uru tun yana k'ananun shekarunshi abu d'aya zaka fad'a masa ya d'aukeshi a kanshi koda da wasa ka fad'a kuwa musamman dayake samun k'warin gwiwa daga mahaifanshi dasu Abi. Saida Habeeb ya shekara biyar sannan Afeefah wadda yake kira da Ummi ta k'ara wata haihuwar wannan karon mace tasamu wadda suka rad'a mata suna Mashhoodah, sai a lokacin Ummi ta fara tuntub'ar Ibraheem Gashua wanda Habeeb ke kiranshi da Abbu a yanzu batun zuwa gida da nuna masa lallai ya kamata ace ya waiwayi gida haka yaje yaga halin da suke ciki ya kuma gabatar dasu a matsayinsu na iyalinshi tunda ga zuri'a sun fara tarawa, mirsisi Abbu yayi yace sam ba yanzu zai komaba idan ya tashi tafiya ma saidai kawai yace ta shirya su tafi amma dai ba yanzu ba ya fad'i hakan ne saboda tsoron komawa dayake baisan da irin kalamin dazai tunkari iyayen nashi ba idan ya koma yasani shi babban mai laifi ne a wajensu ya bijire musu yayi fatali da maganar da suka gindaya masa saboda soyayyar Afeefah data rufe masa ido yana tsoron komawa saboda baisan yadda zasu karb'eshi ba amma hak'ik'a cikin shekara d'aya data wuce zuwa yanzu yana yawan tunanin gida yakan yi mafarkinsu sosai tabbas yana son komawa k'asar sa ta haihuwa. Wannan abinda ya fad'a d'in shine harya haifar musu y'ar hatsaniya tsakanin shi da Ummi wanda wannan shine karo na farko a rayuwar aurensu dasuka samu matsala dan sosai yake biye mata sai abinda takeso akeyi a ganinta lokaci yayi daya dace ace taga mahaifarshi, iyayenshi y'an uwanshi dama tushenshi gaba d'aya. Itama saitayi fushin bata k'ara tayar masa da maganar zuwa 9ja ba shima bai k'ara yimata maganar ba ta zubawa dai sarautar ALLAH ido taga iya gudun ruwanshi. 10yrs After. Habeeb yanada shekaru goma a duniya yayin da Mashhoodah take da biyar ALLAH ya d'auki ran Abi sakamakon ciwon ciki daya turnuk'e shi lokaci d'aya rai yayi halinshi mutuwar data jijjiga familyn su da sauran abokan arzik'i musamman ma iyalinshi da sukafi kowa jinta su Ummi sunyi kuka kamar ba gobe mutuwar uba wani babban gib'i ne a rayuwar mutum wanda duk wani gata da za'ayiwa mutum shi bazaikai wanda mahaifi zaiyiwa d'anshi ba daga k'arshe dai suka bishi da addu'ar samun rahmar ubangiji da dacewa. ALLAH kaji k'anmu badan halinmu ba kayi mana rahma badan aikinmu ba dan alfarma da martabar sayyadil wujuud (S.W.A.)👏🙏 ★...★...★ Tun bayan rasuwar Abi Abbu yafara ganin y'an canje canje a rayuwar shi especially ta b'angaren kasuwancin shi yaja baya sosai tamkar Abi ne ya tafi da rabin arzik'in nashi ga ciwon hawan jini daya kamu dashi saboda yadda ya saka tunanin gida da iyayenshi a cikin ranshi ga wasu mafarkai dayake game da Malam Ahmad wanda ya kasa gane kansu hakan ya k'ara haddasawa jikin nashi rikicewa sosai k'warai da gaske yakeda buk'atar yasa ahalinshi a idonshi, a lokacin Ummi ta k'ara bijiro masa da maganar zuwa 9ja duk da alk'awarin data d'auka a baya cewar bazata k'ara yimasa maganar zuwa Nigeria ba amma yanayin yadda taga mijin nata tasan damuwarshi dai bata wuce ta gida. Sam bai mata musu ba a lokacin dan haka suka shirya sukaje suka samu mahaifiyar Ummi da maganar a lokacin shekara d'aya kenan da rasuwar Abi, sunyi zaton zasusha fama da ita amma ga mamakin su kai tsaye saita amince dama tuni taga dacewar hakan. Nan da nan suka fara shirin tafiya Nigeria Abbu farin cikinshi ya kasa b'oyuwa ta gefe d'aya kuma cike yake da tararrabin irin amsar da zasuyi masa. Cikin y'an kwanaki ya kammala musu duk wasu shirye shiryen tafiya suka d'aga zuwa 9ja k'asarshi ta haihuwa bayan sama da shekaru goma daya d'auka baya nan. Abinda ya tarar ne a ranar da suka iso yayi matuk'ar girgizashi wato labarin rasuwar Malam Ahmad daya samu shekara d'aya data wuce lokaci d'aya kenan data Abi yayi kuka tamkar ranshi zaibar jikinshi, dana sani da d'imbin nadama suka shigeshi ALLAH bai k'addara saduwarsu ba bare harya nemi gafararshi hak'ik'a rasuwar mahaifin nashi ta dakeshi ya zube gaban Hajiya Inna yana kuka da neman yafiyarta tsakanin d'a da uwa sai ALLAH saitaji duk wani fushi datake dashi na tsahon shekarun ta nemesu ta rasa ta rungume d'anta wani irin dad'i na ratsa zuciyarta, hakama sauran y'an uwan nashi da duk sukazo gidan suka rungume shi cikin farin cikin dawowarshi gida, anan Hajiyan ke sanar dashi ai kafin rasuwar mahaifin nasu yace ya yafe masa duniya da lahira wannan kalma ba k'aramin dad'i tayiwa Abbu ba dama damuwarshi d'aya mahaifinshi daya tafi da tabon b'acin ranshi. Bayan komai ya natsa ne ya gabatar musu da Ummi da yaransu biyu da ALLAH ya basu hannu bibbiyu suka amshesu basu nuna musu wani abu ba Hajiya ta rungume y'an jikokinta tanajin dad'i sudai kallonsu kawai suke cikin rarraba idon ganin wasu bak'in fuska da basu sansu ba gasu kuma bak'ake ba yadda suka saba ganin farar fata ba. Da k'yar aka gaggaisa da Ummi saboda ba hausa danma Abbu yakan yimata jefi jefi hakan yasa tasan wasu y'an abubuwan kamar gaisuwa da sauran maganganu marasa tsayi. Goggo Fatu d'aya daga cikin k'annen shi mata guda hud'u ita kad'ai ce Ummi ta kula tun zuwansu tana binta da wani irin kallo na tsana dan a ganinta Ummin itace silar dayasa d'an uwansu yabarsu na tsahon shekaru batare daya k'ara waiwayar suba dan haka taji da Ummin da yaranta duk ta tsanesu bata k'aunar su. Sauran kuwa ba ruwansu sun sakarwa Ummi fuska sosai Hajiya ma ta jata a jikinta sosai hakan ba k'aramin dad'i yayiwa Abbu ba nan da nan yaji duk wasu sauran y'an ciwace ciwace sun tafi dama tunanin gida ne da kuma zullumin yadda dangin nashi zasu amshe shi alhmdulillah kuma dayake masu ilmi ne da kuma aiki dashi yasa basu nuna masa komaiba sun d'auki hakan a matsayin k'addarar shi. Bayan sun huta na y'an kwanaki suka shiga yawon zaga dangi na kusa dana nesa yana gabatar musu da iyalinshi kuma ko ina sukaje ana nunawa Ummi da y'ay'anta soyayya tuni itama taji dangin mijin nata sun shiga ranta dan sunsan abinda suke k'warai da gaske ga karamchi da girmama d'an adam. Gaba d'aya sai kasuwancin Abbu ya sake dawo dashi Nigeria dan bayan dawowar tashi arzik'in nashi saiya k'ara hab'aka da d'aukaka. Alhaji Sulaiman Gashua babban yayansu shiya bashi k'aton gida mai kyau yace yafara zama da iyalinshi anan kafin ya gina nashi yadda zaiyi nashin a nutse daga nan suka cigaba da zama anan tare dasu ya cigaba da ginin daya fara anan kusa da gidan Alhaji Adam Gashua. Ummi batada matsalar komai sai Goggo Fatu data takura mata itada yaranta har gida take zuwa taci mata mutunci duk da bawai sanin ma metake fad'a tayi ba amma dai tasan zagine da cin mutunci, bata tab'a bari Abbu yasani ba tunda dama bata zuwa sai lokacin da baya nan ta rasa abinda ta tsare mata hantara da zagi kuwa ba wanda bata yiwa Habeeb da Mashhoodah abin baya yiwa Ummi dad'i amma batada yadda zatayi. Makaranta mai tsada aka nemarwa su Habeeb suka cigaba da karatun su, har yanzu dai Habeeb yana nan da wannan brain d'in tashi da d'auke abu tafar d'aya. Mrs Salees Mu'az 💝 *EL--HABEEB 💥* ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 4. Hakan yasa yana shiga school d'in sunanshi yayi fice daga malaman har d'aliban sonshi suke musamman dayake kyakkyawa balarabe wasu ma kawai kyawun nashi sukeso dan haka kowa ya shiga neman yadda zai k'ulla alak'a da Habeeb. Zamansu cikin hausawa yasa suka fara jin hausa sosai saidai abinda ba'a rasaba. Haka zamansu ya cigaba da tafiya har Abbu ya kammala ginin daya fara suka koma ciki babban gida ne mai kyau da tsari da aka tsarashi sosai. Tun daga kan Mashhoodah Ummi bata k'ara haihuwa ba saida aka d'ebi kusan wasu shekaru biyar d'in sannan ubangiji ya nufeta da k'ara samun wani cikin sunji dad'i kuma sun yiwa ALLAH godiya daya k'addara musu samun wata haihuwar ta cigaba da rainon cikinta har zuwa lokacin data haihu ta k'ara samun wata y'a macen taci sunan Hajiya wato Karimatu sai suke mata alkunya da Nihlah, Ummi tana yawan zuwa Dubai akai akai dan kaiwa mahaifiyarta ziyara da k'aninta Muhseen. Bayan wasu shekaru. Habeeb ya kammala karatunshi na secondary school ya fito kuma da kyakkyawan sakamako wanda Abbu yaji dad'i sosai harya bashi zab'in irin k'asar dayake so ya cigaba da karatunshi kai tsaye yace Dubai yakeso yaje dariya kawai Abbu da Ummi sukayi a lokacin dan sunsan dalilin dayasa ya zab'i Dubai d'in bai wuce shak'uwar dake tsakaninshi da Maman Ummi ba ko ziyara zasu kai musu yafi kowa murna. Tashin farko da Abbu ya k'ara tambayar shi me yakeso ya karanta a can d'in bai wani dogon tunani ba yace irin na Abbun wato business shiyake ra'ayi, jinjina kai kawai Abbu ya dinga yi yanajin dad'i anan suka bishi da addu'ar samun nasara da sa'a shida Ummi, k'arin jin dad'in nasu ma yaron nasu basai ya zauna a Hall ba tunda ga gidansu Ummi shikam gida yaje ai karatun. Tun daga lokacin Abbu ya shiga yiwa Habeeb shirye shiryen tafiya Dubai shiri yake masa sosai har lokacin tafiyar shi yayi ya d'aga zuwa k'asar Dubai cikeda jin k'warin gwiwar yin abinda ya kaishi k'asar. Fatan nasara HABEEB GASHUA. Gidansu Ummi nan ya sauka daga nan yake zuwa school d'in har lokacin bashida yawan magana miskili ne sosai badai ka ganshi yana hira yana raha da mutane ba saidai ya keb'e kanshi kullum cikin karatu yake d'alibai dayawa a makarantar sunyi zaton kurma ne gashi ba wanda yake kulawa yafi gane yayi zamanshi shi kad'ai wani d'an Nigeria ne da suka shiga makarantar kusan lokaci d'aya Auwal Mahmood Azare shiya dinga shige masa yanason suyi abota da Habeeb d'in farko sam baya kulashi saidai yazo ya zauna a inda yake ya k'araci surutunshi amma uffan Habeeb bazaice masa saidai yagaji ya tashi sai daga bayane sannan ya fara d'an kulashi shima bawani sosai ba baya baya. Ya cigaba da karatunshi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa su Abbu na yawan kawo masa ziyara shima kuma idan suka samu hutu yana zuwa ganin gida. A gurguje. Bayan wasu shekaru Habeeb ya kammala karatunshi cikeda tarin nasarori wanda hatta makarantar saidata bashi lambar yabo ta jinjina masa kuma. Akwai babban kamfani a k'asar wanda suke kasuwanci da k'asashe daban daban su suka rok'i alfarmar ya zauna yayi aiki dasu tun a lokacin kai tsaye baice musu zaiyi ba bai kuma bazaiyi ba yace dai zaiyi shawara da iyayenshi duk abinda suka zartar shi zaiyi. Bayan dawowar shi yasamu Abbu ya sanar dashi abinda kamfanin sukace Abbu yaso Habeeb ya zauna yayi aiki a nashi kamfanunuwan ya taimaka masa amma abin alfaharinshi ne ace yaronshi yana aiki a wancan kamfanin na Dubai dan ya sanshi babban kamfani ne sosai kuma a hakan ma su suka nemi dayayi aiki dasu gaskiya yaron nashi mai sa'a ne dan haka kawai ya umarci Habeeb d'in ya koma yayi aiki dasu d'in ALLAH ya taimaka. Bayan ya d'an huta ya k'ara shiryawa yayi sallama da iyaye da abokan arzik'i ya k'ara komawa Dubai da shirin yin aiki. Sunji dad'in komawarshi sosai suka bashi gida da had'add'iyar mota mai tsada ya amshi motar dai gidan kam yace yanada inda zai zauna ga k'aton office d'inshi dayaji kayan alfarma bashi dai da matsalar komai alhmdulillah nan da nan ya k'ara fasowa gari tuni y'anmatan larabawa suka fara kai masa hari saidai ko a kwalar rigarshi ba abinda yasha masa kai ko kallo basu isheshi ba hakan yasa wasu dayawa suke ganinshi mai bala'in girman kai da fariya wanda kuma a zahiri ba haka bane kawai dai shi haka ubangiji ya halicceshi sam bai cika son shiga cikin jama'a ba yafiso ya dinga kad'aicewa shi kad'ai gashi bayason surutu ko hayaniya. Su Ummi sunso zuwa bayan yafara aikin kasancewar sun d'an kwana biyu basuje ba saikuma taji bikin k'aninta Muhseen da za'ayi ya kusa dan haka suka hak'ura sai lokacin da za'ayi bikin sannan sukaje wannan karon harda Hajiya Inna aka tafi suka sha bikin Muhseen da amaryar shi Abeedah, daga nan suka wuce sukayi umrah sannan suka dawo Nigeria. Bayan dawowar su da y'an watanni ne akayi bikin Mashhoodah inda tasamu mijin cikin y'an uwa dan babban d'an Alhaji Adam ne Musaddeeq wanda tun dawowar su k'asar bayan tafara girma yaji yarinyar ta shiga ranshi sosai baidai bayyana bane sai data kai munzalin fara saurarar samari sannan ya fito ya shiga cikin jerin y'an takara kuma ALLAH yayi shine mijin nata akasha biki iyaye da y'an uwa kowa na murnar wani zumunchin da aka k'ara had'awa. Goggo Fatuu taso wargatsa al'amarin amma ALLAH bai bata iko ba gashi dangi kowa yayi mata caa hakan yasa tayi shiru ta daina sukar lamarin. "Baifi shekara d'aya da fara aikin ba ALLAH ya yiwa Abbu rasuwa, mutuwar data tab'a mutane da dama kasancewar shi mutumin kirki ga taimakon al'ummar musulmi marasa k'arfi duk inda gidan marayu suke yakan sa a nemosu dan ya taimaka musu, katsam sai waya Habeeb yaji wai Abbunshi ya rasu zuciyarshi ta girgiza k'warai da gaske da wannan labarin daya samu saiya dinga tuno irin wayoyin dasuke dashi a kwanakin kullum magana d'ayace dai ya dinga taimakon na k'asa dashi ya taimaki marayu dan su d'in masu rauni ne suna buk'atar masu kulawa dasu zuciyarshi ta k'ek'ashe ko d'igon hawaye babu sai kukan zuci dayake wanda yafi na fili dan a ganinshi shi akayiwa rasuwar saboda shi yayi rashin mahaifi mai sonshi da k'aunarshi, har a lokacin Goggo Fatu ta samu abinyi ganin a gabanshi aka fitar da gawar Abbu amma ba d'igon hawaye a idanunshi wai dama zubin marasa imani da tausayi gareshi amma mahaifinka ya mutu ka gaza yin kuka kamar yin kukan shi zai dawo da mutum babu wanda yabi ta kanta a lokacin kowa na cikin alhinin mutuwa. Bayan rasuwar Abbu da d'an wani lokaci Habeeb ya koma bakin aikinshi cikeda kewar Abbunshi shikenan sun zama marayu a yanzu, gaba d'aya sai Ummi tazama abar tausayi a lokacin takan tuna irin zaman da sukayi dashi cikin kwanciyar hankali da mutunta juna shikenan kuma tasan tayi rashin da har abada bazata maye gurbinshi ba a yanzu gidan daga ita sai Nihlah. Kamar yadda addini ya tanadar idan mutum ya mutu za'a raba gadonshi haka akayi Abbu ma anyi rabon gadonshi an fitarwa da mahaifiyarshi nata kason sannan y'an uwanshi saikuma iyalanshi hak'ik'a Abbu ya tara dukiya mai tarin yawa ga kadarori inda kowanne saidaya samu kaso mai tsoka cikin abinda aka bashi cikin abinda aka bawa Habeeb da k'annenshi harda babban kamfanin Abbun wanda yafi kowanne kamfani ne dayake had'a cinikayya tsakanin k'asashe gefe d'aya kuma akwai masarrafar k'arfe duk a cikin kamfanin dad'in dad'awa kuma k'aton gidan da suke ciki wanda Abbun ya gina a unguwar Nassarawa G.R.A shima mallakinsu ne sun samu tarin alkhairi dayawa wanda wannan duk baya gaban Habeeb. Dole ya ajiye aikinshi yadawo Nigeria dan cigaba da kula da wannan kamfanin da sauran abubuwan da aka bar musu, sosai wancan kamfanin na Dubai yaji ba dad'i sunyi bak'in cikin rabuwa dashi dan fara aikinshi a kamfanin ba k'aramin alkhairi yajawo musu ba da k'ara yin suna kullum cikin kawo sabbin dabaru yake ta kwanyar da ALLAH ya bashi ta yadda kamfanin zai k'ara hab'aka kuma suna ganin cigaba sosai hakan yasa lokacin dazai bar aiki masu kamfanin suka yimasa gagarumar kyauta ta kud'i tsabarsu farko ma cewa yayi bayaso bazai karb'a ba saida suka takura masa shima daya tashi ba duka ya amsa ba ya ciri wani abu ya maida musu sauran dan a ganinshi kud'in sunyi yawa. Bayan dawowar shi yasa aka k'ara gyara kamfanin ya fito ana zamani sosai aka k'ara samun gogaggun ma'aikata aka zuba yafara aiki, Mujaheed shiya d'auka a matsayin P.A d'inshi wato personal assistant manager Mujaheed d'an k'anwar Abbu ne wadda take binshi a haihuwa Hajiya Aisha kuma dama a kamfanin yake aiki yasan takan aikin sosai, bama shi kad'ai ba akwai y'an familyn Gashua dayawa dasuke aiki anan. Ummi taso ta koma k'asarsu Hajiya Inna ta rok'i alfarmar ta zauna dasu saboda matuk'a take k'aunar Ummin har cikin ranta tanajin dad'in zama da ita k'warai da gaske, tsananin girma da mutuncin Hajiya Inna da Ummi ke gani yasa ta amince bazata iya yimata musu ba saitaga kamar ko dan babu ran d'anta ne amma tabbas taso tafiya tunda bataga zaman dazatayi a nan d'in ba. Alhaji Sulaiman Gashua shima yadawo kusa da gidan Abbu anan ya tamfatsa gida suka dawo shida iyalanshi da Hajiya Inna dama tana gidanshi. Har a yau bakin Habeeb bai daidaice da hausa ba magana d'aya zaiyi zaka fahimci ba zallar bahaushe bane a hakan ma Auwal Mahmood Azare wanda sukayi karatu tare shiya taka muhimmiyar rawa wajen koya masa hausa tunda dangin ubanshi hausawa ne so dole watarana zai zauna a cikinsu kamar yasan hakan zata faru kuwa saigashi yadawo cikin nasu dayake yanada brain saiyake d'auke komai duk da yadda hausar take masa wahala amma yana k'ok'arin yinta sosai saidai maganar tashi ce abin dariya idan yanayi shiyasa sau tari suke fad'a da MJ idan yaji yana magana da hausa yayi ta masa dariya shikuma ya hau yaita masa masifa. Ita kanta Ummin har yanzu fama take itama tana magana zaka ganota Nihlah kam dama y'ar garin hausawa ce da hausa ta taso a bakinta dan ma dai tun tana k'arama Ummi tana yawan yimata larabci hakan yasa ta tashi da wasu abubuwan sosai kuma tanajin duk abinda aka fad'a mayarwar ne wani lokacin yake gagararta. M&S💝 *SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪 *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B* INA KUKE MAKARANTA?? INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA.... TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI. 1- *KAUNA CE* NA UMM ASGHAR 2- *RUKUQI* NA FEEDHOM 3- *WANI SO* NA ZEE YABOUR 4- *SO DA ALAKA* NA UMMI AISHA 5- *MUGUN GANI* NA SADIYA NASIR DAN 6- *ABDUL_HAMEED* NA NANA DISO 7- *MUKULLIN ZUCIYA* NA MAMAN KHADY Daya 200 biyu 400, guda uku 500 Guda hudu 700 Guda biyar 750 Shida 800 bakwai 1000 da programs DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA (1000) DUBU DAYA KACAL KAI KA KAI....! TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE- SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU... 1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍 *DAGA CHEF RAHMA NA LELE* 2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA *DAGA AYUSHER MUH'D* 3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI *DAGA HAJJA CE 👈* MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN _GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_ 2083371244 ZENITH BANK AISHA M. SALIS *SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼* +447894142004 IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼* 07065283730 da Shaidar biya duk ta ciki _GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_ +227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey. MUN GODE. *TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022* _Wannan garabasar tamai rabo ce💃🏻💃🏻 sa kud'i kad'an ki debi hani'an😍😂_ *EL--HABEEB* 💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 5. Haka zatayi ta bak'in rai musamman idan taga Aunt Mashhoodah tazo sun zauna da Ummi sunata hira tunda ita bawai komai ne take jiba. Back to story. KATSINA. K'ofar K'aura. Madaidaicin d'aki ne wanda aka lailayeshi da siminti sai ledar tsakar d'aki da aka malaleshi da ita sai k'aramin fridge da y'ar k'aramar TV ta jikin bango kallo d'aya dai zaka yiwa gidan ka gano na masu rufin asiri ne da wadatar zuci. Yarinya ce y'ar kimanin shekara sha bakwai zaune cikin d'akin a kan tabarma sai faman kuka take tamkar ranta zai fita sai wata dattijuwa zaune a gefenta d'aya gefen kuma wata matashiya ce wadda bazata wuce haihuwa d'aya zuwa biyu ba sun sata a tsakiyarsu kukanta take bilhaqqi da gaskiya duk da irin rarrashin da suke mata kuwa amma sai k'arawa kukanta volume take kamar wadda ake yankar naman jikinta. Wannan matashiyar ce ta dafa kafad'arta a karo na ba adadi tun zamansu a wajen cikin sanyin murya da son yin rarrashi tace "Haba *HEEDAYAH* dan ALLAH kiyi shiru haka kar kiyi ciwon kai, tun d'azu fa kike kukan nan ki sassautawa ranki haka mana addu'arki Kabeer yake da buk'ata a halin yanzu ba kukanki ba Kabeer ya mutu kuma muna masa kyakkyawan zaton samun rahmar ubangiji kiyi hak'uri dan ALLAH". Cikin shasshek'ar kuka tace "Aunt Ramlah shikenan fa nida Yah Kabeer mun rabu har abada bazan k'ara ganinshi ba taya zansamu kamar Yah Kabeer Aunt Ramlah? mutumin da tun ina y'ar tatsitsiyata yake dako da d'awainiya da sona yake wahalta min duk d'an abinda ya samu a kaina yake k'arewa koyaushe farin cikina shine nashi taya ba zanyi kuka ba". Ta k'are maganar tareda fad'awa jikin dattijuwar dake gefenta tana cigaba da kukanta itakuma ta shiga jijjigata tana shafa bayanta alamun rarrashi, lallai dole Heedayah tayi kukan rashin Kabeer ya sota ya nuna mata k'auna duk da irin tarin k'alubalen daya dinga fuskanta daga wajen danginshi da mahaifiyarshi akanta saboda wani dalili wanda basa son had'a auratayya tsakanin d'ansu da ita wanda ita kanta yarinyar bata san dashiba kuma batasan akanme suke nuna mata k'iyayyar ba, saura kwana bakwai bikinsu ALLAH yayi masa rasuwa sakamakon accident din daya samu akan hanyarshi ta zuwa Kaduna inda yake sana'ar shi ko shurawa baiyiba ubangiji ya d'auki abinshi yau kusan sati biyu kenan da rasuwar tashi amma har yanzu Heedayah bata bar yin kukan rashin shiba sosai rasuwar tashi ta bugeta kullum cikin kuka da sambatu duk da rubutun dangana da Malam ke amso mata wajen malamin da suke d'aukar karatu bayan sallahr magreebah abin harya fara bawa Umma tsoro, cikeda tausayawa Aunt Ramlah tace "Nikam Umma wata shawara mana mezai hana mutafi da Heedayah can Kano ta d'anyi nisa da garin nan ko yayane maybe ta d'an samu salama ta daina yawan tunanin shi amma sai abinda kukace Umma". Shiru Umma tayi tana nazarin maganar Ramlah to amma saidai ba lallai bane Malam ya amince ganin ita kad'ai ce a gabansu shi Mustapha ba'asa lissafi dashi shi namiji ne saisu yini ma basu sashi a idonsu ba yana can wajen sana'ar shi ta d'inki. "Umma ya kikayi shiru ko baki amince bane". Aunt Ramlah tace tana marairaice murya. Zama Umma ta gyara tareda k'ara gyarawa Heedayah dake jikinta kwanciya tace "To ai ni kad'ai bazan yanke hukunci ba Ramlah, tunda ba yaune tafiyar taki ba kibari zuwa anjima idan Malam yadawo saiki tambayeshi idan ya amince ai bawani abu bane saiku tafi taren indai hakan zai samar mata nutsuwa da kwanciyar hankali". "Insha ALLAHU ma zai yarda Umma ai hakan saiyafi kinga nan fa tana fita ga gida ga gida ko bataso indai zataga gidansu saiya tuna mata dashi". cewar Aunt Ramlah. Kai kawai Umma ta jinjina ta maida kallonta kan Heedayah da kanta ke kan cinyarta tace "Zakibi Auntyn ki gidanta Heedayah?". "Ni Umma banaso inyi nesa dake idan natafi fa bakowa saike kad'ai shi Yah Mustapha ba ganinshi akeba". Murmushi Umma tayi tana k'ara jin tausayin yarinyar na shigarta, kanta ta shiga shafawa tana fad'in "Ba komai Heedayahta indai kinason zuwa kije kinji ALLAH yayi miki albarka yabaki miji nagari kije famfo ki wanke fuskarki kizo kici abinci kinga duk yau baki sawa cikinki komai ba". Amsawa Umman tayi tana k'ara share hawayen idanunta ta tashi ta fita tana gyara d'aurin d'ankwalin ta, duk da kallon tausayi suka bita harta fice kowanne yana k'iyasta halin dazata samu kanta duk ranar datasan ita d'in WACECE ?. Kamar yadda Umma tacewa Aunt Ramlah ta tambayi Malam idan ya yarda hakan akayi kuwa bayan yadawo sallahr Esha'e yaci abinci ya huta taje ta sameshi da maganar da farko dai k'in amincewa yayi sai data dinga faman magiya sannan ya amince cikin murna da farin ciki take masa godiya ta d'ora da fad'in "Kaga Baba tunda ga yadda ta kasance idan mukaje sai a samar mata makaranta ta cigaba kafin ALLAH ya kawo mata miji tayi aurenta". Kai kawai ya jinjina mata yace "ALLAH yasa hakan shine mafi alkhairi". Da ''Ameen" ta amsa sannan ta tashi tabar wajen. Washegari da daddare Heedayah tana shirya kayanta na tafiya tanayi tana kuka tana k'ara tuna masoyinta ashe babu rabon suyi aure kullum buri da mafarkinsu su mallaki junansu a matsayin ma'aurata ashe babu rabon hakan watannin bikinsu ma da akasa yaji yayi masa yawa haka yaje ya tasa babanshi a gaba yanata masa magiyar dan ALLAH yasamu Malam suyi magana a rage shi wllhy watannin sunyi masa yawa hakan akayi kuwa shima baban nashi ya biye masa yasamu Malam sukayi magana aka sauko da bikin har Mustapha yayanta yanata zaginshi a lokacin wai bashida kunya dayake abokinshi ne, dariya kawai yayi masa a lokacin yana masa gwalo, batasan lokacin data k'ara fashewa dawani irin kuka ba ragowar kayan ma sai Umma ce ta k'arasa shirya mata su. Washegari wajen k'arfe sha biyu na rana direban Aunt Ramlah yazo d'aukarta, tunda Heedayah taga dai gadan gadan tafiyar za'ayi har ansaka kayansu a mota tafara kuka ta rirrik'e Umma kamar wadda akace idan tatafi bazata k'ara dawowa ba da k'yar Aunt Ramlah ta jata suka fita ko sallama basuyi da Umman ba, bare da suka fito ta kalli gidan su Kabeer saita k'ara fashewa dawani kukan kawai tana tuno irin rayuwar da sukayi dashi mai dad'i shikenan yanzu mai rabawa ta raba saita k'ara tuno yadda idan yazo ganin gida duk ranar dazai koma Kaduna wajen kasuwancin shi haka zatasa masa kukan shagwab'a ita bataso yatafi ya barta haka zai lalace wajen rarrashin ta har sai yaga yasata dariya sannan zai iya tafiya yabar wajen ko wane irin sauri yake kuwa, yau gashi yayi doguwar tafiyar da har abada bazai k'ara dawowa ba bare tace zasu had'u watarana. A hanya ma saida Aunt Ramlah tayi ta faman rarrashi sannan tasamu tayi shiru daga baya ma barcine ya d'auketa a jikin Aunt Ramlah. ★★★ Habeeb ne da Mujaheed zaune a kyakkyawar harabar gidansu Habeeb d'in kusa dawasu shuke shuke masu ban sha'awa da k'ayatarwa kan wasu kujeru na gini sai table da aka had'a shima da abinda akayi kujerun, soft drink's ne kala kala akai da fruits a yayyanke a plate plate anyi wrapping d'insu da leda. Habeeb sanye yake cikin riga mai gajeren hannu da wando red color marasa nauyi na kamfanin Adidas wanda sukayi matuk'ar haskashi kasancewar shi fari, Mujaheed kuma manyan kaya ne a jikinshi riga da wando na maroon shadda, kowanne kanshi a sunkuye yake da waya a hannunshi hakan yasa babu mai magana a cikinsu kowa hankalinshi nakan waya can kuma Mujaheed yaga Habeeb ya daina kallon wayar ya k'urawa wata k'aramar bishiya ido kamar wanda yake son lissafa ganyen jikinta kallonshi yake tayi amma sam baisan yanayi ba da alamu yayi nisa cikin duniyar tunani. "Gashua". Mujaheed ya ambaci sunanshi cikeda mamakin meye damuwarshi haka? a hankali ya maida kallonshi kan Mujaheed daya kira sunanshi. "Are u okay?" Mujaheed ya tambaya. Saidaya sauke wani nannauyan numfashi sannan yace "Yes I'm fine". yace yana zame tattausan slippers d'in k'afarshi ya mik'eta kan table d'in ya maida kanshi kan wayar. "Banga alamun hakan ba Gashua, yaushe kafara b'oyemin damuwarka? kanaso mufara y'ar haka ne a tsakaninmu ko? kokuma baka yarda dani bane kai kanka kasani bana b'oye maka komai daya shafeni duk wani sirrina na fili dana b'oye kasani Gashua dan me kai kake k'ok'arin b'oyemin bayan kuma nasan akwai wani abu". Ido Habeeb ya lumshe yakai hannu yana yamutsa lallausar sumar kanshi kafin ya bud'e ido ya kalli Mujaheed dake kallonshi cikin sanyin murya yace "MJ, na dad'e a cikin wannan halin tun abin baya damuna yanzu yanaso yayi tasiri a kaina, shiru ya d'anyi kafin ya cigaba da fad'in "Mafarki nake MJ". "Mafarki kuma? kamar yaya Gashua?". Mujaheed yace cikin mamaki yana kallon Habeeb dake shafa sajen fuskarshi. "Mafarkin mace". yabashi amsa kai tsaye batare da tunanin Mujaheed zai fassara maganar ba, cikin matse dariya Mujaheed yace "Kuna wani abune a cikin mafarkin?". Kallon zanci ubanka Habeeb ya jefa masa yace "Kullum tana zuwa min ne fuskarta a rufe da mayafi saitazo zata bud'e sai in farka narasa yadda zanyi I'm confused MJ". ya k'arasa maganar yana d'an girgiza kai da cije lips d'inshi na k'asa. "Tun yaushe kenan?". cewar Mujaheed. "Five years". Habeeb ya bashi amsa. Ido Mujaheed ya zaro yace "Five years fa kace Gashua? hod'ijam inji fulani gaskiya ya kamata ka tashi tsaye da addu'a indai hakane koma wacece ita ALLAH ya bayyana mana ita tafito fili mu ganta ra'ayul aini bata dinga zuwa cikin mafarki tana susuta mana Boss d'inmu ba koya kace mutumin?". Banza yayi masa bai kulashi ba Mujaheed yace "Kokuma wajen masu fassarar mafarki zamuje a fassara mana abinda mafarkin yake nufi?". "No, kamar dai yadda ka fad'a d'in zan cigaba da addu'ar amma idona idon yarinyar nan saina hukuntata dan ba k'aramin wuya take bani ba". yace yana cije lips d'inshi gamida shafa kwantaccen sajenshi. Dariya sosai Mujaheed ya fashe da ita yace "How? kaida har yanzu bakaga face d'inta ba ta yaya zaka iya ganeta a fili? kaidai kawai kayi addu'a Gashua kar a kauce hanya ta mafarkin". Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 *EL--HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) _Ina mik'a sak'on ta'aziyya ta ga Ummi Aysha dama k'ungiyar mu ta HASKE na rashin mahaifiya datayi ALLAH ubangiji yaji kanta yayi mata rahma yasa aljannace makoma yabawa iyalanta hak'urin rashi ya kyautata namu k'arshen yaji kan dukkan musulmai baki d'aya_. No 6. A fusace Habeeb ya d'ago ya kalleshi jin yadda yake tamasa fatan kusantar yarinyar duk da a cikin mafarkin ne, cikin harshen shi na hausa da har yau bai gama daidaita ba yafara masa masifa dan duk miskilancin shi idan aka tab'oshi haka yake zagewa yayita bala'i kamar bashine maganar ma take masa wahala ba. Tsaki Mujaheed yayi yana dafe goshinshi yace "Ka taimakeni ka daina min masifa da hausa Gashua, ka dinga yimin da turanci yadda zan dinga ganewa amma ni wllhy wannan rub'abb'iyar hausar taka bawani fahimtar ta nakeba kuma kace lallai lallai sai kayi". Sosai Habeeb ya k'ara shak'a tsaki yaja ya mik'e ya zura slippers d'inshi ya d'auki wayarshi yabar wajen Mujaheed ya bishi yana masa dariya da kiran sunanshi amma ko juyowa baiyiba bare ya kulashi ya shige part d'inshi dake cikin harabar gidan wanda shima zaman kanshi yake dan kamar wani k'aramin gidan ne saboda girman shi. Kano. Rijiyar zaki. A y'an kwanakin da Heedayah tayi a gidan Aunt Ramlah tafara jin dad'in zaman gidan k'warai kuma damuwarta tafara raguwa ta rage tunanin Kabeer ba kamar lokacin datake Katsina ba musamman daya kasance akwai k'anwar mijin Aunt Ramlah d'in a gidan Zainab wadda suke kusan sa'anni da ita saidai Zainab d'in zata d'an girme mata bayan tagama secondary school ya d'aukota tadawo gidanshi da zama da nufin sama mata gurbin karatu a jami'a wanda bayan zuwan Heedayah shi mijin Aunt Ramlahn Uncle Muhammad ya yanke shawarar samar musu tare Aunt Ramlah tayi ta godiya. Cikin d'an zaman da sukayi suka saba sosai da Zainab ita kanta Zainab d'in sai yanzu zaman gidan yake mata dad'i sab'anin da daga ita sai yaran Aunt Ramlah Nusrah babbar school take tafiya tahfeez tun safe sai yamma sai d'ayar dataci sunan mamansu suke kiranta da Hajiya itakam batafi shekara d'aya bama goyonta ake shiyasa gidan duk yake mata ba dad'i yanzu kam da Heedayah tazo tasamu abokiyar hira. Ba'a d'auki dogon lokaci ba Uncle Muhammad ya samarwa Heedayah da Zainab gurbin karatu a YUSUF MAITAMA SULE UNIVERSITY kusa dasu, sunyi murna sosai suka sameshi sukayi masa godiya. Nan da nan suka fara zuwa d'aukar lecture, Heedayah ta k'ara kyau farinta ya k'ara fitowa sosai Uncle Muhammad yayi musu sabbin d'inkuna da dogayen riguna saboda shiga school ba abinda zata cewa bawan ALLAHn nan saidai ALLAH ya saka masa da alkhairi yasa yagama da duniya lafiya yanada matuk'ar kirki da sanin ya kamata aikuwa ya k'ara fito dasu sosai suke d'aukar wanka idan zasu tafi kuma bana rashin hankali ba dan yawanci ma sunfi using da hijabs irin na yayin nan da akeyi kuma ba ruwansu da shiga shirgin kowa kawai abinda ya kaisu sukeyi. Uncle Muhammad d'aya daga cikin yaran Alhaji Sulaiman Gashua ne a kasuwa kuma yana jidashi da mutunta shi saboda rik'on gaskiya da amanarshi. Yauma weekend Aunt Ramlah da yaranta dasu Heedayah suka shirya tsaf dan zuwa gaida Hajiya Inna mahaifiyar Alhaji Sulaiman dama kuma Aunt Ramlahn tana zuwa jefi jefi wajen iyalan Alhaji Sulaiman d'in dakuma wajen Hajiya kuma tasu tazo d'aya da Hajiyan. Saida Aunt Ramlah lafiyayyen dambun tsaki dayaji gyad'a da zogale sanin yadda Hajiyan ke matuk'ar sonshi ga kuma had'add'en zob'o dayaji kayan had'i wanda shima tasan mutumin Hajiyan ne suka tafi mata dashi. Uncle Muhammad d'in ne ya kaisu da kanshi ya saukesu ya wuce, b'angaren Alhaji Sulaiman d'in suka fara shiga aka gaggaisa suka d'an tab'a hira da uwargidan shi Hajiya Rahma sannan suka nufi b'angaren Hajiya wanda yake duk a cikin gidan. Sosai Hajiya tayi murna da ganinsu ta shiga yimusu sannu da zuwa kamar zata goyasu saboda yadda take musu dan taji dad'in zuwansu sosai dama Aunt Ramlah ta saba dan duk lokacin datazo irin tarbar datake mata kenan akwaita da karrama bak'o. Zama sukayi aka shiga gaggaisawa sannan Aunt Ramlah ta bata abinda tazo mata dashi, aikuwa tasha addu'a daga nan suka shiga hira cikin hirar ne Hajiya Inna ke tambayar Aunt Ramlah ina tasamu kyakkyawar yarinya haka dayake tasan Zainab sun tab'a zuwa sau d'aya da Aunt Ramlah. Murmushi Aunt Ramlah tayi tace "K'anwata ce Hajiya". "ALLAH sarki takawo miki ziyara kenan?". cewar Hajiya. "Wallahi Hajiya saurayin ta dazata aura ne ALLAH yayi masa rasuwa sakamakon accident dayayi ana saura sati d'aya biki ta shiga halin damuwa kullum cikin koke koke to shine zuwan nan danayi na k'arshe muka taho tare to gashi ma har Abban Nusrah ya samar musu makaranta sun fara zuwa itada Zainab". Kai Hajiya ta shiga girgizawa cikeda tausayawa tace "ALLAH sarki, ALLAH yaji k'anshi yayi masa rahma itakuma yabata wani mafi alkhairi". Da "Ameen" Aunt Ramlah da Zainab suka amsa yayin da idanun Heedayah suka cika da k'wallah saboda wani abu dataji ya taso mata game da mutuwar Kabeer, a hankali tasa gefen mayafinta ta goge batare da kowa ya lura ba sai Hajiya data ganta tausayinta ya k'ara kamata lallai dagani ba k'aramin so takewa wannan saurayin nata ba lokaci d'aya taji yarinyar ta shiga ranta sosai. "Malam Muhammad da k'ok'ari an bar muku ne gaba d'aya har dasata a makaranta?". Hajiya ta fad'a cikin dariya. Dariya sukayi gaba d'ayansu, cikin dariya Aunt Ramlah tace "Hajiya ai tunda tafara karatu dole abar mana ita gaba d'aya Hajiya". "A'ah kunso yin dai k'wace kawai". cewar Hajiya tana dariya, nan suka cigaba da hirarsu dayake Hajiya akwai raha haka tayi ta sasu dariya. Sunci sunsha daga abinciccikan da aka aiko musu daga part d'in Alhaji Sulaiman dayake itama Hajiyar daga can ake kawo mata dambun da Aunt Ramlah takai mata shi taci abinta batabi takan fried rice d'in da akayi ba, gashi komai ta wawuro ta mik'o musu irin abunsu na tsaffi gaskiya Hajiya akwai mutunci abinda Heedayah ta dinga fad'a kenan a cikin ranta. Anan sukayi sallahr magreebah sannan Uncle Muhammad yazo, bayan sun gaisa da Hajiya suka tafi bayan sun shiga sun yiwa Hajiya Rahma sallama tayiwa su Heedayah kyautar kayan makeup su Nusrah kuma biscuits, chocolate dasu sweet's itama kam akwai mutunci ta fahimci kamar haka familyn suke gaba d'ayansu. Tun daga xuwan da sukayi shak'uwa ta shiga tsakanin Hajiya Inna da Heedayah kamar irin sun dad'e d'in nan tare ko bata jeba tayiwa Aunt Ramlah waya tace ta turo mata Heedayah wani lokacin ma daga school suke wucewa itada Zainab. ★★★★★★ Ranar asabar da yammaci lik'is bayan sun taso daga islamiyyar da suke zuwa Aunt Ramlah ta aikesu gidan wata k'awarta zasu karb'o mata sak'o, layi d'aya ne a tsakaninsu ba nisa gidan dan haka a k'afa ma suka shiga takawa suna hirarsu gashi dama layin irin dogon nan ne kuma sam ba yawaitar mutane a layin ko ina shiru. Heedayah atamfa ce a jikinta riga da siket purple color da bak'i sai hijab kalar atamfar iya gwiwarta mai hannu, itakuma Zainab doguwar rigace pink color tayi rolling da mayafin rigar a hankali suke takawa kamar masu tausayin k'asar. Tsadaddun motoci ne guda uku bak'ak'e wuluk suka shigo cikin layin da wani irin matsiyacin gudu sukayi kan su Heedayah kamar zasu bankesu ga uban horn dasuke ta dannawa kamar zasu tashi unguwar hakan ya gigita su Heedayah suka rasa inda zasu nufa duk suka diririce ta gefensu sukazo sukabi a tsiyace kamar zasu tashi sama, wani takaici ne ya kama Heedayah ga gabansu dake ta fad'uwa daga ita har Zainab d'in batasan lokacin data tsuguna ta rarumi dutse a k'asa ba ta cillawa motocin duk da irin yadda Zainab take rik'e hannunta dutsen nan bai tsaya ko ina ba sai a bayan motar dake tsakiya wanda hakan yasa dole mai tuk'a motar ya taka birki ba shiri shima na bayanshi ya tsaya na gaban nasu ma ganin sun tsattsaya yasa shima ya tsaya. Banda dukan uku uku ba abinda zuciyar Heedayah da Zainab keyi tamkar tayi tsalle ta fito waje tsabar tsoro amma saboda k'arfin hali irin na Heedayah haka ta tunkari motocin tun ma kafin taga suwaye zasu fito daga ciki, tsananin tsoro yasa Zainab takasa ko motsawa bare tayi yunk'urin hanata zuwa sai tai tsaye tana kallon Heedayah data tunkaresu lokacin duk sun fiffito daga cikin motar kowanne cikin bak'ak'en suit. Tun kafin ta k'arasa tafara d'add'aga hannaye tana musu masifa da bala'in makafi ne su dazasu buge mutane kokuwa dai shaye shaye sukaje sukayi yasa suke gudun rashin hankali da tarbiyya a unguwar mutane?. gaba d'ayansu sukayo kanta da nufin gyara mata zama musamman Aliyu babban bodyguard d'in da harya d'aga hannu da nufin kifa mata mari saikuma yaji muryar maigidan nasu wanda shi sai yanzu ne ya fito daga cikin motar. "Stopped Aleeyuh". ya fad'a cikin tattausan sound d'inshi kuma cikin wani salon magana mai dad'i, mai maganar nabi da kallo idanuna suka hangomin Habeeb Gashua wanda yake tsaye jikin motar ya dafa murfin motar da hannayenshi yana sanye cikin bak'in wando da farar shirt mai dogayen hannu ya matse wuyanshi da black tie yasha torking da bak'ar belt wanda ya bayyana shafaffen cikinshi dayayi kama da wanda ba'a sawa komai a cikinshi sumar nan tasha uban gyara sai k'yalli take zubawa hakama sajen fuskarshi a kwance luf yasha mayuka masu tsada. B'oyayyar ajiyar zuciya Heedayah tasaki wanda babu wanda yaji, gaskiya ALLAH ne ya taimaketa da wannan gabjejen k'aton baikai hannu jikinta ba data kad'e har ganyenta dama kuma duk abinda take k'arfin hali ne kawai amma inbanda bugu ba abinda take, kallonta ta maida kanshi ido ta zaro cikin fad'uwar gaba tana kallon tsabar kyau da tsari wanda ubangiji yayi masa. 