An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  AURE KO BOKO? (Littafi Ga Matasa Maza da Mata) 3 SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com GABATARWA Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai. Duba da halin da matasa ke shiga a kasarmu Nijeriya a yau, daga mazan har matan, akan rashin aikin yi ga wadanda suka samu damar yin ilmin zamani mai zurfi da matsalolin da hakan yake haifarwa, sannan da halin wasu daga cikin manyan 'yan bokon wannan zamani na baiwa boko fifiko akan addini, yasa na yanke shawarar rubuta littafin AURE KO BOKO? Ba don komai ba sai domin ya zamo hannun ka mai sanda ga irin wadannan 'yan boko da matasa masu zurfin ilmi marasa aikin yi. Tasirin furucin iyaye akan 'ya'yan su mai kyau ko maras kyau, hakika shi bakin iyaye kaifin sa da tasirin sa yafi na reza. Sannan 'ya'ya amana ne a hannun mu, kasancewar Ubangiji yayi musu umarnin su yi wa iyaye biyayya sai da yayi tagociya ga cewa banda akan umarnin Ubangiji. Ina fatan wannan dan littafi ya zamo mai amfani ga al'umma, matasa maza da mata, ya zamo sadaqatul jariya ga iyaye na ya yafe min kurakuran da ke cikinsa. - Sumayyah Abdulkadir (Takori) 3rd June, 2021. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowanne gidan radiyo ko kafafen yada labarai ba tare da izni na ba, ko copying dinsa a kafafen sada zumunta, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma daga Lauya na Barr. Sadiq Rufai Wali. GODIYA Ga dukkan members na Takori's online Forum, na gode da kaunar ku da goyon bayan ku. FATAN ALKHAIRI Ga duk makaranta littatafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ina godiya da yabo da fatan alkhairin da kuke yi mun, Allah ya barmu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi. TUNASARWA Wannan littafi da labarin da ya kunsa duk Kirkirar marubuciyar shi ne. Sai a guji zargin cewa an yi ne don wani ko wata, ko wasu gungun jama’a, ko an dauki rayuwar wani. In ka ji wani abu da yayi kama da naka to arashi ne kawai aka samu. -Takori AURE KO BOKO 3 Direban motar wadda mace ce ta yi azamar dauke kan sitiyarin motarta, ta gwammace ta buga wa motar gabanta a kan dai ta kashe mai rai. A take mummunan accident din motocin ya ziyarci kunnen duk wani mahaluki da yake wajen. Motocin biyu sun kwankwatse sun yi raga-raga amma sumul matukiyar motar ta fito cikin shiga ta alfarma jikinta na rawa da karkarwa, don dai ta tabbatar ba ta gogi jikin Safiyyah ba ko kadan, wadda ta yi tuntube da dutse ta fadi a kasa, bakin ta ya fashe. Bata ko damu da damejin da dalleliyar motar ta kirar jiya-jiya tayi ba. Fatan ta da burin ta bai wuce ya zama bata yi sanadin ran wannan kankanuwar halittar Ubangijin ba. Da gudu Halimah ta iso wurin, cikin wani yanayi na fita hayyaci, ta kwala kiran sunan “SAFEEYAH!” da iyakacin muryar ta, tare da daga ta a jikin ta tana girgiza ta cikin yanayi na madaukakin tashin hankali. “Dauko ta mu karasa asibiti mafi kusa a duba ta sosai, don Allah”. Matar ta fada cikin gigicewa. Muryarta da jikin ta na rawa. Guilty ya dabaibaye ta. Halimah sai ta ji kamar ta san muryar, kamar ta sha jin muryar, a very familiar voice wadda duk inda ta ji ta zai yi wuya ba za ta kasa gane ta ba. Da sauri ta juyo, cikin wani yanayi suka hada ido da matar. Gaba dayansu suka zaro idanu cikin mamaki da tu'ajjibi a lokaci guda suka hada baki wajen anbaton sunan juna. “Zarah!” “Haleemah- Leemah!!!” Da wata irin azama suka kama suka kankame juna, Safeeyah na tsakiyar su, suna maimaita kiran sunan junansu. Kukan Safeeyah ne ya sa suka saki juna. Zarah ta sunkuya ta dauke ta tana fadin, “Come on beauty, bude idon ki sosai ki ga Mamanki Zarah, ina fatan baki ji ciwo ba?”. Ta maida dubanta ga Halimah tana kallonta sama da kasa cikin wani irin dumbin mamaki. “Leemah, ke ce kuwa? Daga ina ki ke haka? Ina za ki je?” Idanunta kamar za su fado waje. Murmushi Halimah ta yi, ta ce, “Maama na zan kai asibiti, ta wayi gari da kyanda, nan ne Murtala ba nisa, bari mu karasa maza”. Zarah ta kama hannunta tana hawaye. “I will NEVER let you go Haleemah, sai na ji daga inda ki ka fito, sai na ji labarin rayuwar ki. Sai naji abinda ya maida ke haka. This is not my Leemah! My beautiful, elegant Leemah. Ina Daddyn ki? Ina Hanan? Me kike yi a Kano? Wa kika sani a Kano? Leemah please tell me everything about you….”. Zarah ta fada tana gwama numfashi, ganin cewa da gaske Halimah niyyar tafiya take yi ta bar ta a wurin. Halimah ta san a baya ba ta boye wa Zarah komai, amma yanzu kam ba ta da abun fadi, don ba ta neman taimakon kowa. A gamshe ta ke da rahmar lafiya da wadatar zuci da sama da komai miji nagari, da Ubangiji ya yi mata. Zarah kawai waya ta fiddo a jakar hannun ta, gabadaya hannu ta da jikin ta kyarma suke, ganin Halima ta ki ce mata komai sai kallo. Ba ta bi ta kan surutun mutane a kan accident din su ba, da mai motar da ta bugawa da ke ta kumfar baki da balbalin fada. Ta fadi dai-dai inda ta ke ta cikin wayar, ba jimawa sai ga mota (lemousine) a gabansu, tare da bakanike. Ta ba wa mutumin hakuri ta ce ga bakanike nan zai tafi da motocin a gyara musu, za ta biya komai. Jikinta sai rawa yake don hankalinta duka yana kan Halimah. Tana gudun kada ta tsere ta bar ta. Don bata gama tabbatar da psychogical well being din ta ba. Ta sanya Safiyya a motar, sannan ta ja hannun Halimah suka shiga, ta fada wa direban asibitin da zai kai su, wanda duk zaman Halimah a Kano ba ta ko taba jin sunansa ba. Kwararren likita ba’indiye ne ya duba Safiyyah sosai, ya hada allurai ya yi mata, ya rubuta mata magunguna masu inganci ya ce yanzun nan a je a saya a bata ta sha a take. Zarah ta karbi takardar ta ce su jira ta, ba jimawa ta dawo da ledar magungunan mai tambarin pharmacy din asibitin. Ta bude daya bayan daya cikin hila da dubara ta bai wa Safiyyah, da gani ta saba da baiwa kananan yara magani, sannan ta dauko ta a kafadarta, tana kankame da hannun Halimah suka koma mota, ta ce da direban ta ya kai su masaukin ta. Suna tafe a hanya Zarah ke gaya mata, sun zo seminar lauyoyin Arewa anan Kano ne ita da maigidanta Barr. Zahraddeeni Alhassan, jiya suka zo, nan da jibi za su koma Bauchi. Direban ya shigar da motar gidan saukar baki na Ni’imah Guest Palace, Halimah hankalinta gabadaya ya yi kan Hashim. Duk da hilatar ta da hira mai dadi da Zarah ke yi. Ta dauko tsohuwar wayar ta nokia don ta kira shi ta gaya masa halin da suke ciki, ta tarar da babu ko sisi a ciki sai naira daya, don haka ta ce da Zarah ta maida ita gida, mijin ta bai san za su dade haka ba. Zarah ta yi mata wani kallo, sannan ta girgiza kai ta ce, “Ai in kin ga na maida ke ko, kuma na kyale ki kin koma inda kika fito ko, ko ma daga ina ki ka fito ke kika sani. Abinda nake so kawai ki gaya min labarin rayuwar ki dalla-dallah....in na ce dalla-dalla ina nufin daki-daki; tun daga rabuwar mu ranar graduating dinmu na masters degree a kasar Mexico zuwa yau da na tsince ki a Kano hajaran-majaran cikin yanayin da ban taba zato ba. Jikina na ba ni ko dai kurciya aka yi miki ki ka baro mahaifin ki da 'yar uwar ki?” Sai ta baiwa Halima bazawarar dariya, "kurciyar lafiya ana zaune kalau? Waye makiyina har haka? Kin sanni ko abokin fada bani da. In kina so in sauka daga motar nan, sai kin ba ni aron wayar ki na yi magana da Baban Safeeyyah, yana can yana jiran mu, in muka dade hankalin sa zai tashi”. Ba musu Zarah ta ba ta dalleliyar iphone din ta, tana mamakin kauna da damuwar ta ga mijin ta har haka, canjin rayuwa bai sa Halima ta manta yadda ake operating babbar waya ba, ta karba jiki na rawa ta sa lambar Hashim a ciki, wadda ta ke haddace kamar karatun sallah a cikin kanta. Hashim ya amsa very politely da husky voice dinsa. "Assalamu alaykum, Hashim Yakasai ke magana". “Cheriè, ni ce Halimah, I met an old adorable friend of mine, Zarah Datti, da nake yawan ba ka labari, wadda ta koya min karatun sallah da karatun Alqur’ani a Mexico. Ta tafi da mu masaukinta a wata unguwa da ban sani ba, ta ce, lallai sai mun yi magana za ta dawo da mu gida”. “A ina ne masaukin nata? Sabida zan zo in taho da ku da kaina nan da one hour”. Ta daga kai tana karanto sign board ta ce, “Na ga an rubuta Ni’imah Guest Palace”. Ya ce, “Alright. Ba matsala, ku gaisa kafin na iso”. Zarah dai tana ta kallon ta, tana maganar ta da Hashim cikin tarin nutsuwa kamar yadda ta santa tun a can baya, fatar bakin ta a hankali take motsawa, ta kara sanyaya muryarta, ta zuba ladabi mai ban sha'awa da soyayya mai tattare da kauna a cikin ta, tana mamakin soyayya da yardar da ke tsakanin ta da mijin nata haka. Za ta so ta gan shi, ko don ganin me ya taka haka da ya tafiyar da zuciya da ruhin Halimah-Leemah a kansa har haka!. Dakin da suka sauka ma anan Ni’imah V.I.P room ne, mijin Zarah bai dawo ba tukunna. Abincin da aka ajiye a rurrufe bisa dining ta fara bubbude musu sai tiriri yake yana tashin hadadden kamshi, ta ce su fara ci, suna ci tana baiwa Maama-Safeeyah a baki. Tana mamakin me ya sa yarinyar ta ki bude idon ta har yanzu? Gashi da alamun ba bacci take ba tunda kuwa abinci ma take ci. Amma dai Allah bai nufe ta da tambayar Halimah ba, hankalin ta ya fi daukuwa ga son jin labarin Haliman. Sai da suka gama suka yi sallah, sannan Zarah ta kara rokon Halimah ta gaya mata labarinta. Tana rokon ta da girman Allah kada ta cire ko harafi daya daga ciki da sunan yi masa kwaskwarima ko sakaya mata wani abu a cikin sa. Ta tuna aminci da yardar dake tsakanin su? Halimah ta yarda Zarah mai kaunar ta ce ba tun yau ba, mai son ta da alkhairi ce da tsira a duniya da lahira, don haka ta bude baki cikin nutsuwa ta gaya mata komai, tun daga ranar da ta kade Hashim a ma’aikatar NCC, yadda suka fada a soyayyar juna a kasar Holland, badakalar auren su, zamansu na dan lokaci a Abuja, rayuwarsu ta birnin Kano, zuwan Hanan da wayar su ta karshe da ita. Har kawo rabuwarsu ta yau da mijin ta Hashim da zummar zuwa kai Maama asibiti. A lokacin Halimah ta lura Zarah Datti kuka ta ke yi, kuka ta ke tukuru da ran ta da zuciyar ta, hawaye da majina wani na korar wani. Ba tare da ta damu ko kadan da ta share su ba. (Manzon Allah SAW ya ce ku ji tausayin mai arzikin da ya talauce). Shiru ya ratsa a tsakanin su, bayan Halimah ta kai Ayah. Zarah taci kukanta ma'ishi ta koshi, sannan tasa habar zanin ta tana share fuska, ta dau tissue ta fyace hanci. Tsanar Prof. Numan ta wani irin darsu a ranta. Bata taba ganin mugun uba mai selfish interest irin sa ba. Sannan ta ce. “Halimah ban hada sani da Allah ba, amma na tabbata bautar aure zai kai ki aljannah, sadaukarwar ki za ta baki ceton Annabi, gudun duniyar ki zai tsallakar da ke SIRADI, sannan yardar mijin ki za ta ba ki duk abin da Allah ya tanadar wa matan kwarai a ranar gobe. Allah ya sa ni a damshin ki Halimah!”. Halimah ta yi murmushi, her beautiful serene smiles, mai narka zuciyar mai kallon ta, daidai lokacin da wayar Hashim ta shigo wayar Zarah, tana dagawa taji muryar sa very soft, a takaice ya ce. “Ina downstairs, su fito mu tafi in kun gama”. Ya kashe wayar. Zarah ta tsura mata ido, ganin yadda tayi maza ta mike futuk! Kamar wadda aka tsikara za ta dauki Safiyyah dake cinyar Zarahn. “Amma me ya sa ki ka ce Hanan kada ta gaya wa Daddy inda ki ke, bayan ya gane kuskuren sa?” Halima ta yi wani maqalallen murmushi na gefen baki, “Saboda na sanshi, na san ko waye Daddy na farin sani. He is not giving up easily, ban yarda ya yi nadama haka da wurwuri ba. Ita ma Hanan din kan ba yadda zai yi da abin kunyar da ta kwaso masa ne, beside bana bukatar komai daga gare shi sai albarkar sa, kuma yace bazai bani ba”. Ta dauki ‘yar ta ta nufi hanyar kofa. “To ba ni lambar wayar ki mana Leemah? Ko haka za mu sake rabuwa without each other's contact, kamar yadda ki ka watsar da ni a baya?” Halimah ta ji kunya, hakika Zarah ba kashin yadawa ba ce a rayuwarta, amma a halin yanzu ba ta son yin alaka da kowa, ba don komi ba sai don ta fi son ta tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ta, kada alaka da irin su Zarah ya dinga tuna mata da rayuwarta ta baya. Ya raunata imanin ta da yadda Ubangiji yake so ya ganta. Zarah ba ta tsaya sauraronta ba ta karbi wayar hannunta ta sanya lambarta a ciki ta kira, an yi sa’a da ragowar naira daya a wayar Halimah, don haka kiran ya shiga, ta yi saving mata sunanta da Besty, sunan da ta ke kiranta da shi a baya. Har downstairs Zarah ta rako su tana rike da ledar magungunan Safeeyah. Nan suka tadda Hashim a reception, yana tsaye ya tokare kafarsa daya a jikin bango, sanye yake da jamfa da wando na farin yadi mara nauyi, looking smart and gentle sabida yadda tsafta ta kama jikinsa. Sumar nan baka sidik ta kwanta luf a kansa. Da sauri Halimah ta isa gare shi tana ba shi hakurin tsayar da shi da suka yi. Zarah ta karaso tana murmushi ta mika masa ledar maganin. “I’m so sorry Baban Safiyyah, na dauke su na barka kai kadai. Na dade ban hadu da besty ba, so an zauna ana tattauna bayan saduwa”. Hashim ya yi dan murmushi, ya ce, “babu damuwa madam, mun gode. Za mu wuce, sai gani na biyu”. Zarah ta ce, “ga driver yana jiranku zai maida ku gida sai ya dawo”. Hashim ya ce, “Kuma na tsaida mai adaidaita da ya kawo ni. Ki yi hakuri, next time insha Allah”. Da haka suka wuce suna daga wa juna hannu ita da Halimah. Suka bar Zarah standstill tsaye a wajen harde da hannaye a kirji. Tana ta mamakin wannan al’amari na kawarta. Akan karan-kanta ita bazata iya sadaukarwar da Halimah tayi ba. Sabida tsoron cin amana da halin butulci irin na maza. Sai dai kam ta yaba da zabin nata, ilmi da kwarjini a gun Hashim abin ba’a magana. A tsayin daren bakidaya Zarah ta kwana ne tana tunanin hanyar da za ta bi ta taimaki rayuwar Bestynta Haleemah. Ba za ta iya jure ganinta cikin wannan rayuwar ba. Duk da Halimah ta nuna ba taimako ta ke bukata ba, sannan ba ta ga nakasu cikin rayuwar da ta ke yi ba, zama lafiya ya fi zama dan Sarki a wurin Haleemah. Haka nan a karshen labarin da ta ba ta, ta nuna Hashim ya daina sha’awar aikin gwamnati ko wani aiki da ya shafi zaman ofisoshi, wanda shi ne iya taimakon da za ta iya yi musu. Ga Halima babu takardu balle ita din ta sama mata aiki. Sai ta tuna Halima zata iya sake karbar takardunta online daga jami’ar National Autonomous University Mexico. Zata yi mata wannan kokarin sai dai Halima ta ce bata bukatar duk wani abu da ya fito daga gumin Daddynta. Karatun ta kuwa gumin Daddy ne. A yadda Halima ta ce, he only has passion for POLITICS. Itama ba gaya mata yayi ba, ta fahimci hakan ne daga irin rubuce-rubucen da yake yi akan shugabancin Najeriya. Wani tunani ne ya fado mata, nan da nan ta yi murmushi, don tana ganin ta samu mafita. Waya ta dauka ta loda mata isassun kudi bayan fitar maigidanta aikin da ya kawo su Kano, sannan ta kira mahaifinta. Tsohon gwamnan jihar Bauchi Alhaji Datti Giade. Bayan sun gaisa Zarah ta ce. “Daddy, za ka iya tuna Bestyna Halima Zubair Numan, wadda muka yi karatu a Mexico tare?” Ya yi dan tunani kafin ya ce, “Ko ‘yar gidan Prof. Numan na NCC?” “Ita fa Daddy, dogon zance ne, zaka iya sauraro na na minti talatin?”