An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ÿþ"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Na Mai_Dambu Ramlat Abdulrahman Manga. EJ-1D' FE- DI' 'DDG E3( "*Wanda ya ce ilimi na da tsada, ya je ya taya jahilci ya ji nawa ne kudinsa?*" ŠAYA ATB TEACHING HOSPITAL. "Aunty Hindatu tayi tana kallona, yadda nayi shiru har likitan ya gama bayani bata ce kome, kafin ta" "juyawa gare shi tana faWin. ""Yanzu likita ya zamu da ita? Shin zata cigaba da shan magani ne ko zamu barta tana ganinta."" ""Mrs Jama'are abinda nake son ki fahimta, kanwarki bata yi magana ba, don yadda zamu taimaka mata dole sai tayi magana. Sannan zamu san yadda zamu taimaka mata. Ki sani akwai mutane ire-irenta dole sai mun ji meke damunta, shiru da rashin son magana ba zai saka mu san meke damunta ba."" A hankali ta sauke Ajiyar zuciya kafin ta ce mishi. ""Yanzu babu yadda za'a yi kenan?"" ""Ku zaku fara sakata magana, kafin ni na fahimci Matsalarta, a yadda take dai kana ganinta kasan tana" "bukatar taimako idan tak'i magana haka zamu hakura da ita tunda bata son magana.""" "Mikewa tayi tana faWin. ""Shi kenan Doctor na gode sosai, idan da wani abu zan kara tuntuban ka ko" "na kawo ta."" ""Ba kome Mrs Jama'are!"" ""Na gode sosai! Muje Lubnah!"" Shiru da nayi kafin ta kara cewa. ""Muje Lubnah!"" Firgita nayi tare da kallonta ina faWin. ""Tow tow!"" Na mike ina mai Waukar jakata. Kura min ido likitan yayi ya tashi tare da nufo ni, ganin yadda ya nufo ni yasa ni yin maza na koma bayan Aunty Hindatu, jikina yana rawa. Itama kallonshi take, d'aga hannunsa yayi nayi maza na n rufe idanuna tare da cewa. ""Kayi hakuri ba zan kara ba, kayi hakuri don Allah kada ka dake ni."" Sauke hannu yayi ya sake murmushi ya ce mata. ""Dawo ku zauna."" Zama tayi nima na zauna ina zare idanu. ""Mrs Jama'are! Kanwarki ce kuwa?"" Kallonshi tayi tana son magana amma ta kasa sai gyad'a mishi kai take. Kafin tayi motsi da bakinta ta ce mishi. ""Kanwata ce Doctor Hadi."" ""Tana da aure?"" ""Kamar yadda na gaya maka tana da aure."" Zai sake magana wayata tayi ™ara, jikina yana rawa na shiga buWe jakata. Bakina yana rawa jikina kamar an saka min wuta na Wauka. Kamar zai fasa min dodon kunnena ya daka min tsawa." """Kina ina? Da izinin wa kika fita?"" ""Kayi hakuri Aunty Hindatu ta ce na rakata asibiti gani nan dawowa" "don Allah ka yi hakuri! Kayi hakuri ka yi hakuri!"" Na fada kamar zan yi kuka, jikina sai rawa yake. ""Na baki" "minti goma kacal na ganki a gida!"" ""Na gode sosai, Allah ya huci zuciyarka."" Na fada da sauri ina mikewa na dauki jakata. ""Ina zaki?"" ""Zan koma gida ne Ya Hafiz ya dawo;"" na fada ina kokarin barin office din. ""Kamar ya?"" Ban tsaya saurarenta ba. Nayi waje ina kallon agogon hannuna ba shiri ta biyo ni tana min magana. ""Dama baki gaya mishi ba ne?"" Shiru nayi ban bata amsa ba, muka cigaba da tafiya. Riko hannuna tayi da ™arfi. ""Magana nake miki!"" ""Me kike so na gaya miki? Tun da kika ce mun na shirya zamu fita na gaya mishi, kawai baya son ya ga bana gidan ne."" Murmushi nayi na cigaba da tafiya har inda ta Ajiye motarta, muka isa ta bude da key Win motarta, na zaga na zauna itama ta shiga wayata ce ta kuma kara ji nayi kamar zuciyata zata buga. Dauka nayi na saka a kunne. ""Ke wacce irin jaka ce? Har yanzu kina asibitin ne ko ina?"" ""Kayi hakuri gani nan a hanya!"" Na fada ina kallon Aunty Hindatu da taki tadda da motar. ""Ni zaki renawa hankali ki ce kina zuwa."" Amsar wayar tayi da ™arfi ta saka a kunne daidai yana zagina. ""Jaka dabba wacce bata san ana rufa mata asiri ba, akan me Hindatu zata dauke ki? Itama yar kutumar uba, wallahi kin san halina sai na haWa ki da shi tsohon da ya nace sai kin zauna da ni zaki dawo ki same ni, Yar iska me kiba kamar Aladiya!"" ""Alhamdulillahi Ubangiji ya nuna min halinka, Hafiz rashin mutuncin har kan Mahaifinmu ya sauka kenan? Idan aka gaya min ba zan tab'a yarda ba, amma da kunnena na ji wannan ka sani Lubnah ba zata tab'a dawowa gare ka, Hafiz mai kake yi mata ta koma haka?"" Kashe wayar tayi ta cilla min wayar, ta tadda motar muka bar asibitin. Gidanta na ga zata" "nufa da ni na ce mata. ""Ni ki sauke ni na wuce gida!"" Da mamaki take kallonsu" """Gida zaki wuce?"" Na lumshe idanuna, na bude a kanta. Mamaki da abinda nayi take tana kallona." """Yanzu duk wannan zagin da ya miki?"" Wayarta ce tayi kara, shi yayi sanadin da tayi shiru ta dauka. ""Assalamualaikum!""" """Ki rike sallamarki, wallahi ki wuce mishi da Matanshi, ban da son kai da son zuciya irin naku,mutumin" "nan ya zauna da yar uwarki bata haihuwa, bata kome sai kishi da yunkurin hallaka mishi mata da Yara zaki dauke ta. Hindatu idan kina son ganin Daidai ki mai da mishi matarsa, idan ma kashe ta zai yi ya kashe ta ai ni na bashi Lubabatu, ko kece? Ka ji min mara kunya? Duk abinda yake mata baku gani kun dauki maganar mutane kun daurawa ranku, kowa ba haka ya zauna a dakinshi ba."" Ranta yayi bala'in b'aci, har Baba ya kashe wayar tana jin wani irin ciwo, haka ta nufi hanyar gida dubu, ni dai na san yau na lahira sai yafi ni jin dadi, wani irin tashin hankali nake ji, ni daya na kasa zama da duwawu na, tsabar tsoro da tashin hankalin da zan gani, a kofar gida na same shi. Ba kunya ko tsoron Allah, tana parking ya zo ya bude min mota, yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi. ""Lulu tawa ce, tana cikin rayuwata sai naso tayi dariya ko kuka, sai na so ta ganku daga ita har dattijo da Baban Bauchi, suna tare da ni. Kafin ki iso ga Lulu sai kin fara isa ga Baban Bauchi da Baba Malam, sannan ni mai gayya mai aiki. Ke tinkiya muje, an rufe mata asiri duk da bata haihuwa haka bai saka kun gode min ba, oya muje jakata akwai aiki da" "hukunci me girma!""" """Kai dakiki jahili. Dabba a cikin riga ka sani muna nan tafe bisa kanka ko da mutum kake tsafi muna tare" "da Allah, na jima ina addu'a Allah ya nuna min wannan lokacin kuma na gani da idanuna, ka sani kayi" "kuskure, ka fara shiri domin farautar da zamu yi akanka sai ka gudu zuwa kauyen gyatumarka, ai baka yada a kasa ba, ka tsotsa a nono.""" "Daga haka ta koma motar, cike da bakin ciki da damuwa." Lubnah "A lokacin da muka shiga cikin gidan, kallona yayi yana girgiza kai. ""Me kika gayawa wancan munafukar?""" "Ban iya bashi amsa ba, domin abu daya ne zuwa biyu imma ya dake ni ko ya min wulakancin da ba zan manta ba. Kaina a kasa na cigaba da tafiya, a hankali muka bude kofar shiga cikin gidan, kafin kofar ta bude ya wani haWa kaina da kofar ya wanda yayi dai-dai da buWewar kofar. ""Sannu faduwa kika yi?"" Ya fada min, yana kokarin mikar da ni, ya damko hijab dina muka wuce bangarena. ""Tambayarki nake? Me kika gaya mata!"" Ya fada yana ture ni can na fadi kasa. Har lokacin ban yi magana ba. Wayarshi ce tayi ™ara ya Wauka yana me zama a kan kujerar parlourn. ""Na'am Baban Bauchi, wallahi na gaji ina ga zan rabu da ita kawai idan yaso Yaya Hindatu ta nima mata wanda ya fi ni, haba Baba me nayi da zafi haka? Me yasa suka tsane ni? Me yasa basu kaunata? Idan har akan Luluna ne na hakura, yau shekaru hudu kenan tun auro Karima suka juya min hankalin Luluna, waye bai san yadda nake son Luluna ba, Baba kasan me na shirya mata? Umara na je na biya mana ni da ita zamu tafi watan Mauludi amma tunda haka bai musu ba,.na hakura dama tuntuni Ummana take cewa na hakura amma saboda zumunta da kuma karfin soyayyar da nake mata!"" Ba sai ya shiga share kwalla ba, alamar zai yi kuka kamar yadda ya saba, yadda yake jan hanci da shirin kuka yasa na tashi a hankali na wuce dakina, na rufe kofar na zube a bakin gadona. Ban san lokacin da ya gama waya ba, sai dai yadda yake buga kofar dakin da ihun kiran sunana, yasa da gabana ya fadi sai da naji duhu ya lullube min ganina. ""Lubnah!"" Ya kwala min kira, tsoro da fargaba suka kara cika min rai kamar wata marainiya na amsa mishi a sanyayye na tako bakin kofar na bude ina jingina da kofar, wani irin bangaje kofar yayi da kafad'arshi, na zube a kasa kamar wata guna." "Bina yayi da karfi zai mare ni daga waje aka ce mishi. "" Da dai kada ka wahalar da kanka, dukarta dai ba zai cigaba da yadda muke so ba, ka sake ta mana darling."" A fusace ya juyo yana kallonta. ""Da kin kyale ni na taka yarinyar nan, ta saka sai kukan karya nake a gaban wancan tsohon nata, kina tsammanin akwai mai cire ki daga wannan ukubar nawa ne? Kaf duniya babu yarinyar baki ga kome ba, sai kin ji dama mutuwa kika yi da wannan rayuwar!"" Ya saka kafa ya shure ni, sannan ya bar dakin, shigowa Matarshi tayi tana murmushi ta ce min. ""Ki tattara naki ya naki, ki bar gidan nan kafin dare ya miki" "domin Hafiz nawa ne ni Waya, ina dakatar da shi ne don ni ce uwar Yaransa."" Daga haka ta fita daga dakin, har aka kira sallah azhar ina wurin wani irin jiri da ciwon kai nake ji, a hankali na rarrafa zuwa ban daki na kama ruwa nayi alola sannan na fito, abin sallah na shimfida sannan na tadda sallah, ina cikin sallah Yaransu suka shigo min daki. Ina idarwa Babbar yarshi Yusrah ta ce min. ""Lulu yunwa nake ji, ki bani abinci!"" Karamin ya ce min.. ""Lulu Golden mo zan sha. "" A tsawon zamana da Ya Hafiz Allah bai ba ni haihuwa ba, ko nace na biyewa son zuciya irina shi na kashe kaina da kaina. Shafa addu'a nayi na mike tare da cewa. "" Tow ku zo muje parlourn sai ku na baku. "" Tasowa suka yi suka biyo ni a baya, ina son Yaran ko don Yaran Ya Hafiz ne, mutumin da nayiwa wata irin makauniyar so, har yau bana ganin laifinsa duk abinda zai min tow na san idan ya nutsu da kanshi zai gaya min rashin kyautatawa da ya min, haka yasa na shiga kitchen din parlourna, na shiga hada musu musu abinda zasu ci, a parlour kuwa Yaran suka shiga fada akan remote din tv, daga cikin kitchen na ce musu. "" Ya isa ku bari ko na zo na kwace!"" Shiru suka yi na hada musu na kawo na ajiye musu kowa ya dauki nashi, nima na koma kitchen na hada nawa na fito parlourn na zauna a hankali, ina sha ina kallonsu. Wayata da take daki tayi ™ara da sauri na ajiye" "kofin na nufi dakin, bude jakar nayi na dauka a hankali, na saka a kunnena. ""Na'am Aunty Hindatu!""" "Murmushi nayi na ce mata. ""Mun shirya ai ba kome fa, kawai dai baki fahimci abin ba ne"" na fada ina" "dafe kaina da yake min ciwo. ""Amma nasan baki da lafiya!"" Ihun Yaran da naji a parlourn yasa ni mata sallama babu shiri na fito, wanda yayi shigowar Iyayensu, Yusrah da Yasir suke ihu lokacin da Yasir ya dauki kofin tea na, ya watsawa Yusrah wani abu ne ya dake ni cike da tsoro mara iyaka. Na zuba musu idanu, Allah yaso ruwan ba zafi na tashin hankali, amma yadda yarinyar ta kwala ihu zaka rantse ruwa ta fasashe ne jikinta. ""Me kika aikata Lubnah?"" Kasa magana nayi Uwar ta ce. ""Wai ke me yasa kike haka ne?" "Yaran nan suna sonki amma shi ne kike azabtar da min da Yara.""" """Wallahi!"" Tass ya wanke min fuska da mari, ""ku yi hakuri, ku yi hakuri, ku yi hakuri ba zan kara ba," "don Allah ku yi hakuri don Allah ku yi hakuri!"" Na shiga fada ina tattara kofin Yaran da nawa, ina basu hakuri na nufi Yusrah da ta daina kukan sai ma wasanta da take, zan riko hannunta. Ya Hafiz ya ture ni, ma fadi can. ""Kayi hakuri ba zan kara ba, don Allah ka yi hakuri wallahi ba da gayya ba ne."" ""Ki tafi da Yaran gani nan zuwa!"" Jan hannun Yaran tayi suka fita, ya zuba min idanu yana sauke ajiyar zuciya ya ce min. ""Kin kona min Yara ya kike so nayi?"" ""Kayi hakuri wallahi ba da gayya ba ce!"" ""Ok kina son ki gaya min ba haushina kika ji ba kenan kika kona min Yarana ba?"" ""Wallahi na rantse da Allah!"" Kifa min mari yayi a kan fuskana sai da na daina gani na hucin gadi, kafin na bude idanuna ina kallon kasa. "" Kayi hakuri" "Ya Hafiz ka fadi duk abinda kike so zan yi, don Allah kada ka dake ni.""" """ Na ji ba zan dake ki ba, amma idan na saka ki aiki zaki yi?"" Da sauri na d'ago kai ina gyada mishi kai. """ "So nake ki kira Baban Bauchi ki gaya mishi, kome a kan idanuna dangane da fitar da Hindatu tayi da ke saboda ina zaton kashe min aure zata yi yasa ta fita dake!""" "D'ago kai nayi ina kallonshi, "" ba zaki fada ba kenan? Na kira Baban Bauchi na gaya mishi yadda kika" "kona min Yarana? "" Girgiza kai nayi ina faWin.."" A'a bata ce min na kashe Aurena ba! "" "" Ok kenan ba zaki fada min gaskiya ba kenan? Kin san ina sonki ina kaunarki amma shi kenan! "" Tunda ya fara faWin haka tuni ya kashe min jiki, sai na nemi duk wani abinda ya min na rasa, kaina a sunkuye na ce mishi. ""Asibiti ta kai ni, saboda ciwon kan nan da nake fama da shi, bayan nan wallahi babu abinda ya faru."" Ajiyar zuciya ya sauke a bayyane, tsaki yayi yana faWin. ""Dama shine abinda ya faru baki gaya min ba? Kuma" "idan asibiti ne ai ni nafi dacewa na kai ki ko? "" Daga haka ya fita zuwa dakinsa, ni kuma na gyara parlourn." "Haka na wuni raina babu dad'i, kitchen na nufa na daura tuwon dare, da miyar yakuwa. Ina cikin aikin" "Yaran suka shigo, sai da gabana ya fadi, ihu da wasan banza suke nayi musu fada amma sun ki bari, na musu tsawa, sai suka kama min dariya, karshe haka na kyale su nayi na cigaba da aikina, amma idanuna yana kansu. Ana kiran Magariba na gama abincin, tsoron kada wani abu ya kara faruwa na gama na rufe" kitchen din. """Lulu zan ci abincinki!"" ""A'a da zafi!"" Na fada ina kallon yadda suka zuba min idanu, da gudu suka fita" "zuwa bangaren Uwarsu, sai gasu tare da ita. "" Lulu ba zaki zuba musu abinci sai ki ce musu babu, idan baki basu ba, uban waye zai zai basu? Ni bana son bakin ciki domin ni ba girkin nayi ba! """ """ Tow dama da zafi ne, kada ka basu ne su kona kansu! "" Na fada mata a sanyayye, cikin jin haushi ta ce" "min. "" Dalla ki min shiru kina wani magana kamar wata Mutuniyar kirki, idan da kina da zuciya da tuni kin bar gidan nan, amma kin wani zauna kina tsammanin zaki samu hafiz ne kamar da!? "" Wuce ta nayi na dauko mata abincin na bata. "" Don Allah dubi mace sai kace saniya! "" Ta fada tana kallona, fita tayi daga parlourn Yaran suka bita, ni yanzu magana baya min ciwo ko tashin hankali. Alola nayi na gabatar da sallah magariba, ina kan abin sallah ina addu'a na gabatar da sallah isha, tare da shafa'i da wutir, ina idarwa Ya Hafiz yana shigowa, abincin na fita na hada mishi ya zauna ya fara ci, yana ciro wasu kwalayen magani, ya zuba min a kan kujera. ""Gasu nan kina sha zaki ji sauki!"" Murmushi nayi na ce mishi. ""Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, Na gode sosai Ya Hafiz!"" Dama nasan duk abinda yake yi, zai dawo mu shirya, uwar dakina na wuce na ajiye maganin na shiga wanka na fito na shirya cikin doguwar rigar barci, sannan na fita na dauko ruwan sha na, koma dakin na zauna har ya gama cin abincin, sai da na sha magani sannan na dawo na kwashe kayan da yaci abinci na kai kitchen na wanke na wanke wa sannan na dawo parlourn na cigaba da kallon ina cin abincin na, dakyar na gama na wanke hannuna, sannan na dawo parlourn akan na jira shi, ina zama a kujeran parlourn barci yayi gaba da ni, wani irin barci me karfi da yasa ban iya farkawa ko sallah daren da na saba yi, shiga sallah asuba ya farka da ni, na zubawa parlourn idanu. Dama a parlourn na kwana? Sai naji na muzanta, me yasa Ya Hafiz bai shigo ba? Bayan yasan girkina ne? Ko da yake yaushe rabon ya kwana a bangarena? Idan ba son kai irin nawa ba. Daki na wuce na fada ban daki nayi alola nazo na sauya kaya na gabatar da sallah asuba, ina zaune a wurin na ji motsin bude kofar bangarena, ban yi mamaki ba nasan sai shi. Ina azkar ya shigo da sallama, ya zauna a bakin gadon. ""Malama ki sallame ki zo nan!"" Tunda ya fadi haka, nasan ba wani abu ya zo nima ba, sai ya" gaya min magana ta hanyar hakkinsa. "Haka na tashi na cire kayana na nufe shi, babu wani abu ko sako a'a kawai bude min cinya yayi ya" "shiga tsakanin ya shiga biyan bu™atarsa, yana shiga ko minti goma bai yi mai kyau ba, na ga ya fara kakkafe min tare da matse ni, yana wani danne ni. Can na ji ya fito bakiWaya yana nishi, kafin ya dauki wandonsa ya saka ya bar dakin, a hankali na mike tare da nufar ban daki, flast dina na wanka na juye ruwan zafin na yi tsarki na yi wanka, sannan na fito na shirya zuwa kitchen, na daura abin karyawa da sauri sauri. Na gama wainar fulawa da ruwan tea, na fita na dauko kular makarantar Yusrah, na zuba mata sannan na nufi bangaren Karimah na buga kofar, bude kofar tayi tana hamma daga ita sai kayan barci. ""Dama abincin makarantar Yusrah na kawo!"" ""Tow ko zaki shigo ki shirya ta ne?"" ""A'a ina da wani aiki da zanyi, zai fi kyau ki shiryata!"" Na mika mata abin makarantar na dawo bangarena, ina shirin zama na karya sai ga Ya Hafiz da Yarinyar. ""Ko Karimah bata haifi Yara nan ba, ai na kine, gashi maza ki shiryata."" Haka na mike na amshe na wuce dakina da ita na mata wanka tana ta min kukan banza, har da ihu, ina shiryata Uwarta ta shigo tana faWin. ""Wai me kika mata ne take ta ihu?"" Ni dai ban ce kome ba, tana ganin abin karyawan da na ajiye ta zauna ta fara ci, har na gama ita kuwa ta cinye. Sannan ta kamo hannun Yarta suka fita. ""Yawwa wannan abin ya yaji dayawa, sannan me yasa kika sake garlic karshe yau sai na sha wani abu domin Yayanki baya son wani abu me tashi!"" Ta fada tana murmushi, ni dai ban ce mata kome ba, kitchen na nufa na kara dibo abincin na fito na zauna na fara ci, ina kallon tv, ban gama ba sai ga Ya Hafiz da Yasir, ""shima ki mishi wanka!"" ""Tow"" nace mishi na cigaba karyawa. "" Sai yaushe" "zaki tashi zan kwana ina jiranki ne? "" "" Kayi hakuri! "" Na mike da sauri ina kwashe sauran wainar fulawa." """ Jaka ban san me ATBU suka gani suka baki first class honors ba, dube fa baki san kome ba sai ci, dalla ki" "mishi wanka ki bashi abin karyawa. "" "" Kayi hakuri! "" Na fada ina amsar Yaron bayan na dawo daga kitchen, na wuce na mishi wanka na shirya shi nazo ina bashi tea, ya fara ihu yaran kamar ana gaya" "musu , wani abu da zasu yi a lokacin Uwar ta shigo ta ci kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar kyau. "" Lulu me kike mishi ne?"" Sauke shi nayi ya wuce wurin Uwar, tana kallon kayan parlourna, lokacin haihuwar wannan Yaron Abba ya sauya min. "" Kayan parlournki kamar basu tsufa! "" Ni ban ce mata kome ba, domin tun fil azal haka Allah ya halicce ni, bana son yawan magana, a shekarun baya ina da yawan tsokana da zolaya, amma baya bayan nan bakiWaya kamar an sauya min rayuwa,. Haka nake bana son Magana ko damuwa. ""Yaushe zaki sauya wasu?"" Na gaji da tambayar renin wayo na ce mata. ""Sai kin" "sake haihuwa!"" Rike baki tayi tana faWin. ""Wai sai dai ko ke?"" Yake na mata ban ce kome ba." "Haka ta fita, ina zaune a wurin na gaji gyara parlourn na fara tare da shirya kome a inda yake, ina aiki" "aka kira wayata, dauka nayi Ya Ado ne, mutanen Lagos dauka nayi ina murmushi na ce mishi.. ""Barista ya aiki?"" ""Auta"" ""na'am!"" Na amsa mishi a hankali, ""Hindatu ta kira ni, akan wani batu ya abin yake?"" Tsintar kaina nayi da cewa.. ""kawai zato take amma wallahi ba kome!"" ""Auta gaya min idan baki gaya" "min ba wa zaki gayawa? Kada ki daka ta su Abba kin ji!""" """Ba kome wallahi!"" Na fada ina lashe bakina. ""Auta gaya min gaskiya meke damunki?"" ""Nima haihuwa" "nake son nayi na ga Yarana koda zasu na min kukan banza ne?"" Murmushi yayi ya ce min. ""Shi kenan Allah zai kawo kin ji, sannan zan tafi wani course Canada idan na samu dama zan turo ki tafi kin ji sai a" "duba lafiyarki.""" """Yaushe zaka dawo?""" """Shekara daya da rabi ne, kin ji kiyi hakuri ba zan jima ba! "" "" Allah ya bada sa'a ya bada abinda aka fita" "nima!""" """ Amin Ya Allah! Kin ki aikin gwamnati ko?"" Murmushi nayi kawai, ya ce min.."" Gashi nan zan turo miki" "jari sai ki fara wani abu ko za a dace! """ """ Allah ya saka da alkhairi! "" Na mishi godiya, ya kashe wayar, can nayi shiru ™aran shigowar sako na ga" "ina dubawa na ga Naira dubu dari biyar ya turo min. Kiranshi nayi ya katse ya kira ni. ""Kada ki damu ki" "fara wani abu, Lulu kada ki gayawa Mijinki, ki sami Hindatu ko Inna ki gaya musu, zasu fi baki shawarar da ya dace kin ji.""" """Na gode sosai! Allah ya kara lafiya da nisan kwana, na gode!""" "Amin yayi ta amsawa, bayan na gama na kira Aunty Hindatu, na gaya mata a take ta saka na tura mata" "dubu dari hudu ta ce min, zata gayawa Mama da Abba, ta bar min dubu dari sannan ta gaya min kada na tab'a fadar dubu dari biyar ya turo min, kawai na ce dari ne, kamar yadda ta tsara min haka nayi shiru ta kira Abba ya gaya mishi, ina cikin girki ba sai ga Ya Hafiz ba kamar an wurgo shi, a razane na kalle shi. ""Ina kudin da Adamu ya tura miki?"" Dama na goge alert din farko, ya amshi wayar yana ta dubawa ya ga" "dubu dari ta opay dina, kallona yayi irin kallon kurilla nan. ""Yanzu ke mi zaki yi da kuWi?"" ""Sana'a?"" Na" "fada ina kallon kasa, tura dubu saba'in yahi ya bar min dubu talatin,"" zan ajiye miki, kada ki gayawa" "Hindatu dai na karba!, yawwa ki bawa Karimcy dubu goma, nima ki bani ladar ajiya!......" 08130269641 *Mai_Dambu* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu BIYU "Nasan haka zai faru, sai na tura mishi tare da ita matar nashi. Tow me zance? Na hanata ya min rashin" "mutunci. Yana ganin na tura mata ya ce min. ""Ke matar arziki ce, duk wanda ya zauna da ke sai ya ci daga arzikinki, shi yasa na tsani wani ya shiga min rayuwarki domin Allah ya gani ina sonki ina son zama da ke!"" Gyada kai nayi ina aikin hada abincin rana, yana fita na cigaba da abinda nake a cikin dubu dari biyar ba don Aunty Hindatu ta amsa ba, tabbas da na tashi babu kosisi. A duk lokacin da na samu kuWi haka yake min, ni kuwa kamar wacce yake wankewa bana iya mishi musu, a yanzu ma nasan sai ya" "bididigin ya ji nawa aka turo min, Ya Hafiz dai." "Ina cikin wanke busashen kifi sai ga Matarshi. ""Ashe kyauta muka samu Hajiyata, to mun gode mu" "ga dubu goma amma nasan yafi haka ko darling ne ya karba? Ina ta son na gaya miki."" ""Nima dubu goma suka rage min!"" Na fada daga haka nayi shiru, jin yadda na fada babu wanda a cikin maganata yasa tayi shiru, sannan ta kuma ja bakinta bata kara magana ba, ta bar parlourn ban san me yasa suka mai dani haka ba! Koda yake ni ce na mai da kaina haka. Zan iya cewa a duniya duk yadda Ya Hafiz xai ce koda wuta ne zan iya bin sa ciki domin ina sonshi. Kuma zan iya kome domin shi, don na taso da wata mahaukaciyar kaunarshi ne. Shi yasa duk abinda zai min bana tab'a fushi ko nayi ma Baba zai saka dole" na sauko. "Ina gama hada abincin, Almajirin da yake min aiki ya buga kofar gidan, na je na bude ina faWin." """Kabiru sai yanzu zaka zo? Kasan kana zuwa sayo min kayan lambu?"" ""Aunty kiyi hakuri, na zo Alhaji ya ce ba kya nan."" Shiru nayi kafin na ce mishi. ""Ok shigo ba ka kudin alyahun da zaka sayo min!"" ""Tow Aunty!"" Ban san me yasa Ya Hafiz yake min haka sai dai duk lokacin da yayi min wani abu, na fushi ina jin" haka amma bana iya maida abin. "Kamar yadda aka saba na tura Kabiru ya tafi min aika, don bana son Yaran su dawo ban gama ba, ya ji" "haushina. Shi kuma Kabiru ya fara shara da yan aikace-aikace da yake min. Bayan mun gama na saka mishi abincinsa sannan yayi min sallama ya fita wurin karfe daya saura, ina ganin fitarshi na rufe kofar party dina nayi wanka, na shirya cikin doguwar riga. Sannan na dan yi kwalliya sama-sama. Domin nasan ko ya gani dariya zai ta min, haka na gama shiryawa na gabatar da sallah azhar, ina addu'a ya iso na je na bude mishi, kallona yayi kafin ya wuce na ce mishi. ""Barka da zuwa, ya kasuwa?"" Bai ce amsa min ba, ya wuce abinsa ya nufi daya daga cikin sofa na parlourn ya zauna yana hararan parlourn. ""Na kawo maka abinci?"" ""Kin ga na miki kama da wanda yunwa ya koro?"" Shiru nayi ya kara daka min tsawa. ""Nace kin ga yunwa a jikina?"" ""A'a kayi hakuri!"" ""Hakurin Uban me kike ba ni ne? Akan me kike bani hakuri ne?" "Munafuka annamimiya?"" Shiru nayi na koma gefe ban kara motsi ba, domin zuciyata wata irin tsinkewa take. ""Nawa Adamu ya baki?"" Bakina yana rawa nace mishi. ""Dubu dari.."" ""me kika ce?"" ""Dubu dari biyar!"" Na fada muryana yana rawa, murmushi yayi ya mika min wayata da take kujeran parlourn ya ce min. ""Maza ki kira Hindatu ta dawo da kudin nan ko na miki dan bura uban duka, kuma na sake ki."" Jikina yana rawa na amsa, ya ce min. ""Wallahi ko nutsu ki yi waya da ita. Kuma ki nuna kece kike bukatar kudin ba ni ba!"" Gyada kai nayi nayi na kira ta, a hankali ta dauki wayar tana faWin. ""Auta lafiya kuwa?""" "Murmushin yake nayi idanuna yana cika da kwalla na ce mata. ""Aunty ki dawo min da kudin nan zan.""" """Hafiz ne ko? Ki gaya mishi kudi naci ko uban waye zai kira ya kira amma ya sani ya daina ci da guminki," "sai an jima little girl!""" """ Ni dai ko turo min idan ba so kike gobe ki samu gawata a gidan ba Ni dai ki tura mishi don Allah! Idan" "har da gaske kina kaunata! "" Na fada kamar zan yi kuka, shiru tayi kafin ta kashe wayar, zubawa wayar idanu nayi kamar ina son hango ta cikin wayar. "" Lallai Hindatu tana nima na da magana. "" Ya fada yana kwafa tare da hararan inda nake, wayarshi hannunsa ya ciro. Sannan ya kira Malam Baba. "" Don Allah kada ka gayawa kowa zata dawo da kuWin."" Watsa min harara yayi kafin ya cigaba da kiran wayar har aka dauka. ""Dattijo! "" Daga can bangaren aka amsa mishi da."" Na'am!"" "" Dattijo na gaji da wannan auren, bakiWaya yan uwan Lubnah sun saka min idanu! "" Kamar zan fashe da kuka haka nake rokonshi." "Murmushi yayi yana faWin. "" Dattijo, kamar ni har sai Adamu ya zartas da hukunci a cikin gidana ban isa na sani ba? Gaskiya na gaji zan sako musu yar uwarsu. Tunda basu fahimci irin abinda nake yi ba, ban san me yake faWa mishi ba, amma naga yadda yake gyada kai, can ya koma bashi labarin kome kafin ya daura da cewa. ""Dattijo ni me zan yi da tsiyarta dama wai na adana mata ne tunda me take nima ta rasa, amma tunda abin har ya kai haka, shi kenan ai ba yau Adamu da Hindatu suke shiga min rayuwar gidana da iyalina ba, dattijo kasan yadda nake zaune da ita, kasan halin da nake ciki da ita, ban da ni waye zai zauna da ita a haka mace babu ciki ba sai dai ci baya."" Ji nayi kamar zan mutu, yadda yake gaya min maganar kamar wanda na aikata mishi wani laifi, yana gama wayar ya mike yana faWin.. ""Na baki nan da kwana uku ki karbo kudin nan ko kuma wallahi sai kin bar gidan nan na gaya miki!"" Daga haka ya fita, na" rasa yadda zan yi da rayuwata. "Yana fita na dafe kaina, na rasa meke min dad'i. Wayata ce tayi ™ara na duba Aunty Inna ce, ina" "dauka na ji kwalla ya cika min idanu. ""Auta me Hindatu take gaya min?"" Kuka ne ya kwace min na kasa bata labarin abinda ya faru. ""Kina nufin a dauki kudin a bashi?"" Kamar tana gabana na gyad'a mata kai" "ina faWin ""eh!"" ""Bakya tunanin da matsala kudinki ne fa, wai ma tsaya waye ya gaya mishi kin samu" "kudin?"" ""Ban sani ba wallahi iya na wurina ya amsa saura dubu bakwai!"" ""A cikin dubu darin da yake hannunki?"" Shashekar kuka na ja, ta ce min. ""Anya Hafiz ba asiri ya miki ba? Ai shi kenan zan mata" "magana ta turo miki kuWinki sai ki bashi."" A yadda tayi magana kamar ranta ne ya b'aci, kashe wayar tayi." "Haka na zauna a parlourn har zuwa wani lokaci kafin na mike na wuce dakina, na wanke fuskana" "sannan na fito, na samu Yasir ya dauki remote dina yana dokawa da kasa, ""Yasir bari kada ka bata min!"" Na amsa da gudu ya fita yana ihu, ban kula ba na shiga kitchen na zubo musu abinci, ina dawowa parlourn Ya Hafiz suna shigowa da shi da Karimcy. ""Uban me ta mishi Yusrah?"" ""Rankwashinsa tayi!"" Ta fada tana me kallona, takowa gabana Uwarsu tayi ta amshi abincin ta ajiye sannan ta d'aga hannu zata mare ni ya ce mata. "" Kyale ta! Bashi taci ko ta biya ko kuma ta ji a jikinta."" Daga haka suka juya suka bar" parlourn har da Yaran. "Zama na cigaba da yi har lokacin sallah yayi na tashi nayi sallah, na zauna a cikin uwar dakina ban" "fito ba, abincin da nayi shi zamu ci har dare tunda gidan ba lafiya gara na dumama da dare, ina zaune can wurin karfe biyar na yamma Husnah ta kira ni, dauka nayi muka gaisa ta ce min. "" Auta me ya hadi ki da Ya Hafiz kuma?"" "" Babu kome! "" Shiru tayi kafin ta ce min. "" Hala baki leka Whatsp ba ko?"" ""Eh bani da data ne amma zan leka yanzu!"" ""Gaskiya abin ba dad'i, sannan idan kin san akwai wani abu don Allah ki warware domin dai ba dad'i ayi ta rigima akanki kullum !"" ""Na gode in sha Allah zan yi yadda kike ce!"" Na kashe wayar, ta banki na sayi kati na saka account dina sannan na sayi data, na bude Whatsp dina, a hankali na ga sako yana ta shigowa kasancewar na jima ban bude ba, sako ne dayawa, kamar wanda aka wurgo shi ya fado min daki, kallonshi nake shima ni yake kallo, tsoro da tashin hankali suka ziyarci zuciyata da fuskana, hadiye yawun tsoro nayi, zuwa yayi ya zauna a hankali ya cigaba da kallona. Amsar wayata yayi yana faWin. ""Luluna, ki yi hakuri maganar kudin nan a barshi Hindatu ta rike kuWin kawai ai zaifi kyau ta rike miki kuWinki ko? Yanzu haka Baban Jama'are zai kira, domin Hindatu ta kira shi ta gaya mishi. Don Allah baby girl kada ki kunya ta ni, kada ki kara d'ago tashin hankali akan wanda aka yi kin ji, ki gaya mishi cewa ai mun sassanta kanmu. "" Gyada kai nayi ina kallonshi cike da tsoro, wayar ce tayi ™ara ya saka a kunne yana faWin. "" Gata nan! "" Ya mika min wayar, kamar wacce aka danne min ciwon da" "nake ji, na amsa wayar muka gaisa da Baban Jama'are." """ Lafiya lau Babana!"" Na fada ina kame-kamen me zance, a na shi bangaren ya ce min.."" Ummina gaya" "min me ke faruwa ne? "" Murmushi nayi na ce mishi. "" Babana babu kome ai mun daidaita kanmu."" Murmushi yayi yana faWin. "" Ummina nasan waye Hafiz na san me yake so na san abinda baya so, na san halinsa ciki da waje. Gaya min me yake faruwa? "" "" Babu kome babana, wallahi mun daidaita kanmu;""" """ Idan dai da wani abu ki gaya min kin ji ko? Allah ya muku albarka, Hindatu ta ce Adamu ya baki kuWi," "amma Hafiz ya amshe sannan wanda yake hannunta ma yana harinsu. "" Kallonshi nayi naga yadda ya wani razana, irin yadda nake tsoronshi haka yake tsoron na bude bakina,"" A'a Babana, ba magana makamancin haka, sannan ai kudin ni ce na ce ta turo min na bashi ya rike min!"" Na fada ina kallon" "yadda yake gumi. "" A'a Hindatu ta rike miki kudinki dai, ba batun ya rike miki ta ce ta baki dari kudin" "yana nan ko yayi amsa! "" Kafin nayi magana ya nuna min alamar na fada cewa kudin yana wurina bai" "amsa ba, haka na faWa ajiyar zuciya ya sauke har Baban Jama'are ya gama min tambayoyi sannan ya katse kiran ko magana bai yi da shi ba, wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana na kalle shi, fauce wayar yayi yana tsaki. ""Babu babbar munafuka irin Hindatu na tsane ta!"" Daga haka ya fita a dakin tana mita, nasan Ya Hafiz duk abinda ya saka a gaban sai ya cimma nasara akansa. Duba what'sp nayi bayan fitarsa, ashe rigima ake tsakaninsa da Aunty Hindatu, yadda yake mararaicewa yana bata hakuri tare da nuna shi na fi karfin kudin da ake magana a kai awurinsa, don Allah kada ra kara hada shi da mahaifinsa, idan don yana kula da dukiyar Baban Bauchi yasa take haka zai bar shagon yasan ba suna yin haka don ni ba ne suna yi ne domin yana rike da duk wani dukiyar baban Bauchi ne, amma in sha Allah zai janye hannunsa, Lubna dai Matarsa ce kaf duniya babu wanda ya isa ya raba mu, sannan shi dai ya so Lubnah kuma yana zaune da Lubnah yadda yake girmama lubnah kaf duniya babu wnada yake haka, sannan idan har tana ganin kaunar da yake yiwa lubnah ba don Allah bane, tayi duk abinda za tayi. Wato idan ka ga yadda yake magana cikin nutsuwa da kaskantar da kai zaka rantse da Allah, ya Hafiz na musamman ne, koda yake shi din ai dama can na musamman ne. Sai ya bawa Kowa tausayi har Yaya Umar da yake Maiduguri ya cewa Aunty Hindatu."" Don Allah ki bar maganar nan haka!"" Haka ya Amaar ya ce mata, a kashe zancen duk kannenta maza da mata sai suka shiga kare Ya Hafiz, murmushi takaici tayi ta zabga Left a group din," dama Aunty Hindatu akwai zuciya a kusa. "Daga wannan ranar ban kara samun matsala da shi ba, ranar bayan kwana biyu na kira Aunty Hindatu" "na gaishe ta dakyar take amsa min. ""Aunty Hindu!"" ""Kada ki kira ni haka, ki je can ki cigaba da abinda kike yi!""" """Ki yi hakuri ba zan kara ba!"" Na fada kamar xan yi kuka. ""Ya isa haka, meke damunki?"" ""Ba kome" "kawai na kira na gaishe ki ne!"" ""Allah sarki auta ta fara hankali. Ko kina son kudi ne?"" ""Akwai sauran dubu tara ba sai kin turo min ba!"" ""A cikin dubu darin ne ya rage saura tara?"" Shiru nayi ina tuna katobarar da nayi. ""Nayi amfani da shi ne!"" ""Allah ya kyauta, Baban Bauchi ma ya kusan rabon Zakka ai ina ga yana bamu bana umara zamu tafi har dake ko?"" ""Allah ya amince!"" Na fada a hankali domin nasan matukar Ya Hafiz yasan da batun kuma Matarshi ba zata ba, ba zai tab'a barina na leka ko da kofar gida" ne. """Ya kika yi shiru?""" """Ba kome kawai ina nazarin yadda zan ga dakin Ka'aba!""" "Murmushi tayi tana faWin. ""Kin yi waya da Mama ne?"" ""A'a ban yi ba!"" ""Bata jin dadi fa, tana fama da" "mura."" ""Wayyo Allah Ubangiji ya bata lafiya! Me xan mata Aunty Hindu!"" ""Ki mata farfesu da kayan kamshi!"" Murmushi nayi na ce mata. ""Aunty Hindu ya nusaiba?!"" Dariya tayi tana faWin. ""Tana lafiya ai ta kusan zuwa gida haihuwa!""" """Allah ya kawo ta!"" Nusaiba yar aunty Hindu ce da aka yi aurenta, kuma yar dakina ce. Daga haka muka" "yi sallama, mikewa nayi na nufi kitchen na bude frij na duba nama, zabuwa ce guda biyu ta rage min, ajiyar zuciya na sauke idan na je gidan zan so ganawa da Baban Bauchi. Ko don a tura Mubarak gidan gona kawo min kaji. Murmushi nayi, fitowa nayi na zauna a parlourn. Shigowa Yusrah tayi tana faWin.." """Lulu zanci abinci!"" Tashi nayi na nufi kitchen na zuba mata alale da nayi, sannan na fito na ajiye mata, ta" fara ci ina kallon tv. "Ni dai shirun Ya Hafiz nasan bata lafiya ba, idan kuwa ta lafiya ce tow zaka samu akwai shirin da yake" "yi, don haka ina zaune ya shigo da sallama. Kallonshi nayi ina amsa mishi. ""Barka da dawowa, ya kasuwar?"" ""Alhamdulillahi!"" Ya zauna a dame, dakinshi na wuce na ajiye mishi jakarshi, sannan na dawo na hada mishi abinci, koda na kawo na ajiye mishi, kallona yayi ya ce min. ""Luluna ina cikin tashin hankali!"" ""Lafiya?"" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce min.. ""bari na duba Karima na zo!"" Haka ya tashi tare da Yusrah sun jima kafin suka dawo tare da Matarshi, a lokacin da suka dawo abun ya bani mamaki" domin dukkansu kuka suke sharshar. """Hafiz lafiya?""" "Girgiza kai yayi yana faWin. ""Lulu ki rufa ki min asiri, Lulu."" Sai hawaye, bakiWaya sai jikina yayi azabar" "sanyi bani manta lokacin aurensa da Karima haka ce ta faru yazo yana kuka da tashin hankali, ya Hafiz idan yana cikin tashin hankali bai da nutsuwa, ban san me ya faru ba, amma duk abinda zai girgiza shi yayi kuka nafi shi gudun abun. BakiWaya sai na shiga tashin hankali, yadda yazo ya zauna tare da daura kanshi a kan cinyata, sai jikina ya Wauki rawa, tambayar duniyar nan nayi mishi amma bai ce min cikanki ba sai ce min yake na rufa mishi asiri. ""Na rufa maka asiri me ta faru?"" Kuka Karima ta saka ni ma sai na fashe da kuka, aka rasa me rarrashin wani, har wurin karfe shida sai ga Hajiya, Mahaifiyarshi da kaninsa Tijjani suka zo, nasan a wurina zata sauka duk da bani da wani daraja a wurinta amma nasan wurina ne, shi kuma Tijjani zai sauka a BQ tunda akwai dakuna biyu a bayan. Yadda Hajiya ta ganshi yana kuka yasa ta shiga tashin hankali, nan na kara yarda da cewa ita uwa akan danta ba ruwanta ba abinda ba zata aikata ba. Tana shigowa matar nan ta zube akan gwiwarta, Tirkashi duk abinda zai saka Hajiya Asiya wacce Yaranta suke kiranta da Hajiya, ta saukar da kanta ta roke ka, tow wallahi ba karamin al'amari ba ne, domin nasan Hajiya mace ce mai d'agawa da izza, mace ce mai matukar ji da kanta sannan tana da wani irin girman kai wanda nake da yakinin Ya Hafiz a wurinta ya gada, rike kafana tayi tana faWin. ""Yar nan ki amince ki rufa masa asiri don Allah ki rufa masa asiri wallahi kaf duniya bayan ke babu wanda zai iya rufa masa asiri!"" Duk sai na rude, tun fil azal haka Allah ya halicce ni da saurin rudewa, ko fada ya Hafiz yake take nake shiga tashin hankali, shi yasa bana son abin da zai kawo tashin hankali a tsakaninmu, bakiWaya na shiga tsoro na ce mata. ""Hajiya don Allah tashi ki zauna a sama ni zan sauka! "" Girgiza kai" "tayi tana kuka. "" Yar nan Hafizu yana cikin tashin hankali kece kawai zaki fitar da shi. "" Wani abu ne me nauyi ya danne min zuciyata, na zuba musu idanu. ""Me kuke so Hajiya?"" ""Me muke so? Tambaya kike me muke so? Bama ki ce zaki rufa mishi asiri ba? Ai na gaya maka Lubnah bata kaunarka, amma ka ki ka yarda gashi tana nunawa kamar abin bai dame ta ba."" Sai ta rufe ni da fada, cikin jin haushi ya mike tare da daka mata tsawa. ""Me kike zo yi? Kin zo ki kara birkita min ita ne? Kin san halin da nake ciki kuwa?" "Idan kika rud'a min ita ya kike so nayi? Luluna ya isa!"" Ya rungume ni yana shafa kaina. Kallon Hajiyarsu yayi ya nuna mata kofa ba ita ba har Tijjani da Karima. Suna fita ya zauna tare shafa kaina yana faWin. ""Ki" "yi hakuri, ki yi hakuri."" Me Ya Hafiz yake so a gare ni da yake bani hakuri haka....." *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu UKU "Bani mantawa shekaru biyar da suka wuce haka ya suka saka ni a gaba da irin wannan niman alfarman," "kaina ya daure a lokacin na amince kome ya faru wanda har yau nake ji kamar da ban amince ba, babu abinda zai faru. Koda yake ai zanen ™addarata ce, ""Ya Hafiz me kake bukata?"" Na tambaye shi, sharce hawayensa yayi kafin ya ce min. ""Ba kome pretty!"" Sai naji sunan ya zo min wani irin banbarakwai, saboda rabona da Ya Hafiz ya kira ni da wannan sunan tun farkon aurenmu ludayina yana kan dawwo ba yanzu da nafi kamar da katifa huta ba. ""Hmm me kake bukata?"" Zama yayi ya kwantar da kaina a kafad'arshi, yaushe ya Hafiz ya zama haka? Tow akwai abinda yake bukata. ""Zan gaya miki muje ki yi" "sallah."" Ya fada yana jan hancinsa. Haka na mike na nufi dakina, shima ya fita zuwa bangaren Karimah." Hafiz """Hajiya ni ban kirawo ki nan, ki kara min matsala ba. Kin san irin halin da nake ciki? Yarinyar nan lallabata" "zan yi na rufawa kaina asiri, idan ba haka ba wallahi sai dai na kare a gidan Yari, kin san ban ajiye ba ban bada ajiya ba, sannan shi wancan Mijinki ba shi ne da shi. Don Allah ki ajiye kiyayyar da kike mata, nima hakuri nake da ita kada ki sake ki kara mata wani maganar banza!"" Cikin kaskantar da kai ta ce mishi. "" Ya kake so nayi? Kasan bana son ganka cikin tashin hankali, amma ka gaya min yadda zan bita, ai duk abinda kace shi za ayi Alhaji karami!"" Zama yayi da kyau ya ce musu. "" Nan da sati idan ta amince zan sayar da gidan nan, abinda ya rage zan sayi wani karami a tudun salamanu, bana son danginta da ita" "kanta su san abin da yake faruwa, ina son kafin haka na tafi Umara da ita, domin yadda kome zai tafi. """ """ Umara kuma? Taya Umara kuma? "" Inji Karimcy, kallon an kusan fita Masallaci yayi ya ce mata. """ "Wani sati zamu tafi na gama shirina, zaki bi Hajiya da Yara zuwa Jama'are! "" Ya fada yana fita daga part din, tabbas yayi shirme, amma yasan idan har ya samu hadin kan Lulu kome zai tafi yadda ya tsara." "Lokacin da ya koma, tana zaune akan abin sallah, hannunsa dauke da wata cadi yayi shiru cikin" "doguwar rigan jikinshi. Ya yi jugum kamar wanda yake ciwo, a yau daya na hango ramar da yayi kafin ya kalle ni cikin karfin hali ya ce min. "" Kin idar ne? "" Gyada mishi kai nayi ina kallonshi, domin duk ya bani tausayi sai na rasa me ke min dad'i na matsa kusa da shi na, daura kaina a kan gwiwarshi, shiru yayi kafin ya ce min. ""Allah ya jarabce ni a kwanakin nan, duk yadda nake son nayi ™o™arin dauke kaina amma na kasa."" Shiru yayi yana jan numfashi, ya kwantar da kanshi a jikin kujera yana haki. "" Ya Hafiz me kake" "bukata? Ya Hafiz baka yarda xan iya kome akanka ba ne??""" "Girgiza kai yayi yana faWin, ""Lubnah ba zaki iya ba, ni da nasan ba zaki iya tunda kwanankin baya yan" "uwanki sun bukaci mu rabu gara kawai na sallame ki, na kare rayuwata a gidan Yari, domin nasan karshe na a gidan Yari zan gama rayuwata!"" Na kaWu da jin zai kare rayuwarsa a gidan Yari, haka yasa na shiga" damuwa nayi ta rarrashinsa da mishi alkawarin duk abinda yake so ya gaya min xan mishi. Haka muka cigaba da zama har aka yi sallah isha ya tafi masallaci. Hafiz "Fitar da yayi ba masallaci ya nufa ba, bangaren su Hajiya ya nufa, ya zauna domin sallah dai baya yinta," "kome za ayi sai dai a yi amma idan akan sallah ne ba zai tab'a yin ta ba. Haka ya zauna ya yi shiru Hajiyarsa ta ce mishi. "" Hafizu ka barmu cikin duhu meke faruwa ne? "" Shafa kanshi yayi kafin ya ce mata. "" Ba kome. "" "" Wani irin ba kome? Me ya faru? "" "" Wato Hajiya Yan uwan Lubnah suna son su raba mu. "" Nan ya kwashe kome ya gaya mata, shiru yayi yana kallonsu. "" Yanzu saboda haka ne ya dauko ni? "" Girgiza kai yayi yana lashe busashen lips dinsa yana kallon kasa. "" Ba saboda shi ba ne. "" A hankali yayi shiru ba zai tab'a fada ba, ko zai mutu ne domin bai yarda da Hajiyarsu da Tijjani ba, kai hatta Karima bai" "yarda da ita ba, shi a duniya yafi yarda da Lubnah akan kowa." "Ana idar da sallah ya mike zai fita Karima ta ce mishi. ""Bamu ci abincin dare ba!"" ""Baki da hannu ne," "kin manta halin da nake ciki ne? Ita kanta ta rude balle ni ta san me zata dafa, ki shiga ki dafa muku. "" Ya fita daga parlourn." "Parlourn Lubnah ya isa ya zauna yana kallon tv, sannan yana jin motsinta a kitchen. Yasan zata yi wani" "abu amma shi abinda yake bukata yafi karfin abinda zai ci,. Shiru shiru bata fito ba, sai ya fara tari kamar wanda ya kware." "Haka yasa na ji tarinsa na fito da sauri ina faWin,"" sannu Yaya kwarewa ka yi? Bari na kawo maka ruwa!" """ Na koma kitchen na kawo mishi ruwa da sauri na bashi ya sha yana sauke wata irin ajiyar zuciya da nishi mai karfi, sai da ya tsinkar min da zuciya. Daura kanshi yayi akan kirjina yana ajiyar zuciya. ""Luluna ina cikin tashin hankali, mutuncina da kimata zata zube. "" "" Ya Hafiz meke faruwa ne? Idan Baban Bauchi yaji ranshi zai b'aci"" a wani zabure ya mike zaune yana kamkame ni,"" don Allah kada ki gaya mishi, Innalillahi wainnalihir rajoun, don Allah ki rufa min asiri wallahi idan ya ji zuciyata zata buga. "" Kamar" "yaro me tsoro haka ya koma min, ina son Ya Hafiz son da bana yiwa kaina. Shima kuma yasan haka ina" "sonshi so na hakika, don haka ya kara gigicewa yana mata gungun kamar mai cutar farfadiya. Shafa" bayanshi nake ina bashi hakuri da rarrashinsa. """ Ya Hafiz meke faruwa? "" Shakuwa ya fara tare da buga kirjinsa, haka yasa na mike tare da kawo mishi" "ruwan da na ajiye a saman Centre table, na bashi ya sha. Jin kauri a kitchen yasa na wuce da sauri na sauke jallop din taliya da kifin da nayi na zubawa Hajiya sannan na zuba mishi na zuba nasu karima da Yaranta sai na Tijjani, na saka a katon tire, na fita da shi zuwa bangaren Karimah, koda na isa na samu suna ta hiran halin da Ya Hafiz yake ciki suna jajjantawa. "" Yanzu idan har bai yi wani abu ba zai iya fuskantar fushin hukuma kenan Hajiya? "" "" Eh kai Yar nan, kuma kin ga ai fushin hukuma babban tashin hankali ne domin ba mamaki su wuce da shi gidan Yari! "" Wato sune suke magana amma ni ce hantar cikina yake kad'awa, ""Allah ya kyauta in sha Allah haka ba zai yiwu ba!"" Na fada musu ina ajiye musu abincinsu. ""Zai yiwu kai tunda baki haihu da shi ba, taya zaki fahimci halin da yake ciki, idan kika tuna halin da Uban Yaranki zai shiga kome kika mallaka zaku kashe shi a nan wurin, ki sani ba zance zan rabaki da Hafiz ba. Amma ina ganin lokaci yayi da ya kamata Hafiz ya hakura da ke domin ke ba matar rufin asiri ba ne? Tunda har ta kai ya saka wannan gidan a kasuwa."" Dafe kirjina nayi cikin wani irin bugawa da yake kamar zuciyata zata dirko daga kirjina, ""haba Hajiya me yasa zaki gaya mata? Me yasa zaki bari ta sani? Idan wani abu ne na amince zan fuskanci hukuma akan laifina gara na fusk."" Rufe mishi baki nayi" "ina girgiza kai. "" A'a don Allah kada ka ce haka, ba zaka sayar da gidan nan ba! """ """ Au ka ji ba, saboda gidanta ne, gidan da Ubanta ya saya maku, da ace gidanka ne wani ya isa ya hana" "ne? "" Maganganun Hajiya suka kara birkita min ™wa™walwa sai kaina ya fara juyawa, na fita da gudu na" nufi dakina. "Bayan fitar Lulu suka kwashe da dariya, Hafiz ya ce ""mahaukaciyar banza yanzu zata dauko jikinta yana" "rawa. Amma kun taimaka min."" Tijjani da ya cika bakinsa da abinci ya ce musu. ""Amma maganar gaskiya, ya kamata ka kyale yarinyar nan, iya adalci ta maka tayi maka kome, idan ka cigaba da abinda kuke akwai lokacin da kome zai lalace wallahi."" ""Dalla yi min shiru, ba gara shi ba kai ina sai dai na rike ka na rike matarka."" Inji Hajiya, ""Kyale shi Hajiya ai yadda Lubnah take kaf duniya babu me iya juya ta sama da ni, sannan idan kana ganin zata iya rayuwa babu ni zan gaya mata a gabanka zaka ji me xata ce, kuyi shiru" "gata nan zuwa!""" "A hankali na shigo parlourn ba kome a tare da ni, suka zuba min idanu. "" Ya Hafiz ko zaka zo! "" Shiru" "yayi kafin ya mike yana dafe kirjinsa da yake nuna min alamar yana mishi ciwo. "" Don Allah riki ni, jiri nake ji."" Haka na matsa jikinshi, muka fito har zuwa parlourna, ya zauna a dogon kujera ya kishingida yana lumshe idanunshi. Dakin na wuce na dauko kwatin yan kunayena,. Na ajiye mishi sannan na koma gefe na zauna. ""Ban san me ya faru ba, amma ga shi ka. Biya abinda ake binka."" Kallona yayi kafin ya dauke kai yana dafe kirjinsa. ""Lubnah bar dukiyarki kada yan uwanki su ji, su kara himmar raba mu, ki barshi kawai Allah yana nan."" ""Kudin ne ba zai iya ba?"" Hawaye ne ya zubo mishi ya ce min. ""Wato wani ™addara ne ya fada min, a shagon Baban Bauchi. Gashi saura kwana uku na hada kudin."" ""Baban Bauchi" "bai sani ba ne?"" Dafe kanshi yayi da hannu bibbiyu yana nishi. Ban san lokacin da na kara rudewa ba, na" "riko hannunshi tare da janyo shi jikina ina tab'a shi. ""Ya Hafiz ko mu tafi asibiti ne? Innalillahi wainnalihir" "rajoun! Ya Hafiz lafiya?"" Yadda ya mike min kamar gawa yasa na kara kidimewa, garin juyawa na ci tuntube da center table din parlona, ban damu da zafin ba amma har cikin raina na ji ciwon sai dai halin da Ya Hafiz yake ciki yasa na manta da ciwon da naci, sai na kasa gane kukan da xan yi na ciwon ne ko kuma na halin da ya Hafiz yake ciki ne? BakiWaya na shiga tashin hankali, ban san adadin soyayyar da nake yiwa ya Hafiz ba, haka yasa na kara birkice na rungume shi, ina kuka sosai, domin zuciyata ta karye ainun. Bana son naga abinda zai d'aga mishi hankali, a daren muka kai shi asibitin ni'ima aka bashi kulawar da ta dace har da karin ruwa, Tijjani muka bari a can asibitin muka dawo gida, Hajiya sai kuka take, tana shashekar duk sai naji na damu da kai, dakyar muka dawo tambari inda Unguwar yake, na tura kan motata zuwa cikin gidan, dama motar da yake hawa tawa ce, tunda ya sayar da tashi kwanakin" baya ya dauki tawa yana amfani da shi. "Koda muka fito Hajiyarsu ta ce min. ""Lubabatu dama nace ko."" kallonta nayi ina son naji me zata ce," "sai ta ce min. ""Dama kada ki gayawa Iyayenki halin da ake ciki domin idan kika gaya musu abin ba zai yi dadi ba, idan babanku na Jama'are yayi cewa ga abinda ya faru. Ki zama mace mai rufawa Mijinta asiri haka zai saka Allah ya rufa miki ta yadda baki zata ba."" Gyada kai nayi ina faWin.. ""in sha Allah Hajiyarmu!"" Na fita daga motar na nufi cikin gidan, na rufe bangarena parlourn na zauna nayi ta tunani kafin na shiga na kwanta, karfe biyu da arba'in da biyar na farka sallah dare, ina yi ina gayawa Allah kuka" "ta da matsalata, nayi tawassali da sunayen Allah tsarkaka, Allah ba zai tab'a wulakantamu ba." "Ina zaune har aka yi sallah asuba, sannan na yi raka'atu fijir, ina idarwa na daura da sallah asuba," "sannan na fita na fere doya na daura a wuta, sannan na daura ruwan tea, a hankali nake bin kome ina lissafin yadda xan shawo kan matsalar ya Hafiz, wurin karfe bakwai sai ga Tijjani yazo daukar mota zai je dauko shi, ""kenan ba sai an saka muku abincin ba zaku dawo ?"" ""Eh!"" Ya ce ya fita, kafin bakwai da rabi, na hada abincin Yusrah na kai mata, na tashe ta na mata wanka, sannan na shiryata tana ihu, sai ga Hajiya ta fito. "" Wai me kike mata ne? "" "" Wanka na mata Hajiya zan shiryata ne! "" "" Wanka ko mugunta? Ke fa muguwa ce ba mamaki ruwan da zafi kika yi ta kona mara mutunci, ke baki haihu ba amma salon muguntarki yafi karfinki wallahi ki ji tsoron Allah! "" Kwalla ne ya cika min idanu, na gama shiryata na kawo mata abin karyawanta, tana sha tana kukan rashin mutunci. "" Ni tea din ya min zafi, yana kona min baki kaka yana kona min baki! "" "" Ai dama nasan muguwa zata kashe ki ne! "" Hajiya ta fada tana daukar tea din ta kurba, sai zare idanun tayi tana faWin. "" Takwara ai ba wani zafi, yadda yayi sanyin nan ma kulle miki ciki zai yi! "" Kamar nayi kuka haka na bata doya ta furza min a fuska. "" Ni kin cika yaji! "" Wani irin bakin ciki naji ya cika min rai, na ce mata.. ""ayya Yusra me yasa kike min haka ne? Ki ci don Allah!"" Kamar nayi kuka nayi maganar, sai tura baki tayi tana faWin. ""Ba zanci ba."" ""Ai ba dole ba ne sai ta ci a barta haka don Allah!"" Haka na hakura na barta, na kuma wuce na barsu na kawowa su Hajiya nasu don" ta fara min ihun ita yunwa take ji taliyar jiya bai rike ta ba. "Haka na kawo abin karyawan, tana ci tana faWin. ""Kin iya girki amma salon mugunta irin naki sai kin" "azabtar da mutane!"" Kaina a sunkuye na barta na riko hannun Yusra na kai ta makaranta, har lokacin ban ga Karima ba, sai da na kaita makarantar na juyo zan dawo gida, na hango su Ya Hafiz, na zata zasu tsaya su dauke ni ne, a'a sai suka yi tafiyarsu. Haka ba karasa gidan a gajiya na shiga na hada mishi abin karyawa yana zaune a parlourna, sai da yayi wanka ya dawo ya zauna yana karyawa hajiyarsa ta shigo ita da Tijjani da Yasir da har lokacin bai yi wanka ba. ""Lulu waye zai yiwa Yasir wanka ne ?"" Ya Hafiz ya tambaye ni, ""ni ce!"" Na fada ina daukar yaron da ya fara tsalla ihu, haka yayi ta ihu har kaina ta fara wani irin juyawa, gashi ya cika kashi a pamper dinsa, haka na wanke na mishi wanka na fito na shirya shi, garin shirya Yaron nan na kara fama tuntube na, wani irin kuka ne ya so kwace min, haka na daure na kai shi waje na koma daki na shiga ban daki na fashe da kuka, don sai yanzu na lura da farcen kafana ya fashe, baka hawaye yake zuba min ina jin kamar na mutu da bakin ciki, haka na gasa kafar na fito nayi wanka," na shirya cikin material. "Bayan na saka kwalli da man baki na fito, na samu sauran abin karyawan nawa da yake kitchen" "Hajiya da Karima sun dauka sun cinye, kitchen din na koma na dafa indomie da kwai, na zauna a kitchen din naci, sannan na fito na samu suna ta magana. Shi kuma yana zaune yana jin su, can aka buga gidan na zata Almajirin da yake min aiki ne, na koma daki tare da dauko Hijab na saka sannan na fita na bude gidan, wasu magidanta ne guda biyu, suka shigo gidan. ""Alhaji Hafiz yana nan?"" ""Eh yana cikin bari na mishi magana,!"" Na fada tare da nufar cikin gidan, ""tow mun gode"" haka suka jira na koma parlourn na ce mishi. ""Ya Hafiz kana da baki a waje"" ""sun iso kenan?"" Ya fada yana yatsina fuska. ""Yaya kasan likita" "ya ce kada ka saka damuwa a ranka domin zuciyarka tana dab da bugawa!""" Lumshe idanunshi yayi ya bude a kaina yana min alama da idanu wato naji dai. Sunkuyar da kai nayi "ya fita, shi da Tijjani, Hajiya ta zauna tana ta zuba kwadayi tana bawa Karima labarin yadda ta sha wahala akan Ya Hafiz ni dai na wuce kitchen na wanke kayan da nayi amfani da shi, sai gashi ya shigo kitchen din, ""Ina takardun gidan nan?"" ""Yana dakina!"" ""Ko zaki bani aron gidan na sayar idan na biya bashin da ake bina zan!"" Rufe mishi bakinsa nayi da hannuna, ya sumbaci hannun yana cire bakinshi a hannun ya tako har jikin dogon deeper freeze na, ya haWa ni da jikin freeze din ya shiga sumbatar goshina da manyan kumataina. Abu daya nake bukata a gare shi, shine soyayya amma na rasa ni dai a bangarena bai rasa soyayyar da nake mishi ba, haka ya gigita ni, daidai shigowar Karima kitchen din ta kawo kayan da suka ci abinci da shi, ganin halin da muke ciki yasa ta jan tsaki tayi waje, sake ni yayi ya ce min. ""Maza dauko" "min na manta mun bar mutane a waje!"" Haka na wuce dakin na dauko takardun bakiWaya, na mika mishi kamar wacce aka katse min tunanina da lissafina haka ya amsa ya fita, ban kara ganinsa ba, sai karfe daya da ya dauko Yusra, suka shigo na zuba mata abinci tana ci sai ga Hajiya ta shigo dama tuwo nayi miyar shuwaka, na kawo mata abincinta, ta fara ci tana mita. ""Kin san yadda na tsani shuwaka shine kika yi miyar fisabiilillahi gudawa zanyi!"" ""Ki yi hakuri Hajiya ban sani ba ne!"" Na fada ina bata hakuri, na kara" "kallonshi na ce mishi. ""Yaya Mama bata ji dadi ba, ina son na je na gaishe ta!""" """Daga nan ki gaya musu ya sayar miki da gidanki ko?"" Inji Hajiya, girgiza kai nayi na ce mata. ""Haba" "Hajiya wannan fa duk bata taso ba."" Hayayyako min tayi kamar zata rufe ni da duka, ""Hajiya ai ta gaya" "miki Mama bata da lafiya ne, ki kyale ta an jima ta je. Luluna ki shirya ki tafi kin ji idan na gama zan zo" "daukarki!"" ""Shi kenan na gode!""" *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu HUŠU "Wani irin dad'i ne ya lullube ni, na gyad'a mishi. Ina me da hawayen da suka fara cika min idanu," "murmushi yayi ya ce min. ""Tashi ki je ki fara mata abinda zaki kai mata!"" Mikewa nayi ina ta godiya. Domin ya min abinda ban zata ba, haka na wuce dakina, na sauya kayan na fito ina zuwa na samu basu" "nan shi da Hajiyarsu, kitchen na wuce." Hafiz """Hajiya me yasa baki da hakuri ne? Kina irin wannan ba sai ta fara jin wani abu a ranta ba? Hajiya gaskiya" "ki daina min haka, kin ga yadda Allah ya taimaka asirina ya rufu akan wannan lamarin.""" """ Amma Hafiz kasan dole dai mu kula domin tunda yan uwanta suka fara zargin wani abu dole mu kara" "mikewa. "" Murmushi yayi ya ce mata. "" Hajiya ni ba kamar ki ba, a wurin Lubnah bana bu™atar boka ko" "Malam, idan na tsaya ga kaina ina alfahari da haka, don Allah kada ki saka mata magana a bakinta.""" "Shiru Hajiya tayi tana faWin. "" Tow shi kenan amma ka kula domin kuwa Malamin nan ya ce a cigaba" "da kulawa."" "" Na gaya miki ni ban yi wani aiki da abinda ya fada ba, ni kaina Aljanu ma tsorona suke."" Daga haka ya bar gidan, duk sai Hajiya ta shiga damuwa, ta dauki wayarta ta kira Malaminta, ta gaya" "masa abin da yake faruwa. Shiru tayi kafin can ta ce mishi. "" Toh bari na turo maka da kuWin!""" * "Ina ta aiki gyara kayan miya sai gaKabiru almajirina, mikewa nayi ina faWin. ""Ka iso? Ko zaka fara da shara" "sai kazo ka sayo min kaza."" Durkusawa yayi yana faWin. "" Ina kwana Aunty? Eh na iso shi kenan!"" "" Shi" "kenan kayi sharar ina jiranka!"" Na cigaba da aikina ya shiga share filin gidan bakiWaya, ni kuma na cigaba" "da aikina. "" Kai Uban waye ya baka izinin shigowa?"" Dariya Karimah tayi tana faWin. "" Hajiya ai almajirinta ne. "" "" Eh samun wuri!"" Yana cikin sharar sai ga Ya Hafiz tare da Tijjani, suka shigo ganin Hajiya a filin gidan suka tsaya. "" Hajiya lafiya? "" "" Ina lafiya ashe gidanka har yayi arahar da kowani kare da doki zasu shigo? "" Kallon Kabiru yayi ya hade rai. "" Idan bai shigo ya taya ta da aiki ba me kike so nayi? Ita wannan me ta iya? Kin ga Hajiya ban kira ki, ki zo ku rusa min gida kamar yadda kika rusa gidan Nuru ba, ba" "ruwanki na gaya miki!"" Shiru tayi tana da wani sunkuyar da kai." "Ina gama hada abinda nake ya shigo. "" Luluna sannu ko zaki zo ina son magana da ke?"" "" Tow ""na fada" "wanke hannuna, a bakin kofar parlourn na ji muryan Kabiru na fito na same shi mika mishi atm dina nayi na ce mishi. "" Kaji guda uku, zaka sayo sai kifi kilo biyu da rabi ka ga bani da lokaci ka dawo da sauri don Allah!"" "" Tow Aunty!"" Ya saka kai ya fita, na bi bayan Ya Hafiz zuwa dakina. Ina shiga na same shi a tube, yasan ina da aiki me ya kawo irin wannan lamarin yanzu? Kamar nayi kuka na ce mishi..""Ya Hafiz ko!"" ""Hakkina nake so!"" Yadda yayi min magana take ya koma Ya Hafiz din da na sani, kwabe kayan nayi na haura gadon, .kamar yadda na sani ko minti goma ba ayi ba ya fara nishi daga nan ya sauka ya saka kayansa ya fita, ni kuma na wuce ban daki nayi wanka na sauya kaya, ina fitowa na sami Hajiya da Karima a parlourn, sai wani irin kallo suke bina da shi. ""Akuya tana haihuwa domin ana kwasar Yaranta zuwa kasuwa, ke kuma sai dai ki tsotse min Yaro, bakya gaba ba kya ba."" Shiru nayi na wuce kitchen na wanke shinkafa na zuba karasa da pea da green beans da karas ,na daura akan wuta na juye ruwan zafi a kai. Na daidaita wutar ina jin kamar na hadiye zuciyata. Ina cikin aikin Kabiru ya yi sallama na fito na amshi kayan na wuce ciki suna parlourn suna cigaba da zagina. Abin karyawar da na hada mishi na kawo mishi, sannan na ce mishi..""ko xaka dawo an jima ban gama ba rana ba!"" ""Ba kome Aunty na gode!"" Yayi sallama ya tafi ni kuma na cigaba da aikina wurin karfe biyu saura na zuba abincin yan gidan, sannan na shiga wanka na sauya shigata cikin wata lace peach colour na fito ina gyara daurin dan kwallina, kitchen din na shiga turus nayi cike da mamaki. Hajiya ce ta bude kular abincin da miyar da xan kaiwa Mama, ban ce mata cikanki ba na ce wuce inda na daura farfesun kifin na sauko a hankali, na dauko wata kula na juye shi a hankali, kamar wacce kwai ya fashewa haka ta saka kai ta fita. Bayan fitar ta na d'ago tare da isa wurin kular na kara gyarawa sannan na dauko sauran da na rage na karyawa na kara sannan na gama kome na saka a basket na fito, daidai isowar Kabiru na koma kitchen na dauko mishi nashi sai godiya yake ta min, bayan na sallame shi na dawo na shiga dakina, na tattara duk wani abina me daraja na boye shi, domin nasan ba a abin mamaki ba ne gobe na gani a jikin Aunty Nana ko Haulatu, haka yasa na rufe dakin da kome nawa, sannan na saka key Win a jakata na fito na bar gidan, don shi kan Ya Hafiz" tun dazu ya sake fita da wasu mutane. *Dutsen tashi* "Daidai gidan Marigayi Malam Idris anan gidanmu yake, kafin ka isa gidan Malam Idris, anan aka sauke ni" "da basket guda uku, kafin na samu napep a unguwarmu sai da na fito bakin titin tambari housing estate," "na sha zama don ma Maman Ummi da zata fita ta rage min hanya zuwa bakin hanyar unguwarmu, na" "tsaya kafin na samu abin hawa, haka muka iso gidan." "Yaran unguwarmu yan matasan suka taso da sauri suna faWin. ""Lubnah barka da zuwa!"" Murmushi" "nayi suka dauki kayan ina amsa musu. ""Yawwa Amir kai ia girma haka? Lallai girman dan mutum, Jamal ka ne haka ka zama kato!"" ""Kai Aunty Lubnah ba wani katon da na zama, ga Waheed naj baki ga girmanshi ba sai ni! "" Suka fada murmushi nayi muka isa kofar gidanmu me dauke da shagunan provision. "" Lubancy ke ce daga sama haka? "" Murmushi nayi na ce. "" Eh Malam Anas ni ce! "" Na wuce Yaran suna bina da kayan har cikin gidan, yadda muryata ya karad'e cikin gidan sai da kowa ya fito har da Aunty Innah dama tazo ne? Wani murmushi suka min na karasa har da Aunty Munah. "" Aunty Munah yaushe a" "gari?"" "" Korata kike kenan? Ke dai mugun halinki na kin mutane yana nan har yau baki sauya ba.""" "Murmushi nayi na koma inda Yadiko take alola na durkusa har kasa na gaishe ta. ""Da fatan da" "izininshi kika fito? "" Gyada kai nayi ina kallon kasa. "" Tow sai ki gama ki koma da wuri don unguwarki da nisa!"" "" Haba Yadiko daga zuwa kamar mai Waukar wuta sai a fara mata maganar ta gama ta koma! "" Inji Aunty Munah, daga can dakin aka ce mata. "" Ai baki ga kome ba, sannan yadiko ta mata da kauna tsaya ki ga yadda Mama zata mata. "" Inji Ya Sani da yake dakin yana cin abinci. Ya fito dauke da plat din abinci, "" dube ta kamar Bakuwa"" ya fada yana mita. "" Aunty xamu tafi sai mun kara shigowa. "" "" Ku tsaya mana! "" Na fada ina buWe jakata na dauko dubu daya na mika musu. "" Ban san zan ganku ba, ban saya muku tsara ba;"" "" a'a yayi yawa mun gode ko Waheed! "" ""Maza karba kafin na saka ki wanke gidan! "" Inji Ya Sani, karba suka yi tare da fita da gudu suna godiya. "" Mama tana ciki? "" "" Eh! "" A hankali na ja kafa na nufi parlournta zuciyata tana wani irin tsalle. A hankali na shiga parlourn tana addu'a, ga Aunty Hindatu da take ta fama da laptop dinta. ""Yar renin hankali tun yaushe na gaya miki bata da lafiya!"" Zama nayi a gefenta, tare da daura kaina a kafadarta. ""Am soweer."" Na fada ina wasa da yatsuna. Shafa addu'ar muka yi abinda ya fito a bakin Mama yafi kome dukana.. ""Me ya kawo ki? Da izinin waye kika tawo?" "Bayan ko yau sai da Mijinki ya gaya mana baya gari idan ya dawo zaku zo tare."" Wani irin abu ne ya tsaya min a rai, yaushe Ya Hafiz yayi tafiya, amma sai na yi shiru ban ce mata kome ba. Ta kara da cewa. ""Ya gaya mana Tijani zai kawo Hajiya Asiya an jima Asibiti kuma ya kamata ace kina gidan."" Yadda Mama take shiga ba nan take fita ba, sai naji zuciyata tana wani irin ciwo kamar kaikayi. Ni dai kamar yadda aka saba kaina a sunkuye, wayar Mama ne yayi kara ta dauka tana faWin. ""Na'am Alhaji gata nan tazo!"" Ta mika min wayar. Yadda ya balbale ni da fada yasa nayi shiru kamar yana gabana ya cigaba da cewa. ""Kin san Abokiyar zamanki bata gari, sannan ta bar miki Yarinyarta taya zaki kai yarinyar makota? Ke wacce irin mahaukaciya ce? Don Allah bai baki haihuwa ba sai ki na wulakanta mishi Yarshi? Wai ma da izinin waye kike fito? Ga Hajiya Asiya can da Tijjani sun je gidan ba kowa, ke a rayuwarki idan baki saka mu magana ba, bakya jin dadi ne?"" baba yana yin nashi a waya, ta yadda yake shiga ba nan yake fita ba, haka Mama tana yin tana kamar ta rufe ni da duka. Nasan cewa duk lokacin da zan zo matu™ar ba shi zai kawo ni ba, tow na rantse da Allah kamar yar riko haka nake komawa amma idan ya kawo ni kowa yayi" ta ririta ni. Aunty Hindatu na ta kasa jure fadar Mama ta ce mata. """ Mama dai, ya kamata ku fahimci Lulu ba zata fito don kanta ba, sannan taya zata fito a ce! "" ""Gafara" "can, an gaya miki bamu san yadda kike hure mata kunne ba ne? Ko an ce miki bamu san yaddA kika mata" "wayo kina rabata da kuWinta, me yaron nan ya rage ta da shi? Ko an gaya miki ban san me nake yi ba ne?" "Wallahi Hindatu idan baki daina shiga rayuwar Lubnah da gidan aurenta ba na rantse da Allah sai na miki Allah ya isa, kuma ki zauna yanzu su Hajiya Asiya zasu tawo ku koma gida Wallahi, ina zaman lafiya da Mijina ba zaku kashe min aure ba ke da Yan uwanki! "" Cikin fushi Aunty Hindatu ta shiga hada kayanta Ya Sani daga waje da Aunty Munah, suka shiga kananun magana, yadda Ya Sani yake mita yasa Yadiko ta dirko musu kamar zata rufe shi da duka, har tana faWin. ""Idan wani ya kara shiga rayuwar auren Lubabatu sai na mishi Allah ya isa, tunda burinku shine ku kashe mana aure, idan da kuna da hankali" "tausarta zaku yi ba ku tsaya kai da fata bata yin kuskure, tun kafin ta iso muka san cewa gaban kanta tayi, haba me yasa Lubabatu take haka ne? Yaron nan yana girmama ki amma ke kin dage sai kin zubar da" "mutuncinki.""" Kiri-kiri suka hade kai suka min tas Aunty Munah da haushi ya mata itama barin musu gidan tayi ta nufi "gidan Ya Umar da yake makama jahun, Ya Sani ma haka ya bar gidan babu shiri, ni daya kamar mayya haka suka yi ta fada bayan sun gama, kuma suka sauko tare da min nasiha, har Yadiko ta shigo da abincin da na kawo suka ci da Mama, ni dai kaina yana kasa har lokacin ban d'ago kai ba, sannan ban ce musu cikanku ba. Kai mai karatu wannan sai ya zame maka sabo amma a wurina ba sabon abu bane, da na san haka zai faru da Hajiya tace na fasa zuwa da na fasa. Kiran Sallah la'asar ya saka na mike zuwa ban dakin Mama nayi alola na fito na gabatar da sallah la'asar. Bayan na idar ina zaune sai ga Hajiya da Yusrah, tana zuwa da gudu ta fada jikina tana faWin. ""Lulu shine kika tafi kika bar ni."" ""Yusrah babu Mama sai Lulu ba uwaki ba ce?"" D'ago kai yarinyar tayi ta ce mata. ""Allah ya kiyaye ta zama Uwata, ko Hajiya "" wani diriricewa Hajiya tayi Tijjani ya daka mata tsawa, yana faWin. ""Kun ga yarinya mara tarbiyya, Lubnah haka kike tarbiyyar Yarki!"" Ni dai bance musu kome ba, ina jin suka gaisa da su Mama da Yadiko, sannan aka zubo musu abinci suka ci sosai.. har a lokacin mamaki bai daina kamani ba yadda suka tawo da tsaraba niki -niki, suka bawa su Mama da Yadiko, yadda Hajiya take wani tarerayata, abin sai yafi kome" bani tsoro tabbas Hajiya idan suka saka mu jariri zasu cije shi ya mutu har lahira. Duk uban abincin da na saka musu amma anan da aka kawo musu abinci sai da suka ci kamar ba "mutane ba, har zuwa lokacin idanun Hajiya yana kan kular abincin, sai da Yadiko ta zuba mata hankalinta ya kwanta tana ci tana murmushin, a hankali na tashi na koma dakin Mama na kwanta, wayata ta ce tayi ™ara na Wauka tare da kallon screen din wayar, shine dauka nayi a sanyayye ya ce min. ""Da fatan kin sami kowa lafiya!"" Murmushi nayi nace mishi. ""Suna lafiya!"" Sai yayi shiru. ""Luluna ki yi hakuri wallahi nayi haka."" ""Wani abu ne ya faru kake bani hakuri?"" Shiru yayi yana jina kafin ya ce min. ""Sai kin zo gida zan miki bayani!"" ""Wani bayani babu abinda ya faru, don Allah ka daina damuwa akan haka."" Daga haka na kashe wayar, na kwanta duk da haka sai da ya kira ni ina gani naki dauka har na kwanta kaina azabar ciwo yake, da yake mun san cewa barcin yamma babu kyau amma saboda yadda kaina yake ciwo yasa na kwanta. Karfe shida da wani abu ba ji kiran sallah, sai lokacin na lura da yadda aka lullube ni da mayafi. A hankali ba bude idanuna da suka min nauyi, na dafe goshina ina jin kamar kaina zai rabe gida biyu. Zama nayi ina dafe da kan har Mama ta shigo dakin. ""Baki da lafiya ne?"" D'ago kai nayi ina" "murmushi na ce mata. ""Lafiya lau!"" Na mike da kyar na nufi ban daki na yi alola na fito, na gabatar da" "sallah, itama sallah na samu tana yi ina idarwa na zauna a wurin shiru sai da ta shafa addu'a sannan ta ce" "min. ""Me yasa kika fito ba da izninsa ba?"" ""Ba kome!"" Shiru tayi tana kallon yadda nayi shiru. ""Kina son Abbanku ya sake ni ne?"" Girgiza kai nayi, sannan ta cigaba da min nasiha tare da fada domin babu wani abu me kama da rarrashi a cikin kalma ta don gaya min take zan kashe mata aure ne, tunda nasan cewa akan Hafiz Baban Bauchi bai da hakuri, ni dai ban ce mata cikanki ba har ta gama maganarta sannan ta fita, bayan isha na isa parlourn Abba na gaishe shi, ashe Ya Hafiz ya iso sai lissafi yake tare da gaya mishi" abubu yan da ya faru a tafiyar da wasu dalilai da yasa aka samu matsala. Yadda Baban Bauchi ya yarda da Ya "Hafiz kaf Yayuna maza da mata babu wanda ya yarda shi haka, durkusawa nayi na gaida Baba ya™i amsa min, sai da Ya Hafiz ya ce mishi. ""Baba tana gaishe ka!"" ""Ba zan amsa mata ba, akan me zan amsa mata bayan ta fito ba da izininka ba, tasan irin masifar da take shirin kawo min idan da yau mutuwa nayi da Allah zai saka Mala'iku su d'aga ni su ce ga abinda Yarka take yi!"" Nan dai Ya Hafiz yayi ta rarrashinsa da kalmai masu dad'i, sannan ya kara da cewa. ""Matukar kina son na kaunace ki Lubabatu ki bi Mijinki sau da kafa, don baki san irin asarar da kika janyo mishi ba ne ke da Hindatu itama zan kira Mijinta na ja mishi kunne tunda ku Yahudawa baku san yadda zaku bi aurenku sau da kafa ba. Kuma zan kira Addu'a" "da Umar da Tahir na ja musu kunne kada wani ya kara tura miki kosisi tunda ba zaman aure zaki yi ba.""" "Yadda Baban Bauchi yake shiga yake fita sai ka rantse da Allah wani abu na aikata, wannan shine" "burin Ya Hafiz duk ranar da zan zo matu™ar bai mishi ba koda kuwa ya amince tow sai na fuskanci tashin hankali a cikin gidanmu. Ni kuwa kamar wacce ake watsawa ruwan zafi haka nake jin maganar su kamar danyen guba, nasan Iyaye suna kaunar Yaransu akan kansu amma ni nawa Iyayen sun zaSi abinda za a fada a kansu sama da rayuwata, yadda ya gama fadar ya daka min tsawa akan na roki Ya Hafiz, har a lokacin idanuna wani irin zafi suke min, kaina a sunkuye na ce mishi. ""Ya Hafiz ka yafe min."" Muryana tana rawa, ""Wallahi na yafe miki,matukar ni zan d'aga miki kafa ki shiga aljanna wallahi na d'aga miki ki shiga Allah na yarda da Lubnah Allah ka yarda da Lubnah!"" Wannan yar draman da yayi a gaban Babanmu sai ga Baba yana irin farin ciki domin shi dai yaga yadda Ya Hafiz yake kaunata, Ya Hafiz ya ce mishi. ""Baban Bauchi ka amsa gaisuwar Princess don Allah!"" Cikin murmushi irin na manya ya ce mishi. ""Na rasa ganewa Hafiz yadda kake kaunar Lubnah baka hango laifinta. "" "" Mace ta gari ce, tana da kirki da mutunci. Ba iya soyayya ya bani ita ba, Allah ya yarda da ita ne ya bani ita. "" Yadda Ya Hafiz yake faWan kalaman yabo yasa Baba ya kuma juyowa yayi min nasiha, da nuna min yadda Ya Hafiz yake kaunata kaf duniya babu namijin da zai min irin wannan soyayyar da yake min na rike mijina domin kaf" duniya babu me min irin son da yake min......... *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu BIYAR "Tabbas Ya Hafiz yana kaunata, amma kuma me yasa yake min haka? Me yasa sai mun gama kome da shi" "yake juya min laifin? Ina ga ko yadda ya musu bayani ba haka suka dauka ba, amma zan tambaye shi ko nice ban fahimci yadda suke ganin laifina akan fitowa da nayi ba tare da izininsa ba, domin a sanima da izininsa na fito zuwa gidanmu, a hankali na fito daga dakin Babanmu, a bakin kofar muka hadu da Jalilah yar rikon Yadiko ce, amma yar uwarmu ce sosai, sai dai Jalilah ni da ita bama ga maciji saboda kawai" kowa da abinda yake tsammani a tare da shi. "Ni dai ban san me na mata ba, amma tare muka taso, zuwa yanzu dai auren Jalilah uku, tana zawarci" "sannan yan uwarmu ce na kusa sosai domin Mahaifinta kanin Baba ne, mahaifiyarta kanwar Yadiko, a sanina Jalilah kawar Ya Hafiz ce, kuma kawar Matarsa domin tun aurensu suke tare. Kallo daya tayi min ta dauke kai, nima na dauke kai kamar ban san tana wurin ba. Dakin Yadiko na nufa na ce mata. ""Yadiko zamu tafi!"" ""Tow Allah ya kiyaye hanya, sannan ki daina fitowa ba tare da izinin Mijinki, baki san kin girma ba ne."" Ni dai bance mata cin kanki ba, har ta gama magana na wuce dakin Mama na hada kayana. Ina hada kayana sai ga Ya Umar ya shigo da sallama, murmushi nayi na zauna. Sai da ya fara gaida Baban Bauchi da Yadiko, sannan ya shigo ya samu su Hajiyarsu Ya Hafiz ana ta surfa abinci, kallona yayi yana murmushi ya ce min. ""Auta shi ne baki karaso makama ba?"" Murmushi nayi na ce mishi. ""Ina wuni Ya Umar!"" ""Lafiya lau!"" Kafin ya rufe baki Mama ta tab'e baki ta ce mishi. ""Ai fitowa tayi ba da izinin Mijinta ba!"" Kallona yayi yana murmushi ya ce mata. ""Tsakanin da Allah auta ta wuce sai ta nime izinin zata zo gida nan, kada ki manta Hafiz dai a gidan nan ya taso haihuwarshi ce ba ayi ba, sannan na biyu idan Auta ta tawo babu izininsa meye ribarta? Kayyasa Mama Hafiz da Lubnah dukkansu Yaran gidan nan, kuna nazari kafin yanke hukunci gudun kada a tsaya a gefe guda!"" Da yake sunan Ya Umar sunan Baba Malam ne wato Kakanmu bata iya ko d'aga mishi murya ta ce mishi. ""Mai sunan Baba Malam!"" ""Mama maganar Allah nake gaya miki kafin Hafiz ya auri Lulu mu ne muka fara auren Yaran wasu, yanzu saboda yadda Habibah ta samu wuri wallahi idan zata fita sau dari bai wuce ta gaya min sau biyu ba, mu Yaran wasu muka musu adalci sai mu namu ne ba zasu samu adalci ba? Mama ita yarinya ce bakiWaya shekaru tara ake nima da aurenta idan kuka tsannanta mata bata da inda ya wuce nan ku sani shi Hafiz namiji ne, hmm kayya. Lulu kina son wnai abu ne? "" Da zumudi na mika mishi takardan da nazo da shi. Budewa yayi sannan ya ce min. "" Ok akwai ma a gidan nan kamar jiya aka yanka abokina dan liti zai zo ya saya. Fita yayi ina jin yadda Yadiko take gaya mishi abin da ya faru, itama nan gaya mata gaskiya yayi ya saka Ya Sani ya cire min kajin, duk wannan abin da ake Hajiya kunya ce ta kamata bata iya magana ba, sai sunkuyar da kai itama Mama sanin cewa Ya Umar ya daure ta da jijiyarta yasa bata yi magana ba, a can" "parlourn Baba naji yadda Ya Hafiz yake faWa shi da Ya Umar, koda yake Ya Umar ya gaya mishi magana" "daya ya ce mishi. ""Ka gama duk abinda zaka yi, wa'adin Allah gaskiya ce, ni da kai mun san kome! "" Ba sai" "Ya Hafiz ya fusata ba, ya mike tare da sallama yana faWin. "" Na hakura da Lubnah tunda ban muku adalci ba! "" Nan Baban Bauchi ya dirkowa Ya Umar fada yake kamar zai cire bakinsa, har da cewa. "" Idan kuka kashe mata aurenta ko bayan raina ne ban yafe muku ba. "" Murmushi Ya Umar yayi ya ce musu. ""Ni ba zan kashe mata aure ba, ai ita mace baka ce mata kaso aurenta ki zo mu zauna wannan wani lamari ne" "da Allah yake shirya faruwansa! Ka yi hakuri Baba idan na Sata maka rai!""" "Ko amsa masa sallama Baba be yi ba ya bar gidan, haka Baba ya zauna da Ya Hafiz yayi ta bashi hakuri," har da kiran Hajiya ya bata hakuri wai ta bawa Ya Hafiz hakuri. "Abin bai yi dad'i ba, domin haka muka baro gidan zuciyata ba dad'i. Kaina a sunkuye a cikin motar." """Ban da rashin mutunci irin na Yaran Salamatu don an rufa muku asiri an yi muku alfarmar auren yarku sai ku saka min d'a a gaba? Wallahi kun yi asarar!"" Haka Hajiya take fada," "shi dai bai ce kome ba, zuwawa yanzu ya fara jin wani irin yanayi a tattare da shi, ""Hajiya don Allah ki" "mana shiru!"" Yadda yayi magana a karfafe zaka Wauka ba ita ta haife shi ba, jin yadda ya daka mata tsawa yasa ni na sha jinin jikina na koma gefe da jikin kofar, har muka iso Tambari, na bude motar na fita tare da Waukar kayan da nazo da shi, kaya sosai aka hada min Mama da Yadiko wai kada na tashi hankalina. Bayan na shigar da kome na wuce zuwa part dina na saka kome a muhallinsa, sannan na wuce zuwa kitchen na daura ruwan zafin na zuba a flast, kafin na fito a kujeran Parlour na hango shi. ""Zo nan!"" Ya ce min, na taka a hankali jikina yana rawa domin nasan irin wannan kiran babu alkhairi a cikinsa." "Durkusawa nayi a gefen kafarshi ina me sunkuyar da kaina. Shiru ne ya ratsa parlourn kafin ya ce min. ""Me kika gayawa Umar?"" D'ago kai nayi da sauri ya tsinka min mari, sai da naji wani irin shuuu a kunnena, bakiWaya kaina ya fara min irin wannan ciwon da yake min tare da juyawa. Rike fuskana nayi da kaina. ""Tambayarki nake!"" Tsoro da tashin hankali, ya hana ni magana kara rufe fuskana nake ina" "girgiza kai. ""Tambayarki nake?"" Ya kara zuba min wani irin gigitaccen mari da yasa ni zama da duwawuna, nace mishi. ""Wallahi ban fadi kome ba, ka yarda da ni."" Na fada ina fashewa da kuka, haka yasa take ya kyale ni, ya bar parlourn anan na cigaba da kuka har dare ya raba na wuce daki na kwanta, haka nayi kuka har na godewa Allah, kwanciyar da nayi har na fara barci ya shigo ya bani wata magani na amsa na" "sha, ko minti goma ba ayi ba na fara jin kaina yana wani irin juyawa a hankali na kwanta." "Daga nan ban kara sanin me ya faru ba, sai da asuban fari na tashi na shiga wanka, bayan nayi wanka" "na fito duk yadda naso na tuna mai ya faru na kasa, sallah nafilla nayi na wuce zuwa kitchen, ja daura abinda zan daura sannan na fito zuwa dakin nayi , bayan na idar na koma na fara aikin abin karyawa karfe bakwai saura na nufi bangarensu, na taso Yusrah amma yarinayr nan tayi ta min ihu har da wani abu kamar tana dambe da ni, ihun da take min da kuma yadda nake jin wani abu me karfi a kaina yasa na daka mata tsawa. ""Don Allah tsaya na miki wanka!"" Wannan abin na mata yarinyar nan ta fasa ihu," "sai ga kowa ya shigo ban dakin, ba tare da wani bincike ba ya Hafiz ya rufe ni da duka, kamar zai kashe ni," "saboda karfin azabar duka zubewa nayi akan gwiwata hancina yana zuba da jini. ""Tashi ki mata wanka!""" "˜asa tashi nayi ina kife a wurin, koda ya d'ago ni, sai komawa nayi na kwanta sharaf kamar an jika tsuma, abinda ya saka hankalinsa ya tashi amma saboda rashin imani ya ce min. ""Wallahi idan baki tashi ba, na" "taso sai na kara taka ki, jaka juya wacce bata san darajar haihuwa ba""" """Gara ka gaya mata dai, ban da rashin mutunci ki saka yarinya a gaba da azaba, ke ina danginki gani suke" "ana cutar da ke!""" "Sai dai duk abinda suke yi bai saka na motsa ba, anan suka fahimci fa babu numfashi a jikina, abinda ya" "firgita su har Tijjani ya shigo yana faWin. ""Yanzu kana ganin daidai ne abin da ka yi? Kana tsammanin yadda Umar yake kallon idanunka zai kyale ka ne idan ya ji abinda ya faru? Kana abu kamar mahaukaci yarinyar nan kana amfani da ita yadda bai dace ba, ba fa Ubanta baya sonta ba ne a'a alfarma ya maka saboda Abbanmu, ka sake aka gano yadda kake azabtar da ita wallahi ka ji na gaya maka, ba ruwan kowa da kai ne ka fara waye ne ya fara. Kuna ganinsa zai kashe musu yar mutane bayan kace jiya ka mare ta, yau kuma ka kara rufe ta da duka. Ji yadda take sume ni dai ina shaye-shaye amma wallahi na fi karfin dukar mace kamar yadda kake yin nan ai abin ya koma jahilci kuma!"", daga haka ya fita zai gashi da ruwan gora mai sanyi yana zuwa ya samu fuskata ya zuba min, ajiyar zuciya na sauke ya ce min.."" tashi ki koma part dinki, Yarinyar idan baza du shirya yarsu ba, to su barta ko na kira Baban Jama'are yau wallahi na gaji da iskancinka Hafiz na gaji da muguntarka idan kayi wasa sai na gayawa Abbanmu! "" Sanin cewa dan shaye-shaye ne bai da mutunci zai aikata. Dakyar na tashi na nufi hanyar fita, tunda na shiga parlourna, rufewa nayi na kwanta a saman kujeran parlourn nayi ta kuka ina jin kamar zuciyata zata buga, na rasa gano laifin da nayiwa Ya Hafiz. Zuwan Kabiru na bude mishi kofa nayi na zuba mishi abinci nace ya je yau ba aiki. ""Aunty me ya same ki?"" ""Ba kome!"" Shiru yayi kafin ya ce min. ""Aunty ki yi hakuri kin ji, akwai abinda nake son na kawo miki idan kin amince sai na kowa miki!"" Gyada mishi kai nayi nace mishi. ""Na gode sosai!"" Juyawa yayi ya tafi ni kuma na koma daki nayi wanka na kwanta, buga kofar parlourn da aka yi yasa na fito, na buWe.. ""wani irin abu kazan-kaza ne? Uban waye zai bamu abinci muguwa azaluma ke wacce irin dabba ce. Amma kin iya sakawa wancan dan iskar Yaron ke jaka wawuya wacce iyayenta suke niman kai da ita."" Ni dai tunda ya fara fada na koma jikin bango na makale ban kara sakewa ba. Har ya gama ya bar parlourn, kitchen din na wuce na hada abin karyawan bakiWaya na kai musu. Anan Hajiya ma ta rufe ni da zagi cin mutumci da gorin rashin haihuwa, sai na ji ba zan iya kuka a gabansu ba na fito na dawo dakina, ina zama wayata tana kara wacce take saman center table, dauka nayi fada Baban Bauchi ya rufe ni da shi, har da cewa wallahi na sake na kashe Aurena sai dai na nimo wani uban ba shi ba, yana kashe wayar Mama ta kira ni itama ta min tas har da barazanar zata tsine min,tana gamawa. Ya Umar ya kira ni yana tambayata mai ya faru? Murmushi nayi na ce mishi ba kome." Duk yadda yaso yaji me ta faru nace ba kome wallahi. "Haka wunin ranar ban saka kome a bakina ba, washi gari Hajiya suka bar Bauchi amma ta ce zata dawo" "kwanan don tafiyar ya zame mata dole ne kuma domin danta tayi shi. Sannan tafiyar kusan nice na tura musu kudin mota domin tana zaune ranar Ya Umar ya tura min dubu hamsin ya ce na rike a hannuna," "don haka ta cewa danta a kan idanuna. ""Yayanta ya bata kudi ban san ko nawa ba ne."" ""Shine bakar" "munafuka bata gaya min ba."" Fisgar wayar yayi yana faWin. "" Mai mugun hali! "" Ya fada bayan ya tura dubu arba'in ya bar min dubu goma shima a take ya turawa Matarshi biyar ya bar min biyar, ya je ya cire" musu kudin ya basu dubu sha biyar ya rike ashirin da biyar. Ni dai bance kome ba domin tsoron kada ya kara rufe ni da duka yasa har suka bar gidan ban kara tari ba. "Bayan tafiyarsu da ta tabbatar zasu dawo very soon, haka na cigaba da zama a gidan Ya Hafiz ya min," "Matarshi da Yaransa su min. Haka ya sa bakiWaya na shiga wani irin tashin hankali, idan Yaran suna min ihu wallahi sai naji kamar a cikin kwakwalwar kaina suke ihu hatta jikina wani irin rawa yake lokaci guda sai naji kamar zan mutu, gefe guda kullum sai Ya Hafiz ya bani maganin nan, wanda a cikin sati biyu na" "fara kaunar maganin domin idan ban sha ba, bana iya barci bana iya rintsawa har gari ya waye." "Haka ya kara min kadaici, kullum ina dakina, shima a cikin duhu babu haske. Sannan bana iya" "magana idan na ji muryan Ya Hafiz sai na ji kamar wani abu ya cika min raina, haka yasa tsoronshi ya kara cika min rai da gangan jikina." "Satin Hajiya uku da tafiya sai gata, can gidan da ya saya a zango suka tafi aka ga gidan the next day, ina" "kwance a parlourn sai gashi ya shigo. ""Malama gobe zamu tashi ban ce ki min gayyar mutane ba!"" Ina son na tambaye shi kamar ya gobe zamu tashi? Amma ina d'aga kaina ya bani wani irin tsoro, da sauri na sunkuyar da kaina. Abu daya na iya fada. ""Allah ya kai mu!"" Daga nan ban kara magana ba, tsoron shi da gudun abinda zai yi yasa nayi shiru. Tunda ya gargade ni da kada na gayawa kowa zamu tashi ban sake nayi ko tari ba, amma a cikin raina bana jin dadi haka na shiga hada shirgina ina tattarawa, da taimakon Kabiru muka hada kome na gidan, ya mika min wani leda ya ce min, ki ajiye wata rana idan kika samu lokaci ki karanta addu'ar da yake ciki ko ki saka a miki rubutunsa ki sha akwai amsoshinki a cikinsu, zan yi" "kewar Uwar dakina!""" "Nima godiya nayi ta mishi na rubuta mishi number na, don ba shii da waya, haka washi gari na shiga" "makota na sallame su, sai a lokacin suke gaya min ai su tun sati uku da ya wuce suka san zamu tashi, suka mana fatan alkhairi, na musu godiya sannan muka bar unguwar bayan an kwashe min kayana muka bar unguwar da na dauki tsohon shekaru tara ban yi fada da kowa ba yau Yaya ya d'aga ni daga cikin mutanen kirki ban san inda ya kai ni ba, can zango ya kai mu kusa da titin jirgin kasa, anan ya saya yi gidan. Sai dai ko rabin bangarena bai kai ba, dakuna uku ne, amma kuma suna da girma haka na zuba kome nawa a cikin dakin har ma ya kasa domin idan xan yi sallah sai ka rufe kofar kusan ni daya nayi aikin mai da kome na, sai kitchen da yake waje sai na fito tare da ban daki da yake waje, a da can dakinmu yana da nisa da juna amma a yanzu daga dakinsa sai nawa. Haka a ranar dai a dakina Hajiya ta" kwana akan gadona da danta ni na kwana a dogon kujera. "Washi gari na tashi na fara aikin abin karyawa, ga wani sanyi da yake ratsa ni haka na gama ina" "atishawa. Bayan na gama na kai musu kowa dakinsa, sannan na kawowa Hajiya nata, na koma waje na karya sannan na hada ruwan wanka na shiga nayi, ina fitowa naji kamar zazzaSi zai rufe ni, haka na saka kaya na fito dakin Ya Hafiz, na ce mishi. ""Don Allah ka bani magani bani da lafiya ne!"" D'ago kai yayi yana kallon yadda nake takure wuri guda. Bai ce kome ba, ya ce min. ""Tow!"" Ya tashi ya dauko min har da wanda ya ke bani na sha, ya ce min. ""Ina son na fara ruin nawa business din Ina son kudi amma narasa inda xan samu ko zaki bani aron kudi ne?"" Shiru nayi ina kallonshi kafin na ce mishi.. ""Ai!"" ""Tashi idan kin yi nazarin abinda zaki bani nan kwana uku ina jiranki!"" Haka na fito ina mai barin dakinsa na koma dakina na kwanta, kwanciya nayi haka na fara barci sama sama, na ji an zuba min duka a bayana, bude idanu nayi ina kallon Hajiya ce. "" Kin tashi ko yaya anya ba shaye-shaye kika fara ba? Waye zai daura mana abincin rana yau har da tuwon dare zaki mana! "" Dakyar na mike kaina yana bala'in ciwo, na nufi waje na daura abincin rana, wurin karfe daya na gama nayi sallah na kwanta don ko abincin ban kalla ba, barci yayi gaba da ni wurin karfe hudu na ji an watsa min ruwan sanyi a firgice na tashi Hajiya ce ta saka Yusrah ta watsa min. "" Yawwa takwara gara haka, Uban waye zai mana abincin dare! Mau farar kafa kawai tunda Hafiz ya aure ki, tsiya yake binsa. "" Haka nayi sallah la'asar sannan na wuce na daura tuwon semovita miyar busashen kubewa, abin da na fara fahimta kayan firjina sun fara narkewa gidan ba wuta," "ina cikin wannan nazarin ya Hafiz yanzu da mai aikin wuta, ashe an saka abin invert dinmu bai jona ba ne, haka aka jona mana muka samu wuta, da nazo cin abinci mika min yakin daddawa Hajiya tayi tana faWin.. ""Gashi nan ki na ci da abinci, domin ke na daka na kawo miki . "" Amsa nayi nayi ta mata godiya yaushe na samu gatan da har Hajiya zata min kyauta, ai ko zan mutu ba zata ba ni abinta ba sai ma ta amshi nawa, haka na cigaba da abinda nake, kafin na zubo abinci na fara ci ta ce min. "" Idan ba zaki ci ba, bani abina. "" A hankali na ce mata."" Zanci kai! "" Na bude ledar na fara cin yajin ina barbadawa a cikin abinci. "" Dama sai da na kashe kudi kusan dubu biyar a hada yajin nan, yanzu gashi xan koma bani da sisi dan uwanki" kuwa na mishi magana ya ce bai da shi.... *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu SHIDA "Haka kawai Hajiya ba zata min abu don kanta ba sai dai idan tana da bu™atar wani abu daga gare ni," "shiru nayi domin yanzu bani da kosisi iya dubu biyu ne a cikin account dina, idan na fada ba yarda zata yi" "ba. Don haka nayi shiru haka na kyaleta tana ta rabtabo bayaninta ganin bance mata kome ba, sai ta fara" "masifa ni dai har ta gama bance mata uffan ba, domin nasan kara mata haushi zan yi, haka ta bar dakina zuwa dakin Karimah wacce suke can da Ya Hafiz, suna cin gas meat, shigar Hajiya dakin ta ga sun baje suna ta fama wadaka da abin arziki ga Country Yorghurt a gefensu, zama tayi tana hadiye yawu. ""Yanzu Hafiz haka zamu yi da kai, ka zauna kana cin abin arziki ban da ni. "" Hade rai yayi yana faWin. "" Hajiya matsalata dake baki da hakuri so nake na gama na kira ki! "" Shiru tayi tana kallonshi sannan ya tura mata wani karamin kulli gabanta. Haka ta bude tana tab'e baki alamar ta rena ba haka ta so ba, ta cinye amma" "maganar gaskiya bai ishe ta ba, amma ba yadda ta iya ta nad'e kwadayinta tayi musu sai da safe." "Ina kwance a dogon kujera ta shigo ta kwanta a gadon, bamu jima da fara barci ba invert dinmu ya" "dauke gashi ba maganin sauro, abin ba dad'i haka muka kwana a kuntacce, domin ban saba da irin wannan rayuwar ba, tun tasowata. Haka muka kwana a can dakinsu Ya Hafiz basu yi irin kwanan da muka yi ba, abin sai ya hadu min goma da ashirin, domin dakin wani irin zafi kamar gidan burodi ya Wauka, zarewa ne ban yi ba amma har kusan lokacin da nake tashi sallah dare ban iya rintsawa ba, gashi Ya Hafiz bai bani maganin da yake bani ba, abin sai ya min yawa. Bayan sallah asuba na fito na daura musu abin karyawa da ruwan wanka, na shirya Yusrah sannan nayiwa Yasir wanka na basu abinci, nan Yasir yayi ta kuka har sai da Uban ya fito yana faWin. ""Ke dai azzaluma mace, uban me yayi miki!"" Nasan ba yinsa ba ne, ina da yakinin zai dame na, zai dainaim. Abinda yake yi ya dawo mu shirya kamar baya. ""Ba magana miki ba!"" Shiru nayi sai da ya zaburo kamar zai dake ni nace mishi. ""Ban san me yake damunsa ba"" na fada mishi ina kallon Yaro na yake ta zufa. Karban yaron yayi ya Wan jijiga shi daidai fitowar Hajiya da Karamcy, amai ya fara yi, kuma ai laifina ne tunda na hango ya koshi amma yaki ya daina cin abincin ni kuma na kasa daina bashi wai kada yayi kuka. Sai da ya amayar da abincin da yaci sannan ya sauke ajiyar zuciya. Cikin jin haushi Karimah ta bangaje ni, na taka aman Yaron na zame nayi zaman yan bori. ""Muguwa mai bakar zuciya, ke baki haifa ba. Amma kina son ki kashe min, idan kin yi zuciya ki haifi naki mana. "" "" Gata mata dai ba zuciyar haifa sai na kashi."" Inji Hajiya, ni dai kamar wata sokuwa sai na yi kasake ina kallonsu, ko ya tuna wani abu ne ya fara faWa, da cewa baya son abinda suke yi. "" Luluna tashi da gangan ba zaki cutar da su ba."" Ai kuwa na fara gyad'a kai ina kokarin mishi bayani, haka ya dakatar dani da abinda zan faWa. Haka na tashi na koma daki na sauya kayana, na gyara inda" "Yasir yayi amai na wanke, da yake gidan akwai rijiya." "Ciwon da kaina yake yasa na gyara kwanciyar da nayi a dogon kujera. "" Lulu yunwa nake ji. "" Inji" "Yusrah. ""Na kai muku abincinku wurin mamanki! "" Wani irin ihu yarinyar ta fasa sai da naji kamar ™wa™walwar kaina zai yo waje, wani irin tartsatsi kawai nake ji a cikin kaina, wanda ya tilasta min na dafe kaina, zufa na karyo min. Sai na rasa me yake damuna ga wani irin sound nake ji yana kara a kaina, ji nayi kamar duniyar tana juya min, a hankali na shiga ambaton Allah tare da komawa jikin kujerar na kwanta ina min zuciyata tana wani irin bugawa mai karfi, shigowa Hajiya da Karimah ganin yadda nake ta haki da zufa sai suka ka ja hannun yarinyar suka fita da ita. Ni kuwa suka bar ni cikin wannan yanayin. Karshe har dare ina kwance a wurin, ya shigo suna ta hidimarsu babu wanda ya gaya mishi ga halin da nake ciki, sai da gama abinda ya mishi kafin ya ce musu. ""Yau mugun halin ya motsa taki fitowa!"" Babu wacce ta amsa mishi, haka yasa shi mikewa ya leka dakin dubu babu haske, torch din wayarshi ya kunna" "ya ga halin da nake ciki, ""Innalillahi wainnalihir rajoun, Hajiya Karimah me ya same ta?"" Ya tambaye su," "take suka taso dukkansu suna faWin. ""Tow me zamu sani tunda ita dai bata fitowa cikin mutane."" Da" "sauri ya ciro wayar shi ya kira Abokinsa da yake amsar magani a wurinsa, ™arshe dai zuwa yayi ya dauko abokin domin tun a can ya mishi bayani, shi kuma ya tawo da kayan aiki. Sai da ya fara gwada hawan jini ya ga yadda ya tashi. ""Amma kace matar nan matarka ce?"" ""Eh kai!"" ""Gaskiya akwai wani abu!"" Haka ya cigaba da aikinsa sai da ya saka min ruwa da allurai, sannan ya rubuta mishi magani a sayo min, a lalace dai sai da aka kashe kusan dubu ashirin da biyar, ai kuwa ran shi ya b'aci domin baya kaunar abinda zai" saka ya kashe kudin da ba zasu dawo mishi ba. "Hajiya ta kwana a dakin, amma itama barcinta tayi son ranta." Karimah. """Ni dai ban ga amfanin rike yarinyar nan da kake yi ba tunda ba sonta kake ba, idan har ba sonta kake ba" "ka sake ta ta tafi mana."" A wani hargitsetsan yanayi ya kalleta, kafin ya ce mata. ""Bana kaunar Lubnah ko" "kaWan, amma ba zan sake ta ba. Ita din tsanin arzikina ce sai da na aureta na fahimci ashe arziki a jininsu ne, don haka kada ki kara min wannan maganar.""" "A fusace ta mike tana faWin. "" Gaskiya ba zai yiwu ba, taya zan cigaba da zama da ita bayan duk" "al™awarin da ka yi min bai cika ba. "" Zuba mata idanun yayi yana kallon yadda take masifa kamar zata" "rufe shi da duka. "" Na gaya miki ba zan sake ta ba na gaya miki na kara gaya miki, ina rike da ita ne domin ita din makami ce. """ """ Lallai fa wallahi ba zan zauna da ita ba! "" Ta fada tana ™o™arin mikewa ya janyonta jikinshi yana faWin." """ Ki yi hakuri ita din ta rufa min asiri dayawa, a yanzu da muke tare ina cikin rufin asirinta ne. "" Ya fada yana kallonta. Haka ta hakura amma ita ko zata tafi tsirara sai ta saka shi ya sake ta. Sai tayi sanadin da zata bar gidan in sha Allah. Wannan shine kudirin Karimah gidanta ne gidan Yaranta ne dole ta sakata ta" wahala yadda ranta yake so. "Washi gari na tashi da sauyi ba laifi, a haka na fita na daura abin karyawa. Sannan na hada wanke wanke" "nayi, na share gidan ga jirin da yake ta dibana ina hutawa, fitowa yayi ya ga ina wanke taliyar da na dafa. ""Ina Hajiya ke daya kike wannan aikin ko da yake ai kin saba ne sannu ya jikinki?"" ""Da sauki sosai!"" Shiru nayi ma cigaba da aikin abin karyawan. ""Hmmm jiya ba karamin kudi na kashe ba domin rantowa nayi ko zan samu na mai dawa mai shi?"" Shiru nayi ina jin wani irin yanayi yana yawo a raina, itama jinyar sai dai nayiwa kaina. ""Ya Hafiz bani da kudi, idan na samu zan biya ka."" Hade rai yayi cikin nuna bai san wannan zancen ba. ""Ki kira Hindatu ta baki kuWi ko na tafi da wayarki ko zoben hannunki na je na sayar!"" Wayata kan ba zan iya bashi ba, amma zobe zan bashi domin ina jin kunyar na kira Aunty Hindatu na ce ina son" "kuWi. Haka na cire zoben gwal din na mika mishi, Allah sarki wani tafiyar Aunty Innah umara da Mijinta ta" "kawo min,. Ina son shi domin sunana ne a jikin hatimin zoben wato Lulu. ""Haka zan tafi da shi salon a ce" "satowa nayi?"" Shiga dakin nayi na dauko recipted dinsa, na kawo na mika mishi wani irin kallo yake min yana kallon takardan. ""Kayi hakuri kayi hakuri, don Allah ka yi hakuri, ba zan kara ba. Kayi hakuri "" amsa yayi ya ce min. ""Ki kawo min abin karyawa dakin Karimah!"" ""Tow na gode in sha Allah zan kawo maka!"" Na wuce kitchen din na hada abin karyawan na kai mishi, sannan ya ce min. ""Su yaran mu ne zamu musu wanka?"" Jikina ya Wauki rawa na ce mishi.. ""don Allah Mamarsu tayi musu wallahi."" Wata Uwar ashar ya lailayo ya maka min, wanda ya janyo min shiga dakin da sauri, ganin yadda take kusan tsirara a kwance yasa ni juyawa na ce musu. ""Bari na hada ruwan!"" Haka na hada musu ruwan nazo na dauke su, ihun da Yusra take tana wani zakewa yasa ni muka zube domin kaina ya fara sarawa ai kuwa ta fasa ihu suka fito, ganin yadda muka zube na tashi da kyar ina faWin. ""Zamewa nayi!"" ""Ba dole ki zame ba, kina nan kamar buhun gawayi, ni kan kada ki kashe min Yarana!"" Inji Karimah haka na fara mata wanka yarinyar nan tana ihu da yakushin fuskana tana kuka da dukana, babu wanda ya mata tsawa. A haka ta saka min yatsa a cikin idanuna, hawaye ya zubo min, na wanke ta na kaita wurin iyayen nan ma suka sani na shiryata." "Na fito da Yasir shima haka ya gama zamaninsa, sannan na koma daki na sami Hajiya tana ta shirin tafiya. ""Tow ni dai