'Ashe balarabe ne ma ogan nasu' ta fad'a cikin ranta, Kai tsaye ta tunkari inda yake tsaye har yanzun idanunshi akan Heedayah dake nufoshi, da masifarta ta k'arasa tana fad'in "Ashe dama ba d'an k'asar nan bane kazo kake mana abinda kaga dama a garinmu? to ka maida hankalinka wllhy inba hakaba watarana sai an d'aureka. Maryam Ibraheem Aleeyu M&S💝 *EL-- HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 7. Shiru kawai Habeeb yayi ya tsurawa d'an k'aramin bakinta wanda keta masifa ido dan maganganun nata ma dayawa ba ganesu yake ba sai faman juya baki take tana fad'a. Hannu Aleeyu ya k'ara d'agawa da niyyar maketa jin yadda take ta fad'awa Boss d'insu maganganu Habeeb ya k'ara dakatar dashi a tsawace. "Nunar rana kawai". Abinda ta fad'a kenan daga k'arshe bayan ta juya masa idanu ta juya tayi tafiyarta kallo kawai ya bita dashi harta koma wajen Zainab dake tsaye a k'ame tana kallon ikon ALLAH da tsabar k'ok'ari irin na Heedayah. "Dan ALLAH yallab'ai ka barni inje in casa maka yarinyar can mara kunya yarinya k'arama sai fitsara da rashin kunya". Kai kawai Habeeb ya girgizawa Aleeyu tare dayi musu alama ta cikin idanunshi subar wajen, nan da nan kuwa kowa ya shige mota shima ya koma ciki Mubarak direban dake jansu ya shiga ya tada motar duk suka bar wajen. Lafewa ya k'ara yi a back seat d'in kamar yadda yake ada ya lumshe idanunshi yana k'ara hango d'an k'aramin bakin yarinyar data gama musu rashin kunya yanzu kalmar nunar rana d'in data fad'a na masa yawo a brain d'inshi anya ba zaginshi tayi ba kuwa? lallai saiya nemi ma'anar kalmar nunar rana idan ya kasance zagine to kuwa zaisa a nemo masa ita duk cikin fad'in Kano ya koya mata darasi. "Innalillahi, Heedayah? dama haka kike ban saniba?". Zainab ta fad'a cikin zaro ido lokacin da Heedayah ta k'arasa wajenta. Ajiyar zuciya Heedayah ta saki tareda dafe k'irjinta tace "Wayyo ALLAH nah ashe ni d'in dai jaruma ce ban saniba sai yau". "Jarumar gaske kuwa ni ina zan iya irin wannan abinda kikayi". "Ke nimafa k'arfin hali ne kawai wlhy amma bakiji yadda k'irjina ke lugude ba". "Duk da hakan ma dai kinyi k'ok'ari na sara miki, ke daganin irin motocin nan ai kinsan ba k'aramin mutum bane a ciki". Fuska Heedayah ta yatsina tace "Balarabe ne mafa a ciki nasan duk b'ab'atun dana dingayi ma ba jina yake ba shiyasa ma ya hana bodyguard d'in ya dakeni saboda bayaji nasan da bahaushe ne saiyasa an tumurmusa ni a wajen can, gani nayi kawai yazo k'asar mu kuma garinmu zai raina mana hankali shiyasa nayi musu haka". "Nifa tsoro nakeji kar yaje yayi mana wani abun kinsan masu kud'in nan maybe shirun dayayi na d'aukar mataki ne". cewar Zainab da har yanzu take a tsorace. Hannunta Heedayah taja tana fad'in "Dallah zomu tafi bai isa yayi mana abinda ALLAH baiyi mana ba". daga nan suka cigaba da tafiyarsu suna hira sai bayan magreebah suka koma gida dan saida sukayi sallah ma a gidan Aunt Rumaisa k'awar Aunt Ramlahn ta tsaresu tace sai sunyi sallah sunci abinci sannan zasu tafi. Nunar rana shine kalmar data dinga yiwa Habeeb Gashua yawo a kanshi (Kunji dorawa kai fa reader's 🤣). Shi duk zatonshi wani salon zagine da hausawa suke amfani dashi wajen zagin mutum, dan haka a washegarin ranar bayan sunyi wani taro da ma'aikatan kamfanin a babban d'akin taro na kamfanin bayan antashi ya rage daga shi sai Mujaheed a d'akin, ganin yanata kallonshi yasa Mujaheed yace "Wai kai lafiya kuwa ko kama nake maka da baby dream d'inka ne kake ta kallona haka?". Tsarabar harara yasamu daga wajen Habeeb kafin yace "Tambaya zanyi maka". Saidaya d'auki ruwan faro dake gabanshi yasha sannan yace "Ina jinka meyake faruwa?". Saidaya cije baki yana wani girgiza k'afa sannan yace "What the meaning of nunan rana?". yayi maganar yana tsare Mujaheed da fararen idanuwanshi. "Nunar rana?". Mujaheed ya maimaita yana yiwa Habeeb kallon mamaki. "Yeah". Habeeb ya amsa masa yana k'ara gyara zaman tie d'inshi. "Kai Gashua ka cika shirme wllhy d'an fari sak idan kayi wani abun meye na wani son jin ma'anar kalmar nan". "Malam zaka fad'amin ne kokuwa". "Eh to ya danganta dai shi nunar rana misali kamar yana nufin......shiru yayi yana sosa kai kafin yaja tsaki yace "Kaji ma'anar ta kwanta min ne gata a raina amma dai kabari zan....."Shut up ur mouth, d'an iska dama duk k'aryar kai bahaushe ne kake mana k'aramin kalma ya gagareka". "Kai banason iskanci fa, cewa nayi ta kwantamin bawai ban saniba gaba d'aya zakamin iskanci". "Damuwarka ce". cewar Habeeb yana hararar shi. "To wai me zakayi da itane?". Bai tanka masa ba ya tashi ya tattara takardun dake gabanshi ya diresu a gaban Mujaheed yayi gaba abinshi yana kallon agogon fata dake d'aure a tsintsiyar hannunshi mai cikeda kwantacciyar gargasa bak'a sid'ik, ganin haka yasa shima Mujaheed din ya mik'e ya d'ebi takardun yaji bayanshi. ★★★____★★★____★★★ "Amshi wannan idan kun tashi lecture ki biya ki kaiwa Hajiya". Aunt Ramlah tace tana mik'awa Heedayah wani abu da batasan ko meye ba acikin leda dan duk anyi wrapping d'insu amma dai tasan bazai wuce nakiya da alkakin datayi ba shine za'a kaiwa Hajiyan, hannu biyu tasa ta karb'a tace "Toh insha ALLAH". daga nan sukayiwa Aunt Ramlah sallama suka tafi itada Zainab. Wajen 3pm suka fito daga lecture, sai lokacin ne take ji ashe itama Zainab wai gida zata wuce saboda ta kwana biyu bata jeba sam bataji dad'i ba taso ace tare suka tafi haka sukayi sallama kowacce ta tari tricycle ta fad'i unguwar da za'a kaita. Hajiya murna kamar me saboda zuwan Heedayah itadai ALLAH ya had'a jininta dana yarinyar, bayan sun gaisa ta bata sak'on Aunt Ramlah godiya ta shiga yi kamar ta ari baki k'warai take jin dad'in yadda yarinyar take kula da ita, tashi Hajiya tayi ta fita da nufin tasa akawo mata abinci. Tana zaune bayan fitar Hajiya taga kamar gilmawar mutum da fararen kaya wajen ta kalla kafin ta k'ara juyar da kanta inda yake ada saikuma ta k'walalo ido ta k'ara waigawa dan ganin abinda tagani d'in da gaske ne kokuwa, sanye yake cikin farar jallabiyyah fara tas kuma sabuwa dal sai irin hular nan tashi ka fiya naci wadda ya d'ora sai hirami daya d'ora a kafad'arshi kalar fari da pink, mug ne a hannunshi ya fito daga k'ofar kitchen yafara taka steps d'in dazai sadashi da cikin falon cikin wani irin taku na mazantaka yana juya spoon a cikin mug d'in dake ta fidda turirin zafi. Habeeb Gashua ne wanda idanun Heedayah suka hasko mata shi tuni yawun bakinta yafara k'afewa wani irin bugu da kai kawo zuciyarta keyi tamkar zata fito saboda tsabar tsoro shikenan itakam tata ta k'are dama ashe jiya da aljani tayi fad'a bata saniba dama saida Zainab ta fad'a tace maybe shirun dayayi mata na d'aukar mataki ne gashi kuwa ta tabbata ya biyota har inda take zai cutar da ita, tuni jikinta ya d'auki rawa sosai tafara fad'in innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahmanir raheem da duk wata addu'a data sani ta neman tsari daga shaid'anun aljanu wani irin fitsari na son kufce mata wanda yazo mata a lokacin. Tun fitowarshi daga kitchen d'in ya ganta kuma kallo d'aya yayi mata ya ganeta itace yarinyar datayi masa rashin kunya jiya, amma duk ba wannan ba abinda ya kawota gidan yakeson sani metazo yi wajen Hajiya? sam bai nuna yaga wata halitta a falon ba ya k'araso ya zauna a 1sitter yayi crossing legs d'inshi kanshi a k'asa yana cigaba da jujjuya tea d'inshi. Rawa bakinta yafara tana nunashi da hannu kafin ta k'walla wata uwar k'ara wadda ta ratsa dodon kunnenshi ya runtse ido gam saboda yadda k'arar ta shigar masa k'wak'walwar kanshi amma duk da haka bai d'ago ya kalleta ba so yake su tafi a matsayin shi aljanin ne kamar yadda yaga tayi zato haka nan ya tashi da sonyin irin shigar har dayazo Hajiya na tsokanarshi wai yatuna k'asar su kenan. Da sauri Hajiya Inna ta shigo kamar zata kifa dan sauri tana fad'in ''Lafiya kuwa Heedayah meya sameki?". Cikin rawar baki da murya take nunashi da fad'in "Hajiya gamo nayi wllhy, aljani ne ya biyoni nan dan ALLAH kibashi hak'uri bazan k'ara yiwa wasu rashin kunya ba kinji Hajiya dan ALLAH kibashi hak'uri ya tafi na tuba wllhy". Inda take nunawa Hajiyan tabi da kallo taga Habeeb tamkar baisan me akeyi ba, d'an murmushi Hajiya tayi itama dason yin tsokana tace "To aini banga komaiba Heedayah". Sosai Heedayah ta k'ara tsurewa tace "Hajiya gashi nan fa yana sha miki tea dan ALLAH Hajiya ki rok'eshi yayi hak'uri karya cutar dani". Kafin Hajiya tayi magana sai gani tayi, tayi luuu tana shirin fad'owa daga kan kujerar ido Hajiya ta zaro ta nufi wajen da sauri saidai kafin ta k'arasa Habeeb Gashua ya rigata wanda hakan yabani mamaki sosai tunda kanshi a k'asa yake bare har yaga fad'uwar da zatayi shi kanshi yayi mamakin hakan, tallafota yayi ta fad'a hannayenshi gaba d'aya jikinta ya saki alamun suma tayi lallai yarinyar nan ba k'aramar matsoraciya bace wato tsiwar ce kawai da fitsara. Hajiya na k'arasowa ya sakar mata ita ya juya ya fice batare daya k'ara bi takan shayin ba. A rud'e Hajiya ta janyo wani ragowar ruwa a cikin glass cups dake kan center table ta shafa mata a fuskarta, ajiyar zuciya takawo ta zabura daga jikin Hajiya tana kallon inda Habeeb yake zaune saidai wayam babu shi ba alamarshi, kuka tasa tana fad'in "Shikenan Hajiya na shiga uku harya b'ace ban bashi hak'uri ba". Hajiya da batasan kan labarin ba tace "Wai wanene meya had'aku dashi ne?". A tsorace tabawa Hajiya labarin abinda ya had'asu kwana biyu da suka wuce, dariya Hajiya tayi tace "To kinga wannan saiya zamar miki darasi Heedayah ba kowane mutum zaka gani a hanya ba kaci masa mutunci wasu ba mutane bane suke shigowa cikin mutane su saje dasu kuma ko ina ana samun irin haka abu kad'an zakiyi kuma suzo su cutar da rayuwar ki dan haka ki dinga kiyayewa kinji, wannan da kika gani jikana ne nina haifi babanshi amma ALLAH yayi masa rasuwa mahaifiyarshi ce balarabiya shiyasa kika ganshi haka baiyi kama damu ba saiya d'aukota". Ajiyar zuciya Heedayah ta sauke tana dafe k'irjinta sai a lokacin taji sanyi cikin ranta wllhy duk zatonta aljanin ne da gaske musamman da Hajiya tace bataga kowa ba amma duk da hakan da a tsorace take dan gani take tamkar zai dawo yaci k'aniyarta a wajen dan da ganinshi da k'yar idan zaiyi mutunci wllhy amma fa she's very very handsome guy dole ma yayi kyau ai tunda Arab ne. A zatonku Heedayah ce Habeeb Gashua yake mafarki? *EL--HABEEB* 💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* 💡 (Home of expert & perfect writer's) No 8. Da k'yar Hajiya tasamu Heedayah ta d'an tsakuri abinci dan har lokacin bata koma normal ba gani take tamkar zai dawo ne bini bini ta kalli k'ofar shigowa falon. Tana gama cin abincin tayi shirin tafiya duk da yadda Hajiyan taso ta k'ara zama tace a'a tafiya zatayi akwai abinda zatayi a gidan idan takoma. Tana fita ta shiga waige waige a k'ofar gidan ko zataga irin motocin data ganshi ranar dasuka had'u amma ba komai da sauri tabar unguwar,sai yanzu ne abinda tayi d'azu yakeson bata dariya tafiso idan taje gida su dara tareda Zainab. Lokacin data koma gidan Zainab d'in ma bata dawoba sai bayan data d'an jima da komawa sannan ta koma, aikuwa tana ganinta tajata d'akinsu ta hau bata labarin abinda ya faru a gidan Hajiya, sosai Zainab tahau dariya harda rik'e ciki jin wai har suma saida Heedayahn tayi cikin dariyar take fad'in "ALLAH ya k'ara, maganinki kenan ai to shi Man d'in meyace?". Baki Heedayah ta tab'e tace "Ko k'ala baice ba nifa nafi zaton ma ko kurma ne dan baiyi kama da masu maganar ba". "Toh kodai shine zai maye gurbin marigayi Kabeer?". Zainab ta fad'a tana kashe mata ido, wani kallo Heedayah tayi mata tace "Ai mai maye gurbin Yah Kabeer saiya shirya wllhy shikam banga wani alamun jarumta a gurinshi ba sai tsayi daya ajiye kamar daren sallah". Dariya Zainab tayi tace "Jarumta ai ba'a k'irar jiki take ba anan take". tayi maganar tana nuna saitin zuciyarta da hannunta, d'an tsaki Heedayah taja tace "Dan ALLAH ya isa haka maganar ta isheni". kafad'a Zainab ta d'an d'age suka shiga wata hirar daban. Yauma kamar kullum kuma kamar yadda ta saba zuwa masa cikin barcinshi yauma haka yau kuma sai mafarkin nashi ya canza salo dan a yau d'in da kanshi yakai hannu da nufin cire mata mayafin data lullub'e fuskar tata dashi amma baici nasara ba duk yayin daya kai hannu da nufin tab'ata saiyaji wani mugun shocking ya kamashi dole yake janye hannunshi da sauri haka dole ya k'yaleta yanaji yana gani ta juya ta tafi harta b'acewa ganinshi daga nan ya farka daga barcin. Cikin tsananin b'acin rai ya farka a yanzu wani haushin yarinyar yakeji yadda ta hanashi sukuni a rayuwar shi yarasa uban da zaiyi mata da kullum saitazo gareshi kuma tak'i yarda yaga fuskarta wannan wace irin masifa ce?. A gaggauce ya shiga bathroom yayi wanka yana k'ara jin haushinta ko makarar nan dayayi ita ta jaza masa. K'ananun tsaki ya dinga saki lokacin dayake shiryawa cikin k'ananun kaya blue black d'in jeans da black shirt body hook sai bak'in takalmi sawu ciki simple kwalliya ce amma ba k'aramin kyau yayi ba kayan sun amsheshi matuk'a musamman daya toshe idanunshi da black space wanda bawai yasashi dan gayu bane sai dan b'oye idanuwanshi da kallo d'aya za'ayi musu a gane yana cikin damuwa bayason kuma a dameshi da tambaya saikuma hakan yabada citta 🤩. Designer's kala kala ya faffesa masu bala'in k'amshi da sanyi sannan ya fita zuwa gaishe da Ummi bayan ya rufe kofar side d'in nashi. Kasancewar tasan alhamis ne yana yin azumi shiyasa ma batayi masa tayin breakfast ba bayan sun gaisa sun d'an tab'a hira ya tashi yayi mata sallama ya fita. Tunda su Aleeyu sukaga yanayin ogan nasu suka san yau a sama yake yafi mu'amala da farin glass duk ranar dayasa bak'i kuwa to kuwa kayi hankali dashi dan zai iya sauke maka dan haka suka dinga kaffa kaffa kowa yana kiyayewa. Koda suka shiga kamfanin ma da ma'aikata na gaisheshi ko hannun dayake d'aga musu ma basu samu ba a ranar kai tsaye ya wuce ta elevator ma yabi ranar sab'anin da da kullum yake hawa lifter ba wanda dai yayi masa magana tunda dai sun rabu dashi lafiya saikuma idan ya sauko. Su kansu y'an kamfanin duk wanda yake da appointment dashi a ranar saida yayi hak'uri dan abinda bai taka kara ya karya ba saiya hau mutum da bala'i hatta Mujaheed ranar saida yayi taka tsantsan dashi baisan uwar da akayi masa ba yake ta musu wannan botsare botsaren. Yaso ya masa iya shege amma ba dama saboda mutanen dake wajen da kuma yadda ya wani had'e rai bazakace yasan wani abu dariya ba duk da dai dama bawai yinta yake ba yafi yin murmushi shima saiya dad'e baiyiba. Lokacin da suka fito zasu tafi bayan ya tashi aiki a dak'ile yacewa Aleeyu ya fad'awa sauran bodyguard d'in su wuce zasuje wata unguwa shida Aleeyun baya buk'atar rakiyar kowa, cikin rawar jiki Aleeyu yaje ya sanar dasu ga abinda yallab'ai yace daga nan ya shiga back seat Aleeyu ya shiga driver seat ya tada motar yaja suka tafi batare dayasan inda zasuba gashi yanajin tsoron tambaya. Sai dayaga dai sunata tafiya har lokacin baice masa ga inda zasuba sannan yayi ta maza yace "Yallab'ai ina muka nufa?". Saidaya d'auki y'an mintuna sannan kamar mai ciwon baki yace "ShopRite". "Kaji wata rigimar kuma, me zaije yayi kuma a ShopRite? shidai iya saninshi duk wasu abubuwan amfaninshi musamman ake yimasa order d'insu bai cika using dana nan k'asar ba amma dan fitina yace a kaishi kome zai siya?. Dole ya canza hanya ya d'auki titin dazai sadashi da shopping mall d'in. Koda suka k'arasa ma sukayi parking bai fitaba gashi dai yana gani anzo amma ko alamun fita bashi dashi, sam Aleeyu bai tanka masa ba suka cigaba da zama a haka. Kamar ance d'ago kanka ya hango wasu saurayi da budurwa sun fito daga cikin Mall d'in sai dariya suke yarinyar cikin matsattsun kaya k'ananu da siririn gyale data d'an yafashi akan tulin gashinta ta manna bak'in google wanda ya kusa mamaye rabin fuskar tata, wani irin bugawa gabanshi yayi ganin kamar yarinyar nan datayi masa rashin kunya ya kuma ganta a gidan Hajiya cikin azama ya cire glasses d'in fuskarshi yana k'ara k'ura mata ido da tunanin kodai kamanni suke da waccan d'in to amma abin mamakin komai na k'irar jikinsu iri d'aya so yake ta cire glass d'in idonta yadda zai gane itace koba itaba. Kamar tasani kuwa takai hannu ta cire glass d'in ta mak'alashi a gaban matsattsiyar rigar dake jikinta sai faman taunar chewing gum take tana murmushi alamun yanayin datake ciki yana mata dad'i, sosai Habeeb Gashua ya zaro ido ganin yarinyar ce dama ashe tantiriya ce? to uban meya kaita gidan Hajiya? lips d'inshi ya cije tareda lumshe idanunshi yana d'an sauke numfashi, yana bud'e idanunshi yaga har sun shiga mota sun hau kan titi. Cikin zafin nama ya b'alle murfin motar ya fito ya bud'e front seat yana yiwa Aleeyu alamu ya fito daga motar, zai tsaya tambayar shi ya daka masa tsawa da sauri Aleeyu ya fito shikuma ya shiga yabata wuta kafin ya figeta da uban gudu yabi bayan motar wannan saurayi da budurwar batare daya tsaya saurarar Aleeyu daya rud'e yake tambayar shi lafiya ina zaije? Tsaye Aleeyu yayi yabi bayan motar da kallo yadda ogan nasu yake bata wuta tamkar yana filin tsere ne ya rasa abinda yake damunshi yau d'in nan da sauri shima Aleeyun ya tare mai napep ya shiga ya nuna masa motar Habeeb dake can nesa dasu yace ita zai dinga bi dole yabi yabi bayanshi mana tunda hakk'in kula da lafiyar shi yana hannunshi. Haka nan yaji zuciyarshi na masa bala'in zafi ganinta dayayi dawani saurayin ga yanayin shigarta sam babu nutsuwa da kamun kai a cikinta cije baki kawai yake yana sakin k'ananun tsaki da tunanin wai me ma yasa yake binsu ne? meye damuwarshi da ita haka? ina ruwanshi da ita? duk wad'annan tarin tambayoyin bai samu nutsuwar dazai bawa kanshi amsar suba burinshi kawai ya samesu to idan ma ya samesu d'in me zaice musu? me zaice musu a matsayin amsar tambayar da zasuyi masa na dalilin dayasa yake binsu? wata mota dake gabanshi yaso karawa saboda gudun dayake yayi gaggawar kauce mata wanda anan ne motar dayake bi ta b'ace masa b'at rage gudun yayi yana k'ara hahhangawa kozai ganta saidai ba ita ba alamar ta. "OH my God". yace da k'arfi yana lumshe ido gamida dukan sitiyarin motar da k'arfin gaske cikin tsananin b'acin rai da takaicin rasasu d'in dayayi. Gefen titi ya gangara yayi parking ya fito daga motar, hannu d'aya yasa ya rik'e k'ugunshi d'ayan kuma ya cusashi cikin tulin lallausar sumar kanshi mai azabar santsi da laushi yana yamutsa ta kafin ya kaiwa motar duka da k'afarshi wanda yayi daidai da saukar Aleeyu daga napep ko canji bai tsaya karb'a daga wajen mai napep d'in ba ya nufi inda Habeeb Gashua yake tsaye cikin takaici. "Boss are you okay?". yace a rud'e yana kallon jikinshi da fatan dai wani abu bai tab'a lafiyar shiba. "Let's go". yace yana cilla masa car key d'in batare daya bashi amsar tambayar dayayi masa ba, cafewa Aleeyu yayi, da kanshi ya bud'e motar ya shiga shima Aleeyun ya shiga ya tada motar suka tafi. Kishingid'a yayi a bayan motar ya rufe idanunshi gam yana hasko abinda ya faru yanzu ko zuwa zaiyi ya tambayi Hajiya WACECE wannan yarinyar? to kuma kar tayi tunanin wani abu ne a ranshi har yakeson sanin ita wace to wai duk meye ma nasa tunanin yarinyar a ranshi da har zai hana kanshi sukuni gefe d'aya kuma ga ta cikin mafarkin nan. "Yaa ALLAH". ya furta hakan can k'asan zuciyarshi yana shafo k'eyarshi zuwa dokin wuyanshi dake cikeda kwantaccen k'ananun gashi. Gareku reader's, Heedayah ce kokuma wata ce daban??? A kafta. Maryam Ibraheem Aleeyu (Ummee). Mrs Salees Mu'az 💝 *EL--HABEEB* 💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 9. Har suka k'arasa gidan bai bud'e ido ba, koda sukayi parking Aleeyu yaga bashida haramar fita daga motar yadda yake a hakan nan kuma tsoron yimasa magana yake sai dayaga zaman nashi yak'i k'arewa sannan a hankali yace "Oga mun k'araso fa". Batare daya bud'e ido ba yayi masa alama da hannunshi ya tafi kawai fita yayi ya rufe motar yabar wajen yana fatan koma dai meye ALLAH ya sauk'ak'awa maigidan nasu damuwarshi. Sai bayan wani lokaci sannan ya fita ya shiga cikin gidan duk da baiso shigar ba saboda yadda yanayin shi yake amma kuma ya riga ya saba yana dawowa saiya dangana da inda Ummi take. A hargitse ya shigarwa Ummi ko sannu da zuwan da Neehlah take masa baiji ba baima ganta ba sam, tsareshi Ummi tayi da tambayar lafiya kuwa me yake damunshi? lafiya k'alau yace mata kawai yanayin aikine ya gaji ne sosai ba yadda batayi dashi ba akan ya fad'a mata idan wani abun ne yace ba komai dan haka tace ya tashi yaje yayi wanka ya huta tashin yayi ya fita ta bishi da kallo can k'asan ranta bata yarda da abinda yace mata ba. Ranar ko abinci kasa ci yayi dama kuma ba ma'abocin cin nashi bane sai coffee daya dinga d'urawa cikinshi da zafinshi da komai, wanka yayi ya d'aura alwalah yayi sallah raka'a biyu kamar yadda ya saba kullum kafin ya kwanta sai yayi. jallabiyyahr dayayi sallahr da ita ya cire yasa pyjamas milk color masu kauri cikin nutsuwa ya karanto addu'ar kwanciya barci ya kwanta, yana kwanciya kuwa tunanin yarinyar ya addabeshi daya rufe ido da niyyar yin barci saiya hangosu itada wannan saurayin lokacin da suke dariya. Da k'yar yasamu barci ya d'auke shi da tunanin ta lokacin da barcinshi yayi nisa kuma yarinyar data saba zuwa masa cikin barcinshi tazo abu biyu ya had'e masa, wani irin barci yayi a ranar marar dad'i shiyasa akan kunnenshi akayi kiran sallahr asubah na farko tashi yayi yana jin jikinshi duk ba k'wari wanka yayi yasa jallabiyyah ya fesa turaruka sannan ya wuce masjeed. Bayan dawowar shi bai koma barci ba sai Alqur'ani mai tsarki daya d'auka yafara rairo karatunshi cikin daddad'ar murya dakuma k'ira'ar shi irin ta Mohammad Alkhusary mai dad'in gaske. Barcin dabai komaba kenan dan lokacin daya gama karatun gari yayi haske sosai dan haka yayi wani wankan yafara shirin office. ★ Tun daga ganin yarinyar dayake tsammanin Heedayah ce yake hange hangen inda zai ganta a kullum idan ya fita ya tsiri zuwa gidan Hajiya akai akai sab'anin da dayake d'iban kwanaki kafin yaje ko ALLAH zaisa ya ganta amma bai k'ara ganinta ba kuma bawai zuwan ne batayi ba saidai sab'ani da suke samu wani lokacin data fita zai shigo kokuma idan shi yagaji da zaman ya fita itakuma tazo duk yabi yahana kansa sukuni shi kanshi a karan kanshi idan aka ritsashi akace saboda me yake nemanta bai saniba baisan me zaice ba kuma ya kasa tambayar Hajiya labarin yarinyar. **** Ummi ce zaune akan royal chair d'in da sukayiwa had'add'en falon k'awanya sai k'amshin turarukan wuta ke tashi na asalin larabawa, gefenta Mujaheed ne zaune a k'asan tattausan carpet d'in dake malale a k'asan falon sai d'aya gefen nata Habeeb ne shima a zaune a k'asa kowanne kanshi a k'asa. Kallonsu Ummi tayi d'aya bayan d'aya kafin ta tsaida kallonta kan Habeeb tace "Abbuna Mujaheed ya kawomin k'ararka me yake faruwa ne?". Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace "K'ara ta kuma Ummi?". "Yes" ta amsa masa, kai ya d'an d'aga ya jefawa Mujaheed wata uwar harara yace "Me yace nayi Ummi?". "Yayi min complain akan yanzu ka daina maida hankalinka gaba d'aya aka aikinka sun rasa gane kanka". B'ata rai yayi sosai yace "Ki daina yarda da maganar yaron nan Ummi munafuki ne so yake kawai ya had'ani dake". Ido Mujaheed ya zaro tareda dafe bakinshi yana kallon Habeeb wanda yayi mirsisi kamar bashi ya fad'i maganar ba ya juyar ma da kanshi gefe yana faman kumbura baki. "Babu wani zancen had'i ko munafunci ni kaina shaida ce kuma nasha tambayar ka abinda ke damunka saboda nakasa gane kanka a y'an kwanakin nan meye damuwarka ne Abbana". tace cikin rarrashi tana shafa kanshi, ido ya d'an lumshe yace "Ummiiii babu komai fa kawai dai......."Wllhy k'arya yake Ummi ko last week saidaya janyo mana babbar asara a kamfani ko k'arya nayi?". Mujaheed ya katse Habeeb yana hararar shi. "Asara kuma? wace iri?". Ummi ta tambaya. Zama Mujaheed ya gyara yace "Ummi wasu bak'i ne mukayi daga Abuja mun dad'e muna tsumayin zuwansu anata shirye shiryen zuwansu dayake wannan ne first time da zamuyi hark'alla dasu kuma akwai tarin alkhairai da mukesa ranshi ta dalilinsu, a ranar da zamuyi zaman dasu kowa ya hallara a d'akin taro damu dasu anata jiranshi ya fara magana kinsan me yayi Ummi?". Kai ta girgiza kawai, saida Mujaheed ya harari Habeeb da shima yake hararar shi, cikeda takaicin abinda yayi musu ranar yace "Wllhy Ummi d'an bawan ALLAHn nan kawai saiya tallafe hab'a ya d'ora d'aya kan d'aya yana kallon kowa d'ai d'ai dayake d'akin taron ko A baice ba, danaga haka nayi masa magana yak'i kulani sannan wani daga cikin ma'aikatanmu shima yayi masa magana yak'i kulashi shine sai d'aya daga cikin bak'in namu wani yayi magana dan sunfara gajiya da zama ga shugaban taro kuma baice komaiba, kamar jira yake wllhy Ummi ya hau kan mutumin nan da bala'i wai zai koya masa aikinshi ne daya dad'e yana yi ya dinga masifa duk ya hargitsa d'akin su kuma sukayi fushi sukayi tafiyarsu muka rasa wannan damar, sai gashi har ana rirrik'eshi wai zaiyi fad'a da mutumin, Ummi bansan meya canza Gashua haka ba mutumin dayake da salihi ko hayaniya baiso amma yanzu Ummi idan ya zage yana bala'i baza kice shi bane ya koyi wani zafin rai da masifa dan mutumin dayayi magana daga ma'aikatar tamu ranar da abin yafaru saidaya bashi suspension wai ya rainashi har yanzu bai dawo dashi ba". Mujaheed ya k'arasa maganar yana kallon Habeeb da tunda ya fara maganar yake cije baki yana hararar shi baki ya tab'e yana d'an d'age kafad'a alamun ko a jikinshi. "Haka akayi babana?". cewar Ummi tana kallonshi, rasa abin cewa yayi sai k'asa dayayi da kanshi yana shafa k'eya. Cikin b'acin rai Ummi tace "Kanaso raina ya b'aci ne a kanka?". Da sauri ya girgiza kai batare daya yi magana ba. Kai ta kad'a tace "To ka maida hankalinka kamar yadda kake a baya banaso in k'ara jin labarin ka k'ara yin wani abu dazai dinga ja muku asara a kamfanin ku saboda amana ce a hannunka, abinda duk yake damunka kuma ubangiji ALLAH yayi maka maganin shi tunda bazaka fito ka fad'amin ba a matsayina na mahaifiyarka". A marairaice ya d'ago kai zaiyi magana ta dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu tareda fad'in "Ya isa haka tashi kuje ALLAH yayi muku albarka". Ba musu duk suka tashi suka fice, Habeeb ne a gaba Mujaheed na biye dashi a baya suna fita Habeeb ya nufi side d'inshi da sauri Mujaheed ya mara masa baya ko waigowa baiyi ba bare ya kalleshi yana shiga ya zube kan kujera ya d'age kanshi sama yana kallon roofing falon da adon fitilun da aka k'awatashi dasu. "Meya shigo dakai nan?". yace lokacin da Mujaheed ya shigo falon batare daya d'ago kaiba. "Abinda ka shigo yi kaima?". Mujaheed ya fad'a hankali kwance yana zama kusa da Habeeb d'in, d'agowa yayi yana fad'in "Malam get out tun kafin in sauke fushina a kanka". dariya Mujaheed ya k'yalk'yale da ita yace "Ka dad'e baka sauke fushin naka ba a kaina Gashua yau bazan bar gidan nan ba saika fad'amin dalilin canzawar ka kodai har yanzu baby dream d'inka ke caza maka brain ne?". Shirun da Habeeb yayi yasa yagane eh hakan ne da gaske canzawar shi tanada alak'a da yarinyar dake zuwa masa cikin mafarki k'aramin tsaki Mujaheed yaja yace "Kuma dan ubanka saika dinga zuwa kana sauke mana, wadda zata caza maka k'wak'walwa daban mu kuma daba ruwanmu saikazo kana sauke mana kwandon masifa". Kai ya d'ago tareda lumshe idanunshi yana sauke numfashi gamida shafa sumar kanshi abubuwan duk sun had'u sun cakud'e masa ya yini yana tunanin yarinyar gidan Hajiya idan dare yayi kuma ta cikin barci tazo masa sun sashi a tsakiya ba dole aga canji a wajenshi ba?. Mujaheed duk saiyaji tausayin d'an uwan nashi kuma abokinshi ya kamashi a hakan ma kuma baisan da labarin yarinyar zahiri ba, kafad'arshi ya dafa cikin taushin murya yace "I'm so sorry Gashua ka cigaba da addu'a bata bar komai ba, ni kaina daba ni nake mafarkin nan ba abin ya fara damuna wlhy I'm sorry My brother". Kai kawai Habeeb ya jijjiga masa yana had'iyar wani yawu mai d'aci. "Tashi kaje ka shirya mu fita kasan yauma munada wani zaman da zamuyi saura kuma kaje kayi crossing legs kana kallon mutane d'ai d'ai ubanka zanci wllhy". ya k'are maganar yana dariya. "Nida kai zanga mai cin uban wani d'an iska kawai". Habeeb ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya wuce makeken bedroom d'inshi dan yin wanka. Bai dad'e ba ya fito cikin shigar manyan kaya sabuwar shadda ce fara k'al sai yarari take da d'aukar ido ko gwiwar shi rigar bata k'arasa ba tasha wani uban aiki da ash color d'in zare hakan yasa ya murza hula zanna wadda ta hau da zaren da akayi aikin sai takalmi mai mad'auri irin na maza shima ash color sai farin glass daya manna wanda ya k'ara fito da kyawun dayayi agogon dake mak'ale a hannunshi ma na fata ash ne sai wani azababben k'amshi yake fitarwa wanda ya karad'e dukkan falon tun kafin fitowarshi duk da girmanshi kuwa, fitowarshi yasa Mujaheed dake rik'e da waya a hannunshi ya d'ago kai ya kalleshi y'ar dariya yayi yace "Wow Masha ALLAH so beautiful yanzu wazai ganka yace akwai wadda ke firgita ka cikin barcinka gaskiya koma wacece na jinjina mata". ya k'arasa maganar yana mik'ewa tsaye tareda salute kamar wani d'an sanda. "Useless man". Habeeb yace yana binshi da harara yayi gaba yana d'auko wayarshi a aljihun gaban rigar wadda tafara wani sautin kid'a mai mai dad'in gaske alamun kira ne ya shigo ya fice yana amsa kiran Mujaheed ya bishi yana dariya. Afwan babu yawa 🙏. Kwana biyu za'a jini shiru sakamakon biki dazamu fara gobe in ALLAH ya kaimu saikuma bayan biki insha ALLAH. Nagode. *EL--HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) Alhmdulillah munyi biki lafiya antashi lpy nagode sosai da addu'oen ku dafatan ALLAH yaba ango da amarya zaman lafiya dauwamamme ya kad'e dukkan fitina a cikin aurensu dama sauran wad'anda suka angwance muna musu fatan alkhairi. No 10. Kwanaki sun cigaba da tafiya yayin da har yanzu dai bata canza zani ba game da irin mafarkin da Habeeb Gashua yake, kuma har yanzu dai bai k'ara had'uwa da wannan yarinyar ba wadda kullum tunanin ta yake caza masa k'wak'walwar kanshi yasha komawa ShopRite d'in ko ALLAH zaisa ya ganta amma ko mai kama da ita bai tab'a gani ba. Aleeyu yana mamakin abinda yake dawo dasu Mall d'in tunda tare suke zuwa kuma basa shiga saidai yasashi yayi parking a waje yana kallon masu shige da fice duk da dai bai fad'a masa ba yasan wani abun yake nema kuma da alamu abinda ya tab'a gani kwanaki har ya bishi a mota shiyake dawo dashi gurin koma dai meye ALLAH ya kawowa maigidan nashi mafita gaba d'aya ya wani sukurkuce ya hana kanshi sukuni. Yau kam shi kad'ai ma yadawo Mall d'in bayan sun koma gida daga office ya k'ara yin wanka ya fito duk suka taso danyi masa rakiya kamar yadda suka saba ya dakatar dasu har Aleeyun ma dasuke fita tare yau dakatar dashi yayi yace baya buk'atar rakiyar kowa dan haka aka bud'e masa mota ya shiga yabar gidan. Ya dad'e zaune cikin mota yana raba idanu kan mutane masu shiga da fita amma dai har yanzu zancen d'aya ne babu ita babu alamar ta, idanunshi ya lumshe tareda luma hannunshi cikin sumar kanshi ya shiga yamutsa ta lokaci d'aya yana fesar da wata zazzafar iska daga bakinshi wanda hakan yabawa daddad'an k'amshin mouth freshner d'in dayayi amfani dashi fitowa mai k'amshin banana, da sauri ya bud'e idonshi kamar wanda akace yayi hakan ya k'urawa wata Range Rover fara datayi parking ido haka nan ya tsinci kanshi da son ganin mai fitowa daga cikin motar, koda motar tayi parking ma saida aka dad'e ba'a fito ba hakan kuma baisa ya d'auke idanunshi daga kai ba gabanshi na wata irin fad'uwa daya rasa dalilin yinshi. Luckily idanunshi suka hasko masa hoton wannan yarinyar ta fito daga motar, yau shigar atamfa ce tayi saidai an ciwa atamfar mutunci wajen d'inki saboda yadda duk ta fito da tsarin halittar jikinta gashi bawani mayafin kirki d'an siriri ne ta rataya shi a kafad'arta, lips d'inshi ya cije cikeda b'acin rai ganin irin banzar shigar datayi, kai tsaye ta wuce cikin Mall d'in cikin wani irin taku na yanga da jan hankali tana k'ara gyara side bag d'inta dake rataye, bayanta yabi da kallo cikin jin haushin yadda take bayyana surar jikinta kowa na kallo jiyake tamkar ya janyota ya koya mata hankali. Fita yayi shima daga motar yabi bayanta yana d'ora P. Cap d'in daya fito da ita a hannunshi a kanshi, koda ya shiga ciki baiga alamunta ba sam, tsaye yayi ya tura hannayenshi duka a aljihun wandon jeans d'in dake jikinshi yana wuwwurga idanunshi ko zai hangota. Can gurin turaruka ya hangota a tsaye tana dubawa, cikeda karsashi ya nufi wajen yana zuwa kusa da ita yaja birki ya tsaya dan baisan abinda zaice mata ba, jin alamun mutum a kusa da ita yasa ta d'an juyo sam batayi tsammanin ita yake bi ba dan haka tayi gaba tana k'ara duddubawa shima yabi bayanta, ganin dai da gasken ita yake bi yasa ta tsaya ta juyo idanunsu suka had'u waje d'aya yayin da bugun zuciyarshi ya k'aru itakuma nata yafara daga lokacin. "Malam lafiya kuwa? me kake nema ne a wajena da kake ta bina tun d'azu?". Cikin tsiwa da rashin kunya tayi maganar tana masa wani irin kallo duk da yadda gabanta yake fad'uwa wanda kallon cikin idanun Habeeb ya haddasa mata. Sosai ya had'e rai ya k'ara matsawa daf da ita murya ba alamun wasa yace "Meya fito dake da irin wannan shigar? meye yasa bakya kishin kanki ne?". Sakato tayi tana kallonshi cikeda mamakin abinda yace ikon ALLAH sai kallo bata tab'a ganin mutum ba yazo kuma ya tsareta yana tuhumarta to me yake nufi? "Bakya jine?". yace a zafafe yana bud'e mata idanu, wata uwar harara ta sakar masa tace "Kai dallah malam ya isheka haka ya zakazo kana tuhuma ta batare dana san kai d'in wanene ba daga jin maganar ka ma hausa bata isheka ba alamu sun nuna kai ba d'an k'asar nan bane dan haka ka gaggauta komawa k'asar ku ka nemo yarinyar dakake nema". ta k'are maganar da jan wani mugun tsaki tareda sakar masa harara tayi wucewarta tana cigaba da taunar chewing gum d'in dake bakinta. Tsaye yayi ya kasa katab'us shi bai juya ya fita ba haka kuma bai bita ba ya shiga duniyar tunani. Gaskiya shima kanshi yafara tunanin wadda yagani a gidan Hajiya daban sannan wannan ma daban idan ya canka daidai su d'in twins tunda gashi nan ba abinda ya rabasu da waccan d'in to amma meyasa yaga waccan cikin shigar kamala da mutunci wannan kuma gani biyun dayayi mata duk ba shigar arzik'i ce a jikinta ba. "Bambancin ra'ayi". wani sashen na zuciyarshi ya amsa masa, kai anya kuwa? kodai ita d'in ce take so tayi masa wasa da hankali tayi masa BASAJA shiyasa ta nuna ba ita bace. "Oh my God". ya fad'a cikin tsananin damuwa yana lumshe shanyayyun idanunshi da suka canza kala, baisan iya adadin mintunan daya d'auka tsaye a wajen ba yayi zurfi cikin tunani daga bisani ya fito daga cikin Mall d'in koda yakai dubanshi inda motar data ajiyeta take ba komai alamun har sun tafi kenan. Cikin mutuwar jiki ya k'arasa inda motarshi take ya shiga yabar wajen da gudu ranshi a b'ace. ★★★___★★★ A yau datake ranar alhamis bayan la'asar Habeeb Gashua yakaiwa wani wani orphanage house ziyara wato gidan marayu dake cikin garin Kano, daga shi sai Mujaheed saikuma Aleeyu dake driving d'insu. Sanye yake cikin shadda light blue d'inkin zamani baisa hula ba sai tarin sumar kanshi datasha gyara take ta zuba k'yalli k'amshi kuwa ba'a maganar shi lafiyayyen k'amshi ne mai sanyi da sanya nutsuwa ke tashi a duk ilahirin jikinshi, ya manna siririn farin glass wanda ya k'ara fito da kyawun shi. Kasancewar an san da zuwanshi yasa duk wasu masu ruwa da tsaki na gidan marayun sun hallara dayake wannan shine karo na farko dazai fara zuwa da kanshi basu tab'a ganinshi ba sai tarin alkhairan shi dake riskar su ako da yaushe suna matuk'ar jin dad'in yadda yake taimakawa marayu da tallafa musu dan haka sukayi shiri na musamman dan tarbar wannan bawan ALLAHn. Suna isa aka zagaye motar su, kowa kagani cikin farin ciki da annashuwa fitowar Habeeb daga mota yasa suka k'ara fad'ad'a fara'ar fuskar su suna masa sannu da zuwa shi kanshi bai san lokacin daya d'an saki fuskar tashi ba sab'anin da datake cunkus da ita ya shiga gaggaisawa da mutane. Gidan marayun suka shiga zazzagayawa kamar yadda ya nema dan ganin abubuwan da suke da buk'ata sun shiga hospital d'insu da school da sauran gurare duk inda yaga sunada buk'atar gyara ya kanyi magana tun a wajen tareda yimusu alk'awarin gyarawa insha ALLAHU sunyi murna k'warai da gaske suka shiga godiya da fatan gamawa da duniya lafiya. Check ya rubuta musu a lokacin yabasu bayan kuma gyaran da yayi alk'awarin yi musu, lokacin kam kasa magana sukayi suka rasa bakin godiya hak'ik'a wannan bawan ALLAHn ba mai saka masa sai ALLAH, ubangiji yana son a farantawa maraya. Har bakin motarshi suka rakoshi suna k'ara jaddada godiyarsu da yiwa iyayenshi addu'a wanda yake tsananin jin dad'in hakan yana matuk'ar son yaji ana yiwa iyayenshi addu'a yakan tsinci kanshi cikin farin ciki mara misali, d'aya daga cikin masu kula da marayun ne yace bari a kirawo wasu daga cikin yaran suyi masa godiya sam baiso tsayawa ba suka rok'eshi ya tsaya suma suna son ganinshi. Saida Mujaheed yasa baki sannan ya hak'ura ta tsaya. Kanshi a k'asa yana danna wayarshi yaji hayaniya da maganganu, duk da haka bai d'ago kaiba har suka k'araso suka fara gaisheshi bai amsa ba sai daya kashe wayar ya maida cikin aljihun gaban rigar shi sannan ya d'ago kai da niyyar amsawa idanunshi suka fad'a cikin na yarinyar nan tana sanye da k'aton hijab har k'asa mai hannu ruwan zuma fuskarta d'auke da mayalwacin murmushi wanda ya k'awata fuskar tata sosai saboda jin dad'in ganin wanda yake tallafa musu a yau d'in shiyasa murmushi ya kasa barin kyakkyawar fuskarta. Wani irin fad'uwar gaba ne ya ziyarci Habeeb cikeda tsabar kad'uwa yasa hannu ya fige glass d'in idonshi ko shine bai gwada masa daidai ba still dai itace tsaye cikin sauran yaran tana magana da wata a kusa da ita, da wani irin sauri ya shiga ratsawa ta cikin yaran dayake daga can k'arshe take daga yaran har manyan sai aka bishi da kallo cikeda mamaki. Tsaye yayi a gabanta yana k'ara k'are mata kallo, a kwanakin baya yayi tunanin ko twins ne amma yanzu yafara zargin yarinya d'aya ce take raina masa hankali, tuni idanunshi suka kad'a sukayi jawur, yarinyar kuwa jikinta ne ya d'auki rawa ganin irin mugun kallon dayake jifanta dashi wanda batasan dalilin yi mata shiba baya ta d'an ja kad'an saboda yadda suke daf da juna dashi ya k'ara binta yana fad'in meya kawota gidan marayu kuma? kota fad'a masa kokuma yasa a d'aureta tunda ita munafuka ce, girgiza masa kai kawai take yayin da idanunta suka cika taf da ruwan hawaye so take tayi magana amma ta kasa saboda tsabar tsoron mutumin daya mamayeta lokaci d'aya. Kowa na wajen idanunshi na kansu an rasa kuma wanda zaije yayi masa magana sai Mujaheed ne ya kutsa kai ya isa inda suke yasa yarinyar mutane a gaba sai wasu zantuka yake mata wanda ta kasa fahimtar su hakama mutanen dake wajen ba wanda yasan ko akan me yake maganar, kafad'arshi ya dafa yace "Wai Gashua menene haka? me yarinyar nan tayi maka ne koka santa ne?". Mujaheed yace bayan k'arasawar shi wajen. Hannu yasa ya cire hannun Mujaheed dake kafad'arshi ya k'ara binta inda ta d'an matsa yace "K'yaleni da ita kawai MJ,. yarinyar nan munafuka ce tantiriya ce nan da kake ganinta kuma wllhy saita bar gidan nan a yau". ya k'are maganar yana jifanta da wata muguwar harara, ido Mujaheed ya zaro yace "Are you mad Mr Gashua?". "Eh d'in mahaukaci ne ni Mujaheed". yace cikin d'aga murya. M&S💝 *EL--HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) Jama'a kubi Habeeb Gashua da addu'a yana neman zaucewa😅🤣 Humayrah taki ta sameki fa sweetyn ki ya sukurkuce ya kamata yaga likitan k'wak'walwa 😂. No 11. K'ara rik'oshi Mujaheed yayi yana fad'in "Please Gashua ka tsaya muyi magana ta fahimta mana me kakeyi haka ne?". fisge jikinshi yayi daga rik'on da Mujaheed yayi masa idanunshi sun kad'a sunyi jawur jijiyoyin kanshi duk sun tashi, ganin abin dai babba ne yasa sauran manyan gurin suka nufo inda suke suna tambayar shi lafiya meyake faruwa rai had'e yake kallonsu yace "Dole ku kori yarinyar nan idan ba hakaba duk sai nasa an d'aureku". kowa na wajen mamaki ne ya rufeshi akan me zaice sai an kori yarinya daga ganinta. Mujaheed daya fara fusata cikin d'aga murya yace "Wai yaushe ka zama mara imani ne Gashua? idan baka tausaya mata a matsayinta na marainiya ba ai bai kamata ace ka cusguna mata ba". "Malam ya isheka haka, kayi shiru da bakinka tunda bakasan abinda yake faruwa ba". Sosai yarinyar take kuka duk gaban hijabinta ya jik'e da ruwan hawaye tunanin ta d'aya ta yaya ya santa har yake fad'ar wasu maganganu akanta wanda bata tab'a sanin su ba tafi tsammanin dai wata ce suke kamanni da ita ya d'auka waccan d'in ce. Duk yadda suka so su nunawa Habeeb yadda al'amarin yake sam ya kasa fahimta ya zage sai bala'i yake wanda wasu dayawa daga cikin mutanen wajen ba fahimtar abinda yake fad'a suke ba sun tsinci kalmar dai dole a koreta ita sukafi ganewa cikin maganganun dayake. Sarai sun san waye HABEEB IBRAHEEM GASHUA sun kuma san waye mahaifinshi duk da baya raye lallai idan har basuyi abinda ya umarce su suyi ba zasu iya jazawa kansu dan haka suka amsa masa da to zasuyi abinda yace d'in. Kuka yarinyar take sosai wasu y'anmata kamar ta suna tayata kukan tunani take idan har tabar gidan marayun nan ina zata dosa? wata sani gaba d'aya a duniyar nan banda y'an gidan marayun wad'anda ta bud'i ido ta ganta tare dasu ashe mugu ne mutumin nan basu saniba in har yayi sanadiyyar barinta gidan nan bazata yafe masa ba dan ya d'auki alhakinta bataji ba bata ganiba. Batayi zato ba taji ya kama hannunta k'iiii da uban sauri ya shiga janta har zuwa bakin gate d'in gidan ya tura ta ya maida gate d'in ya rufe, gaba d'aya ido y'an wajen suka zuba masa an rasa mai yin magana ko ya dakatar dashi dama kuma Mujaheed ne mai k'arfin halin yin hakan shikuma ya tsunduma duniyar tunanin anya kan Habeeb d'in bai kwance ba kuwa? to idan ba kwancewar kai ba ya daga ganin yarinya a gidan marayu sai kora ina tausayi da imanin shi suka tafi da har ya aikata wannan aikin?. Wata kujera ya samu ya zauna yayi k'asa da kanshi tareda rufe idanunshi gam kanshi na wani irin juyawa tsabar tension dayayi masa yawa ya rasa ta inama zai b'ullowa lamarin da gaske ne yarinyar nan FUSKA UKU gareta sai taje ta gama tantirancin ta a waje sannan ta dawo gidan marayu to meye amfanin zamanta a gidan marayun yana so yasan wacece ita me kuma ya kaita gidan Hajiya? Wani daga cikin manyan gidan marayun Mujaheed yasamu yayi magana dashi ta fahimta da nuna masa kar su damu insha ALLAHU zata dawo dama a kwanakin nan sun rasa gane kanshi su kwantar da hankalin su, daga nan ya sallamesu suka watse cikeda alhini musamman k'awayen nan nata su biyu da har lokacin kuka suke. Bayan kowa ya watse Mujaheed da Aleeyu suka k'araso inda Habeeb ke zaune har yanzun bai d'ago kanshi ba, kusa dashi Mujaheed ya zauna yana fad'in "Lamarin ka yafara bani tsoro Gashua ya daga taimako kuma zaka b'ige da wannan aiki? dan ALLAH ka fad'amin damuwarka ko akwai shawarar da zan iya baka ko zata iya zama mafita a gareka". Ci kanka Habeeb baice wa Mujaheed ba bai kuma d'ago ya kalleshi ba, yasan bazai kulashi d'in ba dan haka yace ya tashi to su tafi magreebah takawo kai, nan ma banza yayi masa sai dayaga dama dan kanshi bayan dogon lokacin da suka d'auka a wajen sannan ya d'ago kanshi fuskar nan a cunkushe, a razane Mujaheed yayi baya yana zaro ido saboda yadda yaga idanun Habeeb ya canza yayi wani irin ja na ban mamaki Aleeyu ma dake tsaye saida yaji tsoro, bai kula kowa ba ya tashi ya nufi inda motar tasu take duk saurin da Aleeyu ya dinga yi dan ya bud'e masa motar bai samu dama ba yana zuwa ya bud'e ya shiga Mujaheed da Aleeyu suka shiga Aleeyu ya tada motar suka bar farfajiyar gidan. Tunda suka tafi babu mai magana Mujaheed yasan ko yayi masa magana ba tankashi zaiyi ba a wannan lokacin dan haka yaja bakinshi ya tsuke cikin ranshi tunanin ta yadda zai dawo da yarinyar yake batare da Habeeb ya sani ba. Sun d'anyi nisa da gidan marayun can gabansu ya hango yarinyar tsugune a gefen titi ta mak'ure waje d'aya da alamu kuka take, sosai tausayin ta ya kamashi gaskiya Habeeb bai kyauta ba wllhy in haka ne meye amfanin taimakon daya yiwa gidan? "Yi parking Aleeyu". Mujaheed yace yana kallonshi, parking d'in yayi kuwa kamar yadda ya umarce shi, juyowa yayi ya kalli Habeeb daya kishingid'a idanunshi a rufe yace "Dubi yarinyar can Gashua abin tausayi shin baka tausayawa maraicinta ne? kokuma baka gudun ubangiji ya kamaka da hakk'inta? ina rok'on ka Gashua dan ALLAH dan alfarma da martabar annabin mu kayi hak'uri inje in maida yarinyar nan gidan can baka tunanin duk halin data fad'a a yanzu kaine sanadi? please and please Gashua". Ido ya k'ara runtsewa sosai tsigar jikinshi na tashi saboda girman abinda Mujaheed ya had'ashi dashi, shi wanene da za'a had'ashi da girman ALLAH da ANNABI ya juya baya? ai saidai idan bashi da damar yin abun, kuma akwai tunanin daya d'arsu a ranshi yanzu bayan barowar su gidan marayun wanda idan yarinyar tana can aikin zaifi zuwa masa da sauk'i fiye da ace bata gidan ( A tunanin ku me zai aikata reader's??? ). Kai ya kad'awa Mujaheed alamun amincewa batare da kuma ya bud'e idanunshi ba. "WOW thank you very much abokina ALLAH ya saka maka, bari inje". Mujaheed ya fad'a cikin tsananin farin ciki ya fice daga motar cikeda zumud'i dan sam baiyi tunanin Habeeb d'in zai amince da sauri haka ba sanin halinshi da yayi na muguwar kafiya da shegen taurin kan tsiya. Can d'aya side d'in ya tsallaka inda take, ya k'arasa wajenta bakinshi d'auke da sallama, da sauri ta d'ago kai tana kallonshi kukan datake yasa ko sallamar tashi bata amsa ba ta maida kanta k'asa ta cigaba da kukanta mai tab'a zuciya ga duk mai imani, y'an sakanni ya d'auka yana kallonta kafin ya durk'usa a gabanta cikin taushin murya yace "Kukan ya isa haka, munyi magana dashi zan maidake". Cikeda farin ciki ta d'ago kai tana kallonshi tasa hannu tana share hawayen idanunta tana murmushin jin dad'i cikin rawar murya tace "Nagode". "Never mind". ya amsa mata shima fuskarshi d'auke da murmushi da wani irin tausayin yarinyar. "What's ur name?". ya tambaye ta. *"SEEYAMAH*" "WOw nice name, Seeyamah". yace yana k'ara maimaita sunan, tashi sukayi suka jera yana janta da hira har cikin gidan marayun dayake ba nisa sosai sai daya damk'ata a hannunsu sannan ya fito ya dawo wajen motar ya shiga suka tafi. I'm so sorry ba yawa afwan hidima ce dayawa 🙏. Rashin comments dinku yasa gaba d'aya labarin yafara fita a kaina wllhy daga wannan page din bazan k'ara wani ba gaskiya sai naga yanayin comments dinku bawai rashin aikin yine yasa muke rubutun nan ba naga kamar labarin bai muku ba. Mrs Salees Mu'az 💝 *EL--HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 12. Saida suka fara biyawa ta gidansu Mujaheed suka saukeshi sannan suka wuce. ****** Zaune yake kan kujera bayan yagama shan coffee'n nashi na k'aidah, daga shi sai farin boxer ya hard'e k'afafunshi dare ne sosai dan k'arfe biyu ma ta kusa ya gaza samun barci sam sau biyu yana kwanciya barcin yana gagarar shi dan haka ya tashi ya shiga bathroom ya d'auro alwalah yazo ya gabatar da nafilah raka'a hud'u yayi addu'oen shi ya had'o coffee ya zauna kan kujera ya shiga sha duk da irin turirin dayake fitarwa haka yasha yana k'ona masa baki sai kace dole, bayan ya gama sha kuma yayi zaune yana sak'a da warwara kan abinda ya dace yayi duk da dai tun cikin mota ya gama yanke hukunci kan abinda zai aikata saidai yana ganin kamar ba daidai bane abinda shirin yin amma a halin yanzu dai bashida wata dabara data wuce yayi hakan idan ma mutum d'aya ce zai sani koma dai meye zai sani. Da wannan shawarar ya kwanta bayan addu'oen dayayi har barci yayi galabar d'auke shi. Wata sabuwa. Kamar yadda ta saba zuwa masa cikin barcinshi yau d'inma tazo bayan barci ya d'auke shi kuma a yau yayi nasarar ganin fuskar ta, duk da a cikin barci ne ya ganta amma yayi matuk'ar razana fuskar daya gani ta matuk'ar girgizashi dan ba wata bace illa wannan yarinyar fuskarta yagani muraran tana jifanshi da wani irin shu'umin murmushi wani kallo take masa wanda ya kasa fassara shi. Wata irin zabura yayi ya tashi zaune yana ambatar sunan ubangiji yana sauke wani irin numfarfashi tamkar wanda yake filin tsere yayin da zuciyarshi take wani irin zillo tamkar zata fito waje tsabar yadda take bugawa sai gumi ne yake tsattsafo masa ta ko ina. Zaune yayi a tsakiyar gadon ya kasa koda motsa d'an yatsanshi ne, dama wannan yarinyar ce datayi shekaru tana azabtar dashi cikin barcinshi ta hanashi sukuni da jin dad'in barci kamar yadda kowa yake ji. Idanunshi ya rufe yana k'ara hasko fuskar tata wani haushin ta yakeji, lips d'inshi ya cije tamkar zai hudashi ya sauka daga kan gadon ya shiga zagaye bedroom d'in Tofah!!! wata sabuwa inji y'an caca shin a cikin su ukun wacece yake mafarki da ita tsahon wannan lokaci? Heedayah? Seeyamah ce? kokuma waccan wadda har yanzu ba aji sunanta ba??? gareku reader's. Bai ankara ba yaji har har anfara kiran sallahr asubah lallai ba k'aramin lokaci yaja cikin duniyar tunani ba gashi har an kira assalatu, bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya d'aura alwalah ya fito ya zura jallabiyyah ya fita masallaci. Bayan dawowar shi ya kwanta saboda idanunshi da suke masa zafi saboda rashin barci gashi duk sunyi ja sun d'add'aga, bai dad'e da kwanciya ba kuwa wani irin barci mara dad'i ya kwashe shi shi kad'ai yasan yadda yakeji a cikin zuciyarshi. Washegari da wani zazzafan zazzab'i ya tashi ga wani masifaffen ciwon kai daya addabeshi duk yadda yaso ya tashi yayi shirin office kasawa yayi dan haka ya cigaba da kwanciya cikin tattausan blanket d'in daya lullub'a a ciki sam kuma baiyi hausar kiran Ummi ya fad'a mata ba. Ganin shiru shiru bai shigo gidan kamar yadda ya saba ba yasa Ummi taji hankalinta yak'i kwanciya tasan indai lafiya to yanzu ya shirya ya fito har sun gaisa ya tafi office, tasan halin babanta sarai yanzu haka wani abun ne ya d'auki waya ya kirata shine abin ya gagara ya gwammace yayi ta kwanciya a d'aki batasan wani irin hali gareshi haka ba zurfin cikinshi yayi yawa. Wasu y'an mintunan ta k'ara ko zai shigo amma shiru dan haka ta tashi da kanta ta fita zuwa side d'in nashi dan Neehlah tana school bare ta aikata ta gano mata shi. Tayi sa'a tana tura k'ofar falon ta bud'e dan lokacin daya dawo sallahr asubah baisa key ba turata kawai yayi, shiru falon sai k'arar air conditioner dake ta aiki da k'amshin shi na musamman da gaba d'aya side d'in nashi yake d'auka. Kai tsaye bedroom d'in ta nufa ta tura k'ofar ta shiga, tun daga k'udundunewar dataga yayi tasan ba lafiya ba ga kuma A.C daya k'ureta gaba d'aya bedroom d'in ya d'auki wani uban sanyi mai ratsa jiki, saidata kashe air conditioner d'in sannan ta nufi gadon ta tsaya tareda d'an janye blanket d'in fuskarshi ta bayyana yayi saurin bud'e idanunshi ya zubasu kan Ummi dake tsaye wadda saida gabanta ya fad'i saboda ganin yadda idanunshi suka canza launi gaba d'aya gashi sun kumbura, cikin harshen larabci take tambayar shi me yake faruwa?. mayar mata da amsa yayi da yaren datayi masa magana ya fad'a mata abinda yake damunshi d'an k'aramin tsaki taja tace "Abbuna kanada matsala wllhy yanzu saboda ALLAH kana cikin irin wannan halin amma ka gaza kirana a waya ka sanar dani? yanzu akan lafiyar taka ma sai kayiwa mutane zurfin cikin?. "I'm sorry Ummi". yace cikin rawar murya mai data shagwab'a, kai kawai ta d'an girgiza ta samu gefen gadon ta zauna ta fara laluben number a wayarta Dr Huzaifah shine asalin family doctor d'insu dayake dubasu tun bayan dawowar su Nigeria tun ma da ran Abbu, shi ta kira ta sanar dashi Abbanta ba lafiya yayi hanzarin zuwa ya dubashi ya amsa mata da gashi nan zuwa yanzu. Tashi Ummi tayi ta fita bayan ta k'ara ja masa blanket d'in har kanshi, tea ta had'o masa mai kauri wanda yaji had'e had'e irin nasu na Arab bata had'o masa da wani abun ba dan tasan kota had'o dashi ba ci zaiyi ba tea d'inma tasan sai tayi fama dashi haka yake kamar k'aramin yaro idan bashida lafiya. Aikuwa kamar yadda Ummin ta ayyana da k'yar yasha ruwan shayin bayan dogon faman datasha dashi duk ya wani shasshake mata duk abinda yake kuma duk abin nan dayake tunanin nan yana manne da zuciyarshi so yake kawai ya tashi yasan abinyi (Gashua jarabar duniya bakada lafiyan ma 🙄). Kusan a tare Dr Huzaifah da Mujaheed sukazo gidan dan Dr Huzaifah yana shigowa ko rufe gate d'in maigadi baiyiba motar Mujaheed ta kunno kai, anan farfajiyar gidan suka had'u suka gaisa sannan suka nufi side d'in Habeeb wanda ke cikin compound d'in. Baki suka had'a wajen yin sallama Ummi ta amsa musu suka shiga suka gaisa da Ummi Mujaheed yace "Ashe Gashua ba lafiya Ummi?". "Wllhy Mujaheed, zazzab'i ne da ciwon kai suke damunshi". "Ayya ALLAH ya k'ara afwah, ai tunda naje company naga ban ganshi ba nace to ba lafiya dan indai lafiya lafiya wannan Mr business d'in baya makara nayi trying number shi kuma switch off shine nazo ingani saikuma na had'u da Dr shima yazo". Y'ar dariya kawai Ummi tayi jin sunan da Mujaheed ya kira Habeeb dashi wai Mr business, tashi tayi tace "Bari inje Mujaheed tunda gaka ka kula dashi please Dr ayi masa duk abinda ya dace". "Insha ALLAH". Mujaheed da Dr Huzaifah suka had'a baki wajen fad'a, ta fita taja k'ofar. Tashi yayi zaune yana cije baki saboda kanshi dake masa wani mugun ciwo da k'yar yake bud'e ido, Mujaheed ne yasa masa pillow a bayanshi ya jingina. "Sannu Gashua how are u feeling now?". cewar Mujaheed yana zama a bakin gadon. "Alhmdulillah". Yace yana lumshe idanunshi. "ALLAH ya k'ara lafiya". Kai kawai ya gyad'a masa shima Dr Huzaifah yayi masa ya jiki tareda tambayar shi abinda yake damunshi "Zazzab'i ne sai kaina yana min ciwo sosai inajin kamar zai fad'o". yayi maganar yana dafe kanshi wanda yafi takura masa sosai. "Oh sorry insha ALLAH zaiyi sauk'i fatan ka sawa cikinka wani abu?". Dr Huzaifah ya fad'a yana fito da kayan aikinshi daga jaka. Kai kawai ya kad'a masa batare dayayi magana ba. Sosai Habeeb ya had'e rai yana wani yamutsa fuska ganin Dr Huzaifah yana had'a injection a rayuwar shi ya tsani allura kuma tun asalinshi haka yake lokacin da yana k'aramin yaro. Bakin gadon Dr Huzaifah ya k'arasa yana fad'in "Bismillah Mr. Habeeb Gashua". "Ka sani fa bana son wannan abin please ka bani magani kawai Dr". yayi maganar yana cin d'aci da yatsina fuska. "A'a kar muyi haka dakai mana d'an balarabe nayiwa Ummi alk'awarin zan baka dukkan kulawar data dace kuma allurar nan itace best solution dan sam zazzab'in ba magani yake jiba". "Wai Gashua allurar kake wa wannan goce gocen saikace wata mace? haba karka bada maza mana dan ALLAH". Duk da yanayin dayake ciki na jin jiki saidaya dallawa Mujaheed harara kafin ya juyo inda Dr Huzaifah yake tsaye da allura a hannunshi. "Haka nan dai zaka daure mutumina". cewar Dr yana y'ar dariya dan mutum ne mai wasa da dariya. Haka nan yana ciccin magani ya shiga nad'e dogon hannun jallabiyyahr dake jikinshi, Mujaheed sai matse dariyar shi yake yana kallon Habeeb wanda yanayin shi ya nuna kamar wanda zai saki kuka. Matsawa Dr Huzaifah yayi ya saita inda zaiyi masa allurar a hannunshi, runtse ido yayi gam Dr Huzaifah ya tsira masa a inda ya dace. "Ahhhhshh". ya fad'a lokacin da allurar ta shiga jikinshi ya k'ara runtse idonshi yana k'ara damk'e hannun da akayi masa allurar da d'aya hannun kamar zaiyi kuka. "Ahhh kajimin wani sabon iskanci Dr allurar kakewa haka Gashua?". Mujaheed yace yana bud'e baki da sakin dariya. Dariya Dr Huzaifah yayi yace "Ai kad'an ka gani Mujaheed indai Habeeb ne da allura last rashin lafiyar dayayi da ulcer shi ta tashi danayi masa I think har kuka ma saida yayi time d'in". "Ah haba dan ALLAH". Mujaheed ya fad'a yana zaro ido na shegantaka. Kai Dr ya jinjina masa yana dariya gami da d'auko drip yana neman inda zai sak'alashi. Cikin dariya Mujaheed yace "Kutt amma dai anji kunya wllhy ka bada maza wllhy dan ubanshi saiya fita yayi tayiwa mutane muzurai a waje yana tsorata yaran jama'a amma allura kad'ai tana girgizashi ALLAH ya kyauta maka to". Babu wanda ya kula a cikinsu sai zamewa dayayi ya kwanta yana sauke numfashi har lokacin yanayin fuskarshi bata gama daidaita ba. Drip d'in yasa masa sannan ya rubuta magunguna yaba Mujaheed takardar yace a siyo su idan drip d'in ya k'are Mujaheed ya cire masa sannan ya k'ara samun abinci yaci, daga nan yayi musu sallama ya fita Mujaheed yana k'ara yimasa godiya. Nan Mujaheed ya cigaba da zama da Habeeb duk dama dai barci ne ya d'auke Habeeb d'in Ummi ma ta k'ara shigowa ganin jikin nashi ta sameshi yana barci, fita tayi tana yiwa Mujaheed sannu. *EL--HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 13. Har drip d'in da Dr yasawa Habeeb ya k'are Mujaheed ya cire masa bai sani ba yanata barci, sharp sharp ya fita yaje wani babban pharmacy ya siyo magungunan yadawo yasamu har lokacin bai farka ba. Sai abincin daya gani da lemuka da alamu Ummi ce ta kawosu. Sai daf da Azhar sannan Habeeb ya tashi ba laifi ya d'an ji dama dama sosai a jikinshi zazzab'in kuma tuni ya sauka sai ciwon kan da har lokacin bai gama sakinshi ba. "Gashua ya jikin naka?". Mujaheed ya fad'a yana kallonshi bayan tashin shi "Alhmdulillah". yace yana k'ok'arin mik'ewa tsaye ya nufi hanyar bathroom dan yin wanka Mujaheed ya bishi da kallo kafin ya maida kanshi kan wayar da dama ita yake dannawa, ya d'an d'auki lokaci kafin ya fito sanye da bathrobe black color da k'aramin towel a kanshi yana goge sumar shi kai tsaye clothes d'inshi ya nufa ya bud'e wani side wanda kayan shan iska ne kawai na zaman gida ya d'auko wasu riga da wando red color da adon fari a jiki ya koma toilet d'in ya shirya ya fito, gaban mirror ya tsaya ya taje sumar kanshi ya shafa mata mai ya fesa turaruka sannan ya shimfid'a pray mat ya tada sallah. Yana zaune akan dardumar bayan ya idar da sallahr Mujaheed ya kalleshi yace "Ni zan wuce Gashua, accountant yafara kirana kasan munada lissafi dashi yau d'in nan amma tunda ga yadda ta kasance sai mu d'aga lissafin". Kai ya girgiza cikin sanyin murya irin ta marar lafiya yace "No, zaku iya yi ba dole sai ina wajen ba tunda gaka hakan ma yayi". "Okay bari inje ga abinci nan ga kuma drugs d'in nan kan bedside ALLAH ya k'ara afwah". Bai jira amsawar Habeeb ba ya fice dan yasan mawuyacin abune ya amsa d'in. Kallon inda kayan abincin suke yayi an shiryasu cikin babban tray yunwa yakeji sosai kuma bayajin zai iya ci bai sha'awar komi a yanzun ga bakinshi dayake masa wani iri ba dad'i, lumshe ido yayi yana k'ara tuna abinda ke faruwa dashi cikin y'an kwanakin nan kamar wanda akeso a haukata koma dai meye yazo k'arshe insha ALLAH dan zai d'auki matakin dayake ganin yafi masa, saita fad'a masa dalilin dayasa take masa wannan iskancin na canje canjen yanayi datake. Tashi yayi ya fita falon shi ya shiga k'aton kitchen d'in dake cikin falon wanda yaji uban kayayyakin electric, black coffee ya had'a ya koma kan kujera ya zauna ya shiga sha da zafinshi kamar yadda ya saba, sam bai bi takan magungunan da Mujaheed yace ya siyo ba bare yayi tunanin shan su. ★ 9:45pm. K'aramar farfajiya ce wadda aka k'awata ta furanni masu k'amshi sai rumfa irin ta bunu d'in nan teburi ne guda d'aya kacal sai kujeru guda hud'u da sukayi masa k'awanya an wadata ko ina da hasken fitilu masu kyau da d'aukar hankali wannan duk a cikin sashen Habeeb yake nan yake d'an zama jefi jefi yana shan iska duk da bawai zaman gidan ya cika yiba kafin ya zauna d'in ma aiki ne. A yau dai a daidai kuma wannan lokacin yana zaune a ciki yana jiran zuwan Aleeyu wanda sukayi waya dashi yana son ganinshi. K'arar ringtone d'in wayarshi ne yasa ya bud'e idanunshi da suke rufe, hannu yakai ya d'auko wayar dake ajiye bisa table d'in yayi picking yakai kunnenshi sam banji abinda yace ba saboda yadda yayi maganar tashi murya a shak'e kamar mai ciwon mak'ogwaro. Shud'ewar wasu y'an mintunan da basu wuce biyu zuwa uku ba Aleeyu ya shigo cikin farfajiyar ya k'araso inda Habeeb yake, sallama yayi ya shiga ciki. "Yallab'ai barka da hutawa". yace yana d'an rissinawa alamun girmamawa, sallamar kawai ya amsa yayi masa nuni da d'aya daga cikin kujerun wajen cikin mak'alalliyar murya yace "Sit". Kujera Aleeyu yaja ya zauna ya sunkuyar da kai yana jiran yaji abinda maigidan nasu zai fad'a, Habeeb bai k'ara magana ba yayi shiru tareda rufe idanunshi sai faman girgiza k'afa yake, shidai Aleeyu yana zaune yana jiran Habeeb ya gama shan k'amshin nashi yaji kiran dayake masa, muryar Habeeb yaji yace "Ina tunanin zaka gane yarinyar nan da muka gani a orphanage house wadda nace sai tabar gidan?". "Yes sir, zan ganeta". Baki Habeeb ya d'an cije lokaci d'aya yana lumshe ido sannan ya bud'esu akan Aleeyu dayake jiran k'arin bayani. "Inaso ka sace min ita". yayi maganar yana k'ara had'e rai sosai, a razane Aleeyu ya zaro ido yana kallon Habeeb wanda hankalinshi kwance baza kace ma shi yayi magana makamanciyar wannan ba (jama'a kowa yayi ta kanshi Habeeb Gashua ya zama d'an kidnappers 🙆🏃🏃). Wani mugun kallo Habeeb ya jefawa Aleeyu hakan yasa ya danne tsoratar dayayi ya shiga shafa kai da fad'in "Sorry sir". K'aramin tsaki Habeeb yaja yace "Idan ka d'auko ta ka kaita can k'aramin gidana na lamid'o crescent ka tabbatar babu abinda ya sameta ko kwarsane (k'warzane) kunsan mutumin no hausa 😅) banaso ya sameta do you hearing me?". ya k'arasa maganar yana d'an kama gefen kunnenshi tareda yiwa Aleeyu kallon gargad'i, Kai kawai Aleeyu yake gyad'awa da tunanin yaushe maigidan nasu ya koma haka? kidnapped fa kenan duk da baisan dalilin shi na b'oye yarinyar ba, maganar Habeeb ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi "Zaka iya tafiya, kar kowa yasan da wannan maganar bare har yasan ka d'auko wata yarinya yin hakan zai iya ja maka matsala understand?". "Yes sir, yaushe za'ayi hakan kenan?". cewar Aleeyu. "A yau da daren nan". yace kai tsaye yana mik'ewa tsaye tareda zura hannu a aljihun wandonshi ya zaro wani key ya mik'awa Aleeyu, rissinawa yayi ya karb'a key d'in duk da yadda gabanshi yake ta fad'uwa saboda irin aikin da yallab'ai yasa shi. "Good luck". Habeeb yace murya a dashe tareda fita daga cikin rumfar Aleeyu ya take masa baya. "Ka kula". Habeeb ya k'ara fad'a lokacin da Aleeyu yake k'ok'arin fita daga side d'in nashi. "Insha ALLAH". Aleeyu ya amsa masa. Rufe side d'in nashi yayi ya koma ciki, wanka yayi ya d'aura alwalah cikin nutsuwa yayi raka'ah biyu yayi addu'oen shi sannan ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya barci. Abin mamaki kuma sam a wannan daren baiyi mafarkin yarinyar ba kamar yadda ya saba abin ya d'aure masa kai da tunanin me hakan kuma ke nufi???. °•°•°•°•°•° A wannan daren Aleeyu yayi nasarar k'wamuso Seeyamah yarinyar gidan marayu bayan ya k'ulle mata baki ta yadda koda tayi ihu ma babu wanda zaiji ALLAH ya bashi sa'a kuma sam bai samu matsala ba har ya fice da ita ya sata a mota yabar wajen da mugun gudu. Tun a daren ya kira Habeeb ya sanar dashi aiki ya kammala, yaji dad'i sosai ya k'ara jaddada masa ya kula da ita zuwa da safe zai shigo unguwar daga nan sukayi sallama. Plat house ne gidan da Aleeyu yakai Seeyamah had'add'e ne sosai yaji kayan k'awa tako ina masu kyau da tsada, kuka sosai Seeyamah take na fitar hankali tareda yiwa Aleeyu magiyar ya taimake ta maida ita inda ya d'aukota karya cutar da ita, baiyi magana ba bare ya tanka mata yasa ta cikin wani bedroom ya rufo ya koma falo ya zauna yanajin duk ba dad'i ga tausayin yarinyar daya cika masa rai bai san dalilin d'auko yarinyar ba wato bai hak'ura kenan dama, jiyake tamkar ya d'auketa ya maida ita inda ya d'aukota lokacin da shasshek'ar kukanta ke ratsowa cikin falon dayake. A takure take a k'asan royal bed d'in dake d'akin ta matse kanta cikin gwiwoyinta tana kuka mai cin rai waye wannan mutumin daya d'aukota? meye had'inshi da ita? wane laifi tayi masa? tambayoyin datake ta maimaita su cikin zuciyarta ta kasa samun amsar su, kasancewar ya rufe fuskar shi da face mask shiyasa batasan waye ba kuma koda ta ganshi d'in ba lallai ta ganeshi ba tunda ranar da sukaje gidan marayun bata ganshi ba koma dai waye tana addu'ar ALLAH ubangiji ya kub'utar da ita daga sharrin shi. Afwan da kad'an, na shiga busy ne wayar ma sai in yini ban d'auke ta ba hidima tayi yawa 🙏. Mrs Salees Mu'az 💝 *EL--HABEEB* 💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 14. Gajiya Aleeyu yayi da zaman ya zame ya kwanta kan leather chair d'in dake falon yana lumshe idanunshi, so yake yayi barci amma kukan Seeyamah ya hanashi badan karya rasa aikinshi ba daya d'auki yarinyar nan ya maida ita gidan marayun daya d'auko ta, shi dai ba zaice yallab'ai yayi kidnapping d'in nan saboda kud'i ba to dan me yayi kenan? shine amsar da har yanzu ya kasa samu kuma bashida wanda zai tambaya tunda daga shi sai yallab'ai suka san abinda yake faruwa ba'a kuma buk'atar wani ya shigo ciki. Da wad'annan tunane tunanen barci yayi nasarar sace shi cikin rashin jin dad'i. Hankali kwance Habeeb yasha barcinshi, koda ya dawo daga masjeed ma sallahr asubah wani barcin ya k'ara komawa sai k'arfe tara da y'an mintuna sannan ya tashi, bathroom ya shiga yayi wanka, cikin k'ananun kaya ya shirya k'irar kamfanin D&G black trouser jeans da red shirt mai gajerun hannuwa wanda hakan ya bawa cikakkun fararen damatsen shi damar fitowa, bak'in takalmi yasa k'afa ciki ya d'aura Rolex watch black a tsintsiyar hannunshi sai red p.cap daya zaro inda suke tule a ma'ajiyarsu duk da bawai ya cika mu'amala da ita bane yakan dad'e kafin ya sata (Ba irin d'an gidan Mom sayyeed da Aunt jamila ba Abdallah Madugu wadda ta zame masa kamar ibadah 😅). Gaban makeken mirror d'inshi ya k'arasa wanda ke cikeda uban turaruka masu tsada da asalin kyau, body spray ya fara shafawa sannan yabi jikinshi da kalolin turaruka kusan kala uku masu mugun k'amshi da kama jiki uwa uba kuma sanya nutsuwa da kwanciyar hankali ga duk wanda ya shak'a. Bak'in glass ya d'auka saidai bai sashi a idonshi ba ya mak'alashi a gaban rigar ya fice bayan ya kwashi wayoyinshi. Kai tsaye side d'in su Ummi ya nufa dan gaisheta yana k'ofar shiga falon kira ya shigo d'aya daga cikin wayoyin nashi, duba mai kiran yayi yaga Mujaheed ne picking yayi yakai kunnenshi cikin amon muryar shi mai dad'in saurara yayi sallama Mujaheed ya amsa yana fad'in "Mazajeee ya jikin naka?". Baiyi magana ba sai daya k'arasa shiga cikin falon ya tsaya gaban makekiyar TVn dake lik'e jikin bango yace "Alhmdulillah". "Masha ALLAH, ALLAH ya k'ara sauk'i zaka shigo kamfani ne yau?". "Insha ALLAH, but zanyi wani uzuri kafin in k'araso". "Okay no prob, saika shigo d'in". Mujaheed yace tare da hang up d'in kiran. Yana sauke wayar daga kunnenshi Ummi ta shigo falon da sallama taci gayunta cikin bak'ar doguwar riga k'irar Dubai abayah wadda gaba d'aya gaban rigar akayi mata kwalliya da k'ananun stones masu mugun k'yalli hakan yasa suke ta faman walwali suna d'aukar ido ta yane kanta da gyalen rigar wanda ya k'ara fito mata da asalinta na cikakkiyar balarabiya, k'amshi kawai take zubawa mai dad'i tayi kyau abinta idan ka ganta bazakace tana da cikakken saurayi kamar Habeeb ba. Kan kujera ta zauna tana murmushi, ya k'arasa inda take ya tsuguna har k'asa yana gaisheta cikin yaren larabci, cikin sakin fuska ta amsa tana tambayar shi jikinshi ya amsa mata da yaji sauk'i, daga nan dinning area suka nufa sukayi breakfast duk da dai Habeeb sama sama yayi nashi dan hankalin nashi kuma ya koma kan yarinyar gidan marayu wadda baisan sunanta ba, ganin Ummi ne ma yasa har ya tsaya yin break d'in yasan idan yace baya ci fad'a ne zai sha shi kuma ta ritsashi dole saiyaci d'in shiyasa yaci kad'an ya tashi duk da haka saida Ummi tayi masa k'orafin baici dayawa ba sumbata kawai ya sakar mata a kumatun ta ya fice yana fad'in yayi latti ne. Da kallo ta bishi harya fice daga falon yana k'ok'arin toshe idanunshi da black shade d'in dake mak'ale a gaban rigar shi, girgiza kai kawai tayi tana murmushi kullum da uzurin dazai kawo mata idan yaga tana k'ok'arin tilasta masa yaci abinci dayawa daga yace yana sauri saiyace zai gana dawasu bak'i a ranar ko yace akwai important issues da zaije ya gabatar sai yasan yadda dai ya zille mata ya fita ta rasa irinshi cin abincin ma kamar yana masa wahala ne. Ganin yasa d'aya daga cikin security's d'in dake tsaye jikin motar Habeeb ya bud'e masa k'ofar motar, saidai ganin yayi tsaye yasa ya bishi da kallo da alamu yau zasusha fama dashi ganin black shades d'in daya manna. Hannu kawai Habeeb ya tara masa batare dayayi magana ba, kallon rashin fahimta yabi Habeeb dashi da tunanin me zai bashi?. "Give me my key". yace k'asa k'asa yana d'an hararar shi ganin saida yasa shi magana batare dayayi niyyar yiba, da sauri ya mik'a masa key d'in. "Kowa ya tafi bana buk'atar kowa yau". yace yana k'ok'arin bud'e driver seat ya shiga ya tada motar ya fice daga gidan suka bishi da kallo. Kai tsaye unguwar lamid'o crescent ya nufa inda gidan yake, unguwar sam ba yawaitar mutane sai motoci da suke d'an yawan wucewa kasancewar safiya ce kowa na tafiya wajen aiki. Parking yayi a k'ofar gidan bai shiga da motar ba, ya kira Aleeyu yace ya fad'a masa yana waje, nan da nan Aleeyu ya fito ya bud'e masa suka shiga ciki tare Aleeyu na mik'a gaisuwar shi da hannu kawai ya amsa masa ya wuce ciki, suna shiga falon yaja tunga ya tsaya yana kallon Aleeyu da alama so yake ya tambaye shi wani bedroom d'in take amma ya bud'e baki yayi maganar ne aiki Aleeyu ya saba ganin haka daga gareshi dad'ewar da sukayi tare yasa ya fara lak'antar shi. "Left bedroom". Aleeyu yace yana kallon Habeeb, baice komai ba ya wuce ya nufi corridor'n dazai sadashi da side d'inshi na hagu inda bedroom d'in yake, kafin yabar cikin falon ya tsaya ganin haka Aleeyu ya k'araso ya tsaya a bayanshi, hannu yasa cikin aljihun jeans d'inshi ya ciro rafar kud'i y'an five hundred ya cillawa Aleeyu yace "Kaje kayi breakfast itama ka samo mata abinda zataci". daga haka yayi gaba Aleeyu kuma ya fita daga falon yaja k'ofar. Gaba yayi zuwa bedroom d'in, Seeyamah na zaune gefen gado ta k'udundune cikin hijabinta tun bayan sallahr asubah data idar tana zaune a wajen tasha kuka har ta gode ALLAH, idanunta sunyi matuk'ar yin ja sun kumbura saboda kuka da rashin barci dan koda wasa barci bai d'auke ta ba tunda taga bathroom a ciki ta shiga ta d'aura alwalah tazo ta kabbara sallah, kwana tayi tana sallah tana kai kukanta wajen ubangiji subhanahu wa ta'alah ya fitar da ita daga hannun wannan azzalumin daya d'aukota wanda batasan laifin datayi masa ba, to wane laifi ma zatayi masa? su daba fita suke ba kullum suna gida, sai a lokacin nema ta k'ara k'arewa d'akin kallo madaidaicin gado ne royal sai k'aramar drawer saikuma sofa guda d'aya tak kalar gadon su kad'ai ne a d'akin inka d'auke lallausan carpet d'in da aka malale k'asan dashi. Jin alamun takun tafiya zuwa bedroom d'in datake yasa gabanta yayi muguwar fad'uwa ta runtse idanunta tana kiran sunayen ubangiji tsarkaka saboda batasan da wacce yazo ba yanzun saboda tunda ya kawota ma magana bata had'asu ba. Tsaye yayi a bakin k'ofar d'akin ya lumshe ido yana sauke numfashi haka nan ya tsinci kanshi da fad'uwar gaba wanda ya rasa dalilin hakan, Ido ya bud'e yasa key d'in bedroom d'in wanda Aleeyu ya bashi yasa ya bud'e ya bud'e k'ofar ya shiga, daga bakin k'ofar ya tsaya yana k'arewa Seeyamah kallo ta cikin glasses d'inshi wadda take a mugun tsorace kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da hakan daga inda yake tsaye yana iya hango rawar da jikinta yake ta takure waje d'aya cikin babban hijabinta mai hannu pink color. Tsananin tsoro yasa Seeyamah ta kasa d'agowa ta kalli wanda ya shigo d'in tayi nasarar dai shak'o daddad'an k'amshin jikinshi wanda ya baza ko ina tun shigowarshi gidan. A hankali ya shiga takawa zuwa wajen wani dogon stool na zama wanda yake kusa da sofa, stool d'in ya jawo zuwa gabanta ya ajiye bai zauna ba sai daya kai wayoyinshi kan wannan drawer ya ajiye sannan ya dawo ya zauna, daga zaunen dayake ya cusa duka hannayenshi a aljihun wandonshi yana kallonta da yadda jikinta ke shaking ta cikin glass d'inshi. Baice komaiba haka itama bata d'ago kai ta kalleshi ba sai had'add'un takalman shi datake kallo ta k'asan idanunta da suke zubar da ruwan hawaye. Sai daya fesar da iskar daya cika bakinshi da ita ya sauke k'aramin numfashi sannan ya rank'wafa daf da ita ta yadda har yakejin hucin numfashin ta itama take jin nashi wanda ke had'e da wani sihirtaccen k'amshi so take ta d'ago kai taga waye shi d'in amma ta kasa ganinshi take duk yabi ya cika wajen. "Look at me". yace cikin wata irin dakakkiyar murya wadda duk da ba da k'arfi yayi maganar ba amma sai data jita har tsakiyar kanta, bata d'ago ba sai kukanta data cigaba dayi wanda k'asa k'asa ne yanzu kuma yake k'ok'arin fitowa fili. Lumshe ido yayi yana cije lips ganin tak'i yin abinda yace mata. "I said look at me". ya fad'a a tsawace wanda hakan yayi matuk'ar razana Seeyamah ta d'ago kanta ba shiri ta kalleshi hawaye na zarya a kumatun ta, kallonshi kawai take batare data gane ko shi d'in waye ba saboda glass d'in dake manne a idonshi. "Kin gane ni?". yace cikin tsananin had'e rai da tsare gida. Kai ta girgiza da sauri alamun a'a, shima kan ya jijjiga yana d'an taune lips lokaci d'aya yasa hannu ya zare glass d'in idonshi idanunsu suka shiga cikin na juna wanda hakan ya haddasawa Seeyamah tsananin fad'uwar gaba fiye data d'azu ganin wanda ke zaune a gabanta hakan yana nufin shine yasa aka kawota nan d'in kenan? why? me tayi masa haka?. Glass d'in ya mak'ala a gaban rigar shi p.cap d'in kuma ya cire ya jefata kan gado yana fad'in "Yanzu fa?". Kai ta kad'a masa alamun eh ta ganeshi. "Good". ya fad'a yana kad'a kanshi. Shiru yayi kamar bazai k'ara magana ba kafin yace "Zanyi miki wasu y'an tambayoyi, idan kika fad'amin gaskiya zan k'yaleki insa a maidake inda aka d'auko ki sab'anin hakan kuma bazai miki dad'i ba zan d'auki babban mataki a kanki wanda bazai miki dad'i ba kin gane?". Kai ta d'aga masa tana rufe bakinta da hijabinta. Sai daya k'ara tamke fuskarshi tamau yaci d'aci sosai sannan ya k'ara sunkuyawa daf da ita yace "Kinsan waye ni?". A mugun tsorace take hakan yasa batasan lokacin data d'aga masa kai ba alamun ta sani. Mrs Salees Mu'az 💝 *EL--HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 15. Da mamaki sosai shimfid'e a fuskarshi yake kallonta, koda yake ba abin mamaki bane dan tace ta sanshi dan da ace bata sanshi ba bazata dinga bibiyar sa duk inda yaje ba da batayi masa wasa da hankali ba. Seeyamah kam sai bayan data gyad'a masa kai sannan ta gano irin katob'arar datayi na cewa ta sanshi harga ALLAH tsabar kwarjini da cikar haibar shi ne da yadda yayi mugun cika mata ido dad'in dad'awa kuma da bala'in tsoron shi daya mamayeta lokaci d'aya shine ya haddasa mata hakan gashi ta janyowa kanta. Shiru d'akin ya d'auka sai sautin kukan Seeyamah dake fita k'asa k'asa cikin fad'uwar gaba. Knocking door akayi, da k'yar Habeeb ya bud'e baki yace "Yes coming". Bud'e k'ofar akayi Aleeyu ya shiga hannunshi rik'e da wata leda mai tambarin wani restaurant sai daya rissina sannan ya mik'a masa ledar had'i da car key d'in hannunshi, key d'in kawai ya d'auka yayi masa alamu da ido ya ajiye ledar a k'asa, ajiyewar yayi kamar yadda ya umarce shi sannan ya fice tareda jan k'ofar. Har yanzu bai daina mamakin abinda yasa Boss d'in nasu ya d'auko yarinyar ba especially data kasance marainiya idan ba'a tausaya mata ba ai ba'a cutar da ita ba. "Who I'm?". Taji sautin muryar shi a dake wanda yasa hantar cikinta kad'awa, shiru batayi magana ba to kota bud'e baki batasan me zatace masa ba. bata sanshi ba, bata tab'a ganin ko mai kama dashi ba, abu d'aya tasani a kanshi yana yawan taimakawa gidan marayun su koda yaushe akance musu akwai wani bawan ALLAH dayake taimaka musu bayan haka batasan komai a kanshi ba. Iskar daya cika bakinshi da ita ya fesar ranshi yana k'ara b'aci da rainin hankalin da yarinyar take masa bayaso ya fito mata a asalin Habeeb Gashua d'inshi shiyasa yake d'an bida ita a hankali kafin ya fito mata a true color d'inshi. (Ka d'auki abin da zafi Habeeb 🙄). "Who I'm?". yace yana lumshe ido da alamun b'acin rai cikin muryar tashi wanda yasa tsinkewar gabanta ya k'ara tsananta. "I said waye ni?". ya fad'a cikin wata hargitsattsiyar murya wadda saida d'akin ya amsa tareda tashi a fusace yayi ball da stoll d'in dayake zaune, a razane tayi baya tana k'arawa kukanta volume lokaci d'aya tana rufe bakinta da hijabinta jikinta sai rawa yake tamkar mai jin sanyi. Hannu yakai kan sumarshi ya shiga yamutsa ta idanunshi a lumshe ya rik'e k'ugunshi da hannu d'aya yana sauke numfashi. Takowa yayi har gabanta yaja trouser d'inshi sama sannan ya tsuguna daf da ita har numfashin su na had'uwa waje d'aya. "I'm asking u". yace cikin cool voice kamar bashi ya gama hayagaga ba yanzu idanunshi a kanta. Yawun tsoro ta had'iya kafin cikin kuka da rarraba maganar tace "Bal.....ba.......balarabe ne kai, ALLAH shi kad'ai nasani a kanka sai taimakon da kake yiwa gidan marayun mu". Juyar da kai yayi yana lumshe ido gamida cije lips d'inshi, amma yarinyar nan ta mugun raina masa hankali duk wannan tada jijiyar wuyan dayake saboda yanaso yaji actually abinda yasa take canza kamanni take kuma binshi duk inda tasan zaije shine zata bud'e baki tace wai balarabe ne?. Juyowa yayi yana jan tsaki yace "Hakan yana nufin zaki cigaba da zama a nan gidan kenan har zuwa lokacin da zaki gaji ki bayyana min gaskiya understand?". "Dan ALLAH kayi hak'uri ka maidani inda ka d'aukoni wllhy bansan komai a kanka ba daya wuce wannan please help me". Idanunta ya k'urawa nashi hazal eyes d'in yanason gano gaskiyar abinda ta fad'a, itama kallon nashi take da idanunta da sukayi jawur saboda kukan datasha ko iya wannan hawayen data zubar sai ALLAH yayi mata sakayya akansu. Kai kawai ya girgiza yana datse bakinshi kamar zaice wani abu saikuma ya fasa ya janyo ledar da Aleeyu ya kawo ya bud'e ya tura mata gabanta. "Eat". ya furta hakan kamar mai ciwon baki, kai ta girgiza masa wasu hawayen na gangarowa kumatun ta, fuskar sa ya k'ara tamkewa sosai yace "Bana gane body language open ur mouth". Cikin rawar murya tace "I'm full". Wani mugun kallo ya watsa mata hakan yasa ba shiri ta janyo ledar gabanta ta bud'e takeaway d'in dake sama sakwara ce da miyar ganye da akayi mixing da egusi taji naman rago sai k'amshin spices take. Yadda ya tasata a gaba ne yasa ta fara ci a hankali, kallon yadda take gutsurar sakwarar yake tamkar jariri za'a bawa saboda k'ank'antar ta, bai daiyi magana ba ya tashi tsaye ya isa inda ya ajiye wayoyinshi ya d'auki d'aya ya fara danne danne a ciki. Kad'an ta yayyafita ta ture gefe, tana shirin tashi taje ta wanke hannunta yadawo wajen saita fasa tashin tayi k'asa da kanta cikin fad'uwar gaba, hannu yasa ya d'auke takeaway d'in da sakwarar ke ciki yana kallon yadda ta fiffincine ta ya d'auko d'ayan dake k'asa ya bud'e ya tura mata gabanta, abinda ke ciki tabi da kallo potatoes with eggs sai miyar hanta a gefe. So take tayi masa musu amma ta kasa saboda yadda yabi ya tamke fuskar ba alamun rahma samanta dole tasa hannu ta fara ci duk da kawai dai turawa take batare da tanajin dad'in shiba sam bakinta ba wani d'and'ano, shima d'in kamar wancan kad'an taci ta tureshi cikin ranta tana addu'ar ALLAH yasa kar yace saita k'ara ci saikuma aka ci sa'a bai tanka ba, toilet taje ta wanke hannunta a sink ta fito bata sameshi a d'akin ba harya fice, gefen gado ta samu ta zauna ta matse jikinta cikin hijabinta wani kukan nason k'wace mata. Tare da Aleeyu suka tafi kamfanin bayan ya tabbatar an kulle ko ina ta yadda ba zata samu hanyar fita ba. ★________________★ A safiyar ranar orphanage house suka wayi gari da tashin hankalin b'atan Seeyamah lungu da sak'o na gidan ba inda ba'a duba ba, ba ita ba alamunta ba k'aramin tashin hankali jama'ar gidan suka shiga ba, manya da yara musamman k'awayenta da suka shak'u sosai Ikram da Aminah sai kuka suke sauran na kwantar musu da hankali duk da suma d'in dai hankalin nasu a tashe yake. Abin ya mugun d'aure musu kai, ganin suna k'ara b'ata lokaci yasa mutum biyu suka wakilci sauran sukaje suka kai report police station da hoton ta, anan D.P.O d'in ya tabbatar musu da insha ALLAH zasuyi iya bakin k'ok'arinsu wajen ganin sun nemota. Da rana ma waya Habeeb yayiwa Aleeyu yace yayi launch yakai mata, nan da nan kuwa ya cika umarnin shi yayi takeaway na fried rice with chicken da lemon aya ya had'a da fresh milk ya nufi gidan. Tun daga falo yake jin shasshek'ar kukanta, wani tausayin ta ya k'ara kamashi wato har yanzu bata daina kukan ba. Key yasa ya bud'e bedroom d'in ya shiga bakinshi d'auke da sallama, kan darduma ya sameta ta d'aga hannayenta sama tana kuka gamida rok'on ALLAH ya fitar da ita daga wannan wajen. Lumshe ido yayi cikeda tausayin yarinyar ya k'arasa ya ajiye ledar a kusa da ita, kallonshi tayi cikin kuka tace "Bawan ALLAH kaji tsoron ALLAH ka maidani inda ka d'aukoni ka duba maraicina da tashin hankalin da zakusa bayin ALLAHn da basuji ba basu ganiba ka taimakeni ka fitar dani daga nan wllhy bansan akan me oganku yake tuhuma ta ba help me please". Sosai jikin Aleeyu yayi sanyi wata zuciyar na fad'a masa ya fitar da ita kawai yayin da wata zuciyar take masa kashedi da jan kunne na rasa aikinshi da zaiyi wanda da shine yake taimakawa iyayenshi da basuda k'arfi. "I'm so sorry". abinda yace kenan ya juya ya fita dan idan ya tsaya zuciyarshi zata iya karyewa ya aikata abinda bai shirya yinshi ba. Wani kukan ta k'ara fashewa dashi bayan fitarshi, kanta sai wani irin sarawa yake saboda kuka bata ko dubi inda ya ajiye ledar ba saboda ba damuwar ta bace tasan abinci ne dai kuma ba iya cinshi zatayi ba. Kafin kace me zazzafan zazzab'i ya rufeta ruf batayi yunk'urin hawa gadon ba nan saman pray mat d'in ta kwanta ta k'udundune cikin hijabinta tana rawar sanyi. Afwan da kad'an 👏. Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 16. Aleeyu yana kan hanyar shi ta komawa kiran Habeeb ya shigo wayar shi bayan yayi picking yace masa yasamu boutique ya siya mata kayan sawa. Aiki ja wato har kayan sawa ma za'a siya mata kenan ba ranar sakinta? Aleeyu ya fad'a cikin ranshi yana yin reverse yakoma baya inda ya d'an gota wani babban boutique clothing store yayi parking ya shiga ya fara jidar mata kaya duk dogayen riguna ne ya d'ibar mata da skirt and blouse wad'anda basa matse jiki yaje ya biya kud'in ya shiga mota ya k'ara komawa baya inda gidan yake dan kai mata kayan (Aiki ya sameka Aleeyu Lol). Sosai hankalin Aleeyu ya tashi lokacin daya isa yaga halin da Seeyamah take ciki, har lokacin tana kwance akan dardumar tana rawar sanyi bata ma san da shigarshi d'akin ba, ba shiri ya ciro wayarshi a aljihu yayi dialing number Habeeb. Lokacin suna zaune a office d'inshi shida Mujaheed yana gwada masa tsarin wasu gine gine na companies a cikin labtop d'inshi yana zab'ar irin design d'in dayake so kasancewar suna shirin fara gina wani company daya shafi necklace, earrings, bangles and rings kuma zasu dinga fitar da design wa sauran kamfanunuwan da suke yin harkar. Har wayar ta katse baiyi picking ba wani kiran ya k'ara shigowa, k'aramin tsaki yaja dan duk hankalinshi ya tafi ga gine ginen yanaso ya tantance wanda zaifi k'ayatarwa idan aka gina, hannu yakai ya d'auko wayar dake ajiye bisa table d'in kusa da tashi system d'in ya duba mai kiran yaga Aleeyu ne, picked up yayi yayi yakai kunnenshi batare dayace komi ba jin an d'aga yasa Aleeyu yace "Yallab'ai yarinyar nan fa batada lafiya nazo na sameta kwance tana ta rawar d'ari da alamu tana jin jiki gaskiya". Haka nan yaji gabanshi ya d'an fad'i ya dake tareda fad'in "Tun yaushe?". "Yanzu dai dana dawo kawo mata kayan dakace a siyo mata na sameta a haka". Aleeyu ya amsa masa. So yake ya cewa Aleeyun ya samu Dr ya dubata ayi mata duk abinda ya dace amma saiyaji ya kasa fad'ar hakan yaji yanaso ya ganta yaga halin datake ciki dan haka ya tsinci kanshi da fad'in "Okay I'm coming". Yana sauke wayar daga kunnenshi yaga Mujaheed ya k'ura masa ido yana kallonshi, yasha mur sosai yana bankawa Mujaheed d'in harara yace "Kallon na meye?". Tsaki Mujaheed yaja yace "Uban me zan kalla a jikinka kai ba mace ba?". Gira ya d'age yace "Shiyasa ai naga ka tsura min ido saikace wani maye". "Mayu dai ba maye ba". Mujaheed yace yana hararar shi, bai k'ara magana ba sai mik'ewa tsaye dayayi ya d'auki wayoyinshi yasa d'aya a aljihun wandonshi d'ayar kuma ya rike a hannunshi yana k'ok'arin ture kujerar dayake kai baya. "Ban gane bafa wai ina zakaje ne haka?". "Inda ake zuwa". amsar daya bashi kenan yana k'arasawa wajen shelf dan ajiye wasu files daya d'auka kan table d'in. "Kutt amma ka rainamin hankali ma wallahi ina zaman zamana a office ina aikina ka tasoni kace lallai lallai inzo in nuna maka tsarin gine ginen zaka zab'a shine kuma zaka tashi lokaci d'aya kace fita zakayi bak'in halin kama baisa kayi budurwa ba bare inyi tunanin itace tayi maka wannan kiran urgently haka". Tsaki kawai Habeeb yayi, Mujaheed yace "To yanzu maganar da muke fa?". "Please MJ ka k'yaleni haka mana banason hayaniya by 8pm ka sameni a gida mu k'arasa okay?". "Ai ba bawa ka aje ba da zan bika har gida". cewar Mujaheed yana rufe system d'in gabanshi, k'ofar fita Habeeb ya nufa yana fad'in "Ok check your account shi zaiyi maka bayani". Da sauri Mujaheed ya mik'e yana fad'in "Ah haba Dude kar muyi haka dakai mana ka rik'emin salary ai akwai matsala mugu duk wani salon mugunta ka sanshi, wai gidan uwar wa zakaje ne?". Bai tanka masa ba ya fice yana cewa idan ya gama tsayuwar ya rufo masa office d'in. "Mtwss ALLAH ya shirya ka mutum saikace aljani". yayi maganar yana d'aukar system d'in ya fita ya rufe office d'in lokacin har Habeeb ya shiga lifter, shikuma ta elevator yabi zuwa 2nd floor inda nashi office d'in yake. Wani Dr'n daban yasamu ba Dr Huzaifah ba tunda shi na gida ne bayaso kuma kowa yasani har zuwa lokacin dazai sallame ta. Aleeyu na zaune kan sofa Habeeb da Dr Ameer suka shiga bedroom d'in, har lokacin tana kwance a k'asan saidai ta daina rawar sanyin da alamu tasamu barci ne. Bai zauna a bedroom d'in ba saiya koma falo ya zauna bayan ya k'ara jaddadawa Dr Ameer ya tabbatar yayi mata duk abinda ya dace. Yana nan zaune a falon yana aikin danne danne a waya Aleeyu ya fito daga bedroom d'in bai d'aga kai ya kalleshi ba ya cigaba da abinda yake, gefenshi Aleeyu ya tsaya ya d'an rissina yace "Yallab'ai sai kazo fa daga kusa tun d'azu Dr yakeso yayi mata allura tak'i yarda shine yace a kirawo ka". Bai tankawa Aleeyun ba haka kuma bai daina latsa wayar ba ganin haka Aleeyu yakoma bedroom d'in yasan bazaiyi maganar ba. Sai bayan shud'ewar wasu y'an mintuna sannan ya tashi ya nufi bedroom d'in bayan ya k'ara tamke fuskarshi yadda bazata kawo masa wargi ba. Sab'anin da datake kwance a k'asa yanzu akan gado ya hangeta a zaune hawaye kawai ke ziraro mata ta mak'ure waje d'aya jikinta sai rawa yake. "Yawwa Mr Habeeb gara da kazo ai tun fitarka nake fama da ita wallahi taki yarda ayi mata injection". Dr Ameer ya fad'a bayan shigar Habeeb d'akin. Tana ganinshi ta k'ara matsawa can jikin fuskar gadon tana k'ara curewa waje d'aya haka ma rawar da jikinta yake ta k'aru saboda ganin shi datayi. A hankali cikin takunshi na k'asaita da zallar mazantaka ya nufi wajen gadon ya had'e gabas da yamma tamkar baisan wani abu dariya ba ya nutsar da idanunshi cikin nata wanda hakan ya k'ara mata mutuwar jiki. "An gaya miki wasa mukazo yine anan? allura kawai kinzo kina b'atawa mutane lokaci gyara ayi miki ko in b'ata miki rai yanzun nan". Duk da tsoron shi datake bala'in ji hakan bai hanata fara yimasa magiya ba da fad'in ita batason allura a k'yaleta kawai dan ALLAH". Idanunshi ya d'an lumshe kad'an yana cije baki ya nemi gefen gadon ya zauna ya kalli Dr Ameer yace "Yi aikin ka". "Dan ALLAH balarabe kayi hak'uri". tayi maganar cikin kuka tana kallon Habeeb daya d'ora d'aya kan d'aya yana girgizasu, da sauri Aleeyu ya juyar da kanshi yana matse dariyar data taho masa jin sunan da Seeyamah ta kira Boss dashi, shima Dr Ameer d'in sai daya d'an dara kafin ya matsa daf da Seeyamahn ya rank'wafa yana fad'in ta janye hijabin ta nad'e hannun rigar ta. "Dan ALLAH kayi masa magana balarabe kar yayi min allura banaso wllhy". ta k'ara fad'a cikin wani kukan, a fusace ya juya ya kalleta yace "I will slap u idan kika k'ara kirana da wani balarabe". yayi maganar yana maka mata harara kafin kuma ya juyo gaba d'ayanshi ya fuskance ta ya cigaba da fad'in "Ta bud'e ayi mata ko ranta ya b'aci yanzun". Haka nan dole ta yaye hijab d'in ta shiga tattare dogon hannun doguwar rigar dake jikinta gashi ya kafa mata ido ba yadda za'ayi tayi masa musu tana ji tana kallo Dr Ameer yayi mata allurar, y'ar siririyar k'ara tasaki bayan shigar allurar jikinta kafin ta fashe da wani kukan tareda saka kanta tsakiyar gwiwar ta. Kallonta kawai yake shi gaba d'aya ma he's totally speechless ganin yadda take wannan uban kukan daga yin allura (d'an rainin wayo shima fa tsoron allurar yake nasan kun tuna lokacin da akayi masa tashi allurar 🤣 kula ne kawai basuyi ba amma lokacin da Dr Ameer ya tsira mata sai daya runtse idonshi gam yanajin tamkar shi aka tsirawa Lol). Drugs Dr Ameer ya rubuta mata ya mik'awa Habeeb paper, daga nan yayi musu sallama bayan Habeeb yayi masa sallama mai kyau danshi kanshi baisan nawa ya damk'o ya bashi ba aikuwa ya fita yana ta faman washe baki da fad'in gobe da safe zai dawo za'a k'ara yimata wata allurar hakan dataji yasa ta k'ara sautin kukan ta, a rayuwar ta ta tsani allura tablet ko guda nawa ne zata iya sha amma allura kam basa shiri, bazata manta ba duk lokacin da batada lafiya indai za'a yimata allura tofa ranar kowa sai yaji kanta dan sai an taru kanta. Paper ya mik'awa Aleeyu dawasu kud'i daya k'ara d'aukowa, karb'a Aleeyu yayi sannan yayi hanyar fita bedroom d'in duk da baiyi magana ba yasan abinda yake nufi ( jigila ta sameka Aleeyu 🤧). Shiru d'akin ya k'ara d'auka sai sautin kukan Seeyamah dake tashi kad'an kad'an wanda yafara sawa Habeeb ciwon kai, k'aramin tsaki yaja a karo kusan na hud'u kenan kafin cikin dakakkiyar murya yace "Shut up ur mouth". Da k'yar ta had'iye kukanta cikin ranta tana k'ara jin tsanar mutumin duk inda azzalumi yake to wannan bawan ALLAHn yakai ya daketa kuma ya hanata kuka ALLAH ba azzalumin bayinsa bane saiyayi mata sakayya akan wannan zaluncin da akayi mata batasan hawa ba batasan sauka ba batasan laifin datayi ba amma ya rabota da y'an uwanta ya kawota wani waje daban bazata gaji dakai kukanta wajen sarki ALLAH ba. Daga k'arshe ma tashi yayi ya fita daga bedroom d'in, nan kan kujera ya zube yana jiran dawowar Aleeyu ya dafe kanshi da hannayenshi duka biyun. Sai bayan sallah idan Allah ya nuna mana da rai da lafiya hop za'aci nama a hankali 😅. Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) Alhmdulillah! I'm back ina yiwa kowa fatan alkhairi tareda fatan anyi sallah lafiya ubangiji ya amshi ibadunmu Amin. I'm so sorry na rashin update babban uzuri ne ya rik'eni zamu cigaba da yardar ALLAH sai a dinga hak'uri da yanayin yadda posting zai dinga zuwa harkar mai iyali sai a hankali, duk lokacin dai dana samu time zanyi bakin k'ok'arina wajen yin typing. Nagode! 1luv my dearest fans jazakumullahu khair.💝 No 17. Yana nan zaune yana faman tufka da warwara a cikin zuciyarshi har zuwa lokacin da Aleeyu ya dawo gidan hannunshi rik'e da wata leda mai tambarin sunan wani pharmacy wanda ledar kawai zaka kalla ya tabbatar maka da babban pharmacy ne. "Sir ga drugs d'in an siyo". yaji maganar Aleeyu cikin kanshi wanda ya katse masa tunanin dayake sai sak'e sak'e yake cikin ranshi tausayin yarinyar yanaso ya rinjayesa saidai bazai bari tafaru bazata bar gidan nan ba har saita fad'a masa alak'arshi da ita data sawa rayuwar shi ido kuma take zuwa masa cikin barcinshi. Kamar bazai d'ago ba dan yafi mintuna biyar bai d'ago kai ya kalli Aleeyun ba wanda yake tsaye yana jiran umarnin ogan nashi, tsaye ya mik'e key d'in motarshi kawai ya karb'a ya wuce yana fad'in "Kaje ka bata tasha". "Ok Sir". Aleeyu yace yana nufar hanyar bedroom d'in. "Ka tabbatar taci abinci before tasha maganin". Habeeb ya fad'a yana ficewa daga falon yaja k'ofar. Shi yaso ya shiga yabata maganin da kanshi amma saiyaji ya kasa bashida wannan k'warin gwiwar haka nan kukanta ke masa ciwo cikin ranshi kuma yasan tana can tana aikin yinshi dan haka kawai ya zab'i fita daga gidan gaba d'aya. Ba k'aramin fama Aleeyu yasha da Seeyamah ba kafin yasamu taci abincin tasha maganin dan saidaya ciro wayarshi yace zai kira Habeeb dama yace idan tayi masa gardama ya kirashi sai sannan ta d'an tsakuri abincin tana kuka tasha maganin takoma ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya irin wadda tasha kuka ta k'oshi yaushe zata yarda ya kira mata wannan mutumin bala'in tsoron shi takeji tun daga lokacin dayasa aka d'auko ta ta cireshi daga cikin jerin masu tausayi da imani. Shima Aleeyun ajiyar zuciyan yasaki tareda girgiza kai sannan ya fita daga bedroom d'in yaja k'ofar. ★________________★ Y'an sanda sun fara bincike kan b'atan yarinyar da gidan marayu suka kai musu report amma har lokacin basu samu abinda sukeso ba saidai sun tsananta bincike da fatan samun nasara. Wani daga cikin shugabannin gidan marayun ne ya kawo shawarar ya kamata sukai cigiya kafafen sadarwa ko ALLAH zaisa a dace, hakan kuwa akayi sunkai gidajen radio da talabijin nan ma suka bada hotonta a gidajen talabijin d'in da suka kai cigiyar. Duk yadda Mujaheed ya dinga tambayar Habeeb ina yaje ya fita cikin gaggawa haka yak'i kulashi k'arshe ma zagi ya auna masa yace ya k'yaleshi kar ya dameshi Mujaheed yayi k'wafa ya fita ya rufo k'ofar da k'arfi shima yana zaginshi da kallo kawai ya bishi tsaki yaja yayi baya yayi relaxing sosai kan kujerar idanunshi a lumshe yana jujjuyawa. Gaba d'aya yinin ranar bai hasala wani abin kirki ba duk da yadda yaso yayi aikin kuwa, kasa hak'uri yayi saidaya kira Aleeyu yaji ya jikin nata ya tabbatar masa da taji sauk'i yanzu ma ya shiga ya dubata sai a lokacin hankalin shi ya d'an kwanta yasamu nutsuwa. Haka yinin ranar yazo ya wuce bazaice ga wani muhimmin aiki d'aya dayayi a office ba a ranar, da wuri ma yabar kamfanin yatafi gida batare daya nemi Mujaheed ba duk dayaso su k'ark'are aikin dasuka fara d'azu saboda yanaso yayi magana da wad'anda yabawa kwangilar aikin ginin kamfanin da za'a fara dole zai nemi Mujaheed d'in ko zuwa dare ne su k'arasa. Yaso biyawa ta lamid'o crescent yaga halin da yarinyar take ciki saikuma ya fasa kai tsaye ya wuce gida. ★★★________★★★ Bayan magreebah. Kwance yake akan doguwar kujera dake falon nashi yana sanye da farin wando 3quater mai aljihuna gaba da bayan wandon sai k'aramar riga ta shan iska ash color, wani sassayan k'amshi ne yake tashi tako ina a jikinshi da kuma falon wanda aka k'ure A.C hakan yasa falon ya d'auki uban sanyi kamar k'ank'ara kuma ba abinda ya dameshi ga kayan jikinshi bawasu na kirki ba. tamfatsetsiyar wayarshi ce a hannunshi yana latse latse ya hard'e k'afafunshi daga kwancen dayake, number Mujaheed ya lalubo ya danna masa kira jinsa shiru har yanzu baizo ba saidai yana kira akace masa line busy alamun waya yake tsaki yayi ya kashe ya k'ara dialing still dai akace masa akan waya yake wani tsakin ya k'ara ja ya yanke kiran yana tunanin ko da uban wa yake waya? Saida aka d'an d'ebi wasu y'an mintuna sannan ya k'ara trying number cikin sa'a ta shiga bata dad'e tana ringing ba Mujaheed yayi picking bakinshi d'auke da sallama ko amsa sallamar baiyiba yace "Da uwar wa kake waya ne wai tun d'azu?". "Ah ban ganeba an fad'a maka kowa ma irinka ne idan akaji kana waya kan business ne bawata y'ar soyayya da nishad'in nan irin na zamani da y'an mata". "Mtwss! An fad'a maka kowa ma bashida aikin yi irinka? dallah malam kazo ina jiranka karka b'atamin lokaci". Bai jira abinda Mujaheed yake fad'a ba yayi hang up yana fad'in "Useless man kawai wazai b'ata lokacin shi wajen yin wata soyayya salon yara su rainaka ai shi ko soyayyar zaiyi bazaiyi da k'aramar yarinya ba sai wadda ta amsa sunanta na mace ta mallaki hankalin kanta I thought ma sa'ar shi koma wadda ta girmeshi zai aura hankalinshi kwance amma auren k'aramar yarinya ba abinda yake janyowa illah raini da zubar da girma shikuma duk abinda zai zubar masa da girmanshi baya shiri dashi. Bayan sun gama waya da Mujaheed ya kira Aleeyu ya k'ara jin lafiyar Seeyamah, saidaya k'ara jan kunnenshi kan ya k'ara kula da ita sosai kuma kar yayi saken dazata gudu sannan ya kashe wayar yana tuna kukanta na d'azu da yadda take kiranshi da balarabe sai yanzu abin ya bashi dariya amma dayake ba gwanin yinta bane murmushin gefen baki kawai ya saki yana cije lips d'inshi na k'asa. Bayan wani d'an lokaci Mujaheed ya iso gidan wajen Ummi ya fara shiga dan su gaisa, suna zaune a k'ayataccen falon nasu wanda ke tashin k'amshin turarukan wuta na asalin larabawa suna kallon tashar Aljazeerah Ummi da Neehlah, yana shiga idanunshi suka sauka kan Neehlah datake zaune kan kujerar dake facing d'in k'ofar falon suka had'a ido dashi wani k'ayataccen murmushi suka sakarwa junansu ya matuk'ar yimata kyau cikin bak'in wandon jeans da farar riga long sleeve da bak'in agogon fata dake d'aure a tsintsiyar hannunshi, kamar yadda shima tayi masa kyau ainun cikin shigarta material ne bak'i da adon golden na fulawoyi a jikinshi riga da siket kasancewar ta fara yasa yayi bala'in haskata ido ya kashe mata tayi saurin sadda kanta k'asa tana murmushi gamida addu'ar ALLAH yasa Ummi bata ganshi ba Mujaheed bashi data ido wlhy, Kai tsaye wajen Ummi ya nufa ya zauna k'asan k'afafunta yana gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar shi mutanen gida ya amsa mata da "Lafiyar su k'alau sunce a gaisheta". ya ida maganar yana satar kallon Neehlah wadda itama daidai lokacin ta d'ago kanta ya kasheta da wani irin kallo dayasa duk ta daburce cikin y'ar rawar murya wadda ta had'u da siririyar muryar ta tace "Yah Mujaheed ina yini". "Lafiya k'alau k'anwata ya kike?". Yace yana murmushi bayan ya d'ago kai yana kallonta. "Alhmdulillah". Kawai tace ta tashi tabar falon kafin Ummi ta ramfo su duk da hankalin Ummin ma dai yana kan TV, da idanunshi ya rakata da kallo har ta shige ya daina ganinta ajiyar zuciya ya saki ya mik'e tsaye yayiwa Ummi sallama ya fita. Yana dosa kai falon Habeeb wani uban sanyi yayi masa maraba sallama yayi ya shiga har lokacin Habeeb na kwance saidai sab'anin d'azu da wayace a hannunshi yanzu wata y'ar madaidaiciyar laptop ce apple daya d'orata kan cinyarshi yana sarrafa ta, ciki ciki ya amsa sallamar Mujaheed batare daya juyo ya kalleshi ba. Jakar hannunshi ya ajiye wadda shima system d'inshi take ciki ya d'auki remote control na air conditioner d'in ya rageta sosai ya daidaita sanyin yadda baiyi yawa ba kuma baiyi kad'an ba, sai a lokacin Habeeb ya juyo ya kalleshi cikin had'e rai yace "Malam meye haka wai?". "Kamar ya?". Mujaheed yace yana zama kujerar dake fuskantar wadda Habeeb d'in yake kwance, zaune ya tashi yana b'ata rai yace "Ya daga zuwanka zaka canzamin tsarin yadda nakeson d'akina ya kasance". "Kowa ma mahaukaci ne irinka? in banda hauka taya zaka dinga bankawa kanka sanyi haka ko tsoron pneumonia bakayi saboda tsabar bakada hankali wautar d'an fari na d'awainiya dakai". Wata uwar harara Habeeb ya jefawa Mujaheed yace "Banason iskanci, d'akinka ko nawa, inada right d'in inyi duk abinda nakeso a ciki ba matsalarka bace". Baki Mujaheed ya tab'e yana d'age kafad'a yace "To kabari inbar d'akin idan ma cikin k'ank'ara zaka shiga Gashua k'arewar sanyi kanada damar yin haka amma yanzu kam saidai kayi hak'uri". Kai Habeeb ya kad'a yana sakin k'wafa ya daidaita zaman system d'in ya cigaba da dannawa batare daya k'ara kallon sashen da Mujaheed yake ba. "Naga alamun baka lallab'a lafiyar ka ko?". yaji Mujaheed ya k'ara fad'a, banza yayi masa bai tanka shiba, baki Mujaheed ya k'ara tab'ewa ya janyo jakar dayazo da ita ya ciro tashi system d'in ya tashi ya koma kusa da Habeeb d'in ya zauna ya d'auke system d'in dake kan cinyar Habeeb ya d'orata kan wani center table na glass daga gefenshi ya juyo yana fad'in "Malam ka maida hankalinka kan aikin daya kawoni inyi in tafi tsabar jaraba irin taka daren ma bazaka hak'ura ba kana min bak'in cikin huawar da zanyi kayi hak'urin goben shine bazaka iyaba". Habeeb yanajin Mujaheed yanata faman mita k'ala baice masa ba idan ya biye ta Mujaheed sai sun zama kamar zararru shiyasa wani lokacin yake masa banza yayi yagama. Dolenshi ya maida hankalinshi kan abinda zasuyi d'in tunda shiya matsawa Mujaheed d'in saiyazo gaba d'ayansu suka maida hankali Mujaheed ya cigaba da nuna masa tataccen speech kawai ke tashi a wajen har zuwa lokacin da suka kammala suka tsaida mgn. *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 18. Rufe system d'in Mujaheed yayi bayan sun kammala ya ajiyeta kusa data Habeeb, zamanshi ya gyara ya d'auki remote d'in TV da tun d'azu takeyi a tashar larabawa ana labarai channels ya shiga canzawa yana fad'in "Mudai ba larabcin nan mukeji ba bari mukai inda mukafi wayo". Habeeb da bayan gama tattaunawar tasu ya d'auki waya ya cigaba da danne danne ya d'ago ya kalli Mujaheed yana b'ata rai yace "Wai meyake damunka ne MJ akan me zaka canzamin channels?". "To kallon kake? tunda na shigo d'akin nan banga ka d'aga kai ka kalli TVn nan ba". "Dole saina kalla zanji abinda ake fad'a? ba kunne ne yake jiba". Habeeb ya fad'a yana antayawa Mujaheed harara. Baki kawai Mujaheed ya tab'e ya cigaba da neman channels d'in dayake so kan N.T.A. ya tsaya daidai lokacin da zasu fara news ya ajiye remote d'in yana fad'in "Yawwa bari muga abinda duniyar ke ciki". tsaki kawai Habeeb yayi ya maida kanshi kan wayar dake hannunshi shikuma Mujaheed kacokam ya maida hankalinshi kan TVn, bayan mai gabatarwa ya gabatar da kanshi da kuma kanun labaran sannan aka tsunduma cikin gundarin labaran. Labari na farko da mai labaran ya fara karantowa shine na b'atan Seeyamah bayan wasu y'an maganganu dayayi hoton Seeyamah ya mamaye fuskar talabijin d'in a matsayinta na wadda ake nema, tana sanye da k'aton hijabi kamar yadda ya saba mai hannu light blue fuskarta d'auke da k'ayataccen murmushi wanda har beauty point d'inta saida suka lotsa wanda take dashi a gefen kumatun ta na dama "Innalillahi". Mujaheed ya fad'a cikin razana yana zaro ido ganin yarinyar nan ta gidan marayun da suka tab'a zuwa da Gashua wadda har yace saita bar gidan garkuwa akayi da ita kenan?. "Gashua kaga wani abin mamaki". Mujaheed yace cikin fad'uwar gaba yana dafa kafad'ar Habeeb wanda gaba d'aya hankalinshi yake kan wayarshi da alamu wani abu mai muhimmanci yake yi a ciki. A hankali ya d'ago kai idanunshi suka fad'a kan Seeyamah da har zuwa lokacin ba'a d'auke hotonta daga TVn ba, ba zaice gabanshi bai fad'i ba amma dayake namijin duniya ne saiya maze ya shanye fad'uwar gaban nashi ya kalli Mujaheed yana neman k'arin bayani daga wajenshi. "Wlhy wai b'ata tayi ba'a ganta ba har gidan marayun aka shiga aka d'auketa nasan ka ganeta ko? kai jama'a duniya ina zaki damu ne? marainiyar ALLAH bata jiba bata ganiba anje anyi garkuwa da ita Yaa ALLAH". ya k'arasa maganar cikin tsananin jimami yana dafe goshinshi sosai labarin b'atan Seeyamahn ya dakeshi saiya tuno lokacin daya tambayeta sunanta ta fad'a masa da irin murna da farin cikin daya hanga daga cikin idanunta lokacin dayace ta tashi ya maida ita gidan marayun yau gashi anje har cikin gidan inda take tunanin nan ne garkuwar ta bango abin jinginar ta an saceta. Sam Habeeb kasa d'auke idanunshi yayi daga kan allon talabijin d'in idanunshi k'ur akan Seeyamah duk yadda yaso janye idanunshi ya kasa har zuwa lokacin da aka d'auke hoton mai gabatarwar ya cigaba da labaran shi, a hankali yayi k'asa da kanshi ya cigaba da danne dannen dayake a zahiri wanda a bad'ini kawai shige shige yake a cikin wayar batare dayasan ina yake shiga yake fita ba tunanin kacokam ya tafi can wani waje daban. "Wai bakaji abinda nace bane Gashua ka maida kanka ka cigaba da abinda kake?". Mujaheed ya fad'a cikin jin haushi yana kallon Habeeb. "Me kakeso ince MJ? ko zuwa zanyi in nemota da kaina?". "Bakaji na fad'i haka ba amma dai at least ko addu'a ce kayi ta ALLAH ya bayyana ta tunda ba'a san a wani irin hannu take ba anya kanada imani kuwa Gashua?". Wani banzan kallo Habeeb ya jefi Mujaheed dashi kafin yace "Ina nake dashi? ai imani sai sheikh Mujaheed". yayi maganar cikeda gatse. "Ai naga alama kam inba hakaba ai duk wani musulmi mai imani idan yagani zai tausaya har ma yabita da addu'a". Tsaki kawai Habeeb yaja ya zame ya kwanta yana cigaba da duba wayarshi. "ALLAH ya shiryeka ya canza maka halinka". Mujaheed ya fad'a shima yana d'auko wayar shi wadda ya ajiye kan center table tun bayan shigowarshi falon, ko kallonshi Habeeb baiyiba bare ya tanka masa. Yanar gizo Mujaheed ya shiga nan ya fara cin karo da hoton Seeyamah a Facebook da labarin b'atan ta, kai kawai ya girgiza cikeda tausayin yarinyar ko a wani irin hali take ciki yanzu? ALLAHU A'ALAM, ALLAH dai ya tona asirin wad'anda suka d'auketa. "ALLAH ya bayyanaki cikin k'oshin lafiya Seeyamah". Ya fad'a a fili cikin alhini, baki Habeeb ya tab'e cikin ranshi yana mamakin irin yadda yaga Mujaheed ya nuna zallar damuwarshi kan b'atan yarinyar da sai yanzu ma yake jin sunanta. D'aya wayar tashi wadda ke ajiye gefenshi ta fara bada sautin kid'a mai dad'i, kamar bazai d'auka ba saikuma yakai hannu ya d'auka ya duba mai kiran yaga Aleeyu ne batare da shayin komai ba yayi picking ya kara a kunnenshi cikin muryar nan tashi mai cikeda amo da sautin mai dad'in saurara yace "Ya akayi?". Sam bai saurari gaisuwar da Aleeyun keyi masa ba, daga b'angaren Aleeyu yace "Yallab'ai yarinyar nan fa tak'i cin abinci na kad'a na raya amma tak'i kulani kuma dole sai taci abincin sannan tasha maganin ko d'azu da rana ma kad'an ta yafita tace ta k'oshi sai aikin kuka datakeyi tun d'azu". K'aramar ajiyar zuciya Habeeb ya saki yana d'an dafe goshinshi da sakin numfashi kamar bazaice komai ba saikuma yace "Bata wayar". Aleeyu dake tsaye akan Seeyamah datake ta kuka tun d'azu ya mik'awa wayar yana fad'in "Zakuyi magana da yallab'ai". Gaba d'aya jikinta rawa ya d'auka saboda tsoro ita sam batayi tunanin kiranshi zaiyi ba sai dataji yafara magana dashi wllhy mugun tsoron mutumin nan take ji, hannu na rawa ta karb'i wayar takai kunnenta saidai ta kasa magana sai shasshek'ar kuka datake k'asa k'asa wanda yasa Habeeb lumshe idanunshi ya k'ara gyara kwanciyar shi kafin cikin cinkushasshiyar murya ya k'ara had'e rai sosai kamar yana gabanta yace "Ke! kin raina mutane ko?". Girgiza kai kawai tayi kamar yana kallonta tana share hawayen idanunta da d'aya hannun, Aleeyu dai yana tsaye yana kallonta. "Ki kama abinci kici kafin ranki ya b'aci duk ranar da kika bari ya k'ara min complain akan rashin cin abincinki sai ranki ya b'aci banason gardama ki kiyaye". "Bakya jine". yayi maganar a fusace cikin d'an d'aga murya jin tayi masa shiru ya tsani yayi magana ayi biris dashi har saida Mujaheed yabar danna wayar dayake ya kalleshi, cikin dashasshiyar murya ta amsa masa da "Toh". Wata tsanar shi na k'ara samun gurbin zama a cikin zuciyarta, k'aramin tsaki yaja ya kashe wayar batare da sun k'ara yin magana da Aleeyu ba wayar ma gaba d'aya saiya kasheta ya cillata gefenshi yana d'agowa suka had'a ido da Mujaheed wanda yake binshi da wani irin kallon tuhuma, basarwa yayi ya d'auke kanshi gefe Mujaheed kasa shiru yayi yace "Gashua dawa kake waya haka?". "Zoka matseni sai in fad'a maka munafuki". yace yana masa wani irin kallo mai kama da harara. "Oh my God! nifa ba fad'a na nema ba tambaya ce kawai nayi, ALLAH Gashua kazama masifaffe nidai sanin danayiwa wancan Gashuan ba haka yake ba maganar fatar baki ma bata dameshi ba amma lokaci d'aya ka canza ka zama jarababbe magana kad'an saika hau kan mutum da bala'i why?". Banza yayi masa bai tanka shiba, baki Mujaheed ya tab'e ya mik'e tsaye yana fad'in "Naga alamar idan ban bar gidan nan ba duka zaka kai min". "Ai kasan ga mahaukaci ko?". Habeeb yace yana sakar masa harara gamida cije lips d'inshi, dariya Mujaheed yayi yana zura system d'inshi a jaka ya rataya yana fad'in "A'a nidai bance ba Mr Habeeb Gashua good night sai mun had'e gobe". daga haka ya d'auki wayarshi ya nufi k'ofar fita yana cigaba da dariyar shi wadda ta k'ara k'ular da Habeeb sosai ya bishi da kallon takaici yanajin tamkar ya shak'oshi yayi ta dukanshi ganin irin dariyar dayake masa ya maidashi wani shashasha. Zaune Mujaheed yake a cikin motar shi bayan fitarshi da wace yarinya Gashua yake waya har yake mata bambamin idan bataci abinci ba sai ranta ya b'aci? wacece ita? meye alak'arshi da ita? bayaso ya tabbatar da zargin da zuciyarshi take yimasa akan abokin nashi kuma d'an uwanshi amma dole yasa ido, d'azu kafin yazo office yace yana da uzurin dazaiyi kafin yazo dayazo kuma suna cikin aiki an kirashi a waya yabar komai dayake ya tafi yanzu kuma an kirashi yana magana kan taci abinci duk da baiji maganar wanda suke wayar dashi ba ya tabbatar mace ce duk me hakan yake nufi? ya tuno lokacin da Habeeb d'in yayi ruwa yayi tsaki yace dole sai Seeyamahn tabar gidan marayun datake kodai wani abun ya shirya bayan faruwar lamarin yasan halin abokinshi sarai da kafiyar tsiya da taurin kai koma dai meye zaibi ba'asi da diddigi har saiya gano bakin zaren. Motar ya tayar ya fice daga gidan zuciyarshi cikeda tunanika kala kala. Habeeb bai samu nutsuwa ba sai daya k'ara kiran Aleeyu ya tambaye shi taci abinci da magungunan kuwa? Aleeyu ya tabbatar masa da taci kuma tasha maganin ta kwanta. B'oyayyar ajiyar zuciya ya saki lokaci d'aya yana sauke numfashi tareda yamutsa lallausar sumar kanshi, kayan kallon ya kashe ya shige bedroom yayi wanka yasa jallabiyyah blue black ya fesa turaruka sannan ya tada sallah kamar yadda ya saba ko wani dare kafin ya kwanta. ★______★ A daidai wannan lokacin da aka haska hoton Seeyamah a NTA ana cigiyar ta, Heedayah da Zainab ma suna zaune a falo da yaran Aunt Ramlah kasancewar suna duba books d'insu na school ne yasa basu maida hankali wajen canza tasha ba dan indai suna zaune a falon basuda tashar kallo sai Arewa 24 ko MBC Bollywood, Zainab ce ta fara ganin hoton Seeyamah daya mamaye fuskar talabijin d'in a mazaunin wadda ake cigiyar ta ta b'ata kwanaki biyu da suka wuce. A matuk'ar razane ta zaro ido tana k'ara bin fuskar Seeyamah da ido kafin ta girgiza kafad'ar Heedayah wadda kanta ke sunkuye tayi nisa cikin duba littafin hannunta, d'agowa tayi ta kalli Zainab tace "Menene wai?". Hannu Zainab tasa ta nuna mata TV tabi hannun Zainab d'in da kallo, Ido ta k'walalo kamar zasu fad'o k'asa tsabar yadda ta fito dasu. *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). Jama'a kuyiwa Habeeb uzuri baku tunanin ta sanadiyyar d'auke Seeyamah dayayi komai zai bayyana? duk inda na lek'a anata yadawa Habeeb Gashua magana 😅 easy guys mubi komai a sannu har zuwa lokacin da zamu gano bakin zaren, Gashua a cigaba da kidmashin Mom sayyeed da Aunt jamila na bayanka 😝😂🏃🏃. Godiya mai tarin yawa a gareku reader's alkhairin ALLAH yakai muku a duk inda kuke jazakumullah khair 💗💗💗. No 19. Batasan lokacin data saki littafin hannunta ba cikeda tsantsar mamaki da al'ajabi basuda bambanci a komai na halitta hatta dimple d'in da Seeyamah take dashi itama Heedayahn tana dashi a fuskarta wannan lamari akwai d'aure kai da rikitarwa ta sani cewa akwai mutane dayawa masu kama da junansu ako ina amma wannan dai kamar tasu ta b'aci ta yadda idan d'aya ya b'ata za'a iya kama d'ayan ace shine he's totally confused ta rikice da ganin wannan baiwar ALLAH da ake haskawa. "Aunt Ramlah fito kiga wani abin mamaki please kafin a d'auke". Zainab ta k'walawa Aunt Ramlah dake kitchen tana had'awa Abban Nu'aym fruit salad zata kai masa bedroom d'inshi saboda bayacin abu mai nauyi da dare, fitowa tayi tana mitar me zata nuna mata take k'wala mata wannan uban kiran ko knife d'in hannunta bata samu ajiyewa ba. "Aunt Ramlah kalli TV kigani dan ALLAH wata kamar Heedayah wai ta b'ata ana cigiyar ta". Zainab tace tana nunawa Aunt Ramlahn plasma d'in dake manne a jikin bango, itama d'in dai idon ta zaro na mamaki har wuk'ar hannunta na shirin fad'uwa wannan abu da ban al'ajabi yake. "ALLAH buwayi gagara misali, kuga fa wani ikon ALLAH wllhy badan ina ganin Heedayah tsaye a gabana ba da ba abinda zai hana ince itace wannan ALLAH mai hikmah". Aunt Ramlah tayi maganar tana rik'e bakinta. "Wllhy ko nima Aunt tunda basuda maraba da Heedayahn kiga fa Aunt har wannan dimple d'in iri d'aya". cewar Zainab tana kai hannu kumatun Heedayah inda nata dimple d'in yake, kallon Heedayah Aunt Ramlah tayi tace "Heedayah ya kikayi shiru bakice komaiba?". Wani nannauyan numfashi Heedayah ta sauke tace "To ai nikam narasa tacewa Aunt Ramlah ki dubafa babu wani bambanci da za'a iya gane tsakanina da ita komai iri d'aya". "Ikon ALLAHn kenan ai Heedayah mai yin yadda yaso kuma a lokacin dayaso ku cigaba da karatun ku nima bari inje in k'arasa aikina". Aunt Ramlah tace tana komawa kitchen d'in can k'asan ranta kuma tana hasaso abubuwa da dama, sukuma nan suka zauna suna k'ara maida maganar hat yanzu basu bar mamaki ba. Bayan Aunt Ramlah ta gama had'a fruit salad d'in ta zubashi a wani madaidaicin bowl mai kyau ta d'ora kan tray da spoon ta nufi bedroom d'in maigidan nata har lokacin da tunanin datake a ranta. A zaune ta sameshi kan sofa sanye da jallabiyyah ruwan k'asa shima kuma news d'in yake kallo, bakinta d'auke da sallama ta shiga ya d'ago kai yana amsa mata wajen shi ta k'arasa ta janyo wani k'aramin stool ta d'ora bowl d'in akai ta zauna kusa dashi daga gefen gado tana fad'in "Abban Nu'aym kaima labaran kake gani kenan kaga wani abin mamaki da aka hasko yanzu?". Kai ya gyad'a yace "Bakiga yanayi na ba, gaba d'aya mamaki yagama kasheni ALLAH mai yadda yaso yarinya saikace Heedayah". "Wllhy kuwa Abban Nu'aym abin akwai d'aure kai a ciki zuwa yanzu nafara tunanin anya Heedayah ba twins bane ba kuwa?". "Tabbas kuwa nima nayi wannan tunanin gaskiya ALLAH ne ya barwa kansa sani amma kar wannan yasa kuyi wata magana har tasan halin da ake ciki ki k'yaleta kawai". "Insha ALLAH! na sake ma nayi mata magana makamanciyar wannan ai na shiga uku wajen Umma da Baba daidai da rana d'aya basa son abinda zai tada maganar nan har Heedayah ta fahimci wani abu". Kai kawai Muhammad yake gyad'awa yana k'ara ganin girma da k'imar surukan nashi ko shi badan wani irin sirri da ubangiji ke kimsawa tsakanin miji da mata ba da har Ramlahn ta fad'a masa da bazai tab'a sanin Heedayah ba k'anwar Ramlahn bace da suka fito ciki da itaba tsabar yadda basa bambanta su da y'ay'an da suka haifa saima fifitata da sukeyi akan yaran nasu da suka haifa da cikinsu, bowl d'in ta d'auka ta mik'a masa ya fara shan fruit salad d'in. ★★★_______★★★ A ranar kuma a daidai wannan lokacin bayan kammala labaran da aka gabatar na hangi wasu miji da mata daka gansu zakaga jikinsu a sanyaye yake har lokacin mamaki da d'imbin al'ajabin abinda suka gani yanzu bai sakesu ba wanda hakan ya nuna har akan fuskokin su. Mutumin wanda ak'alla yabawa shekaru hamsin baya ya kalli matar tashi wadda a k'iyasin shekarun ta zasuyi arba'in da biyar. Wani nannauyan numfashi ya sauke kafin yace "Lallai Hajiya inaji a jikina wani babban al'amari yana doso mu wanda bamu san ko meye ba". "Cikin raunin murya tace "Ni kaina Alhaji inaji a jikina kamar wani abu daya shafi JAWAHEER zai bayyana yanzu dan ALLAH wazai dubi yarinyar da akayi cigiyar ta yanzu yace ba Jawaheer d'inmu bace ba alamu sun nuna ita d'in twins ce irin identical d'in nan inaji a jikina wannan yarinyar da aka haska jinin Jawaheer ce ina tsoron ranar da zamu rabu da Jawaheer Alhaji". ta k'arasa maganar tana sakin kuka wanda ya dad'e yana cinta tana matuk'ar son Jawaheer kamar ranta kamar yadda shima maigidan nata yake mutuwar k'aunarta, hannu yasa ya rungumota ta gefenshi cikin taushin murya da rarrashi yace Bazamu tab'a rabuwa da y'armu ba Saudah bana fatan in riski ranar saidai a matsayin mu na iyayena kuma masu k'aunar ta dole abin farin cikine a garemu ace ta had'u da asalin iyayenta na gaskiya karki damu kanki muna tare da Jawaheer har k'arshen rayuwar mu insha ALLAH". Ya k'arasa maganar yana goge mata hawayen idanunta yana cigaba da fad'a mata tausasan kalamai na kwantar da hankali ta lafe sosai a jikinshi tana tuno abubuwan da suka faru shekaru sha takwas da suka wuce a lokacin da suka tsinci jaririyar sabuwar haihuwa. Nan gaba zamuji su waye wad'annan bayin ALLAHn Alhaji Mansur Jik'amshi da Hajiya Saudah. Had'add'en bedroom ne mai d'auke da madaidaicin gado da k'atuwar wardrobe sai tamfatsetsen mirror wanda aka cika samanshi taf da kayan makeup da turaruka,gaba d'aya kayan d'akin kalar light blue ne da white har curtains da sauran abubuwa da ake k'awata d'aki dasu, an kashe fitilun d'akin sai bedside lamp dake kunne wadda ta bada kalar dark blue. Kyakkyawar matashiyar budurwa na hanga kwance akan gadon dayasha tattausan bedsheet tayi shirin barci cikin riga da wando masu kauri kalar peach mai haske ta rufe k'afafunta zuwa kan cikinta da blanket mai laushi ba komai a kanta hakan ya bani damar ganin k'ananun kalbar dake kanta wadda ta sauka har kan kafad'unta, rik'e take da had'add'iyar wayarta tana ta faman danne danne tana dariya da alamu tana matuk'ar jin dad'in yanayin datake ciki chatting take da k'awayenta na school cikin nishad'i kiran Fauziyyah ne ya shigo wayar tata a lokacin k'awar tace sosai tare suke school, picking tayi takai kunnenta tareda fad'in "Hello Babe ya daren?". "Banza kina ina muna nan yanzu muka gama ganin abin mamaki a NTA news kinsan Yah Abdul da shegen son labarai TVn d'akin shi kuma tasamu matsala shine fa yazo falo ya kunna a TVn falo". "Wani abun kuka gani a news d'in?". cewar Jawaheer tana k'ara jan blanket d'in sama. "Hmm bari kawai bestie wallahi wata aka hasko ana cigiya kinsan ALLAH badan d'azun nan muka rabu dake ba dasai ince kece kika to dan dai ita wannan ance kwana biyu da b'atan nata kamar kefa Jawa wllhy ina rantse miki bakuda maraba da ita su kansu y'an gidanmu sunyi mamaki wai anya bake bace kuwa nace musu bake bace gaki a online ma lokacin muna magana". Baki Jawaheer ta d'an tab'e cikin yatsina tace "ALLAH ya bayyana ta amma nasan kawai shegen kwakwazo ne irin naki amma ya za'ayi ace komai namu iri d'aya haba saikace a film ke nifa irina ni kad'ai ce a duniya". "Ba zaki gane bane k'awata amma ke kanki da kin gani saikin razana wllhy nidai ban tab'a ganin abin mamaki irin wannan ba amma ba'a mamaki da ikon ALLAH". K'aramin tsaki Jawaheer taja tace "Naji to go and sleep Hajiyata barci nakeji". bata jira cewar Fauziyyah ba ta katse kiran ta santa da nanata magana yanzu idan ta barta zancen dazata isheta dashi kenan shiyasa tayi maganinta duk da har yanzu bata gama yadda da maganar Fauziyyah ba kawai dai taga wadda suke yanayi da ita shine zata dameta da maganar komai nasu iri d'aya ta yaya hakan zata kasance???. Afwan idan nasamu dama gobe zakuga update idan akaji shiru kuma sai zuwa jibi insha ALLAH idan muna da rai da lafiya, ku cigaba da bina wasan yanzu aka fara 🤸🤸karku manta da comments and share. Masu buk'atar a tallata musu hajarsu zasu iya nemana ta wannan number 09139964697. Jummah Kareem 💝 Maryam Ibraheem Mrs Salees Mu'az 💝 Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:3k maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08062991549 Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai 11k Munaturawa Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 20. Aunt Ramlah tana komawa bedroom d'inta ta iske tarin miss call na jama'a y'an uwa da k'awayenta wad'anda suka san Heedayah ciki har dana Hajiya Inna tana cikin dubawa wani kiran Hajiyan ya k'ara shigowa, ta d'aga kiran tana kaiwa kunnenta a rud'e Hajiya ke tambayar ta ina Heedayah idan ta fahimta dai itama Hajiyan taga abinda ya faru a labarai kai wannan abu da mugun d'aure kai yake. "Hajiya yanzu suka tashi daga falo suka koma bedroom itada Zainab". Ajiyar zuciya Hajiya Inna ta saki kafin tace "Alhmdulillah! sai yanzu hankalina ya kwanta wllhy tun d'azu ina cikin alhini da tarin mamaki naga an haska wata yarinya a talabijin wai an saceta basuda maraba da Heedayah komai iri d'aya shine na kiraki inji kan labarin". Zama Aunt Ramlah ta gyara tasan dai ko giyar wake tasha bata isa ta bayyana sirrin dayayi shekara da shekaru a rufe ba ta ina zata fara fad'in Heedayahn 'YAR TSUNTUWA ce? sirrin da iyayenta ma basu tonashi ba wace ita da zata bankad'a shi? murmush ta d'anyi tace "Wllhy muma mun gani Hajiya munyi mamaki sosai amma Heedayah lafiyar ta k'alau yanzu suka gama karatu a falo suka tashi". "Ikon ALLAH, to masha ALLAH ubangiji ya k'ara kiyayewa itakuma waccan ALLAH ya bayyana ta cikin k'oshin lafiya". "Amin Amin". Aunt Ramlah ta amsa mata, har sukayi sallama Hajiya bata daina jinjina maganar ba ita kanta Aunt Ramlahn har lokacin mamaki bai gama sakinta ba, suna gama waya da Hajiya kiran Maman Ilham wannan k'awar tata wadda ta tab'a aiken Heedayah da Zainab gurinta wadda anan suka had'u da Habeeb ta kirata, itama d'in dai tambayar ta Heedayah tayi amsar dai data bawa Hajiya itama ita ta bata itama tana ta mamaki. A wannan dare Alhaji Mansur Jik'amshi, Hajiya Saudah da Aunt Ramlah sun sha amsa wayoyin jama'a da dama kowa da irin tambayar dayake rattabo musu har wani lokacin ma su rasa amsar bayarwa. Jawaheer kam cikin kwanciyar hankali tasha barcinta sam ta manta ma da wata maganar Fauziyyah datayi mata a ganinta idan banda k'arya taya za'a ce anga wata da basuda bambanci da ita ko twins ai kafin kaga masu kama d'aya aikine saidai kowa da kamarshi sai ita za'a wani ce anga irinta shirme kenan. Ta b'angaren Heedayah ma duk juyin da zatayi cikin barcinta sai fuskar data gani d'azu a TV ta fad'o mata sam batayi wani cikakken barci ba sai wajen asubah shima kuma baiyi wani nisa ba aka kira sallah dolenta ta tashi barci cikeda idanunta sukayi alwalah sukayi sallah kuma ba damar komawa tunda su suke aikin gidan gaba d'aya kafin su tafi school musamman yau da suke da lecture by 7@m. A gurguje sukayi breakfast sannan suka tafi da Uncle Muhammad zai saukesu a school d'in dayake yau ya fito da wuri da alama akwai inda zaije. Ta cikin mirror Uncle Muhammad yake k'ara k'arewa Heedayah kallo har sai data tsargu, so yake yaga meye bambancin su da yarinyar jiya amma ya kasa ganowa dole ya maida hankalinshi kan driving d'in dayake tunda shidai bazai iya fad'ar abu d'aya wanda Heedayah take dashi waccan yarinyar bata dashi ba, zuwa yanzu ya k'ara tabbatarwa lallai Heedayah twins ne wani abu ya rabasu to meye abinda ya rabasu d'in? itace tambayar da kowa bai saniba. Gaba d'aya Heedayah saidata tsargu tayi dana sanin zuwan nata school d'inma saboda yadda ake faman kallonta tamkar wadda tayi wani abin kunya duk tasan hakan kuma yanada alak'a da abinda kowa yagani jiya idan baka gani a TV ba zaka gani a waya, farko ma cewa tayi gida zata tafi Zainab ta hanata kuma ba wanda ya tunkareta yayi mata magana saidai nunata da ake tayi da hannu duk inda suka wuce ana binta da kallo maza da mata gaba d'aya abin ya isheta tamkar ta tsala ihu duk saita dabarbance tafiyar ma taso gagararta hannunta Zainab ta kama suka shige Hall d'in da zasu gabatar da lecture su ta ranar anan d'inma dai bata tsira ba dan wasu ma kasa hak'uri sukayi saida sukayi mata magana ta rasa amsar da zata basu, harda masu cewa wai yaushe aka ganta? surutai dai iri iri anata maida magana har zuwa lokacin da Dr Naseer Sufi ya shigo Hall d'in hakan yasa akayi shiru kowa ya nemi wajen zama ya shiga gabatar da abinda ya kawoshi. Sai 8:30a@ sannan aka gama, Dr Naseer Sufi yana shirin fita daga Hall d'in class rep d'insu ya d'aga hannu da fad'in "Sir". tsayawa yayi ya juyo yana kallon mai maganar, tashi class rep d'in yayi ya isa inda yake k'asa k'asa ya d'anyi masa magana kafin ya nuno desk d'in da Heedayah take zaune itada Zainab gabanta fad'uwa kawai yake ta sunkuyar da kanta k'asa amma Dr Naseer Sufi yace ta d'ago kanta dole haka ta d'ago tana kallonshi, ido ya k'ura mata sosai yana kad'a kai kafin kuma ya fice daga Hall d'in gaba d'aya wasu daga cikin student's suka rufa masa baya. Tuni idanunta suka ciko da k'walla ta kalli Zainab tana fad'in "Na shiga uku Zainab dana sani banzo school d'in nan ba yau kiga fa yadda ake faman nuna ni ana magana ta ga Dr Sufi ya ganni yanzu ya fita yana girgiza kai me hakan ke nufi?". "Please calm down mana Heedayah meye abin d'aga hankali a ciki wai? tambaya cefa kawai da amsa kece wance? a'a bani bace finish kuma mutane ma da suke ta wannan shirmen inace an rubuta sunan yarinyar da ake nema Seeyamah ce ko Sawwamah na manta duk wannan shegen Nura Ahmad (class rep) d'inne yaja ai". Heedayah ta bud'e baki zatayi magana kenan akazo aka kirata wai ana nemanta a office d'in VC, ido ta zaro tana kallon Zainab, Zainab bata bari tayi magana ba ta tashi ta kama hannunta suka fita daga Hall d'in. Sai data rakata har wajen office d'in VC sannan ta tsaya tace ta shiga ita kad'ai. Da sallama ta shiga office d'in, tunda ta shigo yake kallonta yanaso yaga bambancin su da yarinyar jiya daya gani a labarai amma shidai baiga wani abu d'aya dazaice ya bambanta su ba. Guri ya nuna mata ta zauna ta sunkuyar da kanta k'asa cikin fad'uwar gaba, sai daya kalleta sosai kafin yace "Whats ur name?". Cikin d'ar-d'ar ta amsa da "I'm Heedayah Abubakar". "What's ur address?". "Rijiyar zaki". Tambayoyi ya shiga yimata kala kala a tak'aice dai a wannan rana saida Uncle Muhammad yazo school d'in ya tabbatar musu da ba yarinyar da ake cigiya bace wannan asalinta ma ba y'ar Kano bace daga Katsina take, dan da farko ma har police sukaso su saka a cikin maganar wai za'a maida ita gidan marayun da k'yar suka yarda da Uncle Muhammad daya dinga rantsuwa, Heedayah kam har kuka saida tayi musamman dataji sun sako maganar y'an sanda da kuma cewar za'a maida ita gidan marayu. Tare ma suka tafi da Uncle Muhammad d'in batare da sun gama lecture d'insu ba duk ta tsorace har abin yakoma bawa Zainab dariya. Ta b'angaren Jawaheer ma hakan ce ta kasance a inda take karatu dan dai kawai ita ba mutunci dataga mutum yana mata kallon k'urilla zata tsaya ta zabga masa rashin mutunci ta k'ara gaba dan haka aka dinga shakkar kallon nata ma dan ba wanda baisan JAWAHEER MANSOOR JIK'AMSHI ba a school d'in. ★__________★ KATSINA K'ofar K'aura. Shagon d'inki ne wanda ke cikeda matasa wasu na kan keke suna d'inki wasu kuma y'an tayin hira ne. Wani matashin saurayi wanda ke zaune kan kujera da keken d'inki a gabanshi amma ba d'inkin yakeba wayace a hannunshi yana danne danne. "Kai! Musty wannan ba k'anwar ka Heedayah bace naga anyi posting a Facebook ana cigiyar ta". ya k'arasa maganar yana nuno masa wayar hannunshi. Wanda aka kira da suna Musty ne ya dakata da d'inkin dayake ya mik'a hannu ya karb'i wayar abokin nashi yana kallon screen d'in, baki ya bud'e tareda zaro ido yana k'ara bin hoton da kallo gabanshi na fad'uwa lokaci d'aya cikin rawar baki yace "Itace wllhy, itace Isma'eel innalillahi wa inna ilaihi rajioun". Bai saurari cewar kowa ba ya tashi ya fice da sauri ba tareda yabawa Isma'eel d'in wayarshi ba duk aka bishi da kallo. Machine d'inshi roba roba ya hau yabashi wuta kafin ya figeshi da uban gudu yabar k'ofar shagon. Yakai kai zai shiga soron gidan kenan sukayi kacib'us da Baba shikuma zai fita, ganinshi duk a rud'e yasa Baba ya shiga tambayar shi lafiya kuwa meya faru?. "Baba mukoma ciki wani abu Isma'eel ke nunamin yanzu a waya". Baba bai musa ba ya juya suka koma cikin gidan tare hankalinshi duk a tashe da tunanin abinda ya faru. Umma tana zaune kan tabarma da wake a tray tana gyarashi suma kan tabarmar suka nemi waje suka zazzauna. "Lafiya dai Malam na ganku haka kamar ba cikin nutsuwar ku ba?". Umma ta tambaya ganin yanayin su kamar akwai wani abu dayake faruwa. "To nima dai zan fita muka had'u dashi zai shigo, muna jinka Mustapha meye ya d'aga maka hankali haka?". Zama Mustapha ya gyara yana fad'in "Yanzu Isma'eel ya nuna min wani hoto wai ta b'ata ana cigiyar ta a Kano". yayi maganar yana mik'awa Baba wayar, shi kanshi Baba saidaya zaro ido ganin Heedayah k'uru k'uru wai ta b'ata, kalmar innalillahi kawai yake ambata cikin tsananin tashin hankali Heedayah ta b'ata amma meyasa Ramlah bata kira ta sanar dasu halin da ake ciki ba? b'atan d'an mutum sukutum da guda?. Umma ya mik'awa wayar ta karb'a ta duba hoton dayake ita mace ce akwai raunin zuciya har tafara hawaye ganin Heedayahnta a matsayin wadda ta b'ata dama rabon ayi hakane yasa tabar gabansu tabi Ramlah Kano? Wayar Baba ya karb'a daga hannun Umma data tsurawa hoton Heedayah ido tana hawaye ya mik'awa Mustapha wayar yana fad'in "Kiramin y'ar uwarka Ramlatu inji dalilin dayasa ta b'oye mana irin wannan muhimmiyar maganar saboda shashanci". Wayarshi ya zaro daga aljihun gaban rigarshi yasa password ta bud'e ya shiga jerin numbers yana neman number Aunt Ramlah. Bata dad'e tana fara ringing ba akayi picking sai yasata handsfree ya rik'e ta a hannunshi yana amsa sallamar Aunt Ramlah. "Ramlah Baba ne zakuyi magana dashi gashi a kusa dani". "Yauwa dama Mustapha dama ina niyyar kiransu, jin haka yasa gabansu ya k'ara fad'uwa, cikin b'acin rai Baba ya fara magana da fad'in "Haba Ramlatu, ya ina ganinki kamar mai wayo ashe ba haka bane inbanda sakarci taya zaki b'oye mana irin wannan maganar?. MG'S SKINCARE In kid'a ya chanza rawarma semutaru asauyata, Wani Kaya se amalende Haka Wani Hadi na musamman se MG'S, Ina ma'abota amfanida kayan MG'S SKINCARE? To bana fa tafi bara munqarawa kayanmu inganci muncire muntsefe munkawo maku qayatattun kayan gyaranjiki da Baki taba amfanida irinshiba a wannan qarnin, Wani irin salo na gishirin kyan daukar magana zakiyi duk kikayi amfanida hadinmu b cika bakiba,ko yayan Hutu basa nuna maki tsadar fataba,duk a 11k fa kachal👌🏻 Beauty kit:11k Student package:7k Soap:3k Bridal kit 18k Kicire kokonto ki warwaro Lalita kidebi Kaya n kerewa SAA Chat:08062991549 or 07046881166 or 07067210195 Call:08064532391 Available in Kano and Kaduna We also have beautiful yet luxury and unique frames for your apartments chat or call 07046881166 Serious buyers only please, Inamasu bukukuwa😍 Kugarzaya @inteesar cakes nd more kuyi order small chops domin bakinku irinsu Cupcake,fishroll,samosa,spring rolls dama duk kayan kwalam da makulashe kunemata 07067210195 Cika alkawari shine takenmu🤝 Thank you *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). D'imbin godiya ga masu bibiyar littafin nan nagani kuma na yaba sak'onnin ku na riskata ako yaushe thank you very much ALLAH yabar k'auna alkhairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke sakallahu khayran.💖 No 21. Gaba d'aya sai Aunt Ramlah ta kasa gane inda maganganun Baba suka dosa musamman dataji yana k'ara fad'in "Duk duniya su ya kamata ace ta fara sanarwa wannan labarin ta inda yake shiga bata nan yake fita ba itama Umma tasa baki sukayi tayi, sosai hankalin Aunt Ramlah ya tashi dataji Umma na kuka take maganar cikin sanyin murya tace "Baba, Umma har yanzu fa ban gane akan abinda kuke magana ba wllhy dan ALLAH ku sanar dani laifin danayi". "Haba Ramlatu ace Heedayah ta b'ata har kwanaki biyu amma baki sanar damu ba? yarinyar nan fa amana ce a wajenmu idan baki fad'a mana ba wa zaki fad'awa? saifa yanzu da Mustapha yagano hotonta a wayar Isma'ila abokinshi ana cigiyar ta sannan yazo hankali tashe yake nuna mana". Aunt Ramlah batasan lokacin datayi murmushi ba idan ta fahimta daidai suma sunga yarinyar nan irin Heedayah suke zaton Heedayahn su ce. Dariya ta d'anyi wadda tasa mamaki ya k'ara kamasu kafin wani yayi magana tace "Ku kwantar da hankalinku Baba wannan yarinyar ba Heedayah bace yarinyar ku lafiyar ta k'alau muma munga hoton yarinyar haka mukasha mamaki wlhi yanzu ma Abban Nu'aym ya dawo da ita daga makaranta suma shugabannin makarantar sunyi zaton itace da k'yar dai suka yadda shine duk ta tsorata ta kasa zaman school d'in ta biyoshi suka dawo gida". "Hukmullah la ajab". Haka kawai Baba ya fad'a yana faman jijjiga kai, Umma da Mustapha ma sakato sukayi suna saurarar Ramlah cikeda d'imbin al'ajabin abinda take fad'a, yayin da Umma kuma ta d'auki tunanin ta cak ta maidashi wani waje daban tana ayyana abubuwa da dama a k'asan ranta. Y'ar dariya Aunt Ramlah ta k'ara yi tace "Baba bari ku tabbatar ma da abinda nake fad'a bari in kirawo ta ku gaisa". murya tasa ta kira sunan Heedayah da k'arfi wadda suke kitchen itada Zainab suna shirin d'ora abincin rana, Heedayah ta amsa tareda ajiye albasar datake yankawa ta wanke hannunta a sink ta fito daga kitchen d'in zuwa falon inda Aunt Ramlah ke zaune kan kujera, wayar ta mik'a mata tana fad'in "Su Baba ne zaku gaisa dasu". karb'a tayi cikin murna tana murmushi takai kunnenta tayi sallama tana gaishe da Baban ya amsa cikin jin dad'i haka ma Umma wadda tuni tabar kukan datake farin ciki ya maye gurbinsa, har da Yah Mustapha saida suka gaisa yayin da Baba ya tubure shi lallai saidai Heedayah ta dawo Katsina shi ya tsorata da wannan al'amari da k'yar Aunt Ramlah ta shawo kanshi ya hak'ura ko dan saboda karatun data fara, haka dai ya hak'ura bada son ranshi ba sai dan irin magiyar da Ramlahn ta dinga zabga masa. Sun jima suna hira har saida credit d'in ciki ya k'are wayar ta katse sannan suka hak'ura, a tare su Baba suka sauke ajiyar zuciya sai yanzu hankalinsu ya kwanta tashi Mustapha yayi ya d'auki wayarshi data Isma'eel daya taho da ita ya k'ara yimusu sallama ya fita. Baba ya juya ya kalli inda Umma take yaga itama kallon nashi take kowa da abinda yake tunani a ranshi, numfashi ya sauke yace "Anya Sa'adatu babu wani b'oyayyen abu a cikin wannan al'amarin? abin nan fa akwai d'aure kai da tsantsar mamaki". "Wallahi Malam abinda yake raina kenan tun lokacin danaji ba Heedayah bace yarinyar nan anya ba y'an biyu bane ba kuwa? dan wannan ba za'ace iya kamanni kawai suke da Heedayah ba dan wllhy idan an kwana dubu ana ce min ba Heedayah bace bazan yardaba kaga abu saikace almara". Umma ta k'arasa maganar tana rik'e hab'arta tana k'ara jinjina girman al'amarin. Shima Baba kai ya shiga jinjinawa hundred percent ya yarda da maganar Umma datace ko y'an biyu ne ba shakka wannan babban al'amari ne dayake buk'atar bincike sosai idan ya kasance hakan ne kuwa zaifi kowa farin ciki zai sada Heedayah da asalin iyayenta duk da yasan ba k'aramin rud'ani da tashin hankali Heedayah zata shiga ba lamarin zai girgizata, Baba sun dad'e suna k'ara tisa maganar da Umma kafin shima ya tashi yayi mata sallama ya fita dama ya fitan wani abin ne ya dawo dashi. Matuk'a Aleeyu yake kula da Seeyamah zuwa yanzu harta fara sabawa da zaman kad'aitakar da wannan azzalumin ya gadar mata, wani har hira suke zama suyi da Aleeyu. Habeeb kuwa tun ranar dayaje batada lafiya har akayi mata allura bai k'ara zuwa ba ako yaushe dai yana kiran Aleeyu yaji lafiyar ta, sau d'aya ya tab'a cewa Aleeyun ya bata suyi magana shima ba wata maganar arzik'i bace cewa yayi idan ta shirya barin gidan ta fad'awa Aleeyu shikuma zaizo ta fad'a masa waye shi da dalilin dayasa take masa BASAJA bai saurari cewarta bama ya datse kiran tasha kuka a ranar har saida kanta yayi ciwo Aleeyu yana rarrashinta bama ta kulashi ba ta cigaba da kukanta zuciyarta na mata zafi. Ta b'angaren Mujaheed kuwa sosai yasa ido akan duk wani takun abokin nashi batare dashi Habeeb d'in yasani ba, yayi busy sosai cikin kwanakin dan anfara ginin d'aya kamfanin na sark'ok'i da fidda design d'insu hakan yasa sam baya samun lokacin kanshi ma. Police suna iya bakin k'ok'arinsu matsalar da har yanzu wad'anda sukayi garkuwar da ita basu kira waya anji daga garesu ba bare aji kud'in da zasu yanka wanda za'a fanshe ta har abi diddiginsu abin dai sai addu'ar ALLAH ya bayyana ta kawai. ★★__________★★. K'arar spoon kawai ke tashi a dinning area d'in Ummi da Neehlah su kad'ai ne masu cin abincin Habeeb kam wayace a hannunshi yana ta faman danne danne kanshi a k'asa ga abincin a gabanshi amma kota kanshi baibi ba hakan yasa da Ummi ta gaji tace "Ajiye wayar nan ka kama abinci kaci". d'agowa yayi ya kalli Ummin ya d'an b'ata fuska da fad'in "I'm full fa Ummi tea ma kawai is okay". Had'e rai Ummi tayi tace "Ban yardaba Abbuna meyasa kake son yin wasa da cikinka ne? maza kaci abinci kafin inyi maka d'ura yanzun". Dariya ce ta tahowa Neehlah jin abinda Ummi ta fad'a tayi saurin maidata tana toshe bakinta ya ganta sarai hakan yasa ya had'e rai sosai yana hararar ta yace "Tashi kibar wajen nan". a marairaice ta d'ago tana kallonshi kafin ta maida kallonta kan Ummi taji ko zatayi magana mutumin nan ya cika takura wllhy indai yana waje ba damar mutum ya sake. "Akan me? banason rigima fa Abbu ya tana cin abincin ta zakace ta tashi kai waye ya takura maka? ka kuma ajiye wayar nan kayi abinda yake gabanka". Saidaya dallawa Neehlah harara wadda duk take a tsorace kafin ya ajiye wayar a kusa dashi yaja plate d'in gabanshi ya fara ci, kad'an ya tsakura ya ture plate d'in ko ruwa baisha ba ya yagi tissue yana goge bakinshi lokaci d'aya yana mik'ewa tsaye tareda d'aukar wayarshi, yana shirin barin wajen Ummi tace. "Zauna, Hajiya Inna ta kawomin k'ararka d'azu dana shiga gaisheta". Zama ya k'ara yi yana kallon Ummin yaji abinda zatace ya yatsina fuska yace "Ummi ki k'yale tsohuwar nan ita indai bata fad'i laifin mutum ba batajin dad'i". d'an rank'washi Ummi ta sakar masa a kanshi ya dafe wajen kuwa yana b'ata fuska yace "Kai Ummi me tace nayi ne? nifa rabon damu had'u ma harna manta". "Eh, ai akan hakan ne tace ka daina shiga gaisheta gaba d'aya why?". "Oops! wllhy Ummi ayyuka ne suka sha min kai saboda ginin danace miki za'a fara amma insha ALLAH yau idan nadawo office zan shiga mu gaisa kafin ta kawo wani laifin tace nayi". duka Ummi takai masa ya goce da sauri yana murmushi ya tashi yayi mata sallama ya fita daga falon ta bishi da kallo tana murmushi. Baki Neehlah ta tura tace "Please Ummi ki samowa Yah Habeeb mata yayi aure ni wllhy yana takuramin dayawa". Dariya Ummi tayi tace "Nice ma zan samo masa? shi zai nemo abarshi da kanshi". Cikeda shagwab'a tace "To ai Ummi shifa baya kula mata bare yasamu matar aure ALLAH nina gaji da zamanshi a gidan nan kawai kibada sadakar shi". "Lallai Neehlah kiyi addu'a kar yaji wannan maganar Abbun nawa zan bayar sadaka?". Ummi ta k'arasa maganar tana dariya, itama Neehlahn saidata fad'i hakan saikuma tayi saurin toshe bakinta tana rarraba ido cikin falon kamar wadda zata ganshi Ummi nayi mata dariya. Kamar yadda yayi alk'awari washegari yana dawowa daga office bai k'arasa gidansu ba yayi parking a k'ofar gidan Hajiya dan yanzu shi yake driving d'in da kanshi ya sallami driver'n sai jefi jefi idan yaji bayajin yin tuk'in yake nemanshi suma bodyguard d'in duk ya sallamesu dama bawani so yake ba Mujaheed ne ya kawo shawarar hakan lokacin daya dawo zai fara aiki a matsayin shi na C.E.O. da yak'i yarda munafukin saiyaje ya had'ashi da Kawu Sulaiman shima ya kirashi yace ya kamata hakan yanzu kuwa ya kori kowa. Sanye yake cikin American suit black and white wandon da rigar ne bak'ake sai walk'iya suke yayin da shirt d'in ciki ta kasance fara k'al mai dogon hannu butterfly tied yayi amfani dashi shima black color ya matse k'ugunshi da bak'ar belt ta kamfanin D&G k'afarshi bak'in takalmi ne cover shoe na kamfanin Gucci kamar yadda hannunshi ma ke d'aure da bak'in agogon fata na Gucci yayi matuk'ar yin kyau sai baza k'amshi yake mai sanyin k'amshi da sanya nutsuwa. Da k'akk'arfan takun nan nashi mai cikeda kuzari da koshin lafiya da ubangiji ya wadata shi da ita yake takawa har zuwa inda k'ofar da ake shiga falon Hajiya duk da irin gaishe shi d'in da maigadi yakeyi hannu kawai ya d'aga masa. Hannu yasa ya kama handle d'in k'ofar ya bud'e ya shiga bakinshi d'auke da mak'alalliyar sallama wanda ya saba yinta a saman leb'enshi ya shiga cikin falon. Idanu, baki, hanci da dukkan gangar jikinshi ya saki yana kallon inda Hajiya Inna take zaune ga yarinyar dayasa aka k'wamuso masa zaune kusa da ita tana ta mata surutu sunata dariya suman tsaye yayi ya runtse idonshi zuciyarshi na kai da kawowa ya damk'e hannayenshi ya k'ara bud'e idanunshi da tunanin basu gwada masa daidai bane saidai still tana nan yana ganinta ita d'ince dai ba wata ba. "K'araso mana maigidana yau an tuna dani kenan duk da nasan yanzu haka Afeefah ce tayi maka magana". Sam baiji wani irin maganganu Hajiyan keyi ba Heedayah kawai yake kallo wadda tun shigowarshi tayi tsuru tsuru ta sunkuyar da kanta k'asa kamar munafuka tana wasa da yatsun hannunta wad'anda suka sha jan lalle ya kama sosai har yayi maroon color. Wani irin juyawa yayi da dukkan k'arfinshi da wata irin sassarfa ya fice daga falon cikin wani irin taku kamar zaki Hajiya da Heedayah suka bishi da kallo baki bud'e.... Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). Wato reader's kunsan ta kan mugunta ko😝😂 kowa fata da burinshi yaga yadda Gashua zaiyi idan yaje yaga yarinyar gidan Hajiya daban wadda yasa aka k'wamuso masa itama kunsan gogan naku ai jarumi ne 😉 mazewa zaiyi ya basar kamar baiga komaiba koya kukace 😅🤣. No 22. "ALLAH mai iko lafiyar Habibu k'alau kuwa yaro saikace mai jinnu". Hajiya tayi maganar tana kallon Heedayah bayan fitar Habeeb, itadai Heedayah batace komaiba to me zatace? duka fa wannan ce had'uwarsu ta biyu bayan wadda suka had'u akan layi, baki Hajiya ta tab'e tana fad'in "ALLAH ya kyauta". Da wani irin sauri yake tafiya lokaci d'aya yana lalubo number wayar Aleeyu ya sauke masa tijara da kwandon masifa wane d'an iskan ne yace yayi sakaci har tasamu damar fitowa? akanme zai bari yarinyar nan ta gudo gashi har ta k'ara zuwa wajen Hajiya saidai kuma sam wayar Aleeyun tak'i shiga hakan yasa ranshi ya k'ara b'aci sosai tsaki kawai yake faman saki yana cije lips, dama a wajen gate yayi parking d'in motarshi bai shigo da ita ciki ba. Bai saurari maigadi daya taso dan ya bud'e masa k'ofar ba ya bud'e da kanshi ya fice tamkar zai tashi sama maigadi ya bishi da kallon mamaki. Har ya bud'e k'ofar motar zai shiga saikuma ya fasa yayi tsaye rik'e da murfin motar kanshi a k'asa yana wani tunani idan ya tafi yabar yarinyar nan anan ai yayi rashin dabara ma dole yasan yadda yayi ya fita da ita dan k'ara tabbatarwa waccan ce kokuma watace daban, dan haka ya juyo a sukwane yakoma cikin gidan bayan ya aro nutsuwa ya d'ora saman fuskarshi. Har lokacin Hajiya da Heedayah suna zaune sai gashi ya k'ara shigowa baiyi magana ba ya nemi kujera 1sitter ya zauna yayi crossing legs d'inshi yana girgizasu, Heedayah kam kallon ikon ALLAH kawai take cikin ranta take fad'in "Da gani wannan mutumin ba mutunci zaiyi ba wllhy jifa yadda yazo ya zauna yana wani girgije girgijen k'afa". "Tohh yau kuma da wannan aka shigo?". cewar Hajiya tana kallonshi, shidai baice uffan ba sai gaisheta dayayi ta amsa tana masa mitar kwana biyu ya yada ita, kamar mai ciwon baki yace "I'm very busy Hajiya but I'm sorry yanzu ma wucewa zanyi akwai important issues dazan gabatar". yayi maganar yana satar kallon Heedayah ta k'asan idanunshi ba wanda zaiyi zaton ita d'in yake kallo saboda yasan takunshi. "Aifa agogo sarkin y'an aiki ina zaka aiki ina kadawo aiki, tohh ALLAH dai ya taimaka yabada sa'a amma kana k'ok'ari kam ALLAH yaji k'an mahaifinka". Da Amin ya amsa itama Heedayah ta amsa, tsaye ya mik'e ya d'auko wallet d'inshi a aljihun bayan wandonshi ya bud'e ya ciro kud'i masu yawa ya ajiyewa Hajiya a gefenta ta shiga yimasa godiya tana sa masa albarka duk cikin jikokinta tafi cin gajiyar Habeeb zuwa goma idan zaiyi saiya mata kyauta kuma ba k'arama ba banda sauran kayan buk'atu na yau da kullum dayake aiko mata dasu duk da cewa dai bata nemi komai ta rasaba haka yake kyauta a jininshi take. "Yauwa Habibu tafi da yarinyar nan ka kai min ita gida dan ALLAH dama shirin tafiya take yanzu". Cak ya tsaya daga shirin fita dayake jin abinda Hajiya ta fad'a, daga Hajiyan har Heedayah sunyi zaton zai musawa abinda Hajiyan tace saikuma sukaji yace "Okay I'm waiting". yana fad'in haka yasa kai ya fice daga falon. (Yo dama nema yake ina zai musa 🤣). "Ni Hajiya da kin k'yaleni kawai na tafi wllhy". Heedayah tace tana tura baki, dariya Hajiya tayi tace "A'a gashi dai zai tafi d'in ke ba sauk'i na nemar miki bama samun abin hawa a layin nan namu ma ai aikine tashi maza kiyi da jiki Habibu d'an gaggawa ne bai son jira". Haka nan ba dan ranta yaso ba ta tashi tasa hijabinta wanda ya tsaya mata iya gwiwar ta mai hannu ash color wanda yahau da atamfar jikinta kalar ash da fari ta rataya side bag d'inta mai sark'a ta yiwa Hajiya sallama, cikin kud'in da Habeeb ya ajiye mata ta zaro 5k ta bawa Heedayah farko k'in karb'a ma tayi sai dataga Hajiyan ta had'e rai sosai zata fara fad'a sannan ta amsa tayi godiya ta zurasu a jaka, farkon shigowa falon inda takalmin ta yake ta k'arasa ta saka Hajiya har k'ofar falon ta rakata sannan suka k'ara yin sallama ta tafi tana tunanin ya zasu k'are da wannan jikan Hajiyan yai ta wani cin d'aci yana cika da batsewa yana ma mutane muzurai itadai yai mata wllhy ba k'yaleshi zatayi ba. tayi maganar a fili har da murgud'a baki. Habeeb bai san hidimar datake bama yana zaune cikin mota yana jiranta sai sakin tsaki yake yana duba agogon hannunshi, tunda ta fito daga gidan ya k'ura mata ido ta cikin glass d'in motarshi cije baki yake yana wassafa irin d'iban albarka da rashin mutuncin dazai shuka mata idan harya kasance itace (Sam ya manta da idan itace d'in dole ta razana idan ta ganshi amma wannan ko a jikinta sai ya alak'anta hakan da duk cikin makircin ta ne). A hankali ta k'araso ta bud'e front seat ta shiga ko gama daidaita zamanta batayi ba ya figi motar yabar layin, kauda kai kawai tayi tana tab'e baki dama tasan dame Hajiya ta had'ata. A wani irin slow motar take tafiya ga sanyin A.C da daddad'an k'amshin turarenshi dana freshner d'in motar da suka had'u suka cakud'e suka bada wani lafiyayyen k'amshi wanda yasa dole Heedayah ta lumshe idanunta tana sakin k'aramar ajiyar zuciya wadda ita kad'ai taji abarta. Duk a zatonta zai tambayeta ta fad'a masa address d'in inda zai kaita saikuma taga ya d'auki wata hanyar daban hakan yasa ta juya ta kalleshi taga ko b'arin datake bai kalla ba taga dai tafiya yake hankali kwance ya murtuke fuska. "Wai Malam ina zaka kaini ne bafa nan bace hanyar gidan".tace hankali tashe tana kallonshi, idan kujerar dayake kai ta tankata to shima ya tanka kawai ya cigaba da bawa mota wuta hankalinta ya k'ara tashi kamar zata sakar masa kuka tace "Dan ALLAH bawan ALLAH kayi hak'uri ka saukeni insamu abin hawa please". Habeeb dai gabanshi kawai yake kallo yana driving d'inshi magiya ta cigaba dayi masa akan ya sauketa amma yayi biris da ita, ganin dai magiyar bazata kaita ba yasa cikeda tsiwa da rashin kunya take fad'in "Wllhy ko ka tsaya in fita ko inyi maka ihu yanzun nan in tara maka jama'a". ta k'arasa maganar tana k'ok'arin bud'e motar saidai da alamu anyi locking d'inta. Sai a lokacin Habeeb ya d'an juyo ya kalleta wani murmushin gefen baki ya sakar mata kafin yace "Koba ihu ba? kiyi ihun mana kiga idan akwai wanda zaizo ya ceceki anan stupid d'in yarinya kawai". ya ida maganar yana hararar ta ya juya ya cigaba da tuk'inshi "To wai ina zaka kaini ne?". Da k'arfi tayi maganar cikin muryar kuka tana faman juye juye kan kujerar datake tak'i zama waje d'aya. Kai tsaye batare daya juyo ya kalleta ba yace "Zan siyar dake ne ki nutsu kuma ki daina min mutsu mutsun nan inba hakaba zan baki mamaki yanzun nan". yadda ya k'arasa maganar cikin hargitsattsiyar murya yasa tayi gum da bakinta ta zauna sosai gabanta na fad'uwa shiyasa fa dama tacewa Hajiya bazata biyoshi ba yanzu batasan gidan uwar dazai kaita ba ga magreebah takawo kai. Haka suka cigaba da tafiya ba tare daya k'ara kallon side d'in datake ba, lokaci lokaci take sanya hannu tana d'auke k'wallar dake taho mata da haka har suka k'arasa lamid'o crescent dayake farkon shiga layin ne suna fara tafiya bayan sun shiga layin yayi parking, kallon inda yayi parking d'in tayi taga wani plat house ne mai kyau sosai kafin tayi yunk'urin yin wata magana ya fice daga motar da azama takai hannu zata bud'e ta fice taji anyi Lock d'inta ba damar fita. "Wllhy bazan yafe maka kukan daka sani ba aikin banza nunar rana kawai". tace tana share hawayen idanunta da hijab d'inta. Knocking door yayi bayan ya shiga gidan ba dad'ewa Aleeyu yazo ya bud'e masa k'ofar daga irin kallon dayake jifan Aleeyu dashi yasha jinin jikinshi saiya matsa masa hanya ya shiga hannayenshi zube cikin aljihun suit d'inshi yana k'arewa falon kallo kamar yaune ya tab'a shiga cikinshi, Aleeyu ya rufe k'ofar yabi bayanshi yana fad'in "Yallab'ai barka da zuwa". Bai amsa ba sai idanu daya tsare Aleeyun dashi, wasu irin idanuwa ALLAH ya bashi kaifafa wanda ko d'a namiji ya kalla dasu wanda aka kalla d'in yakan rissina duk tsaurin ra'ayin shi kuwa bare y'a mace da cikin y'an sakanni yake ladabtar da ko wacece ta cikin idanunshi, k'asa Aleeyu yayi da kanshi yana sosa kai da tunanin laifin me yayi ne ake masa wannan kallon tuhumar? "Where is she?". haka kawai ya cewa Aleeyun fuskarshi a d'aure. "Tana ciki yallab'ai". Aleeyu ya bashi amsa. "Sure?". "Yes sir". Har yanzu dai zuciyar shi bata gama yarda da abinda yake tunani ba hakan yasa batare dayace komi ba ya shiga takawa zuwa bedroom d'in da Seeyamah take ya kama handle d'in k'ofar ya bud'e a hankali wani irin bugawa gabanshi yayi lokacin daya hangeta a zaune kan pray mat da k'aramin Alqur'an a hannunta tana karantawa a hankali, koda wasa Seeyamah bata d'ago kaiba dan duk zatonta Aleeyu ne kawai sai ta cigaba da karatun ta. Ajiyar zuciya da numfashi ya sauke a lokaci d'aya yana dafe goshinshi yanzu dai ko yanaso ko bayaso dolenshi ya yarda su d'in twins ne wani abu ya rabasu to meye ya rabasu d'in? amsar da bazai iya bawa kanshi amsa ba dan haka yaja k'ofar ya k'ara rufewa ya juya. Seeyamah datake ta jiran taga shigowar Aleeyu taji shiru saita d'ago kai ta kalli k'ofar taga an rufeta sai a lokacin kuma k'amshin mutumin da bazata tab'a mantawa dashi ba ya iso hancinta to ko shine yazo? rabon data sashi a idanunta tun ranar da akayi mata allura bata bari tunanin shi yayi tsaho ba ta yakice ta cigaba da karatun ta. "Ka cigaba da kula da ita zuwa jibi zaka maida ita inda ka d'aukota ka gane?". Kai Aleeyu ya gyad'a cikeda jin dad'i dan harga ALLAH ya mugun gajiya da wannan zaman ALLAH yasa karya canza ra'ayi dan sarai yasan halin ogan nashi wahainiya ne wajen canza kala. Kud'i ya ciro masu yawa ya bashi sannan ya fice daga falon. Tunanika kala kala ne ke masa yawo cikin k'wanyar kanshi ya zama dole yaje ya zauna da Hajiya suyi magana yaji wannan yarinyar datake zuwa wajenta ita d'in wacece? meye had'in Hajiyar da ita? yana ganin komai yazo k'arshe yanzu dole ya saki yarinyar nan kafin wani ya ankare. Yana fitowa yasa remote ya bud'e motar ya k'arasa ya shiga, tunda ya shiga motar take faman hararar shi jitake tamkar ta kikkifa masa mari, tayi zaton yana shigowa zai tada motar su tafi sai taga kawai ya rufe idanunshi gamida yin relaxing akan seat d'inshi kamar wanda zaiyi barci gashi dama Aunt Ramlah sau biyu tana kiranta taji ta shiru har yanzu bata koma ba sai k'arya tayi mata tace tana gidan Hajiyan yanzu dai zata taho har Aunt Ramlahn nayi mata fad'an magreebah data kai. Wani bak'in ciki ne ya kama Heedayah mutumin nan mugun d'an latsi ne wllhy ya kawota inda bata soba, ya shiga ya barta tun d'azu tana zaman jiranshi and now yazo kuma ya wani hakimce kan kujera kamar ma bashida alamun tafiya. "Nidai dan ALLAH ka budemin in tafi wai malam meye hakane". Cikin masifa tayi maganar tana hararar shi. Habeeb da har lokacin bai bud'e idanunshi ba kuma a lokacin ne kalmar nan ta nunar rana ta fad'o masa a rai dan shifa har yanzu bai yadda yarinyar nan ba zaginshi tayi ba dan haka yau saita fad'a masa ma'anar ta sannan zai maida ita gida tunda ita fitsararriya ce batada kunya shikuma wancan d'an iskan ba abinda ya sani a hausar ma sai tsabar cika bakin shi bahaushe ne, batare daya bud'e ido ba k'asa k'asa kamar wanda aka tilasta yace "Definition of nunan rana nakeso in sani". Baki Heedayah ta bud'e tana zaro ido jin abinda ya fad'a ita wllhy sam ta manta ma ta tab'a fad'a masa wannan kalmar yanzun ma haushin ya tafi ya barta ne yasa tace haka wannan guy d'in d'an bala'i ne wlhi, fuska ta marairaice tana kallonshi..... Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). This page all dedicated to Aunt jamila Mom sayyeed Aunt Fareedah Maryam Bello Maryam Shuwa Habeebah zailani Haleemah Dayyab Lubnah Oum Ramlah Mummy musaddiq Ice Aisha Smiling Mammyn Baffah Humayrah Da sauran wad'anda ma basuji sunayen suba duk nagode ALLAH yabar zumunchi da k'aunar juna jazakumullah khair 💗. No 23. Taga alamun gayen nan masifa da bala'in mutum bashi zaisa ya canza ra'ayin abinda yayi niyya ba dan haka ta marairaice murya tace "Dan ALLAH bawan ALLAH ka taimakeni ka budemin in fita bama saika kaini ba please". Idanunshi ya bud'e ya kalleta ba shiri tayi k'asa da kanta gabanta na fad'uwa saboda kaifin idanunshi, cikin dakakkiyar murya yace Ashe kuwa zamu kwana anan kenan dan sai kin fad'amin abinda kike nufi da kalmar nan". Batayi gigin k'ara d'agowa bare ta kalleshi tace "Nifa ban tab'a fad'a maka haka bafa". Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace "Kinyi zaton na manta ne? Habeeb baya mantuwa idan kin shirya tafiya zuwa gida yanzu ki fad'amin". ya k'arasa maganar yana k'ara maida kanshi kan seat d'in ya kwantar harda lumshe ido, Heedayah ji take tamkar ta tsala ihu meyasa bazai fahimta bane? magreebah fa tayi har tafara jiyo kiran sallah a unguwar, ta bud'e baki zatayi magana kenan ya rigata da cewa "Wato kinyi amfani da salon zagi irin na hausawa kin zageni ko?". Ido Heedayah ta zaro sosai tace "Zagi kuma? wllhy nifa ba zaginka nayi ba ALLAH". Tayi maganar kamar wadda zata sakar masa kuka, ba tare daya d'ago kanshi daga kan kujerar ba ya bud'e idanunshi yace "Ba zagi bane? meye to?". Saidata tura baki cikeda shagwab'a tace "Kawai fa gani nayi farinka yayi yawa mu a hausa idan akaga irin fararen nan basuda k'wari sai ace musu nunar rana amma wllhy ba zagi bane". Idanunshi ya d'an waro ya taso daga kan kujerar yana fad'in "Sa'anki ne ni? ko abokin wasanki ne ni d'in, nine mara k'wari ko?". ya ida maganar yana nuna k'irjinshi da d'an yatsanshi. "Nidai kayi hak'uri please ka maidani gida Auntyna tana ta kira tun d'azu taji shiru ban komaba". Kai kawai yake kad'awa ya tada motar kuma bawai dan maganar datayi masa ba kawai idan ya cigaba da zama anan zaiyi missing sallah ne da saiya tsaya ta nuna masa inane bashida k'warin a jikinshi shi zata rainawa hankali?. Tafiyar kurame ce akayi ko tari ba wanda ya k'ara yi bayan sun tafi kowa da irin tunanin dayake a ranshi, gaba d'aya shi tunanin Habeeb ya tafi kan ya akayi suna matsayin twins amma d'aya a gidan marayu meyasa hakan? lallai akwai wani b'oyayyen sirri ma'ana ita wannan dayake gani a wajen Hajiya itace take tare da iyayensu? duk yadda akayi ita ta gidan marayun ta b'ata ne tun tana yarinya, dole zaiyi bincike akai amma kafin nan saiya zauna da Hajiya yaji tarihin wannan d'in saboda yasan ta ina zai fara binciken nashi. Haka ya dinga sak'a da warwara har lokacin da suka iso gidan Aunt Ramlah ta hanyar kwatance da Heedayah take masa, yana yin parking Heedayah tasa hannu da sauri da nufin ta bud'e k'ofar motar taji ta a rufe gam runtse ido tayi cikeda takaicin abinda guy d'in nan yake mata ta fuskanci mugun d'an tijara ne amma yanzu ita take nema dole ta kwantar da kai dan haka ta kalleshi a marairaice kafin ma tayi magana yasan abinda zata fad'a shima kuma sauri yake dan haka yayi unlocked tanajin alamun an bud'e tayi saurin bud'ewa ta fice ko godiya bata tsaya yimasa ba. Nagode nunar rana". tace tana d'an d'aga murya yadda zaijita tana fad'a ta shige gidan da sauri tana dariya, baisan ya akayi ba ya tsinci kanshi da sakin wani munafukin murmushi yana cije baki wato yarinyar nan ta maidashi wani abokin wasanta ko? ALLAH ya k'ara had'ashi da ita zatayi masa bayani ne dalla dalla wata k'aramar k'wafa ya saki yana jijjiga kanshi yabar unguwar da gudu. Tana shiga ta samu Aunt Ramlah dasu Nu'aym a falo suna kallo ita Zainab taje gida sai gobe zata dawo, sallamar datayi Aunt Ramlah ta amsa tana binta da kallo tasamu kujera ta zauna tana mata sannu da gida Aunt Ramlah ta amsa tana fad'in "Ke kuwa ina kika tsaya haka har magreebah kuma kinsan nida Abban Nu'aym bamuson kuna kaiwa dare a waje". Shiru ta d'anyi kafin ta lalubo abinda zatace "Aunt Ramlah kinsan Hajiya fa akwai labari ita ta tsareni da hira". Harara Aunt Ramlah ta jefa mata tace "Kar kiyiwa Hajiya k'arya ai munyi waya da ita tun wuri tace ta had'aki da jikanta zai kawoki gida". jin aikin gama ya riga ya gama ma baki ta tab'e tace "Wllhy Aunt Ramlah wani jikanta ne irin arrogant man d'in nan bashida dad'in sha'ani saidaya fara biyawa dani wani gida ya shiga ya dad'e yabarni cikin mota sannan ya fito muka taho". Kai kawai Aunt Ramlah ta kad'a tana fad'in "To ai saiki tashi ki shiga ciki kiyi sallah". tashin tayi ta d'auki jakarta ta wuce bedroom d'insu. ★______________★ Kwana Habeeb yayi yana tunanin su Seeyamah da yadda zai b'ullowa lamarin, dan haka yana tashi da safe bayan yayi wanka ya shirya yaje ya gaida Ummi ya fita ya nufi gidan Kawu Sulaiman inda ana ne Hajiyan take, sai daya shiga side d'in Kawu Sulaiman d'in suka gaisa dashi da matarshi Hajiya Rahma sannan ya fito ya shiga sashin Hajiya. Tana zaune taci wankanta da sabuwar atamfar ta ta kashe d'aurinta irin na tsofaffi sai k'amshin turaren wuta ne yake tashi a falon, tana ganinshi ta washe baki tana masa sannu da zuwa, waje yasamu ya zauna yana gaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar shi lafiyar su Ummi tareda yimasa tayin abin karyawa yace yayi breakfast a gida. "Hajiya nazo ne muyi wata magana dake please". zamanta ta k'ara gyarawa tace "Toh Habibu ALLAH yasa dai lafiya?". Jimm ya d'anyi kafin yace "Hajiya yarinyar nan ta jiya da kika had'ani da ita in kaita gida.....tun kafin ya k'arasa abinda zai fad'a d'in Hajiya ta wani washe baki tana fad'in "Alhmdulillah ALLAH nagode maka, ai karka damu Habibu ni d'in nan zan tsaya maka tsayin daka in shige maka gaba har sainaga tabbatuwar al'amarin nan ALLAH yasa alkhairi masha ALLAH abu yayi kyau ALLAH yasa ayi damu". Duk saiya rasa gane inda maganganun Hajiyan suka dosa ya wani had'e rai yana yatsine fuska yace "Wai me kike nufi ne Hajiya?". "A'a ban gane me nake nufiba? inace kaga yarinya kanaso kazo kanaso in shiga maganar". "OMG! tsohuwar nan kinada matsala wllhy ni na miki kama da wanda zai auri k'aramar yarinya kamar wannan haba ki daina ma wannan zancen please". Tuni Hajiya ta tamke fuska tace "Heedayahn ce yarinya? ALLAH na tuba idan a kauye ne yanzu ai Heedayah tayi wajen yara uku a'a jaririya ce k'arewar yarinta". Hajiya ta k'arasa maganar cikin fad'a tana maka masa harara, goshinshi ya d'an dafe yana murza fatar goshin yace "Nifa ba hayaniya nazo kimin ba Hajiya wata magana ce very important takawo ni akan yarinyar nan". "Ina jinka". cewar Hajiya ta wani juyar dakai gefe ita a lallai ba haka taso ba. "Inaso insan asalin yarinyar nan da abinda ya had'aku har take zuwa wajen ki?". "Duk wannan bin k'wakk'wafin na meye kuma?". Ido ya lumshe yana d'an taune lips d'inshi cikeda gajiyawa da maganar dayake tun d'azun yace "Hajiya dan ALLAH, kaina yafara ciwo saboda maganar danake tun d'azu ki taimaka please ki gayamin". Baki Hajiya ta tab'e tace "Yaron kawunka Sulaiman ne mijin yayarta kuma y'an Katsina ne can shi Muhammadun ya aurota". Kai ya shiga jijjigawa yana fad'in "Kenan y'ar Katsina ce ita d'in?". "K'warai kuwa dalilin zuwanta kuwa shine yaron dazata aura ne ya rasu ana saura sati d'aya biki ta shiga cikin matsanancin hali shiyasa yayar ta taho da ita ko zata samu sauk'in abinda take ji". "Thank you Hajiya". yace yana mik'ewa tsaye, da kallo ta bishi tana fad'in "Wai duk wad'annan tarin tambayoyin na menene saikace wani d'an jarida". Hannayenshi duka ya zube cikin aljihun wandonshi ya saki wani miskilin murmushi yace "Bazaki gane bane Hajiya, nina wuce ayi mana addu'a". daga haka yasa kai ya fice daga falon yabar Hajiya tana rakashi da kallon mamaki. Kamar ance ya waiwaya bayanshi bayan fitowarshi gidan Hajiya ya hangi wata matashiyar budurwa kamar Heedayah wadda a yanzu yakejin sunanta a bakin Hajiya zata shiga gidan Alhaji Saminu wani mak'ocin su Kawu Sulaiman ne kuma abokinshi gidaje uku ne ya raba tsakanin su da gidan Kawu Sulaiman d'in, da sauri ya juya da sassarfa ya nufi gidan saidai kafin ya k'arasa harta shige gidan. "Oh my God!". Yace yana kai hannu kanshi yana yamutsa sumar kanshi gaba d'aya ya kasa barin k'ofar gidan ya shiga sintiri a k'ofar gidan kamar d'an doka sai faman kai da kawowa yake daga k'arshe daya gaji da zaryar saiya jingina jikin wata mota daya gani a k'ofar gidan yayi crossing legs d'inshi hannayenshi duka biyun ya cusasu cikin aljihun jeans d'in dayake jikinshi, idanunshi k'urr akan k'ofar gidan yana jiran fitowarta. Jawaheer tazo aiken Mummyn tane Hajiya Saudah wadda matar Alhaji Saminun Hajiya Kareemah k'awar tace sosai a yadda Mummyn take bata labari tare sukayi school tun zamanin y'anmatancin su, to yau d'in ma wani sak'o tazo kawowa Hajiya Kareemahn. Wayace kare a kunnenta ta fito daga gidan tana amsawa, tsaye tayi daga inda take tana k'are masa kallo idan bata manta ba shine gayen nan daya tab'a tareta a ShopRite har yana mata wasu maganganu data kasa fahimtarsu a lokacin to meya kawoshi nan unguwar? koma d'an gidan ne bata saniba? koma dai waye shi ba damuwar ta bace. "I will call you back". abinda ta fad'a kenan ta kashe wayar ta nufo inda yake tsaye dan d'aukar motar ta fuskar nan tata a d'inke. Ido cikin ido suke kallon juna kowa fuska a tamke kamar wad'anda aka aikowa sak'on mutuwa, shigar jikinta yake bi da kallo yana k'ara had'e rai jeans ne pencil dark blue da farar riga body hook data matseta sai kimono ash color data d'ora akai da wani siririn ash gyale datayi rolling dashi, k'afarta sanye cikin hill shoes black color mai igiya da wata black hand bag dake mak'ale a hannunta, wato yarinyar nan RUWA BIYU ce yau tasa kayan arzik'i gobe tasa na tsiya ko jiya ma hijabi ne ai a jikinta lokacin daya d'auketa a motarshi amma dubi irin shigar datayi yau sosai ranshi ya b'aci yau saiya titsiyeta ta fad'a masa uban dayasa take wannan d'abiar dama ga haushin nunar rana data k'ara cemasa jiya bayan ya sauketa..... Afwan a k'ara hak'uri dani yanayin yadda page d'in yake zuwa ba yawa sosai harkar mai iyali sai hak'uri naji mutane dayawa na complain page d'in yana kad'an I'm so sorry👏🏻👏🏻. Sai masu bina PC suna cewa in basu book din nan daga farko dan ALLAH suyi hak'uri su dinga tambaya a group abin zaimin yawa ga typing ga turawa daga farko kuma anfara nisa mutum ba d'aya ba ba biyu ba dayawa duk da nasan k'auna ce ta kawo hakan amma dai ayi hak'uri a dinga tambaya cikin grup. Nagode. Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). Special thanks for Ameenah Abubakar, Husnah Abdullahi, Mum Elham, Haneefah S.G, Maryam kabuga, Aseeyah Buhari, Mrs Kabeer, Miss Ayshaa, Rabi'atu Musa, Maman sadeeq, Mum Farouq, Oum Anwaar. jazakumullah khair all nagode sosai da yadda kuke nunawa book din nan k'auna fatan alkhairi 💖. No 24. Cikeda b'acin rai yake kallonta harta k'araso inda yake tsaye ko motsi baiyi ba bare ya matsa daga jikin motar duk da alamu sun nuna masa motar tace tunda gashi tazo inda yake. "Excuse me". Ta fad'a cikin had'e rai bayan k'arasawar ta tana wani kad'a car key d'in dake hannunta, sam bai nuna ma yasan abinda ta fad'a d'in ba sai kallon takaici dayake binta dashi yanajin tamkar ya daddalla mata mari hakan yasa ta k'ara k'uluwa ganin irin kallon rainin dayake mata. "Wai Malam baka jine? bakaji abinda nake fad'a ba? ko kurma ne ban saniba?". Ta jero masa tambayoyin a lokaci d'aya tana wani yatsina fuska, sai a lokacin ya d'ago daga jikin motar yayi mata tsaye a gabanta ido cikin ido suke kallon juna kafin cikin b'acin rai ya fara fad'in "Meyasa ke bakida kamun kai ne? yau kiyi shigar arzik'i gobe kiyi ta tsiya why? kina tallan jikinki a waje saboda bakida hankali meyake damunki ne?". Ya k'arasa maganar yana wani zare mata ido, cikeda d'imbin mamaki take kallonshi da tunanin anya mutumin nan kanshi d'aya kuwa? to inba hakaba ina ruwanshi da ita dazai tsareta yana mata wasu maganganu marasa kai taga alamun saita kafta masa rashin mutunci sannan zai shafa mata lafiya dan haka cikin masifa tace "Kai dallah malam bansan hauka, ya zakazo ka tareni kana min wani soki burutsu a ina ka sanni? meye had'ina dakai?". Ta ida maganar tareda jan wani dogon tsaki wanda Habeeb ya jishi har tsakiyar kanshi tsabar yadda ranshi ya b'aci baisan ya akayi ba sai gani yayi ya canza musu position d'in tsayuwar tasu ita ta koma jikin motar shikuma yana tsaye a gabanta ya matseta da k'irjinshi sai huci yake idanunshi sun fara canza kala, cikeda bala'i yake fad'in "Waye mahaukaci? nace wa kike kira da mahaukaci?". Ya k'arasa maganar cikin tsawa, batare da shayin komai ba ta kalli cikin idanunshi cikin tsiwa da rashin kunya tace "An fad'a maka haka, me zakayi? ko akwai matakin da zaka d'auka ne? inba hauka ba ni ban sanka ba kazo kaita min wasu shirmen maganganu wllhy idan bakayi was......Wata wawar damk'a yayiwa bakinta wanda yasa dolenta tayi shiru ba shiri ta saki wata siririyar k'ara amma tsabar taurin kai bata daina antaya masa uwar harara ba tamkar idanunta zasu fad'o k'asa duk kuwa da irin zafin dake ratsa ta, sai daya cije baki kafin ya had'e leb'enta na sama dana k'asa ya murje da dukkan k'arfinshi ta k'ara sakin wata k'arar kuka take so tayi saboda azaba amma bazata iya kuka a gabanshi ba ai kamar ta kasa ne yaga lagonta dan haka ta shanye kukanta ta cigaba da watsa masa harara, so take ta tureshi saboda yadda kusan nasu tayi yawa gaba d'aya yayi mata rumfa ya babbake ko ina bata ganin komai sai shi d'in, a fusace yace "Bakinki yasan irin kalmar da zaki dinga fad'a a kaina Habeeb ya wuce da saninki very stupid". Hannu tasa da k'arfi ta fincike hannunshi ta yarfar dashi gefe tace "Dalla Malam sakeni, idan ka saba iskanci da y'an mata to Jawaheer tafi k'arfinka wllhy aikin banza kawai". Sunan dayaji ta fad'a ne yasa mamaki ya kamashi idan bai manta ba Heedayah yaji Hajiya ta ambata amma ita kuma wannan yaji ta ambaci wani sunan daban mai hakan yake nufi? bai ankara ba yaji ta tureshi saboda yadda ya shiga rud'ani, tsugunawa tayi ta d'auki kayan hannunta da suka watse lokacin daya fincikota. Yana gani ta bud'e motar ta shiga mamaki yasa ya kasa hasala komai bare yayi yunk'urin binta. "ALLAH ya isa mugu azzalumi". tace tana lek'o da kanta ta window'n motar kafin ta bata wuta tabar layin da gudu, tsaye yayi kawai ya kama k'ugunshi da duka hannayenshi yabi motar da kallo har zuwa lokacin da motar ta b'acewa ganinshi. "Yaa Ilahee". Ya ambaci hakan yana dafe goshinshi gami da runtse idanunshi gam g kanshi ke wani irin sarawa yana jujjuyawa wai kodai aljanu ne keson bud'e masa ido ne? Seeyamah, Heedayah again kuma wata Jawaheer daban? hakan na nufin triplets ne kenan? kokuma dai Heedayahn ce Jawaheer? gaba d'aya k'wanyar kanshi ta d'auki zafi ya rasa wane tunanin ma zaiyi. Kamar wanda aka mintsina ya zabura da sauri ya nufi gida, kai tsaye side d'inshi ya nufa yana shiga ya wuce kitchen ya d'auko swan water medium size bottle ya fito tsakiyar falon ya tsaya ya b'alle murfin robar ya kafa kai ya shiga kwankwad'ar ruwan duk da irin sanyin dayake dashi kuwa sai daya shanye shi tas sannan yayi jifa da robar ya rik'e k'ugunshi da hannu d'aya d'ayan kuma ya shiga yamutsa lallausar sumar shi mak'wallaton shi sai kai da kawo yake yana sauke numfashi idanunshi a rufe sam yayi ragon azanci daya bita yaga itakuma inane gidansu shifa yanzu yafara zargin maybe yaran nan aljanu ne suke masa yawo da hankali Seeyamah gidan marayu, Heedayah Katsina ance gidan yayarta take da zama and now Jawaheer itama anan Kano kai wannan lamari akwa mugun d'aure kai amma insha ALLAH zaibi komai step by step domin gano gaskiyar lamari, tabbas akwai wani b'oyayyen sirri inba hakaba ace yara har uku a matsayin su na triplets amma kowa da inda yake rayuwa? Wani dogon numfashi yaja ya zube bisa kujera idanunshi a rufe yayi relaxing sosai yana cije lips. Kusan mintuna biyar yana zaune a haka ko cikakken motsi bayayi har lokacin bai bud'e idanunshi ba sai sak'a da warwara yake kan ta inda ya kamata ya fara da lamarin. Bud'e k'ofar da akayi aka shigo ita tasa ya bud'e idanunshi a hankali ya kalli wanda ya shigo d'in cikakken saurayi ne kamar shi wanda zasuyi kusan sa'anni dashi shima dogo ne saidai shi yanada y'ar k'iba kad'an very handsome guy ne bashi da hasken fata sosai amma kallo d'aya zakayi masa kasan hutu yasamu gurin zama a jikinshi duba da yadda fatar jikinshi take wani shek'i da d'aukar ido. Shigar k'ananun kaya ne a jikinshi blue black d'in jeans ne da lemon green d'in riga mai gajerun hannuwa wanda hakan yaba cikakkun damatsen shi bayyana sai P.cap blue black daya d'ora a kanshi, tunda ya shigo falon shima k'amshin turarenshi ya cika ko ina ya had'e dana Habeeb wanda ke zaune har lokacin yana binshi da kallo ko motsi baiyi ba, duk da cewa yayi farin cikin ganinshi kuwa. Cikeda fara'a da murna ya k'arasa kujerar da Habeeb yake ya zauna kusa dashi. "Matsalata dakai kenan wulak'anci d'an balarabe duk lokacin da muka d'auka bamu had'u ba amma ji irin tarbar daka yimin saboda bakada mutunci". Ya fad'a yana dukan kafad'ar Habeeb d'in da tashi kafad'ar, harara ya watsa masa kafin ya tashi zaune sosai yace "Zaka iya komawa inda ka fito indai saina tashi nayi hauka nayi ihu saboda ganinka saikace wani ubana". "Halin dai yana nan yadda nasani a baya". MUHSEEN yace yana d'an tab'e baki da jijjiga kai, cikin yaren larabci Habeeb ya bashi amsa. "A'a fa karka zageni Malam muma fa munajin larabcin nan ma ismuka, aina tazhab....... kafin ya k'arasa Habeeb yasa dariya (Yaudai naga dariyar Gashua 😂). "D'an iskan abokina". ya fad'a cikin dariyar tareda kamoshi ya rungume, shima Muhseen d'in dariyar yake suka rungume juna cikin farin ciki. Muhseen d'an gidan abokin Abbu ne Alhaji Usman Shareef sun had'u ne ta harkar kasuwancin su ALLAH ya had'a jininsu, bayan kammala karatunshi dayayi lokacin daya dawo 9ja suka had'u ta silar iyayen nasu daga nan suka k'ulla abokantaka duk da Habeeb d'in ma bai bawa zumunchin nasu wani muhimmanci ba amma shikam Muhseen ya d'aukakeshi sosai kuma yana hak'urin zama dashi har a yanzu Alhaji Usman d'in bai yada suba jefi jefi yana zuwa suna gaisawa da Ummi dasu Hajiya da Kawu Sulaiman, shima dai irin Mujaheed ne bakin abin magana basa gani su k'yale dayake ta dalilin Habeeb d'in shima Mujaheed d'in sun saba dashi. shikuma engineering ya karanta yana aiki a wani babban kamfani na software a Abuja amma dayake iyayenshi y'an Kano ne yasa yake yawan zuwa sosai yanzu ma dalilin dad'ewar shi baizo ba sunje wani course ne a Italy na watanni kan abinda ya shafi aikinsu na engineer. Anan kuma hira ta b'arke tsakaninsu duk da dai duk rabinta ma Muhseen d'inne ke yinta, sun dad'e anan sannan suka tashi Habeeb yayi masa jagora zuwa part d'in Ummi dan ya gaisheta, itama tayi murna da ganinshi bayan sun gaisa suka fito compound d'in gidan sukayi sallama Muhseen ya shiga motarshi ya tafi shima Habeeb part d'inshi ya koma dan d'auko key d'in motarshi ya tafi office dama wancan banzan sai kiranshi yake a waya, duk abinnan da ake tunanin triplets na nan daram mak'ale a ranshi da tunanin samun mafita. Yammacin ranar. Danger ce ta tsaida motoci, cikin wad'anda aka tsayar d'in harda Mujaheed wanda bayan tashin shi daga wajen aiki ya biya ta wani waje, tsaki kawai yake ja yana duba agogon hannunshi saboda sauri yake yakoma gida yanada uzurin da zaiyi, kamar ance ya waiga gefenshi ya hango Aleeyu shima zaune a cikin mota yana jira a bada hannu, shifa dama ya dad'e baiga Aleeyun ba to yayi zaton ko har dashi ya kora ne abinda ya k'ara bashi mamaki bai wuce ganin yadda Habeeb yake yawan yin waya da Aleeyu ba dama gashi yana zargin Habeeb d'in akan Seeyamah hakan yasa lokacin da aka bada hannu yabi bayan Aleeyu. Tiryan tiryan ya dinga bin Aleeyu batare daya bari yagane shi yake bi ba har lokacin da suka isa unguwar ta lamid'o crescent Aleeyu ya shiga cikin unguwar shikuma Mujaheed anan bakin titi yayi parking ya fito ya dinga takawa a k'afa yana bin Aleeyu bayan ya toshe idanunshi da bak'in glass ga face mask dayasa, binshi yake yana mamakin unguwar da sukazo d'in sun tab'a zuwa da Habeeb ya nuna masa wani plat house daya siya kuma idan bai manta ba nan unguwar ne. Aleeyu bai dad'e yana tafiya ba yayi parking a k'ofar wani gida, ido Mujaheed ya zaro ganin k'ofar gidan dayayi parking d'in nan ai shine gidan da Gashua ya kawoshi d'in hakan na nufin......bai k'arasa tunanin shiba yaga Aleeyu ya fito daga cikin motar da sauri yasamu wani d'an lungu ya lab'e ya lek'o da kanshi yana kallon Aleeyu ya bud'e gidan ya shiga da wata leda mai d'auke da tambarin sunan wani gidan abinci a hannunshi, mamaki, tsoro, al'ajabi gamida d'imbin tararrabin abinda zaije ya tarar ne a cikin gidan suka sandarar dashi a tsaye a wajen kardai abinda ya dad'e yana zargi tun bayan sanarwar b'atan Seeyamah daya gani ya tabbata idan kuwa hakane me yake damun Gashua? ta ina ya kamata ya shiga gidan addu'a yake a cikin ranshi ALLAH yasa Aleeyun ya fito ko zai samu hanyar shiga yaga meye a ciki. Addu'ar shi taci kuwa dan Aleeyu bai dad'e da shiga gidan ba sai gashi ya k'ara fitowa da sauri ya k'ara lab'ewa har Aleeyun yazo ya k'ara wucewa a mota yabar layin. Cikin hanzari Mujaheed ya fito daga d'an lungun dayake ya nufi gidan, cikin sa'a kuma yana tura k'ofar gate d'in yaji ta bud'e abin mamaki, shiga yayi ya maida k'ofar ya rufe yana k'arewa gidan kallo. A hankali ya shiga takawa zuwa k'ofar babban falo na gidan itama dai yana murd'a handle d'in yaji ta a bud'e shiga yayi ya rufe yana bin ko ina na falon da kallo an k'awata ko ina yaji royal chair shi a lokacin da Habeeb d'in ma ya kawoshi ba asa komai a cikin gidan ba. Dube dube ya shiga yi ko zaiga wani abin amma ba komai hakan yasa ya maida akalar binciken nashi kan d'akunan barcin gidan na b'angaren dama nan ma duk inda ya bud'e ba abinda yake gani a ciki, d'ayan b'arin yakoma ya bud'e bedroom na farko yaga ba komai gaba yayi yasa hannu ya bud'e na biyun idanunshi suka d'auko masa hoton Seeyamah tana zaune akan gado ta tsurawa waje d'aya ido da alamu ta fad'a cikin zuzzurfan tunani, kamar ko yaushe babban hijabine a jikinta ta rufe ko ina na jikinta hatta k'afafunta ba'a ganinsu fuskar tace kawai ta bayyana. Wani mugun bugawa k'irjinshi yayi zuciyarshi tamkar zatayi tsalle ta fito tsabar tsorata da yayi da abinda idanunshi suka gani har wani jiri jiri ne yaji yana neman kada shi..... Masu buk'atar a tallata musu hajarsu zasu iya nemana ta wannan number 09139964697. Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). Jama'a bafa paid book bane anata tambaya na har nagaji da amsawa 😒 free book ne. No 25. Seeyamah ma hankalinta ta maida kan k'ofar taga wani tsaye yana kallonta ba Aleeyu bane sannan kuma ba wancan mutumin dayasa aka k'wamuso ta bane tunda shi yafi wannan d'in datake gani tsayi gashi kuma ya rufe idanunshi, sosai gabanta ya buga tafara tunanin kodai wani ne daban yazo ya cutar da ita? A hankali ya shiga takawa zuwa cikin bedroom d'in yana k'ara jin mamakin abinda yasa Gashua ya kawo wannan yarinyar gidan nan. A tsorace ta shiga ja baya kamar zatayi kuka tana kallon yadda yake k'ara kunsanto ta, yana zuwa bakin gadon ya tsuguna kan gwiwoyinsa yana cigaba da kallonta wani mugun tausayin ta na k'ara ratsashi. "Dan ALLAH karka cutar dani bawan ALLAH kayi hak'uri I'm sorry please". ta fad'a cikin rawar murya tana had'e hannayenta waje d'aya alamun rok'o idanunta duk sun cika da ruwan hawaye, gam ya runtse idanunshi cikin tsananin tausayin ta, hannu yasa ya zare glass d'in idonshi da face mask d'in fuskarshi ido ta zaro ganinshi datayi a gidan nan dan bazata tab'a mantawa da fuskar bawan ALLAHn nan ba shine yayi sanadin komawar ta gidan marayun bayan wannan ogan na Aleeyu ya koreta, duk saitaji wata nutsuwa na shigarta tana rok'on ALLAH ta sanadiyyar shi ta fita daga cikin wannan prison d'in kana ganin fuskar shi kasan mutumin kirki ne. Ganinshi yasa ta saki wani marayan kuka na tausayin kanta da halin datake ciki, da sauri ya tashi ya zauna bakin gadon kusa da ita cikin taushin murya data had'u data rarrashi yace "Please Seeyamah stop crying I'm so sorry". ya k'arasa maganar kamar shima zaiyi kukan gamida zaro wani kyakkyawan k'aramin hanky fari mai adon pink d'in flowers a jiki ya mik'a mata daga aljihunshi ya mik'a mata sai tashin k'amshi mai dad'i yake, hannu tasa ta karba ta shiga sharewa tana sharewar wasu na k'ara zubowa. "Please I'm sorry mana Seeyah, kiyi shiru ya isa haka uhmm? ko kinaso kanki yayi ciwo?". A hankali ta girgiza masa kai. "Ko so kike nima inyi kukan?". Nan ma kai ta girgiza masa "Okay yanzu ki fad'amin waye ya kawoki nan gidan kuma tun yaushe kike anan?". ya ida maganar tareda zaro wayarshi daga aljihu ya danna recording ya ajiyeta kusa dashi, cikin kuka Seeyamah take fad'in "Ba wannan abokin naka bane wanda ya tab'a korata daga gidan marayu yasa aka d'auko ni ya kawoni nan". "Why me kikayi masa?". Yace yana k'ok'arin had'iye b'acin ranshi hak'ik'a Habeeb ya bashi mamaki. "Wallahi ni bansan me nayi masa ba kawai yasa an d'aukoni yacemin wai meyasa nake bibiyar rayuwar shi kuma dole saina fad'a masa waye shi sannan zai maidani na rantse da ALLAH ban sanshi ba bansan wani abu game dashi ba ka taimakeni dan ALLAH". tayi maganar tana shirin k'ara sakin wani kukan cikin sauri yace "No no Seeyah don't cry please insha ALLAH zaki bar gidan nan kinji?". Kai ta gyad'a masa tana fad'in "Ka tafi dani yanzu dan ALLAH". Kai ya girgiza yace "Ba yanzu ba Seeyamah ki kwantar da hankalinki kinji kamar kin fita kin gama ne yanzu dai karki fad'awa kowa zuwana shima Aleeyun dayake tsaronki karki nuna masa nazo zan dawo anjima ko gobe in tafi dake relax ur self ok?". Sosai ta marairaice fuska tana kallonshi gani take tamkar idan ya riga ya tafi bazai dawoba jitake tamkar ta rik'eshi saiya tafi da ita. Murmushi ya d'an saki yace "I'm promise to u insha ALLAH karki damu". ya k'arasa maganar yana mik'ewa tsaye ya maida wayarshi cikin aljihu ya juya zai tafi. "Dan ALLAH karka k'i dawowa ka taimakeni". Mujaheed ya tsinkayi muryar Seeyamah na fad'a cikin rauni. Wani irin tausayin tane ya k'ara shigarshi ya runtse ido tsigar jikinshi na tashi a hankali ya juyo ya kalleta tareda sakar mata wani murmushin yak'e cikin k'asa k'asa da murya yace "I'll promise insha ALLAH". daga nan bai saurari abinda zatace ba ya fice da sauri zuciyarshi na bugawa. Yana fita Seeyamah ta k'ara sakin wani kukan ta cusa kanta tsakanin gwiwarta tana rizgar kukanta gani take tamkar shikenan Mujaheed ya tafi bazai dawoba. Ya dad'e sosai zaune a cikin motarshi ya kwantar da kanshi kan seat d'in motar idanunshi a rufe har lokacin bai gama dawowa daga rud'ani da d'imbin mamakin abinda yasa Gashua ya gark'ame Seeyamah ba me yake nema a duniyar nan? meye ubangiji baiyi masa ba da har zaiyi garkuwa da yarinya, yarinyar ma ta gidan marayu wadda idan ba'a tausaya mata ba ai ba'a cutar da ita ba, tsaki yaja a karo na ba adadi yana tunanin ta ina zai fara yanzu? bazai tab'a bari Gashua yayi abinda ranshi yakeso ba saiya gane kuskuren shi anya ba police kawai zaije yayi k'arar Gashua ba? da sauri ya girgiza kai a fili ya furta "No impossible, to kodai Habeeb zai samu da maganar nan ma kai ya girgiza yasan Gashua farin sani kamar yunwar cikinshi yanzu yana iya yayi masa maganar ya nuna sam baisan ma wani abu makamancin wannan ba ko ya nuna yayi d'in ya d'auki matakin da duk yake ganin zai d'auka dan haka ma bazai yimasa maganar ba Ummi kawai ya kamata ya samu ba wani zancen ya rufa masa asiri yayi ba daidai ba yanaso kuma har cikin ranshi yaji ba daidai d'in yayi ba a nuna masa kuskuren shi, sosai ya aminta da shawarar da zuciyarshi ta bashi hundred percent dan haka cikin hanzari ya tada motar kai tsaye ya nufi gidansu Habeeb wajen Ummi. ★_____________★ Shiru falon ya d'auka bakajin komai sai k'arar air conditioner dake d'akin bayan Ummi ta gama saurarar abinda Mujaheed yaje mata dashi ya kuma kunna mata recording d'in dayayi da abinda Seeyamah take fad'a, ba k'aramin rud'ani da tashin hankali Ummi ta shiga ba a lokacin ta shiga b'acin rai fiye da tunanin mai karatu abin ya tab'ata fiye da tsammani d'anta na cikinta wanda ta haifa shine yayi kidnapping me yake nema a rayuwar nan? wane mataki ne bai taka ba a rayuwar shi? jikinta har rawa yake ta d'auki wayarta ta lalubo number Habeeb d'in ta danna masa kira sai sauke numfashi take sama sama fuskarta tayi jawur saboda b'acin rai, Mujaheed kanshi saiyaji dama baizo mata da maganar ba amma kuma hakan shine daidai bai kamata ya rufe maganar ba bawai dan bayason Habeeb d'in ba kokuma yanaso ranshi ya b'aci bane hasalima yana matuk'ar gudun b'acin ran Habeeb kuma har a yanzun yanaji baiyi wani abu wanda ba daidai ba. Habeeb na d'aga kiran Ummi tace yazo tana nemanshi duk inda yake kuma duk abinda yake ya bari yazo, sam bata saurari tambayar dayake mata ba na lafiya kuwa meyake faruwa ta kashe wayarta ta ajiyeta gefe sai gaman girgiza k'afa take tana huci. Nan suka cigaba da zama ita da Mujaheed ba wanda ya k'ara yin wata magana, ko cikakkun mintuna goma ba'a rufa ba Habeeb ya shigo cikin falon kamar ko yaushe sallama a ciki ciki, Mujaheed nema kawai ya amsa sallamar Ummi kam wani irin mugun kallo tabi Habeeb dashi wanda take yasha jinin jikinshi gabanshi ya fad'i, ido suka had'a da Mujaheed ya wurga masa wani kallo duk da baisan ainihin abinda yake faruwa ba. Gefen Mujaheed ya zauna kusa da k'afafun Ummi yana saurarar abinda Ummin zatace, hannu ta mik'awa Mujaheed sanin abinda take nufi yasa ya d'ora mata wayar akan hannunta bayan ya cire pattern, play ta danna sannan ta mik'awa Habeeb wayar kallonta yayi cikin rashin fahimta tsawar data daka masa ne da kuma muryar yarinya dayaji tana magana tana kuka yasa yayi hanzarin karb'a. Ido ya d'an zaro jin abinda yarinyar take fad'a gabanshi yayi wata irin bugawa ba shiri ya mik'e tsaye yana bin Mujaheed da wani irin mugun kallo shima Mujaheed d'in k'yar yake kallon Habeeb d'in ba tareda shayin komai ba. Tsaye Ummi ta mik'e ta tsaya a gaban Habeeb tana binshi da wani tuhumammen kallo cikin rawar murya Ummi tace "Abbuna meka aikata haka? me kakeso ka zama ne? me kake nema a rayuwar ka da har saikayi garkuwa da mutane? nace me kake nema?". ta k'arasa maganar cikin tsawa tareda sakar masa wani mahaukacin mari a kuncinsa na dama kafin ya dawo daga tsananin rud'ani da mamakin daya shiga na marin da Ummin tayi masa ta k'ara bashi wani marin a kumatunshi na hagu, da sauri Mujaheed ya taso ya rik'e hannun Ummi lokacin datake niyyar k'ara kai masa wani marin. "Dan ALLAH Ummi kiyi hak'uri ki zauna dashi kuyi magana ta fahimta kiji dalilin shi na d'aukar yarinyar please Ummi I'm sorry". "Har wani dalili yake dashi dan ubanshi dazai d'auke yarinyar jama'a? ka sani idan har wani abu yasamu yarinyar mutane ALLAH bazai tab'a barinka ba shashasha sakarai saikuma ta canza harshe cikin yaren larabci ta shiga zazzagawa Habeeb fad'a ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, Habeeb dai yana tsaye tamkar wanda aka dasa kanshi a k'asa idanunshi har wasu ruwa suka tara tsabar bala'in dake cinshi duk wannan fad'an da Ummi take sama sama yake jinta kawai yana kissima yadda zaici uban Aleeyu dashi kanshi Mujaheed d'in tunda munafuki ne shi ta yaya har ya gano Seeyamah tana wajenshi? koda yake ba laifinshi bane duk laifin Aleeyu ne da baiyi sakaci ba da duk haka bata faru ba zai nuna masa waye HABEEB GASHUA. Mayafin doguwar rigar dake jikinta Ummi ta gyara ta cewa Mujaheed suje ya kaita wajen yarinyar, tun kafin taga yarinyar tausayin ta ya kamata kuma take taci burin insha ALLAH tabar gidan marayun kenan ita zata d'auke ta tadawo hannunta da zama zata zame mata uwa uba zatayi mata gatan da zatayiwa d'an data haifa a cikinta. Fita sukayi suka barshi nan tsaye har lokacin bai d'ago kanshi ba ajiyar zuciya kawai yake saukewa ta b'acin rai idanunshi sun kad'a sunyi jawur jijiyoyin kanshi duk sun fito rad'a rad'a dasu, suna fita Mujaheed ya dawo falon kusa da Habeeb yaje ya tsaya yace "Kayi hak'uri abokina banyi haka dan in b'ata maka raiba kokuma dan in had'aka da Ummi ba hakan danayi shine daidai I'm so sorry Ummi tace kazo mutafi tare". bai jira amsawar shiba yayi hanyar fita dan yasan idan zai kwana yana masa magana a lokacin dai bazai tankashi ba gari banza ma anyi magana ya share mutum bare yanzu da ranshi yake a b'ace? ai sai abinda mutum yagani kawai. Sai a lokacin Habeeb ya d'ago kai yabi bayan Mujaheed da wani irin kallo na tsabar takaici jiyake tamkar yayi masa d'iban karan mahaukaciya wllhy sai yaci ubanshi badai shi yayiwa haka ba? k'wafa ya saki da k'arfi yana jijjiga kai gamida cije baki, da k'arfi yake takawa kamar zai tashi sama ya fita daga falon.... Alhmdulillah nasamu sauk'i ku tayani addu'ar ALLAH yasa kar ya dawo tunda akayi cikon dai har yanzu bai k'ara tashi ba ALLAH yasa ya tafi kenan nagode sosai da addu'oen ku a gareni sakallahu khayran💔. Yaudai Gashua ansha maruka😝 fuskar zata k'ara nuna yanzun😂. Wasu zasuce Mujaheed bai kyauta ba nidai yamin daidai aradu ko nice haka zanyi masa😄 Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 09139964697. *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 26. Yana fita yaga Ummi da Mujaheed har sun shiga motar da ake kai Ummi unguwa ƙatuwar Jeef ce black color sai walƙiya take, bai nufi inda suke ba saiya nufi inda yayi parking ɗin tashi motar a fusace ya buɗe ya shiga yana shirin tada ita yaga Mujaheed ya fito daga ya nufo inda yake, so yayi ya figi motar tashi yabar gidan sai kuma ya fasa ya cigaba da kallon Mujaheed ɗin ya fito ya lakaɗa masa dukan tsiya. Glass ɗin motar Mujaheed ya ƙwanƙwasa bayan isowar shi sai daya mula sannan ya zuge glass ɗin tareda watsawa Mujaheed wani banzan kallo, cikin matse dariya Mujaheed yace “Ummi tace ka fito mu tafi gaba ɗaya”. Banza Habeeb yayi masa ya ƙara cewa “Wai bakaji abinda nace bane Gashua?”. A fusace ya ɗago ya kalleshi cikin kufula yace "Na rantse idan baka ƙyaleni ba zan take ka da mota a wajen nan". Ido Mujaheed ya zaro sosai yayi baya da sauri yana ɗage hannaye sama cikin son bada haushi yace "Innalillahi! bayan kidnapping ɗin kisan kai zaka fara Gashua?". Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare maƙwogwaron Habeeb saidai bai tankawa Mujaheed ɗin ba dan yana tarashi ne wllhy saiyaci uwarshi tunda munafuki ne shi, fitowa yayi daga motar bammm ya maida murfin ƙofar da uban ƙarfi ya nufi inda Ummi take Mujaheed ya rufa masa baya yana masa dariya. Front seat ya buɗe ya shiga Mujaheed kuma ya shiga driver seat bayan ƙarasowar shi ya tada motar suka fita daga gidan. Tunda suka tafi ba wanda yayi magana kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarshi jefi jefi Mujaheed ke juyowa ya kalli Habeeb so yake yayi tsokana amma ganin Ummi a wajen kuma bata cikin yanayi mai daɗi yasa yaja bakinshi ya tsuke, shima Habeeb ɗin dayaga hakan kawai saiya kwantar da kanshi bayan kujera ya rufe idanunsa dan zai iya kaiwa Mujaheed ɗin naushi batare daya sani ba. Parking sukayi a ƙofar gidan Mujaheed da Ummi suka fito daga motar shikam gogan naku yasani sarai anzo amma ko motsi yaƙi yi yayi bakam dashi, Ummi ce ta buɗe side ɗin dayake da larabci ta shiga yimasa cikin faɗa kamar zata dakeshi ba shiri ya fito yana wani kumbura fuska kamar zaiyi kuka, gaba Ummi ta tasa shi tabi bayanshi shi dama Mujaheed tuni yana bakin ƙofar yana knocking da alamu Aleeyun yana ciki. Ba'a daɗe ba sukaji muryar Aleeyu yana tambayar waye? shiru akayi ba wanda yayi magana sai Ummi ce data kalli Habeeb wanda ya gane ma'anar kallon datayi masa dan haka murya ƙasa ƙasa irin wanda aka takurawa ɗin nan ya amsawa Aleeyu daya buɗe ƙofar shine. Mamaki ne ya cika Aleeyu yasan ko lokacin dayake ɗan yawan zuwa gidan farko farkon kawo Seeyamah kenan baya masa knocking saidai ya kirashi a waya yazo ya buɗe masa, bai damu ba kuma bai kawo komai cikin ranshi ba dan yasan halin ubangidan nashi bauɗaɗɗen mutum ne da ba'a gane gabanshi bare bayanshi yau kuma ra'ayin knocking ɗin yayi dan haka kai tsaye ya buɗe ƙofar yayi tozali da Habeeb ɗin tsaye bakin ƙofar ya soke hannayenshi cikin aljihun wandonshi yana binshi da wani matsiyacin kallo mai hautsina zuciyar duk wanda akayiwa, wata faɗuwar gaba ce ta sameshi lokaci ɗaya musamman mutanen daya hanga a bayan Habeeb ɗin da sauri ya kauce yabasu hanya suka shiga yana gaida Ummi amma sam bata kulashi ba ta shige ciki suka rufa mata baya banda faɗuwa ba abinda gaban Aleeyu yake shikenan yasan yau yarasa aikinsa tun daga irin kallon da oga Habeeb ke jifanshi dashi daga ni ba sauƙi, Mujaheed ne ya yiwa Ummi jagora zuwa ɗakin da Seeyamah take Habeeb kam daga falo ya coge yayi tsaye tamkar wani dogari har lokacin bai cire hannayenshi daga cikin aljihun wandonshi ba, Aleeyu dayake duk a tsorace ya buɗe baki zaiyi magana kenan Habeeb ya jefeshi da wani irin kallo cikin tsawa yace "Stop it! idan ka sake ka furta kalma ɗaya a nan zan baka mamaki Aleeyu very stupid". Dole tasa Aleeyu yaja bakinshi ya tsuke ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana jiran jin abinda zai biyo baya yasan dai ya riga ya rasa aikinsa duk da dai baisan laifin dayayi ba tunda har lokacin baisan cewa Mujaheed yazo gidan ba kawai dai yayi tsammanin gano shi ɗin da akayi ya ɗauke yarinyar ne ya ɓata masa rai haka. Tana zaune daga ƙasan gadon kan rug ɗin dake shimfiɗe a ƙasa ta cusa kanta tsakanin gwiwoyinta duk da dai ba kuka take ba, jin an buɗe ƙofa an shigo yasa ta ɗago kanta da sauri ta kalli bakin ƙofar tayi arba da Mujaheed da kuma wata mata wadda kallo ɗaya tayi mata taga tsantsar kamannin su da wanda ya ƙwamuso ta, tsaye ta miƙe da sauri tana cigaba da kallonsu har suka ƙaraso inda take hannuwanta Ummi ta riƙo suka tsirawa juna ido kafin Ummi ta janyota jikinta ta rungume ta tsam a jikinta tamkar ta santa, wani irin kuka Seeyamah ta saki wanda tun farkon zuwanta gidan rabon datayi irin shi. Patting ɗin bayanta Ummi ta shiga yi cikin tsananin tausayinta lokaci ɗaya wata soyayyar yarinyar da ƙaunarta na ratsata, Mujaheed yana gefe sai kallonsu yake yana murmushi cikin farin ciki. Ɗago ta Ummi tayi tasa hannu tana share mata hawaye da faɗin "I'm sorry daga yau kukan ki ya ƙare yarinya kisa a ranki kin samu UWA nikuma daga yau na samu ƳA insha ALLAH muna tare har abada". Wani kukan ne ya ƙara tahowa Seeyamah ta ƙara faɗawa jikin Ummi tana kukan, murmushi Ummi tayi ta kalli Mujaheed tace "Mujaheed mu tafi kasan orphanage house ɗin ko?". "Eh Ummi na sani". Mujaheed ya bata amsa "Okay let's go". tace tana maida Seeyamah gefenta na dama ta rungume ta Mujaheed yayi gaba sukabi bayansa Seeyamah na maƙale jikin Ummi kamar wani zai rabasu. Har lokacin Habeeb da Aleeyu na tsaye cikin falon su Ummi suka fito, sosai gaban Seeyamah ya faɗi lokacin data ga Habeeb dan batayi tsammanin tare suke ba a tsorace ta ƙara shigewa jikin Ummi shi kuma ya bita da wani mugun kallo wanda yasa ta ƙara tsorata tayi hanzarin sadda kanta ƙasa, har sukaje bakin ƙofar fita daga falon Habeeb bai biyosu ba kuma bashida niyyar biyo ɗin jira yake su Ummi su fita ya yiwa Aleeyu rashin mutunci juyowa Ummi tayi ta kalleshi sai data harareshi kafin cikin faɗa tace "Tsayuwar me kake a nan?". Baice komai ba ya nufi ƙofa, kallon Aleeyu tayi wanda tun ɗazu ya kasa ɗagowa ya haɗa ido da kowa Ummi tace "Kaima mai tayashi ɗin ba tsayawa zakayi ba tahowa zakayi mu tafi tare muji dalilin dayasa kuka aikatawa baiwar ALLAH wannan abin kai da maigidan naka". Bata saurari cewar shi ba ta fice Aleeyu yabi bayanta jikinsa duk a sanyaye. Mujaheed ne mai driving ɗin Habeeb na gefenshi sai cika yake yana batsewa fuskar nan tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa ba alamun rahma sam, Mujaheed yana so yayi dariya yana tsoro dan yasan wllhy a yadda yake ɗin nan tsaf zai iya kai masa duka shi yadda ya haɗe ran nema ya bashi dariya. Ummi, Seeyamah da Aleeyu sune zaune a back seat Seeyamah ta kwantar da kanta kan kafaɗar Ummi jefi jefi tana sakin ajiyar zuciya motar shiru ko tari ba wanda yayi a ciki kowa da saƙe saƙen dayake a ransa da haka har suka ƙarasa orphanage house ɗin su Seeyamah, kallo ɗaya zaka yiwa Seeyamah ka hango zallar farin ciki da murnar datake ciki wanda har ya bayyana kan kyakkyawar fuskarta sai murmushi take saki ba tareda ita kanta tasan tanayi ɗin ba. Tunda mutanen gidan suka ƙyalla ido sukaga Seeyamah gidan ya ruɗe ya kacame da murna da ƙyar suka yakice wani daga cikin ƴan gidan marayun yayi musu iso zuwa babban office ɗin gidan, gaba ɗayansu suka shiga nan da nan aka sanar da dawowar Seeyamah sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci office ɗin ya cika da mutane maza da mata kowa cikeda farin ciki da murnar ganin Seeyamah ta dawo cikin ƙoshin lafiya ba abinda ya sameta. Bayan ƴan gaishe gaishe da akayi da Ummi da sauran mutanen ɗakin sannan Ummi ta fara rattabo musu yadda al'amarin ya kasance tayi da hausa ta haɗa da turanci saboda yanayin hausar tata. Tashi tayi ta nufi inda Habeeb yake tsaye tun shigowar su yaƙi zama ma gaba ɗaya sai faman muzurai yake daga tsaye saikace soja, hannunsa ta kamo ta kaishi har gaban shugaban gidan marayun Alhaji Abubakar Imam ta damƙa hannun Habeeb ɗin a na Alhaji Abubakar Imam ɗin tace "Wannan ɗana ne dana haifa da cikina kuma a yanzu zan damƙa muku shi a hannunku kuna da damar da zaku kai ƙarar shi gaba abi muku haƙƙin ku a kanshi nidai na fita duk hukuncin da kuka yanke daidai ne". Kowa baki ya buɗe cikin ofishin cikeda mamakin karamci da dattaku irin na matar nan lallai su Ummi basuda yawa a zamanin nan, Habeeb kam wani ƙululun abune ya tokare masa ƙirjinsa ganin abinda Ummi take masa tamkar bata sonsa huci kawai yake fitarwa yana ɗan lumshe ido tsabar yadda ranshi ya ɓaci. Murmushi Alhaji Abubakar yayi yace "Naji daɗi sosai Hajiya kuma samun irinku a wannan zamanin da gaskiya tayi ƙaranci sai an tona madalla da samun uwa kamar ki wannan abu da kikayi yasa naji na yafewa yaronki tunda alhmdulillah Seeyamah ta dawo hannunmu cikin ƙoshin lafiya ba abinda ya sameta babban burin mu kenan kulawa da amanar da ALLAH ya bamu mun gode sosai ALLAH ya saka da alkhairi". Kai Ummi ta kaɗa tana murmushi tace "Jazakallah khair nagode sosai nima sai abu na gaba inaso insa hannu zan ɗauki Seeyamah daga gidan nan daga yau nayi alƙawarin bazata ƙara kukan rashin mahaifa ba insha ALLAH kun yarda zaku bani?". Kabbara ƴan ɗakin suka ɗauka cikeda farin ciki. "Masha ALLAH masha ALLAH, ubangiji ya faranta miki kamar yadda kika faranta mana mun gode sosai ALLAH ya ƙara girma da sutura yayiwa zuri'ar ki albarka". maganganun da suka dinga tashi kenan cikin office ɗin kowa yana yiwa Ummi addu'ar gamawa lafiya. "Zo nan ƴata". Ummi tace fuskarta ɗauke da mayalwacin murmushi tareda miƙawa Seeyamah hannu, cikin sassarfa Seeyamah ta taho ta faɗa jikin Ummin tana sakin wani kuka mai taɓa zuciyar mai sauraro cikin shashsheƙar kuka Seeyamah tace "Nagode Hajiya". Ɗagota Ummi tayi ta girgiza mata kai tana murmushi tace "Daga yau da sunan uwa zaki kirani sunan da kowane ɗa yake kiran mahaifiyarsa dashi ki kirani da Ummi kamar yadda yarana na cikina suke kirana dashi". "Nagode UMMI". Seeyamah tace cikin wani kukan tana ƙara faɗawa jikin Ummi ta matseta tsam itama tana goge ƙwallar data taho mata, duk ɗakin saiya rikice kowa ka gani fuskar shi ɗauke da murmushi na jin daɗi. Ogah Habeeb kam yana tsaye ba wanda ya ƙara bi ta kanshi, shikenan yanzu yarinyar nan ta koma gidansu da zama? wani irin kallo zata dinga yimasa kenan? shidai angama dashi kawai.... Manage please👏🏻 Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 27. Wata takarda aka bawa Ummi tayi signing bayan sun ƙara tattaunawa tsakanin Ummi da Alhaji Abubakar Imam daga nan aka rakosu har bakin motar su sukayi musu sallama, suna ta ƙara jaddada godiyarsu ga Ummi, rungume juna Seeyamah da aminanta Fadeelah da Khairat sukayi suna kukan rabuwa sosai suke jin rabuwar da zasuyi tana taɓa zuciyar su tun suna yara suke tare a yadda suka samu labari ma kusan rana ɗaya aka kawo su gidan sunyi matuƙar shaƙuwa tare suke yin komai ba abinda yake rabasu gashi yau rana ɗaya za'a rabasu, Ummi ce ta ƙarasa wajen cikin tausaya wa take rarrashin su da faɗin sunada damar zuwa a duk lokacin da suka so ganinta suje gidan ƙofar ta a buɗe take, da rarrashi dai da ban baki tasamu sukayi shiru. Duk abin nan da ake Habeeb yana kallon su ta cikin glass ɗin motar dan tun fitowar su ya shige mota ba tareda daya kula kowa ba, ta ciki yake kallon kowa ɗaiɗai yana ayyana abubuwa da dama a cikin ranshi. Idanu ya lumshe yana sakin tsaki lokacin dayaga Ummi tana rarrashin su Seeyamah har yanzu abinda ya faru bai daina ɗaure masa kai ba daki daki yake tuno komai daga lokacin dayasa aka ɗauke yarinyar da zaman datayi a gidan shi ƙarƙashin kulawar Aleeyu zuwa yanzu da komai ya bayyana har gashi Ummi ta ɗauki nauyin kulawa da ita a yanzu, numfashi ya sauke mai nauyi yana ƙara jan wani tsakin ganin har lokacin ba wanda yazo ya shiga motar da niyyar tafiya ya rasa me suke tattaunawa tun ɗazu haka, da zaman ya ishe shi saiya zaro wayarshi daga aljihu ya shiga latse latse. Sai zuwa can sannan su Ummi suka shigo motar bai kula kowa ba kamar yadda ba wanda ya kulashi, sai bayan sun hau kan titi ne ya kula akwai wata ƙaramar mota dake bin bayansu ko tantama bayayi daga gidan marayun ne aka biyo bayan su dan aga mazaunin Seeyamahn a yanzu, ƙarfi da yaji dai Ummi ta ƙara musu yawan ƴan gidan. Suna yin parking ya fice daga motar ya nufi side ɗinshi Mujaheed yaso yabi bayan shi yayi masa magana Ummi ta dakatar dashi. Har cikin gidan Ummi tayi musu jagora suka shiga daga nan suka ɗan ƙara tattaunawa tareda ƙara damƙa amanar Seeyamah a hannun Ummi ta ƙara jaddada musu ta karɓa da hannu bibbiyu saidai fatan ALLAH ya tayata ruƙo. Daga nan sukayi mata sallama har cikin compound ɗin inda motar su take Ummi ta rakosu har suka tada motar suka fita daga gidan su Ummi na tsaye itada Mujaheed da Seeyamah da itama tayi musu rakiya. Sam Ummi bata lura da Aleeyu dake cikin compound ɗin ba sai lokacin da suke shirin komawa cikin gidan, yana tsaye kusa da wata fulawa kanshi a sunkuye tunanin shi ɗaya haɗuwa da Habeeb shikenan yasan ƙarshen aikinsa yazo gashi da shine yake taimakawa iyayenshi da ƴan uwansa saboda shi kansa ya sani Habeeb yana masa biya mai kyau kuɗin dayake bashi yafi na aikinsa Habeeb mai yawan alkhairi ne hakan yasa yake jin daɗin aiki dashi kuma yake samun abinda zai taimakawa iyayenshi a wadace, yayi karatu sosai inda har yayi degree ɗinshi na "Mujaheed kira min yaron can". Ummi tace tana kallon Mujaheed, amsawa yayi sannan ya nufi inda Aleeyu yake tsaye har ya ƙarasa bai sani ba sai daya dafa kafaɗarshi sannan ya zabura ya kalli wanda ya taɓa shi ɗin yaga Mujaheed ne tsaye duk sai yaji kunya ta kamashi dukansu kunyar su yake ji a halin yanzu. "Barka dai yallaɓai". yayi maganar a rarrabe yana ƙara yin ƙasa da kanshi. "Barka dai, muje Ummi tana son ganinka". Mujaheed yace yana yin gaba ba tare daya tsaya jin amsar shiba, shikenan ta faru ta ƙare Aleeyu ya ayyana cikin ranshi yana bin bayan Mujaheed. Rissinawa yayi yana gaida Ummi bayan ƙarasawar su amsawa Ummi tayi ba yabo ba fallasa tana ƙare masa kallo a girme ma zai girmewa Habeeb amma saboda yanada kuɗi ya zama shine babban sai abinda yace masa yake aiwatarwa, sai data gyara tsayuwar ta sannan tace "Yanzu yaro abinda kayi ka aikata daidai kenan? meyasa ka biyewa sakarcin Abbuna kuka aikata wannan mummunan aikin? a shekarun ka kaine ya kamata ace ka saitashi a hanya idan kaga yana shirin yin ba daidai ba 'Kutt bala'i Gashuan ne zai yarda Aleeyu ya shiga sha'anin shi har yayi masa gyara? ai koni sai nayi da gaske sai anci uban juna kafin a daidaita dama ni kaɗai ne nake ɗan iyawa dashi'. Mujaheed ne yayi maganar cikin zuciyarshi yana kaɗa kai wani murmushi na suɓuce masa kan fuskarsa cigaba Ummi tayi da faɗin "Kun taɓa tunanin halin da kuka jefata itada ƴan uwanta wani irin tashin hankali suka shiga kun taɓa tunanin wannan? kai kawai Aleeyu yake jijjigawa yana ƙara yin dana sani kan abinda ya aikata. "Ayi haƙuri Hajiya nayi nasan nayi ba daidai ba ayi min afwah insha ALLAH hakan bazata ƙara faruwa ba". Wani nannauyan numfashi Ummi ta sauke kafin tace "Shikenan ya wuce ALLAH ya yafe mana gaba ɗaya a kiyaye dan ALLAH a dinga kuma auna abu a mizanin hankali kafin a aiwatar dashi". "Insha ALLAH Hajiya nagode sosai ALLAH ya saka da alkhairi ya ƙara girma". Duk da Ameen suka amsa Ummi tace "Bayan wannan aikin da kake a ƙarƙashin Abbuna akwai wani aiki daban dakake yine?". Kai Aleeyu ya girgiza yace "Bana yin komai Hajiya kasancewar ogah mai yawan alkhairi ne koyaushe cikin miƙawa yake hakan yasa banyi yunƙurin neman wani aikin ba tunda abinda yake biyana dashi yana isata harkokin rayuwarta". "To daga yau zaka bar aiki a ƙarƙashin shi.....ido Aleeyu ya runtse cikin faɗuwar gaba dama yasan sai anyi haka "Meye matakin karatun ka?". yaji Ummi ta tambaye shi, idanunsa ya buɗe yace "Nayi har degree biyu duk akan business na nemi aiki ban samuba hakan yasa lokacin dana samu labarin mai kamfanin H.I.A GASHUA yana neman ma'aikata wanda zasu zama bodyguard ɗinshi nazo kuma cikin sa'a nasamu aikin". Kai Ummi ta jinjina tace "Shikenan zamuyi magana da Alhaji Sulaiman kawun yaran nan ya saka cikin harkar kasuwancin amma yanzu dai kaje gida ka ƙyale Abbuna". Sosai Aleeyu ya shiga zuba godiya a wajen Ummi dayi mata addu'a, har suka suka bar wajen itada Seeyamah, Mujaheed ya dafa kafaɗarshi yana faɗin "Ya isa haka Malam Aleeyu yanzu dai muje kabawa Boss ɗin naka haƙuri yau an haɗa masa zafi dayawa". "Anya yallaɓai zan iya tunkarar ogah a yanzu kuwa?". cewar Aleeyu. "Ba damuwa muje gara ayita a ƙare ai yadda kasan kuturu haka yake wajen zuciya shegen". Dariya ce ta kufcewa Aleeyu shima Mujaheed ɗin dariyar yayi yana nufar part ɗin Habeeb Aleeyu ya mara masa baya. Kamar koyaushe falon banda sanyi ba abinda yake fitarwa ya ƙure A.C sai bankawa kanshi sanyi yake, can suka hangoshi kan kujera ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya sai girgizasu yake sarai yaji an shigo ɗin amma yaƙi ɗagowa yaga waye duk da dai yasan bazai wuce Mujaheed ba. Ƙarasawa inda yake sukayi Mujaheed ya zauna kusa dashi Aleeyu kuma gefe yasamu ya zauna kan tattausan carpet ɗin dake malale a wajen. "Ranka ya daɗe ga Aleeyu nan na kawo zai baka haƙuri bisa sakaci dayayi na amanar daka damƙa masa har Mujaheed yayi nasarar shiga gidan yaga abinda ake ɓoyewa a ciki". Mujaheed yayi maganar yana ƙunshe dariyar dake cinsa. "I'm so sorry Boss banyi hakan dan na ɓata maka ba forgive me dan ALLAH". Aleeyu yace yana haɗe hannayen shi guri ɗaya alamun roƙo. "Get out from my room". yace yana wani lumshe ido na ɓacin rai. "Dan ALLAH ka......."I said get out". Habeeb ya katse Aleeyu cikin tsawa wanda dole tasa Aleeyun yaja bakinshi ya tsuke. "Kaga Aleeyu tashi kaje abinka rabu dashi ni banga ma laifin dakayi ba da har kake ta wani binshi kana bashi haƙuri ya daɗe bai haƙuran ba dan ubanshi tashi kaje". tashi Aleeyu yayi ya fita daga falon bayan ya yiwa Mujaheed sallama yana ta mamakin yadda Mujaheed ɗin yake zagin Habeeb ɗin kai tsaye batare da wani shayin komai ba. Baki Mujaheed ya buɗe zaiyi magana a fusace Habeeb yace "Ka sake kai min magana ubanka zanci wllhy ɗan iska mara mutunci". ya ƙarasa maganar yana komawa bayan kujerar yayi relaxing yana cigaba da kaɗa ƙafa sai huci yake yana cije baki, baki Mujaheed ya hangame yana kallonshi kafin yayi murmushi yace "Duk naji na kuma gode da zagin da kayi min amma ka sani Gashua banyi hakan dan in ɓata maka ba nayi hakane dan in ceto ka daga halakar dakake shirin faɗawa a ciki I'm sorry to say kai......."Dan zaka faɗawa Ummi? meyasa ka sakota cikin maganar? meyasa bazaka sameni muyi magana dakai ba kasa mahaifiyata tana fushi dani why Mujaheed?". duk sai Mujaheed ɗin yaji jikinsa yayi sanyi amma har a lokacin baiji wai abinda yayi ba daidai bane yanzu ba gashi ta sanadin hakan ba Ummi ɗauki yarinyar, murmushi ya ɗan saki kafin yace "Gashua bakada fahimtar da zamu zauna muyi magana dakai ta fahimta a tsakanina dakai kai ɗin wani irin mutum ne mai wuyar sha'ani wanda ake rasa gane hagunshi da damanshi dole tasa na samu Ummi da maganar saboda kai ɗin ba zaka fahimce ni ba....."Kazo ka sameni dan muyi magana kaga naƙi fahimtar ka? maganar banza kawai kake". ya katse Mujaheed a fusace, dariya Mujaheed yayi yace "Haba ɗan balarabe yau nafara saninka? kokuma yau nafara zama dakai? Ummi ce kawai zance zata fini sanin halayyar ka saboda ita takawo ka duniyar close the chapter now tambaya ɗaya gareni yanzu meyasa ka ɗauke Seeyamah wane laifi tayi maka? a ina ma ka santa da har tayi maka laifin da zaka yanke mata irin wannan hukuncin? Please answer me". Wani banzan kallo Habeeb ya jefa masa yace "Zaka iya shaƙeni sai in faɗa maka mara mutunci". sosai Mujaheed ya ƙyalƙyale da dariya yace "Kaji ba in ance maka bauɗaɗɗen mutum kace ba haka ba any way nidai nayi abinda ya dace kar ALLAH yasa ka faɗa min abinda ya haɗaku muna zaune a shararren waje zamuji koma menene I'm sorry fa da marukan da Ummi ta daddalla maka ta sanadina ga fuskar nan har yanzu bata washe ba wllhy ta ƙara ja sos.....hannu Habeeb ya dunƙule yana miƙewa tsaye da niyyar kaiwa Mujaheed dukan da saiya kusa sumar dashi ganin haka yasa Mujaheed ɗin yayi hanzarin tashi yabar falon da gudu yana dariya. Tsaye Habeeb yayi yabi bayan Mujaheed ɗin da kallo, Mujaheed yana masa abinda yaga dama ba wanda yake faɗa masa magana son ranshi irin Mujaheed saikuma Muhseen daya biyo bayanshi. Juyawa yayi ya shiga bedroom ɗinshi ya cire kayan jikinsa ya shiga bathroom, yana tsaye saitin shower ruwa na tsiyaya a jikinshi ya zama dole yazo yafara bincike kan yaran nan dayake tunanin su ɗin triplets ne.... Afwan da kaɗan👏🏻. Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 28. Duk abinda ake sam Neehlah batada masaniya kwananta biyu bata gidan tana gidan Aunt Mashhoodah data damu Ummi da waya tana roƙon ta Neehlah taje ta mata ko kwana biyu ne sai a yau ne ranar da Seeyamah tadawo gidan itama daf da magreebah driver'n Aunt Mashhoodahn yadawo da ita, lokacin Ummi da Seeyamah na zaune a falo Ummi na ɗan bata tarihinsu a taƙaice tareda nuna mata ta saki jikinta duk abinda takeso tayi magana. "Oyoyo Umminah nadawo". muryar Neehlah ta karaɗe falon tun kafin shigowar ta, murmushi kawai Ummi tayi tareda girgiza kai itama Seeyamahn murmushin tayi tasamu labarin ta yanzun nan a wajen Ummi, tsaye tayi tana bin Seeyamah da kallo bayan ta shigo falon tana tunanin abinda ya kawo Jawaheer Mansoor Jiƙamshi gidansu to wajen Ummi tazo ko kuwa dai wajenta tazo? to amma itafa ba shiri suke ba hasalima magana ta fatar baki bata taɓa haɗasu ba saboda Jawaheer muguwar ƴar rainin wayo ce sam basa shiri....."ƙaraso mana". Ummi ta katse mata tunanin datake, kusa da Ummi ta ƙarasa ta zauna har lokacin bata daina tunanin abinda ya kawo Jawaheer gidansu ba. "Ummi Aunt Mashhoodah tace tana gaisheki". "Ina amsawa ya kika barosu da yaran?". "Lafiya ƙalau wllhy, Noor mafa harda kukanta wai saita biyoni kuma matsalar akwai school gobe amma tace weekend driver zai kawota ta kwana biyu". "ALLAH ya kaimu, bakiga baƙuwa bane Neehlah?". cewar Ummi tana kallon Seeyamah data sadda kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta murmushi ɗauke a fuskarta. "Na ganta Ummi a ina kika samota?". A taƙaice Ummi ta bawa Neehlah labarin abinda ya faru duk da dai bata faɗa mata cewa Habeeb ne yasa aka kama ta ba, sosai Neehlah tayi mamaki jin ba wadda take zato bace wata ce daban jin tayi shiru yasa Ummi tace "Ya kikayi shiru ne?". Sai data ƙara kallon Seeyamah sosai taga dai basuda bambanci da Jawaheer sannan tace "Ummi abin ne akwai ban mamaki a school ɗinmu fa akwai wata irinsu ɗaya da wannan wllhy ba abinda ya rabasu komai fa Ummi I'm confused wllhy". "Ikon ALLAH dama haka lamarin ubangiji yake ai wasu ma ba ƴan gari ɗaya bane sai kiga kamannin su yazo ɗaya". Kai kawai Neehlah take gyaɗawa tana ƙara karantar yanayin Seeyamahn wadda har yanzu batayi magana ba. "Ga ƴar uwa nan nakawo miki yadda kike da damar yin komai a cikin gidan nan itama tana da wannan damar kar in sake inji wani abu ya ɓullo daga wajenki yanzu amana take a wajen mu". "Insha ALLAH Ummi". Neehlah ta faɗa tana tashi ta koma kusa da Seeyamah ta zauna tana murmushi. "Kema Seeyamah ga Neehlah nan kamar yadda na faɗa miki itace ƙarama duk abinda tayi miki ba daidai ba ki sameni ki faɗa min ALLAH ya haɗa kanku yayi muku albarka". Da Amin suka amsa gaba ɗayansu Neehlah ta miƙawa Seeyamah hannu suka gaisa kowacce da murmushi saman fuskarta jin an fara kiran sallah yasa Ummi ta miƙe tsaye tana faɗin "Oya aje ayi sallah tayi amfani da wannan bedroom ɗin na kusa da naki kaya ma tafara using naki tunda naga kusan size ɗinku ɗaya kafin ayi mata siyayyar nata". sosai Neehlah ta shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka tace "Haba Ummi inama laifin kice muyi using bedroom ɗaya dama fa ya min girma". murmushi Ummi tayi tace "Ba matsala ta zauna a naki bedroom ɗin shikenan?". cikeda murna Neehlah ta rungume Seeyamah tana dariyar farin ciki harga ALLAH dama zaman gidan nan yana mugun ci mata tuwo a ƙwarya tana shan zaman kaɗaici ba laifi gidan kawu Sulaiman ne dama gurin zuwanta kuma shi ƴaƴan shi duk maza ne matan basuda yawa kuma duk sunyi aure tun ma acan Yoben shiyasa har bataso weekend yayi gara idan da school ɗin tana ɗebe mata kewa. "Thank you Ummi". tace tana miƙewa tsaye tareda kama hannun Seeyamah suka nufi upstairs inda bedroom ɗin Neehlahn yake Ummi ta bisu da kallo tanajin farin ciki mara misaltuwa yana ratsata haƙiƙa taimakon maraya ba ƙaramin lada gareshi ba aiki ne mai kyau ƙwarai da gaske, itama upstairs ɗin ta hau ta nufi nata bedroom ɗin dan bada farali. Babban bedroom ne sosai wanda har Seeyamah ta dinga mamakin ace na Neehlah ne kawai ita kaɗai lallai masu kuɗi sunajin daɗinsu, tamkar ɗakin wata matar auren bed, wardrobe, mirror da sauran abubuwan ƙawata ɗaki na masu kuɗi sai ƙamshi yake na turaren wuta. "Bismillah ga bathroom shiga ki fara yin alwalah". Neehlah ta faɗa tana nunawa Seeyamah wata ƙofa dake cikin bedroom ɗin, inda ƙofar take ta nufa da niyyar shiga Neehlah ta biyota da sauri tana faɗin "Oh my God! Seeyamah ki cire babban hijabin nan mana please bakyajin ya dameki ne?". Bata saurari abinda Seeyamahn zata faɗi ba ta fara ƙoƙarin cire mata shi da kanta bata hanata ba ta tayata cirewa. "Yauwa koke fa Sisi". Neehlah tace tana jefa hijabin kan bed, itadai murmushi kawai tayi ta shige toilet ɗin. Ta daɗe tana ƙarewa bathroom ɗin kallo saboda yadda aka ƙawata shi kamar ba toilet ba (dan ma bakiga na oga ɗan kidnapping ba 😂). Alwalah ta ɗaura ta fito ta tarar har Neehlah ta shimfiɗa mata pray mat murmushi kawai suka sakarwa junansu ba tareda wani yayi magana ba Neehlah ta ɗauko hijabin ta miƙa mata sannan itama ta shiga toilet ɗin Seeyamah ta bita da kallo familyn sun burgeta sunada kirki da sanin darajar ɗan adam amma shi wancan meyasa duk bashida su ko kaɗan bashida mutunci da tausayi bai biyo halin mahaifiyarsa ba gaskiya ganin dai tunanin bazai yimata ba tasa hijab ɗin ta kabbara sallah, itama Neehlah bata daɗe ba ta fito wata dardumar ta shimfiɗa kusa da Seeyamah ta ɗauko hijab a wardrobe ta tada tata sallahr. Bayan sun idar ma hira suka cigaba dayi duk da dai duk rabin hirar Neehlah ce Seeyamah bata cika magana ba sai murmushi kawai datake tana jin ƙaunar ahalin har a jinin jikinta. Suna nan zaune sukaji an kira sallahr Esha'e dan haka suka tashi suka gabatar da tasu suka ƙara zaman wata hirar, system ɗinta Neehlah ta jawo tana faɗin "Bari kiga sister na dana dawo daga gidanta yanzu da kuma Big Bro ɗinmu gaba ɗaya". kafin ma Seeyamah tayi magana Neehlah ta buɗe system ɗin tasa password ta shiga ɓangaren hotuna inda pic ɗinta ne kawai dana Ummi da Aunt Mashhoodah sai mai gayya mai aiki Habeeb. "Masha ALLAH Aunt Mashhoodah tafiki kyau gaskiya". Seeyamah tace tana ƴar dariyar tsokana, tuni Neehlah ta haɗe fuska tana jefawa Seeyamah hararar wasa kamar zatayi kuka tace "Dama ta ina zaki haɗamu? su fa acan Dubai aka haifesu itada Yah Habeeb nikam 9ja bansan meyasa aka haifeni anan ba". dariya sosai Seeyamah tayi tace "Dama mutum yana zaɓar inda za'a haifeshi ne?". "Inafa amma nidai banso ba wllhy a rasa inda za'a haifi mutum sai Nigeria". ta ƙarasa maganar tana wani taɓe baki, dariya Seeyamah tayi tana cigaba da duba hotunan tana murmushi tana yin next idanunta suka faɗa kan pic ɗinshi yana tsaye kusa da wani ƙaton tamfatsetsen building daya gaji da haɗuwa sanye yake cikin Italian suit dark blue sai shirt ɗin ciki data kasance white color hannayenshi duka suna sanye cikin aljihun wandonshi ya toshe idanunsa da black shade tamkar wanda baisan ma za'a ɗauki pic ɗin ba dan hankalin shi gaba ɗaya baya kan mai ɗaukar hoton can wani gurin yake kallo daban, daga yadda tsarin wajen yake da irin mutanen dake wajen zai tabbatar maka da ba'a 9ja aka ɗauki hoton ba yayi matuƙar yin kyau duk da fuskarshi ba'a sake take ba haka yanayin tsayuwar tasa ma ta bada citta, haka nan Seeyamah ta tsinci kanta da faɗuwar gaba mai tsanani ido ta ɗan lumshe tayi saurin buɗewa saboda Neehlah dake wajen ita sam Neehlahn ma bata lura da yanayin da Seeyamahn ta shiga ba a lokacin ta fara faɗin "Big B kenan miskili kafi mahaukaci ban haushi kin ganshi nan shine babban yayanmu". Kai kawai Seeyamah ta kaɗa batace komai ba ta cigaba da dubawa duk pics ɗinshi ne kala kala a mabanbantan gurare mafi yawa ma duk ba'a Nigeria aka ɗauka ba gaba ɗaya ba wanda aka ɗauka yana dariya kowanne fuska a tamke kuma hakan baya hana yayi kyau baifi guda biyu tagani ba wanda ya ɗanyi murmushi, tana shirin tambayar Neehlah shikam baya dariya ne taji muryar Neehlahn tana faɗin "Haka fa yake baya dariya shi murmushi ma saita kama yake yinshi kullum ta ALLAH fuska a tamke yana baƙin rai kuma yafiso yadda yake kowa ma ya zauna a haka ko dariya fa akayi a gabanshi saiya kori mutum na rasa irin halinsa Mr ɗacin rai kenan". ta ida maganar tana dariya, itama Seeyamah ƴar dariyar tayi a ranta take faɗin Lallai na tabbatar kuwa ko ita ɗin nan da bata daɗe da sanin shi ba bata taɓa ganin dariyar shi ba ya iya dai mugunta yasan ta kanta. "Kinsan ai kowa da yanayin yadda ALLAH yake halittar sa wasu masu fara'a da sakin fuska wasu kuma akasin haka". Baki Neehlah ta taɓe tace "Nashi fa daban ne Sisi ALLAH Yah Habeeb da wuya kiga haƙorin shi a waje kullum a cunkushe kamar wanda baijin daɗin rayuwa ni wllhy ma na matsu yayi aure yabar min gidan in wataya abina". Seeyamah zatayi magana kenan aka buɗe ƙofa Ummi ta shigo tana murmushi tace "Oh Neehlah kina nan kin tsareta da surutun nan naki ko? a fito maza ayi dinner". haɗa baki sukayi wajen amsa mata ta juya ta fita Neehlah ta rufe system ɗin ta tashi tsaye Seeyamah ma ta miƙe suka fita duk jinta take wani iri daban kamar ba ita ba ba haka ta saba da rayuwar ta ba yau ɗaya ALLAH ya canza mata. Dinning area suka nufa inda Ummi take zaune, Neehlah tajawa Seeyamah kujera ta zauna sannan ya fara serving ɗinsu. "Ummi banga Yah Habeeb ba?". Neehlah tace bayan tagama zubawa kowa ta zauna "Ƙyaleshi kawai yau baiyi niyyar yin dinner ba". tana faɗa taja plate ɗin gabanta ta fara cin abincin Neehlah ma bata ƙara magana ba kowa ya maida hankali kan abincin dayake ci. Da suka gama ma cikin falon suka koma suka zauna suna kallo jefi jefi suna ɗan taɓa hira. ★__★ Matsananciyar yunwa ke rarakar cikinsa dan rabon da wani abu mai nauyi ya shiga cikinsa harya manta saidai yaita bankawa cikin shi coffee saikuma fruits dayake ma'abocinsu ne, yau kam yaji yana sha'awar yasawa cikin shi ɗan abu mai nauyi gashi har wajen 9:25pm baiji kiran Ummi na yazo yayi dinner ba da alamu fa har yanzu Ummi bata sauka ba, shikam yaga ta kanshi wani lokacin idan Ummi tayi fushi takan daɗe bata sauka ba. Tashi yayi daga kishingiɗen dayake ya ɗauki wayarshi ya fita daga side ɗinshi ya nufi nasu Ummi, a hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar falon ya shiga bakinshi ɗauke da sallama duk da dai ba fitar ta akaji ba motsin da bakinshi yayi ne ya tabbatar musu da yayi sallamar dama Ummi da Neehlah sun saba gani, sallamar kawai Ummi ta amsa ta kawar da kanta daga kallonshi tun daga haka ya ƙara shan jinin jikinsa sai ya cigaba da takawa cikin takun nan nashi mai cikeda izza da mazantaka wanda ya zame masa jinin jikinshi. Tun shigowar shi Neehlah tayi tsit kamar ruwa ya cinye ta duk wannan surutun datake tai ɗif da ita ta shiga zare ido, ta ɓangaren Seeyamah ma haka nata harya zarta na Neehlah dan ita banda faɗuwa da gabanta yake har wani rawa rawa jikinta ya ɗauka yana ƙara kusantowa gabanta na ƙara faɗuwa wani mugun kwarjini yayi mata sai taji tamkar ya cika falon shi kaɗai ɗinshi, ta ƙasan ido ta ɗan saci kallon shi kayan shan iska ne a jikinshi marasa nauyi na kamfanin Adidas jan wando da farar riga wadda akayi mata ado da jan layi layi irin wandon gashi dai kayan bana kwalliya ko gayu bane amma sun bala'in haskashi dama ba'a maganar ƙamshi dan yana shigowa falon ya ɗume da ƙamshin sa wanda zuwa yanzu ya riga ya rasa zauna a ƙwaƙwalwar Seeyamah duk inda taji shi saita ganeshi. Kusa da Ummi ya ƙarasa ya zauna ƙasan ƙafafunta ya buɗe baki da niyyar yin magana kawai yaga Ummi ta tashi tabar wajen ta nufi upstairs....... Saura two pages book one ya ƙare karku manta book two isn't free ALLAH ya bada abinda za'ayi patronizing ɗina 300 only ALLAH ya bada ikon siya Amin. Nagode Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 29. Da kallo ya bita lokacin da take hayewa upstairs ɗin zuciyar shi na masa wani irin zafi wai Ummin shi ce ke masa haka yau? duk akan wannan yarinyar, Neehlah da Seeyamah ma da kallon suka bita Seeyamah tasan dalilin fushin na Ummi yayin da Neehlah kuma batasan komai akai ba tayi dai mamaki ƙwarai tunda bata taɓa ganin abu makamancin hakan ya shiga tsakanin Ummi da Yah Habeeb ɗin ba kullum rarrashi da lallaɓawa ne tsakanin su to yau kuma meye ya faru? Ido ya lumshe yana sauke numfashi haɗi da cije baki saboda yadda ranshi ya ɓaci a hankali ya buɗe idanunsa da suka ɗan fara canza launi ya saukesu kansu Seeyamah wani ɓacin ran ne ya ƙara ziyartar sa ganin duk a kanta ne Ummi tayi masa haka gashi kuma ta kunyata shi a gabansu wani mugun kallo daya antaya musu yasa ba shiri Neehlah ta kama hannun Seeyamah suma suka nufi upstairs ɗin jiki na rawa duk da ita Seeyamahn batama ga irin kallon da yake musu ba, da kallo ya bisu har suka ƙarasa hayewa tsaki yaja da ƙarfi ya tashi a fusace ya fita daga falon. Da sauri yake tafiya zuwa part ɗinshi yana shiga ya maida ƙofar da ƙarfi ya rufe ta bada wani sautin ƙara bammm, kan kujera ya zube tareda dafe goshinshi haɗi da lumshe idanunshi yana jin duk ba daɗi basu saba irin haka da Umminshi ba Ummi bata fushi dashi saboda yana ƙoƙarin ganin ya kiyaye ɓacin ranta duk abinda yasan zai ɓata mata bayayi baya ƙaunar fushinta ko kaɗan. A hankali ya buɗe ido yana furzar da zazzafar iska daga bakinshi ya zama dole yaje yabawa Ummi haƙuri yanzu bazai iya haƙurin zuwa safiya bama, cikin hanzari ya miƙe tsaye ya ƙara ficewa daga falon ya ƙara nufar part ɗinsu Ummi, falon ba kowa kamar yadda ya fita ya barshi yana shiga kai tsaye ya nufi upstairs zuwa bedroom ɗin Ummi. A bakin ƙofar ya tsaya yayi knocking daga ciki Ummi ta amsa cewar a shigo handle ɗin ƙofar ya kama ya buɗe ya shiga tareda sallama tana zaune kan sofa da wani littafi a hannunta na addu'oe tana dubawa gabanta kawai ya zube ya dafa gwiwoyinta da duka hannayenshi cikin marairaicewa ya fara mata magana cikin harshen larabci yana haɗawa da turanci banza tayi masa kamar bata ganshi ba hakan yasa ya ƙara marairaice murya kamar zaiyi kuka. Littafin hannunta ta ajiye ta ƙura masa ido duk saiya bata tausayi basu saba irin wannan a tsakaninsu ba ita kanta tasan yaron nata yana matuƙar gudun ɓacin ranta. "Zauna sosai muyi magana". tace har lokacin bata saki fuskarta ba, zamewa yayi yai zaman dirshan a gabanta tareda kamo hannayenta ya riƙe su gam cikin nashi hannun yana kallon ta, dariya yabata sosai ganin yadda yayi ɗin kamar irin ƙananan yaran nan duk yabi ya wani shasshake mata gimtse dariyar ta tayi ta ƙara haɗe fuska dan a yau take so taji dalilin shi na ɓoye Seeyamah baiwar ALLAH yarinyar data taso gidan marayu bataji ba bata ganiba. "Bakason ɓacin raina ko?". da sauri ya gyaɗa mata kai "Kanaso kuma in sauka daga fushin danake dakai?". Nan ma kai ya jijjiga mata alamun tabbatarwa, kai ta jinjina itama tana gyara zamanta tare da faɗin "Dalilin ka na ɓoye Seeyamah nakeso inji yanzun nan". ido ya ɗan zaro dan baiyi zaton abinda zata faɗa kenan ba. "Ummi please abar maganar nan k....."Shut up". Ummi ta katse shi cikin tsawa, shiru yayi ya sunkuyar da kanshi ƙasa cikin faɗa Ummi tace "Tashi kabani waje tunda banida matsayin da zaka faɗa min". "I'm sorry Ummi please zan faɗa miki". "Ina jinka". cewar Ummi tana kallonshi. Bashida yadda zaiyi UWA tafi ƙarfin wasa dole ya sanar da ita abinda bata saniba, daki daki a tsanake ya shiga bata labari tun farkon haɗuwarsu da Heedayah akan layi da haɗuwa da yayi da Jawaheer again kuma yaga Seeyamah a gidan marayu da irin zargin da yayi na itace take sauya kamanni take bibiyarshi duk inda yaje hakan yasa ya ɗauke ta da nufin saita faɗa masa inda ta sanshi da dalilin dayasa take binshi sannan zai saketa har zuwa lokacin da Mujaheed yabi diddigin inda take yazo ya faɗa mata. Sosai Ummi ta nutsu tana jin wannan labarin mai cikeda al'ajabi idan ta fahimta yaran su uku ne kenan kuma duk kamar su ɗaya kuma kowacce da inda take tsai tayi da ranta tana auna kan labarin lallai ko waye dole ya rikice ko ita kanta abin ya matuƙar ɗaure mata kai da shiga ruɗani. Nannauyan numfashi ta sauke kafin tace "A ina ita yarinyar daka gani a gidan Hajiyan take?". A taƙaice yabata labarin Heedayah kamar yadda Hajiya ta sanar dashi yaje kuma yaga har gidan ranar da Hajiya tasa ya maida ita gida. Kai kawai Ummi take jinjinawa cikin zuciyarta tana ayyana wasu abubuwa masu tarin yawa idan har hasashen ta zai zama gaskiya to yaran nan ƴan uku ne maybe wani abun ya tarwatsa su kuma ba wadda tasan da zaman ɗaya a cikinsu danƙari akwai cakwakiya cikin al'amarin nan warware shi sai ALLAH. "Ita waccan yarinyar da kake gani a shopping mall ɗin kasan inane gidansu?". "No Ummi har yanzu bansan inane gidansu ba shine nakeso inyi bincike dan gano gaskiyar al'amarin". Kai Ummi ta jinjina tana faɗin "Hakan yayi tun farko ma da abinda kayi kenan ka tsaya shirme da sakarci tabbas lamarin yana buƙatar bincike kuma na baka goyon baya hundred percent dan ta hakane za'a gano iyayen su na asali jikina yana bani duk inda yaran nan suka fito daga babban ahali suke sanin abinda ya tarwatsa su kuma sai ALLAH zanfi kowa farin ciki idan aka gano real parents ɗinsu ALLAH ya bada sa'a". Cikin farin ciki yake kallon Ummin yana ƙara jin wani ƙwarin gwiwa na shigarshi ada bai bawa abin muhimmanci ba kamar yadda yake jinshi yanzu cikin ranshi saboda mahaifiyarsa data shigo cikin lamarin. "Thank you so much Ummi". yace murmushi na suɓucewa kan fuskarsa, itama murmushin ta saki tana faɗin "Karka damu nidai fatana karka shiga cikin lokacin aikinka abi komai a sannu har zuwa lokacin da ALLAH zai bayyana mana abinda ke ɓoye kar ayi gaggawa idan kana buƙatar wata shawara ka sameni". "Insha ALLAH Ummi thank you very much". Kanshi kawai ta shafa tana murmushi shikuma yayi kissing hannunta. "Good night Ummi". ya faɗa yana miƙewa tsaye da niyyar barin bedroom ɗin Ummi ta dakatar dashi da faɗin "Ya kamata gobe idan ALLAH ya kaimu kuje da Seeyamah a samar mata kayan sawa". tuni yanayin fuskarsa ya canza ya wani haɗe rai yace "Ummi driver fa?". "Ɗazu yake sanar dani anyi masa waya daga ƙauyensu mahaifiyarsa ba lafiya zaije ganota". Ummi ta amsa masa tana tsareshi da ido, shiru kawai yayi yana murza fatar goshinsa daya tattareta shine ma zai kaita siyan kayan sai kace wani ɗan aikinta? "Bakaji abinda nace bane wai Abbuna?". Ummi ta katse masa tunanin dayake, sai daya zura hannu ɗaya a aljihu ɗayan kuma ya shiga shafa sumar kanshi kafin yace "Naji Ummi amma kawai sai a ganni nakai yara siyayya please Ummi suje kawai da Neehlah ko nawane zan bayar ta ɗauki duk abinda takeso". ya ƙarasa maganar yana marairaice murya kar ma Ummin tace zata takura masa shifa gani yake hakan kamar zubar da girma da ajinshi ne kawai a ganshi ya raka yara siyayya. "Kai ɗin kai zaka kaisu, meye a ciki dan ka rakasu? ba yayansu bane?". zaiyi magana Ummi ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu dolenshi ya amsa mata da to sannan ya ƙara yimata sallama ya fice daga bedroom ɗin ta bishi da kallo tana girgiza kai, gani yake wani uban aiki ne kaisu siyayyar da zaiyi. Direct kitchen ya wuce bayan komawa part ɗinshi ya haɗa coffee yadawo falo ya zauna kan 1sitter ya miƙe ƙafafunshi kan center table ya fara sha duk da yadda yake fitar da turirin zafi kuwa ya riga ya saba sha da zafi haka. Bayan yagama sha ma sai daya ɗan jima zaune anan sannan ya shiga bedroom yayi wanka ya ɗaura alwalah ya fito ya shirya cikin pyjamas dark purple masu kauri ya fesa turare sannan ya tada sallah, raka'a biyu yayi, yayi addu'oe ya shafa sannan ya kwanta bayan ya karanto addu'ar kwanciya barci ya shafe jikinsa. Asubah ta gari Mr Habeeb Gashua 🤩. ★★★_________★★★ Duk bakin bed suka nema suka zauna bayan hawowar su upstairs Neehlah tace "Sisi kinga Yah Habeeb ɗin ko?". murmushi kawai Seeyamah tayi ta gyaɗa mata kai batare datace komai ba dan har yanzu bata wani gama dawowa daidai ba gabanta kuma bai daina faɗuwa ba, baki Neehlah ta taɓe tace "Kinga irin halin nashi ko? yanzu haka wani laifin ya yiwa Ummi shine zai huce a kanmu inajin da bamu gudo ba da duka zai kai mana". ƴar dariya Seeyamah ta ƙaƙalo nan ɗinma dai bata tofa tata ba to itakam me zatace a kansa? kuma alƙawari ta ɗaukarwa kanta insha ALLAHU ba zata dinga shiga sabgar shiba dan ita harga ALLAH kallon mara mutunci take masa. Ita ta fara shiga bathroom tayi wanka kafin ta fito har Neehlah ta fito mata da night dress doguwar riga har ƙasa orange color da baƙar hula tana fitowa ta shirya itakuma Neehlah ta shiga bathroom ɗin dan yin wankan. Ko bayan da sukayi addu'a suka kwanta Neehlah tana ta jan Seeyamah da hira taƙi biye mata sosai ita haka ALLAH yayi ta magana bata dameta ba da haka har barci ya ɗauke su. Bayan sallahr asubah Neehlah barci ta koma Seeyamah kam kasa komawa tayi ta cigaba da zama bisa dardumar tana karanto azkar can ƙasan zuciyar ta tana ƙara godewa ubangiji kan wannan ni'imar dayayi mata bayan tsahon shekaru sha takwas data ɗauka zaune a gidan marayu yau rana ɗaya ubangiji ya turo baiwar shi dan ta share mata hawayenta yau gata itama an maida ita ƴa kamar kowane ƴaƴa za'a bata dukkan gata da kulawa tana fata da burin ace wata rana zata zauna da iyayenta haka batasan wani irin kalar farin ciki da murna zatayi ba a duk ranar data haɗu da iyayenta saidai abinda bata saniba a raye suke? kokuwa a mace? wani abu ne yasa suka banzatar da ita suka wofintar da rayuwar ta haka? ba zato taji hawaye na bin kumatunta ranta na wani irin suya batada mutum ɗaya da zata iya nunawa a faɗin duniyar nan wanda zata bugi ƙirji ta nuna shi tace wannan ɗan uwanta ne shi kanshi wanda ya tsinto ta ya kawota gidan marayun ance tunda ya kawota bai ƙara dawowa ba ba'a ƙara ganinshi ba, hijabin ta tasa ta share hawayen fuskar ta. Tun batasan kanta ba take ji a jikinta kamar wata rana iyayenta zasu nemeta kamar zatayi rayuwa da iyayenta bayan rayuwar gidan marayu datayi da farko koma dai meye tana roƙon ubangiji ya zaɓa mata mafi alkhairi idan da rabon zasu haɗu ɗin ALLAH ya haɗa fuskokinsu da alkhairi. Ta daɗe zaune a wajen cikin tunani daga bisani tayi addu'a ta shafa ta tashi ta ninke dardumar ta ajiyeta a mazaunin ta, ƙofa ta buɗe ta fita ta sauka downstairs ta shiga dube duben inda zataga abin shara cikin sa'a ta gansu da abin yin mopping dama abinda ta sauko nema ɗin kenan dan haka ta ɗauka ta koma upstairs ɗin ta fara gyaran ɗakin tayi shara da mopping ta wanke toilet duk Neehlah tana kwance tana uban barci batasan abinda take ba. Downstairs ta ƙara saukowa nan ma ta hau gyaranshi duk da dai ba wani datti a ciki ta share tayi mopping ta maida kayan sharar inda ta gansu ta koma bedroom ɗin har lokacin Neehlah bata tashi ba dayake ba school yau, kwanciya ta ƙara yi itama dan ba ƙaramin gajiyar da ita mopping ɗin falon yayi ba saboda girman shi bata daɗe ba kuwa barci ya ƙara yin gaba da ita. Lokacin da suka tashi ƙarfe goma ta kusa wanka sukayi Neehlah tace ta buɗe wardrobe ta zaɓi duk kalar kayan da sukayi mata ta ɗauka tasa, saita rasa ma wanda zata ɗauka ɗin saboda yawansu kayane gasu nan birjik laces, atamfofi, material's, dogayen riguna,shaddoji da English wear sai wanda ka zaɓa lallai masu kuɗi sun more ba abinda ya damesu (A naki ganin ko? kowane ɗan adam baya rasa abinda yake damunsa). Wata atamfa ta zaƙulo riga da siket saidai tana ɗauko ta ma taga sabuwa ce ko sakawa ma ba'ayi ba niyyar maidawa tayi Neehlah tace sam bata isa ta maida taba tasa kawai meye amfanin kayan, ash color ce atamfar da touch ɗin fari da baƙi ɗinkin simple ne bawata kwalliya kuma sunyi mata matuƙar kyau ta shafa turaruka, hijabinta ta ɗauka zata zumbula Neehlah ta ƙwace ta ɗauko mata mayafi ash mai ɗan girma tace shi zata saka ita ko gajiya batayi da saka hijabi, haka dai ta karɓa ta yafashi tana jinta duk wani iri saboda bata saba ba tafi ganewa hijabanta masu girma tai ta yawo a cikinsu. Neehlah doguwar riga kawai tasa ƙirar Saudi blue black ta yafa gyalen rigar suka sauka ƙasa dan yin breakfast. Saukowar Ummi kenan suma suka sauko cikeda farin ciki take kallonsu tana amsa gaisuwar su kafin ta ɗora da faɗin mai yi musu gyara tazo ɗazu tace mata an gyara ko ina kuma tasan ita tayi kar ta ƙara yi akwai masu zuwa suyi ta amsa da to daga nan suka wuce dinning Neehlah tayi serving ɗinsu dama Ummi batasa ran ganin Habeeb yanzu ba dan indai ba ranar aiki bace sai yakai ƙarfe ɗaya bai shigo yayi breakfast ba. Seeyamah ce ta gyara kan dinning ɗin bayan sun gama duk da yadda Ummi ta hanata kuwa ta kwashe kayan da aka ɓata taje kitchen ta ɗaurayesu daga nan suka koma upstairs dama tuni Ummi ta koma bedroom, Indian film Neehlah ta kunna musu a system ɗinta suka fara kallo. Sai wajen 12:45pm sannan ya shigo gaida Ummi bedroom ɗin nata ya shiga suka gaisa yana shirin fitowa ta ƙara tuna masa maganar fitar da zasuyi dasu Seeyamah anjima to ya ya iya? dolenshi ya amsa dan shi harya manta ma, falon ya dawo yayi breakfast ya ƙara ficewa zuwa nashi part ɗin, fita yayi ma daga gidan gaba ɗaya zuwa inda ake ginin kamfaninsu yaga yadda aikin yake tafiya sannan ya ƙara dawowa gida. Layin Mujaheed ya kira ya faɗa masa anjima da yamma zai masa rakiya dan shikam bazai tafi daga shi saisu ba kamar wani direbansu sam ya manta ma wai fushi yake da Mujaheed ɗin, kira biyu yayi amma duk ba'ayi picking ba sai ana ukun sannan aka ɗaga cikin jin haushi yace "ALLAH MJ idan ina kiranka baka picking akan lokaci saina dinga cin ubanka dan iskanci sai ayita kiranka bazakayi picking ba sai kaga dama". "To mara mutunci kasan uzurin dayake hanani ɗauka ne zakamin tijara". "Wani uzuri gareka daya wuce iskanci? ka shirya anjima after Asr zaka rakani shopping mall". "Shopping Mall kuma? babynka zakayiwa siyayya ne?". "Nabi babyn da gudu dalla malam ka shirya da wuri". bai jira cewar Mujaheed ba ya yanke kiran yana cije baki ALLAH ya tsareshi da wannan ɓata lokacin shikam shi har yanada time ɗin wata mace bare har ya zauna yana wannan shirmen. Sosai Mujaheed ya ƙyalƙyale da dariya jin abinda Gashua ya faɗa wai yabi baby da gudu wllhy wasa wasa Gashua ɗan air ne a bakinshi ma yaji wannan kalmar fa shine harya riƙe ta haka shi sam baiyi zaton ma zai sauko haka da wuri ba a yadda ya san shi da shegiyar zuciya da riƙon bala'i, girgiza kai kawai yayi yana ƙara sakin wata dariyar...... Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 09139964697 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 30. Ya daɗe zaune bayan sun gama waya da Mujaheed kafin ya tashi ya wuce bedroom, kayan jikinsa ya cire ya rage daga shi sai boxer da singlet farare tas ya shiga bathroom yayi wanka. bayan fitowar shi ya shirya cikin ƙananan kaya baƙin jeans ne da riga peach color mai gajeren hannu ya ɗaura baƙin agogon fata sai P. Cap kalar rigar daya ɗora a kanshi ya sanya baƙin takalmi sawu ciki yana cikin fesa turare wayarshi ta fara ringing bai kulata ba sai daya gama fesa turaren sannan ya isa inda take lokacin harta katse wani kiran ya ƙara shigowa yasan dai bazai wuce Mujaheed ba picking yayi yakai kunnenshi batare dayace komai ba ya ƙara komawa gaban mirror'n ya tsaya ya ɗauki wani turaren yana fesawa daga can ɓangaren Mujaheed yace "Gashua ka gama shiryawa ne?". Da ƙyar ya buɗe baki yace "Yes". "Okay nima na shirya gani nan zuwa". "Ok". yace tareda katse wayar ya ajiye kwalbar turaren ya fito falo, zama yayi ya shiga latse latsen waya. Daga Seeyamahn har Neehlah ba wadda taso Ummi ta haɗasu tafiya da Habeeb Seeyamah dai batace komai ba to me zatace? itafa jinta take tamkar ƴar aiki a gidan Neehlah kam fuska ta shagwaɓe tana faɗin "Kai Ummi ALLAH da baki haɗamu da Yah Habeeb ba takuramu kawai zaiyi bazai bari ma ayi siyayyar cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba". Harararta Ummin tayi tace "Sha zamanki tunda bazaki ba". "Zanje fa Ummi kawai dai Yah Habeeb ɗin ne akwai matsawa wllhy ni banson tafiya tana haɗani dashi". "Kin tashi kinje kin shirya kokuwa dai surutu zaki tsaya yi?". Tashi Neehlah tayi ta fita tana tura baki ko yaya tafiya ta haɗasu ya dinga hantarar mutum kenan yana masa tsawa ina dalili. Yanzun ma dai da sukayi wanka Neehlah cewa tayi Seeyamah ta zaɓi duk kayan da sukayi mata tasa, wata doguwar riga ta ɗauka ta material multi color tasa ba yadda Neehlah batayi da itaba kan tasa mayafi tace a'a ta bata hijab tasaka tafi sabawa dashi, hijabin ta ɗauko mata pink kalar datafi yawa a jikin material ɗin ta bata ta saka iya gwiwa ne mai hannu tayi kyau sosai sai ƙamshi take. Neehlah kam mayyar dogayen riguna ce dan haka yanzun ma cikin doguwar rigar ta shirya light brown tayi rolling da mayafin rigar suka zauna zaman jira. Ba'a daɗe ba sosai Mujaheed ya ƙaraso gidan shigar manyan kaya yayi dayake ma'abocinsu sosai shadda milk color harda hula kalar shaddar kamar wani ango nan compound ma ya tsaya ya kira Habeeb ɗin yace ya fito ya ƙaraso, sai daya kira Ummi yace su Neehlah su fito sannan ya fito daga part ɗin nashi ya rufe ya fito cikin compound ɗin. A bedroom Ummi ta samesu tace su fita yana jiransu a waje tashi sukayi sukayiwa Ummi sallama sannan suka fito. Ba ƙaramin daɗi Neehlah da Seeyamah sukaji ba lokacin da suka fito suka hango Mujaheed da alamu dashi zasu fita, suna ƙarasowa suka haɗa baki wajen gaishesu cikin sakin fuska Mujaheed yake amsa musu Gashua kam a cukule ya amsa musu da "Lafiya". Tamkar wanda akayiwa dole ya buɗe front seat ya shiga ya hakimce bayan ya cillawa MJ key ɗin motar, Mujaheed da kanshi ya buɗewa su Seeyamah back seat suka shiga ya maida murfin ya rufe sannan ya shiga driver seat ya zauna yana kallon Habeeb da hankalinsa ke kan waya yace "Wai Gashua ni zanyi driving ɗin ne?". banza yayi masa baiyi magana ba bai kuma ɗago ya kalleshi ba. "Kaji?". Mujaheed ya ƙara faɗa duk cikin neman tsokana da son saiya sashi dai magana. "A'a ni zanyi". yace yana juyawa tareda sakar masa harara, dariya Mujaheed yayi yace "Yaro yaji hausa har dasu baƙar magana haka Gashua". ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin tayar da motar, ƙaramin tsaki Habeeb yaja tareda maida kanshi kan wayarshi ya cigaba da abinda yake. Maigadi ne ya buɗe musu gate suka fice daga gidan, saida suka hau kan titi sannan Mujaheed yace "Ina muka nufa ne Mr. Man?". Kamar yadda baiyi magana ba haka ma bai ɗago kai ya kalleshi ba, Mujaheed ya ƙara faɗin "Wai Gashua bakaji abinda nace bane?". Nan ma banza yayi masa hakan ya hasala Mujaheed ya juyo yana harararshi da faɗin "Matsala ta dakai wulaƙanci wllhy kanaji ana maka magana ka ƙyale mutane banza mara mutunci". Sosai Habeeb ya shaƙa saboda yadda Mujaheed yake kunyata shi da tsinkashi a gaban ƙananan yara su kansu su Seeyamah mamaki ne ya cikasu jin yadda Mujaheed ɗin yake zaginshi musamman Neehlah datafi sanin ko waye yayanta lallai idan ba Mujaheed ɗin ba bataga wanda zaiyi masa haka ya ƙyale ba. "Autar Ummi ina muka nufa ne? siyayyar me za'ayi?". Mujaheed ya maida tambayar kan Neehlah, a ɗarare tace "Kaya ne za'a siyawa Seeyamah". "Okay yayi kyau bari mu duba babban shago saimu shiga ko?". "Toh Yah Mujaheed". Neehlah tace taja bakinta tayi shiru. Mujaheed bai ƙara saurarar Habeeb ba ya maida hankalinsa kan tuƙi sai jefi jefi dayake jan su Neehlah da hira waɗanda sam basu biye masa ba kuma duk yasan ganin wannan uban ƴan baƙin ran ne ya hana Neehlah biye masa a yadda take da ɗan banzan surutun nan, sai yaja bakinshi yayi shiru aka shiga yin tafiyar kurame ba mai magana titin Nassarawa ya hau yana ɗan dudduba kan hanya inda zaiga gurin saida kaya, ganin motar ta ɗauki shiru yasa Mujaheed yayi connecting da wayarshi yasa waƙa ya fara saurara yana bin waƙar. Ido Habeeb ya ɗan runtse yanajin kiɗan har cikin ƙwaƙwalwar kanshi kamar a tsakiyar kanshi akeyi ALLAHn da yayi shi ya tsani hayaniya koya take. "Please MJ ka kashe banaso". yace cikin cool voice yana ɓata fuska. "Why?". cewar Mujaheed yana wani kaɗa kai alamun waƙar ba ƙaramin daɗi take masa ba, a ɗan fusace Habeeb yace "Saboda motata ce inada iko da ita". Murmushi Mujaheed yayi tareda ɗan taɓe baki yace "Gori zakamin Gashua? daɗin abin nima dai inada motar nan kuma ina zamana ka kirani in maka rakiya haba saikace wanda ya ɗauko gawa a mota kai ba za'ayi hira dakai ba Neehlah saboda tsoron ka itama taƙi sakin jiki na kunna waƙa kace ba haka ba to ya kakeso ayi Gashua? kai bazakayi nishaɗi ba bazaka bar wani yayi ba". "Kawai ka kashe banason hayaniya banda ɗan iska ne kai meye abin saurara a waƙoƙin nan ba ma'ana ba komai". "Eh a ƙyaleni ni inaso a haka tafiya dakai matsala ne wllhy Gashua naji ka ƙara nemana rakiya wani wajen ba inda zanje". "ALLAH kayi wasa zan saukeka a tsakiyar hanyar nan". "Ka daɗe baka saukeni ba Gashua". Mujaheed ya faɗa yana dariya, ƙwafa kawai Habeeb ya saki ya maida kanshi kan wayarshi, su dai su Seeyamah suna baya sunajin irin dramar dasu Mujaheed suke tafkawa dama ai abokan wasa ne Neehlah ta ayyana cikin ranta. "Bari dai in ɗan rage volume badan halinka ba karka tadamin iska yanzu". yayi maganar yana ƙara sakin wata dariyar tareda kai hannu ya rage ƙarar, dariya ce sosai ta kama Neehlah jin abinda Yah Mujaheed ya faɗa wai karya tada masa iska amma ba damar yi dole ta haɗiye abarta ta sunkuyar da kai tana murmushi, Mujaheed yana kallonta ta mirror'n motar dai dai lokacin ta ƙara ɗago kai suka haɗa ido ya ɗage mata gira haɗi da kashe mata ido tayi saurin ƙara maida kanta ƙasa tana murmushi. Tun daga nesa ya hango wani ƙaton boutique a side ɗinsu na dama dan haka yayi U town yadawo ɓangaren dama har zuwa daidai boutique ɗin yayi parking tareda kashe motar. "Gashua munzo fa ka fito muje". "Waye zaije ɗin? kuje dasu kawai malam ga ATM nan a biyasu". ya ida maganar yana karkacewa ya zaro ATM ɗin ya miƙawa Mujaheed "No ka barshi kawai zan biya kasan kyautatawa maraya ba ƙaramin lada ne dashi ba". cewar Mujaheed, baki kawai Habeeb ya taɓe tareda ɗage kafaɗu ya maida ATM ɗin aljihu, fita Mujaheed yayi ya buɗewa su Seeyamah da har lokacin basu fita daga motar ba "Bismillah ƴanmata". yace yana murmushi idanunsa akan Neehlah yana jifanta da wani irin kallo wanda duk kunya ta kamata, fita sukayi ya rufe ƙofar sannan suka jera a tare zuwa cikin boutique ɗin. Ƙaton gaske ne ga uban kaya cike sai wanda mutum ya zaɓa matsalar dai kawai duk English wears ne da dogayen riguna dan haka Mujaheed ya yanke shawarar idan sun fita saisu biya inda ake saida abinda ya shafi atamfofi da laces, kasa ɗaukar komai Seeyamah tayi ganin haka yasa Mujaheed yace Neehlah ta zaɓar mata, nan fa Neehlah ta shiga zaɓa Seeyamah tace batason masu wando hakan yasa Neehlah ta fara duba mata masu skirt irin masu faɗin nan tace banda masu matsewa. Ruwan ido yasa har aka ɗauki wani lokaci Neehlah bata zaɓi kayan kirki ba Seeyamah da Mujaheed dai suna biye da ita a baya sai faman surutu take zabgawa. Jin shiru shiru basu fitoba yasa haushi ya kama Habeeb ganin yadda suka shanya shi haka tun ɗazu sun manta dashi number Mujaheed ya kira, yanajin kiran dama ya ayyana da ƙyar idan ba Gashua bane yana dubawa kuwa yaga shi ɗinne murmushi ya saki yayi picking yakai wayar kunnenshi tun kafin yayi magana yaji muryar Habeeb na faɗin "Wai uwar me kuke zaɓa ne haka MJ?". "Ban saniba dalla malam in kana jira ka jiramu in baka iyawa ka tafi abinka ɗan takurar bala'i". Bai jira cewar shi ba ya katse kiran yana dariya yasan ya gama kunna shi, ƙwafa yayi yana sakin huci wllhy Mujaheed ya gama rainashi bari ya tafi ɗin sa nemi abinda zai dawo dasu gida. "Oh my God". ya furta hakan a hankali yana lumshe ido lokaci ɗaya yana shafa sumar kanshi daga gaba zuwa baya tunawa da yayi key ɗin motar baya wajensa yana wajen Mujaheed tsaki yaja ya ƙara dannawa Mujaheed wani kiran "ALLAH ya shiryeka abokina". Mujaheed ya faɗa a fili yana ƴar dariya gami da picking yakai kunnenshi yana jiran yaji abinda zai faɗa "Ka fito ka kawomin key ɗin yanzu". "Me zakayi?". Mujaheed yace yana ɗan zaro ido "Ba damuwar ka bace". yabashi amsa a zafafe "Idan kaga na fito to mun gama siyayyar da zamuyi ne ai kanada ƙafafu ka shigo ka karɓa mana mara mutunci". yana faɗar haka yayi hanging calling ɗin yana dariya tareda faɗin "Autar Ummi quickly please wannan yayan naki bai cika M ba". juyowa tayi tana ɗan ɓata fuska ta shagwaɓe murya tace "Kai Yah Mujaheed Yah Habeeb ɗin?". "Ah ba gaskiya na faɗa ba? ke kanki kinsan halin yayanki ai saidai ki take saboda kinajin tsoronshi". Baki ta ɗan taɓe tace "Gaskiya kam Yah Mujaheed kana fama wllhy kaida kuke tare dashi kullum". "To yana iya? ALLAH ya riga ya haɗa ni kaina watarana shakkar shi nake dan dai kawai ina mazewa ne". Dariya Seeyamah da Neehlah sukayi shima Mujaheed dariyar ya shiga tayasu yana ƙara cewa Neehlah tayi sauri ta zaɓi abinda zata zaɓa su tafi kafin Gashua ya fashe..... *_Zan ƙara yawan pages ɗin ko zuwa 35 ne saimu tsaya kafin mu ɗora book two ALLAH ya bada ikon siya amin_* Afwan da yadda yanayin typing ɗin yake zuwa ban cika jin daɗi ba ga hidimar iyali ALLAH yasa mudace. Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 09139964697 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💥 (Home of expert & perfect writer's). _*Anata tambaya ta book one ya ƙare ne? ƙasan page ɗina na yau na sanar cewar zan ƙara 5 pages saɓanin baya danace iya 30 page book one zai ƙare yanzu zai ƙare ne a 35 pages fatan kun fahimta nagode sosai 💖*_ No 31 Kamar yadda Mujaheed ɗin ya faɗa kuwa Habeeb ya cika yai fam ƙiris yake jira ya fashe sai faman girgiza ƙafa yake yana cije baki shi damuwarshi ma yadda Mujaheed yake kunyata shi a gaban ƙananan yaran su Neehlah daya sani ma tun farko da Mujaheed ɗin ya haɗasu suka taho shi yayi zamansa dan dai kawai kuma Ummi zatace baibi umarnin ta ba. Neehlah dai jin Yah Habeeb nata faman dokawa Mujaheed kira yasa ba shiri sauri sauri ta zaɓi abinda ya kamata ta zaɓa ɗin daga kan English wear dogayen riguna, huluna takalma da sauran kayayyakin adon mata, wajen biya sukaje Mujaheed ya biyasu aka zuba musu a ƙatuwar leda sannan suka fito ma'aikacin wajen ya biyosu da kaya niƙi niƙi booth ya buɗe masa yasa a ciki lokacin har su Seeyamah sun shiga motar, shima Mujaheed zagayawa yayi ya shiga driver seat ya zauna ya kalli Gashua wanda tun fitowar su ya ƙara haɗe rai yana faman muzurai. "Yadai Mr Habeeb Gashua mun barka kanata jira ko?". cikin salon tsokana yayi maganar yana dariya, idan kujerar da Habeeb yake zaune kai tayi magana to shima ya tankawa Mujaheed, wata dariyar Mujaheed ya ƙara saki yace "ALLAH dai ya biya Ogah mun tuba ayi mana afwah kanmu bisa ƙafafunmu". ya ƙarasa maganar yana kama kunnuwan shi. "Na rantse zan fasa maka baki Mujaheed". ya faɗa a hasale yana kallonshi, ido Mujaheed ya zaro tareda buɗe baki yace "ALLAH ya baka haƙuri Boss". Tsaki Habeeb ya saki yayi relaxing kan seat ɗinshi ya rufe idanunshi gami da harɗe hannayenshi kan ƙirjinshi yana faman jijjiga ƙafafu, motar Mujaheed ya tayar ya harbata kan titi suka tafi. Tunda suka tafi ba wanda yayi magana a cikinsu har suka isa Mudassir & brothers shi Habeeb ma duk zaton shi gida suka dawo dayaji anyi parking yana buɗe idanunshi ya gansu a wani waje daban Mujaheed ya kalla kafin yace "Nan kuma ina ka kawomu MJ?". "Mudassir & brothers ne". Mujaheed ya bashi amsa. "Ina ne haka?". yace yana yamutsa fuska. "Wajen siyar da atamfofi ne da sauran manyan kaya can inda muka baro babu irinsu". Shiru kawai yayi baice komai ba hakan yasa su Seeyamah suka fita suka tsaya suna jiran Mujaheed ɗin ya fito su shiga. "Yanzun ma bazaka shiga ba Gashua?". cewar Mujaheed yana kallonshi. "Ka fini sani ai". amsar daya bashi kenan yana danna waya. "Sorry yanzu zamu fito ba daɗewa zamuyi ba". Mujaheed yace yana ƙoƙarin buɗe murfin motar ya fita. "Ku daɗe ma mana kagani idan banci ubanka ba daga kai har su ɗin". dariya kawai Mujaheed yayi ya fita daga motar ya maida murfin ya rufe, relaxing ya ƙara yi sosai yana latsa waya yau dai yaga ta kanshi sai yawo ake dashi cikin gari. Mujaheed bai daɗe da shiga ba kiran abokin nan nashi da suka haɗu a Dubai lokacin dayaje karatu can ya shigo wayarsa Auwal Mahmoud Azare wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen koyawa Gashua hausa ba laifi suna zumunci ta waya bayan ƙare karatunsu kuma shima Auwal ɗin ne ya fara nemansa, murmushi yayi yai picking tareda kai wayar kunnenshi saidai bai furta komai ba shima Auwal yasan bazai furta ɗin ba dan haka yace "ALLAH ya taimaki Ogah". "Azire ya kake?". Dariya Auwal yasa yana faɗin "Azare nefa sunan mutumina tun zamanin school nake gyara maka amma har yanzu baka iyaba". Haɗe rai Habeeb yayi yace "Kai ka sani dai". Wata dariyar Auwal yayi yace "Na shigo garinku fa yau Kano yanzu haka ina cikinta". "Serious?". "Yeah munzo ɗaurin aure ne na wani abokin mu daya auri ƴar Kano so su sun wuce ma tun ɗazu nikuma na wuce Mandawari gidan wani kawuna sai gobe zan wuce da safe nace bari in nemeka mu gaisa". "Oops gashi bana gida yanzu ya za'ayi inaso mu haɗu". "Kana ina?". Kai ya ɗaga ya ƙara kallon ginin dan harya manta sunan da Mujaheed ya faɗa masa ɗazu sunan wajen ya faɗawa Auwal yace ba matsala gasu nan zasuzo shida ɗan kawun nasa zai rakoshi daga haka suka katse wayar. Nan ma siyayya sosai Mujaheed yayiwa Seeyamah harta rasa bakin magana harda Neehlah itama saida yayi mata tata siyayyar. Cikin ma'aikatan wajen ne ya rakosu da kayan wajen mota bayan sun biya akasa musu a booth. Mujaheed na shirin tada motar bayan su Neehlah sun shiga yaji Habeeb yace "Wait.....akwai wanda nake jira zaizo yanzu". "Waye?". Mujaheed ya tambaya "Auwal wanda mukayi school ɗaya a Dubai". yabashi amsa batare daya kalleshi ba. "Maimakon yaje gida ya jiramu Gashua?". "Ina ruwanka? ban cika son shisshigi cikin al'amurana ba". yace yana harararshi, baki Mujaheed ya taɓe bai dai ce komai ba. Nan suka cigaba da zama kowa ya kama waya yanata danne danne har zuwa lokacin dasu Auwal suka ƙaraso wajen, Habeeb da Mujaheed suka fita suka taresu. Jikin motar Auwal suka tsaya suna gaisawa da tambayar bayan rabuwa sosai Habeeb yayi murna da ganin Auwal Mujaheed dayake yanada saurin sabo nan da nan suka saba da Auwal da ɗaya saurayin daya rakoshi Abbas. Wayarshi dake hannunshi ya nemo number Neehlah ya kirata cikin faɗuwar gaba ta ɗaga kiran, tana kai kunnenta taji shi cikeda faɗa yana faɗin "Idan kika sake nazo wajen nan saina karya ki dan ubanki kina ganina da baƙo kinfi ƙarfin kizo ki gaisheshi ko?". bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar. "Yaa ALLAH". Neehlah tace tana dafe goshinta shidai mutumin nan idan bai ƙaƙalo laifi ya ɗorawa mutum ba bayajin daɗi yanzu meye laifinta anan? hannun Seeyamah taja tana faɗin "Please Sisi zo ki rakani in gaishe da baƙon Yah Habeeb kafin a karyani a kanshi". Fuska Seeyamah ta yatsina tace "Nidai kam Neehlah da kinje kin dawo kawai nifa tsoron yayan can naki nake wllhy". "Dan ALLAH kizo muje please banason zuwa ni kaɗai wllhy". Ganin yadda duk ta damu yasa Seeyamah ta buɗe murfin motar ta fita itama Neehlah ta fita suka nufi inda su Habeeb suke tsaye. Tunda suka doso inda suke Auwal ya kafe Neehlah da kallo yanajin wani irin al'amari na shigar shi wanda bai taɓa tsintar kanshi cikin yanayin ba, har suka ƙaraso bai ɗauke idanunshi daga kanta ba wanda har Mujaheed da Abbas dake tsaye a wajen suka gane hakan Habeeb dai baisan me akeba dan kanshi na ƙasa da waya a hannunshi, tsaki Neehlah taja cikin ranta ganin irin kallon ƙurillar da wannan abokin na Yah Habeeb yake binta dashi kamar wani maye, rissinawa sukayi suna gaisheshi lokacin da suka ƙarasa Auwal ya amsa yana wani washe baki, tunda Mujaheed yaga haka wani irin ɓacin rai ya kamashi zuciyar shi ta dinga tafarfasa kawai sai yayi musu sallama ya koma cikin mota ya zauna. Su Neehlah ma suna gaisheshi suka dawo wajen motar su, ta cikin glass ɗin motar Mujaheed yake kallon yadda Auwal yabi bayan Neehlah da kallo kamar zai biyota sai wani murmushi yake yana shafa sumar kanshi tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka yaji a lokacin ko ba'a faɗa masa ba yasan da wani abu a cikin zuciyar Auwal ɗin lallai lokaci yayi daya kamata ya fallasa sirrin zuciyar shi bai taɓa zama yayi maganar data danganci soyayya da Neehlah ba ada bai taɓa tunanin ma sonta yake ba ya ɗauka duk soyayya da shaƙuwa da sukayi na ƴan uwantaka ne sai baya bayan nan ya gane cewar sonta yake. Suna zuwa suka shiga motar Neehlah na ƙara jan wani tsakin ta tsani kallo a rayuwarta kuma tanajin idanun mutumin a kanta lokacin da suka juya baya, shima Abbas wanda suke tare da Auwal mota ya shiga yana jiran Auwal ɗin. "Mutumina wai wace wannan yarinyar da kuke kama da ita ne? badai ƙanwarka bace?". "Yes she is my sister". habeeb ya bashi amsa. "Wow masha ALLAH amma baka taɓa faɗa min kanada ƙanwa haka ba Gashua". Auwal yace yana murmushi. "Kasan komai kamawa take". cewar Habeeb. "Gaskiya ne amma fa she's very beautiful tayi ba ƙarya yaushe zakuyi mata aure ne?". Sai daya dalla masa harara kafin yace "Ina ruwanka?". dariya Auwal yayi yace "Kaifa ba'a maganar arziƙi dakai abokina naga dai ƙanwarmu ce kuma kasan hausawa sunce idan kaga kare yana shinshinar takalmi to ɗauka zaiyi". Wani banzan kallo Habeeb ya jefawa Auwal yace "Kunada matsala wllhy shiyasa dole ƙananan yara su rainaku bakuda girma saina jikinku". "Eh munji ɗin kaidai har yanzu bazaka canza ba wannan shegen son girman naka yana nan muna nan mun zuba ido muga wadda zaka aura". "ALLAH ya tsareni da auren ƙaramar yarinya kowa ma mara aikin yine irinku". "Lokaci ne zai nuna mana hakan dude kaidai kayi addu'ar ALLAH yasa karka folawa ƙaramar yarinya wllhy duk wani girma da jiji da kai bakasan lokacin da zaka saukeshi ba kazo kana ƴar murya". Tsaki Habeeb yayi kawai duk ya ɗauki maganganun Auwal ɗin shirme auren ƙaramar yarinya ko ɗorawa kai wahala. Sallama sukayi da Auwal wanda yake ta ƙara yimasa maganar Neehlah yaƙi kulashi Auwal ya shiga motar shi shima Habeeb ya nufi tasu motar. Tunda suka tafi Mujaheed baiyi magana ba jin ranshi yake duk ba daɗi shi kanshi habeeb ya lura da canjin yanayin da Mujaheed ɗin ya shiga ya buɗe baki ya tambaye shi dalilin hakan ne yake jin wahala. Neehlah da Seeyamah ma sun kula da Mujaheed ɗin ya daina walwala duk da basu san meya canza shi ba. Hanyar unguwar su ya nufa yana faɗin "Su fara zuwa can ɗin basai ya koma ta gidansu ba, Habeeb dai bai tankashi ba har zuwa gidan su Mujaheed ɗin daga nan yayi musu sallama ya sauka Habeeb ya koma driver seat ɗin dan cigaba da tuƙin, amma maimakon ya fara driving ɗin saiya ɗauki waya kawai ya fara dannen dannen waya, kallon juna Seeyamah da Neehlah sukayi cikin mamaki..... Afwan kamar kullum😁 _A ƙara haƙuri dai yanayin labarin ne yanada tsayi sosai so banaso muyi gaggawa mubi komai hankali har zuwa lokacin da ALLAH zaisa muje inda mukeson zuwa_ Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 09139964697 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 32. Sunfi ƙarfin 20min a wajen batare da sun tafi ba kokuma ya buɗe baki yace musu wani abu gaba ɗaya sun gaji da zaman cikin motar, hankalinshi kwance yake latse latsen wayarshi. Sai zuwa yanzu ne Neehlah ta fara tunanin dalilin dayasa yaƙi tafiya idan suka tafi a haka ya zama kamar wani direbansu kenan ya buɗe baki yace wata ta dawo front seat a cikinsu shine ba zaiyi ba kai jama'a ALLAH ya shiryi mutumin nan. Bakinta takai saitin kunnen Seeyamah ƙasa ƙasa kamar munafuka tace "Sisi ki taimaka ki koma gaba nasan abinda yasa yaƙi tafiya kenan wllhy ba kuma zai buɗe baki yace wata a cikinmu ta koma ba". Ido Seeyamah ta ɗan zaro itama cikin ƙasa ƙasa da murya tace "Nifa tsoronshi nakeji Neehlah please ke ki koma gaban". Kai Neehlah ta girgiza tana shagwaɓe fuska tareda zungurin Seeyamah cikin raɗa tace "Please and please Sisi kar muyi haka dake mana". Kan dole Seeyamah ta buɗe murfin motar ta fita jikinta har rawa yake ta buɗe front seat ta zauna, bai juyo ya kalli wadda ta zauna ɗin ba haka kuma bai bar danna wayar dayake ba, Seeyamah gaba ɗaya a tsorace take gani take kamar zaiyi mata wani abun. Saida aka kwashi kusan mintuna biyar sannan ya ajiye wayar ya tada motar suka tafi a tare Neehlah da Seeyamah suka saki ƙaramar ajiyar zuciya, tafiyar kurame dai aka ƙara yi har zuwa lokacin da suka ƙarasa gida. Idi mai bawa fulawa ruwa shine ya shigar musu da kayan sukabi bayanshi, Habeeb ma kuwa cikin motar suka barshi sukayi gaba Neehlah na faɗin tunda dai sun fito lafiya alhmdulillah yau dai Mr ɗacin rai ya zama direba. Bedroom ɗin Ummi suka fara shiga suka sanar da ita dawowarsu tayi musu sannu da zuwa daga nan suka wuce nasu bedroom ɗin lokacin anata kiran sallahr magreebah, suna shiga sukayi alwalah suka gabatar da farali sannan suka koma bedroom ɗin Ummi suna nuna mata kayan anan Neehlah take faɗawa Ummi ai duk Yah Mujaheed shine ya biya kuɗin siyayyar Ummi taji daɗi sosai ta shiga sa masa albarka. Bayan sallahr Esha'e Ummi ta shiga gidan su Hajiya Inna zuwa lokacin tasan Alhaji Sulaiman yadawo gida dan tanaso tayi magana dasu, part ɗin Alhaji Sulaiman ɗin ta fara shiga suka gaisa dashi da matarshi ta sanar dashi akwai maganar datake so suyi dashi da Hajiya nan yace mata taje sashin Hajiyan ta jirashi zaizo. Cikin tsantsar kulawa da mutunta juna Ummi da Hajiya suka gaisa daga nan suka fara taɓa hira har lokacin da Alhaji Sulaiman ya shigo sashen. A tsanake daki daki Ummi ta shiga yiwa su Hajiya bayani daga lokacin da Mujaheed yazo mata da bayanin komai da gidan dataje ta ɗauko yarinyar ta maida ita gidan marayun ta gangaro kan ɗauko yarinyar datayi zuwa gidanta dan cigaba da riƙonta a taƙaice dai tana neman afwarsu na yadda ta yanke hukuncin ɗaukar yarinyar ba tareda neman shawarar su ba. Sunyi mamaki ƙwarai kuma daga Hajiya har Alhaji Sulaiman sunga sanarwar da akayi ta sace yarinyar ashe habeeb ne ya ɗauke ta, sai yanzu Hajiya ta fara tunano lokacin daya shigo yaga Heedayah a wajenta irin yanayin daya shiga da kuma neman ƙarin bayani dayazo ji a wajen ta ikon ALLAH kenan Heedayah ƴan biyu ne? to amma kuma Ramlah bata taɓa faɗa mata ba tace mata Heedayah ita kaɗai ce ƙanwarta, idan hakane kuwa itama zataso ace Habibu ya binciko musu gaskiyar lamarin abin akwai ɗaure kai sosai. Duk cikinsu ba wanda ya kushe abinda Ummin tayi saima yaba mata da sukayi taimakon maraya ai ba ƙaramin lada gareshi ba ubangiji yanason masu taimakawa marayu kuma ɗa na kowa ne, sun ƙara tattauna maganar sannan Ummi tayi musu sallama zata tafi Alhaji Sulaiman na ƙara jaddada mata duk hidimar yarinyar idan ta tashi ayi masa magana Ummi tayi godiya, daf da zata fita daga falon ta tsinkayi muryar Hajiya na faɗin gobe ta turo mata Neehlah da yarinyar cikin girmamawa Ummi ta amsa mata da insha ALLAH zata turosu. Har ta fito ta tuna da maganar Aleeyu ta sake komawa ta roƙi alfarmar ya taimaka ya samar masa wani aikin cikin harkokin kasuwancinsa, ba tare da wata gardama ba ya amince yace insha ALLAHU zai duba yagani mutumin yanada sauƙin kai godiya Ummi tayi ta fita. Bayan fitar Ummi ma su Hajiya sun ɗan jima suna tattauna maganar da Alhaji Sulaiman har lokacin Hajiya bata daina jinjina al'amarin ba tana ƙara faɗa masa irin tsananin kamannin da yarinyar suke Heedayah mai zuwa wajenta ta yadda ba yadda za'a ga ɗaya ace ba ɗayar bace shi kanshi Alhaji Sulaiman yayi mamaki sosai. Sai bayan ta koma sannan sukayi dinner, yau basuyi zaman kallo bama suna gama dinner suka haye upstairs suka shige bedroom Neehlah ta taya Seeyamah jera kayan da aka siyo a wardrobe su kuma manyan aka ware su za'a yiwa mai yiwa su Ummi magana yazo ya karɓa a ɗinka mata. Ummi ma bata daɗe ba ta tashi ta bar falon, lokacin daya shigo ba kowa a falon sai a lokacin ne yazo yin tashi dinner bai wani ci abincin kirki ba ya tashi ya haura sama yaje ya yiwa Ummi saida safe ya sauko ya fita ya koma nashi side ɗin. ★★★______★★★ Washegari bayan sun gama breakfast Ummi ta cewa Neehlah suje da Seeyamah su gaida su Hajiya. Hajiya sakin baki tayi tana ƙarewa Seeyamah kallo har Seeyamahn ta fara tsarguwa da irin kallon da Hajiya take mata tunanin Hajiya anya ba raina mata hankali akayi ba kuwa ya za'ayi ace wannan ba Heedayah bace? kai al'amarin nan akwai ban mamaki da ɗaurewar kai duk yadda taso ta gasgata eh da gasken ba Heedayah bace ta kasa dan haka ta kira number Aunt Ramlah tace ta haɗata da Heedayah a take Aunt Ramlahn ta miƙawa Heedayah wayar dama suna zaune a falone dukansu lokacin, gaisawa kawai sukayi Hajiya ta kashe wayar 'Qadeeran Alaa man yasha'u'. Hajiya ta furta cikin zuciyar ta, lallai al'amarin ubangiji da girma yake wannan yafi ace kama kawai suke da juna komai ɗin ne iri ɗaya. Sun ɗan jima a gidan sannan sukayi mata sallama suka biya ta sashin Alhaji Sulaiman suka gaishe da Hajiya Rahma matarshi shi a lokacin ma ya riga ya fita, har suka fito daga part ɗin Hajiya Rahma batasan ba Heedayah bace duk zatonta itace yau ma tazo gidan. Tun daga ranar da sukaje siyayya Seeyamah bata ƙara saka habeeb a ido ba ita hakan ma saiyafi mata daɗi, tana matuƙar jin daɗin zama a gidan koyaushe Ummi cikin janta a jikinta take haka Neehlah sunyi shaƙuwar ban mamaki cikin ƙanƙanin lokaci suna waya da ƙasashen ta na gidan marayu da kuma wasu daga cikin shugabannin gidan marayun ana jin lafiyar juna a wayar Neehlah. Yammacin Lahadi. Habeeb ne ya fito cikin shirin shi na ƙananun kaya kamar yadda ya saba, baƙin wando da brown ɗin riga mai dogayen hannu ƙafarshi sanye cikin rufaffen takalmi na zallar fata baƙi hannunshi kuma ɗaure da agogon fata kalar brown, sai ƙamshi yake bazawa motarshi ya shiga ya fita daga gidan kai tsaye rijiyar zaki ya nufa gidansu Heedayah bai manta gidan ba duk da cewar wancan zuwan da yayi da dare ne lokacin da Hajiya ta haɗashi da mara kunyar yarinyar nan ya kawota dayake a farkon layin ne gidan. Sai bayan isar shi ƙofar gidan ne ya tuna cewar bama lallai idan yasamu Muhammad ɗin a gida ba. "Yaa salaam". ya faɗa ƙasa ƙasa yana dafe goshinshi tareda hura iskar bakinsa yana ƙara kallon gidan ta cikin motarshi so yake ya samu Muhammad ɗin su fara maganar duk da baisan yadda zai ɗauki maganar ba, fita yayi daga motar yana ƙarewa unguwar kallo kafin ya fara takawa cikin takun nutsuwa ya isa bakin gate ɗin gidan ya ƙwanƙwasa ba daɗewa maigadi ya buɗe ƙofar ya leƙo dan ganin mai bugawa, gaisawa sukayi kafin maigadin ya tambaye shi lafiya wa yake nema? tambayar shi yayi ko maigidan yana nan?. "Kai maigadin ya gyaɗa yace "Kaci sa'a bai daɗe da dawowa gidan ba wa za'a ce yana magana?". Wa zaice masa ne? ya tambayi kanshi yana shafa sumar lallausar sumar kanshi. "Kace masa daga gidan Alhaji Sulaiman ne". "Toh bari a sanar dashi". maigadin ya faɗa tareda juyawa ya rufe ƙofar. Mintuna kaɗan ya ƙara buɗe ƙofar yace "An sanar dashi zuwanka yace a faɗa maka yana fitowa". "Thank you so much". yace a hankali tareda kai hannu aljihun shi na baya ya ciro kuɗi ba tare daya ƙidaya su ba ya miƙawa maigadin, hannu na rawa ya durƙusa har ƙasa ya karɓa ya shiga zabga godiya bai bi takan shi ba ko ya tsaya saurarar godiyar dayake masa ba ya juya ya koma wajen motarshi ya jingina a jiki ya harɗe hannayenshi kan ƙirjinshi ya zubawa gidan idanu. Uncle Muhammad yana fitowa yayi ido biyu dashi ido ya ɗan zaro yana mamakin abinda ya kawo shi yau Mr. Habeeb Ibraheem Ahmad Gashua C.E.O a H.I.A GASHUA ENTERPRISES ne a gidansa? kuma yake nemansa? da sauri ya ƙarasa fuskarshi ɗauke da murmushi cikin girmamawa Uncle Muhammad ya miƙa masa hannu sukayi musabaha ALLAH ALLAH Uncle Muhammad yake yaji abinda ya kawo Mr. Gashua gurinsa sai faman saƙawa da kwancewa yake a cikin ranshi. "Nasan kayi mamakin abinda ya kawoni wajenka ko?". Habeeb yace yana gyara tsayuwar shi, ƴar dariya Uncle Muhammad yayi yace "Ƙwarai kuwa yallaɓai ALLAH yasa dai ba wani laifin mukayi ba?". Kai kawai Habeeb ya girgiza masa alamun a'a, shiru Uncle Muhammad yayi yana jiran Habeeb yayi magana, sai daya ɗan jima kafin yace "Magana ce akan ƙanwar matarka wadda take zaune a gidanka". "Heedayah?". Uncle Muhammad yace cikin sigar tambaya. "Yes". Gashua yace yana jijjiga kai dan gaba ɗaya yama manta sunan nata. "ALLAH yasa lafiya yallaɓai". cewar Uncle Muhammad. "Magana ce nakeso muyi dakai ta sirri a kanta wata magana bata taɓa haɗaku da ita ba game da yarinyar?". "Kamar tame fa yallaɓai?". Duk saiya rasa abinda zaice masa shifa bai saba irin wannan ba to me zaice masa ne ma? ya tambayi kanshi yana murza fatar goshinsa da hannu ɗaya ɗayan kuma ya sokeshi cikin aljihu. "Yallaɓai ina saurarar ka". Uncle Muhammad ya faɗa cikin girmamawa. Numfashi ya ɗan sauke kafin yace "Kwanaki bakaga wata yarinya da ake sanarwar ɓatan ta ba a gidajen talabijin da kafofin yaɗa labarai?". "Ƙwarai kuwa mun gani". Uncle Muhammad yabashi amsa "Kaga kamar su ɗaya da yarinyar gidanka ko?". Maryam Ibraheem Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF. *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 33. "Kaga irinsu ɗaya da yarinyar gidanka ko?". "Gaskiya ne muma munyi mamaki sosai lokacin da muka gani". "Bakayi zargin wani abu ba lokacin daka gani?". ( Su Gashua yau an zama ɗan jarida ba jin kai wajen yin magana ). Cikeda rashin fahimta Uncle Muhammad yake kallonshi ƙasan ranshi yana tunanin ina ruwan Mr. Habeeb ɗin da har yakeson jin ƙwaƙƙwafi. "Eh to banyi zargin komai ba gaskiya tunda inada tabbacin Heedayah ƙanwar Ramlah ce". "Ita ta tabbatar maka da hakan?". Gashua ya ƙara jefa masa wata tambayar, zuwa lokacin dai Uncle Muhammad ya fara gajiya da waɗannan tambayoyin na Mr. Habeeb mutum saikace wanda yayi karatun jarida? shikam gaskiya duk dayake ganin mutunci da ƙima na Habeeb ɗin bazai iya fallasa wannan sirrin ba idan yayi haka kamar yaci amana ne dan haka kawai saiya jijjiga masa kai alamun tabbatarwa. Shiru Habeeb yayi yana tunani kafin can wata dabara ta faɗo masa yace "Please ko zan iya ganin ita Heedayahn?". Kawai dan babu yadda zaiyi ne ya ɗaga masa kai saboda wani irin kwarjini dayayi masa cikin idanunshi wanda ubangiji ya halicce shi dashi. "Bismillah muje daga ciki". Uncle Muhammad ya faɗa yana nuna masa hanya, har ciki yayi masa jagora ya kaishi wani ƙaramin sitroom a cikin compound ɗin da alamu na saukar baƙi ne. "Bismillah ka zauna bari ayi mata magana". cewar Uncle Muhammad yana juyawa yabar wajen, bai zauna ɗin ba saiya shiga ƙarewa ɗakin kallo kujeru ne masu kyau ba laifi sai carpet a tsakiyar kujerun da ƙaramin center table a kai bayan haka ba komai a cikin ɗakin. A bedroom yasamu Aunt Ramlah tana haɗa kayan wankinta da za'a haɗa a kaiwa mai wankewa sai Nusrah dake kwance kan gado tana barci Nu'aym dama baya gidan sunje weekend shida Zainab gidansu Muhammad ɗin dama yanzu can take yin weekend ɗinta. A taƙaice Uncle Muhammad yayiwa Aunt Ramlah bayanin komai ya faɗa mata kuma ta tura Heedayahn sitroom ɗin baƙi a zuwan takai masa ruwa da lemo kawai, ita kanta Aunt Ramlahn tayi mamaki ta fara tunanin dalilin dayasa yakeso ya tono *RUFAFFEN SIRRI* wanda ya daɗe a rufe mutumin ma da takejin labarinshi wajen Hajiya mugun miskili ne baya shiga harkar kowa kuma Heedayah ma ta bata labarinshi ance fa ko dariya bayayi to meya sakoshi cikin lamarin?. Taso tayiwa Uncle Muhammad ɗin musu tsoronta ɗaya kar yaje ya faɗawa Heedayah wata maganar har wani zargi ya ɗarsu cikin zuciyarta abu yazo ya caɓe ba laifin wanda za'a gani sai nata musamman su Baba waɗanda koda wasa basa ƙaunar a nunawa Heedayah wani abu ko kaɗan ne wanda zaisa tayi tunanin wani abun a cikin zuciyar ta, dan dole ta nufi bedroom ɗin su Heedayahn dan cika umarnin mijinta. A gaban mirror tasamu Heedayah tana shafa lotion fitowar ta wanka kenan bayan ta zura doguwar riga milk color. "Yauwa Heedayah Abban Nu'aym ne yayi baƙo zaki kai masa ɗan abin taɓawa yana sitroom". Aunt Ramlah ta faɗa bayan shigar ta bedroom ɗin. "Tom bari inzo". ta amsawa Aunt Ramlahn tana ajiye powder hannunta data gama shafawa. "Okay kiyi sauri". Aunt Ramlah tace tana juyawa tabar bedroom ɗin, lipglosses ta shafa ya ɗauki shinning sai kwalli datasa ta taje girarta ta kwantar da ita dama a ƙa'idar ta sam bata jagira saboda ALLAH ya hore mata tarin gashin gira a ganinta ɓata lokaci ne ta tsaya ƙarawa da wani abu. Turare ta shafa sannan tayi rolling da mayafin rigar ta zura plat shoes fari ta fito zuwa falon kitchen ta wuce tasamu Aunt Ramlah ta haɗa komai a tray ruwa lemo da snacks karɓa tayi ta fito ta fita daga falon Aunt Ramlah ta sauke numfashi tana bin bayanta da kallo. Cikin siririyar muryar ta tayi sallama wadda ta haddasawa Gashua faɗuwar gaba da baisan dalilin taba ya ɗan runtse ido yana cije lips ɗinshi na ƙasa, kasancewar ya bata baya yasa sam bataga ko waye ba kan center table ɗin ta ajiye tray ɗin ta buɗe ruwan ta fara zubawa a glass cup lokaci ɗaya tana gaisheshi jin ba'a amsa ba yasa ta ɗago kai taga wane isasshen ne wannan? tayi sallama bai amsa ba kamar wani arne yanzu kuma ta gaisheshi a matsayin shi na wanda yake gaba da ita still dai bai amsa ba to me yake taƙama dashi ne? ta tsani dizgi a rayuwar ta. Ido ta ɗan zaro ganin wanda ke hakimce akan kujerar ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana faman basarwa, dama shine baƙon Uncle Muhammad ɗin? to ya akayi suka san juna? kin manta Uncle Muhammad ɗin yaron Alhaji Sulaiman ne wanda yake kawu a wajen nunar ranar? wata zuciyar ta faɗa mata haka, sosai gabanta ya faɗi ALLAH ALLAH take ta gama zuba ruwan ta fece dan alamun wannan mutumin ba mutunci zaiyi ba. "Nagode nunar rana". kalmar data faɗa masa ranar daya dawo da ita gida ta faɗo mata a rai da alamu kuma bayason sunan, tsaye taga ya miƙe cikin salon tafiyar shi na gayu da ƙasaita ya nufi bakin ƙofar falon ya tsaya yayi bake bake hannayenshi duka ya sokesu cikin aljihun wandonshi yana binta da wani munafukin kallo wanda ba kowa ne zai fahimci kallon nata yake ba. Tuni glass cup ɗin datake zuba ruwan ya kusa cika amma dayake hankalinta sam ba'a wajen yake ba sai dataji ruwa yafara taɓa hannunta data dafa center table ɗin alamun ya cika harya fara zubewa sannan ta ankara, da sauri ta ajiye robar ruwan ta miƙe tsaye da alamu fa guy ɗin nan ɗan neman fitina ne ji yadda yazo ya wani tare mata ƙofar fita ƙundunbala tayi kawai ta nufo bakin ƙofar kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta. "Excuse me". tace bayan ƙarasowar ta wajen har lokacin bata ɗago kai ta kalleshi ba, ido ya ɗan rufe ya buɗe yana tuno lokacin da Jawaheer itama ta faɗa masa hakan lokacin daya tsaya jikin motar ta muryar tasu ma kanta iri ɗaya ce bambancin su kawai waccan cikin ɓacin rai da hayaniya ta faɗa wannan kuma kamar irin wadda tayi laifi aka ritsata ɗin nan. Maimakon ya matsa ɗin saima ya ƙara gyara tsayuwar shi ya kankane ko ina yana mata kallon ƙasan ido har lokacin bai cire hannayenshi daga aljihunshi ba. "Ple....a..sse". tayi maganar a rarrabe cikin yanayin shagwaɓa wanda har saida ya ɗan lumshe idanunshi yayi saurin buɗesu a kanta yana ƙara matsawa kusa da ita tayi saurin ja baya ya ƙara binta ta ƙara yin baya taci karo da kujera wadda dolenta tasa ta tsaya ta ɗago kai tayi ƙwal-ƙwal da ido tana kallonshi hannunta akan gefen mayafinta tana wasa dashi ƙirjinta sai bugawa yake kamar wadda tayi tseren gudu gashi kusancin nasu yayi yawa duk yabi ya cikata da sassanyan mayen ƙamshin shi mai matuƙar daɗi da sanya nutsuwa hannu ɗaya ya zaro yakai kanshi yana shafa sumar shi yace "Ke Heedayah kike ko Hadiye wuce ki koma ciki ki zauna inason magana dake". ya ƙarasa maganar yana ɗage mata girarshi guda ɗaya. Baki ta tura cikin jin haushi tace "Wace magana ce? ni koma meye ka faɗamin a haka amma fa bayan ka matsa baya". ta ƙarasa maganar cikin ƙunƙuni tana ƙara kumburo baki, bakin nata dama yake ta kallo tun ɗazu yadda take juyashi tana magana yanata faman ƙyalli bai taɓa tunanin akwai wani abu dazai ɗauki hankalin shi a jikin ƴa mace ba sai gashi yau ya shagalta da kallon bakin yarinya yana jin wani irin yanayi a jikinshi daya kasa fassara shi. "Kinsan me zanyi idan baki koma kin zauna ba?". ya tambaye ta yana ƙureta da ido, kai ta girgiza kamar zata sakar masa kuka fatanta da burinta a lokacin ya kauce ya bata waje saboda yadda ya matseta kamar wanda zai shige jikinta. "Rungumar ki zanyi". yace kanshi tsaye murya ba alamun wasa yana wani karkace kai. Kutt lallai dama Man ɗin nan ɗan duniya ne bata saniba? itafa koda wasa akace zai saki irin wannan maganar haka bazata yarda ba, da gaske dama maza basuda kunya duk shiru shirun su kuwa dama kuma ance irin masu simi simi ɗin nan kamar munafukai sunfi sanin takan tsiyar. duk cikin ranta take ayyana waɗannan maganganun bayan ta ƙwalalo ido tareda hangame baki tana kallonshi. "Yes kina mamaki ne? karki ƙara gigin bani umarni ba'a bawa Habeeb umarni saidai shi ya bayar sa'anki ne ni? ko wasa nake dake? Saikace wata ƴar aikinka. ta faɗa cikin zuciyar ta tana ƙara turo baki, kai ya kaɗa yana cije baki kafin yace "Zan gyarawa bakin nan zama yanzu idan baki daina turoshi ba ki ƙara gwadawa kuma ki gani". ya ƙarasa maganar yana zagaye ta ya koma cikin falon ya zauna yayi crossing legs ɗinshi yana wani girgizasu, da harara tabi bayanshi ji take tamkar ta shaƙoshi ya cika rainin hankali wllhy nunar rana kawai. "In taso kiga tsayina ne?". ta tsinkayi muryar shi na faɗa, da sauri ta nufi inda yake ƙasan rug ɗin ɗakin ta nema ta zauna ta sadda kanta ƙasa tana jiran taji maganar dayace zasuyi. Shiru yayi kamar bazai ƙara magana ba harta fara gajiya da zaman ranta fa ya fara ɓaci ALLAH zata masa rashin kunya ta gudu tunda taga alamun shi bashida mutunci. "Daga wane gari kikazo nan?". ya jefa mata tambayar, da mamaki ta ɗago tana kallonshi da tunanin tambayar rainin hankalin dayayi mata, taso tayi banza dashi amma kaifin idanunshi daya kafeta dasu yasa batasan lokacin data furta "Katsina". "Me kikazo yi nan ɗin?". "Karatu". Kai ya jinjina kafin yace "Ya kuke da matar Muhammad?". "Yaya ta ce". "Uwa ɗaya uba ɗaya?". Kai kawai ta gyaɗa masa tanajin tamkar ta fasa ihu wai me yake damun mutumin nan yau? aikin jarida ya koma ne? kokuwa dai bai cikin hayyacinshi inba haka ba meye haɗin shi da ita da zaizo yana mata wasu tambayoyin yaya uwarka ta haifeka. "Ƴan gidan ku basu taɓa nuna miki wata alama ba?". "Alama tame fa?". ta maida masa da amsa. "Baku taɓa zama kunyi wata magana da babanki ko mamanki kan abinda ya shafeki ba?". "Ni bamu taɓa ba". tace tana harararshi ta ƙasan ido haushi duk ya isheta, ƙasa ya ɗan yi da kanshi yana murza fatar goshinshi wanda hakan ya zama kamar wata al'adarshi ne yana yawan yin hakan a lokuta da dama, kai ta ɗago ta dinga zabga masa harara harda murguɗa baki tana ganin zai ɗago kai tayi hanzarin maida nata kan ƙasa tareda miƙewa tsaye zata bar ɗakin dan bazata cigaba da zama yana mata waɗannan tambayoyin na rainin hankali ba. "Sit down ban gama dake ba". ya faɗa cikin haɗe rai yana mata wani irin kallo... Mrs Salees Mu'az 💝 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's) No 34. Second to the last page. Bata koma ta zauna ɗin ba kamar yadda ya umarce ta ɗin tayi tsaye tana tura baki da gunguni wanda baisan abinda take faɗa ba. "I said sit down". yace cikin ɗan ɗaga murya yana buɗe mata ido dan yaga alamun yarinyar magana ɗaya batayi mata. "Ni wllhy bazan zauna ba kawai sai kaita min wasu tambayoyi da ban gane kansu ba". tayi maganar kamar zatayi kuka tana harararshi ta ƙasan ido, kai kawai yake jinjinawa yana kallonta itakam taƙi yarda ma sam ta kalleshi. "ALLAH idan kika bari na tashi zanyi miki abinda bakiyi zato ba so kwanciyar hankalin ki koma ki zauna mu karasa maganar da muke batare da wani yaji kanmu ba kar kiga a cikin gidan ku kike wannan bashi zai hana in hukuntaki ba". Kamar zata saki kuka ta koma ta zauna bakin nan kamar zai taɓo Gashua dake zaune tsabar yadda ta turoshi gaba yau dai tana ganin ikon ALLAH azo har inda take a nuna mata fin ƙarfi da iko ALLAH mutumin nan ba ƙaramin ɗan rainin hankali bane gaban kujerar ya matso sosai yace "Kina kallon TV?". Haushi yasa tace a'a "Why?". ya ƙara jefo mata wata tambayar "Ra'ayi na ne hakan". ta faɗi hakan cikeda rashin kunya, tsaye ya miƙe yana kaɗa kai ya nufo inda take zaune duk da gabanta ya faɗi amma bata nuna alamun haka ba harya ƙaraso gabanta yana zuwa ya ɗora ƙafa ɗaya kusa da ita ya ranƙwafa kanta murya ba alamun wasa yace "Zaki faɗa min gaskiya kokuwa saina baki mamaki yanzun nan?". "Nifa gaskiya na faɗa maka". tace kamar zatayi kuka harga ALLAH ta fara gajiya da halin mutumin nan. "Wai ina wasa dake ne? bazaki faɗa min gaskiya ba". Ganin yadda ya ƙarasa maganar cikin tsawa yasa ta ɗan tsorata ta ɗaga masa kai. "Good! kinga yarinyar da aka haska wadda ta ɓata ake nemanta?". Nan ma kai ta gyaɗa masa hakan yasa yace "Kamar ku ɗaya ba abinda ya bambanta ku me hakan ke nufi?". "Nima ban saniba". ta bashi amsa kai tsaye. "Kin santa ne?". "A'a ni ban taɓa ganinta bama". Kai kawai yake kaɗawa yana cije lips kafin ya tashi daga ranƙwafar dayayi a kanta ya zura hannayenshi duka cikin aljihun wandonshi ya fara zazzagayawa cikin falon ta bishi da harara kamar idanunta zasu faɗo tsabar haushin shi datake ji, ba tare daya juyo ya kalleta ba yace "Zaki iya tafiya amma kina iya gani nadawo koda yaushe idan buƙatar hakan ta taso". Dama kamar jira take jinta take tamkar akan ƙaya, saurin miƙewa tayi ta nufi ƙofar fita har lokacin bai juyo ya kalleta ba, sai data tabbatar data fita sannan ta tsaya daga bakin ƙofar tace "Karka sake ka dawo gidan nan wllhy inba haka ba saina baka mamaki kaima kamar yadda kace zaka bani Mr. Nunar rana". tana faɗa tabar wajen da hanzari tana ƴar dariya tasan dai tagama kunna shi tunda ta faɗa masa wannan sunan yo inba nunar ranar ba me za'a kirashi? ragowar shawara kawai. Lips ɗinshi ya cije tamkar zai hudashi ya runtse ido yana tunanin wane irin raini ne yakeso ya shiga tsakaninsu da yarinyar ne? yaushe ma sukayi zaman da har zata rainashi haka? lallai ya kamata ya goge rainin dake tsakaninsu tun kafin ya ƙara yawa ta wace hanya kenan zaiyi hakan? ƙwafa ya saki ya fito batare di takan abinda ta ajiye masa ba tun ɗazu ya fice daga gidan, motarshi ya shiga ya figeta da wani irin mugun speed ya fice daga layin sam bai iya bin mota a hankali ba a duk lokacin dayake driving. A falo ta samu Aunt Ramlah, zama tayi kusa da ita tana jan tsaki duk yagama ɓata mata rai wannan gayen. "Lafiyar ki kuwa Heedayah meya faru kike tsaki?". Aunt Ramlah ta tambaye ta. "Nida wannan jikan Hajiyan mana ɗan rainin wayo yazo sai wasu tambayoyi yake min marasa kai ko ina ruwanshi dani". "Wane irin tambayoyi yayi miki?". "Nifa Aunt Ramlah sam ban gane ma inda ya dosa ba yana ta wani tambayata wai ya muke dake daga ina nazo me nazo yi nan bla bla bla bla ya isheni da surutu". dariya Aunt Ramlah tayi cikin zuciyar ta tana ayyana anya kuwa wannan mutumin baisan wani abu akan rayuwar su Heedayah ba kuwa? zuzzurfan tunani ta shiga wanda batasan lokacin ma da Heedayah ta tashi tabar wajen ba. Kai tsaye gidan Hajiya yayi parking bai ƙarasa nasu gidan ba. Tana zaune Larai mai aikinta tana shafa mata man zafi a ƙafafunta waɗanda suka ɗan matsa mata cikin ƴan kwanakin nan ya shiga cikin falon da sababbiyar sallamar shi daya saba a ciki, waje ya nema ya zauna Larai na masa sannu da zuwa kai kawai ya ɗaga mata ta rufe kwalbar man zafin dama tagama shafawa ta tashi tabar wajen. Kallon Hajiya yayi yana gaisheta ta amsa tana tambayar shi lafiyar su Ummi a taƙaice ya amsa mata da lafiyar su ƙalau yaja bakinshi yayi shiru. "Yadai maigidan daga ina haka?". cewar Hajiya tana kallonshi murmushi ɗauke a fuskarta, rai ya ƙara haɗewa sosai yace "Ƙarar yarinyar nan na kawo miki Hajiya kija mata dogon gargaɗi a kaina dan ni ba sa'anta bane". "Tooo wace yarinya ce haka?". Hajiya ta tambaya cikin mamaki. "Wannan yarinyar mai zuwa wajenki I mean Heedayah ne ko menene?". "A'a ikon ALLAH, a ina kuka haɗu da Heedayahn ne kuma me tayi maka?". "Ayi mata warning dai Hajiya dan zan iya karya yarinya ba damuwa ta bace". "Eh lallai ba shakka tunda ga ubanta ai dole ka karya ta yau naji neman masifa da bala'i saika faɗa min abinda tayi maka da har kake maganar zaka karyata". Baice komai ba ya tashi ya fice yabar Hajiya tana ta faman mita kamar zata biyoshi. Ya shiga mota kenan kafin ya tayar da ita wayarshi ta fara ringing yana dubawa yaga Auwal Azare ne mai kiran, picking yayi ya kara wayar a kunnenshi kafin yayi magana Auwal yace "Mr. Gashua how far?". "Alhmdulillah ya kaje gida?". ya mayar masa da amsa. "Masha ALLAH ina maganar mu ta kwana ne Gashua please kayi wani abu mana". Sam yama manta da Auwal ɗin yace yana son Neehlah dan haka cikin rashin fahimta yace "Wace magana kenan?". "Habaaa mana mutumina maganar ƙanwarmu mana kasan jiya fa ko cikakken barci banyi ba saboda ita dana rufe idona sai in ganta". ya ƙarasa maganar da iya gaskiyar shi yana sauke numfashi daga ji maganar daga cikin zuciyar shi take fita, takaici ya hana Habeeb cewa komai sai tsaki kawai dayaja jin yayi shiru yasa Auwal marairaice murya yana faɗin "Please say something mana Mr Gashua zaka bani ƙanwar ka da gaske na faɗa dayawa batare da sanina ba". Wayar kawai Habeeb ya kashe bayan yaja tsaki a fili yace "Shege babban banza Neehlah har takai macen da zaiyi irin wannan ruɗewar akanta? wani kiran Auwal ɗin ne ya ƙara shigowa a fusace ya ɗaga kiran yana faɗin "Idan ban zageka ba kace ba sunana Habeeb ba wai mayen inane kai Auwal? akan ƙaramar yarinya kake wannan shirmen dan ubanka ka dawwama baka barci indai a kanta ne karka ƙara sani cikin wannan maganar banza mara aikin yi". "Ɗan iska dama ai nasan halin rashin mutuncin ka bazaka goyamin baya ba to ni sai inda ƙarfina ya ƙare a kanta". Murmushi yayi yana taɓe baki yace "Goodluck Dr Auwal Azire". yana shirin kashe wayar yaji Auwal ɗin yana faɗin "Sanin danayi maka da Gashua ko magana bata dameka ba amma yanzu ka zaƙe da yawa ka koyi rashin mutunci da faɗa what wrong with you Dude?". "Ni kaina bansan yaushe na koma haka ba amma nafi tunanin mutane ne suka canzani". bai jira Auwal yayi magana ba ya kashe wayar yayi switch off ɗinta ma gaba ɗaya dan yasan mawuyacin abune bai ƙara kira ba shi mamaki ma abin yake bashi yadda Auwal ɗin yabi ya ruɗe akan Neehlah shifa soyayyar ma duka gani yake ɓata lokaci ne bare harya ruɗe haka akan mace. Motar ya tayar ya nufi gidansu. A ranar da dare bayan yagama da duk wasu abubuwa daya saba gabatarwa kafin ya kwanta kamar yin wanka gabatar da sallah raka'a biyu da addu'oe shan coffee brush da sauran ƴan abubuwan daya saba yi kafin ya kwanta, yau ɗin ma bayan duk hakan ta kasance ya kwanta yana karanto addu'ar kwanciya barci, ya rufe ido bayan gama karanto addu'ar saurin buɗewa yayi saboda gano Heedayah dayayi kuma ba abinda yake gani irin bakinta lokacin datake faɗa masa nunar rana, tsaki yaja ya buɗe idanunshi ya ƙara juyawa ɗaya gefen tareda ƙara rufe ido still dai ƙaramin bakin nata ya ƙara gani wanda yasha lipstick yaketa shining yayin datake ta juyashi tana magana. "Yaa Ilahee". yace ƙasa ƙasa yana dafe goshinshi gaba ɗaya haushin kanshi ya kamashi me yake damunshi haka ne? ALLAH idan ya kama yarinyar nan sai taji ba daɗi baisan ma wane kalar hukunci zaiyi mata ba kawai dan tsabar mugunta tazo zata hanashi barci hakan na nufin duk mafarkin dayake a can baya ita ce kenan?. Ƙananun tsaki ya dinga ja yana juye juye da cije lips da ƙyar yasamu barci ya kwashe shi a wannan rana batare daya daina ganin Heedayahn cikin idanunshi ba. ★★★________★★★ Washegari bayan ya taso daga office kai tsaye inda ake ginin ɗaya kamfanin nasu ya wuce yaga yadda ginin yake tafiya yayi nisa ma sosai abinka da akwai kuɗi zubasu kawai ake. Daga nan babban shagon da Muhammad yake mallakin Alhaji Sulaiman ya nufa, sosai yaran shagon suka dinga girmama shi sai miƙa gaisuwa suke saboda sun san ko waye sun san kuma kusancin dayake dashi da mai wajen, hannu kawai ya ɗaga musu duk yawansu ya nemi da ayi masa iso wajen manager. Bayan gaisawa da sukayi Habeeb ya nemi Muhammad daya bashi address ɗin gidan matar shi a Katsina zaije yayi wani bincike a can ya tattauna kuma da iyayen matar tashi, Uncle Muhammad yaso musa masa amma tsabar yadda ya cika masa ido da kwarjinin dayayi masa a idanunshi yasa take ya rattaba masa kwatancen gidan shima zuwa yanzu ya fara tunanin anya bata hanyar Mr Habeeb Gashua ɗin za'a gano asalin iyayen su Heedayah ba? wannan ai abin farin ciki ne a gurin Heedayahn dasu kansu su Baban dan haka baiji ko ɗar ba yana sa ran insha ALLAH ta sanadin Habeeb ɗin a gano real parents ɗinsu Heedayahn. "Thank you so much". Abinda yace kenan ya tashi yabar office ɗin Uncle Muhammad ya bishi da kallo shifa har yanzu tunani yake meyasa Mr Habeeb ɗin yasa kanshi cikin wannan lamarin?. Safiyar talata. Bayan yayi shirin fita office ya shiga gaida Ummi kuma yayi breakfast kamar yadda ya saba, bayan yayi breakfast ɗin yana shirin fita Ummi tace ya tafi da Neehlah ya sauketa a school kasancewar har zuwa yanzu driver'n nasu bai dawoba Monday ma saboda batada lecture ne shiyasa bataje ba, ficewa yayi yana faɗin ta fito yana jiranta kar ta ɓata masa lokaci. Dama tunda Neehlah taji Ummi tace shine zai yi drooping ɗinta ta shirya da wuri gudun samun matsala dan Yah Habeeb ba uzuri zaiyi mata ba.... Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 09139964697 *EL HABEEB*💥 ©️Oum Hanan. Writer of DR SAIF *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡 (Home of expert & perfect writer's). No 35. Last page. Neehlah na shiga motar ya figeta da uban gudu kamar yadda ya saba dama already maigadi ya riga ya buɗe masa gate, ko tari Neehlah batayi ba tunda suka tafi ba abinda ke tashi cikin motar sai sautin karatun Alqur'ani mai girma dake tashi kaɗan kaɗan cikin ƙira'ar Khusary wadda yake biyo farkon suratul Ma'idah. A bakin gate ɗin makarantar su Neehlah SKY LINE UNIVERSITY dake cikin birnin Kano yayi parking bai shiga ciki ba. A ɗan tsorace Neehlah ta ɗan saci kallon shi alamun neman ƙarin bayani. "Get out". yace ba tare daya juyo ya kalleta ba, kamar zatayi kuka tace "Yah Hab......"I said get out from my car". ya katse ta cikin ɗaga murya ba shiri ta buɗe murfin motar ta fita yayi reverse ya cilla motar kan titi yabar wajen tana tsaye tana kallonshi yau kuma haka ALLAH yayi da ita ji yadda ya watsar da ita anan kamar kayan wanki ta saba kullum driver ya kaita har cikin makarantar ya sauketa cikin girmamawa da mutunta wa ita wllhy ma matar dazai aura take tausayawa ta shiga uku gaskiya ba fata dai take mata ba koma wacece shi iya masa sai ALLAHn daya halicce shi ina rayuwa zata yiwu a haka? Baki ta taɓe ta nufi gate ɗin tana gyara side bag ɗinta ta shiga cikin school ɗin. Tun daga wajen ajiye motoci na cikin kamfanin ake ta faman miƙa masa gaisuwa kamar yadda ya saba ɗaga musu hannu yauma hakan yayi ya shige cikin kamfanin cikin zafin nama da wadatacciyar lafiya da ubangiji ya hore masa yana shiga kowa ya nutsu waɗanda suke tsaye suka zazzauna kowa ya maida hankali kan aikin dayake, kalaman barka da zuwa ne kawai ke tashi lokacin daya shiga sun riga sun saba da yanayin amsa gaisuwar tashi dan haka ba wanda ya damu kowa ya cigaba da aikin gabansa. Lifter ya hau zuwa 1st floor inda office ɗinshi yake ya buɗe ya shiga, a gyare tsaf ko ina ƙal-ƙal tamkar ba'a amfani dashi sai tashin ƙamshi mai daɗi yake, brief case ɗin ya ajiye kan babban table ɗin dake office ɗin sannan ya zauna kan kujerar yana zama yayi baya ya kwantar da kanshi kan kujerar yana sauke numfashi lokaci ɗaya yana rufe idanunshi tareda jujjuyawa kan kujerar. Buɗe ƙofar da akayi baisa ya buɗe idanunshi ba dan yasan ko waye mutum ɗaya ne yake da damar yin hakan a duk faɗin kamfanin wato Mujaheed. Motsin da bakinshi yayi ne kawai ya tabbatarwa da Mujaheed ya amsa amsa sallamar dayayi idan da sabo ya saba shikam wane hali ne na Gashua bai sani ba?. "Welcome Mr. Habeeb Gashua". Mujaheed ya faɗa yana zama kan ɗaya daga cikin kujeru biyun dake kallon wadda Gashuan yake zaune tare da zube wasu tarin pepper's akan table ɗin, ɗagowa yayi yana buɗe idanunshi ya kalli Mujaheed kamar bazai yi magana ba saikuma yace "Mr. Mujaheed Yusuf meya hanaka shigowa Company jiya?". cikin tsare gida yayi maganar yana janyo computer ya buɗe ya fara danne danne a ciki. "I'm sick". Mujaheed ya bashi amsa. "Why did you call me?". yace har lokacin bai daina latse latse a laptop ɗin ba, shegen wato yau dai ƴan rashin mutuncin ne a kanshi Mujaheed ya ayyana hakan cikin ranshi kafin yace "Wai Gashua me yake dam......."Look MJ I'm still your Boss karka kawomin maganar banza mana". Yace a zafafe yana kauda laptop ɗin gabanshi gefe. "Toooh yau kuma da haka kazo? dan ubanka nabi Boss ɗin da gudu ba wando kai meyasa bakada uzuri ne a rayuwar ka Gashua? ni dalla malam kayi min signing a takardun nan in tafi inada aikin yi a gabana". ya ƙarasa maganar yana harararshi, shima hararar ya jefa masa kafin ya janyo takardun yayi sign, Mujaheed ya miƙe ya ɗauke su ya fita yana maganganu wanda bayajin abinda yake faɗa amma ya tabbatar iskanci yake masa ƙwafa yayi a fili yace "Ubanka zanci very soon wllhy". System ɗin ya janyo ya cigaba da aikinsa a ciki. Neehlah ba ƙaramin ruɗu da tarin al'ajabi ta shiga ba lokacin da Jawaheer Mansoor Jiƙamshi ta shigo cikin school ɗin exactly ba abinda ya rabasu a komai da Seeyamah har yanayin maganar su kuwa bambancin kawai ita Seeyamah cikin sanyin murya take maganar ta wanda hakan ya kasance kamar halittar ta ne hakan, saɓanin Jawaheer dake magana gatsal gatsal ba alamun rissinawa anya babu wata alaƙa kuwa tsakanin Seeyamah da Jawaheer ɗin? tunanin data dinga yi kenan har zuwa lokacin da suka shiga lecture. Da wuri yabar office ranar, yana kan hanya ma Ummi tayi masa waya yaje ya ɗauko Neehlah daga school ƙiri ƙiri dai Ummi ta maidashi driver'n ƙarfi da yaji dole ya canza akalar tafiyar tashi zuwa school ɗin su Neehlahn. Tunda ya shiga cikin school ɗin idanun ɗalibai da yawa suka dawo kan motarshi ana jiran aga wanda zai fito daga wannan zuƙeƙiyar motar saidai ko buɗewa ba'a da alamun yi, Neehlah da sai yanzu ta hango motar tayi saurin yin sallama da ƙawarta Haneefah Isma'eel ta nufo wajen motar. Waya yake lokacin data shiga motar cikin sautin muryar shi mai cike da amo mai haɗe da sanyi cikin tataccen speech yake maganar cikeda ƙwarewa, kamar ance ya kalli gefenshi ya hangeta tana shirin shiga motar ta da niyyar barin school ɗin ido ya ɗan zaro yana ƙare mata kallo da tunanin dama a school ɗin su Neehlah take? magana ake tayi masa daga can ɓangaren wanda suke wayar amma sam bayajin abinda yake faɗa ganin har ta shiga ta tayar da motar tana shirin barin wajen yasa cikin sauri yace "I will call you back Mr Williams". Daga haka ya kashe wayar zai cillata front seat yaga Neehlah a zaune sam ya manta ma da ita a motar tsaki yaja yace "Get out kisamu abin hawa ya maidaki gida yanzu". Yace yana karkacewa ya zaro kuɗi a aljihunshi na gefe 5k ya wurga mata. "Get up". Yace cikin tsawa yana zare mata ido ganin tana shirin yin magana kar ta ƙara ɓata masa lokaci, kamar zatayi kuka ta buɗe murfin motar ta fita ya juya kan motar lokacin Jawaheer ta fita daga gate ɗin makarantar ya rufa mata baya ba tare data lura ma wani yana bin bayanta ba. Tsaye Neehlah tayi ta bishi da kallo harya fita daga cikin makarantar cikin tsananin jin haushi da takaici kamar ta ƙwala ihu wllhy abinda mutumin nan yake sam baya kyautawa tun farko ma daya sani haka yace ta tafi basai ta shiga ba ya fito da ita yau dai tana ganin rayuwa, kafaɗar ta da aka dafa daga bayanta yasa ta juya dan ganin ko waye taga ƙawarta Haneefah ce take tambayar ta lafiya harta shiga motar ta fito? "Hmm kedai rabani da halin mutumin can haka fa ɗazu nace miki bakin gate ya zubeni ya ƙara gaba abinsa yanzu kuma yace wai ina fito in nemi abin hawa ALLAH kamar Ummi taji ta gama ne". ta ƙarasa maganar cikin tura baki kamar zata saki kuka. Ƴar dariya Haneefah tayi tace "Ai kedai ki bari kawai Bestie sam irinsu basuda daɗin sha'ani nima muna nan da wani yayanmu Yah Khaleel wllhy shima haka yake da abin haushi haka muke fama amma dai gaskiya bai kai wannan Yah Habeeb ɗin naki ba". "ALLAH shirye su to". Neehlah tace tana taɓe baki, daidai lokacin Haneefah ta hango motar gidansu anzo ɗaukar ta hannun Neehlah ta kamo tana faɗin "Yauwa ga Isah nan ma yazo ɗauka na kizo muje kawai sai muyi drooping ɗinki zuwa gida". "Kai Bestie ba za'ayi haka ba ba hanyar mu ɗaya bafa kije kawai zan fita in samu drop ɗin napep". "No please kizo kawai meye abin wahala a ciki". kafin tasamu zarafin magana Haneefah taja hannunta zuwa gurin motarsu ta sanar da direban zasu fara ajiye ƙawarta a gida kafin su wuce cikin girmamawa ya amsa ya buɗe musu suka shiga ya tada motar suka bar harabar makarantar. Tiryan tiryan yake bin bayan Jawaheer har zuwa unguwar su saidaya tabbatar yaga gidan data shiga da motar ta sannan yayi reverse ya koma da niyyar zai ƙara dawowa ya ɗora da binciken shi. Tsoro ya hana Neehlah faɗawa Ummi yadda akayi yau da Yah Habeeb da zai kaita da lokacin dayaje ɗaukota kamar yadda da ta ƙudurta tana dawowa zata faɗa mata tasan dai idan Ummi tayi masa maganar kanta abin zai koma haka nan tana zamanta lafiya bazata jawowa kanta ba dan haka taja bakinta ta tsuke sai Seeyamah kawai data faɗawa ita Seeyamahn ma sai abin ya batada dariya ta hau yin abarta aikuwa Neehlah ta shaƙa kamar zata fashe ta haɗe rai da ƙyar Seeyamah ta shawo kanta ta haƙura daga nan kuma ta shiga bata labarin Jawaheer wadda suke tsananin kama da ita wadda a farkon ganinta ma tayi zaton Jawaheer ɗin ce sam Seeyamah bata ɗauka wai kamannin da Neehlahn take faɗa tanayi da waccan ba wata kama ce ta azo a gani ba bare har tayi wani tunani cikin ranta. ★★_____________★★ Kwana biyu Hajiya sam bataji ɗuriyar Heedayah ba dan tun zuwan datayi tasa Habibu ya maida ita bata ƙara dawowa ba batasan wane irin shaƙuwa da soyayya ke tsakanin ta da yarinyar ba tana jinta a ranta sosai dan haka ta fara jajen ta wayar Aunt Ramlah ta kira bayan gaishe gaishe da tambayar iyali Hajiya tace "Wai nikam ina ƴar gidana Heedayah ne kwana biyu tayi min yaji lafiya kuwa?". ƴar dariya Aunt Ramlah tayi tace "Lahh ba komai fa Hajiya kinsan mutuniyar taki ƴar kaga dama ce kuma ko jiya saida mukayi maganar ki da ita". "Toh ya kamata dai tazo a gaisa". "Insha ALLAH Hajiya gobe ko zuwa jibi zatazo". "To ALLAH ya nuna mana da rai da lafiya". "Ameen Hajiya ko ayi mata mutumin naki ta taho miki dashi?". Aunt Ramlah ta faɗa tana dariya cikeda jin daɗi Hajiya tace "Kaji ƴar albarka ALLAH ya saka miki da alkhairi yayi miki albarka ya raya miki zuri'a". Da Ameen Aunt Ramlah ta amsa cikin jin daɗi ta ɗora da faɗin "Kai Hajiya baki raina abin godiya ai bawani abu bane". "Kulawa ai yabawa nagode sosai a gaida maigidan". "Zaiji insha ALLAH". Daga haka suka yanke kiran, bayan dawowar Heedayah daga school Aunt Ramlah take yimata maganar wayar da sukayi da Hajiya tana bikon ta taga kwana biyu bata leƙa ta ba, zama Heedayah tayi tana tura baki da faɗin "Nifa Aunt Ramlah yanzu banson zuwa gidan Hajiyan nan wllhy". "Saboda me?". Aunt Ramlah ta tambaya cikin mamaki, cikin tura baki tace "Wannan jikan nata mana ɗan takurar da matsawa mutane shi indai aka haɗu dashi ba za'a rabu lafiya ba gashi kamar aljani saidai kawai ki ganshi tsulum ya shigo gidan". "To aini kuwa har nayiwa Hajiya alƙawarin zakije gobe ko jibi". "Haba Aunt Ramlah ni gaskiya ba inda zanje". tace kamar zatayi kuka, haɗe rai Aunt Ramlah tayi tace "Aikuwa baki isa ba inama laifin mai nemanka inajin ko jikokin ta bata nema yadda take nemanki sai kuma hakan ya zama laifi? shi wanda kike maganar shi ai bashi ya haɗamu ba kuma bazai zama sanadiyyar rabamu ba Hajiya mutum ce tasan ƙima da mutuncin ɗan adam duk da irin ɗaukaka da tarin dukiyar da ALLAH ya azurta su da ita bata jin kanta ita wata ce dan haka ki shirya kije ɗin kamar yadda ta nema". "To Aunt Ramlah kibari idan Zainab tadawo sai muje tare kokuma ranar Monday idan muka haɗu a school saimu wuce can ɗin ( Dayake Zainab ɗin yanzu duk Friday take wucewa gidansu idan an tashi daga makaranta Heedayah ce kaɗai take dawowa can take weekend ranar Monday sai tazo makaranta daga nan sai su dawo da Heedayahn tare). Kai Aunt Ramlah ta girgiza tace "A'a bazan saɓa alƙawari ba gaskiya goben kawai ki shirya kije". "ALLAH ya kaimu". Ta faɗa ba dan ranta yaso ba sai dan batason musu da Aunt Ramlahn. "Yauwa ko ke fa autar Umma goben idan ALLAH ya kaimu zanyi mata dambun tsaki zaki wuce mata dashi". "Ba matsala ALLAH ya nuna mana". "Ameen". cewar Aunt Ramlah tana maida kanta kan shirin da ake haskawa a TV. Data shiga bedroom ma ita kaɗai ta dinga maganganu wllhy koda sun haɗu idan yayi mata ba ƙyaleshi zatayi ba saidai ya kasheta duk da bata fatan ma su haɗun dashi taga alamun shi ba'a yi masa alkunya. Washegari asabar da wuri ta tashi ta hau gyaran gidan tayiwa Nu'aym da Nusrah wanka ta shiryasu dama indai weekend ne ita take yi musu wanka da safe. Kitchen ta shiga inda Aunt Ramlah take ta fara tayata aikin datake ita Heedayah breakfast ta haɗa musu itakuma Aunt Ramlah tana harhaɗa kayan dambun da zatayi da zoɓo da zatayi mata so take ta kammala da wuri dayake da wuri ma Uncle Muhammad ɗin ya fita yau saboda wasu kayansu da suka ƙaraso a ranar ko breakfast ma bai tsaya yiba ya fita. Tare sukayi dambun da Heedayah mai rai da lafiya dayaji kayan lambu dan ma dai ta fahimci Hajiyan ba komai take so ba ta haɗa mata haɗaɗɗen zoɓo mai daɗi tasa mata komai a wani basket madaidaici aka rufe da wani farin ƙyalle suka gyara kitchen ɗin dan Aunt Ramlah ko ƴar aiki batada ita duk da Uncle Muhammad yaso a samo mata tace a'a bataso har wani gagarumin aiki ne a gidan da sai an nemo wata mai aiki? kuma shi aikin datake ai shine rabauta da samun ladan auren dan haka ita bata buƙatar ƴar aiki ALLAH ya hore mata lafiya ta cigaba da ɗawainiya da hidimar gidanta. Wanka Heedayah ta shiga bayan sun kammala komai, bayan ta fito ta shafa cream ɗin da suke using dashi sama sama tayi kwalliyar ta kamar yadda ta saba kullum powder, lipstick sai kwalli datake zizarawa a fararen idanunta. Doguwar riga ta ɗauko ta atamfa sau ɗaya ma suka taɓa sakata itada Zainab Uncle Muhammad ya kawo musu ita tare, coffee color ce atamfar da ratsin baƙi da milk daga sama ta kamata sosai ta fito da halittar ƙirjinta sosai daga ƙugun ta kuma zuwa ƙasa ta buɗe sosai tayi mata matuƙar kyau ta maƙala ƙaramar barima a kunnenta ta ɗaura baƙin agogon fata ɗaurin ture kaga tsiya tayi na malaha medium size ɗin gyale coffee tayi rolling dashi ta rataya baƙar jaka ta zura plat shoes black ta fesa turare. Masha ALLAH kalmar dana ambata kenan lokacin data gama shiryawa tayi kyau sosai Uncle Muhammad yana ƙoƙari sosai a kansu kuma baya nuna bambanci tsakanin ta da ƙanwarsa a matsayin su na ƴan University da suke shiga cikin jama'a yana ƙoƙarin yaga sun shiga mutane tsaf tsaf haka ne ma Aunt Ramlah tana yawan siya musu kayan makeup a matsayin su na ƴan mata dan ma dai ita kwalliyar bata dameta ba wannan sai Zainab ita ce ƴar kwalliya. Fita tayi bata samu Aunt Ramlah a falo ba dan haka ta wuce bedroom ɗinta itama a bakin mirror ta sameta tana shafa mai tayi wani wankan murmushi tayi tace "Masha ALLAH kinga yadda kikayi kyau kuwa autar Umma". "Kai Aunt ina wani kyau anan? nida ba kwalliya nake ba?". "Kwalliya ai ba ita ce kyau ba Heedayah ke kyan a jikinki yake ALLAH yasa a dace a dawo mana da suruki". Ta ƙarasa maganar tana dariya gami da rufe robar man data gama shafawa kan mirror ɗin, baki Heedayah ta tura tace "A'a nikam Aunt Ramlah ni gaskiya karatu zanyi yanzu na fasa auren". "Lallai kiyi ta kanki yarinya Baba bazai zuba miki ido kiyi wannan dogon karatun ba bakiga ni iya secondary ma akayi min aure ba kema sa'a kika ci kawai ALLAH dai ya zaɓa mafi alkhairi". Bata amsa ba sai cewa datayi "Zan tafi Aunt". 1k Aunt Ramlah ta ciro a purse ɗinta ta miƙa mata ta karɓa ta fita tana yi mata sallama Nusrah dake kan bed itada Nu'aym yana mata wasa sai ɗaɗɗaga mata hannu take tanaso ta ɗauke ta kissing ɗin kumatunta kawai tayi ta fita tana dariya Aunt Ramlah na bada saƙon gaisuwa wajen Hajiya, kitchen ta shiga ta ɗauki kwandon ta fita taja ƙofar falon. Tana fita titi tasamu napep ta shiga zuwa unguwar su Hajiya. Ƙarfe ɗaya da kusan rabi ta shiga gidan side ɗin Alhaji Sulaiman ta fara shiga suka gaisa bata iya zuwa bata shiga sun gaisa da Hajiya Rahma ba saboda mutuncin ta itafa tana tunanin gadon mutunci familyn sukayi nunar rana ne kawai bashida mutunci (Ba ruwan Mero 🤒😃). Da sallama ta shiga falon Hajiya na zaune tasha kwalliyar ta cikin haɗaɗɗiyar atamfa da gani mai tsada ce taci ɗaurinta Irin na tsaffi sai ƙamshin turaren wuta falon yake wa'azi take kalla a Sunnah TV daga bakin Shiek Abdallah Usman Gadon ƙaya, murna sosai ta bayyana kan fuskar Hajiya tana amsa sallamar lokacin da Heedayah ta shiga ita har mamaki abin ya bata lallai ba ƙaramin so ƴar tsohuwar take mata ba, kusa da ita ta zauna bayan ta ajiye basket ɗin cikin dariya Hajiya tace "Ah lallai Ramlatu ta cika alƙawari ai da baki zoba da kaina zanzo har gidan nayi biko". "Haba dai Hajiya". Tace tana murmushi tareda saukowa har ƙasa tana gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da jin daɗi tana tambayar Aunt Ramlah da yara ta amsa mata da lafiya itama tace a gaisheta daga nan ta gabatar mata da saƙon Aunt Ramlah irin farin cikin da Hajiya ta nuna tamkar ranar aka fara kawo mata taji daɗi sosai ta shiga godiya tanasa mata albarka tace ta kai mata kitchen ai yau abincin ranar ta kenan da dare ma shi zataci abinta Heedayah na dariya ta ɗauki kwandon ta nufi kitchen ta ajiye ta dawo suka cigaba da hirarsu da Hajiya. "Nikam Hajiya ba kunun gyaɗa ne a gidan nan yau Aunt Ramlah na tsamiya tace a dama nikuma kinsan na gyaɗa ne mutumina". Heedayah ta faɗa tana kallon Hajiya. "Kin taki sa'a kuwa yau shi Larai ta dama mana yana nan a kitchen da zafinshi kije ki zubo". "Yauwa Hajiya bari inje in zuba". ta faɗa tana miƙewa tsaye ta nufi kitchen ɗin, itama Hajiya ganin lokacin sallahr zuhr yayi ta tashi ta wuce bedroom ɗinta dan gabatar da farali. Hajiya na shiga bedroom ɗin shikuma ya shigo falon, sanye yake cikin ƙananan kaya dark ash ɗin trouser da red color ɗin riga mai dogayen hannuwa ya matse ƙugunshi da baƙar belt ta kamfanin D&G ƙafarshi sanye cikin baƙin takalmi cover writs watch ɗin shi ma baƙi ne na fata sumar kan nan tasha gyara sai ƙyalli take zubawa, tunda ya falon ƙamshin jikinshi ya doke wanda falon yake yi ada nashi ya mamaye ko ina zama yayi ya ɗauki waya ya fara latse latse. Jin alamun motsi a kitchen yayi tunanin Hajiyan ce a ciki dan haka ya tashi kanshi tsaye ya nufi hanyar kitchen ɗin yana ƙoƙarin cusa wayarshi cikin aljihu, ta kawo kai kenan zata fito da madaidaicin mug da spoon a ciki wanda ta haɗa kunun gyaɗar a ciki dayasha madara a daidai lokacin shikuma ya kawo kai zai shiga kitchen ɗin sukayi wani mugun karo saboda ba wanda ya kula da tahowar ɗan uwansa goshinta ya bugi ƙirjinshi mug ɗin hannunta yayi kamar zai faɗi hakan yaba damar abinda ke cikin shi yayi uban fallatsi sai a jikin rigar Gashua da nata gaban rigar, a gigice ta zaro ido tana ja baya ganin wanda ke gabanta yana bin rigar jikinshi da kallo data gama ɓaci cikin ƙyanƙyami da ɓacin rai mara misali ɗagowa yayi dan ganin wace shashashar yarinya ce wannan idanunshi ya sauka cikin na Heedayah datayi tsamo tsamo jikinta na ɗan ɓari har lokacin bata gama dawowa daidai ba dan ba ƙaramin tsorata tayi ba musamman ganin wanda sukayi gwaren dashi, wani mugun kallo mai haɗe da harara ya jefa mata kafin ya nufi inda take tsaye baya ta shiga ja tana girgiza masa kai kamar zatayi kuka shikuma ya cigaba da binta fuskar nan ba alamun rahma sam a samanta tana ja baya yana ƙara kusanto ta har lokacin data kai jikin luckers ɗin kitchen ɗin ta yadda ba damar ta ɗara nan da can dole tayi surrender ta tsaya tana dafe baki sai zazzare idanuwa take irin na marasa gaskiya da alamu tsautsayi ne dama ya kawota gidan nan. Daf da ita ya tsaya kamar zai haɗe jikinshi da nata ya tara mata hannu yana kallon mug ɗin hannunta alamun ta bashi, cikin rawar hannu ta miƙa masa ya karɓa ya ajiye shi can gefe ya juyo yana ƙara matsawa jikinta ba abinda take gani sai shi yama ɗora hannayen shi duka biyun kan luckers ɗin gefe da gefenta yayi mata rumfa yayi kane kane tako ina bata da hanyar guduwa bare tayi tunanin zillewa ta gudu fatan ta da roƙon ta a lokacin ALLAH ya jefo da Hajiya kitchen ɗin ta ceceta dan da gaske kallon mara imani take wa mutumin...... Alhmdulillah Masha ALLAH. A nan nakawo ƙarshen littafi na ɗaya ina roƙon ALLAH ya yafe min kuskuren danayi a cikinsa. _*Shin su waye iyayen waɗannan triplets ɗin ne?*_ *_Meye silar rabuwar su da iyayensu?_* *_Meye zai biyo baya bayan gano asalin nasu?_* _*Shin ta wace hanya ake gano real parents ɗinsu? Habeeb Gashua ne yake yin nasarar hakan ko kuwa dai ta wata hanya ce daban ake ganowar?*_ _*A cikin triplets ɗin nan wace take nasarar ƙwamushe zuciyar Mr. HABEEB IBRAHEEM AHMAD GASHUA?*_ _*Shin cika bakin ma dayake na bazaiyi soyayya da masu ƙananan shekaru ba hakan zai yi tasiri a kansa? *_ *_Wace babbar gudunmawa Ummi ke bayarwa a haɗuwar su Seeyamah da danginsu?_* *_A cikinsu wacece take folawa GASHUA taji duk duniya bata gwani sai shi?_* _*Duk waɗannan tarin tambayoyi dama wasu da kuke hasasowa duk amsoshin su suna cikin EL HABEEB 💥 Book two*_ *A yayin tafiya taci karo da wata mahaukaciya wadda ta bigeta da mota wadda dalilin haka ta dawo da ita gidanta da zama dan nema mata magani, makarin asirin da akayi mata yana jikin yaran wadda da zarar sun haɗa ido zata samu lafiya shin wacece wannan mahaukaciyar? waye kuma ya tsinceta? an samu nasarar kallon juna cikin gaggawa ta yadda asirin zaibar jikin matar ko kuwa saida aka ɗauki wani lokaci? Amsa tana cikin littafin EL HABEEB 💥 Book two* Karku bari a baku labari tafiyar ta musamman ce takun na daban ne salon mai ƙayatarwa ne ta yadda ba zakuyi dana sani ba💃💃💃. _Na fara samun complain sosai daga reader's masu yawa saboda jin yadda nace bazan fara sakin book two ba saina kammala typing ɗinshi sun matsu suji yadda labarin zai kai ƙarshe, so maganar gaskiya banason ƙorafi kuma banaso in karɓi haƙƙin mutane inzo ina musu delaying wajen yin posting ba ba daɗi tafiyar da rayuwar mu ba'a hannun mu yake ba uzururruka suna iya faɗowa mutum ako wane lokaci batare daya shirya hakan ba shi yasa tun farko na yanke shawarar yin hakan idan na kammala sai in sanar da account ɗin da za'a turo kuɗin ta yadda za'a dinga samun update kullum kamar hakan zaifi amma inaso inji ra'ayoyin ku akan hakan duk da dai da wuya in sauka daga kan nawa🫣🤪 ku kanku sai kunfi jin daɗin hakan ba maganar sai nayi typing zan turo saidai inyi editing kawai in sambaɗo muku kunsan idan book ya ɗauko hanya ba'a son jira amma dai duk shawarar dana yanke zan sanar daku ALLAH ya iya mana yasa mudace dan arziƙin Annabi 👏👏👏._ *Masu son a tallata musu hajar su ta yadda zasu samu nasarar samun customer cikin sauƙi zasu iya tuntuɓar wannan number* 09139964697. Akwai paid book ɗina guda biyu _KALLON KITSE_ _WATA SOYAYYA_ Da sauran daɗaɗan littattafan mu na ƙungiyar HASKE WRITER'S ASSOCIATION 💡 waɗanda suka riga suka kammala kaɗan ne daga ciki ba'a ƙarasa ba cikin sauƙi da rahusa kuyi magana ta wannan number dake sama kunsan dai haziƙan marubutan da aka tara a cikin ta ba zakuyi dana sanin zuba kuɗi ku ba😍🥰. *EL HABEEB 💥🔥🔥🔥 Book two for paid 300 only ALLAH ya bada ikon siya da amfanuwa da darasin dake ciki*. Maryam Ibraheem Aleeyu Mrs Salees Mu'az 💝 (Ummee). 09139964697. Downloaded From https://tknovels.com.ng