. “Babu matsala, ina jinki Fatimatul-Zahra’u”. Tiryan-tiryan Zarah ta koro masa labarin Halimah, tun daga haihuwar su da rayuwar su hannun Ubansu babu uwa babu dangi, rikicin aurenta da mahaifinta da hukuncin da ya yanke akan su, wahalhalun da suka sha a ryuwa, har zuwa kan gabar da suke kai a yanzu ita da mijinta Hashim. Sosai ya yi mamaki, don bai taba jin sacrifice makamancin wannan ba, ya kuma tausaya wa Halima ba dan kadan ba. Ya ce, "Dama har yanzu akwai ‘yan boko masu irin wannan gurbataccen tunanin irin Prof. Numan? Aure ai gaba yake da komai, kuma umarnin Ubangiji ne. Har ga Allah ba ta da hakkinsa, domin Ubangiji da Ya yi mana umarnin yin biyayya ga iyaye yayi togaciya kan ban da abin da ya saba umarninSa ne. Ki kira min yaron, ya zo nan gida Bauchi ya same ni, ya taho da dukkan takardun sa". Murna wajen Zarah ba a cewa komai. A take ta kira Halimah ta gaya mata. Ta ce, Hashim ya yi kokari gobe ya tafi Bauchi, ta bada lambar da zai kira idan ya isa tasha za a zo a dauke shi zuwa gidan su Zarah. Halimah ta sha daga da Hashim kafin ya yarda zai je Bauchi wajen Baban Zarah. A cewarsa shi fa ba ya bukatar aiki, da zata je ta wani ce da kawarta ta samo masa aiki, abin da yake so ya san ba zai taba samu ba tunda ba shi da hanyar shigar sa. Bai san cewa Halimah na ganin rubuce-rubucensa ba, kuma ta shigar da zancen cikin labarin da ta bai wa Zarah. Mahaifin Zarah kuma tsohon babban dan siyasa ne, wanda ya yi gwamnan Bauchi har sau biyu, ya yi sanata dinta ya yi minista. A halin yanzu shi ne shugaban jam'iyyar NRC, jam'iyya mai farin jinin da babu kamarta a Najeriya. A yadda ya ji labarin Hashim daga bakin Zarah da 'determination' dinsa, sai ya ga kwarai yana bukatar irinsa matuka a siyasa, musamman a wannan lokaci da siyasa ke gabatowa. Ya gama tsara abubuwa da yawa a kan Hashim tun kafin ya zo, albarkacin Halimah da Zarah. Yana so yarinyar ta samu 'future' mai kyau albarkacin sadaukarwarta da gudun duniyarta. Don ta kara jin tsoron Ubangiji ta san cewa wanda ya tsorace Shi ba zai tabe ba. Ta kara zage damtse wajen biyayyar aure, ta manta da rayuwarta ta baya. Kudin motar zuwa Bauchin ma Halimah ce ta yi fafutukarsa da kyar da sudin ludayi daga cinikin kwan kajinta. Ya shirya a ranar asabar ya kama hanya, bayan Halima ta bi shi da addu'a da fatan alkhairi mai dumbin yawa. ***** BAUCHI Hashim ya sauka a Bauchi lafiya da yamma lis, a matukar gajiye da takure da zaman bus, ya kira lambar da aka ba shi, mutumin ya gaya masa daidai inda zai tsaya ya ce zai iso nan da minti goma sha biyar. Wata 'discussion contineous' ce ta yi parking a gaban Hashim. Mutumin ya fito ya ba shi hannu tare da karbar jakar hannunsa ya bude masa kofa ya shiga ya rufe, sannan ya zagaya mazauninsa ya tada motar. Har suka zo unguwar 'Fati Mu'azu Links' inda gidan su Zarah yake suna hira shi da mutumin wanda ya ce sunansa Marzuq, shi ne babban yaron Alh. Datti Giade, wato mahaifin Zarah. Bangaren saukar bakin gidan su Zarah ya nufa da shi, ya bude masa daki ya ba shi mukullin, ya ce ya huta zuwa gobe ne zai gana da His Excellency, za a kawo masa abinci yanzu. Hashim yana yin sallah, kafin yayi komai Halimah ya kira ya gaya mata saukarsa lafiya, ta hada shi da Safiyyah suka sha hirar su. Da kyar suka yi sallama cike da kewa da kaunar juna kamar kar su rabu, sannan ne ya ci abincin da aka kawo masa. Yayi wanka ya canza kayan jikin sa. Da daddare ma kafin ya kwanta sai da ya sake kiran su. Washegari da safe bayan ya yi wanka ya kimtsa, Marzuq ya zo tafiya da shi wajen Alh. Datti. Cikin nutsuwar sa ta halitta Hashim ya yi sallama a tankareren falon, Alhaji Datti ya amsa a mutunce, tare da cewa, "Shigo ka zauna nan kusa da ni Mallam Hashimu". Cikin matsanancin ladabi Hashim ya gaishe shi. Ga mamakin Hashim sai ya ji ya ce da shi. “Yaya Halimatu da Safeeyyah? Ina fatan ka kira su bayan isowar ka?” Kansa a kasa ya amsa da cewa, yanzu ma kafin ya shigo nan sai da ya kira su, sun tashi lafiya dukkan su. Alhaji Datti ya fara jan sa da hira, cikin sakewa da hila irin ta manya, har sai da Hashim ya fara sakin jiki da shi ya daina nuku-nuku, labarin siyasar Najeriya yake ta bashi da mulkin soja dana farar hula na tun kafin a haife shi. Yana comparing dinsa da wanda ake ciki a yanzu. Yace "ratar dake a tsakanin siyasar da data yanzu mai tsananin fadi da girma ce Hashim, yanzu majority ana siyasa ne kawai don a yi kudi dare daya, yayin da shuwagabannin baya mulki suke don gina al'ummar su selflessly'. Shi Hashim yadda Alhajin ya sakar masa fuska da zuciya kamar ya dade da sanin sa har mamaki yake bashi. Duk zurfin ciki irin na Hashim dole ya saki jikin sa suka fara hira sosai da baban Zarah. Sai da Alhaji Datti ya tabbatar ya kama kurwar Hashim sannan ya sallameshi. Yace gobe da safe zasu gana sosai. Washegari din kuma bai samu ganin sa ba sai azahar. Hashim na shigowa falon yace "koma ka dauro alwala mu yi jam'in sallahr azahar" Hashim yace "ai da alwala ta" "to kai zaka yi mana limanci, bisimillah". Da suka idar da sallahr kuma Alhaji Datti yace "ban ci komai ba Hashim mu fara cin abinci ko?" Tare suka ci abinci bisa ledar cin abinci wadda aka shimfida aka jera abinci nau'i-nau'i. Da suka kammala yace ya raka shi unguwa, Hashim ya fara tunanin Alhaji Datti bai kira shi don komai bane sai don ya zame masa abokin hira. Tare suka tafi ofis din Alhajin, ya taimaka masa kan wasu ayyukan sa, sannan suka dawo gida. Suna sauka a mota yace Hashim ya wuce masaukin sa sai Allah ya kaimu gobe. Haka yayi ta jan Hashim a jikin sa kamar dan cikin sa, kulawar yau daban data gobe, don ya lura in ba da hakan ba bazai samu ya yarda da taimakon da yake son yi masa ba. Ya farfado da matacciyar zuciyar sa akan nasarar rayuwa. He already assumed shi bai zo duniya da sa'a ba. Ya riga ya karbi rayuwar sa a yadda take, baya bukatar wani sauyi a cikin ta. Hashim na so ya koma gida amma kullum Baban Zarah cewa yake sai gobe zamu tattauna. **** "Cheriè, sai yaushe zaka dawo ne?" "Ba ke kika jawomin ba Halima tunda nazo babu wata kwakkwarar magana sai hira da debe masa kewa da taya shi yawo a mota, anyway, he's a nice father. Kuma ina jin dadin zama da shi sosai saboda yawqn ibadarsa. Amma na kusa runtse ido in ce masa zan tafi wajen Halimah ta". Halima tayi dariya tace "ka daure baban Safeeyaah, haka kawai bazai kira ka don kuyi ta hira ba, mu kam dai kada ka damu damu lafiya sumul muke. Ga Sa'adatu ma jiya ta zo mana wuni mun sha hira, ta kawo ma Safeeyah kuli-kuli mai suga tana ta ci tun jiya". Da haka Halima ta kalallame shi ya yarda zai cigaba da zama har Alhajin ya sallame shi. Ilai kuwa washegari Baban Zarah ya kira shi, yau kuma kai tsaye cewa yayi, yana so ya fara ba shi tarihin iyayen sa da na rayuwar sa gabadaya. Domin shi dai ya riga ya samu Da (yana nufin Hashim din). Hashim yayi murmushin nan nasa mai ratsa zuciyar Halima, sai ya samu kansa da kasa musanta bukatar Alhaji Datti Giade, wani abu da bai taba tattaunawa da kowa ba a duniya bayan Halimah. Ya sunkuyar da kai ya gaya masa komai a kan mahaifinsa wanda Ba-Kano ne gaba da baya dan Yakasai, da kuma Innarsa, wadda ita Basudaniya ce. Aurota yayi ya zo da ita Najeriya. Yadda ya yi dukkan karatunsa da taimakon mahaifiyar sa, bayan rasuwar mahaifin su, samun aikinsa da NCC da taimakon Halimah. Bayan ta kade shi da mota. Zuwan su Holland da yadda soyayya ta kullu tsakanin su. Sallamar su da Prof. ya yi bayan auren su, amma ya dan sakaya wasu daga wahalhalun da suka sha a rayuwa ko wadda suke ciki a halin yanzu. A wurin sa fadin halin kunci daka ke ciki ga wani bayan mahaliccin ka, tamkar rashin godiyar Ubangiji ne. Cikin mutuwar jiki Alhaji Datti ya ce ya ba shi takardun sa ya duba, ya ciro su daga jakar goyonsa ya ba shi cikin ladabi. Ba abin da ke fita bakin Alhaji Datti sai, “Excellent… Mimtaaz… jamilan Jiddan!”. Ya dubi Hashim da murmushi ya ce, “Ashe tare da Dr. Of Philosophy nake zaune ni ban sani ba? Dr. of Telecommunication Engineering. Dr. Hashim kana son aiki a jami’ar Bayero? Ko Igbinedeon University? Ko Northwest University ta Kano, ko kuwa ba ka son aikin jami’a ka fada min duk wani industry da ka ke son yin aiki da shi a Najeriya?” Hashim ya sadda kai yana murmushi cike da kaunar karimin dattijon, bafullatanin Giade, ya ce, a ha kali muryar sa ke fita inda ya ce. “Babu ko daya, bana sha’awar aiki ranka ya dade! All the aspirations on it has gone”. Alhaji Datti ya yi murmushi domin ya tsammaci jin hakan dama, ya ce, “Kana son international business kenan?” Nan ma Hashim ya ce, “lala!”. Alhajin so yake ya fada masa da bakinsa ga abin da yake so, yake da buri akai, shi ya sa yake ta zagayewa. Amma Hashim ya ki fada sabida zurfin cikin sa. Yana son ya kara tabbatar da wannan determination din daga bakinsa kamar yadda ya ji daga bakin Zarah, kada ya zamo cewa ya yi pushing ra’ayinsa ga shiga siyasa, wanda wannan ba shi ne abin da yake so ba. Don haka ya ce, "To Hashim gaya min, me ka ke so to earn a living, tunda magidanci dai mai iyali bai zama ba tare da neman na kansa ba, kula da iyali abu ne mai matukar wuya, wanda dole sai da kwakkwarar sana’a mutum zai iya shi cikin sauki’. Hashim ya kara yin kasa da kai. A karo na farko ya ji yana son fadin wannan burin nasa a fatar baki, ba don yana da hope na cewa zai same shi ba, wanda bai taba bayyanawa kowa ba sai alkalamin sa da littafin sa. Ko Halima bai taba bude baki ya gaya mata ba, ya dauki abun ne a matsayin mafarki (dream), which will never born alive. Wanda ba zai taba zama reality ba. “Ni burina kawai siyasa ce ranka ya dade, ina son shugabanci kuma ba ni da hanyar shigar sa ko samun sa. Babban mission dina na son shiga siyasa shi ne; inganta rayuwar matasa marasa aikin yi, kawar da rashin aikin yi (unemployment) wanda ke maida su marasa amfani, marasa imani, kawo sauyi a kan yadda ake mulkar talaka da zama shugaba mai fada da cikawa ba irin shuwagabannin da ke ci yanzu ba. I want to curve POLITICAL DICHOTOMY. Ka ga kuwa buri na zai tabbata a mafarki ne kawai daga nan har gaban abada, tunda ba ni da wata hanyar kaiwa gare shi”. Wani tattausan murmushi ya subucewa Alhaji Datti, ya dubi Hashim da ke duke a gaban sa da manyan idanun sa irin na manyan shuwagannin da suka sha gwagwarmaya a rayuwar siyasa suke kuma da experience na su waye masu leadership motivation ko a kwayar ido. Jin sa yake a ran sa kamar 'yar da ya haifa, Zarah. A sati guda kacal da yayi tare da shi ya gama lakantar duk abinda yake son laqanta akan sa. Wato duk wasu (leadership qualities) ya mallake su har da kari. “Ka zo gidan siyasa Da na, kuma ka shige ta ka gama. Irin ka muke nema ruwa a jallo masu patriotism, sannan masu jini a jika da dimbin ilmi a kananan shekaru, wadanda za su gaje mu tunda mu mun kusa ja baya. Welcome to the NRC (Northern Region Congress party). Gobe za mu wuce Abuja tare in gabatar da kai ga shuwagabannin jam’iyyah. Insha Allahu Hashimu ka shigo da kafar dama, domin akwai rikici da ake yi tsakanin mutum biyu da za mu ba wa takara, zan raba gardama da kai duk su hakura domin kuwa ka fi su cancanta ta kowane bangare, welcome on board!". **** Hashim ya koma masaukin sa a daren ranar yana jin komai dake faruwa kamar a mafarki. Ya kasa hadiye wannan magana a ransa ba tare da yayi sharing din ta ga Halimar sa ba. Ya dauki waya ya kira Halimah wadda ke yiwa Safeeya shirin barci a lokacin. "Cheriè, baka kwanta ba?" Sassanyar muryar Halima ta tambaya. "Ina zan kwanta Sweetheart, ban ji lallausar muryar ki mai tada tsigar jiki na ba? Baki yimin goodnight kiss ba? Bamu yi sallama mun gaida juna ba? Rabona da ke tun safiyar yau. Ga rayuwa na kokarin canzawa incredibly! Kin san wani abu? Daddy yace gobe zamu tafi Abuja ya sanya ni a jam'iyyar su, jam'iyyar NRC dai da kika sani, he sounds kamar dama can ya san buri na kenan a yadda yake magana". Halima tayi murmushi ta canza position din rikon wayar ta, daga dama zuwa hagu, a lokaci guda tana lullube Safeeyah da bargo, bata ce masa ita ta gayawa Zarah ba don bai san ta karanta rubuce-rubucen sa ba. Tace. "Idan wannan shine alherin mu, Baban Safeeyah Allah ya tabbatar da shi, ya hada mu da dukkan alkhairin da ke cikin sa, ya dawo min da kai lafiya". Hashim yayi kasa da murya cikin jin matsananciyar kewar matar sa, ya ce "i'm missing you, Sweetheart, anya zan iya kara wasu kwana bakwan a nan gaba ban zo na gan ki ba, na kuma ga apple of my eyes (Safeeyah)? This is too much for me to bear" Halima ta kara kankame wayar hannun ta, cikin tsananin shauki tace. "Daurewa zaka yi Cheriè, suffer till you succeed. Nothing good comes easy…Halima is there for you forever" "I so much love you Leemah....." ya fada a raunane. "And Leemah loves you more!". Ta fada cikin karsashi. ABUJA Sai ga Hashim tsakiyar jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya a washegarin ranar Alhaji Datti na gabatar da shi. Sosai ya samu karbuwa a wajen dattijan, sabida kwarjini da kamalar da Allah ya zuba masa. Gami da kwalayen ilmin da ya tara a kananan shekarunsa. Duk da baza'a rasa wadanda zuwan nasa ta hannun Alhaji Datti bai musu dadi ba, don shine shugaban jam'iyya komai ya saka ta zauna. Musamman matasan cikin su. Masu shekaru tsararrakin na Hashim din. Hashim kallon komai yake kamar a mafarki lokacin da Alhaji Datti ya zaunar da shi a gefensa, a kusa da shi ‘yan takarar gwamnoni ne na jihohin Najeriya wadanda ke karkashin NRC. Lokacin da Alhaji Datti ya tashi yin bayani a matsayin sa na shugaban jam’iyyar NRC bakidaya sai yace, "Na raba gardamar da ake yi tsakanin mutum biyu, wadanda ke son karbar takarar gwamnatin Kano, wato Aliyu Sardauna da Inusa Zango, na maye gurbinsu da Hashim Ismael Yakasai, ya kawo hujjojinsa a kan cancantarsa da tsammanin da yake da shi na cewa zai fi su yawan mabiya tunda shi ba dan kowa ba ne, sannan matashi ne mai shekaru arba’in kuma haifaffen birnin Kano ne wanda ya zauna a cikin matasa daban-daban mazauna cikin gari (tsakiyar birni) yake kuma cikin irin rayuwar da suke yi. Ya ci gaba da kawo musu manyan dalilansa da misalan sa na baiwa Hashim wannan takara har sai da dukkaninsu suka gamsu, cewa Alhaji yayi don cancanta ne ba don son kai da nuna fifiko na sanayya ba, banda Aliyu Sardauna da Inusa dake ganin son kai ne karara Alh. Datti yayi don Hashim yana dan uwansa. Amma in ba haka ba ta yaya su da aka yi fadi-tashin kafa jam'iyya dasu rana daya za'a hambare su a bawa bako matsayin su? Dattijan kam sun gamsu da cewa Hashim din shi ya fi dacewa da tsayawa primary election idan lokaci ya zo. Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, cikin dan lokaci fastocin Hashim suka soma yaduwa a jihar Kano da kafafen yada labarai, wadanda komai daga aljihun Alhaji Datti dana jam'iyya yake fita, musamman da yake jam’iyyarsu ita ce jam’iyya mai farin jini a wurin talakawa. Sunansa ya soma fita a hankali a kafafen yada labarai. Matsayin dan takarar gwamanatin Jihar Kano karkashin Northern Region Congress party. Watanni uku da fara campaign ganin irin karbuwar sa yasa jam’iyyah ta ba shi gida da full security a unguwar Nassarawa GRA. Halima da Safiyyah suka tare yau a sabon gidansu karkashin rakiyar makwabtanta na arziki da Sa'adatu da Dr. Rabiah yayin da komai ke zuwar wa Halimah kamar a mafarki. Kamar ire-iren mafarkan data saba yi tana farkawa ta ga komai bai faru ba. Ta rasa irin godiyar da za ta yi wa Zarah da ta maida mafarkin Hashim reality, tabbas Zarah ta cika masoyiya ta hakika. Hashim ya zagayo da hannayensa zuwa kafadun Halima, yana sanye da wata lallausar shaddah light pink, 'yar ciki da wando kawai, ya aje babbar rigar bisa kujera. Halima ta sha ado da swiss lace ruwan zuma dinkin bou-bou, sai kamshin davidoff ke tashi a jikin ta. Falon ya kawatu da english furnitures farare kal komai a saukake, amma yana da matukar girma, ta yadda kujeru seti biyu ya dauka, kowacce kala daban da 'yar uwar ta. Suka hade goshin su wuri guda, dogon karan hancin su ma wuri guda yana zungurar na juna. Sai shakar numfashin juna suke, mai cakude da sanyin turaren jikin kowannen su. "Cheriè, pls, in mafarki nake ka taimake ni in tashi" " Halima ba mafarki kike ba, gidan ki ne da jam'iyyah ta baki halak malak, ko mun fadi zabe ya riga ya zama naki". Safeeyah na zaune akan leather tana ta lallatsa kujerar da hannun ta tana shafawa tace "Daddy, nan ina muka zo ne? Kujerar su akwai laushi" dariya suka yi su duka biyun suka isa gareta suka durkusa a gaban ta. "Safeeyah this is your new humble abode. How i wish you can open your eyes and see its serenity?". Ya sumbaci kuncin ta. Safeeya tace "Daddy idona a bude yake amma bana ganin komai, sai duhu". Halimah kasa tsayawa tayi a wurin ta nufi dakin da ya zam nata tana share hawayen tausayin Safeeyah. Ta bar Hashim yana lallabata yana gaya mata watarana zata gani idan Allah ya nufa. Saida ya kai Safeeyah dakin ta, yayi mata addu’a ya rufe ta da lallausar bargo, yarage mata wuta, sannan ya shafa kanta ya bar dakin. Ya tadda Halima a tsaye jikin mudubin jikin bango tana karewa kanta kallo, cikin dan lokaci ta fara ciccikowa, ta fara tada komadar ta, kasusuwan da suka yi mata sarka a wuya sun ciko, ta fara komawa hayyacin ta, duk da yawon kamfen kauyuka da birane bai barin ta hutu sam, kuma tun daga wancan lokacin kawancensu ya farfado da Zarah, dari-darin da ta ke da Zarah duk ta bari. A hankali zuciyarta ta ke budewa daga tsukewar da ta riga tayi a baya, ta fahimci ashe dai tana bukatar 'yar uwa mace wadda zata dinga kaiwa matsalolin ta bayan Hashim, ta soma karbar canjin rayuwar da ya same su tana adopting din sa gradually da budaddiyar zuciya yanzu. Tana wannan tunanin taji Hashim ya zagayeta cikin hannayensa, ya sumbaci dokin wuyan ta ta baya, tace "Hashim!" Yace "...Halimah-Leemah, me kika tanadar min a daren yau?" Ta juyo gabagadi ta fuskance shi, sannan ta maida masa sumbar da yayi mata, tace "Duk abinda kake so, whatever…special Baban Safeeyah!". **** Yawon kamfen da hada-hadar siyasa da ke sa ‘yan siyasa mancewa da iyalansu idan siyasa ta matso, wannan ba haka yake a wajen Hashim Ismael Yakasai ba, duk inda ya shiga, duk runtsin da yake ciki sai ya ware kansa ya kira iyalinsa ya ji muryar diyar sa Safiyyah ya tabbatar ba su da damuwa a kullum, sannan hankalinsa yake kwanciya. Hatta miskiniya Safiyyah da ba ta da idanu ta san sun samu sauyin muhalli, sauyin abinci da sauyin atmosphere. Zaben farko wato (primary election) na kara karatowa, abubuwa na kara yi wa su Hashim zafi, ta yadda zaman gida ya karranta gare shi. A daidai lokacin ne Halima ta bada kaimi wajen addu’ar nasara wa mijinta dare da rana yini da safiya addu'a take yi tana sadaqa, Dr. Rabi'ah gabadaya ta janye adawar data ke yi da Halima sai shishshige mata take, Halima bata taba canza mata fuska ba dai-dai da rana daya, sabida ko kare ne in dai daga dangin Hashim yake tana girmama shi balle Yayar sa uwa daya uba daya. Ta dauki abinda Dr. Rabi'ah tayi mata a matsayin ajizanci irin na dan adam, saidai bazata taba hada matsayin ta da na Sa'adatu ba a zuciyar ta; Wanda ya soka a lokacin da duniya ta juya maka baya shine masoyin ka, ba wanda ya zo don ya rabi ni'imar da Allah yai maka ba. Halima na tsananta addu'ah ne domin amsuwar Hashim Yakasai a Kano farat daya a wajen Kanawan Dabo, ya ja hankalin abokan hamayya kwarai da gaske a kansa, wadanda a baya ba su damu da shi ba, kasancewar sa bako a harkar siyasa. Amma yadda ya samu karbuwa farat daya ya gigita jam’iyyar adawa, musamman da aka buga primary election a tsakanin ‘yan jam’iyyarsu ya haye saman Inusa da Aliyu Sardauna da kaso mafi rinjayen magoya baya. Wannan yasa jam'iyyar NRC (Northern Region Congress) ta kara baiwa Hashim tsaro a duk inda zai shiga haka a gidan sa dama iyalin sa. ***** ABUJA GIDAN PROF. ZUBAIR NUMAN Lokacin da ya shigo gida magriba ta kawo jiki, Prof. Har wannan lokacin haka nan yake zaune kwal shi kadai a tafkeken gida kamar tsohon maye, sai tarin arzikin da ya fi karfinsa kamar ya kashe shi, neman mata kam ya dade da dainawa tunda ya fahimci tsufa ya fara kama shi, kayan alatu na fita hankali har ya rasa yadda zai yi da su a gidansa saboda babu masu mora. Ga tsufa da ya fara cin karfinsa. Domin tenure din sa ta dade da karewa daga NCC. A yanzun shi retired ne daga aikin gwamnati. Zaune yake a gida baya aikin komai. Sai pansho da garatuti da yake karba. Baya zuwa ko'ina sai cin dukiyar da ya tarawa 'ya'yan sa shi kadai ransa. A kujerar falon shan iskarsa ya zauna ya kwantar da kai a masangalin kujera yana lumshe idanunsa. Kwanannan ba tunanin da yake yi sai na Halima. Ta tsaya masa a rai har mafarkin ta yake cikin kyakkyawan yanayi. Wayarsa ya dauka a karo na sau ba adadi ya kira Hanan, wadda ke gidan mijin ta a garin Porthearcourt, ita kam Hanan har ta fara jin tausayin Daddyn nasu, a bisa damuwar sa akan son sanin inda Halima take, ta fara karaya, amma in ta tuno gargadin Halima sai ta kara sarewa. "Idan kika fadawa Daddy kinsan inda nake Allah ya isa Hanan ban yafe miki ba". Ta kuma tuno muguntar da shi Daddyn ya yiwa Haliman. Sai ta ga cewa Halima ta fi ta gaskiya, bata bukatar Daddy a halin yanzu cikin rayuwar ta. Bai ji kanta a lokacin da take neman jin kansa da gafarar sa ba!!! “Yanzu Hanan ba za ki tausaya min ba? Duk soyayyar da na ba ku kin manta, ba za ki gaya min ina Halima ta ke ba sai ranar da na bar duniya ban ganta ba ko? Hanan ki tuna ko waye Daddynku, shi ne mahaifin ku mai sonku da kula da ku, wanda ya yi muku komai da uwa ke yi wa ‘ya’yanta. Na karbi kuskure na kun fi ni gaskiya, ba za ki afuwan ta min ki hada ni da ‘ya ta ba?” Ya soma wani irin tari kuful-kuful, maganar ta sarke ta kasa fitowa, alamun rashin koshin lafiya ya bayyanar da kansa a tare da Farfesa. Hanan couldn’t keep it, ta yi shiru tana hawaye. Ba za ta iya kirga wannan shi ne karo na goma sha nawa da Daddy ke rokonta ta hada shi da Halimah ba. “Daddy sis Leemah ba ta cikin Abuja fa, nima nemanta nake yi ruwa a jallo. Amma insha Allahu zan kara zage damtse wajen neman ta, kuma zan gaya maka da zarar na samu labarin ta”. Ta kashe wayar ba tare da ta jira cewarsa ba. Kada ya karya sauran lagon ta ta karya alkawarin data yiwa Leemah. Sannan a take ta kira Halimah, ta gaya mata komai kan damun ta da Daddy ke yi wajen neman ta. Halimah wadda ke hakimce cikin luntsumemiyar kujerar leather ta falonta, ta yi murmushi ta kwantar da kwayan idon ta kasa tamkar Hanan na kallon ta, sanna tace da kanwar tata. “Kyale Daddy kin ji Hanan, har yanzu bai fara nadama ba, kadaici ne ya ishe shi. Yake neman abokin taya zama, tunda kema kin tashi. So yake na koma mu ci gaba da zama ko? To ni da igiyar AURE za'a kai ni kabari na insha Allahu". **** Hanan Zubair, ta fito daga dakin ta da gudu jin 'yar ta Yusra na callara kuka, sai ta hangeta tana mirginowa daga matattakalar dogon benen su har ta kai kasa... jini ya soma malala kamar an sunce famfo. Wata kara da Hanan ta saki ita tayi sanadiyyar fitowar Saleem a guje shima daga kitchen din falon, kafin Hanan ta idasa saukowa ta cimma 'yar, Saleem ya riga ta. Ya girgizata ya girgizata amma babu alamun akwai sauran rai a jikin ta. Ta rasu!. Hanan da mijin ta Saleem sun shiga wani mawuyacin hali, na rashin yarinyar, duk da ba ta hanyar halal suka sameta ba suna son ta kamar yadda iyaye ke son kowanne da. Babban tashin hankalin su ba'a fi kwana biyar ba kenan da yiwa Hanan check up a asibiti bayan wani zubar da jini da tayi ta yi mara yankewa, likita ta tabbatar musu Hanan bazata iya sake conceiving ba (daukar ciki). Mahaifar ta ta yi rauni. Tun daga lokacin kuma Hajiyar Saleem ta bude masa wuta kan sai ya kara aure, tunda shegiyar ta mutu, kuma an ce bazata sake haifar na halali ba. Da wa zata yi sharing wannan abubuwan alhinin da suka sameta tunda su ba su da uwa? Sai Haleemah kadai. Watakila Halimah ta tausaya mata ta bata Safeeyah ma, ita kuma ta yi alkawarin yi mata kyakkyawan riko fiye dana diyar data haifa. Saleem bai hanata zuwa Kano ba data ce masa zata je wajen Yayar ta Halimah. Duk abinda zai sa ta farin ciki a wannan dan tsukin shi yake yi. Washegari ya yankar mata tikitin jirgin Azman mai zuwa Kano daga Porthearcourt. ***** Hanan ta sauka a Kano da yamma lis, daga nan ta dauki Adaidaita zuwa unguwar data san su Halima suke wato Yakasai. Bata gayawa Halima zata zo ba, surprise take son yi mata. Saidai katon kwado ne yayi mata sallama. Wani dake tsaye daga gefe ya ce da ita. "Ai tunda aka tsayar da Hashim takarar gwamna suka tashi suka koma Nasarawa". Hanan tace "no, ba wadannan ba dai, ko suna ne ya zo daya" yace "in dai Hashim mijin Halima mai kwan kaji ne to shi nake nufi". A take Hanan ta fiddo waya ta kira Halimah. "Sis, gani a kofar gidan ku ana gaya min wai kun tashi" Halima tsabar farin ciki da zuwan Hanan kidimewa ta yi, tace da Hanan ta tsaya anan kofar gidan sun yanzu zata turo direba ya dauketa. Hanan sai ta kara sakankancewa da al'amarin Ubangiji. Ba jimawa direban ya faka a gabanta ta shiga suka nufi Nasarawa. Halima da Hanan suka wani irin rungume juna kafin Halimah ta saketa ta tambayi baby Yusra. Hanan ta nemi waje ta zauna tana share hawaye da gefen mayafin ta, lokacin ne Halima ta lura da tsananin ramar da Hanan din ta yi. Jikin ta yayi mugun sanyi, ta zauna gefen Hanan tana kara tambayar ta ina Yusra? "Ta rasu!" Hanan ta fada tana kifa kanta a kafadar Halimah. Tare da rushewa da kuka. Tiryan-tiryan ta bata labarin yadda Yusra ta fado daga bene ko shurawa bata kara yi ba, da matsalar mahaifarta sannan da halin data ke ciki da mahaifiyar Saleem a yanzu. Halima bata san yaushe ta fashe da kuka ba suka hada goshin su suna ta yi. Bazasu daina dakacen rashin rayuwa tare da mahaifiya ba. Wani tunani ya zo wa Halimah. Hashim ya dade da yi mata alkawarin sada ta da dangin ta na uwa da uba, tana ganin babu lokaci mafi dacewa da hakan irin yanzu, ga ta ga Hanan in Salim ya amince su je tare. "Lokaci yayi da zamu nemawa kanmu gata Hanan, mu tashi mu nemo dangin mu na uwa da uba, mu bar Daddy da halin sa shi kadai don bazai taba canzawa ba". Hanan tace "wallahi ya canza Leemah, ya dade da canzawa. Sune dai suke fushi da shi. Amma ina bayan ki kan mu mu neme su. Kuma a daidai wannan lokacin". Halima ta mike tana kiran Hashim a waya wanda ke can Abuja a lokacin wajen harkokin Campaign dinsu, ta gaya masa zuwan Hanan da shawarar da suka yanke. Hashim ya ce "i'm sorry Sweetheart, ban cika alkawari na ba tuntuni amma yanzu zan cika. Ina nan dawowa gobe, in mijin Hanan zai bar ta tayi kwanaki tare damu sai mu shirya tafiyar da zarar na dawo gobe". Halima tayi godiya, sannan suka yi musayen kalaman soyayyar su da bata ginsar su…. "I'm missing you sweetheart….." "....missing you is all i do Cheriè. Stay blessed". Suka yi sallama. Hanan na kallon ta tana murmushi, ta yarda Halima ta yiwa kanta kyakkyawan zabi a rayuwa. Zabin da bazata taba dana-sani ba! Arziki ba shine kadai kwanciyar hankali ba. In kika cire babun tasu Halima ta fita sa'ar aure. Ga babun ma na neman zama tarihi a gare su. Halima ta gaya mata yadda Zarah ta taimaki Hashim ta hada shi da Baban ta. Da position din da suke kai a yau. Hanan tace "Zarah ai mai son ki ce, she will do more than that. Daddy fa ya dawo min da takardun mu na karatu, tare da asusunan bankunanmu, daga wancan lokacin zuwa yanzu kada ki so kiga abinda ya karu akai. Ni tsoro kudin cikin bankunan ma suka bani. Ya bani nawa yace duk ranar da Allah ya sake hada ku zai baki naki. Sis Leemah kiyi hakuri ki yafewa Daddy, he really regretted". Halima tayi wani murmushi mai ciwo, tace "Hanan bana bukatar komai a halin yanzu don ba aiki nake nema ba, i'm a total house-wife (ni tabbatacciyar matar aure ce). Duka lokutana da lafiyata na sadaukar dasu ga AURE na da iyali na. BOKO na riga na bashi baya, kuma ni Halima in na baiwa abu baya, bana sake waiwaye. Bana bukatar takardun makaranta a halin yanzu da duk wani abu da ya shafi boko. Kudi kuwa wallahi in zai kai su baitul-mali ko ya bada su sadaqatul-jariya ga mabukata gara yayi hakan ya fiye masa alkhairi, amma ni Halima bana bukata." "Sis Leemah, yaushe kika koyi taurin rai ne? Shikenan zan baki mamaki watarana". Safeeyah ta fito daga daki tana laluben bango, tana kiran Halima. Da gudu Hanan ta karasa gareta, ta jima da sanin matsalar yarinyar daga bakin Halimah. Tace "Doty, gani na zo me zan samu?" Ta fada tareda daukanta suka dawo kujera suka zauna gefen Halimah. Yarinyar ta sha ado cikin kaya 'yan kanti ruwan hoda, gashin kanta ya sha gyara don da Halima da Hanan duka ba baya bane wajen gashi. Ubansu bafillace uwar su kuma shuwa. "Aunty Hanan ce?" Safeeyah ta fada tana shafa fuskar Hanan yadda take yi in tana son gane fuskar mutum. Hanan ta lumshe ido ta dafa hannun nata tana fadin "i look so much like your mother, zaki bi ni Porthearcourt? 