zan tafi yau ba zan iya kara zama a garin nan ba!"" Ta fada tana fito da kayanta waje." "BakiWaya nima haka na biyo ta, koda danta ya fito suka fita, ta ce min. ""Ina binki bashi dubu biyar idan kin samu ki tura min kada ki bashi ya turo min tijani zai turo miki number account din da zaki tura min."" ""Tow Hajiya in sha Allah!"" Na fada haka suka tafi na shiga kitchen na hada abin karyawan da zan ci na koma dakin ina kallon roban karin ruwan, can wurin karfe goma sai ga Ya Hafiz da mutumin da ya saka min ruwan, haka ya gama duba ni sannan ya kara min wani ruwan, a ledar da Ya Hafiz yazo da shi maltina ce da fruit, ya ajiye min yana ta min sannu. Yadda ya damu sai da abokinsa ya ce mishi. ""In sha Allah idan ta bi sharaWin da zan gindaya mata ba zata kara shiga wannan yanayin ba, sannan ta cigaba da shan magani. Domin hawan jini mugun ciwo ne!"" Gyada mishi kai yayi sannan yayi ta damuwa da halin da nake ciki, har shi mutumin ya gama aikin da yake ya fita. Ya kalle ni yana faWin. ""Me yake damunki haka da zamu daurawa kanki damuwa har hawan jini ya kama ki?"" Ni dai ban ce kome ba, domin ba ni da abinda zan fada. Bayan ya gama surutunsa ya tafi nima ma samu barci, wurin karfe biyu saura na farka lokacin ruwan ya kare na cire na sannan na wuce nayi alola na gabatar da sallah, na bude friji dina na dauki zabuwa guda biyu na kai kitchen na zuba musu ruwa da na saka a kitchen din don ba zan iya" kowani aiki na ja ruwa a rijiya ba. "Sannan na wuce ban daki nayi tsarki na dauro Alola nazo na gabatar da sallah azhar, tea na hada na" "sha kafin na sha magani na fito waje aiki. Sosai na mai da hankali kan aikina, buga gidan aka yi na mike na je na bude makotanmu ne, na bude suka shigo suna ta fara'a. ""Sannun da zuwa, sannu mu shiga daga cikin."" ""A"" a waje ma ya isa wannan zafin ai kuna shan fama musamman wacce take wannan dakin zata fi kowa shan zafi ita da jin sauki sai ko damina ko hunturu."" Murmushi nayi bayan ma shiga daki na dauko musu kafet na shimfida musu. Sannan na shiga na dauko musu pure water na ajiye musu ina kara gaishe su. Sun amsa sannan na ce musu ."" Bari na kira muku abokiyar zamana! "" Na tashi na buga kofar Karimah dakyar ta fito tana wani hade rai, suka gaisa sama sama, sannan ta koma wata yar yarinya ce ta bani sha'awa, na dauke tana ina faWin. ""Ina Mamanta!"" Murmushi Mamar tayi tana faWin. ""Sunanta Suleimin"" gashi yarinyar tasha wanka an gyarata. ""Allah sarki sunana Lubabatu amma ana kirana da Lubnah!"" Fitowar Yusrah ta ce min.. ""Lulu zan sha tea!"" ""Tow ina zuwa!"" Na shiga dakin da kananun" "kofina uku na hada har da na yarinyar na fito waje na mika musu itama yarinyar na mika mata. ""Har da" "dawainiyya!"" Murmushi nayi ina kallon yarinyar, don ta shiga raina duk inda zan ga Yaro kamar na dauke" "shi nake ji, haka muka yi ta hira ina leka kitchen din, dab Magariba suka min sallama, sannan suka min bayanin gidansu ne a bayan na mu, ita babbar cikinsu sunan ta Maman Abidah ta aurar da ita ma, sai yan mata biyu Na'ilah da Na'ima, sai ta gefenta ita kuma Maman Boy da alamu ita kamar yare ce, Yaronta daya Boy tana sayar da kayan miya da sauransu, sai Maman Suleimin, sai wata kamar Amarya ta ce min. ""Ni amarya ce! Akwai Maman Salim da Maman Yaya basu gama aiki bane amma zasu shigo gobe!"" Na" "musu godiya na rako su waje, suka tafi. Na dawo na karasa aikina tare da jollop din macaroni." Wurin karfe bakwai ya shigo shi da likitan ya kara duba ni ya saka min ruwan karshe sannan ya bani "shawara yadda xan kula da kaina, sannan ya tafi Ya Hafiz ya ajiye min leda bag din da ya kawo min, ya shiga buWewa, yana faWin. ""Gashi nan ki ci, amma ki sani kudin wannan abin da nake miki shima dai rantowa nayi!"" Gyada kai nayi nace mishi. ""Na gode!"" ""Ba fa batun godiya biya zaki yi ai kin sani biya zaki" "yi a tow!"" Daga nan ya mike ya bar dakin." "Sauran kwanakin da suka biyo baya, na ji sauki makotana sun shigo, bayan kwana biyu nima na" "shiga musu muka gaisa sannan na dawo, nayi haka ne don fita hakkinsu, sannan a gefe guda Karimah tana d'aga min hankali rigimar yau daban na gobe daban, haka yasa kullum ya dawo sai ya ji kamar ya" "rufe ni da duka, haka xan ta bashi hakuri." "Kusan wata mun Waya a zango, Ya Hafiz bai tab'a cewa na kira gida na gaya musu mun tashi ba, sai da" "ya ji a ransa. Ya kalle ni da zai tafi kasuwa ya ce min. ""Yau ina ga zaki yi baki me nene babu a gidan?"" Shiru nayi kafin na ce mishi. ""Kayan miya, shinkafa ma ya kare"" nayi ta mishi lissafin abinda babu, koda ya fita wurin karfe goma sai gashi da kayan abinci niki -niki, ya kawo dakina ya ajiye su kwalin madara da milo duk ya kawo dakina ya zuba, sannan ya sakar min murmushi. Tunda na ga haka na fahimci akwai wani abu a kasa, sai dai kamar kullum ina mishi fatan shirya sannan ina da yakinin zai daina abinda yake" yi. Haka na dawo dakina na kara kintsa dakin na fito na daura abincin rana. Ina waje wayata da babu "chaji yayi kara na shiga dakin. Ya Umar na gani kamar nayi kuka na Wauka. ""Yanzu Lubnah kin kyauta baki gaya mana kun tashi ba? Har shi Hafiz din ya iya gaya mana?"" ˜asa magana nayi ina jin shi. Yayi ta fada sannan ya kashe wayar, Aunty Hindatu ta kira ni. ""Auta me ya faru?"" Murmushi nayi mata nace mata. ""Ba kome Aunty!"" ""Lubnah idan kika cigaba da shiru taya zamu taya ki wannan yakin, wannan ba hujja ba ne, Lubnah ki bude baki kiyi magana ki gaya min me ya faru?"" ""Ba kome!"" Na kara fada mata, ""Lubnah ina takardun gidan can?"" ""Don Allah kada ki tambaye ni, don Allah kada ki saka min magana! "" Na fada kamar zan yi kuka, murmushi tayi ta ce min. ""Shi kenan idan kina bukatar kudi zan turo miki da" "dubu dari!"" Ban ce mata kome ba, ta kashe wayar. Zuwa yammacin ranar sai ga Aunty Innah ta shigo ita" "da Aunty Jamilah matar Ya Umar, ganin gidan yasa duk suka yi shiru. Ni dai ban ce musu kome ba, shine" "dai yayi ta fada yana faWin. ""Ai ban san me ye matsalar Lulu ba, ace bana gari domin Allah ya gani nayi tafiya kusan wata guda nayi tare da Karimah kuma na bar mata yaran jiya da muka dawo nake tambayarta ashe bata gaya muku, ai har nayiwa Baban Bauchi bayanin dalilin tashinmu, amma in sha Allah kafin nan da wata shida zamu koma wani hatsari ne ya faru amma an shawo kansa. "" ""Allah ya" "kyauta ya kiyayye na gaba!""" """Amin Ya Allah, Luluna idan zasu tafi ki diba musu tsaraba nan, akwai wasu a dakin Karimah bari na" "kawo sai ki hada musu."" Ya tashi ya fita, can sai gashi dauke da jaka cike da fruit, ya kawo musu da Naira dubu goma a ciki wai su yi kudin abin hawa, Aunty Innah ce ta kawo su a motarta, bayan fitarsa da ya ce musu bari ya tafi muda lawan akwai kayan da aka kawo zai je ya duba, ya fita Aunty Innah ta kalle ni yadda nayi shiru. ""Tunanin me kike yi?"" Ta ciro kuWin da yake cikin jakar ta ajiye min a gefena. ""Mu yan uwanki muna jiranki duk lokacin da kika shirya ba zamu kashe miki aurenki ba!"" Tana gama fadar haka suka mike tare da barin kayan ma bakiWaya basu dauka ba, domin tun kafin su fita Karimah ta fita da" "Yaranta, aka bar ni a gidan ni daya tal." *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu BAKWAI "Zama nayi ina nazarin makomar rayuwata, me nayi na kuskure? Duk da ina son Ya Hafiz amma ban san" "me yasa yake jin dadin daura min laifi ba, shi ya hana ni gayawa mutane, yanzu yazo yana faWin ni ce me yasa yake min haka ne? Me yasa tow? Dama soyayya tana zama kiyayya ne? Ina cikin wannan tunanin Baban Bauchi ya kira ni, wato Abbanmu yayi ta min fada yana faWin nayi haka ne don ba lalata zumuncin da yake tsakaninsa da Wan dan uwansa, wallahi ban isa ba. Haka ya gama fadar shi nace mishi yayi hakuri. A hankali kuka ya zo min can kuma na fara dariya kamar mahaukaciya, domin haka ne kawai zai saka ni" jin dadi. "Tunda na fahimci dariyata tafi kuka saka ni nishadi, na saka a raina na daina kuka akan Ya Hafiz, zan yi" "dariya. Aunty Hindatu ta zo ita da Ya Sani suka ga gidan, babu wanda yayi magana har suka fita. A ranar Aunty Hindatu ta kira Ya Ado ta gaya masa. Murmushi yayi yana faWin. ""Hindatu dadina dake baki da hakuri, mutane biyar suke da iko akan wannan lamarin Baban Bauchi, Baban Jama'are, baba malam, sai ita Lubnah idan ta ce bata yi duk inda nake zan kwana a Bauchi, amma fa sai ita da kanta ta ji a ranta bata yi duk abinda zamu yi ba yadda muka iya."". ""Amma kasan ya sayar mata da gidanta na Tambari?"" ""Tow ya za ayi tsakanin mata da miji sai Allah idan ita ta bashi fa!"" ""Ado kasan sai Lulu bata da hankalin da zata bashi gida ya sayar ko? "" "" Tow waye ya sani kin ga idan tana bukatar wani abu ayi magana batun gida dama ai an saya mata ne domin su huta da Yawon gidan haya tunda ya sayar ya sayi wani."" "" Amma ai a getto area ne! "" "" Ba gashi ta zauna har na wata guda ba ta gaya miki ne?"" Shiru tayi ya cigaba da magana. "" Baba da Mama sune suka involved din rayuwar Lubnah, idan da zasu tsaya mata Lubna zata samu yanci amma fa sai taso idan bata so ba, kuwa koda su zasu shiga ba zata matukar bata bada hadin kai ba. Babu yadda zamu karshe sai dai shara'a tayi aiki kanmu haka magatakarda kin manta da dokar ce. "" "" Ba dokar na manta ba, na hango tashin hankali da bukatar taimako, bata bukatar kome amma kuma" "idanunta yana kukan tsoron da niman taimako, wallahi Lulu da ka sani ba ita ba ce a gabanmu""" "Dakyar ya shawo kanta Ya Sani ya ce mata, ""Ni dai na rasa me shegen Yaron nan yayiwa Abba ne da" "baya kaunar laifinsa, ki ga yadda Lulu ta koma don Allah? Ko ni da nake zukar wiwi wallahi ban ga dalilin dariyar da take ba, ki ga yadda take abu kamar wacce take cikin tashin hankali.""" "Kwafa yayi suka cigaba da tafiya," *** "Ko Ya Hafiz ya ji abinda yake faruwa ne, yadda Yayuna suka fusata, sai gashi ya tafi har Jama'are wurin" "Kakanmu, suka tawo tare yadda mutumin nan yake da mugun hali na tsane na bude idanun na ganshi, domin shima ya taka rawar lalata min duk lissafina, haka yayi ta fada da nuna kada ya ji kada ya gani domin yaji labarin ana son a kashe auren Lubnah da Hafiz, idan suka kashe auren waye zai aure ni?" "Sannan ga misali a gabansu Jalilah tunda aurenta ya mutu waye ya zo da sunan zai aure ta, kada ya ji" kada ya gani. "Abin da basu sani ba ita Jalilah Ya Hafiz take so kamar tayi hauka, duk aurenta uku da tayi ta kasa zama a" "gidan aurenta ne domin tana da yakinin wata rana ya Hafiz xai dawo gare ta. Haka abin ya cigaba da tafiya ba dad'i, a lokacin Ya Hafiz ya tsiro da wani hali shi da Matarshi." "Abinda suke mun ba kome ba ne, sai nuna min da suke ni rayuwata bata da amfani, domin ido da" "ido ya ce min. ""Lubnah baki da amfani a rayuwata, amfaninki kalilan ne, idan aka cire amfanin rashin" "amfanin yafi yawa, kin ga wallahi ko bukatarki na dabi'ar da namiji bana ji, ke kanka dube ki, yanzu ace" "na sake ki waye zai aure ki? Wallahi babu namijin da zai tab'a sha'awar aurenki domin baki da wani abin burgewa mace sai kace saniyar huWa! "" Ire-iren waWannan maganar da yake gaya min ya haifa min da" wani irin yanayi. "Yana yawan gaya min cewa a yanzu dangi ma basu bukata na, babu wanda ya damu da ni, itama" "Hindatu don kudina da yake hannunta ne, idan babu ba zata kara kula ni ba,haka muka cigaba da jin kamar ba ni da wata amfani a rayuwar Ya Hafiz. Tunda ban haihu da shi ba, bani da wani abun da zai burge kowa. Ni kaina nasan be zama dole wani ya bukaci ni a rayuwarsa ba. A hankali na dinga jin kamar" ni din ba kowa ba ce bani da sauran amfani. "A haka watan azumi ya karato, ba zata Baba yayi mana, ya biya mana umara ni da Yayuna. Sai dai me?" "Ya Hafiz najin haka yayi ta kunci da bakin rai tare da rigima da fitina kala-kala, karshe dai ban san yadda aka kare ba Baba ya ce ya cire sunana a cikin masu tafiya yayi replace da Jalilah. Wani irin bugawa zuciyata tayi kamar zata fito, a hankali na kama dariya ina jin kamar ni daya ce bani da amfani a duniyar nan, haka watan azumin nan suka yi shi a can ni ina gida, a lokacin na kara koyan yadda xan bawa kaina nishadi. Sai na fara tunanin sana'a bayan sallah, wanda shima a wunin sallah ya ce ba zan je ba. A Jama'are zamu yi sallah, nan ma na amince muka tafi. Muna dawowa nazo da madaran kuka. Na fara sayar da kankara da Pure water, ta nan bai hana ni ba. Sai dai ya daina bani kudin cefane. A hankali na kara har da zobo da kunun aya da fresh milk. Haka su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka zo min gidan, wuni da Yaransu nayi ta hidima gashi bana iya zama idan nayi baki abu ba abu ba sai dariya. Haka suka yi" "ta kuka a daki, wunin da basu yi ba kenan." "Wani abin da na fahimta shine Ubangiji ya saka albarka a kayan ruwa, domin lokacin sallah layya, nayi" "ciniki har na ji tsoro, ana kawo min ruwan pure water har gida ake sauke min rabin mota, a lokacin da Ya Umar yazo gidan ya dauke karamin firji din a ranar aka kawo min babba deep freezer, wnada nake zuba jakan pure water ashirin ga kayan sanyina a gefe. Yadda kudi suke shiga da fita yasa Ya Hafiz ya fara tashin hankali na fara kudi xan rena shi, idan nayi abinci bana saka nama a wadace ai da can ba haka nake ba, nayi ta bashi hakuri ashe zai zare min tallafi da yake ne, domin ya daina kawo abinci gidan. Haka dai na kara tsayawa a tsaye sai Allah ya yaye mun dariyar da nake, sai dai duk niman da nake ina bawa" Ya Hafiz ne domin bayan na cefane da nake yi kudin kusan shi nake bawa. "Maman Na'ilah ita ce ta tambaye ni aron kudi, na ji tsoro ban iya bata ba. Karshe kamar wacce ta" "matse ni na gaya mata ai kudin wurinsa yake, zuba min idanun tayi kafin ta ce min. ""Lubnah da hankalinki kuwa?"" Shiru nayi kafin ta cigaba da cewa.. ""wacce irin soyayya kike yiwa mijin nan naki ne? Kin san mun san kece kike dauke da hidimar gidan?"" ""Ba kome ai dan uwana ne."" ""Na ji ba wannan ba," "daga yau zaki na kawo dubu uku akwai adashe da muke yi zaki shiga ai zaman tare ta wuce haka, ga" "yayarki nan wata siririya muna haduwa a asibiti ba karamin taimako take min ba, don Allah ki na kawo kudin! "" "" In sha Allah!"" Na fada tun daga ranar ban yarda na kai mata ba, domin kamar wanda aka" "gayawa Ya Hafiz, kullum sai ya kirga abinda nayi yasan na kudin da yake ciki, idan ya dawo zai tambaye ni." "Haka zan dauki kudin cinikin na bashi na mishi lissafin abinda aka kashe, ita Matarshi bata kome ni ce" "dai akansu, haka dai muka ta mikewa abin ba dad'i, kwatsam aka tashi wani biki, Aunty Innah ta kawo min aikin Kunun aya da zobo, domin suma ina bayarwa a kai musu har gida, a lokacin aikin zai min yawa na shiga gidansu Maman Na'ilah na roka su zo su tayani. Haka muka yi aikin dasu. Sannan ka zo aka dauka, washi gari muka sake yi sai da muka yi kwanaki uku muna aikin kafin aka kawo mana kudin aikin naira dubu hamsin, na dauki 20k na basu talatin, Maman da tazo ta kwace ashirin din ta tafi da shi, ban san me yasa matar nan take min karan tsaye ba, amma naji haushi, wasa wasa sai ga Mamansu Na'ima ta saka ni a gaba da amsar kudina ko ina so ko bana so zata dauka, haka muka yi ta fama da ita daga baya da kaina nake tura mata kudin ma, ta daina zuwa. Ban san manufarta ba amma tabbas ta wani" gefen tayi min abinda jinina suka gaza min. "Haka watan azumi ya kara zuwa, ita ta bani shawarar na ajiye kayan za™i na koma sayar da ™an™ara. Ba" "sai ya Hafiz yayi tsaye ya ce bai yarda ba. Sai dai idan zan sayi generator, na ce mishi. ""Ya Hafiz tow ka ba Ni a cikin kudin wurinka mana!"" Ai kamar ya rufe ni da duka. ""Ba zan bayar bada wutar gidana kike amfani."" A lokacin na rasa yadda xan yi ina jin kunyar amsar kudin wurin Maman Na'ilah, sai na kira Ya Sani na tambaye shi nawa ne kudin generator? Tunda sune suke sayarwa. Ashe nayi wayar a kusa da Ya Albashir, sai cewa yayi me zanyi da shi? Na gaya mishi gaskiya washi gari sai ga Mikano daidai da zata" dauki freeze na har da karin freeza. Nayi ta godiya aka turo masu aiki suka min aikin tsaf na sauka akan wutar gidan Ya Hafiz shima dai ai "yana morar generator tunda kowa yasan watan azumi a lokacin nepa suka tadda iskancinsu, ga lokacin ana wani irin agazarin rana." "Duk yadda xan fada farin cikin da nake ciki, kamar na boye ne. Ganin duk yadda zai Sullo min ina" "toshe hanyar don bana son muna rigima, ba sai ya tsiro da fitinar cewa sai dai na kama haya dakin da nake ina biyan kudin wata wata da ruwan da nake tarawa a wajen shima ina biya. Haka na amince na ce nawa xan biya? "" "" Duk wata dubu goma! "" Shiru nayi kafin na ce mishi.."" tow Ya Hafiz ba ragi ne? "" "" Sai dai ku fitar min da kayanki a gidana!"" "" Shi kenan! "" Haka na amince ai ba wani abu ne, haka nayi ta niman kudi ya Hafiz yana amsa da sunan nashi, da sallah yayi nayi musu Winkin sallah don ya ce min hakkina ne nayi musu tunda ai ina samu, nayi mishi nayiwa Yaranshi da matarshi da Yan'uwansa na tura" "har Jama'are aka kai musu, har da Baban Jama'are nayiwa Baba Malam ne ko da wasa ban mishi ba, ai" "kuwa na sha zagi ya kira Baba ya gaya mishi, Hafiz ya bani kudi nayi musu kayan sallah amma naki, haka" "Ya Hafiz ya fada. Sannan ya kara da cewa har su Mama da Yadiko nayiwa, amma a kuWina a lokacin sai da na kwashe kome nawa na sayar har da dan kunnen gwal dina, tow bani da kudin ina sana'a kudin na" hannunsa. "Bayan sallah ina cikin azumi sitta shawal, na fara sauraron karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i" wanda ban tab'a jin kalmar ba sai yau. Ba dai na kara nutsuwa ina sauraren dalilan da suke kawowa ayi shi.. *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu PAID BOOK TAKWAS "Wato akwai wani abinda hankalinmu baya kai sai wani dalili mai girma ya shato shi cikin rayuwarmu, ban" "tab'a nazari akan khulu'i ba, amma kuma me yasa na damu? Me yasa nake son sani akanshi? Kawai sai naji abin bai min na cigaba da nazari akai ba, kawai zan cigaba da zama da fahimtar iyayena. A bangaren Ya Hafiz kuwa nadan wata rana zai dawo yadda muke zai kaunace ni sama da baya, amma kuwa zai yi" haka. Bayan sallah da sati uku. Weekend "Ina aikin hada zobo na dauke tukunyar fresh milk, koda yake ya jima da na sauke amma da yake yana da" "wuyar sha'anin, sai na ta saka idanun akanshi saboda Yaran nan da zarar na sauke tukunyar fresh milk sun ta kara kaina akai kenan, har sai na hada na basu. Hankalina yana kan zobo wanda nake ta saurin haWawa. Sai naji an tab'a murfin tukunyar, da sauri na juya Yusrah ce rike da kofi ta bude tukunyar fresh" "milk din zata har ta saka kofin ta dibo da yake na juya mata baya, a matu™ar razane na kalle ta ina faWin." """Gaskiya Yusrah bakya jin magana maza rufe min ki mai da kafin na zo wurin."" ""Ba zan mai da ba."" Ta" "fada tana kallon cikin kwayar idanuna, abin da ya bani haushi da takaici yanzu ta kone Iyayenta su ce na konata. Mikewa da zan yi kuwa ta kwasa da gudu ai kuwa sai gashi ta taka ledar Bevimix ta zame bakiWaya fresh milk din ya kware a gefen kirjinta, abinka da zafi sai kuwa ta fasa ihu wanda yayi daidai shigowar Mahaifinta da fitowar Uwarta a dakin, wani irin bugawa zuciyata tayi na tsaya cak kafin na karasa da sauri nace mata. ""Kin ga abinda nake gaya miki ko?"" Na yi maza na shiga daki na dauko kamun da aka niko min zan yi kunu na sha na watsa mata a kirjinta bayan na cire mata rigar, bakiWaya iyayen babu wanda ya ce min ci kaina. Haka na zaunar da ita na cire mata rigar ba wani tashi wurin ba, amma yadda take kuka da ihu yasa Uban ya karaso ya bangaje ni sai da na fadi, sannan ya dauki yar ya fita da ita, wasa wasa basu dawo ba har dare habaici da cin mutumci babu wanda Karimah bata min ba, ni dai bance mata uffan ba, wajen karfe biyar Mama ta kira ni. ""Kin kyauta Lubnah wacce irin kishi ne haka yake damunki?"" Bata ba ni damar magana ba. ""Saboda kishi zaki kyale yarinya kamar Yusra ta kona" "kanta?""" "Ni dai ™asa magana nayi har sai da Mama ta ce min. ""Saboda mugun nufinki Allah ya hana ki" "haihuwa domin da ya baki da Yaranki zasu dauki mugun halinki!"" Komawa daki nayi na zauna shiru. Haka Baban Bauchi ya kira ni ya ce sai ya ga wanda ya isa min, wasa wasa sai ga al'amarin ya girma yadda ban zata ba, yusrah kwantar da ita aka yi a gadon asibiti. Sannan wacce take gudun Mama ce. A wannan lokacin na ji duniyar ta min zafi, kaf duniya mutum daya ce ta fahimce ni Aunty Hindatu, dole na bawa Aunty Hindatu special respect a duniyata, ita kaWai sai Ya Ado suka fahimci abin domin abin ya faru da kwana biyu Baban Bauchi ya zo har gida ya saka aka kwashe kayan sana'ar aka fita da su. A wannan lokacin Ya Hafiz ya zata ni yayiwa mugunta. Ya zata ni ya rusa tabbas ya Hafiz ya rusa ni, sai da na kusan zarewa domin babu wnada ya saurare ni, kowa ya juya min baya sai Aunty Hindatu da ita Waya ce take rarrashina, kwana Yusrah biyar a gadon asibiti Hajiya da Baban Jama'are suka iso a ranar Karimah ta" dauki matakin da Baban Bauchi ya goya mata baya. "Ina zaune wurin karfe biyu na rana aka yi sallama a gidan, fitowa nayi ina amsa sallamar. Yan sanda ne" "mata biyu suka shigo. ""Sannunku da zuwa!"" Yadda nayi magana a matu™ar tsorace. ""Kece Lubabatu Usman Umar Jama'are?"" Jikina ne ya dauki rawa. ""Eh nice!"" ""Ok ko zaki zo muje office din Yan sanda!"" Ji nayi kamar ina yawo a saman iska. ""Akan me zan bi ku Office dinku bayan ban yi kome ba?"" ""Eh tow idan muka je zaki ji abinda ya faru!"" ""Tow bari na kira mijina;"" na shiga kiran Ya Hafiz amma bai dauka ba, haka nayi ta kiran Yan uwana har Baban Bauchi na kira Babu wanda ya dauka, sake magana suka yi na fito ko su shigo dakin. Haka na fito a sanyayye da hijab har kasa. Ina kara kiran Aunty Hindatu. Daidai na shiga bayan motar. Dauka tayi tana faWin ""Auta yi hakuri bana kusa ne!"" ""Aunty Yan sanda sun zo zasu tafi da ni!"" ""Akan me?"" ""Ban sani ba Aunty! Don Allah ki zo!"" ""Shi kenan gani nan zuwa!"" Haka ya kashe wayar muka Office din Yan sanda da yake dutsen tanshi, anan na samu Karimah ashe shirinta kenan ita da Uwanta da iyayenta, muka shiga suka amshi wayata da kome suka tura ni cell suka ki min magana, ina zaune wata yar sanda ta shigo ta d'aga hannu tayi ta kifa min mari, yan uwan Karimah suna faWin. """ "Saboda kishi ne ita Allah bai bata haihuwa, koda yake ta kashe mahaifarta da maganin hana daukar ciki" "shine bari ta kashe yar kishiyarta, Allah ya sa yarinyar ta auna arziki!"" An tozarta ni, an ci mutuncina haka" "na kasa ko kuka sai sunkuyar da kai da nayi idanuna bana gani. Muryan Ya Hafiz da naji yana ta fada a waje. "" Akan me zaki shigo da hukuma cikin maganar? Ko an gaya miki ban san yadda zan yi ba ne?" "Gaskiya kin bata min rai yanzu da wani idanun xan kalli iyayenmu?"" Yadda Ya Hafiz yayi ruwa yayi makarbiya yasa ni shiga rud'ani amma ai ya ga kirana. Fada sosai yayiwa Karimah, Aunty Hindatu da Ya Umar da Ya Albashir suka karbi belina, haka na fito kamar wacce ruwa ya mata duka, fuskana ya dan kumbura saboda marin da yar sanda tayi min. A hankali nake takawa har wurin motar Ya Hafiz da ya nuna shi xan bi na je nayi wanka. Haka muka bar office din zuwa gida, a hanya yake cewa. "" Kin san ina sonki, sannan abinda ya faru nasan bakida laifi Yusrah ta gaya min, amma kuma ita mahaifiyarta ba zata ji dadi ba idan na nuna baki da laifi don haka ki amshi laifinki ta haka ne kawai zaki wanke kanki kowa zai gane cewa bada wata manufa kika yi ba!"" "" Ya Hafiz me yasa?"" Na tambaye shi, "" Me yasa ka zabi kuntatta min? Me nayi maka da yake damunka har haka? A sanina ban maka wani abu ba? A sanina ban cutar da kai ba, ina saka ran wata rana zamu koma kamar baya kamar farko-farkon aurenmu, Ya Hafiz duk irin shirun da nayi na cancanci haka daga gare ka?"" Shiru yayi da alamar maganar ya ratsa shi kenan. "" Ka saka kowa ya tsane ni, ka saka kowa yana jin haushina, idan abu ya faru ba zaka gaya musu gaskiya ba sai ka bar maganar a daura min laifi me yasa sai ni? Ya Hafiz rabon da ka nemi ni a shimfidar aurenmu shekara kusan guda dawowarmu zango na gaji wallahi na gaji ka sawwake min nima na gaji!"" Na fada ina kuka domin sai yanzu nake jin kamar bakina ya buWe. "" Ko na sake ki ai baki da wanda zai aure ki?" "Lubnah ki kalli kanki da kyau har abada babu namijin da zai tab'a jin sha'awarki, Lubnah na ajiye ki ne domin kowa yasan ina ™o™ari da mugun halinki, ke har kina da bakin da zaki gaya min magana? Bayan na rufa miki asiri ne, jaka me kama da alade kalle babu abinda wani zai gani na burgewa a tare da ke kazama wawuya, kuma daga hau sai na hana ki farin ciki."" Haka muka isa yana zagina da cin mutuncina har nayi wanka kai karewar masifa kofar ban dakin ya shigo yana cin zarafina. Haka na gama na shirya muka tafi cikin gidan inda Yusrah take da iyayenmu, anan ya min barazanar matukar nayi magana sai ya" sake Baban Bauchi wato Babanmu ya tsine min shi kuma ya sake ni domin ba zai zauna da tsinanniya ba. "Lokacin da muka isa gidan Baban Jama'are yana nan haka Hajiya ma, sai Iyayena da yan uwana." "Tunda na zauna aka bude taron da Addu'a. Aka rufe ni da fada babu wnada ya ji yadda kome ya faru haka na sunkuyar da kaina ina jin Baban Bauchi yana faWin. "" Munafuka ban da kishi da munafunci me kika ajiye ace har degree gare ki ya zama na banza. Sai bakar kishi tow da abinda kike takama da shi na kwashe dama yana gaya min tunda kika fara sana'a kika sauya bakya jin maganarshi, kin yi sabi iyaye masu daura miki mugun abu akanki wallahi kin ji kunya."" "" Amma Baba ya kamata a ji me ya faru? "" Inji Aunty Hindatu, da take wani irin cirra, juyawa yayi a fusace ya zabga mata harara, ya rufe ta da fada da cewa ai ita take zuga ni, haushi ya sa ta bar parlourn ma don bakin ciki haka Baba Malam ya amshi fadar yayi ya ce min. ""Yanzu kin kyauta abin da kika aikata? Da Asiya kike kishi ko da Uwar Asiyah? Yanzu ban" "da mun fi karfin yarinyar nan ina sai dai kotu ta shiga lamarin nan?""" """Malam wallahi ban san cewa haka dai faru ba,.Malam na rantse da Allah ban yi haka domin kona yusrah" "ba yayi hakuri ba da gayya ba ne!""" "Zuba min idanu Malam yayi yana faWin..""Allah ya kyauta amma ina amfanin kishi irin naki? Akan ki aka" "fara kishiya ne?"" Cikin shashekar kuka na ce mishi. ""Wallahi ban san zata shiga ban dakin ba, ka yarda da ni!""" """Kai yanzu Hafiz me ka gani?"" Juyawa yayi ya kalli Baban Bauchi wato mahaifina ya ce mishi. ""Duk abinda" "Baban Bauchi ya ce ai shi kenan!"" ""A'a Hafizillah kada ka cutar da kanka, na ga ™o™arin zaman da ka yi da" "Lubnah idan ba zaka iya da mugun halinta ba sakota na gaji da kullum ana abu daya a cikin shekaru goma kullum Lubna tana saka ni magana.""" """A'a Usman, Lubna ko bata auri Hafiz ba, akwai alakar jini balle kuma alaka ce da ta haWa da ta zuci," "ai ta ce ba da gayya ta konata ba kuma yadda ake ta ririta al'amarin da na ga ciwon ai ba wani babban al'amari ba ne, lamarin mata ne kawai da ririta lamarin da bai kai ya kawo ba, yi shiru Y'ata share hawayenki. Kul na kara jin wani yayi magana da cewa za a kai batun nan ga hukuma kunar da bai wani tashi ba, ga yadda yayi baki kasan ai ba zai tashi ba, sannan kai Hafiz ka tuna akwai ranar da zamu tsaya a gaban Ubangiji, ka ji tsoron Allah kada son zuciya ya kai ka ya baro ka, kawai jikina yana bani haka kawai" "Lubna ba zata aikata kome ba.""" "Kunya ce da bori tasa shi, kame-kame amma a cikin ranshi bai so haka ba yasan Baban Bauchi da za a" bar shi sai ya mari Lubnah shi yanzu yadda zai bakanta mata rai yafi bukata akan wannan abin. "Duk da an ce yau da gobe bai bar kome ba, Iyayena da dangi babu wanda ya hango mutuwar" "tsaye da nake yi saboda Ya Hafiz, Babu wanda ya yarda da cewa ina cutuwa, a'a kowa gani yake kamar ba cuta ba ce ni ce nake cutarsa saboda shi mutumin kirki ne, bayan shi ya shiga rigar mutanen kirki ne. Yayi ado da kwalliya a cikinsa, sannan babu wanda zai kalle shi ya ce mutumin banza ne. Amma bakin maciji ne sanye da tufafi yan adam, haka muka bar gidan, bayan an mana nasiha. Ni dai nasan cewa zuciyata ta gama mutuwa bani da wata amfani. A hankali gidan ya zame mini kamar hell fire, bani da kwanciyar hankali bani da sukuni, idan abin ya dame ni sai na rufe kaina a daki na ki fitowa, a hankali abubuwan suka ta tsanani domin kuwa na daina sayar da kome na daina yin kome, shi kanshi Ya Hafiz da ya fahimci bani da wani amfani sai ya cigaba da azabtar dani da abubuwan da zai saka na ji har na tsani" "zaman gidan, damuwa ya kara tsananta min domin ba wani abu ba ne su min gorin haihuwa." "Bayan wata biyu kusan watan Mauludi, Ya Ado ya dawo, ni ya fara kira a lokacin babbar wayar hannuna" "na sayar domin Ya Hafiz ya zo ya saka ni a gaba yana son kudi haka na hada da wayar da sarkata ta gwal na bashi, kunsan me a duk lokacin da zai same ni yana bukatar wani abu tow ba irin yaudarar da baya min, haka zai zo da soyayya ya cutar da zuciyata, har yau ina da yakinin zai shiryu ya daina abun da yake" min don na fara tunanin kamar shiga tsakaninmu aka yi. "Cikin murmushi na ce mishi. ""Barka da dawowa yasu Aunty Zakiya? Kun iso lafiya?"" ""Alhamdulillahi" "Auta nace ke zan fara kira ki san na dawo!"" ""Masha Allah sannu da hanya madalla!"" Yadda muke wayar" "naki sake jiki da shi, ya sa shi kashe wayar da zai kira wani lokaci, tunda Ya Ado ya dawo Nigeria kullum" "zai kira ni, zamu gaisa daga nan zan yi shiru. Haka zai ta ja na da hira, har ya gaji ya kyale ni." "A hankali abin sai ya zame min jiki, sannan ban kara yarda mun yi tashin hankali da wani abu cikin gidan" "ba, wani abu daya da na fahimta idan na kashe auren ma bani da wani amfani, haka yasa babu amfanin na gayawa kowa halin da nake ciki, sannan kwasar bakin ciki a wurin Ya Hafiz da danginsa kamar shafa ce ta alola. Haka yan uwansa zasu zo musamman Aunty Nana, haka zata yi ta min kome da gadara da iko" "iko, idan nayi magana zata ce gidan dan uwanta ne." "Haka zan zuba musu idanu, kome zai wuce amma idan ban mutu ba zan sha kallo. Idan ka kalle ni" "bani da matsala sam, amma deep in side ina cikin wani irin mugun yanayi ne. Sai dai ba wanda ya san da haka sai wanda Allah ya jarabta da irin halin da nake ciki." * "Yau Dan wake nayi shima dai nice nayi cefanen, musamman duk ranar da ya tashi rashin mutunci ni ce" "zan yi kome har na gidan, ya daina kawo abinci domin kuwa Karimah ta ce mishi ai idan aka kawo kayan abinci sayarwa nake sai dai idan ya tashi ya auno mudu idan ya gadama idan bai gadama ba zai ce na" "ranta mishi, yasan bani da kosisi. Haka zan ta kame kame har na hada abincin aci." "Har lokacin Maman Na'ilah bata bani fuskar da zan tambaye ta kudin ba, abu daya take gaya min. ""Duk" "ranar da zaki yi aikin alkhairi wa rayuwarki in sha Allah zan baki kudinki amma idan har wa Mijinki ne wallahi kwandala ba zan baki ba, karshe ma zance sharri kika min!"". Murmushi nayi da yake tasan ba zan" "yi magana ba, shi yasa nima na barta." """Ke Yusrah kawo min kular Babanki na saka mishi abincinsa tun dazu sai magana nake kin ki kula ni!""" "Cikin rashin kunya ta ce min. "" Eh din ba zan dauko ba ko dauko da kanki mana! Tunda bake kika haife ni ba. """ "Haushi yasa na zo na dauka na kuwa zungure kanta, ai kuwa ta fasa ihu. "" Sai ki yi mara kunya kawai! """ Na je na dauka ina mai komawa kitchen na zuba musu abincin. """Ina kika san zafin d'a ke kin san yadda wahalar daukar ciki da reno yake ne? Ina zaki sani bayan an lalata" "mahaifa da alluran family planner, kawai don ta ce ba zata ba sai ki saka min ita a gaba da fada idan fitsari banza ce kaza tayi mana!"" Ka sake nayi ina kallon Karima tana gaya min magana akan nayiwa" "Yusrah fada taki dauko min kular da xan sakawa Ubanta abinci. Shigowa yayi yana faWin. ""Ya dai kaza" "uwa Yaya mai ya faru Agwagwata uwar albarka?"" ""Waye ban da juyar matarka da ita bata san haifa ba sai dai kashi a masai."" Kumshe bakinsa yayi yana dariya mai sauti. ""Yau kuma waye na samu da suna juya" "au lulu love ce!"" Ya fada yana kallon yadda jikina yake rawa. ""Ita mana ita dai da bata san ciwon kanta ba, wacce dad'i miji ya kaita aka ta zuba mata alluran hana ciki!"" Cikin isgilanci ya ce mata. .""tow waye zai yarda ni ne bana son haihuwa da ita? Bayan nasan ba sonta nake ba kin san idan iyaye suka ga kana kula yarinya sai su dauka wani abu ne a tsakaninku, musamman idan Iyayen yarinyar suka gano cewa yarsu" "bata jin maganarsu sai naka!""" """Ya Hafiz da bakinka kake fadar haka? Kada ka manta da mahaifina da naka Uwa daya Uba daya!"" ""And" "so what? Dube ki kitse ya taru a jikinki ke kanki ba zaki iya gudun minti goma ba, dube ki don Allah har kunya nake na ce ke matata ce, domin dariya zaa ayi min, balle kuma."" Dariya yayi ta min yana fadar cewa..""wallahi matse matsinki wari suke balle kuma can kasar idan kika kwanta kamar an zuba kashi a" "bola!"" Sai naji jikina yayi sanyi duk abinda zai gaya min naji ciwo ya san ni." """Ka sake ta mana Habibi wannan mai kama da dorinar ruwan tsoro take bani!"" Dariya yayi sosai ya ce" "mata. ""Karimcy ba zan iya sake ta ba, kai ko da na sake ta waye zai aure ta? Kada ki manta yadda take tafiya da kyar da kyar waye zai aure ta? Abin dariya nama na jan kare.""" "A hankali na bar abin da nake na wuce daki, na zauna na fashe da wani irin kuka. Ina jin kamar zuciyata" "zata buga wallahi naji zafi amma ya zanyi, ina son ya Hafiz sosai ba wani abu bane fadar da yayi, shigowa dakin yayi ina zaune ya ce min. ""Uban waye zai miki aikin da kika fara? Kin ga Lubnah bana son iskanci da renin wayo, wallahi zan tattaka ki, zaki fita ko sai na zane ki, ga ki katuwa amma kanki babu ™wa™walwa!"" Ba yau ya saba duka na ba, sannan ba yau ce zai daina ba. Tsoron dukan da yake fadar zai yi yasa na mike ina faWin. ""Kayi hakuri!"" A duk lokacin da yazo ya fara wannan masifar ya tsani yayi" "magana nayi shiru, idan ban bashi hakuri ba marina zai ta yi. Har sai na bashi hakuri...." *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu TARA "Haka na fito na karasa aikin, ina kuka na gaji na gaji da abinda yake min, a hankali na gama na koma daki." "Yanayin ba dad'i, ko nace ni ce bana jin dad'insa. Ana haka bikin yar gidan Aunty Hindatu da aka saka ana d'agawa ya taso saboda mijin ba a kasar yake ba, haka yasa aka saka bikin karshen wata June, tun daga kan kayan da zamu saka da kome Yayuna suka min, har lokacin Mama da Yadiko babu wanda yake shiga" "harkata tow ba ma damuwa suka yi da ni ba, idan bani na kira ba tow da babu wanda zai kira ni a cikinsu." "Bikin Maamah yar Aunty Hindatu da za ayi ya saka na dan samu yanci, domin Ya Ado ya kira Ya Hafiz ya" "gaya masa batun bikin da niman alfarman nazo ayi kome da ni, yadda yasan halin Ya Ado bai da sauki yasa bai yi musu ba, shima Ya Ado zai zo da Yaransa." * Yau da wuri Umar ya bar muda lawan kasancewar mashin suke sayarwa shi a bangarenshi amma yana "aiki da ma'aikatan shige da ficen jahar Bauchi. Yana kokarin hawa motar shi wani magidanci ya ce mishi. ""Malam Umar ko?"" ""Eh nine lafiya?"" ""Hmm dama ina son na tambaye ka ne? Ya kuke da matar Alhaji Hafiz ne?"" ""Eh kanwata ce!"" ""Tow gaskiya ku sayi likkafanin da zaku lullubeta idan ta mutu, ni shawara da zan baka kenan idan kun so ku tsaya mata idan kun so ku barta ta cigaba da mutuwar tsaye!"" Daga" haka mutumin ya tsare abin hawa ya bar wurin. "Da wannan tunanin ya iso gida, ya sami Maman Aunty matarshi ya bata labari. ""Ba tuntuni ake gaya" "muku ba, sau nawa ina baki a gidan nan bayan mun gaisa zasu ce don Allah idan ina da yadda zan yi na kaiwa Lubnah Wauki.""" "Haka suka ta tattaunawa da fadar ko da zasu wani abu su Mama ba zasu bari ba, shi yasa kowa yake" shakkar shiga rigimar. Haka suka yi ta tattaunawa a tsakanin al'amarin. * "Haka bikin ya karaso aka fara hidimar biki babu ji babu gani, kullum xan je kuma Ya Sani shi yake kawo ni" "har gida, domin Ya Hafiz ya hana ni kwana. Ranar daurin aure ina ta shirin fita da yake ita ranar ta gama wuninta, tunda asuba nake aikin gidana har na gama da wuri Ya Hafiz ya tambayi Karimah ta ce ba zata ba, haka yasa na gama shirina da wuri, wurin karfe tara na fito ba sai ga Karima ba. "" Zan je bikin fa! "" "" Tow don Allah ki hanzarta! "" Na fada ina kallon agogon hannuna. Tunda Karimah ta shiga daki ta manta da ni sai da na kara mata magana wasa wasa bamu bar gidan ba dai karfe biyu da wani abu. Kamar nayi kuka da gayya tayi haka sai dariyar mugunta take min, Ni dai ban kula ta ba. Har muka isa gidan da ya" cika da mutane. "Muna shiga cikin gidan Aunty Hindatu ta watsa min harara tana faWin. ""Wai ke me yasa baki kome da" "jikinki? Kullum zaki zo sai kin makara."" Zan amsa caran Karima ta ce musu..""jiki duk tarin kitse taya zata" "yi sauri? Ai kun san Habibi yana kokari ko?"" Wani hade rai Aunty Innah tayi tana kallonta cikin haWe giran" "sama da kasa ta ce mata..""An kasa dake ne?"" Da sauri na cewa Aunty Innah..""Inna uwa maba da mama bata yi karya ba, jikin nan damuna yake ni kaina da ina da hanyar rage shi da na rage, gaskiya ta fada!"" Duk da na gama aikin gidan da wuri ita ta makarar da mu. A hankali na wuce bayan na fadi haka na barta nan kunya da yadda sauran yan uwana da yan uwan Ya Hafiz suka mata ca, Mama tana jin su bata amsa ba amma kuma zuwa yanzu ta fara jin kamar akwai abinda suke ™o™arin aikatawa. Dakin Aunty Hindatu nayi na zauna can kuryan gadonta. Shigowa Aunty Nana tayi ta ce min. ""Ke kullum aka yi magana sai ki nuna babu kome, Alhamdulillahi tunda ba kome amma ki sani Ubangiji yana madakata!"" Ta fada min tana wani dauke kai Aunty Nana Yayar Ya Hafiz ce, kuma na hannun damanta uwa uba Karima kanwar Mijinta ne, murmushi nayi na de mata. ""Kiyi hakuri wallahi ni ce na makarar damu kamar yadda ta faWa!"" Na fada mata kamar xan yi kuka. Tsaki tayi ta bar dakin Yaya Asabe da take alolan a ban daki ta fito tana faWin.."" Lubabatu ba zaki daina cutar da kanki ba?"" Washe mata hakori nayi ina faWin "" ba kome fa"" ""da kome mana, na akanki aka fara aure ne Lubabatu meke faruwa a gidanki"" dariya na fara mata, dariya irin wanda kana gani kasan ba lafiya ba, na ce mata..""ba kome wallahi!"" Shiru tayi tana kallon yadda na koma na yi shiru. Ina murmushi. Ina zaune Aunty Hindatu ta kawo min kayan anko dinmu da su, na saka na fito Was da ni. Kowacce ta saka sarkan gwal dinta ni dai bani da shi sai wata fashion da na saka Aunty Munah ta ce min. ""Lulu ina gwal Winki?"" Da yake iya mune a dakin. Zare idanun nayi ina kallonsu. ""Ina gwal Winki?"" Aunty Innah ta kara jefa min tambayar bakina yana rawa nace musu. ""Na sayar da shi?!"" Wani katon salati suka saka tare da zaro idanu. ""Karya kike munafuka gaya min gaskiya ko naci ubanki ina kika kai sarkokin gwal Winki!"" Shiru nayi naki magana, shigowar Yadiko dakin ta ji suna sake tambaya ta ina na kai sarkan gwala-gwalai na. ""Na sayar nace!"" ""Me kika yi da shi Lubabatuna."" ""Inji Goggo alti Yayarsu Baba mace ce mai fahimta da sanin ya kamata, tana da zurfin ilimin addini sosai. Ta ce gaya min. ""Gaya min ina kika kai sarkokin gwal Winki!"" Jikina ne ya dauki rawa. Nace musu. ""Goggo na sayar!"" Wani irin mari Mama ta kifa min sai da na ga haske, na rintsa idanuna bakina yana rawa nace mata. ""Na sayar da su!"" Shiru dakin ya Wauka haka aka bar zancen amma ran Mama ya b'aci. ""Kome kin sayar gidanki, kin sayar kome kin sayar shi yasa kudin Umaranki na shekara biyu na ce kada a baki don baki da hankali!"" Ni dai ban ce musu kome ba. Bayan mun gama muka fito waje, muka bar Goggo Alti da Goggo Uwani sai Yadiko da Mama.. ""Salamatu ina jan hankalinki da ki tashi akan Yarki, wallahi yarinyar nan tana bukatar" "wani a tare da ita, ni dai bana zargi amma yarinyar ko baki kika mata iya ka kenan.""" "Haka muka sha hidimar bikin sannan aka shiga hadadar kai Amarya dama ban saka kaina ba, haka na" shirya muka tattaro muka dawo gida ashe akwai buhun bala'in da yake jirana. Tunda muka shiga gidan Ya Hafiz yake Bala'i da fada zagi da cin mutuncina har sai da nayi kuka. """Ke gaki mai yan uwa har zasu tsare ta da magana suna gaya mata abinda ransu yaso, don na rufa miki" "asiri na zauna dake haka na kuma zauna da wannan fuskar naki mai kama da ta giwar zasu zagar min Mata wallahi sai na sake ki,.na rantse da Allah idan na sake ki ba zaki tab'a samun wanda zai aure ki ba wallahi billahi azmin, wannan tarin jikin naki mugu da shi kamar kashi.""" """Kayi hakuri!""" """Hakurin Uban me kike ba ni? Bayan kaf duniya babu mummuna irinki, ga baki ga muni ga munin hali da" "na halitta, ina kallonki gani nake kamar zan mutu don takaici!""" "Kaina a sunkuye ya gama zagina na ce kuma ce mishi. ""Kayi hakuri na gode sosai, Allah ya baka" "hakuri.""" """Don na rufa miki asiri ina zauna dake zaki ci mutumcin matata!"" ""Kayi hakuri ba zan kara ba!""" """Kina nan tibi-tibi sai kace aladiya!"" ""Na gode sosai!""" """In ba don ina kunya Mama da Baban Bauchi ba wallahi da na sake ki, domin ya gaya min duk ranar da" "na sake ki sai dai ki nime wani uban ba dai shi ba."". ""Kayi hakuri ba zan kara ba.""" "Na fito ina murmushi, abubuwa dayawa sun boya a bayan murmushi na, kuka da ihu sun boya a bayan" "fuskana, amma haka na share na manta da kamar ba ayi ba. A tunani na zancen ya kare, sai dai a wurin Karamcy bai kare ba, domin kuwa bori ta saka mishi a kan sai ya min duka shine zata huce. Ya rasa yadda zai yi da ita kuma yasan matu™ar ta fara fushin nan zai zame mishi tashin hankali, don haka ya fito ya tsaya bakin kofar dakina yana faWin. ""Ke Jaka fito ki bata hakuri!"" Wani hakuri kuma? Kawai daurewa" nayi na fito waje ya ce min muje ki durkusa ki bata hakuri.. """Ni dai gaskiya ba zan durkusa ba domin hakuri kan xan mata amma ban da durkusawa."" Dama kamar" jira yake kawai ya rufe ni da duka. Duka sosai sai da makota Baban Na'ilah da Na'ima tare da basu Boy suka shigo gidan dakyar ai kwace ni a hannunsa. Tunda na shiga dakina na rufe na kwana ina kuka. "Washi gari naki fitowa na daura abin karyawa haka ya gama barazanarshi ya fita, yana fita nima na dauki" "hanya na nufi gidan. Ashe ina fita Karimah ta kira shi ta gaya masa gani nan na fita. Idan nace ban daku ba nayi karya, haka yasa na kwaso jiki na kawo ™ara, sai dai ban kai ga isa gidan ba Ya Hafiz ya kira Baba ya gaya mishi karya da gaskiya, ina isa gida Mama da Yadiko suka fatattake ni, akan na koma, don ba zan kashe musu aure ba, Baba yace musu duk wacce na zauna a wurinta a bakin aurenta, wannan ya bawa Ya Hafiz lasisin mai da ni jakarshi da zaran nayi laifi zai rufe ni da duka, wanda ya cusa min tsoro da" "tashin hankali, wannan dukar da zalinci yasa ni jin dole na rayu ko don na rabu da Ya Hafiz, na gaji." "Kaf yayuna aka rasa wanda zai tsaya min, Maman Na'ilah kaWai ta bani shawarar na fara niman zabin" "Allah, idan da alkhairi a zamanmu Allah ya shiga lamarin idan babu shawara daya ne, na kai shi kotu a raba auren domin idan aka cigaba da irin wannan zaman karshe daya zai iya rasa rayuwarsa. Haka na dukufa da azumi da addu'a sallah dare da sadaka. Sai da na shafe wata hudu cib har zuwa lokacin ba wai ina da nutsuwa bane, sai dai na ji n koma baya na saurari karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i, duk da zuciyata bata yarda da abinda nake nufi ba, amma ni a kaina na gaji, ni a karan kaina ina son na rabu da shi, ina son na bashi iska ko zai gane yadda nake ji, duk wannan lokacin Ya Hafiz bai tab'a nuna yayi nadamar abinda yake aikatawa ba, kai hatta Yaransa suka yi kuka da ni zai min dukar da dai na tsani kaina. Duk wannan abin da yake faruwa kowa yana jin takaici amma ba yadda suka iya tunda ni ban ga hanyar fita ba, bani da wata madogara, sannan ba ni da wata makama, haka yasa na zubawa sarautar" Allah idanu. "A cikin wannan ukubar na samu Maman Na'ilah da Na'ima na ce mata.. ""Don Allah ina son kudin nan" "zan samu, idan ba xan samu ba ki barshi kawai!"" ""In sha Allah zaki samu yanzu ma kuwa!"" Mikewa tayi ta shiga can cikin dakinta, ta janyo abu a kasan gadonta, ta ce min. ""Lubnah shigo mana!"" Mikawa nayi na shiga cikin dakin, ta ciro wata akwatin katako, ta fita tare da dauko wuka ta fasa kan akwatin katako, sai da ta fasa saman sannan ta saka hannu ta bude shi da kyau, kafin ta kalle ni tana faWin. ""Gashi nan ki zazzage shi!"" ˜asa kai hannuna nayi ita da kanta ta zazzage shi tas a gabana. Tow me zanyi da kudin" nan?............... *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu GOMA Wannan shine abinda na tambayi kaina me zanyi da kuWin? A hankali na ji zuciyata bata amince min da "abinda nake shirin ba nace mata. ""Maman Na'ilah ki bar kudin tunda na ga yadda suke!"" Na juya zan fita ta riko hannuna. ""Me yasa kuma Lubnah?"" Murmushi yake na mata. ""Tow me zanyi da shi?"" Yadda nayi maganar sai ita kanta abin ya dame ta, ta zata ko ina zarginta ne ta ce min. ""Wallahi summa tallahi babu kwandala naki da na."" ""Har abada bana zarginki kuma ba zan tab'a zarginki ba, kawai bani da abinda zan" "yi da shi ne."" Daga haka na bar gidan." "Na dawo na samu Karimah da Yaranta da wata kawarta suna ta hira, yadda nayi sallama basu amsa ba" "haka nima ban ce musu uffan ba na wuce dakina, tunda na shiga na zauna bakiWaya naji duniyar tayi min kunci, ko na rabu da Ya Hafiz Iyayena ba zasu tab'a karbana ba. Sai naji bakiWaya duniyar ta juya min baya, bakiWaya duniyar kamar ni daya ce mata amfani a cikinsu, haka nayi ta jin kamar zan mutu. Ina zaune a dakin naji sallamarshi, ban d'aga kai ba ya shigo yana faWin. ""Wani wacce irin iskanci ne da ba zaki yi abinci a gidan ba?"" A da ina ina ya Hafiz zai sauya amma by now sai nake ganin kamar har abada ba zai sauya ba. ""Bakya ji ina miki magana ne?"" ""Me kace?"" Na faWa ina kallonshi. Fita yayi daga dakin ina jin shi yana ta b'ab'atu, kiran sallah azhar yasa na fita nayi alwala na dawo dakin nayi sallah, can sai gashi" da kaya niki-niki a leda har da kayan abinci ya saka a kofar dakina ya fita yayi ya shigo da abincin tunda "na ga haka na fahimci wata ya shirya min, don haka ina zaune ya kawo min takeaway, kamar ba zan" "amsa ba na amsa na ajiye na ce mishi. ""Nagode"" na cigaba da addu'ar da nake, can bayan ya fita na shafa,. Sannan na ja ledar abinci ne mai kyau, dauka nayi na fara ci a lokacin ya fara shigo da kayan abincin, yana zubawa a bayan kofana. Ni dai ban ce mishi cikanka ba balle har ya dauka ko na damu da shi ne, zama yayi yana min murmushin mugunta, ban bi ta kanshi ba ya mike ya fita, haka na gama na fita da ledar da robar na kai waje, sannan na dawo dakina bayan na wanke bakina. Tunda na shigo naji kamar jikina yana sakewa a daddafe nayi sallah Asr, a wurin dai na cigaba da zama ko kwanciya nayi" Allah shine masanin. "Ashe kwanakina hudu me kyau a gadon asibiti, sai ranar na hudun na farka. Naga hannuna daure da" "abin karin ruwa, kamshin abin wanke asibiti ya tabbatar min da asibitin nake, a hankali na yi yunkurin mikewa zaune domin ina jin kamar maganar mutane sama sama, na ji kamar an mai da ni baya, bude idanu nayi a buge amma ban san waye a kaina ba can can naji ana cewa. ""Koma ki kwanta!"" Haka na kara komawa na kwanta tare da lumshe idanuna, ban kara budewa ba sai washi gari da misalin karfe biyu na rana naji Muryan Ya Ado, a hankali na kara mike jikina duk ciwo yake min. ""Sannu Lubnah!"" Inji Umma Kanwar Mama wacce take aure a azare, lumshe idanuna nayi na kara budewa akanta, ta mike da sauri ta shiga ™o™arin taimaka min na zauna ina sauke wani irin numfashi kamar mai cutar asthma." "Kallona Ya Ado yayi a hankali ya ce min. ""Ina ke miki ciwo?"" Girgiza kai nayi alamar babu. ""Sannu ko."" Ya ce min haka ta rike hannuna muka tafi ban daki ta haWa min ruwan wanka nayi da ruwa me zafi, sannan na hada da alwala na fito na zauna a bakin gadon fita Ya Ado yayi ya bamu damar sauya kayana. Bayan na sauya na gabatar da salolin da suke kaina, ina idarwa Umma ta zuba min tea me zafi a daidai shigowar Ya Ado da Ya Umar, sai Albashir da Ya Tahir, Ya Sani, ba Ya Ubaidullahi da Ya Mustapha, suna shigowa Aunty Hindatu da Aunty Innah suka shigo, zama suka yi akan kafet, ina cin abinci a hankali." "Hiransu suke na abin da ya shafe su bayan na gama na shiga ban daki na wanke hannuna da bakina. ""Barista ina ga mu bar maganar nan sai anyi la'asar ko kada mu fara mu katse saura minti goma a shiga sallah! "" Inji Ya Tahir, ""Ok Malam muje ko!"" Kallonsu nayi suma kallona suke yi. "" Kina son wani abu ne Auta? "" Inji Ya Sani, "" A'a bana son kome!"" Nayi shiru suma basu fita ba Ya Umar ya ce min.."" kina son tambayar wani abu ne?"" Yadda yayi min maganar a tausashe yasa na ce mishi. "" Me ya faru na ganni a nan?"" "" Baki da lafiya ne!"" Kallonsu nayi kafin na ce musu. "" Na fara hauka ko? "" Idanuna ya cika da kwalla, fita suka yi na hango tausayi a idanunsu, a for the first time da na hango yarda da aminci a tattare da su, bayan fitarsu Aunty Hindatu ta mike tare da alwala tazo tayi sallah, Umma ma haka, nima a zaune nayi sallah saboda yadda nake jin jiri. Tunda na idar da sallah nayi shiru, maganar gaskiya ko addu'a a yanzu na rasa ta me zanyi, ta rokon Allah ya saka ya Hafiz ya sake ni ne ko ta nimawa kaina mafita ne, shigowar Yan mazan ne yasa ni kallonsu, tare da Yadiko wacce take tsakiyarsu, shigowa suka yi Umma ta ce mata. ""Ina Yaya Salamatu? Yau kwanaki biyar yarinyar nan tana asibiti bata leko ba?" "Wallahi zan kira Inna na gaya mata tunda ita bata tsoron Allah a haka zata kashe Yarta."" Sai a lokacin na kalle su naga yadda Yadiko take zabga min harara. ""Yaushe kika fara shaye-shaye Lubnah meye amfanin wannan abin kunyar da kika aikata?"" ""Yadiko a dai bi kome a hankali kada azo ana danasani!"" Inji Ya Tahir wanda ya kasance dan Yadikon ne na fari. Juyawa tayi a fusace ta fara faWa. Wani irin kara kaina ya" fara na dafe kan ina ™o™arin jin kamar ana buga min abu a cikin kwakwalwata. Rike ni Aunty Innah tayi "tana faWin. ""Duba min alluran da yake cikin farin kwalba da sauri!"" Ba musu Aunty Hindatu ta mika mata," "ta ce mata.. ""fasa min!"" Haka ta bude bakin, sannan ta mika mata, ita kuma ta rike ni domin wani irin jijjiga na fara kamar ana fifigar jijiyar kaina, shiru Yadiko tayi ganin yadda nake jijjiga ga jinin da yake zuba ta hancina, abin ya razanata, dama haka lamarin ya ke. Alluran aka min sannan suka yi tare tare aka" "daura ni gadon tare da daure min hannuna, barci me nauyi ya dauke ni." Hindatu. """Kai wallahi karya ne Lulu bata san amfanin kwayar da ta sha ba, da ta sani ba zata shiga wannan" "yanayin ba, imma an jima ana bata tana sha."" Cikin fada Yadiko ta rufe Hindatu. Tahir ya ce mata."" Yadiko lokaci yayi da ya dace ku san waye yake auren Lubnah kun ga haka muke yiwa Yaran wasu? Me yasa sai ita? Me yasa a duk lokacin da tazo da bukatar a saurare ta ba a bata damar ta fadi abinda yake ranta? Yadiko lokaci yayi da zaku cire kanku, ku kyale mu da Mijinku ya isa haka ya isa haka. Idan da Munah ko Raliya ne a cikin wannan yanayin hakan zaki hana mu magana? Duk lokacin da aka yi abu" "Lubnah ce mai laifi me yasa ko sau daya kun tab'a tambayarta meke faruwa? """ """ Amma ka ga yadda muka samu kayan maye da abin hana daukar ciki? "" Murmushi yayi ya ce mata. """ "Waye bai san Hafiz ba? An gaya miki bakiWayanmu basu san halinsa ba ne? A cikinmu ya tashi fa, a lokacin da Uwarsa ta watsar da shi Abba ya janyo shi jiki saboda nakasar Baban Jama'are, Yadiko ni nan Hafiz ban gaya miki ba ne, Hafiz shine yayi sanadin da na bar shagon Abba, shi yayi dalilin da kowa cikin mu ya bar shagon Abba muka dauki abinda ya mana. Yadiko lokaci ya kure da zamu kyale wannan lamarin."" Yadda suka tsaya akan maganar yasa Yadiko tayi shiru ai al'amarin matukar ba kai ya fadawa" "ba, tow tabbas ba zaka fahimci yadda abin yake ba." "Sai da lokacin Sallah yayi suka tafi masallaci, su Aunty Hindatu suka yi sallah har da Yadikon bayan sun" "idar, suka ci abinci suka ajiyewa yan mazan, lokacin da suka iso an kawo na gidan Ya Umar da Ya Tahir haka suka hadu suka ci, sai karfe tara suka bar asibitin suka kai Yadiko gida." Hafiz "BakiWaya hankalinsa yayi azabar tashi, domin ya hango kwabarsa zata yi ruwa, yasan matu™ar ya rabu da" "Lulu tow ba makawa duk abinda yake zai fito fili haka yasa shi kiran Baba Malam suka gaisa ya ce mishi.. ""Alhaji ka ga sun dauke min matata, bayan ina sonta don Allah ka saka baki su bani matata wallahi ina sonta zan turo maka da kuWin mai a saka a mota a kawo ka kaji alhajina."" ""Shi kenan in sha Allah zan tawo gobe!"" Godiya yayi ta mishi yana kara gode mishi. A hankali ya ajiye wayar yana kallon Karimah da take zaune a gabanshi ta hade rai. ""Baby Karimcy kada ki damu ai!"" ""Ya isa haka!"" Ta fada tana kokarin" mikewa ya janyo ta suka fada wata duniya na daban. *** "Kiran sallah farko akan kunne na aka yi shi, na tashi nayi raka'atu fijir, ina cikin sallah Aunty Innah ta" "shigo, murmushi tayi ta shafa kaina ta wuce ban daki tayi alwala ta zo ta gabatar da sallah nafila, a hankali ta ajiye min wata waya a gefena. ""Ki duba akwai Alqur'ani a ciki zaki iya saurarenshi, ga airbon ki hada da shi kada maganar wani ya kara saka ki cikin tashin hankali har ki razana, domin condition dinki yana da matu™ar hatsari kin ji."" Gyada mata kai nayi, har ta haWa min abin karyawa da magani na sha sannan ta koma wurin aikinta. Sai karfe bakwai ta shigo lokacin ta gama zata koma gida. ""Zan koma na huta an jima zan dawo bakiWaya kin ji kina son wani abu ne?"" ""Duk abinda kika kawo min zanci "" murmushi tayi ta shafa kaina tana me rungume ni a jikinta. Tana bubuga bayana. ""Ki yi hakuri kin ji kome zai wuce wata rana zaki ga kamar mafarki ne kin ji ko?"" Murmushi nayi mata nace mata..""Nagode!"" Haka ta mana sallama ta tafi, wurin karfe takwas sai ga Mama da Abba, tsoron ganinsu yasa na rikice ina mai niman hanyar da zan gudu ban daki, amma ba hali shigowar Ya Ado da yaga yadda jikina yake kerma ya zo inda make ya zauna tare da kwantar da kaina a kafad'arshi. ""Shiiiiii!"" Yake furtawa a hankali, yana matse hannuna rintsa idanuna nayi hawaye na zuba min, a hankali a kafad'arshi. ""Tow Yar gata, yar kwai ko nace yar gwal!"" ""Hajiya Shehu idan kana son tayi aman ™wa™walwarta sai ka gyara wuri ka zauna domin ina ga haka ya dace da ku kai da Yaya Salamatu;"" jin haka yasa shi kallon Umma ya ce mata. ""Aminatu amma kin san abinda tayi bai dace ba?"" ""Ai rashin dacewar yasa zance maka kai ka tab'a tambayarta me yake faruwa a rayuwar aurenta? Yanzu yar gurin kishiyata da muka aurar bariya a lokacin ™a™a ina cewa saboda ita na fari ce uwar ta watsar da batunda mijin nan yayi ta cutarta ba a sani ba karshe sai da ya dauko mata lalura yarinyar nan ta rasu a wurin haihuwa bayan ciwo ya cinye ta ita da abin cikin ina lokacin da yar take kawo karar koranta muke? Sauyin Lubnah yayi yawa. Shirunta cuta ce ga rayuwarta ko ku shiga lamarin ko kuma muna nan daku zaayi kukan mutuwarta. Da yake Allah ya bata wani mugun jiki ne da baya bayyana tashin hankali da wata ce ta kare tas sai kashi da hakora rakwacan! "" Kasancewar Umma Aminatu abokiyar wasarshi ce ita kanta Mama Abokiyar wasan Abba ne domin su Ya'yan mace, shi kuma Wan namiji. Haka yasa ta hana shi magana kuma akwai mutuntawa a tsakaninsu domin Mijinta da ya rasu aminin Abba ne, cikin nuna damuwa ta ce mishi. ""Nasan da Madaki yana raye da shi zai dauki lamarin Lubnah da muhimmanci, gaskiya abin ba dad'i duk da har yau bata ce mana uffan ba, shiru idan yayi shiru mace idan ta tashi mutuwa aman jini take yi saboda lokacin da ya dace tayi magana an rufe mata bakinta."" Ambaton Madaki yasa Abba ya juya yana faWin."" Kai anan zaka lalace ba zaka koma aikinka ba!"" ""Zan koma ina son na ga yadda al'amarin zai kasance ne!"" Juyawa Abba yayi ya zuba masa idanu kafin ya harare shi. ""Kada ka sake ka lalata mata aure domin ba zan dauki haka a matsayin kuskure ba."" Shi dai bai ce kome ba har ya janye ni a jikinsa ya rako Abba da yake Mama zata" zauna da ni. "Har ya dawo ya samu ina karyawa, ban yi magana ba, amsar nashi abun karyawa yayi yana waya da" "Aunty Zakiya har da mika min na gaishe ta daga haka nayi shiru na cigaba da karyawa. Mama ta fara magana a hankali. ""Shi rayuwar aure dan hakuri ne."" ""Ai kuwa idan irin na Lubnah ne kabari ne wurin zamanta kawai domin daga alamu kun fifita zumuncin uban yaron akan Yarku!"" Jin haka Mama ta rufe Umma da Fada itama Umma ta hau sama suka rikito ashe itama yar bala'i ce, daukar airbon din nayi na" "saka a kunne na, na fara ™o™arin kunna karatun Alkur'ani, sannan ba kure karar, yadda ba zan tab'a jin" "muryansu ba. Haka ce ta faru kuwa, sai abin ya zo min da sauki har suka gama hayaniyarsu ban san me" "ya faru ba don Ya Ado yana gefena har barci ya dauke ni. Gyara min kwanciya yayi, bai kashe karatun ba ya cigaba da yi." Karfe daya na rana na farko a lokacin wai Mama ta tafi da na tambayi Umma Aminatu sai tabe baki tayi "wai tana faWin.. ""taga ni da lauya munki bin bayan shegen Yaron nan shine ta yi zuciya Allah yasa ta daka da kafa har Dutsen tanshi idan tana da zuciya."" Wanka nayi nazo na gabatar da sallah, ina addu'a Ya Hafiz da Baba Malam suna shigowa, wani irin bugawa kirjina yayi wanda ban san lokacin da hawaye ya zubo min ba. Gaishe Baba Malam Umma Aminatu tayi tana kallon Hafiz da yake kallona cikin jin dadi. ""Kaso daga gidanka a wuce da ita dungulbi ko?"" Take ya gyara fuskarshi yana kallon Baba Malam.. ""yanzu ba wannan ba yaushe da a sallame ta ne ta koma dakinta. Na kashe wannan maganar domin na" "samu Usmanun na gaya mishi na kashe zancen nan har abada a bashi matarsa Allah ya taya shi riko! """ "Kaina a kasa har aka turo kofar yana kara jaddadawa an kashe maganar, Ya Umar ya ce mishi. """ "Magana dai bata mutu ba, sai yq gaya mana inda ya kai mata da duk abinda ta mallaka. "" "" Umaru ina magana kana magana da nuna min abinda na isa da shi!""" "Gyara tsayuwa Ya Hafiz yayi yana kallona, kafin ya ce musu. "" Gata nan ku tambaye ta yadda tayi da" "dukiyarta? Har shaidu ina da shi, yarinyar nan Alhaji nayi hakuri da ita yarinyar da ta bada jinginar gidanta kawai don a bata kwaya ta sha, meye ne ban mata ba? Kayan sawanta ta haWa ta sayar kome nata ta sayar wallahi na rantse da wanda rayuwata take hannunsa yarinyar nan ba karamin bashi ta cillani ba, Alhaji kasan yadda nake kaunar Lubnah amma ni yanzu idan yan uwanta suka ce ba zata zauna da ni ba, zan iya hakura da ita ba gaji! "" Yadda na kafe ya Hafiz da idanun yasa ji wani abu me daci ya cika min wuyana. Ban san yadda aka yi duk soyayyar da nake yiwa Ya Hazif ya dawo kiyayya ba, shin dama ba soyayya ba ce to idan ba soyayya ba ce mece ce nayi mishi? A sanina dai na kaunace shi, nayi mishi biyayya na wulakanta kaina na boye kaWan daga cikin miyagun halayenshi, kura mishi idanu nayi ban iya magana ba, haka akayi ta rikici ni dai har lokacin ban ce kome ba, kuma bana son na ce kome, haka suka tafi ashe bayan barin asibitin babban rigima aka yi da Baba Malam wanda ya tilasta Abba cewa daga" asibiti idan aka sallame ni a wuce da ni gidan Mijina. Ba zan mutu ba sai naga karshen Ya Hafiz haka yasa koda na warke aka sallame ni ban cewa kome "daga abinda yake faruwa ba, haka suka yi ta bina akan na musamman abinda ya fada karya ne nace musu A'a ai gaskiya ya faWa, wannan abin da nayi ya fusata yan uwana, haka suka mai da ni dakina, tunda na fahimci an gyara min dakin an saka min sabin kayan dakin, sai na tsaya a kaina da zuciyata dole na kwaci kaina a hannun Ya Hafiz, amma ta ya? Shine ta hanyar shigar da shi kotu amma kuma idan na kai zancen kotu ya familyna zasu dauki al'amarin, sai na kara jin na shiga wani irin damuwa mai danne" zuciya. Hankalina yayi azabar tashi. "Bani da hanyar da zan iya yakince Ya Hafiz a rayuwata sai na ji bani da wani kwarin gwiwa, tunda na" "dawo kuwa iskanci da cin zarafi sai da yafi na baya, gori kuwa ina shan shi, tun ina dauke kai har ta kai da idan na rama sai ya dake ni, haka yasa na kara shiga wani irin kuncin rayuwa, domin kuwa Ya Hafiz ya saka Abba haramtawa kowa zuwa inda nake, haka yasa babu wnada ya san halin da nake ciki, sau biyu" ina faduwa a ban daki. Haka zan farka na ganni dauke da karin ruwa. "Faduwar da nayi na biyu ranar Maman Boy ta shigo ta ga na fadi suka kama ni suka kai ni daki, suka yi ta" "min fifita dama ya dake ni kenan ya fita shine na fadi, itama Karimah ta fita abinta. ""Har ga Allah lokaci yayi da zaki samawa kanki Yanci idan kika kai shi kotu kudin wanke muni zaki biya!"" Shiru nayi ina nazarin maganar, bayan fitarsu. Ina kwance na kira Ya Ado." """Ya Ado!"" Amsa min yayi kafin ya ce min.. ""na'am Auta!""" """Ya Ado idan nace zan rabu da Ya Hafiz Abba zai hana ni wurin zama!"" ""Are You ready!""" *Wannan littafin na kudi ne* *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu SHA ŠAYA. "Kamar yana gabana na gyad'a kai ina jan hancina. ""Lubabatu kin shirya rabuwa da Hafiz ko baki shirya" "ba?"" Sai na ji tambayar ya zo min a wani irin rude, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, na rasa meke min dad'i shin mai yayi zafi da zan kashe auren. "" Abba zai kore ni!"" Ina jin yadda ya sauke numfashi ya ce min. "" You're not ready!"" Ya kashe wayar. Haka na cigaba da kuka na rasa yadda zan saka kaina, haka na wuni suku-suku har dare yayi ban daura abinci ba, ko da Ya Hafiz ya dawo ganin babu alamar na daura aninci sai bai ce kome ba, ya fita ya sayo abinci ni kuma ko kallo bai ishe ni ba, ina da sauran kayan tea shi na sha na kwanta. Tun daga lokacin wani irin kunci da kasala ya shige ni, a daddafe nake ibada da alamarun gidan wanda ya dauki idanun ya zuba min, ina kiyaye lafiyata domin duk bayan sati biyu ina zuwa ganin likita wanda su Mama ba su sani ba, haka muka ci gaba da zama, ba ana haka Azizat matar" "Ya Tahir ta haihu, kiri kiri ya hana ni, zuwa." "Nima kuma ban damu ba, ana gobe suna Ya Tahir ya zo gidan da kanshi, ya same shi tunda ya ga Ya" "Tahir yayi ta kame kame. ""Nace ai ta je ita ce!"" ""Ko dai kai ne baka yarda ta je ba, Hafiz mun fa san halinka!"" "" Wallahi Attahiru ba haka ba ne, kasan yanayin ne yanxu tana zuwa ta ga su Inna da Hindatu, zasu zuga ta ai."" Murmushi Ya Tahir yayi ya ce mishi. "" Yaushe zaku bar gidan nan an kusan shekara biyu kenan a gidan nan?"" Shiru yayi yana kame kame kafin ya ce mishi. "" Ai dama wancan gidan ban san lokacin da ta sayar da shi ba! "" Fitowa nayi daga cikin dakina na zuba mishi idanu. Na kasa magana kawai sai ya rude. "" Lulu!"" Juyawa nayi na koma dakin, na kwanta. Wacce irin kiyayya ya Hafiz yake nuna min ne? Me nayi mishi da baya gudun jogana min laifi ko mi kankantarsa? ""Auta! "" Tashi nayi da kyar na leka wajen. Mika min kudi Ya Tahir yayi yana faWin. "" Nasan you are broke, gashi ki rage na abin zuwa gobe suna. "" Kallon kudin nayi nace mishi. "" Ina da kudi Ya Abba ya turo min shekaranjiya, Ya Almu ma ya turo Ya Sani ya ce idan nazo gobe zai bani sabon waya ya ishe ni."" Ina son naga reaction din Ya Hafiz kuwa Allah bai kunyata ni, sai ga eyes ball dinsa kamar zasu fado kasa kuma maganar gaskiya babu wnada ya bani kudin so nake na ga yadda zai yi, ""oya karba nima ga nawa!"" Inji Ya Tahir ya juya yana faWin. ""Ina jiranki fa gobe da wuri domin akwai liyyafa kin san wannan ne farkon samun Ya mace a gidana, kuma ina son nayi surprise dinki ne!"" Murmushi nayi na fito ina rako shi, juyowa yayi ya riko hannuna har kofar gidan wurin da ya ajiye motarshi, ina murmushi ko ba kome nayi farin ciki, nauyin da nake ji a raina ya ragu, a kofar gidan su Maman Na'ilah suka zo wucewa sai rike baki suka yi suna faWin. ""Kunga autar Yadiko da Mama!"" Murmushi nayi ina mai gaishe su, Yaransu da yake bana rabuwa da su, suna yawan shigo min haka yasa suka tawo wurina da gudu, Ya Tahir ya saka hannu a aljahun ya ciro kudi ya bawa Yaran, iyayen suka yi ta godiya tare da ni. Bayan tafiyarsu ya kalle ni. ""Allah ya hadaki da mutane kirki!"" Gyada kai nayi, ban ce kome ba daga haka ya kalle ni. ""Auta you are suffering."" D'ago kai nayi ina kallonshi, murmushi nayi nace mishi. ""Abba yace duk lokacin da na kashe Aurena na nime wani uban!"" Yadda nayi maganar a sanyayye, sannan na d'ago kai ina murmushi, murmushi yayi min ya ce min. ""Mu ai muna raye ba zamu tab'a barin haka ya faru ba."" Shiga mota yayi yana d'aga min hannu, murmushi yayi min tare da jan motar ya bar kofar gidan, na juya ashe ya Hafiz yana tsaye, shiru nayi ashe shi yasa ya janyo ni kofar gida, kuma wani abu maganar kudin nan bai bar ranshi ba, ina isa bakin kofar ya mika min hannu. ""Wata nawa baki biya kudin haya ba!"" Kallonshi nayi a hankali na ce mishi. ""Ai kayi sanadin da aka hana ni sana'ar balle kace na biya kudin haya!"" Bai ce min kome ba sai da ya shiga cikin gidan ya wani taka min kafa sai da kashin kafar naji yadda yayi kara ya ce min. ""Sannu ba da gayya ba ne!"" Yadda nayi zafin kamar an zare min raina haka nake jin ciwon haka nayi ta takawa har cikin dakina wanda ya ragani isa yayi maza ya dauki wayata yayi ta saka number check balance, amma bai ga kome sai wasu yan iska dari biyar da dubu daya, da yake account biyu ne da ni. Haka ya gama dube dube a wayar tunda dama keypad ce, haushi ya kama shi ya wurga min wayar na dauki abina ina me ninke hijab dina, ganin sa gaske naki kula shi. Sai ya daddume ni ya shiga ™o™arin kwace kuWin ni kuwa naki, gani zai zai cutar da ni na gantsara mishi cizo wanda ya saka shi kara tare da shake min wuya kamar zai kashe ni. Sai da ya ga na fara fita hayacina sannan ya sake ni. Dakyar nake sauke numfashi, sannan ya kwashe kudin ya watsa min dubu biyar yayi gaba abinsa. Hawaye ne ya zuba min in sha Allah na fita na fita kenan. Ina kwance a wurin har aka kira sallah Magariba kafin na lallaba shiga ban daki nayi tsarki na zo nayi alwala na shiga dakin nayi sallah ina zaune. A wurin har aka kira sallah isha na mike na gabatar tare da shafa'i da wutir, sannan na kwanta a wurin, idan na kyale ya Hafiz wata rana zai kashe ni. Kwarai na gano kiyayya a cikin" idanunshi. Dama tun can Ya Hafiz bai sona ne? Idan har haka ne tow meye amfanin zaman da shi. Haka na kwana "washi gari na shirya zuwa gidan suna, sai da na biya gidan Maman Na'ilah na amshi jakar kudin nan, bayan na cire mata itama kudin da ban saj nawa bane, na juya na fita tana ta min godiya, daga nan gidan Aunty Hindatu na fara zuwa ita tana unguwar Federal locals ne, nan na fara zuwa, tana ganina ta fara tambayata. ""Auta lafiya?"" ""Lafiya kenan!"" Na shiga na zauna Mijinta Alhaji Mas'ud ya fito cikin shirin zuwa kasuwa. ""Matar roba kece a gidanmu!""gyada nayi, ""Kiyi hakuri har kika kwanta ban samu zuwa ba na tafi umara ne amma ita wannan matar karfen bata gaya min ba sai da na dawo!"" ""Na gode Angon bogi!"" Murmushi yayi ya ce min. ""Tow ayi min addu'a zan tafi kasuwa!"" ""Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya!"" Muka fada ya fita Aunty Hindatu ta bishi har waje sai da ya fita ta dawo tana kallon yadda nake a takure wuri guda. "" Lafiya Lu'lu'a!? "" Kaina a sunkuye na ce mata. "" Na shirya rabu da shi!"" Wani irin sujada tayi tare da ambaton Allah, ta rike hannuna. "" Da gaske! "" Hawaye na zuba min na ce mata. "" Eh! "" Na gyada kaina ina cizon bakina. Wato ban tab'a jin kwarin gwiwa ba irin na yau sai da ta kira conference call bakiWaya aka hadu ina jin su, tambaya daya suka yi min na shirya rabuwa da Hafiz Ali Umar Jama'are? Na ce musu eh ma shirya. Aunty Hindatu ta gaya musu na zo da kudi, da yadda za ayi da" "kuWin. Murmushi Ya Ado yayi ya ce shi kenan. "" Baby girl get ready muna bayanki! """ "Haka muka gama muka tafi gidan sunan amma bamu tafi lokaci guda kowa da tafiyarsu, lokacin da" "muka isa gidan kowacce daban daban ya shiga. Anan muka samu ana ta liyyafar, ina isowa Ya Tahir ya riko hannuna ya kai ni wurin abokansa abin mamaki har da Ya Hafiz a wurin wato don jaraba ya biyo ni, irin kallon da yake min na tuhuma da zargi yasa ni dauke kai, babyn aka kawo min Ya Tahir ya ce min. ""Ga takwara na miki!"" Kurawa yarinyar idanu nayi hawaye na zuba taruwa a idanuna, na d'ago kai ina kallonshi hawaye na zuba min, wannan na gudu wannan na koro wannan, kasa magana nayi ina kallonshi. ""Takwara na miki!"" A hankali nake shashekar kuka ina me rungume yarinayr har cikin raina nake jin kaunar yarinyar. Haka Yan uwana suka taru ana ta taya ni murna ban haihu ba amma yan uwana sun min kara domin duk abinda ya dace nayi sai gashi sun yi min kome har da kayan barkatu. Soyayyar da yan uwana suke min ya wuce tunanin mutum. Haka na tashi na tafi wurin uwar jaririyan nayi ta kuka, ita kan dariya tayi min. ""Lulu Allah ya sani nafi ki farin cikin saka sunan Yarinyar nan, kuma taki ce har abada!"" Haka nayi ta kuka a wurin kukan da na kasa yi shine nake yi ina yi ina kallon yarinyar, yadda nake kuka Aunty Hindatu ta ce a kyale ni, nayi kukan dama tun tuni ake son nayi ban yi ba, sai nayi har kaina ya fara ciwo, suka kai ni dakin Ya Tahir na kwanta, barci ya dauke ni mai karfi. Sai wurin karfe biyu na farka zan yi sallah na ga bakona, ita mai jegon ta bani sabon pant da ledar pad, na gyara jikina na fita wurin yan uwa da ake ta hidimar bikin sunan, Aunty Hindatu bata gayawa sauran dangi ba, iyamu yan daki daya da dakin Yadiko aka san da zancen. Wurin karfe shida nayi sallama na wuce gidan Aunty Hindatu. Itama can ta dawo, ta fito min da kaya kala uku domin gobe da sassafe zan wuce Kaduna wurin" Ya Almu. Hafiz "Karfe takwas ya dawo, koda ya shigo ya g kofar dakin Lubnah a rufe tsaki yayi, yana tambayar Karimah." """Yarinyar nan bata dawo ba ne?"" ""Ba ka bani sandar kiwonta ba fa!"" ""Ikon Allah!"" Ya ce daga nan bai" "kara magana ba, haka har zuwa karfe tara na dawo babu labarin Lubnah, bai damu ba yasan yadda zai ji" da ita gobe.. don haka yake shirya yadda zai cika Baban Bauchi. ** Washi gari. "Asalin tashar Kaduna aka kai ni, wanda yake hanyar Jos, daga nan Aunty Hindatu bata bar wurin ba sai" "da ta ga motar ya tashi, sannan ta dawo gida." "Dama wayata na bari a wurinta, ta bani wani tsohon wayarta da layin duk tsoho ne, amma tana amfani" da shi. Haka yasa na kwantar da hankalina don ko na tafi da wayar Ya Hafiz zai iya amfani da kiran na dawo. "Karfe biyar biyu na rana na iso Kaduna, Ya Almu yazo ya dauke ni. ""Auta sannu da ™o™ari, sannu" "Ubangiji yasa karshen wahalarki kenan!"" ""Amin Ya Allah!"" Na fada a hankali, muka wuce gidansu da yake base na Sojojin sama." "Muna isa Matarshi Aunt Saliha,ta tarbe ni. Ina zata saka ni ina zata ajiye ni. Don farin ciki da jin dadi." "Haka nayi ta jin kamar alfarma aka min. Nayi wanka aka bani abinci naci kaWan, sai kuma na fara jin kamar nayi wani kuskure. Wurin karfe uku Aunty Hindatu ta kira shi tana gaya mishi yadda Ya Hafiz ya rikice yana bin gida gida yana niman inda nake. Shiru nayi da Ya Almu yake gaya min yadda hankalin Ya Hafiz ya tashi ya rasa yadda zai cusa ranshi har Jama'are aka bincika ko ina can. Gashi yau aka yi wani hatsari a hanyar Jama'aren hankalinsa yayi mugun tashi. Sai jikina ya fara rawa na kasa zama ko na zauna zan tashi tsaye. Rike hannuna Aunty Saliha tayi tana faWin. ""Ki saka a ranki, zaki iya yaki da kanki idan kika koma kofar da zaki sake samu ki gudu ma ba zaki samu ba, ki nutsu ki gaya Allah kukanki, Hafiz ba shi bane karshen rayuwarki, kina da naki rayuwar ki sa ranki, zaki rayu!"" Kuka na saka mata har ina shashekar kuka. ""Zan koma kawai ya sake ni."" ""Yes muna tare dake, shi zai bukaci haka a yanzu kuwa kina komawa daga shi har su Abba ba zasu baki damar kare kanki ba, ina magana a matsayin daya daga cikin matan da suke ya™i da matan da suke da irin matsalolinki ne, kada soyayyar da kike ji yayi tasiri a ranki, kwarai zaki koma amma dole muna bu™atar nutsuwarki."" Dakyar ta shawo kaina nayi hakuri tare da rarrashina muka bar zancen Ya Hafiz ba a kara zancensa ba, kawai so suke nayi farin ciki. Kuma na yarda amma na kasa farin cikin. Yaron mai sunan Abba ana kiranshi Zunnur, ya dawo daga wurin Yayarta shi Waya Allah ya basu har yanzu dai basu kara sun wani ba koda yake yan boko ne Original masu" hakoran Abcd. Sai dare da na shimfida hakarkarina na kwanta sai wasu abubuwan suka yi ta dawo min. *** *Mafari tushen kome* 2015- June/July JIBWIS Bauchi state. "Yau ake bikin Yaye mu, kasancewar mun gama Jss3, zamu faWa aji hudu na Senior secondry School. Wani" abu guda uku yake tattare da wannan ranar yanayi uku yanayin da ba zan iya mantawa da shi ba. "Sunana Lubabatu Usman Umar Jama'are, wacce ake kira Lubnah Shehu Usman Jama'are, Abbanmu" "haifaffen garin Jama'are ne na jahar Bauchi. Iyayena bakiWayansu yan Jama'are ne, a unguwar kofar Fada. Gidansu Abba yana da tarihi domin suna cikin Kingmaker idan za ayi nadin sarauta a fada. Yan uwa da sauran dangi suna can." Abba wanda shine da na biyu a cikin gidansu Alhaji Umar Madaki yana cikin amintattun sarki kuma "wanda ake damawa dasu a fadar, wato Kakanmu wanda muke kira da Baba Malam. Abba da Mama auren zumunta ne aka musu har zuwa yau Mama bata taSa yaji ko wani abu ba, haka Yadiko wacce itama bata taSa yaji ba itama yar kanwar Hajiyarsu Abba ne, Abba yayi karatun boko tun daga barewa College zuwa ABU zaria, akan ce kowani mutum da inda bakin rabonsa yake shi Abba ya karanci hada makamashi ne, amma yana gama bautar ™asa ya kama kasuwanci, dama tun yana aji uku aka mishi aure da Mama, tana shiga ta haife Ya Ado, bata rufe shekara ba ta haifi Aunty Hindatu, sannan ta haifi Ya Umar, shima shekararsa daya da rabi ta haifi Aunty Innah, sai a lokacin Abba ya auro Yadiko sanin cewa dukkansu yan uwan juna ne sai suka zubar da kishi suka rungumi juna, itama Yadiko ta haifi Ya Tahir, bai" cika shekara ba aka. haifi Aunty Munah wato aunty Maimunatu. "A lokacin Baba Ali yana tare da Matarshi Hajiya Asiya yar garin Gyembu, wacce suka haihu tare da" "Yadiko tana goyon Ya Hafiz, kwatsam Abba ya tattara iyalinsa ya dawo Bauchi saboda ya samu aiki kuma ga kasuwanci, sai abin ya zo mishi da sauki ga aiki ga kasuwanci, Hajiya ganin yadda Abba yake ta gaba, abin ya d'aga mata hankali domin Baba Ali malamin secondry School ne, sai ta rena mishi tana ganin kamar gazawarsa ce ta haifar masa rashin arzikin har dan uwansa ya fishi, Bayan Baba Ali akwai Goggo Larai da Goggo Uwani, sai goggo talatuwa, su biyu maza sai Babarsu Goggo Alti. Abba wanda ake kiranshi Baban Bauchi bai taba zama ya manta yan uwansa ba, domin ko zuwan shi aikin hajji tare da" "Baba Malam da Goggo Alti suka je, lokacin duniya na kwance........" *Wannan book din paid na kudi* *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu *Littafin nan na kudi ne akan 1500* "*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105" ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641 Posting Arewapen da Telegram SHA BIYU "Shekara na dawowa ya biyawa Baban Jama'are, da Goggo Uwani da Goggo Takatuwa, suka tafi a lokacin" "ta Kano ake tafiya haka yasa a can suka tashi. Ko a Bauchi unguwar da Abba ya fara zama a ibrahim bako, haka ya zauna a lokacin yana aiki a ma'aikatan albarkatun kasa, sai da suka shafe shekaru goma sha biyar, lokacin an haifi Ya Almu da Ya Abba su kan tagwaye ne, Yadiko ta haife su Ya Almus shine Babba, Sai Aunty Raliyah tana aure a Jos, sai kuma Ya sani,da dan lokaci ya ja sannan aka haife ni, na samu gata a wurin Yayuna. Dakinmu bakiWaya mu Biyar ne, Ya Ado, Aunty Hindatu Ya Umaru, Aunty Innah nice na biyar, dakin Yadiko kuwa akwia, Ya Tahir, Aunty Munah, Ya Almu da Abba, sai aunty Raliyah da Sani," bakiWaya gidanmu Allah ya albarkaci iyayenmu da mu biyar ne. "Haka muka taso cikin wani irin so da gata, ni dai ban san sanadin da Ya Hafiz ya dawo gidanmu ba," "amma ma taso na ganshi a cikin gidanmu, kuma abin al'ajabi a dakinku, wato Ya Hafiz kyakkyawa ne tun ina Yarinyar na yi crushing dinsa, kuma bana kaunar na ga wata ta kula shi, Ya Hafiz bai da yawan magana, duk da lokacin da na fara wayo yayuna mata Aunty Raliya ce bata yi aure ba, domin duk yaran" gidanmu suna fara jami'a a gida ne su karasa a gidan mazajensu. "Haka yasa ita Aunty Raliya ba a Bauchi take karatu ba, a BUK ta karanci karatun jarida. Tana cikin" "karatun ta hadu da Alhaji Bilya suka yi aure, ni sai bana ce ba amma a wannan lokacin muka fara" "shakuwa dabYa Hafiz, domin kuwa an hanani zuwa bikin nayi ta rigima har na hakura. Idan na ce muku" "mun shaku tow ina nufin mun yi wani irin shakuwa da duk wanda ya ga yadda muke sai ya ji sha'awarmu, da farko Yayuna maza suna zuwa shagunan Abba, amma daga baya suka shiga barin shagunan daya bayan Waya. Na farko yar rigima ake tsakaninsu a shagon daga baya sai su bar zuwa shagon kuma dama kowannensu yana da abin yi, Ya Ado dama lauya ne, tuni ya samu aiki a Abuja ya koma abinsa sannan ya" haWa da kasuwanci domin abin ya same musu jiki. "Ya Umar shima yana aiki da ma'aikatan shige da fice a nan Bauchi, kuma yana da wani shago da suke" "shigo da mashina, sai Ya Tahir, malamin makaranta ne Tatari Ali Polytehnin, yana sana'ar fitar da tsabar abinci. Ya Almu da Ya Abba, shi Almu sojan sama ne yana garin Kaduna, sai ya Abba da yake sojan kasa yana Maiduguri. Ya Sani dai ya gama karatu yana da shagon da yake kula da su na sayar da generator, Yayuna mata kuwa Aunty Hindatu tana aiki a babban Kotun majastir na nan Bauchi ita ce magatakarda." "Sai Aunty Innah tana aiki a babban asibitin Bauchi babban nurse. Domin degree biyu gare ta, MBS." "Duk yan gidanmu babu cimma zaune, kowa akan kafarshi yake Abba ya ji haushina yadda duk Yayuna" "suka ki zama a tare da shi, don haka ya kama Ya Hafiz ya daura shi akan kasuwancinsa, ban ce muna da kudi ba, amma muna da wani irin rufin asiri da duk wanda ya ganmu tow ya san mun fi karfin a wulakanta mu, wannan lokacin ni daya ce mace sai yar rikon gidanmu Jalilah yar gidan Goggo talatuwa," Babanta Yayan Yadiko ne. "Abban ya Hafiz wato baban Jama'are ya hadu da hatsari wanda yayi sanadin da ya rasa ™afarsa daya," "haka yasa ya daina aiki Abba ya bude masa shago aka zuba kayan kudi, Hajiya Asiyah idan mace muku matar nan ayin kyau domin kaf yan gidan wato iyayenmu babu wacce ta kamo ta kyau, bafilatana ne amma irin masu burin nan. Duk da yan Gyembu ne sai dai mazauna Jama'are ne, yadda yayi burin Baban Jama'are ya kasance abin bai zo mata yadda yake ba, amma tayi making wasu abubuwan wanda daga cikinsu wofatar da Ya Hafiz, wanda haka yasa Abba ya dauke shi, Ya Hafiz ko nace yan gidansu basu son karatu, both mazan da matan. Da yake Allah yana yankarsu da tsada dakyar yan matan suka gama" "secondry School, su kuma mazan dama watsarwa suke su kama abinda zasu iya." "Shagon da Abba ya budewa Baban Jama'are kuwa, Yaran da Uwar ne suka ruguza kome, Abba ya kara" "cika shagon suka sake lalatawa, ganin za ayi na uku Baban Jama'are ya ce a barshi haka shi dai zai koma noma, haka da yayi ya b'atawa Hajiya Asiya rai, Baban Jama'are mutumin kirki ne, haka yasa koda ya koma noman rani da damina, idan. Amfani yayi haka zai cika ya kawowa dan uwansa, shi kuma Abba sai ya mishi hanya yana cire amfanin gona ya haWa shi da masu saya har da saya mishi motar da zata na" "wannan jigilar da shi, da yake yana da kafar roba da yake amfani da shi, Allah ya dafa masa kuma ya" "tsaya da kafarshi amma a haka Hajiya Asiya gani take bai kai Abba ba, shi kuma haka bai dame shi ba." Domin mutum ne mai yarda da Allah. "Ya Hafiz shine Babba, Aunty Nana Asma'u ita ce take binsa Sai Ahmad Tijjani, yake bin Aunty Nana, sai" "Babangida, yake bin Tijjani, sai Yahanasu, kafin Firdausi. Ita Aunty Nana tana auren wani dan siyasa a can azare, sai Yahanasu itama wani dan abokin Abba take aure suna River State, sai Firdausi da take tsalle tsalle taki zaman auren domin Allah ya mata ruwan kyau." "Ya Hafiz yadda bai samu soyayyar mahaifiyarsa ba domin kuwa bata janyo shi a jiki ba, sai da ya zama" "mutum, nan ta fara nunawa ita fa danta ne, babu wanda ya damu shima a lokacin bai da uwa sama da Mama da Yadiko, domin yana da gaskiya da rikon amana, duk inda Abba yake shiga Ya Hafiz ya sani duk inda Abba yake niman kudi Ya Hafiz ya sani. Kome na Abba ya sani kuma haka yasa shi kara samun yarda har da na dangi domin idan ba Abba bane ya ce yayi wani abu ba zai tab'a yi ba. Shima Abba yana ganin" "kamar dan uwansa ne a tare da shi, domin kaf halin Baban Jama'are Ya Hafiz ya kwashe bai bar kome ba." * "Haka na taso da wani mahaukaciyar kaunar Ya Hafiz da fari ni doguwa ce, sannan a yanayin yan gidanmu" "bamu da irin jikin nan da zaka ga mutum kato, a'a muna da yanayi jikin fulanin Jama'are, sannan" "gidanmu yanayin kowa daban, yanayin dakin Mama mu fatarmu tana da dan duhu, yayinda dakin Yadiko Fatarsu take da haske, haka yasa idan ka gan mu zaka yi ta mamakin yanayinmu." Wannan shine labarin dangina da gidanmu. 2015- June/July. "A karo na uku na lashe musabakar Alqur'ani, na fara shiga tun ina jss 1, sannan wancan satin mun Quiz" "and prize, na kasa a garin Abuja wanda na wakilci makarantarmu, tare da rakiyar Yayuna. Allah ya zuba min rawan kai surutu uwa Uba tsokana da son ayi da ni, gashi yau mun yi bye bye da Jss3." "A lokacin ina fama da tashen balaga, wayyo kusan kwaila da rawan kai, haka muka shiga makaranta" "mu hudu team dinmu, nice a gabansu na juya ina kallonsu ina musu bayanin yadda Abuja yake, sai ji nayi kamar nayi kawo da mutum. Na tafi kamar xan fadi, na ji an tare ni. Da yanayin wata gaurayayyen hausa" "mai mix da fulatancin da ta kama harshe tare da wani guntun fashion English aka ce min, ""opps i hope" "baka ji ciwo ba!"" Sai ce min sannu yake, da wani irin murya me sanyi. A hankali na matsa ina faWin. ""Ba kome!"" Na riko hannun Rumana muka yi gaba sai juyawa suke suna kallonsa, ni kuwa naki juyawa don bana ce ga yanayinsa ba sai dai yadda gabana yake faduwa yasa na yi saurin janye su muka shiga cikin Makarantar. Bikin yaye dalibai yayi kyau domin nima naci lamban yabo kala uku, a cikin kuwa har da kyautar kudin da na samu, saboda zama na daya da anyi a ko ina. A wannan ranar mai cike da tarihi har Makarantar Ya Hafiz ya zo ya dauke ni a ranar da ya fara sayan mashin dinsa Simba, tun muna Jss1 kawayena suka san da zancen Ya Hafiz. Rumah Rabi'u Mai shanu, Hafsah Faruq Babaji, Nafisa Sadi Gital, sai ni Lubabatu Shehu Umar Jama'are, sau dayawa cewa ake sunana yayi tsawo ni kuwa ban tab'a ganin" tsawonsa ba. "Wani lokaci shafin ™addara tana budewa a rayuwarmu, ba tare da mun sani ba. Idan da ace wani abun" mun rike tow ba makawa da ba zamu manta da shi ba. "Haka muka sha hutu, sannan muka dawo. A lokacin na dawo da wani irin yanayi na ciwon mara na" "al'ada. Sati na biyu da dawowa, da yake ban yi al'adar da wuri ba sai da na shiga aji na hudu, sannan ranar ita ce ranar da na fara, ciwon ciki kamar zan mutu, zufa nake yi tare da jin wani irin zazzaSi ya rufe ni, ga ciwon ciki kamar xan yi amai. Sabon malamin Chemistry da aka kawo mana ya shigo ya fara kiran sunan kowa sannan shi zai zame mana Form master dinmu, a hankali ya fara kiran sunayen mu, har ya zo kaina ya kira sau biyu ban iya d'ago kai ba, sai da ya kara kiran na uku Ruma ta ce mishi. ""Sir tunda tazo gata nan bata da lafiya!"" A dan hanzari ya kalle da wurin da ta nuna, a hankali ya karasa wurin ya Wan taSa desk Win a hankali na d'ago kai kafin ya tambaye ni na sheka mishi amai a jikinsa bakiWaya, sai a lokacin na zaro idanu ina kallonshi. ""Sorry how are you feeling now?"" Shine tambayar da yayi min, kasa magana nayi ina rike da cikina. Shiru yayi na wani lokaci kafin ya mike ya fita can sai ga yan ss3 sun shigo tare da shi har ya sauya kayan, wata jamfa ce a jikinsa golden yellow, yana shigowa ya ga yadda suke ta irin kyamar tabani. "" Me kuke yi haka? "" Takawa yayi yana kallon yadda suke son taba ni don ni kaina nasan a i mess up, duk aka rasa dabarar da za ayi min sai gashi an buga break, yan class suka fita a dudduke na mike, dawowa bayana yayi zai magana yadda zasu rike ni ya ga hatta hijab dina ya baci da jini! "" Look koma ki zauna!"" Haka na koma na zauna ina jin wani irin ciwo ya ce yan matan. "" Ku tsaya ina zuwa!"" Haka ya fita can sai gashi tare da Malama Malika ta Jss3, dauke da sabon hijab dal a hannunta ta sallami yan matan sannan ta ce min.. ""Lubnah sannu ko!"" Gyada kai nayi, ta bani hijab din na saka, sannan ta dauki wancan ta saka a leda, ta riko hannuna muka fita waje, motar Principle aka saka ni, muka wuce gida, ban san ya aka yi ba sai da nayi sati sannan na dawo lokaci na warware, Ya Hafiz yake" kawo ni. "Tun daga lokacin Malamin nan ya saka min idanun, sannan shi ya rubuta min note akan duk ranar biyar" "ga wata, matukar ba jarabawa ba ne ba'a bukatar nazo makaranta idan kuma nazo, na fara zuwa clinic na makarantar na amshi magani da sanatery pad ni sai ya shiga sani jin kunya haka kawai zai saka ni jin" "na zama yar iska, akwai wani program da kamfanin Always suka yi a lokacin, tabbas sun bamu kyautar" "pad din, haka na ga mutumin nan yana kallona. Ni tun a wurin nayi kyauta da shi domin na tsani yadda yake bina da idanu. Sau biyu na taba kallonsa, idan na Ganshi bana iya d'aga kai na kalle shi domin zubi yake min da gardawan almajirai. A gefe guda soyayyarmu da Ya Hafiz kamar mu cinye kanmu, haka yasa yan gidanmu suke ta ganin ina gama secondry School za'a aurar da ni, ban damu ba. Amma kuma zuwa lokacin da muka shiga ss2 mutumin nan ya fara damuna, don ya saka min idanu yadda ni ban zata ba, sannan duk wani abu nawa yana jin sa ne a bakin Ruma ita kuma sai Allah ya daura mata sonshi da ni, ita tayi ta ziga ni har na fara kula shi, amma ba a makarantar ba a gidan Aunty Inna, domin a lokacin Aunty Hindatu tana tare da Ya Hafiz, Nafisa Sadi Gital kuwa cewa tayi na ci kuWinsa kawai don mun lura wallahi kamar bai da wayo, duk abinda zance ina so zai bani, kuma bai taSa jin zafin cire kudi, Yaran Aunty" Innah kuwa wani irin kashe musu kudi yake domin ni a wurinsa na taSa ganin wasu chocolate. "Amir dan Aunty Innah ya cika shekara biyu, nake gaya mishi ai sati na zagayowa sai ga tarkace har da" "Cake, lokacin Blackberry sai wane da wane ina fama da wata yar Nokia da Ya Hafiz ya kure a daka ya saya min, sai ga Malam Bilal ya kawo min sabuwa dal, ai kuwa Aunty Innah yana kara zuwa ta mai da mishi ya ce shi me zai yi da shi, dukkanmu kallon mai fama da albashi muke masa, bana sonshi domin Ya" Hafiz ya cika min raina da soyayyarshi. "Lokacin da muka shiga Ss3 ya gabatar da kanshi a wurin Abba, maganar gaskiya Abba ya amince da shi" "amma lokacin da ya tambaye ni, kai tsaye na ce ni fa Ya Hafiz nake so, shima kuma Ya Hafiz din ya amince ni yake so, haka da ya kara dawowa Abba ya bashi hakuri tare da gaya mishi an tsayar min da miji domin ya tambayar da yayi min na gaya mishi gaskiya. Koda na je makaranta na samu sakon yana min fatan alkhairi, Malam Hamza Adam ya kira ni office dinsa ya min.. ""Lubabatu gaya min me yasa bakya son Malam Bilal?"" Shiru nayi ya rasa yadda zai saka ranshi.. ""kin san waye kika yi rejected dinsa" "kuwa? Kin san waye shi? """ "Kasa kasa nace mishi. "" Kayan lambu ne da zan tsaya dai ya nuna zan zabe shi. Ni ina da wnada nake so!""" """ Wanda kike so kin san waye shi? "" "" Dan uwana ne fa! "" Na fada ina Wauke kai daga kallonshi. "" Shi kenan Allah ya baku zaman lafiya!"" Daga haka na mike na bar mishi office din. Kafin mu gama makaranta na ji labarin wai ai Wan masu arziki ne, Malam Hamza ya gayyace shi bikin Yaye dalibai shine ya zo. A bakin Ruma naji wacce ta ce min ya bar min sako a wurinta. "" Ki rike na baki sakon da ya bani! """ Tayi ta mamaki. "Haka muka gama makaranta na manta da shi domin ya cikin lissafina, a 2017 muka gama har da" "Jamb, na kuwa cika ATBU, ba laifi point dina ya ja, suka bani business administration, a shekarar da na fara a wannan shekarar Ya Hafiz ya kawo lefena da sadakina har dubu hamsin, duk da a lokacin sadaki yafi haka amma ba yanke mishi ba, Dangina kowa ya goyi bayan auren Yayuna maza da mata kowa yana" "san barka, haka yasa bikin ya zama irin na yar gatan nan, gidan da Ya Hafiz zai zauna Haya ce ya kama a" "fadaman mada, layin gidan Mamar tsohon gwamnan Bauchi Isa yuguda. Duk wani kayan gata an saka" "min anyi min auren gata kowa ya sani, shi kanshi Ya Hafiz yasan yadda Iyayena suke kaunata." Yadda muka fara da soyayyarmu me tsayawa a raina kowa ya ganni sai ya yi maganar aure ya amshe "ni, gashi dai nice karama amma ayi min goyon auta ba don na koyi girki a gabansu Mama da Yadiko, haka yasa nayi ta kula da mijina, watanmu uku da aure Ya Hafiz ya kawo min shawarar tunda ina karatu na fara shan maganin hana daukar ciki yana tausayina nayi karama ga kuma karatu, cikin soyayya da kulawa ya bani wannan shawarar, ni kuma na amsa hannu bibbiyu. Saboda Abba ya gaya min Ya hafiz ba zai tab'a cutar da ni ba, kuma na yarda da wannan magana, haka Kakanmu Baba Malam wanda shi yayi ruwa yayi tsaki akan lamarin ya gaya min haka, ashe kiransu yake yayi ta gaya musu yadda yake kaunata," shi baya fatan na mutu na barshi gara shi ya fara mutuwa. Haka nayi ta karatu ina kuma shan magani ban tab'a fadawa kowa ba. Nayi imani da Allah nice "sanadin matsalata. Duk abinda Ya Hafiz zai aikata ban tab'a ganin laifi ko kuskure ba. Shekararmu daya na fara tsintar wasu abubuwan a jikin wandonsa ko rigarshi wato condom, ban tab'a magana ba, na zama makauniya akanshi bana fadar aibunsa, bai sauya min ba sai da na fara wani irin kiba, wai ashe maganin da nake sha ne. Idan da xan gaya muku yadda Ya Hafiz yake min a lokacin kwanciyar aurenmu ni har mamaki nake, domin kamar wata yar iska haka zai ta min, ni kuma bana son ya ji ba dad'i sai na" "hakura na barshi yayi yadda yake so, kibar da na fara sai ya sa na kasa tabuka abin arziki." "Lokacin ina aji hudu na jami'a, an tura ni IT, wani bank na samu horo. Ranar ya kasance Juma'a haka" "yasa na dawo da wuri kuma mun yi zan tsaya gidan Ya Umar Aunty Azizat ta haihu. Na manta kayan barkan a kan gadona. Na koma gidan dauka, yadda na shiga na ga motarshi jikina yayi bala'in sanyi, domin kuwa ya ce min zai yi tafiya ne zuwa Kano. A kofar shiga cikin gidan na ga takalmin mace, haka na shiga cikin gidan domin ina ga ko Kannensa ne da yake suna zuwa. Koda na shiga ban kawo kome a raina ba, haka na shige can dakina ina d'aga labulen mace na samu akan Ya Hafiz suna masha'a, bugawar da zuciyata yayi yasa na juya parlourn da sauri na zauna, jin karar takuna yasa suka fito, lokacin da suka fito suka same ni ina kallon, murmushi nayi mishi nace mishi. ""Dama baka tafi ba ne?"" A dan razane, ya ce min. ""Eh!"" Yana kallon yadda nake kallon tv, haka yarinyar ta fito tana kallonshi. Shi kuma ni yake kallo. Tana fita na koma dakin na dauki abinda xan dauka na fito. "" Ina zaki? "" ""Ka manta dai sunan Aunty Azizat ne? "" ""Muje na ajiye ki! "" Ya kai hannu zai tab'a ni nayi maza na matsa, ina murmushi na ce mishi." """ Huta kawai! """ "Haka na bar gidan, a can na wuni anan ake gaya min umarar bana ma za a tafi damu, sannan Abba ya" "cire zakkar da yake cirewa duk shekara an bawa Ya Ado kudin ya haWa da na wanda yake hannunsa an saya min gida Tambari housing estate, ina jin haka na ce musu kawai zamu koma can, ganin haka kuwa" "suka mara min baya domin yadda kowa yake sonshi saboda ina sonshi ne, laifin da yayi min sai na barshi" "a matsayin ajizanci. Muka cigaba da rayuwar har muka taso daga unguwar da muke muka koma sabo bayan sallah.. shekararmu biyar cib wanda yayi da yin bautar kasana, Ya Hafiz ya fara kulafunci Yara, a" lokacin hankalina ya tashi nayi ta zaryan asibiti amma babu labari. "Bani mantawa wata rana ina kwance wurin karfe tara na dare ya shigo da wata mata, don zata girme ni." "Ya ce bata daki ta kwana. Haka nayi kuwa na bata daki da na ware shi don bakinmu, kwana Waya sai ya zama kwana biyu kai a takaice dai sai gashi ta share kwanaki a gidan. A cikin wannan yanayin na kama shi da ita, a lokacin na saka a raina gara ya aure ta, yaki har da gaya min wai karuwa ce, na ce haka zai yi hakuri, a cikin lokaci kalilan na shawo kanshi, ya kai sadakin karima, kowa a dangina yaji maganar aurenshi, hmm mutum sai Allah sai ga magana ya fito ta Jama'are cewa ai dalilin aurensa don ni na kashe mahaifina da shan kwayar hana daukar ciki, a lokacin dangi kowa ya juna min baya nima kuwa na tashi da rikici na ce ba gidana ba, Abba da Baba Malam suka zo har gidan suka ci mutuncina tunda ni" bana kaunar Hafiz shi yasa na sha maganin hana daukar ciki ban isa ba a gidan zai zauna da Matarshi. "Haka nayi hakuri na dauke kai, aka yi auren. Suka yi ta min iskanci da renin hankali. Wallahi tun bana" "iya dauka har na fara, abin da ban sani ba akan shi kai kara, abu kaWan ya kai ™arata, ayi ta zagina ana ganin laifina. Kwatsam sai ga Matarshi da ciki aka yi ta murna ana farin ciki. Nima dai nayi murna, nayi farin ciki. Sai dai watanin cikin da auren bakwai, da safe muka samu hatsaniya da ita, kuma Ya Hafiz din Yana nan shi ya raba rigimar, bayan ya fita kasuwa kawai jini ya Salle mata, haka aka kwashe ta zuwa asibiti. Haka muka je ko awa daya na ayi ba ta haifi Yarta mace, aka fito aka gaya mana, muka yi ta murna haka na koma gida na gyara inda jini ya bata na wanke gidan, wurin karfe biyar na yamma aka sallame ta, suka dawo gida washi gari Ya Umar ya zo ya min shegen duka, wanda ya fusata Aunty Hindatu a lokacin tayi ta fada tun daga nan ta tsaya min, wai ashe labarin abinda ya faru Ya Hafiz ya gayawa Baba Malam shi kuma ya kira Abba yake ce mishi ga can Lubabatu zata kashe mata da ciki jini ya Salle mata.. shine Abba ya ce ko a samu wani ya min duka. Ko kuma ya sake Mama. Wannan abin ya" fusata Ya Umar.. "Danginta da kowa yana jin haka, har shi ya Hafiz din, sai da nayi zazzaSi, yan uwanta don gulma sai" "sun zo duba ni. Haka na daure na yi ta hidima dasu har aka gama suna abu daya na musu fintinkau, iyayenta talakawa ne na fitar hankali hatta abubuwan da aka yi na suna daga gidan Iyayena ne, ranar sunan da yamma na shiga naji suna min dad'i. Ni ban kula su ba sai Aunty Raliya da ta wanke su tas ta ce musu. ""Ai ku san tarbiyya irinta gidan yasa aka zane ta kada ta kara aikata shirme, gidan da Yarku take abincin da Yarku take ci daga arzikinmu ne, shi kanshi mijin dai bai da nashi na kanshi sai na matarshi don haka mu yar mu tana da tarbiyya domin bamu sake ta tayi ta bin titi kwaro-kwaro ba. Ga sittin ga degree. Haihuwa kuwa ba akanta aka fara rashinsa ba, Allah ya karawa Nana A'ishah yarda itama har" "tayi wafati Allah bai bata haihuwa ba. Mun san islamiyya domin mun zauna gaban Malamai "" daga haka" "suka yi shiru. Tun daga nan ta koma bayana, Yan uwan ya Hafiz suka koma jikinta hatta Hajiya komawa" tayi jikinta. "Haka aka watse wani renin hankali, sai su bawa yarinyar maganin barci su kawo min ita haka zasu ta" "iskanci wani lokaci kuma haka zasu kawota ko za mutu tana kuka ba zasu amshe ta ba, haka na ci wahalar yarinyar nan. Gashi da na gama bautar ™asa result dina yana fitowa aka so niman min aiki Amma da yake mugunta na ransa ya hana.." "Haka nayi ta rayuwa da kunci da wahala, gashi ya hana ni cigaba Umaran da muke zuwa ya dauke min" "damuwa, idan ya Hafiz yana son wani abu a guna tow wallahi a lokacin zai ta kashe ni da soyayya har sai na fara jin anya ba rashin fahimta bane, amma ina haka dai muka cigaba. Akwai shekarar da Abba ya biya musu Umara shi da Karimah kanta yayi ta rawa haka suka tafi watan Mauludi." "Bayan sun dawo takuma daukar ciki, a lokacin Firdausi ta zo ta zauna a gidan, na ga iskanci ganin" "idanuna. Na gama secondry School ina sha shekaru goma sha bakwai, na gama jami'a ina da shekaru ashirin da biyu, a duniya. Haka kafin ta haihu ya ado ya zo ta sauya min kayan gidan ashe ya samu karin mukami ne, a lokacin na ji labarin tun dukana da Ya Umar yayi suka daina magana, dama shi ne mai tsaya mishi akan kayansa da yake shigo da su ya cire hannunsa. Kai abin fa sai da aka yi zama sosai domin a ganan Abba Ya Ado ya ce mishi.. ""wallahi billahi azmin, duk wnada ya kara taSa Lubabatu sai kotu ta raba ni da shi, saboda me aka sauke Suratu hujara?"" Akan wannan rigimar Ya Umar Win ya shirya min birthday da na cika 23, ina zaune aka zo aka dauke ni, sai gidan Ya Umar a can aka yi birthday party din ya bani motar da kowa sai da yayi mamaki ya ce min na kira Ya Ado na gaya mishi, na kira na gaya mishi na tura mishi motar ya gani shine dalilin shirinsu, tun daga lokacin Yayuna suka dauki nauyin tura min kudi, Amma ya Hafiz ya shiga kwacewa, duk shekara idan muka je Umara sai na sayi yan kunne gwal kamar yadda su aunty Hindatu suke yi domin dukkanmu Yaran Abba mata yake biya mana, har su Aunty" Munah aunti Raliya. "Karimah ta haihu ana saura kwanaki uku ba dawo haka na saya mata kayan Baby, lokacin da na dawo na" "samu an gyara min parlourn, ai kuwa na dawo da kwana biyu aka yi suna yan'uwana a parlour, ga girkin da aka yi musamman ni da muke shiri da yan unguwar suka yi ta shigowa saboda ni, bayan suna shima" "suka tattaro min yaran bakiWaya, haka nayi ta hidima da su har tsawon shekaru biyar cif." Duk wani abinda nake da shi Ya Hafiz ya ga na cigaba ne dai ya raba ni da shi hankalinsa yake kwanciya. * Kiran sallah farko ne ya sani share hawayen da ya zuba min yanzu na fahimci dalilin da yasa min haka. Na "ga tashin hankali a rayuwata na ga abinda zuciya ba zata iya karba ba, amma na amshe shi hannu bibbiyu, danginmu kowa ya juya min baya. Uwar da ta haife ni ta tsame Hannunta a kaina, Mahaifina ya watsar da ni, a koda yaushe nayi kuka Ya Hafiz xai nuna min ai ba kome ba ne, saboda kawai dan karamin mistake ai ba wani abu ba ne can babba da zai saka ni damuwa, Ya Hafiz Dan uwana ne tunda da Baban Jama'are da Babana uwa daya Uba daya, sannan Ya Hafiz ya boye munannan halayenshi ya bayyana kowa kyawawan halaye da Dabi'u, babu wanda zai ga ya Hafiz ya zata yana da mugun hali. Sai dai kowa yasan mai kyau kuma yasan mara kyau, idan da ni ce Ya Hafiz ba zan taba saka shamaki a tsakanin zuciyoyin da suka yarda da ni ba. Amma sai ya lalata min rayuwata da future dina da kuma duk" "wanda zai kalle ni ya tausaya min, sai ya cusa min kin kaina da rashin accepting kaina." "Ya danna min tsoron duk wani d'a namiji da kuma duk wanda zai kalle ni a matsayin mace, ya nuna" "min cewa ni ai ba mace ba ce. Ya kuma gaya min cewa kaf duniya da zuriar Baba Umar Jama'are babu wanda zai ganni ya ji sha'awar zama da ni ko kaunar zama da Ni. Bayan ya ga bani da amfani ya cigaba da ajiye ni domin a ga yadda yake namijin ™o™arin kula da rayuwata. Ba zasu fahimci waye shi ba, sannan idan zasu shekara dubu ba zasu tab'a gano waye Ya Hafiz ba hawainiya ne shi mai sauya launi daga" wannan zuwa wancan..... *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu *Littafin nan na kudi ne akan 1500* "*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105" ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641 Posting Arewapen da Telegram SHA UKU HAFIZ "Da farko bai zata zai haukace akan tafiyar Lubnah ba, bai taSa kawowa a ransa tana da amfani har haka" "ba sai da ya wuni yana bibiyar dangi da yan uwa ko ta je wurinsu, amma babu labarin kai ko a mafarki babu labarin Lubnah haka yasa hankalin kowa ya tashi ban da yan dakinsu da sun san mafarin. Yadda Ya Hafiz yake playing victim sai ka rantse da Allah, ba shi yake yi sanadin barinta gidan ba, aikuwa Washe gari sai ga Baba Malam, shi da Baban Jama'are da Hajiya Asiyah,Goggo Alti da Goggo Uwani sai Goggo talatuwa. Hankalin kowa yayi bala'in tashi, rayuka sun b'aci. Tambayar da Baban Jama'are da Goggo Alti suka mishi ya sake cillashi cikin wani tashin hankalin. ""Me ya haWa ka da Lubabatu da har ta dauki wannan matakin?"" ""Wallahi na rantse da Allah ban mata kome ba, kishi yake janta."" ""Yarinyar da magana ma bai dame ta bane zata yi kishi har na fitina? Hafiz kasan ina da labarin abinda kake aikatawa!?"" Inji Mahaifinsa, take Baba Malam ya rufe shi da fada. ""Ya ana cikin wannan tashin hankalin zaku kara mana da wani. Ku barshi da ji da damuwar da yake damunsa ba a kara masa wani ba, gaya min me kuke son cewa."" Goggo Alti ta ce mishi. ""Baba Hafiz munafiki ne, ba kan Lubnah ba hatta Sirajo sai da Hafiz yayi sanadin barinsa shagon Shehu, yanzu haka ya koma wurin Babana yana zaman shagon, Allah ya gani tunda ka yi sanadin da Babana ya bar shagon na fara tunanin ya kuke zaune da Lubnah kowa yasan yadda kake nunawa ka damu da ita bayan kuma kai ne shaidanin da kake rabata da duk wani farin cikinta, Shehu da kanshi ya kira ni yana gaya min ya kori Sirajo ina laifin ya ce min na ja mishi kunne, bayan abinda Sirajo ya sani gaskiya ne, Ali ka ganshi idan akace min zai dafa mutum ya ci zan yarda domin munafiki ne na gaya muku gaskiya. "" "" Alti ina magana! "" "" Baba dole fa mu fadi gaskiya domin Lubnah kaWai ba zata iya fadar abinda take ji ba, azzalumi mugu hatta dukiyarta sai da ya lalata mata ya kwashe maha'inci, kai akanka ba ka bar kanka na balle wani haba don Allah wacce irin rayuwa kake yi ne haka? Wacce irin manufa kake so ne? Ina tausaya maka Shehu yaranka da ka watsar ka ce basu tausayinka wata rana su zasu dafa maka domin. Wannan munafikin ya hmm! "" Tayi murmushi mai ciwo, tsoro ya kama Ya Hafiz haka dai aka tashi zuciya ba dad'i. Mama ita kanta yanzu ta fara tsoron kada wani abu yake faruwa Lubnah ta bar musu Bauchin, take hankalinta ya dawo kan Lubnah bayan Goggo Alti tayi mata tas, ta ce mata. "" Idan baki tsaya mata ba, wallahi zaki kashe yarki shi Shehu bai da asara haka" "Hafiz bai da asara gara ki tsaya mata kafin lokaci ya kure mata.""" "Wannan maganar ya rikita Mama da Yadiko, don haka tayi ta addu'a Allah yasa Lubnah tana hannu na" "gari, wasa wasa sai da aka kwashe kwana biyar babu labarin Lubnah, haka ya kara fusata Abba wato Baban Bauchi, wanda kai tsaya ya tara Yaranshi da suke Bauchi ya ce ko su dawo da Lubnah ko kuma ya sake Mama, kuma ta bar mishi gidansa wallahi zai aikata, abinda yasa yayi haka faduwar da Hafiz yayi a" "kasuwa, aka kai shi asibiti akace jininsa yayi azabar hawa, ba sai ga Hafiz ya fadi ba. Abin kamar alamara," "sanin cewa Lubnah yake bukata yasa Abba ya fadi haka, shiru Umar yayi kafin ya ce mishi. ""Gobe idan" "Allah ya kai mu zata dawo abin bai kai har ha..."" Tass Mama ta wanke shi da mari ta kara wanke shi da mari. ""Dama kasan inda take kayi shiru!"" ""Dukkanmu mun san inda yake ni na bata kudin motar na kaita tasha!"" Inji Ya Tahir, ba sai yadiko ta rufe shi da duka tana kuka ba, abin fa ba karamin al'amari bane, haka yasa a ranar suka kira Almu shi kuma ya ce ayi hakuri ranar juma'a zai zo. Domin Lubnah ma ya kaita 44 ganin likita bata da lafiya. Da wannan aka kashe case din sai ta zo, kasancewar kowa ya gama jin" ranar da zasu sake haduwa tunda ranar talata aka yi zaman. ** Lubnah "Tun daga ranar da na isa gidan ban kara samun damuwa ba, sai dai rashin lafiyar da nake a tsaye, bana" "cin abinci sosai. A lokacin da Ya Almu suka kai ni asibiti na ciro takarda asibitina na nuna musu. Kallona Likita yayi ya ce mishi. ""Kanwarka ce?"" ""Eh likita."" Basu takarda yayi ya ce yaje yayi test yana jiranmu, haka muka tafi aka yi min test din sannan na zauna zaman jiran, idan mutane na magana sai nayi ta jin maganar har cikin kwanyana yana wani irin ciwo. Haka yasa ina karban result din na kai mishi. Shiru yayi ya ce min. ""Akwai ciwon kai?"" Gyada kai nayi ya gyada kai yana mamaki ya ce min. ""Akwai test din da zan baku sai dai ina ga kamar a Kano ake yi ban sani ba ko an samu asibitin da suke yi anan din."" Bamu hoton ™wa™walwa yayi muka tafi Ya Almu ya kai ni aka min, sannan na dawo kiran wani likita yayi ya zo, yana mai gaya mishi case Win. Kallon Ya Almu suka yi kafin suka ce. ""Officer maganar gaskiya, kanwarka akwai wani sanadarin da yake sakata jin ciwon da take ji, na farko akwai drug din da take sha ta daina wanda ya ke hana wancan sinadarin aiki sosai, na biyu abin ya tab'a mata ™wa™walwa da yasa take jin ciwon kai, a takaice dai Mentally healthy dinta ya tabu, sannan tana fama da rashin lafiya resilant, daga yadda take gabanmu kawai dai saka ka fahimci tana fama da kanta, amma zan bata magani!"" Anan ya Almu ta gaya musu ai ina ganin likita a Bauchi, take suka ce zasu so ganin record dina, shiru Ya Almu yayi kafin ya ce musu, ""daga Bauchi take idan aka ce sai anyi haka zai iya daukar lokaci!"" Haka suka yi shiru suka kallona, kafin daya likitan ya ce mishi. ""Ko zaka samu wani da yake da alakata da ita akan matsalar."" Tunawa yayi da Aunty Innah, don haka ya kirata ya gaya mata abinda yake faruwa. Shiru tayi ta ce ya bawa likitan wayar, ya mika mishi suka gaisa kafin suka shiga tattaunawa da yake abu na masu ilimi da" "sanin ya kamata, na wane da wane,a fagen da kowa ya kware." Maganar da suka yi da Aunty ya sakawa likitan tabbaci da hasashensa. Sannan ya tambaye ta "maganin da nake sha, ta gaya mishi sannan ya canza min wasu magungunan. Ya kalli Ya Almu ya ce mishi. ""Yana da kyau ta ga asalin likitan ™wa™walwa da na zuciya."" Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa. ""Cikin fahimtar da nayi duk da ban duba Sangaren zuciyar ba yana da kyau a san da zuciyar na da matsala ko babu."" Sun jima suna magana wanda rabin maganar ba fahimta nake ba, bayan mun bar asibitin Ya Almu" "ya mai da ni gida, tunda muka isa na zauna a parlourn don shi ya umarce ni na zauna ya kawo min ruwa" "da magani ya bani na sha. Sannan ya ce min. ""An samu matsala a gida, ranar juma'a zan mai dake gida" "kin ji!"" Gyada kai nayi ya cigaba da cewa. ""Zamanki a daki bai da amfani kin ga Saliha bata nan, ki zauna a parlourn kafin ta dawo. Akwai abinci."" ""Yaya tafi zan kula da gidan!"" ""Are you sure?"" Gyada kai nayi ina mai kallon gefe. Amma idanuna kwalla ne yake taruwa a hankali. Fita yayi ya bar gidan na lumshe idanuna na kwanta a wurin, dama ko na zauna a dakin ba barci nake yi ba, ina zama ne nayi ta nazarin yadda Allah zai kawo min mafita tow ina ganin kamar na tsira amma ashe ina zan koma gidan jiya, hawaye ne suka zubo min a hankali nayi ta zubar da hawaye ban sani ko don ina son na samu iskar yanci ne amma ni dai nasan na gaji, ban san lokacin da na dauka ina zubdar da hawaye ba sai da barci yayi" gaba da ni. Ina ga a cikin maganin da nasha akwai na barci ne. "Ina ga rabona da barci me kyau tun muna tambari housing estate, yau sai gashi nayi barci kamar bani" "ba, sai karfe biyar na farka shima muryan Zunnur ya saka na bude idanun yana tambayata Aunty barci kike yi baki yi sallah ba! "" A hankali na tashi ina faWin. "" Na gode Babana da ka tashe ni! "" Ya Almu da yake aiki a laptop dinsa ya ce mishi. "" Father akan me zaka tashi Yarka! "" "" Dady tayi Sallah! "" Murmushi nayi na wuce dakin da nake nayi sallah kasancewar kasaru zan yi, bayan na idar na zauna sai ga Aunty" Saliha da abinci haka na taSa sannan na cigaba da zaman dakin. "Da dare yayi Ya Almu ya kara bani maganin na sha nayi barci sai na samu sau™in ciwon kan, sannan na" "samu barci a hankali tunanin da nake yawan yi ya ragu, sai tsoron yadda zan isa gida, ya zamu kare da Iyayenmu? Sai tsoro ya kara kamani. Haka kwanakin suka tafi har zuwa ranar da zasu mai da ni, da wuri muka bar Kaduna, domin ya ce yana son ya dawo ranar ne, haka yasa muka fita da wuri da yake maganina ya saba da jinina ba wani barci, sai dai nayi kaWan kafin muka iso saminaka. Ya Almu ya sayi tsaraba muka cigaba da tafiya har zuwa rahama rishi, tunda muka iso nabardo na ji tsoro ya kara mamaye ni, kafin karfe biyu na rana mun iso garin Bauchi. Sai a lokacin na rude kamar zan shiWe, har muka iso kofar gidan aka bude get din gidanmu ya shigar da motar, kasa fitowa nayi bayan yayi parking. ""Darling sister shiga gani nan zuwa!"" ""Tow!"" Na fada ina jin wani irin tsoro yana cika ni, ina saka kafana a waje naji kamar an kwashe min karfina haka na cigaba da tafiya har cikin gidan a dan barandar da zata kai ni cikin gidan anan na hango Ya Hafiz tsaye, wani irin bugawa zuciyata tayi naji kamar na juya da gudu. Kanshi a sunkuye da alamu waya yake cikin farin ciki da nutsuwa, kamar ance ya d'ago kai sai a kaina. Ji nayi kamar zan takowa yayi nima na fara yin baya ji nayi an janyo ni baya. Sai da na sake wata irin ajiyar zuciya da naji kamar numfashina zai bar jikina. Baya Ya Almu ya dawo da ni. ""Wani irin hauka ne haka?"" ""Ba ruwanka Malam matata ce!"" Ya fada yana kokarin kai hannu ya riko ni, kunsan a binka da soja ba sai Ya Almu ya sake ledar tsarabar ya kai mishi wata mahaukaciyar naushi ba, sai da ya fasa mishi baki, sai da ya zube a kasa yana mai d'ago kai yana faWin. ""Ni ka nausa?"" Ya fada yana kallona murmushi yayi sannan ya mike tare da nufar cikin gidan, haka na rike rigar Ya Almu. ""Yaya ina jin tsoro."" Shigar Ya Hafiz shi ya sanar da yan gidan mun iso, Ya Ado ya fara fitowa. Ganin yadda nake rike hannun Ya Almu na tirji na ki shiga gidan, isowa yayi ya riko hannuna yana faWin. ""Princess welcome back!"" A hankali na kalle shi. ""Abba yayi fushi ko?"" Girgiza kai yayi ya riko hannuna muka shiga cikin gidan, wanda yayi daidai" "da fitowa Hajiya tana faWin. ""Aure sai kace na jaraba dole ne sai ka zauna da Kanwarsu? Ace kamar Almu" "ya d'aga hannu ya zabga maka naushi akan Kanwarsu aka fara samun matsalar aure ne!"" Lokacin da" "muka isa parlourn ina rike da Ya Ado, har muka zauna jikina bai daina rawa ba, ba zato ba tsammani Mama ta rufe ni da duka, Ya Ado yayi maza ya kare ni, Ya Tahir shima ya taso suka kare ni, haushi ya kama Mama ta dauki takalmi tayi ta dukan mu da shi haka Yayuna maza da matan nan da ake zaune dasu a dakin suka rufe ni, kallonsu na tsaya ina yi, madadin na ga damuwa sai naga suna murmushi. A hankali na daura kaina a kirjin ya Ado na rufe idanuna har Mama ta daina dukarsu ta fashe da kuka, hannu Ya Almu ya saka ya toshe min kunnena. Bude idanun nayi ina kallonshi, murmushi yayi min hawaye na zuba daga idanunsa, ban san me Mama take fada ba, amma yadda suke kuka ya sani zare hannunsa a kunnena. ""Kin zame min ™addara ko numfashi bana iya ja mai kyau kin lalata min suna a ko ina kowa gani yake ina daure miki kugu ki yi yadda kike so, da wanda ya kai ya gaya min magana da wanda bai kai ba mai na miki na cancanci haka Lubnah wannan shine kyautar da zaki min na" "haihuwarki.""" """Idan na isa da ita, ta bi mijinta bana son jin wata kalma su kuma duk wnada ya sake shiga rayuwar" "auren Lubabatu Allah ya isa ban yafe masa ba."" A wannan zuwan Baban Jama'are bai zo ba su Goggo ma basu zo ba. Haka Yayuna suna ji suna gani na bi Ya Hafiz da Hajiya Baba Malam yana faWin. ""Allah ya maka albarka dole ka ga alkhairi a rayuwarka dole kayi gba ba zaka tab'a ganin baya ba."" Wannan" addu'ar da Uba yake yiwa dansa duk saboda yabi son zuciyarshi ne. Haka na cigaba da bin su Ya Almu ya biyo ni da wata karamin akwatin da kayana da maganina yake ciki "sai wayata da Aunty Hindatu ta bashi ya bani, sai da ya bani ya juya ya kwashe ya Hafiz ya buga shi da kasa tare da take wuyarshi. ""Wannan kashedi na maka, abinda zai faru yana zuwa idan na samu labarin ka mata wani abu sai na maka dukar da ba zaka moru ba."" ""Amma dai baka da mutunci!"" Inji Hajiya. ""Ga mara mutunci nan a kasa ya nuna mata Ya Hafiz, tashi yayi ina kallonshi yayi murmushi ya ce mishi. "" Yadda kuka min Allah yana gani kome dai wuce! "" Daga haka ya budewa Hajiya gaban mata ta zauna sai ni na bude baya na shiga. Tunda muka fita a gidan suka shiga zagina. Dakyar ya iya danne kanshi. ""Ina" "shiga dakina ya biyo ni.""" "Ban san yadda zan fada ba, amma a ranar Ya Hafiz ya cika min raina da wani irin tsoro he tell me kaf" "duniya babu wnada ya isa kashe mishi aure, sannan babu wanda ya isa ya kara takowa ko ni na fita, gidansa shine kurkukuna har na mutu be with keep me saboda ya nunawa Yan uwana babu wanda suka isa su mishi. Kun san abinda ake kira tsoro? Anya kusan ma'anar tsoro, to kada Allah ya jarabce ku da tsoro domin tsoro mugun abu ne me kashe rayuwa da kome, sai da ta kai Ya Hafiz ya birkita min ™wa™walwa, ko karar kwano naji sai na ji kamar na mutu, domin ko yaya naji kara zan dawo daki da gudu nayi ta kokarin rufe kofar, domin yadda yake dukana yana min barazanar zai kashe ni, kuma Hajiya tana" gani tana ji. Bata hana shi ba. Wata daya zuwa biyu na manta da wani zancen magani tow ya kwashe yana kawo min wnada yayi "mishi, ko ban sha ba zai matse ni sai na sha, ganin yadda nake kin sha sai ya shiga jika maganin a gora ya daura min sai na shanye, duk saboda me yasa? Saboda yadda aurenmu zai yi survive haka abinda ya" "aikata zai rufe har abada, da bakinsa ya ce min." """Idan na sake ki, zan kara gaya miki ba zaki tab'a samun wanda zai zauna da ke, ki rufawa kanki asiri ki" "dawo dakinki, domin ni dai bani da matsala. Zan zauna da ke kamar yadda wancan tsohon da Malam Babba suke son na zauna da ke. "" Yana murmushin keta, tun daga lokacin duk maganar da zata fito daga bakinsa iya abinda yake aikatawa yake gaya min. "" Ba zan tab'a sake ki ba haka zaki mutu a dakin nan gawarki kawai za a sallata! "" Ire-iren waWannan maganar kawai suka kashe ni, haka kawai zasu turo min Yara suta ihu a dakina, duk yadda naso na fahimci kome ya dagule min, ganin yadda nake kokarin rasa lafiyata ya kara dawo min da maganin ba batun ganin likita ma, sai da na fata shan maganin ya ga da" "gaske na fara dawowa dai-dai sai ya sake daukewa, ko sati ba ayi ba ciwon ya kara dawowa." *** Aunty Innah. "Kuka take tana faWin. "" Don Allah ki saka baki muje my duba ta, sau biyu ina mafarkin tana niman" "taimako, don Allah ki yi wani abu Lubnah tana niman agaji!"" Ta fada tana kuka. ""Idan baso kike ki kashe min aure ba ai ya kamata ki bar gidan nan kada ya dawo ya same ku, ai kune kuka dagula kome! """ """ Mama bamu bane, kune Mama kune kuka hana ta magana, Allah kaWai yasan ciwon da take ji, Allah" "kaWai yasan yadda zuciyarta take cike da rauni."" "" Ai haka ne? Tow ni ba zaki kashe min aure ba, fita ki bani wurin mun gode da muka saka Lubnah a cikin wannan halin!"" Kukan Innah yayi yawa wanda ya janyo hankalin Ya Sani da yake dakin Yadiko, fitowa yayi ya nufi dakin, yana shigowa ya same Innah tana rokon Mama, juyawa yayi ya fita, bai tsaya ba sai gidan wani abokinsa wanda ake kiranshi da Sadiq Bhai, saboda yadda yayi kaurin suna a aikin daba, ya gaya mishi inda zai raka shi. Shiru yayi sannan ya ce" mishi.......... *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu *Littafin nan na kudi ne akan 1500* "*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105" ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641 Posting Arewapen da Telegram SHA HUŠU """Bari na kira maka abokina a zangon ni yanzu na tafi zango al'amarin zai girma fiye da haka."" Haka ya kira" "abokin ya gaya mishi, shi kuwa ya ce Sani yaje, lokacin da ya isa zango suka rufa mishi baya, har kofar gidan da aka rufe ta ciki, buga kofar Sani yayi Karimah ta amsa da cewa. ""Waye ne?"" ""Sani ne!"" ""Ok ka kira shi ya ce kada na budewa kowa ya shiga!"" Wani Ash'ar da ya danna tare da yin baya ya daki kofar sai da ta Salle, daga jikin bangon suka take kofar suka shiga yadda yan sara suka suka cika gidan yasa ta yin" shiru. "Ina kwance kamar a mafarki na ji muryan Ya Sani, bude ido nayi ina kallonshi kafin na lumshe, lekowa" "yayi ya ce musu. ""Don Allah ku nima mana Napep."" Ya fada yana dauko min hijab ya saka min tare da d'aga ni, ya fitar da ni waje aka saka ni a Napep. Ya koma dakin ya rufe ya tawo da key, tun a hanya ya kira Aunty Hindatu ya ce mata. ""Maza mu hadu a asibiti gata nan ina ganin mutuwa zata yi!"" ""Waye?"" ""Lulu!"" Ya fada da karfi, yana tallafo ni, kafin mu isa asibitin kowa ya hallara haka aka wuce da ni" "emergency, ni dai ban kara sanin me ya faru ba." "Sai after few days, na farka shima din bana magana, domin idan na kalle su sai naga suna komawa Ya" "Hafiz haka yasa ko na buWe idanun zan rufe da sauri. Maganar da Ya Umar yake na fahimci an kama Ya Sani, wanda shi kaWai aka kama kuma maganar da ake wai Abba ya zare shi cikin Yaransa, ya kara da cewa ko mutuwa nake ina dawowa na koma dakina idan kuwa Hafiz yace ban koma ba tow kuwa wannan karon sai dai Mama da Yadiko su bar mishi gidansa. Wani irin tsoro ya kama ni, sai da na samu" "sati biyu me kyau aka sallame ni, anan muhawara ya tashi na ce musu. ""Ku bani kuWina!"" ""Me zaki yi da" "shi!?"" ""Ku bani kawai!"" Haka dai muka wuce banki aka cire dubu dari biyu da hamsin, sannan na dawo" "gida da shi, ban d'aga idanun nayiwa Ya Hafiz magana ba." "Ban san ya aka yi na samu wata kwarin gwiwa ba, amma ina bu™atar hujjar da xan rabu da Ya Hafiz," "shi yasa na dawo na gaji da barazanar Abba akan Mama da Yadiko, haka ya cigaba da iskanci kuma har lokacin Ya Sani an wuce da shi gidan gyaran hali, haka na cigaba da zama tsawon kwanaki." "Ranar da Ubangiji ya kawo min karshen duk wata damuwa, shine ranar Talata na tashi na daura abin" "karyawa, nawa iya ni cikina ni daya na daura, bayan na gama na zauna ina hutawa, sai ga Karimah. ""Ke ina ruwan zafin da zamu karya?"" Banza na bawa Ajiyarta ta fita a fusace lokacin na hada nawa na fito na wanke cokalin sai ga Ya Hafiz, yana zuwa ya ce min. ""Ba dake ake magana ba yar dangi?"" Ganin naki kula shi, har na shiga daki ya biyo ni ganin yadda na haWa nawa na nufi wurin kofin yana Wauka bai wata wata ba ya watsa min tafasasshen ruwan zafi a gadon bayana, ji nayi kamar dukka jikina ya matsa min, ga rigar jikina irin robar nan ne mai daukar zafi, yaga rigar nayi na watsa garin cire Braz dina na kwaso har da fatar bayana, zama nayi ina haki domin yau kan Allah ya kawo sanadin kenan, a hankali na d'ago kai na kalle shi, yadda nake kallonshi ya razana karshe fita yayi daga daga dakin, na dauki wayata na kira Ya Umar na ce mishi. ""Don Allah ko zaka zo muje asibiti?"" ""Baki da lafiya ne? Gani nan don Allah ki jira gani nan!"" Ai tun kafin ya iso Ya Hafiz ya gudu, yana shigowa yayi ta kwala min kira, a hankali na fito koda na iso gabanshi zubewa nayi a sume, haka yasa saka shi shiga tashin hankali, yadda na kifa tare da faduwa akan hannuna, shi yayi sanadin gocewar kashin hannuna, yadda fatar bayana ta bare jajjur ya bashi tsoro," "haka ya riko ni, muka nufi asibiti." "Kiran Aunty Hindatu yayi ya gaya mata, itama tazo, kafin kace kwabo Aunty Raliya da take Jos ta iso," "babu wanda ya sake ya gayawa su Mama da Yadiko. Kawai anyi shiru an barsu. Aunty Hindatu ta kanta ta koma zango ta dauko kuWina tare da kayana ta kwaso min. Haka kwantar dani tsawon kwanaki ashirin ana wanke ciwon kafin aka sallame ni don ya kame. ""Yanzu ina zaki?"" ""Jama'are na gaya musu shirina."" Dama Ya ado yasan kome don haka ya ce na jira shi Aunty Munah da take River sai gata, don ta ce ba zata sake barin kallo ya wuce ta ba, Ya Abba daga Maiduguri ya dirko, kwana Waya muka kara gaba sai Jama'are. A gidan Goggo Alti muka fara sauka aka muka huta aka yi girki aka yi sallah sannan aka ci na" "nuna mata bayana da abinda ya faru ba kara da gaya mata gaskiya na gaji dari bisa dari ya goya min baya. Na nufi gidan Kakanmu. Da taimakon Yayuna muka isa gidan, na gaya mishi ya kira Yayansa da Hafiz" domin nazo a raba auren ne har da Matarsa. "Kiri-kiri tsohon nan ya shiga fada wai an zuga ni. ""Ba a zuga ni ba, a yzun na samu amsar tambayoyina," "kai ne sanadin Hajja bakin cikinka ya kashe Hajja yanzu na fahimci yadda aka samu gawar Hajja, tabbas kai ka kashe Hajja sannan itama Dadah kayi sanadin daina ganinta karshe ta mutu bata gani. Imma ka" "kira Yaranka, ko kuma na kashe kaina kuma wallahi Yan uwana da hukuma ba zasu barka ba, mutuncin" "da kake da shi a fada sai ya zube, kimar da ka jima kana karewa zaka rasa. Zuwa gobe ka tara mu anan ko kuma jibi yan sanda su taraka a office Winsu. Kuma zan saka sunanka a cikin waWanda suka kashe ni ba kai ba hatta Abba ba xan kyale shi ba."" Daga haka na fito, ajiyar zuciya nake, amma definitely zuciyata ba" "zata iya daukar wannan kasadar ba, tsohon da nake ji yafi karfin na fada a fatar baki." "A daren Abba sai da ya kira Yayuna babu wnada ya dauki wayar, kai abin fa dole yasa aka hadu kamar" yadda na fada din. *** "A yau da nake tsaye a gaban Baban Jama'are, rike da jakata na zauna a gaban Baban Jama'are da kuma" "Malam Babba, tura kudin nayi a hankali. ""Ya Hafiz ya biya sadakina a shekaru goma sha daya Naira dubu hamsin, yau na dawo mishi da dubu dari biyu,kawai abu daya nake bukata SAKI NA!""" "Mikewa yayi yana faWin. ""Hauka kike? Waye zai aure ki da wannan yanayin naki? Baki ga kina kama da" "dodo ba ne? Kambu ina ruwan kwatarkwashi, na ji xan sake ki shi waye ya gaya miki akwai wanda zai aure ki "" Tass aka wanke shi da mari, Yaya Adam kallonshi yayi cikin huci ya ce mishi. "" Ni barista Adam" "Usman Umar Jama'are na tsaya mata, yau na kara yarda da cewa kai mugu ne hafiz laifi ne don ta nemi" "saki? Ashe dama wannan shine asalinka?""" "Baban Jamaarae ya ce mishi. ""Na gode Adamu, na gode da ka wanke min raina, yau ba gobe ba ka sake" "ta ina alkaliya Hindatu?"" Mikewa tayi ta dawo gaban jama'a, ta ce." """Baban Jama'are ni ba alkaliya ba ce, amma xan iya kiran alkalin ya shiga lamarin!""" """Idan kuka kashe Auren Lubabatu ku sani sai dai ku nima mata wani Uban ba ni ba."" Inji Babanmu. Da" "wani murmushi yake kallona, yana da wanda ya tsaya mishi. Murmushi nayi ina kallon kwayar idanunsa." """Idan ka kore ta, ina da inda zan ajiyeta. Hindatu ki kira mana alkali mu yi maganar da shi.""" """A'a su koma su sassanta kansu, idan abu ya ci tura sai mu kai gaba inji Baba Malam.""" """Wallahi wa Rabbul Ka'aba, ba zan sassanta da shi ba. Idan aka ce dole na koma gidansa zan koma amma" "ku sani zan mutu kuma zamu haWu a gaban Ubangiji shine alkalin alkalai, ba zaku gane yadda nake mutuwa ba ne? Ba zaku gane yadda nake cutuwa ba ne?"" Cire Hijab dina nayi na nuna musu hannuna da yake makale a wuyata. Na kuma kalli Aunty Inna na ce mata. ""Zuge min zif din rigana!"" Tana zugewa, na juya musu baya ruwan zafin da ya watsa min na shayi ne na ce musu. ""Kace na tafi Baba zan tafi idan ka ce na mutu zan mutu, wannan shine abinda dan sonka ya min!"" Kunya ce ta kama Ya Hafiz ya fara kame-" "kame yana faWin. ""Ba fa da gayya na mata ba, wallahi kawai na je zubar da.""" """Habibi kame-kame me kake kai fa kace ka gaji da ita gara ka sake ta, ina dalili mace ba haihuwa ba ka" "zauna da ita sai ciyar ta da ita kake yi, idan ka dawo da ita kuwa mutuwa zata yi da zama da kai domin an gama zugata. Mace sai kace rumfa. Kai ma dai da son rai kake, kasan ko ka ci gaba da zama da ita ba" "haihuwa zata yi ba tunda kai ne ka lalata mata mahaifa, gara ka sake ta kara gaba domin nima na sakata" "na wala"" tana fadar haka ta juya ta bar parlourn, burinta ya cika ta fada fara ya sake ni yadda zata ji dad'inta ita Waya da Yaranta." """Alhamdulillahi Ubangiji ya bata miji na gari, zaka sake ko sai na maka Allah ya isa!"" Inji Baban Jama'are" "mahaifinsa. ""Baba ina son matata, sharrin shaidan ne wallahi ban yi haka don na cutar da ita ba.""" Matsowa yayi gabana domin yanzu yasan tabbas za a raba shi da Lulu Kuma wannan zai kara hankad'o "wasu abubuwan da ya aikata wanda haka yana fitowa kowa sai ya kusan tsine mishi ""Luluna ki yi hakuri ki amince mu koma zamanmu!"" Yadda yake roko da magiya zaka rantse ba shi ya gama cika baki idan ya sake ni sai na rasa majingina ba. Yadda ya gigice da Babanshi ya kara daka mishi tsawa Kakanmu Baba" "Malam ya ce mana. ""Ku tashi ta koma dakinta.""" """Gaskiya ba zata koma ba, domin yanzu haka Lubnah tana ganin likitan ™wa™walwa ne, saboda damuwar" "da take da shi ya shafi ™wa™walwarta kowani lokaci zata iya haukacewa!"" Inji Aunty Innah, kallona kowa ya koma yi cike da mamaki sai lokacin da hawaye yake zuba min. ""Tabbas a yanzu haka ranar Monday zata ga babban likitan ™wa™walwa anan Bauchi muna saka ran idan ya ganta zai daura ta akan magani!""" "Inji Ya Umar," "Zare idanun Mama take zuciyarta yana wani irin bugawa. ""Wani irin likitan ™wa™walwa kuma?"" Inji" "Yadiko, . ""Kamar yadda kika ji Yadiko zamu mai da ta ganin likitan ™wa™walwa, domin dole ta ga likita Lubnah da muka bashi ba ita ba ce wannan, idan kun kalle ta da kyau wannan bata da sake koma me yake damunta ba mu da dauka lokaci ya kure da zata kara."" Ya Ado ya fada yana kallon agogon hannunsa," "Baban Bauchi cikin isa irin nashi ya ce mana. ""Idan kuka kashe mata aure ba dai gidana ba, kuma zan zare ku a cikin zuriar ta."" ""Kai sake ta, sannan na rungume Yaran Yaya Usman a madadin nawa, wallahi idan baka sake ta ba sai na maka Allah ya isa."" Cikin fushi Hajiya Asiyah ta ce mishi. ""Dalla sake ta, me za" "ayi da Macen da bata haihuwa me zaa yi da Macen da bata da amfani.""" "Cikin faWa Yadiko ta ce mata. ""Kike fadar haka Hajiya Asiya? Kike fadar haka Hajiya Asiya? Rashin" "haihuwar waye sanadin mata haka? Ke Lubnah waye ya kawo miki maganin hana daukar ciki?"" Kaina wani irin sarawa yake, hayaniyarsu saka min kaina juyawa yake. Kallon bakinsu nake domin motsinsa nake gani bana jin me suke cewa bakiWaya. Lumshe idanuna nayi na bude a hankali, tare da dafe kaina." "Jijiga Aunty Hindatu da nake kusa da ita tayi, na koma zan zube ta riko ni......." *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu *Littafin nan na kudi ne akan 1500* "*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105" ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641 Posting Arewapen da Telegram SHA BIYAR "Wannan sumar ya haifar da abubuwa dayawa, domin Mama ta tsaya a gefena tsawon wunin da nayi a" "gadon tana tare ni. Tashin hankalin da Ya Hafiz ya shiga abin har ya wuce tunanin kowa. Abu kamar wasa sai gashi lamarin ya wuce yadda ake tsammanin domin hajiya take kara jagula take al'amarin ta hanyar da aka yi wani rikici a cikin family akan aurena, sai da ta kai an rabu gida biyu wasu suna ganin kamar naki Ya Hafiz ne saboda Yan uwana sun zuga ni, Yayinda wasu suke tare da ni saboda ciwon da yake jikina suka ce ai tunda ya yarda da ya aikata ,sai gashi haka ya kawo rabuwar kuma kowa ya amince" "da a rabun, banda Abba da ya kafe shi da Baba Malam sai na koma." "Wasa wasa har tsawon kwanaki uku ina asibiti, yau Mama ta shirya tare da faWin. ""Zan tafi karbo" "takardanki, na gaji da ganin yadda kome yake faruwa shi Babanku ya dage ni ma kuwa ina tare dake babu wanda ya isa miki dole!"" Gyada kai nayi ina mai cigaba da kwanciya, nasan cewa ina cikin tashin hankali, amma a kasan zuciyata ina jin kamar ban mishi adalci ba, anya Ya Hafiz ya cancanci haka? Bayan" "fitar ta sai ga Abba ya shigo, wani irin tsoro ne ya cika ni nayi baya ina zare idan, zama yayi." "Gyara zama Babanmu yayi yana kallon yadda nake zaune a wurin guda, tunda ya shigo dakin, ya ga na" "kurawa window din idanu. ""Lubabatu!"" Ya kira sunana, a hankali na juyo ina kallonshi. ""Nasan lafiyarki lau me yasa kike bawa Yan uwanki da mijinki wahala!"" Kura mishi idanu nayi ina kallonshi. Turo kofar dakin Ya Ado da Ya Umar suka yi a tare, ""me yasa kike bawa zuciyar kowa wahala?"" ""Baba bata da lafiya ka bar wannan maganar idan mun dawo ayi ta!"" Inji Ya Umar da yake yana da zafin rai sosai. Rike shi Ya" "Ado yayi yana girgiza mishi kai. ""Lubabatu Y'ata ce, akan me kuke kokarin shiga tsakaninmu?""" """Saboda ka fifita zumunci akan Rayuwarta, ka rabata da Mahaifiyarta kada tazo ta ga halin da take ciki." "Ka nisantata da kowa nata, Abba idan ka sake ta mutu a wannan yanayin Allah sai ya nuna maka iyakar...."" Tass ya tsinkawa Ya Ado mari, a zuciye yayi waje."" ""Abba zan koma gidansa!"" Juyawa yayi yana kallon yadda nake murmushi. ""No Lulu kada ki mana haka."" ""A'a zan koma Ya Ado, zan koma saura me ya rage a rayuwata? Farin ciki sai dai wasu su yi, amma ni na san nayi hannun riga da shi, Ya Ado na" "gode sosai ka ce likita ya sallame ni kawai na koma dakina.""" "Hankad'o kofar aka yi da karfi Mama ce tsaye tana huci. ""Ba zaki koma ba, kin gama aurensa daga" "kotu muke ga takardanki.""" """Salamatu"" ""Sai me? Uwarshi ta kai kotu me ya rage? Ai dama albarkacin zumunci ne zaku kashe min" Y'a Uwar da tafi ™arfin Mijinta zaka yi tsammanin zata bar Lubnah ta zauna ne? An bashi kudin wanke "muni me ake bukata?""" "Shima kamar wanda aka wurgo shi ya ce mana. ""Wallahi ban sake ta ba.""" """Kotu ta sake ta!"" Inji Mama tana kara kallonshi. ""Kaci albarkacin Ubanka, da sai na saka an maka abinda" "baka zata ba, Lubabatu kuwa ta haramta maka. Adamu kasan yadda zaku yi da ita zaman Bauchi ya kare kuma ka kuma kusantar inda Lubabatu take sai na saka an wulakanta min kai, idan kana jin rashin kunya da fitsara wannan cikin ta haifa min, lauya, magatakarda, Soja, da sojar kasa da na sama sun fika kwaya" "da tijara ahir dinka.""" """Wallahi ban sake ta ba, ina son Matata kuma babu wanda! Ya isa raba ni da ita Baban Bauchi kana gani" "sun raba ni da Matata!"" Ya dawo gabana ya ce min. ""Luluna kina ganin sun raba mu? Luluna ki ce wani abu, ni ne Ya Hafiz dinki. Dube ni ni ne Hafiz Winki!"" A hankali na zare hannuna a cikin nashi, zuciyata tana wani irin bugawa na ce mishi. ""Alhamdulillahi Ubangiji da ka samar min yanci! Ka je na yafe maka kai da Karimcy ka je na bar muku kome na cikin gidan hatta suturata na yafe, Alhamdulillahi Ubangiji na" "gode maka!"" Sai a lokacin na samu damar fashewa da kuka. Kuka nake da dukkan zuciyata." "Cikin irin haukar da ya saba ya ce min. ""Idan baki dawo gare ni ba. Wallahi haka zaki kare rayuwraki" "babu namijin da ya isa kallonki!"" Cikin fushi Mama ta ce mishi." """Ai kai ba Allah ba ne muna nan zaka ga tayi aure kuwa wallahi sai tayi, ka fita kafin na kira a ci" "mutuncinka."" ""Lubnah ki dawo? Wallahi ki dawo ko kuma kina ji kina gani ki kare rayuwarki a wulakance! "" Dariya Mama tayi tana faWin. "" Alhaji ka ji abinda danka yake faWa? Ka ji yadda yake ihu bari na nuna mishi nima ina da fitsararru irinsa, ta leko waje tana faWin. ""Kai Adamu zo kayi min waje da wannan Wan iskan ka nuna mishi yadda ake rashin kunya!"" Ba Ya Ado ba bakiWaya Yayuna maza suka yo dakin wani irin daukar amarya suka mishi, zuwa waje suka ajiye shi.. ""idan ka sake zuwa inda Lubnah take gara ka" "kira kanka gawa domin sai munci Ubanka shege mara kunya dan iska!""" "Suka kore shi sannan suka dawo a lokacin Abba ya mike tsaye, kin yi yadda kike so da Yaranki ku je" "na sallame ku ke da ita Yar so dinku!"" "" Alhamdulillahi Masha Allah, na gode katuro min takardar da wuri domin ina gama idda zan yi aure in sha Allah! "" Ashe maza ma na da kishi, cak Abba ya tsaya ya ce mata. "" Uban waye ya ce zaki yi aure a shekarunki nan? "" "" Allah mana ya ce nayi koda ta dauki kwarinka! "" "" Kai Adamu ka gaya mata wallahi na dawo da ita kuma kada ta wuce yau bata koma dakinta ba, ita kuma kanwarku ba dai gidana ba. "" Yadda Abba ya nuna baya bukatar ganina yasa min wani irin kunci, a hankali Mama ta d'ago hannu zata tab'a ni nayi maza na kare kaina, tare da cewa. ""Don Allah ki yi hakuri!"" Sake baki kowa na dakin yayi suna kallona har shi Abba da bai fita ba, juyowa yayi yana kallon yadda na kare fuskana. ""Lubnah meke damunki! "" Inji Ya Ado da ya tako gabana, "" babu! "" Na furta a hankali ina kallon Mama da itama mamaki ya kusan kashe ta. "" Hafiz yana dukanki ne?"" Rufe bakina nayi ina kallon Abba. "" Gaya min dukarki yake yi?"" Fadawa jikin Mama nayi na rufe idanuna, sake magana yayi ma kame-kame Mama ina ajiyar zuciya. "" Wai a haka za a mai da ta wurinsa! Umar muje Bauchi a" "mai da ita asibiti she need treatment domin basu yadda ya dauka yana azabtar da ita ba. """ "Kiransu Aunty Innah da Hindatu aka yi aka ce zaa koma Bauchi saboda mota daya aka dauko, a ranar" "aka bar Jama'aren, karfe tara na dare muka isa Bauchi, kai tsaya asibiti aka wuce da ni. Sai da muka isa asibiti bakiWaya sai na kasa fita a motar, sai da suka fitar da ni daga motar, haka aka dauko keken marasa lafiya aka wuce da ni, zan iya cewa tun daga ranar sabon jinya ya same ni, hatta zuciyata sai da ta samu" matsala. "Saboda nauyin damuwa dama can kaina ya jima da tabuwa, haka nayi ta jinya har wata guda kowa ya" "koma wurin aikinsa. Ya Umar da Tahir sai Sani da aka sake shi, Aunty Raliya tana zuwa a kai akai duba ni, da duk abinda tasan zan so." * Flash back "Abinda ya faruwa kuwa, tunda Hajiyar Ya Hafiz ta ga kudin da aka kawo tayi lissafinsa zai kara musu wani" "abu da yake mugaye ne, ita da Yaranta Nana da Firdausi suka shirya a kai ™arar Lubnah kotu, yadda dole a amshi kudin da yardan Hafiz ko kada ya yarda idan suka karbi kudin daga baya sai ya ce bai yarda ba, sai kuwa Tijjani yaji maganar shine ya gayawa Baban Jama'are, shi kuma da ya tabbatar an kai maganar kotu, shine ya kira Ado ya gaya mishi, shi kuma ya tura Hindatu, tana zuwa ta tabbatar dama case Win a Bauchi ake son ayi shi, amma tunda sun kawo ba tare da wani dogon magana ba, aka tattauna saboda abin na family ne a office din alkali aka yi magana take alkali ya sake Lubnah tunda uwar shi bata bukatar Lubnah sannan koda ace uwarsa tana son Lubnah dole Hafiz ya kyaleta tunda abin har da irin wannan rayuwar. Ana. Fitowa daga office din Tijani ya kira shi ya gaya masa, sai ga shi har kotun ana ta jajjanta" "lamarin, ihu yayi ta yi yana faWin bai sake ta ba, wallahi bai sake Lubnah ba. Koda Hajiyarshi ta bashi" "kudin wanke muni watsi da su yayi ya ce mata. ""Duk abinda ya faru ke ce kika lalata min kome na, ina" "son Matata kika yi ta saka ni a gaba na cutar da ita, wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba."" Yayi ta rusa kuka har ya zo asibitin." Wanann shine abinda ya faru. ** "A kwanakin da nayi ina jinya, babu wanda ya taba kira min sunan Ya Hafiz, nima kuma nayi ™o™arin" "danne tsoron da nake ji, sai dai kuma irin wannan tsoron baya barin Dan adam, domin abu ne da ruhi ya ginu akanshi, sai da ta kai ta kawo idan za a bude kofa da karfi sai na razana, ga wasu irin nightmare da nake yi,kamar dan mutu tsoro ya gama kassarani, karshe sai aka wayi gari amadadin jini na y sauka a'a jinina hawa yake kamar ana tula mishi gishiri, hatta likitan da yake duba ni sai da ya tambaye Mama ko tana bani wnai abincin da bai dace bane? Ta rantse mishi babu kome, shiru yayi kafin ya shiga tambayarta game da rayuwata kafin yau, bata boye mishi ba, amma yayi mamaki da ji ai ba a jima da kashe auren ba, don haka ya tafi da dare ina kwance ya shigo don Allah ya gani ko magana bana son yi ya shigo ya zauna tare da min tambayoyi, idanuna a rufe nake bashi amsa, abinda yayi matu™ar daure mishi kai, shine lokacin da ya mike ya matso zai duba ni domin ya ce na tashi zaune, wani baya da nayi saura kiris da na fado kasa. ""Is ok ba zan miki kome ba,.amma ki kalle ni mana!"" A dan tsorace na kalle shi nayi maza na rufe idanuna. ""Hajiya haka take yi ne kullum!"" Shiru tayi kafin ta ce mishi, ""wani lokaci ba, musamman idan muna ta yawan baki masu zuwa gaishe ta!"" ""A dakatar dasu, su daina zuwa domin bata da lafiya sosai da sosai, jinya take bukata kafin ki tafi gida ku daura akan naku."" Tabbas ni kaina nasan" "bani da lafiya, domin daga yadda nake razana da firgita." "Koda Yayuna suka zo Mama tayi musu bayani suka ga likita ya gaya musu halin da nake ciki, sai suke" "ganin kamar ba haka ba sai da Aunty Innah tazo ta fara musu bayani abinka da mai ilimin ta ce musu, ta gyara zama tana kallonsu kafin ta ce musu. ""Lubnah tana bukatar kulawa a kowani irin Yanayi, Lubnah tana bukatar rayuwa me kyau no matter how tana bukatar faWin ciki a ja ta a jiki."" Sauke numfashi tayi tana kallon takardar hannunta ta ce musu. "" Mun yarda da ™addara mai kyau ko mara kyau, Allah shi ya jarabci Lubnah da wannan laluran amma da ace tun farko da Hindatu ta fara min magana akan Lubnah" "zata samu wannan matsalar da tun lokacin aka kashe auren! """ """Dalla Malama ki mana bayani kin sa zuciyata sai tsalle take idan ta dirko ta fashe fa? "" Inji Tahir da ya" "gaji da maganar da take yana son Isa ga point din. ""*GAD*""" "Ta furta muryanta yana rawa ta fara magana kamar haka. ""GENERALIZED ANXIETY DISORDER, ake" "kiranshi a turance, cuta ce da take samun dan adam ta sanadin damuwa da tashin hankali tare da matsin lamba, wanda idan ta kai matakin chronic yake haifar da cutar hauka!""" """ Bama depression ba?"" Inji Ya Umar, hawaye ne ya zubo mata ta cigaba da cewa ""A yanzu ta shiga" "mataki na biyu ga cutar, wanda daga shi sai hauka. Yawan razana da miyagun mafarki. Tun ranar da" "Mama ta kai hannu zata ta b'ata ta razana, ya fara jin shakku, idan kun lura ana bude kofar zata zabura.""" "Kuka ta saka a hankali. "" Tana kokarin fita daga staage ta shiga wancan da shine zata fara hauka. Tun da na ga tana yawan dariya ko tayi ta zama shiru nayi fatan ya tsaya a haka ashe har ya isa wannan matakin." """" """ Kin ga ana warkewa ko ba a warkewa? """ "Inji Ya Umar, cikin shashekar kuka ta ce mishi. ""Ana warkewa idan aka hadu da therapy."" Shiru yayi kafin" "ya ce mata. ""Yanzu taya zamu iya magance matsalar Lubnah amma wancan dan kutumar uban na Ganshi sai na kusan kashe shi!"" Mama da take bakin kofar basu san ta fito ba ta ce mishi. ""Me yayi da za a kashe shi? Shi bai yiwa lubnah kome ba, nice a matsayina na uwa na kashe Lubnah na sha ganin damuwa a cikin idanunta amma na rufe nawa idanun bana son na karanta. Balle har na samu damar cewa tayi" "hakuri da ace na karanta ai da yau yarinyar nan bata nakasa har haka ba taya zan yi da Lubnah?""" "Cikin kuka take magana, sanin cewa itama tana da laifi amma lokaci guda ta tsaya sai Yaran suka" zagaye ta suna bata baki. Dakyar Mama tayi shiru. "Shigowa suka yi dakin, suka same ni kwance nayi rigingine, ina kallon sama ni kaina bana ce ga dalilin" "haka ba, amma na tsinci kaina da son kwanciya haka karar bude kofar yasa na rufe idanuna. ""Auta!"" Juyawa nayi ina kallonta. ""Tashi ki ci abinci!"" Duk yadda nake ji a zuciyata bana son ganin Mama tana damuwa balle yau ganin hawaye na zuba mata yasa na mike zaune. Abincin ta kawo min ta zauna a gefena tana mai diba ta bani a baki. Kallon cokalin nayi kafin na bude a hankali na amsa, hawaye na zuba mata tana bani ina ci, a hankali na kai hannuna saman fuskarta na goge mata. Murmushi tayi nima na mai da mata, na cigaba da amsa tana kuka har na kauda kaina domin idanuna yana cika da kwalla. Ruwa Aunty Innah ta bani na sha ina son Magana amma ban san me zance ba, a hankali na ce musu. ""Amma ba zan koma gidan Ya Hafiz ba ko?"" Ya Tahir ya matso gefena ya riko hannuna ya ce min. ""Waye ya ce zaki koma gidan Hafiz?"" Girgixa kai nayi matse hannuna yayi ya ce min. ""Ki kwantar da hankalinki, babu inda zaki in sha Allah. Daga gidana babu wani wurin da zaki kin ji zaki zauna a gidana ko?"" Gyada kai nayi" "ya ce min. ""Kada ki kara tuna wani can da bai da amfani a rayuwarki da namu kin ji!""" Gyada kai nayi suka gaya min kowa ya shirya domin na zauna a gidanshi. Amma firstly lafiyata suke "bukata domin sai da ita zan rayu. Tun daga ranar aka daura ni akan magani, idan Aunty Innah ta taso zata zo ta zauna tana kara tisa min karatun Alqur'ani da azkar. Haka yasa kullum ina cikin Alwala koda kuwa bani da tsarki ne, zuciyata ta samu nutswa. A cikin sati biyar da nayi a cikin babban asibitin Bauchi," duk wnada ya ganni sai ya san na samu nutswa sama da can baya. * Hafiz "Ya gigice domin har Karimah sai da ya koreta, kamar zai yi hauka sannan kullum yana hanyar wurin" "Baban Bauchi, tare da rokon ya saka baki Lubnah ta dawo amma baban Bauchi ya ce yana kan ™o™arin ta dawo ya jira a sallamota, domin har ga Allah tausayi Hafiz yake ji, yadda ya gigice har Jama'are ya je gaban Baba Malam yana kuka wiiwii da yake shima Baba Malam ya Wan ji haushin abin da Hafiz yayi" amma da yake zuciyarsa muguwa ce sai gashi ya kira Baban Bauchi... *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu *Littafin nan na kudi ne akan 1500* "*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105" ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641 Posting Arewapen da Telegram SHA SHIDA "Da yake zuciyarsu ta cika da zalinci da mugunta, yadda yake shiga ba nan yake fita ba shi damuwarsa a" "maida Lubnah dakin Hafiz haka ne zai saka Hafiz ya samu nutsuwa, sai dai shi Baban Bauchi ya tabbatar mishi da cewa case Win bayana hannunsa yana hannun Baban Jama'are, wato mahaifin Hafiz, haka ya saka Hafiz a gaba har gaban mahaifinsa. Bayan sun zauna ba tare da dogon magana ba, ya ce ga abinda" zai yi kuma Umarni ya bada ba ba kome ba. Shiru Baban Jama'are yayi tare da kallon Mahaifinsa. Sannan "ya kalli Hafiz da yayi wani zuru-zuru. Ya ce mishi. ""Baba ka tambaye tsakaninsa da Allah Lubabatu ta" "zalince? Idan ya ce eh yau ba sai gobe ba zata koma dakinsa idan kuma ya kasa ba ni amsar tambayoyin da zan mishi har abada ya rasa ta kenan.""" "A matu™ar razane Hafiz yake kallon Mahaifinsa, ya kuma kalli Baba Malam, kamar ya ce. "" Don Allah" "Baba Malam, ja saka baki wallahi abubuwan ba sauki."" Gyara zama Baban Jama'are yayi ya ce mishi. """ "Wallahi warabbul ka'aba idan har ka tabbatar sau daya Lubabatu ta cutar da kai tow yau zata koma dakinka! "" Wasu irin zufa ke karyo mishi yana sharewa suna kara karyowa." """Ka bawa Lubabatu maganin hana daukar ciki ko baka bata ba?"" Baban Jama'are ya watsa mishi" "tambayar, kamar yayi kuka ya rike hannun Baba Malam. Yana me gyad'a. "" Da bakinka zaka gaya min?"" "" Na bata"" Hafiz ya fada yana shashekar kuka." "Murmushi Baban Jama'are yayi yana kallon danshi, cikin wani irin yanayi na Tausayi me zagaye da" "bakin ciki. Ya ce mishi. ""Ka bata kwayar yan shaye-shaye ko baka bata ba?"" Cikin wani irin kuka ya ce mishi. ""Na bata?"" Cizon lips dinsa Baban Jama'are yayi yana jin idanunsa na cika da kwalla.. ""ka sayar" "mata da gidanta ko baka sayar ba?"" Kanshi a sunkuye ya ce mishi. ""Na sayar Baba!""" """Waye ya shiga tsakaninta da danginta?"" Cikin wani irin gigita ya kalli Babansa ya ce mishi. ""Baba ka gaya" "min ba zan same ta ba har abada, wallahi yanzu na tuba ina son Lubnah kamar yadda ta so ni a baya. Don Allah kada ka raba ni ita.""" "Zuciyar Baban Jama'are yayi laushi amma abinda ya saka Hafiz saduda na karamin al'amari bane. ""Na" "san halinka na san waye kai. Da ka girmama kanka da yau an wayi gari duniya ta girmama ka. Shi girmama ana nimansa ne tun daga yarinta Yaro ya yi abinda Manya suke yi sai ka ga girma ya shige shi. Da yau ka mu'amala Lubnah da adalci ina ga da yanxu kuna da Yara uku zuwa hudu, amma haka ka kashe ta kana ta kwashe duk abinda ta mallaka bayan ta tsaya maka, tayiwa Uwarka, tayi maka, tayiwa Yaranka, tayiwa yan uwanka, wacce irin son zuciya ce haka? Me tayi maka da zafi haka? Na zata kaf duniya idan akwai wanda zaka bawa kariya Lubnah ce, iyayenta suka maka riga da wando suka dauki yarsu mafi soyuwa suka baka, a lokacin akwai wani bawan Allah da ya zo yana sonta da gaskiya yarinyar nan ta juya baya ta ce bata son shi sai kai, yau an wayi gari ka gama lalata mata rayuwa, yau yarinya da bata wuce shekaru ashirin da shida tana zuwa da bakwai tana can tana fama da jinyar bakin cikin da kayi ta cusa mata, Hafiz ni na haife ka amma ni ma ban tsira daga kaidinka ba, me yasa sai Lubnah? Me tayi da zafi ka mata haka? "" Hawaye ne yayi ta zubo mishi yana faWin n. "" Don Allah ka yi hakuri ka rufa min asiri," "Lubabatu ita ce rayuwata, ita ce arzikina. Baba don Allah ka yafe min ka bani lubnah a karo na biyu.""" """Ba zan iya ba kayi hakuri, kaf duniya ni nake da iko da Adamu da Hindatu idan nace su dawo da ita" "zasu dawo da ita amma itama ina son ta shaki iskar yanci, ta san itama mace ce kuma mutum mai yanci, idan na ji labarin ka kuma d'ago maganar nan wallahi akan mahaifiyarka zan sauke shi. Kai na shiga tsakaninku da Lubnah har abada babu aure a tsakanin sai zumunci shima idan ta gadama idan na ji" "labarin wani abu ya faru sai ka gani a kwayar cin tuwonka!""" """Yanzu ni ban isa ba! Yaron nan yayi nadama!"" Inji baba Malam!," """Kayi hakuri Baba kai ikonka akanmu ne, Yaranmu kuwa ka barmu, akansu da ace tun farko ka amshi" "uzrin yarinyar nan da yau maganar bata dawo hannunmu ba, Baba ita gaskiya daya ce, don Allah ka bar yaran nan su dauki path din da kowa ya mishi duk wnada ya zalincin wani Allah ya bi masa hakkinsa."" Rikicewa Hafiz yayi yana kuka yana rokon a bashi dama Waya. Babanshi kuwa ya ce ai yayi watsi da" damarshi tun fil azal yanzu ya cigaba da hakuri kawai. "Wannan abin ya d'aga mishi haka, haka ya dawo wurin Hajiyarsu yayi ta kuka yana tambayarta me yasa" "tayi masa haka, me yasa ta shiga rayuwarshi da farko ya zata zai iya handle din matsalar sai ya fahimci ina kome ya lalace mishi, bai taSa kawowa yana son Lubnah ba sai yanzu da ya rasata, haka yasa ya sha alwashin matukar bai same ta ba, har abada babu me samunta itama Hajiya ta kara tabbatarwa matukar basu dawo mishi da ita sai dai ta kare rayuwarta babu aure. Yadda suke kulla sharri matukar Lubnah bata dawo gare shi ba, abinda zasu mata sai ta zama abin tausayi. Wannan masifar da suke kulawa ya tsaya a tsakaninsu sannan itama Hajiyar zata je har Bauchi ta roke su idan suka ka ki kuwa sai dai su san" "yadda zasu da Lubnah. Wanann shi ne tsarin da suka yi, bayan sun manta da akwai Allah." ** Lubnah "Rayuwa kamar littafi ne, yau idan wannan shafin ya bude maka gobe wani zai kara budewa, haka" "rayuwata ta shiga cikin jerin littattafan da ban san lokacin da na mallake su ba, kwanakina arba'in aka sallame ni, zuwa gidan Ya Tahir. Wanda shi ya fara nuna sha'awarsa akan na zauna a wurinsa. Aka gyara" min dakina ba abinda ba a zuba min ba. "Tunda na dawo na samu nutsuwar zuciya da ruhi, shi yake bani magani ya kuma tsaya a kaina sai na ci" "abinci na sha maganin. Safe da yamma da rana kuma Matarshi tana bani. A hankali nutsuwa da kwanciyar hankali ya fara dawowa a rayuwata. Tseren da muka fara da kaddara ya dawo abu mafi sau™in isowa. Mama gidan Ya Umar ta koma abinta, da suka mata maganar ta koma gidan Abba ta ce bata san da zancen ba, sosai Mama ta dauki wuta domin tafi kowa daukar zafi shi kanshi Abba sai da ta kai ta kawo yana shakkar mata magana, haka ya tafi har Jama'are yana samu Alhaji Ahmed Galadima babban wansu Mama ya roke shi ya saka baki Mama ya dawo, murmushi Yayi ya ce mishi ka zauna da ita tsawon shekaru arba'in ka san wacece ita ka je kai da kanka zata dawo! "" Ba haka Abba ya so, Alhaji Ahmed Galadima ya tirsassa Mama ta koma sai gashi shima ya ce ya lallabata, kai karshe sai gashi ya kira Ya Ado tare da rokon shi da Yan uwansa su saka baki Uwarsu ta dawo dakinta. Ya ce mishi zasu mata magana in" sha Allah. Ai kuwa Ya Ado yana yiwa Mama magana ta ce ita fa ba inda zata koma ba sai dai yayi duk abinda zai "yi, dukkanmu muka yi ta bata hakuri kafin ta amince ta koma amma shima Abba sai da yaji a jikinsa. Tsofaffin nan suna son junansu amma bakiWaya sun koma kamar wasu kananan Yara sai wani jayayya" suke. Haka muka cigaba da rayuwar a hankali ina ™o™arin zama mutum daga layin mahaukata zuwa jinsin mutane masu lafiya da cikakken hankali. "Sai da wata biyu kafin na fara jinin hailata domin shima daukewa yayi saboda tashin hankali, a wannan" "watan na fara kirga kwananki Iddana, da yake kwanaki biyar nake ina gamawa, na gayawa Aunty Hindatu da Aunty Innah, suka sani. Don sun ce idan yazo na gaya musu. Kamar da wasa na daina tunanin wani can Ya Hafiz, na daina tunanin kowa ni yanxu ai mazan tsoro suke ba ni, ba iya maza ba duk abinda za ayi tashin hankali da fada a kai take sai naji kamar zan mutu da tashin hankali. Shi yasa bana shiga ko hayaniyar Yaran Ya Tahir, suna fara zan gudu daki bana son tashin hankali ko yanayi sai naji kamar wani" abu yana yawo a kaina. Haka yasa Uwar tana jin sun fara zata fara fada da kokarin kiran Babansu. "Wata hudu da mutuwar aure duk da ban gama idar ba, ranar na samu bakuntar Ruma Rabi'u Mai shanu" "ta zo min, Nafisa Sadi Gital, Hafsat Faruq Babaji, dukkansu Uku kowacce da Yaranta nayi mamakin da suka ji labarin ina gidan Ya Tahir.. ""ladies a ina kuka ji ina nan gidan?"" ""Jalilah Kamil Jama'are ta gaya mana!"" Lashe bakina nayi, sai kallon tausayi suke min. Yadda nake zaune kowa yasan yadda bana son kallon tausayi domin sai na fara jin wani irin tashin hankali. ""Ku daina min kallon tausayi, ina da condition da mentally ill idan aka cigaba yanayin yana birkita min ™wa™walwa Please."" Yadda nayi maganar sai na ga suna kuka. Which mean sun san da haka, haka suka rungume ni tare sha faWin. ""Lulu in sha Allah zaki yi farin ciki, Ubangiji ya kawo lokacin farin cikin ne."" Murmushi nayi ina shafa bayansu nace musu. ""Alhamdulillahi Ubangiji ya bamu hakurin akan rayuwa."" Daga nan jefi-jefi ina shiga hiran wani kuma nayi shiru nayi ta kallonsu kowacce take gaya min Yaranta da sauran nasarar da suka samu a lokacin suka bani shawarar idan na gama Idda na fara aiki, wani aiki zan yi? Ni da hayaniya yake d'aga min hankali, tow kadai nace musu anan suka wuce sai dare suka tafi bayan sun kawo min kayan alkhairi kala kala. Haka na yi ta shafa rayuwata a hankali har na gama iddana ina kuma ganin likita a kai a kai. A" lokacin likitan shima yana jin dadin ganin yadda nake rayuwa cikin aminci da nutsuwa. "Ranar da Ya Hafiz ya ji labarin na gama Idda, sai da ya kwanta a gadon Asibiti. Yayi ta surutu Matarshi ce" "aka raba shi da ita har da fisge-fisge, abin da ba dadin ji domin sai gashi kamar mai cutar farfadiya haka yake wasu abubuwan." Da na ji labarin na tausaya mishi amma idan na tuna yadda yaso kashe ni sai naji shi ba abin tausayi ba "ne da ya samu wuri kashe ni zai yi da kwanaki na, gara da Allah ya yakin ce min shi da an barni da halina tabbas da na mutu." "Kwatsam ina zaune Aunty Innah ta nima min aikin koyarwa, wai ko dai rage min zaman da nake na" "kadaici, matata kuwa da Ya Hafiz ya rike sun karba aka sayar aka sauya min wata yar karama mai kyau, haka na fara zuwa aiki da ita. Bana shiga rayuwar kowa bana iya d'ago kai kalli mutum, asalima maza tsoro suke bani domin kallon Ya Hafiz nake su. Malamai mata ma sama-sama muke gaisawa." "Haka na cigaba da aikina yaran bani da matsala da su, musamman da suke ™anana. Ina koya musu" "math, yadda na samu nutsuwa a yar wannan lokacin yasa hatta Yaran sun san bana son tashin hankali. Bana son magana bana son hayaniya. Sai Allah ya bani sa'a akansu yadda ko tari basu min nima da na fahimci sun fahimci halina, sai nake saya musu yar choco-choco ina bawa masu ™o™arin cikinsu, ina son Yara ina son ganinsu cikin farin ciki da walwala. Haka yasa yaran idan na shiga ajin sai su yi shiru kafin su mike su gaishe ni, sai na musu alama da da hannu suke zama na cigaba da musu karatu, kasancewar makarantar private ne sai Allah ya taimaka duk ranar Alhamis ina fita da su, PE physical education," saboda Yarar juma'a manya ke fita. "Yau da ya kasance Alhamis na isa Makarantar da wuri, nayi parking sannan na wuce staff office nayi sign" "sannan na nufi hanyar aji sai ga daya daga cikin malaman makaranta ya ce min. ""Mrs Jama'are kina headmistress tana kiranki!"" ""Ok na gode!"" Na juya na wuce office din, ina shiga da sallama idanuna ya" fad'a cikin na...... *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*" Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu *Littafin nan na kudi ne akan 1500* "*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105" ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641 Posting Arewapen da Telegram *Last Free pages* SHA BAKWAI "Wani irin faduwa gabana yayi wnada ya saka ni ji kamar na juya da gudu, me ya kawo Ya Hafiz inda nake" "aiki? Me ya kawo shi? Abinda zuciyata take ta tambayata kenan jikina yana rawa a hankali. ""Shigo mana Malama Lubnah!"" Ya fada yana murmushi, wani irin kuka ne yaso min, na shigo ina gaida headmistress, ""Auta kin tashi lafiya!"" Kasa nayi da kaina ina faWin. ""Alhamdulillahi Aunty Barakah."" ""Masha Allah, ga sabin dalibai ne aka kawo miki sai kuma Malam Hafiz yace yana son yasan Malamar domin dai fada mata yadda zata kula da Yaran "" ""tow!"" Na fada muryana yana rawa. ""Yawwa Madam na gode, ga Yaran Aliyu Hafiz Aliyu Jama'are, Asiyah Hafiz Aliyu Jama'are ."" ""A'a tsaya ba sai kai ne Ex dinta!"" Inji Headmistress, murmushi yayi irin wanda ya saba yaudarar mutane da shi, ya ce mata. ""Madam ba wani Ex raba mu Dole suka yi amma nasan Luluna tana sona!"" ""Aunty Barakah zan tafi Class idan ya gama ya kaai yaran!"" Na aro jarumta nayi waje kafin ta samu damar sake wani Magana, ina tafiya amma bani da nutsuwa duk wnada ta ganni musamman yadda nake kallon office din Aunty Barakah zaka fahimci a tsorace nake, haka na isa ajin yaran suka gaishe ni na amsa tare da zama ina sauke numfashi, daya daga cikin Yaran da suke me suna Munir ya kawo min ruwa da gudu, ya mika min. Murmushi nayi na nuna mishi nawa, murmushi yayi na ce mishi. ""Je ka zauna na gode!"" Komawa yayi ya zauna na fara kiran sunansu, ina cikin kiran Ya Hafiz ya iso class din, tare da Yaransa ni dai ban d'ago kai na kalle shi ba, haka na cigaba da aikina ina kiran sunan Yaran. Yadda yazo ya min rumfa a kaina ya janyo min wani irin tashin hankali da tsoro uwa Uba jikina wani irin rawa yake. ""Luluna, nayi kewarki ina bukatarki sosai ina jin kewar kome naki, ina jin kewar can ™asarki me jekewa jabga!"" Wani irin mikewa nayi jikina yana wani irin rawa. Na fara ja da baya, yana takowa har sai da ya kure ni a bangon. "" Ki dawo ko kuma na saka miki abinda zai saka ki dawo dole!"" Yadda yayi magana yasa ni durkusawa a wurin tare da toshe kunnena. A tsorace hawaye na zuba min ashe ina murna na rabu da shi ashe zai dawo innalillahi wainnalihir rajoun, Ya Allah me nayi da zafi haka, fita yayi ya bar Yaran suna ta min dariya, ni dai ban kula ba bayan fitarsu na ji kaina yana amsawa da dariyarsu, daurewa nayi na fara koyarwa a lokacin Yaron nan ya fara kuka, wato Yasir, kuka irin me d'aga hankali sai ji nayi kaina kamar zai fita shi dai a kai shi Yusrah. Ranar Yaron nan da ya saka ni a gaba da kuka, sai da naji kamar zan yi hauka. Haka ya Hafiz yake zuwa yayi ta min rashin mutunci, idan ta kama kamar dai rufe ni da duka a gaban jama'a, da yake gaya musu ya mayar da ni, yan uwana suka zuga ni, a hankali sai damuwar da na rabu da ita ya fara dawowa, na kasa fadawa kowa domin ya tabbatar min duk ranar da aka kira shi aka mishi magana wallahi zai dauke ni a nime ni a rasa" "wannan yasa Ya Hafiz ya sake dawowa Rayuwata, kamar zan yi hauka rashin mutunci sai wanda ya karu." A hankali na fara kin zuwa aikin sai dai na kwanta idan kuma zan fita zan tafi wurin Aunty Hindatu ko "aunty Innah, idan suka tambaye ni me yasa ban tafi aiki na sai naki basu amsar tambayoyinsu. Ranar dai Headmistress ta kira Aunty Innah tace kusan sati biyu ban zo makaranta ba, Aunty Innah tayi ta fada ta kira Ya Ado ta gaya mishi, kai tsaye ya ce mata. ""Lubnah ba zata ki zuwa makarantar ba, akwai wani abu" "da yake faruwa. Ta je zan tura Sani ya bi bayanta ya kuma yi min bincike idan da wani abu ya gaya min.""" "Haka ta kira ni ta ce na shirya na tafi, kuka ne ya zo min tsoro da fargaba ya cika ni, domin kullum sai" "kira ni da barazanar sai ya dauke ni ko ya kashe ni kowa ya rasa, tunda naki na zo makarantar. Haka yasa na shirya ina kuka na tafi, ina isa wurin parking na fita daga motar sai gashi, yadda ya juyar da ni yayi ta kifa min mari, Malamai maza suka zo ya daka musu tsawa tare da kwatar key motar ya bude zai saka ni, Ya Sani ya rufe shi da duka, wani irin dambe suka kama yi, na shiga motar na rufe kaina ina kerma. Dole Headmistress ta kira Aunty Innah tare da gaya mata abinda yake faruwa, ita kuma ta kira Ya Umar daga muda lawan suka nufo makaranta lokacin an samu an raba fadar da kyar, Ya Sani yana faWin. ""Kai uban" "waye ya tsaya maka a Bauchi shege bagidaje, ka kuma taba Lubabatu sai na karya maka hannu.""" """Wallahi idan ina raye Lubnah ba zata tab'a samun peace of mind ba, matu™ar ina numfashi, sai dai ta" "ga wasu mazan da idanu, amma wallahi babu namijin da ya isa samunta, gara ta kare rayuwarta a matsayin karuwa!"" Zuwan Ya Umar da Yan sanda yasa aka kama ya Hafiz ni kuwa Aunty Hindatu tana zuwa a hankali na saka kafa na fito, wani duhu ne ya lullube min ganina, a wurin na zube sumammiya." "Daga nan ban kara sanin me ya faru ba, sai bayan wani lokaci, na farka na ga Yadiko tana zaune suna" "hira. ""Yar iska munafuka ta koma wurin Uwarta ban isa ba, ni ina nan ina tausayin Jalilah ashe ita ta gaya masa har inda Lubnah take, kai hatta number Lubnah munafuka ita ta bashi, nayi mamakin ashe duk abinda yayi ta faruwa tana sane da ita Hafiz yake hada baki a cutar da ita me Lubnah tayi mata? Ai Sani ya so zane ta, na ce ya kyale ta ta ji Allah zai mata sakayya mene ne a cikin duniyar wanda Lubnah bata gani ba, Allah yasa haka ne mafi alkhairi, zaman Bauchi ya kare itama Lubnan ta bar Bauchi hala wani arzikin ne yake nimanta!"" Inji Yadiko tana fada kallon yadda na tashi a hankali, ina kuma zan tafi? Na gaji na gaji da rayuwar da nake ji nake kamar rayuwata tafi bu™atar mutuwa da wannan rayuwar, na rasa yadda zan yi da kome baya min dadi, sai da nayi alwala na fito na gabatar da sallah azhar da asar, ina idarwa Yadiko ta tura min abinci, kallon abincin nake ina kallonshi kamar naga sabon abu, haka nayi ta kallon abincin. ""Ci abinci Auta!"" Haka na dauki cokalin na dibi jollop din macaroni na kai bakina, ina ci hawaye na zuba min. ""Ba zan hana ki kuka ba, domin lokacin da kika so fahimce ki mun kasa fahimtar ki, yanzu kuwa da muka fahimce ki ba zamu hana ki kuka ba."" Haka yasa na dan ture abincin na cigaba da kukana, shigowar Ya Tahir yana waya. "" Yawwa gata ta farka bari na bata. "" Mika min wayar yayi, na dauka ina shashekar kuka. "" Lulu"" "" bana son sunan nan"" na fada a sanyayye. "" Lily fa! "" Sauke kukan nayi a hankali na ce mishi"" Ya Ado!"" "" Na saka Innah su hada miki kayanki, in sha Allah zan miki booking flight nan da yan kwanaki, am sorry bana nan amma nasan Attahiru da Umar da Sani sun yi duk abinda zan yi, Lily i promise you in sha Allah daga lokacin da kika dawo wurina ba zaa ki sake samun wani threat daga wani ko ayi bullied dinki ba zan tab'a bari ba. Zan zame miki Abba zan zame miki Mama zan zame miki kowa naki, ba zaki kara kuka ba. "" Sai ga hawaye wannan nabin wannan, sharewa nake. "" Ba zai kuma sanin inda kike ba, kai ko takowa ba zai kara ba, in sha Allah ba zaki kara kuka ba. Lily na gaya miki in sha Allah. "" Kukan da nake yi ne ya sa ya kashe wayar. "" Ya Tahir ni daya ce mace da Ya Hafiz ba zai kyale ba? Me nayi haka da wannan sharrin yake bibiyarta rayuwata?"" Murmushi Yadiko tayi tana faWin. "" Baki yi kome ba, sai kara samun kusanci da Ubangiji, ai ba kowa Allah yake jarabta ba dai me imani da" "tawwakali, Allah yana son bayinsa masu hakuri da takawwa, Allah yana son bayinsa masu yarda da imani" "da shi, idan kika amshi ragamar ™addararki Allah zai miki musaya da abinda yafi alkhairi. Allah zai baki" "miji na.. "" ""A'a Yadiko bar kiran wani mijin tsoro nake ji, tsoro nake ji zan iya mutuwa idan naji wannan kalmar! "" Na fada ina cusa kaina cikin cinyoyina. Jikina rawa yake kamar an kunna min lantarki, iya Ya Hafiz da nasan halinsa ma ban sha ta dadi ba balle wani da ban san shi ba. Na rantse da Allah gara a gaya min ranar mutuwata da sunan da namiji, gara na ga mutuwata. Namiji ya shayar dani mamaki namiji ya kashe min duk wani jin dadin rayuwa, mace babu da babu bari ai da ciwo Yaya suna cikin abinda Allah ya bada na jin dadin rayuwar duniya. Amma ni Ya Hafiz ya kashe min wannan jin daWin, waye zai zauna da ni bana haihuwa waye zai yarda ya zauna da ni da cutar hauka, bayan ya Hafiz ya cusa min damuwa a" "raina. Ni a kan kaina na tsani kaina ba zan ina tsayawa kaina ba, taya xan amshi kaina." Wannan kukan da nake ya dami Ya Tahir don haka ya fita. *** "A can office din Yan sanda Baban Bauchi da kanshi ya je yayi belin Hafiz, fuskarshi babu walwala ya ce" "mishi. ""Shin baka yarda da abinda na ce maka ba ne? Ba na ce ka kyale ta na wani lokaci zan duba lamarinka ba ne? Me yasa abinda ba ka yi yanzu ka fara? Na gaya maka ko Lubnah zata mutu a gidanka zata mutu wato ban isa nace kayi abu ba kenan? "" ˜asa yayi da kai yana faWin. "" Ba haka bane, Allah ya gani ina son Lubnah, Kuma ban mata haka da wata manufa ba, Sani ne kawai ya kama ni da dambe, wallahi ba zan iya cutar da ita ba. Bayan ina son raunin baya ya warke don Allah ka yi hakuri ba zan kara magana ba sai ranar da ka min magana in sha Allah. "" Har zuwa yau Abba bai ga gundarin laifin da Hafiz yayi asalima gani yake kamar sharri ne da an fi karfinka, sannan kunyar dan uwansa da amshi case Win a hannunsa, sannan baya son dan uwansa ya hango gazawarsa akan Yaransa wato shi ya iya tankwara Hafiz amma shi kuma nashi Yaransa sun fi karfinsa, haka yasa ya zuba musu idanun su gama abinda zasu karshe dare daya Lubnah ta koma dakinta ko tana so ko bata so, shi ba zaa zubar mishi da zumunci a karon iska ba da darajarshi da kimarsa Yara da Matarshi suna juya shi, ba zai dauka ba. Ace kamar shi sai yadda aka yi da shi. ""Muje ka ajiye ni a gida."" Haka kuwa ya wuce gaba zuwa inda motar Abba yake, don da zai zo ya kira Sani akan yazo ya tuka shi, sai gashi ya ce mishi ai baya gari yana can hanyar Jos dan" banza yana nan bai je ko ina ba yana asibiti. "Haka yasa ya tuko kanshi zuwa office din Yan sanda, ya je yayi belinsa, haka ya tuko Abba zuwa gida, a" "lokacin ya samu Umar ya kawo yadiko yana mai dauke da basket din Abinci, a hankali Mama ta fito tana kallon Abba ganinsu tare da . Hafiz yasa ta wuce bata kalli inda yake ba, sama sama Umar ya gaida Abba din ya budewa Mama mota. ""Ina zaki Salamatu!"" ""Asibiti wurin Lubnah!"" ""Da izinin waye?"" ""Ai bana jiranka akan Lubnah, ka zabi abinda kake so, nima na zabi abinda nake so ai ba kuskure ba ne? Muje" "Umar."" Tana shiga motar Umar ya shiga tashi motar suka bar gidan." "Bayan fitarsu Hafiz ya shiga tashin hankali, kamar yayi kuka yake kallon kasa. ""Abba kayi hakuri amma" "ba zan iya rayuwa babu babu Lubnah ba, gara na mutu da na rasata!"" ""In sha Allah ba zaka rasata ba."" Ya fada yana kara tausayin Hafiz domin har ga Allah tausayin Hafiz din. Dakyar ya shigar da shi cikin gidan. Bai iya cin abincin da aka bashi ba, kanshi a sunkuye kamar zai yi kuka ya rasa yadda aka yi har yayi" shirme haka. * "Ajiyar zuciya na sauke lokacin da nake kallon Mama yadda ta zuba min abinci tare da ita, ina murmushi" "nayi tana bani ina murmushi. "" Mama nifa ina kishin yarinyar nan!"" Inji Sani, ya fada yana hararata. "" Mama ka kalli yadda yake wani hura hanci!"" Murmushi tayi tana faWin."" Sani na, kyaleta tayi maka shigar sauri.""" "A hankali yake murmushi ya dauki spoon ya fara bani abincin shima Mama tana bashi, shigowa Aunty" "Innah tayi tana faWin. "" Ikon Allah yau naga abinda ya ture turatu uwar Turanci a ramin tururuwa, ok nima bari na shiga."" Ta dauki spoon ta fara ci, a hankali tana mai diba itama ta bani, Ya Sani ya bata. Turo kofar da Aunty Hindatu tayi tana faWin. ""Cin amana a jinin gidan Baba Malam Umaru yake oya ku" "matsa min."" Haka yasa ta zauna ta fara ci itama kafin ta kai loma sai da ta fara bani, Aunty Innah ta bata." "Bayan mun gama Aunty Innah ta ce mana.""an sallame ki yar nan!"" ""Na gode sosai."" Haka muka shiga" "tattara kayanmu dama ba wani kaya ba, gidan Ya Tahir na koma," A can gidan kuwa sai ga Hajiya Asiyah tazo Ita da su Aunty Nana Asma'u. Kwanansu daya suka roki Abba "ya basu damar ganina ya ce su sami Yadiko, haka ya gayawa Mama. Mama kuwa ta ce musu. ""Kunzo ku" "kara sa min ita ne?"" ""A'a zamu bata hakuri tayi hakuri Hafiz ya gane!"" ""Ya bita makaranta ya rufe da duka ko?""" """Amma ai Alhaji yace zata koma!"" Inji Hajiya tana murmushi." """Murmushi Mama itama tayi ta ce mata. "" Ba mamaki idan na fitar da gawata Lubabatu zata koma gidan" "Hafiz kamar yadda ya ce ta haramtawa wa wani da namiji in sha Allah ya haramta mishi. Idan kina ganin karya ne ki same shi ki ce ni Salamatu Galadima nace Lubabatuna ta haramtawa Hafiz ya ce bata haramta ba."" Yadda take d'aga murya shi kanshi Baban Bauchi yana ji amma ba yadda ya iya ta kara da cewa. "" Ni ba haifi lubnah kuma naga wanda ya isa mata dole! Wallahi tun daga karamin kotu har babban kotu sai an jimu da shi, ku fita kafin na haukace muku lokacin da kuke musguna mata kun manta tana da uwa ko? Kun zata kowa haka yake, ke baki ji kunya ba ita da take juya zaki biyo ai Lubabatuna ta" "gama da danku sai dai wani ba shi ba.""" "Ba sai ga gagarumin rigima kai karshe suka dauki ai Hafiz bai sake ni ba, magana har kotu, abinda ya" kara lalata lamarin. "Kamar yadda Ya Ado ya ce, ranar da yasa Yayuna maza da mata suka raka Jos tare da rakiyar Mama," "haka nayi ta kuka da xan shiga jirgin. Na k'amk'ame Mama ina kuka.suna tsaye har jirginmu ya tashi, daga nan suka wuce gidan Aunty Raliya, taji haushi tayi ta mita suna sallah la'asar suka baro Jos." Nan suka sami bugun Bala'i da masifa na Baba Malam ya ce shi ya bada umarnin a mai da auren Lubnah "Mama kuwa ta ce babu mahalukin da isa wannan aikin rigimar da ta kaure har Abba ya ce mata.. ""Sai ki zaba aurenki ko Na Lubnah domin ba gaji da lalata min zumunta da kuke da sunan kuna bayan" Lubnan?......... Alhamdulillahi bakiWaya anan na kawo karshen Free pages. *08130269641* "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 18" Lagos "Mun bar Jos karfe biyu da rabi, karfe hudu cib muka sauka. Garin yayi wani irin yanayi na alamar da ayi" "ruwan sama. Tun daga Murtala Muhammad International airport na shaki kyakyawar iskar da babu hadi a cikinta. A hankali nake takawa ina jin kamar an sauya ni rayuwata ™addarata. A yadda na fahimci mutanen garin kowa akan kafarshi yake, yadda suke kujiba-kujiba. D'ago kai nayi ina niman Ya Ado, daga can nesa na hango shi a wurin Arrived, da dan sassarfa na isa babban wurin taruwan baki tare da masu" barin kasar da komawa jahohinsu. """Lubnah"" ya d'aga min hannu, murmushi nayi wanda kana gani kasan yake ne. Hannu ya mika min na" "isa gare shi ya Wan rungume ni, irin side hug din, sannan muka jira kayana ya iso, ya tambaye ni ba gaya mishi sannan ya dauko min. Ya riko hannuna yana faWin. ""Welcome to lagos!"" Yake nayi har muka shiga mota, ina zaune kamar wata bakuwa, duk na kasa sake jiki da shi. Haka muka bar airport din minti goma" "sha biyar ya kai mu estate din da Ya Ado yake zaune. Royal Garden Estate, close alausa Mitv, alausa Ikeja." "A kofar wani gida me kyau muka yi parking, ya kalle ni a hankali ya ce min.. ""welcome to home!""" "Murmushi nayi na bude kofar na fito ina kallon yadda tsarin kowani gida yake ba kamar mu nan arewa ba, karya ka yi parking a kofar gidanka, aka bi motar har cikin gidan ma aka dauke. Sai naji na samu nutswa musamman da garin yake hade rai, alamar zasu sha ruwa don gari ne na ruwa. ""Sweet haka muje" "ko?"" Gyada kai nayi na bi bayansa da yar karamar hand bag dina, har muka shiga cikin gidan. Aunty" "Zakiya ta zo ta rungume ni hannunta dauke da ludayin miya. ""Baby sai yanzu ka dawo, Auta barka da" "zuwa welcome to home!"" Murmushi nayi ina kallonta. ""Muje na nuna miki dakinki a sama!"" Kallon stair din nayi na kalle su a hankali na ce musu. ""Na gode!"" ""Never mind!"" Muka haura saman, dakin farko aka bude min. Juyawa nayi na kalle su a hankali na furta da cewa. ""Tsarki ya tabbata ga Allah gwanin da babu irinsa!"" Ba don kome ba sai don yadda aka tsara min dakin sai nake gani kamar ban cancanci zama a dakin ba. ""Shigo dakinki ne, bamu gama gyara dakin ba amma ki yi maneji kafin a gama!"" Gyada kai nayi ina faWin. ""Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi."" Ban daki ta bude tana faWin. "" Look at the toilet yayi miki? "" Gyada kai nayi ina kallon ban dakin. "" Shi kenan bari na karasa abinci, sai ki yi wanka da sallah muna jiranki. "" Gyada kai nayi, na zauna bayan fitarta na cire kayan da zan saka na shiga nayi wanka da Alwala na fito, nayi ta kallon inda zan fahimci gabas ne, turo kofar Ya Ado yayi yana faWin."" Jikina ya bani kina niman alkibla!"" Karamin murmushi nayi ya nuna min gaban gadon."" Shimfida abin sallah nayi na gabatar da sallah asar sannan na zauna a wurin ina addu'a. Bayan na idar ne na sauya kaya riga da zani na daura, sannan na cigaba da zama a wurin na tsunduma cikin tunani, wanda ni kaina ban san me nake tunawa ba, ni dai na b'ata shiru. Turo kofar dakin aka yi ta zuba min idanu. Juyawa tayi ta sauko kasa, ta ce mishi. ""SAN kazo don Allah!"" ""Wani abu ne?"" Ya tambaye ta yana mikewa da sauri, ""just come!"" Ta fada tana haurawa. Haka suka nufo dakin ya shiga ya ja stool ya zauna a gabana har lokacin ban san sun shigo ba. Itama zuwa tayi ta zauna a gefena. ""Lubnah!"" Ya kira sunana, ban amsa ba, ya kara kiran sunana a karo na biyu, shima shiru dafa ni yayi, na wani irin zabura tare da fasa ihu. Rungume ni Aunty Zakiya tayi tana faWin. ""Sorry Baby girl we're here!"" Ta fada tana shafa bayana, kuka na fashe da shi, tayi ta shafa bayana tana faWin. ""Ya isa haka, muna nan babu me cutar da ke!"" ""Tsoro nake ji, ina jin tsoro!" "Don Allah ku boye ni!"" Har lokacin shafa bayana take tana faWin. ""Wanda zai cutar ke, you in safe place. Daga ni har SAN ba zaku bari wani ya tab'a ki ba!"" Mikewa Ya Ado yayi ya ce mata. ""Doctor ina son ki mana booking ganin neurologist please!"" ""In sha Allah, SAN!"" Haka tayi ta bubuga bayana, har nayi shiru karshe dai barci ne yayi gaba da ni, ta kwantar da ni. Sai da ta gyara min kwanciya lokacin Yaran gidan sun dawo daga makaranta, har sun fara ihu ta ja su zuwa daki ta zaunar dasu. ""Aunty Lubnah tazo, and please bata son ihu ko hayaniya, yana iya dakata faint ko tayi loser control, please ku zama good children, kunji ban da fada Ummu Salma, Adil kai ne Babba kada ka yarda su saka ka magana. Prince kada ki yi ihu ko kukan banza kin ji! "" "" Mommy me ya same ta? "" "" Bata da lafiya ne idan kuka yi sallah" "ku saka ta cikin addu'arku ko?!""" "Gyada mata kai suka yi, suka fito bayan sun sauya kaya. Yaransu uku ne Adil sunansa Usman sunan" "Abba, sai Ummu Salma me sunan Mama. Sai Princess me sunan Maman Aunty Zakiya wato Hauwa'u." "Aunty Zakiya da Ya Ado sun hadu a BUK ne, kusan shekarar shi biyu da fara karatu ta shiga a lokacin ta" "samu medicine ne, wani abun da nake son a sani Aunty Zakiya Bajara ce daga Dass, iyayenta yan boko ne, sosai sannan tana da yayu maza da mata, a lokacin da suka hadu har magana tayi nisa Abba yaki auren, Baban Jama'are ne ya tsaya aka yi kome, domin a lokacin shi Abba Aunty Nana Asma'u yaso Ya Ado ya aura, amma yaki aka yi ta rigima, Baban Jama'are ne ya kashe maganar bayan ya gaya mishi ai Nana Asma'u tana da wanda take so da wannan aka kashe rigimar, itama Aunty Zakiya kamar tasan an yi wannan rikicin, ita da danginta da aka fara zancen auren sun tsaya sosai kuma sun yi abinda ya dace duk" wasu iyayen zasu yi akan Yarsu. "Sun nuna mata fada da gaya mata gaskiya. Ta rike su a matsayin nata, tayi kuma hakuri da kome. Haka" "kuwa aka yi ta zo gidan a matsayin wacce bamu amshe ta ba, saboda Abba ya nuna bata mishi ba. Amma wani ikon Allah ba a shekara ba sai gashi da kanmu muke sonta. Tana da wani irin kyawawan halayen da sai ka ji kana matu™ar kaunarta, a lokacin da aka yi aurensu Ya Ado saro kaya yake yana turowa shagon Abba, a lokacin duk yan makarantasu gani suke kamar ya cika zakewa akan niman kudi, idan aka ce musu dan Bauchi ne. Sai su ce dama yan Bauchi suna kasuwanci haka, domin da kanshi yake shiga kwari yayi sayayya ya cika manyan motoci a turo Bauchi, dayawa idan aka ce musu dan Bauchi ne sai su ce a'a ba dai yan Bauchi ba, domin basu damu da kasuwanci haka ba. A lokacin Ya Tahir yana da shagon" provision haka dai shiga singa ya mishi sayayya ya turo mishi. "Koda ya gama karatunsa, sai da suka tura shi school of law Lagos, ya shekara daya. Bayan ya dawo ya" "tafi service na wata tara, sannan ya dawo BUK a lokacin itama tana gab da gama karatu, a shekarar aka haifi Adil, wanda yadiko da kanta ta zo Kano ta zauna da ita, da har Iyayenta suna damuwa da maganar tazo wanka gida, sai suka ji labarin Yadiko tana nan, abin da yasa Abba ya sauko ya bar Yadiko tazo, don jin Haihuwar da namiji aka yi kuma Ya Ado ya gaya mishi sunansa yayi masa huduba da shi, itama kuma ta tabbatar da haka. Tare da mishi Alkunya da adil. Sai take ta tara mishi nauyi da kunyarta, musamman yadda yake share ta, idan ta zo gaishe shi yayi kamar bai ji ba, wannan soyayyar da ya wayi gari da shi akan Jikansa na farko ya matu™ar amfani iyayen, domin a Bauchi ma har walima aka yi na sunan Usman Adil Adam Usman. Yadiko bata bar Kano ba sai da suka yi kwanaki Hamsin haka Abba ya ce tayi, sannan da zata dawo Ya Ado da ita Aunty Zakiya suka mata shatara na arziki kasancewar tana da jarabawa, yasa bata zo ba sai da Yaron ya cika wata biyu da rabi, sannan suka zo ganin gida. Tunda suka iso dutsen tanshi, Abba ya dauki Yaron ya lullube a wurinsa sai nono da wanka kawai ke sakawa ya bada yaron ko idan zai tafi central. Wannan kaunar yasa ita uwar Yaron bata wani saka yaron a ranta ba, haka da ta tafi gida da Yaron Abba kullum sai saka Mama ta kira ta, a saka mishi muryan Yaron, dan wata biyu iyayenta da dangin sun fi kowa farin ciki, da tayi kwanaki zata koma suka hada mata kaya har da na su Mama da" Abba aka hada mishi zuma da zabi aka kawo musu anan fa ta kara daraja da kima. "Adil na shekara daya a duniya ta fara service inda aka tura ta Niger minna, ai kuwa ta kai Adil wurinsu" "Mama ta tafi service dinta inda zata yi sati uku ta dawo Kano ta karasa domin mijinta yana ta shige da fice akan haka. Yaro kan da ya saba da ganin Abba don haka kawai zai bushi iska ya zo kano ganin Adil kada ku manta yana da wasu jikokin na Yara mata amma shi wannan gani yake kamar na shine bakiWaya, yaron ma ya saba da shi. Ai kuwa shekarar da aka kawo shi Abba ya tafi da shi Umara, saboda gata da soyayya. Iyayen Yaron hakura suka yi suka barwa Abba Yaron. Har suka gama karatunsu. Kwatsam Ya ado ya samu aiki a Abuja yana can ita tana aiki a Bauchi, Allah ya kara mishi wani nasibi a lokacin tana goyon Ummu Salmah, a shekarar suka koma Lagos domin wani Shari'a yayi kuma yayi nasara, sai gashi cikin ikon Allah suna ta gaba a Lagos itama tayi master dinta, wnada ya kara d'aga darajarsu. Abba ya" basu dansu domin zai fi dacewa su daura shi yadda suke so. "Shekararsu daya a lagos ta haifi Princess, yanzu shekarar su biyar kenan. Bayan sun ci abinci, suka yi" "sallah Magariba, sai a lokacin Ya Ado ya zo ta tashe ni. Bayan na farka na bude idanuna addu'a nayi sannan na tashi na shiga ban daki, nayi alwala nazo na gabatar da sallah Magariba, ina idarwa Aunty Zakiya ta shigo tana waya. ""Gata nan Hindatu kada ki fasa min dodon kunnena."" Ta fada tana murmushi." "Mika min wayar tayi tana faWin. ""Gashi idan kin gama muna jiranki a kasa zamu ci abinci."" Karban wayar" "nayi ina kallon kasa. "" Auta kin isa lafiya? Na kira dazun wai kina barci. "" Inji Aunty Hindatu, "" Eh ban jima" "da farkawa ba!"" Na fada a sanyayye. "" Ya kika ga garin? Yayi miki ko? "" Ko bai min ba dole na amsa da dai na cigaba da zama a Bauchi Ya Hafiz yana min barazanar zai sace ni. "" Yayi min! "" Na furta a hankali, ina wasa da bakin hijab din jikina. "" Auta ki saki jikinki kin ji ko."" "" Ehmm! "" Nace mata bayan nan shiru nayi, , Ya Ado yace zaki fara ganin likita ko?"" Shima sai da nayi shiru kafin nace mata. "" Amma ai lafiyata lau."" ""Eh lafiyarki lau kai, amma ana son ki ga likita da kyau."" Shiru nayi ina jin yadda take ta bayani da ta fahimci ba zan iya cewa kome ba, sai ta kyale ni. "" Auta ki tafi ki ci abinci!"" "" Tow sai da safe.""nace mata ina me kashe ki wayar, na nufi hanyar waje, suna ta hira sama-sama cikin nishadi da jin dadi, haka ma sauko na gaishe da Ya Ado da Aunty Zakiya, yaran suka gaishe ni yadda na amsa musu yasa suka fara kallon iyayen, har yanzu akwai rashin sabo a tare da ni, izuwa yanzu ban san yadda zan gyara kaina na fahimci mutanen da suke gefena ba, tsoro nake ji kada a kwana biyu su juya min baya. A hankali na zauna Aunty Zakiya ta saka min abinci, ta ce min. "" A kara miki ne! "" Kallon abincin da ta zuba min nake" ina tunanin. """Auta lafiya? Tana magana baki ce kome ba."" ""Abincin zata rage yayi yawa!"" Na fada muryana yana" "rawa. ""A'a bai su yawa ba, kici kawai idan zaki kara sai a kara miki ba."" Kalaman Ya Hafiz ne suka shiga yawo a kaina. _Jaka sai aikin ci ba haihuwa! Dama a jaka ya dace ki zo ba a mace ba, jakar ma mara haihuwa_ da sauri na tura mata nace mata. ""Don Allah ki rage!"" Haka ta rage rabin abincin, shima ban iya ci a gabansu ba, juya abincin nake ina kallon yadda suke ci, tashi Ya Ado yayi ya dauki plat din ya riko hannuna muka bar parlourn dakina ya mai da ni, sannan ya ajiye min abincin a gabana. ""Zauna ki ci!"" Ba musu na fara ci ina kallon kofar da ya fita, kafin ya kawo min ruwa na cinye abincin kuma ban koshi ba, ajiye min ruwan yayi ya je ya karo abincin ya zo ya ajiye min. ""Bana son kina zama alone ne amma na fahimci kafin ki saba da mutane zaki dauki lokaci."" Shiru nayi haka ya juya ya fita na zauna naci abincin" sosai. "Daga nan na dawo hayacina na tashi na wanke hannuna, na tattara kayan na sauko da shi kasa. Yaran" "suna parlourn babu wanda ya kula ni, ni tun kan su Yusrah tsoron yara nake, haka gidan Ya Tahir Yaransa basu hayaniya idan ina gidan. Shiga kitchen nayi na ajiye kayan abincin. ""Hi"" gabana ne ya fadi, na juya a hankali Princess ce, mika min hannu tayi ta ce min. ""Zamu iya zama abokai?"" Yadda take kallona yasa na dan durkusa na ce mata. ""To!"" Na mika mata hannu, kamar yadda ta mika min, sannan na sake hannunta" na wuce hanyar sama. "Tunda na koma sallah isha nayi, na kwanta tunawa nayi na dauko magani na sha, sannan na kwanta" "a hankali. Tunani mai zurfi nake a sannu sannu barci yayi gaba da ni, daga nan ban kara sanin me nake ciki." Ya Ado """Dr kina nufin ba zan samu ganin shi ba kenan?"" Kallonshi tayi ta ce mishi. ""SAN baya gari ne, da yana" "nan da na gaya maka. "" Shiru yayi yana kallon laptop dinsa, ""ina son na ga ta fara ganin likita duk da tana da maganin da take sha amma yana da kyau ta kara ganin wani likitan, zuciya tayi rauni akan Lulu, duk halin da take ciki mune muka jefata a cikinsa."" "" Ubangiji ya bata lafiya. Ya bamu ikon kula da ita. "" """ "Amin Ya Allah! "" Ya fada yana cigaba da aikin da yake, tana gajiya ta kwanta ta barshi a wurin. Ya Ado" "kasungurmin lauya ne, wanda idan har ka kawo case wurinsa. Tow fa matukar kaina ne da gaskiya" "magana ya ™are, bai cika amsar case Win da aka yi zalinci ba, haka yasa ya kara zama wani gwaska." "Wurin karfe biyu na dare, ya kashe laptop din. Sannan ya shiga ban daki yayi uzurinsa ya fito, sannan ya" "ji kai bari ya leka Yaran da kuma Lubnah. Haka ya leka dakin yara ya kara musu addu'a sannan ya wuce dakin Lubnah ya same tana shasheka tare da zabura, kamar zata farka sai motsi take, juyawa yayi ta fita ya jira Matarshi wacce tayi nisa a cikin barci haka suka shigo dakin tana hamma. Zama tayi a gefen gadon tana shafa fuskar Lubnah. ""Ya Isa haka you safe Lubnah."" Yadda take shafa kanta tare da magana a hankali, har ta bude idanu wanda suka yi ja saboda yadda take mafarki ganin Ya Ado a tsaye yasa ta razana tare da fashe da wani irin kuka. K'amk'ame Aunty Zakiya nayi tare da boye fuskana jikinta, jikina yana rawa. Abin ne da ciwo irin wannan sai anyi da gaske kafin mutum ya manta da shi. Matsowa yayi na kara k'amk'ame ta. ""Ka tafi zan zauna da ita har ta koma!"" Fita yayi jikinshi a sanyayye, yana jin wani irin yanayi yana saukar mishi. Ina jikin Aunty Zakiya har wani lokaci. "" Ya isa haka, tashi ki yi alwala sai ki yi sallah kin ji."" Haka na mike na shiga ban daki nayi alwala sannan na fito na samu ta shimfida min abin" sallah. "Wannan sai da ta ga na fara sallah, sannan ta bar dakin bayan na idar ta shigo ta same ni a wurin da" "nayi sallah na kwanta ina barci, janyo bargo tayi ta lullube ni, ban san me yasa tayi haka ba.. ko kuma tana tunanin idan na farka ba zan iya komawa ba ne, haka yasa na cigaba da barci a wurin." "Duk yadda naso na cire Ya Hafiz na kasa, domin ko yaya na kwanta sai nayi mafarkin Ya Hafiz da irin" "azabar da yake shirin min, haka yasa na kasa yarda da kaina balle kowa. Sannan zuciyata tana raya min Hafiz sai zo gare ni." "Washi gari da sassafe na farka na fara yin Sallah, wanka na yi sannan na duba jakata na dauki magani na" "sha, turo kofar aka yi na kalli me shigowa. ""Lubnah!"" Ya Ado ya kira sunana, ""Na'am!"" Na amsa mishi, shigowa yayi da mug a hannunsa ya janyo stool ya zauna, yana me mika min kofin. Amsa nayi ina kallonshi. "" Na gode!"" Na furta a hankali, zuba maganin nayi a bakina na sha a ruwan tea din. Sannan na rike kofin ina kallon kofin. ""Naso muje ganin likita yau!"" Kafe shi nayi da idanu, kafin na cigaba da kurban tea din ya cigaba da cewa. ""Amma likitan baya nan, gashi zamu tafi aiki zaki iya zama a cikin gidan nan ke" "daya ko?"" Gyada kai nayi ina ajiye kofin a gefe guda......." "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: SHA TARA" """Me yasa sai na ga likitan to?"" Na tambaye shi a hankali, ina dan karce farcen hannuna, ban damu da" "zafin da nake ji ba. Ni kaina ban san lokacin da na zama haka ba. ""Saboda ki samu nutswa da kwanciyar" "hankali zaki ga likitan ™wa™walwa."" ""Na haukace ne?"" Kalaman Ya Hafiz ne suka dawo min. *Ki dawo" "gare ni, ni daya ne ba zan cigaba da miki kallon abar tausayi kuma mahaukaciya ba! Amma duk wanda" "zai zauna dake kallon mahaukaciya zai na miki* da sauri na kalli Ya Ado, ""kana min kallon mahaukaciya ce?"" ""A'a ko daya bana miki kallon haka.""" "Kin yarda nayi na fashe da kuka, Ya Hafiz yayi gaskiya tun a Bauchi nake kallon yadda kowa yake" "min kallon tausayi ko kallon wance rayuwarta ya ™are, haka nayi ta kuka tabbas ina jin ciwo amma ban san yadda zan fitar da zafin ba. Dakyar ya rarrashe ni sannan ya fita, kasancewar maganin akwai na barci tunda na kwanta har suka fita ban sani ba, sai farkawa nayi na ga yar karama not a gefen tiren abincin.." *Idan kin farka ki karya sai ki sauko akwai me aiki tana zuwa mana aiki sunanta Yemi tana nan Please ki karya kin ji* SAN Adamu U.U Jama'are. "A hankali na wanke bakina na zo na karya lokacin karfe daya saura, sannan nayi wanka na sauya kaya" "na fito parlourn kasa, mai aikin ce tana ta aiki a kitchen din. Lekata nayi ma ga tana faman kwashe abinci a cikin kular. ""Good Afternoon Ma!"" Ta gaishe ni, gyada kai nayi ina amsa mata a hankali. Barin kofar nayi na dawo parlourn na zauna a kujeran, lekowa tayi ta ga ina zaune amma na kurawa tv parlourn idanun kuma ba a kunna ba, tana fitowa ta kunna. Sannan ta koma wurin karfe biyu ta fito tana fadin.. ""Zan koma sai an jima!"" Gyada mata kai nayi, ta fita na koma na kwanta sai lokacin na nufi zan kwanta na manta ana kashe tv don haka na saka kai zan fita daga tv aka ce. ""Kin zata zaki iya gudu ne?"" Da harshen turanci. Domin film din da turanci ake yi amma sai tunanin da nake na Ya Hafiz ya juye min irin muryansa. ""Nace kin zata zaki iya guduwa ne? Kin dauka idan kika gudu ba zan iya samo ki bane? "" Yadda na tsaya jikina yana rawa na kasa juyawa gani nake kamar yana bayana. Hawaye ne ya shiga zubo min a hankali na ji motsin takunshi har har gabana.Wani irin rikicewa nayi tare da zubewa a kasa ina jin kamar zuciyata zata fita. Kukan da nake naji ya makale sakamakon ce min da yayi. ""Shiiiiii!"" Hadiye yawun bakina nayi tare da rintsa idanuna, ina me saka hannu bibbiyu na kare fuskata. ""Ya isa haka, bar kuka na gaya miki duk inda kika shiga zan binciko ai, ya isa bar kukan nan ko sai na mare ki ne?"" Ya fada da karfi, ja da baya bayi ya mike tare da zare belt din jikin wandonsa, ya d'aga belt din zai zuga min na fasa wata irin kara me firgitawa, wanda yayi daidai da shigowar Ya Ado yayi mantawa ne ya dawo gidan. Ganin halin da nake ciki yasa shi isowa gare ni, duk na firgita na fita hayancina sai ihu nake, yayi maza ya rungume ni. ""Ya Isa Lubnah ya isa haka. Gani nan Yaya Adamu ne, ya isa bar tsoron haka gani nan a tare da ke. "" Kara rungume shi nayi tare da kifa kaina a gefen kafad'arshi, ina faWin."" Ya nimo ni, wallahi na" "ganshi.""" "Wayarshi ya cire daga aljuhun rigarshi ya shiga kira da shi. "" Doctor ba wani likita ne?"" Daga can ta ce" "mishi. "" Yanzu nake son kiranka ya dawo!"" "" Ok gamu nan zuwa! "" Ya kashe wayar. Jan hannuna yayi zuwa sama ya dauko min hijab dina tare da maganin da nake sha, sannan ya riko hannuna ya kai ni cikin mota, kafin ya kara komawa cikin gidan ya dauko file din da ya manta, sannan ya rufe gidan ya nufo" motar muka bar cikin estate din. "Sai da ya fara zuwa office Winsu, ya bada file din sannan ya dawo ya wuce da ni asibitin, lumshe" "idanuna nayi har muka isa asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos, a wurin parking muka samu Aunty Zakiya tana jiranmu, riko hannuna tayi muka cigaba da tafiya, har cikin asibitin can bangaren likitan ™wa™walwa, muna shiga likitan ya ce mana. ""SAN da kanka?"" Yana kallon yadda na koma bayan Aunty Zakiya ina mai boye fuskana. ""Ku zauna, Doctor ke kuma wuce bangarenku!"" Murmushi tayi tana faWin. ""Shi kenan" "Doctor!""" "Fita tayi tana faWin. ""Dady idan kun fito ka kira ni."" ""Ok Maamah."" ""Why not ki dauke shi kawai!"" Yana" "maganar idanunsa yana kaina. ""Zakiyah ta gaya min sakonka tun jiya, dalilin da yasa na katse abinda nake yi kenan na dawo."" Murmushi yayi, yana kallona. ""Auta ko?"" ""Eh ita!"" Ya Ado ya bashi amsa, cigaba yayi da aiki da computer dinsa. ""Lubabatu Usman Umar Jama'are ko?"" Nan nayi mamakin yadda aka yi yasan sunana. ""26 yrs!"" Daga nan ya zuba min idanu. ""Wannan kibar taki tun da kina da ita ce?"" Kallon Ya Ado nayi, rike hannuna yayi. ""Daga baya tayi kibar!"" ""Tow Adam ai naga duk Yaran gidanku babu me" "kiba sam!"" Ya fada yana cigaba da aikinsa. ""Eh dukkanmu bamu da kiba, itama daga baya tayi shi.""" "Haka ya cigaba da aikinsa. ""Yanzu me yake damunta!"" ""Dawowa nayi na same ta tana kuka da" "ihu, tare da boye kanta kamar wani zai dake ta."" D'aga mishi hannu yayi ya ce mishi. ""Malam fita ka gama naka aikin kalle mu daga jikin window."" ""Amma Ahmad!"" ""Tow zo ka duba ta mara mutunci a ko ina sai ka nuna min halinka na lauyoyi! "" Ya fada yana mikewa, kujeran da Ya ado ya mike ya zauna tare" "da fuskantata. Fita ya Ado yayi ya zuba mana idanu ta window glass din," "Daukar wayarsa yayi ya turawa Ya Ado.. *Ka kalleta da kyau, sannan ka saka idanu akanta akwai" "abinda nake son ka fahimta please* sannan ya ajiye wayar, yana kallona duk da ban san me yayi da wayar ba, amma jikina yana bani wani abu yayi. "" Lubnah! "" Ya kira sunana, har lokacin ina karce farcen hannuna. "" Ya razana ki?"" Shiru nayi ina karce farcen, sake tambayar yayi, ban bashi amsar ba. "" Baki jin zafin farcen ne baki ga jini yake yi ba? "" Ya tambaye ni. "" Gaya min meke damunki?"" Muryana tana rawa na bude baki zan yi magana sai nayi shiru. ""Kina son Ado ya sake asarar da yayi yau ya cigaba da faruwa saboda ke ne?"" Kallon window nayi ina kallon Ya Ado, ""asara kuma?"" Na tambaye shi. ""Wata Shari'a yake yayi mantuwa karshe ya ajiye shari'ar saboda halin da kike ciki! Don haka idan baki son haka ya kara faruwa gaya min meke damunki?"" ""Shi ne yake zuwa yace ba zai tab'a rabuwa da ni ba."" Na fada ina jin kuka na zuwa min. ""Waye kenan?"" Ya tambaye ni, ""Ya Hafiz!"" Na fada ina karce farcen da yayi jini, "" yana ina? "" Ya tambaye ni, "" Bauchi!"" Nace mishi,"" Idan ni na yarda, waye zai yarda kina ganin Ya Hafiz?"" Kallonshi nayi kafin na sunkuyar da kai. "" Sau nawa kike ganin shi?"" ""Jiya da yamma sai da dare sai kuma dazun."" "" Yana razana ki ne?"" Hawaye ne ya zubo min ya ce. "" Ba zai tab'a rabuwa da ni ba! "" Shiru yayi yana kallon yadda nake share kwalla. "" Me yasa baki yarda kin yi nisa da ba zai iya zuwa gare ki ba. """ "Hawaye ne ya zubo min nace mishi. "" Zai zo!""" """ Ciwonki yana jini!"" Ya dauki tissue ya bani na nad'e hannun, sannan ya mike ya nufi wata drower ya" "ciro wata yar box ya tawo gabana yana me saka handglove. Ya dauki abinda treatment ya fara wanke min hannu. "" Babu zafi ne?"" Ya tambaye ni, ""Bana jin zafin ne! "" Kura min idanu yayi. "" Baki zafin spirit din ba?"" Girgiza mishi kai nayi, sai da ya gama sannan ya mike tare da Waukar wayar landline, ya kira wata a cikin wayar. ""Ok ina jiranki! "" Can sai ga wasu nurse biyu sun zo. ""Ki saka mata drip"" da wasu allurai, sannan ya kalli window yayiwa Ya Ado alama da ya shigo, koda ya shiga zama yayi yana faWin. ""Doctor Ahmad lafiya kuwa?"" Komawa yayi ya zauna a kujeran da kyau yana juyawa kujeran. ""Kanwarka" "bata da lafiya, duk da tana shan magani amma da gaske bata da lafiya da zata fahimci me ake so da ita.""" "Gyara zama Ya Ado yayi ya ce mishi.. ""Za a fitar da ita ne wani wajen?"" Girgiza kai Doctor Ahmad yayi" "ya cigaba da cewa. ""Kanwarka tana dama da cutar Deja'vu"" shiru Ya Ado yayi kaman mai son tuno wani abu kafin ya kalli Doctor Ahmad ya ce mishi. ""Kai naso sanin wannan kalmar amma na rasa inda na santa!""" """A bayyane yake wannan kalmar ba wata babba bace amma tana da matukar hatsari ga lafiyar dan" "Adam, bari na maka misali akwai wani lokaci zaka ga kamar ka tab'a ganin wani abu ko wani wuri amma baka tab'a zuwa wurin ba, wani lokaci kuma mutum zaka gani baka tab'a ganinsa ba amma zaka ji a ™wa™walwarka ka tab'a ganinsa!"" Inji Doctor Ahmad, gyada kai Ya Ado yayi yana faWin. ""Anyi haka! Kuma" "sai yanzu na fahimci sunan. To meye alakarshi da Lubnah! Tana gane gane ne?""" Gyada zama Doctor Ahmad yayi domin yana son yayiwa Adamu UU Jama'are. Ya ce mishi. """Wannan yanayi da yake bayyana ganin abin da bai taSa faruwa ba amma mutum ya Wauka ya faru ko" "yana faruwa da shi ana kiransa da Déjà vu (furucin Faransanci ne da ke nufin ""An riga an gani"")." "Déjà vu wani abu ne da ke faruwa a cikin ™wa™walwa, kuma kusan kashi 97% na mutane sun taSa" fuskantar shi a rayuwarsu. Masana kimiyyar ™wa™walwa da jijiyoyin jiki (Neurology) suna da ra'ayoyi "daban-daban game da abin da ke haifar da shi, amma ga manyan dalilai:" 1. ˜wa™walwar ˜wa™walwa (Memory Glitch/Misfire) Ana ganin Déjà vu na faruwa ne lokacin da wani Sangare na kwakwalwa ke yin aiki ba daidai ba na Wan lokaci: * Rikicin Ma'aji da Sanin Sani: ˜wa™walwa tana da wurare biyu daban-daban: wanda ke adana "abubuwan da suka faru (™wa™walwar ajiya) da wanda ke ba mu jin cewa muna da masaniya da wani abu (sanin sani/familiarity). A lokacin déjà vu, wata™ila Sangaren da ke ba da jin cewa an saba da abu (sense of familiarity) ya kunna, ba tare da Sangaren ™wa™walwar ajiya ya kunna don tuna ainihin lokacin da abu ya faru a baya ba. Wannan yana haifar da jin cewa an gani/an saba da abu, amma mutum ya kasa gano" lokacin da wurin da abin ya faru. * Shiga Cikin ˜wa™walwar Ajiya Mai Tsayi (Short-circuiting): Wasu suna ganin cewa sabon bayani da ya "shigo cikin kwakwalwa na iya Waukar wata gajeriyar hanya zuwa wurin ajiye ™wa™walwa mai tsayi," maimakon bin tsari na al'ada. Wannan yana sa sabon abin da ke faruwa ya zama kamar tsohon abin da aka daWe da adanawa. 2. Tsallake KarSar Bayanai (Split Perception) Wani ra'ayi kuma shi ne cewa déjà vu na iya faruwa lokacin da mutum ya karSi bayani daga muhalli sau "biyu a jere, amma a wata hanya daban-daban:" "* Kallon Farko na Rashin Kulawa: A karon farko da ka ga wani abu ko ka shiga wani wuri, wata™ila ba ka" "mai da hankali sosai ba, ko kuma ka gani ne a cikin rabi-rabi (misali, daga gefen ido ko lokacin da ka shagala)." "* Kallon Biyu Cikin Kulawa: Lokacin da ka sake kallon abu Waya, ™wa™walwarka ta danganta shi da Wan" "bayanin da ta Wauka a farkon kallon da ba ka kula sosai ba. Wannan yana haifar da jin cewa an riga an gani, saboda a gaskiya an gani, amma ba ka tuna shi a sarari ba." 3. Jinkirin Bayanai (Delayed Processing) "Wata ka'ida ta ce bayanai na iya shiga cikin kwakwalwa ta hanyoyi biyu daban-daban, kuma idan Wayan" "hanyar ya isa ya Wan makara kaWan fiye da Wayan, ™wa™walwar za ta fassara abin da ya isa da farko a" "matsayin ""yanzu,"" sannan kuma abin da ya makara a matsayin ""tsohon abin da aka riga aka gani.""" 4. Dalilai Masu Ala™a da Jiki "Déjà vu kuma na iya zama mai ala™a da yanayin jiki, kamar:" * Gajiya ko Rashin Barci: Rashin hutawa ko damuwa na iya shafar yadda ™wa™walwa ke aiwatar da sabbin bayanai da ™wa™walwar ajiya. "* Epilepsy (Ciwan Jijiyoyi): A wasu lokuta, musamman idan déjà vu na faruwa akai-akai, yana iya zama" "alama ta ™ananan canje-canje na lantarki a cikin wani Sangare na kwakwalwa da ake kira temporal lobe, wanda yake da ala™a da ciwon farfaWiya (epilepsy). Amma ga yawancin mutane masu lafiya, ba alamar wata babbar matsala ba ce." "A ta™aice, Déjà vu shine kuskuren jin sanin sani (false sense of familiarity) da ™wa™walwa ke yi a lokacin" "da wani abu sabo ke faruwa.""" "Shiru Ya Ado yayi kafin ya ce mishi. ""Haka yana da ala™a da ciwon damuwa kenan?""" Ajiyar zuciya Doctor Ahmad yayi yana me mikewa daga kujeran da yake kallon Ya Ado ya ce mishi. """" "E, akwai yiwuwar a sami ala™a tsakanin Déjà vu da ciwon damuwa (anxiety), amma ba a kowane hali ba." Ga bayanin yadda alakar ke kasancewa: 1. Déjà Vu Na Yau da Kullum da Damuwa (Normal Déjà Vu) "Ga mutane da yawa, fuskantar Déjà vu lokaci zuwa lokaci (misali, sau Waya ko sau biyu a shekara) ba" alama ce ta damuwa ko wata babbar matsalar ™wa™walwa ba ce. * A lokacin da yake faruwa: Déjà vu na iya faruwa a lokacin da mutum yake cikin damuwa (stress) ko "gajiya (fatigue/rashin barci). WaWannan yanayi na iya shafar yadda ™wa™walwa ke aiwatar da bayanan da suke shigowa, wanda hakan zai iya haifar da wannan gajeren kuskuren ™wa™walwar ajiya (memory" glitch). 2. Déjà Vu Mai Ala™a da Ciwon Damuwa (Anxiety Disorder) Mutanen da ke fama da ciwon damuwa mai tsanani (Generalized Anxiety Disorder - GAD) ko ciwon firgita (Panic Disorder) na iya samun déjà vu akai-akai ko kuma su Wauke shi a matsayin wata alama mai ban tsoro. * ˜ara Mai da Hankali: Mutumin da ke da damuwa yakan mai da hankali sosai ga abubuwan da ke "faruwa a cikin jikinsa. Idan Déjà vu ya faru, wanda yake da damuwa zai iya fassara shi a matsayin wata" "barazana ko alama ta hauka, maimakon kuskuren ™wa™walwa na al'ada. Wannan yawan tunani da fassarar da ba daidai ba na ™ara tsananta damuwa." * Depersonalization/Derealization: Ciwon damuwa mai tsanani na iya haifar da wasu yanayi masu ala™a kamar: * Depersonalization (Jin Cewa Ba Kai bane): Jin cewa ba ka cikin jikinka ko duniyar ba gaskiya ba ce. * Derealization (Jin Cewa Duniya ba Gaskiya ba ce): Jin cewa abubuwan da ke kewaye da kai ba gaskiya ba ne. "* WaWannan yanayi na iya kara kama da Déjà vu ko kuma a fassara su a matsayin wani abu na daban," wanda hakan zai ™ara wa mutum damuwa. 3. Idan Ya Zama Akai-Akai Ko Mai Tsanani Ya kamata a nemi shawarar likita idan Déjà vu ya zama: * Aka-akai: Yana faruwa sau da yawa a cikin wata guda ko mako. "* Mai Tsanani: Yana faruwa tare da alamun ban mamaki kamar zazzabi, jin jiri, ko rashin sanin inda" mutum yake. "* A irin waWannan lokutan, déjà vu na iya zama aura (alamar farko) ta wani ™aramin ciwon jijiyoyin jiki" "(kamar temporal lobe epilepsy), wanda kuma ya bambanta da damuwa." "A ta™aice, damuwa na iya haifar da gajiya da rashin barci waWanda ke ™ara yiwuwar Déjà vu ya faru." "Amma musamman, damuwa na iya sa mutum ya firgita da fassarar Déjà vu a matsayin wata babbar" "matsala, wanda hakan ke ™ara masa damuwa.""" "Cikin son sanin wani hali Lubnah take ciki ya ce mishi. "" Ahmad wani hali Lubnah take ciki?"" "" Adam" kanwarka tana fama da "Depersonalization, tana jin kamar ba ita ba ce, tsaya kana waje me ka ga take yi da nake tambayarta? """ "Shiru yayi kafin ya ce mishi. "" Na ga tana karce farcen ta."" "" Good tana ganin ita kamar ba ita ba ce, bata jin zafi ko ciwo idan ta jiwa kanta ciwo, bata yarda da kanta ba kamar yadda take kallon kowa, sannan abinda ya faru da ita yana hunting dinta har shi Ex dinta tana jin kamar yana nan kusa da ita shi yasa take samun attack na Deja'vu akai akai, idan aka cigaba da haka zai haukata ™wa™walwarta domin bata yarda da cewa duk abinda yake faruwa da ita kamar gizo bane gani take kamar a zahiri yake faruwa da ita. Idan har aka tsallake wannan matakin bata dawo hayacinta ba, abu na gaba da zata fara shine Derealization," "shi kuma mutum bai yarda da kome a duniya ba, kowa ma ya gani zai cutar da shi ne. """ "Dafe kanshi yayi yana faWin. "" Innalillahi wainnalihir rajoun, Innalillahi wainnalihir rajoun, Ya Allah na" "tuba ka sassautawa baiwarka. Ahmad gaya min me ake bukata?""" "Gyara zama yayi yana faWin. "" Baya ga maganin da zan daurata a kai, zata fara ganin Doctor Dijah Bala," "wata Therapist ce, a nan Lagos take, zata na bata shawara da yadda zata dawo tunaninta."" "" Zai dauki wata nawa kafin ta dawo daidai?"" "" Tabdijam tow idan har aka samu kulawar da ya dace zata iya dawowa a kasa da wata shida, kai idan ba a samu yadda ake so ba, zata iya kaiwa shekara ko fi da haka ya danganta da inda take, a rage hayaniya da tashin hankali. Soyayya take bukata a yanzu duk abinda zata gani ya sakata nishadi, sai abu na gaba shine mu saka Allah a cikin lamarin ta, Addu'a karatun Alqur'ani, azkar. Sauraren tafsirin malamai daban daban both hausa and English, zuwa wuraren shakatawa da dan tafiye-tafiye idan da hali SAN nasan kana da hali ma, a kaita ko Umara ne, taimaka da" sakata farin ciki yadda zata ji itama mutum ce........... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: ASHIRIN CHIB" Ajiyar zuciya Ya Ado ya sauke deep inside dinsa ya kalli Doctor Ahmad for while kafin ya lashe busashen "lips dinsa. Ya ma rasa me zai ce, sannan daga ina zai fara? Daga shi har Zakiyah basu zaman gida. A" yadda ya fahimci bayanin Doctor Ahmad Lulu tana bukatar wani a kusa da ita kada ya cutar da kanta. """Condition dinta baya bukatar zaman asibiti, idan tana tare da wani a gefenta, zata fi samun sauki da sakewa kuma ko bata magana wasu abubuwan zasu sauya sosai."" Gyada kai Ya Ado yake yana jin kamar ya isa Bauchi ya rataye Hafiz a hankali ya ce mishi. "" Me ya haifar da haka? "" Ya tambaye shi kamar zai yi" kuka. """ Domestic violence and abuse anxiety, yake haifar da haka, daga yadda namiji ya mai da mace kamar" abin huce haushinsa tow daga nan irin wannan abin yake faruwa. Ka ga bata gaya min cewa yana dukarta ba amma daga yadda take ganinsa zai tawo yasa na fahimci girma da yadda ta fuskanci rayuwa a hannunsa. Wai ma waye shi ne haka ya lalata mata rayuwa haka? Kasan ba sai namiji ya kwanta da mace ko yayi mata fyade bane lalacewar rayuwa namiji ya mai da mace kamar dan uwansa namiji wurin duka da cin mutumci yana haifar da irin wannan abin. "Sannan idan har mace zata iya kawo batu gabanka a matsayinka na nata, tana bu™atar a shiga" "lamarinta ne wai me ya same ta ne!?"" Ajiyar zuciya Ya Ado ya sauke ya ce mishi. "" Ahmad kasan me? Iyaye da mu ne, muka aikata haka domin kuwa Yarinyar nan tasha zuwa ki har kirana aka yi ana gaya min nazo na raba auren kanwata tana shan wahala."" A hankali ya Ado ya warware mishi duk abinda ya faru. "" Kune kuka kashe yar uwarku, sannan iyaye suka goya muku baya, a gaskiya ba zan boye maka ba kun zalunci yarinyar nan."" Yadda take magana zaka fahimci har cikin ransa haka ne, sannan ya ce mishi. "" Ka je ka Wauke ta, sannan da kace kun nima mata aiki waye ya gaya maka yanzu aiki ne matsalarta? A yanzu" "ita kanta bata san waye ita ba, kuyi kokarin ganin kun dawo da ita hayacinta. """ "Mika mishi hannu yayi suka sake musabaha, sannan ya saka kai zai fita ya ce mishi."" Zan bawa Zakiyah" "sako ta kawo maka! "" "" Na gode! "" Daga haka ya bar ofishin Ahmad din, shima dama ba wai yazo aikin ba ne, jin Adamu zai zo yasa shi zuwa. Ba zai tab'a biyan Ya Ado abinda ya mishi ba. Kowani mutum yana da yadda kake jinsa a rayuwarka. A lokacin da aka sako shi a gaba sakamakon mutuwar wani mara lafiya aka jingina mishi laifin wanda ya kai da har ana ™o™arin kwace mishi lasin dinsa, Ya Ado ne yayi ta Shari'a har barazana zai da aka mishi amma ya tsaya sai da yayi nasara, sannan ya dawo aikin a lokacin ya kara tafiya karo ilimi tun lokacin yake son ganin ya kyautata Ya Ado domin biyan shi abinda ya mishi, s yanzu" haka zumunci suke da family dinsa da na Ya Ado. "Ina zaune Ya Ado ya zo ta rike hannuna muka tafi har wurin Aunty Zakiyah, ya ajiye ni ya tafi sayo min" "magani, yana dawowa muka wuce gida, bai kai ni gida ba sai da ya wuce da ni wurin saloon. ""Zakiyah ma zata zo anjima ki zauna anan kin ji!"" Babban wurin saloon ne da span. Zare hijab dina nayi, na lullube kirjina na cigaba da zama daya daga cikin masu aikin tazo ta tsafe min kitsona tana murmushi ta ce min." """Ke Fulani ne?"" A yadda tayi maganar kamar ta saba ganin gashi mai yawo balle ni nawa gashi ja ne" "kuma akwai cika da tsawo, gidansu Abba muka yo domin mazanmu ma sun fi mu yawan gashi, amma" "ana yawan cewa ni nafi su gashi. Zamana da Ya Hafiz yasa gashin ya koma baya. Haka ta wanke min tare da tsame min. Muna zaune sai ga wasu yan mata sun shigo, gaskiya sun yi kyau kamar wasu hurul ain, saboda kyau da gayu ga wasu maid da suke dauke musu da jaka suna bin bayansu, tare da wasu security service karti majiya karfi, daga yadda suke tafiya tare da wasu yan mata uku kamar kawayen juna ne." "Wurin zama suka wuce alamar can ne VIP, yadda masu aikin suka yi ta shiga da fita. Me da hankali nayi kan madubin gabana, matar ta ce min. ""Madam ayi miki kitso ne?"" Idan aka bar gashin ma addabata zai" yi domin wani lokaci ji nake kamar na yanke shi na huta. Shafa gashin tayi da ya sauka har gadon bayana. "A hankali ta fara busar da gashin, sannan tana gamawa ta dauko abin kitso. Ina zaune wani delivery" "Man ya shigo ya ce mana. ""Mrs Jama'are nake nima?"" Kallonshi nayi nace mishi. ""Nice!"" ""Mika min wata jakar leda da kwali da tarkace ya ce min. ""Daga Daily Meals! "" Mika min takarda da biro yayi yace nayi sign, haka nayi na mika mishi, ya fita. ""Mijinki ko?"" Girgiza kai nayi ina kallon parkage din, Ya Ado ne." "Haka matar ta cigaba da min kitso har wani lokaci gashi ta kwashi kitson yan dai-dai. Fitowa wata daga cikin yan matan nan, tana zuwa ta ce mata. ""Biolah fix kuke yi da wig?"" Da sauri ta juya tana faWin. ""No ma is just natural hair."" Takowa tayi s hankali, tana mai kai hannu zata tab'a gashin nayi maza na mike ina zare idanu. ""Sorry Ma wai zata ga gashin ne?"" Mai da hijab dina nayi ina kallonsu. ""Shi kenan zauna ba sai ta tab'a ba"" tsoro yasa naki zama, tsaki budurwa tayi ta fita can sai gata wani gaye, da sauri nayi" "kasa da kaina. Kamar da wasa sai ga shagon ta can wurin VIP ya cika da Manya Yara, tana gama min kitso, Aunty Zakiyah tana shigowa. ""Baby girl! Kin ci abincinki kuwa?"" Nuna mata nayi, ta zauna aka fara tsefe mata kitsonta, aka wanke mata nata sannan aka mata parking a lokacin da yan matan nan suka fito, ni dai kaina a sunkuye suka fita sai budurwan nan ta tsaya tana faWin. ""Ke uwar tsoro gashinki yayi min kyau, idan na kara haduwa da ke sai na taSa."" Yan matansu suka kwashe da dariya, irin sun ga abin" dariya ni dai ina bayan Aunty Zakiyah. Yadda na rike rigar ta yasa ta yi ta tab'a hannu. """Badar yarinyar bata burge ki bane, natural hair fa, gashi ja kamar wata baturiya."" Kallon Zuhra tai ta" "ce mata. ""Who care? Duk wata mace so nake ta dawo bayana, bana son ta dawo gabana amma ke da" "yake kin iya kwashe kwashe ke duk wata mace mai kyau burge ki take ko bata da kyau matukar tana da gashi da yake ke kwakwaido ce.""" "Murmushi tayi ya ce mata mata. "" Yes ni kwakwaido ce, amma waye zai damu da haka? Abu daya na" "sani ina cikin madagar KUMO FAMILY GROUP, ko a so ni ko kada a so ni Am Queen! "" Shiga motarsu kowacce tayiwa motar wuta suka bar harabar wurin saloon Win." "Riko hannuna Aunty Zakiyah tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta ce min. ""Yaran masu kuWi ne basu da" "hankali. Muje"" haka na biyo ya har wurin motar, ina ji a raina sun yi dace sun samu abinda suke so. Sun samu irin gatar da na rasa, idan da nima na samu gata haka da ba makawa da ina cikin manya matan" "alfarma. Sai dai yadda na hango fuskarsu ya nuna basu cikin farin ciki, basu jin dadin tasu rayuwar ko" don ni bana jin dadin tawa rayuwar nake hango kowa ma haka? Har muka iso gida zuciyata bata bani "damar kome ba, bayan mun yi sallah naci abinci na sha magani na koma na kwanta. Ban farka ba sai karfe biyar nayi sallah na cigaba da zaman dakin, shigowa Aunty Zakiyah tayi tana faWin. ""Oya zo nan zamu fita ne, ki shirya muna jiranki."" ""Tow!"" Na amsa mata, sannan tana fita na shirya cikin doguwar riga abaya na saka hula na yane kaina. Sannan na sauko kasa. ""Waw you look beautiful Aunty Lulu!"" Yaran suka fada, sai na kasa yarda da haka na fara jin wani irin yanayi kamar sun muzanta ni. ""Baby girl kinyi kyau ko Doctor, she looks good"" jin yadda Ya Ado shima ya kara fada sai na ji wani iri, riko hannuna Adil yayi ya ce min. ""Daga yau ni mun zama abokai ko Dady!"" ""No da ni zata yi aboki!"" Inji Princess, Wai ni yau ake fada a kaina, sai naji hawaye na zuba min abin yayi touched heart dina, a hankali Ya Ado ya ce musu. ""Ba zata yi abota da ku ba, she is my favorite sister, oya ku je wurin Maamah ita take bukatarku!"" Ya fada yana riko hannuna muka fita suna faWin. ""No Dady, a'a kawai ka bamu ita, kaima sai kace Hajiyar Bauchi ta kawo maka wata Barbie din, but Aunty Lulu she look like Barbie!"" Irin wannan maganar da suke sai yasa na fara jin like I miss something important a rayuwata, akwai wanda ya tab'a gaya min you look like Barbie princess, musamman idan kika saka uniform din nan!"" Hawaye ne ya shiga zuba min a idanuna. Dama zan samu wanda zai gaya min yadda nake ni da shekaru goma da wani abu na fuskanci muzantawa da gwatsalewa, har ake gaya min bani da kyau. Fita muka yi har wani unguwa wai Yaba, a nan muka je ashe ogan Ya ado ne yake birthday. For the first time a rayuwata da na shiga irin wannan" taron. "Muna wurin taron, aka yi ta gabatarwa har Ya ado ya mika mishi abinda ya kawo, kasancewar" "mutumin yana ji da Ya Ado sai gabatar da shi yake a wurin manya clients dinsa, yana gaya musu yadda yake aiki, su kuma sai amsar compliment card din Ya Ado suke, sannan ya gabatar da mu a matsayin Family dinsa, tare da nuna musu nice auta a family dinsa. Hannuna yana rike da na Adil. Don tunda muka zo Aunty Zakiyah ta kira shi ta mishi magana, ya zauna a gefena kamar me jin barci kanshi a arm dina, yayi shiru haka sai ya saka min jin nutsuwa. Duk abinda ake yana ji kuma yana sane amma haka da yayi ya haifar min da nutsuwa idan aka yi wani magana da yarvanci na tambaye shi yana bani amsa haka ya sani kara fahimtar yadda yake jin harshen, ina kallon kome har lokacin da Aunty Zakiyah tazo ta d'aga mu, muka je aka gaida mutanen. Har lokacin hannunshi yana cikin nawa. Wasu bakin alfarma aka yi a wurin na Ya Ado da ogansa sun tafi tarbo bakin wani dattijo ne kamar dan arewa, yana tafiya da sand." "Yadda Ya Ado da ogansa tare da wasu team na aikinsu, suka rufawa dattijon na fahimci babban mutum" ne mai daraja. Sannan suna ganin girmansa sosai firm Winsu. "Da yake mun yi sallah magariba muka fito taron, sai duk naji na damu ina son nayi sallah isha amma har" "lokacin kamar yanzu ake taron, muna tsaye manyan yan kasuwa, yan siyasa na garin Lagos. ""Kin gansu nan, dayawansu suna tare da office Winsu Dady ne, idan har Shari'a za ayi ta kasada da rayuwa da dukiya. Office dinsu Dady ake yinta. Amma shi ba kowacce Shari'a yake amsa ba, kuma suma sun san da haka yana kiyayye hakkin Allah."" Inji Aunty Zakiyah, gyada kai nayi ina kallonshi. Jan shi Mutumin nan da ya" "shigo yana taSa bayansa tare da mishi magana da bamu fahimta ba, sai ganin Ya Ado muka yi yana ta" Godiya tare da mikawa mutumin hannu. Haka manya mutane suke ta gaisawa da Ya Ado da yake Ogansa "ya gabatar da shi, sannan a nan y fara magana kamar haka." """A yau sha biyar ga watan Mayun, nake shaida muku na ajiye aikina wato nayi ritaya, yau ina da" "shekaru saba'in cib, duk tun shekarun baya naso na ajiye aiki amma team din da suke sponsor na office dinmu suka ce basu ji ba basu gani ba. Yau amma yau na hakura da aiki inda zan gabatar da Abdulwahab Adekunle Adebayo matsayin shugaban team dinmu. "" A hankali yayi ta kiran sunayen mutane dayawa yana gabatar da matsayinsu. Ya ce a wurin. "" Nasan wasu zasu ce Why Adam U.U Jama'are? Sai dai ko wacce kusurwa tana bukatar jekariya, mu kungiyar da abokan huldanmu sun bukaci jekariya, shi din nan dai gashi koda aka fitar d sunansa da kanshi ya zo ya ce nayi hakuri na cire. Na barshi da abinda yake yi, idan na fahimci Adam UU Jama'are, yana da buri shi yasa bai amshi ragamar shugabancin ™ungiyar SAN ba, koda yake shi din d'a ne a gare ni, nagartashi da amanarshi abin alfahari ne, don haka a yau nake gaya mishi kuma nake sanar da al'umma cewa daga yau duk wani Shari'a da zamu yi ko zaa kawo firm dinmu Adam UU shi zai jagoranci shi. "" Take wurin ya kara daukar tafi. Kafin yayi gode da sauran al'ummar da suka samu halartar Birthday din, sai na ji na gaji haka nayi ta lumshe idanuna. Har wurin karfe goma aka tashi muka bar gidan, koda muka iso gida wanka nayi tare da sallah, na sha magani" sannan na kwanta a hankali barci yayi gaba da ni. *** "Mama yadda ta kafe babu wanda ya isa dawo da auren Hafiz da Lubnah, haka yasa ta tattara ta bar" "gidan Baban Bauchi, wanda haka yayiwa Hajiyarsu Hafiz dad'i. Sannan ta kuma saka aranta duk Inda Lubnah tana zata dawo wurin Hafiz domin ganin yadda halinsa yayi mugun tashin nan bayan an rufe shin nan, ta tambaye shi akan me yasa ya damu da Lubnah bai boye mata ba, ya gaya mata gaskiya abinda ya faru, da kuma dalilin da yasa yake son ganin ya kara dawo da Lubnah, taji tsoro ta kuma kadu, sannan ta saka duk wani abinda take da shi a kasuwa domin a bine kome, sai dai a yanzu kan an binne kome, kome kuma ya rufu kamar yadda suke fata yanzu Lubnah ita ce harinsu, shi yasa yake ta bibiyar Baban Bauchi ya gaya mishi inda take koda a wajen kasar nan ne sai ya nimo ta, Lubnah tashi ce shi Waya daga shi kuwa babu wanda ya isa zama da ita koda kuwa zai mutu ne Lubnah bata isa tarayya da wani da namiji ba." Wannan shine alkawarinsa. "Yau karfe daya na dare ya shigo gidansa, da wata Yarinya a gefensa, yar lukuta da ita ya bude mata kofar" "dakin Lubnah wanda yake nan har da kayan ba a dauka ba, karshe ma dakinsa ya mayar da shi. Yana ganin yarinyar ta shiga, ya wuce dakin Karimcy tana barci, daga gani barcin ta wahala ce domin daga ita har Yaran babu wnada yaci wani abu a cikinsa. Tashinta yayi ta bude idanun tana kallonshi. Ta gaji sosai" "domin zuciyarta ba zata iya daukar ukubar da ya fara gana mata ba ta ce mishi.. ""Ka dawo ka bani hakuri" "ne?"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Ko daya nazo ne na gaya miki gaskiya ko ki fita ki fara girki kamar" "sauran matan ko kuma bakin ciki da yunwa ma sun ishe ki"" shiru tayi sannan ta ce mishi. ""Ba zan yi ko daya ba, kai ne ma zan kafa maka sharadi. Idan kana son kanka da arziki ka ajiye abinda kake aikatawa da wanda kake shirin aikatawa. Kasan nasan abinda yake faruwa, har abinda Hajiya take aikatawa domin rufa maka asiri. Ni kasan ban da sirri ko kashe ni ka yi ina da hujjar da na bada shi ba nan kusa ba har gaba da Bauchi na saka a ajiye min daga ranar da suka ji labarin mutuwata su bayyanawa duniya tasan waye kai. "" Yadda yayi magana da confidence yasa shi razana, bafa kowa bane Lubnah ta ce mishi. "" Ni ba Lubnah ba ce da zan rufa maka asiri ba, bayan ni ba koshi nayi da kai ba. Ruwanka ne ka ja tsumar rayuwarka, sannan ina son kudi a cikin account dina, ko kuma na kira waya nace a saka labarin nan zuwa" "ga Yayun lubnah su ji yadda ka kashe Mahaifinsu da ita Lubnah. """ "Yana murnan ya kashe maciji, ashe bai saure kai ba. Domin Karimah ita ce kan macijin da bai sare" "kanshi ba. Duk sai ya ji kamar zai zauce domin Karimah tafi shi iskanci. Eh ai ko a shekaru Karimah ba sa'arshl ba ce. Domin tun can ta girme shi a bariki suka hadu da ita tana yawo bariki, suka haWu." "Washi gari kuwa da Karimah ta fito ta ga yarinyar da Hafiz ya kwana da ita bata ce mata kome ba, ta" "shiga kitchen ta dauko itace ta shiga dakin Lubnah Hafiz yana barci ta rufe Yar mutane da duka. Dakyar ya kwace ta, tana haki ta ce mishi.. ""Ni ba Lubnah ba ce, wallahi baka isa kawo min wata mace cikin gidana ba. Idan kuwa kayi haka ka saka a ranka nice ajalinta."" Shi fa ya zata kowacce mace kamar Lubnah take, sai gashi lokaci guda Karimah ta goge mishi zero. Sannan ta masa barazanar sai ta kai ™arar shi wurin Baban Bauchi, tunda shi ya zama Wan akuya zata tona mishi asirin da yake rufawa tunda tasan sirrinsa. Wannan abin yasa shi kara shiga hankalinsa, ya koma mata biyayya bai kara shigo mata da mace gidan ba, domin kuwa ta rike mishi wuya, kuma bata girki kudin dai tana samu son ranta. Kuma shima tana cin ubansa dai-dai gwargwado. Duk ya fita hayacinsa bai da hankalin da zai fahimci barnan da yake shi dai burinsa asirinsa ya rufu, a irin wannan yanayin ne aka Baban Jama'are ya fadi jininsa yayi mugun hawa, haka suka dauko shi daga Jamaare aka kawo shi Bauchi, Teaching hospital Bauchi, wannan abin ya" sake gigita Hafiz yayi ta ji kamar yayi hauka. Domin hawan jini da diebetis suka buga shi da kasa.......... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: ASHIRIN DA ŠAYA" "Duk da wannan abinda ya faru, daga Mama har Yadiko sun kyale Baban Bauchi yayi yadda yake so, suka" "bar mishi gidan shi kuwa ya dauki dokin zuciya ya daura a kansa tare da wani irin girman kai da son kai, suma Yaran maza da mata suka zuba mishi idanu yayi yadda yake so ba dai Hafiz ne suka bar mishi." "Sai da Baban Jama'are yayi kwanaki kafin ya dawo hayacinsa, ya kalli Hafiz cikin tsananin bakin ciki." """Hafiz maka baki ba, ba zan ce zaka gani ba. Amma matu™ar Lubabatu bata zalince ba, kai da nutsuwa har abada idan kuwa ita ce ta zalince ka Allah ba zai barta ba, kai Hafiz bana jin yarinyar nan zata iya abinda ya raba ku. "" Juyar da kai yayi domin maganar Allah yana jin zafi da ciwo, yana ji kamar ya cire zuciyarsa idan ya tuna yadda Yaransa suka mai da Lubnah idan ya tuna yadda suke mata wulakanci har akan idanunsa sai yayi kamar laifin nasa ne, donin bakidaya yayi kuskuren da har abada ba zai gyaru ba, kusan da iyayen Lubnah suka juya mata baya, kasa yin kome yayi amma shi dansa yana yadda ya so." "Akwai wani abu da yake faruwa a wannan duniyar daga lokacin da kace na wani bai isa dariya ba, har abada naka ba zai tab'a maka daidai ba, a lokacin da yake ji yake gani ana azabtar da Lubnah shi a lokacin yayi kamar bai gani ba sai ya rufe bakinsa da kunnensa yayi kamar bai ji ba bai gani ba. Share" kwalla da ya zubo mishi yayi. "Sai dai tun daga ranar bai kara yiwa Hafiz magana ba. yadiko taxo ta ga jikinsa, bayan ta koma gida ta" "gayawa Mama ta waya, ai kuwa ranar talata bayan laasar Mama ta zo da matar Ya Umar, suka samu Abba wato Baban Bauchi. Yadda yake wani jiji da kai yasa Mama itama ta nuna mishi daga fada take. Ta wani dauke kai suka gaisa da Baban Jama'are, ya yi kasa da murya ya ce mata. ""Don Allah Hajiya Salamatu, ki koma dakinki haka yanzu ku ba yara bane."" Murmushi tayi tana me faWin. ""Idan na gaya maka gaskiya zaka yarda?"" Ya jinjina kai ta ce mishi. ""Zabi ya bani har abada ba zan dawo gare shi ba kamar yadda Lubnah ta haramtawa Hafiz, idan kuwa ka ga ta dawo ga Hafiz tow mutuwa nayi kasa ya rufe min idanu kenan. Kai ko gawar Lubnah da ta koma gida Hafiz gara wuta ya cinye ta."" Ta fada tana murmushin bakin ciki domin ita Waya tasan yadda take jin ciwon halin da Lubnah take ciki, mikewa tayi tana faWin. ""Muje kin ji Allah ya kyauta,."" Haka ta fita Abba ya ja tsaki yana faWin ""Sai me idan ba ta dawo ba ita Yadiko idan bata koma ba wallahi sai dai aurenta ya mutu don ya gaji ai ba da ita yake rigima ba, ita kuwa da yake tafi shi kwaya tace a gaya mishi ita bata tsoron saki ai idan har ya iya Hajiya Salamatu haka babu wacce ba zai yiwa haka ba, ba zata koma ba Hajiya Asiya su mishi replace abinda suka gaza mishi. Sosai aka yi ta rigima yaran kuwa sun koma gefe dama kowa ya gaji da abinda yake yi, ganin haka yasa Manya gaba cikin family uku suka taru aka dawo da Yadiko domin ya kafe Mama ba zata dawo ba, idan kuma zata dawo sai dai ta dawo da Lubnah kafin shi, ita kuwa Mama ta ce bai ji ka ba tukun, ai yanzu ba da bane Lubnah kuwa tayi musu nisa. Wannan abin ya bala'in bata mishi rai. Shi yasa shima ya kafe ba zata dawo ba. Ita kuwa ta ce tafi nono fari. Faruwan wannan al'amarin ya kara sakawa Baban Jama'are damuwa sosai domin yana ganin ai duk abin nan ya faru ne ta silar danshi. Sannan masu ganin laifin Lubnah yanzu sun dawo bayanta, domin abin da ya faru ya nuna sun so kansu duk abin nan gashi ita ta rasa iyayenta amma shi da yake shafaffe da mai ne gashi nan yana zaune tare da kowa na shi, sai yaji tsoron Allah ya shige shi dansa yayi sanadin auren da aka Wauki shekaru, sannan a lokacin da ya rasa madafa su wadannan mutanen sune suka tsaya mishi. ""Innalillahi wainnalihir rajoun!"" Ya nanata kalmar" nan tafi sau dubu ya tsani kanshi da zuciyarsa. "Lokacin da ya dawo Jama'are, sai kunya da kuma yadda mutane suke ganin laifin Hafiz ya kara susuta" "shi ya dinga blaming kansa wannan abin sai ya kara hurt din zuciyarsa, har sati biyu ya cika Babangida ya" "mai da shi ganin likita. A lokacin da suka hadu da Hafiz ya ce mishi. ""Ban san me kayiwa Lubnah ba," "amma ka sani ba zaka tab'a farin ciki da jin dadin rayuwa ba, sai kun sake zama duk da kowa yana son yaji matsayata akan Lubnah abu daya zan gaya maka a duk lokacin da ka ji inda take kafin wani ya rugaka samunta ka kara niman soyayyarta a karo na biyu, ka dawo da ita rayuwarka idan ta amince idan bata amince ba, tabbas ka tafka mummunar asara a rayuwarka, ka dube ka kai kanka baka da nutsuwa ka cutar da ita ka cutar da iyayenta. Ina ji kamar na mutu da bakin cikinka! "" Ya fada yana jin kuka na zuwa mishi. Haka ya ga likita sannan Hafiz ya kawo shi kasuwar Central. Yadda Baban Bauchi ya ga dan uwansa ba karamin dadi ya ji ba, haka ya dauke shi suka yi ta zaga manya shagunansu, yana karawa bawa dan uwansa hakuri akan batun lubnah wanda yake niman wata guda da faruwa. Ya kuma yiwa Wan uwansa al™awarin. "" Matukar ni na haife ta kuma ina raye Hafiz shine mijin Uwata, ba zan tab'a sauka" "akan kalamai na ba. """ """ Ya Shehu, ka sani matu™ar Lubnah ta gama Idda tana da damar zabawa kanta abinda take so, sannan" "ita kanta zuwa yanzu tana bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali. Hafiz ya mata laifi. "" "" Ai dan uwanta ne idan bata rufa mishi asiri ba waje zata rufawa? Iskanci ne da rashin mutunci ni kuma ina daidai da ita" "duk inda taje zata dawo ko shekara dubu ne!""" "Wannan ya kara nuna son Kai da son zuciya irin na dan Adam, bakiWaya suka saka a ransu idan har ta" "dawo su ke da iko da ita. Anyi hiran nan a gaban Ya Sani shi kuwa ya kira Ya Umar ya gaya mishi, ai kuwa maganar ta fada kunnen Mama, kwafa tayi ta ce Allah ya basu Sa'a tana jiransu." *** IKEJA LAGOS GRA ELYAKUB MUHAMMAD KUMO St. "Aka rubuta da karamin allo, wanda aka yi zanen da wata golden paint, babban gare da zai sadaka da" "cikin gidan irin kafceccen nan ne, mai nauyin gaske nan ne, a hankali hancin wata kyakyawar mota kiran kamfanin Roll Royce , ta cigaba da tafiya izuwa kantamemmen gidan da yake cikin unguwar wanda yake tsakiyar unguwar mai zubin fadar sarki. A hankali yake wuce gidajen da suke yiwa wannan kyakkyawan gida kawayan, har ya isa zuwa kofar da zata sada shi da wannan kyakyawar fadar. Ya jima a cikin motar yana shiru kafin ya tattaro duk wani abinda zai Wauka sannan ya fito daga motar, ya nufi hanyar da zata sada dashi da asalin kofar da zata kai shi main Street na gidan, kofa ce mai security service, yana zuwa wani kare ya fara mishi haushi tare da kad'a mishi bindi a hankali ya isa gaban karen da ya tawo da gudu yana kawaye mutumin murmushi yayi ya ce mishi. ""Max ya kake?"" Ya shafa wuyar karen wanda kana gani zaka fahimci karen Ya sanshi irin sosai din nan. Mikawa daya daga cikin security din key yayi ya ce mishi. ""Akwai abincinsa a boot!"" Daga haka ya isa bakin kofar computer din tayi screening dinsa tare da" "scanner. A hankali ta ce mishi. ""Barka da zuwa Captain Ubaidullah Jibirl Kumo, na'ura ta tantance ka.""" """Na gode Husnah ina sonki da zan kara aure ke zan aura."" Ya fada yana murmushi yana jin ta ce mishi." """Bani da kawazuci sannan ni na'uran AI ce."" ""Ai na sani shi yasa nake kara kaunarki."" ""Na gode Ubaidullahi. "" Daga haka tayi shiru ya wuce idan da sabo ko su, security din wajen sun san draman AI" Husnah fa Oga Ubaid "A hankali ya ke tafiya har zuwa cikin gidan, kyakywan Yara yan mata suka tawo da gudu. "" Uncle" "Ubaid, oyoyo!"" Rungume su yayi sannan ya mike tare da ciro chocolate a aljahunsa ya mika musu yana faWin. ""Oya cigaba da wasa."" Ya wuce su, bai kai entery na gidan ba, sai ga Maid sun fito cikin girmamawa suka bude kofar suna mishi. ""Barka da zuwa Sir!"" Jinjina kai yayi ya cire takalmi a wurin suka rufa mishi baya masu gyara zaman takalmin suka gyara shi kuma yana shiga inter door na gidan ya samu" wasu takalma an zuba mishi maid din tana mishi sannu da zuwa. Kamshin turaren wuta zamani na FAMAS SCENT OF LEGEND GIDAN TURAREN WUTA ya daki "hancinsa, wani irin kamshi ne mai hade da sanyin Ac ya bada wani irin perfect kanshi me shegen dad'i, daga shiga cikin gidan zaka fahimci how yanayin kamshin yake ratsa zuciya da gangan jiki, wata maid ya samu ta ce mishi. ""Barka da zuwa sir muje ta wannan hanyar."" Duk da ba yau ya fara zuwa gidan nan ba, sannan kusan rayuwarsa bakiWaya yayi ne domin gidan nan, amma duk lokacin da abu me muhimmanci ya kawo shi, jagora ake mishi. Har zuwa babban main entrance parlourn na gidan, da sallama ya shiga wani kyakkyawan bafulatani dattijon da ya sha gwagwarmaya ya gyara zaman glass din sa ya zuba mishi" idanun cikin wani irin murmushi yana me amsa sallamarsa a nutse. """Ubaid!"" Ka rasa yayi gaba wani karamin abin wanke hannu ya ajiye file din sannan ya wanke" "hannunsa, tare da shafa hand sanitizer, sannan ya dauki file din ya isa gaban dattijon ya ce mishi. ""Barka da hutawa Alhaji!"" Gyara zaman glass din yayi ya ce mishi.. ""Barka dai Captain! Yau kai Waya ne ina Amaryan lalle?"" Gyara zama yayi yana faWin.. ""tana lafiya, Alhaji Hajiya Dadda tana nan kuwa?!"" ""Tana nan zata fito ai idan ita ce."" ""Allah yasa mu gama bata fito ba."" Ya fada yana murmushi, abin motsa baki aka fara kawo mishi, ana jera mishi a gabansa, har suka gama Alhaji ELYakub Kumo ya ce mishi. ""Fura zaka zuba min."" Mikewa yayi ya zuba masa sannan ya mika mishi shi kuma ya dauki hadaddiyar fruit da" "ya sha madara, ya fara sha yana sauraren Alhaji ELYakub Kumo." """Yau ma sakon ya baka ka kawo min?"" Ya tambaye shi yana murmushi, irin murmushi irin na manya." "Cikin wani deep sorrow voice ya ce mishi. ""Ko don ba ni ba haife shi bane? Amma ai ni na haifi Mahaifinsa."" Sai yayi murmushin takaici irin wanda kana ganin abinda kake so amma kana ji kana gani yafi karfin ka. ""Ubaid ina da ikon hana ™addara ikonta ne?"" Girgiza kai Ubaid yayi yana tausayin dattijon. ""Kayi hakuri Alhaji!"" Murmushi yayi a karo na uku wanda kamar ita din anyi ta ne domin fuskarshi kuma tana kawata mishi fuskarsa da wannan kyakkyawan murmushi. ""Amma kasan ban yi mishi kome ba ko? Ban cutar da Turaki ba, duk abinda zanyi domin ya zama karaya a gare shi nake yi. Amma kasan na tsufa ko? Me yasa Turaki yake gudana? Da farko na dauka don rasa mahaifiyarsa ne yake gudun Ubansa, sai mutuwar Ubansa yasa na hango kiyayyar da Turaki yake min, bani da wani abu da zan rike Turaki. "" Tari" ya fara a hankali yana me ajiye furan ya dauki ruwan da Ubaid ya mika mishi. Kurba yayi yana me "ajiyewa. "" Kowacce rayuwa tana da fuskar da ™addara take bude mata, Turaki shine kaddarata, ban rena" "iyawarsa ba amma ya dawo gabana im dead in side, ya dawo yazo ga tsohon nan da baya jin kome sai kamshin mutuwa! "" Shafa kai Ubaid yayi yana tuno abinda ya faru anan parlourn, numfashi ya sauke a hankali, yaji muryan Hajiya Dadda tana faWin. "" Ba zan ci ba, shima maganin ba zan sha ba. Wuce ki baka wuri tun ban haifi Ubanta ba nake jinya har na haifi Ubanta haka yasa na mutu ne? Ta je can ta cigaba da zama ai dama nasan bayinta ba ne, domin ko jiya wani malami ta gaya min bakin asiri aka mata, sai kuma macen aljan da suke tare wanda har sun yi aure har da zuri'a. Shi yasa bata son zaman cikin mutane."" Ta isa wurin dattijon ta zauna cikin ladabi da biyayya irinta matan da suka ga koya suka ga yau, gashi har gobe ana saka musu ran zasu gani cikin harshen fulatanci ta ce mishi. "" Jam na?"" Kallonta yayi na wani lokaci kafin ya ce mata. ""Lafiya lau Hajja!"" Gyara zama tayi cikin ladabi ta ce mishi. ""Ina son na" "gaya miki, ko zaki yiwa Auta magana ta kira malamin nan zata turo abin nan da ake tura kudi ta ciki!""" "Murmushi yayi ya ce mata."" Hajja kina tsammanin Turaki zai dawo ne?"" Cikin tsantsan biyayya ta ce" "mishi. "" Nasan bayin kanta bane zata dawo, waye nake da shi bayan Harisu? Turaki ita ce nake kallon a matsayin Harisu, ki yi hakuri ki bada umarni ta tura mata kudin. """ "Wato dariyar da Ubaid yake kamar cikinsa zai kulle, ya tab'a zuwa gidan nan bai fita bai dara ba ai" "kuwa? Babu ranar domin ita kanta Hajja comedian ce. Alhaji ELYakub kuwa so yake ta daina yarda da wannan maganar domin wanke ta ake yi. "" Alhaji baki ce kome ba?"" Murmushi yayi yana kallonta. Hango yar karamar kanwarsa da suka hada Iyaye maza wacce aka ce ya je ya ganta ko tayi mishi, yar kwailar nan da suka je ganinta, tayi ta zuba gudu da boya ance saurayi ya zo wurinta. ""Alhaji baki ce kome ba?"" Ta kara fada Hajja a wurinta mace namiji ne, namiji kuma mace, ta juya musu lamarinsu mai sauki ne kusan dabi'ar Fulani da Barebari da nufawa, haka harshensu take taking over na jinsin matukar bada" yaransu zasu yi maganar ba. "Akwai wani abu da Hajja da Alhaji ELYakub suka kasa boye shi, kaunar Jikansu da yake bala'in wahalar" "da su. Domin kaf duniya babu wnada yake juya kakaninsa, kamarshi sauran jikokin basu samu wannan damar ba yo Alhaji ELYakub bai yarda da wasan jika da kaka ba, domin yana da zurfin ilimin addini da na boko, gogaggen dan kasuwa ne, top-notch wanda aka sani a nan kudu da arewa. Mutum ne da yake faWa aji, domin ya bunkasa fiye da kima, hatta Yarbawan lagos suna matukar ganin girmansa, kamar yadda suke ganin girman dan gote. Idan za ayi lissafin attajirai da suka boye kansu ELYakub Kumo yana cikin" manya na farko. "Domin yana da hadin gwiwa da bankunar kasar nan, irinsu First bank, UBA, Union Bank, Zenith bank," "ya kawo wannan hadin gwiwar? Duk da bankunan ne suka bukaci ala™a da shi ba shi ya bukaci ala™a da su ba, akwai lokacin da idan mutum ya isa wani limit baya bukatar ya tura kansa sai anyi da shi, lokaci yake zuwa ayi da kai. Haka ce ta faru. ""Alhaji baki ce kome ba?"" ""Shi kenan zan gaya mishi shi kenan?"" Gyada kai tayi ta gyara zama ta fara bashi labarin da Malamin ya gaya mata akan Turaki wanda kusan tishi ce ai ya saba jin wannan labarin ba sabo ba ne a wurinsa. Karshe ma ga yadda hiran ta kasance. ""Ita" "Turaki ta hadu da aljani suka auri juna har suka hayayyafa yaran suna zuwa cikin gidan nan har wurinki," "yanzu da ayi kiranye kenan?"" Shiru yayi yana kallon yadda ta damu kuma ya ce mata. ""Gaya min me" "Malamin ya ce miki."" Gyara zama tayi ta ce mishi. ""Kin san bana bin makamai amma wannan karon nace bari na hada malami guda biyu, tow ita Waya ta Gombe ta ce min babu abinda ya faru, ™addaranta ce har yanzu bata zo gare ta ba. Amma ni ban yarda da ita ba, don bata ce za'ayi aikin kome ba, ta dai ce kome da yake faruwa haka Allah yaso, idan aka yi hakuri ita Turaki zata dawo da kanta, tow na dai bada abin sadaka ya ce ita bata karban Kudi dayawa shi yasa na fahimci karya take yi, tow ita Waya ta kome tace akwai mata aljani suna tare har suna da Yara da shi, ita Turaki ya auri matar aljani ne, shi yasa shi matar aljani ya dauke shi daga wurin mu, idan har muna so ya dawo sai an biya kudin kamar dubu dari hudu da saniya baka wuluk sai a sayi farin kaza, dan taure baki, kaza buja-buja. Jan dawa, bakin dawa, kaura, da" "fura kwarya goma.""" """Hajja karya yake shi yake son cin kudinki."" Inji Alhaji ELYakub, shiru tayi tana kallonshi idanunta ne suka" "shiga cika da kwalla. ""Alhaji ki fahimci yadda nake ji!"" Riko hannunta yayi ya saka nata a cikin hannunsa ya dunkule hannun a hankali yana bugawa yace mata. ""Fadime, ki yarda da maganar wancan malamin farkon shi mutumin kirki ne, shi kuma wannan dan damfara ne, Fadime ina son ki yarda kaf duniya ba mai yi sai Allah. Ni nasan Turaki zai dawo lokaci ne kawai bai yi ba, idan kika ce zaki dawo da shi da karfi zai koma. Kin tuna yadda ya dawo wasu shekaru kafin lamarin ya lalace haka. In sha Allah Turakinki zai dawo gare ki."" Mikewa Ubaid yayi ya basu wuri can wajen gidan ya fita ya damu daya daga cikin kujerun alfarma ya zauna ya zaro wayarshi. Sai da ya cire shi a key ya tsaya yana kallon hotonsu na kuruciya, suna dariya ya danne bayan Turakin. Murmushi yayi sannan ya cigaba da. Lalubar wayar har ya zo kan number shi wanda ya rubuta Introvert. Wayar har ta gama ringing ba a dauka ba, sai can aka turo mishi" sako da number. *Ya suke?*........... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: ASHIRIN DA BIYU" "Daga wannan babu wani sakon, har leka bayan wayar Ubaid yayi ko zai ga sauran sun makale, amma ina" "iya su kenan kalma biyu, harufa hudu? Wato shi dai ba zai tab'a sauya ba." Cikin fushi shima ya tura masa da Ash'ar. Tunda ya tura ya kai minti goma a wurin ba reply ai yasan ko "sama da kasa zasu hadu ba zai dawo mishi da sakon ba, idan yayi sa'a gobe ma da zai kara tura mishi abu daya ne zai sake turo mishi. Sake kiran layin yayi ya danna mishi busy. Takaici ya saka shi wucewa gidan ya samu Hajja da Alhaji ELYakub sun koma hiransu, mika mishi File din yayi ya ce mishi. ""Wannan sune sakon da ya bani, sannan da farko ban fahimci yadda sakon yake ba, sai dazun nan na fahimci sakon."" A hankali ya fara warware mishi bayanin da Turaki ya turo mishi, shiru yayi yana mamakin yadda, kome yake tafiya ba tare da saninsu ba. Sannan wani abin da ya bashi tsoro yadda aka karkata da kuWi ta wani" hanyar da bai dace ba. """An samu masu hannu a cikin lamarin?"" Bude baki Ubaid yayi zai magana aka turo kofar, Alhaji Mudansir" "ELYakub Kumo ya shigo cikin wata danyen Wagabari dark blue, yayi ya wani irin daukar fatarshi. Sai wani shaki yake kamar dare kwana sha huWu, duk wanda ya ganshi yaga wanda arziki ya zauna mishi, cikin isa" da kasaita ya samu wuri ya zauna cikin girmamawa ya gaida iyayensa. A hankali ya mai da hankalinsa "wurin Mahaifinsu da ya ga ya tattara nutsuwarsa ga Ubaidullahi. ""Yanzu ka mai da mishi sakon kace yayi duk abinda yake ganin ya dace, sauran kuma zan dauki mataki in sha Allah ba zan bar kome ya tafi a haka ba."" Wani irin harara Alhaji Mudansir ELYakub ya watsawa Ubaidullahi ya cigaba da sauraren maganarsu da ba fahimtar inda suka nufa yake ba, tunda kusan a dunkule suke maganar. Mikewa yayi don ya fahimci a al'amarin duniyar nan matukar maganar Turaki ne tow dattijon Mahaifinsu baya sauraren kowa kuma baya fahimtar kome idan har da a furta sunan Turaki a gabanshi ko a gefensa." """Baffa zan leka kamfani.""" "Kallonshi Hajiya Dadda tayi ta ce mishi. ""Saurin me kike yi da ba zaki zauna ta gama magana ba? Ban" "san me yake ciwon ranki idan kika zo ki ka ga ana magana akan Turaki sai ki tsirfo da wani hali."" Daga haka bata kara magana ba, ta dauke kamata kamar ba ita tayi maganar ba, kunya ce ta sa shi komawa ya zauna. Burinsa ya fita waje ya jira Ubaid yaji wani abu suke shiryawa. Bai gama wannan nazarin ba sai ga Alhaji Mujitafa, wanda suke kiranshi Auta. Cikin girmamawa ya gaida Iyayen nasu sannan ya kalli Ubaida ya ce mishi. ""Second love, kai ne da sassafen nan?"" Gyada kai yayi yana murmushi ya ce mishi. ""Uncle Auta barka dai."" ""Barka second love, ina wancan Introvert din ya shiga ne? Na kira bai dauka ba."" Kunshe dariya Ubaid yayi yana kallon Uncle Auta da yake ™ara duba wayarshi. ""Duba ai ba zai gaza turo maka sako ba!"" Dubawa yayi yaga sakon. ""Sorry im busy!"" Tsaki yayi ya ce musu. ""Baffa na gaji da halin Turaki."" Make shi Hajiya Dadda tayi cikin wannan rikitaccen hausar nan nata me juya mace namiji , namiji mace ta ce mishi. ""Kin ci gidanku, mara kunya in gaji da halinta, wani hali ne da ita banda halin kwarai, ita yaron nan Turaki mutumin kirki ce, kowa yasan tana da kirki amma bakin halin zeenatu da yayiwa Turaki sharri, ina da tana nan da nata iyalin, wai yaron dan uwanku kenan kuka juya mata baya ke Auta da nake gani a mutumin kirki amma kike cewa kin gaji da halinta. "" Matsawa can yayi yana jin zafin yatsun hannunta. "" Daddah kece kika bawa Turaki dama yayi yadda yake so, Fisabiilillahi me ya nima ya rasa. "" "" Abubuwa dayawa. "" Inji Alhaji ELYakub Kumo ya fada ya ce mishi. "" At teenage ya rasa Uwa da Kannensa, sai Jasminah itama don ba yadda ta iya da shi ne, tunda su biyu suka rage, tunda ta zama yar amshin shatar zeenatu, koda yake uwarta ce ba yadda ta iya amma a gefe guda ina ganin laifinka ne, Mudansir. "" "" Baffa ni kuma?"" Ya nuna kanshi da muryanshi a shake, "" Eh kai;"" shigowa wasu matan alfarma suka yi tare da wani shima babba a cikin gidan. "" Daddy! "" Ta kira sunansa. Kallonta yayi yana mai mika mata hannu ta zauna a kusa da shi, tana kallon Alhaji ELYakub Kumo ta ce mishi. ""Baffa ina kwana?"" "" Lafiya lau Fadima."" ""Barka da safiya Kawu?"" "" Barka dai Munir!"" Shigowar wata hamshiyar mace parlourn cikin wani uban ado kamar zata biki da daya daga cikin yan matan nan da suka je salon, nunawa yarinayr wurin zama daya yarinyar tayi. "" Badar ga wuri! "" Wani yatsina fuska tayi, tana kallon" gefen da mahaifiyarta ta zauna. Itama nan ta zauna. "Kallon zuri'arshi yayi babu bare a cikinsu dukkansu ahalin Kumo ne, kuma masu hannun jari a" "kamfanin KUMO properties nigeria agency, kamfani ce fa take sayan duk wani kadara da gwamnati zata" "yi gwanjonsa, kamfani ne da banku suke binta, ba iya nan ba akwai wasu iyalan nan, domin kuwa lissafin a bayyane take." Su waye KUMO properties nigeria agency? "Alhaji ELYakub Kumo, dan asalin Gombe ne da ya fito daga garin kumo, ba fulatani ne da ya gaji arziki" "daga iyaye da kakanni domin su ke da sarautar Sarkin Fulani Kumo anan lagos sarautar ce da ita ta Sarkin Fulanin lagos., dogaye ne masu matsakaicin jiki yayinda matan cikinsu suka kasance sirara iyayen suka" kasance yan chubbys. "Alhaji ELYakub yana mata daya Hajiya Fadime, wacce suke kiranta da Daddah. Ita ta haifi Yara shida" maza uku mata uku. "Marigayi Alhaji Haris shi ya fara bada shawarar kafa kamfanin KUMO properties nigeria agency, amma" "har yanzu sana'arsu ta gado sayar da shanu da madara basu fada ba domin bude wani kamfani aka yi na sayar da madarar shanu da namar shanu. Kasancewar Alhaji ELYakub da girmansa ya fada harkan boko, domin lokacin da ya auri Dadda bai gama secondry School ba, tun yana Yaro dan shekaru goma sha uku yake kad'a shanu daga Gombe to lagos, a cikin gwangwaro. Haka yasa wani bayarabe ya bashi shawara ya fara karatu domin Allah ya mishi baiwar iya sarrafa kudi, gashi tun yana wannan shekarun turanci ya" zauna akan harshensa. "Kusan fulanin zamanin da akwai zuciya haka yasa yana dawowa ya fara makaranta, shekara daya yayi" "a primary ya tafi secondry School, yana da shekaru ashirin cib ya gama secondry School, a wannan shekarar aka auren mishi yar baffansa Daddah. Zamansu yayi albarka domin kuwa kuwa an haifi Harisu" "wanda shine Babba,sai Mudansir, Khaulatu, Sameerah, sai Ramatu kafin Uncle Auta wato Mujitafa." "Kamar yadda suke su shidan haka kowane a wurin halinsa daban, Alhaji ELYakub ya gina kansa da" "matsayin da yake ta hanyar sana'ar sayar da shanu daga Gombe zuwa Lagos, kafin wani abu ya faru a gabansa, wani mutum ne ake bi bashin banki, su kuma banki suka zo kwace kadarorin mutumin lokacin duniya tana kwance, a take suka fara kwashe kayan sanin cewa suna tare da bayaraben for while sai ya tambayi kudin da ake bin mutum banki ta fada mishi, cikin ikon Allah sai ya gwada biya, tare da maida wa mutumin kayanshi idan Allah ya hore mishi ya biya shi. Shi dai da farko bai dauki haka a matsayin" wani babban al'amari ba. Bayan an bashi shawarar ya dawo Lagos da zama ai zai fi yana sakawa ana kawo mishi dabbobin "daga arewa, ace duk bayan sati biyu yana hanyar Lagos, a lokacin ya haWa degree dinsa na daya zuwa na" "biyu, ga shi idan ya ce yana da iyali ™aryata shi ake domin a lokacin ya cika shekaru talatin a duniya, haka" "ya nime gida a alaba rago, ya kawo Daddah da Yaranta, dama can ko a Gombe Yaran suna karatu domin" "Daddah tana haihuwar kunika ne, yaran kusan kansu daya idan ka cire Harisu da ya fi su tsawo, tunda" "suka dawo Lagos sai rayuwarsu ta kara inganta, idan aka samu jajjirtaccen namiji akan ilimin Yaransa, tow bakiWaya dauke kome yake yi, haka Alhaji ELYakub ya kasance, ya tsayawa Yaransa musamman harisu da ya kasance mai zuciyar neman na kai, domin shi ya fara bada shawarar Daddah ta fara sayar da fura da nono lokacin bai wuce shekarun sha biyar a duniya ba, da ya gama secondry yana jami'a shi ya fara gayawa Mahaifinsu madadin kudin da yake biyawa mutanen da suka shiga matsala da banki yayi Register da lasin domin ya fara sayan kadarorin mutane, idan ka biya kudinsu ka dauki kayanka, a yanzu an cigaba, shi anan kasar turawa da yake karatu haka suke yi, domin shi a can Rasha ta tafi karatunsa bayanshi babu wnada ya samu wannan damar domin sun dauki irin rayuwar karya da son a san su din wasu ne, Uncle Auta ne kaWai yayi karatu har zuwa Nijar, da yake shi din na. Musamman ne, Allah ya haWa jininsa da dan uwansa Harisu, Haris yana da abokai guda biyu, Jibrin Mahaifin Ubaid, sai Abbas, abokai uku nan sun taso cike da kaunar juna da adalci idan ka cire Uncle Auta a cikinsu wnada ya" kasance Yaro ne. "Jibrin Mahaifin Ubaid, dan Kanwar Alhaji ELYakub ne, ya dauko shi ya kawo shi gidansa tun suna Yara," "shi kuma Abbas dan abokin Alhaji ELYakub ne, mahaifinsa ya rasu Maraya ne, wanda dangin mahaifinsa suka kwashe dukiyarsa suka watsar da shi. Haka Alhaji ELYakub ya haWa su da nashi." "Lokacin da suka dawo gidan ba karamin wulakanci suke sha da Mudansir ba, domin kiri-kiri yake nuna" "musu sun zo cin arzikinsu ne, Jibrin yana da zuciya sosai haka yasa ya daina zama a gidan, don yana jami'ar Lagos a can yake karatu yake zaune sai weekend da yake shigowa, Abbas dai yake nanike Mudansir idan Harisu baya nan, domin yana da bala'in kwadayi da son abin duniya." "Lokacin da Harisu ya dawo sai gashi tare da wata yar kasar habasha, amma haifaffiyar kasar rasha, mai" "suna Annah. Kasancewar Alhaji ELYakub bai hana kowa yadda yake so ba, haka ya amince da abinda dansa yake so, amma da sharadin idan ya gama ya samu lokaci zai aura mishi yar dangi, bai ki ba shima Harisu ya gayawa Annah tana sonshi, haka yasa ta amince, Ubanta mai kudin gaske ne a rasha da Habasha, don kusan da yardan Iyayenta suka tawo gani take idan Harisu ya dawo ba zai tab'a aurenta ba, Annah ba fara bace asalin kalar fatarta na an Ethiopia ne, shi harisu ne ma Faris sosai domin shi ya dauko fatar Daddah don ita farin fatarta har wani jajja ya™e. Irin tarban da suka yi Annah yasa abin ya bawa yan uwan Harisu haushi, amma Jibirn ya goya mishi baya, satin su biyu suka tafi har can rasha aka basu auren Annah, sai dai tunda aka yi Auren yan uwansa suka tsangwami Annah saboda ita bata sallah, haka yana basu haushi bayan sun manta cewa Addini ya bawa maza musulmai damar auren auren Ahalul kitab." "Wani ikon Allah annah tana shigowa sai ciki, wannan cikin ya saka mata kwadayin abubuwa musamman fura da nono, sai tuwon dawa, wanda kusan abincin Alhaji ELYakub ne, haka suka hadu suka yi renon" "cikin har ta haifi danta, namiji Masha Allah." "Lokacin da sako ya isawa danginta, sun zo domin farin ciki. Ranar suna ta ce ta bar addininta na" "Kirista ta koma addinin Muslunci, yaro ya ci suna Bilal wanda Jibirin ya ci Turaki domin a lokacin sunan yaron aka kara bunkasa kamfanin KUMO properties nigeria agency, aka kara fadadda shi, a lokacin Jarin Alhaji ELYakub yayi kasa, sai da Annah wacce sunanta ya koma Nana Aishatu, ta tafi har rasha ta nimo kudi, a wurin mahaifinta iya mata uku ya haifa. Annah Aisha ita ce Babba haka yasa da tazo da bukatarta basu hanata ba, ita ce mutum na farko da ta fara saka hannun jari a Kamfanin, kafin Bilal ya cika shekara" biyu a duniya Kamfanin KUMO properties nigeria agency yayi wani irin bun™asa. "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 23" "Irin bun™asa da ba a tab'a kawowa ba, kasancewar ko a can rasha ita take ji da kamfanin mahaifinta, sai" "Harisu ya ce a bata wani bangare na kasuwanci a kamfanin yadda zata iya jagoranta, duk abinda zai yi sai ya fara da iyayensu sannan ya kawowa abokinsa Jibrin shi yake bashi shawara. Rike kamfanin da Annah A'ishah tayi ya kai kamfanin wata irin matakin nasara, a lokacin ta samu cikinta na biyu, tana kuma jagorantar kamfanin, kafin ta haihu bankin First suka fara kulla Yarjejeniyar kasuwanci, wnada idan aka samu matsala na bashi su zasu fara tuntuba, domin babu kamfanin a kasar nan sai su ne suka fara jagorantar shi. Shekarar Turaki biyu da wata goma aka haifa mishi Yakub wanda suka kiranshi da Baffa," wani irin kaunar Yaran suke kamar su boye su. "Daddah kuwa soyayyar duniya ta daurawa Turaki, sonshi take kusan tun yaye ta rike musu da taki" "basu. Sai a lokacin Mudansir ya koma makaranta, suma matan da suka fara maganar karatu Alhaji ELYakub ya ce sai dai su yi aikin mazansu. Khaulatu dama suna soyayya da Abbas, Sameerah kuma tana tare da wani dan Kano da yake nan Lagos, ELYakub yaso Jibrin ya auri Ramatu amma yaki domin ya riga Harisu aure, matar ce dai take Gombe, itama tana da Yaro Ubaid wanda kusan wata uku ne tsakaninsu" da Bilal Turaki. "Ita Khaulatu tana cikin wani gidan da Alhaji ELYakub ya basu ita da Abbas, haka tayi ta fama itama" "dai ta koma boko damuwarsu shine matsayin da Aisha da harisu suke kai su samu, sai dai irin wannan matsayin ana samun shi ne ta hanyar da ta halatta, haka suka sakawa ransu kyashi da hassada, wanda yasa suka kasa gaba suka kasa baya. Abin haka yayi ta tafiya har zuwa da ta yaye me sunan Baffa, sai ga wani cikin. Murna a wurin harisu da su Daddah abin ya wuce sanin kowa, haka aka haifi wannan karon namiji, a take yayiwa Yaron huduba da Jibrin suna kiranshi Aydin, bayan wannan Yaron bata kara haihuwa ba, sai bayan shekaru goma, ta haifi Fadime. A lokacin KUMO properties nigeria agency ya kai matakin da sai da aka bude mishi branch a Kano Fatakwal da Abuja. Annah Aisha itace bakiWaya CEO na kamfanin yayinda Haris yake vice President na kamfanin wanda ya janyo idanun yan uwansa ya tsaya" akansu. "Kusan rabin dukiyar kamfanin 65% na Annah da Yaranta ne, 5% na masu saka hannun jari ne, 20% Na" "ELYakub ne 10% na Harisu. Annah bata yi duhun kai ba duk yaran ta raba musu hannun jarin musamman Bilal Turaki, wanda ta bashi 25% na hannun jarin. Saboda shi yana karatu a King Abdul Aziz International school Riyad tare da Ubaidullah Jibrin Kumo, haka yasa bai wani san damuwa ko tashin hankali ba, yana aji biyar na secondry School, bayan sun kawo mishi ziyara, Allah ya musu rasuwa bakiWayansu Ita Annah Aisha da Kannensa. Kuma ba a gaya mishi har sai da ya gama karatu suka dawo gida aka gaya mishi a lokacin ya zo ya samu Mahaifinsa da wata mace ba Mommy dinsa ba, kamar yayi hauka don yaji ya tsani. Haka yasa shi yayi fushi ya koma wurin kakaninsa, har izuwa lokacin Ubaidullah bai rabu da shi ba, domin da zai koma Rasha tare suka tafi a can suka cigaba da karatunsu, kaf duniya babu wnada ya fahimci Bilal Turaki sama da Ubaid, yasan halinsa yasan shi sama da sanin da zaka yiwa wani a duniya. A lokacin da Annah Aisha zata rasu a cikin kwanakin ta haWa kan hannun jarin bakiWaya ta tattarawa Bilal Turaki, domin tana jin wani strange abu yana bibiyarta, haka yasa ta haWa kome ta tura Rasha wurin iyayenta da yan uwanta. Bayan haka Haris da ya auri Zeenatu itama tana zuwa ta samu cikin Jasminah a burinta namiji zata kara haifa sai aka yi rashin dace ta haifi Jasminah, wacce suka daurawa jigon 20% na hannun jarin Haris zai bar mata. Shi kuma kamar wanda aka gaya mishi ya raba hannun jarin ya sakawa Ubaidullah 5%. Bilal 5% Hajiya Zeenatu da yarta 10% sai abin ya fisgi hankalinta akan me za a karawa Bilal a kuma bawa Ubaidullah da bai zama kome a cikin KUMO FAMILY GROUP ba. Shi kuwa ya ce ya" yanke. Tsakanin Alhaji Haris da Annah Aisha shekaru shida chib wanda ya tilastawa Bilal Turaki dawowa "Nigeria, shi kan Ubaidullah ya jima da dawowa gida domin har yayi aure da zuri'arshi. A lokacin rasuwar Mahaifinsa ne ya zo gobe tun suna Yara sukan zo bikin sallah karamar Sallah da babbar sallah. Haka sai yasa Kumo Family group matan suka saka buri akan magajin KUMO properties nigeria agency, domin ya haWa degree dinsa na farko yana da shekaru ashirin cib a duniya. Wannan rashin da yayi duk da yana jin zafin mahaifinsa, ya kara pushing dinsa gefe ya saka shi kara zama wani irin mutum me murdaden hali." "Da manya da yara na Kumo Family group kowa shakkarsa yake, bayan gefe guda gasa suke da juna." "A lokacin abinda Alhaji ELYakub yayi shine bawa Bilal Turaki kujeran mahaifiyarsa, kasancewar ita" "ce mafi yawan hannun jari wanda a yanzu Bilal yana da kashi 70% na hannun jarin KUMO properties nigeria agency, sai dai haka kawai ya juya ya koma inda ya fito, ya cigaba da karatunsa. Bai kara dawowa Nijeriya ba sai rasuwar Alhaji Jibirin Kumo,. A lokacin yana da shekaru talatin da wani abu a duniya, akwai ciwon da yaji da yasa shi tattarawa ya koma Germany wurin Ellina, Kanwar Annah Aisha, tana" "auren wani magajin garin Berlin, anan ya cigaba da aiki da babban Cibiyar nukiliya ta Germany." "Yan mata dayawa sun yi kuka akan Bilal Turaki, amma shi ko a kwalarsa. Bai damu da kowa ba a" "duniya sai mutane hudu, Alhaji ELYakub, Daddah, Uncle Auta da Ubaid, haka a wurin kakaninsa na Uwa" "yana sonsu. Turaki mutum ne da baya shiga rayuwar kowa, baya kuma da rawan kai irin na yaran masu kuWi, duk da gadon da yake da shi Bilal niman kudi yake kamar ba attajirin da aka tara mishi ba, an taSa" hira da shi. Aka tambaye shi me yasa yake niman kudi bayan yana cikin manyan matasan Nigeria masu "arziki, budar bakinsa ya a cikin muryansa mai sanyi da dadin amo, ya ce musu. ""Wancan dukiyar ba Bilal yayi faffutukar tarawa ba, dukiya ce da mutane uku suka tara idan nayi amfani da shi akan kaina na zama cima zaune idan na nima da kaina zan iya rike kaina da kuma duk wnada zai zauna a gefena."" Idan bilal" yayi magana mai tsawo haka yana nufin yana son maganar ce. "Kai ko a cikin abokai ne yana iya ware kansa, ya koma gefe yana abinda yaga zai iya. Yana iya daukar" "nauyin abokansa ayi shagali amma shi zaka hango shi can gefe yana wani aiki abinsa. Idan kana son ganin asalin Introvert tow Bilal ne, domin ko lokacin da ya fara soyayya Ubaid da Alhaji ELYakub suka sani, haka da yarinyar tayi rejected dinsa, sune suka san me ya faru. Da abin ya faru sai da yayi kusan kwanaki uku kafin ya tattara ya bar musu kasansu. A lokacin Alhaji ELYakub yaso ya je har wurin dangin Yarinyar ya nuna musu jikanshi ba talaka ba ne, amma ya ce mishi.. ""Ni mace nake so da zata so ni ba" "tare da tasan who am I, kada ka je ina ji a jikina ita din mahadar rayuwata ce.""" "Duk da yan matan da suke hauka da fada da dambe akanshi, haka bai taSa burge shi ko jin a ransa suna" kan daidai ko sau daya basa gabanshi. "Hajiya Khaulatu tana da Yara biyu, Khamis da Khamis baya jin magana, niman mata shaye-shaye, fadar" "area ta dabba. Duk wani iskanci ya kare a gindin Khamis sai yar su ta biyu Badar tare da Alhaji Abbas, wacce take zaman jiran Bilal, don tace sai dai ta mutu bata yi aure ba. Mimi yar wurin Hajiya Zeenatu tsohuwar matar Haris, bayan rasuwarsa aka hada auren da Alhaji Mudansir ELYakub, bayan Jasminah ta haifi Mimi Fatimah, ita bata damu da wani soyayya ba, don ita ce asalin Queen of Kumo Family, ana ji da ita. Zaheeda, yar gidan Hajiya Samirah itama tana son Bilal, don ita har inda yake ta je mishi. Badar kuwa" a gidansa da yake Lekki take zaune. "Sai Nasmat wacce take nan lagos a gidan Uncle Auta, shima Uncle Auta da yake da Iyali Yaranshi" "maza hudu ne, kuma kanana ne, Yakub wanda suke kiranshi da Amir, sai Harisu wanda suke kiranshi da Akhi, sai Jibrin wanda suke kira da Aalim. Kaf duniya daga Ubaid sai Uncle Auta suka san meye Turaki yake so, me yake bukata ja'iri bai da alkibla, akwai wani zuwan da Turaki yayi lokacin Alhaji ELYakub bai da lafiya an dauka mutuwa ma zai yi aka gaya mishi, zuwan da yayi ya tashi wani tashin hankalin da ba taba gani ba, domin ya zo gidan duk babu kowa a gidan domin bai gaya musu yana hanya ba, a lokacin da ya iso gidan domin drop ya dauka har gida, da farko security din basu gane shi ba, domin shigar da yayi sai da ya cire facemask dinsa suka gane shi ne, haka ya shiga gidan akwai wata yar mota da take kai mutane har cikin gidan, ita ya shiga aka kawo shi, zuwan da yayi ya shiga bangaren Daddah anan ya samu Mimi tana yiwa Daddah barna, shi kuwa ya kamata ya zane ta, karshe ya rufe part din Daddah ya" "tawo asibitin, ana ta murnan ganinsa sai ga kira daga gidan, aka kira Hajiya Zeenatu tana isa gidan ta ga" "abinda yayiwa Yarta, ai kuwa ta kawo yarinyar, jin haushi da kishin yadda aka wani zagaye shi ta saka" "hannu a kai tana kuka wai yayiwa Yarta fyade. Wannan abin ya daki Turaki. Kiri-kiri Badar tace mata. ""Karya kike Maman Mimi!"" Da yake yaran a sangarce suke ba wanda ya kwabe ta." "Case Win sai da aka hura shi ya zama babban al'amari, hankalinsu ya kwanta Alhaji ELYakub yana ji yace" "su bar mishi gidansa, bai lalata na wasu ba, zuriarsa ba zasu lalata nasu ba. A lokacin Turaki yayi fushi ya bar musu kasar, suna son ya dawo ko don yanzu a raba matsayi a kamfanin KUMO properties nigeria agency, amma yaki dawowa, yaki yin wani motsi su kansu basu san inda yake ba, idan ka cire Uncle Auta" "da Ubaid, babu wanda zai baka labarin inda Turaki ya™e." "Ita kuwa Daddah cewa take aljanun sun aure mata jika domin yaki maganar aure, ko irin kiranshi Uncle" "Auta yayi haka zata gama surutunta baya ce mata cikanki, har mamaki yake yadda bai damu da magana ba, sam shi magana tafi kome bashi wahala. Don da yayi magana gara ya shiga daki ya kwana ya wuni. Shi har mamaki yake idan ya ga mutane na magana, idan da zai yi magana tow abun da zai magana a kai" me muhimmanci ne. *** Lulu. "Na samu wata biyu, ina zuwa wurin Mrs Dije Bala, sannan gefe daya ya haWa min wani tables na abincin" "da nake ci, domin maganin da haifi yake bani sun yi sanadin da kitse da uric acid ya taru min, haka yasa nake samun wani irin gajiya. A hankali nake bin kome, kullum haka zan tafi wurinta na dawo. Ya Hafiz" "yaso kashe ni ne, Allah bai nufa ba." "A hankali na dan fara samun nutsuwa, ina cika wata uku na gama iddana, a lokacin naji kamar na" "samu yanci, har da wannan iddar ya saka min traumatic domin gani nake kamar Ya Hafiz zai iya cewa ya dawo da ni, a wurin da nake zuwa akwai Reheb, a nan idan na je naji matsalar wasu ashe ni nawa mai sauki ne, domin gashi wasu yaran masu kuWi ne wasu matan masu kuWi amma rayuwarsu ta lalace, akwai wata yarinyar da muka hadu sunanta Baby Mahaifiyarta yar Jos ce, mahaifinta kuma bayarabe amma gata yasa ta lalace, sai gashi ta samu miji shi ya kawo ta wurin Dr Dijah Bala, yarinyar tana da saurin sabo," "duk yadda naso na ki biye mata, haka take makale min." "A bangaren Ya Ado abokan aikinsa har mutum uku suna niman izinin aurena, ce musu yayi su yi hakuri" har yanzu Lubnah she still small girl... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 24" "Wannan kalaman ya saka aka shafa min lafiya, tabbas ina bukatar spaces sosai Ina bukatar nutsuwa" "wanda zai saka naji nima mutum ce kamar kowa, ina bukatar farin ciki da nutswa amma ta ya? Ta hanyar bani duk wani tazara da zata saka ni farin ciki, a hankali rayuwata ta mike, har watan azumi ya zo farkon watan azumin Ya Ado ya mana albishir da zuwa Umara a can zamu yi sallah, Yadiko Abba ya biya mata da ita da shi, Mama kuma Ya Ado ya hada mu ita xata tashi ta Bauchi, mu kuma ta lagos, wani abu da ya kara d'aga min hankali wannan kibar yana damuwa duk yadda nake son rage shi kamar kara shi nake, haka yasa Doctor Ahmad ya hada ni da wani likita anan lagos a cikin wata azumin kafin mu tafi Umara, lokacin da na ga likitan, ya sake tsara min abinci sannan ya hana ni shan kowani magani da zai saka ni nayi slimming domin na fara shan wasu ganyen shayi, ya hana ni. Kamar da wasa na fara shan kiyayye maganin da yanayin, sai dai kuma ko ana gobe zamu Umara, sai da ciwon ciki ya taso min, haka nayi ta daurewa har muka tafi umara a can kuwa kasa mai tsarkin na fadi na suma haka aka tafi da ni asibiti hankali a tashe, lokacin da aka min test anan aka hango cutar fabroid a cikin mahaifana manya guda biyu sune suka hura min tumbina, suka ce aiki nake bukata, Ya ado yace su bani magani da abinda zasu bani kawai mu koma gida ayi min domin bai zo da shirin aikin ba. Lokacin da ya samu Mama da yadda suka yi da likitan, ta ce mishi. ""Wani ba a shirya ba kuma? Kawai mata aikin na hakura guzurin yanzu akwai abinda za a bukata a rayuwar lubnah nace babu shi? Ayi aikin Allah ya bata lafiya kowa rai ya amfana" "baya ga mai shi ne, ni yanzu bata kaina nake ji ba, ta ita nake ji""" Haka aka yi min aiki a washi gari ranar da aka kai azumi ashirin da uku. An cire tare da kashe waWanda "suka fara zuba karin, sannan aka fito da ni. Yayuna a Bauchi kamar su tawo, don sun tabbatar zasu zo Lagos ganina. Sai nake jin kamar ni daya nafi kowa gata, daren ashirin da uku ake ta saka ran alamun laylatu kadr, yadda ake pretending din yanayin sai bai kasance a wannan daren ba, aka wuce zuwa daren 27, wanda tun wunin ranar Mama da take kula da ni take addu'a nima kuwa Addua nake, karshe Mama kasa hakuri tayi ta saka aka bamu keken mara lafiya muka wuce harami, ranar na ga gundarin kauna a wurin mahaifiyata, mantawa da kanta tayi tana zagaya da ni Ka'aba tana ""Allah ga Lubabatuna, Allah ka bata duk abinda ta rasa a baya, Ya Allah ka bata miji na gari. "" Sai da naji kamar buga min guduma tayi domin gabana ne ya fadi. Tsoron maza ya kara shiga zuciyata. Haka take addu'a miji na gari har wasu yan Nigeria da Nijar suka yi ta mara dariya, wai tana ta addu'a kamar ita Waya ta haifa murmushi take kawai ta ce musu, da kun san irin Izayar da na mata zaku ce ta cancanci haka. Wannan ranar Mama bata mai" "da ni asibiti na har aka Sha ruwa, ta mai da ni, sannan ta dawo harami yin sallah tahajju." "Asibitin kuwa ana tasowa sai ga Yadiko da su Ya Ado, da Yaran da Aunty Zakiyah, ai kuwa na ji dadi" "murmushi nake idan suna hira, haka suka yi sahur bayan sun gama suka tafi masallaci, nima a nan nayi sallah bayan sun dawo, Mama ta koma ma sauki ni kuma aka barni Asibitin. Ai kuwa Yadiko suka yi fada da Abba ya ce ta nime abokin tafiyarta ta ce mishi.. ""da yake makauniya ka kawo ba."" Rigima fa wai akan me tazo duba ni, haka ta fada mana da tazo ni dai umarana ta bana a gadon asibiti nayi shi, ranar ya" "kasance juma'a, don haka nima an fitar da ni domin ita ce Juma'a ta karshe, ranar Litinin ake saka ran" "karamar sallah, haka yasa aka fitar da ni. Nayi addu'a Ubangiji ya kawo min nutsuwa da kwanciyar" "hankali, Ubangiji ya bani kwarin gwiwa, Ubangiji ya cire min tsoron wani abokin halitta a raina, na roki Allah ya mantar da ni rayuwar baya. Ya saka min hakuri da dangana." "Ganina a dakin Ka'aba ya saka min yarda da cewa Ubangiji yana nan yana jina, shi din rayayyen nan ne" "da baya mutuwa, bai haifa ba, ba haife shi ba. Sai nayi kukan farin ciki ya saukar min wani nutsuwa na musamman. Naji nauyi da zafin da nake ji yana sauka a raina, na ji farin ciki da rabona da naji shi tun ina JIBWIS, a ranar Mama sai da suka yi magana da su Aunty Zakiyah wai sun ga kamar ba ni, haka muka yi ta ibada, har ranar sallah. Wayyo yadda kowa yayi wanka sallah amma ni ba hali saboda dinkina. Haka na saka abaya mai sauki. Sallah da kwana biyar muka dawo gida, haka na cigaba da jinya satin mu daya da zuwa dai ga Aunty Hindatu da Aunty Innah, Aunty Munah da Aunty Raliyah, wato wani abu da na kara fahimta shine yadda suke yiwa Aunty Zakiyah shatara na arziki, ban yi mamaki ba domin basu isa biyanta Alkhairin da take min, bamu isa biyanta biyan ba, Dr Dijah Bala da Baby sun zo min ya jiki, haka Aunty Zakiyah ta cire musu tsaraban da ta musu. Tace musu nice nayi musu sai nayi ta mamaki, wani ikon" Allah satinsu Aunty Hindatu daya suka koma. "Wata na biyu goshin layya ina jin duk wanda ya ganni sai ya ji na burge shi, domin jikina ya ragu, a" "lokacin da Ya Ado yake basu labarin jinyar da nake fama da shi, Aunty Munah sai da tayi ta Bala'i ita sai ta shigar da Hafiz kotu, aka ce a kyale shi tunda na samu sauki yanzu ai da sauki sosai sai a tafi gaba." "Haka yasa suka tsayar da shawarar ko zan koma makaranta, nima zaman gidan ya dame ni. Don haka na ce tow, na amince da shawararsu na koma jami'a a karo na biyu. Zanyi MBA wato Master Business Administration and specialization, a tsarin tallace-tallace, Ya Ado. Kullum tambayata yake. ""Lulu zaki iya kuwa? Idan kin san har yanzu akwai abinda yake damunki a hakura da shi, kin ga saboda result Winki yayi kyau sun baki shekara biyu da wata shida, idan kina ganin akwai matsala a hakura."" Yadda Ya Ado ya saka hope a kaina sai naji kamar idan nace mishi ban warke ba ban yi mishi adalci ba. Haka na ce zan iya amma har yau ina tsoron shiga Mutane, ya zanyi tow? Zan tabbata ina zaman gida ne, haka na daure sabon shekara na shiga cikin daliban da aka diba, na kwantar da hankalina, a yanayin acadamy calendar dinmu ba zan wuce shekara daya da wata tara zan gama. Haka yasa na nutswa, daga yanayin shigar da nake yasa an Makarantar suka fahimci na fito daga arewa ce, sannan yanayin fuskata, kuwa face mask nake sakawa saboda har yanzu fuskata kamar an buga donut, haka nayi ta rayuwa da tare da mai da" hankali kamar ina yi da wani. Yadda an ajin mu suke mamakin domin kusan nice karama amma yadda nake mukekiya sai ka "dauka na shekara arba'in, a hankali na fara fuskantar body a shame, haka yasa na fara tsargu. Wani lokaci a tsorace nake shiga ajin. Sai ta min dariya ko tsokanata wani lokaci sai naji ana faWin luxury, ko naji ana faWin super Mama, haka yasa na fara jin wani irin yanayi ya fara shigata. Ban san me yasa nake jin wani irin damuwa ba, duk yadda naso na kauda kai amma na kasa sai tsoron da nake binnewa ya fara" "tasowa. Haka muka yi huta First semester din mu," "Haka muka yi hutun sati sati biyu da kwana hudu, zai kama Monday mai kamawa." *** "Yau ya kasance Lahad, ana gobe zamu koma makaranta. Ina ta Wan hada kayan makaranta na nutsu naji" "wayata tai kara, dauka nayi a hankali. Na saka a kunnena. ""RuSaSiyar tsutsa mara haihuwa!"" Ji nayi gabana yayi mugun bugawa a ina Ya Hafiz ya samu numberta yadda yayi ta gaza min magana har sai da naji kaina ya fara sarawa, hawaye ya fara zuba min kamar zan mutu kuma ya rantse min idan na sake na kashe wayata abinda zai min sai na rasa inda zan cusa kaina. Haka ya gama cin mutuncina sannan ya gaya min ko mutuwa nayi a gidansa za a min sutura, kafin ya kashe wayar, wurgi nayi da wayar yadda ya tsorata ni na ji wani irin tsoro ya kama ni. Dakyar nayi barci cike da tsoro wanda ya haifar min da mugun" mafarki da rashin hankali. "Daidai buguwar agogon bangon dakin wanda ya ja burki da wani ""ki...ki"" cikin barci nake amma sai da" "naji gabana yayi mugun faduwa, bude idanu nayi ina kallon hasken waje tare da bishiyar da take kad'awa, hadari ne ya gangamo amma sai naji kome ya tsaya min, barcin ma na nime shi na rasa, Innalillahi wainnalihir rajoun, yau ya xan yi ni da ya dace na farko tun 4am. Da sauri na sauka a gadon na shiga ban daki nayi wanka da brush, sannan na haWa da alwala, na fito ina jin kamar zuciyata zata fado, saboda tashin hankalin. Ina shafa mai na saka kayana, sannan na gabatar da sallah asuba, lokacin ruwa ake tsugawa kamar da bakin ™warya. Ji nayi kome na kaina ya sake kuncewa wai ma yau ba Monday ba ne koda yake abinda ya faru jiya ne ya d'aga min hankali Ya Hafiz me yake nufi da Ni ne,? na dauki jakata na rataya zuciyata tana wani irin bugawa,, sannan na fito parlourn na samu Ya Ado wanda shima cikin shirinsa na zuwa aiki. ""Ina kwana Ya Ado?"" ""Lafiya lau Lulu kin tashi lafiya!"" Gyada kai nayi na nufi" "kitchen inda Aunty Zakiyah take aiki na ce mata. ""Good Morning Aunty Doctor!"" ""Morning My love, kin tashi lafiya"" ""Alhamdulillahi!"" Ta mika min abincina. Tsayawa nayi ina kallon abincin, ina son na yi mata magana amma kuma ban san yadda zance ba. ""My lovely ya dai?"" ""Wai dama abincin!"" ""Idan ba zaki koshi ba kawo a kara meye amfanin niman da muke?"" Sai naji hawaye yana shirin zubo min, na kalleta a hankali na ce mata. ""Na gode!"" ""Kada ki yi min godiya kuma ki dauke hawayenki domin Barista sai ya kusan cinye nama na danye!"" Murmushi nayi da ya kara fitar da kumatuna waje.""na gode!"" ""Sai ki yi!"" Ta fada tana barin kitchen din, kasa fitowa nayi na zauna a saman kujera tamu ta hausa yar tsugunne, na shiga tura abincin. A hankali nake turawa bakiWaya sai naji taste din abincin ya fita min a kai. A yayinda ™wa™walwata da zuciyata suka hasaso min wani lokaci can irin wannan zaman nayi ina cikin abincin." "Hawaye ne ya shiga zubo min ban san me yasa a duk lokacin da zan tuna wani bangare na rayuwata nake jin ciwo da zafi ba, kuka ne ya kwace min,.na ajiye abincin ina mai toshe bakina, na nufi pampo ina shan ruwa. Kalaman da aka fada a can baya yau jin shi nake kamar yanzu ake fada min. *Rubabbiyayyar tsutsa mara amfani, ke ba haihuwa ba sai kayan tsoka kamar tsutsa. Aikin kenan ga baki ga ci darling kama take da irin tsutsan da suke cikin kashi!* Amai ne ya zo min sakamakon kwarewa da nayi da ruwa, nayi ta tari" "wanda yayi sanadin shigowarsu dakin. ""Lubnah lafiya?"" Kasancewar idanuna yayi jajjur sai kukan da nayi" "ya tafi a kan kwarewa nayi. ""Sannu kin kware ko? Kin ma ci abincin kuwa?"" Gyada kai nayi nace mata." """Na ci!"" ""Tow muje parlourn ina ga haka zamu tafi fa!"" ""Abban Naylah bata ci abincin ba wallahi! Bari na mata park dinsa a cikin lunching box ta tafi da shi."" Kallona yayi yaga ina sunkuyar da kai tare da kare" "fuskana, kaina a kasa ina sunsukuyarwa." "Hannunsa ya kai zai tab'a ni, nayi maza na kare kaina daga shi har Aunty Zakiyah suka zuba min idanu." """Ba dukanki zai yi ba!"" Ya fada tana kallona, shi da yake namiji ya kasa jurewa fita yayi yana zaga parlourn. Hannunta itama ta kai na koma jikin bangon kitchen din na makale. ""Ba dukanki zamu yi, Lubnah me yasa kike dawo da abinda ya wuce?"" Wurga-wurga idanuna na fara kamar wacce nayi karya" "ko sata na ce mata. ""Ba haka ba ne,.na zata zai dake ni ne don ban ci abincin ba.""" """Lubnah wani yana threating dinki a makarants ne?"" ""A'a Aunty don Allah kada ki yi da karfi ya dauka ko" "wani abu ake min."" Na fada ina kallonta tare da rike hannunta alamar roko! ""Na ji amma me yasa?"" ""Ba kome!"" Sai ta yi ta kallona da dukkanin zuciyarta take tausayi na. ""Kina da kyau!"" Ta fada shafa kumatuna nayi da suka kasance kamar donout ya sha bugu. Sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa, don nasan hala itama zolayata take. ""Ina jiranku fa!"" Ina ga bai rufe baki ba na rigata fitowa waje, kallona yayi ya ce min. ""Idan kin gama muje. Gyada kai nayi tare da Waukar jakata, na amshi lunching box din na fito ya bude min mota na shiga. Ina kallon kayan wasan Yaran da ruwa yake sauka akansu. Haka muka bar Estate din, ya kunna karatun Alqur'ani a muryan Sheikh Afif, muna tafiya yana bin karatun. Nima a" "hankali nake bi, suratul lukman...." "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 25" """Akwai wani abu ne?"" Ya Ado ya tambaye ni, girgiza kai nayi ina danne damuwar da take fuskata. Tuki" "yake har ya iso makarantarmu, sannan ya juya bayan motar ya dauko lema guda biyu ya mika min daya shi kuma ya dauki daya muka fito tare, har cikin makarantar ya raka ni wurin department dinmu, daga nan ya wuce office din HOD, ban san me ya faru ba, sai dai bayan tafiyarshi, HOD dinmu ya shigo yayi magana sosai sannan ya kara da cewa. ""Cin mutunci ko cin zarafi abu ne da ba a yarda da shi, idan kana ganin zaka yi tow kayi a wajen makarantar nan, daya daga cikin manyan lauyoyin jahar nan yayi dokaciya akan kanwarsa, idan ka sake ko kika sake wani abu ya faru na cin zarafi ku sani abin yana da doka a kundin tsarin mulkin kasar nan, kuma za a hukuntaka daidai da laifinka ko a yanke maka hukuncin zaman gidan kaso!"" Jin hakan na sha jinin jikina, tabbas Ya ado ne, wannan dokaciyar sai ta sama min yanci duk da naki yarda na saba da kowa domin gani nake zasu cutar da ni, s gefe guda barazanarshi ya kara d'aga min hankali, ko barci nake ya kira ni ban isa d'agawa ba, Ya Hafiz ya hana ni sakat, saboda tsananin tashin hankali sai na fara jin kamar anya na cancanci farin ciki? Domin ya Hafiz bai da burin ganin nayi" rayuwa cikin sallama. "Wata rana mun fito sallah wurin alola ya kira ni, yadda na dauka na kasa magana dama kuma ba" "maganar nake ba, haka na ajiye wayar a wurin sanadin da aka sace wayar, koda na tafi masallaci nayi sallah na dawo na duba ban ga wayar ba, a hankali na koma aji, koda na koma gida da kaina, Ya Ado ya kira Aunty Zakiyah ta gaya mishi gani nan wayata ce ta fadi ne, da zai dawo sai ya zo min da sabon. Akan" "washi gari zai kai ni a yi min welcome back, kai tsaye na ce mishi. ""A'a bana so, ka barshi kawai idan aka" "tashi zan dawo da kaina."" Na faWa mishi. ""Tow idan ana son magana da ke fa?"" Shiru nayi ban kara" "magana ba, haka ya kyale ni tunda raina baya son wayar, kuma Alhamdulillahi kin wayar ya kawo min kwanciyar hankali." "Don nasan Hafiz yana can yana niman wayata. Bai samu ba," *** "Yau asabar babu aiki, Hakazalika kowa yana hutun karshen mako. Hajiya Daddah tana dakinta tana" "tattara Alqur'ani dinta mai falle falle. Badr ta shigo dakin. Zama tayi tana kallon Daddah da tunda ta shigo bata d'ago kai ta kalle ta ba, shiru Badr tayi tana mamakin kakarsu a saninsu Yaran mace ake so da kauna, musamman yadda Mamanta take kula da Daddah, duk ana yin haka ne don a samu kyakkyawar alaka mai karfi, amma Daddah ko kallo basu ishe ta ba, a hankali ta ce mata. ""Ina kwana Daddah!"" Yadda kasan da dutse take magana Daddah bata d'ago kai ta mata magana, haka kuma bata amsa mata ba." "Hannu ta kai tsabar reni irin nata zata tab'a jakar Alqur'anin Daddah ta daka mata tsawa. ""Kul na ka taba min kayana, bana son reni da rashin kunya irin naka ni ba abokin wasanka ba ne."" A hankali ta janye hannunta. ""Amma Daddah tun dazun nazo."" ""Assalamualaikum."" Mimih ta rangad'a sallama da muryanta mai sanyi, ""Amin waalaikumunsalam."" ""Daddah ina kwana?"" ""Lafiya lau, takwara ka tashi lafiya?"" ""Lafiya lau Daddah, cika Badr tayi tana kallon yadda Daddah take amsawa Mimi. "" Daddah jiya na turawa Hamma Turaki sakonki."" Bata wani damu ba, don tasan waye Turaki tunda kusan saboda ita ya ki zuwa kasar ya yi fushi sosai. ,yadda bata amsa mata ba ta cigaba da cewa. ""Ya bude yace yana kewarki! "" Anan ne ta ce mata, ""Takwara shi karya bai da kyau, ka daina karya Turaki bata amsa wayar kowa daga Ubaid da Auta bayan nan sai kiran Alhaji. "" Tayi haka ne don yadda Badr take ta cika tana batsewa, gyaran murya Alhaji ELYakub yayi yana rike da sandar shi ya ce mata. "" Fadime ga turaki akan waya!"" Ba tare da ta ji nauyi ba, ta mike da sauri ta isa zuwa gare shi, ta amshi wayar tana faWin. "" Alhamdulillahi Turaki kina lafiya? "" Daga can ya ce mata. "" Hmm! "" "" Turaki yaushe zaki dawo gida, ko dai na mutu zaki dawo?"" Kome ya gaya mata ta sake murmushi tana faWin. "" Tow Allah ya baki hakuri, tunda" "bakya son dawowa ki cigaba da zamanki har Allah ya baki damar dawowa.""" "Kusan ita ce take mishi hiran domin bata yi shiru ba sai magana take tana bashi labari, yadda zaka" "fahimci how she miss him, wani irin kewarshi take daga karshe da aka gama wayar sai da ta fashe da kuka, fita tayi ta kai mishi wayar Badr ta watsawa Mimih harara ta ce mata. ""Munafuka waye ya gaya miki bamu san cewa baya kiran kowa kuma ba ya daukar kiran kowa na gidan nan sai mutane uku, ki bar wawantar da kanki. Mun san kome da kike wannan iyayin kin manta idan da kunya ai babu aure a tsakaninku?"" Murmushi tayi Mimih tayi na wani lokaci kafin ta ce mata. ""Eh kin san ni kawai ana iya kallona ne, amma wani abu ai a bude ya™e muna raye cikin haske amma a inuwarmu akwai duhu me matukar hatsari."" Daga haka ta wuce ta barta ita Waya a dakin Daddah, ranta yayi masifar b'aci, haka ta" gama cika ta batse. "Itama barin dakin Daddah tayi tana jin wani daci daci a ranta, a haka suna son juna amma a zahirin" "gaskiya tsanar juna suke akan Turaki. Tana fita dama da motarta ta zo, shiga tayi ta fisge ta da gudu. Tana ji kamar zata tashi sama, haka ta wuce gidansu tana isa ko parking Mai kyau bata yi ba, ta bar motar a bude ta shiga cikin gidan da gudu, Hajiya Khaulatu da Alhaji Abbas suna lissafi ta shigo a guje. ""QueenB ya dai?"" Da gudu ta haura sama, tana kuka. Hankalin uwar ya tashi ta bita sama, ta samu tana ta razga kuka. ""Me aka miki?"" ""Daddah ce ta ki kula ni, amma Mimih tana zuwa ta kulata."" ""Ba na hana ki zuwa gidan Daddah ba?"" ""But Mom taya xan yi ina son Hamma Turaki."" ""Bana ce ki bar kome a hannuna" "ba."" Nan ta zauna tayi ta mata fada da cewa ta nisanta kanta da Daddah ita zata mata fight samun Turaki, amma ita bata isa ba. Haka ta gama Uban yana bakin kofar yana kallonsu cikin murmushi ya ce musu.. ""indai turaki ne zan yi wani abu guda daya da zai saka kowa ya amince."" ""Ko?"" ""Eh kai, ranar Litinin zamu yi azumi kamar yadda Baffa yake yi. Ba zan manta Harisu ya ce idan yana raye zamu hada auratayya a tsakanin Yaranmu. Kuma akan idanun Baffa aka yi Allah ya jikan Harisu. "" Ya fada yana kallon yarshi, domin yanzu ya fahimci duk abinda zai faru, Yayanshi suna sama da kome, shi yasa yake ta kokuwar" bawa Khamis MD na kamfanin domin a karba a hannun Jasminah tunda ba wani abu take tsinanawa a kamfanin. Haka suka gama kitsa mata kome. "BakiWaya wancan satin nayi shi a zirga-zirga, amma yau da muke weekend. Ya Ado ya hana ni barci. Wai" "sai mu shirya mu tafi beach. A kasale na fito na isa parlourn ina sanye da riga da skirt English wear, duk da na ragu sosai amma yanayin fuskata idan ka kalla zaka Wauka fulawa ce ta ji yis. Haka muka fito bakiWaya muka shiga motar, ina baya da su Adil. Sai hira suke min ina amsawa, koda muka isa bakin ruwan yaran wasa suke Adil ya hau doki, mai sunan Mama tana wasa da ruwa idan ya zo da gudu ta dawo wurinmu idan ya tafi ta bishi da gudu, sai dariya muke mata, Allah sarki Princes tsoro ya hanata zuwa inda muke sai tsoro take tana cewa ruwa zai dauke ta, wani irin nishadi da nutsuwa ya shige ni. Wayar Aunty Zakiyah Mama ta kira na Wauka, da yake wayar tana kusa da ni. ""Mama bata kusa ne!"" Da yake ta saka Mamanmu, mamanta kuwa ta saka Maman Dass. ""Ina wayarki nake kira kullum baya shiga?"" ""Hmm ya fadi ne, kuma nace bana son wani."" ""Me yasa tow?"" ""Ya zan yi Mama Ya Hafiz ya samu numbeta sai d'aga min hankali yake Mama kamar zan mutu idan ban dauki wayarsa ba, idan na dauka kuma na ji gara na mutu na huta, shi yasa da wayar ya faWi naji na samu sukuni."" ""Wato Yaron nan don kutumar ubansa bai kyale ki ba? Waye ya bashi number ki? "" "" Ina zan sani Mama!"" Haka muka gama wayar sannan na mikawa Aunty Zakiyah da take jin mu sai kwafa take, tana amsa suka daura tsinewa Ya Hafiz, sai naji wani irin yadda suka tsane shi. Wurin karfe biyar muka bar Beach zuwa gida, daga nan muka baje domin abinci ma oda Ya ado yayi mana. Daren ranar bayan yara sun yi barci Ya Ado ya tsare ni da fada kamar zai dake, bayan ya gama ya kira Baban Jama'are, ya ce ya shiga tsakanina da Ya Hafiz ya daina shiga harkokina, sai dai maganar da Baban Jama'are ya fada ya saka Ya Ado harzuka, wai ai shi aure rai ne da shi idan akwai yiwuwar kara zama sai Allah ya nufa. Wannan abin ya daki ya Ado, tun daga lokacin na ji na shiga tashin hankali mara misaltuwa domin ji nake kamar zan mutu, kusan sai da na samu tsaiko s karatuna, ai kuwa Ya Ado ya zo Bauchi na tsawon kwanaki uku, zan iya cewa koda ya dawo bai ce mana kome ba, amma na ga kwanciyar hankali a tare da shi. Ya Hafiz bai san waye yake rigima da shi" "ba, bai kuma fahimci yadda ake rigima ba, sai dai wannan karon daga shi har yan gidansu sai da suka yi" "danasanin shiga harkata a gaban jama'a Hajiyarsu take cewa. ""Idan har kai dan sunnah ne ba shege ba," "na maka iyaka da Lubabatu idan kuwa na ji ko a mafarki ka sake shiga Rayuwarta sai na maka baki ka lalace."" Shima Abba ya ce ya zare ni cikin Yaranshi kada na tab'a kiran shi a matsayin Mahaifi, idan kuwa na sake na zo kan gawarshi sai Allah ya tsayar da shi yayi mana hisabi. Babu wnada ya gaya min sai Aunty" Innah. Mama kuwa ta yi tsalle ta ce ai dama sai da ya mutu a haka amma har Abada an rabu kenan. "A bangaren Ya Hafiz, abinda yake damunsa gani yake duk abinda yake da samun da yake yayi baya, duk" "da yadda yake gina Karimah da kanshi amma fa baya ganin haske, duk yadda yaso yayi gaba abun ya ci tura. Haka Hajiya Asiya ta dauke shi zuwa wurin Malaminta, ya zana ya goge, ya kuma buga kasa sannan ya ce mishi. ""Yarinyar nan itace daukakarka, ita ce arzikinka, ita ce kome naka. Amma ba zata tab'a dawowa gare ka ba matukar Yayunta da Mahaifiyarsu suna tare da ita. Ka raba su ko ta halin k'ak'a, amma bari na gaya maka daga ita har danginta babu kofar da wani aljani ko sihiri yayi aiki akansu, gara Ubansu zaka iya juya shi don yana tare da kai amma Yarinyar da kafin ta bar Bauchi ne zamu iya mata wani aikin amma yanzu da take can wata duniya ko anyi ba zai same ta ba domin ba ™aramin kasada ba ce kowa yana tsaye a kanta har matar ubanta, kai babu yan ubanci ko kishi da zai wargaza iyayen balle" "Ya'yan. ""Hajiya Asiya ta ce mishi. "" Malam babu wani hanya da zamu zaunar da ita har abada? """ "Sake zane yayi ya jinjina kai ya kara ya jinjina kai, yana karawa ya buga kasa ya ce musu. "" Kai ina" "rayuwarta da ™addaranta yana can sai dai ya san yadda zai yi ya koma can amma akwai duhun da kai ka kirkiro da kanka kuma zai hadiye ka da shi Ubanta, abu daya xan baka shine ka kusanci inda take duk lokacin da kuka hadu ta yi amfani da wannan turaren, ta haka zaka kara rabata da nutsuwarta. Amma" kada ka sake wani ya shiga tsakaninku.......... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 26" """Ga wannan zoben ka saka a hannunka, akwai lokacin da zakai ka gare ta. A ranar ka hadu da ita kada ka" "sake wani ya shiga cikin lamarin ka daidaici lokaci domin sa'arka zata fara idan har bukatar ya biya zoben zata haske idan kuma ka bari tayi baki bukatar ta lalace. Idan kuka hadu ba zata tab'a bijire maka ba, duk abinda kake so da ita zata maka, koda kuwa cewa kayi ya kashe kanta ko wani nata ne kuwa. "" Jinjina kai yayi yana kallon Malam irin kallon rashin yarda nan, Malamin ya janyo wata kwanon sha ya ce mishi. "" Nasan baka yarda ba. Amma bude wannan abin zaka yarda da ni, ba yau nake maka aiki ba hatta rashin fadar da ta kasa yi mune muke danne bakinta, mun yi haka ne don ka dangwali arziki son ranka. "" Hannunsa yana rawa ya bude kwanon, sai ga Lulu zaune akan abin sallah. Ya cigaba da cewa. ""Ka rufe!"" Ba musu ya rufe, ya kuma ce mishi. ""Bude!"" Mama ce take zuba abinci a takeaway ana fita da shi sadaka. ""Kai din banza kasan har rago aka yanka domin kawai ka nisanci yarta, ita fa a tsaye take ko ta mutu ko tayi rai ita Yarta kawai take son tayi farin ciki."" ""Malam yanzu me ake so?"" Kallonshi Malamin yayi yana shafa gemunsa cikin son abin duniya ya ce mishi. ""Mahaifyarka ta san abinda take biya, ni bana yanke" "kudi amma ana bani kudi me nauyi ne, sannan babban abinda yake lalata min aikina wasi-wasi.""" "Jin haka yasa Hafiz nutsuwa domin yana jin haka a ransa, haka suka bada kusan dubu hamsin," "sannan suka fito daga gidan Hajiya Asiyah tana gaya mishi yadda zai yi, haka dai suka bar unguwar suka wuce gida, bai kwana ba ya dawo Bauchi, bai shigo ba sai karfe tara na dare, kin isa gidansa yayi ya wuce bayan gari a can ya kwana yana sheke ayarsa, washi gari ya isa gida yana muzurai, sai dai ganin wani bako a gidan ya bashi mamaki, sai yayi kamar bai damu ba, bayan ya huta bakon ya tafi sai ga Karimah, ta tsaya mishi a tsaye. ""Waye wancan mutumin?"" ""Ai dan uwana ne?"" ""Kamar ya dan uwanki ne?"" Ganin zai bata mata lokaci ta juya ta bar dakin, shi kuwa zuciya ta kwashe shi ya bita dakin ya ga gadon a wargaje. Yaransa ma gasu nan suna ta barci har lokacin basu farka ba, ga bra dinta da pant dinta a kasa, ba kawai sai Malam Hafiz ya rufe ta da mugun duka ba, kamar dai kashe ta. Dakyar ta kwace ta fita kamar mahaukaciya haka ta bar gidan, ya kama Yaran ya musu wanka. Ya kira Hajiya ya gaya mata, ta ce maza ya sake ta. Ya shirya ya tafi gembu ya aure yar dan uwanta, ya ce mata tayi hakuri zai kira Baban ya gaya mishi yadda suka yi, ai kuwa haka aka yi ya kira shi ya gaya masa, karya da gaskiya Baban Bauchi ya" "tausaya masa tare da cewa yayi hakuri kada ya sake ta,ya zo maza." "Haka ya tattara yaran ya wuce dutsen tanshi, ya samu Yadiko da mai aikinsu suna ta aiki, yadda ya" "shigo gidan hankali a tashe ga yaran a hargitse, yadda ya zauna gaban Baban Bauchi yana rusa kuka yaran na taya tashi, duk sai Baban Bauchi yaji wani abu na damunshi don haka ya ce mishi. ""Ka nimo auren ko yar waye, in sha Allah zan tsaya maka ita kuma babu amfanin zama da mace irinta, abin tausayi Allah ya jarabce ka da rashin mata na gari."" Haka yayi ta rarrashinsa tare da cewa ya bar Yaran a gidan Yadiko ta kula da su, ai daga waje ta ce mishi. ""Gara tun wuri ku nima musu wurin zama amma ni ba zan yi renon yarana da jikokina na kara da na shi, dama ace Yaran Lubnah ce zan karba."" Kiri-kiri ta ce ba zata amsa ba. Haka ya batawa Abba rai ya kira Munah don ya lura sun fi jin maganar Yaransu akan maganarshi. Haka yasa shi gayawa Munah, kiri-kiri ta gaya mishi ai suna tare da uwarsu abin sai ya fusata Abba. Dakyar Yadiko ta rike Yaran zuwa washi gari ya wuce da su Jamaare, daga can ya wuce" Gembu. "Kwanaki biyar yayi ya dawo, sannan ya gayawa Abba, aka saka karshen wata za a tafi gembu a nima" masa auren. *** Lubnah "Duk ranar Lahadi ina da dabi'ar wanki da guga, duk da cewa kuwa ana mana wankin ne. Haka na hada" "kayana na goge su gugar ma kaiwa ake. Monday ya kama Yau da wuri na fita domin muna da test, ina shiga makarantar. Ban san waye shi ba ni dai naga yana ta bina a mota har na shiga department dinmu, wurin karfe daya muka fito. Masallaci muka wuce nayi alwala na gabatar da sallah, sannan na tafi" "cafeteria, na sayi ruwa na wuce hanyar Library. ""Excuse me?"" Aka fada ta gefena, juyawa nayi na kalle" "shi, gabana yana faduwa. ""Sannu ko!"" Ya kara ce min. Ni dai ban amsa mishi ba, da za a lura da ni ba" "karamin rawa jikina yake ba, kallona yayi a tsanake ganin yadda nake raba idanu yasa shi ce min. ""Sunana Rafiq"" kafin ya cigaba da magana na ga wasu yan iskan abokai masu kama da yan kwaya, da" wani irin sauri na bar wurin na bar wurin suka ta min dariya. "Ya Ado ya zo daukana na nufi motarshi, sai ga gaye nan, ya tare ni ai kuwa Ya Ado ya fito yana ganinsa" "ya ce mishi. Barista Yar uwarka ce."" Kallonsa ya Ado yayi da kyau. Ya ce min."" Shiga mota ina zuwa!"" Haka na wuce motar na zauna ya ce mishi. ""Ita ce autarmu, don't mess wrong person, kada ka kuma shiga rayuwarta, kasan har yanzu akwai sauran case dinmu, idan karatu ka zaba tow idan kuma zamu koma kotu ne mai sauki ne. Domin na kare ta babu abinda ba zan aikata ba na gaya maka."" Daga haka ya dawo motar muka bar makarantar. "" Tun yaushe ya fara damunki?"" "" Yau!"" Na bashi amsar a sanyayye, "" baya jin magana iyayensa na kokari amma yana janyo musu magana, ina fatan bai miki wani" "abu ba."" "" Ni tsoro ya bani;"" na fada ina kallon gefen hanya." "Murmushi yayi ya ce min. "" Ba abinda zai miki, na gargade shi."" "" Allah yasa ya ji!"" "" Yana son gobensa zai" "matu™ar wahala bai kiyaye ba, yasan idan na kure mishi gudu sai ya rasa inda zai boya. Da haka muka isa gidan, ya bawa Aunty Zakiyah labarin abinda ya faru tayi ta dariya tana faWin..""idan ubansa ya ji sai ya kusan mutuwa yadda yazo akan case Win kudirat ai kasan basu ji da dad'i a hannunka ba, gaskiya SAN kana vocalno."" Wuce ta yayi yana faWin. ""Ke kuwa kina aman kankara!"" Jin zasu sake layi na wuce sama da sauri Princess tana bani labarin Auntynsu me eyelashes, ko baka da niyyar dariya lamarin Auntynsu" "nan sai ka dara, yadda Princess take takaicin Eyelashes din nan." **** KUMO FAMILY Mansion . "A harabar gidan da aka kawata shi da kayan bud'e baki, aka hadu duk da layya ta kusa amma a duk sati" "Alhaji ELYakub yana da dabi'ar azumi da mazan gidan, idan aka sha ruwa aka yi sallah za a zo kofar harabar Alhaji ELYakub a sha ruwa kafin lokacin isha yayi a kara zama tattauna akan abinda ya shafi" "family din na alkhairi da sharri, cigaba da koma baya." "Da sallama wani dogon matashi, hannunsa rike da wata yar yarinya kyakywa, ga gefe guda" "Matarshi tana dauke da wata baby, da sallama suka zauna domin aka haduwa maza da mata ne, cikin girmamawa ya ce. ""Alhaji Baffa Barka da shan ruwa ya ibada."" ""Alhamdulillahi Khamis ya aikin da can Kano?"" ""Lafiya lau.""Ya fada yana shafa kai Alhaji ELYakub ya kalli matar da take dan takure tana gaida iyayensu, duk da itama kusan har cousin din Abbas ce, Baban Khamis din, amma rayuwar aurenta ba sauki. "" Annah! "" Juyawa tayi tana murmushi ta ce mishi. "" Baffa ya jikin girma? "" Murmushi yayi ya ce mata. "" Alhamdulillahi ya can Kanon da fatan babu matsala ko? "" "" Eh ba matsalar kome!"" "" Masha Allah!" """ Ya furta haka suka sha ruwa ana kiran sallah isha mazan suka tafi masallaci matan suka kafa dandalin" "hira, har mazan suka dawo aka cigaba da hiran. Bayan hira yayi tsawo sai lokacin Uncle Auta da Ubaid" "suka iso da iyalansu. Su kan basu cikin estate din don sun ce ba zasu zauna ba sai ranar da Turaki ya dawo ta ce zai zauna a estate din zasu dawo idan ya ki kuwa dama unguwarsu daya Lekki gidansu ma na kusa da juna. Kuma irin hauka da hayaniyar da ake a KFM basu cikinsa basu sani ba sai sun zo ne a basu labari. Nan hira ya kara dinkewa bayan an yi gaishe gaishe, daga Ubaid da Auta babu wnada ya zo da" iyalinsa domin sun fahimci yadda ake rena musu mata. "Gyada zama Alhaji Abbas yayi karkace kai cikin iya makirci ya ce. ""Baffa idan baka manta ba, akwai" "al™awarin da Marigayi ya kulla a tsakaninmu."" Gyara zaman glass dinsa Alhaji ELYakub yayi yana saurarensa. Ya cigaba da cewa., ""marigayi ya ce idan har ni ko Jibirin dayanmu ya haifi y'a mace yana kamawa Turaki!"" Murmushi Alhaji ELYakub yayi yana kallon Abbas, ya ce mishi. ""Tabbas anyi baka wani zuwanmu Gombe ko? Sai dai a lokacin ba cewa yayi dole ayi auren ba idan Turaki yana ra'ayin yaran sai a" "kulla zumunci idan bai ra'ayi ai baa yi namiji auren dole.""" """ Mujitafa amma ai ya dace Turaki ya ajiye iyalin haka indai ba maganar da ake ta yaWawa na cewa" "yana homo ba! "" Inji Hajiya Khaulatu, lumshe idanu Alhaji ELYakub yayi da karfi, ya jima kafin ya bude kanshi a sunkuye.. cikin dattako ya ce musu. "" Ba zan yiwa Bilal Turaki dole ba, idan ma ya ga dama ya rayu babu mace ba sabon abu bane, domin akwai bayin Allah da suka koma ga Allah babu abinda ya dame su da mace. "" Haka suka yi shiru ya kalli Hajiya Khaulatu ya ce mata. "" Kika ce ana zarginshi ko?"" ""A'a baffa!"" Dakatar da ita yayi ya nuna mata hanya ta bar wurin ya kuma rantse ya baya bukatarta a wurin shan ruwansa. Karshe haka aka tashi abin bai yi dad'i ba, a hanya Uncle Auta da Ubaid suka kira shi, sai da aka yi kira biyar a na shida ya dauka. ""What?"" Wani Uban Ash'aria Ubaid ya watsa mishi, amma ba kula shi ba, sai da Ubaid yayi mishi mugun zagi da cin mutumci kafin ya ce mishi. ""Ubana da yake gefenka yana godiya!"" Bakin ciki yasa, Ubaid sake tsaki ya ce mishi. ""Dan kutumar uba, shege dan" "daudu. Kuma auren dole za a maka idan baka zo naija ba.""" "Nan ma din bai bashi amsa ba sai da yaji Ubaid ya sauke ajiyar zuciya ya ce mishi. ""Ka gama?"" Wani" "uban ashar ya danna mishi, Uncle Auta ya ce mishi. ""Ubaid ya isa haka, Son ka dawo haka?!"" ""Tow Uncle!"" Ya amsa mishi yana sauke numfashi, ""shege waye ya sani ko iskanci kake da wannan ajiyar zuciyar!"" Uncle Ubaid da dama can ya saba da wannan halin nasu. ""Ya isa Son kyale shi haka yaushe zaka dawo Boy!?"" Sai da yayi shiru kamar ba zai magana ba ya ce mishi. "" In sha Allah soon! "" Cikin takaici Ubaid ya ce mishi. "" Soon da baturen da ya kirkiro sun ci kaniyarsu!"" Katse wayar yayi dan ya gaji da" hayaniyar Ubaid ya ishe shi...... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 27" """Wai kai kan yaushe zaku girma ne?"" Cikin takaici Ubaid ya kauda kanshi yana huci, har suka iso" "unguwarsu, sai da ya ga tsaya Uncle Auta ya shiga gidansa sannan ya juya zuwa gidanshi da yake kusa da na Turaki, kallon yadda aka kunna haske gidan yake shi bai tab'a kwana ya wuni ba tare da yasan me yake faruwa a rayuwar gidan ba, don haka yana shiga cikin gidanshi, ya nufi cikin gidan. Matarshi da take ta zaman jiran shi. Mikewa tayi tana faWin.. ""Daddyn Nihla barka da dawowa?"" ""Yawwa Fahimah."" Ya" "fada yana nufar dakinsa, haka ta bishi kamar ta sani ta ce mishi. ""Key zaka Wauka?"" Bai juya ba ya gyad'a" "mata kai. ""Dazun an kawo sako yana store."" Juyawa yayi yana kallonta. ""An kawo sako kika ce?"" ""Eh"" ta" "fada tana matsa mishi a hanya, ta taka a hankali har dakin da aka ajiye sakon, daga rubutun da yake jikin ledar kwalin zuwa girman kwallin yasa shi juyawa ya fita, gidan ya shiga ya samu ko ina fesa. Gwanin ban sha'awa. Ciro wayarshi yayi ya saka a kunne. Yana kira da shi. Rejected din kiran aka yi, sannan ya turo mishi. ""Sorry Man im busy!"" Me Turaki yake haka da yake da muhimmanci sama da shi? Idanunsa ne cika cika da kwalla. *Ba kome nake bukata ba sai lokacinka nake bukata Please ka saurare ni dan" "uwanka* kusan minti talatin yana jiran sakon, amma babu alamar haka." "Sai da ya gama zamanshi har ya mike zai fita sako ya shigo mishi. *Captain Ubaidullahi am sorry, bani" "da lokaci ne! Zan kira ka gobe sai ka sakawa princess naji muryanta.* Rintsa idanunshi yayi yana tuno wani babban al'amari da ya shiga tsakaninsu lokacin da ya dace ya yarda da shi amma ya juya mishi baya, ya bada shaidar da bata dace ba akanshi, yasan ya rusa yarda da take tsakaninsu, amma ba yana nufin haka ya raba su bane asalima yayi haka ne don Turakin ba wai don kanshi ba. Amma tun daga lokacin ya" lura da Turaki yana gudunsa. Wannan yafi kowa yi mishi ciwo a ce Amininka yana gudunka. "Haka ya nufi gida zuciyarsa ba dad'i, ya wuce dakinsa ya kwanta ko kayan jikinsa bai iya cirewa ba," "haka ya kwanta ringigine yana kallon sama, yana ji kamar kome ya dawo da baya ya goge kuskuren da ya aikata. Amma ina kome ya tafi fiye da yadda ba zato, anyi amfani da amintarsu an lalata alakarsu. A hankali ya kwana rabi barci rabi nazarin tsakaninsu, kuma yasan threating dinsa aka yi har yayi magana" "idan ba haka ba, tow da ba zai tab'a bude bakinsa ba." "Karfe shida na safe ya wuce dakin motsa jiki, ya jima yana motsa jikinsa sannan ya dawo yayi wanka ya" "shirya ya samu Amirah tana abin karyawa tana juyawa ta kawo mishi parlourn Wan rungume ta yayi yana sumbatar goshinta. ""Morning beauty"" ""Morning my star!"" ""Ina Nihla?"" ""Tana barci haka ya cigaba da karyawa wayarsa ce tayi ™ara yana dubawa ya ga Introvert. "" Assalamualaikum! "" "" Amin waalaikumunsalam! Barka da safiya."" Daga can ya ce mishi. "" Yawwa ina princess? Ina Mamana? Ina abar kauna?"" Tashi yayi yana hadiye abin bakinsa ya ce mishi."" Tana dakinsu bari na duba ta. Haurawa sama yayi da gudu ya same ta tana juyi, shafa kanta yayi ya ce mata. ""Honey tashi da Appa!"" Ya saka mata wayar a kunne, nan ya shiga mata waka ta fara dariya alamar tana nemansa a zahiri, yadda take raba idanu tana wangale yan hakoranta kwaya hudu zai tabbatar maka tayiwa Introvert din mugun sani, irin sanin da ko shi Ubaid da yake Mahaifinta bata mishi wannan sanin ba, yadda take dariya har da tashi ta" "zauna, zaka girmama shakuwar da yake tsakaninsu." "Sun jima sai da Uban ya cire wayar ya ce mishi.. ""Malam zan tafi aiki? Ka kira Amirah ta bata wayar.""" "Ya fada yana gyara daukar ta. Ya fito da ita yana faWin.. ""Amirah zo ki amshi yarinyar nan ta cika pamper dinta da kashi sai tsami yake."" Ya dauki abinda zai Wauka suka cigaba da wayar shi tunda ya raba wayar" "da yarinyar tuni ya ja bakinsa ya tsuke, bayan ko minti biyar ba a yi da raba shi da yarinyar ba, sai shine" "yake ta zuba a kofar gate ya hango Uncle Auta yana jiranshi, zuwa yayi ya dauke shi. Sannan ya kai shi inda yake aikinsa sannan ya ajiye shi kafin shi ya wuce KUMO properties nigeria agency. Yana shiga yayi parking, office din da yake na shi ya isa ya fara abinda ya kawo shi domin bayan nan yana da kasuwancin da suke yi tare da Mr Turaki. Shigowa aka yi tare da banko kofar, bai d'ago kai ba don yasan cikin marasa kunyar Jikokin Alhaji ELYakub Kumo ne. ""Kai matsayici taya Turaki da baya kasar nan ya san me ke tafiya a kamfanin nan? Sannan maganar haraji!"" ""Khamis Mudansir ELYakub Kumo Please zaka iya fita daga office dina?"" ""Lallai ne ka samu wuri, daga kai har Mrs Thomas zaku yi bayani!"" Y cigaba da ihu da fada da jidali, kamar zai daki Ubaid, shigowa Alhaji Mudansir ELYakub Kumo yayi ya kifa mishi mari sai da ya zauna a kujerar da yake kallon na Ubaid, wannan abin bai saka Ubaid d'aga kai ya san suna wurin ba, ""Dad!"" Sake kifa mishi mari yayi yana faWin.."" Ka yi hauka ne? "" Ya fada cikin zafin rai. Shigowa Alhaji ELYakub yayi yana kallon Ubaid da yake aikinsa kamar babu mutane a dakin ya ce. "" Da fatan dai lafiya ko?"" Murmushi yayi ya ce mishi."" Alhamdulillahi Alhaji barka da safiya. "" "" Barka dai ya me ake tattarawa ne? "" "" Alhaji takardun tax din nan ne nake haWawa, domin CEO ya ce a shigar da kome kafin karshen shekarar nan, ""da kyau!"" Inji Alhaji ELYakub, yana murmushi, ""Mudansir ya ake ciki batun bayanin kenan?"" ""Ni da Abbas mun sakar musu da kuWinsu na 2019-2020."" Alhaji Mudansir ya fada yana kallon Ubaid yana son ta hango yadda zai dauki maganar, murmushi Ubaid din yayi ya ce mishi. ""Sir kudi ya fita ranar biyar ga watan Mayun 2019 daga office dinka, amma bai shiga asusun ofishin haraji na jaha ba, 2020 May 10 ya fita amma bai shiga ba, ga shaidar da office din haraji suka turo haka yana nufin suna bin na tsawon shekaru biyu kafin aka daina tura musu yau muka 2023. Sannan na turawa Lauyar da Alhaji ya haWa ni da shi, wannan tsakaninsu da ofishin haraji na jaha ce, na gama nawa a matsayina mai shiga da fice na kamfani, sai case na biyu, Bankin First ta turo kayanta har na Naira miliyan dari biyu amma ba a tura mata ba, shima ba ni na binciko ba CEO ya binciko kuma ya turo min da sakon. Gasu nan nayi printing Winsu."" Ya hada tare da mika Mrs Thomas da take gefen ta bawa Khamis, wanda ya jike da gumi. Yadda suke wasa da dukiyar kamfanin kamar basu Allah a ransu, shi kuma CEO baya kamfanin" amma kuma twinkle eyes dinsa suna spark a kamfanin fiye da wanda yake kwana gefen kamfanin. "Karba takardun Alhaji Mudansir yayi jikinsa yana rawa, bai taSa tunanin kari da ragi da yake yi a office" "Winsa zai iya fita a takarda tar haka ba, dole ya dauki mataki akan kowani dan iska ya rasa wannan rashin wayon Khamis gashi nan dai kamar me wayo amma bakiWaya daga Turaki har Ubaid suna iya kifar da shi, duk yadda yaso Abbas ya dauke idanunsa akan Khamis din amma a bayan fage sai sun nuna son" zuciyarsu. "Cizon lips dinsa Alhaji Mudansir yake har Alhaji ELYakub ya fita daga office din Ubaid, kanshi kamar zai" "bindiga, ya juya ya kalli Ubaid. ""Ka kula da kanka!"" ""Ka kula da Mimih domin ba san me gobe zai haifar ba, kasancewar ita Waya ce maka."" Hadiye yawun bakinsa yayi yana kallon Ubaid , ko kiftawa bai yi ba, mamaki yadda ya iya mishi barazana da yarsa. A hankali ya fita daga office din, ajiyar zuciya ya sauke" yana mai jin sauki da nutsuwa a ransa. Daga nan ya tattara takardun ya kira Number Lauyar da Alhaji "ELYakub ya haWa su, ya gaya mishi inda zai kai mishi, koda ya kai mishi sama sama suka gaida juna" sannan kowa ya kama gabansa. *** Lubnah "Yau tunda na dawo nake daki, abinci ma yau dakin aka kawo min, ina ci ina kallon handout, ina nazari" "har kusan karfe tara na dare. Ban fito ba wayar da Ya Ado ya saya min kwanan tayi haske kiranshi na dauka ina faWin. ""Ya Ado?"" ""Auta ina lafiya dai ban ganki ba ne?"" ""Bari na fito mu gaisa!"" Ka tattara kome na sauko kasa, na samu suna ta hira zama nayi ina kallon Aunty Zakiyah. ""SAN yarinyar nan bata tsoron Allah!"" Murmushi yayi yana faWin, ""Auta da gaske ne kin shanya Doctor Ahmad?"" Idanuna ne suka cika da kwalla, ina kallon kasa ya cigaba da cewa. ""Tunda nace kin fara karatu hankalin Mama yake kanki tace tana son ki yi aure Hafiz sai ya rabu da ke?"" Ni dai ban ce kome ba, har ya gama maganarshi, na ce mishi. ""Zan koma na kwanta."" Na mike zan tafi ya ce min.. ""Ahmad mutumin kirki ne, ki yi nazari yasan matsalarki kuma zai tsaya miki!"" Da gudu na haura sama, ina jin kuka yana zuwa min, ni tsoron maza nake ji bana son abinda zai hana ni dasu, haka yasa na ki kula Ahmad. Kwana nayi ina kuka domin har" yau ban manta abinda Ya Hafiz ya min ba. "Washi gari tun kafin ya fito na bar gidan, domin bana son Magana ya kuma hada ni da shi, a" "makaranta na karya shima naci ne gudun kada na wahalar da kaina. Wunin ranar har aka tashi bani da walwala, ina hanyar komawa gida Baby ta kirani. ""Yan mata gani a gidanku!"" A shake na amsa mata, sannan na ce. ""Ina hanya!"" Haka na isa gidan a hankali nake takawa, har gidan, motar Doctor Ahmad na hango a harabar gidan, ba don mun yi ido hudu da shi ba da na juya. Haka na daure na shiga na gaishe shi sannan na wuce cikin gidan, na samu Aunty Zakiyah tana gida. Gaishe ta nayi na wuce sama. Baby ta biyo ni. ""Yan mata wai meye ya faru ne?"" ""Babu!"" Na fada mata, murmushi tayi ta ce min. ""Wancan hot guy din fa? Da me shi ko na Wauka?"" Da sauri na juya ina kallonta. Baby irin mutanen nan masu open mind bata iya boye what she want kome ta gani tana so baya bata wahala ta mallaka. D'aga gira daya tayi tana faWin. ""Ko dai naki ne?"" ""Yayi miki da gaske?"" Na tambaye ta domin ina jin kamar zata raba ni da matsalata ce, idan har ta ce yayi mata tow ba makawa zan samu hanyar rabuwa da shi. ""Idan kina son shi zan baku number wayarshi,"" na fada ina kallon yadda take murmushi, ""wallahi yayi min!"" ""Ok ko bari na fito wanka sai na baki number shi."" Na fada ina wucewa toilet, sai da nayi wanka nayi Alwala sannan ka fito na samu tana zaman jirana, abu take zuka na ce mata. ""Yaushe zaki daina shan wannan abin ba?"" mai da shi jakar mata tayi tana faWin. ""Ina kokarin bari in sha Allah."" Ina son gaya mata gaskiya amma kuma san yadda zata dauki maganata ba, kada ya ga kamar don zan hadata da Doctor Ahmad ne, sai na ja bakina nayi shiru na kyale ta har nayi sallah, ina idarwa Adil da Mama suka kawo mana abinci, muka fara ci a hankali, ina lura da yadda bata son abinci, na ce mata. ""Ki daina shan drugs, ki fuskanci rayuwa ki ci abinci domin wallahi zai iya haifar miki da wata matsala daga baya ayi ta kuka da juna."" Murmushi tayi ta ce min. "" In sha Allah zan bari! "" Daga haka ta cigaba da tsakuran abincin tana wasa da shi, har" "muka gama Princess ta shigo ta ce min. """ "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 28" """Aunty kizo Mama tana kiranki! "" Nasan batun Doctor Ahmad ne, ji nayi gabana yana faduwa, kamar zan" "yi kuka haka na mike na shiga ban daki na wanke hannuna, sannan na saka mayafi akan riga da zanin jikina, na sauko kasa na same ta tana duba books din Yaran na makaranta. "" Lulu kin manta da Doctor Ahmad ne a waje?"" Shiru nayi ban bata amsa ba, can dai ta kara magana sannan na d'ago kai ina kallonta kafin na ce mata.""to! "" So nake na ce mata, ta sallame shi amma na kasa saboda yadda bakina yayi nauyi, hawaye ne ya cika min idanun. Komawa sama nayi na dauki Hijab na saka sannan na sauko kasa, na" "samu tana waya da Ya Ado, kusan tare muka sauko da Baby ta mata sallama zata tafi, muka hada hanya a waje na samu Doctor Ahmad zaune. Jan plastic chair nayi na zauna ina dan matsawa can nesa da shi, Baby ta tsaya a bayana tana gaishe shi, sannan ta min sallama ta fita a gidan. Har ta bar gidan yana bin ta da idanu. ""Ki fita harkan yarinyar nan, bata dace da ke ba."" Ni dai ban ce masa kome ba, yadda ya gama" surutunsa haka na tashi muka yi sallama. "Ban san ya suka kare ba, sai dai kwana biyu da zuwan shi ya kira ni a waya yana tambayata me yasa" "na bawa Baby numbersa, shiru nayi bani da ta cewa. Ganin naki magana yasa shi katse kiran, washi gari sai gashi ya zo, shiru duk muka yi yana kallon yadda nake wasa da yatsu hannuna na kasa magana tunda na gaishe shi ban kara magana ba. ""Kin san yarinyar nan bata kyauta ba? Sannan ta gaya min cewa kece kika bata number ta? Akan me zata na kirana any how? Har matata sai da ta fahimci akwai wani abu a kasa."" Sai a lokacin na d'ago kai ina kallonshi. Wato shima dai irin Ya Hafiz ne na shiga gidansa ya gana min azaba da Matarshi, to idan ba mai mata ba, waye zai aure Ni? Ni dai ba samun saurayi xan kara yi ba a karo na biyu, duk tsiya idan ban auri mai mace daya ba zan auri me mata uku na shiga ta huWu." "Wannan abin ya saka min wani irin tsoron shi Ahmad din kansa. Duk mutumin da bai da ikon kasan a gidansa har abada ba mijin aure ba ne. Don haka na tashi na bar shi a wurin haka ya kira Ya Ado ya gaya mishi, lokacin da Ya Ado ya dawo gida ina daki ya shigo dakin, jan stool yayi ya zauna yana kallon yadda nake takure wuri guda. ""Lubnah me yasa ba zaki bawa Ahmad dama ba?"" Yadda yayi magana yasa na d'ago ina kallonshi, idanuna cike da kwalla har ya gama magana ban ce mishi kome sai kukan da na fara ganin yadda nake kuka da gasken gaske yasa shi zuba min idanu cike da mamaki, har washi gari ban fito ba don bamu da class, ina daki a kwance gashi garin an tashi da ruwan sama, haka yasa nayi luff a dakina suka tafi aiki sannan na fito na karya na wanke kayan na koma na kwanta. Karfe uku na fito saboda hayaniyar Yaran na fito na tsaya suka shiga kafin motar islamiyya ya zo ya dauke su na koma na kwanta. Karfe biyar duk suna gidan ban kara lekowa waje ba, na cigaba da kwanciyata. Wurin karfe goma na dare sai gasu nan su biyu yaran sun kwanta ina kwance, kunan wutar dakin tasa nayi kamar ina barci, zama a bakin gadon Aunty Zakiyah tayi tana kallon yadda na sake jikina. ""Ko tayi barci ne?"" Inji Aunty Zakiyah, ""idonta biyu!"" Shima ya ja stool ya zauna yana kallon yadda nake kwance. ""Tashi mun zo magana ne akan Ahmad!"" Tashi zaune nayi ina kallon gefe guda. Tunda kuka fara kawon farillah da musta'abin halin Ahmad, kasancewar shi mutumin kirki ban san lokacin da na fara kuka me karfi ba, sai suka zuba min idanu. ""Me aka miki to?"" ""Kawai ku mai da ni Bauchi na je can ko kashe ni ne gara su yi! "" Shiru Ya Ado yayi yana kallon yadda nake kuka. "" Me yasa tow? "" "" Tsoro suke bani tsoro yake bani, duk wanda zai zo gare ni tsoronshi nake, ku gane ni tsoron maza nake, wallahi cutar da ni zai yi don Allah idan kuna son" "farin cikina ku kyale ni!""" "Ganin yadda nake kuka abin dai yayi ta basu mamaki, har suka fara ganin kamar basu so kansu ba," "don haka Ya Ado da kanshi ya rarrashe ni, na bar kuka suka hada min abinci na sha tea, sannan suka tafi" "na kwanta kusan raba dare nayi ina gayawa Allah kukana, tsoro nake ji shima Ahmad din akwai abinda ya" "gano yasa yake bina, ban san yadda Ya ado ya fahimta da shi ba, amma kuwa na ga ya daina turo min sako ko wani abu sai dai duk ranar juma'a yana turo min da sakon barka da juma'a wato ba zai tab'a give" up ba. "A bangaren Mama kuwa har zuwa tayi akan matsalar sai dai tana zuwa lagos, ganin yadda ta saka ni a" "gaba da maganar aure, ban ce mata kome na tafi makatanta na dawo, na same ra bata daina maganar auren nan ba, bata san yadda abin yake ba, ni dai ban san me ya faru ba, sai dai na bude idanuna na ganni a dogon kujeran parlourn, su Ya Ado suna ta min sannu, dakyar na tashi. Rike hannuna Aunty Zakiyah tayi zuwa dakina Yara na kwanta, ta kawo min magani da tea na sha, yana fada min nayi sallah na zo n kwanta tuni barci yayi gaba da Ni, sai karfe daya na dare na farka a lokacin na samu tana kan abin sallah, tashi nayi na shiga ban daki nayi alwala na zo na gabtar da sallah Magariba da Isha, ina idarwa na daura da nafilla. ""Lubnah?"" ""Na'am!"" Na kalle ta, yadda take kallona tausayi na take ji, haka yasa na matukar jin tausayin kaina. ""Tsoro kike ji ko!"" Hawaye ne ya zubo min, ashe ta sani? Ashe tasan ina jin tsoro; bude min hannu tayi na shiga ina wani irin kuka, ""Ya isa haka ba zan kara miki maganar aure ba, ba xan kara cewa wani ya miki magana aure ba. Jiya naji kamar na rasa ki kenan, ban san ashe haka abin yake ba. Lubnah ko wani ne yace baya son abu ba zan mishi dole ba, balle ke da na yi miki laifi masu tarin yawa, ina jin idan baki yafe min ba Allah ba zai yafe min ba, "" ni dai ina jikinta tare da jin wani dumi me dad'i, haka tayi ta rarrashina tana gaya min nayi hakuri da ™addarata haka ta zo min, satinta uku, ta koma Bauchi ta bar mu da kewarta. Haka na cigaba da rayuwata cikin yanci da walwala lokacin da na samu hutu kamar na je Bauchi, amma haka na hakura duk abinda zai hada ni da Hafiz ina kin sa, a zuwan Mama ne muka ji labarin ya kai sadaki da kayan aure a can garin Mamansa. Wai Abba ya sauya mishi gida, ni dai ban ce kala ba har suka gama hiransu. Karshe barci nayi a parlourn ban san lokacin da" suka gama hiran aka tashe ni na je na kwanta ba. Bayan tafiyar Mama na sha hutu na koma school. "Shekara daya da wasu watanni a lagos wnada yayi daidai da wata na bakwai da fara karatu, haka yasa" "na kara nutsuwa zuwa yanzu karatun shine mijina da duniyata, course mate dina tun suna kirana silver spoon saboda sun gano nice aka musu kashedi akai, suka yi ta min tsiya da tafiya tayi nisa sai suka watsar da makamansu suka kuma janyo ni muka zaka Family, duk yadda zaka so ka kebe da ni na shata layi ba ruwana da soyayya, tsoron maganar namiji nake, department dinmu har sun gano tsoron mazan da nake ji, wani irin tsoron maza da nake ji duk abinda za ayi ayi na karatu amma bayan nan kana fara wani abu, xan fita harkanka. Duk yadda kowa yaso yasan matsalata da maza ban tab'a magana ba, haka" "yasa suka kyale ni, na kuma kame kaina na saka a raina ba ruwana da duk wani dan balaja'u." "Haka kuwa muka kasance har muka kusan gama karatunmu, a lokacin ina da shekaru biyu cib a jahar" lagos. *** KUMO FAMILY MANSION. Kallon Hajiya Khaulatu Daadah tayi cikin wani irin takaici take kallon yarta da son zuciya ya gama rufe "masu idanu. ""Daddah ki bawa Alhaji hakuri wallahi Khamis ba zai kara ba, kuskuren fahimta aka samu!"" Ta fada tana sunkuyar da kai kallonta Daddah tayi cike da mamaki da bakin ciki mara iyaka. ""Yake" "yaronki ce tayi laifi kin zo na saka baki na bawa ita baffanki hakuri Khamis ba zata sake ba."" Murmushi" "tayi irin na manya, sannan ta cigaba da cin mutuncin Hajiya Khaulatu. ""Wato ita wancan Yaro Turaki da bata da kowa sai Allah, kika jifeta da shaidar zur, ita kuma Yaronki da take da Uwa da Uba ka zo kare shi saboda shi ne mai gata, ita wancan tana da waye? Bata da kowa sai Allah. Wai na tambaye ka Khaulatu me Yaron nan Aisha da yayunku suka muku da kuka tsane su haka? Ni a sanina basu muku kome ba idan har akwai abinda zaku yi bai wuce tsayawa da Anne Aisha yayi a Kamfanin Alhaji ba, amma kun tsane shi tare da ita yar uwarku."" Yadda Daddah take shiga ba nan take fita ba, karshe haka suka yi shiru ta kori" Hajiya Khaulatu daga cikin gidan. "Wurin karfe uku na yamma Jasminah ta shigo cikin gidan, ta samu Uncle Auta da Hajiya Samirah. """ "Barka dai datti! "" Yay gaida Alhaji ELYakub Kumo, sannan ta juya ga Hajiya Samirah ta ce mata.. ""Aunty Barka dai ya kike? Yasu Munawara da Abid?"" ""Lafiya lau Jasminah, kin leka Hajiya Zeenatu?"" Yatsina fuska tayi tana kallon Daddah, ""Daddah ya kike ?"" "" Kaci gidanku! Da kazo ai baka gaishe ni ba sai yanzu zaka ce wai ya nake ba yadda nake ina shure-shure."" ""Allah ya baki hakuri!"" Banza Daddah tayi mata, Alhaji ELYakub ya kalli Jasminah. ""Ina jinki!"" Gyara zama tayi ta ce mishi. ""Gaskiya na gaji, tunda shi Turaki ba zai musu magana ba ya kamata a bani damar nayi magana tunda ina da hakkin akan kasona da yake cikin kamfanin!"" Kallonta yayi yana murmushi ya ce mata. ""Turaki yayi magana ki ce ya fito da sonkai? Ke kika ce Turaki yana nuna iko dayawa ko za a bada matsayin CEO baki amince a bashi ba, yanzu kuma ki dawo kina blaming Winsa shi da ba a kasar yake ba. "" Yayi mata magana yana murmushi, bakiWaya ta ji kamar ta nutse a wurin. "" Ita Turaki ta ce ba zata dawo ba, da irin wannan masfar da kuke yi gara kada ta dawo a sakata ta rame. "" Daddah ta fada tana hararansu. "" Yanzu dai me Jasminah take bukata haka kawai Jasminah bata zuwa akan abinda tasan waye a kai ba?"" Shigo da tiren abincin Alhaji ELYakub, tuwon alkama ce miyar kuka wanda yaji kayan kamshi da hadi na musamman. Ajiye tiren abincin Maid suka yi ta yi, har gaban Jasminah. "" Ina jin Jasminah? "" Alhaji ELYakub ya kara magana, yasan abinda ya kawo ta amma tunda ba zata yi magana ba shima shiru zai yi abinda ya fahimta shine ganin Samirah yasa tayi shiru taki magana, suna zaune a wurin har ya gama cin abincin, Uncle Auta ya shigo suka gaisa shine ma Ya kalli Samirah ya ce mata. "" Ya dai na ganki anan? "" "" Yanzu zan tafi, amma Mujitafa me yasa Matarka da Matar Ubaid basu zo birthday din su Abid ba?"" Ta fada tana wani hade rai ita nan an bata mata rai. "" Saboda basu fito daga babban zuri'a masu arziki irin naku ba, su zo anayi ta musu kallon banza da basu isa ba! "" Ya fada yana kallon Daddah da take gyada kai. "" Baffa barka da warhaka, Ubaid ya mika sakon wasu bayanai ga Turaki sauran kuma da a ji da shi, gaskiya Khamis yayi" "laifi dayawa sai dai yana da kyau a dawo da shi, domin ko babu kome yana lura da shashin tallace-tallace. Amma na gayawa Turaki ya ce duk abinda aka gani shi dai na shi ya saka idanun ne kuma ya yayi bakin" "kokarinsa sauran na ku ne. """ "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 29" """Murmushi Alhaji ELYakub yayi ya nuna Uncle Auta ya ce mishi. "" Baka da kunya Mujitafa, wato sauran" "namu ne bayan kai ma kana da kaso a kamfanin! "" Dariya Uncle Auta yayi ya ce mishi. "" Ina ana babbakar giwa wa ke ta zomo, shi dai wancan magajin dubbanin nairori ya ji da kome ni a bar ni a dan aika! "" Anya kuwa? Na fison ka taya shi riko tunda yaki kula maganar CEO shi baya kasan amma idanunsa yana kan kamfanin."" ""Cikakken shugaba kenan, baya tare damu amma idanunsa yana kan kome yasan shiga ya" "san fitar kuWi!"" Jinjina kai Alhaji ELYakub yayi tare da gamsuwa da maganar Uncle Auta, ya ce mishi." """Zenith bank sun kawo kayan wani dan kasuwa nayiwa Ubaid magana!"" ""Eh ya turo min dazun na kuma" "turawa Turakin amma bai ce kome ba!"" ""Alhamdulillahi mu jira mu ji me zai ce. Amma ba zaka mishi magana ya dawo gida ba kenan?"" "" In sha Allah zai dawo, Baffa hukuncin ya isa haka yau shekara kusan daya da rabi da hukunta Khamis, duk da an biya kudin harajin ya kamata a sassauta mishi, Addah Khaulatu sai sintiri take tsakanin gidana da gidan Ubaid, ta amshi number Turaki yaki daukar kiranta, na" "tura mishi apologize letter da suka rubuta bai ce kome ba.""" """Shi kenan Ubaid ya gaya min sannan itama Uwar Yaron tana ta bada hakuri, haka Abbas yana ta bada" "hakuri sai yadda Turaki ya ce ya cire hannunsa nake son ya hakura da kansa, tunda yace akwai mutanen" "da suke bayan Khamis shi kaWai kudin yayi masa yawa, na rasa wnada ya karantar kimiyyar haWa bama- bamai taya ya san kimiyyar shida da fitar kuWi har haka? """ """Baffa Turaki rabin rayuwarsa yayi ta cikin turawa da larabawa ne, yasan makircin kowa, don haka" "kada ka yi mamaki don ya Wan me yake faruwa a kamfanin da kuma yadda yasan yadda za ahada nukiliya da yadda yasan mutane na kaunar kuWi. "" Cikin gamsuwa da bayanin Uncle Auta ya ce mishi. "" Tabbas ya gaya min cewa kamar yadda nake son zuriarta ta zauna lafiya, ya ce Datti a cikin gidan akwai wnada zaman lafiya baya cikin tsarinsu, ya ce Datti ba wai ba zan dawo cikinku ba ne, kawai nafi son nesa da kune domin idan ina tare da ku, kullum sai na fito da sabon tsarin zaman lafiya, su ma kullum sai sun fito da tsarin tashin hankali."" Inji Alhaji ELYakub ya fada yana dariya. ""Baffa sai kace mishi ya cancanci a bashi piece ambassador! "" Dariya suka yi sai a lokacin ya juya ga Jasminah ya ce mata. "" Daughter ya Case dinku dai? "" Komawa Hajiya Samirah tai ta zauna tana mai baza idanunta. "" Uncle Auta a bar maganar! "" Inji Jasminah tana me mikewa ta gyara zaman abayarta. "" Da Abbana yana raye zai saurare ni ba tare da wani ya san me ya kawo ni ba, am so disappointed Datti ka san me ya kawo ni amma ka ki ka bani damar haka, Uncle Auta kasan bani da wata madafa amma ba kome! "" Ta juya tare da Waukar jakarta tana share kwalla da yake zubo mata ba da wata mafita da ya wuce ta kira shi Turaki kaWai ne last hope dinta, sai da ta shiga motarta sannan ya kira Numbersa hawaye na zuba mata, bata taSa kawowa zai saurare ta ba ko zai dauki kiranta. Amma abin mamaki sai gashi ya dauka yana tambayar. "" Da fatan lafiya? "" Cikin shashekar kuka ta ce mishi."" Kasan ciwon da nake ji na kowa ya juya min baya? Kasan yadda nake fama da ciwo na abinda yake damuwana? Kasan yadda nake ruined rayuwar aurena? Ko sau daya ka tab'a jin kukana? Ka tab'a tambayar meke damuna? Brother ka tafi ka bar ni alone baka damu da ni ba, ko don ba ciki daya muka fito ba? I lose Abba, by now I lose everything har career dina, my First child she be mole daga Brother Mijina, nayi magana Mom ta ce na kashe case Win, yayi min barazanar ko na saka ku a sake mishi kayansa ko ya sake ni ya kwace min Yarana."" Ta cigaba da kuka a hankali, sannan ta hadiye kukan tana faWin.. ""ba kome haka Allah ya nufa, kowa yana son na shi amma ni nawa sun yi abonden dina, na" rasa duk wani kwarin gwiwa. But koda gawata aka samu don't blame them just remember that na gaya maka yadda nake "shan wahala na gode wannan shine death note dina!""" "Kashe wayar tayi ta kifa kanta a kan sitiyerin motar, tana jin wani irin kuka yana zuwa mata, wayarta" "tayi ™ara ta d'ago kai tana kallon kiran, dauka tayi domin ta tab'a yarda zai kara kiranta ba. "" Littles" "Queen, are Kumo Family Queen, akan me ba za a kula ki ba? Ki bani nan da awa biyu ki tafi gidan Ubaid ki zauna kada ki damu Yaranki zasu zo gare ki, Abba baya raye amma ba yana nufin xan bar rayuwarki ta" "lalace ba ne, kece kawai kika rage min da muka yi sharing blood, taya xan bar ki? I glad kin kira ni for" "your own, you invited me akan personal life dinki, ki tafi gidan Ubaid ki kwanta kada ki yi drive zan saka Tajudeen ya zo ya kai ki jira yanzu kin ji"" sai ra cigaba da kuka ta kasa magana irin kukan farin ciki ka samu wanda ya tsaya maka, yana jin ta bai kashe wayar ba ta ce mishi. ""Allah ya jikan Mommy da Abba. Allah ya gabatarwa su Baffa, Brother I miss you, I miss something else!"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Ba gani ba? Remember who you are, kada ki sake barin wani ya cutar dake, idan aka yi magana ki ce kina da Turaki akwai wani marayan zaki da yake gurnani saboda ke!"" ""Na gode sosai na gode."" ""Oya share hawayenki bari na kira Tajudeen."" Kashe wayar tayi bayan minti goma sai ga Tajudeen, ya gaishe sannan ta fita gaban motar ta koma baya, anan ta zauna har suka isa gidan Ubaid, a lokacin Amirah tana aiki a kitchen, koda ta shiga a parlour ta zauna har Amirah ta fito. ""Jasmin!"" Murmushi tayi tana sunkuyar da" idanunta da suka yi jajjir har daman idanunka yayi ja. """Brother Turaki ya ce na zo nan!"" ""Ok muje na kai ki daki!"" Ta mike Amiraah ta kaita daki, ta zauna a" bakin gadon. Kanta a sunkuye. Haka Amirah tayi ta hidima da ita tana cikin masu yiwa Amirah kallon bata kai ba. Amma yau don Allah ya d'aga darajar Amirah gashi nan tana hidima da ita. After 3 hours. "BakiWaya family kumo kowa ya shiga hankalinsa, idan ka cire Hajiya Zeenatu wacce take bala'i da masifa." """Wato ni Jasminah ni zaki wulakanta? Har zaki yi involved din Turaki cikin wannan lamari? Ni na haife ki ba shi ba, wallahi idan baki zo ba nan da awa daya sai ka tsine miki."" Ta fada tana ihu. Ba karamin tashin hankali ta shiga ba, idan har Jasminah ta lalata aurenta tow wannan damar da zata rasa abinda take hari" akan Mimih. "Wato wani abu da ya faru, shine yana gama wayar da Jasminah, ya kira Uncle Auta da Ubaid ya ce" "ya basu awa daya kacal su kama Fahad mijin Jasminah a rufe shi kada a bada belinsa, duk wanda yake son karban belinsa a nimo Jasminah ita ce ke da hurimin bada belinsa, sannan aje gidansu a dauko mata Yaranta ko da bala'i. Akwai abinda only money and power kaWai yake iya aiki, kuma ya nuna musu iyakarsu. Sannan duk wani abin da ya shafi Family Noma family sai da Turaki ya dakatar dasu kuma yayi magana da karfi da kudi yasa aka kama Sudais Kanin mijinta aka rufe shi aka rasa inda aka kai shi, sannan ya kashe wayarshi bayan ta tura mata da sakon. *Kada ki kashe wayarki ki saka a ranki akwai babban challenge da zaki fuskanta kada emotion ya sa ki mika wuyarki, kin ji ko baki ji ba. Ba zan kashe miki aure ba domin nasan kina son Mijinki, nasan kina bu™atarshi and ki holding wannan yanayin yadda zaki kwaci" kanki!* "Bai gaya mata wanda zasu kalubance ta ba, amma yadda Mamanta ta tsaya sai ta fito daga inda" "take, amma bata fito ba. Ganin da gaske taki magana kuma taki bayyana kanta. Sai gashi hankalin kowa ya tashi. Shi kanshi Ubaid bai san tana gidansa ba, sai da ya koma domin tunda ta cewa Amirah Brother Turaki ya turo ta bata gaya Mijinta ba, ganin Jasminah a gidan yasa shi duba e-mail dinsa. *Yaran a kai su wurin Hajiya Zeenatu Queen kuma ta zauna a wurinka.* Yana ganin haka, ya fahimci sakon shi. Washi gari ya tafi can KUMO FAMILY MANSION, ya ji yadda ake ciki da maganar Jasminah, haka aka yi ta" "nimanta. Wunin ranar iyayen Mijin Jasminah suka zo, Alhaji ELYakub Kumo ya ce su je gobe su dawo." "Wasa wasa sai da suka yi zuwa uku a cikin kwanaki biyar, kafin Turaki ya bawa Uncle Auta labarin" "inda Jasminah take a je a dauko ta, aka kaita gida yanzu su babban damuwarsu a sake Sudais ita kuwa kamar yadda Uncle Auta da Ubaid sun ce ta ce a kai su kotu ta haka ne zai saka su shiga hankalinsu, yadda take kome da maganar da take yasa Alhaji Mudansir ELYakub Kumo ya Fahimci bakiWayansu tsarin turaki ne, hatta shima Alhaji ELYakub Kumo abinda yake yi tsarin turaki ne, cizon lips dinsa yayi yana kallonsu domin bai taSa yarda Turaki zai iya daure shi ba, Alhaji Nasiru Noma babban abokinsa ne kuma abokin cin mushensa, duk wani halin da Jasminah take ciki Alhaji Mudansir ya sani kawai tsabar masifar" son kudi ne irin nasu. "Yadda Fahad ya sha azaba ga kayansu da aka rike, domin aka zargin kayan akwai miyagun kwayoyi," "burin mijinta shine wani daga cikin manya da suke gefen Turaki su saka hannu yadda idan aka sake mishi kayansa sunansa ba zai baci shi Waya ba, sannan koda yayiwa Mahaifinsa magana yayiwa Alhaji Mudansir magana sai ya ce a'a baya son saka hannunsa a cikin irin wadannan dirty stuff din, shine kawai ya tabbatar da su yi ta threating Jasminah yadda dole zata saka Turaki ko Mujitafa su saka mata hannu. Ai kuwa bukata bata biya ba domin gashi nan dai ba a je ko ina ba kome ya b'aci musu tunda sun tab'a me" yaya irin Turaki. "Case Win Babba ya koma musamman da aka shigo da maganar mole Babbar yarta da ake yi, nan" "Uncle Auta ya ce a kai kotu kawai, ai kuwa kowa ya shiga hankalinsa, masu jiran wani abu ya faru suka fara cewa dama abinda yake faruwa kenan, duk da zaman iya maza da ita sai mahaifiyar dayawa sun yi missing shot din, ita kuwa Uwarta gudun kada Hajiya Khaulatu da Samirah su mata dariya da sauran matan gidan, shi yasa nake rufe kome amma yanzu kan dole fa tayiwa tufkan hanci musamman wancan Tsinannen da yake zuga mata Y'a domin yana bakin ciki ya kasa zama yayi aure yana bin matan banza, kwafa tayi tana kaiwa da komowa, tana kallon Jasminah da take shan tea a hankali.. ""yanzu kin kyauta" "kenan? Duk abinda yake faruwa wato kece mai dan uwa da zai tsaya miki?""" """Lokacin da na kawo miki maganar nan baki saurare ni ba, kowa ya juya min baya the way you turn back," "shi ai mun yi sharing blood da shi ko zaki shekara kina zaginsa ba zai tab'a min ciwo ba because yanzu na san how he meant to me, shi din kaWai ya rage min, tun yarinta kika raba ba ni da dan uwana, yanzu kina nufina na raba da shi? Yau ya tsaya min ya tsaya min """ """Amma dai kin san cewa Mimih itace Queen of Kumo Family!"" Murmushi tayi tana faWin. "" My brother" "Turaki told me that nice be throne of KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY, ni ba don kamfani nake wannan abin ba ina son a san yadda nake rayuwa ne kuma, I'm not here for against you and your lovey daughter I'm here for my life, Alhamdulillahi at least na samu wnada ya fahimci how im dying......." "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 30" "Mikewa tayi tana kuka ta nufi hanyar waje, ""haka kawai nake jin zuciyata take bani wani abu na daban" ban sani ba ko yana da nasaba da yadda kika watsar da ni ne amma ki sani ina kallonki a matsayin Uwar "da ta haife ni, tun da Abba ya rasu na fahimci shi Waya ne yake kaunata. Nasan cewa mafarkinki shine na" "kasance d'a namiji, duk da ™addarata bata hannuna amma nima mutum ce, sannan kuma Mimih itama mace ce da yake ita Yar so ce kina kaunarta. Am I only one da nake rayuwata a duniyata bayan kin raba ni da dan uwana, Alhamdulillahi ya dawo gare ni. "" Daga haka ta fita daga gidan ta rasa wanda zata gayawa kukanta, cikin gidan ta wuce tana tafiya ta kira Numbersa har ya gama ringing. Sai da ta mishi kira hudu kafin ta hakura, a parlourn Daddah ta zauna tana ta ™o™arin hadiye kukanta, sai ga kiran shi, a hankali ta fashe da kuka. Daddah da take lazimi tana kallonta bata fasa abinda take yi ba, dauka tayi tana kuka, tabe bakinta tayi tana mamakin yadda ya sauya lokaci guda. ""Brother!"" Ta kira sunansa cikin kuka. ""Na gaji! Bakin ciki kamar zai kashe ni, zuciyata wani irin ciwo yake min da kaikayi don Allah!""" Kasar kiran yayi ta cigaba da kuka.. """Idan ka cigaba da kiran turaki ai zaka saka hankalinta ya tashi, kai da ya dace ka zama me hakuri ita" "Turaki me tasani? Tunda aka fara wannan rigimar Uwarka yake jin haushin turaki ita fa nata taimako kawai tayi!"" Ita Daddah a duniya duk abinda za a saka turakinta a ciki har a zage shi ta tsani abin." "Sallamar Tajudeen yasa suka yi shiru ya ce mata.. ""Ma Oga yace a kai ki gidan Oga Mujitafa!"" ""Ok!"" Ta mike tare da bin bayansa, a can bangaren Iyayenta suka dauki kayanta, Hajiya Zeenatu tana mata magana amma bata kula ta ba, abu daya ta fada yasa ta tsaya. ""Uban waye zai cigaba da kula miki da Yaranki? Oya zo ki dauki Yaranki, tunda kika ki maganata ba zai yiwu ba kare rayuwata akanki da Yaranki ba."" Ba musu ta shiga dakin kwaso Yaranta, tana jin kamar wani irin ciwo a ranta. Haka suka fita motar suka shiga babbar yarta mai shekaru takwas tana tafiya a hankali, ta kalli Mamansu ganin tana kuka ta daura kanta a gefen hannun Maman. ""Sorry Ammi!"" Wayarta ce tayi kara, ta dauka tana faWin. ""Shii ku yi shiru nayi waya da Uncle dinku!"" Babban ce tayi shiru kananun suka cigaba da kuka. ""Me ya same su?"" Ya tambaye ta, jan hanci tayi tana faWin. ""Kawai sun ji ina kuka ne!"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Zaki koya musu kuka like cry baby, basu wayar. "" Mika musu wayar bata san me ya gaya musu ba sai gani tayi suna ta dariya, har ita Ilham, dariya suke sannan ya ce su bata wayar. "" Zaki zauna a wurin Mujitafa da Ubaid, na gaya miki ba zan kashe miki aure ba, idan lokacin da suka iya saukar da kai suka bukaci" "sulhu shi kenan! "" "" Na gode! "" "" Shii! "" Ya fada yana me mata sai da safe." "Abinda ya faru kuwa kiran Uncle Auta yayi ya ce mishi. "" Ka saka Tajudeen ya dauko Jasminah tana" "cikin damuwa! "" "" Tow Ubana idan na ki fa? "" "" Ai dole ma ka yi tunda bana kusa!"" Da yake wani lokaci idan yayi niyya magana yake kamar ba shi ba, idan bai yi niyya suna binsa amma yana gudunsu, sannan su kansu sun yi mamakin yadda ya ke hidima da case Win, domin kuwa bai cika shiga irin wannan rigimar ba, amma wannan karon shi ne har da kira sau hudu a rana, lallai jini yafi ruwa kauri domin ban da jini babu abinda yake tasiri a rayuwar Turaki kamar jinin da suka hada, ita Waya ce kanwarsa da suke uba daya ita Waya zai kalla ya ce she is my biological sister, ita Waya ce ta rage mishi a su hudu fa aka haifa." Shi yasa yadda ya matsawa Uncle Auta da Ubaid zaka rantse da Allah basu da wani aiki ne sai na shi. "Wannan karamin crisis din ya kara dawo da shakuwar Turaki da Ubaid, wanda yake kiranshi a kai akai." "Dan uwa me dad'i, akwai abubuwan da suke faruwa a wannan duniyar amma idan aka zo kan yan uwantaka sai ka rasa gane kan wasu domin suna rike zumuncinsu da daraja." "Wasa wasa Turaki da yake Russia ya rike case Win domin kuwa ya lura ita kanta Jasminah ta gaji ne," "yadda yake gidan mijinta azaba da kansu suka kawo kansu da kuma fadar abinda suka aikata, Allah kaWai yasan irin abinda ya musu, sai gashi nan sun zube akan gwiwarsu suna rokon a fitar da Sudais ita kuma idan akwai abinda take bukata tunda ba zata zauna da shi ba, ta faWa. Kai tsaye ta ce auren ne bata so, kuma zata rike Yaranta. Wannan abin ya kawo karshen duk wani rikici amma fa Uwarta tayi tsalle ta ce bata isa ba, sai da Alhaji ELYakub ya shiga maganar sannan aka kashe auren, wannan abin yana faruwa, mutane suna ganin don dan uwan mijinka yayiwa yarka fyade ko danka namiji ba wani abu ba ne a rufe kawai don kada a ji kunyar duniya, maganar gaskiya Case din Jasminah bata fada ba ne, amma da shi kanshi Turakin ya matsa mata da tambayar me take ta ce ita saki take bukata, sai da ya sha mamaki da ya tambaye ta reason? Bata iya boye mishi ba, haka tayi ta kuka ta ce mishi. ""Hamma Bilal ya lalata min yarinya ga infection da take fama da shi, Hamma wallahi idan ja cigaba da zama da Fahad zan kashe shi na kashe kaina, saboda a duk lokacin da na kalli yarinyar ji nake kamar xan mutu, ji nake rayuwata ya ™are, taya xan zauna a gidan da aka min laifi kuma aka nuna ba laifi ba ne?"" Tabbas a lokacin jininsa ya haura dubu ko miliyan domin da yana Nigeria ya san wannan abin tow wallahi dai ya cirewa Yaron nan gaba, domin a duniya ya tsani abinda zai tab'a na shi, a tunaninsa mole dinta da yake ba wani can bane a yiwa tufkan hanci ashe har kashe mishi y'a yayi da ransa. ""Idan aka kashe auren shi kenan?"" ""Idan ka min haka zan tabbatar da maganar Abba da ya ce, na daina jin zafin ka kai Ubana ne wata rana."" Kashe wayar yayi ai kuwa aka sake bude sabon case wanda ya shafi zuwa asibiti tare da bincike mai tsanani, sanin cewa idan case Win ya kara girma media ta san da zance Familyn Noma zasu iya rasa abubuwa daga political zuwa wasu power din da suke da shi, sannan zasu kara rasa wasu abokan kasuwanci da suke da tarihin sa a garin Lagos, don haka Uban Mijinta ya zauna da Fahad ya bashi takarda ya sake ta, sannan ya kai tare da niman alfarman ta janye maganar shigar kotu. Dakyar suka shawo kan turaki kawu manya yadda ya kafe daga can yana tsara kome sai ka rantse da Allah yana kasar ne, shi kan Alhaji Mudansir ELYakub cewa yayi yana kasar Iskanci ne irin na rikakken dan duniya, bayan auren ya mutu aka yi ta barka a nan yake gaya musu, duk ranar da ya iso Nigeria dai ya cire gaban yaron wallahi, kai shi fa aka" taba mishi ya dai ya kashe mutum wannan alkawari ne. *** Bauchi. "Shekara daya kenan da bikin Hafiz da Matarshi mai suna Nana, yarinyar yar lukuta da ita, don Hafiz yace" "mata sirara basu da aiki dai jaraba ita katuwar mace abu biyu ne kana fara tarayya da ita zata ce ta gaji kaima kuma dama ba wani jan lamarin yake da nisa ba, sai zaman yayi kyau. Sai dai wannan karon za a" "iya cewa Nana irin mugayen matan nan, kamar yadda Karimah da Yaranta suka yi ta kassara rayuwar" "Lubnah ba, ita kuwa Nana kassara mishi Yara take a hankali, gashi sun tashi daga zango sun dawo dutsen tanshi, bayan gidan Baban Bauchi, idan har ya saka kafa ya bar gidan abincin ranar da na dare a cikin gidan Baban Bauchi take karba saboda ita amarya ce ba zata fara girki ba, sai ta haihu. Idan ta karbo abincin nan Yaran nan loma biyu take basu, sannan wani abu da ta tsarawa kanta gidan a rufe yake bata barinsa a bude yadda babu wanda zai ga Yaran yace suna cikin wani mugun hali, na biyu idan zasu makarantar boko zata zuba musu abinci tare da ja musu kunne suka cinye abincin sai ta tona rami ta binne su. Wannan ya kara saka musu tsoronta, domin ta gaya musu ai Mamansu mutuwa tayi shi yasa" "ba zata tab'a ganinsu ba, suma ba zasu tab'a ganinta ba. Yusra duk bakinta sai gashi ya mutu." "Nana muguwa ce, idan Hafiz ya dawo zai samu suna cin abinci ne, yana shiga ciki zata dawo ta ce musu." """Na samu kun lamushe sai na yanka ku!"" Tana da wata wukarta me sheki, haka sai ya firgita Yaran basu da katabus sai yadda ta ce, shi kuwa Hafiz gani yake tana kula mishi da Yara. Amma a zahirin gaskiya duk wanda ya kalli yaran sai yasan suna ciki. Azabar rayuwa da ukuba ita dai bata duka amma fa yaran suna" girban abinda Uwarsu tayi da Ubansu Yadiko ce kawai ta fahimci halin da Yaran suke ciki domin kuwa ta tab'a zuwa gidan Nana tana barci ya "buga kofar Yusrah da take tsallen kwado, tayi kuka ta yi zufa sharaf, ta ™asa tashi sai Yasir ne ya zo ta buWe kofar Yadiko ta ga halin da suke ciki salatinta ne ya tashi Nana ta fito tana zare idanun tasan ma karya tayiwa Yadiko reni domin ya gaya mata koda wasa kada ta ce zata rena mishi iyayen Lubnah domin zata dawo, ita kuwa ta saka a ranta ko mutuwa zai yi ba shi ba wata Y'a mace. Yadiko tayi ta mata fada tana nuna mata illar abinda ta aikata tayi ta bawa Yadiko hakuri ba zata kara ba, haka yasa Yadiko ta" watsar da lamarin don be shafe ta ba. Bauchi Central Market* U.U.J textile and fabric "Shagon sayar da kayan sawa irinsu atamfa da shadda, lace, da sauransu. Sannan yana da shagunan" sayar da kayan wuta irinsu tv da sauran electric. "A gaban wasu tika-tikan shagon sayar da atamfofin wasu yan mata ne suka zo fitar da Ashobe, yadda" "daya take wani yauki zaka Wauka karkashi ce, tunda ya ga Hafiz take wani kashe murya, shima kuma ya fada mata domin yana masifar son mace yar gayu lokacin baya shi da Lubnah idan tayi gayu ba karamin tafiya da duk wani lissafinsa take ba, shi yana son mace mai gayu duk muninta, ko Lubnah abinda yasa shi ya daina ganin gayunta wannan shegen kibar da ta yi sanadin maganin hana daukar ciki da yayi ta" "bata, amma idan tayi kwalliya kamar ya boye ta yake ji, wannan kallon da yayiwa yarinyar ya dawo mishi" "da Lubnah haka yasa shi kallon zoben hannunsa. Yana nazari da shaukin yadda zai hadu da Lubnah, duk" "ranar da suka hadu kuwa duk rintsi ba zai tab'a yarda ya barta ba, sai ya dawo da ita rayuwarshi tsamo- tsamo......." (Hafiz kada ka ja min lukutar masifa don Allah Innalillahi wainnalihir rajoun ) "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 31" Shi hala dole fa sai ya dawo da Lulu gidansa hankalinsa zai kwantar. Daya daga cikin yaran shagon mai "suna Ukasha ya ce mishi. ""Oga Ashobe suke suna son wannan atamfar kamar turmi hamsin."" ""A duba idan akwai a saka sunan Amaryan da Unguwar da suke."" ""Tow!"" Ukasha ya samu Amaryan da kawayenta. Daya daga cikin yan mata ta ce mishi. ""Babu ragi ne? Muna son cotton da roba ne?"" ""Akai cotton 9k Akwai roba 5500 yake!"" Juyawa Amaryan tayi ga wannan kawarta ta ce mata. ""Mansi kin ji kudin kayan yayi?"" Wani juyawa yarinyar tayi cikin yauki da yanga ta ce mata. ""Duk yadda kika ce haka za ayi."" Murmushi Amaryan tayi tana kallon Ukasha ta ce mishi "" shi kenan ka gaya mishi muna so amma kuma. "" "" Bari na mishi magana! "" Ita Mansi ta samu Hafiz cikin yanga tana mishi bayani, kallo daya yayi mata ya dauke kai yana faWin. "" Ki bawa Ukasha number wayarku da za'a saka jikin kayan. "" Ya fita daga shagon, binsa tayi da idanu, duk wannan abin da take Baban Bauchi yana kasuwa duk iskanci da fitsaran Hafiz baya tab'a yarda ya gwada halinsa a gaban Baban Bauchi, domin ya iya takusan, Alwala suka yi tare da Baban Bauchi suka nufi masallacin da yake cikin kasuwar, amma a ransa ya kyasa da yarinyar addu'a" "yake yasa Ukasha ya amshi number yarinyar. Nana yar uwarsa ce amma yau ganin Mansi ta fama mishi ciwon Lubnah tana budurwa yar shaf-shaf da ita ba kiba ba tarin tumbi, ga ta kamar ka goyata ka gudu da ita. Don haka idan ya koma kafin a tashi sai ta amshi numberrta yarinyar ta matukar burge shi. Don haka yana komawa ya dauki littafin da ake saka sunayen yan Ashobe ya gani sannan ya ajiye bai kuma bi" ta kan zancen ba. Bayan sun tashi Baban Bauchi da Hafiz suka wuce kasuwar wunti inda nan ma aka zuwa wasu kayan. Sai "da ya gama ganin yadda kome yake tafiya sannan suka fito tare a gidan ya sauke Baban Bauchi tunda ya dawo dutsen tanshi ya zama kamar driban Baban Bauchi. Buga gidanshi yayi Nana tazo ta bude. ""Sannu da zuwa!"" ""Yawwa!"" Ya shigo tana bin bayansa a parlourn ya samu Yusrah da Yasir suna cin abincin,, kallonshi suka yi ya wuce bai musu magana sai murmushin da ya musu. Suka cigaba da cin abincin, har ya fito suka mike tare da cewa. ""Aunty Mun koshi!"" ""Sai kun cinye kullum haka kuke barina da abinci!"" ""Kyale su sun koshi ne, ba ayiwa yaro dole ya ci abinci."" Cikin mita ta ce mishi ""shi kenan kana son ka bar ni da abinci."" Haka ta saka yaran a gaba suka wanke hannu suka tafi dakinsu, suka kwanta. uban ya gama" abinda yake ya fita. "Tunda ya sauke Baban Bauchi ya ce mishi. ""Jeka yau naga yaran nan ne a gidan zuwa an jima ka dawo" "ina son mu magana."" Gyada kai yayi yana faWin.. ""tow shi kenan!"" Ya juya zuwa gidanshi, babban" damuwar Hafiz ya san me yake faruwa a cikin gidan yadda yaga motar Umar da ya sauya wata Jeep "Cherokee Ave, shi fa Umar tun da ya bar shagon Baban Bauchi Allah ya haWa shi da wani Imyamuri suka fara sana'ar mashina sai gashi Allah ya yi sanadin mutumin nan hanyar arzikinsa yake, haka yasa kome ya" tab'a yake da albarka. Dalilin zuwan su kuwa bikin Ya Sani da bude shagon shi na sayar da kayan maza a winti na biyu yana "saro agogo da wayoyin zamani a China, kusan shekarar biyu kenan ya fara da sayar da takalma ne, sai ya fara gwada dinka kaya yana sakawa tare da daura hoton a IG da Twitter, Allah da ikonsa da buwayarsa kasancewar Uwa tana tare da da shi, yan uwansa kuwa masu hadin kai ne, sai gashi cikin buqatar mai kowa da kome ya bunkasa ya isa inda ba a zata ba, yanzu haka yana iya dinkawa ango kayan fitar biki, don bikin da aka yi kwanan nan dan gwamna Bauchi state, shi yayi ta kula da shiga da fitar angwayen, ba karamin kudi ya samu ba. Dama yana taru wurin Aunty Hindatu, ai kuwa ganin haka ya samu kudi aka kara mishi ya sake habbaka kayan auren, da sadakinsa da kome na shi, yana nan a hannu yanzu sun zo" ne a gayawa Baban Bauchi shirinsa. Shine ya gayyaci yan uwansa. "Bayan sallah isha, suka hadu a parlourn Baban, suka gaisa aka yi yan hira sama-sama, kafin Umar ya" "kawo zancen da ya haWa su. Daidai shigowar Hafiz da ya koma gefen Baban Bauchi ya zauna kamar zai koma cikinsa tsabar munafunci, ran Tahir ya b'aci. Shiru baban Bauchi yayi kafin ya ce musu. ""Tow Allah ya nuna mana, amma naso da zaku amince da Firdausi, domin naga ai yarinyar itama."" ""Abba Yarinyar da yake so ba jiya suka hadu ba, ba yau ba akala sun kai shekaru hudu suna tare, don tun tana makaranta suka hadu, yanzu kuma sai a kawo wani batu Firdausin da."" ""Tunda kun shirya mishi yadda zai me yasa zaka kawo min batun amincewata."" Yadiko da take bakin kofa ta ce mishi. "" Ai kasan kuwa yadda ka hana Sani zaman shagonka wallahi ba ka da hurumin bashi abinda baya so, Lubnah ma da ya ta kwashe a hannun Hafiz kai ku tashi idan yaso kada ya bashi kwandala yarona ya yi duk wani abinda ya dace wa" "kansa ko ni da na haife shi bai jira ni ba, haka kuwa ba wanda zai mishi dole!""" "Wani irin rikici aka shiga tukawa aka kuncewa, kafin kuma aka kyale kowa yayi yadda ya so, Baban" "Jama'are ya zo da wasu maza , wanda suke dangin Yadiko aka je nimawa Sani auren Halisah, yarinyar danginta yan Tilde ne, don haka suka tafi aka nima mishi aurenta, ganin yadda suka fito daga babban zuri'a kuma yaro yana da abin yi sannan shima Uban yarinyar ya shirya tsaf, kawai aka karbi sadaki da" yanke rana. Wannan lamarin yayiwa kowa dad'i domin domin kuwa dangi kowa ya fara shiri. "An saka ranar bikin wata uku masu zuwa, a cikin wata ukun gidan da Abban ya bashi wanda yake" "kusa da gidan Ya Umar, aka fara gyarawa ana cire tsohon tsarin gidan, aka fara yin gyaran na zamani. Cikin kasa da wata guda da sati biyu aka gama gyaran gidan." "Ashobe kuwa a shagon Aminu da Zubairu, Innah ta cire aka kai dinki na su Lubnah domin Mama ta ce" dole ta zo. *** Lubnah. "Bikin sani zai zo lokacin mun gama jarabawa, sai dai har zuwa lokacin gabana yana faduwa da maganar" "zuwa Bauchi. Domin gani nake kamar duk wani abu zai kara faruwa, haka na sake raina na cigaba da abinda yake gabana. Duk da na dan sauka kaWan, amma kuma ni kaina sai nake ga kamar da sauran yanayin domin jikina yana min nauyi, wani lokaci haka zan ta fama da haki, sau biyu ina zuwa ganin likita da Dijah Bala take hada ni da su, na farko ya ce kitse ne ya taru a zuciyata, na biyu kuma yace wai a cikina sai abin ya saka ni rud'ani, na shiga cikin wani irin tashin hankalin mara misaltuwa nayi shiga, na rasa me ke min dad'i. Ban gaya Ya Ado ba, don yana gayawa Mama zata iya cewa ayi aikin yaushe aka cire min karin mahaifa yanzu kuma wani aikin ni na koma kamar wata kazar mayu, ga shi na daina ganin Baby sai kaina yayi zafi,, ranar wata Alhamis na tafi wurin Dr Dijah Bala. Ta kalle ni a hankali, tana faWin.. ""Ni na ga kamar kina cikin damuwa?"" Jinjina kai nayi a hankali ina wasa da yatsun hannunta. "" Me yake damunki? "" Gyara zama nayi na rasa yadda xan yi magana domin har yau bani da kwarin gwiwa yin dogon magana a gaban jama'a, duk da tana kokarin nuna maka kai ma mutum ne kana da damar fadar abinda yake ranka. Matse hannuna nayi ina motsa bakina nace mata. ""Nan da wata biyu za muje Bauchi bikin Yayana!"" Murmushi tayi tana kallon yadda na matse hannuna da ™arfi. Na kasa fada mata abinda nake son fada, gogewa da tayi da masu irin laluranmu yasa ta matso da kujeran kusa da ni ta rike hannuna da kyau, ""ina tsoron kada Abba ya ce ki koma gidan Hafiz ko?"" Hawayen da nake dannewa ne suka shiga wasan tsare akan fuskana. Cikin shashekar kuka na ce mata.""ba iya shi ba ina tsoron abinda mutane zasu ce ne."" Nan ma nayi shiru ina kallon gefe, jinjina kai take a hankali ta ce min. ""Mutane sun daina maganar kina da kiba ne?"" Da sauri na d'ago kai ina girgiza mata. ""Ashe kuwa tunda basu daina ba, akan me zaki yi kuka? A yanzu Mama da su Barista suna tare da ke, tare da su Innah da Hindatu. Kina jin zasu bari a mai dake gidansa ne? Kada ki manta har yau baki yarda da kanki ba ne. "" Kallonta nake, "" har yau baki yarda kina da goyon bayansu ba ne, baki sani ba ko?"" Hawaye ne ya zubo min, gyara zama tayi tana juyawa akan kujeranta ta cigaba da cewa. "" Me yasa Ahmad ta daina zuwa?"" Shiru nayi ina kallonta na zata ko don an mishi magana ne, girgiza kai tayi tana kallona kamar tasan abinda yake raina ta ce min. "" Kina tsammanin Barista ya hana shi zuwa? A'a ni na gaya mishi ya rabu da ke, a halin yanzu ba namiji kike bukata ba, kanki kike bukatar you need tow love yourself."" Cigaba da kallonta nake, ta mike tana mai isa gaban frij ta dauko min ruwa ta ajiye min tana faWin. ""Har yau baki san yadda zaki kwanci kanki ba, har yau baki san yadda zaki yi fada don kanki ba, yaushe kike tsammanin zaki iya zaman aure bayan nasan wacece matar Ahmad, ya zo nan ya gaya min kin ki kula shi nace mishi ai ke yanzu baya ga kanki bakya bukatar ™arin wani a rayuwarki. Sannan idan ya nace ya aure ki rayuwarki ta baya zaki koma, me yasa muna janyo ki present zamu mai daki past dinki? Daga lokacin da kika fara sanin ciwonki, a lokacin zaki fara tantance waye yake kallonki da idanun basira waye yake kallonki domin biyar bukatar kanshi, ni na gaya mishi ba zai iya gina soyayyarshi yadda ya dace a tare da ke ba domin zuciyarki a rufe yake. A" "duk lokacin da irin wannan abin ya faru ana bawa masu irin matsalarki lokaci ne, don haka kina da lokaci" "ki cigaba da kula da kanki da lafiyarki. Sai me kuma?"" Shan ruwa nayi kafin na gaya mata yadda muka yi" "da likitoci biyu. Murmushi tayi tana faWin, "" na gaya miki dole ki shiga ajin motsa jiki, kina cin abubuwan da na hana ki ci, har yau baki ware abinda zaki ci don lafiyarki ba, da kin kula da haka da tuni wata" "Lubnah ake magana ba wannan ba.""" "Sai na ji kamar nayi knocking heart dina tare da bude kofar ta ce min farka Lulu. "" Yes dole ki fara motsa" "jikinki, ki biya kuWi a unguwarku ai akwai inda ake motsa jikin, sai ki fara ina son na ganki nan da wata biyu."" Kallonta nake ta yi cike da mamaki. "" Kina nufin. Idan nayi zan samu lafiyar jikina? Amma kuma ai kunya nake ji wurin za ayi ta kallona."" Na fada kaina a sunkuye. "" Kina jin kunya ko? Kada a miki dariya, bari na haWa ki da wani yaron da na sani sunan Wasim!"" Gyada kai nayi ina wasa da yatsuna, har ta kira Yaron ta gaya mishi, ashe a unguwar yake ta bani number wayarshi. Sannan na mata sallama na dawo gida, bayan na yiwa Ya Ado bayani ya ce gobe zai tafi har wurin da kanshi ya ga yadda Gym din yake, haka muka kwana ina ta addu'a Allah yasa kada na samu matsala da kowa Allah yasa na kasance jaruma wacce zata iya daukar duk wata matsala, wurin karfe tara na gama shirin zuwa makaranta Ya Ado ya kira ni ya ce min. ""Ki je zasu baki wasu tips and abincin da zaki ci, sai ki amsa idan kin dawo muje a saya ko?"" ""In sha Allah zan amsa kafin na tafi."" Na fada ina shiryawa, bayan na gama na fito na nufi titin unguwar" "da kafa, na je shagon babba ne na gaske....." "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 32" "A hankali nake tafiya ina kallon mutanen da suke wurin karti ne majiya karfi, sai yan mata yan gayu masu" "kyau da su, sai na ji na muzanta, gasu gwanin ban sha'awa yadda suke wani yauki zaka fahimci yan gayu ne da basu son tara kitse, wannan yanyin ya dauke kin dan kwarin gwiwa da nake da ita, a hankali na isa ciki tare da tura kofar sai aka bude ta ciki. ""Lubnah ko?"" Gyada kai nayi ina mai kallon cikin wurin yadda kowa yake rayuwarsa. Wasu suna motsa jiki wasu kuma suna hira can gefe da aka saka wani abu kamar labule mata ne a zaune suna yogo. A hankali nake bin wanda ya min magana, wani office ya bude mana, wata kyakkyawar bakar mace cikin shigar kamala da mutunci zata iya kaiwa arba'in amma yadda take kula da jikinta ba zaka Wauka ta kai arba'in ba, da murmushi ta kalle ni. ""Lulu!"" Ya kira sunana, sai na ji na samu nutsuwa da ita, na gaida da ita murmushi tayi ta ce min. ""Adam ya ce min wai auta zai kawo?"" Sai na rasa a ina na santa, kurban tea dinta tayi tana mai ajiye min wani kofi a gabana. ""Baki sani ba don tun kina yar yarinya muka bar Bauchi!"" Zama nayi ina gyad'a mata kai. ""Sunana Nuratu Abdulfatahi kin tuna gidansu Kafaya?"" Sosa kai na fara ina kallon kasa na tuna gidan har yau ana kiran gidan da sunan. ""Nice Kafaya."" Sai na ji kamar an yantani daga wani yanayi na musamman, muryanta na ji a kaina tana tura min cup of tea din. "" Lokacin da Dr Dijah Bala tayiwa Wasim magana ban san cewa ke ce ba, da nace kawai ki zo, sha kada ya huce "" dauka nayi na kurba ba sugar sai kamshin kayan kamshi, da lemon tsami. Da kamshin ganyen tsamiya. "" Tea din ganyen tsamiya ne, yana taimakawa. "" Ta fada tana murmushi, haka na sha sannan ta cigaba da cewa."" Adam yazo wai biya miki, kawai aka turo min shi OMG kin san rabona da Bauchi shekaru ashirin kenan fa yau ga sai dan Bauchi kuma Wan unguwarmu, dan abokin Babana."" Murmushi tayi kafin ta sha tea din nima rashin sabo yasa na sha kaWan..""Bayan rasuwar Babanmu muka dawo nan, Mamanmu ta cigaba da kula da mu har na samu miji nayi aure" kasancewarmu Yarbawa da aka haifa a cikin arewa sai muka taso da dabi'ar yan arewa bamu manta da "yarenmu ba."" Shiru tayi tana kallon yadda nake kallon tea din. "" Kada ki damu zaki saba da shi."" Ta fada" "tana murmushi, ""Na auri wani dan uwana kuma kabilata, sai dai zamanmu bai yi dad'i ba haka muka rabu da dakyar shima ba ni ce na nime saki ba, mun haifi yara biyu da shi, kamar yadda kike gabana haka nima na kasancewa. "" Sunkuyar da kai tayi ina ganin yadda take dauke kwallar da yake zuba mata, haka na rabu da shi na cigaba da rayuwa, sai Allah ya haWa ni da wani dan kasar ghana yazo nan yana kasuwanci ya koma, wani abu da ya faru shine yadda aka yi ta cin zarafina da kibar da nake da shi."" Ta kalle ni yadda nake kokarin toshe bakina, saboda kukan da yazo min. ""A lokacin kaf narasa wani wanda zai dafa min ga tsohon mijina da yake yawan d'aga min hankali, haka Mr Anwar wanda ya kasance bako a cikin mu, shi ne mutum na farko da ya fara kallona a matsayin mutum mai daraja, duk da an san cewa mijina shi ya sake ni don kanshi amma sai da aka yi ta hango gazawata da nuna min halayyata ce bai da kyau domin tunda ya sake ni bani da hali mai kyau ne, haka na cigaba da taimakon Mr Anwar ya gaya min cewa dole na rayu domin har na fara fama da ciwon damuwa, a irin haka na rasa Yarona karami a wani ruwan saman saboda ya je wurin Babansa, a hanya dawowa ya fada cikin lambatu, sai da na ji ina ma da nice na mutu, sai mace da take tare da ni, Mahaifiyata ta kaWai ta fahimci yadda nake rayuwa, hatta yan uwana sai da suka na tsani kaina na ji bana kaunar kaina. Wannan yayiwa tsohon Mijina dad'i" "bani da zabi dole ya cigaba da abinda yaso. """ "Turo kofar aka yi wata matashiyar budurwa ta shigo tana faWin. "" Momma! Daddy yana ta kiranki fa!""" "Daukar wayar tayi tana faWin.."" Tuba nake Sarkin da yake mulkar zuciyar Kafaya!"" Ban san me ya faru ba sai ga tana dariya tana faWin."" Idan ka sake na kama ka zaka sha wuya! "" Fita yarinyar tayi tana faWin."" Momma baku girma ke da Daddy;"" ta jima kafin ta katse wayar ta ce min. "" Sorry Mijina haka yake baya iya minti talatin bai ji muryana ba."" Murmushi tayi sannan ta daura da cewa. "" A lokacin na rasa kowa dai Mr Anwar shi ya tallafe ni da shawara da yadda zan tsaya domin har rasa aikina nayi, shi da kanshi ya bude min shagon saloon na fara Allah ya saka albarka a shekara daya na samu damar komawa makaranta, shi ya kara bani shawarar na rage jikina, ina cikin haka sai ya bijiro min da soyayyarshi, duk yadda naso kauce mishi haka ya shiga duk inda xan ji maganar mutane, yayi min hidima da ba xan iya tsallake bu™atarshi ba, a lokacin na tsaya da kafata da taimakon shi na san wacece ni, bai taSa nima na da wani fasikanci ba, sai dai gina ni da yayi da soyayyarshi wanda ya saka na fahimci kaina na fahimci ashe nima mace ce, tunda ni na bukaci mu yi aure idan har da gaske yake, bayan wannan yarinyar da take waje, Nasiba, sai Abdullahi da Hafsa, da na haifa da shi. Sannan shi ya kara tsaya min har na bude nan ina aiki da ma'aikatan gidajen kurkuku na jahar nan, a can na hango Mijina Babansu Nasiba, kinsan me yasa na baki labarin nan?"" Girgiza kai nayi, ina share kwalla murmushi tayi ta ce min."" Saboda ki gane kafin ki zo nima ban gina nan domin niman kudi ba, sai da labarina ya gina min nan, asalin nan Labarina ne ya gina min shi ™addarata tana da nasaba anan, a duk lokacin da aka kawo sabuwar daliba abu daya nake tambayar me ya kawo ta me yasa ta zo? Idan tana da past dinta Mai duhu sai na daura mata nawa labarin ta gane nima ban gina nan ba sai da nawa labarin, akwai mata victim irina da irinki, anan muke bude zuciyarmu, ki saki jikinki Adam ya gaya min kome ya kuma bukaci mu taimaka miki, idan har da gaske sauya kanki ke kanwata ce dole na baki special class domin bana son na hada ki da kome, na tuna lokacin da Babanmu ya rasu har kudin da aka biya na motar da zaa dawo damu Alhajinku ya biya mana hatta abincin da zamu ci na tsawon wata shida, kafin mu bar tsohon unguwarmu Alhajinku yana mana aika duk bayan wata shida, kayan abinci da sutura daga baya fitinar dangin Babanmu yasa muka bar" "unguwar, daga muka rasa taimakonsa. Yau ga Lulu da na tafi na barta tana Yar shekara shida a gabana!""" "Murmushi nayi ta ce min.."" zaku school ko?"" "" Karfe bakwai muke tashi idan kin taso sai ki zo ki amshi" "tips dinki! "" Godiya na mata sannan na bar office din, sau yawa mukan yi alkhairi ba tare da mun san zai dawo ko ya tafi ga mizaninmu, duk da abinda Abba yayi amma yau alkhairinsa da rokon marayu ya saka na samu nima wata alkhairin da shi ya aikata. Murmushi nayi duk da laifinsa yau naji ina sonshi ina kewarsa. Don haka da na shiga motar da zai kai ni makaranta, na fito da wayata ina kallon wayar number shi ne don ko na rasa number kowa bana iya manta number shi da Yadiko da Mama, haka nayi ta kallon wayar. Har muka isa makaranta na biya kudin na fara tafiya, sai da na shiga makarantar sannan na samu wuri na zauna. Da yake karfe daya zamu shiga class na kira Number Abba, haka wayar yayi ta ringing bai dauka ba, na sake kiran bai dauka ba, sai a karo na uku ya Wauka. ""Waye ke kira haka?"" Haka yayi ta magana na kasa magana sai hawayen da yake zuba min haka ya gaji ya kashe shi wayar, kuka nayi ta a wurin na rasa abinda yake min dad'i, sake kiran Mama nayi tana dauka na ce mata.. ""Mama ina kewar Abba ina son ganin Abba Mama ina son Abbana, Mama ki koma wurin Abba ko don ni, Mama ina son Jin muryansa da farin ciki da annashuwa, amma na rasa Mama."" Abinda ba zai tab'a sauya our Afrika mother, wato da ta danna min wani Ash'ar tare da zabga min warning idan na kara kiranta akan Abba sai ta ci Ubana sai na tsinci kaina da yin shiru, ban kara magana ba, kai na ga jidali da lukutar masifa, tass ta wanke ni kafin kuma ta sauko tana rashina, daga haka nayi shiru bayan mun gama waya sai ga kiran Aunty Innah ina gamawa Aunty Hindatu ta kira ni, sai ga Ya Umar da Tahir, ban gama nutsuwa sai ga Ya Ado. Ina zaune a wurin ya kira ni na dauka ya tambaye ni ina aji ne? Nace a'a gani a lambun makaranta bari na fito, har a lokacin kuka nake a hankali na dauki jakata na fita yana tsaye ina isa wurinsa na goma gefen da yake tsaye na kifa kaina a gefen hannusa ina kuka. ""Kina kewar Abba ko?"" Jinjina kai nayi, kiranshi yayi bayan sun gama gaisawa ya ce mishi. ""Abba kai min wata alfarma daya?"" ""Ina jinka!"" ""Zaka yi magana da Lulu ne tana kewarka, gata nan."" Kafin ya kara magana ya manna min wayar a kunnena, sai dai kuma nayi danasanin kiran Abba da Ya Ado ya min, Abba ya kara watsa min bakin fentin da ba zan tab'a mantwa da shi ba, sau gani ina wani irin hakki zuciyata, ta kasa Waukar mugayen kalmomin Abba, tun ina jin shi a tsaye a har na jingina da motar na zame kasa, domin kafana sun kasa Waukar nauyina, zuciyata ta gagara daukar maganar da Abba yake gaya min, wani irin nauyi na ji tare da bude bakina ina niman numfashi, fisge wayar Ya Ado yayi ya saka a kunnenshi ya ce mishi. ""In sha Allah ba zan kara kiranka akan Lubnah ba, ba zan kara ce maka ga ta ba, Abba idan ka yi sanadin mutuwar Lubnah Allah ba zai barka ba!"" Kashe wayar yayi ya d'ago ni tare da saka ni a motar domin har an fara taruwa, ruwa wani dan ajin mu ya mika mishi yana faWin. ""Bata tana bukatar ruwa!"" Amsa yayi ya bude min ya kafa min na shanye, sannan aka kira class rep dinmu aka gaya mishi halin da nake ciki ya ce a je da ni gidan, da taimakon Allah na samu nutswa, daga haka na rufe idanuna, a hanya Ya Ado ya kira Mama ya gaya mata, halin da na shiga amma bai san me Abba ya gaya min ba, ai kuwa Mama kamar ta dirko ta wayar fada take yi kamar zata aro baki ta kara. Kuma tayi alkawarin sai ta kunyata Abba shima kamar yadda ya min a" gaban Jama'a domin ranta yayi mugun b'aci..... (Kuna ganin mu bar Mama tayiwa Baban Bauchi tijara a bainar nasi? Yes or no "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 33" "Gida Ya ado ya kawo ni na kwanta, duk da bana jin barci amma na zaSi nayi lumo. Ina jin kamar na ni ba," "taya mahaifin da ya haife ni zai tsane ni ya kira ni da karuwa? Abba ya kira ni da karuwa! Naki zaman aure na biyewa Adamu ya yanka min tikitin karuwanci a lagos, tow in sha Allah idan n kwaso kwanjamau sai dai na kare ni daya na domin suma guduna zasu yi. Bude idanuna nayi tar ina kallon hannuna. Wani irin sarawa kaina yayi kamar an hada karfe da karfe a hankali na ji abu yana zubewa daga hancina, ban kula ba sai da na ga zubar yayi yawa na tashi zaune ashe jini ne, yadda kaina yayi wani irin nauyi haka na koma na kwanta tare da lumshe idanuna, bana son karawa Ya Ado wani damuwar a hankali nayi ta ambaton Allah har na samu sauki na tashi zuwa ban daki na sakarwa kaina ruwan sanyi, can kuwa jinin ya tsaya, na jima a ban dakin na fito na sauya kaya. Na sauko kasa ba kowa sai mai aiki haka na zauna a" parlourn har lokacin sallah yayi na wuce nayi sallah na kwanta barci ya dauke ni. *** "Mama kuwa da suka gama waya, tashi tayi gaban wardrobe dinta, kayanta tayi ta sauko da shi, ta ciro" "wabujejen wando mai matu™ar girma kamar palazzo, ta saka ta dauko wani babban hijab dinta ta saka, sannan ta fito zuwa bangaren Umar ta bugawa matar gidan kofa da sauri aka bude tana ganin Mama ta ce mata. ""Mama ke ce? Fita zaki yi? Lafiya dai?"" ""Central zan je!"" ""Lafiya dai ko? Ai da an gayawa Baban Nawwara ya miki ba sai kin je."" ""Yanzu xan dawo"" ta juya ta fita yadda zuciyarta take tafasa idan ba tsinkawa Abba rigar mutunci tayi a idanun duniya ba, ba zata tab'a jin dadi ba. Don haka ta nufi waje," "tana fita matar Umar tana kiranshi, sai aka yi rashin dace ya shiga sallah, baya kusa da wayar ma." "Mama kuwa tana fita ta samu me keke napap, ta ce ya kaita Central ya fada mata kudin bata damu ba," "ta ce su je. Kawai yadda zata yiwa Abba rashin mutunci kawai take hasashe. Duk da gudun da me Napep din yake amma Mama gani take kamar ba tafiya yake ba, kamar ta rufe shi da duka haka take ji, haka ya sauke wasu mata a unguwar Jaki, sannan ya fito ta masallacin Shehi dahiru Usman Bauchi, ya iso daidai office din Yan sanda na Central ya tsaya ta fita ta biya shi kuWinsa,. Sannan ta tsallaka cikin Central, sai da tayi tafiya sosai kafin ta isa layinsnu Baban Bauchi, an taru a kofar shagon ana cin abincin da ake kawowa kasuwa kullum daga gidan domin saukakawa Yaran shagon kashe kudin abincin. ""Usman Jama'are nazo wurinka ne?"" Da mamaki kowa ya juya yana kallon Mama. Wacce ta hade rai sosai kamar ba ita tayi maganar ba. Da kamar ba zai kulata ba sai can ya ce mata. ""Ki je gida zan zo!"" ""Ba isa ba! Ka gaya min yaushe ka ci maita da kake son kashe min Y'a? Mai Lubabatu tayi maka da zafi har haka?"" Shiru yayi kai dan kanzagi ya taso yana faWin. "" Mama kasuwa ne nan don Allah ki yi!..."" Tass Mama ta wanke shi da mari, ta kara wanke shi da mari sai da yayi baya kamar zai fadi, Baban Bauchi ya ce mata. "" Wacce irin hauka yake damunki? "" "" Irin wanda kake dauke shi! Irin wanda yake kanka, irin wanda ya saka ka yi fatali da zancen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kowa Ni shugaba mai kiwo ne, kuma za a tambaye shi akan kiwonshi. Gaya min kuskure ne don na kashe Auren Lubnah da wannan Tsinannen yaron da ya bata maganin hana haihuwa? Laifine don ka kashe aurenta da azzalumin Yaron nan da ya nemi haukata min ita? Me yasa Victims na mata yafi na maza yawa? Me yasa? Yau da Lubnah daukar wuka tayi ta soke shi wannan shagon ka rufe shi kenan saboda abin kunyar da tayi, amma daure ta yayi a cikin gidansa yana gana mata azaba, muka rufe idanunmu saboda zumunci! Eh kalmar zumunci tana" "daga cikin sunayen Allah, gaya min me yasa ka saka min ita cikim Ukuba? Yau ni Salamatu Galadima na" "zo gabanka da muryata da Muryan Y'ata, idan wani abu ya same ta. Zan tabbatar da na tab'aka na kara" "tab'a ka sai na mai da kai zero plus zero yadda kowa sai ya yi tir da kai. "" Wani abokin shi ya ce mata. "" Hajiya don Allah ki yi hakuri a karasa a gida don Allah, anyi miki laifi muna rokon arziki a bar maganar nan! "" Ta kalli mutumin ta ce mishi. "" Alhaji Imarana! Idan maita ce ni da shi Bismillah, idan kuma ina ganin babu maitar hali ce kawai Ni dashi shege ka fasa! "" Daidai isowar Tahir da Umar hankali a tashe. Har ta juya ta ce mishi. "" Usman Jama'are! Na rantse da Ubangiji Adamu da Muhammad, sai na tsayawa Lubnah, sai na bata kariya sai na hanata kuka akanka da shi wancan Tsinannen yaron, Usman Jama'are idan ka isa da Tsinannen Yaron nan kace ya fita harkan zuriarta ba Lubnah ba wani cikin Yarana wancan shegen. Ya kara mu'amala da su sai na yi Shari'a da kai da su. "" Har ta cigaba da tafiya ta juya cike da takaici ta ce mishi. "" Wallahi billahi azim na kara ganinka tare da Yarana sai na ga uban da ya tsaya maka a Bauchi, ku ai ba mutane ba ne dabbobi ne a cikin shigar mutane. "" Huci tayi kafin ta juya a hankali Umar da Tahir suna take mata baya ta juya tana kallon Baban Bauchi dariya tayi ta ce mishi.."" kamar yadda ka yarda min Y'a a cikin makaranta ka saka kowa ke mata kallon tausayi da hauka yau kai ma ka ji yadda take ji! Feel it I said it how lubnah she survived, ka ji kunyar da taji a duk lokacin da ta fita hayacinta,. "" Ya kara takawa har habansa "" how you feel it? Da kunya ko? Haka take kallon kowa yana jin tausayinta, kun mai da min yarinya wata iri ta koma kamar ba bil adam ba. "" Aunty Innah da suka iso kasuwar da Hindatu ta rufe mata baki, fisge bakinta tayi. ""Na rantse ba zan gushe ba sai na saka kowa yasan waye kai, kai ko ban ce maka Allah ya sakawa Lubabatu ba Allah sai ya saka mata, amma ba kome In sha Allah sai kayi danasani sai ka ji tsoron duniya da mutanen cikinta, sai ka ji kunyar kallon Lubabatuna, In sha Allah sai ta zame maka inuwar gajimare, shi kuma wanda ka daukaka kanta in sha Allah sai ya nuna maka iyakarka."" Daga haka Yaranta suka ja ta, amma yadda zuciyarta yake tafasa ba zata iya tafiya ba sai ta gumawa Abba takaici ta juya ta ce mishi. "" Ka ji kunya duniya da lahira, ta duniya mai gushewa ce ta lahira ita ce wacce zaka kasa kallon har Ubangijinka."" Yasan halinta amma bai taSa kawowa idan wani abu ya faru zata iya mishi tijara har haka ba, bai taba kowowa ko a mafarki haka zai faru ba, amma yau ta kunyata shi a gaban jama'a ta saka kowa yana shi da abinda ya aikata. Shi akan daidai yake kuma bai ga dalilin da zai saka ya sauka akan ra'ayinsa ba. Dayawan dattawan da suke wurin hakuri suka yi ta bashi haka ya bar shagon babu wani abin annashuwa, ranshi idan yayi dubu ya b'aci." "Karshe shima Hafiz sulalewa yayi ya gudu, domin yadda kowa yasan me ya faru, dama an ji aurensu ya mutu amma babu wanda yasan dalilin mutuwar sai yau kuma abin mamaki sai gashi an yi yadda yayi ta azabtar da yar uban rikonsa, a take wasu suka ce su ba zasu iya ba, abokansa da suke zuga shi da daura shi akan mugun hanya basu ce kome ba, amma an samu wasu kananan magana ya fara fita ai kuwa da gaske ne abinda ya faru. Dayawa sun tabbatar da haka, sai gashi mutanen da suke kallon Hafiz da wani mutunci sun daina, wasu ma har daina mishi magana suke domin gani suke ya koma shaidanin da ya raba zaman lafiya ga uban rikonshi, da yayi mishi gata wasu ai gani suke zai aikata domin kawai a ganshi" a wurin amma abinda yake aikatawa ya wuce tunanin me hankali. "........... Mama kuwa a motar Ya Umar aka kaita gida bata yi kuka ba, sai da suka isa gidan Yaran suka" "zagaye ta, ta fara kuka tana faWin. ""Ku kira Adamu ku ji halin da take ciki hankalina yana kanta!"" Lokacin" "da suka kira Ya Ado suka gaya mishi abinda ya faru, kiri-kiri ya ado ya goyi bayan Maman sannan ya gaya musu tana gida ya koma wurin aiki amma kamar barci take. Haka Tahir ya kashe wayar ya gwada kiran" "Lubnah da wayar Mama, a hankali ta dauka. ""Ya Tahir ina Mama? Ina lafiyarta lau?"" ""Gata nan tana ta" "damuwa ne ne halin da kike ciki?"" Daga can ta sakar mishi murmushin karfin halin ta ce mishi. ""Alhamdulillahi, ina Maman take?"" Ta tambaye shi, mikawa Mama yayi mikewa Mama tayi tana faWin.. ""Jinjira kina lafiya dai ko?"" Murmushi tayi tana faWin da sauki kaina ne kawai ke ciwo amma da sauki kin ga gobe xan tafi na amso abincin da zan fara ci na rage kiba, sannan zan fara motsa jiki."" Sai abin ya sakata jin yadda ta shanye kome ta shiga bata labarin abinda ya faru, murmushi tayi ta ce mata. ""Mamana kada ki kara fada da Abba a kaina, ki kyale shi fushi yake da ni zai sauko wata rana, nima kewarshi nake shi yasa amma ba zan kara kiranshi ba, ki yi hakuri kin ji na ki bin umarni ki don Allah ki yafe min!"" "" Waye ya gaya miki kin yi min laifi, Allah ya miki albarka, ke da yan uwanki don ki nutsu ki yi karatu har Allah ya baki lafiya."" Karshe sai ga Mama da ta gama kukan takaici ta koma hira da Autarta ta manta da wasu yaran a wurin, bakiWaya tattara kauna da tausayin ta daura akan Lubnah, sai da suka yiwa wayar fyade ta hanyar cinye katin tass, sannan ta ajiye wayar sannan ta tuna da wasu bayin Allah, nan suka yi ta bata hakuri da kada ta kara biyewa Abbansu shi yanzu kunyar zaman kasuwa ma ya ishe," "haka suka bar zancen aka shiga maganar bikin Sani," Ranar dai Baban Bauchi a asibitin kainuwa da yake nan dutsen tanshi ya kwana saboda yadda jininsa ya "haura, bayan ya dawo ya tara Yaransa bakiWaya ya gaya musu ya sallamawa Adamu Lubnah sannan ya cire Adamu da Lubabatu a cikin Yaranshi ya barwa Salamatu su, kamar yadda suka kashewa Lubabatu aurenta in sha Allah haka duniya zata musu alawadai da abin kunyar da Lubabatu zata kawo musu. Duk parlourn suka yi shiru Sani da yasan idan yayi shiru yayi munafunci ya ce mishi. ""Abba ba ayiwa Ubangiji kutse zanen ™addara da yasa alkalamin ya rubuta, ko kai aka hada da Hafiz sai ka yi kara amma lokaci ne kawai zai bayyana haka, Allah ya kyauta."" Shi ya fara fita daga parlourn domin idan ya cigaba da zama" maganar da zai fita bakin shi ba kyau kuma mahaifa ne ba ayi musu magana ta rashin Wa'a. "Bayan fitar sani yace duk wanda ya kara kula Mama da su Lubnah bai yafe ba, Yadiko da take waje tace" "mishi. ""Wannan dai ita ce ake kira karya domin ba zaka raba su da uwarsu da yan uwansa, kai kar ku sake ku dauki wannan maganar, hakkinku ku kula da Uwarku da Yar kanwarku, kune gatanta."" Yadda Yadiko ta nuna musu nasu kada su dauki maganar shi ya kara kwantar musu da hankali, yayi ta fada" "karshe a daren sai da ya koma asibiti, take Hafiz ya kira Jama'are ya gaya musu cewa ai ga abin da ya faru, sai ga yan Jama'are mota guda, a nan kowa ya nuna Mama bata kyauta ba, jinin halin da Abba yake ciki da kuma ganin yadda yake kwance bai da lafiya, Hafiz ne kanshi ko asibitin yasa aka yi ta zagin Yaranshi da nuna Hafiz ya zama gatanshi tunda gashi ya haife su amma Uwarsu tafi shi moransu, tunda gashi" "kowa ya juya mishi har Yaran Yadiko, suna tsaka da maganar Yadiko ta iso wayyo ai Mama ita nata" "karamar yaki ne, Yadiko da ta ji abinda suke fada da ta fara bala'i da cira kamar zata tashi sama............." "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 34" ' "Shi yasa Allah ya tsinewa mai tadda fitina, domin kuwa rigima sosai aka yi kamar za a daku, wai duk akan" "Hafiz da Lubnah. Ai kuwa lamarin har Jama'are, abinda ya dawo kunnen Mama aka yi ta cewa suna son kashe Baban Bauchi ne saboda dukiyarsa, domin su ci gado musamman Mama da yake ita ce Uwar Yara dayawa, wato ita fitina idan tana barci mafi alkhairi a barta ta cigaba da barcinta kada a tashe ta, amma wannan karon sun tashi lukutar masifa, domin Mama har Jama'are ta cimma Goggo Uwani da Talatuwa da suka haddasa rikicin, ta ce sai sun shiga kotu domin wanke mata suna, da suka ce tana son kashe musu dan uwa. Nan fa hankalin kowa ya tashi rigima ake yi tun karfe bakwai na safe har karfe biyar na yamma sallah yake tashin su dakyar da suWin goshi Mama ta hakura bayan manya daya daga Fada sun shiga lamarin, ta kuma ce a shata mata layi a tsakaninsu, idan wani magana ya fito ba zata yarda ba sai gaban kuliya manta sabo. Jin wannan abinda take shirin yi yasa kowa ya shiga hankalinsa aka fita" harkanta da Yaranta. *** "A cikin kwanaki biyu ko waje bana lekawa, zai yau da Aunty Nuratu ta zo da kanta. Sai na ji kunya ya" "kama ni, a hankali na sauko muka shiga mata hidima. Sai da ta Wan sha ruwa sannan take kallona. ""Ina ta jiranki ina lafiya?"" Murmushi nayi duk da rashin sabo a tsakaninmu, amma yadda take damuwa da lamarina yasa zuciyata sakewa da ita nace mata. ""Ciwon kai da habbo ya hanani fita!"" ""Kina yawan tunani ko?"" Kallon Aunty Zakiyah da ta kawo mata snacks nayi domin ta amsa mata da cewa. ""Ai kullum muna magana akan tunanin nan."" Kallona tayi can ta ce min. ""Duk abinda zai faru ba zai tab'a kai na baya ba, you need to move on. Kin tab'a tsammanin zaki samu freedom haka?"" Murmushi tayi tana kallon yadda na rike hannuna da juna. ""Ba laifinki ba ne, ™addara ce ta zo miki a haka. Sannan idan da kowani mutum yana da iko da ™addaransa da dayawa basu yarda ajn haife su a low background ba, amma da yake mu musulmai ne masu bin tafarkin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama."" Muka karasa salatin tare ta daura da cewa."" Me kike tsoro wanda da baki gani ba? Me kike gudu wanda da bai same ki ba, me yasa ba zaki yi accepting din kanki ba? Tsoro yana da kyau amma rashin karban kai shine asalin tsoron da ake gudu, dayawa masu kashe kansu a duniya tsoron karban kansu suke, accepted yourself, love yourself, and move on, idan kika yi haka zai matu™ar wahala wani ya rusa ki, ko yan uwanki zasu kara jin dadin you accepted yourself, zasu iya miki yaki ne idan sun ga kin karbi kanki a yadda kike, a duniya ma zata girmamaki ne idan kin amshi kanki, ko waye zai girmama ki ne idan yaga kin amshi kanki a yadda kike, duniya da mutanen cikinta basu damu da ka mutu ko ka rayu ba, damuwarsu shine taya zaka gaza a maka dariya, amma daga lokacin da kika nunawa Duniya zaki iya survive idan da mutanen cikinta, ko babu ita da mutanen cikinta zaki iya tafiya da kanki, daga lokacin duniya zata dawo bayanki, zata koma tana yayyataki ai ke jaruma ce, a kowani raunin dan adam zaka samu na kusa da shi sun bada gudummawar maganin warka da raunin, amma idan raunin ya gaza warkewa kowa zai watsa a kan rauni, ki kaunaci kanki, duniya sai ta kaunace ki. Ki koyo saka kanki farin ciki duniya sai ta taya ki farin ciki. Ki kashe tsoron da yake ranki sai ki tayi cikin sallama, idan har kika rayu da farin ciki babu wnada ya isa kallonki ya gaya miki magana, shi mutumin da yayi gwagwarmayar domin ya rayu don lafiyarsa zai matu™ar wahala bai samu soyayyar gaskiya ba, kina bukatar ki girma da kanki ba tare da wani ya ce shi" ya saka ki girma ba. "Open your heart and make a wish, kina son ki rayu ki ga idan Allah bai raya ki ba, ko da zaki yi addu'a" "matukar baki yarda da kanki ba, matukar baki saka yakinin ba tow babu inda zaki domin Allah yana amsar Addu'ar wanda ya yarda da shi ya kuma saka yakinin zai taimaka mishi, idan kika ga matan da suke gym din nan, akwai wacce mijinta har sayar da ita yayi ta tafi karuwanci, akwai wacce Mijinta watsa mata ruwan battery yayi bai samu fuskantar ba ya zube a bayanta. Akwai wacce kullum dukarta yake" "saboda ta haifa mishi yarinya handicap, baki godewa Allah ba da ya miki ni'imar da sauran basu samu ba? Idan da zan bude miki file din kowacce, sai kin ji kamar taki matsalar ba kome ba ne, mu anan ™abilarmu babban abin tashin hankali namiji ya sake ki, za a nuna miki iyakarki, ina son ki zama mace ta farko Bahaushiya daga arewacin Najeriya da ta san kanta ta kuma yarda da kanta. Idan har kin yarda da kanki," "Auntynki Nuratu Kafaya tana kiranki, idan kuma kika sake tsoron nan ya mamamye ki. "" Murmushi tayi ta mike tana me daukar jakarta tare da yiwa Aunty Zakiyah magana. "" Madam zan tafi! "" Fitowa Aunty Zakiyah tayi muka rakata. Cikin wata motar alfarma ta shiga, ta d'aga min hannu, haka naji kamar anya xan iya zama mutum kamar yadda ta ce? Jiki a ma ce na shigo cikin gidan. Ina kallon kasa. ""Ya kamata ki kara gaba, sannan ba zaki bikin Sani ba, ke da Bauchi yanzu sai wani Ikon Allah. Ba zaki ko ina ba, ki zauna ki gina kanki na jima da sakawa a raina ba zaki Bauchi ba, ita dai wacce aka koran nan sai ta zama wacce ake kwadayin ganinta, idan Mama kike son gani Allah ba zai hana mu kudin kawo ta nan ta kwana biyu ba, zamu tafi Bauchi ni da Yayanki, ke da Yara zaku zauna anan, a matsayina na wacce makarancin likitanci, idan muka je Bauchi aikin da muka sha wahalar yi dare daya Hafiz da Abba zasu rusa mana, babu inda zaki kin ji aiki domin ba zamu yi gini wani ya rusa mana ba. "" Ji nayi kamar an kara yanta ni, murmushi yayi ban ce mata kome ba muka shigo cikin parlourn na tayata kwashe kayan da ta kawowa Bakuwa muka kai kitchen. Nan na wuce dakina na kwanta sai lokacin sallah ka tashi nayi, a cikin addu'ar" da nake har da Allah ya bani ikon yarda da kaina. "Sai dai kuma ina gama addu'a naji wasi-wasi a raina, haka na lumshe lekowa har na wani lokaci. Kafin" "na bude ina kiran sunan Allah. Wasi-wasi ya saka ni a gaba, washi gari na shirya na tafi makaranta, karfe biyu na taso, sai na tsaya a gym din, yan wurin na ganina. "" Lulu!"" Fuskarsu cike da fara'a suna ta min barka da zuwa. "" Tunda kika zo baki kara zuwa da fatan dai lafiya domin dukkanmu nan mun zama daya."" Gyada kai nayi ina faWin. "" Ban ji dadi ba ne?"" Ai kuwa a rud'e suka yi ta tambayata meke damuna, na ce ciwon kai nan suka yi ta min sannu sannan na shiga wurin Aunty Nuratu Kafaya, na samu tana tattaunawa da wata mata sai kuka matar take. Itama dai katuwa ce. "" Ku yi hakuri ba ri na jira a waje! "" "" A'a gashi ki tafi daya office din ki bawa Wasim zai miki bayani."" Gyada kai nayi ina faWin. "" Na gode sosai!" """" "Na fito na tsaya a bakin kofar ina raba idanuna, yarinyar ta Nasiba na gani zata fita ta ce min. "" Aunty" "kina son abu ne? "" Gyada kai nayi mata ina mika mata.."" office din Uncle Wasim zaki! Muje na kai ki."" Ina bayanta ta kai ni har office dinsa, da sallama muka shiga, shima yana bako, yadda yake magana a nutse zaka fahimci shi din Coach ne da yake ganin mutane daban-daban. ""Kanwata shigo!"" Ya fada yana murmushi, kafin ya kalli mutumin ya ce mishi. "" Yawwa kamar yadda na gaya maka, zaka iya kawo ta mu" "fara ganin yadda zamu gina lafiyar jikinta. "" Mika mishi hannu Mutumin yayi sannan shima ya mika mishi" ya mike matsawa nayi mutumin ya fita ya zauna yana nuna min wuri na zauna. Mika mishi takardan "Nasiba tayi tana faWin.. ""Uncle ni fita zan yi, naji wai an sake sakamakon Allah yasa ina cikin wadanda zasu diba."" ""Allahummah Amin Daughter Allah ya bada sa'a."" Ya fada yana mata murmushi fita tayi, ya kalle ni. ""Shekara biyu kenan tana niman aikin masu kula da fasinjoji na jirginsa, bata tab'a sarewa ba. Bana ma haka har azumi take da sadaka Allah ya bata sa'a. Kin ga kuwa dole mu taya ta da addu'a Allah ya bata sa'a ko?"" Ya fada yana kallon takardan hannun.. ""Da kibar aka haife ki?"" Girgiza kai. ""Bana son body language, speak!"" ""Tow!"" ""Kin tab'a haihuwa ne?"" ""A'a;"" kallona yayi da kyau, kafin ya ce min.. ""kin taSa birth control ne?"" Anan na sunkuyar da kai ina matse hannuna, bude drower yayi ya ciro wani irin ball ya mingiro min, ""idan kika shiga irin wannan yanayin us it, kina matsawa yana rage damuwa. Me yasa kika sha birth control?"" ""Tsohon Mijina ya bani."" ""Amma yana sonki!"" Matsa ball din nayi murmushi yayi sannan ya ce min.. ""duk mutumin da yake sonka baya naka abin hana daukar ciki am sorry!!"" Shiru yayi ya cigaba da cewa. ""Zaki ragu amma sai kin saka a ranki zaki ragu, kina da saurayi ne?"" Da sauri na kalle shi. ""Oops babu ko?"" Ya tambaye ni yana murmushi. ""Tow daga yau ki saka a ranki, kina son ki burge saurayinki ne, kin san waye saurayin?"" Girgiza kai nayi, murmushi yayi ya ce min. ""Kanki, kanki zaki burge ki ji a ranki soyayyar da zaki yiwa jikinki don kanki zaki yi ba don wani ba. Kin san me? Dole ki fada soyayya da kanki haka zai baki damar kula da kanki, sannan ki yi hakuri da kowa ki yi hakuri da kome kada ki sake wani ya ba'ta miki rai, ki ji a ranki kina da kanki da ya tsaya miki all I want to you love" "yourself, ki yarda da kanki ni kuma zan yi ™o™arin baki step by step na kula da kai." "Wannan sune tsarin abincin da zaki fara ci kullum da wanda ya haramta miki,. Idan kina da soyayya da" "bread da fanta irin naku na Fulani ayi hakuri daga yau an daina shan duk wani abu me zaki, kin ga kibar nan naki idan da za a bincika ba za a rasa uric acid da Diabetes ba, sannan akwai tarin kitse da dole a narka da shi, sai kuma rage cikin abinci mai yawa, idan za a ci a sha ruwa sosai, sai a hada akwai bayani" "akan nan duba ki gani.""" Ga wasu hanyoyi da za su taimaka miki wajen rage kiba da kuma wasu shawarwari a kan abincin da ya kamata ki ci: Hanyoyin Rage Kiba da Inganta Lafiya 1. Kula da Abincin da Kike Ci "* Rage Abinci Mai Sukari da Mai: Ki rage cin abinci mai zaki (kamar su alewa, lemo na kwalba, da waina" mai sukari) da kuma abinci mai yawan mai (kamar soyayyen abu). "* Yawaita Cin 'Ya'yan Itace da Ganyaye: Su na Wauke da sinadarai (fiber) da ruwa da suke sa™i da ciki," kuma suna da ™arancin Kalori (calories). "* Cin Abinci Mai Wadataccen 'Protein': Irin su kifi, ™wai, nono marar mai (yogurt), da wake/gyaWa." Protein yana taimakawa wajen rage yunwa kuma yana ™arfafa tsoka. "* Rage Cin Abinci Mai 'Starch' (Carbohydrates): Abinci irin su shinkafa, taliya, burodi, da fura. Idan za ki" "ci su, ki ci da 'ya'yan itace ko ganye." 2. Yin Motsa Jiki (Exercise) * Yin Tafiya: Ki fara da tafiya mai tsawo ko da na minti 30 ne a rana. Wannan yana da sau™i kuma yana da fa'ida sosai. "* Gudu Ko Gudun Tsalle: Idan za ki iya, ki dinga yin gudu ko ki yi 'skipping' (tsallen igiya) don ™ona Kalori" da yawa. "* Yi Motsa Jiki Akai-Akai: Ki maida shi wani Sangare na rayuwarki, ko da sau uku (3) ne a mako." 3. Shan Ruwa * Yawaita Shan Ruwa: Shan ruwa kafin cin abinci yana taimakawa wajen rage yawan abincin da za ki ci. Ruwa yana da matu™ar muhimmanci ga lafiyar jiki. 4. Kula da Barci * Samun Isasshen Barci: Rashin isasshen barci na iya canza sinadaran jikinki waWanda ke sarrafa yunwa "da koshi, hakan kuma na iya sa ki ci abinci fiye da yadda ya kamata. Ki tabbatar kina samun barci mai kyau na awanni 7 zuwa 8 kowace rana. Abincin da Ya Kamata Ki Dinga Ci" Ga wasu misalai na abincin da zai taimaka miki wajen rage kiba: Nau'in Abinci | Abincin Da Ya Dace Dalili "Ganyaye | Alayyahu, kubewa, kabewa, latas (Lettuce), kabeji (Cabbage) | Suna cike da sinadarai kuma" "suna da ™arancin Kalori. 'Ya'yan Itace Tuffa, lemu, abarba, kankana, ayaba (kaWan) | Masu zaki na halitta, suna da Fiber." "Protein | Kwai (Boiled/Gasashe), Kifi, Nono marar mai (Yogurt), Wake/GyaWa, Naman Kaza (Chicken" "Breast) | Yana sa™i da ciki na dogon lokaci, yana rage sha'awar cin abinci." "Abinci Mai Fiber | Hatsi (Oats), Dambu, Gurasa (Whole Grain Bread), Rogo (idan ba mai yawa ba) Yana" taimakawa wajen narkewar abinci da sau™i a ciki. Muhimmin Bayani: """Ki nemi shawarar likita ko kwararre kan abinci (Dietitian) kafin ki fara wani tsari mai tsanani. Za su iya" "duba lafiyarki su ba ki shawarar da ta dace da ke.""" "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 35" """ In sha Allah!"" Haka na mike ya ce min, ""Lubnah!"" "" Na'am! "" Na amsa mishi, ki duba time table dinmu," "sai ko zabi ranakun da kike so, sai ki nime kayan da zaki na amfani da su."" ""In sha Allah!"" Sannan na fita sai da na leka Aunty Nuratu Kafaya, na mata sallama akan gobe laraba zan fara zuwa ranar Saturday." "Haka na koma gida na samu Ya Ado na mike mishi takardan ya ce mu shirya mu fita, haka muka fita dukka gidan muka je wani super market anan Ikeja, sannan ya kai mu wani shagon sayar da kayan kwallon, ya saya min kayan da zan na fita zuwa Exercise da sassafe da kuma wanda zan na sakawa zuwa" "Gym din, haka ya saya mana har da Yaran da su kansu iyayen muka dawo." Kamar yadda Ya Ado ya kawo kayan Aunty Zakiyah ta amsa ita ta fara nuna min yadda ko bata nan zan "iya dafawa. A ranar dai ban ci abinci dare ba, sai ruwan tea da fruit da sha. Washi gari da safe ya Ado ya cika min water bottle da ruwa ya tashe ni muka fita. Ana sallah asuba muka fita bamu dawo gidan ba sai shiga da arba'in, wanka muka yi na sha nikakken ruwan fruit, sannan na kwanta. Ban tashi ba sai karfe goma, ina fitowa na samu, kunun tsamiya, da faten wake da yaji ganyen alayayu, sai agada, sai da na sha ruwa kafin na karya, ina zaune a parlourn aka yi knocking, Mai aiki ra bude kaya aka kawo, a kwali. Suka shigo da shi Ya Ado yana bayansu. Zuwa yayi nuna inda za a saka sannan ya koma wurin aikinsa. Washi gari ya kama juma'a, shima sai da muka zaga unguwarmu sannan na dawo, kayan da aka kawo machine" "ne na Exercise, Ya Ado yana dawowa daren jiya ya haWa ya gwada aiki da shi a daren jiya." "A ranar bayan sun fita nima kusan a kai na wuni, dadare kuwa abincinsu suka ci ni kuma na ci nawa" "tuwon alkama zalla miyar ayoyo, daga nan kuma na sha fruit na kwanta, ranar asabar karfe goma na tafi Gym, sugar kuwa tuni na yi bye bye da shi, wunin ranar Yorghurt na sha daga kuma sai ya rike min ciki. Karfe biyu na bar gym din zuwa gida yau nayi rayuwa da ban tab'a yi ba, sai nake gani kamar mafarki. Ina typing har na iso Unguwarmu, na karasa gida, a harabar gidan na hango Ya Umar wani murmushi ne ya kwace min na isa gare shi, ya dan rungume yana faWin.. ""Auta manya an zama yan gari. Daga Gym ko?"" Gyada kai nayi ya ce min. ""Shiga bari na gama waya na shigo."" A parlourn na samu Mamana, wani ihu da nayi na isa wurinta da gudu na rungume ta, tana buga bayana. ""Sannu Autana, sannu yar jinjirana! Ai tunda suka ce ba zaki zo biki ba nace ban isa ba, zan zo na ganki kada na mutu ban ga autana ba!"" ""Mama me yasa kike kiran mutuwa? Mama me kika kawo min? Mama ina Yadiko?"" ""Suna lafiya tana ta" "shirin bikin Sani!"" ""Allah sarki!"" Na ji dadi sallah ya tashe mu na ja ta sama, tayi ta mita ita bata son sama, ai kuwa tunda ta hauro tace ba isa da ciwon kafa ba, karshe Abinci ma sama aka kawo mata, ni kuwa dad'i kamar na nutse kasa, tun a daren na gayawa Nasiba ta gayawa Mamanta Mamana tazo daga Bauchi. Kwana muka yi da Mama muna hira tana bani labarin abinda ya faru, hakuri nayi ta bata, karshe" nayi barci na barta tunda na fara Exercise barci ya daina min wahalar yi. "Washi gari Lahadi sai ga Aunty Nuratu Kafaya, ita da Mijinta, Mama ta ji dadi nima na ji dadi gashi" "an hadu ana ta hiran arzikin, sai la'asar Mijinta ya zo ya dauke ta. Koda na zauna ina cikin ganye Mamaki Mama take ta kasa hakuri ta ce. ""Wannan wacce irin rayuwa ce? Yarinyar da rayuwa da ganye ita ba akuya ba ita ba tsutsa ba, Auta dole aka miki ne?"" ""A'a yana cikin kayan karin lafiya ne, idan ina ce kibar" "zata ragu ko ta tafi bakiWaya."" ""Aiho yanzu na fahimci yadda lamarin yake. Allah ya kara lafiya shi yasa" "idan na zoma zan ta dafa miki zogale ina shanyawa da rama da yakuwa."" Haka Aunty Zakiyah tayi ta" "mana dariya, satin Mama biyu ta koma Bauchi ta bar ni da kewarta sai waya kawai muke." "Bikin saura wata gudu muka fara jarabawa, na kara mai da hankali sosai sai fa muka sha wuta na" "tsawon wata guda sannan muka samu hutu, rayuwa tana cike da darasi na musamman Ya Ado da Aunty Zakiyah sun tafi, ni kuma na cigaba da kula da kaina, da taimakon Aunty Nuratu Kafaya, sati daya suka yi wanda aka sha biki da karamin gurmi aka dawo aka bamu labarin wai Yan uwa Ya Hafiz da Yan uwanmu ana ta habaici an tura ni karuwanci suna jiran sakamakon bariki, shine fa Yadiko ta rufe Aunty Nana" "Asma'u da fada ta ce mata. ""Har kina da bakin magana? Karuwanci ai ya kare tunda tana gindinku!""" Rigima sosai a gefe guda Matar Hafiz itama ta kashe auren ne ko yana lilo oho amma dai ana ta "rigima tace tunda ta aure shi ita bata gamsuwa, hakuri take da shi. Aka ce Abba kamar yayi hauka yayi ta fada yana rarrashin Hafiz, wannan ya karawa Hafiz wani irin tashin hankali, yayi ta kuka yana rokon Abba ya dawo mishi da Lubnah shi yasa kaf duniya babu Macen da zata iya rufa mishi asiri kamar Lubnah, yadda ya shiga damuwa sosai Abba shima jininsa yayi ta hawa kafin a gama bikin nan sai da ya kwanta a asibiti sau biyu. Abu fa ba dad'i sai gashi har Abba da kanshi wai ya je wurin Mama yana rokon arziki ta dawo da Lubnah, ai kuwa da Abba da Ya Hafiz Mama ta ce sai ta kai su kotu ta ji Uban da suke bukata da" Lubnah. HAFIZ "Don shi kanshi bai kawo a ransa Lubnah ba zata zo ba, saboda yadda ya santa da Sani, amma wani ikon" "Allah bata zo ba ya kuma kudira a ransa da ta zo sai ya san yadda yayi dawo gare shi yadda ba zata kara barin Bauchi ba sai da izninsa amma dai gashi bata zo ba abin ya bashi haushi, ga Nana da ta gudu ta fasa auren. Gashi ya ga hoton Lubnah a wayar Rufa'i da yake zolayar Aunty Zakiyah ta dauke mishi First love dinsa wato Lubnan kasancewar dan Goggo Alti ne, yana jin su yayi kamar baya wurin yana ganin lokacin da ya bashi number Lubnah da kuma hotonta. Bai nuna zallamarsa ba sai da washi gari ana hira ya ce Rufa'i ya bashi aron wayarshi, zai yi abu ne ai kuwa yana amsa ya binciko number Lubnah wanda Rufa'i ya saka mata bazawarata Lubnah, sai hotonta da ya tura kusan kala goma tayi shi da gym outfits, wani baki da ratsin pink yayi azabar kyau ga kanta da ta saka wata hula me kyau gargasar gaban goshinta sun kara fitar da kyanta da ya boya behind kibar ya fara fitowa, wani murmushi tayi, daya kuma ta fitar da harshe waje kamar tana gwalo, wani kuma tana kan abin motsa jiki na gidan daga ita sai riga da wando ta tufke gashin kanta, wani irin gigicewa Hafiz yayi kamar zai zauce. Bai taSa kawowa a ransa zata dawo kamar da ba. Wannan abin ya d'aga mishi hankali wani hotonta kuwa wani yatsina fuska tayi tana dariya, alamar magana ake mata tayi haka sai kuma ita da yaran, wani kuma a makaranta. Zufa ke karyo masa yana ji ina zai iya ganinta yasan yana ganinta zata fit hayacinta ta nemi dawo mishi, haka ya mai da wayarwa Rufa'i sannan ya koma gidansa yana kallon Yaranshi da suka ci abinci suka koshi, Hajiya tana" "gidan ita fa Fido. Zuba mishi idanun tayi ta ce mishi. ""Duk akan matsiyaciyar yar nan ne?"" ""A'a Hajiya" "Lubnah na gani!"" Ya cire mata hoton ta gwalalo idanun waje kamar tsohuwar mayya tana faWin. ""Ina ka" "samo ta don Allah dama yarinyar nan zata dawo kamar da?"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Hajiya ki taimaka min ta dawo gare ni!"" ""Ba ga zoben nan ba ai shi ne kankat sai kuma shi wancan uban nata kasan yadda zaka yi da shi."" Nan suka yi ta tsara yadda zasu dawo da Lubnah. A daren ranar ya tashi hankalin Baban Bauchi da kuka da rokon ya dawo mishi da lubnah itace daidai da rayuwarsa kasancewar" "akwai sauran yan biki, suka yi ta bashi hakuri da cewa idan Matarshi ce zata dawo gare shi.." "Abu kamar wasa sai gashi Baban Bauchi ya tashi hankalinsa sai da ya kwana asibiti, Goggo Alti tayi ta" "fada. Da Baban Jama'are da Baba Malam suka zo nan suka fara fada ai a dawo da Lubnah. Yadiko da kanta yayi wata ta ce musu. ""Tunda tare aka halicce su ai sai ya je ya dawo da ita, sannan aure babu shi a tsakaninsu tunda har sun karbi khulu'i din da ta bayar, haka maganar ya mutu. Ranar daurin aure a shirin da suka yi akan idan aka zo daurin auren Sani sai a hada da na Hafiz da Lubnah, ai kuwa ana gab da daurin auren Babangida da yazo daga Maiduguri ya same shi yake ce mishi. ""Daurin auren Sani muka zo yi ya nake jin wai za a sake daura auren Lubnah da Hafiz bayan kace ba kai ba ita? A da can ma baka mata dole ba sai yanzu cikarka Uba na gari shine ka dakatar dasu idan ba haka ba wallahi za a kafa mummunar Tarihi a zuriarka domin zan kashe Hafiz idan aka daura auren nan da shi!"" Wannan barazanar da Babangida yayi shi ya dakatar da auren da ake shirin kara daura shi, haushi da takaici ya saka BP dinsa low. Domin yana fama da ita ko ta hau da zaran ranshi ya b'aci zata sauka da gudu, sai dai" a ganshi yana fari da idanun da jijjiga. "Hafiz da Baban Jama'are da Baba Malam sun ji haushin wannan lamarin, domin Hafiz saka su yayi a" gaba da rokon su saka baki amma al'amarin ya koma haka. Wasa gaske haka aka gama bikin Sani babu wata matsaya domin kuwa babu ita shine daga baya aka je rokon Mama tayi tsalle tace abokin mutuwa take nima akan Lubnah. A bangaren Hafiz yana son kiranta amma yana tsoron kada ta gayawa Ado ya mishi rashin mutunci haka yasa ya hakuri da kiran yadda kudirinsa xai cika. *** "Akwai wani abu da na fahimta, tun da na fara kula da kaina da kuma kula da lafiyata, sai na ga kamar nafi" samun kwanciyar hankali. Dadindewa gaba nake kamar ana hankad'a ni. "Kwanaki suna tafiya satika suna gudu, watanin na zuwa daya bayan daya a hankali na gama" "master dina da gagarumin nasara, ga shi dai na sauka sosai, idan ka kalle ni sai ka kara kallona, sai ka yi ta mamaki kamar ba ni ba a cikin wata shida da wani abu sai gani ina kyauta da kayana. Har Bauchi aka kawo aka kai Jama'are aka rabawa yan uwan Mama da Jikokin Goggo Alti, ai kuwa Goggo Uwani da" "Talatuwa suka yi ta fada wai ba asan da su ba, shi yasa aka rabawa waWanda ake so, Mama da bata iya" kyale su ta ce musu ai da na basu kayan sai ta biyo ta kwace yadda basu da mutunci karya su ci arzikin Lubnah....... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 36" "Zuwa yanzu ina son kaina, na fahimci duk wnada zai soka bayan kaso kanka ne ka kuma girmama kanka." "Duk wanda ba zai soka ba babu amfanin zama da shi, amma firstly ka so kanka ka kaunaci kanka yau na ji kaf duniya babu wanda ya dace na so sama da kaina, amma har yau ina jin a raina ya Hafiz shine ajalina yadda nake bala'in tsoronshi har yau ban cire wannan tsoron na a raina. Ina tsoronshi daga kasar zuciyata. Wani irin tsoron shi nake tare da sauran maza bakiWaya. Idan akwai abinda zai hada ni da maza tow na hakura da shi, haka yasa hatta waWanda muke wurin Gym din suma suka kame kansu babu wanda ya tab'a shige min, duk da na sauka amma haka bai hana na cigaba da motsa jikin ba, wani abinda ya fara daukar hankalin mutanen wurin shine ni dai kiba na ke son ragewa amma wani abun mamaki sai ya kasance daga samata na ragu sosai, zuwa kasata sai ya bada shape irin yadda zaka ga wasu suna bukatar domin cinyata zuwa mazaunai na, sai suka fita fess, wanda ya haifar da cikina zuwa kirjina ya wani irin fita kamar dai yadda ke kira coca cola, haka shape din ya fita, a lokacin da na fara yiwa Aunty Nuratu Kafaya magana abinda ta ce min kuwa ya saka ni shiru. ""Ai dama haka halittarki take yanzu kuwa zaki dawo asalin yadda kike, tumbin da ake gani yanzu ba gashi yana ta sauka ba, a hankali kafin nan da shekara daya duk zaki dawo yar cass yanayinki zai fito kamar na yan boko yan yayi."" Kawai sai ban kara damuwa ba, a lokacin aunty Zakiya har da min tsiya wai na koma kamar wata yar Nigeria Film, ni dai ban" kulata ba. *** KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY. "Yau Litinin kusan wata shida da mutuwar Auren Jasminah, mahaifiyarta ta sakota a gaba haka yasa tayi" "give up bakiWaya take kuma jin rayuwarta bata da amfani, sai dai a yadda Uncle Auta da Ubaid suke tsaye a kanta yasa ta ke samun nutsuwa. Yau aka turo mata da shaidar an dauke ta aiki a kamfanin duk da ba aikin da tayi ba kenan amma kai tsaye Turaki ya ga dacewar ta fara aikin haka zai rage mata" "damuwa da halin da take ciki, sannan zata nutsu sosai ta kula da Yaranta." "Karfe takwas yayi mata a cikin kamfanin, kiran wayar aka yi ta dauka tana faWin. ""Na gode sosai, gani a" "office din."" ""Na baki awa 48 ki fitar min da abinda nake bukata daga cikin yanayin ma'aikata zuwa sauran abinda ake bukata."" ""In sha Allah!"" Ta fada, tana kallon office din, tana mai girgiza kanta. Abinda ta fara dubawa ma'aikata nawa ne a cikin kamfanin? Don haka ta fara fita ta isa office din MD Khamis Abbas Kumo, buga kofar tayi amma baa bude ba. Masinjasa yace mata. ""Hajiya bai isa ba an jima kaWan zai" "iso;"" ""tow! Ina ne office din shugaban ma'aikata?"" ""Office din Mrs Thomas kenan muje!"" Ba musu ya" "rakata, ta samu ta zo tana ta aiki ta haWa nan ta haWa can, mika mata hannu tayi suka gaisa nan ta gaya" mata me ake ciki a kamfanin. "Murmushi tayi ta ce mata. ""'kamar yadda kika gani ma'aikata dayawa basu shigowa sai lokacin da" "yayi musu, haka basu tashi sai a lokacin da ya dace, sannan idan wata yayi aka samu jinkirin albashi su ta korafi! Muje ki gani!"" Haka suka cigaba da tafiya kamar yadda dai ake fama da kowacce irin ma'aikatan da kamfanonin, haka inda ake ajiye kayan ma ya lalace, ga ba ma'aikatar da ya dace. ""Sannan Madam ana sata anan kayan da ake sacewa dole ya baki mamaki!"" Ita dai Jasminah tana rubutawa, tana kara mata tambayoyi har suka isa cikin store din da ya lalace. ""Ko last year an karbi kudin gyaran nan sama da miliyan talatin amma ba a gaya ba, ita kanta kamfanin tana bukatar gyara da asalin ma'aikata masu son aiki ba irin wadanda aka lalata su da rashin son aiki ba. Oga Ubaid yana kokari amma da zai yi wani motsi take za a fara mishi gorin yafi yan gidan kamfanin zakewa, yana son yayi aikin amma da zaran ya fara aiki za a fara magana kai ko dakatar da mutum yayi MD zai dawo da shi ko vice chairman, kamfanin nan ana abubuwa dayawa amma baka da ikon magana, akwai abinda nake son ki sani mu kanmu ma'aikata mata we are not safe daga baragurbi irin MD Khamis Abbas Kumo."" Shiru tayi tana me kawo ta wurin ajiyar kayayyakin da ake kwaso kayan gwanjon ta ce mata. "" Kin ga wannan motar da sauran sun lalace idan har xa'a yi amfani da shi sai mun dauki haya, madadin a gyara mana wannan, sannan zuwa yanzu akwai bankunan da suke bin kamfanin nan sauran cikon kuWinsu. Na gayawa Ubaid ya ce ba ruwansa domin ko na bankin UBA da yayi magana karshe sai da aka samu matsala akace yana da hannu a ciki aka so shi frame dinsa da laifin cin hanci abinda na sani idan har CEO ne a kamfanin nan dole a kawo gyara da sauyi don Allah muna bukatar ma'aikata da waWanda zasu tsara mana yadda kamfanin zai yi gaba ba kullum a baya ba, kaf Nigeria ita ce Waya idan har aka samu na biyu tow tasirin kamfanin zai yi kasa ki duba maganata da idanun basira. "" Haka suka gama zagaye kamfanin sannan suka dawo bakin kofar kamfanin suka zauna suna kallon mutane da suke ta zuwa har suka gama bata ce musu cikanku ba, ta mike ta na me nufar cikin kamfanin, office dinta ta shiga ta fara aiki ba kama hannun yaro, karfe daya Ubaid ya shigo, kallonsa tayi tana faWin. ""Sai na fadawa CEO mukaddashinsa sai karfe daya yake shigowa kamfanin."" ""Ai kuwa da kin kyauta dama ya haWa ni da aiki ne nake son na rabu da shi na ji da aikina ko da aikinsa?"" Murmushi tayi ta ce mishi. ""Zauna Hamma Ubaid!"" Zama yayi ta fara tattara bayanin da ta haWa na yau ta ce mishi. ""Yau na leka kamfanin bakiWaya na ga abinda bai dace ace na gani ba, karfi da yaji ana son kashe kamfanin nan meke faruwa ne?"" Ta mika mishi bayanan da ta hada. Murmushi yayi yana faWin. ""Wannan ai tsohon lamari ne, amma idan kina son ganin yadda rayuwar kamfanin yake ki fara da office din Vice chairman, zuwa office din babban sakatare zuwa na MD kafin ki zo na sauran ma'aikatan, ki yi bincike duk abinda baki gane ba ki tuntube ni."" "" In sha Allah! "" Ta ce mishi sannan ya fita, itama sallah tayi a office din sannan ta ji tana son cin abinci, mikewa tayi a hankali, a saninta lokacin da Babanta yake kamfanin abinci da ake ci kyauta ce don jin daWin ma'aikata, fitowa tayi a lokacin ta ga shigar wata mace office din MD, office din Mrs Thomas ta isa ta ce mata. "" Mrs Thomas ya batun abinci har yanzu ana yi kuwa? Don yunwa nake ji. "" Girgiza kai matar tayi ta ce mata. "" Tunda aka yi gobara a dakin girkin aka rufe bada abinci ga ma'aikatan kamfanin nan."" Shiru tayi tana me jinjina kai, sannan ta juyo tare da nufar office din MD, tana isa kafin Masinjan ya mata magana tuni ta tura kanta. Abin da ta" gani yasa tayi baya da sauri. Bata yi magana ba ta juya ta bar wurin. Turawa Turaki sako tayi bayan ta zauna a kujeranta. *Ni dai gaskiya ka cilla ni a uku kamfanin nan sai kai ne kaWai zaka daura shi akan hanya a yanzu kan kome ya lalace don Allah ka dawo.* Bai cika reply messages ba amma yau da ta tura mishi sai ga sakonshi ya dawo mata. _Ki yi duk abinda na zaka ki sannan duk abinda kika ga ya dace ki yi idan na ga abin yayi zan kara tuntubarki_ "Tura baki tayi tana hararan wayar, haka ana tashi ta wuce gida. Koda ta isa gida wasu files ta amsa a" "wurin Ubaid tayi ta bincike, sannan ta cigaba da tura mishi bayanin halin da ake ciki tare da gaya mishi" "ana bukatar sabin ma'aikata amma yanzu a fara gyara kamfanin, haka ya turo musu kudi ya ce kada a tab'a na kamfanin domin yana da lissafi akan kudin kamfanin." "A tsakanin sati biyu aka fara aikin tare da kwashe tsofaffin kayan akayi ta sayar da su ga yan bola jari," "wani abin haushi duk an yi sata wasu ma karafunan kamfanin sarrafa mota na kasar Japan aka sayarwa don asarar tayi yawa, haka sai ya bawa Alhaji Mudansir ELYakub Kumo mamaki tare da Abbas Kumo domin dare daya suka ga ana ta aiki kamfanin ma an sabunta shi, hankalinsu a tashe suka sakata a gaba da tambayar me yake faruwa, karshe har gaban Alhaji ELYakub Kumo aka kaita, ya ce musu. ""Aikin da kuka gaza yi ne take yi kuma Umarni aka bata daga CEO idan zaku iya sai ku dakatar da ita."" Jin haka yasa" suka sha jinin jikinsu. Nan matan suka fara tambayar dawowa zai yi? "Kwatsam Badr ta koma gidansa na Lekki da zama, amma bata kwana a gidan gidan Uncle Auta take" "kwana, ita dai Jasminah bata ce mata kome ba, a can office din kuwa an gyara wurin girki da hall din cin abincin, sannan an hada duk wani abu me muhimmanci kama daga kayan abinci, zuwa sauransu. Tana aikinta tana tura mishi hotuna da bidiyo na abinda take, asalin karatun da Jasminah tayi zanen gidaje wato ita mazanina ce, ya jefota ne domin ta taya shi ganin kamfanin kuma cikin ikon Allah da yake ta san darajar ilminta sai gashi ta kara faWin kamfanin har ta fara bada shawarar a bude sabon kamfanin wannan wurin sai ya zama wurin ajiye kayayyakin kamfanin da za ayi gwanjonsu, ya tambaye ta a cikin wata nawa zata iya aikin? Murmushi tayi ta ce mishi. Matukar akwai kudi a kasa ita bata ganin aikin zai haura wata uku. Jin haka ya gayawa su Mujitafa da Ubaid, tare da Alhaji suka ce sun bata goyan, aka kuwa zuba mata kudi, da mijin Uwarta Baffanta da Mijin Goggonta tare da cousin dinta, da sauran ma'aikata sai gani suka yi an fara aiki babu kama hannun Yaro, haka suka sha bakin ciki, suka kara kai ™ararta Alhaji ELYakub Kumo ya kore su, ita kanta aiki take kamar wata injin, Uwarta kuwa jin labarin kudin da aka zuba mata ta fara lallabata akan ta kwashe Abinda zata iya ta yi aikin ko oho, blocking Mamarta tayi bata da lokacinta, yanzu da take jin batun kudi shine zata dawo da ita jikinta. Daga masu aikin zuwa kan ita kanta mazaniyar basu zaune basu tsaye duk yadda aka so a mata barazana abin ya ci tura har bibiyarta aka fara yi ta gayawa dan uwanta, tow abinka da miskili bai ce mata kome ba, sai dai yana can sai gashi ya saka an kama waWanda suke binta aka hada su da yan sanda, karshe shi kuma yasa" "aka karbo su ya saka aka musu kashedi, su kuma take mata baya." "Idan akwai kudi da karfin iko uban kowa ma zaka taka, ya nuna musu shi fa yana iya kome da kudinsa" "yana sarrafa kudinsa yayi yadda yake so, don haka duk abinda zasu zasu gana ba nasara. A wannan" "yanayin wata ranar lahadi Mrs Thomas ta fito church kuwa da motarta Allah yasa ita Waya ce, aka mata" "kiran gaggawa daga kamfanin a hanyar zuwa suka saka mota ta buge motar Matar nan, kai abin yayiwa Alhaji ELYakub ciwo yayi fada yayi fada. Kuma yayiwa duk wanda ya mata wannan abin Allah ya isa kuma ko waye asirinta ya tonu sai yayi shara'a da shi, Mrs Thomas tayi aiki da kamfanin tun zamanin Iyayen Turaki ita ba kamar sauran ma'aikata ba ne, kamar yar uwa suka dauke ta.. kasancewar tayi dogon suma" wanda ake kira coma....... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 37" "Tashin hankalin da aka shiga a family ba na wasa ba, shi yasa hatta abinda za a kashe KUMO FAMILY" "suka dauki nauyin abin. Wannan abin da ya faru bai saka Jasminah fasa abinda take ba ai an san suna tare da Mrs Thomas, Kuma anyi haka ne domin durkusar da aikin, kamar yadda Turaki ya gayawa Uncle Auta, kullum Jami'an tsaro suke kaita tare da saka idanu akanta, na biyu kuma aka biyar lafiyar abin hawanta, haka yasa kowa yake tsaye a kanta, babban abinda yasa aka yi haka domin gani ake ai idan da ita Jasmin ce da aikin ya dawo hannunsu, sannan kuma zasu yi yadda suke so amma aba a san waye yayi wannan aikin ba. Kamar yadda ta ce wata biyu a cikin wata biyu wanda yayi daidai da saukar daminar bana, wannan wata biyu da aka diba an samu ban iska idan a damina ne aikin ba zai yi ba, amma ganin yadda aka sha isa ba ruwa yasa ta yi aikin cikin nutsuwa, ba dai ga aiki ya fito fess, Alhaji Mudansir ya ce shi ba zai koma sabon building ba, ai kuwa ya samu sako ta email address dinsa da cewa ai dama building din ba na shi bane na CEO. Abin ya bashi mamaki haka ya kara kai ™ara Alhaji ELYakub Kumo yayi mishi fata-fata, amma wani abu da ya tsaya musu a rai yadda kowa ya sha jininsa. Bayan an gama aikin aka fara ™o™arin diban saba'in ma'aikata, a wannan lokacin manya mutane sun so lallai a debi yaransu, a wannan bangaren Uncle Auta shi yake da hakkin sabin ma'aikata. Wannan karon masu degree aka nima ba wasu kasa da diploma, haka yasa tsofin ma'aikata da aka same su da laifin rashin gaskiya aka sallame mu, musamman maza matan dama duk ba musulmai ne, a cikin wadanda aka kuma dakatar har da Badr Abbas Kumo, domin bata zuwa aiki kawai albashin take ciki, nan Uwarta tayi tsalle ta dirke bata yarda ba. Alhaji ELYakub kuwa yace ta gode da ba koranta aka yi ba, waWanda basu da dogon laifi an bar su a tsoron ma'aikatan, wannan abin ya bawa kowa haushi wato sune yan iska zasu zauna a tsohon wuri aikuwa suka ce ba zasu yi aikin da shi ba, shi kuwa ya rubuta musu cewa duk wanda ya bar tsohon ma'aikatan ya bari kenan share dinsa za a rike bakiWaya Saboda an same su da laifi dama. Jin zasu yi biyu babu yasa suka hakura. Hauka suke da zasu asara. An raba abubuwan sanarwar daukar ma'aikata" ta ko ina babu kama hannun Yaro. *** Lubnah "Gym kaWai nake zuwa, bana zuwa ko ina sai zaman ya fara gundura na. Ina zaune a parlourn ni da Ummu" "da Princess ina daura lalle a yatsuna, shekaranjiya ya Ado ya dawo daga Bauchi akan jikin Abba, ya je dole ya ganshi kusan cutar saukar jini da tagayyara da mutum, haka yasa shi ya je har yana ganin ko za akawo shi nan lagos ne, sun dai ajiye maganar idan jikin yaki dole lagos za a kawo shi. Shine Mama da" "aka yi ta rokon arziki ta dawo dakinta, ki tayi sai da na saka baki na rarrashe ta, ta amince ta dawo. Duk" da haka ana d'ago maganata zata takawa kowa burki ita fa mama na lura ta zama yar kunar bakin wake yanzu abu kaWan zata tashi boom. "Da zai dawo ta haWa mishi tsara har da madarar kuka da yake na gaya mata ina ciwon mara kwanaki," "shine ta ce idan aka samu me zuwa zata bani madaran kuka. Kullum da safe ina shan cokali daya na hada ruwan dumi, ba lallai sai da na dumin ba, saboda yana wanke mara da maganin sanyi. Sai lalle da nake so saboda yatsuna, sai magarya, nomi ridi mai gishiri da yaji da mai, gyada mai gishiri, aya da suga na yara ne, ni dai kayan cina har da garin karago, haka dai aka turo min da acca da kome na irin namu masu" gyaran jiki. "Aunty Zakiyah da safe madarar kukan ta haWa min da fruit ta min shaka da shi, sai yar yau da tayi da" "kunun gy'ada wanda ta zuba alkama a ciki, sai da na sha shaka kafin na taSa abincin, a cikin kayan Aunty Zakiyah na ga har da wani hadin daka da Mama ta turo mata, tunda na gana kunshe dariya na, ta zungure min goshi. ""Munafunci kawai surukata ta aiko mun da kayan gyaran aure ne, bana son saka idanu?"" Ban san me ya jefo tambayar kan harshe na ba nace mata. ""Idan nima na samu nutsuwa irin taki haka Uwar mijina zata min hidima?"" Juyawa tayi tana kallona cike da mamaki ta ce min. ""Kina da saurayin ne?"" Girgixa mata kai nayi da sauri ina rike bakina. ""Da gaske kina da interest akan aure?"" Ajiyar zuciya na sauke na ce mata. ""A'a ni fa kawai yazo bakina ne, bawai don ina da ra'ayin yin auren ba ne, sannan wa nake da shi?"" ""Doctor Ahmad!"" Kallonta nayi nace mata, ""don Allah mu bar maganar nan Allah ya gani bana son shi, kuma ban tab'a daukar shi a matsayin wanda zan zauna da shi ba, asalima yaya na dauke shi, don Allah kada wani ya ji ya dauka ko na ajiyewa wani ne!"" ""Lubnah zo ki bani document dinki ga wani opportunity ya samu Allah yasa a dace!"" Fitowa nayi na samu Ya Ado ya nutsu akan computer dinsa, ya d'ago kai yana faWin. ""Oya dauko min takardunki zan rubuta miku VC letter ana niman ma'aikata har da masu irin matakin karatunki."" Haurawa sama nayi da gudu na gaji da zaman gida kusan for good 3 yrs, a yanzu fa ina ina gudu ni kaina sai naga ina burge kaina, ba da kamar wata bukka ba, amma a yanzu jikina a tsantsame. Wargaza wardrobe dina nayi na kwaso takardun na sauko da gudu na kawo mishi, sannan na tsaya a bayanshi ina ganin yadda ake cike vc din. ""Wacce ma'aikata ce a ma'aikatan sufurin kudi ne?"" (Wato ministry of financial) "" Kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY ne!"" Wani yatsina fuska nayi ina faWin. "" Wannan ba zai wani abun arziki ba idan ba zaman shan shayi ba! Amma ai kudi yana aikin gwamnati!"" "" Ki cigaba da jiran aikin gwamnati idan a kasan nan ne kafin ki samu aiki da takardarki, babbar Yarki ta gama jami'a har da yara uku gare ta. Sai dai ko idan kina son koyarwa?"" "" Haba Ya Ado, aikin gwamnati bai da wuya kai da kake lauya fa! "" Na fada ina tura baki. "" Ai suma organization ce ta bude firm Winsu, ba gwamnati ba sannan baki ga su ma da kansu suna shara'a da gwamnatin ba, kudin da suke samu ana bayansu daga kudin da clients dinsu suke biya ne idan za ayi Shari'a, so su ba gwamnati ba ne, su masu zaman kansu ne!"" Inji Aunty Zakiyah, ta kare Mijinta. ""Ikon Allah, a gidan nan ne zaka yi magana da mata miji ya shigar mata kayi da miji matar ta shigar mishi. Ke ba aikin gwamnati kike ba?"" Na tambaye ta ina tura baki. "" Nima da farko wata kungiya ce ta dauke ni aikin wucin gadi daga baya kuma sai asibitin suka ga ana bukatar gurbina. Idan kuma zaki yi aikin goge" "goge da share share ai duk aikin gwamnati ne sai ki zo mu baki!"" Tura baki nayi Princess ta kwashe da" "dariya wai. "" Aunty Lulu idan kika yi haka sai ki yi kama da Moana, ki ga yadda kika yi da face Winki, ko" "Ummu?""" "Kallon iyayen nayi da suke ta min dariya, ""Allah dai na gayawa Mama abinda kuke min!"" Wayar Ya Ado" "ne yayi kara ya dauka yana magana a hankali, "" ok bari na shirya booking Allah ya kawo ku lafiya!""" """ Lafiya Ya Ado!?? "" "" SAN lafiya? "" "" Daddy lafiya?"" Duk lokaci guda muka mishi tambayar. Katse kiran" "yayi ya ce mana."" Jikin Abba yaki za a kawo shi nan ne."" Ya fada yana kallon laptop din, ai kuwa hankalina ya tashi take na nime walwalar da nake na rasa. "" Shi da waye zasu zo?"" Aunty Zakiyah ta jefa mishi tambayar. Tana kallona. ""Shi da Tahir da Mama ta yadiko zata zauna, matar Sani bata da lafiya tayi bari."" Ajiyar zuciya na sauke murmushi tayi ta ce min. ""Zai tab'a samun damar zuwa inda kike ba har abada!"" Hawaye ne ya cika min idanun. Na zauna jikina a mace, ""je ki motsa jikinki, yar lukuta."" Ba musu na wuce don tasan kuka zan yi, haka ya Ado ya ajiye aikin da yake ya koma nima musu jirgin Jos to lagos, bayan nan ya saka Aunty Zakiyah ta nima musu likita anan kuwa cikin ikon Allah wani abokin aikinta Dr Abraham Abati, shi ta samu ta gaya mishi ya ce mata ba damuwa Allah ka kawo su lafiya. Bayan sun gama waya sai ga kiran Aunty Hindatu ta ke ce mata.. ""Maman Abbana, zamu zo muma amma sai zuwa weekend ki gayawa Mijinki na kira yana busy."" ""Wayyo Allah Ubangiji ya kawo ku lafiya, don Allah a zo mana da doya."" "" Amma matar nan baki da kirki a jirgi zamu zo fa! "" "" Ku saka a mota ya rigaku zuwa.""" """Ai kuwa kin kawo shawara me kyau bari na gayawa Raliyah a saka ta jos.""" "Ai kuwa kamar yadda ta fada a group aunty Munah ta ce musu. "" Ku tura mata dankalin turawa tunda" "mun fi kusa zan saka a mota idan zan zo!""" "Haka suka tsayar da magana, dakin da yake gefena na kara gyara musu, da inda Mama zata zauna a" "kasa don tace Allah ya kashe ta ba zata kara yarda da yaudareta ta zauna a sama ba, A lokacin muka mai da hankali a gyaran gidan, washi gari Ya Ado da safe yake gaya min cewa. ""Na tura takardanki!"" ""Na gode!"" ""Naga kin fison aikin gwamnati ko?"" ""Eh mana ga fansho da garatuti, wannan fa idan haukarsu ta motsa zasu kore ka aiki!"" ""Daga nan sai mu ce miki korariya!"" Inji Aunty Zakiyah""Ai duk abinda kike min sai na gayawa Mama ita Waya ta damu da lamirina!"" "" Gaskiya kan yar lukuta autar mu, SAN baka lura da wani abu ba, su fa yan auta kiba ce da su."" Tura baki nayi nace mata. "" Maganarki ba zai yi aiki akan wannan kyakkyawar matashiyar ba!"" Na fada ina barin parlourn, ai sun san ba kibar sai dai idan suna son takura min sai su ce min yar lukuta. Shiga daki nayi na kalli kaina a madubi, wanda yake tsaye zalla. Ka juya ina kallon bayana, sannan na kalli gabana, ni dai kamar ba mace ba babu ya'yan gwaiba da za a gani ya ja hankalin kowa, wai tsaya me yasa nake tunanin jan hankalin wani ne? Na ga yan tsakanin nan sai batun wani ko aure, rintsa idanuna nayi sharrin makiya ko? Zasu sako ni a gaba, na kalli kaina a madubi na ce. "" Ke Lubnah ki nutsu, idan baki manta ba kin sha wuta a hannun Hafiz!!"" Daga haka na cigaba da shirmena a madubi, wayata ce tayi ™ara na Wauka. "" Ashe za a kawo Alhaji ba lafiya?"" "" Sorry Aunty Nuratu, mantawa nayi ban gaya miki ba, za a kawo shi gobe in sha Allah."" "" Allah ya kai mu, Allah ya bashi lafiya."" "" Amin Ya Allah!"" Ta lashe wayar kuma fa naje Gym din ni na ma manta da wani kawo Abba" "sai da na dawo aka tashi zancen, kasancewar yau Laraba." "Da dare muna parlourn Ya Ado ya ce min. "" Ke bani e-mail Winki don na lura yadda kika tsani aikin" "nan ko an turo miki ba zaki fada ba!"" Lubabatushehuusmanjamare'a@gmail.com daga haka na cigaba da shan fruit dina. ""Shima password din sai na roke ki?"" Nifa aikin kamfanin nan sam bai min ba,"" ni wallahi aikin nan haushi yake bani! Lulu@19"" na fada ina hura hanci, "" don Allah dube ta yadda take hura hanci kamar wata sauro ke yanzu baki ji dad'i kin samu aiki a Lagos ba, kin zama big girl!"" Kalaman Abba ne ya" dawo min........ "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 38" """ Idan karuwanci ne dubunki sun yi babu riba."" Hadiye yawun bakina nayi da yayi min kauri yanzu haka" "Abba zai zo ba halin na je na ganshi ko na ji muryansa sai na ji lokaci guda tsoronsu ya kama ni daga shi har Ya Hafiz, wani irin masifaffen tsoronsu ya kama ni. ""Lubnah!"" Kallonsu nayi na mike a hankali zan wuce sama Ya Ado ya ce min. ""Kina tsoro ko?"" Tsayawa nayi ina mai da kwallar da ya cika min idanu ciki na ce mishi. ""A'a kawai im wondering yadda zamu zan ga Abba ne!"" ""Kada ki damu zaki ganshi."" Da sauri na koma sama, ranar dai saboda na saka tsoro da damuwa sai da nayi mafarkin, wai gashi nan Ya Hafiz zai tura shi a rami, amma na kasa zuwa cetonshi, karshe ina ji ina gani ya fada. Da wannan mummunar mafarkin na farka around 3am, ban daki na shiga nayi alwala na zo na gabatar da sallah Nafilla, ina zaune a wurin har aka kira sallah farko nayi raka'atu fijir, ina idarwa na cigaba da addu'a domin wannan lokacin yana da muhimmanci, karfe biyar da wani abu aka yi sallah asuba nima nayi, da na idar sai na ji na kasa fita motsa jiki, haka na kwanta saboda barcin da ya cika min idanu. Ban farka ba sai karfe daya na rana, ashe tun karfe goma su Mama suka iso, ganin kayanta nayi a kusa da ni ga kamshin turarenta na Touch me, da sauri na shiga ban daki nayi wanka na saka wata riga irin bubu din nan na sauko kasa, ba kowa a gidan, wayata na koma na dauko na shiga kitchen na hada abincin da zanci wanda ganye yafi yawa na zauna na fara ci a hankali, ina shan tea, a hankali ina kallon tv. Wayata na kunna, sannan na cigaba da kallon tv ina jin kamar wani abu yana damuna. Can na duba wayar na kira Mama. ""Mama shi ne ko ki tashe ni?!"" Murmushi tayi tana faWin, ""tow sannu ban tashe ki ba jinjiirata na ga kina barci ne kamar mage."" Murmushi nayi na ce mata. ""Kun iso lafiya ya Abba da jikin?"" Bana gabanta amma yadda ta amsa min kamar irin she does care ta ce min. ""Gashi can ana ta fama da shi."" ""Kamar ya?"" ""Tow ai yaki ya tsaya a duba shi dai fama ake yana tirjewa!"" Idanuna ne suka cika da kwalla. ""Allah sarki Abbana Ubangiji ya bashi lafiya."" ""Ke kashe wayar kada ki fara min kuka!"" Haka na kashe wayar ina jin wani iri a raina, karfe shida na yamma ta dawo gidan ita da Ya Ado don Aunty ta dawo da wuri tayi abinci ta kai, naso na" bita ta ce min. Na zauna saboda Yara. Tana kaiwa bata jima ba sai gata nan. "Tow dai gasu Mama ma sun dawo, Kallonsu nayi na tafi na rungume ta. ""Mama ya Abba da jikin?"" ""Da" "sauki matsa min na je nayi isha,."" Ta fada tana wucewa haka na bi bayanta ina faWin. ""Mama zasu min dariya!"" ""Yo ba sai na musu rashin mutunci ba!"" Haka dai ta amsa min anan ta shiga ban daki tayi Alwala da wanka sannan ta fito ya sauya kaya na kawo mata abinci, tana idar da sallah ta fara cin abincin, ni kan gasashen kaza Ya Ado ya kawo mana, na fara ci ina kallonta. Tashi nayi tafi kitchen na hada Yorghurt fruit na dawo dakin ina sha. ""Yanzu haka rayuwarki zata koma ba abinci mai taimakawa sai irin wannan?"" ""Mama kibar da ba aso zan yi!"" Gyada kai tayi tana kallon yadda na ci kaWan na namar sauran" "kuwa na barshi sai Yorghurt din na shanye, muka cigaba da hira.. ""Lubnah!"" Kallonta nayi don yadda ta" "kira sunan yasa na fahimci maganar ba na wasa ba ne. ""Kin san yadda kome yake tafiya ko?"" Gyada kai" "nayi ta cigaba da cewa. ""Yanzu na ji Adamu yana cewa zai nima miki aiki babu wani ne da yake nimanki?"" Wani irin tsoro ne ya lullube ni har nake ji kamar an lullube ni da danyen nama. "" Ko har yanzu tsoron yana nan!"" Bakina yana rawa na rufe shi, domin sai naji kamar xan yi amai ne, a hankali jikina ya Wauki wani irin rawa. Ai kuwa da sauri na shiga ban daki sai da nayi aman abincin da na ci, na dawo na kishingida bata kara min magana ba, ta yi shiru da zancen ranar a wurinta na kwana. Washi gari Yaran gidan da gulma wai. "" Aunty Lulu yau ta kwana a wuri Mamanta."" Sosa kai nayi na ce musu. ""Oh dai Mamana ce!"" Haka na raka su har inda school Winsu yake, daga can kuma zasu wuce islamiyya don an" "sauya musu na yamma nan, idan suka dawo zamu yi karatun dare da su, har da home work." "Bayan na karya su Mama suna ta shirin tafiya Asibiti, Mama take gaya min ai tun asuban fari Ya Ado" "ya kaiwa Tahir abinci, ya dawo ya tafi aiki. Ina can ina baza kafasiti a wurin Uwata. Karfe goma Aunty Nuratu ta zo muka tafi asibitin da ita, daga waje na tsaya ina kallonshi da yake ta barci.. hawaye ne ya zubo min haka na koma na zauna ina kallon ina share hawayen da yake zubo min, fitowa suka yi a lokacin Ya Tahir ya iso yana min tsiya. ""Who is this fine lady? Daga wata kasar take anya ba daga Somalia ba ce!"" ""Ya Tahir zaka fara ko?"" ""No na ga wata hadaddiyar baby doll ce, mai kalar Somalias."" Murmushi nayi ya kai maganin sannan ya fito nan aka yi ta gaisawa da raha. ""Kafaya kin ga yarinyar nan ko a hanya na hadu da ita dai dai na juya nace kamar na santa!"" ""Allah ya ganar da kai Attahiru."" ""Mama da dai kin ce Dahiru zai fi gane yana tsokanata!"" ""Mama don Allah kada ki biye mata!""? Haka muka yi ta hira, wurin karfe biyu sai gashi ya je ya sayo abinci, ni nawa kusan rabi ganye sai fried rice da grilled fish, sai soda drink. Ya ajiye min yana faWin. ""Nasan ba zaki hada kifi da madara ba, shi yasa na amso miki soda!"" Da yake an kebe dakin mutum daya ne, kuma maganar gaskiya a can amenity muke akwai parlourn da family zasu zauna, kuma abin dad'i babu al'umma sosai a wurin haka yasa na sake naci abincin, wanda a lokacin ya lura da yadda nake cin ganye ya ce min. ""Ganye yafi kara lafiya kenan?"" ""Eh shi shinkafar akwai starch a cikinsa, shi kuma yana bin jini ne!"" Matsa lemon tsami nayi akan abincin da kuma kan kifin, ""shi kuma na meye?"" ""Yana narka da kitse da maiko!"" ""Sodar fa?"" ""Ita tana hana ciki cika ya kumbura, ruwan da na fara sha shi zai hana ni cin abincin kamar yadda baa so!"" Jinjina kai yake sai a lokacin Mama ta ce min. "" Tow idan kika auri talaka fa?"" Murmushi nayi nace mata, ""Alayawu, kafi Egu, tafasa, bawon kabeji. Lemo da gwaiba ba arasa su a gidan talaka, rama da yakuwa duk suna da amfani" "zanci ai babu inda Allah baya kai mutum.""" """Yanzu bakya cin kome fa!"" "" Eh duk wani abu me starch bana sonshi, saboda akwai wata ™waya da" "nayi tasha bude tsoka take sai mutum ya bude kamar an hura shi, har da shi a karin kibar jikina."" "" Allah ya kyauta!"" "" Amin Ya Allah! "" Daga haka muka cigaba da hira kar yamma sallah yake tashinmu, wurin karfe biyar sai ga Ya Ado da fruit da abincin dare, nan aka sake bude hira anan na ji sun ce ashe Rufa'i da su Aunty Hindatu da Aunty Innah zasu zo. Shi Ya Tahir zai koma, sai Ya Sani yazo. Idan Allah yana sonka da arziki sai ba ka ikon yiwa Yaranka hidima a kananun shekarunsu da zarar sun girma su biya wannan abin da ka yi musu. Wannan abinda ake kashewa babu kwandalar kowa Ya Ado ne yake a cikin aljuhunsa abu daya yace ba zai dauki nauyin kawo kowa ba. Su kuma da yake sun saka ransu zasu so suka ce ya huta, muna isowa gida na ga sakon River State ya iso doya ce manya manya. Kamar yadda nake zaton" "akwai wani abu da yake faruwa yadda na ga Ya ado da Ya Tahir tattaunawa, ban sani ba amma ko Mama" basu bari ta sani ba. Da muka dawo ina kwance a dogon kujerar parlourn ina kallon wani yoroba film da "yake zuwana nima na zama jikar oduduwa, ina son film dinsu musamman irin na kauye na zamanin baya, yana nuna yadda suke kare martabarsu da kimar kabilarsu." """Lulu!"" Tashi nayi ina amsawa, ""kin san wannan kwayar?"" Kallonsa nayi kafin nace mishi. ""A ina ka" "samu?"" Gabana yana faduwa, ""Kin san shi kenan?"" ""Eh!"" Na fada idanuna yana kawo ruwa, ba dai shima Abba ya fada irin matsalar da nake ciki ba ne. ""A ina kika san shi?"" ""A wurin Ya Hafiz!"" Daga haka ya maida aljuhunsa, ni kuwa na fashe da kuka, bai gaya min kome ba. Amma na ji a raina akwai wani abu. ""Ya Ado mai ke faruwa? Ka gaya min don Allah!"" ""Ba kome kawai bincike muke!"" Duk yadda naso yayi magana yaki, ""ki yi shiru kada Mama ta san me yake faruwa zan tafi Bauchi ranar Monday, idan na dawo" "dan miki bayani!"" Haka ya Ado ya bar ni a dame." "Kamar yadda ya ce kuwa haka ce ta faru, ranar Monday ya wuce Bauchi. Sai dai zuwan shi Bauchi bai" "haifar da Wa mai ido ba, domin anyi wani irin tashin hankali ne akan maganin Baban Jama'are ya ce shi ya kaiwa Abba yayinda yan uwanmu bakiWaya aka zargi Ya Hafiz amma kiri-kiri mutumin nan ya wanke danshi, sannan suka ce ko da basu da arzikin Jirgin sama zasu zo su ga dan uwansa. Karshe haka Goggo Alti ta kashe case Win, amma don goyan bayan sun goyi bayan Hafiz har da cewa ai kafin suyi yunkurin kai Abba lagos waye yake kula da shi, Baba Malam tsohon munafuki har da cewa a gaya min na dawo dakina na daina yawon gantali da karuwanci. ""In sha Allah Ubangiji ya ™are Lubnah wannan fatar sai dai ka ganshi a cikin wasu jikokin da kafi so!"" Inji Yadiko, kai anyi gurmi Goggo Alti ce kawai bata yi magana ba, tace ita bata ga laifin Yaran Baban Bauchi ba, da gaskiyarsu, haka suka bar zancen washi gari shi da su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka bar Bauchi har da Rufa'i aka tawo jos daga Jos suka hadu da Aunty Raliyah suka biyo jirgi, sai tsiya suke ta yiwa Rufa'i wai Allah ya kira shi lagos, amma yana da" rabon zuwa lagos. Da yake shima akwai baki tuni ya kare kanshi. *** Hafiz Ya razana yadda aka fahimci shi yake bawa Baban Bauchi magani tow meye dalilinsa? Amma haka suka "bar zancen shi babban damuwarsa ya ga Lubnah in sha Allah duk ranar da ya ganta ko tana so ko bata so sai ya kwanta da ita, domin a yanzu da yake nan babu wata mace da take tare da shi, ko ya dauko maganar aure za a lalata mishi, ga Baban Jama'are da ya dawo Bauchi shima ya dawo shagon Wan uwansa, hmm wani abu da Yaran Baban Bauchi basu sani ba shine ana ta murkushe kudin shago domin kuwa na karamin barna Hafiz yake yi ba. Wanda haka da Baban Bauchi ya d'ago ne yayi sanadin da Hafiz" ya fara dirka mishi magani. (Wash hannuna ) "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 39" Ganin yadda lokaci guda asirinsa ya nime tonuwa ne Baban Jama'are ya saka shi a gaba da tambayar me "ya faru, sanin cewa Babanshi yana tare da shi amma sai ya kasa faWa mishi gaskiya ya ce musu. ""Kawai don sun tsane ni ne, amma me nayi musu da zasu ji haushi bayan ni nake kula musu da mahaifinsu da suka yi watsa da shi, meye ban shi ba. Me kuma bana mishi kawai ban san me na musu suka tsane ni ba ne."" Wannan magana sai yayi tasiri a ran Uban Hafiz ya cigaba da cewa. ""Idan sun tsane ni saboda Lubnah har yau Lubnah matata ce tunda ba ni na sake ta, kuma ban amince da sakin ga har yanzu ina son Matata."" Yadda yake maganar a dame yasa Uban shima ya shiga damuwa, ya tafi dakin da Baba Malam yake ya gaya mishi, nan dai suka kara kulla wata munafuncin zasu zo lagos su ga halin da Abban" yake ciki su gaya mishi abinda Yaransa suke zargin Hafiz da shi. "Wannan kuwa ya yiwa Hafiz dad'i, wanda ya kai har cikin ransa yaso ya biyo su. Amma suka hana shi," "da yake sun san al'amarin na kudi ne, basu fara zuwa da batun kudin jirgi ba, can bypass suka nufa anan suka biya kudin mota dubu sha bakwai daga Bauchi to lagos, sannan suka dawo idan bar aka samu fasinjoji zasu tafi, a Hajiya da ta ji labarin abinda ya faru bata yi kasa a gwiwa ta kira Malaminta ta gaya masa. Abin da ya gaya ya, ba karamin dadi ya mata ba, ta kuma ta ji a ranta idan har Lubnah zata dawo rayuwar d'anta bata ki tayi kome a kai ba, wannan abin ya saka ta kara tura kuWi. Sai dai shima ai ya boye" mata gaskiya ya barta da duhun zuciya. Bayan haka ita kanta tasan yaudarar kanta take amma da yake ta sauka akan hanyar da ya dace kyaleta kawai ta dace ayi ta ji a jikinta. **** "Lokacin da su Aunty Hindatu suka iso sai da suka fara biyawa asibiti kayansu aka kawo, ina kan injin" "motsa jiki nayi zufa shakaf kunnena ina sauraren karatun Alqur'ani, suka turo kofar. Zuba min idanun suka yi kasancewar na basu baya. A hankali Aunty Innah ta lallabo sai da ta zo kusa da ni na ji an tab'a ni, da sauri na juya ina ganinta ba fasa ihu, tare da rungume ta. Da sauri na koma wurin Aunty Munah da Aunty Raliyah, sai Aunty Hindatu da ita kan har da daukata. ""Auta kece haka kika koma fine lady haka ashe da gaske Tahir yake da yace mana, wallahi kuka ga auta sai kin rantse ba ita ba ce, yarinyar nan ta kara kyau dole idan Hafiz ta ganta ya kusan mutuwa."" Murmushi nayi ina kallonsu na shiga kitchen na dauko musu ruwa da kayan abinci. ""Kun yi sallah ne?"" ""Omo ku ji yadda take magana kamar ba lulunmu ba!"" Inji Aunty Munah, ""kai Aunty Munah Hausar ma dabance da taku;"" ""kwarai da gaske baki ji yadda kike maganar a ganyance!"" ""Ni din nake yanga."" ""Wallahi Innah har da wani kalar shagwaba irin na Ajebo."" Dariya suka bani na haura sama da gudu na sauya kayana, ""Jama'a ku ga yadda take gudu kamar dama can ta saba da zuba gudu!"" Inji Aunty Raliyah, murmushi Aunty Hindatu take tana mai share kwalla da yake shirin sauka mata. ""Kamar ba yarinyar nan ba ce ta kusan haukacewa, yau ku ga yadda ta" "koma?"" Hawaye ya zubo mata, duk sai suka koma tuno abinda ya faru." "Ni dai watsa rywa nayi na sauya kaya sannan na fito kafin nan sai da na kara auna tsawona, na ga dai" "na sauka ajiyar zuciya na sauke na sauko sanye da riga da zani na atamfa, ina zuwa na zauna a gefensu har mun fara hira na mike na hado fruit salad, na zo na zauna ina sha ina kallonsu, murmushi nake. ""Yan mata babu bazawari ne?"" Kwarewa nayi na fara tari Aunty Hindatu ta make Innah da tayi maganar. ""Ke dai baki da girma sai na jikinki yaushe ta samu lafiyar da za'a fara maganar aure?"" Inji Aunty Munah, ""kyale ta mana Lulu take your time, duk abinda ya zo maka mai kyau ko mara kyau daga Allah ne, kada ki yi rushing a hankali Mijinki zai zo miki."" Ji nayi fruit din ya hau min kai, na ajiye shi ina kallon tv. ""Ya Abba" "da jikin?"" ""Da sauki tunda gashi nan yana gane kowa .""" "Murmushi nayi na ce musu. ""Allah ya bashi lafiya yasa zakkar jiki ne."" ""Amin Ya Allah!"" ""Ya batun" "aikinki yaushe zaki fara?"" Tura baki nayi nace mata. ""Dukkanku aikin gwamnati kuke ya ado ya nima min aikin kamfanin ni wallahi tsoron aikin kamfani nake kada sai ka sake jiki a kore ka!"" Murmushi Aunty Raliyah tayi tana kallon yadda nake magana. ""Auta kin ga yadda kika yi kyau da maganar nan, asalin kin fito yan mata babu wnada zai yarda kin tab'a aure, like how you look beautiful and charming, auta gaya min me ye sirrin!"" Rufe fuskana nayi ina dariya, "" bude na ga beautiful lady din da take gabana, wallahi kamar na sace ki Yar nan! "" ""Innah dube ta fa, yadda kika san irin yan 23 uku nan koda yake yanzu wasu daga cikin sa'oinki suke aure dubi yadda ta samu natsuwa da kwanciyar hankali."" Yanzu maganar Wasim da Aunty Nuratu Kafaya ya dawo min daga lokacin da kike tsaya da kafarki a lokacin kowa zai soki."" Murmushi nayi haka suka ci abinci, sannan suka shiga ciki suka yi wanka da hutawa la'asar tana yi muka shirya bakiWaya zuwa Asibitin, tunda Rufa'i ya ganni ya rike baki. "" Adamu yarinyar nan sakata kuka yi a injin amma? Ke Lubnah gaya min wanke ki aka yi a injin ko?"" Dama can na san halins sai haka bai wani dame ni ba, haka muka yi ta hira na leka Abba yana barci. "" Shi barci kullum yake yi ne?"" Murmushi tayi tana faWin. "" Eh yana farkawa har ya ci abinci ma, tow jininsa da yake yawan sauka ake son a iya sarrafa shi."" ""Allah ya bashi lafiya!"" Kuka sai na fara kuka idan har wani abu ya sami Abba bai saka min albarka a rayuwata ba, ba zan yi kyakyawar karshe ba. Kukan da nake yi ne ya dami Mama ta ja hannuna muka fita. Kusan yadda abin ya tashi hankalina. ""Tow meye na kuka?"" ""Mama idan Abba bai yafe min ba, rayuwata zata lalace domin ina jin a raina ni ce sanadin wannan ciwon nashi."" Kura min idanun tayi tana jin wani irin abu a ranta. ""Wani ya zarge ki da cewa ke ce sillar ciwonsa ne?"" Cikin shashekar kuka na bude baki xan yi magana tura min kwakwa tayi a bakina. ""Ya isa haka, ba ke ce sanadin ciwonsa ba haka kuma ba zaki tab'a zama sanadin wani ba, ina da yakinin cewa Ubangiji ya amsa min addu'ata akanki, don haka ki daina kuka akan abinda baki da ikon sawa ko hanawa, kada ki manta Mamanki tana tare da ke a kodayaushe, kofata a bude take."" Haka tauna kwakwan da nake ya hana ni kuka, Mama tana sona sama da baya Mama tana kokarin bada har Rayuwarta domin ni.. ""shekaranjiya nayi mafarkin wani kyakkyawan bafulatani ya dauke min ke."" Ta fada tana murmushi, kallonta nayi sai kuma na tura baki nace mata.""Mama dauke ni fa!"" ""Eh amma na gaya mishi idan ya saka ki kuka ba xan yarda ba, idan ya saka ki damuwa ba xan yarda ba, idan ya sake wani abu ya same ki ba zan yarda ba, domin na hango shi cikin kuraye da macizai ne, sai dai ina ji a jikina shi jarumi ne domin shi Waya rike da sanda ya rike hannunki har wani kyakkyawar gida, kin ga kenan idan ba jarumi ba, babu wanda zai iya ratsa waWannan halittun ya wuce lafiya lau. Da haka nake jin a jikina Ubangiji ya amshi addu'ata ya kuma ajiye ta zuwa" "lokacin da zai biya min ita."" Yake nayi mata domin naga Mama ita fa tayi nisa a kaina,Aqur'an bata jin" "kira. A hankali ta riko hannuna ta zaunar da ni a kujeran da yake gaban wata office. ""Kin san yadda nake" "son ki yi farin ciki kuwa? Kaf duniya babu wanda ya kai ni son ki yi farin ciki, sai dai abu daya zan gaya miki daga yau kada ki kara zama wani ya wulakanta ki, kada ki kuma cutar da kanki saboda zaa ce kina yawon aure kada ki damu ban kuma ce ki rena duk wanda zai zo rayuwarki da sunan aure ba, amma kuma kada ki rena kanki."" Kwantar da kaina anyi a kafadar Mama ina jin wani irin nutsuwa na shiga ita uwa duniya ce ga Yaranta, baya ga ita kanta tana bukatar kowa a tare da ita. Uwa ita take manta da kanta tayiwa danta addu'a. Mama she is amazing mother of me, ta gwammace ta rayu da ni akan aurenta. Mika min goran ruwa tayi wanda ta ciro a jakarta tana faWin. ""Gashi sha na san kina shan ruwa dama da kome!"" Amsa nayi na sha domin bakin a bude ya™e.. ""Mama kina ganin na karbi aikin da Ya Ado ya nima min ni nafi son aikin gwamnati ne!"" Zungure min goshi tayi tana faWin. ""Waye yasan gobe ban da Allah idan kika yi hakuri kafin ki dauki lokaci sai Allah ya sauya miki da abinda yafi alkhairi, ki cigaba da addu'a duk wata rayuwa tana bukatar addu'a, ita Addu'a mukulin dukkan wata Alkhairi ne da toshe duk" "wata sharri."" ""Mamana, in sha Allah.""" """Wai Mama nan kuka zo kuka zauna kun manta da da wasu a cikin."" Inji Aunty Raliyah, ta ce mata." """Raliyah bana son gulma taya zaki biyo Uwa da Autartar!"" ""Allah ya baku hakuri ya kuma bamu hakuri .""" "Dariya na saka muka wuce cikin asibitin mika cigaba da hira, har na manta abinda ya faru. Kusan" "mutane da suke zuwa ganin Abba abokan aikin ya Ado ne, kwanakin su Aunty Hindatu biyar suka juya zuwa gida, nayi kewarsu sosai. Itama Mama tana cika sati biyu ta koma Bauchi aka kawo Yadiko, zuwan Mama ban tab'a shiga wurin Abba ba, amma yadiko tana zuwa ta saka ni a gaba har inda yake zaune suna magana da Rufa'i, yana ganina ya dauke kai, haka na koma bayan Yadiko na tsaya ta ce min.. ""fito ke ai shi ya samar dake idan ya isa sai ya gayawa Allah baya kaunarki sai na san inda zan ajiye lamarin,."" Abinda na lura Abba ya Wan yi sanyi. Haka dai tayi ta surutu koda na gaishe bai amsa ba, ban kara ba. Ina zaune har Ya Ado ya zo yana zuwa na bishi muka bar asibitin. Ashe bayan fitata yake cewa Yadiko. ""Yaushe Yarinyar nan tayi kyan gani haka?"" ""Lokacin da kaso kashe ta Allah bai nufa ba, lokacin da ka ji gara ta mutu da ta cigaba da amsa sunarka. Lokacin da ka ji a ranka baka kaunar ganinta har kake mata fatar karuwa. Allah Alhaji ka ji tsoron Allah ka ji tsoron wanda ya mika lamarinsa ga Allah dubi Yarinyar" "nan yadda ta koma kamar yar tsanar zinari.""" "Jin haka yasa yayi shiru, da Yadiko take gayawa Ya Ado ya sha mamaki, da ya sauko kamar bashi ba," "yana kuma iya gaya mishi yadda yake ji, babban matsalar da yake fama da shi shine rashin barci wanda shi yake haifar mishi da ciwon kai mai tsanani karshe jininsa yayi kasa. Haka yasa aka kara rike shi, basu san me yake damunsa ba, amma idan har akwai wani abu da yake damunsa bai wuce yadda Lubnah taki" komawa gidan mijinta ba. --- A Lagos din kuwa Baban Jama'are ne fa Baba Malam suke ta yawo a garin Lagos basu dan inda Ya Ado "sun kashe kudin hannunsa, gashi an sace wayar Baban Jama'are, wanda da ita yake kiran Hafiz Baba" Malam kuwa yaki bada wayarshi domin kanshi kamar zai juye da suka shigo lagos sun zata kamar Bauchi "ne da bata da girma haka. Haka yasa suka yi ta yawo daga nan zuwa can daga can zuwa nan duk sun galabaita kusan sati biyu, haka yasa suka fara bara, suna samun abinci da zasu ci." *** *Russia* Moscow Zaune yake gaban laptop hannunsa daya yana tallafe da fuskarshi. Idanunsa yana kan files da aka turo "musu yana bin sunayen kowani mutum a hankali idanunsa ya sauka akan Lubabatu Usman Umar Jama'are, jikinshi ne yayi wani iri-iri amsawa yummmmmmm........." "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 40" "A nutse yake kallon dan hoton passport da yake jikin CV din, a hankali yake bin information dinta, wani" "irin abu ne ya ji ya tsaya mishi a rai, lokacin da yaga wurin marital status, sai ya tsinci kanshi da kashe laptop din, yana mai jin wani abu a ransa, amma a fusakarshi bai nuna yadda abin ya dake shi ba, wata zuciya ce ta ce mishi. ""Ba ita ba ce wata ce daban!"" Wani bangare na zuciyar ta sake ce mishi. ""Ina ga ita ce ba wata ba ce."" Zare medical glass din idanunsa yayi ya Wan saka yatsu biyu a tsakanin idanunsa yana dan taSa tare da musu massage, mikewa yayi tare da mika sai da kasusuwanshi suka amsa sannan ya kalli hadadden dakinsa, da yake can yamma da cikin gidan, bude kofar yayi yaji yanayin gidan ya sauya daga sanyin da ya koro shi dazun, yana da wani irin lalura da baya son sanyi sam, dumin da gidan ya dauka ya bashi damar fitowa, sanye yake da trouser brown na kamfanin Adidas, sai rigar shirt din jikinsa na kamfanin polo, kafarshi kuwa sanye yake da safa baki, a duniya abu daya yake gudu sanyi. Infact yana da allergy da sanyi idan ya cika yawa yana iya samun attack na mura mai tsanani, shi yasa a tsarin rayuwarsa tunda ya fahimci baya son sanyi ya haramtawa kanshi shan kankara ko wani abu me sanyi tun yana Yaro har zuwa yau da ya girma. Yadda gidan ya dauki dumi yasan mutane biyu ne zasu kula da yanayin domin har yau kallon Baby boy suke mishi. A hankali yake takawa duk da kasancewar shi" "lafiyayye mai kuzari amma idan lokacin sanyi yazo haka komawa yake kamar kazar da ruwa ta mishi duka, a hankali ya dauko daga stair din da ya sada shi da parlourn, da aka wura wuta a irin gidajen turawa. ""Bilyl!"" Wata dattijuwar baturiya ta kira shi, ""Na'am Granny!"" ""Ka fito?"" Murmushi yayi mata sannan ya isa gaban dinner table ya dauki kofi ya zuba ruwa ya dauka ya sha. ""Na zata ka ayi barci ne?"" Wuce ta yayi ya zauna a daya daga cikin kujerun parlourn da alfarma. Juyawa fararen idanunsa yayi a kanta, ba zaka ce ya kai shekaru arba'in da wani abu ba, asalima yanzu yake jin kanshi. Dai irin yanayinsa na rashin son magana da hayaniya yasa tayi shiru. Yadda ya kalleta nan tasan ya gaji da magana ne. ""Kai dai baka da halin wannan idan shi mace zata gani ta soka tow ba zaka tab'a aure ba sai dai ka mutu a tuzuru."" Wata karamar murmushi yayi wanda ya fitar da asalin yanayinsa na shi ba Bature ba shi ba kuma bafulatani ba, ya mai da kansa ya daura a jikin kujeran. Turo kofar da yake cikin parlourn aka yi ya juya wata mata ce ba zata huce irin sittin da wani abu ba, amma saboda yadda jikinta ya samu kulawa zaka" "Wauka irin yar talatin din nan ne. Sai ka nutsu zaka fahimci ai da wuce shekarunta. ""Turaki!"" Ita Waya ce" take iya kiran sunan shi kai tsaye kamar yadda yan Nigeria suke kiran sunan. Shiru yayi bai amsa mata ba "sai zuba mata idanu da yayi yana kallonta. ""Am sorry, amma ai na gaya maka ba yadda xan yi da Mandy!"" Tabe baki yayi yana cigaba da kallon tv yadda ake shirin bikin Christmas ya kalli kakar da kyau, itama kallon Yarta take tana mata magana da idanu. ""Amma kinsan ba zaki iya rike ta ba me yasa kika dawo da ita Herlim."" ""Amma Mama kin san dai ba zan barwa William Yata ba ko? Mutumin da bai da aiki sai safara da damfara!"" "" ""Ya isa haka Please!"" Ya fada yana dafe kanshi, ya fito waje ya sha iska na so yake a kara mishi wanda ya gani a laptop ba, turo kofar gidan aka yi wata matashiyar budurwa da ba zata wuce ashirin da uku ba, ta shigo tana marisa. Tashi yayi ya wuce kitchen daura tukunya yayi akan gas tare da zuba traditional Herb, ya juya ya kalli yarinyar tana ta marisa da surutu irin na wanda ya sha ya bugu. Shigowa wani matashi da kayanta yana zuwa ya gaishe su sannan ya ajiye ya gaida Turaki ya ajiye key. ""Mandy me yasa bakya jin magana ne?"" ""Mom taya zanji maganarshi bayan ya ce baya sona, cewa yayi baya sona zuciyarshi ya bawa wata can da bata san darajarshi ba, Mom ina son Bil!"" Ta kama shakuwa, rikota Uwar tayi zuwa dakinta ko kafin su isa ban daki ta kwara amai a dakin zuwa ban dakin ban da kirnin giya ba abinda yake tashi. Tana maganar uwar ya shiga wanke mata, sannan ta zube a" "gadon barci ya dauke ta, a lokacin ya gama dafa kayan ya zuba a kofi sannan ya mikawa kakar ya ce mata. ""Granny!"" Yadda ya kira sunanta a kausashe kafin ya fadi abinda yake ranshi ta ce mishi. ""Ka kusan komawa gida ko?"" Yadda tayi magana sai ya kashe mishi jiki. Amma kuma yasan Datti yayi hakuri da rashinsa, Daddah tayi hakuri da rashinsa idan ya cigaba da zama baya jin yayiwa mutane biyun nan" "adalci. ""Zasu so ka kamar ni kuwa? Ina sonka idan na kalle ka iyayenka nake tunawa da su.""" "Wato drama a cikin tsohuwar nan Allah kaWai ya san yawansa, tasan abinda zai iya hana shi komawa" "shine ta fara kirkiro drama domin ita har yau bata yarda mutuwar Mahaifiyarshi ta Allah ce ta faru da ita tafi yarda da cewa kashe ta aka yi, kuma babban abin zarginta Hajiya Zeenatu.. A hankali ta fara girgiza kai ta sake kofin ruwan da yake hannunta ya fashe tare da watsuwa a jikinta. "" A'a Bilyl kashe zasu yi, ka zauna anan. "" Karar fashewar abin yasa Herlim ta fito tana kallonsu. "" Meye kuma? "" Da sauri ta zo ta rike hannunta. "" Herlim ki ji wai zai tafi Nigeria, bayan kashe shi zasu yi."" Murmushi tayi ta ce mata.."" Mama shima fa akwai wnada suke bu™atarshi! "" ""Ai dole ki fadi haka tunda bakya kaunar fadar da yake yiwa Mandy."" "" A'a Mama kada mu yi haka dake Turaki yana da tashi rayuwar kin turke shi wuri guda, akan me? Gaskiya ya kamata ya tafi idan ya samu sarari ya zo ya ganmu!"" Ai kuwa nan ta fashe da kuka ta wuce dakinta ta fara kiran number Sarah wacce take Germany tunda ya zauna a can."" Hello Sarah kin ji wai zasu tura Bilyl Nigeria yadda suka kashe Anna haka zasu kashe min shi."" Murmushi tayi ta ce mata. ""Mama aiki da ya bari ya zo nan da zama ki barshi ya tafi Please Mama shima can suna bu™atarshi Bulal ba yaro ba ne, da za a ce lallai sai ya zauna Bulal yana bukatar iyalin yana bukatar rayuwa akan me zaki rike shi? Wannan son Kai ne!"" Da yake tana son Yaranta Kuma tana jin maganarsu sai ta ce mata."" Shi" "kenan amma sai after bikin Christmas zai tafi!""" """Tow duk yadda kika ce amma ki sani shi fa CEO ne guda fa."" Ta fada mata haka, sai kuma tayi shiru ta" fara rarrashin mahaifiyar tasu. "A can parlourn kuwa kallonshi Herlim tayi tana girgiza kai ta ce mishi. "" Ce mata kayi zaka tafi?"" Shiru" "yayi kafin ya ce mata. "" Eh! "" Ya cika da cin apple din da yake kan table din. ""Kai baka iya lallabata ba ne sai ka na gaya mata magana gatsu?"" Kallonta yayi kafin yaa dauke kai idan ya ce zai yi magana maybe itama ya cabb'a mata mara daWi, kwanciya yayi abinsa bai kara ce mata cikanki ba, ita tayi ta masifa kafin" "ta ce mishi. ""Nasan kana son ka kome amma maganar gaskiya Mama tana tsoron kada wani abu ya same" "ka ne kamar Annah!""" """Sannan ka ga kai ko auren baka yi ba?"" ""Wannan ba reason ba ne!"" Ya furta a hankali, yana cigaba" "da lumshe idanunshi. Shi fa bai ga dalilin da zai saka a cigaba da rike shi domin hatta kayansa yana dakin Granny amma ace bai da yancin motsi mai ™arfi, idan yana son ya fita sai ta tsare shi da tambayoyi kamar wata jami'ar tsaro. Yana daukar haka ne a matsayin soyayyar da take yiwa Mahaifiyarshi shine duk kome ya dawo kanshi. Tabe baki yayi yana jin kamar ya tattara ya bar kasar, amma yadda yaji tana kuka dazun sai yaji kome ya fita kanshi. ""Ok ki ce mata na fasa!"" Ajiyar zuciya Herlim ta sauke ta wuce dakin mahaifiyarsu ta sameta tana shafa hoton mahaifiyar Turaki da sauran kannensa da suka rasu, zama a gefenta Herlim tayi ya ce mata. ""Mama yace ya fasa tafiya!"" ""Zai tafi na ji haka a jikina zai tafi lokacin tafiyarshi ce tayi idan ba haka ba wata rana zai tafi ban sani ba!"" ""Amma dai shi yace ya fasa tafiya."" ""Shekarun baya da ya tafi kin sani ne? A yanzu ma da yace ya fasa zai tafi adalcin da zan mishi kenan ya tafi suma dangin mahaifinsa suna bu™atarshi. Idan nace yayi ta zama da ni yaushe zai tafi? Idan nace ya zauna nayi mishi adalci ne? Hmmm baki san wani abu ba, a ranshi yaji zai tafi gara na barshi ya tafi ba mamaki wata ™addaran ce ya kira shi, amma bana jin zan iya samun nutsuwa idan baya nan, amma haka zan sakawa raina hakuri da dangana, shi namiji ne yana bukatar rayuwa."" Yadda take magana a sanyayye zai tabbatar maka da ita kanta tana son yaki da kanta ne, turawa suna da mugun son Yara, don har sun fi Larabawa kaunar Yara, ita har yau ganin shi take kamar dan karamin Yaron nan, ganin dan karamin yaro tana tuna lokacin da ya rasa Mahaifiyarshi, yadda ya zauna silent na tsawon kwanaki uku baya ko magana da kowa, lokacin da yaji labarin tunda baya kasar a lokacin, ta girdWslmama shirunsa, take kuma girmama duk lokacin da zai yi magana to a wurinsa mai muhimmanci ne. Domin a lokacin da ya ji labarin mutuwar fushi yayi yaki zuwa ga babansa, duk da Baban yana zuwa amma shi ya yanke kafarshi da kasar, koda ya rasu lokacin ya gama karatunsa na farko, cewa yayi ai dama yasan main target Winsu kenan, domin da suka kashe Mamarshi sun san ba zasu samu kome ba, tun tun daga lokacin Granny ta rike a ranta kashe mata ya da suruki aka yi kuma idan har lissafinta daidai ne Turaki shine next target Winsu, Granny babu church din da bata je ba domin rokon abin bautarta ya amintar da soul din jikanta ya nisanta shi da duk wata masifa da fitina, sai gashi ya kara dawowa da wutar son da ya rasa, anan yan mata yadda suke mutuwar sonshi amma shi sam basa gabanshi, shekarun baya ita wannan kwailar dai ita ce yake mata kallon apple of him eyes, baya jin zai kuma kaunar wata mace bayan ita, Granny ta sani idan tana son su yi dogon hira tana ce mishi Labubu shi kenan, zata iya catch attention dinsa da duk wani abu da take so tana kiran Labubu, akwai ranar da ta ce mishi me yasa yake son under age, ai karya hakki ne da cutarwa, ya ce mata. ""Granny me yasa Yaranku suke bin maza duk wanda yace yana sonsu zasu bashi kansu, me yasa?"" Sai ta yi shiru. ""Da zinar wuri gara auren wuri! Gara a mata auren da wannan" "shekarun ta kara samun tarbiyyar Mijinta sama da ta samu tarbiyyar mazan waje.""" """Kai dai akan Labubu baka ji baka gani!"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Luna ita din wata yanki ce ta" "rayuwata amma wani ya tafi da ita!""" ........... Wash "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 41" ............. Washi gari. "Kusan rayuwar Turaki a gida yake yinta, domin tunda ya bar aiki da babban Cibiyar nukiliya ta" "Germany, ya koma zaman gida ba wai bai da abin yi ba ne, asalima abinda ya tara na wancan aikin bai yin kome da ita, amma yana da wata shago da yake sayar da coffee tun kafin ya dawo rasha da zama, domin a love story din Iyayensa a coffee shop suka hadu haka yasa ya tashi da son bude shagon, idan har zaka ganshi a shagon to kuwa abu me muhimmanci yake kawo shi shagon, sannan shagon yana dauke da baki bakaken fata, wanda ya dauke su aiki, shagon coffee din yana rage mishi abubuwa dayawa, musamman idan ya tuna da yadda ya rasa abinda yake so kawai saboda yanayinsa, a gefen shagon akwai gym da ake yi duk na shi ne. A halin yanzu yana da shaguna manya sosai a cikin Moscow, sai dai idan ka kalle shi zaka iya hango murmushi a kan fuskarsa amma a cikin ransa ba murmushi ba ne, kawai yanayinsa ne haka, duk da kasancewa shi haf Nigeria, yana da wata dabi'a duk inda dan Nigeria yake ya kuma samu wata matsala kafin ka ga wani a wurin turaki ya riga kowa zuwa wurin, ya dibi dalibai maza da mata both Muslim da Christian, domin kuwa abinda ya yarda da shi duk wanda ya zo nan daga gidansu yake ba daga ko ina ba, ya yarda Duk wani dan Nigeria danginsa ne. Sai dai wani lokaci da aka yi wani case na damfara da fashi wani Imyamuri a lokacin ya cire inyamurai a cikin mutanen da yake tallafa wa domin gayen yaso cilla shi cikin matsala, amma bincike irin na kasar suka samu bai da alaka da Yaron. Rayuwarshi babu girman kai, sai dai akwai abinda yayi imani da shi, tsoron mutum duk yadda yake da mutane yana tsoron sharrinsu, sannan idan ka ganshi da matasa tow labarin cigaba ne. A yanzu haka a mutanen da ya diba a nan rasha yan Nigeria ne da zasu yi aiki da shi kuma ya gaya musu gaskiya da albashin da zai basu, dayawa sun yarda domin ita kanta kasar babu wani ma'aikatan gwamnati da basu kuka da ita, gara su yi aiki da kamfaninsa. Rayuwarshi a matsayinsa na wanda ya taso cikin maraici ya saka abubuwa a ransa, ya kuma hakura da abubuwa dayawa don idan ya ce kudi ne ko karfi zai nuna soyayyar da yake kulafuci ba zai samu ba. Shi yasa ya yarda da abinda zuciyarshi take gaya mishi duk abinda ya nima Allah yana bashi sai dai ita da ya nima tace bata bu™atarshi me ya kawo ta kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY? Wannan shine tambayar da suke ta birkita mishi lissafi tun da ya ga sunanta kuma ya kasa yin wani abin arziki, idan kana son mutum kome na rayuwarshi sakawa kake a duniyarka, me yasa ya kasa daina sonta? Me yasa ya kasa ganin laifinta? Saboda ta fito fili ta gaya masa abinda yake ranta da abinda ya ta yanke a ranta. Gaskiyarta da kwarin gwiwarta a lokacin ya hango, ba zai ce ko ta tab'a kallonshi a tsanake amma kuma yaji a ransa tunda ta iya siffanta shi da almajirai ta kalle shi koda kuwa sau daya ne, a hankali ya bude idanunsa da suka yi wani luhu-luhu, ya kafa akan agogon parlourn, karfe uku saura na dare tashi yayi ya nufi dakinsa, koda ya shiga sallah Nafilla yayi sannan ya zauna ya cigaba da addu'a yayi addu'ar idan har Alkhairi ne ya kawo ta kamfanin Allah ya tabbatar idan kuma wani abu ne ya kawo ta Allah ya sa ta bar kamfanin da kafarta ba tare da wani abu ya cutar da ita ba, har kusan asuba, sai da yayi Sallah asuba sannan ya kwanta. Barci ne me nauyi ya dauke shi, amma duk da haka cikin barcin mafarkinta ne wanda tun na wancan fuskar yarinta. Yadda ya ganta ya sa shi farkawa dole ya shiga ban daki yayi wanka, ya kuma fito ya haWa coffee da kanshi, yau kan ma an tashi da niki-nikin sanyi domin ta ko ina ™an™ara ne ke sauka. Bai da yawan cin abinci kasancewar nasu na turawa amma a Nigeria yana son abincin Daddah. Dakin ya shiga ya ji gunjin wayarshi tana niman taimako a dauke ta, jan kujeran da yake aiki yayi ya zauna har wayar ta yanke a karo na biyu, yana kallonta ta kara yankewa a karo na uku ne ya Wauka. ""Hmm!"" ""Amma kana Ina nayi ta kira baka dauka" "ba?"" Kurban tea din yayi ya ce mishi. ""Ina kallon wayar!"" Shiru Uncle Auta yayi kafin ya danna mishi" "Ash'aria, murmushi yayi kafin ya ce mishi. ""Me kake yi da cv din har yau baka turo an ga wadanda suka yi" "qualified ba?""" "Shiru yayi kamar bai da ta cewa har Uncle Auta ya kara fusata. ""Dan iska mai zubin yan daudu ina" "magana kana min yanga."" ""Da kaina zan musu interviews!"" ""Da gaske? Zaka zo kenan?"" ""Ina tunanin haka."" ""Baffa ya sani ne?"" Shiru yayi yana kallon coffee din ya ce mishi. ""No zasu ta jirana, i don't like su ta jirana."" Murmushi Uncle Auta yayi yana faWin. ""Akwai abinda zai dawo da kai ne?"" Shiru yayi yana zoben azurfan hannunsa ya sake wata karamar murmushi ya ce mishi. ""Uncle akwai abinda kake gudun na gani ne idan na zo?"" ""Kai tafi can uban me zan boye maka!"" Anan ya shiga bashi labarin yadda suka yi fa Granny, sannan ya sake murmushi yana kallon dakin yana son dakin, ya ajiye dakin nan a matsayin dakin da zai fara honeymoon idan har Allah ya bashi damar yin aure. Can ya ce . ""Uncle Auta, a mutanen da ka diba aiki har da, manta kawai."" Shiru Uncle Auta yayi kafin ya ce mishi. "" Kana nufin akwai wani abu ne?"" Daha kasar zuciyarshi ya furta wata kalma da ya kusan saka shi jin kunya. ""Uncle idan na dawo na hadu da ita fa?"" Sai kuma ya ce . "" Ba haka nake nufi ba!"" "" Har yanzu baka hakura da Lubabatu ne? Anya ba aljana ba ce kuwa ka hadu da ita?"" Tsaki yayi ya share zancen ya ce mishi."" Batun ghost worker's?"" ""Ba shi nake magana na Turaki magana nake akan har yanzu!"" Kashe wayar yayi, sake kiranshi Uncle Auta yayi yaki Wauka, y kira yafi sau goma amma bai dauka ba, bayan wani lokaci Datti ya kira dauka yayi ya saka a kunnensa. ""Mujitafa ya ce zaka zo haka ne?"" Shiru yayi ya fara kame-kame, ""wato"" ""ban sanka da magana biyu ba, kuma ya ce kai zaka yiwa sabin ma'aikata interviews tabbas muna" "bukatar kazo don Allah, kazo don Allah muna bu™atarka!"" Wani irin shiru yayi yana sauke numfashi." *** "Daga Bauchi aka yi ta kiran Ya Ado, da cewa ai su Baban Jama'are da Baba Malam sun zo lagos, amma ba" "a kuma jin labarinsu ba, wannan abin bai yiwa kowa dad'i ba. A wurina cewa nayi Allah yasa su fada hannun yan yankan kai, domin idan sun zo babu alkhairi a zuwan nasu, haka akayi ya bin office din Yan sanda ana niman, dama kuma akwai wata hukumar da gwamnatin lagos ta ware na musamman idan aka kama mabarata ana tara su sannan a saka su a babbar mota ya kawo su arewa, Goggo Alti ce ta d'agawa Rufa'i da Ya ado hankali akan Babansu mara mutuncin tsoho, ni ko a jikina. Haka ayi ta nimansu har inda ake tara mabarata a can aka same su sun sha uban azaba ba uwar azaba ba. Haka aka kai Baba Malam asibiti shima saboda muran da ta kama shi, Baban Jama'are kan da sauki sai kin yar kunyar da take damunsa ya kasa sake jiki da kowa, gidan wani abokin Ya Ado can ya kai su da yake akwai BQ, anan suka zauna don kwanan Baba Malam daya aka sallame shi. Haka suka daurawa kowa dawainiyya da jigila, idan suka zo asibiti dakyar suke komawa masaukina. Yadiko kuwa ta wanke Baban Jama'are da cewa.. ""Ba fa dole aka ce sai kun zo ba, fisabiilillahi kun zo kuna daurawa mutane dawainiyya, yaji da na iyalinsa" "ko yaji da na mahaifinsa, wannan ba yi bane""" Tunda tayi magana sai suka dauke kafa da zuwa asibiti irin sun yi zuciyar nan. Ranar wata juma'a "muka tawo gaida Abba, da sauki ma dai ya amsa min sama-sama, sai dai wani abu da ya dake ni zuwan Doctor Ahmad da kayan dubayya, yadda yake ta kallona da jana da hira, amma naki sakewa da shi, duk abinda yake faruwa a kan idanun Abba, da yake mun zo bayan an sauko juma'a shima Ahmad ya shigo, wurin karfe hudu sai gasu Baban Jama'are, ko basu gane ni bane, da suka shigo suka gaida Baba da jiki nida su Adil muka gaishe su, sai sake Baba Malam yayi yana faWin."" Wannan ba luba ba ce?"" "" Ita ce Baba wani abu ne?"" "" Ita ce dai da gaske?"" Ganin yadda suke ta mamakin ganina sai Yadiko ta ce min. "" Zo ki kai wannan abin waje ki zubar ki ta addu'a ido guba ne."" Haka na fita jiki a mace. Rufa'i da Ya Ado suka shigo lokacin na fita kenan muka hadu a hanya. "" Ya ka mai damu gida!"" ""Ok! "" Yana shiga ya ga su Baban Jama'are, nan ya sha jinin jikinsa. Haka na zubar tare da dawowa dakin. "" Akan me zata koma? Ita tace muku zata ko?"" Inji Yadiko,Gabana ne ya fadi lokacin da na shiga ina jin maganar da take a hasale. ""Yadiko ai Abba ya sallama min Lubnah kaf duniya babu me iko da ita sama da ni, idan shi Hafiz din jahili ne ai ni ba jahili ba ne, aure fa babu shi ko ina zasu sai su je, ke muje gida ga wannan idan ya muku zaku iya tafiya idan kun ga bai muku ba, ku cigaba da xama amma ba gidan Abokina ba domin ina jin kunyar" "shi.""" "Fashewa da kuka Baba Malam yayi yana fadawa Abba ai yana gani amma ya kasa magana. ""Yadiko ki" "taya yarki da addu'a nan fa sati biyu zasu tafi jarabawa, zata fara aiki."" addu'a sosai tayi sannan muka bar Asibitin, ashe basu tafi ba kuma Rufa'i yayi musu bayani da inda zasu je su hau motar Yola amma suka ki, karshe a masallacin asibitin suka kwana. Duk yadda suka so ganina don su kunna min wuta Allah ya taimakawa Ya Ado ya hanani kara zuwa asibitin wannan abin ya dame su, suka yi ta kunnawa Abba magana da tashin hankalin da sai da jininsa ya sauka har ya fara alamar zai suma, aka kore su. Wannan" abin ba wai iya su kaWai ya shafa ba domin Baba Malam ya kira mutanen Jama'are ya gaya musu. "Kusan tun da muka rabu da Ya Hafiz ban kara jin shi ba, ina zaune yau Lahadi, aka kira ni dauka nayi, na" "saka a kunnena.. ""Kina nufin don kin zo lagos kin kin sabe wannan tsutsar jikin naki, zai saka na manta da cewa ke Matata ce? Ki ji da kyau ke Matata ce ni Hafiz Umar Jama'are ban sake ki ba, ki gama haukarki ina nan ina jiranki. "" Ji nayi kai na ya sara, na kasa amsa mishi wani tsawa ya daka min sai da naji kamar guduma ya buga ya kara buga min tsada idanuna jajur ga wani tsoron da ya cika min rai na ce mishi. ""Meye nayi maka ne?"" Aikuwa ya shiga zagina da cin mutuncina da zarafina yana gaya min matu™ar ban je na ga Baban Jama'are ba sai ya bani mamaki ya kara da cewa.. ""Zan miki abinda kaf duniya babu wanda zai yarda ni nayi miki, nafi ki sanin Lagos idan ban saka an dauko min ke nayi yadda nake so da ke" ba shege nake..... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 42" *Traumatic yana da alaka da abinda ya samu mutum na tsawon lokaci ko kuma na tun daga Yarantar "mutum ba wai ina son nunawa mutane cewa Lubnah bata da yadda zata yi ba ne, akan Hafiz Lubnah" "bata da karfin da zata iya karban kanta ba wai ta gaza ba ne, ko yaro ne aka fuskaci domestic violence" "haka zai taso a kangare na taSa jin wani karatun malamin addinin Muslunci da Yaron ya turawa malamin cewa saboda abinda Babansu yake yiwa Uwarsa yake jin kamar ya kashe shi. Na ga a wani blog na Garkuwar Arewa da wata yarinyar ta turo cewa saboda wannan domestic violence ta kasa bawa duk wani d'a namiji, ba ita aka yiwa ba mahaifiyarta Ubanta yake cutarwa amma tana ganin idan ta hadu da namiji irin Ubanta ne! I don't mean to push Lubnah amma akwai irin masu halin da take ciki! Please be" patient with the story Nagode sosai* "Mikewa nayi na ji kamar cikina ya tsarga. Ya cigaba da gaya min duk maganar da ta fito bakinsa, ji nayi" "kamar ana kunce min duk wani abu da yake kaina ya ce min, ""kina son Iyayenki kuwa? Shi kenan sai ki tuna kamar yadda rayuwarmu take baya yadda kowa yayi shiru akanki yanzu ma bata sauya ba, ki gane mana ina sonki, i a son ganin kukanki na ga kina kuka yana min dad'i sannan idan kika sake wani ya min magana akanki hmmmm abinda zai fi haka muni, don haka ki zuba idanun zuwa na sannan ki gayawa Adamu ya kula min da mahaifina."" Wurgi nayi da wayar na koma can kuryar dakin na zauna Kamar marainiya, ko kara wayar tayi sai na zabura, wani irin tsoro ya kama ni. Haka na wuni a dakin har dare ban fita ba, sallah ne kaWai nayi dakyar, ba sai ga zazzaSi ya rufe ni ba, kwanciya nayi a dakin har Ya Ado da Aunty Zakiyah suka zo duba ni ban gaya musu ba. Wayata da take can a yashe Aunty Zakiyah ta dauka tana kallon Ya Ado, duba wayar tayi tana faWin.. ""Lafiya wayarki a can!"" Da sauri na amshi wayar na kashe, na koma na kwanta. Kusan haka suka gama maganarsu suka fita, kwana biyu wayata a kashe idan Mama ko Aunty Hindatu zata yi magana da ni sai dai a wayar Ya Ado ko Aunty Zakiyah, nan Mama ta sha jinin jikinta, ta cewa Ya Ado ya amshi wayata ya bincika, itama zata taya ni da addu'a, Ya Ado ya amshi wayata ya kuma saka ni a gaba da fada har sai da Aunty Zakiyah ta ce ya kyale ni ya daina min faWa, kafin na samu ya hakura washi gari sai gashi yazo yana rarrashina, sannan ban san me yayi ba. Sai ya ce min. ""Daya layin na turawa su Mama wannan Mtn din ba a iya kiranki ba sai dai idan kece zaki kira, sannan wannan ko Rufa'i ban yarda ki bashi ba, idan Hafiz ya kira ki, ki gaya min ki bude baki ki gaya min."" A Bauchi kuwa Mama sai da ta saka aka rufe shagunan da Ya Hafiz yake, duk yadda aka kai da bata hakuri fir taki, shi kuwa kamar zai yi hauka. Da ta gaya mishi zata iya kome akan Lubabatu bai yarda ba, sai da ta saka aka dauke shi a kai aka kai shi office din Yan sanda aka rubuta yarjejeniyar ya fita a harkata tunda abin ya koma yar haka, bata kyale shi ba sai da ta ce ua kyale su Sani su kula da shagon Abba, domin ba ™aramin mamaki suka sha ba jin yadda kusan tun kafin a kwantar da Abba ba a kuma zuwa sari ba, kayan da yake store ya kare tass, ina kudin? Sai shiru karshe da aka kira shi ya zo, ai kuwa ya gudu aka nemi shi sama da kasa babu shi, babu labarinsa. Abin bai yiwa kowa dad'i ba, sannan kudaden da Abban yake da su ba zasu kai ayi sabon sari ba, haka yasa dole aka fara hada abinda ya sawwaka, aka gayawa Mama tace musu. ""Ina ruwana yana da gidaje da filaye ku sayar ai bance ya dauko na shi ya cuce shi ba, balle" "ace a tare zamu raba zunubi ba."" Fir Mama taki ta kuma gayawa Yadiko." *** Turaki. "Duk yadda yaso kaucewa dawowa haka yayi ta ji zuciyarsa na fisgarshi, duk da yana ™aryata kanshi da" "cewa zai dawo ne ba wai don ya ganta ba, asalima don kada a samu matsala zai saka a tura ta tsohon kamfani. Amma kuma da wata bangare na zuciyarshi ya tuna mishi cewa akwai Khamis akan mata ko taure ya sallama mishi, sai ya ji ranshi ya Saci, yanzu idan yayi wani abu za iya d'agota, duk da file dinta ya shigo ta email address kamfanin ne, ba ta hannun Uncle Auta ba, duk yadda yaso ya kaucewa haka amma zuciyarsa ™ara tunzura shi take, sai dai duk yadda ta tunzura shi idan ya tuna tana da aure sai jikinshi ya kara sanyi, wani hanzari ba gudu ba, idan kuma mijinta ya mara hanyar samun aikin fa? ""Tsuk!"" Ya sake wata guntuwar tsaki yana kallon waje, ta parlourn.. ""Bilyl"" kallon Granny yayi tasha rigan sanyi. Murmushi yana kad'a kafarshi. ""Bilyl ko baka da lafiya ne?"" Kallonta yayi irin kallon mamakin nan, zama tayi tana kara bude mishi kalmar rashin lafiya da take nufi. ""Ina nufin ko baka da karfin maza ne!"" Bai cika dariya haka ba, sai dai idan ya ga abu ya wuce lissfinsa, a hankali ya sake wata dariya yana kallon tv a hankali, ya ce mata. ""Granny me ya kawo wannan zancen?"" Yana shafa kai, kallon kanshi yayi a nutse yana kuma lissafin bayaninta wato haka ake kallonshi a mara lafiya. Murmushi yayi ya zuba mata idanun kafin ya juya ga wajen da yake kallo. ""Naga bayan labubu baka sake kula wata mace ba!"" Shafa sajensa yayi yana jinjina kai. ""Granny yau fa alhamis ina azumin Alhamis da Litinin, yana kare mutum" "daga sharrin zina da wasu abubuwan, ni lafiya ta lau, kawai matan ne basu gabana.""" """Tow ko kai gay ne?"" Zare idanu yayi ya kuma tuntsirewa da dariya yana kallonta, tsakaninta da Allah" "take magana ta cigaba da cewa. ""Saboda haka nayi maka booking ganin likita da zai taimaka maka yadda zaka fara jin sha'awar mace."" Mikewa yayi yana faWin. ""A'a ni lafiyata lau, ba sai kin hada ni da aiki ba!"" Ai kuwa tsohuwar nan tayi ta masifa tana binsa ya zo su tafi asibiti amma yaki karshe shiryawa yayi ya" "bar gidan ma, duk da sanyin da ake yi kuwa." Yana isa coffee shop dinsa sai ga kiran Ubaid. Dauka yayi suka fara magana akan kayan da Uba bank suka "kawo musu talla, ya ce mishi ""Ubaid ku biya da kudin hannunku man."" Ya fada yana kallon wasu masoya da suka shigo shagon.. ""Sau nawa zan gaya maka babu kudin nan da kake magana wallahi wannan watan sai da aka tab'a kudinka sannan aka biya albashi, ka fahimci abinda nake nufi, muna ta sayan kaya amma ba halin mu wayar domin ko mun zo sayarwa za a samu babu wasu abubuwan, ka ga a wulakance ake sayarwa sannan kafin su bada kudin ya xama aiki!"" Cike da mamaki yake jin wannan labarin. ""Ubaid me yasa baka tab'a gaya min ba?"" Ya fada ranshi a b'ace, yana kin zafi sosai. ""Duk lokacin da na maka magana zaka ga kamar ina son lallai ka dawo ne, wanda ni bs nufina kenan!"" Shiru yayi yana jin kamar ya dirka ta wayar, ba a tab'a rena mishi hankali irin na yau. Duk yadda Ubaid yake mishi bayani ya fahimta yaki cewa uffan har ya gama maganar shi ta kyale shi karshe ya lashe wayar. Haka ya fara shirin tattara duk wani abu na shi mai muhimmanci, bayan ya gama ya zubawa wayar idanu yana jin wani irin ciwo, tow me yasa suddenly ya sauya ra'ayinsa? Ba zai maganar Lubnah ba ne ta rinjayi sauran? Idan har haka ne tow ya ji kunya, babba ma kuwa. Karshe sai ya watsar da Maganar komawa Nigeria da gaggawa, ya" "tattara ya watsar kamar ma bai da niyya ne ko ya fasa ma bakiWaya, haka kwanaki suka wuce, babu" labarin shirin tafiya Alhaji ELYakub Kumo da yaji shiru ai kuwa ya kira shi nan ma ya fara inda-inda karshe "shima dattijon ya sha zuciya ya ce ya kyale shi yayi yadda yake so, tantance ma'aikata babu bashi nan da wasu kwanaki. Abin ya bashi mamaki yadda kakan na shi yayi fushi, kuma ya hana kowa kula shi, ai saboda ya ga an damu da shine, don haka sai abin ya dame shi, duk yadda yaso ya dauke kai sai ya kasa duk waWanda suke kiranshi yake kin dauka ko yake saka musu busy yau babu ko daya da ya sake kiranshi, duk da baya tare da su amma yana jin dadi da farin cikin kiran da suke mishi haka yana nufin basu manta da shi ba, sannan abu na gaba shima Alhaji ELYakub yayi haka ne don ya nuna mishi ko dashi a" "rayuwarsu ko baya cikin rayuwarsu zasu rayu ba shi bane yake basu abinda suke bukata. Kuma ya gane karatun domin da kanshi yayi ta kiransu amma babu wnada ya dauka sai ma busy da suke saka mishi, tuni sai hankalinsa yayi wani irin tashi, shi kamar kwai yake bai saba da horo ba, bai ma san horo a rayuwarsa ba, haka yasa shi cikin kasa da sati daya ya tashi hankalinsa domin a lissafinsa Alhajin ne bai" "da lafiya suka boye mishi, nan kuwa bulala suke mishi ta hanyar da shima yake yiwa wasu." Ranar juma'a jirgin maxi airline ya sauka a International airport na lagos wato Murtala Muhammad "International airport, da misalin karfe tara na dare, kai tsaye ya dauki drop domin shi bai gaya musu dai zo ba, wannan muguwar dabi'ar nashi ya saba da ita baya fadar yana hanya kuma baya fadar zai bar garin idan har kasan ranar da yazo kawai ya rike domin ba zaka tab'a sanin ranar tafiyarsa, wurin sha daya na dare suka isa gidansa da yake Lekki, ya biya mai motar da ya dauka drop, sannan ya isa bakin gate din yayi magana da mai kula da gidan, a hankali ya fito ya haska masa torch da sauri ya kashe yana faWin.. ""Ka gafarce ni Sir;"" ya bashi hanya ya shiga, haka ya shiga ya nufi cikin gidan shi kuma ya daukar mishi kayansa. Har cikin gidan ya shiga gidan nan kamar yadda kullum ake kula da shi. ""Kada ka gaya musu nazo!"" ""Ok sir;"" ya wuce upstairs ya wuce dakinsa, sai da ya karkade sannan ya gyara da kyau kafin ya samu wuri ya kwanta ya huta, sannan ya shiga ban daki yayi wanka da alola. Kafin ya fito ya gabatar da sallah Magariba da Isha, hada socket yayi na kettle ya dafa ruwan zafi ya shan coffee, ba tare da ya kara niman wani abu ba, ya bi lafiyar gado. Sai lokacin yaji wani irin nutsuwa da kewa irin na abokin tarayya,idan da yana da mata da ya dawo nan kawai zata tarbe shi Yaranshi suna ta murna, Papa ya dawo amma yau ba ko sauro da yasan da zuwansa abin ya dame shi ainun a yanzu ko da Lubnah ko babu ita ya shirya zama da mace koda baya sonta, amma ban da wadancan yaran family dinsu shi bai da" ra'ayin auren family...... (Ku min hakuri bana jin dadi ne) "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 43" "Akidarsa kenan, ra'ayinsa kenan bai da wani ra'ayi na auren zumunci.Sun kasa boye yunwarsu da" "zallamarsu, shi kuma Wan ra'ayine duk yadda kake tsammanin zaka burge shi baya taSa ganin haka a wata tsiya." "Washi gari ya fita Masallaci, yayi Sallah kuma ya dawo da wuri, can dakin Gym dinsa ya shiga yayi ta" "motsa jiki har karfe takwas saura, sannan ya wuce kitchen dinsa, shi fa Allah ya gani yana adawa da duk" "wani abinda zai saka ya ji yunwa, kallon maka makan deep freezer da suke kitchen din yayi, ya bude ya ga ba kome asalima a kashe suke, shiru yayi kafin ya fito parlour ya zauna tare da cire wayarshi a charge" "domin yana dawowa sallah asuba ya saka anan,nan ya cire a Flight mode da ya saka, ai kuwa sai ga kiran" "Granny. ""Bilyl ka iso lafiya?"" ""Eh granny wani abu ne?"" ""Dama na amso maka magani ne likita ya ce yana da kyau da karfi kamar doki!"" "" Granny ba na gaya miki lafiya ta lau ba?"" Cikin rarrashi da tattali ta ce mishi. ""Ai haka ne dayawa haka suke cewa lafiyarsu lau, amma idan aka bincika basu da lafiya."" Takaici kamar ya fasa ihu a hankali ya ce mata. ""Kada ki sake a kawo min maganin nan domin zubar da shi zan yi na gaya miki."" Shiru tayi kafin ta ce mishi.. ""Shi kenan, da fatan ka karya ko?"" ""Granny ni fa ba yaro bane!"" ""Haka ne kan amma ai tunda baka yi aure ba har yau yaro nake kallonka."" Sanin zata saka shi magana da zai haifar mishi da ciwon kai, ya ce mata. ""Granny bari na sauke noodle yana kan wuta zai fara kamawa!"" Ya kashe wayar yana kallon screen din, murmushi yayi yana faWin. ""Granny kece matsalata!"" Sannan ya wuce kan sofa ya zauna, yana mai janyo laptop ya fara aiki a hankali. Resume kan file dinta yayi yana kallo a hankali ya isa kan maritial, ya ga babu wani information haka ya wuce ya ga first class ta fito, dauke kai yayi yana zukar iskar bakinsa sannan ya cigaba da duba wasu bayanin, abin mamaki shine taba nimam 29 yrs ta hada degree da master a wannan yan shekarunta, tribe ya duba ya ga an saka hausa/fulani, hararan file din yayi a ranshi yana faWin. *Hausa Hausa Fulani Fulani, no wani hausa fulani idan na renin hankali ba* a can ya duba ko tana da Yara, aka saka babu, tabe baki yayi yana ainawa a ransa da cewa.*Waye ya sani ko ta tara dozen na yara!* Ya fada fuskarshi tana wani irin ja, irin na kishin nan, bakin ciki ne ya saka shi kashe laptop din ma bakiWaya, waye ya sani ko Yaranta har da budurwa, tsaki yayi a fili. ""Mtseew!"" Kamar wani tsaka, can kuma yayi kwafa irin wanda takaici ya kusan kurmushe shi. Dakyar ya kai zuciya nesa ya cigaba da aikinsa, kusan ita ce mutum na sittin da yayi select" "dinta, sauran kuma ya ture su domin tun daga can yake daukar waWanda suka dace." "Yana gamawa ya turawa Uncle Auta cewa ya gama s tura mishi wanda suka diba, ba dadewa kuwa ya" "turo mishi mutane talatin a bangarenshi, haka yayiwa Ubaid magana ko minti goma ba ayi ba ya turo mishi mutane sha tara, da ta dauka bakiWaya mutane dari da yan kai, daga nan ya tura musu yadda zasu raba mutane ranar interviews din. Sannan da kuma yadda zasu duba su. Sannan ya ce musu a tura musu sakon yau yadda zasu shirya akan lokaci. Haka ya tura musu yadda ya tsara, kowane su zai dauki ya 27 har da Jasminah. A ranar suka gama tsara kome. Yadda yake basu hit yasa Uncle Auta ya kira shi yana cewa. ""Kai don ubanka yaushe ka shigo?"" ""Ni kuma?"" Ya rena mishi hankali, sanin cewa bai gaya musu zai shigo ba, sai kuma ya saka a ransa cewa. ""Kawai ina zargin kamar ka shigo ne."" Murmushi yayi ya ce mishi. ""Na zata ka shigo ne!"" Murmushi yayi ya ce mishi. ""Ka cika zargi!"" Daga haka ya shashatar da" "zancen, suka cigaba da abinda ya tara su. Domin daga karshe conference call suka yi." "Kusan wunin ranar aikin da suka yi kenan, tunda aka kawo mishi abinci mai gadinsa ya amsa ya kawo" "mishi, ya ci ya bar sauran. Can ya kara odar na dare. Kusan sallah yake d'aga shi a wurin bayan ya gama ya wuce ya tafi unguwa. Bai dauki mota ba, sai dai taxi d ya dauka haya, ya tafi kamfanin lokacin an tashi ya shiga dakyar suka bari ya shiga shima sai da ya bada cin hanci, bai nuna musu waye shi ba ya shiga yana kallon yadda ma'aikatan yake, daga nan ya wuce tsohon side, daga can ya hango office din MD Khamis ya bude asalima kamar akwai wani a cikinsa, haka yasa shi isa har kofar office din abinda ake zargi ya gani da idanunsa, daya daga cikin ma'aikatan ce take kuka, da rokon ya barta da mutuncinta sannan ya duba tana da ciki dakyar suka samu cikin kada wani abu ya same cikin rayuwarsu zata shiga" "garari, amma Khamis ya shafawa idanunsa toka ya daka mata tsawa, tura office din yayi yana faWin." """Taso ki tafi!"" Ta cire hular kanshi na face cap din da ya saka ya ri™e. Kunya ne ya kama shi, ""thank you" "sir!"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Ki dauki maternity leave mana idan cikin yayi kwari sai ki dawo, yana da kyau hakan!"" Cikin wani irin girmama ta ce mishi. ""Zan dauka sir!"" Bata san waye shi ba, amma a yadda ya bata umarni, kuma Oga Khamis bai magana ba, haka ya tabbatar mata da shi wani ne, juyawa yayi ya rakata har bakin gate din, sannan ya nufi new side dinsu, ya gama kallon wurin da kyau, kafin ya wuce ya" "fita. Koda ya isa gidan da abinci ya isa, ya haura parlourn sama ya baje." "Next day ya kar shiryawa ya tafi ma'aikatan, ya samu suka bar shi ya shiga yasan Khamis ba zai tab'a" "bada labarin ya dawo ba ko don a tambaye shi yaushe? A ina ya ganshi? Haka ya gama zaga kamfanin har ya hadu da masu sata a kamfanin, haka ya dawo gidan ya rubuta, kome zuwa uku yayiwa kamfanin. Khamis kuwa tattarawa yayi ya gudu Abuja, don yasan idan har suka sake ido hudu da shaidani Turaki" tow sai dai ya bar kamfanin. Shi yasa ya gudu kafin su sake haduwa. *** "Yau kwanaki hudu kenan da aka ce mu je interviews, Ya Ado ya kira Mama ya gaya mata har da su Aunty" "Hindatu, aka yi ta murna a Bauchi Mama kan har da sadaka tayi, domin gani take kamar na amshi kaddarata ne, amma har yau na kasa nutsuwa zuciyata tana wani irin tsalle a duk lokacin da na tuna da Ya Hafiz yana nan sai na ji bakiWaya kome ya rikice min, Ya Ado ya haWa ni da Dr Dijah Bala, ta min yan tambayoyi na bata amsa, ta ce mishi yayi hakuri abin yana barin mutum ne a hankali, amma da zaran wani abu da ya shafi past dina ya dawo tow zai cigaba da hunt Wina, Haka Aunty Nuratu Kafaya ta gaya masa, kusan sati aka saka a zuwa interview din, haka yasa Ya Ado ne ya kai ni kasuwa muka sayi kayan da zanyi amfani da shi, kuma yana da yakinin Allah zai bani sa'a, ranar ashirin da watan June aka saka" zamu. "Yau sha bakwai ina kwance da yamma a parlour kasance Asabar ne, Rufa'i ya shigo da sallama, tashi" "nayi na zauna ina kallonshi yayi dariya yana faWin.. ""Manya Lubnah ki amince na kawo dubu goma a daura mana aure, ni bani da matsala xan amince ki ta juya ni kamar masa."" Murmushi nayi na ce mishi. ""Kai dan Yaro da kai ne zan amince na aure amma ka mugun rena min hankali."" ""Samun kyakkyawar saurayi irina sai an cika form, Gara na miki talla kafin mata su kwace miki ni."" Haushi ya kama ni na kalle shi na yi kwafa, Aunty Zakiyah ta fito tana mana dariya sai zoyalat suke karshe na biye musu aka wuce wurin, haka ya zauna har Ya ado ya dawo ya amshi abinda ya zo amsa ya koma, ranar Lahadi kuwa jin wani irin tsoro ya kama ni nake, ban taba zuwa irin wuri haka ba, nayi su goge karamin fashion hijab din da zan daura akan kayan, sai takalmana da na kara goge shi, sannan na koma na zauna ina ta azkar, domin zuciyata ta gama razana, lokacin da na ga kamfanin da Ya ado ya nuna min, da kuma aikinsu, sannan ya gaya min wani abu.."" kada ki rena kanki, idan kika yi haka ma'aikata zasu yi bullied dinki," "please ki tsaya akanki kada ki bada fuskar da za a wulakanta mana ke, ki yarda da kanki.""" "Daga haka na ji a raina zan yi kome don na wanke Ya ado, ruwan sama aka fara kamar da bakin" "™warya, bayan na ci abinci na kwanta sannan na kara nazarin takardun da zan tafi da su, kafin na hada kome a wani jaka. Washi gari tun asuba Ya Ado ya buga min kofar dakin ya bani wayarshi. Addu'a mama take min kamar ta aro kafa ta biyo wayar, tayi min Addu'ar nasara da sa'a tare da dace, haka na amsa da Amin, bayan mun gama wayar na shiga wanka na hada da Alwala, sannan na yi sallah na shirya tsaf, karfe bakwai saura muka bar gidan tare da Ya Ado da Aunty Zakiyah, ita ta sauka a can asibiti ni kuma Ya" Ado ya kawo ni inda ma'aikatan take. Ikorodu Local Government. "Anan kamfanin yake, kafin mu wuce ya ce min.. ""idan kika fito daga kamfanin idan kin samu abin hawa" "zasu kawo ki can inda mutane suka tsaya sunan wurin Garaj kenan, daga nan zaki samu mota zuwa gida kin ji ko?"" Gyada mishi kai nayi ya dunkule hannunshi yace Goodluck! Murmushi nayi ya kawo ni har kofar kamfanin ya ajiye ni, ya fito zuwa bayan motar ya mika min lema da rigar ruwa nace mishi. "" Ya Ado wannan ma ya isa."" Ciro dubu goma yayi ya ce min. "" Ki rike wannan! "" Murmushi nayi na ce mishi. "" Allah ya kara budi. "" Har ya juya zai tafi ya dawo ya Wan janyo ni jikinshi.."" ki kula kada ki bari a rena min ke kin ji ko? "" Gyada kai nayi, yayi murmushi sannan ya wuce ya shiga motarshi sai da ya tafi na shiga kamfanin, ana ta taruwa, ina shiga na ga matasa ire-irena, ina zuwa wurin na musu sallama babu wanda ya amsa min, kame kaina nayi na koma gefe, domin daga dukkan alamu duk masu zuwa interview ne, har wurin karfe takwas motocin alfarma suka fara shigowa kamfani, gabana ne ya fadi sosai, haka wasu fararen mutane suka fito, ni dai ban tab'a ganin irinsu ba, haka suke fitowa tare da tafiya cikin kamfanin kamar zasu tashi sama, kowa ka gani sanye yake da coat irin na aikin nan black kusan shigar mu ce da su, wurin karfe goma saura wata mota ta shigo kamfanin wanda yayi daidai da fara kiran sunayen mutane, Yara ne guda biyu suka fito, daya tana cin abu a cikin kwali, tana ta zaga wurin. Kiran wasu mutanen aka yi a lokacin na lura bamu wuce ashirin da wani abu ba, haka muka cigaba da zama, har karfe sha biyu ba rana sai ga wata mota ta shigo, a lokacin Yaran nan sun zo kusa da ni suna wasa, masu kula da Yaran" "suna ta tare tare da su, ban san ya aka yi ba sai ganin daya daga cikin yara biyun ta tsaya........" "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 44" "Cak idanunta kawai yake motsawa, a daidai lokacin da aka kira sunana kenan, yadda yarinyar ta tsaya" "zaka zata ko wasa take tana kallon mutane amma ni nasan ba haka ba ne, saboda ya tab'a faruwa da Yasir ya saka abu a bakinsa sai da na rungume shi ta baya na matse mishi cikinsa abin ya fado da amai. Da gudu nayi watsi da takarduna, na nufi yarinyar da kowa ya kama gabanshi tana niman faduwa, na rungume ta ta baya na shiga matse cikinta tare da buga bayan da kaina sau biyu nayi mata na ukun sai ga amai da kwallon abin ya fado, zubewa muka yi dukkan mu, domin ta suma ne, da sauri na kara gyara mata kwanciya a jikina masu kula da su, suka shiga ihu, ""ban ruwa!"" Ka fada musu, mika min suka yi na" "kunsa a bakina na watsa mata sau uku sai gashi ta fara ajiyar zuciya. Nima ajiyar zuciyar nake saukewa," "na tashi duk kayana yayi kura, ashe labarin abinda ya faru har an isar ciki, tallafo yarinyar nayi na zauna" "da ita a kujeran da na tashi. ""Sannu daga yau kada ki kara cin abu a tsaye, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce yana daga kyauwun dan uwanku ya ci abu cikin nutsuwa, haka zai kiyayye daga sharrin shaidan da sauran abokan halitta, idan zaki ci abu ki daina zuwa gaban jama'a kin ji, ki samu can gefe guda ki ci, mutane ba kowa bane normal wani yana da evil eyes, evil tongue, da bad mouth. Kada ki sake tsaya a gaban mutane kin ji."" Gyada min kai tayi na mike tare da kallon masu kula da su. ""Iyayen Yaran nan sun yarda da ku, suka baku amanarsu, sannan sun amince da nagartakun suka bar Yaransu a wurinku, ku kula da aikinku kowacce addini da kabila ta yarda da gaskiya da rikon amana, please ku taya su kula da Yaransu. Allah ya bamu sa'a."" Lokacin da na juya na ga bakiWaya mutanen da suka fito sun koma ciki abinsu, ajiyar zuciya na sauke na tattara takarduna, sannan na nufi ciki don sai yanzu na tuna da an kira ni fa, ina shiga cikin hall din naga wasu daga cikin staff din sai kallona suke irin kallon wulakancin nan, kofofi uku ne, kuma dukkansu an rubuta interview, wurin matan na isa na ce musu. "" Don Allah a wacce kofa aka kira sunana? "" Ina ga wannan ba wani abu ba ne da na fada da zafi, amma daya daga cikin matar ta ce min. "" Kin ajiye mu ne mu ji ko an kira sunanki?"" Kalaman Ya ado ya dawo min na kada na bari a wulakanta ni, kuma kada na wulakanta kowa, murmushi nayi nace mata. "" Sorry! "" Daga nan na wuce na zauna har wurin karfe biyu bakiWaya suka fito mazan suka tafi sallah wasu daga cikin wadanda suka zo interviews din suma sun fito, haka nima na fita nayi sallah, ashe sun rigani dawowa, ina zuwa kuma suka fito wai ashe an yi ta kiran sunana, bana nan. Sai nayi kamar na kunyata Ya Ado ne, haka na tattara kayana wani mutum ya ce min. ""Mrs Jama'are!"" Wani irin kwallar farin ciki ne ya cika min idanu, na juya ya ce min.."" ana kiranki! "" Gyada kai nayi na bi bayansa, wani hadadden office ne, muka bi stair aka kai ni, kusan tattaunawa ake suke suna faWin "" a cikin mutane dari da wani abu bakiWaya mutane sha bakwai ne suka tsallake!"" ""Sha takwas dai Uncle Auta, sha takwai kamar ya?"" Shigowar da nayi yasa suka zuba min idanu, murmushi Macen cikinsu tayi duk da bata kai su shekaru ba, amma da alamar suna ji da ita ga Yaranta s gefe, d'aga min hannu daya wacce na taimaka yayi na mata murmushi. ""Mom ita ce ta ceto rayuwata!"" Mikewa uwar tayi ta mika min hannu. ""Na gode da abinda kika yi, yau kamfani tana alfahari da ke da kuma irin wannan ceto ran da kika yi, min gode."" Gyada kai nayi ban iya amsawa ba. ""Me yasa kika yi missing interview din?"" Wani can na gefenta ya tambaye ni, cikin girmamawa na ce mishi. ""Na farko na tsaya ceton Rayuwarta ne, saboda yar adam ce kuma hakki ne a kaina na tsaya na taimaka mata, na biyu idan da na tafi na barta wani abu ya same ta har abada ba" "zan yafewa kaina ba, koda ace ban samu aikin nan ba, ba laifi amma nayi sa'ar ceton Rayuwarta. """ """ Bayan nan an kara kiranki bakya nan ina kika je? "" Ya kara cilla mun tambayar. "" Ibada na tafi, koda" "na dawo na samu an tashi, duk abinda ake nima a duniyar nan, anan zamu barshi, can ne dolenmu don na rasa wannan damar ba wani abu bane, babbar damar da zan rasa shine rasa sallah nan.""" """ Kina magana da kawazuci, me yasa kika ajiye son kika dauki kawazuci?"" Yar dariya nayi, yadda" "suka kalle ni sai na rufe bakina, kaina a kasa kafin na ce mishi. "" Duk wata mace a duniyar nan idan har ta isa mace uwa ce, ko ta haifa ko kada ta haife ita din uwa ce, idan har da rayuwa ta bamu abinda muke so," "zan ji ciwon idan aka ce Y'ata ce a cikin wannan yanayin, akwai abinda dukiya baya iya siyansa a cikinsu" "kuwa har da Yara, kawazuci ba iya mutane ke raye akanshi ba hatta dabbobi suna da ita. """ "Jinjina kai yayi ya kara da cewa. "" Yanzu idan kamfanin nan tana cikin wani irin yanayi kuma lokancin" "sallah yayi zaki iya tsallakewa ki yi sallah!"" Kallon kasa nayi nace mishi. ""Ba mamaki wanda ya tsaya har kamfanin ya iso wannan matakin bata raye, yau ya tara amma baya nan balle ya ga yadda yake tafiya, an tambayi wani daha cikin magabata me tafi yin addu'a a kai game da Lokaci, ya ce Allah ya bashi aron numfashi ya kara ganin wata lokacin da zai ibada, kamfani bata kai ibadana muhimmanci ba, zan bawa kamfani lokacina amma banda ta ibada ta."" Daga haka suka yi shiru basu kara magana ba, Nima kuma ban ce uffan ba, ina tsaye a wurin karar shigar sakon da aka musu na d'ago kai ina kallonsu, daya babban cikinsu ya ce min. ""Mrs Jama'are, idan aka baki damar aiki da kamfanin nan me kike ganin zaki yi har ya kai ga nasara."" Jan iskar bakina nayi na ce mishi. "" Na karancin hadahadar kasuwanci a degree na farko, na kara yin master a tallace-tallace, idan har akwai abinda xan yi shine zan tsara yadda kamfanin nan zata fito idanun duniya. Zan mai da hankalina wurin daidaita kamfanin izuwa ga sauran takwarorinta na" "duniya, sannan zan bawa aikina muhimmanci sama da kome da kowa na kamfanin. """ """ Mrs Jama'are idan kamfanin ta dauko karyewa, nasan kin san aikin kamfanin me kike ganin zaki mata" "kada ta karye?"" Lashe bakina, na sauke ajiyar zuciya kafin na ce."" A matsayina na karamar ma'aikaciya kuma wacce take da ilmin tsara tallace tallace, shine zan fara duba yadda zan janyo hankalin masu zuba hannun jari, daga gida zuwa kasashen ketare, aanan kuma zan yi ™o™arin rufe duk wata kofa da zata janyo min karyewa a cikin kuwa shine zan zubar da ma'aikata, ba zan debi sabbin ma'aikata ba, tsofin zan kara basu horo sannan na kara inganta ilimin su yadda zasu fuskanci yanayin da ake ciki, za a rage wasu abubuwan da ake yiwa ma'aikata idan kamfani ta farfaWo sai a kara musu, wannan tsarin economic" "ne ta kowacce kamfani da kuma manyan ma'aikatun duniya.""" """ Kina nufin a watsar da tsarin diban ma'aikata kenan? Idan haka ne kuwa har dake a cikin haka ya" "miki?"" Gabana ne ya fadi shi kenan nayiwa kaina, sai nayi murmushi na ce mishi."" Haka ma ba laifi bane, kowacce kamfani tana kokarin ceto rayuwarta ne. Idan har aka duba masalahar kamfanin babu amfanin" "diban ma'aikata, idan kuma kamfanin tana da bu™atar haka ai ba laifi bane. """ """ Mrs Jama'are ko dai zaki gare muradinki ne? "" Inji matar, murmushi nayi mata nace mata. "" Ko daya ni" "ina da nawa ra'ayin ba wai aikin kamfani nake da buri ba, amma a tambayar da aka min dole na bada amsa."" Cidar d garin ya fara alamar za ayi ruwa yasa na kalli agogon hannuna. ""Shi kenan zaki iya tafiya!""" """Na gode!"" Na fita ai nasan ba wani batun daukar aiki, ya xan yi da Ya Ado?" "Ruwan da aka fara yasa da na sauko kasa ba tsaya ina kallon waje kamar yadda kowa ya tsaya, matan" nan sai gulma suke. "Bayan fitar ta ya juyo kujeran, yana ta rubuce-rubuce. ""Bro yarinyar tayi tana da kwarin gwiwa!"" Inji" "Jasminah, ""Kuma da alamu zata yi abinda ya dace, shi dai bai ce kome ba, "" can dai Uncle Auta ya ce mishi. "" Sunan yarinyar kamar yaso na taSa jin sa a wani wuri?"" "" Usman Umar Jama'are, Baristan nan!"" Inji Ubaid, "" wow dole ta samu confidence, irin wannan ake bukata asalin kwarin gwiwa na gani a cikin kalmanta!"" Shi dai shiru yayi can Uncle Auta ya ce mishi. "" Ni kuwa yarinyar ta min, tana da nutswa da hankali!"" "" Oo Uncle Auta fell in love daga kallo daya."" Buga table din yayi ya ce musu."" Bata min ba ta cika surutu, mai surutu baya abinda ya dace!"" Daga haka ya bar office din yana mai riko hannun Yaran.."" Uncle BT amma tana da kirki, me yasa ba zaka dauke ta ba. Ina sonta."" "" Princess idan aka kawo ta kamfani ba zata yi aikin da ya dace ba zata yi ta hira da mutane ne."" "" Uncle BT yana da kirki Please!"" Dan durkusawa yayi yana kallon yarinyar da take murza idanunta. "" Uncle tana da kirki she is a good person!"" Taya zai gaya mata bata da kirki, bayan ta ceto rayuwarta. "" Princess kada ki damu da irinsu."" Idanunta ne suka cika da kwalla, har suka zubo mata ta ce mishi.""please!"" "" Ok ok bar kukan haka kin ji! "" Gyada kai tayi tana murmushi, haka suka fito sai lokacin ya hango tana fita daga kamfanin a hankali tana tafiya ruwa na zuba kaWan kaWan, bodyguard dinsa ne suka fito da lema suka saka mishi bayan ya dauki Yarinyar, suka bude motar ya sakata, ya daura mata belt sannan ya shiga suka tashi motar, a hankali" suka bar kamfanin a bakin gate suka tsaya sakamakon wata motar da ta danno kai. "A hankali nake tafiya har na samu wani abin hawa na gaya mishi inda zai ajiye ni, ya ce na shiga, sai dai" "cikin ikon Allah motar taki tashi dole na sauka na cigaba da tafiya nayi tafiya sosai, kafin na nufi garej, kamar ance na d'ago kaina daga lemar na hango ya Hafiz ban san lokacin da na sake lemar na fara ja da baya ba, murmushi ya sake yana kallona, daidai sake wata irin ruwa mai karfin gaske shaaa, karafuna ne suka dauka rawa, na ji kamar cikina ya hautsine, wani irin abu na ji ya tsaya min a wuyana. Na fara ja da baya, yana bina ina ja da baya yana bina, ga titin ba motar da suke wucewa, hawaye ne ya fara zubo min. Karar horn na ji na kalli wurin, na hango motar kamfanin ce, wani irin kuka ne ya kwace min ganin yadda suka wuce. ""Ba fa mai taimakonki, kaf duniya babu sai ni, ni kaWai ne last hope dinki!"" Yadda yake tawowa ban san me ya tare ni ba, haka na zube yayi kaina zai damke ni, na kare kaina tare da fasa wata irin kara tare da kiran sunan Allah, na rufe idanuna hannuna biyu na saka ina mai kare kaina, wani irin" "kara naji wanda ban san yadda akayi na bude idanuna ba, sai ganin............." (Alhamdulillahi na gode sosai wannan wurin nasan sai an ji kamar a cije ni kuma duk wnada ya zagi hafiz shi da kanshi) "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 45" "Kamar yadda aka ce mata suna suka tara, haka ma Maza sun kashi gida daban daban, domin ni dai ban" "tab'a ganin irin wannan mutumin ba, hannun da ya Hafiz ya kai zai damko ni ita aka murder a baya sai da tayi wata irin ™ara, kafin ni da shi mu farfaWo, bawan Allah nan ya kara sake mishi naushi. Sai na kasa fahimtar tsoron waye zan ji a tsakaninsu Hafiz ne ko wannan mutumin da sauri na kara kifa kaina kasa ina wani irin kuka, ji nayi an lullube ni da abu, an d'aga ni. Muryan mace na ji tana faWin.. ""Sannu muje mota, ai ke ma'aikaciyarmu ce, Sir ba zai bari wani abu ya same ma'aikancinsa ba."" Haka ta saka ni a" "motar sannan ta koma ta dauko min lemana da tarkace na, a hankali na kalli inda Ya Hafiz yake kwance," "mutumin ya murde hannunsa. Sai zabga mishi naushi yake irin na b'acin ran nan, barin wurin muka yi, na" "kifa kaina a kan cinyata, idanuna rufe. ""Wacece unguwa kike?"" A hankali na gaya musu ma cigaba da kuka." --- "A can kuwa Garej Mr Turaki bai yi niyyar shiga al'amarin ba, tunawa da yadda aka yiwa Mrs Thomas yasa" "shi kiran security na kamfanin kafin ya fita da sauri duk da kiyayyarshi da sanyi kuwa, amma ta gane ta ne da lemarta. Sannan Ilham ta kara ce mishi, ga wacce ta taimake ta. Haka yasa shi tsayar da motar, umarni ya bawa Tajudeen akan ya kira sauran security din domin ya tuna abinda ya faru da wancan matar haka yasa shi sauka ya samu Hafiz. Ba zai ce ya yake ji ba, domin abu ne me sauki da mutum zai" "bada labarin yadda ya ji shi, wani babban al'amari ne da Allah kaWai yasan yadda abin ya™e." Yadda ya dage da dukkan zuciyarshi yake kai mishi duka zaka rantse da Allah irin yasan Mafarin "lamarin ne, amma ina shi zuciyarshi abinda ya bashi ita din mace ce me rauni kuma tana bukatar taimakon shi, fisge shi Ubaid yayi yana faWin. ""T meye haka? Me yayi maka? Haba da girmanka?"" Huci yake yana nunawa security Hafiz. ""Ku tabbatar kun hada shi da yan sanda."" Sannan ya juya ya bar wurin ranshi yana soya, ko ruwan da ake yi bai dame shi ba, tunda Ya shiga motar yake jin wani irin zafi. Har suka isa Mansion na Kumo bai magana ba, yana zaune shiru towel Jasminah ta lullube shi da shi tana faWin. ""Sanyi zai kama ka!"" Komawa gefensa Alhaji ELYakub yayi ya zauna yana press din hannunsa a hankali, alamar yana calming dinsa da ya huce wani irin zuciya ce me cike da kishi, dafe kanshi yayi ga hannunsa da ya ji ciwo yayi ja saboda naushin fuskar Hafiz kawai,"" Me ya faru da ita?"" Daddah ta tambaye su hankalinta a tashe, "" Fada yayi da wani!"" Uncle Auta ya fada yana kallonshi. "" Fada!!!"" Duk suka hada baki, domin abin da mamaki Daddah ta ce. ""Wai yaushe ma taso ne?"" ""Muma ganinsa muka yi dazun!"" Ubaid ya bata amsa, cike da mamaki Alhaji ELYakub yake kallonshi. "" Kuna nufin bai gaya muku zai shigo ba?"" Alhaji ELYakub ya tambaye su cike da mamaki, shigowa Alhaji Abbas kumo yayi yana faWin.."" Amma wannan wacce irin abin kunya ne Bilal ya aikata? Duk an dauki videon ana yaWawa a duniya. Baffa ya kamata ka yi wani abu, taya zai shirya interviews without our knewing, ba laifi sai ya je ya kama fada da yan iska idan wani abu ya same shi fa? Ya yake tunanin al'amarin zai kasance ga masu saka hannun jari."" Mikewa yayi bai karasa jin mai yake faWa ba yayi waje abinsa, "" Turaki! "" Ina tuni ya bar cikin gidan abinsa. Shi dansa ne zai saka shi gaba yana mishi ihu, ko dansa da yake abinda yaso baya mishi ihu, "" Bilal listn to me!"" Kwace rikon da Ubaid yayi mishi yayi yana kallonshi. "" Ni Yaro ne?"" Ya tambayi Ubaid, girgiza mishi kai yayi yana faWin."" Muje na sauke ka a gida."" Haka ya shiga motar yana shiga ya fara jera atishawa, yana yi yana karawa. Har suka iso gida, kusan sanyi ya gama kama shi." "Wanda ya haWa har da zazzaSi me karfi, tare da mura. Karshe sai da Uncle Auta ya haWa da kiran likitan family din ya mishi allura. Alhaji ELYakub ya zo shima hankalin Familynshi ya tashi sosai saboda sun san yana da irin wannan ciwon wannan wani abu daya da suke son kara amfani da shi, ba kome bane sai" "maganar fadar da aka yi. Hajiya Khaulatu da tazo ta ganshi, ba ta bar gidan ba sai da ta san yadda ta" "samu Alhaji ELYakub ta ce mishi. ""Tunda babu wanda zai zauna da shi Badr ta zauna da shi mana, zai so" "ya bukaci wani abu idan ya farka."" Uncle Auta yasan manufar yar uwarsa, amma idan yayi magana, zata ce yana hana su samun kusanci da Turaki, haka yasa shi zuba mata idanu, Mahaifinsu kuwa ya amince," haka ta fita tare da kiran Badr tazo gidan tayi jinyar Turaki. Shi kan tunda aka saka mishi ruwa da allurai ya cigaba da barci. *** "Har gida suka kawo ni, kuma har lokacin ban daina kuka ba, domin na razana ba wai Hafiz ba, ganin" "yadda mutumin nan yake dukar Hafiz sai ya bani tsoro matar ta ce min. ""Mun iso nan ne ko?"" A hankali na fito ta rako ni har kofar gidan sai da ta ga shigana sannan suka bar kofar gidan. Tunda na ga motar Ya Ado, kukan da nake ya karu, ban san yadda aka yi ba sai naji kamar an cire min duk wani tsoron Ya Hafiz dake ji, naji a raina idan na kara ganinsa sai dai wani ba shi ba. Haka na shiga parlourn na tsaya daga bakin kofar, zuba min idanu suka yi ganin yadda nake kuka. Tasowa Aunty Zakiyah tayi ta nufo ni. ""Hafiz ko?"" Cikin shashekar kuka na ce mata. ""Eh!"" Haka ta wuce da ni dakin kasa ta haWa min ruwa nayi" "wanka , ina fitowa ta bani magani na sha da tea me zafi na kwanta, karfe shida saura na tashi. Nayi sallah la'asar da ta kwace min, da sallah Magariba, ina zaune a wurin Ya Ado ya shigo. ""Ya interview din?"" Kallonshi nayi idanuna cike da kwalla. ""Kayi hakuri nayi missing dinsa, ban samu yi ba."" Zama yayi s stool yana kallona. ""Hafiz ya bi ki can ko?"" Hawaye ne suka zo min, na cigaba da wasa da yatsuna. ""Shi kenan, wannan karon ya hadu da dai-dai da shi, ya kira ni dazu nace bana gari. Yaji yadda ake ji, and Abu daya xan gaya Hafiz ba Mala'ikan mutuwa ba ne, ya isa haka tsoron da kike ji, kin san yadda nake jin ciwon halin da kike ciki kuwa? Ni ban ce ki yi fada ba amma at least ki tsayawa kanki taya kullum mutum daya zai na koro ki, taya kullum muna murnan kin samu lafiya ashe mu kike kashewa da ranmu, don Allah idan ba zaki iya daina tsoronshi ba, ki koma Bauchi daga nan zan kula da duk wani abinda kike bukata na gaji, na gaji Lubabatu ke daya ce aka tab'a jarabta da ba zaki yakince shi a ranki ba, haba don Allah kullum wani dan iska ya kore ki, ko ya gaya miki wani abu yanzu so kike na kira Mama na gaya mata hankalinta ya tashi d'an jininta da bai hau ba ya haura, akanki tana fada da kowa yanzu idan ta ji Hafiz yazo nan me kike son ta dauke ni, look kowa Ni mutum yana da zuciya a kirjinsa ne, amma ™alilan suke fada da zuciyarsu, idan kin ga zaki iya kwatar kinki shi kenan idan ba zaki iya ki koma Bauchi na gaji, haba don Allah akan ki aka fara ne? Balle ki ce babu wata victim sai ke, fisabiilillahi kina driving dina crazy, na rasa gane waye yake bani wahala a cikinku Hafiz ne ko ke? Nq gaji idan kika rasa wannan aikin in sha Allah karshe watan da zamu shiga zaki koma gida na gaya miki, ko je can ki ta fama ba zan iya miki ba, tunda baki iya kome na sai kuka kina nan kamar wawuya, Hafiz din banza ko ihu ba zaki yi ki tara mishi jama'a" "ba."" "" SAN ya isa haka don Allah ta ji ai!"" "" Ba zaki gane yadda nake ji bane.""" """Na amma itama tana fama mentally ill ne ai, idan har aka ce za'ayi fadar pushing dinta gaba zamu yi" "madadin mu dawo da ita baya, please ka yi hakuri yara kowa ya gudu daki jin kana fada Please. """ "Wannan maganar da tayi yasa shi fita a dakin, na hada kaina da gwiwa na cigaba da kuma har ta gaji ta bar dakin, na san gaskiya ta gaya ya fada amma kuma yadda yake ta fada da cewa ya gaji sai na ga kamar" "ban cancanci haka daga gare shi ba, kuma bakiWaya ya daura min laifi fisabiilillahi don ba shi bane ya sha" "wuta a hannun Ya Hafiz, sai na kasa yarda da zuciyata nice da laifi ba shi ba, haka na kwana da abin a raina da safe ko fitowa ban yi ba, suna sane suka share ni. Ai kuwa zuwa la'asar sai ga kiran Aunty Hindatu fada take inda take shiga ba nan take fita ba, sai da na rena kaina maganar da ta fada min yasa ni shiga hankalina. ""Idan kina son ki karasa mata aure sai ki dawo a cigaba da ganinki ana yab'a mata magana, ko wancan satin sai da aka gaya mata magana dakyar muka dawo gida jininta ya hau, kullum da ke take kwana ke ba zaki iya kwatar kanki ba sai mun taya ki? Fisabiilillahi muna da tamu rayuwar.""" "wannan Maganar ya dake ni, sun gaji da ni, haka na ji a raina sun gaji da ni." *** "Da karfe biyar na asuba ya farka, a hankali ya tashi ya cire robar karin ruwan ya sauke kafarshi, kasa" "tare da saka slipper Winsa, zuwa ban daki, yayi wanka da alwala sannan ya fito ya zauna a bakin gadon har yanzu alluran nan basu sake shi ba, daddafe ya yi sallah sannan ya fito ya sauka kasa kitchen ya nufa ya haWa coffee, sannan ya dawo parlourn ya zauna sai da ya sha, sannan ya koma ya kwanta a kujeran, wani barci ne ya dauke shi." Karfe sha daya na safe yaji maganar mutane a can kasa-kasa. Bude idanun yayi ya zuba musu idanu "Ubaid da Jasminah tare da Uncle Auta, sai Badr da suke ta mishi sannu. Tashi yayi Ubaid ya dauko kular abincin, kallon Badr ya ce musu. ""Who is she?"" Yadda yayi maganar kamar me koyar magana, yasa suka zuba mata idanu har lokacin idanunsa yana kanta.. ""Badr ce yar gidan Hajiya Khaulatu!"" ""Uban waye ya bata iznin shigo min gida?"" Shiru suka yi suna kallonshi. ""Before na bude idanuna ta bar gidan nan ko nayi kwallo da ita!"" Ai ba ita ba hatta Jasminah da sauri ta mike tare da jan hannunta suka fitar da ita kayanta ma aka shiga duka dauko. Sannan suka sallame ta abin tausayi gashi ana ruwan sama. Juyawa yayi ya kafe Uncle Auta da idanu. Yadda yake mishi wani irin kallon tuhuma. ""Ka ga bar min irin wannan kallon ba ni nace ta zauna ba, wallahi Uwarta ce kuma."" Dauke kai yayi yana kallon yadda Ubaid yake motsu-motsu. ""Ban kira sunanka ba!"" Ya cigaba da shan kunun da aka zuba mishi. ""Gayen nan dan uwan Barista Jama'are ne!"" Banza yayi bai kuma kula su ba. ""Please ka bada umarni a sake shi."" Kallonsu yayi ya kama tari yana dafe kirjinsa, kafin ya cigaba da cin abincin. ""Son kayi hakuri mana!"" Cigaba da karyawa yake kamar ba da shi ake ba, iskancin ya motsa kawai bai da niyyar ya amsa musu, kallon" "Jasminah yayi ya ce mata. ""Ki nimo min professional chef.""" "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 46" """In sha Allah zan nima maka mace ko namiji!"" Kallon wayarshi da yake ringing yayi ya ce mata. ""Male!""" "Ya fada dan zafaffe, a yadda yake din nan kamar ya rufe mutane da duka. Kusan haushinsu yake ji, definitely ba sune suke bashi haushi ba, kishin da yake cin ransa musamman da Ubaid yake gaya mishi ai Baristan nan ya zo akan case Win, kamar ya rufe su da duka, amma fuskarshi babu al'amar yana cikin fushi ko b'acin rai. ""Son!"" ""Yau baka da aiki ne a office!"" Ya tari numfashin Uncle Auta, domin kada ya kara ce mishi kome kiran wayar Uncle Auta Hajiya Khaulatu tayi tana ta fada akan me zasu koro mata Yarinyar ba tare da sun kira a zo a dauke ta ba. Lumshe idanunshi yayi ya kwanta da kyau yana jin yadda" take bala'i har da cewa a saka a handfree da yake shima dan yau ne irinta murmushi yayi yana rayawa a ransa idan har da zai ina bude baki ya mata rashin mutunci ga abinda zai gaya mata amma ya koyi wani "abu yana jin dadi idan ya saka mutane suna ihu a kanshi. Tow uban me zata min, idan na kara ganinta a inda nake sai na karya, wannan shi ne abinda zuciyarshi ya gaya masa, amma sai ya share ya kuma" cigaba da kallonshi domin baya son ya karawa kanshi wani zafin kai. "Ubaid da Uncle Auta suna ganin jaraba, mikewa Uncle Auta yayi zai fita ya ce mishi. ""Ka taimakawa" "kanka ka yi aure wannan rayuwar taka bata da amfani."" Shiru yayi bai kula Uncle Auta ba har ya fita da yake bai da mutunci sai ce mishi yayi.. ""Ka nima min auren Nihla!"" Ba Uncle Auta ba, hatta Uban Nihla" "sai da ya kusan faduwa daga kujerar da yake zaune. Saboda kaduwa, kuma kamar ba shi yayi maganar ba, wato idan Allah ya haWa ka da dan iska yana fa kyau ka Wan yadda zaka zauna da shi. ""Amma ka zare" "ne?"" Banza ya musu ya bawa iska ajiyarsu. Mikewa Ubaid yayi har ya isa bakin kofar fita zai kuma ya ce mishi. ""Baka ce kome akan Yarinyar nan ba a tura mata sakon Waukar aiki ne?"" Bawan Allah nan haka yayi shiru ya kyale su, har abin ya fusata Uncle Auta zai magana. Ubaid ya riko hannunsa. "" Shi kenan muje ba sai an tura ba."" Kasan ranshi yana son yayi magana amma kuma yana gudun abinda za a dauke shi, haka yasa shi ya share shi har suka fita. Kwanciya yayi a dogon kujeran parlourn, yana nazarin yadda kome yake tafiya, a hankali ya janyo wayarshi zai tura sako sai ya fasa. Abu daya yake damunsa shin ta isa gida lafiya? Wani hali take ciki? Ko itama ta samu matsala na mura ne? Tsaki yayi da ya tuna matar aure ce, bai san me yasa zuciyarsa take janshi ba, cikin hade rai ya wani cigaba da kwanciyar shi, Granny" "ya kira suka sha hira wanda ita ce ke jan shi da hiran, daga karshe suka yi sallama." "Kwanakin da ya biyo baya ya murmure, amma yaki zuwa family house dinsu. Domin ba zai iya daukar" "renin hankali ba, ranar Monday ya shirya zuwa office. Anan ya ga sabin ma'aikatan da suka Wauka. Duk inda ya wuce gaishe shi ake, har ya shiga elevator da zai kai shi hawa ukku na kamfanin, anan office Winsa yake, yana isa ya nufi office Winsa, zare necktie dinsa yayi ya wurga a can gefe, sannan ya cigaba da aikin da yake yi, sai dai zuciyarsa tana wani irin akilo a duk lokacin da ya tuna cewa basu tura mata sako ba, kusan aikin suku-suku suka yi shi, kafin can ya dauki shawarar da wata bangaren na zuciyarshi ta bashi ya shiga email din Ubaid ya tura mishi sakon a dauke ta aiki. Sanin cewa idan har Ubaid ta ga sakon zai biyo bayanshi, sai ya cigaba da kallon wayar time to time yana jiran kiran Ubaid amma har kusan awa daya babu reply, sai wurin karfe biyu na rana Ubaid ya kira shi, wani tsaki ya ja yana ganin kiran yasan abinda zai gaya mishi bai wuce an tura mata ba, sai me? Haka ya cigaba da aiki can, ya sauka ya nufi masallaci a can suka hadu da Ubaid ya zuba mishi idanu yadda ya wani hade giransa zaka rantse da Allah ai tab'a dariya ba, haka ya idar da ibadar ya nufi waje. Shima Ubaid a gurguje yayi addu'ar ya fito. ""Na ga sakonka, ai ni tuntuni na tura mata sakon."" Yadda ya zuba mishi idanu, kamar zai cinye shi Ubaid ya ce mishi ""ina nufin na gaya mata an dauke ta aiki ne, sai dai nayi mamaki da bata zo ba yau Monday."" Duk da yaji dadin da basu jira shi ba, amma gudun kada a rena shi ya ce mishi."" Na tambaye ka ne?"" Ya fada yana wani hade rai, shima Ubaid tabe baki yayi. Haka suka jera har office Winsa, muka zauna suna kusan Ubaid ke bashi labarin yadda ake ciki a kamfanin shi kuma yana nadewa, yayi shiru har Uncle Auta ya shigo ya samu wuri ya zauna, suka fara tattaunawa wanda shi baza musu kunne yake yana jin me suke" "fada sai can da aka gama maganar ya ce, musu. ""Ku shirya meeting gobe!"" Daga nan ya wuce kan table" "dinsa, kafin ya cigaba da aikinsa. Karshe da ya ga tunaninta zai dame shi sai ya tattarata ya watsar ya" "cigaba da abinda yake yi har kusan uku da rabi lokacin aka kawo musu abinci suka ci sosai, shi kan drinks ya tab'a yana faWin. ""Zance naci towon laushi wurin Dadda!"" Daga haka ya cigaba da aiki. Karfe hudu ake" "tashi, haka yasa yana fita ya hangi inda ya ganta ranar, abin mamaki yake bashi. Tow me nashi a cikin." *** Tabbas an turo min sakon an dauke ni a aikin kusan kwanaki uku da suka wuce amma kuma ban san me "yasa bana son zuwa wurin aikin domin idan na tuna da abinda ya faru sai naga kamar Ya Hafiz zai dawo, ban kuma jin labarin yadda aka kare ba. Har ranar da sati ya zagayo wai ni fushi nake naki kula kowa. Ina daki Ya Ado ya kira Ya Umar yana gaya mishi, an dauke ni aiki amma gashi nan zan fara mishi rashin mutunci, wannan abin ya min ciwo sai da na kasa hakuri yadda Ya Umar yayi ta dura asharia, haka yasa nima na kira Mama nayi ta kuka, itama fada ta min da nasiha tare ta rarrashina. Washi gari ranar talata kamar yadda ta umarce ni na shirya na tafi aikin. Ba musu na shirya tsaf na nufi wurin aikin, da wurwuri kusan kowa ya same ni ina jiransu, haka ya kawo ni Garej na tsaya jiran motar da zai shiga da ki ikorodu. Wurin minti goma sai ga motar tazo na shiga a hankali na zauna tare da jiran su tambayi kudinsu. Aikuwa" bamu jima da tafiya suka tambaye kudin na bawa kwandusta. "Mun isa wurin bakwai da arba'in muka isa ma sauka tare da Waukar jakata, na cigaba da tafiya. Kusan" "ni daya ce bahaushiya daga arewa, har cikin kamfanin na isa, ga ma'aikata ana ta hira. Duba cikin jakar da nazo da shi nayi ka ciro wayata da earpies na saka a kunne na, kuna Karatun Kur'ani na cigaba da ji ina mai lumshe idanuna, a bangaren Staff na zauna na ga dayawan matan wurin sai kwalliya suke ana ta shafe shafe. Abin har mamaki ya bani, can wurin karfe tara da rabi, sai ga wani ya shigo bakiWaya suka gaishe, shima dogo ne kamar yadda na fahimci yan family dogaye ne, ina ruwan dogo hankalinka a gwiwa. Magana aka yi min na bude idanuna. ""Barka daga wacce jaha!"" Wai mika min hannu yayi yana, kallon hannun nayi da kyau. Kafin na ce mishi. ""Ka yi hakuri ni muslma ce daga jahar Bauchi, kuma addinina da al'adata, ta haramta min gaskiyawa da namiji!"" Murmushi yayi cikin isgilanci ya ce min. ""Ok lokaci ne zai gaya mana ke muslman kwarai ce. "" Khamis me kake nima a nan? Baka gudun ya zo ya ganka ne?"" Juyawa yayi yana murmushi ya ce mata. "" Na ga abu ne na biyo laifi ne? Ki gaya mishi kayan" "da yake ta kwasa yana son ya ci ne ko zai bawa masu saka hannu jari ne?""" """Ke taso!"" Inji Uwar Yaran nan, haka na bita zuwa office dinta, ta ce min.. ""ina son na gaya miki wani" "abu!"" Ta fada tana ajiye jakarta, ina tsaye kaina a sunkuye. ""Ki kula da mutuncinki, na ga kamar daga babban zuri'a kika fito, koda ace Iyayenki basu nan ya kamata ki kare musu mutunci, kada ki yarda wani yayi amfani da haka ya ci zarafin ki."" Gyada mata kai nayi ni dai ban ce kome ba, haka tayi ta min nasiha har take gaya min Yaranta suna gaishe ni, murmushi nayi na amsa mata. Wurin karfe goma ta sallame ni, saukowa kasa nayi. Wata budurwa ta ce min . '""Mrs Jama'are ki shiga Oga yana kiranki!"" ""Ok ta ina office" "Winsa yake!"" Shiru tayi kamar ba zata amsa ba, kafin ta ce min. ""Ki bi stair ya ce yana awa na uku first" "floor, gyada mata kai nayi har xan tafi ta ce min. "" Shi kuma wannan waye zai dauka miki?"" Kamar nayi" "kuka na ce mata. ""Ok!"" Na karasa na dauki kayan takardu ne a kwali, haka na cigaba da hawa tun daga hawa na farko na fahimci Allah da girma yake, ai kuwa da na zo hawa na biyu sai da na zauna na huta kafin na cigaba da hawa, har zuwa office Winsa, tunda na isa na buga kofar wato wannan mutumin mugun dan renin hankali ne, nafi minti goma a tsaye sai da zai fita ya fito yana mai cewa, ""Ki same ni a kasa! "" "" Na'am da ni kake?"" Na kara tambayarshi, amma ina har ya wuce ta wani kofa ya rufe tare da dauke kai. Haka na shiga na ajiye kwallin na fito na gangara da gudu, sai da na fadi sau biyu. Kafin na isa kasan. Ina saukowa na samu staff din nace musu. "" Don Allah ina yake? "" Sai da suka bata min lokaci sosai, kafin suka ce ya fita, da gudu na fita na samu yana cikin motar, drive din yana waje, yana ganina ya shiga da sauri na zagaye gabar motar na shiga na zauna, Drive din ya dauko min wasu takardu. Yana faWin. ""Muje bankin First bank ne, sannan ya kamata ace kin san da tafiyar tun jiya."" ""Ayi hakuri!"" Na dauki takardun ina dubawa, na kara kallonshi na ce mishi.. ""ko zaka bani dan hit akan takardun?"" Na tambaye shi. ""Ba matsala wannan takardun saboda kasuwanci za a tafi a zauna, sannan akwai wani hadin gwiwa da zaku yi da First bank, wanda zaki tsara tallar."" A hankali nake bin takardan, amma ai ban tab'a tsara talla ba. Shiru nayi ina kallon takardun gabana, haka yayi ta min karin bayani, lokacin da muka isa, shugaban office din bakiWaya ya zo ya tarbe mu, bayan sun gaisa da shi, sai ya mika min hannu girgza kai nayi na saka hannuna a kirjina, haka suka mana jagora har office din da za ayi meeting din, haka suka yi ta tattaunawa dayawan tattaunawar akan tallar ne, sai da aia juyo kaina sai na ji na dan shiga rud'ani. Kallona yayi ta cikin madubin da ya saka a fuskarshi. Yadda yake kallona sai kaji na samu nutsuwa, don irin kallon nan ne na ki nutsu, a hankali na fara musu bayani tare da nuna musu yadda suke bu™atar ba zai yiwu ba, amma idan aka shirya tallar a kasa kafin a tacce a kuma gyara sai a kai ga gidan tv, na nuna musu idan har aka ce za a dauka a gidan tv zasu caji kudi dayawa. Amma idan aka yi" amfani da kayan aikin zamani ina ga kome zai zo da sauki............... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 47" "Duk wannan maganar da nayi, ban samu kallon arziki daga mutumin da nake ya bi a baya kamar bindi ba," "asalima ana tashi taron yayi gaba abinsa, kyauta da First bank suka bamu haka na lodo shi a hannuna har wurin motar kafin na isa Driven ya buWe min na shiga na ajiye na koma dauko jakata, amma abin mamaki sai nq hango motar a can bakin gate wato zasu tafi su bar ni, haka na karasa da sauri. ""Don Allah ka yi hakuri."" Na bawa Driban hakuri shima na lura kamar hakuri yake bawa Mutumin bayan, shegen ikon tsiya, ni tsoron kallonshi ma nake haka muka bar First bank, muka nufi wani banki mika min table tap din da mutumin ya bawa Driban, shi kuma ya mika min. ""Zaku hadu da wasu mutane akan sayar da wasu filayen wannan ba batun hadin gwiwa ba ne, ki duba zaki ga bayanai akan filin."" Gyada kai nayi, haka nayi ta duba bayanin ina me ciro biro da littafi na fara rubutawa, har muka isa. Haka muka fito ina rike da table tap din, har inda za a zauna. A karon farko da ya kalle ni, ya tsaya kamar yana da abin da zai fada sai kuma yayi gaba abinsa, haka ya sa nima na rufa mishi baya. Koda muka isa office din mun samu ana jiran, sai da suka tattauna kafin aka miko min takardun da zan duba,na gama dubawa sannan na koma gefe na cigaba da tsayuwa, kafana ne ya fara ciwo kasance takalmin kafana yana da dan tudu, haka wunin ranar a zirga-zirga da tattaunawa abinda na fahimta shi mutum ne da ya san darajar nima," "haka muka dawo office a matu™ar gajiya, driban sai sannu yake gaya min sannan ya biyo ni zuwa cikin" "kamfanin yana dauke da kayan kamar yadda nake dauke da su, har zan nufi stair ya ce min. ""No ki zo ga" "inda zai kai mu yanzu!"" Dan murmushi nayi na ce mishi, ""tow!"" Wannan shine adalcin da zance anyi min domin daukar wannan dogon hanyar kamar cewa aka yi kafana ya karye, har office din mutumin muka isa. Muna zuwa na ga Mamar Yaran nan gaishe ta nayi. Ta ce min. ""Kin yi sallah kuwa ga la'asar ta kusa?"" ""Yanzu zan tafi masallaci!"" ""Ok gashi nan nasan baki ci kome ba!"" ""A'a Nagode Aunty!"" ""Amsa kawarki tace na baki."" Hannu bibbiyu na saka na amsa, sannan na mata godiya na bar dakin. Wannan wurin na kara bi na sauka staff office na, nufa tare da ajiye abincin da jakata na dauki wayata na tafi masallaci, sai da nayi la'asar sannan na dawo ina zuwa yadda na bar kayan ba a haka na same shi ba, which mean an bude tare da tab'awa, a hankali na dauki abincin na fito waje na nufi wurin Driban, na mika mishi. ""Gashi ko zaka ci?"" Murmushi yayi sannan ya amsa yana faWin. ""Y sunanki ne? Na ga sai Mrs Jama'are ake fada ya asalin sunanki?"" Ya tambaye ni da hausa, ""Lubnah zaka iya kira da Lulu."" ""Wow sunan yayi dad'i."" Wayarshi ce tayi ™ara ya Wauka. ""Ka turo yarinyar nan!"" ""Ok sir!"" Juyawa yayi ya kalle ni ya ce min. ""Oga yana kiranki!"" ""Ok!"" Na juya da sauri, wasu mata ne suka shigo kamfanin wata mahaukaciyar mota da wannan ne kawo na farko da na ganta, haka suka fito ba tare da wani bata lokaci ba suka nufi main entrance na kamfanin, haka muka jera da su, tunda na ga staff na gaishe su na fahimci suna da alaka da Kamfanin, lokacin da suka shiga elevator, ni kuma sai na bi stair haka nayi ta gudu sauri sauri. Har na isa hawa na uku, office Winsa na nufa. Ina shiga naga matan suna zaune a kujeran office din shi kuma yana ta aikinsa, gaban shi naje na tsaya nace mishi. ""Sir gani!"" Banza ya bawa ajiyata. Haka na cigaba da tsayuwar har kusan minti goma kafin ya ce min. "" Get them out!"" ""Na'am!"" D'ago idanunsa ta cikin glass yayi ya kafe ni da shi. ""Pardon"" na juya da sauri na ce musu. ""Ku yi hakuri yana aiki ko zaku tafi sai ku nime appointment gaba!"" ""Wacece?"" Inji wata kyakkyawar budurwa wacce ban iya kallonta bama, ture ni tayi tana faWin. ""Dallas bani wuri."" Sai da na kusan faduwa. Shigowar Mamar yaran nan da maza biyu nan ne ya sa basu sauke kwandon bala'insu a kaina ba, ina rakube a gefe. ""Aunty Sameerah ya haka ne?"" Inji Babban. Auta babu ruwanka na kawo Batul ce ya bata aiki kamar yadda aka bawa kowa aik."" Shiru yayi yana kallon yadda take ta hayagaga, mikewa Boss yayi ya kalle ni, da sauri na nufi wurinsa naga yana kallon duk wani abu a wurin sai da na dauka na saka mishi a jakarshi, kome sai da na tattara, sannan na raka shi waje, tare da jiransu har suka fita na ja office din na rufe ina jin suna masifa tare da bin stair domin yaki tafiya yana bakin elevator din. Sai da na gama na riko jakarshi muka nufi elevator din tare, haka muka fito tare na kai mishi jakarshi motar, sannan na nufi main entrance na kamfanin na tafi kayi sign kafin na hada kayana, na fito a gajiye. Motar kamfanin da aka ware na mala'ikan shi na shiga aka kai mu har inda zamu shiga motar unguwar, minti goma sha biyar na samu motar unguwar, na shiga. Na gaji tun kafin na isa nake jin barci ina isa wanka na shiga nayi da ruwan zafi sannan nayi Alwala sallah Magariba da Isha, Abinci ma yau daki Ya ado ya kawo min yana murmushi. ""Auta yau na ganki da CEO na KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY!"" Murmushi nayi nace mishi"" Ya Ado kafana yana ciwo na gaji sosai."" "" Allah ya kawo miki miji nagari yadda ba zaki jima ba kin yi aure! Bari na kira miki su Adil su miki tausa. "" "" Na gode sosai!"" "" Ina babu matsala a wurin aikin?"" Girgiza mishi kai nayi, ya fita can sai ga" "Yaran don ma mun sallah isha, haka suka yi ta min tausa abincin da ban ci ba kenan barci yayi gaba da ni." "Duk yadda suka yaso ya kamata da laifi ko na wani abu sai ya lura bata da matsala, haka yasa shi kara" "saka idanun yadda suka yi kome ba tare da saninsa ba, haka zai ci taransu. Bayan sallah isha ya shirya" "cikin kananun kaya ya nufi can family house Winsu tare da Tajudeen, koda suka isa fita yayi Tajudeen ya" "dauki wani kwali ya bi bayanshi, har cikin gidan. Inda ake jiranshi. Da sallama ya shiga Daddah ta mike tana murna, rungume shi tayi tana faWin. ""Turaki ko baki da lafiya ne? Naga har yau baki Maganar aure? Haka zaki cigaba da zama?"" Sai a lokacin duk wunin da suka yi da yarinyar nan bai ga ta dauki waya ba, abin ya bashi mamaki tow ina Mijinta ko ta kashe wayarta ne? To ina ruwansa? Wannan personal life dinta ne. A hankali ya sakarwa Daddah murmushi. Haka suka hadu familyn bakiWaya aka fara cin abinci. ""Baffa ka tambaye shi me yasa yau ya fita da mace akan aiki me muhimmanci?"" Kallonshi Alhaji ELYakub yayi amma ganin kamar ko a jikinsa, ya kuma zubawa Alhaji Mudansir idanun yana son jin dalilin tambayar, amma gogan yana cin abincin a nutse kamar ba shi ake magana akan shi ba. ""Eh Baffa sabuwar dauka ce bata goge kamar Badr ba akan me zai dauke ta, sannan idan har aikin zai dauke su ba" "ga Mimi da Badr ko Batul ko Hanif ba? Irin wannan aikin me muhimmanci taya za a janyo bare a cikinsa.""" """Sata na samu yarinya take aka ce na danne ta, ai gara na dauki bare idan na danne ta xan bata kudi" "zata yi shiru da bakinta "" ya kai hannunsa tare da jan baki kamar zip. Ba yawwa ba dad'i, kallonshi suka yi tayi suna mamakin wannan bakar maganar. ""Tow Turaki me yasa baka dauke su aiki ba?"" Murmushi yayi bai kara magana ba sai da Uncle Auta ya amsa. ""Basu fa turo bukatar haka ba, idan aka ce kowa alfarma" "za ayi mishi ai kuwa ba za'ayi aikin da ya dace ba, idan har aiki suke so su je Hamma Babba ya dauke su!""" """Wannan wacce irin magana ce!"" Tauna kashi Turaki yayi da karfi sai da suka yi shiru. ""Duk me son aiki" "ya tura shaidar bukatar haka, babu wata alfarma kowa nima yake!"" Inji Alhaji ELYakub yana kallon Turaki. Murmushi yayi tare da gyada mishi kai, ai kuwa haka suka gama cin abincin tare da kawo korafi kamar zasu mutu amma Turaki tun maganar farko bai kara magana ba. Haka aka tashi a taron cin abincin. Masu" aiki suka kwashe kayan da aka zuba abincin. "Haka suka dan bude hira wanda korafi ya fi yawa, amma gayen nan ko a jikinsa kusan duk bayanin da" "suke yiwa kakanshi shima bayan jikanshi yake bi, abin har mamaki yake basu, sai wurin tara suka bar tashi zasu tafi ya ce musu. ""Da kuke maganar mace ina gurbin Mrs Thomas ta maye?"" Yadda yayi maganar bakiWaya sai suka yi shiru, haka ya fita daga cikin gidan, Uncle Auta da Ubaid, shi kuma da Taj. Haka suka nufi unguwarsu. Bayan tafiyarshi ne suka saka Ubansu a gaba da roko har sai da ya amince da" batun sauran jikokin su fara aiki a kamfanin. --- "Wato jiya na gaji yau ma a tsaye saye na karya, ina gamawa na shiga mota ina duba abubuwan da suka" "faru jiya, domin abinda Driban ya gaya min kenan ina tattara abubuwan da aka yi zai taimaka min. Karfe bakwai da arba'in yayi min a kamfanin, Ya Ado sai dariya yake min yana faWin. ""Da alamu boss Winki yana da zafin kai!"" ""Ya Ado ba zaka gane ba ne."" Dariya yayi kawai, har na isa office dinsa. A rufe dawowa kasa nayi na zauna na cigaba da zaman jira, dayawan ma'aikanta sun same ni ne a kamfanin, sai ya zamana ana ta gulma. Karfe tara ya iso, karban jakar hannun driban nayi ina tambayarshi. ""Yau me" "ake da shi?"" Mika min table tap din yayi, na ce mishi. ""Thank you!"" Har muka shiga elevator, shi ogan" "yana gaba mu muna baya, office dinsa muka shiga, na ajiye jakar a kan table din na koma gefe na fara" "duba abinda ake da shi, babu fita akwai ganawarsa da masu saka hannun jari, yara zasu zo daga wata gidan marayu zasu gana da shi, haka nayi ta tattara kome ina sakawa a littafina, sannan ka mikawa Driban tables din. Ya kai ya ajiye sannan muka fita da driban ya nuna min inda zasu tattauna. Abin sha muka kawo aka jera sannan muka fito. Wurin sha daya suka shigo bakin, ni da driban muka tarbe su har inda zasu yi meeting din, ina mai musu iso, kafin na haura sama na same shi. ""Sir sun iso!"" Kallona yayi ya ce min. ""Bakya ganin ina aiki ne?"" Yadda yayi maganar kamar a tafashe yake, ""kayi hakuri!"" Na fada ina kallon kasa haka ya gama abinda yake ya dauki top dinsa ya saka sannan ya kalli laptop din na tafi da sauri na dauka, na rufe tare da bin bayansa, kamar zan kifa haka na bishi a cikin elevator ma ina kaf-kaf da da laptop din, haka muka sauko a lokacin na ga wasu team na yan gayu sun iso kamfanin, na bi bayanshi har inda ake meeting ina Kai mishi na juyo zan fito ya ce . ""Have sit!"" Juyawa nayi na kalle shi naga ba ni yake kallo ba, bakinsa yake kallo, zama nayi aia fara meeting, kallonshi nayi ta yi yadda yake magana da turanci da kuma France sai Russian haka yana nufin yaji yare, can kuma naji ya koma harshen" "Germany, ba sai ga bakin suna tafa mishi tare da mika mishi hannu alamar alakar ta kullu......" "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 48" "Duk da sun ji dadin tarban da ake amma haka sukai ta jan da hira.. tare da da nuna mishi bukatarsu," "mutumin nan dan renin hankali ne, maganar ma da kyar yake yin hayaniyar da ake yi ne yasa shi kallona, na mike zan fita daya daga cikin bakin ya kai hannunsa zai tab'a ni ya mishi magana da da Russian, da sauri ya janye hannun da sauri yana mai bashi hakuri, nima kuma yana mai bani hakuri. Ina fita waje na samu rigima ake tsakanin driban da Yan gayun nan. Na tambaye shi ya gaya min shiru nayi domin suna tabbatar suma suna da iko da kamfanin. ""Ok ku kira baki su tafi sai ku shiga!"" ""Uban waye ya baki damar gaya maka magana haka?"" Inji wata yar zafin kai, komawa gefe nayi fitowa yayi da bakin take suka yi tsit kamar basu suke ihu ba, kallonmu yayi da driban muka rufa mishi baya. Har inda motarsu take. Sannan muka dawo dawo a hankali yake yiwa Driban magana yana gama magana muka shiga kamfanin. ""Duk sun shiga halinsu, saboda irin kallon da naga yana wulla musu sai na ji dadin haka ko ba kome shi din jarumi ne akan kome, minti goma da shigarmu ya saka aka kori Yaran zuwa daya building din. Wurin karfe daya sai ga Yaran nan, haka suka shigo suna ta murna, ban yi mamaki ba amma kuma yadda yaran suke murnan ganinsa kamar dama can sun sanshi. Mika min musu hannu yayi suka rungume shi." "Kallonsu nayi yadda yake hira da murna.. ""Wadannan Yaran marayu ne, tun lokacin Maman oga kamfani ta sayi filin gidan marayun, suka yi ta rokon arziki a bar musu filin tow kasancewar filin yana under Christian sai ta basu, tare da cewa ita me zasu bata. Saboda adalcin da ta musu shine suka amshi Muslunci, bayan rasuwarta Baban oga ya rike su da kula da su, haka yasa koda ya rasu shima sai aka cigaba da kula da kamfanin ko bai je ba, haka zai yi video a turo da fadar sunansu, sun sanshi sosai domin ko sabon baby aka kawo za a tura mishi ya saka mishi suna, hatta sunan gidan Marayun sunan" "Mahaifiyarshi ce.""" "Gyada kai nayi, wunin ranar akan Yaran nan muka yi shi, ni kan tafiya sallah nayi da na tafi ban dawo" "ba sai La'asar, tunda na dawo kallo daya yayi min bai kara magana ba. Driban yake tambaya ta dalilin zaman da nayi nace mishi ai na tsaya Sallah la'asar ne. Wurin cin abinci Driban ya ja ni muka tafi, shi kuma muka barshi da Yaran da suka ci nasu. Ganin kusan ganye nace a saka min sai kifi da Dan wake" "kaWan, sannan na dawo na zauna. Haka muka fara cin abinci, ji nayi kamar abu me sanyi yana tsara jikina" "ashe ruwan sanyi ake zuba min, ni kamar na santa. "" Karuwa bakiWaya kin makale mishi, kina abu kamar" "baki san kome ba idan baki kyale shi ba sai na saka an kashe min ke jaka wawuya mummuna baka katuwa!"" Ji nayi kunya ta kama ni kamar na nutse a wurin, "" Badr meye haka?"" Inji Mamar Yaran nan. "" Amma kin san duk wani abu idan na Brother Turaki ne yana da muhimmanci ko? Ita din sabuwar sakatariyarsa ce, sai ki san yadda zaki mishi bayani ya fahimta."" Sai a lokacin tsoro da kunya ya kamata" "Driban da naji matar ta ce mishi.."" Taj baka gaya musu replace Mrs Thomas tayi ba ne?""" """Ma na gaya musu na kai musu a rubuce basu dauka da muhimmanci ba ne!"" Riko hannuna tayi" "Mamar yaran zuwa office dinta, a hanya muka hadu da shi, bai mana magana ba, itama bata mishi ba.. office dinta muka je ta bani kayan da na saka nawa kuma ta kai wani daki ta baza min shi. ""Zauna!"" ""Na gode!"" Murmushi tayi tana faWin. ""Sunana Jasminah ni kanwar Brother Turaki ce, mu biyu muka rage a cikin mu shida. Iyayenmu sun rasu."" Yadda take bani labarin sama sama yasa na dan ji ta bani tausayi. Buga kofar aka yi ta ce a shigo Taj ne ya zo da paper Bag ya mika min. ""Ki sauya kayan!"" ""Na gode na riga da na sauya ai."" Amsa tayi tana faWin. ""Mun gode"" ta amsa tare da mika min,"" yace Idan kin gama akwai aiki da abubuwan da za ayi gobe! "" Mikewa nayi na bi bayan shi, ban jira ta cewar ta ba, muka nufi sama muna hira har muka isa office Winsa. Da dariya a fuskarmu muka isa. Da harshen yarbanci yayiwa Taj magana da sauri ya fara faWin.."" am sorry sir!"" Hakuri yayi ta badawa. Fita yayi ya bar ni a office din ni Waya. Wato da mutumin nan yayi ta min fada da masifa tare da nunawa ban san aikina ba, nazo sai dariya nake kamar wata shashasha, mutumin nan ya ci mutuncina. Haka na sunkuyar dakai nayi ta kuka. Cikin kalmomin da basu wuce a kirga ba ya ce min. ""Zan kore ki."" Haka nayi ta bashi hakuri, karshe na fita. Koda na fito waje stair na biyo a hankali nake tafiya ina kuka. Sai da na sha kukana sannan na koma can staff office na dauki kayana sai kallona ake na nufi office din Aunty Jasmin na dauki kayana. ""Me ya same ki Mrs Jama'are!"" Kasa magana nayi sai kuka nake, a lokacin ya shigo ni kuma na dauki kayana zan fita ta ce min.. ""Wannan fa!"" ""Na gode na jikina ma ya ishe ni!"" Na wuce shi zan fita. ""Koma ki dauki kayan!"" Kamar wanda ya dasa ni haka na tsaya cak kafin wata zuciya ta ce koma ki Wauka, ba musu na" koma na dauka na fita daga office din. """Brother me tayi maka?"" Wani haWe rai yayi ya fara muzurai kamar Wadda aka mishi karya. Haka na fito" "na dawo gidan ban yarda wani ya fahimci yadda nake ki ba, washi gari ya kama Alhamis, kamar ba zan je ba don karfe takwas na isa. Sai gulmar da ake yi naga sauran mala'ikan nayi, karar aka aiki a can sama yasa nayi mamaki me ya samu saman kuma? Staff office na shiga na ajiye kayana a locker na, sannan na rufe na fito ina mai nufar sama office din Jasminah na fara zuwa na ajiye mata kayan sannan na fito, kafin na haura ma uban yan masifa, na ga kofar shi aka cire aka saka na glass sai wajen ana ta haWa karamin parlourn da office ne, wurin yayi kyau sosai. Juyowa nayi na sauko kasa ina jin kamar yau na koma gida, haka na zauna har wurin karfe goma saura sannan na sauko da sautin. Ashe da na zauna abina a sama domin ina saukowa na hadu da bala'i fada yake tare da koran ma'aikata gudu biyu, sai kuka suke suna rokonshi da yayi hakuri. A hankali na sulale daga wurin ina zan iya masifar wannan boss din." Taj yana ganina ya kwala min kira dole na juya haka na je na amshi jakar masifaffen can. "Muna haurawa na samu har an gama aikin, abin ya bani mamaki yaushe na zo har an gama. Office" "dinsa muka shiga Taj ya ce min. ""An yi miki office dinki na wajen nan, nan zaki zauna ke daya babu yawo babu fita ko ina, akwai toilet a can gaba kaWan. Duk abinda zaki yi kama daga sallah zuwa wani abu ba sai kin fita ba, abinci xan na kawo miki."" Yadda yake bayanin saura kiris na kware. Wannan wacce irin takura ne? Muryanshi ce ta dawo ni daga duniyar tunanin. ""Zaki cigaba da aiki daga nan ban da sauka kasa."" Ban san yadda aka yi maganar ta kwace a bakina ba, sai da na rike bakina. ""Amma wannan bauta ce ba aiki..."" Yadda suka zuba min idanu, nayi maza na rufe bakina, da sauri na fita. Sai yayi kamar bai ji ba," shima Taj din kamar bai ji ba aka bar maganar. "Wunin ranar baki muka yi daya office dinsa zuwa kasa, ni da shi mun sauka ya fi sau goma, kafin na" "dawo nayi sallah naci abinci, ina gamawa Taj ya kawo min laptop kiran kamfanin Dellu ya ajiye min, ya kara min da table tap, sai takardu da printing machine. ""Ranki shi dade daga ko ina zaki amshi sakon kuma zaki yi printing dinsa ki tura, bari na nuna miki."" Haka ya shiga nuna min ina tambayar shi yana bani amsa kamar an ce in d'ago kai, masufaffen mutumin nan ne a tsaye a bakin kofar, da sauri na sunkuyar da kaina.. ""wannan anya kanshi daya?"" Na tambayi kaina ko da mq d'ago baya nan, sai sake wani irin net yayi a jikin kofar.. ajiyar zuciya na sauke. ""Idan aka tashi zaki tafi da kayanki ba zaki bar ko daya ba."" Gyada kai nayi, yana gamawa ya bar ni, kamar mayya wata yar wayar da aka saka a wurin yayi kara dauka nayi nace.. ""Hello!"" ""Akwai baki yallabai yasan da zuwansu ne?"" ""Ok rike wayar!"" Na ce sannan na tashi na isa bakin kofar na buga ya ce ma shiga, ina shiga na ce mishi. ""Sir kasan da zuwan baki ne?"" Bai amsa min ba, wannan mutumin dan girman kai ne, tsayuwa na cigaba da yi, can ya ce min. ""Ki duba tap dinki!"" Da sauri na fita na duba, daukar wayar nayi na ce mata. "" A kai su dakin tattaunawa gashi nan zuwa!"" Na koma na gaya mishi suna jiranshi, kamar ya mangare Ni, haka na biyo bayanshi da laptop dinsa. A meet room din har da wannan Khamis din, nan aka yi meeting din ina zaune a next na Masifaffen. Ana gama meeting din Khamis ya zo ya zauna yana mai juya kujerar da nake kai yana faWin. ""Idan kina da wata matsala ina wancan tsohon side din ki zo!"" Yadda Masifaffen ya mike haka nima na mike, tare da bin bayansa. Sai ji nayi mutumin nan ya kai min mari a mazaunai na, yana faWin. ""You too hot baby!"" Wani irin abu naji ya zo min wuya kamar yadda Masifaffen ya tsaya cak haka na juya tare da kifa mishi mari, sai da ya zauna.. ""Koda nazo aiki ni ha kazama ba ce."" ""Muje!"" Haka ya ce ,tare da matsa min na fita ya juya ga Khamis. "" Kayi hauka ne? Ko an gaya maka kowacce mace kazama ce! "" Daga haka" ya bar shi nan da ciwon baki. "Tun kafin mu tashi taj ya gaya min oga zai yi tafiya Abuja, tare da shi ni gobe ba sai na zo ba, tafiyar" "zata dauki kwanaki uku zuwa hudu ranar Laraba zan zo wurin aikin kenan, wayyo dad'i kamar na zuba ruwa na sha. Haka muka tashi na hada kome nawa, har lokacin Masifaffen yana office, hala jira yake na je na tattara mishi kayansa Kamar yadda na fada a raina haka ne fa, shiga nayi na hada mishi kayansa yana zaune, ina gamawa Taj yana shigowa na mika mishi. Ni dai da muka fito motar ma'aikata na shiga," "ya kawo ni Garej, sannan na wuce gida." *** "Wannan marin da Lubnah tayiwa Khamis, ya janyo rigima da meeting. Da aka zauna ya ce ba zai zo ba" "tafiya ne gaban shi, ai kuwa abin ya bakanta ran Alhaji Abbas da Alhaji Mudansir, lokacin da Uncle yake music bayanin rashin mutunci da Khamis yayi karyawa suka yi tare da cewa. ""Khamis me zai yi da low background irinta, idan lalata yan mata yake ba ga yan matan da suka fita haduwa a gari ba. "" Yadda" "suke jaraba da masifa kamar an yanki namar fuskarshi. Haka suka kai ™ara wurin Alhaji ELYakub ya zuba musu idanu ya ce a jira Turaki ya dawo sai ayi magana. Tunda abu ne na bangaren biyu zuwa uku sai aji uku waye mai gaskiya. Abin ai ba na fada bane, nan ma suka yi ta mita. Wani abu da suka kasa ganewa akan Turaki Alhaji ELYakub bai da hakuri kuma baya karban maganar kowa haka yasa suka yi ta jin haushi" "da mitar an ki amsar Maganarsu kome ya faru Turaki ne mai Gaskiya, ba su ba....." "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 49" *Anya kuna fahimtar tafiyar nan kuwa?* "Rigima taki ci ta ki cinya, domin kuwa Hajiya Sameerah ta saka a ranta sai an kori yarinyar da ta" "kwatsamawa danta mari, haka shima Kawun Khamis sun mai da al'amarin babban al'amari, wannan abin da suka ta yi yasa Alhaji ELYakub ya kira Turaki lallai yana son ganinshi, duk da yasan baya gari amma ya mishi al™awarin yana dawowa zai shigo." *** "Ranakun da nayi a gida, sai nake jin kaina kamar wata mai yanci. Nasan duk tsiya ranar Alhamis zan" "koma sai nake ji kamar kada na koma na ji dadin gida, a kwanakin da nake gida ne naji Ya Ado yana cewa zai mai da Abba gida an sallame shi. Sai da suka yi kwanaki a gidan Ya Ado, domin yace ba zai mai da shi gida ba, sai ya nutsu. Kullum muna tare ina zuwa na gaishe shi domin a daya gefen gidan ya ajiye su, na zauna ina karanta mishi karatun Alqur'ani, ranar da zan koma aiki na je dakin na zauna ina faWin. ""Yau naji zaku tafi ni kuma zan koma aiki, Allah ya kai ku lafiya, a gaida mutanen gidan."" Har na gama maganar da nake bai amsa min ba, duk dama baya wani kula ni. Haka na fito ina jin wani irin nauyi a raina, a harabar gidan na sami Baban Jama'are da Baba Malam, sai Ya Hafiz da Rufa'i. Sama sama na gaida iyayena maza na wuce wurin Motar Ya Ado na shiga ko Rufa'i yanzu na daina bashi fuska domin na fahimci shi yake bawa Ya Hafiz wani bayani a kaina. Ina tsaye a wurin ina wasa da wayata. ""Luluna!"" Banza nayi kamar ban ji shi ba fitowar Ya Ado ya ke ce min. ""Auta muje na sauke ko na dawo domin yau akwai inda xan je zan kuma ajiye su Abba a airport shi da Yadiko da Rufa'i, su Baba kuma xasu bi motar kasuwa. "" "" Tow ba kome!"" Na shiga gaban motar na zauna."" Ado kun raba ni da Matata! "" Ya fada yana kallon yadda na dauke kai. "" Luluna ki dawo gare ni!"" "" Wanda muka yi a baya ma Allah ya yafe min!"" Daga haka muka bar gidan, a hanya Ya Ado ya sake murmushi. "" Bakinki ya fara magana!"" Shiru nayi ban ce kome ba. Ya ajiye ni inda zan samu motar Garej, ina fita kuwa na samu motar minti talatin da biyar" "muka isa na biya tare da sauka na cigaba da tafiya a kafa. Horn da naji a bayana, juyawa nayi na ga" "motar Jasminah ne, ta tsaya tare da sauke glass din ta ce min. ""Shigo!"" ""A'a na kusan isa fada mata ina" "murmushi. "" Shigo dai mu karasa!"" Ta fada tana buWe min kofar ta ciki, shiga nayi a hankali ina murmushi. "" Na gode!"" Na daura jakata a cinyata. ""Kawai don oganki baya nan sai ki lafe a gida?"" Murmushi nayi nace mata."" Ai shi yace na zauna!"" Jingina kai tayi kar muka isa cikin kamfanin a tare muka shiga na isa inda zanyi sign na wuce, "" Sai yau kika gadamar zuwa?"" Juyawa nayi na kalleta sannan na ce mata. ""Oga ne ya ce na zauna a gida tunda baya gari."" Sai suka shiga kallon juna irin mamakin nan waye aka tab'a bashi wannan damar haka sai ni? ""Karya ne Oga ba zai tab'a baki wannan damar ba."" ""Stella me ya" "kawo wannan maganar?"" Jasminah ta tambaye ta, ""Ma gani nayi zata yiwa oga karya!"" ""Ta miki kama makaryaciya ce?"" ""No Ma!"" Ta fada, daga haka ta ce min. ""Ki tafi office dinki!"" ""Tow!"" Na ce na wuce abuna, ban kara tsayawa ba, ganin da gaske zan wuce sai wata take cewa. ""Me kika fi sauran mala'ikatan!"" Ban kula su ba, na wuce zan hau elevator, ""ya daina aiki!"" Wucewa stair nayi na fara" "haurawa a hankali, dama ai haurawan ba sabon abu ba ne." "Ina isa office din na samu tarin aiki, na bude table tap din, na fara aiki kamar yadda na gani, na shigar" "da bayanai, na tura mishi office Winsa, na turawa Taj da Jasminah, sai karfe biyu na samu kaina." *** "Yana zaune duk yan uwan babanshi sun taru ana son dalilin kwatsamawa Khamis mari da Lubnah tayi," "yadda yake shan fruit hankalinsa kwance, sai da ya sha ya koshi, ya mike yana faWin. ""Daddah ke da Dattijo ban san dalilin kiran da kuka min ba, gashi nazo babu wani bayani sai tambayar da ni dai nasan da yarinyar bata mare shi ba, sai na karya mishi hannun da ya tab'a da shi, tsalle tsallensa ya tsaya inda yake da iko idan ya shigo wurina ya tab'a min ma'aikta!"" Mikewa yayi bayan ya gama daure takalminsa, ya dauki jacket dinsa ya saka yana mai kallon Uncle Auta ya ce mishi. ""Wallahi sai na kwashe mishi kayan aiki!"" Daga haka ya fita abinsa bayan ya saka Black prada a idanunsa ya nufi waje.. har ya fita sai ya dawo ya ce musu. ""Yaran da kuka turo min na mai da su Office din Uncle Mudansir ina ga zasu dacewa da can!"" Daga haka ya yi tafiyarshi idan kana niman hayaki fidda na koko to Bilal ya kai wannan matakin" "wai sun zo gaban Alhaji ELYakub amma bai hana yayi yadda yake so, kuma ba yadda suka iya." "Don ya zame musu kadangare bakin tulu a karka, a kar tulu. A barka ka b'ata ruwa." """ Baffa kana ganin abinda yayi ko?"" Mikewa Uncle Auta yayi yana faWin. "" Me ya aikata? Ni ban ga wani" "abin da yayi ba. Ku jawa Khamis kunne ya san limit Winsa."" Daga haka ya juya ya fita, "" ka godewa Allah da ita yarinyar tana wurin, shi din yasan darajar jini da ace bata wurin daga abinda ka yi ta fita tow wallahi inda zaka yi fitsari na sai an daura maka leda! Kayi kazamtarka a idan aka baka dama banda inda yake karewa domin mutuncin kansa. "" Inji Ubaid, sannan ya fita daga cikin gidan. WaWannan mutane" biyu sun yi kaurin suna wurin kare Turaki. * "Karfe uku da wani abu suka shigo, bata nan bai wani damu ba. Haka ya wuce Taj yana bin bayansa koda" "ya shiga office ya samu ta ajiye mishi printing din da ya da ce duk wani abinda ya dace tayi. Cire jacket din yayi taj yana me amsa ya rataye mishi ya ce mishi."" Oga na ga ta gama aikin saura kaWan ne?"" Tsayawa yayi yana kallon aikin da tayi. "" Daga ina aka turo wannan abin? "" Ya d'aga wani bunch na white paper, wanda har da pin Winsu tayi. Dauka Taj yayi ya fara dubawa. "" Oh My God! Daga office din Badr ya fito ba sakon nan ba ne?"" "" Kira ta"" ya fada a hasale, fita yayi da sauri yana zuwa ya samu har lokacin bata dawo ba. Shi kuwa sai cira yake ya Wan zauna a gaban table Winsa tare da harde hannu a kirjinsa yana kallon kofar. Yana jin wayarshi yana ringing amma bai dauka ba, asalima dauke kai yayi yana kallon" kofar. "Taj kuwa haka yayi ta bi yana nimanta, bai same ta ba sai da ya fito waje ya hangota rike da ledar" "abinci da kuma daya ledar kamar abu ta sayo mr muhimmanci, a hankali take takawa." "Murmushi nayi lokacin da na ga taj yana jirana, amsar ledar yayi tare da cewa. ""Me kika aikata haka? Na" "bar miki kome amma kika yi shirme haka, yau Allah kaWai zai kwace ki, domin Oga yana can yana jin rigima a ransa. Hadiye yawu nayi na ce mishi.""Me ya faru?"" ""Muje!"" Hannu ya kai zai dauki daya ledar nayi baya da shi. ""Wannan dai!"" Na fada ina murmushi, amma ni daya nasan yadda nake ji, a hankali nake tafiya saboda zuwan al'adata bazata, kuma nasan yau da gobe zan shiga wani irin tasku ne. ""Don Allah ki yi tafiya da jikinki."" Kamar ance na d'ago kai, yana tsaye yana kallona, da sauri na sunkuyar da kaina ina tsoronshi sosai. Lokacin da na shiga, cikin building na kamfanin sauran abokan aikin sai dariya" "suke min, ni ban kula su ba. Haka na wuce na shiga elevator." "Lokacin da na shiga jingina bayana nayi da jikin elevator, bakiWaya naji kamar xan yi amai. Haka muka" "fita har zuwa kofar office dina, daga shi har ni Dan tsorace muke shi yana tashi ya shiga da ledar hannunsa, nima kuma haka na shiga da na hannuna tare da dunkule shi, kasancewar pad ne a ciki. Ajiye ledar yayi ya dauko min takardun ya ce min. ""Mene ne wannan?"" Ba tare da kome ba nace mishi. ""Sakon da ka bar min na yi printing dinsa shine nayi na turo mishi."" ""Ba shi bane ina wanda na baki?"" ""Kamar Ya? Ban gane ba!"" Na fada a hankali, ina cizon bakina. ""Na bar miki akan table Winki fa!"" ""Ni iya shi na gani wallahi azim ban ga kome ba sai su!"" ""Tow ina kika je?"" Ogan ya jefa min tambayar, kaina a sunkuye" "nace mishi.. ""abinci na je sayowa!"" Na fada ina rike ledar hannuna da kyau. ""Babu a kamfanin ne?"" ""Bana son na kamfanin ne!"" Sai a lokacin ya zuba min idanu. Kaina a sunkuye, ""ko karfe nawa zata kai i don't care daga kai har ita ku hada min aikina ina jiran ku!"" Daga ya shuri takalminsa ya bar mu a office" "din. Haka muka fito na kalli Taj nace mishi.. ""kayi hakuri!"" ""Ba kome dauka aka yi domin na Ajiye miki.""" "Shi kuwa yana fita ganinsa ya fito babu jacket dinsa yasa yan mata dayawa binsa da idanu, ga wani" "tafiyar da yake ya zuba hannu a cikin aljuhun wandonsa, can tsohon office din ya nufa, yana shiga ya hadu da Badr. Zuba mata sirrintaccen idanunsa yayi cikin wani irin tsinannen kallo me cike da tsana da" "b'acin ran ya ke bin ta da shi, juyawa tayi ba musu ba tare da ya ce mata bani abinda kika dauka ba, ta" "wuce ya tsaya a wurin ma'aikata sai gaishe shi suke yana amsawa, Alhaji Abbas da yaji labarin yana" "wurin ya fito da sauri. ""Yallabai shigo mana!"" ""I'm ok da nan!"" Can sai gata nan dauke da takardun, nuna mata hanya yayi ba musu ta wuce ya cigaba da tafiya yana latsa wayarshi. Har office dinsa, kamar yadda ta shiga ta dauka haka ta dawo da shi cike da kunya. ,harde hannunsa yayi a kirjinsa. ""Ke ina wasa da ke?"" ""Am sorry sir! Ba zan kara ba ayi hakuri."" Ta shiga bashi labarin. ""Na dakatar dake har na tsawon sati biyu!"" ""Don Allah Hamma kayi hakuri!"" ""Get out of my sign!"" Da sauri ta fito, ni kuwa bawan Allah nan haka ya kira Taj ya kara jibga min kaya, haka har karshe shida ina wurin ga ciwon ciki, shima don bakin mugunta yana office din yaki fita, fitowa yayi lokacin ina amsa wayar Ya Ado. ""Ya ina hanya ne hau aikin ya min yawa ne, kayi hakuri gani nan zuwa."" Na kashe wayar ina mai binsa da harara ""mugu kawai!"" Na fada ina jin marana yana ciwo. Taj ne ya shigo yana faWin. ""Muje a sauke ki a gida!"" A hankali na tashi na nufi wurin da Abayana yake na saka, zuwa yanzu na san na bata jikina, shi yasa na saka pad din a inda na zauna, lokacin da da muka sauko ina ta Addu'a Allah yasa na zauna a baya, cikin ikon Allah kuwa bayan na zauna kafin na shiga haka na bude sabon pad na saka a inda xan zauna, kamar nayi kuka," "bawan Allah nan mugu ne ko saka abin ban yi a jikina ba. Haka na shiga na zauna, ina jin kamar nayi kuka." "Har muka isa gida, na dan haska wayata na dauki pad din da jakata na, musu godiya sannan na shiga cikin gidan da sauri, ban tsaya ba ban dakin yara na wuce na wanke jikina na tura Ummu ta dauko min pant da wasu kayan na gyara jikina, ina sauke ajiyar zuciya. Laptop dina gida na dauko nayi login din na" kamfanin ba fara aiki. ...... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 50" Da yake ke yana gaba ne shi da Taj har suka isa Taj ya dauki jakarshi ya shiga da shi cikin shi kuma ya "wuce masallaci. Taj na isowa ya bi shi suka tafi. Koda aka yi sallah isha taj ya wuce gida shi kuma ya nufi inda motar yake zai duba abu, yana budewa ya kunna wutar motar ya saka hannu ya dauki file din da yake bayan motar, idanunsa ne ya kai kan jinin da yake manne a jikin kujeran. Mamaki ne ya kama shi. A hankali yayi lissafi yau ya zo mata, shi yasa take kome sanyi-sanyi. Kiran Taj yayi ya ce mishi. ""Kace yarinyar nan ta zauna sai Monday!"" Ya kashe wayar, sannan ya koma cikin gidan ya dauko kayan wankin ya zo ya wanke sit din ya jingina da motar yana nazarin har yau bata daina fama da ciwon cikin ba ne?" "Shiru yayi yana nazarin lamarinta, duk da yana jin zafinta amma a duk lokacin da ya kalleta sai ya ga kamar tana boye wani abu fuskarta, idanunta yana fadar abinda fuskanta yake faWa daban. Wayarshi ce" "tayi ™ara ya saka a kunne. ""Oga ban samu numbeta ba, domin bani da shi."" ""Ok""" Haka ya wuce gidan Ubaid ganin Nihla suka yi ta wasa da Yarinyar amma zuciyarshi tana wani irin "yanayi. Bude wayar yayi ya kara bincike ko ya dauki number wayarta yasan gobe zata zo da mood din. Amma bai samu ba abinci ya ci ya nufi gidan Uncle Auta, nan ma fura ya sha yana dawowa gidan ya wuce Gym ya motsa jikinsa. Rabin daren yayi shi akan aiki ne amma bakiWaya Lubnah ce a ransa." "Kusan har gari yayi tsit ina aiki, tashi nayi na dauko faten da wanke na sha. Sannan na zo na kwanta" "saboda hajijiyar da nake ji, haka nayi barci a wahale ban farka ba sai karfe shida na safe. Na shiga nayi wanka na wanke jikina duk na b'ata zanin gadon haka na hada na wanke da kayan jiya, sannan na shafa mai da body spray. Na saka kaya irinta hausawa saboda yau juma'a ce, pad dina guda goma na zuba a" "jakar, domin kada a kara samun matsala." "Doguwar riga ce ta atamfa, sai hijab da na saka yadi biyu da rabi da na saka, na fito Ya Ado ya ce" "min. ""Allah yasa kada a koro ki, kin makara."" Murmushi nayi na shiga muka fita, a inda ya saba ajiye ni ya ajiye ni, na dauki jakata na wuce na jira motar kamr kullum muka wuce, ina isa na biya tare da fita na nufi hanyar kamfanin, a hankali nake tafiya kaina a sunkuye. Har na kusan kamfanin na ji muryan Khamis, gabana ne ya fadi. Na kalle shi dauke kai nayi na cigaba da tafiya, karar horn da aka yi fa karfi yasa ni juyawa. Yau shine da kanshi ba Taj ba. Daina bina Khamis yayi, ya tsaya matsawa nayi a gefen hanyar yayi kan Khamis da motar ya matsa yana ihu da dariya kamar mahaukaci. Da yazo kusa da ni,sai ya rage gudun motar yadda nake tafiya a hankali, bar na shiga kamfanin haka yake bin bayana, ajiyar zuciya na sauke ashe bashi daya ba ne a motar shi kan ma yana baya, daya mutumin nan ne. Fita yayi a motar ya nufi hanyar waje. Mai tuka motar ya ce mishi. ""Kaga ka daina zubawa rauni gishiri."" Zuciya ce take cinsa, bai saurare shi ba haka ya fita can ihun Khamis muka ji, bakiWaya muka fito wajen. Aka yi juyin duniyar nan ya sake Khamis amma fir yaki, sai da nace mishi. ""Don Allah ka kyale shi mana!"" Ture shi yayi ya juya tare da damkar hannuna. Har office dinsa ya kai ni, tare da cewa. ""Daga yau ki tsaya a inda ake sauke ki na gaya miki!"" Ya daka min tsawa, shiru nayi tare da rufe idanuna, haka ya fita ya bar ni kamar mayya a office Winsa, shigowa mutumin da suka tawo tare yayi ya zuba min harara ya daka min tsawa. ""Wacece ke? Me yasa saboda ke yake abinda bai taSa yi ba!?"" Kuka ne ya zo min dai-dai lokacin da ya shigo office, ""Tambayar ki nake ba kuka nace ki min ba!"" Ya daka min tsawa, ""Malam ya isheka haka, ya ishe ka nace!"" Ya fada a masifance. ""Bai isa ba Turaki nima zaka dake ni ne kamar yadda ka dake shi, wace ce ita da kake fada akanta?"" Ture mutumin yayi har waje. ""Kada na kara ganinka a inda nake!"" Daga haka ya rufe kofar. Ai kuwa nima ya juya ya fara min fada tare da cewa na zo ina juya jikina har maza na kai min yadda yake fadar kamar ya rufe ni da duka, sannan ya koro ni waje tare da kiran Taj ya zo ya kawo min aikin, nasha kuka kamar an yi min mutuwa sannan na cigaba da aikin kamar jaka, na jiya ban gama ba, yau aka kara kawo min wani aikin, jikina har ciwo yake abinci kuwa taj ya kawo min faten wake da soyayyar agada, naci sai ruwan tea, wurin karfe biyu ya fito cikin fararen kaya, da hular da ya" "karya, sau daya na kalle shi na cigaba da abinda nake yi." "Shigowar wasu yan mata na family Winsu, ya sani mikewa nace musu. ""Sannunku da zuwa, da mai za" "a taimaka muku?"" ""Mun zo miki kashedi ne ki fita harkan hamma Turaki!"" Kallonsu nake kafin na ce musu."" Ayi hakuri ba zan kara shiga harkansa ba!"" "" Aiki kika zo nan, ba shige mishi ba!"" Yadda suka yi ta min maganar banza ni dai ban ce musu kome ba, sai can na ce musu. "" Mr Turaki ya saka cctv idan kuka matsa dayawa zai dauki mataki! "" Na nuna musu, wurin da camera din yake, sai suka fara baya Baya. Bar suka fita, bayan ya dawo na tattara takardun na kai mishi, ya duba sannan ya watsa min a fuska ya ce" "min. "" Ki gyara basu yi min yadda nake so ba!"" "" Tow"" na kwashe, haka na dawo na zauna karfin hali" nake amma ni daya nasan yadda nake ji da ciwon ciki amma mutumin nan ya kara dawo min da aiki ba. "Hawaye ne ya zubo min, haka na kara zama na fara sabon aiki karshe ya fita abinsa, shigowa Taj yazo ya amshi aikin yana taya ni, ni kuma na zauna ina hutawa, muka yi ta hira da Taj har ya gama min aikin ya" "ce min. ""Aikin na da wahala amma a madadin sai kin sake type kawai copy and paste zaki yi."" "" Kamar ya? "" Na tambaye shi, ina sani. Mikewa nayi kafin ya bani amsa na wuce ban dakin da aka nuna min, na gyara jikina. Ina dawowa na samu baya nan, sai Masifaffen nan ne a tsaye, "" aiki kika zo ko yawo?"" Kasa" "magana nayi ina kasa domin kwarjini ne da shi, baka iya tsayawa ka kare mishi kallo. Kamar nayi kuka haka na wuce bakina yana rawa nace mishi."" Toilet! Banza ya bawa ajiyata yayi gaba abinsa, takaici ne ya kama na cigaba aiki har karfe biyar da rabi, na mike zan hada kayan fitowa yayi fuskarshi a haWe yayi tare da kafe ni da idanu, diriricewa nayi na fara niman inda zan tsaya kawai sai na koma na zauna, ba magana ba zagi amma wannan idanunsa masu kama da na dodanni, sun iya hukunta mutum. Haka na cigaba da aiki har karfe shida ya wuce. Ina wajen, ban san lokacin da hawaye ya fara zuba min ba. Haka na cigaba da aikin ina kuka. "" Lubnah! "" Naji muryan Jasminah, d'ago kai nayi ina kallonta na fashe da kuka. "" Taso muje!"" Haka na taso ina kuka, "" ina zaki kaita?"" "" Bro lokacin tashi ya wuce fa, idan aikin ya mata yawa."" "" Koma ki cigaba da aikinki"" haka na koma na zauna tare da cigaba da aiki ina shashekar kuka, ya juya ya banko mana kofar. Ya cigaba da aikinsa, ina ta kallon wayata ko Ya Ado zai kira ni, amma bai kira itama Jasminah Yaranta suna ta kiranta, haka ta mike tana gaya musu. ""Gani nan zuwa!"" Kallona tayi ta ce min. ""Hankalin Yaran ya tashi."" Cikin dauriya nace mata. ""Ba kome!"" Na fada tana barin wurin na kurawa kofar office Winsa idanun ina jin wani irin haushinsa, haka na dauke kai na cigaba da aikin har na kammala na koma ban daki na gyara jikina koda na fito babu kowa kusa fitilar wurin a kashe office dinsa ma hasken a kashe, da sauri na tafi wurin zamana na kunna wayata, ina d'ago kai muka yi ido hudu da shi, wani irin kara na sake tare da wurgi da wayata. Zube a kasa tare da rike kirjina da amsa min da wani irin ciwo. Ina haki kunna wutar parlourn yayi ya tsaya tare da hade rai. Kuka na saka ina zaune akan gwiwata. ""Ina da abin yi."" Wato yana jirana, da sauri na mike na hada kayan da na zo da shi. Na bi bayanshi da sauri domin ya kashe wutar parlourn, garin binsa haka na yi karo da bayansa cak ya tsaya nima nayi, tare da ja da baya. Ina jan hancina na ce mishi. ""Sorry sir sorry Sir."" Cigaba yayi da tafiya nima na bi bayansa. Har muka shiga elevator, tsayawa nayi can bayanshi ina sunkuyar da kaina har muka fito kasa. Sai da muka fita aka rufe office din bakiWaya. Wurin motarshi muka nufa baya shiga, ni kuma na shiga gaba. ""Har kun taso?"" ""Eh!"" Na cewa Taj da ya tambaye ni, ""kamar kin yi kuka?"" ""A'a ban yi ba!"" Na fada, zai kara magana Masifaffen nan yayi gyaran murya, haka muka cigaba da tafiyar har muka iso gida, fitowa Taj yayi ya bude boot din motar ya ciro min wasu paper Bag har guda uku, ya ce min. ""Inji Oga gobe Saturday akwai meeting din da za a yi a Eko hotel da fatan zaki shirya da wuri."" ""Har Saturday ma akwai aiki ne?"" ""Eh amma ba wai na office ba. Wasu mutane ne zasu sayi kayan kamfanin yana da kyau ki shirya da wuri!"" ""Gaskiya!"" ""Tow ni yau xan tafi Abuja akan meeting, idan ya ji kina musu tura ki kano zai yi!"" Jin haka yasa na ce mishi. ""Tow shi kenan!"" Mishi godiya tare da shiga cikin gidan, Ya Ado na samu yaran sun kwanta, Aunty Zakiyah tana kitchen, gabansa na je na zauna. ""Yaya na gaji aikin nan ba irin nawa ba ne!"" Na fara mishi kuka. ""Mutumin nan bai da imani, kome nayi fada yake min, ba halin nayi mistake yayi ta faWa kamar ni daya ce na fara kuskure."" Murmushi yayi ya ce min. ""Haka kowa yake farawa, sannan ai ya kira ya gaya min yau da gobe kuna da ganawa da wasu yan kasuwan kasashen ketare, shi yasa ba zaki dawo da wuri ba."" Sake baki nayi ina kallon Ya Ado wato Masifaffen nan ya san kan duniya ya kira Ya Ado ya kare kanshi, kada ace na jima har da fada mishi aikin da muke da shi gobe. """ "Ni dai ba zan je ba!"" Na fada ina kuka. ""Tow shi kenan!"" Ya fada yana kallon kayan da ba shigo da shi," kusan kayan ci ne sai pad. Da sauri na maida shi cikin na wuce dakina na can sama na wanka na shiga "nayi sannan na fito na gyara jikina, na fito na ci abinci sannan na dawo na rage sauran aikin na kwanta. Wayyo Allah dad'i nayi barci har karfe tara na safe, don cikin dare da na sauya pad na koma na kwanta ban kara bude ido ba. Sai da na ji ana buga min gadon na bude idanuna."" Kin yi baki suna parlour."" "" Baki kuma? Su waye?"" Na tambaye ta bata kula ni ba tayi tafiyarta, hulata na dauka na saka akan riga da wando na barcin da yake jikina. Ban daki na shiga na yi brush na wanke fuskana sannan na fito,. Na sauko kasa ina faWin. "" Kuma dai weekend din ma ina murna na rabu da jarabar wancan Masifaffen" mutumin me kama da yan damben turawa....... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 51" """Fisabiilillahi ko a gidan gwamnati Asabar da Lahadi hutu ake. Ni yanzu ko Gym na daina zuwa tunda na" "fara wannan aikin me shegen wahala waye ya sani ko sai na gama aikin ma karshe a ce za a kore, Aunty Mutumin nan ya cika barga, haka ya min shekaranjiya wai zai kore ni, ko jiya oho. Kin ga yadda ke tafiya kamar wani robot"" Na sauko har parlourn, ina kwaikwayar tafiyarsa, kawai kamar ance ns duba kujeran da yake kallon tv, da sauri nayi baya ina faWin. "" Innalillahi! "" Nayi baya ina toshe bakina, kafin na juya da wani Muslimin gudu aikuwa na ji abu ya kwashe ni sama, na hantsila tare da dokuwa da kasa, takalmina kafa daya yayi tsalle sai a fuskarsa, Allah ban san lokacin da na ce. ""Na mutu!"" Na tashi na haura sama da gudu, ina fadin shi kenan. Abin ya zo wani iri amma kuma Ya Ado sai da yayi dariya yana faWin. ""Silly girl, don Allah ka yi hakuri bamu san zata fito tana mocking dinka ba don Allah ka yi hakuri!"" Murmushin yake yayi yana faWin.. ""Muna jiranta."" Ya saka kai ya fita, bai san dalilin da yake son ya ganta a kusa da shi ba. Bai sai me yasa yake jin haushinta ba, amma a duk lokacin da ya ganta yana jin kamar ita din da ya sani can ita ce a gabanshi. Sai dai ita wannan ta sauya dayawa. Fitowa yayi waje, wato asalin yadda aka yi ya shiga cikin gidan, ya zo ya tsaya tare da tunanin wanda zai tura cikin gidan sai ga Ya Ado ya dawo daga Gym da yake weekend yana zuwa, kawai sai ya ganshi a kofar gidan, har zai wuce sai ya dawo ya mika mishi hannu suka gaisa ya ce mishi. ""Kana son ganin Lubnah ko?"" ""Eh"" kawai sabo da a fakaice kallon Ya Ado yake yason ya ga ko mijinta ne amma wani abun mamaki sai ya ga suna kama da Lubnah, sai ya kauda kai har ya ado ya ce mishi zai duba ko ta shirya, yana zuwa ya samu tana barci shi ne ya fita tare da shigo da shi cikin gidan. Shine ta mishi rashin mutunci. Lashe bakinshi yayi yana godewa Allah da iya" "shi kaWai yazo bai dauko wani ba, balle ya sha kunya." "Tunda na shiga nake jin kamar zuciyata zata kwace a kirjina, ""wayyo Allah na!"" Na fada a hankali," "kamar xan yi kuka. Buga kofar aka yi daga waje Ya ado ya ce min. ""Ki fito yana jiranki, kuma zaki sani ba dai bakinki bai da lizami ba"" bude kofar nayi da karfi ina faWin. ""Ya ado kun san shine ya zo, ba ku gaya" "min ba."" ""Je ki shirya yana jiranki ai ba zai nuna miki ya ji me kika ce.""" "Kamar nayi kuka haka na haura nayi wanka na shirya tsaf, sannan na dauko abaya na saka tare da" daura hula kafin na saka gyale na nad'e kaina. Haka na shirya ina fitowa Aunty Zakiyah tana mika min "wata yar jaka tana faWin."" Baki karya ba, gashi nan ki karya a can."" Kamar nayi kuka haka na fito kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki. Har waje na fito yana mota, ina zuwa na gwada bude bayan mota" "amma a rufe gaban na zaga na bude na zauna. Kasa kallonshi nayi domin sai yanzu nake jin abin a raina," "har ya tashi motar ban iya ce mishi cikanka ba. Ni kaina kamar na nutse kasa, haka ya cigaba da tuki cikin kwarewa. Wani unguwa muka isa wanda yake bakin ruwa. Yayi horn a bakin kofar gidan. Aka bude kallonshi nayi naga fuskarshi a haWe kamar yaga hadiri. Haka ya shiga cikin gidan, aka zo aka bude kofar inda yake aka yi tare da inda nake. Haka ya fito, ""kafin ki samu abin zagina ki hado kome yana baya!"" Kamar ba fasa ihu haka na ji, a hankali na dauki kayan na bi shi da su. Wani kwali ne mai kyau sai wani jaka paper Bag, muka shiga cikin gidan. A hankali nake bin bayanshi, har muka wuce ta wani lambu kafin muka isa babban fili manyan mutane, kamar na juya saboda yadda ake kallona tare da da shi. Yatsawa yayi kamar zan yi tuntube ya ce min. ""Ki nutsu! Bani kayan!"" Mika mishi nayi muka jera tare har zuwa" "cikin wurin da ake a taron, suna ganinsa bakiWaya suka mike suna ta tafawa ana faWin gashi nan ya zo." "A hankali yake kutsawa wurin manya mutanen da suke can gaban, ni kuma na tsaya daga dan baya" "baya. Juyawa yayi ya hango ni ina tsaye a gaban wasu table. Kallona yayi irin kallon meye haka? Kawai sai na taka wurin da yake na isa, mika min hannu wani mutum yayi amma ban bashi hannun ba, yadda ya bi mutumin da wata lalatacciyar kallo yasa ya koma nan aka gabatar da abinda ya haWa su, sannan suka fara jawabi, tare da tsaya akan abinda ya tara su. Ina jinsu kusan akan taron karawa juna ilimi akan kasuwanci ne, sai wasu fiyale da aka saya, har aka gama maganar ina tsaye, kusan awa daya muka yi kafin aka tashi muka fito, sai hoto ake da shi, a yadda yake hade rai da nuna baya son na shiga hoton na koma can, Masifaffe kawai, na fada a raina. Muna gamawa da wurin muka wuce Eko hotel, kafin mu bar wannan guest house din ya mika min table tap din, wayarshi ya shiga kira, bayan ya kira aka dauka ""Sir kana tare da ita ne?"" ""Hmm!"" ""Lubnah dama kin san jiya na gaya miki zaku Meeting tow ki duba abubuwan da zaku tattauna a wurin meeting din, yana cikin table tap din na shirya kome!"" ""Ok na gode!"" Bai jira me zai ce ba, ya kashe wayar. Haka na cigaba da duba tap din wani abu da na fahimta shine yadda yake tuka motar a hankali kamar ba zai isa inda zamu ba, yana tuka motar yana kallon agogon hannunsa. Ganin na Wauki biro da takarda a cikin jakata na fara rubuta abin da ya dace ina gamawa na ajiye mishi tap dinsa, ai kuwa da azabar gudu ya ja motar muka bar titin, lokacin da muka isa saura minti biyar a fara taron, yana tafiya ina bin bayanshi har inda za'a yi taron, tunda muka shiga ya samu wuri ya zauna aka fara dogon turanci nan, aka fara gabatar da kai, nima na kalle shi ya dauke kai, sannan na gabatar da kaina. Sannan na fadi abinda ya kawo. Bayan na gama na zauna. Cikin abinda bai wuce minti talatin ba, aka fara gabatar da abinda ya kawo an sayar da kayan shi akan kuWi me yawan gaske wasu yaci riba wasu ya fadi sosai, kuma dama kasuwa ta gaji haka, amma ribar tafi asarar yawa, yana gamawa. Muka fito , wani dan kasar China ne ya ce mishi. ""Mr Turaki ko zaka zo mu ci abincin rana ne?"" Sai lokacin na tuna fa na zo da abinci, ""Mr Ma na gode."" ""Haba ko ita ba zata ci ba!"" Kallona yayi ya ga yadda nake kauda kai. ""Itama!"" ""A'a Mr Turaki barta muje ta ci!"" Haka muka wuce aka kai mu wani wurin cikin abinci irin VIP nan! Wurin ya hadu kamar me iya haduwa zama nayi, aka kawo abincin hatta yadda abincin yake tururi sai da ya sa naji cikina yana wani irin ™ara irin ina jin yunwa. Kallonshi nayi na kai hannuna cikin, bai wani damu da ya kalle ni, abincin ya fara ci ina kallon abincin, ""Dig!"" Ya ce min, haka nayi ta juya abincin ina hadiye yawu, tashi yayi tare da barin wurin, da sauri na fara cin abincin, ina" "ci ina kallon ta inda ya bi kada ya dawo ya samu ina ci, na kai loma kenan na hango, haka na ajiye cokalin. Na bar abinci me shegen dad'i. Da yazo ya ga yadda na ci ba sosai ba, haka ya ce min. ""Zan tafi fa!"" Mikewa nayi kamar na juye abincina, sau biyu yana kamani ina kallon abincin har ga Allah ban koshi ba," "haka yayi gaba abinsa, sai da muka shiga mota sai ga masu aikin wurin sun kawo min leda me dauke da" "Chinese dish, kallonshi nayi naga shi ba ma tani yake ba, a hankali na risina ina faWin. ""Na gode!"" Daga" "nan bai tsaya da ni ko ina ba sai Lekki. A kofar wani hadadden gida ya tsaya, fitowa yayi yana mai nufar cikin gidan nima na bishi, muna shiga Yaran nan suka lullube shi da murna, suna ganina suka fara ihu." "Haka na shiga na same su, ya fita ya shigo da ledojin nan, daga nan ya juya yayi tafiyarshi." "Cikin gidan muka shiga ina tambayar su. ""Ina Mamanku?"" ""Ta tafi Kumo Family Mansion"" abinci na" "juye mana muka ci ina kallon yadda suke ta wasa da abincin, na ce a raina Yaran attajirai fa haka suke basu damu da abinci ba kamar irinmu yan medieun class, kazar guda ce muka ci rabi me aikin ta dauki sauran ta saka a frij, muka cigaba da hira har bayan la'asar da malaminsu ya zo, sai lokacin Mamar ta shigo tare da shi, tana kuka idanunta yayi jajjur ganin yadda bakiWayansu suke kallona yaushe nazo. ""Ke me ya kawo ki?"" Kafin na bashi amsa ya shigo yana waya , da hannu ya min alama da na fito mu tafi." "Haka na fita muka wuce gida, kular abincin da nazo da shi na dauka sai nayi wayam, babu kome a ciki, s hankali na ajiye ina satar kallonshi, wani hade rai yayi irin baya son wasa, lokacin da muka isa gidan na fita tare da Waukar kular na rufe mishi kofar, na shiga cikin gidan. Ina shiga cikin gidan na zube a parlourn ina nishi, na gaji sosai. Duk da ban yi wani aiki ba amma kuma zama wuri Waya ya dame ni. Da wuri na" "kwanta bayan mun sha waya da Mama, kai na ji dadi." "Wato wani irin rigima ake a family house Winsu, akan Jasminah sun matsa lallai sai ta koma dakinta , ko" "kuma ta bawa Fahad Yaransa. Ita kuma ta ce sai dai ta mutu da ta bashi Yaranta, akan idanunta ma aka yiwa yarta fyade. Wannan abin ya tab'a Turaki, don haka ya ce a shigar da maganar kotu domin ta bata damar rike Yaranta, uwarta kuwa ta ce idan ta haifeta kuwa ta kai Fahad kotu, sai ta mata baki shine, abinda ya d'aga mata hankali, wani irin kuka take wanda yake damun dan uwanta. Yana ajiye Lubnah ya wuce gidan Noma family, ana cewa gashi nan ya zo a lissafinsu ya zo basu hakuri su kyale ta, sai dai lissafinsu bai zo yadda ya dace ba, domin yana shiga gidan da shi da Barista Abdul Hakim, wanda ya samu yana jiranshi a kofar gidan a tare suka shiga cikin nan, yan gidan na ganinsa suka fara dariya, zama yayi ya ce. ""ina son ganin Alhaji Noma."" Fitowa Dattijon yayi yana wani buWewa kamar kifi ya samu wurin zuba kwai, yana kallon Turaki gabanshi ya fadi amma kuma sai ya dake har ya shigo cikin parlourn ya zauna. ""Na ji ka kafa dokar ko Yaran Jasminah ko dakin Mijinta."" Tashi turaki yayi yana kallon parlourn bakiWaya ya ce mishi. ""Ni kuwa sai naga kamar wannan gidan da duk abinda Noma yake da shi, aro Alhaji" Haris Kumo ya bashi domin akwai sa hannun a wurin nan...... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 52" "Ya mikawa Barista abdulhakim hannu, sai ga takardu. Da aka saka abu kusan shekaru ya kalli Baristan ya" "ce mishi. ""Amma kasan takardun nan sun yi kura? Dai dai kuma kome tar kamar yanzu aka saka hannun!"" Ya fada tare da kardakade takardan, yana mai daura takardan a kan table, ya kuma d'ago kai ya kalli Alhaji Noma. ""Na baka awa ashirin da hudu ina bukatar kudin nan, ko kuma kilu ta ja bau, idan"" daga haka ya mike zai fita Alhaji Noma ya ce mishi. ""Me kake bukata?"" Shafa sajensa yayi yana kallon kanshi a madubi. ""Duk wata matsalar da yake kunno kai a kashe ta ta hanyar da aka bi, ko kuma ni na" "kashe ta, ta irin wannan hanyar?!"" Ya fada yana d'aga kafad'arshi. Yadda ya juya yana faWin. "" Ina da" "thousands of this copys"" sannan ya juya ya kalli mutumin da akalla zai yi sa'ar Babansa ya saka yatsu biyu" "ya saka a saman idanunsa alamar ina kallonka, daga nan ya wuce yana mai barin gidan shi da Barista abdulhakim, "" Amma baka niman zaman lafiya, yanzu kana ganin haka zai yi aiki?"" ""Sosai kai, zuba idanu" "ka ga ikon Allah."" Daga haka suka rabu." "Kamar yadda ya shiga tsakaninsu, haka lamarin ya mutu kamar daukewar wuta. Ai idan kana da kudi" "babu abinda ba zai yiwu ba, sai ikon Allah. Da wannan Jasminah ta samu zaman lafiya, Fahad ya kirata ya ce ya janye ta rike Yaranta idan yaran suka samu lokaci su zo hutu, ta amince aka kashe maganar" "bakiWaya kamar bai tab'a faruwa na, dama ai zancen kenan." *** "Kallon Ya Ado da yake waya da Ya Umar yake tambayarshi. ""Na shiga maganar ne domin na kara nisanta" "ta da shi, sannan yadda suka yi juya hankalin Abba yasa na shiga lamarin amma idanun kamfanin yana kanshi a duk inda yake saboda sun ce suna da case nasu a kasa tow sai CEO din ya kama shi yana ™o™arin cutar da ita ba wani abu ba ne, shi a nashi lissafin ya razanata ne ta amince da shi, amma akwai wani abu" "da na fahimtar da nayi mishi, kamar akwai sanayya da juna!""" "Kallon Ya Ado nayi da kyau kafin na kara mai da hankalina, kafin ya gama wayar anan na fahimci wato" "da wancan Masifaffen rufe shi yayi, da yadda aka fito da shi, sai na ji kamar ni aka ceto daga farmakin Ya Hafiz. Tunda na ji haka sai na ji mutumin ya Wan yi abin arziki, kuma sai ban damu da na ji wani abu daga gare shi ba, washi gari ya kama Monday, sai da na jira Ya Ado ya sauke ni,da wuri na isa na fara aikin da na ga an jibga min, sai da na harari kofar ya kai sau goma, ina tura baki gaba. Tun karfe takwas nake abu daya har wurin karfe goma da ya shigo, na tashi na bi shi na karanto mishi menu na yau bakiWaya. ""Yau bana son ganin kowa!"" ""Ok sir!"" Na fito na cigaba da aikina wurin karfe sha biyu saura wasu mata shigo da sauri na fito na gaishe tare da cewa. ""Yau ya ce ba zai gana da kowa ba, yana da aik. "" Saukar wani" "gigitaccen mari na ji a gefen fuskana, wanda yayi daidai da fitowarshi zai fita. Ban san wacece ita ba amma yadda ta mare ni, ya saka ni jin wani abu. ""Me tayi miki?"" Ya tambaye ta, ""Ubanta ne ya gina kamfanin da zata dakatar da ni!"" ""Ba Ubanta ba ne, amma Ubana da Uwata suka tsayar da kamfanin haka,. Kin yi dacen na fito da sai ta rama domin na gaya duk shegen da ya taSa ta ta rama!"" "" Ni ce shegiya?"" Gefenta ya bi ya wuce, ta kama ihu da fada akan ya kashe mata auren yarta, ni dama tunda na ganta nasan ba arziki ya kawo ta ba, don haka ban wani damu ba. Ganin yadda Jasminah ta zo tana kallonta cikin fushi da b'acin rai. "" Na rantse da Allah, idan baki rabu da shi ba sai nayi ruined rayuwarshi."" Duk yadda ta kai da dakewa, sai da ta ce mata."" Ba zaki iya ba, tun yana Yaro kike kokarin haka me yasa baki yi nasara ba, rayuwarki xa kika cika shi da karya da yaudarawa babu abinda kika sani. Anya ke uwa ce? Shi bai tare miki kome ba, ko ba kome zan ji kamar Abba yana raye!"" Rike ta nayi ina girgiza mata kai, ina faWin. "" Kada ki. Aikata haka, Uwa ce ba a wasa da lamarinsu. "" Kwace hannuna tayi" "tana faWin."" Kyale ni na gayawa wannan matar Abinda take aikatawa, da fari ta ci Amanar Mss Annah" "A'ishah kasancewarta sakatarinyarta, tsiyar ka dauko mutum daga poor background ka ja shi jikinka" "kenan, wannan masifar da bakin ciki na talauci da haushin masu arziki... "" Tass aka dauke ta da mari, wanda ya nuna mata yatsa, tsabar ya bani tsoro haka na koma gefe na na tsaya ina zare idanu. ""Ki girmama ta, koma me take miki."" ""But she hate me! Bata kaunar farin cikina, idan na kara haduwa da ita sai na kashe ta, wallahi i will kill you;"" daga haka ta bar wurin ni dai sai na zama yar kallo. ""Duk yadda ka shiga rayuwar wani kai ma sai an shiga naka, bar ganin Allah ya baka aron numfashi ka zata ya kyale ka ne, ni bana bukatar fansa iyayena. Amma ki sani akwai wani Yaro a garin Kano mai suna Khalid yana nan zuwa."" Daga haka ya wuce ya barta a tsaye a matu™ar razane, domin bata kawo Jasminah zata yi magana ba, har zai shiga cikin office dinsa ya ce mata. ""Daga yau kada ki kara shigo min office har ki Mari sakatariyata!"" Sannan ya shiga cikin, sai da suka bar office din ya kira ni ta wayar landline, na amsa tare da shiga office din, d'ago kai yayi na wani lokaci kafin ya ce min.. ""Mijinki yana dukarki ne?"" Maganar tazo min a bazata sai nace mishi. ""Me ye?"" Wani haWe rai yayi yana min wani kallon bana son renin wayo. Tura baki nayi ina dauke kai. ""Ni kin iya min rashin kunya amma su da suke marinki, baki iya ramawa ba!, daga yau duk wanda ya kara miki kallon banza ki rama idan kika kara sakewa wani ya mari wannan" "fuskar naki sai na kore ki! Kin ji ko?"" "" Hmm!"" Nace ina tura bakina gaba. Bai kara min takaina ba ya nuna min hanyar waje, bakin da yayi aka kira ni daga kasa aka gaya min. Na je na tarbe su, sannan na dawo na kai su dakin Meeting na koma zan shiga elevator, ina shiga Khamis yana shiga, wani irin tsoro ne ya cika min rai, na koma gefe na tsaya.""ki bani abinda kike bawa Oganki mana."" Ni dai ban tanka mishi ba, addu'a kawai nake yi domin wallahi na gama razana, jin yana takowa, na rintsa idanuna da karfi. Jin kofar ta bude nayi saurin xan fita ya dawo da ni, wanda haka yayi daidai da isowarshi bakin kofar. Lashe baki Khamis yayi ina kokarin kwace kaina. ""Sake ta!"" Amma yaki, kafin ya kara wata magana na gantsara mishi cizo, da sauri ya sake ni yana faWin. ""Na gode da cizon kauna!"" Ya fada yana kallonshi, ban san me zai aikata ba, haka yasa ya nufi kofar a fusace shi kuwa Khamis ya rufe kofar da sauri yayi kasa. Da gudu yayi stair na ce mishi. ""Ba fa shi bane me muhimmanci, kana da baki masu muhimmanci. Idan ka cigaba da biye mishi kullum sai ya yi abinda zai bakanta maka rai, zuwa yanzu na fahimci duniyar da kowa yake, tunda na fito daga duniyar da ba kowa yake fahimtata ba, don Allah ka kyale shi ka fuskanci abinda yake gabanka, ni ba abinda nayi kawai kwatar kaina nayi! "" Kallona ya shiga yi yana son yayi magana na ce mishi."" Irinsu haka suke idan aka cigaba da kula su kamar an basu damar yin abinda a so ne, don Allah kayi hakuri ban san dalilinka na jin ba dad'i ba, amma duk da haka nasan don kare mutuncina ne."" Daga haka yayi gaba na bi bayansa har inda aka yi taron, ban san mene ne shirinsa ba, amma tunda aka gama" "taron y sallame ni, na bar office din." "Daga nan Gym na wuce nayi motsa jiki na na gayawa Aunty Nuratu Kafaya halin da nake ciki. ""Ki yi" "hakuri na tsawon wata uku idan baki ga canji ba sai a bar aikin a nime wani ko!"" Anan na karasa wuni lokacin tashi na wuce gida, washi gari da wuri na isa office din, sai dai ban samu shiga ba. Saboda wani tsarin da wannan Masifaffen yake ta kawowa, a yanzu ko kazo sai an baka wani kati idan zaka shiga ka" "nuna, ban san an raba ba da yake da wuri na tafi." "Ina wurin a zaune wata bwn karama ta shigo harabar kamfanin, wani kyakkyawan matashi irin" "larabawan nan, amma yadda ya fito da fara'arshi, yana gaida kowa yasa na fahimci irin ruwa biyu nan ne, ina zaune ya zo ya zauna a gefena. ""Hey Yan mata?!"" Ya d'aga min hannu, kallonshi nayi na ce mishi ""barka!"" Mika min hannu yayi yana faWin ""Tarik Mustapha Takai, babana yana cikin masu hannun jarin Meeting din aka yi jiya, ina shigowa na ga kin yi min! Nice to meet you?!"" Ya mika min hannu yana murmushi, kallon hannun nayi kafin na bude baki zan yi magana sai ga motar Masifaffen nan ya shigo, mikewa nayi na tsaya. Shima ya mike yana murmushi. Da dan saurinsa ya isa wurin motar Yana fitowa suka rungume juna, irin sun san juna nan. ""Uncle B!"" Ya kira sunansa a hankali, daidai na isa wurin na amshi jakarshi shi kuma ya amshi nawa, yana faWin. ""Uncle B taya zaka bawa Miss World jaka kawo na rike miki."" Ya kwace min jaka, wani kallon da Masifaffen mutumin nan yake min ya kashe min jiki, haka yasa na ki bashi jakar na amsa har da nashi, koda muka je ya mika min katin na shiga, shima haka. Tunda muka shiga Tarik Mustapha Takai yake wasu abubuwan sai dai ba halin magana, ni kuwa yadda ya like" "min, sai na ga kamar Masifaffen nan yana wani haWe rai." "Bayan na gama mishi duk abinda zan yi, na sako kasa na amshi ruwa ashe Tarik ya biyo ni, ai kuwa" "muka je har wurin abinci da shi, a yadda na tambaye shi shekarunsa ashirin da biyar ne, murmushi nayi nace mishi. ""Kai kani na ne, na baka shekaru huWu don haka ka girmama ni!"" Daga ni har shi haka muka yi ta zolayar juna, madadin mu bi elevator, sai ya ce mu bi Stair, haka muka ta bi har muka isa office din, wato bawan Allah nan da ya ce mishi. ""Shiga cikin office ina zuwa."" Yana shiga ya rufe ni da fada kamar zai dake ni, nayi shiru ban kara cewa uffan ba, don tunda na ce yayi hakuri ya kara hawa yasa na yi kasa" "da kaina. Bayan ya gama ya shiga, tsabar haushi lokacin tashi bai yi ba na tashi abina, na bar office din." "Wasa gaske sai shakuwa ta shiga tsakanina da Tarik, irin mugun shakuwar nan Yaro ne da bai san kome" "ba sai wauta da shirme, idan ya zo office kuwa ba damuwa ba ne ya fita ya kashe min kudi, ina zaune da karfe daya na rana aka kira ni a waya da yake ranar asabar ne, na dauka ina faWin. ""Waye?"" ""Baki yi saving number na ba?"" ""Sorry na manta ne, Tarik ya kake? Lulu yau ina jin wani irin gajiya ne kuma ina kewarki!"" Murmushi nayi na ce mishi."" Ayya ai zuwa gobe jibi mun koma aiki!"" "" Ni dai ki gaya min gidanki na zo!"" "" Kallon Ya Ado da yake aikinsa na ce mishi. ""Ok!"" Na mishi kwatance, na mike da sauri na nufi kitchen na fara hada abincin da Aunty Zakiyah ta gama na diba mishi na hada fruit salad, sannan na duba samosa na fara soya mishi, sannan na hada abinda xan hada can sai ga kiranshi. Da sauri na dauki wayar na saka a kunne. ""Gani nan!"" ""Ok gani nan fitowa da Yara!"" Haka na fita leke can na ganshi da wata mota ni sai yau na fara ganinta. Horn yayi min na sake murmushi, na d'aga mishi hannu. Yana zuwa yayi parking tare da fitowa da wasu jakukunan, murmushi yayi min ya ce min. ""Sorry na tsaya sayan abu ne, ban karaso ba."" Girgiza mishi kai nayi muka shiga har cikin gidan, ya ajiye kayan yana gaida Ya Ado. ""Tarik Mustapha Takai."" Murmushi Ya ado ya mishi ya ce mishi. ""SAN Adamu Usman Jama'are."" Ya mika" mishi hannu. "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 53" "Cike da mamaki nake kallon yadda yake son sabawa da kowa, ba tare da b'ata lokaci ba Ya ado ya mika" "mishi hannu suka zauna ana ta hira, ya kirA Yaran ya mika musu jakunan da ya kawo. "" Bata gaya min da Yara a gidan ba, ita na sayawa chocolate!"" Irin mutane nan ne masu budaddiyar zuciya, duk abinda suka gani suna so basu boyewa, haka suka yi ta hira yana gaya musu alakarshi da CEO, da gaske kawunsa ne, domin kanwar Uwarsa ta haifi Uwar Yaron, su biyu ta haifa kafin suka rabu ta dauki Yaranta, Namiji da Mace, amma tana Germany da zama shima a can yaron yake jin Kawunsa ya dawo Lagos shine ya biyo shi. Mustapha Takai babban dan kasuwa ne a arewacin Najeriya, irin shegen aure-auren mazan Hausawa ya aurota, ta haifa mishi Yara biyu ganin yadda yake rititata kishiyoyinta suka hanata zama da barazanar zasu kashe ta, shine aka raba auren ba wai don tana kinsa ba ne a'a kawai basu da yadda suka iya ne, da bakinsa yake bada labarin. Haka na kawo mishi abinci da ruwa tare da sobo. Yaci sosai har da santi." Ranar dai a gidan ya wuni da dare bayan isha ya tafi. "Ya Ado ya kalle ni a nutse, ganin ina tattara inda suka ci abincin dare, ya ce min. ""Auta Yaron nan yana" "sonki."" Gabana ne ya fadi ya kalle shi, kafin na ce mishi. ""Ya Ado yaro ne fa, kuma na girme shi bar irin wannan zancen dan masu kuWi ne fa."" ""Eh na sani amma ki dakatar da shi, tunda ba sonshi kike ba."" Murmushi nayi na ce mishi. ""Kada ka damu!"" Haka na ji shi, da na shiga na kwanta ya shiga kirana a waya yana min shiririta. Har lokacin barci yayi na kashe wayar na kwanta. Da safe sai goma na tashi nayi wanka tare da sallah walaha, domin da safe nan na ga jinin ya dauke min, yadda na fito na samu abin karyawa na gama na koma dakin na kunna wayata. Kirana yayi muka shiga waya duk da a takure nake." "Amma haka nayi ta kai zuciya nesa. Domin Yaro ne sosai idan yayi wani abu sai dai ka bi shi da fatan shirya. Ranar Monday da muka hadu da shi, ya makale min, haka muka yi ta kaiwa da komowa, Har Kawunsa ya gaji ya ce mishi. ""Aiki ka zo ko bin mace kamar bindi."" Ban san yadda suka kare ba amma bakiWaya ban kara ganinsa ba, ni kuwa na sha masifa tare da min fada na daina biyewa shashancin Tarik na kama kaina kowa yana kallona, haka na cigaba da aikina. A lokacin Kanwar Jasminah wato Mimih ta shiga zuwa office dinmu wurin Tarik din, da aka ware mishi office a hawa na biyu amma haka zai tare a wurina. Yau ina aiki sai gashi nan, kallo daya nayi mishi na cigaba da aikina, yana tsaye jikin table. Ya shagwabe min fuska. ""Don Allah ki min printing din wannan ki tura min ko ki kawo min."" Dama uban Yan masifa baya nan, na ce mishi. ""Don Allah ka tafi zan kawo maka!"" ""Ba inda zan tafi, sai dai ki zo muje yunwa nake ji!"" Kallonshi nake bakina a sake kafin nace mishi. ""Zaka ja min a kore ni kenan?"" ""Bari na kira shi."" Kiran shi yayi mishi magana da harshen Germany, ban san yadda aka yi ba, ya ce min. ""Taso mu tafi na gaya mishi."" ""Kayi hakuri ba zan bika ba."" Na fada na cigaba da aikina, ai kuwa ya ja kujera ya zauna ya zuba tagumi yana kallona, har kawunsa ya shigo tare da yan uwansa, yadda ya hade rai ya watsa min kallon banza, na rasa yadda zan yi d Tarik haka ya dame ni amma shi Masifaffen duniya gani" yake ni nake kiran Tarik. """Zan dakata da Yaron nan, domin ya hana yarinyar nan aikinta."" Ya fada yana cire tie din wuyarshi sai" "ga Tarik Win ya shigo office din, "" Uncle B please ka ce Lulu ta raka ni ina jin yunwa ne!"" Yadda yayi rikon" "sai da yaji kamar ya mutu, domin ya tsani wani da namiji yana like mata kamar wani kaska. ""Ba inda zata bika, kai baka ganta bata cika shiga abinda bai dame ta ba.""" """ Ok tunda kai ka ki bari na kira San na gaya mishi."" Ya fada yana dauko wayarshi ya kira Ya Ado ya" "koro mishi jawabi. Ya Ado zuciyarshi daya ya ce shi kenan zai mata magana. Ai kuwa ya juya yayiwa kawunsa bye bye, ya bar office Win. Shiru CEO yayi bai san lokacin da ya mike ba, a zafaffe ya nufi waje yana fitowa ya samu suna ta musu, cewa yayi. ""Ku zo muje!"" Y fada kai tsaye haka na hada kayana, na saka a locker na bi bayansu, haka muka je wajen cin abinci na Chinese dish, nan muka je ya kai mu har can VIP aka yi oda, aka jera mana, ni dai ban wani saba cin abinci a gaban jama'a ba, haka Tarik ya yi ta zuba min abinci domin ya ado ya gaya mishi ina kula da abinda Zanci, sai yake zaba min abinda zanci da kuma wanda ba zai yiwu na ci ba, abun sai ya bawa CEO mamaki yana kallon yadda yake cire duk wani abin da ba zan ci ba, har ya kira waiter Winsu ya ce ga irin drinks din da zan sha, sai gashi kuwa an kawo ina kallonshi cike da mamaki. ""Ci wannan tsokar kifi ne, zai fi kici irinsu shrimp da danginsu kaza da sauran danginsu ba naki ba ne. Ci iya mune Uncle ya sayi wurin baki daya."" Tashi kuwa Uncle dinsa yayi ya dauki abincin ya kai wani table din ya ajiye min ya kara zuwa ya dauki juice din da ruwan ya ce min. ""Je can ki ci!"" Tashi nayi na je wajen na basu baya, tashi Tarik yayi ya rike hannunsa. ""Kasan bana wasa a kalmaina!"" Yadda yayi magana yasa ya zauna, ya cigaba da latsa wayarshi ya cigaba da cewa. ""Yarinyar nan matar aure ce. A Muslunce kuwa haramun ne bibiyar matar aure. Ina baka shawarar ka koma Berlin ka ji aiki!"" Gyada kai yayi yadda yayi mishi magana a nutse yasa Yaron ya fahimta. Haka muka gama cin abincin, sannan muka bar shagon, kamfani muka wuce. Haka na cigaba da aiki. Tunda muka fito naga jikinsa yayi sanyi. Har muka tashi, na dawo ban ga kiranshi ba na tab'a shi ya ce min jikinshi ne baya jin dad'i, haka muka yi magana sama sama, da dare kuwa aikin gabana na rage, sannan na cigaba da sabgogina. Ni dai ban san me ya faru ba washi gari na iso na sami Dan uwan CEO, yana ganina ya hade rai. ""Wacece ke?"" ""Ni kuma?"" Daka min tsawa, nayi baya domin a gaban jama'a yake min fada da masifar da na ga kamar gadonta suka yi domin kows a cikinsu Masifaffe ne, ""sir mai nayi kuma?"" ""Ki tafi an dakatar dake!"" ""Me nayi to?"" ""Idan baki min shiru ba sai na mare ki!""dariya nayi na ce mishi. ""Maybe baka san wacece ni ba, idan ka mare ni zan rama no matter how, zan mara kuma da kake min ihu so what idan ka ce na bar kamfanin ni ban fito gidan da ake jin yinwa ba, ba ina aikin nan don cika cikina da yake jin yunwa ba ne, ba zai yiwu kowa ya zo ya ce zai taka ni ba. Kudi ko daukaka muna da shi a gidanmu I'm not beggar da zaka na min ihu,kudin kamfaninku ba zai saka ni nayi arziki ko talauci ba, so ba kai ka Wauke ni aiki ba, amma nasan kana cikin waWanda suka dauke ni aiki."" Na juya na cire ID din da yake makale a wuyata, na juya zan fita bayan na ajiye a kan table din Mrs stalle. Idanuna suka fada cikin na shi, dauke kai nayi, a yau na ga wani abu da ban tab'a gani ba, tsoro da tashin hankali. Haka na gyara zaman jakata na wuce zan bar cikin kamfanin. ""Ban karbi ajiye aikin ba! Kuma ki same ni a office ina" "jiranki!""" "Sannan ya wuce ba tare da ya cewa Ubaid uffan ba, yadda ya wuce haka abun ta bashi mamaki ya ce" "mishi. "" N dakatar da ita ka dawo da ita?"" "" Ka rubuto min korafi a takarda sai na san me zan yi."" Daga ya wuce shi, nima da na kame a wurin kamar an dasa ni, haka sai naji kamar ban cancanci zama a cikin kamfanin ba, haka na juya na bi bayanshi yana tsaye a bakin kofar elevator, ina zuwa na amshi jakarshi. Bai ce min kome ba, haka yasa na sunkuyar da kai. Har muka isa office dinmu daga nan ya shiga cikin na kai jakar na fitar da menu, sannan na gama na fito na zo na zauna kenan sai ga Jasminah da Badr" "kallonta nayi na ga kamar na santa.."" Lubnah me ya faru? "" Nan na gaya mata gaskiya abinda ya faru," shiru tayi kafin ta shiga cikin office din Dan uwanta. Ban san me suka yi ba na ga ta fito daga cikin office "din ta tsaya a kaina ta ce min."" Ki yi hakuri kin ji matsalar akwai munafikai ne! "" Tana barin wurina, Badr ta kalle ni. "" Ke mayya ce? "" Ta tambaye ni, kallonta nayi nima na ce Mata. "" Inda kika ci anan naci nawa"" cikin fusata ya d'ago hannu zata mare ni, ai kuwa na rike hannunta, tare da murda shi, domin ba girma ta tayi ba, na murde hannun da karfi sai da yayi ™ara ™arfi, nace mata. ""Kalle ni da kyau ni ba sa'arki ba ce, kika kara zuwa inda nake sai nayi maganinki!"" Na ture hannunta sannan na cigaba da aikina, kiran wayar" yayi na mike na shiga lokacin har ta bar office din. "Ina shiga na tsaya a gabanshi, tare da sunkuyar da kaina, ya zuba min idanu ban san tunanin me yake" yi ba. _Yarinyar da ya sani a shekarun baya irin yaran nan ne masu hankali kuzari da surutu tare da Rawan kai "da fitina! Yarinyar da kowa na cikin JIBWIS ya santa saboda ™o™arinta da kuma rawan kanta! Yarinyar da ta juyawa duniyarsa baya tare da cewa tana da wanda take so yau ita ce a gabanshi a matsayin sakatariyar kai da kai! He can believe ita ce, bai yarda ita din ce ba, sai dai sunanta da ya zame mishi daidai da ayar da ya haddace ya kuma bata matsuguni na musamman a cikin ™wa™walwarshi. Me yake shirin faruwa? Me yake dawo da kome baya? Me ya kawo ta nan? A yau tana gabanshi ne sannan a gobe bai san wani matsayi zai ajiye ta ba, amma ya kasance yana jin motsinta ina Mijinta? Me yasa take tare da bro dinta! Shin ko Mijinta ne baya kasar? Me yasa yake jin wani babban al'amari a haduwarsu, shi dai yasan bai yi kome ba amma me yasa kowa yake jin ba dadi shi ba wani ririta yayi ba bare a ce ya ware ta!_ Saboda wani abu can ba, ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta a karo na biyu, kafin ya ce mata. ""Ki" "duba na tura miki sako bana son kuskure "" ""Ok Sir!""" "Haka na fita na bar shi ba shiga aiki ina printing, hayaniya da ake yi yana kusanto inda muke yasa ni" "d'ago kai, wani farin bafulatani ni ne ya shigo da yayansa. Cikin girmamawa na gaishe shi tare da sauran Yaranshi, dakatar da sauran Yaranshi yayi ya ce min. ""Ina son ganinki."" Tashi nayi na bi bayanshi har stair su kuma suka shiga office Winsa. ""Lubabatu Usman Umar Jama'are ko?"" Da mamaki na kalle shi, murmushi yayi ya ce min. ""Kina da aure ne?"" Da sauri na d'ago kai na kalle shi kafin na ce mishi. ""A'a;"" murmushi yayi sannan ya ce min. ""Oganki ya sani ne?"" Girgiza mishi kai nayi. ""Ina son ki min al™awarin Waya."" ""Tow ina jinka, Allah ya bani ikon Wauka."" Na fada muryana yana rawa. ""Don Allah kada ki tab'a" "gaya masa, ki bari shi ya bincika haka da kanshi kin ji ko....." "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 54" D'ago kai nayi zan tambaye shi me yasa zan yi shiru? Tow meye alakata da shi? Sai nayi shiru kafin na ce "mishi ""tow!"" Murmushi yayi yana faWin. ""Na gode sai abu daya da nake son niman alfarmanki akai"" a raina na ce kuma dai, murmushi yayi ya ce min. ""Don Allah kiyi hakuri da shi."" Gyada kai nayi, bayan ya gama min magana ya wuce office din jikanshi, murmushi yayi ya zauna akan daya daya cikin kujerun office din, sauka nayi can kitchen na amso ruwa da drinks na fito zan wuce na ji wata tana faWin. ""Wasu ina ganin ba iya golden digger ba ne, har da can Winsu na zinari ne."" Ban kula ba sai nayi kamar ban ji ba," haka na wuce na haura abina ban kula tasu ba. "Ina shiga office din na ga ya daura kafa akan center table din da zan daura ruwan, kallonshi nayi na ga" "ya dauke kai, kuma bai dauke kafar ba, a raina nace. *Jarababbe haka dai zaka kare* a fuskata sai na saka a dan gabansu. ""Kece Lubnah kawar Tarik?"" Murmushi nayi na kalli mutumin da yayi magana, duk da baki ne amma na hango yadda suke kama da Tarik. ""Gashi ya ce na baki!"" Ya mika min wata paper Bag, sai da na kalli CEO da yake tari, kamar ya kware dole na dauki goran ruwa na bude mishi, yana sha ya ce min. "" Ki dauki key mota ki ce Ade ya kai ki Chinese dish ku amso musu abinci. "" Nufar wurin nayi na dauka, sakon da ban amsa ba kenan, na bar office din kamar yadda ya ce haka muka amso abincin sai dai abin haushi muna zuwa suna fita, koda muka iso da abinci, wani kallon banza yayi min ya fara faWa a gaban jama'a. "" Wannan rashin kuzarin da kike yi a aiki ta fara isata, akan me baki zasu tafi basu ci abinci" "ba, wannan ai wulakanci ne. Sai ki je ku raba da mutane.""" """Haba Turaki kayi hakuri mana, ai nan da inda ka aiketa tafiyar minti ashirin ne, sannan sai da suka tafi" "ka kira, Yarinyata na var miki sakon abokinki! "" Gyada kai nayi ina godiya, a wani gaggauce suna barin harabar zuwa cikin main building na kamfanin, ina cikin kokarin zama sai gashi. Kallona yayi nima na kalle shi a sace sai na ga ya wuce office dinsa, kiri-kiri ya hana ni sakon, har muka tashi ban san me ya kai ni ga magana ba, ina riga shi fita amma yau na tsaya, yana fitowa na ce mishi. ""Nace ba, sakon nan ya ce ya bari a office dinka?"" Wani irin shiru yayi kafin ya ce min. "" Na zubar a dustbin."" Daga haka yayi tafiyarshi, haushi ya kama ni kamar na koma office dinsa na dauki kayana, ai zai ga rashin mutunci. Haka" na fito na bar office din nima. "A gida sai masifa nake ina faWin, ""Fisabiilillahi an bada sako bawan Allah nan ya kama ya zubar sai" "kace a kanshi aka saka ni dai wallahi ba zan iya yafewa ba."" "" Tow me yasa ba zaki iya gaya mishi a can ba sai a nan!"" "" Ni wallahi kamar dodo yake min ina son na samu dare daya na gurza mishi rashin mutunci."" Dariya Aunty Zakiyah tayi tana faWin. "" Allah yasa ki iya!"" Abin ba dad'i fa, haka suka yi ta manna min" hauka nayi shiru na kyale su. Washi gari "Ina isa na ga Paper Bag a kan table dina, asalima ya riga ni zuwa, dauka nayi na ga flora gown ce mai" "mayafi, sai turare masu kyau da tsada da kuma chocolate kwali biyu mara sugar da fat, abaya guda biyu. Bayan flora gown din, ban tab'a ba har zuwa lokacin break na mike zan sauka kasa naci abinci sai ga Mrs stalle ta kawo min jakan abinci, ta min tana min wani irin kallon kurulla, ban kula ta ba na amsa ina zauna a kasa naci. Jakar nan dai anan, ina gama cin abincin na tafi nayi alola na zo na gabatar da sallah, ina idar na ji motsinsa, mikewa nayi naga yana kallon jakar yadda ya kalla nima haka na kalla na cigaba da abinda nake, wucewa yayi abinsa, bayan tafiyarshi sai ga Yan matan family dinsu sun zo tare da Mrs stalle da wasu matan office din, suka zo. Daukar jakar daya da na ji ance mata Batul tayi tare da juye shi a kasa, ashe har da wani box na sakar karamin box kamar Pandora, suka yi ta d'aga kayan ita ogarsu ta" "ce musu. ""Ku fito min da shegiya na gaji da ganinta tare da shi."" Suna dayawa amma kuma dole na koyo" "tsayawa kaina, finciko ware din laptop dina nayi dama da kauri. Suna zagayowa na rufe su da bulala" "karfin hali nake, ganin ina shud'a musu yasa suka fara baya har nayi nasarar kure sannan na juya da gudu na nufi elevator, na danna jin muryansu yasa ni juyawa da baya, daidai kofar ta buWe. Muka yi wani irin karo da shi, na fada mishi bakiWaya. Yadda na rikice ban san tare yake da wasu ba, ni dai burina na ceci kaina. Hannunsa nayi a bayana, daidai gadon bayana, dukkan hannu bibbiyu ya rufe ni da shi, kaina a kife a kirjinsa, da xan kwace amma jin kamshin turarensa yasa na nutsu, na kifa kaina a kirjinsa."" Ya isa haka!"" Ya fada tare da janye ni a jikinsa, ya zuba musu idanu, yana kallon abinda suka yi da kayan da ya kashe kudi akansu. Murmushi yayi ya kalli Ubaid ya ce mishi. ""Ban san sunansu dukkan ba, zaka iya koransu a aiki su kuma waWannan jin da su daya bayan Waya."" Sannan ya rako ni har wurin aikina, sai da ya ga na zauna ya tsuguna da kanshi ya kwashe kayan da aka zubar ya zuba a jakan, ya dauki sakar ya zuba mishi idanun. Kafin ya mai da cikin boxs din. ""Turaki!"" Kallon wnada ya kira shi yayi. ""Ka yi hakuri!"" ""Wallahi sai sun bar kamfanin nan ka ji na rantse!"" Kasa magana nayi na kalle shi, ""sir su bar aikin saboda ni?"" Na fada bakina yana rawa, a fusace ya juya tare da cewa. ""Kema na dakatar da ke. Tunda dambe kika zo yi a kamfanin."" Kafin ya rufe baki na hada kayana, na bar office. A ranshi kuwa haka yake son ganin mace, ba kamar sauran kamar mayyu sai hakuri suke bashi ba. Ina barin wurin shima ya wuce office Winsa, Ni kan ba zan iya wannan halinsa ba, misalin uku da rabi na isa gida na huta ban gaya musu" me ya faru ba. Ina samun kaina na kashe wayata su je can da kamfaninsu me shegen matsalar tsiya. Daga nan na rufe babinsa in sha Allah ranar Monday zan rubuta takardan barin aiki. ** "Yana tashi don masifa bai wuce gida ba, ya nufi gidan Hajiya Samirah kumo yayiwa yarta duka, sannan ya" "dawo ya samu Badr itama yayi mata dukar har da ji mata ciwo a hannu, Mimi ma bai kyaleta ba, domin kamar wanda ya sha kwaya haka yake jinsa. Duk yadda Alhaji ELYakub ya so boye b'acin ransa sai da ya yi magana tare da nuna mishi kuskuren da yake aikatawa ai ba a haka, dama already Ubaid ya jima da nuna adawarshi a fili, Uncle Auta ne ya goyi bayansa har ya ce bai ga laifin abinda yayi ba ai ya musu warning me ya kai su wutinsa? Jin haka yasa shi shima yayi zuciya ya bar gidan, kai hatta kamfanin fushi" yayi ya daina zuwa aikin. --- "Yau kwana uku kenan da aka dakatar da ni, na rasa yadda zan gayawa Ya Ado, ina Gym na zurfaffa" "tunanina sai jin wayata tayi ™ara, dauka nayi na ga alart har na dubu dari uku da hamsin an saka salary," "daga KPAN, mamaki nayi albashina na farko kiran Mama nayi na gaya mata ta ce na kira Ya ado na gaya mishi, nace idan na koma gida zan gaya mishi, haka kuwa aka yi ina komawa gida na nunawa Ya Ado shi" "kuma ya karbi kudin ya turawa Mama dukka, ya tura min dubu hamsin ya ce min. ""Wannan ni na baki," "wancan kuma a bar mata tayi yadda take so da shi."" Murmushi nayi ina faWin. ""Allah ya kara budi.""" "Ranar wuni nayi cikin farin ciki, washi gari da safe ina motsa jiki a parlourn aka buga gidan da kaina na" "fita na duba, Jasminah ce. ""Laa aunty kece!"" ""Eh gani nan sauri nake, don Allah ki taimaka mana Oganki yau kwanansa kusan hudu baya nan baya zuwa office ko zaki tab'a mana shi a waya!"" Sosa kai nayi ina yake nace mata. ""Aunty bani da number shi?"" Zare idanu tayi nima abin sai nayi ya min wani iri, shiga motarta tayi ta rubuta min number ta bani tana faWin. ""Don Allah ki taimaka mana!"" ""In sha Allah!"" Sannan ta juya abinta, ni kuma na shiga cikin gidan ina tunanin yadda xan kira shi. Tow me ya faru da ya bar gida? Mutum sai kace mai aljanu. Parlourn na shiga na zauna ina tunanin, kafin na haura sama." "Wayata na dauka nayi shiru ina ta tunanin yadda xan kira shi, a hankali na saka number nayi shahadar kuda na kira Number, har ya gama ya tsinke bai dauka ba, haka na kira bai dauka ba, sai da nayi kira na uku sai gashi ya Wauka. Muryanshi very calm kamar bai san me yake faruwa ba. Na ce mishi. ""Dama na ga sakon kudi ne jiya!"" Sai nayi shiru can na cigaba da cewa. ""Dama ina son nayi submit takardan barin aikina ne."" Na kashe wayar, ina kashewa kuwa ya biyo kiran. ""Me aka miki zaki bar aikin?"" Kashe wayar nayi bakiWaya, na sauke ajiyar zuciya ina kallon wayar da nayi switch up dinsa, ina zaune a wurin Adil ya shigo da gudu yana haki. ""Aunty Lulu ki zo kin yi bako!""zare idanun nayi na ce mishi. ""Baba gaya min waye?"" ""Wannan wanda Abba ya ce oganki ne!"" ""Shi kenan!"" Na fada a raina, kafin na saka jalbab na sauko kasa, ina jin wani abu yana yawo a kaina. Wucewa kitchen nayi na dauko kunun aya da sauran breakfast din da aka yi na dumama masa ce fa sauce din kodar saniya, na kawo mishi a hankali na jera mishi. Sannan na ce mishi ""ka kaci!"" Ba musu ya saka sannu ya fara cin masar da yake miyar da dan yaji tari ya fara na bude mishi kunun aya na zuba mishi ya sha, sannan ya kalle ni, kafin ya ajiye ya cigaba da cin masar, har zuwa lokacin bai ce min uffan ba, nima kuma ban ce mishi ba kaina a sunkuye, nayi mamakin da yaci abincin sosai, ya ce min ya koshi, na tattara kayan na kai kitchen, na dawo na zauna a can gefe. Shiru muka yi kafin ya ce min. ""Gobe ki dawo aiki!"" ""Tow Allah ya kai mu!"" ""Amin Ya Allah!"" Daga haka ya mike zai fita ya ce min. ""Yaranki nawa? Mijinki yana ina?"" Bai tsaya jiran amsata ba yayi" "gaba abinsa, wannan dan renin hankalin, shi kuma haka yake rayuwa kamar me aljanu." "Bayan tafiyarshi Ya Ado ya fara zolayata, ""wato Lubna baki da mutunci, don kina son ganinsa shine" "kika kira shi."" ""Ni wallahi ba kiran shi nayi ba!"" Na fada ina tura baki, dariya yayi suka yi ta tsokanata." Washi gari. "Na same shi a office din ne. Ga sabbin ma'aikata, da gaske koran wadancan yayi. Gaisawa muka yi da" "wata ina ga irin kabilun arewan ko yar Kaduna ko yar Jos, sai dai ban gama tantance ta ba ta ce min. ""Sunana Sarah daga Gombe ™aramar hukumar kaltungo."" Murmushi nayi nace mata. ""Lubabatu daga Bauchi, karamar hukumar Jama'are."" ""Allah sarki akwai yar uwata Ayrah tana sama wurin CEO!"" Gyada kai nayi nace mata. ""Da kyau bari na isa office din!"" Na wuce sama, kofar dama a rufe take, sai da na" "ajiye kaina na kunna table tap, na shiga office. Matar da na hango tafi Sarah a shekaru, cikin girmamawa" na gaishe ta sama sama ta amsa sannan na gaishe ya amsa yana aiki na fara zayyano mishi abinda yake "da su a a yau, ban gama ba sai ga Tajudeen........" "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 55" "Murmushi nayi na juya ina kallonshi, a hankali na ce mishi. ""Nayi kewarka!"" Murmushi ya sakar min ya" "wuce gaban Masifatu ya ajiye document Win da ya kawo, sai lokacin na mai da hankali kanshi ashe ya shaka, wani irin kallon rashin mutunci yake min, yayi shiru rubutu yake a laptop ya rufe ta da karfi tare da mikewa ya fita ya bar ni nan tsaye, anya mutumin nan bai da aljanu? Fitowa nayi na same shi yana magana da Taj, wucewa nayi dan zauna ya ce min. ""Kin gama report din ne?"" Kallonshi nayi cikin mamaki yanzu fa ya fito a office din, ban gama ba sannan ya zo yana tambayar na gama nima share shi nayi kamar ban ji ba, mamaki ya kama shi. Na kuwa hade rai domin ga irin kallon da matar take min na kusa da shi. ""Ina jiranki a mota!"" Ya saka kai ya fita sai da na gama abinda zan na taso na nufi kasa, don ma na bashi haushi stair zan bi ba zan bi elevator ba, kuma a hankali nake sauka ya jima bai kore ni ba. Sai da na shafe minti goma kafin na iso, na hango Taj yana ta leke ta ina xan fito. ""Gani ta nan!"" Na fada ina nufar hanyar waje, ina zuwa na same shi ya cika kamar balloon, sai kallon agogon hannunsa yake, hango matar nan da nayi sai na koma gaba na zauna kuma ai dama gaba nake zama, muka dauki hanyar inda zamu. ""Sir maganar zuwa Japan din yana nan ne?"" Shiru yayi yana kallon table tap din da Taj ya mika mishi. ""Kamfanin Rivers sun tara kayan sosai, dole sai an je da su Japan."" Shiru yayi sannan ya ce mishi. ""Na Kano ma haka, Abuja babu kayan gaskiya."" ""Ka shirya tafiyar har da sakatariya."" Jin an ambace ni yasa na juya na kalli Taj,"" tafiya ina? Har da ni kuma?"" "" Eh ai aikinki har da tafiye-tafiye!"" Yana sane ya fadi haka ya ji ko ya zata fuskanci Mijinta. Hadiye yawu yayi yana kin zuciyarshi kamar aka lugude a kai, wani irin yanayi yake ji a kanshi, yana tsoron kada ta ce tana da miji. ""Amma gaskiya ba zai yiwu ba, domin ko ka tambayi iznin zuwa ba zaa a bar ni ba, ka duba ni mace ce kuma Bahaushiya idan nace zan yi tafiya wata ™asa da wani namijin ai abin ba zai making sense ba, ina ga a cire sunana a bar ni" "anan, abinda ya shafi gida Nigeria. """ """Idan don Mijinki ne, ki bada passport Winsa sai a tafi da shi, but i need you! "" Daga haka ya fita a motar" "domin har mun iso bankin UBA, gaba yayi na fito airah ta ja min tsaki, kallona Taj yayi yana faWin. ""Kina sa'ar Oga, tunda har da mijinki zaku tafi."" ""Ni fa ba zan bishi ba."" Haka na cigaba da tafiya, ya juya yana kallon yadda nake bawa Taj amsa, tsaki yayi yarinya karamar da ya sani a wancan shekarun bata da wannan kula kowa, amma wannan da aurenta ma, sakewa take da kowa shi yaushe zai zama dan iska irin Mijinta, idan da shi ne Mijinta, zai ga yadda zata kula kowa domin a banza zai ta sare kan mutane ne, tsaki yayi ya cigaba da tafiya. Har inda aka yi zaman muka isa sannan muka fita inda aka ajiye kayan, na shiga ina rubuta abubuwan da Taj yake gaya min, har muka gama na juya kenan kawai muka ci karo da shi, kamar xan fadi ya riko hannuna, ya tsayar da ni. Ya harare ni cikin masifa ya ce min. ""Idan Mijinki baya kishinki, ke ba zaki iya kishin kanki ba ne? Kin zauna sai wangale hakora kike da wani? Ki sani ba zaki janyo min masifa a kamfanina ba, idan aurenki aurenki idan kuma kule-kule ne sai ki bar min aikin na gaya miki, kuma xan gayawa SAN yasan abinda kike aikatawa."" Irin kallon da nake mishi na tausayi ne, domin bakiWaya masifarshi ta rufe mishi idanun kawai fada yake kamar zai dake ni, wani abu da yake bani mamaki shi fa idan yana masifar ma baka tab'a jin tashin muryan sai dai ayi ta maganar cikin wuya da baki, irin kada a ji yana fada, tattara kayan nayi na rab'a gefenshi na wuce, kafin na isa wurin motar" "na shiga Taj na min magana na ki kula shi, shima da yazo ya zauna a motar muka bar bankin muna hanya" "amma naki kula Taj, ganin haka yasa shi cewa Taj. ""Ka kai mu Chinese dish."" ""Ok sir!"" Bayan mun dauki" "hanya naji muryan Airah. ""Turaki ni ban ga wani aikin da sakatariyarka take ba, maganar tafiya kuwa sai na yi replace dinta."" Duk muna jinta, ni sai na fi kowa murna cikin farin ciki na ce mata.. ""Alhamdulillahi Ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, kai Masha Allah."" Ganin yadda na nuna farin cikina tare da musu addu'a, ya cika da mamaki yana ta taSa table tap amma zuciyarshi kamar ta dirko daga kirjinsa, har sai da ya kai hannu ya danne kirjin, ko da muka iso shagon ita da Taj ya tura shagon. Tunda na ji ya ce ita da ita da Taj su je su fita su amso na fahimci zai hau masifa ne, dauko airpies na saka s kunnena na kunna wayata. ""Cire!"" Ya fada a fusace, na cire daga kunnen na juya ina kallon titi raina yana b'aci, ""tafiya da ke xan yi idan kin so ki ajiye aiki yau!"" Daga haka ya cigaba da aikinsa. Haka suka dawo muka bar shagon, koda muka iso office mika min abincin Taj yayi na ce mishi. ""Ina azumi!"" ""Yau wacce rana kenan?"" Banza nayi mishi ban kara kula shi ba. Har aka tashi na wuce gida, ina isowa gida abin mamaki na same shi har ya rigani zuwa gidan, na samu suna magana da Ya Ado. Wuce su nayi na tafi cikin gidan. Ban san tafiyarshi ba, sai ganin Ya Ado nayi ya zauna yana kallona. ""Kuna da tafiya ne a kamfaninku?"" ""Eh amma ni nace ba zan samu zuwa ba, saboda."" ""Zaki je, abu daya nake so dake ki kama kanki, sannan ki rike mutuncinki. Kada ki manta Allah yana ganinki, kada ganin bamu nan yasa ki fada wani irin yanayi, ki sani Allah yana kallonki."" Idanuna ne suka cika da kwalla, haka yayi ta min nasiha duk da ni na nuna bana son zuwa amma ya ado ya ce na je, haka na cigaba da jin wannan abin haushin, ranar juma'a ba wani zama muka yi ba, aka tashi yau kan shi da kasan yazo kamfanin don haka da aka tashi, na fito zan je Garej ya tsaya tare da cewa. ""Shigo!"" Kamar ba zan shiga ba, sai kuma na shiga na ja belt na daura, muka cigaba da tafiya. Wannan dan renin hankalin ba abinda ya ce min, har muka isa gida na cire belt din xan fita ya ce min. ""Are you angry?"" Share nayi na bar shi a wajen ai tun da naje ya ga yadda fuskata take masifar haWe, haka yasa shi fahimtar raina a b'ace yake, wai kuma don renin hankali yana tambayata wai ina jin" haushi ne? "Ranar asabar, ina tsaka da barci domin duk jikina a gajiye nake tun daren jiya Aunty Zakiyah ta ce" "zata shiga asibiti. Wurin karfe goma, mai aikin ta ce nazo ina da baki, saukowa nayi shine da su Ilham. Cike da mamaki yaran suka taso da gudu na sauko nima na rungume su. ""Aunty Lulu!"" ""Na'am yau kunne!"" Zama nayi nace mishi. ""Ina kwana?"" Hankalinsa yana kan wayarshi sai latsawa yake, kamar bai ji ni ba, sai da na sake gaishe shi ya amsa, kitchen na nufa na shiga aikin gaggawa domin Yaran gidanmu sun tafi Islamiyya. Babu wani abin karyawa don dumamen tuwo suka ci, doya na fere na turara musu, tare da miyar sauce din kwai, sai kunun tsamiya da na dama musu na shiga fito da shi, na hada bakiWaya a gabansu, yaran na zuba musu. Sannan na koma na matse fruit nayi musu juice da shi na fito na zuba musu. Abin ya bani mamaki yadda yake cikin abincin kamar bashi ba. Komawa sama nayi, wanka da brush nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa, na karya dan daurin dan kwali, Ban san me ya ke fisgana ba, amma na samu kaina da shafe jikina da humra mai kamshi, sannan ka fito na samu ya gama yana fama da wayarshi ne, lokacin da na iso parlourn kura min idanu yayi, sai da na kama shi yana kallona ya wayance kamar bai yi kome ba, na wuce kitchen na zauna a can na karya sannan na fito yaran suka gama cin nasu na tattara na kai kitchen. Sai Santi suke. ""Aunty Lulu zaki raka mu, muje birthday party na yar class dinmu, kuma ance anan son two parent su zo ne, kin san Mom ba zata amince ba," "shine muka zo da Uncle ko zaki bi mu. Please!"" Yadda suka yi maganar kamar nayi kuka, domin na" "fahimci ba wai zuwan kansu ba ne ba mamaki shi ya shirya musu haka. ""Bari ka kira Mijina na gaya" "mishi!"" Na tsinci kaina da fadar haka, bai d'ago ya kalle ni ba har na haura sama na gama abinda zan yi ja fito sanye da wata laffaya akan kayan jikina. Na fito a hankali nake takawa, yadda na iso yaran suka yi ta" "murna, haka muka fita satar kallona yake sau biyu ina kama shi, amma sai wani haWe rai yake.." "A wurin Birthday din hidima sosai aka yi, mu kanmu iyayen yaran sai da suka saka mana wani gasa." "Kusan a tare muka ci gasar, karon farko da naji wata irin soyayyar Yara ya kama ni, domin saboda Yaran nan sai da nayi kawaye Iyayen Yara, dayawa a wurin dauka suka yi ni Matarshi, ce kasancewar an san shi sai ya zamana idanun mutane akanmu, a kyautar da ya bada har da dollar guda ashirin, sai gift da yaran suka bada. A waje haka mutumin nan yana da mutunci, rashin mutuncinsa a office suke. Haka muka gama bikin muka dawo suka ajiye ni a gida, fitowa yayi daga motar yana dan matsa hannunsa, ni duk a tunani na crwa zai yi na gode. ""Idan kika shiga ki yi wanka domin turarenki."" Kambu, banza nayi da shi na wuce humran nawa ne zan yi wanka akan shi wanda idan ba kazo kusa da Ni Rufe bakina nayi wata" "irin kunya ta kama ni, kenan turaren ya. Da gudu na shige parlourn tare da haurawa sama, yayi gaskiya Innalillahi wainnalihir rajoun, wanka nayi tare da tsarkake jikina. Duk kunya ya kama ni, haka nayi ta juyi har lokacin cin abinci yayi, ina cin abincin kawai sai naji gabana yana faduwa, sakamakon tuno maganarshi, gaskiya tafiya Japan ba zai yiwu ba, don ma azumi ya kusa. Haka nayi ta cakalar abincin har Ya ado yace min.."" idan ba zaki ci ba ai ba a miki dole ba! "" Mikewa nayi na dawo parlourn da Yorghurt ina sha a hankali, ni fa yanzu na lura wannan aikin ya kara ramar da ni, domin yan dukiyar fulanina basu" zama a cikin yar bra da nake sakawa. "Haka nayi ta juya maganar, nan har barci ya dauke ni," "Washi gari lahadi, sakon da na gani ya turo min ya ce min. *Daren yau zamu tafi please kada ki hada" "kayanki d wannan perfume din yana da karfi bana sonshi* kambu mutumin nan ya rena min hankali, buga kofar da Ya ado yayi na ce mishi. ""Na'am!"" ""Dazu oganki yake gaya min tafiyarku karfe shida na yamma!"" ""Tow!"" Haka na shiga hada kayana bakiWaya dogayen ruguna ne, humran nan barinsa nayi na dauki body spray sai roll on na hammata, saukowa kasa nayi na samu Aunty Zakiyah na ce mata. ""Wai Aunty Zakiyah humran nan meye amfaninsa ne?"" Dariya tayi tana faWin. ""Kin saka ne?"" ""Eh kai yana da dad'i."" ""Sannu ko, tow na masu miji ne ranar ina ta son hanaki Wauka, amma saboda Maman Amal ta cinye ki da baki kika Wauka."" Kasa kasa ta ce min. ""Na masu maza ne. Idan kika saka namiji haukacewa zai yi akanki "" Da gudu na haura sama ban yarda na ji karshen bayaninta ba, na je na dauka na boye idan" aka samu Mama ko Aunty Hindatu suka zo zan basu su su raba fa Aunty Innah. Allah sarki shi yasa duk ya shiga damuwa. "Har dare ina kwance kawai nazarin yadda zan ganshi ne, karfe biyar da rabi Ya ado ya saka muka fito," na saka kayana a cikin motar dukkan yan gidan suka rako ni. "Yana cikin mota shi da Ubaid da Uncle Auta, kallonshi Uncle Auta yayi ya ce mishi. ""Bilal zaka tafi da Yar" "mutane kuma kace matar aure ce, please and please ka taya ta kare kimar aurenta, don Allah kada ka sake wani abu ya tab'a kimar aurenta Please.""" """Wai wace ce ita da ya damu kansa da ita ne?............" "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 56" "Shiru Uncle Auta yayi, suka fito domin raka Turaki har cikin airport Win, ganin yadda take rungume" "Yayanta yasa shi jin wani irin abu. Šauke kai yayi har suka gama alamar rarrashinta yake ita kuwa sai wani kukan shagwaba take, haushi ya kama shi kamar ya ce ya fasa kowa ya kama gabansa. Anan dai suka daure har suka gaisa da Uncle Auta da Ya Ado, Ubaid ma sama sama suka gaisa da juna. Wurin" bakwai da wani abu jirginsu ya tashi. "Kallon Uncle Auta Ubaid yayi yana faWin. ""Kana ta ja min tai wacece ita?"" ""Lubnarsa yarinyar da ya so ya" "Bauchi. A yanzu Allah ya haWa su a wuri guda amma ita kamar bata san shi ne wanda ya sota a Bauchi ba."" ""A'a renin hankali dai ni dama tun ganinta na ji bana sonta, haushi take bani kawai bata dace da shi ba shine yake haukarshi akanta, gaskiya ba zan tab'a barin ta kara saka mu, rasa shi ba domin babu" "alkhairi a tarayyarsu.""" """Ba ruwanka da ita idan har kaso son alakarku tayi tsawo kada ka shiga tsakaninsa da ita ka ga yadda" "yake jin kishin nan tas zai iya yanke hukunci rabuwa da kai, a yanzu haka bai san bata da aure ba. baffa ya nuna mishi tana da aure kada ya ce zai yi wani abu na daban. Don Allah kada ka yi wani abu da zai lalata alakarku!"" Jin shi Ubaid yake amma yasan tabbas tazo sake yaudarar dan uwansa ne kafin tayi" "haka tabbas ya shiga tsakaninsu har abada.""" "Zance wannan ce karo na farko da nayo tafiya da wani ba muharramina ba, duk sai na takura. Wani" "abinda na fahimta inda muka zauna VIP ne. Tunda muka shiga wurina daban wurinsa daban, amma sau biyu ina kama shi dumu dumu yana kallona, na dauke kai ban kara kallon inda yake ba, har muka isa dubai da rana. Mun bar can dare ya shiga mun shiga dubai da rana, anan muka yi sallah asuba da na duhur, kafin muka dawo airport Win ya zo min da abinci, na amsa ina kallon kasa. Har muka shiga jirgi" ban ci abincin ba. "Haka yasa bakiWaya yayi ta duba ni ko naci abincin, ni kuwa naki cin abincin. Haka muka isa kasar" "Japan da dare anan mukumukun sanyi, abin bai kara bani mamaki ba sai da na ga garin na kara godewa Allah da ya hankad'o ni nazo na ga sabon duniya, mun sauka a Tokyo anan aka yi taron na tsawon kwanaki uku, daga ni har shi bamu haduwa da juna sai zamu tafi taron, idan muka dawo kowa ya shige dakinsa, zai matu™ar wahala ka ga mutum ya leko, a cikin sati daya zuwa kwana goma sau biyu muka zauna a wuri guda. Sai ana jibi zamu dawo ya buga min kofa, ba bude kallona yayi daga sama zuwa kasa ya ce min. ""Ins jiranki!"" Komawa cikin nayi na gyara jikina, sannan na fito sanye da doguwar riga sai katon coat na sanyi da na daura, sannan muka fita yawo. A ranar yawo kan munyi shi, sannan ya ja ni zuwa wurin part na abokansa, a lokacin da suka hadu aka yi ta hira, amma hankalinsa rabi yana kaina, ban san me aka mika min a kwalba ba, dawowa kusa da ni yayi a hankali ya sa hannu a ture ruwan, kallonshi nayi domin ruwan har wani hayaki yake, kallonshi abokan suka yi ya kalli wata daga cikin abokansa mata ya ce mata. ""Tinah kaita ta wanke jikinta."" Muna tashi suka fara mishi magana. ""Me yasa zaka zubar da liquor din da muka ba ta?"" Murmushi yayi ya mike tare da Waukar jakarta. ""Ita muslmace kamar ni, kamar yadda Allah ya haramta haka nima hakkina ne na kare mutuncinta, sannan kuma ai baku gaya min zaku bata wani abu ta sha ba, da ta sha kuwa sai ka hadiye kwalbar!"" Iya nan naji ya mika min jakar muka bar wurin. A hankali muke tafiya daga ni har shi jikinmu a mace yake, na rasa me zance me shi, shima kuma bai min magana ba har muka isa masaukinmu. Sai da na bude kofar na shiga ya wuce abinsa. Washi gari da sassafe ya tashe ni muka je sayayya. Muna gamawa aka wuce da shi airport kafin gobe sun gama kome, da la'asar na dan fito daga hotel din ina tsaye a waje na hango Airah da shi suna magana, yaushe ta zo? Abin ya bani mamaki ganin na hango su yasa ta karaso. Cikin yanga da jan hankali ta ce min. ""Duk iya kwanakin da kika yi da shi bai isa ba sai kin biyo shi?"" Ban fahimci me take nufi ba, don haka kallo daya na mata na dauke kai. Na cigaba da kallon garin sai da ta hauro inda nake zata tab'a ni na rike hannunta. ""Kul kada na ji kada na gani, ni ba sa'ar yinli ba ne don haka ba zaki saka hannunki a jikina ba."" Na ture hannunta, ""karuwa me bin namijin da bai damu da ita ba."" Wannan maganar ya min ciwo, murmushi nayi nace mata. ""Ke ya kamata na kira haka tunda zuwan da kika ce kina so ya nuna baya yin zuwanki sai ni. Yana da kyau na kira ki da Uwar karuwai ni wancan abin ko a kafa aka daura kin shi bana yinsa."" Na wuce abina, ita ta damu da namiji har take faWa akanshi, amma ni da na sha wuta a hannun da namiji har wani abin burgewa ce da su da zan damu kaina. Mtseew, na ja tsaki. Ashe ina barin wurin kai ™arata tayi wurinsa, ban san ya suka kare ba. Da asuba muka hadu da ita a nan airport. Ni ban shiga harkanta ba, kuma ban wani damu da ita ba. Ban san me ya gaya mata ba" "amma tabbas naga ta shiga hankalinta, amma tana harara ta idan muka hada ido ba mistake." "Mun iso Nigeria kai tsaye, da misalin karfe sha biyu saura na dare, kallona yayi ya ce min. ""Ko zaki" "kwana a gidan Uncle Auta idan gari."" Ban barshi ya kai aya ba nace mishi. ""A'a bamu yi haka da kai ba, kawai kai ni gida!"" Na fada ina kallon gefe tsaki tayi haka muka kira Uncle Auta ya zo, ya dauke ni, ni da ita muna baya. Shi da Uncle Auta suna gaba, har kofar gidan Ya ado aka ajiye ni sai da ya buga gidan Ya gaisa da Ya Ado, sannan ya ce mishi. ""Ga amanar da ka bani!"" Murmushi yayi ya ce mishi. ""Na gode sosai da wannan abin da ka yi na yarda kai me amana ne!"" Ya ji dadi, ni kan dakin kasa na wuce ka kwanta, tunda nayi sallah asuba na koma na kwanta sai sha biyu na tashi da mugun mura na kwaso sanyin can, ai" "muryata ta dishe, mura sosai da zazzaSi na kwanta." "Ban sani ba ko Ya Ado ne ya gaya mishi, bayan isha sai gashi da kayan dubayya, ya zo duba ni. Kaya" "niki-niki sai da abin ya dasawa Aunty Zakiyah ayar tambaya. Ganin haka yasa bayan tafiyar naki magana duk yadda taso nayi magana naki, sai ta zuba min idanu." *** Bauchi "Jikin Abba da sauki sai dai ya daina zuwa kasuwa, koda yake kasuwar ma yanzu suna ce domin shagonsa" "ya mutu murus na atamfofi, sauran da yake ba a hannun Hafiz suke ba yasa kome yake tafiya normal, wani abu da Abba yayi shine raba hannunsa da yayi, shine kawai Allah bai bada ikon karya shi ba, amma shagon sai da aka rufe domin babu kome a cikin shagon kamar wacce aka yi mata yasa." Ya nima da lafiyarsa da karfinsa amma yau an wayi gari kome ya kare shi. A haka shima Baba Malam "ya kwanta rashin lafiya, sosai fa ya kwanta jinya. Duk da wannan yanayin da yake ciki sai da ya kai ya kawo yana fama da jinya amma yana sakawa a kira Abba ya tuna mishi lallai ko bayan ransa ne a tabbatar na koma gidan Hafiz, shi Abba ba lafiyar ce da shi ba, amma a haka ya tafi jama'are ya samu tashin hankalin da ya wuce tunanina domin Hafiz ya zo ya gaya musu karya da gaskiya, lokacin da suka dawo daga lagos, bai magana ba kuma Ya ado bai fadawa iyaye mazan abinda ya faru ba, Yadiko ce ta sani, ai kuwa rako su Baba Malam gida domin inda Baban Jama'are zai makale an rufe gidan da yake shirin rikewa Ya Umar ya ce an saka a kasuwa saboda zasu saka kaya a shago, wannan ya kara bawa Hafiz daman zuduma sharri son ransa. Wannan abin yayi bala'in d'agawa Abba hankali wanda ya haifar da saukar jininsa har ya nemi faduwa, don ma Allah ya so da Sani suka tafi.. haka suka yi ta kula da shi, wato cewa Hafiz yayi shi duk abinda zasu mishi zai karba amma su sani ba zai tab'a gudun Lubnah da take karuwanci a Lagos ba, haka yasa har Rufa'i sai da ya bada shaidar Lubnah karuwanci take har da hotonta suka nuna wanda take motsa jiki a cikin gidan. Wannan abin yayiwa kowa zafi Mama da bata da hakuri har Jama'are ta isa aka yi uwa ubanka, wannan abin ya tsaya mata a rai, tayi kuka har ta godewa Allah, Hafiz ya ki rabuwa da Lubnah duk inda ya zauna sai ya zage ya ce shi zai rufa mata asiri, koda ciwo zata kwaso zai zauna da ita a haka, wannan abin ya saka aka manta da itin cutar da yayiwa Lubnah aka" "fara ganin ™o™arinsa da yadda ya ganta kuma zai zauna da ita, sharri kuwa ai dan aike ne." "Haka Abba ya dawo Bauchi da ciwo hade da bakin ciki, Yadiko ta ce mishi. ""Alhaji ai baka ci ta kuka ba," "Maman Lubnah ce da kuka domin ita aka cuta kuma Allah sai ya saka mata, wannan zalinci har ina kuma kaima Hafiz bai barka ba.""" "Wannan abin ya taru ya mishi yawa, ga bakin ciki ga takaicin Hafiz." *** Lagos "Kwana uku a tsakanin wanda yayi daidai da Monday na koma aiki, yadda naga ana kallona yasa na dan" "tsargu. Ashe gulma aka yi me zafi. Wanda Sarah ce ta iya bani labarin wai ai Airah ta ce mata a daki daya muka sauka sannan mun ta yawon dare da sheke ayarmu. Kallonta nayi tare da dariya na ce mata. ""Duk abinda aka fada a kaina da wanda na sani da wanda ban sani ba na yafe, idan kin gadama ki yarda idan" "baki gadama ba ki watsar. Ni ban zo kamfanin nan don shirme ba, su da suka ga zasu iya Bismillah.""" "Haka lamarin ya cigaba da tafiya, ba dad'i ga gidan Jaridu da suka sako shi a gaba da kafe hotonshi a" "magazine ana cewa yana sheke ayarsa da sakatariyarsa, kanwar wani babban lauya a nan lagos, har kamfanin ake zuwa leken asiri wannan yasa na ajiye aikin na tafi hutu don ma Allah yasa saura sati biyu a fara azumi. Kanshi ya dauki wuta haka yayi ta min masifa akan me zan dauki hutu bayan ba ni daya ba ce a cikin wannan tashin hankalin har dashi, kashe wayar nayi na tattara na bar lagos da goyan bayan Ya Ado na tafi rives wurin Aunty Munah hutu, a can na yi sati biyu, Ya ado da fari ya zata ko ina sonshi ne nake wannan abin ni kuwa ba wannan tunanin kawai na gaji da matsalar kamfaninsa ne, wata na biyu kenan a kamfanin amma kamar don ni aka bude kamfanin satin biyu cib Ya Ado yazo da kanshi wai na koma gida Mama tazo. Haka muka iso gidan cike da farin ciki, na ga Mama na ji dadi sosai. Kusan kwana muka yi a tare muna hira, washi muna karyawa ya jifo min tambayar da tasa na kusan kwarewa. ""Ance kina aiki da wani namiji wanda ake ganinku tare waye shi?"" ""Mama oga na ne na wurin aiki."" ""Sonki yake yi ne?"" ""Amma aiki ya haWa mu fa, babu wani maganar so ni yanzu babu aure a gabana."" Shiru tayi kafin" "ta ce min. ""Babu aure a gabanki taya aka yi har wannan hotunan suka Bayyana a idanun duniya.""" "Ta watsa min hoton, wani irin razana nayi tare da rufe bakina. Zan yi magana ta dakatar da ni. ""Bana son" "jin kome a bakinki. Ki ajiye aikin ki hada kayanki mu koma Bauchi..""" ** """Na gaya maka bata bukatarka, wannan gayen da ka daka a kanta wanan ranar shine Mijinta, har yau" "yana nan bai rabu da ita ba, idan akwai abinda kake yi da ita tow ka daina ita din matar aure ce."" Inji Ubaid." "Cike da mamaki yake kallon Ubaid cikin sanyin murya ya ce mishi. "" Zargina kake? "" Gaskiya na gaya" "maka, ka rabu da ita.""" "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 57" "Murmushi Turaki yayi mishi tare da mikewa, ya nufe shi ture shi yayi har suka fito waje. ""Idan na kara" "ganinka, a rayuwata ko a rayuwar lubnah, sai na kashe ka!"" Ya tura shi waje. ""Akan mace zaka rabu da ni? Akan mace zaka lalata alakarmu?"" ""Dama can Alakar ta lalace, ai dama can alakar babu ita, dama can" "babu wata kauna ko soyayya da yake tsakaninmu, stop pretending like kana tare da ni bayan na san kai" "da sauran yan gidan so kuke su kashe ni da goyan bayanka, idan ma Lubnah tana da aure zan cigaba da tafiya ba zan tsaya ba, idan bata da aure zan tsaya na ga me take bukata a rayuwata. Ba kai ba Mujitafa idan ya ce zai nunawa Lubnah yatsa sai na karya shi balle kai karan kade miya, fita kada na kara ganin munafikar fuskarka."" Cike da mamaki Ubaid yake kallon Turaki da ya kore shi. ""Korana kayi fa? Korana kayi Turaki?"" Murmushin takaici ya sake mishi tare da cewa, ""abinda yafi haka ma zan maka fita!"" Ya daka mishi tsawa. Girgiza kai yayi ya fita, duk fuskar da aka bibiya shine bai kyautata Alakarshi da turaki ba, ya san yayi kuskure amma duk lokacin da yayi da wani katobarar kara nisanta kanshi da Turaki yake" ya rasa me yasa yake jin haushin Yarinyar. *** "Tsare Mama nayi da idanu, na rasa abinda zan fada. Amma sai na ji akan kaina Mama bata yi kuskure ba," "ta yiwu wani abu aka kintsa mata, duk yadda aka yi da wani abu. ""Mama Bauchi kuma?"" Yadda nayi maganar sanyin murya sai ta kuma sauko da kanta ta ce min. ""Eh Bauchi zamu koma, mu je ki zauna har Allah ya kawo miki mijin aure."" ""Alhamdulillahi Ubangiji ya amince!"" Na fada mata, domin kuwa babu amfanin zan yi musu da Mama domin duk abinda zata yi tana yi ne domin ni. Can ina tura abincin ta cewa Ya Ado. ""Jiya Yaron Rufa'i ya kawo min hoton abinda yake faruwa , Adamu ka min adalci!"" Girgixa kai yayi cikin ladabi ya ce mata. ""Ni ba zan ce ni adali ba ne, amma nasan ke Adalar uwa ce wacce take tsaye domin Yaranta akan me zan musanta abinda kike da hujja a kai, nayi kuskure babba na sakaci da tarbiyyar da kika bani, amma ki yi hakuri haka ba zai kara faruwa ba."" Akwai wata duniya da Allah da kanshi ya ginawa Uwa domin Yayanta, wannan duniyar iya uwa da ³a´anta suke ninkaya a cikinsa." "Murmushi tayi ta ce mishi."" Ban ga gazawarka, amma Lubnah ba zata koma aikin nan ba, idan har shi shugabanta mutumin kirki ne, da kanshi zai zo nimanta, idan kuwa mutumin banza ne ba zai tab'a zuwa ba sai dai ta je mishi. Nan da sati ba zata aikin ba."" A hankali na saukr ajiyar zuciya, mother like no other." Duk wannan abinda take don mutuncina da kimata take. "Haka na kwashe kayan abincin na kai kitchen suka yi ta hira, haka suka tafi aiki suka barmu, nima ina" "gamawa na ce ta shirya muje gidan Aunty Nuratu Kafaya, haka kuwa muka tafi a can muka wuni sai yamma likis muka dawo a gajiye, har ga Allah mutane sun mana mummunar fahimta, amma yadda na fahimci Mama bata Zafaffa ba, amma kuma ta zuba idanun tana kallonmu ni da Ya ado, maganar gaskiya Ya Ado shi ya ma manta da batun, a daren ta amshi wayata ta kashe, ban wani damu ba na bar mata dama Ya ado ya gaya min na dauke kaina akan kome. Ranar da Mama ta cika kwanaki biyar da zuwa, bayan sallah isha ina sama ina gyara kayana, Princess ta shigo tana faWin. ""Aunty ki zo inji Kakar Bauchi."" ""Ok!"" ""Ok ina zuwa."" Na fada ina tattara kayan, can na fito sanye da riga da wando palazzo sai rigar iya gwiwata kaina sanye da hula, tun kafin na isa parlourn mayyen kamshin turarensa mai mugun kama wuri ya min maraba, da hanzari na sauko ina son gani da gaske ne shi din ne. Da gudu Yaran kanwarsa suka rungume ni. ""Mom ita ce mana kin daina zuwa aiki, waye ya miki laifi?"" Jan kumatunsu nayi na ce musu." """Break na Wauka."" ""Yaushe zaki dawo?"" ""Mama ta ce zan tafi Bauchi!"" Na fada ina satar kallonshi, ya" "fada kamar bai da lafiya. ""Eh zata koma Bauchi da zama!"" ""Kakar Bauchi, ki barta kin ji Mom tace tana da" "kirki, kuma nima ai ta min kirki."" Murmushi Mama tayi tana faWin. ""Tow kishiya amma ba zan bari ki aure min Alhaji ba, domin nima ina da gashi yala-yala irin naki."" Dariya Ilham yayi tana faWin. ""Kaka ai naki yayi fari, ba irin na Aunty Lulu ba ne, ita nata fa ranar donut na ga tayi da shi ko Mom bata donut. Uncle kace kai ma Mom Winka tafi Aunty Lulu gashi, amma tana kama da Mom Winka."" ""Da gaske Bro haka ka fada musu."" Bai ce kome ba, ni ce ma nayi maza na toshe bakinta, na mata rad'a a kunne. ""Bakyau fadar sirrin da kuka yi da wani ko?"" Na fada ina kallon Mama da take kallona. ""Aunty Jasmin ya kwana biyu?"" ""Alhamdulillahi, kin ajiye aiki ko? Brother ma jiya aka sallame shi bai da lafiya!"" Da sauri na d'ago ina kallonshi, ya tara Kaduna, sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa na ce mata. ""Allah ya bashi lafiya!"" ""Amin" "Ya Allah, yaushe zaki koma aikinki?""" "Gyara zama Mama tayi sannan ta ce mata. ""Ta gama aiki da ku ai, zata koma Bauchi ta cigaba da aikin a" "can anan ana bibiyar rayuwarta. Sannan su waWanda hotunan ban san ma'anarsu ba, na ji ance kai ne mai gidanta."" Shiru yayi yana kallon hotunan daya na wurin abinci ne, na biyu na Eko hotel ne, na uku dawowarmu daga Japan. Tasowa yayi ya durkusa a gaban ta. Cikin sanyin murya ya dauki hotunan ya ce mata. ""Kasancewarta sakatarinya, ina bukatarta a kusa da ni. Wannan wani kasuwanci muka yi shine sanadin da ta bi ni hotel, wannan gidan abinci ne bata ma ci ba sai tawowa tayi da shi, na uku tafiya ce na kasuwanci. Na rantse miki da wannan rayuwa da mutuwa take hannunsa, sai da tace min ba zata ba, har wata ta ce zata nace a'a. Mama! "" Ya kira sunanta a hankali, cikin rarrashi da niman afwa ya ce mata. "" Ko bayan ranki, Yarki ba zata zubar da mutuncinta ba, ba zata wulakanta tarbiyyar da kika mata ba." "Mama da ace Yarki zata yi wani abu da tayi. "" Kallona yayi kafin ya sunkuyar da kai kasa, ya cigaba da cewa."" Allah ya sani ita din Mutuniyar kirki ce, kamila ce, Saliha , mijinta ya dace da mace ta gari. Yaranta zasu yi Alfahari da ita a matsayin Uwa ta gari. Don Allah ki barta anan wallahi ni da kaina zan tayaku kare mutuncinta, kamar yadda xan kare uwar Yaran nan da su Yaran Lubnah ma zan kare mutuncinta."" Ceo yana da hikima,. A yadda yake iya kasuwanci da mu'amala da mutane haka duk wanda ya zauna da shi sai ya fahimci haka. Kaina a sunkuye ina wasa da yatsuna ina jin tsigar jikina yana mikewa, ina ™ara jin wani abu yana tab'a ruhina da zuciyata, d'ago kai nayi ban san yadda aka yi na ji yana bani tausayi ba, a yau na ga yadda damuwa take cike da idanunsa, zuciyata tayi rauni ainun. Kasa jure yadda yake rokon Mama nayi, na riko hannun Yaran muka wuce sama, kafin nayi nisa na tsinci wasu kalmomi da suka fito daga bakinsa. ""Ni maraya ne, amma ina da gata. Na fuskanci cin amana tun ina yaro har zuwa yau da nake gabanki, duk cikin mutanen da suke zagaye da ni daga Kanin Mahaifina, sai Jasminah kanwata sune basu tab'a cutar da ni ba, sai Yar autarki. Ita ce bana gabanta. Tun fil azal haka."" Shiru yayi juyowa nayi ina kallon yadda ya sunkuyar da kai kasa. ""Bana zo nan akan ta koma aiki bane, na zo ne na bata hakuri akan abinda aka fada a kanta. Idan ma ina son lalata ai ba zan yi da ita ba domin ta fito daga gidan da yake da babban zaure, ita din fata ce da yakini."" Murmushi yayi sannan ya ci-gaba da cewa. ""Zata iya rubuta takardan barin aikin na gode da bani aronta."" Yadda Mama ta fahince shi kaf duniya babu wanda ya mishi irin wannan fahimtar. Amma tayi murmushi kafin ta ce mishi."" Zan barta na wani lokaci, na ga kamar kana da bukatar haka, amma ka ji tsoron Allah kada ka kara daukarta zuwa wata duniya, yanxu an daina kiwon dabba mutane ake kiwo, idan har na ga wani abu ba haka ba raina zai b'aci. Duk da ban san sunanka ba, amma kayi wani abu da na kasa fahimta, Auta ta kasa zama ta ga kana rokona. "" D'ago kai yayi yana kallon Mama jinjina kai tayi. Ta ce mishi."" Ban san wacce alaka ce a tdakaninku ba, amma" "kuma naga ta kasa zama ta wuce sama da Yara, da kace kai Maraya ne ta tsaya cak, nasan wace ce ita. """ "Murmushi tayi ta cigaba da cewa."" Allah ya dafa mana! "" Tayi shiru, tana kallon Ya Ado, gyada mishi kai" "tayi tana kallon Turaki da yake gabanta, tabbas idan har abinda Ado ya fada mata gaskiya ne, Yaron ya cancanci zama da Lubnah. ""Amma ya batun iyali!"" Shafa kai yayi yana murmushi, kafi ya ce. ""Na so wata yar Bauchi tace bata sona na mata kama da gardawa tun daga lokacin Daddah take karbo maganin aljanu sun aure ni."" Ai kuwa parlourn aka yi ta dariya, Mama ta ce mishi. ""Kuma yanzu baka da wacce tace tana sonka ai kai ba dai budurwa ko?"" Shafa kai yayi ya ce.. ""Mama na baki wuka da Nama ki nimo min wacce zata iya da tsufa."" Rike baki tayi tana faWin, ""ai kuwa zan iya cewa babu wata Y'a a gabana da na baka ita!"" Sosa kai yayi yana faWin. ""Ikon Allah, babu ko kanwar Lubnah ce."" ""Gaskiya bani da ita, Allah ya baka ta gari."" Ta yanke hiran, duk yadda ya so Mama ta yi mishi barin zance akan Lubnah amma fir taki, don shi har yau kallon matar aure yake mata, sai yayi shiru wurin karfe goma suka bar gidan, duk sun fita ina bakin kofar, ina kallonshi. D'ago kai yayi ya kalle ni na dauke kaina, ina jin Jasminah tana" "cewa. ""Mama gobe ta zo aiki don Allah."" ""Ubangiji ya kai mu gobe lafiya!""" Bayan tafiyarsu na riga su wucewa dakin Mama na kwanta da tazo dakin sai da tayi sallah shafa'i da "wutir, bayan ya idar ne ta cigaba da addu'a. Har na fara barci ta ce min. ""Kina son Mai gidanki ne?"" Da wani sauri na tashi zaune ina zare idanu. Kirjina yana bugawa da karfi. Murmushi tayi ta ce min. ""Eh kina son shi Lubnah."" ""A'a wallahi Mama, ni ba wannan a tsakaninmu idan ma ya gaya miki wallahi karya ce."" Hannu ta kai bakina ta rufe. ""Bai gaya min haka ba, amma ni naga haka a tattare da ke, ni Uwa ce kuma dole na fahimci haka amma tunda kin ce bakya sonshi ai shi kenan amma ki sani kafin Azumin baWi ina son ganin mijin aurenki don Allah na baki wannan lokacin ne domin ki samu wanda ya dace da ke, amma ni idan har zaki dauki shawarata wannan mutumin yana bu™atarki sosai. Yana sonki yana kuma girmamaki!"" Murmushi tayi. Sannan ta kwanta kamar nayi kuka haka na ji maganarta taya zata ce yana" "sona bayan kuwa ba wani mutumci muke ba, haka na kwanta sai na kada barci nayi ta juyi." "Tun ranar da Mama ta ce tana son ganin Turaki, Ya ado ya zauna ya mata bayani da rokon da Alhaji" "ELYakub ya roko da kada ya nuna mishi Lubnah bata da aure yin haka zai haifar da daukar kome fa zafi, a haka ya dauka tana da auren in sha Allah akwai jarabawar da yake akan Bilal din yayi nasara da kanshi zai nima mishi auren Lubnah, sai dai a yanzu baya son ya san cewa bata da aure ne. Tun ranar da ya ga CV dinta yake ta fada mishi ta dawo aiki, amma kasancewar shi mai takatsantsa a rayuwarshi yasa yaki nuna ita ce daga Alhaji ELYakub sai kawunsa suka san ita ce, shi yasa da girmamawa suke kara bibiyar lamarin. Duk sun san bata da aure shi Waya suka bari a baya. Murmushi Mama tayi ba mamaki Addu'arta ne Allah ya amsa ya bata mijin maraniya, mijinta ita Waya mijin da kafin a ce wata ta samu irinsa zata wahala, murmushi Mama tayi tare da sujada Allah ya bashi ikon cinye jarabawar da Alhaji ELYakub ya ke mishi." "Sai ga Mama ta kasa barci juyi kadan ta kalli Autarta tausayi da soyayya take ji akanta, kamar ta mai da" "ta ciki, tasan rokon da yake mata ba rokon ta koma aiki ba, ja'iri miskilin banza." *** "A bangaren Turaki kwana yayi yana juyi, karshe sai da ya tafi sallah dare, a jingine da gadon yayi barci." "Yana me jin kamar gari ya waye ya ganshi a office duk baya jin dadi amma haka bai haka shi jin wannan karsashin ba, washi gari da safe da wuri ya tashi likitan yazo ya mishi allura da bashi magani ya sha ya" "shirya sai da ya ga Yaran Jasminah sun tafi makaranta sannan ya tattara ya wuce office, shi da Taj." "Idanunsa a lumshe yana jin Taj yayi horn, ajiyar zuciya ya sauke domin yasan ita ce kawai Taj zai yiwa Horn haka, tsayawa yayi." Duk da saurin da nake domin garin nan bai rabuwa da ruwan sama. Don hadari ne a narke a sama Taj "yayi min horn, na san shi da ogansa ne sai na Wan matsa gefe har ya tsaya. Sauke glass yayi ya ce min. ""Shigo mana!"" Shiga nayi ina faWin. ""Amma kun yi sauri ko?"" Gyada kai yayi yana faWin., ""short cut na bi."" ""Ayya!"" Muka cigaba da tafiya, ""Baki san Oga bai da lafiya ba ne?"" Juyawa nayi na kalle shi tare da cewa. ""Ya jiki?"" Banza yayi min wannan mutumin anya aljanu basu kanshi. Haka muka isa kamfanin zan dauki jakarshi ya dauke abinsa, sake baki nayi ina kallon ya cigaba da tafiya a hankali ba bi shi da idanun, sai nake ganin kamar na san wani da yake irin wannan tafiya da jimawa, juya kaina nayi tare da son tuno a ina nasan me irin wannan tafiyar? Ganin zan bawa kaina wahala amma kuma ina fara tafiya, naji gabana yana wani irin bugawa d'ago kai nayi ina kallonshi ya juyo yana kallona. Nima shi nake kallo, akwai wani alaka da ya tab'a faruwa a tsakaninmu da shi ne? A ina na tab'a ganinshi, zuciyata tana wani irin bugawa, idanunshi cikin nawa. Sunkuyar da kai nayi tare da rike jakata da kyau. Jikina yana rawa, wani irin kuka nake son nayi wanda ban san dalilin ba, kuka ne wanda nake ji kamar nayi kewar wani ko wata a" "rayuwata da jima, nayi kewar wanda ban sani ba waye shi hawaye suka shiga zubo min da gudu........." "*DIJAH BORNO, Zully da Naj, ayi hakuri sai yanzu ku yi maneji yau na ci uwar sabada da aiki ne.*" "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 58" "Zuba min idanu yayi ganin har zuwa lokacin ina tsaye. ""Taj ka shigo da ita ta daina wannan shirmen!"" Ya" "fada yana me nufar cikin kamfanin, zuwan Taj ya tsaya a gefena."" Me ya faru kuma?"" Da sauri na goge hawayen da yake ta zuba na ce mlshi. "" Ba kome"" muka shiga cikin kamfanin, a tunanina yadda ya je har gidan mu yayi bikona. Zai zama me yawan min uzuri, sai dai wannan me shafar aljanun ba haka yake ba, an jima zai birkice an jima zai dawo kamar bashi ba, tun da na fahimci yana da matsalar ™wa™walwa, wanda yake birkita mishi lissafi. Sai na mishi uzuri domin irin wannan halinsa ba iya ni kaWai ba kowa ma tsoronsa yake, a cikin wata biyu da nayi ya kori mutane a cikinsu kuwa har da shugabar gudanarwa na kamfanin sai ya fara bani tsoro. Shugaban gudanarwa, kwashe wasu abubuwan yayi fa akan lallai sai na zo office dinsa nayi wasu cike-cike. Gudun matsala na tafi nayi, sai da na je na ga mutumin bai da kirki sam, domin na fara aikin kenan ya taso ya fara ™o™arin yi min iskanci, kamar wanda aka jefo shi ya daki kofar sai da ta buWe. Ganin yadda razana domin nima na dauki wani bokitin zuba datti, ina ™o™arin kare kaina, sai gashi nan ya zo. Ajiyar zuciya na sauke me nauyi, tare da sake bokitin a kasa. ""Na kore ka!"" Ya fada yana me juyawa na rufa mishi ba, sai da muka isa office Winsa ya zuba min idanu. Ya rasa me yasa kome yake zuwa a haka, na farko ba shigar banza take ba, na biyu bata cika shiga harkan kowa ba abinda yake gabanta ya ishe ta, amma ya rasa me yasa kome yake zuwa kamar an tsara shine. ""Da ba gaya min ba haka zaki zauna ya wulakanta ki?"" Kaina a kasa, na ce mishi. ""Allah ya fishi."" ""Abinda nake son na fahimta kenan, je ki."" Haka na juya na fita, haka muka cigaba da aikin da dad'i ba dad'i ga Airah da ta" "saka ni gaba duk abinda zan yi ban iya ba, kai da ta ishe ni ce mata nayi. ""Ki fita harkata tunda bana shiga" "rayuwarki, ban ga dalilin da zaki shiga rayuwata ba."" Iya wannan na gaya mata na cigaba da abinda yake" "gabana, wani abin da yake ™ara bani mamaki, duk yadda za a kai mishi magana baya bi ta kai." "Ranar wata juma'a, ina zaune ciwon ciki ya dame ni. BakiWaya na kasa sakewa dan abu kaWan haushi" "yake ba ni. Fitowa yayi ya ga na kifa kaina da table din, fita yayi can bayan minti goma sai ga Jasminah. Office dinta muka je, ta haWa ruwan dumi a gora, saboda na gaya mata gaskiya abinda yake damuna, ina kwance ta kawo min tare da cewa. ""Dan saka akan maranki zaki ji sauki!"" Haka nayi ta sakawa ina murzawa har barci yayi gaba da ni, hayaniyar Ubaid na ji yasa na bude idanuna a tsaye yake a kaina.. ""zaki yi danasanin show up da kika yi a wannan lokacin, idan har ba da wata manufa kike bibiyar Turaki ba ki ajiye aikin ki kama gabanki."" Murmushi nayi na ce mishi. ""Ban san me kake nufi ba, ban san me" "yasa kake bibiyata da fitina ba, ka yi tunani idan kanwarka ce fa.?""" """Kanwata Allah ya mata tsari da irin rayuwarki, bari na gaya miki kowa yasan kina juya mishi tunani ne," "lokacin da ya so ki, ai cewa kika yi ba zaki auri mai zubin Gardawa ba, yau kin san waye shi shine bari ki kashe aurenki!"" Ji nayi zuciyata tayi wani irin bugawa kamar nayi kuka. ""Ban fahimci me kake nufi ba?"" Na tambaye shi a rud'e. ""Ubaid me kake aikatawa ne haka?"" ""Bari na gaya mata Jasminah ta sani ba ita Waya ba ce kowa ma yasan yadda take juya mishi tunani, Malamin da ya dauke ku Physic daga 1-2 kika ce kin samu wanda ya fi shi kudi shine wannan, mayyar kudi, kudin wancan mijin naki ya kare ne?"" Tass na wanke shi da mari wanda yayi daidai da shigowarsa, shima ya d'aga hannunshi, amma ya rike hannun yana faWin. ""Me ka zo yi a kamfanina? Ba nace kada na kara ganinka ba?"" Ya janyo shi waje. Murmushi yayi ya ce mishi. ""Wallahi tunda ta mare ni sai ka Sattar da ita."" ""Idan ka fasa ka rena wanda ya halicce ka, tab'ata daidai yake da. Nihla!"" Wani naushi ya kaiwa Bilal shi kuwa ya kauce fada ya rutsa a tsakaninsu, kamar Yara dambe. Zama nayi dirshan nayi na zubawa kasa idanu, sai a lokacin abubuwan da suke ya faruwa ya dawo kaina, jin ihun Jasminah ya sani fitowa kamar wacce ruwa ya yiwa duka, na kai hannu a hankali dafa kafad'arshi na ce mishi. ""Ka bar fadar nan don Allah!"" Sake Ubaid yayi shi kuwa ya kai mishi naushi, ai kuwa akan fuskarshi ya same shi, sai da glass dinsa ya fadi, zai rama na shiga tsakaninsu tare da tallafo fuskarshi.. ""kalle ni ya isa haka, ni ce matsalarka? Ka yi hakuri zan bar aikin ka ji ka yi hakuri kada ka kara fada a kaina don Allah!"" Na mika mishi glass dinsa ina kallon yadda yake jin kamar zai tashi sama. ""Muje ka saka maka magani!"" Jasminah ta ja hannunsa har office ni kuma na hada kayana, na bar office din ina fitowa na ga yadda ake kallona. Sai naji wani irin abu ya tsaya min a rai,na iso gida na samu Mama sai lokacin na fashe da mata da kuka, na zauna a gabanta ina kuka kamar raina zai fita, rike hannuna tayi tana faWin. ""Me ya faru?"" ""Mama dama shine Malamin da ya tab'a cewa yana sona a Bauchi? Mama me yasa ya boye min? Mama me yasa yake faWa da kowa a kaina? Mama me yasa" "na kasa tuna shi sai yanzu?""" "Murmushi tayi ta ce min. ""Yana sonki ne shi yasa yake faWa akanki, yana sonki ne yasa ya zame miki" "izuwa yana sonki ne yasa yake bayyanawa duniya akanki zai tari aradu da fadin kai, yana sonki ne yasa yake faWa da kowa yake yaki da kowa saboda kada ya rasa ki, a yanzu da bai san kina da aure ko baki da aure ba, ya iya kare kimarki ki yi lissafin idan aka ce yasan baki auren kowa akanki. Tow ba makawa sai" "yadda karfinsa ya ™are, shi wannan da gaske yake sonki ba cutar dake zai yi ba. """ """ Yan uwansa basu sona!"" Na fada ina kuka,"" akan me zasu su so ki?""" """Mama ya fi karfina, Mama danginsa wasu irin dangine, na masifa Mama ba zan iya bude mishi" "zuciyata ba, Mama ban tab'a sonshi ba tun farko a yau ma ina kara fada kamar farko bana sonshi."" Murmushi Mama tayi ta ce min. ""Nasan ai zuciyarki a rufe take shi yasa kika ki yarda ko kalli kowani mutum da sunan soyayya, amma ba zan boye miki ba, kina son Bilal Koda baki fada ba."" Kuka na saka" mata ina ta rantsuwa wallahi bana sonshi. "Weekend a gida nayi shi, ranar lahadi sai gashi da Yaran kanwarsa a lokacin na tambaye su basu" "Islamiyya ne,. Suka ce eh basu zuwa. Turawa Uwarsu sako nayi na kama hannunsu na kai su makarantar su Adil na musu registration na Islamiyya, aka basu uniform suka zauna, ko da na dawo na samu yana bada hakuri ne, murmushi kawai Mama take ta ce mishi. ""Ai ni ba ruwana kai da abokiyar aikinka, ni ba ruwana ku yi duk yadda zaku yi amma ka sani Lubnah tana bukatar hutu saboda tayi fama da mentally healthy ill, shi yasa bana son damuwa ya dame ta domin ta kai har matakin GENERALIZED ANXIETY DISORDER, idan har zamanku babu alkhairi kowa ya kama gabansa."" Kasa magana yayi zuciyarsa tayi sanyi ya ce mata. ""Taya ta hadu da wannan laluran?"" Murmushi Mama tayi ta ce mishi. ""Rayuwa ya haWa ta da wannan laluran idan da ranka ai ka sha kallo."" Idanunsa yayi mugun ja, haka yayi ta wasa da kafet" din parlourn. "Mama ta fahimci yana son ya tambaye ta, Abubuwa dayawa amma kuma yadda yake da zurfin cikin." "Tana mamaki ma da yake dogon hira da ita domin irinsu basu cika hira har da kowa ba. A hankali ya ce mata. ""Allah ya kyauta, xan tafi an jima zan zo daukar Yaran ."" ""Allah ya kai."" Abinda na fahimta ya zama Wan gida kowa ji da shi yake da yamma bayan isha da yaso ya samu yaran sun ci abinci sai da ya ci tuwon alkama miyar kuka, sannan ya dauki yaran zuwa gida bayan na biyo shi waje na ce mishi. ""Ka yi hakuri da abinda nayi naga rayuwar mata ne, shine na ce bari na biya musu kudin Islamiyya, amma don Allah ku yi" "hakuri."" Murmushi yayi ya ce min. ""Kin kyauta ai!"" Daga haka ya shiga motar ya bar gidan." "Mama take gaya min mutane irinsu, suna son mace amma aikace suke nuna mata so, basu damu da su" "gaya mata ba domin ya zama old fashioned a wurinsu. Kuma dabi'ar masu irin halinsu ne, suna da zurfin ciki domin kamar basu yarda da kowa ba, sannan basu cika yarda su yi hira da kowa ba sai wanda ya fahimci halinsu, idan baka fahimce su ba zaka yi ta ganin suna wani abu kamar basu ba, ta ce haka suke kuma dai da tayi magana na fahimci yadda yake masifa kamar nayi mishi laifi musamman idan aka yi baki maza ina musu bayani yayi ta wani fushi da fisga karshe korani yake waje ya ce musu zan bada abinda suke so ba,ya kira Taj, idan da taj muke hira yayi ta fushi ranar daga ni har Taj kamar zai rataye mu, don masifa. Ni kuma tausayi yake bani domin idan haka ita ce soyayya gaskiya am not ready," zuciyata a rufe take. "Washi gari kuwa da safe suka zo da Taj, Ashe Ya Ado yasan da zuwansa. Don fushi nayi naki zuwa aikin" "haka kawai zasu daura min hawan jini, a gidan suka karya tunda na fahimci yazo fir naki fitowa ba ayi, kuma ai kakanshi ya ce kada na gaya mishi haka ya share zamanshi har yayiwa Mama kyautar kuWi, wanda ya damu da kuWinsa shi ya ji wurin. Ni bayan gabana balle ya ce don kuWinsa nake, ni magana da" Ubaid ya gaya min ma ya ishe ni. ** KUMO FAMILY "Fada Alhaji ELYakub Kumo yake kamar ya mari Uncle Auta, ya ce mishi.""kasan tana tare da Yaron nan ne" "saboda kai, amma ka gaya mishi wacece Yarinyar bayan ba kaunarshi yake da gaske ba, ina sane da cewa Turaki yana bin ra'ayinka ne yake kula Yaron nan, kada ka kara bawa wani labarin rayuwar Turaki." "Da shi da aka hada baki aka kore shi a shekarar karshen shi a secondry School, kasan sharrin da ya so a" "kulla mishi? Kasan yadda ya lalata mishi rayuwa? Ban da Allah yana tare da shi da rayuwarsa tafi haka lalacewar don Allah kada ka kara gaya mishi kome akan Bilal wanda ya mishi a baya ma, ya isa yanzu meye ribar shiga rayuwarsa?"" Yadda yake shiga ba nan yake fita ba, fada kamar zai mari Uncle Auta. Yayi" fada sosai domin kuwa yana jin zafin abinda Ubaid yayiwa Turaki a lokacin. "Abu guda biyu da suka lalata alakar Turaki da Ubaid na wani abu ne, duk da kowani mutane yana da" "hali me kyau ko mara kyau, idan har Turaki yayi kuskure tow ya dace ya samu mutumin da zai tsaya a tare shi, tow har ana niman haka tow Ubaid ya kai wannan matsayin, sai dai tun suna Yara Ubaid baya kaunar Turaki yayi sabon aboki ko kuma ya taimakawa wani, yayi ta fushi da kuncin rai kenan. Duk yadda za'a gaya maka matukar ba faruwa yayi da kai ba, ba zaka gane ba. Ubaid ya bawa Bilal wahala akan wannan lamarin domin Ubaid yana ganin Turaki da sabon aboki yayi ta fushi kenan har sai ya raba shi da abokin, sai da Ubaid ya kai ko me turaki zai yi to bai iya ba shi Waya ya iya. (Sometimes silent pain" "yana kashe mutane dayawa, lokaci yayi da zaka fadi ra'ayinka lokaci yayi da zaka rusa wancan bond din" da kake gani kamar sasari ne let move together) "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 59" "Abinda ya fara faruwa shine kama yara da aka yi suna lalacewa a cikin Makarantar, wnada a lokacin" "iyayensu suka raye maza sun zo akan case Win, wanda yayi sanadiyar da Turaki ya bar makarantar domin Ubaid ya bada shaidar yana lalacewa irin ta mazan da aka tsinewa, kasancewar akwai kyakkyawar alaka tsakanin kakaninshi na Rasha da kasar Saudiya musamman ta harkan kasuwanci suka kashe zancen ya" koma Rasha wurin kakarshi sai da ya dauki wata goma ya koma Saudiya yayi jarabawar barin makaranta. "Daga nan ya koma can yayi jami'arsa a lokacin Ubaid azo suka yi karatun tare, duk da wannan abinda" "yayi mishi yayi hakuri sai ya kasance duk wani abin asha kiri-kiri Ubaid yake danganta shi da Turaki, amma bai taSa kawowa a ransa yana haka ne don ya cutar da shi ba," "A hankali yayi ta amfani da wannan damar yana raba Turaki da duk wanda ya zo gare shi, ana haka" "iyayensu suka rasu mazan sai da Hajiya Amina mahaifiyar Ubaid zata koma gida Alhaji ELYakub ya amshi rikon Ubaid yace idan ya tafi Turaki zai shiga kadaici, a wannan lokacin kowa ya amshi haka amma kuma a ransu basu son Ubaid din da Turaki domin kowa so yake ya rabu Turaki ya cutar da shi, amma an rasa yadda za ayi, ba a san me ya faru ba. Amma lokacin amma wani satar da aka yi a cikin gidan ElYakub kumo wanda ya girgiza ilahirin family ana cikin binciken baa tambaye shi ba, kawai ya ce ai Turaki ne yayi satan wani abin takaici aka nime kudin ba a samu a wurin Turaki, a lokacin fushin da Turaki yayi dakyar aka shawo kanshi yake kula shi, babban rigimarsu shine akan Mimih wanda aka ce zai aikata, a lokacin ya ce zai aikata ya ci-gaba daga maza ya koma kan mata, tun daga wannan lokacin Turaki ya watsar da shi, amma yana kyautatawa Iyalinsa da duk wani dangin mahaifinsa da na Mahaifiyarshi. Amma ya yanke duk wani abu da yake tsakaninsu, ko rike office din Turaki da yayi ai Alhaji ELYakub ya bashi domin kusan" shima bai da mutunci akan gaskiya zai iya aikata kome. Yadda alakarsu ya lalace musamman yadda yake zargin Turaki yafi kome bashi haushi. *** """Ke bana son rashin hankali, ya zaa yi ace mutum ya zo baki sauko kun gaisa ba."" Tura baki nayi nace" "mata. ""Wurinki dai ya zo!"" ""Amma kanki daya kuwa!"" Mirgina mata kaina nayi nace mata. ""Kin ga shi Waya ne babu kari!"" Make ni tayi, haka ta fita, na tura baki ina ruwana da shi. Ba dai ga shi bayan isha ba, muna parlour muna kallon super story, da yake Alhamis ne, zare idanun nayi kaina yana cinyar Mama tana zaune a kasa nima na kwantar da kaina akan cinyarta. Lumshe idanuna nayi kamar me barci, ai kuwa cikin ikon Allah barci yayi gaba da ni, nan suka shiga hira har tara tayi, na musu sallama ya tafi yana fita daga parlourn Mama ta zuba min mari a kafada. ""Tashi ja'ira yau kin kunyata ni!"" Sosa wurin nake ina tura baki. ""Allah ya shirya ki!"" Tashi nayi na wuce sama, washi gari ba naki zuwa aiki ba, sai ga Taj da aika tulin aiki kamar nayi hauka Mama kuma taki bani goyan baya, haka nayi ta aiki kamar jaka kwana biyu nayi ina aiki. Dole ranar Monday na koma aiki domin aikin kamar zai hallaka ni. Tun da na dawo sai na ga yayi sanyi ba masifar nan, nima kuma wannan karon sai na kama kaina. BakiWaya satin Mama biyu ta bar Lagos, bamu gaya mishi ba. Haka aka fara azumi, azumi na da kwana biyu muka wuce Umara, ashe ta Bauchi Mama itama ta zo haka muka yi ta ibada tayi min addu'a kamar zata kara haifa na, wani jallabiya me tsadar gaske Mama ta saya mishi da agogon azurfa da zube, ta saya mishi da wani turare wanda kuWinsa zai kai Naira dubu dari biyu, hidimar da tayi mishi kamar wani danta haushi suka bani har da kukana bata saya min ba, haka ta haWa min a kayana, wai na kawo mishi haka nayi ta mita ina kuka, sallah saura kwana tara muka dawo, cike da farin ciki muka iso, kwana uku na dawo aiki yadda zaku san bana gabanshi, kallo Waya yayi min yayi ta wani cin magani. Tsarabar Sarah da Taj, Sai na Jasminah da" Yaranta. Shi kuwa ko dabino ban bashi ba. Uncle Auta kuwa da ya min barka da dawowa na bashi "kyautar wani zoben azurfa da turare. Wayyo Allah, ina wutar da za a saka ni. Fushi sosai yayi, ya daina" "min magana sai dai Taj ya min Magana. Ina sane nayi mishi wannan wulakancin. Sallah saura kwana biyar aka bamu hutu kowa yayi Sallah, wannan shine karon farko da zan zo Bauchi sallah." "Sakonsa na wurina da Mama ta bani yaki zuwa gidanmu, ranar na kira Taj ya zo ya amsa na gaya mishi" "inji Mama ta turo mishi. Bayan an sha ruwa Mama ta kira ni, ""ke ce kika bashi number na ya kira sai godiya yake min, wato ke dai ba zaki bar halinki ba, sai yanzu kika bashi sakon?"" ""Mama daga shan ruwa zaki fara min faWa."" Murmushi tayi tana faWin. ""Allah ya shirya ki!"" Nan muka sha hira, ban san Ya aka yi yasan zamu je Bauchi sallah ba, koda yake ba mamaki Mama ta gaya mishi. Haka yazo da katon jaka wai na kaiwa Mama kayan sallah da na azumi da bai mata. Kallon kayan nayi na nad'e hannun a kirjina. Lashe baki nayi nace mishi. ""Kayi hakuri ba zan tafi da kayan nan ba!"" Na fada ina me juyawa zan bar wurin ya ce."" Ai ba ke na bawa ba, wa Mama na ce a kai min idan ma baki ba ai shi san zai kai min!"" Takaici ya sa na juya ina kallonshi amma kwarjininsa da cikar halittarsa ya sa ya cika min idanu. Sunkuyar da kai nayi ina cizon bakina. ""Dauka ba naki ba ne!"" Y fada yana shiga motarshi ya bar gidan nan wannan dan renin hankali ne wallahi, dauka nayi na tura mishi da sakon. *Don Allah wannan ya zama last da zaka kara" "kawo mata kaya because we are not money Morga, min iya da rufin asirinmu*" "Daga haka na wurga da wayar ina hararan kayan kamar na rufe shi da duka. Haka na wuni da takaici," "washi gari muka nufi airport domin da wuri muke son shiga Bauchi, tunda Ya Umar yana hanyar Jos. Abin ya matukar min dad'i sai dai me muna isa airport Win na hango shi. Suka gaisa da Ya Ado a raina na ce *wannan kamar maye* wai ma ya aka yi wancan lokacin na iya biyewa shashancina na kula wannan mutumin, haushin kaina na ji sosai fa. Da gayya na saka airpies a kunne na, har zuwa lokacin da muka tashi tafiya. Ashe shima Gombe zai wuce, tab'e baki nayi har muka bar lagos idanuna a rufe. Karfe daya na rana muka sauka a Jos, muna isowa sallah muka yi a masallacin da yake gefen airport Win, muka yi sallah Aunty Raliyah ta kawo mana kayan lambu da fruit, daga nan muka yi sallama. Bamu tsaya ko ina ba sai a nabardo muka sayi fura da nono, sannan muka wuce Bauchi. Karfe hudu saura muka isa dutsen tanshi, na yi kewar Bauchi sai na zama kamar Bakuwa haka muka isa gidan, da yake cike da yan karban sadaka. Mun samu tarba a wurin Yan uwana da suka zo shan ruwa tunda aka ce zan zo na ga gata sai da nayi kuka don farin ciki. Abba ma ba yabo ba fallasa haka muka gaisa. Ranar sai sha daya Yayuna suka bar gidan na kwana a bayan Mamana, cike da so da kauna nayi kewarta. Lokacin da na tashi sahur na ga sakonshi. _Da fatan kun isa lafiya ya Mamana da Abba tare da Yadiko? Nima na isa lafiya._ share text din naso yi sai na ji ban kyauta ba, kawai sai na tura mishi..*Alhamdulillahi kai ma ya naka tafiyar? Da fatan ka isa lafiya,* can kamar minti Waya zuwa biyu sai ga sakonshi. _Masha Allah, baki ce min akan Mamana ba?_ wani iyayi da shishigi tura mishi nayi da ce. *Oops tana lafiya* daga haka na share wayar na cigaba da abinda nake, bayan na idar da sahur nayi Nafilla, sannan na zauna aka yi sallah asuba, kafin na kwanta ban tashi ba sai karfe daya, muka yi wanka ashe Aunty Zakiyah ta wuce gidanta da yake Ibrahim bako tare da kannenta maza biyu da mata uku, kiranta nayi a waya nace mata. ""Shine baki tashe" "n?""" """Ikon Allah Auta ta zo wurin Mamanta taya xan tashe ta, jinjira tana jin dumin Mama!"" "" Aunty" "Zakiyah gaya min magana mike fa a fakaice fa! "" Dariya tayi tana faWin. ""Allah Yayanki ya ce a bar ki wurin Abba shi yasa ban tashe ki ba, kuma suna bukatar wani a kusa da su. "" Haka na jita, muka rabu na fito n taya su Mama aiki Abba yana tsakar gidan yana jin yadda Mama take waya da Turaki tana ta saka mishi albarka, ta ji dadin wannan sakon da ya aiko mata, bayan ta gama ta kalli Abba ta ce mishi."" Mai gidanta na wurin aikin ta ne ya turo min sako!"" Ina jin ta tana gaya mishi har da wani shadda ya turo bashi yace baya son kayan da sai da aka sabawa Allah sannan aka kawo ni. ""Eh fa haka ne, bayan saSon Allah ya wuce na annobar da aka kawo muku a cikin zuri'a, in sha Allah taraba da yasin zamu cigaba saboda harshenku!"" Inji Yadiko, Mama kan murmushi tayi tana faWin.""Ai shi kenan! Zan turawa Yayana" "ya samu a mishi dinkin layya.""" Bayan isha ta dauki turmin yadiko ya bata tare da sauran kyaututtukan da ya hada har da madara da "milo, duk ta turawa Yadiko, kaya ne me tsada. Washi gari ana gobe sallah aka nimo mana mai lalle ni da Yaran Jiddah da Ummu da aunty Zakiyah aka zo aka mana sallah da yake baki suna zuwa daga Jamaare su ne suka yi aikin kome mu kan ana mana lallen hannu da kafa ni kan ja aka min me kyau da Waukar idanu, a daren muka wuce gidan Aunty Hindatu aka mana saloon a can wurin karfe biyu na dare muka dawo. Washi gari tun asuba muka tashi, muka tashi saboda Masallacin Malam Idris zamu bi. Da wuri muka fita domin bakwai yake sallah idininsa, muna idarwa muka iso gida ta saman dutse, muna shigowa" "gidan aka sake shewa aka rungume juna, nan aka bude chapter yaushe gamo." "Kusan kowa yayi kewata, Aunty Munah tana azare sun zo itama zasu karaso Bauchi, haka muka yi ta" "farin ciki. Har dare ana tare sai hoto ake, sai lokacin Mama ta kawo musu tsarabar da Turaki ya turo ni da shi, ta cirewa Yaranta kowa turmi turmi, dakin Yadiko ma ta cire musu, bayan tafiyarsu na shiga wurin Abba da aka ce yana kirana, kaina a sunkuye yayi shiru. Kafin ya ce min. ""Shi abokin shaidancinki, aurenki zai yi?"" Rike zuciyata nayi amma tabbas yadda Abba yake danganta Turaki da wasu irin kalmai yana saka ni jin wani irin yanayi, mutumin da ko hannuna bai taba rikewa ba, me yasa Abba yake yin haka ne?" "Haka ya gama fadarshi iya hakuri nake bashi ina kara nutsuwar da kai na, har zuwa ya gama abinda yake" "sannan ya ce na je, lokacin da na koma daki Mama tayi tayi tasan me yake faruwa ban gaya mata ba." -Washi gari. Tun safe na ga Mama da Yadiko suna ta aiki kamar zasu yi wani abincin sallah bayan daga gidan Yayuna "ake kawowa sallah da kwana biyu ake wunin gidanmu, haka yasa nayi ta mamaki. Amma ban tambaya ba don yadda suke aikin cikin nishadi, na fahimci akwai wani abu." "Wurin karfe tara muna gama shirin tafiya kallon hawa da yake a g.r.a muke kallon, Ya Sani dasu Aunty" "Inna muna dauki wata sienna muka fita bayan Ya Ado ya turo kudi aka zuba a cikin motar. Muka fita sai kudin da Ya Umar ya bamu, haka muka tafi da kular ruwa da kayan ciye-ciye, haka muka kutsa da kyar zuwa old GRA Bauchi daidai alhayat nan muka samu wuri har an fara wucewa. Sanye nake da wata lace" "mint green wanda aka min dinki Bubu sai daurin da na kafa a kaina mayafina fari ne da takalmi da jakana," "sai madubin da na saka. Ruma Mai shadda muka hadu da ita ina tsaye da lema. ""Lubnah Shehu Umar?""" "Dariya muka saka, na isa inda take ina mai amsar Yaronta alamar sabon haihuwa ce. ""Mai shadda kece haka? Kin zama Mama!"" ""Ke nan ce min zama wata yar 18yrs ba sai ni yar renin wayo!"" Wata yar budurwa Yarta na gani tana mai gaishe ni, ta hado kan kannenta. ""Ruma beautiful familynki kenan?"" Murmushi tayi tana faWin. "" Kema ai naki suna hanya in sha Allah, ki ,zuba idanun suna nan tafe fa wallahi uku uku zaki ya dirke mata duk bayan shekara daya."" Murmushi nayi amma nasan ni ai narasa wanan damar har abada. Haka muka sha hira kafin ta wuce. Sai bayan tafiyarta na nutsu sosai. Ina son Yara, ina son Yara amma ni bani da rabon Yaran domin na gama da mahaifana. Taya xan samu haihuwa ko nayi aure? Ina ga Madadin na sakawa kaina damuwar auren gara na hakura na rike aikina, domin babu namiji da zai aure ne ba tare da ya karu da ni ba. Tab'a ni Aunty Innah tayi na kalle ta. ""Na ga tun kawarki ta tafi kike tunani, shi fa aure da haihuwa na Allah ne idan kika yi hakuri Allah zai baki wanda baki zata ba. Ki kasance mai yarda da ™addara da kuma hakuri da juriya, wallahi ba kowa Allah yake jarabta ba, sai mai imani a jarabce ka ma Allah yana sonka ne ga mutane dayawa suna saSon Allah kuma suna raye me yafi wannan muni, ki saka a ranki kome ya baki rabonki ne idan bai yi niyya ba Alhamdulillahi ba akanki aka fara haka ba. Ki godewa Allah kina muslma mai imani da ™addara." "Alhamdulillahi da Allah ya raba ki da wancan Tsinannen da ko Abba bai bari ba, ke Alhamdulillahi kin auna arziki domin da kina nan tare da shi da kin mutu ba wanda ya san yadda kike cin azaba gashi daga rabuwarku har yau bai kara ajiye mace ba, itama Yarinyar da auro a Gyembu a kotu suka rabu, hmmm yanxu haka a Jama'aren an hana shi aure, domin kuwa cewa suke tunda ya iya rabuwa da ke babu Macen da zai samu ya rike tsakani da Allah. "" Abin sai ya zo min bazata wato idan baka da hakkin mutum sai Allah ya fito da kome sarari, a yadda nake jin labarin kamar a mafarki wai Ya Hafiz ne yake ikirarin sai" samu wacce zata zauna da shi hm....... "[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 60" "A lokacin da ya sake ni yadda yayi ta alfahari da zai samu mata na ribibinsa, sai na ji jikina ya mutu murus." "Haka na cigaba da. Kallon amma bani da karsashi har zuwa lokacin da aka tashi karfe daya na rana muka dawo gida amma naji suna cewa zasu wuce kofar fada a can za ayi kallon na gaske. Tunda nayi sallah duhar nake kwance ina jin hayaniyar mutane. Ban kawo baki gidan aka yi ba, domin ina can uwar dakan Yadiko s gadonta. A hankali barci ya fara fisgata sai dai tashina Hashiya tayi na bude idanuna kanta. ""Mene ne?"" ""Wai kin yi baki ne fa."" ""Ni kuma?"" Na tambayi kaina, na juyar da kai na lumshe idanuna barci ya kara gaba da ni. ""Ke tashi baki kika yi daga Gombe?"" Ban san lokacin da dirko daga gadon ba. Na zare idanu kafin na fito da sauri, riko ni Yadiko tayi tana faWin. ""Ina dan kwallinki?"" Da sauri na koma dakin na hada da Hijab dinta da nayi sallah na fito. A parlourn Abba na ji ana ta hira sama-sama, daga yadda gidan ya dauki kamshin turarensa na san cewa wannan mutumin ya zo gidan mu, parlourn Mama na shiga na samu Aunty Kubra Yar Umma Uwani. ""Auta a ina kika samo mana bature? Ya Salam wani hanin ga Allah baiwa ce."" Banza nayi mata na wuce dakin Mama da take sallah, zama nayi ina kallonta idanuna cike da kwalla, taka idarwa tayi ta kwararo addu'a har da hawayenta. Kafin muka shafa da ita na ce mata. ""Dama kin san da zuwansa ne?"" ""Koransa zan yi ne?"" ""Mama zai ga kamar muna mishi ya wani abu ne?"" ""Kuma haka ko? Matsa can ja'ira. Ko ance ban san kuna turowa juna sakon Barka da shan ruwa" "da kuma Barka da sahur ba?"" Ban kara mamaki ba sai da na ga ashe kayan da muka kawo mata na" "wurinsa ne a jikin matar nan, rike bakina nayi ina kallon abin mamaki anyi mata Winkin riga da zani, ita da" "yadiko kayan suka saka, fitowa tayi tana faWin cewa."" Kubra gaskiya Abdulkarim dan albarka ne jiya aka kai kayan nan da darren amma ki ga yadda ya dinka yau kaya sun min cib ni da Yadiko." "Sake baki nayi wato gidan nan an iya zaga ka ayi abu daga baya ka sani,ji nayi kamar nai kuka. Ina" "tsaye Yadiko ta shigo da wasu roses irin na da can sai wasu dangaran aka shiga zuba cin-cin da na kiya, tangaran kuma aka zuba cake da donut, ke dai Mama da Yadiko sun ci amanata, asalin cin amanata matan nan dun yi shi, sai na rasa bakin magana Hashiya suka kira tayi ta kwashe abincin ta kaiwa parlourn Abba, ni kuma Mama ta ce min. ""Zaki tashi ki gyara jikinki, ke tafi ka kiyi sabon wanka wannan tsamin ranar da kike yi Allah kaWai yasan hakurin da muke yi da wannan lamarin tsamin."" Kallon kaina nake ina mamakin yadda Mama suka ci amanata, ban gama wartsakewa ba Yadiko ta ce min. ""Auta tsayuwar me kike don Allah je ki yi wanka!"" ""Ni wani wanka xan kara?"" Na fada ina tura baki. ""Ai gara ki nuna musu ke kyakyawar kazama ce."" Inji Mama sake baki nayi anya Mama bata ci amanata ba akan Sir Turaki, tura baki nayi ina fadin. ""Mama cin hancin da ya baku ne zaku mai da ni bare?"" Wani d'ago kai tayi ta kalle ni sau daya sannan ta cigaba da aikinsa, make kaina Yadiko tayi tana faWin. ""Wuce maza kafin na kwala miki murfin nan a katon kanki!"" Daga haka na wuce simi-simi, wankar da ban yi niyya ba, shi suka saka ni nayi bayan na fito na samu Mama bude akwatinta wata riga da zani dinkin born style aka yi mishi, ta ciro min ta ajiye da mayafinsa babba me kyau sai turare wanda Yaranta suke saya mata ta ajiye min, da wani takalmi me kyau ga tsada ta ce min. ""Ibrahim ya turo min daga kasar waje ga jakarshi nan, Munah taso na bawa Innah domin ta hannunta ya fado, ni kuwa nace ba zan bada ba, ita Yadikonku ta bawa matar Sani nata. Na ce autata zan bawa."" Ta fada tana ajiye min, ta cigaba da zaro min kaya daga akwatin tana faWa min wanda suka bata, amma ni ta barwa tasa ayi ta dinka min koda nayi aure dangin miji ba zasu ce suturarsu nake sakawa ba. Murmushi nayi nace mata. ""Na gode sosai Mama!"" Na rungume ta ina jin kuka. ""Ke kada ki bata fuskarki!"" Ta ce min tana murmushi, haka na fito bayan wani lokaci Hashiya ta ce min. ""Aunty ki shiga Abba ya koma parlourn Yadiko!"" Tunda ta fadi haka na kai" "kusan minti goma a wurin sai da Mama ta fito na tashi a hankali, na fito waje ina jin gabana yana faduwa. A hankali na tura labulen parlourn na shiga da sallama, idanunsa yana kaina. HaWa idanu muka yi na sunkuyar da kai, ina me shiga parlourn da sallama, na samu wuri na zauna a kasar kafet. ""Barkanku da sallah?"" Muryan mutum biyu na ji sun amsa, shi bai amsa ba. D'ago kai nayi zan kara tambayarsu ya hanya na ga idanunsa a lumshe. Sunkuyar da kai nayi kasa. ""Ya Hanya da fatan anyi sallah lafiya!"" ""Alhamdulillahi!"" ""Lubnah ashe a Lagos yanzu kike aiki?"" Ba zan manta da muryan Malam Hamza ba, cikin murmushin yake na ce mishi. ""Eh Malam!"" ""Jamil ka ji ikon Allah, kuma a kamfanin Malam Bilal" "take aiki ba"" tabbas yanzu na tuna da asalin shine malam Bilal? A raina na fadi haka daidai bude idanunsa wanda yayi kicibis da d'ago kaina, muka zubawa juna idanun. Wani abu nake ji s cikin idanunsa, wanda har jikina yana amsawa, nayi kasa da kaina ina wasa da yatsuna, shi kuma ya cigaba sauke sirrintaccen ajiyar zuciya a hankali a hankali. Yarinyar nan ta shammace shi fiye da yadda yake" "tsammanin, ya zata yana da wayo ne amma shi bai san cewa ita din kallonsa take ganga ba rufi ba," Two hours ago. "Lokacin da ya iso Bauchi awa biyu da suka wuce, yana hanyar Gombe har ya kusan shiga alkaleri ya kira" "Number Malam Hamza duk da sun jima basu gaisa ba, amma akwai wani abu da yayi da har yanzu alakarsu take nan, shine bayan ya bar Bauchi sai da ya bawa Malam Hamza aiki a daya daya cikin kamfaninsu na kano, yanzu haka a can kano yake aiki. Shi kuma Malam Jamil dama karatu zai koma ya mishi hanya ya koma yanzu haka yana koyarwa a jami'ar jahar Bauchi na gadau. Kuma sanadin da suka tsaya da kafarsu, yana kiran Malam Hamza da yake suma basu manta da halaccin da yayi musu ba, yana fada mishi gashi nan a Bauchi shima ya kira Malam Jamil ya gaya mishi, take suka shiga musun inda zai saka, nan suka. Kara kiransa suka gaya mishi rigimarsu, dariya yayi musu ya ce su jira shi zasu tafi gaisuwa ne gidansu Iyayen Lubnah. Mamaki yasa Malam Hamza ce mishi. ""Kana nufin kun dawo da soyayyarku ce?"" Jim yayi kafin ya ce mishi, ""sai na zo dai!"" Ya fada musu, lokacin da ya iso gidan Malam Hamza suka wuce wnada yake Fadamar mada, suka ci abinci sama sama ya tab'a domin tun ranar da Mama ta kira shi tare da mishi godiya,ta ce mishi yaushe zai zo Bauchi? Ya ce mata washi garin sallah zai zo, don haka ya dauko hanya ba ruwansa, a can ma hawan sallah da ayi amma ya gudo. A yanayin da yake tafiyar da rayuwarshi bai san cewa zuciyarshi take janyo shi ga Lubnah ba, duk yadda yake son nisanta kanshi daga gare ta domin bai san matsayinta ba, matar aure ce ko bazawara ce. Shi dai ya san yana son ya zo amma ba zai ce ba don ita ya zo ba, sai dai yadda yake jin a ransa saboda Mama ya zo, amma ko tukin da yake yi so gani yake ba gudu yake ba. Haka ya iso ana ta hawan sallah suka wuce Fadamar mada, bayan sun nutsu ne Malam Hamza ya ce mishi. ""Kun dawo soyayya da ita ne?"" ""A'a muna tare dai a lagos tana aiki a KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY."" "" Wannan shine ake kira almara"" Malam Hamza ya fada yana kallon shi. ""Ita tasan kai ne?"" Girgiza kai yayi yana faWin."" Duk yadda naso ta tuna bata tuna ni ba!"" Jinjina kai yayi yana faWin."" Akwai daure kai, amma kasan bata da aure!"" Wani irin zabura yayi, cikin kallon mamaki Malam Hamza ya ce mishi. ""Baka san bata da aure ba dama? Duk ganinta da kake ka zata tana da aure kai ka ce ina taimaka maka da labarin zaman da take duk tura maka da nake baka duba ba? Har labarin mutuwar aurenta da jinyar da tayi da barinta Bauchi na tura maka ta email dinka!"" Dafe goshinsa yayi yana faWin.. ""Innalillahi wainnalihir rajoun Innalillahi wainnalihir rajoun, innalillahi wainnalihir rajoun. Da na ga baka samu lokacin min reply ba na turawa Alhaji ELYakub da yake tab'a tambayata maganar ka da Lubnah na tabbatar masa da gaske ne domin a lokacin gani suke kamar gamo ka yi ba da gaske ba ce."" Mai da kanshi yayi ya kwantar da shi a saman kujeran yana jin wani irin sara mishi da yake yi. ""Wannan karon dole ka tsayawa kanka, fight for yourself, domin ina jin cewa kamar zata koma hannun dan iskan gaye nan."" Bude idanun yayi akan Malam Jamil ya ce mishi."" Yaushe ka ji zata koma?"" ""Tun kwanciyar babansu a Lagos, Matata Yayarta kawar Yayar Lubnah ce, take cewa Mamansu ta ce da ta koma gara ga gawarta."" Ware idanunsa yayi akan Malam Jamil, kafin ya ce mishi. ""Ku tashi muje!"" Rike hannunsa Malam Hamza yayi ya ce mishi. ""Ina son ka bi kome a hankali, in sha Allah sai inda karfinmu ya kare ba zamu kara barinka, ka rasa ta ba a karo na biyu."" Zama yayi yana sauke ajiyar zuciya, idanunsa sai wani kyalli suke. Malam Jamil yake bashi labarin wahalar da ta sha ji yayi kamar ya bude idanunsa ya ga Hafiz no wonder ya mishi wannan dukar ranar sashe kishi da takaici suka kwashe shi yayi daidai kenan, yana zaune har wurin daya da wani abu suka fita zuwa masallacin suka yi sallah sannan suka dawo suka zauna daga nan ya bawa Yaran Malam Hamza barka da sallah na dubu hamsin, haka suka wuce dutsen tanshi, wurin karfe biyu da wani abu sakamakon unguwa ya cika dakyar" "suka gano gidan, sai da ya kira Mama ya gaya mata gashi nan a kofar gidan ta tura Hashiya ta shigo da su," "lokacin da suka shiga parlourn Abba ta kai su, ta gaya mishi ga Shugaban Lubnah daga Lagos ya zo musu" barka da sallah. "Koda suka shiga Alhaji yayi dattako domin yayi ta mishi tambayar da kure hankali, yadda yake bashi" "amsa tare da fadar waye shi, yasa bakiWaya ya nutsu. ""Yanzu me ya kawo ka Bauchi?"" ""Nazo zumunci da kuma gaisawa da abokan arziki da aka zauna."" Shiru Abba yayi kafin ya ce mishi. ""Kamar shekarun baya ka zo nan kai da wadannan abokan naka ko idan ban manta ba?"" ""An yi haka Alhaji shekaru goma da wani abu;"" gyada kai yayi yana kallonsu, duk da ba shi bane ya bada amma amma kuma sai ya ga yadda suka zo wancan lokacin da kuruciya yau dashi sun zo da shekarunsu. ""Masha Allah;"" nan suka yi ta hira" amma shi bai ce kome ba har aka fara shigo da abincin Abba ya bar musu parlourn. Present "Mikewa nayi xan bar parlourn ya ce min. ""Me yasa kika boye min baki da aure?"" Tambayar ya zo min a" "wani irin bazata, ""ka sani ko tana da wani dalili?"" ""Which dalili zata boye min bata da aure?"" Zubawa kofar parlourn idanun nayi kafin ns cigaba da tafiya. ""Baki gaya min dalili ba?"" ""Ka tambayi Alhajinku yafi ni sanin dalilin haka!"" Ta kowa yayi bayana kafin ya zagayo gabana yana mai zuba hannunsa dukka biyu. ""Na zata idan wani zai boye min kome ba zaki aikata haka ba? Me kika dauke ni?"" ""Malam Bilal ka yi bincike! Kada ka yanke hukuncin da sauri haka."" ""Jamil"" sai kuma yayi murmushi ya juya ya fita, wani irin abu na ji ya tsaya min a raina, ba zan iya barinsa ya tafi haka na, lokacin da na biyo bayanshi na samu Hafiz a harabar gidan, suna kallon kallo tsakaninsa da Bilal. ""Sir ka tsaya mu yi magana."" ""Me yasa zan" "tsaya mu yi magana!""" """ Ka saurare ni Please!""" """Ashe da gaske abinda ake fada min yana faruwa da gaske ne, kwartonki kik..."" Ganin Hafiz nayi a can" "kasa kamar zai tashi amma saboda yadda ya sha bugu. ""Kaci zarafina zan dauka, ba yau na sha jin" "kazaman kalamai daga bakin mutane ba, amma ita din kaunata idan bana nan xaka yi yadda kake so amma ina tare da ita ni kamar inuwa nake mata ka kiyayye kalaman ko na rufe ka har abada.""" "Tashi yayi yana faWin. ""Idan har ina raye aure sai dai ki ga ana yi Lubnah ki dawo rayuwata idan ba haka" "ba wallahi sai dai kowa ya rasa.""" """Na rasa gane kai wani irin jahili ne, amma a yau zan gaya maka abinda ka sani ba. Har abada ba zan" "tab'a komawa rayuwarka ba. "" Kallon CEO nayi a hankali na kai hannuna tare da rike rigarshi. "" Tun daga lokacin da na hadu da shi yake bawa rayuwata kariya ka koyi yadda ake mutunta mutum. "" Na fada tare da sake rigar na juya cikin gida hawaye na zuba min. ""Lubnah!!!!"" Dukkansu biyu kira sunana a lokaci" guda. Alhamdulillahi anan na gama book 1 waye zata amsawa (In sha Allah ranar Monday zan cigaba abubuwa dayawa na tara a gabana don Allah ku bani hutun idan na fara in sha Allah sai na gama zan tsaya amma yanzu ina son na hutawa nima bana jin dadi ga Yarana ma haka basu da lafiya amma zuwa ranar Monday in sha Allah zan dawo da karfina da abubuwa dayawa da ba zaku manta da shi ba Team Lulunhafiz da Team Lunanturaki) An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels