Downloaded From https://tknovels.com.ng Bismillarrahmanin Rahim.......✍️ BLACK WORLD😥 Dik da tsananin tsoron da take a cikin ranta hakan bai hanata ɗago kai ta fara kallonsa tun daga kan Lion chest ɗinsa har izuwa kan his beautiful full neck attention grabber ba. Da kyar take iya motsa idanun nata amma ta dage sai ta kalli face ɗinsa kusa da kusa domin ta tabbatar da mutun ne ko ba mutun ba, because she had never seen a beauty like him. Ta ɗauki a kallah 1 mins tana kallon zanen tattoo na Black Tiger dake saman lion chest ɗinsa, zanen ya fita sosai, ga bakar damusar ta wage baki, waɗan nan garma garman hakwaran nata masu tada hankalin ɗan adam sun zanu da kyau, sai da ta ji mummunar faɗuwar gaba na ganin hakwaran damusar. A lokacin da ta sauke kallonta a kan heart-s romance pink lips ɗinsa sai da ta dakata cak tare da kura masu idanu tana yi masu kallon ƙurillah, ko makiyi ya gansu yasan sun kawatu sun kuma haɗu sun kai a mutu a kansu, sai wani irin shining suke yi kamar ya saka lips balm, kai kyansu ya wuci tunaninku. Ba shakka Allah ya yi halitta a nan sai dai muce Masha Allah, . Tsabar karfin hali irin nata da kyar ta iya hakura da kallon laɓɓan nasa amma sai da ta yi gaba da idanunta izuwa saman romance nose ɗinsa da yake dogo bai zut ba, ɗan dai'dai haka gwanin birgewa, haƙiƙa skin ɗinsa ya kai a shagala da kallonsa, wannan ya babbata da gaske bai taɓa fita rana ba, ya tabbata dai tun yana karami ɓoyesa ɗin ake yi, ni sai yanzu ma na gane dalilin ɓoyesa da babansa yake yi, ashe kyansa ne ya yi yawa da zai iya ja surutun jama'a a kansa da kuma hankulan mutane, in ya fito zai hana dikkan matan da zasu ɗaura idanu a kansa yin wani aiki ya hana zuƙatansu nutsuwa, shiyasa babansa ya ɓoyesa na tsawon shekaru, amma fa a nawa tunanin ni princess Teema ato bamu san dalilin baban nasa ba, abin da muka sani dai komai da dalilin yinsa, da alama nasu dalilin ma mai karfin gaske ne. Bin wasu kyawawan black curly sajen dake gefen kumatunsa da kallo ta yi. Ya ilahi sai ji ta yi kamar ta kai hannu ta shafa ko tsoro babu, suna kwance luf a saman skin ɗin nasa mai kama da madubi saboda kyalli. Ya ji hutu malam. Dik kare mashi kallon ƙurillah da take yi yana tsaye yana cigaba da abin da yake yi tamkar bai san da wata halitta a wajen ba, kamar ba shi ne ya jawota gabansa with his magic ba. Cak ya tsaya daga creating wannan haske da yake ƙoƙarin yi a lokacin da ya ga sauƙar idanunta a cikin kwayar nasa. Bai taɓa tunanin tana da zarrar iya sanya kwayar idanunta a cikin nasa ba, dan a cewarsa zaratan maza masu rai da lafiya ma ba zasu iya ganin face ɗinsa ba bare kwayar idanunsa, sai ga shi ita kuma ta mace ma da kallon idanun nasa, kyansu sun ruɗeta da har ta manta in da take ta kafesu da kallo babu ko kyaftawa. Haƙiƙa hakan ya girgiza shi kaɗan, dole ya dakata da abin da yake yi domin ya dawo da kallonsa a kanta ya ga zata iya su kalli juna ido cikin ido ne? Idan har ta iya ganinsa ido cikin ido bata kawar da kallonta ba to ya zama dole ya kasheta, domin ta cika ƴar baiwa. Babansa ya bashi labarin tabbas dik wadda zata iya kallonsa ido cikin ido in ma mace ko namiji to ya sani tana da baiwar irin nasa, idan ma ya yi wasa zata iya bugesa, kuma kada ya yarda ya zauna inuwa guda da wanda zai ga cikin kwayar idanunsa babu tsoro, idan ya yi hakan tabbas ayyukansa ne zaku koma baya........ Tashin sense. Ita kuwa ya subhanallah, sexy romance eyes ɗin nasa ta kafe da kallo ko tsoro hakan bata ji ba, ita dai taga abu mai kyau ya tafi da imaninta, idan ka kalli idanun nasa a fisge sai ka yi zaton design of fish ne saboda girmansu, amma ba haka bane, romance-s-eyes ne, ga shi shikuma ba ɗan soyayya bane, amma wlh yanayin idanunsa irin na riƙaƙƙun ƴan love ɗin nan, ga shi baya buɗesu dikka, suna ɗan lumshe. Kaifafa dasu tamkar eagle eyes. Idan ya kalleka da su kaifinsu da gwarjinin dake cikinsu sai ya razanaka yasa ka ji faɗuwar gaba. A hankali ya juyosu a kanta, suka ga juna ido cikin ido kuma kusa da kusa. Wlh yarinyar nan ko gezau bata motsa ba, kai ko kyafta idanun nata ma bata yi ba, sai ma ɗan kara warosu waje da ta yi na mamakin kallon cikin nata da ya yi. Ya ɗan ji a jikinsa, ya kuma fara yarda da cewa tana da baiwa irin nasa, domin kuwa ita ma idanunta kaifafa ne sosai, idan baku manta ba Kamran baya iya ganin cikin kwayar idanunsu, shin kun tuna hakan? To ba Kamran kawai ba, dik wanda zai ga Sweetie ko Pretty idan ba mai dakakkiyar zuciya ba babu wanda zai iya jure ganin kwayar nasu gaskiya....... DA ALAMA SUNA DA WATA ƁOYAYYAR BAIWA DA GASKE NE, TO WACE IRIYAR BAIWA KENAN? MU JE ZUWA. Tsabar ta shahara ma har da fara ƙoƙarin motsa hannunta domin ta taɓa face ɗinsa ta kara tabbatarwa mutum ne ko aljani. Sai dai kash bayan idanun nata babu wani abin da yake iya motsawa a jikinta, ya daskarar mata da komai, da zata taɓa shi ta ji karshen rashin tsoro kenan. Kai gaskiya Sweetie akwai karfin hali, innalilahi ni narasa ma a wani point zan ajiyeta, tab kai abin da mamaki gaskiya. Sakin wannan madubin hannun nasa ya yi ta yi kasa kamar zata faɗi, sai kuma ta tsaya a saman iska bata kai kasa ba, amfani ya yi da scepter ɗinsa ya yi magic kafin kyaftawa da Bismillah ta ɓace daga gabansa ta manne da wall na ɗakin ta ɓangaren hagu. Dik da haka bata tsorata ba, hasalima bata kawar da kallonta daga kansa ba, shi kuwa tuni ya zare idanunsa zaga cikin nata. Da kyar ta kai kallonta a kan swan sofa chair dake shirye ta wajen wall glass dressing room dake cikin ɗakin, waɗan nan swan design chiar ɗin sun haɗu matuƙa ga shi sun ji dollof mai laushi da tsantsar kyau da tsada. Komai na cikin bedroom ɗin nan white, gold and milk color ne, sai kuma jikin furniture da aka tsantsarawa kwalliya da zallar madarar gold. My people's Allah ya yi arziki ta yi mubaya'a a wannan empire ɗin, headboard na gadan Black Tiger duniya ce guda, wall headboard ce, wato kayin gadon manne take da jikin bango, a haka aka yita wanda tsawonta ya kai har tana taɓa saman ɗakin, sannan aka bi gefe gefenta da wasu kwayayen fitillu masu bada sky blue ligh mai matuƙar ɗaukar hankali, yanayin yadda aka tsara wall headboard ɗin nan sai mutun ya kwana ya wuni yana kallo ba tare da ya sani ba, saboda haɗuwarsu. Dik wata flowers da kwalliya dake jikin wannan wall headboard ɗin da ɗanyar gold aka yi ta wanda nasan kun san da hakan, design of butterfly ce head na bed ɗin, dai'dai tsakiyar butterfly ɗin gold ce haɗe da wani kwai mai bada haske white light, sai ya haskaka gold ɗin tana wani irin kyalli mai jan hankalin wanda ko baka yi niyar kallon gadon ba baza san lokacin da idanunka zasu kai wajen ba saboda wannan kyalli na gold ɗin. Ita kanta Sweetie bata san lokacin da ta kai kallonta saman bed ɗin tana jinjinawa girman gadon da kuma haɗuwarsa, kamar ba'a duniya ba, kamar kuma ba za'a mutu ba, shifiɗun alfarma dake saman bed ɗin kawai ya isa sanya mutun ya ji ya ƙoshi da komai saboda haɗuwarsu. Shi kuwa sarkin azzalumai wato King Black Tiger, baiwar Allah tana can yana kalle kalle shi kuma yana sihirinsa dan ya kasheta. Tsakar ɗakin nasa ya nuna da scepter ɗinsa, hakan yasa nan take wajen ta zurma tamkar rami mai zurfin gaske, magic eyes ɗinsa ya juya nan take wasu irin kifiyoyi masu kaifi da tsinin gaske suka bayyana cike a cikin ramin har baki, kasan kifiyoyin wuta ce take ci mai tsananin azabtar da har in da suke suna jin hucinta Wasu irin bakaken kunamu masu duhun jiki sosai manya manya da su ne suka sake bayyana a saman kan tsinin kifiyoyin nan, sai wasu snake da suka bayyana a jikin kifiyoyin sun fasa kai da baki, kiris suke jira su fara kai sara. Har lokacin idanunta a kansa, da alama bata firgita ba. Da scepter ɗinsa ya yi amfani ya janyota izuwa gaban wannan rami ta hanyar amfani da magic ɗin nasa. Sai a lokacin ta kawar da kallonta izuwa kan ramin dake gabanta. Wani irin tsorata ta yi na ganin zabga zabagn kunamun dake yawo a cikin ramin, abin mamaki kuma wutar dake ci kasan ramin baya taɓa dabbobin, babban abin da ya ɗaga hankalinta ma shi ne waɗan nan macizai da suka fasa kai suke jiran kiris su kai sara, wannan wani irin zalinci ne? Da me bawa zai ji idan aka jefashi cikin wannan rami? Shin da wutar dake ci a kasa zai ji ko dai da waɗan nan shegun baƙaƙen kunamu da bakaken kumurcin macizan? Ko da kifiyoyin dake tsaitsaye masu kaifin bala'in, hakika kuma ta wannan hanya Black Tiger ya fi yawan kashe dik wanda ya taɓa ganin face ɗinsa, cikin wannan rami yake jefa mutun hakan yasa ko gawar mutun ba'a sake gani, shiyasa tin farko nace maku dik wanda ya shiga cikin wannan part ɗin nasa ba'a sake jin ɗuriyarsa, ya tafi kenan, to ga hanya ta farko da azzalumi Black Tiger yake bi domin ɓatar da su. Mahaukacin razana ta yi, nan take zuciyarta ya fara duka tara tara! Idanu ta zaro tana kallon cikin ramin tamkar kwayar idanun zasu faɗo ƙasa, jikinta dik a daskare ba damar ta yi motsi ma bare har ta ce zata gudu, yadda zuciyar tata take bugawa tamkar ta fasa kirjinta ta fito waje. Kwata kwata kallonsa baya a kanta, amma yana iya sarrafata, haka zalika bai motsa daga in da yake tsaye ba, ga mirrorn da yake creating haske da shi a sage a saman iska. A hankali ya saitata da scepter ba tare da ya kalleta ba, baya baya gangar jikinta ta fara yi yana nufar cikin wannan rami. Ihu take son yi amma babu dama, dan babu wani abin da yake iya motsawa a tattare da ita face idanu, ya datse mata bakinta baiwar Allah ba halin yin kuka sai dai azaba ya kasheta. Saura kaɗan ta ƙarisa afkawa cikin rami azaban zafin wutar har ya fara ɗuma fata izuwa tsokar jikinta, sai raɗaɗi take ji. Dai'dai wannan lokacin Ronnie da ya fito daga cinema dake part na yayan nasa ya turo kofar ya shigo, abin mamaki kuma yayan nasa ya rufe kofar fa, amma yana zuwa ya buɗeta, dik yadda aka yi dama yasan yadda ake buɗe kofar ta koma wacce hanya yayan nasa ya rufe, anya shi ma bashi da tsafi kuwa?. Kofar Black Tiger fa ba irin kofofin da kuka sani bane. Dama da ya yi fushinsa cikin cinema ya shiga ya yi zamansa saman luntsuma luntsuman sofas dake wajen, ya kunna Tv wai dan ɓacin ran da yake ciki ta kau kada zuciyarsa ta buga, sai dai kash ya gaza samun kwanciyar hankali, haka kawai ya rinƙa jin gabansa na faɗuwa shi ne ya ce bari ya dawo su sasanta da yayan nasa kila ya samu natsuwa. Shi ne dalilin dawowarsa kenan. Innalilahi, ba karamar razana ya yi ba a lokacin da ya sauke idanunsa a kan face ɗin Black Tiger, shi hankalinsa ma bai kai kan Sweetie ba tukun nan, saboda ɗakin yana da balai'n girma sosai, so tsakanin in da take da in da black Tiger yake akwai rata sosai, hakan yasa bai lura da ita ba. Kusan mutuwar tsaye ya yi, ya zaro idanu yana ganin abin da bai taɓa gani ba. Ko yanayin kirar jikin Black Tiger bai taɓa gani ba, abin da ya sani dai shi ne kullum na Allah yayan nasa yana cikin wasu irin kaya mai kama da na Spider-Man, sannan kayan tana da wata jela a bayanta kamar dai alkyabba haka, babu abin da mutum zai iya gani a jikinsa, harta idanunsa Ronnie bai taɓa gani ba, ya dai san kullun da sassafe yana zuwa wajen yayan nasa su yi gym a tare.................Ina fatan yanzu kun gane dalilin da yasa Ronnie ya iya dukan master Devil dik da cewa shi ya bashi horo? Yana zuwa da safe kullum su yi gym a tare da Black Tiger ba tare da sanin kowa ba, kullum sai ya tsaya a tsakiyar bayan Black Tiger da kafafunsa Black Tiger yana press up Da shi. Kunga kuwa mutumin da kamar Ronnien shararren ɗan Wrestling zai tsaya a tsakiyar bayansa kuma ya yi press up da shi ai ba zaku haɗa hotonsa da kowa ba, shiyasa Ronnie ya take master Devil a samun nagartaccen horo. Kamar daga sama ya ji ance out!! Kuma tabbas Black Tiger bai motsa kyawawan laɓɓansa ba, ba shi ya yi magana ba amma kuma lion voice ɗinsa ce ta furta wannan out ɗin, shi kansa Ronnie ya shaida lion voice ɗinsa ce. Sai dai ya ɗan tsorata dan Black Tiger bai buɗe baki ba. Kasa motsawa daga wajen ya yi, ya shiga ruɗani sosai na ganin yayan nasa. Kamar walkiya haka idanunsa ta wutsiya suka hango Sweetie da saura kaɗan ta karisa shigewa cikin wannan bakin ramin azabar. Ai a miliyan ya juyo da kallonsa mai gabaɗaya a kanta dan ya tabbatar. Ya subhanallah ai bai san lokacin da ya ƙarisa wajen ba sai dai kawai ya ga kansa a gaban ramin. Ko tsoron yayan nasa bai ji ba ya kai hannu a miliyan ya riko hannunta dake sankare kamar wadda ta zama ice block. Da karfi ya janyota domin ya fito da ita, sai dai ina ya kasa koda motsata, tana daskare kamar gunki. Black Tiger dai yana tsaye kamar bai san da su a wajen ba. A hankali gangar jikin Sweetie ya nufi karisa shigewa cikin ramin. Kin sakin hannun nata Ronnie ya yi yana kallon cikin kwayar idanunta ya ki motsawa daga wajen kuma, a cewarsa sai dai su tafi cikin ramin a tare su mutu tun da yayansa ya ki ya saketa ya samu ya janyota ta fito. Idan ran Ronnie ya kai miliyan to yau ya ɓaci, tin tini yake neman ya sanyata a idanunsa yayansa ya hanasa dama, ashe dama kasheta zai yi shiyasa ya ɓoyeta na tsawon lokaci? Ronnie ya tambayi kansa!. "Ronnie get out!". Lion voice ɗinsa ta daki kunnuwan Ronnie dake tsaye a kan ƙafafunsa sam bashi da niyar motsawa daga in da yake ko ya saki hannun Sweetie, idanun nan nasa sun yi jajir kamar wuta, sai wani uban zufa yake haɗawa kamar wanda aka watsawa ruwa a fuska, saboda hucin wutar dake cikin ramin ta taɓa shi, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin tsananin tashin hankali na wuce misali. Ko motsawa bai yi ba tamkar ba ƴaƴan nasa bane ya yi mashi magana, ga dikkan alamu suman tsaye ya yi, dan bai taɓa tsammanin kamanin Black Tiger haka yake ba, bai taɓa tsammanin ƴaƴan nasa king of beauty, handsome, gorgeous! Sexy man bane, bugu da kari bai taɓa sanin ta haka Black Tiger yake kashe dik wanda ya keto ya shigo cikin wannan part ɗin ba. Magic eyes ɗinsa ya juya, idan ya juyasu kuma alamar zallar madarar rashin imani zai aikata, Ronnie yasan da haka amma yana tsaye bai motsa ba. Wasu irin dogaye dogayen itatuwa marasa ganye ne suka bayyana a bakin ramin suka yi mashi zobe, suma bakinsu kamar kifiya a feke. Still Ronnie bai tsorata ba bai kuma da niyar sakin Sweetie, daga shi har ita azabar zafin wutar karkashin ramin yana taɓasu sosai, hakan ya haifar mashi da wannan zufar da yake haɗawa. Scepter Black Tiger yasa a in da ya turasu gabaɗayansu biyu cikin ramin. A tunaninsa Ronnie zai tsorata ya saki Sweetie idan ya ga zasu faɗa ciki dikkansu biyu, sai dai kash, Ronnie dai da alamar ɗan a mutu ne a kan kyawawan mata. Ya tsare sweetie da ido suna kallon juna ba halin yin magana, ta zaro mashi idanu sai ya kara jin ya samu kwarin gwiwar da zai iya mutuwa a kanta, karku manta kaifafan idanunta suna ɗaya daga cikin abin da yasa yake kaunarta, bare kuma da ta zaro mashi su, ai abin ba'a magana. Ganin haka yasa Black Tiger bai bari sun ƙarisa shigewa ciki ba, ya yi saurin fitar da su dan kada Ronniensa ya cutu. A bakin ramin ya dakatar da su, sai huci mai zafi ne yake fita daga bakin Ronnie, da alama ran maza ya kai ƙololuwa wajen ɓaci. Shammatarsu Black Tiger ya yi ya raba hannun Ronnien da nata, kafin Ronnien ya yi wani motsi tuni ya turata cikin ramin ya kuma yi amfani da magic ɗinsa ya daskarar da Ronnien a wajen dan ma kada ya ce zai bi bayanta. Ya ɓatar da waɗan nan itatuwa da suke bakin ramin sannan ya yi yunkurin rufe ramin a shafe babin Sweetie kenan. Sai dai abin mamaki abin ɗaure kai shi ne, wani irin haske ne ta bayyana a cikin ramin mai hasken gaske, kofar ramin taki komawa ta rufe. Ya yi mamakin ganin hakan daga ta ciki, daga ta waje kuma mamakin bata bayyana ba. Tafiyar magic ya yi kamar wani walkiya sai ga shi a gaban ramin domin ya duba menene? Shi kuma Ronnie yana daskare ba motsi kaman gunki. Sai da ya ji wani irin shock a jikinsa lokacin da waɗan nan magic eyes ɗin nasa suka sauka a cikin wannan rami, hasken dake fitowa daga cikin sai da ta ɗan dishashe mashi gani, amma dik da haka bai girgiza ba. .................Ba komai ya haifar da wannan haske ba face hannun Sweetie, da yake da magic ya turata cikin ramin so tana tafiya ne bisa sarrafawarsa, hakan ya haifar da tafiyar tata a hankali hankali take yinsa, lokacin da zai rufe ramin ta daina ganin komai ta faɗa cikin wuta da kifiyoyin nan sai ji ta yi hanunta ya sake a in da ta nuna bakin ramin da tafin hannun nata tana yin alamar Ronnie dake tsaye ya taimaketa kada ya bari ta faɗa cikin wannan bakin azaban. Wannan nuna tafin hannun nata da ta yi shi ya haifar da wani irin hasken gaske da ya fito daga tsakiyar siraran jijiyoyin tafin hannun nata. Hasken kuma ya hana ramin komawa ya rufu. Tashin sense, me kuke tunani? Kenan Sweetie ma tana da magic ne ko me?!!. Zantukan babansa ne kawai suka dawo mashi cikin kunnuwansa a in da yake ce mashi. "Tabbas a duniyar neman Spender da zai yi zai haɗu da ƴar baiwa mai baiwa irin tasa, idan ya yi wasa ita ce zata zama ajalinsa, in kuma ya bi komai bisa tsari shi zai cinye game ɗin". Tuna wannan magana yasa zuciyarsa ta aminta da tabbas Sweetie ce wannan ƴar baiwar, domin tun daga kan yadda ta kurawa idanunsa kallo babu tsoro daga nan ya ji a jikinsa tabbas tana da baiwar irin nasa, bai kara tabbatar da hakan ba sai yanzu. A maimaikon ya yi amfani da dark magic ɗinsa ya kasheta kawai, sai ya fito da ita a cewarsa bai ga wani halitta da ya isa ya ja da shi har ma ya yi nasara a kansa ba, dan haka zai ƙaryata maganar babansa, a zuciyarsa ya raya zai barta a cikin empeir ɗin ya ga ta yadda za'ayi ta zama ajalinsa, yarinyar da bata wuce ya murkusheta bane zata zama ajalinsa? So Funny, wonder should never end in this world. A ganinsa kenan, ya raina baiwar Sweetie, amma ku me kuke gani my people's? Me kuke tunani? Dan ya karyata maganar babansa nacewa zata yi ajalinsa zai barta da ranta ya ga ta ya zata yi ajalin nasa!. Abin da yake tunani kenan fa, dan haka sai ya fitar da ita daga cikin ramin, ya kuma mayar da ramin ya shafeta kamar bata taɓa bayyana a wajen ba, har wani kyalli tiles na wajen yake yi kamar babu wani magic da ya taɓa wanzuwa a nan, ya saki Ronnie dake sankare, ita ma ya sake mata gaɓɓanta. Kamar walkiya haka ya koma saman swan chair ya zauna tare da ɗaura kafarsa ɗaya a saman chair ɗin, ɗayan kuma yana ƙasa, ya ɗaura hannunsa ɗaya saman laps ɗinsa. Da ido ta bishi da kallo har sai da ya zauna, sannan ta dawo da kallonta a kan Ronnie da yake kare mata kallo, ya ga ta rame, amma kuma ta kara wani irin kyau na musamman. "Ronnie wannan ne yayanka ko? He's so handsome sosai, kamar ba mutum ba, ka ga jikinsa kamar na Robbot ɗin nan da suke aiki a gidan nan, yanayin fatarsu iri ɗaya kamar madara". Tana magana tana zaro idanu irin like wow ɗin nan, ga mamaki sosai a saman face ɗinta, she was so surprised. Wato ita kwata kwata abin da ya faru da ita ma bai bata mamaki ba, bata wani tsorata ba, hasalima kyansa yasa bata ga azabar da yake gabanta wanda har ya yi niyar ɗanɗana mata ba. Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke tare da ɗan lumshe idanunsa kaɗan ya sake warosu a kanta, ya ji matuƙar mamakinta sosai, ya jinjinawa karfin halinta da rashin tsoronta. Kallonsa take yi tana jiran ya amsa mata wannan shi ne yayansa Black Tiger ko ba shi bane. Jinjina mata kai ya yi haɗe da ce mata shi ne. Wari irin kara zaro idanu waje sosai ta yi, she was so surprised na jin hakan, a hanzarce ta mayar da kallonta kan Black Tiger, babu ko tsoro ta ce. "Gaskiya yana da kyau sosai, kaga ɗan bakinsa ɗan karami kamar na Prettyna, amma yana magana ne ko bayayi? Dan naga bakinsa ya yi karami sosai". A ruɗe take maganar. Kamar Ronnie zai ɗan yi murmushi sai kuma ya fasa tare da cewa. "Amma baki ganin mirror ko?". Kai ta jinjina mashi alamar e. Harɗe hannayensa a saman kirjinsa ya yi kafin ya ce. "To ai kamar bakinki ma ya fi na yaya ƙanƙanta, jeki ga mirror a ɗakin ki ki gani". Ya ce ta je ta ga mirror ne dan yana son ta fita daga ɗakin kada Black heard ɗin Black Tiger ta motsa ya ce ya fasa yi mata afuwa ya gana mata wani azaban. Sai dai kash, ita da bata san da wani izaya ba ai gaban mirror dake cikin ɗakin nasa ta nufa domin ta duba face ɗin nata. Sosai Black Tiger ya yi mamakinta, wai ita bata san tsoro bane? Wata ɓangare na zuciyarsa ce ta tuna mashi cewa irin baiwarsa ke gareta fa, dan haka babu tsoro a jininta. Tashin sense, wlh akwai kura kuwa, Sweetie like black Tiger e kam akwai matsala, a cikinsu waye kuke tunanin zai kure wani? Shin da gaske kamar yadda babansa ya faɗa mashi ita ce zata zama sanadiyyar kawo karshensa da shi da zalincinsa ne ko kuma dai shi zai iya karyata maganar babansa ta hanyar barinta a cikin kingdom ɗin kuma ya zamana ba zata iya yi mashi komai ba? Waye kuke tunanin nasa tunanin zai zama gaskiya, baban Black Tiger ne ko kuma shi Black Tiger ɗin?! Muje zuwa, akwai game mai zafi a gaba. Tana isa dai'dai tsakiyar ɗakin in da yake tsaye ɗazun kenan da nufin ta nufi gaban mirrorsa ta duba kanta. Wani irin kara ne ya fito daga jikin mirror tasa tamkar karar shigowar sako. Slowly ya ɗago sharp romance eyes ɗinsa kai tsaye sai saman mirror ɗin masa, while ita kuma Sweetie ta dakata daga nufar wajen. A hanzarce Ronnie ya kariso in da take, jikinsa har kerma yake yi saboda tsorata, da karfi ya fisgi hannunta ya nufi waje da ita, tsoro yake kada bakar zuciyar yayan nasa ya motso kuma. Kamar aljani haka Black Tiger ya ɓace ɓat daga in da yake zaune, ya fito a gaban mirrorsa, wato tsafi fa ba abin da bata sanya mutum ya yi, Allah dai yasa mufi karfin zuƙatanmu kawai, amma matsafi abin tsoro ne. Zubawa mirror idanu ya yi yana kallo kamar Tv, wani irin tambatsetsen jirgi ne mai girman gaske yake landing a Black Tiger international airport dake cikin birnin na Black world, jirgi ne har jirgi, girmansa ya wuci tunaninku, yanayin tsarin jirgin sak yake kama da FR-55, sai dai shi kan jirgin sak fuskar bakar damisa, da alama wanna tana ɗaya daga cikin manya manyan jiragen da Black Tiger yake alfahari da su, dan tsarinta daban ne. Kafin jirgin ta kammala sauka jikin tampatsetsan mirrorn nasa ya rabe kashi biyu, rabi yana cigaba da nuna mashi landing wanna jirgi, rabi kuma ya fara nuno mashi cikin forest in da wasu zaƙwaƙuran matasan warriors ɗinsa ke ta aikin haƙar ɗanyar gold, kai sai dai fa muce masha Allah, amma arzikin gold kam ba'a magana, Black Tiger yana da arzikin da ba'a taɓa yin mai irinsa a duniyar yanzu ba. Dikkansu ya zuba masu idanu yana kallo har jirgin ta yi leading, wasu zaƙwaƙuran manya manyan Robbot ne suka fara kutsawa izuwa gaban jirgin, sai kuma wasu jiga jigan motoci masu ɗauke da sunan Black Tiger irin masu container a bayansun nan suka ɗan matso kusa da jirgin. Wasu Robbot ɗin ne suka zo suka hau bubbuɗe bayan containers ɗin, empty suke babu komai a ciki. Ana buɗe Fp na jirgin Robbot da suka matsa kusa da shi suka kutsa ciki. Wasu jiga jigan manya manyan caton masu ɗauke da hoton motoci a jikinsu waɗan nan Robbot ɗin suka fara fitowa da su daga cikin jirgin. Girman waɗan nan kwalaye sun wuci mutane su iya ɗauka sai dai Robbot ɗin. Yanzu fa kusan manya manyan ayyukan Black world dikka Robbot ne suke yi. Wanna jirgi maƙare yake da kayan billions of dollars, gabaɗaya kayan kyara sabbin motoci masu rai da lafiya ne. INA MASU CEWA BLACK TIGER YANA BURGESU TA ƁANGAREN GYARA KASARSA DA TAIMAKAWA WAJEN GANIN YA KAWO DIK WASU SABBIN TSARE TSARE DA ZATA KAWO MASHI CIGABA? TO A NAN DAI KUN YI GASKIYA, BAKU FAƊI BA DAN KUN SO SHI TA NAN, DAN FA BA KARYA YANA IYA ƘOƘARINSA WAJEN GANIN YA GINA KASARSA, BURINSA SU FI KOWACE KASA CIGABA DA KOMAI DA KOMAI, MATSALARSA DAI WANNAN BAKAR ZUCIYAR TASA TA ZALINCI NE KAWAI, BAREMA RABA UWA DA ƳAƳA DA YAKE YI, ABIN AKWAI TAƁA ZUCIYA. Kafataren companynsa na kyara motoci za'a kai waɗan nan kaya domin a fara haɗa motoci sabbi wanda babu irinsu a duniya, a kullun yana son yaga shi ya fara kirkiro abu in ya so daga baya saura ƙasashe su kwaikwayesa, wannan yasa ya yi dogon nazari kafin ya fito da tsarin motocin nasa. A kallah containers sun kai 50 a wajen, amma sai da suka cika tab da kayan nan da Black Tiger aircraft ta ɗauko. Wani irin ajiyar zuciya ya sauke ganin dik abin da ya buƙata sun sauka lafiya, a hankali ya mayar da kallonsa a kan masu hakar gold, yadda yake kallonsu ya ɗan zare sharp eyes ɗin nan nasa sai ya baku tsoro, kamar ba idanun mutum ba, da alama magic eyes ɗinsa ya juyo ba na ainahin ba. Wani daga cikin warriors dake hakar gold ɗin ne ya miƙe tsaye tare da ihu yana faɗin. "Red gold, red gold!!". Ɗan kara zaro idanun Black Tiger ya yi. "Red gold!". Ya maimaita kalmar. Ga dikkan alamu ya ji daɗin samun red gold a karkashin kasan kasarsa da suka yi, red gold shi ne abu na biyu a tsada a duniya cikin Precious stones and mentals, yana da bala'in tsada fiye da tunaninku, ga balai'n daraja, ya fi normal gold tsada nesa ba kusa ba, samun wanna red gold ɗin a karkashin kasar birnin Black Tiger ba karamar nasara bace, a yanzu haka suna da dukiyar iya karawa da kowace kasa bare kuma ace sun kara samun arzikin red gold? Me kuke tunanin zai faru? Wani irin arziki kuke tunanin Black world ko in ce Black Tiger zai kara samu?. Duniya iya duniya wa Black Tiger fa my people's. Sosai ya ji daɗin wanna karuwa da suka samu, sai dai babu ko ɗikon alamar canji daga face ɗinsa da zai sa ka fahimci ya ji daɗi, yana nan yadda yake kamar hadari. A hankali ya juyar da idanunsa daga magic eyes izuwa ainahin sharp eyes ɗinsa. Kamar walkiya haka ya ƙarisa bakin wanna daular bed ɗin nasa duniya guda. Zama ya yi da alamar nazari ya shiga a kan yadda zai kara bunƙasa kasarsa, yadda zasu ci moriyar wannan red gold ɗin. P-R-I-N-C-E-S-S T-E-E-M-A💘🔥 ___________💘🔥______________ A bangaren Sweetie and Ronnie kuwa, yana jan ta bai dakata a ko'ina ba sai a room ɗinsa. Suna shiga ya saki hannunta yana sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya sha da kyar, ko da yake kusan hakance da kyar suka sha. Ita kuwa room ɗin nasa ta fara bi da kallo tana mamaki ganin kusan komai dake room na Black Tiger irinsa ne a nan, hakan na nufin Ronnie fa ɗan gata ne na karshen kasasheshe. Ganin ba shi take kallo bane yasa ya miƙa hannu ya janyota ta faɗo jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Da sauri ta ɗago kai tana kallon face ɗinsa, while shi ma ita yake kallo babu ko kyaftawa, an jima ba'a haɗu ba, ya sha kewarta matuƙa. "Ronnie meyasa baka je wannan ɗaki da yayankan nan ya ajiyeni ka dubani ba? Ka barni ni kaɗai sai wani mugun mutum da yake zuwa tambayata wai ina Spender? Idan ban gaya mashi ba sai ya yi ta azabtar da ni yana bani wahala, ranar har maciji ya saka mun........". Ta dakata da yin maganar tana sauke numfashi tana ƙoƙarin fara kuka. Bai iya ce mata ko uppan ba saboda har lokacin yana ganin kamar Black Tiger bai kyaleta bane, yana ganin kamar zai zo ya rabasu. "Wani ɗaki wannan mugun ya kaini, ɗakin babu hanya kuma dik in da ka juya sai kaga kanka, (kewaye yake da mirror kenan) a wannan ɗaki ya sakani sai ya turo mun wani bakin maciji mugu, dik ta in da zan gudu sai in ga babu hanya sai dai hoton fuska zan gani, ga macijin shi kuma yasan hanyan sai ya yi ta bina, ina ta ihun sunanka kuma baka zo ba.............". Tana kai karshen maganar ta fara ruwan hawaye masu ɗumi, wato kenan dama azabtar da ita Black Tiger ya rinƙa yi da ya ɗauketa, ya yi ta razanata, Allah sarki wlh razana tafi zahirin mugunta cutarwa da wahalar da zuciya, wani ma idan yana da karamar zuciya mutuwa zai yi idan aka razanar da shi, Allah gara a maka azaba direct a kan ayi ta razanaka da ababen ban tsoro. Wato Black Tiger ainahin bakin mugu ne da babi mix wlh, yasan sirrin mugunta da azabtarwa. Hannu Ronnie ya kai ya fara goge mata kwallar dake idanunta ba tare da ya yi magana ba, saboda shi dai yasan Black Tiger baya yafiya, bai taɓa yafewa kowa ba a rayuwarsa, ya kware wajen yi wa mutane azaba da wuta, so sai yake ganin kamar zai zo ya raba shi da ita. "Ronnie ka yi magana mana". Ta faɗa yanayin voice ɗinta a shagwaɓe sak na PRETTY yau kuma. Jinjina mata kai ya yi, can kasan makoshinsa ya furta. "Zan yi magana Sweetie, amma ba yanzu ba, for now dai kyaleni ki yi shiru". "To yunwa nike ji fa". Ta faɗa tana ɗan kwantar da kanta a wannan faffaɗar kirjin nasa na ƴan Wrestling ɗin. Da sauri ya ɗago kansa haɗe da kallonsa a kanta. "To hau saman bed ɗina ki zauna bari in kawo maki abincin ko?". Da kyar ya iya furta hakan. Da okey ta amsa mashi tare da wucewa ta nufi saman luntsumemen bed ɗin nasa, har tsoron haurawa taji ya kamata, gani take kamar idan ta hau zata jita a sama. Idanunsa a kanta, bai fita ba yana jiran ta haura bed ɗin sannan ya fice. Da yaga kamar ba zata iya hawa ba sai ya ce. "Ki hau babu abin da zai faru". Da sauri ta juyo da idanunta a kansa, kai ya jinjina mata alamar tabbatarwa da babu abin da zai faru. Da sauri ta haye ta zauna, sai da ta ɗan lumshe idanunta ta sake buɗewa saboda daɗi da laushin mattress na bed ɗin, ga wani kamshi na musamman mai kwantar da hankali dake tashi a arear wajen. Juyawa ya yi ya fice daga room ɗin, ita kuma ta fara bin ko'ina da kallo tana mamakin yadda komai yake a shirye tsab gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali, ga fitinannen kamshi mai sanya nutsuwa a zuciya, lallai yanzu ta yarda da zancen Floris da take ce mata Ronnie shi kaɗai ne kanin Black Tiger, kuma ɗan gata ne, a yanzu ta gasgata hakan matuƙa. Shiru ta zauna tana sakawa da warwarewa a cikin kwakwalwarta har ya dawo cikin room ɗin hannunsa ɗauke da katon glass tray mai shake da kayan abinci tab a ciki, abubuwa kala kala wanda bata taɓa ganin makamantansu ba. Saman glass center table dake tsakiyar wasu egg chair a can gefe ya ɗaura kayan abincin, a ɗakin Black Tiger swan sofa chairs ne, a ɗakin Ronnie kuwa egg chairs ne, sunanan kamar design na kwai ne a ka fafake cikinsu aka yi wajen zama, sun yi matuƙar tsaruwa sosai. "Zo in baki ki ci sai ki yi wanka mu je ki rakani". Ya yi maganar yana kai kallonsa a kanta. While ita ma shi take ta kallo, sai yanzu ta lura da ya rame kaɗan ya kuma kara hasken fata, kamar wanda ya jera kwanaki yana zazzaɓin dare. "Ina Floris?". Ta jefa mashi tambayar tana saukowa daga saman bed ɗin. Sai a lokacin ya tuna yau bai haɗu da ita ba, ya je school ya rubuta last exams ɗinsa ya dawo, yana dawowa kuma wajen yayansa ya wuce domin ya gaya mashi ina Sweetie take, a kan haka suka samu matsala ya fita ɗakin a fusace, zaman da ya yi a cikin cineman part ɗin yasa ya samu sanyi a zuciyarsa da har yasa ya miƙe ya dawo wajen Black Tiger domin ya bashi hakuri sai ya sameta a ciki. "Ya ka yi shiru baka bani amsa ba?". Ta yi tambayar ne a kusa da shi, bai ga lokacin da ta sauka bed ɗin ba, saboda ya afaka duniyar tunani. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "I don't know where's she, amma nasan ba zai wuce she's in her room or Delisha room ba". Yana kai karshen maganar ya miƙo mata hannunsa a kan ta kama. Ba musu ta saka ƴan hannayenta saman tafukansa, har ga Allah tana jin daɗin kasancewa a tare da shi. Kamata ya yi ya zaunar da ita saman lallausan duma dake shinfiɗe a wajen, sannan ya sauko mata da trayn haɗe da tambayarta me zata ci. Zubawa abincin idanu ta yi tana kallonsu, bata ma san menene bane bare har ta iya zaɓa, nama kawai ta sani wannan ma dan wanda yake taimaka masu a forest yana kawo masu nama sosai, so tun kafin ta makance tasan ya kamannin namar yake. "Ko dai in zaɓa maki ne?". Ya yi magana idanunsa a kanta. Ɗago kai ta yi suka kalli juna. "Ni fa Ronnie ban san waɗan nan abubuwan ba, amma dai ka bani naman ya fi tun da shi nasani". Tun da ta fara magana ya kafe ɗan bakinta da idanu yana jin wani irin shaukin yadda take motsa laɓɓanta wajen furta word, har ji ya yi baya son ta dakata da yin magana. "Namar jimmina ce da ta ɗawisu, sannan akwai ta ɓauna, wanne zaki ci". Yadda ya yi maganar sai ya burgeku, saboda idanunsa a kan lips ɗinta ya yi, kuma ya yi maganar kamar wanda bakinsa yake ciwo. "Dik abin da ka lissafan nan ban sansu ba, ni dai nama kawai na sani". Hannu ya kai saman tray ɗin ya ciro mata wani haɗaɗɗe tsadadden plate mai shake da namar ɗawisu wanda ya ji gashi mai kyau, sai tashin daddaɗar kamshi yake yi ya ji kayan haɗi. "Kin ki ki faɗa mun sunanki na ainahi ko Sweetie?" Yana magana yana ɗauko kananan wukake haɗe da fork domin ya taimaka mata wajen yanka namar ta samu ta ci. Ɗan siririn murmushi ta saki har sai da dimples ɗinta suka lotsa kafin ta ce. "Sunana na ainahi Sweetie". "Ba gaskiya bane! Sweetie ba suna bane". Shiru ta ɗan yi, wani zuciya yana ce mata ta faɗa mashi gaskiya, ta yarda da shi, shi ɗin ba mugu bane, wani zuciya kuma yana gaya mata kada ta yarda da shi, dan mom ɗinsu ta gargaɗesu a kan kada su yarda da kowa a duniya idan ba Kamran ba!. "Don't restrict yourself, in baki son gaya mun ba sai kin sha wahalar tuna abin faɗa mun dan in ji daɗi ba, don't worry, a dik yadda kike zan ji daɗin kasancewa dake, so forget about the name, yanzu karɓi abinci ki ci". Ya yi maganar ne bayan ya saita mata fork mai ɗauke da gasashen namar ɗawisu a saitin ɗan bakinta. Sosai ta ji wani irin a jikinta na jin furucinsa, jikinta ya yi sanyi, bai kamata ace ya nemi sanin wani abin dangane da ita ta ɓoye mashi ba, amma ya zata yi to? Dole ta bi umarnin mom ɗinsu. Buɗe ɗan bakin nata ta yi ya saka mata namar, suna aikin ganin juna ido cikin ido. "Ka yi rashin lafiya ne Ronnie?". Kai ya girgiza mata alamar a'a, sannan ya ɗaura da cewa. "Me kika gani?" B komai ta bashi amsa tana ƙoƙarin ɗauko ruwan roba dake cikin tray ɗin. Hannu yasa ya karɓi ruwan tare da ɓalle mata bakinsa, sannan ya zuba mata a tsadadden glass cup da ya zo da shi. "Yau zaki bini church ko?". Ya yi magana yana miƙa mata ruwan. Karɓa ta yi ta kafa a bakinta, kusan rabi ta sha kafin ta cire, tana ƙoƙarin ajiyewa a kasa ya kai hannu ya karɓa, bakinsa ya kai ya shanye ragowar tare da ajiye cup ɗin ya zuba mata idanu tana taunar namar da ya bata bayan ta cire cup daga bakinta. "Mu bama zuwa church ai". "Why?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Coz I am a Muslim". "Komai nace maki sai ki ce mun baki sani ba, to ya aka yi kika san church kika kuma san banbancin addininmu?". Ya jefa mata tambayar yana ɗaga mata gera ɗaya, har lokacin idanunsu a kan face ɗin juna. "Saboda shi abu ne wanda ya shafi addini, ko ban san church a ido ba na karanta labarinsa a litattafanmu na addini". Ɗan zaro idanu kaɗan ya yi kafin ya ce. "Okey kenan in na fahimta addininku ya yi magana a kan namu?". Jinjina mashi kai ta yi haɗe da cewa. "Kamar yadda ainahin littafin addininku yake magana a kan musulunci ba". Ɗan girgiza kai ya yi. "Ban gane ainahin littafinmu ba? Ko so kike ki ce yanzu ba na ainahi muke amfani da shi ba?!". Haɗiye namar dake bakinta ta yi kafin ta amsa mashi da. "Kusan hakance, ainahin littafinku ai annabinmu ne ya zo da ita, kuma magana take a akan musulunci da dokokin Allah da dai sauransu, amma yanzu gabaɗaya an canza littafin da rubutun cikinsa, masu son zuciya tun tsawon shekaru da suka gabata sun canza wasu abubuwa, a hankali hankali suka rinƙa zare wasu shafuka masu muhimmanci daga ciki, suna shigo da na san zuciyarsu dan su ɓatar da alumma, haka mom ɗinmu ta ce mana". Tun da ta fara magana idanunsa yake a saman laɓbanta babu ko kyaftawa, sai dai kunnuwansa suna saurarenta da kyau, ƙwaƙwalwarsa kuma yana jujjuya mashi zantukan nata, lallai ba shakka ta zo da babban al'amari, ya za'ayi ta ce an canza masu littafi? Ƴar karama da ita da wanna zancen, lallai so take ta jawa kanta bala'i, dan kuwa ba zata iya wanna faɗar ba!!. Sai da ta dasa aya a maganar ne ya sauke ajiyar zuciya tare da ajiye fork na hannunsa, sannan ya ɗan gyara zama kaɗan. "Addininki ne ya ce maki an canza wasu shafuka cikin littafinmu ko kuma littafinku ne ya ce hakan?". Ya jefa mata tambaya. "Ko ɗaya daga ciki, ba addinina bane, hasalima ni addinina kyakkyawar zato yake yi wa kowa". "To ya akayi kika san and canza littafinmu domin a cigaba da gusar mana da hankali muna tafiya a kan ɓata?". A gaskiya Ronnie yana da saukin kai sosai, kuma ga dikkan alamu yana bala'in jinta har cikin ransa sosai ne yasa har ya iya jure maganganunta, kun san ba kowa zai yarda acewa da littafinsa da kuma malaman da yake bi haka ba, ba wanda zai yarda a ƙaryata malamansa ko kuma ace suna cutar da mutane wajen canza maganar gaskiya izuwa ta karya, amma shi cikin kwanciyar hankali yake yi mata tambayoyi ta hikima haɗe da ilimi, gaskiya ilimi ta yi a rayuwa, tana sanya iya magana da zama da kowa lafiya sosai, jahili yake faɗace faɗace ba mai ilimi ba!. "Zan gaya maka yadda aka yi na sani, zan kuma baka hujoji masu karfi da zaka yarda dani, amma sai na koma wajen mu tukun nan, dan dik hujojin suna forest ɗinmu". Shiru ya ɗan yi yana tunanin yadda za'ayi ta bar empeir ɗin nan har ta je ta bashi hujojin, ga shi yana son waɗan nan hujoji ko dan ya gani da ido, to me abin yi? Dan dai Black Tiger ba barinta zai yi ta tafi ba tare da ta bada Spender ba!. "Zaka taimaka mun na bar nan?". Tambayarta da ya ji takmar saukar aradu kenan, har sai da ya ji kansa ta ɗan juya mashi tana wani sarawa. Idanunsa a cikin nata bai iya bada amsa ba, dan bashi da ta cewa. "Ronnie ina kewar ƴar uwata sosai, ina son komawa forest domin in je in ganta, please ka taimaka mun na bar nan ka ji?". Tamkar zata sanya kuka ta kai karshen maganar. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan jinjina mata kai haɗe da cewa. "Zan taimaka maki ki bar nan kamar yadda kika buƙata, amma da sharaɗi guda biyu, idan kika mun abubuwa guda biyun nan tabbas zan fitar dake daga nan koda kuwa hakan zai zama sanadiyyar mutuwata!!"....... BABBAR MAGANA!!. A hanzarce ta ce. "Menene sharaɗin? Ka gaya mun kome ne zan yi". Cigaba da yanka mata namar ya yi yana faɗin. "Zuwa dare zamu yi wanna magana, zan gaya maki sharaɗin, yanzu dai ci abinci ki je ki yi wanka". Bata yi mashi musu ba, dan ta lura musu yana ɗaya daga cikin abin da baya so, tun zuwanta empeir ɗin ta fahimci hakan a tsakaninsa da su Floris, dan haka sai ta yi shiru tana karɓar namar da yake bata har sai da ta ƙoshi. Sannan ya rakata toilet ɗinsa da kansa ya fito ya barta a ciki, ta yi tsaye tana ganin ikon god, duniya guda kamar ba za'a mutu ba. Shi kuwa ya dawo ya kwashi kayan abincin ya nufi waje da su. Yana fitowa babban parlourn kasa ya isko Floris ta ci kwalliyar sexy dress, ta yi kyau sosai, ɗan rigarta a iya cibiya ya tsaya mata, sai sket da bai gama rufe gwiwanta ba black color, rigar kuma white, da yake in baku manta ba mutanen birnin Black world suna da yelwar tsawon gashi sosai kamar turawa, haka ta sake dark brown hair nan nata har baya, sai sheki yake yi yana curlyn. Ɗan bakin nan nata ya sha lips balm sosai sai sheki yake yi, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya tana rike da wayar Ronnie tana latsawa, ta yi kyau irin sosai ɗin nan. Tun da ya sako kafarsa a saman stair case ɗin yake binta da kallo har ya karisa saukowa. Jin motsin mutum yasa ta yi saurin ɗago kanta da kallonta a kansa. Ganin shi ne yasa ta mike har da haɗawa da ɗan gudunta ta nufesa. Buɗe mata hannu ya yi ta faɗa saman Wrestling chest ɗinsa. Tana faɗawa jikinsa wani Robbot ya kariso wajen ya karɓi kayan abincin dake hannunsa ya juya ya nufi hanyar kitchen da shi. Shi kuwa kamar wata ƴar tsana haka ya ɗagata sama sai saman shoulder ɗinsa suka juya izuwa sama. "I really missed u mine". Ta faɗa tana saƙalo wuyarsa. Yau yana cikin farinciki ya ga Sweetie kuma Black Tiger ya barsu a tare, hakan ba ƙaramin farinciki ya haifar mashi ba, cikin sanyin murya ya amsa mata da. "Missed u too babydoll". Ɗan bakinta ta kai saman lallausan kumatunsa ta fara sumbata tana goge mashi lips balm dake saman lips ɗinta. "Zaki fara ko?". A shagwaɓe ya yi maganar. "Ba kai ne ka barni sai da na yi missed ɗinka sosai sanna ka waiwayeni ba?". Yana cigaba da tafiya ya nufi room ɗinsa ya gangaro da ita izuwa saitin wrestling chest ɗinsa, ya zama suna kallon juna. Fingerprint ya sanyawa door room ɗinsa ta buɗe ya shige ciki da ita yana ta kallon face ɗinta. Saman bed ya sauƙeta, kamar mai jin barci ya furta. "Ki taya Sweetie ta sanya kaya ta shirya ina zuwa". Ta ɗan yi mamakin jin yadda ya yi maga a kasale sosai, ta san shi ɗin shagwaɓaɓɓe ne idan ya yi ra'ayi, sannan tasan riƙaƙƙene ta ɓangaren iya kalaman soyayya, amma bata taɓa jin ya yi magana a irin wannan yanayi ba, bata san cewa yanzu ya fara girma yana jin feeling sosai bane, da ai sai dai ya yi dik abin da zai yi na shagwaɓarsa baya jin komai, amma yanzu girma ta fara zuwa, ya fara amsar sako. Bai jira amsarta ba ya juya ya fita. Bai zame ko'ina ba sai room ɗin Black Tiger. After some minutes. Ya fito sanye da sport wears ya nufi room ɗinsa. ==========🔥🔥🔥=========== ALKALAMIN P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ *Ina yi wa ɗaukacin al'ummar musulmi murnar shiga sabuwar shekara ta 2025, Ubangiji Allah ya sadamu da alkhairan dake cikinta, Allah ya nisantamu da sharrin dake cikinta, Ubangiji Allah ya shiga lamuranmu ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu da ma dikkanin in da musulmi suke, ya Allah yasa mu cika da kyau da imani ya kuma kara mana kaunar manzon rahma manzon tsira.* Wani birki ya ja a bakin kofar room ɗin ta ciki, idanu ya zaro waje yana kallonta, tamkar kwayar idanunsa zasu faɗi ƙasa. Sam bai san lokacin da bakinsa ya furta wow ba. Like wow, ni ma dai sai da na furta wannan wow ɗin a lokacin da idanuna suka sauka a kan Sweetie sanye da kayansa na sport, kun san shi mayen wasanni ne, yana da dik sport wears na wasanni kala daban daban. Floris da iya tsiya sai ta bata riga da wandonsa na football ta saka, wandon ya yi mata tsawo sosai, rigar kuma da yake roba ce kuma sababbi ne bai sakasu ba bare faffaɗar wrestling chest ɗin nan nasa ya buɗesu sai ya ɗan kamata kaɗan. Floris ta gyara mata golden white hairnta tare da sanya mata mayukan gyaran kansa, gashin ya yi bala'in kyau sai sheki yake yi, yanzu ne ma tsantsar kyan gashin ya kara bayyana da ya samu gyara, wlh kamar ka kwace gashin dan kyansa, dole ashe ya zama mafi tsada a duniya, ashe haka yake da balai'n kyau, gyara ne dama bai samu ba. Kasa ƙarisowa cikin ɗakin ya yi, kawai ya harɗe hannu saman kirji yana binta da ido, dik sai ya ji wani irin wahalallen kasala ya kama shi..................... "My ka shigo mana". Cewar Floris dake dake mashi saman bed kamar wata matarsa, ita kuma Sweetie tana tsaye gaban mirrorsa tana ganin kayan yadda ya dace da ita, sai a yau ta tabbatar da ashe kyakkyawa ce ita fa, ta mace da kallon kanta. Jin Floris ta yi magana ne yasa Sweetie juyo da kallonta izuwa door room. Ganin shi ne yasa ta saki cool murmushi har sai da dimple ɗinta suka lotsa. Hakan ba ƙaramin kara jan hankalinsa ya yi ba, sai ya ji shi a wata duniya. "Ronnie na yi kyau?". Cikin sanyin murya ta yi maganar. Jinjina kai kawai ya yi bai iya furta uppan ba, saboda ta yi mugun tafiya da tunaninsa, yama rasa me zai ce. Kara faɗaɗa murmushinta ta yi, ta ji daɗin ya ce ta yi kyau. Floris dai binsu da kallo take yi tana ta sakin uban murmushi abinta, da alama ta ji daɗin kasancewarsu a tare. "Sweetie wai ke bakya shiga damuwa ne?". Cewar Ronnie, bai yi zaton zai ga murmushi a kan face ɗinta ba, saboda a tunaninsa wannan wahala da ta sha zai sa dik wani sauran farinciki da ya rage mata ya kau daga fuskarta. "Meyasa zan shiga damuwa Ronnie?". Still akwai murmushi a saman face ɗinta ta bada amsar. Ta yi maganar tana jingina bayanta da jikin mirror. "Naga kin sha wahala ne shiyasa, a tinanina zaki shiga damuwa a kan hakan, kuma ga ƴar uwarki bata a tare dake, dik da haka baki shiga damuwa a kan hakan ba!". A kasale sosai voice ɗinsa take fita. Ko a jikinta kamar an yakushi kakkausa, cikin sanyin murya ta ce. "Ni da nike da Allah da manzonsa meyasa zan ji wani damuwa dan wani bawan Allah ya cusguna mun? Dik abin da kaga ya faru dani mukaddari ne daga Allah, kuma mu mun yi imani da Allah dole mu karɓi kaddararmu hannu bibbiyu a dik yadda ta zo mana in ma mai kyau ko akasinta!". Baiwar Allah tana magana tana murmushi. Ɗan zaro idanu Floris ta yi tana kallon Ronnie, ta ji sabon karatu yau. Shi ma Ronnie zancen Sweetie ya taɓa zuciyarsa, dan haka ta wutsiyar idanu ya kalli Floris while ainahin kallonsa yana a kan Sweetie, tabbas har cikin ransa ya ji yana son sanin wannan Allah da manzonsa da idan ka riƙesu ka bi umarninsu ba zaka taba shi damuwa ba, dik wahalar da Sweetie ta shiga, ga makanta dik, uwa uba aka rabata da ƴar uwarta, ga rashin iyaye, dik bata taɓa shiga damuwa ba dan ta rike Allah da Manzonsa, dik azabar Black Tiger bai ɗaga hankalinta ba saboda ta rike Allah, hakika zai so shi ma ya san ta yadda zaka bi ka rike Allah har ka more haka, sai dai kuma da kamar wuya in dai yana Black world. "Ya kayi shiru Ronnie?". Cewar Sweetie. Girgiza kai ya yi ba tare da ya furta uppan ba, amma abin ya bashi matukar mamaki kuma ya ratsa zuciya da gangar jikinsa, sai nanata kalmar idan ka rike Allah da manzonsa, ka yi imani da su ba zaka shiga damuwar komai ba, Allah ba zai bari ka ji kunci ba, sai nanatawa yake yi a cikin ransa yake yi, like wow abin ya ƙayatar da shi ba kaɗan ba. "Ronnie zaka je wasa ne?". Floris ta jefa mashi wannan tambaya. Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya yi magana ba, da alama jikinsa ya yi weak sosai, bawan Allah ya ji ɗaya daga cikin karfin ubangijin gaskiya!!. Idanunsa a kan Sweetie, ita ma tana rike da wayarsa da ta karɓa daga hannun Floris dan ta gani, amma kallonta da nutsuwarta na'a kansa, Allah Ronnie ko baka son ganin kowa in yana waje sai ka ji sha'awar ɗaura idanunka a kansa, saboda kyau, sai ma idan yana murmushi tare da ƴanmatansa. Ga shi ya karyawa Delisha kafa tana can tana jinya, wato Ronnie ma fa mugune wata sa'an, yanzu haka ta fara samun sauki tana koyan takawa da sanda, amma ta ji a jikinta kam, ta gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah ne ƴar banza. "Ronnie zan bika wajen wasan ka ji?". Cewar Sweetie. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Zo mu je, time ya cika, tun da kuka zo gidan nan ke da Floris kullum nine bayan shiga wajen wasa". Murya a kasale ya yi maganar. "Meyasa to?". Sweetie ce ta jefa mashi tambayar. "Saboda biye maku da nike yi mana, kullum nine karshe". Floris ce ta karɓi zancen da cewa. "And you're a winner everyday ba". Kashe mata ido ɗaya ya yi alamar haka ne zancenta. "To kuzo mu je". Ya faɗa yana miƙa masu hannu. Kusan a tare suka kariso gabansa, wayarsa dake hannun Sweetie ya fara karɓa ya zura a aljihu kafin ya kama hannayensu, suka nufi waje. Sai daɗi Sweetie take ji yau, hakika tana da karfin tawakkali da imani da Allah Sweetie, ta yadda da kaddara mai kyau ko maras kyau, bata sanyawa kanta damuwa ko kaɗan, idan ta tuna kuncin dake cikin rayuwarta, cikin sauri take tunano girma da niimomin da Allah ya yayi mata, hakan yakesa ta mance ƙuncinta, mu koya daga gareta domin mu ji daɗin gudanar da al'amuranmu cikin nutsuwa, mu kuma kara karfafa imaninmu!!. Sosai filin wasan skaternsu yau ya cika, matasa sai gwada baiwarsu suke yi, ga ƴan gasa sun shirya tsaf, tsabar kaunar wasan da Ronnie yake yi, yanzu haka yana kammala karatunsa zai shiga wasannin duniya gabakiɗaya bisa yardar Black Tiger, ya yi mashi hakan ne dan ya faranta mashi ransa sosai. Kowani matashi yana gwada baiwarsa, babu nuna ragonta, dik sun tsaya tsayin daka dan nuna jarumtarsu. Saman ƙayatattun kujeru na musamman ya zaunar da Floris and Sweetie wanda tun shigowarsu wajen idanun kowa yake a kansu. Saboda kaunar wasannin Ronnie yasa Black Tiger ya gina masu wannan stadium ɗin, dik dan farincikin kanin nasa. Tin da ya sako kafafunsa cikin wajen jama'a suke ihun sunansa da ɗaukar tafi da hannayensu, ji kake fito ya karaɗe ko'ina, da alama suna murnar zuwansa sosai. Ya saye zuƙatan kowa!. Sai da ya sumbaci kumatun Sweetie and Floris sannan ya juya ya shiga fili, nan fa tafi da fito ya kara yawaita sosai. Master Devil ne ya bashi skatersa ya sanya a ƙafafunsa, dik wajen nasa takalmar ce kawai ta fita daban, dan haɗuwa da tsadarta ya wuci tunaninku, dik takalmar wasanninsa da ɗanyar gold Black Tiger yasa aka kyara mashi su, kunga kuwa ai bazama ayi zancen tsada ba, dan akwai kuɗi kam. Zuba mashi idanu su Sweetie suka yi suna ta kallonsa, shi ma idanunsa yana a kansu. Ƴan wasa gabaɗaya sun tsaya layi kowa jira yake yi su fara, sai fito ake yi. Wani katon warriors wanda ya ji horo ya ƙoshi ne ya hura masu usir dan a fara wasa. Tafi da karfin sautin fito ne ya kara karaɗa wajen. Floris ma tafi ta fara yi tana faɗin Ronnienta ne winner. Ganin tana tafi yasa Sweetie ma ta fara yi, yanzu dik abin da Floris ta yi ita ma sai ta yi. Kun san wasan skater kusan yana tafiya ne da zuciyar mutum, kamar gudun doki ne, idan kana a kan doki, to gudunsa ya ta allakane da yanayin bugawa da gwazon zuciyarka, shi ma haka yake. ====================💘🔥 Ko gargada Ronnie bai taɓa yi a wasan skater ba, sai ga shi yau saura kaɗan ya yi wani mummunar faɗuwa Black Tiger ya tare mashi da magic ɗinsa, ba komai ya haifar da hakan ba kuma face Sweetie. Suna tsaka da tafi ita da Floris suna kallonsu suna nishaɗi, kwatsam sai ta nuna takalmar ƙafarsa da yatsanta tana tambayar Floris amma takalmar Ronnie na gold ne ko?. Dan ta gansa yana kyalli sosai. Wannan nuna shi da yatsa da ta yi unexpect magic ɗinta ya fita, baiwar Allah sam bata ma san yadda zata sarrafa magic ɗinta ba, dan bata san da shi a tattare da ita ba, in dai zata nuna abu da hannu to da wuya idan magic ɗin bai fita ba, kuma a iya hannun hagunta ne abin. Wani ɗan siririn haske ne ya fita daga hannun nata kai tsaye sai kan takalmar Ronnie da ta nuna hasken ya nufa, hakan ya haifar mashi da tuntuɓe, da yake Black Tiger yana ganinsu ya ga magic ɗin nata, ya kuma yi sauri ya tare shi, amma dik da haka da yake nata yana da karfi sosai sai da ya sa Ronnien tuntuɓe kamar zai kifa ƙasa, da ya faɗi kuma za'ayi mummunar faɗuwa, saboda ƴan wasa dayawa suna biye da shi a baya, da dik zasu faɗi, wasu su faɗi a kan junansu. Dayawan mutanen dake wajen sun sha madarar mamakin ganin Ronnie ya yi tuntuɓe, sai dai ba wanda ya ga dalilin hakan, shi kansa ya ɗan yi mamaki, dan dai wajen flat yake babu wani gargada, to me ya sanya shi wannan tuntuɓe? Ya jefawa kansa tambaya. Yana can yana wannan tunani har wasu ƴan wasa biyu suka tsere mashi ba tare da ya farga ba, sai da ya ji ihun Floris tana ambatar sunansa ne ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka. Cikin tafasar jini ya fara gwabza wasan, kafin wani ɗan lokaci ya wuce waƴan can. A lokacin da ƴan wasan can suka wucesa har sai da damuwa da rashin jin daɗin hakan ya bayyana a saman face ɗin sweetie, Allah sarki bata san ita ce sanadi ba. Shiru Black Tiger ya yi yana tunanin meyakamata ya yi domin cire magic dake jikin Sweetie? Dan in ba haka ba watarana zata iya zama ajalin Ronnie ba tare da sun sani ba, ko da bai rabata da magic ɗin ba ya zamana shi yake sarrafa magic ɗin nata, dan tsaro, ita bata san da shi a tattare da ita ba, zata yi ɓarna sosai a dalilin hakan. Can wani zuciya ya ce mashi. "To ai kila saboda magic ɗin nata ne yasa aka ce ita ce zata kawo karshenka!". Tuna hakan yasa ya kara ɗaur wanna fuska mai kama da hadarin, dan in kuwa hakan ce da wuya ya iya sarrafa magic ɗinta, tunani ya fara yi a kan wacece ita ma tukun nan ? Ina asalinta yake? Wani shafaffe da mai ya bata magic?. Waɗan nan sune tunanin dake ransa!. Ni dai bana tunanin mahaifiyarsu Sweetie ce ta bata magic, domin kuwa mom ɗinsu baiwar Allah ce mai riƙo da addini, ga shi har ta koyar da su karatun addini da har suka koyawa Kamran ga shi yanzu tana karantar da Ronnie girman Allah, kun ga kuwa mom ɗinsu mutuniyar kirkice, da wuya ta koya masu tsafi. Dik yadda aka yi ko dai mahaifinsu ne ko kuma wannan sadauki mai taimaka masu ɗin, akwai dai cakwakiya da sarkakiya mai ɗaure kai, to Pretty ma tana da shi ne ko dai iya Sweetie ce kawai?. Da alama kuma ita ma Sweetie sai da ta haɗu da Black Tiger ne magic ɗinta ya bayyana, dik yadda aka yi magics ɗinsu yana da alaƙa ko dai wani abin makamancin hakan!!. Lokacin da Ronnie ya matso kusa da su sai da ya kashe masu ido ɗaya. Fito mai sauti Floris ta saki, ita kuma Sweetie da bata iya fito ba sai kawai ta sakar mashi murmushi tana cigaba da yi mashi tafi. A karo na biyu ta sake cewa Floris. "Amma skater kafar Ronnie da gold aka yi ta ko?". Kai Floris ta gyaɗa tare da cewa. "Yeah, da gold yaya yasa aka yi mashi". Ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin yadda suke facaka da gold, bayan kuma Ronnie ya gaya mata irin tsada da darajar da gold yake da shi, amma a haka suke abin da suka ga dama da shi, bata san arzikinsa Allah ya yi masu ba, a tunaninta saya suke yi, hakan yasa take kara jinjinawa karfin arzikinsu. Da gudu Floris ta miƙe ta nufi cikin wajen wasa, da idanu Sweetie ta bita tana mamakin ina zata je to?. Tana zuwa ta daka tsalle ta faɗa jikin Ronnie dake tsaye, abin ku da babu Muslunci a waje, iyayen Floris suna wajen suna ganin wasan, amma ko kaɗan basu damu ba dan Floris tana yawan rungumar Ronnie, shi ma kuma yana ɗaukarta, wani lokaci har goyata yake yi, babu ruwansu......... Kai wato musulunci fa ya yi a rayuwar nan, Allah dai ya bar mu a cikin addininmu har karshen rayuwarmu, samun kanka a cikin addinin musulunci ba karamar ni'ima bace da Allah ya yi maka, yakamata a kullum bawa ya rinƙa yawaita godiya ga Ubangijin taliƙai!!. Da hannu ɗaya Ronnie ya ɗaga Floris, a saman shoulder ɗinsa gabaɗaya ya zaunar da ita, ta ɗaga hannayenta jikka biyu sama ya fara playing skater da ita, dama idan da sabo sun saba yin haka, dik cikin ƴan wasan babu wanda yake da karfin iya ɗaukar wata ya kuma yi playing wasa da ita sai Ronnie, shi kaɗai ne yake iya goya Floris ko ya zaunar da ita a saman shoulder ɗinsa, ta zauna tamkar tana zaune a saman kujera, ya yi ta wasa da ita, shi ya fita daban da sauran ƴan wasa. Da hannu ya yi wa Sweetie alama a kan ta zo. Ba musu ta taso cikin nutsuwa ta ƙariso in da yake. Nan fa kallo ya koma kanta, sun ga madarar kyau. Haka kawai yau Ronnie ya tsinci kansa da jin haushin mutanen wajen dan suna ta ganin Sweetie, bai taɓa damuwa dan sun kalli wani ko wata ba, idan baku manta ba ya taɓa faɗawa Sweetie cewa sai mace tana da kyau ake kallonta, idan ma jama'a basu kallonta ai bata cika mace ba, to sai ga shi yau Sweetie ta cika mace ana kallonta kuma yana jin haushi. Gabaɗaya idanun jama'a ya dawo kanta. Tana zuwa ta tsaya a kusa da shi, dik sai ya ji wasan ta fita a ransa, ji ya yi su koma cikin gida kawai. Amma haka ya daure ya sanya ɗayan hannunsa ya ɗagata sama sai saman shoulder ɗinsa ta ɗayar gefen, ita da Floris suka haɗe hannaye suka ɗaga sama suna sakin murmushi. Nan take wajen ya ɗauki ihu da fito, haƙiƙa Ronnie ya samu horo mai kyau, ko nauyinsu bin ji ba ya fara rolling da su a saman shoulders ɗinsa, abin ya yi matuƙar ƙayatarwa ya kuma ɗauki hankular jama'a, basu taɓa ganin irin hakan na. Su Sweetie kamar wasu ƴan baby. Allah sarki Delisha kuwa tana can tana fama da dogara sanda. Dik abin da suke yi master Devil yana ganinsu, dan yana wajen. Tabbas wasan yau ya kayatar matuƙa, wasa ne da ba'a taɓa yin irinsa ba, Ronnie ya kawo sabon salo ya kuma kara tafiya da zumatan mutane dayawa. __________AFTER SOME MINUTES🔥 Yamma ta yi, rana ta yi sanyi irin bayan la'asar ɗin nan. Barci mai nauyin gaske ne ya ɗauki Sweetie, tana kwance saman bed ɗin Ronnie, dan yaki yarda ta bar room ɗinsa, saboda yana ganin kamar idan ta bar room ɗinsa Black Tiger zai iya cutar da ita, yana ganin kamar zamanta a nan ne zai hana Black Tiger taɓa lafiyarta. Floris tana tare da Angela suna buga triangle game kamar yadda suka saba, Angela ɗaya daga cikin yara marayun Black Tiger ne, kyakkyawar yarinya mai farar zuciya, zubinta sak na ƴan Black world ɗin. Sanye yake da swimming short, babu riga a jikinsa, yau ainahin wrestling surarsa ta bayyana, idan ka gansa a cikin kaya sai ka gansa ɗan siriri zubin Koreans ɗin, ashe ba haka bane, murɗaɗɗen mutum ne sosai, daga wanka ma ya fito. White hairnsa a ɗaure ya busar da ita. Part na Black Tiger ya shiga, a maimakon ya shiga master room na yayan nasa sai ya wuce izuwa gym, ta wani glass way mai matuƙar burgewa da ɗaukar hankali ya bi. Yanayin hanyar idan ka hau kana iya ganin kasa, sai kaga kamar zaka faɗa idan baka saba bi ba, dan zallar glass ne. Like wow, sai dai mu ce masha Allah, amma wanna waje ya amsa sunansa gym ɗin da gaske, ya kawatu da abubuwan motsa jiki kala daban daban masu bala'in kyau. Cikin shigar da ya saba ganin Black Tiger da shi yau ma ya gansa. Kusa da shi ya tsaya, a ɗan shagwaɓe ya ce. "Brother open your face, because you look so beautiful, I want to see you again, Please stop covering your face". Kamar zai yi kuka ya kai karshen maganar, kamar wani ɗan yaro, ashe haka yake magana da Black Tiger, sai dai kada ku manta cikin harshen koreans suke magana!. Wasu irin mahaukatan barbell mai ɗauke da weight plates masu bala'in nauyin da zasu iya kai goma goma ta kowani ɓangare ne a hannun Black Tiger yana ta ɗagasu yana saukewa. Da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci ya jima a gym ɗin yana motsa jiki, ga wani care luxury glass a idanunsa, hakan yasa ba'a iya ganin kwayar, gaskiya Black Tiger hege ne, ganinsa kawai yana firgita hantar manya da ƙananan halittu. Bai tankawa Ronnie ba yana cigaba da ɗaga wannan barbell ɗin kamar bai san da halitta a wajen ba. Ɗan zunɓura baki Ronnie ya yi tare da ƙarisawa wajen, DUMBBELL ya ɗauko ya fara ɗagawa yana kallon kwanjin hannunsa, ga wasu layukan guraye a cikinsa kamar wanda ya zana da gangan, kuma dik horo ne ta yi mashi yawa, cikin nan nasa a shafe manne da baya. Cigaba da ɗaga dumbbell ɗin ya yi yana kara zunɓura baki shi a dole Black Tiger bai kula shi ba ya ɓata rai. Ya kai a kallah 10 mins yana ɗaga dumbbell kafin ya ajiyesu ya nufi gaban yayan nasa wanda tin da ya zo wajen bai kalli in da yake ba, aikinsa kawai yake yi yana ta haɗa uban zufa saboda wahala, wajen kuma gabaɗaya kewaye suke da A.c dake busa sanyi, amma bai hana shi zufa ba. Wlh ba dik kai ba iya ɗaga barbell mai weight plates guda biyar ma, sai a tara maza dubu ba a samu biyu masu iya ɗaga mai biyar ba, shi kuma Black Tiger mai goma kuma manya manya yake ɗagawa, har yau Ronnie a iya mai huɗu kawai yake iya ɗagawa, shi ma sai da Black Tiger ya tsaya tsayin daka sannan ya iya jajircewa. Isar Ronnie gabansa ke da wuya ya sauke barbell ya mayar da shi mazauninsa, sannan ya duka ya yi shirin fara press up. Hayewa saman tsakiyar bayansa Ronnie ya yi yana cigaba da zunɓura baki. Bai kula shi ba ya fara press up da shi babu kama hannun yaro, da yake gwarzon namiji ne ya saba, sai da ya yi press up 200 babu hutawa, shi ma Ronnie yana tsaye a kan kafafunsa a tsakiyar bayan nasa kamar wadda aka sassaƙa, ko gezau bai yi ba. Abin dai gaskiya da mamaki, sun kware kam wajen yin wanna zallar madarar jaruntar. Dikkansu sai da suka yi sharkaf da zufa, gabaɗaya fuskar Ronnie kamar wanda aka watsawa ruwa, shi kuma big man da yake face ɗinsa a rufe sai ya zamana ba'a gane halin da yake ciki. Wucewa ya yi ya nufi room ɗinsa bayan sun kammala. Da sauri Ronnie ya bi bayansa yana saka mashi kukan shagwaɓa a kan lallai ya buɗe fuskarsa ya gani, dan shi gaskiya Black Tiger ya yi mashi kyau, kuma ba zai iya tafiya ba tare da ya gansa ba, in baku manta ba kaunar kyau a jinin Ronnie yake, dik wani abu mai kyau to yana kaunarsa sosai. Tamkar Black Tiger kunnuwarsa sun doɗe, sai ya nuna kamar bai san da wani Ronnie ba, ya shige cikin room nasa. Har ciki Ronnie ya bisa. Toilet Black Tiger ya nufa cikin wani irin tafiya mai matuƙar ban mamaki da al'ajabi, kamar wanda baya taƙa ƙasa. Saman wannan DAULAR bed ɗin nasa Ronnie ya haye ya kwanta, shi fa ya rantse ba zai fita ba sai ya ga face ɗin yayan nasa, ga shi by 5:30 zai tafi church, yanzu kuma 5:06. _____________ SWEETIE ___________🔥💘 Kamar a mafarki ya tsinkayo sanyayyar voice ɗinta tana faɗin. "Where are you Ronnie? Why are you leaving me alone in the room? Do you want the man who made me suffer that day to come back and take me away again?" Idanunta sun yi jajir sun ɗan kumbura, jikinta dik a mace alamar barci bai isheta ba, golden white hair nan nata a watse kamar wadda aka kwato daga bakin kura, sanye take da kayan barcin Floris riga da wando masu dogon hannu launin sky blue, ba karya ta yi kyau sosai, tin da ta yi sallar la'asar take zuba barci. Tana magana tana nufo master room ɗin, dan tasan a nan kaɗai zata same shi, saboda ta je parlourn kasa baya nan, Floris and Angela ta samu, Floris ta ce mata yana wajen yayansa, ko tsoro bata ji ba shi ne ta biyosa, akwaita da karfin halin bala'i yarinyar nan. Haba ai a miliyan kamar wani walkiya haka ya diro kasa daga saman bed ɗin, kafin ƙiftawa da Bismillah har ya kai bakin door room, jikinsa har yana ɗan kerma wajen buɗe kofar ya fito da gudu kamar wanda aka koro. Yana sanyo kai suka yi karo da ita, dan tsabar karfin hali irin nata tana ƙoƙarin buɗe kofar ne ta shigo ciki. Ai bai dakata ɓata lokacin duba in da ta buge ba, hannunsa na kerma ya ja nata suka nufi hanyar barin wajen, ya mance da cewa kuka yake yi wa yayansa a kan ya buɗe fuska, tuni ya wuce. Kamar waɗan da aka rako ya banke kofar room ɗinsa ya shiga da sauri yana sauke ajiyar zuciya. Ita da sam babu tsoro a tattare da ita kuma bata ga abin da zai bata tsoro bane ta ce. "Are you okay?" Bata jira amsarsa ba ta ɗaura da. "Why're you running like that? And why are you panting like someone who is not honest? Then you sigh is like someone who has escaped from a group of enemies". Fuskarta cike tab da mamaki ta yi maganar, dan ita mamaki ya bata!. Janyota jikinsa ya yi kawai yana sauke ajiyar zuciya, har ga Allah a tsorace yake, baya burin ta sake haɗuwa da yayansa, dan shi yasan wanene Black Tiger, mutumin da bai taɓa yafiya ba a tsawon rayuwarsa, bai ma santa ba, baya ɗaga kafa koda kuwa ga tsinke ne, kana mashi ɗaya zai yi maka ɗari, dole ya ji tsoro!. Jinta a jikinsa yasa ta farga babu riga a jikin nasa, cikin sauri ta ɗago ta kalli face ɗinsa, while shi ma ita yake kallo. Watsewar da gashin kanta ya yi har fuskarta yasa bata samu damar ganin face ɗinsa da kyau ba. Hannu ya kai ya tattare mata gashin waje guda, dan su samu damar ganin juna da kyau. Dikkansu sun ji daɗin hakan, barema shi da har wani cool ajiyar zuciya ya sauke. "Ronnie why are you looking at me like that?" Ta yi maganar tana ƙoƙarin barin jikinsa, dan ta ɗan tsorata na ganin kirar halittarsa. Girgiza mata kai ya yi ba tare da ya yi magana ba, a hankali hankali yake sauke numfashi, hannunsa dikka biyu ya ɗaura a saman bayanta ya hanata barin jikin nasa. Da sauri ta ɗago kallonta a kansa. Kurawa juna idanu suka yi kamar waɗan da suka afka duniyar tunani. An rasa mai kawar da kallonsa daga kan ɗan uwa, da alama sun mace a kallon junansu ne. --------- KNOCKING DOOR----------------- Knocking door da aka fara yi daga waje ne yasa suka farga tare da dawowa cikin hanyacinsu, a nutse ya sauke ajiyar zuciya tare da saketa, ya ɗan raba jikinsa da jikin door ɗin ya kuma saketa. Idanunta na'a a kan kofar, ta wani zarosu irin like tana mamakin wanene?. Fingerprint ɗinsa ya sanya a kofar ba password ba, sannan ya wuce ya nufi wajen bed ɗinsa. Kamar ba shi ya wani rungumi Sweetie a yanzu ba. Shigowa ciki Floris ta yi tana ɗan tsuke fuska alamar shagwaɓa. Sanye take da irin wannan shiga tasu ta riga da kuma sket har ƙasa, kayan yana da bala'in kyau, ta ɗaure gashin kanta a tsakiya, hannunta riƙe da Bibel, da alama shirin zuwa church ta yi. Kallo ɗaya Ronnie ya yi mata bai furta uppan ba ya nufi toilet dan ya yi wanka. Da ido ta bishi tana mamakin ganinsa babu riga, sai kuma ta kara yin wani mamakin ganin Sweetie a tsaye a bakin kofa. Kasa haɗiye mamakin nata ta yi har sai da ta ce. "Sweetie me kike yi a nan?". "Babu komai". Ta bata amsa kai tsaye tare da wucewa ta nufi wajen bed ɗinsa. Bayanta Floris ta bi tana faɗin. "Ya ke baki yi shirin zuwa church ba?". Tana ƙoƙarin zama a bakin bed ɗinsa ta answer da. "Na faɗa maki mu bama zuwa church, masallaci muke zuwa, idan kuna da musque zan je can on Friday". Tin da ta fara magana idanun Floris yake a kan ɗan bakinta har ta dire aya. "Sweetie kin mun kama da wata mata da na taɓa gani cikin birnin nan! Sai dai ba sosai kuke kama ba, idan an ganki a fisge ne dai sai a ga kamar ita ce". Cewar Floris. Ba tare da kawo wani dogon tunani ko wani nazari ba ta amsa da. "Kinsan halittun Allah dayawa, dama dai yarinya kika ce ina kama da ita to da sai in ce Pretty ce kila, amma ba yadda Ubangijinmu baya halitta". Karisowa wajenta Floris ta yi, tana mamakin hali irin nata, yarinya sam bata taɓa ɗaukar abubuwa da mahimmanci, akwaita da careless, bata sanya damuwa a ranta, hasalima ba zaka taɓa gane ina alkiblarta a zamantakewa ya dosa ba, ji yadda ta bada amsar cewa da aka yi anga mai kama da ita, tamkar bata da uwa ko wasu ƴan uwan, a yanayin yadda suka taso su biyu cikin maraici ai zasu so ace ga mai kama da su ko dan su ji sanyi a ransu, ko da ba ɗan uwansu bane zasu ji matuƙar daɗin hakan suma yau sun ga mai kama da su, amma ta nuna halin ko in kula, dik yadda aka yi ba iya baiwa kawai gareta ba, ta san tarihin iyayenta, tasan in da za'a iya samunsu, dole akwai abin da take ɓoyewa, yarinya ƴar karama da ko 13 years bata cika ba sai shegen wayo........ Wannan cikin nata ba shakka ya fi tara sirri a cikinsa fiye da yadda yake ɗaukar abinci, dole a jinjinawa Sweetie yarinya mai wayo kuma ƴar baiwa. "Sweetie wai ke baki mamakin abubuwa ne?". Floris da abin yake damunta a rai ta gaza haɗiyewa ce ta jefa mata wanna tambayar, dan ita dai gaskiya tana mamakin rashin bayyana farinciki ko bakincinkin da Sweetie bata yi, baka taɓa gane a wani irin yanayi take!. Ɗan motsa gefen bakinta sweetie ta yi kamar zata ɗan yi tsaki haka, alama ce ta amsa magana ba tare da ta buɗi baki ba, alama ta yi mata da ita bata wani jin mamakin komai a rayuwarta, dan ta ga abubuwa daban daban da suka girmi shekarunta kuma kwakwalwarta ya ɗauka, taga kaddarori da jarabawa daban daban, so yanzu ta daina nuna damuwa. "Kina burgeni sosai Sweetie, and kyanki yana tafiya da ni, Please can we be a friends?". Cewar Floris. Ta yi maganar tana miƙa mata hannu kamar mai shirin yin musabaha. Babu wani ɗaukin hakan a tattare da Sweetie, babu wani shauki, ta jinjina mata kai tare da miƙo mata nata hannun tana faɗin. "Yeah we can". Sam Floris bata ji daɗin ganin yadda Sweetie bata nuna shaukin hakan ba, amma bata nuna rashin jin daɗin nata a fili ba, ta danne ta kama hannunta suka gaisa, daga yau sun zama abokai kuma ƴan uwa. "Amatsayina na abokiyarki kuma ƴar uwarki na ɗauki alawarin koya maki dik abubuwan da na sani a duniyar nan". Cewar Floris. Kanta a kasa tana kallon ƴan yatsun kafafunta da suke ɗan yi mata zafi saboda karon da suka yi da Ronnie a lokacin da take ƙoƙarin shiga room na Black Tiger, so a lokacin ya taka mata ƴan yatsun kafafunta, ƴar ƙaniya tun ɗazun da take tare da shi bata ji zafin ƴatsun nata ba sai yanzu da ya shiga toilet ne ta gane ashe suna yi mata zogi, ɗazun ganinsa ya kwashe zogin. So kanta a ƙasa ta amsawa Floris da. "For sure nima zan koya maki dik abin da na sani a rayuwata, ciki kuma harda addinina". A hanzarce Floris ta amsa da. "Nima zan koya maki nawa addinin". Jinjina kai Sweetie ta yi. "Na yarda ki koya mun dik abin da kika sani dangane da addininki, na kuma yi maki alkawari a dik lokacin da muka yi zurfi cikin koyan addinan guda biyu, idan har baki ji addinina ya burgeki ko kuma ya kwanta maki a rai ba, ko kin gane addinin gaskiya daga ciki ba to ni zan koma naki addinin!". Babbar magana!! A ɗan ruɗe Floris ta zaro idanu waje, mamaki fal a ranta ta ce. "Zaki dawo addinina? Da gaske kike yi please?". Girgiza kai Sweetie ta yi tare da dawo da kallonta a kan Floris, ya tabbata Floris yarinya ce, ai shi addinin gaskiya baya ɓuya yarinya, wuyarta ki fara koyan ilimi daga cikinta, kina farawa ko ance ki bari ba bari zaki yi ba, yo Allah wasa ne?!. "Tabbas in dai kika nutsu kika sami ishasshen ilimi a kan addinina, kika zurfafa tunani, kika yi dik abin da na gaya maki to ba shakka in baki gamsu da addinina ita ce ta gaskiya ba zan bi taki". Cewar Sweetie. Sosai Floris ta ji daɗin wannan furuci na Sweetie, kuruci dangin hauka, ita yanzu a ganinta zata yi wa Sweetie wayo ne ta shigo addininsu, bata san Sweetie kam da wayonta aka haifo ta ba, ko mai shekara 20 ba ya gwada mata dabara ba, yarinya kamar renon tsafaffi, Floris sai dai mu ce welcome to Islam, dan na tabbata dabarar Sweetie ba zai barki ki iya tsallake wanna challenge ɗin ba, bari ma mu zo mu fara shirin tarbar sabuwar baƙuwa a cikin addininmu.............. Fitowa Ronnie ya yi ɗaure da bathrobe a jikinsa, launin milk color, white hairnsa yana ɗigar da ruwa. Kallonsu dikkansu suka kai a kansa, yana da sexy gorgeous body shi ma, kamar yayansa, ga yanayin koreans skin ɗinsa sai dai muce masha Allah. "Beb kai fa nike jira tun ɗazun, ka zo mu tafi". Cewar Floris. Idanunsa a kan Sweetie ya amsa da. "Ten minutes". Daga haka ya wuce dressing room ɗinsa. A gaggauce ya shirya cikin ƙananan kaya crazy, ya fito fes abinsa, ya tsaya gaban mirror ya canza ɗankunnen dake kunnensa, dama suna dayawa har da wani ta saman kunne, dik ya canzasu, ya ɗauki wani haɗaɗen gold pil ya sanya a kusa da lips ɗinsa ta ƙasa, sai ya so ya yi kama da mace, sai ma da ya busar da gashin kansa ya tara ya ɗaure, idan baka ga kirar sexy badynsa ba kaga iya face ɗinsa zaka yi zaton mace ce ba namiji ba, kyau iya kyau. Time da ya fito kasa hakuri Sweetie ta yi har sai da ta ce. "Ni Ronnie na rasa gane da kai da yayanka waye ya fi wani kyau? Kuma sam baku kama da shi fa, shi kamanninsa ma daban yake". Tabbas basa kama, dan Black Tiger dai ba koreans bane, Black Tiger ya fi kama da turawa gaskiya. Ɗan lumshe idanu ya yi yana sakar mata murmushi. "Na fi yaya kyau mana". Cikin zolaya ya yi maganar. A hanzarce ta ce. "Tun da ka amsa ka fi shi to tabbas baka fishi ba, shi ya fika, dan dik wanda yake da abu baya fitowa ya ce yana da shi, sai dai a gaya mashi yana da shi, dan haka baka da kyau". Floris da mamaki ya gama kasheta ne ta tsoma baki kamar wata mara lafiya a in da ta ce. "A ina kika taɓa ganin yayansa har kika san yana da kyau haka?". Ta ji abin da bata taɓa ji bane, dan tasan ko Ronnie bai san kamaninsa ba, mamaki kamar ta sume a zaune. Ɗago kai Sweetie ta yi da nufin ta bata amsa unexpect idanunta suka sauka cikin nashi. Girgiza mata kai ya yi a kan kada ta faɗawa Floris yadda aka yi da kuma yadda yayansa yake, ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru, hakan yasa ta mayar da kanta ƙasa ta rasa abin cewa, ita ga shi ba karya ta iya yi ba. "Sweetie ki amsa mun mana". Cike da ƙaguwar son jin amsa Floris ta sake tamnayarta. Hakan yasa Ronnie ya katsesu da cewa. "Let's go beb". Ya yi maganar tare da miƙawa Floris hannu a kan ta tashi su tafi. Miƙa mashi hannu ta yi ya kamata ta miƙe tsaye, tana matuƙar son ta ji amsa amma ya hanata ta hanyar janta suka nufi waje yana yi wa Sweetie bye bye haɗe da ce mata kada ta kuskura ta fita waje, ta zauna a ɗaki by 7 zasu dawo. Da okey kawai ta bisu har suka fice, gyarawa ta yi ta kwanta tana tunanin rayuwa haɗe da masoyinta Kamran, true love never end, har yau har gobe soyayyar Kamran yana ranta, soyayyar gaskiya take yi mashi, ga shi bata san kamanninsa ba, a haka dai take balai'n kaunarsa, shi kuma kada ku manta soyayyar a mutu yake yi wa Pretty, dan tun faɗowarta duniya sonta ya dasu a ransa, ko yaya wannan abin zai kasance? Mu je dai zuwa. ===========🔥💘============ IDAN MUKA WAIWAIYA FRANCE KUWA. SMART Tsulundun yake tsundume a cikin jacuzzi cikin toilet ɗinsa, har saman lion chest ɗinsa ruwan take, haɗaɗɗen kunfa fari tas ne cike a cikin jacuzzin, hakan ya hana damar ganin tsiraicinsa, ya jiƙa haɗaɗɗen dark black hairnsa da ruwa, hakan yasa gashin ya kwanto mashi rabi a gefe gefen face ɗinsa, rabi kuma a bayan wuyarsa, face ɗinsa gabaɗaya a jike yake da ruwa, zara zara eyelashes ɗinsa suna jike, hakan ya bada damar kyansa ya kara bayyana sosai. Tinanika kala kala ne cike a cikin ransa, wani irin binciken kwakkwafi a kan wani technology da zata ciyar da duniya gaba yake yi, a part from duniyar wata da yake shirin zuwa yana nan yana wata aiki ma dan kara bunƙasa kimiya. So yake ya leƙa duniyar karkashin ruwa bayan idan ya dawo daga duniyar wata, ya sa ana shirya kashi nautilus, wato wani katafaren jirgin ruwa ne wanda zai kai ka karkashin teku cikin kwanciyar hankali, yana dawowa daga duniyar wata yake son afkawa can, burinsa a kullum ya kawo wata kimiya da zata tashi kan duniya, ga shi da bala'in iya zurfafa tunaninsa a kan dik wata aiki da yasa a gaba, ga dogaro ga Allah hakan yasa yake yin nasara a dikkan lamuransa, dayawan masu fikira daga wajensa suke samun fasaha, nutsuwarsa da bin komai daki daki shi ke kara bawa mutane mamaki, jan ajinsa da halin ko in kulansa, bai ɗauki komai matsayin wani abin a zo a gani ba, wasa da makaman kare dangi kamar mai wasa da dunkulen wasa yakan ɗaga hankulan jama'a matuƙa, musamman wasa da rocket da yake yi, yana ɗaga hankulan makusantansa, saboda suna tsoron rasashi, shi kuwa lafiya lou yake komai ɗinsa. Ya ɗaga kai sama idanunsa a lumshe, da alama ba ƙaramin daɗin ruwan yake ji ba, kuma ga dikkan alamu tunaninsa da yake faɗaɗawa tana tafiya mashi yadda ya dace duba da yadda ta nutsu ya nutsa cikin tunanin nasa. While ita kuma mom suna can gym ita da dad suna motsa jiki, mom tana bawa furenta ruwa, kun san ta kware a wannan harkar, wajen gym ɗin gabaɗaya kewaye yake da tsaro na ban mamaki, amma hakan bai hana mom soyewanta da ɗan dattijon mijinta ba. Su fa sam basa tsufanwa soyayya. A hankali ya waro idanunsa jin alamar shigowar mutum cikin room ɗinsa. Kamar wanda baya son motsawa ya juya idanunsa izuwa saman katafaren Tv dake manne da jikin bango a cikin toilet ɗin. Heleena ce tsaye a tsakiyar room ɗin nasa tana bin ko'ina da kallo, ta kwana biyu rabonta da ta shigo cikin ɗakin, yanzu ma sai da ta je ta taso dad a gaba tasa ya yi amfani da laptop ɗinsa ya cire mata door securityn sannan ta shigo. Tana nan dai cikin wannan ɗan iskan shigar tata, sai dai yau abin ta taazzara, dan fa cibiya a waje ne yau, ga wasu ƴan iskan breast ɗinta kamar............ Bari na raga mata kada nan gaba kaɗan ta zama matar Smart in shiga uku. Yau wandon ma tsabar iskanci bai kai kaurin kafafunta kamar na Nennen Mahreen ɗin nan ba, hannunta na ɗauke da tray mai shake da small chop, ita dai ta dage sai ta kawowa Smart small chop ɗin nan, anya ma ba wani abin ta banka a ciki ba kuwa? Baiwar Allah bata san ma kyamarta yake ji kamar ya yi amai idan ya ganta ba, ta bi ta matsawa kanta a kan son shi da son kyatata mashi, ina ga sai mun taimaka mata da tsayuwar dare kila ta dace, matsalar dai taki musulunta ne ita da mom. Ji ya yi tamkar zai yi amai na ganinta da ya yi, ko bai tambaya ba yasan dad ne ya buɗe mata door ɗin nan, to ya zai yi da dattijon nasa? Ai sai hakuri kawai. A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta tare da mayar da idanunsa ya lumshe su, cikin ransa ya fara tunani wanda shi kaɗai ya barwa kansa damar sanin me yake tunawa. Kamar wanda yake mafarki ya furta. "Am coming for it soon". Ya yi maganar tare da sauke ajiyar zuciya. A hankali ya miƙe tsaye tare da zuro kyawawan kafafunsa kasa, ya fito daga cikin ruwa ya nufi ɓangaren towels dake shirye cikin show glass tamkar shop na sayar da su ne. Wata fara kal ya ɗauko mai ɗan girma wadda ta tsaya mashi dai'dai kaurinsa, sannan ya ɗauki wata mai ɗan girma ya nannaɗo hair ɗinsa a ciki domin tsane ruwan. Gaban wash hand base ya nufa. Tsayuwa ya yi a wajen tare da kurawa kansa kallo a jikin mirror dake wajen. Kamar wanda bai san ya face ɗinsa take ba haka ya kafe kansa da waɗan nan idanun nasa. Ya ɗan ɗauki lokaci a wajen kafin ya nufi fita waje, shi da kansa yasan shi ɗin smart ne na gasken gaske, gifted ba. Jin motsin fitowarsa daga cikin toilet ɗin yasa Heleena yin saurin ajiye mashi tray dake hannunta ta juya da sauri, har da haɗawa da ɗan gudu ko ɗar bata ji ba na wannan uban high heel dake kafanta, tana son sanya shi a idanunta amma tafi jin tsoron haɗuwa da shi sama son kallonsa da take, dan a kullum hata kyau, ita ake bari da dakon danasani in suka haɗu. Sarai ya ga fitarta, amma ko a karkashin sillpers ɗinsa ya wuce izuwa dressing room. Jim kaɗan ya fito shirye cikin tsadaddiyar jogger a jikinsa ta kasa, ta sama kuma round neck polo shirt ce, dikka white colors ne. Hanunsa na ɗaure da wata dankareriyar Rolex-pnd wanda a kalla kuɗinsa ya kai 18 million dollars. Sai tashin kamshin perfume ɗin Mf yake yi, wanda kuɗin wanna perfume ɗin ya wuci tunaninku. Wayarsa ya ɗauka ya nufi waje a gaggauce, ko kallan abin da Heleena ta kawo bai yi ba, ya fice. Kamar dai yadda dad ya saba saka mashi takunkumi na idan zai fita sai da tsaro gaba tsaro baya, hakance ta kasance, da ya ce wa dad shi fa yanzu ba yaro bane dan Allah su kyalesa ya shakata, shi jarumi ne ba rago ba. Da sauri mom ta karɓi zancen da cewa shi yaro ne kuma dole ta saka idanu a kansa. Ni dai nace mom bata san dik saka idanunta a kansa na banza bane, domin kuwa shi da dad dai sun mata wayo, sun gwada mata kwarewa suna can bayan fage suna sharholiyarsu da rocket. Kamar zai yi masu gardama, amma farincikinsu shi ne nasa, dan haka ya raba masu sumbatar kauna a kumatu tare da wucewa ya nufi jerin gwanon motocin da aka jera domin shi. Sai dai kamar kullum gidansa ya je ya baro securitys ɗin ya ɗauki tsadaddiyar motarsa ya wuce World ɗinsa, wato duniyarsa, dan yana bala'in kaunar wannan rocket factoryn nan nasa fiye da komai, nan ne duniyarsa, yana alfahari da baiwa da ilimin da god ya bashi. Yau ta kama saturday ne, garin ya yi shiru sosai, kowa yana makale a gida, ga wani uban sanyi dake zuba kamar ana watso dissa, a haka kuma bai sanya jacket a gida ba sai da ya je gidansa ya ɗauki wani katan puffer jacket ya sanya. Weekend ba aiki ba zuwa office, kowa yana cikin gida, su kuma a yau ne suke gwada lunching manya manyan makamansu da suka ɗauki tsawon watanni suna haɗasu, sun yi aiki tukuru domin tabbatar da ingancin dik abin da zasu haɗa, sun sadaukar da lokutansu ba dare ba rana suna aiki, fatan komai ya dai'daita yadda suka tsara kawai suke yi. A lokacin da ya isa world ɗin nasa har an gama shirya komai na tashin makamin, shi kaɗai ake jira da ya zo ya saita in da zata nufa ya saketa, shararren makami ne wanda ya ɗara bmt-59 a girma, a kullum burin Smart ya kirkiran wasu makaman da babu masu kwatankwacin haɗarinsu a duniya, ya zamana su ne na farko da zasu mallakesa, to yanzu ya yi nasarar kirkiran kala ɗaya wanda ya sha wahala wajen kirkirota, ya kuma ɗauki tsawon watanni, yana fatan yanzu idan ya gwadata ta tafi yadda yake so. Babban yaronsa a wajen mai suna Robbert ne ya fara isowa garesa ya tarbesa domin sanyaya mashi ransa. A tare suka ranƙaya izuwa room na GUIDANCE SYSTEMS COMPUTER'S. Wato ɗaki ne mai cike da na'urorin controlling na nuclears ɗin da suke kyarawa, wasu irin mahaukatan systems ne masu ban mamaki, masu aiki babu kama hannun yaro, babu batun sanyin battery ko tsufa, dik bayan kwana uku ake zubo sabbi saboda tsaro, dan kuskure kaɗan idanun suka yi an shiga ɗari ba uku ba, so suna da karfin aiki fiye da tunaninku, dan ba kamar sauran systems da kuka sani bane. Gaban wani dankararen guidance system computer ya tsaya. "Everything is ready sir". Cewar Robbert dake tsaye kyam kamar mutum mutumi ta gefensa. Jinjina kai kawai ya yi tare da sanya hannunsa a saman glass na na'urar, touch screen computer ce. Wasu bakon lambobi ya shigar kafin nan ainahin cikin na'urar ta buɗe, go come ya shigarwa ƙwaƙwalwar rocket da zasu harba ɗin, sanna ya yi setting ɗin iya gudunta da suke buƙata, ya kuma yi setting na iya tafiyar da zata yi da nisan da zata yi ta juyo. Sannan ya duba payload ɗinta da kyau. Already nuclear ɗin tana a saman launch pad ɗinta, su Robbert sun shiryata da kyau, amma dik da haka sai da Smart ya kara duba launch pad ɗin da kyau, ba wai dan bai yarda da ingancin kwarewar su Robbert ba ne, tsaro ce kawai, dan yasan ita samun kuskure a kanta dai'dai yake da ɗaukar rayukan mutane da dabbobi bila adadi. Hege Smart ya san nuclear in and out, tun basu tasheta ba ya haɗa mata heat shields, saboda kara nuna kwarewa a kan aikinsa, kun san na gaya maku nuclear bata haduwa da waje mai zafi, so dole sai an haɗata da heat shields mai karfi wato garguwar zafi wanda suke bata iska mai sanyin gaske, mai kareta daga zafi. Hankalinsa ya mayar kan fetur ɗinta, nasan zaku yi mamakin jin cewa tana da fetur, to ba fetur kai tsaye kamar wanda ake amfani da shi a motocin yau da kullum ba ne. Ana amfani da wasu nau'ikan man gas propellants masu ƙarfi waɗanda suka bambanta da mai na yau da kullum. Ana saka mata Liquid Propellants, Liquid Oxygen (LOX) da Liquid Hydrogen LH2 da dai sauransu. Karfin fetur na yau da kullum ba shi da isasshen ƙarfin samar da kuzari don ɗaga nuclear izuwa sararin samaniya, shiyasa ba'a amfani da shi. Ana buƙatar mai da ke samar da hayaƙi mara yawa don kada ya shafi tsarin nuclear da yanayi. Yanayin Zafi nuclears suna buƙatar mai da zai iya jurewa matsanancin sanyi ko zafi, wanda fetur na yau da kullum ba zai iya yi ba. Fatan waɗan da basu da ilimi a kan nuclear sun samu karin haske?. Bayan ya duba waɗan nan abubuwa dik sun shiryu yadda ya da ce, sai ya dawo da eagle eyes ɗinsa a kan engines ɗinta dan tabbatar da lafiyarsu, dik sai anbi waɗan nan matakan domin gwada nuclear, aiki ne tukuru sosai. Dogon nazari ya ɗan shiga a kan dukkan matsalolin fasaha da na tsaro da za a iya fuskanta wajen tashin nuclear. Sannan ya shiga tsara yadda nuclear za ta tashi, wace hanya za ta bi, da kuma inda za ta sauka, tsarin tashi, da tsarin dawo. Ana bibiyar nuclear yayin da take hawa sararin samaniya don tabbatar da ta bi hanyar da aka tsara mata. Dayawa nasan zasu tambayi ta ya ake yi nuclear ta dawo bayan tashinta, to idan Smart ya harbata in zata dawo zaku gani, kuna tare da Smart zaku samu ilimi kan nuclear matuƙa dan yana da ilimin kimiya fiye da tunaninku, kuna tare da alkamin princess Teema taku ta amana zaku samu ilimi sosai ta bangare dikka biyu, wato boko da Arabic kai harma da kimiya mai tafiya da zamani In Sha Allah. Sai da ya tabbatar komai yana intact, sannan ya danna tashinta. Gabaɗaya jami'an dake kusa da launch pad ɗin sai da suka sanya hannayensu a kunnuwansu suka toshe da karfi, sannan suka sunkuya kasa. Wani irin mahaukacin fita nuclear tayi wanda hakan ya haifar da karamar girgizar kasa a wajen, kun san tana da balai'n karfi, dik in ta fita sai ta girgiza ƙasa. Tsabar karfinta sai da ƙasan wajen da ta tashi ya rufta ya yi wawakeken rami, a miliyan ɗari ta fita. Ajiyar zuciya Smart ya sauke ganin aikinsa ta yi kyau, makamin da ya shafe watanni yana haɗata yau komai ya tafi dai'dai har sun lunchata, abin ya yi mashi daɗi matuƙa. Rest room ɗinsa ya nufa dan ya ɗan kwanta ya huta. Da sauri Robbert ya bi bayansa ko zai buƙaci wani abin ya biya mashi buƙatarsa. Suna shiga cikin room ɗin ya nufi wajen drawers ɗinsa. A hankali ya buɗe drawer, kamar wanda baya son taɓa komai. DIAZEPAM INJECTION ya ɗauko haɗe da sirinji. Wani irin zaro idanu Robbert ya yi na ganin wanna allura ta DIAZEPAM da ya ɗauko, allurar barci ce, wato shi fa Smart baya tsoron a mutu, fisabilillahi ka tashi nuclear ta yi sama sannan tsabar iskanci ka ɗauko alluran barci zaka yi wa kanka? Idan nuclear ta tashi dawowa waye zai tareta?.........🤔 Ko in aka samu wata matsala ba fata muke yi ba waye zai kula da wanna ɓangaren?. Robbert ya tsorata amma kuma bashi da bakin iya yin magana, yana ji yana gani Smart ya dannawa kansa DIAZEPAM ɗin nan a jinin jikinsa. Saman bed ya haye ya kwanta tare da barin kayan alluran a saman drawer Robbert ya zo ya tattare kenan. Nan take idanunsa suka fara dishi dishi yana kallon ɗakin bibbiyu. Robbert yana tsaye a bakin door room yana ta al'ajabin Smart, da yake shi sabon jami'i ne, bai saba da halin Smart namu uban jan aji da jiji da kai ba. Wayar Smart ce ta fara ringing, yana gani dishi dishi ya lalubo wayar daga aljihunsa. Idanunsa bibbiyu take ganin mashi wayar. Sunan mom ce ya bayyana a saman screen ɗin, amma ya gaza iya gane abin da yake rubuce, sai yake ganin kamar Heleena aka saka............😅 Ganin hakan yasa ya ja godon tsaki tare da ya wurgar da wayar a gefensa, kafin wani ɗan lokaci barci ta yi awon gaba da shi. Bashi da number Heleena fa, kawai sharrin alluran barci ne yasa ya ga kamar numberta ne. To Smart team ina fatan kun shirya tarar wanna bujumin nuclear idan ta juyo.🤔 A gaskiya Smart ɗan ikkan zamani ne, wasa yake da nuclear kamar wanda ya samu ƴar tsana, to thank god dai idan ta juyo ta kansu zata dawo ba kanmu ba, ga shi ka yi barci ba mai kashe engines ɗinta ya rage mata gudu a yayin dawowa, sai ta afko maku a miliyan ta yi sama da ku tun da kai iskancinka ya wuce misali, ni dai na yi nan. Smart team sai a shirya zaman makoki dan da alama za'ayi rashi!.🥱 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ==========🔥🔥🔥=========== ALKALAMIN P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ ======JIMETA🔥YOLA======== A tare da Mahreen bappa suka dawo cikin gidan, a lokacin su Jaish sun ɗan jima da tafiya, iyaka rashin jin daɗi bappa ya ji, har kansa ya ji tana yi mashi ciwo, gabaɗaya sai ya ji duniyar ta yi mashi wani irin, dan Allah ya gani yana kaunar Jaish, ya ma mance da auren da ya haɗa a tsakaninsa da Mahnoor, shi yanzu bakincin ɗaukar mashi yaron da suka yi ne a ransa. Shiru ya zauna a cikin ɗakinsa yana tunanin mafita, while ita kuma Mahreen tana ta aikin matsa mashi. Sai faɗi take. "Bappa dan Allah ka tashi ka je ka karɓo mana hammanmu, su dawo mana da shi". Kasancewar hankalinsa baya'a jikinsa sai ya zamana sam baya jin diran kamalan Mahreen a kunnuwansa. Kamar daga sama ya ji tana faɗin. "Bappa Adda Mahnoor fa tana can tana ta kuka, dan Allah ka je ka ɗauko mana shi". Jin batun Mahnoor yasa ya tuna da ita, a hanzarce ya miƙe ya fito. Da gudu Mahreen ta biyo bayansa, dan a tunaninta bayan Jaish zai bi. Ɗakinsu ya nufa domin ya duba ƴar marainiyarsa. Ita kuma Nenne tuni ta ruga gidan Arɗo dan ta gayawa gwaggonta ai an ɗauki Jaish, yau farinciki a wajenta ba'a misiltawa. Sai wani daɗi take ji tamkar wani abin kirki ne ya faru. Tun daga bakin kofa bappa ya fara tsinkayo shesshekar kukanta, hakan ya bashi damar kara ɗaga kafa domin ya isa gareta. Tana a kwance saman mattress ɗinsu, ta haɗa kai da jikin pillow sai kuka take yi kamar ance mata Jaish ɗin mutuwa ya yi ko kuma ba zai dawo ba har abada, ko da yake hakance fa tun da su Ramish sun tafi da shi Abuja, ya bar Adamawa kenan. Sam bata ji shigowar bappa ba, sai dai ta ji an zauna kusa da ita, kamar mai raɗa ya ambaci sunanta, daga jin muryarsa cike yake da karaya haɗe da sagewar dik wani kwarin gwiwa da yake da shi, ba komai yasa ya ji wannan rashin kwari da cire tsammani ba face yadda suka ɗauki Jaish ba tare da sun buƙaci ganinsa ba. Bugu da ƙari Mahreen ta gaya mashi basu yi wa kowa magana ba, sannan shi ma Jaish bai buƙaci da su nemi kowa ba, tun daga nan bappa ya yanke tsammanin Jaish zai waiwayesu, kuma hakance, dan dakamar wuya, su Ramish basu kyauta ba da basu nemi bappa da ya riƙe masu ɗan uwa tsawon watanni kusan shekara ba, hakan ya nuna sun nuna basu son wata alaƙar dake tsakani and basu da buƙatar sake waiwayar garin, gaskiya basu yi halarci ba sam. Amma da yake su maza ne basu ji komai game da hakan ba, da mata ne suka zo ɗaukarsa kun san dai dole zasu nemi wanda ya riƙesa, dayawan lokuta a irin wannan part ɗin maza basu san me ya dace su yi ba, kullum suna tunani ne irin na maza basa waiwayawa su duba raunin tunani, idan kuma ya haɗe masu babu mace a gefensu sai taɓarar tasu ta kara yawa, su kasa yin abin da ya dace, da akwai mata a gefensu cikin wannan tafiya wlh ba zasu bar kauyen nan ba sai sun nemi bappa sun yi mashi godiya har ma su yi mashi kyauta!!. Ta ji voice ɗin bappanta, amma kuma bata iya amsa mashi ba, saboda kukan da ya fi karfinta, da sauri Mahreen ta ƙariso wajen, saman mattress ɗin ta haye tana amabatar Mahnoor, Mahnoor. Bappa ya rasa me zai ce mata, ya rasa da wasu kalamai zai yi amfani wajen shawo kanta, ya rasa me zai yi, ya zauna shiru ba zai iya jure kukanta ba, ya yi rarrashi kuma bashi da kalaman faɗe. Sallamar da suka ji a tsakar gidan ne ya ja suka kai kallonsa bakin kofa shi da Mahreen. "Kawu Ibrahim ka shi go mana". Cewar Mahreen. Allah sarki, shi bappa da farko ma bai ɗago muryan mai sallamar ba, tsabar yana cikin damuwa, sai da ya ji Mahreen ta ce kawu Ibrahim ne ya gane. Hannun Mahnoor ya riƙo tare da ce mata. "Zo muje". Ba musu ta tashi ta bisa. Waje suka fito, Ibrahim kanin mamanta yana tsaye rike da wata sanda a hannunsa, ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin. Idanunsa jajir kamar wuta. "Jaɓɓama lale Ibrahim". Cewar bappa. Da yauwa ya amsa idanunsa na a kan Mahnoor da dik fuskarta ya yi jajir kamar jan kosai saboda kuka, kun san farar fata idan tana kuka, har wani ja na musamman face ɗin yake yi, bare ma wajen dogon hancin nan nata ya yi jajir sosai. Matsowa ya yi ya karɓeta daga hannun bappa yana faɗin ta yi hakuri. Ɗan kwanciya ta yi a jikinsa tana ɓoye fuska, soyayyar Jaish ya ja ta manta da batun kunya har ta bari kukanta na rashinsa ya fito fili kowa ya gani, sai a yanzu dik ta ji kunya ya mamayeta. Sai ta wani ɓoye fuska a jikin kawu Ibrahim. "Ibrahima lafiya kuwa?". Cewar bappa, ya yi tambayar ne bisa ganin kamar ran Ibrahim ɗin a bace, ga idanunsa sun yi jajir sosai. "Babu komai babbo, dama na zo kara tabbatar da abin da na ji kuma nasan dama zai iya faruwa ne, amma kukan Mahnoor ya riga da ya bani amsa". Shiru bappa ya ɗan yi dan bashi da abin sake cewa, Jaish ya jefa shi cikin matsala, ga yanayin al'adarsu yanzu zasu ɗauki laifin dik su ɗaura a kansa, bare dama ya hana Faisal ita, ai shikenan kuma ya kara shiga uku da dangi, sai kuma abin da Allah ya yi. "Bobbo zan tafi da Mahnoor zuwa gida". Ya yi maganar ne rai a dakile, dan idan ransa ya kai miliyan wlh a yau ya ɓaci sosai, tin ainahi yana balain tausayawa Mahnoor baiwar Allah. Bappa bai iya ce mashi ko uppan ba, dan bai san me zai ce mashi ba, kuma at this point bai isa ya ce zai hana shi tafiya da ita ba, shi kansa zai so a tafi da ita, su je Inna ta rarrasheta ko za'a samu ta yi shiru. Ibrahim ya lura da cewa ɓacin ran da yake ciki sam ko rabin na bappa bai kai ba, dan ya lura bacin rai ya hana bappan yin magana. Dan haka sai ya ɗan sassauta ya danne nasa ɓacin ran ya ce. "Bobbo bari muje ko?". Kai kawai bappa ya iya gyaɗa mashi ba tare da yin wani yunkuri ba. Jiki ba kwari Ibrahim ya ja hannunta suka nufi waje, sai binsu da kallo bappa yake yi. Da sauri Mahreen ta bi bayansu, dan kun san tana kaunar ƴar uwarta. Suna tafiya bappa ya shige cikin ɗakinsa, saman ƴar gadonsa ya hau ya kwanta, ya yi iya yinsa ya rufe idanunsa ko zai ji saukin abin da yake ji har barci ta yi awon gaba da shi, amma ina ya kasa, idanun ma sun ki rufuwa. Kamar a mafarki ya hango suit ɗin Jaish da suka tsinto shi da shi makalle a jikin kusa ta bayan kofar shigowa, tun ranar da bappa ya cire mashi suit ɗin ya makala a wajen babu wanda ya taɓa taɓa shi. A hanzarce ya miƙe zaune a saman gadon, tunani ya fara yi a kan watakila zai iya samun wani abin mai muhimmanci a cikin aljihun kayan, hakan yasa ya yi saurin miƙewa tsaye, da sauri ya diro kasa. Kai tsaye kayan ya je ya ciro, a bakin gadon ya koma ya zauna, dik jikinsa a mace bawan Allah. Aljun kayan ya fara laluɓewa. Cikin sa'a ya fito da wallet a aljihun wandon. Ɗan kurawa wallet ɗin ido ya yi kafin ya ajiye a gefe ya sake mayar da kallonsa a kan kayan. A aljihun rigar ya ciro dalleliyar wayar Jaish, ya sha mamakin ganin wayar sosai, gata kamar sabuwa, bata ci screen ko ta lalace ba, sai dai bata kawo wuta, a kashe take. A gefensu ya ajiye kusa da wallet ɗin ya cigaba da binciken aljihun, a nan ya samu passport, dama kun san da niyar yin tafiya Jaish ya bar gida, so ga passport ɗinsa da komai, amma ruwa ya jiƙasu har sun ɗan yayyege, sun kuma manne da juna babu halin bappa ya buɗe ya karanta. Hakan yasa ya ajiye a gefe, cigaba da laluɓar aljihun ya yi har sai da ya tabbatar da babu wani abin da ya bari a ciki. Sannan ya ajiye kayan a gefe ya kai hannunsa ya ɗauko wallet da ya fitar da farko. Da kyar ya iya ɓalle wallet ɗin ya buɗeta, sannan ya fara fito da abubuwan dake ciki, akwai takardarsa na ɗan kasa, ID cards da sauran muhimman cards. Dik babu wanda bappa ya iya karantawa ya gane, saboda rubutun turanci ne a jikinsu, dibasu ya fara yi one by one yana binsu da kallo ba tare da yasan amfaninsu ko me zai yi da su ba. Da yake yasan waya sai ya ɗauko na Jaish ɗin yana ta kallo, ya rasa ta ya zai yi ya kunnata, dan ya danna wajen kunnawa da ya sani na wayoyi amma taki kunnuwa, hakan yasa ya ji jikinsa ta kara sanyaya matuƙa, ya ga rashin amfanin bincikar aljihun tun da bai samu wani abin da zata taimaka mashi ba. Daga karshe ya kwashi komai ya mayar in da ya fitar, ya ɗauki kayan ya mayar ya makalesu, ya dawo ya kwanta yana tunanin yadda zai yi da wannan al'amari, ya saba da Jaish sosai wanda rabuwarsu lokaci guda haka babu ko sallama zai iya haifar mashi da babbar matsala, and ya zai yi da Mahnoor?. Ya jefawa kansa tambaya. A ɓangaren Nenne kuwa, murna kamar zai kasheta, tuni ta je ta kyankyasawa gwaggo ga abin da yake faruwa, sun yi matuƙar jin daɗin hakan, gwaggo har da wani bata shawara da ta ɗaura ɗamarar zaman gidan bappa a yanzu dan ta dawo da ƴancinta da ta rasa a baya, sannan ta tabbatar ta gallazawa Mahnoor har sai Inna ta ji ɗaci a ranta tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu. Ba ƙaramin daɗi Nenne ta ji ba jin abubuwan da gwaggonta ta ce, dan haka ranta fes ta janyo doggin kafafunta ta nufo gidan bappa da su. A hanya ta haɗu da Ibrahim da su Mahreen. Ko tsoron Allah babu bare kunya ta wani dakatar da zu har da cewa. "Kai Ibrahim ina kuma zaka kai su?". Bai tankata ba, ga dikkan alamu basa zaman lafiya da ita, ko kallon in da take ma bai yi ba ya sanya kai zai wuce ya cigaba da tafiya. "Ba da kai nike magana bane Ibrahim? Nace ina zaka je da su?" A harzuƙe ta yi maganar, irin ranta ya ɓaci ɗin nan, ya za'ayi ace tana mashi magana zai bawa banza ajiyarta yasa kai zai wuce?. Still dai bai tanka ba, bai yi kamar yasan da halittar bil'adama a wajen bama, ya cigaba da tafiya hannunsa sarkafe dana Mahnoor. "Ke Mahreen zo nan ki wuce mu tafi tun da ke kam nike da iko da ke!!". Cike da isa da gadara ta yi maganar, irin Mahreen ƴarta ai dole ta bi umarninta. To kun san halin Mahreen ba sai na sake faɗa ba, yarinya ce da bata bin bayan rashin gaskiya komai ƙanƙantarta, dan haka sai ta ce. "Nenne ni kam kawu Ibrahim zan bi, ina gidan Arɗo yau". "Ban yarda da haka ba! Zo maza ki wuce mu koma gida". Cikin gadara ta yi maganar. "Nenne wai idan mun je gidan me zan yi maki? Kawai in je in zauna?". Kai ta gyaɗa mata alamar e, sannan ta ɗaura da cewa. "Kwarai kuwa, ko ban isa in ce ki yi abu bane?". Shiru ta ɗan yi tare da juyawa ta kalli Ibrahim da Mahnoor da suka ɗan yi nisa a tafiyar da suke yi, sun barta tsaye tana biyewa Nenne. "Ni gaskiya Nenne ba zan koma gida ba, wajen ƴar uwata zan je, ke bakiga kuka take yi bane? Zan je ne mu rarrasheta, yau a gidan Arɗo zamu wuni!". Tana magana tana turo baki na rashin kunya da kuma shagwaɓa "Eyee ke da in nace ki je wajen gwaggo sai ki ce mun baki son zuwa ke ba zaki je gidan Arɗo ba, amma yanzu saboda munafurci ne har da cewa a can zaki wuni ko?". Kai ta gyaɗa haɗe da cewa. "Yanzu ma saboda Adda Mahnoor zan je, ba dan ita ba ni Allah ya sawwaƙa in je gidan Arɗo". Salati Nenne ta saka ta sanar da Ubangiji, sannan ta ce. "Kema yanzu kin koyi munafurci koh Mahreen? Wato Mahnoor ta koya maki munafurci da rashin kunya ko?". Ɗan zaro idanu waje ta yi, cike da mamaki ta ce. "Adda Mahnoor da munafurci kuma?". Kai Nenne ta gyaɗa alamar e haɗe da cewa. "Ko karya nayi ne?". Kai tsaye Mahreen ta amsa da. "Wlh karya ne! Adda Mahnoor bata munafurcin kowa, nice ma nan kullum nike kawo mata gulmar Inna Rabi, kuma har faɗa take mun a kan in dai'na gulmar mutane idan basa nan, in ya zama dole na yi maganarsu to ya zamana maganar da zan iya maimaitawa a gaban idanunsu su ji ransu bai ɓaci ba zan faɗa, kullum sai ta yi mun nasiha, ai Nenne ke da wancan gwaggo mai ido kamar na aljanun ne ma kuke yin gulmar mutane, ba har zagin Inna kuke yi ba? Ai ina jinku dik abin da kuke............." Bata kai karshen maganar ba ta yanka a miliyan ta bi bayansu Mahnoor sakamakon cabka da Nenne ta kai hannu zata yi mata. "Mahreen ki dawo nan kada ki yarda ki bisu". Nennen da ranta ya gama ɓaci, ta kawo har wuya ne ta faɗi haka, tana da bala'in son girma, amma sai dai bata san ta yadda zata bi da mutane su girmamata ba, yau ga shi ƴar cikinta ke gaya mata ita ce munafuka kuma ma gulmaciya, me ya kai wannan ciwo fisabilillahi? Alhaki ai kuykuyone, ga shi ta fara gani. Ina kafa me na ci ban baka ba? Kafin Nenne ta dasa aya a maganarta ma Mahreen ta kurewa ganinta, kamar wata haske ta wuce fiwwww, yarinya mai saa mai kuma baiwar iya gudu. Galala Nenne ta saki baki tana jin ɗacin maganganun Mahreen a ranta, karin ɓacin rai ma shi ne yadda Mahreen ta haɗe har da gwaggo ta zage, abin ya bakanta mata matuƙa. Ta ɗan jima tsaye a wajen tana tunani, wucewar da Mairo ta zo zata yi a kusa da ita ta ɗaga mata gaisuwa ne ya fargar da ita ashe a kan hanya take tsaye. Wani irin ƙasƙantacen kuma walaƙantatcen kallo ta bi Mairo da shi, bata amsa gaisuwar Mairo ba, sai wani kallon up and down da take binta da shi, ashe a wajenta Mahreen ta gaji irin wanna walaƙantatcen kallo da take yi wa mutane, wlh dik yadda kake ji da kanka idan aka yi maka irin wannan kallo sai ka ji kamar kai ba kowa bane, ka ji ka kaskanta ka walaƙanta, sam kallon bashi da daɗi. Ganin haka yasa Mairo ta nufi kama kanta ta wuce, salum alum ta kama hanya, dama tasan Nenne bala'i ce, ta gaisheta ne kawai dan kada ace ta ganta bata girmamata ba. "Ke zo nan?". Cewar Nenne. Ba musu Mairo ta juyo ta dawo wajen ta tsaya, cikin sanyin murya ta ce. "Adda gani nan......." Bata idasa maganar ba ta shanyeta dif sakamakon wani bahagon marin da Nenne ta sakar mata tasssss. Nenne bahaguwa ce, haka yaran Arɗo dikka suke lefty, harta Ibrahim bahagone, hakan yasa Mahnoor take bahaguwa ita ma, ta gada wajen mamarta, Arɗo shi ne ainahin bahago, so a wajensa suka gada. A miliyan Mairo ta dafe ƙuncinta, take wasu zafafan hawayen suka faso idanunta a guje suka fara tsere a saman kumatunta, jikinta har ɗan kerma yake yi, hannun da ta dafe ƙuncinta sai rawa yake yi. Tsabar masifa da rashin kunya irin na Nenne wai ƙoƙarin kara mata marin take yi, daga bayansu suka ji muryan bappa yana faɗin. "Kada ki kuskura ki sake marinta". Cikin zafi ya yi maganar, ya jima bai zafafa a magana irin haka ba, tun maman Mahnoor tana nan, yau ransa a ɓace ne yasa ya zafafa. Sanin halinsa da kuma jin ya zafafa yasa Nenne bata kara kai mata marin ba, dan tasan fa bappa ruwa ne ya daki babban zakara yasa ya yi sanyi. "Jeki abinki Maryam". Ya yi maganar ne yana kallon Mairo da idanunta suke jajir, dan fa ba karya ta maru sosai. Wucewa ta yi ba musu, dan tana da ladabi da biyayya. Shi ma bappa zuwa ya yi ya wuce Nenne tsaye a wajen kamar gunki bai ce mata uppan ba ya nufi hanyar gidansu Faisal, dan bappan Faisal ya aiko ya zo yana son ganinsa. Bakinci ta kara taruwa ta yi wa Nenne kaho a wuya, ta rasa da wanne ɗaya zata ji! Wata zuciya ta ce mata ta bi bayan bappan ta je cikin mutane ta ci mashi mutunci ko zata huce haka nan. Wani zuciyar kuma ya ce ta bi bayan Mairo ta laƙƙaɗa mata ɗan banzan duka, hakan zai sa ran bappa ya ɗacaca sosai. Wani zuciya ya ce ta koma gida dik zasu zo ne su sameta tun da gwaggonta ta yi mata alkawarin zata murza kambunta, zata baza mulki a cikin gidan. Tunani dai kala kala cike fal a ranta ta rasa madogara, sai zallar mugunta a bakar zuciyarta. Daga ƙarshe dai da ta ga babu sarki sai Allah, sai ta shafawa kanta ruwan sanyi ta nufi gida tana ta wani kunkuni tana tsinewa bappan da bai san tana yi ba a cikin zuciya. 😥 ======================== BLACK WORLD🔥 Shiru Sweetie ta kwanta saman bed ɗin Ronnie tana tunanin duniya, su kuwa suna church. Can tunanin kyan Black Tiger ya ratso mata ta cikin kwakwalwarta. Ai a miliyan ta tashi zaune tana ɗan sake fuska. Can sai ta fara ganin shi a idanunta yana yi mata gizo, ta mutu a kan romance pink lips ɗinsa. Zuro ƴan kafafunta kasan bed ɗin ta yi, sanna ta diro ƙasa, dan gadon yana da tudu sosai. Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi wajen glasses da ta gani kusa da tampatsetsan mirror. Takardu ne cike tab a cikin glasses ɗin, su handout, Bible, drama books, text books da dai sauransu, Ronnie akwai san karatu sosai, shiyasa yake da tarin takardu sosai. Ƙoƙarin buɗe glass ɗin ta yi a tunaninta dan ta duba ko akwai hotunan Ronnie da yayan nasa, sai dai abin da bata sani ba shi kansa Ronnie ranarsa ta farko ce na ganin yayan nasa a lokacin da ta gansa. Kasa buɗe door ɗin ta yi, dan komai nasa mai mahimmanci killace yake da securitys. Sam bata ji daɗin hakan ba, dan ta so ta gansa. Gaban mirrorsa ta nufa dan ta ga kanta ko zata rage kewar Pretty da take ji. Hannayenta dikka biyu ta sanya ta dafe saman glass na saman table ɗin mirror, ta zubawa kanta idanu ta cikin mirror tana kallon kyan da ubangijin talikai ya yi mata. Tunanin yadda kamannin Kamran ɗinta zai iya kasancewa ne kawai ya faɗo mata a ranta, da shi take kwana take kuma tashi. Kamar walkiya haka ta ga mirror yana ƙoƙarin darewa gida biyu, da farko ta ɗan tsorata, sai kuma ta dake tana cigaba da kallon mirror babu ko kyaftawa. Kamannin face ɗinta a jikin mirror ne ya fara sauyawa izuwa wani kamanni na daban, still bata tsorata ba, sai kara zaro idanu da ta yi tana cigaba da kallon kanta. A hankali ta cigaba da rikiɗa tana canzawa izuwa kamannin da bata taɓa ganin irinsa ba. Wani irin haske ne ya bayyana ta cikin mirror wanda yasa ba shiri ta ɗaga hannayenta izuwa saman face ɗinta dan ta kare idanunta daga samun matsala ta dalilin wannan haske. Buɗe tafukan hannunta da ta yi wajen ƙoƙarin rufe face ɗinta ne ya yi sanadiyar bayyanar nata magic ɗin ba tare da ta sani ba. Bata ankara ba sai ji ta yi wani irin tsawan tarwatsewar mirror ya daki dodan kunnenta. Watsa watsa mirror ya yi a ƙasa, karfi ne ya haɗu da karfi, fitar magic ɗinta yasa ya haifarta wannan, dan hasken nata ya haɗe da wannan haske da ya fito ta cikin mirror, kuma nata yana da matuƙar karfi na ban mamaki, shi ne sila. A miliyan ɗari ta yi kasa da hannunta a in da ta waro idanu tana kallon yadda mirror ya yi watsa watsa, haƙiƙa a wannan karon ta jijjiga sosai, ba ita kaɗai kuma ta jijjiga ba, har da shi Black Tiger sai da ya jijjiga, dan kuwa fashewar mirror nan ba ƙaramar abu bace a wajensa, ba mirror ce kamar kowanne ba, bai taɓa zaton zata buɗe tafukan hannunta magic ɗinta ya fita ba, da bai yi ƙoƙarin razanar da ita ba. And bugu da kari unexpect magic ɗinta ya daki saitin zuciyarsa, kafin ya farga ya kare kansa haskenta ya tarwatsa tasa da har ya ɗan yi baya kaɗan, ya ji hakan a jikinsa sosai, sai dai kuma, a take ya juya magic eyes ɗinsa ya kusar da raɗaɗɗin da ya ji. Zuciyarsa ta bakanta sosai a kan hakan, ba'a taɓa wanda ya taɓa gigin yi mashi abu makamancin hakan ba, dan haka sai ya kudurta a ransa dole ya hukuntata ya kuma durkusar da magic dake jikinta. Ita kuwa sai ƙoƙari take yi ta fahimci abin da ya faru da har ya kawo tarwatsewar wanna mirror haka?. Ji ta yi ɗakin ya fara juya mata, sai ta fara ganin kamar fanka yake yi mata. Da gudu ta bar gaban mirror ta haye saman bed. Nan take wani iska mai karfi ya banko kofar ɗakin ya shigo, tana ƙoƙarin juyar da kallonta izuwa wajen kofar ba zato ba tsammani ta ji saukar wani mahaukacin mari a kuncinta wanda bata ga hannun mutum ba, bata san daga ina marin ya fito ba. Tun da take a rayuwarta bata taɓa jin wani abu mai bala'in zafin wannan mari ba, dik da magic dake jikinta hakan bai hana ta ga wani irin duhu ya gilma mata ba, har wani irin jiri mai karfi ne ya ɗebeta daga zaune, na ƴan sakanni ta gaza gane a wani duniya take, kunnuwanta gabaɗaya sun toshe bata iya jiyo sautin komai. Gabaɗaya kwayayen fitillu masu hasken da suka kawata ɗakin ne suka fara ɗaukewa suna sake kawowa a lokaci guda, dai'dai lokacin da ta dawo cikin hankalinta take ƙoƙarin fahimtar me yake faruwa. Dai'dai lokacin chandelier ɗakin ta jijjigo daga sama ta yo kanta a guje. Ihu mai sauti ta kurma tare da dirowa kasa daga saman gadon, sai wani irin haki take yi tamkar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi. Ga mamakinta sai ta ga tana dirowa kasa chandelier ya fasa faɗowa saman bed ɗin, ya juya ya nufota da karfin gaske. A juye ta nufi baya baya dan ta fita waje. Sai dai kofar room ɗin ya rufe kansa tun bayan shigowar wannan iska da ya jijiigo da chandelier. Ihu take yi sosai dan bata taɓa ganin iska mai karfin wannan ba, ga shi dik in da ta yi sai chandelier ya bi bayanta. Kurewa ɗakin ta yi a in da ta mannu da jikin bango tana cigaba da ihu. Ronnie dake zaune saman chair a cikin katafaren church ɗinsu sai ji yake yi gabansa yana faɗuwa, sai ya ji zuciyarsa ta tsinke, kansa yana sara mashi, dik ya sara nutsuwarsa da sukuninsa, yana jin kamar wani abin ne zai faru da shi. Idan Sweetie ta kurma ihu sai ya ji hakan a cikin ransa, amma sam bai kawowa ransa ita ce take cikin damuwa ba. Pastor na jawabi babu abin da kunnuwansa suke iya ɗauko mashi, idanunsa dai yana a kan pastor, amma baya sauraronsa. Da wani irin karfi na ban mamaki wannan chandelier ya nufeta tsaye a jikin bango tana ihun neman taimako. Lokacin guda da chandelier ya kusa isa gareta ya riƙiɗe ya zama wani irin kaifaffen wuƙa mai dafin bala'in, hasken dake fita daga jikin wannan wuka sai da ya sanyata kanƙantar da idanunta. Kan wukar ta zanen bakar damusa ce, hasken light blue ne yake fita daga dik wata kusurwa na jikin wukar. Kai tsaye wuyar Sweetie wukar ya nufa, da karfi kuma. Wani irin razanannen ihun ta saki mai doɗe kunnuwa, bata da madogara, ba hanyar gudu, tana ji tana gani zata mutu. Ganin cewa wuyarta wanna wuƙa ya nufa yasa ta kai hannayenta ta tare wuyar tata tana ihu, sai dai a wannan karon bata datse idanunta ba. Tana tare wuyarta da hannunta unexpect taga wani haske ya fito daga cikin hannunta ya nufi wanna wuƙa, nan take wanna haske ya dakatar da wukar a dab kusa da ita. Ya ilahi ya lilliahi, ai sumar tsaye ta yi tana kallon hannunta, her first time seeing that she has a unknowing magic, she was so surprised!. Kamar wata wadda aka zarewa ruhi, ido ta kara zarowa tana ganin yadda hasken hannun nata yake tamkar light aka kunna, abin ya yi mugun ɗaure mata kai, tana son ta motsa hannun nata ko wani sassa daga jikinta amma ta kasa, dik sai ta ji jikinta ya yi mata nauyi sosai. Kafafunta ne suka fara gaza iya ɗaukar gangar jikinta, hakan yasa ta ɗan yi tangal tangal kamar zata faɗi. Wannan tangal tangal da ta yi yasa hannunta ya ɗan motsa, hakan ya haifar da motsawar wannan wuƙa da a yanzu yake ƙarƙashin sarrafawar hasken hannunta. Kara zaro idanu sosai ta yi tana kallon wanna abin al'ajabi. Da kyar da suɗin goshi ta iya kama kanta bata zube ƙasa ba. Har lokacin iska mai karfin nan dai yana cigaba da kaɗawa a cikin ɗakin, Black Tiger yana cikin wannan iskar, ya zuba mata idanu ne yana kallon gudun ruwanta, amma kuma ya yi matuƙar mamakin karfin irin na magic ɗinta da har ya iya tare wannan wuka da ya turo mata bai huda fatar wuyarta ba. Idanunta a kan wukar, cikin karyewa da sanyin gaɓɓan jikinta ta yi iya ƙoƙarinta wajen motsa ɗan hannun. Tana motsa shi ma wanna wuƙa ya motsa, dik in da hasken hannun nata ya bi wanna wuƙa ma yana bi, a hankali ta fara matsar da hannunta daga wuyarta, hakan yasa shi ma wukar ya matsa daga saitin wuyar tata da ya yi. Abin al'ajabi ya bata matuƙa, sai kuma kamar wata zararriya ta saki murmushi wanda sai da yasa dimple ɗinta bayyana, ko me abin murmushi a wajen?. Ajiyar zuciya ta sauke ganin tana da hanyar cetan kanta, fara ƙoƙarin tabbatarwa da kanta hakan ta yi ta hanyar juya hannunta ta in da takeso. Dik yadda ta juya wukarma sai ya juya ta nan, wani irin dariya ta fashe da shi kamar wata zararriya. Yi take yi babu kakkautawa idanunta a kan wukar. ========================💔 Lokacin guda kuma ta tsayar da dariyar tata cak, kome ta tuna? Sai kuma idanunta suka ciko da kwallah, a hankali ta furta. "Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, ya Allah.........." Bata kai karshen maganar da take son amayarwa ba kenan taga wanna wuƙa ya faɗi a ƙasa, faɗuwarsa ke da wuya ya haifar da wani irin sauti mai ban tsoro, a take guguwar dake ɗakin ta kara karfafa kamar an watsawa aljanu ruwan addu'a yana konasu. Ba ƙaramin kara razana ta yi ba, da karfi ta furta. "Wayyo Allahna ka kawo mun ɗauki......" Ai bata gama rufe bakinta ba kofar ɗakin ya ɓalle ya buɗe kansa da kansa. A miliyan ɗari ta kwasa ta nufi waje, ta kasa gane cewa sunan Allah da ta ambata a wajen ya rikita dik wani tsafi dake waje, shiyasa take jin wanna guguwa ta kara karfafa wai dan su kare kansu daga kalamanta shi ne suka kara karfin iko. Kai tsaye parlourn ƙasa ta nufo tana ihu, bata tsaya electric stair case ɗin ya yi kasa da ita ba ma, da kanta ta tattake shi ta yi ƙasa. A wanna lokaci ta kasa iya sake ambatar sunan Allah, abin ku da shaiɗan da kuma shirka. Bayanta Black Tiger ya biyo cikin wanna iska, dan ransa ta kara bakanta na sunan Allah da ta kira ta jijjiga mashi hankulan ruhohin tsafinsa. Ya sha alwashin yau zata gane kurenta. Wanna iska ne yasa gabaɗaya kofofi da windows ɗin parlourn kasa suka rufe kansu, fara ƙoƙarin kamata Black Tiger ya yi, ihu take kurmawa tana neman hanyar tsira. A wannan lokacin ne ya riƙiɗa ya zama mutum, da ainahin face ɗinsa ya bayyana, yana sanye da pj a jikinsa. Like wow, kamar wani kafani, kaman ba mutum ba, ga shi ya juya idanunsa izuwa na magic, sai ya kara riƙiɗewa kamar ba mutum ba, zallar madarar kyau. Cak ta dakata da neman hanya da take yi, bata yi zaton shi bane da ba zata gudu ba a cewarta, ita da take son ganin face ɗinsa daman! Ai da tsayawa zata yi kome zai faru ya faru. His first time kasakcewarsa a cikin wanna parlon, bayan ɗakin Ronnie da yake kai ziyara ta hanyar magic bai taɓa fita ko ina ba, yau karo na farko Sweetie ta sanya shi fitowa. Ita ce mutun ta farko da ta fara ganin face ɗinsa bayan babansa, and ita ce mutun ta farko da ta fara sanya shi fitowa har parlon ƙasa, lallai ya tabbata idan bai tsaya ya bada himma ba zata iya cin nasara fa a kansada gaske. Zuba mashi idanu ta yi tana kallonsa, face ɗinsa babu alamar mutumci ko kaɗan, zallar mugunta ce a samanta, in ka gansa sai ka razana, amma yarinyar nan Sweetie ko a jikinta, bata ji tsoron ganin cikin idonsa ba. Wani irin ihu mai sauti na ruhohin tsafinsa ne ya fara karaɗe ko'ina a cikin parlon, hakan ya ja dikkansu biyu suka ɗan yi shock, abin ya bashi mamaki jin wanna ihu. Cigaba da kura mashi kallo Sweetie ta yi tana mamakin hali irin nasa, ga shi kyakkyawa amma kyan ɗan maciji ne, ɗan kunama!. Shi kuma gabaɗaya hankalinsa ya koma a kan sautikan da yake ji wanda ita Sweetie bata iya jiyo hakan, da yake ta ɓangaren tsafinsa ne, shi kaɗai yake ji. Can kamar saukar aradu haka ya tsinkayo wata iriyar murya mai tashin kai, mai kuma karfin gaske cikin guguwa da kuwa, tamkar muryan kartin maza ya ce. "Autan duniyoyi ya bayyana, Autan ruhohi ya bayyana". Shi ne abin da yake fita daga wanna sauti. Jin haka yasa ya tuna wasiyar babansa na karshe a idan yake ce mashi. "Wasiyata a gareka shi ne, kada ka yarda ya fita waje dik rintsi dik kuma wuya, kai ba kamar kowani mutum kake ba, kai ruhin ruhohine, autan duniyoyi ne, jagoran rundunoni ne, gatan manya manya ruhohi ne, nemanka suke yi kamar hauka, kai ɗan baiwa ne, da baiwa aka haifa mun kai, wanna dalilin yasa suka mayar da kai autansu, ni kuma ban yarda da hakan ba, saboda nasan me hakan yake nufi, wanna dalilin yasa na baro duniyar shaiɗanu da kai tin kana karami baka wuci 5 years ba, wannan dalilin yasa ban taɓa barinka kaje wani waje ba, saboda fitarka zai sa DUNIYAR SHAIƊANU su shaida in da kake, bana son su rabani da kai! Kada ka fita daga Black world har sai ka tara karfi sosai wanda zaka iya sanya barazana da tsoro a cikin zuƙatan DUNIYAR SHAIƊANU, wanda karfin ikonka zai iya sanyawa ka kwaci kanka daga ɗaukarka da zasu zo yi...............". "Ka tara karfin iko mai karfin gaske ɗana, na jima ina karɓar yaya maza daga hannun matan garin nan ina sanyawa ana basu horo dik dan na yi maka tanadi ɗana, ka cigaba da horar da su dan su zame maka bayi masu bada rayukansu a kanka!!". A lokacin da babansa yake yi mashi wanna bayanai hankalinsa baya'a jikinsa, a lokacin yana tunanin rashin lafiyar baban ne kawai, bai ɗauki zancen da wani muhimmanci ba, and bayar ɓacewar baban daga fuskar duniya bai sake tunawa da zancen ba sai yanzu. ============💘🔥=========== FOREST NE. Wajen yana cikin tsakiyar dokar daji mai cike da bishiyoyi masu girma, wadanda ganyensu suna rufe hasken rana. Akwai hayaniya mai ban tsoro kamar kuka na tsuntsaye da dabbar da ba a iya ganinta. Duwatsu da Tsaunika. Duwatsu sun kewaye wajen, suna ɗauke da layuka masu kama da alamomin tsafi, suna haskawa da ɗan wuta mai launin kore. Tsaunukan suna da tsayi, kuma akwai tsallake-tsallake na ruwa mai fitowa daga saman tsauni yana ƙara tsoratarwa. Babban kogon dutse shi ne cibiyar wajen matsafan. An yi ƙofofinsa da baƙin duwatsu mai siffar fuskokin aljannu. Jikin kogon yana ɗauke da rubutun tsafi a harshe da ba a fahimta. A ƙofar akwai fitila masu kunne da harshen wuta mai ruwan zuma da jajaye. ======CIKIN KOGON DUTSE======= Ɗakuna Tsafi. Babban ɗaki ne da ke tsakiyar kogon, yana da stage mai ɗauke da kayan tsafi, kayan al'ajabi, kwalabe masu kunshe da ruwa mai launi, ƙananan gumaka, da wukake masu ban tsoro. Ɗakin Hada Magani. A cikin babban ɗakin yake shi ma ta gefe guda. Cike yake da tukwane masu hayaƙi, ganye iri-iri, da fararen ƙasusuwa. Akwai ƙanshi mai kaɗaici da hayaki mai ɗan duhu yana tashi daga cikin tukwanen. Ɗakin Ajiya. Wannan ɗaki yana da duwatsu masu haske kamar gold, manyan littattafai na tsafi da aka ɗaure da sarƙoƙi, da wasu abubuwan al'ajabi kamar ƙwayoyin ido da ƙananan gumaka. Ɗakin Ƙulle-ƙulle. Wannan ɗakin yana da tagwayen layukan duhu a kasa, fitilu masu koren wuta, da gumaka masu kama da halittun ban tsoro suna kewaye. Tsarin Haske. Hasken daga fitila ko wutar tsafi shi kadai yake cike kogon, kuma wutar tana ja da baya idan mutum ya matso kusa. Sautuka. Akwai sautin iska mai ban tsoro, kuka na dabba mara ganuwa, da muryoyin mata suna magana a hankali kamar suna yin tsafi. Halittun Ban Tsoro. Akwai dodanni da halittun matsafa masu kama da inuwa suna yawo a wajen. Daga cikin wani keɓaɓɓen ɗaki dake gefe wanna murya take fitowa, sai faɗi ake yi autan ruhohi ya bayyana, lokacin girgiza duniya ta yi. Ɗaki ne mai cike da ababen al'ajabi da ban tsoro, sai dai akwai tarin takardun tsafi cike a cikin ɗakin, wasu irin dogayen mutane ne su goma tsaye a cikin ɗakin saman stage, dikkansu suna cikin shigar wani irin dogayen kaya har yana jan kasa launin ruwan zuma, sai suka ɗaura fara kal a sama, gashin kansu ya kasance white hair ne, ga shi sun saki gashi dogo har bayansu, dikkansu riƙe suke da litattafan tsafinsu, ga dikkan alamu su ne manya manyan malaman duniyar shaiɗanu. Wani irin mutun mutumi na wata mata dake a cikin ɗakin sai ya tashi hankalin dik wanda ya ɗaura idanunsa a kanta, macece tsirara aka ginata, ga wani sanda wanda daga gani zaka san na tsafi ne wanda aka zira mata shi daga gabanta har ya fito ta bakinta, dik yadda aka yi ta haka suke aiwatar da tsafe tsafensu, shiyasa suka bar alama a wannan waje. Burin waɗan nan azzaluman su cure duniya ta zama abu guda, ya zamana babu wata ƙasa ko gari, dik a zama abu guda ne, su ruguje ɗakin kaba dake kasar Makka su gina fadarsu a wajen, ya zamana gabaɗaya duniya shugaban kasa kuda ɗaya ne wato su kenan, sun shafe tsawon lokaci suna yin wanna shirye shiryen ta hanyar tsaface tsaface dan samun karfin iko.. KOWA DAI BURINSA MULKI, WAI SHIN BASU SAN AKWAI MUTUWA BANE? BURINSU SU MULKI DUNIYA KAMAR SU SUKA HALICCI DUNIYAR?. Bacewar Black Tiger daga cikinsu ya dakatar da su da yin dik wani shirye shiryen da su ke yi domin nufar ɗakin kaba. My people's kun gane cewa ikirarin Black Tiger na mallake duniya a jikinsa abin yake ko?. Mahaifin Black Tiger shi ne shugaban malamai ko in ce bokayen DUNIYAR SHAIƊANU, yanzu da kuka gansu su goma a wanna ɗaki to mahaifinsa shi ne sarkinsu, shi ne shugabansu, shi ne kuma cikon na sha ɗayansu, shi ne mai faɗa aji, rana ɗaya ya ɗauki Black Tiger suka bar DUNIYAR SHAIƊANU, ya je ya sari daji ya kafa birnin BLACK WORLD, ko me dalilinsa na yin hakan?. Kada ku manta fa shi ne sarki a wanna daula, amma ya gudu ya bar wajen, to me dalili?. Burin DUNIYAR SHAIƊANU shi ne su fara ruguje musulunci a idon duniya, burinsu su shafe babin addinin musulunci, su ruguje ɗakin kaba, su gina fadar mulkinsu a filin na ɗakin kaba, su cure duniya waje guda domin su cigaba da juyata ta yadda zasu samu dama su shafe addinin musulunci da gasken gaske, a yanzu haka sai yaki suke yi da musulunci amma ta karkashin ƙasa, ba zaka gane suna yin hakan ba in ba'a faɗa maka ba, kwantan ɓauna suke yi a yanzu, ta ƙarƙashin ƙasa suke aiwatar da komai. Suna ta ƙoƙarin kawo rarrabuwar kai a cikin musulmi, suna ta sanyawa musulmi suna kashe kawunansu, suna ta hasasa gaba a tsakanin musulmi ba tare da musulmai sun gane ba!. (LABARIN EVIL WORLD WATO DUNIYAR SHAIƊANU FA KU KALLE SHI A MATSAYIN LABARIN GASKIYAR ABIN DA YAKE FARUWA A DUNIYA NE, DA KARFI DA YAJI SO AKE YI A YAKI ADDININ MUSULUNCI TA KOWACCE HANYA, DAN HAKA KU TSAYA DA ADDU'A SOSAI, NASAN WASU ZASU GA ABIN KAMAR TATSUNIYA, TO WLH YA WUCI HAKA, YA ZARCE TUNANINKU, KU TSAYA DA ADDU'A KAWAI.) Su waye ne a DAULAR DUNIYAR SHAIƊANU?. Wasu gungun kafurai da yahudawa ne da suka haɗa kawunansu, suka cure a wanna waje domin ganin sun cinwa burinsu a kan musulmai da Musulunci, suna da yawa a wajen, shararrun gima giman matsafansu ko in ce bokayensu su ne waɗan nan mutum 11 ɗin, sannan suna da Jiga jigan TITANS waɗan da suka zarce tunaninku a horarwa. Kusan da tsafi suka yi amfani wajen haɓaka waɗan nan TITANS ɗin, burinsu a nan shi ne idan suka ci addinin musulunci da yaki ta karkashin kasa sosai, idan ya rage masu saura kaɗan, sai waɗan nan TITANS ɗin su karisa yakin su je su ruguje masu ɗakin gaba, tsawon lokaci suka ɗauka suna bawa waɗan nan TITANS ɗin horo na ban mamaki, burinsu shi ne bayyanar TITANS a duniya ya girgiza kowa, ya zamana babu wani makami da zai iya yaƙarsu, sannan babu wani ɗan adam da zai iya tinkararsu, ganinsu kawai yasa hantar duniya ta kaɗa...... Tashin hankali. Ƴaƴan mutane suke satowa su mayar da su TITANS dan gudanar da wannan aiki, a kallah yanzu suna da TITANS mugaye masu zuƙatan shaiɗanu sun kai TITANS 10000, kuma har yanzu ba su daina sato wasu yaran ba. Su waye TITANS? Wasu irin karfafa jaruman da suka jiku da horo ne, wuƙa ko bullet baya iya huda fatar jikinsu, tamkar ba mutane ba haka suke, suna da tsawo da faɗi sosai, sun zarce tunanin dik yadda kuke tunani!!. Da su za'ayi amfani wajen ruguje ɗakin kaba ɗakin Allah. Ya Ubangiji ka kare musulmi da musulunci a dik in da suke, kada ku kalli wanna a iya labari kawai, ku dai ku yi addu'a kawai, Allah ya cigaba da ɗaukaka musulunci!!. ====================== Ganin ya yi shiru kaman mai sauraran wani abin ne yasa Sweetie ta lallaɓa a sace ta bar parlon, bai ankara da ita ba, ta gudu izuwa sama. Shi kuwa ya tsunduma a kogin tunanin waɗan nan zantuka da ya jiyo ne, yana kuma tariyo zantukan babansa. Amma ku me kuke tunanin yasa mahaifin Black Tiger ya bar DUNIYAR SHAIƊANU? bayan kuma shi ne shugabansu a wajen?. Ya ɗan jima a haka kafin ya juyo da magic eyes ɗinsa, sannan Black heart ɗinsa ta matso kusa. Kudurtawa ya yi a ransa in dai haka ne to tabbas sai ya riga Duniyar shaiɗanu mallakar kambun mulkar duniya, dole ya tashi tsaye, dan ba zai taɓa yarda su rigasa ba, bai san cewa shi ne makullin mulkar duniyar da suke shirin yi ɗin ba, dan kuwa in dai baya Duniyar shaiɗanu to tabbas da wuya su iya isar da wanna aiki da suka ɗauko.... Hmmm akwai tashin hankali fa matuƙa. A cikin zuciyarsa ya furta cewa. Lokacin bayyanarsa ga duniya ya yi, lokacin kara tsananta horar da warriors ɗinsa ya yi, lokacin farautar Spender ta kowacce hali ya yi, dole ya mulki duniya cikin kankanin lokaci, dan haka dole ya shiga fadar birnin Black world dan fara gudanar da mulkinsa........... Sweetie ta zame mashi silar abubuwa da dama a ɗan zuwanta birnin, dalilinta yanzu zai bayyana kansa wa birnin Black world. To wai ina Spender ɗin yake? Tayaya zai samo shi? Dan dai kunga dik wahalar da ya bawa Sweetie ta ki gaya mashi in da Spender yake, ya zai yi kenan?. Ɓacewa ya yi daga in da yake tsaye, bai bayyana a ko'ina ba sai a katafaren fadar birnin Black world. Fadar sarki tana da kyan gani mai matukar birgewa. Daga waje, an gina ta da duwatsu masu daraja da aka kawata da zinari da lu'ulu'u. Babban kofar shiga tana da girma fiye da yadda mutum zai iya hangowa, kuma an kawata ta da hotunan zaki da bakar damisa, wanda ke nuna ƙarfin iko da jarumta. A cikin fadar, daki-daki za ku ga hasken fitilu masu daraja da aka yi da lu’ulu’u na musamman suna haskaka ko'ina. Rufi kuwa an kawata shi da zane mai launuka masu kama da taurarin dare, wanda ke nuna darajar sarauta. Kujerar Sarauta A tsakiyar fadar, kujerar sarautar mai martaba take tsaye tamkar zuciyar duniya. An yi ta da zinari mai tsabta, tare da kawata ta da dutse mai daraja na lu'ulu'u da furannin jade. Kafafun kujerar sun kasance kamar zaki da suka yi alamar girmamawa ga sarki, kuma kujerar tana haskawa tamkar rana saboda yawan kayan ado na zinariya da azurfa da aka yi mata, sai dai ta saman kayin kujerar kan bakar damusa ce, sannan ta bayan kujerar gabaɗaya kaifafan kifiyoyi ne da aka yi su da zallar gold, darajar wanna kujera ta wuci tunaninku, a kaf tarihi ba'a taɓa yin kujera mai tsada da kyanta ba. Zauren Masarauta Fadarsa tana da manyan ginshiƙai da aka kawata da rubuce-rubucen hikima cikin harsuna daban-daban. Kowane bangare na fadar yana cike da hotuna masu ban sha'awa na yaƙe-yaƙe da nasarorin da suka bayyana tarihin sarautar. Idan baku manta ba na gaya maku sun sha gwabza yaki wajen durkusar da dik wasu masarautu da suka fisu karfin iko sabdoa zalunci, to hotunan yakin ne na nasarorinsu a manne a bangon!. Tsarin Sarauta An ware wani sashe na musamman ga makullai na zinariya, inda ake adana takardun mulki, kayan alatu, da RAWANIN ZALINCI da sarki ke amfani da su. Kamar yadda aka saba, masu gadi sanye da kayan mayaƙa suna tsaye kowane lokaci suna tabbatar da tsaron fadar. Sam warrios dake gadin fada basu ga giftawar kowa ba a wajen, da magic ya yi amfani wajen shigewa ciki ta babbar kofar shiga. A tsakiyar fadar ya tsaya, babu kowa a cikinta, ko'ina a share fes yana kyalli, ɗan jujjuya idanunsa ya fara yi yana bin dik wata kusurwa lunguna da saƙuna da kallo. A kan dangerous kujerar mulkin ya tsayar da kallonsa. Gizo idanunsa suka fara yi mashi na lokacin da mahaifinsa yake zama a saman wanna kujera, hango babansa yake yi yana sanye da wannan the most powerful CROWN OF INJUSTICE ɗin a kansa yana jawabi. Ba zai taɓa manta lokacin da wani bawa ya yi laifi aka kawosa gaban sarki mahaifinsa ba, yana zaune a gaban Tv a room ɗinsa yana ganin yadda babansa yake wanzar da mulki, dan baban nasa yasan shi zai gajesa, dan haka sai ya sanya yana ganin dik yadda ake mulki ta Tv, yana kuma koya mashi a zahiri idan ya koma cikin gida, hakan yasa ya iya gudanar da komai cikin tsanaki. Yana gani babansa ya sa aka ja wanna bawa, ya ce aje a tsaresa tsawon sati biyu babu abinci babu ruwan sha, sannan a tabbatar da sauran bayi dake tsare suna cin abinci a gaban idanun wannan bawa shi kuma yana ganinsu tsabar zalincinsa. Ajiyar zuciya ya sauke tare da yin magic walk ya isa gaban wanna kujerar. Ya ɗan ɗauki tsawon lokaci yana kallonta kafin cikin nutsuwa ya zauna a samanta. Yana zama nan take fadar ta bada wani irin duhu wanda ya samu sanadiyyar ɗaukewar dik wasu fitillu dake ciki, sanna lokaci guda suka sake kawowa da hasken gaske fiye da yadda suke. Komai na cikin fadar sai da ya girgiza, shinfiɗun dake ƙasar wajen ne kawai basu girgiza ba. Dik ya ga hakan, amma sai ya yi kamar bai gani ba. Ya ɗan ɗauki lokaci a cikin fadar kafin ya fice izuwa room ɗinsa, shap ya fita harkar Sweetie, yanzu abin da yake a gabansa ya sha gaban tunanin mutum, dole ya mance da wata ƴar karamar kwaruwa Sweetie. Ta in da ya saba magana da master Devil wato ta wani ɗakin duhu, in da ko ɗan yatsanka baka iya gani, nan ya nufa tare da kiran master Devil a kan ya zo. Yana zuwa ba ɓata lokaci ya umarcesa da ya sanar da gabaɗaya mutanen birnin Black world a kan gobe zai shiga fada, zai koma kan kujerar mahaifinsa. Sosai master ya yi mamakin jin wanna magana, amma bashi da ta cewa da ya wuce ya isar da abin da aka umarcesa kawai, dan haka sai ya karɓi umarni ya tafi. Ita kuma Sweetie, room ɗin Ronnie ta koma ta takure waje guda, ko tsoron komawa cikin ɗakin bata yi ba. ===========🔥🔥🔥========== ABUJA. Kwance suke a cikin A&E cikin katafaren hospital mafi tsada a garin Abj. Kowannensu yana kwance saman nasa bed ɗin, jaririn Khadija yana hannun ɗaya daga cikin securitys da suka kawosu hospital ɗin, an duba shi an yi mashi dik abin da ya dace. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ==========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Kwance suke a cikin A&E cikin katafaren hospital mafi tsada a garin Abj. Kowannensu yana kwance saman nasa bed ɗin, jaririn Khadija yana hannun ɗaya daga cikin securitys da suka kawosu hospital ɗin, an duba shi an yi mashi dik abin da ya dace. Sai kuka yaron yake yi yana neman abin da zai sanya a cikinsa, yunwa sosai yake ji, ga uwarsa kuma bama a san a wani hali take ciki ba, ta mutu ne ko tana raye? Allah masani. Ko motsawa babu wanda ya yi a cikinsu, kamar babu rai a jikinsu. Sai kai komo wanna security da ya rike yaron yake yi, yana ta safa da marwa ya kasa zama, sai haɗa uban gumi yake yi, ga babyn yaki ya yi shiru saboda yunwa. Ya rasa ya zai yi da shi, ga shi shi ba iya reno ya yi ba, haka dai suke ta fama, idan ya gaji sai ya miƙawa wani daga cikin securitys ɗin, shi ma in ya gaji sai ya miƙawa wani. A haka har gari ya waye, babu wanda ya nufosu domin ya taimaka masu ya sa yaron ya yi shiru, saboda kowa a cikin hospital ɗin tsoronsu yake ji, sun ga jiga jigan jami'ai ai dole su tsorata kowa ya kama kansa, so kwanan tsaye waɗan nan securitys suka yi. Ba halin su koma hotel da suka sauƙa, dan kafin tafiyar Ramish ya ce su kula da case ɗin har komai ya warware, ma'ana su kula da waɗan da aka buge har su sami lafiya. Washegari da safe haka babyn nan ya rinƙa kuka, Allah sarki bawan Allah yunwa yake ji sosai. Waɗan nan securitys ɗin dikkansu har sai da suka ji sun tsani yara saboda kukansa, sai dai kuma wanna baby na Khadija fa ya shiga ransu ba kaɗan ba. Sai misalin karfe 12 uncle Jahiz da wasu securitys ɗin suka nufo hospital ɗin, so yake su wuce Tunisia, shi ne ya biyo sahunsu ya ga shin zasu iya tafiya ne ko yaya?. Har yanzu Jaish yana sume bai farka ba, Ramish ya ce su barshi ya farka da kansa. Tun daga nesa da securitys ɗin nan suka hango uncle Jahiz suka yi saurin nufarsa, har lokacin baby bai yi shiru ba. Tun da suka doso in da yake idanunsa na'a kan babyn hannunsu, mamaki yake yi a in da suka samo baby, dan shi a daren jiya bai ga wani baby ba. Suna ƙarisawa wajen suka fara yi mashi sannu da zuwa haɗe da barka da safiya. Bai iya amsa masu ba, idanunsa na'a kan babyn. Sai da ɗaya daga cikin securitys ɗin ya ce. "Sir mu ƙarisa ko?" Jinjina kai ya yi, sannan ya wuce gaba, har ya yi taku step biyu sai kuma ya juyo, ga mamakinsu sai suka ga ya miƙa hannu a kan su bashi babyn. A hanzarce securityn ya miƙa mashi, basu taɓa ganinsa rike da yaro ba, bama su yi zaton ya iya riƙewa ba. Ga mamakinsu kuma sai suka ga ya iya riƙe jariri ɗanyan haihuwa da kyau. Yana karɓar yaron kuma ya yi shiru kamar wanda ya ji ɗumin jikin uwarsa ko ubansa. A saman kaffaɗar kirjinsa da ya ji training saboda football ya ɗaura yaron, ya janyo towel da suke riƙe shu da shi dama ya ɗan lulluɓe shi da shi, ya zubawa babyn idanu sosai yana ta kallonsa, haka kawai ya ji kaunar yaron tana ratsa shi. Gaba ya wuce securitys cike da mamaki suka rufa mashi baya, a maimakon ya kalli hanya sai gabaɗaya idanunsa suna a kan babyn har suka ƙarisa ɗakin da su Khadija suke kwance. Dr ya buƙaci gani domin yasan me yake damunsu, saboda yana san yau zai wuce kasar Tunisia, ya ƙosa ya mayarwa da King Jaish ɗinsa su ga juna, rashin sanin ya fi dare duhu, bai san yanzu ne ma zasu shiga ainahin tashin hankalin na mutuwa da kuma ɓacewar gawar Gimbiya Zunaira ba, ko shi kansa Jaish ɗin sai ya ji a jikinsa. Buƙatar su haɗu a office babban Dr ya yi, bai ja ko ya yi wata magana ba, yana rungume da baby kamar wani ɗansa ya bi Dr izuwa cikin office ɗinsa. Su kuma securitys suna ta going up and down a cikin ɗakin. Ya ɗauki a kallah 30 mins suna tattaunawa da Dr kafin ya fito fuskar nan tasa babu annuri sam, kamar Dr ya gaya mashi wata magana mara daɗin ji. Motarsa ya nufa ɗauke da baby, bayansa securitys uku daga cikin waɗan da ke gadinsu Khadija suka bi. A tunaninsu tun da zai tafi zai basu babyn, sai suka ga akasin haka, dan kuwa ya manne babyn nan da jikinsa kam, babu alamar zai iya ɓanɓarosa ya basu shi. Yaronma da gulma ji kake yi tsit kamar wanda aka mukkawa nono uwa, har barci ya fara yi. Magana ya yi da securitys ɗin na tsawon 10 mins, bai bawa kowa damar jin maganar da suka tattauna ba, daga karshe ya rufe masu zancen da yau zai wuce Tunisia. Yana gama magana suka amsa umarninsa cikin girmamawa, suna ta jiran ya miƙa masu baby sai suka ga akasin haka, dan kuwa yana gama magana ya sanya aka rufe mashi kofar mota, basu yi gangancin cewa ya basu babyn ba, saboda sun san ba mancewa ya yi da shi a hannunsa ba, saboda dik maganganun da ya yi da su ma idanunsa a kan babyn, so yana sane da shi. Wucewa suka yi suka koma cikin hospital ɗin, shi kuma ya kama hanyar tafiya izuwa hotel ɗin da suka sauƙa. Yana sako kafarsa a cikin room ɗinsu ɗauke da babyn nan Jaish yana farkawa daga doguwar sumar da ya yi tin jiya da rana. A hankali ya fara motsawa yana ɗan kwaɓe fuska, tsayuwa a tsakiyar ɗakin uncle Jahiz ya yi yana kallonsa. Ganin da gaske farkawa yake son yi yasa ya zaga ta ɗayan gefen bed ɗin domin ya kwantar da babyn ya dawo wajen Jaish. Sai dai ina, yana kwantar da babyn ya fara ihu wanda sanadiyar hakan yasa Jaish ya waro idanunsa waje babu shiri. A hanzarce uncle Jahiz ya ɗauki babyn ya rungume haɗe da fara ɗan jijjiga shi ya dawo ta kusa da Jaish da ya gama waro idanunsa waje yana bin saman p.o.p da kallo. A hankali Jaish ya juyo da kallonsa a kan uncle Jahiz dake ta faman ɗan bubbuga jikin baby. Kara zaro idanunsa waje ya yi, bai iya motsa bakinsa ba, dan ko'ina na jikinsa ya yi mashi nauyi, tongue ɗinsa ta yi mashi nauyin da ba zata iya yin magana ba, amma tabbas yana son yin magana, kuma ga dikkan alamu ya dawo cikin hankalinsa, kallon sanayya yake yi wa uncle Jahiz ba kallon bakunta ba. "My son brk da tashi". Uncle Jahiz ya faɗa yana kallonsa shi ma. Bai yi wani motsi ba, bai kuma yi wani yunkuri ba, shiru kamar wanda ruwa ta cinye. "Kana san wani abin ne?". Uncle Jahiz ya sake jefa mashi tambaya. Ido kawai ya kafe shi da shi babu ko kyaftawa. Ganin hakan yasa uncle Jahiz ya ɗan matsa daga in da yake tsaye dan ya ga da gaske Jaish ya farfaɗo ne ko dai ya sake suma idanunsa a buɗe ne, yaga irin kallon da yake yi mashi babu ko kyafawa tamkar in aka zare ran mutum yana kallon wani wajen. Yana matsawa Jaish ya bishi da ido, wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da yin hamdala ga Allah, sannan ya matso ya zauna kusa da jaish ɗin. "Akwai abin da kake so ne my son?". Da kyar ya iya girgiza kai, a hankali ya fara ƙoƙarin motsa laɓɓansa dan ya yi magana. Idanun uncle Jahiz a kansa. Rigasa uncle Jahiz ya yi da cewa. "Zaka yi wanka ne?". A hankali ya gyaɗa kansa sama alamar e, dama abin da yake ƙoƙarin ya gayawa uncle ɗin nasa kenan, amma tongue ɗinsa taki motsawa. Miƙewa tsaye uncle Jahiz ya yi ya nufi cikin toilet, babynsa dai yaki ya kwanta, rike da shi ya shiga cikin toilet ɗin. Ga shi dai katafaren hotel mafi tsada suka kama, amma sai gabaɗaya uncle Jahiz ya raina hotel ɗin, toilet nasu ko na bedroom ɗin Sarina bai kai ba, sam basu ji daɗin sauƙa a wajen ba, amma da yake a kan hanya suke sai ba su wani tashi hankulansu ba. Shiga ya yi ya haɗa mashi ruwan wanka mai ɗan ɗumi, sannan ya fito, a lokacin babyn nasa ya yi barci, cikin dabara ya kwantar da shi a saman bed ɗin, tamkar ya iya reno, sannan ya matso domin taimakawa Jaish ya miƙe tsaye. Ga dikkan alamu Jaish ya dawo dai'dai sosai, dan tambayoyi uku ne yanzu a cikin ransa, ina Momma da dad? Ina Jawad? Ina Auta? Waɗan nan su ne kawai damuwarsa, ya yi kewarsu. Taimaka mashi uncle Jahiz ya yi, da kyar ya iya tashi zaune, har yanzu yana ganin jiri jiri, sanna kansa yana ɗan sara mashi kaɗan kaɗan. Hakika ya sha madarar mamaki na ganin irin yanayin kayan da yake a jikinsa, ko a mafarki bai taɓa ganin irin kayan ba, domin kaya ne na gargajiya wato shadda jampa da wando, shi dai yasan ba irin kayansu bane wannan, bai ma taɓa ganin irin kayan a zahiri ba sai dai idan a waya ya ci karo da videos na Hausawa, amma yau shi ne sanye da irin wannan kaya, to a ina ya samo su? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsa, kuma bai iya magana bare ya tambayi uncle Jahiz. Taimaka mashi uncle ɗin nasa ya yi izuwa cikin toilet, ya fito ya bashi waje, ya dawo cikin ɗakin domin haɗa masu kayansu jirginsu ya kusa ɗagawa, dik abin da yake yi idanunsa na'a kan babyn nan na Khadija, da alamu ya kamu da kaunar yaron sosai sosai, kun san fa kyawawan koreans akwai madarar kyau ba kaɗan ba, dole su shi ga ran mutum ko baya so. After some minutes. Like wow Jaish ya fito da kafafunsa ɗaure da towel a kunkuminsa, ya samu kwarin jiki na wanka da ya yi, a take har ya fara komawa yaron mommarsa, dama ya ɗan yi duhu zamansa a Yola. Kayansa uncle Jahiz ya fitar three-piece suit ya miƙa mashi, sannan ya janyo zip ɗin echolac ɗin nasu ya rufeta. Ba musu Jaish ya karɓi kayan domin ya shirya, uncle Jahiz ya fito waje dan ya sanar da securitys ɗinsu su juya kan motocin zasu wuce airport dan su koma ƙasar Tunisia yanzu. Kafin ya dawo cikin ɗakin Jaish ya kammala shiryawa, like wow ya yi masifar kyau sosai, sai dai gashin kansa a jiƙe yake, bai busar da ita ba, ya zubawa babyn Khadija idanu yana mamakin a ina uncle ɗinsu ya samo wannan kyakkyawan yaro haka?. "Jaish yaron ya yi maka kyau ko?". Uncle Jahiz da ya shigo a yanzu ne ya jefa mashi wanna tambaya. To kun dai san halin yaron Mommarsa, ba sai na sake faɗa ba, dan haka yana jin uncle Jahiz amma bai amsa ba, ya yi banza da shi, sai ma ya wuce ya zauna a bakin bed tare da yin kasa da kai kamar mai nazarin wani abin, da alama kunyarsa da ya rasa a garin Jimeta yau ta dawo, halinsa dai sak ya dawo, an koma gidan jiya malam. Da yake uncle Jahiz ya san halinsa sai bai wani damu dan bai amsa shi ba, ya ce. "Zamu iya tafiya a yanzu ko akwai wani abin da kake son yi?". Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya iya gamana ba, alamar zasu iya tafiya kenan, maganar ce kawai ba zai yi ba, yana son tambayar uncle ɗin nasa a ina suke kuma me ya kawosu nan? Amma ina baya son yin magana yasa ya yi biris da zancen, da alama ma ya karo walaƙanci kaman ba shi ne ya gama shanyewa Mahnoor baki jiya ba, dik ya mance wanna!. Tashin sense, me kuke tunanin zai faru?. Ɗaukan baby uncle Jahiz ya yi ya nufi waje, yana fita yasa securitys da su shigo su kwasan masu echolacs ɗinsu, zasu fara zuwa asibiti su mayar da babyn Khadija sannan su jandadawa Dr da ya kula da su kafin su tafi. Haka kuwa aka yi, karfe ɗaya na rana dai'dai jirginsu ya ɗaga sai kasar Tunisia cikin amincin........ Safe journey our Jaish and uncle Jahiz. =====KINGDOM OF POWER====== Zaune take a saman sofa a part ɗin Mammienta, daga ita sai wani figaggiyr simi, wani riga ne mai siririn hannu wanda ya tsaya mata a iya gwiwowinta, fararen kafafunta suna cikin wani katan bowl mai ɗauke da ruwa launin orange color, skin ɗin Sarina kullum cikin samun gyara yake, ta iya kula da shi matuƙa. Wata kuyanga ce durkushe a saman gwiwowinta a gaban Sarina tana aikin wanke mata kafafunta dake cikin ruwan. Mammie na zaune a saman sofa kusa da ita, Sarina tana riƙe da wasu hotuna tana kallo tana sakin ƙayatattcen murmushi, da alama yau suna cikin matsanancin farinciki daga ita har Mammie ɗin tata, sai hira suke zubawa suna fara'a. Ita kuwa wannan kuyanga kanta a kasa tana aikinta cikin girmamawa, ga dikkan alamu tana bala'in tsoron Sarina. Fanan ce ta shigo cikin ɗakin bakinta a ɗauke da sallama. Babu wanda ya amsa sallamar a cikinsu face kuyangar nan, ita ma a cikin zuciya ta amsa, saboda tana tsoron Sarina ta hukuntata, zasu ce ai ba ita aka yi wa sallamar ba. Wata kuyanga ce ta sake shigowa baki ɗauke da ladabebben sallama. Kusan a tare suka kariso ciki ita da Fanan, ita tana zuwa ta fara aikin shafawa Sarina kayan gyaran jiki a dik wasu sassa na jikinta, ita kuma Fanan saman sofa ta zauna tana haɗe rai kamar hadari. "Lafiya kike wani kwaɓe fuska haka?". Cewar Sarina, ta yi maganar tana wani bin Fanan da kallo mai kama da harara. "Ke Aunty Sarina baki san me yake faruwa ba ko?". Ɗan taɓe baki ta yi kafin ta ce. "Me kuma yake faruwa?". Mammie ma kasa kunne ta yi dan ta ji me yake faruwa. Kara haɗe rai Fanan ta yi haɗe da alamar tausayawa a saman face ɗinta ta fara magana. "Baki san Yah Jawad yana can kamar zai mutu saboda an aurawa Yah Rizwan Chuchu ba ko?". Siririn tsaki ta ja. "To ni me ya dameni da su?". "Kai Aunty Sarina kin san fa Yah Jawad ne yake son Chuchu ba Yah Rizwan ba, ke baki ji tausayinsu bane?". Yamutse fuska ta yi tare da haɗe rai. "Su mutu ma dikkansu idan suka ga dama, ni kinga in abin da ya kawo ki nan kenan tashi ki bamu waje". Ɗan zaro idanu Fanan ta yi like surprise haka. "Aunty Sarina su Yah Jawad ne fa!". "To sai aka yi yaya idan su ne? Nace su mutu idan suka ga dama! Ni ki rabu dani da abin da nima yake rai'na". Da sauri ta dawo da kallonta a kan Mammie. "Mammie kin ji abin da Aunty Sarina take faɗe ko? Su Yah Jawad take cewa su mutu fa". Ta yi maganar cike da yakini da sa ran Mammie zata yi wa Sarina faɗa kuma ita ma ta ji babu daɗi a kan maganar, ina ai sai ta ga saɓanin tunaninta, dan kuwa ɗaure fuska sosai mammie ta yi kafin ta ce. "To sai me dan ta ce hakan?". Zaro idanun sosai Fanan ta yi, she was so surprised jin amsar Mammie tasu. "Mammie ban gane ba!". Tana kara zaro idanu ta yi maganar. "Ba zaki gane ba ai, mu kingan mun nan ba su Jawad bane a gabanmu, kowa ma a cikin Kingdom ɗin nan in ya ga dama ya mutu!!". Cewar Sarina uwar rashin kunya. Kasa yin magana Fanan ta yi, ta zuba masu ido tana mamakin jin furucinsu. "Ke wai baki ma san dik abin da yake faruwa da su Mammie ɗin ce ta haɗa ba ko?". Cewar Sarina. A miliyan Fanan ta kara zaro ido waje tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa haɗe da furta kalmar what!! Ba tare da ta san kalmar ta fita daga bakinta ba. "Kwarai kuwa, mammie ce ta haɗa dik wanna cakwakiya, dan haka ki wuce ki bamu waje uwar ƴan tausayi!". Cewar Sarina again. Yadda kuka san ruwa ya cinye Fanan, tamkar babu ita a wajen ta yi shiru, al'ajabi ya kusa kasheta. "Tashi ki fita ki bamu waje tattaunawa muke yi uwar masu tausayi". Cewar Mammie. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta mike, sumumui sumumui ta nufi kofar fita. "Sakarya kawai wadda bata san ina yake yi mata ciwo a jikinta ba, shashasha wai ke uwar tausayi! Zaki mutu babu wanda ya ji sautin kukanki in dai kika ce tausayi zaki yi a rayuwarki!!" Cewar Sarina dake binta da wani matsiyacin kallo. Sarai ta ji abin da Sarina ɗin ta faɗa, amma bata juyo ta tanka mata ba ta nufi waje kawai tana yi masu addu'ar shiriya. "Ya isa haka my daughter". Cewar mammie ga Sarina. "Allah Mammie Fanan wawiya ce wacce bata san ciwon kanta ba, ni bakanta mun rai take yi wlh". Tana magana tana hararar kuyangar dake gabanta tana wanke mata kafa, kamar kuyangar ce ta yi mata laifi. Kunsan Fanan a part ɗin Momma take yawan zama dan ta sami soyayyar Jaish, da farko ita ma zuciyarta ya fi karkata a irin halin mammiensu, amma zamanta da momma ya canzata izuwa mutumiyar kirki, kunga kuwa ko bata auri Jaish ba ai ta sami babban abu da zai iya zame mata makamin tsira duniya da lahira, wato halayyar kirki haɗe da ilimin addini kenan, ai kunga ta tsira ta kuma ci ribar zamanta da Momma ko?!. Tana barin part ɗin nasu ta wuce King part, kai tsaye ɗakin gyaran jikin su Aneesa da su Mama Haulat suke girka su a can ta nufa, jikinta dik a sake baiwar Allah. Ta sha madarar mamakin rashin samun Chuchu a ɗakin, Aneesa kawai ta samu, ta so tambayarta ina Chuchu and Auta sai kuma ta sami Aneesa tana murzar kuka, shanye tambayar ta yi a ranta tare da hayewa saman bed ɗin, cikin sanyin murya ta fara rarrashin Aneesa tana bata baki har da gaya mata wata bata auran mijin wata. Sam Aneesa taki kulata, dan ita kaɗai tasan me take ji a cikin zuciyar nan tata, tana san Rizwan za'a aura mata Jawad haba dole ta ji zafi. ==========Luv Bird========== A tsorace ta sake shi tare da komawa jefe ta tsaya haɗe da dawo da kallonta a kansa. Dik jikinta kerma yake yi alamar tsoro, a hankali take ta satar kallon su uncle Abbas da suka shigo cikin ɗakin. Allah sarki shi kuwa kasa iya riƙe kansa ya yi, wani irin jiri da ta ɗebesa ne sai da ya yi baya baya ya koma saman mattress ɗinsa ya zauna yana sauke numfashi a hankali hankali mai zafin zazzaɓi, dama saboda ganinta yasa ya samu kwarin gwiwar iya miƙewa. Dikkansu idanunsu a kan King da yake ta aikin binsu da dara daran idanun gadon nan nasu. Momma dake tsaye kusa da uncle Taheer ne ta ce. "Jannat me kike yi a nan kuma? Ya aka yi su Haulat suka barki kika fito daga wancan part ɗin?". Ai tana jin maganar momma tamkar wadda aka kwaɗawa guduma a tsakiyar kai, da karfi ta wage murya ta rushe masu da kuka babu kama hannun yaro. Kasa da kai Jawad ya yi yana tunanin abin da yakamata su yi, dan dai shi wlh ba zai iya hakura da ita ba!. Uncle Taheer ne ya ce. "Haba momma, wai ni ku meyasa kuke son saka yarana kuka ne? Yanzu dai ga shi kin sakata kuka". Harararsa ta yi tare da cewa. "Daga tambayarta zata rushe da kuka ka ce na sakata? To me na yi mata?". Uncle Taheer zai sake yin magana King ya ɗaga mashi hannu hakan ya haifar da nutsuwa tsit na gabaɗaya familyn dake biye da shi, sannan suka kara gyara tsayuwansu tsit alamar sun bi umarni. Uncle Abbas ne ya fara takawa ya ƙarisa cikin ɗakin kusa da Chuchu, hannunta ya riƙo a cikin nasa, cikin sigar rarrashi haɗe da zolaya kaɗan ya furta. "Menene kuma Jannat? Meyasameki kike kuka?". Kamar bai san kukan me take yi ba!. Faɗowa jikinsa ta yi tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, irin kukan nan ne wanda zuciyan mutum yana kusa, zaku ji har wani shessheƙa take yi kamar zata haɗiyi zuciyarta. Cikin kuka haɗe da ɗaga murya, da kyar ta iya fara faɗin. "Daddy wlh ni Yah Jawad nike so, shi ma ni yake so, dan Allah ka cewa dad kada ya rabamu, ni bana son Yah Rizwan". Yadda take magana sai ta baka tausayi, har wani shakewa voice ɗinta yake yi. King ne ya amsa mata da cewa. "Amma ba ke kika ce mana Rizwan kike so ba?". Sautin kukanta ta kara haɗe da faɗin. "Allah dad ni ban ce ba, ni Yah Jawad nike so". Momma ce ta murje idanu haɗe da shafa toka kamar bata san komai ba ta ce. "Da bakinki kika ce Rizwan kike so ba Jawad ba, dan haka zo ki wuce ki koma wajen su Haulat su cigaba da shiryaki anjima akwai taron dinner na musamman". Ƙanƙame uncle Abbas da karfi ta yi tana mai cigaba da kuka tana faɗin. "Daddy ni nasan zaka yarda da ni, tun da dad da momma basu yarda da ni ba shikenan, nasan kai zaka fahimceni, wlh ni ban ce ina son Yah Rizwan ba, dan Allah daddy kada ka bari dad ya kai ni wajen Yah Rizwan........" Bai bari ta ƙarisar da maganar ba ya ɗaura manuniyar yatsarsa a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru, dan yadda take maganar nan tsab zata iya haɗiyar zuciya ta mutu. "Ya isa haka Jannat, ina nan ai babu wanda zai rabaki da Jawad ɗinki, ba wanda zai kai ki wajen Rizwan, ki kwantar da hankalinki". Cewar uncle Abbas da yake aikin goge mata hawayen, sai dai yana gogesu wasu suna kara zubowa kamar ruwa ya buɗewa kansa hanya. Cikin zolaya momma ta ce. "A'a fa matar Rizwan ce kada ka kawo mana shubuha a cikin lamura". Kara ƙanƙame uncle Abbas ta yi tare da cewa. "Wlh ni daddy bana son shi, Yah Jawad nike so". Yadda ta yi maganar a ruɗe ne yasa uncle Abbas ya yi saurin katseta, dan ya lura su momma zasu ruɗar mashi da ita, sai ya yi maza ya ce. "Babu wanda zai kai ki wajen Rizwan, Jawad shi ne mijinki ba Rizwan ba". Jawad da tun da suka shigo kansa na'a kasa ne ya ɗago a miliyan yanzu, idanu ya zaro waje sosai, da kyar ya iya cewa. "Daddy me kake nufi?". Jinjina kai uncle Abbas ya yi kafin ya ce. "Kwarai kuwa abin da ka ji shi ne gaskiya, kai ne mijin Jannat ba Rizwan ba". A hanzarce ya miƙe tsaye, lokaci guda ya ji karfi ta zo mashi, ita ma Chuchu bata san lokacin da ta saki uncle Abbas ta dawo da kallonta a kan flowern nata ba. "Please dad don't play with my heart, ba wai na faɗi hakan dan raini bane, a'a, nasan ka saba yi mun wasanni kala kala, please don't make this as a part of joke to me, zan iya mutuwa idan ka yi hakan". Siririn murmushi uncle Abbas ya saki, a hankali ya kamo hannun Chuchu, ya matso ya riƙo hannun Jawad ɗaya. Ya buɗe tafin hannun Jawad ya ɗaura tafin hannun Chuchu a saman, cike da so da kauna ya fara magana kamar haka. "I knew that koda yaushe muna cikin wasa da kai, but this isn't a joke, Jannat is ur wife, gata nan kuma na miƙa maka ita amana, don't let her tears to come out dik da nasan ba zaka yi hakan ba". Ai mutuwar tsaye ya yi, ya kasa iya sake yin magana, wasu irin zafafan hawayen farinciki ne suka fara wanke fuskarsa, ya kasa fahimtar a wace iriyar duniya yake, gabaɗaya ya rasa me zai sake yi. King ne ya ce. "Eyeee my son ya girma ya yi aure, to me zaka yi mana kuka kuma?". Uncle Taheer ya karɓa ta cewa. "Ni yaya kada ku takurawa ɗana, ku je bari mu yi sirri da shi". Yana magana yana nufar Jawad. Mom ce ta ce. "To mu dai a bamu ɗiyarmu mu tafi da ita, sai ku yi ta sirrinku ɗin". Ta yi maganar tana miƙawa Chuchu hannu a kan ta zo. Kara ƙanƙameta Jawad ya yi, da kyar ya iya furta. "Please Momma ki ɗan bar mun ita a nan ko da na 10 mins ne kin ji? Long time bana tare da ita, and...........". Uncle Abbas ne ya katse shi da cewa. "Babu wanda zai ɗauke maka ita, ba 10 mins ba, even one hour take is your time today". Juyawa momma ta yi ta nufi waje tana faɗin. "Kuzo mu je kada Abbas ya koremu". King ne ya rufa mata baya a in da ya nufi fada dan ya bada umarnin sarkin hatsi ya fito da abinci a girka dayawa a kai gidajen marayu, sannan su tabbatar sun girka abincin da zai kai a ciyar da gidajen prison dake garin gabaɗaya, su ɗauki tsawon sati guda suna ciyar da gidan prison and gidanjen marayu, su rabawa talakawa buhuhhunan abinci da kuɗi makudai dik dan murnar bikin Jawad and Chuchu, sannan su ziyarci asibitoci dan duba waɗan da za'ayiwa aiki kuma babu kuɗin yi, su biya masu kuɗin aikin, wanna hurumin sarkin fada ne, shi zai jagoranci zuwa asibitoci ya tabbatar ya biya kuɗin aiki da magungunar marasa karfi. A wajen ɗaurin aure ma ya yi kyauta da kujerun makka sun kai 50, ya kuma yi kyauta da makuɗan kuɗaɗe ta hanyar raba check, anyi abubuwa da dama, King adalin sarki ne mai taimako sosai. Wai ina maganar waɗan da suka karo masu hari? Muje dai zuwa. Uncle Taheer ma fita waje ya yi ya bar uncle Abbas, Jawad and Chuchu kawai a cikin ɗakin. Zaunar da Jawad a bakin bed uncle Abbas ya yi, sannan ya ja hannun Chuchu suka zauna a tare, yana a tsakiyarsu ya fara yi masu nasiha mai ratsa zuciya. Shiru suka yi suna sauraronsa har ya dasa aya, sannan ne Jawad ya ce. "Daddy please tell me yadda aka yi Jannat ta zama mallakina bayan ka ce mun Yah Rizwan dad ya bamawa?'. Ajiyar zuciya uncle Abbas ya sauke, nan take yanayin face ɗinsa ya canza, alamar ya shiga damuwa, hakan yasa zuciyar Jawad ta kara karaya, dan bai san dalilin sauyawar face ɗin daddyn nasu ba. Sun kasa kunne suna jiran jin me zai ce da su, ita kanta Chuchu ta fahimci uncle Abbas ya shiga damuwa a wanna tambaya da Jawad ya yi mashi. "Rizwan ne ya sami dad ɗinku ɗazun da safe ya sanar da shi a ɗaura aurenka da Jannat ba da shi ba". Zaro idanunsu a tare suka yi, they will not expect that at all, so they shocked. "Dama Yah Rizwan yasan ina son Jannat ne ko dai kai ka gaya mashi daddy?". Jawad ya yi tambayar cikin ƙaguwa da san jin an warware masu komai dallah dallah!. Girgiza kai uncle Abbas ya yi, sannan ya ɗaura da cewa. "Ko ɗaya babu wanda ya gayawa Rizwan kana son Jannat, shi da kansa ya san da hakan?". Sam Jawad bai san lokacin da ya furta. "How and when?". Ba. "Lokacin da ya sanar da dad ɗinku ya sadaukar da soyayyarsa wa kai sai ya wuce room ɗinsa ya je ya fara haɗa kayansa zai koma Dubai, a time ɗin dad ɗinku ya kirani a waya ya ce dik in da nike na zo yana son ganina". "Ban ɓata lokaci wajen zuwa in da yake ba, na same shi a room ɗinsa, I was so surprised time da ya gaya mun furucin Rizwan a kanku, ban iya haɗiye abin a raina ba sai da na bi Rizwan ɗakinsa dan na ji meyasa ya yi hakan". "A lokacin da na shiga ɗakin nasa ya gama shirya echolac ɗinsa domin tafiya, ni na dakatar da shi na kuma umarcesa da ya zauna mu yi magana. Bai yi mun musu ba, ya zauna. Da kallo ɗaya na yi mashi na fahimci ya sha kuka sosai, dan ga idanunsa har sun kumbura, ban nuna mashi kamar na gane yana cikin damuwa or ya sha kuka ba, na yi amfani da fifikon dake tsakaninmu na tambaye shi cikin hikima". ========================😥 "Rizwan meyasa kace ka barwa ɗan uwanka Jannat ya aura?". "Babu komai daddy, naga hakan shi ne yafi dacewa da ni ne!". Ya yi maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa, baya san su haɗa ido da uncle Abbas, dan baya san ya gane yana cikin tashin hankalin da ba zai iya ɗauka ba a dalilin sadaukar da soyayyar tasa da ya yi. "Ko zaka ɓoyewa kowa Rizwan bai kamata ni ka ɓoye mun na, shin ka manta nine daddynku ne?". Girgi kai ya yi alamar a'a bai manta ba. "To ka gaya mun meyasa ka sadaukar da soyayyarka ga Jawad? Shin ya ce maka yana son Jannat ne?". Girgiza kai ya sake yi a karo na biyu, kamar zai rushe da kuka ya ce. "Babu wanda ya gaya mun Jawad yana san Jannat a baya, da idanuna naga hakan, sannan kuma Auta ta tabbatar mun da hakan, har ɗakin nan ta zo ta gaya mun cewa Jawad yana san Jannat tun tana ƙarama, ta nuna mun video da hotunansu a wayarta a lokacin da suke soyayya, na kuma kara bincikawa na tabbatar da hakan ne, a binciken nawa ne ma na gane rashin lafiyan ɗan uwana nine sila, nine na yi mashi shamaki da abar kaunarsa yasa ya faɗi ciwo........." Yaushe Auta ta gayawa Rizwan soyayyar dake tsakanin Jawad and Chuchu baiwar Allah? Allah sarki kila tin kafin ta mutu ta gina masu soyayyarsu dan su cigaba da kasakcewa da juna, ita kuma nata soyayyan shi ne ya zama ajalinta!!. Cikin in ina ya idasa maganar sakamakon sarkewa da muryarsa take yi, ga wasu zafafan hawayen da suka cika mashi idanu, Allah sarki har wani zazzaɓi mai karfi yake ji tana ƙoƙarin kayar da shi. Dik taurin zuciya namiji soyayya tana sanya shi ladab, to ga dai Rizwan da ruwan hawaye saboda rasa Jannat da ya yi!. Tun da ya fara magana tsananin tausayinsa ya kara dabaibaye zuciyar uncle Abbas, yau da yana da yadda zai yi ya raba Jannat gida biyu ya bawa ƴaƴan nasa da ya yi. Matsowa ya yi ya rungumi Rizwan, zuciyarsa tana yi mashi zafi ya hau rarrashinsa a kan ya jure In Sha Allah zai samu wadda ta fi Jannat. Murya a sarkafe ya amsa da. "Ba dai wadda ta di Jannat ba daddy, nasan ba zan samu madadinta bama bare wadda ta fita, Jannat ta dabance a zuciyata daddy, ka tayani da addu'ar Allah ya sassauta mun sonta a rai'na". Tamkar ƙaramin yaro yake kuka yana magana. Hakika uncle Abbas ya fahimci irin tsananin sonta da Rizwan yake yi, abin ya wuci tunaninku, yanzu tsoronsa ɗaya shi ne kada wani abin ya samu first love ɗin nasa, dan a gaskiya soyayyar da Rizwan yake yi mata hakura da ita zai iya cutar da shi matuƙa. "Babu abin da ya fi karfin Allah Rizwan, In Sha Allah zaka samu fiye da Jannat, ina tayaka addu'a a kan hakan, Allah Ubangiji ya yi maka albarka da sauyi na alkhari". Sam soyayya ta rufe mashi ido, yaki yarda zai iya samun wadda ta fi Chuchu, gani yake yi ita ce karshe, daga karshe dai uncle Abbas shiru ya yi ya rabu da shi a mazaunin ba zai taɓa samun madadinta ba!. Sosai Rizwan ya sha kukan da bai taɓa yin irinsa ba tun bayan rasuwar mahaifiyarsu, yau ya kara ɗanɗanar ɗaci a karo na biyu a rayuwansa, da kyar ya iya sarrafa hawayensa suka dakata da zuba, sosai zuciyar uncle Abbas ta karaya, yana ganin kamar tabbas wani abin zai faru da Rizwan, dan irin wanna kuka kai akwai tsorata mutum. Sun ɗauki lokaci a wannan ɗaki, daga karshe uncle Abbas ya buƙaci da ya tsaya ayi ɗaurin aure da shi kafin ya tafi. Da farko yaki yarda, ya ce. "Daddy zuciyata ba zata iya ɗaukar ganin auren Jannat da ɗan uwana ba, Please ka barni in tafi kawai ko zan samu sauki cikin rai'na, burina kawai in bar kasar nan". "A'a Rizwan, babu wani abin da zai sami zuciyarka, Allah yana tare da kai, please ka tsaya ayi wannan ɗaurin aure da kai". Baya iya yi wa daddyn nasa musu, dan haka ya hakura ya tsaya ɗaurin auren, shiyasa a wajen ɗaurin auren kowa ya gansa a wani sake sukuku haka kamar dai wanda baya cikin hayyacinsa, dayawan mutane suna tunanin saboda rashin lafiyan ɗan uwansa ne. A lokacin da uncle Abbas ya kammala gaya masu yadda aka yi suka mallaki juna, gabaɗayansu hawaye ya gama wanke fuskokinsu, jikinsu ya yi matuƙar sanyi, sun ji sun karaya sosai, tsananin tausayin Rizwan ya mamaye duƙatansu!. Da kyar Jawad ya iya cewa. "Daddy ina Yah Rizwan ɗin yake yanzu?". Miƙewa tsaye uncle Abbas ya yi yana faɗin. "Rizwan ya wuce Dubai tun bayan barinsa wajen ɗaurin aure, ina zargin da zazzaɓi a jikinsa ma ya tafi". A ɗan razane Chuchu ta ce. "Zazzaɓi kuma daddy?". Kai ya gyaɗa masu tare da nufar hanyar fita dan ya basu waje su ga juna a matsayin ma'aurata yanzu. Da ido suka bishi har ya fice, kamar abin haɗin baki suka dawo da kallonsu a kan juna a tare, dikkansu fuska jaga jaga da hawaye. Hawayen farinciki, na tausayin Rizwan da kuma na ƙoƙarin rabasu da akayi. "Jannat kin ji sadaukarwar da Yah Rizwan ya yi mana ko? Kin ji ƙoƙarin da Auta ta yi a kanmu dan kada a rabamu ko? Ashe ita ta je ta gayawa Yah Rizwan muna san juma?"? Jinjina mashi kai ta yi tana cigaba da hawaye. "Miƙo mun wayata bari in kira Yah Rizwan ɗin, in mun gama waya sai ki kira mun Autaa cikin gida". Allah sarki anata shagalin biki babu wanda ya lura da auta bata a gidan, baki sun yi yawa kowa zai zaci tana ɓangaren ɗan uwansa ne, sai dai kuma, kowa yasan bata rabuwa da Chuchu, so idan aka yi wa Chuchu kallon farko basa tare, aka sake ganinta na biyu basa a tare, a karo na uku dole a tambaya ina take?. Miƙewa ta yi a hanzarce ta zagaya ta ɗayan gefen bed ɗin ta ɗauko mashi wayar tasa. Zuwa ta yi gabansa ta miƙa mashi tana faɗin. "Ga shi nan". A maimakon ya karɓi wayar sai ya janyo hannunta ta faɗa jikinsa. A tare suka sauke sanyayyar ajiyar zuciya. Hannunta dake rike da wayar ya riko, kamar mai raɗa ya ce. "Wannan flowers ɗin sun yi kyau sosai, wadda ta zana maki ta iya sosai". A ɗan shagwaɓe ta amsa da. "Ai saboda kai aka yi". Ɗan karkata kansa kaɗan ya yi tare da ɗan leƙo face ɗinta. "Anya kuwa? Dan Yah Rizwan dai aka yi, kuma nasan sai da aka kai ruwa rana dake kafin ki aminta ayi shi ko?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "Da baki bari anyi maki ba da kin yi mun asarar kyau kenan, kin ga yadda kika yi kyau kuwa?". Ɗaga kai ta yi suna kallon juna, hawayen fuskarta har ya fara bushewa, a ɗan shagwaɓe ta ce. "Da gaske na yi kyau?". Kai ya gyaɗa mata alamar e, yana yi mata wani irin mayen kallo mai wuyar fassaruwa. "To shikenan yanzu kam tin da kai ne mijina bari in je mama Haulat ta kara gyara mun jikina". Bai san sadda ya ɗan saki murmushi ba a lokacin da ta yi wannan magana. Ya ji sanyi a ransa har da ajiyar zuciya. Kamar mai raɗa ya ce. "Da gaske nine mijinki yanzu? Ke mallakina ce kenan?". Kai ta gyaɗa idanunta sarƙafe cikin nasa babu ko kyaftawa, ko kunyarsa bata ji ba. Shi ma babu ko kunya ya matso dab da ita kamar zai sumbaci lips ɗinta, har ta zaro mashi idanu tana kallonsa, sai kuma ya karɓi wayarsa dake hannunta ya ɗan ja baya yana kallonta. Number Rizwan ya shigar dan ya kira, ta kafe da kallonsa kamar nace zan kwace mata shi. Na'urar ce ta sanar masu da cewa number wayar Rizwan a kashe, sosai ya ji babu daɗi, sai ya ji ya kara karaya, nan take ya kara jin ya shiga damuwa matuƙa. Ganin ya shiga damuwa yasa ta kai hannu ta ɗan shafa kumatunsa. "Yah Jawad ka yi hakuri nasan yana hanya ne, idan ya sauka zai kunna wayarsa". Dawo da kallonsa sosai a kanta ya yi, tin da ta fara magana yake kallon lips ɗinta har ta kai aya. Ɗan rankwafo kanta kaɗan ya yi. "Jannat ina kaunar Yah Rizwan, ba zan iya jure ganinsa a cikin damuwa ba, ban san ya zan yi da rai'na ba". Cikin tsananin damuwa ya yi maganar. Hannunsa ta ɗan riko a cikin nata, can kasa cikin kasalalliyar murya ya ce........... Idan kunga tsayin page ɗinku yana raguwa to rashin comment ɗinku ne sila.🥱 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Hannunsa ya ɗan riko a cikin nasa, can kasa cikin kasalalliyar murya ya ce. "A'a Jannat, na tabbata damuwa ba zata bari ya kunna wayarsa ba, lallai ina san tafiya Dubai a yau". Zaro idanunta waje sosai ta yi, kamar zata yi kuka ta ce. "Dan Allah Yah Jawad ka yi hakuri, babu abin da zai same shi, kuma In Sha Allah anjima yana sauka daga jirgi zamu samu wayarsa a buɗe". Tana magana tana share mashi hawayen dake bin ƙuncinsa, ya shiga damuwa sosai na jin halin da ɗan uwansa yake a ciki. Shiru bai sake yin magana ba, dan shi kaɗai yasan kalar raɗaɗin dake a cikin ransa. ==========================💘 Sosai King ya yi mamakin jin busoshin yaki da ake ta famar busawa a cikin kingdom ɗin, sai dai bai tashi hankalinsa ba, saboda shi ɗin dakakken namiji ne wanda babu tsoro ko miskala zarratin a cikin jininsa. Kai tsaye fada ya nufa domin yasan me yake gudana ake ta buga mashi bososhin yaki har haka. A nan ya isko commander Zafar da sauran wakilan fada gabaɗaya, cikin takun jarumta ya ƙarisa saman kujerar mulkinsa, tin da ya shigo kuma warriors guda biyu suka take mashi baya har izuwa wajen kujerar tasa. Miƙewa tsaye daga saman kujerunsu su commander Zafar suka yi domin bashi girma, har sai da ya zauna saman tasa kujerar sannan suma suka zauna. Dik sun kasa kunne suna jiran umarninsa da abin da zai faɗa. Shi ma idanu ya bisu da shi har na tsawon good 5 mins, kun san halinsa akwai jin kai da izzar sarauta, su kuma suna tsoron fara yin magana hukunci ya hau kansu a kan bai basu iznin ba. Sai da ya cika ya hantse sannan ya ɗan yi gyaran murya cikin nutsuwa, cike da izza ya fara ƙoƙarin buɗe bakinsa domin ya yi magana. Wani bujumin warriors ne ya shigo cikin fadan bisa umarnin salama, sanye yake cikin kayansa na mayaka, dik da cikin hular kayan yaki yake zaka iya fahimtar face ɗinsa babu alama sassauci ko annuri. Shigowarsa ya dakatar da King daga maganar da yake da niyar yi, suka zubawa wanna warriors ɗin idanu. Takowa ya yi cike da jarumta har izuwa tsakiyar fada, sannan ya ɗan risinar da kai wanda kun san wanna dole ce a gidan sarauta, girmamawa ce ga sarki wanda ya rataya a wuyoyinsu dole!. Cike da girmamawa ya ce. "Ranka ya daɗe ina neman izinin yin magana". Muryarsa akwai kaifi a cikinta, maganarsa akwai zarra a cikinta, yanayinsa akwai tsantsar jarumtaka matuƙa, tsayayyen namiji sosai, ga tsawo da cikar halitta matuƙa. Cikin kwararriyar larabcinsa ya yi maganar. King ya ɗauki almost 3 mins kafin ya ɗan motsa lips ɗinsa, cike da izza ya bashi izinin yin magana. Ba tare da ɓata lokaci ba wannan warriors ɗin ya kyankyasa mashi cewa akwai baki a wajen babban gate na Kingdom ɗin wanda suke da buƙatar a basu izinin shigowa dan su yi magana da shi. Nan ma sai da King ya ɗauki ƴan mintoci kafin ya buƙaci sanin wasu irin baki ne?. Kamar ba mutun ne yane magana ba wanna warriors ɗin ya amsa da. "Ga dikkan alamu wani sarki ne da tawagarsa, bamu da masaniyar daga ina suke, amma ga dikkan alamu a kan hanya suke". "Sune silar buga waɗan nan busoshin yakin?". King ya jefa mashi tambaya cikin nutsuwarsa. Cikin dakiya ya amsa da. "Sune ranka ya daɗe". Kallan commander Zafar King ya yi kafin ya dawo da kallonsa a kan sarkin fada da kuma sarkin gida da suke binsa da kallo. "Commander ina san sanin su wanene waɗan nan cikin ƙankanin lokaci". Ya kai karshen maganar tare da ɗagawa wanna warriors ɗin hannu alamar shi kuma zai iya tafiya ba tare da King ɗin ya sake waiwayarsa ba. Cikin zafa ya juya yana taku manyan maza ya nufi waje. Miƙewa tsaye commander Zafar ya yi tare da ɗan risinar da kai alamar ya karɓi umarni, sannan ya nufi waje, sarkin gida ne ya take mashi baya da kara karfafa ida nufin King. =========HOORAIN=========💘 Zaune suke cikin wannan small garden in da Auta ta kamasu suna hiranta ranar da daddare, shi da Ansar da Anwar, hannunsa na riƙe da wayar Auta while tasa wayar tana a cikin aljihunsa, ya kurawa wayar kallo babu ko kyaftawa, Ansar da Anwar suna ta hira a kan bikin da ake gudanarwa, ba'a taɓa biki a cikin gidan ba bayan na uncle Abbas da ya zamana shi ne na karshe tsawon shekaru, daga King har uncle Abbas babu wanda ya taɓa aurar da ɗa or ƴa sai yau, shiyasa murnar ta zarce tinanin mai tinani. Hotonta ya zubawa idanu yana ta kallo, tana tsaye kusa da wasu flowers dake cikin lambun daddynsu, hannunta ɗauke da Felix ɗinta tana shafe lallausan gashin jikinsa, murmushin dake kan fuskarta ya yi matuƙar kara tsatso tsantsar kyan da Allah ya zuba mata, dimples ɗinta dikka sun lotsa, yarinya mai kyau da haiba game da kamala, ga farinjini da sace zuƙatan mutane da murmushi ɗaya kawai!. Tana sanye da alkyabbarta har kasa launin golden and white. Ya luluƙa duniyar tinanin da shi kaɗai ya barwa kansa sanin me yake tinawa, dik da ba'a iya ganin face ɗinsa alamu sun nuna yana cikin kunci da bakinciki game da damuwa, kwata kwata baya tare da su Anwar. Nisawa ya yi a lokacin da ya ji saukar hannun Ansar a saman shoulder ɗinsa. "Mekake tunani ne angon gimbiya?". Cewar Ansar. Ɗan girgiza kansa kawai ya yi alamar babu komai ba tare da ya yi yunƙurin yin magana ba. Anwar ne ya ce. "Our Hero ka kwantar da hankalinka, In Sha Allah ba za'a hanaka gimbiya ba, da izinin Allah ita ɗin rabonka ce". Ansar ne ya amsa da. "Gaskiya ya cika sanyawa kansa pressure dayawa, gimbiya fa ita ta nuna tana sanka, kaga kuwa ina da tabbacin In Sha Allah babu wanda zai yi maka shamaki a tsakaninku, ko King sai ya sarara a wannan al'amari". Shi dai ko uppan bai da niyar cewa, hasali ma kansa a ƙasa bai da niyar ɗagowa bare asa ran zai yi magana. "Kai ma dai Ansar ka faɗa, dik ya bi ya takura kansa kamar...........". Ɗaga mashi hannu Ansar ya yi alamar ya yi shiru, dan ya lura da gaske Hoorain yake a cikin damuwa ba kamar yadda suka saba ganinsa a ɗan siririn damuwa a kan Zunaira ba, yau abin na daban ne, gabaɗaya yanayinsa ya canza, sam baya cikin sukuninsa, yana nan a wani birkice haka. Ni kuwa nace rai wasa ne? Ka ɗauki ran makiyinka ma ya ka kare da faɗuwar gaba da fargaba bare kuma ka ɗauki ran wadda ta fi kaunarka sama da kowa a duniya?! Ai dole nema ka birkice, bama kaga komai ba tukun nan, sai gaba idan abin ya yi tsamari, soyayya ai ba karya bace, aya sukutum Allah ya saukar saboda soyayya, A cikin Al-Qur’ani mai girma, Allah ya yi magana a kan soyayya a wurare da dama. Daya daga cikin shahararrun wurare da Allah ya yi magana a kan soyayya shi ne a cikin Suratul Rum, aya ta 21 Wannan aya tana nuna cewa soyayya da tausayi suna daga cikin ni’imomin Allah, kuma an sanya su domin mutane su more zaman lafiya da juna a rayuwar aure, so kunga kuwa soyayya ba karya bace ba kuma abin wasa bace, mukaddari ne daga Allah. "Hoorain lafiya kake kuwa? Meyake damunka?". Ansar ne ya jefa mashi wanna tambaya. Sun shiga damuwa matuƙa cikin kankanin lokaci na ganinsa a cikin mawuyacin hali. Bai amsasu ba, sai ma kara risinar da kansa kasa da ya yi haɗe da kashe hasken screen ɗin wayar tata yana jan dogon numfashi. Anwar ne da ƙaguwa da san jin me yake damun abokin nasu ya cika mashi ciki ya sake jefa mashi tambayar menene yake damunsa a karo na biyu. Ɗan siririn tsaki ya ja tare da miƙewa cikin zafa ya nufi barin wajen, dan kwata kwata baya san jin magana a kusa da shi, dik wanda zai yi mashi magana muryar Zunaira yake ji a tattare da shi, koma wannene, hakan ba karamun ɗaga mashi hankali yake kara yi ba. Da ido suka bishi har ya kurewa ganinsu, a tare suka dawo da kallonsu a kan juna suna mamakin birkicewar da ya yi har haka, basu taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayi ba!. =========================💘 Cikin ƙanƙanin lokaci commander Zafar ya dawowa King da labarin sarkin Daular Qahtan wato Qahtaniyawa ne ya zo, kunsan manya manyan labarawa sun kasu kabila kashi uku ne, nasan dayawa baku taɓa sanin larabawa mabanbanta bane ko? To gaskiya mabanbanta ne, amma manyan kabilunsu sun kasu kashi uku ne, babbar kabila mafi ɗaukaka a duniya cikin larabawa sune ƙuraishawan Modarawa, kabilun modarawa daga cikin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) ya fito, shiyasa ta kasance ma ɗaukakiyar kabila, daga ƙuraishawan Modarawa sai kuma Qahtan wato Qahtaniyawa, su ne na biyu, sai kuma larabawan kangi, su ne kabilun da suka fi kowanne shahara da ɗaukaka a cikin larabawa. Sosai King Zuhair ya fusata jin cewa sarkin Daular Qahtaniyawa ne ya ziyarcesu, cikin ɓacin rai haɗe da kakkausan murya ya umarci commander Zafar da a je ya yakesu yanzun nan ba tare da ɗaga kafa ba!. To me dalili?. Wanna furuci tasa ta yi dai'dai da shigowar aunty miemie cikin fada, ta dan tsorata jin mahaifin nata yana magana da kakkausar murya haka, dan haka sai ta zama mai risinar da kai game da sanyaya kalamanta da kuma tausasasu a wajen yi mashi magana. Cikin girmamawa ta tambayesa me yake faruwa a dai'dai lokacin da take zaka saman kujerar kusa da shi!. Bai so sanar da ita abin da yake faruwa ba saboda sanin halinta da ya yi, amma bashi da biyunta a kaf kingdom of power, da ita suke yin shawara, yana kaunarta ya kuma san ba ta kawo shawarar banza, dan haka sai ya sanar da ita ga abin da yake faruwa. Shiru ta ɗan yi na ƴan mintuna tana nazari, akwaita da hangen nesa, shiyasa irin su King Zuhair masu saurin fusata suna buƙatar irinta a gefensu dan in sun fusata ta dakatar da su daga ɗaukar hukunci cikin fushi, babu wanda ya fi karfin kuskure da kuma ayi mashi gyara!!. "Daddyna Allah ya kara maka tsawon rai da tsawon kwana, nasan yardar da ka bani yasa ka sanyani a sahun gaba wajen yin shawara domin mu tantance abin da yake dai'dai da kuma ba dai'dai ba, yardar da ka mun yasa nake jin kaina a matsayin mace zaƙwaƙura mai yin abin da ya dace, dan yardarka ga mutum ba ƙaramin abu bane, sai mutun ya cika mai sifofin kamala zai samu wannan matsayi, ina alfahari da kai kuma ina farincikin kasancewa yar cikinka, bana fatan rana ɗaya da zata zo na saɓa maganarka komai kankantarta, hakika da dikkanin ƴaƴan duniya zasu samu uba irinka to tabbas da kowa ba zai so matsawa kusa da mahaifinsa ko nan da can ba, kai ne bangona kuma farincikina, abin alfaharina sanyin idaniyata ni da ƴan uwana, duniyarmu gabaɗaya, ɓacin ranka dai'dai yake da rugujewar Daular Qahtaniyawa daddyna, meyasa zaka ɓata ranka a kan waɗan da kasan already bayinmu ne?"................. Ta kare maganar haɗe da jefa mashi tambayar tana kallonsa. Tun da ta fara magana ransa ya fara sanyaya, yana shiga tsananin farinciki a dik lokacin da ƴaƴansa suka furta suna alfahari da shi, farincikinsa ba mai misiltuwa bane, hakan yasa ransa ta wani irin sanyaya sosai. Fahimtar ya yi farinciki da jin kalamanta yasa ta ɗaura da cewa. "Daddyn yin yaki a halin yanzu da muke cikin nan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, saboda kaga muna da baki daga ƙasashe daban daban, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya rasa rayukansu, ina neman alfarmar da a janye batun yakin nan ayi masu lamauni, nasan kai mai afuwa ne mai kuma tausayin jama'arsa ne". Sosai su commander Zafar suka ji daɗin furucinta, sun kara ganin girmanta, dama can suna tsananin kaunarta saboda sanin yakamatanta suna kuma girmamata, bata da san kai, hukunci cikin adalci take yankewa. Cike da tsantsar so da kaunarta ya ce. "To Raeesa me kike san na yi masu a yanzu kenan? Kin dai san babu wanda na tsana a duniya biyun King Abdul Mutallab da kuma King Al Mustapha". Nisawa ta yi kafin ta amsa da. "Na sani daddyna, kuma kana kan dai'dai, amma idan ba damuwa ni ka bani izinin in je in yi magana da shi". "Kina ganin hakan zai sakaki farinciki ya kuma biya buƙatarki?". Jinjina mashi kai ta yi tare da amsawa da e. Dawo da kallonsa a kan commander Zafar ya yi tare da bashi umarnin da ya yi mata rakiya haɗe da wasu zaƙwaƙuran warriors ɗin su take mashi baya, kada su bari komai ƙanƙantar wani abin ya taɓata. Cikin girmamawa suka risinar da kai haɗe da karɓar umarni. Miƙewa tsaye ta yi tare da karisowa gaban King, ta duka a saman gwiwowinta cikin ladabi da biyayya ta bayyana godiyarta a garesa haɗe da nuna mashi ta yi farinciki na sauraron korafinta da ya yi ya kuma yi amfani da shawarinta. Hannunsa ya ɗaura saman kanta ya fara kwararo mata madarar albarka. Su commander sai tayata amsawa suke yi da amin ya Allah. Tsawon 5 mins tana tsugunne a gabansa har sai da ya gama zuba mata addu'oin nasa ne ya bata umarnin ta tashi su je. Sumbata a goshi ta ɗan miƙe ta kai mashi kafin ta miƙe tsaye gabaɗaya, ta yi gaba su commander Zafar suka rufa mata baya, alkyabbarta sai jan kasa yake yi. ===========================💘 Tin daga nesa ta hango sarkin Qahtaniyawa dake a saman koshashiyar dokinsa, kai daga ganinsa kasan ya ji izza da isa malam, dukiya ta yi mubaya'a, kayan adan da aka kawata dokinsa da yake kai kawai ba karamar dukiya bace, babban sarki ne mai isa da izza, sai dai a karkashin Daular kingdom of power suke, sun taɓa bijirewa umarni da dokikin King Zuhair har ya yakesu. Warriors sun kai 20 zaƙwaƙuran sadaukai ne suka take mata baya, tana a tsakiya, commander Zafar yana gefen damanta, sarkin Fada yana a gefen hagunta, kai daga ganin yadda take taku kasan jinin Modarawa ne yake gudana a cikin jikinta, ga jinin mulki dake ratsa jikinta, ai kunsan abin ba'a magana. Ganinta yasa King Al-Mustapah ya buƙaci sauka daga saman dokinsa, dan ko baa gaya mashi ba yasan ita ta wakilci King Zuhair, dama yasan da wuya King Zuhair ya yarda ya basu fuskar da zasu iya shiga cikin kingdom of power ɗin ko su sami damar yin magana da shi kawai dai sun gwada ne dama, kun san ance a rashin ta yi ake barin arha. King Al-Mustapah yana sauka daga saman dokinsa dikka sauran ƴan rakiyansa ma suka yi kasa, suka sauka. Step biyar tsakaninta da shi ta dakata a wajen tana kallonsa from up to down. Cikin girmamawa ya yi mata barka da zuwa. A maimakon ta amsa sai ta yi shiru na tsawon good 2 mins tana kare masu kallo. Har sun fidda ran zata tankasu, har sun fara tunanin ko dai King Zuhair bai bata damar ta yi magana da su bane, ko kuma wani abin ake shirya masu. Sun luluƙa duniyar tunani kamar daga sama suka tsinkayo voice ɗinta tana faɗin. "Menene ya kawoku nan?". A kanta King Al-Mustapah ya tsayar da kallonsa, tsohon zumar soyayyarta ce ta taso mashi, ya so Aunty MieMie kamar hauka, amma King ya hanashi ita sakamakon tsohuwar mummunar gaba dake a tsakaninsu tun iyaye da kakani, kada ku manta jinin Modarawa basa yafiya kuma basa matuwa, in baku gaji da faɗa ba ko shekara miliyoyin za'ayi ana yi ba zasu gaji ba. Dalilin haukar san ta da yake yi ne ma yasa yake bata girma kamar yadda yake bawa mahaifinta King Zuhair. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• "Dama mun zo ne muna masu miƙa wuya haɗe da mubaya'a kamar yadda muka buƙata a baya mai girma King ya ki yarda, bamu gaji ba a wannan karon ma mun sake dawowa da kokan bararmu a garesa, ki taimaka ki sanar da shi mun durkusa a kan gwiwonmu muna masu mubaya'a da kaskantar da kai, ya yi hakuri mu koma zama kamar da tsawon shekaru da suka shuɗe, wanna gaba na iyayenmu ne ba namu ba..............." Ɗaga mashi hannu ɗaya ta yi alamar ya yi mata shiru, hakan ne ya katse maganar da yake yi. Tin da ya fara yin magana ta fahimci akwai zallar munafurci da tuggu haɗe da sharri da zallar karya a cikin kalamansa, a yanayin karantarsa da ta yi ta fahimci shigo shigo ba zurfi yake san yi masu, so ta gane komai, shekara nawa tana tare da waɗan da suka fishi sanin duniya, zata iya cewa dik duniya bata taɓa ganin bakin bakiri irin King Abdul Mutallab ba, shi ma bai sha ta daɗi a hannunsu ba bare King Al-Mustapah ba. Cike da isa da izza ta ce. "Umarni nike baku ba shawara ba! Ku yi gaggawar barin nan tin kafin rai'na ya ɓaci, ka dai san ba zamu karɓi wani risinawarku ba, dan bamu da buƙata!". Zai sake yin magana ta ɗaga mashi hannun alamar bata da buƙatar sake jin ko uppan daga gare shi, daga haka ta ce. "Commander nan da mintuna 5 idan basu bar nan ba ku yi masu zobe ku yakesu!". Ta yi maganar a dake ba tare da ta kalli in da commander yake ba, yana kai karshen maganar kuma ta juya cikin zafa ta bar wajen. Har ta ɗan yi nisa a tafiyar tata sai kuma ta juyo, cikin kakkausar murya ta ce. "Babu sulhu a tsakaninmu da ku har abada, ayi ta yaki daga nan har illah Masha Allah, muddin ba zaku daina zalinci ba, mu kuma ba zamu ɗaga kafa ba, babu wani sauran azzalumi da zamu bari ya sarara!". Tana kai karshen maganar ta wuce abinta, a hanzarce warrios goma suka rufa mata baya, warrios goma kuma suka tsaya a tare da commander Zafar dan su kori su King Al-Mustapah!. ========After some hour=========💘 King Al-Mustapah ya juya ya koma Daularsa, su commander an dawo cikin gida dan cigaba da shagalin biki, hankalin kowa a kwance, sai kaiwa da komawa ake yi, ana ta hidima, abubuwa sun kara tsananta, haɗuwa iya haɗuwa. •••••••••••••••••••••••••••••••••••💘🔥 Waje ya yi waje, cikin katafaren hall dake cikin kingdom ɗin aka shirya wanna gagarumim taro domin dinner bikin, haɗuwa iya haɗuwa wanna waje ya yi, an zuba sabin furniture da komai da komai, zayyana maku ƙawatuwar wannan waje ma ai ba zai yi wu ba, dan ya zarce tinaninku. An ƙawata kujerar zaman amarya da ango sosai, gabaɗaya cikin hall ɗin matasan ƴaƴan manya manyan sarakuna da shuwagabani masu ji da kansu ne a ciki, iyaye basu halarci wajen ba, saboda abu ne na yara matasa, Auntynsu Jawad ita ce a gaba wajen kawatawa gimbiya Chuchu kwalliya, har yanzu bata san cewa Jawad aka aurawa Chuchu ba Rizwan ba, King ya bar abin sai bayan komai ya lafa za'a yi maganar, iya momma ce kawai ta san a matansa ma. Abu fa ya yi abu, sai dai ango Jawad dik a susuce yake, bashi da kuzari ko kaɗan, hankalinsa dik ya karkata a kan Rizwan yanzu, amma ba karya kwalliyarsa da ya sha ta yi kyau over, dik da akwai ɗan rama a tattare da shi, hakan bai hana haiba da kalama tasa ta bayyana ba, ya fito a jikin Akka ɗinsa, zallar madarar kyau. Sai shirye shirye ake yi da misalin karfe 11 na dare za'a fara gudanar da dinner ɗin. To bari mu garzaya wani part kafin lokacin yin dinner ya cika sai mu dawo dan ganin yadda komai zai gudana. =======BLACK 🌑 WORLD🪐======== Today part in this Black world is the best part amount the previous part's!! I really like this part more than your expectations 💘 because I really like islam, am very very proud to be a Muslim💘 a kullum burina in ga ina magana a kan addinina tare da manya manyan hujoji, ina faɗar niimomin addinina da fifikonsa da kowani addini, kai ba zan iya gaya maku yadda nike kaunar musulmai da musulci ba wlh, Allah dai ka kara mana soyayyar Manzon Allah, amma muna alfahari da musulunci kam ba karya!!. 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 Karfe 7 dai'dai Ronnie suka dawo daga church, yana san zuwa ya ga Sweetie amma ya fi san ya kai ga yayansa a farko, dan haka a bakin kofar room ɗinsa suka rabu da Floris, ita ta shiga ciki shi kuma ya wuce part na Black Tiger. Ya ɗauki a kallah 30 mins a ciki, can ya fito sanye da hoodies masu balai'n tsada a jikinsa, ya yi matuƙar kyau, da alama a part ɗin ya yi wanka, da yake yana da hasken fata sosai sai black color tana bala'in yi mashi kyau launin kayan kenan. Dab zai shiga room ɗinsa ya tsinkayo muryar Floris da Sweetie suna magana, ɗan dakatawa ya yi dan ya ji me suke faɗa. "Kina nufin kin san Jesus?". Cewar Floris. Ta yi maganar mamaki sosai a saman face ɗinta, dan suna dawowa daga church ta yi saurin karisawa wajen Sweetie, a shirmenta wai bari ta yi saurin fara koyawa Sweetie addininta dan ta rinjayeta, shi ne da ta fara magana a kan Annabi Isa (A.S) sai Sweetie ta ce mata ta san shi ai, abin ya bata mamaki matuƙa. Sai ta samu wajen a bakin bed ta zauna dan ta ji daga ina Sweetie ta san Jesus?!. Jinjina kai Sweetie ta yi tare da amsa mata da. "I think mu musulmai ma mun fi ku sanin wanene shi! Kai bama i think ba, mun fi ku sanin wanene shi menene tarihinsa na hakika!". Sanya password Ronnie ya yi a kofar ya buɗe, dan yana san ya ji hujjojin da Sweetie take da shi da har take magana with full confidence a kan addinin nan nata yana san kureta. A tare suka dawo da kallonsu a kansa tin da ya shigo, zama ya yi saman egg-s chair dake fuskantarsu, ya harɗe hannaye a saman kirjinsa yana binsu da kallo. "Beb ka ji Sweetie wai ta san Jesus fa!". Cewar Floris da bata yarda Sweetie ta san Annabi Isa or ta fita saninsa ba!. Kallonsa a kan Sweetie da ita ma take kallonsa. "A ina kika san Jesus bayan ba addinin nin mu kike ba?". Kamar baya san yin magana ya yi ta, kuma shi ma yanzu yana san kure Sweetie ne, saboda ya ga confidence ɗinta ya yi yawa, gara su kureta su gani. "A malamullah mai tsarki wato Alqur'ani, a nan nasan shi, shi ya zo mana da tarihinsa gabaɗaya har ta dalilin da yasa kuke ce mashi Allah, wasunku su ce mashi ɗan Allah". Ta bashi amsa cikin halin ko in kula bare har ta wani damu. "Wanene Jesus?". Ronnie ya wurga mata tambayar dan ya kureta, su ji shin da gaske ta san shi ne ko dai cika baki ne kawai, basu yarda da ana yin karya a duniya ba, dan basa yi, amma a kan wanan magana sun fara tunanin kamar san zuciyarta kawai Sweetie take faɗa, sunga kamar tana san janyesu izuwa addininta ne ba tare da wani hujja ba!. Miƙewa tsaye ta yi cike da jin daɗin tambayoyinsu a gareta, dan dama so take su bata dama ta yi masu bayani game da hujoji domin ta samu Allah ya taimaketa ta tsiratar da su daga duhun kafurci izuwa haske da rahma. Tambayar Ronnie ya yi mata matuƙar daɗi sosai, sai ta ji tamkar ice block ya manna mata a kirjinta. Jingina da jikin wall ta yi tare da harɗe hannayenta a kirji, dikkansu idanunsu a kanta suna jiran bayaninta. A nitse ta fara magana one by one with full confidence. "Jesus wato Annabi Isa manzon Allah ne, yana ɗaya daga cikin manya manyan manzanin da Allah ya turo masu riƙe da litafi, shi ne annabin da aka turowa bani Israela wato yahudawa, shi ne ya zo da littafin injila wanda a yau kuke kiranta da Bible domin isar da saƙon Allah zuwa ga bani Isra'ila................" Katseta Ronnie ya yi da cewa. "Ta yaya Jesus ya zo duniya? And yana da baba ko bashi da shi?". All his though ya ɗaureta a wanna tambaya, dan da wanna suke amfani a koda yaushe su danganta annabi Isa a matsayin ɗan Allah, idan ta bashi amsar Annabi Isa bai da baba kunga ya samu damar kara karfafa cewa ɗan Allah ne shi. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Da ga kai har Floris kada wanda ya sake katse mun maganata, zan yi maku bayani a kan wanene annabi Isa (A.S) dallah dallah, dan da alama ku baku san ainahin wanene shi bama, so yakamata ku san shi da kyau ku kuma san in da kuka dosa!!"......... Tashin sense. Ko tsoronsu bata ji ba ta gaya masu hakan, idanunta a kan Ronnie da yanayin face ɗinsa ta fara canzawa izuwa na ɓacin rai, ita kam Floris tuni dama ranta ya gama ɓaci, ta ya Sweetie zata ce masu basu san Jesus ba? Wannan ma ai rainin wayo ne!. Ko kaɗan bata damu da ganin sun ɓata rai ba, ko a gefen takalmarta, cike da kwarin gwiwa da yakinin in ta yi masu bayani zasu fahimta ta fara magana kamar haka. "Annabi Isa (A.S.), wanda ake kira Yesu Almasihu a Kiristanci, yana daga cikin manyan annabawan Allah da Musulmai da Kiristoci ke girmamawa, kowane yana da fahimtarsa kan tarihinsa da matsayinsa". "Tarihin Annabi Isa (A.S.) a Musulunci". Idanunta a kan Ronnie take wannan magana ko shakkarsa babu bare tsoronsa. "An haifi Annabi Isa ta mu’ujizar Allah ba tare da uba ba, mahaifiyarsa Nana Maryam tana cikin tsarkaka. Wannan lamari ya faru ne saboda umarnin Allah don ya zama alama ga duniya a cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya ta 16 zuwa 34 a nan wannan bayani yake!" "Annabi Isa ya zo da sakon tauhidi, yana kira mutane su bauta wa Allah shi kaɗai, ya kuma tabbatar da shari'ar Annabi Musa (A.S.). Ya kuma kawo mu’ujizai da suka haɗa da warkar da kurma da makafi da maido da matattu bisa iznin Allah". "Matsayinsa a Musulunci. Musulmai ba su dauki Isa (A.S.) a matsayin Allah ba, sai dai matsayin annabi kuma manzon Allah. A Musulunci annabi Isa ba kasheshi aka yi kamar yadda kiristoci suke tunani ba! Allah ya ɗaukaka shi zuwa gareshi wato sama, cikin Suratul An-Nisa shafi na 4 aya ta 157-158 Allah ya yi magana akan hakan!" ____________________🪐💘 "Dalilin Da Yasa Wasu Suke Bauta Masa a Kiristanci. A cikin Kiristanci, Yesu ana ɗaukarsa Ɗan Allah, kuma Kiristoci suna ganin shi a matsayin cikar alkawarin Allah ga ƴan Adam don cetonsu daga zunubi ya kaisu ga rahma!. Kiristoci suna ganin nassoshi da aka rubuta a Littafinsu suna nuna cewa Yesu shi ne Ɗan Allah wanda aka aiko domin ya mutu don zunuban duniya, sannan ya tashi daga matattu, malamansu sun gaya masu irin mu'ujizozinsa hakan yasa suke ganin ya kai ya zama ɗan Allah, saboda ya tada matattu ya kuma warkar da marasa lafiya bisa umarnin Allah. Wannan shine tushen imaninsu kiristoci". "Wasu Kiristoci suna daukar Yesu a matsayin wani bangare na Ubangiji. Wannan akidar ta samo asali daga fahimtar su game da littattafan Injila ko in ce Bible ɗinsu na yanzu!". "Nasan zaku yi mamaki idan nace maku Bible da kuke karantawa a yanzu ba shi ne wanda Annabi Isa ya zo maku da shi ba, and canza maku shi tsawon dubbanin shekaru, amma bari in yi maku bayani yadda zasu fi fahimta da kyau, bari in banbance maku Alqur'ani mai girma da kuma injila haɗe da Bible ɗinku na yanzu, bari ku ga banbancin sai ku fidda na gaskiya". Ta kai karshen maganar tana sauke ajiyar zuciya. Daga Ronnie har Floris babu wanda ya sake tofa ko uppan, sun tsareta da idanu, sai dai dikkansu ransu ya sosu na yadda take ƙoƙarin karyata malamansu da kuma littafinsu, amma sun kasa kunne dan su ji hujojinta. Cigaba da yin maganar ta yi cikin tsanaki yadda komai doɗewar kwakwalwar mutum sai ya fahimci zancenta tsaɓ!. "Bambanci Tsakanin Injila da Al-Qur'ani Mai Girma, and Bible". "Injila wanda Annabi Isa (A.S.) ya kawo shi ne wahayi daga Allah, wanda aka yi niyya ga bani Isra'ila a lokacin. A Musulunci, an san wannan da Injil, amma ba wannan ba ne Littafin Bible da Kiristoci ke amfani da shi a yau. Littafin da Kiristoci ke kira Bible an haɗa shi ne daga rubuce-rubuce daban-daban, ciki har da Tsohon Alkawali da Sabon Alkawali, wanda yawanci ya ƙunshi tarihin Annabi Isa da wasikun manzanni, ba asalin Injila da Allah ya saukar ba, tarihin mu'ujizar Annabi Isa ne suka cika cikin Bible na yanzu, shiyasa kiristoci suka zage a kan lallai Annabi Isa Allah ne tun da zai iya raya matattu, ina da yakinin da anbawa kiristoci ainahin littafin da Annabi Isa ya kawo masu domin su san girman Allah to da tabbas yau za'a wayi gari babu Christians ko ɗaya a duniya, da zasu san girman Allah su san kuma dik abin da Annabi Isa ya aikata dan gane da mu'ujizarsa to Allah ne ya umarcesa ya kuma yassare mashi yin hakan, amma an ɓoye masu gaskiya an barsu cikin ɓata!". Ɗan dakatawa ta yi da maganar tana jan numfashi, tabbas ta lura ran Ronnie ya kara ɓaci. Amma ko kaɗan bata damu ba!. Kasa jurewa Ronnie ya yi har sai da ya ce. "Menene hujjarki na cewa an canza mana littafi ne ba wanda Jesus ya zo da shi muke amfani da shi ba?!". Da ɗan daga murya ya yi maganar. "Amma ai nace kada ku saka mun baki a magana ko ku katseni ko?". Mamakin jin furusinta suka yi, yadda ta yi masu magana kamar tana basu umarni, kallon mamaki Ronnie ya bita da shi ita kuma Floris kallan takaici! Sai dai basu furta uppan ba, ita kuma ko a jikinta. "Idan na gama bayanai da nike son yi sai ku tambayeni in kuna da tambaya, amma yanzu ku yi shiru ku saurareni tukun nan, zan gaya maku komai game da hujoji!". Kasa yin magana Ronnie ya yi, amma ba karya ransa ya sosu, ta wani ajisu kamar wasu ƴaƴanta tana kora masu kashedi, wlh Sweetie akwai balai'n karfin hali yarinyar nan!. Sai a lokacin Ronnie ya kula da kamar wani abin ya faru a room ɗinsa bayan tafiyarsu church, amma bai yi magana ba, ya yi shiru bisa umarnin hajiya Sweetie!. Mirrornsa da ya fashe Black Tiger ya mayar da shi yadda yake, chandelier ta koma mazauninta tamkar bata taɓa motsawa ba, amma a haka Ronnie ya fahimci akwai abin da ya faru a ɗakin!. Cigaba da bayani Sweetie ta yi kamar haka. "Al-Qur'ani littafi ne wanda Allah ya saukar wa Annabi Muhammad (SAW) ta wurin Mala'ika Jibril. Shi ne kalmar Allah tsarkakakke ba tare da canji ba tun lokacin da aka saukar da shi, kuma ya kasance jagora ga dukan al'umma". "Injila. Asalin Injila da Annabi Isa ya kawo an saukar da ita ne da harshen Aramaic, wanda shine yaren Annabi Isa. Amma Bible na yau an rubuta shi ne da Greek da Latin kafin a fassara shi zuwa wasu harsuna. Wannan ya haifar da bambance- bambance masu yawa da kara tsaurara banbanjin tsakanin injila da Bible". "Al-Qur'ani an saukar da shi da harshen Larabci na asali, kuma har yanzu yana nan daidai kamar yadda aka saukar. Wannan yana tabbatar da tsaronsa ba tare da canji ba!". "Injila ta kunshi wa'azi na Annabi Isa, da alheri, da darussan soyayya, da imani, da sanin girman Allah da ranar kiyama. Amma rubuce-rubucen Bible na yanzu sun haɗa tarihin Annabi Musa, annabawan da suka gabata, da wasikun manzanni da su irin su Bulus, wanda ba sahabi ba ne na Annabi Isa (A.S.) Wannan ya sanya kiristoci suna samun akida mai ɗan rikitarwa". "Al-Qur'ani ba wai wa'azi kawai ba ne, cikakken tsarin rayuwa ne wanda ke jagorantar Musulmi wajen ibada, mu'amala, siyasa, dokokin shari'a, da zamantakewa, hukunci kan lahira, mutuwa haɗe da kwamciyar kabari, hisabi da dai sauransu. Ya kunshi hukunci masu ma’ana da shawarwari kan dukkan bangarori na rayuwa, Alqur'ani mai girma ya haɗe komai da komai". "Injila ta asali (Injil) an yi mata canje-canje da yawa bayan Annabi Isa. Bible na yanzu an rubuta shi shekaru da dama bayan barin Annabi Isa duniya, kuma kiristoci suna da nau'o'i daban-daban na Bible, misali, Catholic Bible da Protestant Bible, wanda ya nuna rashin tabbaci kan ainihin littafin, Alqur'ani mai girma shi kaɗai ne babu wani kala daban daban, kai ko suna ba'a sake mashi ba, yana nan a Alqur'aninsa kamar yadda ya sauka!". "Al-Qur'ani ya kasance tsarkakakke tun lokacin da aka saukar da shi har yanzu, ba tare da wani canji ba. An adana shi a kwakwalwa da rubuce-rubuce daga lokacin Annabi Muhammad (SAW). Wannan ya tabbatar da tsaronsa daga duk wani ruɗani". "Annabi Isa ya kira mutane zuwa tauhidi, wato bauta wa Allah shi kaɗai a cikin injila ta ainahi Mark 12 verses 29. Amma a cikin Bible na yanzu akwai akidun Triniti (Trinity) da suka bayyana Yesu a matsayin Ɗan Allah ko wani ɓangare na Ubangiji. Wannan yana da saɓani da asalin saƙon Annabi Isa a Musulunci!!". "Al-Qur'ani yana nan daidai da saƙon tauhidi na Annabawan da suka gabata, yana tabbatar da cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Suratul Al-Ikhlas 112. Ya kuma kawo bayani kan matsayin Annabi Isa da sauran annabawa". "Injila sakon tauhidi ne ga bani Isra'ila daga Annabi Isa, amma Bible na yanzu ya haɗa da bayanan da suka sha bamban da asalin saƙon Allah". "WANNAN SHI NE BANBANCIN ALQUR'ANI DA INJILA DA KUMA BIBLE INA FATAN KUN GAMSU SOSAI?". Ta yi tambayar tana rarraba idanunta a kansu. Babu wanda ya iya furta uppan a cikinsu. Sai dai a lokacin da ta zo wannan gaɓar Ronnie ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi, saboda shi kansa yasan suna da Bible kala daban daban wanda rubuce rubucen cikinsu ma yake kala daban daban! Kamar yadda ta ce akwai Catholic Bible da Protestant Bible, yasan da hakan, so sai ya ji kamar ta ɗan faɗi gaskiya a wannan gaɓar. Ganin kamar zuciyar Ronnie ta ɗan sanyaya ne yasa ta kara jin kwarin gwiwar zata iya cin nasara a kansu, dan haka sai ta cigaba da bayaninta. Tana ƙoƙarin cigaba da yin magana Ronnie ya katseta da cewa. "Shekara nawa ne tsakanin rasuwar annabi isa da kuma bayyanar Bibles na yanzu da kiristoci suka kaddamar a matsayin injila?". Zaro idanun Floris ta yi haɗe da mamakin Ronnie, ta ji kamar ya gamsu da zancen Sweetie ne. Sosai Sweetie ta ji daɗin wanna tambaya da Ronnie ya yi mata, dan tana ganin kamar ta fara cin nasara ne, dan haka cikin farinciki da zumuɗi ta amsa mashi da. "Tarihin rubutun Bible, musamman Sabon Alkawali (New Testament), yana nuna cewa akwai babban tazara tsakanin lokacin da Annabi Isa (A.S.) ya bar duniya da lokacin da aka rubuta kuma aka tattara wannan littafi. Bari dai na yi maku dallah dallah dan ku fahimta". Kara nutsuwa Ronnie ya yi dan ya saurareta da kyau, da alama zuciyarsa ta fara yarda da maganganunta, dan komai ta faɗa tana kawo hujja mai karfi wanda dole ka yarda, kamar a baya yadda ta faɗi ayayon Alqur'ani da za'a je a duba dan tabbatar da gaskiyarta, hakan yasa ya fara gasgatata. "A tarihin Kiristanci, ana tsammanin Annabi Isa ya bar duniya, daga hangen nasu an ce an kashe shi, amma a Musulunci ba a kashe shi ba, Allah ya ɗaukaka shi zuwa sama kamar yadda na faɗa a baya. Wannan lamarin ya faru kimanin shekarar 30-33 AD". AD wato Anno Domini yana nufin bayan haihuwar Annabi Isa ne, BC wato before Charist yana nufin kafin zuwan Annabi isa duniya kenan, to shekarun ake kira da BC, bayan zuwansa kuma AD. Cigaba da bayani Sweetie ta yi cikin sani da kuma kwarin gwiwa. "Bayyanar Sabon Alkawali (New Testament). Rubuce-rubucen farko na Sabon Alkawali, waɗanda aka ce wasikun Bulus ne (Paul), sun fara bayyana kusan shekaru 20-30 bayan ɗauke Annabi Isa daga duniya da Allah ya yi, kimanin shekarar 50 AD bayan zuwansa duniya kenan". "Injiloli guda huɗu ko in ce Bible ɗinkuna yanzu guda huɗu wato Matthew, Mark, Luke, John. An rubuta su kusan daga 60 AD zuwa 110 AD. Injila na Markus wato Bible mark ana ɗaukar shi mafi tsufa, an rubuta shi kusan shekarar 60-70 AD. Sauran injiloli (Bibles) suna tafe daga bayansa". Izuwa yanzu jikin Ronnie ya yi sanyi, saboda jin yadda take zayyano tsawon shekaru baya, ko mai san zuciyar mutum ya ji wanna bayanai nata dallah dallah sai ya san gaskiya take faɗi, sai dai idan yaki aminta da hakan dan san zuciyarsa ne! Amma irin wanna shekaru da take ambata ai babu karya!. "A lokacin shekaru 325 AD bayan haifar Annabi Isa kenan, a taron Council of Nicaea, a karkashin Sarki Constantine, aka fara tsara da tantance irin waɗanda za su shiga cikin Bible na yanzu, kuma wannan ya ƙarfafa canje-canje na ra'ayi da tsarin Kiristanci, kun dai ji Bible naku na yanzu sarakunar da ne suka shirya abubuwan da za'a rubuta a ciki, so ni nasan ba laifinku bane zamanku kiristoci, laifinku a nan shi ne rashin faɗaɗa bincike da neman sanin gaskiya bayan Allah ya baku dama da baku yi na shi ne laifi, kun dogara da littafi guda ɗaya wanda tsara maku shi aka yi ba zancen Allah bane!". "Injila ta gaskiya da Annabi Isa ya kawo ta ɓace na tsawon lokaci, hakan yasa saƙon Allah bai isa ga mutanen yadda yakamata ba. Wannan ne yasa Allah ya saukar da Al-Qur'ani Mai Girma don ya zama tabbataccen jagora wanda ba zai taɓa sauyawa ba, wasu gungun kafurai sun jima suna shuka tsiya da rashin son gaskiya a duniya, amma Allah ba'a yi mashi wayo, da suka ɓatar da injila ta gaskiya sai ya sauko da Alqur'ani wanda wane mutun ya iya canza rubutun cikinsa, karya mutum yake, tsawon shekaru har yau yana nan yadda aka sauke shi!!". Ta kai karahen maganar idanunta a kan Ronnie tana kuma sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai fatan take yi Allah yasa su gane gaskiya. Floris ta rasa abin faɗe, sai idanu kawai take binsu da shi, ta ji abin da ya girmewa shekarunta. "Shin kana da wata tambaya dan kara tabbatar da gaskiya ta da gaskiyar addinanina ne ko dai ya isa haka?". Ta jefawa Ronnie tambaya idanunta a kansa. Zuciyarsa ta gama yarda da zancenta dikka, amma dik da haka dan kara tabbatarwa sai ya ce. "Shekara nawa Annabi isa ya yi a duniya.............. and tare da mahaifiyarsa ya yi rayuwa? Sannan akwai wani dalilin da yasa bai yi aure bane?. And ya rayuwarsa ta kasance a cikin al'umma a lokacin da ya bayyana bai da uba? Ya fisakanci kyara ko tsangwama ne daga mutane? Ko dai a addininki Annabi isa yana da baba ne ɓoye mana aka yi kamar yadda aka canza mana komai?". Ta ji matuƙar daɗin jin wanna tambaya tasa, ranta ya yi sanyi sosai. With full confidence ta ce. "Tarihin Musulunci da Kiristanci ya nuna cewa Annabi Isa (A.S.) ya rayu a duniya na kimanin shekaru 33 zuwa 34 kafin Allah ya ɗaukaka shi zuwa sama. Wannan yana nufin bai mutu ba a hannun mutane, kamar yadda Musulunci ya bayyana Surat An-Nisa shafi na 4 aya na 157-158 Allah ya yi wanna bayani". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗaura da cewa. "Annabi Isa ya taso ne a ƙarƙashin kulawar mahaifiyarsa, Nana Maryam, wacce Allah ya zaɓa kuma ya tsarkake ta daga zunubi. Ya zauna tare da ita yayin ƙuruciyarsa har lokacin da ya fara wa'azinsa. Mahaifiyarsa ta kasance ginshiƙi da gatansa, musamman ganin cewa ba shi da uba". Ronnie fa ya ji abin da bai taɓa ji ba, ga shi maganganunta dai ba zasu karyatu ba, shi kansa yasan gaskiyar take faɗe, saboda idan ba gaskiya bane taya tana karamarta haka ace zata tsara irin wanna dogon karya? Ai ba zata taɓa yiwuwa ba. Cigaba da bayani ta yi. "Dalilin da yasa bai yi aure ba, Allah ya aiko Annabi Isa (A.S.) da takamaiman manufa, isar da saƙon tauhidi ga Bani Isra'ila da warkar da zukatansu daga zalunci da ruɗi. Rashin yin aurensa ba tare da shakka ba ya haɗu da wannan manufar, don ya mai da hankali kan aikin annabci ba tare da wata tangarda ba!". "Al'ummar da Annabi Isa ya fito daga cikinta tana cike da tsangwama da adawa ga saƙon Allah, kuma rayuwarsa ta kasance cike da ƙalubale. A irin wannan yanayi, yin aure ba zai yiwu ba, domin tsangwamar mutane za ta iya shafar iyalinsa idan ya kasance da su". "Allah yana aikawa da annabawa tare da yanayi daban-daban, don su zama abin koyi ga al’umma. Rashin aurensa wata hanya ce ta nuna cewa rayuwa mai cike da ibada da sadaukarwa na yiwuwa ba tare da iyali ba, musamman idan mutum yana da babban aiki na isar da saƙon Allah". A dai'dai wanna gaɓa Ronnie ya samu karin haske sosai, wato hikima ta Allah tana da yawa, rashin yin auren Annabi Isa wani haske ne ga al'umma. Nan take ya kara jin lallai wannan Allah da Sweetie take magana a kansa shi ne Ubangiji na gaskiya. Cigaba da bayani Hajiya Sweetie tamu yarinya ƴar baiwa mai cike da ababen ban mamaki ta yi. "Rayuwarsa a cikin al’umma lokacin da ya bayyana ba tare da uba ba. Fitowarsa ta musamman ce, Annabi Isa ya fito cikin mu'ujiza rashin uba........ Wannan lamari ya haifar da jita-jita daga wasu mutane, suna zargin mahaifiyarsa Maryam da aikata abin da bai dace ba. Amma Allah ya kare Maryam da Annabi Isa ta hanyar da ya sa Annabi Isa ya yi magana tun yana jariri, cikin Surat Maryam shafi na 19 daga aya ta 29 zuwa 34. Wannan mu'ujiza ta tabbatar da tsarkin mahaifiyarsa da cewa shi annabi ne daga Allah". "Wasu daga cikin Bani Isra’ila sun karɓi saƙonsa saboda sunga mu'ujizarsa da kyawawan halayensa. Amma yawancin shugabannin addini da manyan masu mulki a lokacin sun tsangwame shi saboda ya ƙalubalanci mulkinsu da karairayinsu, so sai suka yi ƙoƙarin karyata shi a idan duniya, suna ƙara yaɗa jita-jita kan asalinsa (ba tare da uba ba), wanda ya kasance babban kalubale ga rayuwarsa a cikin al’umma". "Duk da tsangwama, Annabi Isa ya kasance mai rahama, tawali’u, da juriya. Ya yi wa mutane wa'azi, ya warkar da cututtuka, ya kawo zaman lafiya, kuma ya ci gaba da kira ga bauta ga Allah Shi kaɗai, ya jure ya kuma cije". "So a takaice Annabi Isa ya fuskanci tsangwama sosai daga shugabannin addini na Yahudawa, waɗanda suka yi ƙoƙarin halaka saƙonsa saboda yana yi musu tsawa kan zaluncinsu!. Amma talakawa, marasa galihu, da masu buƙatar taimako sun karɓe shi, suna girmama saƙonsa na tausayi da gaskiya, a iya nan zaku iya gane cewa Allah Ubangijin talikai shi ne Allah na gaskiya, dan shi ne mai jin ƙan bayinsa, ya umarci annabi isa da ya wanzar da adalci, ya daraja kaskantattun bayin da aka kaskantar, waye zai yi maku wannan idan ba mahaliccinmu na gaskiya ba? Ko malamanku sun taɓa kwatanta maku irin hakan ne?". Ta jefa masu tambaya tare da tsayar da idanunta a kan Ronnie ta kuma dakata da yin magana tana jiran su bata amsa. Dik cikinsu babu wanda ya iya buɗe baki ya yi magana, dik ta sare masu gwiwa ta kuma sanya sun ji zuƙatansu ya fara karaya da addinin Kiristanci, sun ji sun kwaɗaitu da san Allah da take ambata mai adalci da kuma jin kan bayinsa, ga tausayawa marasa gata, tabbas zuƙatansu sun ji tausayin hakan matuƙa, sai dai da kamar wuya Black Tiger ya bar hakan ta cigaba da yin tasiri a zuƙatansu, saboda kada ku manta jinin kiyayya haɗe da yakar addinin musulunci yake gudana a cikin jikinsa, burin babansa kenan kafin ya bar duniya, kada ku manta babansa ya kaddamar da Duniyar shaiɗanu, kunga kuwa raya Musulunci a cikin Black world abu ne wanda yiwuwarsa tana da matuƙar wahala!!. Floris baki ya mutu, ta rasa abin faɗe, saboda ta ji tsagwaran gaskiya. "Ronnie ku bani amsata, shin a cikin malamanku akwai wanda yake faɗa maku da kuji tausayin na kasa da ku? Ku kyautatawa marasa shi, ku taimakawa gajiyayyu marasa karfi, ku jikan mata da yara?! Akwai waɗan da suke gaya maku hakan?". A karo na biyu bai amsa mata ba, binta da kallo kawai yake yi dan yasan ba'a taɓa gaya masu hakan ba, sai dai tongue nasa ta mashi nauyi ta yadda ya kasa amsa mata. Idanunsa sun yi jajir kamar wuta, kamar ba lafiya ba. Ganin haka yasa Sweetie ta kawar da tambayar da cewa. "Akwai wani tambaya da kuke san sake yi mun dan tabbatar da gaskiya?". Jinjina mata kai Ronnie ya yi, da kyar ya iya furta. "A cikin malamullah ɗinku (Alqur'ani mai girma) a wace sura da wace aya ce Allah ya umarci annabi Isa da ya yi magana a lokacin da yake jariri? And a wace aya da wace surace Allah ya umarci mahaifiyarsa Maryam da ta yi azumin magana?". Nisawa Sweetie ta yi kafin ta ce. "A cikin Al-Qur’ani Mai Girma, Allah ya yi bayani kan waɗannan abubuwan biyu a Surat Maryam, inda aka kawo lamarin Annabi Isa (A.S.) da mahaifiyarsa, Maryam a cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya na 29 zuwa na 33". "Lokacin da Nana Maryamu ta haifi Annabi Isa, ta damu sosai game da abin da mutane za su ce game da ita. Sai Allah ya umarce ta da ta yi azumin magana (wato ta yi shiru kuma kada ta ce komai ga mutane), domin Annabi Isa zai yi magana da kansa don ya bayyana gaskiya. Wannan umarni yana cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya na 26". "Lokacin da ta dawo cikin mutane da jariri goye a bayanta, sai suka fara zarginta suna ƙoƙarin cin mutuncinta a kan ina ta samu yaro? A lokacin sai ta nuna masu shi goye a bayanta ba tare da ta yi magana ba, har sun fara yi mata izgili da iyashege suna dariya a kan ta ya za'ayi su yi magana da jariri?!". "Kwatsam ba zato ba tsammani cikin umarnin Allah Annabi Isa ya buɗi baki a in da ya ce. Lalle ni bawan Allah ne, Allah ya ba ni Littafi, kuma Ya sanya ni matsayin Annab, ya albarkace ni, kuma Ya yi wasiyya da ni game da salla da zakka matuƙar ina da rai, kuma ni mai kirki ga uwata ne, bai sanya ni mai girman kai ba, ni annabi ne ba kamar yadda kuke tunani ba, aminci ya tabbata a gare ni a ranar da aka haife ni, da ranar da zan bar duniya, da ranar da zan tashi da rai". (Fassara maku ayar fa na yi dan ku ji me annabi Isa ya faɗa time da ya yi magana a jaririnsa.) "Ina san wanna Alqur'ani dan na duba wanna aya da kuma sura da kika faɗa". Cewar Ronnie kenan. "Tabbas in na bar wannan gari na koma forest zaka zamu Alqur'ani a wajena, yanzu dai babu yana wajen Pretty". Floris ce ta katsesu da cewa. "Beb ka yarda da abin da ta faɗa kenan?". Dawo da kallonsa a kan Floris ya yi. "Ina ji a rai'na dik abin da ta faɗa gaskiya ne, amma ba zan yarda da hakan ba har sai na ga hujoji a zahiri ba a faɗe a baki ba, dan haka zan nemi Alqur'ani dan na karanta na tabbatar!". A hanzarce Sweetie ta karɓi zancen da cewa. "Tabbas zan baka hujjoji a zahiri da zarar na bar nan". Jinjina mata kai ya yi tare da miƙewa ya nufi hanyar shiga toilet. "Yau muna da gagarumin party a empeir ɗin nan na fidda gwanar kyau, Sweetie ki shirya, yakamata ki shiga cikin wanna gasa fa nasan zaki fi kowa, zaki samu kyauta babba daga wajen yaya". Cewar Ronnie dake nufar toilet. Jinjina kai Sweetie ta yi, a ranta ta kudurta cewa tabbas zata biyewa mutanen birnin nan dan ta rinjayesu izuwa addininta, dan haka zata rinƙa shiga cikinsu, zata bi al'adunsu dik dan ta yi masu mage mai kwamciyar ɗaukar rai, a cikin zuciyart ta furta. "Ya Allah kasa kafin na bar garin nan ko da rabinsu ne na samu su musulunta, Allah ka tayani ka taimaka mun ka dafa mun". Sosai Floris ta ji rashin daɗin cewa da Ronnie ya yi Sweetie ta shirya ta shiga cikin gasarsu da suke yi dik karshen sati, dan tasan Sweetie ta fita kyau nesa ba kusa ba, so tasan zata bugeta ta cinye mata number na farko da take zuwa, sai ta ji ta kara jin haushin Sweetie, dama can akwai sauran haushinta na zagin malamansu da ta yi, sai ya karu mata. Ita kuwa Sweetie raba jikinta da jikin bangon ta yi ba tare da ta sake bi ta kan Floris ba ta nufi hanyar fita faga cikin ɗakin. "Ina zaki je?". Ronnie ne ya jefa mata tambayar. Da sauri ta juyo haɗe da kai kallonta in da yake, yana tsaye a bakin kofar toilet ta waje, ya harɗe hannaye a saman kirjinsa. "Zan je wani ɗakin ne na yi amfani da toilet ɗin, lokacin sallar mangariba ta wuce". Da hannu ya nuna mata hanyar cikin toilet ɗinsa. "Zo ki yi amfani da wanna, daga nan ki yi wanka, Floris je ki kawo mata ɗaya daga cikin irin kayan da kuke sakawa dan yin gasa, mai kyau zaki kawo mata fa".............. Ya yi maganar ne idanunsa a kan Sweetie. Ba musu ta dawo ta nufi toilet ɗin nasa, yanzu ba zata yi gardama da su ba, dan ta ɗaura ɗamarar musuluntar da su dikka birnin da izinin Allah, dan haka ta shirya tsab wajen shiga cikinsu sosai dan ta san takamaiman ina ma suka dosa tukun nan. Sai da ta iso dab da shi sanna ya bata hanya ta shige ciki, shi kuma ya wuce ya nufi waje yana faɗawa Floris ta zo su je bari ya je wajen ƴaƴansa ya duba irin kyautar da aka tanadawa waɗan da zasu zo daga na ɗaya zuwa na goma, ita kuma ta wuce room ɗinta ta shirya ta kawowa Sweetie kaya sanna ta taimaka mata wajen shiryawa. Da okey ta amsa mashi a fili, amma a cikin zuciyarta ta kudurci niyar shiryawa Sweetie mugunta ta yadda ba zata taɓa cin wanna gasa ba, har da shirya irin kwalliyar muguntar da zata yi mata, ga shi Ronnie idan ya fita yanzu sai dai su haɗu a wajen wasa kawai, so ba zai samu damar ganinsu ba bare idan Floris ta yi mata ba daidai ba ya ce ta gyara mata, sai a cikin mutane zasu haɗu. Hakan ne ma ya bawa Floris kwarin gwiwar cewa zata ɓata mata fuska ta dishashar mata da kyanta. Alwala Sweetie baiwar Allah ta ɗauro ta zo kamar yadda ta saba ta gabatar da sallar mangariba, tana idarwa lokacin sallar isha ta yi, hakan yasa ta miƙe ta gabatar da shi. Sanna ta shiga cikin toilet ta yi wanka, tana fitowa ta isko Floris zaune a saman bed ta tsantsara kwalliya kamar wata amarya, tana shirye cikin wani doguwar riga mai kama da weeding gown, ta yi masifar kyau sosai, kwalliyar ya karɓeta matuƙa. Sweetie baiwar Allah har da yaba kyalliyar tata ta yi, cikin sanyin murya ta ce. Floris kin yi matuƙar kyau sosai". Tsabar haushi kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta tina im bata amsa ba Sweetie zata fahimci ta shirya mata wani muguntar ne, dan haka sai ta amsa da thank u. Kawai. A kusa da ita Sweetie ta zauna tana bin kayan jikinta da kallo, irin kayan ƴaƴan sarakuna ne, shigensu wannan sadauki mai taimaka masu a forest ɗin yake kawo masu ita da Pretty suna amfani da shi!. Su hajiya Sweetie manyan ƙasa, girma ya fara zuwa ƴan kirgan danginta sun girma kamar na Auta Zunaira, hakan yasa yanzu take ɓoyesu, kamar dai yanzu yadda ta wani ɗaura towel ɗin Ronnie daga saman kirjinta, ita ma Floris dik da take krista bata taɓa yarda ta fito wanka kirji a buɗe, tana rufe kayanta, Floris ta fi Sweetie shekaru, amma Sweetie ta fita cikar halitta, dan tula tulanta ɗaya ya yi kusan biyun na Floris a girma. In short kwalliya Floris ta tsarawa Sweetie kamar wata ta Allah, kamar dai da gaske take tare da ita, alhalin a karkashin zuciyarta ba haka bane, hasada take da kyan da Allah ya yi wa Sweetie da kuma iliminta, Floris an fara hasada da kishi. Wajen da za'a gabatar da gasa ya cika makil, jama'a suna zazzaune cikin hall ɗin, ƴan matan da zasu shiga wannan gasa suna killace cikin ƙayatatcen ɗaki, dama haka suke yi, sai sun gama haɗuwa a cikin wannan ɗakin sanna sai su fito izuwa saman stage na hall ɗin dan bayyanawa duniya irin kyansu da surar jikinsu. Dikkanninsu matasan ƴan'mata ne da babu wacce ta wuci 18 years a cikinsu, sai dai dikkansu daga 15 years suke, babu wanda take kasa da 15 sai Sweetie da zata shiga gasan a yanzu. Kafataninsu kayan jikinsu irin kayan nan ne da ake cewa aunty tsirara, sun ɗame jikinsu dan fito da surar da Allah ya yi masu, idan ba ku manta ba a baya na gaya maku ƴan'matan birnin suna da sura mai matuƙar kyau da ɗaukar hankalin dik mai kallonsu, to hakance. Sun yi kyau sun kuma saki gashi har baya, kowacce ji da kanta take yi, tana ganin tafi kowa kyau, anyi fente fenten kwalliya kam har an gaji, ga wani uban high heels a kafafunsu, wasu daga cikin sai taunar chewing gum suke yi suna yi wa junansu kallon ƙaskanci da matsayin basu kai ba. Ronnie yana tare da Oxil a saman kujera suna hira a kan yadda gasan zai kasance da kuma wadda zata yi nasara. Oxil dai ya ce Floris ce zata yi nasara dan yasan a kullum ita take bige kowa ta zo ta farko, saboda ko kayan da take sanyawa a jikinta ya take na sauran ƴanmatan kyau da tsada, bare a zo kan kwalliyarta, abin ba'a magana, hakan yasa take zuwa ta ɗaya. Angama kimtsa komai ƴan'mata kawai ake jira su iso. Ga shi Floris ɓatawa Sweetie fuska, me kuke tunanin zai faru a wanna fasa? Ronnie zai yarda da hakan ko yaya?. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ==========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ A dab zasu shiga hall ɗin Sweetie ta tsaya bata shiga ba. Floris ta tambayeta dalili, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Kunyar shiga da irin wannan kaya nike ji Floris". Binta da kallo Floris ta yi, nan take wani kululun bakinciki ya tokare mata maƙoshi, kamar zata haɗiyi zuciya, saboda tafa zaɓo kayan da bashi da kyau sosai ne ta bata, amma kuma sai ta yi bala'in yi wa kayan kyau, saboda tana da round butt, yadda kuka san ita ta yi wa kanta halitta. Floris bata san cewa ba kaya ne yake yi wa Sweetie kyau ba, yanayin shape ɗin jikin Sweetie yake yi wa kaya kyau, in kina da kyau sai kaya ya zauna maki. "Gaskiya Sweetie bai kamata ki shiga ba tin da kince addininku ya yi hani da fidda tsiraici, kinga wannan riga kuma ta kamaki sosai". Cewar Floris. Cike da hasada ta yi maganar. Shiru Sweetie ta yi, sai ta ji kamar da gaske Floris ta gaya mata gaskiya ne, ta yi mata nasiha kanan, wani irin sanyi ta ji a ranta, sai taga kamar da gaske Floris take yi, kamar santa take yi, bata san ba haka bane. "Tom shikenan Floris, zan koma ciki ni kam". Tsabar farinciki ta kasa shanyewa har sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, buƙata ta biya. "To ki koma kam zai fi". Ta faɗa fuska ba yabo ba fallasa ba kamar yadda ta ɗaure face ɗin nata ɗazun ba!. Juyawa Sweetie ta yi ta nufi hanyar komawa cikin gida, ita kuma Floris ta yi maza ta shige cikin room na hall ɗin, wai dan ma kada Sweetie ta canza shawara ta ce zata shiga ciki, shi ne ta yi saurin wucewa ciki ta yadda ko ta juyo ba za ta ganta ba. "Ina kuma zaki je?". Daga bayanta ta ji wannan tambayar. Juyowar da zata yi gabaɗaya komai na face ɗinta ya canza, kwalliyar mugunta da Floris ta yi mata maras kyau ɗin nan, dik kafin ta juyo ga Ronnie kwalliyar ya goge izuwa wani tsantsararren kwalliya na ban mamaki, ta yi balai'n haɗuwa, har da wani gashi dogo guda biyu ya bayyana a gaban goshinta wanda aka naɗa mata shi kamal indomie. Ta yi masifar kyau wanda sai da ta sanya Ronnie zaro idanu, cikin second ɗaya magic ya canza mata kamannin kwalliyar face ɗinta. Da yake ba ganin kanta a mirror take yi ba, sai ta ɗan sakarwa Ronnie murmushi wanda ya kara haukata ƙwaƙwalensa, dimples ɗinta dik suka lotsa. Kamar wanda ya ga abinci Ronnie bai san time da ya haɗiyi yawu ba, ya kasa sake ce ko uppan. "Ciki zan koma" ta bashi amsa tana kara faɗaɗa murmushinta. Hannu kawai ya iya buɗe mata ba tare da ya yi magana ba. Tsaresa da ido ta yi tana kallan irin shigar jikinsa, ya yi kyau matuƙa shi ma, sai dai ya yi aske gera, ya raba gashin gerarsa har kashi uku, hakan ta yi mashi kyau kam matuƙa, sai dai a addinin musulunci Allah ya tsinewa masu haske gashin gyara da masu kankare hakwara su yi wishirya. So hakan yasa Sweetie ta ɗan ji ranta ya sosu, meyasa zai rinƙa aske gerarsa haka? Ga ɗan kunne a kunne har saman kunnensa, bayan haka ga sarkoki a wuya kamar wani mace, har da wani ɗan pil a gefen bakinsa, sun yi mashi kyau kam over, sai dai Allah ya haramta, dole ta san yadda zata gaya mashi ya rabu da sakasu. Kamar ba zata je in da yake ba, amma ganin irin shigarsa yasa ta ji yana da kyau ta je garesa dan ta shiga jikinsa sosai ta samu ya fita daga wanna irin rayuwa. Dan haka sai ta nufesa da sauri. Tana isa garesa ya rikota ya rungume yana sauke ajiyar zuciya, ita ma bata zare jikin nata daga nasa ba, sai ta rungume shi da kyau tana ɗan murmushi. "Kinga yadda kika yi kyau kuwa?". Ya faɗa kamar mai raɗa. Kai ta girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba. "Kin yi kyau sosai da sosai, zo mu je an kusa fara gasar". Kamar zata ce mashi ba zata je ba, sai tunani ya faɗo mata a kan tana san fa ta rinjayesu su musulunta, dan haka dole ta yi aiki tukuru, dole zata ɗan kawar da idanunta a kan wasu abubuwan ta shiga jikinsu sosai. Dan haka sai ta aminta suka shige ciki a tare. Tin da ta ɗaura kafafunta a cikin wajen idanun mutane suke a kanta, kallonta kowa yake yi babu kyaftawa, hakan ya ɗan sosa ran Ronnie, amma ya daure. Floris ta kara jin haushinta sosai, dan tana ganin kamar Ronnie ne ya je ya gyara mata face ɗin nata a cikin room ɗinsa, sai ta kara jin wani irin kululun bakinciki ya tokare mata maƙoshinta, kamar ta shake Sweetie, amma ta girgiza sosai na ganin wanna halitta ƙayataccen kwalliyar, babu wata mace da ta taɓa yin irin wannan kwalliya a cikin birnin, zallar madarar kyau, ga yanayin gashin kanta dik cikin birnin babu mai irinsa, ita kaɗai ce mai irinsa. Amma kuma da Ronnie ya kawo mata Sweetie ɗin kusa da ita, sai ta ƙaƙalo murmushin dole ta yi mashi tsabar iya makirci da munafurci. Bai kawo komai a ransa ba ya haɗasu ya koma wajen zamansa. Zubawa takalmar kafar Sweetie idanu ta yi tana kallon yadda suka ci uban nata a kyau, bata taɓa kallon irinsu ba, da duwatsun lu'ulu'u aka kawata kwalliyarsa, hakan yasa ya kara rinjayar jama'a dayawa wajen kai kallonsu a kan takalmar. A tunanin Floris Ronnie ne ya ɗauko mata takalmar daga ɗakin Black Tiger, amma kuma ba haka bane, dan shi kansa Ronnie bai san da takalmar ba, ruhohin tsafinta suka canza mata komai!. Dik fa abin da suke yi kada ku manta Black Tiger yana jinsu kuma yana ganinsu, sai dai this time bai wani mayar da hankali sosai a kansu ba, ya mayar da hankalinsa ne a kan katafaren ginin companyn motocinsa da ake yi, wato BLACK TIGER SUPER AUTO MOTORS, yana san su zama na ɗaya a duniya wajen kyara motoci waɗan da su suka fara kawo irin style ɗin, yana san su tashi kan duniya ne sosai. So ya fi kayar da hankalinsa a kan ginin da kusan rabin aikin Robbot ne suke yinsa ba ƴan adam na, hakan yasa aikin yake kara sauri yake kuma tafiya yadda ya kamata, ga shi girman companyn gidan sama ne mai hawa goma, Robbot sun taka muhimmiyar rawa sosai wajen rage samu mace mace mutane a kan wanna gini, su suke hawa sama ƙololuwa su yi aiki, kunsan a gini irin haka laburas and engineers suna rasa rayukansu wajen faɗowa kasa daga sama idan aka samu akasi, so yanzu Robbot ke hawa sama wanda su idan ma suka faɗo sai dai su tashi su karkaɗe jiki su kara gaba abinsu, babu abin da zai same su!. So yanzu an samu sauki sosai wannan fasaha ta Black Tiger wajen amfani da Robbot sosai a aikin da ƴan adam suke yi ya yi matuƙar birgewa, saboda ya taimakawa mutane matuƙa. Yanzu hankalinsa baya a kansu sosai. Ko ban faɗa ba nasan kunsan dik faɗin birnin Black world babu wanda za'a samu ta iya doke Sweetie a kyau, dan faɗe ma ɓatawa ne, kun san in ta shiga fili dole mata su matsa mata, hakan ma yasa Floris ta kullah mata tuggun ta hanata shiga wajen, amma ina hakarta bai cinma ruwa ba. Sweetie ta yi gasa kuma ta ci na ɗaya, Angela ta zo na biyu, sai Floris ta uku, ba komai yasa Angel ta zo na biyu ba kuma face alhakin Sweetie ne ya kama Floris, ta mata mugunta reshe ya juye da mujiya, ita da take zuwa na ɗaya kullum yau ta kare a na uku. Idan ranta ya kai miliyan to ya ɓaci, zuciyarta ya sosu, tsabar kishi da kuka ta bar wajen taron, bata ma tsaya an shigar da mark na kowa a Idanta ba, ta wuce ciki da gudu. Sai gobe da safe za'a bawa waɗan da suka ci gasar kyautarsu, hakan yasa Sweetie ta ce da Ronnie zata je ta yi barci dan zata tashi ta yi sallar dare. Sam bai so hakan ba, ya so ta tsaya su yi casun rawar da zasu yi, ya so koya mata rawa, amma baya san shiga hakkinta, sai ya rakota har cikin room ɗinsa ya ce ta kwanta a nan shi zai je wajen rawar, in suka gama rawa kuma ba lallai ya dawo ɗakin ba, kila a ɗakin yayansa zai kwana. Ko tsoro babu a tattare da ita ta amsa da to tare da wucewa ciki, yana tsaye har sai da ta canza kayan jikinta izuwa kayan barcin Floris da ya kawo mata, dressing room ɗinsa ta shiga ta canza kayan, sanna ta zo ta haye gado, da kansa ya rufeta da bargo kafin ya juya ya fita. A tunaninsa Floris tana wajen gasa, dan bai ga fitarta daga wajen ba, hankalinsa na kan Sweetie, so bai san ta fice ba, hakan yasa ya koma can dan su yi rawa da ita. Ita kuwa Sweetie Ronnie na tafiya ta miƙe zaune, dama ba wani barcin da take ji, so take ta dawo dan ta zo ta yi masu bincike a cikin gidan. Kamar wata ɓarauniya haka ta saɗaɗa ta fito waje ta hanyar sanya password na kofar ta buɗe, ya gaya mata password ɗin yanzu. Ko tsoro babu ga dare wajen karfe 12, ga kuma kanta ko ɗankwali babu, kuma tasan akwai ababen ban tsoro a gidan, amma ko ɗar bata ji ba ta nufi part ɗin Black Tiger. Kunsan komai ilimin mutum in dai yaro ne to sai yarintar nan ta nuna, a shirmen yarintarta wai tunani take yi Black Tiger ya yi barci, hakan yasa ta lallaɓa dan ta je ta yi mashi bincike a part ɗinsa, Ronnie ya gaya mata akwai kofar sirri na fita daga cikin Daular nan a saukake, amma kofar tana cikin part ɗin yayansa, shi kansa bai san takamaiman in da kofar take ba, amma zai bincika masu, to shi ne ita uwar ƴan rashin tsoro ta je dan ta fara bincikawa da kanta, bayan kuma Ronnie ya gaya mata ta yi taka tsantsan kada ta sake shiga gonar yayansa, in ba haka ba zata rasa ranta ne a banza, amma kunga yarinyar nan bata ɗauki zancensa a bakin komai ba, ta yi fatali da komai ta yi biris. Babban parlournsa ta shiga, babu komai sai daddaɗar kamshi dake tashi, ko'ina very very clean, kamar sabbin kaya aka zuba. Wucewa ta yi ta nufi ɗaya daga cikin bedroom dake cikin parlourn, ba ainahin bedroom ɗinsa ba. Babu wani ɗar ta gwada sanya password irin na ɗakin Ronnie, ga mamakinta sai gani ta yi kofar ya buɗe, wato ba ina ga daga kan Sweetie karfin hali ya kare yarinyar nan. Kila ma ba dai'dai tasaka password ɗin ba kawai an buɗe mata kofar ne dan a shirya mata tarko, amma sam bata gane ba!. Har da wani ɗan siririn munafikin sallama ta yi yadda kukasan ɗakin Pretty zata shiga. Tashin sense, ai tana shiga cikin ɗakin sai ganinta ta yi a wani irin kungurmin forest, wata duniya daban, wanda ganinsa kawai zai iya sa mai karamar zuciya zuciyar tasa ta buga ya mutu. Ai bata san lokacin da ta kurma ihu ba na ganin wanna kungurmin forest bakin kirin mai cike da abin tsoro, gabaɗaya bishiyoyin cikin forest ɗin suma jikinsu ya yi bakin kirin, ga wasu irin kawunan mutane, ga kasusuwan kwarangwal, abin dai sai wanda ya gani, ga wasu irin inuwa dake gilmawa ta gaban idanunta tamkar na wasu gungun aljanu, a gabaɗaya dajin nan babu wani abu mai ɗan dama dama da zaka iya gani, sai zallar madarar abin tsoro mai firgita kwakwalwa. Dik tsananin karfin hali irin nata sai da ta yi balai'n rasaza, ta kasa iya furta ko uppan, jikinta har kerma ya fara yi, sai ta fara danasanin meya kawota. A hankali wani irin inuwar wani dogon halitta mai tsayin gaske ya fara nufo in da take tsaye, sam bata iya ganin wanna halitta, inuwarsa ne kawai zaka gani. Da kyar ta iya ɗaga kafarta da ya yi mata bala'in nauyi, a hankali ta fara ja da baya, inuwar yana kara tinkarota, jininta sai rawa yake yi, ta kasa iya furta sunan Allah da ya kawo mata ɗauki. Ganin da gaske wannan halitta ita yake nufowa yasa ta zage da iya karfinta na karshe ta tattare karfinta dikka ta juya da karfin gaske dan ta gudu ta fita waje, sai dai kash tana juyowa kofar ɗakin ya rufe kansa da wasu irin mahaukatan locks masu ban mamaki wanda bata san da su a jikin kofar ba sai a yanzu. Nan take gabaɗaya empire ɗin Black Tiger ya ɓacewa ganinta, ya zamana iya dajin ne kawai a wajen, kasar dajin in da take takawa kenan bakin kirin yake kamar gawayi. Tashin sense, wani irin dukan tara tara kirjinta ya yi, da karfi ta wage baki ta kurma ihu, sai dai sam voice ɗinta baya fita, kamar ma bata yi ihun ba. Cike da fargabar abin da zata gani a hankali ta juyo kirjinta na dikan uku uku jikinta na kara tsananta kerma. Wani irin mahaukacin ihu ta saki lokacin da ta gama juyowa ga wannan halitta dake nufota. Tin daga wanna ihu kuma bata sake iya ji ko ganin wani abin ba, ido da ido da ta yi da halittar yasa idanunta suka makance ta dai'na ganin komai, kunnuwanta suka kuramce ta dai'na jiyo sautin komai. Me kuke tinanin ta gani ya makantar da ita? Me kuke tinanin zai faru da ta kurmance? Yanzu wasansu zai fara, shin kuna tunanin dama zasu zubawa Sweetie ido ta musuluntar da su Ronnie ne? Su da jininsu na tsanar musulinci ce? Akwai matsala fa! Sweetie ta taro yakin da a yanzu dai ba iya shi zata yi ba! Saboda a yanzu ita kanta bata san wacece ita ba, bata san baiwar dake gareta ba bare ta yi amfani da shi wajen yakarsu ita ma dan ta taimakawa kanta da mutanen da zasu yarda da ita! Bata san ina ta dosa ba a halin yanzu, fatana dai Allah yasa kada su wujijjiga mana rayuwarta ko ma su shafe babinta a doran duniya!!. ===========================💘 DUBAI.🔥 Al'umma dai sun ki nutsuwa su kwantar da hankalinsu, saboda suna ganin mutuwa zasu yi, jami'an nan sun yi iya ka bakin ƙoƙarinsu kowa ya nutsu dan ma su iya gane kila makiyan suna a tare da su, amma ina kowa neman hanyar fita yake yi, dik da an rufe gates ɗin amma sun ki tsayuwa waje guda. Gungun jami'ai ne suka yi wa ahalin Abu Abdussalam zobe domin su tabbatar da sun fitar da su lafiya lou. Sai dai fa Ramish da aka hara yaki motsawa daga in da yake bare har ya bi ayarin Abu Abdussalam su koma gida. Ya dai ce Bilal ya kasance a tare da Abbie ɗin nasu, shi yana nan bari ya tabbatar da dik wanda ya zo nan dominsu ya koma gida lafiya ba tare da kwarzani ba, ba yadda Abu Abdussalam bai yi da shi a kan yazo su tafi ba amma yaki yarda. Hankalin Abu Abdussalam a tsananin tashe, saboda yasan Ramish ɗin aka hara kunga bai kamata ya tsaya a wajen ba, amma yaki tafiya, burinsa ya kama wanda ya yi wannan harbin. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• Kaiwa suke suna sake komawa, suna safa da marwa a tsakiyar katafaren parlournsu, gabaɗaya zufa ce take ta keto masu, ta wanke fuskokinsu tamkar waɗan da aka watsawa ruwa, gabaɗaya parlourn da suke ɗin A.c ne a kewaye ta ko'ina, amma a haka suke haɗa wannan zuba saboda bala'in zilmi da fargaba da suke ciki, fatansu ɗaya shi ne Leesharh ta ɗauki wanna call ɗin, saboda wannan shi ne kawai damar da suke da shi, in har wanna dama ya kubce masu to abubuwa biyu dole su faru, na farko dole za'a kara tsananta tsaro a gidan Abu Abdussalam wanda ba zasu sake samun irin makamancin wanan dama ba, sannan dole su Ramish zasu shiga binciken wanenen yake yi masu wannan aiki?. Sun san wanene Ramish tsab zai iya kamasu, dan kwararrene a aikinsa, dole su shiga tsananin tashin hankali. Sai kiran wayar hannun Leesharh suke yi babu kakkautawa. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Call ɗin farkon ne ya katse na biyu ya sake shiga, Sharifat tana rike da hannunta ɗaya, call ɗin yana gab da katsewa ta sanya babban yatsarta zata ɗauka. Kamar daga sama aka bugeta ɗaya daga cikin jami'an da suka yi masu zobe, jama'a ne suka ture shi by mistake ya yi baya baya, to da yake ita da Sharifat ce a kusa da shi sai ya bugeta, ta ɗan yi baya ta bugi Sharifat wayar hannun nata ya faɗi ƙasa. Ina cikin cunkosan jama'ar nan ba ta yadda za'ayi ta tsugunna dan ta ɗauki wayar, tashin hankali iya tashin hankali ta shiga, ta rasa ya zatayi, ga shi wannan ɗauka call ɗin da zata yi shi ne aiki na karshe da zata yi wa masu nikaf a shirmenta wai sai su bata babanta. Sosai ta shiga tashin hankalin da har bata san lokacin da hawaye suka fara wanke mata fuska ba. A tunanin Sharifat saboda tashin hankalin da suka shiga a yanzu ne yasa take kuka, dan haka sai ta shiga bata hakuri tana gaya mata babu abin da zai samesu lafiya lou zasu koma gida. Ina ai ita tasan me take tunawa, cigaba da kukanta kawai ta rinƙa yi tana jin zuciyarta tana yi mata zafi. A haka aka fita dasu ta baya, babban tashin hankalinta na biyu bata taho da wayar ba, a tunaninta ta ina zata yi magana da masu nikaf ta ji ta gama aikin ne ko da saura?. Tun da suka dawo gida take kuka ta ki ta yi shiru, Sharifat ta yi lallashi har ta gaji amma ina taki ta yi shiru. Dan dole Sharifat ta rabu da ita ta je ta yi wanka tare da zuwa ta shirya cikin female arabs jallabiya, ta yi kyau sosai. Wayarta ta zo ta ɗauka domin ta kira number yayanta, dan hankalinta yaki kwanciya ganin ba'a tare da shi suka dawo ba, ta shiga damuwa sosai, dan dai kawai ba yadda zata yi ne. Numbersa ta shigar ta fara kira. Wayar ta yi ringing har ta katse ba'a ɗauka ba, Leesharh na kwance saman gado har lokacin tana murzan kukanta. 5 miss calls Sharifat ta yi wa Ramish amma bai ɗaga ba, hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, dik sai ta ji kanta yana jujjuya mata, addu'a ta fara yi Allah Ubangiji yasa yana lafiya. Miƙewa ta yi ta shiga toilet, alwala ta ɗauro tare da zuwa ta shinfiɗa dadduma, sallar mangariba ta gabatar tare da nafilfili ta shiga yi mashi domin Allah ya kare mata shi, wlh Sharrifat tana kaunar Ramish sosai. Addu'oi sosai ta rinƙa yi mashi a cikin sujjada. Ta ɗauki almost 4 hours a saman dadduma tana karatu da addu'oi bayan idar da sallah isha'i da ta yi, har kwallah sai da ta yi mashi!. Abin ya yi matuƙar ɗaga mata hankali. Daga karshe bayan ta kammala ne ta miƙe ta dawo wajen gadon, a lokacin Leesharh ta dai'na kuka sai ajiyar zuciya take saukewa. Wayarta Sharifat ta ɗauka, number Abbie ta kira. Bugu ɗaya ya ɗauka. Kamar zata yi kuka ta ce. "Abbie kana gida ne?". Abu Abdussalam dake kishingiɗe a saman wani shinfiɗa tasa ta alfarma mai kama da shinfiɗar sarakuna a cikin rest part ɗinsa ne ya amsa mata da yana gida kuma yana wajen hutawarsa. "To Abbie gani nan zuwa". Da okey ya amsa mata. Katse kiran ta yi tare da fara matsawa Leesharh a kan ta tashi zu je wajen Abbie. Har da ce mata. "Tin da ni kin ki ki ji rarrashina zaki ji na Abbie ai, sarkin tsoro kawai, ke daga jin anyi harbi da bullet zaki wani fara kuka! A haka kuma zaki auri Yah Bilal kenan?". Allah sarki Sharifat har ta bani tausayi, bata san cewa ba wannan ne a gaban Leesharh ba, hmmm wanna shi ne Sharifat tana goya yar kunama. "Ni Sharifat ki tafi kawai babu in da zan je". Da kyar voice ɗinta yake fita saboda kuka. "Allah babu in da zan je ba tare da ke ba, kawai ki tashi mu tafi". Make kafaɗa ta yi haɗe da tirjewa ita lallai ba zata je ba. Matsa mata Sharrifat ta cigaba da yi dan ba zata iya ganinta a cikin damuwa ta kyaleta ba. Hannu ta kai ta riƙo hannunta tana ƙoƙarin janta ta mikar da ita tsaye dan dole. Cikin ɗaga murya Leesharh da ranta ya gama ɓaci ta ce. "Ki sakeni babu in da zanje nace maki! Wai ana dole ne?!" Sam Leesharh bata san ta daka mata tsawa haka ba, ranta ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci. Zaro idanu Sharifat ta yi ba tare da ta saketa ɗin ba, nan take kuma sai ta ji zuciyarta ya tsorata da Leesharh, a take ta fara tunanin anya kukan tsoro Leesharh take yi kuwa? Anya babu wani abin a kasa kuwa? Kukan ne ya wuci na hankali yanzu kam. Ganin Sharifat ta zaro idanu ne yasa ta fahimci abin da ta aikata, dan haka sai ta yi kasa da kantah haɗe da riƙo hannayen sharifat cikin nata. "Ki yi hakuri sister, ban san na yi hakan ba". Kamar wadda aka sanyawa battery Sharifat ta ce. "Leesharh kukan me kike yi?".............. Ta yi maganar idanunta a kan Leesharh babu ko kyaftawa!. Nan fa Leesharh ta fara zazzare ido tana ƴan kame kame, ta rasa me zata ce, ita da kanta tana neman tonawa kanta asiri. "Am....... Ba........... Ba........ Babu komai". Ta faɗa murya a sarke. "Tun da ni ba zaki faɗa mun ba tashi mu je wajen Abbie sai ki faɗa mashi". Cewar Sharifat. Jinjina kai ta yi kafin ta amsa da. "Okey bari in yi wanka sai mu je". Kamar zata ce mata su je kawai, sai kuma ta ce bari ta kyaleta ta yi wankan zai fi. Toilet ta miƙe ta shiga dan ta yi wanka. Sharifat ta zauna a bakin bed tana jiran fitowarta. A bakin wash hand base ta tsaya tana kallon kanta a cikin mirror, Allah sarki har idanunta sun kumbura saboda kuka, haƙiƙa Leesharh tana cikin tsaka mai wuya baiwar Allah, daga gidan yari ta wuce wannan ukubar kuma, Allah dai ya bata ikon cin jarabawarta. Ta jima sosai tsaye tana kallon kanta kafin daga bisani ta wuce wajen haɗa ruwan wanka, dik jikinta a mace kamar anzare mata laƙa. Sharifat na zaune tana ta istigifari tana rokan Allah da yasa Ramish ɗinta yana nan lafiya, har Leesharh ta fito ɗaure da towel ta sameta. "Kisaka irin jallabiyata mu yi iri ɗaya Abbie zai ji daɗin hakan". Cewar Sharifat, ta yi maganar dai'dai lokacin da Leesharh zata shiga dressing room ɗinsu dan shiryawa. Jinjina kai ta yi haɗe da amsawa da okey sannan ta sa kai ta wuce. In short a shirye Leesharh ta fito cikin kaya irin na Sharifat, tin bata karisa in da Sharifat take ba ta miƙe ta nufeta. Hannunta ta rike suka nufi waje. Kai tsaye wajen Abu Abdussalam suka nufa. Yana kishingiɗe saman shinfiɗar ga kayan marmari a gabansa, yana sanye da white arabs jallabiya, dattijon arziki kenan. Yana ganinsu ya miƙe zaune, a saman shinfiɗar suka zauna, Leesharh ta gefen damarsa Sharifat ta gefen hagunsa. Sharifat tana rike da wayarta irin na Leesharh a hannunta. "Barka da dare Abbie". Sharifat ta faɗa. Bai kai ga amsawa ba Leesharh ma ta faɗi hakan. Cikin muryar dattaku ya ce. "Yauwa ƴaƴana.............. Leesharh menene ya sami idanunki?" Kasa ta yi da kai tana ƙoƙarin fara ƴan kame kame. "Abbie tin daga wajen taron nan da taga anyi harbi ta fara kuka, nayi ta rarrashinta ina faɗa mata babu abin da zai sameta amma taki yin shiru har sai da muka dawo gida". Tin da Sharifat ta fara magana kallonsa yake a kanta har ta dire, sannan ya dawo da kallonsa a kan Leesharh. Yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi maganar Ramish ya shigo wajen bakinsa a ɗauke da sallama. A miliyan Sharifat ta kai kallonta a kansa, shi kuwa hankalinsa sam baya a kansu, yana sanye da sleeping dress riga da wando milk color masu bala'in kyau, ya yi kyau sosai, dik da bashi da fara'a kullum fuska a ɗaure, amma da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci yana cikin damuwa, ya ƙara tsuke fuskarsa sosai, ya haɗe gerar kasa da ta sama. Saman sofas dake wajen ya zauna, sai wani kara tsare gida yake yi yana cin magani. Wani irin mummunar razanannen faɗuwar gaba Leesharh ta ji a lokacin da ta ɗaura idanunta a kan wayar dake hannunsa, tabbas wayarta ce da masu nikaf suka bata, to ya aka yi wayar ta zo hannunsa?. Ta jefawa kanta tambayar. Dakatawa da yiwa Leesharh magana Abu Abdussalam ya yi tare da mayar da kallonsa a kan Ramish. "My son ka dawo?". Cike da ƙaguwa da san jin amsar da Ramish zai bashi ya yi tambayar, cike kuma da tsananin fargabar abin da zai ji. Jinjina kai Ramish ya yi ba tare da ya yi magana ba. "To meyafaru and kiran me suka yi maka?". Cewar Abu Abdussalam. Ya jefa mashi tambaya cike da damuwa, dama tun ɗazun Ramish ya dawo daga wajen taron suna tattaunawa da Abbie ɗin nasu, yanzu ba jimawa jami'ansa suka kirasa a waya shi ne ya tashi ya tafi, ya ce da Abbie yana zuwa yanzun nan, dawowarsa kenan. Wayar Leesharh dake a hannunsa ya miƙewa Abu Abdussalam. Karɓa Abbie ya yi yana jiran a kora mashi bayani, shiru Ramish bai yi magana ba, kamar wanda baya san motsa lips ɗinsa, ya yi kasa da kai kamar mai tinanin wani abin. Gajiya da ƙaguwa da Abbie ya yi da san jin bayani ne yasa ya ce. "My son meyake faruwa ne?". Shiru Ramish ya kara yi har na tsawon good 2 mins. Sai kallansa Leesharh take sata kirjinta na dukan uku uku, ji take yi tamkar zata mutu, gabanta sai mummunar faɗuwa yake yi, alamar rashin gaskiya ne karara ya bayyana a saman face ɗinta, har wani zufa take ji yana keto mata. Ita ma Sharifat sai satar kallonsa take amma ita kallon soyayya take yi mashi ba ta wata manufa ba, dan ma dai tasan baya san yawan kallo ne yasa take kallonsa a sace, da a sarari zata gansa. Sarai Abbie ya gane cewa ƴarsa ta kamu da san Ramish da jimawa, amma ya zuba masu idanu yana ganin gudun ruwansu, baya san kuma ya faɗawa Ramish Sharifat tana sansa, ya fi san Ramish da kansa ta gane hakan ya kuma faɗa santa da kansa ba tare da an haɗa su ba. Sai dai Abbie abin ya fara damunsa yanda har yanzu babu wani canji a tattare da Ramish, ko kallo baya ɗaga idanun ya yi wa Sharifat, abin ya tsayawa Abbie a wuya, ba shi kuma da burin da ya wuce ya ga wannan haɗin ta yiwu, yana ji da ƴar nan tasa matuƙa. Sai da Ramish ya gama hatsewa da jan ajinsa, sannan ya ɗan gyara zamansa, ba tare da ya ɗago ya kalli ko mutum ɗaya daga cikinsu ba ya fara yin magana kamar haka, cikin sanyi murya haɗe da nutsuwa ya ce. "Wannan waya da na baka makunnine na tashi nakiya". Ɗan zaro ido Abbie ya yi, matsalarsa da Ramish kiwiya wajen yin magana, sam baya san buɗe baki ya yi magana yadda ya dace, sai dai ya yi wa mutun in short a dunkule, in ka gane kai ka sani, in ma baka gane ba nan ma kai kasani, kamar wani mai ciwon baki. "My son wai ba zaka bar wanan halin naka ba ko?". Cewar Abbie da ƙaguwa kamar ta kashe shi, yana bala'in san jin karin bayani!. Sai a lokacin ya ɗago da kallonsa a kan Abbie. Yasan a kan me Abbie yake magana, a kan rashin maganarsa ne, dan haka sai bai wani kula shi ba, alamar ba dainawa ɗin zai yi ba kenan!. "Bomb ne a kewaye da hall ɗin nan, wanna wayar ita ce matashin bomb ɗin, shi ne dalilin fitana yanzu". Cewar Ramish. Kallon Abu Abdussalam a kansa ya kara zaro idanu sosai, a hanzarce ya ce. "Bayan harin da aka kawo maka bai yi masu ba shi ne suka kewaye mu da bomb? To su wanene? Wai me ka tsarewa mutane ne?". Cike da tashin hankali Abbie ya yi maganar. Tamkar babu Ramish a wajen, bai sake cewa ko uppan ba. "Yanzu kun cire bombs ɗin ne?". Abbie ya sake jefa mashi tambaya. Wato idan baka da hakuri sosai ba zaka iya zama inuwa guda da Ramish ba, dan zai kasheka da takaici ne, sai ayi mashi magana goma bai amsa ɗaya ba, to in ba mai hakuri ba waye zai iya jure wannan walaƙanci fisabilillahi?. "Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Abbie Yah Ramish wannan ai wayar Leesharh ne!". Sharifat ta katsesu da faɗar hakan, ta yi maganar cike da tashin hankali maras misiltuwa, sannan ta yi maganar tana miƙewa tsaye haɗe da dafe saitin zuciyarta. Ramish and Abu Abdussalam har suna rige rigen kai kallonsu a kanta. A miliyan ita ma Leesharh ta miƙe tsaye.............. Wani irin zufa yana kara tsananta a saman face ɗinta, hankalinta idan ya kai dubu to ya tashi, jikinta sai wani irin kermar wahala yake yi. Da kyar ta haɗiyi wani irin azabbabben wahalallen yawu mai wuyar wuce maƙogwaranta. Miƙewa tsaye shima Abu Abdussalam ya yi kallonsa a kan Sharifat da kwayar idanunta tamkar zasu faɗi ƙasa saboda zarosu da ta yi!. Baiwar Allah jikinta har kerma yake yi, bata taɓa tsammanin makamancin hakan ba ko a mafarki. Ramish kam yana zaune bai miƙe ba, idan ka kallesa in the first place zaka yi zaton Sharifat yake kallah, amma kuma Leesharh yake kallo saboda ya gano abin da yake san ganewa, dama shi tin ainahi bata kwanta mashi a ransa bane yasa ya ce kada ta sake zuwa part ɗinsu, sai ga shi an kamata red handed. My people's me kuke tinanin zai faru a wannan waje? Akwai tashin hankali kuwa!!. Rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya ===========================🔥 ••••••••••••••••JIMETA🔥•••••••••••••••• Tsawon kwanaki biyu babu Jaish babu labarinsa, tin bappa yana sa tsammanin zai waiwayesu har ya dai'na, yanzu har ya fara rage damuwansa a kan haka, bawan Allah sai dai har ƴar rama ya yi saboda damuwa. A ɓangaren Nenne kuwa farinciki kamar ba zata mutu ba, burinta ya gama cika rayuwar Mahnoor ya lalace, ta zama karamar bazawara, bata wuce 15 years ba amma ta zama bazawara, abin ya yi wa Nenne da gwaggo mugu mugun daɗi. Shi kam hamma Faisal ya kafe a kan lallai tin da Jaish ya koma in da ya fito to shikenan a mayar mashi da matarsa Mahnoor, har da cewa dama ai Jaish aljani ne ba mutum ba, dan haka tin da ya koma duniyarsu na aljanu ai ba dawowa zai yi ba, so shi yana nan a kan bakarsa na zancen Mahnoor. Ya bi ya tayarwa da kowa hankali, shi lallai a yanke auren Mahnoor da aljani Jaish a bashi ita ya aura. Tin bappa yana kallan hakan a matsayin shirme har ya fara yarda da hakan ce kawai mafita, in ba haka ba Mahnoor ta shiga uku a wannan ƙauye, abin ku da ƙarancin wayewa da rashin ilimi, zasu sakota ne a gaba da zage zage da kananan manganganu kamar ita ta ɗaurawa kanta, barema da abin ya haɗu da bappa ya hana nasu ya baiwa bare, to wlh ba zasu barta ta yi zaman lafiya har ta ji daɗi a ranta ba, zata kai ta kawo fita ma sai ta gagara yi. So gudun takura mata yasa bappa ya fara tunanin Arɗo ya kashe aurenta da Jaish kawai a ɗaura aurenta da Faisal hakan zai sa ta samu sanyi da rayuwar farinciki. A ɓangaren ita kuwa Mahnoor, kwananta biyu a gidan Arɗo wajen kakarta Inna, kullun ɓuya take yi ta yi ta zuba kuka babu kakkautawa, tana tsananin san mijinta, sai ma yanzu da ya yi mata nisa ta gane ashe shi ne farincikinta. Wlh cikin ƙanƙanin lokaci ta yi wani irin zabgewa ta rame, harta wannan gurun wuyar tata da Jaish yake gani ya burgesa yanzu tsokar wajen ta zabge saura kashi. Mahreen da Jaish yake ba mijinta bama ta rame saboda damuwa da kukan bappa ya dawo mata da Hammanta, kunsan ta saba da shi, bare kuma Mahnoor da ita kaɗai tasan ya take ji a ranta, ya saba da yi mata abubuwa dayawa, yanzu har kasa yin barci take yi. Hankalin bappa ya gaza kwanciya na komawarta gidan Arɗo, dan haka yau ya shirya tsab zai je ya ɗauko. Ba zai iya yin nisa da ita ba. Zaune take a tsakar gida ta buga uban tagumi, tana sanye da kayan fulani, ta yi wanka tsab, sai dai da ganinta zaka san bata cikin walwala, fuska babu annuri, ta buga uban tagumi. Idan ka kalleta zaka yi zatan tana kallan Inna dake ta faman shanya masara a tsakar gidan ne, amma kuma ba haka bane, ta luluƙa duniyar tunani ne. Sallamar bappanta ya dawo da ita cikin hayyacinta. Tana ɗaura idanu a kansa bata san lokacin da ta rushe da kuka ba. Da gudu ta tashi ta nufesa, dik kunya irin tata yau bata san lokacin da ta ce mashi. "Bappa tare da hamma kuka zo?" Miƙewa tsaye Inna ta yi daga duken da take tana shanyar masara, tsakanin tausayin jikar tata ce ya kara kamata. Shiru ta zuba kasu idanu yana kallonsu, ji take yi kamar ta matsa masu kwallah. Bappa ya rasa abin faɗe, bashi da kwarin gwiwar iya sanar da Mahnoor ba tare da Jaish yake ba, dama ya zo da kwarin gwiwarsa ne zai sanar da Inna za'a mayarwa da Faisal matarsa tun yadda yaga sun ɗauki Jaish da wuya ya waiwayesu, sai kuma ya cikaro da wannan kuka da take yi na neman Jaish, anya zai iya sanar da ita wannan magana kuwa?. Ya jefawa kansa tambayar, jikinsa dik ya yi mugun sanyi. Mahnoor ta rungume shi tana ta kuka. Da gudu Mahreen ta fito daga ɗakin Inna, kai tsaye da gudu ta nufi bappa tana faɗin. "Bappa ina Hammanu yake?". Ta ƙarisa maganar idanunta cike tab da kwallah. Riƙota ya yi kawai ya runguma bai iya furta ko kala ba. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ==========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Ta ƙarisa maganar idanunta cike tab da kwallah. Riƙota ya yi kawai ya runguma bai iya furta ko kala ba. Inna da sun gama jikata da tausayi ne ta juya zata nufi ɗakinta dan ba zata iya ganinsu ba. Katseta bappa ya yi ta hanyar ɗaga mata gaisuwa. A daddafe ta amsa mashi tare da wucewa cikin ɗaki da sauri. Tana shiga ta zauna bakin gado tana addu'ar Allah Ubangiji ya sa kada Mahnoor ta gajesu, dan tun tasowar Inna a cikin kalubalen rayuwa take har Allah yasa ta auri Arɗo, ta taso ne a hannun kanin mahaifinta, ta fuskanci wahala wajen matarsa, shiyasa kuka ga tana da hakuri, baiwar Allah ta wahala ne, ta sha fama a gidan. Bayan aurenta da Arɗo ma bata huta ba, gwaggon Nenne har kusan haukatata ta yi a kan kishi a cikin wannan gidan, har yau har gobe kuma basu barta ta huta ba, suna bibiyar rayuwarta da sharri, dan ta tsaya da addu'a ne Allah yake kareta, amma ta sha bakar wahalar da ba zaku so ku ji tarihin ba, yawo a kan bola ne kawai bata yi ba, amma wlh haka kawai zata zauna ta yi ta ihu babu abin da aka yi mata, sai ta rinƙa jin namar jikinta yana wani irin masifar tauna tamkar an ɗaurata saman wuta. Dik wannan azaba ta jure, dan gara mata gidan Arɗon a kan gidan kanin baban nata, ga shi ita marainiya ce ba uwa ba ba uba ba, dik ta shanye wannan har Allah ya bata cikin mamar Mahnoor, nan ma ta ci wahala kamar ta mutu, da kyar ta sha maman Mahnoor ta zo duniya. Ita ma tin zuwanta duniya take shan wahala har ta koma ga Allah, aurenta da bappa kullum cikin ƙunci da kuka take, ya wahalar da ita har Allah yasa ita ma ta haifi Mahnoor. Ita ma Mahnoor tun farkon zuwanta duniya take shan wahala har zuwan Jaish cikin rayuwarta, ta ɗan samo sassauci kuma ace zata sake komawa cikin wahala? Abin da taɓa zuciya matuƙa. Sosai hawaye ya wanke fuskar Inna. Tsabar bakinciki da karayar zuciya har ta kusa furta saɓon Allah, saura kaɗan ta ce Allah baya sansu ne yake ta haɗasu da bala'i. Sai ta yi saurin kame bakinta tana furta istigifari. Allah sarki Allah baya jarabtar wanda baya so, dik wanda ya tsinci kansa cikin jarabawa ya ɗaga hannu ya godewa Allah ya kuma roki Allah da ya bashi ikon cin jarabawar, shi ne kawai ya dace da mumini, idan kaga baka shiga kalubalen rayuwa ma to wlh ka binciki imaninka da saura!. Ganin Inna ta shige ciki yasa bappa ya kama hannun ƴaƴan nasa suka nufi hanyar gida yana jin raɗaɗi a ransa. A hanya suka ci karo da Mairo zata shiga gidansu da yake kusa da gidansu Arɗon ne. Har kasa ta tsugunna ta ɗaga mashi gaisuwa. Cikin ba daɗi ya amsa. Sarai ta kula da babu farinciki a tattare da shi ko miskala zarratin, ga kuma su Mahnoor suna kuka, dan haka sai ta ce dan Allah in ba damuwa tana san yin magana da Mahnoor and Mahreen. Bai musa mata ba ya sake hannunsu ya ce su je wajenta. Da yake Mahnoor kam ta saba da ita kanwar mahaifiyarta ce sai bata yi gardama ba, tana zuwa ma ta rike hannunta tana cigaba da kuka. Cikin gida Mairo ta wuce da su, shi kuma bappa ya samu waje a karkashin wata bishiyar kuka ya zauna yana jiransu. Sun shafi good 30 mins a cikin gidan ka fin su fito, dikkaninsu sun daina kuka, fuska ba yabo ba fallasa, da alama Mairo ta iya kula da yara, tuni ta yi masu dabara sun yi shiru. Ba karamin daɗi bappa ya ji ba, bawan Allah har da sauke nannauyar ajiyar zuciya, ya ji ya kara samun kwarin gwiwa a kan aurenta, sai ya ji ma bai ga abin ɓata lokaci ba, gobe dole ya kamo shanu ɗaya ya kawowa Arɗo a kai gidansu matsayin sadaki, tin da ta sanya mashi yar marainiyarsa farinciki ai dole ta sanyaya mashi rai. Dole ayi wanna aure da wuri ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji. Ita ma ta lura da tabbas ya ji daɗi, sosai ta ji ta yi farinciki da Allah yasa ta sanya shi jin daɗi, da alama ita ma tana son shi sosai. Sallama suka yi mata ya riko hannun su Mahnoor suka wuce gida. Ya so su tsaya hira da Mairo ko shi ma zai samu sassaucin zogin da zuciyarsa take yi mashi, amma kash, saboda su Mahnoor da suke a tare da shi yasa ya ce mata sai dare yana zuwa. Daga haka suka wuce gida. Nenne na zaune a tsakar gida ta baje tana cin ɗinya da addu'a suka iskota, ta yi zaman ƴan bori a kasa tana wani cika tana batsewa. Ko ci kanki bappa bai ce mata ba ya wuce zai shiga cikin ɗakinsa rike da hannun ƴaƴan nasa. "Kwairaga magana nike san yi da kai!". Cike da isa da gadara ta yi maganar, yau babu bappan Mahreen da ake cewa, rashin mutuncin ta motso kwairaga kai tsaye aka kira. Ko a gefen takalmarsa, tamkar bai san da wata halitta a wajen ba ya wuce zai shi ga ɗaki, shi fa namiji kunsan dik in da yake hakan nan dai yake hali baya canzawa, to shi ma fa bappa namiji ne, kun san idan maza zasu kara aure har wani sabon iskanci da waƙalanci ƙwaƙwalensu take karowa, su rinƙa jin kansu a saman iska, sai su ji zasu iya yin komai a kan wanna aure nasu, kamar basu taɓa yi ba, ayi ta rawar kafa ana wani kauɗi kamar angon kare, to yaseen haka suke, a jininsu abin yake. Idan baki da wayau kika biye masu kika kulasu takaici ya sa zuciyarki ta buga, idan kuma kina da wayo kin san in Allah ya kaddara sai an yi sai ki bawa iska ajiyar ɗan albarka, yana kauɗinsa ki yi kamar baki san da halittarsa a cikin gidan ba, wlh da kansa zai damu sosai, ya yi ta jin kamar ya fasa aure, zai ji kamar ba shi ba, dik wani kauɗi zaki ga ta ragu. Amma in kika nuna ɓacin rai yaseen kara wa zai yi dan ya shaƙa maki takaici. To kun dai ga bappa ya karo sabon walaƙanci, da dik iskancin da Nenne take yi mashi yana daurewa baya kin yi mata magana, amma yanzu ina ai banza yake bawa ajiyarta, bata isheshi ya ɗaura idanunsa a kanta ba, ango na Mairo bada kanka a sare ba............😅 Mu dai ba abin da zai hana mu zuwa wanna biki, ai ko dan mu je a kayar mana da shanu a yanka, mu ci nama mu kora fura da nono mu godewa Allah dole fa mu je.......... Nenne sai dai a mutu idan za'a mutu. Ganin bai kulata ba yasa ranta ya yi matuƙar ɓaci, kamar wata aljanar ruwa ta miƙe fuuuuuuu kafafu kamar na shamuwa sai cikin ɗakin nasa. Daidai lokacin ya ciro kayan Jaish dake maƙale a bayan kofa ya miƙawa Mahnoor yana ce mata ta ajiye wannan kaya a ɗakinta na mijinta ne. Kamar wata walkiya sai ganin Nenne suka yi a tsakaninsu. Sai da Mahnoor ta tsorata ta miƙe zata gudu, baiwar Allah ta saba shan ukubar Nenne, to a tinanina dukanta Nenne ta zo yi shi ne zata gudu. Wuyar rigar bappa Nemne ta riƙo, ko tsoron Allah babu bare kunya, a gaban ƴaƴansa ta fara jajjaga mashi jajjagen masifa da bala'i kwando kwando kamar wanda ake yi mata wahayinsu daga duniyar shaiɗanu. Riko hannun Mahreen Mahnoor ta yi tare da ɗan cewa. "Zo mu je gidan Inna Rabi". Mahnoor yarinya mai hankali da sanin yakamata!. Mahreen da faɗa a jininta yake ga kuruciya a kai ne ta ce. "Ke ni babu in sa zanje Adda Mahnoor, ki bari in taya bappa faɗa mu ci uban Nenne". Ai daga bappan har Nenne basu san lokacin da suka dawo da kallonsu a kanta ba. Mahnoor da tsabar zaro ido tamkar kwayar idanunta zasu faɗo kasa ne da kyar ta ce. "Mahreen kina da hankali kuwa? Kin san me kike faɗa kuwa?". "Nasani mana, baki ganin Nenne ta kama bappana da faɗa ne? Ni zan taya shi mu mata shegen duka, ni kaɗai ma na isheta ba sai bappa yasa hannu ba". "Innalilahi wa inna ilahir rajiun". Shi ne kawai abin da Mahnoor ta iya sake faɗa. Shi kam bappa ya rasa abin faɗe, wannan wace iriyar tarbiya Nenne ta bawa ƴarta? Ko da yake maganinta kenan ai, ba ita ta lallata Mahreen ɗin da faɗa ba, tun tana yarinya take yi mata huɗubar dik wanda ya daketa ta dage ta rama, ai ga shi yanzu za'a daki bappanta zata rama mashi, harda uban wanda zata dake shi ɗin za'a ci wato Arɗo kenan. Sai yanzu Nenne ta gane Mahreen da take kauna take fifitawa fiye da komai ta fi kaunar ubanta a kan ita. Mata kalubale gareku, ku so ƴaƴanku duniya ta kisu, kai har Allah da manzonsa ba zasu yi alfahari da su ba, idan kika daure kika kawar da kai kika danne kika basu tarbiya mai kyau kika kisu sai duniya ta sosu Allah da manzonsa su so su. Da karfi Mahnoor ta ja hannunta tare da tsawatar mata a kan ta zo su tafi. Tana kwaɓe fuska ta bi yar uwar tata, sai mita take yi a kan ita a kyaleta su kwashi ƴan kallo da Nenne a kan bappanta. Sai kwaɓar bakinta Mahnoor take ya faman yi har suka fita. Suna fita bappa ya dawo da kallonsa a kan Nenne da ta saki baki tana ganin ikon god, waye ya ce maki Allah wasa ne, hmmmmm kaɗan ma kika gani. "Zaki iya sakeni? Dan ina da abin yi ne!". Ya faɗa yana kawar da kallonsa daga kanta, sam yanzu baya san tashin hankali, dan baya san abin da zai mayar da shi ruwa wajen dukan mata kamar a baya kan maman Mahnoor. Nenne da jikinta ya yi mugun sanyi ta kasa ko motsawa ne ta tsare shi da ido ba tare da ta sake shi ɗin ba. Hannunsa yasa ya kwace wuyar rigar yasa, ba tare da ya sake furta uppan ba ya sa kai ya fice waje ya kyaleta tsaye baki buɗe galala. Nima kai nasa na wuce izuwa kingdom of power na barta baki a sake galala. =========================🔥 ••••••••••KINGDOM OF POWER•••••••••••• Daga ita har Jawad ɗin kyakkyawar shiga irin na ƴaƴan manya manyan sarakuna aka yi masu. Tsadaddun alkyabbars king da kansa ya ɓalle masu a ledarsu, dikka alkyabbar iri guda ne, babu wani bannanci. Sai dai da amarya da angon dik basa a cikin nutsuwa da kwanciyar hankalinsu a lokacin da ake ƙoƙarin shirya su ɗin. Ita Chuchu hankalinta gabaɗaya ya tashi tana neman ina Auta take? Dama a bisa ƙaida babbar aminiyarta ce zata tsaya a gefen hannun hagunta, while gefen damanta kuma angonta ne a wajen, shi ma ango a gefen hagunsa babban amininsa ne zai tsaya a wajen. Sai dai daga shi har ita basu san ina aminan nasu suke ba, shi Jawad ya rasa Jaish a rayuwarsa wanda shi kaɗai ne amininsa kowa yasan da haka. Ita ma Chuchu sai neman Auta take yi shiru bata ganta ba har lokaci ya kusa. Sai gwada numberta suke yi, wayar tana shiga amma ba'a ɗauka. Hankalinta in ya kai miliyan to a tashe yake, ta shiga damuwa matuƙa, ga shi ba halin ta ce Auntynsu Jawad su dakata da yi mata kwalliya bari ta nemo Auta, ba zasu dakata ba, ga momma bata wajen bare ta nemi alfarmar momma ta dubo mata Autar, ita momma tana can tana fama da nata bakin. Dik wannan kiran wayar Auta da Chuchu take yi Hoorain yana kwance saman bed ɗinsa yana kallon kiran, tin bayan barinsa wajensu Ansar ya dawo room ɗinsa ya kwanta. Wayar tana hannunsa ya kasa matsar da ita daga kan face ɗinsa, ya kai ƙololuwa wajen shiga tashin hankali a yanzu, idanunsa sun fara rena fata, dik in ka gansa sai ka ji gabanka ya faɗi saboda yadda yake a hargitse. Haka Auntynsu Jawad ta tsarawa Chuchu kwalliya, amma sai dai kash dik wannan kwalliyar da ake ta faman tsara mata idanunta ƙoƙarin cikowa da kwallah ma suke yi. Auntynsu Jawad ta lura da hakan, dan haka sai ta shiga bata hakuri, a tunaninta Chuchu tana san yin irin kukan da amare suke yi nan ne, bata san ita wanna ba shi ne a ranta ba, Auta take nema yasa zata fara yi masu kuka babu gaira babu dalili. A ɓangaren shi ma Jawad, su uncle Taheer suna yi mashi kwalliya hankalinsa yana a kan tunanin Jaish and Yah Rizwan, yau zai yi aure Jaish baya nan, bashi da babban aboki yanzu, shi ko ƙaramin abokin ma bashi da shi bare babba, Jaish jinin jikinsa ne kawai, komai nasa, ga shi babu shi babu labarinsa. Hakan yasa ya ji tamkar a fasa wanna taran dinner ɗin, yanzu in sun je ma za'a nemi wanda zai karɓi mic ya yi bayani a kan halin ango babu, dan dik wanda zai san halin Jawad to fa ya biyo bayan Jaish kamar yadda dik wanda zai san halin Chuchu to ya biyo bayan Auta, haka suke!. Karfe 11 dai'dai wajen taro ya cika makil da ƴan'mata da samari, kowacce tana ji da kanta, abu ne na jinin sarauta da jinin sarauta suka haɗe a wajen, kowa ji da kansa yake yi, babu mai ɗaga idanun ya kalli ɗan uwa, kowa yana jin ya wuce class ɗin ɗaga ido ya kalli mutum a wannan waje. Da yake su momma ba halartar wajen zasu yi ba sai basu san cewa babu Auta ba, Fanan ita ta mayewa Chuchu gurbin Auta wanda kowa daga cikin family ya gansu sai ya yi magana ya tamabayi ina Auta da Fanan ta maye gurbinta?. Sai dai Chuchu ta ce masu ta shige cikin ƴan biki bata ganta ba. Sam basu kawo komai a ransu ba, dan babu wanda ya yi tunanin faruwar wani mummunar abin a wannan rana. So ga kuma baki dayawa, sai kowa ya ce kila tana wajen ƴan uwan mommarta da suka zo daga Dubai ne, kila zumuɗin ganinsu yasa ta je ta manne masu!. A ɓangaren Jawad kuma Abdussalam wato yayan Sharifat ɗa ga Abu Abdussalam na farko shi ne ya maye gurbin Jaish wajen tsayawa a gefen Jawad suka shigo cikin hall ɗin. Saman kujerar da aka tanadawa amarya da ango Jawad ya zauna, Abdussalam ya tsaya a gefensa, shi ma Abdussalam ɗin ba zai wuci mate na Jawad ɗin a shekaru ba, kyakkyawa ne sosai, da ka gansa zaka san jini ɗaya suke da su Jaish, ga shi very gentle so silent haka. Amma wayayyene sosai, ga ilim both sides, bai da wani fara'a kamar dai Jawad ɗin, ya fi kama da Abu Abdussalam shiyasa akwai yanayin kama da su Jaish a tattare da shi, dan kun san babu abin da ya rabe Momma da Abu Abdussalam. Saman kujerar da aka tanada masu Jawad ya zauna kansa a ƙasa, sai yau sabon kewar Jaish ya dawo cikin rayuwarsa, ji yake yi kamar ya yi ta kuka babu kakkaunatwa, ya kasa hakuri har sai da ya ce. "Where are you my twins brother? I really missed you a lod, I feel like I'm not feeling well cause of u". Dik da ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar Abdussalam ya ji shi, kuma yasan me yake yi wa wannan sambatu, dan haka sai bai kula shi ba, sai ma ya nemi kawar mashi da zancen ta hanyar cewa. "Jawad where's my wife? Tin da nazo fa bamu haɗu da ita ba, taki zuwa in da nike, kuma nasan fushi take yi dani sabida wancan zuwanta Dubai na yi mata ba dai'dai ba, naki zuwa mu haɗu da ita har ta dawo, so nasan fushin ne har yanzu bata huce ba". Magana yake yi a kan Auta wadda tun tana jaririya ya ce da Momma shi fa ga matarsa, tin suna ɗaukar abin wasa har suka fara mayar da wasa izuwa gaskiya, har yau har gobe da my wife yake kiranta, tin bata amsawa har ta fara amsawa, yana santa sosai. "Tana nan zata shigo a tare da Jannat". Jawad ya bashi amsa da kyar, dan har voice ɗinsa bata fita sosai. "Gaskiya yakamata na ganta, i really missed her fa, yanzu almost 8 to 9 month rabon da na sakata a idanuna, this time bata je Dubai ba". Nisawa Jawad ya ɗan yi, cikin yanayi maras daɗi da damuwa ya buɗi baki zai yi magana kawai shararren mc da ake ji da shi a faɗin ƙasar ya yi sanarwa a kan amarya na shigowa. Gabaɗaya kowa kallonsa ya kai a kan kofar shigowa, kowa dama yasan kalar amaryar, wato ƴar wanka ce, bare kuma yanzu da ya kasance ranarta ce, ai abin sai dai kawai ka daure ka kawar da kallonta daga kanta, amma ba wai dan zaka gaji da kallan kyanta da kwalliyarta ba. Miƙewa tsaye Jawad ya yi a lokacin da ta sako kyawawan fararen kafafunta dake sanye cikin Queen cover shoes masu high sosai cikin wajen. Ba komai ya sanya Jawad miƙewa ba face abubuwa guda biyu, na farko kyan da Allah ya zuba mata ya gaurayu da tsararren kwalliyar da ya tashi kan dik wanda zai ɗaura idanunsa a kanta, na biyu kuma ganin Fanan a side ɗinta ba Auta ba, ya girgiza matuƙa na ganin Fanan a gefenta, to ina Auta?. Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsarta. A take ya ji gabansa ya yanke ya faɗi, har wani sara mashi ya ji kansa ta yi!. Dik da cikin alkyabba take kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, hakan ba zai hana kaga tsantsar damuwa da take a ciki ba, idanunta har sun yi ja baiwar Allah. Tin da ta shigo wajen har ta karisa kusa da ango hannunta na'a kan screen ɗin wayarta tana ta faman gwada number Auta, taki hakura sam. Tana ƙarisowa kusa da angon nata ya sa hannun biyu ya riko nata hannayenta da suka sha kunshi dan ya taimaka mata wajen hawa saman stage ɗin dake wajen. Jama'ar wajen ne gabaɗaya suka ɗauki tapi rap, rap, rap, kowa ya miƙe tsaye yana jiran amarya da ango su zauna sannan shi ma ya zauna. Abin ya ƙayatar da mutane yadda Jawad ya taimaka mata wajen haurowa sama. Tsakuwa ta yi a kusa da shi kanta a ƙasa. Kasa dannewa ya yi har sai da ya ce. "Jannat ina Auta?". Kamar jira take yi wani ya yi mata magana ta fashe da kuka, haba ai sai ruwan hawaye wani na bin wani. Kowa ya ɗauka kawai kukan amarci ne. Rikicewa Jawad ya yi, a tsorace ya ce. "Jannat Auta na tamnayeki ba fa kuka nace ki yi ba, ina take?!". Wayarta ta miƙa mashi tana ƙoƙarin juyawa da nufin ta bar wajen, a cewarta zata je ta nemo Auta, dan haka kawai take jin kamar akwai wani tazara mai tsawo a tsakaninta da Autar. Riƙo hannunta da kyau ya yi tare da zama a saman kujerar ya zaunar da ita, sannan ya saketa ya mayar da hankalinsa a kan wayarta, number Autar shi ma ya shiga kira babu kakkautawa. Mc sai cika mutane da surutu yake yi yana yabon amarya da angon da bai san yanzu haka wutar tashin hankali ce yake ruruwa a cikin zuƙatansu ba!. •••••••••••••••••••••••••••••••••GUYSON💘 Kwance yake saman gadan Mommarsa, daga shi sai short, babu ko singlet a jikinsa, ya kudundune a cikin bargo kamar mai jin sanyi, a hankali hankali yake ɗan jujjuyawa a saman bed ɗin kamar wanda bashi da lafiya. Tun da yamma gabansa yake faɗuwa, fargaba kamar zai kashe shi, ya kasa halartar wajen dinner ɗin, zuciyarsa haka kawai take tsinkewa, ya shiga damuwar da bai san dalilinta ba. Bawan Allah jini ai ba wasa ba, shaƙuwa kuma ba karya ba. Haƙiƙa ko mu mun shaida gimbiya Zunaira wata ɓangarece ta rayuwarka Guyson, mun shaida hakan, Allah sarki, rashinta yasa mashi ciwo ba tare da ya sani ba. Ya shiga mawuyacin halin da bai san dalili ba, ya faɗa damuwa ba gaira babu dalili, jikinsa dik tamkar wanda aka tsinkewa jijiyoyin jininsa. Gajiya ya yi da juyin da yake ta faman yi babu wani sauki da ya samu dangane da abin da yake ji a ransa, hakan yasa ya miƙe zaune. Kafafunsa ya zuro kasa, kamar wani ɗan yaro, sai turo baki yake yi, a haka ya miƙe. Sai dai yana da kunya dai'dai gwargwado, dan haka sai da ya ɗauki arabs jallabiya ya sanya a jikinsa, gashin kansa dik a watse kamar wanda ya taso daga ciwo. Waje ya nufa yana jan kafafunsa kamar baya san motsa jikinsa. Part ɗin King ya nufa dan yana da tabbacin zai samu Mommarsa a can. Babu wanda suka haɗu da shi a hanya har ya ƙarisa cikin part ɗin. King baya cikin room ɗin, yana cikin toilet yana wanka. Momma tana kwance a saman bed ɗin King kamar wadda bata da lafiya, ta yi shiru tana fuskantar sama, ita kanta tin ɗazun gabanta yake ta faman faɗuwa, zuciyarta yana ta tsinkewa, ta rasa menene sila. Sai addu'a take yi a kan Allah Ubangijin ya sanya dik wani abin da zai tinkarota na masifa da yake sanyata faɗuwar gaba ya rikiɗa ya zamana alkhari. Dik wani bawa da yake jin kamar wata musifa tana tinkaro shi, yana yawan jin faɗuwar gaba to ga addu'ar da zai yi wanda zai sa Ubangijinmu ya juya wannan abin zuwa alkhari, in ma kaddararsa ce ta zo a haka to Allah zai saukaka mashi abin ya zo mashi da sauki, zan rubutu maku addu'ar da hausa dan ina samun korafi a kan rubuta shi da larabci da nike yi, wasu basu iya karatun larabci ba, so addu'a addu'a ce koma da wace yare ka yi ta Allah zai jika, gata kamar haka haɗe da fasararta dik na haɗa na rubuta maku da Hausa dan ku fi fahimta da kyau, Allah yasa mu dace. "Hasbiyallahu laa ilaaha illa Huwa, alaihi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-‘Arshil-‘Azeem." Fassara. Allah Ya ishe ni, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, a gare Shi na dogara, kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma, shi kaɗai zai iya kareni daga dik wata sharri. Sai cikin Alqur'ani mai girma, Suratul Baqarah Surah ta 2 bayan Fatiha kenan, aya ta 286. Wannan ita ce aya ta ƙarshe a cikin Suratul Baqarah, kuma tana ɗaya daga cikin mafi girman addu'o'in Al-Qur'ani don neman gafara, rahama, da taimako daga Allah, wannan addu'a idan kika yi ta bata da shamaki da isa ga Ubangiji, kika yi ta da tawali'u ki kaddara addu'aki ta karɓu kawai, dan bata da shamaki kai tsaye take wuce zuwa ga rabbil izzati, ita ce addu'a kamar haka. "Rabbanaa laa tu’aakhidhnaa in nasinaa aw akhṭa’naa. Rabbanaa wa laa taḥmil ‘alainaa iṣran kamaa ḥamaltahu ‘ala-l-ladheena min qablinaa. Rabbanaa wa laa tuḥammilnaa maa laa ṭaaqata lanaa bihi wa’fu ‘annaa waghfir lanaa warḥamnaa anta Mawlaanaa fanṣurnaa ‘ala-l-qawmi-l-kaafireen." Fassara. Ya Ubangijinmu! Kada Ka kama mu idan mun manta ko mun yi kuskure. Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora mana nauyi kamar yadda Ka dora wa waɗanda suka gabace mu. Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora mana abin da ba za mu iya ɗauka ba. Ka yafe mana, Ka gafarta mana, Ka jiƙanmu. Kai ne Majiɓincinmu, Ka taimake mu kan mutanen da suka kafirta suke binmu da sharri. Addu'a ta uku a kan Allah ya kareki daga dik wata masifa da kike jin kamar tana tinkaro ki shi ne. "A‘oozu bikalimaatillahi-ttammaati min sharri ma khalaq." Fassara. Ina neman tsari da kalmomin Allah masu cike da kamala daga sharrin duk abin da Ya halitta. Manzon Allah (SAW) ya koyar da wannan addu'ar don neman kariya daga kowanne irin sharri, so addu'a ce mai karfin gaske, idan kika riketa wlh wane mutum sai dai ubangijin mutum!!!. Addu'a ta huɗu kuma mafi tsada, wannan addu'a idan kika yi ta da safe kafa uku, Manzon Allah ya yi rantsuwa a kan babu wata sharri da zata sameki, safe da yamma ake yi, in kika yi ta uku da safe wlh a wannan wunin ranarkam babu wani sharri da ya isa ya kusantoki, dik balai'n mutum nan zai ganki kuma yarbi, Allah zai saukar da Mala'iku daga sama domin baki kariya wunin wannan rana har zuwa yamma, in kika sake yin kafa uku da yamma to fa har zuwa washegari da asuba kina cikin kariyar Ubangiji. Sai dai ki sani addu'a babu cikakkiyar Tauhidi fa Allah baya karɓarta, sirrin addu'a ita ce idan zaki roƙa ki sanya a ranki cewa Allah ya gama biya maki buƙatar ma kawai, ki sa a ranki dama babu wanda zai biya maki sai shi!!. Ga addu'ar kamar haka. "Bismillahil-ladhi la yadurru ma’asmihi shai’un fil-ardi wa la fis-sama’i wa Huwa-s-Sami‘ul-‘Alim." Fassara. Da sunan Allah wanda ba zai yiwu wani abu ya cutar da mai ambatonsa ba a sama ko a ƙasa, kuma Shi ne Mai ji, mai sani a kan komai. A karanta sau uku safe da yamma, domin samun tsari daga sharrin duniya gabaɗaya!. Allah ya cigaba da karemu daga dik wata sharri!. Waɗan nan addu'oi Momma take ta karantawa dan ta samu saukin abin da take ji, hakan ne ma yasa mutuwar Zunaira bai yi mata wani tsananin tasiri ba, Allah ya dafa mata zuciyarta ya ɗan sanyaya dalilin wannan adduoi. Guyson na shigowa ya haye saman gadon, kusa da ita ya matso, tana kwance idanunta a sama, jin motsinsa yasa ta ɗan yi kasa da kallonta izuwa kansa. "Lafiya Omar?". Ta yi maganar da kyar. "Momma jikina ne dik yake mani some how na kasa ganewa, and kaina yana ɗan sara mun, kamar bani da lafiya". Tin da ya fara magana idanunsa suka cicciko da kwallah, dama kun san halinsa mai kukan ciwo ne, da zarar ya fara ciwo zai fara kuka. Allah sarki babu juriya!. Yana kai karshen maganar kuma ya kwantar da kansa a saman laps ɗinta yana shirin fara yin kuka mai gabaɗaya. Miƙewa ta yi zaune a tsakiyar bed ɗin, hakan ya bashi damar kara gyara kwanciyarsa a saman laps ɗin nata. Daidai lokacin King ya fito sanye da jallabiya ruwan hoda a jikinsa, sai tashin kamshi yake yi. Ganin Guyson nasa a saman bed ɗin ga kuma hawaye a face ɗinsa yasa ya kariso da sauri yana tambayar ba'asin meyake faruwa?. Yana ganin King ya kara rushewa da kuka mai ɗan sauti, kukan shagwaɓa har da shessheƙa. Hankalin King ne ya kara tashi, dama shi bai wani san halinsa sosai ba, dan in baku manta ba girman Dubai ne shi, Momma ce tasan kayanta tsab, dan haka bata wani rikice sosai ba, dan tasan a kan ɗan buge hannu a jikin bangoma guyson kuka yake yi bare azo ga ciwon kai ko ciki, ai sai ya wuni yana kuka!. Sakalene.........😅 A hanzarce King ya haye saman bed ɗin yana kara tambayarsa me yake faruwa?. Ya yi maganar tare da kai hannu yana ɗan ɗagosa daga jikin momma. Ai tin bai gama kai hannu jikinsa ba ya miƙe ya faɗo jikin daddyn nasa yana kara tsara kukan shagwaɓar tasa da kyau, har da hawayen iyashege!. Kallon momma da bata wani damu sosai ba King ya yi. "Rahilarh lafiya? Me kika yi mashi?". A rikice ya yi tambayar. "Wai jikinsa ne yake yi mashi ciwo shi ne yake kuka".............. Ta bada amsa tana kai hannu zata taɓa gaban goshinsa. Zaro idanu King ya yi, ya kara shiga damuwa. Muryarsa har tana ɗan sarkewa saboda saurin wajen furta magana ya ce. "Miko mun wayata bari in kira Dr ya zo". Ganin yadda ya rikice ya tashi hankalinsa haka abin ya ɗan bawa momma mamaki, dan ita tasan halin kayanta, a ganinta yanzu haka idan aka bincika ba wani ƙwaƙƙwaran ciwon da yake damunsa. "A'a dare ya yi, ka bari sai zuwa da safe se mu kai shi hos........" Wani irin cin burki ta yi a maganar tata bata karisar ba, ba komai ya ja hakan ba kuma face zaro mata idanu da King ɗin ya yi. Cike da mamaki ya ce. "Rahilarh kin san me kike faɗa kuwa? Mu bari sai da safe fa kika ce?". Kai ta jinjina mashi alamar tabbatarwa da yes hakan ta ce. "Amma lallai Rahilarh baki san me bakinki yake faɗe ba, kinfa san Omar tun yana karamin yake fama da ciwon ciki, kuma kin san yanayin tsananin azabar da yake sha idan ciwon nan ta tashi, ba godiya zaki yi wa Allah ba da yasa yau ciwon ta tashi har yake iya yin magana? Ai hamdala zaki yi ki kuma yi gaggauwar taimakawa wajen kiran Dr dan sauki ya fara samuwa, amma sai ki ce mu barshi sai da safe, Omar ɗin nawa?". Momma dai bata wani damu ba, ta miƙa hannunta ta ɗauko wayarsa dake saman bedside drawer ta miƙo mashi tana ce mashi. "Allah ya huci zuciyarka ranka ya daɗe, ga wayar". Karɓa ya yi da sauri, yana rarrashin guyson, number Dr ya shigar dan ya kirasa ya zo ya duba mashi ɗan lelensa. Sai binsu da kallo Momma take yi, guyson yana kara narkewa haɗe da kukan shagwaɓa. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ==========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Babban Dr na hospital ɗinsa King ya kira, cike da bada umarni ya ce dik abin da yake yi ya bari ya yi maza ya zo gida Omar ɗinsa bashi da lafiya. Cikin girmamawa Dr ya amsa da In Sha Allah ga shi nan zuwa yanzu. Katse kira King ya yi ya hau rarrashin guyson babu kama hannun yaro, kun san irin wannan yanayi da zasu ga mutum ya yi kasa gane me yake yi mashi daɗi irin hakan sam babu daɗi, sai ka ji a takure kake a duniya. Momma jiki dik a mace sosai, komawa ta yi ta kwanta tana tunanin meyake faruwa da ita ne haka?. A haka Dr ya zo part na King ya samesu, da yake kowa ya san Drn King ne sai babu wanda ya tare mashi hanya, suka bashi dama ya shiga har tsakiyar parlon, sallama ya yi haɗe da dakatawa a wajen. Kallon guyson da kyau King ya yi. "Tashi mu je Dr yana parlour ya duba mun kai". Kai ya fara girgizawa, yana kuka ya ce. "Ni daddy bana san Dr ya dubani, ya tafi kawai". "Meyasa to?". King ya jefa mashi tambayar. "Bana san ya yi mun allura, ni dai gaskiya ya tafi zan ji sauki". Yana magana yana kara tsananta kukansa. Lumshe idanunta Momma ta yi kamar mai jin barci, dama ita tasan idan ba Dr Raj ba babu mai iyawa guyson, Dr Raj ma sai in su Ramish suna nan ne zaku ga ya yarda ayi mashi allura, nan ma yana kwance jikin ɗaya daga cikinsu suna ɗauke mashi hankali sannan ake yi. "Dr ba zai yi maka allura ba, i promised you that". Kara ƙanƙame King ya yi yana faɗin a'a shi dai ba zai je ba. Ba yadda King bai yi ba ya ce shi dai a'a ba zai je ba, daga ƙarshe ya hakura ya ce da Dr ya tafi abinsa dan shi ma ya lura ba ciwon cikin guyson ɗin bane ta taso. Haka Dr ya juya ya koma asibiti dan ya cigaba da yin aikinsa. Guyson kuwa King ya cigaba da lallaɓa shi har barci ta ɗauke shi a nan, momma kam miƙewa ta yi ta basu waje, ta koma room nata. Tana shiga ta ɗauki wayarta, wata number ta kira wanda aka yi saving da my happiness. Kwanciya ta yi a saman bed ɗin nata tare da shigewa cikin bargo. Call ɗin ya yanke ba'a ɗauka ba, tana rike da wayar sai ga shi an biyo kiran nata. Cikin sanyin murya ta yi sallama. Baka jin me ake faɗa ta cikin wayar sai dai ita da ta amsa da lafiya alamar gaisuwa aka ɗaga mata. Jim ta ɗan yi kafin ta sake cewa. "Lafiya ta lou kawai dai ina jin jikina dik a mace ne yasa voice ɗina ta yi haka". Shiru ta ɗan sake yi alamar tana sauraran abin da ake faɗe, can sai ta ce. "No ba barci nike ji ba". Shi ma King ganin guyson ya yi barci yasa ya kwantar da shi haɗe da ja mashi bargo ya miƙe ya sauko kasa daga saman bed ɗin. Waje ya nufa. Bai zame ko'ina ba sai room ɗin Auta, dama kunsan baya yin barci har sai ya yi mata addu'a. Ya sha madarar mamakin ganin bata can, har ya mance da ana dinner, fitowa ya yi zai nufi ɗakin mommarta ya dubata a can sai ya tina da ai ana dinner su Jawad, dan haka tana can, bai so ya kwanta ba tare da ya yi mata addu'a ba, amma ba yadda ya iya, sai kawai ya juya ya nufi part ɗin Akka domin ya ganta kafin ya kwanta. Already yar tsohuwa ta yi barci, dama in baku manta ba ba koshin lafiya ne da ita ba tin ɓacewar Spender. Ganin already ta yi barci yasa ya matso a hankali ya tofa mata addu'a tare da rage mata gudun A.c, sannan ya fito ya koma room ɗinsa. Ya sha madarar mamaki a lokacin da ya shiga bedroom ɗin nasa, kara waro idanunsa waje ya yi domin ya tabbatar wa kansa abin da yake gani gaskiya ce ko karya. Babu guyson babu labarinsa, mutumin da aka bari yana barci, da sauri King ya karisa gaban bed ɗin dan ya tabbatar. Tabbas da gaske ne Omar baya cikin ɗakin, to ina yake? King ya jefa kansa wannan tambaya. A hanzarce ya juya ya nufi part ɗin Momma dan ya duba ko ya koma can, a tunaninsa kila da ya shiga ɓangaren Akka ne guyson ya wuce ba tare da sun haɗu ba. Shi kuwa guyson yana tsaka da barci ne ya ji ana ta ambatar sunansa, tin yana jin abin da ɗan nesa nesa har ya fara jin hakan a kunnensa, abin kamar a mafarki kamar kuma a gaske, ba muryar kowa yake ji ba kuma face muryar Auta, tana kuka tana kiran sunansa. Hakan yasa ya farka a firgice, har zufa sai da ta wanke mashi face ɗinsa, ya tsorata sosai na hakan. Kamar zai yi kuka ya fara goge zufar dake face ɗinsa da tafukan hannunsa. Kamar daga sama ya sake jin sautin muryar Auta a kunnensa tana kuka tana kiran sunansa. Ba ƙaramar razana ya sake yi ba, sai a lokacin ya tuna yau fa tun da rana bai sake haɗu da ita ba, tin da suka haɗu wajen ɗakin da Chuchu take ana mata ƙunshi, tuna hakan yasa ya yi saurin saukowa kasa daga saman bed ɗin. Kai tsaye ya nufi waje da nufin ya je room ɗinta ya dubata. Dai'dai zai gifta ta wajen part ɗin maman su Yah Ramish sai ya tuna ai ana dinner, dan haka Auta tana can. Kamar walkiya haka ya hango wani inuwar mutum kamar na Auta ya fito daga part ɗin maman Yah Ramish ya nufi hanyar dake wajen na fita waje. Da sauri ya bi bayanta yana kwala kiran sunanta. Yana zuwa wajen kofar ya yi mamakin ganin a buɗe, yasan wannan kofa ba'a buɗeta fa. Amma sai ya danne ya fito waje ta side ɗin. Wayam babu kowa, tsayawa ya yi yana ƴan waige waige a wajen, babu ko alamar motsin wani halitta, ya ɗan yi mamaki, amma sai ya ce gizo ne kawai saboda ita ce a ransa yasa yaga kamar inuwarta ne. A fili ya furta. "Tun da na fito waje kawai bari in bi ta nan in je wajen dinner ɗin in ga Auta kafin in dawo in cigaba da barcina". Na'am ya yi da wannan shawara dan haka sai ya nufi wata cikakkiyar hanya da take wajen dan ya ƙarisa wajen dinner. Yana tafiya babu tsoro cikin nutsuwa da kamala. Dai'dai zai gifta ta wajen wasu flowers dake shuke kusa da part ɗin uncle Abbas kwatsam ya hango mutum a tsaye a wajen. Ko tsorata bai yi ba, kamar zai wuce ma sai kuma ya tsaya ya ce. "Wanene a nan?". Shiru ba'a amsa mashi ba, ga kuma mutum a tsaye kamar dai macece, wajen da ɗan duhu duhu. Hannu ya zura cikin aljihun jallabiyar jikinsa da nufin ya fito da wayarsa ya kunna light ɗinta domin ya samu damar ganin wacece a wajen!. Kash babu wayar a aljihunsa, hakan yasa ya ji babu daɗi, cikin ɗan ɗaga murya ya sake tambayar wacece a wannan wajen?. A karo na biyu ma ba'a kula shi ba. Ransa ya ɗan sosu a kan hakan, ya ji babu daɗi sosai. Amma sai ya danne tun da bashi da light a hannunsa sai yasa kai ya wuce kawai. Bawan Allah mai hakuri. Cikin nutsuwa yake takawa, ba zaka yi zaton yana taka ƙasa ba saboda yanayin yadda yake tafiya babu wata sauti dake fita. A hankali daga bayansa ya ji takun mutum alamar ana biyo bayansa kenan. Kamar ba zai juya ba sai kuma ya juya domin ya ga wanenen?. Innalilahi wa inna ilahir rajiun, wata iriyar halittar macece halitta na matsafa, gata doguwa mai mummunar fuska, baki kamar waga, batada kyan gani bata kuma da fasali ko kaɗan, ga ban tsoro a fuskarta. Sai dai ko kaɗan guyson bai tsorata ba, ko a jikinsa, sai ma kallon ƙasƙanci da ya wurga mata, cike da confidence ya ce. "Ke kuma daga ina?". Wani irin lankwasa ta yi haɗe da murɗe wuya, ita nan shegiya, ranta ya ɓaci ne dan bai tsorata ba. Ganin tana wannan lankwashe lankwashe bata da niyar yin magana zata ɓata mashi lokaci barci yake ji ne yasa ya sanya kansa ya cigaba da tafiya abinsa, ko ɗigon tsoro babu a ransa, kaman wanda ya saba ganin aljanu, har da jan ɗan siririn tsaki. Cikin wata iriyar kakkausar murya wannan aljana ko ace matsafiya ta furta. "Kai bil'adama maza ka zo nan". Yadda kuka san bai san Allah ya yi ruwan halittarta a wajen ba, ya cigaba da tafiyarsa yana kara jan tsaki. "Kai bil'adama ba nace kazo nan ba? Kada ka kuskura ka kara koda taku ɗaya ne, zaka mutu idan ka yi hakan!".................Ta yi maganar cikin murya mara daɗin ji, kamar muryar ƴan shaye shaye yanzu kuma. Ta yi maganar tare da ɓacewa kamar walkiya ta fito a gabansa. Dakatawa ya yi da tafiyar da yake yi, a hankali ya ɗago da kallonsa a kanta, sai da ya bita da kallon up and down kafin cikin sanyin murya ya ce. "Awww ke nan wai a haka aljana ce ko fatalwa ko? Dallah ni bani hanya na wuce hai, da wani shegen ido kamar kuliya ta faɗa tarko, ji wani muzurai da kike yi tamkar kwarton da soja ya kama a gidansa, kina wani taunan hakwara kamar wadda ta yi shekaru ashirin bata ci nama ba, na zabga maki mari naga karshen iskanci, kina wani huro hanci kamar ana hura balo balo kenan wai hegiya ko?"............... Ya kai karshen masifar tasa yana raɓawa gefenta zai wuce. Riko wuyar rigarsa ta yi ta baya a in da ta yi sama da shi sannan ta wurgar da shi gefe tana wani taunan hakwara, ga wani lanƙwashe kasusuwan gaɓɓanta da take yi, sai wani murɗe wuya take yi tamkar taliya ƴar murji. Haƙiƙa ya ji zafin wurgi da ta yi da shi, abin ya taɓa shi sosai, dan haka sai ya ciza laɓɓansa da karfi, kamar zai yi kuka ya daure ya miƙe tsaye. A fusace ya ce. "Ke mushirika kuma shaiɗaniya! Zaki bani hanya na wuce ne ko kuma sai raina ya ɓaci na gwada maki karfin ikon Allah?". Kamar wata walkiya sai gata ta bayyana a gabansa. Wani irin lankwashe wuya ta yi tana muzurai kamar wata kuliyar da ta shiga tarko, laɓɓanta ta shiga taunawa da karfi tana wani bubbuga kafafunta a ƙasa. Guyson da babu alamar zai ji tsoronta ne ya ce. "Wannan hauka da kike yi kuma fa? Ke ni ina da abin yi, zaki bani hanya ne ko sai na gwada maki yadda ake murɗe kashin wuya, na murɗe taki na karye shege na jefar?". Ta lura fa guyson bashi da tsoro ta wannan ɓangaren, dama kowa da abin da yake tsoro a rayuwarsa, kun dai ga shi rago ne ta fannin ciwo, amma ba haka yake gabaɗaya ba, baya tsoron ire-iren waɗan nan mushirikan. Da manuniyar yatsarsa ya nunata. Cikin fusata ya ce. "Bani hanya na wuce shashasha kawai!!". Ya fara fusata ne, ransa ya fara ɓaci, zuciyarsa tana tafasa, so yake ya je ya ga Auta ya dawo ya kwanta!. Kin bashi hanya ta yi tana cigaba da tauna hakwara tana muzurai. Hannu ya ɗaga da karfi, ya yi bismillah zai wanke shegiya da mari sai ya nemeta ya rasa, ɓat ta ɓace. Siririn tsaki ya ja tare da wucewa ya nufi dinner hall. Ransa a ɓace ya cigaba da jan tsaki yana tafiya. Bai yi nisa da barin wajen ba ya ji alamun ana binsa a baya! Wani sirirn tsakin ya ja, ba tare da ya juya ba ya ce. "Ai sauri zaki yi mu jera kafaɗa sai ya fi, shashashu kawai". Guyson fa yana da gaskiya, wlh ko aljani ne idan ka nuna kana tsoronsa ya dinga azabtar da kai kenan, amma idan ka nuna mashi kai ma shege ne mai ji da kanka, ka rike ayoyin Allah wlh ta kansa zai yi, tuni zai koma yana shakkarka!!. Guyson bai sake juyowa in da suke ba har ya kai hall ɗin nan, dai'dai zai shiga hall ɗin ya juyo, wayam bai ga kowa ba. Tsaki ya sake ja tare da ƙoƙarin juyawa dan ya shige ciki. A wani irin haukace aljanar ta bayyana a gaban idonsa, gashin kanta kamar bukkar shaiɗanu, idanunta kamar jini, bata da fasali sam, ta yi irin wannan bayyana ne dan su tsorata shi, so suke yi ya tsorata dan ya basu kofar da zasu shiga jikinsa su rikka sarrafa shi, aljani baya shiga jikin mutum haka kawai, sai bawa ya tsorata ya bashi kofa. Wannan tsorata da mutum zai yi shi zai basu damar shiga jikinsa, idan mutum ya tsorata wannan firgita da yake yi dik wasu kofofi a jikinsa buɗewa suke yi, to hakan yake bawa aljanu damar samun kofar shi, jama'a sai a kiyayye wannan, arinka daurewa ban da saurin razana a kan abu, wannan razana da kuke yi yana bawa abubuwa da dama hanyar shiga jikinku, ciki harda sihiri idan aka yi wa mutum, bayan sihiri akwai jifa, dik suna samun kofa ce ga hanyar razana. Ko mushirikai sun nufeka da sharri basa iya cin maka har sai sun turo wani abin da zai razanaka, kana razana ka firgita zasu samu kofar da wannan aiki nasu zai shi. Razana ga mutane wannan wajibi ne idan mutum yaga abin tsoro unexpect, to amma ya zai yi ya kare kansa daga mugayen idan ya razana? Amsa a nan ita ce ambaton Allah, idan bawa ya razana ya yi saurin furta sunan Allah, hakan zai yi matuƙar kuɓutar da shi daga dik wata sharri, dan haka ku yi ƙoƙari sunan Allah ya kama bakinku ya zauna, kune da cin riba, Allah ya kiyaye ya kare dikkan musulmi bakiɗaya. A wannan karon ya ɗan tsorata kaɗan, saboda unexpect ta bayyana a gabansa, ga yanayin yadda ta bayyana abin tsoro ne sosai. Sai dai yana ganinta ya yi saurin furta. "A'udhu billahi mina-sh-shaitanir-rajim". Fassara. Na nemi kariya daga Allah daga shaidan, wanda aka la'anta Sai. Allahu la ilaha illa huwa al-Hayyul-Qayyum......... Har zuwa karshe. Ayatun Kursiyyu ita ce mafi girman kariya daga aljanu da shaidanu. Sai a karanta Surorin Kariyar Suratul Falaq (Qul a'udhu bi rabbil-falaq...). Suratun Nas (Qul a'udhu bi rabbinnas...). Suratul Ikhlas (Qul huwallahu ahad...). Sannan a karanta. Bismillahi alladhi la yadurru ma'asmihi shai'un fil-ardi wala fis-sama'i wa huwa Sami'ul-Alim. Karanta Salatin Annabi (SAW). Yawaita salati kan Annabi (SAW) yana kawo tsaro da saukakawa bawa tsoro. Guyson yana karanta waɗan nan addu'oi wannan mushirika ta ɓace ɓat. Guntun tsaki ya sake ja kafin ya ce. "Hakan ma bai yi aiki ba, sai ki sake shiri". Yana gama faɗar haka ya shige cikin ball ɗin abinsa. ===================🔥 Momma ta jima tana wayar da take yi, daga karshe ta tufe da batun Jaish, cike da damuwa take zayyanawa wanda take waya da ita ɗin damuwar da take ciki a kan ɓacewar Jaish. Izuwa yanzu dik wata jarumtarta ta kare, hakurinta ya gaza, tunaninta ya tsaya, dannewa da take yi ta kai makura, zuciyarta ya kara tsananta ciwo, ta yi kuka a ɓoye har hawayenta sun kusa dai'na fita, zuciyarta na raya mata Jaish ya mutu ya bar duniya. Tas ta gama zayyanewa wadda take waya ta ita halin da take ciki. Hakuri ta rinƙa bata tana rarrashinta har sai da ta tabbatar da ta ɗan ji sassauci. Sannan ne suka yi sallama. Gabaɗaya barci ya kauracewa idanun momma, damuwarta ya dawo sabo a kan ɓacewar jaish, uwa kenan, tamkar ta san yana hanyar tunkarosu, sai tunaninta ya kara tsananta a kansa, ta kara shiga damuwa, zuciyarta ba bugawa da sunansa. Ganin kwanciya ba zai haifar mata da komai bane yasa ta miƙe ta je ta ɗauro alwala. Sallah ta zo ta fara gabatarwa domin neman Ubangiji da ya sassauta mata wannan hali da take ciki a wannan masarauta. A ɓangaren King kuwa, lokacin da ya dawo part ɗin momma dan duba guyson sai ya iskota tana sallah. Ganin babu guyson a ɗakin yasa ya juya ya fita, part ɗin mummyn Chuchu ya nufa. Dan yasan guyson yana santa kuma yana zuwa wajenta sosai. Nan ma guyson baya wajen, kamar zai je ya tambayi momma, sai kuma ya tuna kila shi ma ya tafi wajen dinner ɗin ne. Hakan yasa ya ɗan ji sanyi a ransa. Bedroom ɗinsa ya koma. Wayarsa ya ɗauko, number Abdussalam ya kira domin ya tabbatar, ana tsaka da taro kira ya shigo. Cikin girmamawa Abdussalam ya ɗauka. "Omar yana wajen taron ne?". Shi ne abin da King ya tambaya. A lokacin guyson yana tsaye a kusa da shi yana san tamnayarsa ina Auta. Dan haka da e ya amsawa King. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya King ya sauke wanda har sai da Abdussalam ya ji hakan a kunnuwansa. Katse kiran ya yi tare da ɗaura wayar a saman drawer, ya kwanta ya janyo bargo, hankali ya kwanta tun da Guyson yana wajen taron. =========================🔥 Guyson kuwa, yana sako ƙafafunsa cikin hall ɗin dai'dai lokacin MC ya ce da Jawad ya riƙe waist ɗin Chuchu ya sumbaceta. Shiru guyson ya yi yana mamakin abin, shi ba saba zuwa wajen biki ya yi ba, kunsan brothers ɗinsa dik gwabraye ne babu wanda ya yi aure bare ya san yadda ake yi, so bai taɓa sanin yadda ake wasu abubuwa ba, hakan yasa ya haɗe dik waɗan da suke cikin hall ɗin har da su Jawad ɗin da mc ya yi masu sunan ƴan iska..............😂 Bai kare tsinkewa da mamaki bama sai da yaga da gaske Yah Jawad ɗinsa ya mannawa Chuchu sumbata a baki, hakan yasa ya kara zaro idanu waje yana mamaki bawan Allah ustadz. Tabbas yasan hakan ba laifi bane tun da Jannat matar Jawad ɗin ne, shi abin da ya bashi mamaki shi ne ko kunyar mutane basu ji suke wannan iskanci, abin da ya kasance sirrinsu suke bayyanata ga duniya, ina laifin iya ƴan uwansu ne kawai, shi ne har da baki...........? Ni kuwa nace guyson kenan, dan dai bai faɗa soyayya bane, yana faɗawa zumuɗi zai sa ya mance da cewa kiss sirri ne, kila ma abin da zai yi sai ya fi nasu......😂 Ciki ya ƙarisa yana ta aikin rarraba idanu a kan ta ina zai ga Auta?. Har ya ƙariso kusa da su Jawad bai hango Auta ba. Kusa da Abdussalam ya tsaya, yana ƙoƙarin tambayarsa ina Auta sai ga kiran King a lokacin ta shigo. Shiru ya tsaya har sai da Abdussalam ya karisa call ɗin, nan ne ya ce. "Yah Abdussalam ina Auta?". "Kana nufin my wife?". Cewar Abdussalam. Jinjina kai Omar ya yi kafin ya amsa da. "E ita nike nema". "Ai tin da nazo ban haɗu da ita ba, kila tana cikin gida, bata zo nan ba, muma nemanta muke yi". Guyson bai kawo komai a ransa ba, ya juna ya nufi hanyar fita, dan a tunaninsa ko tana ɓangaren Akka, dan haka zai je can ya duba ta. Ƴan dinner sai cin uwar sabada ake yi ana sharholiya, Jawad ansami abin da ake so, wato yiwa Jannat sumbata, ko kunyar mutane baya ji, shi ba goshinta ya sumbata bama, bakinta ya sumbata mai gabaɗaya, buri ta cika yau. Kada ku manta wannan ƙaramin dinner da iya ƴaƴan sarakuna da masu mulki ne kawai a ciki, akwai babbar dinner da za'a gabatar gobe da misalin karfe 12 na dare. ===========================🔥 ••••••••••• BLACK WORLD•••••••••••••🔥 A hankali idanunta suka fara buɗewa, kunnuwanta suka fara jiyo mata sautika na kukan abubuwan da bata taɓa jin irinsu ba. Jiri jiri ta fara gani kamar zata faɗi ƙasa. Lokaci guda ta ji wani irin sanyi ya ratsa mata jikinta har izuwa cikin ƙashi da ɓargo, ga kafafunta babu takalma. Dishi dishi ta fara gani haɗe da wani irin yana kamar ɗakin da ya ɗebi shekaru aru aru babu mutane a ciki, a hankali idanun nata suka fara washewa. Sai kuma menene? Wani irin tabkeken tekun kankara ta gani a gabanta mai shake da ruwa mai bala'in sanyi har da ice a ciki, wannan dalilin ya haifar da uban sanyi da ta ji ya ratsata. A tsorace ta zaro idanunta waje sosai, ta yi iya kallonta bata iya gano karshen wannan kogi ba, tsoron juyawa bayanta ta yi dan kada ta sake cin karon da abin da ta gani ya makantar mata da idanu ɗazun. Tamkar wadda aka ture haka ta tafi luuuu sai cikin wannan tapkeken teku ba zato ba tsammani. Wani irin ihun azaba ta saki sakamakon wani irin sanyi da ya ratsa kashin jikinta, a tsananin razane ta fara ƙoƙarin cetan kanta, Pretty ta fita iya ruwa, dan in baku manta ba Pretty mayyar san ruwa ce, kada ku manta kullum a wajen korama Kamran yake iskota, ita kuma Sweetie kullum tana ɗakinsu. So bata wani iya ruwa ba, hakan yasa ta fara shan ruwan, ita dik ba wannan bane ma damuwarta, bala'in sanyin dake cikin ruwan ne matsalarta, sanyin ya yi mata over. Sai fafutuka take yi tana san cetar kanta, abin mamaki kuma bata nitse kasa ba, ruwan kuma yana da bala'in zurfi. Kamar daga sama taga bayyanarsa a bakin tekun. Kamar wani aljani haka ya bayyana, sleeping dress launin white color ce a jikinsa, ya yi bala'in kyau matuƙa, gashin kansa a sake, hakan yasa ya kara wani irin bala'in kyau, da alama ya kwanta zai yi barci ne ma ta shiga cikin gonarsa ta sanya shi tashi, dan dik wasu alamu na wanda ya kwanta zai yi barci ta bayyana a tattare da shi. Idanunsa suna ɗan lumshe alamar yana jin barci, kwayar idanunsa sun kara tsananta olive green sosai, sai shining suke yi, haka zalika ita ma olive green eyes ɗinta sun kara tsananta kala saboda ɗan duhun dake wajen. Farincikin idanunsa dama idan baku manta ba milk color ne ba fari tas ba, so yanzu ya yi jajir sosai. My people's Black Tiger karshe ne a kyau wlh, dik wasu cikar kyau na ɗan adam ya haɗesu sai rashin mutunci cike a kai. Kafafunsa na sanye da sps, hakan yasa baka iya ganinsu. Ganin shi ne ya bayyana yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, wato ita fa Sweetie wlh ko kaɗan bata jin tsoronsa, in short soma take ta ga bayyanarsa a waje,..........😂 Yanzu da ta ga shi ne har ta ji sanyin ruwan da take ciki ya ragu. Idanunsa a kanta babu ko kyaftawa, ita ma kura mashi kallo ta yi, suka ga juna ido cikin ido like wow, ga idanun nasu kalar iri ɗaya sak, sai abin ya bada wani citta. In a low cool voice sosai ya furta. "Where is Spender? Live or die!". Lion voice ɗinsa ya daki dodan kunnenta ba tare da ya buɗi baki ya yi magana ba, abin yana bata mamaki yadda baya buɗe baki kuma muryarsa take fita har ta furta words. Wani irin kallo ta yi mashi mai kama da harara kafin ta ce. "What's Spender?".................... Ko shakka babu ta yi maganar!. Tashin hankali. Gaskiya Sweetie ƴar yi ce ita ma!. Jiji da kansa ne ta motsa, dan shi baya bada gurbin wasa a lamuransa, wato Sweetie bata ji tsoron in da take bama tukun nan ko?. Da hannunsa ya nunata nan take ta fara nutsuwa kasan wannan tekun. Zaro idanu ta yi haɗe da fara ƙoƙarin yadda zata kwaci kanta. Amma ina ta kasa, tana ji tana gani ta nitse can ƙasa. Wasu irin macizan ruwa ta fara gani a kasan masu kai irin siffar na mutane, abin tsoro, ba halin yin ihu, sai ma ɗirkar ruwa da take yi. Wintsila kafafunta ta fara yi gwanin ban tausayi, ga ruwa tana ɗirka, shi kuwa yana ganinta a kasar ruwan with his magic eyes. Tana ji tana gani kamar zata mutu haka waɗan nan macizan suka zo suka mannewa jikinta, sai dai basu cijeta ba, babu yadda zata yi, sai wiwwintsila kafafu da hannaye take yi, ji take yi kamar ma an shaketa a cikin ruwan ne, yadda take shan ruwan sai ta baka tausayi. Yana ganinta har sai da ya ga ta sha ruwa sosai, kamar zata mutu, idanunta sun yi jajir kamar wuta, ta wahala iya wahala, ta ji kamshin mutuwa, sannan ne ya ɗago da ita saman ruwan. Haba tana yin sama ta fara tari kamar zata mutu, ga macizan dake manne da jikinta tsoronsu take ji kamar ta mutu, amma ba halin ta gudu ko ta rabasu da jikinta, yanzu ta numfashinta ma take yi, tana ƙoƙarin dai'dai ta shi!. A karo na biyu ta sake jin Lion voice ɗinsa unexpext a kunnenta yana sake jefa mata tambayar ina Spender?. Cak ta dakata da kakarin da take yi kamar zata yi amai. A hankali ta ɗago da rinannun jajayen idanunta a kansa. Kamar zata yi kuka ta ɗan tsuke fuska, yana kallonta sosai a cikin ido. Ɗaure fuska sosai ta yi kamar bata san menene dariya ba, sak irin yadda ya wani uban ɗaure fuska, wani irin harara ta dalla mashi ko tsoro babu, a karo na biyu ta sake cewa. "What's Spender?" Babbar magana!. Ta yi maganar ne a kule, wato idan zai kasheta ma gara ya kasheta ba faɗa mashi in da Spender yake zata yi ba. Hannunsa ya sake saitata da shi da nufin ya sake mayar da ita kasar ruwan dan mugunta, ko tausayi bata bashi ba, ko da yake shi wannan mai bakar zuciyar ina ya san wani abu wai shi tausayi? Ai bai santa ba. A hanzarce ta sanya hannunta irin mutum ya tare fuskarsa ɗin nan, haka ta yi saboda tana tsoron komawa cikin ruwan, kuma bata jin komai azabar da zai gana mata zata iya bashi Spender, sai dai ya kasheta amma wlh ba zata bayar ba!. Tana sanya hannunta unexpect magic ɗinta ya fita, ga shi suna saiti da juna, kai tsaye sai kan saitin zuciyarsa magic ɗin nata ya dakesa. Da yake unexpect ne abin hakan ya haifar mashi da jijjiga mai karfin gaske, wani irin jiri ne ya kwashesa ba zato ya afaka da karfi cikin ruwan tekun shi ma, dab kusa da ita ya faɗa. Ba ƙaramin razana ta yi ba na ganin irin jijjigar da ya yi kafin ya faɗo cikin ruwan, ga shi kuma ya faɗo kusa da ita. Wani irin tsoro ne ya lulluɓeta, sai ta kasa juyowa ta kalli in da yake. Shi kuma miƙewa tsaye a kan kafafunsa ya yi a cikin ruwan bayan faɗawarsa kenan. Sai da ya ji a jikinsa lokacin da ruwan sanyin nan ta ratsa jikinsa, ashe babu daɗi ya jefata cikin ruwan sanyin, dik jikinsa sai da ta amsa har ƙashi da ɓargo. Idan ransa ya kai miliyan to ya ɓaci, nan take Black heart ɗinsa ta matso kusa, a fusace ya juyo gareta. Wannan juyowa da ya yi sai da gashin kansa ya pyaɗe mata rugun wuyarta, sannan ya watsa mata ruwan da ya tattaro daga gashin nata a saman face ɗinta. Hannu tasa dan ta sharce ruwan da ya watsa mata ɗin. Kamar daga sama ta ji saukar hannunsa a bayan wuyarta. Da karfi ya damketa. Babu tausayi babu imani ya danna kanta a cikin ruwan nan, da alama kasheta yake da niya. Buga buga ta fara yi tana shan ruwa. Azaba da ya ratsata bata san lokacin da ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ba, ƙoƙarin juyowa garesa ta fara yi, ko kaɗan ta kasa iya motsa shi, fafutuka ta fara yi da hannunta tana neman abin da zata kama dan ta cece ranta, ta ji azaba ƴar kaniya, har ta ji a ranta Spender banza zata iya bashi a yanzu kam, saboda taga alamar mutuwa. Unexpect hannunta ya kai kan heronsa (bananarsa) saboda tana neman abin kamawa sai kawai ta capkoshi da karfi. Ai bai san lokacin da a miliyan ya saketa ba, har baya kaɗan ya yi, ya ji abin da bai taɓa tsammanin zai ji ba a rayuwarsa, dan ma Allah yasa a cikin ruwa suke. Sweetie akwai zuciya, ko da yake haka twins or triplets or quadruple suke, abin a jininsu yake. Yana saketa ta ɗago kanta da karfi, wani irin numfashi da ta ja da karfi sai ta baka tausayi, da karfi ta fara layi a cikin ruwar kamar wadda ta sha wine ta bugu, neman in da zata tsaya domin ta samu numfashinta ya dawo daidai take yi. Tana tsaka da juyi a cikin ruwan ta matso kusa da shi, dama in baku manta ba ai ya ɗan ja baya kaɗan. Tana matsowa kusa da shi, idanunta a datse kam, jin alamar abu yasa ta sanya hannun bibbiyu ta riko shi tana wani irin numfashi mai ban tausayi, da alama ta fita hayyacinta sosai, shiyasa ma bata ji abin da ta kama da farko ba!. Kirjinsa ta kama a yanzu kuma, hakan yasa ta ji kamar dutse ta kama, saboda a dake yake sosai. Da hannunta dikka biyu ta dafa kirjin nasa tana ƙoƙarin fara kwararo amai na uban ruwan da ta sha. Shi kuwa tun da ya koma baya ya datse idanunsa gam, ko me yake tunawa? Kamar dai abin ya yi mugun baƙanta mashi rai ne!. After some minutes.......... Suna tsaye haka. A hankali ta fara dawowa cikin hayyacinta. Idanunta ta fara kokarin warowa waje dan ta ga ina yake? Yanzu kam ta iya tuna in sa take. Tana buɗe ido sai a kansa, yana tsaye idanunsa a datse kam kamar wanda ruwa ya cisa. Wani irin karfinta dikka ta tattaro, da karfi ta danna hannunta dake dafe da kirjinsa, dagewa ta yi harda ciza laɓɓanta da karfi, wureshi ta yi a cewarta ta samu hanya ta fita. Sai dai kash, ko motsawa bai yi ba, kamar dutse mai girman gaske ta yi yunkurin turewa, ko gezau bai yi ba. Ransa ne ya kara ɓaci, da karfi ya waro idanunsa waje, idanunsa sun juya izuwa magic eyes. A maimakon ya bawa Sweetie tsoro sai ma kafe shi da kallo ta yi, dan ita magic eyes ɗin nasa ma kyau suke yi mata........... Trust me Sweetie ƴar duniya ce, ƴar ikka ce, wai magic eyes ɗinsa suna yi mata kyau, kai wannan yarinya tana goge mun hadda. Kamar walkiya haka ya yi amfani da magic ɗinsa ya janyeta baya nesa daga kusa da shi. Ganin ya buɗe hannunsa ya janyeta baya yasa ita ma ta tuna a ranta cewa bari ta gwada buɗe hannunta taga me zai faru tun da ranar taga ta buɗe hannu ta iya sarrafa chandelier. Tana buɗewa magic ɗinta ya fita, da karfi magic ɗinta ya janyo shi kusa da ita, suka sake haɗewa kamar chewing gum, har sai da kanta ya bugi kirjinsa. Yau Black Tiger ya haɗu da ƴar bala'i dai'dai da shi!. Magana ta gaskiya ya fi Sweetie karfin magic, yana dannewa baya san kashetan ne kawai, yasan idan zai kara karfin magic ɗinsa ya fi yadda yake a yanzu yana yin amfani da shi sau ɗaya a kanta zata rasa ranta, baya san ta mutu, saboda yana da buƙatar Spender a hannunta ta kowace hali ne, ita kaɗai ce kuma yanzu a duniya tasan in da yake, kunga dole ya danne. Ita kuma Sweetie dama bata tsoronsa sosai, sai kuma Ronnie ya ce mata yayansa ba zai taɓa kasheta ba har sai ta bashi Spender, sai dai ta sha wahala a hannunsa, dik ranar da ta bashi Spender to ta sani tana yi mashi abu kaɗan zata mutu. Jin ba zai kasheta bane yasa ta kara samun kwarin gwiwa haɗe da kara rage tsoronsa da take ji, shiyasa zaku ga tana yi mashi wasu abubuwa bata nuna tsoronsa. Wannan shi ne dalilan da yasa kuke ganin in sun haɗu kamar magic nata ya fi nasa, kuga kuma kamar bata jin tsoronsa, to ba haka bane, kun ji dalilan. Ƙoƙarin danne Black heart ɗinsa ya fara yi dan kada ya kasheta, ita kuma ture shi daga kusa da ita ta fara ƙoƙarin yi. Hakan ya kona ransa matuƙa, har da sanya hannunta bibbiyu zata ture shi. Cikin fusata ya capko wuyarta ta gaba da hannunsa ɗaya. Da karfi ya shaketa har sai da ba shiri tongue ɗinta ya yo waje. Zaro mata dara daran idanunsa ya yi ba shiri ta lumshe nata idanun, saboda kaifin idanunsa ya ratsata har sai da ta ji kamar an tsira mata allura a jikinta. Hannunta ta ɗaura a saman nasa tana son ya sake mata wuya. Tin da Allah ya haliccita a duniya bata taɓa jin hannu mai laushin nasa ba, she has a very very smooth and soft skin, ko da yake baya fita rana ai dole dama skin ɗinsa ta yi haka. Sai dai akwai yawan jijiyoyi a hannun nasa sosai, gasu ɓaro ɓaro. Bubbuga hannunsa da karfi ta fara yi tana neman agaji. Kada ku manta basu nitse kasan ruwan bane saboda magic ɗinsa, shiyasa suke a sama. Azaba ne ya yi azaba kuma taga bashi da miyar sake mata wuya. A hankali ta sauke hannayenta kasa daga saman nasa, jikinta ne ya fara sakewa alamar rai ya yi halinsa. Sake hannunta da ta yi ya ja magic nata ya fara nitsar da su kasar ruwan. Yana rike da wuyarta unexpect ya ga sun fara nitsewa kasan ruwa, ko kaɗan bai damu ba, da alama ɓacin rai yasa ya fita a hayyacinsa, ya manta ita kaɗai tasan in da Spender yake ga shi ya kasheta bai ankara ba. Zuciya ta ja mashi. Har sai da suka ka kai kasan wannan tekun ne ya farga da in da suke da kuma ta mutu. A hankali ya zame hannunsa daga wuyar tata. Sulalewa ta yi ta kwanta a kasan wannan ruwa ta zama gawa. Ransa a tsananin ɓace, yana ta huci mai zafi ya yi amfani da magic ya dawo da su saman ruwan. Da hannu ɗaya yasa ya saɓi gawarta a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya fito daga cikin ruwan. Idanunsa a datse ya tsaya a bakin ruwan, ko kaɗan bai yi nadamar abin da ya aikata ba. Cikin kungurmin dajin ya kutsa da ita, yana taku cikin zafa, daga shi har ita jikinsu na ɗigar da ruwa!. To ina kuma zai kai gawarta? Me kuke tunanin zai faru?. =========================🔥 •••••••••••••••FOREST••••••••••••••🔥 Zaune take saman wani dutse wanda ruwa yake ɓulɓula daga kasansa, daga gaba kaɗan tabkeken kogi ne a wajen, ita kaɗai take zaune kamar marainiya, tana sanye da kusan irin kayan da suka rabu da Sweetie a wannan rana da damusa ta far masu, sai dai wannan kayan milk color ne. Ta yi shiru haɗe da buga uban tagumi, kamar dai akwai abin da take tunawa. Allah sarki har ta rame, Sweetie ta matsa mata akan ƴar dumurkurewa da ta yi a lokarin da suke a tare, har tana gayawa Kamran cewa Pretty ta fita kiɓa saboda ta fita cin abinci. To yau ina Sweetie take? Ta zo taga Pretty ta yi rama sosai, ta canza kamar ba ita ba, wuyarta sai layin guru zaa gani alamar tsokar nama ya taɓa taruwa a wajen. Kan nan nata ba ɗan'kwali, gashinta a watse, ko gatan tarawa a ɗaure bai samu ba, dama Sweetie take ɗaure mata, to yanzu Sweetie bata nan babu mai yi mata, ita kuma bata iya ba, sai ta barshi a watse har gadon bayanta, dik ya yi datti ma bata wanke ba. A hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauƙa a jikinta, tsabar ta yi nisa cikin duniyar tunanin da take yi ma bata ji alamar ruwan saman ba. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ==========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ A hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauƙa a jikinta, tsabar ta yi nisa cikin duniyar tunanin da take yi ma bata ji alamar ruwan saman ba. Wani irin narkakken hadari bakinkirin ne yake tasowa a gajimare, sai walkiya da tsawa ake yi, amma tamkar sassaka Pretty aka yi a wannan waje, sam bata motsa daga in da take ba. Lokacin guda ruwa ta barke kamar da bakin kwarya, amma Pretty tana zaune shiru, kamar wadda babu rai a tattare da ita. Allah sarki abar tausayi, ga rashin uwa, ga rashin madogara, yanzu kuma ga rashin ƴar uwa, babu Kamran, abin ya yi wa kakanun shekarunta yawa wlh. Tun farkon ruwan saman nan har karshensa a kanta ya kare, daga karshe ma haɗe kai da gwiwonta ta yi tana ruwan hawaye sosai. Ruwa sai dukanta yake yi. Har ruwar ta dakata Pretty bata da niyar motsawa daga in sa take zaune, yadda kuka san ba mutum bace. Ko ɗago kanta taki ta yi. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 "Omnish". Daga bayanta ta ji wata murya an furta hakan. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta ɗago kai tare da juyowa ga muryar. Idanunta sun yi jajir kamar wuta saboda kuka ga ruwan da ya dakata. Yana tsaye cikin wannan shiga tasa ta kullum, face ɗinsa a rufe da hular mayaƙa, tsayuwa cikin jarumta da nuna cikar zarra, ya ɗaura hannunsa ɗaya saman tabkekiyar takobin dake manne a waist ɗinsa, jikinsa dik yayyafin ruwan sama. Tana ɗaura idanunta a kansa ta yi maza ta miƙe tsaye, sai a lokacin ta fara jin sanyin ruwan saman da ya jiƙata, takure jikinta waje guda ta yi, fuskarta gwanin ban tausayi, idanu cike tab da ruwan hawaye, ta kasa yin magana sai dai ido take binsa da shi. Cikin harshen tsabtataccen larabcinsa, ga nitsuwa da kamala a tattare da voice ɗin, kamar baya san yin magana ya ce. "Omnish meya tsayar dake cikin ruwan nan haka?". Tamkar jira take yi a yi mata magana, ai sai kawai ta fashe da kuka mai ɗan sauti. Cikin jarumta da zafa ya tako ya matso kusa da ita, ɗan rungumota kaɗan ya yi a jegen takobin dake waist ɗinsa, ya fara bubbuga bayanta alamar rarrashi. Yadda suke tsaye a wajen sai sun yi maku wani iri idan kuka gansu, in baku manta ba na ce maku wannan sadauki idanunsa iri ɗaya da Pretty, kamar an tsaga kara, dik da fuskarsa a rufe take, in kaga idanunsa da nata sai ka yi zaton kanwarsa ce ita ko yarsa dik da bamu san babban mutum ne ko yaro ba, tin da bamu taɓa ganin face ɗinsa ba. Hannunsa dake cikin wani irin hands gloves mai karfi ya ɗaura saman lallausan kumatunta yana goge mata hawaye, tamkar kara ingizasu yake yi, yana gogewa wasu suna fasowa. Juyo da ita ya yi suna fuskantar juna, ya ɗan rage tsawonsa dan ya dai'daita kansa da tata. "Omnish menene ya faru kuma? Kin manta jiya kin mun alkawarin ba zaki sake yin kuka bane?". Shiru bata amsa mashi ba, bata ma da niyar amsa mashi ɗin. "Omnish ya isa haka kukan, yi shiru ki faɗa mun me ya sameki kuma?". Still shiru bata amsa mashi ba. Dik sai ya ji babu daɗi, ga dikkan alamu ya ji jikinsa ya yi mugun sanyi, da alama tausayinta ya kara ratsa heart ɗinsa ne. "Yau kuma ba za'ayi magana dani bane Omnish?". Cike da tausayawa ya yi maganar, yana jin tausayinta matuƙa. Kai ta girgiza mashi alamar a'a, a take ta tsuke fuska zata fara yi mashi shagwaɓar da ta saba, ashe dai har yanzu halin nan nata na shagwaɓa yana nan. Cigaba da goge mata hawaye ya yi yana kara rarrashinta. Da kyar ya samu ta yi shiru, amma taki ta yi mashi magana. Hakan yasa ya miƙe tsawonsa ya riko hannunta suka kutsa cikin daji a tare yana mai kara rarrashinta. Wanenen kuke tunani zai kasance wannan sadaukin? Meyasa kuma sai dai ya taimaka masu a daji ba zai ɗaukesu ya fitar da su ya kaisu cikin gari ba? Meyasa baya san su bar wannan dajin? Menene alakarshi da su? Ina mom ɗinsu? Ina ne tushensu? Ina dad ɗinsu?. Dik cikin nutswa amsoshinku zasu bayyana, yanzu dai muje zuwa!!. •••••••••KINGDOM OF POWER••••••••🔥 Sai misalin karfe 1 da rabi na dare aka tashi taron dinner. Har lokacin guyson bai rintsa ba, yana ta bin part part na kowa yana neman Auta. Daga karshe ya dawo ɗakin momma dan ya ɗauki wayarsa ya kira numberta, a lokacin momma tana sallah, wayar kawai ya ɗauka ya fito waje. Ya kirata ya fi miss call talatin, amma ina bata ɗauka na. Idanun Hoorain biyu bai rintsa ba, yana ganin call ɗin guyson amma bai ɗauka ba, ya kasa iya yin barci, yana zaune saman bed ɗinsa kamar mai nazarin wani abin, gabaɗaya ji yake kamar jikinsa ba mallakinsa bane ba. Idan hankalin guyson ya kai miliyan to fa ya tashi a wannan dare, ya shiga damuwa na wuce misali. Baya shiri da Mammiensu Sarina amma a cikin wannan dare sai da ya je part ɗinsu ya buga mata kofa, dan dole yasa ta fito ya tambayeta Auta, ta ce mashi bata a part ɗin nan, hankalinsa ne ya kara ɗugunzuma ya tashi. Wajen mommarsa ya dawo dan ya sanar da ita, tana sallah har lokacin, dan haka sai ya samu waje saman bakin bed ya zauna yana jiranta. Ita kanta ganin shege da fice da yake yi mata a ɗaki yasa ta ji ta kagu da ta sallame sallar dan ta ji me damuwarsa da yasa bai yi barci ba har karfe ɗaya da rabi. A ɓangaren ƴan dinner kuwa, Fanan ta ja hannun Chuchu a kan ta zo su wuce wannan ɗaki da yake mallakin amare dan gyarasu, a ka'ida amarya ba zata fita daga cikin wannan ɗaki ba har sai lokacin da za'a kaita ɗakin mijinta, ko dinner aka je nan zata dawo. So ana tashi Fanan ta kama hannunta a kan su tafi can. Wani irin hararar da Jawad ya wurga mata ne yasa Fanan ta yi gaggawar sakin hannun nata tana ɗan sunkuyar da kai. Abdussalam yana ganinsu dik abin da suke yi, dariya suka so ɗan bashi, wato dai Jawad rashin kunyarsa a fili zai nuna? Abdussalam ya tambayi kansa yana kunshe murmushi. Ita kuwa Fanan kasa ta ɗan yi da kai tare da cewa. "Yah Jawad zamu koma ciki ne fa!". Tamkar bai ji me ta ce ba ya yi shiru yana kallon Chuchu dake tsaye kusa da shi. A karo na biyu Fanan ta sake maimaita mashi abin da ta faɗa ɗazun. Kallo mai kama da harara ya wurga mata, cikin sanyin murya ya ce. "Ke kika kawo mun ita ne dama?". Kamar zata gyaɗa mashi kai alamar e, saboda ita ta kawota kam, amma sai taga rashin dacewar ta yi mashi hakan tun da yayanta ne, kuma tana tsoron ya hukuntata, dan haka sai ta girgiza mashi kai alamar a'a ba ita ta kawo ta ba. Hannu yasa ya nuna mata hanya. "Jeki zan dawo da ita da kaina".........Ya faɗa idanunsa a kan Chuchu da ta sunkuyar da kai tamkar bata a wajen, tinanin Auta ce kawai a cikin kwakwalwarta. "Kai malam kamar ya zaka mayar da ita da kanka? Ban gane ba?"...........Cewar Abdussalam, ya yi maganar cike da tsiya da iyashege. "E zan mayar da ita time da na yi ra'ayi"....... With his full confidence Jawad ya mayar mashi da amsa. "Kai ka kawota ne daman? Ji mun wani karfin hali, kinga Fanan kama hannunta ku tafi hai"........... Cewar Abdussalam, yana magana yana ɗaure fuska irin shi fa da gaske yake yi. Gum kamar gunki Fanan ta tsaya ta kasa kama hannun Chuchu saboda tana tsoro, jama'a dik sun watse sun barsu tsaye a wajen. "Fanan kama hannunta na ce ku tafi ko.........".......... Cewar Abdussalam. Bai ƙarisa maganar ba ya dakata saboda wani irin harara da Jawad ya wurga mashi. Murmushi Abdussalam ya ɗan saki tare da riko hannun Fanan yana faɗin. "Zo mu tafi hai sister, kada ya fara saka mana duka". Ba musu ta bishi suka tafi, wajen ya rage daga Jawad sai Chuchun. A hankali ya kai hannunsa ya riko hannayenta, kamar mai raɗa ya ce. "Menene kuma?". Kamar jira take yi ya yi mata magana ta fara kuka, nan take hawaye suka fara ƴar tsere a saman face ɗinta. A ɗan rikice ya ce. "Jannat lafiya kuwa?". Da ɗan daga murya ta ce. "Yah Jawad Auta, ban ga Auta ba, tun da yamma nike nemanta ban ganta ba, tun da rana rabona da ita, ina kiran numberta baya shiga, ya zan yi da rai'na?". Ɗan jawota jikinsa ya yi, shi kansa yana cikin damuwar rashin Autar nan, amma bai taɓa kawo mummunar abu a ransa ba, ya fi zaton tana wajen bakin Dubai tun da ta yi sabo da su sosai. "Auta tana nan a ciki gida, muje zuwa da safe da kai'na zan ɗauko maki ita". Bata san yin ja in ja da shi ne kawai yasa ta yarda da abin da ya ce, ta kuma miƙa wuya a garesa, cak ya ɗauketa suka fito daga cikin hall ɗin. Bai zame ko'ina da ita ba sai cikin bedroom ɗinsa, shi tun ba'a kai mashi ita ba ya kaiwa kansa ita. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Momma tana sallame sallah ko numfashin guyson bai bari ta ja ba ya yi sauri wurga mata tambayar ina Autarsa? Wani irin dum dum Momma ta ji kirjinta ya buga, sai dai bata yi wani mummunar tunani ba, cikin nutswa ta ce. "Ina jin tana tare da Jannat a wajen dinner.........." Tun bata dasa aya a maganar ba ya tari numfashinta da cewa. "Naje wajen bata nan, Yah Jawad ma ya ce rabonsu da ita tun da rana.........." Bai ƙarisa maganar ba momma ta zabura kamar wadda aka kwalawa guduma a kai ta miƙe tsaye, dan ita ma rabonta da Auta tun da rana, dik tinaninta tana a tare da su Chuchu ne yasa bata wani damu ba, sai yanzu ta tuna yadda ta rinƙa ganin giftawarsu Fanan and Chuchun ba a tare da ita ba, kwata kwata bata ga giftawarta ko kaɗan ba, to ina take kenan? Ta jefawa kanta tambaya. Shi ma guyson miƙewa tsaye ya yi yana jiran amsa. Cikin ƙanƙanin lokaci face ɗin momma ta rikiɗa izuwa na tashin hankali. Wayarta dake gefen bed ta ɗauko domin ta gwada kiran number Auta. "Momma don't west your time, her number isn't going now, before i called her more than 30 times she didn't pick the call, yanzu kuma the number was not going, switch off". Momma bata daka ta tashi ba sai da ta gwada kiran number, a kashe suka sanar da ita, hankalinta ne ya kara tashi sosai. A hanzarce ta nufi kofar fita, kamar ta mance da guyson a tsaye a wajen. Ganin haka yasa ya yi saurin rufa mata baya. Basu zame ko'ina ba sai part ɗin King. A lokacin har barci ta fara ɗaukarsa, jin motsin taɓa kofa yasa ya farka. Ganin sune yasa ya yi saurin miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin. Wajen switch momma ta nufa, dama iya lamp ne kunne a ɗakin, so sai ya kunna wutar gabaɗaya. King he was very shocked na ganinsu a tare da kuma ganin yadda suka shigo momma a hargitse, da Momma ita kaɗai ce ba zai ji komai ba, amma a tare da guyson sai ya zaci ba lafiya ba, dik tinaninsa ta ta'allaka a kan ciwon guyson ɗin ne ya hanasu rintsawa. A ƙage da son jin cikakken bayanin meyake faruwa yake binsu da kallo. Ita ma Momma kallonsa take yi ta rasa ta ina zata fara, dik yadda take ji a ranta take kuma tsananin tsorace a kan me ya sami yarta, hankalinta yake tashe ganin face ɗin King yasa ta ji nata tashin hankalin wasa ne a kan wanda shi zai shiga idan ya ji me ya kawosu. Guyson ne ya katse masu kallon juna da suke yi ta hanyar ƙarisawa gaban bed ɗin, tamkar zai rushe da kuka ya ce. "Daddy Auta bata nan, mun duba ko'ina amma bamu gan.........." Wani irin birki ya ci tare da haɗiye sauran maganganun a cikinsa, ba komai ya ja hakan ba kuma face idanu da King ya zaro mashi tare da zabura ya yaye bargon dake jikinsa. Ai bai san time da ya sauko ƙasa daga saman bed ɗin ba. Idanunsa a kan momma ya ce. "Da gaske ne abin da Omar ya faɗa?". Kai kawai ta iya jinjina mashi ta kasa yin magana. "To ina ta je? Kun duba dik part's na cikin gidan nan?". Guyson ne ya tabbatar mashi da tabbas ya duba ko'ina bata ciki. Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne abin da King ya furta kafin ya nufi waje da sauri. Bayansa suka bi, a parlour ya tsaya tare da harɗe hannayensa saman kirjinsa, tunani ya fara yi a kan ina Auta ta tafi? In dai bata cikin kingdom ɗin nan to tabbas hanune ya ɗauketa, saboda ba ta yadda za'ayi wata halitta ta iya ketare gates ɗin nan gabaɗaya ta fita ba tare da saninsa ba! To ina take kenan?. Ya jefawa kansa tambayar da bai san amsarta ba. Zuciyarsa ta cika tab da tunani haɗe da ruɗani mai tarin yawa. A nan momma ta isko shi, cike da tashin hankali ta ce. "Yanzu me abin yi?". Guyson dake tsaye a kusa da momma idanunsa sun ciko da kwallah King ya ɗaura idanunsa a kansa. "Ɗauko mun wayata Omar"........... Ya faɗa tamkar wanda yake koyan yin magana, a hankali. Cikin zafa guyson ya juya ya koma cikin master room ɗin. Kallon juna King da momma kawai suke yi babu wanda ya iya furtawa ɗan uwansa word. A haka guyson ya dawo ya samesu, wayar ya miƙawa King, da sauri ya karɓa ya shiga latsawa. Karata ya yi a kunnensa tare da matsawa gaba kaɗan. Binsa da kallo kawai suke yi momma kamar zata ɗaura hannu bisa kai ta zunduma ihu, wannan bala'i dame ta yi kama? Abin ya yi mata yawa, Jaish ya ɓace shiru shiru tsawon watanni babu shi babu labarinsa, ta danne sai dai ta yi kuka a ɓoye, a fili tana nuna kamar bata damu ba, ta jajirce wajen shanye madarar bakincikin, yanzu kuma ace Auta ta sake ɓacewa basu san ina take ba? Ai gara mata Jaish namiji ne kuma babba ne, Auta fa? Mace kuma yarinyar da ko 14 years bata cika ba, dole hankula su ɗugunzuma su tashi. "Abbas ka bincika mun Zunaira tana ɓangarenka ne!"........... Cewar King da ya kara waya a kunne. Da sauri su momma suka kara nitsuwa haɗe da kara tsaresa da idanu da kyau. Uncle Abbas da yake zaune saman dadduma yana gabatar da nafilfilin dare ne ya yi saurin miƙewa tsaye, dama ya idar yana addu'oi ne. Mammie tana kwance saman bed tana barcin asara, kun san ita fa yanzu ba sallah take yi ba, sai shirka. Uncle Abbas tin ba'a gaya mashi ta ɓata ba ya shiga tashin hankali, yanzu ai suna nemanta ne, a tinanin kowannensu tana cikin gidan, sai da King ya kira kowannensu har uncle Taheer ya ce su dubata, sai a sannan ne idanunsu ya fara rena fata, dan dik in da suke tinanin tana wajen babu ita, a yanzu kwata kwata basu sa a ransu kasheta ma aka yi ba, tun da ba'a ga gawarta ba, sun fi sawa a ransu saceta aka yi. Shi King kam ma kai tsaye King Al-Mustapah ya ɗaurawa zargin yin hakan, dan in baku manta ba ya kawo masu jiyara yau da rana, kuma shi abokin gaba ne, so dole a zargesa. King yana zargin shi ya saceta dan su cinwa wani buri nasu a kan kingdom of power. Shi kuma uncle Abbas yana zargin Queen Zarina ce ta turo mutanenta suka saje da ƴan biki suka shigo suka ɗauke Auta, kowa da abin da yake zargi yake kuma hasashe, sai dai babu wanda ya yi hasashen ta mutu mai gabaɗaya ta bar duniya. Dik tsananin taurin zuciya da jarumta haɗe da dakiya irin na King sai da ya shiga tsananin tashin hankalin da yake ƙoƙarin fita hayyacinsa a lokacin da suka tabbatar da bata a cikin Kingdom ɗin, dan dik wasu sassasa da mutum zai iya zuwa a cikin kingdom ɗin nan sai da suka je suka duba. Kowa ya tashi daga barci har da su Mummy, King ya tashi kowa, commander Zafar kam shi ne mutum na uku da King ya fara tasa daga barci bayan uncle Abbas da uncle Taheer. In short Akka ce kawai ba'a sanar da ita abin da yake faruwa ba, ita ma saboda bata da lafiya ne kada ciwon ya kara tsananta suna iya rasata a kan hakan, shi ne yasa suka ki sanar da ita. Jigum jigum suka zauna cikin parlourn King, su commander Zafar kuwa sun gama kewaye kota ina da warrios a cikin kingdom ɗin anata kai komo wajen nemanta. Lokacin da commander ya zo sanar da Hoorain ga halin da suke ciki gimbiya Zunaira ta ɓata, sai ya tarar da shi da zazzaɓi mai tsananin zafi, jikinsa ta yi zafi jaw kamar wuta, hakan yasa ya fasa gaya mashi halin da ake ciki, ya ɓoye mashi, ya ce ya zo duba shi ne kawai. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Gabaɗaya family hankulansu in ya kai miliyan ta ya tashi, harta maman Yah Ramish ta shiga damuwa matuƙa, mummyn Chuchu har kusan kwallah ta yi, Momma kam ba'a magana, tana tsaye taki zama, kamar wanda aka sassaƙa. Kamar yadda suka ga rana haka suka ga dare zaune a cikin parlon King, lokacin da aka yi kiran sallar asuba ta farko King ya fito waje hararbar kingdom ɗin, dan yana zargin warriors da commander zafar ya wakilta wajen nemanta a dik wasu lungu da saƙo na kingdom ɗin basu duba da kyau ba, so sai ya fito da kansa dan ya duba. Momma ta so binsa, sai dai kunsan a doka irin tasu ba zata fita waje ba, killacesu ake yi, matan sarki bayi da warrios basu da damar ganinsu, suna da ƙaidoji da dokoki masu karfi. So Mummyn Chuchu ta riketa ta hanata fita. Dik yadda King yake tinani abin ya wuci nan, dan babu in da basu duba ba babu ita babu labarinta, da kyar uncle Abbas ya rarrashesa suka koma ɗakunansu dan su shirya zuwa masallaci. Yau gabaɗaya zargin Momma a kan maman Yah Ramish yake, dama ta jima tana zarginta, kawai tana dannewa ne saboda bata san tashin hankali, amma yau a kan ɓatar Zunaira wlh ba zata ragawa kowa ba, dole ta fito da zarginta ta ɗaura a kan wanda zuciyarta take raya mata!!. Lokacin da su King suka dawo daga masallacin sallar asuba, babu ɓoye ɓoye suka sanar da matan cewa Auta fa bata cikin kingdom ɗin nan, ta ɓata, dan haka kowa ya zage da yin addu'ar Allah ya bayyanata. King yana sanar da su gabaɗaya parlourn ya dauki shiru mai tsananin girma fiye da kowanne kuka. Momma zube gwiwowinta a kasa ta yi, nan take hawaye suka fara gudu ba kakkautawa kamar ruwan kogin da ya ketare iyaka a saman face ɗinta. "Ba zan iya yarda ba! Ba zan yarda cewa Zunaira bata cikin kingdom ɗin nan ba! Ba zan iya yarda ta ɓata ba!"....... Haka ta fara sambatu, muryarta na kara tsananta kuka. King da aka san shi da jarumta, yana tsaye a gefe kamar wanda ya rasa hanyar tunani. Idanunsa cike da hawaye da ba ya so su zubo, amma ba zai iya hana su ba. Ya harɗe hannunsa a saman kirjinsa, yana kallon momma ya kasa yin magana. Guyson ne ya ce. " Dad Momma wai me na yi wa duniya har za'a kashe ni da irin wannan bakin azaban ciwo mai tsananin zafin? Da a ɗauke Zunaira ai gara ni a kasheni!"............ Ya tambaya da muryar da ta nuna karayar zuciyarsa. Guyson mai saurin kuka yau dai hawaye taki fitowa, sabdoa azabar dake cikin ransa ba zata iya baiwa hawaye gurbin fita ba!. Yah Jawad wanda idanunsa yake yi mashi gizon Auta tana tsaye kusa da guyson tana murmushi ne ya kasa iya furta word. Kamar ma baya cikin hayyacinsa sosai. Su uncle Taheer sun kasa yin magana, sai kawai kukan zuci da suke yi. Fanan da ta manne da Chuchu ce a cikin ranta ta ce. "Auta ta kasance mai kawo dariya da farinciki a kan fuskar kowa dake gidan nan, ta sanya zuƙatan kowa a nitsuwa, sanyi idaniyar kowa, yanzu ace babu ita? Kai anya zasu iya ɗauka kuwa? Gurbin ta tamkar rami ne mai zurfi wanda babu abin da zai iya cikawa a zuƙatansu". Kowanne daga cikin su yana tuna abubuwan da ta yi na alkhairi, irin murya mai daɗin da ke jansu cikin farinciki, yadda take cika gida da rayuwa da ƙauna. Chuchu dai ganin abin kamar mafariki take yi, hakan yasa bata iya furta word ba, tana dai binsu da ido, gata nan gata nan kamar wadda aka sassaka ta kasa motsawa. Momma kuwa kara fashewa da kuka mai sauti ta yi, hakan ya ja hankalin mummyn Chuchu a kanta, da sun afka duniyar tunanin ina Auta take? Jin kukan Momma yasa suka yi saurin karisowa in da take. A tare Mummyn Chuchu da Maman Yah Ramish suka tsugunna a gabanta, a tare suka kai hannu suka rungumota. Cikin ɗaga murya momma ta ce da mama kada ta sake taɓata!. Tashin hankali. Nan fa kallo ya koma kansu a cikin parlourn, yadda Momma ta yi maganar ya girgiza kowa. King da yake tsaye kaman wanda aka sassaƙa ma sai da ya ji gabansa ta faɗi ya dawo cikin hankalinsa. Mama da bata gane me Momma take nufi ba, a tunaninta saboda raɗaɗin rashin ƴar tata ce yasa take sambatu, sai bata saketa ba, sai ma ta yi ƙoƙarin goge mata hawaye dan ta rarrasheta. A tsananin fusace momma ta kwace kanta daga riƙon mama, take ta fara huci kamar zakanya tana jin yunwa, cikin zafa ta ce. "Idan kika sake taɓani dik abin da na yi maki ke kika nema!!". Babbar magana!. Ganin hakan yasa su Jawad gabaɗaya suka matso kusa da su, so suke yi su kwantarwa da Momma hankali da kalamansu, amma dikkansu babu wanda yake da kalmar da zai iya tinkarar momma da shi. Dan haka sai dai suka matso suka tsaya jugum jugum kaman wasu gumaka. Allah sarki Chuchu da ta ɗauki abin matsayin mafarki ba gaskiya ba, dik da haka hawaye ne yake gudu a saman face ɗinta kamar ruwan pampo, tana tsaye kamar wadda aka sassaƙa, da alama bata a cikin hanyacinta. Wai a haka sun ɗauka sace Auta aka yi, to idan suka san ta bar duniya mai gabaɗaya me kuke tinanin zai faru? Akwai bala'i gaskiya. Da kyar King ya iya motsa laɓɓansa da suka yi mashi masifar nauyi ya furta kowa dake cikin parlourn nan ya je su kyale shi daga shi sai Momma bari su yi magana. Babu musu kowa ya nufi waje, Mummyn Chuchu ta saki momma ta miƙe, a babban parlour suka haɗu suka zauna jugum jugum. Chuchu ta kasa motsawa har sai da Yah Jawad ya tallaɓota ya ja suka fita. King da Momma kawai aka bari a cikin parlon King, harta Guyson mummyn Chuchu ta ja shi sun fita wajen, kamar ba mutum ta rike ba, dik ya sake mata jiki kaman wanda ya sume, Allah sarki bawan Allah, da alama ya fita hayyacinsa ne. King da momma sun ɗauki a kallah 30 mins suna tattaunawa ta sirri, kafin daga bisani King ya rarrasheta tare da gaya mata wanda yake zargi da sace Auta wato king Al-Mustapah kenan, kuma ta kwnatar da hankalinta cikin ƙanƙanin lokaci za'a dawo mata da Auta lafiya lou In Sha Allah, yanzu za'a shirya dakarun yaki domin tinkarar Daular Qahtaniyawa, tun da sun tsokalo yaki dole a yakesu. Aunty MieMie dai bata da labarin dik abin da yake faruwa, tana can ɓangarenta tare da mijinta. Tsabar tashin hankali yasa suka manta da ita ba'a sanar da ita ba!. Momma da kyar ta hakura ta yi shiru, hakan ma dan King ya yi mata alkawarin dawo da Auta cikin kwana ɗaya ne. Cikin bedroom ɗinsa ta shiga ta kwanta, shi kuma ya wuce toilet, wanka ya yi tare da shirin tafiya fada, nan ya buƙaci Commander Zafar da ya kira mashi Hoorain ya kuma haɗa kan mayaƙa tawagar farko. Me zai yi wa Hoorain kuma?. ===========================🔥 Karfe 9 daidai gabaɗaya manya manyan jiga jigan masu faɗa a ji a cikin fada suka haɗu, hankalin kowa in ya kai miliyan a tashe yake, dik sun nitsuwa tsit suna cikin alhini, dik wanda ya ɗaga idanu ya kalli fuskar King ba zai so ya sake ɗaga idanu ya kallesa ba, saboda fuskar a ɗaure take, uban kwarjininsa ta kara bayyana, zarra ga marasa adalci da san gaskiya kenan. Yana dake saman kujerarsa, yau babu wargi bare wasa, su commander Zafar dik sun shiga taitayinsu, kowa yana nan bisa ƙaida, dik sun tattaro hankulansu a kan King Zuhair, shi kawai ake jira da ya yi magana. Dai'dai lokacin da Hoorain ya dimfaro babbar kofar fada da nufin ya shigo ciki dan amsa kiran da King ya aika ayi mashi, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan baya a cikin hayyacinsa sosai, dik ya firgice, tamkar wanda aka zarewa laka, yana yafiya yana jan kafafu tamkar ba sadauki Hoorain assistant commander ba, jarumi mai tafiya cike da zarra da kwarjini mai razanar da zuƙatan dik wasu warriors dake cikin kingdom ɗin, amma yau ya taho tamkar mace yana wani jan kafa. Masu gadin kofar fada har sun bashi hanya, ya matsa gada da su kaɗan har ya kusa shiga fada, kunsan dai'dai in da suke tsaye domin gadin kofar akwai ɗan tazara tsakaninta da kofar, a kasar stage na hawa suke tsayawa, kofa kuma tana sama. So sun bashi hanya zai wuce, ya haura saman step ɗai ɗai har uku zai taka na huɗu kenan ya tsinkayo muryar King ya fara magana cikin kakkausar murya da zafa, dama ga voice ɗinsa da kaifin bala'i, hakan ya yi gaggarumin ɗaga hankulan su commander. "Kaiconku! Kun bani kunya kuma na raina kwarewarku! Commander kana da shekaru sama da talatin kana matsayin mai jan ragamar warriors da suke cikin kingdom ɗin nan, amma yau har a samu wani mai karan kwana da zai iya keta tsaronka ya shigo har cikin kingdom ɗin nan ya ɗauki Zunaira ya fita da ita! A gaskiya ka gaza dayawa Zafar!"............ Shi ne abin da King ya faɗa a kan kunnen Hoorain da ya dakata da yunƙurin shiga fadar ya kasa kunne yana sauraronsu. Kasa da kai commander ya yi, bashi da bakin yin magana tun da ba'a bashi izini ba, sai kawai ya yi ƙasa da kai yana sauraron faɗar King. Cigaba da faɗa cikin zafa King ya yi. "Dole hukunci zata hau kan Hoorain! Saboda shi na ɗaurawa alhakin kula da Zunaira! Shi na ɗaurawa alhakin kada ya bari ko guda ya taɓa mun ita, dan haka idan wani abin ya samu Zunaira dole in hukunta shi!!".......... A dai'dai wannan gaɓa sai da commander Zafar ya yi hanzarin ɗago kansa da kallonsa izuwa kan King, ya ji zazzafar magana da baya jin zai iya jure hakan, wato hukunta Hoorain, yasan hukuncin King bata da sauki, bare kuma a kan Auta, ai ina abin ba zata yi kyau ba. Sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi, gaban maza sai da ta bada dukan uku uku, Hoorain shi ne farincikinsa, sannan ace za'a hukunta shi da laifin da bai sani ba? Gaskiya a wannan gaɓar baya jin zai iya ɗaukar wannan hukunci na King, to amma ya zai yi? Ya jefawa kansa tambaya. Sai sake sake yake yi a cikin zuciyarsa ya daina sauraron abin da King yake faɗa. Kamar daga sama ya ji warriors dake tsaye a kusa da shi ya kai hannu ya taɓa shi yana faɗin. "Master King yana magana". A ɗan zabure ya miƙe tsaye, bawan Allah ya afka duniyar tunani ne bai ji King yana tambayarsa ina Hoorain ɗin yake ba?. Ran King ne ya kara ɓaci na ya yi magana commander bai jisa ba, kun san idan mutum yana cikin ɓacin rai da zarar an mashi abu kaɗan zai tashi ya hau bala'i, to haka abin take. Ɗan risinar da kai ƙasa commander ya yi alamar girmamawa. "Kayi hakuri ranka ya dade, tun ɗazun da kace in kira Hoorain ɗin na faɗa mashi kana kiransa, ban yi tsammanin zai kai har iyanzu bai iso ba!". Sosai ran King ya kara bakanta, a ɗan fusace ya umarci ɗaya daga cikin warriors dake cikin wajen a kan su kira mashi Hoorain yanzun nan, sannan kuma dole ya fuskanci wani hukuncin a kan jinkirin da ya yi bai amsa kira ba. Dik maganganun da suke faɗa a kan kunnunsa suka yi ta, ya ji komai! A maimakon ya shiga cikin fadar ko hakurine ya bawa King ko zai samu sassaucin hukunta shi da za'ayi, sai ya juya ya fasa shiga, cikin sassarfa ya bar wajen. Masu gadi kuwa basu ce da shi ko uppan ba!. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya koma. After 5 mins da shigansa cikin ɗakin ya fito ya nufi katafaren wajen dawakansu, dik da yana sanye cikin kayan yaki ya ɗaura jacket mai girma a jikinsa, ya kuma sanya hular jacket ɗin a kansa, hakan ba zai hana ka gane yana cikin tashin hankali na kin karawa ba!. Saman wannan ƙosasshen jibgegen dokin nasa ya hau. Da karfi ya bawa dokin wuta, kai tsaye babbar gate na Kingdom ɗin ya nufa. Tun daga kan gate na farko har izuwa babba na karshe babu wani warriors da ya dakatar da shi ko ya ce zai hana shi fita ko dai ya tsaya a bincikesa, saboda dik wanda ya kwana ya tashi a cikin kingdom ɗin yasan wanenen Hoorain kuma me matsayinsa, dan haka basu yi gigin dakatar da shi ba, sai ma hanya da suka bashi cikin girmamawa ya danna waje a miliyan. Ina kuke tunanin zai je? Meyasa yaki amsa kiran King? Meyake shirin faruwa ne? Guduwa ya yi ne ko menene?.................... =======================🔥 Dai'dai lokacin da wannan warriors da King ya aika da ya kira Hoorain ya dawo cikin fada dan ya isar da sakon Hoorain baya nan bai gansa ba, a dai'dai wannan lokacin uncle Jahiz ya danno kai cikin fada, ta kofar da zata sadaka da cikin gida kenan. Sun jero a tare shi da Jaish, tin ɗazun suka shigo cikin kingdom of power, yanzu haka basu fara isa ga kowa ba sai da suka iso ga King. A karo na farko a tarihin kingdom of power yau King bai san lokacin da ya miƙe tsaye daga kan kujerar mulkinsa a zabure ba lokacin da ya ɗaura idanunsa a kan Jaish. Tun da King yake bai taɓa jin wani abin na tashi hankali ko na farinciki or al'ajabi da zai sanya shi ya zabura ya miƙe tsaye daga saman kujerarsa ba sai dawowar Jaish unexpext, Ramish ya iya bazata kam gaskiya. Sun jima suna dakon wannan rana shi da Momma, kullun addu'arsu Allah ya bayyana masu ɗansu farincikinsu, sai ga shi Allah ya bayyana shi a lokacin da basu tsammata ba, lokacin da suka fidda rai suka yanke kauna, suna cikin wani tashin hankalin kawai ya dawo garesu unexpext, kai Allah abin godiyane matuka, ya baka wani lokaci, wani lokaci kuma ya hanaka, dik cikin ikonsa da kyautatawansa ne!!. Dik da commander yana cikin tashin hankali da damuwar furucin King a kan Hoorain zai karɓi hukunci hakan bai hana shi ya zaro idanu yana kallan Jaish ba. Gabaɗaya su salama sun zuba mashi idanu, suna san yi mashi sannu da dawowa, amma babu hali, dan King bai bada damar ayi magana ba. King ɗin kuwa, ya tsaya ne tamkar wanda aka dasa. Idanunsa sun zaro waje sosai, kallonsa a kan fuskar jaish ɗinsa da ya ke kallan abin tamkar a mafarki ko kuma zuciyarsa ce take yi mashi gizo. Karisowa gabansa Jaish da uncle Jahiz suka yi, shi Jaish mamakin irin kallansa da King yake yi mashi ya yi, saboda in baku manta ba a baya ya yi loosing memorunsa ne, yanzu ne ya dawo dai'dai, so shi bai san da cewa ya jima baya gida ba, ya mance da rayuwarsa ta baya wato na gidan bappa kaf. Har sai da Jaish ya tsugunna a gabansa domin kwasan gaisuwar ban girma wanda kun san yin hakan dole ce a sarauta matuƙar masu gudanar da mulkin irin King Zuhair ne masu ƙarfin izza. Jin bugun numfashin ɗan nasa a kurkusa da shi ne yasa ya gasgata abin da idanun nasa suke gane mashi, amma dik da haka sai da ya ce. "My Jaish kai ne? Hakika kai ne ɗana, tabbas kai ne!"............. Ya yi maganar cikin murya mai sanyi, amma cike da rawar jiki. Bai jira amsar Jaish ba, ya yi sauri duƙawa ya ɗagosa ya jawo shi jikinsa ya rungume. Rungumar tasa tana da ƙarfi, cike da kewar watanni da suka wuce. Ya rike jaish gam kamar kar ya sake barinsa ya motsa ko nan da can, kamar kada ya raba jikinsu tsantsar so da kauna. "Na jima ina jiran wannan rana, mun jima muna neman ka........... ba zan sake rabuwa da kai ba!". Ya furta cikin farinciki wanda ke haɗe da murmushi mai bayyana farincikin sosai. Jaish da bai gane me King yake magana a kai ba sai ya ce. "Dad ba zamu rabu ba ai dama". Kara kankamesa sosai King ya yi tamkar zai mayar da shi cikin cikinsa. Sai murmushi uncle Jahiz yake yi. Gabaɗaya fada sai da suka ɗan murmusa ban da commander wanda dama shi baya yin murmushi, sannan kuma ya kara haɗuwa da yana cikin damuwa King zai hukunta mashi ɗan gold ɗinsa. Dawowar Jaish ya sanya su farinciki ya kuma sanyaya masu zuƙatansu akan raɗaɗin da suke ciki na rashin gimbiya Zunaira. Yanayin ya cika da farinciki mara misaltuwa, kamar duniya ta tsaya domin wannan lokaci na musamman. Kowannensu yana jin tamkar zuciyarsa tana kara kaunar juna. Wannan haɗuwa ta koma alamar soyayya da ƙarfin alaƙar uba da ɗa, wanda baki ba zai iya misiltawa ba. Uncle Jahiz ne da ya ga abin nasu ba mai karewa bane sai ya matso ya ɓanɓanre Jaish daga jikin King yana faɗin. "Is okey yaya, Jaish lest go to ur mom room, I want to see her reaction a lokacin da zata ɗaura idanunta a kanka". Ɗan ɗaure fuska kaɗan Jaish ya yi. "Uncle sai ka ce wanda ya ɓata tsawon lokaci sai yanzu aka ganesa? Tafiya fa nayi na je na dawo, kaga dad ma sai wani ƙanƙameni yake yi". Tun da ya fara magana idanun King a kansa, sai yanzu suka fahimci Jaish fa bai san komai dangane da ɓacewansa na tsawon watanni ba, dan haka sai King ya ce Jaish ya je wajen mommarsa da wuri, ya ce mashi hakan ne kuma dan yana da yakinin zata rage damuwar da take ciki a halin yanzu idan ta gansa. Aikuwa hakan ce ta faru. Lokacin da suka haɗu da momma a bedroom na King, hawaye masu ɗumin gaske ne suka fara kwaranya daga idanunta, tamkar ruwan sama mai ɗauke da albarka. A hanzarce ta sauko kasa daga saman bed ɗin King, da sauri ta kariso ta rungume shi da karfi, numfashinta yana cike da farinciki mara misaltuwa. Ganin abin take yi tamkar a mafarki, shi kuma mamakin hakan yake yi, dik da yasan cewa Momma tana yi mashi fiye da haka idan ya yi tafiya ya dawo, to amma bata ruwan hawaye a kan tafiyarsa da dawowansa, yau sai ga shi tana hawaye, sai ƙwaƙwalwarsa ta fara bashi lallai akwai wani dalili mai karfi da yasa iyayen nasa suka yi mamakin dawowarsa, ƙwaƙwalwarsa ce ta tariyo mashi yadda King ya tarbesa, abin sai ya yi mashi some how haka. Raba jikinta da nasa momma ta yi ta fara binsa da kallo, tana duba shi daga sama har ƙasa, kamar tana tabbatarwa idanunta shi ne ko ba shi ba. "Kai ne Jaish, da gaske kai ne ka dawo gare ni, Allah mai iko, Allah mai kyauta mai kari!". Ta furta cikin muryar da ta ƙunshi da dukan ƙauna ta duniya. "Momma nine mana, akwai wani abin ne?". Zata yi magana idanunta suka sauka a kan uncle Jahiz dake bayansu, kai ya girgiza mata a kan kada ta faɗa mashi komai. Dan haka sai ta rabu da shi a in da ta ce mashi babu komai. Ya yarda da babu komai ɗin, sai ya ce mata. "Momma zan je in yi wanka, and then am feeling hungry". Cike da kauna ta ce yanzu za'a kawo mashi abinci a bedroom ɗinsa, ya je ya yi wankan. Har ta ɗan samu sassauci a ranta. Yana san tambayar ina Auta, sai dai tamkar an ɗaura tongue ɗinsa, ya ji ta yi mashi nauyi ya kasa tambaya, haka ya wuce bedroom ɗinsa ba tare da ya tambaya ba, sai dai cikin ransa tunanin Autar ce kawai. Momma kuma ta koma saman bed ta kwanta. ••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 A ɓangaren mutanen fada kuwa, neman Hoorain aka shiga yi babu kakkautawa, a nan warriors dake bakin gate suka isar da sakon ai ya fita baya a cikin kingdom ɗin. King ne ya umarci warriors guda huɗu da su bi bayansa cikin gaggauwa su sanar da shi King yana buƙatar ganinsa. Sosai commander Zafar ya shiga tsananin tashin hankali na abin da yake faruwa, har wani irin kaiwa da komowa yake yi a cikin Kingdom ɗin, ya gaza zaune ya gaza tsaye, ya rasa sukuninsa, damuwarsa ɗaya a nan ita ce meyasa Hoorain zai fita daga kingdom of power? Ina kuma ya tafi?. MY PEOPLE'S AKWAI GAGARUMIN MATSALA! ME KUKE TUNANIN YASA HOORAIN YA GUDU? KENAN YA ZAƁI DA YA BAR MAHAIFINSA CIKIN WAHALA A KAN SHI YA KARƁI HUKUNCI?. ==========================🔥 •••••••••••••JIMETA YOLA•••••••••••🔥 A yau ne bappa ya miƙa sadakin Mairo dan cikar burinsa. Katuwar bujumar saniya ya bayar a matsayin sadakin. Tun safe Nanne take faman zazzaga masifa tana aikin aika mashi da tsinuwa da bakaken maganganun. Amma yadda kuka san an shuka dusa a gona, ko kaɗan bai nuna alamar kamar yasan da wata halitta ita wai Nenne a duniya ba, sai hidimar gabansa yake yi, nan da kwana uku za'a ɗaura aure dan Mairo ba budurwa bace, ta taɓa yin aure sai dai bata taɓa haihuwa ba, mijin nata ne ya rasu aurensu da wata biyu. So ba wani bikin da za'a gudanar mai tarin yawa dan dikkansu ba yara bane kuma ba saurayi da budurwa bane. Wunin yau a gona bappa ya wuni shi da Mahreen da Mahnoor, sun bar Nenne da shakan kayan takaici. Tun da suka je gona da safe har yamma suka dawo, tun kuma da suka je Mahnoor bata furta ko uppan ba, tana dai zaune shiru. Da kaga idnaunta zaka san tana bala'in jin barci, dan har sun ɗan kumbura sun yi jajir, jiya yadda taga rana haka taga dare, ta kasa yin barci, Jaish ne kawai a cikin ranta, tana manne da kayansa a kirjinta har wayenwan gari. Da kyar ta iya gabatar da sallar asuba, tun da ta yi sallah kuma ta fito ta kama yin aikace-aikacenta tamkar yadda ta saba yi, bata ma jira sai Nenne ta zo ta yi mata tashin cin mutumci ba, sai ta koma ruwa kawai gwanin ban tausayi. Yanzu haka tana zaune a cikin gonar nan gyangyaɗin barci take yi, sai barcin ya yi kamar zai ɗauketa sai kuma ta zabura ta farka kamar wadda aka razana. Dik abin da take ciki bappa yana sane, ya dai yi shiru ne kamar bai ganta ba, bawan Allah bashi da abin faɗe. Yanzu so yake yi ya samu Arɗo su yi magana a kan wannan aure nata, tabbas Arɗo zai iya warware wannan aure, dan matsayin alkalin kauyen yake, da ace mijin Mahnoor ɗin sun san shi, sun san tushensa, sun san asalinsa ne ya tafi bai dawo ba, to wannan addini ya bada damar a jira na tsawon shekaru biyar, wata mas'haban ta ce shekaru uku in bai waiwayeta ba sai a raba auren, amma basu san shi ba, basu san daga ina ya fito ba, mutum ne ko aljani dik basu sani ba, kaddara tasa aka aura mashi ita, daga baya ya ɓace daga ganinsu to wannan a musulunci wakkwaran bincike za'ayi domin a tabbatar da mutum ne shi ko aljani, idan kuma babu ta yadda za'ayi a bincika kamar dai shi Jaish ɗin to wannan alkali yana iya raba auren!. To yau da daddare ya shirya zai je ya samu Arɗo su tattauna. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Zaune take karkashin bishiyar mango, ta buga uban tagumi, a zahiri zaku ga kamar tana kallon bappa da Mahreen dake aikin cire kananan ciyayin da suke fitowa bappa wajen masararsa. Amma a baɗini tunanin kyakkyawan mijinta take yi, ganinsa kawai take yi a idanunta yana yi mata gizo. Kamar daga sama ta ji an ce............ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Kamar daga sama ta ji an ce. "Mahnoor". Kin ɗago kai ta yi, dan tasan tabbas Hamma Faisal ne, voice ɗinsa ba zai taɓa ɓace mata ba. Bai damu ba dan bata amsa mashi ko ya ɗago ta kallesa ba, sai ya nemi waje kusa da ita ya zauna yana ƙoƙarin sake yi mata magana haɗe da kai hannunsa kusa da face ɗinta da nufin zai goge mata guntun hawayen dake face ɗin nata. Ai a miliyan ta miƙe tsaye daga kusa da shi yadda kuka san wadda aka kawowa wuta kusa da ita. Mamaki ne sosai ya kama shi, bai taɓa tunanin zai zauna a kusa da ita ta guje shi ba, ita kuma auren da yake kanta take karewa mutuncinsa, tana daraja kanta, aurenta da kuma mijinta, so bata ga dalilin zama kusa da wani ba ko da ɗan uwan nata ne, bare kuma shi da ya taɓa santa a baya, babu wannan magana. Miƙewa tsaye ya yi shi ma dan ya yi magana da ita. Sai dai bai kai ga buɗe baki ba da gudu tasa kai ta bar mashi wajen, dama lokacin komarsu gida ya kusa, sai kawai ta nufi gida wani irin zafafan hawaye suka fara zubo mata, ɗacin zuciyarta ya yi mata, yau da Jaish yana nan ai Hamma Faisal ba zai zo kusa da ita har haka har ya nemi yi mata magana ya nemi taɓata ba, gaskiya ta yi babban rashi matuƙa. Da gudu Faisal ya bi bayanta, dik abin da ya faru a kan idanun bappa ya faru, ita kam Mahreen tana zaune ta buga uban tagumi, dik abin da ake yi bata da labari, ta shiga duniyar tunanin ina Jaish yake?. Hmmmm Mahreen ma ta damu da Jaish haka bare Mahnoor da suka saba kwana ɗaki ɗaya, ya yi ta gwada mata soyayya, ai dole ta yi kukan rashinsa wlh. Bappa ya kawosu gonar nan ne domin su rage damuwa, amma ina sai suka zo suka buga mashi uban tagumi suna kuncin abin da yake faruwa. Tana shigowa cikin gida ta wuce ɗakinsu da gudu, a lokacin Nenne tana cikin ɗakinta, so bata ga shigowarta ba. Kusan a tare suka shigo da Faisal ɗin, da yake hankali bata gama isarsa ba, sai ya bita har cikin ɗakin mijin nata, shi a dole zai rarrasheta. Saman mattress ta faɗa tana cigaba da kukanta kamar wadda aka yi wa wahayin hakan. A kan kayan Jaish da bappa ya bata ta kwanta tana jin kamshin jikinsa a jikin kaya, gani take kamar shi ne a wajen. Kamar daga sama ta ji mutum a kusa da ita yana magana ƙasa ƙasa. Ai a zabure ta miƙe zaune, ido cikin ido ta kalli Faisal da yake dab gadan yana kallonta. A miliyan ta miƙe tsaye, bata yi zaton ya biyota ba, tana san cewa ya fita mata a cikin ɗaki, amma kuma ta kasa yin magana, dan haka sai ta wuce ta raɓa gefensa zata fita waje. Da sauri ya riƙo hannunta dan ta tsaya ya rarrasheta, Allah sarki, shi har yau har gobe yana santa bawan Allah. Wani irin fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi da karfi, a zuciye cikin ɓacin rai haɗe da ɗaga murya ta furta. "Ka sakeni Hamma Faisal!!". Ya yi mamakin jin tsawarta a garesa, amma santa ya rufe mashi idanu da baya ganin laifinta, a baya ko ɗaga murya a magana Mahnoor bata yi, idan ma baka da nitsuwa ba zaka iya jin magana ba idan ta faɗa, tsabar yadda take magana a hankali ƙasa ƙasa cikin nitsuwa, amma yanzu rashin Jaish yasa ta fara faɗa. "Mahnoor na ji na sakeki, amma dan Allah ki daina yin kuka kin ji? Ki yi shiru dan Allah sai ki faɗa mun meyasameki, meyasa kike kuka?". Raɓawa gefensa kawai ta yi zata wuce, domin kuwa bata san ya tsaya mata a cikin ɗaki. Bata kai ga fita ba ta tsinkayo muryar Jumma yar Inna Rabi wato amarya tana yin sallama a tsakar gida. Ai da gudu ta ƙarisa fitowa waje. Suna haɗa ido da Jumma ta karisa da gudu ta faɗa jikinta tana kara karfin kukan da take yi, rungumeta Jumma ta yi, dama abin da ya kawota kenan, Inna Rabi ce ta turota da tazo ta jajantawa Mahnoor ɗin, sannan ta rarrasheta, Allah sarki Inna Rabi tana kaunar Mahnoor sosai, dik yadda aka yi sun yi zaman amana da mamar Mahnoor sosai. Wani irin mummunar faɗuwar gaba Jumma ta ji ganin Faisal ya biyo bayan Mahnoor ya fito daga cikin ɗakin shi ma, ga Mahnoor ɗin kuma tana kuka, abin ya yi mugu mugun bata mamaki, to me ya kai shi cikin ɗakin matar aure kuma? Jumma ta jefawa kanta tambayar. Sai ta ji kirjinta ya buga, tasan mutanensu fa wasun su ba hankali ne da su ba, kada ace wani abin ya je ya yi wa Mahnoor da yasa take kuka haka tamkar ranta zai fita. Koke kokensu ya ja Nenne ta fito daga cikin ɗakin, basu ga fitowarta ba sai dai suka ji murya tamkar saukar aradu ta daka masu wani irin uban tsawa. "Uban me kuke tsaya yi mun a tsakar gida kuna wani yi mun koke koke na munafurci zaku hanani shaƙatawa". Jumma uwar rashin kunya idanunta a tsaitsaye kar ta ce. "Kai dama idan za'ayi wa mutum kishi shakatawa yake yi kenan?". Zaro idanu Mahnoor ta yi, ai bata san lokacin da ta dakatar da yin kukan nata ba, lallai Jumma bata san bala'i da ake yi a wannan gida a kan wannan kishi da za'ayi ba ne! Da ba zata yi magana ba!. Fusata Nenne ta yi, ranta ya sosu da jin kalamar Jumma, sai dai ba halin ta yi mata komai, saboda su fa ba ƙaramin aikinsu bane yanzu idan ta daki Jumma mijinta ya zo ya ci uban Nenne ɗin, su mazansu sun iya tarewa matansu faɗa, kai ko yaransu ka daka ba zaman lafiya har sai sun rama. So Jumma matar aurece a yanzu tana tsoron dukarta bata san ya halin mijinta yake ba, kila mai tsauri ne a kan iyalansa. Jumma da ta ga Nenne bata kulata ba sai ta ja hannu Mahnoor suka raɓa jefan Faisal suka koma cikin ɗakin. A saman mattress suka zauna, hannu Jumma tasa tana goge mata hawaye tana cewa ta yi shiru yanzu ai ta zo zasu yi shawara a kan mafita, dan haka ta yi shiru suyi magana. Ƙoƙarin danne kukan nata ta yi, amma abin ya ci tura, ta kasa dannewa, dan hawayenta cigaba da fasowa suke yi. Tun Jumma tana goge mata hawayen har ta rabu da su kawai, dan sun ki tsayawa. Cike da tausayawa ta ce. "Mahnoor yanzu kukan ne kike yi fisabilillah?". Kifa kanta a saman gwiwonta ta yi, tana jin tamkar an ɗaura zuciyarta a saman wuta mai cin bala'i ne, cikin kuka da ɗan ɗaga murya ta ce. "Jumma bappa ya ce zai raba aurena da Hamma a aura mun hamma Faisal..........." Wani irin rushewa da kuka da ta yi ne ya ja ta haɗiye sauran maganganun ta kasa amayar da su, saboda ba zata iya karisasu ba, wato yanzu ba kukan rashin Jaish ɗin ba ma take yi, kukan raba aurenta da shi take yi, Allah sarki abin ya haɗu ya yi mata yawa. A lokacin kuma Faisal ya wuce ya bar gidan saboda Nenne, yana tsoron bala'inta, sai ya kama kansa kawai ya haƙura, kuma Jumma tazo yasan zata rarrashin mashi Mahnoor ɗinsa. "Haba mana bappa, ina hakan ba zai yiwu ba, gaskiya kada ki yarda a raba aurenki da hammanki, ina da tabbacin In Sha Allah zai waiwayeki, ai so ba karya bane, tabbas dik in da yake yanzu haka yana tinaninki, ba zai taɓa jefar dake ba komai zai faru"............ Cewar Jumma!. Wannan magana ta Jumma ta yi dai'dai da lokacin da Jaish ya ke ƙoƙarin kwanciya a saman katafaren bed ɗinsa, ya yi wanka yana sanye da three quter jeans white color and white singlet masu kyau, ya yi matuƙar mamakin ganin yadda gashin kansa ya yi yawa, sai dai bai kawo a ransa ya yi rayuwa a wani waje ne dayasa gashin ta taru sosai saboda rashin datseta ba, ya wanke kansa kawai ya gyarata da mayukansa masu kyau da tsada. Sai dai fa wlh gashin da ta yi yawa ta yi masifar yi mashi kyau, shi kansa ya shaida ta yi mashi kyau, hakan ce ma yasa bai wani damu da yawan gashin ba, sai ya ji ma kamar zai iya barinsa ya cigaba da kashe mashi kuɗi kawai dan ya yi kyau matuƙa. Rage gudun Ac ya yi, ya kwanta kenan sai ya fara tunanin ina wayarsa zai kira number Zunaira ya ce ta zo. Kada ku manta wayar tasa tana hannnun Mahnoor. Miƙewa tsaye ya yi ya fara bincikar ina wayar tasa take?. Ko'ina ya duba bai gani ba. A bakin bed ɗinsa ya koma ya zauna, shiru ya yi yana tunanin in da ya jefar da wayar tasa, ɗan lumshe idanunsa ya yi ya fara tariyo baya dan ya iya gano ina wayarsa take?. Dai'dai lokacin King and Momma suka shigo cikin ɗakin, uncle Jahiz yana biye da su a baya, hakan ya dakatar da shi daga tinanin da yake ƙoƙarin yi na a in da ya jefar da wayarsa. Ita kuwa Jumma cigaba da karfafawa Mahnoor gwiwa ta yi a kan Jaish zai waiwayeta, dan haka dik bala'in da za'ayi kada ta yarda a rabata da aurensa, dan shi kaɗai ne garkuwanta kuma gatanta bayan Allah kenan. Ta yi na'am da zancen Jumma, dan haka sai ta ɗaura ɗamarar gayawa bappa ba zata iya rabuwa da Jaish ba, ta kuma ji daɗin zuwan Jumma, har ta ji ranta ya ɗan sanyaya. Da kyar ta goge hawayenta ta kuma dakata da yin kukan, har da ajiyar zuciya. Jumma ganin ta yi nasarar dakatar mata da kukan yasa ta fara ƙoƙarin kawo mata hira masu daɗi da zai ɗebe mata kewa. Cikin hiran nata ne ma ta sanar da ita tana da ciki har na tsawon wata biyu da sati biyu, sosai Mahnoor ta tayata farinciki, ta ji daɗin maganar matuƙa. Haka suka cigaba da yin hira tana bawa Mahnoor shawarwar haɗe da kara mata karfin gwiwa a kan ta dage ta tsayawa aurenta, kada ta yarda a farraka mata shi. Sosai Jumma ta so jin kwakkwaf a kan ko dai ita ma Mahnoor tana da cikin Jaish ne, ko kuma sun taɓa kwanciya, amma ina Mahnoor taki yarda da faɗa mata komai, da zarar ta kawo zancen Jaish Mahnoor zata doje taki yarda su yi ta. Daga karshe Jumma ta fahimci Mahnoor fa ba zata faɗa mata ba, sai kawai ta hakura, a tinaninta iya kunya ce kawai tasa Mahnoor bazata sanar da ita ba, bata san ba haka bane, Mahnoor tasan wannan sirrin mijinta ne shiyasa taki yarda ta faɗa, sai dai su yi hira na iya labarin da ya shafi kauyen, amma Mahnoor bata yarda a shigo da hiran Jaish ba, da Jumma ta sako maganarsa bakin Mahnoor zai fara haila ta ki bata amsa, sai ta yi kamar bata ji me ta ce ba, daga karshe ta kawo wani zancen ta ɗaura a kai. Har sai da mangariba ta kawo kai, sannan Jumma ta tafi ita kuma Mahnoor ta fito ta kama aikin da ta saba. A tsakar gida ta isko Mahreen tana zaune ta buga uban tagumi kamar dai ɗazun a gona, shi kuma bappa ya wuce masallaci daga nan ya wuce gidan Arɗo dan su yi magana a kan Mahnoor ɗin. After some days. Bayan wasu kwanakin. An ɗaura auren bappa da Mairo tamkar yadda aka ce, yanzu saura tarewa, kwana uku kenan yau da ɗaura auren, babu wani biki da suka gudanar saboda na faɗa maku ita ba budurwa bace, so iya ɗaurin aure ne kawai sai kuma wannan al'adar tasu da suke yi nahawa dutse dan a rubuta sunan ma'aurata, wannan dole ce a wajensu, sannan sai al'adar da suke yi na yanka shanu ayi ta gashi, a can gidansu Mairo kuma an yi al'adar da iyaye da makota suke yi wato a tara nono da fura dayawa ayi ta sha, kowasu makota ranar ba zasu sayar da nono da furansu ba, zasu haɗosa a kawo gidansu Mairo, shi ne nasu gudumawar. Dik bakin da zasu zo sai su yi ta sha babu kakkautawa. So iya abin da aka gudanar a bikin kawai, Mahnoor dai bata je wajen bikin ba, tana wajen Inna kakarta, Mahreen kuwa da bata ga abin da zai hanata zuwa wajen biki ta ci uwar sabada ba ai sai da ta je, ta ci uwar kyalliyar powder gora guda ta zazzage a face ɗinta abinta, kamar aljanar asuba, amma saboda bala'inta kowa ya ganta sai ya ce ta yi kyau sosai, kuma karya suke yi ba wani kyan da ta yi, kawai suna tsoron bala'inta ne yasa suke yabata ɗin munahikai. Kaki yabata ka shiga uku. Har da su Jumma sun je bikin, sun kuma yaba kyan Mahreen ƴar amarya kenan, dan ita ta gama shaidawa kauye yanzu ita yar Diddi Mairo ce ba ƴar Nenne ba, wato a duniya yarinta ma fa duniya ce, ba abin da ya kai shi daɗi, ta dai ce ita ƴar Mairo ce, ta koma tsagin amarya. Kwanaki uku ana ta hidima, yau za'a kawo Mairo ɗakinta ko in ce zata tare a ɗakinta, bappa bai yi mata wani ɗaki na daban ba, ya ce a ɗakinsa zata zauna, so nan kawai ya gyara mata, yaki yi mata wani bukkar.............. Ni Princess Teema na ce anya bappa ba ɗan duniya bane kuwa? Wato so yake bakinciki ya kashe Nenne ko? In ba tsabar minahinci ba ita ma ya yi mata ɗakinta daban kamar Nennen mana! Me na wani ta sauka a nasa ɗakin?. My people's kuzo mu yi gulma, anya ba maman Mahnoor bawan Allahn nan yake gani a tattare da Mairo ba kuwa? To mu dai yanzu zamu koma team uwar gida Nenne dan mu taya Nenne faɗa, haba wannan wani irin bala'i ne, yar cikinta ma ta gujeta ta komawa amarya, to mu ba zamu yi lamurje ba.🙄 To izina garemu mata, shi dai bakin hali yana raba ka da kowa, ciki harda ƴaƴan da ka haifa a cikinka, ya rage naku ku kyautata zamanku da kowa, ku zaku ji daɗi idan kuka iya zama, kai in fa kuka zauna da kowa lafiya wlh sai kunfi abokan zaman nakuma cin ribar zaman, ina fatan kun ɗauki darasi?!!. Wato akwai dirama a gidan bappa fa, dan kuwa ko da ƴan uwan Mairo suka kawota basu kwashe ta daɗi da Nenne ba, dan kuwa irin wanna nasiha da ake yi ace an kawowa uwar gida amana nan da suka zo zasu bawa Nenne amana ta yi masu wankin babban bargo, har da cewa su dai kaiwa bappa amana tin da shi ya rakitimowa kansa ita kuma yake ganin zai iya, dan haka a kai mashi ba dai ita ba!!!. Ta ci masu mutunci fes, dik da haka kuma bai isheta ba, da taga basu kulata ba sun nufi cikin ɗakin bappa sun kai Mairo suna karisa mata jeren da basu gama na. Sai Nenne kam ta fito da tanadin da ta ɗauki sati guda tana shirya masu, wato wuta ta hura yana ci sosai, sai ta banka barkono mai bala'in zafi da yawa a cikin wutar, ai ba iya ƴan kawo amarya ba, gabaɗaya unguwar rikicewa ya yi da tari mai sauti, kun san yadda barkono yake a cikin wuta. Haba ai ba yan kawo amarya ba, harta ita kanta amarya bata tsaya ba, tuni suka ari kafar kare suka cikawa zannuwansu isa. Binsu da barkono da toka wanda ta daka barkonon ta tanƙaɗe toka ta haɗe su wajen guda ta rinƙa ɗaurawa a leda, to shi ta rinƙa binsu da shi tana harbinsu da shi, yana da bala'in zafi ga shiga hancin mutun. Idan ta harba shi ya faɗi kasa ya fashe sai tokan ya tashi sama da garin barkonon, ya yi masu dai kamar guguwar turɓaya yana shiga hanci. Balai'n zafi ne da wannan abin. In short pata pata Nenne ta yi masu, ta zama kamar mahaukaciya, dik wasu abubuwan da aka kawowa amarya sai da ta ta dawo ta watsa shi kaca kaca, abubuwan fashewa dake cikin kayan kuma dik ta bi ta fashesu rugu rugu, kwaryar dama nono da su ludayi da aka kawowa amarya masu bala'in kyau har da kwalliya a jikinsu, dik ta takesu ta fashe, dik wasu tulu na jere sai da ta fashe shi!. Abin dariyar kuma tana gama yin wannan aika aikan bata tsaya ba sai ta gudu gidan Arɗo ba tare da Arɗo yasan ta zo ba, ta gudu ta je gwaggonta ta ɓoyeta a ɗaki ta yadda ko annemeta a yau dai ba za'a ganta ba. Ashe maras kunyar karya ce ita. Idan ran bappa ya kai dubu to ya ɓaci, yana ji da kansa an kawo mashi amarya kawai Nenne zata wani rakasu a guje!. Wlh bata isa ba. Cikin ɓacin rai bappa ya dawo gida domin ya ɗacaca mata kamar yadda ta ɗacaca mashi, ta korar mashi amarya, yau Nenne ta kuresa ta kawo shi har wuya, hakan yasa ya shigo a fusace, sai dai kash, bai sameta ba, wlh yau da ya sameta a gidan da bakaramin duka zai yi mata ba, saboda ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci. Cikin kunan rai ya juya ya fita, kai tsaye gidan Arɗo ya nufa dan ya dubata. Sai dai ko da ya je can Arɗo ya ce mashi bata zo ba, dan bai san tana ciki ba. Da kyar bappa ya iya haɗiye ƙuncinsa ya koma wajen Mairo dan ya basu hakuri ya kuma ɗauko amaryarsa su koma gida a tare. Kai my people's Nenne ƴar duniya ce wato. ===============≠===========🔥 ••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••🔥 Kwance momma take a saman bed ɗin a cikin bedroom ɗinta, ta baro room na King, da kanta ta kaiwa Jaish abinci cikin bedroom ɗinsa, a lokacin ta isko shi yana wanka, sai ta koma room nata dan ta ɗan huta. Sallama mama Haulat ta yi mata a bakin kofar shigowa, tana da kwance ƙasa ƙasa ta amsa sallamar haɗe da bata izinin shigowa. Turo kofa ta yi ta shigo, a ƙasa gaban bed ɗin ta zube gwiwowinta, cikin girmamawa ta ce "Barkanki da hutawa ranki ya daɗe". Shiru na ƴan sakanni momma ta yi kafin ta amsa da. "Akwai wani abin mai muhimmanci ne?". "E dama uncle Jahiz ne yake parlour yake san ganinki". Jinjina kai ta yi ba tare da ta sake magana ba ta nunawa mama Haulat hanyar fita da hannu alamar ta je tana zuwa. Miƙewa ta yi ta nufi waje tana yi mata addu'ar a fito lafiya. A cikin ranta ta amsa addu'ar da Amin, Allah sarki, damuwa ne kamar zai kasheta, shiyasa King yasa a ɓoye mata Guyson ya suma yana gadon asibiti, ga Chuchu ma kwance rai a hannun Allah, dik saboda tashin hankalin ɓatar Zunaira, tun fitar da su Mummyn Chuchu suka yi da shi ashe tin lokacin yake a sume, yanzu haka yana hospital ɗin cikin kingdom ɗin ana duba lafiyarsa, ita ma Chuchun an bata gado. So King ya ce a ɓoyewa Momma da Jaish hakan kada a bari su sani, sannan a ɓoyewa Jaish batun ɓatar Zunaira, a ce mashi tana Dubai, dan in ba haka na za'a samu gagarumin matsala, kun dai san bai jima da dawowa cikin hayyacinsa ba, so a cewar King kafin Jaish ya damu ya fara nemanta har ya ce zai bita Dubai to su kuma sun yi gaggauwar gano in da take!........... My people's shin kuna ganin hakan zata yiwu kuwa?!. Miƙewa momma ta yi, dik sai ta ji jikinta ya kara mutuwa sosai, Allah sarki ciwon Guyson ne yake ratsa jininta ba tare da ta sani ba. Alkyabbarta ta ɗauko ta ɗaura kan kayan jikinta, ta nufi parlourn. Ba karamar mamaki ta sha ba ganin uncle Jahiz rike da jariri a hannu, yaron ya kwanta luf a jikinsa, idanunsa kuma a buɗe sai dai bai yi kuka ba, yana ta faman buɗe baki alamar yana jin yunwa sosai. Tsuma da san jin daga ina ya samo jajiriri yasa momma ta kasa iya zama kafin ta tambayesa, cike da mamaki ta ce. "Jahiz....... Ina kuma ka samo baby?". Zama ya yi saman mai zaman mutum ɗaya sofa kafin ya bata amsa da. "Zauna mama sai ma baki labari, dama kuma hakance ta kawoni wajenki". Idanunta a kansa ta samu waje ta zauna saman two seater. Dik a ƙage take da san jin in da wannan yaro ya fito, ta tsare yaron da kallo, lokaci guda ya shiga ranta, dama ta jima rabonta da jariri a hannu, shekaru wajen 14 fa yanzu, tin kan Zunaira, ai kunga zata so jariri sosai a yanzu. Miƙa mata babyn ya yi. Ba musu ta yi saurin karɓa tana kallon babyn cike da kauna, har da sauke nannauyar ajiyar zuciya. Dawo da kallonta a kan uncle Jahiz ta yi tana jiran ta ji bayanai. Ɗan gyaran murya ya yi kafin ya fara bata labarin haɗuwarsa da su Khadija, yadda suka bugesu da mota da kuma halin da suke ciki a yanzu. A ɗan hanzarce ta ce. "To yanzu ina suke?". "Suna hospital na cikin Kingdom ɗin nan, naga a Abuja ba wani kula da su sosai za'ayi ba, kuma kinga dik wani abin da ya samesu alhakin a wuyarmu zai rataya, shiyasa na nemi takarda daga hospital ɗin can dan mu samu damar zuwa da su nan a dubasu da kyau". Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas haka ne, dik abin da ya faru da su Khadija a wuyarsu ya rataya, sannan ta dawo da kallonta a kan babyn dake ta faman buɗe baki. "Jahiz yaron nan ai yunwa yake ji". Ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe mashi fuska da kyau ta yadda zai samu damar ganin haske da kyau!. "Yeah tun jiya babu abin da aka bashi, mahaifiyarsa tana kwance bamu da tabbacin tana raye ma". Sosai momma ta ji tausayi ya kamata, sai ta ji tana san zuwa ta gansu, amma babu hali, bata da damar fita, dan haka sai ta ce da shi. "Ba damuwa, zan kula da yaron, kai kuma ka kula da marasa lafiyan har zuwa su samu sauki". Miƙewa tsaye ya yi, cikin nitsuwa ya ce. "Yauwa momma ina godiya, dan Allah ki kula da yaron nan sosai, saboda ina kaunarsa, ya shiga rai'na da kallon farko, yanzu dai bari in je hospital ɗin ma in duba su, dan tun da muka miƙasu ga likitoci ban sake komawa ba". Jinjina kai ta yi kafin ta amsa da. "In ka fita ka turo mun Haulat, dan wannan yaron ɗanyen jariri ne da ko wanka ba'ayi mashi ba". Da okey ya amsa mata, sannan ya nufi waje. Kurawa yaron idanu ta yi yana ta kallonsa, kyakkyawa kamar a bata shi kyauta, ga idanunsa a buɗe dara dara. Da fitarsa bai fi minti ɗaya ba sai ga mama Haulat ta shigo cikin hanzari. A gaban momma ta zube gwiwowinta. Miƙa mata babyn momma ta yi tare da miƙewa tsaye. "Ki yi mashi wanka, sabon haihuwa ne, sannan ki bashi madara mai ɗumi, ki yi mashi dik abin da ya dace". Tana kai karshen maganar ta wuce izuwa bedroom ɗinta, dan jikinta babu kwari, alamar zazzaɓi mai zafi ma take ji. Wucewa da babyn izuwa ɗakinta mama Haulat ta yi, ita ma sai kallon yaron take yi, da alama babyn Khadija yana da farin jini matuƙa, dan kowa ya kallesa sai ya kama zuciyarsa da kauna. •••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 A can cikin fada kuwa, ran King ya gama ɗacaca matuƙa, hankalinsa a tashe, ga guyson da Chuchu rai a hannun Allah, ga Zunaira ba labari, Hoorain ya gudu, dan haka sai ya yanke hukunci cikin fushi, ya ce da commander Zafar a je a yaki Daular Qahtaniyawa, a kashe dik wanda ya gwada gardama, a tattaro mashi mata da maza yara da manya dik a gurfanar mashi da su a gabansa, daga yau sun zama bayi a kingdom of power..... Tashin hankali. Cikin fushi ya yanke hukunci fa. A dai'dai wannan lokacin da King yake umartan commander Zafar da a ruguje Daular Qahtaniyawa, ya yi dai'dai da lokacin da Queen Zarina take tsaye a saman kafafunta cikin wani irin ƙasaitacciyar shiga na ban mamaki, gaba da bayanta dikka dakakkun warriors ne da suke gadin lafiyarta ta yadda ko guda ba zasu bashi damar taɓata ba. A saman wani stage take tsaye wanda ƙasan stage ɗin wasu irin mahaukatan manya manyan warriors ɗinta wanda ta gina masu jikinsu da tsafi ne, ganinsu da ido kawai sai yasa zuciyar mutum ta buga ya mutu, basu da kyan gani ga bakar mugunta a fuskokinsu, babu rahma ko ɗigo a tattare da su. Sai dai dikkansu dik da wannan horo da suka samu ga kuma tsafi suna tsaye ne a bayan wani dakakken warriors guda ɗaya wanda shi ne a gaba da su yake jagorantar wannan runduna. Ko baka san fuskar Hoorain ba idan kaga wannan mayaka tabbas zaka iya alakanta shi da Hoorain assistant commander na kingdom of power......... Tashun hankali. Dan daga yanayin tsayuwarsa cikin jarumta da daki zai iya tabbatar maka da basu da banbanci da Hoorain...... Tashin hankali. Kai Hoorain ne ma, dan wannan irin abu haka ba zai taɓa zama waninsa bane, shi ɗin ne!! Tab akwai matsala, kenan Hoorain dama Queen Zarina yake yi wa aiki? Menene yasa ya ci amanar kingdom of power har da mahaifinsa haka? Kenan ya zaɓi wasu a kan mahaifinsa? Ya aka yi Zarina ta san Hoorain? Tin yaushe ya fara yi mata aiki? Aiya mahaifinsa ma zai iya kasancewa abin yarda kuwa? Anya shi ma ba maciyi amana bane kuwa? Kada ku manta a baya alkalamin princess Teema taku ta amana na gaya maku cewa bayan mammiensu Sarina akwai waɗan da suke cin amanar Kingdom of power suke aiki da Queen Zarina, kuma mutane da suke da kusanci sosai da King Zuhair, yardaddunsa ne, in baku manta ba na taɓa faɗa maku zaku sha mamaki a lokacin da gaskiyar zata bayyana, zaku sha mamaki idan kuka gane maciya amanar kingdom of power, ku dai muje zuwa, akwai tashin kai a gaba. ________________________________🔥 Yana tsaye ne tamkar wanda aka sassaƙa, dik da yana cikin hular mayaƙa, hakan ba zai hana ka fahimci babu rahama da imani a tattare da shi ba. Cike da izza da zallar madarar zalinci Queen Zarina take basu umarnin kalar kisar da take da buƙata zasu yi wa kingdom of power, har da cewa su ɗauko mata Jaish su kawo mata shi, dan a duniya idan akwai wanda take so to ya biyo bayan Jaish yaro ɗan Mommarsa, dan haka a kashe kowa a ɗauko mata Jaish, a shekaru fa ta kai ta haifi Jaish, amma kuma zuciyarta ta kamu da kaunarsa dan tabbatar matacciyar zuciya. Allah sarki yaro ɗan Mommarsa, yana can yana sha'aninsa ana mutuwa a kansa bai da labari. Cikin girmamawa waɗan nan bakaken azzaluman mayaƙan nata suke karɓar umarninta, zaluncin mutanen nan ya kai su iya zaro jariri daga cikin uwarsa su kashe shi su jefar da gawar babu abin da ya damesu, basu da tausayi ko ɗigo a ransu, ko da yake zukatan da ake sarrafawa da tsafi yaushe suka ga imani da tausayi?. Akwai cakwakiya, King Zuhair ya bada umarni ga mayakansa da su je su ruguje Daular Qahtaniyawa su kashe kowa su haɗo mashi kan mayakansu da bayinsu su zo su zama bayi a kingdom of power ba tare da ya tabbatar da cewa King Al-Mustapah ne ya ɗauki Zunaira ko ba shi bane, kawai ya yanke hukunci cikin fushi babu bincike. Ita kuma Queen Zarina ta bada umarnin a zo a kashe mata kowa a Kingdom of power a kama Jaish a kai mata shi su yi aure. Me kuke tinanin zai faru?. A gefe guda kuma evil kingdom suna can suna ta gagatumin shirin da idan suka dinfari kingdom of power dole su rugujeta su shafeta a doran duniya, wani irin mummunar kafurin shiri suke shiryawa. Ga shi shi kuma King Zuhair yaki yarda ya karɓi tuban King Al-Mustapah bare ma har su haɗa kai wajen ganin bayan Queen Zarina da su King Abdul Aziz, shi kaɗai kuma ni da ku mun san wlh ba zai iya yin faɗa da waɗan nan masarautu har ukun ba, ga ubansu Black Tiger a gefe, wanda shi tuni ya shirya aje a durkusar mashi da kingdom of power a kawo mashi King Zuhair gabansa ya zo ya yi mashi sujjada ya lashi kafafunsa, batun fitarsa fada ya dakatar da shegun wayakan Robbot ɗinsa ba su afka kingdom of power ba, amma yana nan da shirin a ransa, kuma zasu aiwatar, yanzu so yake ya shiga fada. Hankalinsa ta ɗan kwanta, ya nitsu, bayan haka ya ɗauki mataki a kan Sweetie, idan ta bashi Spender sai su ruguje kingdom of power, wannan ne shirinsa a yanzu. ••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Yau hospital cike yake da ahalin King, Jawad da bai san Jaish ya dawo ba yana hospital zaune kusa da gadan da aka bawa Chuchu, su uncle Taheer dik suna cikin hospital ɗin. Uncle Jahiz ya yi mamakin ganinsu a cikin asibitin, sai dai da ya tambayi me yake faruwa? Basu faɗa mashi Zunaira ta ɓata ba, sai suka ce mashi rashin lafiya ne na guyson da Chuchu. Ya yarda da hakan, dan haka ya je ya duba jikin Chuchu kafin ya fito ya nufi ɗakin da guyson yake kwance. Bawan Allah tamkar babu rai a jikinsa. Uncle Jahiz ya yi mamakin ganinsa a haka, sai ya yi tunanin ko ciwonsa ne ya tashi, dan haka sai ya yi mashi addu'a sosai tare da tofa mashi, sannan ya fito ya shiga wajen su Khadija. Harda mai keken napep ɗin nasu dik aka taho da shi, idan baku manta ba na faɗa maku shi ma ɗan arewa ne, ɗan Kano ne, so da su uncle Jahiz aka ce masu babu kowa nashi da ya zo, sai suka haɗa da shi kawai suka kawo su ana jinyarsu. Dik wannan bidiri da ake yi fa Sarina da Mammiensu suna part ɗinsu hankalinsu a kwance suna shabgar gabansu, sai kulla wani minahincin suke ta faman yi, da alama wannan karan mugu mugun abu Mammie take shiryawa wannan ahali!!. Dai'dai lokacin da uncle Jahiz ya sako kafarsa cikin ɗakin dai'dai wannan lokacin Zee ta fara motsi numfashinta yana fita da karfi karfi. A hanzarce ya ƙariso gaban bed ɗin nata, ɗakinta daban da na Khadija, iya kaɗai ne nan. Ganin tana buƙatar taimakon likitoci ne yasa uncle Jahiz ya yi saurin juyawa ya je ya kira likita. Oxygen suka zo suka sanya mata dan numfashinta ya dai'dai, a saman kujerar da aka tanada dan masu jinya uncle Jahiz ya zauna yana tinanin ina ahalin su Zee suke?. Tsananin tausayinsu ne ya kama shi sosai. Oh ta ko'ina ba sauki fa, to bari dai mu leƙa Dubai muga me ake ciki ne wai!. •••••••••••••••••DUBAI•••••••••••••••••🔥 Tuni Ramish ya miƙawa jami'ansa Leesharh, dama sun jima suna neman kamata, sai yau dubunta ya cika. Sai dai fa ni da ku dik munsan halin Leesharh da ɗan banzan taurin kai, yadda aka rinƙa fama da ita a court ta yi magana lokacin da ta kashe mamarta ta ki buɗe baki ta yi magana haka yanzu ma ta yi. Dik wani azabtarwa sun yi mata amma taki ta yi magana, har ya kai ya kawo bata iya takawa da kafafunta saboda azabtarwa Ramish, amma dik da haka taki basu haɗin kai, daga karshe ma da suka matsa mata sai ce masu ta yi dan Allah su kasheta kawai ta huta, dan ita dai bata ma san a kan me suke tukumarta ba. Wannan magana ya matuƙar konawa Ramish rai da har yasa bindiga zai harbeta ɗin da gaske, Bilal ya dakatar da shi ta hanyar kwace bindigar ya ce dan Allah Ramish ya barshi da case ɗin a hannunsa, zai sakata ta yi bayani cikin ruwan sanyi, Ramish zafin zuciyarsa ta yi yawa, abu kaɗan ya hasala, dan haka ya bar mashi case ɗin kawai. My people's kun yarda Ramish ya barwa Bilal wannan case ɗin? Kada ku manta Leesharh ta ce ta taɓa ganin Bilal a gidan masu nikaf, sannan kada ku manta Bilal shi ya fara nunawa Leesharh kauna da tausayawa a gidan, meyasa Bilal ya hana Ramish ya kasheta? Kai bari dai na barku haka kada masoya Bilal su yi mun zanga zanga, amma dai bani na faɗa ba, Leesharh ce ta ce ta taɓa ganinsa a gidan masu nikaf, dan haka dole mu zargesa!!. Tsabar rainin wayo irin na Leesharh ma, har da ce masu ita fa wannan ba wayarta bace, kuma bata san a kan me ma suke magana ba. Wato masu nijaf sai da suka yi binciken wacece Leesharh kafin su bata wannan aiki, irin wannan taurin kai haka? Dama irinta ƴan ta'addan suke so. Ramish bai so barinta a raye ba, amma Bilal ya ja shi suka bar ɗakin da ake horata a ciki ɗin, sai daɗin baki da kalamai masu daɗi Bilal yake yi mashi dan zuciyarsa ta huce ya mance da batun Leesharh. Yasan wanenen Ramish sarai, yasan idan ransa ya ɓaci ya ce zai yanke hukunci a kan abu to fa sai ya yi, shiyasa yake mashi daɗin baki dan ya mance da komai. (Ni kuwa nace da a yadda yake cikin ɓacin rai yanzun nan King ya yi mashi waya ya ce an sace Zunaira mana😂 me kuke tunanin zai faru?😂 Tab na yi nan babu ruwana😂 🥱) A can gefe kuwa, wuni kuka kwana kuka Sharifat take yi, ta gama shiga tashin hankali da damuwa, Allah sarki, tana kaunar Leesharh tamkar ranta, bata taɓa zaton cin amana daga gareta ba, yau tsawon kwana uku tana kuka a kan rashin Leesharh, har ƴar rama ta yi. Abu Abdussalam ya yi rarrashi har ya gaji, shi ma Leesharh ta kariyar mashi da zuciya, ya ji baya san sake jawo wani jikinsa kuma, hakika ya shiga tashin hankali. Ita kuwa Ummie, wlh ranta fes, sai addu'a ma take yi Allah yasa Ramish ya kashe Leesharh kowa ma ya huta. Ramish da kansa ya yi wa Leesharh azabar da sai da ta zaɓi mutuwa a kansa, irin azaban da yake ganawa manyan ƴan ta'adda da jami'ansa idan suka yi laifi ya rinƙa gana mata, amma Leesharh ta daure ta shanye wannan dukka. Ko sa yake ai ta saba da wahala tun da ta yi zaman gidan AAJ, yarinyar da ake tuhuma da kashe mahaifiyarta ai kunga dole ma zata yi fin hakan. Hmmmm wato fa Dubai ma ta kama da wuta, ta ko'ina dai ba sauki, to bari dai mu leƙa France muga ko da ɗan sauki sauki can. •••••••••••••••••FRANCE••••••••••••••••🔥 Sosai Smart ya sha barcin na good 4 hours, sannan ya farka. Misa call ɗin mom ya kai 10 a wayarsa, sai kiransa take yi yaki ɗagawa, da ƙoƙari irin nata wai so take yi ya zo su yi bankwana da iyayen Heleena zasu koma England, har suka tafi ba'a samu ya ɗaga call ba. Robbert kuma mamaki yake ta yi a kan ya aka yi wannan nuclear da aka gwada bata dawo ba, kada ku manta shi bako ne a wajen, yanzu yake koyan aiki. Batu na gaskiya makamin nuclear ba'a harba shi sama kuma ya dawo, idan aka saita shi in da ake sam ya je aka harna shi ya tafi shikenan, ba zai dawo ba, wannan shi ne nuclear na gaskiya. So already a cikin takekken teku Smart ya saita shi, dan haka yana tashi barci ya je ya duba computersa dan yaga yadda makamin ta tarwatse a cikin ruwa, dama so yake yaga karfin aikinta, idan ta yi yadda yake da buƙata sai su cigaba da haɗa irinta, wannan shi ne gaskiya. Robbert dai kasa hakura ya yi har sai da ya tambayi Smart ya aka yi makamin bata dawo ba. Iska Smart ya bawa ajiyarsa, dan bai amsa mashi ba, ya wuce ya yi wanka tare da sauya kayan jikinsa, ya fito ya umarci yaransa da su cigaba da haɗa irin wannan makami dan ya yi mashi yadda yake so hundred over hundred!. Daga haka ya nufi gidansa. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ •••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••••🔥 A hankali jiki dik a mace Ronnie ya hau saman escletor domin ya haura izuwa parlourn Black Tiger, jiya kwana suka yi suna cashewa, yanzu haka idanunsa dik barci, kuma yana da Exams a school da zai rubuta yau, kamar wanda aka hana shi yin barci jiya, wato shi dik in da sharholiya take yana nan wajen abinsa, bashi da wata damuwa. Allah sarki jiya Floris ta rufe mashi kofan ɗaki hakan yasa ya je ya yi rawa a tare da Angela, kun san jiya ta yi fushi ai, ta kwana kuka Ronnie ya kwana taka rawa abinsa, yo dama shi me ya damesa? Ai sai dai ta kashe kanta da bakinciki, shi bai taɓa cewa yana san ta ba, infact Ronnie bai san menene soyayya bama, kunga kuwa babu fushin wata mace da zai hana shi yin abin da yake da ra'ayi!!. Ko Sweetie tausayinta kawai yake ji, bai taɓa cewa yana santa ba, hasalima wlh a yanzu kam babu soyayyar kowace mace a ransa, Sweetie ma shakuwa da kauna ce irinta kanwa da ya ɗauketa, ita kuma Floris kyanta yake burgesa, that's all. Yanayinsa idan kuka ga yadda yake treating ƴan'mata sai ku yi zatan sansu yake yi ko wani abin makamancin haka, ainahi zuciyarsa tana da rauni a kan halittar macece sosai, amma kuma ai kunga jarumi ne a kan maza sosai, yana zubar da maza a wajen Wrestling, mata ke cin riba a kansa. Yana san zuwa room ɗinsa duba Sweetie, amma ya fi san ya fara zuwa wajen yayansa. Yana zuwa ya buɗe kofar ɗakin da password ya shiga ciki. Ɗan jujjuya koreans eyess ɗinsa ya yi yana neman ta ina yayansa yake? Dan ɗakin tana da girma sosai. Like wow he was so surprised na ganin alamar babu mutun a cikin ɗakin, shiru ya ɗan tsaya tamkar mai nazarin wani abin, yau kwata kwata baya san zuwa school, dik san shi da karatu yau dai baya jin zai je. Calmly ya fara takawa dan ya ƙarisa ciki ya tabbatarwa da kansa da gaske yayansa baya nan. A bakin bed ya zauna yana cigaba da bin ɗakin da kallo, shi ko tsoron ɗakin ma baya ji. Hamma ya fara dakawa alamar barcin tana san a biyata bashin da aka ci daren jiya da ba'ayita ba, ɗan yamutse fuska ya yi tamkar guyson a gabansu Yah Ramish. Shi da zai je ya yi shirin tafiya school sai ga shi ya gyara ya karkata ya kwanta a saman bed ɗin abinsa............ Kafin ƴan mintina barci ta yi awon gaba da shi. Ita kuwa Floris ta sha kuka har kamar ranta zai fita, daga karshe barci ya yi awon gaba da ita zaune a bakin gado, sai da ta kwala kanta da jikin headboard na bed ɗin ne, da ta ji zafi sai ta karkata ta kwanta haɗe da rungumo pillow tana jin kunan rai tana kuma sauke ajiyar zuciya har barci ya yi awon gaba da ita. After some hours. A hankali Sweetie dake kwance s saman bed ɗin Ronnie ta fara motsa idanunta da suka yi mata bala'in nauyi, zara zaran eyelashes ɗinta a jike suke da hawaye, alamar kafin ta yi barcin nan hawaye sun zuba daga idanunta sosai. Jikinta dik tamkar an girka dik wasu gaɓɓai ɗinta, tsokar namar jikinta dik sun yi mata tsami tamkar wadda aka yi wa luguden duka da sandina, harta tongue ɗinta ji ta yi tamkar an sanya igiya an ɗaure mata shi, taci bakar wahala daren jiya a hannunsa ne, yarinya ta ji kamshin mutuwa, Allah ma ya taimaketa yana san Spender a hannunta yasa ya yi ƙoƙari ya yi mata magani ta tashi bata mutu ba, da jefar da ita zai yi. Gashin kan nan nata tamkar wanda aka sanya kum aka baza mata shi, dik ya cukurkuɗe kamar kayan wankin da aka kwato daga bakin kura, idanunta har sun kumbura sun yi jajir da su, har ta kara hasken wahala yar ƙaniya. Ta sha madarar mamaki matuka a lokacin da ta waro idanunta ta ganta a cikin ɗakin Ronnie, bata yi tsammanin hakan ba, ta yi zaton ganin kanta a wata duniyar kamar yadda ya nuna mata tun farko zata yi, ya aka yi ta dawo nan? Ta jefawa kanta tambaya. Allah sarki, ta yi zaton ta yi bankwana da su Ronnie kenan, ashe ba haka abin yake ba, gata ta dawo garesu. "Good morning sarkin barci"............ Kamar daga sama ta jiyo sautin muryar Ronnie ta bayanta. Da sauri ta juyo da kallonta ta wajen. Yana tsaye gaban mirrorsa, sanye yake da wando three quter jeans sky blue, da round neck polo shirts black color, ya yi masifar kyau cikin bakin rigar, tamkar ka sace shi ka gudu. Yana tsaye yana ƙoƙarin sanya ɗan kunne a kunnuwansa, ta cikin mirror ya hango ta farka yasa ya yi mata magana. All his though since yesternight da suka rabu take barci up till now, shiyasa ya ce mata sarkin barci, bai san ita ɗin ma dik kanwar ja bace, ai kusan a tare suka yi barci wato da safe kenan, and ita daga suma ne ta farfaɗo ta zarce da barci. Ajiyar zuciya a bayyane ta sauke mai matuƙar sanyin gaske wanda yasa Ronnie juyowa gareta da kyau. A yau dai ƙaƙalo murmushin dole ta yi ta sakar mashi, dan bata taɓa tinanin zata rayu ba, ta sha bakar wahala, so babu walwala a tattare da ita, infact bata ma jin daɗin jikinta, dik wani sassa na jikinta kamar na nata ba. Bayansa ta kurawa kallo sosai kafin ya juyo, idan ka gansa a yanayin yadda yake tsaye ɗin nan sai ka ji gabanka ya faɗi, ko ta baya ka gansa kasan ya cika cikar halitta sosai, ga faɗin baya sosai saboda wrestling ɗin da yake yi, sexy body kamar na yayansa. Gashin dake kwance a bayan wuyarsa ta zubawa idanu tana kallo, sai a lokacin ta lura gashin kan Ronnie fa kamar combination ne na two colors ba zallar white bane, dan daga tushen gashin nasa zaku ga kamar ruwan toka toka mai haske haka. Ɗan runtse idanunta ta yi tana ƙoƙarin tunani ina ta taɓa ganin irin wannan gashin? Tabbas kafin idanuwanta su dai'na gani a lokacin da take forest wlh ta taɓa kallan mai irin wannan gashi. Wani irin juyawa da wani sadaukin warriors ya yi da karfi ne yasa gashin kansa ya pyaɗeta a wuyarta, da sauri mum ɗinsu ta ɗauketa daga wajen................... Da karfi ta sauke ajiyar zuciya, tabbas ta tuna in da ta taɓa ganin sak irin wannan gashi, tun mum ɗinsu tana a tare da su a forest, akwai wani lokaci da wasu warriors suka kai masu hari zasu ɗauki mum ɗinsu, tabbas a nan cikinsu ta taɓa ganin mai irin wannan gashi, to ko waye shi? Kuma a yanayin girman jiki da kira ba zai wuci kamar Ronnie ɗin ba!. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Ɗan ciza laɓɓanta ta ɗanyi kafin ta motsa jikinta zata miƙe zaune. Sai dai kash, ta ƙasa iya motsawa bare har ta miƙe zaune, gaɓɓanta tamkar an ɗaure mata su. Ronnie ya lura da ita kamar ba lafiya take ba, dan tin daga kan yanayin yadda ta sakar mashi murmushi ya fahimci lallai akwai matsala, dan wannan ba ƙayatattcen murmushin da ta saba sakar mashi bane. "Sweetie are you okey?"................. Da mamaki sosai a saman face ɗinsa ya yi maganar. Ita kuma kyan da ya yi mata a lokacin da ya juyo gareta kawai take kallah. Cikin kasala da nitsuwa ya tako zuwa in da take, jikinsa dik a mace. A gefen bed ɗin ya zauna yana kallon fuskarta, sai a yanzu ya lura da kumburin da idanunta suka yi, da kuma shi kansa face ɗinta. Da yake Dr ne shi ɗin sai ya yi tinanin barcin da ta yi ta zubawa ne yasa idanunta suka ɗan yi ja suka kumbura, bai dai yi tinani maras kyau ba. Ganin ta kafe shi da kallo ne yasa ya ɗaga mata gera guda irin ɗan duniyar nan. Bata san lokacin da ta ɗan wurga mashi hararar wasa ba sai ji ta yi ya ce. "Laifin me kuma na yi yau kike hararata?". Blinking eyes ɗinta ta ɗan yi tare da kawar da kallonta daga kansa, cike da takaicin abubuwan da yake yi wanda suka saɓawa Allah amma a wajen mutanen birnin Black world hakan normal ne, ranta yana ɓaci a dik time da taga Ronnie zai aikata saɓon Allah, saboda tana san shi da rahama tana san ya tsira daga azabar lahira. Ranta ya sosu sosai na ganin ya kara zana zanen tattoo a gefen wuyansa na dama, sannan wannan uban ɗankunnaye da yake sakawa sam bata san ganinsu. Cikin takaicin hakan ta ce. "Ronnie meyasa kake san aikata ba dai'dai bane?". Idanunsa a kanta ya amsa da. "Menene kuma ba dai'dai ɗin da na aikata ba?". Dawo da kallonta kansa ta yi, kamar ta kama kunnen nan nasa ta ja da karfi take ji, bashi da aiki sai zane jiki ya kuma bi fuska da karafuna kaman wanda bashi da mafaɗi, ko da yake kusan bashi da mafaɗin ne ai, tin da dik abin da yake so shi yayansa yake yi mashi, kunga kuwa ai babu mafaɗi. "Meyasa kake zane a jikinka kuma kake san saka waɗan nan karafuna a face ɗinka?". Fuskarsa ce ta sauya izuwa na mamaki, shi bai taɓa sanin hakan wani abin azo a gani bane, ya ɗauki hakan a matsayin kwalliya ne kawai, bai ɗauki hakan wata tsiya ba, dan haka with full of surprise ya ce. "Hakan yana da aibi ne?".............. Jinjina mashi kai sosai ta yi, kafin ta amsa da. "Babban aibi ma kuwa, kuma yana ɗaya daga cikin kananun alamomi na tashi alkiyama!". Ɗan jinjina kai ya yi tare da maimaita kalmar tashin alkiyama, kara rikiɗa face ɗinsa ta yi izuwa na mamaki sosai, shi dai bai san wani tashin alkiyama ba. "Menene kuma tashin alkiyama?". Ya yi tambayar kamar ba shi ya yi ta ba, irin mutum ya yi magana unexpext haka. "Ranar girban abin da ka shuka, ranar da kowa zai karɓi sakamakonsa..........". "Dama akwai ranar da kowa zai karɓi sakamakonsa ne?"................... Kai ta jinjina mashi alamar tabbatarwa, tabbas akwai ranar da kowa zai karɓi sakamakon aikinsa da ya aikata a duniya. Girgiza kai ya yi............... "Impossible, gaskiya ban yarda ba, ta ya za'ayi ki ce mun dikka mutanen dake duniyar nan kowa zai karɓi sakamakonsa? Waye zai basu sakamakon kuma a ina zai gansu har ya basu? Ke kin san adadin mutanen dake duniya kuwa?!".................. Da ɗan kaifi a voice ɗinsa yayin da ya kai karshen maganar. Dama tasan da wuya ya yarda da hakan, amma da yake tana da kaifin ƙwaƙwalwa sosai, ta iya bin mutun dik ta yadda ya zo mata, tasan irin kalamai da hujojin da zata yi amfani da su wajen sanya mutum ya yarda da ita ko yaki ko ya so, sai bata ji komai da jin kalamansa ba, bata wani damu ba, cikin sanyin murya ta ce. "Ronnie ku nawa ne a school ɗinku?". Kai tsaye ya amsa mata da. "Muna da yawa ba zan iya kirgawa ba!". "Good......... Amma kuma dik yawankun nan ya aka yi mai school ɗin naku yasan adadinku da har yake iya shirya maku jarabawa, idan kunci ya bawa kowa marking na adadin amsar da ya bada, sannan waɗan da suka faɗi a sanya masu sun faɗi, har ya rubutawa kowa result ɗinsa ya bashi da sakamakon abin da ya ci dai'dai wa dai'dai babu zalunci?". Shiru Ronnie ya yi dan ta buga mashi misali da hujja mai karfi, shi kansa ya fahimci maganganunta abin dubawa ne, amma da yake shaiɗan la'anannen Allah ne sai ya zuga shi a in da ya ce mata. "To ai mai makarantar makarantarsa ne, dik wanda zai shiga school ɗin dole yasan shi, kuma dole sai ya bada sunansa an rubuta, wannan dalilin yasa ya san sunan kowa". Wani irin daɗi ta ji ya ratsa zuciyarta, haƙiƙa ta ji daɗin wannan amsa nasa, Ronnie ya ɗaure kansa da kansa, ai ko ta ina aka bi da mumini bayyana Allah a wajensa ba abu bane mai wahala, har ta ji ta samu confidence a tattare da ita, dik wani ciwo da take ji gaɓoɓɓinta suna yi mata sai ta ji dik sun ware, cike da murna ta ce. "Mai makaranta sai ya san sunan kowa idan za'a shigar da shi makaranta ko?". Kai ya gyaɗa mata alamar e haka ya ce, yana nan with his full confidence, shi yana jin ya kureta ai. "And dik wanda zai shiga makaranta dole mai makaranta yasan da zamansa ko?". Nan ma jinjina mata kai ya yi idanunsa a kan face ɗinta. "Good.......... Na ji daɗin wannan bayanai ɗin naka, a nan duniya ma mutun ɗan adam ma dan ya gina makaranta sai ya san da zaman kowa wanda yake cikin makarantar, sannan sai ya san sunan kowa kafin ya shiga makarantar bare kuma Allah da ya halicci dikkan duniya da abin da yake cikinta?". Da ɗan mamaki ya ce. "Me kike nufi kenan, ban gane ba". "Girma na Ubangiji ya wuci tinaninka Ronnie, ina san ka sani cewa dai'dai da kwayar zarra a duniyar nan Allah ya san da zamansa, malaman makaranta sai an kawo masu yara ake faɗa masu sunansu har su rike sunan su san da yaran ko?". Jinjina mata kai ya yi alamar e. "To shi Ubangiji shi ne da kansa yake sanyawa bawa suna! Kowani yaro da kake gani da sunansa yake zuwa duniya, iyaye kawai suna isar da sakon sunan ne ga al'umma cewa ga sunan ɗansu". "Ban gane ba, ki mun bayani yadda zan gane"......... Yadda ya yi maganar da alama ransa ya ɗan sosu kaɗan. Tuni ta ji karfi ya zo mata, an taɓo addininta ana bukatar hujoji, ita ai dama abin da take so kenan, su taɓota su ce ta kawo hujoji, dan dole kuma su gamsu, dan kafa hujoji take yi da malamullah wato Alqur'ani mai girma, maganar Allah wasa ce? Idan ka samu mutum mai daɗin baki ya yi maka magana ma ji zaka yi tamkar baka duniya bare kuma ace maganar Allah? Ai ta wuci tinanin mutum. Jingina bayanta da jikin headboard na gadon ta yi, cike da kwarin gwiwa ta fara magana kamar haka. "A cikin Alƙur'ani da hadisi. Allah ya bayyana cewa yana sane da dukkan halittunsa tun kafin su zo duniya. Wannan ya fito fili a cikin Suratul Maryam, Sura ta 19 a cikin Alqur'ani, Aya ta 7, lokacin da Allah ya yi magana game da annabcin da haihuwar Annabi Yahaya A.S". "Yaa Zakariyyaa innaa nubashshiruka bighulaaminismuhuu Yahyaa lam naj'al lahoo min qablu samiyyaa."................ "Ya Zakariyya! Lalle ne, ina yi maka bushara da wani yaro, sunansa Yahaya, ban taɓa sanya wa wani suna kamar shi ba a gabani wato kafin zuwan Annabi yahaya kenan, ba'a taɓa samun mai suna irin nasa ba, shi ne farkon sunan yaya a duniya, zaka iya duba wannan sura da wannan aya dan ka gani" "A wannan aya, Allah ya bayyana cewa ya ba wa Annabi Yahaya suna tun kafin a haife shi. Wannan yana nuna cewa Allah yana sane da mutum, ya kuma ƙaddara duk abin da zai faru da shi, har da sunansa". "Haka kuma, a cikin Suratul A’araf Sura ta 7 a cikin Alqur'ani mai girma, Aya ta 172 da 173, Allah ya ambaci cewa ya ɗauki alkawari da ƴaƴan Adam tun lokacin da suke cikin tsatson iyayensu, yana tabbatar da cewa ya san dukkan halittunsa tun farkon wanzuwarsu. Duk wannan na nuni cewa sunan mutum, tare da ƙaddararsa, yana cikin ilimin Allah tun kafin haihuwarsa". Tsit Ronnie ya nitsu yana sauraronta, shi ma fa yanzu yana san ya ji tana gaya mashi girma da niimomi haɗe da isar Ubangiji, hakan na sanyaya mashi rai. Cigaba ta yi da bashi hujoji, dan tana ganin kamar iya haka basu wadace shi ba, bari ta kara mashi ko kaɗan ne dan narkar mashi da zuciya sosai!. "Cikin hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama wanda Abdullah ibn Mas'ud R.A ya ruwaito shi, Manzon Allah (SAW) ya ce. Lallai hakika kowane ɗayanku ana haɗa halittarsa cikin mahaifar mahaifiyarsa tsawon kwanaki arba'in (a matsayin maniyyi kenan) sannan ya zama ɗigon jini har tsawon kwanaki arba'in, sannan ya zama tsoka tsawon kwanaki arba'in, sai mala'ika ya zo ya hura masa rai, to a wannan gaɓar ne ake rubuta masa abubuwa guda huɗu. Na farko arzikinsa, ajalinsa, aikinsa, da kuma ko zai kasance mai farinciki ko mai baƙinciki, dan haka kada wani bawa ya takura kansa a kan abin duniya, already Ubangiji ya rubuta arzikinsa tin kafin zuwansa duniya" "Ingantaccen hadisi ne cikin Sahihul al-Bukhari, Hadisi mai lamba 3208. Sai Sahihul Muslim, Hadisi mai lamba 2643 dik zaka iya nemo littafan ka duba lambobin dan ka tabbatar!!". "Wannan hadisi ya nuna cewa Allah yana sane da mutum da duk abin da zai kasance tun kafin a haife shi, ciki har da ƙaddararsa da sunansa. Wannan shi ne alamar cewa Allah mai ilimi ne da kuma iko akan dukkan halitta, dan haka Allah yasan komai dake duniya, in takaice maka ma babu wani abin da ya isa ya motsa ba tare da izinin Allah ba, dan haka dik abin da kake yi a duniya Mala'iku suna nan suna rubuta maka, so akwai ranar da zaka girbi sakamako kamar yadda ka aikata ko in ce ka shuka".. (Kai my people's ku tafawa Sweetie!! wani irin fata zaku yi wa Sweetie tamu ta amana? Kun ji wata iriyar basira na misali da ta yi wa Ronnie da makarantarsu kuwa?. To dik wanda ya karanta littafina ya samu karin ilimi da darusa ina rokon da ya ɗaga hannu ya mun addu'a ni da iyayena da ƴan uwana, addu'a kowacce iriyace in dai ta alkhairi ce a gareni wlh ina so, ba abin da zaku biyani da shi face wannan addu'ar, ku mun ita ni da iyayena da ƴan uwana, Allah ya bar kauna 💘) Dik jikin Ronnie ta yi la'asar kai har ma da mangariba, kamar ba shi ba, tabbas ya yarda da maganganunta, musamman ma yadda ta kafa mashi hujoji da malaman makaranta ma, tabbas su da suke mutane kamar kowa ma har suna iya sanin wanda ya shiga makarantarsu da sunansa, su rubuta mashi jarabawa su kuma bashi sakamako bare wanda ya halicci dikkan duniya?! Tabbas babban kuskure ne ma bawa ya yi tinanin Ubangiji baya ganinsa a kan dik abin da yake yi, kuskure ne bawa ya yi tinanin ba za'a je lahira ayi hisabi ba!!. Sau uku Sweetie tana ambatar sunan Ronnie, amma ina bai jita ba, ya afka duniyar tinanin maganganunta. Har sai da ta kai hannu ta ɗan taɓa shi, a ɗan zabure ya sauke ajiyar zuciya. Lafiya Ronnie?"........... Ta faɗa kamar bata san tinanin me yake yi ba. "Sweetie gaskiya na ji kamar na yarda da addininki........." ......... To fah, babbar magana. Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Na tabbata da zaka ji ko ka daure ka koya daga addinina, to da hakika zaka gasgata cewa babu wani addini da ya kaishi, ka daure ka ji kuma ka koya ka ji?". Yau Black Tiger ya shiga fada, ana can anata hidimar shigarsa fada su kuma suna nan, mutane sai shiɗewa suke yi na ganin bayyanarsa, shi kam Ronnie bashi da labari. Kuma hakan ba karamar nasara bace a garesu, dan kuwa wlh da Black Tiger yana nan yana jinsu ba zai taɓa bari Sweetie ta yi waɗan nan jawabin dangane da Addinin Musulunci har ta kawowa Ronnie hujoji cikin hikima wanda zasu ratsa shi har ya ce ya fara yarda da addininta ba, da tuni zai katse masu hiran koma ya rabasu na har abada, kunga kuwa shigarsa fada mu gaba ta kaimu, ko ba komai al'umma dayawa sun samu karin ilimi a kan addininmu. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 "Sweetie na ji kuma na yarda da tashin alkiyama, amma ki faɗa mun menene alamominta?".................. Cewar Ronnie. Haba wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, hamdala ta yi wa Allah da Ronnie ya fara yi mata irin waɗan nan tambayoyi, Allah abin godiya, da ta samu nasara Ronnie ya musulunta tana da tabbacin dayawa zasu musulunta ta dalilinsa, sai dai suna da babban kalubale da barazana a gabansu wanda sai ta tsaya da addu'a matuƙa. "Ronnie alamomin tashin alkiyama suna da yawa, akwai ƙananan alamomi akwai kuma manya manya wanne kake san in fara faɗa maka?". Kai tsaye ya amsa da. "Dikka nike so"........... Ya yi maganar cike da matsuwar san jin wannan bayani, yana san bayananta, saboda komai dallah dallah take yi kuma a nitse yadda komai jahilci da toshewar ƙwaƙwalwar mutun zai fahimceta. Gyaran murya ta yi haɗe da kara gyara zamanta kafin ta fara bayanai kamar haka. "Alamomin tashin alkiyama sun kasu kashi biyu. Alamomin kanana wato al-alamat al-sughra kenan, sai kuma alamomin manya wato al-alamat al-kubra, gasu kamar haka". "Alamomin Kanana sun haɗa da. Mutane za su ga lokaci yana tafiya da sauri, da rana ya yi dare zata yi, kamar kyaftawa da Bismillah, alama ta farko kenan. Ta biyu. Rashin sanin addini. Mutane za su bar koyon addini, ilimin shari’a zai ragu, zasu koma san jin gulmace gulmace da karairayi haɗe da abin da bai shafi addini ba. Na uku. Yawaitar zunubi. Zina, shaye-shaye, da rashin kunya, rashin kamun kai, rashin darana iyaye da magabata, a ci mutuncin malamai da masu faɗar Allah, dik wannan za su yawaita a doron ƙasa. Na huɗu Yawaitar yaƙe-yaƙe, jama'a zasu yi ta yakar junansu, su yi ta kashe kawunansu ba tare da wata dalili ba, su kansu idan ka tambayi meyasa suke kashe juna ba zasu faɗe shi ba!. Na biyan. Matsalolin shugabanci. Shugabannin azzalumai zasu yawaita, zai zamana shuwagabannin basa tsoron Allah, basu da tausayi, suna aikata ɓarna, suna zaluntar waɗan da suke mulka, suna take hakkokin bayin Allah da shi kansa Allahn ba tare da suna nadama ko kwayar zarra ba. Na shida. Kuma na karshe a ƙananan alamumi shi ne. Zama ababen al’ajabi. Mutane za su gina manyan gine-gine suna takama da shi, su rinƙa gasa a gine gine masu girma da tsawo". My people's a nan zan ɗan yi tsokaci, a cikin waɗan nan alamomi na tashin alkiyama ku faɗa mun wanenen bai bayyana ba?!! Dik wanda ya yi imani da Allah da Manzonsa yakamata yasan da cewa duniya ta zo karshe, jama'a har yanzu muna da sauran dama ta tuba, mu tuba mu koma ga Allah dan mu rabauta, wlh babu in da duniya zata kai mutum face halaka, mu yawaita sadaka da istigifari, mu yawaita jin kan na kasa da mu, kada mu rinƙa duba na sama da mu, mu rinƙa duba na ƙasa ne hakan zai sa mu kyautata lahiranmu, mu guji cin amana juna da zalintar mutane!. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 A dai'dai wannan gaɓa Ronnie jikinsa ta sanyaya, saboda yadda Sweetie ta ce jama'a zasu rinƙa kashe junansu babu gaira babu dalili sai ya ji tamkar da mulkinsu take yi, tabbas Black Tiger yana kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba, kuma yasan da hakan yake kara goyawa yayan nasa baya, gaskiya wannan abin ya yi matuƙar taɓa mashi zuciya, yasan dai ita Sweetie bata san ya suke gudanar da mulkinsu ba, dan haka ba dan zalincinsu ta yi maganar shuwagabannin marasa adalci ba, gaskiya ne kawai zallarta. Ganin alamar nadama da tashin hankali a saman face ɗinsa ne yasa Sweetie ta kara samun kwarin gwiwa, ta cigaba da cewa. "Alamomin Manya na tashin alkiyama sun haɗa da Bayyanar Imam Mahdi. Bayyanar Dajjal. Saukar Annabi Isa (A.S). Bayyanar dabba mai magana da mutane wato Dabbat al-Ardh. Fitowar Yajuj wa Majuj. Fitowar rana daga yamma. Babban girgizar ƙasa. A cikin Al-Qur'ani mai girma Allah ya yi Magana Kan tashin Alkyiyama da alamominta a wurare daban-daban, amma ga wasu daga ciki. "A cikin Suratul Zalzalah surata 99 a cikin Alqur'ani kenan, aya ta 1 zuwa ta 8. Allah ya bayyana girgizar ƙasa ta tashin alkiyama. Iza zulzulatil ardu zilzalaha, wato Idan ƙasa ta yi girgiza girgizawarta mai tsanani". Izazullilatil ardu zilzalaha, wato Idan ƙasa ta yi girgiza girgizawarta mai tsanani. Sai kuma cikin Suratul Qiyamah, surata 75, aya ta 1 zuwa 40. Wannan sura tana magana game da tsanani da al’amuran tashin alkiyama. Sai Suratul Takwir sura ta 81 aya ta 1 zuwa ta 14, An bayyana canje-canjen duniya yayin tashin alkiyama, Idan rana ta birkice, kuma taurari suka fadi"................ WAYYO ALLAH KA HANAMU GANIN WANNAN TASHIN HANKALI, MY PEOPLE'S KU CE AMIN, KU KANKU BAKU JI FAƊUWAR GABA DA AKA CE IDAN RANA TA BIRKICE TAURARI SUKA FAƊI BA?..😥 "Sai cikin Suratul Inshiqaq surata 84 aya ta 1 zuwa ta 6. Allah ya bayyana yadda duniya za ta karye"........... Ya Allah kasa mu cika da imani. Ronnie sai da ya ji gabansa ta yi wani irin faɗuwa, kirjinsa ne ta bada dukan uku uku, ya ji maganganu masu girman gaske daga bakin yarinya ƙanƙanuwa mai ƙananun shekaru. Shiru ya yi ya kasa magana tamkar wanda ruwa ya cinye shi, har sai da Sweetie ta kai hannunta ta taɓa shi. Firgita ya yi tare da miƙewa tsaye. "Ronnie lafiya kuwa?". Girgiza mata kai ya yi ba tare da iya furta word ba, Allah sarki nan take zuciyarsa ta karaya, ta yi matukar laushi, ya ji girman Allah bawan Allah, a take ya ji ya aminta da ita ɗari bisa ɗari, ya kuma yarda da addininta, tabbas adininta shi ne gaskiya, tabbas Ubangijin da take ambata shi ne na gaskiya. A cikin wannan hali da suke master Devil ya yi knocking na kofar. Kallonta a kan kofa Sweetie ta kai shi kuma Ronnie ya kai kallonsa saman tv dake kunne. Ganin master ne a bakin kofar yasa ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya matso dab da Sweetie, jikinsa dik ya mutu, kamar zai rungumeta, ya fita tsawo nesa ba kusa ba. Dan haka sai ya rankwafo kanta, kamar zai sumbaci kumatunta, sai kuma ya mayar da bakinsa saitin kunnenta. Har ta zaro idanu tana jiran jin saukar kyawawan lips ɗinsa a saman bakinta, sai kuma ta ji yana yi mata raɗa a kunne. Wani irin ƙayatatcen murmushi ta saki, da alama ta ji daɗin abin da yake faɗa mata, cikin sanyin murya ta ce. "Amma dai sai............" Katseta ya yi ta hanyar zuro hannunsa ta saman shoulder ɗinta ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru. Ba musu ta haɗiye maganar ta cigaba da sauraron abin da yake faɗa mata. Ya ɗauki a kallah 2 mins yana yi mata raɗa kafin daga bisa ya furta. "Anjuma da daddare zaki kara mun bayani a kan Annbi Isa da kuma Imam Madih? Ina san jin tarihinsu sosai, ina tsananin san Annabi Isa sosai". Jinjina mashi kai ta yi alamar to ba tare da ta yi magana ba. Shiru ya yi yana kallan gurun wuyarta, ya dakata da yin dik wata magana ya mace da kallanta. Jin ya yi shiru baya magana, kuma bai ɗago kansa daga gareta ba, sai ta ɗan juyo domin ta kalli me yake yi. Tana juyowa fuskokinsu ya haɗe waje guda, bai ɓata lokaci wajen manna mata sumbata a ɗan bakinta yana sakar mata cool murmushi ba. Gabanta ne ya faɗi sosai lokacin da ta ji saukar lips ɗinsa a saman tata, lokaci guda ta ji wani abu ya tsoki zuciyarta, bata san time da ta sakar mashi murmushi ba, kun san fa murmushin Ronnie idan ya yi wa mutun ko baka so sai ka mayar mashi da martani, sai ka murmusa kai ma. Ƙasa ƙasa cikin salo mai jan hankali kamar mai raɗa ya ce. "Meyasa kike murmushi? Sumbatar ta yi maki daɗi ne?". Bata san time ɗin da ta gyaɗa mashi kai alamar e ba. Sai ji ta yi ya ce. "In kara ɗaya?". Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a. Yadda ta yi saurin dojewa yasa shi kara faɗaɗa murmushinsa. "Gaskiya kyakkyawa ce ke Sweetie". A kunne ya yi mata wannan raɗan. "Kafini kyau ai........." Bata ƙarisa maganar ba ya yi sauri ɗaura babban yatsarsa a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru. "Your lips is so very very soft and sweet like your name Sweetie". Da muryarsa kaman na ƴan maye ya yi maganar. Master Devil ne ya sake yi masu knocking a karo na uku. Ƙoƙarin zullewa ta yi daga kusa da shi dan tana tsoron master ya shigo ya gansu a haka. Ina cikin sauri ya capko waist ɗinta tare da kara matso da ita kusa da shi. "Meyasa kika ce kada na kara sumbatarki?". Ƙasa sosai ta yi da murya wai dan kada master Devil ya jiyota......... "Saboda a addinina hakan bai dace ba, sai idan matarka ce zaka yi mata hakan". "To meyasa?". Ya jefa mata tambaya yana ɗan shafa lips ɗinta da yatsarsa, hannunsa ɗaya yana saman waist ɗinta. "Addinina yana da tsabta sosai, kai kanka ba zaka so ace kowani namiji zai iya taɓa kowace macen da kuke tare wadda ba mallakinsa ba, misali yanzu kaddara ni matarka ce, kenan kowani namiji zai yi mun kiss kamar yadda zaka yi mun, zaka yarda da hakan?". Ai a miliyan ya girgiza kai haɗe da cewa. "A'a ba zan yarda ba, sai dai ni kaɗai zan taɓa matata". "Good...... To kaga addinina akwai hikima da tsabta a cikinsa, shiyasa ya saka dokar matan mutun shi kaɗai zai iya amfani da ita, addinina bai yarda kowa ya taɓa matar wani ba". Sosai ya kara samun kwanciyar hankali da addinin nan nata, saboda kyawawan ayyuka, ga tsabta da cikar dik wani abin da ake so. Master da gajen hakuri sake yi masu knocking ya yi. Ronnie tamkar bai ji shi ba, ya bawa banza ajiyarsa. A hankali yasa hannu ya janye mata dogon gashinta da ya zubo wajen wuyarta, slowly ya kai ɗan bakinsa saman wuyarta, sumbata ya manna mata kafin ya saketa yana lumshe idanu kamar wanda yake duniyar sama jannati, ita kuma murmushi ta ɗan saki kafin ta juya da sauri ta nufi toilet. Shi kuma ya bita da kallo yana ganin yadda round butt ɗinta suke motsawa cikin kayan barcin Floris, gabaɗaya sai ya ji kasalarsa ta kara karuwa mashi, ya ji kamar ya sake janyota jikinsa. Har ta kai bakin toilet zata shiga sai ta juyo, a take idanunsu suka sarkafe cikin na juna. Wani irin abu ya ji yana taso mashi a cikin zuciyarsa, ga wani abu dake tsikararsa a tsakiyar kansa kamar wanda ake tsirawa allura. "Ronnie bari in yi wanka, kuma ina jin yunwa sosai, ko sallan ban yi ba". A ɗan shagwaɓe ta yi maganar. Banda kallo babu abin da yake binta da shi, tamkar wanda ya ga bakon halitta daga wata duniyar. "Ronnie lafiya?". Cike da mamaki ta yi tambayar, tana magana tana ɗan tsuke fuska tana ɗan ɗaure fuska. In a low voice sosai, a kasale kamar wanda yake cikin maye ya ce. "Zallar madarar kyau ne ya hanani yin magana"........... Har cikin ranta ta ji wannan magana, tana matuƙar jin daɗi idan ya yabeta. Ɗan juya idanunta sama kaɗan ta yi, kafin ta ce. "To ni dai kam yunwa nike ji". A hankali ya motsa lips ɗinsa, voice ɗinsa bai fita ba irin magana mai alama da bakin nan ya yi mata wajen furta. "Jeki kiyi wanka ina kawo maki abinci". Jinjina mashi kai ta yi, har zata juya sai ta tuna wani love story da ta fara karantawa a cikin littafinsa da ta gani a ɗakin nasa, dan haka sai ta tsaya ta mannawa tafin hannunta sumbata, sannan ta huro mashi. Wani irin lumshe idanu ya yi dai'dai lokacin master ya sake yi mashi knocking. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya motsa lips ɗinsa ya yi mata raɗa da. "Shige ciki". Juyawa ta yi da sauri ta shige, shi kuma ya nufi kofar. Yana buɗewa master ya tsaresa da kallo yana mamakin meyasa idanunsa ta rikiɗe haka? Anya yana da gaskiya kuwa?. Ya jefawa kansa tambaya. Shi kuwa ɗaure fuska ya yi tamkar bai taɓa yin dariya ba, a ɗan takaice ya tambayi master da lafiya kuwa?. "Babban yaya yana fada yana jiranka". Cewar master. Sosai Ronnie ya yi mamakin jin furucin master, amma sai ya danne mamakin nasa ya nuna kamar yasan da yayan nasa ya shiga fada. Rufu kofar ɗakin nasa ya yi sannan ya wuce ya nufi escalator ba tare da ya sake bi ta kan master ba. A hanzarce master ya rufa mashi baya, yana tafiya yana waiwayi ɗakin Ronnien, hankalinsa bai kwanta da ɗakin ba, bai yarda da shi ba, yana ganin kamar akwai abin da Ronnie ya ɓoye a ciki, kunsan master da shegen gulma. =============================🔥 ••••••••••••••••••JIMETA•••••••••••••••••🔥 Dirama iya dirama ake bugawa a wannan gida, Nenne dai tin da ta gudu gidan Arɗo a ranar bata dawo ba, dan haka amarya Mairo dai ƴan uwanta suka sake hakura suka rakota gidan bappa. Da daddare bappa ya kwana da amaryarsa ita kuma Nenne tana gidan Arɗo ta yi kwanan bakinciki, tana tsoron dawowa kuma saboda tasan aika aikan da ta yi, tana san dawowa kuma saboda ta hana su bappa kwanan farinciki shi da Mairo. Haka dai ta daure ta kwana a gidan Arɗo, da asuban fari sai da ta daidai ci lokacin da maza gabaɗaya suka tafi masallaci, sai ta sato hanya ta dawo gida. Nan ta isko Mairo saman dadduma tana addu'a, bata ce mata ko uppan ba ta wuce izuwa ɗakinsu Mahnoor. Tabbas Mahnoor ta ji shigowarta, amma da yake barci ya ci karfinta sai ta kasa motsawa, daren jiya bata yi barci ba, ta kwana kukan rashin mijinta, barci ya kauracewa idanunta, sai yanzu gabanin asuba ɗin nan ne barci ya ɗauketa, da kyar ta iya gabatar da sallah. Ganin Mahnoor tana barci Mahreen kuma tana cikin ɗakinta ne yasa Nenne ta fito ta shiga kitchen, a dai'dai lokacin ita ma Mairo ta fito domin ta hura wuta, karo suka yi a cikin kitchen Mairo ta ɗaga mata gaisuwa. Ai yadda kuka san bango Mairo ta yi wa magana ba ita ba, ta yi banza da ita. Ita ma Mairo sai ta wuce ta ɗauki bokiti zata ɗebo ruwa. Kwace bokitin Nenne ta yi ta ɗebi ruwa a ciki ta wuce fuuuu sai ɗakin Mahnoor. Ita kuwa Mairo baiwar Allah sai ta koma cikin ɗakinta ta ɗauko wani bokitin mai ragowar ruwan da ta shiga da shi daren jiya dan kada ya yi sanyi sosai idan zasu yi alwala, dama suna shiga da ruwa a bikiti su ajiye a cikin ɗakinsu, da asuba da shi suke yin alwala, ruwan cikin kitchen iska na bugasa ya yi sanyin da in suka zo yin alwala zasu wahala, so yanzu da asuba ita da bappa sun yi alwala sun bar ragowar, sai ya ɗaukosa ta nufo waje. Tana sako kai zata fito waje ta ji ihun Mahnoor. Da gudu ta karisa fitowa, ita ma Mahnoor da gudu ta fito daga cikin ɗakin nata jikinta sharkaf da ruwa. Bayanta Nenne ta biyo da sauri, sai huci take yi Kamar aljanna haka Mahreen ta fito da gudu daga ɗakinta ita ma. Tana ɗaura idanunta da suke gani dishi dishi a kan Nemne ta san cewa ita ce nan ta jiƙa mata ƴar uwa. Nenne zata fara surfa bala'i kenan bappa ya yi sallama, hakan yasa ta haɗiye maganar da take san yi. Da mamaki bappa ya fara binsu da kallo. Tin bai yi magana ba Nenne ta yi saurin cewa. "Wlh Mairo kin ji kunya, yanzu fisabilillah me Mahnoor ta yi maki a cikin sanyin nan zaki jikata da ruwa fisabilillahi?". A hanzarce bappa ya dawo da kallonsa a kan Mairo wadda ta zaro idanu tana al'ajabin maganar Nenne. "Nenne ki ji tsoron Allah, ni yaushe na jiƙa Mahnoor?". Baiwar Allah maganata sanyi sanyi kamar na Mahnoor ɗin. "Oh karya kenan zan yi maki? Wlh idan kika sake ina magana kina magana sai na dirje maki baki". Shiru babba ya yi yana binsu da kallo. Mairo ta buɗe baki zata yi magana kenan Nenne ta sake cewa. "Idan har mace ta kai mace to wlh ta furta uppan taga idan ban dirje bakin hegiya ba! Ni saarki ce?". Tana magana tana girgiza sak dai yadda Mahreen take yi idan tana masifa, ashe gado ta yi. Ita dai Mahnoor baiwar Allah da sai rawan sanyi take yi ta takure waje guda ko ɗaga idanu ta kasa yi bare ma har ta kallesu, sai kerma jikinta yake yi saboda iskar dake kaɗata, ga jikinta sai ɗigar ruwa yake yi. Bappa dai ya rasa wanene mai gaskiya a cikinsu, domin kuwa dikkansu ga bokiti a hannunsu, kuma dik bokitin da ragowar ruwa a ciki, to wacece ta watsa Mahnoor ruwa kenan? Ya kasa gane gaskiya, ga shi Nenne ta fi uban kowa baki a wajen, dole ka yarda da ita ce mai gaskiya. Mahreen da idanunta ke ganin mata dishi dishi saboda barci ne ta fara magana kamar wata ƴar maye. "Bappa wlh dik in da za'a je a dawo ni nasan Nenne ce ta daki Adda Mahnoor kuma ta zuba mata ruwa, dan ita ce bata sonta, Diddi Mairo kam nasan tana sonmu wlh". Mairo da tin da Nenne ta buga mata warning bakinta ya mutu ne ta sauke nannauyar ajiyar zuciya jin cewa Mahreen ƴar cikin Nenne ta yarda da ita, sai dai ita yanzu ta zama ƴar kallo, saboda wlh munafurcin Nenne da iya lauye zancenta ya sha tunanin Mairo. Balai'n Nenne ya wuci yadda ake tunani, zata aikata abu amma cikin second zata mayar da laifin kan Mairo tare da hujojin da dole ka yarda Mairo ta aikata, baiwar Allah Mairo bata da hanyar wanke kanta sai dai Mahreeh ta shigar mata ta faɗi gaskiya, ita yanzu Nenne ta dai'na bata mamaki. Kuma a al'adarsu idan babba yana magana yaro baya saka baki kome zai faru, shiyasa kuma ji Nenne ta dakawa Mairo warning a kan kada ta sake saka mata baki a magana. "Kai makahone baka ganin bokiti da ruwa a hannunta? Ai ruwan dake ciki ne ta jiƙa Mahnoor da ita, tsawon shekara nawa muke tare da kai? Tin Mahnoor tana jaririya na riketa, ban taɓa zuba mata ruwa na sai yau? Meyasa zan yi mata hakan? Meyasa ban yi mata a baya ba sai yanzu?". Cewar Nenne kenan. Kunsan dik abin da take yi wa Mahnoor bappa bai sani ba, bai taɓa sanin tana azabtar mashi da ƴar marainiyarsa ba, so ya ɗauka tsakani da Allah take rike da ita, wannan dalilin yasa ya fara zargin da gaske Mairo ce ta zuba mata ruwa, saboda tsawon shekaru bai taɓa ganin Nenne ta musguna mata ba!. E kam akwai cakwakiya Mairo ta faɗa kaidin Nemne, to ni dai ina bayan fage. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 12 "Allah bappa ba Daddi Mairo bace, ni nasan Nenne ce". Cewar Mahreen. Bappa da ya gama sanin Mahreen bata karya ne ya jinjina kai, ya ji kuma zuciyarsa ta yarda da Mahreen ɗin, dan balai'n Nenne sai ita, Allah mai sakayya a lokacin da bawa bai zata ba, shi ya kasance masifaffe kuma bala'i ga mahaifiyar Mahnoor, shi kuma Nenne ta kasance kwatankwacin hakan a garesa, shiyasa dayawan lokuta baya kula Nenne idan tana yin wannan abin nata, yana kallan hakan a matsayin shi da maman Mahnoor. A kan Mairo ya tsayar da kallonsa, cikin nitsuwa ya ce. "Taimaka mata ta canza kaya". Yana gama faɗar hakan ya wuce ɗaki ba tare da ya sake bi ta kan Nenne ba, ba komai ya sa bai kulata a yanzu fa face dan su Mahreen suna wajen, baya san su rinƙa samun saɓani har suna sa in sa a idanun su Mahreen, hakan zai gurɓata tarbiyar da suke da shi sosai, kuma hakan yanasakawa yara su rage ganin girman iyayen nasu, idan baku dai'na ba a hankali hankali dik wani mutunci da girma ƴaƴan zasu dai'na ganinku da shi. Daga nan sai raini ya shigo tsakani, kana yi wa yaro magana yana kallanka yana cigaba da abin da yake yi, kunga ai hakan ba daɗi, to sai ku kiyaye, faɗar iyaye a gaban yara bama iya rai'nin kawai yake haifarwa ba, zaku saka mashi sha'awar faɗar, idan macece ba zata rinƙa jin shakkar ta gaggayawa mijinta maganganun ba idan ta yi aure, in namiji ne ba zai rinƙa shakkar zagin mata kai har da duka ba idan ya yi aure, akwai abubuwa da dama wanda faɗar iyaye a gaban ƴaƴansu yake haifarwa, kome za'ayi maki ki danne a gaban yara sai kun keɓe nan kam in kin ga dama ɗaga shi ki maka da kasa..........................😒😅 Ajiye bokitin hannunta Mairo ta yi, ta karisa in da Mahnoor take sanyi ya gama lallasata, hannunta ta riko suka koma cikin ɗakin nata, Nenne muguwa ta jiƙa mata mattress ɗinta sosai. Bayansu Mahreen ta bi, Nenne na kiranta ta bawa banza ajiyarta ta shige ɗakin Mahnoor. Bokitin ta ajiye kamar zata bi bayansu, sai kuma ta fasa ta wuce cikin ɗakinta rai a matuƙar ɓace, da ta so ne bappa ya ci mutuncin Mairo, ya yi mata tas, amma bata samu hakan ba. After some minutes. Mairo ta fito daga ɗakin Mahnoor ta wuce cikin kitchen dan yin abin da ya fito da ita dama, ƙoƙarin fara hura wuta ta yi, sannan ta ɗauko bokitin ta cika shi da ruwa ta kawo kusa da murhu, tana ƙoƙarin ɗaura sabon tukunyarta a wuta sai ga Mahnoor ta shigo cikin kitchen ɗin. Ta canza kaya izuwa dogon rigar da bappa ya saya mata a lokacin bikinta. Tana sanye da hujabinta kamar kullum. Cikin girmamawa ta ce. "Daddi ina kwana". Fuska ɗauke da fara'a Mairo ta amsa mata da lafiya ta tashi lafiya. Ita ma da lafiya ta amsa kafin ta ɗaura da cewa. "Bari in tayaki Daddi". "A'a Mahnoor, jeki ki kwanta kawai, ba sai kin tayani ba, ai ba wani aiki mai wahala bane, tuwo zan yi sai sanya maku ruwan wanka". "Ayya Daddi ki bari in tayaki kin ji?". Yadda ta yi magana murya a marairace, Allah sarki barci fa take ji, amma kuma ba zata iya kwanciya ta yi ɗin ba, dan yanzu tana jin tsoron Nennen ta sake zuwa ta jiƙata da ruwa. Da kyar Mairo ta yarda ta tayata ɗin, dan haka sai ta ce to ta yi shara ita kuma bari ta ɗaura ruwa sai ta haɗa kayan wanke wanke kafin nan Mahnoor ta gama shara sai su yi wanke wanke a tare. A bisa ka'ida yau Nenne ce zata yi abinci ba amarya ba, amma da yake bappa yasan bata kwana a gidan ba sai ya ce da Mairo ta ɗaura mashi girkin kawai, kunji dalilin fitowarta da sassafe kenan. Tsintsiya Mahnoor ta je ta ɗauko, cikin nitsuwa ta fara shara hankalinta gabaɗaya yana a kan tinanin mijinta, Allah sarki yau ta kai kololuwa a kewarsa, ji take kamar ta yi ta kuka babu dakatawa, yau da yana nan yanzu warhaka tana kwnace a jikinsa bata fito ba, a gaskiya ta yarda ta yi babban rashi a rayuwarta wanda ba zata taɓa manta shi ba har abada. Dai'dai wannan lokacin da take shara tana tinaninsa.......... Shi kuma yana tsaye a jikin window ɗin ɗakinsa, ya yaye labulen tamkar mai kallan wani abin a harabar kingdom ɗin, a zahiri babu abin da yake kallo, tinani kawai yake yi, tinanin ma wanda bai san namenene ba, kawai a ransa ne yana jin tamkar akwai wani gurbi a ransa da yakamata ya cike wannan gurbin, ya rasa ganewa zuciyarsa, tana yi mashi babu daɗi, kamar akwai abin da ya rasa haka. Hannunsa rike da cup mai ɗauke da cappuccino, yana sha a hankali hankali yana tunane tunane, yanzu ba jimawa suka dawo saga masallaci sallar asuba, sanye yake da kayan barci masu bala'in kyau a jikinsa, sun haɗu da Jawad, amma a hospital ya je ya ga Jawad ɗin. Allah sarki tamkar su cinye junansu saboda so, sai dai Jawad bai faɗa mashi cewa ya yi aure ba, ya dai ce mashi Jannat ce bata da lafiya yake jinyarta. And bai san guyson yana hospital ɗin ba, Jawad kawai ya je dubawa, yana duba shi kuma ya dawo, dan dik baya jin daɗin jikinsa, baya san fita daga cikin ɗakinsa, dama shi ba mai san fita bane sai idan ya zame mashi dole. Yana cikin kuncin da ya rasa me dalili, while ita kuma tana cikin kuncin da ta san dalili. A haka ta gama sharan nan tas, suka yi wanke wanke a tare da Mairo, Mairo na wankewa ita kuma tana ɗaurayewa ta sanya cikin baf, tas suka gama gwanin birgewa sannan Mairo ta kwashe tuwo a kwanikan. Mahreen kuwa tuni ta kwnata a mattress na Mahnoor ta mayar da barci abinta. Bayan Mairo ta sauke ruwan wanka, ta sirkawa bappa ta kai mashi banɗaki, sai ta fito ta shiga ɗaki domin ta faɗa mashi, ita kuma Mahnoor ta fara kwasan kayan abincin ta fara kaiwa kowa ɗakinsa. Tamkar wadda aka koro haka Nenne ta fito daga cikin ɗakinta, tamkar wata ɓarauniya haka ta fara sanɗo, a haka ta nufi cikin toilet ɗin. Jim kaɗan ta fito sai muzurai take yi tamkar an kama ɓera a tarko, dik alamar rashin gaskiya ne a tattare da ita, da alama wani mugun abin ta kullah. Da gudu ta shige cikin ɗakinta, kamar ba ita ta fito yanzu ba, har da kwanciya ta lulluɓa da zaninta. Bappa kuwa ya fito ya shiga banɗaki dan yin wanka. Ita kuma Mairo ta hau sharan ɗakin, da alama Mairo tana da tsabta sosai. Mahnoor kuwa bayan ta gama, a kusa da Mahreen ta zo ta zauna tare da buga uban tagumi, a hankali ta fara jin faɗuwar gaba kaɗan kaɗan kamar wani abin yana shirin faruwa da ita, jingina bayanta da jikin bango ta yi, a hankali ta fara maimaita Hasbunallahu wani'imal wakil domin Allah ya saukaka mata koma menene yake shirin faruwa da ita!. A wani irin haukace bappa ya fito daga cikin toilet ɗin nan, ihun da yake kurmawa da karfi sai ya razana dik wanda kunnuwansa zasu saurara. Cike da tashin hankali da firgici ya faɗo tsakar gidan yana ihu. Mahnoor tamkar bata ji su ba, sam bata fito ba, dan tasan shi da matansa ne, sai ma kifa kanta ta yi a saman gwiwowinta ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Da gudu Mairo ta fito daga cikin ɗakin dan taga menene yake faruwa, Nenne kuwa sam taki fitowa tana ciki kamar bata ji shi ba, sai dai tana can tana zuba uban dariya kamar wata zararriya.Ta toshe baki da pillow dan kada sautinta ya fita tana ta tikar dariya. Mario tana fitowa ta iskosa kwance rashe rashe a kasa yana ta birgima yana ihu kamar wani zararre, daga shi sai kajeran wando a jikinsa, ita ma bai gama sanyata da kyau ba, ga kuma ruwa a jikinsa, da alama ya fara wanka ne ya fito, dik kasa ta buɗe shi saboda ruwan dake jikinsa. Ganin haka yasa Mairo ta fita waje da gudu neman taimako dan taga kamar wani mai ciwon aljanu ko farfaɗiya haka, so ba zata iya ba sai ta yi waje dan neman taimako. Kai tsaye gidansu Arɗo Mairo ta nufa, ko mayafi bata ɗauka ba, hankalinta ne a tashe. Takuwa yi sa'a Ibrahim kawun Mahnoor yana nan, dan haka sai suka taho a tare da shi da Arɗo. Dik ƙasa ya farfasa fatan jikin bappa, saboda yadda yake ta dirza jikinsa a kasa yana ihu, kafin Mairo ta dawo wlh har jiki ne yake fitowa daga fatar tasa, bawan Allah. Ashe ƙarara Nenne ta je ta zuba mashi a cikin ruwan wanka, muguwa saboda tasan Mairo ce ta kai mashi ruwan wankan, kunga yanzu zai ce Mairo ce ta yi mashi mugunta, Allah sarki daga zuwan amarya bappa zai fara ganin laifinta. Wato wlh Nenne da gwaggo anya akwai shaiɗanu irinsu kuwa? Dik abin da Nenne take yi gwaggo take shirya mata shi dallah dallah yadda zata yi komai, shiyasa kuka ga ta dawo gidan bappa da confidence ɗinta. Sun lura aikin bokaye baya kama bappa, shi ne suka dawo ta munafurci da kisisina, komai Mairo ta yi su ɓata, tin bappa baya ganin laifinta har ya zo ya fara gani ya fara jin haushinta, har ma ya saketa, shi ne burinsu, to yanzu Nenne ta fara fito da makaman yakinta, muje zuwa dan ganin yadda wannan wasa zata kaya. Ƙoƙarin kama shi Arɗo dattijon arziki da Ibrahim suka yi dan su kai shi ko da ɗaki ne kada ƙasa ta cigaba da fasa fatarsa. Sai dai ina, sun kasa kama shi, saboda wani irin zillo da yake yi, burinsa kawai a sosa mashi jikinsa, wani irin bala'in kaikayi na musamman yake ji, Allah sarki bawan Allah. Ga shi kararar ta damuna ce ba ta rani ba, irinta ta fi bala'in zafi, kaikayi kamar zai kashe mutum, ga zafi idan ka sosa, wlh Nenne muguwa ce ta karshe, tana ɗaki tana ta dariyar mugunta hegiya. Mairo kuwa kuka kawai take yi da hawaye bibbiyu, Mahnoor ma tana jin dik abin da yake faruwa, amma taki leƙowa, saboda bata san ganin wani tashin hankali a kan wanda take ciki a halin yanzu. Sai da Ibrahim ya fita ya samo wasu manyan maza su biyu, sannan suka zo da kyar suka iya kama bappa. Allah sarki abin gwanin ban tausayi kuma gwanin ban dariya, dan yadda yake birgima sai ya baka dariya, hannunsa dikka biyu a kansa, dan daga kai ya zuba ruwan, tamkar zai ɗaye fatar kansa saboda sosawa, ji yake yi kawai ya yi ta dirje kan nasa a ƙasa ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji. A yanzu ma bai san su wanenen a kansa ba, wlh kuka yake yi sosai, hawaye dik ta wanke mashi fuska. Mairo dik tinaninta yana da wani ciwo ne da bata sani ba. Arɗo da ya gane menene sai ya ce da Ibrahim a kawo mashi ɗanyar kashin shanu, dan shi ne maganinsa. Jin Arɗo ya ce a kawo ɗanyar kashin shanu yasa Ibrahim ya fahimci karatun, ransa ne ya yi mummunar ɓaci, a kule ya ce. "Waye ya saka mashi karara kenan?". Ya yi maganar yana kallon Mairo, da yake akwai zuciya da saurin fushi sai nan take idanunsa suka yi ja ransa ya ɓaci. Mairo da hawaye sun gama wanke mata fuska ne ta fara girgiza mashi kai tana faɗin wlh ba ita bace kuma bata san wacece bace. Ibrahim zai sake yin magana Arɗo ya umarcesa da ya yi sauri ya kawo ɗayar kashin shanun nan da wuri kada su rasa bappan. A fusace ya fice daga gidan, a ransa ya kudurta babu abin da zai hana shi cin uban koma wanene ya saka wa bappa wannan abin........... Lallai Nenne zata sha duka a hannun yayanta kenan. Da kyar suka kama bappa suka kaisa ɗaki, a saman batarman amarya Mairo suka kwantar da shi. Sanya waɗan nan maza biyun Arɗo ya yi da su danne mashi bappan da karfi, haka suka danne hannunsa da ƙafafunsa, Allah sarki yana jin kaikayi sosai hakan yasa da suka danne shi babu halin sosawa sai ya fara zaro idanunsa da suke jajir kamar wuta yana wani irin miƙa yana san kwace kansa, azaba yake ji Allah sarki, wlh dik wanda ya gansa a wannan hali sai ya tausaya mashi, abin akwai azaba ne sosai. Wlh ko leƙowa Nenne taki yi, tamkar bata a cikin gidan. Suna ɗauke bappa izuwa cikin ɗaki ta samu hanya ta fita gidan a miliyan sai gidan Arɗo. Ta je gwaggonta ta ɓoyeta a cikin ɗakin, wato waɗan nan biyun anyi mugaye, kamar waɗan da suka fita daga tsatson Black Tiger............🤔 Da kyar su Arɗo suka iya ceto bappa ta hanyar yi mashi wanka da ɗanyar kashin shanu, suna tsaka da yin wannan aikin ne tamkar saukar aradu suka fara jin kukan jirage a sararin samaniya. Ai a miliyan Mahnoor ta fito waje daga cikin ɗakinta, dan tasan waɗan nan jirage su suka rabata da mijinta, ta manta ma bata goge hawayen fuskarta ba, dama Mahreen ma ta tashi daga barci tin lokacin da bappa yake ihu, Mahnoor ɗin ce ta hanata fita, so yanzu sai suka fita waje da gudu a tare. Tamkar dai a baya yadda suka zo suka ɗauki Jaish, haka yanzu ma jirage ta sama motoci ta ƙasa, kuma a kusa da kofar gidan bappa suka faka motocin. Waje Mahnoor da Mahreen suka fita, yau Mahnoor babu tsoro, dan zuciyarta mijinta kawai yake san gani, burinta ta sanya idanunta a kansa, shiyasa bata tsorata da jirage da motocin ba. Gabaɗaya mutanen kauyen a wannan karon ma fitowa waje suka yi dan ganin su wanene suka zo. A lokacin su Arɗo sun kammala shafe bappa da kashin, hakan yasa bappa ya nitsu tsit kamar wanda ya yi barci, tabarman Mairo kam ya lalace da kashin shanu. Fitowa Arɗo suka yi, dan suma su je suga su wenene?. Kowa a kauyen sai rarraba idanu suke yi, yau shine ganin motonci na biyu a kauyen. Manya manyan bodyguards ne suka fara fitowa daga cikin motocin, da yake dikkansu larabawa ne, sai su Mahreen suka yi masu kallon mutane guda, wai suna kama sosai. Gabaɗaya yan kauyen sai da suka ja da baya lokacin da bodyguards ɗin nan suka bayyana, wasu jiga jigai da su. Bubbuɗe kofofin motocin suka yi gabaɗaya. A hankali uncle Jahiz ya fara fitowa daga cikin motar. Ya zo ya tsaya a kusa da ɗaya daga cikin motocin, yau yana shirye cikin Arabs dressing, har da alkyabbarsa ya ɗaura saman shigar tasa, ya fito a balarabensa sak. Like wow unexpected momma ta fito daga cikin ɗaya daga cikin motocin wanda uncle Jahiz yake tsaye a kusa da shi, tana fitowa guyson ya biyo bayanta, da kallo ɗaya zaka yi mashi in dai kasan shi ka gane bashi da cikakken lafiya sosai. Mahnoor tana ɗaura idnaunta a kan momma da guyson nan take ta gane dik yadda aka yi ƴan uwan Jaish ne, dan jini ba wasa ba, ita kuwa Mahreen da hankali bai gama isarta ba kallon Jaish ta yi wa guyson, kun san na gaya maku guyson yana da tsawo sosai, amma bai kai Jaish ba, kuma Jaish ya fisa cika gaskiya, amma ita kallon Hamma Jaish ta yi mashi. Kowa ya zaro idanu waje yana kallon waɗan nan kyawawan taurarin, barema guyson da kusan rabin ƴan kauyen suke yi mashi kallon Jaish, har sun fara manta yadda Jaish yake. Dik hankalin kowa a tashe, wasu sai kuskus suke yi suna gulmar bappa, wai bappa ne dik ya fara ɗauko masu wannan annoba dangin aljanun ya kawo masu kauye, da bai ɗauko Jaish ba ai da hankalinsu a kwance, yanzu ga shi sai zirya motoci suke yi a kauyensu suna ɗaga masu hankali. Wasu kuwa addu'a suke yi Allah yasa bappa aka zo kashewa tin da shi bashi da aiki sai yayuɓo mutane ya kawosu gidansa ya ajiye. Sai mugun fata suke yi mashi. Jama'a ku tafawa mata......... Meya kawo Momma Jimeta? Mu koma baya mu leƙa KINGDOM OF POWER mu ji ta ya aka yi suka zo kafin mu dawo muji dame suke tafe. Jama'a nace ku kara tafawa mata........ Bayan dawowar Jaish da kwana biyu, sai da suka barshi ya huta, sannan ne momma ta buƙaci da tana san sanin in da ya afka tsawon wannan watanni da ba'a gansa ba, King ne ya ce mata e gaskiya hakan kam yakamata, yakamata su san in da ya je. A lokacin su commander Zafar sun shirya tsab zasu tafi yaki, ba yadda Aunty MieMie bata yi ba a kan King ya dakatar da wannan yakin su yi tsastsauran bincike tukun nan, amma ina ransa a ɓace, zuciyarsa taki sauƙa, hankalinsa baya jikinsa, ya ce babu ja da baya, umarni yake badawa ba shawara ba, kada ya sake jin bakinta a cikin wannan magana, hakan yasa ta ja gefe ta yi shiru, amma wa King kawai, ta nuna mashi ta bar zancen, amma bata bari ba, ta dai umarci su commander Zafar a kan ta basu nan da kwana biyu dik in da Zunaira take su nemota, idan ba haka ba kada su dawo kingdom ɗin nan, shi ne abin da ya faru. A tinanin king umarninsa suka tafi aiwatarwa, amma neman Zunaira suka tafi, saboda dama dan Zunaira za'a je yakin ai, idan aka dawo da ita ba shikenana ba zance ya mutu, idan kun lura ita Aunty MieMie bata san yaki sam sai in ya zama dole, dik da taurin zuciyarta akwai imani da tausayi a cikinsa, tasan yaki yana haifar da matsaloli sosai, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya rasa rayukansu. Guyson ya farfaɗo daga doguwar sumar da ya shiga, sai dai baya magana, dik yadda suka so ɓoyewa Momma rashin lafiyarsa sai da ta gane, dan ta rasa sukuninta, ta shiga damuwa, hakan yasa King ya sanar da ita cikin nitsuwa ta hanyar da yasan ba zata ji raɗaɗi sosai ba. Aikuwa faɗa mata ɗin ya yi amfani, ta buƙaci a dawo mata da shi gida ta yi jinyarsa, a turo nurse su zo su rinƙa kula da shi a gabanta tun da ita babu halin ta je hospital. Hakan aka yi, dan dik abin da zai faranta mata shi King yake yi a yanzu, baya san ganinta a cikin damuwa, dan ma dawowar Jaish ya rage mata abin da take ji a ranta sosai. Jinyar guyson da ta fara yi ne tana faɗa mashi kalmomi masu karfi dan nuna tawakkali da godiya ga Allah, sai Allah ya taimaketa ta fara shawo kansa, kunga kuwa faɗa mata rashin lafiyarsa ya yi amfani, tin da ga shi ta dalilinta ya ɗan samu lafiya har yana iya yin magana. A daren rana na huɗu da dawowa Jaish Tunisia, dama ya yi kwana ɗaya a Nigeria, so a rana ta huɗu da dawowarsa momma ta buƙaci da su zauna su yi magana a kan daga ina su uncle Jahiz suka ɗaukosa, dik ta damu tana san jin hakan, kun san mufa mata batu na gaskiya muna da sanin yakamata ato, taga yakamata ta san daga ina yaronta ya fito ne?. Uncle Jahiz ne ya fayyace masu komai yadda ya kasance da yadda Ramish ya gano in da yake har suka je suka ɗaukosa. Dik cikin parlourn wanda kowa da kowa yana cikin except Jawad da Chuchu da har yanzu Chuchu jikinta bai warware ba, suna hospital, sai kuka take yi taki dainawa, ita dai a dawo mata da Autarta. A gabaɗaya parlourn nan babu wanda ya gane aibi a cikin abinda su uncle Jahiz suka aikata, kowa sai godiya yake yi wa Allah, sai murna suke yi, shi ma Jaish yana zaune kusa da Momma, sai satar kallonsa Fanan take yi, tana san yi mashi sannu da dawowa, amma tana tsoronsa sosai. •••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 "Amma Jahiz wani irin abu ne wannan zaku je ku ɗauke shi ba tare da kun nemi waɗan da suka rikesa kun yi masu godiya ba?". Muryar momma ce ta dakatar da dikka wannan godiya da murna da suke yi ɗin. Mummyn Chuchu ce ta amsa da. "Gaskiya nima naga abin bai kyautu ba sam". Aunty MieMie dake zaune a gefen King ne ta amsa da. "Gaskiya kam ba'ayi masu adalci ba, bai kamata ayi masu haka ba". Miƙewa Jaish ya yi ya nufi hanyar fita daga parlon. Aunty MieMie ce ta tambaye shi ina zai je. Ba tare da ya dakata daga tafiyar ba ya amsa mata da nitsuwa yake so, baya san hayaniya, zai je ne ya kwanta. Miƙewa ta yi ta bi bayansa dan tana san yi magana da shi. A wannan lokacin ne suna fita ya wuce hospital wajen Jawad dan yau tun da rana da ya je asibitin suka gaisa bai sake zuwa ba, Jawad kuma baya fita ko nan da can sai masallaci, so a tare suka je da Aunty MieMie. Sosai momma ta nuna rashin dacewan abin da suka yi, ita ma mummyn Chuchu ta nuna hakan, mama dai bata ce ko uppan ba, ta dake a kan kujera tare da ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya. Momma ce ta nemi King da ya yarje mata zata je ta ga mutanen nan da suka rike mata yaro, har ta ji kaunarsu ya ka mata, uwa kenan, ko yaya ka yi wa ɗanta abu bata mantawa da kai. King yasan condition da take ciki na rashin nitsuwa a kan ɓatar Auta, a yanzu farincikinta suke nema ba ɓata mata ba, dan haka sai ya ce to za'a shirya mata tafiya nan da gobe ta je ta gansu ɗin, wannan shi ne dalilin zuwanta Jimeta, bata ma san Jaish yana da mata ba, bata san irin rayuwan da ya yi a can ba, ita dai ta zo da kanta ne ta yi godiya na riƙe mata yaro da suka yi, to kun ji yadda aka yi, taso su zo a tare da Jaish, amma yaki yarda, ya ce shi gaskiya babu a gajiye yake, kuma baya san zuwa ne kawai. Yauwa ku kara tafawa mata jama'a....... ••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Da gudu Mahreen ta tafi ta rungumi guyson, dan a tunaninta Jaish ne, securitys ɗinsu sun so hana Mahreen isa gare shi, amma kafin su tareta tuni ta isa gare shi, kun santa da iya gudu. Ita dai Mahnoor ta san ba Jaish bane, dan suna da banbanci da guyson dik da cewa guyson ɗin ke binsa a wajen haihuwa, amma suna da banbanci. Momma bata yi mamakin ganin Mahreen ta rungume mata yaro ba, saboda tana ganin Mahreen yarinya ce, sannan kuma hakan da ta yi yasa momma ta kara jin daɗi a ranta, dan alamu sun nuna sun yi sabo da Jaish sosai shiyasa ta rungumi guyson matsayin Jaish. Uncle Jahiz ne ya wuce gaba wajen isa gaban Arɗo dake tsaye a kofar gida yana kallansu, sun ga shi ne dattijo a wajen sai suka nufesa. Sarautar nan dai tana nan, badan momma bama da su uncle Jahiz ba zasu zo nan ba, dan haka cikin isa ya ce da Arɗo suna neman gidan da ɗan uwansu ya yi rayuwa a ciki kafin suka zo suka ɗaukesa kwanaki shidda zuwa bakwai da suka wuce! Arɗo ya ɗan yi mamakin jin yadda Uncle Jahiz ya yi mashi magana kamar wani ɗansa, yana mashi magana ba girmamawa, bai san haka suke magana cike da izza ba su kam. Da hannu ya nuna masu gidansu Mahnoor dake bayansa, dan yasan a kan bakonsu Jaish suke magana. Momma da guyson kuwa, sun yi tsaye suna kallan Mahreen da ta rungume guyson tana zuba mashi surutai haɗe da ɗauki game da sambatun ta san zai dawo garesu dama, har da cewa ta yi kewarsa, ta fara bashi labarin irin kukan da Adda Mahnoor ɗinta ta yi a lokacin da baya nan. Guyson da momma dik babu mai jin yarenta, dan haka basu san me take faɗe ba, sun dai yi shiru suna sauraranta ne. Jin basu yi mata magana bane yasa ta raba jikinta da guyson ɗin ta riko hannunsa ta fara jansa wai ya zo su je su ga bappa, bappa ma yana can yana kewarsa. Ita dai Mahnoor idanunta a kansu ko kyaftawa ta kasa yi, tana kuma tsaye, fuskar mijinta kawai take gani a face ɗin guyson. Sam bashi da kuzari a jikinsa ya dawo da kallonsa a kan Momma, Mahreen sai faman jan mashi hannu take yi. "Bita muje ka ji, dik yadda aka yi a gidansu yayanka ya zauna shiyasa take janka, ga dikkan alamu kallan matsayin yayanka suke yi maka".......... Cewar Momma kenan. Kamar zai yi kuka ya ce. "Momma jikinta dik datti fa! Kalli yadda ta zo ta taɓani ta ɓata mun jiki". Kunsan guyson ɗan wanka ne, ga kayan jikinsa farare kal kal, irin Pakistan na maza riga da wandon nan ne, ya sha rawani a kansa, kyau iya kyau, so baya shiri da datti ko kaɗan, Allah sarki dan ma yana da saukin kai ne yasa bai yi mata faɗa ko ya mareta ba, da su Omaid ne ai da yanzu zancen sun sumar da ita ake yi. "Yi hakuri, ɗaukin ganin yayanka yasa ta yi maka haka, idan mun koma gida sai ka cire kayan ka ji?"................ Cewar Momma. "Momma ni Allah bana san dattin, kice kawai ta sakeni". Momma da ta fahimci zai iya saka masu kuka a wajen, dan wlh ko da wasa baya san datti, sai ta riko hannun Mahreen da take rike da shi, cikin harshen larabci ta ce da Mahreen. "Zo wajena kin ji?......" Bata idasa maganar ba Mahreen ta kwace hannunta, cikin tsiwa ta ce. "Wacece ke da zaki rikeni? Ni ki barni a wajen hamma na". Tana kai karshen maganar ta sake rike hannun guyson. Kasancewar da fillanci ta yi maganar sai momma bata gane me ta faɗa ba. Shi kuma guyson tana rikesa ya fisge hannunsa da karfi haɗe da cewa........... "Kada ki sake rikeni da hannunki dik datti". Da larabci ya yi maganar. In baku manta ba a baya Mahreen ta fara koyar larabci kaɗan kaɗan, dan haka ta ji wannan kalmar da guyson ya ce ta sake shi. Sai kuma a lokacin ta lura voice ɗinsa ba iri ɗaya da Jaish ba, muryarsa na yara ne, kuma ɗan siriri ne sosai. Fahimtar hakan yasa ta yi saurin ja da baya daga kusa da shi. A tinanin momma tsawar da ya daka mata na ta sake shi ne yasa ta ja bayan, dan haka sai ta yi ƙoƙari matsawa kusa da ita ta rikota. Ai ina, a miliyan Mahreen ta juya ta bar wajen tana rushewa da kuka mai ban tausayi, Allah sarki ta gane ba Jaish bane yanzu. Uncle Jahiz da ya tsaya yana turɓune fuska yana binsu da kallo ne ya matso kusa da momma............ "Ga gidan nan, ku shiga ku yi abin da zasu yi kin dai ji yaya ya ce kada mu kwana, yau zamu juya". ....... Ya faɗa ransa a ɗan ɓace, da alama bai so batun zuwansun nan ba sam. Momma ta lura da baya san zuwa, dan ma saboda ita ce, wlh da mummyn Chuchu ko mama ne ba zai zo ba, dan haka sai ta wuce gaba saboda su yi sauri su je su fito. Cikin mutunci ta gaida Arɗo, sannan ta buƙaci da ya yi mata jagoranci izuwa ciki, bodyguards zasu shige cikin su duba babu wani abin cutarwa kafin ta shiga, ta yi saurin dakatar da su, ta ce su bari zata shiga kawai. Mairo Arɗo yasa ta tarbesu hannu bibbiyu, a lokacin da suka shigo bappa baya ɗakin, ya samu kaikayin ta sakesa saboda Arɗo ya labta mashi kashin sosai a jikinsa. Nenne kuma ta gudu gidan Arɗo, so Mairo ce kawai a cikin ɗakin tana ƙoƙarin gyara komai, ta fitar da tabarman da aka kwantar da bappa, ta juye mashi wani ruwan wankar ya shiga wanke jikinsa, da yake isaka na kaɗawa sosai ma har kashin shanun ta bushe a jikinsa. Tabbas momma ta ji kyamar shiga cikin gidan, amma duba irin alkhari da suka yi mata, ɗanta sukutum, first born ɗinta suka kula mata da shi, sai ta danne kyamar ta shiga cikin gidan. Guyson kam ya gudu wajen uncle Jahiz sun koma cikin mota sun zauna. Time da Mairo ta yi masu iso cikin ɗakin, Momma ta so ta ki shiga, amma kuma da ta tuna Jaish sai ta daure ta shiga ciki. Mahnoor kuwa ganin babu Jaish a cikin tafiyar sai ta dawo cikin gida ta wuce ɗakinta ta kwanta, ita kuwa Mahreen bin momma ta yi har cikin ɗakin bappa dan taga me ya kawosu gidansu?. Arɗo ma ya shigo cikin ɗakin dan ya ji me ya kawo su Momma?. Cikin girmamawa Mairo ta tsugunna ta ɗagawa Momma gaisuwa. Sai dai kash babu fillanci, momma bata gane komai da suka faɗa ba, da yake Arɗo babban malami ne yana jin larabci sai ya sanar da momma gaisuwa Mairo take yi mata. Jinjina kai kawai momma ta yi, ta ku ma ɗan ji daɗin ansamu mai jin irin larabcinta, dan haka sai ta faɗa mashi ita mahaifiyar bakon da suka rike ne, ta zo ne ta yi masu godiya bisa rike mata yaro da suka yi. Sosai Arɗo ya yi mamaki, a wani ɓangaren kuma ya ji matuƙar daɗin hakan, ko ba komai sun nuna sun san anyi masu halarci. "Bani na rike ɗanki ba, ɗana ne ya riƙesa, ya shiga wanka bari ya fito sai ku gaisa".......... Cewar Arɗo. Jinjina kai momma ta yi ba tare da ta yi magana ba, dik zama a cikin ɗakin ya isheta, ji take yi kamar zata yi amai, amma haka ta daure har bappa ya fito daga wanka, yana sanye da jampa blue, ta koɗe kam sosai, jikinsa fa dik ya ji ciwo bawan Allah, bayansa ta ɗaye, kai Nenne muguwa ce, ta gana mashi azaba, wannan ma fa wai yanzu aka fara zaman kishin, anya nan gaba Nenne ba zata saka masu wuta ba kuwa.................🤔 Lokacin da su Momma suka zo bai gama dawowa cikin hayyacinsa ba, so bai san da batun zuwan nasu ba. Da ya fito yaga jirage a saman suna shawagi kuma sai ya ce bari ya je ya wanke jikinsa da sauri ya fito yaga menene yake faru? Shi ma dai da kallo jiragen sau ɗaya ya raya a ransa Jaish ɗinsa ne ya dawo garesu. Har kamar zai fita waje da ya fito daga wanka, sai kuma ga kalli sabbin Queen cover shoes masu bala'in kyau a kofar ɗakinsa, hakan ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, shi ne ya ce bari ya shiga ya ga wacece a ciki. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga. Arɗo ne ya amsa mashi sallamar tasa. Yana ɗaura idanunsa a kan momma ya gane cewa mahaifiyar Jaish ce, wani irin farinciki ne ta lulluɓesa, Allah sarki har kasa haƙura ya yi sai da ya tambayi ina Jaish, ko zama bai yi ba. Sai dai da fulatanci ya tambaya, ya manta da basa jin fillanci, sai da ya ji momma bata amsa shi bane yasa ya juya harshe izuwa larabci. Mahreen tana ganinsa ta yi sauri ta zo ta rungumesa tare da saka mashi kuka tana faɗa mashi hamma bai dawo ba sai dai wani mai kama da shi ne ya zo. Guyson kenan. Nan take bappa ya ji jikinsa ta yi sanyi, gabansa har sai da ta faɗi, dik tinaninsa Jaish ya dawo garesu ne. Arɗo ne ya ce mashi ya nemi waje ya zauna momma wajensa ta zo. Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya samu waje ya zauna yana tinanin Jaish. Cikin mutunci da girmamawa ya ɗagawa momma gaisuwa da larabci. A ɗan dake ta amsa mashi kafin ta ɗan yi shiru na ƴan mintuna. Sannan ta gabatar mashi da wacece ita da kuma abin da ya kawota. Sosai bappa ya sake jin zuciyarsa ya karaya, wato godiya suka zo yi mashi ma ba wai sun kawo Jaish bane, sam abin bai yi mashi daɗi ba, ba haka ya so ba, shi bai yi dan ayi mashi godiya ba, saboda Allah da kuma kaunar da yake yi wa Jaish ya yi. Ganin ya yi shiru kaman ya shiga damuwa ne yasa Momma ta buƙaci da ya bata tarihin a ina ya ga Jaish da har ya rikesa na tsawon watanni haka?. Jiki ba kwari ya zayyana mata komai daga farko har karshe, bai ɓoye mata komai ba har da gudun Jaish da ƴan kauyen suka rinƙa yi suna ce mashi aljani, dik ya zayyane mata. A gabaɗaya maganganunsa da ya faɗa abu ɗaya ne ya yi mata daɗi shi ne Jaish ya yi aure, wannan magana ta yi mata daɗi sosai, har sai da ta ɗan murmusa, cike da farinciki a ranta ta buƙaci da a nuna mata matan ɗanta. Bappa ya yi mamakin ganin bayyanar farinciki a tattare da ita daga jin Jaish yana da mata, ya yi zaton zata ki batun auren, ashe ba haka bane baiwar Allah. Tabbas momma har cikin ranta ta ji daɗi, saboda ko ba komai ta kara samun ɗiya mace, sannan kuma zata rama masu alkhairi da suka yi mata, sun cancanci hakan, sun cancanci a rike masu ƴa da amana, dik ɗan halak ba zai manta halacci ba, dan haka tana maraba da Mahnoor from the button of her heart. Kuma ni da ku mun san bappa ya yi matuƙar ƙoƙari a kan Jaish, kada ku manta fa farko ko irin abincinsu Jaish baya iya ci, amma haka bappa ya rinƙa yanka mashi nama yana ci, dik kaunar ƴan kauye da dabobinsu haka bappa ya sadaukar da nasa dabbobin wa Jaish, ai ya yi namijin kokari. Allah sarki ni Princess Teema na ji matuƙar tausayin Fanan, tana murna Jaish ɗinta ya dawo sai aure, ashe mata garesa, heart breaked!!. "Mahreen jeki ki kira Mahnoor a ɗakinta". Cewar Bappa. Cikin kunci, tana guntun kuka ga hawaye a saman face ɗinta ta miƙe ta fita, sai gunjin kuka take yi. Godiya momma ta yi wa bappa sosai tare da nuna mashi jin daɗinta a kan wannan aure, ta kara mashi wani godiya na daban a kan bawa ɗanta mata da ya yi, daga karshe ta rufe mashi da zata tafi da Mahnoor. Tashin hankali, nan fa matsalar take, dan kuwa bappa bai shirya rabuwa da Mahnoor ba, a tinaninsa wai sai dai Jaish ya zo su yi zaman aure da ita a cikin kauyen, shi bai yarda a ɗauketa ba, ita kuwa Momma ta ce mashi ina hakan ba zai yiwu ba, Mahnoor matar Prince ce fa ba wai matan mutum gama gari ba, ai kuskure ne ma su bari wani yaga face ɗinta, nan fa momma ta shiga zayyana mashi dokikin gidan sarauta da tsarukanta da yadda matansu suke kasancewa cikin tsaro da lulluɓe kai, daga karshe ta ce tafiya da Mahnoor dole ne!!! Idan suna da ra'ayi su tashi mutanen da zasu bisu su ga in da suke, amma tafiya kam babu fashi............ Babbar magana. Bappa ya yi shiru cikin ransa yana tunanin yadda zai fara rabuwa da yarsa. Dik tattaunawar da suke yi Ibrahim kawunta yana jinsu, dan yana zaune a tsakar gida, ba ƙaramin daɗi ya ji ba na jin matsayin da Mahnoor ta samu, abin da basu taɓa tsammani ba, ya ji daɗi da suka ce zasu tafi da ita, kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha. A tare Mahreen da Mahnoor suka shigo cikin ɗakin, Allah sarki ashe da ta koma cikin ɗakinta kuka ta je ta rinƙa yi, idanunta har suka kumbura. Suna shigowa bappa ya ce da momma ga matar Jaish ɗin, ya kuma cewa Mahnoor wannan mahaifiyar mijinta ne ta je ta gaisheta. Matsawa ta yi kusa da momma, kanta a kasa ta tsugunna zata gaisheta. Jawota momma ta yi ta runguma tana tsananin farinciki, dan kuwa tamkar an shiga ranta anyi bincike kafin a bashi wannan mata, tabbas irin matar da take mashi fata take kuma yi mashi addu'ar samu kenan, kyakkyawa san kowa kin wanda ya rasa, abin ya yi mugun yi mata daɗi, dik wani bakincinkinta sai ta ji ya kau, tamkar zata mayar da Mahnoor cikin cikinta saboda so da kuma murna. Shi dai bappa dik wannan bashi bane damuwarsa ba, ya za'ayi momma ta ce, zasu tafi da Mahnoor? Gaskiya ba dan su gidan sarauta ba a ja in ja da su ba wlh da shi dai ba zai yarda ba, amma ba yadda ya iya. Dai'dai lokacin Jaish ya kira Momma ta Whatsapp, voice call kuma ya kirata, dan ya gwada number kai tsaye taki shiga. Ganin shi ne yasa ta yi saurin ɗauka, cikin nitsuwa suka gaisa ya tambayeta ya hanya?. Murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha ta ce mashi ai gata a cikin gidansu tare ma da matarsa. Ya ɗauka wasa take yi sai ya ce. "Momma kada ki ɓata lokaci please, ku dawo da wuri dan har na damu na fara kewarki". Ita kuwa sai ta ce mashi ga matarsa nan su gaisa. A ɗan dakile ya ce. "Mata kuma?!". Jinjina mashi kai ta yi haɗe da tabbatar mashi, bada ban ita ta ce matarsa ba da ya ja tsaki kuma ya kashe wayarsa, amma ita ce ya zai yi? Sai ya ce.......... "Please momma kada ki fara wannan zancen auren naki, ni kada ki ce ma zaki ga ƴar mutane ki saka mata ran aurena, bani da lokaci a yanzu, please kada ki mun irin abin da kika yi wa uncle Abbas, zan tabbata cikin kunci". Yana maganar fuska a ɗaure tamau kamar hadari, alamar bada wasa yake yi ba!!. Kunsan momma ita ta haɗa auren uncle Abbas da maman su Yah Jawad, kawai daga ziyara ta haɗa wannan aure, to shi Jaish a tunaninsa irin taga mace kyakkyawa ne ta ce zata zaɓa mashi, kwata kwata bai taɓa kawowa ransa matar ta gaske ce kuma mallakinsa ce ba. Momma da ta rasa me zata ce mashi saboda bata san tsayawa yi mashi dogon bayani ta waya, sai ta ce mashi zasu yi waya anjuma, yanzu bari ta samu ta bar wannan kauyen su kamo hanyar kasarsu shi zai fi. Da okey ya amsa mata, har zai katse kiran kuma sai ya sake ce mata dan girman Allah shi kada ta jajuɓo mashi bala'i yana zaune lafiyarsa. Bata amsa mashi ba ta katse kiran, dan bata san biye mashi yanzu. Bappa dik da bai san da waye take waya ba sai ya ji yana san yin magana da na cikin wayar, dan zuciyarsa na faɗa mashi da Jaish take waya. In short haka momma ta gama dik abin da zata yi, ta kawo makudan kuɗin da suka canza nasu izuwa na Nigeria, miliyoyi ta bawa bappa, suka kara yi masu godiya sosai, sannan ta ce yakamata su tafi da wani ya bisu ya ga ƙasarsu. A nan ne Arɗo ya ce su tafi da kawu Ibrahim. Bappa ma ya aminta da hakan. Sai kuma me?. Momma tana rike da hannun Mahnoor taki saketa, sai da suka je zasu shiga motocinsu Mahreen ta ce wlh basu isa ba, bata ga uban da zai rabata da ƴar uwarta ba. Ita ma Mahnoor ɗin kuka ta saka masu, ta ce wlh ba zata iya rabuwa da Mahreen ba, infact sai cewa ma ta yi da a rabata da Mahreen gara ta hakura da Jaish ɗin har abada. Ganin haka yasa momma ta ce zata tafi da su dikkansu biyu kuma ta yi alkawarin zata rikesu amana, dan ba zata iya barin Mahnoor ba, ai ita taga wa ɗanta matar da babu rabuwa. Nan fa bappa kuma ya ce gaskiya bai aminta a tafi da Mahreen ba, to shi wa za'a bar mashi?. Sai da Arɗo yasa baki ya roƙesa a kan ya dubi girman Allah kada ya raba ƴan uwan nan guda biyu, tare suka taso, tare suke komai, suna bala'in kaunar junansu, idan ya rabasu wlh zai cutar da su ne, ya yi hakuri ya kyalesu su tafi ɗin kawai. Kun san abin isn't easy wlh, rabuwa da yara biyu lokaci guda, yaran ma su kaɗai ka mallaka, a rabaka da su kai akwai wuyar iya ɗauka fa. Da kyar da suɗin goshi bappa ya aminta da su tafi a tare. Kawu Ibrahim ya yi masu rakiya suka tafi. Nenne tana gidan Arɗo bata san abin da yake faruwa ba, daga baya ta ji maganar daga sama, tuni ta rugo tazo dan ta ganewa idanunta, sai dai kash, suna tafiya tana isowa, dan haka bata samu damar ganinsu ba. A lokacin kuma bata san da Mahreen aka tafi ba, da za'ayi bala'i kam. To our Mahnoor safe journey, daga Jimeta sai Abuja, daga Abj sai Tunisia, Allah ya kaiku lafiya. 9:30pm. Su momma suka isa Tunisia, su Mahnoor sai kauyanci suke ta bugawa, da yake Mahnoor tana da kunya, ta san momma surkuwarta ce, sai tana danne kauyancinta. Ita kuwa Mahreen da suka zo shiga cikin kingdom of power, idan baku manta ba dama akwai wasu gumaka na zakuna a bakin gate ɗin, sannan akwai kungin Aunty MieMie. Ai kuwa tana ganinsu ta fara yi wa su Momma hauka wai taga mugun abu. Da kyar Ibrahim ya rarrasheta, haka a wajen shiga jirgi ma ta rinƙa yi masu hauka, ta ki hawa sai da Ibrahim ya ɗagata, Mahnoor dai dik da a tsorace take ta danne bata fito fili ta yi haukar ba, sai dai zuciyarta cike yake tab da tashin hankali, ta gama tsorata. Dama da pr jet ɗin King Zuhair suka zo. Ai Mahreen bata gama yi masu hauka bama sai dai suka nufi family part, a lokacin ne suka ga hauka, ta rinƙa yi masu kuka a kan ita a mayar da ita wajen bappanta, ai nan ba duniya aka kawota ba, kasheta za'ayi. Ta ƙanƙame Ibrahim tana ihu. Ita ma Mahnoor kukan nan take san yi, amma ta danne, idanunta sun ciko da kwallah sun yi jajir. Ta kofar baya motocin su momma suka tsaya, dik da dare ne basu tsaya ta gaba ba, dan in baku manta ba doka ce ba'a ganin matan sarki. Momma tana rike da hannun Mahnoor gam suka nufi cikin gidan, sai ta ce Ibrahim ya jirata a wajen zata turo wanda zai kaisa masaukinsa. To shi Ibrahim ya saba yawace yawace bai wani tsorata sosai ba, amma dai ya ɗan tsorata shi ma, saboda bai taɓa ganin Daula haka ba. Mahreen ta ƙanƙame Mahnoor sai kuka take yi, momma ta yi ta yi tayi shiru amma taki, ita dai a mayar da ita wajen bappanta kada a kasheta, so su da yake basa jin fillanci sai basu san me take faɗe ba, guyson dai ya wuce part ɗin mummyn Chuchu abinsa, ya ce sai su Mahreen sun yi wanka zai dawo wajen mommarsa, sai ɓata rai yake yi momma ta kawo masu ƴan datti, bai ma san cewa Mahnoor matar Jaish bace. Suna sako kafarsu a parlourn momma Jaish dake zaune saman sofa shi da Jawad da aka sallamesu daga asibiti ɗasun ya miƙe tsaye da nufin zai bar part ɗin, dama tun ɗazun suke zaman jiran momma a wajen, so yaga kamar ba zata iso da wuri bane yasa ya miƙe da nufin ya je part ɗinsa ya kwanta. Ai Mahreen tana ganinsa ta dagata da yin haukar da take yi masu, tuni ta manta da in da take, ai a miliyan ta watsa a guje ta je ta faɗa a jikinsa. Mahnoor ma wani irin ajiyar zuciya mai karfi ta sauke, ta kasa kawar da idanunta daga kansa, ya canza sosai cikin kwanaki bakwai, ya koma sak yadda yake da, hasken fatarsa ta dawo yadda take, ga gashin kansa da ya tara a kauye yanzu ta sha gyara, ba ƙaramin kyau ya kara ba, yana sanye da sleeping dress launin up white, shi ma Jawad kayan barci launin up white ce a jikinsa, dama su fa kayansu iri ɗaya suke sakawa, komai nasu kusan ɗaya kamar tagwaye. Cikin zafa Jaish ya finciketa daga jikinsa, da karfi ya wurgata gefe guda, ransa ta yi mummunar ɓaci, kallan ƙazamiya ƙasƙantacciya ya yi mata, bai santa ba ta zo ta wani rungumesa. Ƙoƙarin dalla mata mari ma ya yi cikin fushi, da sauri Jawad ya riƙesa yana faɗin......... "Haba mutumin meyayi zafi haka?". Momma dai turus ta tsaya tana kallonsu, sam bata yi mamakin hakan ba, dan tasan dikka ƴaƴanta sam basa san datti, basa san kazanta, dole Jaish ya gansu a matsayin datti, saboda kayan jikinsu dik a koɗe sosai suke, gara ma ita Mahnoor doguwar rigar bikinta ta saka, shi yana da ɗan kyan gani. Da gudu Mahnoor ta kwace hannunta daga rikon da momma ta yi mata, ta kariso cikin parlourn ta rungumi Mahreen dake ihu ta ji azabar wurgar da ita da Jaish ya yi, ta bugu sosai. Kwace rikon da Jawad ya yi mashi ya yi, da sauri ya nufi hanyar fita waje dan ya je ya cire kayan jikinsa dan ta taɓa, in baku manta ba mugun kyama Jaish yake da shi, kun tuna farkon zuwansa garinsu yadda ya rinƙa kwarara amai saboda bappa ya taɓa shi? To yanzu ma hakance. Akwai tashin hankali, my people's kuna tinanin Jaish zai yarda da Mahnoor a matsayin mata kuwa? Akwai fa matsala. Amma my people's nace ba, who noticed that Jaish and Jawad shekarunsu ɗaya kuma shekarun mstansu ma ɗaya?........ 🤔 A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA.............. MUJE ZUWA AKWAI ABUBUWA A GABA MASU BAN MAMAKI, KUN SAN INA SAN IN YI TA SURPRISING ƊINKU AI. •••••••••••••••••FOREST••••••••••••••••🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ •••••••••••••••••FOREST••••••••••••••••🔥 ••••••••••••••••AFTER SOME TIMES🔥 Zaune Pretty take a kasan wani bishiyar zaitin mai bala'in tsayin gaske. Tana zaune suna fuskantar juna ita da Zunaira, ta yi shiru tamkar mai tinanin wani abin, ga dikkan alamu akwai damuwa a tattare da Zunaira sosai, sai dai ita Pretty a yau babu alamar damuwa a tattare da ita. Meya haɗa Zunaira da ta mutu kuma da Pretty? Muje zuwa. Kada ku manta alkalamina ɗan alkawari ne, dan haka ya yi maku alkawarin samun surprise dayawa a cikin labarin nan, so yanzu haka mun fara buɗe babin surprise ne, Princess Teema taku ta amana Queen of surprises. Muje zuwa dan jin me ya haɗa Auta da Pretty kuma? Ina Team Zunaira? Princess Teema tana tayaku murna Zunaira is alive. Auta tana sanye da kayan Pretty a jikinta, ta yi rama sosai, ta sha jinya ta sha bakar wahala baiwar Allah, har ta fita a hanyacinta, idan kuka ganta yanzu ba zaku taɓa yin zatan ita bace, saboda wahala da ta sha, har duhu sai da hasken fatarta ya yi, idanun nan nata sun kara girma saboda rama. Fuskarta ya ƙanƙance, ita ma yanzu ta zama irin Pretty babu ɗaura ɗan'kwali sai dai su saki gashi har baya, coz ita Zunaira gashin nata ma in ka gani sai ka san ta ci uwar wahala, dik ya cukurkuɗe kamar ba ita ba. Wasu irin fresh fruits ne a gabansu cikin kwanto irin wanda Mammar kamran take amfani da su, wato kwanton da ake zuba timatir. Ba cin fruits ɗin suke yi ba, Auta tana tinanin gida da su Chuchu yanzu tsawon lokaci bata a tare da su, ita kuma Pretty Allah ne kaɗai yasan me a cikin zuciyarta, dan bata bada daman ya fito fili a san halin da take ciki ba. Har yanzu akwai ɗan sauran magani manne a cikin Zunaira in da Hoorain ya caka mata wuƙa, wajen ya warke alhamdulillah, dan har tana iya tafiya da kafafunta. "Alhamdulillah my Queen ta samu lafiya".......... Daga bayansu suka ji wannan murya wanda ko basu juyo ba sun san shi ne, dan shi kaɗai ne garesu a cikin wannan forest ɗin. Auta ce ta juyo haɗe da kai kallonta a kansa, ita kam Pretty bata juya ba, kamar fushi take yi da shi........... Kamar dai kullum yana nan cikin wannan shiga tasa, ga dikkan alamu su Pretty har yau basu san ya kamannin face ɗinsa take ba. Ɗan yake Auta ta yi mashi, baiwar Allah ko tana cikin damuwa murmushi baya ɓata daga kan face ɗinta, murmushi sadakace in ji Manzon Allah (S.A.W) "Na ji sauki Alhdulillah".......... Ta bashi amsa tana ƙoƙarin faɗaɗa murmushinta da dole. Tsareta da idanu ya yi tamkar zai cinyeta, bai sake yin magana ba, ita ma bata sake yin magana ba, ta dai kawar da kallonta daga kansa, tsoronsa take ji sosai, saboda yanayinsa, amma hakan baya hana ta yi mashi murmushi ta kuma yi mashi magana idan ya zo, saboda shi da Pretty su suka ceci rayuwarta, da yanzu babu ita a doran duniya. Ba komai yasa take tsoronsa ba kuma face zubin halittarsa, cikakken sadaukin warrior ne sosai da sosai, and wani lokaci yanayi mata yanayi da Hoorain da ba zata taɓa iya mantawa da shi a rayuwarta ba, ta in da kuma yake yi mata yanayi da Hoorain shi ne rashin yarda ya buɗe fuskarsa a garesu, tin da ta fara samu sauki ta fara magana in ya zo tana rokansa da ya buɗe fuska su ga juna, sai ya ce mata sai wani lokaci, yana yawan zama a tare da ita lokacin da take jinya, suna hira dik da ba sosai ba, amma baya yarda idan ta kawo zancen buɗe fuska, wannan dalili ya ɗarsa mata tsoronsa a ranta, tana tsoron waɗan da basa buɗe fuska a yanzu. Batu na gaskiya wannan ba Hoorain bane, basu ma da haɗi, Hoorain yana Daular Queen Zarina, sai dai shi ma wannan yana da nashi dalilin da yasa baya san buɗe fuakarsa a garesu ne kamar yadda shi ma Hoorain yake da nashi dalilin, amma ba mutum ɗaya bane sam, ita dai Auta tana tsorace da masu rufe face ɗinsu ne kawai wanda dani da ku kuma dik mun san dalilin tsoronta a kansu. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 "Omnish yau ba zaki yi mun magana bane?". ........... Ya yi maganar yana zagowa ta gabansu. Turɓune fuska ta yi, tana turo baki ta ce. "Yau ba zan yi magana da kai ba". ........ "But why?"....... Ya yi maganar dai'dai lokacin da yake tsugunnawa a gabansu. Hannu ya kai ya ɗauki lemu mai ɓawo guda ɗaya daga cikin kwandon gabansu. Cikin nitsuwa ya fara ɓare lemun yana satar kallon Auta ta wutsiyar ido. "Ba kai ne kace ba zaka sake wuce kwana ɗaya baka zo garemu ba, amma yau ka kai kwana biyar baka zo ba". Cewar Pretty sarkin mita da raki. Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar. Tana kai karshen kuma ta miƙe da sauri ita a dole ta yi fushi zata tafi ta basu waje. Sak dai yadda take yi wa Kamran idan ya ɓata mata rai ta yi fushi. Cikin zafa ya yi saurin riko hannunta, Pretty tana bashi ciwon kai da shegen shagwaɓa da saurin kukan nan nata, ga shi bata jin lallashi da wuri............. "Haba my baby, to ki yi hakuri ba zan sake ba, kuma nima ai ba dan san raina nike rabuwa da ku ba, idan da dan san raina ne ba zan rabu da ku ba ai, ina san kasancewa daku sosai, amma bani da damar yin hakan, kiyi hakuri kinji rigimammiya kawai"................. Dik maganganun da yake yi idanunsa a kan Auta da take ta binsu da kallo, ita dai Pretty ta shiga ranta sosai, tana burgeta bare ma idan tana yi wa wannan sadauki shagwaɓa, sosai take jin daɗin kallonsu a tare. Kuka Pretty ta saka mashi wai dan ya ce mata rigimammiya a karshen maganarsa, shikenan ya sake jijjigo wata rigimar............ Dan dolensa ya gyara zama a kasan wannan bishiya, ya ɗaura Pretty a saman laps ɗinsa ya hau rarrashi. A saman kirjinsa ta kwantar da kanta tana turo baki ita a dole ranta ya ɓaci........ Cigaba da ɓare lemun hannunsa ya yi yana satar kallon Auta, da yake face ɗinsa a rufe sai iya idanunsa ne kawai a buɗe, idan ka gansa zaka yi zaton lemun yake gani, amma Zunaira yake gani, ita kuma tana ta kallon Pretty da ta gama tafiya da imaninta. Shiru wajen ya ɗan yi na ƴan sakanni da ya kammala ɓare lamun, sai ya rabata kashi huɗu, Pretty dake zaune saman laps ɗinsa ya ɗauki ɗaya ya sanya mata a baki yana dawo da ainahin kallonsa a kan face ɗinta. Buɗe bakinma Pretty sai ta ja mashi aji sai kuma ta yi shagwaɓa, amma haka ya jirata ta gama shan kamshinta kafin ta ɗan buɗe mashi bakin nata, shi ma kaɗan ta ɗan buɗe. Tura mata lemun ya yi yana dawo da kallonsa a kan Auta, ta sunkuyar da kanta ƙasa, wasu zafafan hawaye suka fara bin ƙuncinta, ba komai ya ja hakan ba face abin da yake yi wa Pretty ya tuna mata da ita da guyson, ta yi kewan ƴan uwanta sosai, ba dan sadauki yana kula da ita yana rarrashinta haɗe da kawar mata da damuwar da take ciki ba wlh da bata san ina zata sanya rayuwarta ta ji sanyi ba, bata taɓa rabuwa da ƴan uwanta ko nan da can ba sai a dalilin Hoorain, wannan abin ba zai taɓa gogewa a ranta ba har abada. Kanta a ƙasa, bai san hawaye take yi ba, sai ya ɗauki lemu guda ɗaya cikin wanda ya raba, bata yi zato ba sai ganin hannunsa ta yi yana ƙoƙarin cusa mata lemun a bakinta. Da sauri ta ɗago kanta, karap suka haɗa ido, ya ɗan yi mamakin ganinta tana kuka, ita kanta Pretty ta yi mamakin hakan. Tashi ta yi daga saman laps ɗinta ta koma kusa da Auta, ɗan rungumota ta yi tana faɗin............ "Allah sarki meyasa kike kuka kuma ƴar uwa?". Shiru bata amsa masu ba, ita kaɗai tasan me take tinani, ita kaɗai tasan raɗaɗin da yake cikin ranta. "Omnish jeki ki kawo mun maganinta kin ji?"............ A faɗa a sanyaye. Ɗan zaro idanu Pretty ta yi, a ɗan tsorace ta ce. "Ciwonta ne yake yi mata zafi?". Kai ya gyaɗa mata a alamar e, hawayenta Pretty ta fara share mata, cike da tausayawa ta ce. "Ki yi shiru ki dai'na kuka, In Sha Allah ciwonki zai yi sauki, yanzu zan kawo maki maganinki, amma ki dai'na kuka, bana san ganin kina kuka"......... Oh Pretty sarkin iya tsara zance idan ta yi ra'ayi, in bata yi ba kuma sai ka yi zatan wawuya ce ko kurma. Jinjina mata kai kawai Auta ta yi ba tare da ta yi magana ba, goge mata hawayen da ƴan hannayenta Pretty ta yi kafin ta miƙe da sauri ta nufi makwancinsu dan ta ɗauko maganin. Tana tafiya ya matsa kusa da Auta sosai, dama wayo ya yi wa Pretty ta tafi shiyasa ya ce ta je ta ɗauko mashi magani, idan ya matso ya ce zai ɗaura Zunaira a kan cinyarsa ko wani abin makamancin haka kuka Pretty take yi ta ce ai kafarsa nata ne ita kaɗai shiyasa ya yi mata wayau ta tafi. Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta, shi kansa sai da ya ji wani irin abu ya tsaya mashi a makoshinsa mai wuyar haɗiyewa. Kallanta ya yi ido cikin ido, gabansa ne ya ji ya fada dum dum haka. Ɗayan hannunsa yasa ya fara goge mata sauran guntun hawayen dake face ɗinta, cikin sanyin murya can ƙasa ƙasa ya ce. "Kin manta cewa kin mun alkawarin ba zaki sake zub da hawayenki a banza ba ne?". Shiru bata iya amsa mashi ba, sai ma ji da ta yi kamar ta tashi ta gudu a wajen, dan dai yana da girma da kima a idanunta wanda ba zata iya yi mashi abin da zai ɓata mashi rai ba ne yasa ta danne, ba za kuma ta taɓa manta halaccinsa a gareta ba. Ƴar Halak kenan. Ganin bata yi magana bane yasa ya sake matsawa kusa da ita sosai, a hankali ya ɗan rungumota da nufin ya yi mata rarrashi irin wanda yake yi wa Pretty. Dik da yake sadauki sai da ya ji wani irin shock a jikinsa, kamar wanda aka jonawa lantarki, har sai da ya ɗan saketa jin abin da bai taɓa ji ba. Amma kuma yana san ta yi shiru kuma ta yi mashi magana, dan haka sai ya daure ya sake rungumota a jikinsa, yana jin wani irin bakon yanayi haka ya daure ya fara rarrashinta tare da tuna mata da alkawarin da ta yi mashi a kan ba zata sake yin kuka ba. Dan dole ta haɗiyi kukan nata, saboda ya iya rarrashi sosai, ko da yake dik wanda zai rarrashi Pretty ta yi shiru lallai ba shakka ya iya rarrashi, dan Pretty sai Allah. Murya can ƙasa ƙasa haɗe da kuka ta ce. "Ka yi hakuri ba zan sake ba". Da yake tana kuka sai voice ɗin nata ya yi tamkar a shagwaɓe ta yi maganar, ba ƙaramin ɗarsa wani abin a ransa wannan magana tata ya yi ba. Ƙasa sake yin magana ya yi, wannan sadauki ya shiga yanayi, abin ku da ba'a saba ba, an saba da datse kan mutane da takoba, ba'a saba shukan fure ba, sai ya zamana kaman wani ɗan fari a gabanta, ya hau aikin binta da ido kawai, daga ta yi mashi shagwaɓa sau ɗaya shikenan ya birkice. (Anya ba zamu kai sadauki wajen Yah Jawad ya koya mashi karatun shuka flowers 😅 ba kuwa my people's?) Jin ya yi shiru bai amsa taba yasa ta yi tinanin ko dai ransa ne ya ɓaci yaki sake kulata, dan haka sai ta kara marairace murya, a wannan karon cikin shagwaɓar gaske ta ce......... "Na yi alkawarin ba zan sake ba, dan Allah kayi hakuri, kaga ma na goge hawayena". Ta kai karshen maganar tana kai hannunta saman fuskarta. Haba tuni sadaukinmu ya kara shiga yanayi, kamar ba shi ba, sai ya ji kamar an canza shi ne lokaci guda, ya kasa iya yin magana. Allah sarki ta zaci fushi yake yi, sai ta kai hannunta ta riko nasa hannun, kamar zata saka kuka ta shiga bashi hakuri. Dik sai kara rikita shi take yi, da kyar ya iya samu ya juya hannunta ya koma cikin nasa, a hankali ya furta ta yi shiru dan Allah ta dai'na magana, dan tana kure tinaninsa. A dai'dai lokacin Pretty ta dawo hannunta ɗauke da sak irin kwaryar da aka basu magani a lokacin da suke jarirai, ganinta yasa ya yi saurin sake Zunaira ya ɗan ja baya kaɗan. Karɓar maganin ya yi Pretty ta zauna kusa da shi, a gefensu ya ajiye ba tare da ya bawa Auta ba, Pretty bata nemi jin meyasa bai bawa Autan ba, sai ta kwanto jikinsa ta fara aikin zuba mashi shagwaɓa da ta saba. Haka suka kasance cikin farinciki suna hira yana satar kallon Auta na tsawon lokaci, har sun shagala sun mance da zai tafi sannan ya kawo masu batun lokacin tafiyarsa ya yi. Kuka suka saka mashi su biyun dikka, Allah sarki wlh basa san zama su biyu a cikin wannan kungurmin dajin, amma to ya zasu yi? Dole su hakura dan sadauki dai bai san ƙasarsu Gimbiya Zunaira ba, ita ma bata san ta ina take bama bare tasan in da garinsu yake, ba hanyar komawa. Hakuri ya rinƙa basu yana rarrashinsu har sai da ya samu suka ɗan nitsu, sannan ya rakasu har sabon bakwancin da ya yi masu ya kuma ƙawata masu shi, bai mayar da Pretty ainahi in da suka taso a tare da mom ɗinsu ba, ya canza mata waje, har yau har gobe kuma yana wahalar neman Sweetie, ba dare ba rana, dayawan lokuta idan ya shigo forest ɗin kafin ya je in da su ke sai ya yi ta kewaye a cikin dajin yana neman Sweetie, kun san na gaya maku kungurmin daji ne mai girman gaske, yana da ɓangarori da dama, idan kana wannan ɓangere ba zaka taɓa zatan akwai mutane a wani ɓangare ba saboda nisan dake tsakani. So kullum a cikin daji yake yawon neman Sweetie, bai taɓa kawowa ransa bata a wannan dajin ba. Har ciki ya rakasu, ya kuma gargaɗi Pretty a kan kada su yarda su fito waje, dan yasan halinta sarai da shegen san zama wajen ruwa, kullum sai ya gargaɗeta a kan fitowa waje, amma kuma kullun idan ya kawo masu ziyara a waje yake samunta, shegen san zama wajen koramu dake aman ruwa ne da ita. Kamar wata ƴar ruwa!. Da kansa ya rufe masu kofar ramin nasu dan ma kada su fito, sai dai kash yana tafiya Pretty ta ce da Auta ta zo su je wajen korama su zauna hai, ita bata san zaman cikin nan, ta fi san waje. Auta kuwa ta bita suka fita, wajen wata korama mai aman ruwa suka je suka zauna suna kallan ruwa......... Pretty sai shirin Allah. •••••••••••••••••••DUBAI••••••••••••••••••🔥 Kwance Sharifat take a saman bed ɗinta, ta ci kuka har ta godewa Allah, yau tsawon kwanaki tara kenan ba tare da Leesharh ba, tana cikin damuwa da alhinin hakan sosai sun rigada sun saba. Gobe zata koma school, dama rashin Leesharh ya ja mata zazzaɓi har na tsawon kwanakin nan bata je school ba, idan kuka ganta sai kun tausaya mata, da alama ba'a taɓa breaking heart ɗinta ba sai a wannan karon baiwar Allah. Miƙewa ta yi zaune, tinanin guyson ne ya faɗo mata a ranta, ta tina kullum sai ya tambayeta ina Leesharh, Allah sarki yakamata ta sanar da shi kalar cin amanar da Leesharh ta yi masu. Can tinanin maganganun su Omaid a kan Leesharh ya faɗo mata ranta, kenan ya tabbata su Omaid suna da gaskiya, dama tin da suka ɗaura idanunsu a kanta suka ce she looks like a criminal, Guyson ya yi ta yi masu faɗa, ashe kuwa zancensu haka ne. Tun da aka kama Leesharh bata yi waya da kowa ba, wayarta ma a cikin jakarta da suka je taron nan da shi ta barshi, dan haka sai ta sauko kasa daga saman gadon. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi bags rack ɗinsu. Tana sanye da Pakistan a jikinta, ta ɗaura gyalen kayan a matsayin ɗan'kwali. Wani irin jiri ne taji yana ƙoƙarin kayar da ita, da kyar ta iya kame kanta ta tsaya da kafafunta. A hankali ta zuge zip ɗin jakar ta buɗe. A miliyan ɗari ta kai hannunta ta murza idanunta tana kara zarosu waje, sam bata san lokacin da bakinta ta furta what!! Ba, da karfi ta yi maganar. Nan take jikinta ya fara kerma, a hanzarce ta zira hannunta a cikin jakar ta fito da wayoyinsu. Wayarta ce da na Leesharh. Da karfi ta furta. "Kenan da gaske kamar yadda Yah Bilal ya ce mun Leesharh ta ce wancan wayar ba nata bane kenan hakan ce? Kenan tana da gaskiya ba wayarta bace wancan?". "Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, Allah sarki su Yah Ramish sun azabtar da baiwar Allah a banza!". Cikin ɗaga murya ta yi maganar. Jikinta har tsuma ya fara yi, burinta ta ganta a gaban Ramish ta sanar da shi wancan waya da gaske ba na Leesharh bane, tabbas Leesharh ba muguwa bace, dama ta kafe a kan wayar ba tata bace, ashe tana da gaskiya. Nan take ta ji karfi ya zo mata, dik wani kasala ya gudu. Da gudu ta juya ta nufi hanyar fita daga ɗakin. A dab kofar fita suka yi karo da Ummie zata shigo ta dubata. Ai tsabar farincikin da zumuɗin ta isa ga Ramish bata tsaya bin ta kan Ummie ba ta yi waje a miliyan. Bata zame ko'ina ba sai part ɗinsu Bilal, Ummie na kiranta amma ina bata saurara ba, wasu irin zafafan hawayen farinciki ne ya rinƙa tsere a saman face ɗinta, ji take kamar ta ɗaura hannu bisa kai ta yi ta zunduma ihu mai sautin gaske ko zata ɗan samu sassauci. Dr Raj kawai ta iso a cikin parlournsu, yana zaune ya tasa laptop a gaba yana bincike a kan wata cuta da ake yawan korafi a kanta a hospital ɗinsu, kamar sabuwar cuta ce da ta keta tsaron likitoci, so a matsayinsa na babban likita ya dukufu a kan neman maganinta babu dare babu rana. Ko sallama babu ta afko masu cikin parlon, a yadda ta shigo da wani ne zai razana sosai, amma da yake jinin Modarawa ne shi ɗin ko kaɗan bai razana ba, sai da ma ya ɗauki 1 min kafin ya ɗago da kallonsa a kanta, izzar sarauta ta motsa. Kallo mai wuyar fassaruwa ya wurga mata, ta wani shigo kamar wadda aka koro, ko sallama babu. Nan take ta sha jinin jikinta, dama idan ba Yah Rizwan ba babu mai sakar mata fuska a cikinsu, shiyasa sam bata wani yinsu sosai. Bai ce mata ko uppan ba ta fara ƴan kame kame tana ɗan juye juye, still dai bai ce ko sannu ba, ya mayar da kansa a kan laptop ɗinsa ya cigaba da aikin dake gabansa. Tsabar tsarguwa da tsorata bai tambayeta ba ta fara magana a rikice tana haɗe word....... "Yah Raj dama Yah Ramish nike nema, dama zan bashi wayar Leesharh ce wlh ba ita ta..............". A miliyan ta haɗiye sauran maganganun a cikinta bata kai karshe ba saboda sauka da idanunta ya yi a kan Ramish dake tsaye bakin kofar shigowa cikin parlourn daga bedroom side ɗinsu. Ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, Bluetooth mai kyau da tsada ce manne a kunnensa, da alama waya yake yi, amma saboda tsabar nitsuwa irin nasa daga sharifat har Dr Raj babu wanda ya iya jin abin da yake faɗe, ƙasa ƙasa cike da class da nitsuwa yake wayar. Yana sanye da sexy sleeping dress a jikinsa, tamkar wani mai aure, ga idonsa kamar dai, to na dai yi shiru, amma da alamar tambaya fa a tattare da shi, sai tashin kamshi yake yi, da alama bai jima da farkawa daga barci ba, yanayin kayan barcin nasa idan ka gansa sai gabanka ya faɗi, shiyasa nace kamar wani mai aure, da alama wlh Yah Ramish ɗan duniya ne sosai, gabaɗaya gaban rigar a buɗe take, faffaɗar kirjinsa a waje, dik macen da ta gansa haka sai kirjinta ya buga, kai ko namiji ya gansa a haka sai kirjinsa ya buga bare mace, ka gansa cikin full kaya ya rufe ko'ina nasa ma sai ka ji ka faɗa da shi bare kuma ya buɗewa mutane gaban kirjinsa dan iya hege. Sharifat da ta zama kamar wadda aka sassaƙa a waje ya wurgawa hegun sexy eyes ɗin nan nasa yana cigaba da magana da wanda suke waya. Yadda kuka san idanunsa allura suka yi mata, wani irin zabura ta yi da ya kalleta, da karfi ta furta. "WAYYO ALLAH". Ta yi maganar tare da juya mashi baya. Allah sarki a take ta birkice kamar wadda aka zarewa kaso hamsin cikin ɗari na hankalinta. Dr Raj da ya ji ta furta wayyo Allah ta, sai ya ɗago da kallonsa a kanta, dai'dai lokacin ta juyawa Ramish baya hannayenta sai kerma suke yi. Ganin yadda ta juya baya da sauri yasa ya juya ya kai kallansa a kan kofar da zata sadaka da bedrooms side ɗinsu, dama tin da yaga ta yi irin wannan juyi ya yi tinanin Ramish ta gani, dan shi kaɗai take yi wa irin wannan abin. Ganinsa a tsaye yasa ya mayar da kallonsa a kan laptop ɗinsa, dan a cewarsa sun fi kusa, baya shiga shirginsu. Tana san gudu ta bar part ɗin, tana kuma san yi mashi magana dan ta ceto ƴar uwarta Leesharh, sai dai ba zata iya juyowa ta sake kallansa a irin wannan shiga ba, yana ɗaga mata hankali kuma yana rikitata, ga shi wandon sleeping dress ɗin ma sai wanda ya gani, ku baku ji sunan kayan bane ma, sexy sleeping dress, ai daga nan zaku gane ba kayan arziki bane, na masu aure ne, shi kuma shirgegen gwauro da shi ya zo ya wani saka su. (Sai su Yah Rizwan sun yi mashi fyaɗe da tsakar dare kila zai dai'na saka kayan ma'aurata 😅😅😅😅😅 na faɗa a saka mun gas😅ni bana tsoron Ramish da💪🌝 ) Dr Raj ya cigaba da aikin gabansa, shi ma Ramish juyawa ya yi ya koma cikin room ɗinsa, saboda dama ya leƙo parlourn ne dan ya duba Bilal yana nan ko baya nan. Jin alamar ya bar wajen yasa ta wani sauke nannauyar ajiyar zuciya wanda har sai da Dr Raj ya jiyota, amma ko a gefen takalmarsa ya cigaba da abin da yake yi. A hanzarce ta juyo, kirjinta na dukan uku uku ta bi bayan Ramish da kallo, har ya kurewa ganinta, komai nasa abin burgewa ne. Wani irin ta ji a ranta, wani ɓangare na zuciyarta yana ce mata ta bi bayansa, wani kuma yana ce mata ta koma cikin ɗakinta. Juyawa ta yi da nufin ta koma ɗakinta, sai kuma ta tuna Leesharh tana cikin azaba, nan take ta ji zuciyarta ya karfafa, tausayin ƴar uwarta ya ratsata, da sauri ta bi bayansa tana karanta dik addu'ar da ya zo bakinta. Tana sako kafarta cikin room ɗin nasa shi kuma yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa zai shiga wanka, ya bawa kofar shigowa baya. Sai da ta ji gabanta ya faɗi time da taga faffaɗar bayansa kamar madara. A bakin kofa ta tsaya kamar wadda take jira ace pet ta yanka a guje ta fita, like tana tsoron cikin ɗakin dai. Sarai ya ji motsinta, sai dai bai juyo ba, ya cigaba da abin da yake yi, tsabar tabbatar bashi da kunya wandon jikinsa yake ƙoƙari zamewa, dan shi babu ruwansa da tana tsaye, meyaka kawota ɗakinsa? Ko ɗakinta ne?. Kamar ta dalla ihu take ji, shi ko kamar wanda bai san da halittarta a wajen ba. Ai bata san time da ta juya a miliyan zata fita ba ganin ya zame wandan jikinsa, tana juyowa kuma suka ci karo da Bilal da yake ƙoƙarin shigowa yanzu. Da karfi sosai ta juya, hakan yasa ta bugesa da karfi, wani irin baya baya ta yi zata faɗi. Cikin sauri ya damko wuyar rigarta dan taimaka mata kada ta faɗi. Ai bata san time ɗin da ta kurma ihu ba, wayoyin dake hannunta dikka biyu suka faɗi ƙasa, ba komai ya saka ta ihu ba face yadda Bilal ya riko wuyar rigarta kusan hannunsa dikka a saman tudun tula tulanta, shiyasata ihu ba shiri. Janyota Bilal ya yi ta tsaya da kafafunta, sannan ya saketa tare da ɗaure fuska sosai, a takaice ya ce. "Meyakawoki nan?". Kasa tsayuwa a kan kafafunta ta yi, cikin sauri ta durkushe kasa tare da fara ruwan zafafan hawaye, hannu tasa ta fara laluɓar wayoyin da suka faɗi ƙasa, tsikar jikinta dik sai wani mimmikewa tsaye yake yi. A karo na biyu Bilal ya sake tambayart me ya kawota nan.............. Sai a lokacin ta ɗago da kanta a kansa, cikin sarkewar murya haɗe da tashin hankali a tattare da ita ta ce. "Yah Bilal dama nazo ne in faɗa maku wancan waya wlh bana Leesharh bace, ashe irin namu ne da kasaya mana, wlh tana da gaskiya ba nata bane, kaga namu wayoyin". Ta yi maganar tana ɗagowa, tana kai karshen maganar kuma ta miƙa mashi wayoyinsu dake hannun, sai kerma hannun nata yake yi yaki tsayawa waje guda. Sai a wannan lokaci Ramish ya juyo, ya ɗaura towel a waist ɗinsa, kallo ɗaya ya yi masu ya wuce ya nufi toilet............ Karɓar wayoyin Bilal ya yi haɗe da furta alhamdulillah da ɗan sauti, da alama shi ma ya ji matuƙar daɗi, bai yi magana ba sai ya nuna mata hanyar fita kawai, a kan ta je. Cike da tsoro ta ce. "Yah Bilal to Leesharh ɗin fa? Zaku dawo mun da ita?". Kai kawai ya jinjina mata tare da kara nuna mata hanya. Da gudu ta raɓa gefensa ta fice tana toshe bakinta saboda wani iri kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro da ya kubce mata. Ajiyar zuciya Bilal ya sauke tare da ɗaura kallonsa a kan wayoyi, tabbas wannan ne wayoyin da ya saya masu, wancan kenan irin nasu ne kawai? To waye mamallakin wancan wayar? Ya jefa kansa tambayar. My people's da ni da ku idan baku manta ba mun san ya aka yi wayoyin nan suka fita iri ɗaya, in baku manta ba a baya na gaya maku masu nikaf sun canza mata ainahin wayar da suka bata da farko, har na ce maku sun bata wani irin wanda Bilal ya saya mata ita da Sharifat sak ko? To wannan shi ya kawo ruɗani a cikin al'amurran, wayoyin iri ɗaya ne, Sharifat guda ɗaya tasan Leesharh da shi shi ne wanda Bilal ya basu, bata san da na masu nikaf ba! Wannan shi ne, kunga Sharifat zata wanke Leesharh ba tare da tasan da gaske wancan wayar ma na Leesharh ɗin bace. Wai akwai case a gaba gaskiya!!. Dama kuma tun farko Leesharh ta ce da su Bilal ba wayarta bane, kunga kuwa yanzu da Sharifat ta kawo wannan tsab zasu iya yarda ba nata ɗin bane, akwai cakwakiya fa sosai, shin masu nikaf zasu ɗauki mataki ko dai shirun banza suka yi? Muje zuwa!. Karisawa cikin ɗakin Bilal ya yi, saman bed ya haye tare da jawo laptop na Ramish ya fara latse latsensa. •••••••••••••••••FOREST•••••••••••••••🔥 Tsaye take gaban wannan korama dake aman ruwan, yanayin yadda ruwan yake zuba abin gwanin ban sha'awa, ka korayen ganyayyaki kewaye da wajen, sannan ga ruwa gudu a kasan koramar yana ta gudu mai haske tar, tsabar haskensa har ya ɗauki kalar sararin samaniya wato sky blue. Ta ko'ina kamshin furanni ne yake tashi saboda yawaitansu a wajen, daga gefe can tsuntsaye nau'ika daban daban ne suke dira a kasa bakin ruwan dake gudun suna shan ruwa sai su sake tashi, yanayi mai daɗi ga iska na ɗan kaɗawa a hankali hankali yana kaɗa furannin dake wajen kamshinsu yana kara tashi. Wajen zai yi matukar dacewa da masoyan dake bala'in kaunar junansu. Ta yi shiru kamar mai kallan ruwan dake kwaranya daga koramar, amma kuma ba shi take kallah ba, hakika hankalinta ya luluƙa duniyar tinanin kingdom of power da kuma Hoorain, wannan abin da ya yi mata ya zame mata babban tabo a rayuwarta da ba zai taɓa gogewa ba. Pretty bata a tare da ita, ta tafi ɗauko masu fruits, so ita kaɗai take tsaye a wajen. Ta yi nisa cikin tinaninsa da take yi ba zato ba tsammani ta ji an rufe mata idanu daga ta bayanta. Hakika ta tsorata matuƙa, dan yanzu abu kaɗan yake razanata yake kuma ɗaga mata hankali. Ihu ta zunduma tare da fara ƙoƙarin kwatar kanta zata zulle. Saura kaɗan ta afaka cikin wannan ruwan gudu a ƙoƙarinta na zullewa. Da sauri ya riketa da kyau, kamar mai raɗa ya ce mata shi ne fa ta nitsuwa kada ta jewa kanta ciwo. Dik da ta ji muryarsa bata yarda ba, dan yanzu bata jin zata yarda da wani a rayuwarta, babu wani sauran yarda a zuciyarta, ƙoƙari ta cigaba da yi dan kwatar kanta. Da yaga haka sai ya zame hannunsa daga idanun nata, dan taga zahiri, sai dai bai saki hannunta da rike dan kada ta faɗi ba, sai ya sanya ɗayan hannunsa a saman Waist ɗinta. Cak ta tsaya da ƙoƙarin zillewa da take yi, nan take ta ji mummunar faɗuwar gaba, da sauri ta yi ƙoƙarin jiyowa dan ta tabbatarwa da kanta shi ne ko ba shi bane. Ganin yadda ta juyo da sauri yasa ya yi saurin saketa tare da ce mata. "Kiyi hakuri"........... Jinjina mashi kai kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba, sai ta buƙaci matsawa daga kusa da shi. Bai bari ta yi hakan na shi sai ya ɗan matsa baya yana kara ce mata ta yi hakuri. Da okey ta amsa mashi tana mayar da kallonta a wajen koramar. Wai shin me ya dawo da shi bayan ya ce ya tafi?. E to tinanin Zunaira ya hana shi tafiya, dan haka sai ya samu waje kasan wani bishiya ya zauna yana ƙoƙarin yankewa kanshi shawarar ya dawo ya sake ganinta ne ko kuma ya hakura ya tafi sai gobe?. Yana tsaka da wannan tinani ya hango gungun mayaka sun dinfarko cikin dajin wanda ko ba'a faɗa mashi ba yasan su Pretty suke nema, tun da ya sha artabo da su a kan hakan. Wannan dalilin yasa ya hau saman bishiyar da yake karkashin ya ɓuya, sai da suka wuce sannan ya sauko ya bi bayansu dan yaga ina suka nufa. Ganin sun bi wani hanya ba ta in da su Pretty suke bane yasa ya ce to bari ya leƙo su Pretty su ɗan sake ɓata lokaci a tare kafin nan ya wuce, kun ji dalilin dawowarsa. Har zai wuce wajen nasu sai ya hango Zunaira tsaye a bakin koramar nan shi ne ya ƙariso gareta, dama tinaninta ne a ransa. "Ina Omnish?". Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa. Kamar ba zata amsa mashi ba, amma ita ɗin ƴar halak ce, akwai tina alkhari, dan haka sai ta daure ta ce. "Ta je kawo fruits". "Amma ba nace kada ku fita waje ba?". Kasa ta yi da kanta tana tinanin amsar da ya kamata ta bashi, a dai'dai lokacin Pretty ta dawo hannunta ɗauke da fruits a kwando. Shiru suka yi daga shi har Auta, cike da mamaki Pretty ta ce. "Kai ne ka dawo?". Yadda ta yi maganar sai ku zaci bata yi wani laifi ba. Binta da kallo ya yi yana mamakin halin Omnish ɗin nan nasa, yarinya ce sai ka rasa a wani mataki zaka ajiyeta. "Omnish wai ba nace kada ku fito waje ba? Ke kika ja Zunaira kuka fito ko?"............ Baki ta turo ba tare da ta bashi amsa ba, saboda ita dai magana ta Allah bata san zaman cikin nan. Jin ta yi shiru yasa ya sake cewa. "To ku wuce mu tafi". Ya faɗa ba tare da wasa ba.............. Ran Pretty bai so ba ta wuce gaba tana tura baki, Auta ta rufa mata baya. Haka suka wuce izuwa ma kwancinsu. Ko da suka shiga sai da ya jima tsaye a wajen yana satar kallon Auta kamar bakinsa da magana, kamar yana san amayar da ita kuma, sai dai kamar yana tsoro, wato dik zafin kan mutum da izzarsa abu guda ɗaya tana ɗarsa mashi tsoro a cikin zuciyarsa, wannan abin kuma ba komai bane face soyayya, wlh in dai namiji soyayyar gaskiya ce a ransa yana ɗarsa mashi tsoro da ɗarɗar a kan ua faɗa ko kada ya faɗa, yana jin matuƙar tsoron ya furta bai yi nasara ba, tinanin abin da zata je ta dawo da abin da rashin nasararsa zai haifar masa yasa yake dasa mashi tsoro a zuciyarsa. Haka ya rufesu, ya ɗan jima tsaye a wajen kafin daga bisani ya tafi. A wannan karon ma yana tafiya suka buɗe suka fito, wlh ita dai Pretty Allah ya gani ba iya zama a wannan waje take yi ba, burinta ta fito waje, gara ma lokacin da Auta take jinya a cikin wajen, a wannan lokaci kullun tana ciki, saboda tana kula da Auta. Sadauki ne ya tsinto Auta a cikin ruwa ya kawota wajen Pretty, shi kuma ya yi jinyarta tsawon lokaci, shiyasa kuka ga ta shiga ransa sosai, dan dik wasu magunguna shi yake saka mata a ciwon, Pretty kullum tana manne da ita, ko nan da can bata san matsawa, suna tare, kusan a tare ita da sadauki suka yi kinyarta. A ranar da Auta ta buɗe idanu da Pretty ta fara yin arba, shiyasa take balain jinta a ranta sosai. Ga dikkan alamu Auta ma bata san zaman cikin ramin nan, saboda da Pretty ta ce tazo su je waje zata ce to, ta bita su tafi, ga shi ita bata gama samun lafiya ba, har yanzu akwai sauran magani a jikinta da ba'a ɓare shi ba. Kuma ita Auta bata san cewa akwai waɗan da suke farautar rayuwar su Pretty tsawon lokaci ba, bata taɓa kawo hakan a ranta ba, a dik tinaninta fita ne kawai sadauki baya san su yi yasa kullun yake yi masu gargaɗi a kan fita, basu san cewa abin ya wuci haka ba. Fitowa suka yi, suka jero kusan tsawonsu ɗaya, Pretty ce ta ce. "Zo mu canza waje tun da nan wajen yasan muna wajen, zo mu je ta can baya akwai wani wajen korama ba zai san muna wajen ba, sai mu zauna mu yi hiranmu a wajen sai can yamma mu koma. Da to kawa Auta ta bita suka cigaba da tafiya. Sun yi tafiy mai nisa sosai har Auta ta fara dafe cikinta wajen ciwon nata, kunsan bata gama samun sauki ba, so sai ya fara yi mata ciwo. Tun tana ji a hankali hankali tana daurewa har ya fara fin karfinta, karkashin wani bishiya ta samu ta zauna tare da dafe wajen tana ƙoƙarin fara kuka. A tsorace Pretty ta dawo kusa da ta zube gwiwowinta, kamar zata yi kuka ta fara tambayarta lafiya? Meyake damunta. Auta bata kai ga buɗe baki ba suka sinkayo sukuwan dawakai masu karfin gaske. Kafin su yi wani ƙwaƙƙwaran motsi dawakan sun bayyana a wajen. Waɗan nan warriors ɗin na ɗazun da sadauki ya biyo bayansu su suka kewayesu. A tsorace Pretty ta fara binsu da kallo tana mamakin ganinsu. Hannun Auta ta riko tare da janta tana faɗin ta tashi su gudu su koma ma kwancinsu. Auta da ciwo ya ci karfinta ne ta kasa motsawa ne yasa ta saki wani wahalallen ihu, janta Pretty ta cigaba da yi tana faɗin ta tashi su gudu. Sai dai ina Auta ba zata iya tashi su gudu ba, haka suna ji suna gani waɗan nan warriors ɗin suka ɗaukesu suka saɓasu saman dawakansu. Sai kuka Auta take yi saboda ciwonta, ita ma Pretty sai kuka take yi saboda an rabasu kowacce warriors daban ne ya ɗauketa. Haka suka juya kan dawakansu suka kutsa da su cikin daji. To nima dai na juya na kama hanyar gida dan maltina ta ta yi sanyi dai'dai sha. Good bye my people's. Wani fata zaku yi wa Auta! Pretty! Leesharh da kuma Sadauki a halin yanzu?. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Sai kuka Auta take yi saboda ciwonta, ita ma Pretty sai kuka take yi saboda an rabasu, kowacce warrior daban ne ya ɗauketa. Haka suka juya kan dawakansu suka kutsa da su cikin daji. Sosai dawakan suke gudu, dan a tunaninsu Auta da Pretty ƴan uwana ne, dama in baku manta ba Sweetie and Pretty suke nema, so sai suka ɗauki Auta a matsayin Sweetie kenan. Suyi nisan zago a tafiyar tasu, dan sun yi tafiya a kallah na good 20 mins a cikin wannan dajin, kuma basu kusa fita ba, sai a lokacin Pretty ta gane ashe fa dajin nan duniya ce guda mai zaman kanta, da a tinaninta iya wajensu ne kawai. Waɗan nan mayaƙa sun kware wajen iya sarrafa dawakai sosai. Dai'dai tsakiyar wasu manya manyan dogayen bishiyoyi masu tsayin da kaurin gaske, basu da cikar ganye sosai, sun yi sama sai suka yi runfa hakan ya haifar da inuwa mai daɗin gaske a wajen, wajen yana da faɗi sosai, waɗan nan dogayen bishiyoyi ne suka yi wa wajen zobe, kasan wajen kuma wani irin tashi ne mai laushin gaske, idan ka matsa gaba kaɗan akwai wani irin yashi mai bala'in laushi wanda ya fi na wannan wajen da suke, shi har lumewa bawa zai yi a cikinsa idan ya shiga, irin wannan yashin da ake iyo a cikinsa ne, idan ka iya ka fitar da kanka in ka faɗa, idan kuma baka iya ba ka lume ƙasa ka mutu. Kunsan dawakai basa iya gudu a cikin yashi mai yawa ko? Hakan yasa dawakansu gabaɗaya suka dakata a wajen suka ki yin gaba suka kuma kin yin baya, kunsan idanun doki daban yake dana sauran dabbobi, shi da kare sun banbanta da sauran dabbobi, su suna iya kallon masifa, misali suna iya kallan shaiɗanu da abin cutarwa, so sun hango yashin dake gabansu mai lumar da mutane ne yasa suka ki yin gaba, dan sun hango mutuwa. Waɗan nan warriors sun yi sun yi waɗan nan dawakai su yi gaba, amma ina sun ki tafiya, sun tsaya a wajen. Dan dole ya tilastawa kowannesu ya sauko kasa daga kan dawakan. Cike da jarumta suke taka kasa, haka suka fara kewaye arear wajen suna duba me dawakansu suka gani da yasa suka ki tafiya gaba suka tsaya a in da suke?. Sauke Auta da Pretty ma suka yi, da gudu Pretty ta zo ta rungume Autar dake ta faman kuka kamar ranta zai fita, har jini wajen ciwonta ya fara yi. Wani dakakken warrior ne ya tinkaresu da nufin ya rabasu, wasu warriors biyu suka rufa mashi ba. Suna zuwa suka kamasu suka ɓallesu, ma'ana suka rabasu, sai ihu yaran nan suke yi, amma ko kaɗan basu tausaya masu ba. Wani tsawa mai sauti wannan warrior ɗin ya daka masu a kan su yi mashi shiru. Ƙoƙarin kwatar kansu daga hannunsu suka fara yi, hakan ya bawa warrior ɗin haushi har ya ɗaga hannu zai dallawa Aura mari, da yake shi ya riketa su kuma warriors guda biyun nan suka rike Pretty, kunsan Pretty ta fi Auta lafiya, so sai fisge fisge take yi yasa su biyu suka riketa. Auta kuma a nitse take sai dai kuka da take ta fama, kuma kukan ma wlh na ciwonta da ya fama take yi. Tsabar rashin imani irin na wannan warrior ɗin da gashi kan Auta ya riketa, ta rasa da wanne ɗaya zata ji, da zafin da gashin kanta yake yi mata na rikonsa ne ko kuma da ciwon dake cikinta?. Da karfi ya ɗaga hannu zai mari bakinta dan su yi mashi shiru, sauran warriors ɗin suna ta kewaye a wajen suna diba menene ya hanasu cigaba da tafiya. Lokacin guda wajen ya ɗauki wani irin shiru na unexpext haka, irin shirun na ban mamaki wanda kamar an datse komai da sauti zai iya fita. Nan take wani irin iska ya fara kaɗawa da karfi karfi. Wani irin haniniyar ƙosasshen jibgegen doki ne ya karaɗe ko'ina a yankin wajen, ya doɗe masu dodan kunnuwa, haka zalika ya razana dawakansu da suke hawa. Wannan warrior da zai mari Auta ne ya fara janyo numfashinsa da karfi sannan ya kurma wani irin ihu mai amsakuwar da sai da gabaɗaya arear wajen ta amsa. A miliyan sauran mayakan suka yi kansa suna tambayar meya faru yake ihu haka?. Kowannensu bai iya kai kashen tambayarsa ba idanunsu suka sauka a kan hannunsa da baya tare da jikinsa. A miliyan suka kai kallonsu kan jikinsa, tabbas babu hannunsa an datse mashi shi. To waye ya datse mashi? Yaushe kuma aka yi hakan? Ba yanzu ya ɗaga hannun zai mari Auta ba? Meyasa hannnun ya fita daga jikinsa?. Wannan shi ne tambayoyin da suke jefawa kawunansu. Kururuwan wannan doki ne ya sake dakar dodannin kunnuwansu, hakan yasa suka ɗaga kai sama suna neman ta ina ne? Ita kuwa Auta da taga abin da ya faru kuma taga lokacin da aka datse mashi hannu sai abin ya yi mugun rikitar da ita da har yasa ta haɗiye kukanta diff, ita ma Pretty shiru ta yi diff. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Can suka hango wani namijin gaske a saman wannan doki dake ta zuba uban haniniyar. A miliyan suka mimmike tsaye suna kallonsa. Yana zaune zaman cikar jarunta a saman dokin, ya rike linzaminta da kyau da hannunsa ɗaya, da alama dokin nasa ma ɗan yi ne, dan kuwa ga shi sai ɗaga kafafun gaba sama yake yi yana wani haniniyar ƙasaita. Wannan namijin gasken rike yake da zabgegiyar takobinsa mai bala'in kaifi wanda jini ya gama wanketa har ɗiga yake yi a ƙasa. Da gani ba tambaya zaka san jinin wannan warrior da zai mari Auta aka datse mashi hannu ne, ga jinin jajir da shi. Mamaki waɗan nan mayaka suka shiga yi a kan yaushe wannan namijin gasken ya zo ya datsewa wannan mayakin nasu hannunsa har ya wuce basu gansa ba?. Kunga a iya nan kawai ya gwada masu fifikon kwarewa a fannin yaki da jarumta, dan kuwa shi ba tsayawa ya yi ya datse hannun nashi ba, yana kan dokin tsabar yana da saiti mai karfi, a miliyan ya tsaga tsakiyarsu ya wuce tare da wucewa da hannnun mayakin da takobinsa, kafin su ankara kamar kiftawa da bismilla ne ya wuce. Faɗuwa ƙasa wannan mayaki ya yi azaba tana ratsa kashi da ɓargonsa. Su kuma sauran mayakan zaro takubansu suka fara yi daga kwankwasonsu. A guje suka dimfari in da yake a saman dokin nasa. Bai bari sun kariso garesa ba ya sauko ƙasa daga saman dokin nasa, kan dokin ya ɗan shafa kafin cikin harshen larabci ya ce da dokin ya je bari ya ɗan buga wasa da waɗan nan ƙananan kwarin. Da gudu dokin ya matsa gaba, wato dokin nan ya horu iya horuwa, gudun bala'i ne da shi na wuce misali, ga karfin gaske, sannan yana jin maganar ogan nasa idan ya yi mashi, da alama sun yi sabo sosai. Mayar da takobinsa mazauninta ya yi, a cewarsa waɗan nan ƙananan kwarin warriors ɗin ba sai ya taga hankalin takobinsa wajen faɗa da su ba, hannunsa ya wadatar, cikin ƴan mintuna zai murkushesu a wuce wajen. Su kuwa da karfin gaske suka dimfaresa, sai wani ihu suke yi suna wani irin haki kamar waɗan da suka je babban filin daga mai cike da mayaƙa dubu zasu yaka. Dikkansu da takobi shi babu komai a hannunsa suka fara gwabza faɗa babu kama hannun yaro. Pretty ta taso da gudu ta zo ta rungumi Auta tana yi mata sannu da jiki. Ganin ciwon na jini yasa Pretty ta kara tsorata, nan take ta kara sautin kukanta, ni da ku dik mun san halinta da balai'n tsoro, bare kuma taga jini, ai tsoro ninkuwa ya yi. Ƙoƙarin tallafawa Auta ta yi da ta tashi su gudu su bar wannan waje. Ina ai Auta ko motsawa daga in da take durkushen saman gwiwowinta nan ba iyawa zata yi ba, dik Pretty ta rikice, ta rasa me zata yi mata sai kawai ta rungumeta suka cigaba da kuka. Su kuwa waƴan can suna ta gwabza yaki har suka isa ga wannan yashi mai lumar da mutum ɗin nan. Namijin gaske ya kashe mayaka biyu, su kuma ko kwarzane basu samu damar yi mashi a fatarsa ba, da alama yasan irin wannan yashi sosai, hakan yasa suna kaiwa wajen ya tura mayaka biyu ciki. Nan take suka fara ƙoƙarin yin iyo dan su fitar da kansu, sai dai ina, ba zasu iya yi ba, suna ji suna gani ga azaban zafi cikin yashin haka suka lume can kasa sai gawarwaki. Haka suka cigaba da gwabza yaki suna gwada mazantaka................... A hankali Auta ta fara ganin dishi dishi sakamakon jinin da ta zubar, jiri ne mai karfin gaske ya fara ɗibarta, kanta yana sara mata da karfi kamar zai fashe. Pretty tana rike da ita sai ta ji ta sakar mata nauyinta gabaɗaya. Kasancewar Pretty ba iya riketa gabaɗaya zata yi ba sai suka tafi gabaɗaya zasu zube a ƙasa............... Kamar daga sama suka ji an taresu, gabaɗayansu ya haɗesu ya capko suka faɗa jikinsa. A tsorace Pretty ta juyo garesa dan taga wenenen? Cikin ranta tana tinanin Sadauki ne, dan ta san shi kaɗai ne mai taimaka masu a dik time da suka shiga matsala. Sai dai kash a wannan karon tana juyowa sai taga bashi bane, dik da shi ma wannan yana cikin shigar mayaka kuma fuskarsa a rufe, tabbas ba Sadauki bane, dan ko da bata san fuskar sadauki ba ta san kirar jikinsa, kuma ba zata kasa iya ganesa ko cikin millions masu rufe da fuska ba!. Zame jikinta daga nasa Pretty ta yi, ta barshi da Auta kawai, cikin nitsuwa ya ɗauki Auta cancak. Ya gama kashe waɗan can warriors ɗin gabaɗaya, kisan walaƙanci wanda ko kare ba zai ci ba ma ya yi masu, Fito ya yi da ɗan karfi, Pretty na ta binsa da kallo tana san sanin wanenen shi?......... A guje dokinsa ya danno zuwa in da suke, wannan fito da ya yi kiran dokin ya yi. Da gudu Pretty ta juya zata bar wajen, dan a tinaninta wajenta dokin zai zo. Cikin zafa yasa hannunsa ɗaya ya riko hannunta bai bari ta gudu ba. Ihu ta saka mashi tana ƙoƙarin kwatar hannunta dan ta gudu. Sai dai ina, bata iya yin hakan ba, yana tsaye har dokin ya ƙariso gabansa, saketa ya yi tare da gyara Auta a jikinsa sosai, sannan ya haye saman dokin da ita. Pretty tana kallonsa tana san guduwa, bata hankara ba sai ganinta ta yi a saman bayan dokin, da hannu ɗaya ya ɗagata sai saman dokin, sannan ya umarci dokin da su tafi............ Shin wanenen shi ɗin?.ina kuma zai kai su?. ============================🔥 •••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••🔥 Kwace rikon da Jawad ya yi mashi ya yi, da sauri ya nufi hanyar fita waje dan ya je ya cire kayan jikinsa dan ta taɓa, in baku manta ba mugun kyankyani Jaish yake da shi, kun tuna farkon zuwansa garinsu yadda ya rinƙa kwarara amai saboda bappa ya taɓa shi? To yanzu ma hakance. Binsa da kallo suka yi har ya fice daga ɗakin, momma bata yi magana ba, dan ta lura ransa a ɓace yake sosai, kada ta shiga hakkinsa. Da sauri Jawad ya rufa mashi baya dan ya je ya ji menene dalilinsa na shiga ɓacin rai haka? Ya kuma rarrashesa, kunsan su ɗin amanan juna ne. Mahnoor ta rungume Mahreen, sai a lokacin ita ma ta samu damar sakin kukan da tun shigowarta arear kingdom of power take san yi amma ta danne. Ƙarisowa wajensu momma ta yi da nufin ta rarrashesu, hakan ya yi dai'dai da shigowar Aunty MieMie da kuma Fanan a tare da ita. Cike da mamaki Aunty MieMie ta fara binsu da kallo, taga yan kauye jiki dik datti, zaro idanu ta yi lokacin da ta ga momma ta ɗago Mahreen ta rungume tana rarrashinta, kasa hakura ta yi har sai da ta ce. "Momma waɗan nan fa daga ina?". Fanan ma mamaki ne ya kamata, sai dai bawai kyamarsu take ji ba, kawai dai mamakin ganinsu take yi. "Fanan ɗaukesu ku je ɗakin Zunaira da su, ki taimaka masu su yi wanka ina zuwa da kaina na basu kaya da kuma abinci". Cewar momma da ta dawo da kallonta a kan Fanan. Fanan yarinya mai biyayya, bata yi wani magana ba ta ce su zo su tafi, sai dai taki matsawa kusa da su dan tana ganin datti a jikinsu. Mannewa da juna suka yi, dikkansu sai kuka suke yi, sun ki motsawa bare a sa ran zasu bi Fanan. "Mahnoor ku yi hakuri ku je tare da Fanan kun ji?". Cewar Momma. Kin motsawa suka yi, Mahnoor ce ma ta yi ta mazan cewa. "Mu kam a mayar da mu wajen bappanmu, ba masan nan". Tana magana tana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Take momma ta ji tausayinsu ya kamata, Allah sarki dole su yi kuka basu taɓa zuwa irin wannan waje ba. Matsawa kusa da su Aunty MieMie ta yi, dan kun santa da fahimta, ta fahimci koma su wanene su ba shakka momma ta ɗaukesu da mahimmanci, sannan kuma da kallo ɗaya ta yi masu ta ji yaran sun burgeta, sai ma taga kamar kannenta, saboda suma fafaren fata ne. Rarrashinsu ta taya momma yi, sannan ta ce Fanan ta zo ta kama hannunsu su je. Sam Fanan bata san taɓasu, dan kada su saka mata datti a jiki, ita ma yanzu ta ji kyamarsu yakamata saɓanin ganin farko da ta yi masu, har da ɗan kawar da kanta wai suna wari, amma da yake Aunty MieMie ce ta ce ta zo ta kamasu su tafi sai bata musa ba, ta matso ta rike hannun Mahnoor kamar wadda ta rike kashi, haka ta wuce gaba suna rungume da juna suka rufa mata baya. Da kallo momma da Aunty MieMie suka bisu da shi har suka fice. Suna fita Fanan ta yi saurin sake hannun Mahnoor tana wani kwaɓe fuska game da toshe hanci, a fili ta furta. "Tab dik gidan nan ba ɗakin wanda ya kai ko kwatan ɗakin Auta a kyau da tsaruwa haɗe da kayan alatu na more rayuwa masu bala'in tsada da babu su a kasar nan, sannan ace waɗan nan ƴan datti kazaman za a kai can, gaskiya an cuci Auta". Sarai Mahnoor ta ji abin da ta faɗa, saboda ita tana jin larabci, ita kuma Mahreen ta ji wasu bata iya jin wasu ba, to kun dai san Mahreen bata gani ta kyale, ta ji ance masu ƴan datti sai ta ce. "Wlh mu ba yan datti bane, mun yi wanka, sai dai idan kece ƴar datti, da wani shegen idonki kamar na Hamma a wajen, wlh kin yi sa'a saboda Hamma zan ɗaga maki kafa, da sai kin ci dukan zaginmu ƴan datti da kika yi!". Cikin harshen fillanci ta yi maganar, hakan yasa Fanan bata gane me ta ce ba. Tab da Fanan ta gane me kuke tinanin zai faru? Hajiya Mahreen manyan ƙasa, bata gani ta kyale, ni yanzu tsorona ɗaya Mahreen ta iya larabci ta kuma haɗu da Sarina! Kam bala'i wato akwai bidiri ba kaɗan ba, dan dai dik da a gidansu take wlh Mahreeh ba zata ɗauki cin fuska da walaƙanci ba. Mahnoor dai bata ce komai ba, sai ƙoƙarin goge hawayenta da suka zubo take yi, dikkansu suna tafiya ne kankame da jikinsu, saboda suna ganin kamar zasu faɗi ƙasa, dan in baku manta ba a hawa na sama suke, ta elvator suka biyo, su suna ganin kamar zasu faɗi kasa yasa suka kame jikinsu waje guda. Suna shiga parlon Auta Mahreen ta ƙanƙame Mahnoor tana ƙoƙarin sake yin kuka, dan ita bata taɓa ganin irin waɗan nan abubuwa ba, ga tsoron mutuwa ga rashin kunya kwando kwando cike da kai tab. Ƙanƙameta Mahnoor ma ta yi suna jan kafaru, da kyar suka yarda suka karisa shiga bedroom. Ai suna shiga ihu Mahreen ta saki, sai ma da idanunta suka sauka a kan manya manyan teddys dake shirye saman bed da wasu a saman sofas dake cikin room ɗin. Ihu Mahreen ta rinƙa yi wai ɗakin aljanu aka kawota zasu kasheta. Ita ma Mahnoor tana san yin ihun amma tana jin kunya, sai ta danne tana ƙoƙarin rarrashin Mahreen. Fanan da sun gana kulata har wuya, ranta ya bakanta sosai ne ta dakawa Mahreen tsawa a kan ta yi mata shiru ko kuma ta dalla mata mari yanzun nan. Ai banza Mahreen ta bawa ajiyarta ta cigaba da ihunta tana faɗin a mayar da ita wajen bappanta. Fanan tana shirin kai wa bakinta bugu momma da Aunty MieMie suka faɗo cikin ɗakin, hakan yasa Fanan ta janye kudurinta haɗe da ɗaure fuska ranta bai so shigowar su momma ba, taso ne ta dallawa Mahreen mari ko guda ɗaya ne, dan ta ji bata sansu ko kaɗa. Wai nace ba, a haka fa Fanan bata san Mahnoor matar abin kaunarta Jaish bace, bata san kishiyarta bace, da ta sani me kuke tinanin zai faru? Muje zuwa, akwai show fa. Da gudu Mahreen ta saki Mahnoor ta yi wajen momma tana ihun a mayar da ita wajen bappanta, ita bata san wannan gidan na aljanu ne. Aunty MieMie da tin fitarsu momma ta sanar da ita su wayesu ne ta hau rarrashin Mahreen haɗe da faɗa mata ba gidan aljanu bane. Ai ina Mahreen ta ce bata san wannan magana ba, ita dai Jimeta kawai za'a mayar da ita. "Momma ki je ki yi wanka ki ci abinci ki huta bari zan rarrashesu". Cewar Aunty MieMie da Mahreen ta ƙanƙame mata hannu. Da yake momma a gajiye take sai ta amsa da to, sannan ta juya ta fita ta barsu da Aunty MieMie ta cigaba da rarrashinsu. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 A ɓangaren Jaish kuwa. Yana shiga bedroom ɗinsa cikin toilet ya wuce, hakan yasa ko da Jawad ya shigo bai samesa a ciki ba. A gefen bed ɗinsa Jawad ya zauna dan ya jirasa, saboda ya fahimci toilet ya shiga, yana zama wayarsa ta fara ruri alamar shigowar kira. Cirosa ya yi daga aljihun wandan kayan barcin jikinsa. Jannawad shi ne sunan dake yawo a saman screen ɗin wayar, wato Jawad and Jannat su ya haɗe cikin soyayya suka bashi sunan Jannawad. Miƙewa tsaye ya yi, ya so yin magana da Jaish, amma kuma dole ya tafi wajen Jannat, dan dama da kyar ya iya fitowa izuwa wajen Jaish, baya san yin nisa da ita saboda halin da take ciki. Bedroom ɗinsa ya nufa kai tsaye, a hanya ya ci karo da Sarina sanye da wasu shegun kaya na barci wanda kusan da su da babu dik ɗaya ne. Riga ce doguwa wanda ta kai mata har ƙasa, ta kuma matseta sosai, sannan shara shara ce, daga gwiwonta izuwa kasa ta gaban ribar a buɗe take, akwai wata tsaga a wajen, dik wasu albarkatu na jikinta a waje, babban abin takaicin ma shi ne yadda rigar ya matseta ya fito da murarar surar jikinta. Tana wani taunar chewing gum hannunta rike da hotuna guda biyu, daga ɓangaransu maman Yah Ramish ta fito, sai wani sakin murmushi take yi, kasancewar bata da fara'a hakan yasa ake zargin murmushinta a dik lokacin da ta yi shi, sai ta shirya mugunta take murmushi. Wani irin ɗan iskan kallo da ya wurga mata ne yasa sai da ta yi tuntuɓe kafarta ya turguɗe ta faɗi ƙasa, babu komai a wajen da zai iya sanyata yin tuntuɓe, amma sai gata ta yi har ta kai ƙasa. Dik iskancinta da rashin kunyarta yau da kyar ta jawo yawu ta haɗiye a wahalce tana ɗan datse idanu. Dik kuma saboda wannan kallo daya dalla mata. Shi kuwa ya rasa yadda zai yi da shegiyar yarinyar nan, idan ya ce zai daketa wlh tsab zai iya kasheta ko ya sumar da ita, kunnenta ya fi na ƙashi tauri, yarinya ana ga annabi tana rintse idanu, in suka biyeta wlh ba zata yi saura a wannan gida ba. Tsabar tabbatar rashin kunya wai sai ta yi kasa da kai tana ɗaga mashi gaisuwa na rashin kunya, irin ita bata ga kamar ta yi wani laifi ba. Yadda kuka san ya dallawa jajir ɗin kumatun nan nata mari, takaici kamar ya take hegiya a kasar, a fusace ya bar wajen gudan kada zuciya ta ɗebesa ya yi mata one blow seven die. Tana ganin ya wuce ta bishi da matsiyacin harara tare da miƙewa tsaye, ta tsaya a kan kafafunta, hannunta dikka biyu tasa ta rike waist ɗinta da shi, kasa ƙasa ta furta. "Ko uban me yasa ma ka warke daga ciwon son Jannat baka mutu ba bakin azzalumi? In dai Mammie tana shakar numfashi ta fetsar dik abin da kake so ba zaka taɓa samu ba, Jannat dai ta haramta a gareka, shi ma kuma Yah Rizwan ɗin da ya aureta ba zata taɓa zame mashi alkhairi ba, sai ya gwammaci mutuwarsa a kan aurenta, dan sai ta ɗanɗana mashi madarar azaba fiye da tunanin mutum, dan yanzu dab take da shiga sarrafawar Mammie na, dik sai kun gane baku da wayo, dik a tafin hannunmu kuke kanann marasa kunya!". Cike da confidence take maganar, ta yi maganar ne bisa rashin sanin cewa Jannat Jawad ta aura ba Rizwan ba, kun san ita da Mammiensu basu da labarin abin da yake faruwa, Mammie na can part ɗinsu a kwance, ta yi karyar ciwo dan bata san ta zo cikin family ayi hidimar biki da ita, shi ne wai bata da lafiya, suna can suna shirya muguntarsu ita da ƴarta.............. Amma my people's me kuke tinanin Sarina take nufi da cewarta saura kaɗan Chuchu ta shiga karkashin sarrafawar Mammiensu? Anya ba wani abin a kasa kuwa?. Hannunta ɗaya ta ɗaga izuwa dai'dai saitin face ɗinta, sannan ta naɗe yatsunta dikka ta bar iya na tsakiyar a tsaya, cike da iskanci da iyashege ta ce. "Fuck you, nonsense guy, zaka zo hannu ne yaro, soon kowa zai ɗanɗani kuɗarsa a cikin gidan nan, sai ma na auri Yah Omerish, a nan ne zaku gane baku da wayo, dan wlh har dad ma ba zan ɗaga mashi kafa ba, na godewa Allah da yasa Yah Omerish bashi da sauki dik ubanku zai ci, ni kuma in juya shi yadda rai'na yake so banzaye kawai, ni yanzu na wuce ajinku". Ta kai karshen maganar tare da fashewa da dariya kamar wata zararriya. Sai kuma ta yi saurin toshe bakinta saboda tana kusa da part ɗin Akka ce, kada sautin dariyarta ya fita ya ja mata wata masifar, a hanzarce ta wuce izuwa part ɗin uncle Abbas, ko tsoron Allah babu bare kunya haka ta tsaga tsakanin waɗan nan part guda biyu, ta keta cikin warriors dake gadi ta nufi part ɗinsu da wannan ɗan iskar shigar nata, dik wani mayaki ya ganta sai ya haɗiyi yawu, sai dai takasance guba a garesu, dan sun san ko mutuwa suke yi ba samunta zasu yi ba, kallanta ma a sace suke yi, dan kamasu suna kallanta ma ba ƙaramin laifi bane, kuma sai sun karɓi tsastsauran hukunci. Shi kuwa Jawad ransa a tsannin ɓace ya karisa part ɗinsa, sam baya san halin Mammie, dik ita take goyawa Sarina baya har ta lalace haka, ya rasa yadda zai yi da su, a yanzu yana takaicin a ce kannensa ne su ɗin. Kwance ya isko Chuchu saman bed, tana kudundune a cikin bargo, jikinta ya samu sauki fa aka sallamosu daga asibiti suka dawo gida, amma yanzu jikinta da ɗumin zazzaɓi, ta kasa iya jurar rashin Auta, idan ta tinata sai kanta ya sara mata. A gefen bed kusa da ita ya zauna, cikin sanyin murya ya tambayeta meyafaru ya ganta a cikin bargo bayan ya barta lafiya lou zata shiga wanka? Ya yi maganar yana kai hannun zai yaye bargon. Kuka ta saka mashi haɗe da yunkurawa ta miƙe zaune. Jikinsa ta faɗo tana faɗin................. "Yah Jawad yanzu da gaske sun ɗauke mun Autata? Ni dan Allah kace su dawo da Auta su ɗaukeni ka ji?". Cikin salon rarrashi ya ce...... "Ki yi hakuri, dad ya tura rungunar mayaka guda sun tafi ɗaukota, nan da kwana biyu war haka Auta tana tare da mu In Sha Allah, yanzu dai sauko ƙasa in baki abinci ki ci kin ji?". Kankame rigar sleeping dress na jikinsa ta yi, kanta ta fara dirzawa a saman kirjinsa, kamar zata haɗiye ranta ta fara faɗin. "Yah Jawad ba zan iya cin komai ba". "Why?". Ya jefa mata tambayar yana riko hannayenta cikin nasa............. "Ban sani ba Auta ta ci abinci ko bata ci ba! A wani hali take ciki dikka ban sani ba, Yah Jawad wlh ina ji a jikina Auta tana buƙatar taimakona, tabbas tana cikin damuwa, domin idan bata cikin damuwa kirjina ba zai rinƙa bugawa da karfi a dik lokacin da zuciyata ta ambaci sunanta ba, wayyo daddyna na shiga uku nikam, nasan idan basu dawo mana da ita ba mutuwa zan yi". Kuka take yi sosai, ya fahimci ta fara fita a hayyacinta, dan haka sai ya zage wajen ganin ya rarraheta sosai, jikinta ya kara ɗaukar zafi sosai, Allah sarki bata san shima cikin wannan tashin hankalin yake ba, damuwarsa ma shi ne Jaish ya samu labarin ɓatar tata, ya twins bro ɗin nasa zai ji a ransa? Wanna yafi ɗaga mashi hankali fiye da komai. Ƙasa ƙasa ya yi da murya sosai, cikin salo mai jan hankali ya ce. "Jannat kina san zuciyata ta buga in mutu ne?". Kai ta girgiza mashi alamar aa bata so....... "To meyasa ba zaki barni in ji da zafi biyu ba? Meyasa ke ba zaki saukaka mun ta ɓangarenki ba? Kina dai gani har yau number Yah Rizwan bata shiga, sannan kuma su Yah Ramish sun ki haɗani da shi a waya, kowa sai ya ce mun baya kusa ko ya yi barci, a jikina ina jin akwai abin da suke ɓoye mun dange da shi da basa san in sani, saboda rashin lafiyarki na daure ban ɗaga jirgi na je na same shi ba, sannan ga ɓatar Auta da ya fi komai ɗaga mana hankali, ki daure ki yi hakuri Auta zata dawo kin ji?". Kai kawai ta gyaɗa mashi amma ba wai dan zata iya daurewa ɗin ba. Da ya fahimci in dai tana nan a cikin kingdom ɗin nan bafa zata iya daure rashin Auta ba, dan haka sai ya yi wa P.A ɗinsa sms a kan ya yi mashi booking flight zuwa Dubai gobe da sassafe, gara ya ɗauketa su je duba Yah Rizwan meyafaru tin da ya bar kingdom ɗin wayarsa bata shiga? Daga nan su ɗan huta a can har a gane Auta ko kuma raɗaɗin ya ragun masu sannan su dawo bayan kura ta lafa. Yana turawa P.A ɗin nasa sakon ya ajiye wayar a gefen bed, sannan ya cigaba da rarrashinta, shi dai bai more aurensa ba, matsaloli sai faruwa suke yi tin kafin auren har kuma yanzu, amma dik da haka bai wani damu ba, saboda shi ma yana cikin damuwar da ba zai iya gudanar da wani soyayya ba a yanzu. Da kyar ya samu ta hakura ya buƙaci da ta zo ya bata abinci a baki, bata yi wani musu ba ta yarda, dan balai'n yunwa take ji, rashin nitsuwa da kwanciyar hankali yasa ta kasa cin abinci. Amma da ya zauna yana bata ta ci sosai, hakan kuma yasa da ta gama ci da ƴan mintuna ta samu barci mai nauyi da daɗi ya ɗauketa wanda tin da aka fara batun aurenta rabonta da ta yi irinsa. Ganin ta yi barci yasa ya ja bargo ya rufeta tare da matsar mata da pillow kusa da ita dan ta ji kamar shi ne a wajen, ya sauko kasa ya shiga toilet. After some minutes ya fito ya shiga dressing room, cikin ƙanƙanin lokaci ya fito shirye cikin brawn and milk arabs jallabiya, dadduma ya shinfiɗa ya tada sallah dan neman saukin abin dake damunsa daga wajen Allah. Sai karfe uku dare ta tsala, sannan ya sallame sallar tare da tsawaita addu'oi, bayan ya kammala ya miƙe ya hau shirya masu kayansu da zasu yi tafiya Dubai gobe. 4:00 dai'dai ya kammala, sannan ya ɗan kwanta kafin asuba ya ɗan rintsa. A ɓangaren su Mahnoor kuwa, kwata kwata sun ki cin abincin da momma ta saka aka kawo masu, saboda basu taɓa ganin irin abincin ba, ga uban yawa, shake da tabkeken tray, nau'ika daban daban abincin sai wanda ka zaɓa. Amma dik sun ki ci, sun takure waje guda sunki sakin jiki, wanka ma Aunty MieMie ta yi wa Mahreen da kyar da suɗin goshi, Mahnoor kuma ta nuna mata yadda zata yi ta yi. Sun ki rabuwa da juna, sunki hawa gado, sun zauna a ƙasa, ba yadda momma bata yi da su ba sun ki yarda, sun tsorata sosai ne. Mahnoor kayan Chuchu momma ta bata ta saka, ita kuma Mahreen kayan Auta, amma kayan Autar sun ɗan yi mata yawa. Da momma taga sun ki cin abinci sai ta ce Aunty MieMie tasa kuyanga Zubaida ta dama masu fura da nono, shi kam ai zasu sha, kun san gidan sarauta ba'a rabasu da tsabtataccen fresh nono da fura ai, dan haka sai Aunty MieMie tasa aka haɗo masu mai rai da lafiya. Nan ne fa suka ɗan sha, Mahreen ta sha mai yawa, Mahnoor kuma saboda kunyarsa momma da take ji kamar ta nitse kasa yasa ta ɗan sha kaɗan ba dan ya isheta ba ta bari. Da kyar suka yarda suka hau gadan Auta suka kwanta, momma tana zaune kusa da su har sai da suka yi barci sannan ta fita, ba komai ya hanata fita ba kuma face kada su yi ta ihu in ta fita, saboda sun ki yarda su hau gadan sai da ta hau a tare da su, sannan ne suka kwanta, da Allah ya yi barci ɓarawo ya sacesu sai ta fita. Bedroom ɗin mama Haulat ta shiga dan ta duba babyh Khadija da yanzu yaro ya sha wanka, kyansa ta kara bayyana matuƙa, kamar ka sace shi ka gudu. Nan ta isko shi da mama Haulat kwance saman gado suna barci, sosai momma ta ji kamar ta ɗaukesa su koma bedroom ɗinta, amma kuma wajen King zata je, Aunty MieMie dake biye da ita ce ta tambayi ɗan waye shi ɗin? Bata faɗa masu ba ta sanya hannu ta ɗaukesa. Tana ɗaukarsa mama Haulat ta farka daga barcin da take yi a razane, Allah sarki mace mai amana, a tinaninta sace shi aka zo yi yasa ta yi irin wanna farkawa. Ganin momma ce yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da risinar da kai ta fara kwasan gaisuwa. A takaice momma ta amsa mata kafin ta sanar da ita zata je wajen King da babyn amma zata dawo da shi. Cikin girmamawa ta amsa da to a dawo lafiya. Juyawa suka yi ita da Aunty MieMie suka fita, daga nan Fanan ta wuce part ɗin Akka cike da al'ajabin ɗan waye momma ta kawo? A ina ta same shi?. Suna fitowa parlon Aunty MieMie ta miƙa hannu a kan a bata babyn, tana san yara sosai. Miƙa mata babyn momma ta yi. Karɓa ta yi tare da buɗe fuskarsa cikin haske dan ta gansa da kyau. Subhanallah, saura kaɗan ta saki yaron nan ya faɗi ƙasa, sai ta yi saurin rikesa da kyau tana zaro ido. Cike da mamaki Momma ta ce. "Lafiyarki Raeesa?". "Momma ina fa lafiya, naga yaron ne tamkar hoton uncle Jahiz yana jariri, hotonsa da take manne a jikin bangon bedroom ɗin Akka". Cike da mamaki sosai ta yi maganar. "Jahiz kuma?". Momma ta jefa mata tambayar ba tare da nuna damuwa ba. "E momma! Uncle Jahiz wlh, Allah sun yi kama ni dai na gani". "Wannan yaron fa da Koreans yake kama, tayaya zaki haɗa shi da Jahiz?! Ko kuna da ƴan uwa koreans ne ban sani ba? Ko kuma Jahiz ya taɓa aure ne?". Cewar Momma, ta yi maganar tare da wucewa gaba dan ta je wajen love ɗinta wato King. "Wlh momma ni dai dik da yake kama da Koreans ya yi mun kama da uncle Jahiz, bamu da ƴan uwa koreans, amma kuma shi ma uncle Jahiz ya so ya yi kama da Koreans time da yake ƙarami, baki ga hotonsa a ɗakin Akka bane?". Momma da ko a jikinta ta juyo ta karɓi babyn haɗe da cewa. "Yanzu dai jeki wajen mijinki dare ya yi, da safe kyazo ki ga babyn da kyau sai ki tabbatar mana da waye yake kama? Nasan dare yasa kike ganin kamar Jahiz a tattare da shi". Tana magana tana cigaba da tafiya ta rungume baby da kyau da kyau. My people's me kuke tinanin zai faru? Babyn Khadija kuma da uncle Jahiz? Muje dai zuwa, is time for surprised.🤍💘🔥 Aunty MieMie taso ta sake yin magana, dan ita wlh wannan babyn da uncle Jahiz ya yi mata kama, amma ganin momma taba saurin isa ga King yasa ta hakura suka yi sallama ta nufi part ɗinta, amma a ranta ta gudurta zata daka sammakon ganin wannan babyn, dan ba zata bari kanta ya kulle ba. Sallama suka yi, Momma ta wuce izuwa wajen love ɗinta, Aunty MieMie ta wuce wajen nata flowern. My people's akwai cakwakiya fa, ni dai komai ta ɗauki zafi ina da Maltina mai sanyi, dan haka kowa ya samo Maltinars mai sanyi ta yadda idan kansa ta ɗauki zafi ƙwaƙwalwa ta ɗauki caji sai ya ɗan korata ko ya kuka ce?. ===========================🔥 ••••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••🔥 9:30 pm. Tsaye Sweetie take a gaban mirror na room ɗin Ronnie, ta fito daga wanka, wasu irin kyawawan kayan barci mai nitsar da tinani ne a jikinta, shi ya saya mata su ɗazun da ya je fada ya ga yayansa sai ya wuce super market ya yi mata sayayyan abubuwan da zata rinƙa tsantsara kwalliya. My people's fitowar Black Tiger fada ya yi bala'in tada tarzoma, ya jijjiga zuƙatan mata da mazan Black world. Ba matan ba ba mazan ba dik wanda ya gansa sai da ya haɗiyi yawu, jama'a dayawa sun mutu a kansa, sai a yanzu ƴan'matan Black world suka fahimci ashe haukar banza suke yi da suke mutuwa a kan kyan Ronnie, ashe ga uban Ronnie a kyau, sai dai kowacce ta gani a banza, infact tsoronsa ma ya hana dik mutanen birnin kallansa sau biyu. Dik wadda ta kalli face ɗinsa na farko bata sake ɗagawa ta kalli na biyu, dan ba zasu iya ba, tamkar mutuwarsu haka suke jinsa, yana razana zuƙata, tun basu gansa ba ya kasance tashin hankalinsu, yanzu kuwa ganinsa ya fi jinsa ashe. Ga shegen kyau amma ba halin ganin kyan a ji daɗi......😥 Jama'an birnin nan babu wanda bai ziyarci cikin empeir ɗinsa ba a yau, dik dan ganinsa, sai dai fa akwai dayawan mutane da suka suma a kallonsa na farko, dama in baku manta ba babansa ya faɗa mashi babu wanda zai iya kallan face ɗinsa kawai ya sake ɗaga idanu ya kalla, iya face ɗinsa kawai ba kwayar idanunsa ba. Wanda zasu kallesa a kallon farko basu suma bama sai masu karfin zuciya, masu raunin zuciya nan take zasu sume, kuma haka ne, jama'a dayawa sun suma saboda raunin zuciya, masu juriya kaɗan ne. Gaskiya a gabaɗaya faɗin birnin Black world ko rabin mai karfin halin Sweetie ba za'a iya samu ba, domin kuwa ita kaɗai ce ta iya kallan kwayar idanunsa kuma ta zauna lafiya. Ni kam anya baban Black Tiger bai tsafe face ɗin ɗan nan nasa ba kuwa? Kowa baya iya kallansa saboda bala'in tsoronsa da suke ji!. Master Devil dik wannan tauri da bakar zuciyar nan tasa ya ƙasa iya kallan face ɗin Black Tiger sai biyu, tin da ya kallah sau ɗaya ya yi ƙasa da kai bai sake ɗagowa ba, haka ma fa wai dan namijin gaske shi ɗin. Abin haushin kuma dik wanda ya ɗaura idanunsa a kan face ɗinsa to fa da wannan kallo ɗayan face ɗin take zama mashi a ransa babu mantuwa, dik birnin fuskarsa ya kama zuƙatansu, tinanin kyansa ne kawai a cikin ransu. Ga shi da bala'in kwarjini da farinjini, idanunsa kamar na riƙaƙƙen ɗan love, ga su kaifafan gaske, akwai sirrika masu tarin yawa a kwayar idanunsa wanda ba zai iya bari a haɗa ido da shi ba. In short shigarsa fada ya wuci tinanin mai tinani, abin ya yi matukar tashin kan jama'ar birnin Black world, sai da hasken fatar Ronnie ta ɗan dishashe lokacin da ya zo kusa da yayan nasa, hasken wata mai dishashe hasken taurari.. Kuɗi ta ci ubanta a wajen bayyanarsa a fadarsa, anyi tsare tsare da zuba sabbin abubuwa, motocin da aka zubo kawai sun kai kuɗin budget na wata ƙasar, dukiya dai ta zube ƙasa ta yi mubaya'a matuƙa. Kunsan yanzu arzikin Black Tiger ya ci uban na da, yanzu suna da arzikin red gold a karkashin kasarsu, kunga kuwa ai abin sai wanda ya gani. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Floris tana zaune saman bed ɗin Ronnie, Allah sarki, Ronnie ya je ya rarraso kayarsa, sun shirya yanzu. Sweetie tana ƙoƙarin gyara gashin kanta, Floris tana daga zaune a bakin bed tana yi mata bayanin yadda zata gyara da kanta, ita ta ce a koya mata ta yi da kanta ba sai ta rinƙa jira ana yi mata ba. Sai santin kyanta da kyan gashinta Floris take yi, ba shakka kayan barcin sun zauna a jikinta, bakara mun kyau ta yi masu ba, yanayin idanun Sweetie idan ta kalleka sai ka ji tsikar jikinka ya mimmike, shiyasa fa Kamran baya yarda ya kalli cikin idanunsu ita da Pretty. Ta cikin mirror gabanta fararen idanun nata suka walwalo mata jarumin nasu tsaye a bakin kofa, sam basu ji shigowarsa ba, a yanayin tsarin kofarsa irin na yayansa ne, zaka iya saitawa kofar sillent, idan ka shigar mata da sillent ko ka buɗe ba za'a san ka buɗe ba, saboda ba zata yi kara komai ƙanƙantarta ba. Sai da Ronnie ya ji wani irin faɗuwar baba, a take tsikar jikinsa ta mimmiƙe lokacin da ya ga walwalin fararen idanunta ta wurga mashi kallo da su, ga shi ta cikin mirror ne, abin sai da ya ɗan razana zuciyarsa. "Ronnie yaushe ka shigo?". Ta jefa mashi tambayar ta zage tana ta ƙoƙari dole sai ta kama gashinta mai bala'in tsantsin da yaki kamuwar nan ta ɗaure, gashin yaki kamuwa ta samu ta ɗaure shi, har wani nishi take yi wajen ƙoƙarin kama shi, sai dariya Floris take yi mata tana tsokanarta da raguwa bata iya komai ba. Jin ta ambaci Ronnie yasa Floris ta yi saurin kai kallonta a wajen kofar, yana tsaye cikin kayan barcinsa sak irin na jikinsu ita da Floris, sai dai na shi ash colar ne, na Sweetie milk color, na Floris black color, ya harɗe hannnu a kirji yana kallansu. "Beb yaushe ka shigo bamu sani ba?". Floris ta jefa mashi tambaya. Yana ta kallan kayan jikin Sweetie bai amsa masu ba, sosai Floris ta ji wani abin ya soki ranta, kamar ta ji zafin kallon Sweetie da yake yi har ya kasa iya amsa mata maganarta. Abin ya sosa mata zuciya, sai ta miƙe da nufin ta fita ta basu waje, tin da ta kalli yanzu shi idan yana tare da Sweetie baya kallan kowa bare har ya gansa da daraja!!. "Floris ina zaki je?". SweetiE ta faɗa itama kallanta a kan Ronnie, ita tana kallan face ɗinsa shi kuma yana kallan zubin kyakkyawar halittarta mai tafiya da imanin namiji mai lafiya. Rai a ɓace a ɗan kule ta ce. "In da ya dace da ni zan je Sweetie". Gashin kanta ya ki ɗauruwa ne ta sakesa ya watse a gadan bayanta dan ta gaji, sai faman haki take yi ta ce. "To ki dawo da wuri"................... Sweetie duniya, sarai tasan ran Floris ya ɓaci ne, amma da yake ta san ta kan tsiya dik yadda suka zo mata a haka take binsu, wasa wasa ita ma ta iya tsiya sosai, sai ta nuna bata san ma Floris ta yi fushi ba, ta nuna abin bai dameta ba har da cewa ta dawo da wuri. Kin amsa mata Floris ta yi, ranta ne ma ya kara ɓaci, wato ko hakuri ba zasu bata ba, sai ma suka nuna kamar basu san tana ɓacin rai ba, lallai dole ta san matakin da zata ɗauka a kansu, ba zata zuba masu idanu su rinƙa kunsa mata bakinciki ba. Da ta zo wucewa a kofar ɗakin, matsa mata hanya Ronnie ya yi, kallansa a kan Sweetie ya ce. "Dama Angela tana nemanki". Ya ilahi, wani irin bakin bargon bakinciki ne ya kara lulluɓe zuciyar Floris, wato har da Ronnie ma faɗi yake ta je bai wani damu da ranta a ɓace ba ko? Lallai ma sun walaƙantata, dole ta nemi hanyar ɗaukar mataki. Bata bashi amsa ba shima tasa kai ta fice da sauri, tana fita ta rushe da kuka mai taɓa zuciya, da gudu ta biyo ta saman escletor, bata ma jira ya yi kasa da ita ba ta taka stairs ɗin da gudu ta sauko ƙasa. A babban parlour ta wuce master Devil dake zaune saman sofa tana jiran Jack akwai aikin da Black Tiger ya basu, so yana zaune yana jiransa ta zo da gudu tana kuka ta wuce, da kallo ya bita yana mamakin meyasakata kuka kuma? Ya dai san ita ce sanyin idaniyar Ronnie, in ka taɓata to ka taɓo karar kwanarka, amma yau take kuka da hawayenta kuma Ronnie yana cikin gidan nan? Anya lafiya kuwa? Ya jefawa kansa tambaya. Ɗayar bakar zuciyarsa ce ta amsa mashi da kila Ronnie ɗin ne ya bakanta mata rai, kila da shi suka samu saɓani, in kuwa haka ne kana da damar shiga jikinta ko dan fansar da kake san ɗauka a kan Ronnie. Jinjina kai ya yi tamkar yana magana da mutum mai rai, sai ya ji ya yi na'am da wannan shawara da zuciyar tasa ta bashi, a hankali cikin zuciyarsa ya furta................ "Now is my time Ronnie, wait for me am coming". Shi kuwa Ronnie tana fita ya tako izuwa in da Sweetie take, hannu yasa a nitse ya fara tayata tattara gashin nata ta ɗaure, yana jin wani love period a tattare da shi mai matuƙar nishaɗantarwa. "Ronnie meyasa ka kori Floris?". Sweetie ta jefa mashi tambaya. "Very very sharp brain, kai Sweetie ke karshe ce, yanzu waye ya faɗa maki na koreta ne da gangan?". Ya kai karshen maganar tare da tsai da idanunsa a kan ɗan bakinta ta cikin mirror dake gabansu. Kunga yadda suke tsaye a gaban mirror nan suke kallan kansu, haka Black Tiger yake tsaye a gaban nasa mirrorn yake kallan dik abin da yake faruwa a gabaɗaya faɗin birnin Black world. "Ai daga ganin yadda ka yi mata na fahimci da gangan ka yi hakan dan ta fita, akwai wani abin special da zaka faɗa mun baka san ta ji ne?". Cewar Sweetie. Jinjina mata kai ya yi, tamkar wanda yake a cikin maye, rage tsawonsa kaɗan ya yi, a dai'dai kunnenta ya saita ɗan bakinsa.................. "So special sosai ma zan faɗa maki, haƙiƙa ke yar baiwar ce Sweetie, Allah ya yi maki baiwar kaifin ƙwaƙwalwa ga iya magana mai daɗi, ga fahimtar halin da mutum yake a cikin cikin ƙanƙanin lokaci, kin cancanci a yaba maki, ba zan taɓa bari wannan kaifin ƙwaƙwalwa taki ta salwanta a banza ba, tabbas idan kika yi karatu jama'a da dama zasu ci riba a tare da ke, al'umma guda zasu karu da iliminki". Tin da ya fara magana idanunta a kanta tana jin tamkar gizo ko mafarki take yi, hakan yasa ta ɗan zaro mashi ido ta cikin mirror, ba zai iya ganin cikin kwanciyar idanunta ba sai ya lumshe nasa yana cigaba da jawabi. Sai da ya kai aya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin matsuwa da jin me yake nufi ta ce. "Ronnie to me kake nufi da kalamanka?". "Zan faɗa maki wani lokaci, yanzu dai ba shi ne a gaba ba". "Menene a gaba to?". A matse da san jin komai dallah dallah ta jefa mashi tambayar. Kara yin kasa da kansa ya yi, ya manna ɗan bakinsa da kunnenta, ya yi ƙasa da murya matuƙa yadda sai shi da yake furta maganar da kuma ita da ake yi a kunnenta ne kawai zasu iya jin me suke ciki, with his full confidence ya fara magana kamar haka. "Ina yi maki albishir da ina san shiga addininki dan kuwa shi ne na gaskiya na yarda d.........." Katse shi ta yi ta hanyar juyowa da karfi garesa, she was so surprised over, she didn't expect that wonderful word from him, she can't forget this days in her life koma da wasa ya yi mata!. Zata yi ihun ban mamaki ya yi sauri rufe mata baki, ƙasa sosai ya kara yi da murya. "Kada ki kuskura ki yi hakan, ina san ki sani dik abin da muke yi yaya yana kallanmu, kuma yana jinmu, raɗa a kunne ne kawai ba zai ji me na faɗa ba, dan haka ki kiyaye, ki yi shiru ki saurareni". Wani irin tsuma ta ji jikinta yana yi, tamkar ana mincininta, burinta kawai ta daka tsalle ta yi murnar ta yi nasara, amma ya zata yi? Dole ta yi shiru ta danne kada murna ya koma ciki idan Black Tiger ya jiyosu, har wani ciza laɓɓanta ta yi saboda irin tsananin farincikin da yake ratsa mata zuciya, tamkar mai jin sanyi haka take jin jikinta yana yi mata. Sarai ya lura da tsananin farincikin da ta shiga, hakan ba karamun kara mashi kwarin gwiwa ya yi ba, ya yi farinciki matuƙa shi ma, kuma tin da ya yardanwa kansa zai shiga addinin Musulunci ya fara jin kansa a wani irin ni'ima, nishaɗi da farinciki na ban mamaki, yana jinsa tamkar ba shi ba, wani irin sakayau yake jin jikinsa yadda kuka san wanda ya kwashi shekaru yana ɗauke da wani kungurmin dutse mai nauyin gaske sai yau aka sauke mashi shi, ya ji komai tana yi mashi daɗi, shi kaɗai idan ya zauna sai ya tsinci kansa da sakin murmushi, wannan ne ya kara bashi kwarin gwiwa ya yarda da babu abin bauta da gaskiya sai Allah, lallai suratul iklas gaskiya ce, lallai ne Allah shi ne kaɗai abin bauta na gaskiya. My best part again!! Lallai ne Allah shi ne abin bauta na gaskiya, ka bisa ka more, akasin haka ka ɗanɗani madarar azaba!!. Cigaba ya yi da cewa. "Zan karɓi addininki saboda na yarda shi ne na gaskiya, na yarda Allah shi ne abin bauta ba Yesu ba! Sannan na yarda da dik abin da kika faɗa mun hakan ne, sai dai ina neman wata alfarma guda ɗaya a gareki". A hanzarce ta yi yunkurin yi mashi magana, hannunsa na saman bakinta tin da ya rufe mata ɗazun, tana san amsa mashi da wace alfarma ce wannan, sai ya yi saurin kara rufe mata baki da kyau. "Kada ki damu, ba sai kin amsa mun ba, nasan so kike ki ji wace alfarma ce, ko baki amsa ba zan sanar dake, ni dai ki yi shiru ki saurareni kada ki yi wata magana". Jinjina mashi kai ta yi alamar to, sai kara tsuma jikinta yake yi, tana jin tamkar ta rumgume shi da karfi saboda daɗi, tabbas idan Ronnie ya musulunta zasu iya cin karfin wannan yakin, shi kaɗai kusan kaso 40 ne cikin ɗari na wannan fafutukar. "Wannan alfarma ba komai bace face ki taimaka mun mu canza yayana, mu yi ƙoƙari ya shiga addinin Musulunci, tabbas yayana yana da zuciya mai kyau, kema idan kika ji tarihin tasowarsa zaki yarda da hakan, yana da san taimakawa mutane, sai dai yana da wata ɗabi'a ɗaya wadda ita ta haifar mashi da bakar zuciya a cikin kirjinsa!!". Dakatawa ya yi da yin maganar yana kallan yadda ta zaro ido tamkar wadda ta yi mutuwar tsaye, babbar magana, wai ta taimaka mashi su musulunta da Black Tiger? Wannan bakin mugu mai bakar zuciyar da babu imani bare tausayi a cikinta ɗin ne zasu musuluntar? Ita ko da take san kowa ba cikin birnin ya musulunta bata taɓa sanya shi a lissafia ba, dan tasan sai dai ta mutu kamar kare ba dai wannan ya musulunta ba, sai dai jikinta ya ɗanɗani azaba da ukubarsa har ya kai ga hallakata, lallai ne yau Ronnie ya zo mata da sabon zance mai haɗarin gaske wanda babban barazana ce ga rayuwarta. TASHIN HANKALI!!!!. Sai dai kuma ta matsu da ta ji wace iriyar dabi'a ce wannan wadda ta canza zuciyarsa izuwa Black HEART?. Dik da ganin tashin hankali ta damuwa haɗe da ruɗani a saman face ɗinta na jin bukatarsa hakan bai hana shi cigaba da cewa. "Zallar san mulkar duniya ce a ran yayana shiyasa yake da bakar zuciya, zai iya yin komai a kan burinsa, kuma wasiya ce daga gabanmu kafin ya mutu, ya umarcesa da lallai ya mulki duniya, ya cika mashi burinsa ya riga Duniyar shaiɗanu yin hakan, mulki ita ce nan tasa yaya ya zama bakin mugu, zaki iya taimaka mun mu jawo shi cikin addinin musulunci, na tabbata in ya musulunta zai ji irin daɗi da sanyin zuciya da nike ji, tabbas dik wani black heart dake cikin kirjinsa zata washe izuwa fara tas, tabbas musulunci alkhairi ce, nima daga yarda zan shiga dik zafin zuciyata na ji ta sanyaya". Allah mai iko da hikima, tabbas hakane, Allah ya nunawa Ronnie aya ta hanyar sanyaya mashi zuciya daga yarda zai shiga musulunci, Allah yana sansa da rahma shiyasa ya kara sanya mashi ni'ima da kaunar addinin a ransa, tabbas musulunci duniya ce kuma gaskiya ce, hanya fara da babu ɗigon baki a kanta, hanyar riskar tsira da nasara. Girgiza mashi kai ta fara yi a kan ita ba zata iya taimaka mashi wajen jawo Black Tiger addinin Musulunci ba, dan ita gaskiya bata shirya mutuwa ba tare da sake haɗuwa da Pretty and mom ɗinsu ba, tana san ƴar uwarta. Kara yin ƙasa da murya sosai ya yi, sannan ya cigaba da cewa............ "Na san damuwarki da abin da kike jin wa tsoro, rasa ranki kike tsoro ko?". Ya jefa mata tambaya. Kai ta gyaɗa mashi alamar hakan ne, ranta take tsoron rasawa, yar kaniya ta ji wahala shakar da ya yi mata a cikin ruwa, daga nan ta fara tsoronsa da shakkarsa. "To ina san ki daina tsoro, ki sani da wata ce ko wani ko minti ɗaya ba zai karaba a duniya idan ya kalli fuskar yayana, amma ke kin kallesa ido cikin ido, kuma baki tsorata ba, daga nan yakamata ki sani cewa yaya ba zai iya kashe ki ba, sai dai ya azabtar dake, na san zaki sha wahala matuƙa, amma banda batun mutuwa". Wani irin kallo ta wurga mashi wanda za'a iya fassara shi da me kake nufi da kace zan sha wahala amma ban da batun mutuwa?. Ya fahimci abin da take san karin bayani a kai, dan haka sai ya ce......... "Tabbas sai dai yaya ya gana maki azaba, amma ba zai iya kashe ki ba, ke ɗin ƙaddararsa ce, dalilina a nan kuma shi ne Spender yana tare da ke, saboda Spender ne yaya ba zai kashe ki ba, da wannan dama zamu yi amfani wajen taimakawa mu juya black heart izuwa white, amma sai kin jure, zaki azabtu matuƙar, idan kuma kika jure har muka yi nasa tabbas sai mun fi kowa jin daɗi". Ɗan dakatawa ya yi yana kallan face ɗinta, yaga alamar ta ɗan sauko jin maganganunsa na karshen nan, kwarin gwiwa ya samu wajen cigaba da ce mata. "Tabbas yana haukar neman Spender, a da na yi niyar yi maki dabara in shiga jikinki dan ki bamu Spender, amma a yau ni nike tsaye a kan kafafuna ina mai umartarki da dik azabar da zai gana maki kada ki kuskura ki bashi Spender har sai mun yi nasara, zan yi ta razanaki dan ki bashi, kada ki yarda ki bashi". A daidai lokacin da ya ce a da can baya ya yi niyar shiga jikinta ya mannu da ita dan ya kwatawa yayansa Spender daga hannunta ba karamun zaro idanu ta yi ba, dan bata taɓa expecting haka daga garesa ba, ya bata mamaki matuƙa. Sarai ya lura da maganar ya girgizata, amma sai ya basar, ya cigaba da karfafa mata gwiwa a kan zata iya, dik da cewa ba lallai ne su yi nasara ba, amma zasu jarraba, kuma yana da yakinin ko basu yi nasara ba zasu samu cigaba sosai, zasu iya canza wasu abubuwa, kuma shi burinsa kenan. Sosai ta ji kwarin gwiwa jin cewa ba zai kasheta ba, dama ita batun kisan ne a ranta, tin da kuwa babu kisa tabbas zata jure dik wata wahala, tabbas zata iya, dama ita burinta su yarda da ita su musulunta. Katse mata tunaninta ya yi da cewa. "Yaya zai yi wuyar musulunta, amma ki sani idan muka yi sa'a ya musulunta to fa tabbas Birnin nan dikka zasu musulunta". Wani irin sanyi ta ji a ranta, nan take ta fara hasko kanta a cikin al'ummar birnin nan tana koya masu karatun addini, nan take ta fara hasaso kalar ladar da zata samu idan suka musulunta, tuni ta mance da wahalar da za'a sha kafin ayi nasara, tin da dikka birnin zasu musulunta idan ya musulunta ai ita ko zai kasheta kafin ya musulunta in dai zai musulunta ɗin wlh a yanzu kam ta yarda, ko zata mutu ba gudu ba ja da baya. Tuni ta saki ranta, cike da kwarin gwiwa ta girgizawa Ronnie kai alamar ta yarda ta amince zata yi dik abin da ya ce. Sosai ya ji sanyi a ransa, sannan ya yi mata raɗar yadda zasu fara tsara plan ɗin nasu, daga karshe ya buƙaci da ta shigar da shi addininta wato ta bashi kalmar shahada. Yana kai karshen maganar ya zame hannunsa daga ɗan bakinta domin ta bashi shahada. Haka kuwa aka yi, a hanzarce ta juyo ta fara yi mashi raɗa ta kalmar shahada a kunne yana maimaitawa a hankali yadda kowa ba zai ji ba, har lokacin yana rankwafe a kanta, ko gaji bai yi ba bawan Allah. Sai da ta kai har karshe, sannan ta matsa baya da shi like three step, sai ta fara binsa da kallo mai cike da kauna da farinciki, tana yi mashi kallon cikakken musulmi a yau. Ya yi shiru yana kallanta yana jiran ya ji me next, sai kawai yaga ta daka tsalle ta faɗo jikinsa tana dariya kamar wadda ta zare. Rungumeta kam ya yi a jikinsa yana jin wani irin farinciki na musamman, ya ɗagata sama ya manneta da kirjinsa suna ta sakin murmushi wa junansu. A kunne ta raɗa mashi. "Is time, get ready to fight my Ronnie, da izinin Allah zamu yi nasara, zamu cetosu daga halaka zuwa tsira". Juyowa ya ɗan yi shi ma ya fara yi mata nasa raɗan. "Kada ki bari yaya yasan da cewa na musulunta fa, zai kasheni dik san da yake yi mun, ko Floris kada ki bari ya sani". Jinjina mashi kai ta yi kafin ta ce. "To taya za'ayi ka yi sallah?". "Kada ki damu da wannan, a ɗakin yaya zamuna yi, dan yana kallan komai dake cikin birnin nan amma banda ɗakinsa, dan haka tin da ya fara shiga fada a nan zamu rinƙa yi". Wani irin daɗi ta ji ya kara lulluɓeta, da karfi ta kara kankamesa kamar zata mayar da shi jikinta, shi ma wani irin daɗi yake ji na musamman. Black Tiger dake ganin me suke aikatawa ya zaci soyayya Ronnien nasa ya fara yi, hakan yasa ma ya kawar da kallonsa a kansu, ya shiga kallan sauran wurare a cikin birnin. Sake Ronnie ta yi, shi ma sauketa ya yi, cikin farinciki ta ce. "Muje ka rakani ɗakin yayanka yanzu!". A ɗan rikice ya ce. "Me zaki je yi a can?". "Kai dai muje zaka gani"........... Bai musa mata ba, ta wuce gaba ya rufa mata baya. Me kuke tinanin zai kaita room na Black karfe a daren nan?. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ "Kai dai muje zaka gani"........... Bai musa mata ba, ta wuce gaba ya rufa mata baya. Me kuke tinanin zai kaita room na Black Tiger a daren nan?. Sun zo zasu fita daga room ɗin kofar taki buɗewa, yanzu ta san password na kofar, dan haka ta yi ta yi yaki buɗewa, da ta gwada sau uku ma sai kofar ya fara karar jiniyar motar ƴan'sanda, alamar ansaka mashi wrong password kenan. Da sauri ta juyo da kallonta a kansa, yana tsaye ya harɗe hannaye a saman kirjinsa, sai kallanta kawai yake yi. "Ronnie meyasa kofar taki buɗewa? Kuma ka ji tana wata iriyar kasa!". Ƙasa ƙasa ya furta. "Saboda yaya bai yarda mu fito yanzu ba, shi ya hana kofar buɗewa, mu koma kawai". Ranta bai so haka ba, ta juya da nufin su koma kenan sai suka ji alamar ana taɓa kofar, da sauri ta juyo da kallonta a kan kofar. Kamar mai raɗa a ɗan tsorace ta ce. "WANENEN?". Ta tsorata jin ana taɓa kofar ne. Gaba ya wuce ya koma cikin ɗakin, a bakin bed ya zauna, ta tsaya tana kallonsa tana jiran amsa. Murya a kasalance ya ce. "Robbot ɗin da suke aiki a cikin empeir ɗin nan ne, baki ji kofar ya yi karar an saka mashi wrong password bane? Shi ne suka zo dubawa, rabu da su ki zo ki bani tarihin yesu da Imam Madih, zasu tafi idan suka gama bincike suka tabbatar da babu wata matsala". Tin da ya fara magana ta shiga mamaki jin kamalansa, lallai akwai tsaro mai karfi a empeir ɗin nan, tabɗijam. Sai da ta ji ya ce ta zo ta bashi tarihin Imam Madih ne ta ɗan saki ranta, cike da fara'a ta ce. "Ba ranar na baka ba?". Kai ya girgiza kafin ya ce. "Ranar tarihin yesu kika bani, kika ce zaki faɗa mun wanene Imam Madih, amma baki faɗa mun ba, kuma ni ina san Yesu sosai, bana gajiya da jin tarihinsa na gaskiya". Shiru ta ɗan yi, ya zuba mata ido cike da kauna yana jiran ya ji me zata ce, kamar wadda aka sakawa battery ta ninka murmushin dake saman face ɗinta, cikin jin daɗin san samun iliminsa da yake yi ta fara faɗin. "Ba iya Yesu yakamata ka mutu a kansa ba, ka mutu a kan fiyayyen halitta manzon rahma manzon tsira zaka ji matuƙar daɗi fiye da tinaninka a yanzu". "Wanenen shi manzon tsira ɗin?". Ya jefa mata tambaya........... Cikin nitsuwa ta tako ta zo kusa da shi, a saman bedside drawer ɗinsa ta zauna, gyara zamansa ya yi ya zamana suna fuskantar juna, dik a matse yake da san jin yadda zata bayyana mashi manzon tsira, jikinsa har tsuma yake yi, shi yanzu yana bala'in san jin tarihin annabawa da Sahabbai da yadda suka rinƙa sadaukar da rayukansu dan mu a yanzu mu ji daɗi. Cikin nitsuwa ta fara kora bayanai masu cike da ilimi da hujjoji masu karfi........ "Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) shi ne manzon Allah na karshe kuma mafificin halitta. Shi ne aka aiko domin ya shiryar da mutane gabaɗaya zuwa ga addinin gaskiya, wato Musulunci, musulunci shi ne yake bayyana mabiya Allah guda ɗaya tak ba Allah biyu ko uku kamar yadda yahudu da nasara suke faɗi ba, musulunci Allah ɗaya ne tak cikin Tauhidi hakan ta bayyana. An haife Manzon Allah a garin Makka a shekara ta 570 Miladiyya, a wani gida na kabilar Quraysh, kuma ya fito daga zuriyar Annabi Ibrahim (Alaihissalam) ta hanyar Annabi Isma'il (Alaihissalam)". Tun daga farkon bata tarihinsa Ronnie ya ji wani irin kaunarsa tana ratsa shi, sai ya ji kamar ta cigaba da bashi tarihinsa har illah Masha Allah. "A cikin Alqur'ani mai girma, cikin Suratul Ahzab sura ta 30 aya ta 40 Allah ya bayyana Manzon Allah a matsayin annabin karshe wanda babu wani annabi da zai sake zuwa bayansa". "Cikin Suratul Anbiya, sura ta 21 aya ta 107, Allah ya ce ba mu aiko ka ba sai domin ka zama rahama ga talikai. Suratul Najm, sura ta 53, aya ta 3 da na 4, Allah ya ce Manzon Allah bai faɗi Al-Qur'ani daga son zuciyarsa ba. Ba komai ba ne sai wahayi da na yi masa, cikin Suratul Ahzab, sura ta 33 aya ta 21, Allah ya ce lallai a gare ku akwai kyakkyawan misali a wajen Manzon Allah, ga wanda ya ke fatan Allah ya cecesa a ranar lahira, to ya ambaci Allah da Manzonsa da yawa". A cikin sunanun tirmidhi, hadisi mai lamba 3148, manzon Allah ya ce lallai ni ne shugaban ƴaƴan Annabi Adam, kuma ba na yin alfahari ko fariya a kan hakan". "Ni ne rahamar da aka bayar." Cikin Sunan Ad-Darimi. Wasu daga cikin ayyukan Annabi Muhammad (SAW) Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi kuma ya yaƙi bautar gumaka. Ya kafa gwamnatin Musulunci a Madina bisa gaskiya da adalci. Ya yaɗa ilimi da hikima.Ya kyautata zamantakewa da zamantakewar aure da rayuwar jama’a gabaɗaya". "Allah ya umarci musulmi da su koyi dabi'un Manzon Allah (SAW), domin duk abin da ya koyar da al'umma ya kasance bisa umarnin Allah ne. Wannan yana cikin abin da ke tabbatar da cewa ya kasance tsarkakakke kuma cikakken misali ga dukkan al’umma". Ronnie ya gama tsumuwa da san Manzon Allah, dan ma Sweetie bata bashi kaso ɗaya cikin dubu na kyawawan halayen manzon rahma ba. Ganin ya tsareta da ido ne yasa ta dakata da yin maganar. "Ronnie lafiya?". Ta jefa mashi tambayar cike da matsuwa da son jin amsa. Girgiza mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, fuskarsa ɗauke da ƙayatattcen murmushi mai kwantar da hankali. "Ni dai ka faɗa mun menene in ba haka ba in fasa baka tarihin Imam Madih". Ƙasa ƙasa kamar mai raɗa ya ce. "Kaunar manzon Allah ce take ratsa zuciyata sosai shiyasa na kasa yin magana, ji nike kamar zan yi kuka". Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta cigaba da cewa. "Ronnie kasan me?". Kai ya girgiza mata alamar a'a,........... "Zan yi maganin yayanka wlh, tin da dai..........." Yatsansa ɗaya ya ɗaura mata a saman lips ɗinsa alamar ta yi shiru, yana wani lumshe idanu alamar barci yake ji. Hakan yasa ta haɗiye maganar bata amayar ba. Shiru ta yi cikin ranta tana tinanin irin tsiyar da zata rinƙa yi wa Black Tiger, har faɗi take yi ba zata taɓa barinsa ya zauna lafiya ba, ta rinƙa takura mashi kenan, sannan ba zata taɓa bari ya damketa ba bare har ya gana mata azaba, cikin wannan tinani da take yi ne tinanin magic dake hannunta ya faɗo mata a rai, cike da matsuwa ta ji menene wannan ta ce. "Ronnie please ka faɗa mun menene a hannu da yake iya sarrafa wasu abubuwa?". Dan zaro idanu kaɗan ya yi like mamakin menene?. Ta gane me yake zarowa idanu, so yake ya tambayi menene amma tongue ɗinsa ta yi mashi nauyi, dan haka sai ta buɗe tafin hannunta tare da saita kofar ɗakinsa da shi. Nan take wannan hasken ya fita da karfi, kafin Ronnie ya yi wani motsi wannan haske ya daki kofar dakinsa da Black Tiger ya datse da magic ɗinsa, nan take kofar ta wangale kanta da kanta. Sai dai kuma magic ɗin ya juyo ta kansu da karfi. Cikin zafa Ronnie ya hanyeta daga in da take zaune magic ɗin ya wuce ya dagi jikin bango sai ji kake kara mai sauti ta fito, bangon ya tsage. Ba komai ya haifar da magic ɗin ya juyo kansu ba face magic ɗin black Tiger dake jikin kofar, na faɗa maku nasa ya fi nata karfi, dama yana binta a hankali ne kawai, so a jijin kofar magic mai karfi ya saka, karfinsa ya daki nata yasa natan ya juyo kanta, Allah ya taimaketa Ronnie ya janyeta da ina ga sai dai gawarta za'a ɗauka, ku duba yadda magic ɗin ya tsaga bangon nan, da haka zai tsagata biyu. Sosai ta tsorata, shi kam Ronnie ko kaɗan bai tsorata ba, sai dai ya yi matuƙar mamakin ganin magic a tattare da ita, bai taɓa expect ɗin hakan ba. "Ronnie dan Allah ka faɗa mun menene wannan? Daga ina wannan haske yake fitowa a jikina?". A tsorace ta yi maganar, muryarta har ɗan sarkewa yake yi. Jikinsa dik a mace ya amsa mata da. "Magic ne a hannunki, yakamata ki koyi sarrafa shi". Kara zaro idanu ta yi. "A ina na samu magic to ni?". "Ban sani ba, nace ki bani tarihinki kin ki bani, watakila a cikin tarihinki zan iya sanin daga ina kika samu magic". Shiru ta ɗan yi, wani zuciya yana ce mata ta sanar da shi dik abin da ta sani dangane da su, wani zuciya kuma yana ce mata a'a kada ta sanar da shi, a wani ɓangare kuma tana tinanin tin da ya musulunta kuma bata da biyunsa yanzu a cikin empeir ɗin nan me zai hana ta faɗa mashi komai? Amma kuma mom ɗinsu ta gargaɗesu a kan kada su yarda da mutane, anya ya cancaci ta yarda da Ronnie kuwa? Ta jefawa kanta tambayar. Ganin ta shiga tinani yasa ya ce. "Ba sai kin wahalar da kanki ba, ni ban matsu da na ji wacece ke ba, haka ma is normal for me, dan haka kada ki damu". Jikinta ne ya yi sanyi jin kalamansa, lallai ya cancanci Ronnie yasan wacece ita, kullum idan tana damuwa akan ta sanar da shi ko akasin hakan yana yawan faɗa mata kada ta wahalar da kanta ta bari, hakan na nuna shi bai wani damu da san jin wacece ita ba, so bai kullaceta da komai ba kenan!. Dan haka sai ta gyara zamanta, cike da tsoron abin da zata faɗa me zai haifar ta fara magana kamar haka!. "Ni dai sunana na gaskiya Omaish ina da sister mai suna Omnish, mu biyu kawai mahaifiyarmu ta haifa, mahaifiyarmu ta sanar da ni cewa mahaifinmu sarki ne mai ji da karfin iko da karfin mulki, baya ɗaukar wasa, jarumin gaske ne da ya kafa tarihi a masarautarsa, mutum ne mai jijjige dauloli a lokacin mulkinsa, ban san wanene shi ba, kuma ban san a wani ƙasa yake ba, mom bata faɗa mana in da yake ba, ta dai ce mana tabbas da kansa zai kawo kansa garemu ko dan abin da yake hannunmu da ta bamu amsarsa (Spender) saboda shi zai kawo kansa garemu, wannan dalilin yasa ta ce kada mu bawa kowa (Spender), mahaifiyarmu gimbiya ce mai ji da kanta, sannan tana da tausayin talakawa saɓanin wasu daga cikin kingdom ɗinmu, na fi tinanin a wajen babana magic yake ba wajen mom ɗinmu ba, domin kuwa mom ban taɓa ganin tana tsafi ba". Katseta ya yi da cewa. "Kina nufin ke yar sarki ce?". Cike da mamaki ya yi tambayar. "Kamar yadda mom ta faɗa mun, hakan ce, sai dai ta ce kingdom ɗinmu bashi da wata amfani a garemu, and babanmu ma bashi da wani amfani a garemu, dan haka kada ma muje in da yake, a banza zasu kashe mu". Shiru ya ɗan yi yana tinanin, tabbas Sweetie ta ɓoye mashi wani abin, har yanzu zuciyarta yana rawa a kan faɗa mashi gaskiyar wacece ita, ba zata iya zayyane mashi gaskiya gabaɗaya ba, sai dai ta tsakura mashi wani abin kaɗan. Fahimtar bata san buɗe mashi komai da ya shafeta ne yasa ya kawar da zancen da cewa. "Jeki kwanta dare ya yi, bari in je wajen yaya tinda magic ɗinki ya bude mana kofa". Make kafaɗa ta yi. "Ni dai sai dai mu tafi tare". Haka kawai ya ji tongue ɗinsa ya yi mashi nauyin ya musa mata, sai kawai ya amince mata suka nufi side na Black Tiger a tare. Yana rike da hannunta suka nufi master room na Black Tiger. Ko tsoro bata ji ba, dan ta kuduri niyar ba gudu ba ja da baya. Ronnie ne ya sanya password a jikin kofar. Nan take ta wangale. Ciki suka shiga, tin da ta sako kafarta ciki take ta faman rarraba idanu tana neman ta ina zata gansa. Da yake ɗakin yana girma sosai, shi kaɗai ya kai girman gidan wani, tsakanin in da King bed ɗinsa da mirror yake ba ƙaramar tazara bace ba. Kai tsaye bakin bed suka nufa, suna isa Ronnie ya sake hannunta ya haye saman bed ɗin ya kwanta, a hankali ya janyo pillow ya rungume yana jin wani irin nishaɗi da bai iya tantace na menene?. Ita kuwa cigaba da rarraba idanu ta yi tana neman ta ina zata ga Black Tiger a cikin ɗakin. Can har ta cire tsammani da ganinsa kamar daga sama taga mutun a bagan mirror yana gyara gashin kansa. S-p dress ce a jikinsa launin up white, rigar tana da dogon hannu kazalika wandan ma doguwa ce har ƙasa, yana tsaye kan kafafunsa ya basu baya. Ajiyar zuciya ya sauke with her full confidence, with a cool voice ta ce. "Big bro good evening". Zaro idanu Ronnie dake kwance a saman bed ya yi, bai yi expecting hakan ba, shi da ya ce su bi komai a hankali tana neman jawo masu bala'i. Kamar bai san da su a cikin ɗakin ba, cigaba da abin da yake yi ya yi....... Hannunta dikka biyu ta riko waist ɗinta da shi, like she didn't care a kan shareta da ya yi, cike da tsiya da neman tsokana ta ce. "Big bro sam kayan nan basu yi maka kyau ba, ka canza wasu dan bana sansu a jijinka". Ai a miliyan Ronnie ya tashi zaune a tsakiyar bed ɗin tamkar wanda aljanu suka fasa jikunsa suka shigesa a lokaci, a razane ya zaro ido yana kallonta, lallai Sweetie ta cika yar neman bala'i, ko ina ruwanta da kayansa? Ronnie ya jefawa kansa tambayar. Ita kuwa, ɗan tawa one step ta yi gaba kaɗan, sannan ta ɗan ɗaga kanta sama kallonta a kansa, cikin salon jan magana da neman tsokana ta sake cewa. "Ni fa ko baka amsa mun ba ban wani damu ba, nasan kana jina, handsome guy kawai, amma ba wai kana da............." Haɗiye sauran maganar ta yi sakamakon wani haske da ya fito daga cikin idanunsa ya daki mirror dake gabansa sai ya juya ya nufota, tafin hannunta tasa cikin zafa ta tari hasken, hakan yasa ya tsaya bai tarwatsata ba. Yadda kuka san wani walkiya haka Ronnie ya diro ƙasa daga saman bed ɗinsa, da gudu ya iso gabanta, cikin zafa ya fisgo hannunta, da gudu ya jata domin su nufi waje. Sai dai kash, suna isa kofar ɗakin sai suka kasa iya buɗeta, ta datse gam.. babbar magana, dama shi Ronnie yasan tin da Sweetie ta ji Black Tiger ba zai kasheta ba ya shiga uku, ba ita kaɗai zata sha azaba har da shi, wayyo Allahnsa. Me kuke tinanin Black Tiger zai yi masu?. ••••••••••••••••FOREST•••••••••••••••🔥 A hankali ta fara yunƙurin buɗe idanuna da suka yi mata balai'n nauyin gaske. Jikinta dik ji take yi kamar ba nata ba, da kyar ta iya buɗe idanun nata, kyakkyawan ganye kore shar ta fara cin karo da shi a ganinta, hasken rana ne yake haskowa ta tsakanin ganyayyakin, sai hakan ya bada wani kala na musamman. Mamaki ne ya kamata ganin an yi mata rumfa da ganyayyaki. A hankali ta yunkura ta miƙe zaune, jujjuya idanunta ta fara yi tana neman ta ina zata hango mutane. Sai dai bata ga alamar kowa a wajen ba. Hannu ta ɗaura a kan cikinta domin ta taɓa ciwonta ta ji, sai ta ji kaya mai kauri a jikinta. Da sauri ta kai kallonta jikin nata. A wani irin zabure ta miƙe tsaye lokacin da ta ga irin rigar dake jikinta. Zaro idanu waje ta yi, nan take ta haɗiyi wani irin yawu mai sauti, fitowa ta yi daga cikin rumfar, hannunta ne ya fara kerma alamar tsorata, kafafunta ne suka fara raunata suna ƙoƙarin kasa iya ɗaukarta, amma haka ta dake ta fara taka ƙasa tana waige waige, tamkar mai neman wani abin. Jacket mai bala'in kyau launin black color ne a jikin nata, jacket ɗin yana da hula, da ta miƙe tsaye tsawonsa ya kai mata har gwiwanta, to jacket ɗin wanenen kenan?. Harda hular aka sanya mata a kanta. Tafiya take kamar zata kifa kasa, tana yi tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Cak ta tsaya lokacin da idanunta suka sauka a kan wasu irin furanni farare da yellows masu bala'in kyau da ɗaukar hankali, sai a lokacin ta mayar da hankalinta a yanayin wajen, fillin ya yi matukar ƙawatuwa sosai, korayen gayyayakin dake wajen sun kara haska ko'ina, ga furannin sai tashin wani irin kamshi mai kwantar da hankula suke yi, furannin suna da yawa sosai, sun kewaye arear wajen. Ga tsuntsaye masu launika daban daban. Wani irin kara ta ji a gaba kaɗan kamar karar zubar ruwa kamar kuma na sahun mutane. Take ta ji jikinta ya mutu na ganin wajen, ga yanayin weather wajen iska mai ni'ima da ratsa jiki. A hankali ta ja kafafunta ta nufi wajen da take jiyo wannan kara. Like wow, tin daga nesa ta hango wasu irin koramu dake aman ruwa mai hasken gaske, wasu irin flowers manya manyan launin white kewaye da kusa da koramar, ga duwatsu masu kyau da ɗaukar hankali, wajen ya kawatu matuƙa. Ai Auta bata san time da ta wani irin sauke sayayyar ajiyar zuciya ba, tin ainahinta tana san irin wannan waje, kun manta nace maku ita da Chuchu suna yawan kallan films masu irin wannan dajin a nan suka sakawa soyayyarsu sunan shuka flowers ɗin kauna?. Wani irin nishaɗi na musamman ne ta ji yana ratsa zuciyarta, har ta saki cool murmushi ba tare da ta sani ba, ji ta yi tamkar ta je ta shiga cikin wannan koramar ruwa ya yi ta zuba a kanta, ciwonta ne kawai ya hanata zuwa, da ba abin zai hanata shiga. A hankali ta ƙarisa tinkarar wajen koramar. Can ta hango kamar an kunna wuta ta gefen koramar ɗan baya kaɗan yana ci, hayaki ta fara hangowa. Ɗan kara ɗaga kafafunta ta yi ta nufi wajen. Wani irin birki ta ja lokacin da ta matsa kusa da hayaki, ta hango Pretty zaune a kusa da wutar tana kara jefa wasu kananan itace dake hannunta a cikin wutar yana kara kamawa, zaro idanunta waje sosai ta yi tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa. A zahiri zakuga kamar Pretty take kallo, amma sam ba ita take kallah ba, namijin gaske take kallah, yana tsaye a saman wata dutse dake kusa da koramar, ya sanya takobinsa a cikin ruwan dake kwarara yana wankewa, ita kuma Pretty tana jin ɗumi kusa da wuta. A fili da karfi Auta ta furta. "HOORAIN!!!!". A tare shi da Pretty suka dawo da kallonsu a kanta. Kafin dikkansu su yi wani motsi cikin ɗaga murya ta sake cewa. "Pretty ki gudu daga kusa da shi, mugu ne! Kasheki zai yi!". Miƙewa tsaye Pretty ta yi, cike da yarinta a muryarta ta ce. "A'a Zunaira ba mugu bane, shi ne ya taimakemu ya kuma saka maki magani a ciwonki, ya canza........." Tsawar da Auta ta daka mata a kan ta tashi daga kusa da shi a karo na biyu ne yasa ta yi saurin haɗiye sauran maganar, tsawa Auta ta sake daka mata. "Kizo mu gudu Pretty, kasheni ya zo sake yi". Hoorain dake tsaye kamar an dasashe mamakin Auta ya gama kashe shi ne ya juyo da jikinsa gareta gabaɗaya ya fuskanceta. Da yar gudunta Pretty ta baro wajen wutar ta nufo Auta, rike hannun juna suka yi da sauri suka juya da nufin su bar wajen, Pretty tana ta faɗin. "Zunaira kin san shi ne? Zunaira kin san shi ne?". Shiru Auta bata amsa mata ba. Cikin Zafa Hoorain ya diro cikin ruwa daga saman dutsen, a gaggauce ya mayar da takobinsa mazauninsa, yaga da gaske zasu tafi, with his full power ya bi bayansu. Gaban Zunaira ya tare, cikin sanyin murya ya ce. "Ranki ya daɗe lafiya kuwa?". A tsawace ta ce. "Ka bani hanya na wuce, idan kuma ka biyoni nan ɗin ka ƙarisa kasheni tun da Allah ya kuɓutar dani a farko ne kuma sai in ji?". Shiru ya ɗan yi kamar mai tinanin wani abin, sai can kuma ya ce. "Ban gane me kike nufi ba ranki ya daɗe"........... Ranta ne ya kara ɓaci, ko kaɗan babu tsoronsa a ranta, dan su ba jinin tsoro bane, a fusace ta ce. "Ba zaka gane ba ai dama, ka bani hanya!!".. Pretty ce ta katsesu da cewa. "Zunaira wai me yake faruwa ne? Kin san shi ne?". Rai a matuƙar ɓace, zafafan hawaye har sun fara tsere a saman face ɗinta, da kyar voice ɗinta yake fita ta kalli Pretty kafin ta bata amsa da. "Ya wuce sani na yi mashi Pretty, kuma shi ne sanadiyar zuwana wannan dajin, shi ya ji mun wannan ciwo dake cikina! Kasheni ya so yi Allah ya yi ina da rabon cigaba da rayuwa, yanzu nasan ya jefa mun ƴan uwana cikin tashin hankali, ya cutar da zuƙata dayawa, ya zaluncemu, daddyna ya yarda da shi sosai amma ya ci amanar yarda, ba zan taɓa yafe mashi ba, na tsanesa fiye da tinanin mai tinani". Tin da ta fara magana ya shiga ruɗani da tantanmar anya Zunairarsa ce kuwa? Dan dai shi yasan Zunairarsa ba haka take ba, bata da faɗa ko kaɗan. Yana can yana tunani ta figi hannun Pretty suka raɓa gefensa zasu wuce. Cikin zafa ya sake tare gabanta, a dai'dai lokacin ta dafe saitin cikinta, saboda figar hannun Pretty da karfi da ta yi ɗin nan ya ja cikinta ya amsa. Tana dafe cikin bai san lokacin da ya matsa kusa da ita ya tallapota a jikinsa ba, shi dai komai zai faru voice nasa a sanyaye cikin nitsuwa, sam baya da hayaniya komai tashin hankalin da zai shiga. "Kin gani ko ranki ya daɗe? Dan Allah ki nitsu sai ki fahimtar dani a kan me kike magana? Ban gane me kike faɗe ba, ni ban sanki da hayaniya da faɗa ba, dan Allah kada ki sauya mun, ki yi hakuri ki fahimtar dani komai, ki faɗa mun meya kawoki nan kika jefani cikin tashin hankali tsawon wata da kwanaki ina nemanki?". Tin da ya fara magana idanunta suke a saman face ɗinsa dik da a rufe take, wani irin kara ɗaure fuska sosai ta yi, cikin zafa ta ce. "Ka sake Ni!!". "Idan na sakeki zaki iya fama ciwonki ne". A sanyaye ya faɗa............."To idan na fama ina ruwanka? Kai da kaso kasheni me zai dameka dan na fama ciwona a gabanka? Jikinka ne ko nawa?". Idan hankalinsa ya kai miliyan to a yanzu ya tashi, dan yaga bil hakki da gaske take yi, bai san meyasa take cewa shi da ya so kasheta ba, shi bai san komai a kan abin da take faɗe ba, tana ta jefashi cikin ruɗani... TO FAH, ME KUKE TINANI MY PEOPLE'S? TO IDAN BA SHI YA KASHETA BA WAYE YA YI HAKAN? MUJE DAI ZUWA. "Nace ka sake ni ko?!". Cikin ɗaga murya ta yi maganar, hakan yasa ya yi saurin saketa, saboda bai taɓa jin ta ɗauki zafi haka ba. Da kyar ta iya tsayawa a kan kafafunta, sannan ta raɓa gefena zata wuce. Da sauri ya zube gwiwowinsa a ƙasa a gabanta, cikin nitsuwa ya fara jero maganganu masu zafi kamar haka. "Ban san laifin me nayi maki da har na cancanci irin wannan hukunci daga gareki ba, amma dai koma menene ina mai neman afuwa da ki yafe mun, kuma ina neman alfarma, ko da ba zaki sake yi mun magana ba, kai ko da ba zaki sake buƙatar ganin face ɗina a rayuwarki ba, dan Allah ki bani damar na mayar dake gida, dan hankalin kowa a tashe yake, kowa kukan rashinki yake yi, dan Allah ki saurareni, ni ban ma buƙaci jin laifin me nayi maki ba, ni dai kawai na karɓi laifin koma menene, ina neman afuwa". Kin saurarensa ta yi, ta raɓa gefensa ta wuce tana rike da hannun Pretty, a fili ta furta......... "Sai dai na mutu a wannan dajin da na yarda da kai, gara yunwa da kishin ruwa su kasheni da na bika da sunan ka mayar da ni gida". Kun san modarawa da balai'n zuciya, to ita ma Auta ta gado, ta fusata ba sassauci. Dafe kansa dake yi mashi tsananin ciwo ya yi, ya sha bakar wahala tsawon kwanaki 35 yana nemanta, daga gari har daji, wani maharbi ne ma da suka haɗu a cikin gari sai ya nuna mashi hotonta ya tambaye shi, shi ne ya ce tabbas ya taɓa ganin kamar ita a bakin ruwa cikin wannan dajin, dalilin da yasa ya shigo nemanta kenan, ya shafi kwanaki 20 ciff a cikin wannan dajin yana nemanta, sai yau Allah ya yi ya ganta, amma taki ta bashi dama ta saurare shi. Miƙewa tsaye ya yi, dik jikinsa ta mutu, ba abin da yake damunsa a zuciyarsa ma kamar yadda take ta ikirarin shi ya kasheta, to shi a yaushe ya kasheta? Wata ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da. "Ko dai kin bayyana mata soyayyarta da ka yi ne yasa take ikirarin ka kasheta, kila hakance ta cutar da zuciyarta har take gaba da kai". Tuna hakan yasa ya yi saurin bin bayansu. Can ya iskosu suna san tsallaka wani ruwan dake gudu mai ɗan girma, ba zasu iya tsallakawa ba sai sun shiga su wuce, to suna tsoron shiga kada ace wajen yana da zurfi, Auta tana dafe da cikinta, ita kuma Pretty tana ƙoƙarin samo itace su sanya a cikin ruwan dan su gwada zurfin ruwan. Gabanta ya kariso ya tsaya, cikin girmamawa ya ce. "Dan Allah ranki ya daɗe ki bani dama, dan Allah ki tsaya ki saurareni, kada ki yanke hukunci cikin fushi, tuba nike yi, nasanki da hakuri da juriya game da yafiya, dan Allah ki yi hakuri kin ji?". "Okey kasanni da hakuri shiyasa ka kasheni dan kana ganin zan yafe maka ko?". Ta gefa mashi tambayar tana kawar da kallanta daga kansa, bata san sake ganin face ɗinsa. "Wlh ranki ya daɗe ni ban kasheni ba, ban taɓa tinanin dede da second ɗaya na cutar dake ba, bani da burin da ya wuce in ganki a cikin farinciki, please ki saurareni". "Amma kuma dik da san farincikina da kake yi hakan bai hanaka caka mun wuƙa a ciki ba ko?". A fusace ta yi maganar!. Wani irin zaro idanu ya yi, sai a yanzu ya yi magana cikin ɗaga murya. "What!!!! Wuƙa a ciki kuma? Ni na caka maki wuka?". Cike da tashin hankali ya yi tambayar......... Ɗan siririn tsaki ta ja tare da juya mashi baya dan bata bukatar sake yin magana da shi. To fa!! Wannan lamari akwai sarkakiya sosai wlh. "Ban gane ni na caka maki wuka a ciki ba? Ki mun bayani".......... Yadda ya yi maganar sai da yasa ta yi saurin juyowa garesa, ko da wasa bata taɓa jin sautin muryar a haka ba, Allah sarki wato koma dai menene akwai tsantsar sansa a ranta har yanzu, tabbas ba bawa yake sanya kansa son wani a ransa ba, dan kuwa da mutum yake sanyawa kansa da Auta ta cire son Hoorain daga cikin zuciyarta. Ganin yadda tashin hankali ya bayyana a tattare da shi ne yasa ta ji yana da kyau ta sauraresa, dan kuwa alamu sun nuna kamar akwai wani abin........... Cikin nitsuwa ta bashi labarin yadda aka yi ya kasheta tsab, yadda suka haɗu a bayan part ɗin uncle Abbas da komai da komai har yadda ya caka mata wuka a ciki tana kallon kwayar idanunsa. Ita dai Pretty ta yi tsaye hannunta rike da sanda tana kallansu....... Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hoorain bai san lokacin da ya zube gwiwowinsa a ƙasa ba, wani irin sara mashi ya ji kansa ta yi, da kyar ya fara maimaita kalmar innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil. Sai da ya maimaita sama da sau hamsin durkushe a wajen, ya kasa ɗago kai ya kalleta ma, idanunsa sun rikiɗe sun yi jakir gwanin ban tsoro, alamar ran maza ya ɓaci. Ganin ya durkushe ƙasa ya sunkuyar da kai yasa Auta ta juya zata bar wajen. Cikin Zafa ya kai hannu ya riko hannunta. Da sauri ta juyo da kallanta a kansa. Can ƙasa ƙasa ta tsinkayo muryarsa yana faɗin. "Bani bane, bani bane ranki ya daɗe, wlh bani bane, tabbas nayi waya dake, kuma tabbas kin ce mu haɗu a bayan part ɗin uncle Abbas a wancan ranar, kuma tabbas na je wajen, amma ko da naje ban sameki ba, na ɗauki good 1h a wajen, shiru baki zo ba, ni kuma ban san ya zan yi ba sai kawai na koma ɗaki na kwanta, tin da na kwanta barci ya ɗaukeni, lokacin da na farka kuma sai na ji gabaɗaya gida ya rikice ana nemanki, na tambayi su Ansar, sune suke bani labarin wai an saceki, dalilin barina masarauta na fito nemanki kenan, dan ina ganin dik waɗanda zasu je nemanki ɓata lokaci kawai zasu yi, ina ganin kamar ina fita zan ganki, na sha wahala wajen nemanki, dan Allah ki yarda dani". Tin da ya fara magana idanunta a kan face ɗinsa, tsantsar gaskiya ce kawai take fitowa daga bakinsa, magana babu in'ina bare kwana kwana, zallar gaskiya! Kuma tabbas ta yi mashi shaidar baya karya!. Akwai cakwakiya fa, kenan idan ba shi ya kasheta ba wanene?. Ji ta yi jikinta ya mutu sosai, dama ga ciwonta yana yi mata zafi, kafafunta ne suka kasa ɗaukarta, nan take ta ji wani jiri ya ɗebeta, kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi sai ji ta yi ta tafi zata kifa kasa. Cikin zafa ya tarota ta faɗa jikinsa, wani irin kuka mai tsuma zuciya ta sanya. Da gudu Pretty ta taho ta zube gwiwowinta a ƙasa kusa da su, ta kai hannu tana taɓa Autar tana ambatar sunanta. Shi ma cikin girmamawa yake kiran sunanta yana faɗin. "Ranki ya daɗe dan Allah ki yarda dani, wlh bani bane, bata yadda za'ayi in cutar take! Hakan ba zai yiwu ba! Na tabbata da kin san matsayinki a raina da kwata kwata ba zaki taɓa yarda da cewa zan iya cutar dake ko da da cizon cinnaka ba ne, dan Allah ki fahimceni". Allah sarki, bai taɓa shiga ruɗani irin na yau ba, bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba, ya shiga damuwa mara misiltuwa, sambatu kawai yake yi ba tare da yasan abin da bakinsa ke fitarwa ba. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ E..............16 Tari sosai Auta ta fara yi, kuka ya ci karfinta, ta rasa me zata yi, idan ta ce ta yarda da shi ba shi ya kasheta ba, to kenan wanene? Akwai mai kama da shi ne a kingdom ɗin? Kai ina hakan ma ba zata taɓa yiwu ba, dole shi ne dan kamanninsa ba zai taɓa ɓace mata ba. Idan kuma taki yarda da maganarsa wani ɓangare na zuciyar tata yana faɗa mata zata cutar da zuciyar bawan Allah, zata cuceshi ta sanya shi a damuwa bayan ita kanta tasan baya karya, iya gaskiya yake faɗe, to ita yanzu ya zata yi da ranta?. Ta jefawa kanta wannan tambaya da bata da amsa. Shi kuwa sai magiya yake yi mata yana rantse mata da Allah akan bashi bane, sambatu kala kala yake yi mata. Ko Pretty da gigin giyar yarinta yake ɗebanta ta fahimci zallar gaskiya a tattare da shi bare ita Auta da tasan shi fiye da kowa, amma ya zata yi? Ta shiga ruɗanin da ba zata iya tsayar da zuciyarta a waje guda ta yanke abin da ya dace da ita ba. Kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita, akwai tsananin ciwo zuciya ta zargi masoyin da ta fi kauna sama da komai ya cutar da ita ko ya ci amanarta, wannan zuciya ta kan iya kamuwa da ciwo, kuma da matikar wahala ta iya sake yarda da wani. Kuka ita ma Pretty ta fara yi tana cigaba da ambatar Auta ta tashi, ta daina yin kuka................ Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin yadda ta rikiɗe da yin tari mai sauti mai kuma karfi har tana kwarewa, cigaba da bata hakuri ya yi yana kara rantse mata da Allah bashi bane. Bata kulasu ba, ta yi wannan kukan har sai da ya isheta, sannan ta tsagaita dan kanta. Yana ƙanƙame da ita, tin yana sambatu shi ma har ya ƙasa iya cigaba da yin magana ya yi shiru. Pretty tin tana kuka har ta yi shiru dan dole. Dan sun lura Auta ba zata ji rarrashin nan da suke burin yi mata ba. Sai da suka ji ta dakata da kanta ne Hoorain ya yi saurin ɗago da kallonsa a kanta, da kyar murya na rawa ya iya ce mata. "Dan Allah ranki ya daɗe ki yi hakuri, wlh bani bane, kuma ba zan taɓa iya cutar dake ba, please trust me!". Shiru ta yi kamar ba zata tanka mashi ba, idanunta a datse gam, jikinsa dik sai kerma yake yi, da kyar ta ɗaga hannunta izuwa saman hular yakin dake face ɗinsa dai'dai saitin kumatunsa. A hankali ta waro idanunta a kansa, sun yi jajir kamar wuta saboda ta sha kuka har ta goge Allah. "Hoorain na san ba zaka yi mun karya ba, saboda baka yi baka saba ba, ina da tabbacin a kai'na kuma ba zaka fara ba, dik abin da yake fitowa daga bakinka zuciyata ta shaida zallar gaskiya ce kawai, na yarda da kai, amma zuciyata tana cikin tashin hankali da ruɗanin wanenen mai kama da kai da ya yi yunƙurin kasheni? Meyasa sai a siffarka za'a zo cutar dani? Dan kawai zuciyata ta shaku da kai? Shin akwai wanda shakuwarmu ta tare mashi wani abin ne ko ta takura mashi?". Lalllai sai ka saurara da kyau zaka iya gane me Auta take faɗe, saboda yadda voice ɗinta ya dashe na kukan da ta sha. Tabbas ya ji maganganunta dikka shi kam, dan a matse yake da buƙatar san jin ta furta mashi ko da kalma ɗaya ne, dako yake yi dama shiyasa ya kasa kunne ya saurara da kyau. Hannunsa dake cikin hand gloves ɗinsu na mayaƙa ya ɗaura mata a saman face ɗinta, zafafan hawayenta yake san goge mata amma kuma yana jin shakka shakkar yin hakan ba tare da ta bashi izini ba, dan haka sai ya ce. "Ina neman alfarma da ki bani izinin in share maki hawaye kafin na baki amsar tambayarki!!". "Meyasa kake san goge mun hawayena?". Ta gefa mashi tambaya. "Saboda bana san ganinsu a face ɗinki, da murmushi mai kwantar da hankula face ɗinki ya dace, kuma da shi muka sanki, bamu san wani abin bayan cool murmushi a kan face ɗinki". Idanunsa a kan face ɗinta yau kam ya yi magana. "Da gaske Hoorain zuciyarka bata san ganin hawayena?". Cike da mamaki haɗe matsuwa da san jin amsar da zai bata ta yi tambayar. Jinjina kansa ya yi. "Tabbas zubar hawayenki babban tashin hankali ne wanda zai iya zama barazana ga zuciyata, bana san shi, hankalina yana tashi sosai kuma rai'na yana sosuwa matuƙa idan naga kin haɗe rai ma ba sai an kai ga kuka ba". "Meyasa kake jin hakan a kai'na?". Ta jefa mashi tambayar ne cike da yakinin abin da take san ji daga garesa zai furta mata ko ranta zai yi sanyi, tabbas ta yarda da shi, tasan baya yi mata karya, sai dai har yanzu zuciyarta yana cikin ruɗanin da Allah ne kawai zai iya warware mata, daɗin daɗawa da ace shi ya yi yunƙurin kasheta tin farko da tabbas ba zai taimaketa a cikin wannan dajin ba, tabbas daga haɗuwarsu izuwa yanzu da ya jima da gama ƙarisa hallakata ya jefar da ita, amma ransa ma ya sadaukar ya cecesu, ya kuma yi jinyarta, sannan ya zube gwiwowinsa a kasa yana neman ta tsaya ya mayar da ita gida, kai gaskiya ko iya waɗan nan hujojin sun isa a gaskata cewa bashi bane ya yi niyar kasheta, to yanzu tambayar a nan ita ce wanenen ya yi niyar kasheta? Sannan kada ku manta yana Kingdom of justice, wato wajen Queen Zarina kenan, to ya aka yi hakan? Lokaci ne zai warware mana komai In Sha Allah, muje dai zuwa!!. "Ban san dalili ba, abin da nasani kawai shi ne bana san tashin hankalinki".. Allah sarki, jin ba abin da ta yi tsammanin ji daga garesa bane yasa ta sauke wahalallen ajiyar zuciya tare da jawo yawu mai wuyar haɗiya ta haɗiyesa da kyar, ta yi tinanin zai ce saboda yana santa yasa baya san tashin hankalinta, sai ta ji akasin haka. Jikinta ne ya kara mutuwa sosai, yanzu ta gama yardanwa kanta da gaske baya santa, dama ranar ta ji yana faɗawa su Ansar baya santa, ashe ita kaɗai take dakon kaunarsa. Fahimtar hakan yasa wasu zafafan hawaye masu ɗumin gaske suka fara wanke mata fuska da gudun gaske. Bawan Allah, ya so faɗa mata amsar da take san ji, ya so ce mata saboda santa yasa baya san ɓacin ranta, sai dai tongue ɗinsa ta yi mashi nauyi, yana jin kamar ba zai iya furta mata ba, dan yana ganin kamar ba zai sameta ba, kamar ko ya faɗa mata a banza ne, ba za'a bashi ba kuma ita ma ba lallai ta yarda ta aminta da shi ba dik da yana ganin kamar tana san shi kuma abokansa suna yi mashi wannan hasashe na tana san shi ɗin. Dagewa ta yi da karfinta ta yunkuro zata bar jikinsa. Cikin sauri ya rikota, ƙasa ƙasa a nitse ya ce. "Zaki fama ciwonki idan kika tashi fa". Tabbas ya fahimci amsar da ya bata ne ta sosa ranta har take san barin jikinsa, amma sai ya yi kamar bai fahimta ba, dik dan ya yi ƙoƙarin tsare kansa daga shiga bala'i. "Kada ka damu Hoorain, a yanzu na samu kwarin gwiwar son mutuwa fiye da rayuwata, babu wata amfanin zamana a duniya tin da burina ba zai cika ba, ka barni ciwon ya fama kawai na mutu............" Bata iya ƙarisa maganar ba kuka ya cikarfinta sosai wanda ya tilasta mata yin shirun dole. Wani irin bargon sanyin jikine ya lulluɓesa, sai ya ji ya yi nadamar faɗa mata hakan da ya yi, yanzu bata da lafiya, kamata ya yi ya faɗa mata kalamai masu sanyi da zasu kwantar mata da hankali, ba ya tsaya biyewa zuciyarsa ba. "Ranki ya daɗe ki yi hakuri, ki sani rayuwanki shi ne namu, kada ki yi mana wasa da shi kin ji?". Pretty dai kallansu kawai take yi, sun yi nisan zango cikin larabcin da suke yi, dama ita ba sosai ta iya ba, sama sama ne haka, ta fi iya turanci a kan Larabci, Sweetie ta fita iya larabci, dan haka sai ta dai'na fahimtar abin da suke faɗe dan sun yi mata nisa, kawai ta hau aikin binsu da kallo. "Hoorain ina san ka dai'na yaudarar zuciyata haka nan, ka barni dan Allah, wai me na tsare maka ne ma da kake wahalar da ni?". Cikin kuka ta yi maganar. Sam bai gane maganar da take yi ba, shi ya rasa ya zai yi, dan gaskiya ya san ko mutuwa yake yi ba zai sameta ba, yanzu haka mutuwa yake kwana yana wunin yi a cikin zuciyarsa dik a kanta, to ina ga ya furta mata soyayya sun kuma kara shakuwa da juna? Me kuke tinanin zai faru a lokacin da za'a rabasu?. "Dik wani abin da bakya so daga yau na dai'na yi, ba zan sake ba kin ji?". A sanyayye ya yi maganar.............. "Ka tabbata dik abin da nikeso zaka yi?". Kai ya gyaɗa mata alamar ya tabbata. Ajiyar zuciya ta sauke tare da zame hannunta daga face ɗinsa, a hankali ta yunkura zata bar jikinsa. "Akwai in da kike san zuwa ne in kai ki?". Ya jefa mata tambaya. "A'a zan sauka daga jikinka ne kawai ina ga sai ya fi mun daɗin faɗin abin da nike san ka yi mun". Jinjina mata kai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, sannan ya sauketa ƙasa a hankali cike da kula yana ce mata sannu. Zama ta yi a ƙasa suna fuskantar juna, tana matuƙar jin azabar ciwon da yake jikinta, amma haka ta daure. "Yaushe zaka mayar da ni gida?." Tambaya ta farko da ta fara jefa mashi kenan. "Yanzu haka a kan hanyar gida muke, ƙoƙarin mayar dake nike yi, sai dai muna da nisa sosai, zamu iya yin kwana biyu a dajin nan kafin mu iya fita". Cikin girmamawa ya bata amsar. "Ka zauna da kyau to sai mu yi magana". Ta faɗa a sanyaye. Matsawa kusa da ita Pretty ta yi suka manne da juna. Kallo ɗaya Hoorain ya yi wa Pretty ya kawar da kansa, ya maida kallansa a kan ruwan dake gudu a gefensu, yana satar kallan Zunaira ta witsiyar ido. "Ranki ya daɗe nafi san in tsaya a kanki dan tabbatar da babu wani abin cutarwa da zai tinkaro in da kike". . Kai ta girgiza mashi kafin ta ce. "Kada ka damu, babu wani abin cutarwa da zai cutar da mu In Sha Allah, yanzu dai zauna". Ba musu ya zauna, amma bai so hakan ba, sai ya lankwashe kafafunsa ya ƙarisa zama daga durkushen da yake. "Ina wayata take?". Ta gefa mashi tambaya. Shiru ya ɗan yi, yana tinanin a ina wayar take, shiga tashin hankalin da ya yi a sanadiyar ɓatarta ya ja ya mance ina ma wayar tata yake. Ganin yana tinani yasa ta fahimci ya ajiye wayar a in da ya manta ne, dan haka sai ta kawar da zancen da cewa. "Hoorain ina san ka mun wata alfarma guda ɗaya kafin mu koma gida". A kanta ya tsayar da idanunsa, sannan ya ɗan jinjina mata kai kafin ya amsa da. "Wace alfarma kenan gimbiya?". "Ina san idan ba damuwa dan Allah ka bari in kalli face ɗinka ko da sau ɗaya ne a rayuwata kafin mu koma gida, ina san kallanka sosai"............ Shiru ya ɗan yi lallai Zunaira ta zo da babbar magana, ga shi a wannan gaɓa ba zai iya yi mata gardama ba, saboda ta kuresa a yanzu, alfarma ta nema wanda ta wuci hakan a wajensa, innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ya zai yi yanzu? Tun yana ɗan shekara bakwai ya fara sanya hulunan yaki yana rufe face ɗinsa, kunga kuwa tin ba'a san za'a haifeta ba kenan, babu wanda ya taɓa matsuwa da ya ga face ɗinsa sai ita, dan haka bashi da kwarin gwiwar kallanta ya ce ba zai iya yi mata wannan alfarma ba, ransa dai bai so ba, amma ya zai yi tin da farincikinta yake so!. "In Sha Allah ba zamu bar cikin wannan daji ba har sai kin kalli face ɗina ranki ya daɗe, na yi maki alkawari, amma ba yanzu ba dan Allah, kin ji ko?". Jinjina mashi kai ta yi alamar to, sannan ta ce. "Ina Abbo?". "Yana gida na barosa"....... Shiru suka ɗan yi kamar babu mutane a wajen. "Hoorain". Ta ambaci sunansa a hankali. Ba tare da ya dawo da kallonsa a kanta ba ya amsa mata da na'am. "Meyasa baka san kallona kai tsaye sai dai ka rinƙa satar kallona kamar wanda bashi da gaskiya?". Ba tare da ya juyo da kallan nasa a kanta ba ya ce. "Saboda in kina tare da ni bana iya ɗaukar minti ɗaya ba tare da na ganki ba, ba zan iya zuba maki ido in yi ta kallanki kai tsaye ba kamar yadda ba zan iya daure ban kalleki ba, shiyasa nike kallanki a sace". Haka kawai baiwar Allah ta ji murmushi ya kubce mata, wato shi baya shakkar faɗar gaskiya fa, bawan Allah. Sosai ya ji daɗi harda sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da ya kalli ta yi murmushi, har ya ji ransa ta sanyaya sosai. "Meyafaru kake sauke ajiyar zuciya?". Ta jefa mashi tambaya. "Saboda kin yi murmushi shiyasa na ji sanyi a rai'na, ban ma san na sauke ajiyar zuciya ba sai da kika yi magana". Allah sarki zuciyar masoya, sai ta ji wani irin daɗi ya kara ratsata, har tana ji kamar ta kasance da shi a cikin wannan yanayi a wannan waje na har abada, ita jin daɗi da daular da suke da shi ba shi ne a gabanta ba, Hoorain shi ne kawai damuwarta, in dai zasu zauna cikin wannan yanayi mai daɗi yana ganinta tana ganin shi to ta gwammaci zama a wannan daji fiye da ta koma wajen ƴan uwanta. Wato soyayya fa hegiyar aba ce, ko da yake ayoyi sukutum ne da ita a cikin Alqur'ani mai girma, dan haka zata yi fin hakan ma in dai so ce, Allah dai ya taimakemu kada ya bamu damar san waɗan da basa sanmu, Allah ya haɗamu da masu sanmu na gaskiya!!. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Sun jima a wannan waje suna hira, tun yana amsa mata kai tsaye har ya dawo binta da okey da kuma e or a'a, dan shi bashi da yawan magana, sai jansa da hira suke yi, dan yanzu Pretty ma ya ware ta fara tayata. Sai da rana ya tsaga ne ya ce masu su zo su koma wajen da ya tanada masu bari ya nemo masu abin da zasu ci. Basu yi mashi musu ba, suka miƙe da kyar Auta tana jan kafafunta a ƙasa. "Ranki ya daɗe ina neman wata alfarma". Ya faɗa yana kallan ƴan fararen kafafunta. Jinjina kai ta yi. "Ina jinka". "Dan Allah ki bani damar in ɗaukeki zuwa wajen". "Meyasa?". Ta sake jefa mashi tambaya. "Saboda bana san ganin kina shan wahala". Wani irin daɗi ta ji ya ziyarceta a ranta, tabbas bata cire ran Hoorain zai sota ya kuma bayyana mata soyayyarsa ba a yanzu. Jinjina mashi kai ta yi alamar ta bashi dama, ai tin kafin ta gama zayyana ta bashi damar ya ɗauketa cak sai saman kirjinsa na zakunan mazajen nan, ya riko hannun Pretty suka kutsa cikin dajin, suka koma in da suka fito, wato wajen da ya gyara ya tanada dominta, waje mai cike da yanayin soyayya da nishaɗi. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 A ɓangare guda kuwa, Sadauki kusan hauka ya yi a lokacin da ya kawo masu ziyara bai samesu a wajen ba, yau a karon farko sai da ya durkushe gwiwowinsa a ƙasa, dik da ba'a iya ganin face ɗinsa sai idanu, yau sai da tashin hankali ta bayyana acikin idanun nasa mai firgitarwa. Cike da tashin hankali da damuwa ya fara kewaye arear wajen yana nenan ta ina zai gansu? Damuwarsa ma yadda Auta take da ciwo a ciki bata warke ba, hakan ta kara ɗaga mashi hankali sosai, jikinsa har kerma yake yi yana tsuma. Ya ɗauki a kallah mintuna 30 yana kewaye a yankin yana nemansu, dan gani yake suna nan a wajen basu yi nisa ba. Wani irin damuwa ya ƙara shiga a lokacin da ya yardanwa kansa basu nan, basu wannan yankin kwata kwanta sun yi nisan zango, ga shi babu wata makama da ya gani wanda zai iya hasashen meyafaru da su? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne kawai kalaman da yake ta maimaitawa, ya shiga damuwa na wuce misali. Da kyar ya iya jan kafafunsa ya kutsa cikin dajin da ya je ya cigaba da nemansu a can ko Allah zai sa ya gansu. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 After some minutes, rana ta take sosai, zaune Pretty da Auta suke a saman dutse kusa da wata bishiyar gwaiva, hannunsu rike da ganyen ayaba mai ɗan faɗi, gasassun kifi ne a saman ganyen ayabar wanda Hoorain ya kawo masu, ga kayan fruits a gefensu, basu san daga ina ya samo kifin ba, su dai ya ce masu su yi zaman jiransa yana zuwa, shi ne ya dawo masu da kifi gasassu kuma ya sake tafiya ya barsu ya ce yana zuwa. Sai rarraba idanu Auta take yi tana jiran taga ta ina zai ɓullo, ta gaji da jiransa, dik bayan second ɗaya kara ɗaukin san ganinsa take yi, bata gajiya da shi, a kullum tana san taga tana a tare da shi. Ita kuwa Pretty tinanin kifin kawai take yi, kunsanta ita da ci akwai amana, sai tinanin kifin take yi, ya bata sha'awa, ta yi mamakin ganin irin gashin da ya yi masu, tana da yakinin a wajen wancan wuta da ya kunna mata dan jin ɗumi ɗazun nan ya gasa masu, ya kamo kifin a kogi kenan ya gasa a can. Gajiya da gafara sa bataga kaho ba Auta ta yi, dan haka sai ta miƙe tsaye, a hankali ta ce. "Pretty zauna ki jirani ina zuwa". "Ina zaki je ki barni?". Ta jefa mata tambaya.............. "Ke dai ba zan yi nisa ba kuma ba zan wani jimaba, ina zuwa yanzu". Jinjina kai Pretty ta yi tana cigaba da gutsirar kifinta tana kaiwa baki abinta sarkin ci kawai, har yanzu dai bata canza hali ba a fagen ci. Saukowa kasan dutsen Auta ta yi, sannan ta miƙi hanyar da take tinanin yana ta wajen. Tana tafiya tamkar mai tsoron taka ƙasa, saboda ciwonta idan ta yi sauri zai fama. Tafiya a hankalin yasa bai ji zuwanta ba, yana tsaye saman dutsen dake gaban wannan koramar, yana ƙarisa wanke takobinsa da bai samu ya yi ɗazun ba. •••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Tin da ta doso wajen ta hangosa daga nesa tsaye saman dutse, gabanta ne ya yi wani irin faɗuwa sosai, kirjinta ya bada dukan uku uku, bata san time da ta ɗaga kafarta da sauri wajen ƙarisawa garesa ba. Sam bai ji alamarta ba, ya bawa hanyar da take zuwa kuma baya yana karisa wanke wanke takobinsa da bai ƙarisa ɗazun ba. Ya kuma ɗauro alwala dan ya yi sallah. A wani irin slow ta ambaci sunan cike da salon da bata san ta iya shi ba. "Hooooooooooraiiiiiiiiiiiiin" haka ta faɗi sunan. Da karfi ya juyo domin ya ji abin ne kamar almara, kamar voice ɗinta kamar kuma ba nata ba, sai ya ji kamar mafarki kamar kuma gizo, hakan yasa ya yi saurin juyowa da karfi. Juyowa da ya yi da karfi yasa kyakkyawar dark black curly hairnsa ya watse kamar wata mace kamar kuma wanda aka hurawa gashin iska ya watse haka. Ya ilahi ya lilliahi! Mutuwar tsaye ta yi tana kallansa, kamar wadda aka zarewa rai, ta kame kam. Shi kuwa cikin zafa ya diro ƙasa daga saman dutsen, da wani irin gudun gaske ya nufota. Zaro idanunta ta yi tana mamakin me zai yi mata da ya nufota da irin wannan uban gudun kuma? Ga lafiyayyar takobinsa a hannunsa. Ku me kuke tinanin zai faru? Yau dai ta ganshi babu hular yaki, ko ya kamanninsa take? Meyasa ya nufeta da gudu dan ta gansa bai rufe fuska ba, meyasa ta yi sumar tsaye dan ta gansa? To ni dai bari in leƙa Black world muga me suke ciki kafin in dawo muga me zai yi mata kuma mu ga ya kamanninsa yake da yake ɓoyewa tsawon shekaru, yau dai komai ta bayyana..........🥱 ••••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••••🔥 A wani irin razane Ronnie ya juyo da kallonsa a kan yayan nasa. Wani irin razana ya yi ganin yadda Black Tiger ya ɗaure fuska tamau alamar babu tausayi babu imani. Nan take wasu irin zufa suka fara keto wa Ronnie babu kakkautawa, shikenan yau Sweetie ta ja mashi yanka kazar wahala, watar azabarsu ce ta tsaya. With her full confidence sweetie ta ce. "Ronnie kada ka damu, kwantar da hankalinka ka dai'na yin zufa, Big bro kana ɗagawa Ronniena hankalifa, kuma ni bana san hakan, ka dai'na kada rai'na ya ɓaci". Yadda ta yi maganar yadda kuka san uwar Ronnien ce take magana. Ronnien da ya kusa sakin fitsari a wando saboda tsorata ne ya kara zaro idanu waje tare da juyowa gareta da kyau ya kuma saki hannunta da ya rike. Sai dai kafin ya kai ga juyowa gareta da kyau Black Tiger ya juyo magic eyes ɗinsa a inda tamkar walkiya haka ya fisgota ta ƙariso gabansa. Cikin zafa rai a matuƙar ɓace ya sanya hannunsa ya yi mata wani irin mahaukacin damka a wuya mai razanarwa wanda sai da ta ji kamshi kamshin mutuwa. Ta ɗauka wasa yake yi, bata san baya ɗaukar wargi ba, a tinaninta idan tana tsokanarsa ta wannan hanya zata iya samun damar shiga jikinsa har su fara aiwatar da plan ɗinsu a kansa, bata san shi ɗin tamkar dutse yake wanda huda jikinsa a shiga ba ƙaramin abu kamar yadda ta zata bane, in ta yi kokarin shiga jikinsa ya zo mata da karar kwana ma ai sai ta mutu ba damuwarsa bane. Wani abin da baku sani bama, da farko wlh Ronnie ya so ya yi amfani da shiga addininta dan su samu Spender ne, dan ya lura tana san addininta sosai, shi ne kuma rauninta, amma da yake Allah ba'ayi mashi wayo kuma ya so shi da rahma, sai ya dasa mashi kaunar addinin a ransa na gaskiya wanda zai ma iya sadaukar da ransa a kan addinin ba tare da ya ji komai ba!!. Da gudu cikin tashin hankali Ronnie ya nufi Black Tiger domin ya bashi hakuri ya saketa. Sai dai bai kai ga ƙarisawa wajen ba ya tsaya cak ya kasa gaba ya kasa baya kamar mutum mutumi. Ita kuma ya ƙara shaketa da kyau da kyau, tin tana iya ganinsa har ta fara gani dishi dishi. Babu imani babu tausayi ya yi wurgi da ita ta tafi ta bugu da jikin swan chair dake ɗakin nasa ta faɗi kasa. A wahalce ta saki wani irin azabbabben kuka mai tsuma zuciyar mai imani ba irin black heart ɗinsa ba, shi ko kaɗan bata bashi tausayi ba. Bai bata damar ta yi ƙoƙarin jawon numfashinta ba ya sanke amfani da magic ɗinsa ya janyota gabansa tana zube a ƙasan, shi kuma yana tsaye kamar wanda aka sassaƙa, ransa a matuƙar ɓace ne. Ko kaɗan bai ji kamar zai tausaya mata ba, kafarsa guda ɗaya ya ɗaga ya sauke mata saman wuyarta, ya taketa ba tare da kalli in da take ba. Wani irin bargon azaba ne ta ji ya lulluɓeta, da gaske niyar kasheta ya yi, hasashen Ronnie ya saɓa hanya da ya ce mata Black Tiger ba zai iya kasheta ba, ashe dai sai in black heart ɗinsa bata motsa ba, tsab zai aikata fin kisa. Sweetie ta shiga gonarsa dayawa, dama kuma already ransa a ɗan ɓace yake sakamakon addaba mashi da duniyar sheɗanu suka yi, suna kutsawa cikin ruhohin tsafinsa suna birkita mashi lissafi, abin yana bakanta mashi, yana ta ƙoƙarin ya rufe dik wata hanya da zasu iya riskar ruhohin tsafinsa ita kuma ta zo zata kawo mashi wargi, shi ne ya tattare haushin waje guda dikka ya sauke a kan!. Bai ɗauke ƙafarsa daka samar wuyarta ba har sai da yaga ta daina numfasawa ta ɗauke diff rai ya yi halinsan! Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Sannan ne ya ɗauke ƙafarsa tare da yunƙurin zai yi ball da ita ta fice mashi daga ɗaki, sai kuma ya tina idan ya yi hakan gawar tata zata tarwatse mashi a cikin ɗaki ta ɓata mashi waje, dan haka sai ya yi amfani da magic ɗinsa wajen ɓatar da ita, kafin kyaftawa da bismilla babu ita babu rabarinta, ta ɓace a wajen. Sannan ya yi amfani da magic ɗinsa wajen dakatar da bugawar numfashin Ronnie, ya yi kamar ya sumar da shi, dan in ba haka ya yi ba yau zai iya kashe Ronnie dan ɓacin rai, saboda yasan ba zai bar shi ya kwana lafiya ba, a kanta zai hana kowa barci ya yi ta kuka, so gara ya yi mashi haka zuwa da safe ya tashesa, kafin nan kuma zai yi ƙoƙarin ganin ya shafe mashi tinaninta a babin rayuwarsa gabaɗaya, e lallai akwai aiki babba. Team Ronnie ina kuke, me kuke tinanin zai faru? Za'a shafe kwakwalwar Ronnie, damuwata ɗaya shi ne ya batun musuluntar da ya yi? Kenan zai koma krista?😥 Innalilahi wa inna ilahir rajiun, wannan yafi komai ɗaga mun hankali, bana san ya koma krista wlh............😥 To bari dai mu leƙa Dubai kila kafin mu dawo abubuwa zasu ɗan yi sassauci. ••••••••••••••••••DUBAI•••••••••••••••🔥 Zaune Sharifat take a bakin bed ɗin dake cikin A&E room ɗinsu, ta buga uban tagumi tare da zubawa Leesharh dake kwnace a saman bed ɗin idanu tana kallonta, yau tsawon kwana uku kenan da Ramish yasa hannu aka saketa saboda ba wayarta bace, Bilal ne ya ɗaukota ya dawo da ita, Dr Raj yana kula da ita, shi ne Dr ɗinta, shi ma sai da Bilal ya sanya baki ne ya yarda yake dubata, da farko ya ce shi ba zai iya duba lafiyar wadda ba'a san asalinta ba, infact shi baya ma san ganinta, sai da Bilal ya umarcesa a kan hakan sannan ne ya yarda ba dan ya so ba!. Tsawon wannan kwanaki ukun Leesharh bata san in da kanta yake ba, da farko ma Dr Raj ya ce ta mutu, sai daga baya suka iya jiyo sautin bugawar zuciyarta can ƙasa ƙasa kamar yana san dakatawa ya dai'na aiki. Allah sarki ta ji horon manyan kai, sai da ta zaɓi mutuwa a kan hakan, a gaskiya Ramish mugu ne bashi da imani wlh, dama ga shi kullum yana maganar kada daddynsa ya yarda da kowa, kai gaskiya guy ɗin nan Ramish bashi da daɗi, ya azabtar da ita over. Dikkan jikinta bandeji, an mammanneta ta ko'ina kamar wata pacin tayar mota, hannunta na dama ma ya samu karaya, wai a haka ma fa dan Bilal yana dakatar da Ramish ɗin, da ya jima da kasheta. Sai kuka shafiat take yi hawaye bibbiyu, kwanaki uku Leesharhnta taki motsawa, tin tana sa rai har ta fara karaya, jikinta dik ya mutu ta fara tinanin ko dai mutuwa da gaske Leesharh ta yi basu sani ba?. Yanzu kun gano daga in da Omaid and Obaid suka gado mugunta da iya horor da mutane ko? Shi kansa Abu Abdussalam sai da ya razana a lokacin da Bilal ya dawo da ita, sosai ya yi wa Ramish faɗa a kan yi wa mutum ɗan adam irin wannan horo babu daɗi, ya ce ko namiji bai yarda ya sake hora shi kamar haka ba ballanta mace wadda ita sam babu gurbin wahalarwa a jikinta, ya rinƙa sassauta zuciyarsa gudun yin danasani gaba. A ɗan fusace ya ce da Abbie. "Abbie danasani fa ka ce?!". "Kwarai danasani My son". Kara ɗaure fuska ya yi kafin ya ce. "Babu wata danasanin da zan yi a rayuwata, dan haka ni ka dai'na faɗa mun hakan". Da yake Abbie yasan halin kayansa sai ya koma sigar rarrashi. "Haka ne son, bana fatar ka yi danasanin nima, amma please ka rinƙa sassautawa, kaga macece fa ita, amma haka ka horata kamar ka riki kartin maza ƴan ta'adda". Kansa a ƙasa ya jinjina tare da cewa. "Amma menene banbancin wanda ya so tasan bomb a wannan hall ɗin da ƴan ta'adda?". Shiru Abbie ya yi, dan babu banbanci, gara ma ƴan ta'adda da sauki a kan wanda zai tashi bomb cikin wannan taro da sama da mutum 1000 zasu rasa rayukansu, har da makotan hall ɗin dik zasu iya kamawa da wuta su haɗa da mutanen dake ciki. Miƙewa tsaye ya yi ganin Abbie ya rasa bakin magana. "Good night Abbie". Ya faɗa ba tare da jiran abin da zai ce ba yasa kai ya nufi waje. Da kallo Abu Abdussalam ya bisa har ya fice, ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaga hannu ya furta zafafan addu'oi kamar haka. "Ya Allah ka shirya mun my son ɗina, Allah ka sassauta mashi wannan zafin zuciya tasa, Allah ka kara kare mun shi daga dik wata sharri, daga karshe Allah ƙasa ya kara zamtowa mai son na gasken gaske wato Allah ka haɗa zuƙansu shi da Sharifat na yi masu aure". Shi kuwa Ramish, bedroom ɗinsa ya wuce, white jallabiyar jikinsa ya cire, ya rage daga shi sai sexy short and singlet............ My people's wai meyasa Yah Ramish yake san sexy kaya kamar wani mai aure ne?...🤔 Short ɗin ta kama shi sosai, dai'dai irin........ Na dai yi shiru kada ace na cika saka ido. Toilet ya nufa dan ya yi wanka ya yi shirin yin barci. Bilal kuwa baya nan ya fita. After some minutes ya fito sanye da sexy bathrobe milk color a jikinsa, ya yi masifar kyau sosai. Mayukansa masu kyau da tsadaya shafa. Yana tsaka da gyara gashinsa ta cikin mirror ya yi arba da face ɗinta t............ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ E..…...............17 After some minutes ya fito sanye da sexy bathrobe milk color a jikinsa, ya yi masifar kyau sosai. Mayukansa masu kyau da tsada ya shafa. Yana tsaka da gyara gashinsa ta cikin mirror ya yi arba da face ɗinta tana tsaye a bakin kofar shigowa, ta kasa gaba ta shigo ciki ta kuma kasa yin baya ta fita waje. Kamar bai ganta ba haka ya yi, ya cigaba da abin da yake yi har ya kammala, bakin bed ya wuce ya zauna, cike da class ya ɗauko wayarsa, number da yake san kira ya shigar, babu suna number, hakan na nufin ba'ayi saving ɗinta ba. Kira ya danna tare da kara wayar a kunnensa, bugu ɗaya aka ɗaga call ɗin cikin sauri. Daga ɗayan side ɗin Sharifat ta ce. "Hello wanenen?". Wannan wayar tasa Bilal, Dr Raj, Rizwan sune kawai suke da phone number, shiyasa Sharifat bata ma san wanene bane, wayarta kuma ba irin nasu bane da in sun kira zai baka suna da location ɗin in da mai kira ya kiraka haɗe da gajeran bayanai a kan mai kiran. Shiru ya yi kamar na minti ɗaya. Yana jinta ta kara faɗin wanene? Bai yi kamar zai amsa ba, ta sake tambaya na uku, nan ma shiru. Ranta ne ya ɓaci, dama ga damuwar rashin lafiyar Leesharh, sai abin ya kara yi mata yawa, dan haka cikin faɗa ta ce. "Wannan wani irin iskanci ne a kira mutum kuma ba za'ayi magana ba? To koma wanenen kada a kara kirana". Sai da ta kai aya a zazzaga masifar tata zata katse kiran ne ta tsinkayo sexy voice ɗinsa cikin nitsuwa ya ce. "Ki kawo mun cappuccino yanzu". Ai tana daga zaune a bakin bed ɗin Leesharh bata san time da ta miƙe tsaye haɗe da ciro wayar daga kunnenta ba, bata taɓa zaton Yah Ramish bane. Innalilahi wa inna ilahir rajiun shi word ɗin da ta rinƙa maimaitawa babu kakkautawa, gabanta sai faɗuwa yake yi, ƙoƙarin tinano abubuwan da ta faɗa cikin masifar da ta zazzaga ta fara yi ko Allah zai sa ta tina komai ta ji ta yi zagi a ciki ko bata yi ba, yau ta shiga uku shi ne abin da zuciyarta yake faɗe. Shi kuwa yana gama faɗar abin da ya yi niya ya katse kiran, a hankali ya maido da kallonsa a kan Ummie dake tsayen mashi a bakin kofa, kamar dai akwai muhimmin abin da ya kawota ɗakinsa, dan bata zuwa part ɗinsu sai dole. "Zan iya sanin abin da ya kawoki nan?". Ya jefa mata tambayar tare da kawar da kallansa daga kanta. "Da gaske ne wai ka saki Leesharh? And da gaske ne wai ba ita ta yi maka laifi ba?". Shi ne tambayar da Ummie ta jefa mashi, daga ganin face ɗinta kasan bata ji daɗin dawowar Leesharh ba, ta haɗe rai kamar hadari, ranta a ɓace matiƙa. Ta tsani Leesharh, bata so ace sun saketa ba, ta so ne su kasheta, amma sai Sharifat ta ce mata an dawo da ita, ta tambayi Dr Raj meyasa aka dawo da ita ya ce mata ta tambayi Yah Ramish, tana shakkar tinkararsa saboda baya ba da fuska, hakan yasa ta tambayi Bilal, shi ma ya ce ta samu Yah Ramish a wajensa zata samu amsa, tin jiya take san tamnayarsa, amma tana tsoron tinkararsa, da kyar yau ma ta samu kwarin gwiwar zuwa garesa da abin ya dameta, wannan ma sai da wannan friend ɗinta mai kibar nan ta kara mata kwarin gwiwar a kan ta je ta tambaya kada ta damu. Idan baku manta ba a baya ita da kawar tata sun haɗa baki zasu kashe Leesharh ai, to shi ne da Ramish ya kamata sai suka ce ya hutasshesu, sai murna suke yi, rana tsaka kawai murna ta koma ciki, gaza jurar hakan suka yi har sai da suka zo dan tabbatarwa. "Abin da kika zo tambaya kenan?". Ya jefa mata tambaua. Wlh Ramish ya tsani Ummie kamar me, babu abin da ta yi mashi kuma, haka kawai bai yarda da ita ba wai. "Shi ne abin da ya kawoni". Ta bashi amsa.............. Gyarawa ya yi ya kwanta abinsa, ya janyo bargo har zuwa saman jikinsa. "Zaki iya tafiya dan bani da alaƙa da wannan magana da kika zo mun da ita". Shi ne amsar da ya bata, yana gama maganar kuma ya jawo remote ya kashe wutar ɗakin tare da kunna lamps, sannan ya kara gudun Ac. Tsaye ta yi tana kallansa, ta ƙasa tafiya. A hankali ya lumshe idanunsa kamar mai barci, zubawa face ɗinsa idanu ta yi tana kallo, nan take shaiɗan bakin azzalumi ya fara ƙawata mata kyansa da surarsa, take a wajen ta ji ta kamu da muguwar sha'awarsa. Tashin hankali!!. Zuciyarta ne ya fara azalzalarta, kun san mutumin fa ba dai kyau ba, jinin Zuhair ai ba wasa ba, ƙasa kawar da kallanta a kansa ta yi, ji take yi kamar ta tafi ta faɗa jikinsa, shaiɗan sai kara rura wutar wannan bakin al'amari yake yi a ranta, ta yi matuƙar kwaɗaituwa da surarsa a wannan dare, dama ita ma idan ba iskanci ba me zai kawota ɗakin santalelen saurayi a cikin wannan dare? Bayan kuma shaiɗan yana nan a tsakani yana yawo tsakanin karya da gaskiya tsinanne. Wlh ta ƙasa juyawa ta bar ɗakin, infact ta ƙasa iya dai'na kallansa, ga shi lamps suna haska fuskarsa da kyau, dan ta bakin bed ya kwanta, cikin dare ga fara kyakkyawar fuska haske na haskata ai kyau iya kyau, ni kuma na ce dik jarabarki wannan handsome guy na King ya fi karfinki In Sha Allah. Sallamar da aka yi daga bayanta ne yasa ta yi wani irin razana tare da zare kallanta daga kan Ramish, jikinta har wani tsuma yake yi da sha'awarsa. Wajen da take tsaye a kwai ɗan duhu hakan yasa Sharifat bata gane wacece ne a wajen ba, ta dai ga mutum, sai ta yi tinanin ko Yah Bilal ne, dan haka sai ta ce. "Yah Bilal good evening". Shiru Ummie ta ƙasa iya amsa mata, sai ma ta juya da sauri ta fice daga ɗakin tana haɗiyar yawun kyan Ramish. Sam Sharifat bata kawo komai a ranta ba, bata san wacece bace, kawai ta wuce ciki dan ta kai mashi cappuccinon da ya buƙata. A gaban bed ta durkushe gwiwowinta, kamar zata saka mashi kuka, murya a raunace ta ce. "Good evening Yah Ramish". Sam bai amsa mata ba, bai ma motsa ba kamar ya yi barci, ita kuma tasan sarai bai yi barci ba, ga zara zaran eyelashes ɗinsa suna ɗan motsawa alamar bai yi barci ba amsawa ce kawai ba zai yi ba, dan haka sai ta ɗaura da cewa. "Yah Ramish dan Allah ka yi hakuri ka ji? Wlh ban san kai bane ka kirani a waya shiyasa na yi zafafan furuci". Nan ma bai motsa ba, kamar babu shi a ɗakin. Miƙewa ta yi ta ɗaura mashi cappuccinon a saman table dake tsakanin sofar a cikin ɗakin, sannan ta nufi waje, dan tasan ko kwana zata yi ba zai amsa mata ba sai time da ya yi niya, gara mata ma ta tafi zai fi mata. Tana tafiya tana waigosa cike da tsantsar kaunarsa, sansa ne yake kara ratsa zuciyarta, tana san cigaba da kallansa amma babu dama, dan haka ta wuce waje da sauri idanunta suna ƙoƙarin cikowa da kwallah. Tana fitowa parlon ta ci karo da Yah Rizwan ya fito daga bedroom ɗinsa rike da cup a hannunsa, yana sanye da white arabs jallabiya, ya yi wani irin rama sosai, da alama daga jinya ya tashi, Allah sarki yana jinyar san Chuchu shi ma kuma Aneesa tana jinyar sansa. "Lil daga ina kike a cikin wannan daren?". Cewar Rizwan. Dakatawa ta yi da nufar waje, da sauri ta juyo garesa, bata yi zaton ya dawo gidan ba, dan bata gansa ba, rabonta da shi tin a kingdom of power ranar bikinsa, dik jinyar da ya sha bata sani ba, ba komai yasa hakan ba kuma face in dai ba wajen Ramish ba bata zuwa wajen kowannensu a part ɗin, ɗan gara ma shi Rizwan ɗin da yana sakar mata fuska wani lokaci idan ta rasa abokin hira tana zuwa bedroom ɗinsa su zauna. "Wajen Yah Ramish na je kai mashi cappuccinon". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. Gyara tsayuwarsa da kyau Rizwan ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Yah Ramish ɗin ya yi maki wani abin ne naga kamar kina kuka?". Kai ta girgiza alamar a'a tana ƙoƙarin shanye hawayen dake san zubo mata. "Mayasaki kuka to?". "Babu komai Yah Rizwan...........". Tana kai karshen maganar ta rushe da kukan da bata san daga ina ya fito ba, da karfi kukan ya kubce mata. Da mamaki Rizwan yake binta da kallo, Sharifat kenan sarkin saurin kuka ga raunin zuciya. Da yaga da gaske take kukan sai ya matsa kusa da ita, a saman table na wajen ya ajiye cup ɗin hannunsa, sannan ya janyota jikinsa ya rungumeta. Ita ma rungunesa ta yi tana kara rushewa da kuka. Baya cikin yanayi mai daɗi sam, amma haka ya daure ya shiga rarrashinta yana bata baki. A haka Dr Raj ya zo ya wucesu ya shiga ɗakin Yah Bilal dan ya sanar da shi condition da Leesharh take ciki a yanzu, dama tin safe Bilal ɗin yake jiran wannan amsa daga garesa. "Ki yi shiru kinji our lil, kinga fa ke kaɗai ce sistermu a cikin gidan nan, bai kamata ace wani abin zai sanya manake kwallah ba". Kun san Yah Rizwan Allah ya yi mashi baiwar iya kalamai masu kwantar da hankali, dan haka koma yaya mutum ya kai ga ɗaukar zafi ko ɓacin rai cikin ƴan mintuna zai rarrashesa. Haka ita ma Sharifat cikin ƙanƙanin lokaci ya rarrasheta har sai da ta yi shiru, sannan ya sanyata murmushi kafin ya raba jikinsa da nata, ya riki hannunta suka nufi bedroom ɗinta. Sai da ya tabbatar ta kwanta tana farinciki sannan ya juya ya fito, kai tsaye ya koma bedroom ɗinsa shi ma. A ɓangaren Ramish kuwa, sai da ya gama shan kamshinsa, ya gama jan ajinsa sannan ya tashi ya ɗauki cappuccinonsa ya fara sha cike da class. Kaɗan ya sha ya ajiye sauran, ya miƙe ya nufi prayer mad set. Dadduma ya ɗauko, already ya ɗauro alwalarsa tin ɗazun, salloli ya zo ya fara gabatarwa yana neman Allah da ya dafa mashi ya saukaka mashi binciken nan da suke yi a kan masu nikaf, nan da next month akwai wani taro da zasu sake yi, baya fatan har a kai ranar wannan taron bai kama masu kawo mashi hari ba, idan bai yi hakan ba za'a iya samu gagarumin matsala su sake kai mashi hari cikin taron kamar yadda suka yi a farko, za'a iya rasa rayuka, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya mutuwa, idan hakan ta faru ranza zai kuntata sosai, saboda dalilinsa ne mutane zasu mutu. So sai addu'a yake yi da Allah ya taimakesa kafin next month. Dai'dai lokacin da yake kwarara wannan addu'a a dai'dai lokacin Leesharh ra farka bayan kwanaki uku tana sume kenan. Dr Raj ya yi namijin ƙoƙari wajen kula da lafiyarta, ya nuna cikakkiyar kwarewa a ɓangaren aikinsa wanda hakan yasa ta farka a cikin hayyacinta. Hannunta da ya samu matsala ma ya sha ɗauri kuma ya sha kula sosai, haƙiƙa Bilal ya yi kokarin a wannan ɓangaren kam dik da bamu san menene ainahin abin da yake a cikin zuciyarsa ba. Ta yi babban sa'a kafin ta farka daga doguwar sumar nan dik wasu raɗaɗin ciwo dake jikinta sun kau, dan haka bata ji wani azaba da ta farka ba, sai da ta zo motsawa dan ta miƙe ne gaɓɓan jikinta suka ce ina ai basu san wannan ba, dole ta koma ta yi lamo a gadan tana kallan saman celling tana ƙoƙarin fahimtar a wace duniya take ma tukun nan, dan ita dai tasan ta baro kanta a hannun Yah Ramish ya danki gashin kanta yana bugata da jikin bangon ɗakin da suke horas da masu laifi, tin wani buga mata kai da bango da karfi da ya yi har ta fara ganin dishi dishi, daga nan bata sake sanin a wani hali take a ciki ba. Sai a yau da taga alamar kamar a gidan Abu Abdussalam take, amma ba halin tashi ta duba, dan haka sai ta mayar da idanunta da suke yi mata zafi ya lumshesu tana furta istigifari a cikin ranta. •••••••••••KINGDOM OF POWER•••••••••••🔥 Baki ɗauke da sallama Momma ta shiga master room ɗin dearlyn love ɗinta, baya a cikin bedroom ɗin, zubar ruwa da ta jiyo a toilet yasa ta fahimci yana ciki, dan haka sai ta kwantar da babyn Khadija a saman bed ɗinsa, ta ɗauki wayarsa domin ta kira uncle Jahiz. 11:00 a lokacin, dare ya yi, sai ta mayar da wayar ta ajiye a zuwan sai da safe kawai su haɗu. Tana ajiyewa King yana fitowa ɗaure da towel a waist ɗinsa. Da sauri ta miƙe ta nufesa, ƙayataccen murmushi ya sakar mata, da alama ya yi farincikin dawowarta sosai. Tana zuwa ta karɓi ƙaramar towel dake hannunsa ta hau taya shi goge jiki tana yi mashi barka da dare. "Kin dawo lafiya?". Ya faɗa fuska ba yabo ba fallasa, yana ta kallanta cike da tsananin kauna mai zafi. "Lafiya lou na dawo har ma da tsaraba". Ita ma tana magana tana kallansa cike da kauna. Kara sakar mata murmushi ya yi kafin ya ɗaura hannayensa a saman lallausan kumatunta. "Tsarabar me kika dawo mun da shi". Ya yi maganar ba tare da ya lura da babyn dake kwance a gadansa ba. "Kamata ya yi ka tambayi ya na sami mutanen ya kuma na barosu kafin ka tambayi tsarabar ko?". Ta kai karshen maganar tare da manna mashi towel ɗin hannunta a face ɗinsa tana ɗan jan dogon hancinsa cikin salo na soyayya. "To ni Rahilarh menene ya dameni da su da zan tambayi ya suke?".... Ɗan ɗaure fuska kaɗan ta yi. "Kai ko kake da damuwa da su". "Kamar yaya kenan?". Da ɗan mamaki ya yi tambayar. "E kai kake da damuwa da su tin da sun baka suruka sun kuma bawa ɗanka mata". "What?". Ya faɗa da ɗan ɗaga murya. Jinjina mashi kai ta yi alamar kwarai kuwa, sannan ta ɗaura da cewa. "Muje in saka maka kaya sai ka zo mu yi magana........." A hanzarce ya katseta da cewa. "A'a Rahilarh, ki faɗa mun wasa kike mun kawai a yanzu ba sai na je ko'ina ba". Ganin da gaske yake yi yasa ta amsa mashi da e wasa ne, dan tasan halinsa, dama tasan zasu kai ruwa rana kafin ya aminta da Mahnoor idan ya aminta ɗin ma kenan, ba zai yarda ƴaƴansa su auri wasu ba idan ba larabawa jinin sarauta ba, shi ma yana da kabilanci sosai kamar dai Akka, basa san wasu bare a cikinsu, a hakan ma dai ɗan gara shi a kan su Akka, shi kabilanci nasa a kan ƴaƴansa ne kawai!. Har wani ajiyar zuciya ya sauke jin ta ambaci wasa take yi mashi, hannunta ya ja suka wuce dressing room dan ta taya shi shiryawa, suna tafiya yana yi mata gargaɗin a kan kada ta sake yi mashi irin wannan wasa baya so, shi ƴaƴansa ba zasu yi aure daga waje ba, a cikin gida zasu yi aure kuma ƴaƴan sarakuna kamarsa zasu aura. Da okey kawai ta bisa har suka shiga cikin room ɗin. Soyayya mai tsabta suka shiga zubawa kafin ta fito mashi da kayan barci, kwana biyun nan ya yi kewarta saboda damuwowi da suke a ciki, daga wannan sai wannan, sai yau ne ya damu damar samunta tana farinciki, ba komai ya sakata a farinciki ba kuma face auren Jaish, ta ji daɗin wannan lamari kuma zuciyarta ta kaunaci Mahnoor fiye da tinanin mai tinani, dik wasu qualities da ake san mace ta haɗa Mahnoor ta haɗa shi, tana da tabbacin idan King ya ganta shi ma ba zai yi ja in ja da zancen ba, wuyarta ya yarda ta ganta ɗin ne kawai. Sun ɗauki a kallah 30 mins a cikin ɗakin suna zuba love ɗinsu suna soyewa kafin ya sanya sleeping dress ɗinsa su fito rungume da juna. A bakin bed suka zauna, sai a lokacin ya lura da babyn dake kwance a saman bed ɗin, cike da mamaki ya jefa mata tambayar babyn waye? Daga ina ta ɗauko shi?. Gyara zama ta yi suna fuskantar juna, cikin nitsuwa ta fara zayyane mashi komai da komai har da zuwanta gidan bappa da abin da ya faru zuwa ga kawo mata baby da uncle Jahiz ya yi. Girgiza kai King ya fara yi kafin ya ce. "Hakan ba zai taɓa yiwu ba! Jaish bai kai yin aure yanzu ba, kuma koda ya kai ɗaya daga cikin ƴaƴan uncle Rahab nike san ya aura, babu ɗana da zai auro mun mace daga waje, dik cikin gida zasu koma su yi aure, dan haka wannan aure ban aminta da shi ba, yazama dole a kwancesa. Shiru momma ta yi tana sauraransa har ya gama faɗarsa, sannan a nitse ta ce. "Dik hukuncin da ka yanke dai'dai ne bana da ja a kan hakan, dan nasan ba zaka taɓa san abin da zai cutar da ƴaƴanka ba, dan gobensu ya yi kyau zaka zaɓa masu mata masu inganci, amma ina san ka mun wata alfarma"......... Ta kai karshen maganar idanunta a kan face ɗinsa. A taƙaice ya ce. "Wace alfarma kenan". Fuska a ɗaure ya yi maganar. "Ina san ka bani sati guda, ka yi shiru a kan maganar har na tsawon sati guda, sannan sai na gabatar maka da matar tasa, idan har bata da qualities da kake buƙata a tattare da matan da kake san ƴaƴanka su mallaka to zan aminta da ka warware auren a mayar da ita kasarsu!". Momma mace mai hikima da dabara, ko me zata kulla masu ta buƙaci sati guda kuma? Mu je dai zuwa. "Rahilarh bafa zan yarda da batun auren nan ba, ni bana ma san ganinta, ban buƙatar hakan kawai a mayar da ita kasarsu a raba wannan aure, dan bana da buƙata". Ganin da gaske yake yi babu wasa kuma babu alamar zai yarda da Mahnoor gaskiya, sai ta fito mashi ta wata hanyar daban. Matsawa ta yi kusa da shi, a saman jikinsa ta kwanta, cikin salon kauna ta fara jansa da wasa, sam bata nuna ta damu da kalamansa ba, dik da ta damu ɗin a cikin ranta, tana kaunar Mahnoor tin daga kallon farko, ba zata taɓa bari a raba wannan aure ba. King sai wani ɓata rai yake yi yana wani ɗaure fuska, cigaba da yi mashi wasanni momma ta yi tana ɓalle botiran rigan jikinsa cikin salo mai jan hankali. Ai bai san time da ya saki face ɗinsa ya fara biye mata ba, dan dama ya kwana biyu yana dakonta kawai dannewa yake yi, ta ji matuƙar daɗin hakan, dama buƙatarta kenan, dan haka sai ta kara zagewa sosai wajen ganin tasa ya shiga wani irin yanayi kafin ta zuba kalaman da suke cikin ranta. Sai da suka yi nisa King ya afka duniyar sama jannati har da yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa yana zuba mata kalamai, yana sarrafata cikin kwarewa. Sai da ta fahimci an kai point ɗin da ba zai iya yi mata gardama ba, a wannan gaɓa komai ta ce zai amsa ne kawai, sai ta ce. "Ban tari numfashinka ba a ɗazun, kuma bana ja da hukuncinka a garemu gabaɗaya, amma dai wannan alfarma na nema da kabani sati guda, sannan ka yarda bayan sati gudan nan in gabatar maka da yarinyar, idan bata yi maka ba shikenana". Haba King ya shiga duniyar da ba'a iya magana sosai, sai kawai ya gyaɗa mata kai alamar ya yarda, da kyar ya iya amsawa da ya yarda. Wani irin daɗi ta ji da har yasa ta shiga kara rikita shi da kyau. Haka suka kashe junansu da soyayya na tsawon lokaci har suka raya darensu kafin babyn Khadija dake kwance a gefensu ya fara kuka. Da kyar King ya iya saketa ya koma gefe ya kwanta yana jin wani irin farinciki, ita kuwa ta fishi shiga farinciki saboda ta samu ya amsa mata buƙatarta, ko ya dawo cikin hayyacinsa bai isa ya musa mata ba, saboda ya rigada ya amsa, ta nan momma take cin galaba a kansa a kullum, amfani da karfin sha'awarsa take yi ta cinma buƙatarta, ba faɗa bare ɓata rai da kunci, cikin ruwan sanyi. (Ina team Ramish? Yanzu na gano a ina Yah Ramish ya koyo wannan iskancin na sanya sexy night sleeping dress, gadan jaraba aka yi,😅 da alama King ya gada wajen hegen feeling 😅ba ruwana kar ace na ce, bari in yi ta nan🥱 ) Gyara kayan jikinta momma ta yi, ta ɗauki babyn Khadija ta sauko kasan bed ɗin, King ya yi aiki iya aiki sai ya kwanta yana binta da ido har ta zago ta side da yake, dukawa ta ɗan yi, kyakkyawar sumbata ta bashi a kumatu tare da ce mashi good night. Zata juya ya yi saurin riko hannunta, idanunsa a kan face ɗinta, kamar mai raɗa ya ce. "Zaki dawo?". Me king yake nufi da zata dawo?...….......🙄 Kash ashe fa surukina ne baban Guyson ɗina, bari dai na yi shiru to kada ace na yi rashin kunya na je ɗakin sirirki da daddare na kallan mashi sirrinsa....😅 Momma da yake itama tana cikin yanayi mai sugar sai ta amsa da zata dawo. Sake hannunta ya yi tare da yi mata alamar ta matso da hannu. Yana yi kamar wanda yake a cikin maye. Ba musu ta matsa dab da face ɗinsa, sumbata ya bata a kumatu kai ɗumi yana kallan face ɗinta, miƙewa ta yi tana ɗan sakar mashi murmushi ta nufi waje. Sam king bai kalli babyn Khadija da kyau ba. Kai tsaye ɗakin mama Haulat ta nufa da babyn, yunwan dare ya tashesa. A saman dadduma ta isko mama Haulat tana karatun Alqur'ani mai girma, kwantar mata da babyn ta yi a saman bed, sannan ta ce. "Ki bashi madararsa yana jin yunwa, sannan da safe ki sameni a ɗaki ina da magana dake". Bata jira amsarta ba ta yi saurin ficewa dan ta koma wajen dearlyn love ɗinta su cigaba daga in da suka tsaya, dan basa gajiya da juna, momma tana shan gyara, kayan gyaranta daga Dubai ake kawo mata su, shiyasa King baya raga mata.................🥱 ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 4:00 na asuba, Jawad ne ya fara farkawa daga nannauyar barci da ya ɗaukesa tin karfe 3 na dare, barcin awa ɗaya ya yi, yanzu haka bai so farkawa ba ya daure ya tashi saboda tafiya da yake gabansu. Bai waiwayi Chuchu ba ya wuce toilet dan ya yi wanka ya yi shirin zuwa masallaci ya zo ya gabatar da rakatainil fajir. Sai zuba barchin wahala Chuchu take yi, ta jima bata samu barci irin na yau ba. After some minutes ya fito ya shiga dressing room. Arabs jallabiya ya sanya a jikinsa launin ash colar, cikin bedroom ɗin ya dawo. A hankali ya haye saman bed dan ya tasheta. Hannunsa dikka biyu yasa ya tallabota a kirjinsa, fuskarta ya zubawa idanu yana matukar jin tausayinta, Allah sarki ta sha kuka da kunci a lokacin da aka ce Rizwan za'a aura mata, bata gama warkewa daga wannan kukan ba ta ɗaura da na ɓatar Auta, har ta yi rama idanunta sun kara girma. Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallanta kafin ya matso da face ɗinsa dab da ita, ya ci burin dik ranar da ya mallaketa ba zai taɓa ɗaga mata kafa ba sai ya ɓareta a ledarta saboda ta jima kyanta yana rikitasa, ya jima yana mafarkinta suna chaskale, sai dai shi kansa a yanzu ba zai so ya yi mata komai ba saboda tashin hankalin da suke a ciki. Sumbatar ɗan bakinta ya yi hakan yasa ta ɗan motsa, kamar mai raɗa ya furta "Jannawad". Cikin magaggin barci idanunta a rufe ta ɗan yi miƙa kaɗan tare da amsa mashi da na'am. "Tashi ki yi wanka ki yi sallah sai mu tafi ko?". Eyelashes ɗinta ne suka fara kerma alamar tana san buɗe idanunta, sannan ta ɗan tsuke bakinta kaɗan. Sosai ya ji hakan a ransa, sai ya ji mamar ya manna mata kiss. A hankali ta waro idanunta a kansa, haka kawai ta tsinci kanta da sakar mashi cool murmushi. Sam bai yi expecting hakan daga gareta ba, ya yi zatan da kuka zata tashin masa kamar yadda ta yi barcin, amma sai yaga akasin haka. Wani irin bargon farinciki ya ji ta lulluɓesa har ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. A shagwaɓe ta ce. "Yah Jawad barcin fa bai isheni ba". Tsintar kansa ya yi da jin tongue ɗinsa ta yi mashi nauyi, kura mata idanu ya yi sosai, tin da aka fara maganar bikin Rizwan sai yau ya ji sanyi ta ratsa ransa. "Yah Jawad tinanin me kake yi?". Ta sake jefa mashi tambayar tana kai hannunsa saman kyakkyawar sajensa dake kwance luff. "Tinaninki nike yi my Jannawad". Cikin salon soyayya ya faɗi hakan ........ Kara ƙayata murmushinta ta yi, a hankali ta fara shafa sajensa izuwa saman lallausan kumatunsa. Wani irin shock ya ji har tafin kafarsa, tsikar jikinsa ne ta fara tashi yana jin wani irin bakon yanayi. "Yah Jawad Allah ina sanka sosai". A ɗan shagwaɓe ta faɗa. Da kyar ya iya cewa. "Da gaske?". Ya jefa mata tambayar yana kallanta kamar zai cinyeta da ido. Ɗan turo baki ta yi tare da girgiza mashi kai alamar a'a ba da gaske ba tana wurga mashi kallo mai cike da hararar soyayya, sanna ta zame hannunta daga kan kumatunsa irin ta yi fushin nan. "Sorry my Jannawad, kada ayi fushi dani, zumar soyayyarki na lasa yasa word ɗina suke kubce mun"............... Bata yi mashi magana ba, ta mayar da kanta saman kirjinsa ta kwnatar, ta rungumesa da kyau tana turo baki. "Meyafaru kuma rigimammiyata?". Ya yi maganar yana kai hannunsa saman face ɗinta. "Ni Yah Jawad mun ɓata fa". "Ba zaki iya ɓatawa dani ba ai". With confidence ya yi maganar. "Meyasa ka ce haka". Ta tambaya tana riko hannunsa dake saman kumatunta. Matso da face ɗinsa dab da ita ya yi, kamar zai raɗa mata magana a kunne, sai kuma ya canza hanya a in da ya kai ɗan bakinsa saman nata. Cike da so da kauna haɗe da salo ya fara bata hot kiss, abin da ya jima yake tsumayi, in baku manta ba har gizon yana yi mata kiss idanunsa suke yi mashi a baya kafin aurensu. Yana yawan mafarkin yana kissing na ɗan bakin nan nata, ashe zai yi hakan da izinin Allah. Bata hana shi ba, dan ita ma tana dakon wannan rana, lips ɗinsa suna burgeta sosai, dan haka sai ma ta tayashi, cikin nitsuwa ta fara bashi kiss mai zafi ita ma. Ba ƙaramin kara rura wutar sha'awarta a ransa ta yi ba, zame hannunsa dake cikin nata ya yi, cikin nitsuwa ya mayar saman kanta, a hankali ya zame hukar kayan barcin dake jikinta, gashin kanta ya fara watsawa yana ƙara matseta a jikinsa. Ita kuma hannunta ɗaya ta zira a bayansa, ɗayan kuma a saman shoulder ɗinsa, ta kara narkewa a jikinsa tana binsa da salo na musamman, ta datse idanunta irin wai kunyarsa take ji, shi kuma ya kura mata ido yadda abin zai fi kara mashi armashi. Sun ɗauki a kallah 5 mins haka kafin cikin dabara ta zame bakinta daga nasa, dan ta lura bashi da niyar saketa. A fili ya furta alhamdulillah, dan ya ɗanɗani abin da ya jima yake tsumaya. Ƙoƙarin barin jikinsa ta fara yi ba tare da ta buɗe idanunta ba. Dan rashin kunya wai kunyarsa take ji. Da sauri ya rikota, kamar zai saka mata kuka ya ce. "My Jannawad ina kuma zaki tafi". Da sauri ta buɗe idanunta jin yau ya yi magana a shagwaɓe, sai ta ji kamar bashi ba, ya yi mata kamar muryar guyson. Sarkafewa idanunsu ya yi cikin na juna, kamar zata yi kuka a shagwaɓe ta ce. "Yah Jawad wanka zan je in yi in ɗauro alwala fa". "Kasancewarki a jikina ya fi wankar, lokacin sallama da saura, Please stay with me ko da na 20 mins ne kin ji?". "Mezaka bani to idan na tsaya?". Ta yi maganar tana ɗaga mashi gera......"Mekike san in baki?"........ Manuniyar yatsarta ta ɗaga ta saita kirjinsa da shi. "Kai nike so". Haɗe goshinsu waje guda ya yi. "Ni ai mallakinki ne my Jannawad"...... "Yah Jawad kasan me?". Kai ya girgiza mata alamar a'a bai sani ba. Ɗan kawar da kallonta daga saman face ɗinsa ta yi, kamar mai raɗa ta ce. "Your lips is so sweet wlh, kuma fa....." Sai kuma ta yi shiru ta ƙasa ƙarisa maganar. "Kuma fa me?". Cike da farincikin jin maganarta ya yi tambayar, sai ya ji kamar ya maida ta cikinsa dan daɗi. Bata yi magana ba, sai ta ɗan miƙe kaɗan, ta kai mashi sumbata a saman lips ɗinsa. Ya fahimci wani kiss ɗin take so kuma tana jin kunyar faɗa mashi, wanda ya yi mata bai isheta ba, dan haka sai bai bari ta zame bakinta daga sumbatar ba ya capki lips ɗinta ya dasa daga in da ya tsaya. Ajiyar zuciya ta sauke dan ta ji daɗi, ya iya kiss mai mantar da mutum in da yake shiyasa ta nemi kari. A hankali ya kwantar da ita a saman bed ɗin bakinsu manne da juna. Rumfa ya yi mata da kirjinsa, ya sanya hannunsa a wuyarta yana ɗan shafawa izuwa shoulder ɗinta, a matse yake yana san taɓa tula tulanta amma yana shakkar yin hakan. Ita kuma ta tura hannayenta a cikin gashin kansa, cike da kaunarsa ta fara wasa da gashin, bukata ya biya ta mallaki abin kaunanta. Dai'dai lokacin da suke zuba wannan soyayya tasu shi kuma uncle Jahiz yana hospital wajensu Khadija, asuban farko ya tafi wajensu. Zee ta farfaɗo sai dai ta ki yin magana a gabansa, mamakinsa ne kuma ya hanata yin magana, saboda shi ne best player ɗinta a ƴan kwallan kafa, bata taɓa tsammanin zata gansa a zahiri ba, sai ma take ganin abin kamar mafarki kamar kuma zafin ciwo yasa yake yi mata gizo tin da shi ne a ranta. Sai dai kuma fa, ganinsa ya tayar mata da hankali a in da ya dawo mata da mutuwar babanta sabo, ta tina yadda suke kallansa ita da babanta a tv a tare. Yau kwananta uku da farfaɗowa, sai dai a kullum ya zo wajenta kuka kawai take yi idan ta gansa, taki yarda ta bashi dama ya yi magana da ita. Idan kuma ya bar hospital ɗin sai ta yi shiru har tana tambayar nurses ina ƴar uwarta da ɗanta? Kullun amsa ɗaya suke bata shi ne ɗanta yana cikin family part, ita kuma Khadija tana ƙarƙashin kulawar likitoci har yanzu. Kullum Zee bata gajiya da tambaya, jikinta yana ta kara warwarewa tana samun lafiya yadda yakamata, dan kwararrun likitoci ne suke kula da ita. •••••••••••••••• FOREST•••••••••••••••••🔥 Shiru ta tsaya tana kallansa bata motsa ba, yana isa gabanta ya jefar da takobin hannunsa a ƙasa ya ɗagata sama ya matsar da ita daga wajen, yana matsar da ita kifiyar da aka saitata aka harbeta da shi ya wucesu sai cikin ruwan koramar. Sauketa ƙasa ya yi tare da juyawa ga in da aka yi harbin kifiyar, sai dai kash bai ga ko alamar mutum ba, wanda ya yi harbin ya gudu ya bar waje. Amma wa kuke tinanin ya yi wannan harbin?. Dawo da kallonsa a kanta ya yi. Har lokacin bata motsa ba, idanunta a kansa babu ko kyaftawa. Ɗan lumshe idanunsa kaɗan ya yi. "Ki yi hakuri ranki ya daɗe". Har yanzu fa bai iya tina face ɗinsa ba'a rufe take ba. Ganin bata motsa ba yasa ya kai hannunsa saman shoulders ɗinta ya ɗan girgiza a hankali yana ambatar sunanta. Wani irin dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali. A fili ta furta. "Hoorain ban taɓa ganin kyakkyawa irinka ba, anya baka fi kowa kyau a duniya ba kuwa?". Ai a miliyan ya kai hannu saman face ɗinsa, jin bai rufe face ɗin nasa ba yasa ya ɗan yi ƙasa da kai yana ɗan ciza laɓɓansa alamar bai so haka ba. My people's dik yadda zan zayyana maku haɗuwar Hoorain ba zaku fahimta ba, kamar shi ya yi kansa, kyakkyawan gaske. Ga tsawo da cikar halitta, yana da kafaɗa mai faɗi, ƙirji mai tsari, ya sa ya zama kamar wanda aka zana. Fatar face ɗinsa fara ce kamar madara, hakan tana bayyana yadda yake mai tsafta da kamshi. yana da laushi da kyan gani, kamar ba mayaki ba, sai sheki skin ɗinsa yake yi, alamar yana kula da kansa sosai. Fuskarsa tana da siffar mai ladabi, very innocent haka, da ganin yana yin face ɗin zaka fahimci ba zai yi yawan magana ba, hancinsa mai tsari kuma dogo mai ban sha'awa, leɓɓansa na sama yana da ɗan kauri kaɗan, na ƙasa kuma ɗan laɓalaɓa haka, irin laɓɓan yana da masifar kyau. Idanunsa suna da siffa mai ɗaukar hankali, suna kama da almond, tare da fari mai tsabta da ban sha'awa Gashin kansa baƙinkirin ko, yana taɓo idanunsa kaɗan ta gaban goshinsa, amma yana da tsawo ta bayansa, yana wani irin sheki yana curlyn kamar na baby's, kamar yadda ake gani a yanayin fashion na zamani. Yana da kwantaccen saje bakin kirin ɗan madaidaici a gefe da gefen face ɗinsa. Yanayin nutsuwa mai ɗaukar hankali, akwai cikakkiyar kamala a face ɗinsa, amma yana cike da kwarjini da karsashi, tafasasshen jini na zakunan mayaƙa, ga ƙarfin zuciya. Wannan da baya sanya hukar yaki idan yana cikin jama'a, ba ya buƙatar yin ƙoƙari dan ya jawo hankalin mutane a kansa, kwarjininsa na halittarsa zata ja mutane kusa da shi. Hoorain ya haɗu matuka gaya. Ganin ya yi ƙasa da kansa bai furta komai bane yasa cikin hanzari ta kai hannayenta dikka biyu a saman lallausan kumatunsa, cike da tsantsar kaunarsa ta fara faɗin. "Hoorain ka yi magana mana". Auta ta so shi bata san kamanninsa bama bare ace yanzu ta gansa a yadda bata zata ba, dan ya wuci kyan da ranta yake ayyana mata, ai wani sabon kaunarsa ne ya kara narkuwa a cikin zuciyarta. Ba kamaramin sabon bakon alamari ya ji ba a lokacin da ya ji saukar hannayenta a saman kumatunsa, ƙasa iya ɗago kansa ya yi bare ya kalleta, ya rasa ma a wani matsayi zai ajiye kansa. "Hoorain dan Allah ka yi mun magana ka ji? Ka yi magana ko zuciyata zata yi sanyi". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. Shiru babu alamar zai ɗago kansa ma bare ya yi mata magana. Matsawa dab da shi ta yi. "Ka ji babu daɗi ne dan na kalli face ɗinka?". Nan ma bai amsata ba. "Ka yi hakuri ban zata dan na kalli face ɗinka zaka ɓata rai har kaki yi mun magana ba". Ta kai karshen maganar tare da zare hannayenta daga kumatun nasa, ranta ya ɗan sosu, da sauri ta juya zata bar wajen saboda wani irin kuka da ya zo mata mai wuyar dakatarwa, tana san shi amma yana walaƙantata har haka, ta yi magana yaki amsa mata, idan da yasan yadda wannan abin yake ƙona mata rai da ko kusa ko alama ba zai yi mata ba. Tana juyawa sai ji ta yi ya capki hannunta, cak ta tsaya tare da ƙoƙarin jiyowa garesa, da karfi ya fisgo ta faɗa saman warriors chest ɗinsa, saboda wani irin wutar santa dake azalzalar zuciyarsa, yau ya kai makurar da ba zai iya dannewa ba, zuciyarsa ta yi cikar da in bai bari ta yi amai ta amayar da abin dake cikinta ba zata iya fashewa, yau dai babu wani dama da zuciyarsa zata iya sake bashi, ji yake tamkar ya mayar da ita cikin ransa ko zai huta da abin da yake ji a ransa. Bata ankara ba ta jita saman faffaɗar kirjinsa, da sauri ta waro idanunta waje, abin da bata taɓa zata ba. Tana ƙoƙarin tantance gaskiya ce ko karya ta tsinkayo sayayyar voice a cikin kunnenta yana faɗin. "I'm so so sorry ranki ya daɗe, tuba nike yi, ba zan iya cigaba da danne abin da yake cikin zuciyata ba, ba zan iya shanyewa ba, dan haka ina mai baki hakuri da kalaman da zasu fito daga cikin bakina, ban san a yadda zaki ɗaukesu ba, na san matsayina da naki ba ɗaya bane, amma dik da haka ba zan iya ƙasa faɗa ba, ki yi hakuri, ki yi hakuri, ki yi hakuri". "Ina.............. Wayyo ya Auta zata ji idan ya bayyana mata sirrin dake ransa? Abin da ta jima tana tsumayi! Ya waɗan nan masoya zasu tsinci kansu a yau? To su dai suka sani, sai Monday, bari in je in kora maltinata mai sanyi in huce, nima zuciyata ta kwanta ta nitsu............🥱 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 18 Ina sanki, ina sanki soyayya maras misaltawa, soyayya mara iyaka, ina kaunarki, ina jinki a jinin jikina, a kowace second zuciyata tana bugawa da sunanki, kece kawai nike kallah in ji ni a wata duniya ta daban, kina so na ko baki sona wannan dik bai dameni ba, abin da nasani kawai shi ne ina sanki, kuma zan iya mutuwa a kanki, sannan zan cigaba da sanki har bugun numfashina na karshe!!". In out of control ya rinƙa zuba kalaman!. Tin da ya fara magana zafafan hawayen murna suka fara wanke mata fuska, fabaɗaya ji take yi kamar bata duniya, har wani iri take ji a cikin zuciyarta tamkar an ɗaura mata ice block ciki. Sambatun zafafan kalaman kaunarta ya cigaba da zuba mata babu kakkautawa, yau ya samu damar amayar da abin da ya kwashi shekaru yana cinsa a zuciya. Jin ɗumin hawayenta suna zuba a kyawawan fararen kafafunsa ne yasa ya dakata da zuba mata kalaman kauna, a hanzarce ya ɗan rabata da jikinsa dan ya tabbatar da kuka take yi ko akasin hakan. Ganin da gaske hawaye sun wanke mata fuska ne yasa ya yi saurin sakinta, kansa ya dafe sa karfi, cike da danasanin biyewa zuciyarsa ya amayar da abin dake ransa ya fara faɗin. "Dan Allah ranki ya daɗe ki yi hakuri! Ban yi tinanin kalamaina zasu yi maki zafi su sanyaki hawaye ba, kasa iya rike kaina yau na yi shiyasa, tuba nike yi". A tinaninsa dan ya ce yana sonta take kuka, yana ganin kamar zata ga ya ƙasƙantar mata da matsayi ne, bai kai ya sota ba shiyasa ya shiga bata hakuri!!. Duka ta kai mashi a kirjinsa da ɗan karfi. Cigaba da bata hakuri ya yi yana danasani, Allah sarki zuciyarsa har ta raunata ganin yadda ta shiga damuwa a ganinsa. Duka ta sake cigaba da kai mashi a kirjinsa tana kuka da hawaye bibbiyu, yana tsaye bai hanata ba, sai ma hakuri da yake bata yana faɗin ta dakesa sosai in dai har hakan zai sa ta huce. Cigaba ta yi tana yi tana ƙara sautin kukanta mai taɓa zuciyar mai sauraro. Sai da ta gaji dan kanta da dukansa, sannan ta kama rigarsa wajen saitin kirjinsa, ta ƙanƙame sosai tare da kwantar da kanta a kirjinsa tana wani irin shessheka mai taɓa zuciya. Cikin kuka mai sauti ta ce. "Why Hoorain? Why, why sai da ka azabtar da zuciyata, ka wahalar da ni sannan zaka bayyana mun sirrin dake ranka? Meyasa? Meyasa baka faɗa mun da jimawa ba? Menayi maka ka bani wahala har haka?". Tana maganar tana bubbuga kirjinsa dake kamar dutse. Shi dai shiru bai ce mata ko uppan ba, dan har yanzu bai fahimci a kan me take yin magana ba, ya ɗauka ya cuci zuciyarta ne da ya ce yana santa. Tsabar farinciki ta rasa a ina zata sanya ranta ta ji sanyi, a cikin tsakiyar kirjinsa ta cusa kanta, dunkule hannunta ta yi tana dukan kirjinsa da ɗan karfi ta fara faɗin. "I really love you Hoorain, ban taɓa san wani abin kamar yadda na soka ba, please ka soni ko bai kai wanda nike yi maka ba". Ina, ai ƙasa iya ɗaukar gangan jikinsa ƙafafunsa suka yi lokacin da ya ji kalmar i love you Hoorain daga bakinta, sai ya ji jikinsa ta yi mashi nauyi, hakan ya ja ya durkushe kasa a kan gwiwowinsa, kusan a tare suka durkushe kasar da ita. Kuka take yi sosai tana goggo kanta a cikin kirjinsa...........(DUKKA WANNAN DAƊI NE FA😅 GIMBIYA ZUNAIRA MANYA ƳAN LOVE, TA IYA BAWA FLOWER ƊINTA RUWA YADDA YAKAMATA🥱) Jin abin yake yi tamkar mafarki ba gaske ba, soyayya wata aba ce mai matikar kwarjini haɗe da karfin gaske wanda a duniyar nan zata iya zama abu na farko mai tsananin karfin da babu biyunsa, komai sai da soyayya ake yi, son Allah da Manzonsa ya ja zamu iya bada rayukanmu a kansu, haka zalika san iyayenmu yasa muke binsu sau da kafa, muke kuma burin ganin farincikinsu ko da zamu rasa namu farincikin mu yi bakinci, su umarcemu ko da bamaso haka zamu aikata dan son da muke yi masu, soyayya ta fi karfin dik tinanin mai tinani. Hannunsa ya kai da kyar ya iya riko nata hannayenta da take ta bubbuga kirjinsa ta rasa ina zata sanya ranta saboda daɗi. Yau ji yake yi kamar zai yi hawaye shi ma, idanunsa sun yi jajir kamar wuta. "Ranki ya daɗe da gaske kina sona? Da gaske kike yi?". Da kyar ya iya faɗar hakan. Kai ta gyaɗa mashi cikin wani irin tsantsar farinciki, ta kasa yin magana. Sake hannayenta ya yi tare da tallabo kanta da take ta gogawa a jikinsa, ya ɗagota suna fuskantar juna. Idanunta a rufe ruf sai hawaye dake ketowa kamar hanyar ruwa. Hannayensa ya kai saman face ɗinta. "Ranki ya daɗe ina neman alfarma a mun inzini in goge waɗan nan hawaye". Idanu a rufe cikin kuka ta ce. "Ka barsu su zuba my hero, ka kyalesu kawa, na farinciki ne". "To ai ni ganinsu a face ɗinki babban tashin hankali ne a gareni, ba zan iya jura ba". Wani irin sanyi ta ji ya kara ratsa zuciyarta. Hannayenta ta ɗaura a saman shoulders ɗinsa. "Dik yadda kake so ka yi my hero, ni dai nasan hawayen ba zasu dai'na fita ba, dan yau zuciyata ta karɓi sakon farincikin da bata taɓa karɓar irinsa ba, saƙon da ta jima tana jira, har mafarkinsa nike yi". Goge mata hawayen ya fara yi cike da tausayi da soyayya. Ina ai kin dakatawa suke yi kamar yadda ta faɗa, yana gogewa wasu suna zubowa, ya rasa ya zai yi, ji yake yi kamar an mallaka mashi ita. Zame hannunsa daga kumatun nata ya yi, da kyar ya miƙe tsaye, cak ya ɗauketa suka nufi wajen koramar nan, dan yaga da gaske hawayenta ba zasu dai'na zuba ba. A saman dutsen kusa da ruwan ya zaunar da ita, a kusa da ita ya zauna tare da sanya kyawawan fararen hannunsa ya taro ruwan dake zuba. Face ɗinta ya fara wanke mata yana cigaba da rarrashinta. Da kyar ya samu ta yi shiru, kasa cikin ruwan dake gangara izuwa wajen da yake taruwa ya tsaya, a gabanta yana kallan face ɗinta, har lokacin idanunta a rufe, da alama akwai ɗan kunyarsa a tattare da ita. "Ranki ya daɗe zaki iya buɗe idanu yanzu na gama wanke maki face ɗinki". A sanyayye sosai ya yi maganar. A cikin ranta ta furta sai kace an ce mashi saboda ya wanke mun face yasa na rufe idanu. Shiru a fili ta yi bata amsa shi ba, kuma bata yi kamar zata buɗe idanun nata ba. Yana tsaye yana kallanta unexpext wani tsuntsu mai bala'in kyau launin blue da ratsin yellow a wuyarsa ya sauƙa mashi a saman shoulder ɗinsa, hannu ya kai cikin dabara ya capko ɗan tsuntsun mai shegen kyau. Zuba mashi idanu ya yi yana kallonsa. Ya ɗan shagala da kallan tsuntsun ya tsinkayo voice ɗinta a ɗan sarkafe ta ce. "Ruwa nike san sha my hero". Ta yi maganar tare da waro idanunta wajen.... Ni kam na ce ai dole ki nemi ruwa gimbiya ƴar daddynta......🥱 Tana buɗe idanu ta yi arba ta kyakkyawar tsuntsuwar dake hannunsa, kara ɗan zaro idanunta waje ta yi, cike da yarinta ta saki murmushi ga hawaye basu gama bushewa ba. A hanzarce ta kai hannu zata taɓa tsuntsuwar. Ɗan ja baya kaɗan da ita ya yi alamar baya san ta taɓa kenan, cike da mamaki ta ɗago da kallanta a kansa. Tin bata nemi jin ba'asin hanata taɓawa da ya yi ba ya yi saurin cewa. "Amin afuwa, ina tsoron ya cizan mun kene yasa na ja baya". Sosai ta yi daɗi ya ratsa zuciyarta, irin wannan kulawa haka, ai sai yasa mutum ya mance a duniya yake, ya mance kowa da komai. "My Hero shi fa tsuntsu baya cizo, ya mun kyau ne sosai fa shiyasa zan taɓa". A ɗan shagwaɓe ta yi maganar, ga murya a ɗan dashe. Kai ya ɗan girgiza mata. "Ni dai gaskiya a'a, banyarda ba, kada in saki jiki baya ciwo ya zo kuma ya cijeki". "Shikenan to, dik yadda kace hakan za'ayi, amma na so riƙesa a kusa da ni in gani, dan yana da kyau". ....... Takowa step biyu ya yi ya kariso dab da ita, a hankali ya ɗan rage tsawonsa, sannan ya matsar mata da ɗan tsuntsun kusa da ita. "Ki gansa a kusa da ke, amma a hannuna". Iyayi ne fa kawai irin nata, dan kuwa tana tsoron tsuntsun, da ya matsar mata da shi kusa da ita sai ga shi tsoronta ya bayyana, wai da ita zata nuna ita jinin bamodare ne, wato jinin King, shi ne har da wani nuna bata tsoro a farko. Yanzu kuma sai ga shi ta koma har da ɗan ja baya, abin dariya ma shi ne ta ɗan kai yartsarta manuniya tana san taɓa jikin gashin tsuntsun, kun san yadda mutun yake dankwalar abu mai zafi ko? To haka take sanya yarsarta a miliyan tana ɗan taɓa gashin ta sake janyewa da gudu. Shi dai Hoorain hakan ba ƙaramin birgesa ya yi ba, a duniya dik abin da ta yi birgesa take yi, sai ma idan ta haɗa da murmushi, ya ilahi ya lilliahi, sai ya ji tamkar ta yi ta cigaba har abada su kasance a haka. SOYAYYA MUGUN WASA. Sai kallan face ɗinta yake yi, tana murmushi da guntun hawaye. Cigaba da wasa da tsuntsun ta yi tana taɓa shi kaɗan kaɗan. Zuciyarta ce ya raya mata yana kallan face ɗinta, dan haka sai ta ɗago kai da sauri. Aikuwa karaf suka haɗa idanu da shi, da sauri ya yi yunƙurin kawar da kallonsa. Yatsunta ta fyasta mashi a saitin face ɗinsa, hakan yasa bai kawar da kallonsa ba, ya cigaba da kallonta ko da akwai wani sakon da zata faɗa mashi. "Meyasa baka san haɗa idanu da ni my Hero?"........... Sake tsuntsuwar dake hannunsa ya yi ta tashi sama, sannan ya ce. "Zo mu je in baki ruwan da kika ce zaki sha". Make mashi kafaɗa ta yi. "Ni dai a'a, sai ka faɗa mun abin da yasa baka san mu haɗa ido". Ajiyar zuciya ya sauke, Auta ita ma ashe ta iya rigima da yake ganinta kamar ba haka ba, ashe dai ta iya ita ma. "A da ne bana san mu haɗa ido saboda ban san ya zaki fassara kallona a gareki ba, kuma ke ma kin san dokace da take a kanmu na haramta mana ɗaura kallonmu a kanku, kin san ba wani mayakin da ya isa yake da ƴancin ya kalleku, kin san hukuncin da yake kansa idan ya yi hakan, ni kuma bana iya ƙasa kallanki a dik time da muka haɗu, shiyasa idan kika ɗago kika kalleni nike kauchar da kallona". Ya kai karshen maganar yana mayar da kallonsa kasa kan kafafunsa dake cikin ruwan gudun. "To ai a da kace, yanzu kuma meyasa kake kin yarda mu haɗa ido?". A ƙagare da san jin amsa ta jefa mashi tambayar. "Babu wani dalili yanzu kam, na dai saba kaucewa a da ne yasa har yanzu ma nike yin hakan". Murmushi ta ɗan sakar mashi kafin ta riko hannunsa da ya harɗe a saman kirjinsa, a hankali ta sauko da ƴan kafafunta cikin ruwan da nufin ta miƙe tsaye. Warware hannunsa ya yi da sauri ya riko nata, a hankali ya taimaka mata ta sauƙo kasa. Unexpect ta sauke ƴan kafafunta a saman nasa dake cikin ruwan. Sosai ya ji wani irin har cikin ransa, ita kuwa sai ta yi baya kamar zata faɗi. A hanzarce ya sanya hannunsa ɗaya ta baya ya riko waist ɗinta. A wani irin slow ya dawo da kallansa saman face ɗinta, sai yaga ashe shi take kallo, yanayin yadda suka tsaya abin ya ƙayatar matuƙa, dama ga yanayin wajen fili ne na masoya, abin ba'a magana. Hannunta ɗaya da ya saki ya riko waist ɗinta da nasa ta kai saman shoulder ɗinsa, da yake ya ɗan rage sawonsa hakan yasa ta iya dafa shoulder ɗin nasa. A kusa da kusa suka kalli zuna, wani azababben kaunar juna ne ya kara ratsa zuƙatansu, sanyi mai ni'ima ya ratsa fatar jikinsu, dikkansu basu ki su dawwama a haka ba. "Hoorain". Ta ambaci sunansa a kurkusa kurkusa ba tare da ta zare kallanta daga kansa ba. Ya ƙasa iya amsa mata, saboda yadda ta yi magana a kusa tasa ya rasa control ɗinsa. He's in out of his control yanzu. "Idan nace zan faɗi kyanka tabbas sai dai na rageta, dan baki ba zai iya zayyana shi ba, meyasa ka ɗauki tsawon lokaci kana mun rowar ganinka?". Ta jefa mashi tambayar tana ɗaga mashi gera guda. Still dai da ido kawai ya bita, ya kasa iya amsawa. "To shikenan mu je ka bani ruwan sha tin da ba zaka yi magana ba". Ta faɗa tana sauƙo da hannunta daga saman shoulder ɗinsa izuwa damatsan hannunsa. Rike waist ɗinta da kyau ya yi, ya kara rage tsawonsa ya ɗauketa cak, bai yi magana ba, kuma ya gagara zare kallansa daga kanta. Ba komai yasa ya ɗauke wuta yaki yin magana ba face zai iya ketare iyakar musulunci idan ya ce zai cigaba da biye mata, dan haka shirunsa shi ne mafi a'ala a garesa!. Bai zame ko'ina da ita ba sai dab in da koramar nan take ta aman ruwa, saman wani dutse ya tsayar da ita a kan kafafunta, da yake dutsen yana da faɗi sai ya hau sama shi ma. Da kyar ya iya faɗin. "Wanke hannunki sai ki tara ruwan ki sha". Ya yi maganar voice ɗinsa tana sarkewa. Cikin wani irin shagwaɓa mai ɗaukar hankali ta furta. "Ni dai a'a ba zan iya ba, kawai ka cire ɗayan hands gloves ɗin nan naka ka tara mun ruwan da hannunka sai na sha". Wani irin bargon sanyin kauna ce ta ƙara lulluɓe zuciyarsa, ya ji matuƙar daɗin maganarta, ga shagwaɓarta dake ƙara kashe shi a koda yaushe ta yi, sai ya ji kamar shi kam an gana sallamarsa a duniya. A hankali ya zare hands gloves ɗayan, ya sanya hannunsa cikin ruwan dake zubowa, tas ya wanke hannayen nasa kafin ya fara tara mata ruwan. Ɗan ƙara matsawa gaba kaɗan ta yi dan ta samu damar sha yadda yakamata. A hankali ta fara sha, ji ta yi tamkar ruwan zuma ne saboda daɗi, ya ilahi ya lillahi, wato ruwan hannun masoyi daban yake in ji gimbiya Zunaira Auta. Zuba mata idanu ya yi sosai yana ganin yadda take shan ruwan gwanin ban sha'awa. Har ta ƙoshi ta cire ɗan bakinta bai farga ba, sai ji ya yi tana faɗin. "Ga shi nima na tara maka da hannuna ka sha". Mamakinta ne ya ɗan kama shi, wai ba ta ce ba zata iya tara ta sha ba? Ya aka yi ta iya tara mashi?...............Ni kuma na ce kanta ne ba zata iya tarawa ba, amma heronta tsab zata iya tara mashi ya sha cikin nitsuwa. Sam baya jin ƙishin ruwa, amma da yake da hannunta mai tarin albarka ta tara mashi nan take ya ji wani irin ƙishin ruwa ta kamashi. Matsawa ya yi ta bayanta, ya haɗe hannayensa da nata, ya tallabo nata cikin nasa kenan, ya kwanto da kansa ta gefen shoulder ɗinta, cikin nitsuwa ya kai bakinsa ya fara shan ruwan. A hankali ta juyo da kallanta a kan wuyarsa, da yake yana da tsawo sosai sai wuyarsa ma ta zamana tana da tsawo da kauri. Bayan wuyarsa wani irin bakin gashi mai curlyn ne a kwance a wajen, gwanin ban sha'awa da burgewa. Ji ta yi tamkar ta kai hannunta ta taɓa wannan gashi, ya tafi da imaninta. Shagala ta yi da kallansa bata ankara ba sai ji ta yi ya hura mata iskar bakinsa a fuska yana ɗan limshe idanu. Ajiyar zuciya ta sauke, bata san time da wani haɗaɗɗen murmushi ya subce mata ba. Shi dai bai yi murmushi ba, kuma babu alamarta ma a face ɗinsa, amma ya ji sanyi a ransa na sakin murmushin da ta yi. Ya shagala da kallan murmushinta unexpext ya ji saukar ruwa a face ɗinsa. Wani irin jan numfashi ya yi tare da limshe idanu, a hankali ya saki numfashin. Ita kuwa kara faɗaɗa murmushin nata ta yi tana ƙara watsa mashi ruwan. "Sai ka yi ta kallanwa daddyna ƴan'matansa ba tare da ka nemi izni ko ka biya ba ko? To ni ba zan bar hakan ta cigaba da faruwa ba". Cewarta kenan, tana magana tana ɗan watsa mashi ruwa....... Oh my people's kun ji Auta da tsara zance, wai ayi ta kallewa King ƴarsa ba'a biya ba. Hannu ya kai saman face ɗinsa, a hankali ya sharce ruwan da ta watsa mashi ɗin, sai ya yi kamar ya datse idanunsa da karfi ya rungumeta a jikinsa kawai kada ya saki idan ya so daga baya ya yi istigifari, dan tana tafiya da imanisa, sai ma idan yana kallan lips ɗinta a yayin da take magana, ohohohoho, ji yake tamkar ya sa hannu ya matse ɗan bakin nan nata ya yi ta sha ba hutawa. Zuba mashi ido ta yi tana jiran taga me zai yi next da ya datse idanu kam haka. A miliyan ya zaro mata idanunsa. Ai tsabar tsorata sai da ta yi baya baya wai zata gudu sai ta tafi luuuu zata afka kasa cikin ruwan dake wajen. A miliyan ta kai hannunta ta capki rigarsa ta saitin kirjinsa, unexpext ta damkosa ɗin, dan haka bai rike jikinsa ba, sai suka tafi a tare suka afka cikin ruwan da karfi. Da karfi ta riƙosa ta kuma datse idanunta gam tana jiran ta jisu a cikin ruwan kawai. Kafin su kai cikin ruwan ya yi zafin namar janyota jikinsa shi ya faɗi ƙasa cikin ruwan, ita kuma ta faɗa saman kirjinsa. Kusan a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya. Shiru suka ɗan yi na ɗan lokaci, da yake ruwan wajen ba zurfi sosai. Ita ta tara motsawa bayan ɗan lokaci, da kyar ta iya tashi daga jikinsa. Shi ma da kyar ya iya miƙewa, hannunta ya riko tare da cewa. "Zo mu je mu leƙa Pretty". Ya faɗa mata hakan ne ba dan komai ba face dan su bar wajen, yana tsoron ta jefa shi cikin wani halin da zata sa ya kauce koyarwar addininsa. Wucewa suka yi izuwa in da ya tsaya ɗazun yana wanke takobinsa. Hular yakinsa ya ɗauka tare da hands gloves ɗinsa ɗaya. Yana ƙoƙarin maida hular a kansa ta yi saurin sanya hannunta a kumatunsa. Hakan yasa ya tsaya yana kallanta. Girgiza mashi kai ta yi alamar bata san ya saka. "Meyafaru?. Baki san in saka ne?". Murya can ƙasa ƙasa ya yi maganar.......... Kai ta gyaɗa mashi alamar e bata, ta yi hakan tare da karɓe hular ta wuce gaba. Shiru ya ɗan tsaya kamar wani mai tinani. Da yaga ta ɗan yi nisa a tafiya sai ya yi saurin bin bayanta suka nufi wajen Pretty. Tun daga nesa Auta ta hango babu Pretty a wajen, hakan yasa ta ƙara ɗaga kafa dan ta isa wajen da sauri, shima cikin zafa ya kara sauri dan isa wajen, saboda a ɗan zamansa da Pretty kafin Auta ta farfaɗo sun saba, kunsan halin Pretty da san jiki da shagwaɓa, hakan yasa suka yi sabo, har fargabar isa wajen yake yi, dan ba zai juri rashin samunta a wajen ba. To nima dai bari na leƙa Black world wata kila kafin na dawo sun samu matsa, amma ina kuke tinanin Pretty ta tafi? Ko waye ya ɗauketa?. ••••••••••••••BLACK WORLD••••••••••••🔥 Wani irin haɗaɗɗen ɗaki ne wanda yake tamkar hospital, komai da kuka sani wanda ya danganci kula da lafiya cikin gaggawa akwaisa a cikin wannan ɗaki, ga bed na majinyata guda uku a ciki manya manyan suna shinfiɗe da kyakkyawar bedsheet na alfarma. Na'urorin gwaje gwaje da na bincikar cuta dik akwai su. Komai na cikin ɗakin nan white color ne, ɗakin ya haɗu matuƙa, ga shi ko'ina tsab tsab sai tashin daddaɗar kamshi yake yi tamkar ba ɗakin jinya ba. Tsaye yake a gaban bed ɗin da take kwance, yana sanye da long coat fari tas har zuwa gwiwarsa, daga ƙasa wandon jeans ne mai bala'in tsada a jikinsa, idanuwansa na sanye da wata iriyar na'ura mai kama da glass, idan ka ganta zaka yi zatan glass ya sanyawa dan fashion ne, amma ba haka bane, na'ura ce da ake iya ganin cikin jikin mutum dan bincike. Duniya ta cigaba sosai, dik in da ya tsayar da idanunsa a nan na'urar zata ɗauko mashi dik abin dake waje a cikin fata da tsoka. Ya zubawa wuyarta idanu yana kallon yadda wani irin kululun jini bakin kirin ya taru a wajen, ba komai ya haifar da shi a wajen ba face take mata wuya da ya yi a daren jiya. Ba ƙaramin kyau Black Tiger ya yi a cikin wannan shiga ba, wlh kamar ka zauna ka tasa shi gaba ba ci ba sha ka yi ta kallansa babu kawar da ido. Ita kuwa tana sanye da kayanta na jiya ɗin, ba'a canza mata ba, Sweetie ta ji wuya maras kunya, da ta ce bata ji ai. Hannunsa dake cikin white hands gloves ya kai saman wani kyakkyawan table dake kusa da bed ɗin wanda yake shake da kayan aiki da dik wani abin da zai buƙata. Cotton and zolpidem ya ɗauko, fasa zolpidem ya yi, cikin kwarewa ya kai hannunsa saman ɗan bakinta, da ɗan karfi ya buɗe bakin nata ya ɗaura mata kwayar zolpidem ɗaya a saman tongue ɗinta, sannan ya sanya cotton dake hannunsa a saman bed saitin wuyar tata ta yadda jini ba zai taɓa bedsheet ba idan ya fasa wuyar tata. Scalpel ya ɗauko don yin yankan, ko ɗigon tausayi babu a ransa yasa wannan Scalpel ɗin a saman fatar wuyarta, ɗago idanunsa ya yi ya kalli face ɗinta na ƴan sakanni kafin ya mayar da kallansa a saman wuyar tata. Cikin nitsuwa ya yanka fatar wuyar yanka mai ɗan girma. Nan take wani irin jini jajir ya faso hanya, wai a haka ma fa ta gefen wuya ne jinin ya taru ba ta gaba ba. Wani cutton ya ɗauko mai ɗan girma ya fara goge jinin dake bulbula kamar famfo. Tiyata fa likita guda ɗaya baya yinsa, saboda babban aiki ne, dole sai da taimakawan wasu a kusa suna miƙo maka wasu abubuwan, amma shi saboda kwarewa shi kaɗai yake yinta. Ganin jinin yaki raguwa ya samu ya yi aikinsa yadda yakamata ne yasa ya ɗauko suction device dan tsotse jinin dake waje a hankali. Nan take kuwa jinin ta tsotse. Sake ɗauko ecy da hemostat ya yi dan ya tsaida jinin da zasu iya yi wa aikinsa barazana daga ƙananan jijiyoyi. Cikin nitsuwa ya sake sanya Scalpel ya yanka namar ciki in da jinin ya taru. Nan take jini bakin kirin ya fara zuba, kurawa namar wajen ido ya yi, sai yaga wajen ya yi wani irin dark brown haka alamar kamar ya samu matsala, ya taketa sosai ne wlh. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, dan ya gano dole ya yanke namar dake wannan wajen, dan haka sai ya ɗauko electrocautery bayan da wannan bakin jinin ya gama zuba. Amfani da shi ya yi ya yanke namar dake wajen haɗe da tsotse jinin tas. Dik da tana sume sai da ta tsuke fuska alamar azaba. Tsab ya fitar da jinin kafin ya kara sa cotton fari tas mai tsabta ya kara tsabtace wajen. Sannan ya ɗauko needle holder da zaren tiyata dan ɗinka wurin. Ko kaɗan babu tausayi a ransa, haka ya ɗinke mata wajen tas ya kuma sanya plaster, daga nan ya tattare dik wasu abubuwan dake wajen ya mayar da su mazauninsu, ya ɗauki s-z ya matsar da shi kusa da shi, sannan ya zare hands gloves dake hannunsa. Ya yi amfani da s-z a hannun nasa dan tsabtaceta. Cikin kwanciyar hankali ya ɗauki remote ya kashe A.c dake ɗakin mai gabaɗaya. Sannan ya cire coat dake jikinsa. Yana cirewa wani Robbot ɗaya daga cikin masu yi mashi aiki ya matso ya karɓi coat ɗin, shi kuma ya nufi waje da sauri cikin zafa abinsa. A ɓangaren Ronnie kuwa, tun da ya yi wannan barci na dare jiya sai da rana ta take sannan ya iya farkawa. Da sunanta a bakinsa ya farka, a razane kuma. Sai dai kuma da kyakkyawar fuskar yayansa ya fara yin tozali ba ita ba. Hankali a tsananin tashe ya ce. "Yaya where's Sweetie?". Black Tiger yana zaune a gefen bed ɗin yana kallansa, yana sanye da kayan shan iska da suka kara bayyanar da kyakkyawar surar jikinsa, shi kuma ya kara haska kayan yadda yakamata. Miƙewa tsaye ya yi ya bar wajen. Cikin Zafa Ronnie ya miƙe zaune a saman gadon, hankalinsa a tsananin yashe ya ce. "Please big bro where's Sweetie? Talk to me please and please". Hankalinsa a tashe ya yi maganar. Black Tiger bai goge mashi tinanin kwakwalwarsa bane kawai saboda Sweetie tana raye, a tinaninsa ta mutu shiyasa ya yi niyar shafe mashi brain, ganin tana raye yasa bai yi hakan ba, ya ɗaga masu kafa. Ƙasa Ronnie ya diro, da sauri ya bi bayan yayan nasa yana cigaba da bashi hakuri da ya faɗa mashi ina Sweetie take, har kuka sai da ya yi, ya cigaba da magiya. Dik kaunar da Black Tiger yake yi mashi yaki faɗa mashi in da take har tsawon sati biyu cir, har zazzaɓi Ronnie ya yi amma Black Tiger yaki kula shi ya faɗa mashi ina yake, shi da ya yi mata aiki dai yana zuwa ya dubata ya canza abin da yakamata a canza, amma yaki sanar da Ronnie har sai da ta farfaɗo cikin ƙoshin lafiyarta, sannan ne ya faɗa mashi tana cikin wannan ɗaki. Ɗakin ma a cikin bedroom ɗinsa take ta wata hanyar sirri da aka yi ta da da glass. Ni kam na ce ko ba komai Sweetie ta ciri tuta tun da ta shiga wannan ɗaki da iya shi da Ronnie kawai suke jinya a ciki, ɗaki na musamman, amma saboda Spender sai ga shi ita ma yau ya kasance a ciki, ɗakin da da ace mutuwa tana da magani to da tabbas za'a iya samun maganinta a cikin wannan ɗaki, saboda kwarewarsa a iya aiki. Sai dai wani abin da baku sani ba, Black Tiger ya fahimci Sweetie ba zata bashi haɗin kai wajen mallakar Spender ba, dan haka ya fara tinanin zai yi mata aiki wajen zare tinanin kwakwalwarta ya sakawa wani daga cikin Robbot ɗinsa dan ya samu Spender. Idan kuma ya yi mata wannan aiki to tabbas ba zata tashi ba, yanzu haka ya sanya a kowacce irin yanayi a shigo mashi da kayan aikin cikin kasarsa domin ya kaddamar da wannan aiki, saboda ya ga Sweetie fa ƴar a mutu ce, bata tsoron mutuwa bare ya yi mata barazana da shi ya ci galaba. Abu mai sauki kawai ya cire ƙwaƙwalwarta ya yi dashenta ga Robbot ɗinsa, sai dai kuma fa, in ya cire ƙwaƙwalwarta ya haura 30 mins bai yi saurin sanyawa robbot ɗin ba to zasu rasa tinaninta, dan kwakwalwar zata dai'na yin aiki kwata kwata......... Babbar magana. Akwai matsala fa. Jin in da take yasa bai wani ɓata lokaci wajen kai kansa gareta ba, a lokacin ta kai sati da farfaɗowa, da yake ciwon ma ba wani babba sosai bane har ta samu sauki ba laifi, tana iya yin magana dik da ba wani sosai ba, kuma Allah ya taimaketa babu wani jijiya da ciwon ya taɓa. Tana ganin Ronnie ta yi saurin miƙewa zaune, dama shi take dakon jira tsawon kwanaki, tun da ta farfaɗo bata ga kowa a ɗakin ba, dan Black Tiger ya daina zuwa tin da yaga ta farka. Ta rasa ina zata sa ranta, ta kwana ta wuni tinanin ina Ronnie yake, bata tinanin a in da take kamar yadda take tinanin a ina Ronnie yake. Shi ne yasa tana ganinsa ta yi gaggawar miƙewa zaune, shi ma da sauri ya ƙarisa cikin ɗakin. Yau satinsa biyu da musulta amma ko sallah bai taɓa yi ba, dan bai san yadda ake yi ba, ita da zata koya mashi gata a kwance bai ma san ina take ba sai yau. Dan haka yasa bai yi ba sam sam, kuma a ƙagare yake da ta koya mashi ya yi ɗin, dan addinin ta ratsa zuciyarsa sosai. Tsabar farinciki yana zuwa saman bed ɗin ya haye, cike da farinciki ya fara yi mata sannu yana kara bata hakuri, zuciya a karaye ya ce. "Sweetie yaya yafi karfinmu, ba zamu iya da shi ba, kawai ki barshi mu hakura". Ya yi maganar tare da riko hannunta yana murnar bata mutu ba. Kai ta girgiza mashi, cike da kwarin gwiwa ta ce. "Bai fi karfinmu ba, kuma bai isa ya fi karfinmu ba, saboda mu Allah muka rike, da izinin Allah zamu canza yayanka, babu gudu ba ja da baya sai ya musulunta, dik azabtarwa da zai yi mana matuƙar ina numfashi ba zan janye kudurina ba". Zaro idanun Ronnie ya yi sosai, cike da tsoro ay ce. "Sweetie kin ga abin da ya faru dake? Baki tsoron idan ya zo da ƙarar kwana ki rasa ranki?". Ko a jikinta ta ce. "Tabbas idan na mutu a wannan hanya sai na fi kowa farinciki, a kan jahadi na mutu, a kan haryar isar da saƙon Allah da hidimtawa addini na mutu, dik wanda ya mutu a kan wannan hanyar ya yi shahada Ronnie, dik kuma wanda ya yi shahada makomarsa aljanna ce, dan haka babu gudu ba ja da baya, a da ina tsora ce da hakan, amma yanzun na kara samun kwarin gwiwar zan iya". Sosai ya yi mamakin jin kalamanta, ya san da farko a tsorace take, to yanzu menene ya bata confidence har haka?. "Kana mamakin menene ya kara mun kwarin gwiwa kenan ko?". Ta jefa mashi tambayar ne ganin cewa ya afka duniyar tinani. Kai ya gyaɗa mata alamar e abin da yake tinani kenan. Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. "Ba komai ne ya kara mun kwarin gwiwa ba face wasu abubuwa da na gano dangane da yayanka". Like wow ya zaro idanu, a ƙagare ya ce. "Wani irin abubuwa kenan?". Ɗan girgiza kai kaɗan ta yi alamar ba zai gane ba kenan, sannan ta ce. "Ba lallai ka fahimta ba, amma dai na gano cewa yayanka yana da bala'in saurin fusata, na biyu kuma baya saurin sauka idan ya yi fushi, na uku kuma tabbas bayan zuciyarsa fara ce, gaban ce aka dabaibayeta da bakar fenti, tabbas idan muka yi galaba a kansa mutane dayawa zasu ji daɗi su huta, ina da yakinin akwai abin da ya rikiɗar da shi izuwa bakin mugu....." Tarar numfashinta ya yi da cewa. "Ai na faɗa maki tsananin kaunar mulki ya rikeɗar da yaya izuwa mugu". Kai ta girgiza mashi alamar a'a, sannan ta ɗaura da cewa. "Ba tsananin kaunar mulki bane ta rikiɗar da shi, akwai abin da ya saɓa, tabbas yana san mulki, amma bayanta akwai abu mai karfi da ya rikiɗar da shi, tabbas zan gano ko menene nan na da jimawa ba dan saukaka aikin mu". Babbar magana, amma me kuke ganin ya rikiɗar da Black Tiger izuwa azzalumi idan ba giyar kaunar mulki ba?. "Sweetie zaki iya kuwa?". A tsorace ya jefa mata tambayar. "In Sha Allah zan iya, samun kwarin haske da na yi a kansa ba ƙaramin taimaka mun zai yi ba, kaga yanzu zan san ta yadda zan gudanar da aikina a kusa da shi, zan san ta yadda zan guji ɓacin ransa da zai iya sakawa ya cutar da ni, sannan zan koyi yadda zan sarrafa ɓacin ransa a dik lokacin da Black heart ɗinsa zata motsa, yanzu ka koya mun yadda zan yi amfani da magic ɗina, dan shi ma zai taimaka mun wajen ganin na sarrafa Black heart na yayanka". Shi kansa a yanzu ya samu kwarin gwiwa jin kalamanta, ya ji kuma kamar zasu yi nasara, dan haka sai ya ce. "Zan koya maki amfani da shi, amma yanzu dai ki bani wani amsa da tin last week nike ta san sanin shi, daga nan sai ki bani labari a kan bayyanar Imam Mahadi, sai ki koya mun yadda zan yi ibada". "Yayanka baya kallanmu ko?". Ta jefa mashi tambayar cike da damuwa tare da addu'ar Allah yasa Black Tiger bai gansu ba, ta manta ne kwata kwata ta saki baki tana ta magana. "Nan cikin ɗakinsa ne, kuma na faɗa maki yana iya kallan ko'ina a cikin birnin nan amma ban da cikin ɗakinsa, dan yana ganin wannan mallakinsa ne komai dake ciki sai da izininsa zai motsa". Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙa godiya ga Allah da yasa a ɗakinsa suke, sannan ta ce. "Me kake san tambayata tin last week?". MY BEST PART AGAIN💘🦋 "Kin san na faɗa maki ina kaunar annabi Isa sosai, to shi ne fa na duba cikin litattafan addinin Kiristanci wato Bible dan na duba tarihinsa da ƴan uwansa, a nan ne na duba tun daga kan Annabi Ibrahim wato daga tushensa kenan, tsawon sati ina bincike ina karantawa, sai da na zo kan ƴaƴan Annabi Ibrahim ɗin ne na rikice, abin ya tsaya mun a rai ina san sanin gaskiya". Ko kaɗan bata yi mamakin jin maganarsa ba, kuma bata so ta ji me ya rikita shi ba, dan a tarihin Annabi Ibrahim akwai abin mamaki, tasan bai wuce batu a kan Annabi Isma'il da Annabi Ishaq bane, dama su tarihinsu yana da ban mamaki da ɗan rikitarwa, sai ka yi karatu mai zurfi zaka iya ganewa, shi kuma bai zurfafa ba dole ya ɗan rikice. "Kin san me ya rikitar da ni?". Ya katse mata tinani ta hanyar jefa mata tambaya. Kai ta girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba.. "Abin da ya rikitar da ni shi ne, ance Annabi Ishaq shi ne rushen bani Isra'ila, shi kuma Annabi Isma'il shi ne tushen larabawa, kuma naga dikkansu ubansu ɗaya ne wato Annabi Ibrahim kenan, to ina san ki babbance mun ya aka yi zuri'arsu ta banbanta bayan kuma iyayensu guda ne, basu taso dikka a matsayin tushen larabawa ba, ya aka yi bani Isra'ila suka fito a tushen larabawa kuma?". Ɗan gyran murya ta yi, wuyarta ya fara ɗan yi mata zafi, saboda jimawa da ta yi tana magana, bata gama samun sauki ba. Abin mamakin kuma shi ne Ronnie fa bai samu damar ganin ciwon wuyar nata ba, sam bai gani ba, shi a tunaninsa ma zazzaɓi ko ciwon kai ya kawota wannan ɗakin, shiyasa kuka ga hankalinsa bai wani tashi sosai ba, da ya gani ai da tashin hankalin da zai shiga abin zai sha gaban tinani, sanin zai shiga damuwa yasa Black Tiger ya yi amfani da magic wajen rufa mashi ciwon ya hanasa gani. Kuma da ya ga ciwon na zai sanyata yin surutu dayawa ba. Cikin nitsuwa da sanyin murya ta fara faɗin. "Haƙiƙa Annabi Ishaq da Annabi Isma'il Alaihimus Salam sun kasance ƴaƴan Annabi Ibrahim (AS) ne, amma sun bambanta ta fuskar zuriyarsu da yadda aka danganta su da al'ummomi. Ga bayanin yadda suka banbanta da dalilin da ya sa Annabi Isma'il (AS) ba a danganta shi da Bani Isra'ila ba ya kasance shi ne tushen larabawa". Ɗan jan dogon numfashi ta yi kafin ta ɗaura da cewa. "Annabi Isma'il (AS) ɗan Annabi Ibrahim (AS) ne daga mahaifiyarsa Hajara, wacce ta kasance daga ƙasar Misra. Zuriyar Annabi Isma'il kuma ta yi ƙaura daga Misra zuwa yankin Makkah, inda aka kafa zuriyar Larabawa ta asali keman, wato Larabawan Adnaniyya. Annabi Muhammad (SAW) fiyayyen halitta kenan shi ma ya fito ne daga zuriyar Annabi Isma'il (AS)". "Annabi Ishaq kuma, ɗan Annabi Ibrahim (AS) daga mahaifinsa Sahra, wacce ta kasance matar farko ta Annabi Ibrahim (AS). Zuriyar Annabi Ishaq ta ci gaba da rayuwa a yankin Sham (Palastine a yanzu kenan) daga cikinsu ne Bani Isra'ila suka fito, waɗanda suka hada da Annabi Ya'qub (AS) mahaifin Annabi Yusuf kenan". "Wannan suna na bani Isra'ila yana nufin zuriyar Annabi Ya'qub (AS) shi Annabi Yaqub ɗim shi ne Isra'ila, ainahin sunansa kenan Isra'ila, waɗan nan ƴaƴansa goma shabin nan da suka cutar da kaninsu Annabi Yusuf su ne suka ci sunan bani Isra'ila, wato yayan Isra'ila kenan. Dan haka dik manzannin da suka fito daga cikin zuriyar Ya'qub, irin su Annabi Musa, Annabi Dauda, Annabi Sulemanu, Annabi Isa (AS), duk daga zuriyar Annabi Ishaq (AS) suka fito, kuma sunan bani Isra'ila ya shafesu". "Annabi Isma'il ba ya cikin zuriyar Isra'ila saboda shi ba ɗan Annabi Ishaq ba ne, kuma ba daga zuriyar Ya'qub yake ba. Dan haka Annabi Isma'il (AS) shi ne asalin zuriyar Larabawa waɗanda suka rayu a yankin Makkah". "A taƙaice yadda zaka fi ganewa shi Annabi Isma'il (AS) ya yi rayuwa a Makkah, kuma an kafa al'adar ibadar Hajji tare da mahaifinsu Annabi Ibrahim (AS). Annabi Ishaq (AS) ya rayu a Palastine kuma ya zama tushen addinin yahudawa da kiristoci, ta hanyar zuriyarsa Isra'ila. Saboda haka dik wanda ba ya cikin zuriyar Annabi Ya'qub, ba a kiransa Bani Isra'ila, to kaga Annabi Isma'il (AS) ba shi da alaƙa da zuriyar Ya'qub saboda shi wani reshe ne na zuriyar Ibrahim (AS) wanda ya yi rayuwarsa a yankin Larabawa". "Alqur'ani mai girma ma ya ya yi magana a kan, cikin Suratul Saaffaat, aya ta 112 zuwa ta 113, Allah ya bayyana cewa Annabi Ibrahim (AS) ya kasance asalin dukkan Annabawa, amma Allah ya sa zuriyarsa biyu daban daban, haka cikin suratul Maryam Allah ya bayyana Annabi Isma'il a matsayin manzo ga Larabawa, ka fahimta ko akwai sauran abin da baka gane ba?". Ta yi maganar tana kallansa. Sosai Ronnie ya fahimci dik abin da ta faɗa, kuma hakan tasa ya kara ganin girman Allah matuƙa, ya samu karin ilimi, yanzu yasan cewa ga daga zuriyar da Annabi Isa ya fito, ashe da Annabi Isa da Annabi Muhammad dik kakanninsu guda ne, ɗaya dai ya fito ta gefen Annabi Ishaq ɗaya kuma ya Annabi Isma'il, amma dikkansu kakansu ɗaya ne wato Annabi Ibrahim, lallai Allah da girma sa hikima yake. Ganin ya yi shiru bai bata amsa bane yasa ta ce. "Ko dai baka gamsu bane Ronnie?". A hanzarce ya girgiza mata kai haɗe da faɗin. "Sosai na gamsu, jinjinawa girman lamarin Ubangiji nike yi shi ya ja hakan, amma kema ai kinsa ba zai taɓa yiwuwa ki yi wa mutum bayani bai fahimta ba ko? Dole ya fahimta dik toshewar ƙwaƙwalwarsa, magana cike da hujoji yadda yakamata, kai ke dai kin ji daɗi". Ajiyar zuciya ta sauke, a nitse ta ce. "Kana burgeni Ronnie saboda son neman iliminka, kana san sanin dikkan abin da baka sani ba, ina addu'ar Allah ya kara buɗa maka ƙwaƙwalwarka, ka cigaba da bibiya kana tambaya ta dik wani abin da baka sani na, In Sha Allah idan na sani zan sanar da kai". Jinjina kai ya yi alamar to, sai ya ji tamkar ya kwace dikkan ilimin dake kanta ya zuba a nasa kan, baya gajiya da neman ilimi shi dai a rayuwarsa. Cigaba da jefa mata tambayoyi dangane da addini ya yi tana bashi amsa, haka suka kasance cikin farinciki har time da barci ya ɗauketa, kin fita daga ɗakin ya yi ya zauna yana ya kallanta cike da farinciki, Allah sarki har yanzu kuma bai san da ciwo a wuyarta ba. Ina kaunar addinina my people's, hakan yasa nake bala'in san part ɗin birnin Black world da kuma Sweetie, dan addinina, wayyo musulunci duniya ce jama'a, Allah ka kashemu muna masu yi maka bauta babu gajiyawa, kasa kalmar shahada ta zama kalmarmu ta karshe a duniya. ••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 KINGDOM OF POWER. Alƙalamina ba iya nishaɗantarwa da faɗakarwa haɗe da ilmantarwa kawai ya tsaya ba, har da bawa ƴan uwana Sa'a da zai canza ya kuma inganta masu rayuwa, ba sai kin zauna kina ta bani bani bani, za'a yi taro a cikin dangi kece a baya dan baki da shi, miji ya gaji da baki kuɗin shiga ƴan uwa, kina zaune dirshan ba zaki nemawa kanki mafita ba. To Alhamdulillah Allah ya bamu ilimin sanin wasu abubuwa, dan haka na zaɓi sanar da mutane na dan ki fita daga jerin bani bani da kike ta famar ɗaurawa miji, kema ki nemi kuɗinki a dama dake, ko ke budurwace a gida zaki rinƙa yin saarki dan ki ragewa mama da baba wasu ɗawainiya, fatana dai kowacce ta kasance cikin farinciki a rayuwarta duniya da lahira, Allah yasa mu dace, bari in koya maku yadda ake yin sabulun wanke kaya, yana da riba sosai, zaku samu na kanku, kuma shi abu ne wanda ake saya kullum dan wanke dauɗa, a yadda komai ya yi tsada idan kika haɗa shi kika ɗan yi ƙasa da farashi wlh ba ƙaramin alkhairi zaki samu ba, ki jikan na kasa dake a dik abin da zaki sa a gaba sai Allah ya jikanki ya dafa maki kema, wlh zaki samu alkhairi sosai a wannan sabulu, makota zasu yi ta shigowa su saya hankalinki a kwance kina ajiye ƴan kuɗaɗenki ki huta da bin miji ya baki ya baki. Ga abubuwan da zaki buƙata. Sabulun wanke kaya yana buƙatar kayan haɗi masu wanke ƙazanta sosai, musamman sinadaran da ke yaki da maiƙo da datti. Ga yadda ake haɗa shi: Kayan Haɗi. Caustic Soda shi wannan ana amfani da shi ne don samar da tushe (base) ga sabulun. Shi ne na farko. Sai ki samo soda Ash (Sodium Carbonate) Sai sulphonic Acid, wannan yana bayar da kumfa sosai. Sai STPP (Sodium Tripolyphosphate) sai Perfume don ƙamshi. Colorant Idan kuna son ƙara launi. Sai Ruwa don haɗin. Yadda zaku haɗa. Ki zuba Caustic Soda (10%) a cikin ruwa wanda ya danganta da yawan kayan haɗinki, sai ki barshi ya narke na tsawon awa 24. Shi ma Soda Ash (5%) ki saka shi a nasa ruwan daban ya narke na tsawon awa 12 zuwa 24. Haka shi ma STPP (2-3%) ki narkar da shi a nasa ruwan kamar dai sauran na baya. Idan suka kai waɗan nan awanni sai ki ɗaukosu, soda ash zaki juye cikin caustic soda, ki gauraya sosai, sannan sai ki juye sulphonic acid, shi ma ki gauraya sosai, sai ki zuba stpp shi ma, a cikin babban waje da zasu samu space zaki zubasu ki haɗe fa. Ki zuba ruwan dai'dai da yanayin kayan haɗinki, idan kinga ya yi kauri sosai zaki iya kara ruwa. Ki tabbatar kin juya sosai ya haɗe jikinsa ko in ce sun haɗe jikinsu. Sai ki zuba perfume and colorant, sannan ki rufe ki barshi na awa 24 kafin ki yi amfani da shi, idan kina son fitar da shi shape by shape zaki iya sayan shapes ɗin ki zuzzuba a ciki ki barsu su kame jikinsi. SHIKENAN KIN HAƊA SABULUNKI, IN SHA ALLAH ZAKU RINƘA SAMUN SANA'O'IN DA ZASU RINƘA YI A CIKIN GIDA DAN TSIRA DA MUTUNCINKU WANDA KUMA JAMA'A ZASU SAYA, DAN DIK KAYAN AMFANI WAƊAN DA AKE AMFANI DA SU YAU DA GOBE ZAN KOYA MAKU, WAƊAN DA DOLE ZA'A SAYESU DA AMFANI. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 19 ••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 KINGDOM OF POWER. Zaune Momma, Mama Haulat and aunty MieMie suke a parlourn momma, mama Haulat tana zaune a ƙasa, Aunty MieMie da momma a saman sofa, babyn Khadija yana rike hannun momma, ya sha kwalliya cikin wasu irin kayan sanyi masu bala'in kyau wanda momma da kanta tasa uncle Taheer ya je shopping ya saya mata su, kayan baby dayawa ya sayo mata, yaro sai sakawa yake yana kara canzawa abinsa, har ya murmure, amma matsalar ɗaya shi ne bai samu nonon uwa ba, ko sau ɗaya bai ɗanɗana ba, Allah sarki. Cikin sanyin murya momma ta fara magana tana kallan Aunty MieMie. "Raeesa kamar yadda na faɗa maki cewar wannan yarinya matar Jaish ce to hakan take, yau da safe na same shi a bedroom ɗinsa domin muyi maganar da shi, sai ya nuna mun shi wlh baya santa, hasali ma ba zai taɓa zama da yar kauye wadda bata yi karatu ba, ya nuna baya santa kuma ba zai taɓa santa ba, har da ce mun shi bashi da lokacin mace a yanzu, shi ma daddynku ya kafe a kan bayan santa, wai sai dai a warware wannan aure". Ɗan zaro idanu Aunty MieMie ta yi, cike da mamaki ta ce. "Amma kuma momma menene laifin yarinyar nan da zasu ce basa sonta?". Allah sarki, ita Aunty MieMie ko kaɗan bata ji kyamarsu Mahreen ba, wato mufa Nigerians dik in da muke mun fita daban, jinin ɗan Nigeria musamman ɗan arewa ci wlh baya kyamar kowacce yare da kabila, zama muke da kowa da zuciya ɗaya, sai dai a nuna mana kabilanci da wariya, amma mu bana nunawa, kowa ɗaya muka ɗaukesa, lallai ya tabbata jinin Nigerians na gudu a jikin Aunty MieMie, jama'a ku tafa mata, bata bar gida ba baiwar Allah. "Hmmm shi dai Jaish kin ji dalilinsa, wai saboda yar kauye, yar datti, ba karatu ce yasa baya santa". Cewar Momma kenan. Ɗan siririn tsaki Aunty MieMie ta je. "To shi kuma daddy menene dalilansa na kinta?". Cewar Aunty MieMie. Shiru momma ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. "Saboda kin san halinsa ai, wai akwai qualities da yake sanwa ƴaƴansa a matan da zasu aura". "To yaga ita Mahnoor ɗin ne da zai ce bata yi ba?". Kai momma ta girgiza mata kafin ta amsa da. "A'a bai ganta ba tukun nan, na dai ce ya bani sati guda zan kawota ya ganta, in ya ganta sai ya yanke hukunci". Shiru suka yi Aunty MieMie tana tinanin mafita. Katsesu momma ta yi da cewa. "To shi ne yanzu nike san mu yi shawarat ta yadda zamu haɗa mata dik wasu qualities ɗin da suka dace ta yadda idan ya ganta zai bada goyan bayan Jaish ya zauna da ita, ni bani da matsala ta ɓangaren Jaish, dan nasan ba zai saɓa umarnina ba, matsalar daddynku ya aminta da ita ne kawai, kunga idan aka raba auren nan magana ta domin Allah an cutar da yarinyar nan da iyayenta, bana jin kamar ko shekaru 15 ta cika, sannan dik bama wannan ba, Mahnoor ta dace a matsayin matar Jaish wlh, iyayenta sun yi mana halacci na wuce misali, bai kamata mu saka masu da sharri ba". Jinjina kai Aunty MieMie ta yi, tabbas dik abin da momma ta faɗa gaskiya ne, bai kamata a yi wa Mahnoor wani abin da ba dai'dai ba, domin yarinyar ta kai dik wani matsayin da ake buƙata matar Prince ta kasance, ta cike dik wasu qualities, ilimin bokon ne dai kawai ya rage mata wanda shi dama ai ba dashi ake zuwa lahira ba, bai zama wajibi ba, rashinsa ba zai hanata zaman aure da kyautatawa mijinta ba, ta samu babban wato ilimin addini, dik wasu abin da ake koyarwa a bokon tushensu daga inane? Dik daga litattafan addini ne, dan haka Mahnoor bata da wata gazawa. Iya shege ne kawai irin na Jaish. "Ranki ya daɗe zan iya yin magana?". Cewar mama Haulat dake binsu da kallo....... Jinjina mata kai alamar e Momma ta yi ba tare da ta yi magana ba. "Ni a ganina tin da haka ne ai matsala ce mai sauki, sai mu gyarata, ta sha gyara sosai, a samu wanda zai fara koya mata karatu Kafin wani ɗan lokaci, ta goge ta canza, In Sha Allah zai sota, kuma shi ma mai martaba zai kaunaceta ya karɓeta a matsayin sirika". Jinjina kai Aunty MieMie ta yi tare da cewa. "Wannan shawara ce mai kyau, sai dai kuma ina da kari a kan shawarar". Zuba mata idanu momma ta yi alamar tana sauraronta kenan. Cigaba ta yi da cewa. "Momma kada ki sake yi wa Jaish maganarta, tun da kin bawa daddy sati ɗaya, to a cikin wannan sati ɗayan kada a yi magana da kowa, mama Haulat ki gyara mana ita, sai ki fara koya mata wasu abubuwan da suka dace dan kauyancin nan da rayuwa kamar na dabobi ya fita a kanta, kun san idan nan da sati ɗaya aka kaita gaban daddy ya aminta da ita to a bisa doka daga ranar zata koma part ɗin Jaish, sannan zata zamana ita kaɗai alhakin kula da cinsa da shansa zai rataya a wuyarta, kun san yadda doka yake babu wadda zata sake kusantar abin da ya danganci cinsa, shansa da wasu privacy nasa ko?". Jinjina kai mama Haulat ta yi, ita kuma momma still dai tana binta da ido bata furta word ba. Cigaba ta yi da cewa. "Dole za'a haɗata da mama Haulat a part ɗin nasa dan ta tayata yakarsa, kun san halin Jaish da shegiyar murɗiya, mama Haulat ai ɗan ɗakinki ne shi kin san halinsa, dan haka ke zaki ɗaurata a hanyar da ta dace domin ta tabbata a matsayin matarsa ya kuma sota, dan haka wannan ragama mun rataya maki shi a wuyarki ko ya kika ce momma?". Ta kai karshen maganar tana tsayar da idanunta a kan momma. Jinjina momma ta yi, sannan ta ce. "Tabbas wannan shawara ta yi, yanzu Haulat ki dage kafin nan da sati guda ki canza mun ita, ta yi kyau sosai, idan Allah ya ɗoramu a kan daddynsu muka yi nasara sai ki bita part ɗin Jaish ɗin kina cigaba da koya mata abubuwa da yi mata gyara, ban yarda da wata kuyanga da ta shiga lamarinsu ba face ke, da ke kaɗai na yarda a gidan nan, nasan zaki kula da su dikkansu biyu, kin san abin da yake so da wanda baya so, dan haka sai ki ɗaurata a kan hanyar da ta dace, wlh ina san Jaish da wannan yarinya, ban san dalili ba". Cikin girmamawa mama Haulat ta karɓi wannan ragama da suka bata tare da tambayar ko akwai wani abin da za'a ƙara sanar da ita?. Aunty MieMie ce ta amsa mata da babu komai zata iya tafiya ta je ta fara aikinta daga yanzu, wato ta je ta ɗaukesu izuwa wajen gyara yanzu kenan, tare da Mahreen za'ayi masu komai dan a ragewa Mahreen ɗin ma wannan hauka da yake a kanta. Miƙewa mama Haulat ta yi ya nufi waje tana yi masu addu'oi masu tasiri da ratsa zuciya. Tana fita uncle Jahiz ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Zeezee tana biye da shi a baya, dama Aunty MieMie tana ƙoƙarin ɗaukowa momma zanjen babyn nan dake kama da shi ne sai ga shi ya shigo. Dan haka cikin girmamawa suka gaisa. Saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna tare da umartan Zee da ta zauna a kusa da Aunty MieMie. Kin yarda ta yi, ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai, ta ji sauki sosai jiki ya yi kyau Masha Allah, ita dai ta samu sallama, saura Khadija da mai keken napep ɗinsu da shi ma ya farfaɗo yana ta fama da nashi jinyar bawan Allah. Zee na ƙoƙarin zama a ƙasa idanunta suka hango mata babyn Khadija dake hannun Momma, ai kuwa zubur ta miƙe, ita da bata san a ina take ba, bata san ba a gidan wargi take ba, bata san a gidan sarauta masu izza da ji da kansu take ba, sai ta miƙe a zabure tare da nufar momma da nufin ta kwace babyn. Tsawa Aunty MieMie ta daka mata tana faɗin basa san shirmen banza, ita bata san a gaban wa take bane? Gaban princess Rahilarh take, dole ta nitsu ta jira komai sai an bata izini, su sarauta ba'ayi masu irin wannan wautar. Shi ma uncle Jahiz dama ya buɗe baki zai dakatar da ita daga tinkarar momma ɗin ne sai Aunty MieMie ta rigasa, dan haka sai ya ja bakinsa ta datseta cif. Allah sarki Zee, jikinta sai rawa yake yi, burinta ta karɓi ɗanta ɗan ƴar uwarta, yau sama da sari biyu kenan tana rokon da abata shi ta ga jininta, amma bata samu dama ba, ta tsumu da san ganinsa har ta gaji, kullun idan uncle Jahiz ya je dubasu sai ta yi mashi kukan ina yaronta, yau dai da aka basu sallama sai ya ce ta zo su je ta ga ɗanta, shiysa yanzu da ta gansa ɗauki yasa ta rasa nitsuwarta, ta rasa control ɗinta, kuma ya haɗu da bata san a gaban wa take ba, shiysa ta yi saurin miƙewa zata je ta karɓesa, shi kawai idanunta yake hango mata, sam bata ga su momma ba baiwar Allah. Ai ƙasa komawa mazauninta ta yi, sai kawai ta tsaya a wajen cak tare da rushewa da kuka mai tsuma zuciya, dama a kusa take, kiris take jira ta fashe dama. Da saurin uncle Jahiz ya miƙe ya nufota, cike da gimamawa ya fara faɗin. "Sarauniya momma ayi mana afuwa, na tabbata ɗauki ganin babyn yasa ta rasa control ɗinta, and bana tinanin tasan in da take shiysa dik ta yi wannan shirmen". Ya kai karshen maganar yana rike hannunta. Baya kaɗan ya jata izuwa in da ta miƙe, cikin nitsuwa ya mayar da ita ya zaunar. Momma da tausayin Zee ya gama narkar da zuciyarta ne ta umarci da su rabu da ita ta matso taga ɗanta, ai jini ba wasa ba. A tinanin momma Zee ita ce uwar ɗan. Ai Zee tana jin an bata dama ta yi saurin miƙewa ta isa gaban momma, jikinta har rawa yake yi wajen kai hannu, tin ba'a miƙo mata shi ba ta karɓesa. Aunty MieMie ma tausayinta ta ji ya kamata, Allah sarki jini ba wasa ba, sai kerma hannunta yake yi ta rike yaron gam idanunta suna ciccikowa da kwallah. Momma mace mai dattaku, hannu ta kai tana dan shafa kanta da yake Zee ta zube gwiwowinta a ƙasa gaban momma ɗin ne da ta karɓi yaron. Rarrashinta momma ta fara yi tare da ƙara mata kwarin gwiwa a kan ta koyi jajircewa. Aunty MieMie ma data ga hakan sai ta tsoma baki suka fara rarrashinta a tare. Uncle Jahiz ne ya fayyace masu cewa Zee fa ba ita ce uwar yaron ba, sisterta ce uwar yaron. Dik da suka ji hakan sun tausayawa Zee sosai, dan daga yadda ta nuna reaction ɗinta a kan yaron nan alamu sun nuna akwai damuwa.......... Wai dan ma basu san tarihinsu ba kenan, da sun sani sai yaya kenan?. Ai su Zee su suga rayuwa, sun sha gwagwarmaya kam ba kaɗan ba. Shiru parlourn ya ɗauka na ɗan lokaci, sai shessheƙar kukan Zee ne yake tashi a hankali hankali gwanin ban tausayi. Aunty MieMie da ta lura kamar akwai yunwa sosai a tattare da Zee sai ta ce yakamata a kawo mata abinci ta ci. Momma ma ta lura da hakan, sai ta amsa da yakamata kam. Aunty MieMie ce ta mika hannu ta karɓi babyn daga hannunta, sannan ta ce uncle Jahiz ya sanya a kawo mata abinci ta ci. Sam bata tambayi wacece Zee ba, dan su suna da ɗabi'ar dik wanda suka gani a tare da ɗan uwansu to fa zasu bashi mahimmanci. Tun da suka ganta tare da uncle Jahiz sun san ba banza take ba, saboda su basa kula abu idan ba ya kasance ya shafesu ba. Miƙewa uncle Jahiz ya yi ya nufi waje. Jim kaɗan ya dawo tare da wasu kuyangu guda biyu da suke ɗauke da tampatsetsan tray mai girma, shake take tap da abinci launika daban daban da a kallah zasu kai kala goma. Kun san larabawa da yawan girke girke kala kala. Kai tsaye saman dining table na momma suka nufa suka shirge abincin, ga kayan drinks kala kala, ferfesu kaji dana ɗawisu, kun san gidan sarauta suna da ɗawisu sosai, ga dahuwar Chinese rice kala daban daban, kai waɗan nan tray sun haɗe komai, har da kayan marmari. Umartar Zee ya yi da ta tashi ta je ta ci abinci, da yake parlourn yana da girma, daga wajen da table ɗin yake zuwa in da suke akwai tazara mai tsayi. Da yake yunwa baiwar Allah take ji sai bata musa ba ta tashi, jikinta har ɓari yake yi ta nufi wajen table ɗin. Da kallo suka bita har ta kai wajen, sannan suka dawo da kallonsu a kan uncle Jahiz dan jin wacece ita daga ina kuma ya samosu. Yasan abin da suke wa binsa da kallo, karin bayani suke jira ya kora masu. Dan haka cikin nitsuwa ya yi gyara murya kafin ya fara kora masu dik abin da suke tsumayan jira daga garesa. Ya yi masu bayanin ne kuma ba tare da ya bawa kowa damar jin abin da ya faɗa ba, zance ake ta sirri!!. Ko ita Zee dake zaune saman table bata ji abin da suke tattaunawa ba, ita dai ta zauna shiru tana bin kayan abincin da kallo, Allah sarki taga duniya, ta rasa da wanne zata fara, yunwa take ji over, dan ma Allah yasa ita ba wawiya bace, da ɗan wayewarta, amma dik da haka sai da ta yi kauyanci a ɓoye, dan kuma kun san zaren ba kalar yadin bane. Dikkansu babu wanda fuskarsa bai nuna alamar mamaki ba a lokacin da uncle Jahiz ya gama basu wannan labari da ya ɗauko ɗan sanar da su su wacece Zee, a fili momma ta furta. "Dikka wannan zalincin su kaɗai?". Jinjina masu kai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Aunty MieMie da ranta ya gama ɓaci har idanunta sun kaɗa sun yi jajir ne ta ce. "Gaskiya ba zata saƙu ba, dole mu kwatar masu ƴancinsu". Jinjina kai momma ta yi alamar tabbas kuwa. Shi ma jinjina kai ya yi alamar haka ne. Da alama labarin tarihin su Zee ɗin ya basu, dan tabbas ya lallaɓa Zee a asibiti, ya gwada mata fifikon shekaru a in da ya yi mata dabara har ta yarda ta bashi tarihin rayuwarsu. Amm kuma sai dai akwai wani abin da ya sanar da su momma bayan tarihin su Khadija ɗin, dan yanayin mamakin da ya bayyana a kan fuskokinsu abu ne mai girma da ya fi tarihin su Zee suka ji, dole akwai wani sirri da ya sanar da su wanda baya buƙatar a ji........... Ni kam nace koma dai me ka sanar da su idan lokaci ya yi ruwan ta yi tsami ni da my people's ai zamu ji ko? Sai kwan ta fashe In Sha Allah mun ji komai ato, mu je dai zuwa. "Gaskiya akwai azzalumai a duniya, yanzu ko ta ina zalinci kawai ake yi, ya ilahi ya lillahi, wannan musifa dame ta yi kama". Cewar Momma da alamar jikinta a sanyayye. Ita ma Aunty MieMie ta yi laushi, kamar wanda ya sheka masu ruwan sanyi, dik da alamar karyewar zuciya da tausayi a tattare da su. "Uncle Jahiz taki cin abincin fa, ko zaka je ka yi mata dabara ta ci tun da kun saba da ita". Cewar Aunty MieMie da ta farga da Zee bata cin abinci. Miƙewa tsaye ya yi, ya nufi table ɗin yana faɗin. "Dama kullum sai mun kai ruwa rana da ita take yarda ta ɗan tsakuri abincin ai, bari na gwada yanzu ma". Momma ce ta karɓi zance da cewa. "Ai dole ne ta shiga damuwa Jahiz, amma In Sha Allah damuwarta ya zo karshe, bari daddunsu ya sarara da musifar da muke ciki na ɓatar Zunaira, tabbas za'a biwa yaran nan hakkinsu, sai mun tsaya masu In Sha Allah". Jinjina kai Aunty MieMie ta yi, kun san tana san jinin ƴan Nigeria ita, saboda jinin mummynsu ne, dan haka ta kudurta a ranta wlh ba zata sarara ba a kan wannan case na su Zee, sai ta ɗaukar masu fansa, kai jama'a jinin modarawa ake magana, su da basa yafe ko harararsu ka yi........😅 Saman table chair dake kusa da ita ya zauna, su momma kuma suka miƙe izuwa cikin bedroom ɗin momma dan su tattauna wani sirri nasu, momma tana mugun shiri da Aunty MieMie sosai, ta su ta zo ɗaya, kun san sai hali ya zo ɗaya ake abota, batu na Allah aunty MieMie mutuniyar kirkice number ɗaya. Chinese fried rice ya zubawa Zee, sai kallan face ɗinta yake yi, ta yi ƙasa da kai tana ɗan murza ƴan ƴatsun hannunta. Cikin harshen turanci ya ce da ita. "Bari in baki abincin a baki to tin da ba zaki iya ci ba". Da sauri ta girgiza mashi kai alamar bata buƙata. "Baki san zuwa ki kalli Khadija ne?". Da sauri ta buɗi baki ta amsa da tana so. "To in dai kina san zuwa wajen Khadija lallai ki ci abincin nan, idan kika ƙoshi sai in kira Fanan ta kaiki ɗaki ki yi wanka sai in kai ki wajen Khadija". Kamar zata yi kuka ta ce. "Zan ci ko dan in ga ƴar uwata, amma dan Allah ka faɗa mun kasan Khadija ne? Ya kai sati kenan ina yi maka wannan tambayar sai ka ce mun ni kaɗai ka sani baka san ta ba, nace maka a ina kasanni ni ɗin ka ce mun a Nigeria, ka fayyace mun komai yadda zan fahimta kuma kaki". Da kyar ta iya karisa maganar, saboda wani irin kwarjini da yake yi mata, kuma ita gaskiya abin yana cinta a rai tana san samun amsa, tabbas ita hotonsa ta gani a hannun Khadija, wlh ko ratsuwa ta yi ba zaga yi kaffara ba shi ne, sannan shi ma da ya ganta ya ce ta yi mashi kama da wata da ya taɓa gani sai dai ya manta a ina, to da waye zata yi kama idan ba Khadija ba?. Bugu da kari shi da bakinsa ya ce babyn Khadija yana kama da shi, ga shi likitoci sun hanasu ganin Khadija saboda condition da take ciki, an yi mata aiki a ciki baiwar Allah, ashe matar nan da ta basu wajen zama a gidata a Abuja ita ta cucesu lokacin haihuwar Khadija bai yi ba ta bata maganin tasar da naƙuda, dalilin haka mahaifar Khadija ya tsage, sai da aka yi mata aiki yanzu, Allah ma yasa tana da rabon shan ruwa a gaba, ai da ta jima da mutuwa saboda irin jinin da ta rasa, amma Allah ya ƙaddara zata rayu. "Zee ni har yau ban ga face ɗin Khadija ba bare in san nasanta ko ban santa ba, sannan kuma na faɗa maki ke na sani kawai, ki ci abinci, likitoci sun ce mun zuwa yamma zan samu damar ganin Khadija, idan muka je sai in ga ko na santa". Shiru Zee ta ɗan yi, ita dai wlh tasan shi ne na jikin hoton nan, sai ma da ta gansa a zahiri yanzu ta kara yarda, amma bari Khadija ta farfaɗo komai zai bayyana ai. Tana can tana duniyar tinani sai gani ta yi ya kawo mata abinci saitin ɗan bakinta. Kai ta girgiza mashi alamar bata so, ta kai hannu ta karɓi spoon ɗin tana sunkuyar da kai. Ta ƙasan ido take satar kallansa, Arabs jallabiya tana yi mashi mugun kyau. A hankali ta fara cin abincin kamar tana tsoron taunawa kada hakwaranta su karye, shi kuma ya zuba mata idanu yana kallanta, ji yake yi tamkar ya santa. My people's me kuke tinani a wannan al'amari, wacece mai kama da Zee da ya sani? Meyasa ya yi kama da babyn Khadija? Kada ku manta babyn Khadija korean ne, ko da yake fa idan akwai jini wlh ba ta yadda ba zaka ga mutum ba, fata na dai Allah ya tashi kafaɗun Akka, dan idan zarginmu ya tabbata babu wadda ta dace da yi mashi hukunci sai Akka. (Ni ina da tantanama, anya uncle Jahiz ko ya gane Khadija zai yarda ya nuna ya ganeta kuwa?🤔 Ya kuke tinanin wannan al'amari?) •••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Luv Bird Shi da ya sami abin da yake so, ai bai saki Chuchu ba sai da ita da kanta ta kwace bakinta, a lokacin kuma ta gama kai shi ƙololuwa, dik ya rasa nitsuwarsa, idanunsa a lumshe, jinsa a sama kawai yake yi, yana ƙoƙarin dakewa ya capki tula tulanta ta yi saurin kwatar bakinta ta yunkura zata bar jikinsa. Cikin magaggin soyayya da sha'awarta ya riƙota, kamar wani ɗan shaye shaye da kyar ya furta. "My Jannawad ina zaki je?". "Knocking na door fa na ji ana yi". Ta faɗa tana kallan zakarar wuyarsa, wato wannan kashi nasu na maza, kashin ta miƙe sosai tana ɗan harbawa. Sai da ta yi magana kunnuwansa suka tsinkayo mashi knocking da ake yi. Sake ta ya yi ba dan ya so ba, da alama da mai buga wannan kofar ya ɗan kara masu ƴan mintuna da Jawad ya yi disvirjin ɗinta, saboda ya luluƙa duniyar chaskale dayawa. Da kyar ya iya miƙewa. Ƙasan bed ɗin ya sauko, jikinsa dik wani iri. Door ya nufa yana ɗan layi. Ya ƙasa iya tambayar wanene saboda nauyi da tongue ɗinsa ya yi mashi. Da kallo Jannawad ta bisa tana jin wani irin kaunarsa a ranta yana kara ratsata. Yana zuwa ya buɗe kofar babu tambaya. Duka Jaish ya kai mashi a kirji daga buɗewarsa. Har sai da ya yi layi kamar zai faɗi, da kyar ya kama kansa tare da waro idanunsa da kyau. "Wani irin iskanci ne wannan? Na kai 5 mins tsaye ina dukan kofar nan, mema na rufe kofar..........?". Bai kai karshen faɗar tasa ba idanunsa suka hango mashi cikin ɗakin, Chuchu dake zaune a saman bed tana binsu da kallo. Idan baku manta ba shi Jaish bai san Jawad ya yi aure ba, ya ɗebo zafin kansa kawai zai zo ya sauke a kansu, ransa ne a matuƙar ɓace saboda momma ta same shi da safen nan a kan batun Mahnoor matarsa ce, shi ne fa ransa yake ɓace, ya zo wajen Jawad dan su tattauna wannan bala'in in jisa, shiyasa ya rinƙa dukar kofar da karfi. Cike da mamaki ya dawo da kallonsa a kan Jawad ɗin, zaro idanu ya yi, shi da farko ma bai lura da yanayin da ɗan uwan nasa yake a ciki ba, sai da yaga Chuchu zaune a tsakiyar bed ne ya fahimci Jawad fa a cikin mayen sha'awa yake. Wani irin bugawa ya ji kirjinsa ta yi, da karfi ya bugi kirjin Jawad har sai da Jawad ya ji ya wastsake, cikin zafa ya danko wuyar rigarsa haɗe da daka mashi tsawa. "Me Jannat take yi a cikin ɗakinka har saman bed ɗinka da sanyin safiyar nan? And wani irin shiga ce a jikinku?". Cikin lokaci ƙanƙani Jaish ya rikiɗe tamkar ba shi ba, har wani huci yake yi, a tinaninsa sheke aya Jawad yake yi da kanwarsa, ga shi ya gansu a wani irin yanayi. Gyaran murya da uncle Abbas ya yi ta bayansu ne yasa suka yi saurin kai kallansu a wajen. Da sauri Jaish ya ɗauke kansa daga kan kallan uncle ɗin nasa, domin kuwa in dai abin da yake zargi Jawad yake aikatawa babu abin da zai ana shi yi mashi hukunci mai tsanani yau, dama su a dokarsu dik wanda ya yi zina dandaƙa ake yi mashi. Chuchu da dama bala'in tsoron Jaish take yi tuni ya sha jinin jikinta, ta takure waje guda jiki na kerma. "My son sake shi, ba abin da kake zargi bane, Jannat matarsa ce, kai ne baka sani ba". Cewar uncle Abbas da ya ji komai da Jaish ya faɗa, dan tun time da Jawad ya buɗe kofar ya shigo cikin parlourn shi ma. A miliyan Jaish ya juyo da kallansa a kan uncle Abbas. Jinjina kai uncle Abbas ya yi alamar tabbatar da abin da ya faɗa. Kara zaro idanu Jaish ya yi. Da sauri ya juyo ga Jawad. Shi ma kai ya jinjina mashi alamar e haka. A wani irin slow Jaish ya zame hannunsa daga wuyar rigar Jawad, like wow he was so surprised. Uncle Abbas ne ya ce. "Jawad P.a ɗinka ne ya kirani wai yana ta kiranka baka picking time na tashin jirginku ya kusa". Da sauri Jawad ya juyar da kallansa izuwa cikin ɗakin, kan wayarsa ya sauke kallansa, lallai kuwa soyayya ta yi daɗi, har ma anyi sallar asuba shi yana nan ya afka wata duniyar. Ɗan dafe kansa ya yi, babu ko kunyan daddyn nasa ya ce. "Sorry daddy, Jannat tasa ban ji kiran ba, amma yanzu zamu shirya mu fito". Jaish dai kamar ruwa ya cinyesa a wajen, faɗi yake yi a cikin ransa shikenan Jawad ya gama yi mashi fata fata da mutumci a idanun kannensu, Jawad ya gama da shi ya ja mashi kima a kan titi, yanzu shikenan Jannat tasan komai, gaskiya idan ya kyale Jawad bai yi mashi hukunci ba ya cuce shi dayawa. Uncle Abbas kuwa cewa ya yi. "Ina zaku je ne dama?". Ɗan sunkuyar da kai na munafinci Jawad ya yi, sannan ya ce. "Daddy wai dama Jannat ce ta ƙasa samun nitsuwa a nan, sai kuka take yi mun ta ƙasa barci, shi ne fa dama zan ɗauketa mu je honeymoon a Dubai". Da yake uncle Abbas ma ɗan zamani ne sai ya ce. "Yanzu kai Jawad ba zaka iya kwantar mata da hankali a nan ba sai kun je Dubai?". Shiru ya ɗan yi yana ƴan kame kame. "Anya kai namiji ne kuwa?". Uncle Abbas ya sake jefa mashi tambaya. Nan ma dai shiru ya yi. "To ni ban yarda ku je ko'ina ba, ku na nan, idan baka iya kwantar mata da hankali a nan na ga ɗan uwanka ya koya maka". Yana kai karshen maganar ya juya ya fice abinsa. Jaish ya gama zuwa har wuya, ɓacin rai kan ɓacin rai, sarai Jawad ya lura da shi, shiyasa ya yi readyn guduwa, dan yasa saboda uncle Abbas yana wajen ne yasa Jaish ɗin ya daure bai aiwatar da abin da ya yi niyya ba. Tsabar tsakiyanci irin na Jawad, uncle Abbas na tafi ya dawo da kallansa a kan Jaish, cike da neman tsokana ya ce. "Babban abokin ango kuma yaya babba zo mu je ka gaisa da amarya, dama tana kewarka ai.........." Bai kai karshen maganar ba ya yanka a miliyan ya fito waje saboda wani irin capka da Jaish ya kai masa a wuya, Allah ya taimakesa ya zulle ya yo waje. Da gudun gaske Jaish ya biyo bayansa, dan yau wlh ba zai kyalesa ba, ya zubar mashi da mutunci, wannan ai iskanci ne, dama ga zafin ɓacin ran anki ƴar kauye Mahnoor matsayin matarsa, sai ya haɗa dikka zai sauke a kan Jawad................. Wayyo abubuwa sun haɗewa Jaish fa😅 Bari mu leƙa wani part mu dawo. •••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 🔥🔥🔥🔥 DUBAI🔥🔥🔥🔥 AFTER SOME WEEKS. Zaune Sharifat take a saman bed, Leesharh na tsaye a wajen dressing mirror tana ɗan gyara face ɗinta, har ta mayar da jikinta ta yi ɓulɓul abinta saboda kulawa na musamman da ta samu daga Abbie, Yah Bilal, and Sharifat, sai ta yi saurin recovery. Sanye take da riga da wando Pakistan mai bala'in kyau launin purple color. Ta gyara gashin kanta, sai dai hannunta har yanzu bai gama warkewa sosai ba, sun koma kamar yadda suke a da ita da Sharifat, suna kula da juna haɗe da nunawa juna soyayya. Irin kayan jikin Leesharh shi ne a jikin Sharifat, sai dai ita nata maroon color ne. Hira da guyson Sharifat take yi a Whatsapp a in da take faɗa mashi Obaid and Omaid sun samu hutun karshen shekara suna gidan King Badeen, sun ki zuwa gidansu sun ce Tunisia kawai zasu wuce. Shi ma guyson kwance yake a saman bed ɗin momma daga shi sai Short, ya rungumo pillow a kirjinsa yana aikin wannan sakalancin nasa da ya saba, shi kaɗai sai turo baki yake yi. Sun nitsa cikin hiran da suke yi wayar Leesharh dake kusa da Sharifat ya hau ƙara. A razane Leesharh ta ɗago da kallanta a kan Sharifat ta cikin mirror, ita ma Sharifat kai kallanta a kan wayar ta yi. Private number ne yake kira, hakan yasa Sharifat ta dawo da kallanta a kan Leesharh, cikin sauri kamar maras gaskiya ta kawar da kallanta tana ɗan kame kame. "Leesharh wayarki na kara kuma private number ne". Cewar Sharifat. Wani irin dum dum Leesharh ta ji kirjinta ya buga, domin kuwa ko bata ɗaga ba tasan masu nikaf ne. Jiki ba kwari ta juyo ga Sharifat. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufo Sharifat. Wayar Sharifat ta ɗauko ta miƙa mata. Tana karɓa wayar ya katse. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da Sharifat ta ɗan yi mamaki. Kunna data Leesharh ta yi haɗe da shiga cikin Whatsapp ɗinta. Sakon Yah Bilal kawai ta gani a ciki har wajen massages guda biyar. Sake satar kallan Sharifat ta yi, sai taga baiwar Allah ta mayar da hankalinta a kan hiran da suke yi da guyson. Buɗe sakon ta yi cikin sauri kamar wadda take kan gangara. "Leesharh zaki bimu ne?". Sharifat ta katseta da jefa mata wannan tambaya. A hanzarce ta fita daga kan mgs ɗin Bilal ta kashe wutar screen ɗin wayar, sannan ta jingina bayanta da jinin stool. "Ba lallai ba, amma Sharifat in tamnayeki dan Allah". Cewar Leesharh ɗin. Da kallo ɗaya zaka yi wa idanunta kaga tsantsar rashin gaskiya da razana a cikinsu. Dakatar da abin da take yi Sharifat ta yi, sannan ta bata hankalinta dikka. "Sharifat dan Allah karin haske da karin ilimi zaki yi mun kin ji". Cikin raunin murya ta yi maganar. "Okey ba damuwa ina jinki". Ta yi maganar tare da ɗaura wayarta a saman pillow dake kusa da ita. "Labari zan baki sai ki yanke mun hukunci bisa ilimin addini kin ji?".......... Jinjina kai Sharifat ta yi haɗe da cewa. "To ina sauraronki. "Misali yanzu Shafiat wasu mata da miji masu halin kirki da dattaku ne suka tsinci wata yarinya, tun tana jaririya cikin tsummarta suka tsinceta, suna riketa tamkar ƴar cikinsu na tsawon shekaru biyar, matar nan ta yi mata komai na rayuwa, haka shi ma mijin matar, ya ɗauketa tamkar ƴar cikinsa, ya nuna mata kauna fiye da tinaninki, duniya dik ta ɗaukar ƴarsu ce, harta danginsu suna ganin matsayin yarsu, Allah bai taɓa basu haihuwa na shiyasa suka cewa kowa ƴarsu, kuma basa kusa da danginsu suna wata ƙasa ne, hakan yasa kowa ya yarda da ita ƴarsu ce". Kara nitsuwa Sharifat ta yi dan jin wannan labari, kun san ta da san karance karancen labarai. "Lokacin da yarinyar ta kai shekaru biyar a duniya sai Allah ya karɓi ran wannan mata tasa, hakan yasa ƴan uwansu suka ki tausayin wannan yarinya a in da suka ce to ya auri kanwar wannan mata dan ya cigaba da rike ƴar ƴaruwanta kenan, haka kuwa aka yi, wannan tsintacciyar yarinyar ta sake samu uwa a karo na biyu, to wannan uwar ce ta riketa har yarinyar ta kai shekaru goma sha huɗu". Sai jinjina kai Sharifat take yi labari ya fara sugar, har da cewa Leesharh ta rinƙa rinƙa yin labarin da wuri please, dan so take ta ji komai da wuri. Cigaba ta yi da cewa. "To dama wannan uwa ta biyu da yarinyar ta samu macece mai masifar san kuɗi, dan haka bata zama, tana zuwa gidan larabawa ta yi masu aikatau, suna bayanta kuɗi sosai, shi kuma wannan mijin yana sana'ar gasa nama ne a ƙasar da suka je in da nace maki dama sun yi nisa da danginsu ɗin. Ana nan watarana wannan mata ya ce zata fara tafiya da yarinyar nan gidan aikinta dan ta rinƙa tayata aiki, mijin yaki yarda ya ce yarsa karatu take yi, matar ta tsayar da bala'i a kan lallai dole wannan yarinya ta bat karatu ta rinƙa binta wajen aiki, dan yanzu kuɗi shi ne mutum, babu abin da karatu yake tsinanawa mutum, in short wannan mata ta fi karfin mijin ta yadda tasa dole ya yarda yar nan karatunta ya salwanta ta fara bin mamanta neman kuɗi aikatau gidan larabawa". "Rayuwarsu ya cigaba da tafiya a haka, suna shan wahala a gidan larabawa, amma haka suke daurewa, sai watarana tsautsayi yasa mahaifiyar yarinyar nan ta zubawa wata yar larabawa ruwan zafi a jiki by mistake, nan take uwar yarinyar ta fara dukan mahaifiyar yarinyar, kuma a gaban yarinyar, sai hakuri yarinyar take bata amma taki yarda, dukanta take yi da dik abin da ta samu, kuma wlh yarinyar ba wani konewa sosai ta yi ba, amma haka ta rinƙa dukan uwar yarinyar, a garin ɗaukar abin duka har ta ɗauki wuƙa ta cakawa mamar yarinyar a ciki". Dai'dai lokacin da ta zo wannan point ɗin sai da idanunta suka ciko da kwallah, ita kuma Sharifat wani irin zabura ta yi tare da zaro idanu, wannan wace iriyar labarice. Leesharh bata bata damar yin wani magana ba ta ɗaura da cewa. "Sosai wannan balarabiya ta razana ganin ta cakawa matar wuƙa ta kuma faɗi ƙasa, hankalinta ya tashi, ta rikice ta rasa ya zata yi, yarinyar matar kuma da ta ga komai yadda ya faru, ita ma tashiga tashin hankali, hakan yasa ta juya zata gudu ta bar gidan ta je ta kira mutane, haka babu tausayi babu imani wannan balarabiya ta kamata, ta damka mata wukar da ta yi kisan a hannunta, sannan ta danneta ta saka mata wuta a baki ta yadda yarinyar ba zata iya sake yin magana ba bare har ta faɗi ga abin da ya faru, in takaice maki labari dai laifin kisa ya koma kan wannan yarinya a matsayin ita ya kashe mahaifiyarta". Idanun Sharifat ne suka ciko da kwallah, saboda labarin ya taɓa mata zuciya. Ita kanta mai bada labarin hawaye take yi. "A takaice haka aka kai wannan yarinya prison, an yanke mata hukuncin kisa amma sai ta yi zaman prison ta jira lokacin da zata cika shekaru 18 kafin a kasheta. Ana haka sai wasu mutane suka zo suka fitar da ita daga wanna gida na prison da sunan zata yi masu wani aiki, yarinyar taki karɓar aikin saboda tana tsoron me zai je ya dawo, sai suka ce mata ai taimako zata yi, wani za'a kashe zata taimaka mashi, hakan yasa wannan yarinya ta yarda, ta karɓi sannan aiki". Ƙara matsowa bakin bed Sharifat ta yi tana sharar kwallah, dik da bata san labarin na gaske ne ko kirkirowa Leesharh ta yi ba abin ya yi mugun bata tausayi. "In takaice maki labari dai sai wannan yarinya ta zo ta fara wannan aiki, kwatsam sai ta fahimci amfani da ita ake yi a cutar da mutane bayin Allah, shi ne sai ta yi ƙoƙarin bijirewa waɗan da suka sakata a aiki, ba zato ba tsammani suka yi mata barazana da sun kama babanta da yake sana'ar gasa namarsa a bakin kasuwa, suka ce dole ta yi wannan aiki idan bata yi ba kuma zasu kashe babanta, ni yanzu abin da nike so ki faɗa mun a nan shi ne meyakamata wannan yarinya ta yi? Kada ki manta babanta da ya yi mata komai a rayuwa, ya inganta rayuwarta ya zama gatanta shi ne za'a kashe idan bata yi wannan aiki ba, sannan kuma aikin da zata yi cutar da mutane zata yi, kai in taƙaice maki kashe mutum ma za'ayi amfani da ita ayi, me kike tinanin yakamata ta yi?". Ta kai karshen maganar wani irin kuka mai tsuma zuciya yana ƙoƙarin kubce mata. Babbar magana, dik wanda ya fahimci wannan labari da Leesharh ta bayar a kan take magana ya sarawa yarinyar nan, lallai ba shakka an cuci Leesharh sosai, ta sha wahalar rayuwa, ashe ba da hakkinta aka kaita gidan AAJ ba ma, innalilahi wa inna ilahir rajiun, kenan ba iyayenta na gaskiya bane ma take san taimakawa, to wacece ita kenan? Ina iyayenta na gaskiya kuma suke? Meyasa aka jefar da ita har waɗan nan suka tsinceta? Wani irin shawara kuke tinani Sharifat zata bata? Wani irin makoma kuke yi mata tinani? Shin zata cigaba da yi wa masu nikaf aiki ko akasin hakan? Tayaya zata kuɓuta daga sharrinsu? Kenan iyayenta cirani suka jo yi a Dubai wannan iftilai ya afka mata? Lallai yakamata mu san labarin Leesharh dallah dallah da kuma in da aka tsinceta! Akwai cakwakiya babba kuwa. Amma ba shakka anyi wasa da rayuwar baiwar Allahn nan. Haka kawai Sharifat ta tsinci kanta da jin cewa wannan labari da Leesharh ta bayar gaske ne kuma kamar dai labarin yana da alaƙa da ita Leesharh ɗin duba da yadda take kuka kamar ranta zai fita..... Ba dole ta yi kuka ba, an kashe mahaifiyarta a gabanta, sannan an ɗaura mata laifi, bugu da kari ana sanya mata wuta a baki ta yadda ba zata iya magana ba, lallai akwai zalinci matuƙa a wannan lamari, ancutar da ita kwarai. Wai ya aka yi masu nikaf ma suka santa? Shi ma wannan babbar abin tambaya ne. To koma dai me lokaci zai yi mana alkalanci. Princess Teema taku ta amana bani da lafiya, da kyar na iya yi maku wannan update ɗin dan kada na barku a cikin kewa, ku mun addu'a, idan kun samu typing errors ma amin afuwa, zazzaɓi da ciwon kai ya sa na kasa iya ƙarisa editing ɗin. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 20 Ganin Sharifat tana hawaye kuma tana kallanta yasa ta ɗan yi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta dakatar da kukan nan da take yi, cikin raunin murya da kyar ta iya cewa. "Labarin ya taɓa mun zuciya sosai Sharifat". Sharifat zargi zuciyarta ya fara yi, dik san da take yi wa Leesharh hakan bai hana ta fara ƙoƙarin gane gaskiya ba. Leesharh tana da kwakwalwa sosai, so ta fahimci kamar kallan zargi Sharifat take yi mata, gudun kada asirinta ya tunu sai ta yi saurin shanyewa, sannan ta kwarara zuciyarta. "A school fa wata class mate ɗita ta bani wannan labarin, ta ce in taimaka mata da shawara, hakan yasa kema na baki dan ki kawo naki shawarar". Ajiyar zuciya Sharifat ta sauke, dan kuwa hankalinta ya ɗan kwanta jin abin da Leesharh ta ce, da a tinaninta a kanta abin yake faruwa, amma tin da ta ce labari aka bata sai ita ma ta ɗauko handkichief dan goge hawayenta. "Yanzu wani shawara zaki bada ke ma?". Leesharh ta sake jefa mata tambayar cike da matsuwa na san jin amsar da zata bata, a ƙagare take. Goge hawayenta tas Sharifat ta yi, sannan ta gyara zama, cikin sanyin murya ta ce. "Kuskure ne dan wasu sun cutar da kai kai ma ka ce zaka cutar da wasu!". Ɗan zaro mata idanu Leesharh ta yi. Ganin hakan yasa ta ce. "Bari na baki missali yadda zaki fi fahimta, waɗan da suka rike mata baba ta sani in suka cutar da shi to tabbas Allah ne zai yi mashi sakayya tin da babu abin da ya yi masu, haka zalika ita ma idan ta ce hujjanta shi ne babanta ta cutar da waɗan da basu ji ba basu gani ba to fa ta sani suma Allah zai yi masu sakayya, bata da ƴancin cutar wani idan ba shi ya cutar da ita ba, in dai shi ya cutar da ita wannan tana iya rama dai'dai da abin da ya yi mata". "Misalin cikin suratun Nahl, aya ta 126 Allah ya ce ‫َّٰصِّلل‬ ‫ْيٌرَّٰص ِبِريَن‬ ‫ۖ َوَلِئن َصَبْرُتْم َلُهَو َخ‬ ۖ ‫َوِإْن َعاَقْبُتْم َفَعاِقُبوا ِبِمْثِل َما ُعوِقْبُتْم ِبِهۦ‬ "Allah ya ce Idan an cutar da ku, yazamana kuna san ramawa, to ku yi ramako daidai da abin da aka azabta ku da shi. Amma idan kun yi hakuri, to haƙiƙa hakuri shi ne mafi alheri ga masu yin ta". "Wannan aya na nuni da cewa idan wani ya zalunci mutum, yana da damar ramawa daidai da abin da aka yi masa, dai'dai fa kada ya ƙara ko ɗiko, amma idan ya yi hakuri ya bar wa Allah, to Allah zai yi mashi sakayya da abin da bai taɓa zata ba". "Haka ma a cikin suratul shura, aya ta 40 Allah ya ce ‫ٌۭة ِّمْثُلَهاَفَمْن َعَفا َوَأْصَلَح َفَأْجُرُه َعَلى لَّلِهۚ ۚ َّنُه اَل ُيِح َّٰظ‬ ‫ُّبلَّٰظِلِميَن‬ ‫َّٰظَٰٓز‬ ‫َج۟اَسِّيَئٍۢة َسِّيَئٌۭة‬ ‫َوُؤ‬ ‫ٍۢة‬‫َج‬ ‫َّٰظ‬ ‫"ٍۢةٌۭةَو‬ ‫۟ا‬ ‫َٰٓز۟ا‬ ۚ‫َٰٓز‬ ‫ِإ‬ "Sakamakon mugunta ita ce mugunta irin ta, amma wanda ya yi afuwa kuma ya daidaita komai cikin ruwan sanyi da yafiya, to ladansa yana wajen Allah, lallai Allah ba ya son azzalumai da zalinci" "Dan haka a shawarata ni dai shi ne ta barsu da Allah, kada ta damu idan sun cutar da babanta, ta sani wanda ya halicci baban nata ya fita sonsa, kuma yana ganin komai, sannan ki sani Allah bai yi alkawarin agazawa azzalumai ba, dik abin da suka yi wa babanta Allah zai yi mashi sakamakon. Cikin suratul Hajj, aya ta 10 inda Allah (SWT) yake cewa ‫َظَّٰلٍم ِّلْلَعِبيِد‬‫َّٰلِب‬ ‫ْيَس‬ ‫َٰذَٰذِلَك ِبَما َقَّدَمْت َيَداَك َوَأَّن ٱلَّلَه َل‬ "Wannan azaba sakamakon abin da hannayenka suka aikata ne, dan Allah ba mai zaluntar bayinsa ba ne, dik wani hukunci da kuka ga ya hau kanku to ku sani tabbas kun aikata ba dai'dai bane aka hukuntaku. Wannan aya na nuni da cewa dik wanda ya aikata zalunci ko wani nau’in cin zarafin mutane, zai fuskanci sakamakon abin da ya aikata, Allah ba mai zalunci ba ne, kuma kowane mutum zai ga sakamakon ayyukansa, ko na alheri ko na sharri". "Haka zalika a cikin Suratul zumar, aya ta 24 Allah ya ce. ‫َأ‬ ‫َلَّٰظِلِميَن ُذوُق ۟ا‬ ‫و۟ا َما ُكنُتْم َتْكِسُبوَن‬ ‫َّٰظِلل‬ ‫َٰيَمِۚة َوِقي‬ ‫َم‬ ‫ْلِق‬ ‫ِۚة‬‫َفَمن َيَّتِقى ِبَوْجِهۦٱٱِه َٰي ُسٓوَء ْلَعَذاِب َيْو‬ Dik wanda ya kare kansa daga mummunar azaba, wato ya guji aikata ba dai'dai ba, to a ranar ƙiyama zai zama wanda ya tsira! Su kuma azzalumai za'a ce masu za ku ɗanɗana abin da kuka kasance kuna aikatawa. Wannan aya ta kara jaddada cewa azzalumai ba za su tsira ba, kuma Allah zai saka wa kowa daidai da abin da ya aikata". "Dan haka dik wanda aka zalunta ya barwa Allah, kada ta yarda ta bari Allah ya kamata tana zaluntar waɗan da basu ji ba basu gani ba, ta koma ga Allah ta kai kukanta a kan babanta, ba wai dan Allah bai san halin da take ciki ba, yana sane da komai, amma ta koma garesa ta kai karansu a kan abin da suka yi wa babanta, kada ta yarda ta cuci kowa". Tin da Sharifat ta fara magana ta ƙasa kunne take sauraranta cikin nitsuwa, kuma tabbas ta gamsu da kalaman Sharifat, tabbas Allah da ya halicci babanta ya fita kaunarsa, dan haka ta bar masu nikaf da Allahn baban nata kawai, shi zai yi mata maganinsu. Tana tsaka da wannan tinanin ne wani sako ya kara shigowa wayarta. Sai da ta ɗan saci kallan Sharifat ta wutsiyar idanu kafin ta buɗe saƙon. Taga Sharrifat hankalinta ya koma kan wayarta da guyson yake kiranta, ya tura mata saƙo a what'sapp ya jita shiru bata amsa ba, shi ne ya kira ya ji lafiya tana online bata bashi amsa ba. "Sharifat ina zuwa, zan je gidan wata class mate ɗina". Cewar Leesharh kenan. Dan yanzu saukin da ta samu har ta koma school. Cikin halin ko in kula ta amsa da. "In zo in rakaki ne?". Da sauri ta girgiza kai tare da cewa. "A'a ba sai na wahalar dake ba, yanzu zan je in dawo, wasu handouts zan karɓa". Jinjina kai Sharifat ta yi, sannan ta sake cewa. "Waye zai kai ki to?". Kai tsaye ta amsa da. "Yah Bilal ne zai kai yi, dama tin da safe mun yi magana da shi". Cike da murna Sharifat ta ɗago da kallanta daga kan wayarta izuwa kan Leesharh ɗin, fuska ɗauke da murmushi kamar ba yanzu ta gama sharar kwallah ba, har farinciki ya baibaye zuciyarta baiwar Allah. "Allah yasa idan kun je kafin ku dawo a hanya ku ƙullah soyayya da Yah Bilal, ai bama zan biku ba dan kada na shiga hakkin masoya, Allah ya mallaka maki zuciyar Yah Bilal sai a haɗa aurenmu". Sharifat da karfin hali take, ita da bata samu nata soyayyar ba take faman nemawa wata, har da wani za'a haɗa aurensu, ko yaushe ta mallaki zuciyar Ramish har zasu yi aute?. Girgiza kai kawai Leesharh ta yi ba tare da ta sake yin magana ba, dan ita tasan abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa ba ta samu soyayyar ɗaya daga cikin King Badeen or King Zuhair familys, bata kai ba, amma Sharifat sai wani hakikancewa take yi tana haɗata aure da Bilal karfi da ya ji, ita a suwa wai?. Mayafin kayan jikinta ta ɗauka tare da matsawa ta mannawa Sharifat sumbata haɗe da yi mata sallama, sosai Sharifat ta zage tana addu'ar Allah yasa kafin su dawo soyayya ta kullu, banda girgiza kai babu abin da Leesharh take yi. Haka ta wuce ta fita abinta. Ita kuma Sharifat ta cigaba da hira da guyson ba tare da ta kawo wani mummunar tinani a ranta ba. After some times. •••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Tuki yake yi a hankali cikin nitsuwa, dare ta yi, a kallah lokacin karfe 10 zata yi, zaune take a kujerar gaban motar hannunta rike da bakar laida mai ɗan girma. Dik da tana sanye da nikaf hakan ba zai hana mu iya gane cewa Leesharh bace, saboda idanunta da yanayin jikinta, kai komai sak Leesharh ce. Yana tuki yana waigowa dik bayan second ya kalleta, har sai da ta gaji ta ce. "Yah Bilal kada fa mu je mu samu accident". Maganar da ta yi ne ma ya kara tabbatar mun da Leesharh ce, dan babu banbanci a voice ɗinsu. "Ai ke ɗin ce, ba zan iya kawar da kallona daga kanki ba, dole ina juyowa in ganki in ba haka ba sai a samu matsala". Ya faɗa yana sauka daga titin sama izuwa na kasa. "Kai Yah Bilal ka fara ko?". "To ya kike san in yi? Dole ce tasa ai". Shiru ta ɗan yi, can kuma sai ta ce. "Samu waje ka tsayar da motar sai mu yi magana ko?"...... Ba musu ya gangara gefen titi ya yi parking, sannan ya juyo ya kura mata ido. "Menene next my lovely wife?". Ya faɗa. Dai'dai lokacin call ɗin Ramish ya shigo wayarsa, bai kai ga kawar da kallonsa a kanta izuwa kan wayar ba tasa hannu ta ɗage nikaf dake face ɗinta. Ƙasa kawar da kallonsa ya yi, da ɗan karfi ya furta wow. Leesharh ta sha make up yau sosai, ta yi kyau matuƙa kamar ba ita ba, sai glowing take yi. Har call ɗin Ramish ya katse yana nan yana kallanta bai yi magana ba. Me kuke tinanin ya haɗasu a wannan dare da har yake ce mata my wife? Dama suna soyayya ne? Ko dai yau suka fara?. "Yah Bilal mu je ka saya mun ice cream sai mu koma gida dare ya yi". A ɗan shagwaɓe ta faɗa. Nisawa ya yi, maza anga kyau iya kyau har ya ji kamar ba'a duniya yake ba. "Wife kin yi kyau matuƙa sosai". Siririn murmushi ta saki kafin ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa. Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta. "A'a barni in kalli face ɗin matata da kyau". Ya faɗa yana zame hannunsa daga haɓar tata. "Kai Yah Bilal ni fa kunya nike ji". Ta faɗa tana kallansa ƙasa ƙasa. Matsar da bakinsa dab da kunnenta ya yi, ƙasa ƙasa kamar mai raɗa ya furta. "Kin girma fa, komai ya ciko dai'dai yadda nike so, yakamata......." Katse shi ta yi ta hanyar jiyowa garesa da sauri. Kashe mata ido ɗaya ya yi tare da matsar da bakinsa saitin kumatunta, sumbata ya bata a lallausan kumatunta. Lunshe idanunta ta yi tare da sauke ajiyar zuciya. Ƙara matsa dab da ita ya yi, kamar zai haɗe bakinsu waje guda, kamar mai raɗa ya ce. "Yau kam za'a bani dama ne ko dai za'a cigaba da hanani kamar a baya?". (What?😳 Kenan ya saba kawo mata harin kiss? Tab akwai matsala, a warware mana wannan cakwakiya ko zan samu damar shan maltina mai sanyi.) Tana kallan cikin idanunsa ta ce. "Yah Bilal ko da can baya ban taɓa hanaka na ai, kai ne dai kake ganin kamar ina hanaka". Gera ɗaya ya ɗaga mata tare da kara matsawa dab da ita sosai, a hankali yasa hannunsa zai ɗan rungumota. A karo na biyu call ɗin Ramish ya sake shigowa wayarsa. Ɗan ciza laɓɓansa kaɗan ya ɗan yi haɗe da janye jikinsa daga kusa da ita, ya koma ya mannu da jikin kujerarsa yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya ɗauko wayar, kamar ba zai yi picking ba, dan yasan wanenen Ramish, tsaɓ zai iya cankar a wani irin yanayi yake ciki da jin voice ɗinsa kawai. Amma sai kuma ya tina in har bai ɗauki wannan call ɗin ba to Ramish zai fita nemansa ne, saboda sun san dik abin da ya sha kansu basa wuce miss calls biyu ma junasu ba tare da sun yi picking ba, shirunsu basu yi picking ba hakan na nuna suna cikin matsala kenan, kunga dole ya fita nemansa. Hakan yasa ya ɗauki call ɗin tare da kara wayar a kunnensa yana seseta nitsuwarsa. Daga ɗayar ɓangaren Ramish ya yi cikakken sallama. Amsawa ya yi idanunsa a kanta, ita ma shi take bi da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa. "Ina kake Bilal?". Ramish ya jefa mashi tambaya. Shiru ya ɗan yi yana tinanin abin faɗe, basu saba yin karya ba, hakan ya ja ya rasa abin faɗe. "Ina zuwa gida yanzu". Ya faɗa yana san katse kiran. Katse shi Ramish ya yi da cewa. "Ka faɗa mun in da kake in zo in sameka yanzu". A hanzarce ya ce. "A'a ba sai ka zo ba, ina hanyar gida yanzu". Shiru Ramish ya ɗan yi, can kuma sai ya ce. "Ka dai san bana magana biyu ko?". Jinjina kai Bilal ya yi alamar e tamkar yana gabansa haɗe da cewa e haka ne. "To ina kake zanzo yanzu". Zaro idanu Bilal ya yi, sai ya ji kamar an kwaɗa mashi guduma a kansa, hankalinsa ne ya tashi, Ramish ya zo ya samesa a nan ai ya shiga uku, me zai ce mashi ya rabu da shi kenan?. Zare wayar daga kunnensa ya yi, ba tare da ya sake yi wa Ramish magana ba ya yi saurin katse kiran, a hanzarce ya tashi motar. "Yah Bilal lafiya?". Ta jefa mashi tambayar tana kallan wayar dake hannunsa. "Sauke nikaf naki, sorry ba zamu iya tsayawa sayen ice cream ba, gida kai tsaye zamu wuce, gobe muna da taro, idan mun taso daga taron zan saya maki ice cream ɗin in kawo maki". Ya kai karshen maganar tare da kunne mota. Da gudun gaske ya figi motar tamkar zai tashi sama, har sai da ya bata tsoro. A can gida kuwa. Ramish yana tsaye a parlournsu, daga shi sai sexy short, babu riga a jikinsa sai white singlet mai kyan gaske, yana tsaye a jikin windownsu dake fuskantar harabar gidan, hannunsa rike da cup and his phone. Shi ma Ramish yana da zanen letter R a damtse hannunsa da ya zana kamar yadda Bilal ya yi zanen B a wuyarsa, yanayinsa ta nuna yana cikin damuwa sosai, saboda abubuwa sun sha kansa matuƙa, ga shi gobe zasu yi wannan taro da yake sa ran kafin taro ya kama masu nikaf kenan, sai dai har yanzu bai samu wata makama da zai iya kamasu da ita ba, babu ma wanu abin zargi da suka bar mashi, abin dai ya sha gaban tinani, dik yadda aka yi su ma shegu ne. Ya yi shiru yana kallan harabar gidansu kamar mai tinanin wani abin, bawan Allah damuwa ta yi mashi yawa, bai san ya taron gobe zata kasance ba. Ba tare da ya juyo ba, cikin nitsuwa ya ce. "Daga ina kake a cikin wannan dare bayan kasan halin da muke ciki?"............ Kamar wani aljani, ko yaushe ya ji yo takun sahun Bilal?. Bilal da ya shigo yanzu ne ya ɗan fara kame kame kamar wani maras gaskiya, dama kamar yasan zai sami Ramish a wajen yasa ya shiga parking space ɗinsu ta kofar baya ba tare da kowa ya gansa ba, dik dan gujewa ƴan gidan kada su gansa. "Meyasa kaki yarda in zo in sameka a in da kake? And meyasa ka katse kirana ba tare da mun gama magana ba?". Ramish ya sake jefa mashi tambaya a karo na biyu ba tare da ya jira ya amsa ta farko ba. Shiru ya kasa amsawa, dan bai san me zai ce mashi ba, ga shi dik in da suke zuwa dama a tare suke tafiya bare ya yi mashi wani karya. A hankali Ramish ya juyo garesa, wani irin dogon ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Me kake ɓoye mun my love". Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallan tuhuma, dan yanzu zuciyarsa ta rigata da kai point ɗin da ba zai iya ɓoye zargin da ya jima yake yi ba, ya daɗe sosai zuciyarsa tana ɗarsa mashi zargi a kan Bilal na ɓoye mashi wani abin, amma a koda yaushe ƙoƙarin kawar da wannan zargi yake yi domin yaga ya kori shaiɗan dake san rabashi da ɗan uwansa ya haɗasu faɗa. "What do you think that I'm hiding for you?". A ɗan razane ya yi maganar, alamar kamar dai da gaske akwai wata a ƙasa. "Ka fini sani Bilal, ka fini sanin abin da kake ɓoyewa". "Wai Yah Ramish lafiyarka yau kuwa? Shin na taɓa ɓoye maka wani abin ne? Tin tasowata har zuwa yau ba a tare muke yin komai ba?..........." Cikin zafa da kunan rai ya ce. "Banda wannan lokacin Bilal, tin da muka taso tare muke yin komai amma banda yanzu!". Yadda ya yi maganar da alama ransa ya fara ɓaci, zuciyarsa ta fara raunata sosai, dan da alamar zarginsa tana san tabbata, idan kuma abin da yake zargi ta tabbata da gaske, magana ta domin Allah zai iya rasa ransa, saboda kowa yasan bayan iyayensa babu wanda yake kauna biyun Bilal, yana sansa kamar ransa, dole zuciya ta buga idan kuwa haka ne. "Yah Ramish why are you talking like that? Talking out of control, and you're shouting like mad............". Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata cak sakamakon wani irin tsawa da Ramish ya daka mashi a kan ya yi mashi shiru. Taku biyu ya yi ya matsa gabansa, dama tin da ya fara bincike a kan masu nikaf Bilal ya zare hannunsa yaki taimaka masa, tare suke yin komai, amma a wannan karon Bilal yaki tayasa, hakan yasa zarginsa a kansa ya karu, sannan ga fita da Bilal ɗin yake yi shi kaɗai a yanzu, idan baku manta ba a ranar da Ummie ta je ɗakin Ramish nace maku Bilal baya nan, ya fita ko?. To kun ga kuma a tare suke fita, yanzu Bilal baya taɓa fita tare da Ramish, sai dai ya fita shi kaɗai, ga yawon dare da yake yi wanda a baya sam baya yi, baya zaman gida ko wajen aiki sosai yanzu, hakan ya kara ɗarsa zarginsa a zuciyar Ramish, sannan sai ya rinƙa kawowa Ramish wasu silly silly abubuwa da basu da amfani ya haɗa shi da aiki yasa Ramish baya aiki bincikensa yadda ya dace, hakan yasa ya ja lokacin bai iya gano gaskiya a kan abin da yake bincika ba, ga shi gobe taron da zasu yi ne. A takaice abubuwa dayawa ya ja Ramish ya fara zargin Bilal tun watannin huɗu da suka wuce. Da karfi Ramish ya damki wuyar rigar Bilal, idanunsa sun ƙaɗa sun yi jajir, da alama yana out of control ɗin da gaske, jikinsa har wani kerma ta soma yi, yana gudun tsono abin da zai iya zame mashi narazana ga rayuwarsa, sannan kuma yana san tono gaskiya ko dan ya san ina ya dosa da suwaye yake tare. "Ka faɗa mun me kake ɓoye mun". Cikin zafa Ramish ya yi tambayar haɗe da ɗan ɗaga murya. Pretending................. Ƙoƙarin nuna gaskiyarsa Bilal ya yi, yana san nuna shi ba mai laifi bane kuma babu abin da yake ɓoyewa, hakan yasa ya dunkule hannunsa da karfi ya kaiwa Ramish duka a kirji. Cikin ɗaga murya ya ce. "Wani irin abu ne wannan? Meyasa na zama abin zargi a gareka? Meyasa zaka ce ina ɓoye maka wani abin? Mekake nufi da kalamanka a kai'na? Ko kana tinanin ni zan iya cutar da kai ne?". (My people's yanzu na ce waye ya kawo maganar cutarwa a nan? Babu rami meya kawo maganar rami? Shin Ramish ya ce Bilal zai cutar da shi ne da Bilal ya kawo batun cutarwa? Ku tayani yin alkalanci a nan wajen.) Da gudu Dr Raj and Yah Rizwan suka fito daga nasu bedroom ɗinsu jin muryar Bilal cikin faɗa yana magana. Innalilahi wa inna ilahir rajiun shi ne abin da suka furta a tare. Zame hannunsa Ramish ya yi daga wuyar rigar Bilal, da hannu ɗaya yasa ya daki kirjin Bilal da karfi har sai da Bilal ya yi baya baya ya bugu da jikin bango. Duuuuuuuuuummmmmmmmmm "You are lying Bilal! There must be something you are hiding for us, and you have to tell us what you are hiding today!!". Cewar Ramish kenan. Bilal domin ya kare kansa ya kuma tabbatar da gaskiyarsa sai ya yi ƙoƙarin kawo abin da zai kawar da batun ya faɗa masu me yake ɓoye masu, sai ya yi ƙoƙarin yin faɗa da Ramish ta yadda hakan zai ja wancan zancen ta kau. Da karfi ya nufi Ramish da nufin zai rama dukan kirjinsa da ya yi. Dr Raj da Yah Rizwan ne suka shiga tsakaninsu da gudu, sanya karfi Bilal ya yi ya bangaje Dr Raj da karfi har sai da ya faɗi a saman sofa. Yah Rizwan kuma ya taresa yana mai daka mashi tsawa a kan ya nitsu su bar shir men nan. Yah Ramish dai yana tsaye yana binsa da kallo, mamaki ne ma ya kama shi, wai yau shi da Bilal ne a irin wannan yanayi? Wannan wace iriyar musifa ce? Su da suke san junansu tamkar su yi wa juna numfashi! To wai me matsalar ne?. Ya jefawa kansa tambaya, jikinsa dik a mace sosai, sam baya san dukan Bilal, dan wlh idan ransa ya ɓaci za'a iya kwasan Bilal ranga ranga, shiyasa yake ya ƙoƙarin koran shaiɗan kada ya kaisa ya barosu, dan har yanzu yaki yardanwa da zuciyarsa Bilal mai laifi ne. Allah sarki zuciya, kun san dama da wuya ya iya karɓar wannan kaddara idan har ba yaga da gaske ido da ido Bilal ya cutar da shi ba. Da sauri Ramish ya juya ya koma cikin bedroom ɗinsa, basu ankara ba sai ji suka yi ya banko kofa da karfi ya murza key, a cewarsa koma menene kamata ya yi ya binciko da kansa, a matsayinsa na babba bai kamata ya tsaya tambayar Bilal ɗin ba ma ai, kamata ya yi ya tsaya da kansa ya binciko gaskiya, zubar da girma ne ma ya tsaya sa in sa da wani, shi da yake da hanyar gane gaskiya, shi da Allah ya bashi ilimi da kaifin ƙwaƙwalwa! Ai bai kamata ya wani damu ba!. Yah Rizwan ne ya ja Bilal suka wuce bedroom ɗinsa, Dr Raj kuma ya bi bayan yayansa Ramish. Sai dai ko da ya je sai ya tadda Ramish ya rufe kofa, har kamar zai yi knocking sai kuma ya tina halin yayan nasa, yanzu a banza zai ɓata lokacinsa dan Ramish ba zai sauraresa ba, hakan saya ya juya ya bi bayan Bilal dan ya je ya ji me ya haɗasu faɗane wai, su da suke kamar twin's................To harshe da haƙora ma watarana ai suna saɓawa bare ƴan adam malam Dr Raj. A ɓangaren su Sharifat kuwa, Leesharh ta dawo daga unguwar da ta je cikin ƙoshin lafiya, ta yi wanka da sallah tana kudundune a cikin bargo saman bed, Sharifat bata a ɗakin, tana wajen Ummie ɗinta, dan Ummie ta ce ta zo su kwana yau a tare dan tana da magana da ita. Shiru ta kwanta tana tunanin duniya, karfe 11 na dare ta buga, time ɗin na bugawa wayarta ya hau ƙara alamar shigowar kira. With her full confidence ta janyo wayar. Ganin private number ya sa ta yi saurin sakin siririn murmushi wanda ya fi kama da murmushin ramakon gayya. Wayar tana gab da katsewa ta yi picking tare da karawa a kunnenta. Shiru aka yi ba'ayi magana ba, a gadarance ta ce. "Hello wanene?". Daga ta cikin wayar ta tsinkayo muryoyi guda biyu suna magana kus, kus, kus alamar suna shirya abin faɗe kenan. Da yake bata jin me suke faɗe sai ta ce. "Idan baku gama tsara abin da zaku faɗa mun tun kafin ku kirani ba me na kirana? Ai da sai ku bari sai kun gama tsarawa ko?". Shiru basu amsa mata ba, cigaba da magana ƙasa ƙasa suka yi. "Okey ni ina da abin yi, idan kun gama shawartawa zaku iya sake kirana, dan nima yanzu jiran call ɗinku nike yi". Ta kai karshen maganar tana ƙoƙarin cire wayar a kunnenta da ta katse kiran. "Kada ki kuskura ki katse mana call". Daga ɗayan ɓangaren aka faɗi hakan. Gabanta ne ya yi wani irin mummunar faɗuwar jin voice ɗin kamar na Bilal. Amma sai ta daure, kun santa da jajircewa, ta nuna kamar bata san masu kiran nata ba, cikin nuna isa ta ce. "Da yake wayarku ce ba sai ku hanani katseta in gani ba". "Ke kin san da suwa kike magana kuwa?". Siririn tsaki ta ja, har da wani wuwwurga idanunta sama da ƙasa ta yi masu kallon up and down kamar tana gabansu, a walaƙance ta ce. "A fagen iskanci ko da shaiɗan nike magana karshe kenan a dik wani zalinci ko? To ko da shi nike magana bai isa ya ɗaga mun murya ya faɗa mun ga abin da zan yi da wayata ba". Da suka fahimci faɗa ta zo da shi, su kuma lallaɓata suke da bukatar yi, dan su suke nema a wajenta, sai suka sassauta murya, cikin nitsuwa aka canza murya, da alama wani ya karɓi wayar. "Dik ba wannan ba, magana muke san yi dake, ajiye dik wani zafin kanki da tashen balajarki a gefe ki sauraremu". Jin haka yasa ta amsa da. "Ina jinku". "Kin san da cewa aikinki bai kare ba ko baki sani ba?". Ya jefa mata tambayar haɗe da yin shiru yana jiran amsarta........... "Zaka iya cigaba da magana, saboda ba zan iya kowace magana in amsa ba, idan ka gama faɗar dik abin da zaka faɗa sai in tattare in baku amsa guda". Ta yi maganar tana miƙewa zaune. "Okey zaki iya yin dik abin da kike so, amma ina san ki sani mahaifinki na hannunmu, ko ki yi mana abin da muke so, ko kuma yau lahira ta yi bako, wlh a daren nan idan baki nemo mana masaniyar a in da su Ramish zasu yi wannan taro ba, tabbas zaki rasa mahaifinki". Tin da take a rayuwarta bata taɓa yin dariya irin wanda ta ƙaƙalo dan dole a yanzu ba. Bushewa da dariya mai ɗan sauti ta yi. Shiru suka saurara suna jinta, har da rungumo pillow ta yi a kirjinta tsabar dariya. Sai da ta yi mai isarta sannan ta dakata haɗe da ɗaure fuska lokaci guda, sannan ta sauko ƙasa daga saman bed ɗin, gaban mirror ta nufa wayar na manne a kumnenta, har ta kusa isa wajen kuma sai ta koma ta kunna wutar ɗakin yadda zata ji daɗin ganin kanta da kyau, sanye take da wando da riga na barci masu kyau launin ash colar. Tsayuwa ta yi a gaban mirror, cike da kwarin gwiwa take bin kanta da kallo, dik sun yi shiru suna jinta, amsarta kawai suke san ji. Raunartar da muryarta ta yi, kamar wata marainiya haɗe da fuskar tausayi, cikin nuna damuwa ta fara magana kamar haka. "Dan Allah kada ku cutar mun da babana, zan yi dik abin da kuke so, ku yi hakuri kun ji?..................." Tana gama faɗar haka ta wani irin ɗaure fuskarta sosai, cikin kakkausar murya ta cigaba da cewa. "Haka kuke son jin na faɗa ko? To baku isa ba, wlh ba zan sake yin abin da kuka ce ba, mahaifina kuma Allah ne ya haliccesa ba ni ba, dan haka shi zai karesa ta in da baku taɓa zata ba, ba zan sake cutar da wani a dalilinku ba, na saka mashi guba na cutar da shi a farko, na sake zama sanadiyar da aka harbesa da bullet, na sake zama sanadiyar da aka shirya bomb da zai kashe mutane dayawa, na cutar da Ramish sosai wanda dole a yanzu na gyara kuskure kada Allah ya kamani, shi kuma babana ku je ku da Allahn da ya haliccesa, sannan kada ku manta idan kun kashe babana ku kuma ku tabbata a duniya kada ku mutu, daga karshe ina yi maku mummunar albishir da cewa wlh tallahi dik da ban taɓa ganin fuskokinku a zahiri ba, to ku sani zan iya gane ne ku, sannan ku sani nasan gidan wannan mata mai kibar, bugu da kari kuma ku sani dik maganganun da muke yi da ku tun daga ranar farko har zuwa yanzu ina da recording ɗinsa in audio a cikin memoryna da na yi mashi ajiya mai kyau, dik time da muka yi waya ina recoding in saka memoryna in yi copy in cire in ajiye dan samun shaida, ku jirani yanzu lokacina ne, dik sai na ɗauki fansan abin da kuka yi mun, kuma Ramish da izinin Allah ya fi karfinku, daga yau ni zan zame mashi garkuwa mai taimaka mashi ta hanyar da bai zata ba, sai asirinku ya tonu azzalumai, kuma ku kwana da sanin cewa nasan wanenen Bilal a cikinku, kuma tabbas dan na taya Ramish aiki zan shiga jikin Bilal, zaku sha mamaki". Babu tsoro ko miskala zarratin a ranta ta zayyano maganganun nan. Tana gama faɗar hakan ta katse wayar tare da kashe shi mai gabaɗaya. Idan hankalinsu ya kai muliyan to fa a yau ya tashi. Ita kuwa kallan kanta a cikin mirror ta yi, a fili ta furta. "Lokacin ku ya fara daga yanzu, wlh ba zan dai'na zargin Bilal ba, kuma zai gane bashi da wayo a lokacin da zan kama shi cike da hujojin da ba zai iya kubcewa ba, zai sha mamakina, sun ɗauka bani da ilimi bani da wayo ko? To su shirya, Bilal kai ma lokacinka ya fara, zaka sha game na karya, zaka gane baka iya cin amana ba, am sorry Yah Ramish, kila idan na tayaka wannan yakin ka iya yafe mun laifukan da na yi maka, is time now!". Ta kai karshen surutan nata tare da juyawa ta isa ga switch, kashe wutar ɗakin ta yi ta wuce izuwa saman bed abinta. Jama'a na ce ku tafawa Leesharh, ana ganinta kamar wawiya ashe tana da wayo, kenan harda recoding na maganganunsu ta rinƙa yi? Lallai ta cika jajirtatciya, kenan saboda ta gane wanenen Bilal ta aminta da soyayyarsa ko dai ya abin yake? Akwai cakwakiya kuwa! Muje dai zuwa dan muga ya wannan wasa zata kaya. Amma kuna tunanin masu nikaf zasu barta da ranta? Kada ku manta ta yi masu barazana da hujoji masu karfi kamar recoding nasu, sanin gidan Hajiya two seater, sanin Bilal da dai sauransu, kuna tunanin zasu barta ta tona masu asiri?. To sai dai muce Allah yasa ta kai wayewar garin gobe, dan gaskiya akwai matsala, suna fa da mutane a cikin gidan, ga shi Sharifat bata ɗakin yau, fatana kada su saka mutanensu su biyo dare su kasheta fa.........😥 ••••••••••••••• FOREST•••••••••••••••🔥🔥🔥 Kwance suka isko Pretty a cikin runfar da ya yi wa Auta a lokacin da suka ƙarisa wajen. Ta yi barci baiwar Allah, ta cinye kifinta tas har da haɗawa da na Auta abinta, dik ta yi masu tas. Kallon Hoorain Auta ta yi, a ɗan shagwaɓe ta ce. "My Hero yunwa fa nike ji". Cike da mamaki ya amsa da. "Ba na kawo maku abinci ba". Taku step biyu ta yi ta matsa kusa da shi. "Ai ɗaukin ganinka yasa na tafi na bar abincin, kaga kuma Pretty ta cinye". Jinjina kai ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Bari in je in kama maki wata in gasa sai in kawo maki, je ki zauna kusa da Pretty". Make mashi kafada ta yi ba tare da ta yi magana ba. Kawar da kallansa a kanta ya yi yana tambayar menene kuma. "Ni dai sai dai mu tafi tare". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. "A'a bana san ki wahala, wajen da ɗan nisa, zauna bari in dawo". Kara make mashi kafaɗa ta yi. "A'a ni ban yarda ba sai dai mu tafi tare". P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ "A'a bana san ki wahala, wajen da ɗan nisa, zauna bari in dawo". Kara make mashi kafaɗa ta yi. "A'a ni ban yarda ba sai dai mu tafi tare". "Haka kike so?". Kai ta gyaɗa mashi da sauri alamar e. Da hannunsa ya nuna mata hanya a kan ta wuce su tafi. Sake make mashi kafaɗa ta yi. "Ni dai ko ka wuce gaba ko kuma mu jera a tare". Ta faɗa tana ɗan karkata kanta. "Meyasa to?". Cike da mamaki ya yi tambayar............... Ɗan ɗaure fuska kaɗan ta yi, cike da zolaya ta ce. "Saboda bana san in wuce gaba ka yi ta kallona, ina tafiya kana kirga mun taku na one by one kana kalle mun shape na bayana kaga ba alkyabba na..........." Ƙasa ƙarisa maganar ta yi sakamakon ɗagowa da ya yi a miliyan ya sauke kallansa a kanta, kwata kwata abin da bai taɓa kawowa a ransa ba kenan, mamakinta ne ya kama shi, ko a ina ta koyi magana har haka........ Ni kuwa na ce tana matsayin masoyiya kuma aminiyar Chuchu ƴar wanka ai fin haka ma zaka ji, su da suka kware wajen bawa flowers ruwa, ai a banza uncle Jahiz yake cewa basu girma ba, ya zo ya gansu tare da flowers ɗinsu a nan ne zai tantace sun girma ko basu girma ba, yaran yanzu ai da wayonsu ake haifarsu. Ganin ya yi shiru kamar wanda ya yi suman tsaye ne yasa ta ɗaga mashi gera guda alamar yane?. Shi kuwa shirun da ya yi tinanin time da take ƴar yarinya da bata wuce 5 years ba yake ɗaukarta idan sun fito ita da su Chuchu yake yi, dan a lokacin an bashi ragamar kula da ita. Ganin ta ɗaga mashi gera guda yasa ya nisa tare da kawar da kallonsa daga kanta, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma dan ya cire mata tinanin nan na banza na cewa yana kallan shape ɗin jikinta yasa ya ce. "Ai na rigada na gama kalle shape ɗin tin bai fito ya zama cikakken shape ba, dan a shekarunki biyar kam ai bai fito ba, kuma a hannunna shape ɗin ya bayyana, dan haka na san..........." Bai ƙarisa maganar ba ta rufe mashi baki ta hanyar harara da ta dallah mashi. Kawar da kansa ya yi tare da juyawa yana jin kamar ya saki murmushi, sai dai bai iya murmushin ba, zuciyarsa ta ji daɗi ganin yadda ta ɗaure fuska tana harararsa. A kule ta ce. "Wannan shi ne babban kuskuren da mace zata yi ta so wanda ya san yarintarta, kullum sai ya yi mata gori, koma dai me zaka ce ka ce, ai a da lokacin da shape ɗin ya bayyana a hannunka kana kallona a matsayin kanwarka ce, yanzu kuma kallon masoyiya kake mun, dan haka manufarka a kallona yanzu ya sauya!". Ya fahimci maganganunsa sun ɗan sosa ranta, dan haka sai ya juyo da nufin ya bata hakuri. Ganin ya juyo kuma taga alamar hakuri zai bata yasa ta juya mashi baya irin ta yi fushin nan. Yana ƙoƙarin fara yin magana ta yi saurin barin wajen ta nufi wata hanya daban tana ɓata rai. Ɗan girgiza kai kawai ya yi, dama yasan fin haka ma zata yi, dama renonsa ce ita, mata, mata, mata sai dai shirin Allah wlh, dik yadda mace take sonka hakan ba zai hanata yin abin da ta yi niyya a kanka ba, kai idan mace bata wahalar da kai ma wlh ba son gaskiya take yi maka ba, wata haka kawai zata kirkiro faɗa, ku yi ta yi har sai ta kureka, sai kuma ta ce wai tana gwadawa ta ga irin karfin son da kake yi mata ne, ta azabtar da kai, idan ka yi complain ta ce baka sonta, mu dai sai shirin Allah wlh. Ganin ta ɗan yi mashi nisa yasa ya yi saurin rufa mata baya. Fahimtar yana biyota yasa ta watsa a guje ta shige cikin wasu dogayen ciyayi dake kusa da korama. Ba shiri ya bita da gudu dan kada ta ci karo da wani abin ya cutar da ita. Yana sanya kansa a wajen ciyayin zai bi bayanta ita kuma tana fitowa da gudun gaske. Karo suka unexpext. Baya baya ta yi zata faɗi ya yi saurin riƙo hannunta. A miliyan ta faɗa jikinsa haɗe da datse idanunta gam, a tsananin tsorace murya na kerma ta ce. "Tamisa, wlh akwai tiger a wajen ruwan nan". A rikice take maganar tana haɗe word, jikinta har kerma yake yi. Shiru ya ɗan yi yana jin yadda kirjinta yake bugawa da karfi karfi alamar ta tsorata sosai. (Anya Hoorain ba shiru ya yi yana jin daɗin tula tulanta da suka taɓa chest ɗinsa ba kuwa🤔 shi ma yanzu ban yarda da shi ba 🥱 team Hoorain kada ku ce na ce, na ce ɗin 😅 a zo a saka mun gas) Kamar saukar aradu haka ya tsinkayo gurnanin damisam a kunnensa. Kafin ya tabbatar da gaskiyar abin da yake ji tuni ihunta ya fasa dodan kunnnesa, da karfi ta zunduma ihun haɗe da cewa. "Hoorain ba ka jishi ba, wayyo daddyna". Yau ta manta da my hero, Hoorain kai tsaye aka ce, ƴar ƙaniya ta hango mutuwa!. A tsananin rikice ta yi maganar tare da sakesa zata gudu ba tare da tasan in da zata nufa ba. Ya fahimci ta rikice sosai, idan ya barta ta tafi ma zata iya afkawa wani wajen ta cutu, idan kuma ya tsayar da ita ba zata taɓa barinsa ya kwaci kansu daga hannun wannan damisa ba, to yanzu me abin yi kenan?. Ya jefawa kansa tambaya, a hankali ya sanya hannunsa a waist ɗinsa dan ya ji ya mayar da takobinsa mazauninsa ɗazun ne ko bai mai da ba. Kankameta ya yi da hannu ɗaya ya hanata tafiya. Ajiyar zuciya ya sauke jin takobin yana nan. Da karfi ta riƙesa tana ihu taki ta yi shiru. Yana tinanin yadda zai yi da ita sai ganin damisan ya yi a gabansu ta fito ta wajen koramar da gudun bajinta. Wani jibgege da shi, ya ci ya ƙoshi, ruwa ya zo sha a wajen koramar ta je ya ganta, kun san kuwa dole ya biyota dama shi ne kuma ya biyota ɗin. Ko kaɗan Hoorain bai ji tsoro ba, ita kuwa jin gurnanin dab da su yasa ta kara ƙanƙamesa tana faɗin shikenan ta mutu yau. Ido cikin ido Hoorain ya kurawa damisan nan kallo babu ko tsoro. Wani irin uban tsalle wannan damisan ya daka sai kansu da gudun gaske. A miliyan Hoorain ya ture Auta gefe da karfi, cikin zafa shi kuma ya durkushe gwiwowinsa a ƙasa, hakan yasa damisan ya wucesu ya dira a bayansu. Cikin zafa Hoorain ya juyo ga damusan tare da miƙewa tsaye, ita ma da ya tureta ta faɗa cikin ciyayi a haukace ta miƙe tsaye, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Hakan yasa suka rabawa damisan hankali gida biyu, ya ganta ya ga Hoorain, ya rasa wazai fara kaiwa farmaki. Tsayuwa cikin jarumta Hoorain ya yi tare da ƙara ɗaure fuska sosai, irin babu wasa a tattare da shi ɗin nan. Yasan halin dabobi sosai, yasan da cewa komai ƙanƙantar motsin da suka yi yanzu damisan nan zai sake daka tsalle ya yi kansu ne dan zai yi tunanin hari zasu kawo mashi. Hoorain yana san zaro takobinsa yana tsoron motsawa, shi ba damuwarsa ya motsa damisan ya yi kansu ba, da kansa shi kaɗai zai yi da da sauki, idan ya yi kan Auta ai damka ɗaya zai yi mata sai gawa. Yana ƙoƙarin zare takobinsa cikin dabara Auta da ta miƙe tsaye a yanzu ne ta kurma ihu tare da nufarsa da gudu. Motsin da ta yi ya yi dai'dai da damisan ya sake daka tsalle ya yi kansu. Hakan ya bawa Hoorain damar zare takobinsa, da karfi yasa hannunsa ɗaya ya sake ture Auta baya ta koma in da ta taso, da karfi shi ma ya yi gefe, a karo na biyu damisan ya sake dira a bayansu, Auta ta sake tafiya ta faɗi cikin ciyayin dake wajen again. "Kada ki tashi". Shi ne abin da Hoorain ya faɗa mata da karfi, amma ina bata jinsa saboda tashin hankalin da take ciki. A lokacin kuma ran damisan nan ya gama ɓaci, ya fusata sai ya nufi Hoorain da karfin gaske yana wani irin buɗe baki. Ko kaɗan Hoorain bai tsorata ba, yana tsaye damisan ya isa garesa, cikin zafa suka fara kokawa yana ƙoƙarin zana mashi fata da takobinsa, daga karshe ma takobin faɗuwa katsa ta yi damusan ya haike mashi, da waɗan nan shegun faratunan hannun nasa ya fara kai mashi gafsa ta ko'ina Hoorain yana ƙoƙarin kaucewa. Tsorata na ganin damisan ya kayar da Hoorain a ƙasa ya haiƙe mashi yasa numfashinta ɗaukewa diff ta zube ƙasa. Shikuwa kokawa suka cigaba da gwabzawa da damisan, ƙoƙarin kama agarar damisan ya fara yi tun da takobinsa ta faɗi ƙasa, in ya kama agaransa dolen dolensa ya risina mashi. Gabaɗaya damisan ya yagushe mashi face ɗinsa, gwabzawa suke yi sosai, daga shi har damisan kowanne daga cikinsu burinsa ya cinma abin da yake muradi, damisan yana haran wuyar Hoorain, shi ma yana haran agarar damusan. Ya sha wahala sosai kafin ya samu ya ture damisan daga kansa, sannan ya miƙe cike da jarumta, da gudun gaske damusan ya yi kansa dan ma kada ya bashi wata damar kara karfafa kansa kenan. Juyawa ya yi da gudu damisan ya rufa mashi baya. Tsalle ya yi ya taka wata bishiyar ɓaure dake kusa da su sannan ya juyo da karfi haɗe da haɗa hannayensa dikka biyu da karfi sosai ya dakawa damisan duka a tsakiyar kai, nan take damisan ya durkushen kafafunsa a kasa yana sakin wani irin kurnani mai ban tsoro da kuma ban tausayi, alamar Hoorain ya ji mashi ciwo a kai. Ko kaɗan Hoorain bai yi niyar kashe shi ba, ganin ya yi ƙasa ya yi mubaya'a yasa ya rabu da shi, a hanzarce ya wuce ya nufi in da take yana sauke numfashi a hankali hankali. Da hannu ɗaya ya ɗagota bayan ta duƙa. Kai tsaye wajen koramar ya nufa da ita. Cikin nitsuwa ya kwnatar da ita a saman dutse, ƙarisawa gaban koramar ya yi haɗe da tarar ruwa ya fara wanke jininsa da damusan ya fidda mashi, har lokacin sai jan numfashi kamar haki yake yi alamar wanda ya gaji. Sai da ya wanke jikinsa tsab kafin ya dawo kusa da ita, cak ya sake ɗaukarta suka ƙarisa gaban koramar. Gabaɗayanta ya sanyata cikin ruwan. Da ihu ta farka tana sambatun damusa zai cinyeta. Shi ma ruwan na jiƙasa, dan kusan a tare suka shiga cikin koramar, sai dai shi ta ɗan baki baki ne, da kyar ya iya ambatar sunanta da ranki ya daɗe. Ina ai bata ma san yana yi ba, ihu ta cigaba da yi tana ƙoƙarin kwatar kanta, da alama bata cikin hayyacinta. Ƙanƙameta sosai ya yi, cike da tausayinta ya matsar da face ɗinsa ɗan dab da ita, sannan ya ce ta nitsuwa damusan ya gudu. Jin hakan yasa ta yi saurin waro idanunta, ganinta a hannunsa kuma cikin indoron ruwan dake kwaranya yasa ta yi saurin juyar da kanta izuwa gefe da gefe tana neman ina damusan yake. "Ki kwantar da hankalinki baya nan, ya tafi". Cike da so da kauna ya faɗa. A tsorace sosai ta ce. "Ina ya tafi Hoorain?". Ta yi maganar tana kai hannunta saman face ɗinsa. "Bai yi maka komai ba ko?" Ta sake tambaya tana shafa kumatunsa". Jinjina mata kai ya yi haɗe da cewa. "Babu wata barazana ranki ya daɗe". Ɗan daure fuska ta yi haɗe da turo baki, a shagwaɓe ta ce. "Hoorain wai kai baka iya soyayya bane sai wani ranki ya daɗe kamar wani bosawa? Babu ko irin sunan love ɗin nan?". Shiru ya ɗan yi tare da matsawa baya kaɗan ya fitar da ita daga cikin ruwan kenan, sannan ya rabata da jikinsa ya sauketa ƙasa a kan kafafunta. "Hoorain baka bani amsa ba". Wannan karan murya a ɗan kasashe ta yi maganar. "Na iya soyayya, sai dai ina tinanin abin da zai je ya dawo shiyasa nike ja da baya, bana san dik abin da zai iya jawo mana matsala da ni da ke". "Ban gane nufinka ba". Cike da mamaki ta yi tambayar. Gyara tsayuwansa da kyau ya yi, cikin nitsuwa ya fara warware mata komai dan gane da abin da yake jiwa tsoron yasa baya san zurfafawa a soyayyarsu, baya san sakin jiki sosai. "Ke da kanki kin san ƴan uwanki ba zasu taɓa yarda da ni a matsayin masoyinki ba, ba zasu taɓa karɓata ba, sannan kin san matsayina da naki daban daban, ke kanki ina jiyewa zuciyata tsoron ki juya mata baya, na san daddynki ba zai taɓa yarda ya bani ke ba, kema kuma kin san da hakan, idan muka cigaba da soyayya na tabbata wahala zamu sha, and nasan ke ba zaki iya jura ba, idan kin ji wahala kaɗan zaki guji zuciyata ki barni a wahale, wannan shi ne kaɗan daga cikin abin da nike guje mana". Tabbas ta fahimci dalilansa, sannan kuma ta gamsu dalilai ne masu karfi da dole zasu iya sanya shi ja da baya, tasan King ba zai taɓa yarda ba, bama azo ga King ba, ko guyson ba zai yarda ba, ranar iya ganinta kawai ya yi ta kusa da part na mayaka ji yadda ya tashi hankalinsa bare kuma ace ya ji tana san assistant commander? Tab ai babu wanda zai goya mata baya, ko Chuchu ba zata bi bayanta ba a wannan gaɓar. Amma dik da haka sai ta kallesa ido cikin ido, cike da tsantsar makauniyar soyayyarsa ta fara magana masu zafa kamar haka. "Tabbas dik abin da ka faɗa haka ne, kuma ka fini gaskiya, amma akwai kalma ɗaya da ka faɗa wanda ba hakan bane kuma ba zan lamunta ba!!". Tattara mata hankalinsa a kanta ya yi yana sauraronta, cike da sa ran zata kawo masu mafita. "Abin da ka faɗa ba daidai ba kuma shi ne cewa da ka yi idan na ji wuya zan juyawa zuciyarka baya, ka yi kuskure! Ban ga wata wahala da zata sa in juya maka baya ba a duniya, soyayyar gaskiya nike yi maka ba ta yaudara ba! Kada ka manta nasoka ne tin ban taɓa ganin kamanninka ba, tun da na taso a rayuwata bani da abin san kalla sama da kai, ka yarda dani, mu haɗa hannu zamu yi nasara! Na yi maka alkawarin a kai'na kuma dalilina dik ƴan uwana zasu canza su karɓeka a matsayin zaɓina hannu bibbiyu, ka mun alkawarin dik halin da zamu shiga ba zaka taɓa ja da baya a kan soyayyarmu ba?". Ta kai karshen maganar tare da buɗe tafin hannunta ta miƙo mashi. Da yake jajirtacce ne babu tsoro a tatare da shi sai bai yi wani tinani ko ya damu ba, shi ma ya buɗe tafin hannunsa ya ɗaura a saman nata. "Na yi maki alkawarin babu gudu babu ja da baya kome zai faru ina kan bakata na ina sanki!". Ajiyar zuciya ta sauke, cikin sanyin murya ta ce. "Tabbas ba zan baka kunya ba, kuma na yi maka alkawarin sai dai a zare raina da soyayyarka a kirjina, ba zan taɓa san wani ba kuma ba zan taɓa yarda a haɗani da wani ba". Wani irin bargon farinciki ne ya lulluɓe zuciyarsa, ya ma rasa abin faɗe, sai dai kawai ya yi shiru yana jin wani sanyi tana ratsa zuciyarsa. "Yanzu meyakamata mu yi?". Cewarta kenan. "Gida zamu tafi yanzu, hanya zamu ɗauka, gobe zamu iya isa". "Har na ji bana san mu koma yanzu, kamar mu kara kwana biyu a nan, wajen akwai daɗi sosai". Cike da yaranta a word ɗinta ta yi magana. Kai ya girgiza tare da riko hannunta da kyau a cikin nasa, ƙasa ƙasa ya ce mu je. Bata yi musu ba ta bi bayansa suka tafi wajen Pretty, har lokacin sai barci take zubawa. Kamar zai tambayi Auta su tafi da Pretty ko su barta a wannan dajin tun da ta faɗa mashi a nan suka sameta. Sai kuma ya ji ba zai iya tafiya ya barta ba, tin da suka ganta haka bata da kowa kenan, dan haka su tafi da ita kawai. "Jirani ina zuwa, ki tashi Pretty kafin na ɗauko dokina". Yana kai karshen maganar ya sake hannunta, bai jira amsarta ba ya wuce da sauri izuwa ɗan baya da su kaɗan. Ita kuma ta wuce ta tashi Pretty daga barci, yana dawowa suka hau saman dokin da dik wani abin da zasu buƙata, wajen da suka yi faɗa da damusan nan ya koma ya ɗauki takobinsa, sannan suka kama hanya, Auta a gaba Pretty a tsakiyansu shi a baya, ba komai yasa yaki saka Auta a tsakiyansu wato kusa da shi ba face kaucewa sharrin shaiɗan. Auta ta manta da tana jin yunwa, haka suka kama hanyar nufar Kingdom of power..... To sai dai mu ce Allah ya kaiku lafiya. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 2:30am. Dare ta tsala sosai, ko'ina ya yi tsit, dik wani na kirki yana cikin gidansa, banda kukan karnikan Ramish su bisho dake tashi babu wani abin da zaka ji. A hankali karan Acn ɗakinta yake tashi. Kasancewar bata da nauyin barci ko kaɗan hakan yasa in abu ya motsa a kusa da ita tana ji kuma yana farkar da ita, dama dik wanda ya yi zaman gidan yari da wuya ya iya nauyin barci. Ta yi nisa cikin barcin da take yi cikin kwanciyar hankali, yau tana farincikin ta amayarwa masu nikaf kunan da ya daɗe yana babbaka ranta, yau ta samu sai'da da salama, har ta ji bata taɓa yin barci mai daɗin wannan ba. Can a tsakar kanta ta ji kamar an taɓa mata kofar ɗaki, dik da tasan ba ita kaɗai take kwana a ɗakin ba, amm tasan yau Sharifat bata nan, kuma da wuya ta dawo cikin wannan daren. A karo na biyu ta sake jiyo an mai da kofar nata an rufe tamkar wani ne ya shigo ya rufe, kamar a mafarki ta ji ana datse keys na kofar wanda tun da suke daga ita har Sharifat babu wanda ya taɓa datse wannan kofar da keys ɗinsa. Hakan yasa ta zabura ta miƙe zaune, ɗakin duhu bakin kirin, dan yau ko lamp dama bata kunna ba. Wani irin ɗan motsi ta ji kamar alamar tafiyar jami'i a yakin sunkuru, ko kaɗan bata tsorata ba, dan ba ƙaramin abu yake tsoratata ba ita. Cikin dabara ta laluɓa ta sauko kasa daga saman gadon, tamkar wata hawainiya ta fara taka kafafunta ta nufi switch. Unexpect ta isa wajen ta kunna wutar ɗakin, nan take haske ya gauraye ko'ina. Ya ilahi ya lilliahi, wani irin mahaukacin razana ta yi. Idanuwanta ne suka yi mata tozali da wani tsayayyen namiji cikin shigar ban tsoro, baka iya ganin komai daga jikinsa, from up to down gabaɗaya bakaken kaya ne a jikinsa, fuskarsa rufe yake da tactical mask, ba zaka taɓa iya gane wanene bane, kafafunsa na sanye da combat boots masu karfin gaske. Ga shi a tsaye a tsakar ɗakinta, ya rufe kofar ɗakin kuma da key babu halin gudu ta fita. Sosai ta razana, da karfi ta waje baki zata zunduma ihu kamar walkiya haka ya wurga mata wani abu mai kamar da karfen star a baki. Wani irin baya baya ta yi kamar zata faɗi, dan dolenta ta haɗiye ihun da take yunkurin kurmawa, jinine ya fara bulbula daga bakinta, alamar abin ya fasa mata baki. Ganin hakan yasa ta fahimci komai, wato kasheta aka zo yi dan ta yi barazana wa masu nikaf. Amm waye kuke tinani mai kwarin gwiwar da zai iya keta camarorin da suke kan titin hanyar ratsowa gidan Abu Abdussalam har ya iso, sannan ya keta dikka waɗan nan jiga jigan securitys ɗin ya shigo cikin gida, ya keta cameras dake cikin gida har da babban parlourn ya iso ɗakinta dik kuma babu wanda ya gansa? Anya wannan makashi ba daga cikin gida kuwa yake ba?. Hannu ya sanya a wajen combat boots ɗinsa ya zaro wata karamar wuƙa mai bala'in kaifin gaske, ga shi har kwayar idanunsa baka iya gani, dan tactical mask idan ka sanya mutum ba zai iya ganin komai na face ɗinka ba sai dai kai ka gansa. So yau ko idanun bata samu damar gani na bare ta iya hasashen wanenen ko ta sa ran zata iya ganesa. Ganin ya zaro wannan wukar yasa ta ƙara tsorata, da gudun gaske ta yunkura zata shiga toilet ta rufo kofar. Sai dai ina, bai bari ba, taku biyu ya yi ya damko gashin kanta. Da karfi ya fisgota da gashin nata ya yi wurgi da ita a saman bed ɗinta. Sosai ta ji azaban jan gashinta da ya yi, amma haka ya daure ta shanye, da gudu ta yunƙura ta miƙe. Sai dai bata kai ga sauka gadan ba ya sanya combat boots ɗinsa ya take kirjinta da karfi har sai da ta bugu da jikin headboard na gadon. A wannan gaɓar azaban da ya ziyarceta ya ja ta saki wani marayar kuka, ga shi bakinta sai bulbular da jini yake yi. Ta maza ta sake yi ta yi yunƙurin tashi zata gudu again tana dafe kirjinta, dan ya taketa a tula tulanta, kuka kunsan dole ta ji azaba over. Kafafunta ya take da combat ɗin nan nasa, har cikin ranta azaban hakan ya ratsata, ta gagara yin kuka, ta ko'ina zogi da raɗaɗi take yi. Matsawa ya yi kusa da ita, ya damko gashin kanta cikin hular kayan barcinta, sai da ya jijjiga kanta da karfi sannan ya bugata da jinin headboard na gadan, nan take goshinta ya fashe. Ko kaɗan babu alamar zai tausaya mata, babu imani a ransa, wuyarta ya sake shaƙowa da karfi, hannunsa na cikin Black gloves. Ya matse mata wuya da iya karfinsa. Tuni ta fara jiyo kamshin mutuwa, tuni idanunta suka fara rufewa ta fara ganin duhu mai yana yana lulluɓe ko'ina, ta dafe kirjinta saitin tula tulanta, ko da zogin da suke yi mata kawai ya kyaleta ai ya isheta ba sai ya kara mata wani ba. Hannunsa ɗayan ya kai saman kumatunta, yana rike da ƴar wukar, sai ya sanya wukar a tsakiyar yatsunsa, hakan ya bashi damar matse mata kumatu sosai har sai da ta ja wani irin azabbabben numfashi. Bata iya ganin idanunsa, amma shi idanunsa kar a kan kirjinta, hakan yasa ya saki kumatunta ya mayar da hannunsa saman kirjin nata, da karfi ya matse mata tuka tulanta dan bakar mugunta, azaba yasa ta ji wani karfi ya zo mata ta fara ƙoƙarin kwatar kanta. Ganin hakan yasa ya ji a ransa yana da kyau ya keta mutumcinta kafin ya kasheta. Wannan tinani nasa yasa ya zame hannunsa daga fatar wuyarta ya mayar wuyar rigarta. Da karfi ya ja rigar ya yaketa. Ko kusa ko alama ba zata iya kwatar kanta daga hannunsa ba, ga shi babu ko vest a ciki, haka ya yage mata riga, ya kuma yage mata wando, ya rage pant a ciki kawai. Kafarsa da ya take nata da shi ya cire. Da hannu ɗaya ya damki kafafun nata ya jata a in da ta dawo tsakiyar bed ɗin, gabaɗayansa ya tafi kanta da nufin aiwatar da abin da yakeso. Dik jikinta ya yi wanka da jinin dake bulbula daga goshinta and bakinta, ko ƙwaƙƙwaran motsi bata iya yi, hankalinta ya fara gushewa, tana ji ya haye kanta haɗe da rabata da komai nata. My people's waye kuke tinanin zai yi wannan aika aikan? Shin ina mazan gidan Abu Abdussalam da har wannan abin zai faru basu sai ba? Ko da yake part ɗinsu yana da nisa da nasu Ummie, amma koma wanenen wannan anyi mai karfin zuciya da kwarin gwiwa, tab wannan masifa haka. Mekuke tinanin zai faru? Allah sarki Leesharh, ko tsoro baya ji zai kasheta cikin gidan ministan tsaro na ƙasa gabaɗaya? Lallai akwai cakwakiya. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Ko tausayinta babu alamar zai ji, da karfin tsiya ya fara ƙoƙarin haike mata, kasancewar wandan jikinsa irin Armored leggings ɗin nan ne sai ta yi mashi wuyar ciruwa lokaci guda, ga shi ba zata yagu ba bare ya yageta. Hakan yasa ya ɗan ɗaga jikinsa daga nata kaɗan, da zafa ya fara ƙoƙarin kwance belt dake jikin wandan dan ya yi abin da zai yi da sauri. __________________🔥 Lokacin guda ya ga wani irin warkiya kamar shocking na wutar lantarki, ya kuma ga wani irin jiri mai karfi ya ɗebesa, daga haka bai sake gane komai ba, sai jin kansa ya yi ya faɗi a saman mattress ɗin rigijib kaman kayan wanki. Ba komai ya ja hakan ba kuma face, lokacin da yake ƙoƙarin cire belt ɗin wandasa ita kuma ta lura da ya bar kanta, hankalinta ne ya dawo jikinta, cike da kunan ran abin da ya yi mata, ga azaban da take ji, cikin dabara da jajircewa irin nata ta sanya hannu ta laluɓi lamp dake saman bedside drawer, da iya karfinta na karshe ta jawosa. Shi kuma hankalinsa dik yana a kan yadda zai zare belt ɗinsa, Allah ya bata dama, da yake bata da hakkinsa sai ta shammacesa ta dakarkare ta maka mashi a kai. Wannan shi ne abin da ya faru. Da kyar ta iya motsa jikinta ta miƙe zaune, shesshekar kuka take yi sosai, hannunta tasa tana tattaro rigar barcin jikinta dan ta ɗan sitirta kanta. Kamar gizo haka idanunta suka hango mata shi yana motsawa a saman mattress ɗin yana san tashi kenan, alamar ba suma ya yi ba dama, zafin buguwa ce nawai ya ji yasa ya faɗi kamar ya suma. Ai bata san lokacin da wani irin karfi ya zo mata ba, a maliyan ɗari kamar wata walkiya sai gata ta diro kasan bed ɗin, kai tsaye kofar room ɗin ta nufa, a gaggauce ta fara ƙoƙarin ɓalle key ɗin ta fita, hannunta sai kerya yake yi, yaki tsayawa waje guda bare har ta iya buɗe kofar. Hankalinta dik a kansa, kun san idan mutum yana tsorace haka abin yake, sai ji ta yi key ɗin ma yaki murzuwa ta buɗe. Shi kuwa a lokacin ya farfaɗo, a zabure ya zaro idanunsa da suka yi jajir waje, ya ji bugu hege. Wani irin miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin ya yi yana zaro idanun kamar ma tare ɓera a tarko. Wayam bai ganta a saman bed ba, hakan yasa ya fara jujjuya jajayen idanunsa yana neman ta ina zai ganta. Ita kuwa kerman da hannunta yake yi yasa kofar taki buɗewa, sai zaro idanu a kansa take yi karjinta tamkar zai fashe saboda bugawa, iya tsorata yau ta yi shi, cikinta ya gama ɗuran ruwa, har gudawa ta ji, kamar fitsari zai zuba mata take ji. Ganinta a wajen kofa yasa a miliyan ya diro ƙasa daga saman bed ɗin, sai ƙoƙarin murza key take yi tana ihu ƙasa ƙasa dan voice ɗinta baya fita. Cikin zafa ya nufeta yana wani uban ɗaure fuska, sai huci yake yi alamar ransa a tsananin ɓace. Yana isa dab da ita Allah ya bata sa'a ta ɓalle key ɗin kofar, yana ƙoƙarin damko gashin kanta ta danna waje a miliyan. A haukace ta fito main parlour na sama, har lokacin jikinta dik jini, bata san ina ta nufa ba ga duhun dare, dik kwayayen fitillu a kashe. A tinaninta ya biyo bayanta hakan yasa ta kara gudu sosai. Dai'dai zata fita parlourn suka ci wani uban karo da shi yana shigowa. Baya baya ta yi ta faɗi ƙasa, da yake akwai duhu a parlourn hakan yasa baka iya gane wanenen, amma ita dik da tana cikin tashin hankali bai hana ta fahimci da Ramish ta yi karo ba, saboda kamshin perfume ɗinsa ya banbanta da na kowa a cikin gidan. Shi kuwa ko a jikinsa bai nemi sanin da waye ya yi karo ba, sarkin yawon tsakar dare a cikin gida kenan, ba shi da aiki sai ya yi ta yawo har garden ɗin dake harabar gida yake zuwa da tsakar dare, ya zauna ya yi ta latse latsen waya, to ya fito yawon nasa ne yanzu ma suka ci karo. Bai bi ta kan wanda ya buge ba yasa kai ya tsallaketa ta wuce ciki. Ita kuma da karfi ta tashi ta fice wajen. Bata zame ko'ina ba sai part ɗin Abbie cikin rashin sani, Allah sarki bata san ina ta dosa ba, gudun cetan ranta kawai take yi. A lokacin karfe 4:00 daidai ta buga, asuba ta kawo kai kenan. Takuwa yi sa'a idanun Abbie biyu yana saman dadduma yana sallah. A haukace ta afka cikin ɗakin, har taso ta ɗan bashi tsoro, amma da yake yana gaban Ubangijinsa sai bai wani damu da sanin wanenen ya afko mashi ɗaki a haukace haka ba. Cigaba ya yi da sallarsa cikin nitsuwa, ita kuwa cikin rashin sani ga duhu yasa ta fara bin jikin bango tana neman gane ina ta shigo ne?. Tabbas lamps na ɗakin a kunne suke, amma bata iya hango Abbie, saboda ɗakin yana da girma sosai, hasken lamp basa kaiwa in da yake. Cigaba da laluɓe ta yi tana haki haɗe da sauke numfashi da karfi karfi. Har ta isa in da Abbie yake ba tare da ta sani ba, tana layi kamar wadda take a make. Tana isa dab da shi a lokacin ya sallame sallah ya miƙe dan ya je ya kunna wutar ɗakin yaga wanene ya shigo mashi ɗaki a irin wannan yanayi haka. Yana miƙewa suka ci karo, a lokacin dik wani karfinta ya kare, tafiya ta yi zata faɗi ƙasa ya yi saurin rikota. Sai da gabansa ya faɗin jin cewa yarinya ce mace kuma kamar babu kaya a jikinta. Amma dik da haka ya yi ta maza ya rungumota a jikinsa gudun kada ta faɗi. Da kyar ya iya riketa suka karisa gaban bed ɗinsa. Sosai ya zaro idanunsa a lokacin da wutar lamp ta haska mashi face ɗinta, a fili ta furta Leesharh da ɗan ɗaga murya. Lokacin ta fara fita a hayyacinta, sam bata gane a hannun wa take ba, hankalinsa ne ya tashi bawan Allah, jiki na kerman mamaki ya kwantar da ita a saman gadansa. Ga bedsheets ɗinsa white color ne sosai, haka ya yi dama dama da jininta. Ɗan kawar da kallansa daga kanta ya yi duba da cewa babu sitira a jikinta, ya janyo white duv ɗinsa ya lulluɓeta da shi har saman kirjinta. Jikinsa dik ya ɓaci da jininta, dama white jallabiya ce a jikinsa. Wajen phone set dake kusa da bedside drawer ya nufa, fili ne da aka yi sa domin ajiye waya, hannunsa har yana ɗan kerma wajen ɗauko wayarsa. Number zaratan samarin gidan nasa yake san kira ya ji menene yake faruwa a cikin gidan haka? Su zo su duba mashi me ya samu Leesharh? Waye ya yage mata kayan jikinta haka?. Sai dai bai kai ga kunna wutar screen ɗin wayar bama bare aje ga call sai ganin ɗakin nasa ya yi ta gauraye da haske an kunna bulbs. A ɗan razane ya juyo ga switch na ɗakin. Sanye take da sleeping gown tana tsaye a kan kafafunta, tsaresa da ido ta yi taba binsa da wani irin kallo wanda za'a iya fassara shi da kallan tuhuma. Ummie kenan. Me kuke tinani ya kawo Ummie a dai'dai wannan lokacin? Abu kamar tasan da Leesharh a cikin ɗakin, ko da yake ɗakin mijinta ne, zata iya shiga a dik time da taga dama, ga shi kuma asuba ya kawo kai, dama za'ayi expect ɗin dik wata mace ta gari a irin wannan lokaci tana ga mijinta zata tashe shi sallar asuba ko?......🥱 From head to toe ta fara bin Abbie da kallo, abin ya yi matuƙar bata mamaki sosai, cike da zargi a idanunta ta mayar da kallanta a kan Leesharh dake kwnace a saman bed ɗinsa tana wani irin numfashi sama sama kamar zata sume. "Omar, me zan gani kenan?". Ta faɗa tana zaro idanun, yau babu batun Abu Abdussalam, da ainahin sunansa Omar ta kirasa, mata duniya ne wlh. Tabbas ya ji mamakin wannan suna da ta kirasa, yau sama da shekaru 30 suna a tare bata taɓa ambatar wannan suna ba sai yau, abin ya ɗan girgiza shi, nan ma wai hankalinsa bai kai ga kan abin da take zargi a ranta ba kenan, ya zaci ta tsorata ne na ganin Leesharh a cikin mawuyacin hali har ya ɗaga mata hankalinta, shiyasa har ta kirasa da Omar ba tare da ta sani ba, bai san babban bala'in dake tinkarisa ba. "Lafiya kuwa?". Ya jefa mata tambayar cike da matsuwar san jin dalilin kiransa da ta yi da Omar ɗinsa. Amma fa bai yi mamakin ganinta a ɗakinsa a wannan lokacin ba, saboda ta saba zuwa, wani lokaci a nan take kwana, yau ta ce da Sharifat zata kwana shiyasa ta tafi ta bashi waje. "Ni kake tambaya lafiya ma ko? Dama abin da kake aikatawa kenan? No wonder wani lokaci kake nuna cewa kafi san wannan shegiya tsintacciyar yarinyar a kan ƴar cikinka, ashe da biyu!!". Ai Abbie bai san time da ya wani irin miƙe da kyau ya tsaya a kan kafafunsa ba, zaro mata idanu ya yi, ji ya yi tamkar an kwala mashi guduma a tsakiyar kai, da tsufarsa da mitumcinsa ne zata zargesa da abin da ko ɗansa ya kama yana yi sai ya ɗauki mummunar mataki a kansa, abin kyama, ya tsufa yana neman cikawa da imani ne zata nemi lalata mashi karshensa da banzan tinaninsu ma mata? Anya akwai hankali a kwakwalwata kuwa? Ya jefawa kansa tambaya. A fili kuwa sai ya ce. "Ban gane me kike nufi ba?". Cikin kakkausar murya ya yi maganar. "Taya zaka gane abin da nike nufi, dama ai shi tabarmar kunya da hauka ake naɗesa, yanzu kai babu kunya babu tsoron Allah zaka hakewa ƴar yarinyar da ko Sharifat ta fita shekaru? Ko tsoron Allah baka ji! Dubi jikinka fa, dik jini, ko tausayin yarinya baka ji ba? Wlh ba zan yarda ba, wannan ƴar iskar karuwar sai ta fita gidan nan a yanzu". Cikin faɗa da ɗaga murya ta kai karshen maganar. Tana kaiwa karshe kuma ta nufosa gadan gadan. Ƙasa magana Abbie ya yi, ya ji bala'in da ta fi karfinsa a yau, sai ya ji abin tamkar a mafarki. Yana can yana tinanin sai gani ya yi ta yaye duv da ya lulluɓe Leesharh da shi tana zazzaga masifar. "Shegiya matsiyaciya, yanzu zaki fita daga gidan nan dan ubanki, karuwa kawai, dama ai na jima ina zargin akwai wata a tsakaninku, ashe kuwa zargina gaskiya ce........." Ƙasa karisa maganar ta yi sakamakon ganin Leesharh tsirara da ta yi bayan ta yaye duv ɗin kenan. Wani irin ihu ta kurma tare da ja baya. "Shikenan zancena ya tabbata, shikenan wlh ya tabbata, da gaske ne zina suka aikata". Kamar wata zararriya haka take maganar, ga shi cikin ɗaga murya. Ganin zata tara masu family yasa ya daka mata tsawar ta yi mashi shiru. A tinaninsa tana jin maganarsa tin da bai taɓa yin magana ta ce a'a ba, sai ya yi tinani in ya yi tsawa zata yi shiru, bai san cewa a irin wannan point ɗin mata basu da saiti sam sam ba. Aikuwa yana daka mata tsawa ta daka uban tsalle kamar wata mahaukaciya sabon kamu, ihu ta yi tare da wurgi da duv dake hannunta wanda ya rufe Leesharh, sannan ta haye saman bed ɗin kan Leesharh, hannu tasa ta fara kaiwa Leesharh bugu babu tausayi ba imani, tana dukanta tana aika mata da muggan zagi kala kala. Leesharh da tuni dama ta sume ai bata jiyo komai, sai zaginta take yi a kan ta tashi ta fita mata daga gida, har da ikirarin yau sai ta kasheta. Da Abbie yaga abin is getting out of hand, zata iya cutar da Leesharh, sai ya yi yunƙurin dakatar da ita. Ai ina kin sauraransa ta yi, ta ko'ina take kaiwa Leesharh duka babu kakkautawa. Ransa ne ya yi mummunar ɓaci, zuciya ta ɗebesa ya dalla mata wani irin mari mai gigitarwa. Ihu mai sauti ta zunduma tare da dirowa ƙasa daga kan Leesharh, ta nufi waje tana faɗin bari ta kira su Ramish sai sun zo sun fitar mata da wannan shegiyar yarinyar daga cikin gidanta, kuma kowa ya zo yaga abin da suke aikatawa, har ƴan aiki sai ta kira. Tashin hankali, my people's me kuke tinani zai faru kuma? Kuna tunanin ya rayuwar Leesharh zata kaya a gaba?. Anya zamanta a gidan zai yiwu kuwa? Abu Abdussalam zai iya wanke kansa a kan babu abin da suke aikatawa da Leesharh kuwa? Kada ku manta a irin yanayin da yake shi da Leesharh gabaɗaya, ni dai a gaskiya ban ga ta hanyar da zai iya wanke kansa a kan wannan ƙazafi da Ummie ta yi mashi ba, dan kuwa ga Leesharh tsirara, ga jini a jikinsa shi da ita, gata a ɗakinsa a kan bed ɗinsa, meya kawota ɗakinsa nasan shi ne tambayar da kowa zai fara yi idan ya zo kan wannan case ɗin, Abbie dattijon arziki, ya kuke tinanin zai ji idan Ummie ta kira su Ramish suka zo suka ji halin da ake ciki? Akwai babban cakwakiya da tashin hankali, part na Dubai ta kama da wuta, bari mu rarrafa wani part ɗin domin mu duba meke wakana. ••••••• KINGDOM OF POWER••••••••🔥🔥🔥 A wayewar garin yau tawagar Auntynsu Jawad zasu koma in da suka fito, ƴan England zasu koma haka ƴan Saudiyya ma, dik cikinsu babu wanda ya san da batun ɓatan Auta, King ya ce a ɓoye maganar a matsayin sirri, saboda fitar maganar zai zamana gazawace a garesu, kuma abokan gaba zasu ji daɗin anyi nasarar yi masu wani abin da bashi da daɗi, za'a rai'na yanayin tsaronsu tun da za'a iya shiga har cikin gida a saci yarinya, and bugu da ƙari fitar maganar zai sa a ce ga hanya mafi sauki na ladabtar da king wato a kwashe ƴaƴansa kenan. A takaice dai fitar bayanin ɓatar Auta babban abu ne a garesu, dan zai sa su Jaish da ake ɓoyewa su sani, Akka zata ji labari, zai haifar da munanan abubuwa da dama, dan haka sirrinta shi shi ne ya fi komai a garesu, hakan yasa King ya sirrinta hakan. Auntysu Jawad tayi farinciki sosai na jin aure ya koma kan Jawad, dan dik bata da matsala da su. Sai dai ta so haɗuwa da Rizwan kafin ta koma, amma ina bata samu dama ba, Rizwan yaki yin waya da kowa, yama kashe wayansa ne mai gabaɗaya. A yau ranar da zata koma gabaɗaya fam sai da suka taru a main parlour na King dan a yi sallama da juna. A nan ne Mammie take samun labaran Jannat Jawad ya aura ba Rizwan ne ya aureta ba. Idan hankalinta ya kai dubu to sai da ya tashi, sai ta ji tamkar ta mutu saboda bakinciki, burinta bai cika ba, har kasa iya zama a cikn parlourn ta yi, hankalinta a tashe ta zame jiki ta yi waje babu wanda ya lura da ita. Shi kam uncle Abbas godiya sosai ya rinƙa yi wa Auntynsu Jawad, sam momma bata kawo masu batun auren Jaish ba, ta ɓoye tamkar yadda suka yi da su Aunty MieMie. Sai dai kuma wani abin guda, dole ta tilastawa su commander Zafar yakar Daular Qahtaniyawa dik da a lokacin da suka dinfari wajen King Al-Mustapah ya sanar da su shi bai ɗauki gimbiya Zunaira ba, kin yarda da shi suka yi dik da commander Zafar yasan gaskiya King Al-Mustapah ya faɗa. Commander ya jima a fagen yaki, idan gaskiya ake faɗe ya sani, haka zalika idan karya ne ma ya sani, amma haka ya take wannan sanin dan basu da wata mafita da ya wuce su yakesu, a kan umarnin King Zuhair suke yanzu, dik wata hanya da Aunty MieMie ta buƙaci da su bi dan nemo Zunaira sun bi amma babu nasara, hakan ya tilasta masu dawowa kan umarnin King suka aiwatar da yakin. Sai dai kuma kash, ko da suka yaƙi Daular Qahtaniyawa babu Zunaira babu alamarta a ciki, sun dai yi masu ɓarna na King karawa, King Al-Mustapah ya yi mubaya'a har ya gaji amma sam babu alamar King Zuhair zai karɓi nadamarsa ya kuma yafe mashi, kafiyar bala'i King Zuhair yake da shi wlh, idan ya tambara magana babu mai iya sanya shi ya canza ya yi ta kenan. A ranar da Auntynsu Jawad da tawagarta suka bar Kingdom of power a ranar su commander Zafar suka kaddamar da wannan yaƙin tare da dawo da labari maras daɗi wanda sam King bai so ji ba shi ne babu gimbiya Zunaira a Daular Qahtaniyawa. Sosai ran King ya sake sosuwa, hankalinsa ya tashi, yau shi da yake kwantarwa da Momma hankali a kan wannan case ɗin, sai yazamana ita ta juyo take kwantar mashi da hankali saboda bala'in ya kai mashi bala'i, ga ɓatar Hoorain assistant commander su, abin sai ya haɗe mashi biyu. A can ɓangare kuma, wannan dai sadauki mai ɗauke da fuska kamar ta Hoorain namu ko ma muce Hoorain namu shi ya jagoranci tawagar mayakan Queen Zarina izuwa kingdom of power. Tabbas ɗayan biyu ne, wannan sadauki ko dai tsafi suka yi amfani da shi wajen sanya mashi irin face ɗin Hoorain dan su firgitar da Kingdom of power, dan kunsan sun san komai ta hanyar mammie, so sun san bayyanar Hoorain a cikin mayaƙansu zai iya sanyawa su yi nasara a kan Kingdom of power, dan mamakin da dangerous warriors zasu shiga ganin Hoorain a cikin mayakan Queen Zarina shi zai iya tallafa masu su yi nasara sosai. Abu na biyu kuma shi ne ko kuma robbot suka sanya mai irin zubin halittar Hoorain, ɗaya cikin biyun nan dole suka yi, dan sak Hoorain ɗinmu yake babu banbanci komai ƙanƙantarsa. To shi dai ya jagoranci tawagar Queen suka nufo su King wanda a lokacin King Al- Mustapah yana ta neman ta yadda za'ayi su shirya da King Zuhair, hakan yasa dik da King ya yakesu bai sa ya janye kudurinsa ba, sai ya haɗa sauran mayakansa da suka rage ya fita ya tari rundunar mayakan Queen Zarina wanda already King Zuhair ya samu labarin zuwansu, sai kuma ya samu labarin King Al-Mustapah ya tare mashi yakin. Abinku da jinin sarauta mai karfi, dik da ya ji hakan bai wani nuna mamaki ko kaɗan ba, sai ma ya nuna kamar bai san suna yi ba, ya umarci commander Zafar da ya haɗa kan wasu zataran warriors su fita su taya su King Al-Mustapah yaki dan su kaɗai ba zasu iya da bala'in Zarina ba. Hakan kuwa aka yi, suka fita domin tallafa masu. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Jawad bai zame ko'ina ba sai part na King da gudu, Jaish bai rabu da shi ba sai da ya bisa har can, dan yau ya ci alwashin sai ya kuntatawa Jawad ya ji idan da daɗi shi ma yadda ya ja mashi kima da mutuncinsa a kan titi. Dai'dai lokacin King ya kammala shirinsa na nufar fada zai fito ya yi breakfast kenan. A bayansa Jawad ya laɓe yana haki yana hararar Jaish da ya tsaya ta gabansa yana bin daddyn nasu da kallo. Abin ya yi matuƙar bawa Jaish mamaki ganin rama a tatare da King, tun da ya dawo dama basu wani zauna sosai ba, so bai wani san halin da suke ciki ba. "Daddy ka ce wannan tuzurun ya rabu da ni, dan kawai na yi aurena na barshi shi ne yake jin haushina zai fasa mun baki yajawa amaryata asara". Cewar Jawad kenan, yana magana yana kara laɓewa a bayan King. Bakinciki ne ya ƙara lulluɓe zuciyar Jaish, lallaima Jawad ya raina mashi wayo yake faɗe a cikin ransa. King da ya rasa abin faɗe ai binsu da ido kawai yake yi, a ransa yake faɗin tun suna yara suke wannan tsiya, har yanzu basu dai'na ba!. " Ko ka zo ko kuma yau sai dai mu kwana a nan". Jaish ya faɗa ransa a ɓace, shi serious ya ɗauki abin, Jawad kuma wasa yake yi, shi fa da ace Jawad wata ya aura ba kanwarsa ba to da da sauki abin, amma tsabar cin mutuncin ya kama ya auri Chuchu da ya gama yi masu jan ido, yanzu haka kawai ya janyo mashi wani abin da ba haka nan ba, wlh ba zata saɓu ba. Amma kuma a matsayinsa na yayan Chuchu ya ji mata daɗin ta samu mutumin kirki wanda yasan ba zata taɓa yin kuka ba a duniya, wani ɓangare na zuciyarsa ya so da ace Auta ma Jawad ya aura, kunga masoyiyar kanwarsa ba ita ba kuka, kuma har abada in dai tana matsayin matar Jawad shi zai cigaba da kula da ita. Sai dai kash, tsakanin Jawad da Auta babu aure, shiyasa ma ya so Chuchu shi ma, da akwai aure kun san dole ita zai so shi ma, ko dan ya ramawa Momma alkhairinta a garesa, sannan kuma Auta ta fi Chuchu komai dik da ita ma Chuchun ba baya ba. Amma babu halin ya aure Auta saboda ya sha nonon Momma a tare da Jaish, kunga babu aure a tsakaninsu, matsayin yaya yake a wajenta, kuma fa ba wani sosai ya sha nonon momma ba, kawai dai rabon auren ƴaƴan momman ne ya fita a ƙaddararsa. "Malam bafa zan fito ka fasawa amaryata bakina ba, wai kai dan kana gwauro sai ka zalinceni ne? Daddy hasada yake yi mun dan shi bashi da wadda take son shi, ka canza wannan bakin halin naka sai ka samu koda kuyanga ce ta ce tana sonka a lallaɓata ku shiga daga c............." Kasa kai aya ya yi sakamakon hannu da Jaish ya kai zai yi mashi wata capka ya zille yana harararsa. Ran Jaish ya ƙara ɓaci, lallai ma Jawad ya kai in da ya kai, shi yake faɗawa magana dan ya yi aure? Danasanin tafiyar da ya yi ya shiga yi, dan da yana nan wlh ba zai bari ayi wannan aure ba. Sai yanzu na gane rabon auren Jawad da Chuchu ne ya kawar da Jaish daga kingdom of power, kun san rabo fa har kisa tana yi, babu abin da bata sakawa, so da alama rabo ta kawo sanadin wannan tafiya, dan kuwa tabbas da yana nan ba zai yarda ayi wannan aure ba, sai ya hana ya zuga a bawa Rizwan ita tun da shi Dubai zai wuce da ita. Kaucewa capka da Jaish ɗin ya kawo mashi ya yi, yana faɗin. "Daddy ka mun tsakani da wannan gwauron, ni yanzu ba class ɗinsa bane, haka kawai zai cutar dani ya zalunceni". King da ya fahimci Jawad wasa yake yi Jaish kuma da gaske ya ɗauki abin sai ya yi ƙoƙarin yi masu tsakani kada faɗar gaske ta tashi, yasan halin kowannensu, waɗan nan kalamai na wasa da Jawad yake jifan Jaish da shi zai iya haifar masu da gagarumin faɗa, shi kuma Jawad ɗin sam bai lura da gaske Jaish ya ɗauki abin ba. Kuma kunsan akwai wani bakinciki a gefe na batun Mahnoor a zuciyar Jaish, sai abin ta haɗe mashi yazama haushin kowa da komai yake ji. "Ya isa haka, menene yake faruwa?". King ya faɗa yana kallon Jaish da har idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kawai dan ance Mahnoor ce matarsa. Ransa a matuƙar ɓace ya zayyanewa King dik abin da yake faruwa, daga karshe ya rufe da cewa. "Ni daddy tun banga yarinyar ba i hate her, kuma bana san in ganta ma a rayuwata, ka ce da momma bana so ta mayar da ita in da ta ɗaukota in ba haka ba kome ya faru alhaki a kan wuyarku, coz i really hated her more than your expectations". Kalamansa cike suke tab da gaskiya, tabbas ya ji ya tsani Mahnoor kuma baya san ganinta, kada kuga laifinsa, dik abin da zai faru bashi da laifi, ya sota ne a baya lokacin da yake matsayin Hamma wanda ko sunansa na ainahi bai sani ba, yanzu kuma yana amsa matsayinsa na Prince Jaish Zuhair Abdul Malik ne, kun san kuma babu ta yadda za'ayi ace Jaish ya karɓeta haka nan tun da dani da ku dik mun san halinsa a baya, kunga kuwa abu ne da ba zai yiwu ya yarda ba duba da yanayinta. King yana ƙoƙarin yin magana ya katsesa da cewa. "And why daddy zaka aurawa Jawad Jannat? Meyasa?". A ɗan takaice King ya ce. "Coz he love her". "Love". Ya maimaita kalmar yana dallawa Jawad wani irin kallon wanda idan ya yi wa su Chuchu shi na tabbata ko yawu ba zasu iya haɗiya ba saboda azaban tsoronsa. Izuwa yanzu Jawad ya fahimci da gaske ran ɗan uwansa a ɓace, kuma shi kansa ya ji ɗacin cewa da aka yi wannan ƴar kauye da Momma ta dawo da su ɗin ne matar ɗan uwansa, shi ya zaci ma wasu ƴan aikin momma ta je ta kwaso, amma kawai sai ace matan ɗan uwansa, ina gaskiya ko shi bai aminta da wannan ba, ransa ta sosu matuƙa, he feel he's blood brother pain, wannan ai ƙaskanci ne a ganinsa. Lallai jikokin Akka sun rai'na capacityn Mahnoor sosai.........😅 Matsawa kusa da Jaish Jawad ɗin ya yi, wani irin tausayin ɗan uwan nasa ya ji, ɗan rungumosa ya yi yana ƙoƙarin kwantar mashi da hankali. King kuwa, waje ya buƙaci da su samu su zauna zasu tattauna. Da kyar Jaish ya yarda ya zauna a bakin bed ɗin daddyn nasa, sai huci yake yi shi ransa a ɓace ancuce shi da aka dangantasa da ita, an zubar mashi da kima. Zama King ya yi a gefensu, sai da ya fara da rarrashin ɗan nasa, suka haɗu shi da Jawad suka taushi wannan zazzafar zuciyar, dan idan zuciyar bata sanyayya ba babu wata magana da zata iya shiga kunnensa har ya iya amfana da ita, hakan yasa suka fara da tausan shi. Sai da suka tabbatar da ya ɗan huce, sannan ne King ya fara bashi labarin yadda Momma ta faɗa mashi komai dallah dallah da yadda aurensa da ita ya kasance, zaman da suka yi da komai da komai. Tin da King ya fara magana basu ce ko uppan ba, suna binsa da kallo suna sauraro har ya dasa aya. Da ɗan ɗaga murya Jaish ya furta. "That's not me dad! Not me! Gaskiya wannan ai sai dai a film ne kawai zai faru, me I can't do that, kawai dai they told momma what the want ne kawai, but isn't true, kuma ni i can't believe that, and i can't accept this nonsense, dik zan yi maganinsu ne". Cike da gaskiyarsa yake wannan magana. Cigaba da tausan shi suka yi, King ne ya ce. "Sorry son, ba mommarka ta ce we should give her one week zata gabatar mana da yarinyar ba? So calm down, after one week sai mu ce we can't agree with her idan muka ganta, that's all". Girgiza kai ya yi tare da miƙewa tsaye. "No dad, ba zai yiwu ba, babu wani one week da zata yi, yanzu zata bar gidan nan, for what reason zata ce matata ce? Ni nace ina san in yi aure ne? Did I say so?". Ya kai karshen maganar tare da nufar waje. King bai dakatar da shi ba, dan ya fahimci lallai yau ran ɗan nasa a matuƙar ɓace yake, saboda Jaish bai taɓa yi mashi magana a irin wannan sigar ba, bai taɓa ɗaga murya fiye da nasa haka ba, kuma ga dikkan alamu Jaish ya manta a gaban King yake ma, dan har da ficewa tin basu gama magana ba, a bisa dokansu Jaish ya cancanci hukunci a kan abin da ya yi yanzu na suna magana da King ya tafi, dik da yake matsayin daddynsa sarki fa sarki ne mai cike da isa da izza a ko ina yake. Ni kuwa na ce ba a ko'ina yake ba, ina da ja a kan wannan magana, domin kuwa a gaban momma dai baby yake zama, babu wani sarauta a wannan waje idan yana............. To dai saboda sirirkina ne na yi shiru, amma da kwance mashi zani a kasuwa zan yi....😅 🔥🔥🔥 Amma sanin halin ɗan nasa yasa bai ce komai dangane da hakan ba, sai ma ya ce Jawad ya bishi ya rarrashesa kada ransa ta cigaba da ɓaci. Da sauri Jawad ya miƙe ya bi bayansa. Shi kuma King parlournsa ya fito dan ya yi breakfast ya tafi fada, yau sarkin hatsi zai fitar da zakka daga runbum kayan hatsi na King izuwa ga talakawan dake cikin kingdom da kawaye. •••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 A yau momma ta tsara Ibrahim kawun Mahnoor zai koma Nigeria, sai dai zai koma ba tare da ya sanya Mahnoor ko Mahreen a idanunsa ba, dan kowa yasan yadda dokan kingdom of power yake, dik da yake kawun Mahnoor yanzu matsayin matar Prince take, bashi da damar ganinta a saukake haka, idan ba ita ta buƙaci ganinsa ba to ko ya so ganinta ba za'a bashi dama ba har sai ta buƙata, kuma sun shiga ɗakin gyara ma abinsu. Ko momma ɗin ma bai samu damar gani ba, ta dai turo a faɗa mashi nan da sati ɗaya (wato idan King ya aminta da Mahnoor kenan) nan da sati ɗaya ya sanar da bappa zasu zo da tawagarsu su kawo masu kayan lefen Mahnoor da sadaki da komai da ake yi a biki, shi ne sarinta. Sannan ta haɗa mashi uban tsaraba, yadika, shaddoji, atamfa, lace da arab abayas and jallabiyas, kayan abinci da makuɗan kuɗaɗe a kan ya kaiwa bappa a rabawa ƴan uwan Mahnoor sai sun zo nan da sati guda In Allah ya ɗorasu a kan King. Tawagar mota guda ta ɗaga a kan a kaisa airport, ya samu gata albarkacin Mahnoor, dan kuwa private jet aka ɗaga ta ɗaukesa zuwa har birnin Jimeta Yola. Yana san ganawa da ƴaƴan nasa, amma babu dama, haka ya hakura dan bai ga fuskar tambayar ina suke bama, saboda warriors da suka kai saƙon Momma garesa bai ga fuskar ya masu magana ba, tsoro ma suma bashi, da wuri dole ya amshi komai suka wuce airport. Yana zuwa baifi da minti 10 ba jirginsa ya ɗaga sai Nigeria. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 UNCLE JAHIZ🔥 Sai da ya tsaya Zee ta ci abincin nan sosai ta ƙoshi, sannan ya ce ta tashi su je ya kaita wajen ƴaƴansa ta yi wanka ta shirya anjuma su je kallan Khadijah. Ajiyar zuciya ta sauke, haƙiƙa ta yi farinciki na jin cewa zata je kallan ƴar uwarta, sai satar kallansa take yi, idan ya kalli face ɗinta kuma sai ta yi saurin kawar da kallanta. Ɗakin Aneesa ya nufa da ita, a lokacin ita kuma tana ƙoƙarin fitowa hannunta rike da wayarta tana kallan hoton Yah Rizwan, Allah ya gani tana san bawan Allahn nan. Sanye take da sleeping dress, yanzu ta tashi daga barci, kamar wata aljana ta samu labarin Yah Jaish ya yi aure ne ta nufo waje, ko wanka bata tsaya yi ba zata je kaiwa Fanan gulmar. Kai Aneesa duniya, da alama ƴaƴan mama ma ba baya ba a kaifin ƙwaƙwalwa, ga Ramish ga Aneesa, ko daga ina ta samo labarin Jaish ya yi aure kuma?. Maganar da iya King and Momma ne kawai suka sani, sai kuma Yah Jawad da aka faɗawa da safen nan, ko uncle Abbas and uncle Jahiz da suke matsayin uba a garesu ma basu sani ba, kai gaskiya Aneesa ta fara bani tsoro. Zata fita shi kuma zai shigo, ɗan karo suka yi, baya ta ɗan koma tana ce mashi sorry haɗe da cewa. "Good morning my lovely second dad". Kanta ya ɗan shafa yana amsa gaisuwar tata cike da kauna, Allah sarki koma dai me Aneesa macece mai fara'a ga iya ƴan uwanta kawai banda bare, a waje kana ganinta zaka san jinin sarauta ya ratsa jinin modarawa dake gudana a jikinta, kuma suna shiri da uncle Jahiz sosai. "Daughter ga friend na kawo maki, ki tayata ta yi wanka ki bata kayanki ta sanya". Ya faɗa yana satar kallan Zee ta witsiyar idanunsa. Da wani irin kallo mai kama da na ƙaskanci ta ɗan bi Zee da shi, ba dan uncle Jahiz ne ya kawota ba da bata ga dalilin da zai sa wannan ƙazamiya ta shigo mata room ba, sai wari ma take yi, ta faɗi hakan a cikin ranta, a fili kuma sai ta ɗan kwaɓe fuska, cike da izza ta ce. "Second dad wacece ita ɗin?". Ya fahimci kyamar Zee take ji duba da yadda ta kwaɓe fuska, amma bai ga laifinta ba, dan haka suke, suna da tsabta basa san datti komai ƙanƙantarsa. "Daughter tana da mahimmanci sosai ga rayuwata, ba kamar yadda kike tinani ba, ta wuce nan, ki kula mun da ita sosai, kada ki ji kamar ba ƴar uwarki bace, ki kalleta a matsayina kin ji?". Ya yi mata hakan ne dan kada Zee ta fiskanci kyara da kyama a wajensu, yasansu sarai, idan ba haka ya bi da su ba wlh Zee zata yi kuka kasancewarta da su. "Second dad ka ganta fa, a hakan ne take da mahimmanci a wajenka?". Cike da mamaki ta yi maganar. Tana yi tana ɗan hararar Zee da wannan idanun nasu na gado.................................... Jinjina kansa ya yi alamar tabbas tana da mahimmanci a wajensa. "To amma second dad meyasa bata yin wanka, ka ji fa wari take yi". Ta sake jefa mashi tambaya. Da yake da larabci suke yin magana, kuma sun zurfafa sosai sai yazamana Zee bata ji sosai, dama sama sama take ji, shi ma dan islamiyyar da suka yi kafin babanta ya rasu ne yasa take ɗan ji. So bata ji irin cin mutuncin da Aneesa take yi mata ba. Satar kallan Zee ya yi kafin ya dawo da kallansa a kan Aneesa da ta turɓune fuska sosai. "Daughter bata da lafiya ne fa, daga hospital ta tawo yanzu, please take good care of her, ni zaki yi wa kin ji my lovely daughter?". Kai ta gyaɗa mashi amma rai bai so ba, dan yadda ta ɓata ran nan babu alamar zata yi na'am da Zee, ta yi mugu mugun rai'na class ɗin Zee, a cewarta ma ko a ƴar aiki ba zata ɗauki Zee ba, gaskiya kuma dik kuyangunsu mata ne masu tsabtar gaske. "Allah ya yi maki albarka Daughter, anjima da yamma zan zo in ɗauketa kin ji?". Sake jinjina kanta ta yi tana cigaba da ɓata fuska. Juyowa ga Zee ya yi, cikin harshen turanci ya ce. "Zee zan dawo da yamma in ɗaukeki, ki zauna tare da Daughter kin ji?". Kanta a ƙasa tana ɗan satar kallansa ta amsa da okey sai ya dawo. Kamar ba zai tafi ba, alamar baya san rabuwa da ita, amma sai ya daure ya juya ya fita. Yana juyawa ta bi bayansa da kallo. Kura mata idanu Aneesa ta yi tana kallan yadda take binsa da kallo har ya kurewa ganinta, sannan ta katseta da cewa. "Kyakkyawa ne uncle ɗina ko?". Aneesa akwai iya shege wlh, cikin harshen turanci ta yi maganar ganin uncle Jahiz ya yi wa Zee ɗin magana da turanci, sai ta yi tinanin ko bata jin larabci ne yasa, kuma ta ganta bakar fata sai ta kara rai'na class ɗinta. Jinjina mata kai Zee ta yi alamar yeah uncle Jahiz kyakkyawa ne. Wani irin kallan up and down Aneesa ta watsa mata kafin ta ce. "Haka ne kam, gaskiya kyakkyawa ne, amma kuma kada ki bari zuciyarki ta yaudareki a kan hakan, dan shi ɗin ba zai iya dai'daita kansa da kowa ba, amma menene a tsakaninku da shi da ya ce kina da mahimmanci a rayuwarsa? Dan dai nasan a familynmu gabaɗaya babu irinku koda na nesa ne!". Cike da shegantaka da rai'nin wayo ta yi maganar, tana wani binta da matsiyacin kallo. Zee ta fuskanci kalaman cin mutuncin a juye Aneesa take aiko mata da shi, dan haka sai ta yi shiru bata sake amsa mata ba, amma tabbas ta ji babu daɗin hakan, a tinaninta Aneesa zata karɓeta hannun biyu tun da basu wuce mate a shekaru ba, sai taga akasin hakan. Jin bata amsa mata bane yasa ta wuce gaba tana faɗin. "Ki karisa ciki akwai toilet, ki yi wanka, sai ki duba dressing room ɗina akwai wani part da na ware zaki ga a jikin glass ɗin na rubuta n-n, ki buɗe glass ɗin ki ɗauki kayan da suka maki a ciki, ni ina da abin yi". Ta kai karshen maganar tare da ficewa. Bayanta Zee ta bi da kallo har ta fita daga cikin ɗakin, sannan ta dawo da kallonta a kan alatun dake makare a cikin ɗakin, one after the other ta fara bin komai na cikin ɗakin da kallo, ita kanta a yanzu ta yarda lallai su Aneesa ba sa'anta bane, sun wuce da class ɗinta, irin wannan Daula haka? Ga yaran gidan dikka kyawawa gaske, ƴan gayu, kamar su suka yi kansu, ga iya wanka da tsabta, sai balai'n shan kamshi da jiji da kai suka iya. Da dai taga tsayuwa ba zai amfana mata kimai ba sai ta wuce ta nufi in da take zatan shi ne toilet na room ɗin, tana tafiya tana zuba ƙauyanci. Ita kuwa Aneesa tana fita kai tsaye ɗakin kuyangun da suke yi mata hidima ta nufa, ko sallama babu ta shige ciki. Ƴan mata guda biyu ne suke zaune saman katan bed ɗinsu suna hira. A takaice ta ce. "Ina da bakuwa a ɗaki, idan ta gama wanka ku wanke mun toilet da P.Z, sannan ku bisa da toilet perfumes kamar kala goma haka, dan bana san in ji wani iska ya canza daga na kamshi da na saba shaƙa, ku kara gyra mun ɗaki, kada ku bari na dawo na ji wani abin in ba kamshi ba". Tana kai karshen maganar bata jira amsarsu ba ta yi wajen. Sun risinar da kai suna ƙoƙarin ɗaga mata gaisuwa, amma ina har ta wuce ta fita abinta. Da kallo suka bita suna kara jinjina halin ƴaƴan King, yaran nan babu mai iya masu sai iyayensu. Tana fita bata zame ko'ina ba sai room ɗin Fanan. Tana shiga ta isko Fanan na zuba barci, ta wani baje a gadanta tana barci cikin nitsuwa, kai ba ɗan'kwali arab hairn nan nata a watse har face ɗinta. Hayewa saman bed ɗin ta yi tana ɗan turo baki. Ƙaramin pillow ta ɗauko, duka ta kaiwa Fanan a tsakiyar baya tana faɗin. "Aunty Fanan tashi ki ji wani labari". Miƙa ta ɗan yi, kamar zata yi kuka, murya cike da barci ta amsa da. "Kai Neesha me kuma na yi maki fisabilillah? Ki barni in cigaba da barci na mana, jiya momma ta kawo mun wasu darty girls sun hanani barci, sai hauka suke mun"................... Gyarawa Aneesa ta yi, ta manna bayanta da jikin headboard na bed ɗin, sannan ta ce. "To cigaba da barcin za ayi maki kafa kuwa". Waro idanunta waje ta yi, cikin magagi ta ce. "Ban gane za'ayi mun kafa ba, me kike nufi?". Cikin halin ko in kula ta amsa mata da. "Ina da tabbacin waɗan nan dirty girls da aka kawo maki daren jiya ɗaya daga cikinsu ce kishiyarki, renon kishiya kika yi jiya". A zabure Fanan ta miƙe zaune, har ji ta yi barcin nata ya watse, tana zaro idanunta ta ce. "Wai me kike nufi? Ban gane kishiya ta ba?"........... Kunna wutar screen ɗin wayarta Aneesa ta yi, cikin halin ko in kula ta cigaba da cewa. "Na zo yi maki mummunar albishir ne, Yah Jaish dai ya yi aure, kuma waɗan nan ƴan kauye da momma ta kawo ɗaya daga cikinsu ce matar tasa..........." Ai katse maganar ta yi ta ƙasa karisawa saboda wani irin capka da Fanan ta kai mata a wuyar rigarta, a haukace ta kai mata capkar, bata ma san ta yi hakan ba, kun san larabawa da balai'n kishi kamar me, tuni hankalin Fanan ya bar jikinta, har wani juyi taga ɗakin nata ya yi mata kamar fanka saboda tashin hankali, sai ta ji kamar kunnuwanta ne suka sharara mata karya. "Ke Aunty Fanan, bafa ce maki na yi nice kishiyar taki ba, mai da wukar, ni mai kawo labari ne kawai". Ta kai karshen maganar tana zare hannun Fanan daga wuyar rigarta. Ta gama aikinta sai ta sauko kasa gadan ta nufi waje abinta. Wato wlh Aneesa yar ikka ce, kawai ta kawo labari ta tafi ta bar Fanan da tafasar zuciya. Lallai ba shakka safiyar yau bata yi wa Fanan daɗi ba, kuma na tabbata ba zata taɓa manta wannan safiya ba, Allah sarki soyayya, ba laifinta bane. Da gudun gaske ta yaye bargon da ta lulluɓa, ƙasa ta diro, wani irin kuka mai karfi ne ya zo mata, da sauti ta saki kukan tare da watsawa a guje sai waje. Bata zame ko'ina ba sai part na uncle Abbas wajen Mammie ɗinsu. Tana shiga kai tsaye bedroom ɗin Mammienta ta nufa. Nan ta isko Sarina da Mammiensu zaune a saman bed, Sarina ta tada kai da cinyar Mammie suna shirya muguntarsu. Ai a haukace ta shigo tana ihu, har ta razana Sarina ta yunkura zata gudu. Saman bed ɗin ta haye ita ma, Mammiensu ta rungumo tana faɗin. "Na shiga uku Mammie, shi kenan rayuwata ta zo karshe, ki taimakeni kada na mutu Mammie". Sarina dai baki ta saki galala tana kallon ikon god. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Rungumeta Mammie ta yi tana faɗin. "Ya isa haka, yi shiru ki faɗa mana menene yake faruwa?". Ƙasa yin shiru ta yi, sai ma wani irin shessheka take yi tamkar zata haɗiyi zuciya ta mutu. A kule Sarina ta ce. "Ke bama san hauka, dalla rufe mana baki ki faɗa mun me yake faruwa?". ........... Sanin bakin halin Sarina yasa ta haɗe malaman jikin waje guda ta nitsu, cikin muryan kuka ta fara kora masu bayanin yadda Aneesa ta kora mata. Wata iriyar zabura Mammie ta yi, dan kuwa tasan da cewa Queen Zarina tana san Jaish, kuma tana san shi ne a matsayin saurayi ba wanda ya taɓa aure ba, in kuwa ya yi aure akwai matsala, dan haka dole su yi saurin kawar da Mahnoor tin kafin ya rasa samartakansa, samartakan nasa Zarina take so, shiyasa kuka ga a yanzu Mammie ta daina goyan bayan Fanan a kan soyayyar Jaish. HMMM BABBAR MAGANA. A baya ta so Fanan ta mallaki Jaish, amma da Zarina ta nuna kwaɗayinta a kansa sai Mammie ta janye, shiyasa kuka ga ta dai'na bawa Fanan dik wata gudunmawa, ita kuma Fanan lokacin da Mammie take matsa mata ta rinƙa zuwa wajen Jaish dan ta samu soyayyarsa, a lokacin bata wani feeling a kansa sosai, daga baya sonsa na gasken gaske ya shigeta, a lokacin ne kuma Mammie ɗinsu ta zare hannunta a lamarin,........................... Tashin hankali, lallai akwai cakwakiya. Mahnoor ta ko'ina sai tarin makiya kike da su, Allah dai ya fiddaki, amma akwai matsala, Mahnoor zata yi kishi da Queen Zarina and Fanan, kai my people's shin kuna ganin wannan abu ne mai ɓullewa ga Mahnoor kuwa? Babban abin takaicin ma shi ne mijin da ake ta wannan bura uba a kansa ɗin ma bai san suna yi ba, hasalima dikkansu ba wanda ya ke kalla da mutunci, dik ya tsanesu, akwai bala'i a kingdom of power wlh, ga dai can Zarina ta tura a ɗauko mata shi, wayyo Allah Jaish yaron Mommarsa zaka yi bayani dan gidanku in ka jika a komar Zarina, ina dai Mahnoor ce baka so? Mu je zuwa zaka so Zarina dan dole ai. Wani irin matsiyacin tsaki Sarina ta ja. A walaƙance ta dallawa Fanan wani tsinannen harara wadda sai da tasa Fanan haɗiyar yawu mai wuyar wucewa. "Shashasha kawai, ke yanzu a kan namiji kike wannan kuka Fanan? Me aka yi aka yi Yah Jaish? To ko mata dubu zai aura cikin minti nawa zaki ci uban shegu ki kaɗasu hanyar yamma? Ke sai kace ba jininmu bane a jikinki! Ni kam anya Mammie Fanan ƴar ki ce kuwa?"........... Cewar hajiya Sarina almasifatu rasa kunya. Bata jira amsar Fanan ba ta ɗaura da cewa. "Ko ƴar autar sarkin aljanu ya aura karshe kenan ko? To ubanta zaki ci kawai, zan yi supporting naki ba dan komai ba sai dan kina sansa, dole in tayaki mu kwato maki shi". Tana magana tana dallah mata wannan makirin hararar. Mammie cikin karayar zuciya ta ce. "Fanan da gaske son Jaish kike yi?". Yadda ta yi maganar zaku fahimci wlh zuciyarta ya karaya matuƙa, tana san ƴaƴan nata sosai, bata jin zata iya marawa Zarina baya ta mallaki Jaish in dai har da gaske Fanan tana san shi, kuma ba zata iya rabuwa da shi ba, ba zata cutar da ƴaƴanta ba gaskiya, dan tasan ya zafin so yake. "Zaki iya hakura da shi?". Cike da tsoron amsar da zai fito daga bakin ƴar tata ta sake jefa mata wannan tambaya. Wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskar Fanan, cikin murya mai ban tausayi ta amsa da. "Mammie wlh mutuwa zan yi idan har na ce zan hakura da Yah Jaish, wlh ina sansa so mai tsanani, ban taɓa san wani abin kwatankwacin jin sautin muryarsa kawai bama.........." Katseta Sarina ta yi cikin tsiwa. "Ke dallah ki dai'na jero mana wasu sambatu, ni natsani jin kalaman soyayya a bakin mace, idan kin ga dama ki dafa shi ki cinye, amma kada ki faɗa mun, kina son shi e kina son shi ya wadatar, ba sai kin kara mana da yadda kike ji a ranki ba"........... Wai Sarina sai shirin Allah, wannan yarinya da ba dan ma jinin Akka na gudu a jikinta ba wlh ina ga shaiɗancinta sai ya wuci yadda ake tinani. Shiru Fanan ta haɗiye sauran maganganunta tana shessheka haɗe da kawar da kallanta daga kan Sarina. Mammie kam shiru ta yi kamar wadda ruwa ya cinyeta, ta rasa abin faɗe, iya abin da ta sani shi ne lallai a wannan gaɓa ba zata taɓa taimakawa Queen Zarina ba, tun da Fanan ta kamu da san Jaish dole yarta ce zata mallake shi............ Bala'i can, kai my people's me kuke tinanin zai faru? Jaish shi kaɗai mata uku, dik bama wannan ba, ya mammie zata kaya da Queen Zarina?. Riko hannun Fanan Sarina ta yi. "Zo mu je ɗaki in baki lecture yadda zaki yi maganain Yah Jaish ya dawo tafin hannunki, a wannan karon bama buƙatar Mammie, dan ita bata san salan zamani ba, na da can ta sani, Mammie ke kuma mun baki aiki kawar mana da matar da aka aura mashi ɗin koma wacece". Tana magana tana janyo hannun Fanan har ta sauko kasan gadon. Cikin shessheka murya a hanzarce Fanan ta ce. "Aunty Sarina bafa wata matar azo a gani bace, wlh tantagaryar ƴar kauyece wadda bata da banbanci da dabbobi, kuma kin ganta yar datti, amma kuma wlh tana da kyau sosai, dan ya fini kyau". Ɗan taɓe baki Sarina ta yi tana ɗaure fuska. "Kin san matar tasa ce? Kin taɓa ganinta ne?". Da sauri ta amsa da. "E jiya fa a ɗakina momma ta kawosu suka kwana, sai kin gansu wasu kucaku da su ƴan datti, ɗakina ya yi ta wari sai da nasa aka kwashe bedsheet da suka taɓa da dik wani abin da suka yi amfani da shi aka zubar da su, na sa aka zuba tirarika sannan na iya kwana". "What?!!" Sarina ta faɗa cikin ɗaga murya. Jinjina kai Fanan ta yi alamar tabbatarwa. "Muje in gansu". A gadarance ta yi maganar. Banda idanu babu abin da Mammie take binsu da shi, ta rasa abin faɗe, tinanin balai'n dake tinkarota kawai take yi a kan wannan case ɗin. "Aunty Sarina yanzu kam sai dai mu je mu tambayi Neesha ta bamu labarin in da matar tasa take, dan Haulat ta zo da safe ta ɗaukesu". Cewar Fanan. A ƙagare da san ganin Mahnoor Sarina ta amsa da su je wajen Aneesa ta basu labarin ina Mahnoor take. Da wannan shawara suka nufi waje hannunsu cikin najuna, har wa yau dai Sarina tana cikin wannan ɗan iskan shigar tata mai tada hankalin maza. Mammie da ta afaka duniyar tinani sam bata san lokacin da suka fice daga ɗakin ba, mafita kawai take tinawa kanta. Basu zame ko'ina ba sai part ɗin King, ɗakin Aneesa kai tsaye suka nufa. A lokacin ta fito daga wanka ɗaure da towel a kirji, tana tsaye a gaban mirro, sai tashin kamshi ɗakinta yake yi. Zee tana zaune a saman sofa ta buga uban tagumi tana bin Aneesa da kallo, tana cikin shigar abaya mai bala'in tsada na Aneesa launin ash colar, ta yi matuƙar kyau sosai, ta yi rolling veil a kanta. Tun sako kafarsu a cikin ɗakin Sarina take bin Zee da wani matsiyacin kallo da in aka yi wa mutum sai ya ji kamar shi ƙasƙantace ne. Ganin haka yasa Zee ta kawar da kanta daga kallonsu, ga shi kuma tana bala'in san kallan nasu, saboda larabawan ainahi suna da tsananin kyau sosai, amma ta lura kamar gabaɗaya familyn King daga mazan har matar dikka tacaccun ƴan duniya ne masu jiji da kansu, babu mai saukin kai da za'a ɗaga idanu a gani ya ɗan tarbi mutum da fuska mai sauki sauki koda ba fara'a ma, gabaɗayansu daga matan har mazan fuska kamar an aiko masu da saƙon mutuwa. Allah sarki bata samu Zunaira da Chuchu bane shiyasa take wannan tinani. Sarina na ƙoƙarin ambatar sunan Aneesa dan ta tambayeta sai Aneesa ta yi saurin katsesu da cewa. "Aunty Sarina nasan bai wuce amaryar Yah Jaish kuka zo tambayata ina take ba, ai dama nasan sai kin so ganinta, to ba fa wata shegiya bace, ku kwantar da hankulanku, yar kauye ce mara gata wanda ko a ƴar aiki ba zan ɗauketa ba, banza ya fi mun ita muhimmanci, dan haka ni ban ga abin da zaku nemi gani a wajen bama, sai dai fa tashin hankalinku ɗaya ne"....... Dakatawa ta yi da magana tana wurga masu kallo ta cikin mirror. Aneesa wlh karshe ce yarinyar nan, wannan idan Allah ya taimaketa Yah Rizwan ya shiga hannunta shikenan kuma sai abin da ta so, yarinya ta iskance tun bata kai ko'ina ba, Allah ya ceci Yah Rizwan. Cike da fadanci Sarina ta amsa da. "Mecece matsala gudan?"..... Shiru Aneesa ta ɗan yi na kamar one min, sannan ta amsa da. "Momma, momma tana bala'in kaunar yarinyar dik da take kazama maras gata". Siririn tsaki Sarina ta je. "Wannan ba matsala bane, ke dai yanzu faɗa mana in da take?". Cikin halin nuna ko in damu Aneesa ta faɗa masu Mahnoor suna ɗakin gyara. Sai dai tasan su Sarina basu isa faɗa da momma ba, dole su gama dik iskancinsu su dawo lallaɓa momma kam, dan ta gagari kowa a gidan, kafun Allah ce ita. Sai binsu da kallo a sace Zee take yi, dan kyansu take san kallansu ba dan komai ba. Juyawa Sarina ta yi, har lokacin hannunta rike da Fanan dake ta sauke ajiyar zuciya saboda kukan da ta sha. Har sun kai tsakiyar ɗakin zasu nufi waje Sarina ta dakata, juyo da kallanta a kan Zee ta yi. Wani irin kallan walaƙanci ta watsa mata up and down kafin ta ce. "Neesha wacece kuma wannan?". Aneesa na cigaba da gyaran gashin kanta ta amsa masu da. "Bakuwar second dad ne". "Wannan kucakar? Daga ina ya samota?".Sarina ta sake tambaya........... Tara gashin kanta Aneesa ta yi ta ɗaure, sannan ta juyo garesu da kyau, ta ɗan jingina bayanta da jikin mirror kaɗan, sillent talk ta yi wajen cewa. "Wannan ne kuma zaki iya tambayarsa, bani da alaƙa da hakan kuma bana san yin alaƙa da hakan shiyasa ban nemi sanin labari a kan meyake tsakaninsu ba". Tana kai karshen maganar ta wuce dressing room ɗinta. Harara Sarina ta bi Zee da shi kafin tasa kai ta nufi waje, kai tsaye ɗakin gyaran suka nufa. Sai dai ko da suka je mama Haulat ta hanasu shiga, saboda doka ce momma ta saka bata yarda ta bawa kowa daman ya shiga wannan ɗaki ba har sai su Mahnoor sun fito. Tatas Sarina ta yi wa mama Haulat, rashin kunya tas ta yi mata wanda ko kare ba zai sinsina ba, sannan ta ja hannun Fanan suka ta fi tana faɗi ko mama Haulat zata mutu yau ba sai gobe ba sai sun shiga ɗakin nan sun ga Mahnoor, ta jira dawowansu a karo na biyu. Ko sannu mama Haulat bata ce masu ba har suka fice, wucewa ta yi ta rufo kofar da Mahnoor suke ciki ɗin, ta zo ta ɗauko kayan marmari dan ta kai wa Jaish yana lambu. Allah sarki mama Haulat baiwar Allah ƴar amana, matar nan tana da ƙoƙari sosai, ba ƙaramin fama ta sha da Mahreen ba kafin Mahreen ta yarda a shafa mata haɗin gyaran jiki a jikinta, har zagin mama Haulat ta yi, amma dik da haka bata tuna ta wani damu ba, sai ma hakuri da ta rinƙa bawa Mahreen ɗin. Abin dariya kuma shi ne Mahreen bata taɓa yarda ta shiga toilet ita kaɗai har sai mama Haulat ta rakata, wanka ma ita ta yi mata yau, dan tsoron toilet ɗin take ji, sai su manne waje guda ita da Mahnoor saboda tsoro. Dik da haka mama Haulat ta jure bata wani damu ba. A ɓangaren uncle Jahiz kuwa, yana barin wajen su Zee ya dawo in da momma take ya karɓi babyn Khadija wanda ya sanya mashi suna da Junior, haka yake kiran yaron, Allah ya saka mashi kaunar babyn nan sosai. Yana ɗaukansa ya wuce wajen King a fada da shi, a nan suka je rabon zakka. Sai dai fa dik hankalinsa yana a kan Zee, tinaninta kawai yake yi, yana jin kamar ya tashi ya zo ya sake dubata, dan yana ganin kamar bata jin daɗin zama da Aneesa, saboda yasan halin ƴaƴan nasa, haka dai yake ta sake sake ya kasa tsayar da abu guda. Da yamma ta yi cikin nitsuwa ya yi wanka ya canza kaya, ya bawa mama Haulat junior ta yi mashi wanka ta shirya shi cikin shiri na musamman, sannan ya koma ya karɓesa, ya nufo wajen Zee a ɗakin Aneesa. Babu kowa a cikin ɗaki, ita kaɗai, ta takure jikinta waje guda, tana kwance saman sofa barci ya yi awon gaba da ita. Ciki ya kariso, a gaban sofar ya tsaya yana kallan face ɗinta, har sai da ya ji faɗuwar gaba lokaci guda, ji ya yi kamar kada ya tasheta, amma kuma ya tina tana san ganin ƴar uwarta, hakan yasa ya fara ambatar sunanta a hankali hankali. Da yake bata da nauyin barci sai ta farka. Ganin shi a kanta yasa ta yi saurin miƙewa zaune tana janjayo kayan jikinta ta gyara. Ɗan kawar da kallansa a kanta ya yi yana faɗin. "Sorry na tasheki daga barki ko?". Kanta a ƙasa ta amsa mashi da ba komai. Sai wani gyara jikinta take yi tana takure kanta bayan komai nata a rufe yake. "Kin shirya mu tafi ne?". Da sauri ta gyaɗa mashi kai. Sannan ta ce. "Dan Allah ka ɗan bani yaran in rike". Ba musu ya miƙo mata shi naɗe cikin kyakkyawan abin rike yaro fari kal mai tsada. Hannunta har kerma yake yi tasa ta karɓesa, ya yi barci, bawan Allah da mama Haulat ta bashi badara ya sha, ta yi mashi wanka shikenan sai ya hau barci abinsa, bashi da kukan banza. "Muje ko?". Ya faɗa yana nuna mata hanya. Gaba ta wuce ya rufa mata baya yana ta kallanta. Kasa hakura ya yi har sai da ya ce. "Zee kayan nan sun yi maki kyau sosai, kin yi kyau". Hankalinta a kan baby ta amsa da ta gode, daga haka bata sake yin magana ba suka wuce izuwa parking space na gidan. Gidan baya na ɗaya daga cikin motocinsa suka shiga, driver ya jasu zuwa hospital na cikin Kingdom ɗin. •••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 Bari mu leƙa wani part. Katafaren gida ne irin contemporary Glass Architecture ne, gini ne na gilashi mai kauri da tsari mai ban sha'awa don bayar da haske da kyau. Hawa biyu me mai amfani da escalator mai amfani da lantarki don tafiyar da mutane sama ko ƙasa cikin sauƙi. Manyan ɗakunan barci guda uku a sama da karamar parlon, sai main parlour mai girma a ƙasa wanda aka kawata shi da kayan alatu launin pink and milk. Akwai wajen wasanni, shakatawa, da filin motoci, grand Living Room, lambun waje furanni masu kyau da kamshi, ga shuke shuke masu ƙawa na musamman. Babban Kitchen na Zamani (Modern Kitchen) mai ɗauke da kayan girki na zamani (smart appliances) Dining Room wajen cin abinci mai ɗauke da fitilu na alfarma. Guest Room, ɗakunan baki guda biyu masu zaman kansu. Restroom, tare da kayan zamani. Hawa Na Biyu (First Floor) Master Bedroom. Babban ɗaki mai ƙunshe da toilet, wardrobe na zamani, da balcony haɗe da kayan alatu na more rayuwa. Mini Library. Wurin karatu da nazari. Gaming Room. Wurin wasanni da na’ura masu ban sha’awa. Cinema Room. Wajen kallon fina- finai na zamani. Office Space. Wajen aiki ko haɗuwa da abokan ciniki. Guest Lounge. Wani parlour na musamman ga baki. Indoor Pool. Ruwan wanka na sama mai gabaɗaya mai ɗumi na musamman. Barbecue Space. Filin girke-girke na musamman, sune a sama. Waje hararbar gida (Outdoor) Swimming Pool. Babban ruwan wanka mai kyau. Garden. Lambun shakatawa da kujeru. Playground. Wurin wasan yara da manya. Parking Lot. Wajen ajiyar manya-manyan motoci, har guda 8. Shake yake da motoci irinsu, Rolls-Royce Phantom, Bentley Bentayga, Lamborghini Urus, Mercedes-Maybach S-Class, Ferrari Portofino. Gidan ya haɗu matuƙa. Sai dai dik girmansa da ƙawatuwansa mutane biyu ne kawai suke rayuwa a cikinsa, daga wata dattijuwa sai jikarta. Tsohuwar dattijuwa mai cikar kamala, da ƴar matashiyar jikarta da ba zata wuci 18 to 19 years ba a duniya. Kyakkyawar gaske ce yarinyar, gata so sillent haka, tin da ta taso a tare suke da wannan kakar tata, da farko rayuwa suke yi a cikin wani kango wanda da shi da banu dik ɗaya ne, dik ya rurrushe babu kofa, gini ne na laka da ya jima ya sha wahala, ci da kyar sha da kyar, idan sun samu cin safe basa sanya ran zasu samu cin rana, basu da gata basu da galihu. Ga jikar tata kuma Allah ya yi mata basira sosai, akwai ilimi da balai'n san karatu, tana zuwa govment school dake kusa da unguwarsu, dik da makarantar a lalace sai a hankali, hakan bai hanata zagewa ta mayar da hankali a kan abin da ake koyar da ita ba, tana da hazaƙa sosai, suna cikin ƙuncin rayuwa matuƙa, amma dik da haka basu kuskura sun yi wani abin da zai kaucewa faɗin Allah ba, sun kula da kansu da dokikin Allah, sun cigaba da jure wahala. Wani lokaci idan yunwa ta yi yunwa har bara suke fita su yi, in kuma suka je yin bara duniya ta lalace sai lalatattun cikin mutane su nemi lallata mata jika, hakan yasa ta datse batun neman taimako wajen kowa, suka dukufa suka mai da lamuransu ga Allah dan ya taimaka masu ba sai an ci zarafinsu ba. Wataranar Friday wannan matashiyar budurwa zata je karɓan hutun kammala primary school bayan rubuta common entrance, sun shirya ɗan ƙaramin party na dai'dai ƴaƴan talakawa, dik da bata kai ko biyar nata wajen haɗa kayan wannan party ba, amma ta shiryar dan ta je ko gani da ido ne taga masu yi. A hanyarta na zuwa school mota ya bugeta, bata ji ciwo sosai ba, saboda mai motan ba gudu yake yi ba, da yake bawan Allah ne mai sanin yakamata ga ilimin addini sai ya tsaya ya ɗauketa ya kaita asibiti. A nan aka ɗan dudduba dik in da ta ɗan kukkuje aka yi mata dressing ɗinsa tsaɓ tare da bata magunguna. Ya biya kuɗin sannan ya ɗaukota a mota tana yi mashi kwatance har ya maido da ita gida. Bayan ya sauketa a kofar gida tana rike da ledar magungunanta a hannu, har zai juya kan motarsa kuma sai ya fasa ya dakata. Dama aikinsa kenan yin aikin alkhairi, yana da tausayi da jin kan talaka, hakan yasa ya kashe motar ya fito, a lokacin yarinyar ta shige cikin gida. A kofar gida ya tsaya ya daka sallama cikin nitsuwa. Daga waje yana iya hango cikin gidan saboda rurrujewat ginin, yanayin ginin ma ya ja hankalinsa ya ji yana san bin bayan yarinyar. A maimakon ya ga yarinyar ta fito sai yaga wata dattijuwa ta fito, cikin girmamawa ya yi mata sannu tare da neman izinin yana san yin magana da mai gidan, a tinaninsa mahaifin yarinyar kenan. Babu wani ɓoye ɓoye ta sanar da shi babu wani mai gida a nan sai ita da jikarta, kuma ba gidansu bane na hayane. Sosai ya ji tausayinsu ya kama shi, da Allah yasa abincinsu na hannunsa sai yazamana sanadiyyar canzawar rayuwarsu, shi ya sai masu wannan Daula da suke ciki a yanzu, ya canzawa yarinyar school izuwa makaranta mai bala'in tsada na manyan kai, ya sanya masu tsaronsu da kyau, a yanzu haka wajen motoci biyar ne suke jerin gwano idan zasu kaita school, rayuwarta gabaɗaya ya canza tamkar ba su taɓa yin rayuwar ƙaskanci da wahala ba a baya. Shiyasa idan ka yi hakuri ka miƙa lamuranka ga Allah sai ka huta wlh, dan Allah idan ya tashi taimakonka ta in da baka yi zato ba zaka ga canjin da babu wanda ya isa ya baka a duniya. Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin waɗan nan bayin Allah. Time to time wannan bawan Allah yana zuwa duba lafiyarsu, ba komai yasa hakan ba kuma face wannan dattijuwa ta sanar da shi iyayen wannan matashiya sun rasu, marainiya ce, shi kuma yana bala'in san ganin ya taimakawa marayu, yana jin ƙan marayu sosai, dik wani abin da suke so ya sayi waya ya basu dan su rinƙa kiransa su sanar da shi, ba kuma su kaɗai ya taɓa yi wa haka ba, shi ɗabiarsa ce taimakon mutane. Yana da tarin makudan dukiya sosai, bashi da aiki sai duba marasa karfi yana tallafa masu sosai, kullum kuma arzikinsa ƙara haɓaka yake ta ƙara yi. Yarinya ta goge ta zama yar gayu, ga kyau ga ilimi, ga shagwaɓa da kyan diri, kamar ka taɓata jini ya zuba. ••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Kwance take a saman wani bed round da shi haka, kamar pool haka bed ɗin yake, irin rest bed ɗin nan ne wanda mattress ɗinsa yake can kasa haka. Ta tada kai da cinyar dattijuwa, sanye take da ƙananun kaya na shan iska, rigar mai siririyar hannu ce izuwa gwiwarta, sai dogon wando mai laushi, dattijuwa ta ɗaure mata gashin kanta kashi biyu, bakinta sanye yake da wani irin lips balm mai shegen kyau da sheki. Sai tashin daddaɗar kamshi take yi. Fuskar nan tata tamkar zata saka kuka, ta shagwaɓesa sosai, tana turo baki ta ce. "Ammo baby ya jima yanzu bai zo gidan nan ba, ya ɗauki lokaci sosai wannan karan, ina kewarsa sosai wlh, ni kamar in je nemansa". Tana da sanyayyar murya mai daɗin sauraro, akwai nitsuwa sosai a cikin kalamanta, sai dai akwai shegen shagwaɓa kuma. Baby shi ne sunan da take kiran wannan bawan Allah da ya taimaka masu, tun tana karama yake ce mata baby ita ma tana ce mashi, so hakan tasa sunan ya zauna, a da idan tana kuka ne yake amfani da wannan suna yana rarrashinta, har dai sunan ta zauna. Shafa kanta Ammo dattijuwar kirki ta yi, cikin nuna tsantsar kulawa ta ce. "Ni kai'na ina kewarsa, ban san me ya hana shi kawo mana ziyara ba, an ɗauki lokaci gaskiya". Cike da tausayawa babyn ta yi magana, dan kuwa tasan yadda suka shaku sosai, tin yarinyar tana karama bata da wajen wasa ko zama sai jikinsa, yana da bala'in san yara kuma yana san ganin yana wasa da su. "Ammo dan Allah mu kirasa a waya mana yau kam". Ta yi maganar tana miƙewa zaune. "Jeki ɗakina sai ki ɗauko wayar ki kawo mu kirasa". Cewar dattijuwa. Wani irin farinciki ne ya lulluɓe zuciyarta, har sai da ta saki ɗan siririn murmushi wanda ya ƙara fito da kyanta. Da sauri ta fito daga cikin wajen, ta nufi ɗakin kakar tata tana sakin murmushi. Da kallo Ammo ta bita tana tausaya mata. Har zata shiga cikin ɗakin sai kuma ta tsaya cak, a hanzarce ta juyo da kallonta baya, shiru ta ɗan tsaya kaman mai nazarin wani abin, kamar mai raɗa ta ce. "Baby come out, I heard your breath, my heart beats with your name". Ta faɗa tana ɗan tura baki. Shiru bata ji alamar komai ba, ɗan motsawa ta yi kamar zata dawo baya, sai kuma ta cigaba da tafiya tana faɗin. "Tsabar kewarka da nike yi ne ya ja nike jin zuciyata tana bugawa da sunanka a kurkusa, ashe ba haka bane". Tana ƙoƙarin tura kofar ɗakin kakar tata sai ta juyo da sauri. Tana juyowa suka yi 4 eyes da kyakkyawan face ɗinsa tana ɗan sakar mata siririn murmushi. Tsayayyan cikakken namiji ne mai cikar surar mazanta, yana sanye da three-piece suit launin ash colar, kyakkyawa ne sosai fari tas da shi, murmushinsa tana da laushi mai kwantar da hankali haɗe da ƙayatarwa, idan ya yi maka shi sai ka ji hankalinka ya kwanta. "Baby waye ya ce ki juyo ne?". Ya faɗa murya a sanyayye ga zaƙi da daɗin sauraro. Idanunsa a kanta, kirjinsa sai da ya buga ganin irin shigar dake jikinta, gata budurwa, komai a cike fam. Turo baki ta yi, tamkar zata fashe da kuka ta ce. "Baby ina kaje kwana dayawa baka zo ba?". Nisawa ya yi, ɗan lumshe idanunsa ya yi. "Baby bana ce ki rinƙa sanya hijabi ba?". Shiru ta yi tana kallansa. Gera ya ɗan ɗaga mata, hakan yasa ta yi saurin cewa. "To ai a cikin gida nike yasa ban saka hijabin ba, amma yanzu zan je in saka". Jinjina kai ya yi. "To jeki ki saka sai ki zo parlon in faɗa maki dalilina na rashin zuwa kwana biyu". Da okey ta amsa mashi tare da shigewa ciki da sauri. Bayanta ya bi da kallo yana ganin yadda take tafiya mazaunanta suna yi mashi kwalele ta baya. Sai da ta shige cikin ɗakin shi kuma ya juya ya koma wajen Ammo yana sauke nannauyar ajiyar zuciya. Bawan Allah yanzu ma daga gidan gajiyayyu marasa karfi ya fito, kayan tallafi ya je ya kai masu. Yana da farar zuciya sosai fiye da tinaninku. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Saman sofa ya zauna yana fuskantar Ammo dake zaune saman nata sofan ita ma, ganinsa ya zo gidan yasa ta dawo saman sofa ta zauna. Cikin girmamawa ta ce mashi. "Ka ganta kuwa?". Kai ya ɗan jinjina mata yana faɗin. "Ai da ban sanyata a idanu na ba ba zan iya fitowa in dawo nan ba". Murmushi Ammo ta saki tana mamakin irin shakuwar dake tsakaninsu, tana ganin shakuwar ta yi yawa sosai, a ganinta basu kai ya yi masu irin wannan ba, sai ga shi kuma ya shaku da su sosai haka. Sallamarta ya katse su. Tin da ta shigo kallonsa a kanta, a saman sofar da yake zaune ta zo ta zauna, cike da zumuɗi ta fara jero mashi tambayoyin meyasa ya kwana biyu bai zo ba?. "Sorry baby, aiki ne ya mun yawa, yau ɗin ma da kyar na samu lokaci na leƙo, kuma yanzu ma ba jimawa zan yi ba, dan yanzu haka jirana ake yi, amma dai ki sani koma menene kina rai'na a koma ina nike". Ya kai karshen maganar idanunsa a kanta........ Zata yi mashi magana suka haɗa idanu da Ammo, girgiza mata kai Ammo ta yi dan tasan abin da zata faɗa, gardama zata yi mashi a kan kada ya tafi, kuma Ammo ta hanata yi mashi haka, ta hanata yin gardama da shi. Shiru ta sunkuyar da kanta tana san yin magana amma ba dama. Ganin kamar taso yin magana sai kuma ta yi shiru ne yasa ya saci kallan Ammo ta wutsiyar ido, dan yana zargin ita ta hanata magana. Dai'dai lokacin Ammo ta miƙe haɗe da cewa bari ta zo. Dabara ta yi zata basu waje, dan ta lura idan tana wajen bai cika yawan magana ba, kamar tana takura masu. Wani lokaci idan baby tana faɗa mata irin hiran da suka yi sai ta yi ta mamaki, a gabanta shiru shiru yake, ba dan tasan halin jikar tata baya karya ba da sai ta karyatata. So a gaban Ammo baya magana sai ta basu baya ne yake zuba hira da baby kamar ba gobe. Aikuwa tana tafiya ya juyo suna fuskantar juna da ita, a nitse ya ce. "Faɗa mun abin da kike san faɗa mun Ammo ta hanaki". Kai ta girgiza mashi kafin ta ce. "Ammo zata yi mun faɗa idan na faɗa maka". Hannayenta ya riko cikin nasa da nufin ya yi mata dabara ta faɗa mashi, sai dai kuma wani irin shock da ya ji har tsakiyar kansa ne yasa ya yi saurin sakin hannun nata yana ɗan jan numfashi a hankali, yarasa me ya shiga tsakaninsa da ita, wata ɗaya ne kawai bai kawo masu ziyara ba, amma kuma a wannan wata ɗayan kullun yana cikin tunaninta, ga shi ya zo kuma ya kasa iya rike koda hannunta saɓanin da da kullum suna manne da juna idan ya zo. "Ba zan faɗawa Ammon kin faɗa mun ba ai, ni kaɗai zan ji, kin ga bata nan ai ko?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e ...... "Good my baby, to faɗa mun menene?". Tsabar shirinta sai da ta fara jujjuyawa wai dan taga da gaske Ammo bata yi masu laɓe ba, kada ta jiyosu, sai kace akwai masu shigowa parlourn dama, ta wani tsaya tana waige wiage. Binta da kallo kawai yake yi, idan tana wannan shirirtar tata ba ƙaramin tafiya da tinaninsa take yi ba, yana jin daɗin ganin tana ire iren wannan abin. Sai da tabbatar babu kowa, sannan ta yi ƙasa sosai da murya, kamar mai raɗa ta ce. "Dama cema maka zan yi kada ka tafi, ni ban gaji da kallanka ba, kuma na yi kewarka sosai"..................... Ajiyar zuciya ya sauke. "Ammo ta hanaki ce mun kada in tafi ne idan na zo?". Ya jefa mata tambayar kallansa a kan yatsun hannunta da suke dogaye kyawawa. Kai ta gyaɗa mashi alamar e, sannan ta ɗaura da cewa. "Ta ce in dai'na takura maka ina maka kuka zaka dai'na sona, wai idan ina yi maka haka zaka dai'na zuwa ma, zaka ce ina damunka". Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa da kwallah. "Da gaske zaka dai'na zuwa idan ina cewa kada ka koma?"....... Girgiza mata kai ya yi, a karo na biyu ya sake riƙe hannayenta, Allah sarki ya saba ne, wani irin shock ya sake ji, hakan yasa ya yi saurin sakinta. Jingina kansa da jikin sofar ya yi, ya fara mamakin wannan abin gaskiya. "Kenan da gaske Ammo take yi zaka dai'na zuwa kuma zaka dai'na sona?". Muryarta ta daki dodan kunnnesa, hakan yasa ya yi saurin dawo da kallansa a kanta. "Ko kusa ko alama, hasalima daɗi nike ji idan kina ce mun kada in tafi". Wani irin daɗi ta ji, har ta saki murmushi, zata sake yin magana Ammo ta shigo hannunta rike da waya hakan yasa ta haɗiye maganar tare da dawo da kallanta a kan Ammo ɗin. "To tashi ki je uncle ɗin islamiya ya zo". Cewar Ammo kenan. Turo baki ta yi, sam bata san rabuwa da shi, amma ba yadda ta iya, miƙewa ta yi yana turɓune fuska ta ce. "Baby na tafi islamiyya". Kai kawai ya jinjina yana kallanta ba tare da ta yi magana ba. Shigewa cikin ɗakin ta yi. Waje Ammo ta samu saman sofa ta zauna idanunta a kansa, sai kallan baby yake yi har ta shige ciki, sannan ya sauke ajiyar zuciya. Yana ƙoƙarin lumshe idanunsa muryar Ammo ta katse shi da cewa. "Har yaushe zaka cigaba da ɓoye mata waye kai?". Wannan kalma tasa ya fasa lumshe idanun nasa a in da ya sauke kallansa a kanta. Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin ya amsa da. "Bansan har izuwa yaushe ba, abin da kawai na sani shi ne ba yanzu zata san wanene ni ba, ni yanzu zan tafi saboda ana jirana, kila in dawo da daddare, kila kuma sai gobe". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye. Da kallo Ammo ta bishi tana mamakinsa, ta ƙasa amsa sallamar da yake yi mata, har sai da ya fice sannan Ammo ta farga da ya tafi. TO FA WANENEN SHI KUMA?. Yana fita ta fito sanye da hijabinta har ƙasa, hannunta rike da kyakkyawan jaka mai ɗauke da litattafan addini da Alqur'ani mai girma. Sallama ta yi wa Ammo tare da nufar waje. Da kallo mai kama da kallan tausayi Ammo ta bita har ta fice. A tinaninta babyn nata ya tafi, sai kumbura kumatu take yi tana ɓata rai ya isa wajen kyakkyawan rumfar da suke karatu, already malam ya zo yana jiranta. A saman table dake wajen ta ɗaura jakarta, saman chair ta zauna tana turo baki. Tin da ta shigo wajen malam yake kallanta, yaga alamar kamar ranta a ɓace, bai iya hakura ba har sai da ya ce baby yau lafiya kuwa?. Babu komai ta amsa mashi da shi tare da janyo jakarta ta fito da Alqur'ani ta fara buɗe in da zata bada hadda. Shi kuwa yana zaune a cikin motarsa, tin da ta fito daga cikin gida ya kafeta da idanu har ta isa wajen karatun nasu, ya kasa tada motar ya tafi, da alama maganar da Ammo ta yi mashi ya taɓa zuciyarsa, kamar ya tado mashi da wani abin. Dik abin da take yi yana kallanta, bai ta fi ba har sai da ta gama bayar da haddanta cikin Suratul tauba, malam ya yi bismillah ya fara ƙara mata, dan ta kawo si dai'dai babu tangarɗa. Ya jima dai yana ganinsu kafin ya tashi motarsa da kyar ya tafi. Da yake baby bata san da wace mota ya zo ba, hakan yasa bata fahimci hana nan ko ya tafi ba, saboda dik motocin da suke parking space ɗin gidan nasa ne. Sai da ta ji tashin mota a yanzu ne ta fahimci ashe yanzu zai tafi. Ta so ta sake ganinsa, amma ba dama, tana ganin motarsa ya danna waje, shi ma ta cikin mirror yake ganinta har ya fita. Yana fita ya kara gudun motar, a miliyan ya keta kan titi ya tafi. Ita kuma ta cigaba da karatunta rai babu daɗi. Dik abin da yake faruwa Ammo tana tsaye a gaban windown parlour dake fuskantar harabar gidan tana kallansu. 🔥🔥🔥🔥FOREST🔥🔥🔥🔥 Sun ci karfin dafiyar da suke yi, abu kaɗan ya yi masu saura su fita daga cikin wannan dajin, sai dai yamma ta yi masu sosai, Hoorain ya fahimci dole sake kwana a forest ɗin nan ya kamasu, dan haka tin kafin rana ya faɗi dare ya yi masu sai ya yi saurin samun waje mai tsaro, mai ƙawa da ɗaukar hankali ya tsaya. Daga in da ya dakata zuwa in da mammar Kamran take basu da nisa, kun tuna wajen zaman su Sweetie na farko kafin Sadauki ya canza masu? To a arear wajen ya dakata ya fara ƙoƙarin haɗa masu wajen da zasu kwana gobe da asuba su cigaba da tafiya. Suna dakatawa Auta ta hau takura mashi da shagwaɓar yunwa take ji, hakuri ya bata har sai da ya gyara masu in da zasu kwanta ba tare da wata matsala ba, saboda kada duhu ya riskesa bai kammala ba. Waje mai kyau da haɗuwa ya gyara mata ita da Pretty kafin ya fara tinanin im da zai samo masu abin da zasu ci. Cike da mama Auta ta ce. "Kai kuma ina wajen kwananka my hero?". Idanunsa a kan kyawawan hannayenta ya amsa mata da. "Ko lokacin da muke gida ma ai bana da wajen kwana, kullun ina kasancewa ne a kusa da family part dan gadin abin da zuciyata ke muradi". Dik da tasan ita yake nufi, amma saboda ta ji ya furta ita ɗin da bakinsa yasa ta ce. "Wacece kuma ko mecece kuma abin da zuciyarka take muradi?". Sarai ya fahimci Zunaira a kullum tana san ganin yana nuna irin zallar son da yake yi mata, hakan yasa take san jefa mashi ire iren waɗan nan tambayoyi. Allah sarki tana san taga yana nuna yana santa tare da yi mata kalamai masu zafi. "Wata ce wadda zuciyata ke kauna". Ya bata amsa cike da tsoron abin da amsar zai haifar, dan yasan halin kayassa. "Ban gane wata ba! Wakenan?". Ta yi maganar tana ɗan ɗaure fuska. "Wata kyakkyawa mai kyan fuska dake ɗauke da lallausan murmushi mai kwantar da hankalin assistant commander, murmushinta yana sakani manta in da nike, murmushinta yana sawa in ji kamar an bani kyautar gida a aljanna, tauraruwar zuciyata wanda haskenta ya haske kirjina dikka, shekin haskenta ya wuci tinaninki, tin daga nesa idan ta doso haskenta yake disashe hasken dikkan wasu halittu dake gefenta, tauraruwar da bana jin za'a samu irinta". Tin da ya fara waɗan nan zafafan kalaman ta tsaresa da idanu tana kallan kyawawan lips ɗinsa yadda yake ɗan motsasu, yana magana one by one, bata san tana sakin cool murmushi ba ma, ta nitsu tana jin ta a wani duniya da babu hayaniya babu wata yana da zata yi mata tsakani da farinciki. Haƙiƙa akwai tsananin daɗi masoyi ya aika saƙon kalamai ga zuciyar da yasan tana matsanancin kausarsa, tabbas zai ɗarsa bishiyar yarda da kauna mai zafi da bata da iyaka a wannan zuciya. Ganin tana zuba sanyayyar murmushi ba tare da tasan tana yi bane yasa bai san lokacin da ya kashe mata ido ɗaya ba. Sai ganinta ya yi ta ɗan zaro idanu tana ɗage mashi gera ta kuma faɗaɗa murmushinta. "Murmushinki abin so ne har ga makiyanki gimbiyata, dik wanda baya san murmushi tabbas bai ga naki bane sarauniya............". Katse shi ta yi da cewa. "A fadar birnin zuciyar my Hero" . Wato sarauniya a fadar birnin zuciyarsa kenan, ta ƙarisar mashi da maganar. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani irin sanyi tana ratsa zuciyarsa. "My Hero kasan me?". Cike da farinciki ta yi maganar. Kai ya girgiza mata alamar a'a ba tare da ya yi magana ba. "Kalli cikin idanuna bari mu yi magana". Ta faɗa tana kallansa. Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce. "A'a ba zan iya kallan cikin idanunki ba". In a silent talk mai kama da raɗa ta furta. "Why?". Ƙasa sosai shi ma ya yi da murya kafin ya amsa da. "Saboda sirrikan da kyawawan idanunki suke ɗauke da su zasu sa zuciyata ta kasa iya shanyewa, ba zan iya ɗauka ba"................. Pretty dai kallansu kawai take yi, yo ita da bata ma gane me suke faɗe, ai gani take yi wani sabon haukan ne suke yi. "Kai da kake matsayin jarumi, namijin gaske, sadaukin da dauloli suke tsoron jin an ambaci sunansa a cikin mayakan da zasu kai masu hari, sadaukin da ya ciri tuta ya kafa tarihin da ba'a taɓa kafa irinta ba a kaf faɗin kingdom of power, sadaukin da sunansa ke firgita manyan maza yasa hantar cikinsu ta kaɗa, kai fa assistant commander ne na gabaɗaya dangerous warriors, shi ne zaka ce kana jin tsoron kallan cikin kwayar idanu na? Meyasa?". Cike da kwarin gwiwa ta yi maganar. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ranki ya daɗe dik ajiye wannan a gefe, mata suna da kwarjinin da dik wani girman namiji da ji da kansa yana jin shakkarsu, ga su dai sune ƙasa da mu, amma Allah ya basu wannan dama a kanmu, wlh wannan gaskiya nike faɗa maki, dik namiji yana jin shakkar mace, sai dai ya danne kawai, dik bama wannan ba".............. Ƙasa sosai ya yi da murya kamar sillent talk, sannan ya cigaba da cewa. "Ke idanunki daban suke da kowace mace, tsoron ganin cikinsu nike ji kada ki hanani yin barci yau". Cikin nitsuwa ya yi maganar................Siririn murmushi ta sakar mashi. "Zan iya samun sunan love apart from ranki ya daɗe?". Unexpect garin amsa mata idanunsa suka sauka a cikin nata. Wani irin azabbabben shock ya ji tin daga tsakiyar kansa har izuwa tafin ƙafarsa dake cikin takalmarsu na mayaƙa. Cikin sauri ya zare idanunsa unexpext ya sake sauke kallansa a saman kyawawan laɓɓanta da ta ɗan ciza na kasan kaɗan hakan yasa ya kara pink sosai. Oh god, zuciyar maza ne ta amsa, nan take ya ji shi a matse kamar yana ƙoƙarin shiga out of control, wani irin jan numfashi ya yi mai cike da fassarori dayawa. Ƙasa iya amsa mata ya yi, sai ya ji gabaɗaya kamar an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗinsa. "My Hero lafiya?". Ta yi mashi tambayar bisa famintar da ta yi na ya shiga wani hali. Nisawa ya yi kafin da kyar ya iya buɗan baki yana ɗan girgiza kai ya ce. "Babu komai Hoonaira". ......... Hoonaira ta maimaita sunan tana kallansa, har cikin ranta ta ji wannan lallausan suna mai daɗin ambato, sai ma da ya faɗa da bakinsa ne ta ji wani irin daɗi na daban. HOORAIN AND ZUNAIRA SHI NE YA BADA HOONAIRA LIKE WOW, ABIN YA ƘAYATAR. "Zan iya tafiya in je in samawa gimbiyata abin da zata ci?". Ya jefa mata tambayar yana kallan gefenta a zahiri, amma a bayan fage face ɗinta yake kallah. "Ni dai a'a ban yarda ba, ni sai ka kalli cikin idanuna sannan zaka tafi, idan ba haka ba ni bazan ci abinci ba". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. Ɗan jinjina kai kawai ya yi, shagwaɓaɓɓiyar nan tasa tana san ɓallo mashi ruwa ne yana zaman lafiyansa. "So kike yau ki hanani barci ko?"........... Kai ta ɗan girgiza mashi. "Zaka yi barci In Sha Allah in dai muna tare". "To amin afuwa na je na kawo wa sarauniyata abincin dai tukun nan, idan na dawo sai ki tsareni ki sakani yin dik abin da kike so"........ Jin in ya dawo ta saka shi yin dik abin da yake so yasa ta aminta da ya je to. Cikin zafa ya wuce yana taku cike da jarumta. Bayansa ta bi da kallo har ya kurewa ganinta, sannan ta riko hannun Pretty suka zauna a wajen da ya tanada masu, cike da tsananin kaunarsa ta fara bawa Pretty labarin irin tsantsar madarar san da take yi mashi. Shi kuwa neman masu abin da zasu ci ya tafiyi dokinsa na biye da shi a baya. Dai'dai zai gifta tsakanin wasu dogayen bishiyoyi ya hango kamar mutun kuma mace tana ƙoƙarin jan abu a kwando. Da yake yana da zuciya mai kyau sai ya nufeta domin ya taimaka mata. Ba kowa bace face mammar Kamran, ta ɗebo kayan lambunta dayawa a cikin irin wannan kwando da Kamran yake ɗebo mata ɗin, kwandon yana da girma sosai hakan yasa take jansa da kyar, dan ya yi mata nauyi. Allah sarki Kamran mai yi mata hidimar baya nan, daga ganinta bata da ƙoshin lafiya, da alama tsananin damuwan rashin Kamran ya haifar mata da ciwo, ta yi rama sosai tamkar ba ita ba, shiyasa ma ta kasa iya ɗaukar wannan kwando, jikinta har wani kerma yake yi. Taimaka mata ya yi ya ɗauka mata suka haura saman tsauninsu, kun san Mamma bata yarda da baki, dan haka shi ma bata aminta da shi ba, sai dai shi ko da ya nufota bai yi mata magana ba, kwandon kawai ya ɗauka mata da hannu ɗaya ya haurar mata sama, a bakin kofar kogonsu ya ajiye mata ya juya ya sauka, bai yi mata magana ba ya wuce abinsa. Dik yadda bata san mutane yau karo na farko da aka taimaka mata ta ɗan ji a ranta ashe ba dikka mutane bane na banza, ashe akwai na kirki? Ashe akwai masu taimako? Bata taɓa zatan akwai wanda zai iya taimaka mata ba a rayuwarta, Allah mai iko, yau ta ga sabon abu. Shi kuwa yana sauka ya bazama nemanwa gimbiyarsa abinci, bai dawo ba sai da duhu ta fara yi, sannan ne ya dawo ɗauke da kala kalan kayan cima da za'a iya samu a wannan dajin. A lokacin Pretty da Auta sun yi alwala sun yi sallah suna zaune a waje guda suna hira. Suna ganinsa suka miƙe, a gabansu ya dire masu kayan da ya kawo masu, Auta ce ta kallesa cikin ido. "My Hero muna godiya da kulawan da kake bamu, Allah ya barmun kai ya kare mun kai da kariyarsa". Ƙasa ƙasa ya amsa da amin tare da miƙewa yana faɗin. "Zauna kici ko? Kinga tun ɗazun kika ce kina jin yunwa". "To kai ina zaka je ba zaka zauna mu ci ba?". A shagwaɓe ta yi maganar. "Ba zan jima ba, yanzu zan zo". Ya faɗa cike da san ya tafi. Bata san sake jefa mashi wata tambayar, dan tasan halinsa sam bai cika san tambaya ba, tana kaucewa abin da baya so, sai kawai ta amsa da okey tare da komawa ta zauna suka fara ciye ciyensu ita da Pretty. After some minutes. Hannunsa ɗauke da wasu itatuwa ya dawo wajen, wuta ya zo ya kunna masu sannan ya matsa gaba ya ɗauro alwalarsa a wajen ruwan gudun dake kusa da su. Sallar mangariba da isha'i ya haɗa dikka ya yi, saboda matafiyi ne shi wanda babu abin ganin lokacin a tattare da shi, hasalima bai iya gane gabas ba sai dai ya kintata ya yi sallar kawai. Bayan ya idar ya yi addu'a sosai, dik Zunaira tana ta aikin kallan motsinsa, a yanzu basa iya ganin face ɗin juna saboda duhu, sai sun matsa kusa da wutar da ya kunna suke iya ganin juna. Bayan ya kammala ya matsa kusa da wutar ya zauna tare da lankwashe kafafunsa yana kara wasu itatuwa a ciki dan wutar ta cigaba da ci har wayewan gari kada ta mutu. Auta and pretty kuma suka tashi suka gabatar da sallar isha'i bayan sun gama cin abin da suka ga zasu iya ci. Shiru ya zauna yana tinanin irin kalubalen da zai fuskanta a kan soyayyarta, sai dai ya kudurta a ransa ko mutuwa zai yi ba zai janye ba tin da ya rigada ya sanar da ita cewa yana santa, sun kuma yi wa juna alkawarin ba gudu ba ja da baya. Ya zurfafa cikin tinanin da yake yi, kamar daga sama ya ji saukar hannayenta a saman shoulders ɗinsa, ta zarosu ta gabansa ita kuma tana ta bayansa, tana durkushen a saman gwiwowinta, ta ɗan manna kirjinta da bayansa kaɗan, hannunta na rike da fresh apple jajir mai kyau da zaƙi. Saitin ɗan bakinsa ta kawo mashi apple ɗin, a daidai saitin kunnensa ta tsayar da laɓɓanta, silent talk ta yi wajen furta mashi............ "My Hero kai fa baka ci komai ba, ni kwata kwata ban ga kaci wani abin na fa, ka karɓi wannan ka ci". Ta kai karshen maganar tare da kara matsar mashi da apple ɗin a dab bakinsa. Rasa me zai yi ya yi, ya rasa a wace duniya yake, ya rasa a wani matsayi zai ajiye kansa, yau shi ne tare da abar da ya fi kauna sama da komai nasa, kuma ga su a ƙeɓaɓɓen waje, har da kulawa na musamman take bashi, bayan Abbonsa babu wanda ya taɓa damuwa da ya ci abinci ko bai ci ba sai ita, kai ba zai taɓa manta wannan rana ba a rayuwarsa. Alhamdulillah ya rinƙa nanatawa a cikin zuciyarsa, ya ƙasa iya buɗe bakinsa ya karɓi kyautarta a garesa. Ƙasa sosai ta yi da murya, kamar mai raɗa ta sake cewa. "My Hero ba zaka ci kyautar da ya fito daga hannu na bane? Ko kuma sai na yi maka kuka ne? Da kaina fa zan baka". Oh my god, wani irin nisawa ya yi, ajiyar zuciya mai daɗin gaske da bai taɓa sauke irinta ba ya sauke, a hankali ya buɗe ɗan bakinsa ta sanya mashi apple ɗin, kaɗan ya gutsira yana jin tamkar babu abin da ya kai wannan apple ɗin daɗi a duniya....... Oh soyayya ruwan zuma. Sosai ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta na ganin ya gutsira, har ajiyar zuciya ta sauke, wannan ajiyar zuciya da ta sauke ji ya yi tamkar ta kara lulluɓe zuciyarsa da bargon farinciki ne. Ita dai Pretty sai sanya kananan itatuwa take ta yi a cikin wuta, sam hankalinta baya ma kansu baiwar Allah. Sake matsar mashi da apple ɗin kusa da bakinsa ta yi, dan farinciki haka ya rinƙa gutsira yana ci har ya cinye ba tare da ya sani ba, cike da zumuɗi ta zame hannayenta daga shoulders ɗinsa, tana ƙoƙarin barin wajen tana faɗin. "Bari in karo maka wani my Hero". A hanzarce ya ɗan juyo ya rike hannunta a cikin nasa. "Please ba sai kin karo mun ba, wanda kika bani ya wadatar, na ƙoshi sosai saboda albarkan dake tattare da hannunki". Ƙayatattcen murmushi ta sakar mashi, wutar tana haskasu gwanin ban sha'awa, bata yi musu da shi ba ta yi na'am da zancensa, sannan ya saketa. A hankali ta dawo gefen damansa ta zauna suna fuskantar wutar, kanta ta kwanto da shi a saman damatsan hannunsa tare da kamo hannunsa guda ɗaya. Sillent talk ya yi wajen ce mata. "Baki jin tsoron dajin nan?"........ Ƙara yin lamo a jikin hannun nasa ta yi. "Ni da nike tare da kai kuma my Hero tsoron me zan ji?". Ɗayan hannunsa ya kai saman hannunta da ta riƙo nasa. "Kina ƙara mun kwarin gwiwa sosai my Hoonaira". A ɗan shagwaɓe ta yi magana ƙasa kasa ta yadda ita kanta tasan ba zai ji me ta faɗa ba. "Ban ji me kika ce ba". Ya tambaya yana ɗan juyo da face ɗinsa saitin tata, irin mutum ya juyo ya kalli gefen shoulder ɗinsa haka. Sake yin maganar ƙasa ƙasa sosai ta yi, still dai bai ji me ta ce ba, hakan yasa ya ɗan kwanto da kansa kusa da nata kaɗan ya kara tambayar me ta ce. "Barci nike ji kuma san yi nike ji". Shi ne abin da ta faɗa. Tabbas akwai sanyi sosai a wajen, shiyasa ma ya kunna masu wannan wutar dan wajen ya ɗan ɗumama. "Tashi in ɗauko maki rigan sanyina na ɗazun ko?". ............ Make kafaɗa ta yi. "Ni dai a'a, ba zan iya tashi ba". Kallan Pretty dake ta doka hamma ya yi, da yake ita ta saba yin barci da wuri baiwar Allah, har idanunta sun yi ja alamar barci. "Pretty ɗauko mun rigan sanyina a wajen kayanmu, daga nan sai ki je ki kwanta dan naga kamar barci kike ji"............ Da okey ta amsa mashi tare da miƙewa ta isa ga kayansu. "ko kema zaki je wajen da na tanada maku ki kwanta ne?". Ya jefa mata tambaya yana zame hannunsa daga kan nata....... "A'a ni dai zan kwanta kusa da wutar nan dan in rage jin sanyi". .......... Jinjina kansa ya yi alamar to. Kawo mashi rigan sanyin Pretty ta yi, karɓa ya yi ta wuce ya je ya kwanta a wajen nasu tana yi masu good night. Cikin sanyin murya haɗe da tausasawa da lallaɓawa ya ce. "Ɗaga in saka maki rigan kin ji?". Jiki dik kasalar barci ta ɗan ɗaga shi tana turo baki. Sorry ya ce mata kafin ya ware rigar ya sanya mata, sannan ta sanya shi dole ya miƙe mata kafafunsa ta tada kai da laps ɗinsa tana daka hamma, lamo ta kwanta a laps ɗin nasa, wutan yana ɗan ratsata kafin wani ɗan lokaci barci mai daɗin gaske ya yi awon gaba da ita. Shiru ya zuba mata idanu yana ta kallan face ɗinta, ya ƙasa zare kallonsa daga kanta, kamar yadda yaga rana haka ya ga dare. Tana kwance a kafarsa yana ta kallan face ɗinta har dare ya tsala, Pretty ta jima da yin barci abinta. Asuban fari Auta ta farka, ta sha madarar mamakin yadda ta kwnata daren jiya ta barshi haka ta wayi gari ta same shi, cike da mamaki da tausayawa ta tambaye shi bai yi barci bane?. Kai ya gyaɗa mata almar e bai yi ba. "Meyasa to?". Ta jefa mashi tambayar tana kallansa. "Tashi mu je mu yi sallah mu cigaba da tafiya, dan mu isa gida da wuri rana na ganin ido". Shi ne abin da ya faɗa a maimakon ya bata amsar tambayarta a garesa. "Ni sai ka bani amsata zan tashi". Kamar zata yi kuka ta faɗa. "Kin manta jiya na faɗa maki cewa bana barcin dare? Kin kanta na faɗa maki gadin gimbiyata kawai nike yi ne?"............... Tina maganganunsu na jiya ta yi, abin ya kara bata mamaki, a tinaninta ya faɗa mata hakanne kawai saboda soyayya, bata san dik kalamansa hakikanin gaskiya ce wanda babu mix ba, baya faɗar kalamai dan jin daɗin soyayya ko kuma daɗin bakinsa, dikkan abubuwan da yake faɗa gaskiya ne kuma yana iya aikata fiye da hakan a kanta. Sai yanzu ta kara tabbatarwa da kanta lallai ta yi babban sa'ar da samun irinsa abu ne wanda zai bada wahala, lallai Hoorain one in million ne. "Tashi to tin da na baki amsa". Ajiyar zuciya ta sauke, cikin sanyin murya ta ce. "Ina kwana". Da alama zuciyarta ta yi sanyi dayawa, dan ta fara yarda son da take yi mashi wasa ne a kan wanda yake yi mata. "Sai da aka gama jera mun tambayiyin ne za'a ce mun ina kwana?". Cikin zolaya ya yi maganar. Siririn murmushi ta saki tana sanya tafukan hannayenta ta rufe face ɗinta. Wani irin daɗi ya ji na ganin murmushinta, lallai wannan safiya tasa ta fara da kyawawan abubuwa. Ta tafi da tinaninsa har ya sanya hannunsa ya kamo hannayenta da ta rufe, ya buɗe dan ya ji daɗin ganin kyakkyawan murmushinta, yarinya mai kyan gani, dik wanda ya ganta sai ya ji daɗi a ransa. Yunkurawa ta yi da sauri ta miƙe tana cigaba da murmushi. Zama ta yi kusa da shi suna fuskantar juna, har lokacin wutar bai mutu ba, a hankali ya saki hannayenta da ya rike yana kallan gefe. "My Hero". Ta ambaci sunansa kallanta a kansa. Kin ɗagowa su haɗa ido ya yi, amma ya amsa kiran. "Idan har da gaske kana sona, abu ɗaya zaka mun in tabbatar da hakan". Jinjina mata kai ya yi alamar to ba tare da ya yi magana ko ya yi wani motsi ba. "Kalli cikin idona sai mu yi magana"......... Kamar ba zai yi hakan ba, sai kuma ya daure ya ɗago da kallansa a kanta. Ya subhanallah, sarkafe juna da kallon kauna mai tafiya da imani suka yi, gabaɗayansu sun lula wata duniya, dik sun kasa yin magana. Sun macewa juna a kallo, ita kanta ganin cikin kwanciyar idanunsa yasa ta rasa nitsuwarta bare kuma shi. Sai da suka ɗauki good 5 mins a haka, sannan ya yi ta mazan lumshe idanunsa yana jin wani abu na mashi yawo daga tsakiyar kansa izuwa tafin ƙafarsa. Cool voice ɗinta ya ji a kunnuwansa tana faɗin. "Na yi fatan mu kasance ma'aurata da wuri". Waro idanunsa a hankali ya yi ya kalleta. "Na fiki yin wannan fata my Hoonaira". Nisawa ta yi kafin ta ce. "Yanzu misali a ce yau daddy ya ce ya mallaka maka ni ya zaka ji?"........... Wani irin lumshe idanunsa cikin salo mai jan hankali ya yi tare da yunkurawa ya miƙe tsaye. Binsa da kallo ta yi. Hannu ya sanya a cikin sumar kansa, a hankali ya ɗan watsa gashin nasa haɗe da ɗan ciza laɓɓansa kaɗan, wani irin nisawa ya yi ya ƙasa magana. "My Hero lafiya kuwa?". Ta yi maganar tare da miƙewa tsaye ita ma........ Kai kawai ya girgiza mata, ya ƙasa magana, wato baki ya yi kaɗan wajen zayyana irin farincikin da zai shiga dik ranar da aka mallaka mashi ita, wow abin ba'a magana, soyayyarsu soyayya ce kafun Allah, ba aba bace da aka ginata yau ko jiya, shekaru ake magana, zuƙatansu sun narkewa juna dayawa da jimawa, a yadda suke ji zasu iya aikata komai a kan junansu. Hannunta ya riƙo cikin nasa, wajen ruwan da suka yi alwala daren jiya suka nufa. Sai da ya duƙa gaban ruwan zai fara taɓa ruwan ne ya yi karfin halin cewa. "Ki dai'na yi mun irin waɗan nan tambayoyi, saboda baki ba zai iya faɗar yadda girmanki yake a rai'na ba, watarana zaki iya sanya zuciyata ta aikata wani abin da ya saɓawa shari'a idan kina irin waɗan nan tambayoyi". Jinjina mashi kai ta yi tare da duƙawa ita ma dan ta ɗauro alwala, kamar zai ce mata tana bukatar yin tsarki kafin alwala, sai kuma ya yi shiru saboda kada ta yi mashi wata mummunar fassara, yasan halinta sarai. Yana ganinta ta yi alwala, shi kuma ya tsaya bai yi ba, har ta gama ta miƙe, baya kaɗan ta ɗan ja ta tsaya wai tana jiransa, ganin hakan yasa ya miƙe tsaye, cikin sanyin murya ya ce. "Jeki ki tashi Pretty, sannan ki yi sallarki ina zuwa"........ Bata yi mashi musu ba ta wuce tana waigosa, shi ma kallanta yake yi har ta kure mashi. Sannan ya matsa daga in da yake zuwa gaba dan ya yi tsarki. Zaune ya isko Auta kusa da wuta, ita kuma Pretty tana sallah. Matsawa ya yi kusa da ita, a gabanta ya zube gwiwowinsa, cike da so da kauna ya miƙo mata flowers da ya ciro mata yana kallan face ɗinta............... Ai tsabar farincikin bata san lokacin da ta saki ɗan kara mara sauti sosai ba. Hannunta har yana kerma wajen sanyawa ta karɓi flowers ɗin, jikinsa ta faɗo unexpect tana murmushi. Rungumeta ya yi yana jin daɗin ta yi farinciki. A hankali ta ɗago kanta daga saman kirjinsa, sumbatar flowers ɗin ta yi, lokaci guda ya ji tamkar kumatunsa ta sumbata, har wani ajiyar zuciya ya sauke, shi kaɗai yasan me yake ji a ransa, cikin ƙanƙanin lokaci ya ji ya kwaɗaitu da san sumbatarta. "My Hero nagode sosai, farkon kyautarka a gareni, ba zan taɓa manta wannan rana ba, ina sanka fiye da yadda ma'aunin tunanin mutum zai iya aunawa". Tana magana idanunta suna ciccikowa da kwallah. Hannu ya kai saitin gemunta, hawayenta da suka cika idanunta ne suka zubo har kan tafin hannunsa, nisawa ya yi, calmly ya furta. "Ki dai'na mun asaran hawayena, please my Hoonaira, kada ki sake bari su zuba kin ji?". Kai kawai ta gyaɗa mashi, Allah mai juya dare ya zama rana, rana ya zama dare, wai yau ita ce tare da masoyinta a nan suke zuba soyayya wa junansu?. Pretty ce ta katsesu da cewa. "Ina jin yunwa sosai Zunaira". Zame hannunsa Hoorain ya yi daga kusa da ita, sannan ya miƙe yana faɗin. "Ku tashi mu fara tafiya, a gaba zan sama maku abin da za ku ci". Ya kai karshen maganar tare da nufar in da ya ɗaure dokinsa daren jiya. Kwantota ya yi ya zo ya ɗaukesu da dik abubuwansu, a yanzu sai ya sanya Pretty a baya Auta a gaba, shi a tsakiyarsu kenan, saboda a jiya da ya sanyasu dikka a gaba sun haifar mashi da matsala ta rashin gudu sosai, dole ya rabasu idan yana san su yi gudu sosai su samu damar isa da wuri kafin rana ta faɗi. Daga haka suka kutsa cikin daji da gudun gaske........ To Allah ya tsare hanya our love birds. 🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥 After some days. A waɗan nan ƴan kwanaki da suka wuce abubuwa sun faru wanda suka haɗa da ganin Khadijah da su uncle Jahiz suka je, and jiya da daddare Khadijah ɗin ta farfaɗo baiwar Allah, amma ta ji azaba ba karya, dan ma ta samu kulawar likitoci sosai ne yasa, sai dai bata magana dik da ta farfaɗo ɗin ma. Time da uncle Jahiz ya ganta sai da ya ɗan razana kaɗan, dan a fili ya furta tabbas ya taɓa kallan wannan fuska, sai dai ya manta a ina ne. (Anya ba raina mana hankali yake san yi ba kuwa?🤔 Shi da yake Tunisia a ina ya taɓa ganinta ita da take Nigeria bata taɓa fita ko'ina ba, ko Abuja bata taɓa zuwa ba sai sanadin Hauwa bala'i, to aina ya taɓa ganinta? Anya zarginmu a kansa ba gaskiya bane kuwa? Mu je dai zuwa, lokaci ne zai warware mana komai.) Abu na biyu da suka faru kuma shi ne su commander Zafar sun ci nasara a yakin da suka tafi, sai dai kuma da kyar suka sha, saboda commander mayakan Queen Zarina wato mai kama da Hoorain namu ya kawo masu babban barazanar da sai da dangerous warriors suka girgiza, sun kasa iya taɓa jikinsa, saboda suna tsoron su taɓa jikinsa a matsayinsa na assistant commandernsu. Shi kansa commander Zafar ƙasa taɓa shi ya yi saboda kowa ya san yana kaunan ɗansa over. In short sai da commander yaga da gaske wannan zai iya hallaka shi idan shi bai kashe shi ba to shi zai kashe shi, sannan ne fa ya bawa warriors ɗinsu umarni da su kashe shi koda Hoorain ɗin ne tin da kashesu shi ma yake ƙoƙarin yi. Sosai mayakan suka yi mamakin jin furucin commander, Allah sarki basu lura ƙoƙarin kashe commander ɗin shi ma yake yi ba, da ciwo mai kama da ciwon zuciya commander ya dawo Kingdom of power, Allah sarki, ya ƙasa yarda Hoorain ne, sannan ya gargaɗi mayakansu da kada su yarda su sanar da King Zuhair abin da ya faru, su rufa mashi asiri su bashi lokacin zai binciko gaskiya, dan ya tabbatar ba Hoorain ɗinsa bane, idan kuma shi ne to tabbas akwai wani abin da aka yi mashi, ba haka kawai ba. To tin da suka dawo wannan yaki commander yake kwance yana jinya, ya kasa samun kwarin zuciyar iya ɗaukar wannan balai'n bare har ya iya tashi ya binciko gaskiya, sai zargi zuciyarsa take ɗarsa mashi, ya yi tinani ya fi dubu a kan hakan, sai faɗi yake yi dama kenan da Hoorain ya gudu daga nan bayan Zarina ya koma ne ko yaya?...... MY PEOPLE'S GASKIYA ABIN DA ƊAURE KAI, ALKALAMIN PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA CE KAWAI ZAI IYA WARWARE MAKU WANNAN CAKWAKIYA, KU DAI MU JE ZUWA. Abu na uku da ya faru a kingdom of power kuma shi diransu Omaid and Obaid, sun samu hutun karshen shekara, azumi ya kawo kai, sun samu hutun dawowa gida su yi azumi, shi kuma guyson yanzu result ɗinsu ya fito har ya yi registration, yanzu guyson namu zai shiga hundred level, ya zama babban yaro, yanzu jami'a yake, sai sakalci da kukan ciwo kam har yanzu tana nan. A ɓangaren su Mammie kuwa suna can suna aikin kullace kullacensu, sai shirya ta yadda zasu taimakawa Fanan suke yi, ita ma Fanan yanzu ta bi bayansu, a kan soyayyar Jaish ta yarda dik abin da suka sanyata zata iya aikatawa. Babbar magana, mu je zuwa. Shi kuwa King, yanzu hankalinsa yana can yana kan neman Auta, tin yana ganin abin kamar da sauki har ya fara ganin abin fa ya zarce tinani, ya baza mayakansa a ko'ina nemanta ake yi, wasu har cikin dajin da su Hoorain suke suka shiga, amma basu samu haɗuwa da su ba. Mahnoor and Mahreen suna ta shan gyara, wa'adin da momma ta ɗibawa King gobe zai cika In Sha Allah, yau sai busy momma take yi tana shirya masu oder kayayyaki na gani na faɗa wanda zasu tashi kai. Sarina dai dik balai'nta bata samu damar ganin Mahnoor ba, dole ta hakura suna jiran gobe a fito da ita su ga wace tsiya ce. Wannan shi ne kaɗan daga cikin abubuwan da suka faru a ƴan kwanaki da suka shuɗe, to mu je zuwa. •••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 7:30am. Agogon kingdom of power mai tsananin kara ta buga. Sanye uncle Jahiz yake cikin shiga ta ƴan kwallo na team ɗinsu, ya ɗaura jacket a kan kayan nasa saboda sanyi da ake yi, cikin nitsuwa yake takowa, daga part ɗin Akka ya fito izuwa part ɗin mama wajen Aneesa kenan. Yanzu likitoci asibin kingdom suka yi mashi waya a kan Khadijah ta farfaɗo daren jiya, dan haka suna bukatar na kusa da ita wanda ta sani ya zo dan suka yanayin kwakwalwarta, ta ki yin magana, ta kuma ki yin motsi ƙwaƙƙwara, to shi suke buƙatar Zee, idan ta zo kila Khadijah zata yi magana ko wani abin da zai sa su fahimci tana cikin hayyacinta kuma aikinsu ya yi kyau. Wannan dalilin yasa ya fito da safiyar nan zai je wajen Zee su tafi hospital ɗin, ga shi cikin satin nan yake san komawa Brazil, dan suna da wasa, hutun da ya ɗauka ta kusa karewa, zai je ya shirsshirta. Bakinsa ɗauke da sallama ya afka cikin ɗakin Aneesa, bai yi tinanin sun tashi daga barci bama shiyasa ya afka kawai. Wani irin birki ya ja lokacin da idanunsa suka sauka a kan Zee dake tsaye gaban mirrorn Aneesa tana shafa mai, daga ita sai towel a ɗaure a kirji, ita kuma Aneesa ta fita izuwa kaiwa mummyn Chuchu labari...... KO LABARIN ME ZATA KAI MATA KUMA?🤔 MU JE ZUWA ZA DAI MU JI. Zee har ta goge ta yi kyau, sai dai ko kaɗan bata jin daɗin zama da su Aneesa, suna tsangwamanta, bare ma Sarina da in dai ta shigo sai ta ci mata mutuncin da kare ma ba zai sinsina ba, amma tana hakuri tana dannewa dan gidansu ta zo, kuma ko ba komai sun taimaka mata, ita burinta Khadijah ta samu lafita su koma Nigeria abinsu. Da yake uncle Jahiz ɗan duniya ne girma cikin turawa, sai ya fara binta da kallo tun daga kafafunta har izuwa kirjinta, sai da ya ɗan tsai da idanunsa a kan kirjinta ma kafin ya kai kallansa a kan face ɗinta. Ta yi ƙasa da kai ta takure jikinta waje guda, tana jin kunyar motsawa daga in da take, jin sallamarsa dama yasa ta juyo, ta yi danasanin ɗaura towel bata sanya hijabi kamar yadda take yi a gida ba, kuma saboda taga babu wanda yake shigowa ɗakin ne yasa bata saka hijabin ba. Ko kaɗan babu kunya a idanunsa ya sake dawo da kallansa a kan kirjinta da suke cike fam, a hankali ya kalli santala santalan cinyoyinta da yanzu suka murje suka yi kyau saboda wanka da sabulai masu rai da lafiya na Aneesa da take yi. Ya kasa motsawa ya kuma kasa kawar da kallonsa daga kanta, sai ma ƙara kurawa kirjinta ido ya yi, ita kuma ta kasa gudu ta bar wajen, to me kuke tinani zai faru? Shi dai uncle Jahiz ba kunya ne da shi ba, ni dai na tafi shan maltina idan na dawo zan ga shi da ita waye zai ɗagawa ɗan uwa kafa, shin zai hakura ya ja da baya ya koma ne? Ko kuma ita zata danne zuciya ta gudu? Su dai suka sani, ni na yi ta nan...............🥱 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Cigaba da karewa albarkatun jikinta kallo yayi, kwata kwata babu alamar zai ja da baya ko ya kawar da kansa, ta gaji da tsayuwa taga alamar bafa dai'na kallanta zai yi ba, dan haka sai ta daure ta fara takawa a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi dressing room na Aneesa. Dik wani step ɗinta ɗaya a kan idanunsa take yi har ta kurewa ganinsa, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan dukar da kansa ƙasa, shi kaɗai ya fara ayyana yadda kyanta yake a cikin ransa, saman sofa ya zauna yana kara jinjina kyan abin da ya gani, to da alama dai ransa ya biya. Shi da bashi da fara'a ko kaɗan, sai ga shi yau ya sanya hannu saman arabs hairnsa, yana ɗan watsa gashin yana murmushi kamar wani sabon kamu......... My people's ni wai ba uncle Jahiz ba ne ya ce ba zai taɓa san mace ba sai ya kai 40 years? Sannan har da wani ce mana babu abin da zai yi da yar yarinya, shi mace daga mai 25 years ya yi sama yake so? Anyi haka ko ba'ayi ba? To inaruwansa da Zee ɗinmu? Zee dai 17 years take da shi, ko Khadijah bata kai 20 ba bare Zee bare kuma a kai ga 25 years, me uncle Jahiz yake nufi? Kada ma ya kuskura ya fara ce mana ya janye kalamansa, dan ba zamu lamunta ba, amma guy ɗin nan ya sha damu dama, to wai an faɗa mashi mata wasa ne?......…....🤔 Shiri Zee ta yi cikin abaya again, kunsan su Aneesa kaso 80 cikin ɗari na kayansu abayas ne, saura kaso 20 ɗin kuma irinsu riga da wando, riga da sket and gown ne. Abaya mai kyau da tsada launin purple color ta sanya, ta yi rolling mayafin a kanta, sai kuma ta ƙasa fitowa waje, saboda bata san haɗa idanu da shi, zuciyarta ta ja baya matuƙa da shi, dama kun san halin Zee ai, yanzu ma saboda Khadijah ta samu lafiya yasa ta yi sanyi take jure komai da ake yi mata, banda haka ai wlh ba sarauta ba, ko uban me uncle Jahiz yake ji da shi bai isa ya karewa albarkatun jikinta kallo haka ba. A yanzu haka zuciyarta ta raya mata uncle Jahiz ɗan iska ne, kada ta yarda da shi ya je ya cuceta ya yi mata ciki kamar Khadijah, wannan shi ne babban dalilin da zuciyarta ya rike yasa ta yi baya sosai da shi, ta ji bata san sake haɗa inuwa da shi, amma kuma tana san ganin Khadija, kuma kun san dole sai ta hannunsa zata samu damar ganinta. Ta kai 30 mins da kammala shiri, amma ta samu waje saman ɗaya daga cikin drawers dake cikin ta yi zamanta tana tinanin mafita a gareta, dan wlh bata ga abin da zai sa ta sake bari ya kalli surar jikinta har haka ba. Shi kuwa zama ya yi yana jiranta, tunanin kyan surarta da kwaɗaituwa da shi yasa bai ga tsawon lokacin da ta ɗauka bata fito ba, sai yake ganin kamar yanzu ta shige. Sai da suka kara wani 20 mins a kan wancan 30, nan ma sai da yaga kiran Dr sannan ya miƙe tsaye ya nufi dressing room ɗin cike da mamakin me ya hanata fitowa? Shi bai san cewa mu ƴan Nigeria muna da alkunya ba, dan shi bashi da shi sai yaga kamar kowa ma bashi da, a'a mu Nigerians muna da shi sosaima. Ya sha madarar mamaki na ganinta zaune shiru ta buga uban tagumi, tinanin Khadijah da ta afka yasa bata ji shigowarsa bama, sai jin sautin muryarsa ta yi yana faɗin. "Zee lafiya kika zauna a nan?". A ɗan razane ta ɗago ta kallesa. Kallo ɗaya ta yi mashi ta yi saurin kawar da kai, ta tsani maza dama idan baku manta ba, da shi kaɗai ta ɗan saki jiki ashe shi ma ɗan iska ne, wani tsanarsa ce ta ratsa zuciyarta, sai ta ji kamar ta gudu ta bar gidan, amma ina zata je to idan ta gudu?. Kanta a ƙasa ta amsa mashi da babu komai. Ko kaɗan bai kawo aransa da wata matsala ba, dan shi yana ganin ai normal ne kallan da ya yi mata. "To tashi muje Dr na jiranmu". Ya faɗa idanunsa a kan kirjinta dik da ta sanya kaya. Da yake bata ma san fita zasu yi ba sai ta ji zancen wani irin, a ranta ta furta yanzu haka zata jera da wannan ɗan iskan? Sannan su shiga mota ɗaya a gidan baya, bayan haka su je hospital? Wlh ba dan Khadijah ba bata ga abin da zai sa ta sake ɗaga idanu ta kalli mutumin nan har ta jera a tare da shi ba. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufo shi, a maimakon ya wuce gaba sai ya ce mata ta yi gaba zai rufa mata baya, aikuwa nan fa ta ce babu wannan magana, kar ta fito ta ce mashi ita a'a sai dai ya wuce gaba ko ta fasa zuwa ta hakura da ganin Khadijah ɗin. Jin hakan yasa bai yi mamaki ba ya wuce gaba, da harara ta bishi tana jin kamar ta dallah mashi mari amma babu dama, zai wani ce ta wuce gaba dan ya ji daɗin kalle mata baya tana tafiya, to wlh ba zata yiwu ba, ta faɗa a cikin ranta tana harararsa. Sai da ma ya ɗan yi nisa sannan ta rufa mashi baya. Ko da suka shiga mota taki ɗagowa ta kalli in da yake, shi kuwa a da idan sun shiga mota latse latsen wayarsa yake yi baya wani kallanta, yau kuwa zura wayar a aljihunsa ya yi yana cigaba da kare mata kallo da kyau kamar wanda ya samu tv. Dannewa ta yi kamar zata yi kuka, amma haka ta hakura har suka isa hospital ɗin. Kai tsaye ɗakin da Khadijah take suka nufa, special room ne da aka ware mata ita kaɗai dan kula da ita sosai, a gaskiya ba karya ta samu kulawar da ta dace matuƙa. Tana kwance shiru idanunta biyu tana kallan sama, da yake ta yi ta shan drip sai bata wani rame ba, har wani haske ta kara yi sosai, ta kusa kamo Zee hasken fata, jikinta ya yi fresh sosai. Tana ɗaura idanunta a kan su ta wani zabura ta miƙe zaune, idanunta a kan uncle Jahiz ba a kan Zee ba, ita kuwa Zee tana ganin ta farfaɗo ta tafi da gudu ta rungumeta tana ambatar sunanta. Tamkar ba Khadijah bace a wajen, ta kafe uncle Jahiz da kallo mai wuyar fassaruwa, lokaci guda kuma wasu zafafan hawaye suka fara wanke kata fuska. Hankali a tsakanin tashe ta furta. "Zee a ina kika samo wannan mutumin............". Sai kuma ta dakata da yin maganar, a hanzarce ta kai hannu ta fara goge hawayenta da suka fara zubowa, a take ta shanye kukan nata. Jin furucinta yasa Zee ta yi saurin raba jikinsu da juna, a tsananin matse da san jin kan zance Zee ta ce. "Khadijah kenan da gaske shi ne a jikin wancan hoton ko? Dama na ce maki shi ne kika ce ba shi bane, kullun sai na kalli hoton nan in kuma kallesa idan mun haɗu da shi, har yau ban taɓa ganin banbancinsa da na cikin hoton ba, amma kuma kin ki ki faɗa mun gaskiya". Da Hausa suke maganar, hakan yasa uncle Jahiz sam bai fahimci me suke faɗe ba. Murya a raunace, da alamar karyewar zuciya a tattare da ita, da kyar ta iya cewa. "Zee kada ki sake yin magana a kan wannan hoto kamar yadda na faɗa maki a baya, na faɗa maki ba shi bane ya tsaya a iya hakan!! Idan kuma ɓacin rai'na kike so to bismilla ki cigaba, and in kuma ban isa in yi maki magana bane nan ma ki cigaba kasa ki dai'na". Kalaman Khadijah sun taɓa zuciyarta, haka zalika wannan abin da ya faru yaja ta kara jin tsanar uncle Jahiz, lallai ba shakka a yanzu ta yarda Khadijah ta ɓoye mata babban al'amari fiye da wanda ya faru da ita abaya, tabbas akwai wata a ƙasa, wlh ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba uncle Jahiz ne a cikin wannan hoto, kuma tana kan bakarta babu gudu ba ja da baya. Tashin sense, wai wani irin ruɗanine wannan? Mekuke tinani? To dai ku kwantar da hankulanku, komai bala'in ruɗani da zaku shiga alkalamina zai warware maku gaskiya, zan zaƙulo maku meyake tsakanin uncle Jahiz da Khadijah and meyasa Zee ta ce shi ne a jikin hoton, shi kuma ya nuna kamar ba hakan bane? To mu dai je zuwa, lokaci ne zai warware mana. Saman chair dake kusa da bed ɗin ya zauna, a tinaninsa kukan da Khadijah take yi na murnar ganin Zee ne, dan ya ga ita ma Zee ɗin tana ruwan hawaye, sai ya zuba masu idanu yana kallansu. Massage ne ya shigo wayarsa, hakan yasa wayar ta ɗan yi ƴar ƙara. Zarota daga aljihunsa ya yi kallansa a kan Khadijah, shi dai yasan wlh ya taɓa kallan wannan fuska, kuma shi bai taɓa zuwa Nigeria ba sai wannan zuwan nasu, to a ina ya taɓa kallanta kenan? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsarta. "Ka samemu a meeting room". Shi ne sakon da ya shigo wayarsa, uncle Abbas ne kuma ya turo mashi wannan sako. Yana gama karantawa ya miƙe tsaye, cikin sanyin murya ya ce masu su kasance a tare da yamma zai dawo ya ɗauki Zee. Dik cikinsu babu wadda ta iya amsa mafi, basu da bakin magana. Bai wani damu ba yasa kai ya fice da sauri, yana fita Khadijah ta hau jerawa Zee tambayoyin a ina ta haɗu da wannan mutumi? Yadda take jera mata tambayoyi zaku fahimci hankalinta a tashe yake. "Khadijah ki faɗa mun gaskiya, dan girman Allah ki fitar da ni duhu, ni ban ce karya kike yi mun ba, amma dan Allah ki sanar dani abin da yake a ɓoye a karkashin zuciyarki, ki sanar dani alaƙar Jahiz da wannan hoto na cikin akwatinmu, dan girman Allah ki faɗa mun shi ne baban baby Junior?". Jin karshen zancen Zee yasa ta yi saurin kai hannunta saman cikinta, sai a lokacin tasan ma babu cikin a tattare da ita, a tsorace ta kai kallanta a kan Zee. "Zeezee ina cikina? Ina yake?". Zama a gefenta Zee ta yi, cikin nitsuwa ta fara kora mata bayani yadda komai ya wakana har suna tsinci kansu a wannan hospital ɗin. Shiru Khadijah ta yi tana jinjina al'amari na ubangiji, idan Allah ya tashi amsa addu'arka sai ya haɗaka da bayinsa da baka taɓa zatan haɗuwa da makamantansu ba, kuma su taimaka maka, lallai ne ba shakka addu'a bata faɗuwa ƙasa banza, sai dai jinkirin amsawa, wannan jinkirin kuma shi ake kira da jarabawa ta Ubangiji, Allah zai jarrabaka da jinkirin amshi yaga zaka cigaba da yarda da tawakkali da shi ne ko dai imaninka bai yi karfi ba?! Lallai ba shakka su Khadija sun yi hakuri, sun kuma ɗauki wannan jinkiri a matsayin jarabawa wanda a yanzu Allah yake basu sakamakon hakurinsu cikin ruwan sanyi, tun da momma ta ce sai an bi masu hakkinsu hakika ba makawa sun san ikon Allah ne da ya amsa addu'oin da suka jima suna yi. "Zee yanzu dai ki kyaleni na huta, idan na kara samun sauki sai mu yi magana". Cewar Khadijah. Na'am da hakan Zee ta yi suka cigaba da jinjina girman Allah. •••••••••••••••••••••••••🔥 A ɓangaren Jaish kuwa, gobe Monday zai koma bakin aikinsa, sai dai fa har yau kudurinsa na bincike a kan wannan ma'aikata da suka tsunduma shi cikin wahala yana nan a ransa, bai janye ba!!. After one day. Aneesa, Fanan, Chuchu ne suka shirya cikin uniform ɗinsu na school. Chuchu ta sha kukan rashin Auta, da farko har ta ce ita ba zata je school ɗin bama, daga baya da Yah Jawad ya rarrasheta sai ta shirya suka tafi, da kansa ya kaisu, sannan shi ma ya dawo ya shirya zuwa office. A tare da Jaish suka tafi kamar yadda suka saba. Sarina kuma bata da class,.tana guda. So gidan ya rage daga Sarina, uncle Jahiz, uncle Taheer, uncle Abbas, su momma, King, Guyson yana nan, su twins, sai Zee da suke asibiti. Aunty MieMie tana part ɗinta. •••••••••••••••••••• Momma da Mama Haulat ne zaune a bedroom na monma suna tattaunawa a kan irin dressing ɗin da yakamata su yi wa Mahnoor a lokacin da zasu kaita gaban su King. Mama Haulat ta kawo jerin kayayyaki na alfarma masu bala'in kyau da tsada da yakamata su shiryata a ciki domin kaita, momma tana dudduba hotunan kayan ne, dikka cikin waɗan da ta yi oder su daga Dubai ne, tun jiya aka kawo kayayyakin kusan mota guda. Mammie da Sarina kuwa, suna nasu shirin dan su zo part ɗin King su kalli Mahnoor, su kalli dame ta fi Fanan? Sun san cewa King ya ce nan da karfe 8 na safe dai'dai a kawo mashi ita ya ganta kafin ya fita fada, shi ne suma suke sauri dan su zo su ganta, saboda sun san idan King ya aminta da ita yadda momma ta kwallafa rai a kan sonta ba lallai su rinƙa samun damar ganinta ba, kunga in King ya aminta da ita zata koma part ɗin Jaish ne, to da ni da ku dai mun san dik rashin kunyar mai rashin kunya baya tinkarar part ɗin Jaish, bayan Auta da Guyson, King and Yah Jawad, sai momma da mama Haulat ne kawai suke iya shiga part ɗinsa, ko su Omaid basa kaunar dosar wajen, dan kun san dalili. So sun san tana shiga part ɗinsa ba zasu taɓa samun damar ganinta yadda yakamata ba. Uncle Jahiz, uncle Abbas, King, Akka su ne zaune a cikin parlon King suna jiran momma, King ya buƙaci da Mummyn Chuchu da Mama and Mammie dik su zo. Akka ta samu lafiya yanzu, jikin ya yi kwari, sai dai fa masifa ya karu, yaseen kana taɓota kaɗan yanzu ka shiga talatin, sauke haushin rashin Spender zata yi a kanku. To King ya bata labarin Jaish ya yi aure, shi ne ta ce wlh bata yarda ba, dan haka dole a warware wannan aure, da kyar autanta uncle Jahiz ya shawo kanta a kan ta yarda ta kalli Mahnoor ɗin ko sau ɗaya ne, taga idan bata dace da Jaish ba sai a warware auren, to shi ne dalilin hallararta a parlourn King, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya cikin shiga ta alfarma, eh mana uwa ga manyan kai ba, ta dake cikin alkyabbar na girma, sai wani kafafa take yi, har da cewa ko ta ga Mahnoor fa ita ba zata taɓa yarda da wannan aure ba, uncle Jahiz da yake yana bin bayan Momma dan tana rufa mashi asiri bakinsu ɗaya, sai ya ce da Akka e dai su bari Mahnoor ɗin ta zo aganta. Wlh uncle Jahiz da momma bakinsu ɗaya, ita ke goya mashi baya, harta batun tafiyarsa kwallan kafa ita ta tsaya mashi, da Akka taki yarda, amma da momma tasa baki sai suka fi karfin Akka dole ta yarda, so in short dik abin da ya ɗebo rufewa suke ita da shi abinsu, shiyasa kuka ga suna mugu mugun shiri da juna, ya fi santa fiye da sauran matan King. Saida momma ta tsaya ta hantse ta zaɓawa Mahnoor wani haɗaɗɗen gown mai kama da weeding gown, daga ta sama daidai da ita zuwa waist ɗinta, kasa ya yi bala'in buɗewa kamar umbrella, rigar launin pink ne da ratsin golden, ga wasu ƙayatattun duwasun alfarma masu kyalli da suke walwali suka kara ƙawata kayan rigar, sannan ga wasu manyan zanen flowers a jikin kayan, rigar ta haɗu, ga tsada kamar me. Wasu half cover masu kwalliya da duwatsun lu'ulu'u momma ta zaɓa mata, takalmar launin golden kalar kwalliyar jikin rigar, ai ku daga jin kwalliyar dutse mai daraja wato lu'ulu'u a jikin takalmar kun san kuɗinsu ya wuci baki ya faɗa. Dankareran alkyabbar launin golden kalar takalmarta momma ta fidda mata, alkyabba ce wanda King Badeen wato mahaifin momma ɗin ya saya mata a lokacin da za'a kai ta gaban King Abdul Malik mahaifin King Zuhair kenan, a lokacin ya saya mata su guda shidda, to da guda ɗaya ta yi amfani sauran biyar ɗin sunan sabbi gal, a lokacin da tasa wannan alkyabbar sai da kowa yasan e lallai ƴar the most powerful King ta fito, alkyabbar ce wanda ba'a samunta a ko'ina, kwalliyar jikinta da duwatsun lu'ulu'u aka yisu, haɗuwar alkyabbar baki ba zai iya faɗarsa ba. Mama Haulat sai da ta sha jinin jikinta jin cewa momma zata bawa Mahnoor wannan alkyabba mai dajara tasa, domin kuwa ita tasan darajar waɗan nan alkyabbars ɗin, momma kuwa dama matan ƴaƴanta ta ajiyewa, sai kuma Allah yasa tana kaunar Mahnoor ɗin, kunga kuwa fin haka ma zata iya yi mata. Dik jikin mama Haulat ya yi sanyi ganin kyautar momma ga Mahnoor, amma haka ta miƙe ta karɓi alkyabbar, nauyi sosai yake da shi, saboda duwasun lu'ulu'u da aka kawata kyalliyarsa da shi. Haka ta nufi waje da shi, kai tsaye ta je ta ɗauko kayanda momma ta zaɓa za'a haɗawa Mahnoor ɗin da su. Kai tsaye ɗakin gyara ta wuce da su. Momma ma wanka ta je ta yi ta shirya, sam babu faɗuwar gaba a tattare da ita a kan wannan matsala, domin ita ɗin macece mai jajircewa a lamuranta, bata san faɗuwa ba, tana da yakinin zata yi nasara. Su mummyn Chuchu dik sun hallara a parlourn King momma kawai ake jira, Sarina da shegen gulma har da wani zuwa ta zauna kusa da uncle Abbas, ta wani kwanto a jikinsa dik dan gulma, kamar da gaske haka take jinsa a ranta, kawai tsabar san kallan Mahnoor ne. One funny thing kuma shi ne yau sai ga Sarina da alkyabbar, saboda su King suna wajen, sai ta yi shigar mutunci, ni ko na ce ashe rashin kunyar tata ta karya ce ƴar ƙaniya. Karfe takwas yana bugawa dai'dai wani irin daddaɗar kamshin perfume mai kwantar da hankali ya fara dukan kofofin hancin kowa dake cikin parlourn King, turaruka masu tsadar gaske da shegen kamshi momma ta sa aka kawo mata, sai Allah yasan daga ina ta samo waɗan nan zafafa turarukan ta feshe sirikarta da shi. Tin su momma basu kai ga shigowa ba kamshin Mahnoor ya aiko masu sallama. Dikkansu sai da suka shaki kamshin suka ɗan lumshe idanu. Kowa ya fara rarraba idanu a kan hanyar shigowa, suna jiran suka ɓullowarta. Like wow lokacin da suka sako kafafunsu a cikin parlon, gabaɗaya kallo ne ya dawo kansu. Momma na ɗan rungume da Mahnoor ɗin suka shigo, suna takawa cikin natsuwa. Like wow tamkar wata tauraruwa haka Mahnoor ta haska, shigar kayan jikinta kawai suke kallah, Sarina alkyabbar kawai take kallah ma tukun nan, bata taɓa kallan irin wannan alkyabbar ba. Mummyn Chuchu ce ta yi saurin miƙewa ta taro momma, dik da basu san wacece momma ta riko ba, amma suna da haɗin kan taimakawa junansu a irin wannan yanayi. Gefen Mahnoor ta zo ta rungumo suka karisa da ita ciki. Mammie da tin da suka sako ƙafafunsu take ta faman leƙo fuskar Mahnoor tana san ganinta amma ba dama, dan alkyabbar ya yi mata yawa, hularsa ya fi kanta sosai, kunsan na faɗa maku na momma ce, dik da lokacin bikin momma ita ma da kaɗan ta fisu, amma dai ya yi mata yawa, hakan yasa hular alkyabbar ya sauko mata sosai, kuma ya haɗu da ta sunkuyar da kanta ƙasa, so ba'a iya ganin face ɗinta. Ita kuwa Sarina bata kai ga batun face ɗin amarya ba, tsadaddun kayan jikinta kawai take kallah, ta mutu da san alkyabbar, sai dai ba samu zata yi ba, dan na manyan mata ne wannan. A gaban King suka kawota, mama sai binsu da kallo take yi, bare Mammie da ta saki baki ta rasa abin faɗe kamar wata gaula. Dama King, uncle Abbas, uncle Jahiz a saman kujerar ɗaya suke zaune mai zaman mutun uku kenan, so a gabansu Mahnoor ta zube gwiwowinta kanta a ƙasa. King ne ya fara cewa Momma ta kaita wajen Akka tukun nan, su fara gaisawa da Akka. Ƙara ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya da kyau Akka ta yi, Queen mother zata yanke hukunci e mana, Akka tamu ta amana. Rikota mummyn Chuchu ta yi, ita ta kaita gaban Akka ta durkushe gwiwowinta. Sannan suka koma saman sofas ɗinsu suka zauna. Ɗago idanu Akka ta yi ta karewa su Momma kallo kamar na mintu biyu, sannan cike da izza ta ce. "Ina Zunaira?"........ Dum dum kirjin kowa dake cikin parlon ya buga except Mammie and Sarina, babu wanda ya taɓa expecting Akka zata nemi Auta a yanzu, nan fa parlon ya koma kallon kallo a tsakaninsu, an rasa mai iya bawa Akka amsa, dan sun san dik amsar da zasu bata ba zai taɓa gamsar da ita ba, babbar magana. Tsit parlourn ya yi tamkar uwar gulma ta yi cikin shega. Can dai uncle Jahiz ya yi ta mazan cewa. "Zunaira bata nan, sun koma school". Shiru Akka ta yi na ƴan mintuna da zasu kai uku haka, sannan ta ce. "Amma kun san a bisa al'ada Zunaira ce take da damar buɗe fuskar amaryar ko?".......... Jinjina mata kai suka yi alamar tabbas sun sani. Ita dai momma shap ta mance da wannan al'ada, tabbas tasan kanwar miji ce kawai zata buɗe fuskar mata, amma ta mance da yake an jima ba'ayi biki ba a kingdom ɗin. Kowa kuma yasan yadda bikin Jawad ya kasance cikin ruɗani da tashin hankali, so ba'ayi dik wasu al'adu nasu ba, dan haka ta mance da batun. Cike da isa Akka ta ce. "To shikenan tun da Zunaira bata nan sai ku mayar da amaryar taku sai lokacin da kuka shirya nuna mana fuskarta Zunaira ta zo ta buɗeta". Ta kai karshen maganar tare da yunkurawa zata miƙe. Innalilahi, kallon juna suka shiga yi, dikkansu tinanin ta yadda zasu dakatar da Akka ta yi hakuri ta ga Mahnoor suke yi. Uncle Jahiz ya fahimci momma ta shiga damuwa sosai a kan hakan, sai ya yi saurin riko hannun Akka dama suka kusa, cike da kalaman yaudara ya ce. "Haba Akka na, to menene banbancin Sarina da Zunaira? Ai dikkansu kannen Jaish ɗin ne, dan haka ko ba Zunaira Sarina tana nan, sai ta buɗe mana amaryar ai". Komawa Akka ta yi ta zauna, cike da isa ta juyo garesu domin ta sanar da su banbancin Zunaira da Sarina kwatsam idanunta suka sauka a kan uncle Abbas, aka ce idanun iyaye suna da kaifi a wajen da ake ƙoƙarin nunawa ƴaƴansu wani banbanci ko fifikon ko dai cin mutunci, ashe haka ne kuwa, ganin uncle Abbas yasa ta ji bata da kwarin gwiwar iya banbanta ƴaƴansa dana ɗan uwansa bayan kansu a haɗe yake. Bata san abin da zai kawo masu rabuwar kai, dan haka sai ta ce. "Gaskiya ne babu banbanci, ke Sarina zo ki buɗe fuskar matan yayanku"...... Dik wanda ya ji maganar Akka a cikin parlon nan yasan ba daga cikin zuciyarta wannan magana ta fito ba, dik sun fahimci ganin idanun iyayen Sarina a wajen yasa ta danne bata faɗi banbancinta da Auta ba. Wani irin takaici ne ya lulluɓe zuciyar Sarina, yanzu ace ita zata buɗe fuskar makiyarsu kishiyar Fanan? Gaskiya ko a iya haka an cuceta. Ita kuwa mammie ranta ne ya yi muguwar sosuwa, wato kenan ko a ina ƴaƴanta suna da banbanci da na King? Kenan ƴaƴanta ba koman komai bane ko a cikin dangi? Tin ba'a je ko'ina ba ana nuna masu su ba komai bane saboda ba babansu bane a kan mulki?. A cikin zuciyarta ta furta lallai yazame mata dole ta tsaya tsayin daka domin mulkin kingdom of power ya dawo tsaginsu, ina ba zai taɓa yiwuwa su zama bayin wasu ba, dole suma su ci gashin kansu, ace har kakarsu da ta haifi ubansu da King ɗin tana ƙoƙarin ware ƴaƴan King daban dan shi ne mai rike da mulki, gaskiya ba zata yuwu ba. Tabbas a nan Akka ta yi kuskure, kuma dayawa mata suna aikata irin wannan kuskure, sai kuga a gida an fi fifita ƴaƴan da ubansu ya fi abin duniya ko yake rike da wani muƙami, wannan babban kuskure ne wanda mun san kuskure ne amma muke aikatawa, Allah bai manta da talaka ba da ya barshi a talauci, haka zalika mai arziki ba wayau ya yi wa Allah ba da yasa ya bashi arzikin ba, dan haka ku daina irin wannan abin da kuke yi, wani ma zaku ga ko ubansu ne karami in dai yana da kuɗi to sai a nuna yafi kowa a gidan, ba'a yin haka wlh, hakan yana ɗarsa gaba da kiyayya a zukata, idan ba'a kiyaye ba sai shaiɗan ya shiga cikin lamurran, a haka ne sai ku ji ana cewa yaya ya kashe ƙaninsa ko ƙani ya kashe ƴaƴansa saboda abin duniya, dik ire iren wannan abin da kuke gani kamar ba matsala bane su suke hasasa waɗan nan abubuwa, dan Allah mu daina irin hakan ba abu bane mai kyau wlh, babu mai arzirtawa sai Allah, shi da yake talaka ai ba yin kansa bane, idan kuwa akwai mai bada arziki bayan Allah sai ku faɗa mun in ji!!!!!. Shi kansa uncle Abbas ransa ya ɗan sosu, amma ya danne ya nuna kamar bai fahimci in da Akka ta nufa ba, shi ma uncle Jahiz ya ji wani irin, amma dik suka danne. Miƙewa Sarina ta yi tana wani ɓata rai ta nufo Mahnoor. A kule ta sanya hannu ta janye hular alkyabbar baya kamar ma da mugunta ta yi abin. Dan yadda ta ja hular har sai da kan Mahnoor ya ɗan jinjiga. Mummyn Chuchu ce ta ce. "Sarina menene haka? Haka ake buɗe fuska?". Mammie ce ta tari numfashin mummy da cewa. "An kinsan bata iya bane, kinga ba'a taɓa biki a gidan nan da wayonsu ba sai bikin Jawad wanda shi kuma ba'a nemi kannensa na jini dan gudanar da komai ba, ina ga da yake amaryar yar gata ce kannenta ƴan gata akasa suka yi mata komai". Wani irin gabaɗaya parlourn suka ji na jin kalaman Mammie, mamaki abin ya bawa King, shi kuma uncle Jahiz ya fahimci kamar abin da Akka ta yi mata ne ya bakanta ranta, momma kam da tasan komai ko kallo basu isheta ba, maman Aneesa dik rashin son zaman lafiyarta da izzarta sai da kalaman mammie suka ɓata mata rai, ga shi dai ba shiri take yi da kishiyoyin nata ba, amma da aka gasawa mummy magana sai ta ji zafi. Dan haka sai izzar sarautar tata ta motsa. Cike da izza ta ce. "Ke saboda baki da hankali Umaima ɗin kike yi wa martani gatsau haka? Sa'arki ce ita? Shin dake ma ta yi magana ne? Ko kece Sarina? To maza ki bata hakuri kafin ranki ya yi mummunar ɓaci". Mama manya, mama harkar izza ba wasa, bata ɗaukar wargi ko ba a kanta ba. Momma ta ɗan yi mamakin faɗar da mama ta tarewa mummy, dan sun san juna kar tu kar. Ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya Akka ta kara yi, a kadarance ta ce. "Yauwa ku cigaba, ai na faɗa maku idan baku yi haka ba ba mata bane ku, ku cigaba da kyau". Shi dai uncle Jahiz dariya ma abin ya so bashi, wai yau mama ce ta da tare wa kishi faɗa, tab abin babba ne. Harara Mammie ta wurgawa Akka ba tare da kowa ya lura ba, a cikin ranta ta ce shegiyar tsohuwa idan baki yi hankali ba ni ce nan ajalinki. A fili kuma sai ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da cewa mummy. "Kiyi hakuri". Wato akwai iyashege a kingdom ɗin nan, wlh matan King sun san kan duniya. Jiki ba kwari Sarina ta bar gaban Akka ta koma mazauninta zuciyarta na tafasa, mammie ta ƙara jin ranta ya ɓaci, ta kara jin lallai dole ta mallaki kujerar kingdom of power ko ta halin yaya ne, da yanzu ita take da mulki a hannunta ai wane kaniyarsu su yi mata abin da suke yi mata ɗin nan. Akka kuwa hankalinta gabaɗaya ta mayar a kan Mahnoor, like wow, she was so surprised seen her beautiful face, abin ta bata yi expecting ba, ita kanta ta shaida Mahnoor kyakkyawa ce, ga gyaran da ta sha, skin ɗinta har wani yellow yellow ya yi yana wani glowing, wlh komai sanin da ka yi wa Mahnoor ba zaka taɓa ganeta a yanzu ba, dan ta haɗu iya haɗuwa, ko makiyi sai ya jinjinawa haɗuwar da ta yi sai dai idan ba zai faɗi gaskiya ba saboda kiyayya. Gabaɗaya su King zuba mata idanu suka yi suna kallanta, a cikin zuciyarsa King ya ce. Dama shi yasan dik abin da Rahilarh zata zaɓa ba abin yasarwa bane, lallai ba shakka wannan yarinya ta dace da jaish. Cike da matsuwa da san jin amsarsu momma ta ce. "Gwaggo (Akka) ya kuka ganta? Ta yi?". Shiru Akka ta yi tana cigaba da karewa Mahnoor kallo, baiwar Allah mai innocent face. Kun san Akka fa babu ɓoye ɓoye, dan haka sai ta ce. "Wannan yarinya anya ba zata iya zama green snake under green grass ba kuwa?". Ɗan zaro idanu suka yi gabaɗayansu, sai dai babu wanda ya iya tambayar Akka dalilinta. Cigaba ta yi da cewa. "Yanayin fuskarta ya nuna shiru shiru sosai ce ita, kun san masu irin wannan fuskar munafikai sun fi yawa a cikinsu".......... Akka tamu ta amana. Shiru parlourn suka yi, dan idan Queen mother tana magana ba'a katseta sai ta gama. Hannu ta kai ta ɗan ɗago haɓar Mahnoor, abinku da kaka, ko kunya bata ji ta fara yi wa Mahnoor leke leke har da gane mata girman tula tulanta, tana yi tana magana kamar haka. "Ni jikokina dik lafiyayyu ne, dan haka suna da buƙatar cikakkun mata, sannan suna san komai ya ciko sosai, saboda gujewa zinace zinace dole mu bincika da kyau mu samo wadda zata iya ɗaukarsu, dole na bincika masu komai". (Nace yanzu kun gane qualities ɗin da King ya zage yake ta cewa sai mace tana da su sannan zai aurawa ƴaƴansa ita? Kun gane irin qualities ɗin ko sai an maku karin bayani? Su kansu sun san abin nasu na gado ne, to dai ga Akka ta buɗe komai mun ji irin qualities da ake nema😅) Tana magana tana sassaukewa Mahnoor alkyabbarta izuwa saman shoulder ɗinta. (Kam bala'i, jama'a Akka duniya ce, a lallai gara ta duba masu, kai aima dole ta duba dan tasan sun yi gadon abin,🤭 tasan wanenen King Abdul Malik kakansu kenan, e dole ta duba aga Mahnoor zata iya ɗaukan Jaish ne ko yaya? Kai wlh wannan tsohuwa duniya ce.) "Shekarunki nawa?". Ta jefawa Mahnoor tambaya. Momma ce ta yunkura zata yi magana, hannu ta ɗaga mata alamar ta yi mata shiru. "Kada na ji bakin kowa a nan, bincike nike yi tukun nan"........ Tsit suka yi suna sauraronta. Baiwar Allah kanta a ƙasa cikin sanyin murya ta ce. "Ban san takamaiman shekaruna ba, amma dai tsakanin 15 da 16 ne". Larabcin Mahnoor yana gargada,.bata kware sosai ba. Jinjina kai Akka ta yi, sannan ta sake cewa. "Mahaifiyarki ta sanar dake abin da ake nufi da aure ko kuma ta barki a sake tana jiran ni in sanar dake? Kin san menene aure? Kin san yadda ake kula da miji? Kin san kalan mijinki kuwa? Kin shirya iya ɗaukarsa?". ........ Yau ga ikon god wajen Akka, tsohuwa zata buɗe komai fa. "A'a bani da mama, babu kuma wanda ya taɓa faɗa mun menene aure". Tamkar zata yi kuka ta bada wannan amsa. Cak Akka ta dakata da ƙoƙari cire mata alkyabba da take yi, da sauri ta dawo da kallonta a kan face ɗinta. "Ke marainiyace?". Murya cike da tausayawa ta jefa mata tambayar. Da e ta amsa mata idanunta suna cikowa da kwallah, nan take Akka ta ji jikinta ya yi sanyi, Allah sarki suna da jin tausayin marayu sosai, haka zuciyarsu take, janyota jikinta Akka ta yi, sannan ta ce. "Ya sunanki?". Mahnoor ta bata amsa. Kwnatar mata da kanta a saman gwiwowinta Akka ta yi tana ɗan shafa bayanta, da ɗan ɗaga murya ta ce. "Princess Mahnoor mata ga Prince Jaish barkanki da shigowa familyn King Abdul Malik". Haba wani irin ajiyar zuciya su King suka sauke, barema momma da ta fi kowa matsuwa da san jin amsar Akka, tun da ta kira Mahnoor da princess shikenan ta yi na'am da ita kenan. Mummyn Chuchu ce ta rangaɗa masu guɗa, nan take suka hau farinciki mara misiltuwa. Sarina and Mammie bakinciki kamar zai kashesu, barema da suka ga fuskar Mahnoor, babu abin kushewa a tattare da ita, ga kyau kamar ita ta yi kanta, uwa uba ta fi Fanan kyau da komai nesa ba kusa ba, kai in short basu da wani abin da zasu nuna mata da shi, ta fi su komai, kamar Sarina zata haɗiyi zuciya saboda taya Fanan kishi. Wato akwai cakwakiya wlh sosai. Kallan su King Akka ta yi, cike da bada umarni ta sanar da su ta aminta da Mahnoor, suma tana basu umarni da su karɓeta a matsayin sirika. Cike da gimamawa suka amsa mata da sun karɓeta hannu bibbiyu ma kuwa. Akka ce ta buƙaci jin yadda aka yi Jaish ya haɗu da marainiyar Allah da kuma me ya kaisa Nigeria?. Babu ɓoye ɓoye momma ta zayyana masu dik yadda aka yi. Sosai suka kara jin tausayin Mahnoor yakamasu, nan take ran Akka ya ɓaci ta ce wlh ita ba zata yafewa Nenne ba, dole su hukuntata azabar da ta ganawa Mahnoor, kun san basa yafe zalinci su ato. A fili Sarina ta yi suɓul da baka wajen cewa. "Ashe ƴan gidan matsiyata ƴan kauye mara galihu ne ma". Bata san ta yi maganar ba har sai da taga kowa yana kallanta, sannan ne ta farga, da sauri ta miƙe ta nufi waje tana ɓata ran wai ta ɓata lokacinta a kallan ƴar gidan matsiyata. Da kallo suka bita har ta fita, a nan ne King ya fahimci lallai akwai matsala idan har basu yi da gaske ba, dole ya zauna shi da momma su tsara yadda zasu kula da Mahnoor ba tare da wani abin ya sameta ba, idan ba haka ba zata fiskanci barazanar kanne miji. In short a nan aka yi komai aka gama, momma ta buƙaci iznin zuwa Jimeta a kai kayan aure da komai da ake yi wa mace kafin a aureta. Akka da kanta ta bata izini. Suka gama tsara komai, sannan mummyn Chuchu da momma suka miƙe suka kama Mahnoor suka fita da ita, mama ma miƙewa ta yi ta basu waje. Mammie ce ta yi fitar karshe. Parlourn ya rage daga King, uncle Abbas, uncle Jahiz sai Akka, tattauna suka fara yi a kan batun, dan su san ta yadda zasu tsara komai. Mahnoor kuwa part ɗin momma suka wuce da ita dan su kara shiryata yau za'a kaita ɓangaren Jaish. Mahreen dai an barota a ɗakin gyara. 🔥🔥🔥BABY AND AMMO🔥🔥🔥 Zaune take a saman sofa tana fuskantar Ammo dake zaune a saman nata sofar, Ammo na kallan Tv ita kuma tana rike da cup mai ɗauke da cappuccino tana sha, center table dake gabanta wani ɗan madaidaicin laptop ɗinta mai shegen kyau da tsada ne a kai, daga gefensa wasu takardunta ne tana karatun exams, na faɗa maku tana bala'in san karatu, kuma Allah ya bata ilimin both side. Sanye take da kayan barci masu kyau, rigace mai laushi sosai mai karamar hannu, sai wani ɗan madaidaicin wando da bai wuce singalalin kafafunta ba, bai kai har kasa ba. Wandan dai'dai da jikinta yake, shi kuma rigan yana da ɗan faɗi kaɗan, tana da dirarren jiki sosai kamar dai su Pretty tamu, sai dai bata da wani tsawo sosai, tsayinta dai'dai da shekarunta. Tana sipping cappuccino a hankali hankali tana duba takardunta, kanta na sanye da hular kayan barcin jikinta. "Baby ni zan shiga in kwanta, karfe 9 ta yi, yakamata kema ki kammala karatun nan da wuri ki je ki kwanta tun da gobe exam kuke da shi kuma da wuri zaku rubuta ko?". Cewar Ammo. "E exam muke da, yanzu zan kammala, saura kaɗan ne". Ta kai karshen maganar tana ɗaura cup ɗin cappuccinonta a saman table ɗin kusa da laptop ɗinta, sannan ta ɗauki takardanta ɗaya da take dubawa ɗin, ƙwaƙwalwarta ya ɗan ɗauki zafi, ta ƙasa gane wannan karatu, tinani take yi ko dai ta kira babynta a waya ta ce ya koyar da ita ne, in ya so su yi karatun ta Whatsapp kamar yadda suke yi a dik sanda wani karatu ya gagara mata. Ita kuwa Ammo miƙewa ta yi ta nufi dakinta tana yi mata sai da safe, da yake ɗakinsu daban daban, sai idan baby ta yi ra'ayi ne ta je ɗakin Ammo su kwana. Wayarta baby ta ɗauko da nufin ta kira numbersa ta sanar da shi ya hau Whatsapp su yi karatu, sai dai bata kai ga kiranba kofofin hancinta suka jiyo mata kamshin perfume ɗinsa, hakan yasa ta yi saurin kai kallanta a bakin kofar shigowa. Yana tsaye ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, kallanta kawai yake yi, sanye yake da wando three quter jeans white color, sai round neck polo shirts sky blue mai shegen kyau, ya yi kyau matuƙa, da alama fitan ba shiri ya yi, duba da yanayin dressing ɗinsa. Zaro idanu ta yi, cike da mamaki mai ɗauke da farinciki ta miƙe tsaye, wani ƙayataccen murmushi ne ya kubce mata kafin ta ambaci baby. Shiru bai amsa mata ba, ya dai kafeta da idanu, idan ka gansa zaka yi zaton gabaɗayanta yake kallah, amma bahaka bane, hankalinsa yana a kan kirjinta, da yake bata sa bra ba, and gasu masha Allah suna tsole idanun mai kallo.......... Anya baby ba barci ya ƙasa yi ba da ya biyo dare kuwa? To mutum dai shi ba karfe ba, kuma shi lafiyayyen namiji, ya kai 30 years, ya zayyi ba zai ƙasa barci ba ɗazun yaga kaya iya kaya? Kada ku ce na ce, tom gaskiya dai na faɗa. "Baby daman zaka zo ne baka faɗa mun ba?". Cikin wannan shagwaɓa tata kamar ta Prettynmu dai ta yi maganar. Ɗan gyaran murya ya yi saboda ya ga kaya har muryarsa ta sarkafe taki fita. "Babu zuwan a lissafina, dole ce ta sa unexpect ya shiga lissafina". Ya faɗa ba tare da ya motsa daga in da yake ba. "Dole kuma baby?". Kai ya jinjina mata alamar e........ "To waye ya yi maka dole ka zo ɗin?". Nisawa ya yi tare da ɗan kawar da kallansa daga kan dukiyan fulaninta, (yau dai ban ce tula tula ba saboda an saka mun ido da wannan suna nawa mai albarka 😅) "Kece kika tilasta zuciyata zuwa, na koma na kasa samun sukini, zuciyata ta damu da san zuwa in ganki". Wani irin murmushi ta saki. "Yes that is my baby, dama nima ina san ganinka"......... A ɗan takaice ya ce. "Meyafaru kike san ganina?". Turɓe fuaka na shagwaɓa ta yi, kamar zata saka mashi kuka ta amsa da. "Wannan karatun ne yake bani wahala, na kasa gane komai, please kazo ka duba mun"............. Tin da ta fara magana ya dawo da kallansa a kan wannan ɗan bakin nata da take turowa, gabaɗaya sai ya ji shi a network, wani irin kasala ne ya saukan mashi lokaci guda. Da kyar ya daure ya tako izuwa in da take. Yana zuwa bai wani ɓata lokaci ba ya zauna a saman sofa yana sauke ajiyar zuciya. Zama ita ma ta yi kusa da shi, sai a lokacin ta ce. "Ina wuni baby?"........... "Sai yanzu za'a gaisheni my ƴan'mata?". Cikin zolaya ya yi maganar. "To zumuɗin ganinka ya ja na manta da gaisuwar, amma yanzu na tina". Ta kai karshen maganar tare da ɗaukar cap ɗin cappuccinonta ta cigaba da kaiwa baki tana ɗan sipping....... Hannu ya kai ya ɗan ɗauki littafin nata ya fara dubawa. Wani irin daɗin cappuccino nan take ji yau, dan baby ya zo. Unexpext ta ga ya sanya hannu ya karɓi cappuccino, a hankali ya kai bakinsa ya ɗan yi sipping, sannan ya cire, cikin nitsuwa ya fara kora mata bayani a kan karatun da bata gane ɗin ba, yana yi yana shan cappuccinon ɗin. Sosai take fahimtar abin da yake faɗe, dan tana san karatun. Sai da ya tabbatar ta fahimci karatun sosai, sannan ya rufe littafin ya cigaba da ɗan sipping na cpn ɗin. "Baby in kawo maka wani cappuccinon ne?". Ta jefa mashi tambayar tana dawo da kallanta a kansa. Kai ya girgiza mata tare da miƙa mata cup ɗin yana faɗin. "Wannan ma saboda ke na sha"....... Hannu ta kai zata karɓa hannunsu ya gogi na juna, nan take wani shock ta ratsa jinin jikinsa, har sai da ya ɗan furta ash ba tare da ya san ya faɗa ba, sai jin shagwaɓaɓɓiyar voice ɗinta ya yi tana faɗin. "Sorry baby". Kai ya jinjina, ta wutsiyar idanunsa yake kallanta, kallansa kuma dik a kan tula tulanta da suka yi mugun tafiya da imaninsa. Sam bata fahimci yana kallanta ba, sai shagwaɓa ta hau zuba mashi tana kara jefa shi cikin saukin................ Kasa jura ya yi, out of control ya kai hannu ya janyota jikinsa, a take ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Ita kuwa ta zaci abin da ya saba yi mata ne na zaman da take yi a jikinsa suna hira, sai ta saki jiki har da ɗan ɗaura hannunta a saman kirjinsa ta sama kusa da shoulder ɗinsa. A hankali ya sanya hannunsa a saman bayanta, dik bata kawo tinanin komai a ranta ba. Slowly ya zame mata hular kayan barci dake kanta ya ajiye a gefe, a hankali ya shiga shafa lallausan black hairnta. A wannan karan ji ta yi gabanta ya faɗi, amma bata yi ƙoƙarin hanashi ba, dan bata san ma me zata ce da shi ba. Cikin dabara ya dawo da hannunsa saman........ P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 26 Cikin dabara ya dawo da hannunsa saman wuyarta. Wani irin al'amari ta fara ji yana ratsata, zata tashi ya yi saurin maida ita ya kwantar, sai ya gyara mata kwanciya ma da kyau. "Baby dare ya yi ba zaka koma bane?". Ta faɗa tana ɗago kanta. Bai yi mamakin jin maganar tata ba, saboda yaga tsoron abin da yake yi mata a cikin idanunta, shiyasa ma ta nemi ya koma bayan a baya kullum ita take damuwa da ya zo. Rinannun idanunsa da suka rikiɗe izuwa jajir ya sauke a kan face ɗinta. Ta ɗan tsorata ganin idanunsa sun sauya launi, hakan yasa ta kara jin tana san raba jikinta da nasa. Ƙasa bata amsar maganarta ya yi, tamkar an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗinsa, sai kawai ya bita da kallo. Unexpext Ammo ta shigo cikin parlon tana faɗin. "Baby ba zaki hakura da karatun nan sai da safe ba kuwa? Dare ya yi yaushe zaki yi barci ba.............." Bata iya ƙarisar da maganar ba ganin su biyu a parlon, ta yi mamakin ganinsa, da tasan yana nan ba zata fito ba. Kunyarsa ne ya kamata. Sannu da zuwa ta yi mashi tana ɗan ja da baya. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kallansa, jinjin kansa kawai ya yi bai iya amsa mata ba, wai yana ɓoye halin da yake ciki kada ta gane. Juyawa ta yi ta koma ciki tana mamakin yaushe ya zo gidan nan? Ko karar motarsa bata ji ba. Ɗagowa daga jikinsa baby ta yi, a ɗan tsorace ta ce. "Baby zan je in kwanta dare ya yi"......... Lumshe idanunsa ya yi, wannan shagwaɓa tata ta kara ratsa shi sosai, sai ya ji ya zo har wuya. Kasa shanyewa ya yi, a hankali ya matsar da face ɗinsa dab da ita. Zaro mashi idanu ya yi tana kallansa da mamaki. Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Can i kiss you my baby?". Wani irin zaro idanu da ta yi tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa. A rikice ta ce. "Baby kiss kuma?". Muryarta na rawa ta yi maganar. Kai ya gyaɗa mata alamar e kiss yake nufi. A wani irin zabure ta miƙe daga jikinsa, kafin ya yi wani yunkuri tuni ta watsa da gudu sai cikin ɗakin Ammo, tana shiga ta tura kofa tana sauke haki da sauri sauri. Sai da ta tsorata Ammo dake kwance a saman bed, a razane ta tashi zaune, dama bata yi barci ba, tana kwance tana tinanin wanda za'a iya alƙanta shi da lamarin su baby ɗin. Ganin ta gudu yasa ya yi saurin miƙewa ya bi bayanta, dan ya santa da shiririta tsab zata faɗawa Ammo abin da ya ce mata. Yana turo kofar yasa kai ya shigo. Tana ganinsa ta saka yar kara tare da kwasawa a guje ta haye gadan Ammo tana riko Ammo da karfi. Shiru ya ɗan yi yana kallanta, ita kam Ammo ta gama fahimtar komai, sai ta tuna kamar bata fahimta ba, ta riko jikar tata tana tambayar lafiyarta kuwa. Cike da shiririta ta fara ƙoƙarin faɗawa Ammon abin da baby ya ce mata. Sai dai bai bari ta faɗa ba ya yi saurin cewa Ammo. "Ɗan bamu waje bari in yi magana da ita". Ba musu Ammo ta saketa tare da saukowa kasa. Da sauri ita ma ta sauko ta ƙanƙame Ammo tana faɗin sai dai su fita wajen a tare. Ɗan jinjina kai ya yi tare da cewa Ammo ta je kawai kada ta damu. Wucewa Ammo ta yi da sauri ta rufa mata baya dan bata san tsayawa. Sun zo zasu fita ya damko baby ita kuma Ammo ta fice. Kuka ta saka mashi mai sauti tana faɗin ya saketa bata so. Shiru ya yi bai saketa ɗin ba, kuma bai yi magana ba har tsawon mintina 5, sannan ne ya rungumota da kyau a jikinsa, murya ƙasa ƙasa ya ce. "Saboda na ce zan yi kissing ɗinki ne kike wannan kukan?". Cigaba da yin kukanta ta yi bata yi magana ba, sai dai ta kwanta luf a saman kirjinsa....................... "To am so so sorry, ba zan sake faɗin hakan ba, saboda ba zan so hawayenki su sake zuba ba, ya isa haka kin ji?". Stilll shiru bata kulasa ba, sai ma ƙara kukan nata da ta yi. Ɗan rage tsawonsa ya yi ya ɗauketa can suka fito daga ɗakin, yana jin wani irin azabbabben yanayi a tattare da shi, amma ya daure saboda ya fin san farincikinta fiye da komai. A tinaninsa zasu samu Ammo a parlour, sai kuma yaga akasin hakan, saman sofa ya koma da ita a jikinsa ya zauna, rarrashinta ta cigaba da yi babu kakkautawa, tin yana jiyo sautin kukanta a hankali hankali har ya dai'na ji, a hankali saukar numfashinta irin na mai barci ya fara dokan dodan kunnesa, alamar ta yi barci kenan. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaga kansa sama ya jingina da jikin head na sofar, a hankali ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya. Ya ɗauki 20 mins a haka kafin ya dawo da kallansa a kanta haɗe da sauko da kansa. Ai ina, ta jima da yin barci har barin ya yi nauyi. Nisawa ya yi tare da miƙewa da ita cikin dabara, ya ɗauketa cak sai bedroom ɗinta. A saman kyakkyawar bed ɗinta ya kwantar da ita, ya janyo mata bargo ya lulluɓeta izuwa dai'dai cikinta, a gaban bed ɗin ya tsuggun dai'dai saitin face ɗinta, kasa kasa kamar mai raɗa ya ce. "Rigimamma kawai, to yanzu ba ga shi kin yi barci ba?". Ya yi maganar yana kallan ɗan bakin nata. A hankali ya dawo da kallonsa a saman kirjinta da gabaɗaya tudunsu suke a waje saboda yanayin kayan jikinta da yanayin kwanciyar da ta yi. A hankali ya ɗan haɗiyi yawu kamar wani da ya ga abin kwaɗa yi. Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya kai hannunsa jikinta, hannun nasa sai wani kerma yake yi. Wuyar rigar tata ya ɗan ja mata sama, sannan ya ɗan sunkuyo da kansa a kanta. Sumbata ya manna mata a baki. Ɗan motsawa ta yi kamar tana san farkawa. A hanzarce ya miƙe kaman maras gaskiya, da sauri ya nufi switch na ɗakin, kashe mata wutar ɗakin ya yi, da sauri ya fice kamar zai kifa ƙasa. Bai zame ko'ina ba sai cikin motarsa, ko da ya shiga ya kasa jan motar ya tafi, ya ɗauki good 30 mins a wajen yana ƙoƙarin controlling na feeling ɗinsa kafin ya iya driving. Da kyar ya iya tada motar da gudun gaske ya nufi gate, da yake gate ce mai amfani da na'ura, da kanta ta buɗe kanta ya danna waje da gudun gaske. Ammo tana tsaye a windown bedroom ɗinta dake fuskantar harabar gidan tana kallansa har ya tafi, sannan ta nufo ɗakin baby. Kamar yadda ya barta haka ta sameta, addu'ar barci ta zo ta yi mata dik da tana da yakinin ya yi mata, dan ya saba yi, sai dai bata san yau kansa ya ɗauki zafi bai yarda ba ya tafi. Bayan ta gama yi mata addu'ar ne ta fito ta wuce nata bedroom ɗin, ta koma saman bed ɗinta ta kwanta cike da tinanika kala kala a ranta.......... ASUBA TA GARI. 🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥 "Haulat bani waje bari in yi magana da ita". Cewar Momma kenan, tana san ganawa da Mahnoor wanda bata yi hakan ba ko sau ɗaya, so yanzu tana san su gana. Zaune suke a bakin bed ita da Mahnoor ɗin, Mahnoor kanta a ƙasa. Miƙewa mama Haulat ta yi cikin girmamawa ta ansa da to tare da nufar hanyar fita. Har ta kai tsakiyar ɗakin sai ta tsinkayo muryar momma tana faɗin. "Nan da 2 hours ki turo mun Mahreen". Da okey mama Haulat ta amsa sannan ta fice waje. Dawo da kallanta a kan Mahnoor momma ta yi, hawaye bibbiyu ne a face ɗinta, da alama ta tina maraicinta yasa take wannan kuka. Janyota jiki momma ta yi ta hau rarrashinta, cike da kauna ta ce. "Kada ki ɗaukeni matsayin sirika, ki ɗaukeni matsayin uwa". Ta kai karshen maganar tana goge mata hawaye. Shiru Mahnoor ta yi tana jinjina halacci irin na momma, zamanta da mama Haulat na satin ɗayan nan har ta koyi wasu abubuwa masu muhimmanci. "A matsayina na uwa a gareki zan yi maki nasihar zaman gidan miji, ki nitsu ki saurareni da kyau, dan a bisa dokarmu a ɓangaren mijinki zaki kwana yau, nan da sati biyu masu zuwa zamu je jimeta, da naso mu je gobe, amma akwai wasu dalilan da yasa sai next two weeks, akwai saye saye da za'a kawo daga Dubai, sai mun haɗa komai zamu tafi, gobe ya yi kusa". Jinjina kai Mahnoor ta yi tana sauke ajiyar zuciya, tabbas tana jin momma tamkar mahaifiyarta, tana kaunarta sosai ita ma. Cikin sanyin murya momma ta fara magana kamar haka. "Ki dage da hakuri da biyayya. Aure yana buƙatar hakuri da juriya. Ki kasance mai biyayya ga mijinki, kuma ki guji nuna rashin kunya ko rashin girmamawa gare shi. Ki kula da addua da ibada. Ki dage da addu'o'i don neman zaman lafiya da albarka a gidanku. Ibada za ta taimaka muku wajen samun kwanciyar hankali. Ki zama mai tsafta da ƙyalli, Haulat zata koya maki kwalliya sosai. Ki kula da tsaftar jikinki, gidanki, da tufafinki. Mijinki mutum ne mai jin daɗi idan ya ga matar da ke da tsafta kuma tana jan hankalinsa, yana da kyankyani ya tsani ƙazanta, a kan kanwarsa ƴar autarsu ya fahimci hakan, dan in ta yi kwalliya wuni yake yi yana yabonta baya gajiya, so yana san kwalliya sosai. Ki koyi maganar mai daɗi da ta dace da shi, dan yana san magana cikin kulawa. Ki guji faɗar kalamai masu zafi ko cin fuska. Kalaman kirki suna gina soyayya kuma suna rage duk wani rashin fahimta. Kula da sirrin gidanki da mijinki. Kada ki yi gaggawar bayyana matsalolinku na gida ga kowa. Kula da sirrinku zai taimaka wajen magance matsalolin cikin sauƙi. Kauna da kulawa. Dik da nasan yana da wuyar sha'ani kuma zai yi wuyar juyowa gareki, dik da haka ki nuna mashi soyayya da ƙauna, sannan ki kula da dangi da abokan arzikinsa. Wannan zai sa ki samu ƙima a gidansu. Hakuri, hakuri, hakuri, ki kasance mai haƙuri. Komai yawan ƙalubale, haƙuri yana da muhimmanci don magance su. Ki rike ibada sosai. Wannan yana kawo albarka a cikin aure. Kar ki yi gaggawa wajen yanke hukunci idan ya yi maki wani abin. Idan akwai matsala, ki nemi hanya mai kyau don magance ta kamar yin nafilfilin dare dan neman maslaha daga wajen Allah. Ki kasance mai ilmantarwa. Karatu da ilimi suna taimaka miki wajen zama mai cikakken basira a rayuwa. Na faɗa na kara faɗa maki, mijinki yana san kwalliya sosai, sannan na manta ban faɗa maki cewa shi mutum ne mai san zanen lalle a hannun mace ba, ko ni da nike mahaifiyarsa idan na yi lalle ya rinƙa magana kenan, ya kalla ya sake kallah, har hoto yake ɗaukar hannuna, Jaish mutum ne mai san lallaɓawa, tin yana karami haka yake, baya san a ɗaga mashi murya, sannan baya san yana magana ki yi magana, ki kula da wannan, baya san cin abincin a kan lokaci, hakan kada ya ɓata maki rai ki ɓata mashi shi ma, cikin ruwan sanyi da sigar soyayya da lalama zaki koya mashi cin abinci a lokacin da kika yi ra'ayi, yana da zuciya sosai, wannan gado ce, dik suna da zafin zuciya da saurin fushi, idan ransa a ɓace kada ki yi saurin kula shi, ki kyalesa na ɗan lokaci ya sauko, in ba haka ba ba zaku kare da kyau ba".......... Ɗan dakatawa ta yi tana mayar da numfashi. Mahnoor kuwa ta kasa kunne tana saurari yadda yakamata. Shiru ta ɗan tsaya na ƴan mintuna tana kallan fuskar Mahnoor kafin ta nisa ta ɗaura da cewa. "Kin ji kaɗan daga cikin abin da yake so ta waje, sai ta ciki, ba zan ɓoye maki komai dangane da mijinki ba, saboda yanzu a ƴa na ɗaukeki ba sirika ba, burinmu mu shawo kan mijin naki ne, dole na fayyace maki komai dan mu yi nasara". Jinjina mata kai Mahnoor ta yi tana kara kasa kunne ta saurara da kyau, saboda tana bala'in san Jaish, dik abin da zai juyo mata da hankalinsa a kanta to tabbas zata yi shi. "Mijinki yana da sha'awa mai karfi wanda zance maki dikkansu haka suke, sai ki shirya, amma yana da dauriya sosai, sannan baya san mace mai shigar manyan kaya, i mean matar aurensa, saboda na karancesa sosai a kan hakan, dayawan lokuta yana san sayawa kanwarsa kananan kaya dan yana yi mata kallan yarinya, so yana san shigar manyan kaya, wannan zan sa a yi maki akwati set guda a wajen haɗa lefenki, so Haulat zata koya maki yadda zaki yi amfani da su". Mahnoor da bata san me ma mommar take nufi ba a maganarta ta karshen nan, ai sai amsa mata take yi to kawai kanta a ƙasa. My people's ku tafawa uwa ta gari, wato dik abin da ƴaƴanta suke yi tana sane tana yin recoding a ƙwaƙwalwarta, ashe ta san Jaish yana san lalle, kun tuna idan ya zo ya samu mama Haulat ta yi mata lalle sai ya yi ta yabawa? Ashe dik tana ganinsa, ashe ta iya karantar abin da yake so da wannan da baya so, gaskiya wannan ita ce uwa ta gari, ba tare da ƴaƴanta sun faɗa mata ga abin da suke so ba ta rigasu sanin abubuwan da suke so, wani lokaci suna son abu basu ma san son shi suke yi ba, amma tsabar kula irin nata ita ta gane hakan, wata uwar ko kasheta zaki yi yanzu ki ce ta kirga maki abubuwa goma da yaronta yafi so ba zata kawo maki su ba, kuma tana sansa ba wai bata sansa ba, wasu ne akwai rashin kula sosai wlh, irinsu ne ƴaƴa su yi ya aikata abubuwa tsabar rashin kula zasu ce basu sani ba, yanzu ku momma bata burgeku ba yadda take zayyano abin da ɗanta tafi so ba tare da shi kansa yasan da yana sansu ba? Abin bai ƙayatar daku ya yi maku daɗi ba? Ki karanci yaronki ki san me yake so ma ke zaki fi kowa jin daɗi da moresa, dan in kika san me yafiso fa wlh dik in da zai je sai ya dawo wajenki, dan zai ga kamar dik duniya ke kaɗai ce kika iya fahimtar kika sansa sosai. So yana da kyau dikkan mata su yi koyi da halin momma, ita ake cewa uwa ta gari wlh. Daga karshe Allah ka haɗamu da iyayen miji na gari irin momma. (Amma fa momma ta gama kwancewa Jaish namu na amana zani a kasuwa😅 zata sa Mahnoor ta raina shi😅) Daga haka Momma ta sanar da Mahnoor abin sa yasa Jaish ya ce bai sansu ba a yanzu, dan haka kada su ji haushinsa ko su ga laifinsa, ya so ta ne a lokacin da baya cikin hayyacinsa, daga karshe ta ɗaura da cewa. "A yanzu ma In Sha Allah zai so ki, zan tayaki yakin neman shawo kansa, kada ki sare ko ki cire rai, mu nan gidan jajirtattune, kema jajircewa zaki yi ki jure har mu yi nasara, sai abu nagaba da zan faɗa maki, in dai ba kin lura ransa a ɓace ba to in ya ce ki bar gabansa ko ki tashi a kusa da shi kada ki tafi, amma idan ransa a ɓace wannan kam ki tafi in ba haka ba ayi ɓatacciya, ki yawaita kasancewa a tare da shi, a kullum karfe 9 na dare yana shan cappuccinon, ni kuma nike haɗa mashi da kai'na, ki zo ki rinƙa ɗauka mashi kina kai mashi, kada ki yarda yana zaune a waje shi kaɗai, kada ki ji tsoronsa dan a labarinku na baya na ji kina tsoronsa, to a yanzu ki ajiye tsoron nan ki rinƙa kusantarsa sosai". "Muhimmin abu nagaba shi ne, yanzu ki sani dik wata ɗawainiya nasa zai dawo kanki, kama daga kai mashi abinci, sanya shi ya ci, shinfiɗa gadonsa, mace mai dabara bata bari kowa ya ga makwancin mijinta, dan haka kada ki bada kofar da zai ce a dawo mashi da kuyangu masu yi mashi hidima a zuwan ke baki iya gyara mashi shinfiɗa ba, ki koyi yi mashi shinfiɗa da kyau, ki ɗara dik kuyangun da suke yi mashi hidima a baya yin komai yadda yakamata kuma yadda zai ƙayatar da shi, dik Haulat zata koyar dake kin ji ko?". Kai ta gyaɗa tana amsawa da e ta ji. Sosai ta fayyace mata dik wasu abubuwan da Jaish yake so da wanda baya so. Dik abin da take faɗe yana shiga kunnuwan Mahnoor yadda yakamata. Suna tsaka da hiran ne Omaid and Obaid suka shigo cikin ɗakin baki ɗauke da sallama. Momma ce ta amsa masu sallamar tana jinsu da kallo. Saman gadon Omaid ya haye yana turɓe fuska ya kwanta a can gefe. Shi kuwa Obaid sarki a rashin hakuri, wani kallo mai kama da harara ya wurgawa Mahnoor. "Momma who is she? She looks like Aunty Chuchu". Ya yi maganar yana kare mata kallo. Baki ɗauke da sallama guyson ya shigo, dikkansu suna cikin white arabs jallabiyas masu bala'in kyau, yau sun fito a larabawansu sak. Saman gado kusa da Omaid guyson ya haye yana turo baki, cikinsa ce take ɗan yi mashi ciwo kaɗan kaɗan, da alama ciwonsa ce take san tashi. Yana kwanciya kallonsa ya sauka a kan Mahnoor da ta yi ƙasa da kanta tana ta satar kallansu Omaid, a ganinta sak suke kama da Jaish, kun san jini ba wasa ba, sun yi mata bala'in kyau, sai dai ta shiga ruɗani wajen ƙasa tantance Omaid and Obaid mutun ɗaya ne ko biyu saboda kamanninsu. Zaro idanu guyson ya yi, da ɗan karfi ya furta. "Momma wannan ba matar Yah Jaish ɗin nan ba ce?". Ya yi maganar yana miƙewa zaune an fasa kwanciya, yaga ta goge ta yi kyau kamar ba ita ba........ Lallai guyson yana da basira sosai, bai fa wani jima da sanin Mahnoor ba, amma dik wannan gyara da ta sha ya iya ganeta. Wani irin ɗan iskan dariyar ƙeta Obaid ya yi kafin ya ce. "Yah Jaish ɗin ne da mata? Tab hau kenan". Ya kai karshen maganar yana sake watsewa da dariya. Shi kansa Omaid jin zancen sai da yasa ya miƙe zaune. "Da gaske Yah Jaish ya yi aure?". Ya yi tambayar yana zare idanu. Guyson ne ya wurgawa Obaid harara kafin ya ce. "To dariyar me kake yi sarki?". Zama Obaid ya yi a saman sofa, cike da iyashege ya fara faɗin. "Yah Omar ba dole in yi dariya ba, wai Yah Jaish da mata? Amma wannan ta shiryawa azabansa ko? Dan dik gidan nan bayan Yah Ramish babu bakin mugu biyunsa, wlh i pity for his wife". Omaid ne ya capki zance da cewa. "Waye ya ce maka ma akwai wadda zata iya zaman aure da shi? Mutumin da bayan bada umarnin babu wani abin da ya iya, su kuma mata suna san soyayya da kulawa haɗe da lallaɓawa kamar jarurai, shi kuma yana abu kamar bosawa bashi da wani shaukin love". Tab wato Omaid ɗan duniya ne, ko daga ina ya san shaukin love kuma? Kana ganinsa kaman shiru shiru ashe A ne shi ma, dama fa masu shiru shirun nan hmmm idan suka yi wata tsiyar sai ƙwaƙwalwa ta kasa ɗauka. Momma dai binsu da kallo kawai take yi abinta. Harara Guyson ya wurgawa Omaid kafin ya ce. "Kai daga ina ka san shaukin love ɗin?". Obaid ne ya amshi zancen da cewa. "Tab ai Omaid ƴan'matansa sun kai uku a school, har faɗa ake yi a kansa sosai, love yake bugawa over"........... Momma ce ta katsesu da cewa. "Kai kuma ƴan'matanka nawa?"....... Ɗan ɗaure fuska kaɗan ya yi. "Momma ni ai bana soyayya, me zan yi da mata? Bani da lokacinsu gaskiya". Girgiza kai kawai guyson ya yi, cikin sanyin murya ya ce da Mahnoor. "Kada ki biyewa waɗan nan, kin yi kyau sosai, ina sisterki da ta yi mun kallan matsayin Yah Jaish ɗin nan take?". Kanta a ƙasa ta amsa mashi da Mahreen tana ɗakin da aka yi masu gyaran jiki....... "Kada ki takura kanki wajen sunkuyar da kanki da sunan kina jin kunyarnmu, mu kannen Yah Jaish ne, kinga mu kannenki ne, ki ɗaukemu a haka kin ji?". Cewar guyson again, yaro mai sanyin hali. "Waye kaninta?". Cewar Obaid, a kule ya yi maganar. Hararar wasa guyson ya wurga mashi kafin ya ce. "Mu mana, mune kannenta". Kallon uku saura kwata ya bita da shi kafin ya amsa da. "A'a sai dai ku, amma ni wannan ƴar karamar yarinyar ba zan ce mata aunty ba, na fita shekaru fa". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa fuuuu ya nufi waje. Da kallo dikkansu suka bisa har Mahnoor ɗin ma, shi a dole ransa ya ɓaci ance shi kanin Mahnoor ba zai ɗauki hakan ba. Dab zai fita Jaish yana sako kai zai shigo. Karo suka ɗan yi, da sauri ya ja baya a ransa yana cewa shikenan yau ranata ba zata yi kyau ba tun da na haɗu da Yah Jaish. A fili kuma sai cewa ya yi. "Good afternoon Yah Jaish". Kallon tsab Jaish ya yi mashi kafin ya amsa da. "Afternoon, from where to where?". Fuska a ɗaure tamau ya yi maganar. Guyson ne ya fara yi mashi dariya, suna bashi dariya yadda suke nitsuwa a gaban Jaish, zaka rantse da Allah malaman da'awa ne idan ka gansu a gaban Jaish ko Ramish, a bayansu kuwa ko shaiɗan sai ya sara masu a rashin mutunci. Matsawa kusa da Mahnoor guyson ya yi, yana dariya ƙasa ƙasa ya ce. "Kinga dik iskancin nan nasu mijinki maganinsu yake yi, tsoronsa suke ji kamar su mutu, baki ga sun nitsu ba?". Ita kanta sai da abin ya so sakata dariya, yadda Obaid ya rinƙa tada jijiyoyin wuya yanzu a nan, amma daga ganin Jaish kamar wani kurman da ya wuni bai ci abinci ba ya zama, ya nitsu tsit. Cikin in ina Obaid ya amsa da. Daga wajen momma ɗaki kuma zai tafi ya kwanta. "Ka aikata wani abin ko?". Jaish ya faɗa yana wurgawa momma dake kallonsa ido. Wato Jaish yasan halinsu sarai, basa zama basu yi wani laifin ba, shiyasa dik in ya haɗu da su sai ya ce sun aikata wani abin. Wani irin faɗuwar gaba Mahnoor ta ji na jin sanyayyar muryar mijin nata, wani irin azabbabben sonsa ne yake kara taso mata, ji ta yi tana san ɗago kai ta kallesa amma tana tsoron su haɗa ido, kuma tana kunyar momma ta kamata tana kallansa, sai kawai ta danne ta ƙara yin ƙasa da kai, amma tabbas tana kewansa, yanzu an kusa sati biyar rabonta da su kasance a hare kenan. Sarai momma ta fahimci har yanzu Mahnoor tana tsoron Jaish sosai, kamar ma yanzu tsoron nasa karuwa ya yi a ranta, lallai sai ta tsaya tsayin daka ta cire mata wannan tsoro idan suna san yin nasara. Wani irin kallo Jaish ya wurgawa Obaid har sai da ya haɗiyi wani yawu mai wuyar wucewa, sannan tin kafin Jaish ɗin ya sake yin magana ya yi saurin faɗa mashi dik abin da ya aikata, wato guyson ya ce Mahnoor Auntynsu ce shi kuma ya ce ba Auntynsu bace dan ya fita shekaru, dan haka ba zai ce mata Aunty ba, tsab ya faɗi abin da ya yi. Momma da guyson sai murmushi suke binsu da shi. Jin abinda Obaid ya faɗa yasa ya ja siririn tsaki tare da karisowa ciki, dan a cewarsa shi ma ai bashi da haɗi da Mahnoor ɗin bare ya ji babu daɗi dan sun ki accepting ɗinta sun yi mata rashin kunya. Saman sofa Jaish ya zauna, shi kuma Obaid ya yi saurin ficewa waje. Cikin girmamawa Omaid ya ɗagawa Jaish gaisuwa, amsa ɗaya ya yi hankalinsa gabaɗaya a kan momma. Ƙasa Omaid ya yi, da sauri ya bi bayan Obaid, dan basa zama inuwa guda da Jaish. Guyson kuma cigaba da hira da Mahnoor ya yi ba tare da damuwa ba, dama abin da yasa a kauye ya ji kyamarsu ma, saboda datti ne, yanzu kuma sun yi tsab dan haka bashi da wata matsala da su. Tin Mahnoor tana noƙewa bata yi mashi magana har ta fara sakin jiki suna hira ƙasa ƙasa, har murmushi ya sakata yi, ko ɗaya kuma bai ambaci sunanta ba, Aunty yake ce mata cikin girmamawa, ita ma ta tambayesa sunansa, ya ce mata Omar amma ana kiransa da Guyson, dan haka sai ta fara ce mashi Yah Omar saboda ya fita shekaru, yanzu kusan 19 years yake da shi. Kallan tsab Momma ta yi wa Jaish kafin ta ce. "Lafiya kake kuwa? Ya ka dawo office da wuri?". Ɗago kansa ya yi da nufin ya yi magana, sai a lokacin ya lura da Mahnoor dake saman bed ɗin ita ma, kallo ɗaya ya yi mata ya dawo da kallonsa a kan momma, irin kallan da ya wurga mata mai kama da yana san tambayar wacece wannan kuma? Sai dai bai tambaya ɗin ba ya ce da momma.. "Kai'na ne yake ciwo shiyasa na tashi office, and am felling hungry". A ɗan takaice momma ta ce. "Baka yi breakfast ba ka fita ko?". Kai ya gyaɗa mata alamar e. "Meyasa baka san cin abinci a kan lokaci ne? Yanzu karfe 12 ta kusa fa amma baka yi breakfast ba? Dole ma kanka zai yi ciwo ai". Shiru ya yi yana ɗan satar kallan lallen dake kyawawan fararen hannun Mahnoor, ga zanen lallen sun fita sosai, sun yi kyau, mayen san lalle ne shi kuma, sai yana magana yana satar kallonsu, da a hannun Mommarsa ce ko hannun Zunaira yake da sai ya ɗauki hannun hoto, amma ita wannan bai santa ba, amma dik da haka ya ji yana kaunar lallenta. Sarai momma tana kallansa dik abin da yake yi, ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin yadda yake satar kallan lallen, lallai ne kowani mutum yana da rauninsa, kuma abin da yake so shi ne rauninsa, tabbas zasu yi nasara In Sha Allah, haka momma take faɗe a ranta. "Ayya sorry, jeka huta yanzu za'a kawo maka abincinka, idan ka ci sai ka sha magani". Cewar momma, ta yi maganar tana kallansa. Sarai ya ji abin da ta faɗa, amma hankalinsa yana a kan lallen Mahnoor, dan haka sai ya jinjina kai kawai ba tare da ya yi magana ba, sannan ya miƙe da nufin ya tafi. Har zai juya sai kuma ya tuna bari ya kalli face ɗin mai wannan lalle. Ya ilahi ya lilliahi, sai da ya ji gabansa ya faɗi time da ya ɗaura idanunsa a kanta. Da sauri kamar wani maras gaskiya ya kawar da kansa tare da wucewa waje da sauri. Murmushi a cikin zuciyarta momma ta saki, har ta harbo jirgi ɗan nata, dan har cikin ransa ya ji kyan Mahnoor ya taɓa shi. Yana fita momma ta dawo da kallonta a kan Mahnoor da Guyson da suke ta hira ƙasa ƙasa ba zaka jiyosu sosai ba, cikin nitsuwa da giramma juna. "Mahnoor tashi Omar ya rakaki wajen Haulat, ku je Omar ka ce da Haulat ta shirya mun ita sosai ta bata kayan da suka dace zata je kaiwa mijinta abinci, bari in je in duba kitchen me suka shirya mashi". Ta kai karshen maganar tana miƙewa tsaye. Miƙewa guyson ma ya yi ya sauko kasa yana faɗin Mahnoor ta tashi su tafi, har lokacin yana jin cikinsa tana ciwo kaɗan kaɗan, amma ya daure suka nufi waje. After some minutes, momma ta dauke cikin parlonnta wasu kuyangu guda biyu suna biye da ita a baya ɗauke da manya manyan trays masu shake da kayan cima wanda ta sa suka shiryawa Jaish. A saman dining table ɗinta suka ɗaura mata, sannan suka zube gwiwowinsu a ƙasa suna jiran jin ko akwai wani umarni da zata basu. Da hannu ta yi masu nuni da su tafi, sannan ta samu waje saman sofa ta zauna tana tunanin irin nasihar da yakamata ta yi wa Jaish a kan Mahnoor. Tana tsaka da wannan tinani mama Haulat ta yi sallama rike da hannun Mahreen. Like wow my people's, wai kunga Mahreen kuwa? Tamkar ba ita ba, har ɗan kumatu ta yi, fatarta ya yi jajir kamar ka taɓa jini ya fita, ta sha gyara da ingantattun kayan gyara daga Dubai, kayan gyara na musamman, tana sanye da abaya mai bala'in kyau wanda momma tasa aka sayo masu. Ita kanta momma tasan yarinyar nan ta yi kyau, sai da ta yi fatan dama ace ita ma Mahreen ta zama sirikarta mana. Mahreen yanzu ta ɗan nitsu fa, kun san da san kwalliya, dik abin da mama Haulat take son ta yi mata sai ta ce ta yi zata yi mata kwalliya, idan ta ce haka sai kuga Mahreen ta nitsu ta bi umarni, a haka aka samu aka yi mata wannan gyara. Tin da ta kalli kanta a cikin mirror taga ta yi kyau shikenan ta kara nitsuwa, yanzu dik bayan awa sai ta ce zata yi wanka a sake yi mata wani make up ɗin mai kyau, dan shegen bala'in san kwalliya. Da hannu momma ta nuna mata kusa da ita a kan ta zo ta zauna, sannan ta dubi Mama Haulat kafin ta ce. "Haulat kawo mun ɗiyata ya zo ta kaiwa mijinta abinci, daga nan ki shirya ki je part ɗinsa ki shirya ɗaki ɗaya wanda zaki koma can da zama". Shiru mama Haulat ta ɗan yi, mace mai amana, ta kasa tafiya kuma. "Lafiya Haulat?". Momma ta tambaya ganin bata tafi ba. Kasa ta yi da kai, cikin girmamawa ta ce. "Ranki ya daɗe wlh bana san matsawa daga kusa da ke ne". Allah sarki, sun saba sosai. Momma tana ƙoƙarin janyo Mahreen jikinta ta rungume ta ce. "Ai baki bar kusa da ni ba, jahadi zaki je ki yi wajen ganin kin saita aure, daga nan ai zaki dawo, yanzu dai ki kuka da yaran naki da kyau". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa da to, sannan ta juya ta nufi waje. Dawo da kallonta a kan Mahreen momma ta yi, yarinya ta yi kyau kamar ba gajin bappa ba. Janta da hira momma ta fara yi tana kara wayar mata da kai. Suka tsaka da hira mama Haulat ta dawo rike da hannun Mahnoor, ya subhanallah, mama Haulat ta iya shirya amarya fa, ta tsara mata kwalliya mai bala'in kyau da dik wanda ya kalla sai ya sake kallah, sannan ya bata wani haɗaɗɗen malesian gown mai bala'in kyau da tsada kaunin brown color, ga Mahnoor da hasken fata sai kalar ta yi mata kyau. Rigar ta bi coca colar shape ɗinta ta zauna ɗas, sannan rigar ta fito da komai yadda yakamata, sai dai sun ɗaura mata kyakkyawan alkyabba a saman kayan, kanta babu ɗan'kwali sai hular alkyabbar, gashin kanta ya sha gyara sai tashin kamshi yake yi yana wani sheki, kai my people's wlh Mahnoor ta haɗu matuƙa. Mahreen tana ganinta ta miƙe da nufin ta je ta rungumota, rikota momma ta yi tana faɗin. "Zauna kada ki ɓatawa amarya kyalliyarta". Jin haka yasa ta koma ta zauna tana faɗin. "Ni momma ba zan yarda ba kwalliyar Adda Mahnoor ya fi nawa kyau". Murmushi kaɗan momma ta yi kafin ta sake cewa. "Anjuma da yamma idan zaku je gaishe da daddy za'ayi maki kwalliya irin nata kema" Cike da yarinta ta ce da momma. "Ki ce Allah za'ayi mun?". Ɗan zaro idanu Mahnoor da mama Haulat suka yi. Har mama Haulat zata yi mata faɗa ta gaya mata ba fa wajen wasa take bai sai momma ta rigata da cewa. "Ba sai na ce Allah ba, za'ayi maki ke dai". Make kafaɗa ta yi tana faɗin. "Idan baki ce Allah ba ni na zan yarda ba........". Bata kai karshen maganar ba mama Haulat ta ɗan daka mata tsawa. "Ke baki da hankali ne? Sa'arki ce ita? Wai bana ce maki ki rinƙa girmama manya ba?.........". Ɗaga mata hannu momma ta yi tare da cewa. "A'a Haulat rabu mun da ƴa, dauki kayan abincin nan ki raka Mahnoor izuwa wajen Jaish saboda yana jin yunwa, ba ruwanku da ƴa ta". ........... Cikin girmamawa mama Haulat ta amsa da okey a cikin zuciyarta tana kara jinjinawa kirkin momma da rashin girman kanta, ba kaman sauran matan King ba, idan su mama ne Mahreen ta isa ma ta zo in da suke ne?. Ai su basa zama kusa da talaka, ina momma ta dabance a cikinsu, bata ɗauki duniya a bakin komai ba. Haka dan tana san farincikin Mahreen sai da ta amsa mata da Allah ɗin sannan Mahreen ta yarda, suka cigaba da hira Mahreen tana zuba mata shirme da hiran kauye da dai sauran shiririntarta. Mahnoor kuwa mama Haulat ta ɗauki tray ɗaya na abinci ita kuma ta ɗauki ɗayan, tamkar wata tauraruwa haka ta bi bayan mama Haulat suka nufi part ɗinsa. Sai kalle kalle Mahnoor take yi, dan idan baku manta ba bata yawace cikin gidan ba, part ɗin momma kawai suka sani sai ɗakin gyara. Bata kara zuba ƙauyancinta bama sai da suka isa part na mijin nata, wani irin daddaɗar kamshi ne ya daki hancinta har sai da ta lumshe idanu tana kara shaka. A saman dining table dake cikin parlonsa suka zube abincin, sannan mama Haulat ta dubeta, cikin mutuntawa ta nuna mata kofar master room ɗinsa da hannun tana faɗin. "Ga ɗakinsa can shiga ki sanar da shi kin kawo mashi abinci". Idanu ta zaro, ɗan bakinta ya sha lips balm sai kyalli yake yi yana ɗaukar hankali, kamar zata sa ihu ta ce. "Mama Haulat tsoron shiga nike ji". Tabbas mama Haulat ta fahimci akwai tsoronsa sosai a ranta, matsawa kusa da ita ta yi, da hannu bibbiyu ta dafa shoulders ɗinta, cike da kaunarta ta ce. "Kina san Prince ko baki san shi?" Kasa ta yi sa kai ta gagara ba da amsa. Mama Haulat ta fahimci kunya ne da ita sosai kamar dai Jaish ɗin, dan haka sai ta ce. "Kada ki ji kunyata, ki ɗaukeni a matsayin mahaifiya, ina san ki faɗa mun kina san shi ko baki san shi". Ƙasa sosai ta yi da murya. "Ina san shi". Ta bada amsa kunya kamar ta shige cikin ƙasa. "To lallai in dai kina san shi dole ki tsaya tsayin daka domin yaki a kan abin da kike so, ki sani Prince ta ko'ina tarin masoya yake da shi waɗan da suke haukar san shi, yana da kyau ki sani tin da momma ta tsaya maki In Sha Allah zaki mallakesa, kada ki ji tsoron komai, ba zai dakeki ba, dan su basa dukan mata, kin gansu hakan nan suna girmama mace musamman ke da kike marainiya, suna da zuciyar tausayin maraya, zaki yi nasara sosai". Cigaba da kara mata kwarin gwiwa mama Haulat ta yi har sai da ta ɗan saki jiki ta aminta zata je, sannan ne ta saketa tana binta da kallo. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi bedroom ɗin nasa. Hannunta har rawa yake yi tasa hannu ta tura kofar tana haɗawa da ɗan siririn sallama ƙasa ƙasa. Tana sanya kafafunta a cikin ɗakin ta waro idanu waje, ya subhanallah ɗakin ya haɗu ne sosai, sai tashin kamshi yake yi. Baya cikin ɗakin, yana balcony yana waya da Jawad, Jawad ya je office ɗinsa bai same shi bane yasa ya kira waya ya tambayi ina yake, shi ne ya ce mashi ya dawo gida baya jin daɗi. Ji ta yi tamkar ta juya a guje ta bar ɗakin, sai dai kuma tana san sanya shi a idanunta, ta yi kewarsa sosai. A hankali ta fara ɗaga kafafunta ta ƙariso cikin ɗakin, a kusa da bed ɗinsa ta tsaya tana kallan yadda king bed ɗin nan ya haɗu. Kamar ance ta ɗan ɗago kai sai ta hangosa saman wasu ƙayatattun kujeru masu laushi da kyau dake wajen yana zaune yana waya. Subhanallah tsare shi da idanu ta yi tana kallansa ta cikin glass ɗin, shi baya kallanta saboda na waje baya kallan na ciki, na ciki ne zai iya kallan na waje. Tamkar yasan akwai mai kallansa ya kara juyowa da kyau yana fuskantar bedroom ɗin nasa. Lips ɗinsa kawai ta tsare da kallo tana tina lokacin da yake bata hot kiss a kauye, yanzu taga lips ɗin nasa su kara tura ja sosai sun ƙara kyau, da yake ya saba mata a baya sai ta ji tana kwaɗayin yi mashi kiss ɗin a yanzu, amma babu dama. Ta shagala da tinanin soyayyarsu a kauye bata ga miƙewarsa ya nufo dakin ba sai ji ta yi ance. "Lafiya? Wacece ke?". Ya yi maganar kuma kallansa a kan zanen flowers ɗin hannunta. A ɗan razane ta kyabta idanunta sau biyu tare da yin ƙasa da kai, a ɗan tsorace cikin sanyin murya ta ce. "Dama abinci ne na kawo maka". Tana matana tana satar kallan kayan jikinsa, ya yi makurar kyau sosai. Pj ne a jikin nasa masu silky launin milk color, kyawawan fararen kafafunsa suna cikin bedroom slippers ash colar mai laushin gaske. Kawar da kallansa a kan hannunta ya yi izuwa kan face ɗinta, dai'dai lokacin ta ɗago kai dan ta kalli meyasa ya yi shiru. Unexpext suka haɗa ido. Wani irin faɗuwar gaba ta ji ya dira mata, shi kuwa wani irin shock ya ji a jikinsa, lokaci guda ya ji tamkar ya san face ɗinta, ƙwaƙwalensa ce ta amsa mashi, kamar walkiya ya ji tamkar an ambaci hamma a cikin kwakwalwarsa, kamar yana san tina rayuwarsa a gidan bappa ɗin. Dik kunyar da take ji ta kasa iya zare idanunta a cikin nasa, shi ma ya kasa kawar da kallonsa daga kanta, yana jin ƙwaƙwalwarsa tana juyawa dama ga shi kansa na ciwo, bugu da kari yana bala'in san kwalliya, haba ai sai abin ya haɗe mashi, domin kuwa kwalliyarta ta fito sosai ta yi wani irin kyau na ban mamaki, ko iya kwalliyar kawai ya isa ya sanya ya kasa zare kallansa a kanta tun da yana son kyalliyar bare kuma ya haɗe da kyanta ga gyara da ta sha, sannan ga shi kamar ya san face ɗin. Ita kuwa Allah sarki soyayyarsa yasa ta mace da kallansa, ta yi kewan kayanta sosai. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ No editing😥 Ita kuwa Allah sarki soyayyarsa yasa ta mace da kallansa, ta yi kewan kayanta sosai. Abin ku da sun taɓa kasancewa masoya masu san junansu sosai a baya, kun san wannan abin ba zai taɓa barin zuƙatansu cikin sauki haka ba, shi kansa Jaish ɗin dik da ya dawo dai'dai ai soyayya ba karya bace, dole idan ya ga face ɗinta ko bai tinata ba zai ji a jikinsa kamar ya santa. Nisawa ya ɗan yi, sannan ya ƙara ɗaure fuska tamau kamar bai san me murmushi ba, a takaice ya nuna mata hanyar fita da hannunsa tare da furta out. Tabbas bata san ma'anar kalmar out ba, amma ta fahimci fita ya ce ta yi ta hanyar hannunsa da ya nuna kofa da shi. Tamkar zata sa kuka haka ta juya ta nufi hanyar fita. Kawar da kallansa daga kanta ya yi yana tinanin wacece ita da har momma zata sanya ta kawo mashi abinci? Idan baku manta ba dama shi bai kalli matar da momma ta sanar da shi mallakinsa bace, an dai ce mashi yana da mata, amma bai ga face ɗinta ba, so yanzu bai san ita ce wannan ƴar kauyen ba, ya fi tinanin ma daga cikin ƴaƴan ƴan uwan momma wato su uncle Rahab daga can ne ta zo ziyara momma ta aikota kawo mashi abinci. Siririn tsaki ya ja tare da hayewa bed ɗinsa ya kwanta, a ransa ya zayyana ba zai ci wannan abincin ba tin da momma ta aiko mashi wata. Hmmmm dama Jaish ai da wuyar sha'ani yake, kowa kuma yasan da haka, sai ka yi kamar zaka fahimci in da ya dosa sai ya sake watsawa mutum ƙasa a ido, ji abin da ya aikata yanzu fa, harda wani ba zai ci abincin ba. Da sauri Mahnoor ta isa ga mama Haulat, wani irin kuka ne ta ji ya kubce mata, dan yadda taga ya ɗaure fuskar nan dik da bata jin turanci sai taga kamar zaginta ya yi, abin ya ƙona mata rai. Tararta mama Haulat ta yi, sam bata yi mamakin ganinta ta fito cikin ɓacin rai har da guzurin kuka ba, dan ita tasan halin Jaish fiye da tinanin mai tinani, tasan dama ya yarda da Mahnoor cikin ƙankanin lokaci haka abu ne mai wuya gaskiya. So bata tambayi Mahnoor ɗin menene ya faru ba, kawai ta riko hannunta suka koma wajen momma. A saman bed suka isko momma ta kwanta tana tinanin duniya, Mahreen ta tafi tare da Chuchu da suka dawo daga school ba jimawa, momma ta ce ta bi Chuchu ta kara koya mata abubuwa. Momma na ganinsu ta miƙe zaune tana kallan Mahnoor dake sharar kwallah, dama tasan za'ayi hakan, kawai shahada ta yi ta gwada dama, to ba'ayi nasara ba. Mahnoor na ƙoƙarin durkusawa ƙasa momma ta yi saurin ce mata ta hauro saman bed. Ba musu ta zauna bakin bed tana cigaba da sharar kwallah. Rungumota momma ta yi tare da bin mama Haulat da kallo alamar tana jiran karin bayani. Girgiza kai mama Haulat ta yi alamar bata da masaniya a kan komai. Da hannu momma ta yi mata alama da ta tafi kawai. Cike da girmamawa ta amsa da to, sannan ta juya da sauri ta fita. Dawo da hankalinta kacokam a kan Mahnoor momma ta yi, cike da kauna haɗe da sigar rartashi ta fara tambayarta me ya faru?. Kamar ba zata faɗa ba, sai kuma ta daure ta ce ya koreta daga ɗakinsa. Ajiyar zuciya momma ta sauke, dama ta yi expecting hakan, so sai ta rarrashi Mahnoor har ta yi shiru, sannan ta ce. "Amma ba nace maki in dai ba a cikin ɓacin rai yake ba ko ya hantareki kada ki matsa kada ki damu ba?". Momma ta jefa mata tambayar. Cikin kuka ta ce. "Momma tsoronsa nike ji"........... Tabbas ta fahimci tsoronsa sosai take ji, dan haka sai ta shiga bata wasu dabaru ta yadda zata bi har Allah ya bata ikon shawo kansa. Ƙasa kunne ta yi tana saurara sosai saboda kaunar da take yi wa mijin nata, dik wasu shawarin momma ta naɗesu a cikin kwakwalwarta, momma bata jin kunyar nuna mata hanyar da ake bi dan maganin mazan gidan King ba, kun san ita ai ta kware, wannan hanya da take bi dan yin maganin King har ya amsa abin da bai niyya ba, shi ta zauna ta warwarewa Mahnoor komai tsab, daga karshe ta rufe mata da cewa in dai har tana san shi da gaske to ta jure ta bi dik shawarin da ta bata. In ta dage ta yi komai cikin nitsuwa tabbas yau Jaish ba zai zulle mata ba, dan rauninsu kenan. Kunya tamkar Mahnoor zata shige cikin ƙasa, ta yi ƙasa da kai kamar ba zata sake ɗagowa ba, sai dai da yake tana san Jaish, zuciyarta ruwan madarar albarka take kwaranyawa momma da ta jajirce a kansu. Momma kuwa, da bata ji kunyar komai ba har da cewa. "Zan yi magana da shi, kuma a daren yau, zan kira shi in sanar mashi da matsayinki a wajensa da kai'na, zan tayaki da yi mashi nasiha, daga karshe zan ce ya kama hannunki ku tafi part ɗinsa, ba zai yi mun musu ba, dan bai taɓa yi ba, tabbas zai karɓe ki idan na buƙaci hakan, amma ni da ke mun san ba dan ransa ya so zai yi hakan ba, dan haka ya rage naki sauran aiki, in kina san ransa ya so kuna shiga part ɗinku ki yi wanka a toilet ɗinsa, kada ki matsa ko nan da can, ki sanya ɗaya daga cikin kayan da zansa mama Haulat ta baki anjuma, ki shirya ki haye bed ɗinsa ki kwanta,kada ki damu da sai ya kulaki ya yi maki magana a daren, kada fa ki rusa mana shiri, kuma kada ki damu da dik abin da zai ce maki dan kin kwanta a bed ɗinsa, in kin kwanta ki yi gaggauwar rufe idanu dan ma ya zaci barci kike yi, tabbas ina da yakinin zai dawo gareki". "Sannan kada ki ji tsoron kwanciya a jikinsa idan har ya hau gadan, dik zafin kansa da kike ganin nan bai kai mahaifinsa a lokacin da yake matashi ba, so ni na faɗa maki dik zafin nan nasa ba zai iya taɓuƙa maki komai dangane da faɗa ko kyara ba a lokacin da zaki zo garesa, in dai kin bi dik tsarin da na tsara maki, lastly dik abin da zaki yi ki sanya nitsuwa a ciki, dik da naga kina da nitsuwa, amma ki kara, dan dik wani namiji yana san mace mai nitsuwa, nitsuwar tana jan hankalinsu sosai". Tsabar daɗin kalaman momma har ji ta yi tamkar ta jawo dare ya yi, a yanzu dai gani take yi tamkar zata iya aikata dik abin da momma ta ce, sai ta ji ta matsu lokacin ya yi, har ga Allah tana kewarsa, kuma ya saba mata da hot kiss kafin su yi barci a Jimeta, to yanzu babu, da kyar take iya yin barci, ga ɗamin jikinsa dik bata samu, kuma tana buƙata, sai ta ji tana buƙatar dare ya yi da wuri yau ta kwana a saman kirjinsa....... Wayyo my belly, Mahnoor is to much, love ya rufewa yarinyar nan idanu fa, Jaish ɗan duniya ne wlh, ya koyawa yarinya abu dan iskanci yanzu kuma ya ce bai san wannan ba, zaka yi bayani ne bari Queen Zarina ta aure samartakanka nan ne zaka gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah Sallallahu........😅 Momma ta karanceta tsab, dan akwaita da iya harbo jirgi mutun da wuri, tuni ta gano Mahnoor fa ita ma a hannu take tana san kasancewa da mijinta, ta ji daɗin hakan, ba ƙaramar dama hakan ya bata wajen kara karfafawa Mahnoor ɗin gwiwa ba. Sun jima a wajen suna hira har 1:30 na rana, sannan momma ta buƙaci da ta tashi suje lokacin sallah ya yi. Miƙewa ta yi ta fita ta nufi part ɗin mama Haulat. Momma na ƙoƙarin miƙewa ta shiga toilet sai ga mama Haulat ta shigo baki a ɗauke da sallama. Dakatawa momma ta yi haɗe da amsa mata sallamar. Zuba mata idanu ta yi tana jiran ta ji dame ta zo. Cikin girmamawa mama Haulat ta sanar da ita Jaish fa yaki cin abincin da aka kai mashi, da mama Haulat ɗin ta je ta sake kiransa a kan ya zo ya ci sai cewa ya yi ba zai ci ba, kada mama Haulat ta sake dawo mashi cikin ɗaki a kan wannan abincin. Jinjina kai momma ta yi tare da yi mata almar ta je kawai babu damuwa. Juyawa ta yi ta fice tana jinjina zuciya irin na yaran King. Toilet momma ta shige ta ɗauro alwala ta fito. Sai da ta yi sallah ta yi addo'inta sannan ta tashi ya nufi dry kitchen nasu, a nan ta sake shirya mashi simple things da zasu ɗan rike mashi ciki, ta ɗauka izuwa part ɗinsa. Tana shiga yana dawowa daga musque sanye da arab jallabiya milk color. Yana ganinta ya ɗan turɓune fuska tare da zama a saman sofa. Kasa saman sinfiɗar gashin jimmina dake parlourn ta ɗaura tray ɗin abincin, sannan ta koma saman sofa ta zauna suna fuskantar juna. Sai kallanta yake yi yana jiran ya ji me zata ce mashi. Sallamar Jawad ya katse maganar da take san yi mashi, so sai ta fasa faɗin abin da zata faɗa ta miƙe ta nufi waje tana faɗin su ci abinci to. Allah sarki Jawad ya kasa zama a office ɗinsa ne jin cewa Jaish bashi da lafiya, dik ya rasa sukuninsa har sai da ya dawo ya gansa. Kallon time a wayarsa Jaish ya yi 2:00 dai'dai yanzu, dawo da kallansa a kan Jawad ya yi. "Bro me ya dawo da kai by this time around?". Zama ya yi kusa da shi tare da kai hannu ya taɓa forehead na Jaish ɗin yana faɗin. "How's your body?".............. "Feeling better Alhdulillah" jinjina kai Jawad ya yi kafin ya ɗaura da cewa. "Ka tayar mun da hankali, all my tougth ciwon ya fi haka". Yana magana ya shafa goshin Jaish. "No ba wani ciwo bane bafa, is just only headache, and momma ta ce rashin cin abinci ya kawo shi". ............ Allah mai iko, gasu dai kamar twins, amma shi Jawad a kan lokaci yake cin abinci, shi kuma Jaish sam bai damu da ci ba, wani lokaci sai yunwa ta yi mashi over ya ji zai iya faɗuwa sai ku gansa ya ɗan ɗauko maltina ko wani drinks ɗin ya sha, dik gudun cin abincin ne fa. Jin haka yasa Jawad ya sauko ƙasa wajen da momma ta ajiye abincin. Buɗewa ya yi ya fara zubawa ɗan uwan nasa abin da ya dace da shi yana faɗin. "Since nike faɗa maka cewa sometimes yunwa zai janyo maka wani big problem ɗin, amma baka yarda, anyway come down and eat yanzu kam". Jaish bai yi wani gardama ba ya sauko kasan suka fara ci a tare cikin plate ɗaya, suna ci suna hira sama sama. 3:00 dai'dai har lokacin suna tare momma ta kira Jawad a waya a kan ya zo. Tashi ya yi cikin sauri ya nufi bedroom ɗinta yana sanar da Jaish ya kwanta ya huta even for one hour bari ya zo. Jinjina mashi kai kawai Jaish ya yi ba tare da ya yi magana ba, hayewa bed ɗinsa ya yi ya kwanta da nufin ya yi barci ko da na 30 mins. Sai dai kuma yana kwanciya tinane tinane suka cika mashi barin har da tinanin yarinyar da ta kawo mashi abinci a yanzu, haka kawai ya tsinci kansa da tinanin face ɗinta yadda ta tsare shi da idanu tamkar ta san shi, da tinanin yadda ta sha kwalliya har lallen hannunta yake fisgarsa gareta. Siririn tsaki ya ja tare da ƙoƙarin kawar da banzan tinanin a cewarsa, sai dai kuma tinanin taki tafiya, saboda idan baku manta ba dama ya ce kamar da akwai wani gurbi da yake ji a cikin zuciyarsa ya rasata, to zuciya kuma yau taga burbin da ta rasa ba dole ta takura mashi ba, ai ya yi ya yi ya dai'na tinanin yarinyar nan sai ya ƙasa. Daga karshe wayarsa ya ɗauko tare da miƙewa zaune a zuwan ya fasa yin barcin tin da wani banzan tinani ya sako shi a gaba. Balcony ya koma ya zauna ya shiga latsa wayar tasa bayan ya kunna data. Sai dai fa ko da ya koma balcony ɗin tinaninta yaki sakesa, dik abin da yake yi face ɗinta ƙwaƙwalwarsa take kwaso mashi, abin har ya fara ɓata mashi rai. A ɓangaren momma kuwa, magana ta sirri suka yi da Jawad har karfe 4 daidai ta cika, sannan suka rufe maganar tasu kowanne ya miƙe dan ya yi sallah, momma na miƙewa ta ce mashi kada ya manta ya turo mata Jannat ɗin fa. Da okey ya amsa mata tare da fita ya nufi wajen Jaish dan su tafi masallaci a tare. After some hours. Bayan sun yi sallar mangariba da isha'i. Momma da Chuchu ne zaune a saman bed ɗin Momma suna jiran mama Haulat ta kawo masu Mahnoor, sai hira suke yi irin ta uwa da ƴa cike da so da kauna. Sallamar mama Haulat ta dakatar da su a in da suka mayar da kallansu a kanta, tana rike da hannun Mahnoor dake sanye da kyakkyawan abaya mai shegen tsada launin army green. Ɗan zaro idanu Chuchu ta yi tana kallan Mahnoor, da yake shekarunsu kusan ɗaya sai girmansu ma yazamana ɗaya. Ƙasa shanye mamakinta Chuchu ta yi har sai da ta ce. "Momma wacece wannan?".... Da hannu momma ta nunawa Mahnoor gefenta da ta zauna, sannan ta buƙaci da mama Haulat ta basu waje kuma nan da 30 mins ta kawo mata alkyabbar Mahnoor zata kaita wajen King. Cikin girmamawa mama Haulat ta amsa sannan tasa kai ta fita. Haɗe Mahnoor da Chuchu momma ta yi a in da ta yi masu nasiha mai ratsa jiki da kyau, sannan ta tambayesu da ya ake yin wankan haila da na janaba?. Ita Mahnoor ta karanta wannan, amma kunya ya hanata faɗa, ita kuma Chuchu iliminta bai kai nan ba, so bata karanta ba, dikkansu biyu babu wadda ta fara period a cikinsu, shiyasa ma Chuchu bata nemi yadda ake yi ba. Ganin sun yi mata shiru ne yasa ta fahimci basu sani ba ne, dan haka sai ta ɗan yi gyaran murya kaɗan kafin ta fara magana kamar haka. "Wannan tambayace da yakamata ace kowacce mace tasan amsarsa, nasan yanzu mata dayawa basu san yadda ake yi ba, amma bari in yi maku bayani dan dayawan mata su karu". Shiru dai suka yi babu wadda ta yi magana, Mahnoor dai ta lura su fa ƴan gidan nan basa jin kunya kwata kwata, mijinta Jaish da guyson ne kawai masu kunya, su biyun nan ne masu kunya a ganinta.............. Lallai Mahnoor baki da kunya in ji ni princess Teema, wai har da uwar mijin nata ma bata da kunya kenan? Amma kuma fa gaskiya ta faɗa, ko shi Jaish daga ina ya samo nasa kunyar? Dan dai momma kam bata da shi, kada ku ce na ce na ce ɗin...........🥱 "Wanka a Musulunci yana da matakai daban daban bisa ga dalilin yin sa. Wankan Haila wanka ne da mace take yi bayan gama al'ada domin komawa cikin tsarki. Ga yadda zaku yi shi. Abu na farko niyya, a zuciya ki yi niyyar wanke jikinki daga haila zuwa tsarkin. Sannan sai bisimillah. Ki ambaci sunan Allah Idan ba a cikin banɗaki kike ba, dan ba'a ambatar sunan Allah a waje mai najasa, so in dai a ɓanɗaki ne no need for bismillah. Abu na uku wanke hannaye, ku wanke hannayenku sau uku. Abu na huɗu alwala. Ku yi alwala kamar yadda ake yi don sallah. Na biyar wanke kai. Ku jika gashin kai da ruwa sosai har ya gama jika. Abu na shidda shi ne wanke jiki gabaɗaya. Ki fara daga gefen dama, sannan ki wanke gefen hagu. Bayan kin kammala wankar zaki iya shafa sabulu mai kamshi ko turare a gefe gefen gabanki don kawar da warin haila. Ku lura da kyau wajen wanke gashin nan, Idan mace tana da gashin da ke tattare, ma'ana ta tsefe kai, to dole ta tabbatar da ruwa ya isa har fatar kanta, kunga kuwa sai ta jiƙa gashin sosai, a wannan gaɓar ana samun matsalar fahimta, wasu suna cewa sai mace ta tsefe kai zata yi wankar haila, to ingantaccen magana ba gashin kanta ake san ruwan ya taɓa ba, fatar kanta ake san ruwan ya jiƙa wanda idan bata tsefe kai bama tabbas sai ruwa ya fi shiga fatarta, dan haka ku lura da wannan". Tin da momma ta fara magana dik suka wani yi ƙasa da kai suna sauraronta da kyau, sai satar kallan Mahnoor Chuchu take yi, taga kyakkyawa ƴar gayu kamar ita. Cigaba momma ta yi da cewa. "Wannan shi ne wankar haila cikakke, shi kuma wankan janaba ana yin sa ne bayan saduwa ko mafarki (nocturnal emission.) Yana daidai da wankan haila, sai dai ba dole ba ne mace ta yi amfani da turare bayan sa. Shima matakan yinsa gasu nan kamar haka. Niyya, bisimillah, wanke hannaye sau uku, wanke al'aura, yin alwala, jika gashin kai da ruwa, wanke jiki gabaɗaya, wannan shi ne wankar janaba". Shiru suka yi, gara mah Mahnoor ta daure ta ce da momma sun gode. Ina fatan ba iya su Mahnoor bane kawai suka ilmantu da ilimin alkalamina? Allah ka kara mana ilimi mai albarka mai amfani ka sakawa iyayenmu da suka tsaya mana wajen ganin mun samu ilimi ingantacce wanda har jama'a suna ilmantuwa daga garemu, a koda yaushe ba zan gaji da cewa ku mun addu'a kowace iriya ce in dai na alkhairi ce a gareni ina kauna kuma zan ji daɗi sannan ina godiya Allah ya bar kauna, ni ko baki kaunata ma ki daure ki mun addu'ar alkhairi please. Chuchu ce ta tambayi momma wacece Mahnoor?. Cikin nitsuwa momma ta fayyace mata ita tsab, sannan ta ɗaura da cewa tana fatan zasu haɗa kai tamkar yadda Jawad da Jaish suke tamkar twins. Riko hannun Mahnoor Chuchu ta yi, fuska ɗauke da fara'a ta ce. "In Sha Allah momma muma zamu kasance tamkar twins kamar dai su Yah Jawad. Sosai momma ta ji daɗin furucin Chuchu, miƙewa ta yi ta nufi toilet tana faɗin bari ta yi wanka tana zuwa. Tana shiga toilet Chuchu ta dawo da kallanta a kan Mahnoor. "Ina fatan zaki ɗaukeni kamar twins sis ɗinki?". Ta tambaya tana kallanta. Jinjina mata kai Mahnoor ta yi tare da cewa In Sha Allah sun zama ƴan uwa. Ɗan rungumeta Chuchu ta yi tana faɗin. "Gaskiya kina da kyau sosai". Ɗan siririn murmushi Mahnoor ta saki kafin ta amsa mata da. "Kema kyakkyawa ce sosai ai". Sallamar Jawad ya katse masu hirar tasu. Da sauri Chuchu ta dawo da kallonta a kansa. Ganin shi ne yasa ta yi saurin sakin Mahnoor ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana murmushi. Rungumeta ya yi yana faɗin. "Shi ne aka barni aka zo wajen momma ko?". "Kai Yah Jawad, yanzu fa nazo kuma momma ɗin ce ta kirani". Jinjina kai ya yi kafin ya ce. "Nima momma ɗin ce ta tura mun text a kan inzo, ina take?". "Ta shiga wanka, Yah Jawad ga matar Yah Jaish fa". Ta yi maganar tana ɗan raba jikinta da nasa. Kai kallansa a kan Mahnoor ya yi, maganganun sirrin da suka yi da momma ɗazun ne kawai ya faɗo mashi a ransa, ƙaƙalo siririn murmushi ya yi ya sakar mata kafin ya ce. "Sannunki". Kasa ta yi da kai tana ɗaga mashi gaisuwa cikin girmamawa. Chuchu sarkin iya soyayya sai ta ce. "Mahnoor kin ji momma ta ce mu zama kamar twin irin Yah Jawad da Yah Jaish ko?". Gyaɗa mata kai Mahnoor ta yi alamar e ba tare da ta yi magana ba. "To wannan shi ne Yah Jawad ɗin da ake magana a kansa, shi ne twins ɗin mijinki, kuma shi ne mijina ni". ....... Dogon hancinta Jawad ya ja, kasa kaɗan ya yi da murya kafin ya ce. "Da gaske ni mijinki ne my Jannawad?". Ya yi maganar yana ɗaga mata gera guda. Dukan wasa ta kai mashi a kirji tana faɗin. "A'a ba kai bane". Hannun nata ya riko. "Sarkin rigima, zo mu je ki bani abinci yunwa nike ji". "Ka manta momma ta ce ka zo ne?". Ɗan jinjina kai ya yi. "Yeah na manta ne, to bari in jirata". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta suka koma saman sofa suka zauna. Shigewa jikinsa ta yi ta hau bawa flowers ɗinta ruwa. Sai datar kallansu Mahnoor take yi tana ayyana irin haka zasu yi da Jaish ɗinta idan ya fara sonta. Lokaci guda ta tina lokacin da suke Jimeta suke soyayya a gonar bappa, gabanta ne y faɗi dik sai ta ji babu daɗi. Jawad da Chuchu basu ji kunyarta ba suka cigaba da zuba soyayyarsu har momma ta fito daga wanka. Umarni ta ti wa Jawad a kan shi da Jaish su sameta a part na King nan da 20 mins. To okey ya amsa mata sannan ya miƙe ya fita. Dawo da kallanta a kan su Chuchu ta yi, ku shirya mu je wajen daddynku ko?. Ta yi maganar tare da wucewa dressing room ɗinta. Tana shiga mama Haulat ta shigo ya kawowa Mahnoor alkyabbarta, ita kuma Chuchu ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsu dan ta shirya da wuri. After some minutes, gabaɗaya sun hallara a gaban King, wato da Chuchu, Jawad, Jaish and Mahnoor. A nan ne momma ta sanar da Jaish wacece Mahnoor, ta kuma ce mashi ta bashi ita amana, ya sani marainiyace, kada ya yi abu domin ita mommar, dik abin da zai yi ya yi domin Allah y kuma duba maraicin yarinyar nan. Kunsan mutumin da kunya, dik abin da momma take faɗa yana jinta amma ya sunkuyar da kansa kasa kamar babu shi a cikin ɗakin. Haɗesu ta yi ta yi masu nasiha mai ratsa zuciya, ta tunatar dasu girman Allah, ta kuma tunatar da su cewa aure sunana ne na manzan Allah wanda ya fi kowani sunna girma da kima, ta kara jaddawa Jaish da ya kula da Mahnoor tsakaninsa da Allah, daga karshe ta rufe da cewa su wuce bedroom ɗinsu da matansu. Sai da ta gama maganarta tsab sannan King ya ɗaura nasa shi ma, cikin nitsuwa ya yi masu nasiha shi ma haɗe da karfafa masu gwiwa ya kuma ja kunnen Chuchu da Mahnoor a kan su yi wa mazansu biyayya, daga karshe shi ma ya rufe da su tashi su wuce bedroom ɗinsu. Miƙewa Jawad da Jaish suka yi a tare, suka wuce gaba Chuchu da Mahnoor suka rufa masu baya. Suna tafiya King ya dubi momma dake zaune a bakin bed ɗinsa. "Na bawa matar Jaish kwautan kujerun makka guda biyar, idan kin je Jimeta ki sanar da iyayenta da wanda ta zaɓa su shirya bana su je Makkah, sannan ina da special kyauta a gareta a matsayina na mahaifi a gareta, akwai kyautar gaisheni da ta zo ta yi zan bata sai kun dawo daga Jimeta". Matsawa momma ta yi jikinsa, ta kwantosa tana zuba mashi godiya, kamar jira dama yake yi haba ai sai ya fara al'amura. 🔥🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥🔥 Cike da tashin hankali Abbie ya bi bayan Ummie dan ya dakatar da ita daga aikata kudurinta. Sai dai ina kafin ya fito parlourn har ta fice. Cikin zafa ya taka da sauri sauri ya bi bayanta. Tana cab zata shiga part ɗin su Ramish ya kwala kiran sunanta. Tana jin ya kirata ta yi saurin rugawa ta afaka cikin part ɗin su Ramish. Allah sarki dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi ya yi, sai ya ji kamar in da yake tsaye ta yi wani irin juyawa da karfi, nan take ya ji kamar zai faɗi. Dafe bango ya yi ya fara bin jikinta ya juya izuwa part ɗinsa. Ita kuwa Ummie, sai da ta shiga cikin part ɗinsu sai ta rasa me zata ce masu ne ma, ta ce su zo suga ta kama Abbie da wata mace nan kuma Ramish ya dallah mata mari kafin ya yi yunƙurin zuwa, dan tasan halinsu sarai, to ya zata yi ta ja su izuwa part ɗin Abbie su ganewa kansu? Ta jefawa kanta tambayar. Tana tsaye a tsakiyar parlourn tana tunane tunane sai ga Ramish and Bilal sun fito a lokaci guda, suna shirye cikin arabs jallabiya zasu tafi musque. Sun ɗan yi mamakin ganinta a part ɗinsu da asuba haka, Ramish dai ya yi kamar bai ganta ba ya zo zai wuceta, Bilal ne ya tsaya tambayarta me take yi a nan?. Dai'dai lokacin su Dr Raj ma suka fito da sauri, suma tsayuwa suka yi dan ganinta a nan. Tashin hankali ne ya bayyana a tattare da ita, kame kame ta fara yi masu, can kuma wani idea ya faɗo mata, da sauri ta ce masu su je part ɗin Abbi yana nemansu abu ne na gaggawa. Basu tsaya tambayarta me yake faruwa ba, dan tun dq suka ganta a nan da wannan lokaci sun san ba lafiya ba, dan haka suka yi zafin namar nufar part ɗin Abbie. Already dama shi Ramish da bai tsaya kulata ba can ya nufa, saboda ya saba zuwa wajen Abbie da asuba su tafi masallaci a tare, so sai ya nufi can. Wani irin daɗi ta ji ganin sun nufi part ɗin Abbie, har da tsalle ta daka tana murmushi, sai kuma lokaci guda ta nitsu tare da wucewa da sauri ta rufa masu baya tana ayyana yadda zakunan samarin Abbie zasu yi kaca kaca da Leesharh, dan in dai suka sameta a haka kasancewarsu musulmai ne kawai zai hana ba zasu cinye namarta ɗanya ba. Suna shigowa suka tsaya cirko cirko kamar waɗan da aka dasa, kallan Abbie suka tsaya yi, Ramish yana rike da hannunsa yana tambayar meyasame shi jikinsa dik jini haka?. Abbie zai yi magana ganinsu Bilal da Ummie sun shigo yasa ya yi shiru, Ramish ya lura da Abbie baya san yin magana a gabansu dan haka sai ya ce masu su je masallaci zasu biyosu daga baya. Ummie kuwa hankalinta a tashe t fara bin gadan Abbie da kallo tana zaro idanu, babu Leesharh babu alamarta a saman bed ɗin, abin ya bata mamaki. Abin da bata sani ba shi kansa Abbie mamaki yake yi haɗe da tambayar kansa ina Leesharh ta shiga, domin kuwa lokacin da ya bi bayan Ummie domin ya bata hakuri kada ta kira su Ramish, kafin ya dawo ne Leesharh ta bar bedroom ɗinsa, da y dawo ɗakin bai sameta ba. Tambaya ɗaya yake yi shi ne ina take ya aka yi kuma ta bar bedroom ɗinsa? Yana shigowa da bai sameta a saman bed ba ya fara nemanta har cikin toilet, sai dai da gaske babu ita babu labarinta a cikin ɗakin, hankalinsa ne ya yi mummunar tashi, dan yana ganin kamar waɗan da suka yi ƙoƙarin cutar da ita a farko ne suka zo suka ɗauketa, abin da zai sanar da Ramish kenan, zai sanar mashi da ya biyan Leesharh bedroom ɗinta ya duba mashi menene ya sameta, bai kai ga yin hakan ba su Ummie suka shigo, shiyasa ya yi shiru?. To ina Leesharh? Waye ya ɗauketa?. "Babu wata matsala?". Cewar Bilal. "Yeah babu zaku iy tafiya zamu biyoku daga baya". Ramish ya faɗa idanunsa a kan Abbie yana kallan tashin hankali a cikinsu. Dr Raj ne ya ce. "Yah Ramish jini ne fa a jikin Abbie kuma ka ce mu tafi?". Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Juyawa suka yi suka nufi hanyar fita, ɗakin ya rage daga Ummie da ta yi mutuwar tsaye, sai Abbie and Ramish. Da wutsiyar ido ya wurgawa Ummie kallo, nan take ta sha jinin jikinta, tin bai yi magana ba ta yi saurin wucewa ta fita waje tana mamakin da al'ajabin ɓacewar Leesharh a ɗakin haɗe da bakincikin burinta bai cika ba, ta so su Bilal su yi kaca kaca da ita, amma Allah ya tsallakar da ita, ciza laɓɓanta ta yi tare da furta akwai gaba ai, wato bata janye kudurinta ba kenan. Me Abbie zai sanar da Ramish? Me zai faru? Ina Leesharh? Waye ya ɗauketa? Dik a gaba zaku ji. Magana suka yi na tsawon 30 mins, sannan Ramish ya fita daga bedroom na Abbie ya nufi bedroom ɗin Leesharh. Da shigarsa bai fi 10 mins ba ya fito ya koma part na Abbie. Jim kaɗan suka fito a tare da Abbie suka nufi masallaci. Yau saɓanin kowacce rana da suke dawowa da wuri, yau sai karfe 9 na safe Abbie da Ramish suka dawo cikin gidan, koda suka dawo kuma part na Abbie suka wuce, nan suka zauna suka cigaba da tattaunawa, da alama wani bincike suke yi a sirrance, ko Ummie basu bari ta sani ba. After some hours. Da misalin karfe 4 na yamma, katafaren hall ɗin da zasu yi taro ya cika makil da jama'a, taro ake gudanarwa bisa ƙaida, doka da girma, dik wasu manya masu ji da kansu a faɗin Dubai sun hallara a cikin wannan taron. Abbie yana zaune tare da Ummie a saman wani haɗaɗɗun kujeru da aka tanadawa familyn King Badeen, su Dr Raj dik suna gefensu except Ramish da yake saman stage yana speech cikin harshen larabci. Sharifat tana zaune a tare da Leesharh waje guda, sun yi shiga iri ɗaya, bakin Leesharh ya ɗan kumbura haka zalika goshinta ma ya ɗan kumbura, tana sanye da face mask a face ɗinta, sannan yi rolling veil ɗinga har ya rufe mata ciwon nata da aka sanya mata white bandeji a wajen. Waye ya yi wa Leesharh dressing na ciwukanta? Ya aka yi hakan ta faru? Me Abbie da Yah Ramish suke shiryawa? Dik kada ku damu zan warware maku komai, ku dai mu je zuwa. Miƙewa Leesharh ta yi, cikin sanyin murya ta ce da Sharifat zata je toilet tana zuwa. Da okey Sharifat ta amsa mata, sannan ta ɗaura mata da cewa ta kula. Jinjina kai kawai ta yi. Hall ɗin cike yake da manya manyan jami'an tsaron, securitys ta ko'ina, tsaro ya yawaita sosai a wajen ne saboda Abbie da yake matsayin ministan tsaron sannan ga manyan jami'ai irinsu Ramish a wajen. Wani keɓaɓɓen waje Leesharh ta je ta samu domin amsa call ɗin masu nikaf da suke ta kiranta tun ɗazun, dama ba wani toilet da zata je, call take san ɗagawa. Filin da ta je a cikin wajen taron ne, amma ta baya wajen wasu ɗakuna da babu kafar mutane a wajen. Ciro wayarta ta yi daga cikin hand back dake hannunta kalar abayar jikinta wato maroon color, ta yi kyau sosai. Tana ƙoƙarin yin picking na call ɗin ta tsinkayo muryar mutane daga ɗaya daga cikin ɗakin dake bayanta suna magana kasa kasa. Fasa ɗaukar kiran ta yi a in da ta ƙasa kunne take sauraransu. Zaro idanu sosai ta yi a lokacin da ta ji suna shirya shirin yadda zasu harbi Ramish, dik yadda aka yi sun riga masu taron shiga wannan hall ɗin, sosai Leesharh ta yi mamakin jin maganganunsu, tasan dai a yadda wannan hall ɗin yake wlh idan ba da wani na jikin family ba babu wanda ya isa ya shigo nan wajen, saboda tsaron da aka zuba ko tsuntsuwa bata isa ta gifta a wajen ba ba tare da an harbeta ba, to ta ina waɗan nan mutane suka shigo wajen?. Yanzu ta kara tabbatarwa tabbas da sa hannun na gida a shirin kashe Ramish, tabbas dole da sa hannun na gida, to waye? Ta jefawa kanta wannan tambayar. Taba tsaka da tinani ta ji ana ƙoƙarin buɗe kofar a fito. A a miliyan ta watsa ta bar wajen ta yi baya, a bayan wasu curtains dake wajen wasu windows kusa da wajen ta ɓuya, a hankali ta ɗan buɗe curtains ɗin tana leƙo kanta dan taga su wanene zasu fito daga cikin ɗakin, daga in da take tana iya gano kofar ɗakin. Wasu maza ne su biyu suka fito cikin shigar three-piece suit launin ash mai haske, fuskokinsu dik sanye da face mask sannan hannayensu rike da sillent pistol gun, kafafunsu na cikin cover shoes na maza, sun yi shiga irin dai shigar dik wasu manyan baki da suka halacci wannan yaran, sun saje da mutane kenan. Mamaki ne ya kamata ganin zanen dake wuyarsu na scorpio, shiru ta ɗan yi taba tinanin a in da ta taɓa ganin irin wannan zane a gidan Abbie, tabbas akwai mai irin wannan zane a gidan Abbie, to waye?. Tana tsaka da tinani sai ta ga sun sa kai sun nufi wajen taron. A hankali ta lallaɓa ta fito ta rufa masu baya, tana tafiya kirjinta na dukan uku uku, a dai'dai wannan lokacin ƙwaƙwalwarta ya tunano mata tabbas wanda ya kawo mata hari daren jiya ma yana da wannan zane a wuya! And bayan shi akwai wani mai irin wannan zanen a gidan. Cigaba da bin bayansu ta yi ƙwaƙwalwarta yana tinano mata abubuwa kala kala da ya danganci abin zargi a gidan Abbie. Tabbas Hajiya two seater ma tana da wannan zanen, hakan na nuni da zanen na kungiyarsu ce kenan? Ko dai yaya?. Sake tunawa ta yi Ummie ta taɓa yin wani bakon matashi mai irin wannan zanen a wuya, babbar magana. Binsu ta yi har zuwa cikin hall ɗin, tana ganinsu suka koma can baya wajen da ba mutane sosai, a nan suka zauna. Jikinta na rawa ta haura saman stage da Ramish yake, dik da tana shakkarsa tana tsoronsa amma ba zata iya bari a kasheshi ba, dole ta je ta sanar da shi, da sauri ta nufi in da yake. Sai dai bata kai ga isa wajen ba wasu jiga jigan jami'ai guda biyu suka tareta, dama suna saman stage ɗin suna tsaron Ramish ɗin ta both sides ɗinsa dikka, so ganinta yasa suka bar wajen suka je suka tareta. Sai maganarsa yake yi cikin kwanciyar hankali ba tare da ya kalli in da take ba, yana ji dai jami'ansa suka ce ta koma ƙasa ba zata samu damar yin magana da shi ba, ita kuwa saboda karfin hali sai ta ce masu ita dole tana san yin magana da shi yanzu, tana yi masu magana tana kallan waɗan can mutane su biyun. Hankalin jama'a ne gabaɗaya ya koma kanta, ta jajirce wai ba zata bar wajen ba, kuma tsoronsu kamar ya kasheta, amma ta ce ba zata bar nan ba har sai sun barta ta isa garesa. Zaro idanu Sharifat ta yi tana kallanta, shi ma Abbie kallanta kawai yake yi. Ganin hankalin jama'a dik ya koma kanta yasa waɗan can mutane suka ga sun samu damar harbin Ramish a yanzu, dan haka sai suka ciro bindigarsu cikin dabara, ga face mask a face ɗinsu saboda sun san akwai cameras a wajen. Saita saitin zuciyar Ramish suka yi, Leesharh tana ganin sun saita zasu yi harbi ta yi kukan kura da gudu ta keta tsakiyar jami'an, cikin zafa suka rufa mata baya dan su kamata, ita kuwa tana zuwa ta daddage da ita karfinta ta ture Ramish daga wajen da yake tsaye bullet ɗin da wadan can suka harbo ya sameta a kirjinta pass. Shi kuwa Ramish gefe ya yi ya faɗi kasa saboda bai wani kame jikinsa ba a lokacin da yake tsaye a wajen. A take Leesharh ta zube ƙasa jini na malala a kamar hanyar ruwa. A zabure Abbie ya miƙe tsaye, jama'ar dake wajen ne suka kiɗime. Cikin abin da bai gaza second talatin ba jami'ai suka kewaye saman stage ɗin, su kuwa waɗan can mutane biyun jami'ai suka nufesu da nufin su kamasu, sai dai me, basu kai ga isa wajen ba mutanen suka miƙe tsaye tare da ɓalle botirin suit ɗin jikinsu, nan take rigar bomb ya bayyana a jikinsu. Cike da barazana suka ce dik wanda ya motsa to zasu tashi wannan waje, so basu damu da rayuwarsu ba, a shirye suke da su mutu, dan haka kowa ya nitsu a sauraresu a kuma basu abin da suke so ko kuma kowa ya mutu. To ni dai ba za'ayi wannan mace macen da ni ba, bari na haɗa kayana na je zuwa gidan baby da Ammo in sha maltina mai sanyi a can ko na huce takaicin mutuwar Leesharh. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 🔥🔥🔥BABYN BABY🔥🔥🔥 Safiyar yau dik jikinta a mace ta farka daga barci, kamar wadda aka jibga gaɓɓanta gabaɗaya ciwo suke yi mata. Da kyar ma ta iya tashi daga barci, sai da Ammo ta matsa mata, kuma tana da Exams in baku manta ba. Saukowa kasan bed ɗin ta yi ta nufi toilet tana hararar Ammo da ta tasheta, ita a dole ranta ya ɓaci. Wanka ta shiga ta yi, sannan ta fito a gurguje ta hau shiryawa, a lokacin har 7:30 ya yi. Sai da ta kammala shiryawa tsab, sannan ta dawo bakin bed ɗinta ta zauna. Sai tashin kamshi take yi. Wayarta ta ɗauko tare da kunna wutar screen ɗin, a gaggauce ta cire password ɗin da nufin ta yi kira, sai kuma ta ga massage da aka turo mata tin karfe 5 na asuba. Baby shi ne sunan da aka yi saving number wanda ya turo wannan sakon. Lokacin guda wani ƙayataccen murmushi ya kubce mata, a hankali ta danna kan massage ɗin ta buɗe cike da matsuwar san ganin me aka rubuta. "Good morning, my love. Waking up every day with the thought of you in my heart is a blessing beyond words. You are the light that brightens my world, the melody that soothes my soul, and the dream I never want to wake up from. This morning, I just want to remind you how deeply I adore you. Your smile is my sunshine, your voice is my favorite song, and your love is the air I breathe. May your day be as beautiful as your heart, as radiant as your smile, and as peaceful as your embrace. I love you more than words can say. Have a wonderful morning, my queen!". A karshen sakon sai ya sanya mata emojin heart da na kiss guda bibbiyu. Shi ne abin da saƙon ya ƙunsa. Tin da ta fara karanta saƙon nan take sakin cool murmushi, wani irin sanyi ta ji yana ratsa zuciyarta, kaunarsa yasa har ta mance da abin da ya faru daren jiya, nan take kewarsa ya kamata. Danna kan reply ta yi domin ta mayar mashi da martani. Rubuta sako kamar haka ta farayi tana yi tana murmushi mai ƙayatar da mai kallanta. "Good morning, my baby. Waking up to your sweet words fills my heart with warmth and joy. You are my sunshine, my peace, and the love that completes me. Every moment with you feels like a beautiful dream I never want to end. Knowing that I have your love makes my world brighter and my heart lighter. I cherish you more than words can express, and I can't wait for the day when I can wake up beside you every morning. I love you endlessly. Have a wonderful day, my baby!" A karshen rubutun ita ma sai ta sanya emojin heart dana kiss guda bibbiyu kamar nasa. Kewarsa da zumuɗin daɗaɗan kalamansa ya ja ta rubuta mashi wannan reply ɗin ba tare da ya mayar da hankalinta a kan kalaman da ta zuba, sai ya yi mata kamar sarauyinta zata rubutawa, bata ma sake bin sakon ta karanta ba kawai ta tura mashi. Tana turawa ko minti ɗaya ba'ayi ba sai ga call ɗinsa ya biyo baya, ta yunkura zata tashi kenan sai ga kiran nasa ya shigo. Cike da zumuɗi ta koma ta zauna tare da yin picking na call ɗin. Kara wayar a kunnenta ta yi, cikin sanyin murya ta ce Hello baby. Daga cikin wayar ta ji saukar ajiyar zuciyarsa, sai da ya ɗan yi gyaran murya saboda ɗan saisaita voice ɗinsa da ya sarkafe saboda daɗin kalamanta kafin ya ce. "Sai yanzu kika tash daga barci ko?". Kai ta gyaɗa kamar tana a gabansa, sannan ta bisa da e. "Menene ya dawo mun dake haka ne baki tashi da wuri?". Shiru ta ɗan yi ta rasa abin faɗe. "Kin shirya tafiya school ne?". Ya katse mata shirun. Kai ta gyaɗa tana haɗawa da e ta shirya. "Ina zuwa yanzu in kai ki, wait for me"....... Mamaki ne ya kamata, bai taɓa kaita school da kansa ba, to why yau ya zaɓi kaita da kansa? Ta jefawa kanta tambayar, tana can tana tunani bata san time da ya katse kiran bama, sai kawai ta ji shiru. Miƙewa ta yi ta fito parlon ɗauke da school back ɗinta a hannunta. Already an shirya mata breakfast ɗinta da komai da komai, so tana fitowa ta haye saman table ta fara cin abincinta cikin nitsuwa. Bayan ta kammala ta goge bakinta da tissue, sannan ta nufi bedroom ɗin Ammo dan su ɗan yi hira kafin ya zo. Bata kai ga shiga ba ta tsinkayo kamshin perfume ɗinsa alamar ya nufo parlourn kenan. Da ƴar gudunta ta juyo ta isa bakin kofa ta laɓe tana ƙunshe dariya. Yana sako kai unexpext ta saka ƙara wai dan ta bashi tsoro. Ko kaɗan bai tsorata ba, sai ma binta da kallan mamaki ya yi. Turɓune fuska ta yi shagwaɓar ta motsa, kamar zata yi kuka ta ce. "Baby, why didn’t you get scared? Do I look like someone who wouldn’t scare you? Is that why you refused to be scared? Well, you’ve disappointed me". She finished her words and turned to head toward Ammo’s room. Quickly, he grabbed her hand and said, "You’re just too dramatic. Alright, I’m sorry. Next time you scare me, I’ll act scared. But for now, time is up, and you’ll be late for school. There’s no time for games. Just go and inform Ammo that we’re leaving". He finished his statement as he released her hand. "Do you promise that next time if I scare you, you’ll act scared?". She asked, pouting. He nodded in agreement. Aminta da hakan ta yi, sannan ta nufi room ɗin Ammo. Da kallo ya bita yana jin wani irin kifiya na santa yana kara cakar kahon zuciyarsa. Yana tsaye a wajen har suka fito a tare da Ammo. Cikin mutunta juna suka gaisa shi da Ammo, sannan ya riko hannunta yana yi wa Ammo sallama suka fice daga gidan. Su kansu drivers da suke kaita school sun yi mamakin ganin ogan nasu zai kaita school da kansa yau, sai dai basu ce komai ba suka bisu da fatan alkhairi. Gidan gaba na motarsa ta shiga, ya shiga mazaunin driver, idanunsa a kanta ya tada motar, da alama fa da gaske ta manta abin da ya faru daren jiya. Da ɗan madaidaicin gudu ya ja motar suka nufi waje. Shiru ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar tana tinanin Exams da take da shi, bata ankara ba sai ji ta yi ya kashe motar. Da sauri ta ɗago kanta ta kalli hanya, tabbas basu iso school ba, bakin wani katafaren super market suka tsaya. Dawo da kallanta a kansa ta yi. Ita yake kallan shi ma, ta buɗi baki zata yi magana ya rigata da cewa. "Wait for me am coming". Ya kai karshen maganar tare da buɗe kofar motar zai fita. Da sauri ta riko hannunsa, hakan yasa ya juyo gareta. "Baby ka saya mun chocolate ga ji? Kullum idan na ce ka saya mun baya saya mun sai ka ce cikina zai yi ciwo, ba zan sha dayawa bafa". Lips ɗinta kawai ya zubawa idanu yana kallan yadda take magana, bai san ko da ya furta. "Ni da kayana amma am mun shamaki da shi". Bai san ya faɗi hakan ba sai da ya ga ta zaro mashi idanu, nan ne ya fara tinanin wai shin me ma ya faɗa ne?. Gudun kada ta jefa mashi wata tambayar yasa ya yi saurin janye hannunsa daga riƙon da ta yi mashi ya fice waje. Yana ji tana ambatar sunansa yaki dakatawa, dan ya yi suɓul da baka. Turo baki ta yi a fili ta ce na yi fushi da kai, ba zan sake yi maka magana ba. Mai da kanta jikin kujerar ta yi ya kwanta tana turɓune fuska. Good 20 mins ya ɗauka a cikin wajen kafin ya fito, tana ganin ya doso motar ta kara turɓune fuska tana harararsa. Bayan mota ya zo ya buɗewa yaran super market ɗin suka jibge mashi niki nikin kayan da ya saya, sannan ya dawo ya shiga gidan gaba. Kunna motar ya yi da gudun gaske suka nufi school, dan ta yi latti. Dik bayan minti sai ya juyo ya kalleta, tabbas ya fahimci fushi take yi da shi, amma bai kulata ba saboda saurin da suke yi. Bai dakata a ko'ina ba sai a cikin katafaren parking space na school ɗinsu, yana yin parking ya sanya hannu a gidan baya ya ɗauki ƙaramin lada daga cikin shopping da ya yi ya miƙa mata. Kin karɓa ta yi a in da ta sanya hannu zata buɗe kofar motar ta fita, ita dai ta yi fushi da shi. Zuba mata ido ya yi yana kallanta har ta buɗe kofar ta fita, bai hanata ba kuma bai yi magana ba, cikin nitsuwa ta fara takawa ta nufi barin parking space ɗin, ko kyafta idanu daga kanta ta gagara yi, kallanta kawai yake yi. Sai da ta ɗan yi nisa, sai kuma ta dakata cak da tafiyar tata, da sauri ta juyo garesa, ganin ita yake kallo yasa ta yi saurin dawowa garesa. Yana dai kallanta bai motsa ba, ta side ɗin da yake ta zo ta buɗe kofar motar tana huci irin na shagwaɓa. A saman laps ɗinsa ta zauna, hannu tasa ta ja dogon hancinsa da karfi har sai da ya furta wash, ƙara ja ta yi tana faɗin. "Shi ne ba zaka rarrasheni ba, kuma kasan na yi fushi, amma shi ne kake kallona zan tafi baka rarrasheni ba ko? To ba kai ka ɓata mun rai bane?". Daga ganin idanunsa zaka fahimci yana cikin yanayi, dik jikinsa a mace, idanunsa sun sauya sun yi ja, sai faman lumshe su yake yi, da kyar ya iya riko hannunta da take ta faman jan dogon hancinsa da shi, can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Ba zaki iya yin fushi da babynki ba ai, shiyasa na zuba maki idanu ina kallanki, na san zaki dawo ai rigimamma kawai". Ya kai karshen maganar yana janyota ta faɗa saman kirjinsa. "To yanzu na bada hakuri kuma na yi rarrashi, baby ya bada hakuri ko?". Ya sake faɗa ƙasa ƙasa yana kallan face ɗinta. "Ni wannan hakurin ya mun kaɗan, sam ban yarda ba, sosai zaka rarrasheni". A shagwaɓe ta yi maganar. Kamar mai raɗa ya ce. "To na yarda rarrashin ya yi kaɗan, kuma zan yi mai yawa, amma sai kin dawo daga school, anjuma da daddare zanzo sai na yi rarrashi mai yawa kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana ɗan shafa bayanta. Ɗago kanta daga saman kirjin nasa ta yi. "Promise me first!". Ta yi maganar tana miƙo mashi tafin hannunta. Ɗaura nasa tafin hannun a saman tata ya yi, sannan ya ce. "I promised you that zan zo da daddare in yi rarrashi mai kyau". Siririn murmushi ta saki tare da matsawa kusa da shi ta manna mashi sumbata a lallausan kumatunsa, ƙasa ƙasa ta ce mashi take care, sannan ta yunkura zata fice daga cikin motar. Rikota ya yi jikinsa dik a mace, a hankali ya ɗan matseta a jikinsa kafin ya matsar da face ɗinsa dab da ita. Sumbata ya bata a kumatu shi ma yana mai faɗa mata ta kula da kanta sosai. Daga haka ya ɗauki ledar chocolate ɗinta na ɗazun da taƙi karɓa ya miƙa mata yana kallanta. Karɓa ta yi da sauri ta fito daga cikin motar, da kallo ya bita tana tafiya har sai da ta kurewa ganinsa, sannan ya sauke ajiyar zuciya tare da dawo da kallonsa ga makunnin motar. Da kyar ya iya tasarta ya nufi gida wajen Ammo da shopping ɗin da ya yi. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Gabaɗaya hall ɗin tsit suka nitsu saboda tsoron bomb ɗin, gabaɗaya yawan jami'an dake wajen sun tsaya cak, kowannensu idanunsa a kan Ramish dake kasa ya kasa ɗago kansa, saboda wani irin ɗaci da ransa ya yi mashi. Bilal yana tsaye a kusa da Abbie, saboda ya razana shi ma ya miƙe tsaye kafin mutanen can su yi barazana da bomb ɗin. Wani irin tsawa mutanen suka daka a kan wai Ramish ya miƙe tsaye, har da cewa shi kaɗai suke da buƙata a taron nan, su basu zo nan da nufin su cutar da kowa ba, shi suke san ɗauka, in yana san cetan ran jama'arsa to dole ya tashi ya bisu. Ajiyar zuciya Ramish ya sauke kafin ya yunkura ya miƙe tsaye. Yana miƙewa suka sake daka mashi tsawa a kan ya sauko kasan stage ɗin ya ƙariso gabansu ya zube gwiwowinsa a ƙasa..... Babban magana!!. Ko kaɗan bai damu da abin da suke faɗe ba, hankalinsa bai tashi ba. Slowly ya kai kallansa a kan Leesharh dake kwance jininta na zuba tamkar an buɗe hanyar ruwa. Ta wutsiyar idanunsa ya kai kallansa a kan Bilal wanda shi ma shi yake kallo. Blinking eyes ɗinsa Ramish ya yi sau biyu, da alama magana ce tasu ta jami'ai, dan kunsan suna karɓar irin wannan horo ta magana da gaɓɓan jikinsu saboda shiga matsala irin wannan sai su yi magana ba tare da sanin kowa ba su fahimci junansu. Jinjina kansa Bilal ya yi tare da dunkule hannunsa sai ya sake warewa. Yana warewa Ramish yasa hannu cikin zafa a aljihun Suit ɗin jikinsa kafin kowa ya ankara ya zaro pistol gun, a tare suka zaro shi da Bilal. Mutanen suna ganin haka sai suka yi ƙoƙarin danna bomb ɗin su kunna, sai dai kafin su yi motsi Bilal da Ramish suka harbesu a tare lokaci guda, Ramish ya harbi ɗaya Bilal ma ya harbi ɗaya a goshinsu. Tare suka zube ƙasa, ashe kallan da Ramish ya yi wa Bilal maganar da suka yi kenan, abin da yasa suka yi haka kuma shi ne idan Ramish shi kaɗai ya ce zai harbesu kafin ya harbi ɗaya ya sake harbin ɗayan to ɗayan zai kunna bomb ɗin, dole a tare za'a harbesu idan ana san kowa ya tsira. Suna harbinsu gabaɗaya jami'an dake wajen suka yi kansu da gudu dan su duba bomb ɗin a kunne yake ko a kashe yake. Mayar da gun ɗinsa cikin aljihunsa Ramish ya yi, juyawa ya yi ya da nufin ya isa ga Leesharh kamar walkiya haka Bilal ya rigasa isa gareta. Bata numfashi kamar rai ya yi halinsa ne. Cak Bilal ya ɗauketa jami'ai uku suka rufa mashi baya izuwa wajen motocinsu, shi kuma Ramish ya haɗa kan family sannan ya bawa jami'an su umarni da su wuce mashi da waɗan nan mutane h-q zai bi ta kansu amma ba yanzu ba, bari ya gama da case dake gabansa na Leesharh tukun nan, zuwa anjuma idan ya tabbatar da Leesharh bata mutu ta dalilinsa ba zai zo ya binciki mutanen. Hankalinsa ya tashi sosai, ya kuma yi mamakin yadda aka yi Leesharh tasan za'a harbesa har ta sadaukar da nata ran a kansa! Dik yadda aka yi tasan wani abin, dan haka in dai bata mutu ba zai tsaya ta samu lafiya ko dan ya samu wasu amsoshi daga bakinta. Kunsan dik taurin zuciyar mutum in dai aka yi mashi irin sadaukarwar da Leesharh ta yi mashi wlh dole zuciyarsa ta raunata ta kuma sassauta, to shi ma hakan ne, sai da ya ji wani iri a ransa, tambaya ɗaya yake yi wa kansa shi ne meyasa Leesharh ta bada ranta ta ceci shi?. Wannan ne babban damuwarsa. Haɗa kan family ya yi suka nufi gida. Da gudun gaske motocinsu suka danna cikin gida, sai kuka Sharifat take yi kamar ranta zai fita, ta shiga damuwa da tashin hankali sosai. Ummie kuwa addu'a kawai take yi Allah yasa Leesharh ta mutu. Suna shiga gida tun motocin basu gama yin parking ba Bilal ya fito da gudu ya buɗe gidan baya ya ɗauko Leesharh a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa Ramish da Dr Raj suka rufa mashi baya, dan su dubata. Da sauri shima Abbie and Sharifat suka fito suka rufa masu baya. Kai tsaye a&e ɗinsu suka nufa da Leesharh. Hankalin Bilal idan ua kai miliyan a tashe yake a zahiri, amma bamu san me yake a cikin ransa ba, shin tashin hankalin me ma yake yi, yana damuwa Leesharh ta mutu ne ko kuma yana damuwar ta bada ranta ta ceci Ramish? To wannan dai dik bamu sani ba. A tare Dr Raj da Ramish suka shigo cikin room ɗin. Bilal yana ƙoƙarin sanya karfi ya yage rigar jikin Leesharh Ramish ya dakatar da shi. Da mamaki suka dawo da kallonsu a kan Ramish ɗin. Dr Raj ya yi mamakin ganin yadda Bilal ya tashi hankalinsa sosai har ya rasa control saboda Leesharh, sai kace wata tasa ta jini ko da akwai wata alaƙa a tsakaninsu! Abin da mamaki, tabbas yasan Bilal mutum ne mai tausayi, amma ya nuna san Leesharh sosai wanda sun san ba halinsu bane. Cikin nitsuwa Ramish ya tako ya kariso bakin bed ɗin da Bilal ya kwantar da ita, in a cool voice ya ce. "Rai'na ta ceta ta shiga haɗari, dan haka da kai'na nima zan cetota daga haɗari". Yana kai karshen maganar ya buɗe drawer dake kusa da bed ɗin, cikin zafa ya kwaso kayan aikin cire bullet irin su. Irrigation Syringe, Retractors, Suction, Machine Forceps, Scalpel, Local Anesthesia, X-ray Machine, Sutures, Sterile Gauze Pads, Antiseptic Solution. A gaban bed ɗin ya zo ya zubesu saman wata tables dake ta gefe dai'dai in da kanta yake. Su Abbie da suka shigo yanzu ne suka tsaya cirko cirko suna kallansa yana aiki cikin zafa da kulawa. Almakashi ya fara ɗaukowa, rigar jikinta ya yanke tin daga farko har karshe, ya tsaga rigar biyu kenan, wani farar vest wadda ta ji jaga jaga da jini ne ta bayyana a ciki. Saman breast ɗinta kaɗan bullet ɗin ya sameta, hakan yasa ya yanke iya hannun vest ɗin kawai. A saman table ɗin ya mayar da almakashin ya ajiye. X-ray Machine ya ɗauko, komai da zafa yake yi duba da halin da take ciki na zuban jini sosai, wannan machine yasa ya fara bincikar dik wasu jijiyoyi da gaɓaɓɓan dake kusa da in da aka harbeta ɗin, dan ya tabbatar da in da bullet ɗin yake ya kuma tabbatar da cewa bai taɓa wata jijiya ko wani joint or kashin jikinta ba. Da sauri Dr Raj ya nufosa domin ya taimaka mashi, hannu ya ɗagawa Dr Raj alamar baya buƙata, shi ma zai rama cetan ransa da ta yi ne da kansa, zai yi iyaka ƙoƙarinsa dan yaga ya ceceta. Sharifat sai shessheƙar kuka take yi tana rungume da Abbie, Ummie dai taki biyosu nan, ta wuce part ɗinta. Abu Abdussalam yana cikin tashin hankali, da kaga face ɗinsa zaka san yana cikin tashin hankali bawan Allah. A hankali Ramish ya sauke ajiyar zuciya lokacin da ya kalli tabbas bullet ɗin bai taɓa koɗaya daga cikin abin da yake gudun ya taɓa ba, bullet ɗin yana tsakiyar namar kirjinta, sai dai saura kaɗan ya huda ƙashinta. Cikin zafa ya ajiye X-ray machine ɗin. Sannan ya ɗauko Antiseptic Solution, a hanzarce ya fara tsabtace wajen da bullet ɗin ya fasa namar ya shiga ciki. Yadda kuka san computer haka yake yin aiki. Tsab ya tsabtace wajen, sannan ya ɗauko Local Anesthesia don rage mata zafi. Dik da idanunta a datse sai da ta ɗan ciza laɓɓanta a lokacin da yake gudanar da aikinsa, alamar tana jin azaba, the way take jin azaba the way take kara datse idanu. Lokacin guda tausayin Leesharh ya ratsa zuciyarsa, dan yasan azabar bullet, su da suke matsayin jami'ai, zaratan jaruman maza ma bata sauki suke iya jure azabar bullet ba bare ita da take mace kuma yarinya, ai dole dik wani mai zuciya a kirjinsa ya tausaya mata. Scalpel ya ɗauko. Shi kansa sai da ya ɗan datse idanunsa a lokacin da yake buɗa namar kirjin leesharh da wannan Scalpel ɗin dan ya samu damar iya zare bullet ɗin. Yana aiki cikin zafa, amma kuma dik wata karfe da zai ɗaura a jikin Leesharh a hankali yake yi mata cikin tausayawa. Yana buɗe namar wajen jini ne ya kara bulbula da karfi tamkar ruwa ya fasowa kansa hanya. Da sauri ya ɗauko Irrigation Syringe da ɗayan hannunsa ya fara tsabtace jinin yana sharesa. Sannan ya ɗauko Suction Machine ya yi amfani da shi wajen toshe jinin dan ya samu saukin yin aikinsa. Abin ku da jami'i, ya kware a wannan fanni na cire bullet. Retractors ya ɗauko, cike da kwarewa ya fara amfani da shi wajen rage tsokar dake ta cikin fatar in da bullet ɗin yake. Bayan ya rage sai ya ɗauko, Chlorhexidine, ya yi mata amfani da shi dan ya kara tsabtace wajen harbi saboda da ya yanke namar wajen an samu zubar jini. Ajiyar zuciya ya sauke ganin cewa komai ya daidaitan mashi yadda yakamata. Forceps. Wannan kayan aiki ne mai kama da almakashi, ana amfani da shi don kama bullet ɗin cikin sauƙi, cikin nutsuwa da tausayawa ya sanya forceps ɗin, a hankali ta kama bullet ɗin. A hankali hankali ya fara jan bullet ɗin yana zaro shi waje. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya ciro bullet ɗin, cikin wani kwano mai ɗauke da ruwa mai sanyi da Dr Raj ya kawo mashi ya jefa bullet ɗin, sannan ya yi hanzarin ɗauko sutures ya fara ƙoƙarin haɗe wajen ya ɗinke mata. Dik cikin ɗakin sai da suka tausayawa Leesharh, harbi a kirji namiji ma yaya aka cika bare kuma a kirjin mace, ai abin da ciwo matuƙa wlh. Ramish bai fita daga ɗakin na sai da ya tabbatar da ya kammala komai, sannan ya nufi waje da sauri. Cikin zafa Bilal ya rufa mashi baya, kai tsaye h-q suka nufa a tare. Shi kuma Dr Raj ya matsa kusa da Leesharh dan ya ƙara dubata, lallai ba shakka shi ma ya ji yana kaunarta yadda ta bada ranta ta cetan mashi ɗan uwansa, a yadda Ramish yasa harbi ba sau ɗaya ba sau biyu ba da ace wannan harbin ta samu zuciyarsa ai shikenan sun rasa shi, amma ta tare mashi, a gaskiya yazama nauyi a wuyansu da su tsaya tsayin daka wajen ganin sun ceci rayuwarta ita ma. Matsawa kusa da bed ɗin Abbie da Sharifat suka yi domin su dubata, baiwar Allah ta ji wahala har face ɗinta ta kumbura sosai lokaci guda, ta zama kamar ba ita ba. Shi dai Yah Rizwan baya nan, ya ɗan yi tafiya zuwa ƙasar China dan bunƙasa kamfanoninsa. To Leesharh sai dai mu ce Allah ya tashi kafaɗunki kawai, Allah yasa kina da rabon shan ruwa a gaba, Ramish kai kuma Allah yasa ka kama masu nikaf mu ji dalilinsu na bibiyar rayuwarka da suke yi mu kuma ji maciya amanar da suke cin amanarka. 🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥 Sweetie ta samu lafiya cikin yardan Allah, sai kuma sabon walaƙanci da ta karo yarinyar nan, sam bata da tsoro, ya battaba dai jikin sarauta ne da gaske yake gudu a jikinta, akwai ta da karfin hali da jajircewa. Zaune suke a saman bed ɗin Black Tiger a bedroom ɗinsa ita da Ronnie tana yi mashi bayanin kan yadda ake gudanar da sallah dallah dallah, Black Tiger ya tafi fada, kun san dama sun ce idan za su yi karatun addini a part ɗinsa zasu rinƙa yi dan a nan ne ba zai iya ganin abin da suke aikatawa ba ko? To hakan kuwa aka yi, tana ta yi wa Ronnie bayani yadda zai yi sallah, tana sanye da doguwar riga irin shigar mutanen birnin Black world, ta yi balai'n kyau, ta saki wannan kyakkyawan golden white hair nata sai sheki yake yi, ya sha gyara, Ronnie ya ce kayan basu taɓa yi wa wata mace kyau irin yadda suka yi mata ba, ta ji daɗin yaba kyanta da yake yawan yi, ranta na sanyaya sosai. Dik abin da take koya mashi yana rikewa sosai a cikin kwakwalwarsa, saboda akwai brain shi ma, ga shegen san karatu kamar me. Suna zaune suna fuskantar juna, kamar wasu yaya da kanwa, gwanin birgewa, yana sanye da hoodies milk color a jikinsa. Sai wani binta da Koreans eyes ɗinsa yake yi. "Sweetie ina san ki faɗa mun a in da zan samu ainahin Ingila in karanta, dan ina san sanin ainahin saƙon da yesu ya zo da shi". Cewar Ronnie kenan, yana magana yana ɗan murza mata ƴan yatsun hannunta dake rike cikin nasa. Sun bajewa Black Tiger a saman bed ɗinsa kamar nasu ne. Floris dai tana can wajen Angela, yanzu Floris ta fara yarda da zugin da master Devil yake yi mata, shiyasa ta ja baya da su sosai, amfani yake san yi da yarintarta ya kama Ronnie, ce mata ya yi idan ta taimaka mashi zata mallaki Ronnie, ita kuma sai ta yarda. Ɗago kai ta yi suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ta ce. "No need ka karanta ingil a yanzu Ronnie".......... "But why?". Ya jefa mata tambayar da alamar damuwa a face ɗinsa, da alama da gaske yake yi yana san sanin ainahin abin da annabi Isa ya zo da shi. "Saboda ingila ba zata dawo duniya ba, Annabi Isa zai dawo duniya, sai dai idan ya dawo shi ma ba zai yi amfani da ingila ba, zai dawone yana mai bin bayan Annabi Muhammad (S.A.W) so dik hukuncin da zai yanke a yayin dawowarsa zai yanke ne bisa amfani da kalamul lah, wato Alqur'ani mai girma". Ɗan zaro idanunsa ya yi, cike da mamaki ya ce. "Kenan dama yesu zai dawo duniya?".......... Jinjina mashi kai ta yi alamar e, sannan ta ɗaura da cewa. "Tabbas zai dawo duniya, wannan magana tana da asali daga hadisan Annabi Muhammad (SAW), wanda ya tabbatar da dawowar Annabi Isa (AS) a ƙarshen zamani. Daga cikin hadisan da suka zo kan hakan akwai. Hadisin Abu Huraira (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) ya ce. Ina rantsuwa da wanda raina ke hannunsa, haƙiƙa zai sauko maku da ɗan Maryam a cikinku a matsayin mai hukunci na adalci, zai kashe batun cin alade, zai hana haraji, kuma kuɗi za su yawaita har ba wanda zai karɓa, hadisin yana nan a cikin Sahih al-Bukhari hadisi mai lamba 2222, sai Sahih Muslim hadisi mai lamba 155". "Sannan Abu Huraira (RA) ya sake ruwaitowa. Annabi (SAW) ya ce. Ba wani annabi da zai kasance a tsakanina da Isa, wato bayan manzan Allah babu wani annabi da za'a sake yi sai Annabi Isa da zai dawo. Lallai Isa zai sauko duniya, kuma zai yi hukunci da shari'ar Musulunci. A cikin Sahih Muslim hadisi mai lamba 2365. Ma'anar Wadannan Hadisan shi ne, Annabi Isa (AS) zai dawo a ƙarshen zamani, amma ba a matsayin sabon annabi ba, sai dai a matsayin mai bi ga shari'ar Annabi Muhammad (SAW) Zai yi hukunci da shari'ar Alqur'ani da Musulunci, ba da Injila ba. Zai tabbatar da adalci, ya kawar da shirka, ya karya gicciye, ya hana cin naman alade, kuma ya hukunta duniya bisa dokokin Musulunci. Wadannan dalilai sun nuna cewa Annabi Isa (AS) ba zai zo da sabuwar shari'a ba, ko ya yi amfani da littafin da ya zo da ita a baya wato ingil, sai dai zai zama mai bin shari'ar Annabi Muhammad (SAW). Wannan yana daga cikin alamomin ƙarshen duniya da kuma tabbacin cewa Musulunci shi ne cikakken addini har zuwa ƙarshen zamani, dan haka ba sai ka wahala wajen neman karanta Ingila ba, ka karanta Alqur'ani mai girma dan ma ka kara sanin girman Allah ka ji ko?". Shiru ya yi yana tinanin lallai ba shakka Annbi Muhammad fiyayyen halitta ɗin ne da gaske kamar yadda Sweetie ta faɗa mashi, lallai zai yi biyayya ga Annabi Muhammad iyaka iyawarsa, tabbas zai karanta Alqur'ani mai girma zai kuma yi haddarta. Ganin ya yi shiru yasa ta ce. "Baka gamsu bane in kawo maka wasu hujojin masu karfin da dole ka gamsu Ronnie?". Da sauri ya girgiza mata mai alamar a'a ya gamsu, sannan ya ce. "Dan Allah ki bani tarihin Imam Mahadi ko kaɗan ne yau kam, kullum sai na tambayeki amma baki faɗa mun". Jinjina kanta ta yi, sannan ta fara magana kamar haka. "Zan baka tarihin Imam Mahadi ko dan saboda yadda jama'a suka ɗaukesa, wasu sun karyata bayyanarsa, wasu kuma sun faɗi yadda zai bayyana ba'a dai'dai ba, sun ruɗar da mutane game da bayyanarsa". Shiru ya nitsu yana jinta, cigaba ta yi da cewa. "Imam Mahdi Allah ya yarda da shi, shi ne ɗaya daga cikin manyan alamomin tashin alkiyama. Addinin Musulunci ya yi bayani a kan zuwansa, kuma ya na da mahimmanci a fahimtar al’amuran da za su wakana kafin ranar alkiyama. Menene Ma'anar Mahdi ma farko tukun nan?". Shiru ta ɗan yi tana kallansa, ganin bai motsa lips ɗinsa da nufin yin magana bane yasa ta ɗaura da cewa. "Sunan Mahdi yana nufin wanda Allah ya shiryar zuwa gaskiya. Shi mutum ne da Allah zai zaɓa domin ya jagoranci al’umma zuwa ga adalci da gaskiya a lokacin da duniya ta cika da zalunci da barna. Asalinsa daga zuriyar Annabi Muhammad (SAW) yake. Yana daga cikin zuriyar Nana Fatima, ƴar Annabi (SAW) Sunansa da sunan Annabi iri ɗaya ne sak. Sunansa Muhammad shi ma, kuma sunan mahaifinsa Abdullah, kamar dai Annabi Muhammad (SAW). Zai cika duniya da adalci. Zai bayyana ne a lokacin da duniya ta cika da zalunci da fasadi, sannan zai dawo da adalci da gaskiya. Annabi Muhammad (SAW) ya ce Al-Mahdi yana daga cikin zuriyata, daga cikin ƴaƴan Fatima ka duba Sunan Abu Dawud, Hadisi mai lamba 4286 a nan manzan Allah ya yi wannan magana". "Manzon Allah ya sake cewa za a cika duniya da zalunci da danniya, sannan Allah zai kawo wani daga cikin iyalina wanda zai cika ta da adalci da gaskiya kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya ka duba cikin sunan Abu Dawud, Hadisi mai lamba 4285, Annabi ya ce Imam Madih zai bayyana ne a Makka kusa da Ka’aba, inda mutane za su rantsar da shi a matsayin jagoransu. Aikin da zai yi a zamansa a duniya sun haɗa da.Yaki da zalunci. Zai jagoranci yaƙi da azzalumai da masu rushe gaskiya. Zama jagoran musulmi. Zai haɗa al’ummar musulmi karkashin jagoranci guda. Zai taimaki Annabi Isa (AS) A lokacin zuwansa, Annabi Isa (AS) zai sauka daga sama, sannan su yi aiki tare wajen tabbatar da gaskiya. Ahlus-Sunnah wal-Jama’ah. Sun gaskata da zuwan Imam Mahdi kamar yadda hadisan Annabi suka tabbatar. Suma ƴan Shi'a sun yi imani da Imam Mahdi, suna cewa shi ne Imam na goma sha biyu daga Imaman su, wanda yanzu yana boye kuma zai bayyana a nan gaba a cewarsu. Wannan shi ne takaitaccen tarihin bayyanar Imam Madih". Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Wani lokaci Imam Madih zai bayyana?. Shin bayan zuwan su dijjal ne zai bayyana ko dai sai ya zo kafin su dijjal?". Kai Ronnie yana da san yawan tambaya, dama kuma dik mai ilimi kuma mai san kara faɗaɗa iliminsa dole ne ya rinƙa tambaye tambaye. Allah sarki ita kuwa tun da tana san ya shiryu, bata gajiya da tambayoyinsa. Gyara zama da kyau ta yi, a nitse ta fara bashi amsarsa kamar haka. "Bayyanar Imam Mahdi, Dajjal, da sauran manyan alamomin tashin alkiyama suna da tsari da Allah ya tsara, kuma akwai bayani a hadisan Annabi (SAW) game da wannan. A mahangar addinin Musulunci, Imam Mahdi zai bayyana ne kafin bayyanar Dajjal, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar musulmi a lokacin wannan fitina mai girma wato fitinat dijjal. Zuwansa ba a lokacin da aka sani ba ne. Annabi Muhammad (SAW) ya ce, lokacin bayyanar Imam Mahdi ba wani abu ne da mutane za su iya hasashe da cikakken tabbaci ba. Amma zai bayyana ne lokacin da musulmi suke cikin matsananciyar bukatar jagora, sun jigata suna cikin kunci da wahala game da azabar azzaluman shugabanni, a lokacin zai bayyana domin ruguje zalincinsu ya zama jagora ga musulmi. Tsakanin bayyanarsa da bayyanar dijjal. A hadisan Annabi (SAW), ya nuna cewa Imam Mahdi zai bayyana ne kafin bayyanar Dajjal, kuma zai yi wa Dajjal tawaye tare da taimakon Annabi Isa (AS) lokacin da Dajjal ya bayyana, Imam Mahdi zai jagoranci musulmi su yi gwagwarmaya da shi. Sai Annabi Isa (AS) ya sauka daga sama, sannan shi ne zai kashe Dajjal a ƙarshe. Hadisin Bukhari da Muslim. An ce Annabi Isa zai sauka a lokacin da Imam Mahdi ya riga ya kasance jagora, sannan su biyu za su haɗa kai wajen yin maganin Dajjal. Annabi Isa zai sauka a kusa da minar Madina mai farin haske (minaratul bayda) a Syria, Bayyanar Dajjal. Fitowarsa ita ce mafi girman fitina ga al’umma, wanda zai zo tare da ƙarya da sihiri mai ƙarfi. Saukar Annabi Isa. Annabi Isa zai zo domin taimakawa Mahdi wajen kawo ƙarshen Dajjal, sannan ya jagoranci sauran al’umma. Zai zo ne bayan Mahdi ya fara gyara duniya. Wannan shi ne ainahin cikakken bayani a kan bayyanar Imam Mahadi". Ta kai karshen maganar tana kallansa. Shiru ya yi yana jinjina girma irin na Ubangiji, wato Alqur'ani ya tabbata ba abin wasa bane, lallai ne ba shakka dik mai tinani ba zai bijire maganar Allah ba. Buɗe baki ya yi domin ya yi magana sai gani suka yi anturo kofar ɗakin an shigo. A tare suka kai kallansu a kan kofar shigowa tana zare hannunta daga rikon da ya yi mata. Ɗan zaro idanu Sweetie ta yi tana kallansa, shi kuwa ƙarisowa ciki ya yi ba tare da ya kalli in da suke ba. Gaban mirrorsa ya karisa ya tsaya, ya gama shirya komai domin cire ƙwaƙwalwarta kamar yadda ya tsara, yau kuma yake sa rai zai yi wannan aiki, shi ne dalilin dawowarsa yanzu kenan. Silent talk ya yi wajen cewa Ronnie ya fita daga ɗakin ita kuma ta same shi a wannan ɗaki da ya yi treating ɗinta last time. Kallon juna suka yi ita da Ronnie, miƙewa Ronnie ya yi ya sauko kasan bed ɗin, sannan ya nufi kofar fita, yana san tambayar yayan nasa me zai yi mata ko dai bata da lafiya ne? Amma sai ya ji tamkar an ɗaure mashi tongue ɗinsa, ya kasa magana, haka ya nufi fita waje. Ita kuma dirowa kasan bed ta yi, idanunta a kansa, shi kuma sam sam baya kallanta, ita kyansa na musamman da ya yi ma take kallah, kowani kaya yasa kyau yake yi wa kayan, ita jacket ɗin jikinsa ma take balai'n kauna, rigar ta yi mata kyau, ga shi har gwiwonsa ya kai, kamar long coat haka jacket ɗin yake. Kafafunsa dake sanye cikin wasu irin armor sandal ta bi da kallo, takalma bakake ne hakan yasa hasken fatarsa ta kara fitowa sosai, kafafunsa kyawawan gaske, faratunan yatsunsa kamar madara, zaka ce bai taɓa taka ƙasa ba. Ganin ta sauko kasa yasa ya juya zai nufi hanyar zuwa wannan ɗakin dan su je ya yi aikin, ba ruwansa da zata mutu, shi dai buƙatarsa kawai ta biya. "One mint big bro". Ta faɗa tana ɗaura hannayenta dikka biyu a saman kugunta. A tare suka dakata shi da Ronnie, dama Ronnie bai kai ga fita waje ba. So jin maganarta yasa suka dakata Dakarawa ya yi da tafiya amma bai juyo ba, ya nuna alamar dai yana sauraronta....... Ko kaɗan babu tsoron abin da zai iya aikata mata kawai ta nufesa, a hankali take takawa har ta isa garesa, ta zago ta gabansa suna fuskantar juna, da kyau ta kara rike kugunta. Slowly ya ɗaura idanunsa a kan face ɗinta, sai da ya ji gabansa ta ɗan faɗi, ita kanta sai da ta ji wani irin shock kamar an jona mata wutar lantarki, amma haka ta daure, cike da kwarin gwiwa zuciyarta na dukan uku uku ta ce. "Why do you want to remove my brain?" She threw the question at him, her face hardening as if to make it clear that she was not joking. Ɗan zaro idanunsa a kanta ya yi, a wannan gaɓar sai da ta ɗan kawar da kallonta daga cikin idanunsa, saboda da ya zaro idanu sun kara kaifafa sosai da ba zata iya ganinsa ba. Ko waye ya faɗa mata zai cire mata ƙwaƙwalwa kuma? Kai Sweetie duniya. When he didn’t respond, she spoke again. "So, you mean to tell me that you can’t retrieve anything from me unless you take my brain? Don’t you think that’s a sign of your failure?" He stood motionless like a statue, showing no intention of answering her. She fell silent, her eyes trailing down to his feet, watching how he slightly shifted them a subtle sign that her words were getting to him. Slowly, she lifted her gaze back to his face, slightly tilting her hips before freeing one hand from the grip she had on her waist. Then, with her heart pounding hard in her chest from fear of him, she forced herself to lift her hand, positioning her fingers right in front of his face. Her chest felt like it was about to burst from fear, but she suppressed it. Shiru ta ɗan yi tana kallan yatsun kafafunsa yadda yake ɗan motsasu kaɗan kaɗan alamar maganganunta suna taɓa mashi zuciya. Slowly ta ɗago kallanta a face ɗinsa, ɗan jijjiga ƙugunta kaɗan ta yi kafin ta zame hannunta ɗaya daga rikon da ta yi wa kugun nata, sannan ta ɗaga hannun nata dai'dai saitin face ɗinsa, kirjinta tamkar zai fashe saboda tsoronsa, amma haka ta danne. Kiyasta mashi yatsunta a saitin face ɗinsa ta yi. Her voice was sharp as she spoke, "I challenge you. Find Spender using only the brilliance of your own mind, without my help, without hurting me to get to him. Find it on your own. If you can, then I will acknowledge that you are truly a man. And I want you to understand something, when it comes to the story of your fate, I am the first page and the last. I am your destiny, and there’s nothing you can do about it!!. If you truly are a man, find Spender yourself." Babbar magana, lallai Sweetie jinjina gareki gaskiya, eyye yarinya ta ƙalubalance Black Tiger, tashin hankali, ya kuke tinanin wannan wasa zai kaya? Mu je zuwa. She ended her words with her fingers still pointed at him, her gaze unwavering. Tin da ta fara magana bai motsa ba yana sauraronta har sai da ta kai aya, sannan ne ya ɗan nisa kaɗan, cikin zafa ya kai hannunsa zai capki wuyarta, dan ya lura bata azabtu bane shiyasa har yanzu take da kwarin gwiwar yi mashi magana, bai san karin gwiwar ya samo asali ne daga dogara da Allah da ta yi ba, ba wai dan bata azabtu bane, ta dai rike Allah ne kawai. Wani irin zulle mashi ta yi, ƙasa ta sunkuya sai ta tafi da karfi ta faɗa saman lion chest ɗinsa, dama ta yi wa kanta alkawarin ba zata taɓa bari ya sake taɓa mata lafiyar jikinta ba, sai dai ayi wacce za'ayi. Ai tana faɗawa jikinsa sai da ya ji komai nasa ya tsaya cak na wucin gadin. Lokacin guda ya ji har ɗan juyi ɗakin ya yi mashi, ita kanta sai da ta rasa nitsuwarta, wani irin azabbabben shock da ta ji wanda bata taɓa jin irinsa ba, sai da ta ji gabaɗaya gaɓɓan jikinta sun mutu. Ronnie dai mutuwa tsaye ya yi tamkar wanda aka dasa, dan kalaman Sweetie sun fi karfinsa, ƴar yarinya da ita wai ta ƙalubalance Black Tiger, wannan bala'i dame ta yi kama?. Cikin zafa yasa hannu zai ɓanɓareta daga jikinsa ya yi wurgi da ita, ina ai bata bashi wannan dama ba, hannu tasa ta riko waist ɗinsa da karfi, dan dolensa ya lafa da yunkurinsa, barema yadda take kara shigewa jikinsa da karfi. Shiru ya ɗan dakata yana tinanin irin hukuncin da zai yi wa wannan yarinyar. Jin ya yi shiru yasa ta sakesa tare da ɗago kanta daga saman lion chest ɗin nasa. Da yake ya fita tsawo sosai sai ta ɗan ɗaga kafafunta sama, a hankali ta kai hannunta ta shafa gefen lallausan kumatunsa, ƙasa sosai ta yi da murya wajen furta. "I am your destiny, hakuri zaka yi da ni fa big bro, I challenged you, kada ka ɗauki zafi sosai mana, ko ka manta a sharaɗinmu babu batun cutarwa ne? Ba zaka cutar da ni ba kuma zaka yi nasarar samo Spender, ka yi hakan zan sara maka kuma na yarda kai namiji ne". Ta kai karshen maganar tare da ƙara ɗaga kafanta sosai, sumbata ta manna mashi a lallausan kumatun nasa sannan ta juya cikin wani irin tafiya mai nuna cike take da confidence ta nufi hanyar fita waje kirjinta tamkar zai fashe saboda tsoro. Ya subhanallah, yadda kuka san an dasa Black Tiger a wajen, ta gogewa Ronnie haddar dake kansa gabaɗaya, nasan ba Ronnie kawai ba, har da ku masu karatu ta goge maku hadda ko? Wannan yarinya Sweetie nan gaba ban san ya zamu yi da ita ba, da alama idan Black Tiger bai yi da gaske ba fa zai rasa bakin magana a gabanta. Tana zuwa kusa da Ronnie ta kyasta mashi yatsu a saitin face ɗinsa kafin ta wucesa, tana taku kamar wata hawainiya, tafiya mai matuƙar ɗaukar hankali, dik wasu albarkatu na jikinta suna motsawa a dik san da ta taka kafafunta ta yi taku ɗaya. Har ta isa kofar room ɗin Ronnie da Black Tiger babu wanda ya iya motsawa daga in da yake tsaye, ita kuma bata juyo ba ta sanya password na kofar kamar yadda Ronnie ya koya mata. Take kofar ta buɗe ta nufi waje abinta. Tana fita ta zube gwiwowinta a kasa a wajen tare da dafe saitin zuciyarta tana sauke numfashi da sauri sauri. Ƙasa ƙasa ta furta. "Allah na gode maka da ka bani ikon da kwarin gwiwa na iya aikata hakan a garesa, Allah Alhdulillah da baka bari bugawar da zuciyata take yi a lokacin da nike gabansa ya kasheni ba, Allah ka cigaba da dafa mun kana kareni, Allah kaga zuciyata jahadi nike san yi, Allah ka cigaba da ɗaurani a kansu, astagfilullah, astagfilullah, astagfilullah, Allah na tuba, Allah ka jiƙaina ka cigaba da karamun kwarin gwiwa kana bani ikon daurewa na yi magana yadda yakamata a gabansa". Tana kai karshen maganar ta fashe da kuka saboda yadda kirjinta yake duka tara tara ya wuce tinaninku, a tsananin tsorace sosai take fa, kawai shegen karfin ne. Ta ɗan jima a wajen tana hawaye kafin ta miƙe da gudu ta nufi ɗakin Ronnie, tana zuwa ta faɗa saman bed tana ƙara rushewa da kuka mai tsuma zuciya. Kamar kuma wadda aka dakatar ta yi saurin miƙewa tana gogewa hawayenta, dan ta tuna Black Tiger zai iya ganin tana kuka, ita kuma bata san bashi wata kofar da zai fahimci tana jin tsoronsa. Babbar magana, yanzu za'a fara buga wasa a Black world, my people's Black Tiger fa ya ji sumbata ya yi sumar tsaye ɗan ƙaniya, ina da ya ce baya ji, yanzu Sweetie zata yi mana maganinsa ai. Ku dai muje zuwa. 🔥🔥🔥 KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER.🔥🔥🔥 Gabaɗaya barci ya kauracewa idanunsa, banda kyakkyawan surar jikinta da ya gani lokacin da ta fito wanka ranar da zasu je wajen Khadijah babu wani abin da yake tunawa, haƙiƙa idan ya ce zuciyarsa ta kamu da san Zee to bai yi karya ba, sai dai kuma yana jin zuciyarsa bata kyauta mashi ba, dan shi yana da ra'ayin auren mace mai 25 years ne ba yarinya kamar Zee ba, dik tinaninsa ya kulle a kanta, sai dai kuma ta wani ɓangare ya fi yarda da cewa ya kwaɗaitu ne da surar jikinta kawai, dan shi ne abin da ya tsaya mashi a ransa. Sai safa da marwa yake yi a cikin tsakiyar parlournsa, kwanciya wannan ya gagara yi, kirjinta daya kurawa idanu wancan ranar kawai ƙwaƙwalwarsa take hasko mashi a idanunsa, gabaɗaya ya gaza iya rike kansa. Time ya duba a wayarsa dake hannunsa. 11:00pm dai'dai, gabaɗaya sai ya ji zuciyarsa tana fusgarsa a kan ya je ya ganta a daren nan, ya yi ƙoƙari wajen ganin ya tursasa zuciyarsa ya hakura da zuwa ganinta, amma ina abin ya fi karfinsa, dan haka dole a cikin wannan dare ya fito sanye da sleeping dress a jikinsa. Kai tsaye part ɗin mama ya nufa, yana tafiya tamkar wanda yake tsoron taka ƙasa, can ƙasan maƙoshinsa ya yi sallama kafin ya tura kofar ɗakin a hankali ya shigo, light na ɗakin a kunne yake, suna kwance saman bed suna zuba barcinsu, Aneesa na gefe ita ma Zee tana gefe, gadan nasu yana da matuƙar girma sosai. Ji ya yi tamkar ya juya gudun kada Aneesa ta farka ta gansa a kansu, amma kuma zuciyarsa ba zata iya hakura ba muddin bata ga fuskar Zee ba. Daurewa ya yi ya ƙarisa ciki yana ji tamkar ba shi ba, wai yau shi ne ya folawa mace under 18 years, gaskiya zuciyarsa dai bata yi mashi adalci ba, shi ne abin da yake ta faɗa yana maimaitawa. Ta side ɗinta ya zo, duƙawa ya yi a saman gwiwowinsa a gaban bed ɗin. Tana kudundune a cikin bargo, tun daga kan yadda Zee take barci mutum zai iya fahimtar ita ɗin macece mai kama kanta, wacce ta san mutumcin kanta, nitsastsiya mai sanin yakamata, dan ko a cikin barcinta ta haɗe jikinta waje guda ta yadda bata ba da kofar da komai ƙanƙantar tsiraicinta zai iya bayya idan barci ya yi nisa ba, ta haɗe kafafunta waje guda ta kuma dungule hannayenta ta turasu a tsakanin cinyoyinta ta kusa da gwiwa, idan ka ganta zaka yi zaton ta takure kanta dayawa, amma ba haka bane, saboda ne da irin kwanciyar ya ja hakan, ga kuma irin tarbiyar da ta samu tun kan kanwar shaiɗan Hauwa ta shiga rayuwarsu ta ruguje komai. Zubawa face ɗinta idanu ya yi sosai yana kare mata kallo, hankalinsa dikka a kan lips ɗinta, Allah ya gani zuciyansa ya biya da wannan black beautyn, Zee dai a Nigeria fara ce tas, amma a gabansu baƙa ce gaskiya, shiyasa ya kirata da sunan black beauty. Hannunsa na kerya ya kai ya ɗan janye bargon da ta lulluɓa ƙasa. Kayan barcin Aneesa riga da wando ne a jikinta, kasancewar bata sanya bra ba sai tula tulanta suna tsole idanun mai kallo. Shi dai da alama kirjinta yana ɗaya daga cikin abin da ya ja ra'ayinsa a kanta. Dawo hannunsa kusa da face ɗinta ya yi dan ya taɓa lallausan kumatunta, sai dai bai kai ga yin hakan ba ta fara motsi tana san farkawa, saboda ta ji alamar kamar ambuɗe mata jiki. Ya janye mata bargo. Aneesa kuwa ta baje abinta sai zuba barci take yi, ta rungumi teddy a kirjinta a cewarta Yah Rizwan ta runguma,........... Kai Hasbunallahu wani'imal wakil, wlh jikokin Akka sai shirin Allah, ba matan ba ba mazan ba, da alama dik sun yi gadon jaraba, kai kun ji Aneesa da wani tsiya, wai Yah Rizwan ta runguma, kai jama'a ana abu a kingdom of power. A hanzarce ya miƙe tsaye, ganin sosai ta fara motsawa zata farka yasa ya yi saurin juyawa zai fice daga ɗakin. Sai dai bai kai ga fita ba ta waro idanunta waje kai tsaye sai a kan bayansa yana tafiya. A zabure ta miƙe zaune a tsakiyar bed ɗin tana kallansa. Bata gane wanene bane, saboda ya bata baya, sai dai zuciyarta ya zargan mata cewa shi ne, saboda shi ne kaɗai a gidan wanda gashin kansa bai yi dark black ba, ya ɗan yi brown brown haka. A hanzarce ta dawo da kallonta a kan jikinta dan ta tabbatar da ba wani abin aka yi mata ba!. Ganin babu komai yasa ta yi saurin saukowa kasan bed ɗin, ashe gara da ta ce da Aneesa su rinƙa barin wutar ɗakin a kunne dan suga mai shigowa, to ga shi ya yi amfani. Bayansa ta bi da sauri dan ta ga wanenen? Tana da karfin hali ita ma, a ranta take rayawa lallai lokacin barinsu gidan nan ya yi tun da dai maza ne suke shigo masu ɗaki da daddare. Da sauri ta fito daga bedroom ɗin nasu ta nufi bin bayansa. Sai dai ko da ta fito bata gansa ba, babu shi babu alamarsa, ɗan waige waige ta tsaya yi a wajen, kamar dai a mafarki ta hango inuwar mutum ta wajen wannan kofa da Guyson ya bi ranar ya je wajen dinner Jawad, kun tuna ranar da ya haɗu da aljanar nan? Kun san ai dama ta part ɗin mama ne kofar yake ko idan baku manta ba? To ita kuma Zee kunga a part ɗin take tare da Aneesa, so tana fitowa sai taga inuwar mutum kamar dai yadda aka yi wa guyson. Ɗan tsorata ta yi, sai kuma ta tina abin da mamarsu take yawan faɗa masu a kan kada su ji tsoron kowa face Allah da ya haliccesu. Tuna hakan yasa ta ce bari ta je ta leƙa kila inuwar wanda ya shigo masu ɗaki ne, yau so take taga wanenen?. Ba tare da tina abin da zata iya gani ba ta nufi kofar, tana taɓa kofar kuma sai ta jita a buɗe. Wai nace ba, meyasa wannan kofar a dik lokacin da wannan inuwa ta gifta kofar yake buɗe kansa da kansa ne? Kun san fa ba'a buɗe wannan kofa kwata kwata, ko da rana a rufe yake, so meyasa in dai inuwa ta gifta kofar zai buɗe? Muje dai zuwa. Jan kofar a hankali Zee ta yi da nufin ta fita waje, daga bayanta ta ji muryarsa ya ce. "Ina zaki je a daren nan, sannan kofar nan ai ba'a buɗeta". A hanzarce ta juyo da kallonta a kansa, uncle Jahiz ɗin ne dai, yana tsaye yana kallanta. Ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin juyo da jikinta a garesa dan ta bashi amsa ta wuce ciki, unexpext idanunta suka kallo mata fuskar mace mai kama da aljana ga wasu kahohhuna dogaye a hancinta har zuwa bakinta, jini na bin jikin kahon, sannan idanunta manya manyan jajir kamar wuta, gwanin ban tsoro. Ai Zee bata san time ɗin da ta zunduma wani irin ihu mai doɗe kunne ba, kwata kwata bama ta san ya akayi ba sai ganin kanta ta yi a kirjin uncle Jahiz, shi kuma fa babu abin da ya gani, ita kaɗai aka tsorata, kada ku manta uncle Jahiz fa na Aliyah ce, Aliyah kanwar Mammie shugaban mashirikai ita mammie ta ce zata auresa in baku manta ba, to ni dai ina ga kila saboda uncle Jahiz ya nuna ra'ayinsa a kan Zee yasa Mammie ta fara ɗaukar mataki, amma ku ya kuke gani?. Kankame shi ta yi tana ihu. Gudun kada ta tashi family yasa uncle Jahiz ya yi saurin toshe mata baki da hannunsa yana kai kallansa a wajen da ta baro take ihun. Shi dai bai ga komai ba face kofa kawai, to meyasakata ihu har haka? Ya jefawa kansa tambaya. Motsi ya ji a bayansu ta wajen part ɗin momma, hakan yasa ya yi saurin janta baya dan ma kada wani ya gansu, ganin kamar razana sosai ta yi yasa ya fara tofa mata addu'oi har lokacin bai zame hannunsa daga bakinta ba. Ita kuma tana ƙanƙame da shi. Addu'oin da yake tofa mata ne yasa ta fara samun nitsuwa hankalinta yana dawowa jikinta, tsoratar da ta yi yasa har ta fita a hayyacinta. Ganin ta ɗan fara nitsuwa yasa ya jata suka karisa shiga bedroom ɗin Aneesa, a saman sofa ya zaunar da ita tare da zame hannunsa daga bakinta, ya kurawa face ɗinta idanu yana kallanta. Ta ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ta iya dawowa dai'dai, hankali a tashe take kallansa, sai kuma ta kasa yin magana. Cikin nitsuwa ya tambayeta dalilin ihun da ta yi, ta kasa bashi amsa, tamkar an ɗaure mata tongue ɗinta, ganin hakan yasa ya ce ta je ta kwanta da safe zasu yi magana kuma kada ta sake fitowa. Ba musu ta miƙe ta isa bakin bed ɗinsu, hayewa ta yi ta kwanta har wa lokacin tongue ɗinta a ɗaure ta kasa iya yin magana. Miƙewa ya yi ya koma kusa da ita, addu'oi sosai ya tofa mata, tin tana satar kallan face ɗinsa har ta lumshe idanu tana sauke ajiyar zuciya alamar hankalinta ya kwanta. Jin saukar ajiyar zuciyarta yasa ya fahimci ta samu natsuwa, bargo ya ja ya lulluɓeta tare da karisawa gaban switch ya kashe masu wutar, sannan ya fita ya janyo kofar ya rufe masu. Dik wannan bidiri da ake yi Aneesa tana can duniyar mafarkin ita da Yah Rizwan, bata farka ba, amma abin mamaki kuma zata iya wayan gari ta bada labarin abin da ya faru daren jiya ɗin, anya Aneesa mutum ce kuwa? Ta fara bani tsoro sosai gaskiya, amma mu je zuwa, ita ma labari zai biyo ta kanta ne, lokacin na nan tafe. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 A tare Jawad and Jaish suka jera har izuwa takiyar main parlour, a nan ne suka rungumi juna tare da yi wa juna good night, a daidai lokacin Chuchu da Mahnoor suka iso wajen. Wucewa gaba Jaish ya yi ya nufi part ɗinsa ba tare da ya kalli in da Mahnoor take ba, shi kuma Jawad ya rike hannun Chuchu yana janyota jikinsa suka wuce nasu part ɗin suna yi wa Mahnoor good night. Shiru ta ɗan tsaya a wajen tana tinanin yadda zata kwana da shi ɗaki ɗaya yau. Ganin tsayuwa ba zai haifar mata da mafita bane yasa a nitse ta taka ta bi bayansa. Tana sako kafafunta a cikin parlonsa ta ji kamshi na daban ba kamar wanda ta ji da rana ba, kenan ancanza mashi perfume, shakar kamshin ta yi ta lumshe idanunta, cikin natsuwa ta ƙarisa shiga cikin parlourn. Mama Haulat ta isko zaune saman sofa tana dudduba wasu sexy sleeping dress dake cikin kwalayensu. Cikin girmamawa ta ce. "Barka da dare mama Haulat". Fuska ɗauke da fara'a mama Haulat ta amsa da. "Yauwa barka dai amarya kuma sarauniyarmu, zo nan ki ɗauki kayanki ki wuce ɗakin mijinki". Ɗan siririn murmushi ta saki kafin ta karisa kusa da mama Haulat, sannan ta ce. "Mama kaya kuma?". Jinjina kai ta yi tare da amsa mata. "E kaya, momma ce ta ce abaki wannan kayan su zaki saka, kuma ta ce karfe tara kije ki ɗaukawa mijin naki cappuccino". Kasa da kai Mahnoor ta yi alamar ta ji kunya ance mijinta. Miƙo mata kayan mama Haulat ta yi ta karɓa tana wani sunkuyar da kanta ƙasa. "Kada ki nuna jin kunya a wannan ɓangaren, domin kunya bata da wani amfani, ki tsaya tsayin daka ki faranta ran mijinki shi ne dai'dai, ki sani yanzu kin shiga layin da Mala'iku zasu yi rubutu a kanki a kan aure, so yana da kyau ki kula sosai, ki sanya shi farinciki domin ki samu rahamar Allah, na ɗaukeki ne tamkar yata, dan haka a matsayina na uwa shawarata a gareki shi ne ki ajiye wannan kunya a gefe" Ƙasa ta yi da kanta wajen amsa cewa ta gode sosai kuma In Sha Allah zata yi amfani da shawarinsu ita da momma, fatan alkhairi da fatan nasara mama Haulat ta yi mata sannan ta ɗaura da cewa sai da safe. Bedroom ɗin ta nufa cikin natsuwa. Baki ɗauke da sallama ta shiga ciki, babu kowa a ɗakin sai tashin daddaɗar kamshi da yake. Shiru ta tsaya tana bin ko'ina da kallo, tinani ta shiga yi a kan ina yake ne? Ko dai bai shigo ɗakin ba ne?. Ta kai almost 5 mins a ɗaya a wajen kafin ta iya fahimtar yana toilet yana wanka ne. A hankali ta taka ta ƙarisa cikin ɗakin, zata zauna a ƙasa sai ta tuna kaman momma da mama Haulat, momma ta ce ta mayar da gadansa wajen zamanta kamar yadda zata mayar da jikinsa gadanta. Tina hakan yasa ta ƙarisa bakin bed ɗin nasa a hankali ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. Shiru ta yi tana bin ɗakin da kallo tana ɗan shafa kwalin kayan dake ƙasar hannunta, bata ga lokacin da ya fito daga wanka ya shiga dressing room ba, amma shi ya ganta a cikin dakin, sai ya kawar da kansa kamar bai ganta ba. After some minutes ya fito sanye da kayan barcisa masu kyau da tsada, kao tsaye bed ɗinsa ya nufo, sai da ya matso kusa da ita ne ta iya gane ya fito, a cikin hanzarce ta ɗago da kallanta a kansa. Unexpectly suka yio four eyes, domin kuwa shi ma ita yake kallah yana jin kamar ya je ya ɗauki lallen hannunta hoto. Kwayar idanunsa ne suka rikitar da ita, a ruɗe ta miƙe daga saman bed ɗin, tsabar ta tsorata har ta ce mashi ina kwana ba tare da ta sam t faɗa ba. Kawar da kallansa daga kanta ya yi ya haye saman bed ɗinsa ba tare da ya amsa mata ba. Lokacin guda ta ji jikinta ya mutu na banza da ita da ya yi, sai ya tsaya kamar wata doluwa. Gabaɗaya ta ji ta karaya da wannan al'amari, sai dai lokaci guda zancen momma ya dawo ranta a in da take ce mata kada ta karaya, ta jajirce kome zai yi mata, tina hanan yasa ta ji kwarin gwiwa ya dawo mata, a hankali ta fara takawa ta nufi toilet ɗinsa dan ta yi wanka. Ta wutsiyar idanunsa ya bita da kallo, yarasa me yake damunsa, in dai ya ganta sai ya ji yana sha'awar ya cigaba da kallonta, ni kam nace saboda ita ɗin mallakinka ce ba tun yau ba, shiyasa kake kasa control na kanka a dik time da ka ganta. Sam bai yi ƙoƙarin hanata shiga toilet ɗinsa ba, saboda marainiya ce, kuma momma ta ce kada ya cutar da ita, dan tana kaunarta, ko dan momma ba zai tsawata mata ba.......... Ni kuwa nace anya Jaish yana da gaskiya kuwa? Wai ko dan momma, munafiki ko dai dan ya ga madarar kyau ba, bani dan momma kawai dai tin ganin da ya yi mata ɗazun ne zuciyarsa ta buga da sunanta, shi ne zai fake da momma, wlh maza aji tsoron Allah, amma dai ba koma zaka zo hannun ne, a lokacin ba wanda zai matse bakinka, da kanka zaka faɗi dan me kake tausaya mata, dan gulma da iskanci irin na jikokin Akka har da wani saboda ita marainiya ce, oh ni Princess Teema, mun dai san kun yi gadan abin, dan haka ba wata marainiya, ka dai ga kaya hankali ya tashi.......😅 (Ba ruwana bani na faɗa ba🥱 jarababbu kawai 🏃) Wayarsa ya laluɓo ya hau latsawa dan ya rage lokacin kafin time na shan cappuccinon ɗinsa ya yi. Ita kuwa wanka a tsara, sannan ta ɗauki towel ɗinsa ta goge jikinta, kayan da ta ajiye a wajen wash hand base ta ɗauko, fito da su daga cikin kwalin ta yi. Cikin natsuwa ta ware kayan. Nan fa ta zaro idanu tana kallansu, wasu irin shegun sexy sleeping dress ne wanda gabaɗaya net ne jikinsu, riga mai siririyar hannu ce zuwa gwiwa da ƴar pant ɗinta wanda ita ma net ce. Shiru ta yi tana tinanin yadda zata yi da wannan kaya. Wani zuciya ne ya ce mata wai shin ba mijinki zaki sakawa bane? Ko dai kin daina san shi ne?. A fili ta girgiza kai haɗe da cewa a'a bata daina san shi ba. Shi kuwa yana ta aikin latsa wayarsa idanunsa suna yi mashi gizo ma lallenta. Kamar ance mashi ya ɗago idanu unexpect ya sauke kakansa a kanta, ta fito daga toilet cikin ɗakin wannan shiga, sai wani kame kame take yi ta kasa sake jikinta, ta takure waje guda tana tafi kamar wadda aka yi wa kaciya. Hannunta yana rike da kayan da ta cire a cikin. Ya ilahi ya lilliahi, ai Jaish bai san time da ya waro idanunta waje ba, abar tasu ta motsa, sai kuma ko me ya tina? A hanzarce ya kawar da kallansa daga kanta kamar wani maras gaskiya. Ita kuwa ƙarisowa ta yi kusa da bed ɗin, kirjinta sai dukan uku uku take yi, kamar wata ɓarauniya haka ta lallaɓa ta zauna a gefen bed ɗinsa. Ai a miliyan ya dawo da kallonsa a kanta, razana ta yi ganin yadda ya watso mata kallo, har kamar zata miƙe ta fasa zama, sai kuma ta daure ta yi zamanta tana tinanin me zai iya ce mata. Nan take ya ji tongue ɗinsa tamkar an ɗaureta, ya kasa yin magana, sai kawai ya kawar da kallonsa daga kanta. Ganin hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya, cikin nitsuwa ta gyara ta kwanta a wajen tare da jan bargo ta rufe jikinta, sai kuma ta juyo tana fuskantar face ɗinsa, dan tana san ganinsa sosai, bata gajiya da kallonsa. My people's me kuke tinanin zai faru, da alama fa abar ta motsawa Jaish, to su dai suka sani, ni bari in leƙa wani ɓangaren ma dawo anjuma muga me zai faru, zai koreta ne ko dai zai yarda su kwana a tare?. 🔥🔥🔥🔥BABYN BABY.🔥🔥🔥🔥 Ɗaure take da white towel mai shegen laushi da kyau a kirjinta, daga wanka ta fito, skin ɗinta sai glowing yake ta yi, tana sanye da hular wanka a kanta. Gaban mirror ɗinta ta tsaya tana ɗan turo baki, santala santalan cinyoyintan nan sai sheki suke yi suna wani glowing, kamar dai jikin Sarina tamu ta kingdom of power, kun san Sarina da shegen san gyaran jiki, to haka jikin baby ma yake. Wayarta dake saman mirror drawer ta ɗauko, kamar zata yi kuka ta shiga contacts ɗinta. Number baby ta nemo, kai tsaye ta danna mashi kira. Wayar ta yi ringing har ta katse bai ɗaga ba. Juyawa ta yi tana kallan kanta a madubin, murya a shagwaɓe ta ce. "Baby, where did you disappear to today? You promised to come at night and comfort me, but now it's already 9 PM, and you haven’t shown up. I’ve been calling your phone even before I took a bath, but you refused to answer. Now tell me, how do you expect me to deal with missing you when you are my heart?". Tana magana tana tura baki. Shiru ta ɗan yi tana kallan kanta a mirror, ita kanta tasan kyakkyawa ce ita. Kamar walkiya lokaci guda unexpect taga wutar ɗakinta ya ɗauke gabaɗaya, lokaci guda duhu ya mamaye ko'ina, wani irin tsorata ta yi, nan take ta fashe da kuka tana kiran sunan Ammo da ɗan ɗaga murya. A hankali ta juyo cike da tsoro tana san laluɓawa ta fito waje, ga kuma wayarta a hannunta amma tsoro yasa ta mance da wayar bare ta kunna haske. Juyowa da zata yi sai ji ta yi ta bugi kirjin mutum. Wani irin razana ta yi da karfi ta waje baki zata yi ihu. Ɗip kake ji an toshe mata baki, ta baya baya ya janyota ya mannata da jikinsa, a hankali ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, sannan ya zuro hannunsa ɗaya a saman flat tummynta. Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne kalmar da take ta maimaitawa a cikin zuciyarta, haƙiƙa ta tsorata, tsoratar ma yasa sam sam bata ji kamshin perfume ɗinsa ba, ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi tana san ta yi ihu, sai dai kuma ta kasa. Ɗan bakinsa ya kawo dai'dai saitin kunnenta, can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "Babyn da ake ta kewa ake masifa a kan bai zo ɗin ba ne fa ya zo". Ya kai karshen maganar yana sauke ɗan bakinsa a saman wuyarta, sumbata ya bata a wajen kafin ya sake cewa. "Shagwaɓaɓɓa kuma masifaffiya kawai". Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, lokacin guda ta ji wani sanyi ya ratsa zuciyarta, sai dai har lokacin jikinta na rawa, tabbas kuma ya ji hakan, sam bai yi zatan zata tsorata har haka ba, do confirm yasan ita ɗin matsoraciya ce, amma bai yi zatan zata tsorata sosai haka ba. Sai sauke ajiyar zuciya take yi ta ƙasa yin magana, kamar an ɗaure mata tongue ɗinta. Tongue ɗinsa ya fitar ya ɗan lashi wuyarta, cikin nitsuwa ya zame hannunsa daga bakinta, a hankali ya karɓi wayarta dake hannunta, saman mirror drawer ya ɗaura wayar dan ma wai kada ta kunna mashi haske idan ta ji ya yi mata wani abin. Sai a lokacin ta samu damar buɗan bakinta, a tsorace murya na kerma ta ce. "Baby please turn on the light, I feel scared". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar. Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Sorry my baby, i didn't think you would be so scared, am so so sorry". Ya yi magana yana juyo da ita garesa. Da sauri ta faɗa saman kirjinsa jikinta na kerma, kirjinta sai dukan uku uku yake yi. Wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ya sauke, rungumeta ya yi a jikinsa sosai, a hankali ya hauro da hannunsa ta saman bayanta izuwa kanta, hular kanta ya zare ya jefar a ƙasa, hannun nasa ya tura cikin gashin kanta ya fara shafawa a hankali hankali. Ɗayan hannunsa kuwa, kai tsaye sai saman mazaunanta ya ɗaurasa, a hankali ya shiga motsa hannun nasa a wajen yana jin laushin mazaunanta suna kara fusgarsa. A rikice ta yi saurin ɗago kanta daga kirjinsa, yanzu kam murya babu shagwaɓa, magana straight ta ce. "Baby mekake yi haka kuma?". Tana magana tana zaro idanu while tana rarraba idanun nata sosai da nufin ko zata ɗan kalli face ɗinsa tun da wutar lamp a kunne. Ƙasa bata amsa ya yi, a hankali ya rankwafo da kansa a kanta, bata ankara ba sai ji ta yi ya haɗe fuskokinsu waje guda, tana ƙoƙarin sake yin magana a rikice kwatsam sai jin lausasan lips ɗinsa ta yi a saman tata. Ya ilahi, wani irin zaro idanu waje ta yi, tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa. Sumar tsaye ta yi mashi, ta ƙasa iya taɓuka komai, dik wasu kofofi na jikinta sai da suka ɓune domin karɓar saƙon baby, lokacin guda ta rasa control ɗinta, ta rasa gane a wace duniya take ciki. Ƙanƙame kayan jikinsa ta yi tana jin yadda tsikar jikinta yake wani irin mimmiƙewa, ta ji bakon alamari. Shi kuwa hot kiss ya shiga bata a cikin wannan duniyn. Shi ma nan take ya rasa control ɗinsa, da alama ya jima yana dakon zuwan wannan rana. Bata san lokacin da yasa hannunsa a hankali ya zame towel dake jikinta ya jefar a ƙasa ba, sai jin hannunsa a saman tula tulanta ta yi. Wani irin zabura ta yi ta fara ƙoƙarin kwace bakinta daga nasa, nan take idanunta suka ciko da kwallah tab. Jin tana ƙoƙarin kwace kanta daga hannunsa yasa ya yi sauri kara matseta a jikinsa sosai. Hannunsa dake saman tula tulanta ya haurar da shi sama izuwa saman wuyarta, ɗayan hannunsa kuma ya mayar saman mazaunanta. Gabaɗaya ta rikice, kuka ta hau yi mashi tana neman kwace kanta. Ai ina kin bata damar yin hakan ya yi, sai ma da ya ga kamar kafafunsa ba zasu iya ɗaukarsa ba saboda daɗi, sai ya ɗauketa cak bakinsa manne da nata suka faɗa saman bed. Hayewa kanta ya yi, cigaba da hot kiss ɗinta ya yi, ya mayar da hannunsa saman abubuwanta dake ɗaukar hankalinsa suna tafiya da imaninsa a dik time ɗin da ya ganta. Sosai yake matse mata su kamar wanda ya rasa control ɗinsa, sai wani irin numfashi yake zuba mata kamar wanda aka ɗaurawa buhun sement a saman cikinsa. Shiru ta nitsu tana kuka da hawayenta, ta ƙasa iya taɓuka komai, tana jinsa ya rinƙa bidiri a kanta, har sambatu ya rinƙa zuba mata, cike da tsananin sha'awarta ya kama hannunta ya ɗaura a saman bananarsa yana faɗin ta yi mashi wasa da shi cikin sambatu. Ihu ta so yi amma babu dama, dan yaki sakar mata ɗan bakinta, hannun nata ya haɗa da bananarsa ya ɗan matse yana jin wani irin shock a jikinsa. Yadda kuka san mai kiss ɗin huce takaici, ga dikkan alamu ya jima yana tsumayin ɗan bakin nan nata, shiyasa yau da Allah ya bashi dama ya capketa yaki saki, ta yi iya yinta yaki saketa har ta gaji ta yi lamo a saman bed ɗin tana jinsa. Lokacin da ta ji ya saki bakin nata, tana ƙoƙarin yi mashi magana sai ta ji bakin nasa a saman nipples ɗinta, suman kwance ta yi mashi, ai tamkar ya ɗaure tongue ɗinta, wani irin miƙa ta yi alamar sako ya ratsata da kyau da kyau, bata san lokacin da ta riko rigan jikinsa da karfi ta fara zuba mashi surutai na sambatu ba. Cigaba da tsotse mata su ya yi yana shafa hips ɗinta da hannunsa ɗayan, so yake ya taɓa gabanta amma kuma kaman ya ƙasa samun kwarin gwiwar isa wajen, a saman cibiyarta ya dawo da ɗayan hannunsa yana shapa mata yana ɗan yin ƙasa da hannun nasa yana san isa baban sashe. Can a cikin ƙwaƙwalensu kamar saukar aradu suka tsinkayo muryar Ammo tana kwala kiran sunanta a kan ya tin daga shiga wanka bata fito ba?. Jin muryan Ammo yasa dikkansu suka dawo cikin hankalinsu, a hanzarce ya saketa, gabansa da ta miƙe zat zafi sosai take yi mashi, gabaɗaya ya ratsa nitsuwarsa, shi babu abin da ya ragu dangane da abin da ya matsa mashi ya sanya shi zuwa wajenta ma face abin da ya ƙaru. A karo na biyu Ammo ta sake kiran sunanta, da sauri ya diro ƙasa daga saman bed ɗin, kai tsaye hanyar fita daga ɗakin ya nufa. Kunna switch na ɗakin ya yi ya sake ganewa kansa abin da zai kara ɗaga hankalinsa zai kuma hana shi yin barci. Ido cikin ido suka kalli juna da ita tana hawaye, ganin yana kallanta yasa ta yi saurin datse nata idanun. Shi kuwa tula tulanta ya ɗan zubawa idanu na ƴan sakanni kafin yasa kai da sauri ya fice. Sai da ya kunna wutar ne ma ta kalli ashe kayan barci ne a jikinsa, abin ya kara bata mamaki, wato dai ya kwnata zai yi barci ne barcin taki zuwa shi ne ya zo rage zafi, Allah sarki shi bai rage ba ta ƙaru mashi. A hanzarce ya fito parlourn, Ammo na zaune a saman sofa, bai bi ta kanta ba ya yi maza ya fice waje. Da kallon mamaki Ammo ta bishi tana al'ajabin yaushe ya zo gidan nan kuma?. Yana fita baby ta fito da gudu daga ita sai towel a jikinta, ta ɗauki towel ɗinta da ya jefar mata a ƙasa ta maida. Jikin Ammo ta faɗa tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, hankalinta a tsananin tashe ta fara ce da Ammo baby yana san ya cuceta. Ganin tana kuka yasa Ammo ta yi saurin rungumeta tare da fara rarrashinta. Ina ai kin yin shiru ta yi, ta ce ita dai baby ya cuceta, ashe shi mugu ne azzalumi. Haka ta rinƙa faɗan maganganu munana a kansa, da dai Ammo taga ba nitsuwa zata yi ba sai ta buge mata baki da ɗan karfi, a ɗan fusace ta yi suɓul da bakan cewa. "Mijin naki kike zagi haka? Kina da hankali kuwa?". Ai a miliyan baby ta tsayar da kukan da take yi, da sauri ta ɗago daga jikin Ammo, muryarta har rawa yake yi wajen tambayar Ammo me ta ce. Harara Ammo ta watsa mata kafin ta ce. "Kwarai abin da kika ji shi na faɗa, cewa na yi mijin naki kike zagi?". "Miji kuma Ammo?". A rikice ta yi tambayar. Jinjina mata kai Ammo ta yi alamar tabbatarwa. Ruɗani ta shiga, ta rasa gane kan zance, a ɗan tsorace ta ce. "Ammo taya baby ya zama mijina kuma ni ban sani ba? And shi ma bai sanar da ni ba". Tana magana wasu hawayen suna zubo mata. "Kwarai shi ɗin mijinki ne, kuma ban faɗa maki haka dan ki sanar da shi na faɗa maki ba, na faɗa maki ne dan kada ki fara ganinsa kaman mutumin banza, ba hakan yake ba, shi ɗin one ne in million, ko da sunan wasa kada ki sanar da shi na faɗa maki ke matarsa ce, dan bamu yi da shi zan sanar dake ba". Ta kai karshen maganar tana kai hannunta zata goge mata hawaye. Meyasa yake ɓoye cewa ita matarsa ce? Da alama kuma babu wanda yasan da wannan magana har iyayensa sai Ammo, to me dalilinsa na ɓoyewa?. "Ammo yanzu kina nufin baby mijina ne? To amma meyasa ni bai faɗa mun ba?". Ta yi maganar kamar wadda take cikin zumuɗi da matsuwar san jin amsa. "Tabbas mijinki ne, lokacin faɗa maki ɗin ne bai yi ba shiyasa bai sanar dake ba, dan haka kada ki sake zaginsa, dik abin da yake so shi zaki yi mashi, kuma kada ki kuskura ki sake yi mashi iyaka da jikinki kin ji na faɗa maki, jikinki mallakinsa ne, yanzu ma ina da tabbacin bai tafi ba, dan zai yi wuya a yadda ya fitan nan ya iya barin gidan nan yanzu, dan haka ki je ki bashi hakuri ki kuma faranta mashi rai kafin ya tafi, bana san ya tafi da damuwa". Tun da Ammo ta fara magana ta tsareta da idanu tana kallanta, sosai ta ji daɗin wannan magana, bata ji kamar a duniya akwai wanda take so biyunsa bayan Ammo, tana kaunarsa fiye da tinanin mai tinani, shi ne gatanta bayan Allah da Manzonsa da Ammo, a ko yaushe tana addu'ar Allah ya bashi mace ta gari wadda zata kula da shi kada ya sha wahala, dan shi ɗin na musamman ne a ranta, ashe ma ita zata kula da kayanta, wannan abu gaskiya ya yi mata daɗi. A fili ta furta. "Baby yanzu zaka sha soyayya irin na mata da miji, Ammo bari in je in same shi a waje ina zuwa, bari in je in rarrashe shi"....... "Eyee wato ko kunyata babu kike faɗin hakan ko?". Cewar Ammo............ Ɗan turo bakinta ta yi tare da watsawa Ammo hararar wasa ta kaka da jika, a shagwaɓe ta ce. "In tsaya jin kunyarki ki kwace mun shi? Kin ga babyna kyakkyawa ko? To babu wani kunya, yanzu tun da nasan mallakina ne shi ba zan bada kofar ire irenku su rinƙa samun damar yin magana da shi bama, dole na kula da shi sosai ta yadda zan hana shi ganin kowacce mace, ni dai yanzu ina zuwa kada ya tafi". Ta kai karshen maganar tana miƙewa, kamar ba ita ta gama murzan kukanta a yanzu ba. Da kallan kauna Ammo ta bita, tun da take bata taɓa kallan baby a cikin irin wannan farinciki ba, lallai yau Ammo ta ji daɗi, ta yi farinciki matuƙa, tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Cikin ɗaki baby ta koma, wayarta ta ɗauko domin ta rubuta mashi sakon ya jirata tana zuwa, sai ta tsinci sakonsa a cikin wayar ya turo mata minti uku da suka wuce. Be patient, my baby, I am so sorry and will not do it again. Don't be angry with me. I love you so much. Stop crying like that. I can feel the pain in my heart. Go to bed and have a good night's sleep". Shi ne abin da ya rubuta mata, kana ganin rubutun zaka san baya cikin hayyacinsa sosai, saboda dik ya haɗe word ya kwaɓesu, amma ta fahimci me yake san rubutawa, hakuri ya bata a kan abin sa ya yi mata. Cool murmushi ta saki a lokacin da ta kammala karanta sakonsa, a hanzarce ta danna reply. "Wait for me am coming now". Shi ne abin da ta rubuta mashi. Tana turawa ta ajiye wayar, a hanzarce ta fito da kayan barcinta ta shirya, riga da wando ce irin na jikinsa, shi yake saya mata komai, dan haka kayan barcinsu iri ɗaya yake saya tin ba yau ba, so ita ta ɗauka shakuwa ce yasa yake yi masu haka, dayawan abubuwa iri ɗaya yake saya masu. Feshe jikinta da turaruka masu daɗin kamshi ta yi, sannan ta ɗauki wani kyakkyawan hula ta sanya a kanta, dan kayan barcin basu da hula. Ko hijabi bata saka ba ta fito abinta, da alama irin renon da ya yi mata kenan, ya sabar mata da ƙananan kaya. Ammo na zaune a parlon ta zo ta wuce tana ce mata. "Ammo bari in je in rarrashi mijina in kwantar mashi da hankali". Taɓe baki ƴar tsohuwa ta yi. "Ke daga ganin sarkin pawa sai miya ya yi zaƙi ko? To wlh na dai faɗa maki kada ki yarda ki nuna mashi kin san mijinki ne shi". Ɗan murguɗawa Ammo baki ta yi. "To ya ranki ƴar tsohuwata? Kin san dai kullum dama ina faɗa maki ina san baby ko? To tun da na jima ina sonsa yanzu kuma na gano ashe shi ɗin mallakina me zan jira to?". Ta yi maganar tana ɗagawa Ammo gera guda. Yauwa my people's kunga laifin baby? A ta je ta kula da kayanta, ai irinsu baby ba'a sakaci da su, ni na bata goyan baya ɗari bisa ɗari ato. "Raina fes babyna, kina da gaskiya, shiyasa ai na sanar dake mijinki ne dan ki kula da shi kada ki bada kofar wata ta shigo, ai irinsu baby basu da yawa a duniya, maza ki kula da shi ƴar albarka". Na ce kunga laifin Ammo? Gara ta sanar da jikarta gaskiya dan su rike baby da kyau, irin wannan hidima da ya yi masu ai basa yi sake ya zulle masu ba, kai suna da gaskiya, jeki baby ki saka mana baby a kwana ya kwana yana kiran sunanki a cikin barcinsa ato, ni Princess Teema tare da my people's muna alfahari dake kuma muna bin bayanki ko ya kuka ce?. "Tsohuwata bari in je zan dawo mu sha hira yau, tayani da addu'a kekam". Ta kai karshen maganar tare da sanya kai da sauri ta fita, a ranta take ayyana ai ba zata taɓa sanar da shi tasan gaskiyar shi mijinta ba ne ba, a haka zasu cigaba da tafiya tana ƙara narka soyayyarta a ransa har sai ya furta mata da bakinsa, yo bata san ta mallakesa bama tana rikita mashi lissafin ƙwaƙwalwa bare yanzu da tasan nata ne shi ɗin! Ai baby sunanka sorry kuwa, dan wannan jika ta Ammo da alama ita ma ba tayar baya bace. Yana zaune a cikin motarsa ya kifa kai da steering motarsa yana jin wani irin raɗaɗi a ransa, sha'awar matar tasa tana neman kashe shi. Sam bai ga lokacin da ta nufo shi ba, sai ji ya yi ta buɗe kofar side ɗin da yake, yana ɗago kai dan yaga wanene ta yi saurin faɗawa jikinsa tana turo baki. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya iya ce mata. "Baki yi fushi dani ba baby?". Ƙasa ta ɗan yi da kai. "A'a na yi, amma Ammo ta tikasta mun da in zo in baka hakuri, kuma ta ce komai kace kada na yi maka gardama saboda ba zaka taɓa cutar da ni ba, kai ba mugu bane". ....... Ka ji baby da dabara, wai Ammo ta tilasta mata, ohohoho baby sunanka sorry, dan na lura babyn nan naka dabara gareta. "To amma ke kin yarda da hakan? Kin yarda da zancenta?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e ta yarda, sake sauke nannauyar ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce. "I can't control myself whenever I'm in front of you, but I'm sorry. In Sha Allah, I'll learn to control myself. I know I shouldn't have done that to you, and I will change, okay, my baby? Please don't be mad at your baby." "I will never be mad at you my baby. Please forgive me too, okay?" Rungumeta a jikinsa ya yi yana sauke numfashi a hankali hankali mai ɗauke da sirrika da dama. Hannunta ita kuma ta zura a. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Hannunta ita kuma ta zura a bayansa tana kwantar da kanta a saman kirjinsa da kyau. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara zubawa Allah godiya a cikin ransa, lokaci guda ya ɗan ji yanayin da yake ciki ta ɗan ragu, a kunne ya raɗa mata zata raka shi wani wajen?. Da sauri ta ɗago kanta, dama sarkin yawo ce ita ɗin, dan haka sai ta amsa da e zata raka shi. Ƙasa ya sake yi da murya kafin ya ce to gyara zamanki mu tafi. Da sauri ta gyara ya kunna motar haɗe da janyo kofar ya rufe, da gudu suka danna izuwa bakin gate. Gateman ya buɗe masu kofar suka nufi waje. Ina kuma zai kaita?. Za dai mu dawo mu bisu mu gani, dan sai munga komai.....👀🥱 🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥 A hankali ya juya ta ɗayar side ɗin ya zura kafafunsa kasa, kamar zai miƙe sai kuma ya fasa, kome ya tina sai ya juyo da kallansa a kanta, ɗaure fuska tamau ya yi kafin ya ce. "Momma bata faɗa maki ɗakinki daban da nawa bane?". Kun dai san yaran momma baya san raini, shiyasa kuka ga baya shiga harkar kowa, shiyasa yaki yin aure dan ma kada mace ta rai'na shi, a gaskiya Jaish ya rai'na mata dayawa, Allah zamu yi maganinka. Kai ta girgiza mashi tare da cewa. "Momma bata faɗa mun ba".............. Da hannu ya nuna kofar fita kafin ya ce. "Fita mun daga ɗaki, akwai ɗakuna dayawa a cikin part ɗin nan, ki ɗauki wanda ya yi maki, kada ki bari mu sake haɗuwa dake, dan bana san sake ganin face ɗinki". Ya kai karshen maganar tare da yunkurawa zai miƙe ya bar ɗakin. Cike da tsoro ta ce. "Ni momma ta ce mun a ɗakin da kake zan kwa............" Yanke maganarta ta yi saboda wani irin matsiyacin kallo da ya dallah mata, nan take ta ji tamkar an sanya kaca an ɗaure mata baki, da kyar ta haɗiyi yawu mai wuyar wucewa. "Bana magana biyu, idan na yi na farko na yi kenan, na biyu zai iya zame maki abin da ba zaki taɓa iya mancewa da shi ba". Cikin natsuwa ya yi maganar yana ƙara kaifafa voice ɗinsa, yana kai karshen maganar ya wuce ya nufi balconynsa yana jin wani ɓacin rai, shi kansa bai san ainahin abin da ya ɓata mashi rai ba, ya dai danganta ɓacin ran da ce mashi da ta yi a nan ɗakin zata kwana, amma da ni da ku mun san ainahin ɓacin ran daga ina ta samo asali. Wato abar tasu ta gado ce ta motsa, shi kuma baya san raini, shi ne silar ɓacin fa, amma sam bai gane hakan ba, sai wani haɗe rai yake yi............ Mahnoor da bata saba da irin halinsa na yanzu ba, idan ya yi abu ɗaya sai ta ji zuciyarta ta karaya, yanzu ma haka ne, dik sai ta ji anya ba zata hakura da shi ba kuwa? Ta jefawa kanta tambayar. Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta lallaɓa ta miƙe, jikinta babu kwari ta nufi waje idanunta suna cikowa da kwallah. A parlour ta tsaya tana tinanin anya zata sake yarda su haɗu kuwa? Dan ya ce kada ta sake bari ya kalli face ɗinta, anya ba zata shiga ɓuya kamar yadda ya buƙata ba kuwa?. Ta ɗan jima tsaye a parlourn tana tunane tunane har sai da ta kalli babu wata mafita sannan ne ta wuce ta nufi bedroom dake kusa da nasa. Ta yi mamakin ganin akwai komai a cikin ɗakin kusan kamar irin na bedroom ɗinsa. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi bakin bed ɗin ta zauna. A ranta ta kuduri niyar ba zata sanar da momma abin da yake faruwa ba, zata yi shiru har ta ga me zai iya faruwa gaba, tana da hankali ta fahimci ba komai zata rinƙa faɗawa momma ba, yakamata tasan abin da yakamata ta rinƙa faɗa mata da wanda bai dace ba. Shiru ta kwanta a saman bed ɗin cike da tunane tunane a ranta. Shi kuwa sai da ya gama zaman da zai yi a balconynsa har zuwa karfe 8:40, sannan ya miƙe ya dawo cikin bedroom ɗin, shikaɗai ba wanda ya taɓa shi yake ta faman ɗaure fuska kamar wanda aka cewa wutar jahannama zai zama makomansa, yana ta faman jan tsaki, sai wani haɗe gera yake yi, a fili ya furta momma tana san lalata mashi komai ta ja mashi raini dama ga Jawad ya gama zubar mashi da mutunci ya auri Chuchu, wannan abin ta kona mashi rai sosai. Mu fa mun san silar dik wannan ɗaure fuska da kake yi yaron Mommarsa, in zaka cire girman kai ka ajiye batun zata rai'naka ka daure ka rungumi ƴar matarka ka kawar da kai ma da ya fi maka, ko ya kuka ce my people's? Mu zaka ce baka san raini? Uhm na dai yi shiru. Saman bed ɗinsa ya haye, har ya kwanta sai kuma ya tina da batun Auta, da sauri ya miƙe zaune, a hanzarce ya ɗauko wayarsa, call ya danna na wata number da aka yi saving da pure heart. Kara wayar a kunnuwarsa ya yi yana sauraron yadda suke zayyana mashi cewa number a rufe take. Yau kwanaki uku kenan yana kiran number a kashe, haka kawai a ransa ya ji tabbas akwai abin da ake ɓoye mashi dangane da Auta, dan kuwa ko Dubai ta tafi suna waya a kullum, ya za'ayi ya kira su Yah Ramish ma su ce mashi bata zo gidan Abu Abdussalam ba, ya kira kakansu King Badeen ya ce mashi bata nan, ya kira uncle Rahab kuma sai ya rinƙa ce mashi ko ta yi barci ko bata kusa, to gaskiya shi yanzu ya fara tantama a kan wannan lamari. Yunkurawa ya yi zai miƙe ya nufi waje, dan ya je ya samu momma ta faɗa mashi gaskiya ina Auta take? Shi yanzu dik bai yarda da maganganunsu ba. Yan yunkurawa sallamarta ta daki dodan kunnnesa. Ta wutsiyar idanu ya kallenta. Tin daga kan kyawawan fararen kafafunta da ya kalla ya gane wacece, dan lallenta. Kawar da kallansa daga kanta ya yi yana jan siriri tsaki, a ransa yake faɗin ba dan wannan yarinyar marainiya bace babu abin da zai hana shi sakinta a daren nan, amma yanzu ma bai sanya a ransa zai zauna da ita ba, yana dai ƙoƙarin tina mafita, saboda shi dai wlh ba zai zauna da wannan yarinya ba. A gabansa ta zo ta tsugunna, tana sanye da hijabi black color zuwa gwiwowinta, ya dai rufe kayan barcin jikinta, hannunta ɗauke da cup of cappuccinon. Cikin sanyin murya ta ce. "Hamma ga cappuccinonka nan". Tsawa ya daka mata mai firgitarwa a kan ba ya ce kada ta sake bari su haɗu ba? Tsawar da ya yi mata ne har yasa ta saki cup ɗin ya faɗi ƙasa ya tarwatse, hakan yasa ransa ta kara ɓaci har ya ɗaga hannu zai dallah mata mari, sai ta yi saurin sunkuyar da kanta ta ɓuye shi a tsakanin cinyoyinta. Wani tsawa da ya sake daka mata a kan ta fita mashi daga ɗaki koku ma ya ɓaɓɓallata ne yasa ta yi saurin miƙewa da gudu zata fita. Mama Haulat kuma jin tsawan yasa ta shigo da gudu domin ta duba menene?. Karo suka yi da Mahnoor a bakin kofa zata fita, da sauri ta yi ƙoƙarin riketa dan ta tambayi ba'asi, sai dai ina, Mahnoor bata bada damar a riketa ba, da gudu sosai ta danna waje tana sakin kuka mai tsuma zuciya. Dawo da kallonta a kansa mama Haulat ta yi, cikin girmamawa ta ce. "Ranka ya daɗe lafiya?". Wani irin hararar da ya dallawa mama Haulat ɗin ma har sai da yasa ta ji ƴaƴan hanjinta sun kaɗa. Siririn tsaki ya ja tare da miƙewa ya zo ya wuceta ya nufi waje yana huci kamar ba lafiya ba. Kai tsaye part na King ya nufa, dan ya fahimci momma a kan Mahnoor bazata wani goya mashi baya sosai ba, King ne kawai zai rarrashesa. Sai dai kuma maganganu suka yi a kan Auta sosai kafin ya sanar da King shi fa baya san Mahnoor, ya tsaneta a kusa da shi, dan haka shi ko a rabata da in da yake, ko kuma shi ya bar gidan ya koma Dubai. Rarrashinsa sosai King ya yi kafin ya faɗa mashi cewa ya bashi nan da kwana goma zasu tsai da matsaya a kan hakan, amma yanzu dai ya yi hakuri suna tsaka da wani muhimmin aiki ne. (Aikin neman Auta kenan, kun san Jaish bai san ta ɓata ba, kuma an ɓoye mashi, so shiyasa ya ce mashi suna aiki kawai.) Aminta da zancen King ya yi, dan haka sai ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa ransa a ɓace sosai. Kafin ya koma mama Haulat ta goge wajen da cappuccino da Mahnoor ta kai mashi ya zuba, so ta gyara ko'ina tsab. Yana zuwa ya haye bed ɗinsa ya kwata, yau ba za'a sha cappuccino ba kenan. Amma fa ko da ya kwanta barci ta gagara zuwa, gabaɗaya ya rasa me yake yi mashi daɗi, shi kaɗai sai kunci yake yi har zuwa karfe 2 na dare. Ganin bashi da wata manufa yasa ya miƙe jiki ba kwari ya shiga toilet, alwala ya ɗauro ya zo ya fara gabatar da nafilfili, surorinma dik a daddafe yake karantasu, sai dai kafin ya idar da raka'a biyun farko tuni jikinsa ta wastsake ya koma normal. Qur'ani kenan my people's, dik damuwar da kake ciki kana fara karanta shi cikin ƙanƙanin lokaci zaka ji ka wastsake watsau, Allah dai ya ƙara ɗaukaka musulunci da musulmai bakiɗaya. Sai da ya yi sallar rakatainil fajir sannan ya bar saman daddumar ya wuce toilet, wanka ya yi ya shirya cikin arabs jallabiya brown color, ya nufi masallaci. Bai tawo ba sai karfe 8 na safe, jiya kwata kwata bai yi barci ba kenan. Yana dawowa karfe 8 ɗin ma dan kada su haɗu da momma sai ya wuce part ɗin King kai tsaye, dan a tinaninsa Mahnoor ta sanar da momma walaƙancin da ya yi mata daren jiya, shiyasa ya gudu. Sai dai abin mamakin shi ne ko da ya je part na King baya nan, ya tafi fada, ya sha madarar mamakin jin hakan, me ya fitar da King fada da safe haka? Ya jefawa kansa tambaya. Ganin babu mai bashi amsa yasa ya wuce kai tsaye ya nufi fadan. Sosai ya kara shan madarar mamakin ganin dik wasu masu muƙami a fada sun hallara, dik wasu manyan fada suna ciki, Aunty MieMie, uncle Abbas, uncle Jahiz, uncle Taheer, harda Guyson dik suna ciki, abin ya yi matuƙar ba shi mamaki. Dai'dai lokacin da ya sako kansa a cikin fadar sai ji ya yi uncle Abbas ya ce. "Wannan babbar gazawa ce a garemu ace katafaren kingdom kamar wannan wanda babu biyunsa a kasar nan, ga tarin tsaro wanda ba'a taɓa yin biyunsa a duniya ba, dik wasu abubuwa muna da su, amma har a shigo a ɗauki Zunaira a cikin masarautar nan a fita da ita yau tsawon satika shidda, kai gaskiya wannan babbar gazawa ce a garemu, kuma a gaskiya Zafar na rai'na tsaronka, ka bani kunya". Haba wani irin dum dum Jaish ya ji kirjinsa ta buga, har wani sara mashi ya ji kansa ya yi. Uncle Jahiz zai yi magana suka farga da Jaish dake tsaye a bakin kofa yana binsu da kallo yama rasa abin faɗe, sai yake jin kamar karya kunnuwansa suke yi mashi, kamar kuma mafarki yake yi, kenan dama Auta ba Dubai ta tafi ba? Kenan abokan gaba ne suka ɗauketa? Babbar magana lallai yau babu zaman lafiya. Ganinsa tsaye a bakin kofar shigowa ne yasa gabaɗaya suka yi shiru, King ne ya bishi da kallon mamaki, dan bai yi zatan zai zo fada a yanzu ba. Uncle Abbas ne ya yi karfin halin cewa. "Jaish ka shigo ciki mana, me ya tsayar da kai a bakin kofa kuma?". Ba musu ya ƙariso ciki, sai dai yana addu'ar Allah yasa karya kunnuwarsa suka jiyo mashi, har zuciyarsa ta fara yi mashi tsananin zafi, dan ba zai iya ɗaukar maganganunsu ba in dai gaskiya ce. A sofar kusa da uncle Abbas ya zauna, kansa a ƙasa cike da fargabar amsa da zai iya samu daga bakin uncles ɗin nasa ya ce. "Uncles ku faɗa mun da gaske abin da na ji kuna faɗa haka ne? Kada ku ɓoye mun kamar yadda daddy ya yi, dan Allah ku faɗa mun, daddy ya ce tana Dubai, and kowa na kira a Dubai kame kame kawai yake yi mun, ga wayarta a kashe baya shiga, please second dad ka faɗa ina Zunaira take? Kasan ni mai iya karɓar kaddara ce a dik yadda ta zo mun, to ka faɗa mun zan yi imani da koma menene ya sameta in kuma hakura". Dik wanda ya ji zantukan Jaish yasan cikin tsananin damuwa da ɓacin rai yake kalamansa, kuma sun san wlh karya ne ba zai iya ɗaukar wannan kaddara ba, kawai yana san su faɗa mashi ne ya ji wani hali Auta take ciki, idan suka faɗa mashi kuma sun san idan akwai abin da ya fi hauka ma zai yi masu, dan ba karamar yaki za'ayi ba, ba zai saurari kowa ba!. Shiru fada ya yi suna sauraron kalamansa masu kama da sambatu, dan kamar bai san me yake faɗa sosai ba, dik cikin fadan nan babu wanda bai tausaya mashi ba, saboda kowa yasan yadda yake da Auta, shi fa ya yi renonta, dik wanda ya ga Auta a lokacin yarintarta to tabbas zai ga Jaish a bayanta, a tare suke koda yaushe, shiyasa suka yi sabo sosai, har su commander sun tausaya mashi matuƙa. Allah sarki commander har ya yi wani irin mummunar rama sosai, saboda tashin hankalin da yake ciki a kan Hoorain, babbar abin da ya ɗaga mashi hankali ma shi ne King ya bada umarnin gani da kisa a kan Hoorain, saboda a tinaninsu amanarsu ya ci, kun san ya gudu ne ai, so sai aka saka dokan gani da kisa kai tsaye kawai a kansa. Tsit fada ya yi, kowa jiran abin da King zai ce suke yi, gabaɗaya hankulansu a tashi. King kuwa, sai da ya ɗauki a kallah 5 mins yana nazarin abin da zai faɗawa Jaish ɗin, dan yana fargabar kalar balai'n da Jaish zai tayar masu, shi kansa yasan bafa za'a wanye lafiya ba. Gyara zamansa ya yi tare da ɗan yin gyaran murya, cikin natsuwa ya ce. "Zan faɗa maka komai, amma ba yanzu ba sai mun haɗu da daddare a ɗaki, yanzu kaga muna wani tattaunawa ne mai matuƙar muhimmanci dan haka ka bari sai mun kammala". Kirjinsa ne ta amsa da karfi, ɗan dafeta ya yi kafin ya ce. "No Please dad, ba zan iya kara koda one minute bane idan har ban ji gaskiyar in da Auta take ba, you know my condition dad, please kada.............." Hannu kin ya ɗaga mashi alamar ya yi ba sai ya ƙarisa ba. Dakatawa da yin maganar ya yi yana sunkuyar da kansa ƙasa, saboda wani irin bugawa da karfi da kirjinsa take yi. "Zan faɗa maka menene yake faru". King ya faɗa.............. Da sauri Jaish ya ɗago kansa zuciyarsa na harbawa da ɗan karfi karfi, cike yake da fargabar abin da zai ji, baya san jin zancen da gaske bata nan. "Lallai ne tabbas Zunaira ta ɓata". Cewan King agin........... Dum dum ya ji kirjinsa ta sake bugawa, take ya ji hankalinsa na neman gushewa, a wani irin zabure ya miƙe tsaye kamar wanda ya rasa control ɗinsa. Hankalinsa a matuƙar tashe ya miƙe tsaye, uncle Abbas ne ya yi saurin riko hannunsa yana ƙoƙarin mayar da shi ya zauna, ya ƙasa yin magana, yau tsawon sati shidda babu Auta babu labarinta, gaskiya wanna abin ya girgizata shi. Dole ya koma ya zauna yana tunanin yadda zai yi?. King ne ya cigaba da bashi labarin yadda komai yawakana. Daga karshe ya rufe mashi da cewa. "A yanzu dai bayan assistant commander Hoorain babu wanda ya rage muke zargi da sace Zunaira! Dik wanda muke tunanin tana hannunsu ko suna da sa hannu a saceta mun bincika bata nan a hannunsu, Hoorain ne kawai bamu san in da yake ba, kuma muna kyautata zaton shi ya ɗauketa!!". Tashin hankali, wani irin zaro idanu commander Zafar ya yi, kenan dama King yana zargin Hoorain har haka ne? Sam bai taɓa yin wannan tinani ba. Shi kuwa Jaish zaro idanu ya yi, a miliyan ya sake miƙewa tsaye, zuciyarsa ce take tafasa tamkar an ɗaura dalma a wuta, jikinsa har tsuma yake yi yana tuna idan da zai ga Hoorain a yanzu sai Allah kaɗai yasan me zai faru. Dik su uncle Abbas kallansu a kansa, sun tausaya mashi matuƙa, sun kuma shiga damuwa dan abin da suke gudu shi ne yake shirin faruwa. Su commander Zafar dik kallansu a kansa, suma sun tausaya mashi matuƙa. Yana tsaye yana fuskantar King, a take ya fara zuba huci kamar mayinwacin zaki, ya buɗe baki cike da ɗacin rai zai yi magana unexpect aka turo babbar kofar fadar aka buɗeta. Gabaɗayansu kai kallansu a kan kofar suka yi. Ai a miliyan commander Zafar ya miƙe tsaye daga zaune a saman sofar da yake yana kallan kofar shigowar. A tare uncle Jahiz da Aunty MieMie ma suka miƙe tsaye. Shi kansa King abu kaɗan ya hana bai miƙe tsaye ba. Guyson and uncle Abbas suma a tare suka miƙe tsaye. Dikkansu sun zaro idanu tamkar idanunsu zai faɗi ƙasa, a matuƙar razane suke binsa da kallo. Tsaye yake cikin jarumta sosai, yana ɗauke da Auta a saman shoulder ɗinsa, gabaɗaya jikinsa jini ya lalata, ga fuskarsa babu hularsu na mayaƙa, so face ɗinsa ma dik ya yi dama dama da jini, da alama yaki ya gwabza kafin ya iso kingdom of power. Pretty na tsaye a gefensa ta riƙe hannunsa ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya tallabo Auta da shi dan kada ta faɗi, ita ma sai jini ne yake zuba a jikinta........... To me ya faru da su kenan?. Ciwon dake cikinta ne ya fama yasa jininta yake zuba, kallo ɗaya zaka yi wa Hoorain sai ka razana matuƙa, saboda yadda face ɗinsa take ɗaure kamar hadari, ga wani irin fusata dake kan face ɗinsa, jikinsa har lokacin tsuma yake yi. Guyson ne ya katse masu wannan shirun da cewa. "Tabbas Auta ce, tabbas ita ce a saman shoulder ɗinsa". Kafin guyson ya gama yin magana Hoorain ya tako cikin jarunta ya nufi cikin fadar. Sai dai yana zuwa tsakiya wasu zaƙwaƙuran warriors dake cikin fada su huɗu suka zare takubansu tare da yi mashi zobe, saboda sun san hukuncin da King ya yanke mashi shi ne hukuncin kisa. So sai suka kewayesa suna jiran King ya bada umarni su datse mashi kai. Cikin fushi da kakkausar uncle Taheer ya ce. "Kai ƙasƙantacen bawa har ka isa ka ɗauki Zunaira da dattin hannunka? Baka san doka irin na masaurar nan bane? (Dokar dik wanda ya taɓa jikin wata gimbiya hukuncin sare hannu ne ya hau kansa) Ko ka manta da dokar ne kare kawai?". Ransa ta sosu ne matuƙa. Ko kaɗai Hoorain bai yi kamar ya ji abin da ya faɗa ba, haka zalika ko kaɗan bai ji tsoron warriors da suka kewayesa ba, hasalima bai dakata daga tafiyar da yake yi ba, kai tsaye ya nufi King. Sai binsa warriors ɗin suke yi suna jiran umarnin King da ya tsaresu da idanu yana ganin ikon god. Su commander Zafar dik sun rasa bakin magana, kowa King yake jira kawai. Hoorain bai dakata ba har sai da ya isa gaban King, a nan ya sauke Auta da idanunta biyu amma azaba ya gabata koda motsawar kirki. Allah sarki, a yau Hoorain ya sha azabar wahala wajen cetarta ita da Pretty, mayakan da suke neman su Pretty ne suka kawo masu hari a dab hanyarsu na dawowa gida, an gwabza yaki ba karya, da kyar ya iya kashesu, wani mayaki ne ya ture Auta ta faɗa saman wani dutse ta fama ciwonta. Almost mayaƙa 30 ya yi faɗa da su, ya sha wahala sosai. Yana sauke Auta cikin fushi uncle Taheer yasa kafa ya takesa a kirji da karfi har sai da ya ɗan yi baya baya kamar zai faɗi, bawan Allah a gajiye yake, bai shi da kuzari sosai shiyasa uncle Taheer ya iya turesa ɗin. Wani irin zabura commander ya yi, tamkar shi uncle Taheer ya ture, har wani girgiza ya yi, wlh idan kuka ga commander sai kun tausaya mashi, saboda yadda idanunsa suka yi jajir ganin irin abin da aka yi wa Hoorain. Uncle Taheer cikin ɗaga murya ya sake cewa. "Kai kare ba da kai nike magana bane?". Shiru Hoorain bai yi kamar yasan da halittarsa a cikin fadan ba, sai ma juyawa da ya yi yana san sauka kasan stage ɗin dan ya isa ga Abbonsa. King dai ya rasa bakin magana, banda kallansu babu abin da yake yi, yana ƙoƙarin gane gaskiya ne shiyasa ya yi shiru, kun san dama yana zargin Hoorain shi ya saceta, to ga shi kuma shi ya dawo da ita, abin ya sanyasu a ruɗani, shiyasa King ya yi shiru yana ƙoƙarin tantance gaskiya. Ran uncle Taheer ne ya kara baƙanta matuƙa, cikin fusata ya umarci warriors da suka kewaye Hoorain ɗin da su yi mashi dukan mutuwa har sai ya durkusa a saman gwiwonsa. Da yake suma sun jima da takaicin Hoorain a ransu, sun jima suna bakincikin yadda ya zama shugaba a garesu, shi ne mai basu umarni kuma sun fisa shekaru, so hassada na cinsu sai basu tsaya jiran umarnin King ba, a hanzarce suka fara kai mashi duka wai dan ma kada King ya dakatar da su basu daka shi yadda yakamata ba. Da ganin yadda suka rufesa da jibga zaka iya fahimtar dukan huce takaici suke yi mashi. Wani mayaki ne ya taka shi a kirji da karfi har sai da ya yi baya baya zai faɗi ɗayan mayakin ya sake taka shi ta baya ya yi gaba gaba ya faɗi ƙasa ya buga kansa da jikin bakin stage ɗin. Ko kaɗan bawan Allahn nan bai yi yunƙurin zai rama dukan da suke yi mashi ba, saboda yasan koma me ya faru laifinsa ne, shi yake ƙoƙarin kai kansa in da Allah bai kaisa ba, so a ganinsa ya cancanci wannan hukuncin. Amma ku kunsan da Hoorain zai motsa dik waɗan nan mayaka sai sun gaza tafiya a kan kafafunsu ko? Dan dai ya barsu ɗin ne. Sosai suka shiga jibgarsa kamar waɗan da aka saukarwa da wahayin yin hakan. A hankali Auta ta motsa, da kyar ta miƙe tsaye a kan kafafunta, idanunta har sun rine saboda kuka, ta ƙasa iya buɗan baki ta yi magana. King yana kallanta ta fara lallaɓawa zata sauƙo kasan stage ɗin, amma kuma King ɗin bai dakatar da ita ba, ya bita da kallo kawai kamar dai babu shi a fadan. Anya ba wani abin King yake shiryawa ba kuwa, irin wannan shirun?. Cikin mayaƙan ta keta ta isa gaban Hoorain dake kwance suna dukansa, da kyar ta iya buɗan baki maganarta can ƙasa bata fita ta fara faɗin. "Ku kyale shi, ku barmun kayana, kada wanda ya sake dukan mun shi, ni ku dake ni a madadinsa, ku kyale mun shi". Su uncle Abbas dik an rasa mai bakin magana, shiru kawai suke binsu da kallo. Sai da suka ga Auta ta nufi wajen nasa ne uncle Abbas ya yi yunƙurin sauka ya kamata kada su jimata ciwo. Sai dai bai kai ga sauka ba uncle Taheer ya rigasa sauka cikin zafa, yana wani huci na kishi kamar zai haɗiyi zuciyarsa. Ita dai Pretty tana tsaye a bakin kofar shiga fada. Commander Zafar tamkar zuciyarsa zata fashe saboda tsananin tashin hankali, ga shi kuma babu halin ya yi magana bawan Allah, dole ya daure ya ɗauki dik hukuncin da aka yankewa Hoorain. Ta wani ɓangaren kuma fa commander ya sha jinin jikinsa ya kuma shiga ruɗani na ganin Hoorain da Auta, shi dai yasan sun yi yaki da Hoorain da mayakan Queen Zarina, to ta ya aka yi yanzu kuma Hoorain ya dawo tsaginsu, shi fa wannan abin ya ɗaure mashi kai...... Na tabbata kuma my people's kanku ya ɗaure sosai a kan wannan al'amari, kada ku damu alkalamin princess Teema taku ta amana zan warware maku komai dallah dallah. Uncle Taheer yana saukowa ya damko hannun Auta, da karfi ya ɗan jata ya mikar yana mai daka mata tsawa a kan wani dalili zata je wajen Hoorain dake matsayin bawa ƙasƙantacce mai gadinta. Fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, soyayyarsa ya rufe mata idanu, bata ji bata gani ta sake komawa zata tsugunna a kusa da Hoorain ɗin dan ta hana warriors ɗin nan dukansa. Kunsan jinin Modarawa da balai'n kishi, to haka larabawa ma suke da kishi, kishi bala'i ya rufe idon uncle Taheer, cikin fushi ya sake fisgo hannunta, da karfi ya fincikota, yana san janta su bar wajen. Ƙoƙari kwace kanta ta fara yi tana kuka hawaye bibbiyu. Ransa ne ya kara ɓaci cikin zafa ya cire hannu ya dalla mata mari a kumatu, shi kansa bai san ya yi wannan mari ba, kishi ce kawai. Wannan mari tamkar zuciyar uncle, uncle Jahiz, Guyson, King and Jaish ya mara, barema Jaish da sai da ya wani ja dogon numfashi a lokacin da marin ya sauka a kumatunta, a take idanunsa suka rikiɗe suka yi jajir, gabaɗaya gashin jikinsa har wani mimmiƙewa suke yi saboda ransa ya ɓaci. Guyson bai san lokacin da ya ce. "Uncle Taheer who the hell are you da zaka mareta? For what reason ma?". Uncle Taheer da yake cikin fushi ai bai ma san ya yi ba, kuma bai san guyson yana magana ba, sake cire hannu ya yi zai kara mata mari sai ji ya yi cak an damki hannunsa, ita kuma sai kuka take kara yi, a take yatsunsa biyar suka fito ruɗu ruɗu a face ɗinta. Wani irin zufa ne yake ketowa Hoorain a gefe da gefe face ɗinsa, jikinsa na wani irin tsuma, wasu zara zaran jijiyoyi ne suka bayyana a wuyarsa, da karfi ya damki hannun uncle Taheer, zuciyarsa na tafasar marin da ya yi wa kyakkyawan face ɗin Hoonairarsa. Ita kuwa dakatar da kukanta cak ta yi ganin Hoorain ya miƙe, sosai ta ji daɗi, dama ita bata san ya kwanta ya bari su yi ta dukansa ɗin nan. Da karfi Hoorain ya murɗe hannun uncle Taheer baya, ji kame kass ya karya mashi kashi, cikin ɓacin rai ya ɗauke fuskarsa da wata azababbiyar mari mai sanya mutu zuwa duniyar shaiɗanu a mafarki ya dawo. Take uncle Taheer ya gansa a wata iriyar duniya mai cike da wasu dodanni masu ban tsoro, marin assistant commander yasa ya bar duniyar mutane ya rasa hankalinsa. Sake kara mashi wani marin Hoorain ya yi take uncle Taheer ya zube ƙasa tamkar fawa, da alama sumewa ya yi. A hankali ya dawo da kallonsa a kan Auta, har lokacin huci yake yi kamar me. Su kuma warriors dake dukansa cak suka dakata suna binsu da kallo, har lokacin King bai yi magana ba, bai ma yi niyar yin magana ba, uncle Jahiz nema ya ɗan yi ƙoƙari wajen buɗe baki yana san cewa kowa ya samu waje ya zauna su jira umarnin King, sai dai bai iya yin magana ba sakamakon nufar su Hoorain ɗin da Jaish ya yi cikin zafa. Miƙa hannun Hoorain ya yi ya riko hannun yana ce mata sorry, a hankali ya ɗaura ɗayan hannunsa a saman lallausan kumatunta in uncle Taheer ya mareta, yana ƙoƙarin rarrashinta sai gani suka yi Jaish ya sanya kafa ya taka shi da karfi, sai wani huci shi ma yake yi tamkar wani zaki. Shi ma Jaish ba dukan uncle Taheer da Hoorain ya yi bane ya bakanta mashi rai har yasa ya taka Hoorain ɗin, a'a shi dan me Hoorain zai taɓa Auta da hannunsa a matsayinsa na mayaki? Wannan shi ne ya bakanta mashi rai har yasa ya takasa. Baya baya Hoorain ya yi saura kaɗan ya faɗi, amma abin ku da jarumi sai ya rike kansa yana mai ɗago da kallonsa a kan Jaish ɗin. Cikin fushi Jaish ya yi kansa, zaro takobi daga ƙugun ɗaya daga cikin warriors dake wajen jaish ɗin ya yi da nufin y sare hannun Hoorain dan ya taɓa Auta. Allah sarki rashin sani ya fi dare duhu, basu san irin gwagwarmayar da Hoorain ya sha wajen kare Auta ya ceci ranta har suka samu damar sake iya ganinta ba, ai ba dan shi ba da sai dai wata ba dai ita ba, amma saboda basu sani ba har ƙoƙarin datse mashi hannu suke yi. Ganin Jaish ya zaro takobin mayakin nan ne yasa Auta yin zafin namar shiga tsakaninsa da Hoorain, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita ta fara ƙoƙarin bawa Jaish hakuri muryarta na sarkewa. Ina ai bai saurareta ba, dan ransa ya ɓaci sosai shi ma, hannu yasa ya tureta gefe da karfi ta tafi zata kifa. Kamar walkiya haka Hoorain ya tareta ta faɗa jikinsa, hakan ba ƙaramin kara kona ran Jaish ya yi ba, zuciyarsa ce ta ƙara fusata, gadan gadan ya nufesu, yana zuwa ya sanya hannu ya damki wuyar Auta zai sake tureta gefe guda. Kankame Hoorain ta yi tana faɗin. "Yah Jaish dan Allah ka yi hakuri ka rabu da shi, wlh bashi da laifi......" Bata ƙarisa maganar ba Jaish ya saukar mata wani marin a gefen ƙuncinta, abin da bai taɓa yi ba bai kuma taɓa sa ran zai yi ba a rayuwarsa sai ga shi yau ya yi, ko a mafarki bai taɓa zatan akwai wata rana da zata zo ya ɗaura hannunsa a jikin Auta ba, sai ga shi yau ɓacin rai yasa ya yi hakan. Haba ai yana sauke mata wannan marin ran maza ta ɓaci, a miliyan Hoorain ya kai hannu ya danki wuyar Jaish, sai wani irin huci yake yi yana furzar da wani irin numfashi mai tsananin zafi daga bakinsa. Yana damkar wuyar Jaish sai da King ya miƙe tsaye, gabaɗaya waɗan da suke cikin fada sun yi wani irin zaro idanu tamkar idanunsu zasu faɗi ƙasa, commander Zafar yau sai da hantar cikinsa ta ƙaɗa, mayaki da capkar wuyar Prince da kansa, tashin hankali, lallai yau akwai bala'i. Warriors dake cikin fada gabaɗaya suka zari takubansu suka yi kan Hoorain, da karfi shi ma ya zaro takobinsa da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma ya shake Jaish da shi. Mamaki ya hana Jaish motsawa. Ɗaga takobinsa Hoorain ya yi ya sauketa a in da ja layi a floor na fada, cikin kakkausar murya yana huci ya ce. "Dik wanda ya matso kusa da ni sai na datse kansa na rantse!!!". Tashin hankali, da yake dikkan warriors sun san halinsa sun kuma san fin haka zai aikata idan ransa ya ɓaci, sai dikkansu suka ja suka tsaya tamkar an sassaƙasu. Ido cikin ido Hoorain ya kalli Jaish, cikin kakkausar ya ce. "Dik ranar da ka sake ɗaura hannunka a jikinta, na ratse sai na datse hannunka, ba kai ba dik wanda ya sake taɓata tabbas zai iya rasa ransa, ni ka dakeni iya dukan da zaka yi mun, ai ni na yi maka laifi, ita kuma me ta yi maka? Meyasa zaka taɓata?". Yadda kuka san babu Jaish a cikin fada, tamkar ba shi Hoorain ya shakewa wuya ba, idanunsa sun yi jajir kamar wuta, mamaki yana shi ya gwada kwanji da Hoorain ɗin ma. "Hoorain kana da hankali kuwa? Kasan kuskuren da kake san tabkawa kuwa? Ka manta a ina kake ne? Kasan bala'in da kake san jefa kanka a ciki kuwa?". Cewar commander, cike da tsananin tashin ya yi maganar. Ɓacin rai dai shi yasa idanun Hoorain suka rufe, baya ji kuma baya gani, a yadda yake ji yanzun nan ko King ya zama shamaki a tsakaninsa da ita ko kuma ya taɓa lafiyarta to fa zai iya kawar da shi. Tashin hankali!!. "Umarni nike baka da ka gefar da takobinka kasa kuma ka zube ƙasa a saman gwiwonka ka bawa Prince hakuri". Cewar commander Zafar again, yana magana tamkar ya manta wanene Hoorain, ya manta ya ɗan nasa yake idan ya fusata. Guyson ne ya matsa ya riko hannun Auta domin ta bar wajen kada wani abin ya sake samunta. Sai dai ina, fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, kuka sosai ta ke yi. Kai jama'a wato akwai tashin hankali a Kingdom of power, HOORAIN YA SHAKE JAISH SABODA AUTA! BABBAR MAGANA, WANI IRIN HUKUNCIN KUKE TINANIN HOORAIN ZAI IYA FUSKANTA? NA FARKO ANA ZARGINSA DA SACE GIMBIYA, NA BIYU YA SUMAR DA UNCLE TAHEER, NA UKU YA TAƁA JIKIN GIMBIYA HAR YA RUNGUMETA, NA HUƊU UWA UBA YA SHAKE WUYAN PRINCE JAISH DA KANSA, ME KUKE TINANIN ZAI IYA FARUWA NE WAI?. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Guyson ne ya matsa ya riko hannun Auta domin ta bar wajen kada wani abin ya sake samunta. Sai dai ina, fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, kuka sosai ta ke yi. Shi kuwa Hoorain cigaba da daka masu warning ya yi a kan taɓa Zunaira, ɓacin rai ta yi ɓacin rai........ Da sauri Auta ta matsa kusa da Hoorain, dan taga kamar bashi da niyar sakar mata Yah Jaish ɗinta, shi kuma Jaish ɗin yana tsaye tamkar wadda aka sassaƙa, to ta ji tsoron kada Jaish ya mutu dan taga idanunsa kamar wuta. Kusa da Hoorain ta isa, ɗan hannunta ta kai saman nasa tana ja tana faɗin. "My Hero ka sake shi mana, Yah Jaish ɗina ne fa, please ka sake shi, kada ka illama mun shi". Tana magana voice ɗinta baya fita sosai, muryarta ya dashe sosai saboda kuka. Hoorain da ya yi nisa sam baya jin kira, ko kaɗan bai ji kalamanta ba, sai ma ƙara shake Jaish da ya yi. Uncle Jahiz ne ya sauko kasan stage ɗin, da sauri ya matsa in da suke, dan hankalinsa ya tashi sosai na ganin jinin dake zuba daga cikin Auta wanda ba kowa ne ya lura da shi ba, har ta fara ganin jiri jiri saboda ta rasa jini sosai. Yana zuwa ya ɗauketa cak ta baya ya nufi hanyar fita da ita. Ihu ta fara zunduma da voice ɗinta da baya fita sosai, sam bai saurara mata ba sai da ya fice da ita, bai kuma zame ko'ina da ita ba sai parking space, pretty ta bi bayansu, cikin motarsa ya sanyata, da kansa ya kunna motar, da gudu ya figeta suka nufi hospital na kingdom ɗin. Hannu Jaish yasa ya damki hannun Hoorain ɗin, da karfi ya ɓanɓarota daga wuyarsa, Hoorain sam bai yi ƙoƙarin hanasa ba, saboda dama shi idan da shi zasu daka ba zai tanka ba, saboda sun kai su dakesa ɗin ne, amma su taɓa gimbiyarsa flowers zuciyatsa kam wlh ba zai bari ba. Dan haka yana ganin Jaish ya ɓanbare hannunsa daga wuyarsa, cikin fusata sosai Jaish ya kai mashi wani duka mai firgitarwa a kumatu har sai da ya yi tangal tangal kamar zai faɗi ƙasa, amma ya yi ta maza wajen rike jikinsa ya tsaya cak. Uncle Abbas ne ya yi saurin tasowa ya matso ya rike Jaish ɗin, dan idan ya barsu abin ba zai yi kyan gani ba. Commander Zafar gwanin ban tausayi, har idanunsa sun ciko da kwallah dik jaruntar nan tasa, kowa yana da rauninsa, tabbas ba shakka Hoorain shi ne raunin commander Zafar. Jan hannun Jaish uncle Abbas ya yi suka nufi kofar fita fada ta kofar shiga cikin gida. Da karfi Jaish ya kwace hannunsa daga hannun uncle Abbas, ransa in ya kai miliyan to ya ɓaci, har kamar Hoorain ne zai rike mashi wuya? Lallai yau bai ga mai iya dakatar da shi ba daga yi wa Hoorain illah ba!!. Shi kuwa uncle Abbas sam baya san abin ta wuce haka, fatan abin ya tsaya a haka kawai yake yi. Gadan gadan cikin zafa ya nufi Hoorain ɗin again. Ni da ku dik mun san a nan dai Hoorain ya tabka babban kuskure, ai ko zai shaki kowa banda Jaish dake matsayin yaya ga Zunaira, amma dai soyayya ce ta rufe mashi idanu, kuma idan kuka kwantanta abin da kanku zaku ga shi ma Jaish bashi da laifi, dan kowani yaya na gari zai tsayawa kanwarsa ce a koma inane, kuma shi dai Jaish ba soyayya yake yi ba bare muce yasan zafin da masoya suke ji, dikkansu dai cikin rashin sani suke, amma dai abin bai yi daɗi ba gaskiya. Cikin zafa ya nufi sauka kan stage ɗin ya ƙarisa gaban Hoorain sai ji ya ji an rike hannunsa ta baya, cikin zafa ya juya dan yaga wanenen?. Yana juyawa suka yi ido huɗu da Aunty MieMie, ƙara ɗaure fuska sosai ya yi yana wani huci yana san kwace hannunsa, shi kuwa Hoorain yana tsaye a kan kafafunsa ya sunkuyar da kansa ƙasa zuciyarsa tamkar zata yi bindiga. Cikin dakiya King ya ce. "Abbas kama shi ku tafi".......... Matsawa uncle Abbas ya yi yana riƙosa suka tafi, ba dan King ba da bai ga abin da zai sa yau ya kyale Hoorain ba. Kallan Aunty MieMie King ya yi kafin ya dawo da kallonsa a kan commander Zafar, tsab King ya gama fahimtar soyayya ce take a tsakanin Hoorain da Zunaira, wannan bakincikin ita ta hana shi yin magana, dan ya fahimci Zunaira tana san Hoorain sosai, shi kuwa ko mutuwa zasu yi bai ga dalilin da zai sa ya bawa Hoorain Zunaira ba, dan bai shirya ganin yarsa a matsayin karamar bazawara ba, kowa dai yasan mayaƙa rayuwarsu babu tabbas, a kowani lokaci suna iya mutuwa, kuma ko da King ya ƴanta Hoorain ɗin ya zama ɗan ahali ba zai taɓa zama mai ƴanci da rayuwarsa ba, saboda ya riga ya tarawa kansa tarin makiyan da ba zai iya faɗa dasu domin ƙwatar kansa ba, dik in da ya je masu san ɗaukar fansa a kansa suna kewaye da shi, dan haka shi King yasan me matsalar, dole kuma ya dakatar da wannan soyayya cikin sauri tin kan abin ya yi nisa ya fi karfinsu. Hmmm King a ganinsa soyayyarsu bata yi nisa ba kenan, my people's mu gaya mashi wannan soyayya ta fi shekaru 8 ne ko dai mu barshi su masoyan su nuna mashi karfin soyayyar dake zuƙatansu?. Tsit fada ya yi kowa idanunsa a kan King, jiran word ɗinsa kawai suke yi, saboda babu wanda ya isa ya yi magana idan ba ya yanke abin da ya dace a kan wannan case ɗin ba. Commander dai ji ya yi ƙafafunsa sun gaza ɗaukarsa, hakan yasa ya koma saman sofa ya zauna tare da sunkuyar da kansa ƙasa, domin shima ya rigada ya gane Hoorain ya fahimtar da Zunaira abin da yake ransa, idan baku manta ba dama commander yana hana shi kusantar Auta, ashe dik irin wannan yake gudun mashi, so yanzu ya fahimci soyayya suke yi da Auta, kuma ya fahimci King Zuhair ma ya fahimci hakan, Allah sarki yasan ko mutuwa Hoorain yake yi ba za'a taɓa bashi auren Auta ba, saboda ba kowa ma yake yarda ya bawa mayaƙa yayansa ya aura ba bare ita da take matsayin gimbiya, tab ai abune wanda sai in Allah ya ƙaddara akwai aure a tsakaninsu ne Allah zai kawo sanadi, amma kam akwai matsala. Good 10 mins King ya ɗauka shiru yana binsu da kallo kafin ya ɗan yi gyaran murya, with sharp voice ya fara magana kamar haka. "I think ka fahimci abin da na fahimta a tsakanin yaran nan ko Zafar?". Dum dum commander ya ji kirjinsa ta buga, dan ya fahimci in da King ya dosa. Da kyar ya iya jinjina kai cikin girmamawa ya amsa da ya fahimta. "Ba sai na faɗa maka hukuncin da ya dace da Hoorain ba, ka fi kowa sani tin da tare da kai aka kafa waɗan nan dokoki da hukunce hukuncen, dan haka ina mai baka umarnin da ka hukunta shi yadda yakamata, daga karshe ka datse alakar dake tsakaninsa da Zunaira bana san sake yin magana a kan hakan!!". Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, haba King, wani irin zalinci ne wanna? Ta ya za'ayi kace uba ya hukunta ɗansa bayan kasan hukuncin yana da tsauri da tsanani sosai? Wannan babban zalinci ne wlh. Tamkar commander zai yi kuka, idanunsa sun tsananta ja sosai, kansa a ƙasa cikin girmamawa ya ce. "Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, dan girman Allah ina neman alfarman da abawa wani daga cikin mayaka damar su hukunta Hoorain, ba zan iya hukunta shi ba". Wlh dik taurin zuciyar Aunty MieMie na jinin Modarawa sai da ta ji zuciyarta ya karaya a wannan gaɓa, saboda abin da ciwo ace uba ya hukunta ɗansa hukunci mai azabtarwa, kuma dole ya yi yadda hukuncin take a rubuce idan ba haka ba dikka a azabtar da su, innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, wannan abin akwai taɓa zuciya. "Amma dai kasan bana magana biyu ko Zafar?". Cewar King. A tinanin King fa idan ya sanya commander ya hukunta Hoorain to tabbas Zunaira zata fita a ransu gabaɗayansu, dan uba da ɗa ba wasa ba, shiyasa ya yi masu irin hakan, burinsa kawai ya yanke alakar Hoorain da Auta. Hmmm akwai matsala. Shiru commander ya sunkuyar da kansa yana jin wani irin raɗaɗɗi na ratsa zuciyarsa, haƙiƙa bai taɓa yin danasanin zamansa da su King ba sai yau, ya ji da ace shi ba musulmi bane bai san girman Allah ba da babu abin da zai hana ya kashe kansa a kan ya yi wa Hoorain wannan hukunci, amma bashi da zaɓin da ya wuce ya yi mashi ɗin, dan haka sai ya miƙe jikinsa na kermar tashin hankali. Da kyar ya iya taka kafafunsa ya isa in da Hoorain yake tsaye. Guyson ne ya juya da sauri ya bi bayan uncle Abbas da ya fita da Jaish, dan kun san guyson akwai tausayi, ya ji bashi da kwarin zuciyar kallan commander Zafar a halin da yake ciki. Aunty MieMie ce ta yi saurin juyowa ga King da nufin ta taushesa ta bashi hakuri wani ya hukunta Hoorain ba mahaifinsa ba. Sai dai tana ƙoƙarin buɗe baki King ya ɗaga mata hannu fuskar nan tasa babu alamar wasa, ya ɗaureta tamau kamar hadari, ya ɗaga mata hannu alamar ta yi mashi shiru. Zuciyoyi dayawa sun karaya a cikin fada, dayawan jama'ar dake ciki sai da idanunsu ya tara ruwa mai ɗumi, dik mai imani sai ya tausayawa commander idan ya gansa. Riko hannun Hoorain ya yi, jansa ya yi suka juya suka nufi hanyar fita, da kyar yake jan kafafunsa saboda rashin kwarin jiki. Da kallo kowa ya bisu, warriors dake cikin fada kuwa daɗi suke yi suna faɗin Allah ya kama commander yau, ba ya iya hukunta ƴaƴan mutane ba, to yau abin ya juyo ta kansu ai shikenan shi ma ya ɗanɗani yadda iyaye suke ji a lokacin da yake azabtar masu da ƴaƴa. "Ku shirya mana motoci zuwa hospital duba Zunaira, sannan ku ɗauki Taheer ma zuwa hospital". Shi ne abin da King ya faɗa kafin ya koma saman kujerarsa ya zauna yana jin wani irin kuna a ransa, wai Hoorain da Zunaira suna soyayya, wannan abin ya kona mashi rai matuƙa, har ji ya yi kansa na sara mashi. Dik wannan abin da yake faruwa a cikin gida babu wanda yake da labari sai Mammien su Sarina and mama da suke da c.i.d, kun san suna da masu saka masu ido a lamarin fada, so har sun samu information a kan abin da yake faruwa. JAISH kuwa kai tsaye part ɗinsa uncle Abbas ya wuce da shi, sai huci yake yi, wlh ba dan King ba yau bai ga abin da zai hana shi yi wa Hoorain dukan mutuwa ba. Tab yadda Jaish fusata haka kuna tunanin ko mutuwa Hoorain yake yi zai yarda ya bashi auren Auta kuwa? Hmmm akwai dai matsala. A bakin bed uncle Abbas ya zaunar da shi yana tausan shi a kan ya yi hakuri. Hannu ya ɗaga tare da cewa uncle Abbas. "Second dad it is okey, zaka iya tafiya babu komai". Yadda ya yi maganar yana fitar da huci mai zafi zaka iya fahimtar har yanzu bai huce ba. Kin matsawa daga kusa da shi uncle Abbas ya yi, dan ya fahimci komai zai iya faruwa idan ya tafi ya bar shi a haka. Dan haka sai ya zauna tare da shi ya cigaba da rareashinsa. Shi kuwa guyson part ɗin momma ya wuce kai tsaye dan ya faɗa mata abin da yake faruwa, zuciyarsa ba zata iya ɗaukar hukuncin da King ya yankewa commander Zafar and Hoorain ba, abin akwai ciwo sosai, hukuncin ya yi masu tsauri sosai, ace uba ya kai ɗansa ɗakin duhu dan hukunta shi, bayan ya gama hukunta shi da kansa kuma zai jefa shi a gidan yarin masarautar tare da horo mai tsanani bayan na ɗakin duhu, wlh commander ba zai iya ɗaukar wannan musifar ba, dole su momma su saka baki ko za'a samu sassauci. Yana ƙoƙarin shiga part ɗin momma ciwonsa ta tashi, wani irin azabbabben murɗa mashi da cikinsa ta yi ne yasa ya dafeta da karfi yana sakin ihu mai ɗan sauti kaɗan. Wani irin numfashi ya fara fitarwa da zafi zafi yana kara dafe jikin bango, a hankali ya fara jujjuyawa ko zai ga wani a kusa ya taimaka mashi, dan ko motsawa ba zai iya yi ba. Dai'dai lokacin Mahnoor ta fito daga part ɗin Jaish cikin shiga ta girma wato ta matar Prince wanda mama Haulat ce ta ƙawata mata shigar, so zasu je gaishe da Akka ce ita da Chuchu, shi ne ta ce bari dai ta fara duba momma kafin su je wajen tsohuwa. Chuchu na can suna sallama da Yah Jawad zai tafi office, sai aikin rungume juna suke yi kamar ba gobe. Ganinsa ya dafe bango yana hawaye yasa Mahnoor ta yi saurin nufarsa tana tambayarsa lafiya kuwa?. Riƙo hannunta ya yi ya kasa yin magana, da hannu ya nuna mata part ɗin monma a kan ta taimaka mashi su je can. Daddagewa ta yi tasa karfinta dikka zata taimaka mashi, gabaɗaya ya sake mata nauyin jikinsa saura kaɗan su zube ƙasa, da kyar ta iya kamewa ta iya ɗaukar nauyinsa, sai kuka yake yi sosai yana cigaba da dafe cikinsa da hannu ɗaya. Ya yi mata nauyi sosai, amma haka ta daddage ta tallabosa da kyar suka nufi part ɗin momma. Allah ya taimaketa momma tana parlor zaune ita da Mahreen and Zee suna hira, momma kenan, mai farar zuciya, ta haɗe ƴan'matan dikka ta rikesu abinta, babu kyara ko kyama. Suna shigowa cikin parlourn saura kaɗan su zube ƙasa gabaɗayansu, a hanzarce momma ta miƙe ta taresu. Kuka ya kara sakawa mai sauti yana nunawa momma cikinsa babu bakin yin magana. Wlh idan ciwon guyson ya tashi sai kun tausaya mashi, ba karamar wahala yake sha ba...... WAI MENENE DALILIN WANNAN CIWO NA TSAWON SHEKARU HAKA? AKWAI AYAR TAMBAYA GASKIYA, TO MUJE DAI ZUWA. Gabaɗaya ya sakewa momma nauyinsa, saman sofa ta kwantar da shi tana tambayar lafiya tana kallan Mahnoor. Cikin natsuwa Mahnoor ta ce ita ma bata san me ya same shi ba, kawai ta gansa ne a bakin kofar shigo part ɗin. Riko hannayensa momma ta yi tana tambayarsa meyake yi mashi ciwo. Cikin tsananin ciwo da azaba ya fara nuna mata cikinsa yana kara tsananta kukansa. Da yake momma tasan irin azaban da yake sha idan ciwon ya tashi sai hankalinta ya tashi sosai. Wayarta ta ce Mahreen ta miƙa mata, dama wayar tana kusa da ita. Ɗauko wayar ta yi ta miƙa mata tana kallan guyson ɗin. "Ji fa, kato da shi ne yake yin kukan ciwo, Adda Mahnoor kalle shi fa, wannan anyi wawa gaskiya". Tana magana tana harararsa. Ko kunyar idanun mommarsa bata ji ba take yi mashi wannan iskancin. Ɗan buge mata baki Mahnoor ta yi tana kallanta. Hannu ta ɗaura a saman bakin nata ta hau murjesa tana faɗin. "To me na yi maki zaki buge mun baki?". Momma dai hankalinta baya a kansu, ƙoƙarin kiran number Dr Raj kawai take yi. Ta kuwa yi sa'a bugu ɗaya ya ɗauka, a lokacin ya bi bayan Ramish yana faɗa mashi Leesharh tana da buƙatar karin jini idan ba haka ba zasu iya rasata, an gwada jinin Bilal and shi Dr Raj ɗin dik jininsu bai yi irin nata ba, o negative take da shi, ashe shiyasa take da shegen janircewa da taurin rai, jinin sojoji ke gareta. Dr Raj ya yi iya yinsa a kan Ramish ya tsaya a gwada jininsa idan ya yi a sanya mata ya ce ba zai bata jini ba, dan yana jin nau'in jinin nata yasan irin nasa ne, bama sai an gwada shi ba, amma dai ya ce ba zai bayar ba, a sayi sabo a saka mata ko kuma a nemo ƴan uwanta dik a in da suke su zo su bata, dan ta bada ranta ta cecesa ba wai hakan yana nufin shi sai ya tsaya mata a kan komai ba, ya yi abin da yakatama ya yi, shi yanzu ma ya fara zarginta ne, dan da ya zauna ya yi tinani ƙwaƙwalwarsa ta basa dik yadda aka yi tana da masaniya game da komai, ashe banza kwanaki ya saketa, ya yi kuskure, dik yadda aka yi ta san komai, wannan abin ya baƙanta mashi da yasa ya ji ya tsani zuwa in da take. Tun da ya sanya kafa ya bar ɗakin da ya cire mara bullet bai sake waiwayarta ba, Dr Raj yake kula da ita karkashin umarnin Bilal, abin kuma da baku sani ba shi ne, kamar Bilal ne yake kara tunzura Ramish a kan Leesharh, saboda Ramish ɗin ya ja baya da ita. Amma shi Bilal abin da bai sani ba shi ne, Ramish yana amsa mashi dik abin da ya faɗa mashi da fatar baki ne kawai, ba wai dan yana ɗaukar hakan a matsayin gaskiya ba, in short da Bilal da Leesharh dikka yanzu suna a karkashin sarrafawar Ramish ɗin ba tare da sun sani ba, dik yasa masu question mark, dik bincike yake yi a kansu ta ƙarƙashin ƙasa domin ya gane gaskiyar abin da yake faruwa. Waɗan can guy da suka harba a hall ɗin nan da Ramish ya je ya gansu sai da ya razana matuƙa, domin kuwa ya sha ganin ɗayan guy ɗin a tare da Bilal several times, and akwai hotunansu tare da Bilal a wayar Bilal ɗin, hakan yasa Ramish ya kara tsananta zarginsa a kan Bilal matuƙa. And kuma yaki bari Bilal yaga gawarwakin mutanen, hakan ma tana daga cikin aikinsa, lokacin da zai je h-q duba mutanen Bilal ya so su tafi tare, amma sai ya ce a'a zai je shi kaɗai, ashe kuwa gara da ya tafi shi kaɗai ɗin, dan yana ganin mutumin ya ce ba zai bari Bilal ya fahimci komai ba, dan in da gaske Bilal yana da masaniya a kan komai idan yasan wanda suka kashe mutuminsa ne to zai iya katsewa Ramish yunkurinsa na gane suwaye suke da sa hannu a lamuran. Shiyasa ya canzawa kowa a gidan yanzu, ya kuma dai'na bari suna samun damar haɗuwa da shi, yanzu haka tin safe Dr Raj yake san haɗuwa da shi ya rokesa da ya taimaka ya bawa Leesharh jini amma ya gagara samun damar ganinsa, kuma yana cikin gidan, ganinsa ne ya hanasu dama. Sosai Bilal ya shiga damuwa a kan ɗauke mashi wuta da Ramish ya yi, yanzu haka tun jiya bai samu damar haɗuwa da Ramish ɗin ba, ya yi ya yi su haɗu abin ya gagara. A ɓangaren Ramish ɗin kuwa, wlh jinyar kansa yake yi sosai, domin kuwa dik wasu bincike da zai yi mutanen da zai zarga suna da sa hannu a yunƙurin kashesa sai ya gansu a tare da Bilal, duniya yau Ramish ya rasa me yake yi mashi daɗi, ya shiga tashin hankali da kunci da bai taɓa shiga makamancinsa ba, tun daga jiya kirjinsa take yi mashi wani irin azabbabben ciwo mai tsananin gaske har yau, haka yake daurewa yana aiki. Wani lokaci sai ya ji kamar ya dakatar da binciken nan domin fargabar abin da zai iya cin karo da shi, yana tsananin fargabar abin da zai binciko, zuciyarsa tana rawa a kan binciken nasa, sai ya ji kamar ya haƙura kawai, gara ya zauna da Bilal ɗin a haka bai binciko gaskiya ba sai ya fi mashi, amma kuma yana san sanin gaskiya ta wani fannin. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Cikin natsuwa Dr Raj ya yi picking call ɗin momma. Hankalinta a tashe ta fara zayyana mashi ciwon guyson ya tashi, ai yana daga zaune bai san time da ya miƙe tsaye ba, muryarsa a ɗan dishashe ya ce what. A tinanin Dr ciwon Guyson zata ɗauki a kallah shekaru biyu ko uku kafin ta sake tashi, amma sai suka ga akasin haka. A hankali ya koma ya zauna tare da haɗe natsuwarsa waje guda, sannan ya ce momma ta yi gaggawan kiran likitoci da wuri so zo, lokacin yi mashi aiki kuma bata yi ba, dan bayan shekara ɗaya ake yi mashi, so da yin wancan aikin bai kai shekara ba yanzu, to me matsalar? Dr ya tambayi kansa. "Bari in kira Jaish ko Jawad su yi gaggawar kiran Drs yanzun nan, idan Drs sun iso sai mu yi waya dan su duba mun shi su ji menene matsalar kuma". Cewar Dr. Jinjina kai momma ta yi tare da katse kiran ta dawo da hankalinta a kansa, a hankali ta fara tofa mashi addu'oi tausayinsa yana kara ratsa mata zuciya. Zee da Mahnoor tun da suka ga Momma ta tashi hankalinta har haka sai suka fahimci lallai ciwon nasa babba ne ba karami ba. Ita ma Mahreen yadda taga momma ta tashi hankali sosai sai ta sha jinin jikinta, lokaci guda ta ji tausayinsa ya kamata, a hankali ta dawo kusa da momma ta zauna suka shiga tofa mashi addu'oi a tare. "Mahnoor kira mun mijinki idan yana ɗaki". Cewar momma, ta yi maganar ba tare da ta kalli Mahnoor ɗin ba. A hanzarce ta amsa da to haɗe da miƙewa ta nufi waje. Gabaɗaya Zee jikinta ya yi sanyi, sai ta ji tausayin guyson ɗin ya kamata, barema yadda taga yake juyi kamar zai faɗo ƙasa daga saman sofar sai momma ta taresa, sam baya a cikin hayyacinsa, kuka kawai yake yi yana dafe da ciki. Kun san ciwon cikin maza babbar azabace babba sosai. Dab Mahnoor zata shiga part ɗinsa uncle Abbas kuma yana fitowa, karo suka ɗan yi, baya ta yi da sauri tana sunkuyar da kai ƙasa. Cikin girmamawa ta ɗaga mashi gaisuwa. Fuskarsa babu annuri sam ya amsa mata gaisuwar, tsabar tashin hankalin da suke ciki ma sam bai lura da wadda ta ɗaga mashi gaisuwa ba, shi ya zaci Chuchu ce ma, bai wani tsaya ba, ya yi gaba ma kafin ya amsa gaisuwar tata. Ciki ta shiga tana waigo uncle Abbas ɗin har ta kusa daka tuntuɓe. Bakinta a ɗauke da ɗan siririn sallama ta tura kofar bedroom ɗinsa, bata jira ya amsa ba ta shige ciki. Tana sauko kanta dai'dai lokacin ya miƙe tsaye yana zare idanunsa a kan screen ɗin wayarsa dake hannunsa, kamar dai wani abin tashin hankalin ya gani. Me kuke tinanin ya gani?. Jin an turo kofar yasa a slow ya ɗago da kallansa a kanta, ɗayan hannunsa na dafe da kansa dama, a hankali ya koma gefen bed ɗinsa ya zauna idanunsa a kanta, fuskar nan tasa kamar hadari. Sosai ta tsorata ganin halin da yake ciki, sai ta ji shakkar tinkararsa ta isar mashi da saƙon momma, kamar ta juya a guje ta fita, amma tina cewa sakon momma ce sai ta daure ta nufesa. A gabansa ta tsugunna tana faɗin. "Barka da safiya Hamma".......... Wani irin kallan kasan idanu ya bita da shi, kansa ne yake sara mashi tamkar zai fashe, idanunsa sun kara tsananta ja sosai. Sam bai amsata ba, bai ma da niyar amsawa. Ganin hakan yasa ta kara yin ƙasa da murya cikin girmamawa ta ce. "Hamma momma ta ce kazo Yah Omar bashi da lafiya.........." Zaro mata idanunsa da ya yi yasa ta yanke maganar tana sunkuyar da kanta ƙasa da sauri. Yau wani irin kallo yake binta da shi kamar bana lafiya ba, kamar kuma na haushi ko na tuhuma. Miƙewa tsaye ya yi yana cigaba da satar kallanta ya nufi waje. Da sauri ta miƙe ta bi bayansa, kai tsaye part ɗin momma suka zame, yana saka kafarsa a parlon call ɗin Dr Raj na shigowa wayarsa. Bai yi picking ba ya yi zafin namar karisawa ciki dan yaga momma a birkice. Yana zuwa bai tambayi meyafaru ba dan kowa yasan da kwanan zancen ciwon nan, dan haka sai bai wani ɓata lokaci wajen tambayar meyake damunsa ba, hannu kawai yasa da sauri ya ɗagosa, sai saman shoulder ɗinsa. Bai tsaya sauraron kowa ba ya yi zafan wucewa izuwan ɗakinsu na jinya. Da sauri momma ta rufa mashi baya, su Mahnoor dik suka rufa masu baya. Ana cakwakiya a kingdom of power fa, Auta dai lokacin sun yi gaggauwar karɓarta, sai dai kafin su isa hospital ɗin ma ta sume, saboda ta rasa jini sosai. Akwai cakwakiya fa, ga Leesharh tana san karin jini Ramish yaki bata, ga kuma Auta a hospital, ga guyson rai a hannun Allah, Khadijah ma bata gama warwarewa ba, Hoorain yana karɓar horo a ɗakin duhu, kai abubuwa dai babu sauki. To bari mu leƙa wani wajen kila a samu ɗan sauki kafin mu dawo. 🔥🔥🔥🔥BABYN AMMO🔥🔥🔥🔥 Sai karfe 12 dai'dai baby ya dawo da ita, sai Allah kaɗai yasan in da ya kaita, tana zaune a saman laps ɗinsa, a hankali yake tuƙa motar tamkar baya san taɓa komai, saboda tana a kan laps ɗinsa ne kuma ya ja hakan. A parking space na gidan ya yi parking na motarsa, kamar mai raɗa ya furta sunanta, shiru bata amsa mashi ba ta wani yi lamo a kirjinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sake ambatar sunanta, a karo na biyun ma shiru ta yi mashi bata amsa ba. Rankwafo da kansa a kanta ya yi, hannunsa yasa yana ɗan shafa kumatunta, a hankali ya ɗan zira yatsansa manuniya a cikin bakinta yana ɗan shafa bayanta da ɗayan hannunsa, ƙasa ƙasa yake ambatar sunanta cike da so da kauna. Tana jinsa kin amsawa ta yi, sai da ta ji ya zura yatsarsa a cikin bakinta ne ta kama ta ɗan fara cizawa a hankali hankali. "Dama baki yi barci ba ne?". Ya faɗa yana ɗan leƙo face ɗinta. Kanta ta ɗago suna fuskantar juna, kamar zata yi kuka ta amsa da bata yi ba. "To meyasa akaki amsawa baby da na yi magana"........... Turo baki ta ɗan yi. "Saboda in ja maka aji ne mana, ni baby fushi nike yi da kai ma"..... Ɗan lumshe idanunsa ya yi kaɗan. Can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "To mu je ɗaki in rarrasheki, nasan Ammo ta yi barci yanzu". Da sauri ta zaro idanu haɗe da girgiza kai. "A'a baby ba sai ka rarrasheni ba, ni nama huce, mu je ciki ko?". Kai ya ɗan girgiza. "Ni ba zan shi ga ba, ke dai jeki sai da safe zan zo". Kuka ta fara ƙoƙarin saka mashi, da sauri ya ce. "A'a ba sai kin yi kuka ba, na ji zan rakaki ciki, tashi mu je to". Hannu tasa ta laluɓo hannun motar ta buɗesa, sannan ta zuro kafafunta waje ta fito. Bayanta ya biyo shima ya fita, kofar ya rufe kafin ya riko hannunta a cikin nasa suka nufi ciki. Tabbas kuwa Ammo ta yi barci abinta, shi kuwa yana san ya ɗan latsa babynsa amma yana fargabar kada ta yi mashi irin na ɗazun, dama yanzu ma ɗar ɗar zuciyarsa yake yi da ita, ya kuma ƙasa sanar da ita cewa mallakinsa ce ita dan ya samu abin da yake so. Haka dai ya daure ya rakata har bedroom ɗinta, ta kwanta saman bed ya kashe mata wutar ɗakin ya fito, kai tsaye motarsa ya koma, yana shiga bai ɓata lokaci ba ya tashi motar ya nufi hanyar gidan dan dare ta yi, sai dai zuciyarsa cike da tinanin baby kamar yadda ita ma zuciyarta cike da tinaninsa har barci ya ɗauketa. ASUBA TA GARI. 🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥 A hankali Ronnie ya dawo da kallonsa a kan yayan nasa, razana sosai ya yi ganin Black Tiger ya juya idanunsa, ko ba'a faɗa mashi ba yasan wani muguntar zai aikata, hakan yasa hankalinsa ya yi wani mummunar tashi, yana ƙoƙarin buɗe baki ya taushi yayan nasa sai gani ya yi Black Tiger ya nufi toilet waje. Yana ganinsa ya fice daga ɗakin, da sauri ya bi bayansa dan ya taushesa, sai dai kuma yana fitowa sai bai gansa ba. Hakan yasa ya yi gaggawar nufar bedroom ɗinsa dan ya duba Sweetie, hankalinsa ya tashi sosai, jikinsa har yana tsuma. A gaggauce ya sanya password ɗinsa ya buɗe kofar. Turus ya tsaya a lokacin da yaga babu Sweetie babu alamarta a cikin ɗakinsa. A miliyan ya nufi toilet dan ya dubata, Sweetie tana ja mashi masifa, tana yada mashi da hankali, ita wai ba zata bi komai a hankali bane? Sai ta ja tashin hankali ya kashe shi ne?. Babu ita babu mai kama da ita a cikin toilet ɗin, hankalinsa ne ya kara tashi. Ina Sweetie ta yi?. Main parlour ya nufo cikin zafa, ga shi yau yana da wasa sannan in the next two days zasu yi graduation a school, yana da tarin abubuwa dayawa, akwai partyn da zasu yi dama, yagama tsara yadda zai shiryata su tafi school ɗinsu tare ta je tana neman rusa mashi komai. Floris kawai ya isko a parlour tana zaune tana tsara yadda zata yaudaresa su fita Black world kamar yadda Master Devil ya karantar da ita. Tana ganinsa ta yi wanu irin razana wadda sai da ya sanya shi dakatawa cak yana kallanta, a cikin ransa ya ayyana tambayar meyafaru take razana da kallansa? Ko dai bata da gaskiya ne?. A fili kuwa tambayarta ya yi ina Sweetie? Fuska a ɗaure tamau ta amsa mashi da. "Ina da haɗi da ita ne da kake tambayata? Ko dama muna kasancewa tare ne?"....... Ya ɗan yi mamakin jin amsarta a garesa, amma da yake neman Sweetie yake yi sai bai tsaya ɓata lokacinsa wajen biye mata ba. Da sauri ua juya ya nufi escalator zai koma sama, a hanyarsa na komawa saman ne ya hango Delisha ta side ɗin ganganrowa ƙasa. Hegiya ta ladabtu, ai tana ganinsa ta dukar da kai cikin girmamawa ta haɗe hannayenta dikka biyu tana yi mashi alamar gaisuwa. Hankalinsa baya a jikinsa, so bai wani bi ta kanta ba ya bazama sama, neman Sweetie ya fara yi kamar hauka, yana nemanta yana neman yayansa..... My people's ina kuke tinanin Sweetie ta shiga?. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Dik in da yake zatan zai ga Black Tiger babu shi a wajen, sosai hankalinsa ya kara ɗugunzuma ya tashi, har wani jiri yake gani mai karfi yana ɗebarsa. Shiru ya tsaya yana ɗan tinani ina yakamata ya kara dubawa ko zai gansu. Can ya tina yankamata ya duba side na master Devil ko ita ko Black Tiger ɗayanzu yana can. Da sauri ya nufi wajen yana jin kansa na ɗan sara mashi, Sweetie and Black Tiger zasu iya kashe shi da fargaba watarana. Gabaɗaya warriors dake empeir ɗin har da Robbot dake aiki sai da suka dukar da kansu ƙasa a lokacin da ya fito waje dan zuwa part ɗin master Devil. Bai bi ta kan kowa ba ya yi saurin nufar part ɗin. Zaƙwaƙuran warriors guda huɗu haɗe da Robbot biyu ne suka rufa mashi baya a lokacin da ya nufi part ɗin dan bashi tsaro. Babu ko excuse yana zuwa kai tsaye ya afka katafaren parlon master, shiru ya ji babu alamar motsin kowa, hannu ya ɗagawa warriors da suka take mashi baya alamar su dakata a wajen, sannan ya nufi stair case da zata sada shi sama. Parlourn master ko'ina tsab tsab a gyare ga kamshi da yake tashi....... Kai tsaye bedroom na master ya nufa, yana zuwa ya tura kofar ya afka ciki abinsa...... Wani irin birki ya ja a bakin kofar yana zaro idanu, tamkar kwayar idanunsa zasu faɗi ƙasa. Tin da yake a duniya bai taɓa ganin babban mutum kamar master tsirara ba sai yau. Ya ilahi ya lilliahi, master Devil tsirara haihuwar uwarsa, ga Oxil da Barack dikkansu tsirara suna aikata liwaɗi, abin takaicin ma su uku ba su biyu ba, kowannensu yana ganin tsiraicin junansu. Do hakan ba wai laifi bane a Black world, saboda basu da addini, suna abin da suka ga dama, sai dai shi Ronnie abin ne ya bashi mamaki dan bai taɓa gani ba. Shiru ya yi yana kallansu, sai a yanzu ƙwaƙwalwarsa ta tariyo mashi yadda Oxil yake san yi mashi kiss a kumatu wani lokaci ya ce zai yi kissing na lips ɗinsa, idan baku manta ba Oxil mutuminsa ne sosai, so a dik lokacin da suka haɗu da shi yana san yi mashi kiss, ashe sing na luwaɗi yake nuna mashi. And shi kansa master ya jima yana sha'awar Ronnie sosai, ba ma shi kaɗai ba, masu sha'awar Ronnie Allah ya yi yawa da su a faɗin birnin, sai dai shi kuma Ronnie Allah ya gani tin tasowarsa luwaɗi yana ɗaya daga cikin abin da ya tsana, kyama abin take bashi, shi ko zina bai taɓa sha'awa bare luwaɗi, kuma yana da feeling a kan mace sosai, sai dai Allah ya nufesa da rahma ya karesa daga afkawa ɗaya daga ciki. A tare master da Oxil suka juyo da kallonsu a kan kofa jin an turota. Master ya haye kan Oxil yana sucking ɗinsa, ga shi dikkansu suna da kirar wrestlin, lafiyayyu da su, shi kuma Barack yana tsaye a tsakiyar bed ɗin master hannunsa riƙe da rubar penis oil yana shafawa bananarsa yana wani murjeta sai kyalli yake yi, ko kunyar junansu basa ji. Dikkansu idanunsu jajir alamar shegiyar ta motsa, barema master da ya fisu lafiya da karfi, jikinsa dik jijiyoyi a mimmiƙe zara zara alamar jarababbene sosai, dik namijin dake da jijiyoyi sosai a jiki alamar jaraba ta yi mashi yawa. Dik da sanyin Ac dake ɗakin sai haɗa zufa suke yi saboda yadda suke sucking na junansu da zafa zafa babu wasa, sai wani nishi suke yi suna sambatu wa junansu. Ƴan iska sun ga Ronnie kyakkyawa, ga kyan fuska ga kyan jiki, uwa uba ga kayan aiki ga shi da kiran karfi shiyasa dik suke haɗiye yasu a kansa ko kunya babu. Ronnie dai sumar tsaye ya yi, sai ya ji tamkar mafarki yake yi, a cikin zuciyarsa ya ayyana zai tambayi Sweetie abin da su master suke yin nan kam menene and me hukuncinsa. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Ganin Ronnie ne yasa master ya zare bananarsa daga bayan Oxil ya miƙe tsaye ya sauko ƙasa daga saman bed ɗin, ko kunyar a ga tsiraicinsa bai ji ba ya tsaya a tsakiyar bedroom ɗin yana kallan Ronnie, dama a kan network yake ya kuma jima yana sha'awar Ronnie sai ya ji wani irin azabbabben sha'awarsa ya sake kama shi da ya gansa a yanzu. Tsikar jikinsa har wani mimmiƙewa yake yi, burinsa kawai ya gansa a kan Ronnie yana biyan buƙaransa. Master na miƙewa tsaye take Ronnie ya ji wani irin amai mai karfi ya kwace mashi,saboda kyamar da suka bashi. Da gudun gaske ya juya ya fice daga cikin bedroom ɗin. Sai dai bai kai ga ƙarisa sauka stairs case ya yi ƙasa ba amai mai karfin gaske ya ɓalle mashi. Dan dole ya durkushe a wajen ya fara tikar amai kamar zai amayar da abin dake cikin cikinsa. Shi kuwa master yana ganin Ronnie ya fita ya ɗan ciza laɓɓansa da ɗan karfi, yaso ace Ronnie ya nuna ra'ayinsa a kan wannan harka da yau sun yi bidir a kansa, da sun kashe kishin da ya jima a ransu, amma ya kwabsa masu, sai dai suna san dole ko ba yau ba sai sun ɗanɗani daɗinsa. Oxil ne ya sauko kasan bed ɗin, kusa da master ya matsa, hugging ɗinsa ta baya ya yi tare da ziro hannunsa ta gaba ya capki bananar master yana yaba ƙoƙarin bananar, wai zazzafa ce, dan tana bashi wuta, auzubillahi. Barack ne ya matsa ya rungumi master ta gaba, cike da jaraba ya haɗe bakinsa da master suka fara kissing na juna. Sai dai shi master dik ba su bane yanzu a gabansa, ya kwaɗaitu ne matuƙa da Ronnie, ji yake yau idan bai kwana a kan Ronnie ba babu zaman lafiya. Cigaba da murjan juna suka yi dan jin daɗi da morewarsu. To ina team Ronnie, kun dai ji da mata da maza dik sha'awarsa suke yi ko? To sai ku taya ɗan yaron nan da addu'a Allah yasa kada ya afka tarkonsu ya karesa. Shi kuwa Ronnie amai ya yi tin na hankali har ya fara yin na rashinta, dan tamkar zai amayar da ƴaƴan hanjinsa gabaɗaya, ya yi nadamar zuwansa part ɗin master. Wlh gwanin ban tausayi a lokacin da yake amai ɗin, yana wani irin kakari mai sauti dake kwazura kirji. Sam daga master har abokan sharholiyar tasu babu wanda ya biyo bayan Ronnie bare asa ran zasu taimaka mashi. Sai da ya yi amansa sosai sannan ya miƙe, da kyar yake iya taka kafafunsa yana wani tangal tangal kamar zai faɗi ƙasa ya nufi ƙasa yana kara tsananta tsakar wannan shaiɗancin a ransa. Da kyar ya iya fitowa parlon, a nan ya tarar da warrios da suka rakosa, wucesu ya yi ya fita waje. Da sauri suka rufa mashi baya, bai zame ko'ina ba sai part ɗin Jack, dik wahalar da ya sha a kan aman da ya yi dai tinanin Sweetie na ransa, dan haka ya nufi wajen Jack domin ya duba ko ta je can. Babu ko excuse nan ma ya afaka ciki, Jack shi ne assistant master Devil. Nan ma babu kowa a parlour, gabansa ne ya ji ya faɗi saboda tinawa da ya yi a halin da ya isko su master, sai yake ganin kamar a cikin irin makamancin wannan hali zai sami Jack ma. Dik sai ya ji kamar ya fasa shiga, har zai juya sai kuma ya tina Sweetie tana da matikar mahimmanci a wajensa, dan haka yana da kyau ya je dan dubata. Sama ya haura yana faɗin Hasbunallahu wani'imal wakil, Sweetie ta ce mashi ya rinƙa faɗin hakan a dik time da ya samu dama, hakan zai karesa daga dikkan wasu sharruka dake nufosa, so sai ya zaɓi ya faɗeta a wannan lokaci. Ko da ya zo dai'dai bakin kofar Jack sai da gabansa ta faɗi, jirjinsa ta ɗan buga da karfi, fargabar abin da zai gani yake yi, sai ya ji kamar ya juya ya koma, amma ya cigaba da tsananta furta Hasbunallahu wani'imal wakil a cikin ransa kafin ya tura kofar kamar mai tsoron a kama shi. Kamar mai yin laɓe ya ɗan turo kansa ya leƙo cikin ɗakin. Ai a miliyan ya janyo kofar ya rufe bayan ya cire kansa, dafe saitin zuciyarsa ya yi yana tinanin kenan dikka warriors na yayansa haka suke. Kun san me ya gani yasa shi rufe kofar nan kuwa? Jack ne tare da wasu ƴan'matan biyu tsirara suna holewarsu, shi master da maza biyu, shi kuma Jack da ƴan'mata biyu. Tsabar Jack tantiri ne ma yana kan ɗaya yana rike da breast ɗin ɗaya. Gabaɗaya Ronnie yasa me yake yi mashi daɗi, bayin Allah Ronnie san da yake krista ma yana kyamar waɗan nan laifuka ina kuma ga hasken musulunci ta ratsa zuciyarsa? Ai dole ya tsaneta sosai, musulunci ai ba wasa ba. Dafe kansa dake tsananta sara mashi ya yi, da sauri ya juya ya nufi part ɗin Black Tiger a cikin ransa yana tsinewa Master and Jack, ƴan iskan banza takadirai kawai. Bedroom na Black Tiger ya dawo, babu kowa a ciki, saman bed ya zauna tare da haɗe kai da gwiwonsa yana tinanin in da sweetie ta tafi, baya ma tinanin ina yayansa nasa yake, yafi tinanin Sweetie. A daidai lokacin da yake tinaninta ita kuwa tana cikin wani irin hudu mai tsanani a wani ƙungurmin daji mai ban tsoro da ɗaga hankalin dik wani halitta mai rai, zaka saurara iya saurarawanka ba zaka taɓa iya jiyo sautin komai ba, babu wani motsi, duniya dik ta yi tsit. Ɗaɗaɗaure take a jikin wani irin sarka mai kifiyoyi, a jikin wani bishiya aka ɗaureta wanda kasar wannan bishiya wutace sosai take ci, turiri da numfashin wutar yana azabtar da ita matuƙa, gabaɗaya jikinta ya ɗauki zafi rau, tin tana iya daurewa har ta fara ruwan hawaye, ga shi ta juya gabas da yamma gudu da arewa sam sam babu alamar kowa, duhun dake wajen yasa ta gaza iya gane a ina ma take, ta gaza gani gabanta. Sosai ta yi tsananin tsorata, ga wutar sai ƙara ci yake yi yana haurowa sama, jikinta har kerma yake yi tana haɗa wani irin uban zufa mai ban tausayi. A yau dai ta gama saddakarwa mutuwa zata yi, dik namar jikinta har ya fara laushi, hankalinta a tsananin tashe yake baiwar Allah. Sai dai kuma dik da wannan azaba ko kusa ko alama bata ji kamar zata janye kudurinta a kan canza zuciyar Black Tiger da ta yi niyyar yi ba, sai ma ƙarin kwarin gwiwa da Allah ya bata. ••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 Lokacin guda haske ya gauraye wajen, gabaɗaya idanunta ta datsesu da karfi saboda ganin wannan haske ya kashe karfin ganinta. A hankali ta sake waro idanunta domin ta ga daga ina wannan hasken ya fito?. Ba daga ko'ina ya fito ba face daga saman kan toliyar scepter King ɗinsa, kunsan kansa da ɗanyar gold aka yi ta, to ita ce ta bada wannan haske sosai. Ganin hasken scepter ɗin yasa ta fahimci shi ne ya zo. Cike da balai'n tsoron ganin face ɗinsa ta ɗago idanunta da suke jajir kamar wuta ta ɗaura kallanta a saman face ɗinsa. Sai da ta ji gabanta ya yi wani irin mummunar faɗuwa na ganin yadda face ɗinsa take a ɗaure tamau, ta sha jinin jikinta ta kuma razana matuƙa, har kerma jikinta ya fara yi. Sunan Allah ta fara ambata a cikin ranta tana addu'ar Allah ya sake bata nasara a kansa yanzu ma kamar dai ɗazun, dan tana san fara yi mashi nasiha tare da faɗa mashi girman Allah ko zata samu wannan bakar zuciya ta ɗan ragu, dan haka sai ta fara neman Allah ya kareta tin ma bata fara nasihar tata ba. Babu tausayi ko ɗigo a ransa ya nuna wutar da scepter ɗinsa, nan take wutar ta kara haurowa sama kusa da kafafunta dab, dama a rami ya hura wutar. Hankalinta ne ya kara tashi matuƙa, a ruɗe ta fara ƙoƙarin jan kafafun nata baya domin azabar ta yi mata yawa. Sai dai kashi a jikin itace take ɗaure, ba halin ta yi baya da kafafunta, babu space ta baya, dole ta bar kafafun nan nata su gasu. Idanunsa a kan face ɗinta, babu alamar zai tausaya mata ya sake yunkurin ɗaga scepter ɗinsa zai nunata da shi. Cikin dakiya da kakausa kuma wahalalliyar murya ta ce. "Kai kam baka jin tsoron Allah ne? Baka da tausayi da imani a cikin bakar zuciyarka ne? Meyasa kake san kashe mutane bayan kuma ba kai ka haliccesu ba? Ko baka taɓa tinanin cewa Allah zai tambayeka a kan ran da ka ɗauka bane? Me suka yi maka ka kashesu? Ko kai ka haliccesu? Ko baka san da cewa mamallakin rayukan zai tambayeka bane? Baka san akwai ranar tashin alkiyama ba ko? Baka san akwai ranar da kowani bawa zai fuskanci hukunci dai'dai da abin da ya aikata ba? Baka san akwai ranar da mulki, kuɗi, kyau, matsayi, ilimi, isa, taƙama, izza ba zasu tsinana maka komai ba ko? Baka san akwai ranar da zaka tashi matsayin ƙasƙantacce ko tufafi babu a jikinka ba?". Dakatawa da yin maganar ta yi tana jin wani irin kuna da numfashin wutar nan take yi mata, tana ji a jikinta sosai. Fasa nunata da scepter ɗin ya yi, ya dakata yana jin maganganunta. Ganin ya dakata yasa ta ji kwarin gwiwar cigaba da magana, take ma ta ji zafin wutar ya gudu ganin yana sauraronta. "Baka san wannan rana zata zo ba ko? Baka san akwai wata rana da zata zo da Ubangijinmu zai tara dikkan duniya waje guda ba ko? A ranar Alkiyama, dukkan masu mulki, sarakuna, shugabanni da azzalumai za su hallara a gaban Allah. A wannan rana, babu wani mutum da zai iya da'awar mulki ko iko, domin Allah ne kaɗai zai kasance da mulki da iko. A wannan rana Allah zai ce. Limanil mulku liyawm? Wanenen mai mulki a yau? Hasbunallahu wani'imal wakil. Babu wanda zai iya samun bakin amsawa Ubangiji wannan tambaya, wane mutum, Allah da kansa ne zai sake amsa tambayar da cewa babu wani mai mulki sai Allah subhanahu wata'ala. Wannan yana nufin cewa dukan iko da mulki na duniya wofi ne, sai wanda aka yi da adalci da tsoron Allah, shi ne kawai zai iya zama mulki mai amfani har ranar lahira. Kai da kake zalinci me zaka ce a ranar lahira? Ka tanadi abin faɗe ne?!!". Ta jefa mashi tambayar tana wani irin huci sakamakon wannan wuta, ga kuma kululun bakinciki da ya tirnike mata zuciya. Da kyar ta ɗaura mashi da maganar bayan ta ɗan huta ta gama sauke numfashinta. "Idan ma baka yarda da maganata ba to ka duba a cikin Alqur'ani, cikin Suratul Ghaafir, sura ta 40 aya ta 16. Allah ya ce 16 ‫سورة غافر – آية‬ ‫َي ْو َم ُه ْم َبا ِر ُزو َۚن َلا َي ْخ َف ٰى َع َلى ٱل َّل ِه ِم ْن ُه ْم َش ْى ٌۚء ِّل َم ِن ٱ ْل ُم ْل ُك ٱ ْل َي ْو َۖم ِل َّل ِه ٱ ْل َوا ِح ِد ٱ ْل َق َّها ِر‬ Fassararta A ranar da za su bayyana gabaɗaya a gaban Allah, babu wani abu da zai ɓuya daga gare Shi. Sai Allah Ya ce. Wanenen mai mulki a yau? Sai kuma ya amsa da kansa dan babu mai iya amsawa, zai ce mulki nasa ne shi kaɗai, Allah shi ne malikyaumiddin, mamallakin ranan sakamako kenan" "Kasan me ake nufi da tashin alkiyama kuwa? Kasan masifarta kuwa? Kasan balai'n da tashin hankalin dake cikinta kuwa? Na tabbata da bawa yasan balai'n dake cikinta da ba'a wayi gari da azzalumi ko guda ɗaya ba a duniya, kai koda sau ɗaya a samu wanda ya mutu ya dawo duniya ya faɗawa mutane musifar dake lahira da duniya ta tsabtata daga ƙazantar da take a ciki". "Amma ni Omaish jika ga Abdul Mutallab ina kalubalantarka da ka je ka karanta suratun Az-Zalzalah (‫ )الزلزلة‬tana daga cikin surorin da ke cikin Al-Qur’ani mai girma. Tana da ayoyi takwas 8, kuma tana cikin Juzu’i na 30. Wannan sura ta yi cikakken bayani game da ranar tashin kiyama, in da ƙasa za ta girgiza da fitar da dik abin da ke cikinta, wato dikkan mutanen da suka mutu aka binnesu kenan. A wannan rana, kowane mutum zai ga sakamakon ayyukansa, komai ƙanƙantar su. Wannan sura tana ƙarfafa imani da ranar sakamako, kuma tana ƙarfafa mutane kan su aikata alheri domin gudun sakamakon munanan ayyuka, dan haka zan so ka karantata tare da fassararta dan ko ba komai bakar zuciyarka na tabbata sai ta ragu, babu wanda zai ji labari game da lahira zuciyarsa bata kaɗa ba, ko shaiɗan ubanku a zalinci shi ma hantar cikinsa kaɗawa take yi a dik time ɗin da aka yi batu kan lahira". Ta ɗan dakata tana jan numfashi mai fita dakyar sosai kafin ya daure ta ɗaura da cewa. " Bayan suratul Zalzalah akwai wasu surori da Hadisai da suka bayyana Tashin Alkiyama da Masifunta, ina kalubalantarka da ka karanta su dikka. A cikin Al- Qur’ani da Hadisai masu yawa, an yi bayani mai zurfi game da tashin Alkiyama, tsayuwarta, masifunta, da yadda za a yi hisabi kafin Allah ya raba hukunci. Daga ciki akwai suratul Az-Zalzalah wadda take magana a kan yadda ƙasa za ta girgiza kuma ta fitar da abin da ke cikinta. Sai suratul Waqi’ah surata 56 ta yi bayani yadda mutane za a rarrabe su zuwa rukuni uku a kiyama. Na dama sune Ahlul Janna wato ƴan aljanma, sai na hagu Ahlun Naar, ƴan wuta kenan, da waɗanda suka yi wa Allah hidima sosai As-Sabiqun. Sai suratul Takwir sura ta 81, ta yi bayani kan yadda rana za ta narke, taurari su faɗi, da kuma yadda dabbobi za su taru. Sai suratul Infitar, surata 82, ta yi bayani kan yadda sama za ta tsage, ƙasa ta zube, kaburbura su bude, kuma mutane su san sakamakon ayyukansu. Sai suratul Inshiqaq surata 84, ta yi bayani yadda sama za ta tsage kuma mutane su hadu don hisabi". "Hadisai Masu Bayani Kan tsanani da tsaruwar Alkiyama, masifu da bala’o’in tashin Alkiyama akwai bukhari, hadisi mai lamba 4635, sai Muslim lamba ta 157, Annabi Muhammad (SAW) ya ce. Kiyama ba za ta zo ba sai rana ta fito daga yamma. A cikin Muslim again, a ranar Alkiyama, mutane za su tsaya tsawon shekaru 50,000 kafin a fara hisabi, shekaru dubu hamsin da, ba kuma irin shekarun duniya ba, wuce nan, sannan za'a sauko masu da rana dab kansu, wanda ya yi aikin alkhairi ya bi Allah da manzonsa zai kasance ne a ƙarƙashin inuwar alarshin Ubangiji. (Allah kasa muna daga cikin masu samun wanna ni'imar) Za a yi tambaya kan imanin mutum, ibadarsa, arzikinsa da yadda ya kashe shi, da iliminsa da yadda ya amfani da shi, idan aka yi maka wannan tambaya me zaka ce?" Ta jefa mashi tambaya tana kallan yadda face ɗinsa yake kara rikiɗewa. Babu alamar zai iya buɗar baki ya yi mata magana, dan haka sai ta cigaba da cewa. "Bayan dikka wannan fa akwai hayewa gadar airaɗi, kafin nan akwai musifun kabari, kasan me siraɗi kuwa?. Annabi (SAW) ya bayyana cewa akwai wata gada mai tsananin siranta da ke kan wutar jahannama, wato gadar Siradi. Wasu za su haye gadar cikin sauri kamar walƙiya, masu aiki na kwarai kenan, wasu kamar iska zasu wuce saboda tsabar kyan aikinsu, wasu kamar doki, wasu kamar tafiya a kafa, wasu kuwa za su fadi cikin wuta saboda zalincisu. Ga shi gadar tana da kaifi fiye da takobi kuma tana da duhu mai tsanani, kai da kake aikata zalinci me kake tinanin zai faru da kai idan baka tuba ba?". Ta kai karshen maganar tana ciza laɓɓanta da karfi saboda azaban zafin wutar ya kai mata makura. Allah yasa kun samu karin imani a kan tunatar daku lahira da na yi.💘 Wlh a dik time da na tina lahira sai na ji gabaɗaya duniya ta isheni ta fita a rai'na, sai in ji gabaɗaya na rasa me yake mun daɗi, ranar haka nike wuni sukuku, my people's akwai aiki a gabanmu babba, wlh kiyama ba karya bace, tashin hankalin dake cikinta bawa ba zai iya ɗauka ba, dan haka ku kullu ɗamara domin neman gobe mai kyau, duniya dikka kyalkyali banza ce, ruɗin shaiɗan ne ma yake ƙawata maku duniyar, dan haka ku yi wa kanku kiyamul laili tin kafin dare ya yi maku! Allah kasa mu dace ka yi mana kyakkyawar karshe. Ƙasa cigaba da yin magana Sweetie ta yi saboda azabar da ya isheta, ta gagara yin magana kuma. Ga dikkan alamu maganganun Sweetie sun yi tasiri a ransa, saboda kuwa ya tsaya cak ya gagara motsawa, wannan ma a tunaninsa Sweetie tana magana ne a kan Annabi Isa, kun san shi suka ɗauka a matsayin Allansu, so ya zaci tana faɗa mashi Annabi Isa zai tuhumesa a kan zalincin da yake aikatawa ne, dan haka sai ya ji kalamanta sun taɓa zuciyarsa sosai, dama ai komai taurin zuciya sai dai in bata ji batu a kan Allah ba, dole ta yi laushi sai dai idan mamallakin wanna zuciya ya ki yarda ya saduda ne kawai. Ita kuwa Sweetie a hankali ta fara ganin dishi dishi, kafin wani lokaci numfashinta ya ɗauke cak saboda wutar ta yi mata yawa. A daidai lokacin da numfashinta ya ɗauke a dai'dai wannan lokacin barci ya ɗauke Ronnie kwance a gadan Black Tiger. Bawan Allah aman da ya yi ta shararawa ta jijjiga shi matuƙa, jikinsa dik ya mutu shi ya haifar mashi da barci. Allah kasa kalaman nan nata su kara tasiri a zuciyar Black Tiger ko dan ta yi nasara, Sweetie ta sha wuyar rayuwa wlh, tun daga forest fa, ga kuma makanta, kai ta wahala fa, ina maganar Allah ba wasa ba wlh, dole zuciya ta girgiza wai dan ma bai da sani a kan hakan, ma'ana bai karanta ya gani muraran ba, ai da yau bashi ba kwanciyar hankali bare barci. Ina matuƙar kaunar part ɗin BLACK WORLD, saboda addinina, Allah ka kashemu muna masu imani da kai.💘 🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥 In short, sati guda cur Zunaira ta yi a hospital a kwance kafin ta farfaɗo, a cikin sati ɗayan nan abubuwa sun faru wanda suka haɗa da kwanciyar commander Zafar a gadan asibiti, yanke jiki ya yi ya faɗi tin ranar da King ya umarcesa da ya hukunta Hoorain, suna isa bakin kofar ɗakin duhu bayan ya tura Hoorain ciki ya rufe kofar kawai sai ya yanke jiki ya faɗi, ranga ranga aka ɗaukesa zuwa hospital, yanzu haka satinsa ɗaya a hospital amma bai farfaɗo ba, doguwar suma ya faɗa, bawan Allah. Sannan ciwon guyson yaki sassautawa har sai da Dr Raj ya bar Leesharh ya tsallako ya taho kingdom of power da kansa domin shi ya saba da yi mashi dik abin da ya dace. Kwana uku da kwanciyar guyson ya yi dirar mikiya a kingdom of power ɗin, a ranar da ya zo a ranar ya shawo kan matsalar, amma har yau bai koma ba yana nan, Bilal ya ɗauko wasu Drs suna kula da Leesharh a Dubai Tin ranar da Auta ta dawo Mahnoor bata sake haɗa ido da Jaish ba, dan baya zama kwana biyun nan, tin asuba yake fita, baya dawowa wani lokaci sai karfe 12 ko 1 na dare, shi ma aikinsa ta sako shi a gaba. A ɓangaren King kuwa, babu gudu babu ja da baya a kan hukuncin da ya yanke a kan Hoorain da Zunaira, dik da commander yana asibiti hakan bai hana shi jefa Hoorain a ɗakin duhu ba, saboda kun dai san yadda zuciyarsu take, ina da tabbacin a cikin kaso ɗari da wuya a samu kaso ɗaya na sarakuna da zasu iya bawa mayaƙa ko bayinsu auren ƴaƴansu, abu ne wanda baya yiwu sai wani nufi na Allah. Lets cut the story saboda labarin dake gaba mai muhimmanci ya fi na baya yawa, dan wlh ainahin rikicin bai fara ba, so nike in haɗa kan familys ɗin waje guda, idan baku manta ba na faɗa maku family's daban daban ne ko? To so nike in haɗa family's waje guda, sannan kowanne ya komawa ahalinsa, a nan ne za'a fara ainahin cakwakiyar, masu yawan damuna a kan ban juyo story a kan Kamran ba, to Kamran yana nan, shi ma shugaban wani ahali ne na daban, bayyanarsa kuwa zai zo da ruɗani da cakwakiya, dan kusan shi ne key na buɗe bakin zaren dikkan waɗan nan cakwakiyoyin, soon zai dawo cikin labari da bazata na ban mamaki. (Amma bari matarsa Pretty ta kara girma😅 dan yana dawowa sai aure😅 kada ku manta mom twin's ta bashi aurenta fa, matarsa ce, saura mammarsa ta yarda kawai mu sha biki ko ba sadaki🥱 ƴan special grp zaku biya mashi sadakin ko?) To masu matsawa a kan Pretty and Sweetie ƴaƴan King Zuhair ne na ce sannunku, wato kuna nufin King ya auri mom twin's kenan ko? Amma fa kun iya hasashe, to muje dai zuwa, yanzu zamu buɗe babin surprise, get ready, bari in fara tashin kanku a cikin pages na kwanaki nan, an sha gwagwarmaya a pages ɗin baya, na week ɗin nan kuma bari mu sha surprises, gaba sai ayi cakwakiyoyi, let's go. So lets cut the story kaɗan a nan. Tin da Zunaira ta dawo gida take yi wa momma kuka a kan ta taimaka tasa baki daddynsu ya kyale Hoorain, ita ta yarda a rabata da shi amma dan Allah a barmata shi ya shaki iskar ƴanci, a yafe mashi hukuncin da ya hau kansa. Momma ta tsausayawa Auta matuka, amma babu yadda zata yi, domin a kan batun Hoorain King zai iya saɓawa kowa, momma ta same shi da maganar daren jiya, warning sosai ya daka mata tare da rantsuwa da girman Allah ba zai taɓa bawa Hoorain auren Zunaira ba, kuma idan suka matsa mashi tabbas ran Hoorain suke yi wa, saboda a kan wannan magana zai iya sanyawa a kashe Hoorain mai gabaɗaya kowa ya huta. Tashin hankali. Dik wasu masu karfin gwiwar tinkarar King su yi magana da shi sun kasa iya shawo kansa a kan wannan magana, kai in takaice maku Queen mother da kanta sai da ta sararawa King a kan wannan batu, domin ya ɗauki zafi fiye da tinaninku, Akka dan dolenta ta kyalesa, uncle Jahiz ya yi iya yinsa a kan King ya duba ya yafewa Hoorain, sai dai ina, ya ce wlh ba zai yiwu ba, daga karshe ma da aka ce mashi Auta taki cin abinci zata iya cutuwa. Murje idanunsa ya yi ya ce ta mutu idan taga dama, amma babu ita babu auren mayaki, da ya bata shi gara ta mutu ɗin. Tashi sense, jin wannan furuci na King yasa suka fahimci ba fa zai saussatawa Hoorain ba tun da dik yadda yake san Auta ya ce ta mutu ai shikenan kuma sai dai a bishi da ido. Daga haka suka sallama babu Auta babu Hoorain. Dik wannan bidiri da ake yi wlh Jaish yana jinsu bai saka baki ba, dan bai ga abin faɗe ba. Dik duniya an rasa mai shawo kan King a wannan gaɓa, yaki bawa momma damar ta zauna da shi ma, dan yasan zata iya kuresa, da ta zo ɗakinsa zai fice izuwa part na Akka, saboda baya san sassautawa kowa a kan wannan al'amari. ••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 AUTA😥 Kwance take a saman bed ɗin momma, yanzu King ya saka mata tsaro da idanu sosai wai dik dan kada ta je wajen Hoorain, bata fita ko nan da can, tana cikin ɗaki, ita ma ba dan bata da lafiya ba King ya yi niyar hukuntata saboda kawai dan ta so Hoorain ta yi laifi, rashin lafiyarta ya ja ya kyaleta. Guyson yana zaune kusa da ita yana cigaba da dannar zuciyarta yana bata hakuri, su Mahnoor suna tare da momma a parlour suna hira, momma dai tana ganin musifa kala kala a cikin gidan nan, sai dai ta dogara ga Allah shiyasa har yanzu bata faɗi ƙasa ba. Wayar momma dake kusa da ita ne ya fara kara alamar shigowar kira. Ɗauko wayar ta yi, lokaci guda ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, a fili ta furta Hasbunallahu wani'imal wakil, sannan ta yi picking call ɗin. Daga ɗayan ɓangaren aka ce. "Hello momma". Gabanta ne ya sake bada dum dum, da kyar ta iya amsawa. Kai tsaye ta cikin wayar aka ce mata. "Ina Zunaira?". Mai maganar kamar muryar Abu Abdussalam haka. Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Zunaira tana barci......." Bata gama faɗar hakan na diff aka katse kiran. Miƙewa tsaye ta yi, cikin hanzari ta nufi part ɗin King tana faɗawasu Mahnoor kowacce ta wuce ɗakin mijinta dare ya yi. Miƙewa suka yi gabaɗayansu, Mahnoor ta wuce part ɗin Jaish, a sati ɗaya da Mahnoor ta yi da Chuchu har ta koyi wasu abubuwa, Chuchu tana koya mata kula da miji, Mahreen ma sai kara wayewa take yi a wajen mama Haulat, Pretty tana tare da Mahreen a wajen mama Haulat, yanzu hankalin kowa a tarshe yake a kingdom of power. Mahnoor ta nufi part ɗin Jaish, Mahreen and Pretty suka nufi wajen mama Haulat, dama ita Chuchu tana kirjin Yah Jawad a yanzu, Zee ma miƙewa ta yi ta koma bedroom na Aneesa, yau Khadijah ta dawo cikin family part, an sallamota daga asibiti, shi kuma mai napep ɗinsu da yake ya samu karaya har yanzu bai samu sauki ba. Sai kuka Auta take yi guyson yana ta rarrashinta, shi ma dai ba wani ƙoshin lafiya sosai ke garesa ba, amma ya daure yana ta lallaɓata. Zuciyarta kamar zai fashe ta ɗago kanta, fuskar da ya yi jaga jaga da hawaye, muryarta a dashe ta ce. "Yah Omar ka faɗa mun me Hoorain ya yi da ya cancanci wannan hukunci daga wajen daddy? Bafa shi ya ce yana sona ba, ni na fara cewa ina sonsa, kenan laifine in so wanda zuciyata take so?". Ta kai karshen maganar tana mai da kanta ta kifa a saman pillow. "Ba laifi bane, amm kuma ki sani abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hangosa ba, tabbas daddy ya ɗan kauce a wani gaɓar, amma ki sani saboda sanki yasa ya yi hakan dikka". Cewar guyson. "No Yah Omar, ba so bane, idan so ne ku so abin da nike so, zuciyata zafi take mun Yah Omar, ni kam ina ganin mutuwa kawai zan yi". Da sauri ya katseta da cewa. "Kada ki sake cewa ba sanki muke yi ba, kin san yadda kike a zuciyar kowa dake gidan nan kuwa?". Miƙewa zaune ta yi tana goge kwallah. "Yah Omar idan har kana sona kuma kana supporting ɗina to ka tabbatarmun da hakan yanzu ta hanyar kaini wajen Hoorain!". Tashin hankali, zado idanu guyson har kamar idanunsa zasu faɗi ƙasa. "Kin san me kike faɗe kuwa?". Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas tasan abin da take faɗe....... "No Zunaira, no, i can't do that, kin san hukuncin da zamu fuskanta a kan hakan kuwa? Kin san daddy zai iya tsaremu a prison ko baki sani ba? Kin manta cewa dik wanda ya taka dokar daddy hukunci na hawa kansa ko da ɗansa ne ko?". Ya jefa mata tambayar cikin ruɗu da tashin hankali. A hankali ta koma ya kwanta, wani irin kuka ne ya ci karfinta, tana wani irin shessheka ta fara magana ƙasa ƙasa. "Ni dama nasan kai ma kana cewa kana supporting ɗina ne kawai dan ka kwantar mun da hankali amma ba wai dan kana san zaɓina ba". Tana kuka tana faɗa. Allah sarki guyson, idanunsa sun ciko da kwallah sosai, kamar zasu zubo, murya ya karaye ya ce. "Zunaira ki dai'na faɗin hakan, wlh da gaske ina san zaɓinki, ina sansa sosai, dik abin da kike so ina sonsa, amma ki fahimceni, babu ta yadda za'ayi na kaiki wajen Hoorain, idan daddy ya sani kinsan ransa zai yi mummunar ɓaci, kuma zai hukunta mu". Miƙewa zaune ta yi, so take yi ta yi mashi wayo ya kaita taga jaruminta, kasan bed ɗin ta sauko a in da ta nufi jikin bangon kusa da toilet, binta da kallo ya yi yana mamkin in zata je. Kafin ya farga sai yaga ta fara buga kanta da jikin bango tana sambatu a kan kowa baya san zaɓinta gara kawai ta kashe kanta kowa ya huta. Dim fa salan yaudarar guyson take san yi, tasan halinsa da raunin zuciya, zai iya aikata komai idan yaga zata cutu, shiyasa ta yi mashi dabara haka. Da gudu ya diro kasan bed ɗin, kai tsaye ya nufeta, cikin zafa ya damko hannunta ya janyota ta faɗa jikinsa, hat gaban goshinta ya fashe ya fara jini, hawaye guyson ya fara yi, cikin kuka ya ce mata. "Ba zaki kashe kanki ba, tabbas zan kaiki ɗakin duhu wajensa koda daddy zai hukuntani, ɗauko alkyabbarki ki zo mu tafi". Ya faɗa tare da saketa yana kai hannu ya fara goge hawayensa. Bata bi ta kan kukan da yake yi ba, da sauri ta ce. "Yah Omar ba sai na saka alkyabba ba, kawai mu tafi". Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce. "No ki sitirta jikinki, kinga dai kayan barci ne a jikinki, maza ɗauko alkyabbarki bari in duba akwai mutane a parlour ne". Ya kai karshen maganar tare da nufar parlourn yana cigaba da goge hawayensa. Dressing room na momma ta nufa da gudun gaske. Alkyabba ta ɗauko ta fito, tana fitowa shi ma yana shigowa cikin room ɗin, ya duba parlour babu kowa. Murya ƙasa ƙasa ya ce. "Zo mu tafi babu kowa a parlour". Ai tin kan ya faɗi haka ta yi saurin wucewa. Hannunta ya riko suka fito, ina wannan hanyar sirrin nasu da Hoorain ya taɓa kawota wajen a lokacin da mayakan Queen Zarina suka kawowa kingdom ɗin hari? Kun tuna lokacin da ya ɗaukota daga gonar King ya kawota wajen su momma a wajen?. To ta wannan hanya suka bi, underground kenan, ko da suka shiga wajen sun rufo kofar kamar ba'a taɓa buɗewa ba, da sauri ya kunna hasken wutar wayarsa, saboda babu haske a wajen. Hannunta ya ja da sauri suka bi ta wajen, sai shera hawaye take yi, shi kuma sai rarrashinta yake ta kara yi. Sun yi tafiya mai nisa kafin su tsaya a wani waje mai ɗan faɗi idan da hanyar suka rabu kashi uku, tsayawa ya yi yana tinanin wani hanya ce wadda zata sada shi da prison na kingdom ɗin nan? Dan a cikin prison ɗin ɗakin duhu yake. Ya ɗauki a kallah 5 mins yana tinani kafin ya jata suka sake miƙewa kai tsaye suka nufi wajen. Kunsan masarauta idan ta kai masarauta akwai ire iren waɗan nan hanyoyi na sirri ta ƙarƙashin ƙasa waɗan da zasu sadaka da kowani ɓangare na cikin Kingdom ɗin ya kasa, dik salan dabarun yaki ne. Guyson kamar bai san komai ba, amma sai ga shi yasan hanyar sirri, kai tsaye ya kaita har in da ɗakin yake, sannan ya tsaya da kyau wajen tinanin a dai'dai ina kofar take? Amfani ya yi da ƙwaƙwalwarsa da Allah ya bashi wajen gano kofar,. Duƙawa ƙasa ya yi Auta ta haye saman shoulder ɗinsa, karfinsa yasa wajen miƙewa da ita tsaye, dan shi tsawonsa ba zai kai ya iya buɗe kofar ba, sai ya ɗagata dan ta buɗe. Hannunta tasa wajen tura kofar, ba koface kamar kowacce kofa ba, tiles ce ta yadda ba za'a taɓa gane akwai kofa a wajen ba sai wanda yasan da wajen, so dikka kofofin hanyar underground ɗin nan tiles ne ta ciki. Tura tikes ɗin ta yi ta buɗe ta ciki kenan, tiles ɗin ya buɗe ta in da Hoorain yake kenan. Ganin ya buɗe yasa guyson ya ce. "Ki haura ki je ki gansa, kada ki wuce 5 mins dan kada a nememu, sannan ki kula akwai masu gadinsa daga ta waje, kada ki bari su ganki". Okey kawai ta amsa da shi kafin ta yi gaggawar haurawa ta fito ta cikin ɗakin, Allah sarki guyson, saboda yana san farincikinta saman shoulders ɗinsa ta taka da kafafunta ta haura sama, amma ko kaɗan bai damu ba, shi dai taga Hoorain ta yi farinciki ya wadatar. Tana hayewa ta ce ya mashi. "Yah Omar ɗakin akwai duhu sosai, ka miƙo mun wayarka zan haska in gansa". Kai ya girgiza mata kafin ya ce. "A'a ki je haka kawai, idan kika saka haske a ɗakin masu gadinsa dake waje zasu san an shigo ciki, da waje haka ki laluɓi in da yake kawai a cikin duhun". Juyawa ta yi ta kalli cikin ɗakin, wani irin bakin duhu ta gani mai razanarwa, a hankali ta sake jiyowa ta kalli guyson dake kallanta. "Ki je babu abin da zai faru In Sha Allah, ki kula sosai". Shiru ta tsaya tana jin tsoron shiga cikin ɗakin, saboda duhun. Kara mata kwarin gwiwa sosai guyson ya yi har sai da ta yarda ta miƙe tsaye, a hanzarce ta mayar da tiles ɗin ya rufe, ta fara laluɓen Hoorain a cikin duhu tana ambatar sunansa ƙasa ƙasa. Ɗakin tsit baka jin motsin kowa, tamkar babu halitta mai rai dake a ciki. Sai yawo take yi a cikin duhu amma sam bata ga alamar zata ga halitta a ciki ba, har ta fara karaya ta fara jin kamar zata hakura. Can wani tinani ya zo mata a kan ta yi shiru tsit in dai yana cikin ɗakin tabbas zata ji sautin numfashinsa ko kuma bugawar zuciyarsa. Haka kuwa aka yi, ta tsaya shiru tare da kasa kunnuwanta dan saurara. A hankali sautin numfashinsa haɗe da bugawar zuciyarsa dake fita da karfi karfi ya fara ratsa dodan kunnenta. Natsuwa ta kara yi domin sauraron ta ina sautin yake fitowa. Fahimtar daga ina ya fitowa yasa ta fara takawa ta nufi wajen a hankali hankali tana sanɗa. Unexpectly ta ji ta daka tuntuɓe a in da ta buga kanta da kirjinsa, ko bata ga face ɗinsa ba tasan kirjinsa ne daka, da sauri tasa hannunta ta fara laluɓar jikinsa dan ta ji a wani hali yake ciki. Allah sarki, ɗaure yake cikin sarkoki masu girma da kauri, a tsaye yake a kan kafafunsa, a horon dama babu kwanciya, idan wata guda aka yankewa mutum haka zai kasance a tsaye tsawon wannan wata gidan, abinci ma masu gadi zasu bashi a baki, bashi ba motsawa, shiyasa dik wanda ya shiga ɗakin dubu dik ranar da aka fitar da shi kafafunsa basa iya takawa. Dan ko dare ne a tsaye zaka yi barci, kafafu da hannaye dik a ɗaure suke da sarƙa, kuma an ware maka su ba ta yadda zaka yi ka zauna, abin dai gwanin ban tausayi. Sosai hankalin Zunaira ya tashi, bugawar da kirjinta yake yi ne ya kara tsananta, kuka ta fashe da shi tare da fara jijjiga Lion chest ɗinsa tana ambatar sunansa a hankali. Shiru bai amsa mata ba, babu alamar zai amsa mata ba, kuma yana numfashi bare ace ya suma, yana jiyota, magana ne ya ƙasa yi mata tamkar an ɗaure tongue ɗinsa, Allah sarki azaba ce ta yi mashi yawa, a yadda yake ɗauren nan jini ne yake zuba daga damatsan hannunsa da ya sha horo wajen warriors da King ya wakilta dan hora shi, sun dakesa da bulalar kaca mai kifiyoyi a jiki, sannan suka zanya mashi gishiri a dik in da fatarsa ta fashe dan tsananta mashi horo, ya kara jin azaba kenan. Da yake a cikin duhu ne ɗin Zunaira bata ga wannan ba, ita dai kuma kawai take yi tana jijjiga ɓulɓul ɗin breast ɗinsa. Ganin ba zai amsa mata ba yasa ta laluɓi saman face ɗinsa ta ɗaura hannunta a kumatunsa, a hankali ta ɗaga kafafunta ta kara tsawo, a saman kirjinsa ta kwantar da kanta tare da laluɓar ɗan bakinsa da hannunta dan ta yi shin an rufe mashi baki ne. Yatsanta ta tura cikin bakinsa tana cigaba da ambatar sunansa, gabaɗaya kayan jikinta sun ɓaci da jininsa ba tare da ta sani ba. Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, can ƙasan maƙoshinsa, da kyar ya iya furta. "My Hoonaira". Jin alamar kamar ya yi magana yasa ta yi saurin ɗago kanta daga kirjinsa tare da kara ɗaga kafafunta ta haɗe fuskokinsu, hankalinta a tsananin tashe ta ce. "My Hero ka yi magana ne? Ka yi mun magana ne? Please kana jina? Meyasa ka yi mun shiru?". Out of control take zuba surutan nata. Silent talk ya yi wajen cewa. " P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Silent talk ya yi wajen cewa. "My Hoonaira dama zaki sake yin tinanina har kizo in da nike?". Kuka mai narka zuƙatan masoya ta saka mashi, a hankali take ɗan bubbuga hannunsa a saman lion chest ɗinsa, da kyar muryarta ya samu damar fita ta fara faɗin. "Kamanta dama na faɗa maka ko zan mutu babu gudu ba ja da baya ne? Ba zan taɓa iya rabuwa da kai ba, kai ɗin jinin jikina ne, please my Hero kada wani wuya yasa ka juya mun baya, In Sha Allah zamu yi nasara, nasan daddy yana kan fushi ne, idan ya sauko zai saurareni, please ka t............". Wani irin tari ne ya kubce mata wanda ya sanyata dan dole ta haɗiye sauran maganganunta, hannunta tasa da sauri ta toshe bakinta gudun kada tarinta ya fita ya sanya masu gadin su fahimci akwai mutum a ciki. Su fa Modarawa haka suke da zuciyar bala'i, kada ku ga laifin King, zuciya a jininsu take, basu isa su cirewa kansu ba, shiyasa kuka ga King a haka, wai baku ga dikka jikokin Akka idan sun fusata haka suke rikiɗewa su zama basa ji kuma basa gani bane? To gado ne shi ma wannan tin zamanin jahiliyyah. Allah sarki yana san rungumarta ya rarrasheta amma babu dama, saboda dikka hannayensa a ɗaure suke. Yana jin raɗaɗin kukan da take yi har cikin ransa tana ratsa shi, amma babu halin taɓuka komai, muryarsa bata fita sosai yake ta faman ce mata ta yi shiru ta daure, sam bata jin me yake faɗe, sai da ta yi kuka sosai har tasa zuciyarsa ta fara yi mashi ciwo, sannan ne ta komar da kanta saman kirjinsa ta kwantar tana shessheka mai taɓa zuciya. A hankali ta zame hnnunta daga ɗan bakinsa, sannan ta ɗago kafafunta tare da sanya hannayenta ta saƙalo wuyarsa da shi, ta haɗe fuskokinsu waje guda, murya a sarkafe ta ce. "My Hero, promise that ko wani hali zamu shiga tabbas zaka tsaya a kan soyayyarmu babu gudu ba ja da baya". A yadda take maganar lausasan lips ɗinta suna taɓa nashi yasa gabaɗaya ya jisa a wani sabon babin na yanayi, gabaɗaya sai ya kara jin kasala sosai, dama ba wani kwari ne da jikin nasa ba. Da kyar ya iya cewa. "Ba zan taɓa juya maki baya ba my princess, dik wahalar da za'a bani matsawar ina numfashi to tabbas zuciyata zata yi kowacce bugawarta ne da sunanki, ba zan janye ba sai dai a kasheni ko kuma ke ki juya mun baya!!". Kai ta fara girgizawa kafin ta ce. "Ba zan taɓa juya maka baya ba ka ji?". Kai kawai ya jinjina mata yana cigaba da sauke numfashi mai ban tausayi. ••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 Khadijah and Zee ne zaune a saman sofa a part ɗin mama bedroom na Aneesa. Su biyu ne kawai a cikin ɗakin, sai hira suke yi Zee tana jin daɗi Khadijah ta samu lafiya. Khadijah dai ciwo bai rage mata komai ba, sai kiba ma da ta kara, kumatunta ɓulɓul gwanin sha'awa, momma ta ce ta fara bawa babynta nono tin da ta samu lafiya, dan nonon uwa ba ƙaramin abu bane, idan yaro ya rasa shi ma sai kuga ya girma ga shi ga shi nan ne kawai. So tana rike da babyn a hannunta, dikkansu kayan Aneesa suka sanya, sun yi kyau matiƙa, sai dai dik in ka kalli face ɗin Khadija zaka kalli tana cikin bakinciki, dan damuwa na cunkushe a ranta, wai a hakan ma dan likitoci sun ce ta cire damuwar dake ranta in ba haka ba zata iya kamuwa da ciwon zuciya, shi ne fa ta ɗan rage. ••••••••••••••••••••••••••••🔥 "Aunty Khadijah tin da kin samu lafiya yakamata mu koma Nigeria ko?". Cewar Zee. Yadda ta yi maganar tasa Khadijah ta zargi wani abin. Cike da mamaki Khadijah ta ce. "Kina da matsala da nan ɗin ne?". Kai ta jinjina da sauri tana amsawa da e tana da matsala. Nisawa Khadijah ta ɗan yi kafin ta amsa da. "Meyasa Zee dik in da muka je sai kin yi wa wajen mummunar zato ne? A nan ɗin ma nasan cewa zaki yi kina zargin wani abin ko?". Kai Zee ta gyaɗa. "To Aunty Khadijah ki faɗa mun wani waje ne da na yi wa mummunar zato bai zama sharri a garemu ba? Kina dai gani mai napep da ya ɗaukemu daga kawo Kaduna da nace ban yarda da shi ba, kin dai ga sace mu ya yi izuwa Abuja, Allah ya kuɓutar damu, muka sake faɗawa gidan matar can, ita ma na ce maki ban yarda da ita ba, haka kika matsa mu zauna da yanzu babu junior ta sacesa, nan ma Allah ya karemu da kariyarsa, muka tsallaka rijiya da baya, kinga kuwa ai ba kya tuhumeni a kan dan nace nan ma ban yarda da su ba, basu kwanta mun a rai ba". Tun da ta fara magana Khadijah take binta da kallo tana sauraronta har ta kai aya, sannan ta ce mata. "To ke yanzu meyasa kike zargin wannan gida?". Ajiyar zuciya Zee ta sauke, juya harshe ta yi izuwa turanci, sannan ta ce. "Saboda wannan ɗan kwallon, ina zargin yana shigo mana ɗaki da daddare, sannan kuma yana yawan sakawa dik wani motsina idanu..........." A hanzarce Khadijah ta katseta da cewa. "Wani ɗan kwallon kenan?". "Jahiz mana". Ta bata amsa tana kara ɗaure fuska. Zaro idanu sosai Khadijah ta yi zata yi magana daga bakin kofa suka jiyo muryar Aneesa cikin harshen turanci ita ma tana faɗin. "My second dad ba yadda kika ɗaukesa yake ba, ke ba abin alfahari bane ma a wajenki ki ce kin taɓa ganin shi a zahiri? Na tabbata dik wanda zaki ce wa kin taɓa ganin uncle na a zahiri ma ba yarda zai yi ba, domin baki yi kalar wadda ta taƙa matsayin da zata samu damar ganinsa a zahiri ba". Ɗan siririn tsaki Zee ta ja, a kule ta ce. "Then so what? Kuma da kike wannan magana ce maki aka yi wata tsiya ce shi? Ko an faɗa maki Nigeria irin nan ne da zamu yi alfahari da ganinsa?". Zee ta samu Khadijah ta samu lafiya yanzu kuma su Aneesa sai sun sarara mata, dama saboda lafiyar Khadijah ta koma baya ta yi zaune, yanzu kuwa kowa zai sha mamakinta, ba ɗaga kafa. Wani irin matsiyacin kallo Aneesa ta wurga mata kafin ta ce. "Ni ba mate naki bane okey? Ki rike words ɗinki da kyau kada ki bari su kubce maki a kai'na, dan zaki yi danasani, rubbish useless people kawai". Ta yi maganar tana dalla masu harara. Da sauri Zee ta buɗe baki zata mayar mata da martani, a hanzarce Khadijah ta tareta da faɗin ta rufe bakinta a wajen. Ranta ne ya ɓaci sosai, ba zata iya yi wa Khadijah musu ba, dan haka sai ta miƙe da sauri ta nufi waje, Khadijah na kiranta amma bata tsaya ba, ta ce ita ta bar wannan ɗaki ma ba zata sake dawowa ba, gara ta kwana a waje da ta sake kwana a ɗakin, kun san mutuniyar da shegen zuciya. Tana fitowa ta nufi elvator, ƙasa mai gabaɗaya ta yi domin ta fita waje. Ita da bata san ko'ina ba amma saboda zuciya sai gata a tsakar kingdom ɗin, ta ko'ina warriors ne suke shawagi dan tabbatar da tsaro. Shiru ta ɗan tsaya tana kallan yadda hasken bulb suka haska harabar kingdom ɗin tamkar rana, ko allura ka jefar zaka iya tsinta. Wani ɓangare na zuciyarta ne ya zugata wajen ce mata ta ɗan yawata cikin kingdom ɗin mana ko zata huce kafin ta koma ciki ta je su kwana a tare da Pretty, dan ba zata sake komawa part ɗin mama ba, kun san zuciya da sake sake, sai ya rinƙa saƙa mata tabbas Aneesa ta ci mutumcinta. A hankali ta fara taka kafarta tana tunane tunane ta fara kewaye cikin harabar family part. Wasu warriors guda biyu ne suka nufota cikin takun jarumta. Ta ɗan ji tsoro da ta gansu, amma haka ta daure ta cigaba da tafiya suna tinkarar juna. A gabanta suka tsaya, cikin girmamawa suka ce ko tana buƙatar wani abin ne ta fito? Kai ta girgiza masu kafin ta amsa masu da bata buƙatar komai, shan iska kawai ta fito yi. Ɗaya daga cikin warriors ɗin ne ya nuna mata hanyar babban garden na family part, sannan ya ce mata ga wajen shan iska a can ai idan tana da buƙata. Ta ji daɗi sosai, sannan ta nufi wajen tana yi masu godiya. Juyawa warriors ɗin suka yi suka koma bakin aikinsu........ Sosai Zee ta baza idanu tana kallan ƙawatuwar garden ɗin nan, ga wasu irin flowers masu kamshin daɗi, a hankali iska ke kaɗawa yana ratsa jiki, sai ta ji wlh zata iya kwana a nan wajen, haɗuwar wajen ya tafi da imaninta. A hankali ta nufi karisawa wajen da luntsuma luntsuman sofas dake wajen wani ƙayataccen rumfa dan ta zauna a can, tana tafiya tana waige waige dan ta kurewa ko'ina kallo a cikin garden ɗin. Unexpect suka ci karo da mutum, a razane ta juyo da kallanta a kansa domin ta ga wanenen?. Tana juyowa dai'dai lokacin ya ɗaga hannu zai dallah mata mari sakamakon cappuccino dake hannunsa ta buge mashi ya zube a white sleeping dress dake jikinsa,.hakan ya kona mashi rai sosai, ga wayarsa da ta buge ya faɗi ƙasa, ya ji zafin hakan natuƙa. A fusace ya cire hannu zai dallah mata mari, da sauri tasa hannunta dikka biyu a face ɗinta domin ta kare lafiyar fatarta daga marinsa. Ta datse idanunta gam tana jiran ta ji saukar mari sai kuma ta ji shiru bai mareta ba. A hankali ta ɗan waro idanunta domin taga meya hana shi sauke mata wannan mari. Tsaye yake ya mace da kallan face ɗinta, dalilin da ya dakatar da hannunsa ga isa fatar kumatunta kenan, da alama a kallan farko ya fola, idanunsa a kan dogon wuyarta mai kyau da ƙawa. Ganin ta waro kallanta a kansa ya sa ya dawo da kallonsa a saman face ɗinta. Kara waro idanunsa waje ya yi yana kallan haɗuwarta, lokaci guda ya wani ja numfashi tare da mai da kallansa a saman kirjinta. Ita kuwa ganin face ɗinsa ba ƙaramin girgizata ya yi ba, ta ga kyau na jinin Akka tamu ta amana, sai taga kamar ya fi kowa kyau a gidan. Yo dama yana kanin Ramish ba dole ya yi kyau ba. Slowly ta kai kallanta kasa saman kyawawan fararen kafafunsa dake cikin wasu kyawawan takalma na yawo a tsakar gida, a hankali ta fara binsa da kallo har izuwa sama dai'dai wuyarsa, sai ta ji nauyin karisa kai kallanta saman face ɗinsa dan kada su haɗa idanu. Kasa Dr Raj ya yi da hannunsa ya fasa marin nata, sannan ya ɗan kawar da kallonsa a kanta yana maidawa kan wayarsa dake ƙasa, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi. Ganin yana kallan ƙasa yasa ta kai kallanta wajen ita ma. Wayarsa yake kallah, ɗan satar kallansa ta ɗan yi kafin ta duka zata ɗauka mashi wayar. Dai'dai lokacin shi ma ya duƙa zai ɗauki kayansa ya wuce, ba tare da sun ankaraba suka kai hannunsu kan wayar a tare, ta rigasa ɗauka, amma da hannunsu ya goge juna wani shock da ta ji ne yasa ta saki wayar, shi ma sai ya ja hannunsa baya kaɗan. A hankali ya ɗago da kallansa a kan face ɗinta, while ita ma dai'dai lokacin ta ɗago da nata kallan a kan face ɗinsa, wato wannan fa shi ake cewa soyayya a kallan farko, the most luckys persons. So idan ta tashi shiga mutum fa wlh bata excuse, wani lokaci ma zaka haɗu da yarinya da rana, sai da daddare idan ka koma ka kwanta santa ya shigeka im ka tinata, so, so, so, a karshe dai ao ita ce silar kowa a duniyar nan, bari dai mu cigaba. Sarkafe juna da kallo suka yi, Dr Raj ya ga jinin Nigerians ya rasa natsuwa da control of his heart. Ita ma Zee taga ɗan balarabe jinin modarawa jinin Akka tamu ta amana ta rasa natsa natsuwar. Sun ɗauki a kallah 2 mins a haka suka kallan juna ido cikin ido kafin ta yi ta mazan zare idanunta daga kansa, sannan ta miƙa hannu ta ɗauka mashi wayarsa. Wai ni kam ba Zee bace ta ce babu ita babu maza? Har da wani cewa ta tsani maza! Ko dai ba ita bace nikam?! Kaina ya ɗaure, ina ƴan special grp kuzo ku warware mun kullin dake kai'na,...........🥱 Cikin sanyin murya ta ce. "Am so so sorry, this is ur phone". Ta yi maganar tana miƙa mashi wayar. Miƙewa tsaye shi ma ya yi, a maimakon ya karɓi wayar sai ya harɗe hannayensa a kirjinsa yana binta da kallo. Ɗan ƙasa kaɗan ta yi da kanta, kamar zata saki murmushi saboda wani irin bargon farinciki da ta ji ya lulluɓe zuciyarta ba tare da tasan dalilin farincikin ba. Ya ɗauki a kallah 2 mins again yana ta kallanta kafin ya miƙa hannu ya karɓi wayarsa, cikin natsuwa ya juya ya nufi hanyar fita, yana tafiya yana waigota, wai a haka ma dan King ne ya yi mashi waya da ya same shi a main parlour, da ba zai tafi ya barta ba, sao ya tsaya jin wacece ita, amma King na jiransa, dan haka ya wuce yana kara waigota. Ita ma wucewa gaba ta yi, tana tafiya tana waigosa, da alama ta ya burgeta. Saman ɗaya daga cikin sofas na wajen ta zauna tana dawo da kallonta a wajen, ta fara rarraba idanu tana kara jinjina irin dukiyar da aka narka a wajen. •••••••••••••••••••••••••••••🔥 Mammie and Fanan, zaune suke suna shawarin yadda zasu ɓullowa lamarin Fanan da Jaish, mammie ta ci alwashi kuma ta yi rantsuwa da Allah sai Fanan ta auri Jaish, idan ba haka ba Jaish ɗin ya mutu kowa ya rasa, sai tsara yadda zasu wahalar da Mahnoor suke yi, yanzu Mammie ta gama tsara yadda za'ayi Fanan ta koma part ɗin Jaish da zama tare da mama Haulat kenan, ta kuma tsarawa Fanan ɗin irin abin da yakamata ta yi wa Mahnoor idan ta koma can da zama. Ita kuma Sarina ta gama tsara mata yadda zata buga barikanci wajen samun soyayyar Jaish ko yaki ko y so, har da faɗa mata wai idan dare ya yi ta rinƙa saka sleeping dress tana zama a parlour da sunan zata yi kallo, hakan zai rinƙa jan hankalinsa a gareta, Sarina dai ta bata shawarin zama karuwar cikin gida sosai,......... My people's me kuke tinani a kan wannan shawari na Sarina? Anya kuna ganin hanya ce mai ɓillewa Fanan kuwa?. A gefe guda kuwa, Sarina and abokanan rashin mutumcinta ne suke zaune a rest parlourn uncle Abbas suna shirya wani makircin, Omaid dai sai chatting yake yi a Whatsapp da sabuwar budurwarsa, shi kuwa Obaid sai tsarawa Sarina yadda komai zai gudana yake yi, shiri suke yi a kan yadda zasu ganawa Mahnoor azaba, tana neman da su tayata tun da kunga su suna da kunama da kwari, shi ne ta nemesu a kan wannan harka, dama kun san mutanenta ne. Obaid sai tsara mata yadda za'ayi yake yi, shi kuma Omaid yana chatting. Sosai Sarina ta so yi wa su Obaid wayo wajen tambayarsu wanenen Omerish? Sai dai bata fito ta tambayesu wanenen shi kai tsaye ba, gudun kada su zargeta, ta fake da ce masu. "Obaid na yi mafarki wani kyakkyawan saurayi mai cikar mazantaka da jarumta, dogo mai kama da daddy, ga shi da fuskar kwarjini da haiba, fari tas kamar momma, yana da saje irin na daddy, sai dai kwayar idanunsa irin na Auta ce wato hazel, sannan sunansa Omerish". Lokacin da ta ambaci sunansa sai da dikkansu suka ɗago da kallonsu a kanta, lokaci guda kuma ko me suka tuna suka yi gaggawar kawar da kallonsu daga kanta suka cigaba da abin da suke yi. Ta fahimci sun yi shock da jin sunan da ta ambata, hakan yasa ta kara tsananta zarginta a kan abin da suke zargi ita da Mammiensu. Cigaba ta yi da yi masu zabara dan su faɗa mata wanene Omerish kuma me hotonsa yake yi a wajen momma da har ta iya ɓoyewa a kasan bed ɗinta bata san kowa ya gani (kun tuna envelope da ta ɗauka a kasan bed ɗin momma? Hotunan dake ciki kenan, a jikin hoton matashin ne aka rubuta Omerish, a nan tasan sunansa). Sai dai da yake suma A ne wajen dabara da kaifin ƙwaƙwalwa sai suka shashantar da ita, suka tsara mata labarin karya wanda dole in mutum ya ji ya yarda da su. Suma da wayansu ashe. A ɓangaren guda kuwa, Chuchu and Yah Jawad sai kashe junansu da love suke yi, yanzu hankalin Chuchu ya kwanta dan Auta ta dawo, sai kashe Yah Jawad da salan soyayyarta take yi tana rikita mashi ƙwaƙwalwa, dik abin da ta iya dange da soyayya tana iya kokarinta wajen koyar da Mahnoor, amma ita Mahnoor wai kunyar kwatantawa Jaish take ji, ga tsaronsa dake ranta, yanzu sun dawo wasan ɓuya ne ma, in yana nan bata fitowa parlour, sai ta tabbatar ya fita, kuma bata zuwa bedroom ɗinsa, saboda ta samawa kanta lafiya. Suna tsaka da zuba soyayyarsu King ya yi wa Jawad massages a kan ya zo main parlour ya samesa yanzun nan. Dan dole ba dan ya so ba ya fita zuwa parlourn a tare da Chuchu ɗin. A wani ɓangare kuwa Pretty and Mahreen da mama Haulat ne suke zaune suna hira, mama Haulat na koya masu abubuwa dan kara wayar masu da kai. Daga gefen su mama kuwa, mama tana can kishi kamar zai kasheta, ita kuma mummyn Chuchu tana fama da takaicin abin da yake faruwa tsakanin Auta da commander Zafar, ita a ganinta ai ba laifi bane dan Hoorain ya so Auta, saboda Auta fa tana da kyan da dik wani namiji ya ganta sai ya kyasa, kuma kada ku manta mummy ƴar talakawa ce, so bata ga dalilin da zai sa a wulaƙanta talaka kaman ita kuma ta goyi baya ba. Waɗan nan sune kaɗan daga cikin abin da yake faruwa a cikin kingdom of power ta kowani ɓangare kenan. Mu koma kan labari in da muka dosa kenan. •••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Cigaba kuka Auta ta yi tana kara faɗa mashi zasu yi nasara, ya jure saura kaɗan ne, dama dik abin da bawa yake so sai Allah ya jarrabcesa a kansa, to suma su ɗauki wannan a matsayin jarrabawarsu. Suna tsaka da karfafawa junansu gwiwa unexpect suka ga haske ya gauraye cikin ɗakin. Kafin ta yunkura domin ganin wanene sai ji ta yi an damki hannunta. Da karfi aka figeta, ta kofa aka fita da ita. Dikkansu biyu idan hankalinsu ya kai miliyan to ya tashi, bana kaman Hoorain da ya shiga tashin hankali kamar zuciyarsa zata buga, damuwarsa ɗaya shi ne za'a hukunta mashi ita, hakan yasa shi a damuwa. Ita ma bata kanta take yi ba, hankalinta a kansa, ta kara ja mashi wani musifar, sai ta ji ta yi danasanin zuwanta wajensa, yanzu za'a kara mashi azaba kan azaba. Ba kowa bane ya ja hannunta face King, idan baku manta ba na faɗa maku yasa idanu a kanta, dik wani motsinta yana sane da shi, so tin da suka fita ita da guyson suke a kan idanunsa, ya gansu sarai, yanzu haka ya kama guyson ɗin ma yana main parlour, shiyasa ya yi wa su Jawad dikka massages a kan su same shi a parlourn, dan zai ɗauki tsastsauran mataki a kan Auta da guyson, bawan Allah guyson dik ya sha jinin jikinsa. King bai zame da ita ko'ina ba sai main parlour, sai kuka take yi tana yi mashi magiya a kan ya yi hakuri ta tuba ba zata kara ba. Sam bai saurareta ba, yana zuwa ya tsayar da ita a tsakiyar parlourn, da karfi ya ɗauke fuskarta da mari sai da ta tafi ta kifa ƙasa. Da gudu Chuchu ta yunkura zata tashi ta nufi Autar. A miliyan Jawad yasa hannu ya riketa, tana ƙoƙarin kwace hannunta King ya daka masu wani irin tsawa wanda ya sanyata komawa jikin Jawad a miliyan ta lafe, tin da suke basu taɓa ganin King cikin ɓacin rai irin na yau ba. Kowa yana cikin parlourn banda su Zee da suke ba ƴaƴan familyn ba, sannan Jaish ma baya nan, amma tin daga kan su uncle Jahiz da suke cikin kingdom of power har kansu Omaid dik suna parlourn, su Mammie, uncle Abbas dik kowa ya hallara. Dan ran King ya ɓaci. Akka tana zaune saman sofa ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ita kanta bata goyan bayan wannan alaƙa ta Auta and Hoorain. Sai huci King yake yi, Auta and guyson dik suna zube a ƙasa suna kuka, shi guyson King bai dakesa ba, taya Auta kuka kawai yake yi, ita kuwa nan take shatin yatsun king ruɗu ruɗu suka fito a face ɗinta, ta masu ne matiƙa. Mummyn Chuchu ce ta yi ta mazan buɗe baki, cikin girmamawa ta ce. "Allah ya huci zuciyarka, dan Allah ka yi hakuri, ka kyale Zunaira haka, kada ka hukuntata a bisa laifin da ba yin kanta bane". Aunty MieMie ce ta capki zancen da cewa. "Daddy ni kaina baka taɓa sanya hannu ka dakeni ba, ba ni ba, na tabbatar gabaɗaya tun daga kai'na har kan Obaid baka taɓa ɗaura hannunka a jikinmu da sunan duka ba, kuma dik mun san cewa kafi san Auta fiye da kowa, dan Allah daddy ka dubi irin san da kake yi mata, ka yi mata afuwa ka dubi irin san da take yi wa Hoorain..........". Kasa ƙarisa maganar Aunty MieMie ta yi sakamakon wani irin kallo da King ya wurgo mata, cikin kakkausar murya ya ce. "Wlh na yi rantsuwa da girman Allah, ba zan taɓa bawa Hoorain Zunaira ba, idan zata mutu ta mutu, ba zan yi kaffara ba, wlh billahi na yi mata iyaka da shi, babu ita babu shi, idan taki kuma to tabbas zan sa a kashesa". Ai Auta tana jin karshen maganar King bata san lokacin da ta zabura ta miƙe tsaye ba, kisa kuma? Ta maimaita a ranta, ba komai ya ɗaga mata hankali ba face tasan mahaifinta baya magana biyu, tsab zai aikata abin da ya yi niyya, tabbas zai iya sawa a kashe Hoorain. Cigaba da magana cikin bada umarni King ya yi yana mai kara kausasa murya. "Daga rana irinta yau ko parlourn nan na haramtawa Zunaira fita, zata kasance ne a cikin ɗakin mahaifiyarta, dakin takalma ban yafe ta yi domin fitowa waje ba, sannan na taraku a nan ne dan ku shaida na bawa Abdussalam aurenta, (Abdussalam ɗin Abu Abdussalam kenan) ko taki ko ta so shi ne mijinta, kuma ba zan jira wai sai ta girma ba, dan girma ya kare tin da har tasan ta je wajen Hoorain, har tasan tana san Hoorain, cikin ƙanƙanin lokaci za'ayi auren ya wuce da ita Dubai!!!!". Da alama ran King ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, dik cikin parlourn babu wanda bai tausayawa Auta ba, har momma ta ji tamkar tasa kuka, amma ta daure tana jin zafin hukuncin King a ranta, amma fa Mammie ta ji daɗin hakan, dan ita burinta ta gansu cikin kunci a kullum. Ƙasa ɗaukarta kafafunta suka yi, durkushewa ƙasa ta yi a saman gwiwowinta a gaban King, tana kuka tamkar ranta zai fita, ta kasa yin magana sai kerma da jikinta yake yi, lokaci guda jikin nata ya ɗauki zafi raw kamar wuta, alamar zazzaɓi, kanta na sara mata da karfi karfi, tana san rokon King da ya yi hakuri ya yi mata afuwa amma ta kasa iya buɗan baki ta yi magana. Lokacin guda wani irin lallausan kamshi ya daki hancin kowa dake cikin parlourn, gabaɗayansu sai da suka shaki wannan kamshi suka lumashe idanu. A miliyan Auta ta kai kallanta a kan kofar shigowa cikin parlourn. Da karfi ta furta. "Yah Omerish". Ta yi maganar ne ba tare da taga kowa a wajen ba, da alama kamshin perfume ɗinsa da ta ji ne ta furta sunansa. Lokaci guda gabaɗaya parlourn suka kai kallansu a kan kofar shigowa ganin taga wajen ta kuma furta sunan da basu taɓa jinsa ba. A miliyan Sarina ta miƙe tsaye tana cigaba da kallan kofar shigowa tana shaƙar wannan daddaɗar kamshi da yake buga mata hanci. Ruɗewa Auta ta yi ta fara ƙoƙarin nufar kofar fita. Tsawan da King ya daka mata ne yasa ta dakata cak kallanta a kan kofar shigowa. A hankali aka turo kofar parlourn, Jaish ne ya sanyo kai kafin Smart namu na kasar France ya rufa mashi baya. Ihun sunansa da karfi Auta ta yi Yah Omerish sannan ta tafi da gudun gaske ta faɗa jikinsa tana sakin kuka mai sauti. Gabaɗaya parlourn zaro idanu suka yi suna kallonsa. A miliyan momma ta miƙe tsaye tana dafe saitin zuciyarta dake mata barazanar tarwatsewa........... King kuwa, ya zaro idanu ya kalli Auta ya sake kallan Smart, saboda kaman dake a tsakaninsu, shi dai Auta kawai ya sani, to wanenne wannan mai kama da ita ɗin? Ya jefawa kansa tambayar cike da mamaki game da ƙaguwa da san jin wanene?. Cikin wani irin murya a mai kama da marairacen murya momma ta furta. "Omerish meya kawoka nan? Meyasa ka zo? Meyasa baka sanar da ni zaka zo ba?". A miliyan King ya dawo da kallonsa a kan Momma, ita ma Akka ta dawo da kallanta a kan momma, nan ta dikka family suka dawo da kallonsu a kan momma. "Dama ni nasan tabbas a shekarun baya karya Rahilarh ta yi mana, a lokacin da wancan matsala ta faru tabbas nasan Rahilarh munafurtarmu ta yi". Cewar Mammie da ta gaza iya haɗiye abin da yake ranta. Sarina kuwa, miƙewa tsaye ta yi kallanta a kan Smart da ya rungume Auta yana cigaba da goge mata hawaye yana kallan momma, shi bai bi ta kan King bama, dan bai ma san wanene King ba, iya momma da yaranta kawai ya sani, bayansu shi bai san kowa a cikin kingdom of power ba. My people's me kuke tinanin ya kawo Smart kingdom of power? Me alaƙarsa da momma? Ya aka yi yasan su Jaish bai san su Ramish ba? Me ya faru a shekarun baya da suke ikirarin momma ta munafurcesu?. To dama na faɗa maku a week ɗin nan zaku sha surprises, taku dai har kullum Princess Teema queen of surprise!!. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥=========== MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 34 "Omerish". King ya maimaita sunan kallansa a kan momma da ta miƙe tsaye tana zaro idanu. Lokacin guda ta fara kame kame alamar rashin gaskiya. "Wani isasshe ya sanya Zunaira kuka a cikin gidan nan? Dama abin da kike ɓoye mun kenan momma? Yau tsawon 2 month kenan tin kafin na yi tafiya (duniyar wata) har na yi na dawo kullum idan na kiraki na ce ina Zunaira sai ki yi ta kauce mun, ashe zalintarta ake yi kika ɓoye mun? Shiyasa hankalina ya gasa kwanciya mana! Me ta yi maku kuma waye ya mareta a face ɗinta?!!" Cewar Smart, ya kai karshen maganar cikin kakkausar murya. Gabaɗaya parlourn tsit suka yi an rasa mai bashi amsa, dan dik sai da suka sha jinin jikinsu ganin kwarjin dake face ɗinsa, an rasa mai tanka mashi, shi kansa Jaish shakkarsa yake yi dik da sun yi sabo matuƙa, amma yana shakkar wani ɗan abin da ya saɓa ya haɗasu. Akwai wanda ya taɓa tina lokacin da Jaish yake yi wa su Omaid nasiha time da zasu koma school? Kun tina a cikin nasihar da yake yi masu ya ce in basu natsu sun mai da hankali a kan karatu ba zai mayar da su ƙasar Faransa! Kun tina wannan lokaci? To wajen Smart yake nufi kenan, baku ji su Omaid ɗin sun ce ya yi hakuri gara masu Yah Ramish a kan Faransa ba? Basa san zuwa wajen Smart dan ubansu zasu ci, sau biyu suka taɓa kai mashi ziraya kafin su dawo sai da suka haddace rabin Alqur'ani mai girma, suka natsu kaman wasu malaman da'awa, da suka koma Dubai sai suka watse...........😅 King dai kusan suman tsaye ya yi, saboda ganin abin yake yi tamkar a mafarki, ya aka yi Smart yake kama da Zunaira over haka?. "Okey ba zaku iya faɗa mun wanda ya mari Zunaira ba sai ran kowa ya ɓaci ne?". Smart ya yi maganar cikin kakkausar murya again. Tsit suka yi har lokacin an rasa mai iya tanka mashi, Sarina tini ta sha jinin jikinta, a tinaninta yadda Smart yake a hotonsa da ta sato daga ɗakin momma haka yake a zahiri, sai taga ina, wannan da zafi sosai yake. •••••••••••••••••••🔥 Uncle Abbas ne ya yi ta mazan miƙewa tsaye, cikin sanyin murya ya ce. "Mahaifinta ya hukuntata". Wani irin kallo ya jefi uncle Abbas da shi wanda yasa su Dr Raj zaro idanu waje, dan kallo ne mai kama da mugun kallo. "Saboda shi mahaifinta ne sai aka ce ya zalinceta? Meta yi mashi? Shi yaga face ɗin Zunaira ya yi kalar wanda za'a ɗaura hannu da sunan duka a kai ne?". Yana magana yana bin uncle Abbas da mugun kallo. Tashin hankali, zaro idanu gabaɗaya parlourn suka yi, barema ita momma da ta fi kowa shiga damuwa, dan kana ganinta zaka san tana cikin tashin hankali. A karo na biyu uncle Abbas ya sake yin karfin halin cewa. "Mahaifinta fa nace maka ba wani ba, and wanenen ma kai da ka shigo mana cikin family without our permission?". Shiru Smart ya yi na ƴan sakanni kafin ya ce. "Then so what idan mahaifinta ne shi? Akwai in da aka bashi damar ya zalinceta ne?". Shiru gabaɗaya parlourn suka yi suna kallansa da mamaki, hankalin kowa a tashs, wai King yau ake cewa meyasa zai hukunta Zunaira? Tashin hankali lallai Smart ya zo da sabon alamari. Uncle Abbas ne ya sake yunkurawa zai yi magana Smart ya ɗaga mashi hannu cikin zafa alamar ya ja bakinsa ya yi mashi shiru a wajen. Cike da isa ya ce. "Bana san na sake jin ka bani amsa, babu wasu mutane a cikin parlourn ne sai kai?". Ya yi maganar yana mai da kallansa a kan King da ya rasa bakin magana kawai yana kallan momma. Jaish ne ya ce. "Yah Omerish uncle Abbas ne fa, he's our second dad, why kake yi mashi magana haka?". .............. "So what idan kanin dad ne? Da shi na yi magana ne da zai rinƙa amsa mun?". Zaro idanu Akka ta yi tana kallan Smart. (Akka taga wanda ya fita iya hau😅) Shiru Jaish ya yi bai sake yin magana ba, dan shi yasan waye Smart. Akka ce ta katsesu da cewa. "Wanenen kai wai da ka shigo cikin family na kake neman tayar mana da hankali ka canza mana alkibla?". Ta faɗa tana ɗaure fuska sosai. Dan ita ma Akka ta sha jinin jikinta ne yadda taga yake mugun kama da Auta, sai ta sha jinin jikinta. Wani irin kallo ya bi Akka ɗin da shi, shiru bai amsa mata ba, bashi ma da niyar amsa mata. Mummyn Chuchu ce ta miƙe tsaye, cikin sanyin murya da magana cike da dattaku da sanyin word irin na uwa ta ce. "Ai kamannin dake face ɗinsa kawai ya isa ya baku amsar wanenen shi ba sai kun nemi ji daga bakinsa ba, babban yayanku ne mana, ku baku ga kamanninsa da Zunaira ba ne? Baku ga kamanin Rahilarh a face ɗinsu bane?". Ai a miliyan su Dr Raj suka zaro idanu, a zabure mama ta miƙe tsaye, hankalinta a tashe sosai ta ce. "No........ Impossible!!, ta ya aka yi ya zama yayansu? Kin dai san bayan Ramish babu wani babba a gidan nan ai!". Uncle Jahiz ne ya miƙe tsaye shi ma, a kan momma ya tsayar da kallonsa, a nitse ya ce. "Momma ki warware mana wanene shi, dan nasan ke kaɗai zaki bada wannan amsa mu fita cikin duhun ruɗani". Yana rufe maki Smart ya dubi King ido cikin ido, talk without respect ya ce. "Me Zunaira ta yi maka ka daketa?".............. Subhanallah, idanun da jama'ar cikin parlourn nan suka zaro sai ya bawa mutum tsoro, hankalinsu ne ya kara tashi, ba'a taɓa yi wa King magana yadda Smart ya yi a yanzu ba, King fa, tab lallai akwai matsala. Momma ne ta katse shi cikin ɗan ɗaga murya. "Omerish daddynku ne fa! Meyasa zaka yi magana haka without respect?"........ Ɗan waro idanunsa a kan King ya yi kafin ya ce. "Ko baki faɗa mun ba i already knew that she's my dad, bcoz of his face, yana kama da su Ramish, so ai already knew that, kawai ya faɗa mun dalilin da yasa ya daki Zunaira?". Tashin hankali, King kuma daddyn Smart? To fa!! Ya aka yi hakan ta kasance? Daddynsa na Paris fa? Waye shi da har suke kama sosai?...... Tsit suka yi, gabaɗaya Mammie ta ji cikinta sai murɗawa yake yi, mama hankalinta ya kara tashi sosai, a tinaninta Ramish shi ne magajin mahaifinsa, tana jin daɗi itace mai power, har tana hasashen gaba kaɗan ita ce zata zama mai murza kambun power crown da ya fi kowani crown karfin iko, ta yi mulki san ranta, ta gama tsara plan ɗinta rana tsaka kawai a wargaza mata komai a wani ce Smart ɗan King ne? Tab aikuwa ba zai yiwu ba. Auta dai ta kwanta shiru a jikinsa tana shessheƙar kuka, Omaid and Obaid da yake sun san ko waye Smart sai suka kara natsuwa suna kallan wannan tashin hankali da aka shiga. Ita kuwa Mammie burinta kawai a warware masu wannan cakwakiya dan tasan wani mataki yakamata ta ɗauka. "Tambayarki fa nike yi Rahilarh, wanenen wannan?". Cewar King, dan hakurinsa ta fara kurewa, saboda ya zo har wuya yanzu, abin ku da jinin sarauta, basa ɗaukar raini, maganar da Smart ya yi mashi without respect shi ne ya bakanta ransa yake san hukunta Smart, amma sai yasan wanene shi tukun nan, dan tin da ya ɗaura idanunsa a kan Smart ɗin ya ji wani irin kaunarsa ya ratsa mashi zuciya........ Babbar magana!!. "Ɗan kane". Tashin hankali, momma ta bawa King amsa tana kallan cikin idanunsa. Zaro idanu King ya yi tare da sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, ɗana kuma?. Ya maimaita kalmar a cikin ransa. Lokacin guda ya ji wani irin sanyi ta ratsa zuciyarsa, dik da bai san ta ya aka yi Smart ya zama ɗansa ba, ba shakka ya ji sanyi a ransa, sai dai kuma ta wani ɓangare ya ji ransa ya sosu matuƙa, dan dik cikin ƴaƴansa babu wanda ya taɓa yin gigin yi mashi magana yadda Smart ya yi mashi, kowa respecting ɗinsa yake yi sosai. Uncle Jahiz da ya ji zancen kamar a mafarki ne ya yi saurin cewa. "Momma how comes hakan zai kasance bamu sani na?". A ruɗe ya yi maganar. Wani irin tsawa mama ta daka wajen cewa. "Ina hakan ba zai yiwu ba! Ta ya akayi ya zama ɗansa? Hauka ne abin?!!". Kowa ya ji maganganun mama yasan meyasa take faɗin hakan. Ita dai mummyn Chuchu shiru abinta, amma dai ita ma ta ji babu daɗi a ranta dik da tasan cewa dama ba ita bace da mulki tin da Ramish ya girmewa Bilal, amma dai ranta ya ɗan sosu kaɗan bayyanar Smart. Mammie kuwa mutuwar tsaye ta yi, tabbas tasan momma ta ɓoye Smart a rikicin da aka yi a baya, amma bata taɓa zatan irin wannan bayyana Smart zai yi ba, yaro ya fi ubansa zafa, wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, ya dame King a zafin zuciya da jiji da kai, ga shi da magana kai tsaye babu wata ɗar ɗar, kuma magana a kaifafe, ga uban kwargini. Sosai hankalin Mammie ya kara yashi over, tinaninta ɗaya ya za'ayi su ga bayan King ga wani zakin ɗan nasa ya kara bayyana, idan ma ta ce zata auri King ɗin wlh waɗan nan zakunan ƴaƴan nasa zasu iya cinyeta da ranta, kai ta ko'ina abin babu sauki a gareta. "Ki yi mana bayani ta ya aka yi wannan ya zama ɗana?". Cewar King kenan. Jinjina kai momma ta yi kafin ta ce. "Kowa ya samu waje ya zauna". Babu musu suka koma saman sofas da suka tattashi suka zauna suna jiran momma ta kora masu bayani. "Omerish ka samu waje ka zauna bari mu yi magana ko?". Cewar Momma. Bai musa ba ya wuce saman sofa mai zaman mutun uku ya zauna tare da zaunar da Auta a saman laps ɗinsa, sannan ya ce Guyson ya taso ya zo ya zauna a kusa da shi. Da sauri guyson ya taso, dama tin ɗazun yake san yin magana amma ya kasa, dan shi ya fi kowa sabo da Smart, dik in aka yi karamar hutu a school sai ya je France, Auta kuma sai ta je Dubai Smart yake tura jirgi ya ɗaukota karkashin kulawar Jaish ba tare da sanin kowa ba, wani lokaci kuma Jaish ɗin ne yake ɗaukarta daga kingdom of power ya ce sun tafi yawo sai su wuce wajen yayan nasu a Faransa ɗin, in short dai guyson ya fisu sabo da shi sosai. Shi kuma Smart ya fi shakuwa da Auta, dan kamar yadda take kama da shi a fuska haka jininsu ya yi matuƙar haɗuwa, tamkar ransa yake santa, yanzu haka dalilinta ya zo kingdom of power, dan tin kafin ya tafi duniyar wata yake san momma ta haɗa shi da ita, amma momma tana yi mashi kona kona, ba komai yasa ba kuma face Auta ɗin ta ɓata a lokacin, momma tana gudun faɗa mashi ta ɓata dan kada ya ce zai zo ko ya ɗauki wani mummunar mataki, shiyasa taki faɗa mashi, idan ya kira guyson ma ya haɗa shi da Auta shi ma ya yi ta yi mashi kwana kwana dan momma ta hanasa faɗa, haka Jaish ma, daga karshe da ya gaji ne yana dirowa daga tafiyar da ya yi ya ɗaga jirgi sai kingdom of power, kun ji dalilin zuwansa. Gabaɗaya parlourn tsit suka yi bisa umarnin King, sun zuba idanu suna jiran su ji me momma zata ce, kowa idanunsa a kanta. Akka ta lura Smart ya fita zafa sai ta natsu, dan ta lura shi ya gado ainahin zuciyar king Abdul Malik, su King Zuhair dik basu gada yadda yakamata ba, ga wanda ya fisu zafa, tsit kuke jinta a parlour kamar babu ita!!. Gyara murya momma ta yi kafin ta fara jawabi dallah dallah kamar haka. "Kamar yadda na faɗa Omerish ɗanka ne to hakan ne babu shakka a wannan al'amari". Kirjin mama and Mammie ne suka bada dum dum da karfi!!. Hankalinsu ne ya kara tashi, lokaci guda suka fara haɗa gumi, momma ta jiƙa masu aiki, mama kam kasa hakura ta yi har sai da ta ce. "Ta ya aka yi ya zama ɗansa shi ne zaki yi mana bayani!". Momma bata bi ta kanta ba ta cigaba da cewa. "Dama ba mutuwa ya yi ba, a lokacin da ka kafe lallai sai na dawo maka da shi, na yi magiya kaki saurarona, dik kunki fahimtata, kun ki fahimtar abin da nike faɗe, har daddy a wannan karan bai fahimceni ba, su Yah Rahab kowa yaki fahimtata, Yah Muhammad ne kawai ya iya fahimtata, a wannan lokacin ne dan Omerish ya tsira da ransa ya kuma rayu sai muka haɗa baki da Yah Muhammad a kan mu shirya maka ya mutu sai ya tafi da shi kasar France in da babu wanda zai sake ganinsa domin ya rayu............" Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon wani tsawa da Akka ta daka mata. "Rahilarh dama ba gaskiya bane mutuwarsa? Amma kika jefamu cikin tashin hankali? Kina ji kina ganin mahaifinsa ya rinƙa ciwo kaman zai mutu dalilin mutuwarsa, amma kika share kamar babu zuciyar tausayi a kirjinki, e lallai". Kasa da kai momma ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Goggo ki yi hakuri, wlh a kullum ina kukan ciwon da Yah Zuhair yake yi a kan mutuwar Omerish, na shiga damuwar da ban taɓa shiga ba, har na karaya na yanke shawarar zan dawo da Omerish in yaso a kashesa da gaske kowa ya wuta, amma Yah Muhammad ya ce a'a in daure komai zai wuce, wlh goggo ina tsananin san Omerish shiyasa na yi hakan, amma dan Allah ki yafe mun, kai ma Yah Zuhair ka yafe mun, nasan na yi kuskure............" Wai me ya faru a baya ne da yasa har aka so kashe Omerish ɗin?. To mu je dai zuwa, wanda zata bada labarin abin ya faru a baya bata bayyana ba tukun nan, idan ta bayyana zaku ji komai. Katse mata magana King ya yi da cewa. "Kin cuceni Rahilarh, kin cuceni wlh". Yana kai karshen maganar ya miƙe da sauri saboda wani irin zafi da zuciyarsa take yi mashi, yasan zai iya faɗuwa a wajen idan ya cigaba da tsayawa saboda zafin zuciya. Bedroom ɗinsa ya shiga da sauri yana huci, da sauri momma ta miƙe ta bi bayansa, Aunty MieMie ce ta yi saurin sake miƙewa ta rufa mata baya. Nan fa parlon ya koma kallon kallo, su Mammie da suka san abubuwan da suka faru a baya sun gane kan maganar da momma take yi, su kuma su Sarina da basu san tarihin baya ba sai basu gane kan maganar momma ba bayan cewa Smart ɗan King ne. Bari in kara maku wani haske kaɗan kafin mu wuce gaba. Tabbas Smart ɗan King ne, kuma shi ne babban yayansu, ya fi su Ramish dikka. Ya aka yi ya fi su Ramish?. Mu je dai zuwa, kada ku manta ita ma mummyn Chuchu tana da babban yaro da ya fi Ramish amma ya rasu, kada ku manta na faɗa maku hakan a baya. Akwai wani abin da ya taɓa faruwa a kingdom ɗin a lokacin da momma ta haifesa bai wuci kwana uku a duniya ba, so a lokacin momma ta gudu Dubai ba tare da sahalewar King ba, saboda ta ce zata tafi ya hanata, ita kuma tana ganin ɗanta zai mutu ne idan tana Kingdom of power, shi ne ta gudu bai sani na. Time da ta koma Dubai, ta yi ta yi ta zauna iyayenta suka ki yarda saboda King ya ce bai aminta ba, ya ce ta dawo, ta yi ƙoƙarin yi masu bayani a kan in ta koma tabbas ɗanta zai mutu, amma suka ki fahimtarta, hakan yasa ta yanke shawarar shirya masu cewa Smart ya rasu. Ta kuma yi nasarar yin hakan tare da taimakon yayanta wato daddyn Smart na Faransa kenan, sai da kowa ya aminta da Smart ya mutu, sannan daddynsa ya tafi da shi France. Momma bata taɓa yin kwana biyu bata yi video call da yayan nata ta ga ɗanta ba, hakan yasa Smart ya tashi da sanin ita ce mahaifiyarsa, yana yawan tambayarta ina daddynsa, kullun sai ta ce mashi sai ta zo ɗaukarsa zata zo tare da daddynsa. Time da ya kai 20 years sai ya matsa mata a kan lallai yana san ganin daddynsa, a lokacin ne ta kira shi video call ta juya camera ta shiga ɗakin King, so a lokacin ya fara sanin daddynsa shi kuma King bai lura da video call take yi ba, so bai ga ɗan nasa ba, da yake yayan momma ɗin yana yi mashi komai yasa bai damu da yazo ga iyayensa ba, dan suma sun ɗaukesa kamar ɗa dama Allah bai taɓa basu haihuwa ba. Kun ji a in da Smart ya samo kamanninsa da daddynsa na France ko? Daddyn nasa yayan momma ne uwarsu ɗaya ubansu ɗaya wato King Badeen kenan, kunga dole a samu kamanni ai. Shi kuwa daddyn nasa tun yana yaro ya tafi kasar France, a can ya yi karatu ya kammala, har ya samu aiki sannan suka fara soyayya da mom ɗin Smart ɗin, suka yi aure, a dalilin haka ya samu takardar ƙasa ya zama ɗan ƙasa har ya iya shiga siyasarsu. Momma kuwa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen nunawa Smart ƴan uwansa gabaɗaya, dan bata san kan ƴaƴanta su tashi a wargaje, tana san su tashi kansu a haɗe, su kaunaci juna, ta kuma yin nasarar samun hakan, tabbas sun tashi cike da kaunar juna dikkansu, sun san juna. Sai dai shi kuma Smart ba iya kannensa kawai ya sani ba, a lokacin da ya girma ya gama karantu sai ya fara bincike a kan ƴan uwansa, a nan ne ya san su Ramish dikka, dik kuma yana kau taimakawa su Ramish a bakin aikinsu sosai, domin dayawan lokuta da taimakonsa Ramish yake samun karin girma har ya zo matsayin da yake, amma su basu san shi ba, kuma basu san yana taimaka masu ba. In short shi ne ma ya binciko in da Jaish yake time da ya ɓata, sannan ya turawa Ramish address ɗin, so dik abin da suke yi yana gani kuma yana sane da su, momma take hana shi zuwa ga kingdom of power, ta ce ba yanzu ba sai ya kara girma, dan tsaro. Harta gidan Smart dake France in da yake yawan zama in ya bar gidan daddynsa, wannan gida da sunan Zunaira ya ginata, gidanta ne da ya mallaka mata, yana da nasa na daban, ya zaɓi ya rinƙa zama a nata ne kawai, yanzu haka yana nan yana kan bincike a kan masu nikaf dan ya taimakawa Ramish ba tare da sanin kowa ba, shi ɗin garkuwan gabaɗaya familyn marigayi King Abdul Malik ne, dan yasan kowa su ne basu san shi ba, kuma yana taimaka masu ta hanyoyi daban daban wanda mutum ba zai taɓa zata ba idan dai ba faɗa mashi aka yi ba. Jama'a nace ku zo mu haɗu mu tsinewa tsafi, tsafi karyar banza ne da na wofi, idan ba karya ba ne meyasa dik tsafin Mammie bai iya gane mata Smart ba? Meyasa ta kasa iya gane cewa yana raye har ma ya girma? Kullum sai dai ta kare a hasashe shegiya, karyar banza da wofi, wlh idan mutum zai koma ga Allah ma da ya fi mashi, tsafi dik surkullen banza ne shegu. Wannan dalilin yasa kuka ga Smart and his dad musulmai ne, saboda dad ɗinsa yayan momma ne, balarabe ne, mom ce baturiya kuma krista, kuma tana da kyan hali, dan ita ta makale lallai tana san daddy. To in short dai kun ji yadda labarin Smart ya kasance ko? Nasan a iya wannan bayanin kun fahimci in da na dosa, ba zan tsaya dogon bayani sosai ba, dan akwai labari a gaba sosai, gaba zaku ji karin bayani dai. Mu cigaba da labarinmu. ••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Tsaye momma ta isko King a tsakar ɗakinsa, sai huci yake yi, ransa ya kai ƙololuwar ɓaci, zuciyarsa sai tafasa take yi, momma bata kyauta mashi ba, tasa Smart ya taso baya ganin girmansa, bai ma san shi ba, wannan ai zalinci ne. Da alama King ya samu ɗan da zai iya sanya shi ya gane yadda zafin kaunar ɗa yake da yasa commander Zafar ya hukunta ɗansa ɗaya tilo a duniya, dan ga dikkan alamu King yana tsananin kaunar Smart over, dan shi ne first born ɗinsa, har ciwo ya kwanta lokacin mutuwar Smart na karya da momma ta shirya. Wato fa idan Allah ya tashi kama mutum wlh baka isa ka iya canka ta wace hanya zai kamaka ba, ga shi dai cikin ruwan sanyi ya kama King bama aje da nisa ba, zakuwa muga yadda wannan cakwakiya zata kaya. A gabansa momma ta zube gwiwowinta a ƙasa, cikin sigar ban hakuri ta ce. "Dan Allah ka yi hakuri Yah Zuhair, wlh ban yi abin da na yi dan na cutar da kai ko wani abin makamancin hakan ba, na yi ne kawai saboda san da nike yi wa Omerish, ba zan iya jurar rashinsa ba, kuma kai da kanka ka shaida da tabbas zai iya mutuwa a wannan lokaci, ba kai da kanka daga baya ka ce in dai'na haihuwa a nan in rinƙa komawa Dubai in haihu a can ba? Kaga da ban yi mashi hakan ba da mutuwa zai yi, kana ganin yadda Jaish ya tsira da kyar fa, kasan komai, dan Allah ka mun afuwa ka ji?". "Kin cutar dani Rahilarh, cuta mafi munin da ba zan taɓa mantawa da shi ba!! Ki duba yadda ɗana ya taso, ya taso cikin kafurai, bai san darajar manya ba, ki kalli yadda yake magana da ni tamkar ɗansa ne ni, gaskiya kin cuceni". Cikin zafi ya yi maganar, bai taɓa shiga ɓacin rai irin na wannan rana ba, abin da ciwo matuƙa wlh, dan ma tana matsayin ƴar kawunsa ne, kuma Akka na bala'in kaunarta, da wlh sai ya hukunta hukunci mai zafin gaske. Aunty MieMie da take binsu da kallo ne ta samu waje saman sofa ta zauna, bata taɓa kallan daddynsu a cikin irin wannan yanayi ba, gaskiya ko mafarki ta yi akwai ranar da zata zo King da momma su samu gagarumin matsala irin wannan idan ta tashi daga wannan mafarki sai ta yi sadaka kuma ba zata taɓa yarda da hakan ba, sai ga shi a zahiri ya faru, ita dai tasan sosai King yake bala'in san momma. Mummyn Chuchu da ta shigo tun ɗazun ne ta matso tare da rike Momma dake durkushen tana ƙoƙarin faɗuwa, ƙoƙari buɗe baki ta yi dan ta taushi King. Cikin zafa ya ɗaga mata hannu alamar baya da buƙatar jin komai daga garesu, infact su fita mashi a ɗaki baya san ganinsu. Ganin ya ɗauki zafi sosai hakan yasa mummy ta miƙar da momma tare da ce mata. "Rahilarh ki yi hakuri mu je, zuwa da safe idan ya huce sai muyi magana ko?". Hawaye sosai momma take yi, dan ita kanta tasan bata kyautawa King ba, haba wani irin zalinci ne wannan? A lokacin da ya samu labarin rasuwar Smart yana zaune a saman kujerar mulkinsa sai da ya miƙe tsaye, bai san lokacin da ya cire crown ɗinsa daga kansa ba, ya jijjiga sosai, kwana uku bai fita fada ba yana jinyar zuciyarsa, da taimakon Allah da addu'ar iyaye da abokan arziki ya samu zuciyarsa ta iya ɗaukar wannan kaddarar, shi ma ya kusa mutuwa, ashe dik shirin momma ne, gaskiya abin akwai ciwo, babban abin da ya fi kona ran King ma shi ne yadda Smart bai ɗaukesa da daraja ba, yanayin tarbiyarsa kaf ta sha banban da tarbiyar jikokin Akka, dik ya damesu a komai ya shanye, King ya yi takaicin hakan matuƙa. Waje gabaɗayansu suka fita, suka kyale King shi kaɗai a cikin ɗakin yana ta huci. A bakin kofa mummyn Chuchu ta tsaya ita da Aunty MieMie suka hau sharewa momma hawaye suna tausanta har sai da ta yi shiru, sannan suka rakata ɗakinta. A parlour kuwa kowa ya yi mutuwar zaune da jin abin da momma ta faɗa, su uncle Abbas an rasa abin faɗe, Akka kuwa ta kara ɗaukar zafi, abin ya bakanta mata rai, momma ta yi masu ba dai'dai ba, a fusace ta miƙe ta nufi part ɗinta domin ta je ta kira Husaininta wato King Badeen ta sanar da shi abin da ƴaƴansa Momma da baban yayanta wato daddyn Smart suka aikata. Da sauri Dr Raj ya miƙe ya bi bayan Akka, a cewarsa kada ciwon zuciyarta ya tashi ta sume, bari ya yi saurin bin bayanta......................... Sarina kuwa, dik abin da ake faɗa baya shiga kunnuwanta, hankalinta na'a kan Smart, sai kallansa take yi kamar zata cinyesa da ido, taga kyau iya kyau, tini ta yi rantsu da Allah ga mijinta nan ya bayyana. Mammie ma alkawari ta yi wa kanta a kan lallai ne wannan shi ne mijin Sarina, dama ta ce first born na King yarta zata aura, to ga shi ya bayyana. Uncle Abbas and uncle Jahiz ne suka yi gaggawar bin bayan Akka da Dr Raj. Miƙewa Jaish ya yi tare da cewa Smart ya zo su je part ɗinsa ya kwanta ya huta zuwa da safe zasu sake zama, dan case bai kare ba, yanzu ma aka fara. Jawad da shi ma already ya san da Smart saboda shi ɗin kamar ɗan momma yake, shi ma miƙewa ya yi tare da riko hannun Chuchu yana faɗa mata ta tashi su raka Yah Omerish part ɗin Jaish kafin su dawo su tafi nasu dare ya yi. Smart rike da hannun guyson and Auta da ta yi shiru ya miƙe tsaye, Jaish ya yi gaba ya rufa mashi baya. Miƙewa Obaid and Omaid suka yi, har zasu wuce su fita Omaid ya juyo da kallansa a kan Sarina, ƙasa ƙasa ya ce. "Aunty Sarina kinga Yah Omerish ɗin yanzu ko? Ko dai har yanzu a mafarki kika san shi?". Ta fahimci gatse ya yi mata cikin maganar, amma sai ta danne ta ce e ta gansa, a cikin zuciyarta kuma mamakin Omaid take yi, dan lokacin da tambayesu wanene Omerish shi Omaid bai yi magana ba, ya yi ma kamar bai jita ba, ashe ya ji ɗan kaniya, rashin kunya yasa ya yi banza da ita. Wucewa suka yi suka nufi waje abinsu. Mammie ce ya miƙe tana cewa Sarina su tashi su tafi dare ya yi. Miƙewa suka yi suka fita, parlourn ya rage mama, uncle Taheer da kuma Aneesa, mama ta gaza motsawa daga in da take zaune, tamkar ruwa ya cinyeta, ta rasa ganewa kanta, momma ta rusa mata plan, a ranta ta kuduri niyar wlh ba zata hakura ba, ba zata bari ba gaskiya, sai ta ɗauki mataki. Bedroom dake kusa da nasa Jaish ya kai Smart, cike da kauna ya ce mashi. "Yah Omerish wannan bedroom ɗin ya yi maka ko dai na canza maka wani?". Hannu Smart ya ɗaga mashi bayan ya saki hannun guyson, sannan ya ce. "Is okey, Omar ku zauna bari in yi take bath ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da sake hannun Auta. Juyo da kallansa a kanta ya yi, cikin sigar rarrashi ya ce. "Sorry our baby, daddy sai ya biya wannan marin da ya yi maki, bari Allah ya kaimu wayewan gari kin ji?". Ya yi maganar yana ɗan shafa kumatunta in da shatin hannun King suka fito ruɗu ruɗu. Kai ta jinjina mashi tana kara shagwaɓe fuska. "Hau saman bed ki kwanta ina zuwa". Ya faɗa yana nuna gadan da hannunsa. Ba musu ta haye har lokacin tana ɗan sauke shessheƙar kuka a hankali hankali. "Yah Omerish ni ma bari in je in yi wanka sai in sa a kawo maka abinci". Cewar Jaish. Jinjina kai Smart tiger ya yi, kafin ya ce. "No need anything now, ka dai je ka yi wankarka, ba sai kasa an kawo mun komai ba". Ya kai karshen maganar tare da ɗan rungumar Jaish ɗin kamar yadda suka saba a al'adarsu ta France, sannan ya nufi toilet. Matsawa kusa bed ɗin Jaish ya yi, cike da kauna ya kara rarrashin Auta da guyson kafin ya wuce ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin. Yana fita kai tsaye nasa bedroom ɗin ya nufa. Wani irin daddaɗar kamshi na daban ne ta dokin hancinsa ba wanda ya saba ji ba, alamar an canza mashi room freshener kenan. Shakar kamshin ya yi haɗe da ɗan lumshe idanu, alamar kamshin ta ratsa shi sosai, akwai daɗi kam. Mamaki ya yi a kan waye ya canza mashi room freshener kuma?. A bakin bed ya zauna tare da rage kayan jikinsa, short and singlet kawai ya bari a jikinsa, miƙewa ya yi ya nufi toilet yana tinanin wannan cakwakiya na. Tura kofar toilet ɗin ya yi tare da yin addu'ar shiga ya sanya kansa. Tura kofar da ta ji anyi ne yasa ta juyo a miliyan dan taga wenenen? Tana tsaye a gaban jacuzzi wajen shower, ta kunna ruwa ta cika boket tana wanka, dan ita bata san shiga cikin jacuzzi, tafi yarda da ta tara ruwa a boket sai ta yi wankanta. Ta gama sanya kumfar sabulu a gabaɗaya jikinta ta juyo gatesa. Ɗan zaro mata idanunsa ya yi yana binta da kallo kamar ba shi ne ya ce kada ta bari su sake haɗuwa ba, ya ga kaya ɗan rainin wayo, dama da guntun jarabarsa ta kwanaki uku da suka wuce da ya sameta tana barci a parlournsa, to bai gama watsakewa daga wancan bama sai ga shi yau ya sake yi babban kallo wanda da wuya ya iya tsallekawa ko kuma ya ce zai kwantar da wannan tarzoma dake shirin tashi Saboda da alama abar ta motsa. Kasa gaba ya yi ya shigo cikin toilet ɗin, ya kuma kasa yin baya ya fita, ya tsare yar mutane da ido, yasata jin kunya in ban da rashin kunya irin na jikokin Akka. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Love page, yauwa kwana biyu mun sha gwagwarmaya sosai, to yau kam bari mu ɗan yi nishaɗi mu leƙa duniyar masoya kafin mu ɗaura da surprises ɗinmu. Ita kuwa tana ganinsa ta saki kara tare da juya mashi baya. Ɗan ɗaure fuska ya yi tare da jan siririn tsaki, wai irin shi zai basar kada a rai'na shi ɗin nan, sai ya wani tsare gida, cikin dakiya ya ce. "Ke bana ce kada ki bari mu sake haɗuwa ba?". Yana maganar kuma yana karewa halittar jikinta kallo dan tabbatar rashin kunya irin na jinin Akka. Shiru ta yi, ta ƙasa amsa mashi, ji ta yi tamkar ta nitse ƙasa saboda kunya. Wani siririn tsaki ya sake ja kafin ya juya da sauri ya fice yana haɗiyar yawu, wai shi a dole zai basar ya danne. Saman bed ɗinsa ya haye ya kwanta, janyo wayarsa ya yi domin ya ɗan rage lokaci kafin ta fito. Sai dai kuma yana taɓa wayar tamkar ya kunnawa ƙwaƙwalwarsa tinaninta ne, gabaɗaya ya nemi sukuninsa ya rasa, har wani zufa ne ya fara keto mashi a gefe da gefen face ɗinsa, gabaɗaya a matse yake amma ya nuna zai danne hakan. A hankali ya jefar da wayar tasa ba tare da ya farga ba, wasa wasa ya ɗan fara juyi a saman bed ɗin ƙwaƙwalwarsa na kara tinano mashi kyan surar jikinta, ga shi sai glowing take yi, hasken fatarta ya ƙara fitowa sosai, har wani yellow yellow ta yi. Haba tini notikan ƙwaƙwalwarsa suka fara kwancewa. A haka ta fito ɗaure da towel ɗinsa a kirjinta ta same shi, yana jin motsin fitowarta sai ya danne juyin da yake yi, ya kwanta ya kifu tsit kamar wanda ya yi barci, ɗan rainin wayo kuma abar tana damunsa sosai, amma wai irin kada ta rainasa ɗin nan, sai ya dake. Ita kuwa baiwar Allah, bata wani kallesa sosai ba, saboda kunyar babu kaya a jikinta, da sauri ta shiga dressing room dan ta shirya. Yana ganin ta shiga ya yi saurin miƙewa ya nufi toilet wai dan ma kada ta dawo ta same shi a haka har ta gane halin da yake a ciki, sai ya gudu cikin toilet yana matse bananar tasa dan ya samu sauki. Cikin ɗaya daga cikin kayan da momma tasa mama Haulat ta kawo mata na barci ta shirya. Ta yi wani irin kyau da in dai namiji lafiyaye ne ya ganta to fa ba zai iya hakura ba. Hijabin da take sallah ta ɗauka ta ɗaura a saman kayan, sannan ta fito ta nufi part ɗin momma dan ta ɗauko mashi cappuccinon, Allah sarki sam bata gajiya da kyautata mashi dan tana san kayanta, shi kuma sai sinki sikin iskanci da iyashege cike da ƙwaƙwalwarsa. Mama Haulat ce kullum take kara karfafa mata gwiwa a kan ta cigaba da matsar da kanta a garesa tabbas watarana zai waiwayeta, shiyasa kuka ga har yanzu take shiga bedroom ɗinsa bata dai'na ba, ita kuma Chuchu tana kara koya mata yadda zata narka zuciyarsa a soyayyarta, yanzu ta ɗauki darasi sosai abinta, jira take yi kawai wani abin ya haɗasu yaga zallar madarar soyayya. Allah sarki momma uwa ta gari, dik da tana cikin damuwa a kan abin da ya faru a tsakaninta da King, hakan bai hanata ta shiryawa ƴaƴanta abin da suke so ba, ta shiryawa Jaish and Omerish cappuccino kamar yadda suka saba sha a kowacce dare kafin su kwanta. Mahnoor tana zuwa ta ɗauki cappuccinonsa kamar yadda ta saba, a lokacin momma tana cikin toilet tana wanka dan ta koma wajen dearlyn love ɗinta ta rarrashi kayanta......🤭👀 Bata tsaya jiranta ba ta ɗauki cappuccinonsa ta fito. Har lokacin da ta koma bedroom ɗin yana cikin toilet bai fito ba....... Wai me ya tsayar da Jaish a cikin toilet ne?........👀🥱 Ɗan ƙaniya yana can yana ƙoƙarin controlling na kansa ya haɗiye kwaɗayinsa ya danne abar gadon, sai dai ya gaza iya yin hakan, sai ma kara tashi hankalinsa yake yi ta sanadiyyar tinano mashi surarta da ƙwaƙwalwarsa yake ta yi, dik ya kiɗime, abin tausayi kuma abin dariya. Saman table ta ɗauka cappuccinon, sannan ta ɗauko perfume da Chuchu ta bata mai sanyin kamshi ta feshe jikinta da shi. Kamar zata fice waje izuwa bedroom ɗinta, sai kuma ta tina da kalaman mama Haulat da kuma Chuchu ɗazun in da suke ce mata ta dai'na kwana a wani waje in ba a saman bed ɗinsa ba, komai zai ce mata kada ta damu ta daure watarana zai wuce kuma zata yi nasara. Tina waɗan nan kalaman yasa ta cire hijabin jikinta ta mayar da shi d-room ɗinsa, sannan ta dawo ta haye saman bed ɗin, kwanciya ta yi haɗe da rufe idanunta tana tinanin abin da zai faru idan ya fito ya sameta kwance a saman bed ɗinsa. •••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 A gefe guda kuwa, Dr Raj da ya bi Akka yaga babu wata matsala, ga kuma su uncle suna tare da ita, sai ya yi saurin ficewa daga ɗakin, dan dik hankalinsa yana a kan yarinyar da suka yi karo ɗazun. (Zee) Burinsa kawai ya sake sanyata a idanunsa dik da bai san wacece ita ba. A karon farko yau ya yi wa garden sallama da ɗan sauti. A lokacin Zee tana kwance saman sofa ta takure jikinta waje guda, har barci ya fara ɗaukarta, dama kun san ta ce ba zata koma part ɗin mama ba, gara mata ta kwana a waje, so shi ne ta yi kwanciyarta a nan har barci yana shirin ɗaukarta. Ganin alamar bata ji sallamarsa bane yasa ya sake yi mata sallama cikin natsuwa. A ɗan razane ta waro idanunta. Da yake ta fara barci sai bata iya gane wanene bane dik da hasken dake wajen. Ganin mutum yasa ta yi saurin miƙewa zaune idanunta a kansa, tana san tantance wanene?. Wucewa ya yi izuwa saman sofa ya zauna yana kallanta shi ma, sai yanzu ta iya gane ashe mutumin da take mafarki ne a yanzu, wannan ɗan barci da ya ɗauketa har mafarkinsa ta fara yi. Ƙasa ta yi da kanta tare da cewa. "Good evening". Kallanta da yake yi irin kallan nan ne na ke special ce da kika sace zuciyar jinin Zuhair lokaci guda. Ta tafi da imaninsa ta yadda kunnuwansa suka ƙasa iya jiyo mashi sanyayyar muryarta tana ɗaga mashi gaisuwa. Sai da ta sake ɗaga mashi gaisuwar sannan ne ya fahimci ashe magana take yi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa mata. Ganin alamar zama ya zo yi a wajen yasa ta miƙe tsaye domin ta koma ciki, sai satar kallansa ta kasan ido take yi, taga ɗan kyakkawan mamansa kani a wajen Ramish namu na amana. Step biyu ta ɗan taka zata taka na uku kenan ta tsinkayo sexy voice ɗinsa yana faɗin. "Ina kuma zaki je?". Cikin natsuwa ta juyo, dik da bata san wanenne shi ba tana respect ɗinsa sosai. "Ciki zan koma". Ta bashi amsa tana ɗan ɗago kallanta dan ta saci kallansa da kyau, tana san ganin face ɗinsa sosai amma bata san su haɗa ido. ........... "Ciki kuma?". Ya maimaita maganar da alamar mamaki a saman face ɗinsa. Kasancewar da turanci ta ɗaga mashi gaisuwa sai kawai ya cigaba da yi mata magana da English ɗin. Kai ta gyaɗa mashi alamar e ciki. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "To kafin dai ki shiga cikin z ki bani abata da kika sace kada ki tafi da ita". Ya yi maganar yana kara gyara zama haɗe da ɗan wasa murya. Zaro idanu sosai ta yi, take tsoro ya bayyana a saman face ɗinta, a ɗan ruɗe ta ce. "Wani abu kenan? Ni ban ɗauki komai ba wlh". Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka. Miƙewa tsaye ya yi, a hankali ya yi step biyu ya matsa kusa da ita sosai, ƙasa ya yi da murya kafin ya ce. "Kawai ki bani abata tin kafin kowa ya jimu, kin san da cewa a wannan masarauta dik wanda ya yi sata cire mashi hannu ake yi ko?". Kai ta girgiza alamar bata sani ba tana zaro idanu. Kara taka step ɗaya ya yi ya sake matsawa kusa da ita sosai, kashe muryansa kaɗan ya ɗan yi, kun san doctors da shegen iya soyayya da iya magana. Da sauri ta ɗan ja baya ganin ya matsota sosai, har cikin ranta ta ji tsoron kalamansa, dan ta ɗauka da gaske an sace mashi wani abin ne zai kala mata sharri. "To in baki sani bama yau kin sani, dik wanda ya yi sata datse idanunsa muke yi, ga shi ke kuma kin mun sata, amma babu komai ki dawo mun da abata da kika sace zan rufa maki asiri ba zan sanar da kowa ba bare a cire maki hannu". Yana maganar yana kara matsawa kusa da ita. Kara tsananta tsorata ta yi, a hankali ta fara ja da baya tana san matsawa daga kusa da shi, dan yadda ya matsota ɗin nan kwarjininsa ya kara yi mata yawa. Sai dai kuma dik in ta taka taku ɗaya ta matsa baya, shi kuma zai taka taku ɗaya ya matsa kusa da ita, a haka suka rinƙa yin baya baya tana ce mashi ya yi hakuri ita wlh bata yi mashi satar komai ba, shi kuma yana ce mata a'a bai yarda ba sai ta bashi abarsa da ta sace kafin ta tafi. A haka har suka kurewa bangon wajen, a ɗan tsorace ta juya taga sun isa wall glass dake wajen rumfar, a tsorace ta juyo da nufin ta kallesa sai ta ga ya matsa dab da ita sosai, har suna iya jiyo numfashin juna, ya kuma yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa yana kallan face ɗinta. Lokaci guda ta ji ta yi nadamar fitowarta, gara mata ɗakin mama ashe a kan wajen nan, dik sai ta shiga tashin hankali, a tinaninta wani abin zai yi mata. Narai narai da idanunta da suka ciko da kwallah ta yi zata yi mashi kuka, dik zafinta dai shi ta kasa zazzaga mashi masifa ko ta faɗa mashi san ranta, ya yi mata kwarjinin da ba zata iya yin hakan ba. Yana tsaye ya dafa hannunsa ɗaya a jikin bango ta bayanta, ɗayan kuma yana rike da wayarsa yana kallnta. Sai da ya ga hawayenta sun fara salwanta a banza suna bin saman kuncinta ne ya ɗan waro idanu kaɗan, calmly ya furta. "Ashe haka kike da tsoro da saurin kuka?". Ya yi maganar ba tare da ya zare kallansa daga kanta ba. Cigaba ta yi da kukanta bata bashi amsa ba, dan bata da abin faɗe. Ɗan nisawa ya yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗimi daga bakinsa, sannan ya ce. "To ai ke bama ki tambayi abin da kika sace mun ɗinba da kika tsaya kina mun asarar hawayenki". Sai a lokacin ta ɗago manyan idanunta kaman na kawunta Sadiq, a cikin nasa idanun ta sauke kallanta, lokaci guda sai ta ji kukan nata ya tsaya cak sakamakon wani irin kallo da ya wurga mata mai narkar da zuciya, bata san time da ta shanye kukan ba, sai ji ta yi hawayen sun dai'na zuba. Da sauri ta yi ƙasa da kanta, kun dai san mu Nigerians da kunya kamar me muke.............🥱 Zira wayarsa a cikin aljihun wandan sleeping dress dake jikinsa ya yi, sannan ya sanya hannunsa ya riƙo hannunta ɗaya, ƙasa ya yi da murya cikin wani irin salo mai kwantar da hankali ya ce. "Malama wadda ban san sunanta ba, kuma ɓarauniyata maza bani abata da kika sata, dan babu in da zaki je sai kin bani kayana". Yana magana yana ɗaga gera guda kamar wani...................🤫 Muryarta na sarkafewa saboda kuka, ga wani shessheƙa da take yi, kun san mutuniyar akwai zuciyata, so sai shessheƙa take yi alamar zuciyar tana a kusa, da kyar ta ce. "Allah ni ban sace maka komai ba, dan Allah ka yi hakuri ka barni in ta fi ciki". Ta yi maganar cike da san ta kwace hannunta daga rikon da ya yi mata, saboda a takure take, bata saba ba. Shi kuwa kara rikota da kyau ya yi, a karo na biyu ya sace cewa. "To ai baki ma tambayi abin da kika sata mun ɗin ba"........ Kawar da kallanta daga kansa ta yi tare da cewa. "Me na sace maka to?". Ɗan rankwafo kanta kaɗan ya yi, dan ya fita tsawo sosai, a dai'dai saitin kunnenta ya kawo ɗan bakinsa, kasa kamar mai raɗa ya ce. "Zuciyata kika sace mun, kuma sai kin bani ita kafin ki tafi daga nan". Abin ku da ita ba soyayya ta taɓa yi ba, hasalima kunga ta tsani maza, so bata san komai ba, sai ta zaro idanu sosai, cike da ruɗani ta ce. "Zuciya kuma?". ......Kai ya jinjina mata alamar e. "Ta yaya ake satar zuciya kuma shi da yake cikin jikin mutum?". Ta yi maganar tana dawo da kallonta a kansa...... Ya fahimci tabbas wannan yarinyar bata san me soyayya ba, infact bama ta taɓa yin soyayya ba, ba ƙaramin daɗin hakan ya ji ba, dan dama kun sansu da bala'in kishi, sun fi dik wasu nau'i na larabawa kishi, so sai ya ji daɗin ya yi sa'a shi zai fara koya mata soyayya kuma ya aureta da wuri dan ma kada wani ya ganta ya ce yana so. Tab kuna ganin King zai aminta Dr Raj ya auri Zee kuwa? Kun dai san shi da kabilanci ko? Ya aka yi na Mahnoor da Jaish ma? Kuma kun ji ya ce dikka ƴaƴansa a cikin ƴaƴansu uncle Rahab zasu yi aure ko? To muje dai zuwa, zamu gani yadda za'ayi. "Kin taɓa yin soyayya?" Ya jefa mata tambayar cike da fargabar amsar da zata bashi, dan in ta taɓa yin soyayya Allah zuciyarsa zata yi ciwo sosai saboda kishi, dik da yana ganin alamar kamar bata taɓa yin soyayyar ba, amma dai gara ya tambaya ya ƙara tabbatarwa. Sai harbawa zuciyarsa take yi kamar wanda zai shiga court kuma yana sa ran hukuncin kisa za'a yanke mashi, dik saboda fargabar amsar da zata iya fitowa daga bakinta ne fa. Kai ta girgiza mashi kafin ta buɗi baki ta amsa da. "No, ban taɓa yi ba kuma bana sha'awar in yi".................... Wani irin daɗi da ya lulluɓe zuciyarsa ne har bai san time da ya ɗan matse hannunta da yake rike da shi a cikin nasa ba, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke a bayyane har sai da yasata kallansa a cikin ido. Kara yin ƙasa da murya sosai ya yi, cikin salo mai tafiya da imani sosai ya ce. "Har da ni baki sha'awar yin soyayya ko kuma ban da ni?". Ya kai karshen maganar tare da ɗaga mata gera guda saboda yaga tana kallansa............... Ya subhanallah, Zee bata san lokaci da ta kara waro idanunta haɗe da afkawa duniyar tinani ba. Hannunsa dake saman wall glass ɗin ya dawo da shi saman face ɗinta, a hankali ya ɗan goge mata hawayen da ya yi saura a face ɗinta, wato Dr Raj ba iya Dr bane kawai, shahararren ɗan love ne, kawai dama bai samu wadda ta sace zuciyarsa bane yasa yake wani jiji da kai, yanzu ba ga shi ya yi la'asar har da rarrashi ba. "Answer me mana, har da ni baki sha'awar yin soyayya?". Yadda ya yi mata maganar cikin wani irin salo sai da yasa Zee ta yi saurin girgiza mashi kai alamar a'a ban da shi, shi kam za'a iya yin soyayya da shi, bata san ta girgiza mashi kai ɗin ba, kawai salon maganarsa cikin natsuwa mai kwantar da hankali yasa ta bashi wannan amsa. Wani irin sanyi ya ji ta ratsa zuciyarsa. Matsawa kusa da kunnenta sosai ya yi, cikin raɗa yana rike da hannunta yana kuma kallan face ɗinta ya ce. "Kina so na?". Ya yi maganar yana kashe mata idanu ɗaya yana ɗan canza yanayin face ɗinsa, dan yana fargabar amsar da zata iya bashi, ba zai iya ɗaukar ta ce bata san shi ba, dik da yasan mawuyacin abu ne ta ki yin accepting ɗinsa, dan jinin Akka fa sai dai mata su kawo kansu garesu, basa tambayar soyayya su, a karon farko ya roki soyayya a hannun ƴar Nigeria, yo to mu Nigerians dama wasa ne? Haba dole ka roki soyayya malam Dr Raj, dan mu ɗin na daban ne malam. Shiru Zee ta yi ta kasa magana, da alamu kamar suman tsaye ta yi, wato a duniyar nan idan Allah ya kaddara ga mijinka fa shikenan babu wanda ya isa ya canza, idan ba wata kaddara ta Ubangiji ba fisabilillah ina Zee ina Dr Raj? Mutanen da ƙasa ba ɗaya ba, babu abin da ya haɗa, babu dangin iya bare na baba, kaddara kawai ya kawo ƙasar, shi kansa Dr Raj kun san suna shafe shekaru 6 zuwa sama basu leƙo kingdom of power ba, amma da Allah yasa dole a kaddararsa akwai haɗuwa da Zee sai ga shi ya zo ta sanadiyyar ciwon guyson, wato komai yana da sanadi, jama'a kawai ku bawa Allah zaɓi ku koma gefe ku haɗe hannayenku ku jira iko na Allah ku ga me zai faru. Shiru ta tsaya ta kasa bashi amsa, dan bata da abin faɗe, shi ma shiru ya yi yana jin zuciyarsa na harbawa da karfi yana jiran jin amsarta....... Kuna tinanin Zee zata amsa soyayarsa kuwa?. ••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Rangaɗa kwalliya Sarina ta yi cikin wannan ɗan iskar shiga tata na fidda tsiraici, ta yi kyau a idanun ƴan iska kam, amma a idanun masu koyi da Manzon raham tabbas a shaiɗaniya zasu kalleta. Ta ɗaura silky-c a kanta, ta zubo jelar gashinta har gadan baya. Sai kuma ta ɗauko alkyabba ta sanya a jikinta saman kayan, sai zuba kamshin wani shu'umin perfume da Mammie ta bata ta sanya take yi. Na ce ba, mu faɗawa Sarina cewa kafin ta yi irin wannan shigar domin nunawa Smart surar jikinta Heleena ta rigata yi ne ko dai mu bari shi da kansa ya bata gurbi irin wanda ya bawa Heleena? Kai tsaye family part ta nufo, tana taku tamkar wata hawainiya, kamar bata san taka ƙasa, ga wani shegen takalma high heel da take sanyawa. Kai tsaye part ɗin momma ta nufa cike da yauki da yanga haɗe da duniyanci. A tinaninta Smart yana part na momma, sai da ta shiga taga akasin haka, momma kawai ta samu zaune a saman bed ta buga uban tagumi tana tinanin yadda zasu karkare da King yadda ya ɗauki zafa haka, tana san zuwa part ɗinsa amma tana shakkar abin da zata tarar a can. A fakaice Sarina ta bita da kallan banza da harara a cikin zuciyarta tana saƙa ta tsani mommar nan kamar me. (Amma kuma suna san jinin momma kamar su mutu, ni narasa wannan bala'i wlh.) Cike da makirci ta ce. "Momma barka da dare". Da yake yau momma bata a cikin mood mai daɗi sai ta amsa mata da yauwa kawai. Zama ta yi a saman sofa, tana san tambayar ina Smart yake tana kuma fargabar amsar da momma zata iya bata. "Sarina kira mun Omar ko Omaid su zo su kaiwa yayanku cappuccino kada dare ta yi". Cewar momma. A hanzarce ta ce. "Wani yayan namu?". A takaice momma ta amsa da. "Babban yayanku". ...... Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, a ƙagare da san ganinsa ta ce. "Momma kawo kawai in kai mashi". Shiru momma ta ɗan yi kafin ta ce. "Anya kuwa Sarina! Yayanku fa sha'aninsa yana da wuya ne, kada in turaki ya ɓata maki rai, da kin bari su Omar da suka saba da shi sun kai mashi". ........ A hanzarce ta fara girgiza kai kafin ta ce. "Momma babu abin da zai faru In Sha Allah, zan kai mashi, ai yayanmu ne". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye tana wani rawar kafa. Momma kamar dai ba zata bata ba, amma sai ta ce kila tun da Smart bako ne a nan bari ta bata kila ba zai yi mata komai ba. Dan haka sai ta nuna mata in da cappuccinon yake ta kuma faɗa mata cewa Smart ɗin yana part na Jaish. A hanzarce ta wuce ta ɗauka tana sauke ajiyar zuciya, faɗi take a ranta buƙatarta ya biya, domin kuwa tana haɗa idanu da shi idan ya shaki kamshin perfume ɗin nan nata shikenan ya gama yawo, ya dawo tafin hannunta, turare ne mai karfin sihiri da in ya shaka sai yadda ta yi da shi kuma, shiyasa kuma ga take neman haɗuwa da shi a taren nan ta kowani hali, to ga dama ta samu. Ɗaukar cappuccinon ta yi ta nufi waje da sauri, sai wani rawan kafa take yi, ita a dole zata je wajen saurayi. Me kuke tinanin zai faru? Shin zata samu nasara a kan da kuwa?. Mu je dai zuwa. •••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 A ɓangaren mama kuwa, sun jima a parlourn kafin ta iya miƙewa jiki ba kwari ta nufi part ɗinta, uncle Taheer da karyayyar hannunsa shi ma ya miƙe ya nufi nasa bedroom ɗin, jinyar kansa fa yake yi, amma dan balai'n san jin gulma ya fito dan ya ji family dik sun haɗu a parlourn. Miƙewa ita ma Aneesa ta yi ta nufi bedroom ɗinta dan ta je ta kwanta, ita ko ajikinta babu abin da ya dameta. •••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 A hankali hankali Mahnoor ta fara jin cikinta yana murɗa mata, ɗan dafe shi ta yi tana tinani da fargabar kada ya fito toilet ya sameta kwance mashi a bed. Da kaɗan da kaɗan ciwon cikim nata ya ɗan fara karuwa. Hakan yasa ta ɗan juya domin ta kwanta ta ɗayan jefen nata, a tinaninta hakan zai sa ciwon cikin ya ragu. Juyowa da zata yi suka yi 4 eyes da shi yana tsaye wajen mirror, tin ɗazun ya fito daga toilet ɗin bata lura ba, ya shafe jikinsa da mayika ya shirya cikin sleeping dress masu kyau da tsada, sai kuma me? Ya ƙasa manta surarta a ransa, ya zo zai haye bed ɗinsa ne ya sake yin kyakkyawan gani cikin wannan shiga nata, ga shi tana kwance a miƙe, dama ta ɗazun bata gama sakinsa ba, ga idanunsa nan jajir kamar wuta, so abar bata sake shi ba, sai ta kara ninkuwa sosai. Shiaysa ya tsaya a wajen mirror ya kasa ƙarisawa wajen bed ɗin, dama da nufin ya zo ya korata ya fito daga dressing room ɗinsa, ganinta a irin wannan shiga yasa ya kasa ƙarisawa wajen, ya yi tsaye yana karewa jikinta kallo. A zabure ta miƙe zaune tana kallansa. Yadda ta miƙe sai ji ya yi zuciyarsa ta motsa, ya ji kamar ya ce mata ta koma ta kwanta, amma ya ƙasa faɗe. Zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin ta yi tana kallansa ta kasa kawar da kallanta a kansa, dik kunyarsa da take ji ta kasa cire kallanta a kansa saboda kewarsa da ya addabama zuciyarta. Tana ƙoƙarin miƙewa cikinta ya yi wani irin murɗawa da karfi wanda sai da yasa ta yi saurin dafe shi ta saki yar kara haɗe da komawa ta zauna ta fara miƙewa. Ai yana tsaye a lokacin da ta yi wannan yar kara ta dafe cikin nata tamkar jikinsa haka ya ji, har ɗan zabura ya yi. Idanunta ne suka cicciko da kwallah tana cigaba da kallansa, shi ma ya ƙasa zare kallansa daga kanta. Ƙasa da murya ta yi, da yake tana jin ciwo sai muryarta ya yi kamar shagwaɓa take yi mashi. "Yah Jaish cikina ciwo yake yi mun". Tana gama faɗa hawayen da suka cika mata idanu suka zubo. Yanzu ita ma ta fara bin bakinsu Chuchu tana ce mashi yaya ba Hamma ba. Shiru bai matsa daga in da yake tsaye ba sai da ya ga da gaske take kukan, sannan ne ya tako cikin natsuwa ya matso kusa da bed ɗin. Kamar zai taɓata sai kuma ya fasa, muryarsa tana ɗan sarkewa ya ce. "Tashi muje hospital sai a dubaki tin dare bai yi ba". Yana kai karshen maganar ya nufi keys set ɗinsa, key motar da yake da ra'ayin hawa ya ɗauka ya nufi kofar fita. Yana gab da fita ya tsinkayo muryarta cikin kuka ta ce. "Yah Jaish ba zan iya tashi ba". Cak ya tsaya, dan yadda ya ji muryarta ta kara tada wani hatsaniya a cikin zuciyarsa. A hankali ya juyo, gabaɗaya ya rasa meyake damunsa, ya gagara yi mata faɗa ko tsawa, sai wani tausayinta da ya ji ya kama shi. A hankali ya tako ya dawo in da take zaune. Wani zuciya yana ce mashi ya rabu da ita ta taka da kafafunta, wani kuma yana ce mashi ya ɗauketa, daurewa ya yi ya duƙa ya ɗauketa cak, shi kaɗai yasan me yake ji, haka ya nufi waje da ita, bai damu da kayan da yake jikinta ba, dan yasan ba zai haɗu da kowa ba, dare ne kuma ya san yanayin tsarin gidan nasu. Haka kuwa bai haɗu da kowa ba har suka isa parking space. Gidan gaba na motarsa ya sanyata, mazaunin driver ya shiga, a hankali ya kunna motar yana ɗan satar kallanta ya fito daga parkin space ɗin suka nufi katafaren gate ɗinsu. Tin kafin ya iso warriors dake tsaron wajen sun wangale mashi gate ɗin. Yana zuwa kawai ya danna hancin motar waje. A hankali yake tukin motar yana ɗan satar kallonta ta gefen ido, shi kansa yasan fa haɗuwa iya haɗuwa ta yi, ta tafi da imaninsa ba kaɗan ba, ji yake kamar ya kai hannun ya taɓa wanan lallausan haɗaɗɗen skin ɗin nata, ga yanayin rigar jikinta mai cuf ne, gabaɗaya tudun tula tulanta a waje, ga su kamar an hura balo balo ɓul ɓul, sai kallesu yake yi ta wutsiyar ido. Ga shi yadda ta turo mashi ɗan bakin nan nata tana hawaye sai yake ji kamar ya kama shi ya sha, sai Allah kaɗai yasan me yake ji a yanzu, hakan ma yasa yake driving a hankali gudun kada a samu matsala. Dan fa ta rikita shi. Ita kuwa kukan shagwaɓa take yi mashi a yanzu kamar yadda Chuchu ta koya mata, saboda tun da ya ɗaukota daga cikin ɗaki ta ji cikin nata ya dai'na ciwo, amma bata dai'na kukan ba ta cigaba da yi, in baku manta ba ta riga ta saba da soyayyarsa a lokacin da bai san wanenen shi ba, so tasan salonsa daban yake da kowa. Wannan dalilin ma yasa take wannan aikin turo mashi ɗan bakin nata alamar shagwaɓar dan tasan a kauye yana san hakan sosai. Dukkansu cikin zuƙatansu tunanin juna kawai suke yi, sun kuma rasa mafita wa kansu. Shiru yake cigaba da driving yana tunanin yadda zai yi ya ganta a jikinsa yanzu, notikan ƙwaƙwalwarsa sun gama kwancewa a kanta, ai yama yi ƙoƙari da ya iya dannewa har zuwa yanzu bai aikata komai ba, da alama ya faɗa tarkon kauna a karo na biyu. Kwatsam ba zato ba tsammani sai jinta ya yi ta kwanto jikinsa saman lion chest ɗinsa, ta ɗaura hannunta ɗaya a saman plat tummynsa, ɗayan hannun nata kuma yana a bayansa. Ai bai san time da ya ja wata mahaukaciyar burki har sai da ta tsorata ta kara ƙanƙame shi ba sosai haɗe da saka mashi kuka mai ɗan sauti ba. Wani irin yanayi ya ji a jikinsa, bai taɓa expecting ɗin haka ba, ga shi ta ɗaura hannunta dai'dai saitin mararsa dake ta faman murɗa mashi yana yi mashi ciwo tin ɗazun da ya ɗaura idanunsa a kanta, dik sai ya ji shi a wata duniya ta daban. Ko da ya taka burkin motar ya ƙasa iya motsawa saboda tsumin gauranta na tsawon shekaru ta kara motsa. Ita kuwa saboda tsabar iya shege sai kara shigewa jikinsa ta yi tare da samun damar fashe mashi da kukan shagwaɓa mai karfi tana wani shafa tummyn nasa a hankali hankali. Kasa jurar hakan ya yi ga kukan da take yi mashi yana ratsa zuciyarsa, a hankali ya sauke wani daddaɗa kuma sanyayyar ajiyar zuciya mai cike da sirrika da fassarori kala kala. A hankali ya kai hannunsa ya kama hannunta dake saman tummynsa dan ba ƙaramin rikita shi take yi ba taɓa shi da take yi. Wani sabon kara rikicewa ya yi lokacin da lallausan fatar hannunta ya sadu da tasa, ga wani sihirtatcen kamshi da take yi na gyaran mama Haulat da ta sha ga perfume da Chuchu ta bata, nan take ya nemi natsuwarsa ya rasa. Ai bai san time da ya ɗaura ɗayan hannunsa a saman bayanta ba. Ita kuwa ta zage sai kukan shagwaɓa take zuba mashi mai ratsa kashi da ɓargo. "Menene yake damunki da kike kuka haka?" Ya faɗa a sanyaye da kyar kuma, yadda ya yi maganar sai ya baku mamaki, sakamakon ya shiga yanayi. Kara marairace kukan nata ta yi ta kara shagwaɓa shi irin shagwaɓar da ko kaki ko kaso dole ya huda fata da kashi ya shiga cikin zuciya ya yi kane kane, bare shi da dama tun farko zuciyarsa ta mutu a kan wannan shagwaɓa tata. "Yah Jaish ba kai ne ka tsayar da motar da karfi kasa cikin nawa ya kara yi mun ciwo ba, kuma yanzu ka daina kulani ba kamar a Jimeta ba". Ta yi maganar tana kara narke mashi. Ai tuni malam Jaish ya mance da ita ƴar kauyece mai ƙaranci wayewa da ilimi haɗe da ƙarancin shekaru ne, bai san lokacin da ya rungumo kayassa ya fara rarrashi ba, ko ita kanta rarrashin bai san daga ina ta faɗo bakinsa ba, shi dai kawai ya tallaɓota da hannunsa bibbiyu, kasa sosai ya yi da murya kafin ya fara rarrashin nata cikin salo mai jan hankali. "Am so sorry, daga yau ba zan sake shareki in dai'na kulaki ba kin ji? Amin afuwa a dai'na kukan nan haka yana birkita mun ƙwaƙwalwata sosai". Wlh bai san kalaman da suke fita daga bakinsa ba, dan yana irin gaɓar nan ne da komai aka ce maka e zaka amsa da shi. Da alama duniyar chaskale da ya faɗa ne yasa har da faɗin sorry bai san ya furta ba. (Yaron Mommarsa ya shiga koma🥱) Kara narke mashi ta yi tana canza style ɗin kukan nata ta ƙara yadda zai kara ratsa zuciyarsa yasa dole ya yi mata abin da bai san ya yi ba. Har da wani irin shessheƙa take yi mai kara jan hankalinsa tana kuma ɗan murza mashi kanta a saman lion chest ɗinsa. "Please ya isa haka ko? Ko dai so kike ki jefani cikin wani yanayi ne?". Kamar wanda yake a cikin maye ya yi maganar. Ni kam na ce yanayi kuma na nawa?. Kai ta girgiza mashi alamar a'a tana kara turo mashi ɗan bakin nata. Hannu yasa cak ya dawo da ita gabaɗayanta saman laps ɗinsa ba tare da yasan ya yi hakan ba, ɗan matseta a jikinsa ya yi yana sauke sanyayyar ajiyar zuciya. Damar rungumesa da kyau ta samu tare da kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa ta wajen wuyarsa. Wani daɗin laushin skin ɗinta ne ya ɗebesa har ya fara shafa lallausan kumatunta ba tare da ya sani ba. Ita kuma da abin nema ya samu, sai ta saki jiki da shi sosai tana ta zuba mashi shagwaɓa sosai da sosai tana kara rikita shi. Sosai heronsa ta miƙe zat tamkar zata fasa wandonsa, hakan yasa ya haɗe ƙafafunsa waje guda sosai, ya matse heron nasa a tunaninsa zai iya sarrafa kayansa, da farko dai ya samu nasarar dannewa, amma tun da ya dawo da ita jikinsa ai ina sai abin ya fi karfinsa. Sai ma da ta sanya hannunta a saman arab hairnsa tana yi mashi abin da take yi mashi a kauye, ai nan take ya fara fitar da wani irin numfashi yana wani kara ƙanƙameta, idan heron tasa ta matsa mashi sai shi ma ya matseta sosai a jikinsa. Cikin dabara ya sanya hannu ya kwantar da kujerar motar da ita da shi dik suka kwanta tana saman lion chest ɗinsa, ya manta da a kan hanya suke ya kuma mance da ciwon ciki take yi suka fito zuwa hospital na kingdom ɗin, dik ya mance waɗan nan. Da zafi zafi ya fara shafe mata jiki yana jujjuyata, daga ƙarshe ma datse idanunsa ya yi, sai dai a lokacin da hannunsa suka sauka saman tula tulanta dan dole yasa ya buɗe idanu domin yaga me ya taɓa mai bala'in laushi da daɗi hakan nan. Ita ma a lokacin ta yi maza ta dawo da kallonta a kansa hakan yasa suka yi four eyes da juna, wani irin kunya ce ta dira mata, shi kuma wani irin daɗi ne ya mamaye mashi zuciya. A hankali ya ɗan juya da ita, ya zamana ita ma tana kwance saman kujerar ne. A hankali ya zame mata hannun rigar sexy night dress ɗinta. Ai bai san lokacin da ya waro idanunsa da suke jajir kamar wuta waje ba. Zaro su ya yi yana bin sexy bodynta da kallo. Yanzu ma dai muraran ya gansu a kurkusa da shi, wani irin sabon tsumi ne ya tashi mashi, ganinsu a fili haka ya sake tada tsumin gauranta, sosai numfashinsa ta fara fita da sauri sauri har sai da ta ɗan tsorata, ta wani datse idanu tana jiran ta ji me zai yi mata, ta natsu tsit. Kamar daga sama ta ji saukar hannunsa a samansu wanda sai da ta ji tsikar jikinta ya tashi, amma ta daure ta cigaba da datse idanu bata buɗe ba. Yau babu kunya a tattare da shi, dama Jawad ya ce kunyar rashin kunya ne, ashe kuwa haka ne, yau dai da ya samu yar matarsa yana yi mata son ransa to fa kunya ta gudu. Siraran hannun night dress ɗin ya fara zame mata su ya rabata da rigar gabaɗaya, sannan ya samu damar ganin kayansa a fili da kyau. Like wow, sun sha gyara wajen mama Haulat abin ba'a magana, dik sai ya kara rikicewa, hannunsa dikka biyu ya kai ya fara matsesu kamar wani ya ce zai kwace mashi su. Sai sauke ajiyar zuciya yake aikin yi kamar wanda ya yi wani gagarumin aikin ya gaji. Yau an sami abin da akeso Kukan shagwaɓa ta saka mashi a hankali hankali, hakan ba ƙaramin kara birkita mashi lissafi ƙwaƙwalwarsa ya yi ba, sai ya kara samun confidence na cigaba da matse mata su. Sai da ya ji kukan nata ya ɗan yawaita ne sai ya ɗan kwanto kanta kaɗan, dai'dai sai tin kunnenta ya ce. "Kukan me kike yi kuma?". Da kyar ya yi maganar. Turo ɗan bakin ta yi. "Ni Yah Jaish zafi suke mun, kana kara sanya ciwon cikina ya dawo sabo fa". Ni kam na ce ciwon ciki ko rashin kunya?. Wani irin abu ya ji tamkar an caka mashi allura, yadda ta yi maganar tamkar kara ingiza zuciyarsa ta yi, can kasan maƙoshinsa ya furta. "Am so sorry, amma dai yau ki barni na ji ɗumin kayana, ba kema haka kike so ba?". A miliyan ta zaro idanunta waje. "Ni kuma Yah Jaish? Yaushe nace maka ina son hakan?". Tana magana tana zaro idanu da mamaki a saman face ɗinta. Matso da ɗan bakinsa saitin kunnenta ya yi. "Ai kina jin daɗi ne idan ina taɓasu shiyasa nace kema kina so, kuma ba ke kika faɗo jikina ba?". Yunƙura ta yi zata miƙe tana faɗin. "Ni na faɗo jikinka ne kawai dan ka rarrasheni na ciwon da cikina yake mun, amma bari na koma seat ɗina in zauna, in cigaba da kukana idan mun koma gida mommata ko Yah Omar su rarrasheni tun da dama su suka saba rarrashina idan ina kuka, kai dama babu ruwanka dani kace..............." Bata kai karshen maganar ba ta yanke tsit sakamakon jawota da ya yi ta faɗo saman lion chest ɗinsa ya kuma haɗe bakinsu waje guda, zazzafar kiss ya shiga bata babu kama hannun yaro. Ita ma mayar mashi da martani ta fara yi har da zura tongue ɗinta a cikin ɗan bakinsa tana kara tayarwa da baban Allah tsumin samartakansa. (Bari in yi sauri in je in faɗawa Queen Zarina ga shi nan Mahnoor zata kwacewa saurayinta samartakansa ta zo ta rabasu, ni ba zan ci amana ba, dole in sanar da Queen dan akwai amana🥱) Cigaba da bata kiss masu zafa ya rinƙa yi tare da mayar da hannayensa saman tula tulan nata yana aikin matsesu. Dik suka rikita juna a cikin mota, ita ma kun san ta jima tana kewar kiss ɗinsa. Cikin dabara ya zame ɗan bakinsa daga cikin tata. A hankali ya shammaceta ya mayar da shi saman nipples ɗinta, bata yi zaton hakan ba sai ta ji ɗan zafi ya ziyarceta. Ai bata san lokacin da ta waro idanunta waje ba, a saman kansa ta ɗaura hannayenta dikka biyu ta fara aikin zuba mashi kukan shagwaɓa dake kara rikirkita shi tana kara ingiza zuciyarsa yana yin abu da zafa zafa. Wannan ƴar shagwaɓa da take zuba mashi ba ƙaramin kara tura zuciyarsa gaba wajen ingiza mashi ya kai babbar level yake yi ba. A miliyan ta kwace kanta daga garesa tare da zabura zata bar jikinsa a lokacin da ta ji saukar hannunsa a saman mararta. Riƙota ya yi tare da dawo da ita jikinsa yana girgiza mata kai alamar kada ta tashi bai iya furta word ba, jikinsa dik a mace. Ba dan ta so ba ta koma ta kwanta, sai dan bata son ta yi jayayya da shi. Matseta ya yi a jikinsa yana wani irin fitar da numfashi kamar wanda yake............ . Shiru ta lafe har na tsawon awa guda bai iya motsawa ba, ƙoƙarin danne samartakansa kawai yake yi dan kada ya yi aika aika a cikin mota, da ma dai a gida ne sai ya saki ji. Sai da suka yi awa ɗaya da rabi a wajen kafin ya ɗan iya motsawa ya tada kujeran motar, ya kara rungumota da kyau a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, ya fara ƙoƙarin kunna motar dan su tafi. "Yah Jaish bari na koma saman seat ɗina in zauna sai mu tafi". Ta faɗi hakan ba tare da maganar ta fito daga cikin zuciyarta ba, dan ita ma bata son barin jikin nasa, ta dai faɗa ne kawai. Kai ya girgiza mata alamar a'a kawai ba tare da ya furta word ba, sai ma kara matseta da ya yi a jikinsa yana ɗan shasshafa bayanta da hannu ɗaya, sannan ya tashi motar a kan su tafi............ ••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 DR RAJ. A ƙagare yake da san jin amsar da Zee zata bashi , dan yana....... P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ DR RAJ. A ƙagare yake da san jin amsar da Zee zata bashi, dan yana sanin me zai yi next. Ita kuwa sai da ta tsaya shiru a kallah na tsawon 5 mins tana kallansa kafin ta girgiza mashi kai alamar a'a bata san shi, sannan ta ɗan kwace hannunta da yake rike da shi, rage tsawonta ta yi ta duka ta raɓa gefensa ta wuce. Shock rooted him to the spot, his mind struggling to process the reality before him. Was it truly Akka’s blood that had dared to confess love, only to be rejected? The thought felt strange, almost unreal. For almost thirty minutes, he remained standing there, lost in deep thought. Deep down, he knew Zee had feelings for him, he had seen it in her eyes. But the way she responded had unsettled him. After a while, he convinced himself that she was only playing hard to get and that he could win her over. With a composed demeanor, he walked back to the sofa and sank into it, replaying the intense moment when their eyes had locked. Pulling his phone from his pocket, he dialed Yah Ramish’s number, eager to know whether he had finally given Leesharh to the blood or he was still stalling, just as he always did. wlh Ramish ɗan duniya ne, idan ba kana da hakuri ba zaka iya rataye kanka saboda bakincikinsa, mutum kamar dutse, in ya yi magana ba canzawa, ko da yake ba za'ayi mamaki a tin da kanin Smart ne, duk jirgi ɗaya ya kwasosu ya kawosu dama, ƴan rainin wayo da kawunansu kamar na Akka ...........🥱 Sau biyu yana kiransa bai ɗaga kiran ba sai a karo na uku, murya can ƙasa ƙasa ya ce Hello. Dr ya fahimci barci ma yake yi, amma sai ya daure wajen cewa. "Yah Ramish good evening". A mainakon ya amsa gaisuwar tasa sai ya ce. "Is there any special reason why you're calling me at this time?"........ Shiru Dr ya ɗan yi, kamar zai katse kiran ya kyalesa ya cigaba da barcinsa sai kuma ya daure ya ce. "Yah Ramish dama batun blood ɗin nan ne, please mana ka bata ka ji our hero?.........". Bai gama rufe baki a maganar ba ɗiff Ramish ya katse kiran, ajiyar zuciya ya sauke yana mamakin halin yayan nasa, mutun ne babu ɗigon tausayi a ransa. Ajiye wayar a gefensa ya yi ya cigaba da tinanin Zee abinsa. •••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥 Sanye take da sleeping dress riga da wando masu zubin pajamas, tana tafiya tana taunar chewing gum kamar wata wadda abin suka motsa. Daga bedroom na mama Haulat ta fito, tana tafiya tana wani kwarkwasa da rangwaɗa, ji take yi ta fi kowa tun da ta yi kwalliya, yanzu mama Haulat ta koya mata yanga, kamar ba Mahreen tamu ta bappa ba, har yauki take yi, kun santa da shegen san kwalliya tin a kauye, to da ta zo yanzu kullun cikin kwalliya mai kyau da ɗaukar hankali take, ta zama big girl mai class yar gayu. Sai dai har yau har gobe tana kukan sauyawar da Jaish ya yi, ya tashi daga hammanta izuwa Jaish, kuma kullun idan ta gansa bata gajiya da yi mashi magana, ko ya amsa ko karya amsa sai ta yi mashi. Kai tsaye part na mama ta nufa dan ta je wajen Zee, yanzu sun fara sabo da su Zee, kuma Zee tana koya mata karatu bata da matsala, rike take da takardanta ma a yanzu, ta yi jagwalgwalan rubutunta kamar tafiyar tsutsa shi ne zata kaiwa Zee ta duba mata. Har zata shiga part ɗin mama sai ta kalli kofar part dake fuskantar nasu mama ɗin a buɗe. Mamaki ne ya ɗan kamana ganin cewa bata taɓa kallan kofar a buɗe ba, da sauri ta dakata daga shiga side ɗin mama, babu ko tsoro a ranta, bata san bedrooms ɗin su waye a wajen ba kawai ta nufa abinta, tana tafiya babu ɗar ɗar bare waige waige. Kai tsaye ta shige ciki. Babu ko sallama ta afaka masu cikin parlournsu. Suna zuane a saman sofa suna aikin latsan waya, Obaid ya tada kai da cinyar Omaid yana video call da Sharifat, shi kuma Omaid yana waya da ɗaya daga cikin class mate ɗinsu, su da basa murmushi saboda muguntar da ta yi masu yawa sai ga Omaid yana ɗan murmusawa alamar waya ta yi daɗi kenan. Shirye suke cikin sleeping dress ɗinsu iri ɗaya, kayan ya yi matikar yi masu kyau, Omaid ya tara gashinsa ta yi tsawo, shi kuma Obaid ya yanke arab hairn nasa, ya yi irin askin guyson, kuma ya yi kyau, ga shi dikkansu sun yi gyaran fuska, ƴaƴan momma fa ɗaukar wanka a jininsu yake, wlh dik kalar wankan da suka ɗauka kyau suke yi wa wankan. Ganin mutum a tsakiyar parlon nasu yasa Obaid sarkin zafa ya miƙe zaune yana binta da kallo tare da katse call da yake yi, shi kuma Omaid kallan wutsiyar ido ya bita da shi suna mamakin zubin halittarta, a cewarsu ta yi siririya sosai. "Who are you?". Omaid ya faɗa ba tare da ya kalli in da take tsaye ba, kallan gefe ya bita da shi. To ita dai ba jin turanci take yi ba, dan haka bata san me suka faɗa ba, da ɗan gara ma larabci ne yanzu ta iya dik da ba wani mai zurfi sosai ba, amma zata iya maganar minti uku cikakke da kai da larabci, abin da yasa kuma ta yi saurin iyawa saboda zamanta da su mama Haulat, babu wani yare da zasu iya magana da juna dole sai larabci, hakan yasa ta yi saurin iyawa. So bata san me suka faɗa ba, sai bata amsa su ba, ta tsaya shiru tana binsu da kallo, taga zubin halittar Jaish a tattare da su, kun san tun da suka zo basu haɗu da ita ba. Obaid sarkin zafa ne ya daka mata tsawa cikin harshen larabci. "Zaki faɗa mana wacecce ke da abin da ya kawoki part ɗinmu ne ko sai na tashi na kakkaryaki?". Yana magana yana kara ɗaure fuska. Sarai ta ji wannan magana da ya faɗa, kun san bata barin ko ta kwana, jin zai daketa da ya faɗa yasa ta sanya hannu ta rike waist ɗinta da kyau, kallan up and down ta bisu da shi kafin cikin tsiwa ta ce. "Tun da kai ka halicceni ba sai ka dakeni in gani ba! Kana tinanin ma barinka zan yi ka taɓa ni ne? Wlh baka isa ba, ramawa zan yi". Tana jajjagen masifar tata kuma tana kallon kofar fita, ta gama yin ready kis take jira ta yanka waje a miliyan. Kun san Obaid dama shi baya da hakuri ko kaɗan, aikuwa ransa ya gama ɓaci, a gabaɗaya kingdom of power babu wanda yake yi masu nasiha cikin ruwan sanyi ma ya zauna lafiya sai Jaish bayan Momma, amma saboda tsabar aljanun kanta na guguwar bishiyar kuka ce zata tsaya a tsakiyar parlournsu, su tambayi meya kawota har ta ce zata faɗa masu magana, wlh yau sai dai wata ba ita ba koma ƴar uban wanene ne. Sai huci yake yi ya miƙe tsaye, Omaid ne ya yi saurin rike hannunsa yana faɗin. "Kai mezaka yi mata?". A fusace ya amsa da. "Mekake tinanin zan yi mata? Ni ka sakeni dan Allah hai". "Obaid kana tinanin in ka taɓa wannan tsinken tsintsiyar zata rayu ne? Ka rabu da ita kada ka je ka yi kisan kai, ka ganta fa kamar sandar mopa...........". Ana ƙoƙarin bashi hakuri a taushesa amma yarinyar nan tun Omaid bai gama rufa baki ba ta cafke zancen da cewa. "Tun da dik cikinku babu ɗan iskan da ya yi mun halitta sai ku rufe babin batun halittata, da kake ce mun sanda kai ya kake? Da shegen idanunka manya manya kamar na shaiɗan"......... Kai jama'a ko a ina Mahreen ta taɓa ganin shaiɗan har tasan idanunsa manya ne? Omaid kai ma ka shiga layin littafin Mahreen. Ai sake Obaid Omaid ya yi, wato ya je ya lallasata kenan tin da ita bata san mutunci ba. Tana tsaye ya nufota cikin zafa, sai da ta bari ya kusanta sai ta yanka waje a miliyan. Ai da gudu ya rufa mata baya, shi kuma Omaid ya cigaba da yin wayarsa abinsa. Kai tsaye part ɗin momma ta nufa da gudun gaske. Tana sanyo kai suka ci karo da guyson da ya fito daga bedroom ɗin momma zai koma nasa dare ta yi. Karo suna yi a in da ya ɗan yi baya yana dafe goshinsa da ta bugesa. Ita kuwa da yake tasan abin da ta tsokano sai bata tsaya ba, a guje ta raɓa gefensa zata wuce, da sauri ya riko hannunta, cikin natsuwa ya ce. "Lafiya kike gudu haka a cikin daren nan?". Ƙoƙarin kwace hannunta ta yi dan ta ruga da gudun ta karisa ciki. Shi kuma bai gama rufe baki ba sai ga Obaid ya iso wajen da gudu. Da karfi ya sanya hannu zai fisgota daga rikon da guyson ya yi mata yana wani huci. A hanzarce guyson ya dakatar da shi ta hanyar cewa. "Ku dakata mana, lafiya Obaid ka biyota? Me ta yi maka?". Har lokacin ƙoƙarin kwace kanta take yi ta gudu. Ɗaure fuska sosai Obaid ya yi, cikin ɓacin rai ya zayyana mashi dik abin da ya faru, daga karshe ya ce wlh idan bai karyata pieces ba ba zai iya yin barci ba yau. Dik da guyson yana rike da ita yana ƙoƙarin kashe wutar da ta kunna bakinta bai rufu ba, dan kuwa tana jin Obaid ya ce sai ya karyata cikin tsiwa ta ce. "Ka karyani tun da ni itace ce, da wani shegen ido kamar na shaiɗan na faɗa na kara faɗa". Me guyson zai yi idan ba murmushi ba, shi ya rasa wace iriyar yarinyace, ji fa, ana ƙoƙarin kashe wuta tana kara kunna wani. A fusace Obaid ya matsota yana faɗin. "Yah Omar dan Allah ka kyaleni in karya yarinyar nan". "Dakata dakata Obaid, wai baka ga mace bace? Me zaka daka a wajen? Su mata ai babu gurbin duka a jikinsu ko?...........". Guyson bai gama rufe baki ba ta capki zancen da cewa. "Kai kana tinanin kana da karfin dukana ne da kake wani tadada jijiyoyin wuya? Wlh ni na ci dubu sai ceto, kuma kai ma ka sakeni tun da baka da wani karfi mai kukan ciwo kawai". A karshen maganar tata da guyson take yi, wai bashi da karfin tare mata faɗa tin da yana kukan ciwo, larabcin nata ne a karkace. Sarai Guyson ya fahimci kalamanta, ya fahimci zaginsa ta yi, amma da yake shi ɗin damone sarkin hakuri, sai ya yi kamar bai ji ba, yasan idan ya barta da Obaid wlh ko momma ba iya kashe wannan wuta zata yi ba, dan ko an bashi hakuri ya tafi sai ya sakar mata kunama ko kwari, basa yafiya ai, dan haka solution kawai ya kashe wutar a nan mai gabaɗaya. Capka Obaid ya kai mata da karfi zai shaki wuyarta Guyson ya yi saurin janyeta da karfi sai ta tafi ta faɗa saman kirjinsa, a hanzarce ya ce. "Obaid ka kyaleta mu yi magana mana". "Ni Yah Omar ka barni in take bakin yarinyar nan sai hakwaranta sun cire gabaɗaya". "Aa Obaid, ba za'ayi haka ba, ka bari za ta baka hakuri..........". Bai kamala kai karshen maganar ba ya dakata sakamakon turesa da karfi da ta yi har ya yi baya kamar zai faɗi. Cikin tsiwa ta ce. "Kai ɗan iska ne ashe? Allah ya isa da ka rungume ni". Tana magana tana galla mashi harara. A zabure Obaid ya nufeta yana dunkule hannunsa ɗaya zai kai mata duka a baki, damo sarkin hakuri bai gaji ba ya sake shiga tsakaninsu, bai damu da kalamanta ba, dan yasan yarinya ce, kuma girman kauye ce, fin haka ma zata aikata, kuma shi wlh burgesa take yi sosai, yana san mace mai confidence kamar Aunty MieMiensu, hakan yasa in dai ya shigo bai ganta a wajen momma ba sai ya tambayi ina take, tun da suka sha gyara suka fito a ƴan gayu take burgesa take kuma yi mashi kyau, shiyasa ya zage ya tsaya rabata faɗa da Obaid. Ran Obaid ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, dan haka sai ya sakar mata kunama guda biyu. Tana ganinsu ta zunduma ihu tare da daka sufa ta ƙanƙame guyson, kamar ba yanzu ta turesa tana kiransa da ɗan iska dan ya janyeta daga capkar Obaid ba, sai ga shi yanzu da kanta ta rungume shi tana ihu kamar zata tashi gidan da kuka, tana faɗin ya taimaka mata. A lokacin momma ta tafi wajen King ta je ta rarrashesa ko zai sauko, so bata nan. Part na su Jaish kuma ba kusa da na momma yake ba shiyasa basu ji ihunta ba. Da gudu Omaid ya iso wajen dan ya ji ihun, a tunaninsa lallasata Obaid yake yi yasa take kuka haka, so gudun kada ya kasheta yasa ya biyo bayansu da gudu. Riketa sosai guyson ya yi yana ƙoƙarin kare mata kunamar. Obaid yana tsaye yana kallansu, a tinaninsa kunamar ba zata yi wa guyson komai ba tun da Mahreen ya sakarwa, sai dai bai ankara ba sai gani ya yi ɗaya ya sakewa guyson harbi a kafa, dai'dai lokacin kuma Omaid ya iso ɗin. Azaban zafi yasa ya yi gaggawar saketa tare da tsugunnawa ƙasa yana ƙoƙarin riko kafar nasa. Ita kuwa yana saketa ta yanka a miliyan sai bedroom na momma. Kusan a tare Omaid and Obaid ɗin suka zube gwiwowinsu a gaban guyson ɗin tare da kai hannunsu a kan kafar nasa, hankalinsu ne ya yi mummunar tashi, ga shi Jaish and Omerish suna gida, yau sun shiga uku, sun san idan brothers ɗin nasu suka samu labarin kunama suka saki ya cutar da guyson yau ba mai karɓarsu, dama Jaish ya jima da hanasu sake kunamar nan, amma basu dai'na ba. Hankalinsu a tashe Obaid ya fara bawa guyson hakuri kamar zai yi kuka, Omaid kuma miƙewa ya yi tare da zura wayarsa a aljihun wandon sleeping dress ɗin jikinsa, sannan ya tattare karfinsa dikka ya ɗauki guyson cak, sai sorry suke ce mashi, kai tsaye cikin bedroom ɗin momma suka wuce da shi, tuni fuskarsa ta wanke da hawaye, rago a ciwo ba. Sosai yake kuka ga harbin kunama da balai'n zafi. Abin mamaki, ko da suka shigo bedroom ɗin momma basu ga Mahreen ba, kuma tabbas nan ta shigo, sai dai ɓuya ta yi a wani wajen dan kada Obaid ya biyota ya kamata, ita bata wani damu da kunamar ya harbi guyson ba, ita dai ba ta samu ta tsira ba ai shikenan kuma. Saman bed suka kwantar da guyson, a gaggauce Omaid ya fara ƙoƙarin cire mashi dafin kunamar, shi kuma Obaid ya ɗaura kan guyson ɗin a saman cinyarsa ya hau rarrashinsa yana goge mashi hawaye yana kara bashi hakuri da ya yafe mashi. Hankalinsu a tsananin tashe matuƙa. Wlh Mahreen sai shirin Allah, haka kawai ta ja bawan Allah ya samu tsarabar harbin kunama, har wajen ya kumbura sosai, ita kuma ta gudu abinta, wlh idan aka bar Mahreen da su Obaid su kaɗai sun isa su tada kingdom ɗin nan, zasu tada zazzafar yaki wlh. •••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 SARINA. Tana shiga parlon Jaish ta zare alkyabbar jikinta ta ajiye saman sofa, wai dan Smart ya kwaɗaitu da kyakkyawar surar jikinta...................... Yarinya, wai mu faɗa mata daga cikin masu jajayen kunnuwa masu yawo kusan tsirara ya fito ne ko dai mu yi shiru?. Zuciyarta na shakkar tinkarar bedroom ɗin, amma burin da take da shi a kansa ya fi wannan yawa, san nan Mammienta ta kara mata kwarin gwiwa tare da ce mata yana shakar wannan kamshin perfume ɗin shikenan ba zai iya yi mata musu ba, dan haka sai ta ji ta kara samun kwarin gwiwar tinkarar bedroom ɗin tun da babu abin da zai yi mata. A maimakon ta yi mashi sallama irin ta addinin musulunci ma sai ta wani kashe murya ta ce. Excuse me. Bata jira umarni ba ta turo kofar kawai ta shiga, tana ta faman yauki kamar hawainiya. Tana sanya kanta cikin ɗakin ta ja birki a bakin kofar ta tsaya, lokaci guda cup ɗin hannunta ya suɓuce ya faɗi kasa ya tarwatse, gabaɗaya cappuccinon ya malale a ƙasa. A miliyan ta zaro idanunta gabaɗaya waje, tamkar zasu faɗo ƙasa, cikin wani irin karuwin murya ta ce. "Wow, handsome, gorgeous and sexy guy with sexy body". Babbar magana!!!. Ba komai yasata yin wannan zabura da sambatun ba face Smart, kyakkyawa kuma kakkarfar surar jikinsa ya ruɗar da ita, ya fito daga wanka kenan yana sanye da bathrobe na Jaish a jikinsa, so bathrobe ɗin ta yi mashi gajere dan ya fi Jaish tsawo, bata gama rufe mashi cinyoyinsa ba, kun san mutumin da balai'n kyau, ga arab hairnsa a jike yana ɗigan ruwa, sajensa ta kara kwanciya luf, fuskarsa ta kara haske sosai, hakan yasa ya tashi kanta matuƙa. Anya a jikokin Akka a mata ba Sarina bace ta yi gadon abar kuwa? Jarabar yarinyar nan dayawa yake. Yana tsaye a gaban mirror yana shiryawa, Auta tana kwance a saman bed ɗinsa ta yi barci, shi kuma guyson ya tafi wajen momma tun ɗazun. A hankali ya ɗago idanunsa ta cikin mirror ya yi mata kallo guda ya kawar da kallonsa, cigaba da abin da yake yi ya yi tamkar bai san da halittarta a wajen ba. Ganin hakan yasa zuciyarta ta saƙa mata ai ta matsa kusa da shi ya samu damar shakar kamshin perfume ɗin nata kafin ta cigaba da santin kyan jikinsa, har tinani take yi a ranta gata kwance a saman lion chest ɗinsa tana wasa da ɓul ɓul ɗin breast ɗinsa saboda jarababbiya ce ta karshe yarinyar nan. Ta manta ma da batun ta ɓarnatar mashi da cappuccino, ta ɓata mashi ɗaki dan jaraba amma dik bata bi ta kai ba, cikin yanga ta fara taku tana jin faduwar gaba, amma haka ta daure ta isa gabansa. A kusa da shi ta tsaya na ƴan sakanni, sai da zuciyarta ta tabbatar mata da ya shaki kamshin perfume ɗin, sannan ta kara matsawa kusa da shi, Sarina bata tsoro kuma bata da hankali my people's, ko da yake Mammienta ce ta ce mata in dai ya shaki kamshin shikenan ta yi mashi dik abin da take so bashi da bakin yin magana sai abin da ta ce kawai. Dan haka tana ganin alamar ya shaka ta matsa dab da shi, yana ƙoƙarin zuba lotion a hannunsa dan ya shafa a jikinsa kawai sai ganin hannunta ya yi ta rike robar man, a tinaninta zai ɗago ya kalleta ne dan ta rike robar, sai taga akasin haka, bata san shi daban yake da kowa ba, ba komai yake ɓata idanunsa dan kalla ba. "Yah Omerish ni yakamata in zuba maka man ka shafa ai, idan kana so ma ni zan iya shafa maka ai, tin da kai nawa ne". Cikin salon kirsa da kisisina ta yi maganar tana wani make murya kamar akuya mai jego. Shiru bai yi kamar yasan da wata halitta a wajen ba, a ransa yana tinanin wai a cikin kannensa ne a ka samu fitsararriya mara kunya har haka? To me aikin Jaish kenan da bai gyarawa shegiya zama ba? Dama su Jaish haka kenan suka saki gidan kowa yana yin abin da ya ga dama basa cin kaniyarsu su gyara masu zama? Lallai da sake, dole ya sako tarbiya kuwa, dan ba zai ɗauki wannan iskanci ba, me banbancin kannen nasa da Heleena da ya ɗaurawa karar tsana kenan? Ai basu da wani banbanci, ya gyarawa Heleena da ba abin da suka haɗasu ma zama bare kannensa? Kunsan da farko ita ma Heleena ta so ta kawo mashi iskanci ta rinƙa taɓa jikinsa, watarana kawai ya ware rana ɗaya ya ci uban hegiya daga lokacin ta haɗa malaman jikinta ta natsu, shiyasa kuka ga tana tsoronsa kamar ta mutu, bugu ta ci a hannunsa. Yana tsaka da tinani unexpect ya ji saukar hannunta a saman hannunsa da yake rike da robar tana faɗin. "Yah Omerish bari ma kawai in murza maka man da kai'na". Tashin hankali, lallai Sarina ta wuce yadda ake tinani. Sake mata robar ya yi ya zame hannunsa, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, a tinaninta aikin Mammienta ya ci, ta samu kan Smart, sai ta wani ji bargo mai sanyi ya lulluɓe zuciyarta. Kawo robar man kusa da ita ta yi, tana ƙoƙarin zuba man a hannunta da nufin ta murza mashi a jikinsa tana wani fari da ido unexpect ta ji lokaci guda ta dai'na gane komai, sai ta ji kamar bata duniya, irin mutum ya ji komai ya tsaya mashi cak, shi kansa robar man dake hannunta sai ganinsa ta yi a can tsakiyar ɗakin, wani irin jiri mai karfi ne ya ɗebeta ta tafi ta zube ƙasa. Ba komai ya ja mata hakan na face wani irin mari da Smart ya ɗauketa da shi, tass kake ji, kunnuwanta gabaɗaya sun dai'na jin sautin komai. Bai bari ta dawo cikin hayyacinta ba yasa kafa ya yi ball da ita sai da ta tafi ta bugu da jikin bango. Daga nan ta ƙarisa dai'na gane komai gabaɗaya. Taku biyu ya yi ya isa in da take, hannunta da ta sanya a saman nasa lokaci da ta karɓi robar man ya take da kafarsa, ga shi in da ya taka ɗin ta wajen kashi ne, hakan yasa ta ji wani irin azaba ya ziyarceta. Da karfi ta kurma wani irin ihu mai sautin gaske, ɗauke kafarsa daga kan hannunta ya yi ya take bakinta da take yi mashi ihu da kafar tasa, take bakin nata ya fashe sai jini. Belt ya ɗauko daga dressing room na ɗakin, yadda kuka san wanda yake jibgar katan gardin namiji haka ya fara saukar mata belt ɗin nan a jiki. Ihu ta fara kurmawa mai sautin gaske, ko a jikinsa tamkar wanda aka saukarwa da wahayin duka haka ya yi mata lilis har sai da ya ji zuciyarsa ta ɗan samu natsuwa, sannan ya dakata da dukan nata, dik ya fashe mata jiki, ga shi ba kayan mutunci bane a jikinta bare su ɗan saukaka mata zafin belt ɗin, ga belt ɗin da kauri, ta zanu ba karya. Ga shi Jaish baya part ɗin bare su ji ihunta su kawo mata agaji, yana can hospital shi da Mahnoor, shiyasa Sarina ta daku babu wanda ya kawo kata agaji. Ihunta ya tashi Auta daga barcin da ya ɗauketa. A tsorace ta miƙe zaune a saman bed ɗin. Ganin zane Sarina yake yi yasa Auta ta fara ruwan hawaye. Yau Sarina sai da ta kira ainahin sunan Mammiensu na yanka saboda jibgar da ta sha. Bakin bed Smart ya koma ya zauna, cikin kakkausar murya ya daka mata tsawa a kan ta tashi ta zo gabansa. Ai tuni tsawansa yasa ta dawo cikin hayyacinta, dan muryarsa a kaifafe take. Wai a haka ma Smart fa bai ɗauki zafi ba, ransa bai ɓaci ba, da ransa ya ɓaci ai sai dai wata ba Sarina ba, ace a cikin kannensa a samu mai irin halinsu Heleena kuma yana raye? Tab wlh dik sai ya gyara masu zama kafin ya bar kingdom of power. Sam ta kasa iya miƙewa da kafafunta, da jan jiki a kasa ta iso gabansa, sai kerma jikinta yake yi, bakinta ya kumbura suntum saboda take ta da ya yi, gabaɗaya singalalin hannunta sun yi ruɗu ruɗu da belt ɗin, abin ku da farar fata, tini jikinta ya zama jajir kamar jan gauda. A gabansa ta ƙariso tana kuka ƙasa kasa. Ko kallon in da take bai yi ba ya umarceta da ta yi mashi kneel down ta ɗaga hannunta sama, daga nan har wayen gari ba zata bar wajen ba, in kuma ta yi koda motsi ne sai ya kakkaryata, daga karshe ta rufe mashi baki tsit baya san ya ji komai ƙanƙantar sauti ya fita daga gareta. Yau dai Sarina ta faɗa koma. Wayarsa ya ɗauko domin ya kira Jaish ya zo ya faɗa mashi wanenen uban Sarina a cikin familynsu? Dan a cewarsa uban nata ma yana da buƙatar a gyara mashi tarbiyarsa, dan bashi da tarbiya shi ma, saboda idan yana da tarbiya a cewarsa da zai bawa Sarina tarbiya yadda yakamata, dan haka daga ita har ubanta yau zai gyara masu zama, irinsu ne ke ɓatawa larabawa suna...... Tashin hankali, lallai Smart ya dame su King ya iskancin, kam bala'i uncle Abbas zai bawa tarbiya lallai akwai cakwakiya. A lokacin da ya kira Jaish wayar tana cikin mota shi kuma yana cikin hospital ya je kiran nurses, so bai yi picking ba. Jefar da wayar a gefensa ya yi tare da miƙewa ya shiga dressing room domin ya shirya ya zo ya kwanta, sai lokacin da Jaish ya kirasa zai iya sanin hukuncin da zai yi wa Sarina, dan yanzu wannan duka da kneel down ɗin dik ba hununci bane, ta dai yi ne zuwa yasan ubanta sai ya san kalar hukuncin da ya dace da su. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Da kyar Jaish ya iya driving suka isa hospital ɗin, ko da ya kashe motar sai da ya ɗauko good 5 mins a zaune shiru ita kuma tana kwance a jikinsa, sannan ya buɗe kofar motar a hankali, kafafunsa ya fara zurowa wajen da ita a jikinsa ya fito, da hannunsa ɗaya ya tura kofar motar ya nufi hospital ɗin. Har zai shiga sai ya lura da yanayin kayan jikinta, to kun san su da kishi ko da ba matansu ba bare matansu, hakan yasa ya fasa shiga ya juyo da ita, cikin motar ya mayar da ita tare da fita ya nufi cikin hospital ɗin shi kaɗai yana wani lumshe idanu yana kame jikinsa wajen guda, da kyar ma yake tafiyar. A dai'dai wannan lokacin ne call ɗin Smart ya shigo wayarsa, Mahnoor tana ganin call ɗin har ya katse, shi kuwa nurses mata guda biyu ya je ya taho da su a kan su zo su dubata a ciki. Suna isa wajen motan babban Dr ya biyo bayansu yana kwala kiran sunan Prince Jaish, dakatawa Jaish ya yi domin su gaisa, su kuma nurse ɗin ya ce su shiga su dubata a ciki. Gaisawa suka yi da Dr, cikin girmamawa dr ya ce meyasa bai kirasu a waya sun zo gida sun dubata ba ya fito a cikin daren nan. Ɗan jinjina kai ya yi kafin ya ce babu komai su tara next time, daga haka ya ce wa Dr ya je kawai. So shi kansa Dr ya sansu da kishi, dan ko Auta ce bata da lafiya Jaish baya bari namiji ya dubata sai dai bace, dan haka dik da Dr bai san wacece bace sai ya juya ya koma ciki, a tinaninsa ma Auta ce. Dr na tafiya ya koma cikin mota ya zauna yana jin tamkar ba shi ba, wani zazzafar abar ce ma take sake taso mashi, kamar ba lafiya ba. Shiru ya ɗan jingina kansa da jikin kujerar motar yana jin mararsa tana ɗan murɗa mashi a hankali hankali, ba komai ya ja hakan ba kuma face jarabar tasa. Yana jin nurses ɗin suka yi mata dik tambayoyin da yakamata kafin su fita su je su kawo mata magungunan da suka dace, sannan suka yi masu sallama. Kuɗi ya ɗebo a cikin motar tasa ya miƙa masu ba tare da yasan adadin da ya ɗeba ba. Godiya suka yi mashi suka juya suka bar wajen. Tamkar jira yake yi su tafi, suna barin wajen ya janyota jikinsa yana jan numfashi a hankali hankali. Ajiyar zuciya ta sauke tare da saƙalo wuyarsa, can ƙasa ta ce. "Yah Jaish mu koma gida, dare ya yi ina tsoro". Jinjina mata kai kawai ya yi, sannan ya kunna motar yana ɗan shafa bayanta da hannunsa ɗaya. A hankali yake driving yana cigaba da shafa bayanta har suka isa gida. A yanzu ma ɗaukarta ya yi kamar yadda ya ɗaukota a farko suka fito. Tsabar yana cikin wani yanayi ko wayarsa bai ɗauka ba bare ya duba ko an kirasa, a cikin motar ya bar wayar suka nufi ciki. Ni kuwa na ce tab yau Sarina ta shiga uku, ga shi call ɗin Jaish Smart yake jira kafin ya yanke mata hukunci, lallai yau zata kwana a durkushe a saman gwiwowinta, waye ya gaya mata kowa ake yi wa iskanci a tsira, uncle Abbas ma ta ja mashi za'a sake yi mashi tarbiya......... 😅 Jaish bai sauke matar tasa a ko'ina ba sai a saman bed ɗinsu. Da kyar ya iya ƙarisawa da ita saman bed ɗin ma, sannan kwanta a gefenta yana sauke numfashi a hankali hankali. Hannunsa yasa ya laluɓi remote daga cikin drawer kusa da bed ɗin, wutar ɗakin ya kashe kafin ya juyo gareta. Tin ma bai gama juyowa ba ta matsa ta shige jikinsa, ita ma dai tsabar tana san kasancewa da shi a cikin mota ta baro maganin nata, ta shige jikinsa tana tura hannunta saman kansa. A hankali ya ɗaura hanunsa a saman mararta, can ƙasan maƙoshinsa da murya kamar wanda yake cikin maye ya ce. "Ya cikin naki?". Kamar zata yi kuka ta ce. "Bai yi sauki ba, mu je ka bani magungunana kila zai yi sauki". (Wato fa mu ƴan Nigeria da gaske ne fa dik in da muke mun fita daban, wato sai mu koyi abu ma kuma mu fi wanda ya koya mana iyawa 🥱 Allah ya yi mana baiwa matuƙa, ga dai Mahnoor nan ta kware har tana san fin Chuchu dake koya mata soyayyar ma.) Rungumota sosai ya yi. "Zan baki maganin, amma kafin nan nima bari in samu nawa maganin kin ji?". Kamar mai rokanta ya yi maganar. "Baka da lafiya ne daman Yah Jaish?". Ta gefa mashi tambayata tana zame hannunta daga kan nasa Kai ya ɗan jinjina mata kafin ya amsa da. "Yeah bani da shi, amma kece sila". Ya kai karshen maganar tare da haɗe bakinsu waje guda, sam bai bata damar yi mashi magana ba bare ta tambayi ya aka yi ta zama silar ciwonsa. Hot kiss ya shiga bata babu kama hannun yaro, a hankali ya....... P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 37 Hot kiss ya shiga bata babu kama hannun yaro, a hankali ya kai hannunsa saman tula tulanta, lokaci guda ya kara birkicewa sosai, cikin fitar hayyaci ya capki hannunta ya ɗaura a saman bananarsa. A zabure ta kwace hannunta tare da kwace lips ɗinta, nan take tsoro da shakkarsa ya shigeta, narai narai ta yi mashi da ido, sai ta ji tana san gudu ta bar ɗakin ta koma nata, kamar zata yi kuka ta ce. "Yah Jaish ni cikina ya dai'na ciwo zan koma ɗakina". Tamkar wanda yake a cikin maye haka ya rikota, cikin fatar hayyaci ya fara sambatu kamar haka. "Please don't go leave me, stay with me here, ki bani magani kin ji? Please and please". Tamkar ba yaron Mommarsa ba, lokacin guda ya zame mata kaman ƙaramin yaro, banbancinsa da guyson a lokacin da yake cikin ciwo kuka ne kawai, kun ga shi guyson yana kuka, shi kuma ya marairace murya ne kamar zai yi kukan kawai, amma bai yi ba. Wani irin tausayinsa ne ya kamata, amma kuma akwai tsoronsa sosai a ranta, ƙasa ƙasa ta ce. "Yah Jaish to a ina maganin naka yake sai in ɗauko maka kasha kafin na tafi ɗin". A tunaninta da ya ce ta bashi magani ta zaci kyawa zata ɗauko mashi yasa, bata san ita ce maganin da kanta ba. "Ai kece maganin, kanki kawai zaki bani zan samu saukin azabar da nike ji". Ya faɗa yana kara janyota jikinsa yana kuma dafe mararsa da hannunsa ɗaya. Sai a yanzu ta gane nufinsa, yanzu ne ta fahimci in da ya dosa, haba wani irin tsoro ne ya dira a ranta, ina ba zata iya bada wannan magani ba, dan Jumma ta faɗa mata akwai wahala kuma akwai zafi........ Kun ji yar ƙaniya, tasan akwai wahala da zafin ne kuma ta ɗauki shawarar momma, mama Haulat da Chuchu ta rinƙa kwanciyan wa bawan Allah a jiki tana sanya mashi kayan anty tsirara tana yawo a bedroom ɗinsa tasa al'amura dik suka tattashi ta yadda ba zai iya shanyewa ba, sai da ya zo har wuya in da ba zai iya jurewa ba sannan ta ce wai ba zata iya ba? Tab aikuwa bata nemi zaman lafiya ba!. Da karfi ta kwace kanta daga riƙon da ya yi mata, jikinta har ya fara kerman tsoro, hankalinta dik ya tashi, laluɓawa ta yi da sauri tana san sauka daga gadon. Shi kuwa da ya ga da gaske tafiya zata yi ta barshi, ga shi ba iya jurewa ya danne zai yi ba, sai ya capkota cikin zafa. Ƙoƙari kwace kanta ta fara yi tana faɗin ya saketa cikinta na yi mata ciwo, haba ai da ya fahimci yana sakinta guduwa zata yi sai ya shareta, cikin zafa ya zare kayan jikinta ya kuma yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa. Tana ganin haka ta fara yi mashi ihu tana bubbuga kirjin nasa tana san miƙewa ta gudu. Da ta hakura ya bita a hankali ma sai ta samu sassauci, amma ta gwada mashi gardama ta gwada zata kwaci kanta, shi kuwa yana hannu ya danneta ya yi mata ta karfin tsiya, hakan ya haifar mata da jin ciwo daga ciki ga zubar jini sosai da ta samu, dan ko kaɗan bai sarara mata ba, cikin fitar hayyaci ya yi abin, dan wlh kunga a yadda yake ai yama yi mata ƙoƙari da ciwon yana tsaya a iya haka, suma kuwa sai da ta yi sau biyu, dik kuma bai jitaba ya yi ta bidirinsa har sai da ya ɗan samu gamsuwa, da alama ya manta da cewa disvirjin yake yi ba wai an taɓa yi ba, sai da ya yi sau uku, nan ma tsabar jaraba bata wani isheshi ba, ya dai hakura ne kawai kada ya yi kissan kai. Abin kuma kamar abin haɗin baki, a lokacin da yake disvirjin na Mahnoor a lokacin shi ma Jawad ya yi disvirjin na Jannawad ɗinsa, shima sai da suka kai ruwa rana sosai, daga karshe shi ma ta karfi kawai ya yi mata, dan ya kai two weeks yana binta tana yi mashi kuka ta nuna bata so, aikuwa yau kam ya saka mata karfi ya buɗeta, sai dai shi bai ji mata ciwo ba, dan bai fita hayyacinsa kamar Jaish ba, ya dai sumar da ita, shi kuwa Jaish mai gabaɗaya sai da ya jawa ƴar mutane jinya mai lasisi. Tsabar tabbatar rashin kunya irin nasa kuma bayan ya dawo hayyacinsa ya mayar da kayan jikinsa, sai ya je ya kira mama Haulat, wai ba zai iya kiran momma ba, saboda ba zai iya haɗa idanu da ita ba, sai da ya gama rashin mutuncinsa sannan kunyar tasa ta rashin kunya ta dawo. Ita ma fa mama Haulat ɗin zuwa ya yi ya ce mata ta je bedroom ɗinsa Mahnoor tana kiranta, daga haka ya gudu garden abinsa, wai shi ba zai bari ya haɗa idanu da kowa ba. Kuma fa tsabar rashin mutunci bai wani ji tausayin Mahnoor ɗin ba, shi dai ya biya buƙatarsa ya ɗan samu sassaucin abin da yake ji, so bashi da wata matsala da ita, wato ita ta sani kenan idan ta rayu ma........ My people's shin mu faɗawa Jaish ko dai mu kyalesa tun da ya ɗanɗana ya ji abin da ake ji? Ɗan rai'nin wayo da kanka zaka dawo nemanta, ba dai ka ɗanɗana ba, zaka gane baka da wayo, mu je dai zuwa, ranar da zaka ƙasa barci zai zo ne. Innalillahi Queen Zarina ta tura a ɗauko mata shi dan samartakansa ga shi yau ya bawa Mahnoor samartakar tasa, innalilahi wa inna ilahir, shi mutum ne mai addini hakan yasa Queen Zarina bata iya ganin halin da yake a cikin ta madubin tsafinta, tab akwai cakwakiyoyi matuƙa. Mama Haulat baiwar Allah, ita ta gasawa Mahnoor jiki da ruwa mai zafi da ta haɗa mata, sai dai kuma har ta yi mata dik abin da zata yi mata ta gama Mahnoor bata farfaɗo daga wannan doguwar suma da ta yi ba, kuma jinin yaki tsayawa dan ta samu rauni daga ta ciki, hankalin mama Haulat in ya kai dubu to ya tashi a wannan lokaci. Jikinta na kerma ta tallabi Mahnoor zuwa cikin bedroom ɗin, ta fahimci ciwo ta ji sosai daga ta ciki, dan haka sai ta cire bedsheet ɗin da jinin ya lalata, ta kudundunesa, ta kwantar da Mahnoor a saman sofa ta ɗauki bedsheet ɗin ta nufi wajen momma da shi. A lokacin momma ta dawo daga wajen King kenan, tana ƙoƙarin kwantawa mama Haulat ta shigo bakinta a ɗauke da sallama. Da kallon mamaki momma ta bita kafin ta amsa sallamar tare da kafeta da idanu alamar tana jiran jin abin da ya kawota. A gaban momma ta zube gwiwowinta ƙasa, cikin girmamawa ta fara neman izinin magana. Kai momma ta ɗaga mata alamar ta yi magana tana jinta. A natse ta ce. "Ranki ya daɗe princess Mahnoor dai ta kawo budurcinta ga mijinta ga kuma shaida nan ina tafe da shi, sai dai an samu matsala sosai ta zubar jini da alamar ta samu rauni daga ta ciki". Ta kai karshen maganar tare da ware bedsheet ɗin ta nunawa momma shaidar da ta kawo na jinin Mahnoor dake jikin shi. A lokacin da mama Haulat ta ce Mahnoor ta kaiwa Jaish budurcinta ba ƙaramin daɗi momma ta ji ba, a bayyane ta sauke ajiyar zuciya mai sanyin gaske, har ta ji dik wata damuwa tata ta gudu, amma a lokacin da ta ji zancen karshe na cewa Mahnoor ta samu rauni take farincikin nata ya tsaya cak, dama dai tasan Mahnoor zata sha wahala, dan dik ƴaƴanta babu rago, sai dai bata kawowa ranta wahalar har haka bane, hankalinta ya tashi sosai, da sauri ta fasa kwanciyar da take da niya. Kasan gadan ta sauko, bata bi ya kan mama Haulat ba ta yi gaggawar nufar waje, kai tsaye ta nufi ɓangaren Jaish ɗin, hankalinta dik a tashe matiƙa. Da sauri mama Haulat ta miƙe ta rufa mata baya dan su je su san abin yi. Ko da momma taga Mahnoor ta tausaya mata matuƙa, dan ta ganta a wani irin yanayin da dik zuciya mai imani sai ta tausaya mata, sai dai kuma momma bata tambayi ina Jaish ba, dan ita kanta ta san ba zai tsaya ba, saboda shegen kunyar nan tasa ta rashin kunya in ji Jawad, so sai bata ma nemesa ba, da kanta kawai ta tsayawa Mahnoor ɗin ta yi mata komai ta hanyar kirar likitarta mace dan ya zo ta dubata. Shi kuwa Jawad da yake iya suma Chuchu ta yi bata samu rauni ba, da kansa ya yi treating kayassa, sai dai fa akwai cakwakiya matuƙa, domin kuwa tun da ta farfaɗo banda kuka babu abin da take yi mashi, ya yi rarrashin duniya taki ta kula shi, ta dai ce wajen mummynta zata koma wlh ba zata zauna da shi ba tun da shi mugu ne. Dik abin da take faɗe he's not minding her word, hakuri kawai yake cigaba da bata yana rarrashinta dan yasan ya yi ɓarna. •••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥🔥 A ɓangaren Smart kuwa, Sarina tana ganin ya shiga dressing room ta lallaɓa ta miƙe da nufin ta gudu, kasa iya taka kafafunta ta yi, dan haka sai ta koma ta zube ƙasa, da ciki ciki ta fara ja wasu zafafan hawaye suna tsere a saman ƙuncinta, wani irin azaba ta ji lokacin da ta gwada mikewan nan, da kyar ta cigaba da jan cikin nata har ta fice daga ɗakin. Ganin komawa part ɗinsu ba zai yiwun mata ba saboda nisa ne yasa ta nufi part ɗin King dan a ganinta shi ne kawai zai iya cetanta daga hannun Smart. Amma kuma sai da ta ɗauko alkyabbarta ta sanya a jikinya kafin ta fice tana ja da ciki. Tasan in ta je wajen King da irin wannan shiga zata yabawa aya zaƙinta ne, sai ta mayar da alkyabbarta. A lokacin da ya fito bai sameta a cikin room ɗin ba, wani irin ɗaure fuska ya kara yi, a ransa ya ce lallaima wannan yarinyar ta jawa kanta bala'in da babu wanda zai iya tare mata, har kamar shi ta isa ya sakata kneel down ta tashi ta gudu? Tab ta ɗebowa kanta wutar gasa kanta da kanta. Auta dai tana zaune a saman bed, ta dai'na kuka amma bata iya mayar da barcinta ba, ya kuma ganta, sai dai ya mayar da hankalinsa a kan kamo Sarina, ya ce sai ya dawo zai rarrashi Auta. Cikin takun jarumta ya bi bayanta, sai dai bai san ko'ina a cikin fam part ɗin ba, dan haka da ya fito sai da ya ɗan tsaya a bakin kofa yana tinanin ina yakamata ya bi. Ƙasa ya yi da kansa domin yin tinani sai yaga jininta a kasa saman tiles, da ta ja jikinta a ƙasa jininta ya ɓata ko'ina, bin jinin da kallo ya yi ya ga hanyar da ta bi, ransa a ɗan ɓace ya bi wajen, ta ja ya kuduri niyar yi mata abin da bai shirya ba. Dik abin da yake faruwa Mammie ɗinta tana ganinsu ta madubin tsafinta, ta so ɗaure hannun Smart a lokacin da yake dukan Sarina ta kafar mashi da hannun, sai dai ta kasa sage mashi koda jijiya guda ɗaya, saboda ni da ku dai dikka mun san yadda yake da riƙo da addini, ko jijiya guda ɗaya ta kasa sagar mashi, infact ko kusa da shi abubuwan tsafin nata sun ƙasa zuwa, wannan dalilin yasa ta baro part ɗinsu ta zo domin ta kwaci yarta. A main parlour na part ɗin King Smart ya isko Sarina, tana jin motsi ta juya, tana ganin shi ne ta daddage ta kurma ihu mai amsakuwar da sai da ya daki kunnuwan dik wanda bai yi barci ba a cikin part ɗin except Jawad and Jaish da suke duniyar sama jannati. Cikin zafa King ya fito daga bedroom ɗinsa sanye da arabs jallabiya saboda wannan ihun, ita ma Mammie da sauri ta karisowa wajen, da yake uncle Jahiz ma bedroom ɗinsa yana cikin part na King sai ya fito da gudu, dama Dr Raj yana kan hanyarsa na zuwa wajen King, so jin ihun yasa ya yi saurin karisowa. In short cikin short time gabaɗaya family suka haɗu a cikin parlon, kowa sai tambayar kansa yake yi me yake faruwa?. Mammienta na ganin haka ta yi wa uncle Abbas sms a kan ya zo main parlour babu lafiya. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai ga shi ya zo, gabaɗaya kowa ya tsaya cirko cirko kaman masu shirin kaurewa da yaki, an rasa mai bakin iya tambayar Smart me yake faruwa?. Da yake momma ce ta yi karshen zuwa wajen sai yazama sun ɗauki almost 5 mins babu wanda ya iya kallan Smart ya tambayesa dalili, sai King ne ma ya yi kokarin buɗan baki zai tambayesa sai ga momma ta kariso wajen da sauri tana faɗin meyake faruwa ne?. King ɗin ma bai fasa tambayar da ya yi niyya ba, dan haka tana rufe baki ya ce. "Omerish meya haɗaka da kanwar taka kuma?". Shi King dama mamakin shigar jikin Sarina yasa ya ɗan yi shiru ma, dan ba kaya bane na hankali da musulunci, kaya ne na Allah wadarai, so abin ya bashi mamaki ganin irin wannan shiga a jikin ƴaƴansu. Ja da take yi da ciki yasa alkyabbar da ta sanya ya yi sama kayan suka bayyana. A wannan karan har da su Zee and su Pretty, Auta dik sai da suka haɗu a parlourn, su Jaish da matansu ne kawai basa nan. Mu koma baya kaɗan kafin mu ɗaura daga labarinmu, a lokacin da Zee ta baro garden ta baro Dr Raj kenan, tana kan hanyarta na nufar bedroom ɗin momma suka ci karo da mama da ta fito daga part na Akka. To kun dai san yadda halin mama yake da kyara haɗe da tsangwama, ga shegen walaƙanta mutane da ƙasƙanci. Hakan yasa tana ganin Zee ta bita da kallan walaƙanci kafin ta yi mata zagi ta uwa ta uba wanda ko kare ba zai ci ba dik da bata san wacece ita ba, daga karshe ma ta kirata da bola kazama, a tinanin mama ƴar aiki ce Zee momma ta kawo, dan haka sai ta rufe zancenta da cewa. "Kada ki kuskura na ganki ta arear side ɗina da sunan kin zo mun aiki, dan bana da buƙatar irinku a masu yi mun aiki". Wato idan jininka bai haɗu da mutum ba fa bai haɗu bane kawai, ga shi dai babu gaira babu dalili mama ta tsani Zee, har ta yi mata wannan ƙasƙantaccen zagi mai muni haka. To ita ma dai Zee kun san ba shiru take yi ba, dan haka a karshe ta ce. "Ai ko zan yi wa kowa aiki a cikin gidan nan ke kam ba yi maki zan yi ba, banza ma irinki shashasha mara mutumci". Amma da Hausa Zee ta yi maganar, hakan yasa mama bata fahimci abin da ta faɗa ba, ta daiga tana magana kawai. Hmmm Zee fa bata san mamar Dr bace wannan, haka kawai ta tsani mama ta kuma zageta fes har da ce mata shegiya mai idanun mujiya dik da Hausa, ta kara da cewa dik ranar da hannunki ya taɓa jikina zaki gane baki da wayo, dan sai na lillisaki wlh. Ta dai tsaya tana surutanta ita kuma mama ta kara gaba. Sai da ta gama babu mai bata amsa sannan tasa kai ta wuce part ɗin momma tana kunkuni ciki ciki. Uhmmm rashin sani ya fi dare duhu, wato akwai cakwakiya matuƙa, mama bata kaunar Zee, haka zalika Zee bata shiri da Aneesa kanwar Dr ɗin, ga shi kuma Dr ya folawa Zee, ita ma ta fola mashi, baiwar Allah ga shi farkon soyayyarta kenan, kuna ganin zata cinwa nasara a wannan soyayya? Zata kai labari kuwa?. To mu je dai zuwa. •••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Shiru Smart ya yi har sai da momma ta sake jefa mashi tambayar me yake faruwa?! A maimakon ya bata amsa sai ya jefa mata tambayar wanenen uban Sarina a cikin ƴan uwan daddynsu?. "Omerish ka faɗa mun meyafaru tukun nan ka ji?". Cewar momma, cikin sigar rarrashi da kwantar da murya ta yi maganar. Da yake a duniya babu wanda Smart yake kauna biyunta bayan Allah da manzonsa, yana san momma fiye da komai ɗinsa, kuma yana yi mata biyayya da dikkannin iyawarsa, dan haka sai ya sanar da ita dik abin da yake faruwa cikin kauna da girmamawa. Salati gabaɗaya parlourn suka sanya a cikin zuƙatansu except Mammie da ta san komai ita. Shi kansa uncle Abbas and King the was very shocked da suka ji abin da ya faru, mamaki uncle Abbas yake yi na yaushe Sarina ta girma har ta yi wannan bushewar idanu bashi da labari. Suna tsaka da mamaki Smart ya katsesu da tambayar wanenen uban Sarina?. A lokacin Akka ma tana wajen. King ne ya yi saurin cewa. "Nine ubanta". Sam Smart bai so ace daddyn nasa bane ubanta, saboda bai yi niyar raga mata ba, amma dik da haka sai ya yi wasu daga cikin abin da ya yi niyya. Cike da izza ya ce. "Daddy kenan dama haka kake tarbiyantar da amanar da Allah ya baka? Ko ka manta amana ce Allah ya baka kuma zai tambayeka? Nasan kasan da haka sai dai in ce maka ka mance ne?". Akka ce ta ce. "Omerish yana da kyau kasan irin maganganun da zaka rinƙa faɗawa mahaifinka da kuma in da ya dace kayi magana da shi! Idan tarbiyarsu bata yi maka ba sai ka yi naka ai, nan gidan sarauta ne masu amfani da dokoki masu karfi wanda dole ka bisu, kuma kasan da cewa mahaifinka sarki ne ba wai irin mahaifin haka kawai bane!!". Cikin faɗa Akka ta yi maganar saboda ranta ya sosu sosai na yadda Smart yake gatsa magana ba tare da ya taunata ba. Su sun kasa gane ba wai raini bane Smart yake yi wa King, haka maganarsa take without respect, shi haka ya taso, daddynsa na France bai taɓa ƙoƙarin yi mashi katsalandan ko ya yi mashi wata gyara a cikin magana idan yanayi ba, so haka ya taso babu wani respect na kowa sai dai shi ayi respecting ɗinsa, amma su basu san cewa bawai baya san King bane yasa yake mashi hakan, ku kanku kun gani bama King da yake daddynsa ba, hatta su Ramish da suke ƴan uba tsananin kaunarsu yake yi bare iyayensa, shi dai haka yanayinsa take ne kawai, idan ka fahimcesa zaku zauna lafiya, akasin haka ciwon zuciya ya kasheka. "Dama abin da zan yi kenan ai Akka, tarbiya zan sake basu daga farko, kuma da kuke maganar sarauta a wajen wasu ne daddy yake sarki ba a wajen mu ba, a wajenmu mahaifi ne, and zan zo ki san cewa nima sarki ne a nawa daular! Dan haka mind your tongue old woman". Without respect again ya yi wa Akka magana, hakan ya sosa ransu King sosai, saboda uwa ba wasa ba. Cikin kakkausar murya King ya ce. "Omerish yana da kyau ka rinƙa sanin da waye kake magana kuma me zaka faɗa, ka koyi tauna magana kafin furtata!!". "Dad I knew what am doing, so bana da buƙatar wani gyara kuma, sai dai in gyara maku........". Tashin hankali. Tsawar da King ya daka mashi ne yasa shi yanke maganar, kun san su sarauta basa san katsa landan, kuma kowa yasan idan King yana magana ba'a bashi amsa ko a yi mashi gyara har sai ya bada izinin ayi magana, amma shi Smart bayan ya bada amsa ba tare da izini ba amsar babu girmamawa a cikinta sai ma kamar ƙasƙanci, dole su King su harzuƙa matuƙa. Uncle Abbas ne ya yi ƙoƙarin tausayin King, dan yaga kamar ya ɗauki zafi sosai. Katsesu Smart ya yi da cewa. "Ku faɗa mun uban yarinyar nan dan na san irin hukuncin da zan yi mata ita da uban nata, na san wannan ba ƴarka bace dad". Kallan momma King ya yi irin kallan nan na kinga abin da kika ja mun, dama momma da kyar yanzu ta samu ta shawo kansa, ga shi tin gari bai waye ba Smart zai sake haɗata faɗa da shi kuma, ya zo yana magana babu girmamawa irin na gidan sarauta, kuma dama a yanzu kafin su shirya da King sai da ya ce mata shi babu abin da ya fi yi mashi ciwo a cikin wannan al'amari kamar yadda Smart baya respecting ɗinsa, yana yi mashi magana gatse gatse haka, ya so ace shi ya bawa ɗansa tarbiya ya koya mashi yadda zai girmama mutane na gaba da shi, sai dai kash abin bai zo yadda yake so ba. Da kyar momma ta shawo kansa a in da ta yi mashi alkawarin zata zauna da Smart, tabbas zata koya mashi girmama mutane, da kyar dai ya yarda da ita ya kuma yafe mata, yanzu kuma ga sabon aiki Smart ya ɓallo mata again, me kuke tinanin zai faru?. Bala'i, wato akwai riki fa, a haka ma King bai san aikin da Smart yake yi ba, idan yasan ga aikinsa a tinaninku zai yarda ne? Wlh ko momma tasan gaskiyar aikin da yake yi ba aminta zata yi ba bate King, akwai cakwakiya a gaba fa. In short Smart bai bar parlon nan ba sai da suka yi kaca kaca, dan kuwa ana ƙoƙarin kashe wuta mammie ta ce bata yarda ba, tun da ya dakar mata ƴa sai ya biya, ai ba shi ya haifar mata ita ba, aikuwa ya gwada mata shi ma ɗan yau ne, dan har ya yi niyar zaneta ita ma, ya haɗesu ya zane uncle Abbas ya ce wannan kuma ba zata yiwu ba, a karshe da suka fusata shi har uncle Abbas ɗin ya yi niyar haɗewa da su ya hukunta King ya shiga tsakani. Ran momma in ya kai miliyan ya ɓaci, hakan yasa ta ce Smart ya wuce bedroom ɗinsa kada ya sake yin magana da kowa a gidan sai komai ya sesetu, ransa ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, a fusace ya nufi bedroom ɗinsa har yana huci, kunsan akwai ciwo idan mutumin da yake da iko da kai ya baka umarnin da zuciyarka bata so, abin akwai ciwon da sai mai juriya zai iya dannewa, dan haka shi ya gagara dannewa saboda zafin zuciya. Gudun kada ya ɓata ran mahaifiyarsa yasa yana shiga bedroom ɗinsa ya ɗauki wayarsa da key ɗin motar da Jaish ya ɗaukosa daga airport ya fito, suna parlon har lokacin momma tana bawa su Akka hakuri ya zo ya capki hannun Auta dake tsaye kusa da Pretty, sun rike hannun juna suna kallan wannan tashin hankali da yake faruwa, bai sake yin magana da kowa ba kuma bai bi ta kan kowa ba ya ja hannun Auta suka fice daga parlourn. Allah sarki zuciya, a gaggauce King ya bi bayansa domin ya ji ina zai je a wannan daren haka shi da bai san ko'ina a ƙasar ba?. Momma ta yi mamakin ganin King ya bi bayansa, bata yi zatan zai yi saurin nuna zallar soyayyar da yake yiwa ɗan nasa a fili a cikin ƙankanin lokaci haka ba, ta manta da cewa ita zuciya bata da ƙashi, idan ta so abu dole a bata ko a samu matsala. Ko da King ya fito bai same shi a wajen ba, a hanzarce ya nufi parking space ko zai same shi, sai dai kafin ya isa parking space ɗin sai ya hango ɗaya daga cikin motocin Jaish ta kutsa waje warriors sun buɗe mashi gate. Sosai King ya shiga damuwa, da sauri ya koma ciki domin ya sa momma ta kira mashi shi ya dawo gida kada ya ja mota yana cikin fushi a samu matsala. To a tinaninku ina Smart zai tafi a cikin wannan dare? To mu je zuwa dai. ••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 A ɓangaren Dubai kuma, Ramish ya aminta ya baiwa Leesharh jini bisa umarnin Smart, dan ya yi mashi massage kamar yadda ya saba yi mashi, ya umarcesa da ya bata jini kuma ya kula da ita sosai har ta samu lafiya, domin da ita kaɗai zasu yi amfani wajen kama masu nikaf, ita ce kaɗai zata zama sanadiyar kamasu, dan tasan komai kuma tana da hujjijo a kansu, komai yana da sanadi, dan haka ita Leesharh ita ce sanadin da zasu yi amfani da ita wajen kamasu cikin ruwan sanyi, dan mutanen shegun kai ne, dole a kara masu tarko. Wannan dalilin yasa Ramish ya aminta ya bada jininsa, (sorry ranan a wajen rubuta jinin Leesharh zan rubuta O negative na rubuta O positive, typing errors aka samu, sai daga baya da ina sake duba page ɗin na gani, so O negative take.) Yanzu yana kula da lafiyarta sosai, a rana yana daurewa ya leƙa in da take sau ɗaya ya tabbatar tana cikin kulawa mai kyau, kwanaki sun suɗe amma har yanzu bata farfaɗo ba, sai dai jikin nata yana ta kara kyau tana samun lafiya yadda yakamata. Wannan kenan abin da yake faruwa a Dubai, mun ɗan ji halin da suke ciki, bari mu leƙa wani ɓangaren ma mu san a wani hali suke ciki, dan na lura rikicin dake cikin kingdom of power ba zai kare ba, yanzu ma wasan zai fara, so dole in rinƙa takaitawa muna laƙa wasu ɓangarori dan jin yadda ake ciki. 🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥 Bayan wasu ƴan kwanaki. Abubuwa masu ɗan yawa sun fara a cikin waɗan nan kwanaki da suka shuɗe wanda suka haɗa da jinyar da Sweetie ta sha bayan dawowarta daga wajen wutar can da Black Tiger ya so konata Allah ya nufa tana da sauran shan ruwa a gaba, Allah ya ɗaurata a kansa ya sanya mashi ɗigon tausayinta a ransa, ba komai yasa ya tausaya mata ya barta ba kuma face yadda ta tuna mashi da akwai ranar da zai faɗi abin da ya aikata wato ranar lahira kenan, waɗan nan kalaman nata sun sa ya ɗan ji kamar zuciyarsa ta ɗan yi sanyi wanda hakan ya ja ya kyaleta. Abu na biyu da ya faru a kwanakin da suka shuɗe sun haɗa da rokar Black Tiger da Ronnie ya yi a kan ya sanya Sweetie makaranta tun da tana da ilimi kuma tana da san karatu ga ƙwaƙwalwa. Da yake shi Black Tiger idan ba aikinsa bane ya biyo ta kanka sam bashi da mugunta, sai ya aminta a kan Ronnie ya yi mata komai da ya dace. Hakan kuwa aka yi, Ronnie ya shige gaba wajen yi mata komai yadda yakamata. A ɓangaren ita kuma Sweetie, sabon walaƙanci yarinyar nan ta karo, bare ma yanzu da Ronnie ya koya mata yadda zata yi amfani da magic ɗinta, ohohoho, yanzu tana bawa Black Tiger ciwon kai, ga shi ba yadda ya iya da ita, idan ya yi mata magic ita ma ta yi mashi, ta saka shi a gaba bata san ta barshi ya zauna lafiya, yana aikin neman Pretty dan yasan Spender yana hannunta a yanzu, ita kuma Sweetie tana distracting ɗinsa a nan, tin ranar da Sweetie ta ƙalubalancesa a kan ya nemo Spender da kansa daga lokacin ya shiga nema, a nan ne ya gano yana hannun wata yarinya mai kama da Sweetie wato Pretty kenan. Yanzu haukar neman Pretty yake yi, ya fita harkar Sweetie dan yanzu bata da amfani a wajensa, ba dan Ronnie bama ai da Black Tiger ya jima da kasheta an rufe babinta ya nemo Pretty ya karɓi Spender, so Ronnie ya ce yana santa, kunsan shi ya nuna yana san su Floris ma yasa aka kawosu empire ɗin, a takaice dai yanzu Sweetie zaman Ronnie take yi a birnin, amma ta takurawa Black Tiger dan tana san ya musulunta, tana san kuma ta shiga jikinsa sosai ta yadda ko da ta kuresa ta ja yasa a kureta a gari to da kansa zai sa a dawo da ita. Kun san idan mutum yana yawan shiga harkarka ko baka so ko kana so, to dik ranar da aka ce babu wannan mutumi sai ka ji wani irin a cikin ranka, irin abin da take san yi wa Black Tiger kenan. Kuma dayawan lokuta Allah yana ɗaurata a kansa tana tsira ba tare da ya yi mata hukunci ba. ••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 Zaune Ronnie yake a bakin bed ɗinsa yana kallan kyakkyawar fuskar Sweetie dake zuba barci, tana shirya cikin wani kyakkyawan sleeping dress, tin da ta yi sallar asuba take zuba barci saboda gajiya da ta yi, daren jiya bata yi barci ba, ta bi Ronnie wajen casunsu da suka saba, har karfe 1 na dare suka dawo, da suka dawo kuma sai suka zauna zaman karatu har karfe 3, tana koya mashi karatun addini da dik abin da yakamata ace musulmi ya iya. Abin da yasa yanzu take yarda ta bi Ronnie ko'ina har church ɗinsu, saboda tana san ta shiga jikin mutanen birnin sosai, ta ga yanayinsu, ta san karfin tsaurinsu a kan addininsu, ta san zasu iya karɓar musulunci cikin sauki ne ko kuma sai an sha wahala, wannan dalilin yasa take yarda ta je ko'ina dan da'awarta. Yanzu haka wajen casun da suka je jiya ta yi nasarar jan ra'ayin wasu ƴanmata guda biyu da suka yaba da kyan halinta har suka ce suna san kulla abota da ita, da taimakon Ronnie ta samu suka amsa zasu musulunta a sirrance suma, kunga kuwa ashe shiga cikinsu da take yi babban nasara ne. Yau zata fara zuwa school, amma ta kwanta sai barci take zubawa. Ronnie yana san tashinta kuma yana san barinta ta huta. Zuba mata idanu sosai ya yi yana kallanta, sai yaga alamar kamar zara zaran eyelashes ɗinta suna motsawa, ɗan blinking eyes ɗinsa sau biyu ya yi ya sake kafesu a kanta, a nan ne ya fahimci idanunta biyu bata yi barci ba. Wani irin cool murmushi ya saki kafin ya ce. "Maza tashi ki shirya zuwa school". Miƙa ta ɗan yi tare da waro kyawawan fararen idanunta, ganin yana murmushi ya sanyata sakin cute smile ita ma wanda sai da tasa Black Tiger dake kallansu ya ji murmushin nata ya burgesa. Hannunta ta kai ta saƙalo wuyan Ronnie kafin ta miƙe zaunta. "My brother waye ya faɗa maka ba barci nike yi ba?". Ta jefa mashi tambayar tana kai hannunta saman kumatunta, irin mutum ya ɗan tallabo kumatunsa haka. Miƙewa tsaye ya yi tare da riko hannunta. "Tashi ki shirya, idan kin gama shiri zan faɗa maki ya aka yi nasan idanunki biyu". Ya kai karshen maganar tare da janyota, tana yi mashi yauki da yanga ta sauko kasa, a hankali ta fara turo baki tana gallah mashi hararar wasa, bai wani damu ba ya ja hannunta izuwa toilet. Fitowa ya yi ya kyaleta domin ta yi wanka. Shi yanzu ba school yake zuwa ba, dan ya gama saura bautar ƙasa, sannan kuma akwai partyn da zasu yi wanda aka ɗaga, da last week zasu yi sai aka ɗaga sai next week. Da kansa ya fitar mata da uniform ɗin nata, har bakin toilet ya je ya tsaya tare da yi mata knocking, kanta ta ɗan leƙo hannunta dik kumfa. Miƙa mata uniform ɗin ya yi an hi iron ɗinsu sun yi kyau. A maimakon ta karɓi uniform ɗin sai ta shafa mashi kumfar dake hannunta a face ɗinsa, siririn murmushi ya saki, da a baya ne lokacin da yake krista da ya shiga cikin toilet ɗin, amma yanzu Alhdulillah yasan wasu hukunce hukuncen na muslunci, sai kawai ya yi murmushi yana faɗin zaki fito ne ai. Da biyu Sweetie ta yi mashi hakan, dan ta tabbatar karatun da take karantar da shi ya nutsa cikin kwakwalwarsa ne ko dai ɓata lokacinta take yi, ashe kuwa ya nutsa yadda yakamata kuma yana amfani da abin da ya karanta. Karɓar uniform ɗin ta yi ta koma ciki tana cigaba da murmushin ta yi nasara ita ma. Shi ma komawa bakin bed ya yi yana murmushi haɗe da jinta a ransa tamkar ƴar uwarsa na jini. Wlh yadda suke gudanar da rayuwa ita da Ronnie haƙiƙa yana matuƙar burge Black Tiger, Ronnie bai taɓa kawo yarinyar da suka shaku suke wasa tamkar yaya da kanwa ba irin Sweetie, ga shi yanayin face ɗinsu yana shege, wani irin farinciki na musamman Ronnie yake yi idan yana tare da ita, hakan yasa Black Tiger yake raga mata sosai, saboda tana sanya ɗan ƙaninsa a cikin farinciki. Wayarsa Ronnie ya ɗauko da nufin ya fara latsawa kenan dan ya gaji da zama shiru, sai ya ji an turo kofar toilet. Da sauri ya kai kallonsa wajen. Ai bai san time ɗin da ya miƙe tsaye ba. Ya ilahi Sweetie ta yi masifar kyau a cikin wannan uniform ɗin. Mini skirt ne da bai gama rufe mata santala santalan cinyoyinta ba launin ash colar, sai riga mai dogon hannu launin white color, ta ɗaure gashin a tsakiya ta saki jelar har baya, yau bata wanke kanta na dan daren jiya ta wanke. Sai kyalli gashin nata yake yi sosai, abinku da golden white, kun san yana kyalli sosai. Ga sock ɗinta white color sosai. Haba ai Ronnie bai san time ɗin da ya fara santin kyan da ta yi yana yabawa ba. Kashe mashi idanu ɗaya ta yi kamar yadda yake yi mata, sannan ta kariso gabansa tana tambayar ta yi kyau?. Wlh Black Tiger yana iya ɓata awa guda yana kallan rayuwar Sweetie da Ronnie, gwanin ban sha'awa da burgewa, yanzu ma haka zuba masu idanu ya yi yana kallansu. "Haba my lovely sis, ai faɗe ma ɓatawa, kinsan ke makurar kyau ce". Ya faɗa yana buɗe mata tafin hannunsa. Buɗe nata tafin hannun ta yi kafin ta ce. "Ban mu sha my brother". Tafa hannu suka yi kafin su kai tafin hannunsu saman ɗan bakinsu suka manna mashi sumbata sannan suka hurawa juna, lokaci guda suka saki ƙayatattcen murmushi kafin su rungumi juna, abin gwanin birgewa, na tabbata ba iya Black Tiger kawai ba, dik wanda ya gansu ba zai so ya dai'na ganinsu ba, saboda sun haɗu, idan suna tare suna bata show. "Bro bari in je wajen big bro ina zuwa". Ta faɗa tana raba jijinta da nasa, yanayin tattarar skirt ɗinta gwanin birgewa, ya sha tattare sosai har ya ɗan yi kamar umbrella. Bai tambayeta me zata je yi a part na Black Tiger ba, sai kawai ya bita da to, dan yasan ko ya tambaya ba faɗa mashi zata yi ba. Da sauri ta nufi waje, shi kuma ya shiga dressing room dan ya ɗauko mata school back ɗin nata da dik abin da ya dace. Nima na haɗa kayana na tafi shan maltina. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Yanzu ita ma ta gama iya buɗe kofar Black Tiger, ko ya rufe da magic sai ta buɗe ta shiga, shiyasa ya daina wahalar da kansa dan rufewa ma, ya kyale masu kofar a buɗe kawai. Ciki ta shigo yana dai tsaye a gaban mirror bai motsa daga in da yake ba, a tsakiyar ɗakin ta tsaya tana kallansa yadda ya yi kyau cikin wani irin shiga na musamman, ga wani zazzafar long coat da ya ɗaura a saman kayansa saboda sanyin da aka tashi da shi yau, ya yi kyau matuƙa. A dik lokacin da ta kalli Black Tiger jaruminta na farko wato Kamran shi kawai take tinawa, a kullum tana tinaninsa fin sau a kirga, da shi take kwana take kuma tashi, burinta ɗaya ta gansa, a kullum sai ta yi wa kanta wasu tambayoyi kamar haka, a ina yake? A ina zata gansa? Yakamanninsa suke? Shin yana tinata ne ko ya manta da ita? Meyake yi a halin yanzu? A koda yaushe sai ta yi wa kanta waɗan nan tambayoyin da bata da amsarsu bata kuma da in da zata sami amsarsu, wata rana har kuka take yi idan ta tunasa. Amma har yau bata iya sanar da Ronnie soyayyar Kamran dake ranta ba, tabar sirrin a ranta. Meyasa idan taga Black Tiger take tina Kamran? Shin suna da wata alaƙa ne ko dai kawai a ranta ne take jin kamar girma da cikar Kamran ya kai Black Tiger dan bata taɓa ganinsa ba?. Cikin sanyin murya ta ce. "Big bro good morning". Shiru bai amsa mata ba, bai ma yi kamar zai amsa ba, yana cigaba da dudduba abin da yake ra'ayi zai fita zuwa fada, anjuma za'a buɗe katafaren hospital da ya ginawa Ronnie, za'ayi taran partyn buɗe hospital ɗin, ba ƙaramin dukiya Black Tiger ya zubar a wannan taron ba, an shirya abubuwa sosai, and dik a cikin Daularsa za'ayi, kuma hospital ɗin ma a cikin Daular tasa take. So yana da abin yi sosai yau, shiyasa ma yau dressing ɗinsa ta fita daban da kowacce rana, yau ranar Ronniensa ne. Bata damu dan bai amsa maganarta ba, sai ta sake cewa. "Big bro na yi kyau?". Tana magana kirjinta na harbawa da karfi karfi, dan tasan bata taɓa zuwa wajensa ta fita lafiya ba, kullum sai sun yi dirama ɓatacciya kaman wasu tom and Jerry. Nan ma shiru bai amsa ta ba, kuma dama tasan hakance zata biyo bayan, dan sai ka yi mashi magana sama da guda uku bai amsa ko ɗaya ba, ba wanda yake sanya shi yin magana sai time da ya yi ra'ayi. Cikin natsuwa ta tako ta nufi in da yake tsaye, jingina bayanta da jikin drawer mirror ta yi, yazamana suna fuskantar juna, kallansa gabaɗaya yana a kan mirrorsa tamkar bai san da wata halitta a wajen ba. Shiru ta ɗan zuba mashi idanu na ƴan sakanni kafin ta sanya hannunta cike da tsoro ta shafi kyakkyawan bakin gashin dake kwance a gefe fuskarsa. Hannun nata har yana kerma saboda tsoro. Hakan yasa dan dole ya dawo da kallonsa a kanta, wannan yarinya ta zame mashi kashin wuya, ya faɗa a ransa yana kallonta. Wlh Sweetie ta san kan duniya, ido ɗaya ta kashe mashi kafin ta ce. "Big bro na yi kyau?". Zaman lafiya yau yake so, dan yana da abin yi masu muhimmanci a gabansa, dan haka sai ya ɗaga mata gerarsa guda ɗaya alamar yes ta yi kyau. Ajiyar zuciya ta sauke yau karo na farko ya amsata dik da bai buɗi baki ya yi magana ba, amma ta ji daɗin abin da ya yi. Ita ma ta fahimci yau ya yi so sillent over, da alama akwai abin da yake gabansa sosai, dan haka ba zata ja tsokana sosai ba, saboda idan ta ce zata ja sosai zai iya yi mata illah dan yana aiki, yanzu tagama karatarsa tsab, tasan lokacin da zata ja shi da tsokana ba zai cutar da ita ba, wato idan ta same shi baya yin aikin komai, nan kam sakan jiki take yi ta hakura mashi. Hannu ta sake kaiwa zata shafi sajensa da nufin ta yi mashi bye bye. Carap ya capki hannun nata da hannunsa ɗaya, dan idan tana taɓa shi ɗin nan tana sanya mashi kasala. Kallon juna ido cikin ido suka yi ba tare da kowannansu ya furta word ba. A hankali ya saki hannun nata tare da yin ƙoƙarin juyawa ya cigaba da abin da yake yi. Ita kuwa a ranta ta ji lallai kafin ta tafi sai ta sake taɓa sajensa, dan haka yana saketa ta sake kai hannun zata taɓa sajen nasa. A wannan gaɓan wuyarta ya damko da hannunsa tare da janyota ta matso dap da shi har suna iya jiyo sautin numfashin juna. Dik da ya shake mata wuya bata damu ba, dan ta samu abin da take so ne, wato ya matsar da ita dab da jikinsa kenan. Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman lion chest ɗinsa, ɗayan hannun nata kuma ta shafi gefen face ɗin nasa. Tabbas ta ji shakar da ya yi mata, amma ta daure bata nuna alamar ta ji ba. Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Ke bakya da tsoro ne?". Cike da mamakinta ya yi maganar, har ga Allah tana bashi mamaki yadda bata nuna tsoro, kun san irin haka dole ya bawa mutum mamaki, wannan rashin tsoron da take nunawa yasa har yana jin kamar tana burgesa, yana san mutum mai confidence. Ɗan ɗaga idanunta sama ta yi ta yi fari da su, hakan ba ƙaramin kyau ya kara yi mata ba, ga shi ya tsareta da idanu, shi kansa yasan ta kara kyau matuƙa yadda ta yi da idanun nan nata, amma bai nuna alamar yaga ta yi hakan ba, sai ya kara ɗaure fuska sosai. Cikin wani irin sexy voice ta ce. "E to ban taɓa yin tinani a kan jin tsoron ba, amma tin da ka yi magana yanzu zan yi tinani in ga ko ina ji ko bana ji". Tana magana tana jujjuya idanu kyanta na kara bayyana matuƙa, ga shi suna kurkusa da juna sosai Ya fahimci iyashege ya yi wa yarinyar nan yawa, dan haka sai ya zare hannunsa daga wuyarta yana kawar da kallonsa daga kanta. "Big bro do you know something?". Ta faɗa tana cigaba da shafa kyakkyawan sajensa da hannunta ɗaya. Bai kulata ba ya mayar da hannunsa a saman mirrorsa yana ƙoƙarin bincikar in da Pretty take a halin yanzu. Kun dai san kingdom of power masarauta ce ta mahaddara Alqur'ani mai girma, King mahaddaci ne, ba karamar abu bane Black Tiger ya iya laluɓar Pretty a cikinta, sai in ta fito daga wajen da mahaddata suke ta kutsa ko ta irin part ɗin uncle Abbas da sauransu haka. So Black Tiger ganin Pretty zai yi mashi wahala matuƙa a cikin kingdom ɗin, sai ya zage. "Sau da dama ina challenging ɗinka da ka yarda mu yi muhawara kaki ko? Why? Ko kana tsoron zan kayar da kai ne?". Ta kai karshen maganar tana ɗaga mashi gera guda. Burinta kawai ya yarda rana ɗaya ya bata dama, idan ta fara faɗa mashi girman Allah, da niimomin Allah sai ya musulunta ba tare da ya shirya ba, idan kuwa bai musulunta ba to tabbas ta cire ran zai iya musulunta a duniya. Shiru dai bai kulata ba, kamar bai san da ita a wajen ba. Ƙasa ta yi da kafafunta da ta ɗaga, ta gaji har sun fara yi mata zafi, a hankali ta zame hannunta daga lion chest ɗinsa, kallan kofar fita ta yi, ta yi readyn guduwa sannan ta yi wasu maganganu ƙasa kasa kamar word biyu haka wanda bata bawa kowa damar jin me ta faɗa ba. Tana kai karshen maganar ta yanka a guje zata yi waje. Quickly ya juyo magic eyes ɗinsa, with his magic ya janyota ta dawo gabansa. Capka ya kai hannunsa zai yi wa wuyarta, zulle mashi ta yi ta faɗa kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya. Hannunsa yasa cikin zafa zai ɓanɓareta daga jikinsa, ina ai kin yarda ta yi, sai tasa magic ɗinta ta taresa. Me kuke tinanin ta faɗa mashi tasa ya harzuƙa lokaci guda haka?. Wlh Sweetie sai shirin Allah, dama masu shiru shirun nan basu iya fallewa da rashin kunya ba, ku duba lokacin da take forest tare da su Kamran, salihar yarinya mai natsuwa, yanzu gabaɗaya Ronnie ya wayar da ita sai kuma ta zama tantiriya a rashin jin magana ga tsokanar bala'i. Ganin ba zata sake shi bane yasa ya juya tare da ɗagata da kyau mai gabaɗayanta ya ɗaurata a saman lion chest ɗinsa, sannan ya nufi balconynsa da ita, magic walk ya yi hakan yasa ya isa da wuri. Tin da Sweetie take bata taɓa sanin a wani hawa yake ba, bata san yana da nisa da ƙasa sosai ba, da yake da elvator ko escalator suke haura sama sai bata ganin nisansa. Yana fita balconynsa ya tsaya a dab glass dake wajen. Sai kallan face ɗinsa take yi tana yi mashi tsiya na sambatu kamar haka. "Big bro kana da kyau fa, amma matsalar baka murmushi, dik da hakan kuma kyanka bai ɓaci ba". Cike da zolaya ta yi maganar. Hannunsa ya kawo saitin face ɗinta, kyawawan yatsunsa ya kyasta mata a saitin face ɗin nata, da sauri ta kai kallanta a kan ƴatsun nasa, kasa ya nuna mata a kan ta kalli wajen. Da yake bata san in da suke ba sai ta kai kallanta wajen with her full confidence. Ai tana ganin nisan kasa wani irin ihu ta kurma, a miliyan tasa hannunta ta saƙalo wuyarsa ta ƙanƙamesa sosai. Ihu take yi tana faɗin dan Allah ya yi hakuri ya riketa kada ta faɗi kasa. Kun san idan kana sama ka kalli kasa mai nisa har wani irin jiri zaka ji yana ɗebanka, ka ji kanka yana juyawa. Ganin ta tsorata sosai yasa tsabar mugunta irin nasa sai ya sa hannunsa da karfi ya ɓanɓarota daga jikinsa, tana ihu tana ƙoƙarin riƙesa ya jefata kasan kamar wata kayan wanki yana kallan face ɗinta. Datse idanunta gam ta yi tana ihu tana kalmar shahada, ta gama saddakarwa mutuwa zata yi, tin da take da shi bai taɓa yi mata abin da ya razanata har hanjin cikinta suka kaɗa ba irin wannan. Gabaɗaya komai na jikinta sai da ya girgiza, cikinta ya kaɗa matuƙa. Juyawa ya yi ya koma cikin bedroom ɗinsa ransa fes, a cewarsa ko ba komai yau ya yi maganin yar ƙaniya. Ita kuwa tana tsaka da kurma wannan ihu sai jinta ta yi a saman wani abin tattausa, a tinaninta dik kasa zata faɗa. A zabure ta waro idanunta waje tare da wani irin yunkurawa da karfi sabowa amai da ya zo mata da karfi. Wato Black Tiger ɗan duniya ne, da magic nasa ya yi amfani ya dawo da ita saman bed ɗinsa, ya jinjiga mata yayan hanji a banza kawai. Amma kuma ya ɗarsa mata tsoro sosai a ranta, ya nuna mata mutuwa kusa da kusa, ba ta ce mashi bata san tsoro ba? To da alama yanzu kam ta sani. Kasan bed ɗin ta sauko tare da durkushe gwiwowinta a ƙasa tana tari da karfi karfi ta dafe kirjinta da hannunta ɗaya, dan tsananin wahala da ta sha. Ƙoƙarin yin amai a wajen ta yi, amma ta kasa, dan aman yaki fitowa. Kamar ta fita a hayyacinta. A hankali Ronnie da ya shigo tun ɗazun ya matsa kusa da ita, shoulders ɗinta ya tallabo yana ce mata sorry. Tana jin voice ɗinsa ta yi saurin miƙewa tsaye tare da kai kallanta a kansa, sai dai tana miƙewa jiri ya kwasheta, dan har yanzu ƙwaƙwalwarta yana nuna mata tana faɗuwa ƙasa ne, a fili ta zame zata faɗi Ronnie ya riketa da kyau yana kara faɗa mata sorry. Shiru ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi ƴar ƙaniya, dama bata taɓa haɗa inuwa da Black Tiger ta sha lafiya ba na faɗa maku. Rikota da kyau Ronnie ya yi suka nufi waje yana kara ce mata sorry, sai rarraba idanunta take yi tana neman ta ita zata ga Black Tiger? Sai dai babu shi babu alamarsa a ɗakin, da alama ya fita. Kumbura kumatu ta yi a ranta ta kudurta idan ta dawo daga school yau ba zata kyalesa ya zauna lafiya ba, zata takura mashi sosai, sai ta fance wahalar da ita da ya yi. A yarinya bata daddara ba, muje zuwa buga wasa, zamu ke waye zai yi nasara. Kai tsaye Dining room Ronnie ya wuce da ita, bawan Allah shi yanzu ya dai'na tambayarta me Black Tiger ya yi mata idan ta je wajensa ya ganta a wahale, dan ya gaji da jin diramarsu, wani lokaci ma dariya suke bashi, wani lokaci kuma ya yi hawaye, kamar wasu maguna, basa haɗuwa inuwa ɗaya sam. A baki ya rinƙa bata breakfast ɗin tana ci har ta ƙoshi, sannan ya ce su je ya kaita school idan ta dawo sai su je wajen koyan mota ya fara koya mata. "Lovely bro kai baka yi breakfast ɗin ba". Ta faɗa kalamanta cike da kulawa sosai. "Sai na kaiki na dawo zan yi, time ya tafi ne". Ya faɗa tare da miƙewa, ya ratayo hannu ɗaya na school back ɗinta a shoulder ɗinsa. Hannunta ya ja tare da wucewa suka nufi waje. Bata sake sanya Black Tiger a idanunta ba har suka tafi school tare da rakiyar motoci guda gona ciff, ita da Floris suka tafi. Primary 4 aka sanyata bisa umarnin Ronnie, dan ya ce zai rinƙa koya mata karatu sosai a gida, ba zai yarda ta fara daga primary one ba dan ta girmewa hakan, ita kuma Floris tana jss two yanzu. Dikkansu gidan baya suka shiga, Ronnie yana tsakiyansu. Sai hira yake yi da Sweetie, ta kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa tana ta farinciki yau zata je school, har yanzu cikinta yana juya mata tana jin kamar zata yi amai amma kuma aman yaki fita. Black Tiger shi ma yasan ta kan tsiya. Ko da suka isa school ɗin sai da suka tsaya yi wa juna kalaman kauna na rabuwa da juna, daga karshe Ronnie ya ce mata. "Ki kula sosai da kanki, idan kin dawo daren yau zamu yi wata magana ki tina mun, sannan don't believe anybody kin ji?". Kai ta gyaɗa mashi tana kallansa. Alama ya yi mata da kansa a kan ta matso. Matsawa ta yi dab da shi, sumbata ya bata a kumatu yana murmushi, ita ma sumbatar ta bashi. Takaici yasa Floris ta buɗe kofar side ɗinta zata fita kenan ya yi saurin riƙo hannunta, a hanzarce ta dawo da kallonta kansa, while shi kuma a hankali ya kai kallansa a kanta. Da ido Sweetie ta bisu da kallo, sumbata ya bawa Floris ɗin ma a kumatu ita ma. Thank you ta furta ba tare da ta mayar mashi da martanin sumbatar ba ta fice da sauri tana tinanin kalaman master Devil in da yake sanar da ita yana matsanancin sha'awar Sweetie, ta yi mashi hanya ya sameta zai yi mata kyauta na musamman. Ita fa Sweetie sam bata kishi da Floris, saboda babu wata alaƙa ta soyayya a tsakaninta da kowa sai Kamran, shi kaɗai zuciyanta yake so, Ronnie san yaya da kanwa take yi mashi, shiyasa bata kishi da Floris, ita kuma Floris kishi take yi da ita sosai da sosai, kamar ta kasheta take ji. Floris kuwa ta yi master Devil alkawarin ranar partynsu Ronnie idan kowa yana cikin hidima a cikin empeir ɗin, tabbas zata kawo mashi Sweetie har cikin bedroom ɗinsa, daga nan sai ya ƙarisa sauran aiki, wannan agreement ɗin suka yi da shi, yanzu abin da yake jira kenan, a wannan rana ta partyn su Ronnie an shiryawa Black world gagarumin shirin da a tinaninsu Black Tiger bai sani ba, a daren ranar suka shirya sace Ronnie idan jama'a sun yawaita, a cewarsu Black Tiger ba zai iya ganinsu ba dan dare ne kuma abubuwa sun yi yawa, dik tunaninsu capacityn Black Tiger ya gaza haka, master ya tsara zai yi amfani da Sweetie da rana, da daddare su ɗauke Ronnie. Kai wato akwai tashin hankali fa. Sannan a wannan rana ta partyn akwai gungun mutanen da suka jima suna shirya hanyar kwatar birnin Black world daga hannun Black Tiger saboda ɗinbin arzikin da suke da shi, so zasu yi amfani da wannan rana ta party su yi shigar sunkuru su yakesu su kwace birnin. Daga gefe kuwa a wannan rana Duniyar shaiɗanu suke san zuwa ɗaukar autansu wanda shi kansa Black Tiger ɗin bai san da su ba, babansa bai bashi tarihinsu ba, so bai yi shiri a kansu ba, amma kuma zai iya zulle masu in har bai fita wajen wannan party ba, dan suna kan nemansa ne, fitar da zai yi zuwa wajen wannan party shi zai sa su gansa, suna ganinsa second ɗaya ya yi yawa zasu bayyana a in da yake. Abin da baku sani ba shi ne, gabaɗaya in da Black Tiger yake fa a tsare take, in dai zai kasance a cikin gidansa ko fada to bazasu iya ganinsa ba, already babansa ya tsare wajen, so hall da za'ayi taron babu tsari, dan bayan mutuwar babansa ya gina wannan hall ɗin, dan haka yana fita wajen za'a iya ganesa. Fatan yanzu kuna kan fahimtar ɓoyesa da babansa ya rinƙa yi na tsawon shekaru a hankali hankali. Shi kuma kunga bai san da wannan ba dikka, hakan ma tasa ya yi wa Ronnie alkawarin tabbas zai je wajen partynsu, shi Ronnie zai bawa cake idan ya yanka kafin ya bawa kowa, shiyasa na ce maku dukiya ta yi kuka, an ɓarnatar da ita a kan wannan taro, saboda manyan kai zasu je wajen, kujerun zama ma a musamman aka yi odersu daga ƙasar England, kujeru ne na masu bala'in kyau da tsada. In short abubuwa manya manya ne suke shirin faruwa a wajen wannan party. A ta ɓangaren Sweetie kuma ta yi shirinta tsab na zuwa wajen, ta kuma shirya sanya Ronnie ya fara dik abin da zai fara da sunan Allah, kai my people's akwai cakwakiya a wannan rana wlh, za dai mu gani. Gabaɗaya masu kaunar Ronnie a birnin sai murna suke yi, Black Tiger da kansa ya sanyawa wannan rana suna red diamond day, saboda a wannan rana zai fara kyauta da dukiyar red gold ɗinsu da suka samo a ƙarƙashin ƙasa, sai ya saka wa ranar red diamond day. Sai shiri suke yi, Ronnie buri ya cika zai shiga hospital ɗinsa ya fara aiki. Sannan kwana biyu tsakani akwai gagarumin Birthday party ɗinsa again, wato wannan birni akwai shagali idan abubuwa basu lalace ba a ranar partyn buɗe hospital. A tinaninku su waye zasu yi nasara? Duniyar shaiɗanu zasu samu damar ganin ɗan autan nasu har su ɗauketa? Master zai cinwa burinsa a kan Ronnie and Sweetie? Waɗan can gungun mutane masu san kwace birnin zasu cinwa burinsu? Sweetie zata cinwa burikan da ta tsara wa birnin a ranar partyn? Mu je zuwa. ••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Su Sweetie sai da suka wuce har class ɗinsu, sannan Ronnie yasa suka juya kan motocinsu izuwa gida cike da kewarta. •••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 40 🔥🔥🔥🔥DUBAI.🔥🔥🔥🔥 Ɗago da kallonsa a kanta ya yi da nufin ya tsawatar mata ta cire hannunta ya yi aikinsa. Sai dai kash, yana ɗagowa suka kalli juna sai ya ji tongue ɗinsa ta yi mashi nauyin ya daka mata tsawan, gabaɗaya sai ya ji wani iri a jikinsa, tamkar an sanya igiya an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗin nasa ne, ido cikin ido suka kalli juna a kurkusa, kun san yana da matuƙar wahala ku ga juna ido cikin ido zuciyoyinku basu amsa da wannan kallo ba, so har cikin ransu suka ji wannan kallo ya ratsasu. Ai bata san time da ta zame hannunta daga saman wuyan rigar ba, sai dai ji ta yi ya sanya hannunsa ya yi kasa da rigar. Shi kansa tin da yake dubata wlh bai taɓa mayar da hankalinsa a wani halitta tata ba sai a yau, a yau ɗin ma ba komai ne ya ja hankalinsa a kansu ba face tana zaune idanunta biyu, yadda ta zauna yasa gabaɗaya tula tulan nata sun tsastsaya cir, saboda babu bra daga ta ciki, so suna nan muraransu. Ga shi yadda ya ja wuyar rigar ta ɗan yi ƙasa sosai, hakan ya basu damar bayyana. Wlh sai da ya ji gabansa ya faɗi, lokaci guda ya nemi natsuwarsa ya rasa, da kyar ya iya cire audigar, hannunsa ma sai ɗan kerma take yi, tamkar wanda zai yaɓa wuta, gabaɗaya sai ya ji shakkar sanya hannunsa a waje, kamar dai ba jarumi Ramish namu na amana ba, lokacin guda ya zama ɗan farinsa, har wata ƴar guntuwar munafukar zufa ce take keto mashi a gafe da gefen face ɗinsa, lokaci guda ya shiga cikin wani hali. Ita ma dai cikin wani halin take, saboda yadda hannunsa ke taɓa fatar wajen gabaɗaya ya ruɗar da ita, sai wani mutsu mustu take yi tamkar wanda ake yi wa cakulkuli, da yake shi ma yana cikin yanayi sai bai fahimci tana mutsu mutsu bama. Da kyar ya gama mata, yana gamawa ya ɓallo maganninta ya miƙa mata, lokaci guda face ɗinsa ta sauya, gabaɗaya ilahirin jikinsa tsuma yake yi, a gaggauce ya juya ya nufi hanyar waje, ko tsayawa ta sha maganin a gaban idanunsa ma ba zai yi ba, yana miƙa mata adadin da zata sha cikin zafa ya wuce waje. Bai zame ko'ina ba sai cikin bedroom ɗinsa, da alama dai abar tasu ta gado ce ta motsa. Ga shi shi kuma ba mijin aure ba tare ya rage zafi, sai ya kwanta yana ɗan juyi a saman bed ɗin nasa. A gefe guda kuwa, Ummie tana nan tana shirya yadda zata samesa ta biya buƙatanta, wannan friend ɗinta mai kibar sai tsara mata yadda zata yi ta same shi take yi, harda bata shawarar ta bugar da shi da kwaya a cikin abinci ko ruwan sha tun da Sharifat ce mai kai mashi abinci, sai ta yi amfani da wannan damar ta zuba mashi kwaya, idan ya sha ta tinkaresa tsab zai yi abin da take so cikin fitar hankali ba tare da yasan ya yi ba(Auzubillahi). Aikuwa Ummie ta karɓi wannan shawara, har ta tsara ranar da zata aiwatar da wannan aiki. Wlh a duniyarmu ta yau mata irin Ummie su suka fi yawaita, Allah jama'a mu ji tsoron Allah, budurwar zuciya! Ƴarta tana san mutum ita ma tana so dan jaraba, shi kuwa ko ɗaya daga cikinsu bai ga abin ɗaga idanu ya kallah ba. A ɓangaren Leesharh kuwa, haɗiye maganin ta yi tare da komawa ta kwanta, zuciyarta cike tab da tinanin yadda suka kurawa juna ido cikin ido, lokaci guda tinanin Sharifat ya faɗo mata a ranta da yadda take nuna tsantsar kaunar da take yi wa Ramish. Auzubillahi minashshaiɗanirrajim ta furta tare da korar tinaninsa a cikin kwakwalwarta tana addu'ar Allah kada ya sake sanya mata tinaninsa a cikin kwakwalwarta, dan bata san tina abin da ƴar uwarta take mutuwar so. Daga haka ta datse idanunta gam tana ƙoƙarin tilastawa kanta yin barcin dole. A ɓangaren shi kuwa, a wannan dare dai barci ta gaggaresa, dan yaga abin da bai taɓa gani a zahiri ba, hankalinsa ta tashi sosai, sai juyi yake yi a saman bed barci yaki zuwa, ga shi abin takaicinma shi ne yadda tunanin tula tulan nata suka tsaya ga idanunsa da ƙwaƙwalensa, wai a hakan ma iya tudunsu ya gani ba dukka ba, dik ya rasa sukuninsa. Idan ya yi yunƙurin tilastawa kansa mancesu ma, sai face ɗinta ta fara yi mashi gizo. Daga karshe dai siririn tsaki ya ja tare da miƙewa zaune, take ya fara kuncin rai kamar wani ne ya yi mashi laifi. Miƙewa ya yi yana wani ɗaure fuska ya nufi toilet, abar ta miƙe zat taki kwanciya, dama ga yanayin kayan jikinsa ba masu rufin asiri bane, kana iya ganin halin da abar take ciki. Alwala ya shiga ya ɗauro yana kara kwaɓe fuska. Dadduma ya zo ya shinfiɗa tare da canza kaya zuwa Arabs jallabiya ya hau yin sallah ko zai samo saukin wannan jaraba. Ita ma dai Leesharh barcin ne ya kauracewa idanunta, tambayoyin da ya yi mata ɗazun a kan masu nikaf shi e yake ta yi mata yawo a cikin kwakwalwarta. 🔥🔥🔥🔥BABYN BABY.🔥🔥🔥🔥 Kwance take saman sofa mai zaman mutum uku, ta tada kai da laps na Ammo, tana sanye da Negligee mai shegen kyau launin maroon color, ta ɗaura silky-c a kanta, sai tashin kamshi take, ta gama shirin yin barcinta tsab. Tana tsananin kewan babynta, yau tsawon kwanaki biyu kenan bai kawo mata ziyara ba, sai dai su yi waya, shi ma wayar baya wuce two mins sai ya ce mata zai sake kiranta ya katse, baya yin awa biyu bai kira ta ba, hakan yasa ta gane abubuwa ne zuka yi mashi yawa, amma tana cikin ransa, shiyasa baya iya ɗaukar awa biyu bai kira ba, idan ya kira kuma minti biyu ya ce zai sake kira. Tabbas ta damu saboda tana kewarsa sosai, amma kuma ta yi mashi uzuri saboda tasan tana cikin ransa. Yau tsabar kewarsa da ya yi mata yawa ma bata iya cin abincin dare ba, yoghurt kawai ta sha, ba yadda Ammo bata yi da ita a kan ta ci wani abin ba, amma taki, ta ce a ƙoshe take, Ammo ta fahimci tabbas kewar mijin nata take yi shiyasa take cikin wannan hali. Shiru parlourn babu abin da zaka ji yana tashi sai kamshi da sanyi Ac, tv dake kunne ma ƙasa kasa yake magana ta yadda ba'a iya jin abin da ake faɗe a ciki sosai. Wayar baby dake kusa da ita ne ya fara ruri alamar shigowar kira. Ko bata dubaba ta san shi ne yake kiranta, dan ringintone na musamman ta saka mashi. Cike da zumuɗi ta miƙe zaune tare da kai hannu ta ɗauki wayar, kamar yasan ta cika da kewarsa, miƙewa tsaye ta yi ta nufi bedroom ɗinta tana satar kallan Ammo ta ƙasar ido. Kawar da kanta Ammo ta yi kamar bata gansu ba, oh su baby ma wai yanzu idan za'ayi waya da baby sai a gudu daga kusa da Ammo, kai wannan yarinya ita ma tana yin san ranta fa. Sai da ta shiga cikin ɗakin ta yi saurin ɗaukar kiran, yana gab da katsewa ta ɗaga. Faɗawa saman bed ɗinta ta yi tare da rungumo katuwar teddy ɗinta dake saman bed ɗin, ta kwantar da kanta a saman wata teddy tana turo baki, sai ta ji tamkar a saman kirjinsa ta kwantar da kanta. Shi kuwa tun da ta ɗauki wayar yake jiran ta yi magana, dan a ƙagare yake da san jin voice ɗinta, sun yi kewar juna. "Hello baby". Ta faɗa tamkar zata saka mashi kuka. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke wanda sai da ta ji zuciyarta ta amsa. "Baby ina kewanka sosai fa". Still cikin shagwaɓar nan dai ta yi maganar. Nisawa ya yi, shi kaɗai yasan halin da yake ciki a wannan dare. "Am so so sorry my baby, nasan dama dole kina kewata sosai, zan zo da safe In Sha Allah kin ji?". Yadda ya yi maganar kamar wanda yake cikin maye, voice ɗinsa ma bata fita sosai................. Sarai ta fahimci yana cikin wani hali ne, dan haka a matsayinta na mace ta gari, wato house wife material sai ta fara ƙoƙarin yadda zata ga ta kwantar mashi da hankali har ya ɗan samu natsuwa ko zai iya yin barci, Allah ya gani tana san mijin nan nata, ta yi takaicin ɓoye mata kansa da ya yi, da tabbas zata tsaya tsayin daga wajen nuna mashi soyayyar da zata sa ya mance komai, ba zata taɓa barin damuwa yasamu burgin zama a zuciyarsa ba, zata cikasa da soyayyar da koda an ɓata mashi rai a waje babu gurbin zaman wannan ɓacin ran, sai dai kash, ya ɓoye mata shi mijinta ne, yanzu dik abin da zata yi mashi ba zata yi wanda zai wuce tsakanin yaya da kanwa ba, saboda kada ya tuhumeta da cewa a ina ta koyi hakan kuma shi ba yayanta bane ya za'ayi ta yi mashi hakan? Kun gane me take gudunwa dai ai ko?. "Baby meyasa ba zaka zo yanzu muga juna ba?". Cike da kula sosai ta yi maganar........ "Aiki sosai nike yi beb, amma da safe zan zo". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Tom shikenan". Yadda ta yi maganar sai ya ji kamar tana da wata magana a ƙasa, dan haka sai ya ce. "Akwai wata matsala ce?". Kai ta gyaɗa tamkar tana a gabansa kafin ta amsa da. "E akwai maganar da nike san mu yi dama". ........ "Okey to faɗi ina jinki?". Yana magana yana pressing na laptop dake gabansa, alamar aiki yake yi sosai. "Baby anya maganar a zahiri ba zata fi a waya ba kuwa?". Ta jefa mashi tambayar. Zame hannunsa daga kan laptop ɗin ya yi, cikin natsuwa ya ce. "Na baki dikkan attention ɗina a yanzu yi maganar ina jinki". Hannu tasa ta ɗan toshe bakinta saboda dariyar da take guntsewa ya kusa kubce mata, da alama akwai abin da take ɓoyewa ne. "Talk now, am listening". Ya sake faɗa...... Juyawa ta yi ta gyara kwanciyarta, sannan ta janyo bargo ta lume a ciki, ta kara rungunar teddy ɗinta da kyau, sannan ta haɗe natsuwarta waje guda, cikin sanyin murya ta ce. "Dama baby a baya ka taɓa ce mun idan na samu wanda nike so in sanar da kai da kanka zaka yi bincike a kansa in ya cancanta sai ka aura mun shi ko?". A karshen maganar ta jefa mashi alamar tambaya tare da dakatawa domin tsammatan amsa daga garesa. Lokaci guda ya ji kirjinsa ta yi wani irin bugawa dum dum da karfin, bai san time ɗin da ya zaro idanunsa waje ba, cikin tashin hankali ya ture table ɗin laptop dake gabansa ya miƙe tsaye, sanye yake da kayan barci masu zubin pjs a jikinsa. A hankali ya taka ya nufi gaban wasu curtains dake cikin bedroom ɗin, yaye curtains ɗin ya yi nan take wata kofar glass ta bayyana, tura kofar ya yi ya fito balconynsa, daga sama yadda yake kallan garin gwanin ban sha'awa, sai dai shi kallan takaici yake yi gimbiya baby ta kona mashi ransa. Shiru ya kasa yin magana har sai da sake cewa. "Baby baka jina ne?"....... Sarkafewa voice ɗinsa ya yi, da kyar ya ɗan yi gyaran murya kafin ya amsa da. "Ina jinki". Kamar zata yi kuka ta ce. "Kana jina amma shi ne ka yi shiru?". A wannan karan jinjina mata kai ya yi tamkar yana a gabanta, sannan ya amsa da. "Sorry yanzu ina jinki yi magana".... Fuskarta cike da ƙayatattcen murmushi ta cigaba da cewa. "To yanzu baby na samu wanda nike so kuma yake sona, yanzu haka ya zo nan gida kawo mun ziyara kazo ku gaisa..........". Katseta ya yi cikin tsawa yana huci. "Waye ya bashi izinin ya zo gidan?". Yadda ya futar da words ɗin sai ya baka dariya, dan a harxuƙe ya yi maganar....... "Baby ai kai kace idan na samu mai sona na kawo shi zaka aura mun, to naga ina son shi shiyasa nace ya zo ku gaisa da kai and kuma wlh yana......." Tsawan da ya daka mata cikin kakkausar murya ne yasa ta haɗiye sauran maganganunta, bata yi zatan zai ɗauki zafi har haka ba. Cike da ɓacin rai da fusata a fili ya ce. "Ya jirani gani nan zuwa, sai na ji uban waye ya bashi izinin yin magana dake, kema wait for me tukun nan, bari na zo". Yana kai karshen maganar ya katse kiran ba tare da ya jira reply ɗinta ba....... Cikin zafa ya wuce ta ɗauki key ɗin motarsa, kamar ba shi ne ya gama cewa ba zai samu damar zuwa gidan yana aiki ba, tuni ya mance da aiki ya figi mota sai gidan Ammo. Ita kuwa, yana katse kiran ta miƙe a zabure, lokaci guda ta ji tsoro ya kamata, yanzu ya zata yi idan ya zo? Ta jefawa kanta tambayar. Da gudu ta diro kasan bed ɗin ta nufi waje. Bata zame ko'ina ba sai wajen Ammo, a lokacin ta koma cikin bedroom ɗinta. Tana zuwa ta sanar da Ammo wautar da ta tabba kuma ga baby nan zuwa. Siririn murmushi irin nasu na manya Ammo ta yi, cikin natsuwa ta fara faɗa mata yadda zata yi idan ya zo ta kwantar mashi da hankali har ya fahimci wasa take yi mashi, daga karshe ta gargaɗeta da kada ta sake yi mashi irin wannan wasa, domin zata iya sanyawa ya shiga wani hali, yanzu in da ya ɗauko mota a fusace ya biyo daren nan idan wani abin ya faru fa? Irin wannan wasa yana da kyau ta san lokacin yinsa. Sosai ta ji shawarin Ammo tare da yi mata godiya. Suna tsaka da hakan suka ji wani irin horn da aka rinƙa bugawa a gate ɗin a haukace, da gudu baby ta diro ƙasa ta nufi waje, da kallo Ammo ta bita tana tausayawa rayuwarta, saboda already baby ya faɗawa Ammo ɗin dalilin da yasa baya san kowa yasan matarsa ce, saboda familynsa, shi ɗan babban ahali ne masu ji da karfi da izza, so yasan abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa su yi accepting baby a matsayin daughter in low ɗinsu ba, wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ya ɓoyeta, shi kansa ba shi da kwarin gwiwar iya tinkarar familynsa da ita a matsayin mata, tsawon shekaru ya rasa yadda zai yi, ga shi yana santa kamar ya mutu, ba zai iya rabuwa da ita ba, musamman mahaifiyarsa da yasan ko zai mutu ba zata aminta da marasa asali ba, ya auri baby tun bata wuci 10 years ba a duniya, amma har yanzu ya gaza samun kalaman da zai iya tinkarar familynsa da shi wajen sanyasu su aminta da ita. Uhm babbar magana!!. Bedroom ɗinta ta nufa da gudu, tana zuwa ta haye saman bed tare da shigewa cikin bargo tana sauke numfashi da sauri sauri kirjinta na ɗan bubbuga mata da ɗan karfi karfi. Da karfi ya banko kofar bedroom ɗin nata ya shigo, har sai da yasa gabanta ya faɗi sosai, da ta yi niyar yin pretending kamar tana barci, amma turo kofar da karfi yasa ta zabura ta miƙe zaune tana zazzara idanu. Fuskarsa babu annuri ko ɗigo a kanta ya afko cikin ɗakin, ransa a matuƙar ɓace sosai, numfashinsa ma kama yake yi da mai huci. Cikin kakkausar murya ya ce. "Waye ya baki izinin yin magana da wani har ki kawo shi cikin gidan nan?". Sosai ta tsorata da ganin yanayinsa, jikinta na rawa ta diro kasan bed ɗin, dik sai ta ji ta kasa yin magana. Cikin kakkausar murya ya sake cewa. "Ina mutumin yake and ina Ammo da ta barki kika kawo wani cikin gidan nan"......... Cike da tsoron abin da zai iya aikata mata ta amsa mashi da. "Baby to ba kai kace dama in kawo dik wanda nike so zaka aura mun ba?". Hmmm a lokacin da ya yi mata wannan magana fa bata wuci 9 years ba a duniya, amma tsabar iyashege wai bata manta da zancen ba. Kuma shi cikin wasa ta yi maganar fa. "Ina mutumin yake na ce?!!". Cikin tsawa ya yi maganar. Satar kallan kofar fita ta yi, kafin ya ankara sai ganinta ya yi ta watso da gudu zata nufi waje. Ai cikin zafa a miliyan ya kai mata capka a ciki. Ihu ta so kurma mashi saboda tsorata sai kuma ta danne, shi kuwa tsabar yana cikin ɓacin sai sai ya yi wurgi da ita a saman bed tare da kara daka mata tsawar ta faɗa mashi ina mutumin da ta kawo ɗin yake?. A hanzarce ta miƙe tsaye tare da dirowa kasan gadan, jikinta na kerma amma taki faɗa mashi gaskiyar cewa wasa take yi mashi, dan Ammo ta ce kada ta yi saurin faɗa mashi su bari kishin tasa ta ɗan zafafa. Kin yin magana ta yi tana kumbura kumatu. Kara hasala sosai ya yi, ya zo har wuya, gadan gadan ya nufota da nufin kai mata duka tun da taki faɗa mashi ina mutumin, ɓacin rai yasa bai tsaya tambayar mai gadi akwai wanda ya zo gidan ne ko babu ba? Hankalinsa dik a kanta shiyasa ita ya fara tinkarowa kai tsaye. "Where's ur phone?". Ya faɗa cikin tsawa, ya yi maganar kuma yana kara tinkarota gadan gadan tana ja da baya har suka kurewa jikin bango. Rumfa ya yi mata da kirjinsa, yana huci ya sake tambayarta ina wayarta? Dan a tinaninsa yanzu kenan tana hira da maza ta wayar, dan haka a yanzu zai yi rugu rugu da wayar ba kuma zai sake saya mata wani ba, sai yanzu ya gane ashe kuskure babba ya tapka da bai sanar da ita cewa ita matar aure ce dan haka ta nisanci mazan waje ba, yazama dole yau ta san matsayinta. Shiru ta ki yi mashi magana, hakan ya kara zafafa kunan da ransa yake yi, cikin fushi ya cire hannu zai ɗauketa da gigitaccen mari. A hanzarce tasa hannu ta kare fuskarta haɗe da fashe mashi da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Dakatawa da yunkurinsa ya yi yana huci sosai, ya ɗauki zafin da har zata kaisa ga aikata aikin danasani, shi da bai taɓa dukan mace ba yau ya kwantanta, kuma a kan wadda yake kauna fiye da komai, sai ya ji rashin daɗin hakan a ransa. Cikin zafa ya juya zai je wajen Ammo ya ji dalilinta na barin baby ta kula wani namijin bayan ita tasan komai. Yana juyawa baby ta yi saurin riƙo hannunsa tana kuka. Ƙasa ta zube gwiwowinta a gabansa ba tare da ta saki hannun nasa ba, cikin kuka ta ce. "Tin da nike da kai ban taɓa ɓata maka rai ba a rayuwata sai yau, tabbas ba zan manta da wannan rana ba a rayuwata, ka yi hakuri baby ba zan kara ba, na tuba ka ji? Bana fatan wara rana ta zo wadda zan ɓata ran wanda na fi so sama da komai a duniya, wanda ya so ni ya kuma sanyani da farincikin da ban taɓa zata zan shiga ba a rayuwata, tabbas na yi kuskure". So mugun abu ne wani lokaci, lokaci guda ya ji zuciyarsa ta sanyaya, jin kukanta yasa ya ji zuciyarsa ta karaya, yana santa baya san kukanta. Dan haka a hankali ya juyo gareta yana sauke ajiyar zuciya. Ɗan duƙawa ya yi yasa hannunsa ya ɗagota, sai hawaye take ta shararawa. Rungumeta a jikinsa ya yi yana jin zuciyarsa ta sanyaya. Sai shessheka take yi, kukan gaske ta yi, dan bata taɓa tinanin ransa zai ɓaci har haka ba, sai dik ta yi nadamar abin da ta aikata. "Baby ka yi hakuri ka yafe mun ka ji?". Ta faɗa tana kara shigewa jikinsa. Kasa ƙasa da kyar ya iya cewa. "Babu komai bab ɗin babynta, komai ya wuce, yanzu ki faɗa mun ina mutumin yake sannan meyasa zaki fara soyayya da wani ba tare da kin sanar da ni ba?". Wato dai har yanzu bai huce ba, buƙatarsa a faɗa mashi ina mutum yake kawai. "Am so sorry my baby, wasa nike yi maka, ni babu wani da nike so a duniya sai kai". Wani irin ajiyar zuciya mai sanyin gaske ya sauke, cikin sauri ya ce. "Are u sure?". Kai ta gyaɗa mashi alamar yeah. Ai bai san lokacin da ya rungumeta kam a jikinsa ba, bai ma san time da ya hau zuba mata ruwan albarka ba, cikin sambatun nasa ne yake haɗawa da. "Kada ki yarda ki kula kowa, ke ɗin mallakina ni kaɗai". ....... "Baby mallakinka kuma?". Ta faɗa irin like bata san komai ba. Kai ya jinjina mata tare da amsa mata da e. "Baby to kenan ba zan yi aure ba tun da ni mallakin ka ce". Cikin shagwaɓa ta yi maganar dan ma ya ɗauka har yanzu yarinta na damunta bata san komai ba........ Wato ita ma baby yar duniya ce fa, tasan kan tsiya kala kala, wai ya ɗauka har yanzu yarinta na ɗawainiya da ita bata san komai ba. "Babu wanda zaki aura sai babynki, ke ɗin matata ce ni kaɗai, dan haka kada ki kula kowa kin ji?". Da alama yana out of control yake wannan sambatu, dik dan murnar bata kula kowa bane fa, kamar ba yanzu ya gama bambami kamar zai tashi gidan ba. "Baby kai zaka aureni kuma?". Ta tambaya like bata gane me yake nufi ba........ "Yeah ko baki san hakan ne?". Ya jefa mata tambayar tare da ɗan raba jikinsa da nata yana kallan face ɗinta dan yaga reaction ɗinta. Tafukan hannayenta ta kai ta rufe face ɗinta tana murmushi. Shammatarta ya yi ya ɗauketa cak sai saman bed yana faɗin. "Kin ɗaga mun hankali over, kin sa na ji wani irin, dan haka yanzu zo mu yi hira babu in da zan je, kwantar mun da hankali kamar yadda kika ɗaga mun, yau i think ma a nan zan kwana". Ya kai karshen maganar yana kwanciya da ita a saman bed ɗin. A cikin kirjinsa ta tura kanta tana faɗin. "Zan ji daɗi idan ka kwana a nan, dama haka nike so, kwantar da hankali kuma yanzu kuwa zan kwantar maka". Rungumeta sosai ya yi tare da ja masu bargo ya rufesu har kai. .............To baby sai dai mu ce asuba ta gari Allah yasa iya barci kawai baby zai yi....👀🥱 Bari mu leƙa wani part mu dawo muga ya za'a kwantarwa da baby hankali, sai mun bi kwakkwaf😅 🔥🔥🔥BLACK WORLD.🔥🔥🔥 Yau ta kama Sartuday, bayan kwanaki biyar kenan da fara zuwan Sweetie school, daren yau za'ayi babban partyn su Ronnie. Tin safe ake ta shirye shirye, kayan da Black Tiger ya sayawa Ronnie da zai saka a wajen wannan party lallai ba'a taɓa wani ɗa da ya taɓa sanya kwantankwacin irinsu a faɗin birnin ba, dan kuɗin kayan kawai ya kusa kuɗin jirgi guda ɗaya cikin jiragen Black Tiger. Tun kwana uku da suka wuce Ronnie da Sweetie suka haɗu suka zaɓi kayan da suke ga ya yi masu da irin design da suke so, kayan ya haɗu matuƙar haɗuwa, three-piece suit ce ajin karshe a tsada na Ronnien, cover shoes da zai haɗa da kayan ma almost hundred million take. Ita kuwa Sweetie dama wani irin daddatsetsen gown ya zaɓa mata wanda ya sha kwalliyar duwatsu na alfarma, kayan sun kai makurar haɗuwa, sai dai fa ita da Floris aka saya masu iri guda, kuma Ronnie ne ya ce hakan, dan shi har yau har gobe yana san Floris sosai, matsayinta bai canza a zuciyarsa ba, ita ce dai ta ja baya da shi. Kayan nasu ita da Ronnie kalarsa ɗaya, yadda kuka san amarya da ango, dikka milk color ne, sai murna Ronnie yake yi ana ta hidima, jama'a na ta kai koma, dama jiya za'ayi partyn fa, sai Sweetie ta ce da Ronnie a ɗaga zuwa yau saboda girma da falalar ranar jumma'a bai kamata su yi party a ranar ba. Aminta ya yi da hakan shiyasa ya riko yayansa da a ɗaga wannan taro zuwa yau, da yake Black Tiger bai san dalilin ɗagawar ba sai ya yarda, da yasan saboda addinin Sweetie ne ba zai yarda a ɗaga ba, saboda bayan san musulunci, a jininsa tsanar addinin take. Kada ku manta autan ruhohi ne shi ɗin, kunga tsanar addinin a jininsa take. Abin da baku sani bama, da Ronnie ya same shi da batun dakatar da halaccin luwaɗi a birnin sai ya ce kowa yana da ƴancin yin abin da yake so, dan haka shi ya halatta yin hakan, kada Ronnie ya kara zuwa mashi da wannan zance kuma kada ya kuskura ya hana kowa aikata luwaɗi ko zina, shi ya yarje masu su yi, su more rayuwarsu. Da farko Ronnie ya damu sosai, har yake jin kamar ya gudu ya bar birnin saboda kyamar abin dake ransa, amma Sweetie ta tsaya tsayin daka wajen nusar da shi cewa ya yi hakuri watarana komai zai wuce, ba'a da'awa cikin sauki dama, kuma dama yadda suke ƙoƙarin nan dole shaiɗan ba zai so hakan ba, idan shaiɗan ɗin ya gwada ringayarsu ta ɓangarensu suka ki yarda Allah ya tsaresu daga sharrinsa, to sai ya koma masu ta wani ɓangaren, tana da tabbacin shaiɗan ne ya koma jikin Black Tiger yasa yaki yarda da wannan doka, dan haka ya kwantar da hankalinsa zasu yi nasara a kan big bro, da sun yi nasara kuma shikenan komai zai tafi yadda suke so, da kansa zai yarda da dokar, su zasu zama masu kafa doka kai tsaye ma ba sai sun ji ta bakinsa ba. Da kyar dai Sweetie ta iya shawo kansa ya yarda, dik wani abin da Sweetie zata ce addininta ya yi hani da shi to shi kuma Black Tiger sai ya halasta wannan abin wa ƴan birnin, dik dan kiyayyarsa ga Musulunci, amma dik da haka Sweetie bata taɓa nuna ta damu ba, saboda tana koyi da annabawan Allah waɗan da suke da hakuri da juriya mai tarin yawa dan cinwa nasara...... ALLAH KA BAMU IKON YIN KOYI DA SU. ••••••••••••••••••••••••••••♥️ An ƙawata hall ɗin da za'a gudanar da wannan party matuƙa, yanayin tsarin hall ɗin hakika ya ƙayatar kuma kowa ya gani yasan anzubar da makuɗan kuɗaɗe ba kaɗan ba. Kayan Ado wato decorations masu zafi da tsantsar kyau. Yanayin theme na wajen launin white and gold ne, an zubawa gold ɗin kwayaye masu bata haske a in da suka kara haskaka wajen matuƙa, gold ɗin ya kara haske da ƙawata wajen. A gabaɗaya wajen an ƙawata shi ne da wasu irin kyawawa kuma tsadaddun balloons, furanni masu kyau, da kujeru masu rufi (chair covers) da ribbons masu launin gold and white. A saman haɗaɗɗun tables dake wajen gabaɗaya akwai wasu centerpieces masu kyau irin su furanni, kyandiru da fitilu masu kyalli da suka kara ƙawata wajen. Tables na wajen sun kasance a tsari mai kyau. Table da tsadadden kujerar da shugaban party zai zauna wato VIP table a gaban hall ɗin yake, yana fuskantar kowa kenan. Wajen da aka shirya abincin da aka shigo da su dan rabawa a wajen part ɗin yana ɗan nesa da wanen tables ɗin. And manya manyan fitilu dake wajen masu duhu ne amma na alfarma, ga wani katan chandeliers mai wuta launika daban daban da ya kara ƙawata wajen a sama tsakiyar hall ɗin. Wajen kujerar zaman Ronnie namu and Black Tiger namu ya kasance da ƙarin haske na musamman don jama'a su samu damar ganinsa da kyau. My people's wajen nan ya haɗu, kuɗi sun yi kuka, tun daga kan tsarin wajen zaku gane ɗan gata kuma shalele ne zai yi party, abin ya haɗu fiye da tinaninku. Shi kansa Black Tiger sai shirye shiryen zuwa wajen yake yi, dan tun karfe 4 na yamma za'a fara, kwana za'ayi ana yi. Ronnie kuwa tini ya gama shirinsa, dan yau rana ce ta musamman a garesa, yau zai shiga office ɗinsa a matsayinsa na babban Dr, apart from this hospital ɗin gabaɗaya mallakinsa ne. Ku kunsan abin ba'a magana sai shiru!!. Tin karfe uku Ronnie ya tafi wajen part da nufin Sweetie zata biyosa daga baya, dan ita ta ce sai 4:30 zata zo, zata ɗan yi barcin rana ne, ya so su jera a tare, amma taki yarda. Sam bai nemi Floris ba, saboda yana tinanin zata zo a tare da Sweetie. So sai ya yi gaba, ya sha kwalliyarsa, sai dai har yau yana saka waɗan nan chairs and ring ɗin, ga earing, a yau ma dik ya zubasu a jikinsa, ya yi kyau kam matuƙa sai dai haramun ne, amma ya yi wa Sweetie alkawarin a hankali hankali zai dai'na sakawa In Sha Allah, ta taya shi da addu'a. Kun san sabo da yin abu barinsa lokaci guda abu ne mai wahala Sai dai kuma tana can part na master Devil ba tare da sanin kowa ba, akasi aka samu tsakaninta da master ya yi mata fyaɗe, ya yi mata fyaɗen kuma ta ji ciwon sosai da yasa ta rasa jini sosai, kun san ba za'a haɗata da master ba dama, shararren mai bawa ƴan Wrestling horo, zakwakuri kuma zakaran da ya buge kowa except Black Tiger and Ronnie a faɗin birnin, namiji mai ji da karfi da lafiya ita kuma ƴar yarinyar da bata wuce Sweetie ba, da kaɗan ta fi Sweetie fa, kun ga kuwa dole karonsu ba zai yi kyau ba, ya kuwa yi mata fata fata saboda bashi da imani da tausayi, ko da yake shigarsu na banza ya ja masu ai, yana kan network ta samesa, shi kuwa ya cika aiki ya rage zafi da ita, ɗan ikka, ko da yake ba laifinsa bane, dik maza masu yin gym shegen jarabar tsiya suke da shi, saboda gym da suke yin nan yana kara buɗa jijiyoyin jikinsu ya faɗaɗa halittarsu hakan yasa sha'awarsu yake yawaita matuƙa ta yadda ba zasu iya zama babu mace a kusa ba. So master yana tsoron fitar da ita zuwa hospital dan a iya saninsa yasan cewa budurwar Ronnie ce ita, so fitar da ita zai iya haifar mashi da babban matsala mai girman gaske, hakan hasa ya turata cikin toilet ɗinsa, a cikin jacuzzi ya sanyata ya rufe kofa da key, jininta na ta zuba har ta rasa ranta ba tare da ya sani ba, shi a cewarsa sai dare zai ɗauketa zuwa hospital a lokacin babu wanda zai sani, bai san cewa rai ya yi halinsa ba. Sai dai fa dik abin da ya faru Black Tiger ya sani, amma ko a jikinsa saboda bashi da wata alaƙa da hakan, dama Floris Ronnie ya kawota empeir ɗin, dan haka shi ko cin namarta ɗanye ake yi ba abin da ya sha mashi kai, shi idan kunga yana magana a kan abu to fa ta shafe shi ne, idan bata shafesa ba ko kallo baya ɗaga idanu ya yi. So dik abin da suke aikatawa yana sane da kowa. Fyaɗen da master ya yi wa Floris ne yasa bata zo janyo mashi Sweetie ba, kunga babu ta hanyar da zai samu Sweetie, da ya tabbatar wannan dama ta kubce mashi, cike da ciza yatsa na zafin rasa wannan dama ya fara ƙoƙarin shirya ta yadda zai yaudari Ronnie ya fitar da shi daga birnin, su je wajen birnin ya biya buƙatansa da shi kafin ya halaka shi, amma fa dik a tafin hannun Black Tiger yake dik wani shirinsa........... Hmm da shi ya raina capacityn Black Tiger ne, a tinaninsa ai baya kallan cikin ɗakinsa shiyasa idan ya shiga cikin yake sheke ayarsa son ransa. Bai san gar Black Tiger ya san komai ba, dik sheke ayar da suke yi shi da su Oxil yana sane da su, harta aman da Ronnie ya rinƙa yi ranar dik yasan da hakan. (Wato guy ɗin nan Black Tiger ɗan duniya ne, wato dik wani iskancin da suke yi yana gani?🤔 Anya Black Tiger yana da feeling kuwa?🤔 Ina ƴan team ɗinsa? Maza ku fito ku faɗa mana ya aka yi yake iya kallan dik wani iskanci kuma baya jin komai?🤔) ••••••••••••••••••••••••••••••••••••♥️ Da misalin karfe huɗu dai'dai bayan Sweetie ta yi sallar la'asar, wanka ta tsantsara, ta shirya cikin wannan gown ɗin, da kanta ta gyara gashin kanta, Ronnie ya ce zai kawo mata mai gyata ta ce bata so, zata yi da kanta, dan haka da kanta ta gyara kayanta. My people's Sweetie ta yi masifar kyau a cikin waɗan nan kaya, omg, her wellcome and goodbye so masha Allah, ta ko'ina tana cike ɓulɓul, yar 13 years kamar wata ƴar 15, sai kara cika take yi dan hankalinta a kwance yake tana samun farinciki sosai daga bro ɗinta Ronnie, wani ɗan siririn chain na zinari da Ronnie ya bata ta sanya a wuyanta, ɗaya daga cikin chains da yake sakawa ne, ta ce ya yi mata kyau sai ya bata, tsadar bala'i ne da ya shi. Kara haskakawa gurun wuyarta ya yi, ga fararen hakwaranta na kara haskawa, wlh kyan da ta yi a yau baki ba zai iya faɗarsa ba, ku hasko yadda wannan golden hair ɗin nata yake kyalli, ba'a gyara shi bama tin ainahinsa mai kyalli ne bare kuma ya sha gyara? Ku kanku kun san dole ta tafi da imanin dik wanda zai kalleta. Wasu shegun high heel ta sanya a kafafunta, irin covers ɗin nan ne, rigar tata na ja mata har ƙasa, a gaban mirror ta tsaya, ta juya ta sake juyawa, ita da kanta tasan ta yi kyau. Black Tiger yana ƙoƙarin nasa shirin shi ma, so hankalinsa sam sam baya a kanta. Haba cikin wani irin taku mai kama da tafiyar hawainiya ta nufi waje, sai tashin kamshi take yi, kai tsaye bedroom na big bro ta nufa, tana tafiya tana wani yauki, dik Ronnie ya koyawa yarinyar nan sanka sanka na iyashege wlh, kowani rana sabon babi take buɗewa. Dai'dai lokacin da ta buɗe kofar ta danno kanta ciki, shi kuma yana tsaye a kusa da bed ɗinsa yana ƙoƙarin ɗaura necktie na wuyarsa. Ya subhanallah, my people's Black Tiger ya haɗu, idanunsa kalar nata sak dama idan baku manta ba na faɗi wannan, yadda kuka san ya karawa idanun kala, sai suka yi olive sosai, da alama hankalinsa a kwance yake. Sanye yake da three-piece suit shi ma irin na jikin Ronnie, da kalar da komai iri ɗaya ne, ya yi masifar kyau sosai, mutum zai iya ɓata tsawon wuni guda yana kallan guy ɗin nan bai gaji ba! Dark black curly hair nan nasa ya yi mata wani irin gyara na musamman da ya sha bambam da gyaran da yake yi kullun, kai daga ganinsa kasan yau rana ne na musamman a garesa. Tana shigowa ƙamshin perfume ɗinta ya haɗe da nasa sai ya bada wani sihirtatcen kamshi na musamman. Tin da ta shigo idanunta suke a kansa, baki ta saki tana kallah halittar Allah, lallai ba shakka Allah ya yi halitta a wannan waje, Black Tiger ya haɗu. Like wow abin yaƙayatar over, ita da shi sai suka fito tamkar amarya da ango, saboda yanayin shigarsu. Sarai ya ji shigowarta, amma yaki ɗagowa ya kallesa, dan kada ku manta kashin wuyarsa ta zame mashi. Tin daga kan haɗadɗun cover da suke kafafunsa har zuwa dark black curly hairnsa ta bi da kallo a cikin zuciyarta tana furta wow. Kuma abin da zai baku mamaki da ita dik wannan yabon kyansa da take yi tana mutuwa da san kallansa fa bata taɓa jin sansa a ranta ba, ita dai Kamran take so, shi kuma yanayi mata kyau tana jin daɗin kallonsa, hasali ma ta fi jin Ronnie a ranta sosai fiye da shi, ko kila saboda krista ne yasa hakan?. Misali yanzu da ace babu Kamran to tabbas zata iya yin soyayya da Ronnie, amma ban da Black Tiger, amma fa Kamran na raye, dan haka babu kowa a ranta sai shi. Cike da yanka irin ita mai class ɗin nan ta tako izuwa gabansa, zuciyarta na harbawa da karfi tasa hannu ta riko necktie ɗin nasa da yake ƙoƙarin ɗaurewa tana faɗin. "Big bro bari in hutar da kai". Sam baya san ɗaga ido ya kalleta, dan haka sai ya yi ƙasa da idanunsa wai dan ma kada su haɗa ido. Sai da unexpect ya sauke kallan nasa a kan yatsun kafafunta. Waro idanu ya yi da kyau a kansu, da yake ta cire takalman nata a kasan carpet dake gaban bed ɗin kafin ta ƙariso in da yake, hakan ya bashi damar ganin yatsunta, sosai ya zaro idanunsa waje a kansu. Kafarta na dana yatsunta guda shidda ne ba biyar kamar na sauran mutane ba. Ganin hakan ya yi mugun ɗaga mashi hankali, lokaci guda ya ji jiri ya ɗebesa, kafin ya ankara ya tafi zai kifa, gabaɗaya ya rinjayeta suka faɗa saman mattress ɗin, tsikar jikinsa ne ya fara tashi sosai na ganin yatsun nata da ya yi. To me dalili kenan?. Jikinsa har kerma yake yi, lokaci guda ya ɗago da kansa da kallonsa a saman face ɗinta, ya danneta ta yadda ko numfashi bata iya yi da kyau. A take idanunsa suka rikiɗe suka yi jajir kamar wuta, kwayar idanunsa suka tura olive sosai, harta kumatunsa sai da ya fara kerma kamar mai rawan sanyi, wani irin yanayi da ya shiga ya in ka gansa sai ka razana. Lokacin guda ya fara yin wani irin jijjiga mai karfi gaske a kanta. Wani irin mahaukacin razana ta yi, bata san lokacin da ta fara ambatar sunansa da kyar da kyar tana ƙoƙarin yadda zata yi ta turesa daga kanta, da yake yana kanta sai tana iya jiyo yadda zuciyarsa take harbawa da karfi karfi gudu gudu sosai na wuce misali. Hankalinta ne ya ƙara tsananta tashi sosai, cikin ruɗani ta rinƙa ƙoƙarin turesa daga kanta, amma ta ƙasa koda motsa shi. Shi kuwa ya ɗauki a kallah minti biyu yana wannan jijjiga kafin gabaɗaya ilahirin jikinsa ya sake alamar ya mutu ko ya suma a kanta. Tashin hankali, to ita yanzu tayaya zata iya cetan ranta? Kun dai san ba iya ɗaukar nauyinsa zata yi ba ko? Ga shi ko numfashi bata iya yi, wai menene ma ya rikiɗashi lokaci guda haka? Meyasa ya shiga wannan hali daga ganin yatsunta shidda ne ba biyar ba?. Uhm akwai matsala fa. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Azabar da ta ji tamkar zata mutu ne yasa ta ware tafukan hannunta tana san yin amfani da magic ɗinta ta ɗaga shi daga kanta. Ta kuwa yi sa'a ta samu damar yin hakan. A gefenta ta kwantar da shi, sannan ta shiga mayar da numfashi da karfi karfi, kun san idan mutum ya rike numfashinsa na ƴan sakannin yana saki da karfi karfi zai fita. To haka ita ma ta yi, ta kwanta shiru tana mamaki wani irin masifa ce yau take shirin faruwa da su kuma? Black Tiger da suma? Kai abin babba ne dik da a wajen Allah wannan ba komai ba ne, amma da mamaki daga kallan yatsun kafafunta sai ya suma, dik taurin zuciyar da balai'nsa, ga magic, amma farar ɗaya ya sume haka? Kai akwai matsala gaskiya. Ta ɗauki a kallah 3 mins kwance shiru haka kafin ta samu numfashinta ya daidaita, miƙewa tsaye ta yi da kyar, har lokacin tana yin ɗan nishi kaɗan kaɗan alamar da gaske ya yi mata nauyi over. Juyo da kallonta a kansa ta yi, yana kwance flat tamkar babu rai a jikinsa. Shiru ta ɗan yi tana tinanin abin da ya faru da ita daren jiya ga mafarke mafarken da ta rinƙa yi. Me ya faru daren jiya kenan?. Saman bed ɗin ta haye, a daidai wajen kansa ta zauna tare da haɗe hannayenta dikka biyu ta tallabo kumatunta idanunta a kan face ɗinsa. Cikin natsuwa ta fara ambatan sunansa da big bro. Sai dai ina ko motsawa bai yi ba, cire hannunta ɗaya ta yi daga kumatunta ta mayar saman nasa kumatun. A zabure ta zare hannunta daga jikinsa saboda wani irin azabbabben zafi da jikinsa ya yi kamar wuta, lokaci guda jikinsa ya yi wani irin zafin zaw. Miƙewa daga zaune ta yi ta durkusa a kan gwiwowinta, sannan ta kai hannunta saman necktie da yake ƙoƙarin ɗaurawa kafin ya sume. Kwance tie ɗin ta yi ta ajiye a gefe, sannan ta hau ɓalle botiran rigar jikinsa, ta buɗe rigar sama ya rage saura na biyun da na ciki. Addu'oi ta fara tofa mashi tana fatan Allah ya tashi kafaɗunsa, tana san zuwa ta kira Ronnie amma bata san tafiya ta barshi dan bata san me zai iya faru a bayanta ba, baya bata kaɗan. Ta jima sosai tana yi mashi tofin addu'oi ba tare da wata barazana ba, sannan ta sauko ƙasa ta nufi toilet, bowl ta ɗauko mai ɗauke da ruwa mai sanyi a ciki, sai towel fari tas ɗan madaidaici da ta ɗauko. Har zata nufosa sai ta ce bari ta ɗauko almakashi dan ta tsaga singlet ɗin jikinsa tun da shi bashi da botir bare ta buɗesa kamar yadda zata buɗe sauran kayan jikinsa, ba iya ɗagasa zata yi ta cire shi ba kuma, so dole ta tsaga shi da almakashi kawai. Dan haka sai ta duba a cikin drawers ɗinsa, a wajen mirror ta samu almakashi. Har zata juya ta bar gaban mirror idanunta suka sauka a kan wajen partyn Ronnie da abin da yake faruwa a wajen. Shiru ta ɗan tsaya tana kallan gabaɗaya al'ummar dake wajen, lokaci guda ta ji wani irin mummunar faɗuwar gaba a lokacin da taga fuskar Ronnie, shi kuwa sai murna yake yi yana farinciki. A cikin zuciyarta ta ce. "Dik in da faɗuwar gaba yake ba alkhairi bane yake biyowa baya, ya Allah ka dubemu da idanun rahma, ina jin kamar wani abin ne zai faru, ga big bro ya suma, idan na tina Ronnie ko in na gansa sai gabana ya faɗi, ya Allah ka juya mummunar kaddararmu izuwa kyakkyawa ko kuma ka sassauta mana ita daga cikin niimominka ya rahmanin rahim". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta nufi Black Tiger, tana tafiya tana waigo mirror nasa. Har ta haye saman bed ɗin hankalinta na a kan mirrorn. A gefenta ta ajiye bowl and towel ɗin, sannan ta hau cire botiran sauran kayan ciki, tas ta cire kafin ta sa almakashin zata tsaga farar singlet ɗin ciki. Tana kan yankawa sai ta ji mirror ta yi wani irin kara. A tsorace ta kai kallanta kansa jikinta na kermar kirjinta ya bada bugun dum dum lokaci guda. Sai dai ko da ta kai kallanta a kai bata iya gane komai ba, domin wannan kara da ya yi alama ce da akwai matsala a birnin, so ba aikinta bane ba zata gane ba, dawo da kallonta a kan abin da take yi ta yi. Wani irin zabura ta yi a lokacin da ta kalli ta yanke jikin Black Tiger da almakashin da ta kai kallanta a kan mirrorsa, karar mirrorn ne ya razata har ta yankesa bata sani ba. Sosai ta tsorata tsikar jikinta na tashi ganin jininsa jajir kamar wuta. Sai dai kuma jininsa na fita gabaɗaya ɗakin sai da ya amsa, a take wani irin haske mai karfin gaske ya gauraye ɗakin, zuciyar Duniyar shaiɗanu ta buga alamar autansu ya samu wani ɗan matsala kenan, take suka hau kururuwa mai karfin gaske, sai dai ita bata ji saboda ɗakinsa babansa ya tsareta, idan baku manta ba sai da ya fita main parlour ne ma Duniyar shaiɗanu ta iya gane cewa yana raye ko? To basa iya gane komai idan yana ɗakinsa, yanzu ma saboda jininsa da ya zuba ne yasa suka ji zuciyarsu ta girgiza. Da alama Sweetie zata shiga komarsu, dan kuwa wanda ya fitarwa da Black Tiger jini wlh ba zasu taɓa kyalesa ya rayu ba, sai sun ga bayansa! Wannan alkawari ne, a kan autansu babu abin da ba zasu yi ba!!. Hmmm akwai matsala fa, Sweetie ita ta fara ganin Black Tiger ido da ido, ita ta fara sa ya fita fada har duniya tasan face ɗinsa, yanzu kuma ita ta fara fitar mashi da jini a jiki!!. A gaggauce tasa wannan towel ɗin ta hau goge mashi jinin jikinta na kerma. Ko kaɗan jinin yaki tsayawa, hakan ba karamin ɗaga mata hankali ya yi ba, da gudu ta diro kasan bed ɗin ta nufi waje dan ta je ta kira Ronnie ya zo ya kawo mata agaji, dan abubuwan is getting out of hand a gareta. Sun fi karfinta!. A tsakiyar main parlour suka ci karo da Ronnie, karo suka yi ta yi baya zata faɗi tana jan numfashi da sauri sauri. Rikota da hannu ɗaya ya yi yana faɗin lafiya kuwa take irin wannan gudun?. Ƙasa yin magana ta yi tana sauke numfashi da ɗan sauri sauri. Allah sarki Ronnie, haka kawai ya ji jikinsa ta bashi ba lafiya ba, saboda har cikin ransa ya ji wannan fitar jini na Black Tiger, shiyasa ya ce bari ya zo ya duba. Da hannu ta nuna mashi sama ta ƙasa yin magana. Hannunta ya ja da gudu suka haura sama ɗin yana jin gabansa na faɗuwa. A yadda ta bar Black Tiger haka suka shigo suka same shi. Da gudu Ronnie ya haye bed ɗin yana tambayarta me yake faruwa?. Bata ɓoye mashi ba ta faɗa mashi dik abin da yake faruwa. Zaro idanu sosai ya yi kafin ya ce mata. "In kalli kafan naki da ya gani ya suma" a hanzarce ta fito da kafar tata ta nuna mashi. Yana ganin yatsunta shidda ne wani irin zabura ya yi zai miƙe tsaye, sai kuma ya daure ya koma ya zauna. "Bro lafiya?". Ta jefa mashi tambaya. Kai ya girgiza mata alamar babu komai. Shiru ta yi tana tinanin lallai akwai matsala wanda Ronnie ya sani kawai faɗa mata ne ba zai yi ba, amma tana fatan Allah yasa alkari ce a garesu bakiɗaya. Ronnie a matsayinsa na likita A-box ya ɗauko domin taimakawa yayan nasa, ga shi a kusa da kirji ta yankesa. Tsab ya gyare komai, sannan ya ce ta ɗebo wani ruwa su sanyayawa Black Tiger jiki saboda zafin da jikin ta yi. Tana ƙoƙarin sauka daga bed ɗin mirror ta kara yin kara a karo na biyu. A miliyan Ronnie ya kai kallansa a wajen. Ai bai san lokacin da ya diro kasa daga saman bed ɗin ba, kamar walkiya ya isa gaban mirror ya tsaya. "Sis zo ki ga wani abin". Ya faɗa yana zaro idanu waje sosai. Da sauri ta kariso wajen tana faɗin. "Meyake faruwa ne? Ɗazun ma mirror ya yi kara lafiya kuwa?". Tamkar idanunsa zasu faɗi ƙasa saboda zarosu da ya yi ya ce. "Ina fa lafiya, muna cikin tashin hankali, birnin nan babu lafiya ga yaya ya suma yanzu ya zamu yi?". A kusa da shi ta tsaya kafin ta ce. "Meyake faruwa da birnin?". .......... Yatsansa yasa ya yi mata pointing na wani ɓangare daga jikin mirror kafin ya ce. "Kinga nan wajen birnin nan ne, kinga mutanen da suke wajen nan to yaki suka kawo mana, dama jiya yaya ya faɗa mun akwai waɗan da suke haransa dan su kwace birnin nan daga hannunsa bayan kowa yasan birnin nan nasa ne, to ga shi yanzu sun dinfaro cikin birnin nan da shirinsu yaya kuma babu shi yanzu ya zamu yi". Cike da tashin hankali da fargaba ya yi maganar!!. Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Ka taɓa ganin wanda ya rike Allah ya rasa mafita?"........................ Kai ya girgiza mata alamar a'a...... "To ka yarda dani zamu yi nasara ko da big bro ko babu shi, trust me ba zamu taɓa faɗuwa ba dan mun rike Allah, Allah ina mai rantsuwa ina kuma mai imani da Allah Allah ba zai taɓa kunyata mu ba, ka yarda dani". Ta kai karshen maganar tare da ware mashi tafin hannunta. Ba tare da shayin komai ba ya ɗaura nasa tafin hannun a kan hannunta alamar ya yarda da ita. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Mu je wajen mayakan da suke birnin nan ka ji?". Hannunta ya damke sosai yana faɗin. "That's why I love u my sis, kina da basirar saurin warware mana matsala, lets go to". Ya kai karshen maganar yana sakin hannunta. Haɗa hannun suka sake yi alamar zasu yi aiki a tare kuma zasu yi nasara In Sha Allah. A tare suka nufi wajen Black Tiger, sannan a tare suka ja bargo suka rufesa tare da yi mashi fatan farkawa cikin gaggawa kafin abubuwa su fi karfinsu su caɓe masu. Da gudu Ronnie ya ja hannnunta suka nufi waje Sweetie tana ta ƙoƙarin sanya ƙwaƙwalwarta a chaji wajen san gano menene ya janyowa Black Tiger wannan matsalar?. A gurguje suka fito kofar empeir ɗin, akwai wani stairs case mai bala'in tsawo a bakin empeir ɗin wanda ya kai step 30 haka, a gurguje suka tattakasa suka sauko ƙasa. Master Devil suka fara nema, dan shi ne master ɗin warriors ɗinsu, dan haka sai suka nufi ɓangaren mayakan Daular, hannunsu rike cikin na juna, Allah sarki abin da basu sani ba shi ne master Devil ya haɗa hannu da mutanen can, ya ci amanarsu dik saboda dukan da Ronnie ya yi mashi ranar. Amma fa shi Black Tiger yasan da cewa master ya haɗa hannu da mutanen, kuma master ɗin ne ma ya nuna masu hanyar da zasu bi su shigo Daular a saukake su ci su da yaki. Dik Black Tiger yasan komai, sai dai a yanzu babu amfanin sanin da ya yi, bai tina hakan zata faru da shi ba shiyasa ya yi shirin yakarsu shi kaɗai, sai dai kana naka Allah yana nasa, ga shi dai yanzu ya shiga wani hali. A can part na warriors suka isko master Devil yana zaune saman chairs kamar bai san komai ba. Suna shiga wajen tin kafin su ƙarisa in da yake suka fara faɗin. "Master ka haɗa kan warriors ɗin nan yaki ya tinkaromu a kurarren lokaci"......... Master dake zaune ko a jikinsa ya ce. "Babu wani mayaki da zai shirya yaki har sai King Lucian (Black Tiger) ya bada umarnin hakan". Cak Ronnie ya tsaya jin amsar master, ransa a ɗan ɓace ya ce. "Ni na bada wannan umarni dan haka ka haɗa kansu". Miƙewa tsaye daga saman kujarar da yake zaune ya yi, cikin kakkausar murya ya ce. "To ba zan yi ba! Ba zan bi umarnin naka ba!!". A fusace Ronnien ya nufesa da nufin sake dakasa kamar a baya. Yana tsaye bai yi wani motsi ba irin alamar akwai abin da ya taka haka. Da sauri Sweetie ta rike hannun Ronnien tana faɗin. "Bro don't mind him, ka manta muna da abubuwa a gabanmu ne?". Ciza laɓɓansa master ya yi, ya so ne dama Ronnie ya zo da nufin su kaure da faɗa ya janye masu hankali har gungun matanen can su yi wa Daular zobe su rufesu da yaki ba tare da sun farga sun shirya ba, amma sai Sweetie ta hana shi, ya ji zafin hakan kuma ya kara tsanar Sweetie sosai. "Bro kai da kanka ka bawa warriors ɗin umarnin da su shiryawa yaki kada ka daka ta wannan kazamin mutumin". Cewar Sweetie, tana bala'in tsoron master Devil idan baku manta ba tun farkon zuwanta birnin, sai dai kuma yanzu wutar tsanansa ne yake ruruwa a cikin zuciyarta saboda lalatar da yake yi, and tana tare da Ronnie, dan haka tana jin kwarin gwiwar zaginsa dan Ronnie ya fisa karfi kuma zai tsaya mata. "Babu wanda ya isa ya bawa warriors ɗin nan umarni a nan sai ni". Cewar master, dik abin da yake yi fa yana so ne ya ɗauke masu hankali har a cin masu. Ronnie zai yi mashi martani Sweetie ta hana shi, daga karshe ta ja hannunsa suka haye saman dogon stage dake wajen domin su yi magana da warrios ɗin. Jikinta har kerma yake yi ta ɗauko wani katan laspeaker ta miƙa mashi domin ya yi magana. Karɓa ya yi kafin yasa hannu ya buga belt ɗin dake wajen mai sautin gaske domin ya samu attention na warriors ɗin. Aikuwa yana bugawa gabaɗayansu suka juyo a kansa, kan kace me dik sun haɗu a gaban stage ɗin, da gudu master ya hauro sama shi ma da nufin ya dakatar dasu, shirinsa shi ne ya capke Ronnie da kokawa ya dakatar da su. Ronnie ya fahimci hakan, dan haka sai da ya bari ya hauro yasa kafa da karfi ya takesa a kirji da karfi a in da ya yi baya baya ya ganganra kasan stage ɗin, ya faɗi ƙasa a gaban warriors, cike da bada umarni ta cikin laspeaker Ronnie ya ce da mayakansu na Robbot guda biyu da su kama master su jefa mashi shi a cikin prison na empeir ɗin. Tsalle Sweetie ta buga tare da cewa. "Good my bro". Warriors biyu ne suka capki master suka wuce da shi, ga shi robbot ne bai isa ya gwada masu fin karfi ba, kuma Ronnie shi ne mutum na biyu bayan Black Tiger da aka shigar masu da su rinƙa bin umarninsa a cikin kwakwalwarsu, dan haka tin da ya ce su kai master prison ba makawa sai sun kaisa. Attention ɗinsa Ronnie ya bayar a kan sauran warriors da sun haura sama da 3k a wajen, cike da bada umarni ya ce su yi maza su shiryawa yaki basu da isasshen lokaci an kawo masu hari. Sannan ya ware wasu warriors da zasu iya kai 300 ya umarcesu da su tattara mata, tsofaffi da yara, su tarasu waje guda, su basu karisa kada su bari wani abin ya samesu. Daga karshe ya wari wasu warriors ɗin ya umarce da idan yakin ya ɗauki zafi fiye da tunaninsu to fa su tashi jiragen eagle dromes na yaki su fara ɓarin wuta daga sama. Yana kai karshen wannan magana bai gama rufe baki ba suka fara jin rugugin tashin wuta daga cikin empeir ɗin. Cikin ɗaga murya Ronnie ya ce ku je, daga haka ya riko hannun Sweetie da gudu suka sauko kasan stage ɗin suka nufi cikin empeir ɗinsu wajen Black Tiger kenan. Wato idan ka yarda da Allah wlh cikin sauki zai kare ka daga sharrin dik wanda ya nufeka da sharri ba tare da kasan ya yi ba, kun dai ga aya a kan Floris, ta nufi Sweetie and Ronnie bayin Allah da sharri, to da yake su Allah kawai suka rike ga shi ya juyar mata da aniyarta a kanta, my people's me kuke tinanin yasa Black Tiger a cikin wannan hali? Ya kuke tinanin wannan yaki zai kasance babu Black Tiger? To mu dai bari mu je wani part ɗin mu dawo. •••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥 Zaune Auta take a gaban tabkeken s-p na gidanta da Smart ya mallaka mata, tana sanye da short army trouser mai shegen kyau da ya tsaya mata a iya gwiwa, sai kuma white shirt daga ta sama, ta yi shiru haɗe da buga uban tagumi tana tinanin Hoorain. Manya manyan ƙosassun dolphin fish ɗinta suna ta wasa a cikin ruwan, sai fito da kansu waje suke yi suna taɓata dan ta zo su yi wasa amma taki kulasu, tana cikin damuwa, kun san dolphin idan ka saba wasa da su da sun ganka za su yi gaggawar fitowa saman ruwa, so ita a koda yaushe suka zo France ita da Jaish tana wasa da su sosai, ita ma tasa Smart ya saka mata su ɗan wasa, amma wannan karon sai ga shi taki kulasu, sai tsalle suke yi su fito su koma. Hoorain kawai take tunani baiwar Allah, ta yi rama sosai, yau kwananta biyu a gidan nan tare da Smart and Pretty, sai dai ko kaɗan bata san a wace duniya take ba, ga shi tin da suka dawo Smart bai natsu ba bare har ya san halin da take ciki, baya zama saboda aikinsa, wani lokaci sai cikin dare yake dawowa,lokacin kuma sun yi barci. Ita kuma Pretty dama ba wani cika damuwa da abubuwa ta yi ba, bama zata fahimci halin da take a ciki ba bare har ta tausaya mata ko ta bata shawara. Ji take tamkar ta sanya hannu bisa kanta ta kurma ihu ko zata samu sauki, wayar da Smart ya bata wanda zata rinƙa kiransa idan tana buƙatar wani abin sai ruri yake yi ta ɗaura shi a saman kujerun dake kawayen da wajen, da alama ta yi nisan da bata ma jiyo ringin na wayar ba. Guyson ne kuma yake ta kiranta, dan ya gaza samun kwanciyar hankali da sukuni, jiya ita ta kirasa da number da yake ta haddace numbersa, ta ce mashi ya dubi girman Allah ya je ya haɗata da Hoorain a waya, da farko yaki yarda, daga baya da ya fahimci zata iya cutuwa sai ya ce tabbas zai je koda dad zai jefashi cikin prison ne, to shi ne yake ta kiranta yanzu bata ɗaga ba hankalinta ya yi nisa. A can cikin gida kuwa, Pretty ce tsaye a gaban dressing mirror na ɗakin Smart, bata san cewa bedroom ɗinsa bane, ta tashi daga barcinta kawai ta je ta afka cikin ɗakin a garin neman hanyarta na san fita waje ta duba Auta, ta san Auta tana yawan zama a wajen dolphins ɗin nan, sai dai bata iya fitar da kanta wajen ba, sai dai su je a tare da Autar, saboda hanyar yana da sarkakiya sosai. Ganin kanta a cikin wani bedroom ɗin yasa ta fara kewaye a ciki tana zuba ƙauyancinta, taga bedroom ɗin ya fi nasu haɗuwa da ƙawatuwa sosai, ta ga abubuwan da bata taɓa gani ba, Allah ya yi zata zo France, dan suna rike da hannun juna ita da Auta a lokacin da Smart ya ja hannun Auta suka baro kingdom of power, sai Auta bata saki hannunta ba ta jata suka tafi a tare. Time da suka je airport Smart ya nuna ba zai tafi da ita ba, sai Auta ta ce ya kyaleta kawarta ce kuma suna san juna, dalilin da yasa ya zo da ita kenan. Leke leke ta shiga yi mashi kamar ya aikata, kun san ita Pretty kifin rijiya ce, ba kamar Sweetie take ba, wayonta da sauki, ga bala'in tsoro ba confidence, sai shegen shagwaɓa da cin abinci. Amma idan baku manta ba ita ɗin gwana ce wajen iya fitina, bata ganin abu bata taɓa ba. Dan haka sai ta shiga yi mashi taɓe taɓe, dik abin da ta gani sai ta taɓa. Cikin taɓe taɓen nata ne hannunta ya kai ta buɗe drawer mirror, tsautsayi dai baya wuce ranarsa, Smart yana rufe drawer da password, idan ya buɗe ya ɗauki abin da zai ɗauka, da ya tura drawer zata sake shiga password, so yau da ya tura drawer sai bata turu da kyau ba bare ta shiga password, hakan ya bata damar buɗewa. Wasu robobi ta gani a ciki kamar na zuba magunguna haka, tsabar fitina da kiran ajali wanda in ya kira dole a amsa sai tasa hannu ta ɗauki roba guda ɗaya, har da ɗan saka karfinta wajen buɗe robar da ta ɗauko. Tana buɗewa wani abu ya fita kamar hayaki haka, shakarsa ta yi a take ta saki robar ya faɗi ƙasa. Lokacin guda jini ya fara gangaro mata daga hancinta da kuma hakinta, ji ta yi tamkar am shake mata wuya wuya da karfi, hannunta dikka biyu ta kai ta riki wuyar tata tana kwalalo idanu waje. Da kyar ta iya juyawa tana san barin wajen, sai dai ko motsa kafafunta ta ƙasa bare ta iya tafiya. A take a wajen ta yanke jiki ta faɗa saman kirjinsa, dan yana tsaye a bayanta, da ta juyo ta fita a cikin hayyacinta ne yasa bata iya gane akwai mutun a kusa da ita ba. Shi kuwa dama ya fito daga wanka yana cikin dressing room yana shiryawa zai fita, to ya fito daga dressing room ɗin kenan yaga ta ɓalle marfin robar, shi ne ya kariso wajen ya tsaya a bayanta, ta cikin mirror dake gabansu yake kallan yadda jini ya fara zuba daga hancinta har izuwa bakinta. Fararen kaya tas ne a jikinsa, da ta faɗa jikin nasa kaf ta ɓata shi da jini. Allah ya cecesa yana sanye da face mask a fuskarsa, dan shirin fita ya yi, da wlh a tare zasu mutu da ita, dan in ya shaki wannan chemical ɗin shi ma ba zai tashi ba, dama sai sun saka face mask, hand's gloves da wasu irin riguna na leda kafin suke buɗe chemical ɗin, kun tuna yadda suke aiki a wajen haɗa makamansa ko? To haka suke yi kafin amfani da waɗan nan shegun chemical, kisa suke yi nan take, ita kuwa da fitina da rashin sani ta je ta buɗe. Sosai ta bakanta mashi rai, domin waɗan nan chemical ɗin suna da wahalar samu, shiyasa ma ya ɓoyesu a gida, wannan ɗan kaɗan ɗin da ta zubar mashi millions of dollars yake, chemical ne mai haɗarin gaske na haɗa nuclear mai karfi sosai, yanzu haka gabaɗaya ya tsastsaga mata kafa, saboda sake shi da ta yi ya faɗi ƙasa ya ɗan taɓa ƴan kafafunta. Jininta a kafa ne ya fara zuba, lokaci guda ta sandare kamar wadda lantarki ya busar. Siririn tsaki ya ja ya rasa me ɗaya zai fara yi?. Daga bayansa muryar Auta ta katse shi da cewa. "Yah Omerish kaga Pretty? Yanzu na je ɗaki ban ganta ba". Da yake ya bawa kofar shigo baya ita kuma Pretty tana kwance a kirjinsa sai yasa Auta bata iya gane Pretty na ɗakin ba. Ya lura da akwai shakuwa sosai a tsakanin Auta da Pretty, dan haka sai ya ce mata. "Jeki parlour ina zuwa". Ya yi mata hakan ne dan kada ta ga gawar Pretty hankalinta ya tashi, dama daga jiya zuwa yau ya fahimci tana cikin damuwa, daren jiya da ya dawo ya shiga bedroom ɗinsu, a nan ya sameta tana sambatu cikin barci, yau da safe kuma kafin ya shiga wanka sai da ya tsaya a jikin window ɗinsa ya zuba mata idanu tana zaune wajen dolphins, dama ya sa a ransa yau idan ya dawo daga office ya je ainahin gidansu ya dawo zai tambayeta me yake faruwa?. Juyawa Auta ta yi ta fita hankalinta bai kai kan jinin kafar Pretty dake malale a kasa ba. Tana fita ya raba jikinsa da nata, da hannu ɗaya ya ɗagata izuwa balconynsa, saman ɗaya daga cikin kujerun dake wajen ya kwantar da ita. Ita kuwa Auta parlour ta koma ta zauna tare da buga tagumi tana jiransa. A gurguje ya fito daga cikin bedroom ɗin nasa, rufe kofar ya yi dan ma kada ta Autar ta shiga taga gawar Pretty, bai tsaya bi ta kanta ba ya nufi waje yana ce mata yana zuwa. Ta yi mamakin ganin yadda yake tafiya tamkar zai haɗa da gudu, amma bata kawo wani mummunar tinani a ranta ba, tana san tambayarsa ya ga Pretty, sai dai kafin ta buɗi baki tuni ya sauka ƙasa. Shiru ta yi tana tinanin ina Pretty ta shiga kuma?. Can kunnuwarta suka tsinkayo mata wayar dake ruri a waje. Da sauri ta miƙe ta nufi waje. Filin dolphins ɗinta ta koma, wayar natan ne dai yake ruri. Tana zuwa ta ɗauka, guyson ne yake kiranta, a hanzarce ta yi picking tare da kara wayar a kunnenta tana faɗin. "Hello Yah Omar". A maimakon ta ji voice ɗinsa sai jin muryar Hoorain ta yi ya amsa mata da Hoonaira. Ai bata san lokacin da ta zube ƙasa a wajen ba, tamkar zata kurma ihu saboda daɗi, har ta rasa abin faɗe ma. Shi kuwa yana kwance a kan gadan jinya, da shi da Abbonsa dik suna gadan jinya, gara Abbonsa ma ya ɗan samu lafiya, ya farfaɗo yana iya gane waɗan da suke kansa. Shi kuwa Hoorain yana gab da mutuwa King ya samu labarin daga bakin masu tsaronsa cewa Hoorain zai iya rasa ransa a kowani lokaci daga yanzu, hakan yasa King ya ce a fitar da shi a kaisa hospital. Time da aka fitar da shi ranga ranga aka wuce da shi hospital, baya iya taka kafafunsa ma, sai ɗaga shi warriors suka yi. Jiya aka fitar da shi, yanzu a can guyson ya je ya kai mashi waya ba tare da sanin King ba. Wai me ya faru a kingdom of power bayan tafiyar Smart ne?. Cikin bedroom ɗinsa King ya nufa hankalinsa a tashe. Shi kuma Smart kai tsaye babban gate na kingdom ɗin ya nufa. Sun zo dai'dai wani waje dake kusa da fadar King ta biyu, idan baku manta ba na faɗa a baya fada gudu biyu ne a kingdom of power, so King baya amfani da ɗayan, saboda ainahi na mahaifinsa King Abdul Malik ne, to fadoji a da suna haɗe ne, sai ka shiga ta cikin ɗaya zaka je ɗaya, bayan hauwar King Zuhair mulki sai ya rabasu, aka toshe kofar tsakiyar aka buɗewa kowanne nasa kofar yana cin gashin kansa. So sun zo giftawa ta dai'dai wannan fada na King Abdul Malik wani irin haske ne ya bayyana daga cikin fadar ya shiga cikin motar tasu, sarai Smart ya ga hakan, amma hankalinsa ta yi gaba wajen tuƙi, bai wani bi ta kan hasken ba, ita kuma Auta dama ta kifa kanta a kan gwiwowinta tana kuka, Pretty dake zaune kusa da ita a kanta wannan haske ya sauƙa, dama saboda ita ya fito, saboda Spender dake tattare da ita, dik yadda aka yi da akwai alakar Spender da wannan fada, ina ga yana daga cikin dalilin dayasa King Zuhair ya rufe fadar ƙin faɗawa mutane gaskiya ya yi, dik yadda aka yi akwai abin da ake ɓoyewa, amma lokaci zai warware mana komai. Ba iya haske ne kawai ya fita daga cikin wannan fada ba, akwai abubuwa da dama da suka nuna alamar bayyanar Spender a wajen. Sai dai da yake Smart da gudu suka gifta wajen sai basu ga komai ba bayan wannan haske. Akka dake cikin bedroom ɗinta tana kwance sai da ta zabura ta miƙe zaune a lokacin da su Pretty suka gifta wannan fada, a jikinta ta ji hakan, take ta ji jiri na ɗibarta, jikinta ne ya fara tsuma. A lokacin su uncle Abbas sun koma part ɗinsu. Wayarta Akka ta ɗauko, number King Zuhair ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka, a lokacin suna tsaye a tsakiyar bedroom shi da momma suna ƙoƙari neman Smart dan ya dawo. Muryar Akka na kermar ta ce. "Zuhair dik yadda aka yi Spender ya dawo cikin Masarautar nan, ku yi gaggawar gano in da yake". Yadda take magana ya yi matuƙar ɗaga hankalin King, a hanzarce ya ce mata. "Ki kwantar da hankalinki Akka dole nema mu nemosa, gani nan zuwa kin ji?". Da okey ta amsa mashi kafin ta katse kiran, hankalinta ya yi matuƙar tashi, dik yadda aka yi Spender abu ne mai tsananin haɗarin gaske kuma barazana ne ga al'umma shiyasa take shiga damuwa sosai,!. Kingdom of power dai ya rikice. A ɓangaren su Mammie kuwa, kuri da cika baki ta rinƙa yi a kan wlh ba zata kyale Smart ba, sai ta ɗauki mummunar mataki a kansa, dan haka dole su fara gagarumin shiri, ta yi rantsuwa da Allah ba zai daki Sarina a banza ba, uncle Abbas dai shiru ya yi yana jin surutan nata ba tare da ya ce uppan ba. Ɓangaren su Khadija kuwa, ita dai Khadijah tana cigaba da kula da babynta babu wani damuwa abinta, yaro sai kara wayo yake yi yana rikiɗewa yana komawa jinin Akka sak, dik yadda aka yi akwai alaƙa ta jini tsakanin yaron nan da Abdul Malik family. Ita kuwa Zee tana nan da wannan hali nata, ta koma bedroom ɗin mama Haulat a part ɗin Jaish da kwana, dan ta yi fushi ta sallami part ɗin surukarta mama, ta fa kamu da san Dr Raj, amma ta tsani uwarsa, kai wato akwai dirama a gaba fa. Ita ma Fanan ta koma bedroom ɗaya a part ɗin Jaish ba tare da sanin momma ko yarjewarta ba, shi ma Jaish bai sani na, shi yana can ma garden a can ya kwana, yaki dawowa part ɗinsa, wai baya san kwata kwata su haɗu da momma dan tabbatar rashin kunya. A ɓangaren shi kuwa Jawad yau kwanan zaune ya yi yana rarrashi, ita dai ta ce ba zata zauna da shi ba, sai dai kuma bata da kafar tafiya wajen mummyn nata. A can kuma mummyn nata tana can tana faman sallar dare tana rokan Allah da ya rabata da shaiɗanin da yake ƙoƙarin ruɗar zuciyarta dan kawai Smart ya bayyana a matsayin ɗan kin, shaiɗan na san ruɗarta a in da take ta jin rashin daɗin bayyanar nasa, ance zuciya bata da kashi, haka ne kuwa, domin kuwa ga shi nan dai mummy ma shaiɗan nasan kai ta ya barota, tsawon shekaru yana zaune da kowa da zuciya ɗaya da amana, bata ɗauki duniya da zafi ba, yanzu kawai abu na neman birkice mata. Sai addu'a take yi tana karatun Alqur'ani mai girma, to fans ɗinta sai ku tayata da addu'a kada shaiɗan ya yi galaba a kanta. Idan muka waiwaya ɓangaren Mahnoor kuwa, momma ta kira wayat Jaish har ta gaji ya ki ɗagawa, dan a cewarsa bai san me zai ce mata ba ɗan albarka. Haka momma ta tsaya Dr ɗinta mace ta yi wa Mahnoor dik abin da ya dace, ta kuma bata magunguna da suka dace sannan ta tafi, baiwar Allah ta ga bone ita kam. Ita kuwa Mahreen sai dai shirin Allah, dan kuwa a cikin dressing room na momma ta laɓe tana ganin su Omaid suka rinƙa jigila da guyson suna ƙoƙarin gyara ɓarnar da suka aita. Da kyar suka samu suka iya cire mashi dafin kunamar, amma ya sha kuka kam, dik abin da suke yi a kan idanun Mahreen suke yinsa, a ranta take cewa. "Wannan Yah Omar ɗin dai an yi rago, kannen nasa ma sun fishi jarumta, sai ka zauna kana kukan ciwo dan wauta?". Daga gefe can kuma uncle Jahiz ne ya je neman Zee a part ɗin mama bayan ya baro bedroom na Akka, dan ba zai iya barci ba sai ya sanyata a idanunsa, ya kamu da zazzafar soyayyarta ne da alama. Da ya je bai ganta ba sai ya tambayi Khadijah ina take?! Nan take faɗa mashi ai bata nan. Bai kawo a ransa matsala suka samu da Aneesa ba, yasa hannu ya ɗauki babyn Khadija ya nufi waje da shi, Allah ya gani yana kaunar yaron nan over, kamar shi ya haifesa haka yake jinsa. Bayansa Khadijah ta bi da kallo, take fuskarta ta bayyana alamar damuwa da rashin jin daɗi, gabanta faɗuwa yake yi a dik time da ta kalli uncle Jahiz. Kai tsaye part na momma ya nufa dan duba Zee a wajen. While shi ma Dr Raj yana can bedroom ɗinsa yana fama da juyi da tinaninta. Ita kuwa ta haye bed ɗin mama Haulat ta yi kwanciyarta, har da shigewa cikin bargo. My people's anya gaba ƙwaƙwalwarku zata iya ɗaukar cakwakiyar kingdom of power?......🤔 To kun ji abubuwan da suka faru bayan barin smart kingdom ɗin, dan haka mu koma Paris ɗinmu. Auta ta buɗi baki zata wa Hoorain magana sai jin voice ɗin mace ta yi daga bayanta tana faɗin. "Wacece ke kuma?". A miliyan Auta ta juya dan ganin wacece? Ita dai tasan babu wata mace a gidan nan tun da suke zuwa, a nan suke sauƙa idan suka zo, Smart baya kaisu gidansu wajen mom ɗinsa, a nan suke zama, to bata taɓa ganin mace ko ta ji muryar mace ba, kuma wannan ba muryar Pretty bane gaskiya. To ko muryar waye?. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Wata kyakkyawar baturiya ce tsaye a kan kafafunta, tana nan dai cikin irin wannan shiga tasu ta turawa, ta zubo gashinta ta zaman shoulder ɗinta ta gaba, ga wani shegen high heel a kafafunta mai tsinin gaske. From up to down Auta ta bita da kallo kafin ta ce. "Ke yakamata in yi wa wannan tambayar". Tana kai karshen maganar ta cigaba da yin wayar da take yi. Cike da takun ƙasaita ta tako izuwa gaban Auta, hannu tasa ta kwace wayar dake hannunta, cikin zafa Auta tasa hannu zata kwaci wayar. Hatana ta yi tare da binta da wani kallan ƙasƙanci kafin ta ce. "Kin dai ɗan yi kama da baby, dik yadda aka yi kina da wata alaƙa da shi, amma hakan na shi ne zai sa na ɗaga maki kafa ba, ke har kin isa ina magana zaki cigaba da yin waya?". Auta zata yi magana suka ji alamar an buɗe kofar parlour, to jinin sarauta dai ba karya ba, cike da izza ta ce. "Bani da lokacin shashasshu irinku, bani wayata". Kallna banza ta bita da shi, zata yi magana kenan suka ji muryan Smart yana kwala kiran sunan Auta, harara ta dallawa yarinyar kafin tasa kai ta wuce ciki. A parlour ta iskosa yana zaune saman sofa, kusa da shi ta je ta zauna tana faɗin. "Yah Omerish gani nan". Kamar zata tambayesa wacece a gidan nan kuma dama akwai mace a gidan ne, sai kuma ta yi shiru, ranta a ɓace wancan mata katse mata waya da jaruminta. Hannunta ya riko cikin nasa, a natse ya ce. "Menene yake damunki?". Wai a ina Smart ya baro mana gawar Pretty ne? Wato ko a jikinsa tun da ba Auta bace ta mutu ko?. Da farko kamar Auta zata ɓoye mashi abin da yake faruwa, amma da taga bata da wani sauran hanya sai ta sanar da shi game da soyayyarta da Hoorain, da ɓatar da ta yi zuwa forest da taimaka mata da Pretty ta yi da komai dai dik ta sanar da shi, ta kai karshen maganar tana kuka dan ta tina irin soyayyar dake tsakaninsu. Shiru Smart ya yi ba tare da wani yanayi ya bayyana a tattare da shi ba, kamar dai bai damu ba. Miƙewa ya yi tare da riko hannunta suka haura sama, sai sharar kwallah take yi, dama ga bakincikin an kwace waya an hanata yin magana da shi. Da alama Smart da King halayyarsu iri guda babu banbanci, amma my people's me kuke tunani ne, wai shin ya Smart ya yi da Pretty ne? To mu je dai zuwa, koma dai menene lokaci zai yi mana alkalanci. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Ummie and friend ɗinta hajiya two seater ne zaune a saman sofas a parlourn Ummie, yanzu hajiyar ta zo, daga gani kasan akwai abin da suke shiryawa, sai kuskuskus ƙasa ƙasa suke yi, hajiya two seater dai kusan kullun tana cikin nikaf matar nan, sai idan ta zo keta tsaron gidan Abbie ne securitys suke ce mata sai ta cire nikaf kafin ta wuce, dan su ga wacece, ko da kuwa Ummie ta yi masu waya ta sanar da su bakuwarta na zuwa, to basa barin ta wuce sai sun ga face ɗinta. Nikaf or face mask baya keta gate na farko na gidan Abbie, dole ka ciresa kafin ka wuce. ••••••••••••••••••••🔥 Jakarta ta buɗe ta ciro kwalin STENDRA guda ɗaya ta miƙawa Ummie tare da miƙewa tsaye, ƙasa ƙasa ta ce. "To ni zan wuce dare ya yi, yanzu ma ba dan saboda ke ba ba zan fito ba, ga sakonki nan, kada ki wuce saka mashi guda ɗaya idan ya yi yawa ne biyu dan gudun matsala a iya ganoki, dan yana da karfi fiye da tinaninki". Yadda take maganar tsab zaka fahimci wannan ta yi degree a iya munafurci da makirci. Jinjina kai Ummie ta yi tare da miƙewa tsaye tana zuba mata godiya, sai uban murmushi take yi burinta zai cika. Gaba hajiya two seater ta yi tana kara jaddada mata kada ta wuce sanyawa Ramish wannan kwaya guda ɗaya kacal, dan yana da karfi sosai, daga karshe ta rufe mata da cewa idan ya sha da minti 15 zata fara yi mashi aiki, dan haka sai ta shirya. Ummie baki har kunne ta amsa da to. Har Hajiya zata fita parlourn Ummie ta yi saurin cewa. "To ya batun Leesharh fa? Yakamata mu yi gaggawar kawar da yarinyar nan tin kan lokaci ya kure mana, kina ji dai ya faɗa maki Abbie yana tarayya da yarinyar nan a ɓoye, kuma ni ba zan iya jurar hakan ba". Ranta a ɓace ta kai karshen maganar. Ajiyar zuciya hajiya two seater ta sauke kafin ta ce. "Kada ki damu, ai yanzu yazama wajibi mu ɓatar da Leesharh, idan ba haka ba zata zame mana babban barazana, amma kada ki damu zan dawo gobe dan jin result na maganin nan, a nan zamu tattauna maganar tata in faɗa maki hukuncin da muka yanke, amma kafin nan ki shiryawa Leesharh fita barin cikin gidan nan, kin dai san ba ta yadda za'ayi mu iya ɗaukarta a cikin gidan nan saboda mahaukatan tsawon nan naku masu sanya hantar cikin mutum ta kaɗa da kuke da shi, amma ki nemo wani aika ko wani dalilin da zai sa ta fita daga ita sai driver kawai". Jinjina kai Ummie ta yi, har zuciyarta ya ayyana mata yadda zata aika Leesharh shopping ita da driver kawai ba tare da Sharifat ko bodyguards ba, tasan ta yadda zata ɓullowa komai. Sallama suka yi ta raka hajiya zuwa wajen elvator, sannan suka yi bye bye hajiya tana yi mata addu'ar samun nasara a kan dikkanin burikanta. Ciki Ummie ta koma, dama ita take haɗa mashi abinci dayawa lokuta, Sharifat mai kaiwa ce kawai. Da sauri ta nufi dry kitchen dan shirya mashi cappuccino, dan tasan zai buƙata. Sai dai fa, bata kai ga fara haɗawa bama sai ga Sharifat ta shigo cikin kitchen ɗin tana faɗin. "Ummie na je bedroom ɗinki bakya ciki, Yah Ramish yana san cappuccino"............ Wani irin faɗuwar gaba Ummie ta ji ya dira mata, sai ta ji shakkar saka wannan magani, amma da yake shaiɗan la'ananne ne sai ya fara kara mata confidence a kan ta jajirce zata yi nasara, har da raya mata ya yi cikar buri da biyan buƙata ya fi kwana masallaci, take ta ji kwarin gwiwa, cikin dabara ta ce. "Okey zan haɗa mashi, amma jeki ɗaki ki jirani ina zuwa". Ta faɗa tana satar kallan cameras dake cikin kitchen ɗin. Da okey Sharifat ta amsa mata tare da juyawa ta komai ciki, tana sanye da jelly dressing. Kamar yadda ta saba haɗa mashi cappuccino haka ta haɗa yau ma, bata zuba maganin a cikin kitchen ɗin ba, saboda Cameras dake ɗaukarta, sai ta ɗauki cup ɗin ta fito waje. Kai tsaye bedroom ɗinta ta nufa, sai dai bata kai ga shiga ciki ba ta tsaya a wani ɗan corridor dake tsakanin parlour da bedroom ɗin, a wajen babu Camera kuma akwai ɗan duhu, a nan ta tsaya ta fito da maganin, a maimakon ta saka mashi guda ɗaya ko biyu kamar yadda aka yi mata kashedi, sai ta ɓallo guda huɗu ta banka mashi a ciki. Tsayawa ta yi har sai da maganin ya narke a ciki, sannan tasa spoon ta gauraya shi sosai, sai ta bar spoon ɗin a cikin cup ɗin. Kana ganinta kaga maras gaskiya, amma da yake Sharifat yarinya ce sai bata iya fahimtar halin da Ummie take ciki ba, fargaba kamar zai kashe matar nan, amma saboda karfin hali sai dannewa take yi. Ta zo ta miƙawa Sharifat plate and cup ɗin, sannan ta wuce cikin toilet ɗinta tana jin kirjinta tamkar zai fashe saboda fargaba da tsinkewar zuciya. Ita kuwa Sharifat, karɓa kawai ta yi ta wuce abinta, zuciyarta na ta tuna mata Leesharh. •••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Zaune yake a cikin bedroom ɗinsa yana tinanin yadda aikinsa yake gudana, ga mama ta sako shi a gaba tana saka mashi pressure sosai a kan bayyanar Smart, ta matsa mashi wai sai ya yi mata bincike dan ita bata yarda Smart ɗan King bane, wai sai dai momma saboda kwaɗayin mulki ta hayo Smart a matsayin ɗa. Jama'a kun ji mun wata lukutar bala'i a wajen mama, fisabilillahi momma ta yi kala da masu yunwar mulki? Kada ku manta fa ita momma ƴar King Badeen ce! Sannan kanwa ga su Abu Abdussalam ƙososhin gwamnati, ga daddyn Smart wato babban yayanta president ne, su uncle Rahab dik jiga jigan ƴan siyasa ne, bayan haka shi kansa Smart ya isheta har ta gama rayuwarta bazata nemi komai ta rasa ba, kuna dai gani Auta Gimbiya Zunaira yar karamar kanwarsa ma ya mallaka mata tampatsetsan gida har haka bare mommarsa? Jama'a ku tayani gani, Jaish kawai yana da dukiyar da zai iya rike gabaɗaya ahalin King har da su mama ɗin har karshen rayuwarsu ba zasu nemi komai su rasa ba, kai in short auta kawai ta mallaki dukiyar da ya take na uncle Abbas a yawa daga hannun brothers and uncles ɗinta, ji da ita suke yi, amma wai irin wannan mata mama take cewa ta hayo yaro dan yunwar mulki? Hankali zai ɗauki wannan batu kuwa?. Shiyasa Ramish bai wani bi ta kan batun ba, saboda shi yasan wacece momma da ahalinta, kada ku manta a hannun Abu Abdussalam ya girma, Abu Abdussalam kuma ai kunga yayan momma ne dik da cewa yayan daddynsu ne ma, dan haka shi yasan momma ba zata yi hakan ba, shi zai fi kowa bada labari a kan kirki da adalcin familyn momma. Akwai lokacin da ya so barin gidan Abu Abdussalam ya koma gidansa da ya mallaka da ɗinbin dukiyarsa, amma Abbie ya ce babu in da zai je su kasance a tare, so shi yasan halin gabaɗaya ƴaƴan King Badeen. Shiru ya yi yana tinanin yadda zai kama masu nikaf, shi yanzu wannan ne a gabansa ba bala'in mama ba. Sallamar Sharifat ya dawo da shi daga duniyar tinanin da ya afka. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa. Ita kuwa kallonsa ta shiga yi babu kakkautawa, yana sanye da pj's a jikinsa launin light milk. Hannunta ɗauke da cup na cappuccinon da ya buƙata ta kawo mashi, gabansa ta kariso ta ɗaura cappuccinon a saman table tare da komawa gefe guda ta tsaya tana jiran ko zai buƙaci wani abin. Yunwa yake ji, tin safe rabonsa da abinci, abubuwa sun sha kansa, dan haka sai bai ɓata lokaci wajen ɗaukar cup ɗin ba. Cikin natsuwa yake sipping na cappuccinon ba tare da ya kawo a ransa akwai wani abin a ciki ba, saboda kullum ita ta saba kawo mashi abincin, kunga ba zai taɓa yin zaton ansa wani abin ba. Sai dai fa ya ji ɗanɗanon cappuccino ya ɗan canza, kamar ya yi zaƙi dayawa fiye da kullum, amma sai ya yi tinanin sugar ce ta kubce, yana jin yunwa dan haka ba zai tsaya ƙaƙalen nan nasa da ya saba ba. "Yah Ramish in tafi?". Ta faɗa tana kallan face ɗinsa. Kai ya gyaɗa mata alamar e ta tafi. Juyawa ta yi tana tafiya tana waigosa, while ita kuma Ummie tana can tana murnar burinta ya cika, so take kawai Sharifat ta dawo ta tambayeta ya sha ko bai sha ba. Sharifat na fita ya miƙe tsaye yana cigaba da shan cappuccinon, da yake yana jin yunwa har ya kusa shanyewa ma saura kaɗan. Parlournsu ya fito, babu kowa, da alama Bilal ya yi barci, dama shi Rizwan baya nan. Kai tsaye ya nufi ɗakin da Leesharh take kwance rike da cup ɗin. Ƙasa ƙasa ya yi sallama, tun daren jiya da ya fita ɗakin bai sake dawowa ba, dan baya san sake haɗa idanu da ita, ta caza mashi kai jiya. Zaune take a bakin bed ɗinta, ta fito daga wanka kenan ba jimawa, yanzu tana iya yin wanka saboda ciwon ya warke, sai dai har yanzu tana karkashin dokar kada ta bar ruwa ya taɓa wajen, so cikin dabara take wankar. Yau tana sanye da riga mai siririn hannu zuwa gwiwowinta, sai doguwar wando daga ƙasa, Dr ya ce ta rinƙa barin wajen ciwon nata yana shan iska, shiyasa yanzu riguna masu siraran hannu kamar vest kawai Sharifat take kawo mata, anma kusa sallamarta, dan sauki ya samu. Jin motsin mutum yasa ta ɗago idanunta, dama tana rike da wayarta tana latsawa ne. Tana ɗagowa ya yi saurin cire idanunsa a kanta, dama kallan tsab ya tsaya yake yi mata kamar an ce mashi tana kama da wata ko ance mashi idan ya zo ya kare mata kallo za'ayi mashi tambaya a kanta a ɗakin jarabawa. Kuma abin da zai baku dariya surar jikinta yake kallah ba ita ba, bare ma shape ɗinta, in baku manta ba na faɗa maku Leesharh tana da shape sosai, tana da diri. Ji ya yi kamar an sungulesa da ya tsaya kare mata kallo. "Barka da dare Yah Ramish". Ta faɗa tana mayar da kallanta ƙasa. Shiru ya yi bai amsa ba. Almost 3 mins yana tsaye, sai can kuma cikin natsuwa ya ce. "Zaki iya zuwa ɗakin binciken mu? Dan ina buƙatar hakan, akwai wasu tambayoyi da nike san amsoshinsu daga gareki". Ya kai karshen maganar tare da ɗan gyara tsayuwarsa da kyau. Kanta a ƙasa ta ce. "A shirye nike dan amsa dikkanin tambayoyinka". Jinjina mata kai ya yi, ya kuma ji daɗin amsarta da har yasa ya sauke ajiyar zuciya. "Zamu iya tafiya yanzu". Ya faɗa tare da juyawa ya yi gaba. A hankali ta miƙe tsaye, vail dake ɗaure a kanta ta ware ta yafa a kan nata dan ya ɗan rufe mata shoulder ɗinta, bata jin daɗin ganin jikinta a buɗe ko da kaɗan ne, kun dai san mu Nigerians wlh mun fita daban, mun fi kowa kunya fa nike faɗa maku, kunya kuma shi ne cikon addini, idan babu kunya ba za'a samu tausayi ba, idan babu tausayi ba za'a samu imani ba, idan kuma babu imani ku faɗa mun me amfanin mutum?.......🤔 Bayansa ta bi yana tafiya kamar wanda bashi da lafiya saboda kasala. Ta yi mamakin ganin ta hanyar da suka bi, ta kai shekara a gidan amma bata taɓa sanin wannan waje ba, kuma a part ɗinsu ne, bata taɓa zatan akwai wani hawa a sama bama, saboda a tinaninta su ne a hawa na karshe, ashe akwai wani hawa, ta sha madarar mamaki lokacin da ta kalli wani siririn stair case mai amfani da remote a cikin part ɗin nasu. Har tsoron haurawa sama ta ji, dan taga stair case ɗin kamar zai nitse da ita ne, yana nan a kanannane kamar indomie, fargabarta na biyu ma kada su hau ya karye da su dan ya yi sirantaka. Sai da ta ga ya hau babu abin da ya faru sannan ita ma tasa kafarta kamar ba zata taka ba ta hau. Ai a miliyan ta sauko jin stair ɗin yana yin kamar akwai spring a jikinsa, irin idan ka taka sai ya yi ƙasa, in ka cire kafa sai ya yi sama, dik confidence ɗinta ta ji ba zata iya hawa wannan waje ba. A jikinsa ya ji kamar ta kasa haurawa, dan dama already yasan wannan stair case ɗin matsoraci ko mai hawan jini ba zai iya hawa ba, sai su jaruman maza. Sai da ya haura sama gabaɗaya sannan ya juyo da kallansa a kanta, while ita ma shi take kallah. Da hannunsa ɗaya ya yi mata alamar ta hauro. Without any scare ta amsa mashi da. "Ina jin bazan iya haurowa ba ne". Shi mamaki take bashi yadda take magana with full confidence a koda yaushe, tin lokacin da take cikin azabarsa in zai tambayeta sau dubu to sau dubu zata bashi amsa cike da gwarin gwiwa, bata taɓa sarewa ba, lokacin da ta amsa masu wancan wayar ba nata bane ma ya dan yi mamakin jin yadda ta amsa ɗin, babu ko shayi, so hakan yana ɗan bashi mamaki gaskiya. "Babu abin da zai faru ki hauro". Ya faɗa yana ƙoƙarin juyawa. Kai ta girgiza tare da cewa. "Dama ban ce akwai abin da zai faru ba ai, saboda ka hau a gabana babu abin da ya faru, kawai dai ni ɗin ce ba zan iya haurawa ba saboda hankalina bai kwanta da stair ɗin ba". Babbar magana, a gaisheki Leesharh iyalan Nigerians, ina san ƴan kasata wlh, mu ɗin na daban ne fa!!. Cak ya dakata tare da juyowa gareta, yama rasa abin faɗe, wai dama bata ce akwai abin da zai faru ba ai. To tin da shi yake da buƙatarta dole ya yi abin da take so, dan haka ba dan ya so ba ya ajiye cup ɗin dake hannunsa a saman wajen, sannan ya sauko ƙasa, da hannu ya nuna mata hanya yana faɗin. "To yi gaba zan biyoki a baya". Kai ta sake girgizawa. "Ni ai ba wai cema na yi ba zan iya hawa ni kaɗai ba, hawan ne gabaɗaya ba zan iya yi ba". Gaskiya Leesharh yar air ce. To ya zai yi? Dole ya ɗan duka ba tare da ya sake yin magana ba ya ɗauketa cak ya nufi sama. Sai kuma me, ƙoƙari sauka daga jikinsa ta fara yi tana faɗin. "Ni ka saukeni bana so". Ai tamkar ba shi ba, ya bawa banza ajiyarta, bai sauketa ba sai da ya shiga tsakiyar ɗakin ya sauketa, bai bi ta kanta ba ya juya ya koma ya ɗauko cup ɗinsa, saman chair dake gaban wata computers ya zauna domin ya fara aikinsa. Ba tare da ya kalli in da take ba ya yi mata nuni da chairn kusa da shi sannan ya yi magana cikin bada umarni a kan ta zo ta zauna. Ta tsaya sai kuncin rai take yi wai dan ya ɗauketa, tana ɗaure fuska ta nufo shi, ya bata haushi. A natse ta tako ta iso wajen chair ɗin, tana zama shi kuma ya ɗaura cup ɗin hannunsa a saman table ɗin tare da juyo da gabaɗaya jikinsa a gareta, ya zamana suna fuskar juna, sai dai kallansa naa kan computer gabansa. "Ki mun alkawarin dik abin da zaki faɗa mun gaskiya zaki faɗa!". Ya faɗa yana dawo da kallansa a kanta. kai ta ɗan jinjina. "Ko a da can baya ni bana karya, wani dalili yasa na yi maka sau ɗaya kuma bana fatan na kara yi". Mamaki ya ɗan yi jin ta ce ta yi mashi karya sau ɗaya. "Ƙaryar me kika yi mun a baya?". Ba tare da shayi ko shakkar komai ba ta amsa da. "Cewa da na yi wancan wayar ba tawa bace, hakikanin gaskiya tawace!". Ɗan zaro idanunsa ya yi, like so much of surprise. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Nasan da hakan, sai dai ban yi tinani zaki amsa mun da bakinki naki bane a yanzu, nasan cewa wayarki ne tin a ranar da muka kamaki". Mamaki ne sosai ita ma ya kamata, a ƙagare da san jin cikakken bayani daga bakinsa ta ce. "Ya aka yi kasan waya ta ce sannan kuma meyasa kasan nawane ka sakeni?". Hankalinsa ya mayar kan computer dake gabansa, da yake irin torch screen computer nan ne sai ya sanya yatsarsa yana latsata. Cikin natsuwa ya ce. "Na sakeki ne saboda na fahimci controlling ɗinki ake yi, komai da kike aikawa command ake baki, to ba ke nike da buƙata ba, masu sakaki ɗin nike da buƙata wanda kuma sai na sake ki ɗin zan iya cin masu". Ya kai karshen maganar tare da zame hannunsa a kan computer sannan ya dawo da kallansa a kanta, da yatsarsa manuniya ya nuna mata screen na computer yana faɗin. "Zanen hannunki da zanen hannun dake jikin wayar dikka ɗaya ne, ta haka na san wayarki ne". Da sauri ta kai kallanta a kan screen na computer, hotunan zanen hannunta da kuma zanen hannun dake kan wayar ta gani, lokacin guda ta haɗiyi wani irin yawu mai wuyar wucewa, ashe kenan yasan komai ya zuba mata idanu, tab lallai ya cika cikakken jami'i, yasan kan aikinsa da kyau. Wani zuciya ce ta jefa mata tambayar amma meyasa ya azabtar dake dik da yasan zai sakeki kuma ba ke yake da buƙata ba? Shiru ta ɗan yi dan bata san wannan amsa ba. Shi ma dai shiru ya dakata yana jin wani irin sauyi a jikinsa, lokaci guda zufa ta fara ketowa daga gefe da gefen fuskarsa, hannunsa yasa ya ɗan shafi zufar yana mamakin menene kuma ya kawo zufa a face ɗinsa? Sai jin jikinsa ya yi tamkar an takuresa waje guda, ya ji kamar a matse yake, bugawar zuciyarsa ce ta sauya izuwa da karfi karfi. "Amma Yah Ramish meyasa kasan zaka sake ni ka sanya aka horani?". Muryarta ta katse mashi tinani. Da sauri ya dawo da kallansa a kanta, jikinsa na wani irin tsuma na daban da bai taɓa jin irinsa ba, dik karfin sha'awarsa idan ta motsa jikinsa baya yin irin wannan tsuma, to abu ne da ya haɗu da wanda yake da gadan abar, ga maganin overdose aka bashi, kunga kuwa ai sai abin da Allah ya yi kawai. Zuba mata idanu ya yi bai iya bata amsa ba, ta ɗan yi mamakin irin kallan da yake yi mata, sai ta ɗan kawar da kanta daga kallansa. Gabaɗaya sai ta ji ta tsargu sosai, kamar a takure take, kun san idan mutum yana kallanka sai dik ka ji kamar baka da natsuwa. Kamar zata jurewa kallan, amma sai ta kasa yin haka, dan a cikin ƙanƙanin lokaci ta ji tsoro ya kamata kuma gabanta na faɗuwa. Muryarta ƙasa ƙasa ta ce. "Yah Ramish yanzu da kasan ina da alaƙa da dik wani abu da yake faruwa da kai wani mataki zaka ɗauka a kai'na?". Cike da fargabar amsar da zai iya fita daga bakinsa ta jefa mashi wannan tambaya. Shiru bai iya amsa mata ba, sai wani irin abu da yake ji a jikinsa tamkar ana jona mashi lantarki a sake cirewa. Da karfi ya kame jikinsa yana ɗan girgiza kai tare da datse idanunsa. Tsorata ta kara yi da yanayinsa, amma bata kawo batun can a ranta ba, ta yi zatan hukuntata zai yi shiyasa ya gayyatota ɗakin, Allah sarki ta ɗauka wancan hukuncin da ya yi mata bai ishesa bane. Ta shagala da tinanin dalilin sauyawarsa lokaci guda bata ankara ba sai jinta ta yi a jikinsa, bata ma san lokacin da ya fisgota ta faɗa jikin nasa ba. Wani irin razana ta yi, a miliyan ta zabura zata kwace kanta, ina ai da karfi ya riketa, saboda yadda jikinsa ke buɗewa da karfi haka ya ƙanƙameta, gabaɗaya jijiyoyin jikinsa maganin yana kara buɗasu, jinin jikinsa dik yana tafiya ya taru a kan bananarsa, dik ilahirin tsikar jikinsa mimmiƙewa suke yi, lokaci guda wasu zara zaran jijiyoyi suka bayyana a jikinsa, tun daga kan hannunsa har izuwa kan bananarsa, sai gumi yake haɗawa, fuskarsa ta jiƙe sharkaf tamkar an watsa mashi ruwa Da karfi ta tattara dikkan ilahirin karfin da ya rage mata tana ƙoƙarin turesa cike da tashin hankali. Sai dai ina ta kasa, cikin fitar hayyaci da karfi ya rabata da jikinsa kaɗan, yasa hannu ya capki wuyarta, cikin zafa ya haɗe bakinsu waje guda ya shiga bata kiss da zafa zafa babu kakkautawa, ya manta bata da lafiya, ko da yake baya a kan saiti.......... Kam bala'i wato akwai cakwakiya a lokacin da zai dawo kan saiti, wlh Ummie ta cucesa, ta zubar mashi da kima a idanun Leesharh............😅 Har lokacin Leesharh bata sare ba, cike da jajircewa ta cigaba da ƙoƙarin kwatar kanta, shi kuwa da zafa zafa ya kai wa tula tulanta capka, kamar wanda yake faɗa da doki haka yake abubuwan nasa, sai wani irin numfashi mai zafi yake fitarwa, shi kansa sha'awar ta fi karfinsa a yanzu kam, ga wani irin zafin da bananarsa take yi mashi sosai. Miƙewa tsaye daga saman chair ɗin ya yi da ita a jikinsa, a lokacin ne ta samu damar kwantar bakinta daga nasa, saketa ya yi yana ƙoƙarin ɓalle rigar jikinsa. Ai da gudu ta nufi hanyar sauka ƙasa dan taga wannan bala'i ya wuci tinaninta. Sai dai kuma kash, stair case ɗin sauka kasa da remote yake aiki, shi kaɗai ne kuma yasan in da remote ɗin yake da yadda ake amfani da shi, saboda haka ba hanyar fita, dan suna hawa stair case ɗin ta naɗe kanta, ko daga waje yanzu babu wanda zai iya shigowa ciki, dole shi ne zai iya yin kasa da stair ɗin a samu hanyar fita. Tashin hankali. Ganin babu hanyar fita yasa ta zunduma ihu sosai tana faɗin. "Dan Allah Yah Ramish ka yi hakuri, wlh gara ka kasheni dan laifin da na yi maka a kan ka yi mun abin da kake da niyar yi, wlh ni ba wai na karɓi aikin kasheka da gangan bane, hasalima da farko ban san kasheka ake san yi ba, wayo suka mun na karɓi aiki, amma dan Allah ka yi hakuri, ni yanzu na dai'na yi masu aiki, ka saurareni dan Allah". Tana magana out of control, barkate haka take zuba word ɗin cike da tashin hankali. Shi kuwa ko kaɗan baya jinta, gabaɗaya ya tsaga kayan jikinsa ya zubar kasa. Ai hankalin Leesharh kara tashi ya yi, ihu ta cigaba da zundumawa tana sambatu kala kala cikin fitar hayyaci, ga shi ɗakin ko'ina a rufe, kuma koda zata shekara tana ihu wlh babu mai iya jiyota, ko da ma an jiyota babu hanyar kawo mata ɗauki, dan remote tana hannusa, baza ma a ga stair case ɗin ba bare har a ce za'a ɓalleta a shigo. Bata karasa ruɗewa da shiga tashin hankali bama sai da ta buɗi idanu ta gansa tsirara haihuwar uwarsa a gabanta, harta short ɗin jikinsa ya tsageta ya cire, har lokacin zufa ce take cigaba da keto mashi babu kakkautawa. Wani irin ihun da Leesharh ta saki sai ta baka tausayi, amma shi da baya hayyacinsa bai ma san ta yi ba. A miliyan ta watsa da gudu zata bar wajen. Cikin zafa ya damki gashin kanta haɗe vail da ta yafa, da karfi ya fisgota ta faɗa jikinsa. Da hannu ɗaya ya ɗauketa cak sai saman sofa dake cikin room ɗin. Sai ƙoƙarin kwatar kanta take yi taki bada haɗin kai ta natsu, sai dai daga san da ya yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa ko motsinta ba a sake gani ba, dan ya kanainayeta ta ko'ina ba hanyar gudu babu hanyar motsawa. Wani irin matsa da yake yi wa tula tulanta yasa har ya fama mata ciwonta yana jini ba tare da ya sani ba, gabaɗaya ihunta ya dai'na fita, dan karfi ya saka mata, kuma kun san karfi ba ɗaya ba, dole ta natsu. Daga karshe da yaga rigarta zata takura mashi ma ketata ya yi ya zubar abinsa, ya samu damar ganin tula tulanta da kyau ba'a cikin riga ba, ai kuwa ya hau murzarsu yana turnushe ƴar mutane in out of control. Wato Ummie ban san me zan ce mata bama, haka kawai tasa Leesharh taga yaron mama tsirara, mutum mai ji da class da ji da kansa, shikenan yanzu ta zubar mashi da mutunci ta gama, yanzu kuna tunanin Leesharh zata yarda Ramish ba ɗan iska bane? Allah sarki bawan Allah ba halinsa bane, ita kuma ta taka sahun ɓarawo, akwai case dai. Weekend ɗin nan ba zan samu damar yi maku posting ba, da nace ba zan yi Friday bama, amma dai zan daure ko baya yawa gobe na yi maku, ina busy ne sosai wlh. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Tun Leesharh tana iya jin abin da yake yi mata sama sama har ta dai'na jiyo komai, diff ta ɗauke ta dai'na numfashi kuma ta dai'na motsawa. Shi kuwa dai dik bai san da wannan ba, ga shi dare ta yi sosai, Abbie ya yi barci, Bilal ma shiru, da gara idan shi idanunsa biyu ne tun da ɗakinsu ne sai ya iya buɗewa ya shiga. A can cikin gida kuwa, saboda tsinuwa ya tabbata a kan Ummie shiryawa ta yi cikin kayan barci ta nufo part ɗin su Ramish, tafiya take yi tamkar wata ɓarauniya, tana yi tana waige waige har ta shige ciki, kai tsaye bedroom na Ramish ta nufa, dan Sharifat ta sanar da ita cewa tana kai mashi cappuccinon ya fara sha, shiyasa ta shigo da confidence ɗinta, dan a tinaninta izuwa yanzu ya gama tsumuwa yana haukar neman mace, har da bada tazarar minti biyar ta yi a kan sha biyar ɗin can, ya haɗu minti ashirin da shan maganin kenan, dan a cewarta by then ya fita a hayyacinsa ta yadda ba zai iya gane ita ce ma ta zo ba, kawai zai afka mata, ita fa bata san wannan uban magani da ta loda mashi har guda huɗun ko ya yi wannan aika aika dole sai ya kwanta ciwo ba, dan ya fi karfin mutun ya iya ɗauka, dik bata yi wannan tinani ba, buƙatarta dai kawai ya biya ita kam. Sosai ta ji wani irin fargaba da faɗuwar gaba a lokacin da ta shiga cikin bedroom ɗin baya ciki, turus ta tsaya a tsakiyar bedroom ɗin tana bin ko'ina da kallo, hegiya ta wani sha kayan barcinta wanda ina da tabbacin na Sharifat ne ko kuma waɗan da suke sayar da irin kayan barcin basu san ita zata saka ba shiyasa suka sayar mata, wajen cup na breast kamar mutun ya saka hannu bisa kai ya kurma ihu, dik abin duniyar ya kare empty wajen yake, ko dame ma zata burge Ramish ɗin? Dik Abbie ya shanye kayansa......😅 Kada ace na ce to nace ɗin, ai dik ita ta ja, da ta rufawa Abbie dattijon arziki asiri ai da dik bamu ga komai ba, yanzu kuwa mun ga fatar da dik ta yamutse ne a wajen, kamar tsohuwa na tsotsar lemun tsami. Allah da masu sayar da irin wannan kayan barci zasu san ita zata saka ta ci mutumcin kayan nan haka na tabbata ba zasu sayar mata ba, kayan amai zuciya yaki tashi, abin ka rufe shgiya da dukan mutuwa, ta ja bawan Allah ya yi zina a banza, tun daga kan King Abdul Malik har zuwa kan gimbiya Zunaira Auta babu wanda ya taɓa yin zina a cikin familynsu sai Ramish da kaddara ta afko masu ta sanadinta, wannan abu da ciwo yake wlh, idan King ya ji ya zuciyarsa zata yi? Idan mama ta ji ya zata yi? Zasu iya ɗauka kuwa? Da wani ido Ramish zai ga Leesharh? Da wani ido ita zata gansa? Zata yi mashi uzuri kuwa? Innalillahi wa inna ilahir rajiun, wannan mummunar kaddara ce a garesu. Gaskiya akwai matsala. ••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 Almost 30 mins tana tsaye turus kamar birin da yunwa ta yi wa lahani ya rasa madafa, tsoronta ɗaya ace ya fita gidan ne, dan tasan tabbas ya sha maganin kan tin da Sharifat ta ce ya sha, ita fa ba tinanin haɗarin da zai riski kansa a ciki take yi ba, tsoronta shi ne ta yi asarar maganinta kuma ta ciwa wannan dare buri kenan yanzu ta yi asararsa, wannan shi ne tsoronta da kuma damuwanta...... Uhmm. Da kyar ta iya jan matattun kafafunta da dik Abbie ya shanye komai ta ƙarisa wajen toilet ɗinsa domin ta duba ko yana ciki, har ayyanawa take yi a ranta wai ga shi a cikin jacuzzi maganin ne ta kama shi a can ya ƙasa fitowa, saboda mutuwar zuciya har ta ayyana yadda zata tsunduma cikin jacuzzin su fara rakashewa tun daga can kafin su dawo saman bed...... Ni kam princess Teema ina ganin wani masifa a wannan gida na Abbie. Tura kofar toilet ɗin ta yi, cike da sa ran ganin abin da ta zata ta kutsa kai ciki. Sai dai wayam babu kowa a ciki, idan ranta ya kai miliyan to ya sosu a yau, take ta ji kanta ya sara mata, jikinta tamkar wanda ta yi mangaribar jemage. Juyowa ta yi ta nufo waje, kai tsaye ta nufi balconynsa a nan ma tana ayyana ganinsa a saman kujerun dake wajen ko kuma cikin ƙaramin pool dake wajen. Sai dai kash, babu shi babu alamarsa. Hankalinta ne ya tsananta tashi sosai, a gaggauce ta nufo waje. Tana fitowa parlour suka yi kiciɓis da Bilal. Wani irin kallo ya bita da shi mai cike da mamaki da al'ajabi. Shi dai ya san cewa kishi a jinin modarawa yake ko tarihi ta shaida babu wani jinsi na larabawa da suka kai rabinsu a kishi, tabbas yasan Abbie mutum ne mai bala'in kishi, tun da suke da su yau sama da shekaru 20 basu taɓa kallan abin da ya wuce face ɗin Ummie ba, kullum tana cikin abaya da rolling veil, yau rana tsaka ya ganta da irin wannan shiga a part ɗinsu kuma daga cikin bedroom na Ramish?. Tabbas ko a iya haka Abbie yasan akwai waɗan da suka ganta da shigar barci wlh zai iya haɗiyar zuciya ya mutu saboda kishi, wani irin bala'i ne wannan Ummie take san ja masu?. Gaggauwar kawar da kallansa daga kanta ya yi daga kallo guda, shi kansa taya Abbie ɗin nasu kishi ya yi, shiyasa ma ya kawar da kallansa tare da sa kai zai wuce yana mamakin wannan al'amari. Saboda rashin tsoron Allah da mutuwar zuciya sai cewa ta yi. "Bilal kaga Ramish ne?". Ya ɗan yi mamakin jin tambayar tata, amma sai bai kula ta ba, sam bai bata amsa ba ya yi gaggawar wucewa. Har zai shiga cikin bedroom ɗinsa sai kuma ya fasa ya dawo ya shiga na Ramish dan ya duba lafiya? Wani irin bala'i ne Ummie zata fito cikin irin wanna shiga daga bedroom ɗinsa?. Bin bayansa da kallo ta yi shaiɗan yana raya mata ai babu wani banbanci a tsakanin Bilal da Ramish ɗin, tun da tana a kan tsini kuma bata ga Ramish ba kawai ta bi Bilal ɗin ta yi manege da shi. Tashin hankali. Aikuwa saboda shaiɗan ya ci galaba ga zuciyarta sai ta bi bayan Bilal cikin bedroom na Ramish, zuciyarta na bugawa da karfi karfi amma haka ta daure saboda cikar burinta.............. . Yana fitowa daga balcony ya je leƙa Ramish a wajen kawai unexpect ya ga mutum tsaye a tsakiyar bedroom ɗin. Siririn tsaki ya ja tare da kawar da kallansa daga kanta tamkar bai ganta ba, ya zo zai wuce ta gefenta kenan muryarta ta katse shi da cewa. "Bilal magana nike san yi da kai". Sam babu alamar zai dakata daga tafiyar da yake yi, saboda baya san ya sake ɗaura idanunsa a kanta, wanda ya yi ma bisa kuskure ne kuma yana fatan Allah ya yafe mashi, dan shi a matsayin uwa ya ɗauketa. Ganin ya bawa banza ajiyarta yana ƙoƙarin fita waje me yasa ta yi zafin namar juyawa, taku biyu ta kamosa a in da bata yi wata wata ba bata bari kanta ya kulle ba ta yi gaggauwar faɗawa saman faffaɗar bayansa har da sauke ajiyar zuciya. Ai a wani irin haukace Bilal ya juyo, tsabar tashin hankali bai san time da ya tureta da karfi har sai da ta faɗi ƙasa da karfi ta buga kanta a jikin bango ba. Cikin zafa ya yi niyar sanya kafa ya taketa, amma sai kuma ya tina da Abbie da su Abdussalam, dan haka sai ya yi gaggawar zafin namar barin bedroom ɗin ya barta shanye a ƙasa, hankalinsa ya yi tsananin tashi sosai, har ciwo sai da ya ji kansa yana yi mashi. My people's ganin reaction na Bilal mai ya tina maku? Ku duba ku ga yadda ƴaƴan King ke kyama da korar zina daga garesu, dubi yadda Bilal ya zabura ya harzuƙa daga fahimtar nufin Ummie, amma a haka ta sanya Ramish aikatawa, anya zai iya yafe mata kuwa?. To ni dai bari na yi tsokaci a nan na isar da sakona da nike san isarwa, babban kuskure ne ku ɗauki yarinya karama ku aurawa babban mutumin da kunsan ba zasu tsufa karfinsu ya kare a tare ba!!. Dik yadda aka yi iyayen Ummie kuɗin Abbie suka bi suka aura mata shi, dan ba sa'anta bane shi ɗin, nesa ba kusa ba ya tsere mata, yayan momma ne fa, daga daddyn Smart sai shi, kunga kuwa ba ƙaramin bane, momma ma ku duba shekarun Smart sai ku kiyaste nata shekarun, haba abin babu tsari wlh irin wannan aure, yanzu ga shi shi Abbie karfinsa ya kare ya tsufa, ita kuma a yanzu ne take da buƙatar namiji, kunga kuwa dole a sami gagarumin matsala, irin haka ne suke faɗawa zinace zinace da lesbian, kuga suna bin yara ƙanana sa'annin ƴaƴan cikinsu, wlh wasu iyayen ku ji tsoron Allah, ku sani idan kuka yi wa ƴarku haka dik halin da ta faɗa kuna da kasan zunubi a ciki, ku gudanwa ƴaƴanku faɗawa wannan halaka, masifa ce babba wlh!!!. To na isar da saƙona a ɓangaren Ummie, Allah yasa zaku ji kokena ku kuma gyara!!. •••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Bedroom ɗinsa Bilal ya wuce yana huci tamkar zai haɗiyi zuciyarsa, rufo kofar nasa ma ya yi tare da murza key wai dan ma kada ta biyosa. Wayansa ya ɗauka cike da tashin hankali ya fara kiran number Ramish dan ya ji ko dai yana da masaniya dangane da abin da Ummie take nema. Sai dai kash, three miss calls ya bugawa Ramish amma bai ɗaga ba, a lokacin yana can yana zuba aiki. Jefar da wayar tasa a saman bed ya yi ransa tana kara zafafa ya shiga toilet dan yin wanka. Ita kuwa Ummie, jiki dik ya yi mangaribar jemage ta miƙe tsaye, tana ɗan dafa bango tana layi ta nufi waje, mararta kamar zai fashe saboda ciwo na abar da ta tara, ta rasa ya zata yi da ranta. A gefe guda kuwa Sharifat tana can tana neman Leesharh, dan ta je ɗakin da take jinya bata sameta ba. Har ɗakin Ramish ɗin Sharifat ta zo ko Leesharh na a ciki nan ma ta ga wayam, cike da damuwa ta koma bedroom ɗinsu. Wayarta ta ɗauka ta hau kiran number Ramish dan ta tambayesa ina Leesharh? Sai dai bai ɗauka ba, ɗaura wayar a saman phone set ta yi tare da kwanciya tana tinanin ina Leesharh ta tafi. Can wani ɓangare na zuciyarta ya ayyana mata ai Leesharh tana tare da Ramish ɗinki. Wani irin zabura Sharifat ta yi ta miƙe zaune tana furta auzubillahi minashshaiɗanirrajim, dan zuciyarta ba zai iya ɗaukar wannan bala'i ba, kishi ne da ita nasu na gado, zata iya kashe Leesharh a kan Ramish, dan nata ne ita kaɗai. 😅 (To nima zan iya kashe maltina roba goma a kan guyson, dan nawa ne ni kaɗai) Sai da ta ɗauki almost 5 mins tana ta nanata sunan Allah a ranta dik dan koran tunanin Leesharh na tare da Ramish, da kyar ta samu ta rabu da tinanin, sannan ta koma ta kwanta tana fatan Allah ya mallaka mata Yah Ramish ɗinta, haƙiƙa idan Sharifat bata mallaki Ramish ba za'a sami gagarumin matsala. To my people's me kuke tunanin zai faru a gidan Abbie? Uhm muje dai zuwa. ••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥 Cikin bedroom ɗinsa ya wuce rike da hannunta, a gefen bed ya zaunar da ita tare da ɗauko tissue paper, hawayenta ya share mata tare da yin shiru yana mamakin karfin hali irin na daddyn nasu, ace mutum kamar Hoorain ai bai cancanci ace King ya hana shi wani abin idan ya nema ba, wannan sam ba halacci bane, mutum tun tasowarsa yana yi maku hidima, ya sadaukar da ransa saboda kare rayuka, dukiya, martaba da kimar masarautarku, sannan shi ne zai zama abin walaƙantawa a gareku dan kawai ya fita a matsayin bawanku mai yi maku hidima?. Har King yana da bakin cewa Hoorain ya tara makiya ba zai bashi ɗiyarsa ya aura ba? To saboda su waye ya tara makiyan? Ba dik dan saboda kare rayukanku ya tara makiyan ba?. Kuma shi King da yake wannan magana a gabaɗaya kingdom ɗin suna da biyun Hoorain da mahaifinsa ne? Yau da za'a kawowa kingdom ɗin hari ace babu tawagar Hoorain da mahaifinsa kuna tinanin kingdom of power zata kai labari ne? Wlh ko zata kai labari sai da taimakon su Ramish, amma dik da haka yau Hoorain da mahaifinsa sune abin walaƙantawa da ƙasƙantar a gaban al'umma dan kawai Hoorain ya kamu da son Auta wanda ba shi ya ɗaurawa kansa ba, gaskiya yana da kyau ya gyarawa kingdom of power ɗin nan zama su san cewa babu wata aya ko hadisi da ta banbanta matsayin talaka da mai kuɗi, sai dai ayar da ta banbanta tsakanin mai tsoron Allah da mara tsoron Allah. Ganin ya yi shiru yasa ta yi tinanin shi ma zai ji kyamar talakawa ne, bata san shi ɗin cikakken mai amfani da iliminsa bane. "Yah Omerish kai ma baka san my Hero ko?". Ta faɗa tana shessheka. Dawo da kallonsa a kanta ya yi, cikin sigar rarrashi ya ce. "Meyasa ba zan so abin da shalelena take so ba? Matikar bai saɓawa faɗar Allah ba tabbas zan zama mai goya maki baya my sweetheart". Ya kai karshen maganar yana janyota jikinsa. Zaro wayarsa daga cikin aljihunsa ya yi da nufin ya yi call sai ga kiran momma ya shigo. Katse kiran ya yi ya sake kiranta, bugu ɗaya ta ɗauka, cikin natsuwa da girmamawa ya ɗaga mata gaisuwa. A maimakon ya ji ta amsa sai ya ji muryan King yana amsa gaisuwar tasa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Dama yanzu zan nemeka Dad"......... Daga ɗayan ɓangaren King ya ce. "A ina kake tun jiya muke nemanka a waya a kashe?". Raba jikinsa da Auta ya yi, sannan ya miƙe tsaye ya nufi balconynsa dan ma kada Auta ta ji hiransa da King, dan ya sha alwashin ba zai ragawa kowa ba muddin suka kawo mashi tsaiko a kan abin da ba Allah bane ya haramta, su sun zaɓi kenan su yi wa yarinya auren dole su tabbatar da rayuwarta a cikin kunci da bakinciki? To shi bai zaɓi hakan ba kuma ba zai zaɓa ba, infact bai ga wanda ya isa ya hana Zunaira abin da take so ba matuƙar bai saɓawa shari'a ba. Saman ɗaya daga cikin kujerunsa dake wajen ya zauna yana faɗin. "Ina Paris"...... Ta karfi King ya maimaita kalmar Paris kafin ya sake cewa. "To ka yi maza ka dawo in san ganinka". Jinjina kansa ya yi kamar yana a gaban dad ɗin nasa, sannan ya ce. "Dad menene batu a kan Zunaira and Hoorain?". King daga in da yake tsaye ya wani haɗe rai tare da komawa bakin bed ya zauna, momma dake zaune a bakin bed already ne mamaki ya kamata na ganin ya haɗe rai, da kallo ta bisa tana san fahimtar me yasa ya ɓata rai haka? Kada dai ace Smart yana yi mashi wannan iko da ya saba, dik sai hankalinta ya tashi. "Wannan magana ai na gamata, na bawa Abdussalam aurenta, kuma this coming Friday za'a ɗaura shi, dan haka bana da buƙatar sake tada wannan magana, dalilin ma da yasa na ce ka yi gaggawar dawowa kenan, saboda bikin"........ Shiru ya natsu yana sauraron dad ɗin nasa har ya kai aya a magana, sannan ya ɗan gyara zamansa tare da jan dogon numfashi, cikin sanyin murya ya ce. "Amma ita Zunaira ta ce Hoorain take so ba Abdussalam ba!......".. Katse shi King ya yi da cewa. "Ni kuma Abdussalam nike so ba Hoorain ba". Shiru Smart ya ɗan yi, kamar ba zai sake tankawa ba, sai kuma ya ce. "Menene yasa baka san Hoorain dad?"...... A fusace King ya ce. "Saboda rayuwarsa bata da tabbas! Daga yanzu zuwa kowani lokaci zai iya mutuwa, ban shirya ganin rayuwar Zunaira a gantale ba! Dan haka na yi rantsuwa da girman Allah na kara yi ba zan bashi Zunaira ba, kada kuma ka sake mun maganarsu, dan na gama yanke hukunci, wlh a kan wannan magana sai dai Zunaira ta nemi wani uban!!!". Tashin hankali. Haƙiƙa Smart ya fahimci dad ɗinsa ya ɗauki zafi dayawa, kuma a yadda ya yi wannan rantsuwa yake magana a fusace haka ya tabbata iya gaskiyarsa yake faɗe, and kome zasu yi ba zasu taɓa canza mashi ra'ayi, dan haka sai ya ce. "Okey dad, na yarda da maganarka, na yarda Zunaira ba zata auri Hoorain ba, but ina san ka saki Hoorain ya koma yadda yake rayuwa kamar da". Ya kai karshen maganar tare da ɗago idanunsa, unexpect ya yi arba da fuskar Auta tsaye a bakin kofar balconyn tana kallansa tana hawaye, bai yi zatan tana kusa ba, yanzu ta ji dik abin da suka faɗa da King. Daga cikin wayar King ya ce. "Already ni na saki Hoorain, yanzu haka yana hospital yana jinya, idan ya samu sauki zai koma bakin aikinsa, dan mun yi yarjejeniyar hakan da mahaifinsa, ya mun alkawari Hoorain zai rabu da Zunaira har abada, shiyasa ma na sakesa". Jinjina kai Smart ya yi zuciyarsa na ƙoƙarin pushing na fushinsa ya bayyana, shi kuwa yana ƙoƙarin danne zuciyar tasa saboda kada ya yi jayayya da mahaifin nasa, yana da ilmin addini sosai, so yasan rabo tana kisa, idan ya tsaya ya ce zai ja da dad ɗin nasu in Allah ya ƙaddara za'ayi wannan aure to suna iya rasa King ɗin, hakan ne kuma baya so, shiyasa ya sassauta zuciyarsa ya aminta da haka, gara mashi su bi wata hanya su saka King ɗin kaffara kawai a kan su yi ja in ja da shi su rasa shi na har abada, a kan batun aure da batun yara ba'a jayayya, idan ma'aurata sun rabu ba'a gardama a kan ƴaƴa, misali ace uwa ta ce ita zata rike uba ya ce abasa kayansa, irin haka ma Allah yana ɗauke ƴaƴan kowa ya raba faɗa, so a kan aure da yara ba'a ja in ja. "Dad zamu yi magana anjuma". Yana kai karshen maganar ya katse kiran diff ba tare da ya jira amsarsu ba. Alama ya yi wa Auta da hannu a kan ta zo. Da ƴar gudunta ta tafi ta faɗa jikinsa tana sakin kuka mai tsuma zuciya. Rarrashinta ya fara yi cike da so da kauna. Cikin kuka ta fara faɗin. "Shikenan Yah Omerish kai ma yanzu baka goyan bayana? Yanzu ka koma bayan dad? Kai ma baka san my Hero?". Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ya ce. "Kin yarda da ni?"....... Kai ta gyaɗa mashi alamar e ta yarda da shi. "To i promised you that In Sha Allah zaki zama mallakin muradin ranki, burinki zai cika wannan alkawarina ne, alkawari kuma kaya ne". Cike da gaskiyarsa ya yi maganar, babu wasa ko golaya dan ta yi shiru yasa ya faɗa mata haka. A ruɗe ta ce. "Yah Omerish how? Ta yaya zan mallaki Hoorain bayan daddy baya sansa, kuma ya yi rantsuwa da girman Allah ba zai bashi ni ba, sannan kowa a gida baya sansa, har Akka bata sansa, and nan da one week dad ya ce zai aura mun Yah Abdussalam". Tana magana zafafan hawaye suna bin kuncinta. Ɗan jinjina kai ya ɗan yi kafin ya ce. "Haka ne dik abin da kika faɗa, and nasan abu ne mai wahala yiwuwar aurenku, amma In Sha Allah daddy da kansa zai sanya maku albarka a ranar aurenku, darasi zan bawa gabaɗaya familynmu ta yadda gobe ko da kuɗi aka basu ba zasu taɓa sake kyamar talaka ko na kasa da su ba". Zaro idanu waje ta yi, cike da ƙaguwa na san jin abin da zai yi masu ta ce. "Me zaka yi masu da har zai sa su koyi darasi?". Hannu yasa yana share hawayenta ya amsa mata da. "Kada ki damu, ke dai keep praying for me". Ya kai karshen maganar yana duba wayarsa dake ruri alamar shigowar kira. Number momma ce again, kuma yasan dad ne, dan haka sai bai yi picking ba, saboda yana san ya ɗan yi tinani a kan irin lesson da yakamata ya koyar da familyn nan nasu, su san cewa mutum ɗan adam ba abin rainawa bane, da talaka da mai kuɗi dik Allah ne ya yi su.. Jama'a na ce mu jinjinawa momma, lallai ba shakka jinin momma ce yake gudana a jikin Smart, a gabaɗaya kingdom of power momma ce kawai bata kyama ko kyarar talaka, ita ce kawai ta ɗauki kowa dik ɗaya suke, ita ce uwar marayu irinsu Mahnoor, Zee, Khadijah and Mahreen, lallai ba shakka momma baiwar Allah ce kuma jininta ya fi karfi a jinin SMART!! Dan kunga shi ma baya gudun talaka bawan Allah!. Pretty ce ta katse masu hiransu ta hanyar miƙewa zaune a saman kujerar da take kwance, kwata kwata Auta bata lura da ita ba tun shigowarta, dama a saman kujerar ya kwantar da ita, sannan ya wajen ya yi mata allurar da ya ceto rayuwarta. Sai dai kuma ya yi matuƙar mamakin ganin ta yi saurin farfaɗowa, yasan dai zata iya kai kwana biyu a sume kam, sai kuma ga shi ko awa biyu bata yi ba ta farfaɗo, abin da bai sani ba shi ne ita fa Pretty ko da bai yi mata wannan allura ba zata farfaɗo, saboda poison dake cikin chemical ɗin bai yi mata lahani ba dan ita ma akwai irin abin dake jikin Sweetie a jikinta, kuma ita ma hannunta yana iya yin magic, sau da dama tana ɓarin abu ta hanyar magic ɗin, amma rashin sani yake sakawa ta yi zatan kawai ɓari ta yi, bata san da shi a hannunta ba. Da kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa a ransa yana mamakin tashinta a yanzu. Cike da kula da so da kauna Auta ta ce. "Pretty ina kika shiga ina ta nemanki". Tana aikin turo baki bata yi magana ba, miƙewa daga jikin Smart Auta ta yi ta koma wajenta dan ta ji menene yake damunta. Shi kuma Smart miƙewa ya yi yana faɗawa Auta zai je gidansu wajen mom sai kiransa take yi, yanzu ba jimawa zai dawo, daga karshe ya ce mata kada ta sare kuma kada ta bar Hoorain cikin kewa ta rinƙa kiransa a waya In Sha Allah kukanta zai tsaya. Da okey ta amsa mashi tana murna, har da sakin murmushi. Kai yasa ya nufi waje a ransa yana tina ta yadda zai yi ya yi maganin King, lallai ba zasu koma kingdom of power a yanzu ba, dole su dakatar da auren Abdussalam, sai after one month zasu koma, dole ya yi magana da momma dan su shirya komai a tare ta yadda ba zasu rasa King ba. My people's kuna ganin shirin nan zai shiryu kuwa?. Auta zata mallaki Hoorain kuwa a yadda King ya datse dik wata alaƙarsun nan?. Muje dai zuwa, zamu ga shin Smart ne zai yi nasara ko King!. 🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 44 🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥 Tafiya take yi tana waige waige ta fito daga part ɗin mama ta nufi part ɗin momma domin ta duba Zee, har yanzu uncle Jahiz bai dawo mata da babynta ba, yana can ɓangaren Aunty MieMie suna hira, Aunty MieMie ta rike baby gam, ta ce sai dai uwarsa ta biyo shi part ɗinta, ma'ana sai dai Khadijah ta dawo part ɗinta da zama, dan ita ta samu yaro, dama bata da shi, uncle Jahiz ya ɗauka wasa take yi, aikuwa ta nuna mashi da gaske take yi, dan fa ta dage Allah ba zata bada babyn nan ba, uwarsa kawai ta dawo part ɗin da zama dan yaron ya shiga ranta. Sai waige waige take yi dan bata gama sanin hanya ba, hanyoyin akwai sarƙakiya, idan ba ka san cikin family part sosai ba zaka iya ɓacewa, shiyasa take ta waige waige, taga hanyar shiga part ɗin King and Akkas part, sai ta ruɗe ta rasa ina zata bi. Unexpect suka ci karo da mutum, ya fito daga bedroom ɗin King, King ne ya kirasa a yazo a kan batun Spender, so shi ne dalilin zuwansa. Karo suka yi ta ɗan yi baya tana goge goshinta da ta buge da kirjinsa, da yake ita ta fi Zee ladabi da kuma hankali sai ta durkusa kasa tare da ɗaga mashi gaisuwa. Ido uncle Abbas ya zuba mata yana mamakin ganinta, dan shi bai san ta a kingdom ɗin ba. Jin bai amsa mata bane yasa ta ce. "Kayi hakuri ban ganka bane shiyasa"...... Jin kalamanta yasa ya yi saurin ce mata. "Babu komai tashi ki je abinki". Miƙewa ta yi tana yi mashi godiya tare da satar kallansa ta ƙasa ido, gaba ta yi ba tare da tasan ina ta dosa ba, dan bata gane hanyar part ɗin momma ba. Da kallo uncle Abbas ya bita baya san kawar da kallansa daga kanta. Har ta ɗan yi nisa ta tsinkayo muryarsa yana faɗin. "Zo ina da tambaya"........ Juyowa ta yi ta dawo gabansa, tana ƙoƙarin tsugunnawa ya yi saurin cewa. "A'a ba sai kin durkusa ba, magana zamu yi a tsayen ma is okey". Ƙasa ta yi da kanta tana amsa mashi da okey cikin harshen turanci. "Zan iya sanin wacece ke?". Ya jefa mata tambayar yana ɗan sunkuyo da kansa ya kalli face ɗinta. Lokaci guda ta ji gabanta ya faɗi, sai ta ji wani irin fargaba mai razanarwa, tsoronta ɗaya kada yasa a hukuntata dan bata da wata alaƙa da masarautar, kada ya ce waye ya kawosu? To waye zata ce mashi tun da ita ko sunan uncle Jahiz bata sani ba bare ta faɗa mashi sunan wanda ya kawosu. Ganin ta yi shiru ta rasa abin faɗe yasa ya ce. "Zaki iya tafiya". Dan ya lura tambayarsa ya saka ta a cikin damuwa, lokaci guda hakan ya bayyana a face ɗinta. Ai yana cewa ta tafi ta yi gaggawar juyawa har kamar zata yi tuntuɓe, da kallo ya bita yana jin kamar wani abin a ransa, mamakinsa ɗaya shi ne a ina aka samo waɗan nan black beautys ɗin?.... Ni kam na ce to dama mu Nigerians ai shegen shiga rai ne da mu ato, dik in da muka je sai mun ratsa zuciyar mutane, bare ma mu arewacin Najeriya ai daban muke. Har sai da ta kurewa ganinsa sannan ya ja dogon numfashi tare da wucewa ya nufi elvator domin ya yi ƙasa ya koma part ɗinsa, mammie na can tana jiransa ya dawo ta zazzage mashi jajjagen masifar da ta jajjaga ta ajiye mashi. Shi kuwa yana nan zuciyarsa ta shiga wani yanayi. Babbar magana, muje zuwa my people's, ba'a fara komai ba, RAWANIN ZALINCI zai baku mamaki gaba kaɗan, fatana dai Allah ya ara mana lokaci!!. Sai da Khadijah ta shiga almost part uku a cikin amma bata iya gane part ɗin momma ba, daga karshe ta lallaɓa ta koma part na mama ta yi kwanciyarta zuciyarta cike da tunanin ina Zee? Bata damu da tunanin ina babynta kamar yadda ta damu da tunanin ina Zee ba?. Dan ta san halin yar uwar tata da shegen zuciya bata ɗaukar raini. A ɓangaren guda kuwa, mammie dai ta yi jigilar aikin gasawa Sarina jiki, Sarina anji jiki, dan ma Allah ya taimaketa a ba kan tsini ta isko Smart ba, ai da bata rage ba, amma dik da haka ta jibgu ba karya, jiki dik ya yi ruɗu ruɗu ya kumbura, ta sha ruwan zafi kam ba karya. Idan muka waiwaya gefe guda kuma, a can hospital ɗin Kingdom ɗin, a lokacin da King ya saki Hoorain, kwance yake a saman bed na hospital ɗin, sai da ya yi good two days kafin ya dawo cikin hankalinsa, amma fa har lokacin baya iya tafiya, tin da yake a rayuwarsa ba'a taɓa yi mashi irin wannan horo mai bala'in tsananin ba, wannan ɗakin duhu wlh karshen azaba ne, amma kuma da yake ba bawa yake sanyawa kansa so ba, dik wannan wahala da suka bashi wlh soyayyar Auta ninkuwa ya yi a ransa, sai ya ji ma tamkar buɗe kirjinsa suka yi suka zuba mashi santa na wannan azaba da suka yi mashi. A ranar da ya farfaɗo ma da sunanta ya farfaɗo a bakinsa, sai dai yana buɗe idanunsa da Abbonsa ya fara yin tozali, ya ji matuƙar daɗin ganin mahaifin nasa, sai dai kuma da buɗar bakinsa ya ce. "Abbo Hoonaira bata sake zuwa wajena ba ne?". (Yana tinanin tin da ta je wajensa a ɗakin duhu kenan bata sake zuwa ba, dan tun wannan rana da ta je wajen nasa King ya zo ya ɗauketa, zafin ɗaukarta da aka yi yasa zuciyarsa ta tsananta ciwo, dalilin suman da ya yi kenan sai yau ya farfaɗo.) Ɗan girgiza kai Abbo ya yi irin alamar tausayawa ɗan nasa, shi ma ya rame sosai, dama ga tsufa, ga ciwo, ya sha wahala dattijon arziki, zuciyarsa ta rauta a kan Hoorain da Auta sosai, sai yake jin kamar ba zai iya sanya karfi wajen rabasu ba, ga shi kuma ya yi wa King alkawarin zai rabasu, dama a tinaninsa karfi zai sakawa Hoorain ɗin, zai ce mashi ya zaɓa ko shi ko Auta, kowa dai yasan dole Abbonsa zai zaɓa ko da hakan zai yi sanadiyar rayuwarsa tun da iyaye dai ba'a haɗasu da komai, to commander ya ji jikinsa ya mutu a kan wannan mataki da yake san ɗauka. "Abbo dan Allah ka amsa mun, Hoonaira bata zo bane?". Ya faɗa cikin raunatacciyar murya. Jinjina mashi kai commander ya yi alamar e bata zo ba, ya kasa iya furta word, dan ba shi da abin faɗe. Tafukan hannunsa Hoorain ya buɗe tare da matsar da hannunsa kusa da hannun Abbon nasa, da yake commander yana zaune a saman chair na masu jinyar majinyata. Hannun Abbon nasa ya riko cikin nasa. Cikin wata iriyar wahalalliyar murya irin na wanda ya sha azaba, da kyar da kyar ya fara magana cike da dakiya da jarumta, wlh ba dan assistant commander ne shi ba, ya saba da wahala saboda irin horan da ya karɓa, Allah da ba zai iya ɗaukar wannan horo ba, ba'a taɓa sanya mutum a ɗakin duhu ya wuce kwana uku ya fito a raye ba, kwana ɗaya idan mutum ya yi aka fitar da shi sai ya sha jinya na satittika, kuma kafafunsa basa iya takawa, amma shi almost week, ya fito kuma bai yi wani dogon jinya ba ya farfaɗo, ba shakka yana da jarumta sosai, commander ya iya renon ɗan nasa, ya mayar da shi zaki ɗaya tamkar da dubu. "Abbo ina san Zunaira, ina santa fiye da yadda nike san rayuwata, a da kafin in bayyana mata soyayyata a gareta ina jin kamar zan iya dannewa in mutu da santa, amma tin daga ranar da na bayyana mata na gane cewa tabbas ba zan iya hakuri na danne sonta har in koma ga Allah ba, please Abbo ka taimaka mun, dik wani hukunci da zaku yi mun ku yi mun na yarda, amma dan Allah kada ku rabani da Zunaira, ba zan iya jurar wannan zafin ba, gara mun zafin wuta a kan wannan zafi, ban taɓa neman wani abin a wajenka na rasaba, shiyasa a kullum nike kara yin alfahari da kai, a yanzu ma ga buƙatata na kawo maka dik da nasan kai ma baka da iko a kan hakan". Ya kai karshen maganar wasu zafafan hawaye da suka cika mashi idanu ne suka zubo ta gefe da gefen kunnensa saboda yana kwance ne. Idanunsa jajir kamar wuta, kirjinsa na suya matiƙa, yana jin zafi tamkar an ɗaura shi a saman wuta, ya rasa a ina zai sanya ransa ya ji daɗi. Wani irin zabura commander ya yi, dan tin da yake da Hoorain bai taɓa ganin hawayensa (tin da ya yi wayo kenan ba tin yana jariri ba) lallai girman san da Hoorain yake yi wa Zunaira ya wuci misali, yau saboda santa ya yi kwallah? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, yanzu da wani idanu commander zai kallesa da kudurinsa na rabasu?. Take commander ya ji ko mutuwa zai yi sai dai ya mutu amma ba zai iya cewa Hoorain ya rabu da Zunaira ba, ba shi da wannan kwarin gwiwa, Hasbunallahu wani'imal wakil, shi ne kalaman da commander yake ta mainaitawa a ransa. A dai'dai wannan gaɓa guyson ya kawo mashi waya domin su yi waya da Auta, ai saboda farinciki Hoorain bai san lokacin da ya miƙe zaune tare da tsige drip dake manne a hannunsa ba, murna a wajensa ba'a magana. Yana magana da ita zafafan hawaye suna bin ƙuncinsa, wlh sai da guyson ya taya shi zubar da hawaye, ya tausaya masu matuƙa, sai yake jin tamkar ya ɗaura masu aure kawai, sai dai bashi da damar yin hakan, sai kawai ya hau tayasu da addu'a, ga azumi ya kawo kai, sai ya yanke shawara a cikin zuciyarsa a kan zai sanar da King zai tafi saudiya ya sauke farali, idan ya je ya yi alkawarin tun ranar da ya dira har ya dawo sunansu ne zai kasance a bakinsa, addu'a ba dare ba rana zai yi masu, wannan hali da suke ciki dole a yi saudiya da sunansu, in ba haka ba akwai matsala, shi yasan idan ba Allah ba babu wanda ya isa ya canza rantsuwar King a kansu!!. Bayan sun gama magana da ita ko in ce wancan baturiya ta kwace wayar ne ya bawa guyson wayarsa tare da dawo da kallansa a kan Abbonsa. "Abbo ina wayata?". Ya faɗa yana goge hawayensa. Allah Akbar, my people's soyayya idan ba'ayi dace ba wlh musifa ce, yau assistant commander of dangerous warriors ne yake hawaye a kan mace? Macen ma under 15 ba wata macen azo a gani ba, innalilahi akwai matsala fa. Kasa jurar ganin halin da yake ciki guyson ya yi, dan ya ga kamar Hoorain fa ya samu matsala, da gudu ya juya ya bar room ɗin, dan yana da raunin zuciya bawan Allah. Shi kansa commander ji yake yi tamkar ya taya ɗan nasa hawaye, dan wani irin tausayinsa ne ya kama shi matuƙa. Hannu kawai ya kai yana taya shi goge hawayen yana faɗin. "Hoorain ya isa kukan nan haka ka ji? In Sha Allah Allah yana tare da kai, idan gimbiya matarka ce babu wanda ya isa ya zama barazana ko shamaki a tsakaninku, ina da yakinin Zunaira matarka ce, ka yi hakuri". Rungume Abbon nasa ya yi, cikin zafin zuciya da raɗaɗi ya ce. "Abbo dole waɗan nan hawaye ba zasu dakata daga zuba daga idanuna ba har sai na dakatar da na Hoonairata, saboda a cikin zuciyata na ji kuka take yi a yanzu, dan Allah ka bani wayata domin in kirata in dakatar da nata hawaye zaka ga nawa ma sun dakata". Out of control yake maganar. A dai'dai lokacin da ya yi wannan magana tabbas kuka Auta take yi, dan a lokacin tana bawa Smart labarin abin da yake a tsakaninsa da my heronta. Soyayyar gaskiya daban take, ya so ta tin tana jaririya ai dole ya iya fahimtar halin da take ciki. Abbo ya fahimci Hoorain fa baya cikin hayyacinsa dan haka sai ya ce. "Ka yi shiru wayarka tana hannunsu Ansar, yanzu zan sa a karɓo maka, ya isa haka ka ji?..........". Commander bai gama tufe baki ba sai ga sallamar Ansar and Anwar aminan kwarai sun shigo, da ka gansu zaka fahimci suna cikin damuwa da tashin hankali, ba jimawa suka bar hospital ɗin, wanka suka je yi, dama suna a tare da shi suna taya commander jinya bayin Allan, su suka yi jinyar commander ɗin ma har ya warke, yanzu kuma suna taya shi yin na Hoorain. Hoorain yana ganinsu ya zabura yana faɗin su bashi wayarsa. Ansar ne ya ciro wayar daga aljihunsa tare da na Auta da yake wajensa ya miƙa mashi yana faɗin. "Our lion lafiya kuwa?". Ai ina bai amsa masu ba, kunna wayarsa ya yi, jikinsa har yana ɓari ya shiga contacts, sai kuma me? Ya rasa wani number zai kira, dan bashi da numberta na Paris, wayarta ma ai gata a hannunsa. Da karfi ya ɗaga wayar tasa ya yi wurgi da ita dan takaici, sai dai Ansar ya yi gaggawar capke wayar bata isa kasa ba, da tarwatsewa zata yi, ransa ne ya kara jagulewa, zuciyarsa tana tafasa ya juya ya kifa kansa da jikin bango yana wani irin huci mai fita da karfi karfi. Gabaɗaya sai da suka yi matuƙar tausaya mashi, take jikinsa ya kara tsananta zafi sosai, zazzaɓi ne ta rufesa sosai. Miƙewa tsaye daga kan chair commander ya yi tare da tallabo ɗan nasa da kyau domin ya taushesa, ya san shi da ɗan banzar zuciya, tsoronsa kada ya je ya haɗiyi zuciya dan ɓacin rai ya mutu su shiga uku, idan Hoorain ya mutu ina zai sanya ransa?. A gaggauce su Ansar suka matsa kusa da shi dan su taushi zuciyar zaki kada ta buga. Sai huci yake yi bai iya cewa komai, ya dai datse idanunsa gam alamar baya san ganin kowa. A dai'dai wannan lokacin kuma Smart yake rarrashin Auta yana yi mata alkawarin zata mallaki Hoorain while shi ma commander alkawari ya shiga yi wa Hoorain a wannan lokaci a kan in dai yana raye to da izunin Allah zai mallaki Zunaira, ya yi hakuri ya daure har ya samu lafiya. Sai dai ina, Hoorain bai iya amsawa ba, bayan wannan huci babu wani abin da zaku ji yana fita daga garesa. A ɓangare guda kuwa, Chuchu dai ta lallaɓa ta gudu ta koma part ɗin Akka da zama, tun safe take can, har dare taki komawa part ɗinta, da yake yau Jawad ya je office to bai dawo da wuri ba, saboda aikin King na gina wasu makarantu dan marasa galihu, so wannan aiki ta tsayar da shi, sai ana kiran mangariba ya shigo gida. A gaggauce ya yi wanka ya wuce musque. Bai dawo ba sai da ya yi sallar isha'i a wajen, sannan ya dawo gida. Part na King ya fara zuwa, sai da suka gaisa suka ɗan yi hira kaɗan kafin ya wuce wajen momma domin su gaisa, dan tun safe basu haɗu ba. Ita ma suka ɗan taɓa hira na kamar ten minutes, sannan ya yi mata sallama ya fito, yasan yana da mara lafiya, hankalinsa dik yana a kanta, dan ma dai ba laifi ta samu sauki saboda wadataccen kulawa da ta samu daga wajensa. Bedroom ɗinsa ya nufo yana tinanin yadda zai yi da ita yau, dan gaskiya batu na Allah a matse yake, yana hannu, ita kuwa tsoronsa take ji, jiya ya yi ya yi da ita ta bashi haɗin kai, amma ta murje idanu ta ce bata san wannan zance ba, ko taɓata taki yarda ya yi, da ya taɓata zata saka mashi kuka, ya rasa me zai yi mata, ga shi su kuma jarabarsu fa ba irin wadda za'a iya dannewa ta dannu bane, shiyasa kuka ga suke yawan san shan cappuccino, dan yana ɗan sassauta masu, kun gano su ko?. Ya yi mamakin ganin bata a cikin bedroom ɗin, ya kuma san bata part na momma, dan da tana can momma zata ce mashi gata nan su wuce a tare. Toilet ya nufa cike da tinanin ina ta tafi? Wanka ya yi ya fito ya shirya cikin sleeping dress ɗinsa masu kyau. Waje ya fito sai tashin kamshi yake yi, kai tsaye ya nufi part na Akka, dan yasan bata wajen mummynta, bata cika zuwa can ba, in bata wajen momma to tana wajen Akka. A yayin da yake nemanta shi kuma Jaish yana kwance saman bed ɗinsa barci ta gagaresa, tin ranar da wannan abin ya shiga tsakaninsa da Mahnoor bai kara yarda sun haɗa hanya da momma ba, tsabar rashin kunya da safe idan ya tashi barci kafin ya tafi office sai ya kirata a waya su gaisa, haka da rana da yamma ma, wai shi kunya yake ji, ita kuwa momma ta ɗauke Mahnoor daga part ɗinsa, ta kafa mashi tarkon da sai ya kawo kansa, shiyasa ko ya kirata a waya dan su gaisa yana ɓuyan mata bata wani damuwa, dan ta san halin kayanta, tasan maganinsa. Mahnoor baiwar Allah sai da ta yi kwana guda a sume, sannan ta farfaɗo, ta sha jinya da ruwan zafi, tun tana ihu idan za'a sakata ruwan zafi har ta saba, yanzu a duniya babu wanda take tsoro biyun Jaish, kuma tana san sa fa, amma tsoronsa ya lulluɓe san, idan ta ji sunansa ma gabanta faɗu yake yi, bata san jin dik wani abin da ya dangancesa, zuciya kuma da bata da ƙashi, idan ta ɗan ji shiru bata ji ɗuriarsa ko da suna call da momma bane dik sai ta bi ta damu kanta tana san jin ko yana lafiya, ita dai idan yana lafiya shikenan hankalinta ya kwanta, wani ɓangare na zuciyarta yana bala'in san kallan face ɗinsa, dan tana kewarsa sosai. Wani ɓangare kuma tsoronsa!!. So kwance yake yana ta juyi ya kasa yin barci, tinanin yadda ya ɗanɗani zumarta ne kawai a cikin ƙwaƙwalwarsa, yau tun safe tula tulanta suke yi mashi yawo a cikin idanunsa, ya rasa gane wani matsayi zai ajiye kansa, abin har tana san fin karfinsa. •••••••••••••••••••••••••••••••••🔥 Jawad. Barci ya isko Akka take yi, hakan yasa ya lallaɓa ya ja da baya, kai tsaye ya nufi bedroom na ƴan'matan dake cikin part ɗin na Akka. Tun bai shiga ciki ba ya tabbatar da tana wajen, dan wani irin kamshin perfume dake tashi a ciki, yasan babyn tasa yar wanka mayyar san kamshi ce. Har wani ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tura kofar ya shiga. Saboda wawta irin ta Chuchu, wai fa ta gudun mashi ne a haka, sai ta bar kofar bedroom ɗin a buɗe........... ANAYA BA DA GANGAN TA BAR KOFAR A BUƊE BA KUWA? 😅 A lokacin da ya zo ta jima da yin barci abinta, ba ƙaramin daɗin hakan ya ji ba. Dan haka yana zuwa bai wani ɓata lokaci ba ya sureta sai cikin part ɗinsu. Saman katafaren bed ɗinsu ya direta tare da hayewa shi ma, tana ɗan motsawa a hankali tana san farkawa ya yi gaggawar kashe wutar ɗakin, shi fa yau sallarsa, tsuntsu daga sama gasasshe, dama a hannu yake. Bai bari kansa ta kulle ba ya hau ɓalle botiran kayan barcin jikinta. Can cikin barci ta ji ana rabata da kayanta, a razane ta farka tare da fara ƙoƙarin saka mashi ihu tana turesa. Murya can ƙasan maƙoshinsa ya ce. "My Jannawad Yah Jawad ɗin ki ne fa".......... Cike da tsoro ta amsa mashi da. "Ni ai yanzu nace bana sanka ko? Dan Allah Yah Jawad ka kyaleni, ni wlh na fasa auren, ni kawai komawa zan yi........". Bai bari ta ƙarisa maganar ba ya zira yatsarsa a cikin ɗan bakin nata dan ya samu ta yi shiru, cikin sigar rarrashi ya fara bata baki, har da ce mata. "Na yi maki alkawari this time kasheki da daɗi zan yi, ba zan baki azaba ba sai daɗi, ki yarda da ni, idan har ban saki kin yi ihun daɗi ba to na yarda ki fasa auren". Make mashi kafaɗa ta yi tare da gabza mashi ciwo a yatsar tasa har sai da ya saketa ya zare yatsar tasa daga bakin nata. Cikin muryar shagwaɓa mai kara narkar da zuciyarsa ya mutu a kanta ya kuma motsa abar tasa ta ce. "Ni dai bana so kuma ban yarda ba, ni na dai'na yarda da kai, ba wani daɗi face azaba". Shiru ya ɗan yi, can wata dabara ta faɗo mashi a ransa, a natse ya ce. "To yanzu me kike san na yi maki sai ki yarda ki zauna da ni?". A hanzarce ta ce. "Romance kawai ban da wancan abin" Oh ni Princess Teema jikar Muhammad 🤔 yaran King suna yin abin da suka ga dama, wai romance take so ban da zuwa duniyar mercury! Kai jama'a ashe tasan romance yar rainin wayo, ko da yake yadda suka kware wajen bawa flowers ruwa ita da Auta dole su san komai, sai dai basu san cewa karon farko babu daɗi ba, a tinaninsu zafin ba wani mai yawa bane, to bama gara Chuchu a kan Auta ba, ita fa Hoorain assistant commander da kansa take so, gata yar firitu ko rabin shekarunsa bata kai ba, gara Chuchu da ɗan girmanta ai, ba zata ji wani wahala sosai ba. Abin ya so bashi dariya, wannan shi ne abin nema ya samu, dan kuwa har ya ga yadda zai sanyata kukan daɗi ta yadda bazata san time da zai shiga bama sai dai ta jisa a ciki, yanzu ya kara tabbatarwa da Chuchu yarinya ce, ai shi kam shal zuciyarsa, daga nan duniyar earth sai duniyar mercury, dan haka da sauri ya ce mata ya amince da dokarta, romance kawai ban da zuwa duniyar mercury. Faɗowa jikinsa ta yi tana sauke ajiyar zuciya irin ta ji daɗi zasu yi romancing juna kawai. Shima wani sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke abar tana kara miƙewa. Hannunsa dikka biyu ya tura cikin vest ɗin jikinta, kayansa ya capko dikkansu biyu yana kai ɗan bakinsa saman lallausan wuyarta, tongue ɗinsa ya fitar ya fitar ya fara lashe wuyar tata. Hannayenta ta kawo jikinsa, ta sanya ɗaya ta bayansa ɗayan kuma ta ɗaura a saman kirjinsa, wlh Chuchu ba dai iya bawa flower ruwa ba, ta kware sosai, dan kuwa cikin rigar barcin jikinsa ta tura hannunta, a hankali ta fara murza mashi kan nipples ɗinsa cikin salon da ko kaki ko ka so sai ka je duniyar mercury ka dawo. Take Jawad ya rasa ɗan control da ya ɗan rage mashi, dama dannewa yake yi, haba sai ji ya yi bafa zata dannu ba, Chuchu na neman ta fisa iya bawa flower ruwa, ko da yake an kwana biyu ya tara abar ta yi mashi yawa ba zai iya wani rikewa sosai ba a yanzu. Ai da ɗan karfi karfi ya shiga matsa tula tulanta. Kukan shagwaɓa mai kara tayar mashi da hankali ta saka mashi, tana wani irin narkewa a jikinsa saboda sakonsa yana ratsata da kyau. Ya ƙasa iya tambayarta dalilin kukan nata, sai wani irin numfashi yake saukewa mai ɗumi. "Yah Jawad kai baka iya romance ba, a hankali fa ake yin komai, hakan ne zai sa mutum ya ji shaukin ya kuma tambatar romancing ɗin nasa ake yi, amma kai kana matse mun su da karfi ba zan ji wani feeling ba face zafi". Tana magana tana turo baki. Ina ai Jawad sama sama kawai yake jiyota, wannan bayani da tun kafin ta zura hannunta a cikin rigarsa ta yi mashi da ya ɗauka, amma yanzu bai ɗauki komai ba. Yayin da yake cikin wannan jin daɗi shi kuwa jaish yana kwance mararsa tamkar zata fashe mashi saboda ciwo, abin takaicin barcin ma yaki zuwa, da zarar ya rufe idanu wannan abin kawai yake tinawa ya rasa yadda zai yi da ransa. Miƙewa ya yi ya nufi toilet dan ya ɗauro alwala, sai wani uban kame jikinsa yake yi amma abin ya ci tura, yana ta wani jan tsaki tamkar akwai wanda ya yi mashi laifi. Alwala ya ɗauro ya fito, dadduma ya zo ya shinfiɗa ya tada sallah. Sai dai kuma ina, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, hakkin Mahnoor na kansa ya tauye mata, dan haka sallarma ta gagaresa yiwuwa, dan Allah ba zai barshi ba. A cikin sallar tasa ma sai ya ɗauko wannan surar ya fara karantata dai'dai, sai ya kareta da wata surar, da yaga fa abin ba zata yiwu ba zai tabka saɓon Allah, sai ya sallame sallar kawai ya nufo waje, har lokacin yaki yarda ya je in da momma take ko zai sami damar gani matar tasa ya ji sanyi a ransa, shi dai yana jin kunyar su dikkansu biyu har Mahnoor ɗin. Garden ya nufa domin ya ji ko zai samu sassauci a can. Nan fa ya isko Dr Raj da ya tasa Zee a gaba wai sai ta faɗa mashi tana sansa kafin ya kyaleta ta shiga ciki, ita ma Zee munafuka ce, ta iya iyashege sanka sanka, da gangan ta fito garden dan kawai ta haɗu da shi, kwana biyu tana yi masu wasan ɓuya shi da uncle Jahiz, sam sam basa samun damar ganinta, ga shi Khadijah ta koma part na Aunty MieMie, to sun koma tare, hakan yasa Dr Raj bai san in da suke ba, gara ma uncle Jahiz ya san in da suke, amma dik da haka tana wasan ɓuya da shi. To yau zuciyarta ta kai ƙololuwa wajen san ganin Dr, ta ji ba zata iya jurewa ba shi ne ta zo garden da nufin ta fito shan iska ƴar ƙaniya, waye ya ce mata so wasa ne. Abin dariyar kuma tun karfe 8 na dare ta fito garden ɗin, ta zauna tana ta raba idanu tana jiran ya zo, har karfe 9, zaman awa guda ta yi, dik da haka ko yunƙurin komawa ciki bata yi ba, dan tasawa ranta sai ta gansa zata koma. Sai 9:30 ya fito rike da cup na cappuccinon yana ƙoƙarin kiran number Aneesa da ta zo garden ɗin ta samesa, yau ya kawo har wuya ba zai iya jurar rashin ganin Zee ba, shi ne zai kira Aneesa ta bincika mashi wajen waye Zee ta zo a gidan dan yasan in da take, har ya ayyana a ransa in ma ta koma garinsu ne to wlh gobe dole ya ɗaga jirgi ya je ya ganta, dan soyayarta na azalzalar zuciyarsa. Bai kai ga kiran number Aneesa ba ya shigo cikin garden ɗin. Yana shigowa suka yi four eyes da ita, hakan tasa ya fasa kiran Aneesa ya katse kiran. A tare suka sauke ajiyar zuciya na ganin juna, sai dai kuma dan rashin kunya tana ganinsa ta wani miƙe irin basarwan nan, irin bata damu ba ta nufi hanyar fita daga garden ɗin tana ɗaga mashi gaisuwa, a zuwan wai ita zata bashi waje tun da ya zo zama ne. Kai Zee yar duniya ce, sai ta nuna sam sam kamar bata wani damu da shi ba. Sai da ya bari ta zo zata ratsa gefensa ta wuce ya yi gaggawar tare mata hanya, a hanzarce ta ɗago kai dan ta tambayesa dalilinsa na tareta, sai dai kuma tana ɗagowa idanunsu ya sarkafe juna, take suka mace da kallan juna, suka afka duniyar bawa flowers ruwa ba tare da jirgi ba. Sun ɗauki almost 5 mins a haka kafin ta daure ta kawar da kallanta tare da cewa. "Zan wuce ne ina san hanya". Ƙasa sosai ya yi da murya kamar wani kwarton da ya je abinga ɗin matan makocinsa. Yana kashe murya yana lumshe idanu ya ce. "Ina kika shiga two days kika barni a wahale ina ta fama kamar mara gata? Kin san wahalar nemanki da na sha kuwa?"...... Ɗan taɓe baki ta yi irin ita bata wani damu ɗin nan ba, sannan ta amsa mashi da. "A kan me kake nemana to?". Wai irin ita bata san komai ɗin nan ba. "A kan love ɗinki dake cikin zuciyata". Yadda ya yi maganar wlh sai mutum ya ji tsikar jikinsa ya tashi, ashe Dr rikakken ɗan love ne, sai ma idan yana magana yana wani lumshe idanu yana ɗan cizan kyawawan lausasan lips ɗin nan nsa, sai ka ji tamkar ka rungume shi. Ita ma dai Zee haka take ji, tamkar ta rungumesa saboda yadda yake yi, da alama wannan abin a jinin jikokin Akka yake, shiyasa Ummie ya mutu a kan ganin Ramish, ga nan ita ma Zee ta ji tamkar ta rungume mana Dr namu na amana, Dr mai kiwon lafiya kuma mai kiwon zuciya mai ɗauke da soyayya. "Ai ni na faɗa maka bana sanka". Da kyar ta iya faɗar hakan, saboda kwarjinin da ya yi mata, ga wani irin haiba da kyau, hasken fitillu suna haska shi da kyau. Kashe mata ido ɗaya ya yi yana binta da wani irin mayen kallo, lokaci guda ta rasa natsuwarta, take ta yi ƙasa da kanta. Shi wuka gera guda ya ɗaga cikin salo mai jan hankali slowly ya ce. "Da gaske bakya san Dr?". Ai ƙasa buɗan baki ta yi magana ta yi, ta rasa ma a wani duniya take, just imagine, irin wanna kyakkyawan jinin Modarawa ya tsaya yana yi mata magana irin haka ai dole ta rasa abin faɗe, tana ma da ƙoƙari da ta iya dannewa ta bashi wasu amsohin, kanin Yah Ramish fa, haba Zee ta yi ƙoƙari gaskiya. "Idan kika amsa mun cewa baki sona a yanzu da muke haka kafin 5 mins ta buga to zan hakura kin ji beautyta?". Ya kai karshen maganar yana riƙo hannunta da take ta faman murza ƴan yatsun nata saboda rashin abin faɗe. Shiru ya zuba mata idanun har tsawon five minutes bata iya ko motsawa ba, ko ɗago idanu ta kallesa ta kasa. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yanzu ya kara tabbatarwa da kansa ta fola mashi. Matsawa kusa da ita sosai ya yi, ƙasa da murya ya yi a dap kunnenta, sannan ya ce. "Okey furta mun wannan kalma mai tsadar gaske da zuciyata take mararin sauraro daga wannan hot sexy lips ɗin naki! Please beauty kada ki cigaba da jan rai'na, zan iya saka maki kuka". Kalamansa na karshe cikin zolaya ya yi su. Make kafaɗa ta yi, sai a lokacin ta samu damar cewa. "A'a ni ba wani kalma da zan faɗa maka, kawai ka bani hanya na wuce ina jin barci". Ta kai karshen maganar tare da raɓawa gefensa zata wuce tana kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata. To fa shi ne ya tare mata hanya ya ce ba zata wuce ba har sai ta ce tana san shi, shi ne Jaish ya zo ya samesu suna wannan rigimar, ya ƙanƙame hannayenta dikka biyu cikin nasa yana yi mata magiyar ta ji tausayinsa ta ceci barcinsa na dare yau ta furta mashi wannan kalma idan ba haka ba babu shi babu barci. Haba ai Jaish yana ganin haka hankalinsa ta kara tashi, ya ji lallai shi ma yana buƙatar matarsa, sai dai ba zai iya zuwa ba, wuce Dr ya yi ya shiga can cikin garden ɗin ya kwanta saman sofa, tsabar yana cikin yanayi ko ɗagawa yayan nasa gaisuwa bai yi ba, kamar ma bai gansa ba, Dr ya ɗan yi mamakin hakan, amma sai ya yi tinanin ko daga barci ya taso ne ya fito. Da kallo Zee ta bi Jaish har ya shige ciki, da yake jini ba wasa ba sai ta ga ya yi mata kama da Dr. Shammatarta Dr ta yi a hanzarce ta kwace hannunta daga rikon da ya yi mata da sauri ta bar wajen ta nufi cikin gida tana ɓoye murmushinta. Ranta ya sanyaya ta ga sahibinta, kai tsaye ta wuce part na Aunty MieMie. Da farko ya yi niyar rufa mata baya ya capkota, amma sai ya fasa dan yana san zuwa ya duba lafiya Jaish yake kuwa?. Ta kallo ya bita har sai da ya ga ta shiga part na aunty MieMie sannan ya juya ya koma cikin garden ɗin wajen Jaish. •••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥 Da gudun gaske suka shiga bedroom na Black Tiger, har lokacin yana nan yadda suka barshi, ko motsawa bai yi ba. Da gudu Ronnie ya nufi gaban mirrorsa domin ya fara controlling na kwakwalen robbot ɗin nan dan su yi mashi abin da ya dace, kun san sai ana yi ana taimaka masu wajen shigar masu da abin da ake san su yi. Katafaren torch screen computer na Black Tiger dake kusa da mirror ya buɗe domin ya shiga sarrafasu. A gaggauce ya ce da Sweetie ko akwai wani abin da zata iya taimakawa yayansa da shi domin ya farfaɗo? Saboda ba zai iya controlling na Robbot ɗin nan dikka shi kaɗai ba, za'a iya samun gagarumar matsala idan Black Tiger bai tashi ba. Dawo da kallanta a kansa ta yi, cike da tashin hankali ta ce. "To ai ban san menene ya same shi ba bare in san abin da zai taimaka mashi da shi". Da yake yana cikin tashin hankali kuma yana tsananin buƙatar Black Tiger a yanzu sai ya amsa mata da. "Abu ne wanda ya danganci magic ɗinsa, ba kin ce dik wasu ruhohin tsafi suna tsoron ayiyin Allah ba?". Yana magana yana ƙoƙarin kunna laptop ɗin. Kai ta gyaɗa mashi alamar yeah haka ne matsafa suna tsoron ayar Allah. "To ki taimaka ki tofa mashi ayoyin su samu su sake sa zai tashi kin ji?"........ Jinjina kai ta yi tare da nufar bed ɗin da gudu, hayewa sama ta yi jikinta har kerma yake yi, hankalinta na kara tsananta tashi ya hau tofa mashi addu'oi babu kama hannun yaro. Shi kuma Ronnie ya gama kunna laptop ɗin sai kuma ya rasa menene password ɗinta, tashin hankali!!. Zaro idanunsa ya yi tare da fara ƙoƙarin gwada password da dik yasan Black Tiger yana amfani da shi wanda zai iya buɗewa. Sai dai dik wanda yasa ace mashi wrong, take wani irin zufa ta fara keto mashi a face ɗinsa, yanzu ta ya zasu yi controlling waɗan nan robbot ɗin har su yi nasara? Ya yi iya gwadawansa ya gagara buɗewa, warning suka fara yi mashi a kan dama guda ɗaya ta rage mashi, idan har ya sake saka wrong password to laptop ɗin zata tufe kanta da kanta, idan kuma ta rufe sai afta 24 hours zata buɗe. Tashin hankali. Ai Ronnie bai san lokacin da ya zube gwiwowinsa a ƙasa ba, suna cikin tsaka mai wuya. Ganinsa a haka yasa Sweetie ta ce. "Ronnie lafiya kuwa? Menene yake faruwa?"......... Murya a raunace ya ce. "Ba zamu yi nasara ba Sweetie, ba zamu kai labari ba"....... Tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa saboda zarosu da ta yi, hankalinta ya tsananta tashi, a rikice ta diro kasan bed ɗin ta nufosa, a gabansa ta zubar da gwiwonta ita ma, ya sunkuyar da kansa ƙasa yana tinanin mafita, a zuciyarsa yake cewa shikenan yanzu za'a kwace masu birninsu? Yanzu wasu ne zasu mulki birnin nan? Su zasu zama bayinsu kenan? Ga shi kuma dayawa daga cikin mutanen birnin sun marawa waɗan da suka kawo masu harin baya, saboda kowa dai yasan matan wannan birni sun tsani Black Tiger da RAWANIN ZALINCI da ya ɗaura a kansa yake mulkarsu, dan haka sai suka yi mashi tawaye, dik suka rufawa waɗan can baya, harta wasu daga cikin bara gurbin warriors ɗinsa sun juya mashi baya wannan dalili ya kara tada hankalin Ronnie fite da tinanin kai tinani. A yau dai Allah ya nunawa Black Tiger karfin ikonsa dik na banza ne, wato idan Allah ya ga dama ya tashi kamaka cikin minti ɗaya zai yi maka kamun da dik danginku zasu taru a rasa mai kawo komai ƙanƙantar mafita a lamarin. Hannu Sweetie tasa ta tallabo kumatun Ronnien, idanunsa sun tsananta ja sosai, jikinsa dik ya yi sanyi, kamar zata yi kuka ta ce. "Menene yake faruwa Ronnie?". ...... Ajiyar zuciya ya sauke, bai ɓoye mata komai ba ya zayyana mata dik abin da yake faruwa da cinsu da yake da ake shirin yi, ga shi mayakansu sun yi wa Black Tiger tawaye, bugu da kari matan birnin dik sun juya mashi baya sai ƙalilan masu tsoro azaba da izayar Black Tiger ne suka ki kwaye mashi baya, amma kusan rabin birnin sun bi bayan waɗan can, yanzu maganar da ake yi ma sun dinfaro cikin empeir na Black Tiger domin su fitar da shi su gurfanar da shi a gaban kowa su kashe shi su kwaci CROWN OF INJUSTICE ɗinsa su ɗaurawa kansu, sannan su zauna a saman powerful seat ɗinsa. My people's me kuke tinani a wannan yanayi? Kun dai ga irin aya da Allah ya ajiyewa Black Tiger, dan haka yakamata bawa ya sani dik wani karfin iko da mulki da yake ji da shi second ɗaya ta yi wa Allah yawa ya yi watsa watsa da rayuwarsa ya mayar da shi abin tausayi, dan haka aikata ba dai'dai ba dan Allah ya baka wata dama sam ba mafita bace a gareka, dan zaka faɗa hanyar da ba zaka iya fita ba, Allah dai yasa mu fi karfin zuƙatanmu yasa mu dace. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ "Ronnie ka dai'na saurin sarewa daga samun rahamar Ubangiji, In Sha Allah Allah zai kawo mana mafita, yanzu dai mu yi shawarar meyakamata mu yi?"....... Muryarsa a rautace sosai ya ce. "Dama ɗaya muke da shi Sweetie, dama ɗaya ta rage mana, idan har muka saka wannan password na karshe ba dai'dai ba shikenan laptop ɗin zai rufe kansa sai after 24 hours za a sake gwadawa". Tashin hankali, zaro idanunta waje ta yi, lokaci guda kuma sai ta sauke ajiyar zuciya, domin ta tina maganar Allah a cikin suratul baqara, sura ta biyu aya ta 153. Allah Madaukakin sarki yana cewa. "Ya ku waɗanɗa kuka yi imani! Ku nemi taimako, natsuwa, hakuri da sallah ga Allah. Lallai Allah na tare da masu hakuri". Wannan aya na koyar da cewa a dik lokacin da mutum ya shiga cikin wahala ko tashin hankali, to ya nemi taimako ta hanyar haƙuri, natsuwa da sallah, domin Allah yana tare da masu waɗan nan sifofi. Haka zalika a cikin suratul baqara aya ta 155 Allah ya sake cewa. "Kuma lallai ne za mu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da rashi daga dukiya, rayuka da ƴaƴa". Wannan yana nuni da cewa kowane mutum zai fuskanci jarabawa, kuma mafi dacewa a yi haƙuri da dogaro ga Allah. A cikin muslim, hadisi mai lamba 223 Manzon Allah (SAW) ya ce. Hakuri haske ne. Wannan yana nuna cewa hakuri yana da haske mai nuna hanya a cikin duhun matsaloli. Dan haka yana da kyau su yi hakuri su kuma natsu sosai dan samo mafita mai kyau ba wanda za su yi danasani ba. Karar da mirrorsa ya yi ne ya kara firgitasu, dan alama ce ta tashin hankali sosai. Miƙewa tsaye suka yi a tare, a gagauce Ronnie ya kai kallansa a kan mirror, idanunsa ne suka ciko da kwallah tab, dan ana cinsu da yaki babu karya, abin ya mugun ɗaga mashi hankali. Sosai Sweetie ta ji ta karaya a wannan lokaci, dan ganin hawaye a idanunsa, dik sai ta ji ta tausaya mashi over. Matsawa kusa da shi sosai ta yi, cike da tsoron abin da zai je ya zo ta ce. "Ronnie bari in gwada saka wani password ɗin mu gani". Bawan Allah yana cikin ɗimuwa sam bai ji kalamanta ba ma. Ganin bai amsa mata ba ne yasa ta miƙe ta kai hannunta saman madannan laptop ɗin, jikinta na kerma ta fara ƙoƙarin dannawa, bata ta san abin da zata rubuta ba, kawai dai ta sanya a ranta Allah ba zai taɓa mata kunya ba dan da shi kawai ta dogara. Hannunta na kerma sosai ta kai saman later R zata danna sai ganin wani hannun daga bayanta ta yi ya rigata da danna later R ɗin, ai a miliyan ta zabura ta juyo, dan tasan wannan ba hannun Ronnie bane, hannun Black Tiger ne, saboda yanayin hasken skin ɗinsa shi da Ronnie akwai banbanci sosai. Tana jiyowa sai ganinsa ta yi a tsaye a bayanta, ko yaushe ya farfaɗo? Ta jefawa kanta tambayar, jikinta na rawa ta kai kallanta a kan face ɗinsa. Wani irin razana ta yi ganin yadda ya canza, fuskar nan tasa babu imani babu annuri, wlh ko mai taurin zuciyarka ka gansa a wannan yanayi sai ka ji wani irin ajijiya ya ɗebeka, sai hantar cikinka ta ƙaɗa. Take ta sha jinin jikinta. Ronnie ma a milyan ya miƙe tsaye, dan shi ma bai ga time da Black Tiger ya miƙe ba, kawai ya gansa ne a bayan Sweetie. Tsuru tsuru suka tsaya an rasa mai iya magana, ita Sweetie ma jikinta har ɓari yake yi, saboda yankar da ta yi mashi a kirji, tsoronta ɗaya irin hukuncin da zai yanke mata, ta shiga zilimi a kan hakan. Shi kuwa bai bi ta kansu ba ya cire password na laptop ɗin wanda ya kasance sunan Ronnie ne, dik wahalar da Ronnie ya sha ashe sunansa ne password ɗin, wato da gaske ne fa rashin sani ya fi dare duhu. Cikin ƴan mintocin da basu gaza uku ba ya shigar wa da Robbot ɗin nan abin da yake buƙata bayan buɗe laptop ɗin. In short cikin mintocin da basu gaza 30 ba ya ci rabi da kwatan yakin nan yana tsaye a in da yake bai motsa ba yana sarrafa kwakwalen robbot ɗin, dik abin da yake faruwa Sweetie da Ronnie sun yi shiru suna kallo ta cikin mirrorsa, zubar da jini kawai ake yi, maza zubewa ƙasa suke yi tamkar anyiwa sauro feshin magani, umarnin rashin imani ya bawa robbot ɗin nan nasa, dan kisan walaƙanci da rashin imani da tausayi suke yi wa mutane. Wani irin tsorata Sweetie ta yi na ganin yadda maza ke zubewa ƙasa, a tsorace ta kai kallanta kan face ɗinsa, yana tsaye kamar mutum mutumi, sai ma kara ɗaure fuska da ya yi, yau bata ga fuskar iya ce mashi ko uppan ba, hasali ma jikinta kerma yake yi, yau karo na farko bata san kallan face ɗinsa, saboda tashin hankali da fargabar da zuciyarta yake ciki. Sai dai fa ya jinjinawa Sweetie da Ronnien a cikin zuciyarsa, dan sun yi namijin ƙoƙari, da sun san password ɗinsa tabbas zasu yi nasara a wannan yakin, hakan yasa ya jinjina masu sosai, shiyasa ma ya yafe mata ciwon da ta ji mashi. Suna tsaye a wajen har Black Tiger ya kammala abin da zai kammala, sannan ya umarci Robbot ɗin nasa da su haka mashi rami mai zurfin gaske a tsakiyar birnin, a kofar empeir ɗinsa kenan, sannan su cika ramin da dikkan mutanen da suka juya mashi baya, su bisu da fetur da matches, sai kuma ya sake umartar wasu robbot ɗin da cikin awa biyu su tsabtace mashi birninsa dan baya san ganin datti ko wani jini jini or gawarwaki ko kaɗan, dik gawarwakin da suka mutu a jefasu cikin ramin da za'a haƙa dan kona waɗan da suka juya mashi baya, daga karshe ya ce yana da buƙatar mutanen birnin waɗan da ba su juya mashi baya ba da su hallara a gaban fada nan da kwana uku!!!. Wani irin zabura Ronnie ya yi ganin wannan umarni da yayan nasa ya kaddamar, hankalinsa ne ya yi mummynar tashi, da umarni ɗaya Black Tiger zai sa a kona mutane sama da dubu biyar? Kuma a konasu da ransu, kai wannan hukunci ta munana sosai, kun san yanzu musulunci ta ratsa zuciyar Ronnie sosa, da a baya ne ko mutane nawa Black Tiger zai sa a kashe baya damuwa, da kalma ɗaya Black Tiger yake sawa a tashi kauye guda daga cikin kauyukan birnin, a gaban Ronnien an sha bada umarnin kashe mutum sama da dubu kuma baya wani damuwa, amma yanzu sai ya ji ina wlh ba zai iya ɗauka ba, hankalinsa a tsakanin tashe ya ce. "Yaya please ka yi masu afuwa tun da babu yadda zasu yi da kai, kasan ba zasu yi nasara a kan ka ba, ka yi hakuri ka kyalesu kawai". Muryarsa na rawa ya yi maganar. Sweetie ce ta bi Ronnie da kallo tana san karin bayani, dan bata fahimci komai ba. Kallanta shi ma Ronnie ya yi, cike da tashin hankali matuƙa ya kora mata bayanin abin da Black Tiger ya yanke. Innalillahi wa inna ilahir rajiun, shi ne abin da ta furta kafin nan cikin fitar hayyaci ta ce. "Saboda me zaka kashe rayuka masu tarin yawa haka? Saboda sun bijire umarninka? Ko dan saboda suna neman ƴancin kansu? Saboda suna ƙoƙarin gujewa mulkin injustice ɗinka?! Saboda suna nemanwa kansu sauki? Shi ne zaka sanya a konasu da ransu? Shin waye ya baka izinin kashe rai? Ko baka san cewa ba kai ka haliccesu bane? Ko baka san cewa mahaliccin waɗan nan rayuka ya yi hani da kashesu ba ne? Ko baka san cewa kai ma ka bijirewa mahaliccin bane shiyasa suma suka bijire maka? Kana tinanin kashesu shi ne mafita a gareka? To ka saurara ka ji hukuncin dik wanda ya kashe rai daga nan sai ka san a wani matsayi kake. Allah maɗaukakin sarki a cikin suratul Hijr surata 15 aya ta 29 ya bayyana yadda ya halicci mutum daga turɓaya kuma ya busa mashi rai, ka je ka karanta wajen dan kasan menene ma rai da kuma yadda aka samar da shi. Haka zalika cikin suratul tin sura ta 95 aya ta 4 Allah maɗaukakin sarki ya ce. Lalle ne mun halicci mutum cikin mafi kyawun sura daga halittuna, darajan ɗan adam ya fi dikkan sauran halittun Allah!! Allah ya bayyana a bayyane cewa kashe rai ba tare da dalilin da ya cancanci kisa ba haramun ne, cikin suratul isra'i Allah ya ce kada ku kashe rai wanda Allah ya haramta, sai dai bisa haqqi. Wanda aka kashe ba bisa hakki ba, hakika mun ba wa magajinsa iko na neman hakkin ransa, amma kada ya wuce gona da iri a kisan, domin hakika wanda aka kashe ba bisa haqqi ba shi an taimake shi ne" Kazalika a cikin Suratul Ma’ida sura ta biyar 5 aya ta 32 Allah ya sake yin magana a kan haramcin kashe rai. Allah ya yi gargaɗi mai tsanani ga al’umma da suke kashe juna da zalunci, a cikin Suratul Baqara sura ta 2 aya ta 195, manzan Allah ya ce kisa yana ɗaya daga cikin manyan zunubai". Da alama tashin hankali ya rufe mata idanu da take zazzaga mashi waɗan nan karatun, ta mance a in da take, a wannan karon shi ma Ronnie sam bai yi gigin hanata ba, dan burinsa ta kowacce hanya su dakatar da Black Tiger daga kashe waɗan nan mutane, shiyasa ya kyaleta ta faɗa mashi girman Allah ko zai saduda ya hakura zuciyarsa ta sanyaya. Sai dai kash, kamar babu alamar saduda a tattare da shi, dan kuwa babu alamar zatukanta sun ratsa ƙwaƙwalwarsa, sai ma juyawa da ya yi ya cigaba da yin abin da yake yi, babu alamar mutanen birnin zamu samu koda kwayar zarra na sassauci daga garesa. Ganin hakan yasa suka kara shiga tashin hankali matuƙa, Ronnie ya shiga damuwar da har idanunsa sai da suka ciko da kwallah, ita kuma Sweetie a cikin zuciyarta ta sha alwashin yau ko mutuwa zata yi sai da ta mutu amma ba zata barshi ya cigaba da wannan bakin zalinci na CROWN OF INJUSTICE ɗin ba, yanzu ne lokacin da zasu rinƙa fito na fito da shi dan faɗa mashi gaskiya sai dai komai zai faru ya faru, dik wata rufa rufa da tsoro yanzu zasu ajiye a gefe su yi shahada su yi fito na fito. Dan haka tana ganin bai wani saurareta ba ya cigaba da yin aikinsa a matsayin ta shiga tsakaninsa da laptop ɗin, hannayensa dikka biyu ta riko cikin nata, tsabar tsoro sai kerma jikinta yake yi, amma tausayin mutanen birnin ya rufe mata idanu a in da ta zaɓi mutuwa dan cetonsu. Cikin dakiya ta ce. "A gaskiya ba zaka kashe kowa ba big bro, ya isa haka nan, zunubin da ka kwasanwa kanka a baya shi muke ƙoƙarin ganin ka tsarkaka daga shi, dan haka Allah ba zaka sake kwasanwa kanka wani zunubi ba, dan muna kaunarka!". A wannan karan cikin sanyin murya ta yi maganar, dan ta lura dik wasu tada jijiyoyin wuyarta a banza yake tafiya, shi Black Tiger ma wlh idan ka yi mashi magana cikin natsuwa da tausasa kalamai ka fi cin riba a kansa sama da idan ka ɗaga murya, in ka ɗaga murya ma ai sai dai ka ci azaba a hannunsa ba dai riba ba. My people's me kuke tinanin zai faru? Black Tiger zai janye kudurinsa a kan mutanen birninsa kuwa? Zai yafe masu? Shi da Sweetie da Ronnie waye zai yi nasara?. Muje zuwa. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Washegari da safe, sai almost karfe 8 Ramish ya iya farfaɗowa daga sumar da ya yi bayan wannan aika aika da ya aikata, yana gama samun natsuwa dama ya sume kwance kusa da ita. Bilal ya buga wayarsa tun da daɗin rai har ya fara shiga tashin hankali, ya ƙasa zaune ya kasa tsaye, dan haka gari na wayewa ya fita gidan da sunan ya je nemansa, ko kaɗan bai kawowa ransa cewa Ramish na sama ba, sai ya yi waje nemansa. A lokacin da ya farfaɗo ji ya yi jikinsa tamkar ba nasa ba, gabaɗaya ya canza, kansa ne take sara mashi tamkar zata fashe, wani irin jiri yake gani sosai, da alama har yanzu maganin nan bata gama sakinsa gabaɗaya ba bawan Allah, idanunsa tamkar wuta saboda ja, har lokacin jijiyoyin jikinsa a tsaitsaye basu koma sun kwanta ba, arab hairnsa tamkar wanda aka kwato daga bakin kura, gabaɗaya a hargitse yake, idan ka gansa sai ka tausaya mashi, shi ma kenan, to ina ga Leesharh kuma? Ya kuke tinanin zata kasance?. Ya sha madarar mamakin ganin babu tufafi a jikinsa, ɗan waige waige gefensa ya fara yi, ai a miliyan ya zaro idanunsa waje lokacin da ya ga Leesharh kwance a gefensa cikin jini, ga sofar da suke kai ɗin fara ce tas, hakan yasa gabaɗaya jini ya yi kaca kaca da waje. Dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi ya yi, idanunsa ya datse gam, take ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo mashi abubuwan da suka faru daren jiya. Tsab ya tina komai, innalilahi wa inna ilahir rajiun shi ne kalmar da ya rinƙa maimaitawa a ransa, ya maimaitata ya fi sau hamsin a in da yake zaune, tamkar wanda ya yi mangaribar jemage, lokacin guda jikinsa ta yi mugun sanyi, da karfi ya dafe forehead ɗinsa, wani irin ihu ya kurma da karfi wanda bai san dalilin yinta ba, ga dikkan alamu zafin da zuciyarsa ta ɗauka ne yasa hakan. Dama na faɗa maku dik ihun da za'ayi a cikin wannan ɗaki na waje ba zai iya ji ba, bangon wajen tamkar soundproof yake. Miƙewa tsaye ya yi, yana tangal tangal tamkar wanda ya sha barasa ya bugu ya nufi gaban computers dake wajen, da kyar ya iya ƙarisawa wajen, hannayensa dikka biyu yasa ya dafe dest ɗin, wani irin huci ya fara fitarwa da karfi karfi, numfashinsa na fita da wani irin ɗumi mai ban tausayi. (Abin akwai ciwo gaskiya, ace tin da ka taso baka taɓa zina ba, baka taɓa sha'awar yinta ba, hasalima kyamatarta kuke yi, rana tsaka ka tsinci kanka da aikatata! Wlh dole ya ji zafin hakan, yanzu ya zai yi? Da wani ido zai ganta? Shin zai iya gane me ya janyo mashi aikata hakan? Idan ya gane wani mataki zai ɗauka? Shin zata yi mashi uzuri ta yarda ba halinsa bane?.) Ƙwaƙwalwarsa ce ta sake tariyo mashi yadda ya haikewa yar mutane a daren jiya, take ya tuno kalamanta da take faɗin. "Yah Ramish kada ka yi mun irin wannan hukunci, ka yi mun dik abin da kake so da ya danganci azabtarwa, amma dan Allah kada ka rabani da mutumcina, wlh ni marainiya ce da bani da kowa, bani da iyaye, mutuncina shi ne kawai abin da ya rage mun mai daraja a tattare da ni, ka dubi girman Allah kada ka lalata mun rayuwa, ni ban karɓi wannan aiki saboda na cutar da kai ko wani abin makamancin hakan da gangan ba". Tana kuka hawaye sharɓa sharɓa tana kora mashi waɗan nan jawabin. Ai hankalinsa ne ya kara tashi, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, cikin fitar hayyaci yana huci ya sake kurma ihu da karfin gaske, cikin zafa yasa hannun da karfi ya fara watsi da gabaɗaya computers dake wajen, da karfi ya ɗaga dest ɗin mai gabaɗaya ya yi watsi da shi komai dake kai suka zube ƙasa suka tarwatse watsa watsa, dunkule hannunsa ya yi ya fara bugun jikin bangon wajen da karfi karfi yana huci har sai da ya yi raga raga da yatsun hannunsa ya jiwa kansa ciwo, gwanin ban tausayi ya zube gwiwowinsa a kasa a wajen tare da haɗe kansa da jikin bango, a dik lokacin da ƙwaƙwalwarsa ta tina mashi cewa Leesharh ta gansa tsirara kuma har ya yi abinga da ita sai ya ji tamkar ya rataye kansa, ya ji kamar ya yi ta buga kansa da bango har sai rai ya yi halinsa, zuciyarsa na azalzala mashi da ya yi ajalin kansa kawai, sai dai shi ɗin mai addini ne yasan hukuncin wanda ya kashe kansa. Lokaci guda mugu mugun tausayin Leesharh ya rufesa, kalamanta dake yawo a cikin kansa shi ne cewa da ta yi marainiya ce ita, hakan yasa ya ji wani irin kululun bakinciki ya tokare mashi maƙoshi, da kyar ya miƙe tsaye hannunsa na zubar da jini, in da take ya nufa har lokacin yana tangal tangal kamar zai faɗi. Kallo ɗaya ya yi mata ya yi saurin kawar da kansa, kasancewar babu tufafi a jikinta sannan gata cikin jini. Gabaɗaya ya ji ya tsani kansa, Innalillahi wa inna ilahir rajiun. Shiru ya yi ya rasa madogara, dan kuwa ko kayan da zai saka a cikin wannan ɗaki babu, wancan kayan nasa kuma ya yagesu gabaɗaya ya zubar. Ya jima tsaye a wajen saboda rashin madogara, daga karshe dai ya laluɓo wayarsa can kusa da computers da ya farfasa, Allah ya cecesa wayar bata yi komai ba. Uban tilin miss calls ya samu wanda ciki na Bilal ya fi na kowa yawa, ga na Ummie da ta yi ta kiransa daren jiya dan jaraba, wai so take ta tambayi ina yake sai ta je ta same shi, bata san a lokacin baya duniyar nan ba, yana can duniyar mercury. Sam bai bi ta kan miss calls ɗin ba, number Sharifat kawai ya laluɓo ya dannawa kira. Bugu ɗaya ta ɗauka, cikin kuka ta yi mashi sallama, yau karon farko a rayuwarsa ya ji faɗuwar gaba ta riskesa, tamkar yasan me Sharifat take yi wa kuka, wato ta nemi Leesharh bata ganta ba, kun san tun daren jiya take nemanta. Daurewa ya yi ya yi ta maza wajen cewa. "Ki je bedroom ɗina ki ɗauko mun pjs set biyu ki kawo mun wajen stair case na ɗakin bincikenmu dake sama, ki ajiye mun a wajen ki tafi". Yana kai karshen maganar ya yi gaggawar katse kiran dan ma kada ta kawo mashi zancen dalilin kukanta, dan yasan kwanar zancen. So ba karya ba, tana bala'in sonsa hakan yasa ta iya gane baya cikin kwanciyar hankali da natsuwarsa, ta tabbatar yana cikin tashin hankali daga jin voice ɗinsa, dan haka ita ma nata hankalin ne ya kara tsananta tashi, ta rasa ina zata sanya ranta ta ji daɗi, ga shi ta tambayi Ummie ko taga Leesharh Ummie ta ce mata kada ta sake yi mata batu kan Leesharh, gabaɗaya ta rasa wanda zata je wajensa ta ji sanyi a ranta, Abbie baya nan ya fita. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta fito waje, da yake tana cikin tashin hankali sai bata wani damu da ta yi tinani a kan me Ramish zai yi da pjs har set biyu ba, kawai ta nufi bedroom ɗin nasa. Shi kuma wurgi ya yi da wayarsa tare da kifa kansa da jikin sofar da Leesharh ke kwance tamkar gawa, sai wani irin zufa ce take keto mashi, gabaɗaya face ɗinsa tamkar wanda aka watsawa ruwa......... 10 mins tsakaninsa da kiran da ya yi wa Sharifat ya miƙe ya ɗauki short ɗinsa ya maida jikinsa, sannan ya nufi wajen romote na stair case ɗin. Jikinsa dik rashin kuzari, da kyar ma ya iya danna romote ɗin stair ɗin ta yi ƙasa. Allah sarki yau sai ga Ramish da leƙa waje wai dan zai sauko ƙasa, leƙawa ya yi domin ya duba akwai mutane ko babu, jikinsa har tana ɗan kerma. Ganin babu kowa yasa ya yi zafin namar saukowa kasa ya ɗauki kayan da ta ajiye mashi kamar yadda ya buƙata, a gaggauce ya koma sama kirjinsa na harbawa da sauri sauri. Yana haurawa ya naɗe stair case ɗin sama, sannan ya hau ware set ɗaya ya sanya a jikinsa, jikin nasa ma ta wani sassa dikka jininta ya yi mashi wanka. Yana gamawa ya wuce da set ɗaya zuwa in da take. Dan dole ya ɗaura idanunsa a kan aika aikan da ya yi domin ya sanya mata kayansa. Dik da sun yi mata yawa haka ya sanya mata, sauri sauri ya kai hannunsa saitin bugawar zuciyarta ya ji tana raye ne ko dai ba'a iya fyaɗe abin ya tsaya ba har da kisan kai ya yi?. Jin kamar kirjin nata na bugawa can kasa kasa ya sa ya yi gaggawar miƙewa tsaye ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye ya nufo ƙasa da ita, har lokacin hannunsa na zubar da jini, da kyar ya iya naɗe stair case ɗin sama. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa da ita, yana shiga ya mayar da kofar ya rufe tare da murza key, dan ko Bilal bai yarda ya san abin da ya faru ba, shiyasa ma bai kaita A&E ɗinsu ba ya wuce da ita bedroom ɗinsa kai tsaye, a cewarsa zai rufe kayansa shi kaɗai, a cikin kwakwalwarsa ya fara tinanin ko dai ya yi mata allura manta komai ya shafe mata kwakwalwarta ne?. Wani zuciya ce ta ce mashi zai tabka manyan laifuka guda biyu kenan, idan ya yi mata hakan ya gama cutarta duniya da lahira, zata manta kowa ta manta komai, dik wasu mutane masu mahimmanci a rayuwarta zata manta su? Kai ina wanna babban zalinci ne, wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da kai tin da asirinka zai rufu ai kawai kada ka wani damu da dik abin da zai faru, dama ai marainiya ce bata da kowa, dan haka kayi mata alluran kawai. My people's kuna ganin yiwa Leesharh allura da zai yi shi ne mafita a garesa? Shi ne zai sa asirinsa ya rufu? Ko shi ne zai sa komai ya wuce? Idan ya yi hakan kuna gani ya kyauta mata kuwa? Ya yi mata adalci? To muje dai zuwa. A saman bed ɗinsa ya shinfiɗe ta tare da ɗauko remote ya kashe A.c, a gaggauce ya fito ya rufota a cikin ɗakin, kai tsaye ya wuce A&E, dik wasu abin da yasan zai buƙata ya haɗa a cikin A box sannan ya ɗauko ya dawo bedroom ɗinsa, sake kulle kofar ya yi, a gaggauce ya hau yi mata aiki dan kada a rasata. A lokacin da yake yin wannan aiki a lokacin shi kuma Bilal ya dawo daga yawon nemansa, sai ya nufi ɗakin binciken nasu domin ya shigar da number Ramish ɗin a cikin computers ɗinsu ya yi traking na number dan ya ga in da ɗan uwan nasa yake. Ya sha madarar mamakin ganin yadda ɗakin ta yi watsa watsa, computers ɗin dik anyi raga raga da su, sai dai bai damu da fashesu da aka yi ba, dan yasan babu wanda zai yi wannan aiki sai Ramish, damuwarsa ɗaya shi ne meyasami ɗan uwansa har ya fashe masu kayan aiki haka?. A gaggauce ya juya ya nufi bedroom na Ramish. A dai'dai lokacin Ramish yana kan yi wa Leesharh allura, turo kofar ya yi da nufin ya shigo sai jinta ya yi a datse, hankalinsa ne ya tashi sosai, knocking ya fara yi dan yasan akwai mutum a ciki, idan ba ku manta ba shi ne ya yi na karshen fita ɗakin daren jiya, so yasan bai rufe da key ba, dole Ramish ya dawo yana ciki kenan. Cike da tashin hankali yake knocking, amma shiru Ramish bai ko ɗago ya kalli door ɗin ba. Bilal na ƙoƙari juyawa ya bar wajen dan ya je ya tambayi Abbie ko yasan wani abin dangane da Ramish daga jiya zuwa yau kwatsam kallansa ya sauka a kan jinin hannun Ramish da ya ɗiga a wajen, ai hankalinsa ne ya kara tashi, take ya kara tabbatarwa da kansa ba lafiya ba, dole yasan me yake faruwa, sake sake daban daban ne cike a cikin ransa a kan Ramish. Baya ya koma da karfi yasa karfi zai ɓalle kofar, wata iriyar duka ya kaimata, jijjiga kofar ta yi amma bata ruguje ba, sake yin baya ya yi ya zo da karfi ya daki kofar da shoulder ɗinsa, nan ma jijjiga ta yi bata ruguje ba. Sai a karo na uku ne kofar ta ruguje ƙasa, cikin zafa ya afka cikin ɗakin kirjinsa na harbawa da sauri sauri, yana ta raba idanu game da zarosu yana tinanin ta ina zai kalli ɗan uwansa. Shi kuwa Ramish da iskanci ya gama cika mashi kai dik abin da Bilal yake yi yana jinsa, bai taka mashi birki ba kuma bai yi niyyar buɗe kofar ba, dan haka ko da ya rugujeta ya shigo ma ko ɗagowa ya kallesa Ramish ɗin bai yi ba, ya cigaba da abin da yake yi kawai. Me kuke tinanin zai faru kenan? Shikenan Bilal ya gansu? Asirin Ramish zai tonu kenan ko yaya? Shin Bilal zai fahimcesa ya yi mashi uzuri ya rufa mashi asiri kuwa?............. To azimi ya zo ina gab da tafiya hutu, shiyasa nike san leƙa maku kowani part dan kusan halin da ko'ina suke ciki kafin mu tafi hutu, dan haka mu leƙa kingdom of power mu dawo. 🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥 Tafiya take yi tana ɗan ɗingisa kafafunta zata je part ɗin mama, bata gama warkewa daga jibgar da Smart ya yi mata ba, cikin daren ta fito dan ta je wajen maman Yah Ramish, kun san Sarina da mama suna shiri sosai, tana tafiya tana latsa wayarta tana ɗan turo baki, still dai tana cikin wannan karuwan shigar nata na sleeping dress. Alamar bata daku da kyau ba, dan babu alamar nadama a tattare da ita. Dai'dai zata shiga part ɗin mama ita kuma Mahreen tana fitowa daga part ɗin momma zata je wajen mama Haulat a part ɗin Jaish. Tana fitowa suka ci karo da Sarina. Baya kaɗan ta yi tare da bankawa Sarina wani irin matsiyacin kallo na uku saura kwata kafin ta ce. "Amma ke dai dabba ce ko? Dan naga dabobi ne suke tafiya basa ganin gabansu, suna sukuwa dik in da kansu ya nufa". Ta yi maganar tare da riko waist ɗinta da hannu bibbiyu, irin dai yadda take cin uwar sabada a kauye idan aka taɓota. Yanzu larabci ya fara zama sosai a bakinta, rashin mutum sabo take karowa, dan ta fara wayewa, infact kallan kauyawa marasa hankali ma take yi wa Aneesa and Fanan, gani take basu san me suke yi ba tun da basa kwalliya. Amma kuma tana matuƙar girmama Chuchu saboda ɗaukar wankarta, kun san mutuniyar da shegen san kwalliya, idan kana kwalliya ai biyayya zata yi maka sau da kafa ku zauna lafiya ka koya mata yadda ake yi, akasin haka kuwa ka gurji rashin kunya da rashin mutunci daga wajenta. Mamaki ya hana Sarina yin magana, kallonta ta fara yi from head to toe, yau rashin kunya da fitsara ne suka haɗu waje guda. Wani irin faɗuwar gaba Sarina ta ji a lokacin da taga face ɗin Mahreen, dan ta ganta kyakkyawar gaske, gata yar siririya zubin turawa, komai dai masha Allah, ta sako kayan barcinta masu kyau, a daren ma sai da aka yi kwalliya, ai yanzu tun da ta iya kwalliyar nan kowa sai ya sarara mata, dan na safe daban na rana daban da dare daban, yanzu ta zama mace mai class kamar Chuchu tamu ta amana. Ita kuwa Mahreen tana wannan girgiza tana binta da harara, wai a hakan ma ta raga mata ne dan ta ɗan yi simple make up a face ɗinta, shi ne ta samu rangwame, ba dan haka na masifar da Mahreen zata yi mata sai ya fi hakan. Takaici yasa Sarina ta cire hannu ta zabga mata dalleliyar mari mai tsada, dan a cewarta bata da lokaci ɓata baki a kan yarinyar da bata wuce tasa bulala ta yi mata dukan mutuwa ba, dama ga takaicin Mahnoor ta kwacewa Fanan Jaish ya cika masu zuciya, sai ta nemi sauke hakan a kan Mahreen. Aikuwa tana saukewa Mahreen wannan mari ta yi tsalle ta dira ta ce idan Sarina ta isa Allah ya kasheta, wlh bata ga mai hanata rama marin nan ba, Sarina bata yi zatan zata yi yunƙurin rama marin ba shiyasa bata wani kauce daga gabanta ko ta yi wani yunƙurin ba, unexpext ta ji saukar hannun Mahreen a face ɗinta ta dalla mata mari mai tsadar gaske, ji kake tass da karfin tsiya, kai tsabar Mahreen ta kware a faɗa ma sai da ta daka tsalle ta buɗe hannunta da kyau kafin ta dalla mata marin. Ai wani irin baya baya Sarina ta yi tamkar zata faɗi kasa ta yi gaggawar dafa bango, har wani jiri ta gani yana ɗebanta, ta maru ba karya, lokaci guda ta ji kamar wadda aka ɗaura a saman fanka yana juyawa da ita. Mahreen kuwa ko da ta rama marin bata tsaya a iya nan ba, cikin jajjagen masifa ta ce. "Waye ubanki da har zaki mareni in kyaleki? Wlh kin yi kaɗan, kin ci karya kin kwana da yunwa, shegiya mai kirar akuyoyin Nenne". Kunsan a kauye haka suke cewa idan suna faɗa, sai su ce waye uban mutun da zai dakesu ba zasu rama ba? So kalaman bala'inta na kauye ta yi amfani da shi a kan Sarina, dan ita bata ɗauka ma wani kalmar azo a gani bane, kawai faɗarsu na yara take faɗen hakan, ita kuwa Sarina wani irin mugun zafi kalmar ta yi mata, wai waye ubanta, lallai yana da kyau ta gwada mata uban nata kuwa. A fusace ta cakumo wuyar kayan barcin jikinta da nufin ta naɗa mata ɗan banzan duka, to kun san a ɓangaren faɗa kam dai su Sarina kifin rijiya ne, babu wayon faɗa, basu iya faɗa da hannu ba dan ba yi suke yi ba, a barsu dai da faɗa da baki nan suka fi kauri, ita kuwa Mahreen ta yi dambe da mazan kauye ma bare wata Sarina, dan haka tana cakumo mata wuyar riga Mahreen ta yi kasa kamar wadda zata yi sujjada kawai ta finciko kafar Sarina da karfi, kan kace me sai ga Sarina ta zube ƙasa wanwar kafafu a buɗe, ɗaya ya yi can ɗaya ya yi can. Tana ganin ta faɗi kasa ta yi gaggawar haye ruwan cikinta, yadda dai ta yi wa ƴaƴan ɓoɗejo bogaza, haka ta haye kan Sarina ta hau kai mata duka a kirji kan tula tulanta. Ba shiri Sarina ta fara ihun neman taimako, yau ga wadda ta fita hau ai. Ai tana wannan ihu kamar tana kara ingiza Mahreen ne, hular kayan barcin dake kanta Mahreen ɗin ta ciro ta cusawa Sarina a cikin bakinta da ta wage take ihun, wai dan ma kada ta tara mata jama'ar gidan bata gama cin ubanta ba a zo a rabasu, dama Sarina ba karfi ba, yanzu kuma ga rashin lafiyar dukan da tasha bata gama warwarewa ba, hakan yasa ta gaza iya kwatar kanta, Mahreen ta rinƙa kaiwa tula tula naushi abinta, ga shi ta tura mata hula a cikin baki ba halin yin ihu. A dai'dai wannan lokacin guyson ya zo giftawa zai je part na Mommarsa dan yaga Mahreen ɗin, yau throughout basu haɗu ba, ya je school, bayan ya dawo kuma yana tare da uncle Jahiz, yana san uncle ɗin nasa sosai dan yana da ra'ayi a kan kwallan kafa sosai, so ita zai je gani, har yau wajen da kunama ta harbesa tana ɗan yi mashi zafi kaɗan kaɗan. Amma ya rufawa su Omaid asiri bai sanar da kowa abin da ya faru ba. Ai yana ga abin da yake kafuwa a miliyan ya kariso wajen, yana zuwa bai yi wata wata ba yasa hannu ya ɗagata cak ya sauketa daga kan Sarina. Kun san faɗarta baya karewa, da gudu ta yunƙura zata sake haye Sarina ya yi gaggawar ƙanƙameta yana tambayar me yake faruwa?. Ƙoƙarin kwatar kanta ta yi da ta cigaba da jibgar Sarina tana wani huci kamar wadda ita aka jibga, sai dai ina ta ƙasa kwace kanta, kuma da hannu ɗaya ya riketa, hakan zai tabbatar maku ba wai karfi ne bashi da shi ba, shi dai kawai goyon kaka ne. "Lafiya meya haɗaki faɗa da Aunty Sarina a cikin wannan dare kuma?". Cikin wannan sanyin nasa ya yi maganar. Ganin ta kasa kwace kanta ne yasa ta ce. "Ni ka sakeni in gamasa cin ubanta". Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin kalamanta, ya ma rasa me zai ce. Ita kuwa Sarina lallaɓawa ta yi ta miƙe tsaye, har wani tangal tangal take yi kamar zata faɗi. Hular da Mahreen ta tiɗɗa mata a cikin bakinta ta zaro shi tare da harbin Mahreen ɗin da shi, a fusace ta ce. "Yau sai na ga waye gatanki, sai naga waye ubanki a ƙasar nan, sai kin yabawa aya zaƙinta........". Ai Sarina bata gama rufe baki ba ta wani daka sufa zata yi kanta tana faɗin. "Sai dai ubanki ba nawa ba, shegiya mai kama da akuyoyin Nenne, kuma tun da kika zagi bappana wlh sai na cire maki hakwaran sama". Wato dai kowa yana san iyayesa kuma babu daɗi idan aka zagan makasu, amma kuma kai a lokacin da zaka zagi wani ba zaka ji rashin daɗin yin hakan ba sai an rama ne zaka san iyaye suna da daraja kuma kana sansu, ita fa ta fara zagin uban Sarina, amma yanzu kun ji da Sarina ta rama shikenan abu yazama laifi an zagi bappanta ba zata bari ba, har da zubar da hakwaran Sarina zata yi, kai Mahreen duniya. Ƙanƙameta da kyau guyson ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Ki natsu mun in ji me ya haɗaku faɗa". Juyo da idanunta kansa ta yi, cike da rashin kunya ta yi mashi kallan uku saura kwata kafin ta ce. "Ji yadda yake magana kamar wani babban mutun bayan kai mai kukan ciwo ne kawai, kai da rarrashinka ake yi kamar karamin yaro ne zaka ce zaka raba faɗa? Kai fa zan iya zaneka ka yi kuka". Babbar magana!!. Bawan Allah a maimakon ya ji zafin kalamanta sai ma ya saki cool murmushi kafin ya ce. "To na ji zaki iya zaneni, yanzu dai muje part ɗin momma sai ki zaneni a can". Sarina kuwa hannu ta kai zata kai mata capka ya yi saurin janyeta daga tsakaninsu shi ya shiga tsakanin nasu yana rike da hannunta, a natse ya ce. "Aunty Sarina dan Allah kiyi hakuri, kada ki biye mata, baki ga yarinya bace?". ..... Ai bai gama rufe baki ba ta sake yin tsalle ta dire haɗe da cewa. "Wlh ni ba yarinya bace, kuma ma ai na fika tun da ni bana kukan ciwo". Sarina kuwa, dama zata yi magana da ya yi magana ne, amma jin Mahreen ta capki zancen tana jajjaga mashi masifa yasa ta haɗiye maganarta tana huci. Shi dai har yanzu ko kaɗan kalamanta basu wani taɓa shi ba bare har su ɓata mashi rai, kara burgesa ma take daɗa yi, dan haka bai kulata ba ya sake duban Sarina ya ce. "Aunty Sarina dan Allah ki yi hakuri kin ji?". Sarina na ƙoƙarin cewa ya kyaleta ta taka Mahreen yadda yakamata ko zuciyarta ya huce, sai Mahreen ɗin ta rigata da cewa. "Kada ta yi hakuri, ta zo ta lililili ta likeni ta zurani ta bakin allura ta sake fitarwa karshen kenan idan ta isah"...... Yau dai guyson yaga ta kansa, ana ƙoƙarin kashe wuta ita kuma tana kara hurata. Sake kaimata wawura Sarina ta yi ya yi saurin janyeta, ita kuma ana janyeta tana wani matsowa zata kaiwa Sarina duka har da wani dunkule hannu wai ita nan jaruma, sai wani kyafta idanu take yi. Guyson dai da yaga wannan abin fa ba karewa zai yi ba sai ya shammaceta ya ɗauketa cak yana bawa Sarina hakuri ya nufi part ɗin Momma, rai a ɓace Sarina ta ce wlh ba zata kyaleta ba, sai dai kada su haɗu, in suka haɗu sai ta fasa mata baki, ita kuwa Mahreen ya ɗauketa ma bakin bai mutu ba, faɗi take. "Wooooo ƙatuwar banza ta sha duka, kuma na daki banza ba yadda zaki yi". Kai Mahreen sai shirin Allah. Bai sauketa a ko'ina ba sai a tsakiyar bedroom na momma, babu kowa a ɗakin sai Mahnoor dake kwance saman bed tana barci, momma taki yarda ta matsa ko nan da can, ta ce a gadanta zata rinƙa kwana tun da ba a nan King yake kwana idan yana ɗakinta ba, gadanta ne ita kaɗai, so Mahnoor zata iya kwana a kai, tun Mahnoor na noƙewa har ya saki jiki ta ɗauki momma matsayin uwa kawai. Yana sauketa ta riko waist ɗinta da hannu dikka biyu tana binsa da wani irin kallo. Ɗan sunkuyar da kansa ƙasa ya yi alamar kunya da kamala kafin ya ce. "To sarkin faɗa kallan me ni kuma kike mun? Ko dai kina duba ta in da zaki ɗauki fansa a jikina ne dan na hanaki yin faɗa?"....... Kai ta ɗan girgiza mashi alamar a'a, sannan ta ce. "Ina mamaki ne". Ɗago da kallansa a kanta ya yi kafin ya ce. "Mamakin menene kuma?". Ɗan nisawa ta yi kafin ta amsa da. "Ashe kana da karfa fa? Ban yi zatan kana da karfi ba ai, kuma da kake maganar ɗaukar fansa ai ko zan ɗauki fansa a kan kowa ban da Hammana (Jaish) da mai kama da shi, kana kama da Hamma shiyasa idan ka rabamu faɗa da mutane bana komawa kanka da faɗar". Siririn murmushi ya saki har sai da dimple ɗinsa suka lotsa, sannan ya ce. "To nagode da nike cin darajar kamannina da Yah Jaish nike tsira daga dukanki, amma in tambayeki mana?"........... Tsaresa da ido ta yi alamar tana jinsa ba tare da ta yi magana ba........ "Meyasa kike san yin faɗa ne?". Shi ne tambayar da ya jefa mata. Kai ta ɗan ɗaga sama kamar mai tunanin wani abin, can ta sauko da kallanta a kansa, ya yi shiru yana jiran amsa..... "Idan aka taɓoni ne bana iya bari, yanzu ma ban yafewa wannan mai kama da akuyoyin Nenne ɗin ba, dik ranar da muka sake haɗuwa sai na cire mata hakwaran sama dikka". Shi dai yarintarta da shiriritarta dik yana burgesa, ga shegen san kwalliyar nan nata yasa ya kara jinta a ransa, dan shi ma kamar yadda yake ɗan wanka haka yake san ƴan gayu, bare ita da take caras cas, ga kyau da kirar jiki mai kyau, dik kalar wankar da zata ɗauka kyau take yi sosai. "Please ki dai'na faɗar nan haka ya isa kin ji?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar yana kallan janbakinta da ya ɓata mata gefe gefen baki saboda faɗar da suka gwabza. "Ni ba zan dai'na yin faɗa ba matsawar za'a rinƙa shiga gonata". Cikin tsiwa ta yi maganar......... Girgiza kai kawai ya yi, sannan ya matsa kusa da ita dab, ya kai hannunsa saman lips ɗinta domin ya gyara mata jan bakin ba...... A miliyan ta ja baya kaɗan tana faɗin. "Kai ma na lura ɗan iska ne mai san taɓa jikin mata, yanzu ka ɗaukeni ban yi maka wata magana ba na yafe maka shi ne har ka samu damar taɓa mun baki ko?". Nisawa ya ɗan yi kafin ya kallenta from up to down, sannan ya ce. "To ai ke ba za'a kiraki da ƴan'mata ba, baki wuce munzalin ɗaukarki da nike yi ba, ke yarinya ce"........ Ai rike waist ɗinta da hannu dikka biyu ta yi, cikin tsiwa ta ce. "Wlh ni ba yarinya bace, me banbancina da ƴanmatan?"........ Kai Mahreen akwai shegen san girma...... Shi kuwa matsawa kusa da ita kaɗan ya yi tare da kai hannunsa saman ƴan kirgan danginta da ta fara, sannan ya ce. "Wannan shi ne abu na farko da ya fara banbantaki da ƴan'mata, ke baki da breast ai, kin gansu fa yanzu suke fitowa ƴan ƙananan da su, ki bari sai sun girma sai ki fara haɗa kanki da manyan mata"....... INNALILLAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, KAI ANA WANI SHA'ANI A KINGDOM OF POWER, AMMA GUYSON MA ƊAN DUNIYA NE. Tsit Mahreen ta yi ta rasa abin faɗe, ga shi yasa hannu ya taɓa mata su, yau dai bakin ya mutu. Shi kuwa cigaba ya yi da cewa. "Akwai banbancinki da ƴan'mata dayawa bayan breast ɗinki, juyo in nuna maki sauran". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin riko hannunta ya juyar da ita. Ai a miliyan ta fisge hannunta tare da saka mashi kukan shagwaɓa da take yi wa bappa a kauye, ta faɗi ƙasa kamar dai yadda take yi a kauye, birgima ta fara yi tana faɗin sai ya biyata taɓa mata kirji da ya yi. Ganin Mahnoor tana motsawa zata farka ne yasa ya yi gaggawar yin ƙasa shi ma, bakinta ya sanya hannunsa ya toshe yana faɗin ta yi hakuri zai biyata taɓawa da ya yi.... NI KAM INA FATAN ALLAH YA KAWO MAI SANYA BAKIN MAHREEH YA MUTU! MASU FATAN GANIN MAHREEN A LABOUR ROOM SU ƊAGA HANNU. Rungumota ya yi ya hau rarrashi, nan ma ashe wani laifi ya kara ya taɓata, kwace kanta ta yi tana cigaba da kukan ta miƙe ta nufo waje, wai zata je ta faɗawa Momma ya taɓa mata breast ɗinta ya kuma rungumeta ashe ɗan iska ne shi ɗin. Bayanta ya bi da sauri dan ya bata hakuri, sai da suka zo dab da bedroom ɗinsa ya capketa, tana ƙoƙarin kwace kanta ya turata cikin bedroom ɗin, shiga ya yi ya rufo kofa har da murza key.......... To ko me zai yi mata?. ••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥 Kwace Dr Raj ya isko Jaish saman sofa yana ɗan juyi a hankali hankali, cike da kauna ya tambayesa menene yake damunsa haka, miƙewa zaune ya yi yana wanu nuku nuku, kun san shi da kunya sosai, dan haka ya ƙasa iya sanar da Dr ga abin da yake damuwansa, sai kawai ya ce babu komai barci yake ji. Dr ya fahimci tabbas akwai abin da kanin nasa yake ɓoye mashi, amma tin da ya nuna baya san faɗa mashi sai kawai ya kyalesa ya ce to ya tashi ya shiga ciki mana. Ba musu ya miƙe ya nufi ciki, a lokacin ya kai kololuwan da ba zai iya cigaba da rike kansa ba, har ya nufi bedroom ɗinsa sai kuma ya fasa ya juyo ya nufi na momma, a cewarsa zai je gaisheta ne kawai..... GAISUWA TSAKIYAR DARE KUMA? WAI BA SHI NE MA YAKE KIRANTA A WAYA DA SAFE BA? TO ME NA GAISUWAR DARE TUN DA NA SAFE MA A WAYA AKE YINTA? TO MU DAI MUNA NAN DAI'DAI DA KAI ƊAN RAININ SENSE. A sama farkon page ɗin nan na yi magana a kan kashe rai ba bisa haqqi ba da Sweetie ta faɗawa Black Tiger, to waɗan ne rayuka ne suka kalatta a kashe su wato bisa haqqi kenan, zan kawo maku su a jere domin ku sani. A Musulunce, an haramta kashe rai ba bisa hakki ba, amma akwai wasu nau’ikan laifuka da shari’a ta halatta a yankewa hukuncin kisa, ga sunan kamar haka, na farko, idan mutum ya kashe wani da gangan ba tare da dalili ba, shari’a ta yarda a kashe shi a matsayin ramuwar gayya. Wannan hukunci yana nan cikin Alqur’ani, suratul baqara sura ta 2 aya ta 178, Ya ku waɗanda kuka yi imani! An wajabta muku hukuncin ramuwar gayya a kan kisanku. Duk da haka, iyalan wanda aka kashe na da damar yafiya ko karɓar diyya kuɗin fansa kenan, maimakon a kashe wanda ya aikata kisan. Abu na biyu zinacewar mutumin da ya taɓa aure. Mutum da ya taɓa yin aure wato baligi ne, yana da hankali, idan ya aikata zina, to hukuncinsa kisa ne ta hanyar jifa da duwatsu. Wannan ya tabbata a cikin hadisai, cikin muslim lamba ta 1690 da bukhari lamba 6814, Idan namiji da mace sun aikata zina kuma sun taɓa yin aure, to a jefe kowannensu da duwatsu har su mutu. Sai dai, dole ne a samu shaidu huɗu ko kuma mai laifi ya furta da kansa. Laifi na uku riddah ficewa daga addinin musulunci. Mutumin da ya musulunta, daga baya ya fita daga addinin Musulunci shari’a ta yarda a yi masa hukuncin kisa. Annabi (SAW) a cikin Bukhari hadisi mai lamba 6922 ya ce. Duk wanda ya canza addininsa ya fita daga Musulunci, ku kashe shi. Sai dai, malamai sun yi bayani cewa dole a fara ba wa mutum dama ya tuba kafin a aiwatar da hukunci. Na huɗu fasad a kasa. Fasad fil-Ardh Wato Fashi, Ta’addanci, da cin zarafi. Mutane da suka aikata manyan laifuka irin su fashi da makami, ta’addanci, ko cin zarafin mutane a ƙasa, shari’a ta yarda a yanke musu hukuncin kisa. Allah cikin suratul ma'ida ya ce. Lalle ne sakamakon waɗanda suke yaƙi da Allah da Manzonsa kuma suke yin ɓarna a ƙasa shi ne a kashe su ko a gicciye su ko a yanke hannuwansu da ƙafafunsu, ko kuma a kore su daga ƙasarsu. Wannan wani kaskanci ne a gare su a duniya, kuma a Lahira suna da azaba mai girma da tsanani. Wannan hukunci yana kan barayin da suka aikata fashi da makami, masu tayar da fitina, da waɗanda suka haddasa ruɗani a cikin al’umma. Na biyar luwaɗi da maɗigo. Homosexuality. A shari’ar musulunci, idan an samu mutum yana yin luwaɗi (homosexuality), hukuncinsa kisa ne, kamar yadda wasu hadisai suka nuna, a cikin tirmidhi hadisi mai lamba 1456 da Abu Dawud lamba ta 4462. Idan kuka kama mutum yana aikata aikin mutanen Lut, to ku kashe shi da wanda ake aikata da shi. Sai dai, malamai sun yi saɓani kan yadda za a aiwatar da wannan hukunci. Waɗannan su ne manyan laifukan da shari’ar musulunci ta halatta a yankewa hukuncin kisa. Sai dai dole ne a bi ƙa’idojin shari’a sosai kafin a aiwatar da hukunci, don kauce wa zalunci. Haka kuma, addini ya fi son yafiya da gyara fiye da ɗaukar fansa. Fatan kun gane? Ina san ku rinƙa sanin hukuncin addini ne dan shi ne hukunci na gaskiya, shiyasa ma nike kawo maku kwararan hojjoji faɗar Allah. Allah kasa mu cika da imani P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin bedroom ɗin, rashin mutane a ciki yasa ba'a amsa mashi sallamar tasa ba, kuma dama already yasan momma bata ciki, dan ɗazun ya sameta a part na King, kawai dai ya zo ne dan ya rasa in da zai je. A saman sofa ya zauna yana tinanin me mafita a garesa? Dan shi ya rasa abin yi, ya yi shiru cikin tinanin da yake yi ba tare da ya lura da akwai mutun a cikin ɗakin ba, wayarsa dake aljihunsa ce ta fara ruri alamar shigowar kira. Shiru ya ɗan yi tamkar ba zai ɗauki kiran ba, sai da ta kusa katsewa ne ya ciro wayar. Yah Omerish shi ne sunan da yake yawo a saman screen ɗin, jikinsa dik kasala, da kyar ya iya yin picking tare da kara wayar a kunnensa. Kamar wanda yake cikin magagin barci ya ce. "Hello, good evening Yah Omerish". Daga ɗayan ɓangaren Smart dake kwance a saman rest bed dake wajen balconynsa ya amsa mashi da. "Evening how was your day?". .........Da kyar ya amsa da Alhdulillah, idan yana magana sai ya ji kamar yana kara jefa kansa cikin wahala ne. (Na manta na ce ba zan sake saka turanci a cikin rubutu na ba, saboda su Sumayya sun yi complain kuma na ji kukansu dama ba yarenmu bane bamu da gadonsa, shegen iyayi ne kawai irin namu,🥱 yanzu idan turanci ta mutu muna da gadonsa ne? Yen yen yen mun ishi mutane. Wai mu ba zamu tsaya mu daraja yarenmu ba, ance Hausa novel ko uban me ya kawo turanci a ciki?🤔 Hegu masu jajayen kunnuwa sun sa wasu basa kallan yaren iyaye da kakanni da daraja, sun gurɓata mana tinani, sai shegen iyayi da feleƙe muka iya😅 to ni dai mutane na ƴan Niger sun kawo korafi kuma na karɓa mun raba jaha da masu jajayen kunnuwa, Allah yasa kada na rinƙa mantawa ina rubutawa, kun san sabo da rubuta shi ne yasa ko kace ba zaka saka ba sai ka manta ka saka, amma zan yi ƙoƙarin dainawa!!.) "Ina momma? I have been calling her number since isn't going". Ya faɗa yana miƙewa zaune. Dan ya ji alamar motsi a parlourn ƙasa, dan haka sai ya miƙe zaune dan ya saurara da kyau. "Ka kira number dad tana tare da shi yanzu". Jaish ya faɗa yana ɗaga kansa sama. Unexpect kallansa ya sauka a kan bed ɗin momma, ɗan zaro idanunsa waje ya yi yana kallanta, sam bai yi zatan ganinta a cikin ɗakin ba. Miƙewa tsaye ya yi a hanzarce, tun daga Smart bai sallamesa ba ya katse kiran tare da nufar in da take kwance. Like wow abin ya birgesa ya kuma bashi mamaki, ga shi momma bata nan, so the thing sweet him over. Shiru ya ɗan yi yana tinanin me yakamata ya yi kenan? Ya zuba mata idanun yana yi mata mayen kallo yadda ta kudundune a cikin bargon, kallo ɗaya ya yi wa face ɗinta ya fahimci ta sha kuka kafin ta yi wannan barci, a cikin zuciyarsa ya ji wani abin ta ɗan sokesa ganin busassun hawayen nata, kun san akwai tsohon soyayyarta a kasar zuciyarsa, so idan wani abin ya sameta baya jin daɗi, amma kuma yaki yardanwa kansa ya yi accepting ɗinta hundred. Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta ayyana mashi momma zata zo ta same shi, ai tuna haka yasa ya yi gaggawar sanya hannunsa ya ɗauketa cak har da bargon momma ɗin dik ya haɗa ya nufi bedroom ɗinsa da ita, buƙata ta biya, wai ita momma a nan ta ɓoyeta sai ya kawo kansa ya bada hakuri ne, to ga shi dai ya ɗauke matarsa abinsa. MAHNOOR SAI DAI MU CE ALLAH YA BAMU ƳAN TWINS IRIN UNCLES ƊINSU OMAID AND OBAID.....🥱 (Yauwa kun takurawa jikokin Akka fa my people's, kun saka masu idanu saboda suna da sha'awa sosai, ku rufe mun baki shiru, kada na kara jin wata ta takurawa jikokin Akka, dik duniyar yanzu ba haka ta zama ba? Ba haka kuke ba wai? Ko kun ɗauka bamu sani bane? Mun san komai dan haka ku dai'na takurawa jikokin Akka dik haka kuke😒 kuma ni dai bana ganin laifinku, dan dama a karshen duniya sha'awa zata yawaita sosai shiyasa za'a samu zinace zinace, da addini nike rubuta littafina ba da ka ba!! Na san me nike yi, wasu abubuwan sai gaba idan suka bayyana zaku ce mun karanta a littafin Princess Teema da jimawa) Shi kuwa Smart Jaish yana katse kiran ya kira number King tare da miƙewa ya nufo waje domin ya duba waye mai motsi a parlourn ƙasa bayan ya san dare ya yi, yau a gidan Auta zai kwana da su, dan jiya sun yi mashi complain a kan ba zasu iya cigaba da kwana ba tare da shi ba, suna tsoro, shiyasa ya ce wa daddynsa ya yi tafiya, amma yana tare da su, baya san kaisu gidansu kuma, dan baya san dad ɗinsa yasan ya je Kingdom of power ko ya haɗu da mahaifinsa, momma ta ce ya ɓoyewa dad ɗin nasa, dan ba ƙaramar dirama za'ayi ba, King zai ce a bashi ɗansa, shi kuma daddyn Smart kun san aikin da suke aikatawa da Smart a ɓoye wanda idan King ya ji ba zai taɓa yarda ba! Ko ita momma ta ji wannan aiki ba zata yarda ba!! So kun dai san daddynsa ba zai taɓa yarda ya koma kingdom of power ba, yanzu ita momma ta rasa yadda zata ɓullowa wannan al'amari, ita kanta yanzu tana san Smart ya dawo gareta tun da already yanzu King yasan yana raye, to burinta ya dawo kusa da ita tana jin ɗuminsa, ta kuwa san yayanta dai ba zai yarda ba, wlh akwai cakwakiya ba kaɗan ba, sai ma King yasan aikin da Smart yake yi tukunan, a nan ne za'ayi yaki kam. Bugu ɗaya King ya ɗauka, dan a lokacin yana hira da momma ne a kan dawowar Smart ɗin, ya ce ya umarceta da ta dawo mashi da ɗansa kamar yadda ta ɗaukesa ta kai shi can, to hiran da suke yi kenan, ta yi ƙoƙarin tausansa a kan ya bari zuwa ɗan wani lokaci, a take ya gwada mata ɓacin ransa tare da ce mata wlh ko wata ɗaya ba zai iya bari Smart ya kara a can ba, dole ya dawo wajensa ya ji ɗumin ɗansa da ya rasa tsawon shekaru. Da okey kawai ta amsa mashi, amma ta sha jinin jikinta, dan bata san da wani ido zata iya fuskantar mommyn Smart da sunan zata ɗauki ɗanta ba, Allah sarki, babban damuwarta ma shi ne su daddyn Smart ɗin Allah bai basu haihuwa ba har suka tsufa, sun ɗauki son duniyar nan dik sun ɗaura a kansa, kuna dai ganin yadda suke rayuwa, idan baka sani ba ba zaka taɓa cewa ba su suka haifesa ba. ••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 "Good evening dad". Ya faɗa yana tako stair case a hankali cikin natsuwa. "Evening my love how was your day?". Da Alhamdulillah ya amsa kafin ya ɗan yi shiru yana cigaba da tafiya a natse. "Dad where's momma?". Ya faɗa yana warware igiyar rigar barcin dake jikinsa, dan ya ji igiyar ta ɗan kama shi sosai, shi ne zai sukurkutata. "My son kowani lokaci mommarka kawai baka san yin hira da ni ne?". Cikin murya mai rauni King ya yi maganar, Allah ya gani yana bala'in san Smart fiye da tunanin mutum. "No dad, ina san yin hira da kai mana, in the morning zamu yi hira sosai, but now give momma the phone I want to ask her something". Jinjina kai ya yi tare da miƙawa momma wayar ya miƙe ya nufi toilet, dama wanka zai shiga suka tsaya hira da mommar. Kasa shi kuma Smart ya sauko parlourn akwai duhu babu haske, kai tsaye ya nufi switch dan ya kunna wutar...... "Hello momma". Ya faɗa. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa da. "Son how was your day?". "Alhamdulillahi what of you?". .... Da Alhdulillah ita ma ta amsa mashi. Dai'dai lokacin ya kunna wutar parlourn haske ya gauraye ko'ina. Zaune take saman sofa mai zaman mutun biyu, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, hannunta rike da cup da mai aikinsa ya haɗa mata hot tea mai kauri. Sanye take da sleeping dress, gown ne zuwa kyawawan cinyoyinta kusa da gwiwa, sai yar pant daga ta ciki, launin kayan pink color hakan yasa ta yi kyau sosai cikinsu, ga skin ɗinta luwai luwai, ta zubo gashin nan nata ta gaban saman shoulder ɗinta, kun dai san Pretty bata shiri da yunwa, shiyasa ta fito cin abinci abinta, ita kuwa Auta tana ɗaki sai gwada number Hoorain take yi baya ɗauka saboda ya karɓi alluran barci ɗazun, ya birkicewa commander a kan ta ne yasa commander ɗin ya ce a watsa mashi alluran barci ko kwakwalwarsa ta huta, shiyasa take ta kira ba'a ɗaga ba, har kuka ta yi. Zuba mata idanu Smart ya yi yana kallan yadda take shan tea ɗinta a natse, bata ko ɗago kai ta kallesa ba, abincinta kawai take ci, wlh Pretty akwai miskilanci fiye da tunaninku, ba komai take ɗaga idanu ta kalla ba sai abinci ne bata yi mashi hakan. Wani irin faɗuwar gaba ya ji ganinta a cikin wannan shiga. "Son baka jina ne?". Momma ta faɗi hakan har sau uku, amma bai ji ko ɗaya ba, saboda hankalinsa yana a kan Pretty, yarinya kamar wata aljana. Har momma ta katse kiran ta sake kiransa, jin karar wayar yasa ta ɗan ankara tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ya katse kiran ya kirata, har lokacin bai zare kallansa daga kanta ba, ita kuma tamkar bata san da mutum a wajen ba, tea ɗinta kawai take sha, ko irin ta ɗago kanta ɗin nan, ya ɗan yi mamakin ganin ta nuna tamkar bata san da mutum a wajen ba. Karisawa ya yi tsakiyar parlourn, a saman sofa mai zaman mutum biyu ya zauna, cikin natsuwa ya sanar da momma so yake ya koyar da daddynsa cewa babu banbanci tsakanin talaka da mai kuɗi menene shawararta a kai?. Yana magana yana kallan ɗan bakin Pretty da take ta fama hura tea ɗin wai dan ya yi sanyi, ya yi mata zafi ne. Daga ɗayan ɓangaren momma ta ce. "Wannan shawara ce mai kyau, amma dole da kanka zaka yi amfani, idan ba haka ba ba zaka taɓa iya juya zuciyar daddynka ba". ..... Da ɗan mamaki a tattare da shi ya ce. "Ni kuka momma? To meyasa ni?". Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa ta nufi waje dan ma kada King ya jiyota, kai tsaye rest parlourn ɗinsa ta nufa, saman sofa ta zauna sannan ta ce. "Saboda kai ne raunin daddynka, idan akwai wani abin da yake tsananin so to ya biyo bayanka gaskiya, dan haka dik abin da zaka yi mashi ko tarko da zaka kafa mashi ya kasance ka haɗa da kanka hakan ce kawai zata sa ya yi gaggawar saukowa har ya gane abin da kake so ya fahimta". Shiru ya ɗan yi, ya fahimci abin da momma take nufi, amma dan ya tabbatar sai ya ce. "Momma I didn't understand".... Sarai tasan ya fahimci abin da take san faɗa, dan tasan yaranta da saurin ɗago abu, amma tun da ya nemi bayani dallah dallah bari ta yi mashi yadda zai fahimta. "Ka samu ƴar gidan mutunci ƴar gidan talakawa ka kawo mashi da sunan zaka aura, ka nuna mashi idan ba ita ba zaka iya mutuwa, ta hakance kawai zai sa zuciyarsa ta sassauto tun da abin ya biyo ta kan sanyin idanuwansa.........." Katseta ya yi a hanzarce da cewa. "Kuma sai na aureta ɗin?"........ Ta jima tana san ya yi aure yaki yarda, da ta kawo mashi maganar ma sai ya sauya zance, to yanzu tana ganin dama ne ta samu wanda idan ta bari ya kubce mata bata san ranar yin aurensa ba kuma, dan haka zata iya yin komai dan ya aminta da wannan shawarin nata, cikin sanyin murya da tausasawa haɗe da kalamai masu kaifi ta ce. "A'a ba sai ka aureta ba ai, kuma zaka iya auren nata ma idan ya so daga baya in daddynka yaga yau an wayi gari da kafarsa ya taka ya je gaban talakawa ya nemi alfarmar su baka aure, ya gane ashe talaka yana da rana kuma yana da darajar da za'a je neman abu a wajensa wani lokaci, to kana iya sakinta idan buƙatarmu ta biya". A hanzarce ya ce. "No momma, ban yarda da hakan ba, ban yarda na aurenta na saketa ba, ni auren ma ba zan yi ba, kawo wata shawara!". Ya kai karshen maganar yana kai kallansa saman cinyoyin Pretty, da yake rigar tata zuwa gwiwowinta ne, ga shi kuma tana zaune sai rigar ta ɗan yi sama kaɗan, lokacin guda ya ji wani abu a ransa. "Okey to yanzu ka fara soyayyar karya da yarinyar, sai mu bi iyayenta a bayan fage mu faɗa masu idan daddynka ya turo a nema maka auren su ce ba zasu iya bashi ba, dan ma ya kara sanin talaka ma yana da abin da za'a iya nema a wajensa, su hanaka yarinyar kai kuma kace idan ba ita ba mutuwa zaka yi, daddynka zai sha fama sosai, yana tsoron ka mutu hakan zai sa ya yi learning lesson, daga nan zaka iya rabuwa da yarinyar ba sai an kai ga aure ba, please don't say no to me my son, wannan ita ce kawai shawarar ta hanyar da ya dace mu koyawa daddynka darasi mu kuma sanya ya yarda da Hoorain, na san zaka so farincikin Zunaira fiye da kowa a cikinmu". Kalamai dai masu daɗi ta rinƙa zuba mashi, dik dan ya aminta, kun san uwa ta gari tasan yadda zata shawo kan ɗanta har ma ta yi mashi wayau, wanda ya haifeka ya wuci gaban tinaninka, sai dai ya ganka kawai. Shiru ya yi yana tinanin maganganunta, tabbas tana da gaskiya, wannan hanya ita ce kawai zata sanya King ya yarda talaka ba abin walaƙantawa bane, dan watarana za'a iya zuwa neman wani abin a wajensa, sai dai shi kuma how comes zai yi soyayya abin da bai iya ba, bai taɓa yi ba, ya zai yi yanzu?. Katse mashi tinani momma ta yi da cewa. "Ka amince ko my son? Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya". ...... Momma na kalaman yaudara my people's, har da addu'oi tun bai amsa ya aminci na, kawai dan tasa ya ji ba zai iya karyar mata da gwiwa yaki yarda ba, har da kara nuna confidence ɗinta, dik ta sare mashi gwiwa ta kashe mashi jiki har bai san lokacin da ya amince mata ba. Ai wani irin sanyayyar ajiyar zuciya da ta sauke sai da ya ji ransa ya yi sanyi shi ma, mahaifiyarsa ta yi murna saboda shi har tana sauke sayyar ajiyar zuciya, kai abin ya yi mashi daɗi, a ransa ya kudurta ba zai taɓa bata kunya ko yasa ta ji babu daɗi ba, In Sha Allah zai kasance mai sanyata farinciki kamar na yau. Ya yi nisa cikin tinanin da yake yi sai magana take yi mashi tana zuba mashi ruwan albarka amma bai ji ta ba, hankalinsa ma ya koma kan Pretty da ta miƙe ta nufi kitchen dan ta gama shan tea ɗin. Sai da ya ga shigarta cikin kitchen ɗin sannan ya kawar da kallansa daga kanta, yana ƙoƙarin amsawa momma addu'oin da take yi mashi Pretty ta zumduma ihu tare da kwasowa a miliyan ta fito daga cikin kitchen ɗin. Kai tsaye wajen shi ta nufa, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana ihu. Shiru ya yi yana ƙoƙarin gane a wani irin yanayi yake ne?. Da gudun gaske tigernsa ya fito daga cikin kitchen ɗin ya biyo bayan Pretty, tun da suke gidan bata taɓa sanin yana da zaki da kuma damisa ba, dan bata taɓa ganinsu ba, idan baku manta ba a sama gabaɗaya damisa da zakin suke, so basu cika saukowa ƙasa ba sai cikin dare, in baku manta ba a farko farkon littafin na faɗi hakan, so shiyasa Pretty bata taɓa saninsu a cikin gidan ba, gata mayyar tsoro, na tabbata da tasan da su a gidan ba zata yarda ta zauna ba, idan kuma ta zauna to fa ba zata yarda da fito waje ba, zata koma zaman ɗaki kan gado. Wani irin tsalle tiger ya daka ya yi kansu zai yagusheta, dan ta je garin ajiye cup a saman table ta taka mashi bindi, bata lura da shi ba, shi ne ya biyo ta. Ai a miliyan Smart ya rungumeta suka kwanta a sanan sofar sannan ya juya da ita ya zamana ita ta koma saman sofar shi kuma ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa ya tare mata damisan, hakan yasa damisan ya sauka a kansa. Zubawa wuyarta idanu Smart ya yi yana kallan tsokan wajen gwanin ban sha'awa, idan baku manta ba suna da gurun wuya mai shegen ɗaukar hankali, aikuwa ya ɗauki hankalin Smart namu na amana. Ita kuwa ta datse idanu gam tare da kankame rigarsa ta wajen kirjinsa. Dirowa kasa tiger ya yi daga jikinsa yana wani girgiza, da karfi ya fara jan hannun Smart da bakinsa irin ya matsa ma bashi Pretty. Jan da tigern yake yi mashi ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka yana kallan wuyarta, komawa saman sofar ya yi ta gefenta ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, hannunsa rike da wayarsa momma na jin dik abin da yake faruwa, sai tambayarsa take yi waye mai wannan ihu amma bai ji ba, dan ya zare wayar daga kunnensa. Tsalle damisan ya yi zai haye kanta Smart ya yi saurin riƙosa ya rungume irin alamar rarrashi, ita kuwa har lokacin bata motsa ba, kamar dai suma ta yi. Da kyar ya rarrashi damisan ya tafi, dawo da kallansa a kanta ya yi, yadda ta faɗa jikinsa ne kawai a ransa, a lokacin sai da ya ji gabaɗaya komai nasa ta ɗauke diff. A yanzu ma sai da momma ta katse kiran ta sake kiransa, doguwar numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, sannan ya katse ya kirata. Tana ɗagawa ta hau tambayarsa lafiya wacece take ihu haka. Bai ɓoye mata ba ya sanar da ita dik abin da ya faru. Yana gama faɗa mata ta tari numfashinsa da cewa. "Shikenan ma mun sa yarinyar da zamu yi wannan aiki da ita, kuma ga shi Zunaira ma tana kaunarta, daddynku zai koyi darasi sosai, kuma yarinyar tana da natsuwa, ka kula da ita bari in binciko iyayenta, nasan mara galihu ce itama, dan Zunaira ta ce mun a daji suka haɗu da ita, bata da kowa, ni kuwa nasan ba zai taɓa yiwuwa bata da kowa ba, dan haka bari in fara bincike a kan iyayenta kai kuma ka fara kulla soyayya a tsakaninku".. Tashin hankali!!! My people's momma zata jijjigo babbar aiki, domin binciko iyayen Pretty ba ƙaramin abu bane,!! Kuma zai iya zama abu mara daɗi a garezu, akwai show, momma zata tono wani babban............ Na dai yi shiru amma akwai cakwakiya. "Momma wannan yarinya ce karama and......" Katse shi ta yi da cewa. "Ai yarinyar ta fi, saboda ka ga ba aurenta zaka yi ba, idan babbar mace ce ka yi soyayyar karya da ita zata iya fara sanka da gaske, kaga in ka barta baka aureta ba kuma an cutar da zuciyarta, amma ita yarinya bata san soyayya ba, ko ka rabu da ita a lokacin da buƙatarmu ta biya lafiya lou ne".. Ni kuwa na ce ba dai yaran yanzu ba, da sanin komansu ake haifansu ato, dan haka kamar Pretty ta san soyayya mana momma!. Ya gamsu da zancen momma, amma sai ya ce ta bashi lokaci ya yi tunani ko zuwa gobe ne. A kan haka suka tsayar da zance, daga haka suka yi sallama. Katse wayar ya yi ya tura cikin aljihu tare da ɗan sunkuyo da kansa a kan Pretty, sai a lokacin ya fahimci suma ta yi, mayyar tsoro kawai. Miƙewa ya yi ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa ya nufi switch, kashe wutar parlourn ya yi ya haura sama yana tinanin a kan zantukan momma..... My people's me kuke tunanin zai faru? Momma zata gano iyayen Pretty? Su waye iyayen nata? Smart zai yi accepting soyayyar karya da Pretty idan ya gama tunanin nasa ko ba zai yi ba? Muje zuwa, kada ku manta Pretty dai an yi mata miji, mom ɗinsu ta bada ita wa Kamran kafin ta ɓata ko? In kun manta na tina maku!!. ••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥 Ko kaɗan kalamanta basu huda zuciyarsa ba, babu sassauci a tattare da shi, ta kankame hannunsa gam tana yi mashi magiya, amma ina babu alamar zai sassauta. Sun kwashi good 30 mins a haka tana mashi magiya bai kulata ba, taki sakar mashi hannunsa, kuka take yi hawaye bibbiyu wai ko zai tausaya mata, amma ko kaɗan bai ji komai ba, kuma idanunsa suna kan face ɗinta fa, yana ganin yadda take kuka, amma ina zuciyar ta riga da ta bushe. Ihu Ronnie ya kurma tare da matsawa kusa da su yana faɗin. "Please big bro for give them, Sweetie konasu fa ake yi". A rikice ya yi maganar cikin fitar hayyaci. Kun san already kafin Sweetie ta rike hannunsa ta hana shi latsa laptop ɗin ya rigada ya shigarwa da Robbot ɗin umarnin abin da zasu yi, so ita Sweetie a tinaninta tun da ta rike hannunsa shikenan ba zai samu damar bada umarnin ba, bata san aikin gama ya rigada ya gama ba, ta tsaya tana yi mashi magiya already su kuma robbot suna aiwatar da aikinsu. Injuna na zamani suka yi amfani da su wajen haka ramin cikin ƙanƙanin lokaci, sannan suka hura wuta tamkar yadda ya umarcesu. Dik wanda ya bijirewa Black Tiger sai su kama shi su jefa shi cikin wanna balbalin wutar, yana ihu yana basu hakuri haka zasu jefa shi ciki gwanin ban tausayi. Wannan ihu da Ronnie ya kurma abin da ya gani kenan ya razana shi ya tashi hankalinsa, sai jefa mutane cikin wutar robbot suke yi. Hankalin Sweetie idan ya kai miliyan to ya tashi, wai abin takaicin ma har da ƙananan yaran da basu suka yi mashi laifi ba, iyayensu ne suka bijire mashi, to uwa ta yi gabas ai dole ta kama hannun ƴaƴanta su wuce gabas ɗin da shi ko? To idan aka jefa uwar cikin wuta sai a jefa ƴaƴan ma su da ba su san komai ba uwarsu kawai suke bi. Gabaɗaya birnin ya rikice da ihu da magiya na ban hakuri, amma Black Tiger yana tsaye yana ganinsu tamkar wani dutse ko karfe bai sarara masu ba, tamkar babu zuciya a kirjinsa, babu alamar ma sun bashi tausayi ko ɗigo a ransa. Ihu Sweetie ta kurma, da karfi ta fara kai mashi duka a kirjinsa da hannunta dikka biyu tana jijigasa da karfi tana faɗin ya rabu da mutanen nan ya kyalesu, ya rabu da yaran da ba su ji ba basu gani ba, ya dubi girman Allah ya sauke RAWANIN ZALINCIN dake kansa ya ɗaura na adalci, sambatu take cikin fitar hayyaci tana kai mashi duka babu kakkautawa. Yana tsaye tamkar gunki, ko kaɗan babu alamar zai tausaya. A cikin kwakwalwarta Sweetie take jiyo ihun mutanen nan ta cikin mirrorsa, sai dai ba zata iya taɓuka masu komai ba. Tashin hankali da firgici ne suka yi mata yawan da ba zata iya ɗauka ba, hakan yasa tana cikin sambatu tana kai mashi duka kawai numfashinta ya ɗauke diff ta zuba ƙasa a gabansa... BA SHAKKA YAU BLACK TIGER YA FITO A AINAHIN BLACK TIGER ƊIN NASA, BABU SASSAUCI. A miliyan Ronnie ya yi kanta yana ambatar sunanta, shi ma hawaye yake yi bibbiyu, zuciyarsa ta gaza iya ɗaukar wannan masifa da tashin hankalin, tun yana ambatar sunan Sweetie cikin ɗaga murya da kaushi, har voice ɗinsa ta dai'na fita, kan kace me shi ma ya sulale ƙasa a wajen ya sume... Innalillahi wa inna ilahir rajiun. BLACK TIGER dai ko a jikinsa, sai ma cigaba ya yi da yin aikinsa yana latsa laptop ɗinsa. My people's kuna tinanin Black Tiger zai iya canzawa kamar yadda Sweetie da Ronnie suke so kuwa? Zai iya sauke RAWANIN ZALINCIN dake kansa kuwa? Kuna ganin team Ronnie and Sweetie zasu yi nasara kuwa? Sweetie tana yawan cewa zuciyar Black Tiger mai kyau ne akwai dalilin rikiɗewarsa izuwa bakin mugu, shin menene wannan dalilin? Ya Ronnie zai ji idan ya ji Floris ta mutu? Har da iyayenta suka bijirewa Black Tiger,.shin suma har da su aka kona? Wani irin hukunci master Devil zai karɓa a hannun Ronnie and big bro?. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Zaune ya isko Ramish a saman bedside drawer yana ƙoƙarin treating na hannunsa. Cikin zafa ya ƙariso wajen yana tambayarsa meya same shi a hannun nasa? Ina ya je daren jiya?, meyasa yana ta kiran wayarsa baya ɗagawa?. Cikin tashin hankali ya yi maganar. "Get out from here!". Shi ne abin da Ramish ya faɗa cikin kakkausar murya. Gadan gadan Bilal ya nufosa. "Babu in da zanje har sai ka faɗa mun abin da ya sameka". Tsawa ya daka mashi a kan ya fita mashi a ɗaki kuma ya tabbatar kafin nan da 30 mins ya gyara mashi kofar da ya ɓallah. Da ya fahimci Ramish yana kan tsini sosai sai ya juya ya fita gudun a samu matsala, kai tsaye ya nufi wajen Abbie. Yana fita shi kuma Ramish ya miƙe ya nufi in da Leesharh take kwance a balconynsa saman kujera, rufe kofar balconyn ya yi ya ƙarisa wajen a gaggauce, dan bai gama yi mata abin da ya dace ba. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 🔥🔥🔥🔥DUBAI.🔥🔥🔥🔥 Bayan wasu kwanaki da basu haura one month ba, akwai dalilin da yasa na yi maku wannan tsallake, idan mun yi gaba zan dawo baya domin yi maku bayanin abin da ya faru a waɗan nan kwanaki, muje dai zuwa. Ramish da kansa ya yi jijyar Leesharh ba tare da sanin kowa ba, bai bari kowa yasan da abin da ya faru ba sai babban yayansu wato Smart, dan ya gane mai taya shi aiki shi ne babban yayansu da mama ta takura mashi a kan ya yi mata bincike ba ɗan King bane, yana ganin hoton Smart ya gane yayansu ne saboda kamanninsa da su Zunaira, to yarasa wani irin shaida kuma mama take so bayan kamanninsa da kannensa. Amma fa ko da ya faɗawa Smart ga abin da ya faru bai sanar da shi ya yi mata fyaɗe ba, ya dai faɗa mashi yana zargin Ummie and Bilal, da Smart ya tambayesa dalilinsa na zarginsu sai ya sanar da shi cewa akwai wata rana da ya fita cikin hayyacinsa har ya kusa yi wa mai aikinsu fyaɗe, lokacin da ya dawo cikin hankalinsa ya zauna yana tinanin meyasa ya birkice har haka, meyasame shi? A lokacin ya ce bari ya gwada jinin jikinsa ya gani, a nan ne ya gane wasu kwayoyi sun ratsa jininsa wanda kuma yana da tabbacin ba alluransu aka yi mashi ba, da bakinsa ya sha, in kuwa haka ne to dole ko Ummie ko Sharrifat ɗaya cikinsu akwai wanda ya sanya mashi waɗan nan kwayoyi cikin abin shansa, dan baya cin abinci a waje, dik in da ya je sai ya dawo gida yake ci, kuma Sharifat ce kawai mai kawo mashi abu ya ci, to kun ji yadda aka yi Smart yasan abin da ya faru. Batun fyaɗe ya rufesa iya shi da ita kawai, ita ɗin ma da farko ya so yi mata allura ya mantar da ita komai, amma daga baya da ya yi dogon tunani sai ya ce kila tana da ƴan uwa bayan iyaye, idan ya yi hakan ya yi mata zalincin da ba zata iya yafe mashi ba, gara ma fyaɗen da ya yi mata a kan wannan alluran, da ya kwantata hakan da kansa, ya ce yanzu shi ayi mashi allura ya manta su Smart gabaɗaya a rayuwarsa, sai ya ji ina ba zai iya yi mata ba, dama kullum a rayuwar nan idan zaka yi hukunci ka kwatanta da kanka ka gani, hakan ce zata sanyaka yin adalci, yana ɗaya daga cikin abin da yasa kuka ga ni Princess Teema bana san kashe mutane a cikin littafina, saboda kwatanta abu da kai'na ya zame mini jiki, so idan na kwantanta irin raɗaɗin da zasu ji a kai'na sai in ji kai ba zan iya jurewa ba, wlh shawara nike baku domin tsira, kasance mai kwatanta abu da kanki tabbas zaki zama adila mai yiwa mutane adalci cikin sauki, Allah dai ya shige mana gaba ya dafa mana. Ba zan baku labarin abin da ya faru bayan farfaɗowar Leesharh tsakaninta da Ramish ba, saboda ina da dalilin ɓoye hakan, sai gaba zaku ji komai, iya abin da zan faɗa maku a nan shi ne Leesharh dai ta shafe complete sati yana wahalar jinyarta kafin ya iya shawo kan matsalar, a jinyar tata ma abubuwa da dama sun faru, jinyarta yasa bai bi ta kan bincikar dalilin da ya kawo kwayoyi a cikin jininsa ba, yana busy sosai, ga shi jinyar tata cikin sirri yake yinsa, abin ku da rashin gaskiya yana cikin tashin hankali a koda yaushe, bashi da wata natsuwa, sannan ya jefa kansa a cikin damuwa da rashin walwala dik dan abin da ya aikata wanda bai taɓa zatan ko a mafarki zai aikata ba, ya shiga zulumin kullum cikin fargabar asirinsa zata iya tonuwa, ya zama wani irin sukuku haka. A haka ya shafe makonni uku yana fama, sai a cikin mako na huɗun nan ne ya sami natsuwa da kwanciyar hankali dalilin komawarta dai'dai, sai dai fa idan zai kwana yana yi mata magana bata amsa mashi, har yau ta gagara ɗaga idanu ta kallesa, wani irin tsananin bakinciki ne a ranta wanda take jin tamkar ta kashe kanta, abin takaici, shi kuwa Allah ya jarrabesa da tausaya mata matuƙa, ya gagara watsar da alamarinta ya kama aikin gabansa, yana ganin koma me ta yi mashi ya cancaci hakan, saboda shi ne silar kuncinta a rayuwa, dan haka baya jin komai idan ya yi magana bata kula shi ba. Sharifat ta yi haukar nemanta har ta gaji ta fawwalawa Allah komai, ta sanar da Ramish and Bilal sai dai da ta cika matsawa Ramish ya ce mata kada ta sake yi mashi maganar Leesharh idan ba haka ba zai saɓa mata. Shi ma Bilal ya yi haukar nemanta kamar menene, ya shiga damuwa matuƙa. Amma shi Abbie bai damu da rashin ganinta ba, dan ya tambayi Ramish ya ce mashi tana nan suna tsaka da aiki ne ta bashi haɗin kai tana gabatar mashi da wasu hujoji, sai ya yi amfani da abin da ya faru da ita a ranar na kasheta da aka shiga za'ayi a ɗakinta, sai ya ce wa Abbie ai ya ɗauketa daga gidan nan ne dan kada a sake yunkurin kasheta, ya kaita waje mai tsaro sai sun gama aiki zata dawo, Abbie ya yarda da maganarsa, yasan baya yi mashi karya. A zahirin gaskiya ya ɗauketa daga gidan Abbie tun washe garin ranar da abin ya faru, tun time da Bilal ya ruguje mashi kofa, a wannan rana da daddare ya fita da ita daga gidan ya mai da ita gidansa, a nan ya yi jinyarta, shiyasa su Bilal basu san in da take ba, sun yi neman duniyar nan babu ita babu labarinta. •••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 Zaune take a saman sofa mai zaman mutum uku a cikin parlonsa, ta yi shiru tare da buga uban tagumi tana tunanin irin rayuwar da ta sha, ta fuskanci challenges dayawa baiwar Allah nan, yanzu kuma ɗan mutumcin da take ji da shi ɗin ma babu, tinaninta ɗaya shi ne waye zai aureta a haka? Shikenan ita ta zo duniya a wahalce kuma zata koma a wahalce babu wani gata?. Kanta a kasa tana kallan yatsun kafafunta da suka ɗan ya fayau, dik ta yi rama sosai saboda bata cin abinci, kullum tana cikin tinani. Size ɗin kayan da take sakawa a da yanzu sun yi mata yawa, sai dai ƙasa da su, saboda rama, sai idanu kawai zaka gani. Sleeping dress doguwar riga ce a jikinta launin maroon color, ta sanya ɗan ƙaramin hijabi a kanta, rabonta da abinci tin daren jiya da ta sha tea, bakinta sam babu ɗanɗanon komai, bata sha'awar cin komai kamar wata mai ƙaramin ciki. Ko kaɗan bata ji motsin shigowarsa cikin parlourn ba, dan ta yi nisa a cikin tunanin da take yi, har ya shigo ya wuceta ya nufi kitchen, ta luluƙa duniyar tinani. Haka zalika bata ji dawowarsa ba sai ganinsa ta yi ya zauna a saman sofar da take zaune hannunsa ɗauke da cup and small chop a cikin plate, yana sanye cikin sleeping dress riga da wando launin milk color, ya yi kyau sosai, sai dai shi ma ya rame sosai alamar yana cikin damuwa, dik wanda ya yi complain a kan ramansa sai ya ce aiki ne ta yi mashi yawa. Har Smart ya yi complain a kan ramansa, amma sai ya ce zai rinƙa kulawa yana ragewa kansa pressure dan ya maida jikinsa. Yana zama ta zabura ta miƙe zata bar wajen. A hanzarce ya ɗaura plate na small chop a saman table dake kusa da su ya kai hannunsa ya riƙo nata hannun, in a low voice sosai ya ce. "Please Aesh, ya isa haka gudun nawa da kike yi, dan Allah ki ji tausayina, ko iya haka ya kamata ki fahimci ba da gangan na yi maki hakan ba, idan da da gangan ne ba zan kwashi up to one month ina kula dake ina kuma yi maki magiyar da ki yafe mun ba, ki mun magana ba, dan Allah". Jikinta ne ya hau kerma, dan a duniya tsoronsa take ji matuƙa, murya na rawa ta ce mashi. "Tabbas da gangan ka ci mun mutumci, ka mun tabon da ba zai taɓa gogewa a cikin zuciyata ba, ka zalinceni, dama a lokacin da ka kamani ka sakeni ka ce mun in ka yi bincike ka ga da sa hannuna a abubuwan da suke faruwa zaka mun abin da ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata, ga shi kuma ka mun ɗin kamar yadda ka faɗa, tabbas ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata! Ka cuceni ka zalinceni! Dan Allah ka kashe ni in huta da wannan rayuwa". Ta kai karshen maganar zafafan hawaye suna zubowa a saman kumatunta. Shiyasa aka ce ka rinƙa tauna magana kafin ka faɗeta, baka san me gobe zata haifar ba, ga shi maganar da ya taɓa faɗa mata na in ya kamata da laifi zai yi mata abin da ba zata manta da shi ba ta riki maganar a ranta wanda kuma shi ba hakan yake nufi ba, jama'a ku tauna magana kafin faɗinta dan gudun abin da gobe zata haifar, shawara ce daga alkalamina!!. Kalamanta sun kara narkar mashi da zuciya, shi dai burinsa ɗaya shi ne ta yafe mashi, amma taki sauraronsa ma. Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya saki hannunta ba, cike da tausayawa da kulawa ya ce. "Dik abin da zaki faɗa a kai'na na yarda na kuma ɗauka, yanzu dai dan Allah zauna ki sha tea, ni dai ki rinƙa cin abinci koma me zaki ce a kai'na ki faɗa, lafiyarki shi ne fata na kawai". Ya kai karshen maganar yana miƙo mata cup dake hannunsa, tea ne mai zafi sai tiriri yake yi. Allah sarki, a jikinta tana jin ba da gangan ya yi mata hakan ba, sai dai zuciyarta taki yarda da hakan, wani lokaci har tausayi yake bata yadda yake neman ta yafe mashi, amma ta gaza yarda da shi, ta kuma rasa dalilin kin yarda da shi da zuciyartata ta yi. "Ba zan iya cin komai ba, saboda ban san yanzu ina rayuwata ta fuskanta ba, dan Allah ka kyaleni ko yunwa zata kasheni in huta tun da kai ba zaka kasheni ba". Kanta a ƙasa ta yi maganar....... Nisawa ya yi kafin ya ce. "Babu abin da zai samu rayuwarki, zaki yi rayuwa kamar kowacce mace mai ƴanci, dan Allah zauna ki sha tea kin ji?". Cikin sigar rarrashin da ya koya dan dolensa ya yi maganar. "Har abada ba zan taɓa yin rayuwa mai ƴanci ba, a rayuwar yanzu ka kai budurcinka gidan miji ma ya ka kare da walaƙanci da tozarci in baka samu miji na gari mai tsoron Allah ba bare ace ka zubar da mutuncin naka a titi ka shiga gidansa empty, me kake tinanin zai faru? Kana tinanin zan yi rayuwa mai ƴanci ne? Kana tinanin akwai wata daraja da ta rage mun wanda zai kalleni da ita ne?........."... Katseta ya yi ya hanyar ɗaga mata hannu kafin ya ce. "Baki zubar da mutuncinki a titi ba, tabbas babu wanda zai ganki a matsayin mara daraja kin ji ko? Dan Allah Aesh ki yafe mun, ki yafe mun kin ji? Nasan na cutar dake, amma kin ki yarda ba da gangan na yi ba, kin ki yarda ba halina bane, da kin san yadda na tsani zina da baki yi ƙoƙarin danganta ta dani bama, kin san irin hukuncin da nike yi wa mazinaci wanda ya yi wa mace fyaɗe kuwa?". Cike damuwa a ransa ya kai karshen maganar............ Sai a lokacin ta ɗago da kanta ta kallesa, hawaye suna cigaba da gangaro mata masu ɗumin gaske, da kyar ta iya cewa. "Babu ma wanda zai aureni da har zai ganni da daraja, ka kwantanta a kanka, shin zaka iya auren macen da wani ya lalata ya yi mata fyaɗe? Ko ka ɗaukeni a matsayin kanwarka na jini, ya zaka ji idan aka ce anyiwa kanwarka fyaɗe?"...... Dum!! Dum!!!! Shiru ya yi bashi da bakin bata amsa, dan yasan ko kusa ko alama ba zai iya ba, ba zai iya auren wanda wani ya lalata ba, haka zalika ba zai iya barin wanda ya yi wa kanwarsa fyaɗe ya cigaba da numfashi a duniya ba, ba zai kyalesa ba har sai ya yi mashi mummunar kisa, batun aure kuma, shi yaushe ma ya taɓa yin tinanin auren bare har ya yi tinanin irin macen da ta dace da shi, iya abin da ya sani dai shi ne ko soyayya da wani mace ta taɓa yi ba zai kulata ba bare har a kai ga aure. Cikin matsanancin kuka ta ce. "Ka gani ko? Kai kanka ba zaka iya auran ragowar wani ba, to taya kake tinanin ni zan samu wanda zai iya karɓar ragowarka?". Cikin zafin zuciya ta yi maganar, tana kai karshen ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata ta juya da nufin ta bar wajen da sauri....... Cikin zafa ya riko hannunta, kin juyowa su kalli juna ta yi, sai wani irin huci take fitarwa mai ɗimin gaske, kai ka zaci zata iya haɗiye zuciyarta a lokacin ko kuma ta kone saboda zafin da zuciyarta ya ɗauka, yana yi mata wani irin suya mai azaba, abin da ciwo matiƙa gaskiya. "Idan na aureki shikenan zaki yafe mun?" Ya faɗa yana kallanta. Ai a miliyan ta juyo da kallanta a kansa, ido cikin ido suka kalli juna, wani irin faɗuwar gaba ta ji ya risketa, ta kasa iya magana, dan bata da abin faɗe....... "Ni zan iya ɗaukar ragowata ai ko? Budurcin mace shi ne mutuncinta right?". Ya faɗa kamar ya jefa mata tambaya wanda yasan ba amsa mashi zata yi ba. Dan haka sai ya ɗaura da cewa. "Tabbas budrucin mace shi ne martaba da kimarta a idanun mijinta, dan haka ni zan aureki, dama ni na karɓi budurcin naki, dan haka zan kalleki da kima da daraja, kuma zaki yi rayuwa mai ƴanci kamar kowace mace ko ma in ce fin kowace mace tun da kema kin kawo mun budurcinki, kin aminta da hakan?". Idanunsa a cikin nata ya yi maganar, tabbas saboda tausayinta da kalamanta na ta rasa gata yasa ya yarda zai aureta, domin kuma ta yafe mashi, ba zai so ya yi sanadiyar shigarta kunci na har karshen rayuwarta ba, gara ya aureta ko ba komai dama shi ya buɗeta, tabbas ba zai yi mata gori a kan komai ba. Kai ta fara girgiza mashi alamar bata yarda ba, tsananta kukan ta yi, har wani shessheƙa take yi, tamkar zata haɗiyi zuciya, cikin kuka mai tsuma zuciya ta ce. "Ba zan iya aurenka ba saboda ƴar uwata, Sharifat ta mun komai a rayuwata, dan haka ba zan taɓa bakanta mata ba, da ta shiga cikin ƙunci gara ni na tabbata a cikin bakinciki, a lokacin da na rasa gata, nike matsayin mara galihu, nike cikin tsakiyar rana a dokar sahara, a lokacin da duniya ta juya mun baya, farinciki ya kaurace daga rayuwata, na cire tsammanin yin farinciki har abada, a lokacin Sharifat ta tsaya tsayin daka wajen ganin sai da ta sakani dariya a rayuwata, ta sakani na ji cewa ni mutum ce, ta sakani na ji cewa ashe ina da sauran farinciki a rayuwarta, ta zame mun uwa, uba ƴar uwa, ɗan uwa, bata kyamaceni ba, ta jani a jiki tamkar ƴar uwarta na jini, ta kyautatawa rayuwata, dalilinta nasan kai'na har nasan darajar mutuncin da yau nike kuka a kansa dan ka keta mun shi, ba dan ita ba da ban san darajar mutuncin nawa ba, Sharifat ta wuci tinanin mai tinani a rai'na, dan Allah kada ka sake yin magana a kan aure tsakanina da kai, dan kai ne burin ƴar uwata!!". Tana kai karshen maganar ta kwace hannunta da sauri ta haye sama tana kara rushewa da kuma mai taɓa zuciya. Gum ya tsaya tamkar wanda aka sassaƙa, yau ya ji sabon labari wai Sharifat na san shi, abin da bai taɓa ji ba bai taɓa tinani ba ko a mafarki, a cikin ransa ya ce ko mata sun kare a duniya shi me zai yi da Sharifat? A yadda ya tsani uwarta ina zai kaita? Tab lallai akwai cakwakiya kuwa. Ya jima tsaye a wajen ya rasa madafa, daga karshe ya yanke shawarar bin bayanta, dan ba zai iya jurar ganinta da yunwa ba. Sama ya haye yana tinanin mafita a garesu gabaɗaya, dan a gaskiya ba zai iya jurar ganinta a halin da take ciki ba, yana da ilimin addini yasan cewa mutum ya shiga damuwa a dalilinka na wuni ɗaya ma babban musifa ce a gareka bare ace tsawon wata kuma yana neman zarcewa har abada idan bai ɗauki mataki ba? Ina zai kai wannan zunubi haka? Gaskiya da sake. Kwace ya iskota a saman bed ta kifa kanta a saman pillow tana kuka tamkar ranta zai fita. Wani irin tausayinta ne ya kara kama shi, tabbas yasan da ciwo abin, amma ya zai yi to? Kaddararsu ce ta zo a haka. Gaban bed ɗin ya karisa, a saman bedside drawer ya ɗauka cup ɗin hannunsa kafin ya zauna a gefenta, hannunsa dikka biyu yasa ya ɗagota tare da juyo da ita suna fuskantar juna, Allah sarki ta datse idanunta gam tamkar zata fashesu. Slowly santa ya fara shigarsa ba tare da ya sani ba, a da iya tausayi ne kawai, amma yanzu gangar jikinsa ta fara karɓan wani sabon saƙon na daban!. "Aesh nasan na yi abin da baki ba zai iya zayyana kuncin da kike ciki ba, yanzu da bakinki ina san ki faɗa mun me kike san na yi dan ki shiga cikin farinciki kamar a baya?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar...... Tana san kwace kanta daga garesa amma ta rasa kuzarin yin hakan, sai ta hakura kawai ta natsu tana cigaba da kukanta. Ganin bata da niyar bashi amsa ne yasa ya kai hannunsa ɗaya saman ƙuncinta ya fara goge mata hawayen da basu da niyar dakatawa daga zuba, hannunsa ɗaya kuma ya tallabota........ "Please talk to me Aesh". Cikin wani irin slow ya yi maganar, ga murya ƙasa ƙasa. Ganin waɗan nan hawaye basu da niyar dakatawa ne yasa ya mannata da kirjinsa dan ya rarrasheta, hankalinsa yana tashi sosai idan ya ji kukanta, sai ma idan ya tuna da cewa marainiya ce ita, sai ya kara jin hankalinsa ya tashi...... "Aesh ki faɗa mun abin da kike so in yi maki ki dai'na wannan kuka ki fita a halin da kike ciki". Da ga ji voice ɗinsa kasan yana cikin damuwa matuƙa. Kai ta hau girgiza mashi alamar babu komai, ƙanƙameta a kirjinsa ya yi yana jin wani irin abu da ba zai iya gane ko menene mane yana ratsa kashi da ɓargo har zuwa ƙwaƙwalwa da zuciyarsa. Tun tana iya kuka mai ɗan sauti har sautin ya dai'na fita, daga karshe ta yi diff alamar barci ya ɗauketa a jikinsa babu shiri, kun san idan mutum ya yi kuka sosai yana saurin yin barci, to ita ma dai ta yi ba tare da ta shirya ba, kuma bata sanya komai a cikinta ba, da yunwa ta yi barci, hanjinta dik a tattare sun naɗe. Jin numfashinta ya sauya zuwa irin na mai barci ne yasa ya dawo da kallonsa a kanta, a nan ya tabbatar da ta yi barci. Kwantar da ita ya yi a hankali cike da kulawa, sannan ya zubawa face ɗinta da ya yi jaga jaga da hawaye kallo na ƴan mintunan da basu gaza biyar ba. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan matsar da bakinsa kusa da ita kaɗa, a fili ya furta. "Isn't all my fault Aesh, am so so sorry, by the grace of god I will make you happy irin wanda haki taɓa samu ba a rayuwarki, ba zan bari ki sake yin kuka a kan wani abin ba, zan gyara abin da na ɓata da kai'na". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye. Bargo ya ja ya lulluɓa mata kafin ya nufi switch. Wutar ɗakin ya kashe sannan ya nufi waje, zuciyarsa cike da tinanin bata sanya komai a cikinta ba, tabbas kuma yasan tana jin yunwa, amma haka ya nufi nasa bedroom ɗin. Saman bed ɗinsa ya kwanta, tunaninta ne kawai a cikin kwakwalwarsa, tin da wannan abin ya faru a tsakaninsu bai sami barci mai natsuwa da daɗi ba, kullum a daddafe yake yi kamar dai yau ɗin dai, da kyar ma barcin ta yi awon gaba da shi. Ransa cike da tinaninta (Oh ni Princess Teema, kowa da kalar nasa cakwakiya da kaddarar a cikin RAWANIN ZALINCI, ita kuma Sweetie tana can tana fama da mai black heart ɗinta, shi ne kaddararta kuma ita ma ita ce kaddararsa, Auta da nata kaddarar, kai kowa ma da na shi bala'in da yake ciki, to ni kuma ina da Maltina mai sanyi, ba abin da ya fi rai'na, idan komai ya ɗauki zafi sai na kora kayana.) ••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥 Kai tsaye bedroom ɗinsu Smart ya nufa da ita, kwance ya isko Auta idanunta a rufe, ya yi zatan barci take yi, dan haka sai ya shinfiɗe Pretty a gefenta, ya zauna saman bedside drawer ya hau tofa masu addu'oi. Dik abin da yake yi Auta na jinsa, sai da ya kammala ya rufesu da bargo ya fito ne ta miƙe zaune, ta gagara yin barci saboda tinanin Hoorain ɗinta, ta gaza samunsa a waya. Uban ta gumi ya buga a tsakiyar bed ɗin tana tinanina mafitarsu ita da shi. Wayar ta ne ya fara kara alamar shigowar kira, jikinta har yana kerma wajen miƙa hannu a gaggauce ta ɗauko wayar. Wani irin zabura ta yi har ta miƙe tsayea tsakiyar bed ɗin ba tare da ta san ta yi hakan ba, dik kawai saboda murnar number Hoorain ne ya kirata. Jiki na tsuma hannu na kerma ta yi picking tare da kara wayar a kunnenta. Kasancewar bai san number ba saboda number waje ce ba ta ƙasarsu ba sai ya yi sallama haɗe da tambayar wanene?. Da ka ji yadda yake yin magana zaka fahimci yana cikin tsananin ciwo da rashin kwanciyar hankali...... Idanunta ne suka cicciko da kwallah, a raunace ta ce. "My Hero Hoonairar kace, ni ce". Ta yi maganar tana zube gwiwowinta a saman mattress ɗin. Shi kuwa yana jin haka yana daga kwance a gadan asibitin ya zabura ya miƙe zaune, tamkar zai ganta a gabansa ya ce. "Hoonaira, Hoonaira dama........dama......". Ƙasa yin maganar ya yi saboda sarkafewa da voice ɗinsa yake yi. Commander dake kwance a gefensa saman bed na masu jinyar majinyata ya fara yin barci ne ya tsinkayo muryan ɗan nasa cikin kuka kaman yana sambatu, hakan ya sa ya tashi zaune, dama wutan room ɗin a kunne. Ganinsa manne da waya a kunne ne yasa ya fahimci waya yake yi da Auta, dan ita kaɗai zai yi wa wannan rikicewar. Binsa da kallan tausayi commander ya yi yana jin zuciyarsa na kara raunata. •••••••••••••••••••••🔥 "Calm down my hero, na dawo gareka ai a yanzu, kuma ba zamu taɓa rabuwa ba, please ka kwantar mun da hankali ka ji?". Cewar Auta...... Allah sarki soyayya, jinjina mata kai ya yi tamkar yana a gabanta tamkar kuma wani ƙaramin yaro wanda ake san yi wa dabara da alawa, dik ya susuce kamar ba jarumin assistant commander namu ba...... Abbo dai kallan tausayi kawai yake binsa da shi. "Promise me that zaka dai'na damuwa ka ji?". Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata....... "Na yi alkawarin zan dai'na damuwa, ni ma ki mun alkawarin zaki dai'na kuka, kuma ki share hawayenki na yanzu da suke zubowa, kada ki bari su sake zuba kin ji my life?". Kai ta gyaɗa mashi alamar to ba tare da ta iya amsawa ba........ "Kece rayuwata Hoonaira ta, kece farincikina, ina san ganinki, na yi kewarki, please kizo in ganki kin ji?"....... Da kyar ta iya faɗin. "Bana nan my hero, ina wajen Yah Omerish, amma zan zo muga juna ka ji?". A dai'dai lokacin da suke yin wannan magana shi kuma King suna yin meeting shi da uncle Jahiz, uncle Abbas and Akka, suna ƙoƙarin tsayar da magana a kan aurenta da Abdussalam and dawowar Smart kingdom of power saboda ya zo ya riki mulkinsa, dama nasa ne, tashin hankali kenan, akwai cakwakiya. Sake jiki suka yi suka zubawa juna kalaman soyayya masu narka zuciya, tin Auta tana kuka har sai da ya sanyata dariya kai ɗan sauti, tini yasa ta mance da ta taɓa shiga kunci a rayuwarta, haka ta koma ta kwanta ta rungumo pillow, har da ce mashi. "My Hero da na rungumi pillown nan sai na ji kamar kai a ruguma, ka tuna mun forest". Shi ma komawa ya yi ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya, cike da kauna da kulawa ya ce. "Soon watarana zaki rungume ɗin ba pillow ba" ....... Hoorain fa bai lura da Abbonsa ya tashi ba, kawai ya hau zuba love word abinsa. Ai taɓe baki commander ya yi yana mamakin ɗan nasa, tinani yake yi wai yaushe Hoorain ya iya magana haka? Shi dai yasan ko magana ta minti guda ɗansa baya yi, mutum kamar kurma, amma ji yanzu yadda yake zuba wasu zafafan kalamai kamar ba shi ba, har tantama commander ya yi a kan anya jarumin zakin ɗan nasa ne kuwa?. Shi kuwa Hoorain lumshe idanu ma ya yi yana cigaba da bawa flower ɗinsa ruwa, daga karshe ma ya juyawa Abbo baya yana faɗin. "Kin tabbatar?". Tana daga kwance ta kara matse pillow a kirjinta kafin ta ce. "Tabbas da safe zamu yi video call, na tabbatar"....... Ajiyar zuciya ya sauke, wani bargo mai sanyi ne ya lulluɓe zuciyarsa, ya yi kewarta over. "I really love you my Hoonaira, i promised to be with you with happy or not, kece farincikina kuma kwarin gwiwata". Da kyar ya iya kai karshen maganar, saboda bai saba dogon magana ba. Yau dai Auta baki har kunne, sai murmushi take saki. Ba su suka rabu da juna ba sai karfe 3, nan ma shi ya ce ta kwanta ta yi barci kada ta makara tashi sallah, da safe zai kirata. Bata yi mashi musu ba ya amsa da to, cike da kwarewa a iya bawa flower ruwa ta sumbaci wayar tata tare da ce mashi ya sanya a ransa kumatunsa ta sumbata, ƙara lumshe idanunsa ya yi yana jin wani irin yanayi mai daɗi, sai ya ji dama da gaske ne mana kumatun nasa ta sumbata, ai da ba zai iya yin barci ba yau. Jin ya yi shiru bai yi magana bane yasa ta ce. "My Hero ni ba zaka bani na barcin bane?". A shagwaɓe sosai ta yi maganar. Sumbatar take nufin shi ma ya yi mata tamkar yadda ta yi mashi. Haba ji tamkar an yi mashi bushara da aljanna, juyowa ya yi tare da kai wayar ɗan bakinsa ya manna mata sumbatar kenan idanunsa suka sauka a kan Abbonsa da ya buka tagumi yana kallansa, commander ya bushe a zaune kamar wanda aka sankarar, a ransa yake faɗi ashe har da sumbata ɗansa ya iya bai da labari? Kai wannan abin mamaki ne a wajensa. Wani irin kunya ne ta lulluɓe Hoorain, ga shi ya rigada ya kai sumbatar, sai ya rasa ya zai yi kawai ya yi gaggawar cire wayar daga bakinsa tare da fara kame kame kaman maras gaskiya, yana jiyo sanyayyar muryarta tana faɗin. "My Hero wannan sumbata ta isa ya rikeni daga nan har zuwa safiya in kwana cikin farinciki haɗe da mafarkinka". ...... Amma ya ƙasa iya bata amsa, sai ma ya yi gaggawar katse kiran kawai yana kallan Abbo...... Ajiyar zuciya commander ya sauke, can ƙasa ƙasa ya furta. "Dole in yi maka aure my lion". Ya yi maganar ne ta yadda Hoorain ɗin bai ji me ya faɗa ba. A hankali ya koma ya kwanta tare da juyawa Hoorain ɗin baya irin alamar bai ji komai ba. Ajiyar zuciya Hoorain ya sauke, kunya ta gama rufesa, tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki ya juya ya bawa Abbon nasa baya yana lumshe idanunsa. A maimakon ya yi barci sai ya hau tinanin Hoonairansa yana nishaɗi. Ita kuwa yana katse kiran ta kara rungume pillow tana sakin murmushi har barci ya yi awon gaba da ita. 🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥 After one day. A hankali ta fara motsa idanunta tana san farkawa, Ronnie dake kusa da ita ne ya yi gaggawar matsawa ya riko hannunta, cikin sanyin murya ta fara ambatar sunanta a natse, shi tun daren jiya ya farfaɗo bawan Allah, ita kuwa da yake ta fisa tausayi sai yau ta farfaɗo, dan zuciyarta ya raunata sosai. Waro idanunta da suka kumbura luhu luhu suka yi jajir waje ta yi, saman celling ta kafe da kallo kamar wadda bata a dai'dai, kamar taga bakon abu, sai ambatar sunanta Ronnie yake yi amma ina kamar bata a wajen, sai da ya sa hannu ya shari kumatunta ne ta juyo da kallonta a kansa. Suna haɗa idanu ta zabura ta miƙe zaune, cikin fitar hayyaci ta fara sambatu kamar haka. "Lovely bro yanzu big bro ya kashe mutanen nan dikka har da yaran da basu ji ba basu gani ba? Ko kuma ya hakura ya kyalesu?". A ruɗe take maganar tana jan numfashi da karfi karfi tamkar zata sume. Ya lura bata a daidai, dan haka sai ya ce mata. "A'a ba dikka ya kashesu ba, ya yi wa wasu afuwa". Tabbas karya ya yi mata, kuma wannan shi ne karyarsa ta farko a duniya, shi baya karya wlh, amma saboda kwanciyar hankalinta ya yi. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke, a fili ta furta. "Alhamdulillah, ko ba komai mun yi nasara tun da muka iya sanya shi ya yafewa dubban al'umma"...... Ronnie dai jinta kawai yake yi, a cikin zuciyarsa yana cewa, lallai yarinya baki san waye big bro ba, bai taɓa yafiya ba a rayuwarsa, idan ya zartar da hukunci to fa dik abin da zai faru sai dai ya faru amma babu mai canza wannan hukunci, a haka suke rayuwa tun daga kan mulkin mahaifinsa har shi ɗin, babu wanda aka taɓa yi wa afuwa daga hukuncin da ya yanke a wannan birni, harta iyayen Floris Black Tiger ya kashe, an konasu a cikin wannan wuta, bai ragawa kowa ba, master Devil kawai ya bari a cikin maciya amanar nasa, shi ma akwai dalilin da yasa ya barshi, nasa hukuncin ta musamman ya tanada mashi. Zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin ta yi, jikinta na rawa saboda murna ta ce. "Lovely bro bari in je in ga big bro, dole na yi mashi godiya bisa wannan abin da ya yi, ya yi namijin ƙoƙari wajen yi masu afuwa". Ta kai karshen maganar tare da yunkurawa zata miƙe. A nan ne ta fahimci akwai drip a manne a hannunta, saboda zafin da ta ji, ta lankwatsa hannun ne ta dafa jikin mattress zata miƙe, shiyasa ya yi mata zafi. Shi kuwa tana wannan magana ya yi gaggawar kai hannu zai dakatar da ita saboda bai san a wani irin hali Black Tiger yake a yanzu ba, kada ta je yana kan tsini ya yi mata illah, dan ba imani ne da shi ba kuma ba gane kansa ake yi ba. "Ronnie yaushe aka saka mun wannan abin kuma?". Ta faɗa tana kallan drip da ya kusa karewa, ɗan kaɗan ya rage. Sake hannun nata ya yi kafin ya amsa mata da tin wuraren la'asar, yanzu kuma mangariba ta kawo kai. Zaro idanu ta yi tana tambayarsa wai yau yaushe ne ma? Nan ya sanar da ita ai kwana ɗaya ta wuce, tun jiya take sume ai. Kara zaro idanu waje ta yi, jikinta har kerma ya fara yi, a natse ta furta Hasbunallahu wani'imal wakil. Rarrashinta Ronnie ya shiga yi yana bata baki har ta hakura ta koma ta kwanta zuwa san da drip ɗin ya kare, sannan ya cire mata, a gaggauce ta sauko ta nufi toilet dan yi wanka ta ɗauro alwala ta hau biyan bashin sallolin dake kanta, shi kuma Ronnie ya fita ya nufi bedroom na Black Tiger dan ya yi sallah a can, baya sallah a ɗakinsa saboda kada Black Tiger ya gano ya musulunta. After some hours da basu wuci biyu ba, shirye take tsab cikin sleeping dress masu shegen kyau, riga ce mai ƙaramar hannu da dogo wando launin ash mai ɗan duhu, hakan yasa ta yi balai'n kyau saboda hasken fatarta, ta gyara golden hair ɗinta sai sheki yake yi, sai tashin kamshi take zubawa, ta yi sallar isha'i saura cin abinci, tana tsaye a gaban mirror tana kallan kanta tana kuma tinanin su Pretty, kewarsu ce a ranta yau sosai, har ta ji hawaye sun cika mata idanu, ta matsu ta ga Kamran ɗinta ido da ido, har mafarkinsa take yi, yana ranta a kowani dakika na rayuwarta. Ta nausa cikin tinaninta sai ji ta yi ya ɗan rungumeta ta baya yana faɗin. "Lovely sis tinanin me ake yi har na shigo baki ji ni ba?". Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗago kallanta, ta cikin mirror suka kalli juna, cool murmushi suka sakarwa juna kafin ta amsa mashi da. "My twins sis and my Kamran nike tinawa, yau da kewarsu nike tare"....... Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa mata da. "Soon zaki je ki gansu, yanzu dai bari in dubi Floris ina dawo, tun jiya da safe da na ganta ban sake ganinta ba"........ Allah sarki, bai san tun jiya ɗin ta mutu ba, tana kunshe cikin toilet master na gidan yari. "Okey nima zan je duba big bro, amma ni fa ina ganin kamar Floris fushi take yi da kai". Tana magana tana kallansa ta cikin mirror. Jinjina kansa ya yi kafin ya amsa da. "Tabbas haka ne, nima na lura da tana fushi dani, shiyasa zan je bata hakuri, kin san yadda nike kaunar Floris kuwa my sister?"...... Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata sani ba..... "Ina kaunarta fiye da kai'na, komai nata birgeni yake yi, amma ta ci saurin yin fushi, kuma ita tana kaunata over, before ki zo ita take bani abinci a baki fa, na yi missing na wannan moment ɗin, bari in je in bata hakuri daren yau ta ciyar da ni abinci a baki". Faɗaɗa murmushin dake saman face ɗinta ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Gaskiya kam ka je ka lallaɓa mana ita ta zo mu ci abincin dare a tare, nima ina missing ɗinta sosai". ...... Jinjina kansa ya yi tare da manna mata sumbata a gefen kumatunta, kara faɗaɗa murmushin ta yi tana kai hannu ta ɗan shafi gefen nasa kumatun. Saketa ya yi tare da fara tafiya baya baya yana kallanta, ganin irin tafiyar da yake yi ta cikin mirror yasa ta juyo dan ta gansa da kyau. Tana jiyowa suka haɗa ido, kashe mata ido ɗaya ya yi yana cigaba da sakin cool murmushi har ya kai jikin kofa. Kamar dai kullum, sumbata ta manna a hannunta ta hura mashi, ajiyar zuciya ya sauke haɗe da juyawa ya cire password na kofar ya fita. Tana ta murmushi bata zare kallanta daga kansa ba har sai da ya kurewa ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke tare da raba jikinta da jikin mirror, cikin natsuwa ta taka ta nufo waje ita ma. Kai tsaye master room na Black Tiger ta nufa, tana tafiya tana tinanin a wani irin yanayi zata same shi?. Tana zuwa ta buɗe kofan without any scare and any excuse ta afaka cikin ɗakin. Tsaye yake a tsakiyar ɗakin ɗaure da towel a waist ɗinsa, da alama daga wanka ya fito, dan ga dark black curly hairnsa nan yana ɗigar da ruwa, hannunsa rike da wani ɗan ƙaramin towel yana goge kyakkyawan gashin kan nasa. Da yake ta kudurta a ranta kome zai faru babu gudu babu ja da baya sai ta daure bata juya ta gudu ba, kada ku manta ta taɓa ganinsa a yanayin da ya fi haka, a farkon ganinta da shi da ɗan ƙaramin short ta gansa, gara yau towel ɗin tana da ɗan tsawo ta kai mashi har zuwa gwiwa. Tun daga kan tafukan kafafunsa ta fara kallansa har izuwa sama, ita kanta ta shaida he's so sexy, handsome and cute, yanayin jikinsa sai yasa ka fola..... Tana sauke kallanta a kan face ɗinsa sai taga shi ma ita yake kallo, dan fa ba karya ta yi kyau cikin shigarta. Suna haɗa idanu ya yi gaggawar kawar da nasa kallan yana ɗaure fuska, ta fahimci sam sam baya san ta kama shi yana kallanta, dan haka sai ta yanke shawarar zata rinƙa dannewa ba zata bari ya san ta san yana kallanta ba. Kai Black Tiger da Sweetie duniya, wato babu maganin Black Tiger sai Sweetie, a gana mata azaba amma kuma yana jin daɗin kallanta, musamman idan tana tare da Ronnie tana sakin cute smile ɗin nan nata mai narkar da zuciya. Cikin dauriya da natsuwa ta tako ta nufo in da yake, bai yi kamar yasan tana zuwa ba, ya cigaba da yin abin da yake yi. A dab gabansa ta tsaya, hannu ta kai ta karɓi ƙaramin towel dake hannunsa, zuciyarta na harbawa da sauri sauri, ta yi ƙasa da murya cikin siga mai jan hankali da salo ta ce. "Dama ni nasan kai adali ne, kai ɗin mai tausayi ne, kai ɗin jarumi ne, kai ɗin mutum ne da dik in da ake neman cikakken namiji ka kai nan har ma ka wuce, ba zan taɓa mantawa da alkhairinka na yafewa mutanen birnin nan ba, tabbaa yadda kake da balai'n kyau zuciyarka ma haka take". Ta ɗan dakata da yin maganar tare da kai kallanta a kan face ɗinsa, sannan ta fara goge mashi Lion chest ɗinsa da towel ɗin. Mutuwar tsaye ya yi yana tinanin shi kuma a yaushe ya yi wa mutanen birnin nan afuwa da har take yi mashi irin wannan yabo? Sai dai kuma yabonta a garesa ta ratsa zuciyarsa, ya ji daɗin hakan sosai, sai ya ji dama ta cigaba da yi kada ta dakata...... Batu na gaskiya yabo tana karya zuciyar koma wani irin mutum ne, ki gwada ware rana guda ki yi yabo da zafafan kalamai ga wanda yake kusa dake kiga yadda zai shiga cikin farinciki a wannan lokaci, gaskiya ne abin da hankali bai bayar ba rashinsa ba zai bayar ba, abin da kwamciyar hankali bai bayar ba rashinsa ba zai bayar ba. Haƙiƙa Sweetie ta fahimci yabon da ta yi mashi ya yi tasiri a cikin zuciyarsa, dan har da sauke ajiyar zuciya ya yi, kuma ta ji hakan, dan haka ta shiga farinciki ita ma. "Kana da kyau sosai our big bro, haka zalika zuciyarka ma mai kyau ce tsarkakekkiya". Yadda take magana cikin salo mai ɗaukar hankali yasa bai san lokacin da ya amsa mata da. "Amma kuma jiya kin ce zuciyata bata da kyau ai?"....... Kam bala'i ashe kalamanta na jiya sun shiga kunnuwansa, magana da ta yi mashi a tsawatance yasa ya ji ba zai iya ragawa kowa ba, da ace jiya ta yi mashi magana yadda ta yi mashi yau da tabbas za'a samu rangwame, sai dai kash, ta fusata ita ma, tabbas magana cikin natsuwa yana iya canza komai. "Jiya ai ɓacin rai ne yasa na yi maka magana a haka, amma tabbas kai mutum ne mai farar zuciya". Ta kai karshen maganar tare da ɗaura mashi ɗan towel ɗin nasa a saman shoulder ɗinsa, sannan ta juya da nufin ta matsa daga gabansa, ta koma saman sofa ta zauna ta jirasa yasa kaya ya fito ta kara yi mashi godiya, bata san karya Ronnie ya sharara mata ba. Tana juyawa ɗan ruwa ruwan da ya zuba a wajen daga gashin kansa yasa ta zame, baya baya ta yi ta faɗa jikinsa, buga kanta da kirjinsa ta yi a in da ta tsuke fuska kamar zata yi kuka. Tana ƙoƙarin yin ƙasa daga jikin nasa yasa hannu ɗaya ya tallabota tare da juyota garesa, face ɗinta ya zubawa idanu yana kallan yadda ta datse nata idanun tana jiran ta ji ta isa ƙasa. Yau yabon da ta yi mashi ne ya sanyaya mashi rai har yasa ya ceceta bai bari ta kai ƙasa ba, dama ransa tun jiya a ɓace na juya mashi baya da mutanensa suka yi. Kurawa juna ido suka yi gabaɗaya kamar sun mance a wani duniya suke, sun shagala da kallan juna gangar jikinta ya gaza iya jurar tsawuyar da ta yi ɗin, dan kusan a iska take, bayan wuyarta ya tallabota da hannunsa. Kerma kafafunta suka fara yi a in da ta yi ƙoƙarin zubawa ƙasa, cikin zafa ya fisgota mai gabaɗaya ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa, yasa hannunsa ɗaya ya tallabi tsakiyar bayanta. Like wow, abin da bata taɓa expecting zai yi mata ba, wai ya taimaketa, bata taɓa zata ba, sai ga shi ya yi hakaɗin sanadiyyar daɗaɗan lafuzanta a kansa, abin fa ya yi mashi daɗi ne sosai, sai dai shi ba'a gane farincikinsa ko bakincinsa shiyasa bata wani gane sosai ba. Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman lion chest ɗin nasa ta gefe, dan dikkanta bata gama cike rabin faɗin kirjinsa ba, ƴar karama a gabansa. So sai ta ɗaura hannunta a gefen chest ɗin nata, a hankali ta ɗago da kanta dan ta kalli face ɗinsa, ya kura mata idanu yana yi mata kallan kurillah. Habawa sarkafewa idanunsu ya yi cikin na juna kamar ɗazun. Sun ɗan jima a haka kafin ya yi gaggawar kawar da kallansa a kanta tare da saketa, kamar wani mara gaskiya ya juya da sauri ya nufi clothes set ɗinsa. Bin bayansa da kallo ta yi har ya shige cikin wajen, ajiyar zuciya ta sauke, cikin natsuwa ta taka ta isa gaban sofars ɗinsa, saman ɗaya ta zauna, tsabar laushi har lumewa da ita ya yi, tagumi ta ɗan yi tare da afkawa duniyar tinani, faɗi take yi a ranta ta fara yin nasara, ji take yi sun kusa canza zuciyarsa, amma ita dik a tinaninta yafewa mutanen birnin da Ronnie ya ce mata ya yi ne take ganin sun fara nasara ba. Uhm akwai sauran aiki a gabanki Sweetie, dan wannan mai black heart ɗin kam bai ji komai a ransa ba. Zaman good 10 mins ta yi a wajen kafin ya fito shirye cikin sleeping dress ɗinsa, yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallan irin kyan da ya yi cikin wannan kaya, dai'dai lokacin kuma aka turo kofar ɗakin aka shigo..... A hanzarce ta kai kallanta wajen kofar nasa dan ganin wanene?. Wasu.................. Dama a karshen littafin nan na yi maku alkawarin baku wasu addu'oi na mallakar zuciya ko? Da na yi niyya sai a kashen littafin, amma duba da ramadan ya gabato, a cikin Ramadan ma buƙata zata fi saurin biya yasa nace bari na baku the most important ɗin, ku yi shi a cikin watar Ramadan, ki yi shi da kyakkyawar niyya, ina uwa da ɗanta yake zinace zinace, yake yawace yawacen banza bin abokan banza da shaye shaye? Ina mata masu shan wahalar namiji? To dik dai ku matso, ku yi shi da tsarkakakken niyya sosai Da farko dai zaki yi. Astaghfirullaha Rabbi min kulli zambin wa atubu ilayh kafa ɗari dai'dai, sannan ki yi salati ga annabi kafa goma. Amma fa sai kin yi alwala, zaki iya farawa karfe sha biyu na dare, za kuma ki iya farawa karfe 2 na dare, idan kin yi alwala kika yi sallah raka'a biyu, sai ki zauna, ki gabatar da abin da na faɗa a farko, sannan ki yi salati, ga salatin ma a rubuce ga waɗan da basu iya ba. Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin, kama sallayta ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima innaka Hamidum Majid. Bayan kin yi wannan sai ki gyara zama sosai a kan dadduma, ki ɗaga hannayenki sama ki fara addu'ar kamar haka. Allahumma aslih zawji ( sai ki ambaci sunansa, wato suna da kike yiwa ɗin kenan) waj’alhu min as salihin, waj’alhubniyyatahu nafi’atan lid duniya wa akhirati. Da kyakkyawar niya fa, ki sanya a ranki tamkar Allah ya gama biya maki buƙata, ki ji cewa bayan Allah babu wanda zai yi maki. Sai Rabbana hablana min azwajina wa dhurriyyatina qurrata aƴunin waj’alna lil-muttaqina imama. Wannan addu'a tana da mahimmanci kowace uwa ta kasance tana yi, yana cikin Suratul Furqan. Sai Allahumma inni as’aluka an tahdi zawji ila sabilika al-mustaqim, wa an tub’idahu ‘an ma yughzibuka, wa an taj’alahu min ahlil taqwa wal istiqama. Wannan addu'oi masu tsadar gaske ne, idan kika yi sho da tawali'u zaki sha mamaki, zaki gode mun kamar babu gobe. Sai Allahumma inni a’udhu bika min jahdi al bala’ wa su’il qadha’ wa shamatati al a’da’, wa min kulli sharrin dhahirihi wa batinihi. Wannan addu'a tana matuƙar kariya daga dik wata sharri na abin halitta, wannan ba dan miji ko wani zaki yi ba, kanki zaki yi wa dan Allah ya kareki, amma zaki iya yiwa kowa yaki dan ya shiga kariya, wlh wlh wlh addu'a ce mai karfin gaske. Tsarin yin wannan addu'oi dama kwanaki 40 zaki ɗauka kina yinsu cikin dare bayan kin yi sallah raka'a biyu, kinga ga Ramadan ya zo, zali samu saukin tashi ki yisu, sai ma buƙatunki sun fi biya, shiyasa na baku a yanzu dan ku yi da ramadan, saura sai mun haɗu a karshen littafin, saura wata budurwa ta je ta yi wa sarauyinta ta zo ba aurensa zata yi ba, wlh babu ruwana, ya Allah dik wanda ba da kyakkyawar niya zata yi wannan addu'oi ba Allah kada ka amsa mata, dan ba da ni za'a cutar da wata ko wani ba!!. Yauwa ina da wata ƴar rokan alfarma a gareku my people's, kunga dai azumi ya zo, Please a taimaka a sakani a addu'a, wlh addu'a in dai ta alkhairi ce a gareni kowacce iriya ce ina so, please my people's, ina kannena da suke gida, ƴan yaran nan da basu wuce 10 ya yi ƙasa ba, please a sanyasu su yi wa princess taku ta amana addu'a, kun san addu'ar yara da karɓuwa yake, to a taimaka a mun wannan alfarma, dik wadda ta je ta hajju ta jefani cikin addu'arta, ina godiya Allah ya bar kauna 💘 🔥 💘 🤍 much love my people's, sai mun haɗe gobe. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 48 Zaman good 10 mins ta yi a wajen kafin ya fito shirye cikin sleeping dress ɗinsa, yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallan irin kyan da ya yi cikin wannan kaya, dai'dai lokacin kuma aka turo kofar ɗakin aka shigo..... A hanzarce ta kai kallanta wajen kofar nasa dan ganin wanene?. Wasu kyawawan robbot ne gungu guda da a kallah zasu kai su 8, gabaɗayansu kowanne ɗauke yake da katan tray mai shake da kayan abinci kala kala, ga wasu irin abin rufe abinci wato food cover masu shegen kyau da tsada launin golden suna ɗaukar idanu aka rufe abincin da su, kai tin daga kan masu ɗauko abincin zaka fahimci robbot ne na musamman da zasu kaiwa mutum na musamman abinci, harta tafiyar da suke yi cikin tsari suke yinsa, a tare suke ɗaga kafafu su sauke. Ai zuba masu idanu Sweetie ta yi tana kallan yadda suke taku gwanin birgewa, kai tsaye suka nufi can wani ɓangare na ɗakin, kun san ɗakin da shegen girma yake, wajen da yake cin abincin zaka yi zatan ba'a ɗakin yake ba saboda girmansa. Sweetie bata kara tsurewa ba har sai da suka yaye white curtains dake wajen, ai wani irin zaro idanu ta yi tana kallan tsaruwar dining room ɗin, kun san a baya Black Tiger baya fita, hakan yasa yake da haɗaɗɗen dining room a cikin bedroom ɗinsa bayan na parlournsa. Sweetie ta sha madarar mamakin ganin set na table ɗin dake ciki, haɗaɗɗun chairs har guda 24 ne a wajen, ko shi da waye yake zaman cin abinci yawan chairs har haka? Ta jefawa kanta tambaya, my people's dining room ɗin nan ya haɗu, ga wasu decorations masu ɗaukar hankali, manya manyan flowers da kayan more rayuwa, sai dai kuma kusan dik da ɗanyan gold aka yi su, yo Black Tiger da WC ɗinsa ma na gold ne me ba zaku gani na gold ba?..... Shi dai wannan sarki wlh sai shirin Allah. Glass wall ne wajen, haka zalika glass door ne, tura kofar suka yi suka shiga ciki, shi kansa table ɗin abin kallo ne, ya tsaru matiƙa, samansa suka hau shirya mashi abinci kamar yadda suka saba. Suna kammala shirya komai suka kunna ligh launika daban daban dake wajen bayan sun kashe white light ɗin, take wajen ya ɗauki wani irin launi mai ɗaukar hankali, sai ma da suka kunna kenduran dake saman table ɗin, ya ilahi ya lilliahi, haɗuwa iya haɗuwa. Sweetie kam dai sumar zaune ta yi, sai taga tamkar ba a duniya wannan dining room ɗin yake ba. Fitowa suka yi su 7 sun bar ɗaya a ciki, suka nufi waje ba tare da sun yi komai ƙanƙantar magana ba, da kallo Sweetie ta bisu tana mamakinsu, ita dai yau taga abin da ya goge mata hadda, tambayar kanta ma take yi ashe Black Tiger yana cin abinci? Abin like wow, ya ƙayatar. Shi kuwa gaban mirror ya wuce, wasu document ya ɗauka yasa hannu, takardu ne na katafaren ginin da za'ayi mashi a cikin empeir ɗin, tamkar fadar sarki ne shi ma, tsarin ginin ya fi wanda yake ciki komai da komai, sai dai ya ce da zallar gold za'ayi mashi ginin, dan yana san zarce kowani sarki a mulkinsa. Ni kam na ce mu da mun san tarihin sarkin romawa da su habashawa, a zamanin da manyan sarakunan da suka yi gidan ɗan yar gold a tarihi ma ai suna dayawa, amma yau ina suke? Sun koma ga Allah, to a zamanin nan ma mun samu King Black Tiger, ginin ɗan ƴar gold za'a zuba mashi, my people's yake kuke ayyana wannan gini a ranku? Ɗanyar gold fa? Tab Black Tiger zai tashi hankalin duniya, ai dole ne ma kowani sarki zai so kwace birnin daga hannunsa, ko dan tarin arzikin da Allah ya basu, aww ace fadarsa da komai na gold, dole hankalin duniya ya tashi, ga katafaren filin saukar jirginsa a saman ginin gabaɗaya, ginin dai ya tsaru matuƙa, a zamanin yanzu banda sarakuna da suka shuɗe kafin zuwan manzan Allah (SAW) a zamanin yanzu shi ne mutum na farko da zai yi irin wannan gini, abin dai ba'a cewa komai. (Ni kuma na ce ya kuke tunani idan ya kammala wannan gini Sweetie ta zama Queen a ciki? Ronnie ya zama Prince? Su dake a fada su ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya suna zartar da hukunci irin na addinin musulunci, ya kuke ganin haɗuwar wannan sabon empire ɗin nasa zata kasance da waɗan nan taurari guda biyun a cikinta?.🤔) Sai dai har yanzu bai sakawa sabuwar empire ɗin suna ba, ya ce dai su fara kaddamar da ginin sai an kammala zai faɗi sunanta a rubuta a farkon shiga.... Amma kuna tunanin wani irin suna zai bawa empeir ɗin nan?. Yana kammala sa hannu a kan document ɗin, sai ya sanya hannu a kan wata takardar da ya umarci a biya dik mutanen birnin asarar dukiyar da aka yi masu a sanadin wannan yaki, waɗan da basu bijire mashi ba kuma suka rasa nasu a biyasu diyya na makuɗan kuɗaɗe masu zafi, sannan ya cike wasu takardu na sabbin ma'aikatan da yake san buɗewa na sarrafa abinci da abin sha wanda kowani ma'aikata ɗaya zai iya ɗaukar ma'aikata sama da 500, kunga ya ragewa mata zaman banza, kuma fa shi a ƙaidarsa maza basa aiki sai dai su tafi bakin daga, mata ke yi mashi aiki a dikka ma'aikatunsa domin su samu abin dogaro da kai tun da basu da maza da zasu wani ɗauki nauyinsu........ Yaseen Black Tiger shegen kwaro ne, wai yanzu kun yarda da batun Sweetie da ta ce tana da yakinin akwai abin da ya canza zuciyarsa daga fara zuwa baka? Kun yarda wani lokaci mutumin kirki ne shi, wani lokaci kuma bakin shaiɗani, sai ka rasa gane ina ne takamaiman alkiblarsa wlh, wani lokaci dai ga shi mutum, wani lokaci kuma kai bashi da kyan gani fagen mugunta. Sai da ya kammala abin da yake yi tsab sannan ya nufi dining room ɗin nasa, da alama ya mance da ita a cikin bedroom ɗin. Wani robbot na tsaye a wajen yana jiran ya kariso ya yi serving ɗinsa. Sai da ta bari ya shiga room ɗin ta miƙe ta bi bayansa tana kara jinjinawa girman arzikin da Allah ya bawa birnin nan. Ba tare da neman izininsa ba ta shiga cikin room ɗin, wannan robbot na ƙoƙarin zuba mashi abinci ta yi gaggawar dakatar da shi tare da cewa. "Zan yi serving ɗinsa kada ka damu". To kun san abubuwan nasa idan ya rigada ya basu umarni kawai zasu aikata abin da ya ce ne, dan haka wannan robbot ya riga ya karɓi umarnin yin serving ɗinsa, sai ya hanata ya cigaba da yin aikinsa, ba ta isa jayayya da Robbot ba, dan idan ta yi ma ita ce zata sha wahala shi babu ruwansa, dan haka sai ta ja chair dake kusa da shi ta zauna tana kallan face ɗinsa, ya ɗaure fuskar nan tamau yana tinanin gina katafaren football stadium saboda Ronnie, kun san yana sha'awar wasannin. Kammala zuba mashi abin da ya buƙata wannan robbot ɗin ya yi tare da matsar mashi da plate ɗin gabansa. Chopping stick ya ɗauko guda biyu, zubawa abincin idanu Sweetie ta yi tana mamakin wannan wani irin abinci ne? Bata taɓa gani ba, a hankali ta fara bin sauran cimar da kallo, dik launikan abinci ne da bata san ma da me ake yinsu ba, ga wasu dai kamar nikakkun nama da kwai, wasu kuma kamar damammen shinkafa da yoghurt, abubuwa dai kala kala, baki ta taɓe tana jin ko kasheta za'ayi ba zata iya cin abincin Black Tiger ba, gara ma nasu Ronnie wanda ta sani ne. Abin da bata sani ba anan shi ne, ta sha cin irin wannan abinci a hannun Kamran, kun san a lokacin bata gani shiyasa bata san irin abincin da yake bata tana ci ba, wlh babu wani banbanci tsakanin cimar mammar Kamran da na Black Tiger, dik irin ɗaya ne, sai dai nata local ne na talakawa, nasa kuma na manyan kai, amma dik iri ɗaya ne, amma har da cewa sun yi mata wani irin ba zata iya ci ba, bayan su ta ci ta girma har ta ƙosa ta yi kumatun da in ta yi murmushi suke birge big bro, eh manaaaaaaaaaaaa.😅 Ɗibar abincin ya yi da chopping stick, abincin wani ball ball haka ash colar, yana ƙoƙarin kaiwa ɗan bakisna cool voice ɗinta ya daki dodan kunnnesa in da take cewa. "Ka yi bismillah kafin ka ci". Ta yi maganar tana kallansa. Tamkar bai jita ba, kamar bai san da halittarta a wajen ba ya cigaba da ƙoƙarin sanya abincin a bakinsa. Cike da tsoro a gaggauce ta kai hannu ta rike hannunsa, kirjinta na bugawa da karfi ta ce. "Please say Bismillah before you eat.........". Bata gama rufe baki ba robbot dake tsaye ya yi gaggawar kai hannu ya damki wuyarta ta baya tare da capke hannunta da ta rike hannun Black Tiger, dan dolenta ta saki hannun big bro, da hannu ɗaya wannan robbot ya ɗagata daga saman chair ɗin, kai tsaye ya yi wurgi da ita izuwa saman wani kyakkyawan sofa two seater dake wajen wanda an ajiye shi ne dan ɗan hutawa idan ka kammala cin abinci, dama ana san idan ka ci abinci ka ɗan miƙe kafafunka ka huta ko da na 30 mins ne, a nan ne abincin zai shiga cikinka da kyau. Bata san ba'a kusantar Black Tiger ba idan ma'aikatansa suna nan kusa, yanzu mutum zai bakunci lahira, ita ta samu har ta zauna a kusa da shi shi ne zata kama hannunsa, a tinanin robbot ɗin riko hannunsa da ta yi ta hana shi cin abinci cutar da shi zata yi shiyasa ya yi mata abin da ya yi mata. Kai tsaye ya nufi kanta domin ya zartar da hukuncin da suke yiwa dik wanda ya kusanci Black Tiger. Wuyarta ya rike tare da sanya ɗayan hannunsa zai ɓalle mata makogoron wuya shikenan ya kasheta, yana ƙoƙarin yin hakan Black Tiger ya dakatar da shi tare da ce mashi ya barta ya koma bakin aikinsa, daga haka ya cigaba da cin abincinsa babu wani bismilla da ya yi. Ita kuwa ta sha shakar robbot sai da ta ji kamshin mutuwa, ta zaro ido tana numfashi sama sama. Shi kuwa Black Tiger a cewarsa ya sa a barta ne saboda ba zai iya ɗaukar haukar da Ronnie zai yi mashi ba, kun san yasan Floris ta mutu ai? To ace Sweetie ma ta mutu, ai wlh Ronnie zai yi mashi hauka mai zigidir mai lasisi, yanzu ma bai san taya zai iya shawo kansa ba idan ya gane Floris ta mutu, saboda har ga Allah Ronnie yana kaunar Floris fiye da tinaninku, akwai soyayyarta ma a kasar zuciyarsa wanda bai san da ita ba, kun ga kuwa babu zaman lafiya idan ya gano meke faruwa, ina ga wlh irin hukuncin da zai yi wa master kare ba zai shinshina ba. Tana ƙoƙarin miƙewa zaune domin ta samu damar shaƙar numfashi da kyau sai ga Ronnie ya shigo wajen, ko excuse babu, hankalinsa a tashe ya ce. "Big bro please ka tayani neman Floris, dik in da nike zatan zan ganta a cikin empeir ɗin nan babu ita, na tambayi Angela ta ce mun tun shekaran jiya bata kara ganinta ba". Cikin ruɗu yake maganar, har word ɗinsa suna harhaɗewa. Miƙewa tsaye Sweetie ta yi, take ta ji faɗuwar gaba, a kiɗime ta ce. "Ina ta shiga to? Karfa ace wani abin ya sameta a wajen yakin da aka yi....... ". Cikin zafa Ronnie ya katseta da cewa. "No lovely sis, babu abin da ya sameta, nasan dai fushi take yi da ni shiyasa kila take san bani wahala ta ɓuya, kila ma ta gudu wajen parents ɗinta ne"..... Shi kansa faɗuwar gaban nan yake ji, amma yana ƙoƙarin dole dole sai ya karyata zuciyarsa a kan wani abin ya sameta. Shiru Sweetie ta ɗan yi kamar mai tinanin wani abin, can kuma sai ta ce. "Muje wajen parents ɗin nata mana mu dubata". .... A gaggauce ya amsa da. "Good idea, lest go". Ya faɗa tare da juyawa da sauri. Cikin kakkausar murya Black Tiger ya dakatar da shi ta hanyar ce mashi kada ya kuskura ya fita bedroom ɗin nan nasa a wannan daren. Turus Ronnie ya tsaya, lokaci guda zuciyarsa ta tilasta mashi dole ya yarda wani abin ya sameta, dan Black Tiger bai taɓa hana shi yin komai ba idan ya sa a gaba, tun da kuwa ya hanasa zuwa nemanta dole akwai abin da ya saɓa, to me kenan? Tashin hankali da fargabarsa ɗaya kada ace mashi ta ji mummunar rauni ko wani abin makamancin haka, shi kwata kwata ma bai kaita ga batun mutuwa ba tukun nan. tashin hankali. Bai ma san har iyayen nata dik babu su ba. Kallan yayan nasa ya yi, faɗuwar gabansa tsananta ya yi sosai, saboda yasan yayansa na ganin komai dake faruwa a birnin, tabbas yaga abin da ya samu Floris, amma yasan ko ya tambayesa ba zai sanar da shi ba. Dan dolensa ya dawo cikin room ɗin, saman chair ya zauna tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, murya a raunace ya ce. "To big bro da safe zan iya zuwa nemanta?"...... Jinjina mashi kai Black Tiger ya yi alamar e, sannan ya cigaba da cin abincinsa. Umartar robbot ɗin shi ma Ronnien ya yi da ya yi serving ɗinsa. Cikin gaggawa kuwa ya yi, hankalinsa ya ɗan kwanta tun da yayan nasa ya ce da safe ya je nemanta. "Sweetie ki zo ki ci abinci". Ya faɗa yana ɗaukar chopping stick, cikin natsuwa ya yi bismillah can cikin zuciyarsa kafin ya fara cin abinci. Kai ta girgiza mashi alamar ita ba zata ci ba, sannan ta miƙe ta dawo saman chair ɗin zuciyarta cike da tinanin ina Floris take? Tabbas akwai abin da ya saɓa haka take ji a ranta. Zama ta yi suka sanya Black Tiger a tsakiyansu, shi da Ronnie suna cin abinci ita kuma ta buga uban tagumi tana binsu da kallo. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Washegari da misalin karfe 9, shirye cikin ƙananan kaya masu kyau ya fito daga cikin bedroom ɗinsa, wata irin trouser ce mai kama da army one, sai shirt milk color ya sanya daga ta sama, yau har da black glass and p-cap milk color ya sanya a kansa, sannan ya sanya ankle boots masu shegen kyau da tsada suma milk color, ya yi kyau matiƙa. Hannunsa rike da wayarsa. Kai tsaye bedroom ɗinta ya nufa, yana tafiya cikin natsuwa da kamala. Bakinsa a ɗauke da siririyar sallama ya tura kofar bedroom ɗin ya shiga ba tare da ya jira izininta ba. A wani irin miliyan ta juyo da kallanta a kan kofar, tana ɗaure da towel a kirji ta fito daga wanka, gabaɗaya jikinta ruwa. A maimakon ya juya ya bata waje, sai ya ɗan shagala da kallanta irin kallan kasan ido ɗin nan, ita kuwa tana ganin shi ne da gudu ta bar wajen ta shiga dressing room na ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke yana mai ɗago kansa sama kaɗan, kamar wanda yake magana da wani ya ɗan jinjina kansa kafin ya ƙarisa shigewa cikin ɗakin. A saman side bed ya zauna yana bin ɗakin da kallo, a ransa ya hayyana yaushe ta tashi daga barci har ta yi wannan gyara, ta ko'ina kamshi ne yake tashi, yarinya mai tsabta kamar dai shi. Can a cikin tinanin nasa surar jikinta ya ratso mashi ta cikin kwakwalwarsa, ajiyar zuciya ya sauke kamar wanda ya gamsu da abu, sannan ya ciro wayarsa domin ta ɗebe mashi kewa kafin ta fito, dan baya san yawan tunane tunanen nan da yake yi, ƙwaƙwalwarsa tana da abin ɗauka mai mahimmancin da ya fi wasu tinane tinanen. Almost 10 mins yana zaune a haka kafin ta fito sanye cikin ɗaya daga cikin abayas da ya saya mata, ta yi matuƙar kyau kasancewar abayar milk color ita kuma chocolate color, ta fita sosai, yadda ta yi rolling veil ɗin sai ya baka sha'awa, ga wani kyakkyawan fashion flat shoe a kafafunta, launin kayan jikinta, sai tashin kamshi take yi sosai. Wucesa ta zo ta yi ba tare da ta yi mashi magana ba ta nufi waje, sai satar kallansa ta witsiyar ido take yi. Cikin sanyin murya ya ce. "Aesh come here, wajenki na zo"........... Kamar ba zata tsaya ba, sai ta tina dik in da ta je a cikin gidan ma yana iya biyota, so is better for her to stay with him hare. Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo garesa ba, ta yi ƙasa da kanta dan ita kunyar haɗa idanu da shi ma take yi. Miƙewa tsaye ya yi, cikin kamala ya kariso in da take tsaye. "Wani waje nike san mu je". Ya faɗa idanunsa a kan face ɗinta. Bata da bakin tsayawa yi mashi gardama ko ja in ja da shi, dan haka sai ta jinjina mashi kai kawa ba tare da yin magana ba. "Zamu iya tafiya?". Ya tambaya yana mai da kallansa kan yatsun hannunta da ta haɗesu waje guda. Jinjina mashi kai ta yi alamar e zasu iya tafiya. Nuni ya yi mata da hannu a kan ta wuce su je. Ba musu ta yi gaba ya rufa mata baya cike da tausayi da kulawa. Kai tsaye harabar gidan zuka nufa, mai gardi guda ɗaya ne a wannan gidan, dan haka ya umarcesa da ya buɗe masu gate bari su je unguwa, dik tinanin mai gadin Leesharh matarsa ce, ya yi aure kenan, amma abin da ya bashi mamaki shi ne ya aka yi ogan nasu ya yi aure maganar bata fita ba? Sam bai ji zancen a hukumansu ba. Wani zuciya ce ta amsa mashi da ai auren sirri ya yi tun da ga shi ya ce ko su Bilal sun zo gateman ɗin ya ce masu babu kowa a gidan, dik yadda aka yi auren sirri aka yi, saboda bai taɓa sanyawa ransa Ramish zai kawo mace haka nan ya ajiye a gidansa ba, ya kullaceta ba tare da suna da aure ba, saboda kowa dai yasan Ramish ɗan wani family ne, ba zai yi wannan shashancin ba. Sosai gateman ɗin nan yake ƙara shan mamaki a dik lokacin da ya kalli Leesharh, saboda yadda take chocolate color, abin yana bashi mamaki yadda aka yi Ramish ya aminta ya aureta, sai dai kuma sun yi matuƙar dacewa da juna sosai. Gate ya wangale masu, cikin natsuwa ya umarceta da ta shiga gaban motarsa, babu musu ta shiga ta zauna kanta a ƙasa bata san meyake yi mata ciwo ba ita da kanta. Cikin motar ya shigo shi ma, a natse ya tada ita ya danna waje. Suna fita can ƙasa ƙasa cikin natsuwa ta ce. "Meyasa kake san fita kai kaɗai ba tare da tsaro ba bayan kasan aikin da ya kawoni gidanku a kanka? Kasan masu farautar rayuwar kusan sun fi masu kaunarka yawa". Tana damuwa sosai a dik lokacin da ya fita shi kaɗai, sai taga kamar ba zai dawo ba, kamar za'a kashe shi a hanya, dan tasan haɗarin masu nikaf. Yana driving a natse ya ce. "Kin damu da ni ne?"....... Shiru ta yi bata amsa mashi ba, bata ma da niyar amsa mashi ɗin. "Aesh meyasa kike shiga damuwa a kan rayuwata?". Ya sake jefa mata tambaya. Dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali kafin ta amsa mashi da. "Babu komai, kawai dai dan nasan ana farautanka ne, and masu nemanka ɗin da alama sun fi yawa a kewaye da kai"......... "Ba gaskiya bane Aesh, dole kina da dalilin damuwa da rayuwata, meyasa zaki ɓoye mun?".......... Ya yi maganar dai'dai zai fita daga ainahin main gate na arear tsadaddiyar unguwar tasu ya sake ce mata. "Allah kuma yana kewaye da mu gabaɗaya daga ni har masu farautar rayuwar tawa". Lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya, ai shikenan ya gama magana tin da ya ce Allah kuma babu wani sauran gyara ko ja in ja, dole a yi shiru. Securitys dake tsaran main gate ɗin nasu ne suka dakatar da motarsa, saboda basu san motar ba, sabuwa ce ba normal motocinsu da ya saba shiga unguwar da su ba, sannan basu ga face ɗinsa ba, sai suka dakatar da shi dan bincikarsa, sai da ya saukar da glass ɗin motar sannan suka gansa. Cikin girmamawa suka sara mashi haɗe da tambayar dama shi ne?. Kai ya jinjina masu tare da mayar da glass ɗin ya rufe, dama tinted ce, ya ja motarsa kawai suka cigaba da tafiya yana dannawa securitys ɗin horn alamar gaisuwa kenan. Sai satar kallan juna ta kasan idanu suke yi dikkansu biyu, gabaɗayansu suna yunwar san kallan juna, saboda su kansu sun san sun yi kyau matuƙa, suna san bawa idanunsu abinci amma kamar suna tsoron haɗa idanu da juna. "Aesh yaushe zaki bani haɗin kai wajen bincikena? Ki bani cikakken bayani dan kama mutanen can". Ya jefa mata tambayar tare da dawo da kallansa a kanta........ "Anytime". Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. "Are you sure and are you serious?"........ Kai ta jinjina mashi alamar e ta tabbatar. Sosai ya ji daɗin amsarta, dan yana san cigaba da abin da yake yi, yana burin kama masu nikaf, and yana san tambayarta wasu tambayoyi a kan abin da ya faru a tsakaninsu a wancan ranar, amma yana shakkar tambayarta saboda har yanzu bata yarda ba da gangan ya yi mata ba, da ta aminta da shi ne he has a lot of question for her, amma babu dama, dan haka sai ya shanye wannan tambayoyi a ransa zuwa time da zai samu dama. Shiru motar ta kasance na ɗan wani lokaci, yana tuki yana tunanin abin da yakamata ya fara yi. Da yake yana sharara gudu sai cikin ƙanƙani lokaci suka isa wani haɗaɗɗen wajen cin abinci na masoya mai bala'in tsari, tsada da kuma haɗuwa, gabaɗaya yankin wajen ice ne kewaye. Ya lura in dai a gida ne Leesharh ba zata taɓa cin abinci ba, amma in suka fito waje ko dan idanun jama'a ba zata kunyata shi ba, komai ya ce ta yi a waje yana da yakinin zata yi dan kada ta bashi kunya, shiyasa dik da baya cin abincin waje yau ya daure zai jarraba saboda ita ta ci ta ƙoshi. A katafaren parking space ɗinsu ya tsaida motar tasa, cike da kulawa ya ce. "Muje ko?". Ai ta shagala da kallan kyau da tsaruwar wajen, kai Dubai ba dai kyau ba wlh, ga komai nasu cikin tsari, bata taɓa kallan irin wannan gidan cin abincin ba ko a mafarki, ba abin da ya fi ɗaukar hankali ma irin abubuwa sky blue da suka yi amfani da shi a wajen, ga golden da ya ji light mai haske, gaskiya ne wannan gidan cin abincin ya ci sunansa paradise ɗin kamar yadda yake a rubuce da manyan baki. Buɗe motar ya yi ya fito, ganin ya fita yasa ta yi gaggawar bin bayansa, dakatawa ya yi yana jiranta, tana ƙarisowa in da yake yasa hannu ya riƙo hannunta, ai a miliyan ta ɗago da kallanta a kansa, sai taga sam ba ita yake kallo ba, da gangan kuma yaki kallan nata, dan baya san ta hana shi yin abin da ya fito da shi, ya fito da ita ne domin ya samu ta rage damuwar da yake a ranta, yau dai ɗaya ta yi farinciki sosai. Cikin natsuwa ya fara takawa ya nufi cikin wajen, ga mamakinta sai gani ta yi ƴan'mata da samari masu class da ji da kansu sun tsaya sai ɗaukarsa hoto a wayoyinsu suke yi, saboda kyan da Allah ya yi mashi, kun san su kyawawa dik in da suka shiga ko sun shirya ko basu shirya ba sai mutane sun yi ta ɗaukarsu hoto, wai a hakan ma ya sanya p-cap a kansa fa, basu wani ga face ɗinsa da kyau ba, amma haka suka rinƙa kashe mashi hotuna ta ko'ina babu kakkautawa. A nan ne wasu suka ɗauketa ita da shi a tare, and a media suka ɗaura hotunan, shi ko a jikinsa, in da yasa kai kawai yake tafiya cikin natsuwa, ita kuma ta damu sosai, dan tana tsoron abin da zai iya faruwa, tana tsoron masu nikaf su gani saboda suna bibiyarsa ta kowacce hanya. My people's me kuke tinanin waɗan nan hotuna zasu haifar?. Sosai ta waro idanu tana kallan yadda cikin wajen ya yi bala'in haɗuwa, sofas masu bala'in kyau, laushi da kuma tsada, waje ne na manyan kai. Zama suka yi saman sofar da ya zaɓa masu, sannan ya saka oder abin da yake ganin zasu iya ci, online oder ake yi, sannan sai ka biya ta online ɗin ka yi komai za'a kawo maka, sp kana ci zaka tashi ka tafi babu wani tsayawa yin payment, haka tsarinsu yake. Yana oder bai fi da mintuna uku ba sai ga shi an fara shirga masu abin da ya buƙata a gabansu saman table, dik a takure take saboda kallansu da jama'a suke yi, dik ta in da ta juya idanun jama'a a kansu, ga uban hotuna da ake kashe masu light ta ko'ina. Zuba mata idanu na ƴan sakanni ya yi kafin ya ce. "Ɗauki chopping stick or spoon mu ci abinci". Ɗago kai ta yi ta kallesa da nufin ta yi mashi gardama, amma sai ta gagara yin hakan saboda idanun jama'a dake a kansu, kuma ya yi mata wani irin kwarjini, yau idanunsa a kaifafe suke sosai, dan dole ta ɗauki spoon dan da shi ta saba, shi kuwa sai ya ciro wayarsa ya fara latse latse dan baya jin kamar zai iya cin wannan abinci, bai saba da waje ba. Tana jin yunwa over to over, dan haka sai ta fara cin abincin a natse, sai dai kaɗan kaɗan take ci. Dik abin da take yi attention ɗinsa yana a kanta, bcoz ta ci ta koshi ya zo da ita tun da taki ci a gida. Ya lura ɓata masu lokaci zata yi, dan sai su wuni a wannan waje bata gama cin wannan ɗan abinci ba, ɗan kaɗan kaɗan take ɗebowa kamar bakinta na ciwo, sai ya ajiye wayarsa a saman table ɗin ya kai hannu ya karɓi spoon ɗin nata, cikin natsuwa ya ɗebo abincin mai ɗan yawa ya kai mata saitin bakinta. Ɗago kai ta yi ta kallesa, while shi ma ita yake kallah ta cikin glass ɗin nasa, bata san disga shi a cikin mutane sai ta buɗe baki ya fara bata dai'dai san ransa, har lokacin hotuna ake ɗaukarsu. Yana tsaka da bata abincin ne gabaɗaya yankin gidan cin abincin nan ya karaɗe da jiniya ta ko'ina, tamkar za'a tashi garin. Yana zaune bai motsa ba, ita kuwa hankalinta ya tashi sosai, dan idan ba a gidan Abu Abdussalam ba bata taɓa jin jiniya irin haka ba, a gidan Abbie kawai tasan idan za'a fita ko za'a shiga wannan jiniya yake tashi, to waye ne kuma ya zo a yanzu?. Bata kammala tambayar kanta ba sai ganin wasu jiga jigan jami'ai sun danno cikin restaurant ɗin a guje ta yi, ba dan tana tare da shi kuma taga bai motsa ba da ba abin da zai hanata tashi ta gudu. Gabaɗaya big girls and big boys dake wajen babu wanda hankalinsa bai tashi ba, babu wanda bai ji tamkar ya tashi ta gudu ba, bare ma yanda jami'an nan suke muzurai tamkar zasu ɗauki rayuka nan take. Ko'ina tsit kake ji, jami'an gabaɗaya sun yi tsayuwa jarumta sun kewaye wajen gabaɗaya, shi dai Ramish tamkar bai san da zuwansu ba, yana cigaba da bata abinci a baki, ya lura ta tsorata sosai, dan haka sai ya yi ƙoƙarin ɗauke mata hankali daga kansu ta hanyar tambayarta a ina ta haɗu da masu nikaf har suka bata contacts na kashe shi?. Tana ƙoƙarin bashi amsa wani very handsome jami'i ya danno kai ciki, he was so cute, handsome and gorgeous, sai dai shi chocolate color ne ba balarabe bane, and zubin Nigerians ke garesa, cikakken namiji ne mai rai da lafiya, kyakkyawa ajin farko, very hot guy, yana da tsawo dai'dai misali, Ramish ya fisa tsawo da kaɗan. Sanye yake cikin kakinsa, wasu zaratan jami'ai guda huɗu suna take mashi baya, kai tsaye in da su Ramish suke ya nufo. Yana isa wajen waɗan nan jami'an da suka rakosa suka yi gaggawar kewaye kowani angle na table ɗin da su Ramish ke kai, shi kuwa guy ɗin haɗe kafafunsa ya yi cike da jarumta ya ɗaga hannu ya sarawa Ramish. Ajiye spoon na hannunsa Ramish ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye, hannu ya bashi suka yi musaba cike da kulawa yana faɗin. "Saukar yaushe my guy?". Sai a lokacin Leesharh ta ɗago kai cike da tsoro dan taga wanenne?. Ai bata san lokacin da ta zabura ta zaro idanunta tana kallansa ba, kamannin dake kan face ɗinsu har ya ɓaci, sun yi kama sosai tamkar ƴan uwa na jini, sai dai kowa da yadda yake kallan mutum, shi ma Ramish yaga kamanninta da friend ɗin nasa, sai dai ba can sosai ba, shi kuma friend ɗin nasa bai ma bi ta kanta ba bare har yaga ko suna kama or akasin hakan. Izini Ramish ya bashi a kan ya zauna mana, kun san sofas na table ɗin irin two seater ɗin nan, ɗaya ta side ɗin nan ɗaya ta side ɗin can, table yana tsakiya, so shi da Leesharh suna saman sofa guda, abokin nasa sai ya zauna a ɗayan shi kaɗai. ...... Cike da mamaki guy ɗin ya ce. "My Man yaushe ka fara cin abinci a restaurans kuma?". Cewar jami'in kenan ba. Zama Ramish ya koma ya yi kafin ya amsa mashi da. "Ba ni zanci ba, ga wadda na kawo ta ci nan". Ya kai karshen maganar yana nuna Leesharh da hannunsa. Sai a lokacin guy ɗin ya lura da ita a wajen, cike da mamaki ya yi mata kallo ɗaya kafin ya mayar da kallansa a kan Ramish, sannan ya ce. "My man wacece wannan ɗin? And I was so surprised ganinka tare da mace, the thing looks some how to me, i never expect that for now, amma dai nasan gaba kila in yi expecting ganinka da mace, but now kai I was so surprised". Ya kai karshen maganar yana sake dawo da kallansa a kan Leesharh, dan shi kansa yaga kamannin dake tsakanin fuskokinsu. Ita kam ba iya kamanni kawai ba, gabanta ne yake faɗuwa idan ta gansa, ji take yi kamar ta san shi? Sai dai a ina? Ita da bata san kowa ba bayan iyayenta da suka tsinceta sai mutanen gidan AAJ, gidan aikinta ita da mamarta yanzu kuma ƴan gidan Abu Abdussalam, su kawai ta sani. Kai tsaye Ramish ya amsa mashi da. "She's my wife to be In Sha Allah"...... Dum!!! Dum!!! Zaro idanu guy ɗin ya yi yana kallan Ramish, sai kuma ya ɗan saki murmushi kaɗan kafin ya ce. "Amma baka taɓa yi mun wasa ba, meyasa yau kake san yi mun? Ka manta ka ce kai babu abin da zaka yi da mace a rayuwarka ne?". ....... Harara Ramish ya bisa da shi kafin ya ɗan saci kallan Leesharh ta wutsiyar ido, take ya ga face ɗinta ya sauya saboda ta ji ya ce babu abin da zai yi da mace a rayuwarsa, wato kenan dama abin banza suka ɗauki mata kenan?. Shi kuma wannan guy ɗin bin Ramish da kallo yake yi yana jiran amsa, bai san da cewa Ramish neman amincewanta ma yake yi taki ba, yanzu ba batu ake yi na me zai yi da mace ba tukun nan, batu ake yi na yana neman hanyar da Leesharh zata aminta da shi. Spoon ya ɗauka tare da fara ɗebo abincin yana kai mata ɗan bakinta ba tare da ya sake bi ta kan abokin nasa ba, dan ya lura idan ya biye mashi zai cigaba da faɗar maganganunsa da ya rinƙa faɗa a baya wanda kuma zai sa Leesharh ta ƙara arzuƙa ta ki yafe mashi, zata ce dama a banza ya ɗauki mata shiyasa ya yi mata abin da ya yi mata kenan, dan haka gara ya fiske kawai. Abokin nasa ya lura da baya san maganganun da suka wuce, dan haka sai ya yi mashi fatan alkhairi tare da juyowa ga Leesharh ya hau tsokanarta da sunan amaryarsu. Ƙasa da kai ta yi tana jin gabanta na faɗuwa, har ga Allah tana jin kamar jini na fusgarta idan ta ga face na guy ɗin. Lokaci guda Ramish ya ji kishi sosai a kan maganan da guy yake yi mata tana amsawa, ransa ta sosu, sai ya ce ta tashi su tafi cin abincin ya isa haka, kun san mutanen da kishin bala'i, ya ce wa guy ɗin kuma ya wuce gida zasu haɗu zuwa dare........... TO WANENEN WANNAN GUY ƊIN KUMA?. Yana kai karshen maganarsa ya miƙe tsaye tare da riko hannunta, kamar zata kwace kanta sai kuma ta daure ganin jami'ai a wajen, ta san kuma shi ba ƙaramin jami'i bane, kada ta ja mashi raini, dan haka sai ta hakura ta biye mashi har suka fice daga wajen, haƙiƙa ya jinjinawa halaccin da ta yi mashi, ta daure ko sau ɗaya bata kunyata shi a idanun mutane ba, abin ya yi mashi daɗi sosai!. Suna fita cikin wajen ta kwace hannunta, bai ce mata ko uppan ba ya shiga gaban mota, kafin ma guy ɗin ya fito sun bar gidan cin abincin da gudu gaske. A maimakon ya zame da ita gida, sai ya wuce da ita wajen shakatawa da wasanni dik dan ya samu ta sauko ta yafe mashi, ranar yau gabaɗaya ya sadaukar mata, ya sanya a ransa ba zai mayar da ita gida ba sai can tsakiyar dare, watakila zata ji sanyi a ranta. Amma fa yasa a ransa tana yafe mashi zai mayar da ita gidan Abbie ya cigaba da aikinsa. To bari mu je Paris mu dawo mu bisu wajen shakatawar mu ga me zai faru a can kuma, amma kuma tinanin Leesharh zata yafe mashi kuwa? Zai kama masu nikaf? Wani irin hukunci zai yi wa Ummie a lokacin da zai gane ita ta cutar da rayuwarsu?. 🔥🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥🔥 Washegari da safe babu yadda Auta bata yi da Pretty a kan ta zo su sauka kasa ba, amma taki, ta ce wlh babu ita babu batun sauka kasa akwai damisa a wajen. Dan dole Auta ta rabu da ita a saman ta sauka, wunin ranar dai a ɗaki Pretty ta wuni har dare, ko abinci a ɗaki Auta ta kawo mata. Sai can dare bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ne Auta ta shiga toilet dan ta yi wanka, a lokacin ita kuma Pretty ta yi wankarta, ta shirya cikin wani sleeping dress mai shegen kyau, launin purple color, ta yi kyau matiƙa. Yunwar dare take ji yana addabawa cikinta, ga Auta tana cikin toilet, tinai ta fara yi a kan mafitarta, dai'dai da second ɗaya ba zata iya jurar yunwa ba. Saukowa kasan bed ɗinsu ta yi, cike da tsoro ta nufo parlourn sama. Sai wani lallaɓawa take yi kamar wata ɓarauniya, wai dik dan kada damisan nan ya ji sautin takunta, a hankali ta turo kofar bedroom ɗinsu, kanta ta sako waje ta leƙo dan ta duba. Watam parlourn babu kowa, ƙarisa buɗe kofar ta yi ta kara fito da jikinta waje da kyau ta leƙa. Da gaske dai babu kowa babu komai, ai a miliyan ta yanka da gudu sai ɗakin Smart. Babu ko excuse ta afka mashi cikin ɗaki. Yana tsaye a tsakiyar bedroom ɗin rike da wayarsa, sanye yake da haɗaɗɗen bathrobe launin up white a jikinsa, kamar sako yake typing a cikin wayar. Da gudu ta tafi ta faɗa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, kun san ta saba yi wa Kamran haka, so bata wani damu da waye shi ba. Har sai da ta buge mashi waya ya faɗi ƙasa, dan bai yi tsammanin wani zai shigo ba, sao gata ta shigo har da faɗawa jikinsa. Cak ya tsaya, slowly ya dawo da kallansa a kanta. Kun san halinta da shegen shagwaɓa, tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Omerish yunwa nike ji, kuma ina tsoron wannan damisan naka, ka je ka kawo mun abin da zanci dan Auta tana toilet"....... Ai rasa abin faɗe Smart ya yi, wai shi ne zai je ya kawo mata abin da zata ci, kai sai kace a mafarki, tab lallai wannan yarinya ta zo da sububa a lamuranta, tana da buƙatar gyara. Ya luluƙa duniyar tinanin me zai yi mata sai ji ya yi ya fashe mashi da kuka, kun san halin mutuniyar, yo ita ina ruwanta da yana da izza? Ai shi ya jiyo shi da sarautar tasu, ita dai abinci ta sani sai shagwaɓa, dan haka yunwa take ji dole a bata abinci in ba haka ba ta yi ta kuka daga nan har wayewan gari. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 49 🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥 Wani irin ratsa mashi zuciya kukanta ya yi, amma sai ya yi ƙoƙarin dannewa haɗe da ƙoƙarin daka mata tsawa, sai dai kash, ya gagara iya rabata da jikinsa, dan ta ƙanƙame shi gam tana kukan ita dai lallai ya samo mata abin da zata ci tin da shi ya ajiye Tiger and Lion a gidan. Dan dole ta tilasta mashi ya sassauta muryarsa tare da sanya hannu ya ɗan rungumeta kaɗan, already ya iya rarrashi tun da yana rarrashin Auta, sai dai Autar kawai yake yi wa ban da kowa, gara ma guyson idan yana ciwo yana bi ta kansa. Matsawa ya yi da ita ya zauna a saman side bed, sannan ya rabata da jikinsa ya zaunar da ita a gefen, in a low voice sosai ya ce. "Wait for me here bari in je in kawo maki abincin". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye. A miliyan ta riko hannunsa cikin nata, tana kuka sosai, cikin shessheƙa ta ce. "Ni dai sai dai mu tafi a tare, ba zan iya zama ba, dan ina tsoron waɗan nan Tiger ɗin naka". Wai my people's bakwa tinanin meyasa Pretty bata maganar su Sweetie? Ko sau ɗaya bata yi maganarsu ba, tamkar babu su a babin rayuwarta fa, kada ku manta kuma ita da Sweetie suna bala'in san junansu over to over fa, basu da magana da ya wuci na juna!. Dan dole ba yadda ya iya ya riko hannunta a kan ta miƙe su tafi, sai dai kuma ina, make kafaɗa ta yi alamar ba hakan take so ba, da kallon mamaki ya bita yana jiran jin karin bayani. "Ni dai sai dai ka goyeni". Ta faɗa tana kara fashe mashi da kuka. Shin kun tuna cewa dik in da zasu je goyonta Kamran yake yi saboda shegen tsoronta? Ko kun manta?. To ita babu ruwanta da banbancin dake tsakanin Kamran and Smart, ita dai a goyeta, dik su suka sani, waye ya lura jinin sarauta ya fi karfi a jikin Pretty ba Sweetie ba? Sweetie tana da saukin hali, ita kuwa Pretty sai shirin Allah, idan ta yi magana ba canzawa, ga shegen shariya da izza, wai a haka ma fa bata san kanta ba, idan ta waye ta girma me kuke tinanin zai faru? Tab ina ga su Jaish sai sun sarara mata a izza da isa. Dik yadda aka yi babansu Sweetie hegen kwaro ne.... 😅 Shiru Smart ya yi yama rasa abin faɗe, wai ya goyata, to shi ko da yake kaunar Auta sau biyu ya taɓa goyonta a bayansa. Ga idanun yaran da shegen kaifi, komai zafin da ka ɗebo da ka haɗa idanu da su sai ka ji sun yi maka wani irin gwarjini ka kasa amayar da abin da ka ɗebo masu, shiyasa Sweetie take sha a hannun Black Tiger take cin galaba a kansa, da zarar sun haɗa ido sai ya nemi dik wata zafansa ya rasa, abin har yana bashi mamaki, shi ma dai Smart mamaki abin ya fara bashi, sai dai ko kaɗan bai kawowa ransa cewa suna da wata baiwa bace, kawai yana ganin kamar dan yarinya ce, and kuma ta taimaki Auta, shiyasa yake raga mata. Kuka ta sa mashi tare da zama a ƙasa zata fara birgima, yadda dai take yi wa Kamran. Ai bashi da zaɓin da ya wuce dole ya goyata, dan kuwa ya ƙasa ɗaukar zafi a kanta, sai dai har zai goyata kuma sai ya fasa, zama ya yi a side bed ɗinsa tare da ɗauko laptop ɗinsa, umarni ya bawa mai aikin nasa a kan ya kawowa wannan kararar yarinyar abin da zata ci ya huta da jarabarta. Yana gama aikawa ya juya zai cigaba da aikinsa, sai kuma ya gagara iya shareta ya barta zaune a kasan, abu kamar ba lafiya ba, dik zafinsa dai ya gagara ɗauka a kanta, kuma ya gagara iya shareta. To menene dalili kenan?. "Zo ki zauna a saman bed bari a kawo maki abincin". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kanta. Gabaɗaya sai ya ji tsikar jikinsa tana tashi, sai ya ji wani irin yanayi ya sauka a jikinsa. Gata kamar wata ƴar tsana a gabansa, haka ta miƙe tana turo baki ta koma kusa da shi ta zauna. Cigaba da aikinsa ya yi yana jin wani irin a zuciyarsa, ya kuma kasa gane me yake ji. Yana tsaka da aiki yana tinane tinane sai ji ya yi ta kwanto saman damatsan hannunsa ta gefen wide chest ɗinsa. Sai da kirjinsa ta amsa, amma ya daure ya cigaba da aikinsa, kun san mutuniyar da shegen san jiki dama, ta kwanta a jikin nasa ma bai yi mata ba sai da ta sa hannunta a jikin nasa tana yawo da shi tana tattaɓa mashi jiki, kamar wadda ta tafi duniyar tinani, sai shafe mashi jiki take yi tana turo baki, yadda take yi wa Kamran, abin a jininta yake. Gabaɗaya sai jin tsikar jikinsa na kara mimmikewa yake yi, yana ƙoƙarin rasa natsuwarsa. Dannewa ya yi ya cigaba da aikinsa, kamar daga sama ya ji saukar hannunta a saman flat tummynsa tana murje ƴan yatsunta a wajen. Wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, Auta tana yawan yi mashi dik irin kwanciyar da ta ga dama a jikinsa, amma bai taɓa jin wani abin ba sai a kan wannan ƴar rigimar. Ita kuwa cigaba da shafe jikin nasa ta yi tana yawo da hannunta ta ko'ina. Smart dai ya daure iya daurewarsa, amma abin tana neman ta ci tira. _____________ A wani irin miliyan ya kaiwa hannunta capka, dan ta yi ƙasa da shi tana ƙoƙarin taɓa mashi duniyar mercurynsa. Ai a miliyan ya capki ƴan hannayen nata. Yana capketa ta yi gaggawar ɗago da idanunta a kansa, while shi ma ya ɗan juyo da kallansa a kanta. Suna haɗa idanu ya ji gabaɗaya ya nemi abin faɗe ya rasa, yarinya kamar wata aljana, dik sai ya ji kamar an shafe mashi komai a brain ɗinsa, bai ma san lokacin da ya saki hannun nata ba, ya mace da kallonta bai ji time ɗin da ta ce mashi. "Meyasa ka rike mun hannuna ba"..... Kai kun ji mun iskanci wajen Pretty, ita bata ji me take yi mashi ba, tambayar dalilin rike mata hannu ma take yi!!. Malam Smart dai da alama ya afka duniyar mercury abinsa, dan sam baya jin abin da take faɗe, tana magana tana turo mashi baki, hakan ba karamin tafiya da shi yake kara yi ba. Shigowar mai aikin nasa ne ya katsesu, a hanzarce Smart ya kawar da kallonsa daga kanta tare da cigaba da aikinsa..... A saman table ya shirya masu abinci, a tinaninsa har da Smart ɗin zai ci abincin, sai ya kawo masu wadatacce. Ai tin mai aikin bai kammala gere abincin ba ta yi gaggawar barin jikin Smart ta nufi table ɗin, ba wasa da abinci. Da ido Smart ya bita da kallo yana mamakin me yake damunsa a kan yarinyar nan? Shi idan ya haɗa idanu da ita ma idanun nata suna sa ya ji faɗuwar gaba. Ita kuwa abincinta ta je ta fara ci ba tare da wata damuwa ba, kuma bata sake bi ta kansa ba abinta, ta barshi da tinanin wacece ita?. A lokacin ita kuwa Auta ta gama shirin barcinta, ta haye gado tana ta mamakin ina Pretty ta shiga ita da ta ce ba zata sake fita waje ba? Yanzu kuma me ya fitar da ita?. Wayarta ta jawo domin ta fara aikin da suka saba. Number my hero ta fara kira, sai dai wayar ta yi ringing har ta katse ba a ɗaga ba, hakan yasa ta sake kira, nan ma shiru, sai a karo na uku ne aka ɗaga. Ana picking ta sanya mashi kuka shagwaɓa haɗe da tuhumarsa meyasa bai ɗauki kiranta tun call na farko ba. On the other side commander ya amsa mata da. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe, barci jarumin naki yake yi"........ Subhanallah tamkar Auta zata natse a kasa saboda wani irin kunya, bata yi zatan commander bane ta hau zuba mashi sakalci da shagwaɓa. Kasa ta yi da kai tamkar tana a gabansa, har da sa hannu ta rufe idanunta kafin dai'dai ta natsuwarta sanna ta amsa mashi da. "Ina wuni Abbo"....... Ajiyar zuciya ya sauke idanunsa a kan ɗan nasa dake ta sharara barci ya amsa mata da. "Lafiya lou gimbiya, ya kike ya yayan naki?"..... Alhdulillah ta amsa mashi, cike da yarinta ta yi gaggawar katse kiran tana kwanciya, cikin pillow ta tura kanta tana murmushi ita kaɗai, kuruciya da daɗi, a maimakon ta tsaya su yi gaisuwa mai kyau a matsayinsa na sirikinta, sai ta katse kiran tana murmushi, yanzu Abbo ya zama wani abin kuma a wajenta. So take ta turawa Hoorain ɗin sakon dik time da ya tashi ya kirata, amma tana tsoron kada Abbo ya karanta zata ji kunya, sai kawai ta fasa turawa ta kwanta tana tinanin rayuwa. Wayar tata ce ta fara ringing alamar shigowar kira. A gaggauce ta duba number, dan a tinaninta jarumin nata ne ya tashi. Sai dai kash, new number ta gani. Kamar ba zata ɗaga ba, sai ta tina su Yah Omaid zasu iya kiranta, ga su Yah Jawad, Yah Rizwan dan haka she have to take a new number. Picking ta yi tare da kara wayar a kunnenta tana yin sallama cikin natsuwa. Other side cikin natsuwa ya amsa mata da. "My wife kin manta da ni ko?"...... Siririn murmushi ta saki kafin ta ce. "Yah Abdussalam ni na isa in mance da kai ne? Kana rai'na, kawai dai bana cikin natsuwa ne yasa ban kiraku ba"....... Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke wanda sai da ta jiyo shi. "To na ji daɗi tin da ba'a manta da ni ba, fatan wife ɗina tana nan lafiya?".... Da alhamdulillah ta amsa mashi tana jin wani irin fargaba yana ratsa mata zuciya, dan tana jin kamar call ɗinsa ba alkhairi bane a gareta, abokin wasan ta ne tin da ɗan kawunta ne sun saba wasa sosai, sai dai yau tana jin wani irin da take magana da shi. "Wife kin kusa tabbata da gaske a matsayin wife ɗin nawa". Ya faɗa cike da murnan hakan. Ita kuwa zaro idanu waje ta yi a hanzarce ta ce. "Yah Abdussalam me kake nufi?"....... Ya ɗan yi mamakin jin tambayar tata, sai dai kuma ya yi tinanin ko bata san shirin da ake yi bane, dan haka sai ya ce. "Daddy bai sanar dake cewa ya bani ke bane? Kinga ya tabbata da gaske zaki zama wife na, abin da na jima ina mafarki kenan, burina ya kusa cika!". Cike da fara'a sosai a saman face ɗinsa ya yi maganar, yana kwance a saman bed ɗin kakansa the most powerful King, wato mahaifinsu momma King Badeen kenan, ya tada kai da laps na kakan nasa ne yake wannan surutu, sai shafa arab hairnsa King Badeen yake yi yana siririn murmushi irin nasu na manya, da alama shi ma ya ji daɗin wannan haɗi da za'ayi, dan sai albarka yake ta zubawa abin.,........ Tab magana ya je wajen manya, akwai matsala kuwa, dan ni dai na duba banga hanyar ruguje wannan magana ba, dan King ba zai iya kallan idan sirirkinsa King Badeen ya ce ya fasa bawa Abdussalam na gida Zunaira ya ɗauka ya baiwa bare ba, akwai case kuwa, shin Smart zai yi nasara kuwa? Shirin su momma zai yi aiki kuwa? King zai yi azumin kaffarar nan kuwa? Rantsuwa dai ya riga da ya yi, uhm Allah sarki assistant commander Hoorain sorry, alkalamina bai yi maka adalci ba ko? Ba laifina bane, laifin King ne!!. Idanunta ne suma ciko da zafafan kwallah sosai, cikin natsuwa ta ce. "Daddy bai faɗa mun ba Yah Abdussalam". Da kyar ta iya ƙarisa kai karshen maganar....... "Ayya ina ga wani abin ne ya sha gabansa, amma da zai faɗa maki, kila shirye shiryen da suke yi ne ya ɗauke hankalinsa......". A gaggauce ta tari numfashinsa da cewa. "Shirye shiryen me suke yi kuma?". Ta yi tambayar cike da fargabar amsar da zai bata, kunnuwanta ba zasu iya ɗaukar cewa shirye shiryen bikinsu ake yi ba, sai dai kuwa kash, abin da take gudunwa bata tsira ba, dan kuwa da buɗan bakin Abdussalam cike da murna ya amsa mata da. "Shirye shiryen bikin mu mana, baki san nan da 3 days za'a ɗaura auren ba ko? Wlh na matsu wannan rana ta zo in mallakeki, sai naga lokaci ma ya dai'na gudu, baya sauri a yanzu..........". Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon wani irin ihu da ta zunduma tana faɗin. "No dad no, please don't do that to me!!". Da farko ta yi zatan zata iya jurewa har su kammala waya da Abdussalam ba tare da ta nuna mashi bata san shi ba tun da Smart ya ce mata ta kwantar da hankalinta in dai yana raye sai ta auri zaɓin ranta, to amma da ta ji saura 3 days aurensu sai ta karaya, tuni ta firgice ta fita hayyacinta, ta haukace. Wurgi da wayar ta yi ta diro kasan bed ɗin, sai hello Abdussalam yake faɗi, amma ina bai san ta wurgar da wayar ta yanka waje da gudu tana kuka ba. Bata zame ko'ina ba sai bedroom na Smart, a lokacin yana aikinsa ita kuma Pretty tana cin abinci. Babu ko sallama a haukace ta afka masu cikin ɗakin. Da gudu ta tafi ta faɗa saman jikinsa a kan bed ɗin tana sakin kuka mai sautin gaske. Cike da mamaki yake binta da kallo, dan shi ɗin mai natsuwa ne sosai, so komai nasa a natse yake yi, dan haka bai wani tashi hankalinsa ba, ya bita da kallo na ƴan mintunan da basu gaza biyu ba. Sai da ya ga kukan nata ba mai karau bane, sannan yasa hannu ya ɗagota tare da ture laptop ɗinsa gefe guda. Daidai lokacin ita ma Pretty ta taso da gudu ta nufo su, dan dik wannan shirmen nata tana jin kaunar Auta a ranta. Ɗagota ya yi tare da raba jikinsu, sai ya zamana suna fuskantar juna, cikin natsuwa ya ce. "Is okey my sweetheart, yi shiru na ji meyake faruwa kin ji ko?". Ina kai ƙasa yin shirun nan ta yi, tamkar ranta zai fita haka take kuka, da kyar voice ɗinta yake iya fita ta faɗa mashi abin da yake faruwa. Lallashinta ya hau yi tare da kara tina mata alkawarin da ya ɗauka mata, ba makawa in dai yana raye Hoorain zata aura ba kowa ba, dan haka ta kwantar da hankalinta, daga karshe ya rufe da cewa zai karɓi wayar hannunta, ba zai sake bari ta yi magana da kowa ba, dan kada su rinƙa kiranta suna faɗa mata wasu maganganu har su ɗaga mata hankali. So mugun wasa, cikin sauri ta tari numfashinsa da cewa. "Yah Omerish idan ka karɓi wayata da wani waya zan yi magana da Hoorain?"....... Ya fahimci sweetheart ɗin nan nasa ta yi nisa, ita dai Hoorain kawai, dan haka sai ya ce mata akwai wayarsa ai, dik time da take so ta zo ta ɗauki nasa ta kira Hoorain ɗin, amma bayan Hoorain bai yarda ta kira kowa ba........ "Yah Omerish har da Yah Omar kada na kira?". Cike da fargabar kada ya hanata waya da guyson ta yi tambayar. Ai kuwa kai ya jinjina mata, harda Guyson ɗin kenan, abin ya sosa ranta sosai, dan guyson wani ɓangare na bugun numfashinta ne, amma ya zata yi to? Dole ta bi umarnin yayan nata idan tana san zaman lafiyarta. Miƙewa ya yi ya ɗauki wayarsa ya nufi waje, dan ya je ya yi waya da King, a nan ya barota ita da Pretty yana jin zuciyarsa babu daɗi, dan wlh ya tsani abin da zai ɓata ran Zunaira.............. Me kuke tinanin zai cewa King, kuna ganin wannan al'amari zata canza kuwa? Uhm muje zuwa. Kwanciya ta yi a saman bed ɗin nasa tare da tada kai da lap ɗin Pretty tana tinanin me rayuwa zai sake zuwan mata da shi, ita kuma Pretty ta hau shafa arab hairnta!!. Shin kun san meyasa gabaɗaya litattafaina stars ɗina mata basa taɓa haura 13 to 14 years suke aurensu? Kun san dalilina na yin hakan? Saboda a kullum burina shi ne na yi koyi da manzan Allah (SAW) kuma kuma na kwaɗaita maku yin koyi da shi. Manzan Allah ya ce ku aurar da ƴaƴanku mata tun suna ƙanana, su girma a ɗakin mazajensu, bature masu jajayen kunnuwa kuma ya ce maku aurar da yara ƙanana tauye masu hakkinsu ne, wai a barsu su girma su san ƴancin kansu, uhm Allah mai iko, akwai wanda ya kai manzan Allah sanin hakkin ɗan adam ne? Akwai wani malami da ya isa ya gwada mashi sani ne? Dik duniya da kuke gani da dik wani cigaba da ake samu wlh kwaikwayo ne daga abubuwan da Allah ya halitta turawa da masu kimiya suke yi, zan kuma tabbatar maku da haka, so dik duniya babu wanda ya kai manzan Allah ilimi, dan kuwa masu tinƙaho da ilimin ma wato masu jajayen kunnuwa daga iliminsa da ya koyar suke satar nasu fasahar. Sannan kuma halittun Allah suke kwaikwayo su bunƙasa shi, to shi kuma manzon Allah Allah da kansa ya koyar da shi, kenan karatun waya fi a nan? Dan haka shi ya fi sanin hakki mutum fiye da kowa, amma a haka ya ce ku aurar da yaranku tun suna ƙanana, su kuma masu jajayen kunnuwa sun hure maku kunne sun kwaɗaita maku ku bar yarinya ta yi karatu ta girma ta san ƴancin kai, Uhm aikuwa wanda bai ji bari ba ya ji oh oh, zaku ga sanin ƴancin kai idan ta zo tana gogayyar kafaɗa dake, kina ta bari tana faɗa maki tasan ƴancin kanta tasan me ya dace da ita, sai ma ta tuna ta fiki sanin abin da yakamata, ga shi nan ai kuma muna gani, yarinya ta nuna ta fi uwarta sanin abin da ya dace ta yi. Ba ace kada a bawa mata ilimi ba, dan ilimin mace ilimin al'umma ne, amma ta samu ilimin a ɗakin mijinta, idan anyi aure ma ai ana karatu. Babban illame garemu kin abin da manzan Allah ya faɗa, shiyasa ga shi nan zinace zinace dik ya ishi al'umma, lesbian da sauransu, ƴaƴa sun girma suna son aure kun ce sai sun yi karatu, da zarar yarinya ta fara period dik wasu kofofi na sha'awarta yake buɗewa, a wannan lokaci aure kawai take so, a nan ne idan baki yi hankali ruɗin samari haɗe da kawaye ya jefata ga halaka, ni dai ina mai baku shawara, a kullum ku kasance masu amfani da maganar MANZAN ALLAH, babu ruwanku da abin da duniya zata ce, kun gannin nan zancen duniya bata gabana, a ko'ina faɗar Allah da manzonsa nike ƙoƙarin bi. To ni dai fatana kullun na rinƙa kwaɗaita maku koyi da fiyayyen halitta, dikkan rubutuna ina yinsa besa koyarwar manzon Allah, kuma dik idan kuka natsu kuka duba darusa ne a gareku. Allah ya bamu ikon koyi da fiyayyen halitta. And lastly har ya gama rubuta littafi a rayuwata star ɗita ba zata taɓa haura 15 years ba In Sha Allah, na baku satar amsar yadda zakuna gane Stars mata na littafaina, ba zasu taɓa haura 15 years ba........😅 STORY🔥♥️ 🔥🔥KINGDOM OF JUSTICE🔥🔥 Wato RAWANIN ADALCI kenan, shi ne sunan masarautar nan na Queen Zarina, wasu suna kiranta da kingdom of justice, sai dai kuma sunane saɓanin aiki, dan kuwa babu koda kwayar zarra na adalci a cikin wannan masarauta, mulki suke yi mai cike da zalinci wato mulkin kama karya, babu adalci a tafiyarsu, babu tausayawa bare jin ƙai. To meyasa kenan sunan masarautar ta kasance na adalci?. Muje zuwa zaku ji tarihi a nan zaku fahimci daga ina aka samo matsala ta sauyawar abubuwa. Fadar Sarauniya wato Qeen Zarina, ita ce zuciyar masarautar zaluncin. Babban katafaren gini ne da ya kai girman wata gari gabaɗaya. Ga wata katanga dake ɗauke da gicciye-gicciyen bayi da aka kashe don tsoratar da mutane birnin su yi biyayya dan dolensu, in ba haka ba su bi sahun waɗan da aka gicciye suma. Ƙofofin fadar guda uku ne kuma gabaɗayansu suna da ƙaho na zinariya, dik wanda baa bashi izinin shiga ba ya keta ƙofar, fatar jikinsa za ta ƙone nan take, tsabar karfin tsafin Queen Zarina. Gidajen bayi a cikin kingdom ɗin suna a cikin duhu, babu haske, babu kwanciyar hankali, ana ɗaure su da sarƙoƙi, ana azabtar da su idan suka yi ba daidai ba. Ana azabtar da mutanen da suka yi laifi a wurin, wasu ana yanka su, wasu ana narkar da fatarsu da wani abin sihiri nata dan nuna barazana ga ƴan baya tare da tilasta masu dole su yi biyayya ko kuma suma su riski irin wannan tsastsauran hukuncin. Qeen Zarina tana da wani ɗakin sirri da ke ƙasa (underground) wanda ke cike da abubuwan al’ajabi, kamar wurin bautar da jini dan ƙarfafa mulkinta da sauransu. Suna da ƙasashe da yawa da suka mamaye, ana bautar da mutanen waɗancan ƙasashe a matsayin bayi. Dik wata ƙasa da ta ƙi biyayya, suna kisan jama'arta gabaɗaya ko kuma su tilasta wa yara da matan su zama bayin fadarta masu yi mata hidima. Queen Zarina ita ce uwar zalunci, tana amfani da doka mai tsauri dan riƙe ƙarfinta. Ba wanda zai iya yi mata ƙarya, domin tana da sihirai da sirri mafi ƙarfi da zata iya gano karya suke yi mata, dan haka dole yake tilastawa mutanenta faɗa mata gaskiya koda sun san kashesu zata yi. Tana da Jagororin mabiyan sihirinta. Wata macece mai suna bokanya Ruhgara, da ke kula da manyan bokaye da matsafa da ke fadar Queen Zarina. Su ke tabbatar da cewa dik wanda aka kama yana tunanin cin amana, sai a hallaka shi kafin ya yi wani abin. Ana kiran shugaban warriors ɗinsu da black scorpion, wato bakin kunama mai harbi ɗaya sai lahira. Warriors ɗinta ba mutane ne na yau da kullum kamar yadda kuka sani ba, a'a ita ta ƙunshi mayaƙa marasa tausayin da aka horar tun suna yara don su zama na musamman, gabaɗa warriors ɗin renon black scorpion ne. Mai tsaron dukiyarta. Wanda ke kula da taskar zinariya, azurfa, da kayan sihiri da aka kwace daga ƙasashe da suka mamaye, wani bakin mutum ne, mai hudun launin fata sosai, ga shi shirgege gwanin ban tsoro, mummunar gaske, fuska babu alamar annuri ko ɗigo, in ya yi maka duka ɗaya sai mutuwa, yana da faɗi sosai. Sannan warriors ɗinta mutane ne da suka haɗa da, mayaƙan Jini wato mutanen da aka yi wa wani sihiri mai karfin gaske, suna jin karfi da lafiya ta yadda suke ganin babu wani bala'i da zai iya shafan su, kuma idan aka sare su, jinsu na iya dawowa su cigaba da yaƙi, wato saboda da tsafi suke amfani ko an saresu suna iya tashi su koma normal yadda suke su cigaba da yaƙi, waɗan nan mayaƙa ne masu haɗari wanda har yanzu tana kan sihircesu ne, bata fara amfani da su ba, sune mayaƙanta na rukunin farko a ɓangaren haɗari. Wlh ba dan kingdom of power masarauta ce ta Allah sun riki addini ba da ba zasu taɓa sha a hannun wannan azzalumar mata ba! Makircinta ya zarce yadda kuke tinani!!. Akwai masu take masu baya, wato su kuma mutane ne da aka horar tun suna ƙanana dan su zama tamkar dawakai a fagen karfi dik dan su zama masu saurin kashe mutane babu imani babu tausayi. Maza da mata da ke ɓoye suna satar sirrin wasu ƙasashe domin tabbatar da babu wanda zai iya yin juyin mulki, shiyasa kuka ga har cikin kingdom of power suna da ƴan leken asirinsu waɗan da suke binciko masu menene ke wakana a manyan masarautu. Magana ta gaskiya babu wanda ya isa ya yi masu tawaye. Mutane basu da ƴanci. Dik wanda aka samu da yunkurin yin tawaye, daga shi har danginsa dikka sai an hallaka su. Basa son wata daula ta yi ƙarfi ko kwatansu. Dik wata ƙasa da take kokarin girma ko samun ƴanci, warriors na masarauta suna zuwa su mamayesu su kuma kwace komai. Yadda kuka san Queen Zarina renon BLACK TIGER ce, wlh zalincinsu kusan ɗaya, sai dai Black Tiger ya fita haɗari ne da karfin tsafi. Sannan tana sihirce mutane. Idan aka samu wani yana tunanin cin amana, mayakan sihiri suna iya hango hakan kafin ma mutum ya furta shi, sai ta sa a sihirce sa, a mayar da shi wani gunki ko kare ko dai wata ƙasƙantacciyar dabba a ajiye shi a kofar gate ɗin farko na shigowa masarautar dan ya zama ya kare a kaskance kuma ya zama izina ga masu tasowa. Wanna ba dalilin yasa ƴan birnin suke yi mata biyayyar dole!. Masarautar tana da zinariya fiye da kowacce ƙasa except birnin BLACK WORLD. Sannan a tsarin Queen Zarina babu wata ƙasa da za ta iya yin ciniki ko kasuwanci ba tare da izinin ta ba, muna magana a kan kasashen da ta mamaye, kasuwancin dik waɗan da suke kewaye da ita a karkashin sarrafawarta suke yi. Bayin basu da wata ƙima da daraja, a haka kuma wai sun fi talakawar da ake mulka kima, idan ka zama bawa a wannan kingdom ɗin, to ka san rayuwar ka ba taka bace. Wannan kingdom da fadar Sarauniya tana da ƙarfi fiye da sauran ƙasashe. Za su iya mamaye kowace ƙasa, kuma babu mai iya taka masu birki sai KING ZUHAIR, wato KINGDOM OF POWER sune kawai suke zama babbar barazana ga ZARINA! Black Tiger kam bai ma san da wanzuwan Zarina a doran duniya ba!. Doka mai tsauri, dik wanda yayi gaban kansa ko ya yi magana kan zalunci, ana hukunta shi da azaba mai tsanani. Masu iko sunfi kowa daraja. Dik wanda ba shi da arziki ko gata, rayuwarsa bata da kima. Ana amfani da bayi da kuyangu. Akwai kasuwannin bayi da ake siyar da su kaman dabbobi, kuma manyan gidaje sun cika da kuyangu da ke aiki ba dare ba rana kamar injuna. Mu leƙa cikin fadar Sarauniya ZARINA mai cigiɓi cigiɓin nau'ikan azaba. Babban gini ne mai girma da ɗan duhu. An gina shi da baƙin dutse na zinariya, yana da hasken fitila ja da launin shunayya. Akwai manyan azurfa da zinariya da aka ƙawata ginin da su. Sarautar ta tara dukiya daga harajin da ake karɓa daga talakawa da ƙasashen da suka mamaye, bayin Allah su sha wahala su yi noma sai su karɓe kaso biyu cikin uku na amfanin gonar su barsu da kaso ɗaya wai haraji, hakan yasa rumbun hatsin QUEEN ZARINA ya cika har yana amai da kayan abinci, girman wannan rumbu kuwa ya kai girman gari guda daga cikin garuruwan kasar. Amma hegiyar matar nan bata sadaka bare kyauta, gara ta bar abincin ya yi ta cike koma lalacewa ne ya yi a kan ta bawa talakawa!!. Fadar ta cike take da bayin dake hidima. Kowanne yanki na fadar akwai kuyangu da bayi masu bauta mata. Babban zaure mai girma. A nan ne take karɓar baki da shari'a, akwai dogarai masu sanye da rigunan karfe da takubba kamar warriors. Sai ɗakin sirri a cikin fadar, wani ɗaki ne da ba kowa ke da damar shiga ba, anan ne take shiryawa ko boye wasu sirrikan mulkinta. Bari mu taɓo tahiri a kan Queen Zarina wadda kuka jima kuna jin labarinta ba tare da kun san menene ainahin tsamar dake tsakaninta da Kingdom of power ba, bama ku san wacece ita ba, shin yarinya ce, babba ce, matar aure ce, ko dai bazawara or budurwa, dik baku sani va, to yanzu labari ya juyo ta kanta, bari mu faɗa maku ya take domin yanzu story zai juyota. Kingdom ɗin nan ba kawai mai arziki bane, yana da cikakken iko a duniya. Nasan ko a iya haka kun fahimci dalilin da yasa a koda yaushe suke cikin takun saƙa da King Zuhair, dan shi baya barin mulkin zalinci ta cigaba da tafiya. Tabbas kujerar mulkin da Queen Zarina take zama banbancinsa da na King Zuhair kalilan ne, ita ma nata diamond seat ne, sai dai na shi ya fi nata girma sa ƙawatuwa. Ta dake saman kujerar nan tana haɗe cikin alkyabbarta launin gold mai daraja, ba karya kyakkyawar gaske ce, zubin Iceland lady, jajir da ita kamar ka latsa jini ya fita, ga gashin kanta light brow, ka zalika kwayar idanunta light brown, babbar macece ba yarinya ba, ko dai in ce uwa, sai dai yanayin zubin halittarta zaka yi zatan irin ƴan 25 to 30 years ɗin nan ne. Da ka kalli face ɗinta kaga zallar madarar rashin imani, babu annuri kuma babu dariya ko kaɗan, doguwa ce sosai dik da take a zaune, kun san matan Iceland da shegen tsawo sosai Masha Allah. Gabaɗaya amintattunta da manya manyan bokayen cikin fadarta suna ciki, daga gefen damarta wata kyakkyawar matashiyar budurwa ce zaune a saman kujera ta mulki irin wanda Queen take kai, sai dai nata kujerar bai kai na Queen girma, kima da kuma daraja ba. A shekaru yarinyar nan ba zata wuci 17 years ba, ta tsantsara kyau cikin shiga na ƴaƴan manya manyan sarakuna da ake ji da su, ba karya kyakkyawar yarinyar ce irin uwarta sak. Wani kamshakin dakakken namiji mai kirar lafiya da karfi ne ya danno cikin fadar, cikin tafiyar jarumta da nuna isa, yana cikin shiga irin na manya manyan sarakuna masu karfin iko, da ka gansa babu tambaya kasan basarake ne, jiga jigan warriors huɗu suna take mashi baya har ya ƙariso saman stage da Queen take, yana shigowa gabaɗaya manyan cikin fada suka miƙe tsaye except Queen and her daughter. A saman kujerar gefen damanta ya zauna, yana zama kowa ya koma ya zauna, yana zama bai fi da minti biyu ba sai ga wani zaƙwaƙurin cikakken namiji mai zubin jarumta shi ma ya shigo, da alama family ake san haɗawa kafin ayi abin da za'ayi, dan wannan matashi ma dai falimy ne, saboda shigar dake jikinsa irin ta Prince. Gefen wannan matashiyar budurwa saman kujera ya zauna. Gabaɗaya ko'ina tsit kake ji tamkar babu halittu a cikin fada. Queen hannunta na rike da wani ɗan karamun akwatin lu'ulu'u mai shegen kyau yana kyalli launin gold. My people's a tinaninku a kingdom of power ake cin amana da munafurci ko? To kun yi kuskuren tinani, bana jin akwai kingdom ɗin da ya kai nan cin amana da munafurci dik wannan uban tsaro da kuka gani da izayar da Queen Zarina take yi wa masu tinanin cin amana kafin ma su aiwatar, wlh dik da haka ta ko'ina akwai makarkashiya da suka mamayeta, ku dai mu je zuwa. ZARTAR, shi ne shugaban bokayen a ɓangaren yanke hukunci a kan abin da ya shafi bayi da sauransu. Gabaɗaya fada ta zuba mata idanu suna jiran jin mezata ce. Ita kuwa shiru ta yi na tsawo a kallah good ten minutes kafin ta ɗan kara dakewa a cikin alkyabbarta zubin Uk, cikin kakkaifar murya ta fara magana kamar haka. "Zartan har yanzu kana nufin baku iya gano in da wannan makulli yake ba? Dik karfin ganinka, dik karfi eagle eyes ɗinka, amma baku iya sanin in da yake ba?". Kasa gabaɗaya bokayen fada suka yi da kansu, Zartan da ya kasance wani tsohon dattijo mai farar gashi kal, ga shi dogo da shi zubin Uk, idanunsa tamkar na mage gwanin ban tsoro, yana sanye da fararen kaya da wani dogon mayafi dake ja har ƙasa, gashin kansa da kayan jikinsa iri guda ne, yana da wani tabo a goshinsa kamar zanen katan maciji ya fasa kai. Zartan yana ɗaya daga cikin Kim family, Kim family kuma su ne familyn Queen Zarina kenan, kazalika yana da kafa a fada sosai. Miƙewa tsaye ya yi cikin girmamawa ya ce mata. "Ina kara miƙa hakurina a gareki, dik iya hangen da zamu yi mun hakanga bamu ga wannan makulli ba, amma dai tabbas wannan makulli baya kingdom of power, tabbas yana ta wani wajen ne na daban".......... Tsufa ta fara yawaita a tattare da shi, domin kuwa maganarsa ma bata fita sosai. Mai da kallanta a kan wannan sarki da ya shigo ɗazun ta yi, a natse ta ce. "Baka da abin faɗe ne a kan wanna case ɗin Ude?"...... Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. "For now dai babu, amma abin da zan ce shi ne zamu yi nasarar mamaye ko'ina, mu cure duniya ya zama abu guda kuma mu mulketa, ko Zuhair yana so ko baya so dole sai ya zube gwiwowinsa a ƙasa ya lashi kasan takalmarmu ya kuma goge mana saman, daga karshe ya zama bawanmu". Wani irin shu'umin murmushi ta saki saboda Ude ya faranta mata ranta sosai, tana matuƙar yunwar ganin ta cure duniya ya zama abu guda ɗaya, babu wasu kasashe dik a zama ɗaya, sannan ta zama ita ke mulkarsu dikka, ta murza kambunta ta juya kowa, dik wanda yake san sanyaya ranta to ya yi mata kamalai irin wanda Ude ya yi mata a yanzu, koda hukuncin kisa tasa aka yankewa mutum in dai ya yi mata irin kalaman Ude tana iya yafe mashi. "Amma ya batun Nieelarh da MUZAFFAR FAMILY fa?. Cewar Queen kenan..... Nieelarh ƴar cikin Queen Zarina ce, ita ce kuma wannan kyakkyawar matashiyar yarinya dake gefenta. MUZAFFAR FAMILY wasu jiga jigai ne daga cikin birnin waɗan da su ke da arzikin dik wani abincin da ake ci a cikin birnin, sannan sune politics family dake kasar gabaɗaya, mutane ne masu karfin iko da isa, da ace yau zasu ɗauke wa birnin Justice dik wata tallafi hakika da birnin ta cika da yunwa matuƙa. So head of the familyn wato MUZAFFAR ya kasance mutum mai girma a fada, sannan mutum mai girma a birnin, dik bala'in Zarina tana raga mashi, wasu daga cikin mutanen birnin suna cewa akwai wata alaƙa a tsakaninsu, wasu kuma suna cewa saboda karfin musuluncinsa yasa bata iya tsafacesa har ma take shakkarsa. To dik bama wannan ba, haƙiƙa karfin musuluncinsa yasa bata iya tsafe familyn Muzaffar har ta samu damar sarrafasu san ranta kamar yadda take yi wa sauran jama'a, amma ba hakan ce tasa take shakkar Muzaffar family ba, akwai wani sirri nata da shi dattijo Muzaffar ya sani wanda kuma ga dukkan alamu tana tsoron ya fasa kwai shiyasa take shakkarsa sosai, to a halin da ake ciki yanzu ɗaya daga cikin Muzaffar family ya nuna ra'ayin yana san ƴarta Nieelarh wanda kuma dan dole ta amsa da ta yarda da batun, amma ta ƙarƙashin ƙasa tana neman ta yadda zata yi ta warware wannan batu, saboda ba zata yarda haɗa jini da musulmai ba a cewarta, ta kuduri niyar ko ta halin yaya sai ta ruguje wannan batu, sai dai kuma ba zata iya yin fito na fito da Muzaffar family ba!. Amma me kuke tinanin zai kasance sirrinta da bata san ya fashe kowa ya sani da har take daurewa ta yi wa Muzaffar family sauki haka?. Ɗaure fuska sosai Ude ya yi kafin ya amsa da. "Haƙiƙa Nieelarh ba zata shiga Muzaffar family ba, dan hakan ƙasƙanci ne da faɗuwa a garemu". With his full confidence ya yi maganar, haƙiƙa yana da tabbaci a kan maganarsa!. Ɗan Nieelarh fa ƴarsa ce, ba zai bari hakan ya faru ba!. Jinjina kai ta yi cike da farincikin amsoshin Ude a ranta, sannan ta miƙe tsaye, cike da bada umarni ta ce. "Zartan ku cigaba da binciken ina Spender yake ta maduban dubanku, ku tabbatar kun yi gaggawar binciko shi, Ude ina da magana da kai, ka sameni a ciki main parlour". Tana kai karshen maganar ta yi gaggawar juyawa alkyabbarta na jan ƙasa sosai ta nufi wani katafaren diamond door da zai sadata da cikin katafaren gininsu na alfarma wanda ya kasance shi ne family part ɗinsu. Gabaɗaya mukarraban fada suka miƙe bisa girmamawa a gareta har sai da ta bar fadar sannan suka koma suka zauna. Tana fita kofar wasu mahaukatan zaƙwaƙuran warriors suka take mata baya zuwa kofar shiga cikin part ɗin nasu!. Cikin kakkausar murya mai amon bada umarni Ude ya kara jaddadawa bokayen royal palace ɗin abin da Queen ta faɗa, daga haka ya miƙe ya bi bayanta ya bar Nieelarh da Beer wato kanin Zarina ne shi ɗin. Kai tsaye katafaren parlournsu na alfarma Quren ta shiga, still dai hannunta rike da wannan akwatin. Saman wani luntsumemen sofa mai zaman mutum uku ta ajiye akwaitin, sannan ta fara safa da marwa a tsakiyar parlourn tana ɗan bubbuga hannayenta cikin juna, alamar tana cikin damuwa..... A haka Ude ya shigo ya sameta, cike da kula sosai haɗe da nuna damuwar ganin halin da take ciki ya ce. "Lafiya kuwa ranki ya tsananta fiye da kowacce rana?". A gaggauce ta juyo da kallonta a kansa, cikin kakkaifar murya ta amsa mashi da. "Ba zai taɓa kasancewa lafiya ba ka ganni a tsaye, kasan da cewa in dai bamu samu Spender ba tabbas Muzaffar family sai sun ɗauke Nieelarh daga garemu, sannan zata iya shiga wannan addini nasu, dik bama wannan ba, damuwata shi ne Zuhair ya tsugunna ya goge mun takalma, na mayar da shi bawa na dattijo mai goge goge a royal palace ɗina, na mayar da matansa kuyanguna, na mayar da ƴaƴansa masu yi mun hidima, mazan kuma masu ɗeben kewa, na sa ya ɗanɗani ɗacin da ya ɗanɗana mana na kashe mun mahaifi da ya yi ya kuma ruguje Thomas family!!". "Wannan kuduri naki ba zai taɓa kasancewa ba, na sha faɗa maki ki hakura kawai". Wata murya ce ta furta hakan a yayin da take ketowa izuwa cikin parlourn. Kyakkyawar matashiyar yarinya ce da bazata wuce 23 years ba duniya, fara ce tas kamar madara, kyakkyawar gaske ajin farko, tana shirye cikin alkyabbarta na sarauta na alfarma wanda ya sha kwalliya da duwatsun lu'ulu'u, da ganinta kasan jinin sarauta ce. Kwayar kyawawan idanunta sun kasance hazel eyes ne mai ɗan duhu, hakan yasa ya yi kama da green eyes sosai. Idanun nata basu da girma sosai, amma suna da kyau matuƙa. Queen Zarina zata yi magana Ude ya rigata da cewa. "Ke Rishma kina da hankali kuwa? Ita kike faɗawa magana gatsau haka?". Da wani irin kallo ta bisu, da kaga wannan kallan kasan na takaici ne, sannan ta ce. "Ude idan baka tuba ba, babu shakka zaka mutum a kaskance, zaka mutu mutuwa mafi munin da ko kare sai ya fika daraja a wajen mutuwa........." Dan dole ta haɗiye sauran maganar nata saboda wani irin uban tsawan da ya daka mata, ba shiri ta yi tsit tana jin kirjinta na bugawa da karfi karfi. "Keeeeee Rishma, ki iya harshenki ko kuwa na datse maki shi a yanzun nan!!!!". Shi ne abin da Ude ya faɗa...... "Ude ba zan iya harshe na ba, ka rigada ka ketare iyakarka, na dai'na jin tsoron dik wanda baya tsoron Allah, tin kan lokaci ya kure maka Ude ka tuba...... ". A miliyan ta haɗiye maganar nata sakamakon nufarta da ya yi gadan gadan tare da cire hannu zai ɗauke mata fuska da mari. Sai dai kuma bai kai ga sauke mata marin ba aka rike hannunsa cak ta baya. Cikin wani irin fusata ya yi zafan juyowa dan yaga wani mai karan kwana ne ya rikesa. Sai wani irin huci mai zafi yake fitarwa, ran maza ya ɓaci. Ita dai Queen tana tsaye tana binsu da kallo. "Kada ka sake ka ɗaura hannunka a jikinta Ude, idan kuma ka yi gangancin yin hakan tabbas hannunka ba zai sake kasancewa naka ba, dan sai na datse maka shi!!". Shi ne abin da wanda ya rike hannun nasa ya faɗa. Wani kyakkyawa mutum ne wanda da ka gansa kasan ɗan uwan princess Rishma ne, dan suna kama sosai, yana tsaye tsayuwar jarumta, cikakken namijin gaske ne, fari tas da shi, yana sanye da wani irin kaya mai kama da na warriors, sai dai ba su bane, wannan kayan jarumai ne. Mamaki tamkar Ude zai sume a wajen ne ya bayyana a saman face ɗinsa, da kyar ya iya cewa. "Rishan ni yau kake kira da Ude?"....... Wani irin kallan kuna ya bisa da shi kafin ya yi wurgi da hannunsa da ya rike, sannan a gadarance ya ce. "Da kana da wani suna ne bayan Ude?". Babbar magana!. Kum san menene yake tsakanin Ude da Rishma and Rishan? To Ude babban yayansu ne, ya juya masu baya saboda Queen Zarina, ba zaku taɓa fahimtar wani kulli bane a wannan masarauta sai nan gaba kaɗan, ta ya aka yi su Rishan suke matsayin musulmai shi kuma Ude dake matsayin babban yayansu yake katon krista? Ya aka yi Ude dake matsayin mijin Queen bai zauna a kujerar mulki ba sai ita? Meyasa yake biye mata kaman ita take da shi? Meyasa ya juyawa ƴan uwansa dikka baya ya bi addinin matarsa ya kuma damka mata ragamar garin a hannunta tana yin yadda ta so? Ina dattijo mahaifinsu Rishan yake? Menene dikka wannan rikicin. Gaba kaɗan zaku sha mamaki a kan wannan masarauta da kullin dake cikinta, akwai gagarumin case. Sumar tsaye Ude ya yi, ya ƙasa yin wani ƙataɓus, bai taɓa zatan kannensa zasu juya mashi baya ba, su kuwa sun gaji da yi mashi nasiha ne, sun gaji da biye mashi suna sa ran zai juyo ya musulunta su koma yadda suke a da can baya, ya karɓi karagar mulkinsa ya cigaba da gudanarwa bisa adalci kamar a baya, sun gaji da dik abin da yake yi, yanzu babu wani sauran ɗaga kafa, dole su yi fito na fito da shi dan su samu salamar ciwon dake cikin zuciyarsu. Wucewa Rishan ya yi ya riko hannun Rishma tare da janta suka fice daga cikin parlourn. Ko sau ɗaya Queen Zarina bata yarda ta ɗaura idanunta a kan Rishan ba, alamar akwai wata a ƙasa kenan, ta dai bisa da kallo da ya juya yana tafiya tana mamakin rikiɗewarsa..... A gabaɗaya kingdom of Justice ɗin nan, babu cikakken jarumi na cikin gida biyun Rishan, shiyasa suke shakkarsa, zance na gaskiya har Ude shakkarsa yake yi, idan yana magana a waje ba'a tankawa, namijin gaske ne. Har suka kurewa ganinsu Ude bai iya furta word ba, ya shiga ruɗani. Tsafin Zarina ya kasa yin aiki a kan mutane biyun nan, wato da Rishan da Rishma, kullum suna tare da Dattijo Muzaffar shi yake taimaka masu da shawari a kan dik abin da ya taso masu, su biyu suke rayuwarsu bayan juya masu baya da yayan nasu ya yi!. Sai dai suka fice daga parlourn ne ya dawo da kallonsa a kan Zarina dake tsaye kamar bata a wajen, a hankali ya buɗi baki zai yi mata magana kenan ta yi saurin ɗaga mashi hannu. "Har yanzu yara ne, ka yi masu uzuri". Ta kai karshen maganar tare da wucewa fuuuuuu kaya na jan ƙasa, kamar wata kunfa ta wuce sama, tana wani taku mai kama da magic walk, sannan fuskarta ya nuna tabbas akwai wani abin, sai dai ita baka taɓa iya karantar ina ta dosa, baka sanin me zata aikata sai lokacin yin abu kawai kaga aiki da cikawa, ba shakka akwai abin da take da niyar yi a kan Rishan da Rishma, saboda yadda ta kallesu da suna barin parlon ba kallan lafiya ba. Matsawa kusa da stair case ɗin Ude ya yi yana cigaba da kallonta har ta kurewa ganinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya koma fada. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Zaune suke cikin wani haɗaɗɗen park mai matikar ɗaukar hankali, ya kaita yawace yawace sosai daga karshe ya biyo da ita a nan dan su ɗan huta. Sai dai fa dik wannan yawon da suka yi taki sakan jiki da shi. Dik in da suka je tana takure waje guda, bata ma san motsawa, dan dai yana matsa mata ne yasa take yarda tana binsa. Zaune take saman wani tsadadden kujera dake cikin park ɗin ta gefe tana kallan yadda big girls suke nishaɗi suna kaiwa da komowa, ta yi nisa cikin tinanin mafita a gareta, so take yi dik ta yadda za'ayi ta guje mashi, dan ta ɗaukarwa kanta alkawarin ko zata ci amanar kowa ban da Sharifat da Jasra na gidan AAJ, dan waɗan nan mutane biyun sune duniyarta, dan haka a kan ta auri Ramish gwara ta gudu ta bar gidan Abbie, ba zata zauna ba. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 50 Zaune take saman wani tsadadden kujera dake cikin park ɗin ta gefe, tana kallan yadda big girls suke nishaɗi suna kaiwa da komowa, ta yi nisa cikin tinanin mafita a gareta, so take yi dik ta yadda za'ayi ta guje mashi, dan ta ɗaukarwa kanta alkawarin ko zata ci amanar kowa ban da Sharifat da Jasra na gidan AAJ, dan waɗan nan mutane biyun sune duniyarta, dan haka a kan ta auri Ramish gwara ta gudu ta bar gidan Abbie, ba zata zauna ba. Tana can tana tinani shi kuma ya yi masu oder kayan sha mai tsabta, tsada da haɗuwa, bata san time da ya yi ba sai gani ta yi an ajeye mata abu a gabanta. A hankali ta ɗago da kanta ta ɗan saci kallansa ta ƙasan ido, while shi ma ita yake kallo, ya ga ta saci kallonsa, amma sai ya basar kamar bai gani ba ya ce mata bismilla ta sha mana. Kai ta ɗan girgiza mashi kafin ta amsa mashi da a'a ba zata sha ba ta ƙoshi. Ƙasa sosai ya yi da murya, tamkar mai raɗa ya ce. "Please Aesh, ko kaɗan ne? Ba dan ni ba, dan Allah"...... Yunƙurawa ta yi zata yi mashi magana ya yi gaggawar sake cewa. "No Aesh, don't say anything please, kawai ki sha". Haɗiyi abin da ta yi niyar faɗa ta yi, sannan ta kai hannu ta rike stro dake ciki haɗaɗɗen cup ɗin, ɗan jujjuyasa ta yi kaɗan kafin ta ɗan duka ta sanya bakinta. A hankali ta ɗan zuƙa. Slowly ya ɗan lumshe idanunsa, dan har cikin ransa ya ji wannan zuƙa da ta yi, nisawa ya yi kafin ya ɗan kawar da kallonsa daga kanta yana mayarwa kan wayarsa dake vibrate. Call ɗin Bilal ne ya shigo, kamar zai yi picking sai kuma ya fasa tare da kashe wayar ma mai gabaɗaya, ya tura cikin aljihunsa sannan ya harɗe hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa, gabaɗaya ya zuba mata waɗan nan dara daran idanun nasa yana kare mata kallo. A hankali take cigaba da shan abin tana ɗan tsuke fuska alamar ya yi mata sanyi sosai. Kamar ance ta ɗago ido tana ɗagowa suka yi four eyes, ɗan zaro idanu ta yi like wow and like kallan me kake mun?! Shi kuwa gera guda ya ɗan ɗaga mata kafin ya sauke ajiyar zuciya, abin gwanin birgewa sosai....... Wani irin kallo ta wurga mashi mai kama da harara, shi kuwa ya yi mata nuni da idanunsa izuwa kan cup ɗin alamar ta cigaba da shan abin da take sha bai san iskanci. Make kafaɗa ta yi tare da girgiza kai, sannan ta ɗan ture cup ɗin gaba alamar ba zata cigaba da sha ba kenan. Ɗan jinjina kansa ya yi like irin yarinya baki sanni ba ne. A fili kuma sake nuna mata cup ɗin da ido ya yi alamar ta cigaba da sha...... Wannan kallo dai mai kama da harara shi ta sake binsa da shi kafin ta nuna mashi cikinta da hannu alamar ta ƙoshi ba tare da ta yi magana ba, alamar dai yau ƴar kurma kurma suke jin yi. Ɗan kawar da kallonsa daga kanta ya yi kafin ya ɗan yi gyaran murya kaɗan, sannan ya ce. "Aesh you're giving me to much of headache". Tamkar bata ji sa ba ta cigaba da binsa da wani irin kallo, har cikin zuciyarta take rasa natsuwarta a dik lokacin da take kallonsa, sai dai kuma bata wani ɗaukar hakan a matsayin wani abin azo a gani, ta fi ɗaukar abin ma a matsayin tsoronsa saboda abin da ya shiga tsakaninsu. Suna a haka masu kawo oder suka sake sauƙe masu tsadaddun plate masu shake da kayan fruits kala kala very fresh a ciki. A gabanta yanzu ma suka sauke, kallansa ta yi cike da mamaki kafin ta ce. "Wannan fa?".... "Is yours". Ya bata amsa yana kallan yadda kankanar ta yi balai'n kyau, sun yankata shape of heart kanana da manya, gata jajir zata yi zaƙi. "Ni gaskiya na ƙoshi mu tafi gida". Ta faɗa kallanta a kansa..... "Babu in da zamu je matsawar baki sha fruits ɗin nan ba". With full confidence ya bada amsar, irin da gaske yake yi ɗin nan. Bata da zaɓin da ya wuce dole dole ta sha, tamkar zata saka mashi kuka ta kai hannu saman plate ɗin, sai kuma ta ƙasa ɗaukar komai, saboda yadda aka yayyanka fruits ɗin shape of heart ya yi matuƙar birgeta, tamkar ance masu masoya ne suka yi oder, basu san waɗan nan abokan faɗa bane. Ta shagala da kallan fruits ɗin tana tinanin wanda yakamata ta fara ɗauka unexpected ta ga hannunsa a cikin plate ɗin, a hanzarce ta saci kallansa, sai dai kash, tana ɗagowa suka haɗa ido, da sauri ta kawar da kallonta a ranta tana faɗin shegun idanunsa a wajen kamar ball, sai ya yi ta kallan mutum, kuma ga idanun nasa da shegen saka mutum cikin shakku da tsoro, sai yasa ka ji baka yarda da kanka ba, shi tsabar kwarewarsa a aiki ma kana haɗa ido da shi zaka ji baka da gaskiya koda kana da shi, yasa ka ka ɗaurawa kanka laifin da baka aikata ba dan bala'i irin nasa.... Kai Leesharh da Ramish duniya ne, wai yasa ka kaɗaurawa kanka laifin da baka aikata ba, wlh Leesharh akwai ƴar air nike faɗa maku, ta za'ayi baka aikata laifi ba ka ce ka yi? Ko da yake sai dai idan baka tsargu ba, tsab zaka ce ka yi bayan baka yi ba. Shikuwa bawan Allah, kankana ya ɗauka tare da sanya mata a hannunta. "Idan na tsaya jiranki ki zaɓa za mu kwana a nan, oya take this one". Ya kai karshen maganar yana sanya mata shi a cikin hannunta, sannan ya janye hannunsa baya. Ɗan ɗaure fuska ta yi tare da wurga mashi hararar kasar ido, a cikin zuciyarta ta ce mugu kawai, ba zan yafe maka ba koma me zaka yi mun. A fili kuma ta kai kankantar saitin bakinta ta ɗan gatsa. Wani irin sanyin daɗi ta ji kankanar ta yi mata, ga zaƙi ga shi daga freezer aka cirosa, ai bata san time da ta sauke ajiyar zuciya ba, babu wanda ya ce Leesharh kara ta sake mayar da ragowar bakinta a gaggauce zata sake gatsa, sai dai kuma bata kai ga gatsan ba ya kai hannu ya kwace kankanar, dama ta gatsi rabin heart a gatsan farko, dan haka sai ya kwace rabin ya kai ɗan bakinsa. Ai a miliyan ta ɗago da kallanta a kansa, kawar da kansa ya yi tamkar bai aikata komai ba, harara ta dallah mashi kafin ta sake daukar wani kankanan. Sarai ya kalleta, amma ya yi kamar bai ganta ba, shi dai burinsa ya ga ta dawo da walwalarta tamkar da, ya ga ta koma fara'a tana murmushi ta saki jiki, shiyasa yake tsokanarta dan ta saki jiki da shi. Amma ita kuma sai wani dojewa take yi tana nuna halin bosawa, irin ita fa ba zata sauko ɗin nan ba. Haka ya cigaba da tsokanarta har ta sha fruits ɗin mai ɗan yawa, sannan ta ɗauki tissue dake wajen ta goge bakinta. Tana cire tissuen daga bakin nata ya miƙo mata hannu alamar ta bashi, ba musu ta miƙa mashi, a tinaninta zai jefar ne, sai kuma taga akasin haka, domin kuwa bakinsa ya goge shi ma kafin ya jefar. Mamakinsa ne sosai yakamata, bata yi zatan hakan ba, shi kuwa ido ya bita da shi yana karewa jikinta kallo, lokaci guda tinanin abin da ya faru a tsakaninsu ya dawo mashi cikin kwakwalwarsa, a wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ya tsinci kansa, ya kasa iya zare idanunsa daga kanta. "Yah Ramish please ka mayar da ni gida ka ji? Kaga fa har karfe 9 na dare ya yi, a waje fa muka yi sallar azahar ga shi har dare bamu koma ba, Allah barci nike ji". Ta kai karshen maganar tana ɗan ɗaure fuska, wai irin yasan ba da wasa take yin nan ba......... A cikin zuciyarsa ya furta. "Why Aesh take mun kama da royal family? Meyasa ko magana take yi sai in rinƙa ganin kamar Zash ne yake magana?". A fili kuma sai ya ce. "Kina san mu koma?"............. Kai ta gyaɗa da sauri alamar e. Jinjina kai ya yi kafin ya ce to ta tashi su tafi. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana ta faman buga hamma, miƙewa ta yi cikin natsuwa, sai dai tana ɗaga kafa da nufin su tafi kafa ya ce baki isa ba. Wani irin murɗa mata da cikinta ya yi ne yasa dan dole kafarta ta dakata, abin kamar wasa, da farko dai sai ta daure, a karo na biyu tana sake yunkurwa zata ɗaga kafa cikin ya sake murɗa mata da karfi, ƴar kara ta saki wadda bata ma san ta saki ba, a gaggauce ta sanya hannu ta dafe cikin nata, wasa wasa ta sake sakin ihu mai ɗan sauti wanda dik bata san ta yi ba. Da farko shi ma ya zaci wasa take yi, sai da ta yi kara na biyu ne ya fahimci da gaske take yi, cikin natsuwa ya miƙe ya iso in da take, hannunsa yasa ya tallabota yana faɗin. "Aesh are you okey?". Kai ta shiga girgiza mashi cikin azaba tana datse idanunta gam da karfi, ganin da gaske take yi kuma hankalin jama'a ya fara dawowa kansu yasa bai tsaya ɓata lokaci ba ya yi gaggawar ɗaukarta cak suka nufi cikin motarsu. Ta ƙanƙame shi sosai tana datse lips ɗinta alamar azaba take sha. Gidan gaba ya sanyata tare da zagowa ta ɗayan side ɗin ya shiga. Kifa kanta da gwiwonta ta yi tana cigaba da datse lips ɗinta tana ɗan murkusoso tamkar wadda take shirin yin ɓarin ƙaramin ciki. Hannunsa yasa ya janyota jikinsa, cike da tashin hankali yake tambayarta menene yake damunta? Bai taɓa sanin zai damu da ita dan ta shiga damuwa ba sai yau, ya shiga tashin hankalin da bai san ya shiga ba. Ƙasa iya amsa mashi ta yi, tana cigaba da murkusosonta tana nishi sama sama. Gabaɗaya sai ya rikice ya rasa meyakamata ya yi mata, sai kawai ya rungumeta a jikinsa yana mai ce mata sorry kawai...... Ta ɗauki lokaci mai ɗan tsawo a haka kafin cikin ya fara lafa mata, a hankali numfashinta ya fara komawa daidai. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya duba time a diamond watch dake manne a hannunsa. 9:40pm. Nisawa ya yi kafin ya yi ƙasa sosai da murya, cikin natsuwa ya ce. "Aesh are you okey now?"..... Kanta na daga manne da chest ɗinsa ta gyaɗa mashi alamar e. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Thank god, but menene yake damunki haka?". Kai ta girgiza alamar ita ma bata sani ba, sannan ta ɗan yunkura zata bar jikinsa. Cikin gaggawa ya yi ƙoƙarin hanata yana faɗin. "Ba zaki fama ciwon naki ba idan kika tashi?".... (Kun ji mun Ramish da iskanci, kawai dai ka faɗi gaskiya, ba wani ba zata fama ciwonta ba, dama ni tin daga yanayin sleeping dress ɗinka nike zarginka da uhm uhm na yi shiru saboda su maman Sultan, amma da na faɗi wani abin, bazaki fama ciwonki ba idan kika tashi, kai Ramish ɗan duniya ne, bariki da kasuwa yaseen 😅) Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e ba zata fama ba...... Ba tare da ya sake yin magana ba ya saketa. Miƙewa ta yi da kyar ta koma ta jingina bayanta da jikin kujerar motar tana jan numfashi a hankali hankali. Sorry ya yi mata kafin ya ce bari ya tada mota su koma gida da wuri dan ta kwanta ta huta. Kai kawai ta iya jinjinawa, dan ji take yi tamkar an ɗaure mata tongue ɗinta.... Kunna motar ya yi idanunsa a kanta ya fara driving, dik fa wannan damuwa da ya shiga bai san ya yi ta ba. Kai tsaye gida ya wuce da ita yana tinanin lokacin cigaba da yin bincikensa ya yi, yakamata ya kama masu nikaf yanzu, yakama Leesharh ta bashi haɗin kai wajen bashi amsar waɗan nan tambayoyi da yake da buƙata da sauran evidence da suke hannunta, sai dai ya so kaita hospital duba da family Dr ɗinsu wato Dr Raj baya nan, amma bala'in kishinsu na jinin Modarawa yasa ba zai iya kaita ɗin ba, dama dai Dr Raj na nan ne, dan haka ya gwammaci ya wuce da ita gida ya je ya ɗan dubata da kansa........... Ramish namu na amana, zaka yi bayani, wlh akwai case tsakanin Leesharh, Ramish and Sharifat, ga Abbie a gefe wanda shi already yasan yarsa na san Ramish, sannan ya rigada ya basa, kuna tinanin su King Badeen zasu yarda Ramish ya auri bare ya bar Sharifat? Kuna tinanin Mama zata aminta? King Zuhair zai bari? Uhm abu ne da kamar wuya, dama dai ba'a san da batun Sharifat bane kila iya mama da King Zuhair su zame barazana da shamaki tsakaninsa da Leesharh, amma an san da batun Sharifat ai har su Abbie shamaki zasu zame tsakanin Leesharh da Ramish, akwai case ba babba kuwa. Da yake yana sharara gudu sosai sai suka isa gida cikin ƙanƙanin lokaci, yana tsayar da motar a garaje ya juyo da kallonsa a kanta da nufin ya yi mata magana kenan sai ya ji saukar numfashinta irin na mai barci, ƴar ƙaniya ta ji wuya har ta yi barcin dole. Shiru ya zubawa kyakkyawar face ɗinta idanu wanda tun da yake da ita bai taɓa kare mata kallo irin haka ba. Zuciyarsa ce ta furta wow, shi kansa ya shaida ta haɗu, amma girman kansa ba zai bari ya yardanwa zuciyarsa da ta haɗu ɗin ba. Sauke kallansa ya yi izuwa saman kirjinta, lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tinano mashi yadda ya ganta tsirara a wancan ranar, take ya tunano yadda yaga tula tulanta muraran a fili. Wani irin yawu ya haɗiya yadda kuka san ba lafiya ba, da alama abar tasu ta gado ta motsa kenan. In faɗa maku abin da baku sani ba my people's, tin lokacin da yake jinyarta na wannan harbi da ta kare mashi, tin lokacin tula tulanta suka zauna mashi a ransa, dan kullum sai yaga tudunsu, daga karshe ya gansu muraran, amma bai bari kowa yasan sun birkita mashi lissafin ƙwaƙwalwa ba, nima saboda shegen bin kwakkwafina yasa na gano har na faɗa maku, dan haka kada ku bari yasan na faɗa maku......🥱 Ji yake yi tamkar yasa hannu ya yi kasa da zip ɗin rigarta dan ya ga koda iya tudunsu ne ko zai ji sauki, take wani ɓangare na zuciyarsa ta tina mashi a matsayin da suke yanzu shi da ita, kallan ɗan iska fa take yi mashi wanda kuma ba halinsa bane, kunga idan ta kama shi ya zuge mata zip ƙasa mekuke tinanin zai faru? Ai ko mutuwa yake yi bazata taɓa yardar ba halinsa bane. Tina hakan yasa ya hakura ya juya haɗe da buɗe side door ɗinsa ya fito, ba dan haka ba Allah saboda rashin kunyarsa sai ya zuge mata zip kasa ya gansu, amma yanzu neman wanke kansa a gareta yake yi, ba zai yi wani kuskure ba kuma. Dik a gajiye yake. Cikin takun jarumta ya zago ta side ɗinta, kofar ya buɗe, cikin natsuwa yasa hannu ya ɗauketa cak ya fito da ita, da kafarsa ya take kofar ya mayar ya rufe, sannan ya nufi ciki. Bata da nauyin barci sam, amma saboda azaban ciwon da ta sha sai barcin nata ya yi nauyi sosai, shi ma dik a gajiye yake, da kyar ya iya ɗaukarta da kyau. Bai zame da ita ko'ina ba sai cikin bedroom ɗinsa, kwata kwata ya mance cewa ba matarsa bace, ya mance ba ɗaki ɗaya suke ba, (saboda iskanci ba) sai da ya shinfiɗeta a saman bed ɗinsa sannan ya tina ashe ba bedroom ɗinta ya kaita ba. Siririn tsaki ya ja tare da cewa sai ya yi wanka zai mayar da ita nata bedroom ɗinta, a gajiye yake sosai, bari ya yi wanka ko zai samu karfi. Wanka ya shiga a gurguje, sai dai da kyar ya iya yi saboda barci da ya ci karfinsa ga gajiya. A daddafe ya fito ya shirya cikin sexy sleeping dress ɗinsa masu matukar kyau da ɗaukar hankali. Yana zuwa ya ganta kwance saman bed ɗin nasa tamkar yadda ya barta, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kwanta a gefenta, a cewarsa bari ya ɗan huta kaɗan sai ya tashi ya mayar da ita bedroom ɗinta, sai dai kuma yana kwanciya barci ta yi awon gaba da shi, dan a wuya yake dama. To my people's ya kuke ganin farkawarsu suga juna bed guda zai kasance? To ni dai na yanki gabas, bari in leƙa wani ɓangare in dawo. 🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥 A hankali take dafa bango tana kuka ta nufo kofar fita daga bedroom ɗin, lokaci guda ta ji sansa na juyewa izuwa kiyayya, dan ya gwada mata zallar rashin imani da tausayi, baya kula da ita sai idan buƙatarsa ta taso, gaskiya Yah Jaish ya kai makura wajen san kansa da zalinci. Da kyar ma ta iya mayar da sleeping dress ɗinta jikinta, yadda kuka san mai koyan tafiya haka ta zama. Parlournsa ta fito, azabar da take ji yasa ta ji ba zata iya taka kafafunta har ta isa part na momma ba, dan haka sai ta ce gara ta shiga bedroom na mama Haulat ta kwana a can, zuwa da safe sai ta koma wajen momma. Parlourn gabaɗaya baibaye yake da duhu, wutar a kashe take. A haka take laluɓawa da yake tasan a in da ɗakin mama Haulat ɗin yake, sai ta nufi can, hawaye wani na bin wani tamkar an buɗe tap...... Da kyar ta iya gano kofar ɗakin, tana ƙoƙarin laluɓar handle na kofar ta tura ta shiga sai ji ta yi kamar daga sama an ɗauketa cak, ga shi cikin duhu ne, amma kuma dik da ba haske ta gane shi ne, dan idan zata ƙasa gane kowa ban da sanyin zuciyarta, shi ɗin na daban ne da ya fita daban ko a cikin duhu. Sai dai a tinaninta abin da ya yi mata yanzu zai sake mai da ita ya yi mata dan azzalumi ne a cewarta, dan haka sai ta fara ƙoƙarin kwatar kanta. Bai kulata ba, ya cigaba da tafiya, sai mutsu mustu take yi, amma dik a banza, dan bata tashi sanin in da take ba sai da ta ji kanta a cikin ruwa mai zafi sosai. Ihu ta zunduma, a cikin duhun ta fara laluɓar abin da zata samu ta kama ta fita, ruwan ya yi mata zafi sosai. Sai dai bata iya taɓo komai ba, har shi bata ji motsinsa ba, yana sakata a cikin ruwan bata sake jinsa ba. Tsananta kukanta ta yi tare da fara faɗin. "Na shiga uku, momma wlh Yah Jaish zai kashe ni, wayyo bappana, dan Allah ku mayar da ni wajensa". Tsabar ta birkice tana kuka haɗe da sambatu bata ji lokacin da ya janyota ya mannata da kirjinsa ba, shi ma ya tsunduma cikin ruwan. Sai da ta ji sanyayyar muryarsa yana faɗin. "Babu wanda zai mayar dake wajen bappan naki, kina nan tare da ni, ya isa haka kukan"......... Sai sannan ne ta gane ashe tana jikin mutum. Cike da tsoro ta sanya hannunta tamkar mai tsoron taɓa abu ta fara laluɓarsa cike da fargaba. Tabbas shi ne, ƙoƙarin raba jikinta da nasa ta yi tana kara tsananta kukanta, cikin sauri ya kara kankameta yana faɗin. "Ina zaki je kuma?". "Yah Jaish dan Allah ka kyaleni haka, wlh ba zan iya ba, zan koma wajen momma ne in ce ta mayar da ni wajen bappana". Ƙara matsar da lip ɗinsa dab da kunnuwanta ya yi, cikin raɗa ya ce. "Ni na bada izinin a mayar dake ne? Ko kin manta ni nake da iko da ke ne?". Shiru ta yi ta rasa abin cewa. Hannunsa yasa ya kara jawota jikinsa, cikin dabara ya ɗan yi ƙasa da hannun nasa a in da ya fara bubbuɗe mata kafafunta ruwa yana ratsata da kyau. Kankamesa ta yi saboda zafin ruwan, tana san kurma ihu amma tana fargaban abin da zai iya sake aikata mata, rufin asirinta dai ta yi shiru....... Shi kuwa, sai da ya buɗe mata kafafu ruwa ya ratsata da kyau, sannan ne ya hauro da hannunsa sama, saboda tsabar tabbatar rashin kunya sai ya sanya hannu a saman nipple ɗinta, a hankali ya fara shafowa, a kunnenta ya fara raɗa mata. "Wajen yana yi maki zafi ko? Na basu wahala ko?"........ Kai Jaish akwai tsaurin ido, kunyar rashin kunya, ko da yake ba laifinsa bane, dik kunyar mutum ya zo wannan ɓangare sai dai ace mashi karuwan master room. Banza da shi ta yi tamkar bata ji shi ba, ba wai kuma dan raini ko wani abin ba, sai dai bata da abin faɗe, ya goge mata hadda kaf. Cigaba ya yi da shafasu abinsa, yana raɗa masu wasu sexy word a kunne wanda bai bawa kowa damar jin abin da yake faɗa mata ɗin ba. Ai bata san time ɗin da ta natsu tsit ba, kukan nata ma da take yi sai daga baya ta nemesa ta rasa, bata san lokacin da ya gudu ba, kalaman mijinta ya ɗauke kukan ba tare da ta shiryawa hakan ba, cikin ƙanƙanin lokaci yasa ta saki jiki da shi, ta kwanta shiru a saman kirjinsa tana sauraron hot words ɗinsa, har ɗan sakin murmushi ta fara yi. Uhm maza, maza sai shirin Allah, yanzu dai har ya yi mata wayo ta yarda da shi, shikenan ya samu abin da yake so, da abar tasu ta motsa hankalinsa a kwai yana da in da zai rageta. •••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 A can gefe guda kuwa, tattabaru biyu suna can suna nasu aiki, sai rarrashi Jawad yake yi dan ya karya alkawari, ance mashi iya romance ya zarce har izuwa babban sashe, dan haka Jannawad dai taki yarda, muma team ɗinta ba zamu yarda ba, ai iya romance kawai muka ce, me ya kaisa ga babban sashe idan ba rashin alkawari ba? Chuchu kada ki yarda. Bawan Allah ya ɗan ban tausayi, ya dukufa da girmansa da kimansa, da mutuncinsa a gari, kowa daraja shi yake yi sai ga shi ya kwantar da kai yana yi mata karamar murya, burinsa kawai ta ce ta yafe mashi, gaskiyar Jaish da ya ce Jawad ya gama jan mashi mutunci a kan titi ya yi yaga yaga da shi, shikenan fa yanzu Chuchu tasan abin da suke da shi, kai gaskiya Jaish kada ka yarda, idan ka yafe mu ƴan team naka bamu yafe ba, idan kuma ka raba wannan aure King ya tsine maka kabi bola babu ruwanmu, ko ya kuka ce my people's.......😅 ••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥 A ɗayan ɓangaren kuma sai dirama suke bugawa, hakuri iya hakuri guyson ya bata a kan dan Allah kada ta sanar da momma abin da ya yi mata, dik izzar sarautar nan tasu har dukar mata da kansa ƙasa ya yi yana bata hakuri, amma taki fir ta ce dole ya buɗe mata kofa ta fita, shi kuma ya gargame ya ce sai ta yafe mashi. Faɗi yake yi. "Dan Allah kada ki je ki faɗawa su momma, zan buɗe maki nawa rigar nima ki rama ba shikenan ba?". Ya faɗa yana kallan face ɗinta. Kallon uku saura kwata ta watsa mashi kafin ta amsa da. "To ni ce maka aka yi ƴar iska ce? Ni ina da mutumci kuma ina da karfi, ba sakaliya irin ka bace". Ta kai karshen maganar tare da murguɗa mashi baki. Marairace mata murya ya yi tamkar zai yi kuka, ƙasa ya kara yi da murya sosai kafin ya ce. "Ni dai please don't let anybody to know kin ji? Ki yafe mun ba zan kara taɓawa ba"...... Tsalle ta yi ta dire kafin ta ce. "Okey dama kana da niyar sake taɓawa kenan ko?". A hanzarce ya girgiza mata kai kamar wani yaronta, bawan Allah yanzu ma fa kuskure aka samu ya taɓa ɗin ba halinsa bane, ashe bala'i ya taɓowa kansa bai sani ba. Harara ta dallah mashi kafin ta fara zagaye shi tana binsa da kallon up and down. "Shekarunka nawa ne?". Ta faɗa tana dawowa ta gabansa, irin ita babban nan. ...... "19 to 20 haka". Ya bata amsa a sanyayye, shi dai damuwarsa kada ta faɗawa su Jaish, idan zata tsaya a iya faɗawa momma shikenan bashi da wata matsala, amma idan su Jaish suka ji me za su ce? Kuma wlh yasan idan ba lallaɓata ya yi ba kowa a cikin kingdom ɗin nan sai yasan ya taɓa mata kirji ta ja mashi raini har wajensu Omaid, to wai shi me ma ya kaisa ne?. "19 to 20 years? Ashe ma baka wani fini sosai ba, amma ya aka yi ni jaruma ce kai kuma rago? Kenan girman banza ka yi?". (Allah mai iko🤔 wani abu sai Mahreeh, shekaru 7 fa ya bata amma wai bai wani fita ba saboda shegen san girma.) Kai ya girgiza mata a karo na biyu. "Ni ba rago bane, kawai bana iya jure rashin lafiya ne, kuma ciwon nawa yana da tsanani sosai ba yadda kika zata ba, ban da ɓangaren ciwo babu wani abin da ba zan iya yinsa tamkar jarumi ba". Tun da ya fara magana idanunta a kan kyawawan roman lips ɗinsa irin na Auta........ "Kai ko lips ma baka da shi, ji bakinka kamar babu saboda ƙanƙata". Tana magana tana binsa da irin kallon da take yi wa su Abu a kauye. Shiru ya yi dan bashi da abin faɗe, tun da ance bashi da baki ai dole ya yi shiru....... "Buɗe mun rigarka nima in taɓa shikenan sai in yafe maka". Ta faɗa tana kai kallanta ƙasa, ita kanta abin ya yi mata nauyin da ba zata iya haɗa ido da shi ba idan zata aiwatar da hakan, amma saboda tarihin rayuwarta bata yafiya yasa ba zata iya haƙura ba sai ta rama..... Shi kuwa, wani irin sanyi ya ji a ransa, ko ba komai zata rufa mashi asiri idan ta rama, dan haka a hanzarce ya ɓalle butiran rigar ya cire mata, kanta a ƙasa taki ɗagowa saboda iskanci ya cika ƙwaƙwalwarta, kai wlh Mahreen sai kun sakata a addu'a, ni kam Princess Teema ta fi karfina!. Zare white singlet dake ciki ya yi, ya rage daga shi sai short, sannan ya ce mata. "To ga shi na cire maki ki rama". Tamkar zai yi kuka ya yi maganar. Slowly ta fara kallansa daga ƙasa tana haurawa sama. Ƴar ƙaniya sai da ta ji wani irin mummunar faɗuwar gaba, kirjinta ya bada bugun dum!!! Dum!!! Saboda kirjin nasa da ta gani, a tinaninta bashi da karfi, sai kuma ta kalli yana da murɗaɗɗen jiki, ta yi mamaki sosai, amma fa ta kasa iya yin sama da kallonta, a iya kirjinsa ta tsayar da idonta, dik rashin kunyarta ta ji shakkar haɗa ido da shi at this moment. "Taɓa ki rama to". Ya sake faɗa idanunsa a kanta, ko kaɗan bai ji burgesa da take yi a da ya ragu a ransa ba, sai ma karuwa ya yi, yana mugun san confidence ɗinta da tsayawa a kan maganarta idan ta yi. Babu kunya ba tsoron Allah ta ɗago hannunta na ta kerma ta nufi kirjinsa da shi da nufin ta taɓa ita ma ta rama. The way tana matsar da hannunta garesa, the way hannunta yana tsananta kerma, amma dik da haka ta danne, ta nufesa. Ya zuba mata idanu kawai yana jiran ta aiwatar da nufinta ya mayar da kayansa. Tana gab da taɓa shi sai ta dakata tare da fashe mashi da kuka mai ɗan sauti. Ɗan zaro idanunsa kaɗan ya yi, a rikice ya fara tambayarta lafiyarta kuwa? Me kuma ya sake samunta?. Kin kula shi ta yi, ta cigaba da kukanta. Matsawa kusa da ita sosai ya yi ya hau rarrashi, yarinya sai kace mai aljanu, shi yanzu to me ya yi mata da take kuka. Yana can yana tinanin me ya yi mata sai jin voice ɗinta ya yi tana cewa. "Saboda kasan ba zan iya ramawa bane yasa ka ce in taɓa nima, wlh to Allah ya isana kuma ban yafe ba.........". Cikin ɗaga murya ta yi maganar. Gudun kada tasa a gane halin da suke ciki yasa ya yi gaggawar janyota jikinsa ya rungumeta, muryarsa har tana kerma wajen cewa. "Please kiyi shiru, zan yi dik abin da kike so, amma please ki yi shiru kin ji?". Kin kula shi ta yi tana cigaba da kukanta. Damuwa da tashin hankali yasa ya yi gaggawar kamo hannun nata ya ɗaura a saman kirjin nasa dai'dai nipple ɗinsa, a rikice ya ce. "To ga shi nan yanzu ai kin taɓa kin rama, dan Allah ki yi.......". Kasa iya kai karshen maganar ya yi sakamakon idanu da ta wurgo mashi, ga shi suna kusa kusa da juna, ta bushe mashi tamkar wadda aka zarewa ruhi, ƴar ƙaniya ta ji ta taɓa kirjin maza, tuni bakin nata ya mutu, kukan ma ta nemesa ta rasa. Ya ɗan tsorata ganin yadda ta kafesa da ido bata wani motsi, a rikice ya kai hannu ya fara jijjiga kumatunta yana ambatar sunanta. Ina bata motsa ba, a nan ya fahimci sume mashi a jiki ta yi, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya rage tsawonsa ya ɗauketa zuwa saman bed ɗinsa, sai faman nisawa yake yi. Ya tsira daga bala'inta!! Yana kwantar da ita aka fara knocking na door ɗin nasa, wani irin fargaba ya ji, gabansa ne ya yanke ya faɗi, murya na rawa ya tambayi wanenen? Daga waje Omaid ya amsa mashi da shi ne. Ai sake rikicewa ya yi, abin da yake gudu ne yake shirin faruwa, wato kannensa su kama shi da ita shikenan girmansa ya zube. Rasa me zai cewa Omaid ya yi, ga shi bai isa ya hana shi shigowa cikin ɗakin ba. My people's ko kuna da wani abin cewa? Ko kuna da dabarar da zaku faɗawa guyson ya yi dan ya tsira daga Omaid ya gane suna tare da Mahreen?. To idan kuna da shawara ku yi gaggawar bashi kafin in dawo daga Black world. 🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥 Washegari da safe, sanye take cikin jelly dreass launin pink, ta yi masifar kyau, ta ɗaure haɗaɗɗen gashin kanta, da karfi da ya ji Sweetie ta koyi yawo babu ɗankwali, aka ce zama da maɗauki kanwa shi ke kawo farin Kai. Tsaye take a tsakiyar bedroom na Ronnie, kyawawan kafafunta na sanye cikin flip floor launin white color, ɗan bakin nan nata ya sha lips balm sosai, sai wani sheki yake yana wani ɗaukar hankali, sai launin dark purple lips ɗin nata ya kara turuwa sosai, idanunta sun kara kyau tamkar ta sanya kwalli alamar tana cikin farinciki sosai kenan. Ronnie dake zaune a tsakiyar bed ɗinsa sanye da pj's dress a jikinsa ne ya harbeta da wani ɗan ƙaramin throw pillow yana faɗin. "Ba zan barki ba, sai kin faɗa mun shirinki". Yana jefo mata pillown ta yi gaggawar juyowa haɗe da buɗe tafin hannunta, take magic ɗinta ya fita ya daki pillown, kai tsaye ya koma ya daki face ɗin Ronnien. Ƙayataccen murmushi ta saki kafin ta ce. "Alhaki cuicuyo, yanzu dai pillownka ya koma kanka". Tana magana tana kara faɗaɗa murmushinta, wlh sai ka ji ba zaka taɓa gajiya da kallanta ba matuƙar tana wannan sanyayyar murmushin nata. Shi kansa Black Tiger bai san ɗauke idanunsa daga kanta idan tana yi, shi ma dai Ronnie yana kyatsawa sosai, tana bashi a jikinsa. Cikin zafa ya miƙe tare da dirowa kasan bed ɗin. Da gudu ta watsa ta nufi waje tana faɗin. "Idan ka isa ka kamani, in ka kamani zan baka satar amsa"....... Tsayawa ya ɗan yi tare da riko waist ɗinsa da hannayensa dikka biyu, a ɗan kule ya ce. "Is better for you da ki tsaya ki faɗa mun, in ba haka ba in na kamaki i will give you a hot punishment"...... Tana ƙoƙarin buɗe kofa ta amsa mashi da. "Fara kama ni ɗin tukunnan before you think about the hot punishment da zaka yi mun ɗin"........ "Kin rai'nani ko? Yau Allah ba zan barki ba". Ya kai karshen maganar tare da bin bayanta da gudu. Tini ta buɗe kofar ta yi waje tana dariya tana kara faɗin maza ya zo idan ya isa. A gaggauce Black Tiger ya matsar da su daga gaban mirrornsa, dama su yake kallo, wani irin farinciki yake ji idan yana kallansu, amma kuma baya san su kama shi yana kallonsu, in dai yasan za su zo bedroom ɗinsa sai kuga ya fiske kamar bai san da su a empeir ɗin ba, alhalin munahiki ɗan air daɗin ganinsu yake ji, har da wani pretending ya yi gaggawar barin gaban mirror ya dawo tsakiyar bedroom ɗin nasa, sanye yake da bathrobe, linƙaya fa zai je yi a cikin karamar pool ɗinsa dake sama, amma da yaga suna dirama sai ya tsaya kallansu. Da gudu Sweetie ta faɗo cikin bedroom ɗin nasa tana dariya tana kara faɗin Ronnie ya zo in ya isa. Da gudu shi ma Ronnie ya faɗo ɗakin yana faɗin Allah sai ya kamata yau, dan dole ya gwada mata akwai banbanci tsakanin mata da maza, ta ce idan bai kamata ba shi rago ne, dan haka shi ba rago bane dole ya kamata. Bayan Black Tiger ta zo ta tsaya tana haki tana faɗin. "Yi sauri ka zo, gani a bayan big bro kuma our shield". Wani irin Black Tiger ya ji a ransa, kenan Sweetie tana yi mashi kallan shi garkuwansu ne, bango majinginansu? To in dai haka ne meyasa zai rinƙa cutar da ita? Meyasa ba zai ɗauketa kamar Ronnie ba tun da ita ma ta ɗaukesa yaya tamkar yadda Ronnie ya ɗaukesa?......... Da gudu Ronnie ya nufota, a guje ta fara kewaye Black Tiger yana binta tana tikar dariya tana kara tunzura shi a kan ya zo ya kamata. Sosai hakan ya yi wa Black Tiger daɗi, sai yake jin kamar dikka kannensa ne na jini, farincikin da suke ciki suna nishaɗi ya nishaɗantar da shi shi ma matuƙa. Sosai ta yi gudu har ta fara gajiya, kun san kewaye take yi hakan ya haifar mata da ganin wani irin jiri mai karfi yana ƙoƙarin ɗibanta. Ronnie ya lura da haka sai ya ce. "Now is my time, zan kamaki in kuma hukuntaki".... Tana haki sama sama ta ce. "Ba zaka taɓa kamani ba saboda big bro ba zai bari ka hukuntani ba". Tana kai karshen maganar ta tafi zata kifa dai'dai lokacin ta zago ta gabansa. Cikin zafa yasa hannu ɗaya ya riko wuyar rigar jikinta, tafiya ta yi gabaɗaya ta faɗa jikinsa tana numfashi sama sama, ta sanya hannunta ɗaya a saman shoulder ɗinsa ta wajen damatsan hannunsa tana cigaba da yin haki. Da gudu Ronnie ya zago da nufin ya kamata, tin bai ƙariso ba ya ce. "Nakamaki ai yanzu". Ya kai karshen maganar haɗe da sa hannu zai capko shoulders ɗinta. A miliyan Black Tiger ya ɗagata da hannu ɗaya ya juya da ita alamar ba zai bari Ronnie ya kamata ɗin ba kenan........... Sosai Ronnien ya yi muguwar mamakin ganin hakan, bai taɓa tinanin hakan ba ko a mafarki, kenan Black Tiger ya shigar mata faɗa? Ya jefawa kansa tambaya, lokaci guda kuma ya ji wani irin sanyi a ransa, dan hakan ma wata nasara ce a garesu, tabbas ko a iya haka big bro ya fara canzawa, Allah mai iko. Amma saboda su cigaba da samun nasara sai bai nuna mamakinsa a fili ba, sai ma ya haɗe fuska tare da cewa. "Kenan haɗe mun kai zaku yi? Yanzu big bro kenan ka shigar mata? Wannan ojoro ne, kuma ban da ojoro, ka bari kawai in kamata". Ya kai karshen maganar tare da sake kai mata capka zai kamata, sake juyawa da ita Black Tiger ya yi, saboda sun tafi da imaninsa har bai san time da ya ce. "Ba zan bari ka kamata ɗin ba". Wlh bai ma san ya yi wannan magana ba. Daga ita har Ronnien sai da mamaki ya daskarar da su na ƴan dakiku, kai abin al'ajabi wai ba zai bari Ronnie yakamata ba, like wow abin ya ƙayatar ba shakka, da alama yau Allah ya amsa addu'ar Sweetie yasa zuciyar big bro ta fara sauyawa, dama ta jima tana yi mashi addu'a, kullum tsakar dare sai ta tashi ta yi nafilfili ta yi mashi addu'a, har ta fara cire ran addu'arta zai amsu, ashe kuwa yana hanya. A cikin zuƙatansu gabaɗaya suka shiga faɗin alhamdulillah, alhamdulillah sun nuna godiyarsu ga Ubangiji matuƙa, yau big bro nasu ya shiga maganarsu, kai ba zasu taɓa manta wannan rana ba. Cigaba da binta Ronnie ya yi yana san kamata mamaki kamar zai kasheta, shi kuwa Black Tiger ya cigaba da kaucar da ita yana faɗin Ronnie ba zai kamata ba, tin da ta kasance mai rauni tana da shi wanda shi kuma ba mai rauni bane. A takaice dai sai da Ronnie ya gaji lilis ba tare da ya iya kamata ba, shi kuwa Black Tiger yana tsaye waje guda ya yi nasarar wahalar da Ronnie har ya gaji ya durkushe a wajen yana haki yana faɗin. "Wannan ojoro ne, ba dan kai ba big bro Allah da na kamata, kuma ni ban yarda da wannan ojoron ba, amma ba komai zamu haɗe anjuma ne ai". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Bari in duba parents na Floris, zan je in apologies, zan ɗaukota in dawo da ita, i really missed her to much". Lokaci guda face ɗin Black Tiger ya sauya jin kalaman kanin nasa, dan yasan me zai biyo baya idan Ronnie ya je can, ga shi bashi da hanyar dakatar da shi. Shiru ya yi bai iya dakatar da shi ba har ya fita daga bedroom ɗin har lokacin yana haki kaɗan kaɗan. Yana fita Black Tiger ya sauke Sweetie, cikin gaggawa ya wuce ya nufi wani siririn stair case dake cikin bedroom ɗin ya haura sama in da pool ɗinsa take. Da kallo Sweetie ta bi bayansa tana jin wani irin fargaba, gabanta na faɗuwa sosai. Almost 5 mins tana tsaye a wajen, daga karshe ta yanke shawarar bin bayansa, domin tana san yin magana da shi. Ba tare da tsoro ko tinanin menene a saman ba ta yi maza ta haura ita ma...... Like wow, wani irin yanayi ta tsinci kanta a lokacin da ta haura saman nan, domin kuwa wani haɗaɗɗen waje ne wanda sai ka yi zatan ba a duniya kake ba, blue light ne a wajen, tamkar ɗaki haka aka yi shi, kazalika blue light ne a cikin kwayayen bulb dake cikin pool ɗin, hakan yasa suka sanya ruwan ya koma blue sosai, ga wani kamshin dake tashi a wajen, abin dai ba'a magana. Yana tsundume a cikin ruwan, ya lume gabaɗaya jikinsa, iya kansa ne kawai a waje, ya ɗaga kan nasa sama haɗe da lumshe kyawawan shape eyes ɗin nasa tamkar mai tinanin wani abin. Tabbas ya ji motsinta, amma bai ji kamar zai buɗe idanunsa ba. Cikin natsuwa ta tako ta nufo in da yake, a gabansa ta tsugunna tare da kurawa kyakkyawan face ɗinsa idanu. Lokaci guda ta ji wani irin shock a jikinta, ko idanunsa a rufe wlh kwarjini ne da shi sosai........ "Please ka faɗa mun menene ya samu Floris?". Ta jefa mashi tambayar cike da fargabar amsar da zai bata, kirjinta har wani dukan uku uku yake yi, Allah Allah take yi kada ya ce mata wani abin mummuna sosai ne ya sameta, har yanzu dai basu bata mutuwa ba. Shiru bai amsa ba, kuma bai motsa daga in da yake bama, saboda kwata kwata baya san tina zancen.......... "Tabbas akwai abin da kake ɓoye mana, tabbas akwai abin da ya samu ƴar uwarmu, tabbas naga hakan a cikin idanunka a lokacin da Ronnie ya ce maka zai je dubata, please ka sanar damu menene ya sameta ko zamu ji sanyi a ranmu". Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa da kwallah, saboda tabbas taga rashin jin daɗi a kwayar idanunsa a lokacin da Ronnie ya ce zai je ya duba iyayen Floris ya basu hakuri. Nan ma dai shiru bai yi magana ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa. "Shirunka ya fi komai kona mun rai, shirunka dai'dai yake da amsar cewa Floris is not alive, shin haka ne?"...... Ai bai san lokacin da ya tsinci kansa da girgiza mata kai alamar a'a ba haka bane, kuma ya yi hakan ne gudun balain da zasu tayar mashi ita da Ronnie, yau ita ce ranarsa ta farko da ya fara yin karya a kan wani abin dan gudun samun matsala da su. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta canza murya zuwa na nuna kauna da soyayya ta ce. "Har ƙasa na ji sanyi a rai'na, to faɗa mana in take?". Ta kai karshen maganar tana kallan zara zaran eyelashes ɗinsa da suka kara tsawo sosai suka kara bayyana saboda rufe idanun nasa da ya yi. Ɗan zuba masu idanu ta yi na ƴan sakanni kafin ta mayar da kallonta izuwa saman kyakkyawan wuyansa, a hankali ta mai da kallonta izuwa kan lallausan gashin kansa da yake bakin kirin yana wani curlyn, kaɗan ya kwanto mashi ta gaban goshinsa ya manne saboda ruwan da ya jiƙasa, hakan ya kara fito da tsantsar kyansa. Kan kyawawan romance pink lips ɗinsa ta dawo da kallonta, shiru ta zuba masu idanu tana jin tamkar tasa hannu ta taɓa su saboda sun haɗu matuƙa, sun kuma tafi da ita. ........ A hankali ya waro idanunsa wajen domin ya kalli meyasa ta yi shiru a wajen. Yana buɗe idanu ta yi saurin dawo da kallanta kan idanun nasa, zubawa juna idanu suka yi babu ko kyaftawa, kamar waɗan da suka afka duniyar tinani. Cikin dabara ta kai hannunta cikin ruwan ta ɗan ɗebo, saboda tsabar shegen tsokana ya yi mata over yarinyar nan, cike da tsoron abin da zai iya aikara mata a face ɗinsa ta watsa mashi ruwan. Wani irin lumshe idanu ya yi, har cikin ransa ya ji saukar wannan ruwa, sai ya ji tamkar ba ɗaya yake da ruwan da yake ciki ba, ji ya yi wanda ta watsa mashi ɗin tamkar na daban ne. Slowly ya sake waro idanun nasa a kanta haɗe da ɗan zarosu kaɗan. Tsorata ta yi, a tinaninta hukuntata zai yi, dan haka sai ta yunkura ta miƙe da gudu zata bar wajen. Cikin zafa ya sanya hannunsa ya capki dogon gashin kanta ba tare da yasan ya yi hakan ba, ai tafiya ta yi gabaɗaya ta afka cikin ruwan ta faɗi saman lion chest ɗinsa. Lokaci guda ya ji wani iri a jikinsa, while ita kuma tsorata ta yi sosai, da kyar ta iya janyo numfashinta ta cigaba da tafiya daidai, murya na kerma ta fara faɗin. "Wayyo na shiga uku, am so so sorry big bro, na tuba ba zan sake ba". Tana magana tana zazzare idanu haɗe da ƴan kame kame, take ta yi kasa da hannunta izuwa cikin ruwan ta ɗaura saman flat tummynsa. Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, slowly ya ɗan yi blinking eyes ɗinsa ya sake tsaidasu a kanta, while ita ma shi take kallah, a yanzu ma sake tsare juna da kallo suka yi, take ya fara hasko wasu sirrika na musamman dake tattare da kwayar idanunta, kamar dai akwai wani buri da take san cinmawa a rayuwarta. Ita ma kuma karanta kwayar idanun nasa take yi, saboda taga alamar akwai abin da yake hidden masu. Tsit wajen ya yi, sun mace da kallan juna, cikin salo ya ɗan motsa romance lips ɗinsa da nufin ya yi mata magana ba tare da ya kawar da kallansa daga kanta ba, sai ta rigasa da cewa. "Please our big bro ka faɗa mun ina Floris take?". Ta yi maganar tana ɗan hauro da hannunsa izuwa saman lion chest ɗinsa ta cikin ruwan kenan. Babu riga a jikinsa fa, daga shi sai Swimming short, ya cire bathrobe ɗin. Tamkar wanda bakinsa yake yi mashi ciwo, baya san motsasu haka ya ɗan motsasu wajen cewa. "She died". Idanunsa a cikin nata ya yi maganar....... A razane ta wani irin zaro mashi eyesball ɗinta tamkar kwayar zasu firfito su faɗi ƙasa, tana ƙoƙarin yin magana cike da tashin hankali ya yi saurin sanya hannunsa ya rufe mata baki, a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a ta yi shiru. With his lion voice ya fara yi mata bayani wanda bai bawa kowa damar sauraron abin da yake faɗa ba, sai da ya kai karshe daga nan ga rufe maganar nasa da cewa ta san yadda zata yi da Ronnie kada ta bari ya birkice sosai, ta taya shi ɓoye mutuwar Floris har zuwa wani ɗan lokaci, kada su sanar da Ronnie. Ai yadda kuka san ruwa ya cinye Sweetie, ta kasa motsawa daga in da take, tamkar wadda ta sume, idanunta a kansa kuma babu ko kyaftawa. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 51 🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥 Kurawa face ɗinta idanu ya yi, sai yau ya tabbatarwa da kansa cewa Sweetie kyakkyawar gaske ce, ta sume mashi amma idanunta a buɗe, ɗan lumshe idanunsa kaɗan ya yi tare da sake buɗesu a kanta, hannunsa ya ɗago, tafukan hannun nasa ya ware tare da shafa face ɗinta da shi, take ta ja doguwar numfashi, da alama magic ya yi mata ta farfaɗo. Kamar mai raɗa haka ya fara raɗa mata cewa kada ta bar Ronnie ya fahimci abin da ya faru, ta yi mashi dabara, daurewa ta yi ta yi ta mazan cewa sai dai idan shi ma zai yi mata wani alkawari, in ya yi mata hakan ita kuma ta yi mashi alkawarin Ronnie ba zai taɓa shiga wata damuwa ba izinin Allah. Jama'a ku tafawa addu'a, lallai ne addu'a bata taɓa faɗuwa ƙasa banza, sai dai jinkirin amsawa, da izinin Allah addu'ar Sweetie a kansa ta karɓu, black heart ɗin ta fara sassautawa!. Jinjina mata kai ya yi alamar ya yarda da batunta tin ma bai ji wani irin alkawari bane, Ronnie amanarsa ne, kun san da cewa amana mahaifinsa ya bar mashi Ronnie? Kun san da cewa sai da ya rokesa da kada ya bar hawayen Ronnie ya zuba a banza?. Kun san da cewa kafin mahaifinsu ya rasu ya yi wa baban nasu alkawarin in dai yana numfashi to ba zai taɓa barin hawayen kanin nasa ya zuba ba? Shiyasa kuke ga zai iya aikata komai a kan kanin nasa, kuma yana bala'in sansa na haƙiƙa shi ma, ba wai dan iya alkawarin da ya ɗauka bane yasa yake kula da shi, yana kaunarsa sosai. Ɗaga ƴan kafafunta ta yi tana san kai tsawonsa dan ta yi mashi raɗa a kunne, sai dai ina, bata iya kaiwa tsawonsa ba, ya fita nesa ba kusa ba, yana da tsawo sosai. Ganin hakan yasa ya rage tsanwonsa ya ɗan rankwafo kanta, hannu tasa ta saƙalo wuyansa kafin ta gwada sake ɗaga kafa ko zata kai. Sai dai kash bata kai ba, hakan yasa ya ɗagata cak sai saman lion chest ɗinsa, hakan ya bata damar kwanto kanta a saman shoulder ɗinsa, ta kai ɗan bakinta saitin kunnnesa, nan ta fara yi mashi raɗan yarjejeniyar da zasu yi kafin ta yi mashi aikin kula da Ronnie, idan ya aminta tabbas zata kula da Ronnie sosai wajen sanya shi farinciki. Hakika maganganunta sun zo da tsauri, sai dai kuma farincikin Ronnie ya fi mashi komai, kuma babu in da Ronnie ɗin yake samun farinciki na wuce misali face a wajenta, dan haka yazamar mashi dole ya aminta da wannan yarjejeniya in ba haka ba akwai matsala. Shiru ya yi yana tinanin ya amince ko kuwa ya daure ya juri tashin hankalin da Ronnie zai shiga?. A wannan hali Ronnie ya shigo wajen ya samesu, fuskarsa ɗauke da damuwa matuƙa ya ƙariso in da suke. Ai yana sauke kallansa a kan yayan nasa da Sweetie bai san time da ya saki cool murmushi ba, sun yi matuƙar burgesa, da sauri ya tsugunna a gaban pool ɗin, cikin sanyin murya ya ce. "Wow you guy's looks so very cute and amazing"....... Maganarsa ya fargar da Black Tiger har ya yi saurin zare kallansa daga kanta, kamar wani maras gaskiya ya yi saurin saketa ya kuma ɗan yi ƙasa kaɗan ya kara lumewa a cikin ruwan kaman mai san ɓoye wani abin. Ita kuwa, da tsantsar tashin hankalin da take ciki yaki ɓoyuwa a kan face ɗinta ne ta juyo da kallanta ga Ronnie, tamkar zata yi kuka, ta ƙasa yin magana, dan yanzu ganinsa yasa wani irin tausayinsa ya kamata. Take yanayin face ɗin Ronnie ya canza, dan ganinta cikin damuwa bai yi mashi ba, kamar mai tsoronta ya ce. "Lovely sis big bro ya yi maki wani abin ne?". Ya yi maganar yana satar kallan Black Tiger ta wutsiyar ido. Kai kawai ta iya girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba. "Big bro me ka yi wa lovely sis ɗita?". A ɗan shagwaɓe ya yi maganar. Banza da shi Black Tiger ya yi, sai ma ya kara lumewa cikin ruwan, tamkar bai san da su a wajen ba, da alama kuma akwai abin da baya san su gani a jikinsa shiyasa ya yi ƙasa a cikin ruwan........ Ronnie fa ya zo da kokensa ne a kan bai ga iyayen Floris ba, ya tambayi mutanen birnin kuma kowa ya ce mashi bai gansu ba, shi ne ya dawo wajen yayansa da kokensa dan ya nemo mashi su, amma yana tarar da su cikin wannan yanayi ya tsinci kansa a cikin farinciki maras misaltawa. Rarrashin Sweetie ya hau yi yana ce mata ta yi hakuri zai rama mata idan ma yayansa ne ya yi mata wani abin, ita dai da okey kawai ta amsa mashi, amma na ciki kam yana ciki. Sai da ya tabbatar ya sanyata ta yi murmushi, sannan ya juya ya ce da Black Tiger. "Big bro ina iyayen Floris?". Ai Sweetie bata san lokacin da ta ce mashi. "Sun gudu sun bar birnin nan wai saboda big bro ya kona masu ƴan uwa". Ɗan zaro idanu Black Tiger ya yi jin ta fitar masu da hanyar da bai zata ba, dama yana tinanin abin faɗawa Ronnie, gaskiya Sweetie she was very smart, ya jinjinawa ƙwaƙwalwarta wajen iya fito da mafita cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ransa ta sanyaya matuƙa da samun mafitarsu. Shi kuwa Ronnie ido ya zaro, kamar zai ɗaga murya, sai kuma yasa kukan shagwaɓa tare da cewa shi lallai bai yarda ba! Dole big bro ya nemo mashi in da suke, dan shi yana kaunar Floris, yana san ta dawo su cigaba da rayuwa kamar da. Nan ne fa Black Tiger ya samu damar ce mashi zai nemo mashi su soon ya kwantar da hankalinsa, yana magana yana satar kallan Sweetie da ta tsare lip's ɗinsa da kallo. Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke, ya ji sanyi a ransa za'a nemo mashi su. Sweetie ce ta riko hannunsa ɗaya cikin nata, kamar mai raɗa ta ce matso ka ji wani abu lovely bro. Matsar mata da face ɗinsa ya yi yana ɗan murmusawa. Matsowa ta yi dab kunnensa, raɗa ta fara yi mashi tana sakin murmushi,. A hankali hankali murmushin dake saman face ɗinsa ta fara faɗaɗa alamar kalamanta akwai sugar, suna shigarsa yadda yakamata. Satar kallansu Black Tiger ya fara yi yana mamakin irin shakuwar dake a tsakaninsu, a yanzu fa Ronnie ya fi farinciki idan yana tare da ita sama da idan yana tare da shi, abin akwai mamaki. Tsabar daɗi da murnar jin kalamanta bai san lokacin da ya afka cikin ruwan ba shi ma, a jikinta ya faɗa hakan yasa suka yi kasan ruwan, dan bata da karfin ɗaukarsa. Shi dai Black Tiger abin ya birgesa matuƙa, suna kashe shi idan suna tare!. Juyawa Ronnie ya yi cikin sauri ta dawo saman jikinsa, sannan suka ɗago saman ruwa, take ta fara jan numfashi da karfi karfi, saboda ta dannu kam. Riketa Ronnie ya yi yana faɗin ta tsaya ya hura mata numfashinsa dan nata ya daidaitu. Sai dai bai kai ga yin hakan ba take ta dawo daidai tamkar wadda aka yi wa magic, runguneta Ronnie ya yi yana faɗin sorry a gareta. Ɗan rungunesa ita ma ta yi kafin ta amsa mashi da ba komai. Cikin wasa ya ce. "Let play a game". Ɗan zaro idanu ta yi, game kuma a cikin ruwa, ta jefawa kanta tambaya a cikin zuciya. Tana can tana tinani Ronnie ya zaro hanki (handkerchief) daga aljahinsu, dik ta jiƙe da ruwa, ɗaure mata idanu ya yi kafin ya saketa, ya sumbaci lallausan kumatunta sannan ya ce to ta kama shi a cikin ruwan idan ya kirga one to ten. A cikin ranta ta ji da biyu Ronnie ya ce su yi wannan wasa, amma ba zata ki yi ba ko dan alkawarin da ta ɗaukawa yayansa na sanya shi farinciki na musamman, so zata yi dik abin da yake so matsawar bai saɓawa shari'a ba. Cauting from one to ten ya yi kafin ya lallaɓa ya gudu bayan Black Tiger ya ɓuya, sannan ya ce mata let's go. Lalluɓarsa ta fara yi tana tafiya a hankali. Shi ma a hankali hankali ya baro bayan Black Tiger ya matsa ya dawo ta bayanta, ya zamana tana tafiya yana biye da ita a baya, sam bata jisa ba, gabaɗaya hankalinsa a kan Black Tiger, ya tsare yayan nasa da kallo kamar mai nazarin wani abin. Sai nemansa Sweetie take yi tana zagaye cikin ruwan, ga shi ruwan ya fi karfinta, dan har wuya ya kai mata, dan dai ba ruwan gudu bane, da ba zata tsira ba. Ta sha kewaye a wajen bata ji alamarsa ba, dab kusa da Black Tiger ta tsaya, suna fuskantar juna ba tare da ta sani ba, Ronnie na bayansu, a shagwaɓe sosai ta saka kuka tana faɗin. "Ni lovely bro ka zo ka kwance mun wannan abin, ka ɓuya nakasa ganinka..........." Bata kai karshen maganar ba Ronnie ya tureta da karfi ta tafi sai saman lion chest na Black Tiger. Murmushi ya saki kafin ya ce. "Dama a manne da juna na sameku, ni na rabaku, yanzu kuma da zan tafi shi ne na mayar daku yadda na ganku". Yana kai karshen maganar ya yi zafan fita daga cikin ruwan wai dan ma kada Black Tiger ya kama shi, abin gwanin ban dariya kuma gwanin birgewa. Yana fita bai dakata ba ya yi gaggawar barin wajen ya koma cikin bedroom ɗin Black Tiger. Ita kuwa Sweetie ƙoƙari kwace abin dake idanunta ta yi dan ta samu gani, sai dai ta ƙasa, saboda yadda kuka san padlock aka sanya aka datse hanki ɗin, yaki kwancuwa ko kaɗan. (Anya ba Black Tiger ya rike shi ya hana shi kuncuwa ba kuwa? Ɗan duniya ba! Ka gansa kaman wani salihi, ɗan rainin wayo.😅) "Big bro please remove this thing for me". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Kamar babu Black Tiger a wajen, ya yi banza da ita idanunsa a kan face ɗinta, kaman mai nazarin wani abin. Laluɓe ta fara yi tana ɗan tattaɓa jikinsa dan ta tabbatar da yana wajen ne ko dai baya nan, ta yi magana without reply, shi ne take zaton ko dai baya wajen ne. Lokaci guda ya yi wani danko hannunta ɗaya cikin zafa, ba komai yasa hakan ba kuma face a garin laluɓenta take ƙoƙarin sake capke mashi hero kamar dai ta ranar..... Ajiyar zuciya ta sauke jin ya damki hannunta, hakan yasa ta fahimci yana wajen kenan. Can ƙasa ta tsinkayo lion voice ɗinsa yana faɗin. "Na yarjewa yarjejeniyarki, amma kada ki wuce gona da iri". Yarjejeniyar me kuke tinanin ta ce su yi? Sweetie akwai wayo sosai wlh, da alam tarko ta ɗana mashi. "To shikenan na yarda, amma yanzu dai kwance mun wannan abin". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. "Hakan baya cikin yarjejeniyarmu, and ai bani na ɗaura maki ba". Ya faɗa a sanyayye sosai................ Ɗan rainin wayo, so yake ya yi ta kalle mata fuska kada ta san ya kalla, shiyasa ya ce ba zai kwance mata ba, saboda ba kara mun kyau ta yi ba a yadda ruwa ya jiƙata, gashin kanta ya kwanto har face ɗinta, lip's ɗinta sun kara kyau matuƙa saboda ruwa da ya taɓasu, gashin gaban goshinta sun kara kwanciya luff, ko makiyinta ya ganta yasan ta yi kyau over, kuma sai ya shagala da kallonta bare kuma shi Black Tiger da ba kiyayya suke yi ba, bashi da wata matsala da ita, hasalima yanzu yana san ta kasance da su dan ya lura kaso 60 cikin ɗari na farincikin Ronnie yana tattare da ita, so bashi da wata matsala da ita yanzu...... Ni kuwa nace ba dole ta zama farincikin Ronnie ba tun da ta bashi kalmar shahada, ta janyo shi cikin haske, dole ya yi farinciki idan yana tare da ita. "Please mana our big bro, nasan baya cikin yarjejeniyarmu, amma kuma ai akwai batun kada ka bari wani abin cutarwa ya zo kusa da mu ko?". Ta faɗa tana ƙoƙarin kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata. "Wannan ai ba abin cutarwa bane, da na cutarwa ne Ronnie ba zai ɗaura maki ba". Ya yi maganar tare da sakinta. Yana saketa tamkar wadda aka turo haka ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa again...... "Allah abin cutarwa ne shi ma". Cikin muryar kuka ta yi maganar. Banza da ita ya yi, bai da niyar kwance mata, ɗan rainin wayo dan bai gaji da kallan madarar kyan da Allah ya yi mata ba, sai ya fake da cewa ai ba shi ya ɗaura mata ba, dan haka ta nemo Ronnie ya kwance mata, har da dagewarsa irin da gaske yake yi shi fa. Kamar zata yi kuka ta bar jikinsa ta fara laluɓar hanyar fita. Allah ya bata nasara ta samu ta fito, idanunsa a kanta bai hanata ba, haka ta fara laluɓe har ta isa wajen stair case, ga ruwan dake zuba a jikinta, bata san ta isa wajen ba, tana ɗaga kafa ta sauke sai ta tafi gabaɗaya ta yi ƙasa, tin daga kan step na farko ta yo kasa har karshe, dik kuma yana ganinta bai taimaka mata ba, bai kuma yi amfani da magic wajen tsayar da ita ba, ya barta ta isa ƙasa dik ta bubbuge jikinta, har ta dan ji ciwo a hannu. Azaban da ta ji ne yasa ta saki ihu mai sautin da ya ja hankalin Ronnie dake zaune saman sofa yana shan tea mai zafi sosai. Da gudu ya ajiye cup ɗin a saman table dake gabansa ya nufota yana tambayarta lafiya kuwa. Kuka ta saka mashi kawai ba tare da ta yi magana ba, duƙawa ya yi ya ɗauketa cak ya yi waje da ita, har ya canza kayansa izuwa na sport, sarkin san wasanni ba. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya koma da ita, a nan ya kwance hanki ɗin ya yi ta rarrashinta har ta yi shiru, sannan ya ce ta je ta yi wanka ta canza kaya, ba musu ta bi umarninsa. Yau da ta yi wanka irin shigar mutanen birnin ta yi, wato umbrella gown mai maɗauri a tsakiya, ta yi kyau sosai, gashin kanta saboda samun kwanciyar hankali ya kara tsawo sosai, har ya kusa zarce mazaunanta, ya kuma kara tura kala sosai. Kwace saman bed ta iskosa yana kallan chandelier ɗin ɗakin nasa, a gefensa ta zauna, cike da nuna kauna ta ce. "Lovely bro ina san zuwa church ɗinku". Zaro idanu ya yi tare da dawo da kallonsa a kanta. "Mezaki je ki yi?". Ya yi maganar tare da miƙewa zaune suna fuskantar juna. "Babu kawai ina san zuwa ne in gani". Shiru ya ɗanyi kafin ya ce. "To gobe idan kika dawo daga school zamu je a tare by 4:00 ko 4:30 haka". Sosai ta ji daɗin amincewarsa, cike da murna ta matsa ta sumbacesa a kumatunsa, siririn murmushi ya saki kafin ya ce. "Kin san wani abu sister?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata sani ba. Tana ta sakin ƙayataccen murmushi. Kashe murya sosai ya yi kafin ya ce. "Ina san ganinki a tare da big bro, kuna kyau sosai, dan Allah ki rinƙa kasancewa a tare da shi, kinga yanzu kin fara canza mana shi ko?". Shiru ta ɗan yi alamar kamar bata ji daɗin maganar ba, sai kuma ta saki siririn murmushi kafin ta bashi amsa da. "Ina fatan ya sauya, ya canza ya zama musulmi, ina yi mashi kwaɗayin rahamar Allah sosai". Ɗan zaro idanu Ronnie ya yi. "Kina nufin ba kya san yayana? Dik abin da kike yi mashi kawai kina yi ne dan ya musulunta?". Jinjina mashi kai ta yi alamar ba shakka haka ne, sannan ta ɗaura da cewa. "Ko kaɗan babu soyayyarsa a rai'na, soyayar Kamran ce kawai a raina, and na fi jin sonka a rai'na ma sama da yayanka, ina jin yayanka tamkar ɗan uwana ne na jini wanda ina ga hakan ce tasa bana jin sonsa na soyayya a rai'na, kasan wani abu?". Kasa bata amsa ya yi ko ya motsa daga in da yake, ya kafeta da ido mamaki kamar ta kashe shi, shi dik tinaninsa tana san yayansa shiyasa yake tayata yakin neman soyayyarsa, bai san ita wanda take so ma daban ba ne...............Dik da bai amsa mata ba hakan bai hanata cigaba da yin maganar da take da niyya ba. "Yayanka ya haɗa dik abin da kowacce mace zata so a duniya, nasan kasan da cewa komai isar mace idan ta gansa sai ta faɗa mashi, amma ni kaunarsa nike a matsayin ɗan uwa na jini haka, soyayyar Kamran ne kawai a rai'na". Shiru ya yi na almost 3 mins kafin ya nisa, sannan ya saki ƙayatattcen murmushi. "Sister a labarin da kika bani kin ce mun Kamran ma ba musulmi bane ko?"............. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "To meyasa baki taɓa tsayawa ki jajirce a kansa lallai sai ya musulunta ba? Ko shi baki yi mashi kwaɗayin rahamar Allah ne?"....... Shiru ta yi kamar mai tinanin abin faɗe, da alama ya ɗaureta da magana. "Baki da amsa ko? Dama ai ba zaki iya bani amsa ba, amma ni zan baki amsa, dalilin da yasa kika tsayawa big bro kika zage kina san ganinsa a cikin ni'ima ta Ubangiji ba komai bane face so, shi ne wanda kike yi wa so na gaskiya, dik wanda zaki so to a bayansa ne........." A gaggauce ta tari numfashinsa da cewa. "No Ronnie, ko ɗaya ban taɓa san yayanka ba, in dai kaunarsa". Jinjina kai ya ɗan yi. "Kin san soyayya ne ma da zaki iya banbanta wanda kike kauna da wanda kike so?". Ya tambaya kamar shi ma ya san me so ɗin, da dalilin ɓacewar Floris daga garesa ne fa ya fara fahimtar me soyayya, amma har ya fara zaƙewa zai nuna shi ya sani. Da sauri ta jinjina kai kafin ta amsa da. "Niko na san soyayya, soyayya ai ayoyi gareta a cikin Alqur'ani mai girma, idan ka ɗauki suratul Ali Imran sura ta uku aya ya 31 da ɗaya, wanna aya tana magana ne a kan ainahin soyayya ma, wato soyayyar Allah ga bayinsa, sai kuma cikin suratul Ar rum, sura ta 30 aya ta 21, wannan tana magana ne a kan soyayyar ma'aurata wato mace da namiji, kazalika cikin suratul ma'ida, sura ta biyar aya ta 42, nan ma magana ce kan kauna, cikin suratul Maryam, sura ta 19 aya ta 96, Allah yana magana a kan soyayyar da yake sakawa a tsakanin mumunai maza da mata kenan, soyayyar da ta fi kowannen wato soyayyar Allah, Allah ya ambaceta a cikin suratul Ali Imran, sura ta uku aya ta 159, kaga kuwa ni ce na san soyayya ciki da wajenta". To dik wanda ya ce soyayya karya ce ya yi karya, dan soyayya ayoyi gareta a cikin Alqur'ani, so ba karya bace wlh, ni ba dan bani da isasshen fili ba ai da na baku tarihinsa amma ba komai ku tara a littafina na gaba idan Allah ya kaimu da rai da lafiya!. Jinina kai ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Dik na yarda kin karanta waɗan nan, amma baki iya banbanta so da kauna ba, ki yarda kawai". Hararar ta dalla mashi kafin ta ce. "A'a ba zan yarda ba, ni Kamran nike so, babu mai canza hakan". Ya fahimci yarintar ce ta motsa, sannan kuma a gaskiya bata san so da kauna ba abu guda bane, sai ya ce bari ya yi mata dabarar fifikon shekaru. "Na yarda Kamran kike so, kuma zan tayaki yakin nemansa, yanzu abu ɗaya zaki yi mun sai nima na zage mu nemo Kamran". Yana magana yana lumshe idanu alamar barci yake ji. Cike da zumuɗi ta ce. "Faɗi abin da kake san in yi, matsawar bai saɓawa shari'a ba zan yi". "So nike ki ƙara kusanci da big bro, ki rinƙa matsa mashi a kan wasu abubuwa har zuwa mu yi nasara, da zarar mun yi nasara big bro ya musulunta, to zamu shiga neman Kamran, da taimakon Allah nasan ba zamu sha wahalar nemansa ba zamu gansa". Ya kai karshen maganar yana komawa ya kwanta, dan har gyangyaɗi yana ɗaukarsa. Cike da matsuwar san ganin Kamran ɗinta ta amsa da ta amince, kuma zata yi iya ka yinta ko da kuwa zata wahaltu, amma tabbas zata zage. Sosai ya ji daɗin hakan, bai sake furta word ba ya lumshe idanunsa, kan kace me barci ta yi awon gaba da shi. Ita kuma miƙewa ta yi ta sauko ƙasa daga saman bed ɗin, ta nufi wajen books set ɗinsa, wani katan Markus Bible ta ciro tare da wani notebook and pen, saman dining table ta koma ta zauna tare da fara dube duben abin da take da buƙata. AFTER ONE DAY. Zaune Ronnie yake a saman dining dake cikin parlournsa, ya tasa haɗaɗɗun kayan abinci a gaba yana yin breakfast, yana ɗan motsa baki da small chop yana latsa wayarsa, baya san cin abinci ba tare da ita ba, jiranta yake yi ta zo su ci, shiyasa hankalinsa gabaɗaya yake a kan wayar yana ɗan motsa baki. Ya yi bala'in kyau cikin tsantsararren shigarsa na army green shirt and black trouser, ya sanya p-cap a kansa, while kafafunsa suna cikin Crocs launin army green, kyakkyawan white hairn nan nasa ya sha gyara sai kamshi yake tashi yana wani sheki, yau dai babu su earing sosai a kunnensa, dan ya fara rage sanyasu, ya ma cire pil na wajen lips ɗinsa, kazalika ya cire na gaban goshinsa wajen gerarsa, kuma yanzu ya dai'na raba gerarsa gida biyu ta hanyar aske dogon layi a tsakaninsu da yake yi, dik wasu abubuwa da basu dace ba ya bar yi, saura sanya ɗankunnen ne kawai, shi ma yanzu guda ɗaya yake sakawa, ita ma yana fatan dai'nawa, kun san sabo, idan ka saba da abu yana da wuyar bari, shiyasa ••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥 Ya yi nisa cikin abin da yake yi sai ji ya yi an rufe mashi idanunsa ta baya. Ɗan turo baki ya yi kafin ya ce. "Lovely sis zafa ki yi latti, kinga dai almost 7 yanzu"........ Kausasa murya ta yi, ta kwaikwaiyi muryar gardawa wai dan ta nuna mashi ba ita bace, ko iya abin ma bata yi ba, ga murya irin na yara, ta zage ta faɗaɗa makogoro wajen cewa. "Wannan ba lovely sis ɗinka bace, aljana ce". ....... Siririn tsaki ya ja tare da sakin cool murmushi kafin ya ce. "Ai bama ki iya abin ba, da wani muryarki kamar na mage, zo nan ki ci abinci kada ki ɓata mun lokaci hai". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya ɓanɓare hannunta daga face ɗinsa, sannan ya fisgota ta dawo ta gabansa. Ɗaure fuska ta yi tana turo baki, ita a dole ya ɓata mata rai tun da bai bari ta razana shi ba. Tana shirye cikin uniform ɗinta, yau ta sanya lips balm mai ɗan launi mai kuma kyalli, wanda hakan yasa kyallin ya kara kawata dark purple lips ɗinta, sai wani sheki yake yi yana ɗaukar idanu, shi kansa Ronnie sai da zuciyarsa ta amsa ganin laɓɓanta. Sake hannunta ya yi tare da nuna mata saman nata chair ɗin yana faɗin ta zauna ta yi breakfast sauri sauri ya je ya kaita school. Zama ta yi ba tare da ta yi mashi magana ba, wai ta yi fushi da shi. Cikin fushi ta ɗauki chopping stick tare da matsar da plate mai shake da Chinese spaghetti mai ɗan faɗi faɗi haka, an zuba girki a wannan waje, ga wasu dakwalan cinyoyin ƙosassun kaji, sai tashin kamshi yake yi. Yana ta fitar da tiriri kaɗan kaɗan ta sanya chopping stick ɗin ta fara ɗebowa, kaɗan kaɗan ta fara kaiwa ɗan bakinta, amma da yake spagh ne har ya ɓata mata gefe gefen bakinta zuwa kumatunta. Shi ma janyo nasa plate ɗin ya yi tare da ɗauko chopping stick ɗinsa, a hankali ya nannaɗo spagh ɗin tare da kaiwa ɗan bakinsa yana ɗaura phone ɗinsa a saman table ɗin. "Lovely sis today food was so delicious". Ya faɗa ba tare da yasan fushi take yi da shi ba........ Shiru bata amsa mashi ba, sai ma cigaba da danna spagh a baki take yi babu kakkautawa, wai tana turawa dayawa ne dan ya san tana jin haushi, shi kuma bai gane ba. Jin bata amsa ba yasa ya sake maimaita maganarsa tare da dawo da kallonsa a kanta. Tamkar bata a wajen ta yi banza da shi. Cike da mamaki ya ce. "Lovely sis are you okey kuwa? Am talking you refuse to answer me, why?". Cikin sanyin murya ya yi maganar haɗe da alamar damuwa, dan bai ji daɗin hakan ba. Banza ta yi da shi tana danna spagh dole dole, tin na bakinta bai kare ba zata danna wani dan ya fahimci cin takaici take yi.... Shiru ya ɗan zuba mata idanu na ƴan sakanni kafin ya iya fahimtar fushi take yi da shi. Ɗan siririn murmushi ya saki, ya cigaba da kallonta har sai da ta danna spagh a bakinta tana ƙoƙarin nannaɗo shi ta tura gabaɗaya cikin bakinta sai ya yi saurin sanya hannu ya riko bayan wuyanta tare da juyo da face ɗinta ya zamana suna kallon juna, bai bari ta nannaɗe spagh ɗin ba yasa ɗan bakinsa ya fara nannaɗe mata yana ci, ƙoƙarin cinye kayanta ta yi da saurin shi ma ya yi zafin namar ci sosai, sun shagala da rije rijen cinyewa basu ankara ba sai ji suka yi bakinsu ya haɗe da juna, dan sun cinye spagh ɗin gabaɗaya har sun iso junansu ba tare da sun sani ba. Zaro idanunta waje ta yi tana kallonsa, shi kuwa cikin salo ya kashe mata ido guda kafin ya ɗan janye laɓɓansa baya kaɗan yana sauke ajiyar zuciya. Sorry ya furta tare da yunƙurawa zai miƙe ya bar wajen. Cikin sauri ta riƙo hannunsa, a hankali ya juyo da kallonsa a kanta, marairace fuska ta yi kafin ta ce. "Ni ce na yi maka laifi, for give me please". Jinjina mata kai ya yi haɗe da cewa. "Babu komai, ci abinci da wuri mu tafi". Ba musu ta saki hannunsa ta ɗauko chopping stick ɗin ta cigaba da nannaɗo spagh ɗin. Komawa shi ma ya yi ya zauna haɗe da ɗauko nasa stick ɗin suka cigaba da ci a tare. "Lovely bro rufe idanunka in baka wata bazata". Ba musu ya rufe, ɗauko katan cheeseburger da ta fi karfin bakinsa ta yi. "Open your mouth". Ta faɗa tana kallansa. Bai yi tinanin komai ba ya buɗe bakin nasa, dakarkarewa ta yi ta danna mashi burger a bakinsa tare da watsawa da gudu ta yi sama tana faɗin. "Gobe ma ka sake idan na tsorataka kada ka tsorata"..... Ai sai da ya ji numfashinsa ta ɗauke na wucin gadin, da kyar ya iya ciro burger daga bakinsa, dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, da gudu ya miƙe ya bi bayanta dan ya kamata ya rama. Kamar wasu ƴaƴan mage haka suke, basa zama waje guda basu tsokani juna ba, musamman ma ita, kullum sai ya tsokanesa!. Bedroom ɗinsa ya fara leƙawa, bata a ciki, da sauri ya wuce bedroom na yayansa, yana ɗaure fuska a kan yau ba zai kyaleta ba. Sai dai ko da ya shiga bedroom na yayan nasa ma bata a ciki, babu ma kowa, ya ɗan yi mamakin ganin ba kowa. Har toilet ya leƙa bai ga kowa ba, da sauri ya fita ya haura sama izuwa gym area nasu ko ta maƙale a can. Sai dai bata a can ma, yawon nemanta ya hauyi, ton yana nemanta cike da burin ya ganta ya ɗauki fansa, har ya fara nemanta cike da damuwar ina ta shiga?. Wasa wasa har tsawon good 20 mins yana nemanta bai ganta ba. Da sauri ya sauko ƙasa dan ya duba harabar empeir ɗin, hankalinsa ya tashi sosai a yanzu kam, dan yasan empeir ɗin yana da wajaje daban daban, akwai wurare masu haɗari, akwai kuma wuraren da idan ta shiga tabbas ba zata iya fita ba, zama ta iya rasa ranta idan ta shiga, hankali tashe ya bazama nemanta. A dai'dai wannan lokacin ita kuwa tana wata duniya ta daban, dan a lokacin da ta gudu ta haura sama, bedroom na Black Tiger ta nufa, saboda ta haɗa da sallama dik ta yi mashi na zata wuce school. Sai dai da ta shiga bata samu kowa a cikin bedroom ɗin ba, sai ta gudu balconynsa dan ta ɓuya a can, nan dai ta ga kamar a nan ma zai iya ganinta, hakan yasa ta dawo ta shiga dressing room, kun san nan akwai drawers da sauransu, so zata samu wajen laɓewa ba zai ganta ba. Sai dai kash, tana shiga suka ci karo da Black Tiger yana sanya kaya, yana tsaye a ta kusa da kofa wajen shoe set ɗinsa dake shirye cikin wasu mahaukatan glasses masu tsadar gaske, wani irin white light ne a cikin glases ɗin nan masu masifar haske da suka haskaka zafafan shoes ɗin nasa, yana san ya yi selecting na wanda zai sa ne, daga shi sai B- short wanda ko haɗaɗɗun cinyoyinsa bai gama kaiwa ba a jikinsa, tamkar dan iya penis ɗinsa aka yi short ɗin, Lion check ɗin nan nasa a buɗe, ya ɗaura wani small white towel a kansa, da alamar yana tsane ruwan dake gashin sa ne. Aikuwa tana shigowa ta sauke kallanta a kansa, while shi ma ya juyo da kallonsa a kanta slowly, ya ji motsi ne yasa ya ɗago. Ai sumar tsaye ta yi, a zahiri kamar shi take kallo, amma kuma ina hankalinta ya yi nisa, kamar wadda aka daskarar!. Shi kuwa kallonta ya fara yi tin daga kan santala santalan cinyoyinta da suke tamkar madara har izuwa saman kirjinta da yanzu suka fara cika pam sosai, yanzu girma ya fara zuwa, matasan tula tulanta sun fara ciccikowa sosai. Ga yanayin uniform ɗin nasu sai dai shiru, kun san ba addini ne da birnin ba, mini skirt ɗin nata ko gwiwa bai rufe ba, a dai'dai tsakiyar tsala tsakan laps ɗinta ya tsaya, daga sama rigar ma dai sai shiru, dan ya kamata sosai, har kana iya ganin shatin tula tulan, sai dai ita tana sanya jacket na school ɗin dan suturta kayanta, amma yanzu dai bata sanya ba, saboda basu kai ga tafiya ba, dama idan zasu tafi ne take sakawa. Jacket ɗin yana parlor tare da school bag ɗinta!. Wlh yau dai sai da ƙwaƙwalwarsa ta amsa, barema yadda yana skin ɗinta wajen cinyarta, tamkar ka latsa jini ya fita, tin ainahi dama babu abin da yake mugu mugun tafiya da shi sama da golden white hair ɗinta da idan ya sha gyara yake wani irin kyalli na musamman, sai ga shi yau ta sake shi ma bata ɗaure ba, dan bata kammala shirin tafiya ba, sai zata tafi school zata ɗauresa. Me kuke tinanin zai faru da dikkansu suka bushe da kallan juna? Waye zai fara dawowa cikin hayyacinsa?. 🔥🔥🔥🔥DUBAI.🔥🔥🔥🔥 Kiran farko na asuba ta farkar da shi daga ɗaddaɗar barcin da yake yi. A hankali ya waro fox-s eyes ɗinsa da suke jajir alamar barci bai ishe shi ba. Yunƙurawa ya yi ya miƙe zaune, jikinsa dik ciwo yake yi mashi tamkar ba lafiya ba, slowly ya waigo da kallansa ta side da take kwance. Ga mamakinsa sai ya ga babu kowa a wajen, wayam, ina ta yi to? Ya gefawa kansa tambaya, sai ya ji tamkar a mafarki ne dama ya kawota bedroom ɗinsa ba a zahiri ba. Miƙewa ya yi jiki ba kwari ya nufi toilet. Jim kaɗan ya fito ɗaure da white towel a kugunsa. D-room ya wuce domin shiri. Sanye da white arabs jallabiya mai bala'in kyau ya fito, sai ya kara fita a ainahin arabs guy ɗin nasa, ya yi kyau sosai, sai tashin kamshi yake yi, yau dai kamar yana ji da mutumci, dan da ya gabatar da sallar rakatainil fajir sai ya ɗauko alkyabba mai shige da na sarauta ya sanya a saman jallabiyar tasa, alkyabba ce ta manyan malamai ba ta sarauta ba, yau kuma ya koma gefensu Abu Abdussalam, wato ya yi shigar manyan malamai, har da rawani ya yi a kansa, ga dikkan alamu daga masallaci zai wuce wani wajen. Bai je ya dubata ba, ya wuce ya fita bayan ya ɗauki wayarsa da car key. Ita kuwa, tsakiyar dare ta farka sai ta ganta a gado guda da shi, shi ne ta lallaɓa ta gudu bedroom nata zuciyarta cike da zargin ko ya yi mata wani abin ne, har da kara duba jikinta da kyau dan ta tabbatar, dik da bata ga wata alama ba, amma tabbas tana zargi dole ya yi mata wani abin, hakan yasa ta ji ta kara jin haushinsa sosai, ta tsanesa, dan tana ganin kamar halinsa ne neman mata kenan, amma fa ba har kasar zuciyarta ta yarda da cewa yana neman matan ba, kawai dai kokari take yi ta tirsasa zuciyar tata wajen ganin ta ɗaura mashi tuhuma dole dole. Ko da ta koma bedroom ɗinta bata iya rintsawa ba, ta kwana cikin tinani da zilimin abin da yake faruwa, zuciyarta ya rinƙa ingizata a kan meyasa zata yarda ta zauna a gidan da daga ita sai namijin da ba muharraminta ba? Kuma ga abin da ya taɓa shiga tsakaninsu! Ai wannan ita da kanta ta kawo kanta, dan haka koma me yake yi mata ita ma da nata laifin, dan haka kawai ta gudu ta bar gidan nan shi ne mafita a gareta, idan ba haka ba za'a samu matsala, zata tabka danasani fiye da a baya, dan ita wlh babu batun yarda da aurensa a ranta, ba zata taɓa yarda ta auresa ba, Sharifat take yi wa kwaɗayin samunsa!. Da wannan tinani da zulumi ta kwana har asuba, da kyar ta iya tashi ta yi sallah, sannan ta koma ta kwanta, tsawon kwanaki biyu tana ƙoƙarin shirya yadda za'ayi ta samawa kanta mafita ba tare da saninsa ba, dik iya binciken da take yi ta rasa samun mafita, idan ya fita baya nan har bedroom nashi take shiga ta yi ta yi mashi bincike, amma dik ta rasa samun mafita. A ɓangarensa kuwa, yana mamakin wanenne yake yi mashi bincike a ɗaki, dan bai taɓa kawowa ransa zata shiga bedroom ɗinsa bama bare har ta yi mashi bincike, ga shi kuma su biyu ne kawai a gidan, abin da ɗaure kai sosai, bai kawo komai a ransa ba, kuma bai tuhumeta ba, sannan kwana biyun nan yana ɗan busyn da baya samun wuni a gida, kazalika baya samun haɗuwa da ita sosai, wani lokaci kafin ya dawo ta yi barci, kuma yanzu garƙame door ɗinta with key take yi abinta, kun san zuciya da iya sake sake, tini ta saka mata wai idan ta yi barci yana zuwa ya yi amfani da ita, shiyasa ta dai'na yarda ta ci abincin idan ya sayo mata, sai dai ta girka a gidan, dan zuciya ya raya mata ai kila yana sanya mata maganin barci ta sha ya yi amfani da ita, ta dai kasa yarda da shi gabaɗaya!. Yau garin an tashi da hadari sosai, iska mai daɗin gaske ne yake kaɗawa, hadarin ya yi bakinkirin, zaune take a bakin bed ɗinta ta kurawa tvn dake fuskantar balconynta idanu, wata kyakkyawar balarabiya yar jarida ce take ta magana a cikin tvn, da alama akwai abin da yake faruwa, dan news dake fita daga bakinta gabaɗaya maganace a kan rashin zaman lafiya da suka tashi da shi a yau, ta natsu tsit tana sauraron matar. Sanye take da riga da wando arabs dress wanda zaku ga rigar ya kai mata har gwiwa, while wando kuma dogo ne wanda kasansa yake da faɗi. Ta ɗaura silky headband milk color kalar kayan nata kenan a kanta. Ta yi masifar kyau sosai da sosai, fuskarta fayaw, kamar bata da lafiya, mood na face ɗinta looks some how haka. Lokaci guda ta ji kamar a takure take, tamkar dai akwai wanda yake kallanta, hakan yasa dik ta ji babu daɗi, ta jita a tsarge, cike da fargaba gabanta na faɗuwa ta juyo da kallanta a kan kofar shiwowa cikin bedroom ɗin. Tsaye yake ya harɗe hannayensa a saman wide chest ɗinsa tare da ɗan ɗaure angry face ɗinsa, kamar dai shi ma his mood for today isn't good. Bin sexy sleeping dress ɗin jikinsa da kallo ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, gudun kada ya ganota yasa ta yi saurin kawar da kallonta daga kansa, tasan kwararrun jami'ai suna amfani ne da motsi da kuma idanun mutum wajen gano mai laifi ko mai gaskiya, dan haka sai ta yi juriyar zare kallanta a kansa, ba wai dan bata sha'awar ta yi ta kallansa ba, saboda kowa ya gansa sai ya sake kallah. Dan kawai ta kare kanta kuma ta tabbatar da shirinta. TO ME TAKE SHIRYAWA KENAN? HAR DA WANI TA TABBATAR DA SHIRINTA!. Shi kuwa binta da kallon tuhuma ya yi, yadda ya ga idanun nan nata bai yarda da ita ba, dole akwai abin da take shiryawa wanda bai sani ba, dan haka sai ya gyara tsayuwarsa a jikin door ɗin, ya harɗe hannunsa a saman kirjinsa da kyau ya cigaba da binta da kallon dan gane ina ta dosa. Gabaɗaya sai ta tsargu, ita kaɗai sai ta rinƙa sauke ajiyar zuciya tana ɗan dafe kirjinta, sai kuma ta rinƙa satar kallonsa ta kasan ido wanda dik yana kallonta, alamar rashin gaskiya dai ya tabbata kamar yadda yake zargi. "Aesh". Ya faɗa ba tare da ya kawar da kallonsa daga kanta ba. Kin amsawa ta yi, dan tana ganin ko magana ta yi zai gane bata da gaskiya. Nisawa ya ɗan yi kafin ya juya, kamar bai gane komai ba ya ce. "Tin da ba zaki yi mun magana ba to na tafi, zan fita nan da 30 mins, zan dawo da wuri, pray for me". Ya kai karshen maganar tare da barin wajen ba tare da ya sake ɗaure idanunsa a kanta ba. Wani irin daɗi ta ji da ya tafi, da gudu ta diro kasan bed ɗin tana sauke ajiyar zuciya, bukatarta kenan. Kai tsaye kofar ɗakin ta nufo domin ta leƙa shi, ya yi matuƙar kyau cikin wanna dressing ɗin, dama daurewa kawai ta yi ta ki kallansa, tin da ya tafi shi ne bari ta leƙa ta kallesa. Sai dai kash, tana leƙowa suka yi four eyes, dan kuwa ba tafiya ya yi ba, ya ɗan yi baya ne ya tsaya a wajen tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana bin kofar ɗakin nata da kallo, kamar yasan zata zo leƙa shi. Ai suna haɗa ido bata san time da ta kurma ihu ba, saboda ya mugun bata tsoro, bata yi zaton zata gansa a haka ba, ga shi ya ɗan saki manyan idanun nan nasa sai ya yi kama da ya zarosu, hakan ya kara razanata. Abin gwanin birgewa gwanin ban dariya. Da gudu ta juya ta koma cikin ɗakin tana cigaba da kurma ihu. Har da turo kofa zata murza key kamar wata mai aljanu. Hannu ɗaya yasa ya tare kofar ya hanata rufewa. Ai a miliyan ta saki kofar ta koma ciki, ta ji haushin da ya kamata zata leƙa shi, sam bata so haka ba.... Oh su Leesharh ana so ana kai wa kasuwa, wai ita mai amana, ta zage ba zata ci amanar Sharifat ba, to da alama soyayyar Ramish ne zai kasheta........ Suna yi ina shan maltina and exotic mai sanyi......🥱 Turo kofar ya yi ya dawo ciki. Tana tsaye a tsakiyar ɗakin ta yi ƙasa da kai tana kuka. Ko me na kukan kuma?. Oho mata dai. Tsayuwa ya ɗan yi na sakanni a bakin door ɗin, sannan ya taka izuwa ciki, mamakin kukan nata yake yi, amma kuma ya ji daɗi yadda ya gane cewa tana san kallon shi, in bata san shi ba zata rinƙa leƙosa tana san kallonsa idan yana waje ba. A gabanta ya tsaya kafin ya kai hannu ya riƙo hannayenta cikin nasa. Wani irin shock da ta ji ne yasa ta yi saurin ɗago kanta, while kukan nata ma ta ji ya tsaya cak. Ƙasa sosai ya yi da murya kamar mai raɗa, cike da class haɗe da sigar rarrashi ya ce. "Aesh menene abin kuka kuma? Na yi maki wani laifi ne yanzu kuma?". Ya subhanallah, ai yadda ya yi magana yasa bata san lokacin da ta ji gabaɗaya ya kwance mata notikan ƙwaƙwalwa ba, ta ji tamkar ba'a duniya take ba. Rasa abin faɗe yasa ta ce. "Ba kai ne kake ta kallona ba". Ita kanta tasan bata da dalilin yin kukan nata. "Da wani idanu kika kalleni har kika san ina kallanki?". Ya faɗa kamar mai raɗa. Irin wannan kallon nata mai kama da harara mai matukar tafiya da imanin nasa ta bishi da shi kafin ta yi ƙoƙarin kwace hannunta daga nasa tana faɗin. "Ni ban kalleka ba, kuma ka dai'na kallona". Ta kai karshen maganar tare da kwace hannunta da nufin ta bar wajen, tana ɗaure fuska, kamar wata maras gaskiya ta yi saurin kai hannu saman face ɗinta tana goge hawayenta, saboda tsabar karya na zuciyarta har da raya mata nadamar zub da hawaye a gabansa da ta yi, a gaggauce ta nufi toilet dan ma kada su sake haɗa ido. Sarai yana lura da dik wani motsinta, ya tabbata yau bata da gaskiya, akwai abin da ta ɓoye mashi, amma koma menene zai gano ne, binta da kallo ya yi yana mamakin yadda idan tana tafiya surar jikinta yake motsawa cikin natsuwa da ɗaukar hankali. Sai da ta kurewa ganinsa sannan ya juya ya fita zuciyarsa na saƙa mashi abubuwa daban daban a kanta. Shirinsa ya yi tsab cikin tsadaddun kayansa, sannan ya ɗauki car key da wayarsa ya fice daga gidan, tana tsaye a jikin window tana kallansa har ya fita, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, lokaci guda ta saki cool murmushi dan ta kalli yadda ya buɗe gate ɗin, kenan ta samu abin da take so. A gaggauce ta saki curtain na window ta dawo cikin bedroom ɗin, echolac ɗinta ta janyo daga cikin dressing room, jikinta na kerma saboda sauri, please call me hijab ɗinta dake saman bed ta ɗauka, a gaggauce ta nufo stair case, ko tura kofar bedroom ɗin ta rufe bata yi ba, kirjinta sai bugawa yake yi, fargaba kamar zai kasheta, har ta fara haɗa gumi. Cikin sauri ta yi ƙasa, bibbiyu take tsallake stair case ɗin. Tana fitowa harabar gidan har da haɗawa da gudunta wajen isa wajen gate, kamar yadda ta ga ya yi haka ita ma ta yi wajen buɗewa, ta kuwa yi dai'dai, kaifin ƙwaƙwalwarta dai yana taimaka mata wani sa'in. Ta sha madarar mamakin ganin yanayin arear a zahiri, tsayawa ta ɗan yi wajen yin ƴan waige waige tana kallan hamshaƙan gidajen dake wajen, gaskiya sun haɗu iya haɗuwa. Ganin zata iya shekara a wajen ba tare da ta gaji da kallan ƙawatuwar arear da gidajen dake wajen bane yasa ta yi gaggawar jan echolac ɗinta ta kara gaba. Tana tafiya tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Ganin yadda take yi ne ma yasa Officers dake tsaron main gate suka tareta haɗe da tambayarta wacece ita kuma ina zata je?. Bata ɓoye masu wacece ita ba, har da yi masu kwatancen Ramish, ta ce masu ita ce suka fita da shi rannan, Officers ɗin sun ganeta sosai, sai suka saussauta muryoyinsu a kanta wajen tambayarta ina zata je da ta fito yanzu? Kuma meyasa take tafiya take waige waige haɗi da sauri haka kamar zata faɗi? Lastly ina Ramish da ta fito ita kaɗai?......... Yau Ramish ta north gate ya fita, bai biyo ta main ba, shiyasa basu ga fitarsa ba. Murya na rawa ta hau basu excuse ɗin cewa Ramish yana gida ita kuma zata je gidan Abu Abdussalam ne duba ƴar uwarta Sharifat, ta yi maganar cike da fargabar kada ace sun ga fitarsa su gano karya ta yi masu su mayar da ita gida ko su kirasa a waya, jin cewa sun tambayi ina yake neman yasa ta yi zatan kila basu ga fitarsa ba, tin da tasan gate uku ne arear take da shi. Da farko sun so su ɗan yi kokwanto a kan fitarta, amma da suka tina wanenen Ramish sai suka ji ba zasu iya ja da ita ba, kada yazamana shi ya ce ta tafi su kuma su kutsa cikin lamarinsa su ja wa kansu, dan haka sai suka bata hanya cikin mutumci har ma da ɗaga hannu su sara mata, ta ci albarkacin Ramish. A hanzarce ta wuce, bata sake waigosu ba har ta yi nisa, dan tana tsoron waigowa su sake jefanta da wani tuhuma. Tafiya take yi ba tare da ta san ina ta nufa ba, har da saurinta gudun kada ruwan sama ya jiƙata, ta ga garin nata kara narkewa da hadari. Tsawon good two hours tana tafiya, idan ta gaji sai ta zauna ta huta, ta yi tafiya mai nisan da har ta dai'na jiyo ƙamshin arear tasu. Daga karshe da wahala ta yi wahala kafafunta dik sun yi mata tsami sai ta nemi waje saman wani kujera da ake shiryawa a bakin hanya dan jiran ƙananan jiragen ƙasa masu kama da bus ɗin nan, a nan ta zauna tana mayar da numfashi, ga wani irin kishirwa da take ji, saboda tafiyar da ta yi. Tinawa ta yi a ranta yau saura sati a fara azumi, lokaci guda ta ji zuciyarta ta buƙaci da sanin ina zata samu mafaka? Afkawa ta yi duniyar tinani dan nemanwa kanta mafita, bata yi aune ba sai ji ta yi ruwan sama mai karfin gaske ya kece kamar da bakin kwarya, juyawa ta yi gabas da yamma, kudu da arewa babu mafaka a wajen, sai dogayen bishiyoyi dake can nesa da ita, wani irin tsoro ne ya dira a ranta lokaci guda, sai ta ji tamkar ta koma, sai dai kuma ita kanta bata san ta wani hanya ta bi ta zo nan ba, tafiya kawai ta yi ta yi. Wasa wasa ruwa na kara yawaita while gari na kara tsananta duhu, bata da mafitar da ya wuce ta zauna a wajen, dan babu mafaka a kusa. Tana ji tana gani train na farko ya zo ya tsaya a gabanta har tsawon mintuna biyu, a zaton drivern shiga zata yi, suna cika mintuna biyu kamar yadda yake a dokansu drive ya tasheta ya kara gaba. Kazalika train na biyu ma ya zo ya tsaya, nan ma bata iya miƙewa ta je ta shiga ba, dan bata da wajen zuwa. A haka tana zaune a wajen har train huɗu suka wuce, ruwan sama ya yi mata dukan gaske, ga shi ko kaɗan ruwan yaki tsagaitawa, bata san lokaci ba, dan babu abin duba time a hannunta. Ganin ruwan nan bashi da niyar tsayawa kuma cigaba da zamanta a wajen nan ba zai haifar mata da ɗa mai ido bane yasa ta miƙe tare da jan echolac ɗinta ta fara tafiya tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tin tana iya ganin dai'dai har jiri ya fara ɗibarta, har lokacin ruwan sama bai dakata ba, nisa sosai ta yi daga in da take, a daddafe take tafiya kamar mai gocewar kashin kafa. After some hours. Almost 6 hours ana zuba ruwan sama, daga bisani ruwan ta rage zuba amma bata ɗauke dikka ba, irin yap yap yap mai ratsa jiki ya sanya mura ɗin nan shi ne yake cigaba da zuba. Tin daga farkon ruwan nan har karshensa a kanta ya kare, a yanzu an kai gaɓar da ba zata iya cigaba da jurewa ba, tafiya cikin duhun kai yasa har ta fita cikin jama'a bata sani ba. A dai'dai wannan gaɓa ta kasa iya cigaba da tafiya, kanta yana yi mata wani irin azabbabben ciwo mai tsanani, sai kakkarwa take yi, hakwaranta sai ba da sauti mai karfi suke yi, gabaɗaya ta takure ilahirin jikinta waje guda, ga wani irin jiri dake fisgarta da karfi karfi. Dai'dai kasan wani dogon karfen sadarwa wato internet, tana ƙoƙarin ɗaga kafafunta dan ta cigaba da tafiya, sai dai ina, ta kasa, tana ɗaga kafa bata san time da jiri ya fisgeta da karfi har ta saki echolac ɗin hannunta ta tafi gabaɗayanta zata kifa ƙasa ba. Sai dai bata kai kasan ba ya yi gaggawar tarota ta faɗa saman wide chest ɗinsa. Kamar daga sama haka ya faɗo gabanta, yana sanye da waterproof jacket mai girman da ya wuce gwiwansa, ya sanya hular jacket ɗin a kansa, dik da yana sanye da face mask, hakan ba zai hana ka gane angry face ɗin nan nasa a yau ta fi ta kullum kasancewa a ɗaure ba, harta idanunsa sun yi jajir kamar bashi da lafiya, wasu zaratan maza guda biyu ne tsaye a bayansa dikkansu rike da umbrella, ɗaya ya rike mashi ne ya tare mashi ruwa, ɗayan kuma ya rikewa kansa a in da ya biyo bayansa dan su bashi tsaro. Ransa ya matuƙar ɓaci sosai, with his harsh voice ya bawa matashin dake bayansa umarnin da ya ɗauka mashi echolac ɗinta su tafi. Yana gama bada umarnin ya ɗan duƙa ya cicciɓeta sai saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya juya da ita. Bata kara sanin in da kanta yake ba sai da ta farka ta ganta a cikin bedroom, ga wani irin ɗumi mai daɗi dake ratsata, tana ƙudundune a cikin duv mai laushin gaske. Lokaci guda ta ware hancinta ta shaki daddaɗa kuma niimanraccen kamshin dake kai komo a cikin ɗakin, slowly ta fara bin ko'ina na cikin ɗakin da kallo, while tana jin kamar jikinta ba mallakinta bane, dik sai ta ji gangar jikinta tamkar baya a tare da ita. Tana ɗago idanu sai kan drip dake ɗaure a hannunta, zaro eyesball ɗinta waje ta yi dan ta kara tabbatarwa da kanta haka ne. Lokaci guda ta ɗan nisa tare da cigaba da jujjuya eyes ɗinta dan ta tantace a in da take. Sai dai kuma, har ta gama iya kallanta bata iya cinkar a ina take ba, ɗan lumshe idanunta ta yi na ƴan mintunan da ba zasu gaza biyu ba. A hankali ta sake waro idanunta. Ai a miliyan ta zarosu waje ganin shi a tsaye a gabanta, blinking eyes ɗin nata ta yi two time kafin ta tsayar da kallanta cak a kansa, ta tabbata ba mafarki ko gizo bane, shi ɗin ne kenan. Angry face ɗin nan nasa babu alamar wasa kuma babu walwala ko kaɗan, tamkar bai taɓa sanin menene sakin fuska ba, ya sha kunu ya murtuƙe, ko sannu bai ce mata ba, sai dai ya kai hannu ya fara ƙoƙarin cire drip dake manne a hannunta, dan ya kare. Sosai ta sha jinin jikinta, ta tsorata da ganin yanayinsa, muryarta na ɗan kerma ta furta. "Good afternoon Yah Ramish"...... Tamkar mutum mutuminsa ne a wajen ba shi ba, ya yi banza da ita, kamar bai ji ba. Sake shan jinin jikinta ta yi tana zazzare eyesball ɗinta kamar an tare ɓera a tarko. Bata yi yunkurin sake ɗaga mashi gaisuwa ba, saboda tasan confirm ya jita, amsawa ne bai yi niyya ba. Zare drip ɗin ya yi ya ajiye gefe guda tare da juyawa ya nufi waje. Bayansa ta bi da kallo, daga kan yanayin sleeping dress dake jikinsa ta iya fahimtar yanzu dare ne ba rana ba, ta sha mamaki sosai na ganin cewa dare ya yi, ita da ta sume a tsakanin azahar da la'asar, bata ma san kwana ɗaya ya wuce ba, dan tin jiya ta sume, sai yau ta farfaɗo, dan ma Allah ya taimaketa ta samu kula daga hannun Dr Raj da ya dawo jiya, kuma gobe zai koma kingdom of power, wani dalili ya dawo da shi, ba dan kular da ta samu ba ai da ta ɗanɗana a jikinta. (Ina tantamar anya Leesharh bata da kara mun ciki kuwa? Idan ma ba ciki akwai aljanu a kanta gaskiya 😅 kai nama fi zargin cikin ne yake sakata yin abubuwa off head haka.) Wasa wasa tsawon kwanaki biyu Ramish baya kulata, baya yi mata magana baya kuma amsa nata maganar, alamar fa ran maza ya ɓaci sosai, tin bata wani damuwa har abin ya fara taɓata, sai take jin tamkar a rami aka haƙa aka sanyata, dik ta fara fita hayyacinta, tinani kala kala ne cike a cikin zuciyarta, wani lokaci ta ce bari ta same shi ta bashi hakuri, sai ɓangare na zuciyarta ya ce mata waye nata ne shi ɗin da har zata ce dan baya yi mata magana kuma baya amsa nata maganar zata damu? Shin sun haɗa dangi ne? Mijinta ne? Ko ubanta ne? Uwarta ne? Ko yayanta ne? Waɗan nan tinane tinanen su suke sanyawa ta ji ba zata iya tinkararsa ta bashi hakuri ba, ga shi kuma zuciyarta ta kasa jurar rashin maganar nasa, tana jin kamar ta fasa ihu. Har jikinta ya warware shi yake cigaba da kula da ita, time na shan magani da ya yi zai zo ya bata, idan ya fita ba zata sake ganinsa ba har sai zai sake bata wani maganin. Ko abinci ba shi yake kawo mata ba, wata dattijuwa ce take kawo mata, kuma idan ta yi wa dattijuwar maga sam bata amsa mata, abin ya dameta sosai, ga shi ba gidansu da ta sani ya dawo da ita ba, wannan gidan kam ma gabaɗaya ta rasa gane kansa, ko ta leƙa ta window ba abin da take gani face pool dake ta baya da basket ball area da gine ginen dake waje, abin ya jefata a ruɗani sosai matiƙa. Uhm bata san cewa ita ce kawai makaminsu guda ɗaya da suke da shi dan isa ga masu nikaf ba, tsaronta da lafiyarta abu ne mai matuƙar muhimmanci a garesu, shiyasa ma ya canza masu gida, ya kawota waje mai tsaro sosai, damuwarsa yanzu ta samu lafiya ya samu hujjojin dake hannunta ya fara gabatar da aikinsa. Yau takama Friday, zaune take a saman dadduma bayan ta yi sallar isha'i, ta yi shiru tana askar, amma tinaninta dik yana a kansa, yau ta kai har kololuwa sosai. Good 30 mins ta ɗauka a zaune a saman daddumar tana addu'ointa kafin nan ta miƙe, jiki dik babu kwari ta nufo bakin bed ɗinta da hijabin a jikinta, yau ko lunch bata yi ba saboda damuwa a kansa. Dik halin da take ciki kuma sarai yana sane, dan ya dasa mata Camera a cikin ɗakin, haƙiƙa ya ji babu daɗin kin yi lunch da ta yi, amma ya danne ya cigaba da harkokinsa. Tana zama a bakin bed ɗinta sai ga dattijuwan ta kawo mata abincinta kamar yadda ta saba, haɗaɗɗen abinci mai rai da lafiya, sai tashin kamshi yake yi, tsohuwar ce mai girka mata. Sosai ta yi mamakin ganin lunch da ta kawo Leesharh bata ko taɓa shi ba, kamar yadda ta ajiye babu abin da ya motsa shi daga wajen, amma kasancewar Ramish ya ce ko word ɗaya kada ta yarda ya haɗata da Leesharh ɗin yasa bata tambayeta meyasa bata yi lunch ba? Sai kawai ta kwashi kayan abincin ta wuce ta fita bayan ta ajiye mata dinner ɗinta kenan. Dogon tsaki Leesharh ta ja bayan fitar tsohuwar, sannan ta dallawa kayan abincin harara tamkar su suka yi mata laifi. A dai'dai lokacin da take wannan abin sai da ta so sanya Ramish murmushi, saboda yana kallanta, dan dai bai iya murmushin bane da yau sai ya yi. A ransa ya ce ko me dinner ɗin ya yi mata take harararsa kuma? Yarinya sai faɗar bala'i!. A fili kuwa cigaba ya yi da feshe jikinsa da daddaɗar perfume ɗinsa, yana shirye cikin kayan barci, kwanciya zai yi idan ya je ya bata drugs ɗinta ya dawo. Ita kuwa, gyrawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike da tinaninsa, tana jin tamkar ta tashi ya je bedroom ɗinsa ta sanyasa a idanunta ko zata ji sanyi. Amma girman kanta da rike amanar Sharifat yasa ba zata iya ba, a haka ta daure ta lumshe idanunta alamar barci take san yi, ba zata ci dinner ɗin ba kenan. Da kwanciyarta bai fi five minutes ba sai ga shi ya shigo bedroom ɗin bakinsa ɗauke da sallama ƙasa ƙasa. A hanzarce ta miƙe zaune idanunta a kansa, shi kuwa ya ɗaure angry face ɗinsa sosai, yana tafiya cikin natsuwa. Kai tsaye gaban bed ɗin ya nufo, bai ko kalli in da take ba ya hau ɓalle drugs ɗinta yana miƙa mata a kan ta karɓa ta sha. Ƙin karɓa ta yi ta tsare shi da kallo, ya san me take yi wa dan haka sai ya zuba drugs ɗin a saman wani small plate dake wajen, sannan ya ɗauko ruwa ya buɗe mata bakinsa, ya ajiye mata su ready kafin ya juya ya nufi hanyar fita abinsa, wato idan ta ga dama ta sha, in kuma bata yi niyya ba sai ta barshi ko ohonsa, ai jikinta ne zai gaya mata. Anya ba dan ma babynsa yasa yake damuwa da ita ba kuwa?. To mu je dai zuwa. Ganin fita zai yi yasa ta yi gaggawar miƙewa tsaye, muryarta na rawa ta ce. "Yah Ramish dan Allah ka tsaya ina san yin magana da kai". A tsorace ta yi maganar, dan tana fargabar abin da zai iya faruwa a tsayawarsa ko buɗar bakinsa. Tamkar ba da shi ta yi magana ba, ya cigaba da tafiyarsa. Ai a miliyan ta watsa da gudu ta tare gabansa, har sai da ya ji wani irin shock jin yadda ta yi gudun, ya ɗan ji fargabar kada ta faɗi. Meyasa ya damu da ita haka? Meyasa kuma yake kula da ita har haka? Meyasa baya san wani abin ya taɓata ko kaɗan ne? Akwai ayar tambaya fa a lamarinsa!. Ƙara ɗaure fuska sosai ya yi, ya haɗe gerar sama da ƙasa, kwata kwata yaki yarda ya kalleta, with harsh voice ya ce. "Bani hanya in wuce!"....... Marairace fuska sosai ta yi, tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Ramish dan Allah ka yi hakuri, na san na yi kuskure, amma na tuba ba zan sake ba!"........ Ƙara daure angry face ɗin ya yi, murya a kausashe ya ce. "Kuskure?! Da wani abin ya same ki shi ma zaki kirasa da kuskure ne?! Kin san risk da kika gefa kanki damu bakiɗaya a ciki kuwa? Kin san yadda ake farautar rayuwarki kuwa? Kin san halin da kike ciki kuwa? Kin san matsayin lafiyarki a wajena kuwa?!". Tin da ya fara magana idanunta a kansa, bata taɓa ganin ya yi magana cikin zafa har haka ba, hasalima baya ɗaga murya a magana sai yau, da alama ta yi babban kuskure ne ba karama ba. "Ka yi hakuri, wlh ba zan sake ba ko da sunan wasa?" Cikin marairacewa sosai ta yi maganar. Nisawa ya ɗan yi, yadda ta marairace murya tasa ya ji wani irin a cikin ransa. "Shin kin san mutanen da suka biyoki daga fitarki har izuwa in da kika je kuwa? Kin san rayuwarki tana gab da zuwa karshe a lokacin da muka isa gareki kuwa? Ko kin ɗauka na damu ne saboda ciwon da kika jama kanki na ruwa da ya dakeki?". Ya kai karshen maganar tare da kai hannu ya damkar rigar jikinsa, karfi yasa wajen tsaga rigar gida biyu, jifa ya yi da ita gefe tare da sanya hannun nasa ya yi mata nuni wide chest ɗinsa da gabaɗaya yankar wuka ne a wajen, sai dai ya sha treatment sosai, almost yanka 4 masu zurfi ne a wajen, ga ɗaya a saman shoulder ɗinsa wajen damatsan hannunsa. "Diba abin da kika ja mun, ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu wani maganar ake yi a kanki ba wannan ba, kin yi zatan saboda abin da ya faru a tsakaninmu ne yasa na ɗaukeki daga gidan uncle? To idan ma haka kike zata kin yaudari kanki, ina san ki san cewa a gidan uncle rayuwarki cike take da barazana, ko kin yi zatan ban san attacking ɗinki da aka yi a ɗakinku daren ranar bane? Dik ina sane da komai, that's the reason why na ɗauke ki daga gidan, amma dik baki yi tinanin komai ba kika sa kafa kika fita". Cikin ƙunan rai ya yi maganar!. Ta bashi haushi sosai!! Wani irin zaro idanu ta yi a lokacin da ta ga yankar dake jikinsa, ta tsorata sosai, ashe yana kan gaskiya fushin da yake yi da ita, ashe ta tabka babban kuskure na fita da ta yi ba tare da izininsa ba, yanzu ta ja mashi ciwo, ta kuma ja dole ya canza masu gida, ta ja mashi abubuwa da daman da bai bayyana mata ba, ciki har da rasa abokin aikinsa da ya yi, sun kashesa, sun zo harbinza da bindiga ba tare da saninsa bane babban yaron nasa ya tare masa, harbin ta same shi Allah ya yi mashi cikawa, dik a bayanta da suka bi, da ita za'a kashe Allah yasa bai ajiyeta ƙara zube ba, dik motsinta yana sane da shi, lokacin da ta fita daga gidan watch dake hannunsa ta buga mashi alarm na an buɗe gate na gidan, Allah yasa bai yi nisa ba shi ne ya juyo ya dawo, dan in baku manta ba yana fita ba'afi da 10 mins ba ta fita ita ba, so bai yi nisa da ita ba, da yana nesa ma ai da ta jima da mutuwa. Shi da farko ma bai yi zatan ita ce ta fita ba, ya yi zatan ko wasu ne suka shiga cikin gidan, sai da ya juyo ya dawo, can ya hangota a hanya tana tafiya!. Lokacin da ya biyo bayanta ya so ɗaukarta tin time da ta fita arearsu, amma sai ya lura da wata black car dake biye da ita a baya, hakan yasa ya kira babban yaronsa da ya zo da wata mota mai tinted su bi wannan mota. Mutanen dake bibiyarta sun cigaba da binta suna san ta matsa daga idanun mutane su ɗauketa su aiwatar da nufinsu a kanta, shi ma kuma ya cigaba da binsu dan ya kamasu, abin da yasa bai yi gaggawar bayyana ya kamasu ba shi ne dan bai san su nawa bane, watakila bayan wannan mota akwai wani a ɓoye bai sani ba, hakan yasa suka cigaba da binsu da taƙa tsantsan. Lokacin da ta fita daga cikin mutane sai suka yi ƙoƙari kamata, amma sai suka ga kamar asirinsu zai iya tonuwa, wannan dalilin yasa sai suka yi yunƙurin harbinta daga ɗan nesa da ita kenan, a zuwan idan suka harbeta sai su gudu kawai, Allah yasa Ramish ɗin ya fita shi da yaronsa suka tinkaresu, a nan suka yi wannan faɗa har suka jijji mashi ciwo, suna tsaka da faɗar ne ɗaya ya zari gun zai harbi Ramish kenan babban yaronsa ya tare suka fasa mashi ƙwaƙwalwa, haƙiƙa Ramish ya ji zafin mutuwan yaron nasa, saboda sun haura sama da shekaru 7 suna a tare, sun saba kaman ƴan uwa. Waiwaye adon tafiya🔥 Ina ranar da suka je wajen cin abinci a tare da shi har aka yi ta yi masu hotuna? Waɗan nan hotuna su suka baza media har masu nikaf suka san in da suke, a take suka tura mutane suka biyo bayansu, a nan ne suka rinƙa bibiyarsu har suka ga arear da suke, shi ne suka cigaba da gadin fitowar Leesharh ita kaɗai, sai a wannan lokaci Allah ya basu dama, to kun ji a ta yadda suka yi suka san in da suke har suka bi bayanta. Ta shiga tsananin tashin hankalin da yasa gabaɗaya ilahirin jikinta ya fara kerma..... "Yah Ramish ka yi hakuri, kwata kwata ban kawowa rai'na akwai abin da zai iya faruwa dani dan na fita ba, ina mai baka hakuri kuma ina mai jajanta maka a kan rashin da ka yi". Tana magana idanunta suna ciccikowa da kwallah, haƙiƙa ta ji babu daɗi matuka a kan abin da ya faru, hannunta na kerma tana san taɓa ciwon nasa ta kara bashi hakuri, dik ta bi ta ruɗe kamar wata zararriya. Kan kace me hawaye sun fara zarya a saman face ɗinta, jikinta dik ya yi la'asariyar jemage. Yana tsaye tamkar wanda aka sassaƙa, bai sake ce mata komai ba. Hannunta na rawa sosai kamar wadda aka sanyawa lantarki, cikin tsananin damuwa ta ɗaura a saman wide chest ɗinsa, hawayen face ɗinta suna tsananta gudu matuƙa. Sai da ya ji wani irin shock a jikinsa jin yadda ta taɓa shi. Slowly ta ɗago da kallanta a kansa, while shi ma ita yake kallo. "Sannu ka ji? Ni na tsani kaina, ban san meyasa a koda yaushe nike aikata irin waɗan nan abubuwa ba, kwata kwata bana amfani da ƙwaƙwalwarta da tinanina, kullum sai na aikata abin da zan zo ina danasani, na shiga uku na, wai menene yake bibiyar rayuwata haka ne? Shin na yi wa wani laifi ne? Wani zunubi na aikata?". In out of control take surutan nata, tana magana tana kara tsananta kukanta...... Lokacin guda tsananin tausayinta ya mamaye zuciyarsa, hannu yasa ya riko hannunta dake saman kirjinsa, muryarsa a ɗan sarke ya ce. "Ya isa haka, komai da ya faru ya rigada ya wuce, je ki yi dinner ki sha magani sai ki kwanta ko?". Kai ta fara girgiza mashi tana wani irin kuka irin wanda zuciyar mutum yake a kusa ɗin nan.. "i can't eat anything Yah Ramish, na tabka babban kuskure, ni ban san menene ma ya shiga kai'na ba, ni mahaukaciya ce kawai wanda bata da tinanin kanta, kullum cikin jefaka a cikin masifa nike, na tsani kai'na". ..... "Aesh! Stop saying all this, ke yarinyar kirkice mai zuciyar zinari, dik abin da kike aikatawa rashin samun ishasshen ilimi ne da kuma ƙarancin shekaru ga rashin natsuwa da kwanciyar hankali, amma tabbas ke yarinyar kirkice, ke ɗin jaruma ce, ba kowace mace zata iya kwatanta abubuwan da kika yi ba, cikin mata dubu da wuya a samu goma da zasu iya abin da kika yi, mahaifinki fa suka kama, amma dik da haka kin jure kin ce ba zaki yi masu aiki ba, Allah zai kula da babanki, In Sha Allah babu abin da zai same shi, zai dawo gareki cikin aminci". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar.......... "A'a Yah Ramish, ni mahaukaciya ce kawai, kuma zan tabbata a haka tin da bana tinani da ƙwaƙwalwata". Tana magana tana girgiza kai, tamkar wadda ta zauce, ta fita a hayyacinta sosai!. Ya lura da ta ruɗe dayawa, dan haka sai ya jata a jikinsa tare da ɗaukarta suka koma bakin bed ɗin, cikin sigar rarrashi ya rinƙa lallaɓata har ya samu ya shawo kanta ta natsu, da kansa ya janyo mata dinner ɗin ya ce ta ci, bata musa mashi ba ta fara ci kamar yadda ya buƙata. Binta da kallo ya yi yana jin wani irin yanayi a tattare da shi har ta kammala cin abincin, ta ci sosai saboda tana jin yunwa matuƙa, and tin da ta fara cin abincin kanta a ƙasa, taki yarda su sake haɗa idanu. Bayan ta kammala ya bata magani ta sha, sannan ya umarceta da ta kwanta sai da safe. Ba musu ta kwanta, ya rufa mata bargo kafin ya miƙe ya nufi waje. Har ya kai tsakiyar bedroom ɗin ya tsinkayo voice ɗinta tana faɗin. "Yah Ramish forgive me please, i made a big mistake that word can't explain, na tuba ba zan sake ba". Ba tare da ya juyo in da take ba ya jinjina mata kai da to, sannan ya ce. "Have a wonderful sleep and sweet dreams". Yana gama faɗa ya yi waje da sauri. Shiru ta kwanta tana tinanin irin balai'n da ta rinƙa jefasa a ciki, yakamata a yanzu ta tsaya mashi ne, ta taimaka mashi dan ya kama waɗan da suke farautar rayuwarsa. Da wannan tinani a ranta barci ɓarawo ya saceta sai sauke ajiyar zuciya take yi. In short a cikin kwanaki biyu sun samu fahimtar juna da jituwa, sai dai dikkansu sun ɗan ja baya da juna, shi saboda abubuwa ne da suka yi mashi yawa, ita kuma saboda kare amanar Sharifat, dan ta ji a ranta kamar ta fara jinsa a cikin zuciyarta, shi ne sai ta ja baya da shi, tana gudun abin da zai rinƙa haɗasu waje guda, wannan tsohuwa dake kawo mata abinci ita ta cigaba da kula da ita, ko parlour bata fita, kullun tana ƙunshe a cikin bedroom tana kallo, wani lokaci ta yi karatun Alkur'ani mai girma. Wannan kenan a Dubai, bari mu leƙa KINGDOM OF POWER kuma mu ga me yake wakana. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥 52 Zama mai matuƙar muhimmanci yau King yake gabatarwa tare da dikka wakilan fada ta dattawa a cikin zauren majalisar tattaunawar cikin fada, yau magana ce ta musamman wanda hakan yasa suka haɗu a zauren Majalisar tattaunawa dake cikin wajen. Sannan yana da manyan baki daga kasar Iceland, ya saukesu a masaukin baki na cikin fada, suna cikin meeting sai sun kammala zai saurari bakin nasa. A cikin zaman da suka yi ɗin sun tattauna batutuwa masu muhimmanci sosai da abin da zai kara ciyar da mulkinsu gaba, abin da zai kawar da dik wani abin da zai kawo masu tangarɗa or tseko, sannan suka tattauna batu a kan zalincin da Queen Zarina take yi wa jama'arta, nan ma suka tsayar da matsayan yakarta su kasheta kawai a halin yanzu kowa ya huta, sai a canza tsarin mulkin masarautar tata izuwa ta addinin musulunci. Batu kan Spender ma ya ratso ta cikin tattaunawar nasu, sannan batu a kan cin amana ma ya ratso, saboda harta manyan wakilan fada ɗin ma yanzu King ya fara zarga, bcos yana mamakin yadda za'ayi su yi magana a tsakaninsu kuma ace Zarina ta samu labari, abin yana bashi mamaki, yanzu ya fara yarda da zancen Ramish na ce wa kada ya yarda da kowa har su uncle Abbas ɗin ma, dan haka ba komai ya tattauna da wakilan fada ɗin ba, ya bar wasu batutuwa a ransa da nufin zai yi shawara da Smart and Ramish. A cikin wannan zama dai Aunty MieMie tana ciki, sannan Akka ma ta halacci zaman a matsayinta na Queen mother, yana da kyau Momma ta halatta ita ma, saboda ita ce ainahin sarauniya, matar da sarki ya fi so ya fi ji da ita ita ce babbar Queen ba wai uwargida ko ta tsakiya or amarya ba, babbar Queen yana ta'allaka ne a kan yadda sarki yake santa, ya kuma aminta da ita. So a matsayin momma na babbar Queen ya ci ace anyi wannan zaman da ita, amma King ya ce a'a baya da buƙatar hakan, saboda bala'in kishi irin nasa, yana daga cikin dokikin da ya zartar a kan kingdom ɗin, wato hana matansa fita, hana su zuwa fada, hanasu zuwa dik wani taron meeting. A wannan zama dai King ya sakowa su commander Zafar zancen auren Auta, har da commander a taran, dan ya warware sosai, shi kansa Hoorain ya warware har an sallamesu, yana room ɗinsa yana karasa jinya manne da waya a kunne yana bayin ruwa wa flowernsa. Wani irin faɗuwar gaba commander ya ji a lokacin da ya ji batun auren, amma sai ya danne, domin ya nunawa King ne Hoorain ya rabu da auta, a zahiri kuma ni da ku mun san ya kasa iya tinkarar Hoorain da batun su rabu ɗin, so ya barsu suna cigaba da soyayyarsu, ya shararawa King karyar sun rabu, to yanzu ga shi King ya zo da babban al'amari mai girma, wato auren auta. Shiru ya yi yana tina lion ɗinsa, Allah sarki maraya bawan Allah. Shi kuwa King cigaba ya yi da cewa. "Jibi za'a ɗaura auren, abin ya zo ne ba shiri cikin gaggawa, dan haka a tsananta tsaro sosai a cikin masarautar da kewaye, sannan a shirya gagarumin bikin da ba'a taɓa yin irinsa ba, muna tashi wannan taro a turawa manya manya sarakunan nan gabaɗaya gayyata, wannan nauyi ya ta'allaka ne a wuyarka aminta". Ya kai karshen maganar yana bin amintan da kallo. Cikin girmamawa ya risinar da kai haɗe da cewa ya karɓi umarni. Dawo da kallonsa a kan commander King ya yi. "A tsananta tsaro sosai, sannan ka shirya dakaru yadda yakamaya domin ana gama bikin nan da kwana biyu zaku shafe Zarina daga doran duniya, zalincinta ya kai matakin da babu gargaɗi ko ɗaga kafa, mun daka mata warning har ya fi sau uku, dan haka mun cike ƙaida, a rufe babinta kawai!!". Jinjina kai commander ya yi, cikin girmamawa ya karɓi umarni, sai dai fa kowa a cikin wajen yasan commander ya canza, ya shiga cikin yanayi lokaci guda. Sarai King ma ya lura da canzawar, amma sai ya yi tamkar bai gani ba, ya cigaba da jawabinsa da irin tsare tsaren da yake da ɓuƙata a gidan, gagarumin biki za'a gudanar, bikin ƴar Auta guda! Dole sai an shirya, za'ayi taran da ba'a taɓa yi ba. Har aka tashi wannan zama commander bai sake cewa uppan ba, ya risinar da kansa ƙasa yana sauke numfashi a hankali hankali, a ransa yake faɗin ba zai iya sanar da Hoorain ga abin da yake wakana ba, dan za'ayi babban tashin hankali sosai. Ko da ya koma ɗaki ya samu Hoorain bayan an tashi zaman, mannne da waya ya iskosa, hakan yasa jikinsa ta kara mutuwa, cikin gaggawa ya juya zai fice daga ɗakin. Hoorain ɗin ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa. "Abbo Gimbiya tana gaidaka". Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, cikin sauri ya nufi kofar fita. "Abbo Gimbiya zata yi magana da kai". Hoorain ya sake dakatar da shi. Zuciyarsa tamkar zata fashe, hankalisa a tsananin tashi, ba dan ya so ba ya juyo ya dawo, wayar ya karɓa tare da mannata a kunnensa. Tsaresa da kallo Hoorain ya yi yana nazarin fuskar mahaifin nasa, take ya fahimci akwai wani abin dake damun baban nasa. "Abbo barka da safiya". Daga can Auta ta faɗa, sai sakin murmushi take yi, tana zaune daga ita sai wani simple gown mara nauyi da ya tsaya mata a iya gwiwa, hannun rigar ɗan siriri kamar na vest, ta ɗaure throw pillows guda biyu a saman laps ɗinta, tana zaune bakin ruwan da dolphins ɗinta suke ciki, sai janta da wasanni suke yi, amma taki kulasu. Ita kuwa Pretty sarkin sakalci da shiririta tana sama tare da Smart, taki yarda ta rabu da shi, dan tsoro, dik in da zai je kafarta ƙafarsa, yanzu haka yana sama gabaɗaya yana gym, ita kuwa tana zaune saman chair tana kallansa, dan dole Smart ya fara yin sabo da ita, yanzu har yana jinta a cikin ransa, kun san idan mutum yana yawan zama a tare da kai, dole yau da gobe ka fara jinsa a cikin ranka. "Barkanki dai Gimbiya, fatan kina lafiya ya shirye shiryen azumi?". Commander ya tambaya yana ɗan juyawa, dan baya san kallan da Hoorain yake yi mashi, yana tsoron ya fahimci wani abin, bai san tini ya harbo jirginsa ba. "Abbo ina nan lafiya, na yi kewarku sosai, ina san dawowa ko dan na ganku". Ta faɗa cike da zumuɗi. Rasa abin faɗe commander ya yi, dan gabaɗaya hankalinsa baya jikinsa, to kawai ya iya ce mata, nan ma sai da ta kara maimaita maganarta a zuwan bai ji me ta ce da farko ba. Tin bata yi sallama da shi ba ya miƙewa Hoorain wayar ya yi gaggawar ficewa daga ɗakin. Manna wayar a kunne Hoorain ya yi kallansa a kan Abbon nasa, a hanzarce ya ce. "My princess zan sake kiranki anjuma, yanzu bari in ɗan yi wani abin". Cike da muradin san bin bayan Abbonsa ya ji meke damunsa ya yi maganar....... Kai ta fara girgiza mashi tamkar tana a gabansa. "No my Hero, ni ban yarda ba, kwata kwata fa ko two hours muna waya bamu yi ba, ni dai Allah a'a, ka bar dik abin da zaka yi ɗin sai anjuma, now is my time". Nisawa ya ɗan yi. "Ai ko iya wannan shagwaɓar ta isa tasa dole na in ƙasa iya katse kiran, Hoonairata kina narkar mun da zuciyata da shagwaɓarki". "Uhm uhm ba na ce kai ma ka mun kaki ba, naku sa yin fushi da kai, haka jiya na ce ka mun murmushi ka ce baka iya ba ko?". A shagwaɓe sosai ta yi maganar. Komawa ya yi ya kwanta, salanta yasa ya manta da yana san bin bayan Abbonsa, ɗan mirginawa ya yi ya kwanta ruf da ciki, cike da tsantsar madarar kaunarta ya ce. "Ban iya bane ne, amma kema kin san da na iya dole zan yi maki, but ki koya mun yadda ake yi zan yi maki". In a low voice sosai ya yi maganar, kamar wani yana yi mashi laɓe..... "My Hero ni nasan ba zaka taɓa iya yi ba, ɗan garama shagwaɓar kila zaka iya kwatantawa"......... Murya kamar yana cikin mayen madarar kauna ya ce. "To mu yi video call sai ki koya mun shagwaɓar, zan yi maki, kece fa, ai dolena in yi". Bin kayan jikinta da kallo ta ɗan yi kafin ta ɗan turo baki kaɗan. "My Hero ka bari zuwa dare ko anjuma sai mu yi video call ɗin, yanzu babu k........". Ƙasa ƙarisa maganar ta yi, saboda ta ji nauyin ce mashi babu kayan arziki a jikinta, kuma tasan idan ta faɗi hakan ma kishinsa ne zai motsa ya yi fushi, dan shekaran jiya da suna waya ya jita tana magana da Robbot mai kawo abinci a take a wajen ya ce mata wanene, da buɗar bakinta sai ta ce mai girki ne, aikuwa taga kishi, dan cikin ɓacin rai har mantawa ya yi ya daka mata tsawar a kan me zata yi magana da mai girki namiji? And babu masu girki mata ne sai maza? Take ya hau ya fara masifar da bai san ya iya ba, ya kuma ya manta cewa princess ɗinsa ce, kishi ta rufe mashi idanu. Da kyar ta shawo kansa, da kyar ta samu ya ɗan sassauto har ta sanar da shi Robbot ne ba mutum ba, dik da haka ya ce baya san ta rinƙa magana da shi, ai namiji ne koma Robbot ɗin ne, dole ta yi alkawarin ba zata sake ba, ta kuma bishi da love word masu zafi, a takaice dai a wannan lokaci bai iya yin soyayyar ba, dik da kalaman da ta zuba mashi, ransa ya rigada ya ɓaci sai kawai ya ce mata sai anjuma, ya katse kira ya zauna yana huci shi kaɗa. Wannan dalilin yasa bata ce mashi babu kayan arziki a jikinta ba, dan kishin zata motsa, zai ce akwai maza a gidan, tasan rigimarsa bata karewa a kan kishi, har yau idan ya kirata sai ya ce ina wannan Robbot ɗin, kuma yana tambaye fa kawai dan ya ji shin tana kusa da shi ne ko dai ta yi nesa da shi kamar yadda ya ce mata, kai Hoorain ba dai kishi ba, ko da yake jinin Modarawa haka suke dikkansu! Balai'n kishin tsiya daga mazan har matan!. Kamar zai tambayeta meyasa bata san su yi video call a yanzu, sai kuma ya basar da cewa. "To shikenan Allah ya kaimu, ki gaida mun da Pretty and Yah Omerish". Da okey ta amsa mashi kafin ta ce. "To ka bani na barci". Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke har sai da ta jiyo shi kafin ya manna wayar da ɗan bakinsa ya bata sumbata. Ɗan lumshe idanunta ta yi tamkar da gaske ya yi wa kumatunta, a hankali ita ma ta bawa wayarta sumbatar, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, har a ransa ya ji kamar da gaske ta yi mashi, ya ji daɗi sosai. Da kyar ya iya katse kiran, ya jima a kwance kafin ya tashi da kyar ya bi bayan Abbonsa. A ɓangaren King kuwa, shirye shirye suka fara yi babu kama hannun yaro, suna gama zama yasa Momma ta kira Smart ta bashi umarnin a kan ya dawo da Auta, nan da gobe su dira a kingdom of power, sai dai King ya ce kada su kuskura su sanar da Smart ɗin auren Auta za'ayi, a ɓoye mashi sai ranar ɗaurin aure ya ji a masallaci, ita ma Auta a ɓoye mata sai an ɗaura auren sannan a bayyana mata, a dawo da ita ta shiga dilka da halawa game da kunshi da sauran gyare-gyare.... Kam bala'i, lallai King ya shirya da zafansa, wato sai an ɗaura aure zasu sani, tab akwai cakwakiya. Momma ta ji zafin hakan, amma yazamar mata dole ta bi umarnin King, dole su hakura. -------------------------------------------------🔥 Rasa mafita yasa shi nufar kofar da nufin ya buɗe kawai. Sai addu'a yake yi Allah yasa ba shigowa ciki Omaid zai yi ba, ga shi ya cire kayan jikinsa, ga mace kwance a saman bed ɗinsa, me za'a zarga kenan? Ya gefawa kansa tambayar. Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka yasa hannu ya buɗe door ɗin. Suna haɗa ido Omaid ya ce. "Yah Omar barci zaka yi ne?". Ai bai san time da ya gyaɗa mashi kai ba, alamar e barci zai yi. "Dama na zo mu yi hira ne fa, yau na ɓata da Obaid, amma tin da barci kake ji no need, bari in je wajen Momma kawai". Kara langwaɓar da kai guyson ya yi, ya ƙara shagwaɓe fuska alamar da gaske barcin yake ji. A hankali ya jinjina kai yana ƙaƙalo hammar dole. Juyawa Omaid ya yi yana yiashi good night. Ai yana barin wajen ya mai da kofa ya garƙame tare da juyawa da gudu ya koma cikin ɗakin, saman gadan ya haye ya zauna tare da buga uban tagumi tana tinanin meyakamata ya yi ne?. Nan fa ƙwaƙwalwarsa ta bashi amsar ya bari sai dare ya yi sosai, kowa ya yi barci sai ya mayar da ita bedroom ɗinta. Na'am ya yi da wannan shawara, sannan ya fara binta da kallo, gabaɗaya ta tafi da tinaninsa, bare ma ɗan bakin tsiwar nan tata, ga shi ɗan ƙaramin amma sai iya fito da magana. Hannu ya kai saman ɗan bakin nata ya ɗan ja da ɗan karfi kafin ya ce. "Masifaffa kawai!". Ya yi maganar idanunsa a kan yatsun hannunta dake zara zara ƴan sirara. Haka ya yi ta bi yana karewa surar jikinta kallo har dare ta tsala, sannan ya miƙe ya zura jallabi a jikinsa. Ya nufo waje, sai da ya gama leƙe leƙensa ya tabbatar babu kowa, sannan ya zo ya ɗauketa ya mayar da ita bedroom ɗinta. Wani irin ajiyar zuciya ya rinƙa saukewa time da ya dawo bedroom ɗinsa, saman bed ya haye da nufin ya yi barci, yau ko sleeping dress ba za'a saka ba, sai dai kuma barcin sam sam taki zuwa, tinaninta ne kawai fal a cikin ransa har kusan asuba, yarasa dalilin dayasa yake tinaninta sosai haka. Daga karshe dai ya miƙe ya ɗauro alwala tare da hayewa saman dadduma ya fara nafilfili tin da kyan Mahreen ya azalzali zuciyarsa ya hanasa rintsawa. -----------------------------------------------🔥🔥🔥 Ko daga ina ya koyi yiwa mata wanka? To dai yau ya yi wa Mahnoor wanka, kuma da kansa ya bata kayan da yake so ta saka, sannan ya rungumeta suka kwanta a tare. Zuciyarsa fara tas yau, ya yi barci mai shegen daɗi, ita ma ta yi barci mai shegen daɗi, yau gata ga Hammanta. Washegari da safe, bayan sun yi sallar asuba dama sun koma barci, karfe 7 ta farka, cikin sanɗo ta kwaci kanta daga garesa, a hankali ta sauko kasan bed ɗin, kai tsaye ta nufi waje, bedroom ɗinta ta koma, alkyabbarta ta ɗauko ta ɗaura a saman kayan jikinta, cikin sauri ta fita ta nufi bedroom na momma, wai dan ma kada momma ta gane a tare da mijinta ta kwana, irin ta nuna a part ɗin momma ta kwana, dan sun yi da momma ɗin a kan ba zata koma wajen Jaish ba sai ya zo ya bada hakuri, shi ne wai zata yi wayau. Zaune ta isko momma a saman King sofas set masu bala'in kyau na cikin bedroom ɗinta, hannunta rike cup na cappuccinon tana sha. Binta da kallo ta yi, sosai Mahnoor ta shiga shakku da kame kame ganin irin kallon da momma take binta da shi. Daurewa ta yi ta kariso gabanta ta tsugunna dan ta kwashi gaisuwa. Still binta da kallon mamaki Momma take ta yi. "Ina kwana Momma?". Shiru momma bata amsa gaisuwar ba, wani irin faɗuwar gaba Mahnoor ta ji, addu'a ta shiga yi Allah yasa ba fushi Momma take yi da ita ba. A dai'dai wannan lokacin Omaid ya shigo, a kusa da Momma ya ƙariso ya zauna. Yana sauke kallansa a kan Mahnoor ɗin ya ce. "Momma wannan mahaukaciyar fa?". Shiru dai Momma bata tankasu ba, kallanta a kan Mahnoor babu ko kyaftawa, kuma ba kallan tuhuma take binta da shi ba face kallan mamaki, abin abin dubawa ne!. Zama Mahnoor ta yi a kan kafafunta, ta rasa abin yi, sai kawai ta yi ƙasa da kai tana jiran hukuncin da za'a yanke mata....... Cikin natsuwa ya yi sallama ya shigo, yana sanye da white arabs jallabiya, a kusa da momma shi ma ya je ya zauna, ya wani ɗaure fuska kamar ba Jaish da ya gama holewarsa daren jiya ba, har mamakinsa Mahnoor ta yi, ya wani basar kamar bai ganta a wajen ba, cikin ladabi da biyayya ya ɗagawa Momma gaisuwa. Nisawa ta yi tare da maido da kallanta a kansa, a hanzarce ya yi ƙasa da kai yana ɗan shafa kansa. Amsa mashi gaisuwar Momma ta yi tana kare mashi kallo tamkar mai san gane wani abin. "Momma dama zan je office ne na ce bari mu gaisa first". Ya faɗa yana satar kallan Mahnoor dake kallan ƙasa. Tini Omaid ya natsu tsit kamar babu shi a wajen, da zai yi wa Mahnoor walaƙanci, da ganin Jaish yasa ya janye kalamansa ya bita da ido kawai........ "To shikenan, idan ka je office ɗin ka gyara shirin dake office ɗin naka, dan jeren da ka yi a wajen bai yi ba sam sam". Cewar Momma. A hanzarce ya ɗago ya kalleta jin abin da ta faɗa. Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta yi mashi alama da Mahnoor da ido. Da sauri ya yi ƙasa da kai, kunyar rashin kunyar tasa ta motsa!.. Sallamar guyson ne tasasu kai kallansu a bakin kofa dikka har da Mahnoor ɗin. Ai yana sauke idanu a kanta bai san time ɗin da ya kwashe da dariya ba, har da rike ciki yana duƙawa ƙasa. Kallan mamaki ta bisa da shi, ta rasa gane me yake yi wa dariya. Ai Momma ma bata san time da murmushi irin nasu na manya ya kubce mata ba ganin yadda guyson yake dariya, dama tun ɗazun dariya kamar zai haukatata, da kyar ta iya dannewa ta ɓoye, sai ga shi guyson ya zo ya sanyata murmusawa. Ɗan tsuke fuska Mahnoor ta yi tana bin guyson da kallo. Cikin dariya ya ce. "Aunty Mahnoor wace mahaukaciyar ce ta yi maki wannan make up ɗin? Kin ganki kuwa? Ko aljana Bilkisu sarkin kwalliya bata gwada maki hauka ba yau". Ya kai karshen maganar tare da kara kwashewa da dariya mai sautin gaske. A hanzarce Mahnoor ta kai hannu ta shafi face ɗinta, jin alamar kwalliya yasa ta yi gaggawar ɗago ido ta kalli Jaish. A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta kamar ba shi ba. "Yah Omar kana nufin kwalliya aka mun?". Ta faɗa tamkar zata yi kuka. "Aww dama baki san da kwalliyar ba?". Cikin dariya ya yi maganar!. Takaici kamar Omaid ya kifa mata mari, shi kallan wawuya yake yi mata, ya tsani wawta a rayuwarsa. Miƙewa tsaye ta yi, jiki ma ɓari ta isa wajen guyson. "Yah Omar wlh ban san anmun kwalliya ba, faɗa mun ya na yi?!". A rikice take maganar. Har lokacin dariya taki sake shi. Hannunta ya riƙo tare da janta suka nufi gaban tampatsetsan mirror Momma. A wajen ya tsayar da ita tare da nunata ta cikin mirror da hannu yana cigaba da dariya ya ce. "Look at you". A hanzarce ta kai kallanta kan mirror. Ai a miliyan ta wani irin zaro idanu waje, take kuma ta ji wani irin kunya ya kamata, gabaɗaya face ɗinta uban kwalliya na mahaukata. Kunya tamkar ta natse ƙasa, ta gagara juyowa ta kalli su Momma, sai dariya guyson yake cigaba da yi, ta tsaya a wajen tsit kamar daskararren man shanu. Kallan Jaish Momma ta yi tare da cewa. "Me ta yi maka da ka yi mata irin wannan kwalliya haka?". Ƙasa ƙasa ta yi maganar ta yadda babu wanda ya ji sai ita da shi ɗin. Nan fa shi ma kunyar rashin kunyar tasa ta motsa, ƙasa ya yi da kai, kamar yana tsoron yin magana ya amsa da. "Babu kawai na tina abin da ta taɓa yi mun ne a garinsu". Cike da mamaki Momma ta bishi da kallo. "Kenan yanzu ka tina wacece ita a gareka?". Kai ya ɗan jinjina alamar e ya tina, kuma ba tin yau ma ya tina ba, tin ran zuwan Smart, akwai wani rana da ta shiga ɗakinsa a lokacin yana rike da wayarsa, idan baku manta ba har ya miƙe tsaye yana kallan wayar kuma yana kallanta, tin a wannan rana ya tina rayuwarsu na kauye, ba komai yasa ya tina ba face kallan video bikingsu da ya yi a media, ranar da aka yi bikin in baku manta ba na ce maku akwai masu vivo wato ƴan gayun kauyen da suka rinƙa ɗaukarsu a video, to a wannan rana ya tina wacece ita a garesa ta sanadiyyar wannan video, amma ya yi shiru bai nuna mata kamar ya tina komai ba, sai dai zuciyarsa ta gagara hakura har sai da ya nemi Mahreen ya kalleta ba tare da saninta ba, kaunar Mahreen a jininsa take wlh, dan ita ta fara kula da shi a kauye, kowa ya gujesa ban da ita, shiyasa take ta daban a ransa!. Ganin ta gagara motsawa a wajen ne yasa guyson ya riko hannunta tare da cewa. "Let me escort you ki je ki wanke face ɗin naki a part naku sai mama Haulat tai maki wani make up ɗin mai kyau". Sam bata yi musu ba ta bisa, dan dama so take yi ta bar wajen. Kunyar momma yasa ta gagara motsawa. Ta kasan ido Jaish ya bisu da kallo har suka fita, sannan ya miƙe tsaye. "Momma ina zuwa". Tsabar farincikin da Momma ta shiga na tina Mahnoor a rayuwarsa da ya yi yasa ta gagara yin magana, sai sakin cool murmushi kawai take yi, shi ma ya lura da yadda ta shiga farinciki, ya ji daɗin abin matuƙa. Bayan su Mahnoor ya bi, dama ba wani fita da zai yi, kawai ya biyota ne ya ga yadda zata kare da ƴan gida, wato a fakaice dai ya rama abin da ta yi mashi, ta sanya shi jin kunyar bappa matuƙa, tamkar ya natse cikin ƙarƙashin ƙasa a wancan ranar, to shi ma yau ya rama kunya tamkar ta natse cikin ƙasa. Lokacin da ya shiga bedroom ɗin har guyson ya wanke mata fuskar yana tayata goge shi da towel, ya ce ta zauna a saman mirror chair bari ya yi mata wani kwalliyar mai kyau, dan shi ma ya iya make up sosai zamansa da Sharifat a Dubai, so ta zauna zai yi mata wani kwalliyar mai kyau. "Waye ya ce ka wanke mata fuska Omar?". Daga bakin kofa suka jiyo voice ɗinsa, a tare dik suka kai kallansu a kansa, yana tsaye ya ɗaure fuska tamau,wai irin sai ya ja mata rai sosai kafin ya fahimtar da ita yasan wacece ita a garesa, yanzu ba zai faɗa mata ya tina komai ba. "Yah Jaish baka ga kwalliyar bashi da kyau bane? Shiyasa fa na wanke mata zan yi mata wani". A ɗan shagwaɓe ya yi maganar!...... "A haka nike san ta rinƙa kwalliya kullum, kada ka sake wanke mata, kuma a haka zata fita, in bata san a ganta sai dai kada ta fita daga nan ta zauna, amma ni irin kwalliyar nike so". Ya kai karshen maganar tare da shigowa ciki, bilhakki da gaskiyarsa fa ya zage yake maganar, wai irin kada ma su zaci wasa yake yi. Kallan juna suka yi ita da guyson, take idanunta suka cika da kwallah, kenan sai dai ta yi ta zama a cikin ɗaki ba zata fita wajensu Chuchu ba?. Ga shi ya ce irin kwalliyar kawai yake so, wannan ai ba kwalliya bace, hauka ce. Shi ma guyson sam bai ji daɗin batun ba, amma da yake yayansa ne ya zartar da hukunci, sai kawai ya yi na'am da hukuncin, ya kuma yi dabara ya zame jikinsa ya gudu abinsa, ba ruwansa da shiga tsakanin ma'aurata. Yana fita suka ci karo da Mahreen zata shigo part ɗin, dan tin jiya bata haɗu da Mahnoor ɗin ba. Sai da gabansa ya faɗi, take wani irin fargaba ya lulluɓesa. Sai dai kuma sai satar kallonta ta katsan ido yake yi, Chuchu ƴar wanka ta tsantsara mata kwalliya mai shegen kyau, ta wani kele cikin riga da wando arabiyans dress, ta yi rolling na veil a kanta, gata fara launin kayan dark ash, sai kyanta ya kara bayyana, ɗan bakin nan nata ya sha lips balm kamar zai ɗiga, sai wani turo shi take yi, kamar ma bata san rufe shi sosai, sai wai yauki take yi bata san taka kasa. Kamar wani maras gaskiya ya ce mata. "Sannunki". Yana magana cike da ƴan kame kame, kamar fa tsoronta yake ji, shi kaɗai ya bi ya dibirbirce. Harara ta dallah mashi wadda ta sanya shi haɗiyar yawu da kyar, cike da gadara ta ce. "Kada ka sake yi mun magana, kai ɗan iska ne ni kuma mai mutumci"..... Kai innalilahi, wai kunji ita mai mutumci, to ai mutum baya cewa ga abin da yake da shi, dik wanda yake da abu ba sai ya faɗa ba, mutane da kansu zasu faɗa mashi yana da kaza, dik mai cewa yana da shi to bashi da shi ne, in yana da ba zai faɗa ba, yanzu fisabilillah kunga Mahreen ta yi kalar mutumci? Innalilahi wannan yarinya zata kashe mutum da dariya, ko da yake dama ance yabon kai jahilci ne, kuma hakan ce, jahilci na ɗawainiya da ita shiyasa take yawan yaba mashi kanta, ban da jahilci ba zata yi ba ai, zata bari ne a yabeta!. "Ki yi hakuri". Shi ne abin da ya faɗa mata, kai ta sa zata wuce tana wani dallar mashi harara da waɗan nan shegun idanun nata masu saka shi ya shiga shakku da zargin kansa ko ya yi mata laifi ne. Har ta ɗan yi nisa da shi sai ya juyo da kallonsa a kanta. "Ki yi hakuri Mahreen, ba zan iya dai'na yi maki magana ba, dan kina daga cikin mutanen dake burgeni nake kuma kauna". Ya faɗa idanunsa a kanta. Cak ta dakata da tafiyar da take yi, wai irin ita ma zata yi na ƴan gayun nan, cike da yanga ta juyo, from head to toe ta bisa da kallo kafin ta ce. "Ni kuma bana sanka, bana mu'amala da ƴan iska, bana san ragwayen mutane, kuma daga yau ba sunana Mahreen ba, Aunty Chuchu ta ce sunana big girl, dan haka sunan da zaka rinƙa kirana da shi kenan, big girl". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta cigaba da tafiyanta. Binta da kallo ya yi yana mamakin yadda take da shegen tsiwar tsiya, wai big girl, siririn murmushi ya saki, lallai Chuchu ma bata san zaman lafiya da take koyawa Mahreen rashin mutunci kala kala, yo in banda abin Chuchu ma Mahreen har za'a kara koya mata wani abin bayan sanka sankan rashin mutuncin da ta iya? Tab gaba akwai show kenan, lallai kuwa. A wani ɓangare na zuciyarsa kuma tinani ya fara yi a kan me zai yi ya birge wannan haɗaɗɗiyar babyn mai tafiya da hankalin mai lafiya, shi dai har yau kome ta yi birgesa take yi!. Ya jima tsaye a wajen yana tinanin abin da zai yi ya birgeta har ta fara respecting ɗinsa, daga karshe ya wuce zuwa in da zai je. Shi kuwa Jaish guyson yana fita ya wuce saman bed ɗinsa ya kwanta yana satar kallanta ta witsiyar ido, sai da ya kwanta sannan ya ce ta mayar da kwalliyar dake kan face ɗinta tamkar yadda ta tashi ta gani, haka yake san ganinta. Yana gama faɗar hakan ya mai da idanunsa ya lumshesu. Shiru ta zauna tana jin tamkar ta fasa ihu, a cikin zuciyarta ta ce bata san sai yaushe zata ji daɗin rayuwarta ba, kullun tana cikin ƙunci ita. Cike da damuwa ta fara yin abin da ya umarceta. Allah ya shirya mana Jaish, ku ce Amin! Wai ya tina wacece ita ɗin ma ba zai barta ta samu farinciki da natsuwa ba, sai ya wahalar da ita kafin ya faɗa mata yana santa? Wannan ai iskanci ne, raina ya fara ɓaci fa........🥱 To bari mu leƙa wani wajen mu dawo. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 BAYAN WASU ƳAN KWANAKI. Tun da ta tashi da safe yau bata ji motsinsa ba, kuma bata nemesa ba, sai dai a karkashin zuciyarta ta damu matuƙa da san jin ina yake yau bai leƙota ba? In dai yana nan baya taɓa ɗaukar 2 hours ba tare da ta sanya shi a idanunta ba, to ina ya je yau?. Zuciyarta ta jefa mata tambayar da bata da amsarsa. Shiru ta luluƙa duniyar tinanin dik abubuwan da suka rinƙa faruwa a tsakaninsu, take irin salon da ya rinƙa nuna mata a fitansu da suka yi ya fara dawo mata a cikin kwakwalwarta. Lokacin guda ta saki murmushinta mai kayatarwa wanda ya kan jima bai samu gurbi a face ɗinta ba, sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanunta, cikin ƙankanin lokaci ta tsinci kanta cikin wani irin farinciki na musamman, har da wani nisawa kamar.......... 🤫 Can kuma da tinanin Sharifat ya ratso cikin brain ɗinta, cikin gaggawa face ɗinta ya yi saurin canzawa, siririn tsaki ta ja tare da haɗe rai. A hankali ta miƙe ta sauko kasan bed ɗin, waje ta nufo domin tasamawa kanta abin da zata sanya a bakin salati, dan yunwa ya fara addabawa cikinta. Kitchen ta nufa, gidan babu kowa sai daddaɗar kamshi dake tashi. Dattijuwar dake kula da ita ta yi barci a nata bedroom ɗin dake kusa da na Leesharh ɗin. Hot tea ta haɗawa kanta mai daɗi, sannan ta ɗauko small chop a plate ta nufo waje, da alama yau bai yi breakfast a gida ba, dan kuwa alama ta nuna ba'a shiga kitchen ɗin nan ba yau. Bedroom ɗinta ta koma, bata jin daɗi dai, amma haka ta tuttura abin da zata iya ci, sai da ta ji cikinta ya ɗan cika, sannan ta miƙe ta fito da kayan waje, komawa ta yi ta hau gado, ta cigaba da tunane tunanenta wanda babu jimawa barci ya yi awon gaba da ita again. Wunin ranar dai gabaɗaya a ɗaki ta wuni, sai zuba barci take yi tana kara tashi. Wasa wasa sai har karfe 10 na dare bata ji motsinsa ba, abin ya gefata a cikin damuwa matuƙa, har ji ta yi kanta na yi mata ciwo, tinani ya fi ɗari a cikin ranta, wani ɓangare na zuciyarta ya ce mata baya nan, wani kuma ya ce mata yana nan yana cikin bedroom ɗinsa kila wani abin ne yasame shi yasa ya kasa iya fita, dan haka ta je ta duba shi. Tinani dai kala kala, daga karshe sai ta miƙe ta nufi toilet, a gurguje ta yi wanka haɗe da ɗauro alwalar barci, fitowa ta yi ta shirya cikin ɗaya daga cikin sleeping dress ɗinta dake gidan, ta shafa mayukan da ya saya mata, ta yi shirinta tsab, ta kuma yi kyau sosai abinta, ta hau gado ta kwanta a zuwan zata share tinaninsa a ranta, amma sai kuma ta kasa, domin kuwa tana kwanciya tinanin ya dawo mata sabo pil. Dogon tsaki ta ja tare da miƙewa zaune, hararar ɗakin ta fara yi sai ka ce shi ya yi mata laifi, siririn tsaki ta sake ja kafin ta zuro kafafunta kasan bed ɗin ta miƙe tsaye, kai tsaye ta nufi waje, tana tafiya tana harare harare. Har ta kai bakin door sai kuma ta dawo ta ɗauki hijabi ta ɗaura a saman sleeping dress ɗin nata, ta wuce tana kumbura kumatu. Kai tsaye ta nufi master room ɗinsa, ko tsoron nufar ɗakin bata yi ba, amma ta ji tsoron abin da zata tarar dangane da shi, fargabarta ɗaya ace bashi da lafiya ne ya kasa fitowa waje. Siririn sallama ta yi a bakin kofar shiga bedroom ɗin. Shiru babu alamar motsin mai rai da ta jiyo, jim ta ɗan yi kirjinta na bugawa da ɗan karfi karfi, tana fargabar tura kofar ta ga menene a ciki. Almost 3 mins tana tsaye a wajen, tsananin fargaba yasa ta ji tamkar ta juya ta hakura da zuwa ta duba shi, amma zuciyarta ta kasa amsar hakan, ba zata iya barci ba ko ta koma, ba zata samu sukuninta da natsuwarta ba idan har bata tabbatar da yana lafiya ba. Tamkar mai rawar sanyi tasa hannu ta tura kofar bedroom ɗin nasa, kirjinta na tsananta bugawa, da kyar ta sake yin wani sallamar kafin ta kutsa kai ciki. Lokaci guda ta saki nauyayyar ajiyar zuciya ganin babu kowa a ciki, sai sanyi da kamshin mai ratsa zuciya dake ta shi, tin da babu kowa a ciki hakan yasa ta fahimci lallai lafiyarsa lou tin da har ya fita baya nan. Ta ji sanyi a ranta, dan haka ta ɗan tsaya tana bin bedroom ɗin da kallo na ƴan mitocin da basu gaza 3 ba, tana yawan jinjinawa tsabta da shegen san kamshinsa, baya shiri da datti ko kaɗan. Haka ta gama kalle kallenta ta juya da nufin ta bar ɗakin. Step biyu ta taka sai kuma ta tsaya cak kallanta a ƙasa, kamar wadda aka dakatar. Can kasan maƙoshinta kamar mai raɗa ta ce. "Ka yi hakuri ba da gangan na shigo maka ɗakin ba, akwai dalili". Ta kai karshen maganar tare da ɗago da kallanta a kansa. Yana tsaye a bakin door na shigowa, ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, sanye yake da sleeping dress, da alama bai jima da dawowa ba, hannunsa rike da cup, kamar dai daga kitchen ya fito, da alama tin safe bai ci komai ba, ga alamar wahala a tattare da shi, yunwa da gajiya ya tattara a saman face ɗinsa, idanunsa sun yi jajir sun ɗan kumbura, kamar wanda barci ke binsa bashi, face ɗinsa ta ɗan yi fayau haka, kamar wanda ya taso daga zazzaɓi, sai dai ya yi kyau sosai, lips ɗinsa sun kara tura red sosai alamar ya ɗan rasa natsuwarsa na ɗan lokaci. Wani irin faɗuwar gaba ta ji ganin irin dressing dake jikinsa, ga rigar ma gabaɗaya gabanta a buɗe, wide chest ɗinsa a waje. Ɗauke kallanta daga kansa ta yi tana jin kirjinta na bugawa da karfi karfi. Ya tsareta da ido babu ko kyauftawa, tabbas ta yi kyau cikin wannan hijabi, sai dai shi, dressing dake ƙarƙashin hijabin yake san kallah, ta rufe ta kuntata shi, gabaɗaya kallansa a kan surar jikinta, idanunsa kamar wani ɗan maye yau!. "Am...... In..... To..... Ummm zan iya wucewa in tafi bedroom ɗina?". Ta yi maganar voice ɗinta na sarkewa, kamar wata maras gaskiya. Ɗan ɗage shoulders ɗinsa ya yi tare da sake saukesu alamar whyn't, zata iya wucewa kenan. Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, kanta a ƙasa taki sake ɗagowa su haɗa ido, dressing ɗinsa yana haukatar da tinaninta sosai, dan haka bata san cigaba da kallonsa yana canza zuciyarta, zai sanyata ta ci amana a banza, ita kuma ba zata ci amanar Sharifat ba!!!....... LEESHARH tamu ta amana mai amana, wai ba zata ci amana ba, ta dage fa a kan lamarinta, ta riki gaskiya da amana, mazamaza ku yi koyi da ita!!......😅 A hankali ta tako tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta matsa kusa da door ɗin, a tinaninta idan ta matsa zai bata hanya, sai ta ga akasin haka, yana tsaye yana binta da mayen kallo kamar a buge yake. A ɗan gefensa kaɗan ta dakata, kamar zata ɗago ta kallesa sai kuma ta fasa, cikin natsuwa ta furta. "To ai babu hanyar wucewa sai ka matsa"........ Bai san lokacin da ya ɗaga gera guda ba, irin haka ne? Sai kuma ya ɗan matsa mata hanya kaɗan wanda shi kansa yasan ba zai ishata wucewa ba, wato dai barin bakin kofar ne ba zai yi ba saboda iskancin nasa yau kuma ta motsa. Sarai ta fahimci magana yake nema da ita, dan haka sai ta yi kamar bata gane ba, ta matsa tare da ɗan kame jikinta, ta raɓa shi zata wuce. Yana binta da kallo sai da ta isa dab da saitin kirjinsa yasa ɗayan hannunsa ya janyota jikinsa, take ya sauke wani sanyayyar ajiyar zuciya, ita kanta ajiyar zuciyar ta sauke, har da wani ɗan kwantawa a jikin nasa, irin ita ma tana ra'ayi kenan. Can kuma sai ta tuna da ƴar uwarta Sharifat, da sauri ta yunkura zata bar jikinsa tana wani ƴan kame kame. Hannunsa ya ɗaura a saman bayanta kafin ya furta. "Menene kuma?"....... Tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Ramish Sharifat fa? Kasan dai kai take jira ko?.........". Wani irin kallo mai kama da harara da ya wurga mata ne yasa ta yi saurin haɗiye maganar nata. Gently ya ce. "Daga yau kada ki sake mun maganarsu a nan, na tsanesu dikkansu, kuma su nike zargi a kan abin da ya faru a tsakanina dake, zan kuma tabbatar da hakan soon". Zaro idanu ta yi jin cewa Sharifat tana daga cikin waɗan da yake zargi, ita dai zata iya rantsuwa da Allah Sharifat ba zata aikata wannan ɗanyan aiki ba, ɗan gara ma Ummie zata iya cewa zata iya aikatawa, amma Sharifat da take baiwar Allah, yarinya mai hankali da natsuwa, kai gaskiya da kamar wuya wlh. "Amma Yah Ramish Sharifat fa.........". Yatsarsa ɗaya ya ɗaura a saman lips ɗinta alamar ta yi mashi shiru, wani irin shock ya ji lokacin da ya ji soft lips ɗin nata, sai da tsikar jikinsa suka mimmiƙe, da sauri ya ɗauke hannunsa tare da cewa. "Me kika zo yi a ɗakina ma tukun nan?"....... Shiru ta ɗan yi, dan bata san me zata ce ya kawota ba, bata son yasan ta damu da shi har ya yi zatan ta fara son shi ne, dan ita babu gudu babu ja da baya a maganarta. Jinin Hausa Fulani, magana ɗaya take yi babu sauyi....... My people's mu gaya mata gaskiya ko mu barta duniya ta gaya mata?. Yen yen yen, wai magana ɗaya take yi ƴar ƙaniya, na make bakinta ne maras kunyar karya. Ki zauna nan ga su Sahibatu can suna rububin Ramish kamar su mutu, sai sun kwace shi zaki ga riƙon amana a idonki ƴar ƙaniya. "Babu amsa ne?. Ko dai kin zo duba ni ne? Kin yi kewata ne?". Cikin ɗan zoyala ya yi maganar. Lallausan kallo ta bishi da shi mai narka zuciya kafin ta ce. "Ko ɗaya, meyasa zan zo dubaka? Meyasa zan damu da kai? Meyasa zan yi kewarka bayan bani da wata haɗi da kai?"........... "Da gaske baki da haɗi da ni?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e bata da haɗi da shi. Rage buɗuwar idanunsa ya yi, ya zamana tamkar mai jin barci, sannan ya juyar da ita ta zamana bayanta ne ke manne da kirjinsa, hannunsa dake saman bayanta ya dawo da shi saman shafaffiyar cikinta, sannan ya rage tsawonsa a in da ya ɗaura kansa a saman shoulder ɗinta, can ƙasa ƙasa a cikin kunnenta ya ce. "I think ba zan rasa baby a nan ba, because I play my game yadda yakamata, kuma irin wannan dogon jinya da kika sha nasan ma dole na ci kwallo". Yana magana yana shafa cikinta.... (Kam bala'i, wato ma kenan Ramish da gangan ya yi wannan aika aikan? Leesharh ta yi gaskiya kenan? Bala'in can, lallai ya kai ɗan duniya na karshe wlh, iye wai ya ci kwallo?.🤔 Yau ga ɗan iska da tsakiyar rana!🤔) Ai bata san lokacin da a miliyan ta ce. "Wlh babu, kuma ba zai taɓa yiwuwa ba ko a mafarki, ba zan taɓa haifar ɗan shege ba, wlh babu, babu wani cikinka a jikina, ni babu komai". A tsananin rikice take maganar, tana yi tana zaro idanu, ya ɗaga mata hankali ainun, ina zata sanya ranta idan aka ce ciki ya shiga tsakaninsu? Ai kawai tana ga kashe kanta zata yi....... Ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin yadda ta rikice haka, koba komai ta sakar mashi jikinta a jikinsa yadda yakamata, da ta wani takure gabaɗaya baya jin daɗi yadda yakamata. "Kina ganin kamar wasa nike yi ko? To gara ma ki yarda mu yi aure sai mu haifi babynmu a gidanmu na aure na sunnah, idan ba haka ba zaki haifi babyn da zaki ƙasa bashi amsar wanene ubansa kuma ya aka yi kika same shi idan ya titsiyeki". Ya kai karshen maganar yana ɗage mata hijabinta cikin dabara. "Na shiga uku na, Yah Ramish da gaske kake yi? Dan Allah ina da ciki? Shikenan na shiga uku na, na karya maganar da babana yake faɗa mun kullum, na karya alkawarin da na yi mashi cewa zan kare mutumcina, shikenan yanzu kowa zai san abin da ya faru? Shikenan kowa zai ganni da cikin da bani da amsar ina na same shi idan an tambayeni? Sharifat zata ganni da cikinka? Na shiga uku rayuwata ta kare a banza a wahale tare da rashin madogara!" Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa tab da kwallah, zuciyarta ya karaya matiƙa, ta shiga tashin hankali da fargaba. Shi kuwa tura hannunsa ya yi cikin rigarta bayan ya ɗage mata hijabin, cigaba ya yi da shafa cikin nata, kamar mai raɗa ya ce. "Ina fatan babyna ya yi kama da ni, dan ma kowa ya san nine ubansa!!". Kam bala'i yau ga tabbatar rashin kunya da bushewar ido wajen Ramish........ Haba ai kara birkice mashi ta yi, jin hannunsa a saman fatar cikinta ya sa ta yi gagawar kwace kanta ta raba jikinta da nasa, tini hawaye sun gama wanke mata fuska, idanunta sun yi jajir, yanzu ta fara tinanin sauyawar da jikinta ya yi a ƴan kwanakin nan, gaskiya da alama gaskiya a zancensa, ciki ne da ita, tana da tabbacin cikin ne ma yasa take damuwa a kansa, shiyasa kenan take kasa iya barci in bata kallesa ba, babynsa kenan yake sanyata dik wannan abin?. Wani irin ihu mai sauti ta zunduma tare da zube gwiwowinta a ƙasa a wajen, sannan ta dafe kanta dake barazanar tarwatse mata, kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ta saki mai sautin gaske. Har cikin ransa ya ji kukan nata ya ratsa shi, sai ya ji wani irin tausayinta ya ninku a ransa, tamkar zai faɗa mata gaskiyar cewa zolayarta yake yi, amma kuma ya ji dole ya barta a kan hakan dan ta aminta da shi su yi aure su rufawa juna asiri. Tsugunnawa ya yi a kusa da ita, ajiye cup ɗin hannunsa a gefensu ya yi sannan ya janyota jikinsa, ya rungumeta sosai tare da fara rarrashinta. Ai ina, taki sauraronsa, sai ma kara tsananta kukan nata da take yi tana faɗin ta shiga ukunta. Shiru ya ɗan yi yana tinanin me ya dace ya yi mata wanda zai iya shawo kanta cikin gaggawa ta yi shiru su samu su yi magana. Ya yi iya tinanin da zai yi amma dik ya kasa iya tinano hanyar da zai shawo kanta, saboda shi soyayya ba layinsa bane, bai kware a kanta ba. Zuba mata idanu kawai ya yi yana kallan yadda take kukan, har cikin ransa hakan yake sosa zuciyarsa, ganin fa ba zai iya jurar kukan bane yasa ya yanke shawarar yin abin da yake ganin ita ce mafita a garesa. Wato ya matsa dab da ita, cikin zafa ya haɗe bakinsu waje guda domin ya bata hot kiss da zai sanyata haɗiye kukan dan dolenta. Aikuwa ya yi nasara, dan kuwa suman zaune ta yi mashi, ta yi tsit tamkar ruwa ya cinyeta, yau ne ranarta na farko da wani ya fara kissing ɗinta, shi kuwa daga neman hanyar da zai samu ta yi shiru, sai ya zarce da bata zazzafa mai kwance notikan ƙwaƙwalwa. Bai ma san time ɗin da ya miƙe da ita a jikinsa ba, gabaɗaya ya wuce balconynsa da ita bakinsu manne cikin na juna, ita dai ta ƙasa koda motsawa, saman rest chiar ya zauna da ita tare da kara manneta da jikinsa. Sai da ya bata masu zafi san ransa, sannan ya saketa tare da rungumeta yana sauke ajiyar zuciya. Almost 10 mins suna a haka kafin ya ɗan saussauta rikon da ya yi mata, word in out of control ya shiga yi. "Please Aesh believe that zan dawo maki da dikkan farincikinki da ya gushe, ki yarda mu yi aure, i promised you that ba zan taɓa bari ki yi kunci ba, you will never regret kasancewarmu a ma'aurata, please Aesh trust me"...... Cikin wata iriyar murya tamkar wadda take a buge, kamar bata cikin hayyacinta ta ce. "Yah Ramish zaka aureni ne kawai ba dan kana sona ba, sai dai kana tausayina kuma kana san rufe ɓarnar da ka aikata a gareni, baka san familynka su san cewa ga abin da ya faru, na san halin larabawa sosai, na zauna da su tin ina karama, wlh dan ka rufe ɓarnarka yasa ka aminta zaka aureni, na tabbata baka sona, saboda ko a ƴar aikin gidanku ban kai na zo ba, tsautsayi da rufe maku gaskiya yasa na shigo cikin familynku, masu aikin gidanku dik mutane ne da suka kammala diploma, baku ɗaukar jahilai a masu aiki, amma ni jahila ce da ko secondary ban kammala ba, babu wani ilimi a kai na, amma an rufe maku hakan ta hanyar kirkirar mun takardu na karya wanda ke nuna na yi karatu, bayan ko kusa ko alama ban yi ba, kaga kai ba saa'ata bane, ba zaka taɓa san jahila wadda bata da gata ba, wacce kuma aka ɗauki hayarta domin ta kasheka, ko ka manta ni ɗin na shigo gidanku dan in kasheka ne? Ka mance da cewa na taɓa poisoning ɗinka? Ka manta da cewa na taɓa zama silar da aka harbeka da gun? Ka manta da cewa na yi maka abubuwa dayawa dan ganin ka mutu?". Ta kai karshen maganar tana ruwan hawaye. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Dik nasan da hakan, amma ina san ki san cewa in har zan ki ki saboda wannan dalilin, to tabbas zan ki Bilal, saboda dik abin da yake faruwa da sa hannunsa a ciki dik da bani da cikakkiyar hujja mai karfi sosai a kan hakan, dik hujjojin da nike da su a kansa basu da karfi sosai, amma suna tabbatar mun da yana da sa hannu a ciki, ki sani ni ba dan na rufe abin da na aikata a gareki yasa zan aureki ba, sonki nike yi Aesh". Babbar magana, kenan Ramish yasan da sa hannun Bilal a yunƙurin kashe shi da ake yi? Shiyasa ya juya masu baya kenan? To mu je zuwa. Wlh Ramish karya yake yi mata, bawani yana sonta ne, batu na gaskiya yana tinanin tana da ciki shiyasa yake san ta yarda su yi aure dan kada su haifi cikin a waje, ta yadda Allah ya tashi kama shi kuma sai ya sanya mashi kaunar yara ta yadda baya jin zai iya zubar da ciki, yana san ta haifa mashi, kamar yadda Leesharh ta yi hasashe hakan ce, ba wai dan hana sonta zai aureta ba ɗan rainin wayo. Amma kuma dani da ku dik mun san akwai son nata a zuciyarsa, sai dai shi ɗin ne bai yarda da hakan ba, baku jin baya wani magana sai su yi sauri su yi aure ne? Idan da ya yardanwa kansa sonta yake yi, to da tabbas zai rinƙa yi mata abubuwa na masoya, amma a'a, shi damuwarsa kawai su yi aure. "No Yah Ramish, na tabbata baka sona, nafa san halin larabawa, tin ina karama na tashi a cikinku, nasan dik wani hali naku, kuna da kishin zubewar mutumcinku, bare ma kai da ka fito daga cikin babban family masu karfin faɗa aji a kasar, dole ka yi komai dan mutumcin gidanku". Ta kai karshen maganar tana tari mara sauti sosai. "Aesh yanzu baki yarda da maganata ba kenan?". Shiru bata iya amsa mashi ba. Kara matsawa jikinta sosai ya yi, cikin sigar rarrashi ya fara yi mata dabara dan ta yarda. Ko da sunan wasa ba ya san abin da ya aikata ta fita, ko dan kakansu King Badeen, and ace ɗa ga King Zuhair yana da ɗan shege? Kai ai abin babba ne. Uhm aka ce maka namiji a fagen kalaman yaudara to fa an rufe kofa, dan kuwa Ramish sai da yasa ta yarda da cewa da gaske yake sonta, amma taki yarda ta amsa zata auresa, sai ta ce ta yarda da yana sonta, amma dan Allah ya kyaleta haka nan, idan ma saboda ciki ne ya mayar da ita Nigeria in da babu wanda ya sansa bare har mutumcinsa ya zube, zata reni cikinta a can ta haifesa ta kuma rike kayanta, ba zata taɓa kama sunansa a bakinta ba. Kai kawai ya girgiza, lallai yau ya yarda Leesharh yarinya ce sosai mai ƙaramin tinani, wai ba zata taɓa ambatar sunansa ba, tab bata san me haihuwar bane, ai wlh time da yaron zai titsiyeta a kan ina ubanta san da zata ji takura ta faɗa mashi ma babu wanda ya sani, kuma dik bama wannan ba, a Nigeria tasan ƴan uwanta ne? Sannan shi dik bama wannan ba, yana bala'in san yara, bare kuma ace jininsa, a gaskiya yana son kayansa, dole idan akwai cikin nan ta haifa mashi kayansa ta bashi ko me zai faru sai dai ya faru, babu wani Nigeria da zai maida ta da ɗansa!!. Babbar magana, ya kuke ganin wanna cakwakiya zata kaya?. Bala'in can, ya mama uwar jiji da kai zata ji a lokacin da Ramish zai kawo mata bastard matsayin jika? Tab ya King zai yi?. Shiru ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi a hankali hankali. Tamkar a mafarki suka ga wutar gidan ta ɗauke gabaɗaya, a ɗan razane ta yunkura zata bar jikinsa, ta ɗago kai tana kallan saman ɗakin. Tin da ya ga hakan yasan akwai matsala, dan wuta bata taɓa ɗaukewa haka nan. Tana ƙoƙarin barin jikinsa ya yi saurin rikota, kamar mai raɗa ya ce mata. "Yi shiru kada ki motsa". Muryarta a dashe ta ce. "Yah Ramish meyasa wutar ta ɗauke? Ni dai nasan tsawon shekaru ba'a ɗauke wuta a kasar nan! Ko dai kai ka kashe ne?............" Yatsa ya ɗaura mata a saman lips ɗinta. "Kada ki sake yin magana, yi shiru, and ki zauna a nan ina zuwa, kome zai faru kada ki motsa daga nan". Ya kai karshen maganar tare da saketa. Tana san tambayarsa ina zai je, tana tsoron ya ce ta yi shiru kada ta yi magana, wayarsa na aljihinsa, amma bai kunna ligh ɗinta ba, cikin sanɗa ya nufi waje. Yana fitowa ya ji takun tafiyar kartin mutane suna haurowa saman stair case ɗin, shiru ya ɗan yi yana mamakin yadda suke da karfin hali da dabarar iya kashe wutar gidan dan kada camera ta ɗaukesu, dama shi yasan zasu biyosu, saboda dama bai yarda mota ɗaya ce ta bi bayan Leesharh ba, dole sun saka masu ido, sai dai bai sa a ransa zasu yi saurin biyosu ba, ya yi zatan zasu ɗan kwana biyu su yi shiri, fatansa a nan yanzu shi ne Allah ya bashi sa'ar kama ko mutum ɗaya ne da ransa, dan samu amsoshin wasu tambayoyi nasa. Yana tsaye yana tinani sai ji ya yi an bangajesa za'a wuce, har sun iso in da yake ba tare da ya farga ba. Wanda ya bangajesa ɗin ya yi gaggawar fitar da light mai bala'in haske ya dalle mashi fuska da shi, hakan yasa ya kashe mashi kwayar idanunsa baya iya ganin su waye ne. Ya yi ƙoƙarin kwace hasken, amma ina ba zai yiwu ba, dan baya iya ganinsu ma bare har yasan waye ya rike hasken ya kwace. Tamkar saukar aradu haka ya ji saukar wani irin karfe a kansa, sun kashe mashi ido da haske baya ganinsu sun dakesa da wani katan karfe a kai, take wani irin jiri mai karfin gaske ta ɗebesa, dik hasken dake haska shi duhu yake gani a wannan lokaci, kan ka ce me ya zube ƙasa baya numfashi. Kawar da light ɗin daga kansa suka yi zuwa kan wasu dake bayan mai rike da light ɗin, wasu irin shirga shirgan mutane ne masu sanye da bakaken kaya haɗi da manya manyan boots a kafafunsu, ga hands gloves, mask, baka iya ganin komai a jikinsu sai jajayen idanun da suka yi ja saboda kayan maye!!. "Ku shiga ku ɗauko mun ita, shi wanna angama da shi!". Wanda ya rike light. Wucewa karti uku suka yi izuwa cikin ɗakin, saura suka tsaya a tare da ogan nasu mai rike da light ɗin. My people's me kuke tinanin zai faru ne? Ni kaina page ɗin yau sai dai in kora Maltina and exotic kawai in yi shiru, mu leƙa Paris mu dawo!!. 🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥 Smart ya ɗauki a kallah 10 mins suna tattaunawa da King, da alamar rashin jituwa kuma a maganganun nasu, dan yadda Smart yake maganar zaka fahimci dikkansu ransu a ɓace yake. Daga karshe cikin fushi ya katse kiran, sannan ya yi off na wayar gabaɗaya tare da miƙewa ya nufi cikin ɗakin, haka ya rinƙa rarrashin Auta har tsawon kwanaki. Yau takama weekend, Saturday, Smart yana tare da su a gida, bai je ko'ina ba, a ƴan kwanakin nan ya yi matuƙar sabo da su Pretty, tin tana bakanta mashi rai har ta dawo tana burgesa a dik abin da take yi, ba abin da ya fi ɗaukar hankalinsa a tattare da ita sai olive eyes ɗinta da kuma shegen shariyarta na jinin sarauta, tana bala'in burgesa yadda bata daga idanu ta kalli mutum, sannan tana matuƙar burgesa yadda take da tsoro, idan ta tsorata ba ƙaramin kyau take mashi tana tafiya da imaninsa ba, wani lokaci da gangan yake tafiya waje filin dolphins na Auta ya barsu a ciki, idan ta farga da baya kusa da su ta tsorata ta fara kuka kyau matuƙa take yi mashi. Sanye yake da pj a jikinsa, suna sama gabaɗayansu, Auta tana gyarawa Pretty gashin kanta suna ta hira, shi kuma ya tasa laptop a gabansa yana ta aiki dangane da bincikensa. Auta da Pretty suna sanye da hoodies na mata a jikunansu, Auta ta sanya hular kayan a kanta, ita kuwa Pretty daman kun san ba sanya ɗankwaki take ba koda ba gyaran gashi ake yi mata ba!. "Yah Omerish me kake yi ne haka? Naga kamar zanen kunnan mutum da ido?". Cewar Auta, ta yi maganar idanunta a kan laptop dake gabansa, da yake suna kusa da shi sosai, a saman duguwar sofa set guda suke. Hankalinsa a kan aikinsa ya amsa mata da. "Ina san kirkirar karfin ji ne fiye da komai, abin da zai iya dauko sauti tin daga nisan kilomita 10 a tafiya da ƙafa". Cike da mamaki ta sake cewa. "Yah Omerish to naga hoton kunne, me kake yi da shi?"........ "Kwaikwayon halittar Allah zan yi! Kamar yadda muka kwaikwayi halittar idanun mutum muka fidda camera haka nike san kwaikwayar halittar kunne dan in samu majiya mai karfi". Ai Auta bata san time ɗin da ta saki Pretty ta miƙe ta dawo kusa da shi sosai ba, cike da mamaki ta ce. "Yah Omerish dama Camera idanun mutum aka kwaikwaya ne?".... Kai ya jinjina mata kafin ya amsa da. "Komai da kimiya take kirkira ai kwaikwayo muke daga halittar Allah, babu wanda ya isa ya kirkiro wani sabon abu a duniya, sai dai ya kwaikwayi wanda Allah ya yi, Ubangiji ya rigada ya halicci komai, kawai dai mu muna zamanantar da shi ne"..... Kara shiga mamaki sosai Auta ta yi, ita kuwa Pretty bama su isheta kallo ba, mashirmaciya, kwanciya ta yi tana kallan sama kamar wata dake da motsi a kai, babu ruwanta da tattaunawarsu. "Yah Omerish to tayaya kuka kwaikwayi ido? Tayaya Camera yake kama da shi?". Cike da zaƙuwa da san jin amsa ta tambayesa. Dakatawa da aikin da yake yi ya yi, sannan ya juyo da kallonsa game da hankalinsa a kanta, cikin sanyin murya ya fara bata ilimi kamar haka!. "Abubuwa da dama muka kwaikwaya daga idon mutum muka kirkiro Camera, cikin abubuwan da muka kwaikwaya sun haɗa da. Lens da Focusing wato mayar da hankali. Kamar yadda ruwan ido wato lens yake daidaita haske domin samar da kallo mai kyau, ya iya fahimtar menene a gabansa, haka ma camera ke amfani da lens dan mayar da hankali wato focus ga abubuwan da take ɗauka, kin ga a nan mun kwaikwayi ido". "Abu na gaba shi ne. Aperture wato kofar shigar hasken shiga. Ido yana da wani ɓangare da ake kira da pupil, wanda ke buɗewa ko rufewa don daidaita adadin hasken da ke shiga. To haka camera ma, tana amfani da aperture wanda ke sarrafa yawan hasken da ke shiga camerar, nan ma kinga idanu muka kwaikwaya". "Na uku shi ne. Retina da image sensor, wato fuskar karɓar hoto. A cikin idon mutum, retina ce ke ɗaukar hoton da haske ya samar, sai ta aika wa kwakwalwa ta hanyar jijiyoyin gani, ƙwaƙwalwa itake tantance menene a wajen ba ido ba!. To haka a camera ma, akwai image sensor, wato kamar CMOS ko CCD wanda ke ɗaukar hoton da haske ya samar sannan ya juya shi zuwa hoto har ma a iya adanawa kamar yadda ƙwaƙwalwa take adana hoton da ido ya gani, in kaga abu ai ka rigada ka gani ne, ya zauna a kwakwalenka". "Na huɗu shi ne Autofocus, wato daidaita tsawo. Kamar yadda idon mutum ke daidaita mayar da hankali kan wani abu cikin sauri. To haka camera ma tana amfani da autofocus system dan tabbatar da cewa hoton yana cikin sharp. Abu na biyar shi ne HDR, wato high dynamic range da Contrast Perception. Ido yana iya bambanta haske da inuwa fiye da yawancin Cameras. Dan haka an ƙirƙiri HDR technology a camera ne dan taimakawa wajen ɗaukar hotuna masu daidaiton haske da duhu sosai, kuma har yanzu mun ƙasa iya kirkirar camerar da zata iya daidaita abu sak yadda ido zata iya yi, dik da kullum muna cikin kara faɗaɗa bincike ne dan gano manyan abubuwa masu amfani da zasu daidaita komai, shiyasa zaki ga duniya tana kara gaba Camerori masu karfin ɗauka suna kara fitowa, har yanzu ƙoƙari muke yi muga camera ta yi karfin ɗauka kamar ido dik da mun san babu wanda ya isa ya yi abu dai'dai da Allah, muna dai kwatantawa ne iya baiwar da Allah ya yi mana!". "Dik da cewa camera ta zamani tana da fasahar da ke kama da yadda idon mutum ke aiki ko in ce maki mun kwaikwayi ido mun kirkireta, to har yanzu idon ɗan adam ya fi ƙarfi wajen fahimtar launi, haske, da zurfin hotuna fiye da kowace camera da muka ƙirƙira a duniya, muna dai iyaka bakin ƙoƙarinmu, amma Allah ya wuci tinanin mutum, babu wanda ya isa ya yi dai'dai da shi, sai dai mu yi ta kwaikwayo dan samawa al'umma saukin abubuwa!". Ya kai karshen maganar yana ɗan jan lallausan kumatunta, ta wani natsu tana suararonsa. "To shi ne yanzu Yah Omerish kake kwaikwayon kunne?". Like wow ta yi tambayar, abin ya bata mamaki ne sosai, wato dai dik wani kimiya kwaikwayo ne daga Allah, sai dai su Allah ya basu baiwar iya zaƙulo halittun da idan sun kwaikwaya sun yi wani fasahar da shi zai taimakawa al'umma sosai, lallai su ƴan baiwa ne sosai!!...... Jinjina mata kai ya yi alamar e yana kirkiro naura mai karfin ji sosai ne, zubawa laptop ɗin nasa idanu ta yi tana kallan yadda yake ta ƙoƙarin faɗaɗa bincikensa, ya zuba tsantsar basira a kan aikinsa. Suna a haka tiger ɗinsa ya shigo wajen da gudu yana gurnani. Ai daga Auta har Prettyn dikka haukace mashi suka yi, gabaɗaya suka rungumesa suna ihu. Sai suka sa ma ya rasa me zai yi, saura kaɗan su jefar mashi da laptop a ƙasa Allah yasa ya tare. Ya ƙasa yin komai dan sun nukunkume shi, ga ihun da suke yi. Cikin harcen farasanci ya rinƙa cewa damisan ya tafi, amma shi ma yaki tafiya, dan iskanci, sai ma tsalle da ya yi zai haye jikinsa. Ai wani ihun da Auta ta kurma sai da ta sanya damisan dakatawa. Daga bisani ya juya da gudu ya bar wajen, ajiyar zuciya Smart ya sauke kafin ya ce. "To sarakan tsoro, sai ku sakeni ai tin da ya tafi". Auta ce ta fara cewa. "Yah Omerish ka leƙa tukun nan ka tabbatar da ya tafi ko yana nan". "Matsoraciya kawai, ya tafi, kuje ku shirya ma ku zo mu je in kaiku yawo tin da weekend ne". Ai da jin haka Auta ta yi gaggawar sakinsa, dama ta jima tana rokon ya fita da su, sai ya ce masu yana busy, to yau dai zasu fita, cike da ɗauki ta ja hannun Pretty suka nufi stair case dan su je su shirya. Da kyar Pretty ta yarda ta bita, sai da ta ce mata tiger fa ya sauka ƙasa gabaɗaya, yana harabar gidan, sannan ne ta yarda ta bita, suna shiga bedroom ɗinsu suka garƙame da key wai dan ma kada tiger ya biyosu ciki. Shi kuwa komawa ya yi ya zauna yana jiran ya ga wanenen zai auro saman, dan zuwan da damisan nan ya yi wajensa labari ya kawo mashi a kan ya yi baƙi, yana fahimtar dabbobin nasa, kun san idan ka zauna tsawon shekaru da dabba kuka saba to fa zaka iya fahimtar dik abin da take ciki. Yana zama sai ga wasu zaƙwaƙuran matasa biyu sun hauro saman, ɗaya fari tas kaman madara, ɗayan kuma chocolate color, kusan kansu ɗaya, and ɗaya farin kaman bature ne, ɗayan kuma Africans ne, dikkansu kyawawan gaske ne, tsayayyun maza, dik in da ake neman namiji to sun kai, ko da yake tin da kuka gansu a tare da Smart kun san suma ba baya ba, dan baya abota da marasa fasali marasa ilimi. Kai tsaye suka nufosa, da ido ya bisu har suka iso shi, hannu ya miƙa masu suka yi musabaha kafin su samu waje saman sofa suka zazzauna. Cigaba ya yi da aikin da yake yi tare da faɗin. "Zash yaush ka dawo?". Wannan handsome chocolate guy ɗin ne ya amsa mashi da. "Yesternigh". Jinjina kai ya ɗan yi kafin ya juyo da kallansa a kan ɗaya farin. "Bobo is there anything problem?". Fuska ɗauke da damuwa Bobo ya amsa mashi da. "Yeah". Zuba mashi idanun suka yi suna sauraransa. Cigaba ya yi da cewa. "My baby, yau da kewarta na tashi sosai". Ɗan kawar da kansa Smart ya yi. "Sorry, komai zai wuce, abu kaɗan ya rage mana".... Nisawa Smart ya ɗan yi kafin ya kawar da kallansa daga kansu, a ransa yake faɗi shi bai ga amfanin damuwar da bobo yake yi a kan wani abin bama, yakama ne ma a ce ya manta da kowa da komai na rayuwarsa ta baya tin da yanzu komai ya canza. Uhm wanenen bobo da ake so ya manta da komai na rayuwarsa ta baya? Mu ji tarihinsa kaɗan, dan shi ma yana daga cikin manyan stars na RAWANIN ZALINCI. RAWANIN ZALINCI labarine a kan ɓangarori biyar, dan haka manyan jaruman cikin littafin zasu iya kasancewa su bakwai ne, amma idan kuka san wanenen Bobo zan banbanta maku sani abin. -------------------------------------🔥♥️ BLOOD CROWN. shi ne sunan masarautar su Bobo, masarauta ce da aka kafata a kan jini tin zamanin kakanni. A cikin masarautar BLOOD CROWN, a dokance dik wani sarki ko sarauniya da zai hau karagar mulki sai an zub da jinin wani a matsayin hadaya. Ana kiran wannan al'ada da suna kariya wacce suke ganin ita ce take kare masarautar daga lalacewa ko hare hare daga masarautu, ita ce take hana kowa iya tinkararsu, kuma suna ganin hakance ma ta hana King Zuhair yakarsu, a cewarsu sun rufe mashi ido da baki ba zai iya yin komai a kansu ba, dan suna sadaukarwar jini!!. Bobo shi ne babban Prince na wannan masarauta, yana da kanne mata ƙanana guda biyu, ya shaƙu da kannen nasa matukar shaƙuwa, yana bala'in sansu fiye da kansa, sun taso cikin gata da kula, a lokacin da ya kai shekaru 22 sai mahaifinsu ya fara shirye- shiryen yadda za'a fara koya mashi sarauta, dan shi ne kawai magaji. Sam sam mahaifiyarsa bata so ba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa mutanen garin basa san haihuwar ƴaƴa maza, dan za'ace za'a basu mulki, kuma kafin su hau mulki sai sun zub da jinin wanda suka fi kauna. Shiyasa suke san haihuwar ƴaƴa mata, har murna suke su shirya shagali idan suka haifi mace, amma in suka haifi namiji, wlh kuka suke yi yadda kuka san gidan makoki, gidan suna sai ya koma gidan mutuwa!!. Mahaifinsa jarumin gaske ne na bugawa ga jarida, kazalika mahaifiyarsa, zakanya ce sosai!. Sai dai masarautar tasu ƙazantar dake cikinta ya zarce tinanin mai tinani, suna bautar da mata, suna wahalar da su, sun ɗauki mace a matsayin abar sauke sha'awarsu kuma baiwa a garesu, mata basu da wani galihu basu da gata, dik wani aikin karfi mata ne ke yi, dik wani zalunci suna yi masu, a dik time da suka ga dama ko a cikin daji ne zasu haiƙewa matansu su biya buƙatarsu, noma mata ne suke yi, kai komai da maza zasu yi matan ke yi, a cewarsu ai mata bayinsu ne, babu tausayi babu imani, fyaɗe da zinace zinace ya yi over, ba zaku so tona ɓarnar da suke aikatawa ba wlh, amma a hankali idan tafiya ta yi nisa zaku ji komai!. --------------------------------🔥🔥 Bobo ya fara karɓar dik wani horo da ya danganci mulki salum alum, sai dai a lokacin da aka zo kan batun sadaukar da jini kafin ya ɗale kan kujerar mulki, aka sanar mashi cewa dole sai ya kashe wanda yake tsananin so kafin ya hau gadon sarauta. Wannan ita ce hanyar tabbatar da biyayyarsa ga mulkin da aka gina a kan jini!. Tashin Hankali. Nan fa Bobo ya ce babu wannan magana, dan dik duniya mutum huɗu yake so, daga kannensa mata guda biyun nan, sai mahaifiyarsu da kuma mahaifinsu, dan haka ko mutum ɗaya ba zai iya kashewa ba, babban abin takaicin ma wai shi da kansa zai kashe mutumin da yake kauna, sannan ya lashi jininsa a kan harshensa, dik dan ya nuna zallar rashin imani, a cewarsu ta hakance kawai zasu iya gamsuwa da cewa namiji mai dakakkiyar zuciya ce yake mulkarsu. Sai dai kuma ba zai iya bada wanda ya taɓa yin mulki ba, misali ace ya bada mahaifinsa, hakan ba zai yiwu ba, dan already babansa yana da tsari ya ɗale dangerous seat kuma ya ɗaura blood crown a kansa. Bobo ya shiga ruɗani da tashin hankali a in da ya fara bincike a kan masarautar tasu, gadan gadan ya shiga wannan bincike. A nan ne fa ya gano wani sirri mai ban tsoro, wato sarautar BLOOD CROWN tana da asirin duhu. Ba wai kawai ana kashe mutane ne dan cimma muradi ba, rawanin da kowani sarki yake sakawa a yayin hawa mulkinsa rawani ne da yake da wata asiri mai kyaucewa hankali. Dik wanda ya sanya rawanin nan a kansa, zuciyarsa ba ta ƙara jin tausayin mutum, daga nan ya rabu da imani da tausayi. Bobo ya gano cewa dik sarakunan da suka gabace sa, rawanin ya mai da su masu mugunta, yana rage musu tausayi kuma yana ƙarfafa su su yi zalunci ba tare da rashin jin daɗi ko kunya ba. Wannan yana nufin idan har shi ma ya sanya rawanin to zai zama azzalumi kamar su. Babbar magana! Ya shiga ruɗani mai girma gano cewa yana da yaya namiji da mahaifinsa ya kashe domin ɗale kan kujerar mulki, ya sadaukar da jininsa ga BLOOD CROWN kenan, bala'i iya bala'i Bobo ya shiga a wannan lokaci, nan fa ya fara tinanin mafita a garesa dama ƴan uwansa bakiɗaya, dan ba zai taɓa iya bada ko mutum ɗaya daga cikin huɗun nan ba, ba kuma zai iya bari a cigaba da wannan ɓarna ba, saboda a lokacin shi ya musulunta ba tare da saninsu ba, a makarantarsu ya karɓi musulunci daga abokinsa wato Smart, tare suka yi karatu a ƙasar France, a lokacin da aka ce ya karɓi mulkinma hutun school ya dawo, daga nan suka rikesa wai karatun ya isa haka, lokacin hawansa gadan mulki ya yi! Dama shi ya matsa yana san karatun!. Daga nan Bobo ya fara shirin wargaza mulkin zalunci. Sai dai hakan yana da gagarumin hatsari da barazana ga rayuwarsa da ƴan uwansa. Sama da sau goma ƴan majalisar masarauta tana yin zama a kansa, sun tursasa mahaifinsa a kan ya sanya shi dole ya ya zaɓi wadda ya fi kauna ya kasheta a karawa CROWN ɗinsu karfi, dan da alama zasu iya fuskantar marazana daga wasu masarautun idan basu yi gaggawar bada jini sun karawa RAWANIN karfi ba. Sai dai dik yadda za'ayi da Bobo anyi yaki buɗar baki ya ce ga wadda ya fi so, da zarar an yi mashi magana sai ya ce su ɗan kara mashi lokacin. Ya yi kokarin canza dokokin masarautar, amma ƴan majalisar masarauta sun dakatar da shi game da daka mashi zazzafar warning a kan zai iya rasa ransa idan ya yi kuskuren taɓa doka guda ɗaya daga littafan dokokinsu, dole ya bi komai kamar yadda ya ganta a rubuce, tsawon shekaru suke a kan wannan tsari. UHM ABIN TAKAICIN MA WAI WANDA YA FI KAUNA ITA ZA'A KASHE, WLH BASU DA IMANI KO KAƊAN MUTANEN NAN!!. Bobo ya yi iya tinanin da zai yi, amma ya kasa samawa kansa mafita, saboda sun fi karfinsa, bai isa ya yi fito na fito da su ba, sun fishi yawa, hakan tasa ya koma gefe ya yi shiru dan tinani a natse ko za'a samu mafita. Daga karshe ya yanke shawarar fitar da sirrin familynsa ga abokai ko zai samu maslaha, hakan yasa ya kira Smart a waya ya sanar da shi ga halin da yake a ciki, ashe dama sarautarsu ba ta Allah da annabi bace, sosai Smart ya yi mamakin jin hakan, a lokacin suna a tare da Zash, dan su ukun a tare suka yi karatu. In short dai Smart ya ce da Bobo ya ɗauki ƴan uwan nasa ya bar ƙasar, dan faɗa fito na fito da su lokaci guda ba zai yiwu ba, dole sai sun yi shiri, idan kuma ya ce zai zauna a tare da su har su yi shiru zasu iya matsa mashi, idan bai biya masu buƙatarsu ba zasu iya kashe shi, dan ya rigada ya san sirrin RAWANIN JINI. Wannan dalilin yasa Bobo ya shirya makirci cikin dare ya ɗauke mom ɗinsa da kannen nasa dikka biyu ya gudu da su zuwa kasar France, Smart ne ya tsaya mashi tsayin daka sosai, mom ɗinsa dama a tsananin tsorace take, hankalinta a mugun tashe, tana cike da fargabar waye ɗanta zai zaɓa ya fiso, tsoronta kada ace ita ce, kun san wanda baya tsoron Allah da shegen tsoron mutuwa, wlh billahi dik wanda baya tafarkin Allah shegen tsoron mutuwa ne da shi kamar me, dik wanda yake da karfin imani baya tsoron mutuwa, dan already yasan sai ya mutu, kuma idan na kwarai ne shi yasan lahira ta fi mashi duniya sau miliyoyin miliyoyi, dan haka zai so ya tafi lahira ma sai ta fi mashi. Mom ɗinsa tana tsorace, dan ita tasan wannan al'ada, amma kannensa mata basu san wannan al'adar ba. Lokacin da ya shirya ya ɗaukesu daga kasar ba karamar daɗi mom ɗinsa ta ji ba, sai dai kuma taki ta musulunta har wa yau, ba yadda bai yi da ita ba, har ya faɗa mata cewa saboda addinin musulunci yasa bai yi sadaukarwar jini ba, musulunci yasa bai zaɓeta an kasheta ba, dan haka ta musulumta shi ne addinin gaskiya, amma matar nan ta ce babu wannan magana, ba zata musulunta ba, har da cewa Allah ya yi wa Musulunci albarka da ya kuɓutar da su, amma dai ita ba zata musulunta ba, Smart ya ce mashi ya cigaba da binta a hankali kamar yadda shi ma yake lallaɓa mom ɗinsa ta musulunta, idan suna da rabo watarana za'a dace, to haka dai suka yi, kunji kaɗan daga tarihin Bobo. Amma fa har yau har gobe neman Bobo suke yi dan su kashe shi, ya karya alkawari da dokokin BLOOD CROWN, suna nemansa kamar hauka, yanzu an dai'na tinanin ya hau mulki ma, tinanin kashe shi kawai ake yi, jininsa za'a baiwa BLOOD CROWN! Tashin sense, kai akwai cakwakiya fa, bamu fara wasan ba, ku jira bayan bikin Auta balbalin kura zai taso daga sararin samaniya, gobara zata taso daga kogi, wanda kwantar da wannan bala'i sai Allah kawai!!. Kada ku ga laifin mahaifiyar Bobo na kin musulunta, saboda mijinta ya taɓa hawa gadan mulkin BLOOD CROWN, kamar yadda mijinta ya sanya wannan RAWANI imani da tausayi ya fita a ransa, haka zalika ita ma majalisar dokokin masarautar masu alhajin kula da BLOOD CROWN suka cire mata dik wani tausayi da imani, shiyasa bata yi wa su Bobo da sauki, wlh barema Bobo, yana shan wahala a hannunta, tana tauye masu hakkinsu, bata san barinsu su sarara, harta ƴaƴanta mata, tana da bakar zuciya na mugunta sosai, kafin su iya samu ta dawo na kwarai to fa sai ranar da aka ruguje BLOOD CROWN!!. UHM AKWAI RINA A KABA!!. INTERMISSION. NAN SHI NE TAAKIYAR LITTAFIN RAWANIN ZALINCI.🔥♥️ --------------------------------🔥♥️ To fa, mun zo dai'dai wani gaɓar da dikka masarautu biyar na RAWANIN ZALINCI suka gama bayyana, zan lissafo maku su sai in baku aikin zaƙulo stars ɗinku daga kowacce masarauta. Na farko akwai KINGDOM OF POWER, na biyu CROWN OF INJUSTICE wato BLACK WORLD, na uku akwai KINGDOM OF JUSTICE, masarautar Queen Zarina kenan, na huɗu akwai EVIL KINGDOM, masarautar su Yusuf, na biyar akwai, BLOOD CROWN, masarautar su Bobo, dama na ce maku masarautu biyar ne, kuma dik mugan abokan gabane da basa shiri kwata kwata, kuna dai gani yakar juna suke yi, RAWANIN ZALINCI ya zo da sabbin salo na daban, stars na littafin nan su bakwai ne zuwa takwas, kowanne kuma zai fito daga ɗaya daga cikin masarautun nan, KINGDOM OF POWER ce kawai take bada stars guda biyu, yanzu aiki ya ragunmaku, dikka masarautu biyar sun bayyana, saura a fara ainahin yakin bayan bikin Auta kenan, dama in da nike ta fatan in iso kenan, kuma Allah ya kawo mu!. A yanzu ba zan kira maku Stars da kowacce masarauta zata bayar ba, daga matansu har mazansu, saboda kuna tare da dayawansu ne baku san daga ina suke ba, idan kuka san daga in da suka fito a nan ne zan bayyana maku kowani masarauta da stars ɗin da ta bayar, amma ku cigaba da canki cankanku...... 😅 (Kam bala'i, gaskiya RAWANIN ZALINCI ya zo da salo na daban, wai har yanzu laluɓar stars ake yi! Tab to akwai show a nan gaba, ku mu je dai zuwa, zaku sha mamaki fa.😅 To amma a Black world dai mutum biyu muke da su da zasu iya zama star, akwai Ronnie da King Lucian, amma bamu sani ba ko wani zai bayyana a gaba, sannan a masarautar Queen Zarina akwai Rishan ko kuma Ude, na gaba, a masarautar evil kingdom akwai Yusuf da Adam.😅Masarautarsu Bobo wannan kun rigada kun sani na faɗa maku cewa Bobo na daga cikin stars guda shiddan nan, a kingdom of power kuma waye kuka zaɓa a matsayin star? Wannan fa ba zaɓina bane, zaɓin ƴan special grp ne, ni tukun nan ban zaɓa maku stars ɗin ba, ku jirani bayan bikin Auta da Abdussalam akwai tada tarzoma, dan lallai kwakwalwarku zata yi caji fiye da tinaninku, muje zuwa cikin labari my people's) ----------------------------------------🔥🔥🔥 Kwanciya Bobo ya yi a saman sofa yana kallan Zash dake latsa waya, shi ma Smart Zash ɗin yake kallo, kamar suna zargin ya ɓoye masu wani abin ne. Shi kuwa hankalinsa gabaɗaya a kan wayarsa. Bobo zai yi magana phone ɗinsa ta gara ringing. Cikin natsuwa ya cirota daga aljihunsa yana ɗan lumshe Amber eyes ɗinsa kamar yana jin barci, lovely sis shi ne sunan dake yawo a saman screen ɗin, picking ya yi tare da matsar da wayar can gaba domin su ji daɗin ganin juna da kyau, video call ta kirasa. Wata kyakkyawar yarinya ce mai kama da shi sosai, idanunta starry Eyes ne masu bala'in kyau, kwayar idanunta Jade ne, suna wani walkiya kamar ruwan hawaye ne kwance a cikinsu, kuma haka suke, shi kuma Bobo phoenix Amber eyes yake da shi, shi ne ya banbanta shi da ita!, hancinta sharp nose take da shi, ga yawan eyebrows very thick dark brown. Yana picking kuka ta saka mashi cikin shagwaɓa har sai da tasa Zash da Smart suka juyo da kallonsu a kan Bobo ɗin. Shiru ya ɗan zuba mata ido yana kallan yadda take kukan, kamar wacce aka sanya dole ta yi kuka. A tausashe sosai ya ce. "Pinkish lafiya kike kuka?". Da sauri wata kyakkyawar yarinya kamanninsu ɗaya kamar tagwaye ta kwace wayar tare da faɗin. "Bro wai kuka take a kan kewarka". Ta faɗa tana kallansa. Juyar da kansa Smart ya yi ya cigaba da yin abin da yake yi, miƙa mashi hannu Zash ya yi a kan ya bashi wayar. Ba musu ya miƙa mashi yana kallansu da ido. "Beauty ina babyn take bata bari in faɗa mata yaushe Bobo zai dawo". Cewar Zash. Baki beauty ta washe kafin ta ce. "Laaaa Yah Zash dama kuna tare? Shi ne baka nemanku ko? Kullun zamu kira Bro amma bama sanin kuna tare". Ta faɗa tana ɗan zaroviolet eyes ɗinta...... "Sorry aiki ne suka yi mun yawa, amma a mun afuwa, yanzu dai bawa wancan rigimammiyar da kullum idan ta kirasa sai ta yi mashi kuka". Maman Sultan saboda ke da Aisha Jajeri na kara yawan page ɗin nan. Dan haɗani da Allah da kuka yi!!!. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 53 Miƙawa Pinkish wayar ta yi, har lokacin tana kuka hawaye bibbyu ta karɓa, idanunta a tsaitsaye, gashin idanun nata a tsaitsaye alamar bata da kunya ko kaɗan. Zuba mata idanu ya yi yana kallan yadda take kuka bilhakki da gaskiyarta, kai abin ma dariya ya so bashi, ta wani zage, taki ɗago kai ta kallesa, tana kallan ƙasa, a tinaninta Bobo ne, wai ita nan zata gwada mashi ranta a ɓace yake sosai dan ya yi maza ya dawo!. "Bana ce ki rinƙa rufe kanki kuma ki rinƙa sanya sutura masu rufe jiki ba?". Shi ne abin da Zash ya faɗa cikin sanyin murya. Ai tana jin voice ɗinsa a miliyan ta ɗago da kanta, tana sauke kallanta a kansa bata san time da ta waro idanu waje ba, wani irin walwali Zash ya gani na idanunta kamar in an haska madubi a rana, tana ganin shi ne ta yi gaggawar miƙewa zaune, yau babu shagwaɓa sam sam, cike da mamaki ta ce. "Yah Zash dama kai ne? Amma ai kaman Yah Bobo na gani, ko dai numberka na kira ne dama? Kuma dai Yah Bobo na kira fa". A dibirbirce take maganar, tana wani kame kame. Zuba mata idanu ya yi yana kallan yadda take wani muzurai kamar maras gaskiya, tasan sun yi alkawarin zata rinƙa sanya ɗankwali da sutura ta kwarai, bata san shi ya karɓi wayar ba da ba zata taɓa yarda ya ganta a haka ba, kuma wlh tana rufe jikin nata dan cika alkawarin da ta ɗaukar mashi, yau ne kawai aka samu matsala bata rufe ba, tashinta daga barci kenan, yanzu tasan kome zata ce ba zai taɓa yarda tana rufe jikinta ba!. "Yah Zash ina rufewa fa, kuma yau ɗin ne na manta ban rufe ba, ka tambayi Aunty beauty zata faɗa maka". A dibirbirce yanzu ma ta yi maganar, word ɗin suna sarke mata. Shiru dai bai amsa mata ba, hakan ya kara dibirbirtar da ita ya yi, tana san ya yi magana dan ta san ransa ya ɓaci ne ko bai ɓaci ba,.amma ya yi shiru. "To Yah Zash bari in ɗauko kayan in saka ka ji?". Ta faɗa tana kallan cikin idonsa zat tana jiran me zai ce, ko kunyarsa bata ji ba. Kuma fa zata kai irin 15 years haka, amma babu ko kunya, ga shi kayan barcin jikinta irin riga mai ɗan siririn hannun nan ne, ga cup na breast, ya fitar da gabaɗaya shatin nipples ɗinta, ga tudun breast ɗin nata ma dikka a waje. "Yah Zash ka yi magana mana". Tamkar zata sanya kuka ta yi maganar. Siririn harara ya bita da shi kafin ya ce. "Sai da kika ganni ɗin ne zaki ce bari ki je ki saka kaya? Ya muka yi dake time da na zo gida last?"...... A word ɗinsa ta fahimci bai ji haushi ba, ransa bai ɓaci ba kenan, dan haka sai ta saka mashi shagwaɓa, tana turo baki ta ce. "Da gaske Yah Zash ina saka kaya manya, wai baka ga yanzu na tashi daga barci bane?". Harara ya sake binta da shi kafin ya buɗi baki da nufin magana sallamar Auta ta karaɗe kunnuwansu. Gabaɗaya kai kallansu suka yi a kansu. Ai Smart bai san time da ya zaro idanu yana kallan Pretty ba, ta yi masifar kyau cikin English wears ɗin nan, ya ilahi kowa ya ganta sai ya sake waigawa, Auta ta kasheta da haɗuwa, madarar kyanta ya kara bayyana. A ransa ya ce kaga yarinya kamar ita ta yi kanta, ƴar karama sai shegen kyau da shegen miskilanci. Pretty ba hankali, ko sannu bata cewa su Bobo ba, ta wuce ta yi zamanta saman sofa, ko kallan in da suke ma bata yi ba, kamar bata san da halittarsu a wajen ba. Ita kuwa Auta cike da zumuɗi ta ƙarisa wajensu, wajen Zash ta fara nufa tana faɗin. "Yah Zash tin da nazo nike tambayar Yah Omerish ina kake? Sai ya ce mun ka tafi Dubai". Hannu ya miƙa mata ta bashi nata tana murmushi, zaunar da ita kusa da shi ya yi kafin ya amsa mata da. "E jiya na dawo, na yi kewarki sosai my sweetheart"..... "Nima na yi kewarka sosai, kullum sai na tinaka". A shagwaɓe ta faɗa. Cike da zolaya ya ce. "Da gaske anyi kewata ɗin nan kuwa?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e da gaske. Wani irin kallo ya wurga mata mai kama da hararar wasa yana faɗin. "To meyasa ba'a kirani ba tin da an yi kewata?". Zata yi magana ta ji murya cikin harsh voice ance. "Yah Zash wacece kuma wannan?!". Bawan Allah shi ya ɗan manta ma waya yake yi!. Dawo da kallonsa a kan wayar ya yi kafin ya amsa masu da. "She's my sweetheart". Ya faɗa yana ɗan riko shoulder ɗinta, ya matsar da ita jikinsa kafin ya ɗan sauko da wayar dan su samu damar ganinta sosai. Cool murmushi ta sakarwa Pinkish kafin ta ce. "Sannunki". Ɗaure fuska sosai Pinkish ta yi, sai ma da ta ɓalla mata harara kafin ta amsa da. "Yauwa". Saura kaɗan su saka Zash murmushi, Pinkish bata da hali mai kyau, ita sam sam bata san mutane, ji yadda ta haɗe rai fa, amma fa a ganin Zash ne bata san mutane shiyasa ta ɗaure fuska dan taga Auta, ku fa a ganinku me yasa ta yi hakan?. "Yah Zash she looks like Yah Bobo". Cewar Auta kenan. Jinjina mata kai ya yi kafin ya sanar da ita kannen Bobo ne, kara faɗaɗa murmushinta ta yi baiwar Allah, sannan ta kara ce masu sannu. Fuska a ɗaure tamau ta ce. "Wacece ke kuma?". Tana ta fara'a ta amsa da. "Sister Yah Omerish ce ni". Bata ƙarisa maganar ba beauty ta leƙo da kanta ta cikin wayar, wani irin haɗaɗɗen murmushi ta sakarwa Auta kafin ta ce. "Wow they looks alikes, you're so cute, pretty and beauty like him, i like you!". Sosai Auta ta ji daɗin kalamanta, tana murmushi sosai ta ce. "Same, I like more, and you're very beauty more than me". Girgiza kai ta ɗan yi. "Not more than your, lest than your okey?"........ Zata yi magana harsh voice ɗin baby ya katsesu da cewa. "Then so what if she's beauty? Am also beauty more than........". Zash ne ya katse mata maganar bata karisa ba ta hanyar zaro almond eyes ɗinsa, ya yi mamakin jin yadda take faɗa, dik da yasan dama mafaɗaciya ce kamar mom ɗinsu, ba'a taɓata ta yi shiru, to amma me Auta ta yi mata da zata fara faɗa da ita kawai ba gaira babu dalili?. "Pinkish are you hard what you're saying?". Cewar Zash. Shi dai Smart ya koma kan aikin da yake yi, yana yi yana satar kallan Pretty da ta kwanta tana kallan sama kamar mai motsi a kai, ta yi shiru kamar dai bata tare da su haka. While shi kuma Bobo hankalinsa na'a kan tiger dake kwance a can kusa da pool dake wajen. Pretty bata san da tiger a wajen ba. Ganin Pinkish bata nuna mata so ba yasa ta tashi daga wajen, dan bata san mutum ya nuna mata kiyayya. Kusa da Smart ta zauna hankalinta a kan Bobo ta ce. "Yah Bobo sannu da zuwa". Hararar ya wurga mata kafin ya ce. "Sai yanzu kika ganni?". "Sorry Yah Bobo waya nike yi fa". Dawo da kallansa a kanta ya yi kafin ya ce. "A'a kin dai'na san Yah Bobo yanzu, Yah Zash ya fini"....... "Yah Omerish ka faɗawa Yah Bobo ban fi san kowa ba, dikkanku ina sanku kamar rai'na". Ta faɗa kamar zata yi kuka. Hannunsa Smart yasa ya janyota jikinsa, can ƙasa cikin sigar rarrashi ya ce. "Kyale Bobo, yana cikin damuwa ne zai sauke mana a kanki, bashi hai"..... Take ta ji tausayin Bobo ya mamaye zuciyarta, cike da alhini ta ce. "Yah Omerish meyasa me shi?". "Matsala ce ta gida shi da mom". Kamar zata yi kuka ta dawo da kallonta a kansa. "Sorry Yah Bobo ka ji? Believe Allah Everything it will come to and end". Jinjina kai ya yi kafin ya ce. "In Sha Allah our sweetheart"..... Shi kuwa Zash ya zage sai bawa Pinkish hakuri yake yi, ita kuma ta kafe a kan bafa zata hakura ba, dan ranta ya ɓaci, daga karshe ma kashe wayar ta yi tana kuka, ya rasa me ya yi mata ya bakanta mata rai har haka. Pinkish manyan ƙasa!. "Yah Omerish mu tafi to". Cewar Auta. "No my sweetheart, baki ga su Bobo sun zo ba, mun fasa fita, sai gobe". Take fuskarta ta nuna rashin jin daɗin hakan, ta so yau tun da sun samu dama su fita, amma kash hakan ba zai yiwu ba, miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi barin wajen. Har cikin ransa ya ji cewan bata ji daɗi ba, amma ya yi kamar bai gane ba, hannun Pretty ta riƙo tare da cewa. "Pretty zomu je bedroom ɗinmu mu kwanta mu yi hira". A miliyan Pretty ta ɗago da kanta. "Fitar fa?". Ta jefa mata tambayar tana kallanta, yarinyar nan tamkar bata san da halittar mutane a wajen ba, wlh da a gidan sarauta cikin gata Pretty ta tashi za'ayi bala'i, wato dik miskilanci mutum sai ya sarara mata, wannan ma ba wayewa ne da ita ba, da yake dai a jininsu abin yake ne sai gata tana dakonsa. "Yah Omerish ya ce ba zamu fita yau ba sai dai gobe". Auta ta bata amsa tamkar zata yi kuka. Girgiza kai Pretty ta fara yi kafin ta ce. "A'a ni ba zan yarda da hakan ba, tin da ya ce zai kaimu yawo to sai ya kaimu!". Cike da gadara ta yi maganar, sak dai yadda shi yake magana da gadara kamar kowa mallakinsa ne a karkashinsa yake, ashe ba laifinsa bane, sarauta ke ɗawainiya da shi, to yau dai ya samu dai'dai da shi.........😅 Da mamaki gabaɗayayansu suka ɗago da kallonsu a kanta, sai a yanzu Zash ya san da ita a wajen, shi ma Bobo dik da ta zo ta wucesa bai ɗago ya kalleta ba, hankalinsa a can duniyar tinani, sai a yanzu ya ganta. Shi kan Smart wlh burgesa take yi, sai ma idan tana magana, a yanayin yadda yake kallan abin nata kamar yarinya irin ce mai cike da class da ji da kanta, zaku iya zama da Pretty tsawon wuni a waje guda word ɗaya bai haɗaku ba, in baka mata magana bata yi wa mutum, idan ma ka yi mata ɗin ma sai ta yi niyya zata amsa, kamar wata mai aljanu. A ɗan rikice Auta ta ce. "Pretty Yah Omerish ne fa, meyasa zaki ce haka? Shin ba yayanki bane shi?". Ɗan turo baki ta yi, kuma dik maganar da take yi kallanta a ƙasa, bata ɗago kai ba bare ta haɗa ido da kowa. "To shi Yah Omerish ɗin ba shi ya yi mana alkawarin zai kai mu ya wo ba? Waye ya ce mashi ana saɓa alkawari? Ko bashi da ilimi ne? Kuma shi ɗin waye ne shi da ba za'a faɗa mashi gaskiya ba? Dole ya cika alkawari ya fita da mu!". Babbar magana, mai ilimi tana magana, wai Pretty ce zata cewa wani bai da ilimi, ita da lokacin da mamansu ke karantar da su tana karkashin korama tana shakar iska mai ni'ima, Sweetie na kwasan ilimi, amma da ɗan guntun karatunta da bai wuce primary 3 ɗin bane zata ce wai wani bai da ilimi, kai Pretty ƴar duniya ce wlh. Zash da Bobo kallan Smart suka yi, har suna haɗa baki wajen tambayarsa wacece Pretty. Mayar da kansa a kan laptop ɗinsa ya yi, bashi da amsar da zai basu, dan shi ma bai san wacece ita ba. A karo na biyu suka sake tambayarsa, kawai sai ya ce masu sistersa ce. Da mamaki suka sake binta da kallo, kwata kwata bata yi kala da ƴan gidansu ba, kalarta daban, ko iya kyakkyawan eyesball ɗinta kawai ya isa ya fahimtar da mutane ba zubin larabawa gareta ba, amma sai basu yi wani dogon tinani a kan komai ba, suka yi shiru kawai. Auta na kokarin yi mata magana ta wuce izuwa in da Smart yake zaune, ƴar rainin wayo bata ganin mutane ashe tasan in da kowa yake zaune. A kusa da shi ta tsaya, tana zuwa ta riko hannunsa a cikin nata, cikin shagwaɓar da take yi wa Kamran, without respect ta ce. "Ka tashi ka kaimu yawo ka cika alkawarinka!". Kamar Momma ke bashi umarni, ba abin ya maketa ta mutum mashi a wajen ya yi kisan kai ba............ Shi yanzu ya fara yi mata kallan mai matsala a ƙwaƙwalwa, har ya fara tinanin yin scanning na brain ɗinta. Tsawa Auta ta daka mata a kan bata da hankali ne? Ita bata san babba bane?. Kuka ta saka tare da faɗawa jikinsa, ita ba ruwanta da wani babba, bata ma nemi sanin ko waye shi ba ato, kawai tin da ya yi alkawari bai isa ya karya ba, dole ya cika mata. Babbar magana, ai rasa abin faɗe ya yi, su Zash sun tsaresa da ido kawai suna binsu da kallon mamaki, yau sun ga wadda Smart yake ragawa,.abin wlh ya yi mugu mugun basu mamaki. Shi kuwa banza da ita ya yi, kamar bai san tana yi ba, ta rinƙa kuka kamar wadda aka saukarwa da wahayin yinsa, Auta dai sake baki ta yi ta rasa abin faɗe. Cigaba da aikinsa ya yi yana tinanin tafiyarsu kingdom of power jibi da za su yi, zasu je su amsa kiran King. Ya yi nisa cikin tinanin da yake yi sai ji ya yi tamkar wanda aka tsayarwa da gabaɗaya jinin jikinsa, cak ya ji kowani kofa na jininsa ya dakata da yin aiki, lokaci guda ya jisa a duniyar mercury. Slowly ya dawo da kallonsa a kanta. Tana kuka tana yi mashi wasa da cibiyarsa kamar ya sakata, sam bai ji lokacin da ta ɗaga mashi riga ba, sai jin ɗan yatsarta ya yi a cikin cibiyarsa. Ai wani irin shocked da ya yi sai da yasa su Zash hankalinsu ya dawo kansa, amma basu fahimci dalilin shocked ɗin ba, saboda basu iya ganin me Pretty ɗin take mashi ba, dik da haka sai suka tambayi dalili. Kai kawai ya iya girgiza masu, Pretty na nema kiran ruwa, dama yaya, su da suka yi gadan abin, lallaɓa rayuwarsa yake yi amma yarinyar nan zata jefa shi cikin bala'i. Da kyar ya iya riƙo hannunta a cikin nasa, a take ya ɗaure fuska wai irin ta zaci ba wasa yake yi ɗin nan ba. Sai dai tana ɗago kanta suka kalli juna ido cikin ido sai ya nemi dik wani zafin da ya ɗauka ya rasa, kwayar idanunta sun sanyaya mashi rai lokaci guda. "Tashi muje to". Shi ne kawai abin da ya iya faɗa mata. Ba musu ta miƙe daga jikinsa........... "Zash muje yawo". Ya faɗa yana kallonsu. Miƙewa Bobo ya yi ya kwanta yana faɗin sai sun dawo shi babu in da zai je. Shi kuwa Zash ya miƙe tsaye yana faɗin su je zai samesu a can bari ya je gidansu Bobo ya ɗauki Pinkish and beauty sai su je a tare daga nan sai su wuni a nan a tare. Sosai Bobo ya ji daɗin wannan al'amari, saboda ko ba komai yau zasu huta da masifar mom ɗinsu. Haka kuwa aka yi. Smart dan dolensa ya ɗaukesu suka fita, in ba haka ba Pretty ba zata barshi ya zauna lafiya ba, sai dai kuma ko da suka fita ɗin ma bai tsira ba, dan tana manne da shi, dik in da zai shiga taki rabuwa da shi saboda shegen tsoro. Sai ma da suka shiga katafaren wajen shaƙatawa dake ƙarƙashin teku, wajen ne na glass da kana ciki kana iya kallan yadda manya da ƙananan kifaye da sauran halittun ruwa suke shawagi. Ita dai Auta ta saki jiki sai kallo take yi tana ɗaukar hotuna kala kala, kai tsaye tana turawa Hoorain ɗinta. Ita kuwa sarkin tsoro ta ƙanƙame shi dan dole ya rungumeta suka rinƙa yawo a ciki. Da suka je restaurant na cikin wajen, dik san abinci irin nata a wannan rana dai ta ce ba zata ci wannan abincinba, ba yadda Smart bai yi ba taki, har ce mata ya yi zai bata a baki, amma taki yarda, ba komai yasa taki ci ba face abincin ruwa ne, a wajen basa sayar da komai sai namomin cikin ruwa, gani ta yi sun bata kyama sosai wasu halittun, sai daga baya Smart ya fahimci tana da kyankyani ne, dan haka sai ya ce a kawo mata kifi wanda aka cire kayarsa tsab, dan yasan halinta, ba iya gyarawa zata yi ba, ta ci kaya ta barshi da wahala. Da aka kawo mata ta ji daɗi sosai ta kuma ci, dan shi wannan ta saba ci a wajen Kamran!. In short yau dai sun sha yawo sosai yadda yakamata, a taƙaice dai kafin su koma kingdom of power sun yi sabo sosai da sosai, sai dai dik zaman da suke yi su uku a cikin gidan da iya Smart kawai Pretty take magana, bata taɓa cewa su Bobo ko sannu ba, har ranar da zasu tafi kingdom of power sannu bai haɗata da su Bobo ba, kuma a tare suke zaune, nan suke kwana, amma yarinyar nan tamkar bata san da su a gidan ba....... Dole in ɗan taƙaita wasu gurare domin manyan gurare da suka fi mahimmanci suna gaba, so dan haka mu je zuwa!!. Mu je ga kingdom of power. Su uku suka shirya tafiya kingdom of power, suka bar su Bobo su kaɗai a gida cike da kewarsu, Auta baki har kunne zata je ta ga Hoorain, ita dai Pretty koma ina zasu je bata da matsala, bama ta san ina suka nufa ba, kawai tana rike da hannun Auta har Bobo and Zash suka kaisu airport, har suka shiga cikin jirgi suna manne da juna!!. (STOP MY PEOPLE'S!! Na ce stop!!. Yaseen irin ƙwaƙwalwar mutane ne da ni! Wlh irin ƙwaƙwalwarku nike da shi!! Ta ya za'ayi ku rinƙa ce mun kamar ba ƙwaƙwalwar mutane irin naku nike da shi ba wai?! To irin naku ce da ni, kawai dai abin da na sani shi ne kowa da irin girman ƙwaƙwalwarsa, kun gane ai?. Masu mamakin yadda na haɗe masarautu biyar dikka nike story a kansu, kuma kowanne da cakwakiyar, dik yawan mutanen ciki bana mance ko mutum ɗaya ko na ɗauki sunan wanna na bama wannan kuma stop na ce yauwa kuna ganewa ko? Tabbas ku zaku ga akwai wahala, amma ni a wajena Allah ba wani abin bane, dik suna a cikin kwakwalwata ne shiyasa bana mantawa, kuma batu na gaskiya ni ina rubutu da zuciya da ƙwaƙwalwata ne shiyasa, idan na sanyawa zuciyata zan yi abu to is very very hardly na kasa yi! To paka paka kwakwalwarmu iri ɗaya ne kun ji? And amsar last tambaya shi ne e ni ina karanta Bibles sosai gaskiya, tin ina primary school na fara karatunsa, a hannun wata friend ɗina mai suna Rejoice James na fara karɓa na fara karantawa, kuma har yau idan na yi ra'ayi ina karantawa, so karatun Bible ba haramun bane ba!. Daga ƙarshe kuma ita rubutu baiwace sosai wlh da Allah yake bawa bayinsa, ina kuma miƙa ɗinbin godiyata a garesa da ni'imar da ya yi mun, ina alfahari da ilimin addinin dana zamani ya bani, ka zalika ina farinciki da ni'imar rubuce rubuce da ya yi mun, bugu da kari ina godiya da basira game da falalar ƙwaƙwalwa mai girma da ya bani, alhamdulillah, babu abin da zan iya biyan Allah da shi face godiya game da bauta bisa ƙaida, wlh ina matuƙar alfahari da farincikin da dik wani littafin da na rubuta da kuma wanda zan rubuta a gaba, dan dik littafan da na rubuta alhamdulillah na samu abin da nikeso. Dan wlh dikkansu sun faɗakar, sun wa'azantar kai babu ma kamar wannan RAWANIN ZALINCI, littafin nan ya fita daban sosai, tin ban kammala shi ba na samu sakonni da dama a kan yadda mutane suka karu da shi matuƙa, gaskiya I really appreciate that!! And really like you guy's. Much love...💘 🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥 Tin kafin jirginsu ya yi landing airport ta cika da shirga shirgan sabbin motocin da King ya sayo dan wannan biki. Jaish ne ya jagoranta tawagar zuwa ɗaukarsu, Jawad and uncle Jahiz dik suna tare, guyson ma ya je, amma su Omaid sun ki zuwa. Jirginsu na sauka ba tare da ɓata lokaci ba suka fito, Auta na rike da hannun Pretty, while shi kuma yana bayansu. Jaish da Jawad ne suka fara nufarsu, fuskar Smart tamkar wanda aka aikowa da saƙon cewa wutar jahannama zai shiga, shi kansa Jaish sai da ya ji gabansa ya faɗi ganin face ɗin yayan nasa. Sannu da zuwa suka haɗe baki wajen yi mashi shi da Jawad, sai dai bai amsa ba, ko kallon in da suke bai yi ba, burinsa kawai ya isa gida su yi ido biyu da King, yau sai ya sanar da shi dalilinsa na hana Auta wanda take so, ya sanar da shi dalilinsa da yasa yake san lalatawa yarinya rayuwarta....... KAI YA AKA YI SMART DA AKA ƁOYEWA BATUN AUREN YA SAN DA ZA'AYI BIKIN? WA KUKE TUNANIN YA FAƊA MASHI?. Kai tsaye mota ya nufa, da sauri suka rufa mashi baya, bai ce da su ko uppan ba ya shiga mota, sai huci yake yi, ita kuma Auta da bata san me yake faruwa ba, sai murna take yau zata sanya Hoorain a idanunta, bata sanar da shi zata dawo ba, wai surprise take san yi mashi. Dik ta ƙosa su isa gida, ga shi dare ne, daɗin satar hanya ta je wajensa kenan. Jaish yana san tambayar yayan nasa me yake faruwa, amma yana fargabar amsar da zai iya bashi, dan haka sai ya danne har suka isa gida. Motocinsu na dakatawa ya juyo da nufin ya tambayesa, sai dai ina, kafin ya yunkura tuni Smart ya yi waje, kafin ya fito ya bi bayansa ma har ya shiga elvator ya yi sama abinsa. A gaggauce Jaish ya bi bayansa dan jin meyakefaruwa. Ita kuma Auta ita da Pretty suka biyo Yah Jawad zuwa cikin gida, Auta ta yi mamakin ganin cikar jama'a a gidan nasu, amma bata kawo cewa batun aurenta ake yi ba, hankalinta ma baya a kansu, burinta kawai ta je ta yi wanka ta isa ga abin kaunarta su ga juna, ta yi kewarsa sosai. Kai tsaye part na King Smart ya nufa, sallamar ma a cikin zuciyarsa ya yi, ya kuwa yi sa'ar samun momma a ciki, yana shiga ya tsaya a bakin door tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana bin King da momma da kallo, suna zaune saman bed, suna duba jadawalin yadda taron zai kasance, da kuma ɗinbin dukiyar da suka ware dan yi kyaututtuka. Jin motsin shigowa yasa suka yi gaggawar kai kallansu kan door. Wlh dikkansu sai da gabansu ya faɗi time da suka ɗaura idanunsu a kansa. Muryar momma har rawa yake yi wajen cewa. "Omerish har kun iso ne?" Idanunsa a kan King ya yi shiru bai amsa mata ba, aka ce ɗan na gada ya fi ɗan na koya, dik jaruntakar King sai da ya ji ya sha jinin jikinsa, saboda wani irin kallon da Smart yake binsa da shi, kuma kun san idan mutum bai yi adalci ba to fa shi kaɗai ya rinƙa tsarguwa kenan yana jin kamar ba daɗi. "Omerish lafiya kuwa?". Momma ta faɗa a dame, ta yi maganar tare da saukowa kasan bed ɗin da nufin ta nufesa. Sai dai bata kai ga nufarsa ɗin ba ya ɗaga mata hannu kallansa a kan King. With harsh voice ya ce. "Why? Metayi maka da ka rantse dole sai ka kuntatawa rayuwarta? Shin kai akwai wanda ya yi maka irin hakan ne?!". Ya maganar ko kaɗan bai kyafta idanunsa daga kallon da yake yi wa King ba. Momma zata yi magana ya yi saurin cewa. "Momma please let me ask him first, ya faɗa mun dalilinsa na san sanyamu cikin bakinciki". Cikin natsuwa King ya ajiye file na hannunsa a saman bedside drawer, sannan ya sauko ƙasa, idanunsa a kan ɗan nasa ya amsa da. "Saboda na hanata auren mutumin da da shi da gawa dik ɗaya ne shi ne kake ganin na kuntatawa rayuwarta?". Kai tsaye Smart ya amsa da. "Ba wai gani nike ka kuntatawa rayuwarta ba, kai tsaye na tabbatar da ka kuntatawa rayuwarta!". Babbar magana!!. "Zunaira ba zata auri mayakin can ba, saboda da shi da gawa dik ɗaya ne, daga yanzu zuwa kowani lokaci a kan hanyar mutu yake, kobama haka ba, Zunaira jinin sarauta zata aura kamar ita, wannan shi ne gata a gare ta!....." "Gata!". Smart ya maimaita kalmar kafin ya ce. "Dad kowa ma a kan hanyar mutuwarsa yake, ba abin mamaki bane a wajen Allah ka mutu ka bar mayakin da kake ikirarin shi gawa ne, and koma menene shi waye ya mayar da shi hakan? Ba kai bane? Ai bai cancanci haka daga gareku ba, kada ka manta rayuwarsa ya saka dan cetar taku da kula da dukiyarku, me aibunsa? Shin ba irinsu nema yakamata ku sakawa da kyakkyawar alkhairi ba?!". Cikin harsh voice ya yi maganar, dan ya fahimci sankai ne kawai yake ɗawainiya da daddyn nasu. "Omerish yana da kyau ka san cewa ni fa daddynku ne, ba zan taɓa yin abin da zai cutar da ku ba, kuma yakamata ka koyi magana da ni cikin girmamawa, saboda gidan sarauta kake, baya ga ni mahaifinka ne ni sarki ne mai jagorantar al'umma guda!!". "Dad a haka na iya magana, da kowa a haka nike yi!!". Ran King ne ya kara ɓaci sosai, dama tin ɗazun danne ɓacin ran nasa yake yi saboda baya san su samu saɓani da ɗan nasa. "Okey, to Hoorain bawane, kare ne mai tsaronmu, dan haka a kan wannan hanya zai mutu, Zunaira ba zata taɓa zama mallakinsa ba, Omerish ka fita mun daga ɗaki!!". Cikin tsananin ɓacin rai King ya yi maganar!. Smart ya ɓata mashi rai sosai, bai so ace Smart yana magana no respect haka a garesa ba, abin ya koma mashi rai matuƙa. "Dad Zunaira ba zata auri zaɓinka ba, zaɓinta zata aura, kuma Hoorain shi ne zaɓinta, shin akwai wanda ya taɓa tauye maka hakkinka ne dad da zaka nemi ka tauyewa rayinya nata?!". Shi ma Smart cikin fushi ya yi maganar. Abin da momma take gudu shi ne ya faru, tin ɗazun sai ƙoƙarin dakatar da su take yi, amma abin ya ci tura, ga shi har sun jawo ɓacin rai ya shigo cikin al'amari, shaiɗan yana neman yin galaba a tsakaninsu...... "Zamu gani idan kai ka haifa mun Zunaira ɗin sai kasa ta auri wanda ba zaɓina ba!!". King ya faɗa da kausasshiyar murya. "Zaka gani dad, tin wuri kafin ka ji kunya ka canza wannan abin, idan ba haka ba kana ji kana gani zan hana wannan aure". Tin da ya shigo ɗakin yana tsaye yadda yake bai motsa ba, sai iya magana cike da iko da isa!. Cikin zafa gadan gadan King ya nufesa yana faɗin. "Ni kake faɗawa zan gani kuma zan ji kunya?. To idan har ka haifu kasa in ji kunyar!!". Ko kaɗan bai ji tsoron daddyn nasa ba dik da yana nufosa ya amsa mashi da. "Zakuwa ka gani, in dai baka canza ka bawa Zunaira zaɓinta ba to tabbas zaka sha kunya, kuma Allah ma ba zai kyaleka ba, zalincin ya yi yawa...". Kara hasala zuciyar King ya yi, da zafa ya ƙarisa wajen da nufi ya ɗauke Smart da zazzafar mari, sai dai kuma Momma ta yi gudun shiga tsakaninsu, yau taga tashin hankalin da bata taɓa zata ba, hankalinta a tsananin tashe ta rike hannun King da yake ƙoƙarin kaiwa Smart mari, jikinta har kerma yake yi ta fara bawa King hakuri. Shi kuwa Smart ko jezau bai yi ba, kamar ba shi aka nufa da mari ba. "Rahilarh ki matsa mun daga gabana, dik abin da ya faru ba ke kika ja mun ba? Dik cikin ƴaƴana akwai wanda ya isa ina faɗa yana faɗa ne? Dik suna da tarbiya kuma suna respecting ɗina, kin cutar da ni Rahilarh, kin zalunci zuciyata, kinsa yau ɗan cikina, ɗan da na fi kauna sama da kai'na ne ya tsaya a gabana ina faɗa yana faɗa har yake ce mun zan yi danasani a rayuwata saboda rashin tarbiya!"....... Nisawa Smart ya yi, ya ji King yana ƙoƙarin zagan mashi daddynsa na France, wato shi ne bai bashi tarbiya ba, maganar ta kora ransa sosai, cike da takaici ya ce. "Suma ƴaƴan dake da tarbiyar nan gaba kaɗan zasu dai'na yi maka biyayya idan har zaka cigaba da tauye masu hakkokinsu kana zaluntarsu dan wani san zuciya taka, suma zasu dai'na bin umarninka a lokacin da zasu fahimci suna da ƴancin kansu". Cikin kunar rai ya kai karshen maganar. Ran King idan ya kai miliyan to fa a wannan gaɓar ta ɓaci, zuciyarsa a tafashe ya kwace rikon da momma ta yi mashi, yana huci kamar wani zaki ya damki wuyar rigar Smart. Momma bata ɓata lokaci ba wajen sake shiga tsakaninsu, cike da tashin hankali ta fara faɗin King ya yi hakuri ya sake shi a bi komai a hankali, tasan koma me ya faru ita ce sila, kowa laifinta zai gani, kuma hakan take laifinta ne, ita ta kai Smart in da tarbiyarsu ya saɓa da na gidan sarauta, krista ce fa ta tarbiyartar da shi, kunga kuwa dik abin da suka gani sai dai su ja baki su yi shiru kawai. "Momma ki kyalesa ya yi dik abin da yake ganin zai iya yi, amma dai Zunaira ba zata taɓa auren zaɓinsa ba!". Smart ya faɗa ko a jikinsa, dan shi zafin da King ya ɗauka ma ko ɗaya bata dame shi ba, saboda yasan ba komai bane idan aka danganta da zafinsa idan ya ɗauka. Rai a matuƙar ɓace Momma ta ce. "Omerish idan ka sake saka baki kan batun auren Zunaira ban yafe maka ba, haba mana, kasheni kake san yi ne? Meyasa baka tinanin kuncin da zaka sakani a ciki? Meyasa ka canza kake san ɓacin raina abin da a baya shi kafi tsana fiye da komai? Meyasa menayi maka da zafi haka?". Ranta ya kai kololuwar ɓaci ne, tana san sasanta abu shi kuma Smart yana neman kara lalata komai, shiyasa ta yi wannan furucin!. Jin saukar kalamanta ya yi tamkar saukar aradu, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, a fusace ya sa hannu ɗaya ya ɓanɓare hannun King daga wuyarsa, cikin zafa ya juya ya bar ɗakin yana wani huci kamar mayinwacin zaki. Yana fita King ya dubi momma, a dakile ya ce. "Kin gani ba? Kinga irin abin da kika ja mun ba? To daga yau na haramtawa Omerish komawa kasar France, ya dawo kenan, ba zai sake komawa ba, dole ya zauna da mu a nan ya koyi tarbiya da girmamawa na gidan sarauta, ki kira iyayensa na can ki sanar masu na ɗauki ɗana kenan!!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya koma cikin ɗakin, ransa sai tafarfasa take yi. Shiru momma ta tsaya, ta rasa waye zata bi, ga Smart ya ɗauki zafi ya fita, ga kuma King shi ma ya ɗauki zafi, to waye zata bi dan ta rarrashesa kenan? Ta jefawa kanta tambayar, yau fa ake yinta. A gefe guda kuwa. Auta ta tsala wankarta tsab, sai murna take yi zata ga jaruminta, dan kada a gano akwai wanda zata je gani yasa bata saka wani kayan azo a gani ba, sai ta sanya sleeping dress masu mutunci, riga mai dogon hannu da wando shi ma dogo. Ta sanya headband a kanta, ta ɗauki wayarta ta nufo waje, wai dan ma idan ta haɗu da wasu kada su zargi wani wajen zata je. Har ta kai bakin kofa ta juyo ta ce. "Pretty ina zuwa, dik wanda ya zo nemana ki ce ina wajen Yah Omerish kin ji?". Pretty dake kwance saman gado bata amsa mata ba, yau miskilancin ta motsa kenan. Sanin cewa ta jita yasa Autar bata damu da sai ya amsata ba, ta yi gaggawar wucewa kawai ta fita. Jikinta sai tsuma take yi tana san kallan jaruminta. Tana fita dai'dai lokacin kuma Abdussalam ya shigo part na family daga ɓangaren uncle Abbas, ya zo ganinta ne, dama ya yi kewarta sosai, so ya samu labarin ta dawo shi ne da marmarinsa ya zo ganinta. Ita kuwa a lokacin ta fita ta kofar baya, sai nemanta guyson ma yake yi, Chuchu and Aneesa dik suna ta nemanta, cikin sanɗa da dabara ta nufi ɓangaren mayaƙa, tana tafiya tana ɓuya. Har ta isa ɓangaren warriors ɗin. Kai tsaye ta nufi bedroom ɗinsa, sai murna take yi, a lokacin yana kwance saman bed ɗinsa, ya idar da sallar isha'i ba jimawa, ya yi wanka yana sanye da white arabs jallabiya mai shegen kyau, ya ɗauko wayarsa da nufin zai kirata kenan ya ji knocking, a tinaninsa Abbonsa ne ko su Ansar, sai bai yi magana ba ya ajiye wayar tare da saukowa kasan bed ɗin ya nufi door. Ba tare da tambayar wanene bane yasa hannu ya ɓalle key na door ɗin ya ja ya buɗe. Ai bai san lokacin da ya zaro ido tare da blinking sau biyu a lokacin guda ba ganinta da ya yi. Cikin gaggawa ta raɓa gefensa ta shige cikin bedroom ɗin tana dariya, ƙasa juyawa ya yi ya koma, sai yake ganin abin kamar a mafarki, ko kaɗan bai yi zato ba, kuma ko kusa bai ji labarin ba, shi dai ya ga baki suna ta zuwa, idan baku manta ba Abbonsa ya ɓoye mashi lamarin, so bai da labari. Saman drawer dake kusa da bed ta zauna tare da ware tafukan hannunta ta rufe face ɗinta tana sakin cool smile. Ya jima tsaye a wajen yana al'ajabi kafin ya juyo ya dawo ciki, rufe kofar da key ya yi, gabaɗaya sai ya ji ya ƙasa iya ɗaga idanu ya kalleta, wani irin zazzafar sonta ne yake kara fisgarsa. Da kyar ya karisa in da take, a bakin bed ya zauna suna fuskantar juna, sai ya yi ƙasa da kai ya kasa magana ita ma ta rufe fuska tana murmushi ta ƙasa magana. Abin like wow gwanin birgewa, yadda suka zauna abin ya ƙayatar, kamar wasu mata da miji da suka mallaki juna!. Almost five minutes suna a haka kafin ya ɗan nisa, kansa a ƙasa yaki ɗagowa ya ce. "What a wonderful surprised! Gaskiya ba zan taɓa manta wannan rana ba my Hoonaira". Taki cire tafukanta daga face ɗinta ta ce. "My Hero ka ƙara kyau sosai, ka ɗan yi kiba abinka"........ "Na sha drips ba adadi ai dole na yi kiba, kema ai kin kara kyau sosai, kinsa na ji tamkar yau na fara ganinki". Cike da mamaki ta ce. "Dama ka ganni ne?". Ta yi maganar ne saboda taga ko sau ɗaya bai ɗago ido ya ganta ba, kansa a ƙasa, kuma ya ce ta kara kyau, ko a ina ya ganta?..... Bata san ɗan ikka ne yana satar kallanta ba, mai kunya irin na Jaish😅 Kai ya jinjina mata alamar ya ganta mana. "My Hero kai ne fa kullum kake damuna a kan yaushe zan dawo, na dawo cike da muradin zuwa in ganka, na zo kuma ka yi ƙasa da kai, kaki ɗagowa mu kalli juna, to me yasa?". Cikin shagwaɓa sosai ta kai karshen maganar. Ɗan ɗago idanunsa ya yi ya saukesu a kan kyawawan kafafunta dake cikin wasu kyawawan flip flops masu laushin takawa. "Ni ai na ganki". Ya faɗa idanunsa na ɗan rawa, kamar yana tsoron ɗagowa ya kalli kayan jikinta ne!..... "No my hero, ni gaskiya ban yarda da irin wannan kallon ba, ni fa yanzu nasan gaskiyar abin da yake cikin zuciyarka kamar yadda kasan nawa, meyasa zaka cigaba da azabtar mun da kanka wajen hana idanunka kallan abin da kasan zai zama mallakinka koma in ce ni taka ce?". Kamar zata saka mashi kuka ta yi maganar. Nisawa ya ɗan kara yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗimi, lallai ba shakka yau ta yi mashi abin da tasa saura kaɗan farinciki ya kashesa, dan a lokacin da ya buɗe kofar nan ya sauke kallansa a kanta saura kaɗan numfashinsa ta dakata da breathing!. Slowly ya ɗago da kallonsa izuwa saman face ɗinta, cikin natsuwa ya ce. "Ba wai ina hana kaina kallanki bane, bana san kallan ya wuce na Musulunci ne, nasan in dai na ɗaga idanu direct na kalli face naki to fa zan zarce kallan musulunci, dan ba zan iya hakurin zare kallona daga kanki ba". Ya kai karshen maganar yana tsayar da idanunsa a cikin nata, kallansa take yi kawai tamkar ta mayar da shi cikin kirjinta haka take ji. Take idanunsu ya sarkafe cikin na juna, suka mace da zubawa juna kallon kauna, wani irin salon kallo da suke aikawa junansu mai cike da saƙonni da suke nuna tsantsar kewa da kauna juna tin da nike a wajensu kawai na taɓa kallan irin wanna salon kallon. Ko waye ya koya mashi? Gara ita Auta mun san daga ina ta koyo, shi fa? Mu dai mun san banda yaki babu abin da ya iya!. "My Hero na yi kewarka fiye da yadda zato zai iya zata". Ta yi maganar ba tare da cire kallonta daga kansa ba. Ajiyar zuciya ya sauke. "Gaskiya na fiki shiga cikin kewa, kullum tinaninki ya zame mun tamkar iskar da nike shaƙa, kome nike yi ke nike tinawa, kina rai'na fiye da yadda tinani zai iya tinani". Cigaba da sakar mashi narkakken smile mai narka dakakkiyar zuciyarsa na warriors ta yi. "Please ina neman alfarman da a cire mun hannun nan in ga fuskar Hoonairata yadda yakamata". Ya yi maganar yana ɗan satar kallan dogon kyakkyawan wuyarta zuwa ƙasa kaɗan, ya ɗan yi mamakin ganin sauyawarta, kwata kwata fa bata cika wata biyu da barinta kingdom ɗin ba, amma ta sauya sosai, ya yi mamakin ganin yadda kirjinta ya ciko sosai, sai da ya ji tsikar jikinsa ta tashi, sai da ya ji kamar an jona mashi lantarki, ya yi danasanin kai kallansa wajen!. "Ni dai a'a, kunyarka nike ji, ba zan iya buɗe fuskata ba". Ta faɗa tana zuba mashi wani irin salon kallo na musamman, ɗaya ne daga cikin irin salon da ta tanada zata rinƙa yi mashi a gidan aurensu. "Yau kuma ni ake kunya?". Cikin sanyin murya sosai ya yi maganar. Kai ta jinjina mashi alamar e kunyarsa take ji!. Shiru ya ɗan yi, can kuma sai ya ce. "Kenan yanzu idan muka yi auren ma haka zaki mun? Ki ta rufe mun fuska da sunan kunyata?"...... Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. "E haka zan yi, idan ka takura sai ka rabani da kunyar in daina ji, kaga sai ka samu sauki". Wani irin daɗi ya ji ta lulluɓe zuciyarsa, ƙasa ya yi da murya, cikin tsigar dabara ya ce mata. "To shikenan, amma yanzu dai please a barni in kalla ko sau ɗaya ne?". Kai ta ɗan girgiza tare da faɗin. "Ni kunya nike ji! Ba zan iya ba". Cikin wannan shagwaɓa tata mai tafiya da imanin ta yi maganar, sai ya ji tamkar an tsira mashi allura a tsakar ka. "Please my Hoonaira, wannan kunyar zai cutar da ni fa, Please mana, shin baki son in ji daɗi ne?". Murya a raunace ya yi maganar..... "To rufe idanunka sai in buɗe maka"..... Ba musu cikin sauri ya datse idanunsa, dan a tsananin ƙage yake da san ganin face ɗinta. Zame hannayenta daga face ɗin nata ta yi, sannan ta riko hannunsa da hannunta ɗaya, ɗayan hannunta kuma ta bayyanar da kyakkyawar diamond ring da ta ɓoye a ciki ta yi, ware kyawawan yatsun hannunsa ta yi a in da ta zura mashi ring ɗin a yatsarsa dake kusa da babba na tsakiyar nan, sai wani irin balai'n kyalli zoben yake yi. Tamkar dan hannunsa aka yi ta!. Shi kuwa har cikin tsakiyar ransa ya ji ya amsa a lokacin da ta riko hannunsa, gabaɗaya sai ya ji tamkar ba'a duniya yake ba, amma ya daure yana jinta ta sanya mashi zoben, bai ta shi jin tamkar yana duniyar mercury ba sai da ta kai ɗan bakinta ta sumbaci ring ɗin, ai bai san lokacin da ya waro idanunsa waje ba, kai tsaye sai saman face ɗinta ya sauke kallonsa, nan fa ya kara kiɗimewa sosai, dan wani irin sihirtatcen kyau da ta kara yi, kumatunta ɓulɓul. A take yanayinsa ya fara canzawa, dannewa ya yi tare da ƙoƙarin kawar da dik wani tinani. Muryarsa na ɗan sarkewa ya furta. "Ring ɗin nan ya yi tsananin kyan da shi kansa kyau ya jinjina mashi, zan iya sumbatarsa?". Ya yi tambayar idanunsa a kanta babu ko kyaftawa. Yatsa ta kai saman ramin da ya lotsa a kumatunsa, wato kyakkyawan dimples ɗinsa. "Zaka iya sumbata, ai naka ne, my hero dimples ɗinka sun fi nawa kyau sosai". Tamkar wadda ta jonawa lantarki haka ya ji da ta taɓasa, wani irin azabbabben shock ya ji, da kyar ya iya dannewa, ya kai hannunsa saitin ɗan bakinsa ya sumbata, sai ya ji tamkar lips ɗinta ya sumbata, dama saboda ta sumbaci ring ɗin ne ya ce zai sumbata shi ma, dan ya ɗaura lips ɗinsa a in da ta ɗaura tata!. Ƙasa jure jin hannunta a kumatunsa ya yi, tana jefasa cikin wani yanayi, hakan yasa ya kai hannunsa ya riko hannun nata, a hankali ya zameta daga face ɗinsa, sai dai kuma ya kasa iya sakinta, dan wani irin tsantsar kaunarta dake fusgarsa, ga skin ɗinta very soft shiyasa ya kasa iya sake mata hannu. Ganin abin yana neman zame mashi wata matsala ne yasa ya ce. "My Hoonaira kada fa a nemeki a cikin gida"....... Ɗan zaro mashi eyesball ɗinta ta yi kafin ta ce. "Uhm nemakam ai nasan sai anyi, ban ma san ina zan ce na je ba". "To mu je in mayar da ke kada a samu matsala". Yadda ya yi magana da mutum yana waje ko yaki ko ya so sai ya so bawan Allahn nan ya cigaba da yin magana kada ya dakata, cikin wani irin sigar soyayya mai sanyi da tafiya da imani ya yi ta. "Amma ai ban gaji da kallonka ba". Tamkar zata yi kuka ta faɗa........ "Nifa naki ne, mu je ki koma ciki sai gobe mu sake kallan juna". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa rike da hannunta. "To amma zamu yi video call idan na koma bedroom ɗina?". Kai ya jinjina mata, sannan ta miƙe tsaye, jan hannunta ya yi suka nufi kofar fita, da kyar yake iya ɗaga ƙafafunsa, dan dik ta saukar mashi da wani irin kasala na musamman. A bakin door ɗin ya saki hannunta ya buɗe kofar, sai da ya leƙo waje ya tabbatar da babu kowa, sannan ya ce ta zo su tafi. Cikin natsuwa ta fito, janyo kofar ya yi tare da jan hannunta suka nufi hanyar komawa. Suna tafiya suna hira gwanin birgewa, tana faɗa mashi cewa lallai yau har waye wan gari suna video call, shi ma da giyar soyayya na ɗebansa ya ce mata sallar asuba ne kawai zai sa su yi sallama. Allah sarki soyayya. Sai daɗi take ji har suka isa kusa da door ɗin da zai sadata da cikin gida, sun kuwa yi sa'a basu ci karo da kowa ba. A bayan wasu dogayen flowers dake wajen ya tsaya tare da juyowa suna fuskantar juna, daga in da suke suna iya kallan kofar shiga cikin gida, sannan akwai hasken bulb dake wajen Flowers ɗin da suke haskota, sai dai a in da suke ɗin ba haske sosai bane, hasken kaɗan ne yake riskarsu. Zubawa kyakkyawan face ɗinta idanu ya yi. "I will going to miss you my Hoonaira". Ya faɗa can ƙasa ƙasa. Jingina da jikin bangon dake ɗan gefe kaɗan ta yi, sannan ta ɗan ɗago kanta kaɗan dan ta samu damar ganin face ɗinsa, kunga ya fita tsawo nesa ba kusa ba, cike da salo mai jan hankalin da yakamata ace ta bari sai bayan auren nasu ya rinƙa yi mashi irin wannan salo ta ce. "My Hero zan fi kewarka sosai fa". Wani irin kafiya ya ji ta soki zuciyarsa, ta kara birkita mashi lissafi. "Rabuwa da kai tamkar za'a rabani da numfashi nane, ina jin zan bar iska da haskena a nan in shiga cikin gida, na tabbata babu wata light da zata iya haska mun bedroom ɗina, dan na baro light nawa a nan, bana san komawa ciki my Hero, zan ji tamkar a ƙarƙashin ƙasa nike". Tin da ta fara magana idanunsa a kan ɗan bakinta har ta dire aya, sam kunnuwansa basu saurari kalamanta ba, hankalinsa ya yi nisa sosai. Ai tana dire aya ta rufe baki ya tsinci kansa da matsawa dab da ita, a hankali ya matso da face ɗinsa dab da tata, tana tsaye tana kallansa bata ce mashi ko uppan ba, soyayyarsa ya rufe mata ido, hankalinta ya yi nisa a kallan face ɗinsa..... "My Hoonaira, can I have a one kiss?". Ya faɗa murya can ciki ciki a dishashe kuma, yana jin faɗuwar gaba sosai, tamkar zai rasata ne haka yake ji. Ita kuwa da yake sonsa ya rufe mata ido sai bata san lokacin da ta ce mashi. "Whyn't". Ba. Haba aikuwa wani irin sanyi ya ji ta ratsa zuciyarsa, slowly ya haɗe face ɗinsa da tata, kirjinsa na harbawa da karfi karfi sosai ya sanya hannunsa ɗaya a saman waist ɗinta, ɗayan hannun nasa kuma ya ɗaura a saman bayan wuyanta, cike da tsantsar kaunarta ya haɗe bakinsu waje guda. Ko kaɗan bata yi ƙoƙarin taka mashi birki ba, sai ma hannunta ɗaya da ta ɗaura a saman faffaɗar kirjinsa, ta ɗaura ɗayan kuma a saman bayansa. Hot kiss ya shiga bata cikin salon da bai san ta ya aka yi ya iya bama, ita ma mayar mashi da martani ta shiga yi cikin salon soyaya mai kara narka zuciya, ai bai san lokacin da ya janyo waist ɗinta ta tafi gabaɗaya ta faɗa saman kirjin nasa ba, macewa suka yi da kissing na juna babu kakkautawa. Woooooo yau Hoonaira ta bawa heronta abin da ba zai taɓa mantawa ba, gabaɗaya ya fita a hayyacinsa, ya ƙanƙameta sosai sai juya tongue ɗinsa a cikin bakinta yake yi, abin mamaki, ko waye ya koya mashi kiss cikin salo har haka kuma? Shi da yake so silent bai san komai ba!. Sai da ya sha lips ɗinta son ransa, ya gama yin musayan yawun bakinsu, sannan ya saketa yana wani irin numfashin da kana ji kasan yana a cikin tsananin buƙata, ƙasa iya yi mata magana ya yi, idanunsa a ƙasa ya yi mata nuni da kofar shiga cikin gida, alamar ta tafi da sauri tin kan shaiɗan ya cigalaba mai gabaɗaya a kansu wajen sanya shi ya aikata fiye da abin da ya yi. Ita kanta gabaɗaya jikinta tamkar an zare mata laka, bata da karfi ko kaɗan, da kyar ya iya jan kafafunta ta nufi cikin gida, ko sau ɗaya bata waiwayosa ba, shi kuwa, tana tafiya ya ɗago idanunsa ya tsareta da kallo har ta shiga ciki, lokacin da ta turo kofar nan sai ya ji tamkar kofar zuciyarsa ta datse, gabaɗaya sai ya ji tamkar an jefasa cikin kunci da matsi, da kyar ya juya ya nufi bedroom ɗinsa. Yana zuwa ya faɗa saman bed ɗinsa ya fara juyi dan samawa kansa sassaucin abin da yake ji. Ita kuwa kai tsaye bedroom na Momma ta nufa, sai dai ko da ta je babu kowa, hakan yasa ta fito ya nufi wajen King, har zata shiga sai kuma ta fasa ta koma bedroom ɗinta. A lokacin Pretty ta jima da yin barci abinta. Saman bed ta haye tare da ɗauko wayarta, lokaci guda ta ɗauke wuta na ƴan mintuna, gabaɗaya abin da ya faru a tsakaninta da shi ne ya dawo mata cikin kwakwalwarta, lumshe idanunta ta yi tana tariyo yadda ta ji tausasan lips ɗinsa wanda ta san babu wata mace da ta taɓa ɗanɗanawa sai ita, dama kuma mallakinta ne, shi da ko face ɗinsa ba a gani yaushe wata zata samu damar ɗanɗanar lips ɗinsa? Ai ba wannan magana, ita ce first and last in ji zuciyarta. Lokaci guda ta saki cool murmushi, bargon sanyin ne ya lulluɓe zuciyarta. Wayarta ta janyo tare da danna mashi kira. A daidai lokacin da kiran ya shigo yana juyi a saman bed ɗinsa, dik yagama birkicewa ya fita a hayyacinsa. Wayar ta yi kara har ta katse bai ɗaga ba, sake kira ta yi, a karo na biyu ma bai iya yin picking ba, sai a karo na uku ne ya miƙa hannunsa da kyar ya ɗauki wayar, ba tare da duba mai kiran ba kawai ya yi picking, manna wayar a kunnesan ya yi ya ƙasa iya yin magana. Daga can ɓangare ta saka mashi shagwaɓa tana faɗin. "My Hero shi ne kaki picking da wuri?". Wani irin zoki bananarsa ta kara yi mashi ma jin sautin muryarta, da kyar ya iya amsa mata da. "Am sorry my Hoonaira". Zare eyeballs ɗinta ta yi kafin ta ce. "Ya naji voice ɗinka a haka? Ko dai ka fara barci ne?". Ɗan datse idanunsa ya yi tare da girgiza kai irin wanda yake cikin tsananin azabar nan, ya ɗan datse lips ɗinsa na kasa da hakwaransa, bai iya ce da ita komai ba. Jin shiru yasa ta sake maimaita tambayar tata, a zatanta barci yake yi. Da kyar ya iya sake lips ɗinsa ya amsa mata da e barci ya fara yi. "To mu bar wayar sai da safe ko?". Ta jefa mashi tambayar, ko kaɗan bai iya sanin amsar da bakinsa ya bata ba, daga haka ya saki wayar ta cigaba da juyinsa dan nemawa kansa sassauci. Ita ma cire wayar ta yi daga kunnenta tare da katse kiran, dan yadda ta ji ya ce sai da safen ya yi mata kama da wanda barci ta rigada ta ci karfinsa, so bata tsaya neman kiss na good night ba, gyarawa ta yi ta kwanta zuciyarta cike da tinanin kiss da ya bata. Saboda gajiyar hanya yasa tana kwanciya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. Tana yin barci bai fi da minti biyu ba sai ga guyson ya shigo cikin bedroom ɗin ya zo nemanta...... Ganin tana barci ya sa ya matsa dab da ita, addu'oi ya tofa mata kafin ya fice abinsa. A ɓangaren Smart kuwa, yana barin bedroom na King ya wuce nasa, a gurguje ya yi wanka ya yi shirin kwanciya, rufe kofarsa da key ya yi ma saboda kada su zo su damesa, dan ya san Jaish zai zo, kuma yana kan tsini za'a iya samun matsala. Kuwa hasashensa gaskiya ce, dan kuwa Jaish ya zo nemansa, sai dai da ya ji kofar a rufe sai ya juya ya koma bedroom ɗinsa cike da damuwar menene yake damun ɗan uwan nasa. A daren wannan rana dai kusan rabin family ba barcin daɗi suka yi ba, cike da kunci da bakinciki wasu daga cikinsu suka kwana, har shi kansa King zuciyarsa tamkar zata fashe haka ya kwana. Momma ma dai hakan ce, Jaish cike da damuwa da tinanin san sanin abin da yake faruwa ya kwana, haka shi ma Jawad, abin dai sai shiru. Washegari da safe, misalin karfe bakwai na safe, kiran gaggawa King ya aikawa da kowani members na family da ya hallara a cikin main parlournsa, aikuwa basu ɓata lokaci ba wajen hallara gabaɗayansu except Smart da kwata kwata ya ce ba zai sake taka kafafunsa a in da daddynsa yake ba har sai ya canza magana, kada ku manta kuma momma ta yi zazzafar magana a kan kada ya sake saka baki a kan bikin Auta, shiyasa ya yi banza da kiran daddyn nasa, ya ga massage ɗin kuma, yana kwance saman bed ɗinsa, wani ɓangare na zuciyarsa yana ta tinanin Pretty, dan da safe war haka a France tana ɗakinsa ne tana damunsa da zata sha tea ya je ya bata, yau dik sai ya ji babu daɗi da bata zo ta damesa ba, a ɗayan ɓangaren zuciyar tasa kuwa, bakinciki ne tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu!!. Gabaɗaya family sun haɗe a main parlour, har da su Mammie, kowa ya natsu tsit yana jiran fara maganar King, Sarina burinta kawai taga Smart ya shigo cikin parlourn, dan a yunwace take da san kallansa. Fanan sai satar kallan Jaish da ya yi ƙasa da kansa yana tinanin zuwa ya duba Smart take yi, Khadijah and Zee suna part na Aunty MieMie. While ita kuma Aunty MieMie ɗin tana nan a wajen meeting da za'ayi. Gyaran murya King ya ɗan yi wanda ya janyo hankalin gabaɗayansu a kansa, natsuwa suka yi tsit dan sauraran abin da zai faɗa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kalli Jawad da Jaish ya fara magana a natse cikin bada umarni. "Bakin Dubai sun sauka, ku shirya motocin zuwa tarbarsu a airport cikin ƙanƙanin lokaci". Ya faɗa tare da dawo da kallonsa a kan Auta dake zaune kusa da Chuchu ta kwanto jininta, dama ba komai yasa ya tattara ƴaƴan nasa dikka ba face yana san ne ya nuna masu cewa lallai ya isa da kowannensu, da alama kalaman Smart na cewa watarana zasu bijirewa maganarsa ta tsaya mashi a rai, shiyasa yake san kara nuna masu shi mai iko ne da su. "Zunaira!". Ya ambaci sunanta. Da sauri ta ɗago daga jikin Chuchu, cike da respect ta amsa da na'am dad. "Anjuma by 2 za'a ɗaura aurenki da yayanki Abdussalam, shi ne taran jama'ar da kika gani a gidan nan, abin ya zo cikin gaggawa ne, dan haka ki shirya". Ya kai karshen maganar tare da juyo da kallonsa a kan su Momma. Da farko ya ce ba za'a faɗawa Auta ɗin ba sai an ɗaura auren, amma da Smart ya yi mashi waɗan can kalaman sai ya ce bari ya sanar da ita ya gwada masu shi ke da iko da su, kun gane irin abin ai?!!. Wani irin zaro ido da Auta ta yi, tsabar rikicewa da shiga tashin hankali bata san lokacin da ta zamo daga saman sofa ta zube gwiwowinta a kasa ba, a kiɗime ta fara faɗin. "Dad Hoorain fa? Shi fa nike so dad, wlh Yah Abdussalam yayana ne kawai, Momma ki faɗawa dad, Akka please ki faɗawa dad cewa Yah Abdussalam yayana ne kawai, small dad ka faɗawa dad ina san Hoorain ka ji?". Cike da tashin hankali take sambatun, ba komai ya girgizata har yasa ta fita hayyacinta ba face tasan King magana ɗaya yake yi, yanzu ya rigada ya yi kenan, wannan abin yasa ta kusa zaucewa, surutu kawai take yi ba tare da tasan me yake faɗe ba!. Wani irin tsawa da King ya daka mata a kan ta natsun masa ne yasa bata san lokacin da ta zabura ta miƙe ta faɗa jikin guyson tare da kankame shi gam ba. Cikin kakkausar murya King ya ce. "Na rigada na gama magana, ƴan awanni kaɗan suka yi saura!!". Dik cikin parlourn nan babu wanda bai razana da ganin yadda King ya ɗauki zafi sosai ba! Dayawa daga cikinsu sun tausayawa Auta, mussamman ma Chuchu da tini hawaye sun gama jiƙe mata fuska, ita ma Fanan hawaye ya jiƙe eyelashes ɗinta sharkaf saura su zubo, Aneesa ma dai idanunta sun yi jajir alamar ta tausayawa sister tata. Cikin kiɗimawa Auta ta fara faɗin. "Daddy mutuwa zan yi idan har ka aura mun Yah Abdussalam, wlh nasan zan mutu ne kawai, Yah Omar ka faɗawa daddy zan mutu". Ta faɗa cikin wani irin murya mai tsananin rauni dake taɓa zuciya. Miƙewa tsaye King ya yi, dik jikunnan dayawa daga cikinsu ya mutu, mussamman ma uncle Jahiz da yake ganin kamar suna da ƴancin yin abin da suka ga dama, kun san shi ma renon masu jajayen kunnuwa ne, so sai yake ganin kamar King ya tauye mata hakkinta ne. King kuwa ya fusata sosai, sai yake ganin ja in ja da shi da Auta ta fara yin nan kamar zancen Smart ne ya fara tabbata, nan fa hankalinsa ya yi mummunar tashi!. "Hoorain kike so ba?". King ya faɗa murya ƙasa ƙasa. Da sauri ta fara gyaɗa mashi kai alamar e shi take so, take su momma suka fara jin daɗi har da sauke ajiyar zuciya, dan suna ganin kamar zai aminta da batun ne.......... "Tabbas ba zan hanaki aurensa ba, tin da shi kike so to bismilla gaki ga shi". Wani irin daɗi da ta ji har bata san lokacin da ta zabura ta raba jikinta da na guyson ba, sai dai kalaman King na karshe sun sa ta ji tamkar duniya ya tsaya mata cak, gabaɗaya brain ɗinta ya dai'na iya tariyo mata komai, cak ta yi na wucin gadin.. "Tin da Hoonaira kika zaɓa tashi ki je garesa, amma kuma ki shafeni a babin rayuwarki, ki cireni daga matsayin mahaifinki, ki kaddara baki taɓa sanina ba, nima na cireki daga jerin ƴaƴana, ki nemi wani uban, Obaid shi ne ɗan Auta na a yanzu, Zunaira ta mutu a rayuwata!!". Su ne kalaman da suka gigita ƙwaƙwalwar dik wanda yake cikin parlourn, dan kuwa babu wanda ya taɓa tinanin King zai tsani Hoorain har haka, ita kam Akka ko a jikinta, dan ita ce ma ta kara takawa King birki a kan batun, bai yanke hukunci ba sai da suka yi zama da ita da uncle Abbas, a nan ne fa ta ce wlh ba zata taɓa yarda Zunaira ta auri warrior ba, dan haka bata aminta ba, wannan dalilin yasa shi ma King ya kara tsananta a kan hukuncinsa. Amma my people's baku ganin kamar irin wanna tsana da King ya yi wa Hoorain akwai wata dalili mai karfi a ƙasa kuwa? Anya iya kasamcewarsa warrior ne yasa ya yi mashi mummunar tsana haka? Kai ina zargin da wata ƙullalliya a ƙasa. (Ni dai a nawa tinanin fa to kada ku ɗauka gaske ne, a nawa hasashen na ce Allah yasa ba shi ne uban Hoorain ɗin ba😅 dan kun san sarakuna suna iya tarewa da kuyangunsu, matar commander Zafar kuma kuyangarsu ce, balai'n can, wannan fa hasashena ne, dan ina ganin akwai dalili kai karfi na tsanar wanna haɗi da King ya yi, amma ku kai dubanku kan yadda Hoorain tun tasowarsa fuskarsa a rufe bata bayyana ga kowa ba zaku gane dalilin hasashena!! Me dalili rufe fuskar? Meyasa King bai damu da ya buɗe fuskarsa ba? Kai akwai fa bala'i!!! Amma mu je zuwa bayan bikin!!! King fa hege ne😅😅😅 ba dai ruwana na yi shiru sirikina ne kada ya hana aurenmu da guyson nima in shiga uku!!🥱) Ai tsabar tashin hankali Jaish da Jawad basu san time da suka miƙe tsaye a tare ba, uncle Jahiz uncle Abbas uncle Taheer suma a tare suka miƙe, kalaman King ya gigitasu. Momma kam ta kasa motsawa daga in da take, guyson ma dai ya kasa motsawar ne, dan ya ji abin da ya girmawa shekarunsa. Dik rashin kunyar Omaid and Obaid sai da suka ji zuciyarsu ta raunata a yau, Aunty MieMie tamkar wadda ruwa ya cinyeta. Cike da tsananin tashin hankali da kiɗima Auta ta zabura ta diro ƙasa, ai tsabar ruɗu bata san lokacin da ta isa gaban King ba. Tana kuka tamkar ranta zai fita ta riko alkyabbarsa, muryarta da kyar yake fita ta fara faɗin. "Na shaga uku na boni na lallace, wlh daddy bana san Hoorain, ka fiye mun kowa da komai a rayuwata, kai ne sanadiyar zuwata duniya da har na san daɗi da rashinsa, ka yafe mun daddy, wlh ba zan sake yin maganar kowa ba sai na Yah Abdussalam, shi ne zaɓinka kuma zaɓina, na karɓesa hannu bibbiyu ina mai biyayya, daddy tin da nike da kai ko magana cikin ɗaga murya baka taɓa yi mun ba, amma a dalilin wannan magana har marina ka yi, tabbas ko zan rasa rai'na ba zan sake kaucewa maganarka ba, dan Allah ka yi hakuri ka yafe mun, wanenen Hoorain? Ban san shi ba daddy, momma ku faɗawa daddy ko zan mutu na yarda zan zauna da Yah Abdussalam, Mummy, mama, Yah Jaish, Yah Jawad, Aunty MieMie, daddy, small dad, Yah Omar, Yah Omaid ku faɗawa dad ba zan sake ba, ya janye kalamansa a kai'na, na shiga uku na lallace yau!.........". Da kyar ta iya kai karshen maganar, a wannan gaɓa kusan dikkansu idanunsu sai da ya ciko da kwallah. Guyson, Chuchu da Aneesa kam hawaye sharɓa sharɓa. Jawad yana san zuwa ya ɗagota, amma kuma bai isa ba, saboda tsarin gidan sarauta, in har ba King ne ya basu umarni ba to fa ko mutuwa take yi a wajen haka zasu daure su bita da ido. Ban da sambatunta da shesshekar kuka babu wani abin da zaku ji yana tashi a cikin parlon, King yana tsaye tamkar wanda aka sassaƙa yana jinta, ƙoƙari yake yi ya danni zuciyar Modarawar, dan fa ya hasala matuƙar. Ganin kukan nata ya yi yawa, tamkar zata rasa ranta yasa Queen mother ta miƙe ta isa wajen, dan bayan Akka babu wanda ya isa ya tsoma baki a cikin wanna case ɗin ba tare da izini ba. Hannu tasa ta ɗago Zunaira, cike da sigar rarrashi ta ce. "Ya isa haka, shikenan ki yi shiru"....... A birkice ta fara tattaɓa hannun Akka tana faɗin. "Akka dad bai yafe mun ba, yaki ya yi mun magana, dan Allah Akka ki ce mashi kome yake so shi zan". ......... Hannu Akka tasa ta rufe mata baki. "Ya isa haka, ya yafe maki, Ke Rahilarh zo ki kamata ku je". Ta yi maganar tana dawo da kallonta a kan Momma......... UHM KING A KAN YA NUNAWA SMART YANA DA IKO DA ƳAƳANSA ZAI KASHE AUTA!! WLH SMART ƊAN DUNIYA NE, DA KALMA ƊAYA TAK YA TARWATSA ZUCIYAR KING YASA YA KUSA ZAUCEWA!! Ai tin bata gama rufe baki ba Jaish ya matsa ya ɗauketa cak, cikin sauri ya juya ya fice da ita daga cikin parlon, sai yan zu ya fahimci ɓacin ran Smart, ashe abin da yake faruwa kenan........ "Dikkanku ku tashi ku je". Cewar Akka kenan, ta ce da su mummy su tafi. Ai a hanzarce dik suka miƙe suka fita, wannan ya zama izina ga su Aneesa, dama abin da yasa King ya tarosu kenan, dan ya zama izini a garesu, sun kuwa tsorata ba kaɗan ba, dan sai da suka zub da kwallah, dikkansu addu'a suke yi a kan kada Allah ya ɗora masu san wani bare face zaɓin mahaifinsu. Da kyar suka shawo kan King ya hakura, sannan ya wuce fada dan tarban manya manyan baki, Abu Abdussalam da kansa ya tako har KINGDOM OF POWER ya zo wanna ɗaurin aure, abokan Abdussalam tawaga guda suma sun iso yau, abubuwa dai babu kama hannun yaro. Ita kuwa Auta tin da ta yi shiru ta dakata da wannan kuka ba wanda ya sake jin bakinta ta furta wani abin, ta zama ganganji kawai, dan ainahin ruhinta yana tare da Hoorain, Allah sarki yana can bai san me yake faruwa ba, da safe ya yi ta kiranta almost 10 miss calls bata ɗaga ba, dik ya bi ya shiga damuwa, amma haka ya yi shirinsa sosai, dan yau gidan ya kara cika, tsaro zai tsananta a kingdom ɗin, ga kuma baƙi, dole ya shirya ya fita da wuri, amma ya so ya yi waya da ita dan ya bata hakuri a kan abin da ya faru jiya, amma ba dama, haka ya shirya suka nufi masallacin King dan tabbatar da tsaron rayuka, sai tsokanarsa su Ansar suke yi a kan ya kara kiba, sai dai shi gabaɗaya tin da ya tashi baya cikin mood mai kyau, sai ya ɗauki abin a matsayin ko halin da ya shiga daren jiya ne silar mutuwar jikinsa, dan gaskiya bai taɓa shiga yanayi irin na jiyan nan ba, da ace lokacin da yake juyin nan ta zo kansa tsab zai iya yi mata fyaɗe, dan gabaɗaya a out of control yake!. In short a yau da misalin karfe biyu na rana dai'dai bayan saukowa daga sallar azahar ne dubban jama'a suka shaida da ɗaure auren ABDUSSALAM OMAR BADEEN tare da amaryarsa PRINCESS ZUNAIRA ZUHAIR ABDUL MALIK a kan sadaki na zallar zinari da ya haura darajar 100 million, kowa ya shaida wannan ɗauri aure da aka yi da misali karfe biyu dai'dai, jama'a sai murna suke yi, tabbas Momma ta yi murnar da ya kasance ɗan yayanta Auta ta aura, amma tawani ɓangaren ta yi tsananin bakincikin da ya kasance ƴarta bata samu zaɓin ranta ba. Ƴan uwa sai murna suke yi, yau King ya yi kyaututtukan da bai taɓa yin makamantansu ba, uncle Abbas, Uncle Jahiz dik sun yi tarin kyaututtukan da baki ba zai iya faɗarsu ba, duniya ta amsa da wannan biki, jikokin the most powerful King Badeen sun mallaki juna, ƴan uwa sun yi matuƙar murna ban da guyson da shi yasan komai. Shi kuwa Smart yana cikin bedroom tun da Momma ta yi wannan furuci shikenan bai sake fita ko parlour ba, a cikin bedroom ɗinsa yake sallah, tsawon sati ya ɗauka yana ƙoƙarin danne zuciyarsa a kan iyayen nasa, shiyasa ma yaki fitowa, dan yasan idan har zuciyarsa bata kwanta ba ya fito to fa zai iya tabka babban aiki, zaman sa lafiya ya zauna a ɗaki kada ya ja zuciyarsa ta ɓatawa momma rai!. Hidima ta kara tsauri, sai kai komo ake yi, manyan baki daga sassan duniya daban daban sun halatta, harda manyan sarakuna daga Nigeria, masu mulki da sauransu, almost good one week aka ɗauka anata shagulgula, ita dai Auta ta zama tamkar kurma, bata uhm bata uhum-uhum, tazama abar tausayi, dik yadda aka jata haka take bi, taki furta ko word ɗaya. Hoorain ya yi kiran duniyar nan har ya gaji, sai ya ce ko dai shagalin biki ne ya yi mata yawa bari ya barta zuwa ɗan lokaci!!. Yau za'ayi dinner, tin da su Aunty MieMie suka fara shiryata take zaune shiru bata ce ko mai ba, Allah ne kaɗai yasan me yake a cikin zuciyarta.... Anyi aladun larabawa daban daban wanda ya shafi girma da sarauta, anyi al'adar Henna Night wato laylat al-henna. Wannan rana ce na farinciki inda ake taruwa dan sawa amarya albarka, ana waka, rawa da annashuwa. Family mata da ƙawayen amarya ne ke halarta. Ana yawan amfani da garwashi da turaren wuta, da wake-waken larabawa da duma-duma. Sai dai dik Auta binsu kawai take yi, bata yi ko magana ba, da alama zuciyarta ya rigada ya mutu, gangar jikinta ce kawai ta rage tana motsawa!. Bayan Henna night sun yi Zafaf. Ana nuna dukiya ta amarya, riguna masu kyau, kayan ado, turare, da kayan ɗaki masu ƙyalli. Wannan yakan zama wani biki daban, ana gayyatar mutane su zo su kalla. Familyn King suna ajiye wa amarya and ango manyan gift boxes masu shaƙe da zinari da lu'u-lu'u dan ɗaukaka amarya su nuna girma ta family ɗinsu. Dik kafin dinner suka yi wannan fa. Bayan ankammala shi ranar Saturday da daddare sun yi Gaisuwa da Karramawar Sarauta. Ana gudanar da gaisuwar sarauta tare da masu manyan cikin gida, ƴan majalisar sarauta, da jakadu daga ƙasashe daban-daban. Kamar yadda manyan sarakuna da shuwagabannin suka zo daga Nigeria, to amarya da ango zasu je har fada su gaisa da su!. Su kuma zasu gabatar da kyaututtuka daga sarkin garin, ministoci, da shugabanni zuwa ga amarya da ango. Sai dai nan ma Auta bata ce ba zata bi Abdussalam ba, ta bisa, suna shirye cikin tsadaddun shirinsu na jikokin the most powerful King Badeen, alkyabbar da Auta ta sanya ma da lu'ulu'u aka yi duwatsun masu hasken bala'in dake jikinsu, cover shoes dake kafafunsu daga ita har Abdussalam dik sun kasance da duwatsun lu'ulu'u aka kawata kwalliyarsu wanda hakan yasa suke ta zuba kyalli suna ɗaukar ido. Bayan gaisuwar sarauta sun gudanar da raye-raye na gargajiya wanda ƴan'matan family ne suke gudanarwa bisa al'adar. Sun yi rawa irin su Ardah. Maza na sarauta sukan tsaya da takubba suna wakar girmamawa da rawar alfarma ana buga daff da tabl, kayan kiɗa na gargajiya. Sai dai fa Jawad ya yi, amma Jaish dik yadda yake san Auta yaki yi, dan ya ce shi fa bai ga amfanin yin al'adar nan ba, King kuwa ya ce auran Autarsa ce dole ayi dik al'adun da suke yi, kunga haɗuwar da guyson ya yi cikin warriors wears ɗin nan kuwa? Ya yi bala'in kyau sosai, ya riko takobi a hannunsa, a tsakiyar hall na gidan aka gudanar da wannan biki, Omaid and Obaid dik sun yi, Jaish ne dai ya ki yi, shi kuwa Smart ko in da suke bai leƙo ba, yana cikin bedroom ɗinsa. Shi ma Abdussalam ya yi, kuma dik sun yi masifar kyau sosai, uncle Taheer, Uncle Jahiz dik sun yi, su Ramish kam ko bikinma basu zo ba, sun ce sai bikin ta dawo Dubai kawai, idan an gama a kingdom of power aka miƙe masu amaryar su zasu tarbeta a Dubai, tin da abin dik family ne sai suka kasa kansu gida biyu A daren ranar da aka gama wannan bikin raye-rayen sai suka gudanar da Gidauniyar Alkhairi. Wasu sarakuna na amfani da bikin aurar da ƴaƴansu dan buɗe asusun tallafi, bayar da gudummawa ga marasa galihu ko yin aikin alkhairi da sunan amarya, sai dai shi King ita kanta Auta daga cikin ɗinbin dukiyarta ta buɗe wannan, shi ya jagoranta ta buɗe wannan gidauniya, shi kuma ya yi kyautar motoci, gidaje da kuma kujerun makka, Jaish ma ya yi kyaututtuka da sunan Auta tamkar dukiyarsa zata kare, sai dai ko kaɗan bai girgiza ba, shi ma uncle Abbas ya yi kyaututtuka, ya taka ya je prison da kansa ya yi freeying masu ƙananan laifuka, ya yi belinsu sannan ya basu kuɗi dan nemawa kansu aikin yi, baya ga haka yasa anyi girke girke da dama aka kai gidan prison ɗin dan ciyar da waɗan da suke ciki. Shi kuma uncle Jahiz gidan marayu ya je, nan ya bada millions dan tallafa masu, dik da sunan Auta suka yi suna fatan Allah ya bata farinciki da kwanciyar hankali mai ɗorewa a gidan aurenta, su kansu sun san zama da wanda baka so ba kara mun abu bane, shiyasa dik suke wannan, kowannensu da abin da ya yi, Dr Raj ma yana nan, ya yi kyaututtuka da dama, Ramish, Bilal and Yah Rizwan suma sun yi mata kyaututtukan da baki ba zai iya faɗa ba. Abubuwa dai sai wanda ya gani, sai dai wacce ake yi dominta ko kaɗan bata a tare da su, umarnin daddynta kawai take bi yasa ta ja bakinta ta yi shiru. DINNER NIGHT.🔥 Ango ya sha kyau cikin bisht wato kayan sarauta na maza, rawani da takalmin fata na alfarma, dukiya ya yi mubaya'a a wanna waje, komai nasu very luxury. Su Aunty MieMie sun shirya amarya a cikin wasu haɗaɗɗun p-k, wani shegen gown ne mai bala'in kyau da tsada, tana jan kasa, ga alkyabba mai kwalliyar lu'ulu'u, takalmar kafanta kawai ya isa yasa ku fahimci auren ƴar gata ake yi. Babu karya, ko makiyi yasan Zunaira ta yi kyau sosai, sai dai ko kaɗan babu walwala a saman face ɗinta, alamar tana cikin tsananin tashin hankali, a haka ta shigo cikin hall ɗin, mc yana ta faman zuba kirari a gareta, Chuchu tana rike da hannunta, ɗayan side ɗin kuka Aneesa ce ta riketa, su Khadija dik sun shirya sun halicci dinner ɗin bisa umarnin Aunty MieMie, Pretty ce kawai taki zuwa, ta dai cewa Momma ba zata je ba dan bata san hayaniya, shiyasa ta yi zamanta a parlourn Momma tana kallan tv. Kiɗan larabawa mai shehen daɗin mc ya bada umarnin a saki da shigowar tauraruwar amarya, tana shigowa wasu jakadun mata suka hau fesheta da turarruka wasu suna watsa mata furanni. Dama sai zuba kamshin turarukan larabawa su oud, musk, sandalwood take yi, dik wanda yake cikin hall ɗin nan sai da dandatsetsen sarkar zinarin dake wuyarta ya ɗauke mashi hankali, kai kyau fa iya kyau Auta ta yi, walwalar ne dai da babu shi ne matsalar. Abdussalam dake tsaye yana jiran ƙarisowa dik ya kotsa ta iso ya ji me yake damunta da ta haɗe rai haka, shi ya rigata zuwa, a tsarinsu ba tare suke shigowa ba, shi zai shigo da abokansa, ita ma tare da kawayenta. Kun san menene babban abin takaicin my people's? Hoorain yana wajen wannan dinner, yana gab da bakin kofar shigowa, sai dai kuma zuciyarsa bata yarda mashi abin da kunnuwansa suka ji yo a masallaci ba, yana ganin kamar bikin Aneesa ake yi bana Auta ba, yaki yarda, shiyasa bai nuna damuwa ba, kuma King ne ya wakilta shi a kan tsaron kofar shigowa dinner, yana tsaye yana aikinsa yana ta faman tinaninta, a ransa yake faɗin ya yi mata uzuri na rashin ɗaukar call ɗinsa da bata yi ba, kila saboda jama'a ne yasa busy ya yi mata yawa, amma dik a dame yake da ta ɗauki waya su gaisa. Suna isa bakin stage ɗin Abdussalam ya yi saurin matsawa ya riƙo hannunta a in da ya taimaka mata ta hauro sama, dik da kanta a ƙasa, kuma tana cikin alkyabbarta sai da gaban Hoorain ya faɗi lokacin da ya ga Abdussalam ya riƙo hannun amarya, wai a haka ma bai san hannun waye ya riko ba, da ya san hannun Hoonairarsa ce me kuke tinanin zai faru?....... KAI WHAT A HEART TOUCHING PAGE 😥 Saman haɗaɗɗen King seat da aka tanada masu suka zauna, suna zama mc ya yi umarni da a juya kiɗar zuwa karatu dan a buɗe taron da addu'a. Haka kuwa aka yi, suratul Fatiha suka sanya bisa tsarin musulunci da kuma tsarinsu, sannan aka buƙaci manya suka gudanar da addu’a dan yi wa amarya albarka. Dik dai wani al'adunsu suka yi shi suka gama, saura sanyawa amarya ring and kiss, sai cin abinci da abin sha kafin a fara sake kiɗa dan yin nishaɗi. Mc ya buƙaci da ango yasa wa amaryarsa zobe, sai tambayarta yake yi meyake damunta, amma taki ta yi mashi magana, shiru tin da ta zo wajen. Ya shiga damuwa matuƙa, amma a haka ya daure zuwa a gama taron, wani dankareren diamond ring kusan shigen wanda ta sanyawa Hoorain a hannu daren jiya ɗaya daga cikin abokan Abdussalam ya miƙo mashi, Ring ɗin yana cikin box ɗinsa. Unboxing ɗinsa ya yi tare buɗewa, wani irin kyalli yake yi yana ɗaukar ido. Miƙewa tsaye ya yi tare da riƙo hannunta ya miƙar da ita, ya tsayar da ita suna fuskantar juna, sannan ya kama ƴan yatsunta ya zura mata ring ɗin, take hannun nata ya kara wani irin kyau na musamman. Tafi rap, rap, rap, gabaɗaya cikin hall ɗin ya ɗauka, abin ya ƙayatar. Muryan mc suka ji yana faɗin yanzu Ango zai sumbaci amaryarsa kamar yadda suka saba yi!. Aikuwa kamar jira Abdussalam yake yi, Mc na bada dama ya yi saurin sanya hannunsa ya ɗago haɓarta da tin da ta zo wajen bata ɗago kanta ta kalli kowa ba. Ɗago kanta ya yi tare da matsar da face ɗinsa dab da ita, cikin salon nuna mata soyaya da kauna ya kai bakinsa zai sumbaceta. Daidai lokacin ta ɗago kallonta kai tsaye sai saman fuskar Hoorain da ya yi mutuwar tsaye yana kallanta, tin da ta miƙe Abdussalam ya sanya mata ring ya gane ita ce, shiyasa ya yi mutuwar tsaye!!. Dik da cewa akwai hular warriors a face ɗinsa, hakan bai hanata ta hango tashin hankalin dake cikin idanunsa ba, kwayar idanunsa tamkar wuta saboda ja, kuma kallanta kawai yake ko kyaftawa bai yi ba, Ansar na tsaye a gefensa ya ɗaura hannunsa a saman takobin dake waist ɗinsa. Abdussalam yana dab da zai haɗe bakinsa da nata sai gani ta yi Hoonaira ya tafi gabaɗaya ya yi ƙasa, take a wajen numfashinsa ta ɗauke ɗiff. Ai bata san lokacin da ta zunduma ihun sunansa har sai da ta razana dik abokan ango da su Chuchu dake wajen ba, lokaci guda kuma zancen King ya dawo mata cikin kwakwalwarta na sharaɗin da ya gindaya mata idan har tana son ya yafe mata, ya ce to kada ya sake jin sunan Hoorain a bakinta, ko da sunan wasa kada ta sake ɗaga idanun ta kallesa, Allah sarki da farko ta yi niyar ta zumduma a guje ta yi kansa, amma da ta tina maganar King sai kawai ta kara zunduma wani ihun da bata kai karshen yinsa ba ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a wajen. A miliyan Abdussalam ya yi kanta yana ambatar sunanta, su Chuchu dik kanta suka yi kamar yadda su Ansar suka yi kan Hoorain da suka tabbatar da baya numfashi, babu rai a jikinsa!!. Cike da tashin hankali Ansar da Anwar suka ɗaukesa, haka ita ma Auta Abdussalam ya ɗauketa ya sauko kasan stage ɗin da ita, da gudu su Chuchu suka rufa mashi baya, nan fa taro ya hargitse, hankula sun tashi sosai. Hospital suka wuce da Hoorain a in da gwajin farko Dr ya tabbatar masu da babu rai a jikinsa, ita kuma Auta wuce suka yi da ita cikin family part, King ya umarcesu da su kaita part na bayan fam part ɗinsa a in da babu kowa a wajen, babu hayaniya babu ribibi, su kai ta can Dr's su zo su duba lafiyarta, sabon part ne da ba'a buɗe ba, dama na uncle Jahiz ne in da idan ya yi aure zai zauna kamar yadda uncle Abbas yake da part ɗinsa. Nan aka wuce da ita, a take aka kira likitoci guda uku suka dukufa a kanta dan ceto rayuwarta, ita dai bata mutu ba, amma zuciyarta na dab da bugawa, shi kuma Hoorain zafin kishi da soyayya yasa ya haɗi zuciya take rai ya yi halinsa! Lallai ba shakka Hoorain ya kurɓu gabar soyayya mai zafin gaske!!. Wlh a lokacin da Dr yake sanar da su Hoorain ya rasu Ansar yanke jiki ya yi ya faɗi sumamme, shi kuma Anwar capko wuyar rigar Dr ya yi, kamar wanda ya rasa hankalinsa ya fara faɗin wlh Dr ya tasan masu ɗan uwansu ko kuma ya kashe shi shima, abin dai very very heart touching, heartbreaking.......😥 Wlh page ɗin nan ya yi mugu mugun taɓa ni, Allah sarki, ashe da rabon kafin ya mutu zai yi kissing Zunairarsa, to King yanzu dai Hoorain ya bar maku duniyar, sai ku dafa Zunaira ku cinye, amma my people's kuna tinanin Commander Zafar zai yafe jinin Hoorain ya tafi a banza kuwa? Baku ganin kamar commander zai juya masu baya ya yakesu? Kada ku manta commander shine kaso sittin cikin ɗari na karfin kingdom ɗin, warriors dik umarninsa suke bi, ya kuke gani idan ya juya masu baya?!. Wlh akwai case ba na wasa ba, ni dai bari in je in kora Maltina ko zan samu sassaucin abin da nike ji a cikin zuciyata!!!. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 54 Sai da kingdom of power ta tsaya cak na ƴan wasu ɗakinku a lokacin da labari ya karaɗe kunnuwar mutane Hoorain ya mutu, shi kansa King sai da ya yi zazzafar razana, ai Commander Zafar cewa ya yi karya ne, ba Hoorain bane ya mutu sai dai wani, amma shi ɗansa yana raye, dik yadda aka so a fahimtar da shi Hoorain ya mutu ya zo su gana da gawarsa ya yi mashi addu'a kafin a je a rufesa, amma commander ya ƙaryata, ya ce wlh shi babu gawar da zai zo ya yi sallama da ita, dan shi ɗansa na raye. Ansar ya lura lallai commander ya zaune ce, ba kuma zai taɓa fahimtarsu ba, dan haka sai ya ce su sanar da King ko zai iya sanya commander ya fahimtar har ya sami damar yin bankwana da ɗansa. Haka kuwa aka yi, suka sanar da King ga abin da yake faruwa, suna san yin jana'izar Hoorain amma commander ya ki yarda ya zo ya gansa ma bare har ya yi mashi addu'a. Cike da alhinin abin da ya faru King yasa a kira mashi commander. Babu kunya babu tsoron Allah King ya iya kallan commander ido cikin ido ya sanar mashi da ya ɗauki dangana Hoorain dai ya mutu. Murmushi commander ya yi kafin ya ce. "Allah ya kara maka tsahon rai, na tabbata ba Hoorain ɗina ne ya mutu ba, wani Hoorain ɗin ne, Hoorain ɗina yanzu na barosa a waje". Jin waɗan nan kalamai yasa King ya fahimci commander fa ƙwaƙwalwarsa ta shiga cutar da ake kira da I-M-R-S, lallai ko zasu shekara suna faɗa mashi Hoorain ya rasu ba zai taɓa yarda ba, dan shi Hoorain yana yi mashi gizo, yana kallansa da idanun da babu mai kallansa sai shi. INNALILAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL!! KENAN YANZU COMMANDER YANA KALLAN HOORAIN KOWA BAYA KALLANSA? YANA YI MASHI GIZO? BABBAR MAGANA!! LALLAI KUWA BA ZAI TAƁA YARDA DA HOORAIN YA MUTU BA!!. Yana tsaye a tsakiyar fada yana kallan King, sai kuma ya juyar da kallansa izuwa kofar shigowa, gwanin ban tausayi ya fara faɗin. "Yauwa my lion, wai cewa suke yi ka mutu, na ce masu baka mutu ba, zo ka gwada masu kanka!". Ya kai karshen maganar yana riko iska a matsayin Hoorain da ya shigo fada a yanzu. Wlh a dai'dai wannan lokacin gabaɗaya ƴan majalisar fada sai da idanunsu ya ciko da kwallah, shi kansa King sai da zuciyarsa ta karaya, gaskiya bai taɓa ganin soyayyar uba da ɗansa irin tsananin soyayyar dake a tsakanin Commander da Hoorain ba. "Ranka ya daɗe ba ga shi nan ba! Ai dama na faɗa maka bai mutu ba, ga shi ka gani ma da idonka". Allah sarki, daga yadda yake magana zaka fahimci sambatu ne kawai, dik yana rikice, gwanin ban tausayi, ya yi maganar yana nunawa King iska a matsayin Hoorain dake gabansa. Aunty MieMie dake zaune a kusa da King wacce bata jima da shigowa bace ta miƙe tsaye, wani irin kuka ne mai karfin gaske ya kwace mata, dama ta shigo ne ta ɗan taushi zuciyar baban nata, dan ta ga ya ɗauki zafi sosai, tana zaune aka kawo labarin mutuwar Hoorain, ta ji hakan a ranta sosai, sai yanzu kuma ta ga abin da ya fi mutuwar tasa zogi, ba zata iya zama ba, da gudu ta ruga cikin gida alkyabbarta na jan ƙasa tana hawaye. Allah sarki commander dattijon arziki, cike da damuwa ya ce. "Lafiya ranki ya daɗe ta tafi tana kuka? Ko wani abin ne yake faruwa?". A ruɗe ya yi maganar. Dik cikin fada babu wanda ya iya bashi amsa, sai sharan kwallah da kowa yake yi, bare ma sarkin hatsi da tuni hawaye sharɓa sharɓa sun gama jiƙa fuskarsa har sun jiƙa wuyar rigarsa. Da mamaki commander yake binsu da kallo, cikin ruɗu ya fara faɗin. "Malam liman lafiya kuke kuka? Ko dai akwai abin da yake faruwa ne? My lion ka ji labarin wani abin yana faruwa ne?". Ya yi maganar yana kallan gefensa a zuwan yana kallan Hoorain. A gizon da yake gani girgiza mashi kai Hoorain ɗin ya yi yana ce mashi babu wani abin da yake faruwa, watakila kukan farinciki suke yi. Jinjina kai commander ya yi tare da mayarwa gizon nasa amsa da. "E ina ga kukan farinciki suke yi, suma suna murnar biki ne, to shikenan jeka abinka ni bari in zauna a nan mu gama magana kan yakin da zamu tafi jibi". Jinjina mashi kai gizon nasa ya yi tare da juyawa ya bar wajen ya nufi waje. Wlh dik taurin zuciyar king sai da idanunsa suka kawo kwallanh, bai taɓa zatan zai shiga damuwa a mutuwar Hoorain ba sai da commander ya shiga cikin wanna hali, amma kuma fa dik da haka sam bai yi danasanin abin da ya aikata na raba masoyan ba, shi yana ganin yana a kan dai'dai!! -------------------------------🔥🔥🔥 Cikin ƙanƙanin lokaci likitoci suka yi nasarar shawo kan Auta har ta farfaɗo, sai dai kuma, Dr ya sanar da in dai basu bata abin da take so ba, to wlh zuciyarta tana gab da bugawa, yanzu haka ta samu babban rauni a zuciya. Sosai ƴan uwan suka girgiza da jin wannan labari, a in da suka ce kada a kuskura a sanar da ita Hoorain ya mutu, King kuma ya ja Abdussalam gefe a in da ya sanar da shi ya san dik ta yadda zai yi ya maye gurbin Hoorain a cikin zuciyarta gudun kada su rasata, sai dai abin da King bai sani ba shi ne, soyayyar Auta and Hoorain daga Allah ne, babu wanda ya isa ya maye gurbin Hoorain a cikin zuciyarta kamar yadda babu wanda ya isa ya maye gurbinta a cikin zuciyarsa!. Abdussalam ya tambayi wanenne Hoorain kuma, sai King ya ɓoye mashi, ya ce dai ya yi ƙoƙarin janyota a jiki ya kwantar mata da hankali, King baya san Abdussalam ya san komai!. -----------------------------🔥🔥 Tin da momma ta samu labarin mutuwar Hoorain ta shiga tantama da tashin hankali, zuciyarta na ayyana mata akwai wata babbar dalilin da yasa King ya gwammaci gara Hoorain ya mutu a kan ya auri Zunaira, sosai momma take zargi da biyu ma King ya saka Hoorain ɗin gadin hall ɗin dinner dan zuciyarsa ta buga a lokacin da zai ga Auta da wani, abin ya tsayawa momma a rai, shiru ta nutsa cikin tinaninta tana tariyo rayuwar baya, ɗauko tinanin ta yi tin daga kan lokacin da matar commander take raye, ita dai tasan ma tin kafin commander ya aureta kamar ita ce kuyangarsu ba kuyanga Zubaida ba, wato ita ce wacce King ya amincewa da ta rinƙa zuba mashi abinci tana kuma girkawa kamar yadda ya aminta da kuyanga Zubaida a yanzu! Take ƙwaƙwalwar momma ya fara shiga ruɗani, sai a lokacin kuma ta tina ita fa bata taɓa kallan face ɗin Hoorain ba a tsawon rayuwarta! Wani irin mummunar faɗuwar gaba ta ji a lokacin da ta tina bata san face ɗinsa ba! Saura kaɗan kwakwalwarta ya kama da wuta a lokacin da tinanin dalilin mutuwar mahaifiyar Hoorain ya ratso cikin kwakwalwarta, yanzu ta fara tantama a kan mutuwarta, anya kuwa ba kasheta kawai aka yi da gangan ba? Meyasa da ta ɓace babu wanda ya sake yin maganarta bare ma har ya nemota? Meyasa King bai tsaya tsayin daka sun nemota ba tin da amintacciyarsa ce a lokacin?. Kai ganin ƙwaƙwalwarta yana ƙoƙarin tarwatsewa ne yasa ta miƙe ta nufi wajen Smart, dan wannan tinani ya fi karfin kwakwalwarta. A ɓangaren su mummyn Chuchu dik tinanin da suke yi kenan, wato meyasa King zai tsani Hoorain har haka ne wai?. Gida ya rikice da koke koke, gidan biki ya koma gidan mutuwa!. Kwance momma ta isko Smart, ya ja bargo har zuwa saman chest ɗinsa, hannunsa rike da phone ɗinsa yana latsawa. Ya yi nisa cikin abin da yake yi, har momma ta shigo bai ji shigowarta ba, a kusa da shi ta zauna, ganin hankalinsa ya yi nisa a taɓa waya yasa ta kai hannu ya karɓi wayar. Sosai ta ji mamakin ganin yadda ya zabura zai kwace wayar, sam bai yi tunanin ita bace. Yana ganinta sai ya kara ɗaure fuska tare da komawa ya kwanta yana ɗan kawar da kansa gefe. Bata yi magana ba, amma ta sha jinin jikinta ganin yadda ya ɗaure fuska, alamar ransa a ɓace har yanzu kenan. Juyo da screen ɗin wayarsa ta yi dan taga me yake gani da ya zabura dan an kwace wayar haka. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallan screen ɗin, sai kuma ta dawo da kallonta a kansa, lokaci guda ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, cike da zolaya ta ce. "Wannan ita ce sirikar tawa ne?". Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma gyara kwanciyarsa da ya yi zai ja bargo ya rufe har face ɗinsa. Rike bargon ta yi, cikin sigar tausasawa ta ce. "Ɓacin rai ne ya sanya ni yin wancan furicin, ba wai dan wani abin ba". A ɗan takaice ya ce. "Amma dai ke kanki kinsa daddy ba'a a kan dai'dai yake ba ko? Meyasa ba zaki yi ƙoƙarin mai da shi hanyar dai'dai ba!"........ "Omerish wannan sarauta ce ba siyasa ba, sarauta da siyasa akwai banbanci matuƙa, kai siyasa ka sani baka san sarauta ba, karfin izza da isa a sarauta yake ba'a siyasa ba, ba komai ake juyawa da karfi a sarauta ba, dik abin da ka gani sai dai ka bishi a haka yadda yake a dokance.........". Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin ya ce. "Babu wata dalili da zata sanya in yi shiru in bar iyayena a kan hanyar halaka, and babu wata dalilin da zai sa in yi shiru a kan saɓon Allah ana aikata ɓarna ba dai'dai ba!!". Ya kai karshen maganar yana sake mata bargon. Ɗan matsawa kusa da shi ta yi. "Zaka iya dawowa nan?". Ta yi maganar tana nuna mashi saman laps ɗinta da hannu. Shiru ya yi mata kamar bai ji ta ba. "Zan faɗa maka wata magana ne"......... "Momma zaki fara ko? Please ki barni in more ɓacin rai'na". Kai ta ɗan girgiza. "Naki gaskiya, zo ka ji wani magana". Ta yi maganar tana jan dogon hancinsa............. Ajiyar zuciya ya sauke... "Momma dayawan mata sun iya kalaman yaudara, shiyasa bana haɗa hanyata da mace, haka mom take mun irin wannan abin, idan dad ya ɓata mun rai bata barina in more ɓacin rai'na bare in yi fushi in ki kula dad, sai ta zo ta mun kalaman yaudara tasa na manta, shi ne kema zaki mun abin da take mun ko?". (Malam Smart mu dai mata ba kalaman yaudara muka iya ba, tausasawa da tausayi muka 😇 iya, ko ya kuka ce my people's?) Da hannu ta kara nuna mashi saman laps ɗinta ba tare da ta yi magana ba, dan dole ya dawo da kansa samansu ya kwanta yana kallanta. Kyakkyawar dark black curly hairnsa ta fara shafawa, ta lura ransa ya ɓaci sosai, sai ta nemi kawar da zancen da suke yi ta hanyar cewa. "Wannan ce sirikar tawa?". Ɗayan hannunta ya riko cikin nasa, yana ɗan rarrabe yatsun hannun nata ta amsa da. "A'a kawai dai na ajiye hotonta ne, amma bamu da wata alƙa". Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Ka tabbata kawai ka ajiye hoton ne?". Kai ya gyaɗa mata alamar e. "To meyasa ka ajiye shi kuma meyasa kake ta kallanta?"...... "Kai momma zaki fara ko? Ni kam ma dake da mom ban san wace ta fi wani ba, ni fa ba kallanta nike yi ba"......... Kallan gefen ido ta wurga mashi, da sauri ya sake cewa. "Da gaske momma ba kallanta nike yi ba".................. "Omerish har na shigo ɗakin nan fa baka san na shigo ba saboda ka shagala da kallonta, in baka faɗa mun gaskiyar wacece ita ba wace zaka faɗawa?". Cikin sigar tausasawa ta yi maganar. Yatsanta na tsakiya ya riko, ring da Jaish ya sanya mata ranar ya fara ƙoƙarin zaresa daga hannun nata, sannan ya ce. "Momma kawai kyau take mun, and ina san wasu ɗabi'u nata, that's all". Ya kai karshen maganar tare da cire ring ɗin. "Kana sonta ne?". Ta jefa mashi tambayar. Da sauri ya girgiza mata kai kamar wani baby. "Momma ni fa ki rabani da sharrin mata, kina ganinsu ƴan yaudara ne, ya na kare dake da mom ma, bare in karawa kai'na wata". Ita momma sam bata damuwa da yanayin maganarsa without a respect, saboda tasan ya yake tin yana karami, a koda yaushe tana bibiyarsa, to tasan ba wai raini bane, haka ya iya magana. "To shikenan na ji baka sonta, yanzu dai ta shi ka yi lunch ka ji? Zuwa dare zan zo mu yi magana, ina da magana mai mahimmanci da kai". Ta faɗa tana bin hoton dake saman screen ɗin nasa da kallo, saboda ita kanta ta yi matuƙar burgeta, ta fita sosai a hoton, sai murmushi take yi dimples ɗinta sun lotsa, ga eyesball ɗinta su tura olive sosa, kamar ka saceta ka gudu!. Jinjina mata kai ya yi haɗe da sakin hannunta ya karɓi wayarsa. "Ki sa Jaish ya kawo mun lunch ɗin a yanzu". Ya faɗa yana miƙewa daga saman laps ɗin nata, dama yunwa yake ji, kawai baya san kulasu ne yasa bai bi ta kan lunch ɗin ba. Ya kuma cire mata ring ɗinta, dan ya ɗan kama hannunta har ya yi mata shaida, shiyasa ya cire kamar yadda a baya Jaish ya cire ya canza mata. "Allah ya yi maka albarka". Shi ne abin da ta faɗa kafin ta miƙe ta nufi waje. Da kallo ya bita yana jin wani irin kaunarta tana kara narka zuciyarsa, yana san mahaifiyar nan tasa over!. Komawa ya yi ya kwanta shiru yana cigaba da kallon hotonta. Kamar daga sama ta witsiyar ido ya ga alamar mutum a tsaye a tsakiyar ɗakin. A hanzarce ya juyo da kallansa. Ɗan binta da kallo ya yi kafin gently ya ce. "Wai ke baki iya sallama bane?". Ya yi maganar kallansa a kanta cak. Turo mashi baki ta yi. "A ina zan ajiye maka abinci ya yi mun nauyi sosai a hannu". A maimakon ta bashi amsa sai ta faɗi abin da take da buƙata. "Ina Jaish da nace ya kawo mun abincin?". Ya tambaya yana wurga mata harara...... Shiru bata amsa mashi ba, dan tana ganin bata da alaƙa da wannan tambayar tin da ita bata ma san wanene Jaish ɗin ba, kawai momma ta shiryata ta ce ta kawo mashi abinci.... Ganin ta yi shiru yasa ya fahimci nufinta, yanzu yana iya karantar shirunta sosai. Kai Pretty duniya, wato tana bawa Smart sabon karatu. Bin kayan jikinta da kallo ya yi, a ransa ya ce dik yadda aka yi momma ta sanyata saka wannan kaya, arabian abaya ce mai shegen kyau launin dark purple, ta yi masifar kyau sosai, sai dai kan nan dai babu ɗankwali, ta saki gashi har baya. A ransa ya ce shegen kyan bala'i ne da ita, kowani irin dressing ta yi kyau yake yi mata tamkar dan ita aka yi kayan! Ya zauna a jijinta zam zama har sai ka ji sha'awar irin dressing ɗin a ranka. Ganin ya yi shiru yana bin jikinta da kallo ne yasa ta dongwarar mashi da try ɗin abincin a tsakiyar bedroom ɗin, a cewarta tin da ba zai faɗi in da za'a ajiye mashi ba ai tana da damar ajiyewa a ko'ina tin da ba shi ya bata hannun nata ba da zata tsaya tana rike da abincinsa tsawon lokaci, ga shegen nauyin tsiya, dama da kyar ta ɗauko shi, ba dan Momma da Allah ba zata ɗauko ba!. "Ke zonan!". Ya faɗa with harsh voice, wai irin ta san ba da wasa yake yi ba, ta tsorata ta zo. Banza da shi ta yi tana cigaba da tafiyarta zata fita. Dab zata fita sai ji ta yi an damko gashin kanta ta baya. Wani irin kara ta saka mashi saboda zafi tare da juyowa da sauri. Angry face ɗinsa a ɗaure tamau, in a harsh voice ya ce. "Ina kiranki kina tafiya ni sha'anki ne?". Ya yi maganar ba tare da ya saki gashin nata ba. Tana turo baki tana yamutse fuska saboda zafin damkar gashin nata da ya yi ta ce. "Ai ke na ji ka ce ta zo ba ni ba, ni sunana Pretty, da Pretty ka ce da na tsaya ko ban zo ba". Kam bala'i, lallai Pretty ƴar duniya ce......... 😅 Rasa abin faɗe ya yi, dan wlh idan ya biyewa yarinyar nan mari ɗaya zai yi mata ta mutu........... "Ni ka sake mun gashi kada ka cire mun su, zafi yake mun". Shagwaɓaɓɓiyar voice ɗinta ta daki dodan kunnensa. Ɗan sauko da kallonsa a kanta ya yi, da karfi ya sake jan gashin nata baya dan mugunta. Hakan yasa ta ɗaga kanta sama dan dole. Ɗago kanta yasa ya kalli face ɗinta a kurkusa, har cikin zuciyarsa ya ji wani iri na ganin kwayar idanunta, ga idanun fari tas tamkar audiga, kwayar olive ɗin kuma ya tura kala sosai, pink lips ɗinta ya tura sosai shi ma, dik yadda aka yi bata jima da yin wanka ba, soft skin ɗinta sai sheki yake yi yana wani glowing. Yaran nan Sweetie and Pretty sun mori jiki sosai, shape ɗinsu tamkar su suka yi wa kansu! Ya shagala da kallanta sai ji ya yi ta gabza mashi cizo a hannu, wai dan ya ja mata gashi ta ji azaba sai ta kama ɗayan hannunsa ta gabza mashi cizo da karfi kuma taki sake fatar, sai kara datsewa take yi da hakwaranta. Zuba mata idanu ya yi yana kallanta ba tare da ya saketa ba, tinanin abin da zai yi mata yake yi, dan dole ya hukuntata!. Da taga cizon kamar bai wadatar ba, bai saka shi ya sakin mata gashi ba, sai ta sake shi haɗe da dunkule ƴan hannayenta da basu wuce ya kama ya karya ba ta fara kai mashi duka a damatsan hannunsa. Abin ma gwanin ban dariya, wai ita nan dukansa take yi dan ya ji zafi ya saketa, bayan hannun nata ba auki kamar sandan snooker. Siririn tsaki ya ja kafin ya sa hannu ɗaya ya ɗagata cancak kamar ƴar tsana ya wurga a saman bed ɗinsa kamar wata kayan wanki. Tana ƙoƙarin miƙewa ya daka mata tsawa a kan ta zauna. Ai ina bata tsoron tsawar tasa, dan haka ta yi tashinta, yana tsaye ta zo ta wucesa zata fita. Juyowa ya yi yana kallan yadda take tafiya ko a jikinta, yau ta goge mashi hadda, wai me zai yi wa yarinyar nan ne ta fara jin tsoronsa? Shi kowa a gidan nan yana tsoronsa amma ban da yarinyar nan, ita dik wasu tsawa da hargagi game da jan ido dik bata tsoransu. Ganin zata fice daga ɗakin ba tare da ya hukuntata bane yasa ya ce. "Yauwa my tiger come in.......". Ai bai gama rufe baki ba ta watso a miliyan ta juyo, ihu ta zunduma tare da ɗale jikinsa, ta ƙanƙame shi gam tana faɗin. "Dan Allah Yah Omerish ka ce kada ya shigo, wlh cinyeni zai yi"...... Mamaki ne ya kama shi, ashe tasan sunansa Yah Omerish kenan, wato dama iskanci ne ya yi mata yawa a kai kenan? Wannan yarinya wlh sai shirin Allah, shi ya rasa ma me zai ce mata, ta wani ƙanƙame shi, wato dai bata tsoron mutane sai dabbobi, yanzu ya gane me zai rinƙa yi mata, dole ya ɗauko abubuwan tsoro ya kawo nan dan ta rinƙa respecting ɗinsa idan tana san zaman lafiya. Ihun da take ta zundumawa ne ya farkar da shi daga duniyar tinanin da ya afka. A ɗan tsawace ya ce. "Sauka mun daga jiki ki je Tiger na jiranki a bakin kofar shigowa, ba ke bakyaji ba?". Kara ƙanƙame shi ta yi tana cusa kanta a kirjinsa ta ce. "Yah Omerish wlh ina jin magana, dan Allah ka ce ya tafi, wlh ba zan sake ba". Bilhakki da gaskiya take ihun nata!!. "Kin yi alkawarin zaki rinƙa jin magana idan aka yi?". Kai ta shiga gyaɗa mashi da sauri sauri, tana faɗin ta yi. Hannu yasa ya rungumota a jikinsa sosai ya fara faɗin. "To ki yi shiru ihun ya isa haka kada ki tara mana jama'a, zo ki zauna mu ci abincin a tare". Kin sake shi ta yi, sai dai ta dakata da zunduma ihun, cikin shesshekar kuka ta ce. "To ka ce kada Tigern ya shigo ka ji?". Yadda ta yi maganar har cikin zuciyarsa ta ratsa shi, ga shagwaɓa ga muryar kuka, abin sai ya haɗe. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "To ba zai shigo ba, amma idan kina ihu zai shigo ne, sakeni mu je ki ci abinci". Wato shi ma yasan ita sarkin son abinci ne fa!. Ba musu ta sakesa tana shessheƙa. In short a tare suka ci abincin, kuma wunin ranar a bedroom ɗinsa ta wuni har dare, taki fitowa wai kada Tiger ya kamata, shi kuma yaki zuwa ya je ya rakata, dan bashi da matsala na zamanta a bedroom ɗin, tana ma ɗebe mashi kewa ne, da rana ta yi sanyi ma hayewa saman bed ɗinsa ta yi a kusa da shi ta kwanta, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita. --------------------------------------🔥 A takaice tsawon sati biyu Auta tana jinya, ban da uhm da mmm babu abin da take cewa, tana kwance shiru a wannan part ɗin, Abdussalam sai ƙoƙarin shiga ziciyarta yake yi ta hanyar zuba mata kalamai masu sanyi da tausasawa game da kulawa, amma dik taki kula shi, sai ma layi da ya shata mashi a kan kada ya kuskura ya matso kusa da bed ɗinta, bai yi mamaki ba, dan yana tinanin zafin ciwo ne, shi kwata kwata bai san da batun soyayyarta ba, wlh da ya sani ko kaɗan ba zai taɓa yarda su yi aure ba, yana san farincikinta sosai, so bai sani ba, ya zaci kawai bata son ayi mata aure a yanzu ne, shiyasa idan ya zo wajenta yake yawan ce mata kada ta damu shi zai iya barinta har ta kammala karatunta kafin su yi zaman aure, dan hankalinta ya kwnata har ce mata yake yi zai iya barinta a kingdom of power cikin ƴan uwanta ya koma Dubai, dik dan ta samu farinciki, amma ina, ita dik ba wannan ne a gabanta ba, hankalinta ya yi nisa, wai a haka ma bata san Hoorain ya mutu ba, ta yi alkawarin babu wani namijin da zata mallakawa jikinta, a cewarta zata yi ta avoiding ɗin Yah Abdussalam har ya gaji ya sawwaƙe mata ta kawo kanta ga Hoorain ɗinta, ta ci alwashin in dai Hoorain bai sameta ba, to tabbas kashe kanta zata yi, dan jikinta mallakinsa ne, ta yi mashi wannan alkawarin tin tana France. Ya kuke tinanin zata ji idan ta san ya mutu? Anya ita ma zata rayu kuwa?!. A ɓangaren Smart kuwa, wlh yadda kuka san baya gidan, kuma dik abin da yake faruwa yana sane, amma bai shiga harkarsu ba, ya zuba ido, sai dai kuma kamar akwai abin da yake shiryawa daddyn nasu, dan ya ɗaukarwa kansa alkawari idan King ya yi sanadiyar mutuwar Zunaira to tabbas wlh ba zai rabu da shi ba, kuma ya san in dai tasan Hoorain ya mutu da wuya ta tsallake ita ma. Uhm akwai cakwakiya fa!!. Cigaba da rayuwarsa Smart ya yi, sai kiransa daddynsa yake yi yana cewa ya dawo, amma sam babu alamar komawa, dan ya ce ba zai bar kingdom of power ba har sai ya gyara masu zama, azumi ta iso, Momma zata je Dubai gaisuwar azumi, sai ana gobe za'a ɗauki azumi zata dawo, to shi ne abin da Smart yake jira, so yake yi momma ta tafi, sannan su yi uwar watsin da za'ayi, kunga bata nan bare ranta ya ɓaci ya ji babu daɗi!!. Uhm Zunaira ta shafe two weeks a saman gadan jinya ba tare da sanin Hoorain baya raye ba, tana nan tana tattalin soyayyarsa a cikin zuciyarta, ta yi mashi ginin da babu mai iya rusa mata!! Kullum tana kan ƙoƙari kara yawan son nasa a ranta!! Ba ci ba sha, dik ya rame ta lalace fiye da tinanin kai tinani, bata da wani walwala, wannan ma wai dan su Chuchu sun ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali, wlh shi kansa King tsoron zuwa dubata yake yi, saboda yadda ta rame bata a cikin hayyacinta, abin ya yi mugu mugun taɓa shi, sai dare yake zuwa dubata, har a yanzu yana ganin kamar idan aka ja lokaci kaɗan zata miƙa wuya ta hakura, shiyasa bai fara nadama ba, ban ji kamar bai kyauta ba, ya cigaba da tinanin dik in da aka yi one month zata mance da komai ta fara sabuwar rayuwa da Abdussalam. Uhm akwai cakwakiya sosai!. Shi kuma commander har aka yi jana'izar Hoorain aka binnesa ba tare da ya gana da shi na karshe ba, dan bai yarda da ya mutu ba, shi yana ganin ɗansa. Auta ta yi ta yi su kaita ta ga Smart, amma sun ki, sun ce mata baya nan, dan King yasan haɗuwarta da Smart ba zai yi mashi kyau ba, ta yi ta yi su bata waya ta yi kira nan ma abin ya ci tura, King ya gargaɗi kowannensu da kada su kuskura su baiwa Zunaira waya, su kyale ta har a samu ta samu lafiya ta mance da wani Hoorain, ya ce a barta sai ta fara sabuwar rayuwa da Abdussalam ta nisa sai a faɗa mata Hoorain ya rasu a wannan lokaci ba zata damu sosai ba. Uhm King yana ganin cewa soyayyar yarinta ce kawai Auta take yi, bai san abin ba haka bane, ya sha gaban yarinta King!!. Mu je dai zuwa, lokaci ne zai banbanta maka da cewa soyayyar yarinta Auta take yi ko kuwa na gaskiya!!!. -----------------------------------------🔥🔥🔥 🔥🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥🔥 Fito da Leesharh suka yi da nufin su tafi da ita, tsabar rashin imani ma gashin kanta suka damko suna janta da shi. Dai'dai zasu gifta shi in da yake kwance yasa hannu ya damki kafar wanda ya riketa ɗin, da karfi ya yi wurgi da shi tare da miƙawa tsaye a kan ƙafafunsa. A take suka saki Leesharh suna kallonsa da mamaki, ba su yi zaton zai miƙe ba. Wlh bibbiyu yake kallonsu saboda wani irin jiri dake ɗibarsa, ba karya sun buga mashi karfen sosai a kai. Haka ya daure ya rike kansa yana binsu da kallo, so yake yi ya san su waye su? Ya cire mask dake fuskokinsu ya gani. Wanda ya rike da light ɗin ne ya ɗaure wutar a saman stair case, hakan yasa haske sosai ya baibaye wajen, suna iya ganin juna yadda yakamata........ "Ku kashesa, dik da baya daga cikin waɗan da aka bamu aiki a kansa, amma ya zame mana maciji a bakin kofar wucewarmu, dan haka ku kashesa mu samu hanyar wucewa". Ogan nasu my light ne ya yi maganar. Masu nikaf ma a yanzu basu san Ramish ne yake tare da Leesharh ba, dan suna tinanin ita kaɗai ya zo ya ɓoye a gidan sai masu tsaronta, shiyasa suka bada wannan aiki na a dauko Leesharh kawai, da sun san Ramish yana gidan zasu bada aikin a kashe shi a ɗaukota ne!! Lokaci guda wani murmmunar faɗuwar gaba ta dira zuciyar Ramish, domin kuwa voice ɗin nan ta yi mashi kama da wanda idan shi ne lallai zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba. Cike da karɓar umarni suka nufosa gadan gadan, dama su biyar ne. Dik da halin da yake ciki haka ya daure suka fara kokawa. Kuka sosai Leesharh take yi tana tari mai sauti saboda tashin hankali........ Suna fara faɗa ya ji wani karfi ya zo mashi, Allah ya taimakesa ya jibgesu sosai har suka fara gudu da kafafunsu. Nan fa ya bi su suka sauka ƙasa parlour kenan, suna gudu yana binsu, yana san kama mutum ɗaya ne ya cire mashi mask ya ga su wanenen. Har suka fita wajen gidan, dik bai dai'na binsu ba, gudun cetar ransu suke yi. Dai'dai zasu sha kwana ya kama ogan nasu ta baya, kokawa suka fara yi a in da Allah ya bashi nasarar cire mashi mask ɗin nasa. Yana cire mashi kuma guy ɗin ya kwace kansa yana ƙoƙarin gudu, sai dai ya juyo kafin ya gudu, kuma juyowan nasa ne yasa Ramish ya yi mutuwar tsaye yana kallansa ya kasa iya cigaba da binsu. Wani irin zaro idanu ya yi yana kallonsu suna gudu, muryarsa na rawa ya furta. "RAJ". Girgiza kai ya shiga yi yana faɗin. "No ba Raj ba ne, wlh ba shi bane, kawai idona ne, tabbas bana gani da kyau". Wani irin jiri da ya ɗebesa ne yasa ya zube gwiwowinsa a kasa a wajen yana cigaba da sambatun cewa wannan ba Dr Raj kaninsa bane!!!!. Tabbas Dr Raj ya gani, haƙiƙa ba karya idanunsa suke yi mashi ba!! Innalilahi wa inna ilahir rajiun Tashin hankali!! Wai ni Teema mafarki nike yi ne ko gaskiya? Da sanya hannu Dr Raj a masu san ganin bayansa ko kuma dai wani dalilin yasa yake tare da sh?. Kai kaninsa ne fa! Kenan da Dr Raj da Bilal tafiyarsu ɗaya? How? Ko dai Dr Raj ba ɗan mama bane? Kai akwai rikitarwa wannan lamari, ya Ramish zai yi ransa? Innalilahi wa inna ilahir rajiun!!! Wannan shi ne ainahin tashin hankali. Special na ce yau zan baku page mai sauki sauki ko? To ga shi nan da sauki saukinsa 😅ku karanta ƙwaƙwalwa ta ƙara ɗaukar wuta, ina ga page na yau ma ya fi na jiya tsanani 😥😅 to ina masu chorry🤓 Kada ku damu, zan baku update da zan ɗan saukaka maku a cikin satin nan.🥱 Mun iso INTERMISSION ne, dole komai ya ɗauki zafi, akwai kwayayen da zasu fashe soon!! Ku dai ku cigaba da bibiya, kun san bana yin abu sai da kwakkwarar dalili ko? To zaku ji dalilin soon. By much love 💘 🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ========🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S 55 Ramish ya jima a wajen sosai kafin ya iya yunƙurawa ya miƙe tsaye, jiri yana cigaba da ɗibansa. Kasa iya juyawa ya koma ya yi, sai ya tsaya cak yana tinani, kansa ya kulle, abubuwa sun cakuɗe mashi. Shessheƙar kuka da ya ji daga bayansa ne ya sanya shi yin gaggawar juyowa. Tsaye take tana haki tana kuma shessheƙar kuka mai ratsa zuciya, kasa hakuri ta zauna a cikin gidan ta yi, shi ne ta fito da gudu ta bi bayansa, hankalinta a tsananin tashe, fargabarta ɗaya shi ne kada su ci galaba a kansa. Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da ya ganta, ta ɗan duƙa tana haki sama sama. Hannayensa ya buɗe mata alamar ta zo, babu musu ta ruga da gudu ta faɗa jikinsa tana sake fashewa da kuka, tsananin tsoro ne kwance a cikin idanunta, ya lura da hakan shiyasa ya ce ta zo garesa ko zata ɗan sassauta. Tattara dik sauran karfin da suka rage mashi ya yi ya ɗauketa cak, dan tsayuwarsu a waje babban haɗari ne, they have to be enter in. Ta fahimci yana cikin tsananin damuwa, dan haka sai ta ɗago da kansa daga saman kirjinsa, ɗan zuba mashi idanu ta yi yana tafiya kafin tasa hannunta dake ta faman kerma ta ɗan shafi face ɗinsa. "Yah Ramish sun ji maka ciwo ne?". A ruɗe ta yi maganar. Hakan yasa ya dawo da kallonsa a kanta. Kai ya ɗan girgiza mata alamar a'a ba tare da ya yi magana ba!! Wani irin yawu mai wuyar wucewa ta haɗiya game da sauke ajiyar zuciya. Da kyar ya iya nufar ciki da ita. Unguwar so sillent sosai. Suna shiga ciki ya fito da wayarsa bayan ya sauketa a tsakiyar bedroom ɗinsa, kunna wayar ya yi, emagemcy number na masu gyaran wuta ya kira tare da sanar da su buƙatarsa, sannan ya katse kiran. Wani zuciya ce ta ce mashi ya kira Smart ya sanar da shi halin da yake ciki ko zai samu sauki a ransa, dan gabaɗaya zuciyarsa ta zanto tamkar an ɗaura garwashin wuta a kai. Idan har da gaske ya san Dr Raj, to ba shakka shi ne wanda ya gani a yanzu!! Kamar zai kira Dr Raj ɗin ma, sai kuma ya fasa, tinanika kala kala ne sosai a ransa. Ita kuma tana tsaye a kusa da shi, a dai'dai wannan lokaci aka dawo da wutar gidan, masu gyaran wuta har sun iso sun gyara. Gaban mirror ya nufa, face ɗinsa ya zubawa idanu yana kallan kansa. Lokaci guda gabansa ya yi wani irin mummunar faɗuwa sakamakon wani tinani da ya yi, wayarsa ya kawo face ɗinsa, number mamansa ya fara kira ba tare da ya duba time ba. Bugu ɗaya ta ɗaga, ɗan gyaran murya ya ɗan yi kafin ya yi mata sallama. Tana daga kwance a saman katafaren bed ɗinta bata san time da ta miƙe ba jin muryarsa wani irin, cike da tsananin tsoron kada ace wani abin ne ya same shi ta amsa sallamar tare da tambayarsa ko lafiya yake?. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Lafiya lou mama, aiki na sha na gaji". Wani irin ajiyar zuciya da ta sauke sai da ya jiyota, alhamdulillah ta furta sau uku a jere tana ɗan rintse idanu. "Mama menene ratar dake a tsakaninmu da Raj? And Mama kada ki ɗauki tambayata da wata manufa please ke kika haifeni da gaske?".......... Ai bata san lokacin da numfashinta ya ɗan dakata na ƴan dakiku ba, zaro idanu sosai ta yi, lokaci guda ta rikice. "Ramish wani irin tambaya ce wannan kuma?". Ta yi maganar word ɗinta suna harhaɗewa........... "Mama ai dama na ce kada ki ɗauki tambayata da wata manufa, kawai na yi ta ne ba dan wani abin ba sai dai ina san sani". "Wallahi billahi ni na haifeka Ramish, meyasa kake tantama?!!". Daga yadda ta yi maganar ya fahimci da iya gaskiyarta ta yi, dan haka ita ta haifesa, sai dai idan Dr Raj ne ba ɗanta ba, dole akwai wata a ƙasa. "To mama Raj..........." Ƙasa ƙarisa tambayar ya yi, dama zai tambayeta ita ta haifi Dr Raj ne, sai kuma ya tina yanzu zata iya zargan wani abu, shi kuma bayan Smart baya san kowa yasan abin da yake faruwa bare har su ɗaga hankalinsu haka, ta haka ne kawai zai iya cin nasara a aikinsa, rufe sirrinka shi ke kaika ga nasara, and kuma ya tina yana da jinin Dr Raj a bedroom ɗinsa a gidan Abu Abdussalam, yana nan a ma'adanarsu na gwaje-gwajen lafiya, ya taɓa gwada shi a lokacin da ya yi wani ciwo, a lokacin sun tsorata sosai, sai suke ga kamar yana shan miyagun kwayoyi shiyasa suka yi mashi gwaje- gwaje sosai shi da Bilal. Tina yana da jinin yasa ya fasa yi mata tambayar tare da kawar da zancen zuwa zancen gidan da abubuwan da suke faruwa, a zuwan zai je gobe ya ɗauko jinin ya zo ya gwada ya gwada nasa sai ya tabbatar, ya so ma da ya samu jinin mamar tasu, dan ya kara samun tabbaci, lallai da wuya ne idan Dr Raj ɗanta ne, akwai dai wata a ƙasa. Zama a gefen bed Leesharh ta yi tana ta kallansa yadda yake waya da mamarsa a natse. Bayan ya kammala ya katse kiran, zubawa kansa ido ya yi yana tinanin kalaman yayansu, wato Smart, a kullum yana faɗa mashi kada ya yi saurin yanke hukunci a aiki, ya koyi hakuri da danne abubuwa game da zurfafa bincike, ya zamana mai tsananta bincike da rufe sirrin dik abin da yake yi, shiru ita ce babban makaminsu a matsayinsu na jami'ai, idan yana zargin na kusa da shi, kada ya kuskura ya bari su iya gane yana zarginsu, ya yi masu sillent walk wajen kamasu, ya barsu su cigaba da rayuwa da shi kamar yadda suke a baya, amma shi yasan irin takunsa a kansu, yana lallaɓawa wajen bincike a natse ta yadda zai haɗa hujjojin da idan ya yi masu kamu ɗaya ba zasu sake dawowa ba!!. Tuna waɗan nan kalamai na Smart yasa shi sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da furta alhamdulillah. Yana furta hakan ya ji sanyi ta ratsa zuciyarsa, a hankali ya ɗago da kallansa a kanta ta cikin mirror, while ita ma shi take kallah, zubawa juna idanu na ƴan mintuna suka yi, ta shagala da kallan kyansa sai jin sexy voice ɗinsa ta yi ya ce. "Zaki iya bani haɗin kai a yanzu dan mu iya kamasu?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e, dan yanzu ta fara tsorata da al'amarin mutanen nan, kuma ita suke hari sosai, dan sun san ta iya ganesu, idan basu gaggauta kawar da ita ba zata tona asirinsu, ai kun san da suna ganin kamar bata da hujjar nunasu ko da an kamata ne, shiyasa suka saki jiki, amma sai suka ga ba haka bane, kuma ita ma Leesharh ta yi babban kuskure! Domin ba'a nunawa mutane irin wannan cewa ansan wani abu a kansu ko kuma za'a iya fito na fito da su, kun tuna lokacin da suka kirata tana gidan Abbie?. Ba ta ce masu tana da hujoji a kansu har da recoding ba? To wannan shi ne babban kuskuren da ta tabka, da ta yi shiru bata sanar da su cewa tasan wani abin ba, da wlh ba zasu nemi rayuwarta har haka ba....... Ku ɗauki darasi a nan, kuskure ne faɗawa wani abokin faɗa naka cewa kasan wani abin a tattare da shi wai dan ka yi mashi barazana, idan har baya san wannan abin ya fita a duniya to tabbas zai iya cutar da kai koma ya yi ƙoƙarin kawar da kai wa duniya, ba a iya labari ba, a gaske ma ya fi faruwa! Kowa ya iya harshensa, sai dai a ga komai a aikace kamar yadda Smart ya bawa Ramish shawara! Kuma kamar yadda Smart ɗin yake yi! Kun taɓa jin ya faɗi shirinsa wa wani ne? Ai sai dai ku gansa a aikace kawai!!. "Bari in yi wanka in zo sai mu fara aiki ko?". Ya faɗa yana kallanta. Jinjina mashi kai ta yi. Toilet ya nufa, har zai shiga kuma sai ya tina da dattijuwar dake gidan, wani zuciya ce ya ce mashi ya je ya dubata, wani kuma ya ce to ya bari sai ya yi wanka, hakan kuwa aka yi, ya ce bari ya yi wanka ya fito. Yana shiga toilet Leesharh ta miƙe ita ma, dik da a tsananin tsorace da gidan take hakan bai hana ta daure ta nufi toilet ɗinta ba, dan ita ma ta yi wanka. After some minutes ta fito shirye cikin kayan barci riga da wando masu covering jiki yadda yakamata, ta ɗaura Arabian hijab a saman kanta, kwata kwata hijabin bai wuci zuwa kirjinta ba. Kitchen ta nufa ta ɗauko cappuccino cup ɗaya da plate na small chop, sai tashin kamshi take yi ta nufi stair case ɗin, tana tafiya tana waige waige, tsabar tsoro sai ji take yi mamar ana bin bayanta. Dai'dai zata wuce bedroom na wannan dattijuwa ta nufi nasa sai ta ji kamar motsi a ciki. Dakatawa da tafiyar ta yi, a hankali ta lallaɓa ta matsa jikin kofar. Ajiye cup and plate ɗin hannunta a kasa ta yi, kamar wata ɓarauniya ta sanya hannu ta ɗan tura kofar bedroom ɗin kaɗan ta buɗe!!. Ai bata san lokacin da ta zaro ido saura kaɗan ta zunduma ihu ba. Matashiyar mace da bata haura 23 years ba ta gani tsaye a tsakiyar ɗakin, tana sanye da irin fighter wears ɗin nan a jikinta, rike take da waya tana magana ƙasa ƙasa alamar munafurci take kullawa. A hanzarce Leesharh ta juya kallanta izuwa kan gado, nan ta hango kayan dattijuwan, wato kenan matashiyar yarinya ce ta yi shigar dattijai ta shigo cikin rayuwarsu ita da Ramish? Sai a yanzu Leesharh ta tina wannan dattijuwa ai sun jima tare da ita a gidan Abu Abdussalam, kenan dama ashe ba dattijuwa bace?. No wonder take iya aiki lafiya lou ba tare da ta nuna gajiya na tsufa ba, babbar magana, yarinya ce kenan ashe, kam bala'i lallai masu nikaf basu fitowa ba sai da suka shirya, ashe suna da gaskiya da suka ce suna da mutane dayawa a gidan Abbie. Shi Ramish ya kalli dattijuwa ce shiyasa ya ɗaukota ta kula da Leesharh, a tinaninsa tin da tsohuwa ce ba zata yi wani mugunta ba, bai san ya tabka babban kuskure ba!!. Zuba mata idanu Leesharh ta yi tana karantar bakinta abin da take faɗe....... "Dikkansu suna cikin koshin lafiya fa, babu abin da ya samesu, sai kun kara zazzafar shiri a kansu!!". Shi ne abin da Leesharh ta iya karanta daga bakinta na abin da take faɗe. Saura kaɗan ta zunduma ihu saboda tashin hankali, mamakinta ma ɗaya shi ne yadda wannan matashiya ta yi shigar tsofaffi, ba zaka taɓa cewa ba tsohuwa bace, har da wani ɗan duƙawa idan tana tafiya, wato idan mutane suna san abinka sun fika dabara, ji zukekiyar budurwan nan fa, amma suka mai da ita tsohuwa, har da tamu tamun fata suka saka mata, kai mutum abin tsoro ne, babu mai iyawa ɗan adam sai ALLAHN da ya haliccesa. Ta shagala da tinane-tinanen da take yi sai gani ta yi dattijuwa zamu ce ko matashiya yanzu kuma?. To oho dai, sai ganinta ta yi ta katse kiran ta nufi wajen bed ɗin, nan ta ɗauki kayanta na dattijuwan ta fara maidawa jikinta, da alama wanka ta yi, shiyasa ta cire kayan. Wani irin zaro idanu Leesharh ta yi tana ganin yadda budurwa take rikiɗewa izuwa tsohuwa cikin ƙanƙanin lokaci, amma sun iya shiri, harta fatarta mai tamu tamun ma ashe ba fatar gaske bace, ashe sakawa aka yi, yanzu ga shi ta ɗauko shi tana mayarwa, har farin gashin kanta ashe attachment ne, shi ma ta mayar. Take ta koma ainahin tsohuwa. Tsabar tashin hankali Leesharh bata san lokacin da ta saki kofar ta dafe kirjinta ba, da karfi yake buga mata ne. Baya baya ta fara komawa har ta isa wajen stair case ba tare da ta sani ba. Ta jima a tsaye a wajen tana tinanin meyakamata ta yi kafin nan ta dawo ta ɗauki cup and plate ɗinta ta nufi bedroom ɗinsa, wani ɓangare na zuciyarta tana faɗa mata da ta sanar da shi, wani ɓangare kuma yana faɗa mata a'a ta bar abin zuwa gaba su ga me zai faru!. Zuciyarta cike da zulumi da wannan tinani ta ƙarisa bedroom ɗinsa. Bakinta a ɗauke da sallama ta tura kofar ta shigo. Yana zaune gaban bed yana duba wasu hotuna na Bilal da masu nikaf, ganinta yasa ya ɓoye hoton da Bilal yake a ciki a karkashin latop ɗin dake gabansa, da alama baya san ta fahimci Bilal yana cin amanarsa. Saman table ta ɗaura cup ɗin cappuccinon, cikin sanyin murya ta ce. "Good evening Yah Ramish". Ta yi maganar tana satar kallansa, wai good evening kamar ba yanzu suka rabu ba, dik fa ta shiga ruɗani da tashin hankalin abin da ta gani ne yasa sam ta mance da yanzu suka rabu. "How was your day?". Ya faɗa ba tare da ya juyo da kallonsa kai tsaye a kanta ba, amma yana satar kallanta ta witsiyar ido, shi ma ya biye mata ya bata amsa ba tare da yasan a ruɗe take ba. Alhamdulillah ta amsa mashi da shi kafin ta juya ta nufi waje tana faɗa mashi ga cappuccinon nan ta kawo mashi, sam fa ta mance da zasu yi aiki, da alama wannan dattijuwa ta rikitar mata da tinani sosai. Shiru ya ɗan yi har sai da ta kai bakin door zata fita, gentle ya ce. "I need 10 mins from your time". Ya yi maganar tare da juyo da kallonsa a kanta. Juyowa ita ma ta yi, ɗan tsuke face ta yi. "Yah Ramish small chop zan je in ci fa, am feeling hungry............". A karshen maganar tata da shagwaɓa ta ƙarisa. Sai dai bata iya kai karshen maganar gabaɗaya ba ta zubawa kayan jikinsa idanu, kai Ramish duniya ne, karshe ne guy ɗin wajen iya dressing, haƙiƙa sleeping dress suna mubaya'a a jikinsa yadda yakamata, kamar ba shi ba, ya yi masifar kyau cikin kayan, wando ce zuwa gwiwarsa da rigar da bata da botira sai siririn maɗauri a gaban rigar wanda idan ya daure ma faffaɗar kirjinsa zata kasance a buɗe, siffar bathrobe, to amma shi bai ma ɗaure igiyar ba, ya ji daɗi buɗe wide chest ɗin nasa da kyau, abin dake tafiya da imaninta kenan. Shima kuma har cikin ransa ya ji matuƙar daɗin ganin dirin da Allah ya yi mata, sai ya ja dogon numfashi kafin ya ce. "Shin an hanaki ci a nan ne?". Kai ta girgiza kamar wata yarinya ƙanƙanuwa. Kallan gefen ido ya wurga mata kafin ya ce. "Zo ki ajiye shi in yi maki wasu tambayoyi, idan na kammala sai ki je ki ci ɗin"..... Jinjina mashi kai alamar to ta yi kafin ta dawo cikin bedroom ɗin. A saman bedside drawer ta zauna bayan ta ajiye small chop ɗinta a kusa da cappuccinonsa. "Zo ki zauna a nan". Ya faɗa yana nuna mata kusa da shi. Kamar ba zata je wajen ba, sai kuma ta ga ai bincike yake yi, kila wani abin zai nuna mata, a gefensa ta zauna, wani irin shakar kamshin perfume ɗin jikinsa ta yi ta ɗan lumshe idanu, shi ma dai shaƙar nata ƙamshin ya yi ya lumshe idanu. "Aesh shin kin san ɗaya daga cikin waɗan nan mutanen?". Ya yi maganar tare da nuna mata hotunan dake kan screen na laptop ɗin gabansa. Kai kallonta a kansu ta yi, shiru ta zuba masu idanu tana kallonsu, tabbas ta taɓa kallonsu dikkansu, sai dai ta manta a ina ne, ɗaya na tsakiyar nan tabbas akwai ranar da ta ga idanunsa kurkusa da ita, to amma a ina ne? Shiru ta nausa cikin tinaninta ko Allah zai sa ta iya tina in da ta taɓa ganinsu, sai dai kuma ina ta gagara tinawa. Jin ta yi shiru ne yasa ya juyo da kallansa a kanta. "Ko dai har yanzu baki dawo dai'dai bane? Har yanzu akwai tsoro a ranki ko?". Ya jefa mata tambaya. Ɗago da kallonta a kansa ta yi, suna haɗa ido bata san time da murmushi ya kubce mata ba, haka kawai ta tsinci kanta a cikin farinciki da kwarin gwiwar jin zata iya yin komai a kansa........YAU BA BATUN AMANAR SHARIFAT KENAN, WAI ZATA IYA YIN KOMAI A KANSA KAI LEESHARH DUNIYA.😅 Zubawa smile ɗin nata idanu ya yi yana kallanta, hannu tasa ta rufe fuska tana cigaba da murmusawa.......... Matsar da face ɗinsa dab da ita ya yi, ƙasa ƙasa ya ce. "Murmushi yana yi maki kyau, amma yanzu dai murmushin me kike yi daga tambaya?". Kai ta girgiza mashi alamar babu komai. "To faɗa mun shin kin sansu ne?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e ta sansu. Ajiyar zuciya ya sauke. "To faɗa mun a in da kika sansu". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya riƙo hannayenta, ya zamesu daga face ɗinta. Dakatawa da yin murmushi ta yi tare da kura masu idanu, take wannan dattijuwa ta faɗo mata a cikin ranta, ɗan limshe idanunta ta yi tana tina abubuwan da ta gani a jikin wannan dattijuwa. Nan take ƙwaƙwalwarta ya tuna mata wani irin zanen tattoo na harafin B a wuyarta wanda kuma irinsa ne a wuyar Bilal kuma irinsa ne a wuyar dik mutanen dake jikin wannan hoto, hakan na nufin dik team nasu ɗaya kenan. Dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali. "Yah Ramish ba zan iya ce maka ga in da na sansu ba, amma dai ka sani koma a ina ne to a gidan Abbie ne, dan dai kaga bana fita, tin da na karɓi wannan contract ɗin na shiga gidanku to ai kaga bama fita, dik yadda aka yi dik suna gidan Abbie, ka bincika cikin dayawan masu aikin dake gidan, har hawa na sama da kasa dik ka bincika suna ciki, kai har cikin securitys ɗin nan ma dikka". Tin da ta fara magana yake bin ɗan bakinta da kallo, babu abin da yake tsaye a ransa irin kissing ɗinta da ya yi ɗazun. "Zaki iya bani wata alama da zan iya ganesu da shi?". Ya yi maganar kamar ba shi ya yi ta ba. Shiru ta ɗan yi kamar mai nazari, sai kuma ta ce. "Zanen wannan B dake wuyarsu, dik ƴan cikin team ɗin suna da wannan zane..........". Bata karisar ba ta yi shiru sakamakon ta tuna taga wani zanen scorpion a waist na tsohuwar can ta baya sama da mazaunanta kenan, dan fighter wears dake jikinta bai rufe mata ƙugu ba. Shiru ya zuba mata idanu a lokacin da ta dakata tana tinani. "Yah Ramish ba iya zanen B a wuya ba, suna da wani tambari na kunama a waist ɗinsu, tabbas na gani a wajen........" Kasa ƙarisa a wajen waye ta gani, take ta ji ta shiga ruɗani, zazzare eyesball ɗinta ta yi tana kallansa. Dik abin da suke tattaunawa a kunnen wannan dattijuwa suke yinsa, saboda ta sanya masu abin jin magana a ɗakin kasan bed ɗin Ramish ba tare da Ramish ɗin ya sani ba, dan haka dik maganganunsu tana daga kwance bisa bed ɗinta, ta maƙala bluetooth a kunne tana jinsu, hannunta rike da wayarta tana rubutawa masu nikaf sako da cewa su yi saurin ɓoye dik wasu zanika dake jikinsu, dan Ramish ya san da zanen kuma zai iya zuwa a kowani lokaci dan ya yi bincike, dan haka su nemi plaster mai irin fatarsu maza maza su rufe zanen!. "Aesh har yanzu akwai abin da baki san in sani ko?"........ Cikin gaggawa ta girgiza mashi kai tare da cewa. "A'a ina san ka san komai, dan haka zan faɗa maka komai, amma ina tsoron irin labarin da zan ji a kan babana ne! Wannan yasa zuciyata take rawa a kan in yarda da kai ko kada na yarda". Allah sarki uba, wato har yanzu ta gagara iya ciresa a ranta ta danne ta yi abin da ya dace, tana san babanta sosai, kuma mun san cewa abu ne mai matuƙar wahala ta iya daurewa a kansa. Hannunsa yasa ya riko nata, cikin sigar tausasawa ya fara sanar da ita kada ta damu, babu wani abin da zai sami babanta, ta faɗa mashi komai a yanzu. Hawaye ne suka ciko idanunta sosai, muryarta na rawa ta ce. "Zan faɗa maka, na yi alkawarin ko zan rasa rai'na zan faɗa". Jinjina mata kai ya yi. "Ba zaki mutu ba, muna nan tare dake In Sha Allah har sai kin......" Fasa ƙarisa maganar ya yi, dama zai ce har sai ta haifa mashi babynsa, sai ya tina idan ya yi wannan magana kuma zai ja ne su canza topic na magana, a halin yanzu kuma yana cikin matsuwa da san jin abin da yake da buƙatar ji. "Suna dayawa a gidan Abbie, nasan zaka san wata mata mai kiba dake zuwa wajen Ummie, to ita ce nan wadda ta kawoni gidanku bayan masu nikaf sun damƙa mata ni, bayan ita akwai wata mai aiki a hawa na biyu, tana nan fara tas kamar baturiya, to haƙiƙa ba farar fata bace, shiri aka shirya aka sauya mata jiki ta hanyar make up, baya ga wannan akwai ɗaya daga cikin securitys ɗinku wanda ina zargin shi, dan akwai ranar da muka ci karo da shi a harabar gida, na juya zan ce mashi sorry sai na kalli zanen B a wuyarsa, na sha mamaki sosai, amma haka na wuce ina ta kallansa dan in gane face ɗinsa, amma yana sake da face mask, tabbas suna da yawa a gidan Abbie". Ta kai karshen maganar hawaye na bin kuncinta. Abin like some how haka Ramish ya jisa, babu abin da ya fi bashi mamaki ma shi ne har da kawar Ummie a ciki, kenan har da sa hannun Ummie? To me suke nema da shi ne? Ya samu bayani sai dai babu hujja. Shessheƙar kukanta ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka, janyota jikinsa ya yi ya rungume yana kara karfafa mata gwiwa a kan kada ta damu, babu abin da zai samu babanta dan ta fallasasu. A can kuwa wannan dattijuwa ta ji komai, dan haka sai ta bada sanarwa a team nasu da ayi gaggawar kashe Hajiya two seater yanzu, dan Leesharh tasan face ɗinta har ta fallasata ga Ramish, su kasheta kawai, saura kam su kyalesu tin da Leesharh bata san ainahin face ɗinsu ba, amma wancan bakar fata da suka sanyawa farin fata na roba dan ɓadda kama ita ma su kasheta da sauri. BABBAR MAGANA, RAMISH YANA AIKI WANNAN MATA TANA WARWARE MASHI, DIK WASU HUJOJI DA LEESHARH TA BASHI DAN ISA GARESU SAI LALATAWA WANNAN DATTIJUWA TAKE YI BA TARE DA YA SANI BA, ALLAH SARKI, YANA ZATAN YANA DA HUJOJI BAI SAN DIK BABU KOMAI BA. Tsoro yasa Leesharh ta gagara sanar da shi wannan dattijuwa ma ba tsohuwa bace ba, yarinya ce wacce kuma ƴar team ɗin su masu nikaf ce. My people's me kuke tinanin zai faru? Uhm INTERMISSION muke, yanzu wasan zai ɗauki zafi, bari mu ga karfin ƙwaƙwalwar Ramish, shin zai iya kamasu dik da matar can ta lallata makaman da ya samu ne? Shin zai iya gane wannan dattijuwa yarinya ce? Shin zai iya rigasu isa ga hajiya two seater ne, ya wasan zai kaya, mu je zuwa, hojojin Leesharh basu kare ba, bata bashi recoding da ta yi ba da sauran maganganunta da su, amma zamu ga ya wasan zai kaya!!. 🔥🔥🔥🔥BABYN BABY🔥🔥🔥🔥 A cikin kunnuwanta ya fara zuba mata raɗa na hot sexy word masu tafiya da imani, tini baby ta narke mashi ta hau zuba mashi shagwaɓa babu kakkautawa, birkice mata ya yi ya shiga kissing ɗinta ta ko'ina. Ko kaɗan bata yi ƙasa a gwiwa wajen fara mayar mashi da martani ba, cikin salo mai jan hankali ta shiga shan lips ɗinsa na kasa tana tura hannunta cikin gashin kansa, abin da ta jima tana sha'awa kenan lip's ɗinsa........ Idanunsa a datse sosai cikin fitar hayyaci ya capki tula tulanta ta hau matsewa kamar mai murje gyaɗa soyayye, sake mashi jiki sosai ta yi haɗe da kara tura mashi kirjin nata dan ma ya ji daɗin yi da kyau. Ai kuwa ba karamun kara susuce mata ya yi ba, take ya zame bakinsa daga nata ya mayar da shi saman nipples ɗinta. Cikin dabara ya zame kayan dake jikinta kaf ya hau sarrafata san ransa. Can har kamar zai yi mata mai gabaɗaya ko me ya tina sai kuma ya fasa tare da sakinta ya juya mata baya cikin gaggawa, bata yi mamakin ganin hakan ba, dan ita ma a tsorace take kada ya yi abin da ya yi niyar, dan haka ta ji daɗin sakinta da ya yi, bata wani damu dan ya juya mata baya ba, ta kwanta shiru tamkar mai tinanin wani abin, a haka bata san lokacin da barci ya yi awon gaba da ita ba. Shi kuwa ya jima a haka har sai da ya samu sauki, sannan ne ya miƙe ya nufi toilet, bai bi ta kanta ba. Wanka ya yi, ɗaure da towel ɗinta ya fito, bashi da kaya a gidan, ba kuma zai iya mayar da wanda ya cire ba, hakan yasa ya haye bed ɗin ɗaure da towel, kara gudun Ac ya yi tare da janyo masu bargo ya rufe su, janyota jikinsa ya yi ya rungume sosai, daga haka barci ta yi awon gaba da shi. Asuba ta gari!. Da misalin karfe 5:30 ta farka, a hankali ta zame jikinta daga nashi, a hankali ta lallaɓa ta miƙe ta nufi toilet. A gurguje ta yi wanka, ta fito ta sanya abaya tare da shinfiɗa dadduma ta tada sallah, sam bata tashesa ba, dan tasan bashi da kayan sakawa a gidan, so dole sai ya koma gidansu zai yi sallah. Bayan ta idar da sallah ta ɗan yi karatun Alqur'ani mai girma zuwa 6:20. Nan ta tashi ta shirya cikin school uniform ɗinta. A shiriritarta dai wai school zata wuce ta barshi yana barci sai time da ya tashi ya tafi gida. Parlour ta fito, babu kowa sai niimantaccen kamshi dake tashi, kamar zata nufi kitchen sai kuma ta dawo ya nufi ɗakin Ammo. Zaune ta isko dattijuwa a bakin bed ɗinta, da alama bata jima da shigowa cikin bedroom ɗin ba. Sosai Ammo ta yi mamakin ganinta cikin uniform, har kasa rufe mamakin nata ta yi ta ce. "Baby lafiyarki kuwa?"..... Ɗan zaro siren eyesball ɗinta ta yi alamar mamaki ita ma kafin ta ce. "Ammo me nayi?"...... "Na ganki da uniform ne, ina zaki je?".... Ajiyar zuwa ta sauke. "Ammo na zaci ma wani abin na yi, school zan tafi mana"..... Harara irin ta jika da kaka Ammo ya wurga mata kafin ta ce. "Ban san sakalci fa, mijin naki yana kwance a ɗaki ne zaki shirya tafiya school ba tare da ya sani ba, ko breakfast fa baki kai mashi ba, ina da tabbacin ko tea baki je kin ɗauka a kitchen kin kai mashi ba". Karisowa bakin bed ɗin ta yi ta zauna tana faɗin. "To Ammo dama ai ba'a nan yake breakfast ba, dan haka idan ya tashi zai koma gidansu ya yi"....... "Eyeeeee". Ammo ta faɗa tana kallanta....... "Lalai kuwa, haka ake yi wa miji ko?". Ta jefa mata tambayar tana harararta. "To Ammo ya zan yi mashi? Ai naga ba'a nan yake yin breakfast ba". Ta faɗa tana turo baki. "Ba shakka, amma kuma da anyi magana sai ku ce ai ku ƴan zamani ne kun fi mu sanin yadda ake kula da miji ko? Yanzu haka zaki tafi ki barsa?. A haka kina bashi kulawa kenan?". Ta kai karshen maganar tare da jefa mata tambayar....... Shiru baby ta ɗan yi, daga bisani ta ce. "Ammo zaki fara mitar nan taki ko? To ni tin kan ki rufeni da surutu bari in je in kai mashi tea ɗin in zo in tafi school, yau ko breakfast ma ba zan yi ba". A shagwaɓe sosai ta yi maganar, ta kai karshen tana yunkurawa zata miƙe. Cikin sauri Ammo ta riko hannunta. "Zauna in faɗa maki wasu sirrikan rike miji, kinga kina nan zaune kina shirme wata zata kwace maki shi"....... Zaro idanu ta yi tare da dafe kirji. "Na shiga uku, wata ta kwace mun shi kuma Ammo?". Gyaɗa mata kai Ammo ta yi alamar e. "To Ammo me na yi da wata zata kwace shi. Anya yanzu kina sona kuwa Ammo?"...... "Shakka kike yi a kan san da nike maki ko ƴar ƙaniya?". Ta jefa mata tambayar tana sake hannunta da ta rike....... "Ba dole in yi shakka ba, kin ce wata zata kwace mun baby". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. "Saboda san da nike maki yasa na faɗa maki gaskiya, bar shiririta lokacin na kurewa ki saurari abin da zan faɗa maki". TO BARI MU ƊAUKI WASU SIRRIKA DAGA WAJEN DATTIJUWA AMMO, BUGUN DA KENAN, BARI MU SAMU KARIN DABARU!!. Natsuwa baby ta yi tana turo baki, ita a dole Ammo bata santa tin da take batun wata zata kwace mata babynta. Kwantar da kanta a saman laps na Ammo ɗin ta yi tare da saurarawa tana jin jawabi. Cikin natsuwa ta yadda zata fahimta Ammo ta fara mata magana. "Abin da nike so dake a nan shi ne ki natsu ki tattare hankalinki da natsuwarki gabaɗaya a kansa, kada ki yarda ki bari yasan yana san abu ba tare da kin yi mashi wannan abin ba, ma'ana kafin ya fahimci yana buƙatar abu ya kasance har kin tanada mashi wannan abin........"..... Gajan hakuri irin nata yasa ta katse Ammo da cewa. "To ta yaya zan san yana san abu?". A matse da san jin amsa ta yi maganar, dan tana san babyn nata sosai, tana san abin da zai faranta mashi!. "Dik zan koya maki yadda zaki sani, amma yanzu ki yi shiru ki saurari sirrikan yanzu". Jinjina kai ta yi alamar to tare da kara natsuwa......... "Yanzu da kuka tashi barci kamata ya yi tin kafin ya tashi ki je ki tsala wanka, ki shirya cikin kaya masu kyau, da safe ba'a saka kaya masu nauyi ga miji, ko dan ya fita wajen aiki yana tinanin surar jikinki yakamata ki sanya kayan da zasu bayyanar da komai a garesa, kayan da zasu sanya komai ya tsaya a ransa ta yadda fitarma idan ba ya zame mashi dole ba ba zai fita ba, in kuma dole ce ya fita to zaki zama mutum na farko a cikin tinaninsa. Ki shirya cikin waɗan nan kayan, ba kuma kayan barci ba, na zaman gida masu ɗaukar hankali, sannan sai ki haɗa mashi zazzafar tea mai bala'in kamshi da daɗi, ko baya shan tea da safe kafin komai ke zaki koya mashi ta hanyar yi mashi mai shegen daɗi, hakan zai sa dik ranar da baki yi mashi ba zai tambaya. Ki ɗauki tea ɗin nan ki kai mashi, sannan ki tashesa daga barci, ya fara cin karo da kyakkyawar fuskarki da haɗaɗɗen shigarki, zaki ga yadda zai rikice, ko bai nuna maki ba zaki ga yadda yake satar kallanki............ Daga nan ki yi mashi barka da tashi kafin ki zauna a kusa da shi, cikin tausasan kalamai ki ce ku je kiyi mashi brush ya zo ya sha tea. Wlh ko bai nuna maki ba zai ji matuƙar daɗi a ransa, tashinsa daga barci ma cikin salon so da kauna zaki yi mashi, cikin natsuwa. Ki rinƙa yawan nuna mashi kina san kasancewa a tare da shi, hakan shi zai sa ya kara sanki. Namiji yana san yabo sosai, yana san kuma anuna mashi shi wani ne, misali ki nuna mashi shi ɗin mai daraja ne sosai a cikin rayuwarki, ki nuna mashi kamar shi ne komai naki, komai sai da shawara da izininsa zaki yi, ba ƙaramin daɗi suke ji ba, ko basu nuna ba yana sanyaya masu rai, yana da kyau ki fahimci shi fa namiji ba komai ne idan ya burgesa yake fitowa fili ya nuna ba, idan kina da natsuwa daga yanayin reaction ɗinsa zaki fahimta abin ya yi mashi sosai, ba sai kin tanbayesa ba, dan in kin tambaya ba lallai ya faɗa maki ba, dan haka namiji yana san ki nuna kin damu da shi, idan ya baki kyautar abu, ko da abin bai yi maki ba, ki kasance mai nuna dik duniya babu abin da ya yi maki sama da wannan abin, sannan idan kuna zaune ki rinƙa yawan yaba wanna abin kina faɗin babu abin da kike so sama da wanna, misali ace ya saya maki sabon waya, ko da wayar nan ta kai watanni a hannunki, idan kuna zaune ki ce kai amma ina bala'in kaunar wayar nan, tana da daɗi rikewa, bana jin zan iya rabuwa da ita, ina kaunarta, baby ka iya zaɓe kuma ina alfahari da kai, wlh ko bai yi magana ba ki lura da yanayinsa a wannan lokaci, daɗi suke ji har cikin ransu idan suka sayi abu aka nuna an damu da shi kuma ana kaunarsa, amma su sayi abu wata ma ko godiya bata yi, wata kuma daga godiya shikenan, a hana taya zaku yi expecting gaba zai sake ganin wani abin ya yi sha'awar saya maku? Ai ba zai so ma ya sake kawo maku kyauta ba, amma idan kina yabawa ko da time to time ne wlh ko baki ce kina san abu ba ya rinƙa saya yana kawo maki kenan, wata sai ya sha wahala ya saya mata abu, idan suna zaune sai ta hau zagin abin, a'a bata rike chaji, bata da kyau, bata da camera, ni nagaji da ita, ban da wahala babu abin da take bani, da ita gara babu, me hakan? Sai ka ce yaki? Ai gobe ko kuɗi sun yi mashi yawa bai sake saya ya kawo maki, gara ki yi ta yabonta, Allah basshi idan kuna zaune cikin nishaɗi kuna hira sai ki ce laa baby wayar nan tawa ta samu matsalar abu gaza, ina santa sosai, na ji zafin wannan matsala da ta samu, kamar in yi kuka, hakan zai sa ya ji zai saya maki wadda ta fita, haka ake wa miji, cikin taushi da tausasawa, su ɗin kamar yara suke, baki ganin yaro idan kika nuna mashi karfi a kan abu sai ya saka maki kuka ne? To suma idan kika nuna masu karfi sai su wahalar dake su saka maki ruwan bala'i, cikin taushi ake bi a ci riba, sannan idan baya nan ya koma gidansu ki yawaita kiransa kina yi mashi shagwaɓa a kan ya dawo kina kewarsa, hakan zai san ya ji lallai kin damu da shi, yanzu abin da nike so dake tashi ki je ki cire uniform ɗin nan ki shirya cikin kaya masu kyau, sannan ki kai mashi tea, ki bar school ɗin har sai ya tashi da kansa ya buƙaci da ki shirya ku tafi school kin ji ko?". Ta kai karshen maganar tana kallanta. Zaro siren eyes ɗinta ta yi, kamar wadda aka sakawa battery ta ce. "Laaaa Ammo a ina kika iya dikka wannan? Dama tsofaffi ma sun iya love ne?"..... Hancinta Ammo ta ja kafin ta bata amsa da. "Ai ku babu abin da kuka iya ban da shirme, ko sanin in da yake yi wa mijinku ciwo baku sani ba, ban da cika shi da i love you da kiss babu wani abin da kuka iya, ni tashi ki je ki yi abin da nace maki, zuwa dare na kara maki wasu sirrikan". ...... Ɗan taɓe baki ya yi. "Ammo wai har da kiss kika sani?". Dukan wasa ta kai mata. "Da ban san shi ba ai da ban haifo ubanki har ya haifoki ba, maza tashi nikam, ni ai naso babyn naki da ya yi maki mai gabaɗaya ne bakin rashin kunya da shegen iyayin nan ya mutu, ban so yau da safen nan in ganki kin fito da kafafunki ba". Ɗan tsuke fuska ta yi. "Ammo me kuma mai gabaɗaya?". "Jeki ki kula mun da angona, idan ya tafi zan faɗa maki". Ta faɗi hakan ne dan tana san ta tashi ta je ta shirya kada ya farka ya ganta a haka. Wato kaka duniya ce, ba kunya zata fayyace maka komai ta wayar maka da kai ta kuma ɗauraka a hanyar da ta dace wadda zaka samu zaman lafiya a gidan aurenka. Miƙewa ta yi tana faɗin. "Baby yau zai sha mamakina, zan kashe shi da love Ammo, kin tina mun wani kalar love ma da na ce zan yi wa baby irinsa"...... Harara Ammo ta bita da shi. "Ke dai ba ke bace ƴar fari bare in ce wawtar farintaka ke damunki". Zata mayar da martani Ammo ta yi saurin cewa. "Jeki sai kin dawo ma yi magana". Wucewa ta yi yana turo baki, da kallo Ammo ta bita tana yi mata addu'ar Allah ya kara kauna a tsakaninta da mijin nata, dan bayan Allah da manzonsa shi ne kaɗai gatansu. Bedroom ɗinta ta koma, a gurguje ta cire uniform ɗin nata, sannan ta shirya cikin wasu sexy wears, wandon jeans ne crazy sosai wansa ya yi matukar fitar mata da shape na hp ɗinta, ta sanya wani ɗan karamun rigar da bai wuce kasan cibiya ba, ta yi matuƙar kyau over, zuba perfume sosai a jikinta ta yi, ita kanta ta san ta haɗu, kitchen ta nufa, nan ta isko an ajye mata hot tea a cikin cup, ta ji daɗi sosai, ta san aikin Ammo ne, sai kamshi ne yake tashi a cikin tea ɗin. Bedroom ɗinta ta koma tana wani yanga, dama gwanace a iya sanya ƙananan kaya, bata ma sanya manya. A saman bedside drawer ta ɗaura plate na tea ɗin, sannan ta zauna a gefen bed ɗin ta kusa da shi, zubawa face ɗinsa idanu ta yi. Yadda yake barci gwanin birgewa, matsar da lip's ɗinta dab da shi ta yi, hot sumbata ta bashi a samansu, wani irin laushinsu da ta ji ne yasa bata san time ɗin da ta fara kissing ɗinsu ba, ta capki na kasar ta fara tsotsa a hankali. Hannunta ta tura cikin gashin kansa ta fara shafawa, jin daɗi abin yana kai mata karo yasa ta gyara zamanta a in da ta kwanto da rabin jikinta a kansa, ta datse idanunta gam tana wani narke mashi. Shap ta mance da wani abu wai barci yake yi ta zo tashinsa. A hankali ta ɗan waro idanunta dan ta kalli face ɗinsa. Aikuwa tana warosuwa suka yi four eyes. Zabura ta yi tare da zare eyes ɗinta, da gudu ta zare bakinta daga nasa ta miƙe zata gudu. Sai dai ina, cikin zafa ya capki hannunta tare da janyota ta dawo jikinsa, datse idanu gam ta yi tana ɓuye fuska........... "Ina zaki je bayan baki kammala abin da kika fara ba?". Cikin wata iriyar kasalalliyar murya ya yi maganar!. "Baby dama ai tashinka zan yi, kuma ka tashi, kaga na kammala abin da na fara kenan". A shagwaɓe sosai ta yi maganar. "Are you sure?". Ya faɗa yana tattare gashin kanta da ya zubo mashi a fuska dan ya samu damar ganinta da kyau.............. "Da gaske fa baby". Ta faɗa tana turo baki. Sumbatar ɗan bakin nata ya yi. "So open your eyes ki ga wani abin". Make shoulder ta yi kafin ta ce. "A'a ni kunyarka nike ji". Ɗan capko lips ɗinta na ƙasa ya yi ya ɗan tsotsa kafin ya sake tare da juyawa da ita, ya zamana ya yi mata rumfa da kirjinsa, kamar kai raɗa ya ce. "To bari dai in rabaki da kunyar mu gani ko za'a bani soyayya yadda yakamata". Ya kai karshen maganar tare da................. 🥱 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =======🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 56 "To bari dai in rabaki da kunyar mu gani ko za'a bani soyayya yadda yakamata". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa ya zame hannunta da ta rufe fuska. Cikin salo ya fara bata hot kiss na good morning. Sake jiki ta yi ta fara taya shi. Nan suka shiga aikin da suka saba, har tea ɗin ya huce ba tare da ya sha ba, yau ya samu abin da ya fi tea, sai ya rinƙa juyata san ransa!. Ammo dai tana ɗaki abinta, ya zo ya tare masu a gida!!.......😅 🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥 A hankali ta fara takawa tana yin baya baya, so take ta gudu ta fita daga room ɗin, ya tashi kanta, tsantsar kyansa da kyan jikinsa yasa ma ta iya shagala da kallonsa, idan ba haka ba idanunta sai su makance. Dik in ta yi taku ɗaya shi ma sai ya matsota, sai dai ita bata ganin yana matsowa, saboda ya ɗauke mata hankali, idan kuka kalli idanunsa wlh ko kaki ko kaso sai ka shagala da kallonsu. Ta kai bakin kofar ba tare da ta san ta isa wajen ba, ji ta yi ta tafi baya baya gabaɗaya, saboda bata san ta kai karshe sai fita ba. Gabaɗaya zata faɗi ta rintse idanunta gam ta saddakar kasa zata faɗi, sai ji ta yi ta faɗa saman lion chest ɗinsa ya tallabota da hannunsa ɗaya. Ɗan tsuke fuska ta yi haɗe da ɗan matse ɗan bakinta. A hankali ta waro idanunta waje tana ɗan matsesu. Subhanallah ai mutuwar tsaye ta yi tana kallon cikin idanunsa, ga shi a kurkusa da ita!! Wow, shi ne kawai abin da zuciyarta take iya furtawa, a gaskiya Black Tiger karshe ne, madarar kyau babu sirki. Shagala suka yi da kallan juna, ya kafeta da ido kamar mai karantar wani abin a saman face ɗinta. Almost five minutes suna a haka kafin ta ɗan motsa kaɗan, hakan yasa ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Kamar wanda ya yi mata wani abin take ta lumshe idanunta tamkar wadda barci ya ɗauke, hakan yasa eyelashes ɗinta suka kara fitowa sosai, tsantsar kyanta ya kara bayyana. A wani irin slow ya dawo da kallonsa saman wuyarta da ya cika da tsokan guru, hankalinta a kwance ta murmure, wuyar nan nata ya kara tsantsar kyau, ko kaɗan tin da ya fara kallanta bai kyafta ido ba, kamar ba mutum ba, kun san ko yaya ka ɗan kalli abu zaka kyafa ido, to amma shi ina bai kyafta ba. Hannunsa ɗaya ya ɗago ya ɗaura a saman wuyarta, kamar mai yin wani abin ya zana mata layi a wuyar, nan take wani irin haɗaɗɗen diamond chain mai bala'in kyalli ya bayyana a wuyar tata dai'dai yadda ya zana layin. Wow ni kai'na sai da na furta hakan, wlh wuyarta yadda kuka san ka zauna ka ɓata lokacinka mai tsawo kana kallo, tsantsar kyan wuyar ne ya bayyana, ga wani irin kyalli da sarkar yake yi ya yi bala'in kara haskakata. Ɗan karkata kansa kaɗan ya yi kamar mai leƙa wani abin, fuskar nan tamau kamar hadari, cigaba da kallanta ya yi, ita kuwa tin da ta lumshe idanu bata sake buɗewa ba, dik yadda aka yi akwai abin da ya yi mata. Slowly ya dawo da kallonsa a saman kirjinta da suka ɓulɓul da su, ɗan ɗauke wuta kaɗan ya yi. Hannun nasa ya ɗaura a saman face ɗinta yana mai da kallansa wajen, nan take wani haɗaɗɗen make up ya bayyana a face ɗin nata. Wani irin fitinannen kyau ta kara, tamkar ba ita ba. Sake karkata kansa kaɗan ya yi, kamar irin yana duba ta yi ko bata yi ba haka?!. Zuba mata ido sosai ya yi, ya ɗauki a kallah good 10 mins yana kallanta. Magic eyes ɗinsa ya juya, nan take gashin kanta ya yi wani irin tsantsaruwa, ya sha gyara yana wani irin kyalli, dama abin dake ɗaukar hankalinsa kenan kalar gashin nata yadda yake wani kyalli, kun san abu golden white da ɗaukar hankali, wani irin ɗaure gashin nata da ya yi tin da nike ban taɓa ganin irin wannan style ɗin ba, take wasu kyawawan furanni suka bayyana a saman gashin nata, wani irin kyalli pil da ya ɗaure mata gashin yake yi, dik yadda aka yi diamond ne shi ma. Take kyanta ya kara fitowa sosai. Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, nan take idanunsa suka rikiɗa suka koma ainahin kalarsu. Yatsansa manuniya ya ɗaura a saman face ɗinta, ɗan guntun gashin da ya bar mata a gaban goshinta ya sanya yatsar ya ɗan kawar da shi gefe yana ɗan kara karkata kansa, da alama tabbatar da kyanta a ransa yake yi. Kamar mai yi mata zane a fuska haka ya gangaro da yatsar tasa ta gefen kyakkyawan siririn sagenta har zuwa haɓarta, kasa ya cigaba da yi da yatsar tasa har izuwa wuyarta, ɗan kaɗan chain ɗin dake wuyar tata ya yi da yatsar tasa kamar mai kaɗa jita, sai kuma ya wuce chain ɗin izuwa saman tudun tula tulanta. A karo na biyu ya sake ɗan ɗauke wuta tin kan hannunsa ya isa wajen! Haka ya ja mata layi har tsakiyar tula tulanta dikka biyu, sannan ya cire hannunsa tare da ɗan canza idanunsa kaɗan kamar yana yi mata magic. Slowly idanunta suka ɗan fara rawa alamar tana san buɗesu, har lokacin bai kyafta idanunsa ba.......... Har ya ɗan ban tsoro na rashin kyafta idanun!! A hankali ta waro idanun nata, kai tsaye sai saman face ɗinsa. Motsa kyawawan lips ɗinta ta yi wajen furta. "Big bro kai karshe ne wajen kyau". Ta faɗa tare da sakin wannan ƙayataccen murmushi nata wanda ko daga nesa ta yi yana ratsa zuciyarsa bare a kurkusa da shi. Wlh sai da zuciyarsa ta amsa lokacin da ta saki wannan murmushi. Sai dai daga yadda yake bai motsa ba bare a sa ran zai yi magana, kamar an datse lips ɗinsa ma. Hannunta ta ɗaura a saman shoulder ɗinsa, ta dafa shi ta miƙe daga saman kirjin nasa, dama yanayin kwanciyar da ta yi ya ɗallabota ne. Kallansa ta yi ido cikin ido, ƴan kafafunta ta ɗago tare da matsar da face ɗinta dab da shi. Hannu ta ɗaura a saman lallausan kumatunsa kafin ta ce. "Handsome!". Ta faɗa tare da sanya yatsarta a daidai in da mazaunin dimples suke. "Nice dimples, sai dai babu smile bare kyan dimples ɗin su karu". Ta faɗa tare da gangaro da yatsar tata izuwa kusa da lip ɗinsa. "Sexy roman lips!". Ta kai karshen maganar tare da kara ɗaga kafafunta sosai, unexpected ya ji saukar sumbata a kumatun nasa. Ai a lokacin bai san time da ya lumshe idanunsa ba, ba da yaki ko kyaftawa ba? To yanzu lumshe su ma ya yi. Lausasan lips ɗinta sun yi matuƙar tasiri a ransa. Tana sumbatarsa ta juya ta nufi waje tana wani irin taku wanda dik in ta taka sai gabaɗaya ilahirin jikinta ya motsa a hankali, ga yanayin uniform ɗin nata, sam bata san ya sanya mata chain and make up ba. Binta da wani irin kallo wanda dik bala'inka ba zaka iya fassara wani irin kallo bane ya yi. Har ta kurewa ganinsa ya kasa zare kallonsa daga kanta, kuma bai ce uppan ba, ko motsawa daga in da yake ma bai yi ba!. Sai da ta wuce ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, lumshe idanun ya yi tare da sake warosu, juyawa ya yi ya cigaba da abin da yake yi zuciyarsa cike da tinani wanda ni dai ban gane wani irin tinani bane...............🥱 Zuciyar Big bro kamar dutse take, dik bakinka baka isa ka tsaga cikinta kaga me yake tinawa ko me yake ciki ba, dole ka hakura sai ya fito da ita fili ka gani!! Da alama Big bro yau ya ga wani sabon al'amari daga Sweetie, to ni dai ba ruwana ato!!. Ita kuwa tana fita ta tsaya a bakin kofar bedroom ɗin nasa, Astagfirullah ta shiga nanatawa sama da kafa 100 kafin ta nufi ƙasa zuciyarta cike da tinanin abin da take yi!!. Parlour ta sauko, tana sauka suka ci karo da Ronnie da ya nufo sama zai sake komawa bedroom na yayan nasa ya sake dubata. Yana ganinta ya nufeta da sauri yana sauke ajiyar zuciya!. "Lovely sis ina kika shiga?". A ruɗe ya faɗi maganar. Kin kallonsa ta yi, ta ɗaure fuska kafin ta ce. "Ba ko'ina mu je ka yi dropping ɗina a school". Tana kai karshen maganar ta nufi in da jacket ɗinta and school bag ɗinta yake. Da sauri ya bi bayanta, dik wahalar da ya sha wajen nemanta sai ta zo ta wani wucesa tana wani ciccin magani?. Jacket ɗinta mai kama da boyfriend Jacket ta ɗauko tare da sanyawa. Tana ƙoƙarin zuge zip ɗinsa sama sai taga wani haɗaɗɗen chain a wuyanta, a hanzarce ta kai kallanta da kyau kansa. Dai'dai lokacin Ronnie ya kariso wajen yana faɗin. "I forgive you lovely sis, and why kike ɓata rai? Ko dai kun haɗu da Big bro ne ya ɓata maki rai...........". Bai ƙarisa maganar ba sakamakon sauka da idnaunsa ya yi a kan chain dake wuyarta. Ɗan zaro idanu ya yi yana faɗin. "Wow, kinga kyansa kuwa? Kinga yadda ya yi maki kyau kuwa?. Nasan Big bro ne ya baki! Amma waye ya yi maki wannan haɗaɗɗen make up ɗin da har kika fito tamkar Queen of the world?". Cike da tsantsar kaunarta ya yi maganar!. Ɗauko school back ɗinta ta yi tare da wurga mashi ta wuce gaba tana harararsa. Capke jakar ya yi, a hanzarce ya rufa mata baya. Yana isota ya riƙo hannunta. "Yau sai ɓata rai kike yi? Na yi maki wani laifi ne?". Kin kula shi ta yi, wasa wasa har suka shiga mota, sai magana yake yi mata taki amsawa har suka isa school, motocinsu na parking a parking lot na school ɗin bata jira sun buɗe mata kofar motar ba ta ɓalle ta fito abinta. Da ido Ronnie ya bita yana mamaki, jikinsa dik ya yi sanyi, a cikin ransa ya ce ko dai Black Tiger ne ya hanata yin magana? Haƙiƙa ya shiga damuwa sosai da bata kulasa ba. Ya yi nisa a cikin tinanin nasa, sam bai san time da ta ɗauki jakarta ba, sai ji ya yi ta manna mashi hot sumbata a kumatu tana faɗin. "So much love my lovely bro". Ta faɗa tana murmushi haɗe da juyawa ta nufi hanyar tafiya. Ai bai san time da ya saki ƙayataccen murmushi game da sauke ajiyar zuciya ba, da ya ɗauka fushi take yi da shi. "You're the only my brother that making me happy anytime, I really love you my pleasure". Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba, tana cigaba da tafiyarta. Tin da ta fito idanun gabaɗaya student a kanta, su kansu sun shaida da ta yi fitina yau ɗin nan, kalar kyanta ma na daban ne. Dik kyan mutanen birnin sun jinjinawa nata. Kasa hakura ya yi da jin kalamanta, da gudu ya fito ya bi bayanta. Sai da ya kamota ya manna mata sumbata a kumatu, sannan ya juya ya koma mota yana yi mata fatan alkhairi tare da fatan ta kula da kanta kuma ta yi karatu sosai. Da okey ta amsa tana yi mashi bye bye, ji ya yi kamar kada ya tafi ya barta, amma haka ya daure suka juyo suka dawo gida. Dik sai ya ji gidan babu daɗi da bata nan, dan haka wunin cikin ɗaki ya yi, ya takure kansa har zuwa lokacin tashinsu school, tin da sauran lokaci ya tsara wanka tare da shiri cikin sport wear ɗinsa ya nufi school ɗin nasu. A lokacin da suka iso school ɗin tana zaune ita da wasu ƴan'mata kyawawa guda biyu da ita uku, zaune suke a garden na school ɗin nasu suna hira, basu komai a class ne suka fito waje. Yana zuwa kuma aka buga tashi. Fitowa wajen motar ya yi tare da jingina bayansa a jikin motar yana jiranta. Tana jin an buga tashi ta yi saurin yiwa ƴan'matan sallama tare da wucewa, dan tasan already ya zo, baya lattin zuwa ɗaukarta. A tare ƴan'matan suka ce zasu rakata, kowa son ta yake yi, suna san yin ƙawance da kyakkyawa, ita kuma very friendly take, bata da matsala. Amince masu ta yi suka rakota wajen motar, yana tsaye tin daga nesa yana kallonsu, sun nufo shi, tamkar wata a cikin taurari haka ta kasance a cikin waɗan nan ƴanmata, dik ta haskesu, ta dishashe haskensu da nata. Tin bata ƙarisa isowa ba ya buɗe mata hannu, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana murmushi. Kallan juna ƴan'matan suka yi, lokaci guda suka sha jinin jikinsu tare da komawa gefe suka tsaya shiru, sun gane Ronnie sarai, dik wanda yake cikin birnin dole ya sansa. Basu taɓa zatan Sweetie daga Black Tiger Empire ta fito ba, lallai yanzu ta kara samun girma da daraja a idanunsu fiye da a baya, dole su yi respecting ɗinta sosai, tab ai ta wuce class na ƙawance da su, dama tin da yake kawota baya fitowa shiyasa basu san mai kawota da kuma mai ɗaukarta ba sai yau. "Bro this is my friends Loosi and Rose". Ta faɗa tare da raba jikinta da nasa, sannan ta ce. "Rose this is my brother". Ta yi maganar tare da nuna shi da hannu!. Cikin girmamawa suka zube gwiwowinsu a ƙasa game da yin ƙasa da kai suka fara zuba irin gaisuwar da suke yi wa manyansu a birnin, wato dik wanda ya fito daga cikin Empeir ɗin haka suke gaida shi. Ɗan ɗaure fuska ya yi kafin ya yi masu alama da hannu a kan su miƙe ba tare da ya yi magana ba. Ba musu suka miƙe tsaye, da hannu ya yi masu alama da su tafi. Cikin hanzarin suka bar wajen suna sake waigosa, Allah ya gani Ronnie burin dik wata yarinya dake cikin wannan birnin ne, har manya kwaɗayinsa suke ji. Riƙo hannunta ya yi, ya shige cikin mota yana janta ta shigo. Tana ƙoƙarin shiga daga bayanta sai ta ji an ce. "Omaish O Mutallab ka book ɗinki". Da sauri ta juyo, shi ma Ronnie ɗan leƙowa ya yi dan ya ga wanenen?. Wani matashi ne da a kallah zai iya kai 19 to 20 haka, uniform na seniors ne a jikinsa, a Ss3 yake, ta mance da book ɗinta ne a set ɗinsu wajen small library ɗin nasu, shi ne ya biyota da shi, dama burinsa ya samu wani abin da zai haɗa shi magana da kyakkyawar nan, shiyasa yake yawan bibiyarta, dik in da take sai ya je wajen, sai Allah ya yi yau ya samu damar yin magana da ita, ta hanyar ta kammala karatu ta bar book ɗin a wajen saboda sauri!. Ƙarisowa ya yi in da take, miƙa mashi hannu ta yi ya miƙe mata book ɗin. "Thank you". Ta faɗa tare da juyawa. "Am baki ji ba Omaish". Ya faɗa cikin sanyin murya. Juyowa ta yi tare da ɗaga mashi gera irin alamar lafiya?. "Seriously you're so cute and pretty". Ya faɗa yana ɗan shafa kansa. Ɗan sake face ɗinta ta yi kafin ta ce. "Thanks". Ta faɗa zata sake juyawa sai ya katseta da cewa. "My name is Michael, can we be a friend?". Ya yi maganar tare da miƙo mata hannu wai su yi musabaha, daga haka sai sun zama abokai, dik abin da yake yi bai lura da Ronnie dake kusa da su a cikin mota yana kallonsu ba. Yana miƙo mata hannu Ronnie ya zuro nasa hannun ya capki nasa tare da fitowa waje daga cikin motar. Ai yana ganin Ronnie a zabure ya zube gwiwowinsa a ƙasa a gabanta tare da buga hannunsa a kirji, sannan ya risinar da kai kasa alamar girmamawa. Ɗaure fuska sosai Ronnie ya yi, yanzu yasan darajar mata, saboda musulunci ta ratsa shi matuƙa. "Michael I don't want to see you close to my sister again!!". Ya faɗa with harsh voice, cikin bada umarni, babu wasa a tattare da shi, da alama ya san kishi a yanzu!!. Da ido ya yi mata alama da ta shiga mota, da sauri ta faɗa ciki tana ɓoye murmushin dake san kwace mata bayan taga yadda ya ɗaure fuska. Bata san me da me ya faɗawa Michael ba tana daga ciki ya shigo ya sameta bayan ya gama kenan, ta so jin yadda zasu kare, sai dai ina, tana ciki! Haka ya shigo ya sameta suka nufi gida, a hanya ya daka mata zazzafar warning a kan kula maza, ya ce babu ruwanta da su, ko matan ma bai ce ta saki jiki da kowa ba, bai dai hanata ƙawance da mutane ba, amma nesa nesa, dan matsayinsu ba ɗaya ba!!. Okey ta amsa mashi da shi, yarinya mai jin magana, (Ba irin Pretty abokiyar faɗan Smart ba, wai ke ka ce ba Pretty ba, kai Pretty duniya!!) Sai ta ce mashi harta matan ma bata buƙatar kowa a kusa da ita, shi kaɗai ya isheta. Ya matuƙar jin daɗin kalamanta a in da ya manna mata sumbata a goshi. Haka suka isa gida. A tare suka fito daga cikin motar suka nufi cikin gida, kai tsaye bedroom ɗinsa suka nufa tana faɗa mashi ya zo ya yi mata home work, da okey ya amsa mata suka wuce ciki. Abinci yasa aka kawo masu kamar kullum, a tare suka yin lunch bayan ya jirata ta yi wanka, ta tsantsara kyau cikin wandon jeans baki mai kwalliyar pink a jikinsa, and pink long sleeve shirt, ta yi matuƙar kyau, ta sanya headband baki a kanta, wannan sarka da Big bro ya bata yana nan a wuyanta sai kyalli yake yi, a school ɗinsu babu wanda bai yi magana a kan sarkar nan ba, uncles ɗinsu ma sai da suka yi magana, saboda haɗuwarsa, dik wanda yasan abu mai tsada dole ya jinjinawa wannan sarka, dan dubabbannin miliyoyi ake magana a wajen. Wato Big bro wuyarta tana burgesa, shi ne ya kara kawata mata shi yadda zai ji daɗin kallo, wlh Black Tiger ɗan duniya ne!!. Kafin ta gama wanka ya shirya masu komai, tana fitowa ta yi sallah suka yi lunch, sai suka yi karatu na awa biyu a in da ya koya mata Home work ɗin nata da aka bata, ta ji matuƙar daɗi sosai da sosai, sai murna take yi. Hira suka zauna yi har la'asar ta kawo kai, sannan ne suka miƙe, a lokacin Black Tiger baya nan, yana fada, hakan yasa suka wuce bedroom ɗinsa suka yi sallarsu a can, sannan suka zauna ta ɗan koyawa Ronnie karatun addini dai'dai gwargwado, bayan sun kammala around 4:30, sai ya ce su je trainin, su ɗan motsa jiki kaɗan kafin su shirya zuwa church kamar yadda ya yi mata alkawari. Cike da murna ta ce. "Muje amma zuwa church ka bari sai zuwa gobe". Cike da mamaki ya ce. "Why?". Kashe mashi ido ɗaya ta yi kafin ta ce. "Akwai dalili, akwai abin da nike san kammalawa ne". "Sisterrrrrrrr". Ya faɗa yana ɗan jan sunan alamar kamar warning yake yi mata. "Don't worry ba zan yi abin da zai kawo mana problem ba". "Are you sure?". Sure ta bashi amsa tana wucewa gaba!. "To please kada ki yi magana sosai, and komai zaki gani ki yi shiru kin ji?". Jinjina kai ta yi alamar ta yarda. Ɗan gudu ya yi ya kamota tare da rike hannunta suka wuce suka nufi gym ɗinsu. Yana zuwa ya hau motsa jiki, a hankali ya fara cigaba da koya mata, push up ya fara yi, a nan Black Tiger ya zo ya samesu suna yi, bai bi ta kansu ba ya fara nasa gym ɗin, tin da ya shigo wajen ta tsaresa da kallo, ya yi masifar kyau cikin wasu shegu kuma tsadaddun gym wears, shi kuma sam bai kalli in da take ba ya fara aikinsa. After some minutes Ronnie ya ce mata ta zo su fara faɗar takobi da ya fara koya mata last week, cike da murna ta fara tsalle tare da tasowa ta nufesa. Wani keɓanɓɓen waje suka shiga can ɗan gefe da gym ɗin, wajen tamkar duniyar mafarki yake, ga ruwa yana zuba ta sama kaɗan kaɗan kamar shower haka. Dai'dai tsakiyar da ruwan yake zuwa ta zo ta tsaya yana jiƙata, shi kuma zaro takobi marasa tsawo da nauyi sosai guda biyu ya yi, ya miƙa mata guda ɗaya ya riki ɗaya a hannunsa, sannan ya ciro hulunar faɗa masu kariya ga kan mutum, ya bata ɗaya ya ɗauki ɗaya, gabaɗaya wajen shake yake da kayan yaki kala kala. Faɗar wuƙa suka fara yi ruwan nan na zubowa a kansu yana cigaba da jiƙasu, yanzu ta ɗan fara iyawa ya fara yi mata manya manya, da a hankali hankali yake yi mata. Ita ma ta zage tana san ta ko yi abubuwan, dan suna burgeta, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa take san Ronnie, saboda iya faɗarsa ga shi ɗan wrestling, bugu da kari yana da horon mayaƙa, abin ƙayatarwa kuma ɗan wasa ne, kwallon kafa, basket ball, kai dik wasanni yana bugawa har snooker bai bari ba, ga su skater dikka, shiyasa ta ce ya koya mata ita ma ta zama kamarsa. Cigaba da wasan takobinsu suka yi gwanin birgewa, tana ɗan tsoro tsoro sai da ya ce mata kada ta damu, ta kawo mashi kowani irin hari ne ba zai ji ciwo ba, zai iya tarewa, ita kuma ta ce kada ya zo bai tare ba ya ji ciwo, kai ya girgiza mata alamar kada ta damu, shi fa da yayansa yake wannan training ɗin, dan haka zai iya tarewa, kuma idan har bata kawo hari kowacce iriya ce ai ba zata taɓa iya yaki ba, dan haka dole ta kawo hari. Jin abin da ya ce yasa ta ɗaga takobin hannunta da karfi ta nufesa zata sara mashi a wuya. Ɗan juyawa gefe ya yi a in da ta wuce ita da takobin nata gabaɗaya ta tafi zata kifa, hannunsa ɗaya da bai rike takobi ba yasa ya tallabo flat tummynta, dama tafiya ta yi zata kifa, sai ya tarota ta gaba gaba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗagowa cikin zafa, wai irin ita ma yanzu zata fara yi mashi da zafa tin da ta ga yana tarewa, ashe da gaske zai iya tarewa ba zai ji komai ba!!. KAI SWEETIE WANI LOKACI AKWAI SHIRIRITA, TO MEMA TA IYA DA HAR TAKE GANIN IDAN TA KAWO MASHI HARI BA ZAI IYA KAREWA BA?! WAI ITA A TINANINTA TA ƊAN IYA WANI ABIN.......😅 Yunkurin sake kai mashi sara ta yi, ina ai sai ya fara wasa da ita tamkar wata ƴar tsana, ya cigaba da bata wahala har sai da ta gaji ta ce. "Lovely bro am tied, ka barni haka, ko sau ɗaya ban yi nasara ba fa". Jefar da takobin ya yi tare da jawota jikinsa yana faɗin. "Ai in dai a kai'na ne ba zaki taɓa yin nasara ba, muje ki yi wanka". Turo baki ta yi. "Soon zan yi nasara". Jinjina kai ya yi. "Zan yi fatan hakan, zan so gani lovely sis ɗita ta yi nasara". Raba jikinta da nasa ta yi tana jefar da takobin kasa kafin su nufi cikin gida. Wanka ta fara yi kafin ta bashi waje ya shiga, shi ma wanka ya yi. Shiryawa ta yi cikin wani haɗaɗɗen gown fari irin mai breast cuf ɗin nan, so kana iya ganin tudun matasan tula tulanta da suke gwanin birgewa, ta yi masifar kyau matuƙa, ga kayan ya fitar mata da coca cola shape ɗin jikinta sosai, dan irin malesian gown ɗin nan ne, ya bi surar jikinta and rigar bai kai mata har ƙasa ba, da kaɗan ya rufe mata cinyoyinta, ta sanya wani high heel, yadda kuka san wacce zata tafi club party, ta zuba chewing gum masu balai'n kamshi a bakinta tana wani tauna, da alama yau da rashin mutumci take ji. Fitowa ta yi ta nufi sama kololuwa tana gyara headband ɗin kanta, wai hoto zata je ɗauka a saman, ɗazun taga wayar Ronnie a wajen. Tana haurowa shi kuma yana saukowa sanye da pj's dress a jikinsa, ya yi fitina a cikin kayan. Wuceta ya yi tamkar bai ganta ba, ita ma wucewa ta yi kamar bata gansa ba. Har ta ɗan yi nisa sai kuma ta ɗan ɗaga hannunta sama kamar mai neman wani abin a sama, a hankali ta juyo tare da cewa oh irin ta gane magana take san yin mashi ɗin nan. Gently ta ce. "Hi big bro! One minute please!". Ta faɗa tana sauke hannunta izuwa saman waist ɗinta. Dakatawa ya yi da tafiyar ba tare da ya juyo ba, alamar dai ya bada one minute da aka tambayar. Cike da yanga ta tako ta nufosa, dik Ronnie ya koya mata wannan iskanci, shi ya yi mata wayo ya ce ta rinƙa yiwa Black Tiger haka zasu yi nasara, bata san wayo ya yi mata dan yasa su rufta da san juna ba, shi a nasa tinanin idan ba soyayya ba akwai matuƙar wahala Black Tiger ya iya canzawa, sannan ba zai taɓa musulunta ba idan ba ya kamu da soyayyar musulma ba, Sweetie ta faɗa mashi babu aure a tsakanin namiji krista da mace musulma, to shi ne yake san Black Tiger ya rufta kogin sonta, idan ya yi zurfi sai ace ba zai mallaketa ba sai ya musulunta, wannan ne shirin Ronnie, amma bai sanar da kowa ba, ko ita Sweetie ya ɓoye mata, shi dai burinsa yayansa ya dawo hanyar tsira, shi ai ya ɗanɗani daɗin musulunci har sha'awa yake yi wa wani, Allahu Akbar, musulunci duniya!! Musulunci ya yi, wanda baya musulunci wlh an barsa a wahalarce, ya kuma bonu ya lallace!! Yanzu dai Ronnie ma ya shirya na shi plant ɗin, zai baza capacitynsa ba tare da saninsu ba. Sai dai shi kuma Ronnie ɗin abin da bai sani ba shi ne, DUNIYAR SHAIƊANU ba zasu taɓa barin Black Tiger ya yi aure ko ya yi soyayya ba sai dai wani ikon Allah, amma wlh babu batun so ko aure a tsarin da suka tsara mashi da sihirinsu tin yana yaro, sai dai mu musulmai mun san suna nasu ne Allah kuma shi ne the best planner, ya gama tsarawa Black Tiger dik wani abin da zai yi a rayuwarsa. A tsarin DUNIYAR SHAIƊANU manyan malamansu ma masu takewa mahaifin Black Tiger baya basu da ikon yin soyayya ko aure, dan sun ce mata rauni ne, su ba zasu taɓa yarda da abin da zai raunata zuƙatansu ba, mahaifin Black Tiger shi ne kaɗai aka amincewa da ya rinƙa tarewa da mace, shi ma ɗin kuma idan ya tare da mace har ta samu ciki ta haihu, to tana haihuwa za'a kashe uwar su ɗauki ɗan, dan a cewarsu uwa mace barinta haɗari ne, dan mata suna da zuciya mai rauni da tausayi sosai, so zata iya koyawa yaron rauni da tausayi. Ga dikkan alamu ita ma mahaifiyar Black Tiger kasheta suka yi. (Ni kam ma anya ba gawarta bane suka yi mutun mutuminta a cikin fadarsu na in da na ce maku sun cakawa mace wani dogon karfe tin dafa bakinta har ya fito ta gabanta? Kun tina wajen? Da alama tin da aka yi gunkinta ita ce matar shugaban nasu wato uban Black Tiger kenan) Bala'i can, akwai cakwakiyar na gasken gaske. Amma my people's ya kuke gani idan Allah yasa Black Tiger ya musulunta, kuma yasan daɗin uwa ya fara neman uwarsa? Me zai faru?. Uhm gaskiya musuluntar Black Tiger yana da matuƙar wahala, saboda ko da ya so su ba zasu kyalesa ba, dan ma dai yana cikin killacewar da babansa ya yi mashi ne, amma dik ranar da ya fito shikenan ya koma cikinsu, yanzu haka sai shirin yadda zasu samu su ɗaukesa suke yi, akwai kalubale mai girman gaske a gaban Ronnie da Sweetie, amma da yake Sweetie ba haka ta zauna ba, tana kai kukanta ga Allah tana faɗa mashi sunan Black Tiger a kowacce Sallah nata idan ta yi, da izinin Allah kuma Allah ba zai basu kunya ba!!. Kai my people's kun ji Ronnie ko? Zai jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, wai ya yi wa Black Tiger and Sweetie wayo su kamu da san juna! shi ma fa ɗan duniya ne wasa wasa!!. Yana tsaye ta iso in da yake, zagowa ta yi ta gabansa ta tsaya!. "Shi ne zaka ganni kamar baka ganni ba ka wuce ko?". Ta jefa mashi tambayar kamar zata saka mashi kuka. Shiru bai tankata ba, sai ma da ya ɗan kara ɗaure angry face ɗinsa. "Kasan me? Kome ka yi kyau yake maka, da ka ɗaure fuskarma ka kara kyau ne".......... KALAMAN RONNIE TAKE YI MASHI, DIK SHI YA KOYA MATA!! Idanunsa a kan kirjinta bai ce ko uppan ba, kunga yanayin rigar tata, so yana iya kallan tudun tula tulanta. Yatsun hannunta ta kyasta mashi a saman face ɗinsa, nisawa ya ɗan yi tare da cewa. "Ke wai bakya jin tsoro ne a rayuwarki?". Zazzakar muryarsa ya daki dodan kunnuwanta. Ɗan siririn murmushi ta saki wanda har sai da fararen hakwaranta suka bayyana. "Menene kuma tsoro?". Ta yi maganar tare da gyara rigar jikinta da kyau. Sai ka ce dole aka sakata ta sanya rigar, ta biyewa Ronnie zai yi mata wayo bata sani ba, wato fa dik iliminka idan mutum ya rigaka zuwa duniya to fa wani abin sai ka sarara mashi! Yanzu dai ya nuna mata fifikon shekaru!. Kasa yin magana ya yi ya tsareta da idanu yana kallon tula tulanta da suke tsole mashi idanu a maimakon face ɗinta. Ƴan yatsun hannunta guda biyu ta sake kyasta mashi a saitin face ɗinsa tare da hura chewing gum da take tauna ta yi balo balo kenan. Kamar wani maras gaskiya da sauri ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta yana wani ɗaure fuska irin ya basar ta kamashi yana kallonsu ɗin nan. "Big bro, face ɗina fa zaka kalla mu yi magana ba wani waje ba, da ni kake magana ba da kirjina ba, wai nace ba, mema kake kallo a kirjin nawa? Ko dai............". Dakatawa ta yi da yin maganar ta kasa ƙarisawa sakamakon zaro mata kaifafan sexy eyes ɗin nan nasa da ya yi. Wato wannan ƙaddarar tasa ta zama tacacciyar ƴar ikka, kuma yasan dik waye ya ja mashi hakan, dole ya ɗauki mataki, yarinya ce ta wuci dik yadda yake tunani, yanzu ya shiga uku tun da ta kama shi yana kalle mata tula tula, wannan zance ba zai tsaya iya nan ba, to wai ma me ya kaisa? Shi anya ba zai ɓatar da yarinyar nan ba kowa ya huta?. Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da, ai ba zaka iya ɓatar da ita ba, ka manta ita ɗin kaddarar ka ce, zama da ita dole, wannan shi ne ba saki ba karin aure, mutu ka raba takalmin kaza in ji hausawa..............😂 Kai Hasbunallahu wani'imal wakil, wato ana wani iyashege a wannan gida.😂 Zata sake yin magana tana ƙoƙarin huro chewing gum ɗinta ya ɗan sanya mata zarra ta hanyar matsar da face ɗinsa dab da ita yana zare mata ido. Ai a miliyan ta yi baya, ta tsorata sosai. Ɗan gocewa high heel na kafarta ya yi saboda baya da ta ɗan yi ba shiri, hakan yasa chewing gum da ta huro ya ɓata mata fuska, tafita ta yi ta zube ƙasa a saman gwiwowinta!. Wuceta ya yi da sauri ya sauka ƙasa, dan tana neman kawo mashi wani sabon al'amari. Turo baki ta yi, a fili ta ce. "Allah ba zan barka ba, tin da ka sanya na faɗi kasa kuma na ɓata face ɗina da chewing gum sai na ɗauki fansa, ai a yarjejeniyarmu mun yi da kai ba zaka taɓa mun abin da bana so ba kuma ba zaka taɓa bari na cutu ba, amma da kanka ka cutar dani yanzu". ME KUKE TINANIN ZATA YI MASHI?. Tana ƙoƙarin miƙewa Ronnie ya hauro sama da gudu yana faɗin. "Sister come and see our surprise, Big Bro ya yi mana surprised mai matuƙar kayatarwa, za'ayi shagali a ranar white Happy and Sad day ɗinmu, zamu fi kowa kyau". MEMENE WHITE HAPPY AND SAD DAY? kalar fari shi ne fav kalar Black Tiger, wannan dalilin yasa ya sanyawa wannan rana sunan white Happy and Sad day, sau ɗaya suke shagalin wannan rana a shekara, rana ce da babansa ya mutu, kuma rana ce da a cikinta babansa ya karɓawa birnin Black world takardar zama ƙasa mai cin gashin kanta, wato rana ce da suka samu ƴancin kai! So ranar suna shagali da rana, da daddare kuma su yi kuka da jimamin mutuwar babansa, the whole ranar white clothes suke sanyawa, komai fari tas............ Wato babu kamar addinin musulunci fa my people's, wai ayi shagali da rana, da daddare kuma ayi kuka na jimami, kai jama'a Allah ka dawwamar da mu a cikin musulunci!!. Miƙewa ta yi tana faɗin. "Menene white Happy and Sad day kuma?". Hannunta ya zo ya riko yana faɗin. "Muje ki ga kayan da Big Bro yasa aka kawo mana daga kasar England, idan kika gani zan faɗa maki menene white Happy and Sad day da irin shagali da kuka da muke yi"...... "Shagali da kuka kuma?". Ta tambaya cike da mamaki......... Wai shagali da kuka, dole kanta ya kulle...................... "Let's go zan yi maki bayani idan muka je bedroom". Ya kai karshen tare da jan hannunta, bayansa kawai ta bi mamaki kamar ya kasheta!!. My people's wannan rana ta W.H.S.D ɗin nan nasu fa ba ƙaramin gagarumin rana bane wanda kura zai tashi a cikinsa, uhm zamu sha shagali kuma mu sha kuka, kowacce shekara da Floris ake yi, amma wannan babu ita.............. 😥 -----------------------------------------------🔥 🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER.🔥🔥🔥 A yau jirgin momma ya ɗaga zuwa Dubai, tamkar Smart ya zuba ruwa a ƙasa ya sha haka yake ji, ya ji daɗin tafiyanta matuƙa, ta so tafiya da Auta dan ta kaita can ko zata huta ta ji sauki, amma King ya hana, saboda ya ƙasa samun natsuwa, yana cikin fargaba da tashin hankali, dan yana ganin kamar zai rasata ne kawai, saboda dik yadda kuke tinani abin ya wuci nan, Zunaira ta lallace ta rame, tamkar mai ciwon H.I.V, abin gwanin ban tausayi, uncle Jahiz sam baya san zuwa wajenta, saboda tana saka shi kwallah!. Zaune take tare da Chuchu a saman bed a cikin part da aka kaita, sai ƙoƙarin janta da hira Chuchu take yi domin su samu ta ɗan saki jiki da su, sai dai ina, dik hiran da Chuchu take yi mata taki tofa ko uppan, kanta a ƙasa tana kallan yatsun hannunta da suke ɓulɓul a da, yanzu sun rame sosai, kamar ba nata ba!. Dafata Chuchu ta yi tana faɗin. "Auta dan Allah ki ce wani abin mana! Tsawon awa biyu muna tare, ni kaɗai nike ta yin magana kinki ki amsani, kina son nima in kara ciwo a kan wanda nike ciki ne?". Cikin raunatacciyar murya Chuchu ta yi maganar, tamkar zata yi kuka, idanunta sun cicciko da kwallah, ta rame sosai ita ma, tamkar ita take jinya!. Kanta a kasa ta ɗan girgiza alamar bata san Chuchu ta yi ciwo, amma bata iya yin magana ba. Kara matsawa kusa da ita Chuchu ta yi, ta buɗe baki zata yi magana kenan sallamar Abdussalam ya katseta. Sanye yake da arabs jallabiya dark ash, shi ma ya rame sosai, saboda ciwon nata. Ganinsa yasa Chuchu ta miƙe tana faɗin. "Zan dawo zuwa anjuma". Ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin. A in da Chuchu ta tashi ya ƙarisa ya zauna, a hanzarce Auta ta ɗan ja baya tamkar wadda aka matsowa da wuta kusa da ita. Ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, cikin sanyin murya ya ce. "Zunaira ki faɗa mun dalilinki na guduna? Na tabbata yansu kam na ciwo bane! Dole akwai wani dalili, dan kin samu sauki"......... Kin yi mashi magana ta yi, sai dai har cikin ranta ta ji wani irin yadda ya kira sunanta, bai taɓa kiranta da Zunaira ba, kullum my wife yake cewa, da alama yau hakurinsa ya kare ne!. "Ki yi magana kin ji? Ki kalleni a matsayin yayanki ba miji ba, ki faɗa mun damuwarki, ni kuma zan tsaya a wajen ganin na fitar dake daga damuwar"........... "So nike kawai ka sake ni, shi ne damuwata". Abin da ta faɗa kenan ba tare da ta ɗago da kanta ba, da kyar muryarta yake iya fita saboda kukan da ta sha. Wani irin zaro idanu Abdussalam ya yi, a hankali ya maimaita kalmar saki kafin ya ce. "Ai ko wata bare na aura ba zan saketa ba Zunaira bare ke da kike matsayin kanwata, ke da nike tsananin kauna tin kina yarinya, Allah ya mallaka mun ke ya cika mun burina kuma yanzu ki ce in sakeki? Tukun nan ma saboda me?". Shiru ta yi mashi dan tasan ko zata mutu ba zai taɓa sakinta ba, aurensu ai babu saki, su a ƙaidar familynsu ma ba'a saki, babu wacce aka aura aka saka, ko bare suka aura nasa saki bare na gida, ai kun san wannan aure ba mai mutuwa bane!. Ganin ta yi shiru ne yasa ya kai hannunsa ya riƙo nata. Zabura ta yi zata kwace kanta ya yi gaggawar riketa da karfi, dan dole ta natsu bata iya kwacewa ba. Cikin taushi da tausasawa ya ce. "Zunaira please, ki tausaya mun, ki ji kan zuciyata, wlh ina sanki, kuma kome kike so zan yi maki, dan Allah ki faɗa mun menene yake damunki, Zunaira kalli yadda na rame fa saboda ke, please my wife, Yah Abdussalam ɗinki ne fa? Ko kin manta ne? Kin dai'na so na ne? Please kada ki bari zuciyar da bata san komai ba face sonki ta cutu, bata san komai ba sai begenki, please my wife help me and accept me as your husband, na yi maki alkawari zan sanyaki farinciki koda ni zan kuntata". Tamkar zai yi kuka ya kai karshen maganar. Shiru ta yi idanunta suna zub da zafafan hawaye, take kalaman Hoorain suna ratso mata cikin brain ɗinta a in da yake ce mata. "Hoonairata kada ki yarda ki yi magana da wani namijin a bayan idona, ki rike mun amanar kanki, ke tawace ni kaɗai". Tina hakan yasa ta kai kallanta a kan hannunta da Abdussalam ya rike, take zuciyarta ya buga da karfi, ba iya magana da wani ba har hannunta ta bari ya rike. Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi tare da kwace hannunta da karfi, da gudu ta miƙe ta fito parlour, ƙasa iya cigaba da tafiya ta yi, da ta so ne ta fita waje, amma sai ta ƙasa saboda jiri, bata gama samun lafiya ba, a tsakiyar parlourn ta zube gwiwowinta a kasa, rushewa ta yi da kuka mai sauti, cikin kukan ta fara sambatu kamar haka. "Am so so sorry my Hoorain, yau na karya alkawarin da na ɗauka maka, na bari wani namiji ya taɓani, ba zan yafewa kai'na ba har sai ka yafe mun, ni taka ce kai kaɗai, kai kaɗai kamar yadda kake nawa ni kaɗai". Cikin fitar hayyaci take wannan magana, sam bata lura da Chuchu dake zaune a saman sofa a cikin parlourn ba. Allah sarki Chuchu, ta kasa komawa family part ta bar autar ne, shi ne yasa ta zauna a parlourn tana jiran idan Abdussalam ya fita sai ta koma su cigaba da yin hiran. A dai'dai wannan lokacin kuma King yana can suna kai ruwa rana da smart, ga tashin hankalin da yake ciki na ciwon Auta, ga zafafan questions da Smart ya jefesa da su. Yana tsaye a tsakiyar bedroom na daddyn nasa, yana sanye da sleeping dress, dan shirin kwanciya barci ya yi, while shi kuma King yaka zaune a saman bed ɗinsa, babu ko sallama Smart ya shigo mashi cikin ɗaki, kallo ɗaya King ɗin ya yi mashi ya kawar da kansa, a cewarsa yana fushi da Smart, a tinaninsa hakuri Smart ya zo bashi, sai dai bai san wata fitinar ce ma ta kunno kai ba. Wai irin ya nuna ransa ya ɓaci sosai ɗin nan kuma yana fushi da shi shi ne har da wani cewa Smart ɗin. "Meya kawoka room ɗina?". Ya yi maganar yana wani ɗaure fuska. Shiru Smart ya yi yana cigaba da binsa da kallo. "Idan ba zaka yi magana ba ka fice mun daga ɗaki". Ya faɗa yana nuna mashi hanyar fita. Man ma shiru Smart ya yi, maganganun momma na ta yi mashi yawo a kunne in da take cewa tana san su yi magana amma tafiya Dubai ya zo da sauri, dan haka idan ta dawo zasu tattauna a kan matar commander, kada ya kula kowa a gidan, ya kasance a ɗaki kamar yadda yake. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Meyasa ka cika san kanka da zalinci ne dad?". A sanyayye ya yi maganar!. A hanzarce King ya zaro idanu yana kallansa. "Omerish ni kake cewa ina da san kai'na da kuma zalunci? Ni kam anya baka shan wani abin kuwa?"....... Idanunsa kar kan dad ɗin nasa ya ce. "Dama shi mara gaskiya a kullum cikin hargagi yake, dad baka da gaskiya, kana da zalinci da son kai, baka san zaluncinka ya tonunwa duniya shiyasa kake ƙoƙarin hahhaura abubuwa a kan wasu". A zabure King ya zuro kafafunsa kasan bed ɗinsa, yana zaro ido kamar an tare ɓera a tarko ya ce. "Zaluncin me na yi Omerish? Dan na aurawa Zunaira wanda ya dace da rayuwarta shi ne na yi zalunci?". Ya kai karshen maganar yana miƙewa tsaye, yana wani furkaki!. "Dad ni fa ba ɗaya nike da sauran ƴaƴanka ba, kai kanka kasan da hakan, kasan cewa yaran momma gifted ne, shiyasa kake jansu a jikinka fiye da ƴaƴan kowa saboda baka san su ja baya da kai har su fara tinanin akwai abin da kake binnewa, kasan da cewa ko da iya Omaid and Obaid aka barka sai sun tona ɓarnar da kake yi cikin ƙanƙanin lokaci bare kuma ni". Kara firgita King ya yi yana zazzare idanu. "Omerish ya tabbata yanzu kam da gaske akwai abin da kake sha!". Ya faɗa yana nufosa. "Dad babu wani abin da nike sha, yanzu ni ba wannan ne ya kawoni ba"..... "Batun Zunaira ne ya kawoka ko? To Zunaira matar aute ce, sai ka zare bakinka a cikin maganar ta". Cewar King!! Kai Smart ya ɗan girgiza. "Ba'a banza makiya suke kirana da Smart ba, tun da har makiyana suka yarda ni Smart ne yakamata kai ma daddy kasan ni ba irin saura bane, ba shakka batun Zunaira yana daga cikin abin da ya kawoni, amma bashi ne the best ba, the best shi ne so nike ka faɗa mun wacece uwar Ramish?! Dan dai kasan Aleezarh (Mama kenan) ba ita ta haifeshi ba!!". Tamkar kwayar idanun King zasu fito su faɗi ƙasa, lokaci guda wani irin gumi ya wanke mashi fuska, a rikice word ɗinsa suna harhaɗewa ya ce. "Idan ba Aleezarh ce ta haifesa ba kai ne uwarsa? Wai Omerish anya kana da hankali kuwa? Lallai ba shakka Rahilarh ta mun cuta da ba zan taɓa mantawa da shi ba, ta mayar da kai mara hankali ma.......". Ƙasa ƙarisa maganar ya yi saboda tsawa da Smart ya daka mashi. "Ya isheka haka dad! Kowani lokaci sai ka zagi momma a kai'na for what reason? Ka zageta kuma ka zaganmun iyayena, dik saboda kana san ɓoye laifukanka, just tell me wacece uwar Ramish kuma meyasa ka yaudari Aleezarh da shi? Me ya yi maka da ka ja mashi irin wannan bala'i da dik in da ya yi neman rayuwarsa ake yi? Laifin me ya aikata a gareka? Ka faɗa mun sannan ka bani amsar menene a tsakaninka da mahaifiyar Hoorain da har ka zage ka rabasa da Zunaira". Ɗan dakatawa ya yi yana mayar da numfashi kafin ya sake cewa. "Dad kai azzalumi ne sosai, ka faɗa mun su waye suke bibiyar rayuwar Ramish, dan nasan tin da har ka iya yaudarar Aleezarh da Ramish a matsayin ɗanta to ba shakka kasan su waye suke neman kashesa, Raj shi ne kawai ɗan Aleezarh namiji sai Aneesa, Ramish ba ɗanta bane, kuma kai ka san uwarsa, dole kuma ka faɗa mun ɗan waye". Yau ake yinta, Ramish ba ɗan mama ba, how comes to? Ya aka yi ita kanta bata san ba ɗanta bane? Kam bala'i lallai King shahararren ne, iyeeeee, ya aka yi Smart yasan dikka wannan sirrin wanda su momma basu sani ba? Sannan ya aka yi yasan suna da alaƙa da maman Hoorain bayan momma da ta yi tinanin ma bata faɗa mashi ba? Gaskiya Smart hegen kwaro ne, wato akwai badaƙala, wacece uwar Ramish to tin da ba mama bace? Amma da alama irin son da King yake yi mashi shi ne ubansa, tab QUEEN OF SURPRISED na fara baku a jikinku, yanzu kuka fara shan surprise ma ai, mu je zuwa. King da ya gama nuna zallar hasala a face ɗinsa, abin da mutane suke cewa tabarmar kunya da hauka ake naɗeta, ya ɗaure fuska zai yi magana cikin tsawa kenan Chuchu ta afko cikin ɗakin a guje tana zunduma ihu, hakan yasa duk suka kai kallansu a kanta. Tana zuwa a haukace ta nufi King tana faɗin. "Daddy Auta ta rasu, Yah Abdussalam ne ya faɗa mata cewa Hoorain ɗin da take so ai ya mutu dan haka ta zo su yi zaman aure, shikenan ta faɗi ta dai'na numfashi!!". Ai King bai tsaya jin karashin maganar ba ya nufi waje, saboda yasan dama ance zuciyarta gab yake da bugawa, to ga shi Abdussalam ya fasa abin da suke rufe mata, ai dole ziciyarta ta buga. Shi kuwa Smart tin da Chuchu ta ambaci Auta ta rasu ya rigasu barin bedroom ɗin ya nufi in da take. Yana shiga ya sami Abdussalam sai tattala mata tuwa yake yi a kanta yana ambatar sunanta, amma ko motsawa bata yi ba, da kallo ɗaya Smart ya yi mata ya fahimci tabbas babu rai a jikinta. Innalilahi wa inna ilahir rajiun. Allah sarki kada ku ga laifin Abdussalam, shi bai san ciwon son Hoorain take yi ba, shi bai san ance kada a sanar da ita ba, da ta fito parlour tana sambatu a kan Hoorain ne ya biyo bayanta, a nan ya ji ashe san Hoorain ne a ranta, shi kuma yasan Hoorain ya mutu, shi ne ya sanar da ita ya rasu, hakan yasa ta yanke jiki ta faɗi zuciyarta ta buga. A fujaje King ya shigo cikin ɗakin, tamkar ya haukace ya yi kanta zai taɓata, ai cikin wani irin kuna da fitar hayyaci Smart ya capki wuyarsa, dama ya faɗa mashi in Zunaira ta mutu to fa sai dai ayi gawa biyu wlh!!. Page ɗin yau bai samu wadataccen editing ba, nasan zaku samu typing errors dayawa P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 =======🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 57 Daidai lokacin su uncle Abbas suka shigo cikin parlourn, dan Chuchu sai da ta je ta kira kowa na familyn, da alama Chuchu ta zauce, dan kalar kukan da take yi sai da uncle Jahiz ya kamata ya hanata dawowa part ɗin, ya miƙata ga Jawad ya yi mashi gargaɗin kada ya barta ta fita, saboda za'a samu matsala. Kin yarda ta yi tana tigewa sai da Jawad ɗin ya sanyata a ɗaki ya rufe kofar da key, sannan ya kira Dr Raj da ya zo ya yi mata alluran barci ko zai samu hankalinta ya kwanta. Yau sai da aljannun dake kan Aneesa suka motsa saboda tsananin tashin hankalin da suka shiga. Uncle Jahiz and uncle Jahiz sun yi sun yi su zare hannun Smart daga wuyar King amma sun kasa, saboda wani irin damka da ya yi mashi na takaici da fitar hayyaci, shi kuma King like ruhinsa ya bar jikinsa saboda tashin hankali, bai taɓa zatan ɗan cikinsa zai yi mashi abin da Smart ya yi mashi ba ko da wasa, hakan yasa ya yi wannan sumar tsayen. Ihun da guyson ya zunduma a lokacin da ya shigo cikin parlourn ne yasa Smart juyowa, Allah sarki, hankalinsa ya yi nisa wajen hukunta King ne, da ba zai taɓa bari guyson, Omaid and Obaid da Momma su ji batun mutuwar Zunaira a yanzu ba, dan abin zai yi mashi yawa, yasan ba zasu iya ɗauka ba, kazalika shi ma zai iya ɗaukar komai ban da tashin hankalinsu. Ganin cewa labarin yana yaɗuwa a cikin gidan zai iya ja momma ta ji labari ne yasa ya saki King ba dan ya so hakan ba. Yana sakinsa King ya zube ƙasa a saman gwiwowinsa idanunsa sun kaɗa sun yi jajir, yau zuciyarsa ta karaya, ya shiga tashin hankalin da ko a mafarki bai taɓa zatan shiga ba, yana kaunar Zunaira tamkar ransa, idan ta mutu a gaskiya zai iya mummunar cutuwa. Ɗan uwa ɗan uwan ne my people's, uncle Abbas and uncle Jahiz ne suka rungumi King suna tausarsa dik da basu san me ya haɗa shi da Smart ɗin ba. Shi kuwa Smart kan Auta ya nufa, Abdussalam yana rike da ita yana ta famar girgizata yana kwallah, ya tattala mata ruwa a kanta ya kai 5 bottle, hakan yasa suka yarda da ta mutu ɗin ne, ruwa ba zai tasheta ba sai dai ALLAHN da ya yi ruwan ne zai iya tashinta. Wani irin gigitaccen tsawa da Smart ya dakawa Abdussalam har sai da yasa gabaɗaya waɗan da suke cikin parlourn suka natsu, a zabure Abdussalam ya ja baya da gudu. Bai bi ta kan kowa ba ya ɗauki gawarta ya saɓa a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya nufi kofar fita, dik an rasa mai bakin iya ce mashi uppan. Har ya kai bakin kofa ya juyo ya kalli King ido cikin ido. "Ka jira dawowata, sai ka ɗanɗani irin azabar da ka ɗanɗanawa Zunaira a zuciyarta kafin mutuwarta, kuma sai ka faɗa mun dikkan amsoshina!!!". Yana kai karshen maganar ya ja hannun guyson da yake tsaye a bakin kofar tamkar an sassakasa, kamar wanda aka zarewa laka, tin da ya yi ihu sau ɗaya bai sake ko motsawa ba, amma ransa na jikinsa kuma ba suma ya yi ba. Shi kuwa King Allah ne kaɗai yasan irin halin da ya shiga, ji ya yi tamkar bashi a duniya, Zunaira ta mutu? Ina kin yarda ya yi kamar yadda har yau commander Zafar yaki yarda da Hoorain ya mutu, an je an binne Hoorain, har kabarinsa su Ansar su je da shi, amma yaki yarda ɗansa ne, dan shi yana ganin Hoorain a gizo. To haka shi ma King a yanzu yaki yarda Zunaira ta mutu, ya shiga wani irin hali na tsakanin rayuwa ko mutuwa, wato shi ma a yanzu yana ɗanɗana abin da commander yake ɗanɗana, sai dai kuma dik da ta mutu wlh bai yi danasanin hanata auren Hoorain ba! Ko kaɗan bai ji mamar bai kyauta ba da ya hanata Hoorain tashin sense!!. -------------------------------------🔥 Suna fitowa suka ci karo da Jaish and Omaid da Obaid suna biye da shi a baya. Cike da tashin hankali Jaish ya tambayi Smart me yake faruwa?. Ko dakatawa Smart bai yi ba bare yasa ran zai samu amsa daga garesa, kai tsaye ya nufi wajen motocin gida. Bayansa suka bi gabaɗayansu Jaish yana faɗin ina zai je da ita? Bai amsa mashi ba sai ya ce ya yi maza ya bashi keyn motarsa bari ya wuce da ita, dan ba za'ayi jana'izarta a nan ba, ran Smart ya ɓaci over. Jaish bai yi musu ba ya ɗauki mashi keyn motarsa, sai dai a tare suka nufi airport, da jet ɗin Smart ɗin zasu yi amfani. In short kai tsaye ya ɗauki gawar Auta zuwa Dubai, rabonsa da Dubai tin wani zuwa da ya taɓa yi bincike a kan Ramish, tin lokacin bai sake zuwa ba, yanzu tsawon shekaru wajen 10, amma yau saboda mutuwar Auta ya wuce da gawarta can. Bai sanar da momma zai zo Dubai ba, babu wanda ya sani sai Jaish and guyson da suka tafi a tare, Omaid and Obaid ma sun barosu a kingdom ɗin sai kuka suke yi, ya ɗauki guyson ne ma dan yasan sai ya yi jinya, kada ya tafi ya barshi matsala ta afku da shi. Tin kan su hau jirgi ya kira Ramish a waya, ya sanar da shi ya zo airport ya ɗaukesu, ya ɗan yi mamakin jin sun zo Dubai, amma sai ya shirya tsab cikin suit masu bala'in tsada, ya ce da Leesharh bari ya je airport yana zuwa. Da yake ita tasan me a gidan, tasan tana tare da bakar azzaluma yarinya mai ɓadda kama a matsayin tsohuwa, sai ta shiga tashin hankali da damuwa over, a tsorace take ya tafi ya barta da wannan tsohuwa. Hannayenta ya riko cikin nasa yana kallan face ɗinta. "Aesh ba zan jima ba, babban yayanmu ne ya zo, shi kawai zan je in ɗauko kin ji?". Shiru ta yi kanta a ƙasa, kamar mai tinanin wani abin, tana zaune a saman bedside drawer ɗinsa, shi kuma yana zaune gefen bed ɗin suna fuskantar juna. Kafin ya ankara sai ganin hawaye ya yi yana ɗiga a ƙasa, ashe kuka take yi da ta sunkuyar da kanta ƙasa.......... "Aesh lafiya kuwa? Meyasa kike kuka?"........ Shiru bata amsa shi ba, ita tasan bala'in da zata shiga idan ya tafi, tsoron matar take ji......... "To zaki bini mu je tare ne?". Ya jefa mata tambayar yana sakin hannunta ɗaya ya ɗago haɓarta. A gaggauce ta gyaɗa mashi kai alamar e zata bishi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To shi ne sai kin yi kuka? Ai da sai ki faɗa mun kina tsoron gidan ne mu tafi tare". "Kina tsoron mutanen da suka zo ɗin nan ko? Ba zasu sake dawowa ba In Sha Allah, so feel free and enjoy your life with your husband to be In Sha Allah". Ya kai karshen maganar yana ɗan leƙa face ɗinta. Wani irin shessheƙa ta yi kafin ta kai hannu tana goge hawaye, ta kasa yin magana. Ƙasa sosai ya yi da murya wajen cewa. "Yau ɗaya naga abin da kike tsoro Aesh, dik yadda aka yi akwai abin da yake baki tsoro kuma yake ɗaga hankalinki a gidan nan! To faɗa mun menene sai in kawar maki da shi kada ki rinƙa jin tsoro". ....... KAI WATO RAMISH MA FA AKWAI ƘWAƘWALWA, A RANSA YA JI AKWAI ABIN DA YAKE BATA TSORO NA DABAN, BA WAI DAN MUTANEN CAN SUN KAWO MASU HARI BANE, AKWAI WANI ABIN DAI!!. Da yake ita ma tana da basira sai rashin yin tinani kafin ta yi abu, sai ta ce mashi. "Yah Ramish tin da ka iya gano cewa akwai abin da yake bani tsoro, to ka gano ko menene da kanka ba sai na faɗa ba". "Haka kika ce?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e haka ta ce. Ɗaura yatsarsa a saman kumatunta ya yi. "Zaki gani, cikin ƙankanin lokaci zan gano". Ya faɗa yana ɗan ja baya kaɗan daga kusa da ita. Tab kunga Leesharh ta yi amfani da basira a nan ko? Tasa zai fara binciken me abin tsoratarwa a gidan, idan Allah ya taimakesa sai ya kama tsohuwar nan da hujja dumu dumu, kamar Leesharh tana highlighting ɗinsa a kan abin ne. "Shirya ki zo mu je, saura bai wuce 20 mins jirginsa ya sauƙa ba". Ya faɗa yana kallanta. Miƙewa ta yi ta nufi waje ba tare da ta yi magana ba. Da kallo ya bi bayanta, idanunsa a kan mazaunanta dake motsawa a hankali, nisawa ya yi tare da haɗiyar siririn yawu kamar wadda aka ajiyewa kayan fresh marmari a gabansa!. Tana fita suka yi karo da tsohuwar nan, gabaɗaya tray ɗin hannunta ya faɗi kasa abincin da ta shiryawa Ramish ɗin ya zube ƙasa. A razane Leesharh ta ɗago ta kalli face ɗin matar kafin ta mayar da kallonta a kan kayan abincin da suka watse a wajen. Idan ran tsohuwar nan ya kai dubu to ya ɓaci, sannan hankalinta ya tashi sosai, Leesharh ta lura da hakan, sai ta ce. "Mama kada ki damu ba sai kin ɓata rai ba, Yah Ramish ba zai ci abinci a gida ba yau, zamu ci a waje, ki gyare wajen kawai ki je ki huta abinki". Ta kai karshen maganar tare da wucewa zata bar wajen. Ai tsabar ɓacin rai tsohuwar nan bata san lokacin da ta kai hannu ta damko wuyar rigar Leesharh ta baya ba, tana zazzare ido ta kasa yin magana. Ko kun san meyasa bata yin magana? Saboda muryan yara ne da ita, za'a iya gane ba tsohuwa bace, shiyasa ta yi acting matsayin kurma, yanzu kunga ne dalilin da yasa na ce maku tun da take kula da Leesharh bata taɓa yin magana ba?. Da mamaki Leesharh ta juyo da kallonta a kan matar. A miliyan ta saketa tare da girgirza kai alamar tana bawa Leesharh hakuri kenan, mamaki kamar zai kashe Leesharh, me dan an ɓarar da abinci zata tashi hankalinta? Sai kace babu wani abinci a gidan? Abin da mamaki!. Alama tsohuwar ta nuna mata a kan zata iya haɗa masu wani abincin yanzu ba sai sun ci a waje ba!. Shiru Leesharh ta yi tana san gane nufin tsohuwar nan a kansu, meyasa ta damu da abinci yau bayan a da ko ta kawo masu basu ci ba bata damuwa, wata rana ma a waje suke fita su ci, bata damuwa sai yau? To why? Leesharh ta jefawa kanta tambayar, lokacin guda ta ɗan ɗauke wuta. Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta saki wani ƙayataccen murmushi, kai ta jinjinawa tsohuwar a kan ba damuwa ta shirya masu wani abinci, a cikin ranta ta ce. "Zaki san da jinin Nigeria kike yi, yo mu da dik duniya ta jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwa mu bare ke da iskancin naku ma bai da lasisi, mu kuma Najeriya dik iskanci masu iskanci sai ya jira, sai da suka sara mana, ni kaɗai na isheki ba sai Yah Ramish ya sa baki ba, zaki gane ke karamar ƴar iska ce, ba zan taɓa bari ki san nasan komai a kanki ba! Cikin ruwan sanyi zamu yi amfani dake mu kama iyayen gidanki, ai ke yanzu kina da amfani a wajenmu, zan taya shi bincike wajen yin amfani dake". JAMA'A KU TAFAWA NIGERIA!! KU TAFAWA LEESHARH!! HABA AI JININ NIGERIA BADAGA NAN BA, KOWA SAI YA JIRA ALLAH KUWA!!. Wucewa ta yi tana tinanin in dai tana san yin magananinsu to dole ta kasance tana da kusanci da Ramish sosai, ta hakance zata sanyasu su da kansu su kama kansu. Da wannan tinani a ranta ta yi wanka ta shirya cikin haɗaɗɗen arabs abaya, ta ji yayansa zai je ɗaukowa, sai ta shirya da kyau dan kun san siririki ne Smart........... 😅 Ba karya ta yi fitina sosai cikin white abayan, ta yi rolling veil a kanta, ta ɗauki karamar fashion bag and flat shoe dik white color kalar rigar, sai tashin kamshi take zubawa ta nufi bedroom ɗinsa. Bakinta a ɗauke da sallama ta shigo cikin room ɗin. Yana zaune a in da ta barsa hannunsa rike da cup of cappuccino, yanzu tsohuwar ta kawo mashi cappuccinon da kayan abincin ta fita, har ta sake shirya masu wani kenan, yanzu ya ɗauki cappuccinon bai kai ga sha ba!!. Ai tana gani bata san lokacin da ta ƙariso cikin room ɗin da sauri ba, shi kuwa yana ɗaura idanunsa a kanta ya kafeta da kallo, ta yi fitina sosai, yanzu a ƴan kwanan nan wani irin sihirtatcen kyau take karawa na musamman. "Yah Ramish cappuccino zaka sha?". Ta jefa mashi tambayar a ya yin da ta iso wajensa. Kai ya jinjina mata haɗe da cewa. "Aesh you're so pretty, zo ki sha cappuccino sai mu tafi ko? Lokaci na kurewa". Ya kai karshen maganar tare da kai cup ɗin bakinsa da nufin ya kurɓa. Ai bata san lokacin da ta tafi kamar zata faɗi cikin dabara ta buge cup ɗin ya faɗi ƙasa ba, cup ɗin ya fashe cappuccino ya zube a ƙasa. A hanzarce ya ɗago kai yana ƙoƙarin yin magana sai faɗowa ta yi jikinsa mai gabaɗaya tare da fara salatin karya a zuwan zamewa ta yi ta faɗo jikinsa ba da gangan ba. "Aesh lafiya kuwa?". Ya faɗa yana kallon face ɗinta, ta datse idanu wai irin ya zaci da gaske ne ma. Yunƙurawa ta yi zata bar jikinsa saboda shegen iya basaja. Rikota ya yi yana kallan face ɗinta. "Aesh yakamata in kai ki hospital a dubaki, naga kamar jiri yana damunki". Ya bata satar amsa, sai kuwa ta ce. "Nima abin yana bani mamaki, kawai ina tsaye na ji jiri ya ɗebeni". Sorry ya ce mata tare da kai hannunsa ɗaya saman goshinta ya taɓa. "Ga shi jikinki babu zafi, amma dik da haka bari mu dawo zan ɗauki mataki". Langwaɓewa ta yi a jikinsa wai irin ta kara nuna bata da lafiyar nan. "Aesh ko dai mu wuce hospital ɗin nan ne?". A ɗan rikice ya yi maganar. "A'a mu je airport ɗin dai mu dawo". Ta faɗa tana sake yunkurwa zata bar jikin nasa. Sake riƙota ya yi, take suka zubawa juna idanu a kurkusa, wani irin kallo mai cike da sirrika suke aikawa junansu. "Idan kika tashi jiri ba zai sake ɗibarki ba? Ko in kaiki mota da kai'na?". Ya faɗa idanunsa sosai a cikin nata. Ƙasa iya basa amsa ta ta yi, abin da yake cikin zuciyarta yana neman fin karfinta. "Aesh" ya faɗa yana mai da kallansa kan soft lips ɗinta da suke ɗan kerma kamar mai jin sanyi. Bata iya amsawa ba. Zai sake yin magana wayarsa ta fara ringing. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Let's go, kinga kin sa har jirginsu ya sauka ban isa airport ba, dan ma babu nisa nan da 5 mins zamu isa". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa da ita a jikinsa. A haka suka nufi waje. Ajiyar zuciya ta sauke, hankalinta ya kwnata, burinta na ɓata mashi lokaci ta hana shi shan wani cappuccino ko cin wani abin ya cika. Sai dai daga shi har ita basu lura da cappuccinon da ya zube a kasa ba, ya canza kala daga brown zuwa dark green sosai, kamar ba cappuccino ba, suna fita wannan tsohuwa ta yi gaggawar zuwa domin tattare komai, a gaggauce ta goge cappuccinon da ya zube, tasan basu sha komai ba, dan dik abin da suke faɗa kada ku manta tana jinsu, ranta bai so hakan ba sam, ranta ya sosu, haka ta kwashe kayan abincin ta fita da shi tana tinanin irin hukuncin da zata yi wa Leesharh, ba zata kyaleta ba sai ta hukuntata! Dan tana ganin kamar ita take sanya Ramish yana tsallake tarkonsu, kuma hakan ce, sau da dama Leesharh tana shiga tsakaninsu ba tare da ta san ta shiga ba, kamar dai yadda ta ɓarar da abincin ɗazun da suka yi karo, kun ga bata san akwai wani abin a cikin abincin ba ta ɓarar, to haka dayawan lokuta sai sun yi shiri a kansa sai ta shiga tsakani ta watsa komai. Daren jiya Ramish zai fita ta hana shi ta hanyar ce mashi tana tsoro kuma ita ba zata iya fita waje a daren nan ba bare ta bisa, haka ya fasa fita, kuma sun shirya mashi mugun abu a fitar da zai yi, kunga Leesharh ba tare da saninta ba a nan ma ta shiga tsakaninsa da su!!. ---------------------------------------🔥🔥 Bai direta a ko'ina ba sai a cikin mota, da gudun gaske ya shiga ya figi motar suka bar gidan. Saboda gudun da yake yi yasa suka yi saurin isa airport, a dai'dai lokacin su Smart suka fito daga cikin jirgin yana rungume da gawar Auta. Ai Ramish yana ganinsu haka bai san lokacin da ya ɓalle kofar motar ya fito waje ba, take ya ji zuciyarsa ta amsa, hankali nan da nan ya tashi, a ruɗe ya ce. "Yah Omerish meyake faruwa? Meyasameta?". Dai'dai lokacin Bilal ya yi parking motarsa shi ma ya fito. Smart bai yi magana ba ya buɗe gidan baya na motar Ramish ya kwantar da Auta a ciki, sannan ya yi juyo ga su Jaish. "Ku bi Bilal izuwa gidan uncle, bari in je ni da Zunaira, ka kula da Omar". Fitowa ita ma Leesharh ta yi daga cikin motar tana kallan Smart, sai da gabanta ya faɗi yadda ta ga face ɗinsa. "Aesh shiga gidan baya ku zauna da Zunaira". Cewar Ramish kenan. Da sauri ta shiga tana kallan Smart, ta ɗaga kan Auta ta ɗaura a saman cinyarta, sai a lokacin ta lura da guyson, Allah sarki ta jima rabonta da shi, tin da ya koma kingdom of power bai sake zuwa Dubai ba, ta yi kawarsa sosai mutumin kirki. Gidan gaba na motar Ramish Smart ya shiga ba tare da ya yi masu magana ba, yau first time na haɗuwar Smart and Ramish face to face kenan, Ramish ya ci burin ya haɗu da yayan nasa mai tayasa aiki mai taimaka mashi, sai dai sun haɗu a wani irin yanayin da word can't explain how they're feeling, sai ma lokacin da su Ramish zasu fahimci Zunaira bata raye, uhm!!. Bilal na kallon Ramish har cikin ido, ba dan Smart dake wajen ba da babu abin da zai hana bai ci kwalar rigar Ramish ya faɗa mashi dalilinsa na gudunsa ba, ya kirasa a waya baya ɗauka, ya nemesa kamar hauka bai gansa ba, wlh har kuka sai da ya yi da hawayensa, ashe dama Ramish yana cikin Dubai, to me ya yi mashi da zafi har haka da zai yi mashi irin wannan hukunci? Tare suka taso, tare suke komai, rana tsaka Ramish ya gujesa dole abin ya gigita shi, har rama sosai ya yi wlh, albarkacin Smart yasa bai yi magana ba, yasan koma menene yanzu tin da yayan nasu yana nan zai warware masu komai, zai aje ye su ya ji menene ya haɗasu faɗa. Shi ma Ramish kallon Bilal ɗin ya yi ido cikin ido, lokaci guda ya ji zuciyarsa ta damu, wlh yana bala'in son ɗan uwan nasa fiye da kansa, dik sai ya ji bai kyauta ba, ko da Bilal yana da sa hannu a cutar da shi bai kamata ya juya mashi baya ta irin wannan sigar ba, kuma yasan Bilal ɗin ba zai iya jurewa ba, amma haka ya sharesa, gaskiya bai kyauta ba, take ransa ta ɗacaca, haka ya shiga mota ya tayar suka bar airport ɗin zuciyarsa cike da tinani kala kala. Bilal ma zuciyarsa tana zogi ya tada motar suka wuce gidan Abbie. Suna fitowa airport Ramish ya ce. "Yah Omerish ina zamu je?". Kai tsaye Smart ya ce. "Gidanka, and kada ka bari kowa ya san muna nan, kada momma ta sani shiyasa ban wuce family house ba". Shin kun san dalilin zuwan Smart Dubai kuwa? Zai fara ne daga kan King Badeen kakansu kenan, wato Akka bata isheshi gani ba, bari ya fara da mai bawa Akkan da kanta umarni kafin ya koma kansu, yanzu zuwan na King Badeen ne, sai sun faɗa mashi a wace aya ce Allah ya banbanta mutane, ya ce kuma a yi banbaci kamar yadda suke yi, tun daga nasi har bakara sai sun nuna mashi a in da ya ce mai arziki mai daraja ne mara arziki kuma mara daraja ne, uhm abin babba ne. My people's ni fa bana san kanku ya ɗauki zafi sosai shiyasa nike sake maku cakwakiyar nan a hankali hankali, kun gane ai?. Ina tausaya maku ne.......🥱 "In Sha Allah babu wanda zai san kuna nan, amma Yah Omerish please tell me meya samu Zunaira". Cikin raunin murya ya yi maganar. "Mutuwa ta yi". Smart ya faɗa can ƙasa ƙasa. Ai wani irin mahaukacin birki da Ramish ya taka sai da Smart ya buga kansa da jikin glass na door, tashin hankali, ita kanta Leesharh bata san time da ta zabura ba!!. Ƙasa iya yin magana Ramish ya yi, tamkar wanda aka datsewa baki, da bai taka burki bama ai da mutuwa zasu yi, dan babu abin da zai hana bai saki kan motar nan ba, irin wannan tashin hankali. A miliyan ya juyo da kallansa a kan Smart da yake kallon hanya, da hannu ya yi mashi alamar da ya kunna motar su je. Kasa yin magana Ramish ya yi, sai yake jin kamar kunnuwarsa basu ji mashi abin da yayan nasa ya faɗa daidai ba, yana san sake tambayarsa tongue ɗinsa ta yi mashi wani irin balai'n nauyi. Sake nuna mashi hanya Smart ya yi a kan su tafi, dan dole ya tashi motar yana ta faman sauke ajiyar zuciya yana addu'ar Allah yasa ba dai'dai kunnuwarsa suka ji mashi ba. Sai ƙoƙari haɗa kalmomu dake kama da mutuwa a cikin zuciyarsa yake yi dan ya fitar da kalmar da Smart ya faɗa ba mutuwa ba, wai irin zai ce wata kalma mai kama da mutu kenan sai ya ce haka Smart yake son cewa ya manta ya ce mutuwa. Da haka suka isa gida, tin bai gana kashe motar ba Smart ya fito ya buɗe gidan baya, ko kaɗan bai bi ta kan Leesharh ba ya ɗauki Auta ya nufi cikin gida kamar gidansa. A gaggauce Ramish ya kashe motar ya bi bayansa, ita ma Leesharh da gudu ta rufa masu baya. A parlour saman kujera ya shinfiɗe Auta, sannan ya ciro wayarsa ya dannawa number Zash kira, yana ɗagawa ya ce mashi. "Mun iso everything is ready". Yana kai karshen maganar ya katse kiran. Dai'dai lokacin Ramish ya shigo ciki, har tsoron sake tambayar yayan nasa yake yi, dan zuciyarsa ba zata iya ɗaukar jaddada mashi mutuwar Auta ba, a bakin kofa ya tsaya ya ƙasa ƙarisowa ciki. Binsa da kallo mai ɗauke da fassara kala kala Smart ya yi kafin ya ce. "Zoka zauna mu yi magana akwai in da nike san zuwa". Kai ya ɗan girgiza yana kallon gawar Auta ya sake kallan Smart, alamar ba zai iya ƙarisowa ciki ba. Nisawa Smart ya ɗan yi kafin ya ce. "Zunaira bata mutu ba, shikenan zo ka zauna". Wani irin dogon numfashi da Ramish ya ja tare da dafe saitin zuciyarsa shi zai tabbatar maka da suna bala'in kaunar Auta fiye da kawunansu, sonta a cikin jinin jikinsu yake!!. A hankali ya karisa ya zauna kusa da ita, dai'dai lokacin ita ma Leesharh ta shigo. "Zunaira bata mutu ba, ta shiga doguwar suma ne, Zash zai kawo likitocin da zasu lura da ita, zan barta a nan a hannunka, ka bata kulawa sosai wanda nasan ba sai na faɗa maka ba zaka yi hakan, kada ka bari kowa yasan tana raye, ina san dad ya ɗanɗani azabar da ta ji a zuciyarta lokacin da ya yi mata sanadiyar mutuwar wanda take so, ko mijin nata kada ka bari yasan tana raye, zamu bari a matsayin ta mutu, sai ta samu lafiya sosai, idan tana san zama da Abdussalam ɗin sai a barsu, idan kuma bata so sai a raba auren". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a kanta. Yau tin da ya ɗaura idanunsa a kan Ramish yake yi mashi wani irin kammani kamar Hoorain haka! Shi da yake yasan kamannin Hoorain tin yana Paris, akwai hotunansa ma dayawa a wayarsa wanda shi Hoorain ɗin yake turawa Auta a lokacin da suke soyayya!. "Yah Omerish amma me yake faruwa ne? Dama bata san Abdussalam ɗin ne aka yi auren?". Ramish ya tambaya!. Jinjina mashi kai Smart ya yi kafin ya faɗa mashi dik abubuwan da suka faru na yadda King ya hanata Hoorain har hakan ya yi sanadiyar mutuwar Hoorain ɗin, da ta ji Hoorain ɗin ya mutu shi ne ta shiga doguwar sumar nan! Sosai Ramish ya ji ɗacin abin da dad ɗin nasu ya yi, tsabar ɓacin rai bai san lokacin da ya ce. "To shi dad ɗin akwai wanda ya taɓa hanashi san ransa ne? Amma me Hoorain ya yi mashi bayan soyayya da Zunaira? Hukuncin ya yi tsauri". Kai tsaye Smart ya ce. "I think Hoorain ɗansa ne ko kuma suna da wani kwakkwarar alaƙa a tsakaninsu"............ Wata uwar zabura Ramish ya yi, with harsh voice ya ce. "Ɗansa kuma? How comes?".......... Dan furzar da iska mai tsananin zafi daga bakinsa Smart ya yi kafin ya ce. "Dik ajiye waɗan nan batutuwa, yanzu dai zan turo jami'ai guda goma su yi tsaron gidan nan, zan turo wasu biyu daban kuma su yi tsaron Zunaira sosai, ban yarda a bata komai daga wani waje ba ba tare da sanin jami'an dana wakilta ba, ban yarda ta ci wani abinci ba face wanda waɗan nan jami'ai zasu girka mata, sannan su zasu rinƙa yi mata komai, kai dai ka saka idanu a kansu, kuma zata so ganinka a kusa da ita. Idan na gama bincike a kan koma menene you will get the result, maybe zan dawo gareku cikin satin nan, maybe kuma zan iya fin hakan". Tashin sense, shiru Ramish ya yi yana mamakin abubuwan da suka faru, wannan wace iriyar musifa ce? Ya jefawa kansa tambayar. Zuba mashi idanu Smart ya yi yana kallan face ɗinsa, dik yadda aka yi Smart yana hasashen Ramish ɗan waye, tausayinsa ne sosai ya kama shi, ya zai ji idan aka toni asalinsa? Gaskiya King bai yi mashi adalci ba sam sam. "Don't trust anybody my brother, idan da dama kanka ma kada ka yarda da shi gabaɗaya, ka kula sosai". Cewar Ramish.............Jin jina kai Ramish ya yi kafin ya ce. "Yah Omerish ina jin kamar Raj ba kanina bane, saboda abubuwan da suka faru". Tausayinsa ne ya sake kama Smart, kamar kuwa yasan gaskiya. "Kaninka ne, ka dai'na barin shaiɗan yana sanya maka banzan tinani a ranka, keep praying, everything will came and end"........ Shiru ya ɗan yi, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin zuciyarsa. Smart zai sake yin magana idanunsa suka sauka a kan Leesharh dake manne da jikin bango tana binsu da kallo. Ɗan zaro idanu Smart ya yi, saboda tsantsar kamanninta da Zash da ya gani, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Dai'dai lokacin Zash ɗin ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama, ga wasu shahararrun Drs guda uku biye da shi a baya. Miƙewa tsaye Ramish ya yi yana faɗin. "Zash wanene ya faɗa maka ina nan?". Harara ya wurga mashi kafin ya ce. "Awww our bro ka ɗauka sai ka faɗa mun in da kake ko?". Ɗan ɗaure fuska ya yi tare da cewa. "Stop please, wai ya aka yi kasan gidana?"....... "Kana mamaki ne?". Smart ya katsesu. Da sauri Ramish ya juyo da kallonsa a kan Smart ɗin. "E Yah Omerish, friend ɗina ne fa, kuma ni ban taɓa zuwa da shi nan ba, ban san ya aka yi yasan nan ba". Miƙewa tsaye Smart ya yi. "Ni na turo shi wajenka domin in san dikkan ƴan uwana, ba jami'i kasa da kai bane kamar yadda kake tunani, shi bama SWAT bane, ya shiga jikinka ne kawai bisa umarnina, assistant ɗina ne a wajen aiki, jajirtaccen jami'i fiye da tinaninka, yanzu kuma ni na ce ya zo nan da Drs dan su duba Zunaira". Mamaki ne ya kama Ramish, dama ya yi mamaki a lokacin da Zash ya shiga hukumar SWAT, dan da kallo ɗaya ya yi mashi yasan wannan kwararren jami'i ne sosai, amma sai ya bar abin a ransa, suka cigaba da kasancewa a tare, ashe kuwa hakan ce, jami'i ne. Yana can yana mamaki har su Drs sun dukufa a kan Auta dan jadada aikinsu. Smart bai jira ba ya wuce haɗe da yi masu sallama, haka ya zo ya wuce Leesharh ba tare da ya sake ɗaga idanu ya kalleta ba. Mayar da hankalinsu su Ramish suka yi kan samawa Auta lafiya, babu wanda ya damu ko ya mayar da hankali kan kamannin Leesharh da Zash bare har su yi bincike!!. A can kingdom of power kuwa, lokacin da King ya tabbatar da Zunaira fa mutuwa ta yi ta bakin Jaish, wlh yanke jiki ya yi ya faɗi, sai dai suka kwashesa zuwa hospital, doguwar suma ya yi, sai da ya shafe kwana biyu a sume likitoci suna ta kokarin a kansa, daga bisani aka dawo jinyarsa a gida bayan ya farfaɗo, sai da ya ɗauki good 3 weeks yana jinya, baya furta komai sai dai ya yi ta binsu da kallo, kuma dik da haka bai yi danasanin hana aurenta da Hoorain da ya yi ba, ya dai yi fatan da wani take so ba Hoorain ba ba shakka da zai bata shi ko da ba jinin sarauta bane, Hoorain ne dai baya kaunar haɗa jini da shi. Momma bata san Auta ta rasu ba, sun ɓoye mata, ko da ta dawo daga Dubai sai ce mata suka yi tana wajen uncle Muhammad na France, wato daddyn Smart kenan, hakan yasa bata wani damu ba. King dai ya sha jinya, dan wlh har Auta ta farfaɗo ta fara samun lafiya sosai shi bai koma dai'dai ba, kuma kusan kamar commander ya zama, dan wani lokaci sai ya rinƙa magana kamar Auta tana kusa da shi, kamar yana tare da ita suna hira. Abin ya tada hankula matuƙa, yanzu uncle Abbas shi ne yake kula da mulkin kingdom of power, King yana jinya. Gudun kada guyson ya samu taɓin hankali yasa Smart ya sanar da shi Auta bata mutu ba tana raye, ya kuma sanya Ramish ya haɗasu suka ga juna, ranan sun sha kuka sosai, tin da Auta ta farfaɗo bata yi magana ba sai ranar da guyson ya zo wajenta, a nan ne ta yi magana, ta yi kuka, ta kuma yi wa Hoorain addu'a, daga nan Ramish ya ce tun da ana hutun school a bar guyson ya kasance a tare da ita, dan a dalilin zuwansa wajenta sauki ya kara samuwa har tana magana, Smart ya yi na'am da hakan, shi kuma yana kingdom of power, rashin lafiyar da King yake ciki yasa bai tada balli a kan amsoshin da yake so ba, ya ɗaga kafa zuwa dad ɗin nasa ya samu lafiya. RAMADAN KAREEM!!. Ana gobe za'a ɗauki azumi, sai shirye shirye ake ta yi na tarar wata mai falala mai albarka, unexpected Smart ya ga diran mom ɗinsa a kingdom of power, ta ce ba zata iya zama ba tare da shi bane, tin da yaki dawowa shi ne ta biyo bayansa, ya ji matuƙar daɗin ganinta, ya kuma jin babu daɗi yadda ya bari ta yi kewarsa, matar da tin da ya taso fara'a kawai yake gani a face ɗinta, ta so shi fiye da yadda take san kanta, macen kirki adala, ya yi mata addu'ar samun haihuwa sau ba iyaka, ya ji dama ace yana da damar sama mata aihuwa da sai ta gaji da ƴaƴa. Sosai su momma suka karɓeta hannu bibbiyu, momma ma ai sai zama yar kallo ta yi a tsakanin Smart da mom ɗinsa, dan kuwa ya tare a wajenta abinsa, kafin ya je wajen momma sau ɗaya ya je wajenta sau uku, kun san zuciya bata da ƙashi, sai momma ta fara danasanin kai mashi su da ta yi, tana ganin kamar ya fi son mom ɗin tasa a kan ita da ta haifesa, bata san ba haka bane, shaƙuwa ce kawai, kada ku manta tun yana jajiriri fa, mom ɗinsa ita ta yi mashi komai, kunga kuwa dole ya fi shaƙuwa da ita, momma fa time to time take zuwa wajensa, a shekara sau ɗaya take zuwa idan ta samu damar zuwa Dubai gaisuwar azumi, kunga kuwa dole ya fi shaƙuwa da mom ɗinsa, amma batu na so da kauna ai baya haɗa momma da kowa, it kaɗai ce babu ta biyunta!!. Zaune suke a parlourn momma, da momma da mom ɗin nasa suna hira, nan momma take cewa mom ta yi wa ɗan nata magana ya yi aure mata. Murmushi mom ta yi kafin ta ce. "Ai baya son yi, ta kyalesa sai time da ya yi ra'ayi, ga shi nan Heleena tana can tana haukar sonsa amma yaki kulata". Jim momma ta ɗan yi, dan tasan Heleena da ake magana a kai, sai bata ce komai ba, dan kada ta ce wani abu mom ta ce bata son familynta. A can gefe kuma King ya gama sanar da uncle Abbas cewa yana nemanwa Smart auren Sareena, dan sun dace, uncle Abbas kuma ya ce Allah ya basu zaman lafiya, wato ya bashi kenan, uhm yau ake yinta. SAREENA ZAƁIN KING GA SMART, HELEENA ZAƁIN MOM ƊINSA, PRETTY ZAƁIN MOMMA, wa kuke tinani zata zama zaɓin Smart kuma?........ Suna tsaka da hiran sai ga Sareena ta shigo cikin part ɗin, tana san ganin Smart ɗin ne, ta jima tana san ganinsa bata samu dama ba, shi ne ta daure ta zo part ɗin momma ko yana ciki, tana tsoron zuwa room ɗina. Yau dai tana sanye da abaya har ƙasa, sai dai da alama shegen shigar tata ta yi daga ta ciki. A saman carpet ta zauna tare da ɗagawa su momma gaisuwa kamar wata ta Allah. Fuska ba ya bo ba fallasa momma ta amsa. Shiru ta yi tana tinanin me zata ce ne ta samu bayani a kan Smart, shin yana gidan ne ma ko baya nan, ta ƙosa ta ji. A daidai wannan lokaci mama Haulat ta shigo ɗauke da abincin Smart cikin wani luxury tray na alfarma. Duba time momma ta yi, karfe 8:30 na dare, kallon mama Haulat ɗin ta yi. "Lokacin cin abincin nasa ma ya yi, bari mutuniyar tasa ta zo ta kai mashi"....... A saman table mama Haulat ta ajiye abincin tare da juyawa ta nufi waje. Jiki na ɓari Sareena ta ce. "Momma abincin Yah Omerish ne?". Kai Momma ta gyaɗa mata alamar e. A hanzarce ta miƙe, jiki na ɓari ta ce. "To bari in kai mashi momma". Oh ta samu dalilin zuwa in da yake!. "A'a Sareena, Omerish bai aminta da kowa ya kai mashi abinci ba face Pretty, ko su Jaish ya ce baya so, ita kaɗai ya yardanwa, kuma kin san dokace ma ta wannan gidan ba kowa yake kaiwa Prince abinci ba sai wanda ya naɗa da kansa kuma ya amincewa". HAKIKA DOKARSU CE HAKA, BAMA ABINCI BA, BABU WANDA YA ISA ZUWA KUSA DA SMART A MATSAYINSA NA PRINCE MAGAJIN MULKI IDAN BA WANDA SHI DA KANSA YA YARDANWA BA KUMA KO ABINCIN DA ZAI CI SAI AN TANTACETA SOSAI, KO ITA PRETTY DA YA AMINTA TA RINƘA KAI MASHI ABINCI BA TA ISA TA KAI ABINCIN KAI TSAYE BA, DAGA KITCHEN SAI AN TANTACE KOMAI TSAB AN TABBATAR BABU WANI ABIN CUTARWA SANNAN TA WUCE TA KAI MASHI. Shi da kansa ya ce wa momma bayan Pretty bai yarda da kowa ya taɓa abincinsa da sunan zai kawo mashi ba, yana jin daɗin cin abinci da ita shiyasa ya ce ita zata rinƙa kawo mashi, saboda su ci a tare, kun san Pretty da shiririta da sakalci, idan suna cin abinci tana sanya shi nishaɗi da har ya ci abinci sosai ba tare da ya sani ba, yana mugu mugun son kasancewa a tare da ita, sai ta kai karfe 1 na dare a ɗakinsa, yana aikin bincikensa a kan familynsa, ita kuma tana zuba mashi shirme tana bashi nishaɗi, wani lokaci sai ta yi barci a bedroom ɗin nasa, sai ya kammala abin da yake yi zai mayar da ita nata ɗakin, a tare suke kwana da Mahreen a part na momma, to nan yake kaita idan ya tashi kwanciya barci. Da momma ta ce to ya auri Pretty ɗin mana kawai sai abin ya fi bada armashi, sai cewa ya yi shi bai ce yana sonta ba ai, kawai dai yana jin daɗin kasancewa da ita ne, tana ɗebe mashi kewar Zunaira tana kuma saka shi nishaɗi. My people's anya kuwa kun yarda da Smart? Wai tana saka shi nishaɗi! Ina team ɗin Pretty, kada ku yarda zai lallata maku ɗiya, in ba iskanci ba ka aureta ɗin mana, zaka wani ce nishaɗi take baka!. Wani irin ɗaure fuska Sareena ta yi, ranta ne ya yi maki, kamar zata sake yin magana sai kuma ta yi shiru, ta zauna tana jin tamkar ta haɗiyi zuciyarta......... Tsabar sakalci irin na Pretty ko sallama bata yi ba ta afko cikin parlourn, tana sanye da sleeping dress white color, riga ne da wando dogo, ta saki gashin nan har baya, Momma ta yi ta yi da ita ta rinƙa ɗaura ɗankwali amma yarinyar nan taki fir. Tana turo baki ta zo ta zauna kusa da momma, sarkin son jiki har da kwantowa a jikinta tana shagwaɓe fuska. Momma tasan halinta sai cewa ta yi. "Yunwa kike ji ko?". Kamar zata yi kuka ta amsa da e yunwa take ji!. "To ai ga abincin yayan naku, tashi ki je ki kai mashi sai kuci kamar da kuka saba". Cewar momma.. ita dai mom da bata jin larabci sai binsu da ido kawai take yi bata san me aka faɗa ba. Jin momma ta ce ta tashi ya ɗauki abincin Smart ne yasa Sareena ta gane e lallai wannan ita ce Pretty da ake ta magana, binta da kallo ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, saboda tsantsar madarar kyau da ta kallah, tasan babu abin da zata gwadawa Pretty sai rashin kunya wanda bata san cewa shi ma Pretty number ɗaya bace, sai dai idan ba'a zo ɓangaren ba!. Ziciyarta ne ya cigaba da kara ƙawata mata kyan Pretty, tinani ta fara yi a kan me zata yi mata ta rabata da Smart, ya zamana ma ko inuwarsa ba zata sake gani ba, bama ta san wacece Pretty ko yar wacece ba, ita dai tin da ta ganta a part ɗin momma sai ta zaci ko daga cikin ƴan uwan momma na Dubai take!. Tana can tana tinane tinane bata san lokacin da Pretty ta ɗauki abincin Smart ta fita abinta ba, sai waigawa ta yi taga babu abincin kuma babu ita ma Prettyn. Siririn tsaki ta ja wanda ta manta a gaban momma take. Miƙewa ta yi ta nufi waje, a cikin ranta tana faɗin lallata kyan Pretty kawai zata yi shi ne mafitarta, zata ɓata mata fuska kaca kaca ya yi damage ta yadda kowa zai ji kyamarta. Tana fita ta nufi part ɗinsu Omaid dan su shirya wannan mugunta a tare, dan ta rantse ba zata bar Pretty ba. Ita kuwa Pretty kai tsaye ta wuce bedroom ɗinsa, babu ko sallama ta afka ciki abinta, yana zaune a saman bed ɗinsa sanye da sleeping dress kalar na jikinta sak, dama shi ya saya mata tin a France, so su uku suka yi ankonsu, shi da ita da Auta, yana rike da wayarsa suna chat da Ramish yana jin ya lafiyar Auta a yanzu. Ta wutsiyar ido ya kalleta, tin ɗazun tinaninta ne a ransa, yana tina yadda zata kare da azumi gobe, anya zata iya yi kuwa? Bata fa shiri da yunwa, ga shi gaskiya girma ya fara zuwa, kirjinta sun cicciko, period kawai ya rage ta fara yi, dole ma ai ta yi azumi, sai dai za'a sha fama kam, bala'i tab zai fi kowa fama da ita, dan daga shi sai momma take jin maganarsu. Tin ɗazun yake ta tinanin mafita a kan azumin. Ajiye masu abincin ta yi a saman carpet ta nufo shi, a gefen bed ɗin ta zauna tana tura baki. "Bana ce ki rinƙa yin sallama ba? Kuma bana ce idan kin zo ki rinƙa gaishe ni ba?". Ya gefa mata tambayar yana cigaba da katsa wayansa. Unexpected ta faɗo jikinsa tare da sanya mashi kuka tana faɗin. "Yah Omerish wai mama Haulat ta ce gobe za'a fara azumi babu ni babu cin abinci sai dare?". Tana kukan kuma dan iyashege tana tura hannunta a cikin rigarsa ta kasa, so take ta taɓa cibiyarsa, wai ita da yake yi wa faɗa a kan saka ɗankwali da yin sallama, shi ne ta kwanta a jikinsa take yi mashi wannan sakalci da iyashegen, Pretty sai shirin Allah wlh, dama abin da take ta yi wa kuncin rai kenan, shi ne taki faɗawa momma ta zo tana juyeshi a nan, dan tasan ya fi kowa biye mata a gidan! My people's me kuke tinani idan Sareena ta zubawa Pretty acid a fuska? Dan dai kun san su Omaid zasu bata goyan baya, uhm P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 58 Tsaye yake cikin arabs jallabiya milk color, ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana aikin kai komo a cikin bedroom ɗinsa, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin tsananin tashin hankali gane da ciwo, tamkar ba King ɗinmu ba, ya rame matuƙa, ya yi wani irin haske sosai, sai idanu kwala kwala farare tas zaka gani, gabaɗaya a dabaybaye yake da damuwa. Tsayawa ya yi a gaban windown room ɗinsa dake fuskantar harabar family part, kalaman Smart ne kawai suke yi mashi yawo a ransa, ta wani ɓangare na zuciyarsa kuma rashin Zunaira, ta ko'ina ba sauki, babban abin da ya fi ɗaga mashi hankali shi ne kamar yadda Smart ya ce sai ya faɗa mashi uwar Ramish, to abin tashin hankalin a nan ne shi ne allura ce take shirin tono jibgegiyar garma mai girman gaske, domin kuwa ba faɗar uwar Ramish ɗin ne matsala ba, matslar shi ne ya aka yi ya baiwa mama Ramish a matsayin ɗanta ita kuma bata san ba nata bane? Wannan shi ne ainahin tashin hankali da yake ciki, dan tono yadda aka yi ya bata Ramish babban bala'i ne ga gabaɗaya kingdom ɗin wanda sai ta shafi kowa da kowa, idan Smart ɗin ma bai yi hankali ba zata zama sanadiyar mutuwarsa ko na mommarsa or guyson, dama shi guyson a kan hanya yake, taimakon Allah yasa bai mutu ba yake fama da ciwon ciki mai zuwa dik shekara kenan, wannan ba karamar bala'i bace, gara ma sanin me yake a tsakaninsa da matar commander a kan wancan bala'i na Ramish, siririn da a ka rufe tsawon shekaru 30 amma Smart ko daga ina ya jiyo sirrin har ya bankaɗo shi?. WANNAN SMART SAI DAI SHIRIN ALLAH, YA TAYARWA DA DATTIJO HANKALI YA BARSA CIKIN CIWO DA AZABA!! Haƙiƙa King ya shiga tashin hankalin da bai san ranar fita ba. Batu a kan maman Hoorain wato matar commander wannan tabbas suna da alaƙa, kai tin ba yau ba, tin kafin King ya yi aure suke tare, bari in maku tarihin, sun sha soyayya nakin karawa, saboda matar commander uwarta baturiya ce ubanta balarabe, shiyasa ta fita daban a masarautar, sai dai kuma tana matsayin baiwarsu, King Zuhair ya kamu da sonta sosai, yadda kuka ga Auta ta so Hoorain, haka suma suka so juna, sai dai kash, King Abdul Malik ya ce ko mutuwa King yake yi ba zai taɓa aurar baiwa ba, ya haramta masu mallakan juna, wannan dalilin yasa suka kasance a tare a bayan fage, suka rinƙa sheke ayarsu har King Abdul Malik ya fitar mashi da mata, wato da Mummyn Chuchu da Mamansu Aneesa, bai yi gardama dik da cewa baya sonsu ba, dan shi ai yana tare da wacce yake so a ɓoye. Aka aura mashi su, ya cigaba da kasancewa da matar commander har ita ma ta yi aure, tsantsar soyayyar da suke yi wa junansu yasa suka gagara rabuwa dik da suka yi aure, haka suka cigaba da rayuwa har shigowar momma rayuwarsa a wani zuwa Dubai da ya yi, already Mummyn Chuchu and maman Aneesa ba zaɓinsa bane, shiyasa kuka ga ya fin san momma sama da su, dan ita ce zaɓinsa ta biyu bayan maman Hoorain. Maman Hoorain da suka yi aure ba'a cikin kingdom of power suke zaune da commander ba, amma dik da haka suna da wajen da suka ware wanda suke haɗuwa ita da King dan holewarsu. A takaice lokacin da ya auri momma ta fahimci yana daga cikin sarakuna masu tarewa da kuyangunsu, shiyasa ta yi ƙoƙarin canzasa, kuma ta yi nasara, dan ta canzasa a lokacin da bai taɓa zata ba, a lokacin momma har ta haifi Jaish, lokacin ita kuma matar commander ta haifi Hoorain bai wuci 2 years ba a duniya, a ranar da za'a haifi Hoorain anyi gagarumin yakin da a ranar ne aka kashe King Abdul Malik, lokacin da maman Hoorain da maman Aneesa suna naƙuda, ranar anyi tashin hankali sosai. Bayan komai ya lafa aka yi jana'izar King Abdul Malik kamar yadda yake a dokar sarauta, daga nan King Zuhair ya karɓi karagar mulki, momma ta yi nasarar raba shi da matar commander, tin daga lokacin kuma ya tuba ya zama adalin sarki mai mulki tsakani da Allah, sai dai matsalar da aka sake samu a ɗan gaba kaɗan kafin matar commander ta ɓata da kuma bayan ta ɓata, wannan matsala lokacin da zaku san shi bai ba, dan wannan matsala shi ne yake da alaƙa da Ramish da kuma yaudarar mama da King ya yi, WANNAN SHI NE GASKIYAR ABIN DA YAKE A TSAKANIN KING AND MATAR COMMANDER ZAFAR, TO YANZU A TSAKANIN KING DA COMMANDER WANENE AINAHIN UBAN MARIGAYI HOORAIN? KAM BALA'IN CAN!! UHM WANNAN CAKWAKIYA SAI SMART YA WARWARE MANA! DAN KO SHI KANSA KING ƊIN BAN JIN YANA DA TABBACIN HOORAIN ƊANSA NE KO NA COMMANDER, ITA KANTA MATAR COMMANDER ƊIN BANA JIN TASAN AINAHIN UBANSA, WANNAN SHI NE KWAMACALA. KU DAI MU CIGABA DA ZUWA, AI KWAMACALA MA TANA CAN GABA!! Hege Smart ya jefa King da kansa a cikin zulumi da tashin hankali shi kuwa yana can yana more rayuwarsa da Pretty, sai nishaɗi suke yi, ga King ya ƙasa zaune ya kasa tsaye, wlh tin da kuka ga King ya girgiza a kan batun Ramish, ba shakka ba karamar ɓarna bace zata bayyana, babban bala'i Smart yake son jijjigo mana wanda gara kowani irin cakwakiyar a littafin nan a kan wannan, tabbas King Zuhair and King Abdul Malik sun bar baya da kura, abin sai shiru, sai lokaci ya nuna mana kawai!!. ZAN BAKU MAMAKI FA, DAMA SUNANANE QUEEN OF SURPRISE, KU YI FATAN BAYYANAR KAMRAN LAFIYA KU DAI!! ----------------------------------------------🔥🔥🔥 "Azumi fa akwai lada, idan kika yi zaki samu lada sosai, kuma waye ya ce maki ana wahala a azumi?". Ya yi tambayar yana ajiye wayarsa a gefe, sannan yasa hannu ya rungumota da kyau. Kai ta shiga girgiza mashi. "Ni ko akwai ladan tin da akwai yunwa bana so, ni ba zan yi ba". "Ɗago kanki ki kalleni". Ya faɗa yana tattare dark black curly hairnta da ya zubo ta gaba ya tufe mata fuska, tattare mata ya yi ya tara a baya, sannan ya riko haɓarta da hannunsa ɗaya yana kallan face ɗinta, dik ta yi jaga jaga da hawaye!. "Idan kika yi azumi zuwa dare zan saya maki su chocolate dayawa". Sarkin son zaki, kowa ya san halinta sha zuma ce......... "Ni dai kawai idan zaka saya mun saboda Allah haka ka bani to, idan kuma sai na yi azumi ne na hakura ka riƙe kayanka". Ta faɗa tana ƙoƙarin sake fashewa da kuka. .......... "To ya isa haka, yanzu mu je mu ci abinci kafin mu yi batu a kan azumi........." Bai iya ƙarisa maganar ba ya dakata sakamakon wani irin shock da ya ji na saukar hannunta a saman mararsa, a fujaje ya waro idanunsa sosai a kanta, turo mashi baki ta yi, ita a tinaninta jiran amsarta yake yi, bata ɗauki taɓa mashi cibiya da take yi a wani abu ba, sai ta ce. "Ni fa koma me za'ayi ba zan yi azumin nan ba, dan ba zan zauna da yunwa ba". Tana magana tana sake turo baki. Nisawa ya ɗan yi tare da rakwafo da kansa kaɗan a kanta, kamar mai san raɗa mata magana a kunne, cikin dabara ya haɗe fuskokinsu tare da capke lips ɗinta na ƙasa ya fara tsotsa. Zaro mashi idanu ta yi wanda sai da tasa ya kara jin tsikar jikinsa yana tashi, hannu bibbiyu tasa tana ƙoƙarin tureshi ya sakar mata baki, shi kuwa ya kara riketa da kyau, tirgewa ta fara yi tana mutsu mutsu zata kwace kanta, ina ai yaki bata dama sai da ya yi kissing ɗinta da kyau, sannan ya saketa tare da jingina kansa da jikin headboards na bed ɗin. Ita kuwa kuka ta saka tare da barin jikinsa, hannayenta bibbiyu tasa ta fara goge bakinta wai yasa mata datti kuma yawunsa babu daɗi dan babu zaƙi ita ga sha zuma, zaki kawai take martabawa. Bilhakki da gaskiyarta take kuka tana ta dirza ɗan bakinta wai tana goge in da nasa ya taɓa mata, sai tufar da yawu take yi, waje ta nufa da gudu, sam bai ji fitarta ba. Kai tsaye ta wuce wajen momma, tana zuwa ta faɗa jikinta tare da sanya mata kuka mai sauti, har lokacin mom tana wajen suna a tare. Da yake momma tasan hali, sakalcin Pretty ya wuci tinani, sai ta ce mata. "Ke da waye kuma babyn Yah Omerish? Yau ba'a kai mashi kara ba sai aka kawo mun?". Momma bata san yau shi ya yi laifi ba, yau kararsa aka kawo ba na mutane da aka saba kawowa or kai mashi ba. Ita dai momma ba ruwanta, ta fita daban, dama a ko'ina akwai na kirki dana banza, ita dai bata nuna kabilanci da kyamar wasu da ba nasu ba, kowa nata ne da hannun bibbiyu take rungumesa!!. Cikin kuka ta ce. "Momma Yah Omerish ne ya sa bakinsa a cikin nawa, kuma yasa mun yawunsa da babu zaki babu daɗi a cikin nawa, ya kuma sha mun nan". Ta kai karshen maganar tana nuna lips ɗinta da hannu!. Ajiyar zuciya momma ta sauke, dama tasan za'a yi hakan one day one time, saboda su jaraba gadonta suka yi, ita kuma Pretty ga ɗan banzan kyau kamar ita ta yi kanta, ai keɓewarsu waje guda abu ne mai haɗari sosai, shiyasa take ta lallaɓa Smart ɗin ya aureta kawai sai ayi dik wacce za'ayi, wlh ita Momma ta san cewa Smart yana bala'i kaunar Pretty, dan kuwa ita ce mace ta farko bayan ita da mom ɗinsa and Auta da taɓa shiga rayuwarsa har ta zauna kusa da shi, abin gaskiya yakamata ta ɗauki mataki. Tana can tana tinani sai ji ta yi Pretty ta miƙe zata bar jikinta tana faɗin. "Bari in je in faɗawa Zunaira abin da Yah Omerish ya yi mun"..... Ita fa Pretty bata ma san dik gurmin da ake yi a kan Auta ta mutu ba, dan tana waya da ita idan ta je wajen Smart, so dik bala'in da ake yi a kingdom ɗin ko a slippers ɗinta, hankalinta a kwance.. A hanzarce momma ta rikota tare da cewa. "Ba sai kin faɗawa kowa ba kin ji my baby? Kada ki faɗawa ko Zunaira ɗin ce ma, ki bari iya ke da ni zan rama maki abin da ya yi maki!". Girgiza kai ta yi. "Ni Momma ki bari in faɗawa Zunaira, ai ita ma ta faɗa mun da Hoorain ɗinta ya sha bakinta"....... Ai momma bata san lokacin da ta zaro idanu waje ba, bala'in can, yaushe Zunaira ta iya dikka wannan abin? Yaushe aka yi hakan? Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Gaskiya King ya yi kuskure da ya hanasu mallakar juna, abin har ya kai haka?. Tana can tana tinani Pretty zata gudu, kuma fa wajen Smart ɗin zata koma dan yarinta, shi ne kawai zai kira mata Auta a waya ta kuma faɗa mata ya sha mata baki, kai kuruci dangin hauka. "Zo mana my baby, baki san shi Yah Omerish ɗin mijinki bane? Shi zai aureki ai! Kada ki faɗawa kowa abin da ya yi maki, ki rufe sirrinku". Momma ta faɗa mata hakan ne dan ta samu ta yi mata wayo kada ta faɗawa kowa, sai dai ina, taki fir, ta ce babu wannan magana, ita wlh sai ta sanarwa da Zunaira abin da yake faruwa. Cigaba da lallaɓata momma ta yi, dan ta samu ta yi shiru, tasan idan ta ce zata yi abu to wlh sai ta yi ne, idan kuma ta ce ba zata yi abu ba ko me zaka yi mata ba fa zata yi ba, ai abin da kunya ta faɗawa Auta ga babban yayansu ya yi mata kiss, haba zata zubawar da Smart mutunci................😅 To shi ɗan air me ya kai shi dama, ko da yake ba laifinsa bane, laifin Prettyn ce, ƴar rainin wayo sai ta rinƙa yi mashi abubuwa, ta godewa Allah ma da abin ya tsaya a iya kiss, badan yana da dauriya ba yadda suke da gadan abar ai wani canza ake ba wannan ba, in ba iskanci irin nata ba ina ruwanta da cibiyarsa? Dan ta saba yi wa Kamran haka, shi Kamran a lokacin da take yi mashi ai kunga bai ma san me feeling ba, time da ya fara jin feeling ya sanar da mammarsa kuma ai kunga kashe mashi sha'awar ta yi da magunguna, ko kun manta lokacin? Saboda ma kada ya shiga haɗari ya yi ciwo tasan babu mata a forest ɗin shiyasa take bashi magungunar kashe sha'awa, wannan yasa dik abin da Pretty take yi mashi baya jin komai bawan Allah, amma Smart fa? Ai kunga da banbanci, dole idan ta yi mashi ya yi mata...........😅 Da kyar momma ta shawo kanta ta hanyar yi mata alkawarin cartoon na kayan zaƙi, sannan ne ita ma ta yi alkawarin ba zata faɗawa kowa ba, ajiyar zuciya momma ta sauke kafin ta miƙe haɗe da riko hannun Pretty ɗin ta ce da mom tana zuwa bari ta duba Smart. Da okey mom ta amsa, bata jin larabci bata ji me suka tattauna da Pretty ba. Bedroom na Smart momma ta nufa da ita, a parlourn ta ce mata ta zauna bari ta zo, da okey ta amsa tare da zama saman sofa tana turo baki ita kaɗai kamar wadda aka yi wa wani abin. Ciki momma ta wuce, yadda Pretty ta bar shi haka momma ta shigo ta samesa, idanunsa a lumshe, da alama tashi jarabar ta fi ta kowa, har sallama momma ta yi mashi amma bai jita ba, hankalinsa ya yi nisa sosai. A saman bedside drawer ta zauna tare da kai hannu ta ɗan shafi lallusan gashin kansa. Nisawa ya ɗan yi ba tare da ya yi magana ba, sai dai ya waro idanunsa da suka kaɗa suka yi jajir kamar wuta. "Omerish". Momma ta ambaci sunansa cikin sanyin murya, bai iya amsa mata ba, sai dai ya ɗan juyo da kallonsa a kanta, sai a lokacin ya farga da Pretty bata a cikin ɗakin, a hanzarce ya yunkura ya gyara zamansa yana ɗan wawwaigawa nemanta!. "Bata nan ta fita". Momma ta bashi amsa, dawo da kallonsa a kan mommar ya yi, da yake shi ba kunya ne da shi ba, renon masu jajyen kunnuwa sai ya ce. "Momma ta je ta faɗa maki na yi kissed ɗinta ko?"....... Jinjina mashi kai momma ta yi alamar e, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To ina take ta zo muci abinci". Ya faɗa yana kawar da kallonsa daga kanta. "Tana parlour, amma yanzu dai ba wannan ba, idan kun kammala cin abincin sai ka ɗauketa ku je ka siya mata cartoon na kayan zakin da na yi alkawari, sannan ina da magana da kai". Juyowa gareta ya yi. "Kayan zaki kuma a daren nan?". Kai ta jinjina mashi alamar e kafin ta ɗaura da cewa. "Sai da na yi mata alkawarin kayan zaki sannan ta yarda ba zata sanar da kowa abin da ka yi mata ba". Da mamaki ya ja ɗan siririn tsaki haɗe da cewa. "To me a ciki momma dan ta sanar da na yi kissing ɗinta?"......... Momma bata yi mamakin jin hakan ba, dan tasa daga ina ya fito, ba ruwansa da wani kunya. Kawar da zance ta yi da cewa. "To ni dai ina san kuje ka saya mata kayan zaki". Ita dai momma tasan kunya, kuma tasan wannan ba magana ce da za'a fitar da shi ba, yana matsayin Prince ace Pretty ta fitar da wannan magana ai sam bai yi ba! "Momma zakin nan fa cuta ce a gareta, baikamata take sha ba". Yana ɗan ɗaure fuska ya yi maganar. "For today dai ka saya mata". Shiru ya yi yana tinanin yadda zai yi ya rabata da zakin nan ya huta. "Omerish ". Ta ambaci sunansa tana kallansa. Dawo da kallonsa a kanta ya yi. "Na'am Momma". Tattara natsuwarta ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Omerish kana son Pretty, meyasa ba zaka yarda ka aureta ba kawai tin da ire-iren waɗan nan abubuwa sun fara shiga tsakaninku?".......... "Momma saboda na yi kissed ɗinta ba shi ne zai nuna ina santa ba, kiss daban soyayya daban that's all!". Shiru momma ta ɗan yi, yana neman goge mata hadda, wato kiss ba wani abin bane, e lallai ma Smart, wato zai gaji babansa kenan!!. "Na yarda kiss daban soyayya daban, amma kuma ai kasan haramun ne ka yi mata hakan ko?". Shiru ya yi bai bada amsa ba, babu kuma alamar zai yarda da zancen momma ɗin ma. "Please ka yarda ka aureta ga ji my son? Ina san yarinyar sosai, na tabbata zaka ji daɗin zama da ita, kuma nasan kana sonta kai ma......." Saurin katseta ya yi da cewa. "Ni bana sonta momma, ki dai'na faɗa mun haka".... Murmushi irin nasu na manya ta saki kafin ta ɗan girgiza kai, a ranta ta ce ta yaro kyau take bata ƙargo, a fili kuma sai ta ce. "Na yarda baka sonta, amma nikuma ai ina sonta ko?". Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba, can kuma sai ya ce. "Momma please ki bari in yi dinner, am feeling hungry, ta ya za'ayi ki fara cewa in auri wannan ƴar yarinyar da na kai in haifeta". (Ku ji iskanci, wai ya kai ya haifeta amma a haka ya sha mata baki.🤔) "Amma kuma ai dik da ka kai ka haifeta ɗin zaka iya kissing ɗinta ko?"........ Wani irin kallo ya wurga mata haɗe da cewa. "Mommaaaaaaa, zaki fara ko? Shiyasa jiya naki zuwa wajenki, saboda kada ki cigaba da kawo mun zancenta, ga mom ta dameni da zancen Heleena, so kuke yi in daina zuwa wajenku ko?.........." "Mom ɗinka ai bata san ka rabu da ita ne shiyasa take son ka auri Heleena, kaga zaku kasance a tare, nima bana son ka rabu da ni shiyasa nike son ka da Pretty, please ka duba mu mana my son". Cikin tausasawa ta faɗa. "Momma mata mayaudara ne, please ku kyaleni haka, ni bana da sha'awar wata mace ta shiga rayuwata a yanzu, Please kada ku katsa mun farincikina". Ya kai karshen maganar yana saukowa kasan bed ɗin. Riko hannunsa ta yi da sauri, hakan yasa ya dakata a bakin bed ɗin ba tare da ya karisa sauka ba. "My son meyasa yanzu baka son farincikina sosai ne?". "Mommaaaaaaa, zaki fara ko?". "Gaskiya na faɗa ai". Kai ya girgiza. "Kenan kin san ina sanki kuma ina san farincikinki, kawai so kuke ku wahalar dani"....... "Haba my aboy".... "Mommaaaaaaa wai ba zaki manta da wannan suna ba?". Ya faɗa yana binta da kallon kauna. "Sai ranar da matarka ta haifa mun jika zan daina ce maka sunan in mayar kansa, idan kana son na dai'na faɗa to ka yi aure ka haifa mun jika". Ta kai karshen maganar tana shafa kansa. Cikin sanyin murya ya ce. "Dik abin da kike so kin san shi nike yi mommata, kuma farincikina, this time ki ɗan bani lokaci zan yi tinani, zan yanke hukunci"........... Jinjina kai ta yi tare da cewa. "Okey tom amma ka yanke hukunci mai kyau, sannan ka rinƙa kulawa a zamantakewar da Pretty, kada ka zurfafa abubuwa"...... Ya gane nufinta, wato kada ya rinƙa taɓa Pretty har a kai ga kiss, ya gane in da ta dosa, sai ya miƙe kawai ba tare da ya sake yin magana ba ya nufi wajen abincin nasa. Miƙewa momma ta yi ta nufi waje tana sanya mashi albarka. Tana fita ta turo mashi Pretty, babu ko sallama ta afka mashi cikin ɗaki, alamarta ya gani ta wutsiyar idanunsa, bai ce mata ko uppan ba, a kusa da shi ta zauna tana kallan abincin. Tana zama ya kai hannu ya capki shoulder ɗinta haɗe da cewa. "Saboda na yi kissed ɗinki shi ne zaki kai karata wajen momma?". Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Saboda me zaka saka mun yawunka da babu zaƙi kuma babu daɗi? Kuma na goge bakinka da ya taɓa nawa tas, na tufar da yawun naka ma". "Da gaske?". Ya tambaya. Kai ta gyaɗa mashi alamar e tana yamutse fuska. Ɗan ciza laɓɓansa ya yi, alamar ya ji haushin abin da ta yi wai ta tofar da yawunsa kuma ta goge bakinta in da nasa ya taɓa. Hannunsa ɗayan yasa ya janyota jikinsa, da karfi ya matseta tare da kai ɗayan hannunsa ya matse mata ɗan bakinta, lips ɗinsa ya kai saman tata, sai da ya tsotsa son rana, sannan ya cika mata yawunsa sosai a bakinta, ya kuma matse hancinta yasa dole sai da ta haɗiye kafin ya saketa tare da ɗaukar spoon da nufin ya fara cin abincinsa, yawa wani irin sauke ajiyar zuciya, shi kaɗai yasan me yake cikin zuciyarsa!!. Kuka ta saka mashi mai sauti yana faɗin Allah ya isanta, ta yi maganar tana kai hannunta saman lips ɗinta ta hau gogesu dana dirzasu da karfi karfi. Shi kuwa abincinsa ya cigaba da ci ko a jikinsa, yana ganinta ta wutsiyar ido tana ƙoƙarin goge bakinta. Sosai ya ji daɗin hakan, koba komai ya haɗiye yawunsa sosai, har zata ce yawunsa babu daɗi ta tufar, to ai ga shi yanzu ta haɗiye. Miƙewa ta yi da gudu zata fita daga ɗakin, da sauri ya kai hannu ya rikota tare da mayar da ita ya zaunar. "Ina kika fita daga ɗakin nan yau ba sai gobe ba tare da tiger zaku kwana a ɗaki guda, in kuma kin ce ba haka ba fita ki gani". Ya kai karshen maganar tare da sake mata hannu. Kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi tare da kwantawa a saman carpet ɗin ta juya mashi baya. Banza da ita ya yi ya cigaba da cin abincinsa kamar bai san tana yi ba!. A can gefe kuma, uncle Abbas yana sanar da Mammien ya yi wa Sareena miji wato Smart, haƙiƙa Mammie ta ji daɗin wannan haɗi, dama burinsu kenan, yau zata zuba ruwa bisa ƙasa ta sha, har ta kira Sareena a waya a kan ta zo ta ji daddaɗar labari!!.. Shi kuma King yana nan damuwa sai kara ninkuwa a ransa take yi, ya yi zaton ya rufe sirrin da bawan da zai iya sani, ya aka yi Smart ya sani to?. Shi fa King a tinaninsa idan ya yi wa Smart aure shikenan zai koyi sanin darajan mutane da girmamasu, shiyasa ya nema mashi auren Sareena!. Kun san aure yana canza abubuwa sosai. A ɗayan ɓangare kuwa uncle Jahiz sai ƙoƙari shiga zuciyar Zee yake yi, while ita kuma ta rigada ta kamu da soyayyar Dr Raj, shi kaɗai take gani, dik in da uncle Jahiz zai je suna a tare da baby Ahmad, wato yaron Khadijah, yaro ya yi wayo yanzu, har rarrafe yake yi, Allah sarki mai keken napep ɗinsu dai ya samu sauki ya koma Nigeria, sun karɓu numbersa a zuwan idan sun dawo zasu nemesa su gana, uncle Jahiz ya yi mashi kyautar makudan kuɗaɗe. While shi ma uncle Abbas yana can yana fama da tinanin Khadijah a cikin kwakwalwarsa, yarinyar tana burgesa sosai. Ita kuwa Akka tana can tana fama da tashin hankali, dan King ya sanar da ita batun da ake ciki, dik yadda aka yi ita ma ta san wasu sirrikan da suke ɓuye. Mammie kuwa ta sako Mahnoor a gaba yanzu, burinta ta rabata da Jaish wanda banda wahalar da ita babu abin da yake yi dama, yana sonta, amma sai ja maga rai yake yi, yasata ta yi ta abubuwan wahala dik saboda iskanci irin nasa. Chuchu na can tana fama da jinya, dan har yanzu bata warware daga ciwon rashin Auta ba, Aneesa ma jinya take yi. Mama kuwa tana nan tana raba jaraba na wanna hali nata, ta ki yarda Smart ɗan King ne har yanzu, ta matsawa Ramish sai ya yi mata bincike, ya dai ce mata to kawai, dan shi ma yanzu abin da yake kansa kawai ya ishesa. A gefe guda kuwa, guyson da yake Dubai kullum sai ya kira Jaish video call ya ce ya haɗa shi da Mahnoor, idan ya haɗasu sai ya roketa ta haɗa shi da Mahreen, sai dai Mahreen ɗin bata karɓar wayar, sai Mahnoor ta rike mata suna hira, masifa take zazzaga mashi amma shi daɗi yake ji, Mahnoor tana yi mata faɗa sosai a kan masifar da take yi mashi, amma taki dai'na wa, ta ce ai ɗan iska ne shi, shi dai kome take faɗa murmushi kawai yake yi, dan burgesa take yi, kuma burinsa ya cika idan ya ganta. Daga gefe guda kuwa Sareena da team ɗinta ne suke ta shirya munafurcin da zasu yi wa Pretty. Ta ce su zuba mata Acid, Omaid ya ce. "Amma ke Aunty Sareena kanki baya ja, ai kina zuba mata acid ko zaki mutu cikin minti ɗaya Yah Omerish zai kamamu, hmmm baki san shi ba ko? Shegen kwarone in faɗa maki, yana ganin idonmu zai san mu muka aikata!. Ke da zaki kawo shawarar da zaki sanya ya tsaneta ko ta tsanesa! Baki san soyayya bako? Ai ko kin zuba mata acid idan sonta yake yi da gaske ba zai dai'na sonta ba, dan soyayya babu ruwanta da kyau or muni". Obaid ne caɓi zancen da cewa. "Haka ne, acid ba zai sa Yah Omerish ya rabu da ita ba, kuma wlh in dai acid ne zamu zuba mata to watan cin ubanmu ne ya tsaya, abin da zai sa ta tsane shi ko ya tsaneta shi zamu kirkira". KAI WATO GASKIYAR SMART, ƳAƳAN MOMMA BA DAI KAI BA, UHMM SU TWIN'S SHEGUN KWARI NE YARAN NAN, AKWAI BASIRA, A MAIMAKON SU YI AMFANI DA BASIRAR DAN TAIMAKO, SAI SUNA KARAR DA SHI A MUGUNTA DA SHIRYA TUGGU, KAI WAƊAN NAN YARA SAI SHIRIN ALLAH. Shiru Sareena ta yi, sai yanzu ta ɗauki haske da suka faɗa mata, cikin zaƙuwa da zan jin meyakamata su yi mata ta ce. "To ku bani idea, kai'na dik ya kulle, ban iya tina komai". Omaid ne ya ce. "Zamu faɗa maki abin da zamu shirya amma ba yanzu ba, bari mu yi tinani da shawara". ....... Sosai ta ji daɗi, dan bata taɓa kawo kukanta garesu basu share mata hawaye ba, shiyasa take sonsu, dan haka cike da murna ta bar ɗakin ta nufi part ɗinsu. Su kuma suna shiga tsara tsarin yadda zasu yi da Pretty ba tare da kowa ya ganosu ba!! ME KUKE TINANIN ZASU SHIRYA MATA?. ---------------------------------------------🔥🔥🔥 🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥 Wasu irin shegun kaya Big Bro ya saya masu, kayane da basu taɓa ganin irinsa ba, kuma iri ɗaya ne ita da shi, komai nasu iri ɗaya tamkar tagwaye, har takalma dik iri guda, sai dai na Ronnie takalmar akwai ratsin baƙi kaɗan a ta kasa, nata kuma babu, amma ban komai iri ɗaya ne. Wani irin daɗi da ta ji bata san lokacin da ta daka tsalle ta haye jikin Ronnie tana dariya ba, shima rungumeta ya yi yana murmushi, kayan sun yi fitina ba kaɗan ba, gown ɗin nan nata ba'a magana. Juyi da ita Ronnie ya fara yi a cikin ɗakin suna dariya gwanin birgewa. Lokaci guda kuma Ronnie ya dakata cak, a hankali ya sauketa ƙasa, saboda ya tina Floris, last year da ita aka yi shagali, yanzu kuma babu ita, take idanunsa da mood ɗinsa suka canza, wucewa ya yi ya sauna a gefen bed kusa da kayan. Sweetie sarkin basira ta gane me matsalarsa, ga kuma alkawarin da ta yi wa Big Bro na ba zata taɓa barinsa ya shiga damuwa ba. Da sauri ta matso kusa da shi. "Lovely bro!". Ta kira sunansa da ɗan sauti. Shiru bai amsa mata ba, tin da take a rayuwarta bata taɓa yin rawa ba sai yau saboda shi, playing na music mai sauti ta yi a cikin tvnsa, sannan ta riƙo hannunsa a kan ya tashi su yi rawa. Da farko tirge mata ya yi, amma da ta ja shi da karfi sai ya miƙe, jikinsa a mace ya fara, amma da suka yi nisa take ya mance da damuwa ya saki jiki yau suka taka rawa tamkar ba gobe, ashe ita ma ta iya, yi ne kawai bata yi dama. Dik abin da suke yi Big Bro yana kallansu, yana zaune yana shan green tea, ba karamin burgesa suka yi ba, sai ma indan suna tsaka da rawa Ronnie ya ɗagata sama ya ɗaura a saman wuyarsa, ta buɗe hannayenta kamar fanka ya fara juyi da ita suna sakin murmushi. Ronnie ya samu Sweetie ba kiba, ƴar caras sai ya yi ta ɗagata kamar ƴar tsana. Sosai suka sanyaya ran Big Bro yau. Buga karfe 7 dai'dai da agogo ya yi ne ya dakatar da su da abin da suke yi, lokacin sallah ya yi kenan, sauketa Ronnie ya yi tare da manna mata sumbata a kumatu, sannan ya ce. "My only sis much love one in million". Sumbatarsa ita ma ta yi kafin su haɗu tare su tattare kayan nasu suka je suka shirya shi a wajen da ya dace, sannan ta shiga toilet. Shi kuma ya haye bed yana jiran ta fito!!. AFTER SOME MINUTES. Zaune suke a saman bed yana koya mata yadda ake amfani da waya, dan ya ce zai saya mata mai kyau, ta mai da hankalinta gabaɗaya a kan abin da yake nuna mata, cikin sanyin murya ya ce. "Sis ina san kin mun karin bayani a kan tsafi da kuma yadda yayana yake kwace ƴaƴa maza daga hannun iyayensu ya sanyasu a cikin sojojin yaki a renesu a matsayin warriors, iyayensu basu da ƴancin morarsu ko kaɗan, dik warriors ɗin nan namu da kika gani ta haya Big Bro ya tarasu". Ya kai karshen maganar tare da kashe hasken screen ɗin wayar ya ajiyeta a gefe, dan karatu zasu yi. "Tsafi wannan dogon karatu ne, zan ɗauko maka tarihinsa daga farko ne yadda aka yi ya wanzu a duniya, shi kuma raba uwa da ɗaya wannan babban kuskure kuma babban laifi wanda Allah yana iya yi wa wanda ya yi hakan mummunar hukunci ko ya aiko mashi da bala'i mai girma". Natsuwa ya yi yana sauraronta, cigaba ta yi da cewa. "A cikin Al-Qur'ani mai girma ALLAH ya bayyana wahalar da uwa ke sha wajen samun ɗanta, wanda ke nuna girman soyayya da tausayin uwa ga ɗanta, dik wannan wahala ba zata taɓa tsanar wannan ɗa ba sai ma kauna da take yi mashi. Cikin suratul luqman sura ta 31 aya ta 14 Allah ya ce. Mun yi wa mutum wasiyya da mahaifiyarsa. Mahaifiyarsa ta ɗauke shi a cikin rauninsa da ƙari, kuma ta shayar da shi a cikin shekara biyu. Mun ce masa ka gode wa ni da iyayenka, zuwa gare ni makomar ku take, wanna yana muna maka girman uwa!!". "Kazalika cikin suratul Abasa sura ta 80 aya ta 34 zuwa 36 Allah ya ce. A ranar da mutum zai guji ɗan'uwansa, mahaifiyarsa da mahaifinsa, matarsa da ƴaƴans. Mafi girman mutanen da zaka ji zafin rabuwa da su kenan, shi ne yasa ake kwatance da su. Wannan yana nuna cewa a duniya soyayyar uwa da ɗa tana da matuƙar ƙarfi, har yana da wahala a raba su. Rabasu ma shi ne karshen zaluncin da bawa zai yi wa mata!!" "A cikin Bukhari Manzon Allah (SAW) ya ce. Lallai Allah yana jin tausayin bayinsa fiye da yadda uwa take jin tausayin ɗanta. Girman soyayyar dake tsakanin uwa da ɗanta babban abu ne da har Allah yake kwatance da shi Manzon Allah ma yake kwatance da shi. Wannan hadisi yana nuna irin ƙauna da kulawa da uwa take ma ɗanta, wanda idan aka raba su, yana da matuƙar wahala ga ita da yaron ma gabaɗaya". "Kazalika cikin tirmidhi Manzon Allah (SAW) ya haramta raba uwa da ɗanta, ku ji fa haramtawa ya yi, har ya ce. Dik wanda ya raba uwa da ɗanta, Allah zai raba shi da ƙaunarsa a ranar Alƙiyama, innalilahi wa inna ilahir, kaga kenan abin babba ne sosai!!". "Raba uwa da ɗanta abu ne mai matuƙar raɗaɗi, kuma addinin Musulunci ya hana hakan. Iyayen suna da haƙƙi a kan ƴaƴansu, kuma raba su ba tare da wani dalili na shari'a ba babban zalunci ne, gaskiya yakamata mu yi dik mai yiwuwa wajen dakatar da Big Bro daga raba ƴaƴa da iyayensu, idan ba haka wlh wata balai tana gab da afka mashi, saboda dik abin da ka ji Manzon Allah (SAW) ya haramta to ba kara mun abu bane". Ta kai karshen maganar tare da ɗago kallonta a kansa. Gabaɗaya mood ɗinsa ya canza, ya shiga damuwa jikinsa dik ya yi sanyi. Cigaba ta yi da cewa. "Batu a kan tsafi kuma wani abu ne da Allah ya la'anci masu yi, ba abu bane mai kyau, bari in ɗauko maka shi daga farko, a cikin suratul Baqarah sura ta 2 ayata 102 Allah ya ambaci Harut da Marut, wasu mala'iku ne guda biyu da Allah ya saukar zuwa ƙasa a zamanin Annabi Sulaiman (A.S) domin su jarabta mutane da ilimin sihiri (tsafi). A lokacin mutane da yawa sun fara amfani da tsafi don cutar da wasu, musamman ma dan raba miji da mata, ko dan cimma wata mummunar manufa nasu. Allah ya aiko da Harut da Marut zuwa garin Babila wato Babylon a Iraki, domin su gwada mutane da basu ilimin sihiri, amma kafin su koyar da wani, sai su ce masa. Mu fitina ne, kada ka yi kafirci. Wato suna faɗawa mutum cewa. Wannan ilimi ba domin amfani da shi bane. Mu kawai jarabawa muke yi kar ka yi amfani da shi zaka fita daga addini!!" "Yayin da mutane suka cigaba da karɓar wannan ilimi, da yawa daga cikinsu sun yi amfani da shi wajen cutar da juna. Allah ya nuna cewa wannan ba nufinsa bane, kuma wannan ilimin bai fito daga Annabi Sulaiman ba. Annabi Sulaiman bai taɓa yin sihiri ba! Kuma bai koyar da shi ba, shayatu ne suka buɗe ƙofofin tsafi ga mutane, sannan Harut da Marut suka kasance jarabawa ga masu raunin imani". "Amma a yau an canza maganar, mutane suna amfani da ruwayoyin israiliyat da suke cewa akwai Mala'iku guda biyu da suka bijirewa Allah har ya kawosu duniya, wanda nasan kai ma ka karanta wannan ruwaya". Ta yi maganar tare da dakatawa tana kallonsa. Shiru ya ɗan yi kamar yana tinanin shin ya karanta ne ko bai karanta ba?. (My people's kun san me? Wlh rubuta sunan israiliyat yana ban wahala sosai😅 wani lokaci sai na zo rubutawa sai in saka ilsiyat😅 kai ko karanta sunan akwai wahala, israiliyat😅) "Ka manta ko?". Ta jefa mashi tambaya, kai ya gyaɗa mata alamar e. "Ni ban manta yadda yake a rubuce a littafan yahudawa da kiristoci ba, bari in faɗa maka ko zaka tina. Cewa suke yi Harut da Marut sun faɗi wata jarabawa daga Allah, inda suka sauko duniya cikin surar mutume ba tare da izinin Allah ba. A ƙarshe, sun ci jarabawar, sun yi kuskure, sai Allah ya azabtar da su. Akwai labarai da ke cewa Allah ya zaɓi su su zaɓi azaba a duniya ko azaba a lahira, sai suka zaɓi su sha azaba a duniya. Wasu riwayoyin har suna cewa suna rataye a cikin rami a Babylon suna shan azaba har yanzu. Dan haka babu wani Mala'ika da ya saɓa maganar Allah, sai shaiɗan wanda girman kansa ya ja mashi, in short tsafi abu ne wanda Allah ya harabta shi gabaɗaya, ina fatan Big Bro ya dai'na". Ta kai karshen maganar tare da jan kumatunsa, ya yi shiru ya tsareta da kallo. "Sweetie waye ya baki magic to ke?". Yadda ya yi tambayar ka rantse da ALLAH ba shi ya yita ba. Ɗan zaro mashi idanu ta yi har sai da yaga kyallin idanun nata a idonsa. "Ni ma wlh ban sani ba, rana tsaka kawai na gansa, amma ina ga wanna ina zargin wani abin". "Kamar me kenan?!". Shiri ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Zan faɗa maka gaba, yanzu dai zo mu yi karatu, ina san ka koya mun wani karatu". Gabaɗaya mood ɗinsa ya canza, saboda ya ji bala'i zai iya saukowa yayansa, ba zai iya jurar hakan na, so hankalinsa a tashe. "Jeki ki kawo books ɗinki mu yi karatun". Ya faɗa yana ɗauko wayarsa zai duba time, so yake ya ga ko lokacin yin dinner ɗinsu ya yi ne. Saura 30 mins su ci abincin, dan haka yana da lokaci koya mata karatu, idan suka ci abinci kuma bedroom na Black Tiger zasu wuce su je su takurawa rayuwarsa da hira!!. ======🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 59 Tattaro takardunta ta yi ta dawo kusa da shi ta zauna, ajiye wayarsa ya yi, dik mood ɗinsa babu daɗi, ya ji matuƙar damuwa a kan yayansa, hankalinsa ya tashi, haka ya hau koya mata karatu cikin natsuwa da fahimta yadda zai shiga kwakwalwarta sosai. Tana bala'in son karatu sosai yarinyar nan, ga ƙwaƙwalwar tata kuma akwai ja ba karya. Sun yi nisa cikin karatun da suke sai jin voice ɗinsa ta yi ya ce. "Sis ranar kin ambaci yayana da sunan Fir'auna, kin ce zalincinsa kamar na Fir'auna wanenen shi Fir'auna ɗin?". Shi dai a dame yake, yana san a ce ga abu guda ɗaya da yayansa yake yi na kirki, amma babu, kome zalinci yayansa yake yi. Shiru ta ɗan yi tana tinanin a yaushe ta ce wa Black Tiger azzalumi Fir'auna kuma? Lallai ba shakka Ronnie yana kaunar yayansa sosai, wato dik abin da aka danganta yayansa da shi baya manta wannan abin. Can ta tuna a ranar da yake kona mutanen birnin da wuta, tabbas a wannan rana ta kirasa da azzalumi Fir'auna kawai, still a ranar da ya ce zai konata ita ma har ya kaita daji ya ɗaure, ba shakka a wannan rana ma ta kirasa bakin azzalumi kuma Fir'auna, lallai Ronnie, wato bai manta ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Ɓacin rai yasa na kirasa da wannan suna, amma ba haka bane, zalincin da yake yi ne ya bakanta mun rai"........ Yana rubuta mata wani note ya ce. "Okey Fir'auna azzalumi ne kenan? Shiyasa kika danganta shi da yayana?". Ya kai karshen maganar yana ajiye pen dake hannunsa, kai my people's Ronnie yana da very very good hand writing, wlh rubutunsa ba dai kyau ba!!. "E gaskiya Fir'auna azzalumi ne sosai, yayanka yana kwace yayan mutane ya mayar da su sojojin yakinsa dan ya tara runduna mai razanar da zuƙatan manyan masarautu, ya kuma yaki dik masarautar da yake so saboda karfin sojojin yaki, shi kuma Fir'auna yana kashe dik wani yaro namiji da za'a haifa a Masar, dan baya son a samu wani namiji da zai girma har ya kwaci mulkinsa, bokayen fadarsa ne suka shaida mashi da za'a haifo wani yaro daga cikin banu Isra'ila wanda zai tsigesa daga kan mulki ya mulki kasar, wannan dalilin yasa fir'auna yake kwace yaya maza yake kashesu, amma da Allah ya tashi nuna mashi shi Allah ya sha gaban tinanin ɗan adam, sai yasa fir'aunan da kansa ya reni Annabi Musa ɗin har zuwa girma, kuma ya yi sanadiyar hallakarsa, so yayanka bai da zalunci kamar na Fir'auna, ka kwantar da hankalinka, shi kuskuren da yake in da yake kwace ƴaƴa maza ya rabasu da iyayensu ya mayar da su warriors dan kawai ya zama mai karfin iko a duniya!!". Shiru ya yi yana kallon ɗan bakinta. "Har yanzu baki faɗa mun wanenen Fir'auna ɗin ba ai! Ni yanzu ban san waye shi ba da har yake kashe ƴaƴa maza!". .......... Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Fir'auna yana ɗaya daga cikin manyan sarakunan Masarawa, kuma Alqur'ani ya ambaci shi sau dayawa a matsayin mai girman kai da zalunci. Ya kasance mai mulkin kama karya wanda ya zalunci banu Isra'ila, yana da'awar cewa shi ne UBANGIJI. Amma a ƙarshe, ALLAH ya kunyata shi kuma ya hallaka shi a cikin ruwa. Ba'a taɓa tantirin ɗan iska biyun Fir'auna ba, kuma daga kansa ba za'a sake ba!! Fir'auna yasan gaskiya amma yake take sani, bakin munafuki ne azzalumi!, karfin mulkinsa ya wuci yadda kake tunani!!!". "Fir'auna yana da ƙarfi sosai a lokacin da yake mulki. Alqur'ani ya bayyana wasu abubuwa da ke nuna ƙarfinsa. A cikin suratu Zukhruf, sura ta 43 aya ta 51 ALLAH ya ce. Fir'auna ya ce. Ya ku mutanena! Ashe ba ni ne mai mulkin Misra ba, kuma ga waɗannan rafukan ruwa suna gudana daga ƙarƙashina? To shin ba kwa gani ne?" "Cikin suratul Qasas sura ta 28 aya ta 38, Fir'auna ya ce. Ya ku shugabanni! Ban san wani abin bauta wa gare ku ba sai ni. To ya Haman! Ka hura mini wuta a kan tubali, sa'an nan ka gina mini hasumiya, dan in iya hawa zuwa ga UBANGIJIN Musa. Kuma lalle ne, ina ganin shi mai ƙarya ne, innalilahi wa inna ilahir rajiun!!. Wannan yana nuna girman kai da alfaharin Fir'auna da mulkinsa, har yana isgili da cewa zai hau zuwa ga UBANGIJI dik dan ya nunawa mutanensa karfin ikonsa da isa wanda zai yi amfani da hakan wajen tilasta masu su bauta mashi!!" Cikin suratul Qasas sura ta 28 aya ta 4. ALLAH ya ce Lalle ne, Fir'auna ya yi girman kai a cikin ƙasa, kuma ya raba jama'arsa kungiyoyi. Yana raunana wata ƙungiya daga cikinsu, yana kisan ƴaƴansu maza, yana barin mata su rayu. Lalle ne shi mai ɓarna ne. Fir'auna ya bautar da Banu Isra’ila, yana tilasta musu aiki tukuru a matsayin bayi, zaluncinsa ma ba zai faɗu ba!" "Amma da yake ALLAH gafurur rahim ne, sai ya aiko Annabi Musa (AS) da wahayi dan ya kira Fir'auna zuwa ga gaskiya, amma Fir'auna ya ƙi. Cikin suratul Taha sura ta 20 aya ta 24 ALLAH ya ce. Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle shi ya ƙetare iyaka, kada ka manta Fir'auna shi ya reni Annabi Musa ɗin har ya girma, shi ne ma yasa ya rai'na Annabi Musa sosai, sannan Annabi Musa baya iya yin magana saboda harshensa a naɗe take bata fitar da magana, cikin suratul Zukhruf sura ta 43 ayata 52 Fir'auna ya ce. Ko kuwa ni ne mafi alkhairi daga wannan wanda ba shi da kimar magana, kuma kusan ba zai iya bayyana magana ba?. Fir'auna ya raina Musa saboda ba shi da harshen da ke fita da kyau, har isgili yake yi mashi a kan maganarsa!!" "Sannan Fir'auna ya kirawo bokayensa dan su fafata da Musa, amma Allah ya kunyata su. A zamanin Fir'auna sihiri ya kasance sanannen abu, kuma bokaye sun yi amfani da shi dan cin galaba kan Musa (AS). Fir'auna ya nemi su yi sihiri dan su nuna cewa shi ne mai iko, amma Allah ya nuna cewa sihirinsu ba komai ba ne. "Cikin suratul A'raf, sura ta 7 aya ta 116 da117 annabi Musa ya ce. Ku jefa abin da kuke jefawa. Sai da suka jefa sai suka sihirce idon mutane kuma suka razana su, suka zo da babban sihiri. Sai muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa. Ka jefa sandarka. Sai ga shi tana haɗiye abin da suka yi ƙarya da shi". "Cikin Suratul TaHa sura ta 20 aya ta 66 zuwa 69 ALLAH ya ce. A'a ku jefa. Sai ga igiyoyinsu da sandunansu suna ɗanɗanawa kamar su masu tafiya saboda sihiri. Sai Musa ya ji tsoro a zuciyarsa. Muka ce mashi. Kada ka ji tsoro! Lallai kai ne mafi rinjaye, ka jefa abin da ke hannunka, zai hadiye abin da suka aikata. Lallai abin da suka aikata sihiri ne, kuma ba zai yi nasara ba!!". "Waɗannan ayoyi sun bayyana cewa Fir'auna ya dogara da sihiri ne, amma Allah ya kunyata bokayensa ta hanyar annabi Musa (AS). Kuma kaga dik iskanci da girman kan nan na fir'auna?". Ta jefa mashi tambayar tana kallonsa, kai ya gyaɗa mata alamr e, nisawa ta ɗan yi kafin ta cigaba da cewa. "Dik iskancinsan nan yana bala'in tsoron mutuwa kamar ransa, ka lura, dik mai aikata laifuka wlh bala'in tsoron mutuwa ne da shi, bawan ALLAH baya tsoron mutuwa! Amma fa a lokacin da mutuwar ta riskesa sai ya yi ƙoƙarin tuba ya koma ga Allah, kaga kenan dama yasan ALLAH kenan". "Cikin suratul Yunus, sura ta 10 aya ta 90 zuwa 92. ALLAH ya ce. Mun tsallakar da Banu Isra'ila daga cikin teku, sai Fir'auna da sojojinsa suka biyo su da zalunci da girman kai, har da ruwan ya rufe shi, sai ya ce. Na yi imani, lallai babu abin bautawa sai wanda Banu Isra'ila suka yi imani da shi, kuma ni ma ina daga cikin musulmai. Allah ya ce. Yanzu? Bayan kuwa a da ka kasance mai ƙi, kuma daga cikin masu ɓarna? To yau za mu cece ka da jikinka, domin ka zama alama ga waɗanda ke zuwa bayanka, kuma lallai mutane da yawa sun kasance gafalallu daga ayoyinmu. Wannan ayar ta nuna cewa Fir'auna ya tuba ne a lokacin da ya ga hallaka, amma Allah bai karɓi tubarsa ba". Uhm dik iskancin mai iskanci ba zai taɓa kai Fir'auna ba, amma shi kansa da ya kira kansa da ALLAH da ya ji azabar fitar rai ya shaida babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH har ya yi ƙoƙarin tuba, wannan kawai bai ishi mutane ishara da su kama ALLAH gam du rike ba? Me kake nema a duniya da har zaka yi bautar mutum irinka ko wata dabba? Wai ni har Fir'auna ma ya shaida ALLAH ALLAH ne to kai kuma a suwa da ba zaka damki hanyar gaskiya ba! Ku duba iskancin Fir'auna a bayan kasa fa? Amma da yaga mutuwa har da su zuba! A wasu ruwayanma cewa suka yi Mala'ika ya toshe bakinsa ya hanasa tuba, amma ni wannan ruwaya ban tabbatar da ingancinta ba, abin da na sani daga Alqur'ani da ayoyinta shi ne ya ce ya tuba ya shaida ALLAH ALLAH ne kuma ya zama musulmi daga ranar, ALLAH yaki karɓar tubansa!!. Darussa daga rayuwar Fir'auna "Dik wani mulki ko iko ba shi da wani amfani idan ba ayi amfani da shi ta hanyar da ALLAH ya umarta da adalci ba. Girman kai da zalunci suna haifar da hallaka!!. ALLAH yana iya jarrabtar mutane da iko dan ganin yadda za su yi amfani da shi. Tuba tana da muhimmanci, amma idan mutuwa ta zo, ba za a karɓa ba!. Wannan shi ne tarihin Fir'auna a taƙaice daga Alqur'ani da binciken tarihi". Ta kai karshen maganar tana kallonsa!.... MASU KARATU DIK WANDA YA KARANTA NAN YA DAURE YA FURTA ASTAGFIRULLAH KO DA SAU UKU NE, TUBA TANA DA KYAU SOSAI, DAGA NAN A DAURE A JEFA TEEMA TAKU TA AMANA A ADDU'A KUN JI MY PEOPLE'S!. "Mu je mu yi dinner". Ta faɗa tana miƙewa................ Hakika ya ji a gaskiya lokaci ya yi da yayansa zai daina mulkin zalinci kada ALLAH ya hallakasa, yanzu ya fahimci zalunci bata da wata amfani face halaka mai muni!. Ganin bai amsa mata bane yasa ta ja dogon kyakkyawan shap nose ɗinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe ya sauko ƙasa. Ta fahimci halin da yake a ciki, dan haka sai ta ce mashi. "Kada ka damu, Big Bro ya kusa zama adalin sarki mai jin ƙan mutanensa, da zarar ya musulunta shikenan komai zai canza, kuma zamu yi nasara, ina jin hakan a jikina, ban taɓa jin cewa lokacin samun saukinmu ya gabato ba sai a ƴan kwanakin nan, tabbas da izinin mai dikka zamu yi nasara Bro". Sosai ya ji daɗin kalamanta har ya samu zuciyarsa ta yi sanyi ya iya cin abinci mai ɗan yawa, ba dan kalamanta ba da wuya yau ya iya cin abinci sosai, ko da suka je wajen cin abincin ma, suna ci tana jansa da tsokana tana kara kwantar mashi da hankali har suka kammala, sannan suka miƙe suka nufi bedroom na Black Tiger. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Zaune suke a cikin room ɗinsu ita da Leesharh, yanzu Leesharh ta samu abokan zama, wato Guyson and Auta, kullum suna tare, yanzu Ramish yana iya fita bata da matsala, dan akwai mahaukatan tsaron da Smart ya zuba masu tamkar ba zasu bar mutuwa ya shiga ya ɗauki ransu ba, ga jami'ai guda biyu dake gadi a cikin gida waɗan da suke parlour, ɗayan jami'in shi yake yi masu girki, so yana kasancewa ne a cikin kitchen, ɗayan kuma yana zama ne a parlourn kuma shi yake kai masu abinci har cikin bedroom ɗinsu idan sun buƙata, tsuhuwa ta dai'na yi masu girki sai dai ta yi wa kanta, a tinanin Ramish suna jin daɗin zama da tsohuwar ce ma shiyasa bai mayar da ita gidan Abbie ba! Yanzu tsohuwar burinta kawai taga ta bar wannan gida, dan a tsorace take kada asirinta ya tonu a kamata, tun ranar da ta ɗaura idanunta a kan Smart ta shiga tashin hankali da fargaba, abin dariyar kuma wai zuciyarta ta kamu da son Ramish matuƙa!!. ---------------------------------------🔥🔥🔥 Sai hira suke yi Leesharh da guyson, amma ita Auta tana zaune ta jingina kanta da jikin bango, hannunta riƙe da wayar da Smart ya saya mata sabo, ta fara warwarewa baiwar Allah, amma ba karya ta ji jiki matuƙa. Sai ƙoƙarin janta da hira suke yi amma taki kulasu. Wayar tata ce ta ɗan yi kara alamar shigowar sako, ɗan nisawa ta yi kafin ta kai kallonta a kan sakon. "My Queen yanzu kin manta da ni tsawon lokaci, na sha wahala kafin na samu numberki, meyasa baki nemeni ba? Ko dai yanzu baki san kalamaina ne?". Shi ne abin da yake rubuce a jikin sakon. Shin kun tuna lokacin da wani guy yake turo mata saƙonni? A lokacin da take tare da uncle Taheer? Kun tuna lokacin tin kafin ma ta fara soyayya ta zahiri da Hoorain! To wannan guy ɗin ne, kun san ta canza wayoyi har sau uku, shiyasa ya rasa numberta, sai yanzu ya samu sabon da Smart ya bata last week, kuma wannan sabon number mutane biyar ne kawai suke da shi. Daga Smart, Ramish, leesharh, guyson sai Jaish, ko Momma bata da shi, ko daga ina ya samo number? Ko da yake mai san abinka ya fika dabara. Siririn tsaki ta ja wanda yasa Leesharh da guyson dawo da kallonsu a kanta, har suna haɗa baki wajen tambayarta lafiya kuwa. Kai kawai ta girgiza masu alamar babu komai. Kallo juna suka yi, guyson ne yasa hannu ya karɓi wayar tata domin ya duba me ta gani take yi wa tsaki!. Daidai lokacin ɗaya daga cikin jami'an ya yi masu sallama a kofar room ɗin tare da shigowa. A tare Leesharh and guyson suka kai kallonsu a kansa haɗe da amsa mashi sallamar, ita kuwa Auta ta lumshe idanu tana san yin kuka, ta tina kalaman guy ɗin, idan baku manta ba a da can ta ce tana bala'in son kalamansa. "Akwai wani abin ne?". Guyson ya tambayi jami'in. With full respect ya ce. "Abinci ne is ready, in kawo maku ne?". Jinjina mashi kai guyson ya yi alamar e ya kawo. Juyawa ya yi cike da jarumta ya fice daga ɗakin. Miƙewa Leesharh ta yi tana faɗin. "Yah Omer bari in yi wanka kafin muci abincin". Da okey ya amsa mata, kofar bedroom ta nufa dan fita, har ta kai wajen muryarsa ya dakatar da ita. "Aunty Aesh kada ki manta da yi mun Nigerian tea anjuma fa". A miliyan ta juyo da kallonta a kansa. "Yah Omar wacece kuma Aunty Aesh?". Signal da gera guda ya yi mata kafin ya kashe mata ido ɗaya. "Kece Aunty Aesh namu mana, ko kin ɗauka ban san Yah Ramish ɗinmu na ƙoƙarin tsaraki kekuma kin ki bada haɗin kai bane? To ni narigada na bashi ke shiyasa ma nike kiranki da Aunty". Hararar wasa ta wurga mashi. "Ni Yah Ramish yayana ne kawai, bayan haka babu wani abin". Ta kai karshen maganar tare da juyawa zata cigaba da tafiya. "Uhm mun san komai fa Aunty Aesh, shiru kawai nike yi, sai wahalar mun da yaya kike yi, ya yi ta faman lallaɓaki yana san ganin kina farinciki, sai ki ta wani sha mashi kamshi kina nuna ke bakya sonsa bayan kuma nasan sonsa kike kamar hauka, dik ina ganinku ai, sai kuma na faɗa mashi kina sonsa kawai ja mashi rai kike yi". A miliyan ta sake juyowa dai'dai lokacin da ta kai bakin kofa. "Yah Omar fisabilillah a yaushe ka ji na ce ina sonsa ni?"........ Harara ya wurga mata shi ma tare da cewa. "Uhm me hotunansa suke yi a sabuwar wayar da ya saya maki? Wayar nan ko sati bata yi a hannunki na amma har kin cikata da hotunansa da kika rinƙa ɗaukarsa ba tare da ya sani ba, idan ya zo nan dik in da ya yi kallonki a kansa kamar yadda shi ma dik abin da yake yi yana satar kallonki, dik fa nasan komai, kawai idan zaki bada kai ki rungumo mun yayana ki kula mun da shi gara ki bada kai, idan ba haka ba kuma wlh basu mutuwar sonsa Allah ya yi yawa da su, kina ji kina gani wata zata kwace maki shi". MY PEOPLE'S KU TAFAWA KAIFIN ƘWAƘWALWA IRIN MA ƳAƳAN MOMMA, ASHE GUYSON YA HARBO JIRGINSU, YASAN KOMAI! Rasa bakin magana ta yi, dan ya faɗi komai, bata da wani sauran kalami. Auta ce ta katsesu da cewa. "Aunty Aesh ki ja ajikinki hai, rabu da Yah Omar ɗin nan, ki tabbatar kin wahalar da Yah Ramish kafin ki yarda, amma fa ki rinƙa yi mashi kwalele sosai saboda ya kara rikice maki yana cigaba da sunkuyar maki da kai yana neman amincewarki, ki wana shi ki ja mashi rai sosai". Cikin sanyin murya sosai ta yi maganar. Ba kara mun daɗi suka ji ba yau Auta tasa baki a maganarsu, har suna rige rigen amsa mata. Guyson ya ce mata. "Aww haka zaki ce ko Auta? Yah Ramish ɗin namu za'a wana, to sai na faɗa mashi!". Ita kuma Leesharh cewa ta yi "That's my lovely sis, shiyasa nike sonki, kin iya bada shawara, kanki na ja"................Ɗan yake Auta ta yi wanda aka ce ya fi kuka ciwo, cikin sanyin murya ta ce. "Yah Omar hakan shi ne maganinku, kai ma ai naga kana san wannan yarinyar da kake yawan cewa Yah Jaish ya haɗaku a waya, ina komawa gida zan hure mata kunne ta tabbatar ta baka wahala kafin ta amince maka". Kun san ita Auta bata san su Mahnoor ba, lokacin da suka zo kada ku manta ta tafi Paris, da ta dawo kuma tana cikin zulumi, ita totally bata cikin natsuwa, kunga ta ɓata zuwa forest, ta dawo ba jimawa ta wuce Paris, yanzu kuma tana nan Dubai, so bata san su waye su ba tukun nan!!. A fujaje ya zaro idanunsa waje. "Please my pleasure kada ki zuga Mahreen, wlh yanzu ma haka azabtar da zuciyata take yi, Chuchu na can ta kara lalata mun ita da banzan shawara, ki rufa mun asiri, yanzu haka ni a matsayin ɗan iska nike a idanunta"........... Zaro idanu Auta ta yi, a hanzarce ta ce. "Yah Omar ɗan iska kuma? Kai ɗin ne ɗan iska?" "No Auta, kome ya faru ni naja take kirana da hakan, kuma yarinya ce, so ba yadda kika ɗauka bane, manta ma da maganar waye ya turo maki wannan sako?". Ya yi maganar tare da nuna mata wayarta........ "Ban san wanenen ba ne". Ɗan jinjina kai ya yi kafin ya ce zai yi bincike a kan number ya ga wanenen, daga haka ya ciro wayarsa ya ɗauki number sannan ya miƙa mata nata wayar. Ita kuma Leesharh ta wuce ta nufi bedroom ɗinta. Wanka ta tsara a gurguje, ta shirya cikin wani haɗaɗɗen abaya mai shegen kyau, ta yi rolling veil a kanta, ta fito so Masha Allah, sai tashin kamshi take yi. Waje ta nufo cikin hanzari. Har zata koma wajen su Auta sai wani zuciya ya ce mata ta je ɗakin Ramish, haka kawai ta tsinci kanta da san zuwa can, wucewa ta yi ta nufi can tana jin gabanta na faɗuwa, Hasbunallahu wani'imal wakil ta furta a cikin zuciyarta kafin ta ƙarisa wajen door ɗinsa. Knowking ta ɗan yi dan a tinaninta kila yana a ciki. Sai dai kuma shirun da ta ji ba'a amsa mata bane yasa ta fahimci babu kowa a ciki. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya zata bar wajen, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi, har ta yi step biyu na taku sai kuma ta dakata tare da juyowa ta kalli kofar, a hanzarce tasa hannu ta tura kofar tare da afakawa ciki....... Shiru babu kowa sai sanyin Ac da niimantaccen kamshi dake tashi. Ajiyar zuciya mai ɗan sauti ta sauke tare juyawa zata fita. Unexpected ta hango kafar mutum a bayan labule wanda ko ba'a faɗa mata ba tasan kafar dattijuwa ce!. Mamaki ne ya kamata na ganin dattijuwa a cikin bedroom ɗin, wato knowking da ta yi a farko ne yasa ta farga ta ɓuye kenan, to me ya kawota ɗakin? Me take yi mashi a ciki? Shiru ta natsa cikin thinking ɗinta, can kome ta tina sai ta saki ƙayataccen murmushi tare da juyawa ta nufi waje. Bedroom ɗin ta murzawa key ta baya sannan ta nufi bedroom na dattijuwar. Bincike ta hau yi mata babu kakkautawa kamar an aikota, ta kuwa yi nasarar samun wasu hotuna na mutane daban daban. Sannan ta yi nasarar gano cewa wannan matashiyar budurwa ta jima tana son Ramish, hakan ba karamun daɗi ya yi mata ba ta samu hanyar tunzura tsohuwar nan har sai ta tona asirin kanta da kanta!!. Bata ɗauki komai a cikin ɗakin ba, sai dai ta yi snaping na wasu pic a wayarta, sannan ta mayar da komai yadda ta samu kafin ta dawo ta nufi bedroom ɗinsa, murza key ɗin ta yi ta buɗe, ba tare da tsoro ba ta shiga ciki, har lokacin dattijuwa na laɓe a bayan labule. Ciki ta shige tare da zama a gefen bed tamkar tana jiransa, da alama akwai abin da ta shirya a ranta wanda bata bawa kowa damar ya sani ba. Da zamanta a gefen bed ɗin da shigowarsa room ɗin dik bai wuce ratar mintuna biyar ba, tana jin motsin zai shigo ta yi gaggawar kwanciya tamkar wadda barci ya ɗauka, irin kwaciyar da ta yi kamar unexpected barci ya ɗauketa haka, ta dunkule waje guda. Sosai ya yi mamakin ganinta a room ɗinsa, har lumshe idanunsa ya ɗan yi ya sake warosu a kanta dan ya babbatar ba gizo mane ba!. Samun tabbacin hakan yasa ya sauke ajiyar zuciya tare da ƙarisowa ciki, ko kaɗan bai game dattijuwa tana cikin room ɗin ba!. Gaban bed ɗin ya iso, ɗan rage tsawonsa ya yi tare da sanya hannunsa ya gyara mata kwanciya da kyau, wlh har ya rame saboda damuwa a kan masu nikaf. A fili ya furta. "Ɗaukarki fa nazo yi Aesh". Ya yi maganar tare da zama a kusa da ita. A hankali ta ɗan motsa wai irin mai barci yana son farkawa ɗin nan! "Aesh". Ya ambaci sunanta a hankali. Sake motsawa ta yi haɗe da cewa ummm irin mutum a cikin barci ya ji an kirasa ɗin nan. "Zaki iya tashi yanzu ne ko dai in kyaleki sai zuwa gobe mu je?". Jin ya kira batun fita ta yi saurin sake cewa ummm, an ji yawo ba, har da juyawa wai irin ta farkan nan, ita ma fa Leesharh A ce wlh. Cikin dabara ta ɗan buɗe idanunta, a lokacin yana bin surar jikinta da kallo, yadda ta kwanta mashi a saman bed ɗin nan yau da ita mallakinsa ne da ta sha mamakinsa, ya kwaɗaitu da ita sosai yanzun nan, idanunsa a kan kirjinta da suka fito sosai saboda yanayin yadda ta kwanta. Ita kuwa ganin ba face ɗinta yake kallah ba yasa ta yi gaggawar satar kallon bayan labule, aikuwa nan ta ga dattijuwa tana leƙosu, ta ji daɗin hakan sosai, zata shaƙa mata bakinciki, a cewarta tin da ta gano yarinyar tana son Ramish soyayya na gaskiya to ba shakka da kishi zata amfani wajen sanyata ta tonawa kanta asiri. Mai da idanunta ta yi ta datse gam tare da juyawa ta ɗaura kanta a saman laps ɗinsa, irin wai tana gigin barcin nan. Har cikin zuciyarsa ya ji ta amsa, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. Hannunsa ya kai saman lallausan kumatunta, cikin sanyin murya ya ce. "Aesh zaki iya tashi kuwa?". Ya yi maganar idanunsa a kan shape na HP ɗinta, tin da ya shigo bai kalli idanunta bane da zai gane barcin karya take yi, gabaɗaya hankalinsa a kan surarta. Marairace murya ta yi irin muryar barci, cike da shagwaɓa ta ce. "Yah Ramish barci nike ji sosai amma ka tashe ni"............... 🤔🥱 "Sorry to cigaba da yin barcinki kin ji?". Kai ta ɗan girgiza tare da juyawa ta yi kwanciya ruf da ciki, dan ta ga ya kurewa kirjinta da HP ɗinta idanu, sai abin ya bata kunya sosai, kun san mu fa Nigerians da kunya aka sanmu, mu ɗin ma arewaci ne masu kunyar, so Leesharh dai da sauran kunyarta...... "Yah Ramish ai ka rigada ka kori barcin tin da ka tasheni". Ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa game da waro idanunta. Dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, dai'dai lokacin ta miƙe zaune tana kallon kasa. Kallo ɗaya ya yi wa idanunta yasan ba barci ta yi ba, ya ɗan yi mamaki, a ransa ya ce ko dai kewata Aesh take yi ne yasa ta zo bedroom ɗina ta kwanta da ta ganni kuma dan kada in ce me ya kawota shi ne ta yi acting kamar barci ne ya ɗauketa a wajen? Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya yi wannan tinani, sai ya ji daɗi, ko ba komai yau ta damu da shi. "Yah Ramish yaushe ka dawo?". Ta yi maganar tana bin ɗakin da kallo, wai irin ta nuna kamar bama ta san nan ta shigo ta kwanta ba. "Kai me yakawoni bedroom ɗinka kuma? Kai innalilahi barcin nan bai mun dai'dai ba!". Ya faɗa tana ƙoƙarin sauka bed ɗin, wai tana son nuna mashi barci ne ya yi mata yawa bata san nan ta shigo ta kwanta ba , dama bedroom ɗinta zata wuce sai gigin barcin ya kwasheta. Bata san ya gama gane komai ba, ya ganota. Binta da kallo ya tsaya yana yi, wai irin zata yi basajan nan, ta manta a gaban babban jami'i take!. Ganin ya yi shiru yana kallonta yasa ta yi gaggawar yunƙurawa zata sauka ta bar gadan tana ƙoƙarin danne murmushin dake san kubce mata. ANKAMA WATA TA YI KARYA..😅 Hannunta ya capko tare da janyota ta faɗa saman kirjinsa. Sai da dattijuwar nan ta ji kirjinta ya amsa, wani irin zafi ta ji a ranta, abin ya komata sosai. Kai kallanta a kan kafar dattijuwar dake leƙowa ta gefen labule Leesharh ta yi, nan ta ga matar ta matse yatsun kafafun nata a kasa, nan Leesharh ta gane abin ya ciza mata zuciya, bata so ba!. Cikin wani irin kasalallen murya ya ce. "Me kika zo yi bedroom ɗina?". Ya yi maganar tare da sanya hannun ya zame pil da ta kama veil da ta yi rolling a kanta......... "Ni fa Yah Ramish ban san cewa bedroom ɗinka na shigo ba, na fito daga wajensu Auta ne barci kamar zan yi hauka, shi ne na afko nan ban sani ba". Ta kai karshen maganar tare da dafa kirjinsa zata miƙe. Mayar da ita ya yi ta kwanta, veil ɗin nata ya cire ya ajiye a gefe, haɓarta ya ɗago ya zama suna fuskantar juna. Ɗan zuba mata idanu kamar na ƴan sakanni kafin ya ce. "Meyasa kike wahalar da ni ne Aesh? Meyasa ba zaki yarda mu yi aure ba?". Satar kallon kafar dattijuwar ta yi kafin ta ɗan kalli sama, nan taga tana lekansu bata dai'na ba, dawo da kallonta a kansa ta yi, sillent talk ta yi mashi ta hanyar motsa lips ɗinta, babu wanda zai iya fahimtar me ta ce mashi sai shi ɗin, a fili ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce. "In kuwa haka ne zan kasance cikin dakon wannan rana, sannan kuma a ranar zan baki kyakkyawar kyauta da na tabbata zaki ji daɗinsa sosai". Ya kai karshen maganar tare da matsar da ɗan bakinsa dap kunnenta, ya cigaba da cewa. "A wannan rana babu shakka ba zan kyaleki ba sai na yi round two, dan kin bani wahala sosai". Ɗago da kanta ta yi, a hankali ta kai ɗan bakinta saitin kumatunsa, zazzafar sumbata ta bashi wanda sai da ta sanya dattijuwar nan sakin labulen da ta rike ta ɗan yaye tana leƙansu, idanunta sun yi jajir sun cika da kwallah, wlh Leesharh ta iya tsiya. "Nima ina da kyakkyawar kyauta yau a gareka, amma idan na baka me zaka bani?". ME KUKE TINANIN ZATA BASHI?. Ai bai iya bata amsa ba saboda wani irin tayar mashi da hankali wannan sumbata tata da ta yi, ji ya yi tamkar wanda aka jonawa lantarki. Jin ya yi shiru yasa ta sake maimaita abin da ta faɗa tare da ɗan ɗago kanta da kallonta a kansa, tana ɗagowa bakinsu ya haɗe dan in baku manta ba ya kai bakinsa ya yi mata raɗa a kunne. Tana ƙoƙarin yin gaggawar zame kanta ya ce ina baki isa ba, ai rikota ya yi ya fara rage zafin da ta haɗa mashi, hot kiss ya shiga bata tare da cusa hannunsa a cikin kyakkyawar gashin kanta da ya sha gyara. Ai tsabar takaici dattijuwa bata san time ɗin da ta furta no ba, sai dai Ramish ya yi nisan da bai jita ba, amma ita Leesharh ta ji time da ta faɗa, hakan yasa ta kyalesa yana kissing ɗinta bata hana shi ba, sai ma hannu da ta kai ta rungumesa da kyau. Haba ai kara haɗa mashi zafi ta yi, ya matseta sosai a jikinsa, yana ƙoƙarin tura hannunsa cikin rigarta cikin fitar hankali sai aka yi knowking na door ɗin wanda hakan ya ja ta yi gaggawar kwace bakinta daga nasa. Idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kaman ɗan maye, murya kamar na ɗan maye ya ce mata. "Aesh please bayan kiss ba zan yi maki komai ba, please ki barni in kara kaɗan". Out of control yake maganar, idanunsa a limshe. "Yah Ramish knowking ake yi shiyasa". Ta faɗa tare da janyo vail tana ƙoƙarin maidawa kanta. Ɗan ciza lips ɗinsa gam ya yi, sai kuma ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa, sam bai so hakan ba. Miƙewa ta yi ta nufi door ɗin tana jin wani irin farinciki na musamman a ranta. Tana buɗewa suka yi four eyes da guyson. "Aunty Aesh ke fa muke jira ki zo mu yi lunch amma shiru tun ɗazun". Yana magana kallansa a kan Ramish da ya waro eyes ɗinsa da suka rikiɗa izuwa red sosai. A natse ta ce. "Muje to". Guyson yana zargin wani abin, dan ya ganta gabaɗaya a hargitse, amma bai ce komai ba ya juya da nufin su tafi. "Omar kuje ku yi lunch ɗin, fita zamu yi da ita". Muryar Ramish ya daki dodan kunnensu, ya yi maganar tare da miƙewa ya nufosu. Wucesu ya yi cikin sauri yana faɗin. "Aesh ki sameni a mota". Kallon juna suka yi ita da guyson kafin ta saci kallon dattijuwa, a ranta ta ce ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, yanzu masu nikaf zasu samu labarin hakarsu bai cin ma ruwa ba, sun so tagayyara rayuwarta, idan ta kammala aikinta su kasheta, idan kuma asirinta ya tonu su Ramish su kasheta, sai ga shi da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, su samu labarin soyayya ma take da Ramish ɗin, su san sonta yake yi kamar ransa, sai su mutu da haushi, rayuwarta bai tagayyara da suka yi fata ba!!. "Yah Omar bari in je". Hararar wasa ya wurga mata kafin ya ce. "Ina da meeting dake Aunty Aesh, sannan kada ki wahalar mun da yaya, ki yi mashi dik abin da yake so dan faranta mashi, na baki amanarsa". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya tafi. Bayansa ta bi da kallo har ya kurewa ganinta, siririn murmushi ta saki a ranta ta ce ta yi sa'ar ƴan uwansa masu saukin kai ne kuma suna kaunarta...... Ni kuwa ya ce tab lallai kuwa mafarki kike yi, dan kuwa a yaran King Auta da guyson ɗin ne kawai masu sanyin halin, uhm kada ki yi fatan shiga kingdom of power da sunan zaman aure kina matsayin bare, inai maki fatan idan Allah ya yi aure tsakaninki da Ramish ku yi zamanku a Dubai, idan ba haka ba mama kawai ta isheku bala'i, baku zasu karɓeki matsayin sirika ba!!. Bayansa ta bi tana cigaba da godewa Allah. A cikin mota ta iskosa zaune yana jiranta, gidan gaba ta buɗe ta shiga, kanta a kasa saboda kunyar sumbatar da ta yi mashi ɗazun, kunna motar ya yi ba tare da ya kalleta ba, kai tsaye suka nufi office ɗinsa. Suna tafiya tsohuwar nan ta yi gaggawar fitowa ta nufi bedroom ɗinta, idanunta sun yi jajir kamar wuta, har da guntun kwallah a face ɗinta, ranta ya ɓaci Leesharh ta yi mata taboooooooooooooo. TO! Ina mai farincikin sanar da ku cewa book ɗina mai suna MACE MAI DARAJACE, zai saukan maku da zafizafinsa very soon, wannan book ɗin na yisa ne kawai dan matan aure da kuma waɗan da suke gab da yin aure, ko zawarawa wanda ba aure zasu yi ba ban yarda su karanta mun littafi ba, ba novel bane, littafi ne da dan ma'aurata na yi shi, na jima ina tsara shi ina kuma tattara dik wasu muhimman abubuwa a cikinsa, book ne da ya haɗa komai da komai na rayuwar aure da sauransu, kada wata budurwa ta buɗe mun book tam!!! 2k yake, akwai sirrika kala daban daban a cikinsa, akwai kayan gyare gyaren abubuwa daban daban, kai baki ba zai iya faɗar abin dake cikin book ɗin nan ba, in kina buƙata kai tsaye ki mun magana, amma ba yanzu zan sake shi ba, saura kaɗan, idan na tashi sakansa zan sanar da ku!!. Amma dik mai so tin yanzu ta mun magana in san da ita, an zuba abubuwa a ciki, akwai salo kala kala sai wanda ya karanta zai gane, bana san buɗe me a ciki saboda kada na baku satar amsa, amma fa akwai abubuwa a ciki ba karya!!. IN SHA ALLAH RAYUWARKI ZATA CANZA KAMAR HAKA IDAN KIKA SAMU DAMAR MALLAKAR WANNAN LITTAFI KUMA KIKA YI AMFANI DA ABIN DAKE A CIKI!. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 60 Auta da guyson kuwa a tare suka yi lunch ɗinsu, Auta taki ci da farko, sai da guyson ya yi ta lallaɓata sannan ne ta ci. Shi kuwa Ramish yana yin parking motarsa a parking lot na h-c ɗinsu kan kace me wasu jiga jigan jami'ai sun kewaye motar, sosai Leesharh ta tsorata daga ciki, dan a tinaninta tin da taki tayasa aiki shi ne ya kawota su lallasata irin na wancan karan!. Zuba mashi idanu ta yi tana kallan yadda ya ɗaure fuska tamau tamkar hadari, abin sai ya yi mugun bata tsoro. Buɗe mashi door ɗin aka yi, ba tare da ya sake kallan in da take ba ya fito waje abinsa. Shiru ta yi a ranta tana tinanin ya zata yi? Sai gani ta yi an buɗe mata door na side ɗinta, kallon jami'in da ya buɗe mata ɗin ta yi, wani shirgegen balarabe ne mai tsawo da cikar halitta. Fitowa ta yi jiki ba kwari, tinanin irin azaban da jami'an nan suka bata a farkon karonta da su ne kawai ya faɗo mata a rai, tin da ta zo duniya bata taɓa shan azaba irin wanda suka gana mata ba, a lokacin har ji ta yi da sun bata wata dama kaɗan tsab zata kashe kanta ta huta!. Ta yi nisa a cikin tinaninta sai ji ta yi anja hannunta, almost 3 times yanayi mata magana bata ji shi ba, shi ne yasa ya kama hannunta kawai. Zaro idanu ta yi tana kallonsa tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, da ta san nan zai zo ba zata rakosa ba. Binsa kawai take yi tana karanta lailahaillah anta subhanaka inni kuntu minaz- zalimin, gabaɗaya jikinta kerma yake yi. Ya lura da ta tsorata sosai, hakan yasa ya yi ƙasa da murya sosai wajen cewa. "Aesh babu abin da za su yi maki fa, a yanzu wannan zuwan na daban ne, ba irin wanda kika yi a baya bane!". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa mashi da to, manya-manyan jami'ai guda shidda ne suke take masu baya har izuwa cikin office ɗinsa. Already mai zane yana zaune yana jiransu. Saman wani lallausan seat ya ce mata ta zauna. Ba musu ta zauna tana kallon office ɗin, ɗauko mashi wata chair dake kusa da table ɗinsa yasa aka yi aka kawo mashi kusa da ita, zama ya yi suna fuskantar juna, sannan ne ya ce. "Ki faɗa mashi fuskokin waɗan da kika sani daga cikinsu, dan gabaɗaya waɗan da kika ambata na bincikasu a gidan Abbie babu su". In baku manta ba dattijuwa tasa sun ɓoye shaidar da za'a iya kamasu da shi, so ya bincika bai iya kamasu ba, dan haka dole su kasance suna da zanensu. Ganaɗaya jami'ansa tsayuwa suka yi a bayansa suka binta da kallo suna jiran ta fara zayyano bayanai. Lokaci guda ya ji hakan ya kona mashi rai, a ɗan dakile ya ce da jami'an dik su fice mashi daga office, dan bai ga amfanin su tsaya suna kalle mashi ita ba, shi kaɗai zai ganta kuma ya ga zanen da za'a zana. Abin har murmushi yaso ya sakata, sai ta danne tare da cewa. "Yah Ramish ina tsoro sosai". ......... Hannunsa ya miƙa ya riƙo nata, cikin natsuwa ya ce. "Babu abin da zai faru kin ji? Please ki daure". Jinjina mashi kai ta yi tare da juyo da kallonta a kan mai zanen, cikin natsuwa ta fara bashi bayanan yadda suke a zahirance. Zanasu ya fara yi har da face mask na fuskokinsu, tana cigaba da yi mashi bayani yadda yakamata har suka kammala, bata yi kuskure ba sam sam, zanen ya fita sosai. Ana kammalawa kallo ɗaya Ramish ya yi wa zanen ya gano su wanenen daga cikin securitys ɗinsu, ya girgiza sosai da ganinsu, zubawa hoton zanen idanu ya yi yana kara tambayarta ta tabbata sune babu kuskure, kai ta gyaɗa mashi alamar ta tabbata. Nisawa ya yi kafin ya karɓi zanen, sannan ya cewa mai zanen ya haɗa kayansa ya je, already dama ya biyasa hakkinsa. Mai zanen yana fita Leesharh ta matsa kusa da shi. "Yah Ramish akwai abin da nike san faɗa maka fa, ko in ce akwai abin da nike san baka, amma dan Allah idan na baka kada ka tambayeni daga ina na samu ka ji?". Dawo da kallonsa tsam a kanta ya yi. "In Sha ALLAH ba zan tambaya ba". Ya faɗa yana sake riko hannunta cikin nasa. Wayarta ta fitar daga aljihun rigarta da ɗayar hannunta, kai tsaye ta shiga picks, hotunan da ta ɗauka a ɗazun bedroom na dattijuwa ta fitar, miƙa mashi wayar ta yi tana faɗin. "Dik waɗan nan suna da sa hannun a abubuwan da suke faru, and ka nemosu zaka samu dik abin da kake so daga bakunansu". Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, a ransa ya furta alhamdulillah almost 3 times, kai amma ya ji matuƙar daɗi, koba komai yanzu ya sami wasu da face ɗinsu yake a buɗe, a gaskiya Leesharh ta taimaka mashi, ya kuma ji daɗi, dole su nemo waɗan nan fuskokin. Cigaba ya yi da duba hotunan a tinaninsa zai ga wasu, sai kawai ya fara ganin hotunansa kala daban daban a cikin wayar, dik kuma bai sani ba ta yi ta ɗaukarsa, sun yi fitina hotunan ba kaɗan ba, saboda yadda ta ɗaukesu bai sani ba, kun san hoto idan baka sani ba aka ɗauketa wlh ya fi kyau, ba karamun daɗi ya ji ba, ɗago idanu ya yi ya kallenta, while ita ma shi take kallo. Suna haɗa ido ta yi gaggawar sunkuyar da kanta ƙasa. Matsar da kujerarsa dab da ita sosai ya yi tare da ɗaura hannunsa a saman shoulder ɗinta, ya kashe masu selfish mai bala'in kyau, murmushi ne ya subce mata tasa tafukan hannayenta ta rufe face ɗinta tana yin ƙasa da kai!. "Waye ya ce a saci mun hotunana ba tare da izinina ba?!". Ya faɗa yana janyota jikinsa. "Kai Yah Ramish ni da hotunan yayana kuma ka ce meyasa na sata? Yayana ne fa!". Ta faɗa tana cigaba da rufe fuska. Haɓarta ya ɗago. "Ni ban yarda da wannan wayan ba, kawai a bani amsar me ake yi da hotona". Ya kai karshen maganar tare da matsar da bakinsa saitin kunnuwanta. "Ko dan kinga kyakkyawan guy yaron mamarsa shi ne kika kyatsa kika kware mun e ƴan'mata?". Ɗan turo baki ta yi. "Ni ba wani kyatsawar da na yi". "Da gaske?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "To me kike yi da hotunana? Faɗa mun in ji!". "Ni babu abin da nike yi da su". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Masu sunanki suna mai daraja basa karya fa, faɗa mun gaskiyar me kike yi da su?!". Kara rufe face ɗinta da kyau sosai ta yi kafin ta ce. "Zuwa dare zan faɗa maka, amma yanzu please ka barci". Ɗan lumshe idanu ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Mu je gida ko mu je yawo?". Shiru ta ɗan yi, can sai ta ce. "Yah Ramish yaushe zaka kai ni gidan Abbie in ga ƴar uwata?". Take mood ɗinsa ta ɗan canza, alamar bai ji daɗin maganar bama, amma sai ya ce. "Ba yanzu ba, sai mun kammala binciken da muke yi, zuwanki gidan a yanzu babban haɗari ne sosai". Da zata ce ya kaita a yanzu, amma ganin ya nuna alamar rashin jin daɗi yasa ta hakura, sai ta ce su wuce gida kawai dan tana san kasancewa da guyson and Auta. Bai musa mata ba ya ɗauketa suka wuce wajen cin abinci mai kyau da tsada game da tsaro, daga haka suka wuce gida ya mayar da ita ya sake dawowa h-c ɗinsu dan su cigaba da bincike a kan wannan zane da ta basu game da hotunan waɗan can fuskokin!. 🔥🔥🔥🔥JIMETA🔥🔥🔥🔥 Ai tijara Nenne ta tsayar masu a kan ko sama zata haɗe da kasa yau sai bappa ya fitar mata da Mahreen, idan kuma ba haka ba zai ga jajjagen bala'i, banza da ita ya yi tare da wucewa ya shiga cikin gida abinsa, ransa fes tin da Mahnoor dai ta koma ga mijinta, yanzu damuwarsa a nan shi ne kewarsu da ya addaba mashi. Ɗakin Diddi Mairo ya wuce ya je ya kwanta a zuwan anjuma zai koma wajen kiwonsa. Yana cikin kwanciyar ne ya ji mutum a kansa, ɗago kai da zai yi sai ganin Nenne a tsaye da zabgegen wuƙa tana kaɗa ƙugu kamar sandar snooker a kan lallai ya fitar mata da Mahreen, cikin sauri ya miƙe zaune yana kallonta, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce. "Amma baki da hankali ko? Ko dai wani abin ne kika sha a yau?". Wata uwar harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Gaka babban mahaukaci kuma azzalumi! Ka sayar da ƴarka ga masu kuɗi, wlh sai ka fitar mun da Mahreen ko kuma in kasheka a cikin ɗakin nan, bakin shaiɗani kawai"....... Ransa ne ya yi mummunar ɓaci jin kalaman da take dangantasa da su, wai baƙin shaiɗani, cikin fushi ya miƙe tsaye suna fuskantar juna. Yau ya koma ainahin kalarsa, wani irin gigitaccen mari ya ɗauketa da shi wanda sai da yasa ta yi baya baya kamar zata faɗi ƙasa. Ranta ne ya yi mummunar ɓaci da yasa ta ɗaga wukar da gaske zata buga mashi a ciki, sai dai ina, kafa yasa ya taketa ta yi baya ta bugu da jikin bango ta faɗi kasa wukar ma ya faɗi ƙasa, sandar kiwonsa ya ɗauka ya hau jibgarta tamkar an saukar mashi da wahayi. Jin ihunta yasa Diddi Mairo shigowa ciki da gudu, hankalinta ne ya yi mummunar tashi ganin abin da yake faruwa, dama ita tasan shi da iya duka tun da ya yi ta jibgar mahaifiyar Mahnoor, so ta ɗauka ya dai'na ne, ganin hakan yasa ta kara shiga taitayinta, tsoron zuwa bashi hakuri ma ta yi, sai ta ja baya tana ruwan hawaye. Shi kuwa sai da ya tabbatar ya jiwa Nenne ciwo, sannan cikin fushi ya ce. "Ki tashi ki tafi gidan Arɗo na sakeki, kada in kara ganin kafarki a gidan nan!!". Ya kai karshen maganar tare da jefar da sandar ya nufi waje cikin fushin da tun bayan mutuwar maman Mahnoor bai sake shiga fushi irin wannan ba!. Rushewa Diddi Mairo ta yi da wani irin kuka mai tsuma zuciya, bata taɓa tinanin zai iya sakin Nenne ba, saboda auren gida ce, sannan kuma kanwa ce ga mahaifiyar Mahnoor, ai ko ba komai sirirkinsa Arɗo ya yi mashi halaccin da ba kowa zai iya yi ba. Amma kuma idan aka dubi tsawon shekarun da Nenne ta kwashe tana gana mashi azaba kowa yasan ya yi hakuri, kwata kwata bashi da kwanciyar hankali da ita, masifar yau daban na gobe daban, ga rashin zaman gida, bini bini tana yawon makota, ko girki bata zama ta yi mashi bare sauran abubuwan da yazamana hakki a kan mata ta yi wa miji, kai ya yi namijin ƙoƙari sosai da halinta dik da cewa shi kansa yasan alhakin maman Mahnoor ce yake bibiyarsa shiyasa ya haɗu da ukubar second wife, amma dai ya yi nadama ai!. Kasa miƙewa da kafafunta Nenne ta yi, da ta yunkura zata miƙe sai ta faɗi, hakan yasa Diddi Mairo ta matso ta taimaka mata, yau dai babu bakin masifa, bata hana Diddi Mairo taɓata ba, ita ta taimaka mata suka fita waje, zata kaita ɗakinta Nenne ta ce a'a ita gidan Arɗo zata wuce, dan tasan halinsa idan ya dawo ya sameta ba zasu wanye lafiya ba, kara mata wani azaban zai yi, dan haka gara ta tafi kamar yadda ya ce ya saketa ta tafi ɗin. Ba yadda Diddi Mairo bata yi da ita a kan ta zauna ba, amma ta ce ina babu wannan magana, haka ta lallaɓa ta yi ta bin jikin bango har ta isa gidan Arɗo da kyar. Allah ya taimaketa Arɗo na cikin gida baya waje a tare da jama'a, hakan yasa ta wuce ciki kawai. A tsakar gida ta isko iyayen nata goggonta na ta faman raba bala'in da ta saba, sai zage Inna take yi kamar an aikota. Ai tana ganinta ta nufeta tana tambayar lafiya kuwa?. Faɗawa jikin goggonta ta yi tana faɗin ai Kwairaga ne ya saketa bayan ya yi mata wannan ɗan iskan dukan. Salatin da Goggon tasa ne yasa Arɗo fitowa daga bukkarsa da azama. Yana ganin Nenne ya ja dogon tsaki tare da cewa. "To yau kuma wace bala'i kika je kika taɓo yar bala'i?". Take ta sha jinin jikinta ta natsu tsit, kukan ma haɗiye shi ta yi, cikin kamalarta with full respect ta ce. "Bappa ne ya sake ni kuma ya dakeni.........." Wani irin harara da ya dalla mata ne yasa ta yin gaggawar shanye sauran maganar game da haɗe malaman jikinta waje guda ta kara natsuwa. "Wato sai da kika tunzura shi ya sakeki ko? To ai ga gidan nan, sai ki zauna ki ci abin da uwarki take ci! Ke kuma tin da ba zaki ɗaura yarinyar nan kan hanyar gaskiya ba, sai ku cigaba da zama ki tasata gaba kina kallo!!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya koma cikin ɗakinsa. Cikin bala'i Goggo ta ce. "Lallai ma kam, ya dakar mun ɗiya ya kuma saketa shi ne baka ga laifinsa ba bare ka yi zancen ɗauka mata fansa kake wani cewa ita ce da laifi? To wlh ba zata saƙuba, idan kai baka san darajarta ba ni na sani, yau Kwairaga ba zai kwana da lafiyarsa ba, ke ɗauko mun mayafi in tafi in faɗawa su kawunki Iro da Ilu su zo su tafi su ɗauka maki fansa, ai ba daga saman bishi kika faɗoba, kuma ba kwaranyoki aka yi daga ruwan makwarara ba da wani matsiyaci can ɗan haure wanda bai gaji arjiki ba zai taɓa lafiyarki ya zauna lafiya, wane mutum, jini da tsoka ce ke gudana a jikinki kema, kuma rai ne dake, sannan iyayene suka haifeki!!". Ta kai karshen jajjagen bala'in tata tare da jan Nenne suka wuce ɗaki. Inna dai bata ce masu ko uppan ba, dan tasan ko ta faɗa ma ba ji zasu yi ba! Sai dai ma su hauta da balbalin bala'i, su sauke haushi a kanta! Shi ma Arɗo yana jiyosu, amma ko a kasar sillpers ɗinsa bugun China bai damu ba. Inna na tsaye a wajen goggo ta fito da mayafi fuuuuuu kamar wata haske ta wuce ta nufi waje, salati kawai Inna ta rinƙa nanatawa a ranta tana addu'ar Allah ya shiryi su goggo ta kuma shiga tsakaninsu da Bappa, dan tasan su Ilu mahaukata ne, tsab zasu illata bappa, shaye shaye suke yi, can cikin birni suka gano wani gidan giya, tun da suka san wajen a nan suke zuwa su sha su yi nakil har su yi guzuri, su dawo suna tangal tangal suna ashariya, ga shi giyar da suke sha ma irin na gero ne, uban aiki da caji kenan, haka suke hauka, Inna tasan ba hankali suke da shi ba, tsab zasu iya kashe bappa ba, hankalinta ne ya yi mummunar tashi sosai. A daidai wannan lokacin kawun Mahnoor Ibrahim ya shigo cikin gidan bakinsa a ɗauke da sallama. A buɗe kuma a gaggauce Inna ta yi kansa tana faɗa mashi ya je ya sanar da bappa ga abin da yake faruwa tun wuri yasan in da dare ta yi mashi kafin su Ilu su tattara zugarsu su je su yi masu illah. Sosai shi ma Ibrahim hankalinsa ya tashi, cikin gaggawa ya juya ya fita, sai addu'a Inna take yi na Allah ya kawo sauki a kan wannan al'amari, ita kuma Nenne tana ɗaki tana murzan kuka. TO KUN JI ABIN DA YA FARU A JIMETA BAYAN TAFIYAR SU MAHNOOR KENAN, SHIN A YANZU YA BAPPA YAKE? YANA RAYE KO SU ILU SUN KASHE SHI? NENNE TANA GIDAN ARƊO KO YA MAYAR DA ITA GIDANSA? INA DIDDI MAIRO? UHM TO MU JE ZUWA 🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥 Tsaye take a sama mai gabaɗaya tana kallon yadda duniya take, birnin ba dai wutar lantarki ba, 24 hours ba'a ɗaukewa, ko'ina tankar kamar rana ce, duniya dik ta yi shiru saboda dare da ya tsaya, iska mai matuƙar ni'ima ce take ta faman kaɗawa a wajen, shi kansa Ronnie ya jima da yin barci, ita kuwa barcin ne ya gaggareta ta hauro sama ta tsaya ko tsoro babu, kamar wata aljana, ba komai ya hanata yin barci ba face fargaba da tinanin zuwanta church gobe, abin ya tsaya mata a rai, ta duba Bibles ya fi sau goma, dik da ta tara hujojin tinkararsu, amma gabanta yana faɗuwa matuƙa, tana fargabar lamarinsu. Sanye take da sleeping dress wando zuwa gwiwa da riga nai ɗan madaidaicin hannu launin milk color, ta sanya headband a kanta mai shegen kyau, birnin yana da matuƙar kyau da ɗaukar hankali idan ka kallesa daga sama da daddare, gabaɗaya jikinta ta yi weak, tinaninta ɗaya shi ne ya zamanta da su zai kaya?. A hankali hankali iska yake kaɗa kyakkyawan golden hair ɗinta yana wani rito har yana dawowa ta gaba yana rufe mata idanu, da yake headband ɗin nata ɗan siriri ne wanda ya tsaya mata a iya forehead ɗinta. Ta luluƙa duniyar tinani sosai, sam bata ji alamar motsin mutum ba sai ji ta yi ya zuro hannunsa a daga ta bayanta izuwa saman shafaffen cikinta. Wani irin azabbabben tsoro ne ta ji ya kamata, ga shi dim light ne a wajen ba iya gane fuskar wanenen sosai zata yi ba. Da farko ta zaci Ronnie ne daga yanayin hannunsa a saman cikinta, amma da ta juyo sai ta ji wannan faɗin kirjin ya fi na Ronnie gaskiya. Kwata kwata bata kawowa ranta Big Bro bane, dan tasan is very very hardly ace yanzun nan bai yi barci ba, and kuma ko bai yi barci ba abu ne wanda ba zai yiwu ya taɓata haka kawai ba, sai dai tinaninta bai faɗa mata gaskiya ba, dan kuwa shi ɗin ne. Kasa barci shi ma ya yi, gabaɗaya tinaninta ne ya tsaya mashi a rai, tin daga kan yadda ya riketa da safe ya sanya mata chain a wuya, har zuwa karonsu ɗazun da yamma, kayan da ta sanya ɗasun sun ciza zuciyarsa sosai, ta yi fitina a cikin kayan, da zarar ya kwanta surar jikinta kawai yake tinawa, abin da bai taɓa ji ba a rayuwarsa wai feeling a kan mace sai yau, gabaɗaya ya rasa natsuwa da kwanciyar hankali, musamman kyakkyawan wuyarta da ya kawata mata da chain, wannan abin ya ciza zuciyarsa matuƙa ya hanasa sukuninsa, dik ya bi ya susuce lokaci guda, abin ku da bai taɓa ji ba, gabaɗaya sai yake jin kamar bashi da lafiya, jikinsa sam babu kuzari ko kaɗan, da kyar ma ya iya haurowa saman, ta magic eyes ɗinsa ya san tana sama, dama fadarsa zai nufa ko zai samu saukin abin da yake ji, sai ya haugota a saman, hakan ya kara ciza zuciyarsa da ya ji ba zai iya tafiya wani waje ba, dole ya kawo kansa gareta ba dan ya so ba!. Muryarta na rawa cike da tsoro ta ce. "Wa..... Wa... Waye ne?". Shiru babu alamar zai kulata.... WAYYO NI TAƁA KIƊI TAƁA KARATU KUMA TAƁA CAKWAKIYA DA TASHIN HANKALI, KAI JAMA'A, JIYA MUN TAƁA KARATU, SHEKARAN JIYA MA MUN TAƁA KARATU, LAST THREE DAYS AGO AN ZUBA CAKWAKIYA, YAU KUMA MUNA TAƁA AL'AMURA...😅 A tsorace ta sake tambayar wanenne? Ina ai tamkar babu shi a wajen, hakan yasa ta fara zargin ko shi ne, dan shi ne baya magana cikin kankanin lokaci idan yana waje, tin da take da shi ma ai bai wuci a kirfa time da ya yi magana a waje ba, tabbas zuciyarta ta fara zargin shi ne, dama tin daga kan yanayin Lion chest ɗinsa ta zargi hakan. Tana can tana ƙoƙarinta na gano wanenne unexpected ta yi hannunsa na yawo a saman cikinta yana ɓalle mata butiran rigarta. Waro idanu waje sosai ta yi tare da sanya hannu tana san taɓa kansa dan ta gane wanene? Tasan gashin kansa da na Ronnie akwai banbanci tin daga kan yanayin gyaran gashin. Bata iya kai hannunta kansa ba, saboda ratan tsawo dake a tsakaninsu, sai kuma ta yi hannunsa tsam a saman fatar cikinta alamar ya gama ɓalle botiran rigar. A yau idanunsa kawai tariyo mashi yadda mutanen birnin suke saduwa da juna yake yi, dik yadda suke holewarsu yana gani, amma bai taɓa jin wani abin a ransa ba ko kaɗan, amma yau da ta ciza zuciyarsa sai ga shi gabaɗaya tinanin yadda suke yi ne a idanunsa. Lokaci guda ya birkice ya fita a hayyacinsa. Jin abin na neman fin karfinta yasa ta fara ƙoƙarin ture koma wanenne tana san kwace kanta, aikuwa kara matseta a jikinsa da karfi ya yi tare da sanya hannunsa ya dagata gabaɗayanta sai saman Lion chest ɗin nasa, yana tsaye a kan ƙafafunsa yana wani irin numfashin da bai taɓa makamancinsa ba, yau ya ga bala'in da bai taɓa shiga cikinsa ba ko da wasa. Cikin zafa ya kaiwa ƴan matasan tula tulanta capka, dama iya rigar ce a jikinta, babu ko ƴar vest daga ta ciki, hakan yasa yana ɓalle botiran ya samu damar bayyanarsu waje!. Wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali lokacin da ya capkosu, lokaci guda kuma ya ɗauke wuta na ƴan sakanni saboda wani irin azabbabben daɗin da ya ratsa zuciyarsa wanda bai taɓa jin irinsa ba, yau yadda kuka san ya sha wani abin! ALLAH da dik bai san wannan abin ba, bai taɓa sanin me mutanen birnin nan suke ji idan suna aikatawa ba, bai taɓa sanin meyasa master Devil ya nacewa wannan jaraba har bai bar mata da maza ba, da kowa yi yake yi, so dik bai taɓa sani ba. WANDA YA FAHIMCI ADDU'AR SWEETIE TA YI TASIRI A KAN SHARRIN DUNIYAR SHAIƊANU YA CE ALLAHU AKBAR! YAU BIG BRO YA JI FEELING MAI ZAFI! Ya ilahi ya lillahi, ai Sweetie bata san lokacin da ta kware baki zata zunduma mashi ihu ba, dik da cewa a yanzu ta gane cewa shi ne!. A cikin wani irin zafan gaske ya haɗe bakinta da nasa ya hanata yin ihun, jikinsa na wani irin kerma kamar mazari, gabaɗaya tsuma yake yi, har wani irin zufa yake haɗawa. Wani irin hegen daɗi ne ta kai mashi har tsakar ka saboda ya ji sugar kiss da bai taɓa ji ba a rayuwarsa. Ita dai Sweetie ta ɗauke wuta diff kake ji, ta ji abin da bata taɓa ji ba ita ma, dikkansu ne yau ne farkonsu a wannan sabga. Sai wani irin gurnani yake yi tamkar mayinwacin zaki, still kuma yana tsaye ko alamar gajiya bai yi ba, gabaɗaya ilahirin jikinsa ya sauya, tana a kan Lion chest ɗinsa yake sarrafata ta hanyar da shi kansa bai san yasan hanyar ba, bai san ya aka yi yasan da hakan ba! Gabaɗaya ya susuce ya fita a hayyacinsa, while ita kuma ko motsi bata sake yi ba, tamkar sumewa ta yi!!. TO INA IYAYEN SWEETIE? YANZU FA BIG BRO YA FARA JIN FEELING, SAI KU SAKA IDANU A KANTA TIN KAFIN TARBIYYAR DA KUKA BATA YA SAMU TANGARƊA!!. DAN DAI KUN SAN BA KYALETA ZAI YI BA TIN DA YA FARA FEELING, BARE KUMA YANZU DA YA JE DUNIYAR MERCURY YA JI ABIN DA SU MASTER DEVIL SUKE JI! UHM ALLAH KA BARMU DA IYAYENMU, DA YANZU MOM TWIN'S TANA NAN FA DA SWEETIE BA ZATA ZO NAN BA HAR WANI ABIN YA FARU, GASKIYA RAYUWA BABU UWA AKWAI CIWO SOSAI, AKWAI KUMA KALUBALE, LALLAI BA SHAKKA UWA BABBAN BANGO CE, LALLAI UWA ITA CE RAYUWARMU, ALLAH KA BARMU DA IYAYENMU, KA BAMU IKON TARBIYANTAR DA ƳAƳANMU KUMA!. KU DUBA YADDA RAYUWAR TWIN'S PRETTY AND SWEETIE YAKE SABODA RASHIN UWA! KOME ZAI FARU KI DAURE KADA KI YI NESA DA ƳAƳANKI MUSAMMAN MA MATA, ALLAH MA YA TAIMAKESU MOM ƊIN TASU TA TSAYA TSAYIN DAKA WAJEN NASU ILIMI KAFIN TA RABU DA SU, UHM GA KARANCIN SHEKARU!.......😥 TO! Ina mai farincikin sanar da ku cewa book ɗina mai suna MACE MAI DARAJACE, zai saukan maku da zafizafinsa very soon, wannan book ɗin na yisa ne kawai dan matan aure da kuma waɗan da suke gab da yin aure, ko zawarawa wanda ba aure zasu yi ba ban yarda su karanta mun littafi ba, ba novel bane, littafi ne da dan ma'aurata na yi shi, na jima ina tsara shi ina kuma tattara dik wasu muhimman abubuwa a cikinsa, book ne da ya haɗa komai da komai na rayuwar aure da sauransu, kada wata budurwa ta buɗe mun book tam!!! 2k yake, akwai sirrika kala daban daban a cikinsa, akwai kayan gyare gyaren abubuwa daban daban, kai baki ba zai iya faɗar abin dake cikin book ɗin nan ba, in kina buƙata kai tsaye ki mun magana, amma ba yanzu zan sake shi ba, saura kaɗan, idan na tashi sakansa zan sanar da ku!!. Amma dik mai so tin yanzu ta mun magana in san da ita, an zuba abubuwa a ciki, akwai salo kala kala sai wanda ya karanta zai gane, bana san buɗe me a ciki saboda kada na baku satar amsa, amma fa akwai abubuwa a ciki ba karya!!. IN SHA ALLAH RAYUWARKI ZATA CANZA KAMAR HAKA IDAN KIKA SAMU DAMAR MALLAKAR WANNAN LITTAFI KUMA KIKA YI AMFANI DA ABIN DAKE A CIKI!. KADA KU MANTA BAFA NOVELS BANE, LITTAFINE DAI NA..............🤫🥱 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍 ======🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 61 Wani irin iska mai bala'in karfi da ya daki windows ɗin bedroom ɗinta ne yasa ta farka a haukace daga nannauyar barcin da ya ɗauketa, gabaɗaya face ɗinta ya yi sharkaf da gumi, wannan mafarki ya jijjigata. Lokacin guda ta ga wan irin iska mai bala'in karfin gaske ya banke windows ɗinsu gabaɗaya ya rugujesa ƙasa, datse idanunta da karfi ta yi, take ta ji room ɗin nasu ya fara jujjuya mata tamkar fanka yana wani irin rugugi, DUNIYAR SHAIƊANU ne suka kawo mata ziyara dan kawai ta yi mafarkin Autansu na soyayya, bala'i can Black Tiger fa ba zai taɓa yin soyayya ba sai wani ikon ALLAH, mafarki kawai Ronnie yake yi da ya ce yana fatan yayansa ya faɗa sonta, amma burin Ronnie ba mai cika bane, dan ba zasu taɓa barin Black Tiger ya yi soyayya ba, Autan ruhohi ba zai taɓa samun rauni ko tawaya ba, bakar zuciyarsa da zaluncinsa suke so, kuma su kansu sun san Black Tiger yana da zuciya mai kyan da idan ya bar tafarkinsu za'a ji daɗinsa, amma ina ba zasu taɓa barin hakan ya faru ba. Dirowa kasa daga saman bed ɗinta ta yi, da gudu ta nufi hanya fita dan ta gudu bedroom na Ronnie tana ƙoƙarin yin ihu sai dai voice ɗinta yaki fita sosai, a razane ta fara ƙoƙarin ɓalle kofar bedroom ɗin nata ta fita amma ina abin ya ci tura, ta gagara buɗewa, an datse kofar da karfin gaske, juyawa ta yi tana kallon yadda guguwar nan yake dinfaro cikin room ɗinta, gabaɗaya ilahirin jikinta ɓari yake yi, idanunta sun yi jajir saboda barcin da yake a kanta wanda bai isheta ba. Wasu irin muryoyi masu karfi ta ji a cikin guguwar ana magana da wasu yarukan da ko kaɗan bata taɓa jinsu a duniya ba, hankalinta ne ya kara tashi matuƙa. Gadan gadan guguwar ya nufota yana dunkule waje guda yana fitar da kalar wuta daga cikinsa ga hayaki. Hannunta ta sanya ta kare fuskarta tare da furta lailaiha illah anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, hasbunallah wani'imal wakil. Lokaci guda ta ji an taɓa jikinta, a gaggauce ta zame hannunta daga saman face ɗinta tare da waro idanunta waje. Nan ta yi arba da kyakkyawan face ɗin Ronnie yana tsaye, idanunsa dik barci, gashin kansa a watse kamar wani mahaukaci sabon kamu! "Sis lafiya kike ihu haka?". Ya jefa mata tambayar cikin muryar barci. A miliyan ta kai kallonta bayansa dan ta duba guguwar. Juyawa ya yi shi ma ya kai kallansa wajen, wayam babu kowa, INA GUGUWAR?. Windows ɗinma a datse suke gam. A tare suka dawo da kallonsu a kan juna. Ɗan girgiza kai ya yi. "Akwai wani abin ne". Ya yi maganar idanunsa suna washewa daga barcin da yake yi. Haka kawai ta tsinci kanta da ƙasa faɗa mashi abin da ta gani da irin mafarkin da ta yi, sai ta ce mashi babu komai. Ɗan zubawa face ɗinta idanu ya yi yana kallon irin razanar dake a kan fuskar tata, sai kuma ya ɗan juyar da kallonsa izuwa in da ta kurawa idanu, a cikin zuciyarsa ya fahimci akwai wani abin, dole wannan ihun da ta rinƙa zundumawa wani abin ta gani, amma sai ya ce mata. "Muje ki kwanta in tayaki ki yi addu'a babu abin da zai faru In Sha Allah". Shi da yake bai san da batun Duniyar Shaiɗanu ba, sai ya zaci ko dai yayansa ne ya razanata ta hanyar magic, so yasan ba zai cutar da ita ba shiyasa ya ce su je ta kwanta. Ba musu ta bisa ya rakata wajen bed, kwanciya ta yi tare da fara karanto addu'oi, shi ma addu'oin ya tayata karantawa waɗan da ya iya, ya shafa mata sannan ya ja mata bargo tare da miƙewa ya nufi bedroom ɗinsa dake manne da nata. Tana kallonsa bata iya ce mashi ko uppan ba, tamkar an ɗaure tongue ɗinta har ya fice. Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyar da kallonta tana kallon windown, tamkar ba windown da ɗazun ya ruguje ba, to me yake faruwa da ita ne?. Ta jefawa kanta tambaya, ni kuma na amsa mata da kin fara shiga sabgar Duniyar shaiɗanu ne ta hanyar ƙoƙarin sauya masu Auta, dole su yi tattaki dan daka maki zazzafar warning, ai ke yanzu rayuwarki tana cikin gagarumin haɗari mai karfin gaske, dole ki dage da addu'a tare da fatan Allah ya raba Black Tiger da duniyar shaiɗanu, dan kuwa shi kaɗai ne zai iya tsaya maki ya kwaceki daga hannunsu, gara ki yi addu'ar ya fita daga makircinsu, idan ya fita, zai fitar dake kema!!. My people's dik yadda aka yi Sweetie and Ronnie suna da alaƙa ta jini mai karfi gaske, saboda irin tsananin kaunar da suke yi wa junansu, sannan idan kuka yi duba da yadda Ronnie zai rungumi Sweetie, ya bata hot sumbata, ita ma zata rungumesa, amma ko kaɗan basa jin feeling ɗin juna, hakan ya nuna akwai jini mai karfi a tsakaninsu, Sweetie ta fi Floris kyau da komai da komai, amma meyasa Ronnie baya feeling soyayya a kanta sai a kan Floris? Blood is thicker than water gaskiya, dik yadda aka yi suna da alaƙar jini mai karfi, za dai muga ta ina wannan alaƙa zata fito gaskiya, ko da yanayin yadda na faɗi Ronnie zaku san yana kama da Sweetie sosai. Da kyar barci ya ɗauketa, shi ma sai can wuraren asuba haka. Shi dai Black Tiger dik wannan bidiri da ake yi bai da labari, yana can hankalinsa a kwance yana barci, Sweetie na can tana mafarkin ya shanye mata baki!. 🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥 Fitowa ta yi daga cikin toilet ɗinsa ɗaure da towel a chest ɗinta, yanzu kwata kwata ta dai'na fita waje, kusan a cikin bedroom ɗinsa take wuni, saboda takunkumin da ya sanya mata, yana tsoratar da ita. A maimakon ta sanya kaya anjikinta, sai ta faɗa saman bed ɗinsa haka nan tare da minginawa ta ƙudundune jikinta a cikin bargo, lokaci guda ta saki siririn murmushi tana kallon sama, yau wani irin nishaɗi na musamman take ji! Kamar ba Pretty tamu ta zamani ba!. Ta yi nisa a cikin halin da take sai ganin mutum ta yi a saman bed ɗin yasa hannun yana ƙoƙarin janyo bargon da ta rufe jikin nata da shi, ƙoƙarin hana shi ta yi ta hanyar juyawa, sai shi kuma ya matsa ya yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa. Turo baki ta yi kafin ta ce. "Ni banaso, dan Allah kada ka taɓa mun bakina". Harara ya dalla mata kafin ya sanya hannu ya janye bargon kasa gabaɗaya, ya rage daga ita sai towel ɗin da ya haura sama gabaɗaya santala-santalan cinyoyinta a waje!. Jan dogon numfashi ya yi tare da saukewa a hankali, hannunsa ya ɗaura a saman cinyar tata ya ɗan shafa tare da lumshe idanu alamar abin ta kai mashi karo!. Me kuke kallah my people's? Na ce me kuke kallah a nan? Maza ku ware! Matarsa yake latsawa ba kowa ba, dan haka bamu san sa ido. Kwarai kun jini da kyau matarsa na ce!! Ya aka yi tazama matarsa, na san tambayar dake ranku kenan, ku bari idan lokaci ya yi zaku san yadda aka yi, babu wanda yasan matarsa ce sai ni, shiyasa nima na sanar da ku, ko momma fa bata sani ba wlh, ita kanta Prettyn bata sani ba, amma tabbas matarsa ce ta sunnah ma kuwa, ɗan rainin wayo shiyasa yake abin da yaga dama da ita, momma ta tambaya kuma ya ce wai ba haka ba, wai my people's a ina kuke har Smart ya mallaki Pretty baku sani ba? Gaskiya ba zan sake bari a yi maku rufa rufa ba, zan rinƙa buɗe maku kun ji ai!. Uhm King yana can yana nema mashi auren Sareena, shi kuma ya yi son ransa da ƴar babyn matarsa mai sakalci da shirirta, ga Mom ta tsaya nema mashi auren Heleena, dik ashe ya manna masu hauka ne, zaɓin Mommarsa ya ɗauka ya rabu da King and Mom, Smart ya cika ɗan halak mai son farincikin mahaifiyarsa mai kuma bin umarninta, ta umarcesa a kan Pretty kuma ya bi, surprise yake san yi mata mai zafi shiyasa yaki faɗa mata cewa matarsa ce, amma ya kuke tinanin King zai karɓi wannan al'amari? Shin zai yarda kuwa? Kada ku manta ya rigada ya karɓa mashi auren Sareena fa!.... QUEEN OF SURPRISE NIKE, yau ma na tashi kanku da batun auren Smart and Pretty, ko ya hakan ya kasance, amsar zaizo maku daga bakinsa a time da yake sanar da Mommarsa, uhm akwai kallo fa! Bala'i Pretty bata san cewa ita ɗin mallakinsa bace!!!. Yunƙurawa ta yi zata miƙe ta bar wajen, hannu ɗaya yasa ya mayar da ita ya kwanta tare da kai hannu zai warware towel ɗin, dik iskanci da rashin jinta ashe tasan suturta tsiraici, a miliyan ta sanya hannu ta damki towel ɗin nata tana ƙoƙarin zunduma mashi ihu. Cikin sanyin murya ya ce. "Kina buɗe baki zan kira Tiger, kuma ki cire mun hannunki daga wajen". Shiru ta yi tana girgiza kai ta fasa yin ihun, saboda tsoron Tiger yasa ta zame hannunta daga rikon da ta yi wa towel ɗin, take idanunta suka ciko da hawaye. Banza ya yi da ita tamkar bai ga hawayen ba, cikin natsuwa ya sanya hannu ya warware towel ɗin gabaɗaya ya yi mata zindir. Tsabar tabbatar duniyanci irin na Smart sai yasa hannunsa yana kewaye ƴan matasan tula tulanta yana kallon face ɗinta. "You toooooooooo small for me! Shekarunki nawa?". Ya yi maganar yana mai da hannunsa saman lipa ɗinta. Hawaye ne suka fara gangarowa a idanunta, kun san dik yadda mace take da san bayyana tsiraicinta wlh a lokacin da tula tulanta suke tasowan girma ta tsani a kallan mata su, amma saboda iskanci irin nasa, ya san da hakan sarai, kawai dan ya bakanta mata rai ne ya buɗe mata su. "Mena yi maki da kike kuka?". Ya faɗa a ɗan kausashe. Wai a cewarsa yanzu zai reneta ne sai ta girma, amma kunga ɗan rainin wayo yana shanye mata baki, daga reno kuma ana ta...............🤫 Kai ta girgiza mashi alamar babu abin da ya yi mata. "Baki da bakin yin magana ne?". Da kyar ta iya ce mashi tana da shi. "To idan na sake yi maki magana kika amsa mun da kai ba ki buɗi baki kin yi magana ba sai na yi maki irin ta jiya". Tana ruwan hawaye ta ce to. Munahiki har cikin ransa yake jin sugar kallan surar jikinta, amma saboda iskanci wai renonta zai yi, gabaɗaya hankalinsa a tashe fa yake, dik abar ta motsa, har idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kamar wuta, yana wani ciccijewa. Uhm to malam Smart mun dai san komai! A dai'na wani shassha mana kamshi ana wani ɗaɗɗaure mana fuska. (Kambalai kun san me na tina? Yadda haɗuwar Pretty and Heleena zai kasance, ga Sareena a gefe, yadda Heleena ke mutuwar son Smart anya akwai zaman lafiya kuwa? Ga shi su turawa mata ɗaya suke yi, idan Heleena ta san ya yi aure shikenan tasan ba zai kara wata mata ba sai dai idan kashe Pretty zata yi sai ya aureta, akwai badakala! Pretty dake son Kamran kuma shi aka bata ya kuke ganin wannan bidir zai faru idan tasan ita matar wani ba Kamran bane?!) A gefe guda kuwa Zee ce zaune a main parlour na ƙasa a party ɗin Aunty MieMie, tana shirye cikin abaya mai shegen kyau launin dark purple, ta yafa mayafin a kanta, ta yi matuƙar kyau sosai. Tana zaune saman kujera mai zaman mutum uku, shi kuma Dr yana zaune a saman kujera mai zaman mutum biyu suna fuskantar juna. Sanye yake da ƙananan kaya masu kyau da tsada. Zee tana rike da baby Ahmad yaro mai wayo kuma bai lafiya, yana girma yana ƙara kyau kamanninsa da familyn Akka yana ta kara bayyana! Ya fi kama da uncle Jahiz sosai, sai dai banbanci yanayin zanen face ɗin baby Ahmad sak Korean face ne, kazalika yanayin haskensa, ya fisu haske nesa ba kusa ba!. Ta yi ƙasa da kanta tana jin kunyarsa, sai zuba mata love word yake yi babu kama hannun yaro, Zee ta faɗa dayawa fa!!. A gefe guda kuwa, Mahreen ce rike da wayar Momma suna waya da guyson, ya ci sa'a yau momma ce ta bata wayar shiyasa ta karɓa, ba dan haka ba ta ce ta wuce class ɗinsa, kai Mahreen duniya, wai ta wuce class dinsa, ai Aunty Chuchu ta ce mata ai ita matar manya ce ba ta yara ba, to ita a tinaninta manyan a shekaru ake nufi, bata san Chuchu tana magana ne a kan babban gida ba, shiyasa ta ce ta wuce yara sai manyan kai, manyan kai a fagen kuɗi ake magana!! Kuɗi kuwa kowa ya san guyson akwaisu ba'a magana!. Sai shirme take zuba mashi shi dai ko kaɗan bai damu ba, sai murmushi yake yi yana kwance a saman bed ɗinsa yana fuskantar celling, ya baro Auta and Leesharh a bedroom ɗinsu suna a tare. A gefe guda kuwa hira sosai Aunty MieMie da Khadijah suke yi, Aunty MieMie tana san yi mata wayo ta faɗa mata wanenen daddyn Ahmad, dan tana zargin uncle Jahiz ɗinsu, amma Khadijah ta ce mata bashi bane, shi ne nan take son nuna mata fifikon shekaru ta yi mata wayau!. A can gefe kuwa, gabaɗaya manyan cikin fada sun hallara sakamakon diran wani bako sabon fuska da basu sani ba, da alama matafiyi ne da hanya ta biyo da shi ta nan, dik a jigate yake yi, daga ganinsa ya sha wahala, magana yake yi da harshen da basa ji, kun san nace maku Kamran yana da yare wanda suke magana da shi da Mammarsa, to da shi ya yi ƙoƙarin yi masu magana da Fada, ko kaɗan bai yi turanci ba, dan ya manta yaushe rabonsa da turanci, tun rabuwarsa da su Pretty tsawon almost 2 years yanzu ake magana, ya sha bakar wahala a wajen neman su Pretty, shi yanzu ma ba babansa yake nema ba, Pretty yake nema, dan ya nemi babansa har ya gaji bai iya sanin in da yake ba, dama kuma mammarsa tasan ba zai taɓa iya ganewa ba, shiyasa ta yi mashi ɓaddakama, dan tasan idan ya doshi in da babansa yake, to fa ba shakka ko shi Kamran ɗin bai gane ba babansa ya gane ɗansa, ita kuma ba zata so hakan ba, dan bata shirya rasa shi ba, bai san tarihin babansa bane shiyasa ya nemi zuwa in da yake, matsa mata da ya yi yaki cin abinci zai kashe kanshi a banza yasa ta yarda ya je, amma ba wai dan ya haɗu da baban nasa, kawai dai ta rabu da shi lafiya. MAMMA FA TA IYA MUGUNTA YASEEN!!. Tsawon shekaru biyu yaro na shan azaba yana wantagaririya a hanya, har ALLAH ya jefosa kingdom of power. Idanun King a kansa babu ko kyaftawa, gani yake kamar ya gane wannan fuska dik da cewa ya canza, ya rame saboda wahala, ya yi duhu, amma kamanninsa ya dawo, dik askin da mammarsa ta yi mashi gashi ya sake fitowa fiye da na da a wajen, so kamanninsa sun bayyana. "Sarkin gida ku ɗaukesa zuwa ɓangaren baki, ya ci abinci ya huta zuwa gobe sai mu san me ya kawo shi". Cewar King da tin da ya fara maganar har ya dire aya bai zare kallansa daga kan Kamran ba. "Commander kasa a kula da shi sosai zuwa gobe". Ya sake faɗa still kallansa a kan KAMRAN sosai, har mamakin irin kallon da King yake yi mashi KAMRAN ɗin ya yi, sai dai kuma!. Uhm my people's abin da baku sani ba a nan shi ne, da Kamran da Hoorain uwarsu ɗaya, Hoorain mahaifiyarsa ya taimaka a daji lokacin da ya je neman su Auta ba tare da ya sani ba, kuma babu wanda ya san KAMRAN da HOORAIN uwarsu ɗaya, harta commander bai sani ba, saboda KAMRAN a forest aka haifesa, da cikinsa ta shiga dajin, KAI MY PEOPLE'S YADDA KUKE TINANI FA BA HAKA STORYN YAKE BA, KU JIRA BAYYANAR GASKIYA KAWAI, DAN DIK YADDA ZAKU YI TINANI WLH IDAN BA NI NA WARWARE MAKU BA BA ZAKU TAƁA GANO BAKIN ZAREN BA, DAN A DABAYBAYE KUKE, KU DAI KAWAI KU JIRA, LOKACIN BAYYANAR GASKIYA TA YI AI, YANZU ZA'AYI TA ZAƘULOSU ONE AFTER THE OTHER! BA DAI KAMRAN YA BAYYANA BA? TO KU JIRA AKWAI BABBAR CAKWAKIYA, WAI KUN ƊAUKA A BANZA NIKE TA CE MAKU AKWAI BABBAR CAKWAKIYAR NAN NE? UHM NA CE UHM, ABIN SAI SHIRU KAWAI, KANKU ZAI ƊAUKI CAJI OVER. Kamannin Hoorain King yake gani a tattare da fuskar Kamran shiyasa ya kura mashi ido yana ta kallonsa, da farko ma ya ɗauka Hoorain ɗin ne, shiyasa ya shiga ruɗani, sai da ya dawo hayyacinsa sosai ya iya gane cewa Hoorain ya fi Kamran haske nesa ba kusa ba, sannan Hoorain ya fisa kyau nesa ba kusa ba, Hoorain ya fisa tsawo. Dik cikin fada babu wanda ya lura da kamannin Hoorain a furkar wannan bako face King, shi kaɗai ya lura da wannan, da yake ma ba ganin face ɗin Hoorain ɗin suke yi ba, akwai waɗan da ma basu san shi a zahirance ba! Miƙewa sarkin gida ya yi tare da cewa ya nufi in da bakon nasu yake durkushe a saman gwiwowinsa, dik ya galabaita sosai, umarni ya bawa warriors guda biyu da suka shigo da shi a kan su ɗaukesa zuwa ɓangaren baki matafiya. Basu ɓata lokacin wajen ɗaukarsa zuwa can ba, commander ya miƙe ya bi bayansu. Har yau har gobe commander yana kallan Hoorain a idanunsa, cutar bata sake shi ba. Tsabar mugutan irin na King kuma ya ce ba za'a kaisa hospital ba, dan idan suka tsaya mashi cutar ta sake shi, ya gane da gaske Hoorain ya mutu to tabbas zai yi masu bore, zai dai'na kare rayukansu da dukiyarsu, shiyasa ya ce a rabu da shi ya cigaba da imagine ɗin har abada!. My people's me kuke tinanin zai faru ne wai? Uhm true colorn King yana ta kara bayyana, ta bakinku ƴan special grp ko dai a kan King RAWANIN ZALINCI take ne? To ku je dai zuwa, gaskiya tana ta bayyana tana zaƙulo kanta!!. In da one tambaya! Meyasa Mammar KAMRAN ta ce idan ya kusanci babansa tamkar ya kusanci mutuwarsa ne? Meyasa ta ce wajen babansa ba in da zai je bane?. P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 62 Momma gabaɗaya kanta ya shiga ruɗani, tinani a kan mahaifiyar Hoorain ya sakota a gaba sosai, dik tinanin da ta yi sai result ɗin ya bata cewa Hoorain ɗan King ne, dik yadda zata yi wannan amsa yake fito mata, gabaɗaya kanta ya ɗauki zafi matuƙa, jikinta har zafi ya yi saboda wannan tinani da damuwa game da tashin hankali!. Da yake tana da alkunya ita, sai ta ji ba zata iya faɗawa Smart abin da mahaifinsu ya aikata a baya ba, dik da cewa ta san yasan sarakuna wannan al'adarsu ce, so ba wani abin bane a wajensu, amma ta ji nauyin hakan matuƙa. Bata ma san Smart kam ya fita sanin komai ba!!. Ita kuwa Mama sai ƙoƙarin banƙaɗo dalilin da zai sa ace Smart ba ɗan King bane take yi, dik ta damu kanta, ba yadda za'ayi ta ci burin ɗanta Ramish ya gaji karagar mulki za'a wani ce mata ga wani ɗan da zai gaji ubansa ba nata ɗan ba, gaskiya ba zata yarda ba!. Rashin sani ya fi dare duhu, Allah sarki har ta ban tausayi, ya zata ji a lokacin da za'a ce mata Ramish ba mallakinta bane?!!. Mummyn Chuchu dai yanzu ta cire rai da mulki baiwar Allah, da farko tana sa rai, amma yanzu tin da bayan Ramish ga Smart shikenan sai ta hakura ta fawwalawa Allah lamuranta. UNCLE ABBAS PART. Bakaramar rikici ake bugawa a tsakanin Mammie da Aliyah ba, dik kuma rikicin a kan King Zuhair ne, sun yi sunyi tsafinsu ya gagara kama shi, Aliyah ta yawace bokaye daban daban amma kowannensu amsa ɗaya yake bata shi King Zuhair ya fi karfinsu, ba zai tsafu ba, bama King kawai ba, ƴaƴansa gabaɗaya nan gani nan bari ɗumaman mayya, shiyasa kuka ga da suka yi niyyar tsoratar da guyson ya zage aljanar tas, to jinin Zuhair sun fi karfin wani sihiri ya taɓasu, shiyasa suka kasa cusawa Smart soyayya Sareena, saboda ya fi karfinsu. A yanzu kwakkwaran shiri suke shiryawa mai zafin gaske wanda suka ɗaukarwa Queen Zarina alkawarin zasu salwantar da jinin mutum ɗaya daga cikin ƴaƴansu ko ƴan uwa domin ta yi masu bakin sihiri a kan jinin King Zuhair, to dama kun san ZARINA tana kullace da kingdom of power, aikuwa ta yi gaggawar aminta da wannan shiri, ta kuma rattaɓa alkawarin zata yi masu aiki, yanzu Mammie tana cikin zulumi da damuwa matuƙa a kan waye zata sadaukar da jininsa ga Zarina? Ba zata iya bada jinin Sareena ba, saboda sheɗancinsu ɗaya, Sareena tana bin abin da take so, kuma ƴaƴa biyu gareta, yanzu dole ta sadaukar da jinin Fanan muddin tana son cikar burinta!!! Uhm ana tashin hankali ba kaɗan ba a Kingdom ɗin nan. Sareena kuwa tana can har da zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda uncle Abbas ya faɗa mata cewa ya bada aurenta ga Smart, sai murna take yi, har da wani cewa yanzu lokacin cin uban dik wanda ta gani a part ɗinsa ne, dan shi ɗin mallakinta ne ita kaɗai, sai tsantsara kwalliya take yi zata je wajensa, wai fa ba shi zai zo hira ba, ita zata je wajensa, dik da a tsorace take da shi, amma tana da kwarin gwiwa a kan yakininta, ta yi imanin ba'a jin daɗi sai an sha wahala, kuma ta yi imanin yanzu babu abin da zai yi mata tin da har ya karɓi aurenta hakan na nufin yana sonta, bata san cewa shi bai ma san wainar da ake toyawa ba!!. Shi kuwa Kamran an kaisa part na baki, commander ya sanya tsaro a kansa sosai, sannan anbashi kulawa a matsayinsa na bakonsu, sun bashi abinci mai rai da lafiya, sun kuma tsaya mashi ya yi wanka ya canza tamkar ba shi ba, ya fito a ainahin yaron mammarsa, babu abin da yake ransa face tinanin Pretty, baya tinanin mammarsa kamar yadda yake tinaninta, saboda yasan mammarsa mace ce da zata iya tsayawa kanta a kowani hali, jaruma ce kuma sadaukiya, so Pretty kuma macece mai rauni da bata san kanta ba bare har ta san me duniya yake ciki, tinanin twins ne kawai a ransa, tsawon waɗan nan shekaru biyun bai taɓa yin minti biyu ba tare da ya tuna amanarsa kuma twin's ɗinsa ba, suna ransa tamkar yadda yake a ran Sweetie, kunga kullum tana tinaninsa, amma Pretty ko maganarsa bata yi, ko da yake ita yarinya ce da ba zaka taɓa iya gane cikinta ba, bata magana bare kasan ina ta dosa, waya sani ko tana tunasa bayyanawa ne kawai bata yi! My people's, KAMRAN team, ina mai baku hakuri a kan abin da ya faru, kun san bana yin abu haka kawai sai da kwakkwarar dalili, na san kun ji zafin auren Pretty da Smart, amma nasan idan kuka ji dalilina da kanku zaku jinjina mun, tafiyar yanzu ta fara, kada ku manta yanzu muka gota tsakiya kaɗan, ina da dalilina mai karfi na yin hakan, amma kun kusa ji soon!! Ku yi wa KAMRAN fatan samun wacce zata kasance alkhairi a garesa, ba son rai'na bane nike raba masoyan nan, dalili yake sanyawa!! Amma kada ku damu a karshen page ɗin nan zan faranta rayukanku!......🙌💘 *CROWN OF JUSTICE*🔥🔥 Katafaren government house na ƙasar, zaune dattijo MUZAFFAR yake a saman wani dandatsetse kuma lallausan kushin mai bala'in tsada a cikin katafaren parlournsa, yana rike da wani littafin mai suna The Franklin scandal yana karantawa, yana cikin shigar manya-manyan malaman larabawa masu kima da mutumci, fuskarsa sanye da farar glass, ya sha rawani mai bala'in kyau na manyan malamai, farin balarabe ne tas wanda da ka gansa kasan mutumci da kima game da kyau haɗe da dukiya sun yi mubaya'a a wannan waje. Daga bakin kofa wasu zaƙwaƙuran securitys ne ke gadinsa, ya natsa cikin karatun da yake yi sai ji ya yi an yi mashi sallama. Cikin sanyin murya ya amsa, murya mai cike da dattaku da kima. Wani security ne ya shigo cikin parlourn, with full respect ya ce. "Sir Prince Rishan ne yake neman iso"....... Gyara zamansa cikin natsuwa dattijo ya yi kafin ya ce. "Ka ce ya shigo"....... Sara mashi securityn ya yi alamar girmamawa kafin ya juya ya nufi waje. Yana fita bai fi five seconds ba sai ga Prince Rishan ya shigo cikin shigarsa ta alfarma irin ta ƴaƴan manya manyan sarakuna da ake ji da su. Zuba mashi idanun dattijo ya yi yana kallonsa har ya kariso, a saman kushin da yake zaune ya zauna, amma kafin ya zauna sai da ya duka kasa, dik wata sarauta ya ajiyeta a gefe ya tsugunna a gaban dattijo ya kwashi gaisuwa. Hannu dattijo yasa ya shafi lallusan gashin kansa kafin ya amsa gaisuwar. Kusa da shi ya zauna, kallo ɗaya dattijo ya yi mashi ya gane cike yake da damuwa, dan haka sai ya rufe littafin dake hannunsa ya ajiye a gafe, sannan ya juyo da hankalinsa game da natsuwarsa a kan Prince Rishan. A natse ya ce. "My son akwai wata damuwa ne?". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Papa akwai damuwa sosai ma, amma papa please meyasa baka san faɗa mun gaskiyar lamari a kan waɗan nan mutane biyu?". (Ude and Zarina yake magana) Dogon ajiyar zuciya Papa ya sauke kafin ya ce. "Rishan tono gaskiyar babu abin da zai kareka face bakinciki, koma menene ya rigada ya wuce, ka bar maganar, yanzu ina Rishma?". Ciki ciki ya amsa da tana gida, da alama ransa bai so amsar Papa ba sam. Wai menene gaskiyar da Rishan yake son sani?. Batu ne a kan mutuwar babansa wanda yake zargin kashe shi aka yi, dan shi bai samu damar ganin gawarsa ba, a lokacin da abin ya faru baya nan, kuma zarginsa gaskiya ya ce, dan familyn Thomas ne suka kashe shi, wato familyn Zarina kenan, ita ta yi poisoning na King Ranveer da hannunta, poison ɗin kuma daga hannun mahaifinta Thomas ya fito, so ita ta kashe sirikin nata, domin kawai Ude ya karɓi mulki ita kuma ta kwace, burinta kuwa ya cika, sai dai ta bar baya da kura, domin kuwa Papa ya san komai, ta so rufe mashi baki amma abin ya ci tura, shi kuma Papa yanzu abin da yasa baya son bayyana gaskiya saboda Rishan shi kaɗai ne, ba zai iya yaki da su ba, zasu cutar da shi ne kawai, dik da suna bala'in shakkarsa da tsoronsa, amma aka ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, Papa yana ganin kamar zasu iya cutar da Rishan and Rishma, shiyasa ya ki faɗa masu gaskiya, har yau Rishan ya gagara samu natsuwa, zuciyarsa tana faɗa mashi lallai dole ya nemo waɗan da suka kashe babansa. Kun san meyasa na baku wannan tarihi? Saboda a gaba kaɗan zaku tsinci kanku a alaƙa da wannan tarihi, bana son ina gaba in dawo baya shiyasa na faɗa maku a nan kawai, dan a gaba ba ɗauko tarihin daga farko za'ayi ba, za'a ɗaura ne daga kan in da Rishan ya tsaya!. And Papa yana zargin da sa hannun Ude a kashe King Ranveer, saboda bai yarda Zarina kawai ta kaddamar da wannan aikin ba!. Lallaɓa Rishan Papa ya rinƙa yi har ya hakura ya daure ya sake suka sha hira da Papa ya mance da batun su Zarina, sai dai a karshe da ya tashi tafiya ya ce da Papa. "Papa zan kashe Ude tin da yaki komawa musulunci, kuma kasan hukuncin wanda ya yi ridda!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa zai fita. Miƙewa tsaye Papa ya yi, sai da ya gyara alkyabbar jikinsa, sannan ya gyara glass ɗinsa kafin ya ce. "Kada ka yi saurin yanke hukunci Rishan, ka kara mashi lokaci zuwa nan da ko ƴan watanni ne, idan babu haske sai mu san hukuncin da zamu yi mashi, koba komai yayanku ne". Kun san me my people's, wlh ba dan Rishan baya shiri da su Zarina baya taimaka masu ba, tabbas da babu wanda zai iya cinsu da yaki, saboda shi ɗin namiji ne kuma jarumi ne, tamkar yadda kingdom of power suke da commander Zafar, haka jarumtarsa yake, tsab Rishan zai iya kayar da commander, saboda commander Zafar ya tsufa, shi kuma sabon jini ne, amma Zarina saboda rashin wayo insert of ta kallaɓasa ya zama mai tsaya masu wai take faɗa da shi, ko da yake shi ma ba zai yarda ba, dan ya tsaneta tin kafin Ude ya aureta, tun yana yaro ya tsaneta sosai!. Jinjina kai ya yi tare da cewa. "A kullum kai kake dakatar da ni Papa, kuma In Sha Allah ba zan taɓa gajiya da bin umarninka ba". Ɗan kara sakin fuska Papa ya yi haɗe da cewa. "ALLAH ya yi maka albarka Rishan, In Sha ALLAH kana cikin kariyar UBANGIJI babu abin da zai sameka, sannan zaka kasance cikin farinciki, na gode kuma na yi murna da har yau baka cireni a matsayin uba da ka ɗaukeni tin King Ranveer yana raye ba, ALLAH ya albarkaci rayuwarku, ka kula da Rishma sosai, ka tsaya da taka tsantsan". Amin ya amsa da shi tare da juyawa zai fita, har ya kai bakin kofa sai kuma ya juyo, ya yi mamakin ganin yadda Papa yake yawan kallonsa a kullum idan ya zo zai tafi. "Papa meyasa kake yawan cewa in kula da Rishma da kai'na?". Ya jefa tambayar cike da sa ran zai samu amsar da yake so, dan abin na damunsa ta yadda ko a waya ya kira Papa sai ya ce mashi ya tsananta kula sosai, abin ya fara ɗaure mashi kai. Murmushi irin na manya Papa ya yi dik dan ya kwantar mashi da hankali kafin ya ce. "Babu komai, kawai ina so ne in tabbatar da amanar da King Ranveer ya bani na rike amanar sosai, dan haka ka kula, ba zan gaji da faɗa ba, dan amanace ku a gareni!!". Shiru ya yi tare da juyawa ya cigaba da tafiya, ko kaɗan bai gamsu da amsar Papa ba, ya dai yi shirun ne kawai, kuma hakance, Papa na ɓoye mashi gagarumin gaskiyar da yakamata ace ya sani, amma Papa ya dubi abin ta wata fuska ta daban shiyasa ya ɓoye!. 🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥 Bayan wani lokaci. Zaune Auta take a saman bed ɗinta ta yi shiru tana tinanin rayuwa, wasa wasa yau ta shafi almost 3 month ba tare da Hoorain ko jin sautin muryarsa ba, abin har ya fara zame mata jiki, yanzu ta fara yarda da Hoorain baya duniya, Leesharh tana bedroom ɗinta tana wanka, guyson ya koma kingdom of power saboda an buɗe school, dole ya koma. Ramish baya nan ya fita, a yanzu ya yi nasarar capke mutane kaso 60 cikin ɗari na masu nikaf, sai dai dik wanda ya kama sun ki faɗa mashi wanenen mai turosu, ya azabtar da su har ya gaji, amma sun ki faɗa, sun ce su haya killers ne, idan sun karɓi contract ko kashesu za'ayi alkawari suke ɗauka basa taɓa tona asirin wanda ya sanyasu aiki, sannan su idan suka karɓi aiki fa ko mutum me zai yi sai sun kashe shi, ko duniya dikka zai basu idan sun karɓi aiki a kansa sai sun ƙaddamar. Ba karamun ɓacin rai Ramish ya ji ba, ya sanar da Smart ga abin da yake faru, Smart ya ce mashi kada ya damu ya kashesu gabaɗaya a rage mugun iri a cikin al'umma, kuma idan ya kashesu kada ya sake saka hannunsa a neman wanda ya sakasu, ya bar mashi aikin dan matsalar daga cikin gida ta samo asali, wanda ya sakasu yana cikin kingdom of power, su kansu basu san ainahin wanda ya sakasu ba, dan haka ya bar binciken shi zai kama koma wanenen a nan, saura kaɗan ya tattara dik wasu hojjijinsa ya tinkaresu gadan gadan! Wannan ne ma dalilin zamansa a kingdom of power bai koma Paris ba, shi ne kuka ga ya yi shiru kamar babu abin da yake yi, uhm babban ɓarna yake yi masu ta karkashin kasa ba tare da sun sani ba,. BALA'IN CAN, WANDA YA SANYASU KUMA YANA KINGDOM OF POWER?! HOW TO?! KUMA WHO?. UHM AKWAI ABUBUWA FA!!. Ba kara mun shocked Ramish ya ji ba a lokacin da ya ji abin da yayan nasa ya ce, ya so ya faɗa mashi wani abin da zai kwantar mashi da hankali yasa ya ji sanyi a ransa, amma ina sai ma kara mashi zafin da ya yi ta hanyar cewa kada ya kuskura ya sake zuwa gidan King Badeen, dan baya son kowa ya zargi wani abin, sannan shi Smart ɗin a zuwansa wancan karon da ya kawo Auta basu yi rabuwar daɗi da kakan nasa ba, ya yi masu tas bai ragawa kowa ba, ya kuma ce masu in dai kannensa basu auri waɗan da suke so ba to su ce shi ba jinin King Zuhair bane!!! Har da ce masu ya yi ya yi masu alkawarin Zunaira zata rayu ne kawai da abin sonta, ba zata zauna da Abdussalam ba! Sannan kuma Ramish ma yana da wacce yake so, kuma bare ce, yaga wanda zai hanasu zama ma'aurata tun da su babu abin da suka iya sai son kai, to shi kuma zai gwada masu a cikin Rahilarh ya haifu, ba su yi rabuwar daɗi ba dai, dan King Badeen ya nuna kafewarsa a kan babu auren bare a cikin zuri'arsa, dik gida zasu dawo su yi aure, har da cewa shi ma Smart ɗin ya dawo gida ya zaɓi mata! Shi kuwa ya ce zai gwada masu shi ɗan yau ne. DA ALAMA SHIYASA YA AURI PRETTY DAN YA GWADA MASU SHI MA YA AURI BARE, KAI SMART ƊAN DUNIYA NE WLH!! Wannan dalilin yasa ya ce wa Ramish ɗin kada ya kuskura ya je gidan King Badeen, dan yana zuwa zasu kama shi su yi mashi auren gida ne tin da Smart ya ce yana da bare wacce yake so, sannan yasa Ramish ɗin ya cire sim ɗinsa ya ajiye a ƙasa, yanzu yakin ya koma na cikin gida, bari a saita na cikin gida tukun nan, dama kun san idan kana son yin gyara to ka faro daga cikin gida, a nan ne zaka iya cin nasara, amma idan ka faro daga waje, kana gyara a cikin gida ana warware maka komai!. To kun ji abin da ya faru a zuwan Smart gidan kakan nasu, a lokacin Momma tana gidan uncle Rahab abin ya faru, da ta dawo baban nata bai sanar da ita ga abin da yake faruwa ba, sai ya kira King Zuhair ya sanar mashi, nan King Zuhair yake sanar da shi cewa shi ma Smart bai barsa ba, ya fi karfinsa, abin da yagadama kawai yaron nan yake yi, nan fa ran King Badeen ya kara ɓaci ya kira uncle Muhammad wato daddyn Smart na Paris, dan shi kaɗai kawai a duniya Smart yake jin maganarsa bayan Momma. Sosai King Badeen ya yi wa uncle Muhammad faɗa a kan irin tarbiyar da ya bawa Smart, yaro kwata kwata baya ganin girman manya, sannan baya da tsoro, dik wata barazana a banza!. Hakuri uncle Muhammad ya shiga bashi kafin ya ce bari ya kira Smart ɗin. Da ya kirasa sai dai a maimakon ya yi mashi faɗa sai ya ce. "Son me kaje kake yi wa tsoffin nan ka tunzurasu har haka ne? Daddynka ya kirani last week, yau kuma kakanku ya kirani, ka je kana goda masu iko ko? Kasan fa su sarauta ne, babu mai nuna iko a gabansu". Kai tsaye ya amsa da. "Daddy tsoffin ne basa a kan hanyar da ta dace shiyasa nike mayar da su kan hanya, kasan ba zan yi abu mara kyau ba ai ko my lovely dad?". Kamar mai shagwaɓa haka ya yi maganar, ALLAH ya gani yana kaunar daddynsa over. Murmushi daddyn nasa ya yi. "That's my son, nasan gyara kake yi shiyasa ma da daddynka ya kirani ban kiraka ba, dik yadda aka yi nasan basu aikata dai'dai, cigaba da dawo da su kan hanya my son, zan yi alfahari da kai, amma ka yi sauri ka dawo ka ji? Ina kewarka over"...... Da okey kawai ya amsa tare da cewa i love you dad, love you too shi ma ya ce, daga haka suka yi sallama. NA CE YANZU KUN GANE MAI KARA SANGARTAR DA SMART KO? KUN JI UNCLE MUHAMMAD WAI YA CIGABA DA DAWO DA SU HANYA, KAI WATO ALLAH KA BARMU DA IYAYENMU!!. ---------------------------------------🔥🔥🔥 Baki a ɗauke da sallama dattijuwar nan ta shigo room na Auta, irin dogayen rigunar shan iskan nan ne a jikin Auta ɗin, rigar tana da ɗan siririn hannu, while a dai'dai gwiwarta ta tsaya mata, tana gajin dattijuwar ta yi gaggawar saukowa ƙasa daga saman bed ɗinta ta nufeta da sauri, kwandon mai shake da kayan fruits dake hannunta Autar ta karɓa tana faɗin. "Mama ai da baki wahalar da kanki ba, sai in zo in ɗauka da kai'na". Ta yi maganar tana kallon kayan fruits ɗin kafin ta ɗago da kallanta a kan tsohuwar, yau shi ne kallonta na farko da fuskar dattijuwar. Wani irin faɗuwar gaba ta ji dan taga wannan kamar ba tsohuwar gaske bace, kada ku manta yaran Momma they're gifted!. Amma sai ta kawar da tinanin nata tare da juyawa ta koma wajen bed ɗinta, a saman bedside drawer ta ɗaura kwandon tana cigaba da kallon dattijuwa ta kasan ido, juyawa ta yi tana tafiya har da ɗan ɗingisawa irin na tsoffi............... Yanzu Fisabilillah my people's ku faɗa mun mutum mai irin zuciyar Auta meyasa zaka so kasheta? Yarinyar da babu ruwanta, bata da girman kai, ga girmama manya, bata duba da talaucinsu ko aiki a karkashinsu da suke yi, da zarar mutum ya girmeta zata bashi girma koma wanene!. Komawa saman bed ɗinta ta yi ta zauna tare da ɗauko wayarta tana duba sakon mutuminta, dan koba komai a yanzu kalamansa suka sanyata farinciki, tana samun annashuwa. ..............Wai ina mijinta Abdussalam ne? Allah sarki ya dawo Dubai, dan a tinaninsa ta mutu, har ya cire rai da ita, sai dai kuma har yau har gobe sonta yana a cikin zuciyarsa, kullum sai ya yi mata addu'ar samun rahama, ita kuwa tana nan ta mance da wani Abdussalam, dan Smart ya ce mata kada ta damu Abdussalam ya saketa, yanzu ita ba matar kowa bace, so dan haka ta mance da wani Abdussalam ta fara sabuwar rayuwa!. Amma fa dan ta yi farinciki Smart ya faɗa mata haka, ba wai dan Abdussalam ɗin ya saketa ba!!!. Ɗan siririn murmushin da tsawon watanni bai samu gurbi a face ɗinta bane ya bayyana a fuskarta a lokacin da take karanta saƙon guy ɗin can, hannu ta miƙa ta ɗauki apple a cikin kwadon fruits da dattijuwa ta kawo mata, wato tana shan fruits tana karanta saƙonsa abin zai fi sugar. Bakinta kai tsaye ta kai apple ɗin zata gatsa kenan unexpected taga harbi da kifiya an harbi apple ɗin hannun nata ya faɗi ƙasa tare da kifiyar. Zabura ta yi ta miƙe tsaye tare da gefar da wayar hannunta dan ta tsorata sosai. Cikin natsuwa ya tako izuwa cikin ɗakin, sanye yake da security uniform, wlh kayan sun yi bala'in yi mashi kyau matuƙa, tamkar dam shi aka yi, uniform ɗin su Smart ne, ƙasa ya yi da kansa cikin girmamawa ya ce. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe, ban yarda da inganci apple ɗin bane shiyasa na dakatar dake daga sha, sannan a doka sai na bincike abinci kafin ki ci, ban bincike bane shiyasa na hanaki ci!". Da kyar ya iya kai karshen maganar saboda yadda words ɗinsa suke sarkewa, da alama hakan yana da nasaba da yanayin shigarta, ɗaya ne daga cikin jami'an dake kula da lafiyarta, mai kawo masu abinci ne!. Ya kai karshen maganar tare da mayar da kwari da bakarsa ya maƙala a bayansa kamar wani warriors!. A wani irin slow ta ɗago idanunta ta sauke a kansu. Murya tamkar a mafarki ta ce. "Ina ainahin mai kawo mana abinci?". Nisawa ya yi, har yanzu kaifin ƙwaƙwalwarta yana nan bai ragu ba, dik da ciwon da ta sha, tsawon wata uku tana jinya, amma babu abin da ya sauya!. Ta yi mashi tambayar ne dan tana son ya sake yin magana ta tabbatar da abin da take zargi!. "Baya nan, an canzasa da ni ne, daga yau nine zan rinƙa kawo maku abinci". Cikin wannan sanyin murya tasa dai ya yi maganar!. Kurawa fuskarsa idanu sosai ta yi, yana sanye da mask a face ɗinsa, iya idanu kawai zaka gani a waje. Ya ɗauki tsawon wata ukun nan a tare da su, amma yana tare ne da securitys da suke bakin gate, baya daga ta ciki, shiyasa bata san shi ba, yau ne ganinta na farko da shi da Smart ya canza shi ya ce ya dawo ciki ya zama mai kula da ita sosai!. "Ban taɓa tinanin zaka yi mun wasa da hankali ka yi tinanin ba zan iya ganeka ba! Dik duniya My hero ne kawai zai iya irin wannan harbin da ka yi, saboda shi ɗin bahago ne, da hagu yake harbi, da hagu yake faɗa, da hagu yake komai, kuma nasan da cewa tabbas kai ne shi, dan kana shigowa nan zuciyata ta amsa, ta bada bugun da tsawon wata uku bata buga haka ba, a kansa kawai zuciyata take yin irin wannan bugu". Ta kai karshen maganar idanunta sun cicciko da kwallah sosai. "Ranki ya daɗe ban gane a kan me kike magana ba!". Ya faɗa can ƙasa, cikin wannan sanyin murya tasa dai. Zafafan hawaye ne suka fara bin kuncinta, rasa me zata ce mashi ta yi yasa ta durkushe gwiwowinta a saman mattress ɗin tare da rushewa da wani irin kuka mai tsananin taɓa zuciya, kukan da ta ɗauki sama da wata uku yana cinta a zuciya ta kasa samun damar yin sa sai yau. Har cikin ransa ya ji tsananin zafin kukan nata, amma sai dai Smart bai bashi damar ya kusanceta ba, bashi da ikon rarrashinta a yanzu, dole ya daure ya juya zai fita cikin zafa sabo kukan nata yana taɓa shi, idanunsa a kanta sosai. HOORAIN!! Ba shakka shi ne, Auta bata yi karya ba, kuma zuciyarta bai buga a karya ba, soyayyarta a garesa gaskiyace, dole idan ya kusantota ta ji hakan a ranta. QUEEN OF SURPRISE na ce ku karɓi wannan yau kuma!!. Tabbas Hoorain yana a tare da ita a cikin wannan gida, kuma Smart ya ɗaukesa daga kingdom of power tun lokacin da Dr ya ce zuciyarsa ta dai'na harbawa, ya umarci su Ansar da su yi shiru kada su faɗawa kowa. To bama shi ne surprise ɗin da QUEEN OF SURPRISE na zo baku ba, babban surprise ɗin shi ne kun san da cewa Zunaira matar Hoorain ce? A rana ɗaya aka ɗaura auren Smart and Pretty, Zunaira and Hoorain, da sa bakin Abbonsa kuma, shi ya yi mashi waliyi, kamar yadda uncle Muhammad ya zama waliyin Auta. Idan baku manta ba Smart ya ce mata ya yi mata alkawarin zata mallaki Hoorain, a lokacin da King ya ce mashi ya kawo mashi Zunaira, suka ɓoye batun aurar da ita zasu yi, basu san dik abin da suke yi a gidan Smart yana sane ba, tuni yasan aurenta za'ayi, wannan dalilin yasa ya ɗaura mata aure da Hoorain tin kafin su dawo kingdom of power, ita kanta bata san da wannan aure ba, shi kansa Hoorain ɗin bai sani ba, iya Abbonsa ne kawai ya sani. Shiyasa kuka ga da ana ta batun bikinta da Abdussalam ya yi banza da su , dan yasan me ya aikata, ya so sanar da su cewa Auta matar aure ce a ranar da za'a ɗaura aure, amma lura da ya yi da irin tsanar da King ya gwadawa haɗin Auta da Hoorain yasa ya dakata da sanar da su ya shiga wani bincike, dan haka a kan auren Hoorain aka ɗaura na Abdussalam, yanzu Hoorain ne mai mata ba Abdussalam ba, abubuwa sun yi wa Smart yawa sosai ne a lokacin da Hoorain ya mutu a idon duniya shiyasa ya ja gefe yana kallonsu yana wani aikin na daban, a nan ne ya fara binciko tarihin maman Hoorain da King, wannan dalilin yasa ya dakata da barin Hoorain da Auta su yi zaman aure, sai ya bar Hoorain a Paris ya bar Auta a kingdom of power. Time da ta ji labarin Hoorain ya mutu ta suma ya dawo da ita Dubai, da ya sanar da Hoorain hankalinsa ya tashi sosai, har kuka ya yi mashi a kan ya barshi ya zo ya ganta, wannan dalilin yasa ya sanya shi ya yi shiga irin na jami'ansu dan ya biyosu su zo wajenta ya ganta, da ya zo kuma ya rinƙa haɗa Smart da Allah a kan ya barshi ya kasance a gidan, ya yi mashi alkawarin ba zai taɓa bari ta ganesa ba, sanin irin karfin son da yake yi mashi yasa Smart ya ce Hoorain ya kasance da securitys dake bakin gate kada ya zo ciki, dan kada a samu matsala, a hana Hoorain yana samun damar ganinta daga nesa, sau da dama tana tsayawa a jikin window tana kallan harabar gidan, ta nan yake ganinta. Yau kawai da safe Smart ya ce Hoorain ya koma mai kula da ita a cikin gida, wancan jam'i dake kula da ita kuma y koma bakin gate, har yanzu da nike yi maku magana Hoorain bai san Auta matarsa bace, kamar yadda ita ma bata san shi ne ainahin mijinta ba, sannan bayan Smart, commander, uncle Muhammad babu wanda ya san da wannan magana. Abin da Smart yake gudu shi yake son faruwa ga shi da kallo guda Auta ta gane heronta, wai a hakan ma ya ja mashi kunne a kan kada ya yi wani motsin da zai sa ta gane shi, kada kuma ya yi mata magana, sannan idan ta kama dole ya yi magana to ya canza murya yadda ba zata gane ba....... Smart yana so ne ya gama bincike, ya tabbatar da Hoorain ɗan waye ne a tsakanin King and commander kafin ya basu damar sanin sun mallaki juna, shiyasa yake yi masu iyaka a yanzu. KAI JAMA'A KU TAFAWA SMART, YA CIKAWA AUTA ALKAWARINTA YA TSAYA MASU SUN MALLAKI JUNA, SAI DAI KWAI CAKWAKIYA MAI GIRMA A GABA, YANZU HOORAIN DAN WAYE NE? SHI NE BABBAN TASHIN HANKALIN, KADA AZO YAZAMANA YAYANTA! DOLE SMART YA NESANTASU DA SANIN CEWA MA'AURATA NE SU, SANNAN KUMA YA SU KING ZASU JI, BA SHAKKA SMART YA CIKA ƊAN HALAK. (Wai an ce maku a banza na bar Hoorain ya shanyewa Auta baki ne?🥱 To matarsa ce halacɗinsa, a book ɗina ai ba'a taɓara kun gane ai? Sai idan akasi aka samu misali kamar Leesharh da Ramish wanda su kunga kaddara ce ta afka masu, amma haka kawai a book ɗina ba'a lalata gaskiya, ina ƙoƙarin tsayawa tsayin daka wajen ganin na tsabtace rubutuna, yauwa idan da aurene a sha shagali!.) A gaggauce ya fice daga ɗakin. Tana ɗago kai taga baya nan ta yi saurin dirowa kasan bed ɗin, a lokacin har anfara kiraye kirayen sallar isha'i, waje ta nufo da gudu dan ta bi bayansa, saboda wlh tasan shi ne, heronta ne. Shi kuwa yasan zata biyosu dama, sai ya ɓuya mata a in da ba zata gansa ba, dan kada ta ganesa ya karya alkawarin da ya ɗaukawa Smart yaja Smart ɗin ya mayar da shi Paris ya sake nesantasu, gara mashi a nan koba komai yana samun damar ganinta bawan Allah, shi ma fa ya sha jinya, almost 1 month yana fama, sai dai Smart ya ce mashi ya yi hakuri Zunaira bata yi aure ba, an warware auren, dan haka ya kwantar da hankalinsa, sai a sannan ne ya samu natsuwa!!. QUEEN OF SURPRISE ina miƙo gaisuwar gareku my people's.....….. 🙌💘🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 ======🔥🔥🔥========= MALLAKIN🔥 P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ ‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬ ‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬ ‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬ 63 Waje ta nufa da gudu domin ta duba shi, tamkar wadda bata a cikin hayyacinta, dik ta firgice tana wani irin kuka mai tsuma rai, dama a kusa zuciyar take, kiris take nema!. Daga in da yake laɓe ya ji ba zai iya barinta ta fita waje da irin wannan shiga dake jikinta ta nufi securitys ɗin nan ba, kun san shi da shegen kishi, ina ai ba zai iya daurewa ba. Kasa cigaba da ɓuya ya yi, tana dab da buɗe kofar parlour ta fita ya yi gaggawar nufarta. Ta baya ya sanya hannu ya toshe mata baki game da rufe mata idanun da ɗayan hannun nasa. Baya ya yi da ita kai tsaye sai bedroom ɗinta. Ciki ya mayar da ita, bai saketa ba har suka kai wajen bed, yana zuwa ya zaunar da ita tare da zame hannunsa, sannan cikin sanyin muryan nan yasa dai ya ce. "Kada ki sake fita ko parlour ne!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa zai fita. Cikin zafa ta miƙe tsaye, hawaye tamkar an buɗe tap an kure mashi gudu, da kyar voice ɗinta yake fita ta ce. "In dai baka son in fita waje to ka bayyana mun kanka matsayinka na herona, in kuma ba haka ba ka cigaba da ɓuya to tabbas ba iya waje ba, gidan dikka zan bari koma duniyar bakiɗaya, dan ban ga amfani zamana a raye bama, ace kana numfashi kuma muna waje ɗaya sannan kana guduna! For what reason?" Ta jefa mashi tambayar a yayin da zuciyarta tamkar zai yi bindiga saboda tsananin tashin hankali da damuwar abin. Dik abin da suke yi Smart yana kallansu, dan idan baku manta ba ya zuba secret cameras sosai a gidan ta in da babu wanda zai san da su, so dik abin da yake faruwa yana gani. A lokacin ya kammala zubawa Pretty iskancinsa son ransa, ya kwanta yana jinta tana kuka ƙasa ƙasa, ya ce idan ya ji bakinta tana kuka sai ya sanya wuta ya konasa, shi ne yasa take kuka ƙasa ƙasa dan kada ya ji!. Banza da ita Hoorain ya yi ya cigaba da tafiyarsa, zuciyarsa tamkar zata yi bindiga shi ma. "My Hero". Ta ambata cikin wani irin murya mai matuƙar raunin da komai taurin zuciyarka sai ka ji ta ratsaka, shi kansa Smart wani irin tausayinta ne ya kama shi sosai, hakan yasa ya fita daga side na camerar tasu ya shiga massage na wayarsa, dama da phone ɗinsa ya yi connected na cameras ɗin. Cak ya dakata da tafiyar da yake yi jin sunansa da ta kira. Saukowa kasan bed ɗin ta yi, ta tsaya a wajen, cikin rawar murya ta ce. "Dama akwai ranar da zata zo kana raye ina kuka ka nuna baka san ina yi ba? Dama dik alkawarin da ka mun ba gaske bane? Dama wasa kawai kake yi mun? In kuwa haka ne meyasa ka bari na kamu da sanka har haka? Meyasa ka cutar da zuciyar da bata san komai ba face kaunarka? Meyasa a dik duniya ni kaɗai ka zaɓi ka cutar? Menayi maka my Hero? Wannan shi ne sakamakon son da na nuna maka kenan? Abin da zaka saka mun da shi..............". Kasa ƙarisa maganar ta yi saboda wani irin kululun bakinciki da ya toshe maƙoshinta, cikin wani irin tari mai sauti ta fara ƙoƙarin cigaba da maganarta, sai dai ina, ta gagara yin hakan, sam sam voice ɗinta yaki fita, hannu tasa ta dafe saitin wuyarta tana cigaba da tari mai sauti wanda sai da ta sanya shi juyowa babu shiri. A dai'dai wannan lokacin wayarsa ta yi kasa alamar shigowar sako. Hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro wayar, ganin message na Smart da ya yi saving numbersa da babban yaya ne yasa ya yi gaggawar buɗe sakon. "Ka rarrasheta kawai tin da ta rigada ta ganeka, but kada ka yi crossing line dana ja maka!". Smart ba zai iya jure ganin ta a irin wannan hali ba, shiyasa ya ce ya rarrasheta kawai!. Shi ne abin da saƙon ya ƙuntsa, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, dama ko Smart bai yi mashi massage ba, ba zai taɓa tafiya ya kyaleta a wannan hali da take a ciki ba, dama dole zai tsaya ya rarrasheta, dan zuciyarsa ba zata iya jura ba, yanzu ma da kyar ya danne. Tin da yake a rayuwarsa bai taɓa danne wani abu mai tsananin azaba ba irin wannan tashin hankali da ta shiga! Idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kamar wuta!. Cikin natsuwa ya taka ya nufi in da take, mayar da wayarsa a cikin aljihunsa ya yi, a gabanta ya tsaya tare da yin ƙasa da kai, cikin natsuwa ya ce. "Am so so sorry Hoonaira, ba zan sake kwantanta makamancin hakan a gareki ba, dan Allah stop all this, please kin ji?". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa ya riko nata dake wuyarta tana tari. Kara jaddada mata da tuba yake yi ya yi. Ina ai babu bakin magana, ta rigada ta kure maganarta, yanzu idan ta buɗe baki zata iya haɗiyar zuciya!. Ganin hakan yasa ya saki hannun nata tare da nufer dispenser ya ɗebo mata ruwa mai sanyi sosai a cikin cup, sannan ya dawo in da take a tsaye. Miƙe mata ruwan ya yi a kan ta sha, sam baya son taɓa jikinta saboda yasan ba matarsa bace, shiyasa yake yin ɗan nesa nesa da ita. Karɓar ruwan ta kawo hannunta zata yi, sai dai ina, kakkarwa sosai hannunta yake yi wanda yasan ba zata iya rike cup ɗin ba, hakan yasa ya matsa dap da ita tare da sanya mata cup ɗin a baki a kan ta sha!. A hankali ta fara karɓar ruwan tana sauke wani irin ajiyar zuciya mai ɗauke da sirrika dayawan da take buƙatar lokacinsa domin buɗe mashi waɗan nan sirrika. Lokacin guda Smart ya ji soyayyarsu ya yi matuƙar birgesa, take ya ji gabaɗaya jikinsa ta motsa, har ɗan lumshe idanunsa ya yi irin abin ta shigesa yadda yakamata ɗin nan. Tana gama shan ruwan ta faɗo saman massive chest ɗinsa tare da rushe mashi da wani sabon kukan. Ai ɗauke wuta ya yi na wasu ƴan sakanni, lokaci guda ya jisa a duniyar mercury, ƙasa motsawa ya yi bare ya rabata da jikinsa, wani irin azabbabben shock ya ji tin daga tsakiyar kansa har izuwa tafun kafarsa, uhm abin ba'a magana. "Why? Why zaka mun haka? Wani laifi na yi da na cancanci irin wannan hukunci? Meyasa? Meyasa?". Daddaɗar muryarta ne ya daki dodan kunnensa yasa ya farfaɗo daga duniyar tinanin da ya afaka. Ta yi maganar kuma tana riko rigarsa wajen massive chest ɗinsa. Kasa magana ya yi, sai dai ya kai hannunsa ya riƙo hannunta dake a saman kirjin nasa, gam ya damke hannun nata tamkar wani ya ce zai kwace mashi ita! Shiru dai bai iya yin magana ba!!. Lokaci guda Smart ya ji sa a duniyar samar iska, juyo da kallonsa a kan Pretty dake kwance tana kuka ya yi, shaukin soyayyar su Auta ya ɗebesa har bai san lokacin da ya janyota jikinsa ba, wai shi ma zai yi irin na Hoorain ya rarrasheta, sai ya shiga ce mata. "Ya isa haka, ki yi shiru." Daga haka bai san me zai sake cewa a gaban ba, sai ya yi shiru yana kallan face ɗinta, cigaba da kukanta ta yi tana shessheƙa. A ransa ya ce ko kukan ma take yi kara kyau take yi, tamkar ita ta yi kanta. Ya kai karshen zancen zucin nasa tare da kai hannunsa ya shafi lallausan lips ɗinsa da suka tura pink sosai saboda kukan, sai wani ɓari suke yi tamkar mai jin sanyi, hancinta ya yi jajir, kazalika kumatunta ma ya yi jajir. Ɗan jan dogon numfashi ya yi tare da saukewa a hankali kafin yasa hannu ya ɗan shafi lallausan kumatunta!. Cigaba ta yi da kukanta tamkar bata san yanayi ba, haka ya bi ya rinƙa tattaɓara har lokacin da barci ya ɗauketa a jikinsa, ajiyar zuciya ya sauke a fili ya ce dai gobe zaki yi azumi dik rigimarki!. Shi kuwa Hoorain yana san ya yi mata rarrashi mai kyau, amma yana jin tsoro saboda da kunnuwansa kuma da idanunsa ya gani kuma ya shaida ita matar Abdussalam ne, dan haka sai ya rabata da jikinsa ba dan ya so ba, ya rarrasheta tare da ce mata ta zauna kada ta sake fita yana zuwa. Yana fita Smart ya yi mashi sakon a kan ya shirya kayansa yau zai dawo kingdom of power, saboda Auta ta rigada ta ganesa, kada azo a samu matsala, kar su jiƙa mashi aiki ba tare da ya gama bincikensa ba, su yi abin kunya, ai kunga da kunya idan bincike ya bada cewa yaya da kanwa ce su ɗin, so dole ya rabasu. Sosai Hoorain ya ji zafin hakan, amma bashi da zaɓi, dole ya bi maganar babban yaya idan yana son cigaba da kasancewa cikin farinciki. Dole ya haɗa kayansa a ranar ya koma kingdom of power, ita kuma Auta Smart ya sanar da ita ta yi hakuri Hoorain zai dawo gareta nan da ɗan lokaci, ta kasance cikin farinciki, kuma ya basu dama su rinƙa yin waya da juna. Uhm lokacin da Hoorain ya dira a kingdom of power babu wanda bai girgiza ba, musamman ma King da shi ya gama saddakarwa Hoorain ya mutu, ya ji zafin cetan ransa da Smart ya yi, hakan yasa ransa ya ɓaci matuƙa da har ya fusata ya ce Smart ya wuce ya koma Paris, shi kuma Smart ya ce sai ya gama abin da ya kawosa, dama shi bai zo zama a kingdom ɗin ba, dan haka idan ya kammala dole zai koma in da ya fito, dan a can ya fi wayo. A wannan dare dai King da uncle Abbas game da Akka suka yi zaman meeting su uku wanda babu uncle Jahiz a ciki, a nan ne Akka ta ce. "Idan muka aura mashi Sareena ina da yakinin zata iya mantar da shi dik wannan bincike da yake son yi, kuma ina da tabbacin zata iya sauya shi ta yadda zai dawo yana jin maganarmu". Uncle Abbas ne ya karɓi zancen da cewa. "Ina fatan hakan ya kasance, in ba haka ba tabbas zamu shiga bala'in da gara mutuwa a kanta, zai zama dik abin da muka yi a baya ya tashi a banza".......... Shi dai King ya yi ƙasa da kansa bai iya sake cewa komai ba! Kun san wani irin zulumi King yake a ciki? Batu ne a kan Hoorain! Kun san da cewa su Akka basu san alaƙar dake a tsakaninsa da matar commander ba? Shi ne tashin hankalinsa na biyu bayan batu kan Ramish, yana tsoron gaskiya ta bayyana, mutumcinsa zata zube, kuma ai yanzu ya tuba. Su Akka kuma suna cikin zulumi ne a kan batun Ramish, suna tsoron Smart ya bankaɗo gaskiya, dan dikkansu abin ya shafa!! Shi ne fa suke san aura mashi Sareena wai dan su rufe mashi baki..... KAI SMART ƊAN DUNIYA NE, YA HANA SU AKKA SAKAT YA TAFI YANA SOYAYYARSA DA PRETTY!! WATO DIK SUN SAN KOMAI DAKE FARUWA! UHM AKWAI KALLO A GABA WLH!. Ganin King ya yi shiru yasa Akka ta ce. "Zuhair lafiya kuwa?". A hanzarce ya girgiza mata kai alamar babu komai, shiru suka zuba mashi idanun suna kallonsa, da yake sun san halin da suke a ciki sai suka ce kila shi ma fargabar abin da Smart zai iya tonowa ne yasaka shi a cikin damuwa, hakan yasa suka hau rarrashinsa suka tausansa tare da cewa kada ya damu da Smart ya auri Sareena komai zai canza, ita Sareena tana jin maganarsu, dan haka zata zama wadda Smart yake jin maganarta In Sha Allah!.... My people's kuna ganin haƙarsu zai cinwa ruwa kuwa? Anya zasu iya sanya Sareena ta zama wacce Smart yake jin maganarta kuwa? Muje dai zuwa. Haka suka yi wannan zaman meeting suka tashi ba tare da kwakkwarar mafita ba, da alama uncle Jahiz bai san me yake faruwa bane yasa babu shi a wannan zama. Ita kuwa Mammie tana can tana shirya yadda zata ɗauki Fanan daga gidan ba tare da kowa ya nemeta ba, wato ta rufewa ƴan gidan baki kada su nemi in da suke. A gefe guda kuwa ana can ana ta rabon kayan masarufi saboda azumin da za'a tashi da shi gobe, sarkin hatsi King ya bawa ragamar kula da wannan, talakawa sun wadatu da kayan abinci kam babu karya, ga tarin dukiya da aka raba masu dan sayan kayan abinci!!. YANZU NE CROWN OF POWER WATO (KINGDOM OF POWER) ZATA KAMA DA WUTA, YANZU WASAN ZAI FARA. ƘAƘA KARA ƘAƘA, GA HOORAIN GA KAMAR, SANNAN GA KING AND COMMANDER A TSAKIYA, UHM MAI WARWARE WANNAN CAKWAKIYA INA GA SAI MAMMAN KAMRAN KAWAI!!. 🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥 A hankali take salallaɓowa kamar wata ɓarauniya, misalin karfe 6 ne na safe, sanye take da uniform ɗinta, yau sport wears na school ɗin ta sanya, ta yi kyau a cikin kayan sosai, tin da take a cikin empeir ɗin bata taɓa shiga cikin kitchen ba sai a wannan karan, dan haka sai ta nufi kitchen ɗin cikin sanɗa. Sai dai fa a lokacin da ta isa cikin dry kitchen ɗin nasu sai da ta waro idanu waje, duniya guda ta gani, gabaɗaya ta zama ƴar kallo, ta ko'ina Robbot ne suke ta aikin kai komo, aikin dake gabansu kawai suke yi! Ajiyar zuciya ta sauke, almost 10 mins tana tsaye tana karewa kitchen ɗin kallo kafin ta karisa ciki. Babu wanda ya kulata, nan ta fara ƴan waige waige tana neman ta ina ne wajen girki da wajen shirya abinci suke!. Ta ɗauki a kallah good 10 mins kafin ta iya gano wajen girki a ciki. Can ta hango katafaren trys mai shake da kayan girke girke da ake kaiwa Black Tiger, sun kammala shirya mashi breakfast yadda yakamata, lokaci kawai suke jira ya cika su kai mashi, kun san shi ba'a haura lokacinsa kamar yadda ba'a nufara idan lokaci bai cika ba! Dole sai lokacin ya cika sannan ake zuwa kai mashi kome ya buƙata Can ta nufa kirjinta na dukan uku uku, tana zuwa tana satar kallon robot ɗin, dan tana ga kamar zasu ganota. Sai karanta Hasbunallahu wani'imal wakil da kuma lailla haillah anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, ta haɗa da ayar kariya. A cikin suratul yasin, aya ta 9. ‫َأ‬ ‫ْل‬ ‫َأ‬ ‫َنٰـُهْم َفُهْم اَل ُيْبِصُروَن‬ ‫ْمَسًّۭد ٰـَف ْغَشْيا‬ ‫ًّۭد‬ ‫َوَجَعْلَنا ِم ۢن‬ ‫ۢن ًّۭد َبْيِن ْيِديِهْم‬ ‫َسًّۭدا َوِمْن َخ ِفِه‬ Ta karanta wannan aya, tana karantawa tana nufar wajen abincin. Kuma wannan addu'a ya taimaka mata Allah ya datse ganinsu basu ganta ba har ta isa wajen, cikin gaggawa tasa hannunta ta ciro wani robar ruwa da ta ɓoyesa a wajen cikinta, a gaggauce ta ɗauke ruwan dake a saman tray ɗin da suka sanyawa Black Tiger ta sanya mashi wanda ta zo da shi, a miliyan ta bar wajen ta gudu ta koma parlourn. Wannan aya ta cikin suratul yasin, aya ta 9. ‫َأ‬ ‫ْل‬ ‫َأ‬ ‫َنٰـُهْم َفُهْم اَل ُيْبِصُروَن‬ ‫ْمَسًّۭد ٰـَف ْغَشْيا‬ ‫ًّۭد‬ ‫َوَجَعْلَنا ِم ۢن‬ ‫ۢن ًّۭد َبْيِن ْيِديِهْم‬ ‫َسًّۭدا َوِمْن َخ ِفِه‬ Aya ce dake makantar da idanun abokan gaba dan cinma mutum, wannan aya Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yake karantawa a dik lokacin da mushrikai suka nufosa, a lokacin da ya bar garin Makka ya yi hijira zuwa Madinah, lokacin da suka shiga kogo da sayyidina Abubakar wannan aya Manzon Allah (SAW) ya karanta hakan yasa Allah ya datse idanun mushrikan da suka biyo bayansu, basu samu damar ganinsu ba, a lokacin da Manzon Allah ya yi tafiya da Nana A'isha ma ayar nan ya karanta suka kau daga idanun makiya, so wannan aya tana da matuƙar muhimmanci ga Musulmi ya riketa, musamman a rayuwar yanzu da tsaro ya zama abin da ya zama, so na baku shi sadaka ku mun addu'a ta alkhari da bakunanku masu albarka!. Suratul Fatiha da Ayatul Kursiyyu ma suna daga cikin abin da Annabi (SAW) ke karantawa don neman kariya daga wajen Allah!. -----------------------------------🔥🔥 A miliyan ta nufi waje rike da robar ruwansa da ta ɗauko a cikin tray ɗin, tsabar murna sai murmushi take saki. A parlour ta isko Ronnie yana tsaye, yana shirye cikin hoodie mai bala'in kyau, yau garin nasu akwai sanyi sosai, ga iskar dake kaɗawa kamar za'ayi ruwan sama, damuna ta kusa dawowa, a wasu yankuna ma ta dawo!. "Good morning lovely bro". Ta faɗa tana tsananta murmushinta, ji take yi yau tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha...... A tinaninku me ta saka a cikin ruwan da ta bawa Black Tiger?. Hararar ya ɗan dalla mata kafin ya ce. "Ina kika je kuma bayan kin san ina jiranki". "Sorry my bro, na je wani wajen ne, mu tafi yanzu". "Ba za'a faɗa mun in da aka je ɗin ba?". Hannu tasa ta rufe fuskarta tana ɗan murmushi mai ƙayatarwa....... "Me zaki yi da robar ruwa ke da kike azumi yau?". Ya jefa mata tambayar yana kallan robar ruwan dake hannunta. "Mantawa na yi da ina azumi na ɗauko har zan sha sai na tina, yanzu dai please let's go". Ta kai karshen maganar tare da wucewa ta ɗauki jacket ɗinta and school bag ɗinta, ta miƙa mashi school bag ɗin kafin ta sanya jacket ɗin, tana ƙoƙarin zuge zip sama ta wuce gaba tana faɗin su je. Bayanta ta bi yana yaba irin kyan da ta yi yau, ya ce ta fi kyau a cikin sport wear ɗin nan, godiya kawai ta yi mashi suka wuce izuwa wajen motocin. Ba tare da ɓata lokaci ba suka wuce school. Kamar kullum yana sauketa ya dawo gida. Yana dawowa bedroom ɗinsa ya nufa ya kwanta, dan dama barci bai ishe shi ba, daren jiya bai samu ishasshen barci ba, dan tin da ta farkar da shi da ihunta da ya koma bai rintsa ba. A ɓangaren Black Tiger kuwa, dik karfin tsafinsa Allah ya datse idanunsa sakamakon addu'ar da Sweetie ta yi, so bai ga lokacin da ta canza ruwan shansa ba, saboda haka ana kawo mashi abinci kamar yadda ya saba ya ci ya ƙoshi, sannan ya zuba ruwan nata a cikin cup ya sha ba tare da tinanin wani abin ba. Sai dai kuma yana shan wannan ruwa sai me? Take a wajen ya fara kwarara amai tamkar zai amayar da kayan cikinsa, wani irin amai bakinkirin kamar bakar leda mai bala'in yauki ya fara kwararawa tamkar ba daga cikinsa ya fito ba, gabaɗaya ilahirin jikinsa ya hau kakkarwa tamkar wanda ake jonawa kantarki, lokaci guda gabaɗaya empeir ɗin ta yi wani irin azabbabben duhu na ƴan ɗakiku kafin daga bisani ta sake yin haske, wani irin juyi yaga gabaɗaya room ɗin nasa tana yi mashi, kansa dake barazanar tarwatse mashi ya dage, lokaci guda idanunsa suka rikiɗe zuwa Jade eye mai duhu kafin su koma normal. Wasu irin zaratan jijiyoyi ne suka bayyana sosai a gaban goshinsa, dafe cikinsa dake tsananin murɗa mashi da hannu guda ya yi, a take a wajen ya zube ƙasa a saman gwiwowinsa ya hau murkusoso a wajen. Robot dake serving ɗinsa abinci ne ya yi gaggawar ɗaukarsa cak daga wajen, sai dai kafin ya motsa da shi daga wajen Black Tiger ya daina numfashi gabaɗaya. Dik wannan abin dake faruwa Ronnie yana can yana barcinsa, ba shi ya tashi ba sai karfe 1:30 dai'dai, kai tsaye bedroom na yayan nasa ya nufa, sai dai a lokacin ya iskosa yana barci, bai san ba barci yake yi ba, tin wannan suma da ya yi Robot ya dawo da shi saman bed ɗinsa shi ne har yanzu bai farfaɗo ba! Ronnie ya ɗauka barci ne, so sai ya wuce cikin luxury toile ɗinsa ya watsa ruwa, sannan ya ɗauro alawala ya fito. Shiryawa ya je ya yi cikin pj's dress ya zo ya tada sallah domin yin azahar sai ya je ya ɗauki Sweetie a school. First time ɗinsa da yin azumi kenan yau, amma bai ji wani wahala ba, saboda iska da sanyin da suka tashi da shi. Ko da ya idar da sallah bai bi ta kan yayan nasa ba ya fito ya nufi wajen parking lot ɗinsu. Cikin motarsa ya shiga tare da escort ɗinsu suka wuce ɗaukota. Yau dai ita kaɗai take zauna abinta tana jiransa, dik ƴan kawayen nata ma sun janye jiki da ita, saboda sun gano daga BLACK TIGER EMPIRE take, suna bala'in tsoro sai suka ja baya, ta yi ƙoƙarin nuna masu babu komai, amma sun ki yarda da ita, sun ce ina ta wuce class ɗinsu!. Ko da ta dawo daga school bata zame ko'ina ba sai part ɗin Big Bro, dan tasan me ta yi mashi, so burinta kawai ta zo ta gansa, ta ga abin ya yi aiki ne ko bai yi ba! Da ta zo taga yana barci sai ta ji babu daɗi, dan sai ta yi tinanin bai sha ruwan ba, dan haka jiki babu kwari ta juya ta koma bedroom ɗinta. Ronnie ya so zargan wani abin, amma kuma sai ya kawar da hakan ta hanyar korar shaiɗan. Wanka ta yi ta shirya cikin malesian gown wanda ya kai mata har ƙasa, ya bi coca cola shape ɗinta ya zauna ɗas, hp ɗin nan nata ya fito sosai, gata ta ko'ina ta cika ɓul-ɓul. Kasancewar yau suna azumi babu batun yin dinner, sai suka zauna yin karatu kawai har zuwa bayan la'asar. Bayan sun yi sallah sai ta ce su wuce church, har lokacin Black Tiger yana nan yadda yake tin safe, bai farfaɗo ba!. Church suka wuce ita da Ronnie, amma sai da ya ja mata kunne sosai a kan kada ya ji bakinta ta yi magana, da okey kawai ta amsa mashi. Ta so su gana da Black Tiger kafin su tafi, amma ina, bata samu wannan dama ba, dan a tinaninsu barci yake yi. Addu'a sosai ta yi a lokacin fitarta empeir ɗin, shi ma Ronnie ta ce ya yi addu'a, ba musu ya yi, dan yasan dik abin da zata ce ya yi to mai kyau ne. Tin da suka doshi katafaren ginin church ɗin ta ji gabanta yana wani irin faɗuwa, yana bada bugu dum dum, amma ta cigaba da ambato sunan Allah har suka ƙarisa ciki. A tare suka sauko ita da Ronnie, yau sai ta saje da kiristocin ma, dan kan babu ɗankwali, kun san a irin wannan birni dama yaushe zasu samu ɗankwali? Ai babu, so haka ta fito dan sonta da zuwa church ɗin. Hannunta Ronnie ya kama suka ƙarisa ciki. Wani irin mamaki ne ya kamata ganin yadda aka ƙawata ginin church ɗin, an zuba kayan alatu na more rayuwa, ga wasu irin luntsuma luntsuman kujerun zama mai sa mutum ya mance in da yake, ga wani sanyin Ac mai ni'ima dake dukan kowa. Can saman stage father church ne zaune saman haɗaɗɗen kujerarsa mai kama da King seat, yana sanye cikin suit while face ɗinsa da white glass, daga bayansa wani katan bookshelf mai girman gaske wanda yake shake da tulin Bibles da littafan tarihi, ga wasu kyawawan flowers decorations a kusa da bookshelf ɗin, sannan a gaban father church akwai wani katafaren table mai shake da wasu littattafai da kuma bell na bugawa dan samun attention na mutane!. Gaskiya Church ɗin ya haɗu babu karya. A saman waɗan nan haɗaɗɗun kujerun suka zauna, mutanen birnin suna cike sosai, da alama wannan Church na manyan kai ne, dan dik waɗan da suke ciki jikinsu ya nuna alamar jin daɗi da hutu!. Kowa ya natsu tsit sun mayar da hankali a kan Father church wanda shi ma a yanzu ya shigo, gyaran murya Father ya yi kafin ya fara jawabinsa game da buɗewa da addu'a tasu ta kiristoci, a cikin addu'ar ne ya ce sun fara da sunan UBANGIJI Jesus....... Pastor na faɗin haka ta yi gaggawar miƙewa tsaye, with harsh voice ta ce. "Karya ne, Annabi Isa ba Allah bane, kuma shi bai taɓa ce maku shi Allah bane, infact shi ce maku ma ya yi ku bi Allah ku yarda da shi manzan Allah ne sai ku tsira, amma babu in da ya ce maku shi Allah ne, idan kuma akwai shi ka bani hujja, in dai ka kawo mun in da ya ce maku ku bini nine Allah to na yarda daga yau zan ajiye addinin musulunci na bi kristanci!!". Babbar magana, tashin hankali kenan!!! Zaro idanu Ronnie ya yi yana kallanta, dama a ransa yasan dik jan kunnen da ya yi mata a kan kada ta yi magana in suka zo dik na banza ne, saboda ya san ba'a ɓarna a gabanta ta yi shiru, sai dai bai taɓa zatan ta haka zata yi fito na fito da su a bainar nasi ba, tana neman jefasu cikin cakwakiya tasa shi ma a gano ya musulunta, shi wai ya zai yi da Sweetie ta ɗan rage zafa a kan addini ne? Ya jefawa kansa tambaya. A hankali ya ɗago ido dan ya saci kallonta. Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Dik matsoraci baya da'awa, ni bana tsoron dik wani hukuncinsu, abin da na sani shi ne dole ko a bakin zaki nike zan faɗa cewa Allah shi ne Allah shi kaɗai, ba zan taɓa yarda da akasin hakan ba, koda ina tsakanin mutuwa da rayuwa!! Ka dai'na tsoron bayin Allah, ka ji tsoron mahaliccin bayin ne kawai!!". Da farko ya yi niyar dallah mata harara, zafafan kalamanta yasa ya fasa, saboda ta fishi gaskiya. Kallan tsab pastor ya yi mata kafin ya tambayi who's she?. Ronnie yana ƙoƙarin basa amsa ta rigasa da cewa. "Mai gaskiya wadda bata goyan bayan karya kuma bata shakkar faɗar gaskiya a koma ina!! Sannan kuma wadda take rike da fitillah mai haske ta zo haskaku a cikin duhun da kuke, ta fitar da ku daga cikin duhun kai zuwa hasken musulunci". Tin da ta fara magana Black Tiger yake kallanta yake mamakin karfin hali irin na yarinyar nan, kai ka ji wai mai gaskiya, Sweetie akwai abin dariya wani lokaci, bilhakki da gaskiyarta ta zage zata yi masu wa'azi, ta ɗaure fuska tamau wai irin su san ba wasa take yi ba. Fitarsu ke da wuya Black Tiger ya farfaɗo daga sumar da ya yi, shi ne ya zauna yana kallansu. "A cikin injila ta yahaya chapter 1 verses 1 a nan ne Yesu ya ce shi ne Allah!". Cewar pastor kenan. Da gadara da full confidence ɗinsa ya faɗa, shi nan irin shegen nan, wai ya kawo hujja...... A karo na biyu Ronnie ya yi mamakin biyewa Sweetie da pastor ya yi, bai yi tinanin zai biye mata ba, abin da bai sani ba shi ne, shi maras gaskiya a dik in da yake in dai ka yi magana sai ya biye maka, saboda yana san wanke kansa ya nuna shi mai gaskiya ne, mai gaskiya na ainahi baya damuwa da sai jama'a sun yarda da shi, burinsa kawai Allah ya yarda da shi, idan Allah ya yarda da shi to da izininsa zai sanya jama'a su yarda da shi!!. Wani irin sanyi Sweetie ta ji ya ratsa zuciyarta, abin nema ya samu, dama so take pastor ya biye mata ta kaisa ƙasa, har ita zai kawowa wani hujja, muje zuwa. Gyaran murya ta yi kafin ta fara da cewa. "A'a, cikin Bible gabaɗaya babu in da aka ce Annabi Isa (A.S) shi ne Allah!!. Akwai wurare da ake nuni da cewa shi yana da matsayi na musamman, amma a cikin littafin Injil (Bible) dayawa daga cikin maganganun Annabi Isa (A.S) suna nuna cewa shi bawan Allah ne kuma manzon Allah. Dik kuma zan kawo maka hujjoji masu karfin da zaka gamsu idan ka buƙata". Binta da kallo gabaɗaya jama'ar cikin church ɗin suka yi, shi kansa pastor kaman ya ɗan tsorata ne ko yaya ne, sai ya ce. Ta fitan mashi a church yanzun nan. Gyarawa ta yi ta zauna kafin ta amsa da babu in da zata je har sai ta gama amayar da abin da ya kawota, babbar magana kenan. Rai a matuƙar ɓace pastor ya bada umarni ga securitys su zo su fitar da ita. Kan kace me wasu shirga shirgan securitys sun shigo cikin zafa da nufin sun zo su ɗauketa su yi waje da ita. Aikuwa suna zuwa Ronnie ya miƙe tsaye, da wani irin mugun kallo ya bisu wanda yasa suka ci wata uwar birki ba tare da sun shirya ba, kun san gabaɗaya birnin tsoron Ronnie suke ji, shi ne zakarar da ya buge kowa, dan haka suka kasa motsawa daga in da suke tsaye, saboda tsoronsa. Hararar ya bisu da shi kafin ya nuna masu hanyar fita da hannunsa ɗaya, ba tare da ya yi magana ba, ai a miliyan suka juya suka fita. Ta witsiyar ido ya bi pastor da kallo kafin ya tsayar da kallansa a kan Sweetie, cikin natsuwa ya ce. "Kina da hujoji a kan maganarki ne?". Ya yi mata wannan tambaya ne ba dan bai san tana da hujjijo ba, sai dai ya kare kansa, irin ya nuna shi bai san komai ɗin nan ba, kuma yana yiwa su pastor kwaɗayin Rahmar Allah, so zai so ta cetosu daga duhun kai izuwa haske. Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas tana da hujjijo kafin ta ce. "Ina da hujjijo kwarara sosai Ronnie". "To kawo mana su". Ya faɗi hakan tare da komawa ya zauna. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, hankali ya kwanta, buƙatarta ta biya, rai ya yi sanyi, abin nema ya samu, dan haka cikin natsuwa ta cigaba da cewa. "A cikin Injila ta yahaya chapter 17 verses 3 yana rubuce cewa. Kuma wannan ita ce rai madawwami (Allah kenan), su san kai Allah wanda kai kaɗai ne na gaskiya, da kuma wanda ka aiko Yesu Almasihu wato Annabi Isa kenan" "Wannan yana nuna cewa Allah shi ne kaɗai na gaskiya, kuma Yesu (Annabi Isa) manzonsa ne. In bai yarda ba ya duba cikin Bible ɗin yanzu zai ga hakan, dan haka Annabi Isa dai bai ce ayi bautarsa ba, kuma dik mai kaunarsa na gaskiya ma ba zai bauta mashi ba!!". "Kazalika cikin injila ta Matiyu chapter 26 verses 39 tana nan a rubuce lokacin da Annabi Isa (A.S) ke addu'a yana cewa. Ya UBANGIJINA ka ɗauke mun wannan kofin, amma kada nufina ta cika, sai da sanka". "Wannan yana nuni da cewa Annabi Isa yana da UBANGIJI da yake roƙonsa dik abin da yake da buƙata, ba shi ba ne ALLAH. Sannan a cikin injila ta Markus chapter 12 verses 29 Annabi Isa (A.S) ya ce. Ku Isra'ilawa ku ji UBANGIJI ALLAHNMU UBANGIJI ɗaya ne tak da bashi da abokin tarayya. Wannan ya bayyana cewa ALLAH ɗaya ne, ba Annabi Isa ba, dan da bakinsa ya ce ALLAH ɗaya ne kuma ba shi bane!!". "To amma me yasa wasu Kiristoci ke cewa Annabi Isa ALLAH ne?". Ta jefawa kanta tambayar da tasan babu mai bata amsa, dan haka sai ta bawa kanta amsa da cewa. "Akwai wasu wurare da aka fassara su da cewa Annabi Isa yana da wata alaƙa ta musamman da ALLAH, kamar Yahaya chapter 1 verses 1 da ka ambata a baya". Ta yi maganar idanunta a kan pastor, dan shi ya ambaci cewa a shafin farko na Injila ta yahaya Annabi Isa ya ce shi ne ALLAH, dan haka sai ta ce. "A farkon shafin layin farko tana nan a rubuce cewa. Abu kalma ce, kuma Kalmar tana tare da ALLAH, Kalmar ita ce ALLAH...........Waɗanda suke da ra'ayin Trinity, wato masu ra'ayin cewa UBANGIJI uku ne, Uba, ɗa, da ruhu mai tsarki, to su sukan yi amfani da irin waɗannan ayoyi su kafa hujja kan cewa annabi Isa ne ALLAH. Amma a cikin Bible gabaɗaya, babu inda Annabi Isa ya ce shi ne ALLAH, ko ya umarci mutane su bauta masa, sannan kai kanka ka sani har yanzu akwai saɓani tsakanin masu tafsirin Bible kan wannan batu, kuma da yawa daga cikin Kiristoci da kansu sun yarda cewa an canza Bible tun asali, kawai san zuciyarsu suke bi kamar dai kai ma, ina da tabbacin kasan an canza Bible. Wannan yasa musulmai suke da aqidar cewa Annabi Isa (A.S) bawan ALLAH ne kuma manzonsa, ba ALLAH ba, saboda ku kuna da Bible sun fi kala goma, mu kuma Alqur'ani guda ɗaya ce, tin ranar da aka saukar da ita har yau babu ko wasali ɗaya da aka canza, bama wanda ya isa ya canzata!! Saboda kalamul lah ce ita!!". Ta kai karshen maganar tare da dakatawa tana mayar da numfashi. Ronnie ya ji daɗin wannan batu, abin ya yi mashi sugar sosai, ya sanyaya ransa, har wani ajiyar zuciya ya sauke, ya ji kwarin gwiwar zai tsayawa Sweetie tin da ta faro wannan batu ta dire aya, ta yi mashi kaca kaca da pastor yau. Sai dai basu ankara ba sai gani suka yi pastor ya harbo bell dake gabansa sai kan gaban goshin Sweetie ya sauƙa, take ya fasa mata goshi sai jini, cikin tsawa da kakkausar murya ya ce. "Yarinyar banza, ni zaki zo kina kalubalanta? Yaushe aka haifeki da har zaki ƙaryata littafanmu? Wacece ke a duniya? Littafan da suke tun tsawon shekaru aru-aru? Ke har kin isa in duba Bibles saboda ke? Ku mutane kun ji fa! Wannan ƴar wannan aba ce take ja in ja da ni!". Ya yi maganar yana ɗaga hannu yana kallan mutanen dake a cikin church ɗin. Kun san aka ce idan kare bashi da gaskiya sai ya fara daka haushi dan ya tsira daga harin mutane, to shi ne shi ma Father church yake yi kenan, dik ya bi ya firgice yana wasu muzurai, shi nan bilhakki a kan gaskiyarsa yake! My people's me kuke tinanin zai faru a cikin wannan Church ɗin? Uhm akwai kallo fa. Musulmi ku ce Allahu Akbar! P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️ For more information 08161390581 Whatsapp me only!!. 🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘 Downloaded From https://tknovels.com.ng