'Ya ta ta rasu, ke kadai kika rage mana". Safeeyah tace "idan na tafia wa zai zauna da Mom da Daddy na?" Da sauri Hanan tace "Mom zata haifo wani baby.., nikuwa bazan sake haifowa ba, I have only you”. Halima tayi murmushi ta wuce ciki ta bar su don samawa Hanan abinda zata ci, ta barta suna ta tafka musu itada Safeeyah kan tafiya Porthearcourt. Komai ta ce sai Safeeyah ta yi gardama. Bata ce komai akai ba don ta san Hashim ba zai taba bari ba. Mai raba shi da Safeeyah sai Allah! Balle Hanan da tun fil azal jinin su ba gamuwa yayi ba. ***** Tun yammacin ranar suka fara shirye-shiryen tafiya Maiduguri da Numan ta jihar Adamawa. Salim ya ce ko sati ne Hanan tayi ba komai, watakila shima yayi joining dinsu ta jirgi in sun isa Maiduguri. Hanan ta bawa Halima lambarsa ta hada shi da Hashim, nan da ban abota ta kullu. Washegari suka shiga kasuwar kantin kwari don sayen tsaraba, komai kwasowa suke tun daga kan kayan abinci da na masarufi da suttura. Sai da suka cika boot din motoci uku sannan suka koma gida gefen maghriba. Suna zaune a falo da daddare sun kunna tv suna sauraron labarai suna shan soft-drinks, Safeeya na bisa cinyar Hanan tana bata lemon, tashar ARTV ta Kano ake nunawa. Abokan hamayyar Hashim ne ake programme da su inda suke ta bankado sirrikan Hashim na baya duk don su bata shi a idon talakawa. Jam'iyyar adawa ta tabbatarwa manema labarai cewa shi tsohon ma'aikacin NCC ne wanda Commission din ya kama da laifin sama da fadi da kudi masu yawa na ma'aikatar shekarun baya aka kore su shi da matar sa. Sannan Hashim ba ba-kano bane cikakke tunda kuwa uwarsa Basudaniya ce. Ya sato 'yar uban gidan sa ya aureta bada sanin mahaifin ta ba... maganganu dai gasunan barkatai na tozarci da kage wadanda baka raba 'yan adawar siyasa da irin su. Hanan mikewa tayi ta kashe talbijin din tana tsaki, tace "'yan media sai Allah ya gyara wajen yada abinda basu da tabbas akan sa. Sara da sassaka dai baya hana gamji tofo, don haka ya rage nasu su fadi duk abinda suke son fada". Halima bata ce komai ba amma tabbas ta girgiza da wannan sharrin da aka yi musu akan NCC. Hanan ke kwantar mata da hankali tana gaya mata siyasa ta gaji haka, sai in baka shigeta ba. Washegari da daddare Hashim ya dawo cikin wani yanayi, har da jini a goshin sa da jikin kayan sa. Halima ta kidime ta shiga tashin hankali tana tambayar sa ko lafiya? Murmushi yayi yana share goshin sa da hankicin sa sannan yace "kada ki damu Sweetheart, ana bibiyata ne, so suke su kashe ni amma Allah yana nan. Sun tare mu a kan hanyar Kaduna da kyar sojoji suka kwace mu. Ana zargin ‘yan PRP ne kuma hukuma ta shigo cikin maganar. Sannan an zuba tsaro sosai yanzu a gidan nan. Don haka tafiyar jirgi zamu yi gobe zuwa Maiduguri, daga can ma zuwa duk inda zamu je jam’iyya zata dauki nauyin kula da mu". Halima na kuka tace "No Cheriè, ka bari sai after election ma je, na fasa, ina tsoron kada wani abu ya same ka acan din". Hashim ya rungumota yana fadin kada ki damu, Allah na tare damu, after election ne zuwan zai yi wahala, gara muje yanzu mu huta. Ai kuna da address din duka na Adamawa da Maidugurin ko?" Tana share masa digon jinin ciwon goshin sa tace " Hanan ta karbo addresses din duka wajen Baban ta" Hashim yayi dariya ya ja dogon karan hancin ta "wato baban ta ita kadai, banda mu?" Ta sunne kanta a kafadar sa tana fadin "na yafe mata shi". Hanan tace ita a dakin Safeeyah zata sauka, don haka tun kan Hashim ya shigo sun kuke a daki itada Safeeyah sun kwanta. Hashim kuma wanka Halima ta taimaka masa yayi, ya ci abinci ya sha maganin ciwon jiki sannan suka soma tsara yadda tafiyar su ta goben zata kasance. Kafin a koma fafatawa a fagen soyayya. ****** WASHEGARI ADAMAWA, Nigeria Gidan Modibbo Hussaini Muhamad Numan ba boyayye bane a garin Numan ta jihar Adamawa. Tunda suka shigo Numan suka yi tambaya sau daya aka yi musu jagora har gidan Modibbo Hussaini, Modibbo Hussaini dattijon bafullace talaka likis, kani yake ga mahaifin Alh, Zubair Numan. Yana da matan aure hudu da 'ya'ya bila adadin da jikoki duk a gida daya. Kusan ace Modibbo Hussaini shikadai ya ragewa Prof. A dangi, daga shi sai wata kanwar kakarsa Goggo Iyami. Bata tsufa cancan ba kuma yaranta duka mata ne sun yi aure duk sun hayayyafa. Sauran manya a zuri'ar su duk sun rigaye mu amma 'ya'yan su matasa suna raye a nan Numan. Salim kusan tare suka sauka da shi a Adamawa, tare suka hadu a filin jirgi Shuwagabannin NRC na jihar Adamawa su suka zo da motoci suka dauke su zuwa Numan, kasancewar dan takarar gwamnan Adamawa ma dan jam'iyyar su Hashim ne. Modibbo ya fito zai tafi gona, sai gani yayi ana faka masa dindima-dindiman motoci a kofar gida. Dakatawa yayi cikin tsoro yana kallon motocin wadanda dukkansu tinted ne. Mai tsaron lafiyar Hashim shi ya fara fitowa ya bude masa kofa, sai da ya fito sannan Salim ya fito, sai matan nasu guda biyu da Safeeya a hannun Hanan. Dukkan su suka karasa gaban dattijon suka tsugunna, shikuma cewa yake "maraba - lale ku shigo daga zaure in shimfida muku tabarma". Duk suka duru a dan karamin soron na Modibbo, hannu ya baiwa su Hashim amma suka ki, suka gurfana irin na surukuta suna gaishe shi. Modibbo yace. "Nafi ganewa ku bani hannu mu gaisa, shine abinda muslunci ya yarda da shi kun ji?" Duk sai suka mika mai hannun. "Samari da 'yammata daga ina? Ban waye da ku ba". Halima ce ta wakilci Hanan, wajen yi masa bayanin ko su waye su. 'Ya'yan Zubairu Muhammadu Numan na garin Abuja. Kafin ta rufe baki Modibbo ya fara kuka, ya kama hannun Halima da Hanan yana fadin "na gayawa 'ya'yana duka ko bana raye, ko bajima ko ba dade zaku zo ne!". Tausayin dattijon yasa Halima kuka, tace "wallahi Baffa mun dade muna so mu zo, Allah ne bai yi ba. Life's hustling and bustling (kujuba-kujubar rayuwa) bata bar mu ba sai yanzu. Kuyi hakuri ku yafe mana". Hanan tace "Daddy ma yayi nadamar rashin neman ku da baya yi, yace ba da jimawa ba zai zo shima" Modibbo sai yayi murmushi kawai yace. "Ki kyale babankin nan kin ji? Ko ya nememu a halin yanzu neman bashi da amfani. Wanda ya tozarta zumunci da sannu Allah zai tozarta shi. Ku dai tun da kunyi hankalin zuwa neman mu mun gode Allah, mun kuma ji dadi kun kawo kan ku gida". Ya tashi ya shiga gida, ya fitowa dasu Hashim kwarya cike da damammiyar fura da taji nono kindirmo, nan suka jefa ludaya suka hau sha cikin marmari shi da Salim, Hanan da Halima kuma yayi musu jagora zuwa cikin gidan wajen matan sa. Yawancin 'ya'yan Modibbo manyan maza ne, sai auta mace wadda itama tayi aure. Har gidanta aka kai su wato Abuwa. Daga nan aka dinga raka su gidan 'ya'yan Modibbo daya bayan daya da kuma gifan Goggo Iyami. Ita kam kukan farin ciki ta saka ta rungume su Halimah. Hashim yasa aka shishsshigo da duk tsarabar suka yo musu a bayan motocin su. Nan suka wuni sur, shakuwa ta shiga tsakanin Hashim da Saleem, da magriba ta kawo jiki bayan sun yi sallah tareda Modibbo suka yi masa sallama kan zasu shiga cikin Adamawa su kwana, gobe da safe zasu biyo su dauki su Halimah. Halima da Hanan dakin goggo Iyami suka kwana, ta kwana basu tarihin iyayen su da kakannin su na wajen Uba, tace gara da baku biyewa Ba-amurken uban ku ba, in bai yi wasa ba sai rashin zumunci ya kai shi wuta. Hanan dai hakuri take basu tana gaya musu Daddy ya canza, shi ya batta adireshin su da kan sa, kuma kwanannan zai zo ya nemi gafarar su. Halima in an yi zancen Prof. Bata cewa komai akai, shiru take yi, don a ganin ta itace mai tabon Prof. Numan fiye da kowa. Kudade masu yawa Hanan tayi ta rabo, ta kuma cewa Baffa da goggo iyami nan bada jimawa ba za'a buge gidajen su ayi musu na zamani. 'Ya'yan su kuma idan akwai wadanda sukayi karatun zamani a bata guda uku zata tafi dasu Porthearcourt ta sama musu aiki. Goggo Iyami tace “daga Auwalu sai Basiru sune sukayi wannan abun digirgir a cikin Adamawa, sauran iyakarsu sakanni in dire. Na ko ji suna batun neman aikin nan”. Shikuwa Hashim cewa yayi duk wadanda basu yi karatun ba a bashi, bayan zabe idan Allah ya sa yayi nasara zai dauke su ya basu ayyuka tare da shi. Yau dai gidan Baffa Modibbo kamar an musu bushara da shiga aljannah, haihuwa mai rana, abinda Zubairu bai yi musu ba a shekaru talatin yau gashi 'ya'yan sa sun musu a rana daya. Washegari da wuri suka kama ha yar airport, bayan motar su taf da tsarabar Numan, wadda aka yi wa kyakkyawan packaging, inda suka hau jirgin da zai kai su Maiduguri. Don ganawa da dangin mahaifiyar su marigayiya Safeeyah. ****** A Maiduguri Daddy ya gayawa Hanan akwai kanwar mahaifiyar su Hajja Falmata a raye, tana aure a cikin Maiduguri, har lambar wayarta ya bata, ashe dama ya san da wanzuwar kowa ya kuma san inda suke, ra'ayin sa na kada a rabe su shi da 'ya'yan sa balle su raba shi da su ne ya hana shi dangana su da su. Suma kuma dangin marigayiya Safeeyah daga baya fushi sukayi suka bar masa 'ya'yan sa. Saboda sun sha zuwa takanas tun daga Maiduguri tun yaran na kanana don su gansu baya bari, haka zasu zo su koma wutsiya a zage ko ruwan gidan sa basu sha ba. Musamman Hajja Falmata. Da yake ta sha kiran sa a can baya don ta ji lafiyar yaran ya dade da saving no.dinta, kafin ta yi fushi ma sam ta daina kiran. A cewar ta in 'ya'ya ne itama Allah ya bata, Zubair Numan, ya jika nasa ya shanye. Sai yanzu da Hanan ta bude masa wuta kan ya hadata da su ne kuma da yake shiri yake nema da 'ya 'yan nasa helter-skelter sai bai yi musu ba, ya bata lambar Hajja Falmata tare da bata hakurin abinda yayi musu a karo na sau ba adadi. Ita kam Hanan in don wannnan ban hakurin ne na Daddy ta gaji da jin sa, ta haddace duk wata kalma dake cikin sa, hatta da yadda zata yi ta isa gidan ta inta je Maiduguri Daddy ya gaya mata. Hanan in don ita ta dade da yafewa Daddyn tana fata Halima ma ta yi hakuri ta yafe masa. Amma ta lura Halima har gobe ko zancen Daddy bata so ayi mata. A hankali ta san watarana zata huce, domin kamar ita tafi cutuwa da matakin da Daddy ya dauka akan su bayan auren su. Ya kaita wata rayuwa wadda bata taba sanin akwai a duniya ba, idan ya kwace kudin da yake mallakin sa kwalayen karatu fa ai gumin su ne! Haka kulawar da Allah ya dora a wuyan sa ya watsar bisa ganganci da son zuciya. Halima ta cancanci tayi fushi da mahaifin su amma in tayi la'akari da hakkin haihuwa ya kamata tayi hakuri ta bashi dama ya gyara kurakuransa kamar yadda yake son yi a halin yanzu. Motocin suka yi parking a kofar gidan da aka kwatanta musu wanda ke unguwar (Hausari). Hanan da Halima zasu iya rantsewa har wani irin contentment suka ji ya tsirga a zuciyar su lokacin da suka shiga gidan da aka ce anan ne kanwar mahaifiyar su take aure. Lokacin da suka shiga mayalwacin falon ta wanda ya ji komai saisa-saisa alamun akwai rufin asiri amma babu tarin arziki. Suka yi arba da ita tana saukowa daga matattakalar benen dake cikin falon alamun daga dakunan barcin dake sama ta sauko. Waya ta ke yi amma da Halima ta daga ido ta dubeta suka hada ido, bata san sanda ta saki wayar hannun ta fadi kasa ba, sabida gani tayi kamar Yayarta marigayiya Safeeyyah ce tayi wankan kuruciya ta tsaya a agabanta tana kallon ta. Hanan ce ta karasa ta russuna tana tsince mata wayar data yi filla-filla. Ta dago ta mika mata, bata karba ba sai ta tsaya kamar mutum-mutumi tana kare musu kallo a tsanake. Halima ma ta taso ta jeru a gefen 'yar uwar ta Hanan, suka tsaya a gaban Falmata su biyu. Hajja Falmata zata yi shekaru hamsin da doriya amma tsabar kula da lafiyar jiki bai fi ka bata 40 a idon ka ba. A hankali tasa fuskar Halima cikin tafukanta, sannan ta ambaci sunayen su a hankali ba tareda sun gabatar da kan su ba. "Hanan & Halimah!" Ta fada cikin sassanyar murya, basu yi wata wata ba su kuma suka tafi zuwa jikin ta suka rungume ta. Ita kuka su kuka. Sun yi shi har sun ji babu dadi. Ba mai lallashin wani, kasancewar a falon zaure suka baro su Hashim. A karshe Hajja Falmata ta tambayesu yadda aka yi Prof. Ya yarda yanzu ya barsu suka zo garetaàà, tace "ni dama na san in dai Safeeya ce ta haife ku, to watarana sai kun kawo kan ku gare ni, shiyasa na hakura na rabu dashi na tura masa aniyar sa". "Amma ko a boye ba sai ki neme mu ba Hajja? Tunda kinsan zuwa yanzu dai duk inda muke mun yi hankali da hangen nesan sanin cewa muna da dangin da muke bukata a jikin mu? Bazamu rayu da Daddy shikadai ba kasancewar sa uba a garemu kuma namiji tilo a cikin mu. Adda in bamu yafe muku ba kuma kuna da hakkin mu…....". Halima ta fada cikin kuka sosai. Hajja Falmata ta janyo su suka zauna a tare bisa doguwar kujera, tana shafa bayan Halima da hannun ta tace "ko me zan gaya miki bazaki gane ba, har gobe baki gama sanin babanki ba, ba kankanin abu ke canza masa ra'ayi ba. Marigayiya ta sha wahala akan sa ba kadan ba. Ka rabu da shi in ya ce ka rabu da shi, shi ya fiye maka alkhairi, in ba haka ba zai wulakanta ka". "Duk da haka for our sake hujjar ku ta kyale mu kwata-kwata tayi rauni Hajjah" Halima ta kalubalanta. Hajja Falmata ta kara jan ta cikin jikin ta sosai, kamshin turaren bare-barinta ya ratsa Halima, tace. "Na karbi kuskure na Halima and Hanan, I apologize ku yi hakuri ku yafe mini, bacin rai ne, akwai sanda yayimin korar kare tun daga bakin gate don nace zan dauke Hanan, wallahi kullum da ku nake kwana da ku nake tashi a rai na. Ku yi hakuri ku yafe mini, amma ina matukar son sanin yadda aka yi kuka san ni, ya kuma bar ku yanzun kuka zo". "Mu fara yin sallah tukunnna, dogon labari ne, and please Hajja ki samawa Baban Safeeyah abinda zai ci, bana barin shi da yunwa". Halima ta fada cikin kulawa, a fuskarta kauna da soyayyah ne a kwance zallah. Hajja ta kai mata rankwashi a tsakar ka tace "uwar ki nake, ba abokiyar wasan ki ba" Hanan tace "in dai Halima da Hashim ne zaki ga fin haka. Zasu iya rungumar juna su sumbaci juna a gaban ki" Halima ta kai mata duka ta goce, Hajja na dariya ta ce "that's wonderful. Love is overall". Hajja Falmata tasa aka budewa Hashim da Salim falon mijin ta sannan ta shiga hidimar abincin su. Sai da sukayi sallolin dake kansu sannan ta shiga suka gaisa, tayi identifying kanta matsayin kanwar mahaifiyar su Hanan ta gaya masu tarihin komai tun bayan rasuwar Safeeyah da dalilin ta na barin yaran. "Yanzu da Allah ya nufa suka girma ai gashi sun biyo ni da kafafun su". Inji Hajja Falmata, ta fada musu ita kadai ta rage a dangin mahaifiyar su sai 'ya'yan ta bakwai dake gidan aure maza da mata. Sai wani Yayan su a kasar Togo. Gobe duk zasu zo su ga 'yan uwan su. Na Togo kuwa zata saka lokaci ta rakasu wajen sa shima ya gan su. Ta yaba kwarai da kamalar mazajen 'ya'yan nata musamman Hashim, wanda da ganinsa ka ga responsible gentleman. Shi kuwa Salim ka ga dan gata irin Hanan. Ta fita ta barsu tareda matan nasu suka ci abinci sannan su Hashim sukayi musu sallama kan zasu je su nemi masauki. Ya sumbaci Safeeyah yace "Sophy goodnite" ta shafa fuskarsa da hannayen ta tace "goodnite Daddy, gobe in zaka zo ka tahomin da kuli-kuli" yace "kuli-kuli kuma Safeeyah?" Tace "eh, mai sukari ba! Irin wanda Anty Sa'a ke kawomin" yace "an gama my princess". Ya daga ido yana kallon Halimah, wadda ke yiwa Safeeyah dariya, fararen hakoranta gabadaya a waje, kullum da abinda zata kirkiro mai wuyar samu tace uban ya kawo mata, shi kuma ko zai yi yaya sai ya nemo shi. Yanzun ma yace "kice ma Hajjah don Allah a nemo mana kuli-kuli mai sukari, ko nawa ne zan biya" zai rike ta, tayi saurin ja da baya, juyawar nan da zai yi sai ya ga Salim da Hanan na kallon su, sai ya shafa kai ya cira kafa yana fadin "goodnight sweetheart". Salim dai burgeshi suke, basa taba gundura da juna. Kullum kamar sabon aure, to aure ne da aka gina bisa doron soyayyah ta saboda Allah wadda tayi karanci a wannan zamanin. 80% na auren zamanin nan an gina shi ne for worldly materials. Shiyasa baya karko kuma baya zuwa ko'ina ranar da babu worldly materials din, ko ayi ta zaman hakuri da juna. Hanan ta ce "ai kawai ki hakura da hira da Hajja daren yau ku tafi kya dawo da safe". Ta fadi haka ne ganin yadda idanun Halima da Hashim ke ragaita da ya juya zai tafi. Hashim din ya sake juyowa, sai idon sa cikin na Halimah, sai kuma Halima ta ji kunya tayi saurin shigewa cikin gida. Murmushi yayi sannan suka fita shi da Salim suka tadda escourts din su suka tafi cikin gari suka kama masaukin da zasu kwana zuwa gobe. Kusan kwanan zaune aka yi tsakanin 'ya'yan da Antin nasu. Duk labarin rayuwar su sai da suka warware mata. Ita kanta Hanan sai yanzu ta ji wani abun game da rayuwar da Halima ta yi a birnin Kano, sai da suka yi hawaye dukkan su don bata san Halima ta je Abuja neman gafarar Daddy ya yi mata korar kare da mugun baki ba sai yau da Halima ta fada da bakin ta. Ta tabbatar Halima ta fi ta shan wahalar rayuwa, don dai ta kasance mai zurfin ciki da wadatar zuciya ne. Hajja Falmata ta kara janyo Safeeyah jikin ta jin cewa makauniya ce. Bata raba daya biyun mugun bakin da Prof. Yayi wa Halima ne ya sauka akan 'yar ta. Ta ce "Yaa Ilahi! Shin? Ina Zubairu zai je da hakkin Halimah!" Ta tambaye su su duka biyun. "Shin kun taba cin kayan gyara na mata?" Su duka suka hada baki suka ce "menene kuma kayan gyara na mata?" Hajjah Falmata ta aje kunya tayi musu bayani dalla-dalla, cewa suka yi su basu taba sanin wannan abun da ta ke fada ba sai yanzu. Hajja Falmata dai cannot control her tears. Ta yi kuka sosai a gaban su ta zargi kanta da butulci ga 'yar uwar ta da cin amanar zumunci. Halin Uban su bai zama hujja ba na wannan kyaliyar data yi musu a gabadayan rayuwar su. Rokon Halima da Hanan kawai take kan su yafe mata in ba haka ba Allah ma ba zai bar ta kan wasarere da zumuncin nan ba. Tace. "Na san mahaifin ku yana son ku, kuma yana da halin da zai kula da ku, kuma baku bukatar komai daga gare ni, amma kulawar 'ya'ya mata sai UWA mace. Na yi kuskure dana biyewa bacin zuciya da halin baban ku. Don Allah ku yafe mini". Halima ta ce "ni kam komai ya wuce a waje na Hajjah, idan Allah ya rubuta abu zai faru babu dan adan din da ya isa ya kankareshi" Hanan ta zumburo baki tace "ni sai kin bani kayan mata din zan hakura, ko na kara samun soyayyar Salim tunda maman shi so take a yi min kishiya". Hajjah ta ce in don wannan ne kin zo godan sa Hanan, sana'ata kenan gyaran mata, daga gari-gari zuwa ake wajena, balle ku 'ya'ya na na kaina, ai sai na ga abinda ya turewa buzu nadi". Washegari 'ya'yan Hajja duk suka zo gidan, sabida wayar data yi musu kan zuwan su Halima, Habiba itace babba, yaranta biyar, anan Maiduguri take aure, sai Salima mai bin ta tana da yara uku, ita kuma tana aure a Lagos. Sauran duk maza ne su biyar, daya ma'aikacin banki ne yana da aure wato Saifullahi, sauran ukun Yunus, Suraj da Alkali suna jami'ar Maiduguri, autan Hajja Usman da suke kira (Danzaki) yana ajin karshe a sakandire. Yau Hanan da Halimah sun wuni sur cikin su Aunty Habiba da zumunci rin na dangin uwa wanda biro yayi kadan ya bayyana shi. Habiba tayi musu dilke da halawah ta yarfa musu kananan kitson bare-bari yiri-yiri yakai kusan guda dari uku, tun zuwan ta gidan bata huta ba tana ta gyara su, ita kuwa Hajja cewa tayi gyaran da bata yi musu na aure ba shi zata yi musu yanzu don haka dole su kara kwanaki a Maid koda su Hashim zasu yi gaba ne su bar su. Ita da kanta zata maida kowacce har gidan mijin ta. Hashim ya so yayi gardama Salim ya taushe shi, ya nuna masa muhimmancin ya bar su din, wani experience da basu taba samu a rayuwar su ba. Hashim da Salim suka tafi a ranar, cike da kewar matan nasu, suka bar Halima da Hanan wajen Hajja Falmata da 'ya'yan ta. Ai kuwa Hajjah bata tsaya sanya ba, gyara take musu na musamman kamar yau zata kai su dakin aure. Hatta Safeeyah ta sha kitso da lalle wajen aunty Habiba. Ta kuma yi musu guzurin wanda zasu tafi dasu. Sai da maigidanta Alhaji Buba ya dawo ta nemi iznin sa, na dukkan su itada yaranta da surukarta Bintu zasu raka su Halima gidajensu. Salim shi ya yankar musu tiket na zuwa Porthearcourt dukkansu, shi kuma Hashim ya yanki na Kano. Sati guda kenan rabon Halimah da Hashim, wani lokaci ne da basu taba dauka ba tare da juna ba tun auren su. Don haka yau da suka dawo in ka ga rawar jikin da Hashim ke yi sai ka tausaya masa, yana da meeting a Abuja amma fasa zuwa yayi, ya kuma kasa controlling kansa gaban surukar sa Hajjah Falmata da yaran ta, bai san sanda ya ce, "Ke ce kuwa Leemah? Kin zama very young, your skin is glowing.... Hajjah me kika shafa ma Maman Safeeyah haka?" Dariya duk suke masa domin kuwa ya kama Halima kam-kam ya rike a gabansu, yana kokarin sumbatarta tana gocewa. Ba shiri duk suka zaizaye suka bar musu falon. Ai kuwa da ya sunkuci Halima bai direta ko'ina ba sai a gadon barcin su. A wannan daren, a wanna ranar, a wannan mintocin, al'amuran da suka gudana tsakanin ma'auratan masu tsauri da nauyi ne a zuciya da ruhin su. Daga Hashim har Halimah sai da sukayi hawaye domin kaunar junan su; tamkar Hajjah ta kara ma auratayyar su wani maganadisu ne mai jan zuciya da ruhi. Hashim bai iya daurewa ba, sai da ya jirkito da Halima saman sa, cikin wani irin shauki ya ce. "Leemah, you became a virgin, menene wannan sirrin? Don Allah ki gaya mani? I’m perflexed (na rikice)". Hajja ta ja kunnen ta ba'a fadima miji irin wannan sirrin, amma Halima da Hashim sai Allah! Ji tayi bazata iya boyewa Hashim ba, ita fa ko tari ta yi, ya kuma tambayi dalilin jin sa ba yadda ya saba jin sa ba, to zata fayyace masa bazata boye ba, balle wannan babban al'amarin da itama ya gigitata, bata san haka auren ya ke ba sai yau. Duk da tana jin kunya amma bata jin akwai wani sirri da ya saura tsakanin ta da Hashim; they are not ordinarily mata da miji; su abokan juna ne kuma sirrin juna. "Actually..... Hajja ta bani wani abu na ci…" ta fada tare da saurin rufe idon ta, ta kuma kifa kanta a tsakanin kafadunsa. Kunya kamar ta yi yaya! Dariya yayi, ya sumbaci idanun dake rufe. A hankali yace "Hajjah deserves an accolade, Allah ya bamu sa'ar zabe insha Allah sai ta maimaita Hajjin ta a dalilin wannan babban gata data yi mani". Kwanan su Hajjah Falmata uku gidan Halimah suka wuce Porthearcourt ta airport din Malam Aminu. Suka raka Hanan, can ma suka kwana uku, sannan suka koma Maiduguri, amma kullum suna makale da waya, kamar masu tsoron.....kada kaddara ta sake giftawa ta nesanta su da juna. ***** ABUJA Prof. Zubair Numan, na zaune a makeken falon sa abin duniya ya ishe shi. Shi daya tal! Kamar tsohon maye a tafkeken gidan sa amma kamar marayan da bashi da wani gata. Kwanan nan kuma tarin fuka ya sanya shi gaba (tuberculosis). Daga shi sai ma'aikatan sa da hadiman sa wadanda duk maza ne kabilu. Ya soma tunanin to ko shima auren zai yi ne irin na Hanan da Halima ya samu mai debe masa kewa da miko-miko? To amma idan yayi aure yanzu at the of 70 yaya sunan auren nasa? In dai ba wadda zata yi masa takaba ta cinye dukiyar da ya wanzar da rayuwar sa yana tarawa Hanan da Halimah zai aura ba? Yana nan zaune yana tufka da warwara shi da zuciyar sa ya soma jiyo wani irin hucin zafi, ya kuma rasa daga ina zafin ke fitowa, kan a jima kuma yaji atmosphere na dakin na sauyawa da wani irin kauri mara dadi. Mikewa yayi da kyar yana tari yana rarraba idanu cikin son fahimtar abin da ke faruwa, kawai sai ya ga ashe daga na'urar sanyaya daki ne (A/C) hayaki kawai take fiddawa da wani irin kauri, baya raba daya biyun wuta ce aka karo mai tsananin karfi ta janyo sanadin hakan. Kafin yayi wani action A/C din ta kama da wuta ganga-ganga, sai kuma gabadaya wayarin na lantarkin gidan ma ya kama jikake taratsa-tsa....lantarki na haduwa da dan uwan sa yana bada feshin wuta daga inda duk wata wayar wuta take a falon. Kan ayi haka kwan lantarki yayi bindiga, duhu ya mamaye falon, sai hasken tartsatsin wuta. Da gudu ya soma neman hanyar tsira cikin tsananin gigita, amma kasancewar dare ne kuma kwayayen lantarkin falon sun yi bindiga sun tarwatse sai ya rasa hanyar kofa. A lokacin ne ya fara salati yana kiran yaran sa "Jonathan.......Jafaru.....Solomon.." da iyakacin muryar sa, amma ina! Basu ji shi ba sabida suna can baskwata, sun gama ayyukan su na yau, ga wuta ta kama ganga-ganga har ta fara cin kujerun falon, labulaye da kayan kallo. Da gudu ya dinga lalube har yaji hannun sa ya kama marikin kofar da bai san ko ta ina bace, ya murda ya shige ciki yana salati hadi da ihu, ashe dakin barcin sa ya fado. Nan ma tuni lantarkin dakin ya laso wutar, hayaki ya turnike har ba ya iya ganin komai. Amma ya san duk wasu muhimman takardunsa da kadarorin sa suna cikin dakin nan. Wani salati da ya saki mai kamar ihu ya nufi kwabar da yake adana komai ya soma kokarin budewa. Tsabar rikicewa tasa ya manta password din. Prof. Numan bai san sanda ya fashe da kuka ba, ya daina hangen dukiya ya koma tunanin yadda zai yi ya tsira da ran sa. Gabadaya bai san inda ya jefa wayoyin sa ba. Ya fi tunanin ya baro su a falo ne bisa centre-table daidai inda ya kwanta dazu. Ya tabbatar in ya cigaba da tsayuwa yana tunanin hanyar tseratar da dukiyarsa to zai kone ne ayi biyu-babu shi da dukiyar. Hatta takardun Halima da komai nata suna cikin kwabar. Dabara ta fado masa....ya afka toilet, ya taka masai ya bude tagar ya danna kai, amma karafan da aka yiwa tagar makari dasu suka hana ko rabin kafadun sa shugewa. Haka ya dirgo daga kan tagar zuwa cikin bahon wanka. Karar da kashin kafarsa ya bayar ya tabbatar masa in ba karyewa ba to tsagewar kashi. Sai ya tuna da kan telephone din cikin bandakin. Da rarrafe ya isa inda telephone din yake, hannun sa na rawa ya daga, yayi dialling code din kiran maigadi, yana jin maganar maigadin a kunnen sa yace. "Seun, ina ciki zan mutu.....gobara a daki na......ku kawo min dauki na rasa hanyar fita…. ina toilet....". Daga haka ya saki kan wayar sakamakon hayaki da tarnaki da turirin wuta da ya sarke shi. Ya soma tari yana kokawa da numfashin sa wanda ke neman daukewa gabadaya. Ba abinda yake son gani a wannan lokacin sai HALIMAH don ya fidda rai da rayuwa......!!! Seun, bai yi wata-wata ba ya kira 'fire-service' wadanda aka fi sani da 'yan kwana-kwana. Duk ma'aikatan gidan sun fito da gudu jin ihun Seun. Da wutar da komai Seun ya danna kai cikin gidan don kubutar da ubangidan sa. Kasancewar ya san kan gidan sosai haka ya danna kai da kayan sojojin sa ya zagaya ta kofar baya zuwa sassan Prof. Ya fiddo shi daga toilet rai a hannun Allah. Shi kansa Seun wuta ta fara cin kayan jikinsa, Prof.kuwa hayaki da tururin wuta ya shidar da shi tuni. Fatar kafarsa ta salube. Dai-dai lokacin da jiniyar 'yan kwana-kwana ta shigo layin. Kafin a shigar da shi Ambulance ya daga ido da kyar yana kallon yadda dankareren gidan sa ke cin wuta....gidan da ya narkar da biliyoyi ya gina domin 'ya'yan sa Halima da Hanan...ya kuma kwashe tsayin shekaru biyar yana gina shi.....Gidan da yayi rayuwa da Safeeyah.....Gidan da ya kunshi duk wani tarihi na rayuwar 'ya'yan sa...... dukiyoyin da ya tara cikin sif ya hanasu ci........yau gashi wutar duniya na lashewa a banza.....!!! Duk tarin wahalarsa na NCC yana cikin sif dinnan, komai ya kone kurmus! Hatta kwalayen karatun Halima da ya kwace basu tsira daga konewar wuta ba... Idanun sa suka shiga wani irin lumshewa a hankali yana fadin "YAA SALAMU SALLIM!". Wani bangare na zuciyarsa na ta amsa-kuwwar fada masa "....this is the end of Zubair Numan.........da tarin dukiyar sa da izzar sa........" wani bangare na musantawa da cewa ".... kana da sauran dama ta neman Lahira tunda da sauran numfashin ka....... Rai dai! Aka ce baya taba rabuwa da rabo, sai dai idan ya kare! Daga haka idanun sa da kwakwalwar sa suka rufe suka tsaya da aiki gabadaya. Bai kara sanin me ke faruwa a duniya ba..... **** Zabe na kara karatowa, al'amuran siyasa da kalubalenta na kara tsanani ga su Halima. Abokan hamayyar siyasa sun sanyoshi gaba, duk wani siririn zare na rayuwar sa saida aka zaquloshi na nuna yayi sama da fadi ne da wasu kudade a NCC shine dalilin da Zubair Numan ya kore shi, ya rufa masa asiri ne sabida yana auren diyar sa da ya sato ya aura. Amma da yake an ce Zakaran da Allah ya nufa da cara..ko ana ga muzuru ana ga Shaho sai ya yi. Jam'iyyar NRC ta sanyawa Hashim tsaro yadda ya kamata shi da iyalin sa. Sannan daga shi har matar sa Halima masu karar da rabin dare a tsaye ne cikin Ruku'i da Sujudi. Don haka zamu iya cewa; hassadar masu hassada bata taba siyasar Hashim da komai ba, tamkar taki take zame masa. Wanda ya rike Allah da Manzon sa ya kuma yi riko da gaskiya to zai yi ta yin gaba ne komai sharrin mai sharri. Kullum farin jinin sa karuwa yake a idon al'umma, sunansa kara tambari yake a jihar Kano. **** RANA MAI DIMBIN TARIHI Rana mai dimbin tarihi ga Halimah da Hashim itace ranar da aka gudanar da zabe (secondary election) a tsakanin duka jam'iyyun Nijeriya. Inda a kowacce mazaba jam'iyyar (Northern Region Congress Party) wadda aka fi sani da Jam'iyyar talakawan Arewa ita ce kan gaba, tun daga presidential har gubernatorial. Al'ummar jihar Kano musamman matasa maza sun fita kwan su da kwarkwatar su sun dangwalawa YAKASAI (sunan sa kenan a Siyasa). Tun daga sanda suka ji missions and vissions din sa a BBC debate na ‘yan takarar gwamnoni; cewa shi akan cigaban matasa zai tsayar da administration dinsa domin sune future din Nigeria. Ban taba ganin Engnr. Halima Zubair Numan ta yimin kyau irin na yau ba. Ban taba ganin fuskarta na fesar da annuri irin na yau ba. Tana tsaye a polling unit na Kano-Municipal tareda Hashim da Safeeyah rike a hannun ta, cikin jikin ta ya girma sosai. Sanye take da laffaya koriya shar mai ratsin fari wato kalar tutar Najeriya. A cikin rumfar da suke zaune akwai Dr. Rabiah da mijin ta, Sa'adatu da mijin ta Lawal. Ta bangaren Halima kuma mutanen Numan ne kwansu da kwarkwatar su, ga kuma Hajjah Falmata ma sun zo da dukkan 'ya'yan ta. Hatta Salima dake Lagos ta zo don tsayawa da Halima a wannan muhimmiyar rana mai dimbin tarihi a gareta. Bayan kammala zabe suka dawo gidan Halima dake Nasarawa. Kowa yayi mamakin rashin ganin Hanan don tun kan su taho filin zabe suke jiran isowar ta, da lokaci ya kure dole suka taho babu ita don wayoyin ta duka sun ki shiga. A daren ranar kafafen yada labarai suka sanar da zababben gwamnan jihar Kano wato Engnr. Hashim Ismail Yakasai. Za'a rantsar dasu nan ba da jimawa ba. ***** Likitoci rankatakaf! Suka rufu a kansa don kakarin nemo ran sa. Hayaki da turirin wuta ya salube duka fatar kafafun sa. Ya kuma yi lahani a mashaqar numfashin sa. Prof. Zubair Numan, yana raye ne kawai amma bai san a duniyar da yake ba, har tsayin kwanaki uku. Seun, shine tare da shi, tun ranar da abin ya faru yake gwada wayar Hanan amma bata shiga, shi kuma bai da layin mijin ta, sai a rana ta biyar ne yayi sa'ar samun ta. Hanan ta yi shirin tahowa Kano, anko suka yi na laffaya ita da Halimah sai kala daya banbanta, nata purple ne light and dark, don tsayawa tareda Halima ranar zaben mijin ta, wayar Seun ta risketa, "where have you been Hanan? Daddyn ki na kwance rai a hannun Allah a asibiti, gidan ku ya kone kurmus! Sai abinda ba'a rasa ba ya saura.......". Tsananin tashin hankali yasa Hanan mancewa da batun tafiya Kano ta wuce Abuja kai tsaye daga Porthearcort. A yadda Hanan ta samu jikin Daddy sai zuciyar ta tsinke. Komai ya kwace mata. Ta kifa kai a kan kirjinsa tana kuka. Amma ta yanke a ranta bazata gayawa Halima a yau ba, kada tayi spoiling farin-cikin ta. Zata bari sai hada-hadar siyasa ta lafa. Ko Hasheem bata gayawa ba yau ranar farin-ciki ce a garesu kuma sun cancanceshi komai kankantar sa. Duk da Halimah na fushi da Daddy ai Uba-Uba ne. Dole hankalin ta ya tashi in taji abinda ya same shi. Hanan na can Abuja suna jinyar Daddy itada Salim da Seun, Halima da Hashim na Kano suna celebrating victory din su, ba tare da sun san abinda ya faru a Abuja ba. Salim ma bai fada masa ba. Ba jimawa kuma aka rantsar dasu Hashim suka yi hijira zuwa "Government House Kano State". Karkashin rakiyar babbar aminiya Zarah Datti Giade da dukkan iyalin Alhaji Datti Giade da 'yan uwan su na jiki da makwabtansu na Yakasai da abokan arzikin Inna Haajar da na unguwar da suka fara zama a Kano. Da Halima ta nemi ba'asin rashin zuwan Hanan, cewa tayi ita da Salim sai daga baya zasu zo taya murna, sun yi tafiya mai muhimmanci zuwa jihar Calabar. "Kowanne irin muhimmanci ke da tafiyar, yakamata a ce a wannan ranar babu ke tare da ni Hanan?". Halima tayi korafi. Hanan ta daga ido ta dubi Daddyn su, wanda ke kwance kafafu a salube sai juya kai yake saboda azaba, hawaye masu dumi suka cicciko idon ta. Tsakanin shi da Halima bata san wa tafi tausayawa ba yanzu. Halimah has gone through a lot. Yau ce ranar girbar hakuri da sadaukarwar ta, ranar farin-cikin ta bazata lalata wannan farin-cikin data tsinkaya a muryar Halimah ba. Ta kakalo murmushi ta ce. "Your excellency, First Lady of Kano, kai na bisa wuyana. Amma tunda nace miki tana da muhimmanci to ki yarda tana da shi din. Ina nan tafe bada jimawa ba, bani Safeeyah in mata "congratulations". Dariya Halima tayi jin sunan da kanwartata ta kira ta dashi. She's indeed Kano first lady after being Kano last lady! Tace "Safeeyah na can cikin yara, yau ta manta bata da ido. Harka kawai take yi da mutane kace-kace" Hanan tayi murmushi cike da kauna da kewar yarinyar sannan suka yi sallama. Hajja Falmata da Goggon Numan ne suka shigo karamin falon da Halima ke zaune tana waya da Hanan, suka shiga lissafin abinda za'a sallami bakin Numan da shi da na Maiduguri Halima na amsawa tana bada order ta wayar hannun ta. Kwanaki bakwai sur ba abinda ake a gidan gwamnati sai hidima da bidirin farin-ciki kala-kala. Halima da His Excellency basu samu kansu ba sai daren ranar asabar da kowa ya tafi, bangaren nasu ya saura daga su sai Safeeyah, hatta ma'aikata sun nabba'a a bangaren su. Hashim ya mikar da Halima dake zaune ya ja ta cikin jikin sa a hankali. "Words are not enough to express my gratitude, for your being with me through light and dark, through struggles and obstacles, for your sacrifice and infinite love,....Halimah you are my life and source of every happiness of today, i assure my love, heart and everything in my possession. I LOVE YOU with all my heart… HALIMAH!" Halima ta zama wordless, kalaman Hashim sun gama kashe ta, kawai sai ta tafi cikin slow-motion ta kanannade a jikin sa kamar macijiya. Dare ne da suka gudanar da wata irin sassanyar soyayya wadda hasken zuciya da yalwar farin-ciki ne ya jagorance ta. Contentment da sukunin zuciya ya kawatata yayi mata ado da alharini, domin sun kasa bayyana iyakar kaunar da suke yiwa juna a daren yau da kuma dimbin godiyar su ga Ubangiji. Watanni biyu bayan tabbatuwar Hashim a kujerar gwamnatin Kano Halima ta haihu, ta haifi 'yar ta mace lafiyayya, tun a asibiti da Hashim ya dauki yarinyar Halima ta roke shi ya sanya mata sunan ZARAH DATTI. Ai kuwa daga jin wannan albishir Zarah ta dauko hanya ta taho daga Bauchi, da akwatunan kayan barkanta damkam, da ita aka yi radin sunan takwarar ta. Still Hanan na bada uzurin basu dawo daga Calabar ba, wani muhimmin aiki ne ya rike su, zuwa yanzu kam Halima ta fara zargin akwai muhimmin abin da Hanan ke boye mata. ***** Watannin Prof.kusan uku kenan a asibiti, ya murmure sosai, konannun kafafun sa sun kame sun zama tabo, amma ya rame sosai, kullum hirar sa dai HALIMAH ce, da rokon Hanan ta nemo masa Halima kafin ta Allah ta kasance da shi akan gadon nan bai ga Halima ta yafe masa ba. Ya tabbata hakkin ta ke bibiyar rayuwar shi. Hanan sai dai tayi zugum ta kasa ce masa komai, don ko jiya Halima ta jaddada mata in ta fadiwa Daddy ta san inda take Allah ya isa bata yafe mata ba! Kuma har abada bazata yafe mata ba". Yau Salim ya zo ya dauki matar sa suka fice, suka bar Daddy shikadai a daki, amma kafin ta fita sai da ta kunna masa talbijin don ta taya shi hira, kasancewar bata kunna masa sam sabida gudun kada ya ji sunan Hashim a kafafen yada labarai. Yau kuma Salim ya janye hankalin ta da soyayya yayi tagiya ne ya dawo, kuma Seun yayi nisan kiwo, ta kunna masa tv tace. "Daddy, bazamu jima ba, zamu je mu sha fresh-air mu dawo”. Murmushi yayi mata yace. "Allah yayi miki albarka Hanan, ke da 'yar uwar ki a duk inda take". Wani programme da ake haskawa ne ya dauki hankalin sa a NTA Abuja, misalin karfe tara da rabi na dare aka sako shirin a takaice ba gabadaya ba. Debate ne na 'yan takarar gwamnonin jihar Kano na dukka jam'iyyun Najeriya wanda BBC Hausa ta shirya kafin ranar zabe. Kowanne dan takara aka kira zai tashi ya yi bayanin missions and visions dinsa da ya tanadar wa al’ummar Kano idan ya samu nasarar hayewa kujerar gwamna. Dan takara na biyu da ya mike daga jam’iyyar talakawan Arewa jam'iyya mai farin jini (NRC) shine Engnr. HASHIM ISMAIL YAKASAI, ihu da sowar mutane kadai (in applause) abin burgewa ne. "Sai GWAMNAN MATASA......." Shine inkiyar sa, camera ta hasko kyakkyawar basudaniyar fuskarsa ta ruwa biyu, sosai tayi fresh ta cika allon talbijin din. Ya soma magana cikin tsararriyar Hausarsa mai accent din Kanawan Usul. A takaice ga bayanin nasa; shi gwamnatin sa ta matasa ce, don su suka tsaya suka zabe shi, don haka su zasu fi kowa cin gajiyar ta, bai tsaya siyasa ba sai don taimakawa matasa marassa aikin yi wadanda suka samu damar yin ilmin zamani da ma wadanda basu samu ba don tsamo su daga afkawa laifuffukan da ake yi a kasar mu Najeriya a yau. Babban mission dinsa shine gina future generation. Samar da aikin yi da sana'o'i ga matasa da kuma kawar da cin hanci da rashawa da koyawa matasa tsayuwa akan diga-digan su..... Prof. kara matsowa ya yi gaban talabijin din don ya tantance fuskar wa yake gani haka… it's so familar...... haka muryar ma.... hakan bai ishe shi ba sai da ya dauki medicated glass dinsa ya manna. Nan ya tabbatar ba kowa ba ne, P.A din Halima ne, Hashim Isma’eel Yakasai, kuma mijinta a halin yanzu. Ba jimawa kuma aka hasko shi a matsayin zababben gwamnan jihar Kano ya je bude wani sabon asibitin jiha......an kira sunan sa sau ba adadi, an kuma nuno shi sau ba adadi...ba wani bane Hashim Yakasai ne. Jikin Prof. ya mutu murus, daga inda yake zaune, bai san sanda ya miki tsaye ba, ya kuma koma jabar! Ya baje cikin kujerar da ya tashi. Ya rasa inda zai sa kansa da mamaki da tu’ajjibi. Zama ya yi kamar wani zararre, shi kadai sai safa da marwa yake a dakin asibitin. Nadama mai tsanani na huda zuciya da bargon sa. Ya yarda wani bai isa ya azurta wani ba, kamar yadda wani bai isa ya talauta wani ba. Ya tuna kalamai na karshe da Hashim ya gaya masa, rana ta karshe da ba su kara takowa kofar gidansa ba bayan korar karen da yayi musu da mugun baki, har zuwa inda yau ke motsi ko inwar su bai kara gani ba. “ALLAH NA KOWA NE!”. (Inji Hashim). Tabbas yau ya yarda Allah na kowa ne!!! Allah shine kadai mai azurtawa kuma mai talautawa ba dai mutum ba!!! "WA MAN YATTAQIL-LAAHA YAJ’ALLAHU MAKHRAJA. WA YARZUQHU MIN HAITHU LAA YAHTASIB, INNALLAHA BAALIGU AMRIHI- QAD JA’ALLAHU LIKULLI SHA’IN QADRA’' Fassara; “Duk wanda ya ji tsoron Allah zai ba shi mafita, Ya azurta shi ta inda ba ya zato. Hakika Allah mai isarwa lamarunsa ne, Allah ya sanya wa kowanne abu gwargwadonsa”. **** Daddy bai gayawa Hanan da Salim ya san inda Halimah take yanzu ba, ya gama gane boye masa suke yi amma sarai sun san inda take. Ko abinda ya gani a talbijin bai fada ba. Shiru yayi ya cigaba da kwanciya a gadon sa kamar mai barci lokacin da ya ji dawowar su. Zazzabi mai zafi ne ya rufe shi wanda nadama ce mai tsanani silar zuwan sa. Kallo daya suka yi masa suka gane jikin sa na karkarwar zazzabi suka kira likitan sa ya zo ya duba shi, yayi masa allura sai ya samu barci. Bayan sayi biyu da yin haka aka sallami Daddy daga gadon asibiti. A gidan sa bangaren ma’aikata ne kawai bai kone ba wato baskwata da harabar waje da wajen adana motoci. Ko rigar sanyawa bai tsira da ita ba. Amma motocin sa suna nan. Don haka Solomon da Jonathan da Jafaru suka bar masa baskwatan su suka koma bangaren Seun. Amma Hanan sai ta kasa tafiya ta bar Daddynta a wannan muhalli cikin wannan yanayi. Zuwa yanzu ta san hankalin Halima ya gama kwanciya is high time ta san halin da mahaifin su ke ciki. Hanan da Salim suka roki Daddy kan zasu tafi da shi gidan su a Porthearcourt kafin asan abin yi a kan gidan sa shima kuma ya kara samun kulawar Hanan ya karasa warwarewa. Da kyar Daddy ya yarda, don cewa yayi ina aka taba haka? Uba da zama a gidan ‘yar sa? Sai da Minister wato Baban Salim ya sanya baki yace “yadda zan je in zauna a gidan Salim idan lalura ta kama haka kake damar ka je ka zauna a gidan Hanan, kafin ka kara samun sauki a san yadda za’ayi da konannen gidan”. Hanan ta kira Baffa Modibbo Hussaini bayan sun isa Porthearcourt, ta gaya masa duk abinda ya faru da Daddy cikin watanni ukku. Aka ce naka-sai-naka! Modibbo cewa yayi cikin kidima ga shinan zuwa Abujar. Tace basa Abuja sun wuce gidan ta da shi a Fatakwal zata turo masa tikiti ya zo shi da duk wanda ke son zuwa. Hakan kuwa aka yi. Daddy bai san hawa ba bai san sauka ba, sai sallamar Kawunsa da ‘ya’yan sa da Goggon sa Iyami ya ji akan sa, yana zaune falon Hanan sanye da farar yar shara da wando na shan iska wanda Salim ya dinka masa da yawa, Hanan na gefen sa tana firfita masa shayin na’a-na’a kasancewar garin yayi lumshi an tafka ruwa. Sabida tsabar kunya da jin tozarta sai ya fashe da kuka. Ya gurfana gaban Baffan sa Modibbo Hussaini yana bashi hakurin watsar da su din da yayi (don ba su da komai), ya manta dan uwa shine suttura, shine mutunci duk kudin ka duk mukamin ka. Akidar sa ta BOKO mara amfani ce bata amfana shi da komai ba, ya yiwa BOKO gurguwar fassara. Yanzu kam duniya da yake makaranta ce ta koya masa darasi kala-kala. Modibbo Hussaini murmushi yayi, ya dago shi daga durkuson da yayi a gaban sa suka zauna tare. Ya ce da shi “in Allah ya baka ‘ya’ya to ya baka komai na rayuwa, ka kula da su ka rike amanar su. Ka godewa Allah da ‘ya’yan da ya baka ka wulakanta su. Yau gasu sune kadai marufar asirin ka su suka tallafi kowa naka, a lokacin da kai ka watsar dasu ga duniya. Auren nasu da baka so shi ya suturta ka! Zubairu mecece duniya? Wallahi aikin banza ce. Ka dauke ta da zafi don kurum Allah yayi maka falalar rayuwa. Ka yi ta istigfari domin kuwa aure sunnar Annabi ne, kuma ya ce wanda ya ki sunnnar sa baya tare da shi…..hakika ka nesanta kan ka da Manzon Rahma (SAW) tunda kana adawa da sunnar sa. Kai baka yi ba, sannan ka ce ‘ya’yan ka ma bazasu yi ba? To lasisin aikata zina ka basu ko me?” Haka Modibbo Hussaini ya cigaba da lugwigwita zuciya da ruhin Prof. Numan da wa’azi da nasiha mai shiga jiki, baya cewa komai sai hawaye da “astagfirullah” a fili. Baffa yace “afuwa ta da kai Zubairu guda daya ce ka nemi kamilar mace cikin dangi ka aura, ga nan Saddiqa diyar Goggon ku iyami mijin ta shekarar sa guda da rasuwa bata taba haihuwa ba, ka rufawa kanka da ‘ya’yan ka asiri ka mutunta kanka da tsufanka ka aure ta. Sannan zan taimaka kayi tattaki zuwa ga HALIMATU ka nemi gafarar ta. Hakika ka cutar da ita, ka wahalar da ita, ka wulakanta amanar marayu da Allah ya baka. Bar ganin kai ka haife su, su kan su ‘ya’yan daka haifa amanar Allah ne a hannun ka. Wadda idan ka ci ta tun a duniya sai Allah ya tuhume ka kafin ma aje lahira idan basu yafe maka ba………”. Daddy kuka yake ta yi sosai yana fadin “don Allah a tashi a rakani wajen Halimahtus-Sa’adiyyah, na riga na ji a talbijin tana Kano koda sun boye mani, kuma ko a kafa zan kai kaina Kano daga nan Fatakwal”. Hanan a yadda ta ga yanayin Daddy ta san yana nufin abinda yake fadi. Tsoro ya kamata kada ya faki idonta ya tafi Kano a kasa. Ita Allah ya isan da Halimah ta yi mata take ji. To gashi ya ce already ya san komai. Gwamna kuwa ba boyayye bane a kowacce jiha balle gidan sa. Ko ta kai shi ko basu kai shi ba zai iya kai kansa, don haka ta yarda zata dauki Allah ya isan Halimah ta kai Uban ga ‘yar sa, in ya so daga baya ta nemi gafarar ta. Sun shirya tafiyar ne dukkan su familyn har Baffa Modibbo da Goggo Iyami, don dai su cikawa Halima ido ta amshi mahaifin ta. Salim ya ce “wannan family matter ne don haka ba zai bi su ba, ya kaisu filin jirgi ya sanya su a jirgi mai zuwa Kano. Sannan ya koma bakin aikin sa. Suna sauka Kano Hanan ta kira His Excellency (yadda take kiran Hashim) ta gaya masa suna filin jirgi itada su Baffa ya aiko a tafi dasu. Bata gaya masa yau har da Daddy-Professor suke tafe ba. Nan da nan kuwa sai ga motar gidan gwamnati irin doguwar civilian dinnan, ta zo ta kwashe su zuwa Governmnt House. Tun daga bakin get na farko da shirgin sojoji masu bakin kaya da bindigogi suka tare su zasu yi bincike suka samu waya daga ofishin cikin gida kan cewa bakin na ‘Her Excellency’ ne kuma bisa iznin mai girma gwamna kada a bincike su. Daddy baya komai sai sharar hawaye, ya daga kai yana kallon duniyar da Halimah ke ciki, her humble abode, kuma duk wadannan matakan tsaron don kare lafiyar ta ne data ‘ya’yan ta da mijin ta. Lallai Allah baShi da abokin tarayyah! Kuma shine mai daukakawa da kaskantawa da azurtawa da talautawa a lokacin da ya so, ba dai mutum dan adam ba!!! Imanin sa ya karu a yau, taqawa ta kara dabaibaye shi. ***** GOVT. HOUSE, KANO “Ranki ya dade kina da baki”. Her Excellency Halimah Zubair Numan ta sauke kanta daga kirjin maigidanta, wanda tun shigowar sa gidan bayan sallar asubah daga tafiyar da ya yi zuwa kasar Spain yake yi mata wata irin tausa, sabida gajiyar da ya san ya tara mata a daren jiya, tausa ce irin ta tun lokacin amarcin su, ya je kasar Spain ne domin rakiyar Alhaji Datti da ya yi ganin likita wanda ya zame musu UBA, kuma bango abin jingina tun bayan da Hashim ya lashe kujerar gwamnatin Kano. Shike tafiyar da komai na administration din Hashim a matsayin legal adviser. Har gobe kuma shine shugaban jam’iyyar NRC. “Amma na gaya miki in ba abu mai matukar muhimmanci ba kada ki kira ni da wannan layin ko?” ‘Yar sandar ta kame kamar Halimah na ganinta. “Ki yi hakuri Your Excellency, na kira ki ne don na fahimci sun fi kowa muhimmanci a gare ki, kuma His Excellecy ya san da zuwan su, shi ya bada iznin a bar su su shigo, sun ce MAHAIFIN KI ne da kanwarki ciki daya”. Halimah ta sandare da waya a hannunta daga kwancen da take, ta rasa a yanayin da maganar matar ta zo mata. Daddy a gidanta? Wato Hanan sai da ta kawo shi hankalinta ya kwanta? Ta dubi Hashim, shi kuma ya bude mata kyawawan idanunsa da suka kada cikin neman karin bayani. Kokarin sumbatar tafin kafar ta yake yi ta janye, “Ka tashi Your Excellency, wai Daddy ya zo gidan nan. Ban san da wacce ya zo ba”. Hankalinta a matukar tashe yake don da gaske ba ta san da wacce ya zo ba. Ta san Hanan ba za ta ci amanarta ba, amma yanzu ta san tunda sun zama prominet political figure nemansu ko sanin inda suke ba zai yi wa Daddy wuya ba. Hashim ya kama Halima da dukkan hannayensa, murmushin kwantar da hankali ya yi mata, sannan ya sumbace ta son ransa, “Go to your father Halimah… na tabbata alkhairi ne ya kawo shi. Ki karbe shi da duk wacce ya zo da ita. In ba mu kasance masu yafiya ba musamman ga iyayenmu, to hakika ba mu gode falalar Ubangiji a gare mu ba”. Ya mikar da ita tsaye, da kansa ya canza mata rigar barcin jikinta zuwa doguwar rigar abaya, sannan shi ma ya canza. Ya dauki waya ya bada umarnin a shigo da bakin nan har falonsa. Hannun Hashim cikin na Halimah, a lokacin da suke saukowa daga matattakalar bene. Safiyyah ba ta gidan, an kai ta wata makarantar makafi ta musamman a kasar Ingila (West of England School for the Blind, Exeter). Daga nesa Halimah ta tsaya tana kallon mahaifinta, Prof. Zubair Numan, ya tsufa matuka, sannan ga alamu na rashin wadatar lafiya a tare da shi. Dogon wandon sa ya boye tabon kafar sa. A gefensa Hanan ce da Baffa Modibbo Hussaini. Da gudu Hanan ta taho ta rungume Halimah, wadda ta tsaya a inda take, ta kasa cira kafa gaba, ta rasa a wane yanayi ta tsinci kan ta, Hanan kuka ta ke tana rokonta ta yafe wa Daddy, yayin da Prof. ke takowa zuwa gaban Halimah yana hawaye. A yadda ya ga Halimah da Hashim sai tsoron Allah ya kara ratsa zuciyarsa. Ba su yi aune ba suka ga Prof. ya zube gwiwoyinsa a gaban Halimah ya rike kafafun ta yana ta kuka. Da sauri Hashim ya tsugunna ya dago Prof. Numan. Halimah ta rungume mahaifinta ta saki kuka mai tsuma rai. Shi yake neman afuwa da gafarar su, amma kukan da yake yi ya sa ko muryarsa ba ta fita sosai. Haduwar Halimah da mahaifin ta Prof. Numan bayan wucewar shekaru goma is very emotional… ya yi nadama… ya yi nadama… ya yi nadama! Ya ga ishara iya ishara. Daga Hashim har Halimah babu wanda bai tausaya wa Daddy ba, suka kuma yafe masa da kyakkyawar zuciya. Tun a satin suka tafi da shi asibiti a Egypt don a binciki lafiyarsa ciki da bai, cututtuka kala-kala likitoci suka gano a jikin Prof. Numan, sukari (diabet), hawan jini sannan kodarsa ta tabu. Hashim da Halimah suka tsaya tsayin daka a kan lafiyar Prof. Numan, har ya warware. Tun a Egypt da Hanan ta gayawa Hashim abinda ya faru da Daddy da gidan su na Abuja yake wani shiri ba tareda sun sani ba. A karshe ya taho ya baro su tare da mahaifin su a kasar Egypt, yace su huta sosai, sai ya ce su dawo sannan su dawo. Wannan zama da sukayi a kasar Egypt tareda Daddyn su a daki guda ya farfado da soyayyar su ta tun fil azal. Suna ta kula da shan magungunan sa. Motsi kadan yace “Halimah….Allah yayi miki albarka”. Hanan ta ce cikin shagwaba “ni ban da ni?” “Har dake autar Daddy, amma ta Halima special ce, kamar yadda take special a gareni”. Hanan ta ji kishi tasa kukan shagwaba, sai ya jawota jikin sa yana lallashi yace “a ko’ina akwai auta, kuma Hanan ita kadai ce autar Daddy, shalelen Daddy”.. duk suka fashe da dariya. Yaji labarin Safeeyah iri-iri a bakin Hanan, Daddy sai da ya kara yin kuka. Ya tuna bakin da yayiwa Halimah da tsohon ciki. Yayi ta istigfari yana rokon gafarar Halimah. Halimah tace “Daddy, nifa ban yarda bakin ka ne ya kama Safeeya ba, Ubangiji na yin halittar sa ne yadda ya so, da baki ko ba baki. Don haka don Allah kada ka kara tunanin kai ne silah”. Ya dauki baby Zarah yana mata wasa yace “amaryata Zahra’u duk kyan nan naki makauniyar nake so a matsayin uwargida, don Allah ku kaini in ganta”. Halima tace lokacin hutun su ya kusa, zata dawo gida maybe kafin mu koma ma”. Hashim yayi musu waya cewa su taho, kuma su sauka ta Abuja. Hakan kuwa aka yi. Halima da Hashim kwance a bayan mota ‘Rolls-Royce’ data dauko su daga filin jirgin saman Nmadi Azikwe hannun Halimah cikin na Hashim yana murzawa a hankali, cewa yake “me kike shafawa hannun naki haka Leemah? Laushin ya isa, kamshin ya isa, kada ki haukata ni daren yau, na sha wahala wata guda fa, Allah kadai yasan yadda akai na kawo yau inda nake”. Halima sai dariya take masa da fararen hakoranta. Tana kara shigewa jikinsa. Hanan da Salim mota daban suka shigo tare da Daddy. Sai gani tayi direba ya dauke kan motar zuwa unguwar su, unguwar data yi duk wata dabdalar kuruciyar ta zuwa girmanta wato Asokoro. An kuma doshi get din gidan su. Seun, ya bude tangamemen get din, da Halima ya fara tozali da mijin ta kwance a bayan mota, dadi da farin ciki suka rufe shi. Yace “H for Halimah H for Hanan”. Bakin sa kawai Halima ta kalla ta gane abinda ya ce. Murmushi tayi tana daga masa hannu. A lokacin ne Halima ta daga ido ta hango wani ‘cute mansion’ wanda yafi gidan su na baya tsari da kawatuwa. Da sauri ta juya ta dubi Hashim, shi kuma ya lumshe mata ido, yace. “Safeeyah da Zarah sun gyarawa angon su gida ne. Suna neman albarkar sa…”. Halimah ta fada kirjin Hashim da karfi ta saka kuka. Shikuwa Prof. Hawaye yake yi yana shiwa Hashim da Halimah albarka. Yana cewa cikin ransa; “Watakila har ya mutu baza’a daina nuna masa ishara ba…..”. **** Sun tafi sun bar Daddy a sabon gidan sa karkashin kulawar su Seun, Minister Usman Baban Salim shi ya tsaya wajen ganin Daddy yayi (court affidavit) na takardun kadarorin sa da suka kone, don ganin cewa ya sake mallakar su. Itama Zarah Datti, ta kira Halimah a wannan daren tace gata a kasar Mexico musamman don ta sake karbawa Halima takardun karatun ta ta biyo maigidanta Mexico wani aiki da ya kawo shi. Tace Halima tayi affidavit na takardun ta ta tura mata online ba sai ta je ba. A karo na farko da Halimah ta ji sabon ‘hope’ akan ilmin da ta sha wahala ta yi. A da, ta dauka ta baiwa takardun nan baya kenan bazata kara waiwayar su ba har abada. Amma tunda ta karbi Daddy, ai dole ta karbi takardun ta. Kaddara ce Allah ya rubuta musu kuma ta riga ta faru, an jarrabesu sun kuma cinye jarrabawar su, dole yanzu su karbi kyakkyawan sakamakon da Ubangiji yake ta yi musu. In har sun kasance masu godiya a gare shi. Ta je aka yi mata affidavit, ta rubuta application ta yi scan ta turawa Zarah. Kafin sati sai ga gabadayan takardun Halima sun dawo mata. Ta yi kuka ta yi kuka ta godewa Allah. Ta yi musu kyakkyawan adani tare da takardun Hashim. Duk da haka bata da wani buri da su bayan ajiyewa. Ta riga ta sadaukar da rayuwar ta da lokacin ta da ilmin nata ga maigidanta da iyalin ta. Tunda ba abinda ta nema ta rasa daga mijin ta abin kaunar ta, Hashim. Gagara-gasa a cikin maza, mijin marainiya, namiji dan goyo (inji Halimah). An saka daurin auren Daddy da Addah Saddiqa a Numan sati mai zuwa, don haka a gabadayan satin nan shirye-shirye suke yi da shirin tafiya Numan ranar alhamis, kasancewar Juma’ah bayan masallaci za’a daura auren. Hanan ta kira Yayarta Halimah cikin raha tace “Sis Leemah, ya kamata mu hadawa Daddy lefe fa na gani na fada”. Dariya Halimah tayi ta ce “kin kawo shawara mai kyau, yanzunnan zan sa Sa’adatu ta hado komai tunda sana’ar ta kenan”. Hashim da Halimah sun dade da baiwa Sa’adatu kanwar Hashim jari mai tsoka tana zuwa Dubai tana shigo da kayan sanyawa na mata, lesussuka, dogayen riguna da takalma da jaka na mata, ta bude kayataccen shagon ta a kantin kwari, international business take ba kama hannun yaro kuma Allah yasa mata nasibi a ciki. Dr. Rabi’ah kuwa duk da ba wani mugun shiri ne tsakanin ta da Halimah ba kamar Sa’adatun itama basu barta haka ba, a baya a Legal take koyarwa amma yanzu Hashim ya maida ta jami’ar Abuja (Gwagwalada). Sannan ya bata jari kwatankwacin na Sa’adatu. Ta karba, amma tace ita bata ra’ayin kasuwancin aikin ta ya wadace ta. Kulawar da take baiwa Halimah yanzu, ko itace Inna sai haka, duk da a cikin ranta tana fadin Halima ta cikawa Hashim gida da ‘ya’ya mata da makauniyar da bazata moru ba, saidai ta zame masa liability, amma a wajen Halima Dr. Rabiah ta riga ta baro gini tun ran zane, ba wani abu da zata yi mata na nuna kauna a yanzu da zai wanke dattin ta riga ta yaba mata a zuciyarta acan baya. To dama babu yadda za’ayi ace mace ta rayu babu irin wannan daga dangin miji, koda ba dukkansu ba, musamman Hashim da ya daukaki Halima a idon duniya bakidaya, baya zartar da komai sai yayi shawara da ita saboda ya yarda da intellectual positive thinking din ta. Ana rade-radin ma baya daukar shawarar mashawartan sa sai ta Engnr. Halima Numan (Mrs. Engnr. Hashim Yakasai). Akwai lokacin da Dr. Rabiah ta yi masa wannan shaguben; cikin raha; da kai da Halima bamu san wanene gwamnan Kano ba. Hashim sai yayi murmushi kawai ya girgiza kai. Abinda ya sani shine; idan ana bada kujerar bakidayan ta zai iya baiwa Halimah Numan, karewar daukar shawarwarin ta, wadanda duk na ilmi ne da taimaka masa ga kaiwa ga nasara cikin siyasar sa. Kai sai ka dauka akan ‘Political Science’ tayi dukkan karatun ta. Nan kuwa ba komai bane tsabar bincike ne, bincike take yi ba dare ba rana akan ‘political theories and tactics’ tana dora mijin ta bisa turbar shahararrun political scholars irin su John Situart Mills, Adam Smith, Max Weber, Thomas Hobbes, Anthony Giddens, Karl Max da sauran su wadanda sune suka kirkiro ilmin siyasa a zamanance. Babu son zuciya ko fariya a cikin shawarwarin Halima, sannan bata almubazzaranci da dukiyar al’ummah duk da damar hakan data ke da ita inda halin ta ne. Ita kawai (Legal Adviser) ce ta Hashim bayan Alhaji Datti, kuma tana da albashinta mai tsoka akan hakan daga aljihun gwamnati. Sa’adatu ta kammala hadawa Daddy lefe ta dauko akwatunan har set 3 ta kawowa Halimah, Halima na dubawa tana yaba komai, an zuba komai mai inganci na gani na fada tamkar Addah Saddiqan da za’a kaiwa yarinya ce budurwa, suka kwasa suka tafi Numan. Kwana biyu da zuwan su Baffa ya daura auren Daddy da anty Saddiqah, da ta ga lefen da su Halima suka yi mata sai da ta fashe da kuka, ta kudurtawa ranta rike marayun nan da uban su tsakani da Allah da dukkan amanar da zata iya. A wannan zuwan da su Halima suka yi Numan, duk wani jinin Malam Muhammadu dana su Modibbo Hussaini sai da ya shiga list din wadanda Hashim zai samarwa sana’a kwakkwara, ko aiki ga wadanda suka yi karatu, kowa ya san a wannan bangaren gwamnatin sa tafi bada karfi, kuma ya shigo siyasa ne solely akan hakan sabida yanada good experience da feelings din matasa marasa aikin yi. Halima ganin irin hidimar da Hashim ke yi da danginta wani tunani ya darsu a ran ta. Bayan sun kaiwa Daddy amaryar sa Abuja sun juya gidajen su, a daren ranar Halima ta tadda Hashim a main falon sa, yanata sanya hannu a takardun kwangila da zai baiwa matasa masu (first class degree) a Kano, Halima na zuwa ta zaune masa bisa cinyoyi ta sunkuya ta sumbaci kwantaccen sajensa “time for bed Baban Safeeyah”. Wato lokacin kwanciyar su yayi. Hashim ya ce “ki dan yi hakuri na karasa Leemah, in ban gama yanzu ba goben ba iyawa zan yi ba, inada wasu ayyukan masu tarin yawa a ofis…”. Ina! Halimah bata saurareshi ba domin sassanyar sumbar da take zuba masa, dama ta san “baya wuce tayi” kuma ba’a dauki dogon lokaci ba ta dora shi akan network yadda take so, aikin da ba’a karasa ba kenan har washegari. Saida komai ya lafa, suna kwance cikin jikin juna tamkar a haka aka halicce su, Halimah tace “your excellency, yakamata mu je Sudan mu nemi dangin Inna”. Hashim yayi shiru, yana shafa kwantaccen gashin kanta bakikkirin. Wani tunani mai kyau da shi bai taba yi ba sabida yawan al’amuran dake kansa. Yace “insha Allah Sweetheart, zamuje cikin wata mai kamawa, Yaya Rabia ta taba zuwa ta san adireshin su, zamu tafi gabadayanmu har yara lokacin Safeeyah ta zo hutu. Nagode da tuna min muhimmin abinda hankali na bai taba kaiwa ba. Har sauran dangin Baban mu in akwai zan nemo su duk inda suke. Washegari ya kira Yaya Rabia ya gaya mata shawarar da Halimah ta kawo, Dr. Rabi’ah sai ta ji kunya, sun baje suna ta cin gajiyar mulkin Hashim sun manta da dangin Inna, sai Halimah ce ta tuna su. Tace “sunan garin su Inna Jazeera, yakamata mu tafi har Safeeyah su ganta”. Ya ce Safeeyah na nan zuwa hutu daga Exeter next week, har da ita zamu tafi insha Allah”. Daga ranar Hashim ya soma yi musu shirin tafiya kasar Sudan dukkan su, cikin sati biyu komai ya kammala, Halimah ta ji dadin zuwa Sudan domin dangin Inna sun karramata, sun musu tarba ta musamman, kannen mahaifin Inna su biyu ne El-Bashir da El-Mansoor sai kanwar Inna Fadhilah tana da aure da ‘ya’ya takwas, sai kuma wata Kaka ga su Inna dattijuwa mai suna Saratu. Hashim yayi musu goma ta arziki, ya kuma yi alkawarin ziyartar su akai-akai in ya samu sarari, ko shi bai zo ba Halimah zata zo. Rashin zumuncin da aka yi a baya baza’a sake maimaitawa ba insha Allahu. Har manyan gonaki ya sayawa El-Bashir da El-Mansoor kasancewar su Manoma ne a garin na Jazeerah. Suka dawo gida ranar Lahadi, kowanne ya koma bakin aikin sa. Shekaru biyu akan karagar gwamnatin Kano, Halimah Zubair, ta gama farfadowa, ta dawo ‘yar gayenta har fiye da baya sanda take shugabar NCC. Wannan duka ya faru ne da taimakon Zarah Datti, aminiyar kwarai. Halima ta saki duk wani kalubale da canjin rayuwa ya janyo mata. Kula suke da mahaifin su da matar sa sosai wadda ta kama su ta rungume da dukkan kauna da soyayya kamar ita ta haife su, dama kuma Yafendo ce a garesu. Zarah na da shekaru uku Halima ta sake samun ciki, Allah mai girma da daukaka, wannan karon sai ga ‘yan biyu maza Allah ya baiwa Halimah. Farin cikin da Hashim yayi ba mai misaltuwa bane, yayin sadaqah yayi kyauta har ba adadi don nuna godiyarsa ga Allah. Sai dai har gobe ko ‘yan 100 zai haifa yayi rantsuwa ga manema labarai babu kamar “Safeeyah” a zuciyar sa. Dan sauran burbushin Halimah da Dr. Rabiah keda shi a ranta game da Halima kan cewa ta cikawa Hashim gida da ‘ya’ya mata sai ya karasa vanishing. Inda Allah ya taimaketa a zuciyar ta kawai take fadi bata taba furtawa Halima ko Hashim sun ji ba, la shakka da dan sauran kimar data ke dashi a idon Halimah ya karasa zagwanyewa. Hashim kuwa karfin zumunci da girmansa a wurin Ubangiji yake dubawa da har ya yafewa Dr. Rabi’a abinda tayi musu ya cigaba da zumunci da ita, Halima kuma dama tun fil azal ba mai halin kullaci bace ga wanda ya saba mata. Kowa tana mashi uzuri ne, uzuri sau sab’in kafin tace yayi mata laifi. Rainon ‘yan biyu, ba abu ne mai sauki ba ga kowacce uwa, duk da kuwa Halima na da mataimaka ‘ya’yan Baffannin ta na Numan da ‘ya’yan Aunty Habiba, dangin ta duka (paternal and maternal) sun samu kyakkyawan rufin asiri albarkacin Halima, komai su take dorawa bata fiya dora bare akan harkokin ta ba sai a inda ya kamata a ce baren ne zai yi. Balle kuma dangin Hashim da sai ta sa yayi musu sau dari kafin kowa nata. Daga haihuwar twins wadanda Hashim ya sanyawa suna Mujahid da Mubarak, ba’a rufa watanni shidda ba sai ga sabon ciki a jikin Halimah. Hankalin Halimah yayi mugun tashi. Hashim ya fito daga wanka a ranar sai ya samu Halima zaune a gefen gado ta hada kai da gwiwa tana rasgar kuka. Bai san sanda ya saki tawul din da yake tsane kai da shi a kasa ba, ya nufe ta da sauri ya dagota cikin rikon sa “lafiya Leemah? Me ya faru?” Halimah ta janye jikin ta ta sake komawa gefe tana cigaba da rusar kuka. Lallashin duniya Hashim yayi kafin ta iya gaya masa pt-strip ya nuna mata tana da shigar ciki. “Mujahid da Mubarak are only 6 months Cheriè. Yaya zan yi dasu idan na kara haihuwa yanzu?” Wata ajiyar zuciya Hashim ya saki kafin ya tarairayo Halimah ya rungume tsam-tsam. “Zan taya ki da komai Sweetheart, inna ce komai ina nufin har nakudar, har rainon, goyon. Breast-feeding kawai zaki yi, shima don bani da shi a jiki na ne. Ko kullum zaki haifo min Da indai daga jikin ki zai fito ina matukar son sa Halimah. Na roke ki, kada ki bari shaidan ya shiga zuciyar ki har yasa miki waswasi, ya raunata imanin ki. Haihuwa kyauta ce daga Allah da sai wanda ya ga dama yake baiwa. So ki sa a ranki Ubangiji ya san zaki iya shiyasa ya baki, tunda dai alhamdulillah muna da halin ciyar dasu da tufatar dasu, ilmantar dasu da tarbiyyantar da su. Pls Sweetheart kada ki karya min zuciya in yi tunanin kin soma gajiya da haihuwa da ni…..”. Da sauri Halimah ta toshe masa baki, ta hanyar sanya tattausan bakin ta cikin nasa. Cikin wani salo mai burgewa take sumbatar Hashim kusufa-kusufa. Al’amarin da bai yi masauki a ko’ina ba sai akan makeken gadon barcin su. Soyayya ‘yar usuli ta gaskiya wadda bata fading, sun kuma tabbatar bazata yi fading ba har ranar da suka daina numfashi. Washegari kuma sun tashi da shirin tafiya Bauchi duba Alhaji Datti dake fama da rashin lafiya. Sun samu jikin nasa da sauki, Zaarah da yaranta ma suna gidan, nan suka hade da Zarahn Halimah sai kiriniya. Alhaji Datti yayi musu nasiha mai ratsa jiki kamar yadda ya saba ya karawa Hashim da hikimomin shugabanci kamar yadda yake masa kullum. Da Halimah da Zarah suka kebe a dakin Maman Zarah, Halima ta kokontawa Zarah halin da take ciki na kwanikar data sameta. Amma kamar Hashim itama Zarah kwantar mata da hankali tayi, ta ce “ki godewa Allah Besty, nawa ne suke nema da kudin su basu samu ba har suke zuwa asibiti ayi musu artificial? Ba sai mun je da nisa ba akan haihuwa ko Hanan ta ishe ki ishara”. Tun daga ranar Halima tayi wani kyakkyawan kuduri a zuciyarta wanda bata gayawa kowa ba. Bayan sun dawo gida ta daidaici lokacin da Hashim yake cikin kyakkyawan yanayi, sai ta zo ta zauna a jikin sa, ta kwantar da kai bisa kafadarsa. Cikin wata lallausar murya take magana; “Cheriè, ka yi min alfarma in hada kayan Zarah in kaiwa Hanan ita gobe -goben nan, amma ba hutu irin wanda take zuwa ba, na barwa Hanan ita halak-malak, amincewar ka cikin dimbin alfarmomin ka da basa karewa a gare ni nake nema”. A hankali Hashim ya dago fuskarta cikin tafukan sa, sai ya ga hawaye fal a idon ta, tana tsananin tausayawa ‘yar uwarta matsalar rashin haihuwa. Yace “C’mmom Halima shine sai kin yi kuka? Kin fi karfin kowacce alfarma a gareni in har inada ikonta. Allah ya taya su riko, Zarah ta zama ‘yar su ko dama rabin rayuwar ta ai yafi yawa a hannun nasu”. Halima don farin ciki sai ta makale shi tana kuka sosai. Hanan sai ganin Her Excellency Halima tayi a washegari a gidanta, da kayan Zarah rankatakaf ko pant daya bata bari ba. “Ga ‘yar ki mun kawo miki duniya da lahira, Safeeyah bai iya bada ita amma ga Zarah mun baki”. Hanan ta kifa kai a cinyar Halima tana kuka, ta rungume Zarah. Shima Daddy da yaji abinda Halimah da Hashim suka yiwa Hanan sai da ya ninninka albarkar da yake sanya musu a kullum. (Allah ka hada kanmu da ‘yan uwan mu, ka fidda hassada da ganin kyashi tsakanin mu da su, ka sa zumunci ya zame mana silar shiga Aljannah- Takori). MURFI Engnr. Hashim ya gama tenure din sa with much success, yayi mulki irin wanda ba’a taba yi na farar hula a Kano ba, ya bar tarihi wanda ya tsaya a zuciyar Kanawa. Don haka ne yana gamawa basu barshi ya sauka ba suka sake tsayar da shi karkashin jam’iyyar NRC. Ita kanta NRC ta kara daukaka a dalilin farin jinin Hashim. Don haka wannan karon basu sha wahalar kamfen ba Hashim ya sake lashe kujerar gwamnati a Kano. Bayan karewar tenure ta biyu, shekaru takwas kenan akan karagar gwamnati, sai shugaban kasa na lokacin wanda dan jam’iyyar su ne ya bashi Minister of Youth and Sport. Wanda shine mukamin da yake kai a halin yanzu. Don haka su Halima sun yi kaura da jimawa sun koma Abuja a unguwar Ministers’ Hill Colorado Close. Hanan sun samu sauyin wurin aikisun koma Lagos, can ta hade da Salima suke zumuncinsu diyar Hajja Falmata. A lokacin Zarah ta gama primary a hannun ta. Zumuncin Halima da Zarah Datti, wani irin kawance ne mai wuyar samu a wannan zamanin, sun tashi daga kawaye sun koma ‘yan uwa, kuma sirrin juna, bata banbanta Zarah da Hanan akan komai, musamman bayan rasuwar Alhaji Datti, Hashim shi ya zamewa su Zarah babban Yaya ya rungume komai nasu ita da mahaifiyar ta. Shi yake musu komai a bayan ran alhajin duk da cewa ya bar musu gado mai yawa. Haka rayuwa ta cigaba da mika musu incredibly. Da kyakkyawan zumunci abun koyi. **** BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU (WEST OF ENGLAND SCHOOL FOR THE BLIND, EXETER). “Safeeyyah Hashim! Safeeyyah Hashim! Safeeyyah Hashim!”. Kawai kawai kake ji ya na tashi a loudspeaker, ranar yaye daliban kwalejin makafi ta garin Exeter, England. Komai itace ta farko, best in Braille (wato rubutun makafi), best in music, best in sport, best in english literature sannan ta karbi kyautar wadda tafi kowa da’a da iya guiter (garaya). Safeeyah ‘yar baiwa ce ba tun yau ba, Allah da ya halicce ta (visually impaired) bai barta haka ba. Sai ya yi mata karamomi masu yawa wadanda mai lafiyar idanu ma bai da su. Kwakwalwarta na matukar ja, sannan tana matukar so da tausayin iyayenta. Ta shiga ran mahaifin ta fiye da duk ‘ya’ya takwas da Allah ya bashi. Tunanin sa a kullum yadda zata yi coping a gidan aure ne, ko wane miji ne zai aure ta ya rike masa ita da daraja ba wulakanci babu gori? A kullum in yayi wannan tunanin hankalin sa yana tashi, ya gwammace ya ajiye ‘yar sa yayi ta ilmantar da ita yana kula da rayuwar ta. To amma shi al’amarin Ubangiji ba haka yake ba. Ya riga ya rubutawa kowa rayuwa tun zuwan sa duniya. Ita Safeeyah a karan kanta bazata iya rabuwa da iyayenta zuwa gidan aure ba. Tana kammala sakandire West of England School for the Blind Exeter ta yi sponsoring karatun ta na jami’a zuwa ‘Royal Blind College’. Bayan kammalawar ta ta dawo gida tana da shekaru ashirin da daya. Sai ga Muhammad Mujtaba, Da na fari ga Zarah Datti, wanda ke karatu a Aviation School, Zaria. Ya tuburewa mahaifiyar sa Safeeyah yake son aure. Zai iya da dukkan lalurorin ta a yadda Ubangiji yake son ganin ta. Kwatakwata shekaru uku ya baiwa Safeeyah. Zarah ta rasa ta inda zata bullowa Muhammad domin da gaske yake yaki komawa makaranta yace sai ta je ta fadawa Aunty Halimah an tsayar da magana zai yarda ya koma. A karshe Zarah da maigidanta Barr. Zahraddeen suka samu Minister Hashim da kokon barar su, tare da alwashi iri-iri na zasu rike Safeeyah a gidan auren ta tamkar tana gaban sa. Hakika Hashim ya shiga tsaka mai wuya a wannan dan tsakanin, bashi da niyyar aurar da Safeeyah ga kowa, don guje mata halin maza sabida lalurar ta. Amma Zarah tafi karfin komai a wurin su in har suna da iko. Itace tsanin duk wani mataki da suka taka a yau. Don haka bai iya ya juyawa wannnan bukata baya ba, amma yace har sai Muhammad ya gama karatun sa. Shekaru biyu bayannan akayi auren Safeeyah da Mujtaba. Kuma a yadda Zarah ta fada din, a gidan su Safeeyah da mijin ta ke zaune don dai ta kula da ita, kuma Mujtaba ya nuna shi dan halal ne bai hada soyayyar Safeeyah da komai ba. A nakashen da take. Ba jimawa Safeeya ta samu gurbin karo karatun digiri na biyu a jami’ar Exeter. Ta zamo abin kwatance a kasar mu Nigeria, duk wasu jami’o’I da suke da Special Education a Nigeria nema suke Safeeyah ta zo ta koyar tare da su. Kwalayen ta abin kwatance abin alfaharin iyayen ta. Daga shekaru Talatin da Biyu, Safeeyah tana kan ‘Professorial Chair’. “Nakasa ba kasawa bace. Ba nakasashshe sai kasashshe”. Inji gidan radiyon BBC a lokacin da suka sako programme din su akan rayuwar Prof. Safeeyah Hashim Ismael Yakasai. Masha Allahu laquwwata illa billah. Nan na kawo karshen littafin AURE KO BOKO? Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah ya yafe mini, alkhairin da amfanin da ke ciki, Allah ya raba mana ladansa ni da ku bakidaya. Sumayyah Abdulkadir ke cewa; Mu hadu a sabon littafi na MASARAUTAR MU!...... Wanda tare suka fito da Aure ko Boko na 3. Yana nan shima a kasuwa. Nagode muku bisa dimbin kaunar ku gareni. Allah ya bar mu tare cikin Alherinsa…. Har zuwa ranar da muka daina numfashi. MASARAUTAR MU!!! BAN TABA RUBUTU SOLELY AKAN GIDAN SARAUTA BA, SAI A LITTAFIN MASARAUTAR MU! GARZAYA KI NEMI NAKI DON YA BANBANTA DA GABADAYAN LITTATAFAN TAKORI DA KIKA KARANTA. DON JIN LABARIN HARGITSIN RAYUWAR ‘SA’ADE’ A GIDAN SARAUTAR ASKIRA. SUMAYYAH ABDULKADIR 07030137870 WHTSP ONLY (MATA KAWAI) An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels