An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KIDA A RUWA Book 2 1 .........2016         Shekaru uku da wasu watanni kenan da kama Zak-Shadow. Abubuwa da yawa sun faru marasa daɗi harma da masu daɗin ta wani fannin. Sai dai rinjayen marasa daɗin ya danne masu daɗin ta yanda har idanu basa ganinsu. Misalta kalar tashin hankalin da su Mammah suka shiga a wancan lokacin ɓata baki ne. Babu irin shigi da ficin da Imran baiyi ba amma ko damar ganin Zak-Shadow an hana musu har na tsawon watanni. Daga baya shima Imran ɗin suka kama shi.       A farko manyan sojoji da yawa sun tsaya akan case ɗin da son ganin abubuwa sun dai-daita Zak-Shadow da Imran sun fito, sai dai daga baya sai suka fara janye jikinsu baya aka bar General Yusuf kawai da gwagwarmaya. Dan har cikin ransa ƙauna ɗaya tak yake ma Zak-Shadow da Imran. Faɗi tashin COAS yasa aka fara shirin miƙa case ɗin kotu, a lokacin Zak-Shadow nada watanni tara a rufe, kuma har lokacin ba'a taɓa barin kowa ya gansa ba sai masu tsaronsa sai shi COAS ɗin kawai.        Kasancewar al'amarin shiri ne na musamman da kowa ya rasa bakin zarensa a zaman farko na kotun aka yanke hukunci. Sun yanke ma Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi hukunci zaman gidan yari na shekara ashirin da biyar, shi kuma Imran Abbas shekara biyar. Ya rabbi wannan al'amari ba zuri'ar Mammah da gidan su Imran kawai ya girgiza ba, ƙasa gaba ɗaya ce ta girgiza, dan a take matasa masu kishin ƙasa da wasu kungiyoyi suka fara zanga-zangar lumana akan basu amince da hukuncin da aka yankema Zak-Shadow da Imran ba. Wannan zanga-zanga taso kawo hargitsi daga baya, hargitsin kuma ba kowa ne ya haddasa shi ba sai ƙungiyar duhu da suka fuskanci ana neman warware musu nasararsu. An saka matakan tsaro masu tsauri daya tilasta matasan komawa gida aka koma ka-ce-na-ce a media kawai, tare da addu'ar neman ɗauki ga UBANGIJI, Sai gargaɗi ga ƴan siyasa akan ALLAH ya kaimu zaɓe na gaba, dan duk mai hankali ya kalli abinda ya farun da idon basira yasan lallai hukuncin nan na siyasa ne kawai...       A ɓangaren Mammah ba'a magana. A wannan karon duk dauriyarta da iya danne abu sai da ta kwanta jiyya, kusan watanta biyu kafin ALLAH ya bata lafiya, sai dai ciwon hawan jini ya riga yayi tasiri a gareta. Hakama ƙannensa da sukafi kowa ɗaga hankalinsu, sai da takai har su Ma'aruff suka ce sun fasa aurensu da ake gaf da yi, amma Mammah tace bata yarda ba bata amince ba. Dan haka tana samun lafiya aka hau shirye-shiryen bikinsu, dama gininsu tun kafin a kama Imran ya dawo da shi anan cikin gidan, bayan an kama shi kuma Uncle Nasiru ya tsaya akai aka cigaba bisa shawarar Mammah. Satin Mammah ɗaya da baro asibiti, da yay daidai da sati biyu ciff da yankema su Dada hukunci akai bikin Ma'aruff da Ja'afar, sai dai bikin baiyi wani armashi ba, dan aure kawai aka ɗaura amare suka tare. Idan ka cire yara irinsu Nimrah dake shagalinsu kowa ƙarfin hali kawai yake, har dai akai aka tashi lafiya...      Kasancewar ba wani taro akai sosai ba gidan shiru babu hayaniya, su Gwaggo Khadijah ne dama kawai sai wasu tsiraru daga mutanen Kano suka zo. Tun bayan sallar isha'i aka maida amare sashensu, dan tunda aka kawosu anan sashen Mammah aka ajiye su sai yau da biki ya tashi. Ganin har ƙarfe goma babu Ma'aruff babu Ja'afar Mammah tai kiran Bilal tana tambayarsa su.         Amsa ya bata da, “Mammah gasu nan fa a ɗakinsu. Da alama kuma basu da niyyar tafiya sashensu. Wanka ma da ƙyar na samu sukayi suka canja kaya”.          Murmurshi Mammah tayi tana ɗan girgiza kai cikin danne damuwa, “Kaga basu wayar”.     Da to ya amsa mata, yana nufar ɗakin su Yaya Ma'aruff ɗin dake jikin nasu shi da Ammar. Sai da yay knocking ƙofar suka bashi izinin shiga sannan ya shiga da sallama. Mammah dake saurarensa tace, “Saka wayar a amsa kuwwa”.       Sakawar yay kamar yanda ta bashi umarni, ya sanar mata ya saka. Kai tsaye ta furta, “Ma'aruff! Ja'afar!”.       A tare suka amsa mata, dan suna zaune ne a bakin gado su duka, “Yanzu kuna ganin abinda kuke shirin yi dai-dai ne kenan?. Karku manta yanzu suna da hakki a kanku, ɗaya kuka tauye sai ALLAH ya tambaye ku. Abinda kukeyi bashi zai dawo da Imran da Muhammad cikinmu ba, miyasa bazamu karɓi ƙaddara muyi haƙuri bane. Addu'a itace maganin komai. Dan haka ina baku umarnin tashi ku wuce Bilal da Ammar su raka ku sai da safe...”         Ma'aruff da idonsa ya kaɗe murya a cinkushe ya ce, “Amma Mammah.....”      “Bana son jin komai, ku tashi ku wuce kawai. Bilal kaje kai da Ammar ku rakasu.”      “To Mammah”. Bilal ya amsa yana share hawayen da suka cika masa ido. Dan Ja'afar ma kuka yake. Haka shima Ma'aruff ɗin gefe ya kauda kansa ya share nashi. Babu abinda ke cizon zukatansu sai tuna yanda suka shirya wannan ranar da ɗokin zuwanta tare da Dadansu da Yaya Imran, amma sai gashi yau anyi komai babu su, kuma suna raye, suna a gari ɗaya amma ƙaddara tai musu shamaki. Ba yanda suka iya dole sukabi umarnin Mammah, dama sunyi wanka, suka shirya cikin kayan barci iri ɗaya dan basa wani buƙatar wasu kaya saɓanin waɗan nan.      Ammar da gaba ɗaya baida isashiyar lafiya tunda aka yanke hukuncin nan nasu Dada da ƙyar ya iya binsu saboda umarnin Mammah. Ma'aruff shine babba, shi suka fara takawa har falon sashensa daya ƙawatu da kayan more rayuwa, babu abinda ke tashi sai ƙamshin sabbin kaya dana turare da sabon fenti. A ƙofar bedroom ɗin da yake da tabbacin Lailah na ciki yay knocking, bai jira amsarta ba ya buɗe kaɗan ya leƙa. Hangota can a kan katafaren gadon da aka saka mata ya sashi ɗan sauke numfashi, kafin ya buɗe ƙofar gaba ɗaya yana sallama. Bai damu data amsa ba, ya juyo yana kallon su Ja'afar da ke tsaye.     Nuni yay musu su shigo, dan haka suma duk sukai sallama ya amsa sannan suka shiga. A bakin gadon ya zauna kusa da ita, su kuma suka zauna a sofa ɗin ɗakin su duka. Duk da sun girmeta, matsayin ƙanwa take ma a garesu, dan uwa ɗaya uba ɗaya take da Imran, itace autarsu ma. Amma a tare matsayin matar Yayansu a yau suka fara gaisheta.      Da sauri ta girgiza kanta tana share hawaye batare data buɗe fuskarta ba. Dan itama dai irin ciwon dake zuciyarsu shine a tata zuciyar. Cikin rawar murya ta gaishesu batare da ta amsa gaisuwar da su sukai mata ba. Dan kai tsaye ta ce, “Yaya ina yininku”.     Amsa mata sukai da kulawa, kafin Ja'afar yay mata gajeruwar nasiha da addu'a. Shima Bilal yay mata a taƙaice. Ammar dai kasa cewa komai yayi sai addu'a da fatan zaman lafiya. Cikin abinda bai fi mintuna goma ba suka kammala suka fito zuwa sashen Ja'afar...    A sashen Ja'afar ɗin ma dai shine yay musu jagora har bedroom ɗin Shariffat. Itama dai komai na funichars ɗinta irin na Lailah ne, kala ce kowa wadda yake so aka saka masa. Ga ƙanshin turare na tashi kamar dai sashen Lailah ɗin. Ita kam a kwance suka sameta, sai da Ja'afar ɗin yay sallama sannan ta tashi zaune, fuskarta na lulluɓe itama cikin lifaya. Suna zama ta fara gaishesu. Suka amsa mata da kulawa. Yanzu kam Bilal ne yay mata nasiha ita, Ammar yay addu'a. Anan ma basu wuce mintun goman ba sukai musu sallama suka fito...        Kamar haɗin baki su Ja'afar na fita a sashen Ma'aruff Lailah ta saki kukan da take riƙewa. Haka ma su Bilal na fita Shariffat ta fashe da kuka. Dan su dukansu auren nan tamkar fami ya zama ga damuwar family's ɗin nan nasu guda uku. Sai dai babu yanda aka iya da ƙaddara. Ma'aruff ya haɗiye abu mai nauyi daya tsaya masa a maƙoshi, tare da matsawa kusa da Lailah ya jawota jikinsa a karo na farko a rayuwarsu ya rungumeta. Sai kawai ta sake sakar masa kukan da yafi na farko. Murmurshi yayi mai ciwo. Kafin ya fara magana cikin ɗacin murya sai dai tana fita da sanyin sauti mai tafiya da lallashi...          “Yau rana ce ta farin ciki da ɗunbin tarihi a garemu, rana ce da iyayenmu sukaci buri a kanta damu kammu. Sai dai gata ta cika babu waɗanda mukema kallon iyaye na biyu a tare damu. Lailaty ƙaddara batai mana adalci ba, miyasa zata ɓoye mana su a lokacin da mukafi buƙatar su...?”       “Saboda makirci da zaluncin azzalumai ne Yaya Man. Kuma bazamu yafe musu ba..”      “Tabbas bazamu yafe musu ba Lailaty, za kuma mu cigaba da gayama UBANGIJI kukanmu da kai ƙararsu gareshi. Dan sun cutar damu.” hawayen da yake riƙewa suka shiga gangarowa suna sauka akan kafaɗarta. Da sauri ta ɗago tana kallonsa a karo na farko, sai ya kauda kai gefe yana murmurshi. “Bafa kuka nake ba, abu ne ya faɗa min a idona”.        Hannunta mai ɗauke da lallen da daƙyar suka yarda akai musu ita da Shariffa takai saman kyakkyawar fuskarsa mai kama data Ja'afar matuƙa, dan kamanninsu na saka mutane da yawa yarda su Twins ne. Fuskar ta maido saitin tata dan tabbatar da abinda ta gani, sai dai suna haɗa idon ya ɗaga mata gira kaɗan, cikin son kauda mata zargin dama yanayin nasu ya matsar da fuskar sosai gab da tata. Ƙoƙarin komawa baya tayi yay saurin riƙota ya hana hakan, nan ma tai ƙoƙarin kife kanta a kafaɗar tasa ya sake hanawa ta hanyar riƙo fuskar da duka hannayensa biyu, a bazata taji lips ɗinsa kan nata. Sai kawai jikinta ya kama rawa ta daburce, dan abunda batai zato ko tsammani bane daga garesa. Tun tana mutsu-mutsu harta nutsu dan tuni ya mannata da fuskar gadon dole ta sallama.      Sai da ya tabbatar ya tabbatar mata da wannan ranar da sun zama ɗaya ta hanyar sumbatarta yanda ya dace kafin ya haƙura. Gaba ɗaya kunya ta sanyata naɗewa a jikinsa tama kasa tashi. Shi ko murmushi kawai yake yana shafa bayanta. Yo banda ALLAH ya rage ma aya zaƙi ai wannan ranar tanadin da sukai mata shi da Ja'afar ɗinsa ba'a magana. Amma ina ƙaddara tace musu bata yarda ba, sai dai kawai ayi wani abun dan sauke haƙƙi da rahamar UBANGIJI mai sassauta zukatan bayi da ikonsa..........✍️ _Alhamdullahi barkanmu da dawowa a littafi na biyu. Duk da dai na barku da jira, Amin afuwa uzuri ne yasa aka samu dogon hutun. Ina fatan kuna cikin ƙoshin lafiya kuma bakuyi fushi ba 😘. Kar ku damu faka-faka ne in dai naga kuna so kuma. Dan in babu kwarin gwiwa daga gareku rubutun bazaiyi gudu ba kamar yanda muke fata. Karna cikaku da surutu kumuje zuwa kawai dan book 2 ɗin nan hummmm ba'a mana, in sha ALLAHU sai ya tashi kanku fiye da yanda kuke tsammani, na tattaro muku tari-tarin abubuwa a cikinsa da sai kun karanta kawai zaku gane abinda nake nufi 😘😘😘💃._ KIDA A RUWA 2 2... ..........Da ƙyar ya lallaɓata ta tashi tayo alwala, shima yayi suka gabatar da salla tare da addu'oi masu tsaho da rabinsu duk akan Yaya Imran da Dada ta ƙare. Bayan sun kammala ya riƙe hannunta, murya a sanyaye ya ce, “Yanzu ya za'ayi kenan?, ango na shigowa da kaza ni da Twiny na mun shigo hannu rabbana. Ina fatan aminan juna zasu yafe mana, amma in sha ALLAHU zamu biya wannan bashin ranar da kuka haifo mana Haysam da Imran”.          Murmurshi tayi tana mai sinne kanta saboda kunya. Shima sai ya sake murmusawa yana mai jawota jikinsa ya rungume gaba ɗaya yana sanya mata albarka. Cike da jin kunya tana naɗe a jikin nasa ta amsa da, “Amin na gode. In dai kaza ce mun yafe muku. Dan ko ma kun kawo bazamu ci ba”.        “Oh baki kuka haɗa kenan?”.    “A'a fa”. “Faɗi gaskiya dai Lailaty, dan gara mu sani, musan yanda zamu tafiyar da rayuwar aminan juna kada wata ran a haɗe mana kai a tare”.        Ƴar ƙaramar dariya tayi tana mai yunƙurawa zata bar jikinsa. Sai shima ya miƙe yana murmurshin da kamata ya ɗaga cak ya ƙarasa da ita zuwa gaban gadon. Zata janye ya hana hakan, sai ma ƙoƙarin warware lafaya ɗin jikinta da yake yi. Ba yanda ya iya kuma dole ta bashi dama yayi yanda yake so. Daga ƙarshe ya rikice mata dan rigace doguwa a ciki mai mannewa a jiki data fidda komai na halittar da UBANGIJI yayi mata masha ALLAH. Ita ko duk ta daburce saboda kunya, ƙoƙarin ganin ta ja lafayar ma ta fara dan rufe jikin nata. Amma ya hana hakan ta hanyar riƙe hannun nata yana shinshinar wuyanta dake fidda wani ƙamshi na musamman daga shiryayyun turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387 na musamman da aka shirya musu, dan hatta kayan gyaran jikin da akai musu duk daga gare ta ne. Abinka da tuzurun ango ji yay komai ya ƙwace masa. Tuni ya manta da batun bazasu iya taɓa amaren nasu ba anan kusa kamar yanda suke ayyanawa a zukatansu. Su kansu su Lailah sun sakankance angunan nasu zasu barsu sai nan gaba kodan halin da ake ciki, amma sai ga saɓanin haka, dan jikin Ma'aruff har rawa yake ya ɗagata cak zuwa gadon bayan ya sake manne lips ɗinsu tamkar ɗazun.....      ★Banbancin da aka samu tsakanin Ja'afar da Ma'aruff shine, shi da farko lallashin tashi gimbiyar Shariffa kawai yayi a farko. Ya mata nasiha akan muhimmancin haƙuri duk da shima nasihar kamar yana yinta ne harda kansa. Hannu yasa ya share mata hawayen da suka jiƙe fuskarta sannan ya kamata ya miƙar shima yana miƙewa. Kusancinsu ya sakata jin kunya sosai ta kasa daurewa ta duƙar da kanta tana kallon ƙafafunsu. Amma sai ya saka hannu ya ɗago fuskar tata ta hanyar kamo haɓarta. Cike da raɗa ya furta,          “Sherry kalleni mana”.     Kanta ta girgiza alamar a'a.   Ya sake ƙanƙance murya da matsar da fuskar tasa gab da tata ya ce, “Why?”.       “Ina jin kunya Yaya J”.    Ta bashi amsa hawayen da take riƙewa na silalowa a saman kyakkyawar fuskarta”.        A hankali ya haɗiye abinda ya tokare nasa maƙoshin, kafin ya sake matsota jikinsa da ƙyau ya rungumeta. Murya a shaƙe irin ta mai damuwa ya ce, “Kina son nima na miki kukan?”.       Kanta ta girgiza masa alamar a'a tana jan shashsheka. Ya fara ɗan buga bayanta kaɗan-kaɗan alamar lallashi, sannan ya cigaba da faɗin, “Kiyi haƙuri, ko nace muyi haƙuri. Haka ALLAH ya tsara komai bamu isa canjawa ba. Ki ƙarfafa ni Sherry dan nima gab nake da faɗuwa. Ina jin tamkar bamuyima Dada da Yaya Imran adalci ba a wannan ranar. Kamar mun fifita buƙatarmu akan halin da suke ciki. Kwanaki goma sha huɗu kacal da yanke musu hukuncin zalunci da bamu da tabbacin kuɓutarsu an ɗaura mana aure. Miyasa su Mammah suka kasa fahimta ne?”.       Kuka mai raɗaɗi Shariffat ta saki, dan kalamansa na fita tamkar yana karanta abinda ke cikin zuciyarta ne. Ita ƙanwar Aunty Hafsat ce, kuma cousin's suke da su Imran, hasalima a gidan su Imran aka riƙesu su biyar ciff sakamakon rasuwar mahaifinsu tun ita bata wuce shekara tara a duniya ba. Yanda su Ja'afar ke ɗaukar Imran Yayansu jininsu haka suma suke kallon Dada a garesu. Da ƙyar Ja'afar ya share nashi hawayen, ya fara lallashinta da daɗaɗan kalamai. Sannan ya kama hannunta zuwa bayi sukai alwala. Sun gabatar da salla da addu'oin da suma a nasu ɓangaren mafi rinjaye suka tafi akan Imran da Dada. Shine ya fara miƙewa, ya je wadrobe ya ɗauka mata kayan barci ya dawo inda take. Kamata yay ya miƙar yana faɗin, “Kukan ya isa haka, canja kaya dare na ƙara yi, ga kaina na ciwo ina son na kwanta”.      Hawayenta ta share, ta amshi kayan ta nufi hanyar bayi. Bai hanata ba ya kai zaune bakin gado. Da gaske kansa ciwo yake kamar zai faɗi, dan haka ya kai kwance kawai yana rage fitilar ɗakin. Fin mintuna goma sannan ta fito, idanunsa a lumshe dan motsinta kawai yake ji. Sai dai jin shiru babu alamar ta ƙaraso wajen gadon ya sashi buɗe idanun a hankali. A mamakinsa can ya hangota kan sofa ta kwanta. Ya ɗan murmusa da buɗe baki a hankali cikin murya mai taushi ya kira yi sunanta..        “Sherry!”.     Amsawa tai a ƙasan maƙoshi, sakamakon kuka daya disar mata da murya.      “Mi kike yi anan?”.   Tana faman cuɗa hannayenta a waje guda ta ce, “Zan kwanta ne”.      “Kuma anan?”. Kanta ta jinjina masa. Sai ya ɗan girgiza kai yana wani murmushin. Cike da lallashi ya ce, “Toyi haƙuri ki dawo nan. In dai nine babu abinda zai faru barci kawai zamuyi. Zoma kimin addu'a kaina ciwo yake sosai”.      Ciwon kai daya ambata ya sata tashi ba musu ta nufesa. Sai dai sai faman gyaran wuyan riga take duk da mai ƙwala ne bai kuma mata yawa ba. Hasalima kayan wando da riga ne sun mata burun-burun. Hannun daya miƙa mata alamar tazo ta side ɗin da yake ya sata nufar can. Zata zauna a side drawer ya riƙo hannunta dole ta zauna a bakin gadon kusa da shi har jikinsu na gogar na juna. A haka ya ɗaura hannunta saman goshinsa da sanyin sa ya sashi sakin ajiyar zuciya. Ita kuma ɗumin goshin ya ratsata. Baiyi magana ba itama batace komai ba ta fara masa addu'ar ciwon kai tana tofa masa da shafawa. Fin mintuna biyar ta kammala, tana masa sannu zata miƙe ya hanata, zatai magana ya ce, “Shiiii!” yana kamota gaba ɗayanta a haka ya hawo da ita gadon, maimakon ya barta ta kwanta a gefensa sai ya barta a jikinsa a haka yaja musu bargo dan akwai ɗan sanyi-sanyi.      Ina ƙasa Shariffa ta shige ko zata huta da kunyarsa. Ga zuciyarta nata bugawar tsoron da har yana iya ji. Har cikin rai bata tunanin wani abu zai faru, a ganinta halin da suke ciki akan su Dada ai basu da lokacin wani abu kuma a yanzu. Amma mi a bazata taji saukar hancinsa akan wuyanta yana bin ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Da aka zazzage musu kala-kala a jikin. Ga wanda akai musu gyaran jiki. Ga kabasa da akai musu turaren kaya. Ga khumra kusan kala uku da aka basu suka shafa, gana man gashi, ga oils. Hatta ƙanshin sashen duk turaren wutar SHUWA INCENSE AND MORE ne. Al'amarin kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan tana tunani kawai sai jin saukar lips ɗinsa tayi a cikin bakinta. Kafin tayi wani yunƙuri ya sake matseta yana yanda yaso. Da ƙyar ya iya raba lips ɗinsu yana faɗin, “Sherry wannan wane irin turare ne mai canja tunani da hana gangar jiki zama lafiya ya rabbi.”       Bai ma bari ta bashi amsa ba ya sake ɗaukar wani sabon salon mai gigitarwa, ai duk yanda yaso control ɗin kansa da batun damuwa da barinta ba yanzu ba shima a nashi ɓangaren lissafin ya canja gaba ɗaya. Dan kuwa dai mai afkuwa ta afku ya bar Sherry ɗin tasa da kuka da magiyar neman ceto. Sai dai a wannan gaɓar babu mai jinta balle ya kawo taimakon, kamar yanda babu mai jin kukan aminiyarta Lailatyn ya Ma'aruff dake can itama tana amsar sakamakon nata ƙamshin turaren.      Masu karatu sai ku gayama Maman Abdull kayanta sun haɗa yaƙin ƙasa da ƙasa. Tai maza ta kawo ɗaukin ruwan zafi inba haka ba mu tattaro mumu zuwa gidanta a bamu rabonmu. Koda yake nifa na riga na kama nawa rabon mutanena. Kuma ku garzaya ku amshi naku dan wlhy turarrukan nan ba ƙarya, ni shaida ce a kansu ƙwarai da gaske. Ba amare kawai ba har uwargida kina buƙatarsu kodan faranta ranki da ƙamshi, balle ma idan oga yaji shima fa zai iya rikiɗewa zuwa Yaya Ma'aruff da Yaya Ja'afar. SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Kar ku bari a yi babu ku, tana aika kaya a duk inda kake har wajen Nigeria makwaftanmu. Ga arha ga mutunta customers abin sai wanda ya gani. SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Tabbaci ne na haƙiƙa daga ni Bilyn Abdull dan na gwada na tabbatar😘😘💃. Washe gari sai ga angunan da aka kora tsitt kake ji, suna can suna aikin lallashi da sanya albarka. Dan kuwa suma dai sun isa duniya mai tsada da sai ɗan gata ɗan ƙwarai ke zuwanta har ya zame masa tarihi a ranar farko. Babu abinda zasuce da UBANGIJI sai godiya. Tare da addu'a da fatan ALLAH ya fito musu da su Dada anan kusa dan farin cikinsu ya ƙara girma. Maman Abdull kam dole ne taci ƙyauta ta musamman...........✍️ KIDA A RUWA 2 3 ..........Itama dai Nabeeha tun da batun kama Zak-Shadow ya ɓulla hankalinta ya tashi, a lokacin suna umara ita da uwarta. Dan bayan tabar gidan da ita umara suka tafi ita da yaran kaf, wai first lady ce ta biya musu. Hankali tashe ta matsawa uwar suka dawo Nigeria, duk wani tsalle-tsallen tashin hankali da ita akayi sa, kamar abin arziƙi ta dawo gidai, sai dai ana fara bikin su Ja'afar mahaifiyarta ta janye ra'ayinta ta sake barin gidan ta koma gidanta ba'ai bikin da ita ba sam, daga baya kuma ta janyeta suka koma Dubai inda harkokinta sukafi yawa yanzu. Sai bayan da aka yanke ma su Dadan hukunci da fin wata uku ta ɗanzo ƙasar, shima basu wani jima ba ta sake komawa, acewarta bazata iya zama cikin tashin hankali da damuwar tuna Haysam na tsare ba, tsarewar da har lokacin an hana kowa ganinsa kusan shekara ɗaya. Tun daga nan data koma bata sake waiwayen ƙasar ba sai a 2016, sannan Zak-Shadow da Imran nada shekaru uku a gidan yari. A kuma lokacin ne aka saki Imran saboda kai-kawon da matasa suka cigaba da yi har lokacin batare da nuna gajiyawa ba, na Zak-Shadow ne dai yayi tsamari da yawa, shima kuma sunce bazasu sare ba zasu cigaba da gwagwarmaya... A dalilin dagewar General Yusuf Shu'aibu... Na ganin an saki Dada kamar yanda aka saki Imran akai masa ritaya, dan kuwa ƙungiyar duhu sun fahimci shine ke tsaye kan matasan dake kai-kawo akan al'amarin Zak-Shadow da Imran ɗin, ga shi kuma sunci nasara akan fidda Imran saura Dada, dan haka sukai gaggawar sakawa a daƙileshi dan zuwa yanzu sunyi matuƙar jan hankalin ƴan siyasa a cikin tafiyar tasu fiye da zaton mai hasashe. Satin Imran ɗaya da fitowa aka sauke General Yusuf Shu'aibu Tafida aka maye gurbinsa da wani. Wannan canji yayi matuƙar kawo ka-ce-na-ce da cecekuce a cikin ƙasa dama kafofin yaɗa labarai, sai dai gwamnati ta toshe kunnuwanta da yin kunnen uwar shegu da komai ta nuna babu gudu babu ja da baya. Bayan ɗaukar lokaci komai ya lafa dole ƴan ƙasa suka amshi sabon canji. General Yusuf mai ritaya yaji zafin abinda ya faru, sai dai bai nuna ba ya shanye komai tare da komawa gefe kamar yanda akaso. Abu ɗaya ne bai haƙura da shi ba shine ganin Imran ya koma kan aikinsa, duk da shi a lokacin ya nuna baya buƙatar cigaba da aikin soja kuma. Amma Janar ɗin ya tsaya tsayin daka ya fahimtar da shi ammafanin cigaba da aikinsa ne kawai zasu samu taimakon fitowar Zak-Shadow batare daya cika shekaru ashirin da biyar ɗin da aka ɗiba masa ba. Jin haka yasa Imran yarda ya koma kan aiki duk da kuwa a lokacin watansa ɗaya kacal da fitowa a kurkuku... Tabbas shawarar Janar tayi amfani, dan kuwa komawar Imran aiki ta bashi damar ganawa da Zak-Shadow a karo na farko. A lokacin daya samu umarnin samun wannan damar sai da hawaye suka zubo masa. Imran na matuƙar son Haysam, soyayya irin mara misali ɗin nan da UBANGIJI ne kawai mai tafiyar da ita a zukatan bayi batare da sun san taya take gudana ba...... >>><<•>><<< 21/11/2016 Ranar Litinin ƙarfe goma sha ɗaya na safe Imran ya nufi Special Military Corrections Facility, North Central Command Base inda Zak-Shadow yake. Rana ce da ta fi kowace rana nauyin da sanya zuciya zumuɗi da rauni a lokaci ɗaya a ƙirjin Major Imran Abbas. A daren jiya bai runtsa ba tunda ya samu tabbacin amincewar zuwan nasa. Kai gaba ɗaya ma kasa zaune kasa tsaye yayi tun da yaga sakon janar mai ritaya ya shigo wayarsa _(An amince. Zaka iya ganin sa gobe. Imran kada ka yi wani abu da zai rikita zuciyarka wannan dama ce muka samu)_ Sai zuciyarsa ta tsaya cak tana mai tsitsinkewa, kai jikinsa kansa tsuma ya dinga yi har sai da Aunty Hafsat ta jeho masa tambaya. Amma sai bai iya bata amsa ba ya girgiza kai kawai. Shekaru uku kenan ba tare da yaga fuskar Haysam ba. Shekaru uku na tambayoyi, na tunani, na laifi da raɗaɗin rabuwa. Shekaru uku na jin kamar mutuwa mai yankewa ta yanke wannan alaƙar ta har abada. Zaman prison bai jikata zuciyarsa ba kamar tunanin halin da Haysam ke ciki. Cikin dabara ya kai hannu yana share guntayen hawayen da suka taru masa a gefen ido... Washe gari tunda sassafe ya baro gidansa saboda tsabar zumuɗi, maimakon office kuwa kai tsaye Special Military Corrections Facility North Central Command Base ya wuce. Haka ya samu waje can nesa da prison ɗin ya tsaya zaman kusan awanni uku har lokacin da aka bashi ya cika sannan ya kunna motar ya karasa. A hankali motar sa ta tsaya a gaban babban ƙofar ƙaton gate ɗin. Tsaron wajen ya banbanta da duk wani waje da Imran ya taɓa gani, dan shi ba'a nan aka ajiye shi ba a nashi zaman. Birgedun sojoji biyu a wajen ƙofar, camaras a jikin bango, wasu guards suna sintiri cikin takun da ke nuna horo mai tsauri a wajen. “Major Imran Abbas?” ɗaya daga cikin guards ɗin ya tambaya. “Eh, ni ne”. Muryarsa ta yi nauyi kamar anyi masa sarƙa a wuya saboda yanda yake jin kansa da zuciyarsa dake bugawa da sauri-sauri. “Follow me, sir.” Kansa kawai ya jinjina, a ƙasan zuciyarsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya bi guards ɗin zuwa wani dogon corridor da yake a tsaftace alamar ana kula da wajen sosai fiye da kima. Daga can suka kai shi wani ɗaki da shima yake zagaye da camaras kamar tsiya. “Ka ajiye wallet, takardu, da belt. Za a bincika ka kafin a shiga.” Babu wani nuna damuwa Imran ya cire belt ɗinsa dan wannan yasan dokar soja ce. Bai taɓa tunanin zai zo wannan wuri saboda Haysam ba. Bai taɓa hango cewa watarana ƙaddara zata kwaso su zuwa wannan ramin mai tudu da kwazazzabo ba. Bayan an kammala bincike sa yanda ya dace suka fita a ɗakin, wani ƙaramin ɗakin ganawa suka kai shi, wanda ke da tebur biyu da gilashi tsakanin su. Amma shi an canja musu saboda matsayinsa daga shi har Zak-Shadow ɗin, dan haka aka basu ɗaki na musamman ba tare da gilashi tsakanin su ba. Wani irin duka zuciyar Imran take tamkar ƙarfen agogo dake bada sakanni na motsawa ne da ita. Minti biyar.. Minti goma.. shiru. Sai zuciyar Imran ta ƙara ƙarfin bugawa kamar bugun gangar yaƙi, dan adadin mintinan da aka saka zai iya fitowa sun cika.. Dai dai nan kuwa aka buɗe ƙofa a hankali. Sojoji biyu suka shigo da Lt. Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi. Sai dai ba irin Zak-Shadow ɗin da duniya ta sani bane a baya. Wannan Zak-Shadow ɗin ya canja da canje-canje masu yawan gaske, musamman a suffa ta soja zuwa wani abu daban, gashinsa ya yi tsawo sosai sama da yadda yake da, fuskarsa ta ajiye saje saɓanin da da babu ko ɗigon gashi a fuskarsa saboda kasancewarsa soja, fuskar sa ta ɗan rame amma kwarijin da cikar kamalar da gizago zaratan MAZAJEN na nan shimfiɗe a kanta. Ga tambarin sallarsa ya sake fita baƙi sosai akan goshinsa saboda hasken zaman waje ɗaya da fatarsa ta sake yi, ainahin haskensa na da kafin wahalar soja ta dusar da shi ya sake bayyana. Idanun nan kam sun wani sake juyewa kamar na kumurcin maciji. Hannunsa na sanye da ƙananan cuffs saboda dokar prison. Shi dama can bamai ƙiba bane, amma jikinsa a buɗe yake da ginannen ƙarfi irin na masu kulawa da tattali, dan haka ko a yanzu bazakace ya rame na tashin hankali ba, dan daga ganinsa kasan bai daina motsa jikin ba, zaka tabbatar da haka saboda takunsa dai nasa ne na soja mai ji da kansa, ko a cikin jeji, ko a cikin duhu. Ko a cikin bainar jama'a wannan takun ƙasaitar da jarumta baya canjawa. Ya ɗan tsaya kafin ya zauna. Sai kuma ya kalli guards ɗin da juyayyun idanunsa ya kaɗa kai kaɗan. Su sun san nan ɗin ba wajen wargi bane, dan ko KURA TA RAME TAFI ƘARFIN WAWASON ƘANANUN NAMUN JEJI. Ga shi dai a tsare, amma takashi ko manyan KAYA sun gagara, shiyyasa a tsaren yake amma girmamawa babu abinda ya canja. Ai ko mahaukaci yasan kallon ZAKI sai daga nesa, a nesan ma daga bayan keji, dan ko hannu ya samu zai iya yin wawaso. Yafi ƙarfin kallon banza ma balle ace za'a dake shi. Fitar kuwa sukai da sauri suka barsu su kaɗai. Shiru ya cika ɗakin. Shiru mai nauyin da ko ƙarar bindiga da harbi bai zama lallai ta iya yankesa ba. Su duka biyun sun zubama juna ido ne kawai kamar masu kallo a cinema. Imran ya ji hawaye sun cika masa ƙwayar ido. Amma ya danne. Zuciyarsa na ƙaraji. Dole ya kauda nasa idanun da kansa gefe yana ƙoƙarin haɗiye hawayen. ReceivedZak-Shadow ya ɗan girgiza kansa, tare da zama, a hankali ya jingina bayan sa da kujerar. Juyayyun idanunsa suka sauka a fuskar Imran daya sake juyowa kamar yana lissafa duk wani abu da bai faɗa masa ba shekaru uku da suka shuɗe. Ganin Imran bashi da niyyar yin magana shi ya motsa nashi lips ɗin da sukai jazur cikin dakakkiyar golden voice ɗinsa dake cike da izza da amo ya furta, “Major Imran Abbas.” Kalmomi uku ne kacal. Amma Imran ya jisu har cikin tsakiyar zuciyarsa da brain. Da ƙyar ya iya dauriyar amsa wa da. “Sir…” Muryarsa ta kasa fita gaba ɗaya saboda sabbin hawayen dake cika masa idanu.........✍️KIDA A RUWA 2 4 ........Dada dake kallonsa kallo mai cike da ƙauna daga UBANGIJI ya ɗan ɗaga hannunsa yana masa Alamar ka tsaya ka nutsu. Sai kuma ya sake motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta “You’re a soldier Imran… but seeing you like this is giving me a headache. What’s happening to you?why are you acting like a woman?”. Shima ya ɗan kawar da kansa gefe saboda idanunsa na son suyi wani abu saboda hawayen da suka sakko a fuskar Imran sharrrr. Kuka ko ɓacin rai ne shi kansa bai ma san wannene yake ji da ganin hawayen Imran ɗin ba. Cikin dakewarsa, idanunsa na kallon gefe ya sake furta, “Bazan tambayeka yaya kowa yake ba? Dan hakan shine mafi girman abinda zai sosa min ZUCIYA. Na ganka, shi ne abinda yafi komai muhimmanci Imran.”         Da ƙyar Imran ya tsaida hawayensa. Fuskarsa da murmurshin ƙarfin hali ya ɗan matsa gaba, hannayensa duk biyu ya ɗaura kan teburin. “Munyi ƙoƙari.. Munyi komai… amma suka zaɓi yimana wannan zaluncin Haysam…”       Dada ya katse shi da murya mai sanyi amma mai ƙarfi da nutsuwa, “Ba zalunci bane. Siyasa ce. Dama kuma ita siyasa ai ba ta rabuwa da jini.”      Kai Imran ya girgiza. Cikin son ƙarfafa kai ya ce, “Na fahimta, kenan sun kulle ka saboda sun tsorata. Sun tsorata da kai. Sun tsorata da gaskiya. Sun tsorata da abin da ka sani”.        “Na sani.”      Dada ya furta a hankali yana ɗan murmurshi. Shiru ya sake mamaye ɗakin kowa da abinda yake tunani, fin sakan goma ya maida kallonsa kan Imran kai tsaye, kallon da ya tattara shekara uku masu zurfi: jarunta, kewa, hikima, da raɗaɗin da ya gama zagaye zuciyar mutum daga mutum ta zama tamkar dutse.         Imran ya katse shirun da faɗin, “Kurakuraina suka kawo ka nan Haysam, zan sadaukar da rayuwata domin ganin ka fita kuma” ya share hawayen da suka sake silalo masa, batare daya bari yayi magana ba ya cigaba da faɗin, “Bayan rufe mu sun sauke COAS shima, sai dai bai daina gwagwarmaya ba, dan yanzu haka da tsayawarsa nazo nan.”        Idanu Dada ya lumshe a hankali, batare da kula zancen Imran na farko ba ya furta, “ALLAH ya saka masa da alkairi, dama nasan ba zasu barshi ba shi da duk masu goya mana baya. Imran… ka dawo min nan idan ka samu lokaci. Muna da magana mai tsawo. Kuma kada ka sake jin damuwa. Kai kaɗai ne wanda ban taɓa zargi ba.”       Idanun Imran suka sake zubo hawaye saboda wannan kalmomi na ƙarshe. Cikin jinjina kai ya ce, “Zak… har abada damuwa bazata barni ba in har kana a wannan wajen. Dan haka bazan taɓa barin ka a nan ba har abada”.        Dada ya yi murmushi. Ba mai annuri ko farin ciki ba. Murmushi ne kawai irin na jarumta da taurin zuciya. Shi yasan fitarsa a wannan wajen sai wani ikon ALLAH, amma ba abune mai sauƙi ba.       “Karka damu Imran. Ina a nan ne. Amma ba zan tsaya nan ɗin ba kamar yanda ƙaramin tunaninsu ke basu”. Sai ya jingina da kujera yana ɗan lumshe ido. “Kamar yanda na gaya maka kai ƙoƙari ka dawo. Idan ba haka ba ka fara zargina da guduwa, dan babu gudu babu ja da baya sai na ƙarasa wannan aikin”.        Tabbas Imran ya tabbatar da alwashinsa cikin idanunsa da suka sake rikicewa, ya kuma san wanene Zak-Shadow ɗinsa, kaɗan daga aikinsa ya aikata dukkan abinda ya ƙudurta. Zama ya gyara cikin sassauta murya dan baya son akai ga matakin da Haysam ke harin saboda komai zai sake jagulewa ne.       “Dan ALLAH kar akai ga haka MAZAN FAMA. Ina sha ALLAHU zan dawo. Zan dawo duk rintsi, zan......”        Motsin buɗe ƙofar da ake yi ya katse Imran. Sojojin ɗazun ne suka dawo, hakan ya sasu fahimtar lokaci ya cika. Dan haka kafin ma suyi magana Dada ya miƙe abinsa, sai kuma ya ɗan zubama Imran ido na sakan ɗaya, kafin cikin dakakkiyar muryarsa ya furta, “Imran…”      Imran ya ɗago kai yana kallonsa fuskarsa cike da damuwa da kewa..           Ƙaramin murmushi yay masa, tare da furta, “Ka tsare min kanka. Daga yanzu ka saka a ranka sabuwar ƙaddara ta fara motsi.” Daga haka ya juya abinsa yay gaba, ya bar Imran cikin shiru mai nauyin da bin bayansu da kallo, idanunsa cike da hawaye, dan a wannan ƙadamin yama manta da kansa a matsayin soja.......       <<>><<>><<>><<>>  Imran ya ɗan sake murmusawa yana shafa kai, cike da girmamawa ya ce, “Sir zan sha ruwan dai, abinci kuwa amin afuwa kada madam tayi fushi nabar nata”.       Ƙaramar dariya Genaral yayi duk da kuwa shima ba mutum ne mai yawan fara'a ba. Cike da dattako ya ce, “Gaskiya bazan so ɗiyata kam tai fushi ba. Amma duk da haka sai kaci, dan na saka an shirya maka ne na musamman”.     Babu yanda Imran ya iya dole ya haƙura suka hau teburin cin abincin da aka cika da kayan daɗi. Sai da suka fara cin abincin cikin nutsuwa falon shiru janar ya katse shirun da faɗin, “Ina fatan babu wata damuwa tare da Haysam? Yana cikin ƙoshin kafiya?”.        Sai da Imran ya haɗiye abincin bakinsa sannan ya jinjina kansa, sai dai fuskarsa ta janza zuwa damuwa. “Alhamdullih Sir. Babu wata bayananniyar damuwa ta zahiri. Dama kuma mun san bayan killacewa babu abinda zai yarda ya ɗauka ga wani na ƙasƙanci in dai Haysam ne. Dan har yanzu JININ MAZA na'a kan FARCE”.       Sosai Janar yay murmurshi mai faɗi. Ya ɗauki ruwa yana tsiyayawa a kofin gilashi. “Wato Imran da ƙasar nan tasan asarar da tayi na killace Haysam na kwana ɗaya kawai data jima da yima kanta da kanta ALLAH ya isa. Balle ma ace na tsawon shekaru uku da wasu watanni. Irinsu Haysam a ƙasa tamkar hasken diamond ne a tsakiyar sahara. Amma ban san miyasa ba, maimakon aga haskensu anfi kallon wahalar ɗakkosu da gujewa zafin saharar ne da yawanta..”         “Sir bazasu fahimta ba, irinku ƙalilanne ke fahimta saboda zukata masu ƙyau da ALLAH ya baku. Amma wlhy a tsayin rayuwata ban taɓa cin karo da mutum mai tsananin kishin ƙasa da son cigabanta ba irin Haysam. Mutum ne shi mara tsoro, mai tsayawa akan gaskiyarsa koda kuwa ace zata ƙona shi. Sannan yana so da sauri, shiyyasa yake komai da sauri. Amma na rasa miya tare musu?”........✍️ 5 .......Falo ne babban gaske, sai dai gaba ɗaya an kashe fitulun cikinsa sai wasu candles da basufi uku ba kacal aka bari suna ci, suma a cikin kwalba suke dan haka haskensu baida tasiri mai yawa sosai. Yanayin duhun wajen ya ɓoye ainahin fuskokin mutanen dake zaune a cikin falon harma da sirrin tsarinsa, koda yake fuskokinsun ma a rufe suke da facemask ta yanda koda ace akwai hasken wutar baka isa tantance su wanene ba. Cikin wani ɓoyayyen harshe suke magana, harshen da babu makamncinsa a ƙasarmu. Sai ɗan ƙarar kofuna alamar akwai abinda ake sha, sai ko room hitter dake basu ɗumi saboda yanayin sanyi da ake ciki. (Waɗan nan sune manyan munafukan shaiɗanci, kowannen su nada laƙabin suna, dan babu mai amfani da sunansa na yanka balle kasan ainahinsa a addini ko yanki balle harshen yare. Hasalima gamayyace daga ɓangarori ta waje da cikin gida).           Ɗaya daga cikinsu ne ya ajiye kofin shayin hannunsa, tare da yin gyaran murya. Lokaci ɗaya abokan zaman nashi duk suka nutsu, tare da maida dukkan hankalinsu garesa. Cikin harshen da suke maganar ya furta, “Ya kamata muyi abinda ya tara mu, dan bamu da lokaci isashshe”.        “Tabbas haka ne Black Spider. Yanzu minene a teburin mu?”.      Zama Black Spider ya gyara, tare da nutsuwa sosai ya ɗauki remote yana dannawa. Hoton Zak-Shadow ne ya bayyana a jikin ƙaton majigin daya cinye kusan rabin bango, tsayayyen jarumin soja, da ko'a hoton kasan eh da gaske Gwarzan maza ne, dan kuwa a cikin uniform ɗin aiki yake, alamu kuma sun tabbatar yana kan aiki akai masa hoton batare daya sani ba, hakan kuma bai hanashi fita da ƙyau ba kuma tartar har kwarjininsa na dukan zukatan maƙiya koda basu bayyana a fili ba. Amma yanda duk suka ja numfashi a lokaci guda zai baka tabbacin hakan.       Black Spider ya fara jawabi kamar haka, “Wannan mutumin ya lalata shirye-shiryemu a gabashi da yammaci da yawan gaske da bazasu ƙididdigu ba koda a kintace. Mun ƙyaleshi badan yafi ƙarfinmu ba, sai dan bashi dama ya gama taka irin tashi rawar kafin mu canja masa salon kiɗa. Lokacin mu ya yi a wannan gaɓar. Duk da a baya Target ɗinmu Zak-Shadow ya ci gaba da zama cikas a shirye-shiryenmu. Dabarun mu da yawa sun durƙushe a gabansa. Amma yanzu, lokacin da muke jira ya iso garemu, wato dama ta dawo hannunmu.”       Cikin wata ƴar iskar dariya Viper ya amshe zancen da murya mai taushi amma cike da shaiɗanci irin ta shaiɗanun azzalumai, “Kamar yanda Black Spider ya faɗa a yanzun nan babu jimawa mun tabbatar da bayanin sirri ta hanyar yaran Dagger. Zak-Shadow ya bar sansaninsa na tsaro domin wata tafiya ta sirri a jejin, sai dai bamu san inda ya nufa ba, amma hakan mu ba damuwarmu bace kai tsaye, duk da dolene mu sani dan aikinmu ya tafi yanda ya dace akansa. Wannan shi ne gibin da ba zai taɓa tsammani ya bari ba a gaɓar da zai fuskanci illarmu mai muni, dan zamu zuba masa dafinmu mai ƙarfi da har abada babu makarin warkewarsa a zuciyarsa”.       Dariya suka kece da ita a tare, sai kuma suka koma tsitt kowa ya nutsu. Dagger da sam bai dara ba sanda ake dariyar, sai ma danna hannunsa da yake a kan tebur da ƙarfi cike da fusata, dan shi kaɗai yasan adadi tsanar da yayma Zak-Shadow a duniyar nan, saboda shine ya kashe masa ƙaninsa a wani hari na bayanan sirri da basu san yaya akai Zak-Shadow ɗin ya bankaɗo ba a kansu. Cikin kaushin harshe ya fara faɗin, “Sirs! Nayi muku alƙawari gamu mayaƙanku ba za mu bari wannan dama ta sulale ba! Dole mu kafa tarkon da zai karya ƙarfinsa gaba ɗaya. Zan jagoranci ɓangarena da ƙyau kuma da tabbatar cikar buri fiye da baya! Dan ina son da hannuna na gurfanar da shi a ƙasan ƙafafu na cike da ƙasƙanci da wulaƙantarwa. Dolene ya ɗanɗani fiye da abinda na ɗanɗana a wancan karon, da ace zaku bani dama bashi ba kaf ahalinsa sai na shafe babinsu a doron wannan ƙasar, na kuma........”      Mr Specter ya katse shi cikin jan girma, dan kuwa dukansu Dagger matsayin yaronsu yake, matsayinsa kawai shine shugaban mayaƙansu, hakan na nufin amfani ake da shi domin cimma manufa, kawai dai ita tunkunyar sharri ba'a banbance farfesun kayan ciki a cikinta, haɗawa ake har kashin dabbar da ruwan *_Typing📲_* *_💦KIƊA A RUWA...!!💦_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_GENERAL FICTION_* _Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._ *_BOOK 2_* _Chapter 6_ __________________ _A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ INSTAGRAM 👇🏻👇🏻👇🏻 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP 👇🏻👇🏻 wa.me/2349030398006 TIKTOK 👇🏻 https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1 Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻 __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ ..........“Ku fara da gaskiyar Ojo. Akwai wani abu da bai dace ba. Kuma akwai hannaye da yawa da suka fi mu ƙarfi har a cikin gida. Sai dai fuska biyun su tasa sun zame mana masu lulluɓin biri”.     Shiru ya cika ɗakin. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar Imran. Cikin kasa haƙuri ya furta, “Idan kuwa har akwai masu fuska biyu zan kasance mai tsoro da shakkar mu'amulantar kowa?”.        “Wannan shine gaskiyar magana, amma a ciki akwai ɗaya tamkar da dubu. General Yusuf Shu'aibu Tafida. Col. Haydar Galadima (Faro), Brigadier General Abraham Yohana, yaranmu Dabo, Yusuf. Amma saura duk ka ajiye kowa. Akwai saƙo a ɗakina na ajiye maka, idan ka haɗa da wannan zai baka abinda nake buƙatar ka fahimta. Dan na tabbatar daga yau bazasu sake barinka ka ganni ba.”      Da ƙyar Imran ya iya furta, “Janar ya shiga SIYASA...”          Cak numfashin Zak-Shadow ya tsaya, hakama bugun zuciyarsa kafin su dawo a tare. “SIYASA?!”. Ya furta yana tsatstsare Imran da idanu.       Kai tsaye Imran ya jinjina masa kai. Sai kawai Dada yayi murmurshi tare da wani ɗan lumshe idanu sannan ya sake buɗesu luuu akan Imran. “Na amince kayi aiki da shi Imran....”      Cikin tsatstsareshi da idanun shima Imran ya ce, “Zak… kana nufin kaci karo da mutanen da kowa yaji tsoron ɗaga su?”.      Wani ƙaramin murmushi mai zafi, mai ɗaci ya bayyana a gefen labban Dada. “Ni ba wanda nake tsoro, Imran. Amma gaskiya… ita ce abin da suka hana ni gani tsawon shekaru uku. Ni kaina kuma na yarda da hasashen General, ta irin hanyar da suke kai, kawai zamu bi mu gano su, mu kuma yaƙe su” ya ɗanyi shiru na sakan biyu. Sai kuma ya cigaba da faɗin, “Yau na baka wannan rubutun. Ka tafi da shi. Kada ka bari kowa ya gani a yanzu har Janar. Dan kai kaɗai nake son kayi waɗan nan binciken”       Idanu kawai Imran ya kafeshi da su ya ma kasa magana. Wato idan Zak.. ɗinsa na wani abu a wasu lokutan yakan ga tamkar mai aljanu ko mai gani har hanji da yara kan faɗa. Kai har ɗan duba ma zai iya kiransa, amma yasan duk ba haka bane, tsabar kaifin basira ne kawai da iya sanin kan duniya da mutanen cikinta da ALLAH ya bashi.     Shi ko Dada ganin kallon da Imran ɗin ke masa, sai kawai ya jingina da kujera a hankali ya lumshe idanunsa. A haka ya ce, “Ban san miya baka mamaki ba ka tsaya kana kallona bayan lokacin ka ƙayyadadde ne. Idan rana ta yi zaka gane me yasa naga mutuwa ta fi wannan shari’ar sauƙi.”     Imran ya kasa magana yanzun ma, a haka har lokaci ya ƙare, masu tsaronsa suka buga ƙofa. Miƙewa kawai Dada yayi zai bar gurin, sai kuma ya tsaya ya kalle shi for the last time yasan kafin a sake ganin juna sai bayan shekaru. Dada ya lumshe ido tare da furta masa a hankali kamar sirrin da baya buƙatar iska ta ɗauka zuwa gaba a tsakanin su.       “Ka zama hasken da nake bukata a waje. Ka cigaba da zama UBA kuma nagartaccen MIJI a cikin GIDA”. Daga haka yay gaba batare da ko waiwayen Imran ba. Shi ko Imran ya kasa motsi sai kai-kawo furucin ƙarshe na Zak-Shadow ɗin ke masa amsa kuwwa a cikin kai, dan magana ce a dunƙule ya bashi kuma mai ƙarfi.....    (((★)))(((★)))(((★)))          ★ 2021..... ★        Duk wanda yasan gidan a shekarun baya takwas da suka shuɗe yanzu idan ya zo ba lallai ya gane ba. Domin kuwa gidan nan da Mammah da yaranta tara mai sassa biyu kacal a yanzu ya zama mai sassa da yawa sakamakon iyalanta da suka ƙara yawa. Kamar yanda Dada ya barma Imran wasiyyar dawo da ginin su Ma'aruff a cikin gida a wacan lokacin hakan ta tabbata, duk da kuwa shima Imran ɗin dole ya bar ragamar a hannun Uncle Nasiru sakamakon prison ɗin daya shiga na shekara uku.      Duk da suna cikin ɗacin yanayi Uncle Nasiru yayi abinda ya dace harda kuɗin aljihunsa. Anyi bikin Ma'aruff da Ja'afar da amarensu Shariffa da Lailah, sai dai bikin baiyi armashi ba sakamon jarabawar da wannan ahali suke ciki a wancan lokaci na rasa jigon gidan da suke ma kallon Uba bawai yaya kawai ba. Amare sun tare a gidan Mammah kowace da ɓangarenta, kuma Alhamdullah dukansu masu tarbiyya ne da suka fito daga gidan tarbiyya. Dan kuwa akwai abubuwa da yawan gaske da suka bambanta su da surukar gidan ta farko Nabeeha. Mammah mace ce mai sauƙin kai da sanin haƙƙin ɗan adam, tana da zafi idan kace zaka kawo mata wargi, dan in har kaji muryarta a sama lallai an kaita maƙura ne. Duk wanda yazo jikinta ya zama ɗa na halak da zata haɗe da nata ƴaƴan ya riƙe babu bambanci a ciki, wannan yasa biyayya da nutsuwar Aunty Shariffa da Aunty Lailah ya basu fiye da abinda suke zato da farin ciki a gidan aurensu. Dan kuwa suna matuƙar kiyaye al'amarin Mammah a matsayinta na uwa, hakama ƙannen su Ma'aruff sun maida su ƴan uwansu na jini ba dangin miji ba, sai hakan ya bada masalaha da shaƙuwa mai ƙayatarwa da birgewa a wannan gidan, idan ka cire rashin Dada dake zagaye da zukatansu dan suna jin hakan a ransu a kowacce rana tamkar sabo. Babu ranar banza da zata zo ya wuce ba'ai hirar Dada ba, za kuma ka samu hatta su Ma'aruff dake magidanta kuma manya yanzu a gidan sai sunyi kuka suma. Mammah ce kawai jaruma mai danne komai a gabansu sai dai idan tana ita kaɗai ta share hawaye.       Shekarar su Lailah ɗaya a gidan duk suka haihu, kuma Alhamdullah haihuwar tasu babu wani nisa tsakani. Dukan su yara maza suka samu, kuma yaran sunan Dada da Imran aka saka musu wato Haysam da Imran. Sai dai ana musu alkunya da Abees da Aheel. A shekarar da Imran ya fito bayan ya gana da Dada sau biyu sannan suna cika shekara uku-uku da aure suka sake haihuwa, sai dai wannan karon Shariffa mace ta samu, ita kuma Lailah Namiji. Bayan haihuwar tasu ne kuma Imran ya sake tada saban aikin gyaran gidan na su Mammah. Dan kuwa gaba ɗaya aka rushe sashen Mammah dana su Zak-Shadow tunda Nabeeha ba zama take ba sai jefi-jefi take zuwa gidan, shima ɗaukar wani abu ne ke kawota,  wani lokacin ma sai tazo ta fita su Mammah basu sani ba. A wannan karon ne akama gidan gyara fiye dana baya, dan komai da fasalinsa an canja, hatta Ammar da Bilal an musu nasu ɓangaren. Sai ya zama anyi sashe huɗu ta can baya, an fitar da gate ta wancan Street ɗin, ta cikin gida akwai katanga tsakanin ɓangaren su Ja'afar ɗin dana su Mammah da Dada da suma suke su biyu. Tsarin ya bada kamar gida biyu. Dada da Mammah a sashe ɗaya, su Ma'aruff su huɗu a sashe ɗaya sai dai kowa da part ɗinsa, akwai katanga tsakaninsu amma akwai ƙofar da zaka iya shigowa sashen su Mammah basai ka zagaya ta wajen gate ba. Wannan gyara shine ya sake sauya gidan Mammah daga mai sashe biyu na talaka mai ƙaramin ƙarfi zuwa na masu rufin asiri da wadatar zuci a yanzu, ga irinmu ma talakawa kai tsaye zamu kirashi ana masu kuɗi..... ))))(((()))))((((       A ɓangaren Imran yanzu haka dai shekarunsa biyar kenan da ganawa da Dada dake cika shekaru 8 a prison, kamar yanda Dada ɗin yay hasashe ya faɗa kuwa ba'a sake bashi damar ganinsa ba. Babu irin shiga da fitar da baiyi ba amma sun hana masa damar sake ganinsa. Dan haka Janar ya zauna ya lallashesa akan yayi haƙuri komai yana da lokacin sa.      Badan hankalin Imran ya samu kwanciya ba ya haƙura. Sai dai ya maida hankali akan binciken dukkan abubuwan da Dada ɗin ya bashi. Sannan yaje ya ɗauki saƙon daya ce ya ajiye masa. Inda saƙon ya fahimtar da shi abinda Dada ya shirya. Dole ya ajiye batun damuwarsa da kewarsa a gefe ya maida hankali akan aiki yanda ya kamata....       Burin Janar ya cika na shigewa cikin siyasa tsundum da sha'anin ƴan siyasa. Cikin nasara ya lashe kujerar da aka tsaida shi a takarar ɗan majalisan tarayya. A yanzu haka yayi ɗan majalisa shekara huɗu kenan. A kuma yanzu haka ana shirin sake buga tambarin sabon zaɓe, babban shirinsa kuma shine fitowa takarar shugaban ƙasa. A gefe kuwa Imran ya sake samun girma zuwa Colonel saboda kwantar da kai da yayi shima bisa shawarwarin General ɗin dana Dada..... ✷✷>><<✷✷>><<✷✷ ★SCHOOL★           “Yau sai naga waye ubanku a cikin ƙasar nan, ƴan iskan yara kawai kamar wasu ƴan daba ku kama min yarinya da duka, koni dana haifeta da ubanta bamu taɓa dukanta haka ba. To wlhy idan kuna taɓa wasu ku zauna lafiya yanzu kun taɓoma kanku kuwa, dan har prison sai na saka ubanku yayi bama ku ba.......”       “Ranki ya daɗe dan ALLAH kiyi haƙuri, mahaifinsu bashi da laifin komai sune sukai miki ba daidai ba. Wlhy mu kammu yaran nan sun kai mana wuya a makarantar nan, kawai dai babu yanda muka iya ne.....”       “Oh babu ma yanda kuka iya? Wato tsoronsu ma kuke ji saboda uban su ne shugaban ƙasa, yara na irin wannan ta'addacin amma kuke iya barinsu a cikin makarantar ku harda faɗin babu yanda kuka iya.....”       Kasa cewa komai principal yayi, sai ma haƙuri daya cigaba da bama hamshaƙiyar matar da kallo ɗaya zakai mata kasan matar babban mutum ce a ƙasar. Dai-dai nan akai knocking ƙofar ofishin, principal ya bada izinin shigowa. Wani matashin saurayi ne da alamu suka nuna shima ma'aikaci ne a makarantar, yay sallama ya shigo sannan ɗalibai biyu dake bayansa riƙe da wata matsakaiciyar budurwa da bata wuce 15years ba suma suka shigo. Zaram matar ta miƙe tai kansu, jikinta har rawa yake ta kamo hannun yarinyar da suka riƙo kanta naɗe da ƙaton bandeji, fuskata kuwa da ganin yanda tai suɓu-suɓu kasan tasha maruka da kuka ta kuma ci bugu, dan idanun jazur suke suma luhu-luhu. Jikinta yarinyar ta faɗa, yayinda ita kuma ta ɗauki dogon salati ta dire tana mai ɗago yarinyar a jikinta.........✍️ Wannan aiki nasan sai Zakanya da vice ɗinta Damisa🤣. _Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_* _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899* *_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_* *_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._* *_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_* *_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._* *_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_* *_Akwai VIP Telegram 💃_* *_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_* *_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_* _(2k)_ *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*. _(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* 7 .......Cikin matuƙar bala'i da ihu matar ta ce, “Babbar bala'i kai, wlhy bazan yarda ba, dolene ma yaran nan suje police station dan sai nayi shari'a da su.....”      Da sauri matashin malamin nan ya katseta da faɗin, “A'a ranki ya daɗe kada ai haka. Mudai bari a zauna dasu aji miya haɗasu, duk da nasan Naja'atu da Ruƙayya fitinannun yara ne amma basa faɗa sai da dalili...”          “Oh yanzu na fahimta, to kodai kaine ka sakasu su aikata ma saboda kana nemansu? Dan ba abin mamaki bane idan muka dubi yanda malamai suka koma fasiƙanci da ɗalibansu a makarantu”.       “Innalillahi wa'ina ilaihiraji'un, Hajiya wane irin magana ce wannan? Dan na faɗi abinda yake gaskiya kuma sai ki aibantani da yaran da suke tamkar ƴaƴanki. Amma dai.....”        “Teacher Khalil ya isa haka. Ka fahimta kawai ranta ne ya ɓaci. Yanzu dai ka kira gidan su yaran sannan azo min da su nan yanzu nan”.      Sosai ran wanda aka kira da Teacher Khalil yake a ɓace da zancen matar, sai dai bai sake cewa komai ba ransa na ƙuna ya shiga neman layin wanda yasan Yaya ne gasu Ruƙayya, amma fin kira goma bai shiga ba. Ganin ba samu zaiba principal yace ya sake kiran wata number mana, canja kiran yay zuwa ɗayar number da yake da ita, cikin sa'a kuwa ta shiga. Koda aka ɗaga cikin nutsuwarsa yay bayanin daya dace, a ƙarshe ya sanar da ana buƙatar ganin wani nasu babba daga haka ya ajiye wayar ya fita a office ɗin.... Mintina kaɗan Teacher Khalil ya dawo, sai da ya shigo sosai matasan ƴammata biyu suka bayyana. Ta gaba fara ce tas kuma ƙyaƙyawa, siririya daga ganin fuskata kasan zatai rashin ji. Wadda ke biye da ita ma da zasu iya zama kai ɗaya black beauty ce masha ALLAH, itama dai daga ganin fuskar nan kasan zatai tsiwa. Su duka sanye suke da uniform skirt peach color da farar riga long sleeve shirt, sunyi zanzaro da skirt ɗin, sai ɗan ƙaramin baby hijjaf fari shima da iyakarsa matashin ƙirjinsu da ake kiran kamar su da suna ƙwailoli. Daga ƙasa safa ce doguwa data zo har gwiwar ƙafa saboda skirt ɗin nasu kaɗan ya zartar gwiwar sai takalman sandal baƙaƙe na ƴan makarnta. Ga shi dai uniform ne ana saka shi badan ado ba, amma yayi musu matuƙar ƙyau da zaunawa a madaidaicin jikinsu ɗas kamar ka lashesu. Ga wani ƙamshin turare mai sanyin daɗi na fita a jikin nasu da gogaggun uniform ɗin su da suka sha karin guga kamar batun safe suka sakasu ba.      A makarantar ba'a dukan ɗalibai sam, dan makaranta ce ta kuɗi kuma ta ƴaƴan manyan ƙasa. Duk wanda aka gani a school ɗin lallai ubansa yaci ya ƙoshi ne. Shiyyasa daga ƴaƴan masu mulki saina jami'an gwamnati dana manyan ƴan kasuwa. Dan makarantar ma ta baƙin haure ce ƴan ƙasar waje ba ƴan ƙasa ba. Rabi da kwatar malaman cikinta duk masu jajayen kunne ne, sauran tsiraru irinsu Teacher Khalil ne kawai ƴan ƙasa baƙaƙen fata, sai kuma shi kansa principal ɗin shima dai ɗan ƙasa ne.       Da farko idanu principal ya zuba ƙyawawan ƴammatan biyu, yayinda matar nan ke zuba musu uwar harara kamar idannunta zasu zubo. Hakama ƴarta dake lafe a jikinta tun shigowar yammatan dake sa'ointa ta sake mannema uwarta tana harararsu. Suko sun wani tamke fuskoki suna cika suna batsewa. Haɗa ido baƙar tayi da yarinyar, tako watsa mata uwar harara da nunata da yatsu biyu alamar saita tsokale idon...      Wani irin takaici ya sake mamaye zuciyar uwar, dan ta kasa gane ita zata tsokalewa ido ko ƴar tata tunda itama hararar take. Baki ta buɗe zatai magana principal ya katseta sakamakon ambaton sunan yaran da yayi.        “Ruƙayya Imran Abbas”.   A cinkushe farar tace, “Yes Sir!”. Ya sake maida idonsa ga baƙar ya ce, “Naja'atu Muhammad”. Itama cikin tura baki tace, “Yes Sir”.       “Ku miyasa bakwa jin magana ne, yara kamar ibilis ne malamin ku kullum cikin kawo ƙararku ake. Yanzu ku duba yanda kuka fasa mata kai, inda abin yazo da ƙaddara fa...?” .......Adeel ibn Ubaidullah Qureshy. Cikakken balarabe ne ɗan asali gaba da baya. Jinin sarauta dan kuwa daula babba suke da ita a yankin larabawa. Sannan zuri'arsu zuri'a ce mai ɗunbin dukiya da kaso huɗu na arziƙin Dubai yana da alaƙa da shi. Adeel irin gagararrun yaran nan ne da giyar mulki data kuɗi ke ɗawainiya da su. Dan kuwa iya shegen da yake zubawa a cikin Dubai ba'a magana.      Harkar business ce ta haɗashi da Hajiya Hasiba, a dalilin First Lady da suke aminta. Sunyi wani zaman meeting Hajiya Hasiba ta kasance kujerarta kusa data Adeel a meeting room ɗin, irin ta ajiye wayarta a table sai aka irin kirata ɗin nan, bata ɗaga ba kasancewar suna a halin meeting har kiran ya tsinke, dai-dai screen ɗin wayar na komawa yanda yake ƙyaƙyƙyawan hoton Nabeeha dake a fuskar wayar Hajiya Hasiba ya bayyana. Sai ko karaf a idon sa. Cak ya tsaya da bayanin da yake ya zubama wayar ido, abokan meeting ɗin nasa sukaji shiru duk sai suka ɗago suna kallonsa, cike da basarwa ya ɗauke idanunsa ya cigaba da jawabinsa, amma bini-bini idonsa nakan screen ɗin wayar Hajiya Hasiba har aka tashi.       Hajiya Hasiba ta lura da kallon da Adeel kema wayarta, amma sai bata kawo komai a ranta ba har suka wuce. Mizai faru da daddare kawai sai ga Firt lady ta kirata wai Adeel nason magana da ita, idan ba damuwa kuma so yake su haɗu. Mamaki ya kama Hajiya Hasiba, ta tambayi ko lafiya? First Lady ta bata amsa da cewar wai akan wani hoto ne da ya gani a fuskar wayarta sanda suke meeting. Sosai Hajiya Hasiba ta zaro idanu tana dafe baki, kafin ta ce, “Kai ranki ya daɗe ɗiyarki ce fa Nabeeha, kin san dai tana da aure kin kuma san waye mijinta da fitinarsa”.      Cikin nuna rashin damuwa First Lady tai murmurshi da faɗin, “Yo ALLAH na tuba sai me Hajiya Hasiba, aure nawa ne a wannan zamanin da shi gara babu. Ke dai kawai ai sha'ani. Mijinta kuwa girman kansa na banza ba ko sisi, kin san waye kuwa Adeel? Hummm na baki dama daga nan zuwa minti talatin ki bincika sai ki yanke hukunci. Ni dai na isar da saƙo yace zai turo mota a ɗaukeki a kaiki inda yake ”. Daga haka ta yanke wayarta.      Shiru Hajiya Hasiba tai na tsawon lokaci, dan babu abinda ke zuwa mata a zuciya da brain sai fuskar Zak-Shadow. Amma dai ta daure ta fara binciken waye Adeel kamar yanda First Lady ta bata shawara. Tun a ambaton farko kanta ya nema bugawa, jin nasabar gidansu kawai, jin ɗan waye daga zuri'ar daya fito. Data bincika arziƙin zuri'ar tashi kawai bama shi wadda ya mallaka ba bata san ta rikito a kujera ba tsabar rawar jiki. Har lokacin da za'a ɗauketa yayi bata iya ta dawo a hayyacinta ba saboda matsanancin mamaki. Ai babu ɓata lokaci ta shirya a gurguje tabi ɗan aiken. Ai ko kanta da zuciyarta sun nema fashewa saboda inda aka kaita matsayin wajen hutawarsa. Wani mahaukacin azababben garden ne da in ka kirashi da suna aljannar duniya bakai ƙarya ba. Ga masu hidima zagaye da wajen da wasu mugayen masu tsaro ya subahanallah. Ita dai haka aka kaita har inda yake jiki na ɓari.      Kallo ɗaya yay mata ya maida kansa ga laptop ɗin gabansa, a haka cike da isa ya nuna mata wajen zama. Sai ta dinga jin kamar ba Adeel ɗin juya bane da sukai zaman meeting, koda yake ko'a jiyan dama yanda yake magana da isa da ƙasaita kasan akwai girma da izza. Amma a yau ɗin ba'a magana. Ya share fin mintuna goma sannan ya gyara zamansa, babu wani tauna harshe ko girmamawa kai tsaye yana kallonta ya furta, “Yarinyar dana gani kan wayarki nake buƙata, ina fatan ba hotonki bane dan naga kuna kama sosai, tsufa kawai zaki nuna mata”.      Kan Hajiya Hasiba a ƙasa tana murmurshi ta ce, “A'a bani bace. First born ɗina ce, sunanta Nabeeha”.       “Nice...”    Ya faɗa cike da iskanci yana ajiye kofin hannunsa. Sai da ya ƙara busar iska ya cigaba da faɗin, “Za'a iya kawo min ita a yau? Zan bada ko nawa ake buƙata, daga biliyan 1 zuwa sama”. ..........“Sir kawai fa dan na taka ita Ruƙayya ɗin ne ban kula ba, kafin na bata haƙuri sai ta hankaɗe ni ta ƙwace wayata ta jefar a ƙasa ta fashe, ni kuma na zuba mata ruwa a jiki ƴan class suka yi dariya. Itafa Nimrah ɗin ma bata ajin ta fita, kawai tana shigowa ba tambayar ba'asi ta hau dukana itama Ruƙayyan na tayata, ni kuma naji wahala na cijesu kawai suka gwara kaina da bango wai aljanunsu ya tashi...”         “Da dai kin fito kin faɗi gaskiya yarinya da yafi miki”. Cewar Ruƙayya tana hararta. Uwarta zatai magana principal yay saurin tarar numfashinta. Idanunsa akan su Ruƙayyan ya ce, “Ke haka akai?”.       “Sir ta ɓoye asalin zancen”.    “To miya faru?”. “Yarinyar nan ƴar iska ce Sir, a bayan desk ɗinmu suke ita da ƴar iskar ƙawarta, kullum sai suna damunmu da kallon Film ɗin iskanci a waya, mun musu magana akan idan suna kallon rashin tarbiyyarsu a waya suna saka Bluetooth amma sun ƙi dainawa. Kawai yau suna kunnawa na juya na ƙwace wayar na fasa banza, shine tazo zata min hauka ni da Ninah muka sauke mata nata ƙaramin hau ɗin”.      Rawa jikin yarinyar ya fara, ta fara rantsuwa ita sharri su Ruky sukai mata. Uwarta ma bala'i ta fara wai za'a ma ƴarta sharri bazata yarda ba. Kodai principal ya bari ƴan sanda su tafi dasu Nimrah ɗin ko kuwa tai ƙarar makarantar gaba ɗaya. Cikin takaici Ammar ya ce, “Hajjaju ya kike Abu kamar baƙya ganewa ne, shin anan akwai wai mai tsoron zuwa police station ɗin ne anan akace miki. Yaran nan sun faɗi abinda ya faru har sukai rikici da ƴarki, maimakon ma ki damu da abinda take aikatawa kina neman juye wa mutane shirme. To muma bazamu yarda ba, dan bazata ɓata mana tarbiyyar yara ba, banda ma rashin kula har yara na kallon banza da wofi a waya iyaye basu sani ba, kuma miye na zuwa da waya makaranta? Gasu nan ko waya basu da ita yaran nan kuma basu taɓa damuwa ba duk da sun kai ƴammatan daya dace ace an barsu da ita, idan anyi maganar ku daina bama yara waya ko ku dinga kula dasu idan kun basu musamman masu tashen sabuwar balaga irin su kuga kamar an raina ƙoƙarinku ne. Ba haka bane, a irin wannan gaɓar waɗan nan abubuwa suke kwaɗaituwa a zukatansu, dan haka muma bazamu yarda ba, yaranmu masu tarbiyya ne, bakuma za'a ɓata mana su anan ba, kuma yanda sukai mata sun min dai-dai....”     Hayaniya sosai ta kaure a office ɗin tsakanin Hajiya da Ammar, sai da ƙyar aka fitar da Ammar itama Hajiyar principal yace taje zasuyi bincike akai. Dan haka an bama yaran suspension na sati ɗaya su duka ukun har sai an tabbatar da gaskiyar mai laifi. Suko ƴan sandan data kira suka sallamesu. Suma ƴan sandan sanin makarantar ta jiga-jigai ce basu ja da nisa ba suka wuce.        Yaya Ma'aruff dake hararar su Nimrah ya ce, “Sai ku wuce muje masu kunnen ƙashi. Hankalinku ya kwanta ai ko. Banda ma fitina ku kuma haifeta da zaku hukuntata? Ba kusan hanyar kai report bane, jibeku da kawuna kamar kullun magani”.      Babu wanda a cikinsu bai cika baki da iska ba. A haka suka fito suka shiga mota shima Yaya Ammar na zuba musu tashi hararar.....           ★ Koda suka iso gida ko kallon inda suke su Yaya Ma'aruff basuyi ba suka shige ciki abinsu. Kallon juna Nimrah da Ruƙayya sukayi, cikin marairaicewa Ruky ta ce, “Wlhy yau akwai matsala Trouble Queen....”     “Babba ma kuwa”. Aka faɗa daga bayansu, a tare duk suka juya, Mu'azz ne daya zama matashin saurayi ɗan shekara goma sha takwas, dan kuwa ya kammala Secondary ɗinsa ma yana shirin shiga jami'a. Yanzu kam Nimrah ce tace, “Ya Mu'azz kaji tsoron ALLAH”.          “Oh, to da tsoron ku nake ji. Ba kunce ku baƙwa jin magana ba. To Daddy ma na nan zuwa dan Uncle J ya kirashi shima”. Wani mugun ƙwalalo idanu waje sukayi a tare, shi ko ya kwashe da dariya yana barin wajen. Da sauri sukabi bayansa, amma yaƙi tsayawa har suka shigo falon. Cak kuwa suka tsaya, ganin kowa yana nan har su Aunty Lailah. Yaya Ja'afar ne ya fara zuba musu harara da faɗin, “Sannunku ƴan wrestling ko ƴan boxing ma zance ban sani ba nikam”. *_💦KIƊA A RUWA...!!💦_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ *_GENERAL FICTION_* _Wannan labari ƙirƙirarre ne. Sunaye, wurare, da abubuwan da suka faru duk ƙirƙira ne, ba su da alaƙa da gaskiya ko wani, koda Bilyn Abdull ce 😂._ *_BOOK 2_* _Chapter 10_ __________________ _A KANO KI KE…? Kina neman inda zaki siyi abinci mai daɗi? Kina ƙiyar yin girki gashi zaki yi baƙi?, kina neman inda zaki yi order abinci mai daɗi wanda zaki fita kunya?. Masu abinci suna suka tara, akwai abinci mai daɗi akwai a lallaɓa. Kina son ki siyi abincin da zaki ɗauka a saudia ki ke? Kuna son ku siyi abincin da in kuna ci zaku dinga murmushi saboda daɗi da khamshi?. LEEMARS_DELICIOUS itace kat a wannan ɓangare, tazo muku da nau’in abinci kala-kala na gargajiya da na ƙasar waje. Tana siyar da MANDI RICE, GRILL CHICKEN, CHICKEN BIRYANI, FUNKASO, ALELEN GWANGWANI, BREAD POCKET da sauran su. Fannin abin sha akwai natural ZOƁO mai zaƙi, wanda aka yi shi da ingantattun kayan marmari masu ƙara lafiya, akwai wanda bashi da zaƙi domin masu ciwon sugar da masu gudun ƙiba._ _me ku ke jira? Maza ku garzaya shafin ta na instagram ko TikTok domin ku ganewa idanun ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take ƙasan rubutun nan._ INSTAGRAM 👇🏻👇🏻👇🏻 https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP 👇🏻👇🏻 wa.me/2349030398006 TIKTOK 👇🏻 https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1 Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da kuɗi gida.❤️❤️🫶🏻 __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ ........Su Nimrah dake laɓe da tunanin za'a sake maganar makarantarsu jin shiru su Mammah ma sun ɗauki wani zancen daban suka bar wajen. Suna shiga ɗaki Nimrah ta ce, “Trouble Buddy! Kin san mi zamuyi?”.      “A'a sai kin faɗa”.   “ALLAH in dai Daddy ya dage sai ya kaimu Boarding ɗin nan randa aka kaimu samun wata Senior ɗin zamuyi mu lakaɗa mata dukan da a washe gari za'a kirashi ace an koremu gaba ɗaya. Idan mun dawo gida mu dage masa kan bamu san munyi ba aljanu ne damu da gaske.”       Sai da Ruky tai dariya sosai sannan ta ce, “Sai da ke Hot Pepper! Amma fa ni kin san wani lokacin ina da ɗan tsoro, kada muje wajen ƙaryar aljanu a samo wani ustazu ya daki banza da sunan Rukya, ko'a ƙara na kwanaki yace zai aurama su maigadi mu.”          “Ai ke banza ce. To bari kiji ALLAH bazasu bari a dake mu ba. Balle ma in har za'a Boarding ɗin nan dole muyi sanadin da za'a haɗa harda Fiddo da Bintu”.      “Muguwa naga mu kaɗai mukai laifin? ALLAH ki dinga jin tsoron ALLAH Ninah”.      Itama dariya tayi yanzun kam, ta wani juya idanunta manya cike da iyayi, “Yo da tsoronki nake ji Ruky. Bazaki gane ba idan muka haɗu mu duka sai Boarding ɗin ma tafi daɗi idan ta zama ƙaddarar mu. Mu haɗu mu dinga darje bakin ƴan iska da duk suka nuna mana yatsa.”       Tafawa sukai suna dariya.... Nace ALLAH dai ya shirya waɗan nan yara🏃🏼‍♀️. Daddy Imran ka rufa mana asiri ka barsu a Day school ɗinsu, kada wataran suja maka ka sake komawa inda Dada yake.🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️😂. ____________★          Aiki gida dai ya tabbata akan ƴan caskalen gidan Mammah, dan kuwa a bazata washe gari tunda safe sai ga Imran a gidan, suna tsaka da barcinsu ya saka Aunty Biebah taso masa su. Da farko sai faman layi suke suna ma Biebah kukan shagwaɓar ta barsu su barci suke ji, amma suna cin karo da Daddy suka watsakke, a tare suka zube suna gaishe shi. A taƙaice ya amsa musu tare da faɗin, “Oh barci ma kuke yi har zuwa yanzu? Batun breakfast, shirya ƙannenku zuwa school duk wa zai yi?”.       “Daddy kayi haƙuri, ALLAH bamu san barci ya sake ɗaukar mu ba”.     “Na baku mintuna goma ku wuce ku shiryo su Abees”.      Kafin ma ya gama rufe baki sun fice a sashen. Kai tsaye sashen su Yaya Ja'afar suka nufa kamar zasuyi kuka, dan suyi sauri sai suka rabu. Nimrah ta shiga sashen Yaya Ma'aruff ita kuma Ruky na Yaya Ja'afar. Shigowar Nimrah dai-dai da fitowar Aunty Lailah daga ɗakin su Aheel, fuskata da murmushi ta ce, “A'a Ninah miya faru ba'ai shirin makaranta ba?”.      Kamar Nimrah zata saki kuka ta ce, “Ammie kin manta muna suspension? Zan shirya su Aheel kije ki kwanta kawai”.        “Oh na manta, amma Ninah aikin zai muku yawa, ga haɗa breakfast ɗin gida gaba ɗaya, ga gyaran sashen ku. Kije kawai bari na shirya su kinji”.       “Ammie Dady fa na nan”. Cikin ɗan waro idanu Aunty Lailah ta ce, “Gidan Yayan yazo da sassafen nan?”.      Kai ta jinjina mata. Dai-dai da fitowar Yaya Ma'aruff ya ce, “Wayo yazo da sassafe?”.       “Wai ya Imran”.   Murmurshi kawai Yaya Ma'aruff yayi yana girgiza kansa da faɗin, “ALLAH yanzu gaba ɗaya Yaya Imran ya canja zuwa Dada, da dai babu ruwan shi da faɗa amma yanzu ya gaje halin twiny sa. Ninah zo nan”.        Sum-sum Nimrah ta iso inda yake, zama tai a ƙasan lallausan carpet ɗin tace, “Uncle good morning”.       “Morning sarakin ƙiriniya, ke dai ke da Ruky ku saka mutane surutu shine jin daɗin ku ko. ALLAH idan baku canja ba duk randa Dada ya dawo gidan nan sai kun gane Yaya Imran bai iya komai ba”.        Caraf Nimrah ta ce, “Uncle kenan Dada shi mugu ne?”.       Dariya yanda tai ɗin yaso saka Ma'aruff, amma sai ya danne ya murmusa kawai. “Dada ba mugu bane, amma baya son rashin ji, ku tambayi Ammar zai baku labari dan shi ma da rashin ji ya fara Dada ya saita shi da horon sojoji. To kuma idan baku nutsu ba duk randa ya dawo jiki magayi”.            “In sha ALLAHU zamu ma bari, amma dan ALLAH Uncle wai shi Dadan yana wace ƙasa ne? Yaushe kuma zai dawo? ALLAH ina son na ganshi, kaga sai a hoto muka taɓa ganinsa shima sau ɗaya ne Mammah tasa aka tattare hotunan aka ɓoye”.       Sai da Yaya Ma'aruff ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan yay ma Nimrah murmurshi kaɗan. Bayan su masu hankali har yanzu daga Mu'azz har su Nimrah basu san Dada na prison bane, kawai ance musu yana wata ƙasa ne yin wani aiki mai muhimmanci. Dan ko Biebah ba komai ta sani ba sai kaɗan-kaɗan daga cikin lamarin shima dan ya watsu a media ne lokacin...       “Ninah in sha ALLAHU Dada zai dawo, ina ji a jikina nan kusa ma kuwa zai dawo gare mu. Ku dai ku cigaba da addu'a kawai. Dan zuwansa garemu zai iya zama tamkar haɓo ne kinji”.         “ALLAH yasa Uncle, kuma in sha ALLAHU kullum zamu dinga zama mu da su Abees muna addu'ar”.     To ALLAH yay muku albarka. Ina Sisin taki?”.     “Mun raba aiki ne tana can zata shirya su Abees”.         “To kinga tunda ga Ammien ku na shirya su Aheel anan tashi muje, ni zan janye Yaya Imran ɗin sai kuyi sauri ku haɗa breakfast kawai”.     Sosai farin ciki ya kama Nimrah, koda suka fito suka leƙa sashen Yaya Ja'afar sai suka sami Rukyn ma ba aikin take ba, tana gyarama Afrah gashi ne dan har an musu shirin makarantar ma. Sai kawai ta kamota suka fito zuwa sashen Mammah, ta ƙofar baya ta kitchen Yaya Ma'aruff yace su shiga, shi kuma ya zagaya riƙe da hannun Afrah dake zuba masa surutu, dan itama dai akwai baki ta gado su Nimrah ɗin..... Tun a haɗa breakfast Nimrah da Ruƙayya suka san ALLAH ɗaya ne. Masu aiki kuwa na ƙoƙari kwarai-ƙwarai da gaske. Suna wayyo-wayyo Uncles ɗin nasu da Auntys na dariya suka jera a babban family dining table ɗin makeken falon Mammah. Dan dama haka suke cin abincinsu a tare tun daga na safe har na rana ga wanda suke a gida. Na dare kuwa dama kowa yana nan. Kowa na ƙoƙarin kammalawa ya wuce aiki suko suna haƙilon gyaran kitchen, ga Mu'azz ya saka rayuwarsu gaba. Daya motsa sai ya ƙwala musu kira.        “Ninah bani kaza, Ruky baku ajiye abu kaza ba”.      Suko takaici ya ƙulesu sai su ɗakko a hasale su dangwarar masa. Dariya kamar ta kashe su Aunty Shariffa. Aunty Biebah ce ma suka bata tausayi bayan tafiyar Daddy Imran tace su gyara falo kawai bari ta tayasu gyara bedrooms tunda dai can ai babu camara balle Yaya Imran ɗin ya gani. Dan koda zai wuce sai da ya sake jaddada musu idan ma basuyi ba zai gani ta cctv Camaras dake zagaye da gidan tako ina. Wannan ya sake sasu tsorata suka dage. Duk da taya sun da Aunty Biebah tayi basu kammala komai ba sai 12 da wani abu, a wahale sukai wanka sukazo falo inda su Aunty Shariffa ke hira dan su basa zuwa aiki, shiyyasa koda yaushe suna sashen Mammah suna ɗebe mata kewa. Balle yanzu hirar na armashi Mu'azz yana gida zaune kafin ya wuce University. Yau kuma anyi sa'a Aunty Biebah ma dake gab da kammala master nata bazataje school ba. A ƙasan lallausan carpet ɗin falon suka zube kowa na maida numfashi.      Mu'azz ya kwashe da dariya cike da mugunta. “Oh ALLAH yau ga mata sunyi aikin gida. Ku a haka za'ai muku aure kuje kunayi, dan ALLAH ji Ninah kamar an tsamo mage a ruwan zafi, gara-gara ma Ruky”.         Kamar Nimrah zatai kuka ta ce, “Mammah kin jisa ko, wai nice mage a ruwan zafi”.       “Shi kuma muzuru ko?”. Cewar Biebah na jifansa da filo. Cafewa yay yana dariya da faɗin, “Kai small Mom muzuru kuma. Dan ALLAH kar ki saka yaran nan su raina ni mana. In ba haka ba ALLAH zan zuga Daddy a kaisu boarding school ɗin nan mu huta. Su Ayyan sun ishe mu”.        “Idan su basu tafi Boarding school ba ai kai ka tafi, tunda baka san inda za'a cillaka karatun ba”.      Kallon Aunty Shariffa mai maganar yayi da faɗin, “Kai Mamy banda fata, kin san bakin iyaye da saurin kama ɗa, in sha ALLAHU nikam ina nan cikin garin nan babu inda za'a kaini”.          Mammah dake fitowa a ɗaki ta ce, “Ni dama za'a kaika wani ƙasan da yarana sun huta da damun su da kakeyi babban banza”.      “ALLAH Mammah na tafi kema sai kinyi kewata. Suma haka kuma, dan sun san ina rufa musu asiri a gidan nan. Amma tunda kun shigar musu yara duk zaku gane kuran ku. Daga yanzu ko tarin banza kukayi zan fara rubutawa ne, kuma Dada zan ajiyewa yanda zaku fi caskaluwa dan na Daddy mai armashi ne yanzu”.      A tare suka kwashi fillo suka shiga jefa masa. Gashi sun kasa tashi saboda ƙafafinsu sunyi dayin wahalar aiki. Aiko mi za'ai in ba dariya ba. Da ƙyar Mammah ta raba faɗan nan ta hanyar janyesu ta shafa musu man zafi a ƙafafu. Ga shi lokacin yin girkin rana yayi. Haka suka shiga kitchen ɗin suna sharɓar hawaye, ga camaras da suke ji kamar su fincike su su yardar su samu a tayasu. Amma ba dama, dan duk bayan wani ɗan lokaci sai Daddy Imran ya kira waya ya tabbatar musu duk yana kallonsu dan yayi connecting da wayarsa, suma kuma sun san haka ɗin ne tun ma ba yanzu ba..........✍️ Gaskiya kuzo muje balling Trouble Buddy da Trouble Queen kafin Daddy Imran ya kaisu gadon asibiti🤣🤣.     _Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_* _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899* *_ASSALAMU ALAIKUM MUTANE NA MASU ALBARKA_* *_Maza ku matso MASOYAN Bilyn Abdull da IDANU suka hana karatun novels...._* *_Tofa Bilyn ku ta samo muku hanya mai sauƙi da kina aiki, ko kina kwance kina hutawa, ko kina inda baki son yawan surutu earpiece ɗinki kawai zaki maƙala a kunne ko Bluetooth kisha sauraren littafin KIƊA A RUWA.... Cikin sauƙi.... 💃_* *_Kar dai na cika ku da zance. Zamu fara saida littafin KIƊA A RUWA.... Na saurare (Audio) kenan akan farashi mai sauƙi da rahusa._* *_Akwai VVIP AREWAPEN kenan 💃_* *_Akwai VIP Telegram 💃_* *_(Ƴan WhatsApp ku haƙura kawai ƴan ta'addar bati sunfi yawa a cikinku gaskiya tsoron rashin m ɗinku nake 😂🤣)_* *_Telegram Audio 2k ne kacal ba tsada 💃. Sai kusaka ta wannan account ɗin👇_* _(2k)_ *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (2k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_Ƴan NIGER🇳🇪 kuma bazamu barku a baya ba in sha ALLAHU zaku biya (Telegram vip 1,500 CFA) domin littafin KIƊA A RUWA..... na ji Audio-vocal. Sai ki biya tanan👇_*. _(1,500 CFA)_ *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 1,500 CFA vip telegram _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_AREWAPEN (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_Ƴan WhatsApp kuzo muyi shawara idan zaku iya amana ayi harkar nan daku 😂, dan bana son a barku a baya duk da dai bakwa ji, ba raga min zakuyi ba na sani duk da ƙaunar da nake muku 🤣😂._* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* 11 .........Kwanaki kusan biyar su Nimrah na cin ƙaniyarsu da aiki, sun jikatu matuƙa sunyi laushi, kuka da roƙo babu kalar da basuyi ba, hakama kawunansu sun bama Daddy Imran haƙuri amma yace idan suka bar aikin nan Boarding fa babu fashi. Da ga ƙarshe dai suka zagaye suka kira Aunty Ummie a waya suna mata kuka suka sanar mata. Dama kwana biyu bata leƙo gidan ba saboda aiki. Aunty Mommy kuwa basa ƙasar ita da mijinta sai a satin nan zasu dawo. Ita ko Aunty Mimi ciki gareta tsoho haihuwa ko yau ko gobe shiyyasa Mammah ta hanata zuwa gidan.      Alhamdullahi zuwan Aunty Ummi da suke kira da Big Mah-mah ne ya cecesu a hannun Daddy Imran. Dan bayan an sako massalacin juma'a yazo gidan gaida Mammah ta tareshi da daɗin baki da ban haƙuri har ya haƙura masu aiki su dawo gobe. Amma duk da haka da sharaɗin daga yanzu kullum dasu za'a dinga shiga kitchen yin girki. Da wannan ALLAH ya ƙwacesu. Masu aiki suka dawo, su kuma suka samu sauƙi. A cikin satin ma suka koma zuwa islamiyya dan suspension ɗin ta ya ƙare, sai kuma karatun da akayi basa nan ya sakasu a gaba. Sati ya zagayo suka koma boko ma, amma duk da haka sai da akai zama da Hajiya ta kafa sharaɗin babu su ba yarinyar ta, dole kuma a raba musu wajen zama sannan case ɗin ya mutu. Dan an dai gane ƴarta na kalle-kallen banza a waya da gaske kamar yanda su Nimrah ɗin suka faɗa......         >>>>><<<<<<     Yau ta kasance juma'a, dan haka an tashesu da wuri. Sai dai shiru babu drivern su babu alamarsa. Sun san maybe ya fara zuwa ɗaukar su Abees kafin yazo nan, duk da kuwa a kulum su yake fara zuwa ya ɗauka kafin su ƙarasa makarantar su Abees ɗin saboda suna rigansu tashi. Tun suna kallon agogo har suka sare, ga mafi yawan ɗalibai duk sun wuce anzo an ɗaukesu. Makarantar su nada doka kuma ma tilas zuwa ake ɗaukar kowane ɗalibi bawai buɗe musu gate ake su fito ba kawai.      Sun gaji ga Ruky na ciwon mara, dan ita in zatai period ba ƙaramin jikata take ba. Ganin ta fara kuka hankalin Nimrah ya tashi. Ofishin Principal ta nufa amma ta tasar baya nan wai sun shiga meeting da malamai. Da gudu ta dawo wajen Ruky, ta sameta durƙushe azaba ta isheta, bata son suje clinic ɗin cikin makaranta dan an riga an tashi. Idannunta na cika da ƙwalla itama ta kamata ta miƙar. “Tashi muje wajen security ko zai taimaka ya barmu mu fita kawai, amma shima Baba Driver bai ƙyauta mana ba”. Da ƙyar da ƙyar Ruky ta iya miƙewa suka isa gate ɗin, cikin sa'a suna isowa sai ga motar Yaya Ammar na isowa. Ajiyar zuciya Nimrah ta sauke, dai-dai Mu'azz na fitowa daga motar, ya ƙaraso inda suke da sassarfa yana faɗin, “Lafiya kuwa? Miya sami Ruƙayyan?”.         “Yaya ciwon mara, muyi sauri mu tafi kasan idan ya fara tsanani sai suma. Amma Yaya driver fa?”.       Sai da ya buɗe musu suka shiga yake bata amsa yana reverse. “Baba driver accident yayi, yanzu haka ma yana asibiti”.      “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, badai da su Aheel ba?”.      “A'a bada su ba, shi kaɗai ne yaje ɗakko motar Ummie (Aunty Lailah suke cema Ummie, Shariffa Ammie) daga wajen wanki”.         “Ya rabbi, ya jikin nasa?”.     “Gaskiya yaji jiki sosai, dan har yanzu ma ba'a bari an gashi ba. Motar kuwa tama tashi aiki, dan babbar mota ce ta haye shi”.       Gaba ɗaya jikin Nimrah ya ƙara sanyi, ita kanta Ruky dake fama da kanta hankalinta ya sake tashi, a haka suka iso gida ciwon marar ya ƙara tsanani, dole ma sai Mu'azz ɗaukarta yayi. Gaba ɗaya hankalin ƴan gidan a tashe yake da hanlin da baba driver ke a ciki, dan mazan gidan duk suna can. Ganin hanlin da Ruky ke ciki kuma duk sai suka maida hankali a kanta. Babu bata lokaci aka kira family doctor ɗin su, da yake ya san matsalarta yana zuwa allurai yay mata....      Basu sami ganin Baba Driver ba sai ranar Lahadi da yamma. Gaba ɗaya gidan suka shirya suka je suka duba shi. Yaji jiki kam kwari da gaske, amma Alhamdullah yana samun dukkan kulawar data dace. Ga matarsa an ɗakko tana jiyyarsa. Komai na asibitin Kuma su Yaya Ja'afar ne suka biya. Received at 6:57 PMSosai matar ke godiya akan yanda suka bama al'amarin mijinta muhimmanci, inda wasu ne ko'a jikinsu, ƙilama suce sai an biyasu motar miliyoyin kuɗin data tashi aiki. Amma su bata motar suke ba ta lafiyarsa sukeyi.         Shima Baba Driver kallonsu kawai yake yana hawaye, dan baya iya magana har yanzu. Su duka sun ɗauka yana kuka ne kawai akan halin da yake ciki. Dan haka Mammah tai masa nasihar haƙuri da tawakkali akan ƙaddara. Kusan awar su ɗaya suka koma gida suna sake jimanta al'amarin. Satin baba driver biyu ya fara samun sauƙi, zuwa yanzu kuma Mu'azz ke jigilar kai su Nimrah makaranta da ɗakkosu kullum. A haka kwanakin tafiyar Mammah da Yaya Ammar suka cika zuwa Egypt ganin likita. A tare suka mata rakiya airport cike da kewa, dan Ruky da Nimrah harda kukan su. Ƙarshe Uncles ɗin nasu suka koma lallashinsu da tabbatar musu ai sati biyu kawai zatai ta dawo. Haka suka dawo gida. Tafiyar Mammah da Yaya Ammar da kwanaki biyar al'amarin karatun Mu'azz ya taso, dole su Yaya Ma'aruff suka fara batun neman driver, dan su basu da isasshen lokaci, wani lokacin ma da ƙyar suke ƙulla sati uku a ƙasar. Ammar yana fama da aikinsa, ga Bilal ma baya ƙasar, ko yana nan aikinsa shima ya ishesa, bazasu so kuma matansu kullum na gantalin kai yara makaranta da ɗakkosu ba, balle Biebah da bata da magana yanzu sai ta project ɗinta. Sunata tunanin ina zasu samu sabon driver mai amana kamar Baba amma sun rasa makama.     Shawarar kota hanyar Baban za'abi Yaya Ma'aruff ya bayar, dan haka suka amince da hakan. Bayan sun taso kasuwa suka nufi gidansa dake can wani ƙaramin ƙauye, sai dai atanan yankin babban birnin yake. Sun sameshi jikinsa Alhamdullah, sai dai ƙafa data samu nakasa sosai har yanzu anata fama. Sun sake jajanta masa da ajiye masa alkairin da basa gajiyawa wajen yi masa sannan suka sanar masa abinda ya kawosu. Cewar suna son ya sama musu wani drivern mai amana kamar shi dan sun yarda da shi. Da farko shiru yayi idanunsa na cika da ƙwalla. Sai da Ja'afar ya ce,        “Baba wannan ai ba abin kuka bane. Mun yarda da kai ne da amanar ka shiyyasa muka sake biyowa ta kanka, kuma in ma ALLAH ya baka lafiya muna maraba da dawowarka cikinmu”.     Hawaye Baba ya share, “Na sani ku mutanen arziƙi ne masu tarin alkairi, har abada kuma bazan manta da tarayyata da ku ba. Amma mizai hana ku cigaba da kai yaran makaranta da kanku?”.         “Baba bazai yiwu ba, kasan yanda uziriri sukai mana yawa dai, idan muka ce mune zamu kaisu za'aita samun matsala. Ga boko ga islamiyya, ga cefanen gida kai Mammah anguwa da iyalanmu”.         Baba yay shiru zuciyarsa na kai-kawo, dan yasan bazasu fahimci mi yake nufi ba daman kai tsaye, shi kuma tsoro bazai barshi fitowa ya buɗe musu komai ba kai tsaye, sai kawai yace to su bashi lokaci zai kira a waya. Cikin gamsuwa sukai musu sallama suka tafi. Cikin damuwa matarsa ta ce, “Wai miyasa kake ta musu kwana-kwana malam? Mutanen nan mutanen kirki ne, banyi zaton zasu zo da damuwa kanada damar musu maganinta ka kasa ba”.        “Ba kasawa nai ba Tabawa, kawai ina duba al'amarin ne dai kawai, kin san yanda rayuwa ta lalace yanzu ba kowa ke raɓarka da ƙyaƙyƙyawar zuciya ba. Ko ni ɗin ma alkairin su da hukuncin UBANGIJI ne ya sauya ni daga dalilin raɓarsu”.     Cikin rashin fahimta ta ce, “Kamar ya? Ban gane ba malam!”.     Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba ya barta da wasi-wasi. Awa ɗaya ba'ayi da tafiyar su Yaya Ma'aruff ba Baba Driver yayi baƙo. Kasancewar matarsa tasan mutum ya saba zuwa wajensa bata kawo komai a ranta ba ta shiga ciki gida ayyukanta ta basu waje. Dan yana jiyyar a ɗakin soro ne...              “Rabe! Kana ganin taurin kanka zai cigaba da baka nasara ko? Halin da kake ciki bai zame maka aya ba kenan?”.       Murmurshi Baba Driver yayi mai ciwo, idanunsa cike da ƙwalla ya ce, “Ba darasi ne ban ɗauka ba Ari, ina tausayin bayin ALLAHn nan ne. Wlhy mutanen nan munanen kirki ne su da mahaifiyarsu. Sannan ya kamata mu yarda ba laifinsu bane akan abinda ya faru baya, shima kansa wanda ake son azabtar da su ta dalilinsa mufa sani rayukanmu ya jajirce wajen karewa, ALLAH ne ya ƙaddara za'a tarwatsa mu a ƙauyukanmu har mu watse irin haka. Hasalima mutanen nan dake munana shi a garemu sune silar faruwar komai akan waɗan can abubuw......”         “Rabe! Kana nufin wuyanka yayi kaurin bijirema su Oga Dagger ko? Amma kasan minene hukuncin yin hakan a gareka ko? Karka manta kana cikin ƴantattun da aka bama damar zuwa su rayu a cikin mutane har suyi aure su hayyafa cikin ƴanci. Baku san wahala da azabar da mu dake cikin jeji kullum a ɓoye muke sha ba. Mutanen nan da kake ƙoƙarin karewa ance maka kaje kai musu wani abu ne? Information ɗin abinda ke gudana a rayuwarsu kawai akace ka dinga kawowa. Musamman ita wannan yarinyar Nimrah, amma taurin kai yasa ka zauna kana kawowa mutane ƙauli da ba'adi, gashi nan har sai da ka jama kanka zaman guri ɗaya, da da ƙarar kwana ma yanzu wani labarin ake ba naka ba. Ni dai yanzu ga saƙo, Oga Mole da Oga Dagger sunce gobe zasu turo sabon driver ka turashi ga mutanen nan ya maye gurbin ka, zaɓi ya rage naka kayi koka kuskure kai ne zakai kuka, dan a yanzu ba kai za'a hara ba ƴaƴanka ne ko matarka”...       Yana gama faɗa ya miƙa batare da ya saurari magiya da roƙon Baba Driver ba..... ★>><<<<★>>>><<★         ★DUBAI★    Ganin yanda Nabeeha ke faman haɗa kaya ya bama Ismat data kawo mata breakfast har ɗaki tsoro. Duk yanda taso daurewa saita kasa. Cikin damuwa ta ajiye tray ɗin da take ɗauke da shi ta nufeta. Hannunta ta riƙe cikin rauni da damuwa ta ce, “Aunty wai mi kike yi haka ne? Ina zaki kike haɗa kaya?”.          Hannun nata ta fisge, kukan da take faman riƙewa tun daren jiya saboda taurin zuciya a karo na farko ta fashe da shi..........✍️ 12 .........“Ismat zan koma ƙasata, wlhy na gaji da wannan rayuwar, bazan iya ɗaukar huɗubar Momy ba, gara na koma gidan mijina nai zaman jiran dawowarsa ko nan da shekara hamsin ne ma ba ashirin da biyar ba”.        Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ismat ta sauke, dan koba komai itama an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi dama. Ta kama hannun Nabeeha suka koma bakin makeken gadon ɗakin da yaji shinfiɗu na alfarma, dan duk da haɗuwar gidan da komai na cikinsa ɗakinta na musamman ne. Gyara irin na ƴar gata Adeel yasa akai mata. Hannayenta duka a cikin na Ismat ta ce, “Aunty wlhy koni ina bayanki ki koma gidanki, dan ita Momy idannunta sun rufe da son kuɗi bata duba abinda muke so koya dace damu. Ita kawai tafi kallon abinda zata samu. Gamu dai a cikin ƙaton gida a kuma ƙasa irin ta Dubai da kowa ke buƙatar yazo, amma wlhy Aunty Jiddah ta fimu kwanciyar hankali, tana rayuwar auren ta ga yaranta abin sha'awa, shiyyasa wlhy nima na fara ji a raina zanyi na nata na koma gidan Abba na bashi haƙuri na samu miji nayi aure. Dan in har muka cigaba da rayuwa da Momy anan wataran sai mun lalace, dan waɗan nan shaggun mutanen babu abinda suka iya sai son mata kamar su babu matan a cikin nasu ƙabilar”.        “Ismat wlhy ni duk bama wannan ba, babban abinda ke bani mamaki da Momy itafa kawai na kashe aurena saboda wannan mutum yace mata aurena yake son yi, haba miyasa ba zatai tunanin daya dace ba, dukiya irin ta mutumin nan, da nasaba ta gidan mulki, mulkin ma mai ƙarfin gaske ne zai zauna wani auren baƙar fata ƴar Africa saboda rainin hankali da ɗaukar mutane jakai. Kiga yanda suke wulaƙanta matan African fa kamar wasu dabbobi dan ko bayi na baya sun fi matan da ake kawo musu suna iskanci da su a yanzu mutunci da daraja. Wlhy Ismat ina son mijina, duk da ina jin takaicin auren shegiyar yarinyar nan har yanzu a zuciyata....”        “Na sani Aunty, ki share wani batun yarinya kawai muyi tafiyar mu, dan uwarta mune zamu miki maganinta, da ƙafarta zata bar gidan batare da kowa ma ya sani ba ta koma ƙauyen su, idan tace ita ƴar hau ce mu ƴan hau-hau ne to”.      Ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske Nabeeha ta saki, tana mai jin nutsuwa da gamsuwa da zancen autar tasu. A gefe zuciyarta na jin matsanancin kewar mijinta da buƙatar son kasancewa da shi da akoda yaushe take yaƙi da kanta a kai, sauƙi-sauƙin ma da take samu kullum cikin mafarkinsa da yanda yake tafiyar da ita a shimfiɗa take, shiyyasa take samun sassauci da jinsa kamar a kusa da ita har yanzu.....         Da baya-baya Hajiya Hasiba tabar bakin ƙofar ranta a matuƙar ɓace da tattaunawar yaran nata. Ƙayataccen ɗakinta ta shiga, ta zauna a bakin makeken nata gadon hannunta dafe da kanta. Jitake kan nata na wani mugun sara mata, sai dai abinda ke mata kai-kawo na takaicin yaran nata na son danne ciwon. Lallai lokaci yayi da zata nunama su Nabeeha ita ba sankaran uwa bace sha-sha-sha kamar yanda suke tunani. Taya zata bari ma Nasiru yaci nasara a kanta, bayan ya rabata da Jiddah ya rabata da Nabeeha da Ismat da suka rage mata kuma. Ta jima da fahimtar soyayyar da Ismat kema Ja'afar, sai dai bata damu ba ganin yanda shi Ja'afar ɗin yaƙi kulawa, amma yanzu ta fahimci Ismat na zuga Nabeeha ne su koma gidan ubansu saboda son da take ma Ja'afar, kenan da sunje sun kwantar ma da ubansu kai itama sai ya aura mata shi, shekenan ita kuma A'isha ta haifama ƴaƴa ko? To kuwa zasuci ubansu.       Da wannan tunanin tai ƙwafa, tare da miƙewa zuwa gaban wadrobe ɗinta, ta ɗibo duk passport ɗinsu dake wurinta, cire na Nabeeha da Ismat tayi ta canja musu waje, daga haka ta hau shirin fita. Dan tana buƙatar ganawa da Adeel yanzu nan basai gobe ba.....         §§§§§§§§§§§§§§§§        ★EGYPT ★                     “Mammah muje ki huta yau kam kin gaji fiye da kullum. Ga su Yaya Ma'aruff nata kira nasan burunsu kawai suji yanda results ɗin suke ne. Aunty Ummi ma naga ta kira video call ta WhatsApp”. Received      Murmushi Mammah tayi, cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, “Ammar yarana duk sunyi kewata ne, nima ina tsananin jin kewarsu. Dan haka ni kam ba sai sati biyun nan ya cika ba zuwa jibi tunda sunce babu wata damuwa suna bamu maganin nan kawai mu koma gida”.          “Duk yanda kike so haka za'ai Mammah”. Yay maganar yana ɗan rungumota ta gefe, dama kuma suna tafiyar ne hannunta riƙe a nashi. A yanda ya ɗan rungumetan yana dariya itama yana murmurshi da kai masa rankwashi a kai yasa basa kallon gabansu balle mai tahowa. Karaf kuwa sukaci karo da wani abun da ya saka Mammah faɗin, “Subahanallahi”. Shima sai Ammar ɗin ya sake ta yana waiwayawa da ambaton, “Ya salam”. A dai-dai lokacin shima wanda sukai karon ya ambaci, “Subahanallahi” ɗin yana kaiwa duƙe da son riƙo takardun hannunsa da suka tarwatse a ƙasa. Cikin sauri Ammar ya bishi shima yana ƙoƙarin taimaka masa da sake faɗin, “I'm sorry sir”.        Fuskar mutum da murmurshi ya ce, “Karka damu ɗana, nima harda nawa laifin hankalina nakan takardun ne shiyysa ban lura da tahowarku ba. Mama kiyi haƙuri kem......”     Ya kasa ƙarasawa saboda dai-dai ya ɗago ne zai kalla inda Mammah ɗin take sukai ido biyu. Dan itama ta miƙo masa takardar data ɗakko ne datai gefe zatai magana a lokacin, sai ta dakata cak tana kallonsa. Ko shekara dubu tayi bazata manta wannan fuskar ba a duniyarta, balle shekarun da basu wuce talatin ba. Jin sunyi shiru Ammar daya gama tattarowa shima ya juyo yana kallon su, Mammah ya fara kallo datai tsaye ƙyam baki buɗe tana kallon mutum, da sauri ya maida kallonsa kansa shima. Ai da sauri ya wani ja baya yana waro idanu waje da faɗin, “Ya rabbi! Mammah waye shi?”.       Mammah da gaba ɗaya kanta yay wani dimmm ta gagara cewa komai, sai hannunta dake ƴar rawa har sai da Ammar ya matso ya riƙota jikinsa, sai dai har lokacin idanun nasa akan mutumin da alamu ya nuna shima dai yayi sumar tsugunne ne......         >>✿<<>>✿<<>>✿<<                    “Assalamu alaikum”.     Aka kwaɗa sallama daga bakin ƙofar falon bayan anyi knocking har sau biyu. Ƙaramin tsaki Mu'azz dake zaune shi kaɗai a falon yana cin abinci yaja, ya tsani tashi yana cin abinci, dan yana tashin shike nan abincin ya fita a kansa kuma. Hanyar kitchen ya kalla inda yake jiyo surutun Nimrah da dariyar Biebah. Sai kawai ya ɗaga murya ya ce, “Ninah!”.        Daga can ta ce, “Kai Yaya Mu'azz miye kuma dan ALLAH? Bana kawo maka harda ruwa ba”.           “To uwar son jiki, dalla fito kiga waye ana knocking ne”.       Baki a sama ta fito, tana sanye cikin shirt da riga na lass milk da furanni coffee. Tayi ƙyau sosai daka ganta kaga ƴammatan zamani masu shegen iyayi da rawar kai. Harta nufi ƙofa ya ce, “Haka zaki fita ba hijjab?”. Baki ta ƙara turawa gaba, ta dawo ta ɗauka hijjab da sukan ajiye a falon saboda irin haka, dan Mammah ta saba musu sakawa musamman idan akai baƙon ido ko suka saka ƙananun kaya, wani lokacin ma sai taga kamar anfi takura mata da sakawa fiye da Ruky da Aunty Biebah. Sai da ta saka ta zura hannayensa sannan ta nufi ƙofar da aka sake bugawar, sallamar maigadi ta amsa tana buɗe ƙofar. Ya ɗan ja baya yana gaisheta.           “Baba ni dai ka daina rissina min dan ALLAH. Ina wuni?”.     Murmurshi maigadin yayi da faɗin, “Ai girmanki ne Hajiya. Dama baƙone yazo yace kuma sabon driver ne Malam Buba tsohon Driver ya aikosa”.      Ɗan jimm tayi sai kuma ta ce, “Okay to bari na sanarma Yaya Mu'azz, dan su Uncle's duk basa nan. Ammie da Ummie ma sun tafi gidan Mom (Aunty Mimi suke kira Mom) data haihu ɗazun”.        Fuska ɗauke da murmushi ya ce, “ALLAH sarki ALLAH ya raya, ya albarkaci abinda aka samu”.      “Amin ya rabbi”. Ta faɗa tana rufe ƙofar ta juya ciki. “Yaya wai sabon driver ne, kuma Baba Driver ya turoshi”.      Ɗagowa Mu'azz yay yana kallonta, sai kuma ya maida kansa ga television yana faɗin, “Oh to sannunsa da zuwa. ALLAH ya iyakance min jigilarku kullum kuna damuna da surutun ku da fitina. Ki haɗa abinci ki kai masa dan abinci nake ci sai na kammala na fita mu gaisa”. Received          Sai da ta cika baki da iska cikin ƙunƙuni ta nufi kitchen tana faɗin, “Ni wlhy yau ƙafafuna duk ciwo suke, dan anga Mammah bata nan sai wahala ake bani, yau tunda muka dawo school ban huta ba komai ni....”      Fiiiffgg! Filon kukera da Mu'azz ya jiho ya sameta a baya. Tako dage ta ƙwalla ƙarar data saka Biebah fitowa daga kitchen da gudu tana tambayar lafiya da riƙo Nimrah ɗin. Kai Mu'azz ya girgiza cike da takaici yana nuna fillon daya jefeta da shi.        “Small Mom fillo fa kawai na jefa mata dan tana min ƙunƙuni shine take wannan ihun. Wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH. Wai uwar wa ma ya hanaki bin su Ammie ne kamar yanda Ruƙayya tayi?”.         “ALLAH sai na gayaka da Uncle, kuma ai dai naji zafi. Tunda na dawo kaketa sani aiki, na maka gyaran ɗaki, kace na maka ɗan wake, duk baka gani ba sai da ka ci zalina”.      “Oh gori kike min saboda kin min gyaran ɗaki da ɗan wake? Lallai ma Ninah ni ko”.     Kai Biebah ta girgiza da jan ƙaramin tsaki ta koma ciki tana faɗin, “Kudai bazaku taɓa canjawa ba ALLAH ya shirye ku. Ba sai ku cinye kanku ba jarababbu. Wlhy na ƙagara Mammah ta dawo gidan dan kun isheni”..........✍️      15 ........Shi ma'abocin ibada ne da ƙoƙarin ganin ya kiyaye dokokin UBANGIJI da kusantuwa da shi a lokacin da yake rayuwa kamar kowa. A yanzu daya ɓuya bisa faifan ƙaddararsa da jarabawa da makircin masu makirci hakan bai sauya komai ba. Sai himma da dagiya da hakan ya ƙara masa wajen sake kaɗaice UBANGIJI da bauta. Halin da yake ciki bai taɓa sakawa yaji kasawace ko tauyewa daga UBANGIJIN SA ba. Bai kuma taɓa jin nasara ce ga azzalumai ba. Bai taɓa mantawa da ƙasar da talakawan ƙasar ba. Yanda yakema kansa addu'a da zuri'arsa haka yake addu'a ga ƙasa baki ɗaya.      Tabbas a siffa ta jikin ƙarfi da ALLAH ya bashi zuwa yanzu ya risina, sakamakon canjawar tsarin abincinsa zuwa zaɓin wanda ake ciyar da shi a yanzu. Shiyyasa ya zaɓi ɗaukar matakin yin azumi yau, gobe ya huta, azumi ibada ce mai girma, sannan kariya ce daga jarabawar ɗan adamtaka ta lafiya da halittun jiki da UBANGIJI ya ni'imata mu da su musamman akan abokan rayuwa. Nauyin jiki da raunanuwar ƙarfi bai sa ya gaza wajen ƙoƙarin cigaba da ƙarfafa ƙashi da tsoka da sauran ƙarfin daya rage masa ba, dan a cikin wannan nan dai tsukun ɗakin da yake ciki yakan gudanar da ibadarsa ya kuma motsa jiki da salo-salo irin nashi. Rashin ƙarfafa damuwa a zuciya, ya bashi kariya daga cututtukan zamani irin su hawan jini balle ciwon zuciyar da maƙiya ke fatar masa a kowane motsinsu. Ya riga ya amince UBANGIJI shine mai komai da kowa, idan kunga alkairi daga gareshi ne, saɓanin hakan daga shaiɗan ne ko halayenku ko jarabawar da zata sake ɗaukaka darajar ku zuwa wani mataki na duniya ko lahira. Yayi imani da hakan shiyyasa damuwa ta kasance abu na ƙarshe da zai iya cewa yana yi. A duk sanda ya tuna da ahalinsa musamman jajirtacciyar uwa irin Mammah, yakan mata addu'a da fatan samun nutsuwar zuciya daga shiga damuwar halin da yake a ciki. Hakama ƴan uwansa da suke masa kallon uban da matarsa daya tabbatar soyayyarsa mai ƙarfi ce a zuciyarta. Hatta ƴar amanarsa tana nan zaune daram a zuciyarsa, yana kuma mata addu'a da fatan rayuwa mai nasarori a yau da gobenta, sai dai daga ita har Nabeeha yana jiran wani lokaci ne da zai sawwaƙe musu suje suma su sake gina sabuwar rayuwar su.        Bai yanke hukuncin fita a wannan wajen ba, dan bashi da wani tabbacin fitar. Sai dai yana fatan aikin daya ɓuya domin yinsa da hana Imran shiga cikin tarnaƙin su tabbata. Dan in har ALLAH ya bashi tsohon rayuwa a kurkukun nan, akwai matsayin da Imran zai kai a gidan soji da zai sa babu wanda ya isa hanashi zuwa ziyartarsa a-kai-a-kai. Idan kuma har UBANGIJI ya bashi damar cika shekarun da suka ɗiba masan ya tabbatar lokacin da zai fita koda bashi da ƙarfin jiki dana aiki, yana da zuciyar bin waɗan can azzaluman ɗaya bayan ɗaya ya hukunta su da hannunsa. Balle ma ko a yanzu ya gama shirya in har yay wasu shekaru a wajen nan sai ya nema hanyar dinga fita yana aiki yana dawowa koda a ƙarshe zai bayyana kansa a ƙarasa yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai koma kashe shi kai tsaye....        Motsin buɗe ƙofar da akai ya saka tunaninsa katsewa, dan yana duk wannan tunanin ne tare da push-up daya sabama kansa yi sama da ɗaruruwa a kowane rana koda yana azumi. Dan haka har yanzu jikinsa a bubbuɗe yake sai dai raguwar ginanniyar tsoka da bata samun sinadarin da take buƙata kamar baya. Daga yanda yake push-up ɗin kawai ya ɗan ɗago idanunsa ya kalla yaran sojin guda biyu ya janye yana cigaba da abinsa.      Suma sake nutsuwa duk sukayi, dan su sun san badan zaki na keji ba basu isa ziyartar ko gefen dajin da yake farauta ba. A tare suka ƙame tare da yin salute ɗinsa, kafin na gefen damarsa ya furta, “Sir kana da vistor ne”.       Cak ya ɗan tsaya na sakan, sai kuma ya cigaba da abinda yake batare da yace da su komai ba. Fin mintuna uku, dan har sai da ya cika adadin da yake buƙata kafin ya tashi da ƙyau tamkar ba shi ya gama push-up ɗin ba yaja ƙaramin towel dake jikin ƙarfen gadon kusa da sallaya ya fara goge hannunsa zuwa wuyansa. Sanye yake cikin uniform ɗin prison ɗin, amma hakan bai hana su kasancewa fes ba alamar baya barinsu da datti, sai dai sun koɗe sosai alamar tsufa da gajiya. A karo na farko ya furta, “Tsawon shekaru biyar kenan a tsarin jadawalin da doka ta sharɗanta a kaina No visitors, no communication. Miya canja hakan a yau daga dokar?”.      Sake duƙar da kawuna sukai, kafin ɗayan yay magana cike da girmamawa. “Sir muma bamu sani ba. Umarni kawai aka bamu na zuwa da shi inda kake”.       Idanu ya zuba musu sosai su duka biyun. Wani ɗan murmurshin gefen baki da shi kaɗai yasan yayi kayansa yayi. Ya ajiye towel ɗin a kan ƙarfen gadon ya taka a nutsensa cike kuma da tafiyar nan tasa ta nutsuwa, dattako zuwa gabansu bayan ya saka slippers a ƙafarsa.        “Ku aikata aikin soja, Captains. Na fahimta.”      A tare suka sara masa, zukatansu na sake jin rauni, ƙaunarsa da girmamawa.     “Sir… I’m sorry.” Suka sake faɗa a tare. Bai ce da su komai ba face miƙa musu hannayesa duk biyu. Dan doka ce fita da shi sai da handcuffs. Jikin sojan har ɗan rawa-rawa yake a ƙoƙarin ɗaura masa handcuffs ɗin, haka dai ya gama suka koma gefe suka bashi hanya. Shine ya fara fita sannan suka bi bayansa har ɗakin ganawar. Vistor ɗin nasa ya juya baya, dan haka bai fahimci ko wanene ba sai da ya zauna a kujerar da aka tanada domin shi.....   <<<>>><<<>>>    ★EGYPT★        “Mammah dan ALLAH ki daina kukan nan ya isa haka”.     Ammar ya faɗa cikin tashin hankali muryarsa na rawa idanunsa shima cike da hawaye. Sai kuma ya dubi mutumin da shima ke sharar hawaye ya ce, “Bawan ALLAH ka min bayani dan ALLAH. Minene alaƙarka da Mammah ta? Ku taimaka ku sanar min kada zuciyata ta fashe, dan kukan Mammah ba ƙaramin azabtarwa bace mai ƙuna a zuciyata”.         Hawaye mutumin ya sake sharewa da handkachiff harda ɗan fyatar majina. Kafin ya kalla Ammar cikin rawar muryar alamun tahowar wani sabon kukan ya ce, “Ɗana ka kwantar da hankalinka, duk da ban san wanne a cikin ƴaƴan nawa ba ina ji a raina ko Bilalu ko Abdul-rasheed (Ammar) ne kai. Dan kune dai ƙananu da zan iya gani a wannan shekarun ba Haysam ko su Ja'afar da Ma'aruff ba”.     Kafin Ammar yay magana cikin zafi Mammah ta ce, “Har kana iya cigaba da riƙe zuri'ata a cikin ƙwaƙwalwarka amma ka gagara waiwayen inda nake Tasi'u....?”         “Wlhy Adda A'isha kunya ce ta hanani, tsananin kunyarki nake ji da tsoro da nadamar son zuciyata. Ina ganin bazaki sake kallo na ba a rayuwarki, bazaki sake son ji koda daga wani ne kina da ɗan uwa irina ba. Adda A'isha ni azzalumi ne butulu da ban cancanci gafara daga gareki ba balle marigayi Yaya Abdul-rasheed, dan kuwa mun kasance butulu da ga ni har Bashir da danginsa......”         “Bashir bai kasance butulu a gareni ba, dan kuwa na tabbatar idan shine a raye komai girman laifin da yake ganin ya min bazai ɓoyema ganina a tsaho waɗan nan shekarun ba. Haba Tasi'u, kun maida ni mara kowa a duniya, mara gata, mara dangi gaba ɗaya. Badan Yaya Nasiru ba da nace ban san daɗin zuri'a ba a duniya. Da ƴaƴan Kawu kamar sun waiwayemu munata zumunci har bikin su Haysam duk dasu a kayi suma yanzu sun sake ɗauke min wuta gaba ɗaya saboda ƙaddarar rayuwa da muka sake shiga. Shike nan kowa ya juya bayansa a garemu dangina dana Abdul-rasheed idan ka cire Jamilu da su Khadijah saboda kawai sune ciki ɗaya da Abdul-rasheed. Wlhy idan kowa zai barni banyi tunanin harda kai ba da muke ciki ɗaya Tasi'u, kada ka manta nice na fita a cikin Inna ka kwanta, sannan nice na gama sha daga jikinta ka amsa. Miyasa zaka gujeni tsawon shekaru ashirin da shida, a talatin kaɗan ne babu rabona da kai fa Tasi'u. Miyasa? Miyasa haka?”.         “Wlhy kunya ce kamar yanda na sanar miki Adda, dan ALLAH ki yafeni ki gafarce ni na tuba”.     Yay maganar yana sauka ƙasa ya durƙusa a gabanta tare da riƙe ƙafafunta duk da kuwa shekarun dattijantaka sun bayyana a gare shi shima. Bata hanashi ba, sai kuka da take itama. Ga Ammar dake rungume da ita shima tuni kukan yake, dan a duniya basa ƙaumar ganin hawaye Dada da Mammah na ɗiga. Tsohon lokaci suna a haka kafin Mammah ta fara tsagaita nata kukan ta kama dattijon tana miƙarwa da faɗin, “Shike nan ya isa. Na yafe maka  ka share hawayenka. ALLAH ya yafe mana gaba ɗaya. Ya jiƙan Inna da Baba da Abdul-rasheed da Bashir. Amma dan ALLAH karka sake yin nesa da ni kaji”.        Tashi yay ya koma kan kujerar yana share hawayen nasa da faɗin, “In sha ALLAHU har abada bazan sake nesa dake ba Adda, na baya ma kunya ce da nadama ta sakani dole. Amma wlhy a kullum cikin begen son ganinki nake keda zuri'arki”.        “ALLAH ya rufa mana asiri”.   Mammah ta faɗa tana shafa kan Ammar alamar lallashi. Ɗakin ya sake ɗaukar shiru na wasu mintuna kafin ta kallesa ta ce, “Mi kake yi a Egypt? Ko nan kake aiki?”.         “A'a nazo ganin likita ne kawai. Yanzu ina Paris. Sai dai kusan shekara ma biyar kenan na koma ƙasarmu, kawai dai ina zaune a kudanci ne sakamakon tsoro da fargabar tunkarar ki.      Murmurshi Mammah tayi mai ƙayatarwa da faɗin, “Ja'iri ashe kana shakkata?”.          “Adda wlhy ina yi dan kece madadin Inna a wajena. Ya bayan rabuwa ya iyalai?”.       “To sai godiyar ALLAH, Iyalai kuma duk gasu nan sun girma sun zama magidanta. Duk da dai Bilal da Ammar da Biebah basu kai da yin aure ba. Amma Alhamdullah duk komai ya dai-daita babu abinda zamuce da UBANGIJI sai godiya”.         “Alhamdullahi naji daɗi sosai wlhy Adda. Kice yanzu gida ya cika da ƴan jikoki na”.       “A ya cika kam. Dan a ƙalla yanzu kana da jika goma sha bakwai zuwa sha tara nan gaba kaɗan, dan yanzu haka yau ɗin nan Mimi ma ta sake haihuwa ta huɗu. Matan Ma'aruff da Ja'afar ma duk suna da ciki a yanzu haka na uku-uku duk da ƙarami ne.”        “Kai Masha ALLAH lallai zuri'a ta haɗu. Ina yaron kirki Haysam?”.     Shiru Mammah tayi na sakanni, sai kuma tai murmurshi gajere da faɗin..........✍️ 16 ..........“Yana lafiya shima Alhamdullah. Kai fa ina fatan dai ƙanwata ta koma ko ka sake sabon aure?”.     Kansa ya ɗan shafa yana murmurshi, sai kuma ya ce, “Ta koma bayan taga na koma da kuɗin gidan nan, dan har mun sake haihuwar yara biyu ma. Amma ta rasu shekara kusan bakwai data wuce. Sai yaran yanzu kawai.” ya ƙare maganar idanunsa na tara ƙwalla. A take tausayinsa ya sake kamata. Ta shiga jajantawa da masa ta'aziyya. Shima Ammar yay masa ta'azziya. Dan har yanzu bai san ainahin wanene shi ba, tunda sanda wacan abun ya faru suna yara sosai musamman shi da Mimi ma da basu wuce shida zuwa bakwai ba maybe, sai dai ya fahimci ɗan uwan Mammah ne na jini koda kamanni da yanayin tattaunawar tasu.      Cikin share sabbin hawaye Tasi'u yake amsa musu. Mammah dai ta babbashi haƙuri daga haka ta koma jansa da hira harya saki jiki shima yana jan Ammar a jikinsa...... %><%><%><%><%>          Kwance take a madaidaicin gadon ɗakin daya kasance guda biyu iri ɗaya hannunta da waya tanata faman zabga murmushi, kai da gani kasan wani abu dake ƙayatar da ita take kallo. Dai-dai nan Ruky ta buɗe ƙofar bayinsu ta fito, ɗaure take da towel alamar wanka tayo, ganin yanda Nimrah ke zabga uban murmurshi bakinta har kunne yasa ta matsawa kusa da ita ta yarfa mata raɓar ruwankan dake ta bin farar fatarta.        Ɗagowa Nimrahn tai da sauri irin na firgita, dan haka Ruky ta ƙyalƙyale da dariya. Cikin harara ta kai hannu ya goge ruwan data yarfo mata ɗin ta ce, “Ƴar wulaƙanci miye na yarfa min ruwa?”.      Ruky na ƴar dariyarta har yanzu ta ce, “Gani nai kinata faman washe baki kamar ƴar tallar makilin, wai har yanzu hoton jaririyar kike faman kallo?”.         “Humm bazaki gane ba Ruky ALLAH jarirai nada ƙyan kallo, ina son jariri sosai, shiyyasa kike ganin duk sanda su Ammie suka haihu nake tarewa a sashensu. Ke nifa ko aure nayi duk shekara zan dinga hauhuwa”.       “Kambu, Ninah amma baki da hankali, duk shekara fa?”.     “Eh wlhy, ke ni ƴan bibbiyu ma”.   Zama kusa da ita Ruky tai da mai a hannu ta ce, “To ALLAH ya baki. Ni sai da kikai maganar haihuwa ma kika tuna min da sayyadi Kamal. Hummm bawan ALLAHn nan fa da gaske kamar yanda ƴan ajinmu ke gulma ya mutu a kanki Ninah, idan yana karatu hankalinsa duk a kanki. Ga kuma Teacher Khalil, yanda ya wani dage yana karemu randa muka suburbuɗi Hibba Abubakar na sake tabbatar da zancen Maimoon Qasim fa”.      Baki Nimrah ta taɓe tana gyara zama. “Ruky rabani da wannan shashancin kinji, ni wlhy duk basu min ba.”        “Kai Ninah kiji tsoron ALLAH, wlhy duk ɗinsu sun haɗu, dama dai kawai kice ba yanzu ba ne sai na yarda, dan mukace mun kawo samari yanzu ai ƙaniyarmu Uncle's zasu ci, musamman Uncle Bilal da akoda yaushe yake mana gargaɗin nan. Amma ALLAH nidai ina son soyayya, kinga idan naga Seniors ɗin mu na lobewar nan da boyfriends ɗinsu, ko mazan da ƴan mate ɗin mu sai naji kamar na bama Anwar ko Uncle Haneef ɗin gidan Mamy dama”.          “Lallai Ruky baki da hankali, yo ALLAH na tuba ko soyayya zanyi mi zan wani yi da ƴan tamatsitsin yaran school ɗin mu. Yo yaushe suma aka gama aikarsu kiran yayunsu gida. To ALLAH bari kiji, ko dariya naga kimma wannan Anwar ɗin sai na ci masa mutunci. Karki maida mu marasa aji mana, ƴan yara da su inama laifin kamar Yaya Ammar haka. Amma kosu Teacher Khalil nawa suke”.        “Hhhh shegiya Ninah, wato marasa aji? To yaushe ma muka gama tafasar balle mu ƙone har kike batun wani aji. Shekara sha biyar fa muke. Ga aunty Biebah nan harta kammala master ɗinta bata ma zancen aure, ta dage sai Dada ya dawo gida zatai aure. Hakama Aunty Ma'u dake ƙoƙarin kammala Secondary ita da Aunty Halimatu, balle azo kammu haihuwar jiya inji Yaya Mu'azz. Da kike kiran su Teacher Khalil yara kuma, ai bana jin Yaya Ammar zai girmesa. In baki so kamarsu ba tsoho kike so kamar su Daddy ko mi?”.        “Ƴar wulaƙanci, kamar su Daddy kuma? Kamar shekarun Uncle Ammar dai, amma kamar su Daddy ai da kunya ƴar soyayyar nan bazaka samu ka bajeta ba, kin san kuma nifa ina son harkar nan ta love ba wasa” tai maganar tana kashema Ruky ido ɗaya, bata jira cewar ta ba ta cigaba da faɗin, “Ya Mu'azz kam bar ɗan rainin hankali, shima sai kace ba haihuwar jiyan ba. Ya gama mana rashin m ɗinsa dai sai mun riga shi aure. Dan mu yanzu idan Daddy yace rana ɗaya za'a haɗa auren da Small Mom da su Aunty Ma'u mune next. Shifa, sai ya jira Uncle Bilal, Uncle Ammar da Yaya Khalifa ma ƙila, to ko Yaya Imam ya girmesa.       “A'a wlhy kar ki masa baki, duka shekara nawa Yaya Khalifa ɗin ya bashi, sai dai ayi musu tare, gara Yaya Imam to, kuma shima tare suke tafi a school ai”.     Cike da dariyar mugunta Nimrah ta ce, “Oho dai, ko haka ɗin mun more masa. Ke muyi gulma mana. Dan ALLAH baki ga wai kamar Uncle Bilal da Aunty Ma'u akwai wata a ƙasa bane?”.       “Humm wlhy na gani, ranar graduation ɗin su Small Mom sai wani kallon ƙasan ido yake mata.” dariya suka kwashe da ita harda tafawa. Nimrah ta ce, “Wlhy soyayya tayi Besty, idan ban samu ɗan soyayya ba na rako mata duniya”. Cikin dariya Ruky tace, “Muna son soyayya zaki ce, ai duk wanda yazo sai mun tantance shi walle karki damu, love ai duniya ce”. “A wlhy love duniya ce, shiyyasa nake son maƙalewa a sashen su Mamy, dan in ana bajakoli su da su Uncle's nasha kallona”. “Muguwa, wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH, tun baki tafasa ba zaki ƙone. ALLAH yasa su ganoki suci ƙaniyarki, kinga sai ai miki auren ai”. “Shegiya ni da ke ai duk sammakal ne, zatace ta tadda muje mu”. Dariya suka sake fashewa da ita suna tafawa.....     Buɗe ƙofar ɗakin nasu ya saka su yin shiru, sai kuma duk suka rufe bakunan nasu da hannu. Biebah ta hararesu.        “Anya kuna duba agogo kuwa? Kuke mana irin wannan ihun dariyar haka kamar sabbin kammu”.       “Kai Mom ALLAH hira ce kawai tai daɗi”.      “Kuma da ihu haka? Na sake jin wannan dariyar kamar ba mata ba sai na ɓata muku rai. Dalla ku bani wayata kuyi shirin barci ku kwanta” tana gama faɗa ta amshi wayar tata da Nimrah ke kallon hoton baby, Dan su basu da waya Uncles nasu sunce ba yanzu ba. Juyawa tai ta fita tana mai rufe musu ƙofar. Gwalo sukai ma bayanta a tare, kafin Nimrah ta miƙe zuwa bayin itama dan yin wanka. Bata wani jima ba ta fito, lokacin har Ruky ta gama nata shirin barcin ta haye gadonta, dan kowa da nashi. Ƙasa-ƙasa suka cigaba da hirar a haka kuma duk ta sanari har Nimrah ta shirya itama ta haye nata gadon.        WASHE GARI da wuri suka ta shi, babban burinsu tafiya gidan Aunty Mimi ganin baby musamman ma Nimrah da jiya ba'aje da ita ba. Dan tana barci su Aunty Shariffa suka wuce da Ruky, sai yau Biebah tace zasu je tare tunda itama bataje ba taje Tahafiz, amma tace mata yau ma sai sunje sun dawo daga Tahafiz suma sannan. Rashin sabon barcin safe saboda makaranta yasa suna kammala salla sukai bitar karatun Alkur'ani dan sun san yau sayyadinsu zai amshi hadda sukai azkar kowa ya miƙe. Ruky ta fara gyara ɗakinsu ita kuma Ninah ta wuce gyaran ɗakin Biebah. Koda ta shiga ɗakin Biebah harta sauka ƙasa taya masu aiki haɗa breakfast ita kuma. Sun kammala gyara ɗakuna har bedroom ɗin Mammah duk da bata nan basa gajiya da gyarawa sannan suka shiga wanka. Dama bedrooms suke gyarawa da sama ɗakin su Yaya Ammar, sauran wajaje kuma masu aiki. Shirin sukai cikin uniform ɗin islamiyya su ash color na wando da hijjab har ƙasa tsahon hijjab ɗin yasa da yawansu basa yin rigar suke saka t-shirt a ciki. Fitowarsu dai-dai da fitowar Biebah daga nata ɗakin tana wani kalar sassanyan ƙamshin turare. Su duka kasa haƙuri sukai sai da suka tanka.       “Woow Small Mom kin sayi sabon turare ne? Wlhy wani ƙamshin bala'i mai kassara jiki”.       Murmushi tayi tana ɗan girgiza kanta. “Yan biyun Mammah kenan iyayen iyayi ƴammatan gobe. To wannan ƙamshin da kuke ji ba turaren kanti bane, haɗaɗen turaren gida ne dan khumra ce ma kawai na ɗan shafa sai kabasa da nayi a kaya na, nima a sashen Aunty Lailah na samoshi. .......Gaba Biebah tayi tana musu dariya, dan in dai halayen Twins ɗin gidan nasu ne tafi kowa sabawa. Suna sakkowa dining suka nufa, Mu'azz ne kawai zaune yana kari shima sanye da uniform ɗin islamiyyar. Cike da neman magana Ruky ta ce, “Su Yaya yau kuma da yunwa aka tashi?”.      Harara ya wulla mata, batare daya tanka ba ya cigaba da danna doyarsa a baki. Nimrah tai dariya tana zama a kujerar kusa da shi. “Kaga rabu da ita Yayana. Kasan ita Ruky wani lokacin uwar gulma ce. Ina kwana”.       “Ai ke da ita duk sammakal. Wannan saurin gaisuwar bana ALLAH bane faɗa min nawa kike so?”.      Dariya Biebah da Ruky suka sanya. Cikin ɓata fuska da tura baki Nimrah ta ce, “Kai Yaya sai kace wata mayyar kuɗi, kai shike nan bazamuyi shirin arziƙi ba sai ina son kuɗi”.           “A to nasan halinki ne ai Ninah”.     Tashi tai a kusa da shi ta canja kujera, ya ce, “Oho dai”. Bata kula shi ba, dan dai-dai nan ma su Abees suka shigo da gudu suma sanye da irin uniform ɗinsu. Tuni Nimrah ta miƙe tana faɗin, “Oyoyo my Afry”.      Ai ko da gudu Afrah tai kanta, ta ɗagata sama tana juyi da ita suna dariya dan ƴar gidanta ce. Su Aheel kuwa wajen Ruky da Biebah da Mu'azz sukayi suma. Nan fa surutun falon ya ƙaru, dan bayan yaran sun gaishesu suma duk zama sukai Ruky ta saka ma kowa abinci a gabansa. Sai da Biebah ta tsawatar ma surutun basu sannan sukai shiru kowa ya maida hankali ga abincinsa. Shaf-shaf suka kammala suka fito karsu makara.       Yau sabon driver ɗin su ne zai kaisu. Wanda suna haɗa ido da shi yau ma gaban Nimrah ya faɗi, dan haka ta kauda kanta gefe tana gaishe shi kamar yanda su Biebah ke gaishe shi. Dan ba yaro bane. Gaba Mu'azz ya shiga shi da Abees da Aheel. Su kuma ita da Ruky da Biebah suka shiga baya, sai Afrah da Ayyan tare da su. Mu'azz ne ya dinga nuna masa hanya har suka iso. Islamiyyar su babba ce sosai, dan harda securitys. A inda ya dace yay parking duk suka fita. Karaf suka haɗa ido da Nimrah, yanda tsigar jikinta ta wani tashi sai da ta ambaci hasbunalahu wani'imal wakil a zuciyarta. Da sauri ta kama hannun Afrah suka bar wajen. Shima kansa ya kauda yana maida idanunsa kan Mu'azz.       “Ɗana zan tafi ne ko zan jira ku anan har ku fito?”.     “A'a Baba zaka koma gida, sai ƙarfe ɗaya kuma in sha ALLAHU sannan an tashi su Ayyan kazo ka ɗaukesu mu kuma ka taho mana da abinci, sai anyi la'asar kuma ka dawo ka ɗauke mu.”           “To to ba damuwa ALLAH ya nuna mana”.     “Amin ya rabbi, zadai ka gane hanya ko?”.      “Sosai kuwa, karka damu zan gane. Ai na taɓa aiki tanan wajen sosai dan nayi taxi”.      “Oh ALLAH sarki, shike nan sai an jima ɗin to baba”. Daga haka shima Mu'azz ɗin yabi bayan su Nimrah da tuni sun shige.....     }}}{{{{}}}}{{{{           “Alhamdulillah Sir! Yanzu kam komai ya kammala kenan, sai jiran umarnin fara campaign”.      “Haka ne Imran, amma ni duk ma jikina yayi sanyi. Badan al'amarin Haysam ba banga abinda zai kai ni shiga siyasa ba. Dan siyasar ƙasar nan sirrikan cikinta basu da daɗin tonawa. ALLAH dai ya rufa mana asiri ya ƙara kare mana imaninmu”.        “Amin ya rabbi Sir. Amma abubuwan dama ko ba'ace komai ba duk mai hankali yasan akwai ɗunbin kwamacala a ciki kam. ALLAH dai ya kare mana ku, ya azurtamu da shugabanni na gari.”     “Iyakarta kenan kam. Mu dai ku cigaba da mana addu'a, ku dinga saka yara na mana.”         “In sha ALLAHU Sir za'a ƙara dagewa, dama anayi a koda yaushe. Sir nace yanzu bazaka sake sama mana damar ganawa da Haysam ba. Wlhy ina cikin matsanancin matsin zuciya na kewarsa matuƙa. Shekara biyar ba kwana biyar ba”.      Sosai tausayin Imran ya sake cika zuciyar Janar, dan har idanun Imran ɗin sun cika da ruwan hawaye. Cikin kwantar da murya ya ce, “Kayi haƙuri Imran, na san kai da zuri'ar Haysam da iyalinsa dole ne ku kasance cikin bege da kewarsa. Kuma hatta muma muna cikin wannan yanayin. Amma ina sha ALLAHU aski ne yazo gaban goshi, kasan kuma masu iya magana sunce daman yafi zafi. Dole ne mu cigaba da daurema zukatanmu, dan wannan gaɓar da muke da babban shiri a kansa tafi kowace gaɓa nauyi da haɗari, idan mutanen nan suka fahimci muna da wani shiri wlhy zasu iya kashe Haysam ta guba da hanyoyi masu sauƙi dan a yanzu sun fimu kusanci da shi. Mu cigaba da masa addu'a kamar yanda muka saba, tunda muna samu labari mai daɗi akan kasancewar sa cikin koshin lafiya daga yaron nan Captain Ibrahim, na yarda da yaron bazai kawo mana zancen daba haka yake ba, muma shaida ne tunda ya kawo mana wasiƙa da muka tabbatar daga Haysam take. In sha ALLAH ko ban samu mulkin nan ba a wannan karon zan ƙara ƙaimi Imran”.         “Maganarka haka take Sir, kayi haƙuri nima kewa ce da damuwa harta sani faɗar hakan. ALLAH ya saka maka da alkairi ya bada ladan zuminci.”      “Karka damu Imran, wlhy har cikin zuciyata nake jinku kai da Haysam da Haydar, dan naji matuƙar daɗin aiki da ku fiye da yanda kuke tunani. Shiyyasa nake jinku tamkar ƙannena da muka fito uwa ɗaya uba ɗaya. Zan iya bada rayuwata akan ganin Haysam ya fita, dan ya yimin abubuwa da bazasu ƙirgu ba. Sau biyu Haysam na tarar harsashi a wajen bani garkuwa, kuma duka biyun a jikinsa suka ƙare har yay jiyya. Taya zan manta da irin wannan ƙanin a duniyata in dai ina numfashi.”        Hawaye Imran ya share yana ɗan murmurshi, ya ce, “Ka cancanci fiye da haka a wajenmu Sir. ALLAH dai ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, ya kuma cika burin alkairi”.      Sun cigaba da hira da duk ta shafi batun Dada da siyasa. Kafin Imran yay masa sallama ya fito. Da yake cikin ɓadda kama yake maimakon gida sai ya ɗauki hanyar kasuwa, dan jiya Mimi ke sanar masa haihuwar ta, yanzu haka ma ya bari Aunty Hafsat zata je can barka. Wani shago ya fara shiga, sai da ya tabbatar babu mai bin bayansa daga gidan Janar sannan ya fito ya nufi babban shagon su Ma'aruff da yafi kowane shago girma da cikar kaya a kasuwar. Dan kuwa ƙaton waje ne da zaka iya samu abubuwa da yawa da duk ya shafi kwalliyar jiki. Ɓangare-ɓangare ne, akwai atamfofi, abayas, lesuka, shadda, materials, kayan yara tun daga kan jarirai har zuwa samari. English wears na mata dana maza, mayafai. Kai duk wani abinda ya shafi sutura ta maza da mata, yara da manya akwai ta. Sai bangaren kayan kwalliya, akwatina, cosmetics komai har zinari suna sayarwa. Kai shagon nan dai sai Alhmdllh, dan ko yara masu aiki sunfi ashirin a ciki. Suko manyan gwasake na office abinsu. Ga camaras tako ina da suke kallon shiga da fitar kowa daga ofisoshin nasu...         A tare ma ya taddasu a office ɗin Ja'afar, dan sakatariyansu batama yi yunƙurin fara zuwa neman masa izinin shiga ba sanin wanene shi a wajensu. Sai ma gaisheshi data shiga yi cike da girmamawa. Ya amsa mata a taƙaice yana wucewarsa yay knocking direct, sannan yay sallama ya shiga. Cike da farin cikin ganinsa da girmamawa suke masa barka da zuwa. Ma'aruff ya ajiye kofin tea ɗin hannunsa da yake sha yana miƙewa ya gyara masa kujera, dan basuyi breakfast a gida ba saboda sun makara aka haɗa musu suka taho da shi.         “Cin abinci a office sai kace tuzurai?”. Imran ya faɗa cike da tsokana. Dariya sukayi a tare. Ja'afar ya ce, “Yaya makara mukayi wlhy, kasan kuma twiny da wutar ciki ya azalzalan dole muka taho da shi. A haɗo shayi ko coffee ko kunu?”.      “Haba sai kace wani ku, sai da Auntynku ta cika min ciki na fito nikam. Bani ruwa mara sanyi kawai it's okay”.         Ja'afar na dariya ya kawo masa ruwan, da kansa ya zuba masa a kofi sannan ya zauna suna gaishe shi a tare. Da kulawa ya amsa musu, da faɗin, “Gobe su Mammah zasu dawo ko?”.      “In sha ALLAHU Yaya, wlhy duk kewarta ta ishemu gidan ba daɗi. Autocinta ma duk sunyi sanyi ko ƙiriniyar basa yi da ƙyau kwana biyu”.         “Ai ni kaina kewar tata nake. Jiya da safe dana leƙa gidan duk sai yay min wani iri. Dan itama Ammah ta maƙale a ƙauye taƙi ta dawo Abbah nata ƙorafi”. Received at 2:05 PMReactions    Cikin dariya har suna haɗa baki wajen faɗin, “Ai jiya da muka je da daddare yanata faɗa, wai yau tunda safe zai aika driver a ɗakkota, shi ya gaji su Mabruka nata bashi kwamacalar abinci, tuwon ma jiƙaƙƙe suke masa”.       Yanzu kam dariya suke harda Imran. Dan rikicin Abba sai Hajjo ke iya masa. Itama idan ya rikice mata wani lokacin sai ta haɗa shi da Mammah da yake ɗauka tamkar babbar ƴarsa ake samun lafiya. Sun cigaba da hirarsu har suka gangaro kan batun Bilal da shima dai watan gobe zai dawo gida in sha ALLAHU. Sai magana auren Biebah data dage ita bazatai aure ba sai Dada ya fito, in ba haka ba ita da aure har abada. Imran da yasan ga shirin da suke yace su barta kawai in sha ALLAHU komai zai warware. Bai bari shagon ba sai bayan sallar azhar. Ya haɗo shopping na kayan babys da turamen atamfa har akwati biyu aka kai masa mota. Gida ya wuce kai tsaye, zaije ya ɗan samu ya huta bayan la'asar sai ya leƙa gidan Mimi yaga baby dan dama siyayyar duka tata ce......✍️ 18 .........Sai da sabon driver ya tabbatar su Nimrah sun gama shigewa sannan ya koma cikin mota. Wayarsa ya ciro daga aljihu ƙarama tecno, ya kashe ta ya cire murfin da batteryn ta. A mamakina rigarsa ya ɗan ɗaga ya zaro leda mara girma sosai, koda ya kwance ta tsumma ne fari ya fara bayyana da aka nannaɗe wani abu a ciki. Ya shiga warware tsumman sai ga ƙaramar bindiga ta bayyana, ƙaramar takardar dake tare da bindigar a nannaɗe itama ya ɗauka ya warware layukan waya da yawa suka bayyana. Ɗaya a ciki ya ɗauka ya saka a wayar ya maida batteryn ya kunnata.       Kira yayi tare da kaita kunensa yana gyara zama. Ba'a wani jima ba aka ɗaga daga can. Kasancewar speaker ɗin wayar a buɗe take sosai yasa ake iya jin abinda nacan ke faɗa. Gaisuwa suka fara kafin nacan ya cigaba da faɗin.            “Ai harna fara tunanin sakawa a bi bayanka Mole, naji har kwanaki uku babu wani bayani daga gareka. Ina fatan dai lafiya? Ka samu karɓuwar da muke so a gidan?”.        Iska mai ƙarfi ya furzar cikin damuwa da ɗacin da yake ji a cikin maƙoshinsa ya furta, “Oga na samu ƙarɓuwa kam, sai dai akwai matsala gaskiya.”           “Matsala kuma? Yarinyar bata tare da su ne?”.     “Tana nan a gidan. Ta girma sosai ta zama budurwa. Sai dai babu wata alamar dake nuna tasan tana da wasu iyaye bayan su. Da alama abinda Goje ya taɓa sanar mana na an mantar da ita iyayenta gaskiya ne.”         “Amma uwar nan tata muguwa ce gaskiya. Tabbas da ace tana raye har yanzu ba ƙaramin barazana zata zame mana ba ita da ubanta.”      “Ai ko yanzu ta zame mana, dan ban san ta inda zan fahimtar da Uwa wanene ni ba har tai mana abinda muke buƙatar daga ƙarshe ta dawo hannuna”.       “Karka damu dole mu tafi mataki na biyu ne kawai gaskiya. Amma ka bari zan yi magana da oga muji wace shawara ko shiri yake da shi akan hakan. Tunda dama ya kamata mu sanar da shi da kanka zakai aikin yanzu, dan kar a samu irin matsalar da Buba yaso bamu. Yanzu a gidan kake kwana?”.      “A'a haba kaima kasan bazan kwana a nan ba. Dan wannan Imran ɗin da kuka raina shima shegen kansa ne. Tunda ya ganni alamun tsarguwa suka bayyana akan fuskarsa. Dole sai nayi taka tsantsan da shi. Dan ni kasan bana raina abokin gaba”.         “Kamar ni kake, dama su Oga ne ke ɗaukar Imran mai sauƙi, sun kasa fahimtar irinsu sunfi illa fiye da shi wanda suka ɓoye ɗin da bai iya shanye abu. Amma ka barsu za'aje gaɓar da zasu gane shima ba abinda zasuyi wasa da shi bane. Kai kuma ka ƙara yin taka tsantsan”.      “Ba damuwa sai na jika”. Daga haka sukai sallama ya sake kashe wayar ya cire layin ya maida shi inda yake tare da bindigar nan. Sannan ya tada motar yabar wajen..... (Hummm wa kuke tunani wai?) }}}}}}}}}{{{{{{{{{     ★PRISON★           Bai san fuskar ba, bai taɓa ganinta ba. Dan haka ya zubama vistor ɗin nashi jirkitattun idanunsa masu bulale abokan gaba koda bai tanka ba har na tsayin minti ɗaya. Tabbas ALLAH ya bama Dada basira mai ƙarfi, nutsuwa, dattako da sirrin iya aiki matsayin jami'in tsaro. Zakai matuƙan shan mamaki idan akace maka a wannan kalon na minti ɗaya kacal ya fahimci fuskar bogi ce a tare da mutumin, hakan na nufin yayi amfani da facemask wajen ɓoye ainahin fuskarsa.       Wani murmushin da sam bai niyyasa bane ya suɓuce masa, murmushi daya saka vistor ɗin nashi murmusawa shima, duk da bai fahimci ma'anar murmurshin Dadan ɗin ba shi. Shiru ya sake biyo baya a cikin ɗakin batare da yunƙurin tankawar kowannensu ba na tsawon lokaci. Tamkar Dada na ƙirga lokutan zamansa a wajen ne, minti biyar na cika daga agogon ɗakin da suke ya miƙe tsam batare da yace komai ba ya juya zai bar wajen.        “Bai kamata ka ƙosa haka da wuri ba, domin mu mutuwa ne, ana rayuwa da mu ne dole, tun daga ranar haihuwa”.     Cak Dada ya tsaya a takunsa na uku, sai dai bai juyo ba bai kuma ce komai ba har tsahon minti guda cir. Kafin a hankali cike da ƙasaitarsa mai tafiya da nutsuwar masu izza ya juyo gaba ɗayansa. Idanun nan nasa masu kaifi da zafi ya zuba masa, kafin a bazata yay wani sakaran murmurshi mai cike da ma'anoni masu ƙarfi da ya nema tarwatsa zuciyar vistor ɗin a cikin ƙarjinsa. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kansa. Sai kuma ya buɗe lips kaɗan, gira a sama ya amsa masa da.         “Ni kuwa kaga anan sai banga siffofin kamala irin na mutuwa mai cika umarnin UBANGIJINA ba. Siffofin akuyoyin dake gudun tsiran neman mafaka a yayin da ruwan sama ya sauka kawai na gani a gabana”.       Sosai fusata ta nuna a fuskarsa vistor ɗin, duk yanda yaso danne fusatarsa hakan na neman gagara. Idanunsa sun yi ja sosai har hannunsa na rawa sai da ya dunƙuleshi a cikin juna ya matse yatsun. Dada dake kallon hannun nasa ya kauda idanunsa yana murmurshi. Ai ko sai hakan ya sake hasalashi, a kausashe ya daki tebirin yana furta, “Mune akuyoyin kenan?”.        “Amsa mai ƙyau”.     Dada ya bashi amsa kai tsaye yana sake takowa ya dawo wajen. Duk da hannunsa akwai handcuffs cike da salon manya ya juya kujerar ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya suna kallon juna ido cikin ido. Dai-dai lokacin masu tsaronsa suka shigo saboda bugun teburi da baƙo yayi.        “Sir! are you all right?”.    Kansa kawai ya jinjina musu batare da ya kallesu ba balle yin magana.     “Okay”. Suka faɗa suna salute ɗinsa da ɗan kallon baƙon da ya gama kaiwa wuya suka fice. Sai kuma ga wasu sun sake shigowa niƙi-niƙi da kwalaye. Su kam gaisheshi sukai kawai tare da sanar masa oga ne ya aikosu da kayan zasuyi aiki a ɗakinsa. Kamar zai ce wani abu sai kuma yay shiru da basu dama da hannu suka wuce ɗakin nasa. Ya ɗan bi kwalayen da kallo. Har sai da baƙon nasa yay wata dariyar iskanci da izgili. A wulaƙance ya ce, “Karka ji ka damu fa, mun ƙara maka matsayi ne, dan bai ƙyautu ace lokacin da mutanenka ke ihu da kururuwa kai kunnenka baya ji ba, idanunka basa gani ba. Shiyyasa muka kawo maka gift ɗin da zai baka damar ji da gani kusa da kai gab...”        Tsahon sakanni bashi da niyyar tankawa daga kalamansa, sai hakan ya bama vistor damar taɓe baki da sake faɗin, “Kana jin tsoron rasa rayuwa ne? Ko faɗa ka bada amsa ne kake jima fargaba?”.      Da wani irin salon luuu Zak-Dada ya ɗago idanunsa yana kallonsa cike da izza da nutsuwarsa da ALLAH ya mallaka masa a kowane hali. Sai kuma ya ɗan matso kaɗan ya dafe duka hannayensa dake sanye da handcuffs a saman table ɗin, idanunsa ya sake ajiyewa kai tsaye cikin nasa tamkar zai soke ruhinsa da su. Da golden voice ɗin nan tasa mai razanasu ya furta, “Jarumin gaske sulƙen yaƙi da linzamin dokinsa ne kawai GUZIRINSA. Duk lokacin da kaji abokin faɗa ya zagaye kansa da MAKAMI ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi na faɗa maka tsoro ne ya saka shi”.        “Tsoro!?”.    Baƙo ya faɗa cike da son aro jarumta da ƙarfafa kai na dole. Sai kuma ya murmusa yana ɗan buga yatsunsa akan tebur.    “Kana da yawan cika baki a magana. Amma ka sani mu ba da suna muke aiki ba. Idan suna ya bayyana, haske zai shigo. Idan haske ya shigo, tsarin ya lalace. Mu mune mazaunan ƙasa a ɓoye. Mu ne masu murɗa jijiyoyin gwamnati. Mu ne masu rubuta dokar da gwamnati ke karantawa.” Ya sake matsawa kusa kusa sosai.       “Yau shekaru takwas kenan muna kallonka daga nesa. Kana tunanin wannan gadarar taka ce ta baka wannan filin? Ko har yanzu gurɓataccen tunaninka na cigaba da baka wancan ƙarfin ikon da kake gadara da shi a baya har yanzu yana da tasiri? Ka manta cewa ƙasar nan tun kafin ka yi tunanin kare ta, mun riga da mun shafe shekaru muna sarrafa zuciyar manyan da kake kira shugabannin cikinta. Kalli kanka mana, har yau baka ɗauki darasi daga ikonmu bane?. Mu muka bar ka a nan. Mu muka hana a kashe ka. Mu muka hana a sake buɗe shafin ka. Ba wai saboda kana da muhimmanci a garemu bane. A’a…” Ya yi kakkarfan numfashi yana wani murmushi, ya cigaba da faɗin, “…saboda muna son ka zauna ka kalli yadda ƙasar da ka ɓata shekarun ƙuruciyarka a kareta ta koma filin WASAN ƘWALLON ƙafarmu. Da jinin abokanka, zuri'arka, ƴan ƙasar taka zata zame mana mai danshin da zamu ji daɗin gudu a kanta. Kaɗan da zamu rage a cikinsu ka kalli yadda suke bauta mana. Ka kalli yadda za mu rusa duk tsarin da ka kare rayuwar taka a karewa. Ka bar gudanar da tunanin cewa kai ka san makircin ƙasa. Kai ɗan wasa ne a wani katafaren wasan da muka fara shekaru masu yawa da suka wuce tun kan haihuwarka, kaga hakan yayi kama dana masu TSORO?”.       Ya ƙare dogon sharhin nashi yana gyara zama da jifan Dada da kallon raini yana wani dariyar iskanci da izgili. Sai dai maimakon yaga Dadan ya firgita ko nuna tsorata da matsanancin tashin hankali kamar yanda sukai tsammani sai yaga saɓanin hakan a bayyane. Domin kuwa da wata nutsuwa da baƙon bai taɓa gani ba, ya ɗaga kansa ya kalle shi da idanun da suka saba ganin bala’i ba tare da girgiza ba.........✍️ A gaya masa gaskiya ko a barshi da Dadan kai?. To bari dai mu gaya masa ko kaɗan ne 😂💃. 😝Kai kam baƙo duk wanda ya baka shawarar zuwa wajen nan ba sonka yake ba, yo ubanwa ke zuwa gaban zaki yay wasa ya kwashe kayan wasan salin alin ya koma gidansu yay barcin hutu.🥱. Amma dai bari muji amsar da MAZAN FAMA zasu baka🤣. Barkanmu da dawowa, ya weekend?😎 19 .........Ana fitowa sallar azhar driver ya kawo musu abinci da ɗaukar su Aheel. Babu yanda Ruky bataiba suje su amso Nimrah taƙi, dan ita kam haka kawai ganin mutumin nan tayar mata da hankali yake ta rasa dalilin haka. Tana zaune a inda Ruky ta barta ta dawo ta sameta. Tana ma buɗe abincin ta sake ɓata fuska ganin minene a ciki. Dariya Ruky tayi, dan tasan Nimrah bata damu da doya ba sam. Harararta tayi kuwa, ƙarshe ta miƙe wai ita ta ƙoshi bazata ci ba. Sanin butsutsunta yasa Ruky bata takura mata ba, anan ma ta barta ita ta koma aji. Sai da taci iya abinda zata iya ta rufe sauran ta koma ajin itama.       Sun cigaba da ɗaukar darasi, Nimrah nata mutsu-mutsun yunwa, gaba ɗaya sai Ruky ta damu, har cikin ranta taji haushin su Kulu da suka aiko musu da doya bayan sun san Nimrah bata ci. Jakarta ta ɗakko ta ciri kuɗi tare da miƙewa taje gaban sayyadinsu cikin ladabi ta sanar masa zata fitsari. Bai hanata ba dan hakan normal ne. Tana fita maimakon restroom sai ta wuce shop ɗin makaranta. ALLAH ya taimaketa ta samu sauran meatpie bai ƙare ba ta amso mata biyu ta dawo tunda suna da ruwansu. Sai da ta zauna sannan ta saka mata a hijjab. Kallonta Nimrah tayi, sai kuma ta tattaɓa abinda ta ajiye mata akan cinya. Wani irin ƙaunar Ruky ce ta sake cika mata zuciya. Idanunta cike da ƙwalla ta ce, “Thanks you Sweetheart”. A hankali. Murmushi kawai Ruky tai mata.       Cikin hijjab ta shige tana ci, duk da kuwa hakan doka ne ba'a ciye-ciye a aji. Amma da yake Sayyadi Kamal nada wani ƙudiri a ransa game da Nimrah ɗin duk da ya fahimci abu take ci baiyi magana ba. Haka ta kammala tasha ruwa sannan ta fito itama ta maida hankalin ta a karatun. Ya kammala ya fita wani malamin ya shigo, haka dai har lokacin tashi yayi. Yau dai sambarka ƴan caskalen Mammah basuyi faɗa da kowa ba. Abinda take ji aduk sanda suka haɗu da driver yasa tai juriyar ƙin kallonsa a yanzu har suka isa gida. Ita ta fara fita ta shige ciki. Baƙar yunwar da take ji ya sata wucewa kai tsaye kitchen tace su Kulu su dafa mata noodles da ƙwai soyayye ɗaya. Kafin ta shige ɗakin su. Ruky na kwance a gado tana maida numfashin gajiya, dan haka ita bata zauna ba sai ta wuce bathroom kawai yin wanka. Kafin ta fito kuwa an kawo mata indomie ɗinta har Ruky na ƙoƙarin ɗanɗanawa. Doke mata hannu Nimrah tai tana ƙwacewa, Ruky ta lunƙuma wadda ta ɗiba a baki tana dariya da faɗin, “Shike nan ke in kina jin yunwa sai baƙar rowa”.        Cike da jin haushi ta bata amsa da, “Ai sai na musu rashin mutunci yau a gidan nan, sun san bana cin doya sukayi, maimakon su dafa min wani abun”. Ta ƙare maganar da ƙwafa idanunta na cika da ƙwalla. Dan harga ALLAH taji haushi, sai dai bata san miya hasala zuciyarta ba kuma har kamar haka. Itama Ruky ta fahimci a hasale Nimrahn take dan haka batace komai ba ta wuce bayi tana murmushi...       Shaf-shaf suka kammala shirin zuwa gidan Aunty Mimi. Sunyi ƙyau cikin abaya iri ɗaya kalar brown da adon duwatsu masu haske. Daga Ruky har Nimrah akwai son kwalliyar tsiya. Ga iyayi kuma da ƴammatanci kamar ba ƙwailoli ba😝🏃🏼‍♀️. Koda yake sunce su ba ƙwaila bane ba😂, dan duk abinda cikakkiyar budurwa ke taƙamar da shi suna da. Fes suka fito abinsu, kai tsaye ɗakin Biebah suka shiga, itama dai ta shirya cikin nata gayun, sannin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387 suka biyo ya sata ɗauke kwalbar tana ƴar hararsu.        “Kai waɗan nan yara baƙwa mantuwa”.     Dariya suka kwashe da ita a tare, Ruky ta ce, “Humm Small Mom ya zamu manta da wannan daddaɗan turaren, ai kafin a kawo mana namu muma sai su Ammy sun ɗiba mana komu sato”.             “Ai dama kun saba ɓeraye”.      Dariya suka sanya a tare nan ma. Ta daddagwala musu kowa ya shafa suna faman lumshe idanu. Dan ƙamshin turarrukan ba ƙaramin ratsa zukatan mai shaƙa suke ba. (Nima shaida ce masu karatu. Wlhy maza ku garzaya neman turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387.  Kaf turarrukanta babu na yarwa, nayi amfani da su na gani, koma nace ina kan yin amfani da su a yanzu haka. Tana kawo turarrukanta ne masu inganci da tsaftatacen ƙamshi. :Akwai Turare wuta da khumra kaloli har uku: black khumra, white khumra, brown khumra. Akwai oil perfume da kullacham ma, akwai Genine da Turare kabasa kaloli uku shima: white, black, and brown kai harma abinda ban lissafo ba. Dan tana saida kayan gyaran jiki suma na amare dama mata ƴan ƙwalisa uwargidaye masu san gyaran fata batare da kin ɓata skin ɗinki da mayukan bleaching ba. Karku ji komai ta gida ce tana nan zaune a garin Kaduna kuma tana aika kaya aduk inda kake harda kasashen ƙetare ma. Duk mai so kawai ya nemeta ta nan. Tana bada har sari ma fa masoya. +234 704 229 3387😌💃🏼🥰👍🏼).           “Kai kuko wane kalar ƙamshi kukeyi haka? ya subahanallah”. Mu'azz ne mai maganar yana faman buɗe hanci. Dariya Ruky da Biebah sukayi, Nimrah kam da duk take jinta cikin rashin daɗin zuciya murmurshi kawai tayi. Ganin haka yasa Mu'azz kallonta, cike da kulawa ya ce, “Yaya dai Ninah? Ko baki da lafiya ne? Naga tunda muka baro makaranta baki da walwala”.     Kai kawai ta girgiza masa alamar ba komai. Bata basu damar magana ba ta ce, “Ku muje ALLAH na ƙagara naje naga Baby”. Tana gama faɗa ta fice a falon gaba ɗaya. Duk da kallo suka bita suma fuskokinsu na nuna damuwar. Koda suka iskota a waje babu wanda yace komai, kasancewar Mu'azz ne zai jasu sai ta sauke ajiyar zuciya. Ita ta shiga gaba Ruky da Biebah na baya. Su Afrah dama suna can, dan daga makaranta can driver ya kaisu kai tsaye. Koda maigadi ya buɗe musu gate bata ganshi ba, dan haka ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya.      Suna ɗaukar titi kowa ya fara mata tambaya, saita wayance tace kewar Mammah ce. Duk sun gamsu, dan sun san Nimrah da Mammah sai ALLAH. Nimrah akwai ƙulagucin iyaye, dan haka tai bala'in sakin jiki da Mammah duk da har yanzu bata manta da Ummanta ba, sai dai bata iya tuna fuskarta sosai saboda ƙarancin shekaru na wancan lokacin. Tunda ta fara hankali da wayo cikin hikima Mammah ta koyar da ita yima mahaifanta addu'a kwanciyar kabari cikin aminci. Kulawa da take samu yasa bata jin maraici, ba kuma ta taɓa zaman yin kukan rashinsu ba sakamakon babu wani abu na labarinsu data sani ko take ji a yanzu balle ya tuna mata abubuwa a kansu. Garama Ummanta wasu ƴan abubuwan kan mata flash ɗin baya game da ita a cikin zuciya musamman idan Mammah ko su Aunty Ummi da zasu iya zama sa'annin Umman ita da Ammie (Aunty Hafsat mahaifiyar su Ruky kenan Matar Imran) takanji kamar Ummanta.     Suna isowa tun Mu'azz bai gama kashe motar ba ta fita da gudu tai cikin gidan. Dariya kawai sukai mata. Aunty Biebah na addu'ar ALLAH ya cika musu burinsu na fitowar Dada sarari wataran Nimrah ta haifa musu Baby gudan jinin sa. Ita kanta bata san yanda zata misalta irin farin cikin da wannan ranar zatazo musu da shi ba balle Mammah....         “Oh ya ALLAHU ka shirya min Ninah jama'a ke da wa?”.     Zama Nimrah tai kusa da Aunty Mommy dake rungume da Baby tana saka masa kaya an mata wanka tana murmushi, sai da ta shafa kan babyn sannan cikin shagwaɓa ta bama Aunty Momyn amsa.       “Mum ba kowa fa, kawai ina gudu na fara ganin Baby ne. Jiya fa dan mugunta Ruky ina barci taƙi tada ni suka taho”.         Aunty Mimi data kasa haƙuri ta ce, “Ai Dada zai sha fama a wajen nan dai kam. ALLAH yasa sanda zai dawo kinyi hankali Ninah”.      “Mamy shi Dada ina ruwansa da hankalina koda ya dawo? Kuma ALLAH inada hankali”.           Kasa haƙuri sukai kowa sai da ya dara. Ita kam ko'a jikinta tunda ta samu ta amshi Babyn gaisuwa ma sama-sama tai musu ta koma gefe. A haka su Biebah suka shigo niƙi-niƙi da kaya suna sanar da zuwan Daddy Imran. Dai-dai lokacin kuma Aunty Hafsat ta fito daga bedroom ɗin Aunty Mimi da alama salla tayi. Ai ko zaram Nimrah ta miƙe ta nufeta tana faɗin, “Ammie na dan ALLAH Babyn nan kalleta da ƙyau dawa take kama?”.      Dariya Aunty Hafsat tayi ta ce, “Da ke. Sai dai ALLAH yasa kada tayo ƙiriniyar taku ke da hassanar ki”.       Aunty Lailah dake fitowa a kitchen ita da Aunty Shariffa sai ƙanwar mijin Aunty Mimi ta ce, “A'a gara dai ta biyo komai da komai zaifi armashi Aunty”. Nan ma dariyar aka shiga yi, a haka Imran ya shigo ya samesu. Sai da ya zauna kowa ya gaisheshi cike da girmamawa sannan ya dubi Nimrah data ƙanƙame Baby bata da niyyar bayarwa.          “Daughter baza'a bani Babyn bane?”.     Murmushi tayi har haƙoranta na bayyana, sai kuma ta miƙe ta je gabansa tana faɗin.........✍️ 20 .......“Daddy ai kaine za'a baka. Amma minti biyar zatayi ka sake bani. ALLAH ji nake kamar kada na ajiyeta fa. Daddy dan ALLAH na dawo nan da zama har ayi suna?”.         “To Nimrah in kin dawo makarantar fa?”.     “ALLAH Daddy in ta dawo nima sai na dawo”. Ruky ta faɗa itama. Cikin girgiza kai yace, “Ai bama zan bari ku dawo ɗin ba. Daga yau ba zaku sake zuwa ba sai ranar suna.”      Zasu fara magiya ya ce, “Okay nace Mammah tai zamanta kada ta dawo goben kenan?”.       Ai tuni suka saki batun dawowa gidan suka fara murna jin Mammah zata dawo. Abin zai birgeka har su Auntys ɗin farin ciki suke yi. Shi dai Imran yay ma Baby addu'a sosai ya ɗan zauna suka taɓa hira sannan ya miƙe zai tafi. Dole Aunty Hafsat ta miƙe suka wuce tare. Su kuwa sai anyi sallar magriba sannan koma isha'i.... >>>><<<<★★>>>><<<<           ★DUBAI★   Cikin zafin rai take magana kuma da harshen turanci. Shi ko yayi sabale yana kallonta dan komai tayi birgeshi take. Shi kaɗai yasan irin wutar masifar sha'awarta da yake ji tsahon shekaru. Ya kuma kasa binta ta ƙarfi batare da yasan dalili ba. Bayan kuma hakan abu ne mai sauƙi a garesa duk da kuwa yasan tana da aure. Yasan inda wata ce ba ita ba yanda yake narkama uwarta kuɗi duk da hakan ba komai bane a garesa da tuni ya mata fata-fata ta yanda ko rayuwarta sai ya ce ga yanda zatayi sannan zata gudanar da ita.       Yanzu haka yana ƙasar Garmany ne harka business ɗinsa Hajiya Hasiba ta tura masa saƙon kudirin Nabeeha, yana gani hankalinsa ya tashi, a take ya kira duk wani Companyn sauka da tashin jirage yasa aka rufe damar Nabeeha na barin ƙasar. Amma duk da haka hankalinsa yaƙi kwanciya a daren ya baro ya dawo dubai ɗin. Kai tsaye gidan nasu yayo, cikin sa'a kuma ya sami Nabeeha a falo zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka. Zama yay kusa da ita da kai hannu zai taɓata ta zabura, shine take zazzaga masa ruwan masifa data sakashi zuba mata ido kawai yana kallonta...         Su Ismat dake laɓe farin ciki ya kamata, dan itama wlhy ta tsani guy ɗin nan, dan bata da wani burin daya wuce Nabeeha ta koma ɗakin aurenta. Ta haka ne kawai itama zata samu cikar nata burin na mallakar Ja'afar. Cike da munafunci Amima ta dannama Hajiya Hasiba kira da mahaifiyarsu data shigo gari tun cikin satin daya gabata. Aiko cikin mintinan ƙalilan suka iso dan duk suna kusa da gida ne dama. Wata tsawa Hajiya Hasiba ta dakama Nabeeha. Cikin zafin rai ta ɗaga hannu zata mareta caraf Adeel ya riƙe hannun.        Cike da gadara ya ce, “Karma ki fara dan ina ganin mutuncinki na haihuwarta da kikayi, amma da a maimakon riƙe hannun nan naki sai dai ki jisa a ƙasa yana lilo”.     Maimakon jin zafin abinda yay mata murmushi Hajiya Hasiba tayi daga ita har ƙanwarta Mamawo. Cike da girmamawa suka shiga faɗin, “ALLAH ya huci zuciyar babba ɗan manya jinin alkairi. Nayi kuskure ayi haƙuri raina ne ya ɓaci. Taya zata zauna tana gaya maka irin wannan shirmen..”        “Karki damu ta isa ne ai, girmanta ne. Ni zan koma kawai, amma zan dawo anjima anan zanyi dinner”.     “An gama ranka ya daɗe”. Hajiya Hasiba ta faɗa cike da girmamawa. Yayinda Mamawo ke wani shegen murmushi tana binsa da wani kallo zuciyarta cike da abubuwa. Amma a zahiri baka isa karantar abinda ke ranta ba dan cikakkiyar ƴar bariki ce data iya takunta. Yana ficewa suka koma yima Nabeeha faɗa da nuna mata karfa ta dawo tana dana sani da wannan damar da ALLAH ya bata. Wai miye akai akayi wani Haysam can da bata da tabbacin yana ma raye ko an jima da kashe shi ne.       Kuka ta saka musu cike da bori da rashin kunya tabar wajen. Dole sukai shiru bayan duk sun ja tsaki. Bayanta itama Ismat tabi zuciyarta na zafi. Koda ta shiga ɗakin taga Nabeeha ta kwanta tana kuka zaman lallashinta tayi, ganin taƙi yin shiru ta ɗauka wayarta a karo na farko ta danna kiran Jiddah, abinda sai ta jima batayi ba saboda duk haushinta suke ji akan gaskiya da take gaya musu.    Batai zaton zata ɗaga mata ba ma, amma sai gashi ta ɗaga cikin tsaftatacciyar sallama. Da ɗan rawar murya Ismat ta amsa mata, sai kuma ta fara gaisheta. Ɗan jimmm Jiddah tayi kafin ta amsa tana kallon Abban su dan taje barka gidan Aunty Mimi ne shine ta biyo gidan gaishe su. Kukan da Ismat ɗin ta fashe da shi ne ya saka Jiddah faɗin, “Ismat lafiya kuwa? Ko wani ne ya rasu?”.        “Aunty babu wanda ya rasu, kawai abubuwa ne suka mana yawa. Mom ta takura dole sai Aunty Nabeeha ta kashe aurenta ta auri wannan mayen mutumin. Jiya mukai shirin gudowa kawai ta sace passport ɗinmu ta ɓoye. Yau kuma sai gashi yazo. Aunty ki taimakemu ki sanar da Abba yazo ya tafi damu. Wlhy gida muke son dawowa, aunty Nabeeha na son komawa gidan mijinta”.       Jiddah dake jin jikinta ma na rawa ta ɗan saci kallon Abbansu. Ai ko yayi kicin-kicin da fuska yama maida hankalinsa a television inda ake hira da ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyar SGP, wato tsohon janar ɗin soja kuma ɗan majalisan tarayya mai ci Janar Yusuf Shu'aibu Tafida. Yawu masu kauri ta haɗe, cikin damuwa ta maida kallonta ga Hajiya Zuwaira da suke kira Ummu a gidan. Idan ka cire Nabeeha da Ismat da har yanzu basa ko gaisheta. Kai Ummu ɗin ta girgiza mata alamar ta kwantar da hankalinta, dan taji komai itama kasancewar hansfree ta saka wayar.      Cikin dauriya Jiddah ta ce, “Wannan shi nake nuna muku tun farko amma kuka kasa ganewa Ismat daga ke har Aunty Nabeeha. Yanzu dan ALLAH yaushe rabonku da kiran wani a cikinmu har Abban, aƙalla shekara uku kenan fa. Ni kuma kun saka ni a black list kona nemeku bata shiga harta WhatsApp. Ni yanzu a wannan gaɓar mizan iya yi, wane tabbaci ne dani akan baku biye ma Momy ɗin ba akan ƙudirinta.....”         “Wlhy aunty bamu taɓa aikata wani abu saɓanin abinda kike tunani ba mu kammu balle Aunty Nabeeha”.     Duk da Jiddah bata da tabbaci sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, duk da tasan wacece mahaifiyarsu akan son duniya babu abinda bazata aikata ba. Itafa ko uwarmi zasuyi suyi ba ruwanta tunma suna ƙananunsu indai kuɗi zai shigo fine. Hawayen da suka cika mata ido ta haɗiye, ta ce. “Shike nan Ismat ki bani zuwa gobe, yanzu haka ma bana gida naje barkar Aunty Mimi ne data haihu. Amma zan yi magana da Abban”.           “To aunty dan ALLAH ki taimaka mana, ke kaɗai ce hope ɗinmu a yanzu wlhy”.      “Karki damu in sha ALLAH duk yanda muke zan taɓoki, ni dai fatana ku cigaba da riƙe mutuncinku kada ku biyema Mom”.     “In sha ALLAHU Aunty ki mana addu'a”.        “Ita nake muku kullum”. Daga haka ta sauke wayar. Tun kafin ma tai magana Uncle Nasiru ya dakatar da ita da faɗin, “Tashi ki wuce gida dare yayi? ALLAH ya bamu alheri”.      Yanzu kam sosai idonta ya tara hawayen, ta waiwaya tana kallon Ummu. Kai ta jinjina mata alamar taje, tabar komai a hannunta kawai. Sai kawai ta miƙe tai musu sallama ta fita. Dama ita ta tuƙo kanta. Aiko tana shiga motar ta kife kanta a sitiyari kawai ya fashe da kuka. Ta jima tana kuka har sai da maigadi yazo yana mata knocking glass sannan ta haƙura ta share hawayenta taima motar key...... <%>°<%>°<%>       PRISON             Wani zuba masa kaifafan idanunsa yay a hankali, tare da sakin wani murmushi mai zafi da izza, mai tabbatar da cikakken izgili da raini fiye da nashi. Dan a ƙarshe da wani salo irin na maida mutum banza sakarai Dada ya taɓe baki. Sannan cikin son tunzurawa ya ɗan karkatar da kansa, fuskar sa ta cika da izza mai nutsuwa. Like yana magana da wani shasha can ya furta,        “Tofa! kaga fa kana ƙoƙarin bani mamaki.” Ya yi murmushi mai ɗan kaifi, ba na farin ciki ba, na jarumin da ya saba da iya riƙe nauyin abu a zuciya da ƙwaƙwalwa batare daya bari abokin gaba ya fahimci lagonsa ba. Cikin halin ko in kula ya cigaba da da ɗin, “Ka zo nan kana min barazana da dorinar ƙarya, ka ce ku ne ƙasa, ku ne haske, ku ne gwamnati. Amma duk da wannan ƙarfin ikon naku kuma kuka zaɓi ɓoye fuska kamar masu tsoron haske a gaban ZAKIN dake ɓoye cikin keji?. Gaskiya ban yarda da wannan ƙarfin ikon naku mai kama dana ƴan wasan kwaikwayo ba, ya kamata ku koma ku canja shiri.”       Ya ɗan sake matsawa gaban tebirin sosai yana sassauta murya kamar mai son yin raɗa idanunsa na sake shiga cikin na baƙon, sai dai  muryar tasa ta cika da nauyin, da ƙarfi irin na masu izzar ƙarfin zuciya da jarumtar ƙwarai dake jinsu ko a ɗaure su ba masu risinawa wawaye bane.       “Ɗan aike!. Ka manta da abu ɗaya.”      Shiru ya mamaye ɗakin. Baƙon ya tsaya tamkar an dasa shi a wajen yana kallon Zak-Shadow da jin ƙaguwar son barin wajen dan wani irin firgitashi al'amarinsa keyi, dauriya kawai yake da dannewa saboda sanin akwai camara a jikinsa dake ɗaukar komai. Kai tsaye kuma duk abinda suke tattaunawa ƴan ƙungiya ma na kallonsu........✍️ 21 ........Tunaninsa ya katse sakamakon cigaban kalaman Zak-Shadow masu zafi da sanya zuciya raɗaɗi.          “Idan kaje ka sanar da iyayen gidanka saƙo daga ni Haysam Abdul-rasheed Shehu. Ku na mallakar gwamnati, amma ba kwa mallakar ƘASA. Ku na mallakar masu muƙami, amma ba kwa mallakar mutanen da suke amsa sunan KASAR. Ka sanar musu. Idan suna tunanin zasu sarrafa ni kamar karnukan su… to su sake tunani tun kafin lokaci ya ƙure musu. Ka faɗa musu. Wannan ba ƙarshen wasan ba bane, farkon rugujewar su ne, domin kuwa yanzu ne za'a FARA WASA na GASKIYA. Ka faɗa musu. Wanda yake da cikakken iko ba ya zuwa ya gaya wa wanda yake tsoro barazana. Domin wannan zuwan naku tabbatar min yay da kun MATSORATA ne, kuma ni abin tsoronku ne. Na ji ƙamshin wannan tsoron naku tun shigowarka nan. Ka faɗa musu. Idan kun kasance da ikon da kuke ikirari… ku kasheni kawai zai fi muku sauƙi da samun cikar burin ku cikin salama” ya ɗan yi dariyar da ta sake tsokano zuciyar bako. Batare da bashi damar cewa komai ba ya cigaba da faɗin,      “Ka faɗa musu. In har kukai sakacin ƙin kasheni da ɗaukar zantukana cika baki, to ku shirya… ku shirya wasan da muka fara ba lissafin saƙar zaren ginin gidan GIZO-GIZO ba. Ka faɗa musu. Shi wannan filin da suke cika bakin samarwa domin ƙwallon ƙafa, da jinin da zasu jiƙa ƙasar domin ta tausasa. Ni ne zan samar da filin WASAN, sannan na jiƙa ƙasar da jinin jikinku. A maimakon buga wasan ƙwallo na ɗaura muku sarƙar mata a ƙafafuwa ku zagaye filin da takun RAWAR ƘOROSO. Ka faɗa musu. Ni nake tsara gangar da masu kiɗanta, kuma tabbas in sha ALLAHU sune zasu taka wannan rawar fa. Ka tafi ka faɗa musu. Na gane kun TSORATA. Sannan wannan SAƘON daka kawo zai zama kuskurenku na farko. Na biyun zai biyo bayan fitowata daga nan. Ka faɗa musu. Idan har iyayensu sun haifesu da alfaharin igiyar aure, kamar yanda ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi A'isha da Abdul-rasheed suka haifeni da wannan alfaharin ku rubuta kalamaina ku ajiye da yaƙini a saman dutse. Sannan ku shirya.”      Ya turo kujerar ya tashi a hankali yana sakin murmurshin ƙasaita tamkar sarki ya miƙe daga gadon mulkinsa. Ya zubama agogon hannunsa idanu na sakanni tare da sake sakin murmushi mai ma'anoni da yawa sannan ya fara takun dake nuna alamar barin wajen. Da sauri shima baƙon ya kalla agogon nashi mai ɗauke da camara saboda kallon da Zak-Shadow yay ma agogon ya tabbatar ɗayan biyu ne, ko dai ya fahimci camara ɗin ce ko ya tsargu....      Dada da yay takun da bai gaza biyar ba ya tsaya cak, tare da juyowa a hankali, idanunsa suka sauka a kan mutumin. Fuska ta bogi, amma mugunta ta gaskiya.... Murmushi ya sake saki da ɗan taɓe baki. Cikin salon isar da saƙon ƙarshe a inda yake da tabbacin masu aiken na kallonsa yanda ya dace domin idanunsa kam a kan agogon mutumin ya furta,       “Ni bana kare gwamnati. Bana kare hukumar soji. Bana kare kujerun ƴan mulkin mallaka. Amma ku sani. Na kare ƙasa. Na kare mutanen ƙasa. Na kare gaskiya duk da ƙarfin ikon UBANGIJI mai IZZA da cikar mulki na gaskiya. Wannan kuma… Shine abinda kuke tsoro. Zan ƙara tabbar muku, idan har kuka bar Haysam Abdul-rasheed Shehu a raye, zai cigaba da tabbatar muku wannan tsoron a cikin ZUKATA. Bance zan iya komai ba, amma bazan taɓa raina kaina a gaban ALADU irin ku ba”. Ya ɗan yi shiru yana murmurshi mai ciwo, dan kowace kalma yana fitar da ita ne daga zuciyarsa kamar takobi mai kaifin gayawa jini ya wuce.      Baƙo da zuciyarsa ke dukan uku-uku cike da ƙarfin hali ya ɗan taɓe baki, numfashinsa dake fita da rawa ya fisgo da ƙyar dan neman ƙwace masa yake. A karo na farko ya ji wani abu ya motsa masa a ƙirji, ba tsoro bane kawai, ba kuma bakin ciki bane kawai. Bayyanan nen rauni ne dake tuna masa, shima fa ɗan ƙasa ne tamkar Zak-Shadow, yana da dangi a ciki ba iyalai kawai ba, yana da ƙarfin ikon kiranta tushe ba son tara dukiya da ƙarfin ikon son mulki kawai ba....    Dada daya gama fahimtar raunin nasa dake son bayyana ya juya zai fita abinsa yana murmurshi, sai kuma ya sake tsayawa tare da juyowa a lokaci guda. Da tabbatar wa ya ce, “Ya kamata na sake jaddada muku domin fita hakki. Kar ku barni a nan domin in gani daga shirin shirin ku. Idan kukai wannan sakacin zan zauna in rubuta yadda zan rushe ku daga cikin ɗakin nan da wawancin ku ke sakaku kallonsa keji”. Ya kammala da murya mai sanyi, amma mai ɗauke da tabbataccen iƙirari.        “Kuna da duhu. Ni kuma ina da hasken da yake huda duhun nan naku. Saƙo na ƙarshe, duk wanda ya sake zuwa inda nake da saƙon ku, zan bashi amsar da zai maido muku. Sai dai GAWARSA ce zata dawo da amsar da gangar jikinsa ba BABU RUHI....”        Ya saki murmushi tare da salute da yatsa ɗaya kacal sannan ya juya abinsa cikin takun nan nasa da wanda basu fahimcesa ba ke kallon na izgili da izza. Ƙofar ya buɗe ya fita ba tare da ko waiwaye ba yabar baƙo da rawar zuciya da jiƙewar gumi, ga shi ya gagara koda motsi a wajen tamkar wanda gangar jikinsa ta mutu ta barshi da fitar numfashi kawai........ <%><%><%><%>          Cike da nutsuwa take haɗa masa abincin karin a gabansa, duk da kuwa tana daga tsaye ne shi a zaune kan ɗaya daga kujerun daning ɗin. Ya zuba mata idanunsa na girma fuskarsa da murmurshi. Sai da ta kammala zata matsa ya riƙo hannunta. Kallonsa tayi itama a karo na farko, sai dai fuskarta ita sam babu walwala alamar akwai abinda ke damunta ko ranta a ɓace yake.       “Juwairiyya mike damunki ne wai?”.      Yanda yay maganar cikin taushin murya yana sake tsatstsareta da idanu ya sata sunkiyar da kanta. Sai dai batace komai ba. Numfashi ya ja ya fesar tare da sake matsa hannunta cikin nashi, ya buɗe baki zai magana kenan takun fitowar wani daga cikin yaran ya sashi yin shiru yana sakar mata hannun. Itama matsawa tai kaɗan dan mai fitowar har ya bayyana. Ba kowa bane face Abdul-rasheed da suke kira Imam saboda sunan aboki, amini kuma mahaifi gasu Dada da yaci. Imam shine babban ɗanta a gidan, sa'anni suke shi da Mu'azz koma muce ya girmesa da kusan 2years. Yarone nutsatstse yana tsananin kama da Uncle Nasiru, akwai mai bi masa Halimatus'sa'adiyya. Sai Bintu sa'ar su Nimrah, itama dai ƙawarsu ce dan ƙiriniyarsu ɗaya da ita, idan suka haɗu sam basa jin bari musamman idan an samu hutun makaranta sukan haɗu anan ko gidan Mammah ko gidan Daddy Imran. Adam da Sadiq sune ƙananu a gidan, dan Hajiya Zuwairah ta haifesu ne ma kusa-da-kusa sakamakon gwanne data samu, ta haifi Adam da wata uku ta sake samun cikin Sadiq, hakan yasa tsiransu nasu ba yawa.        “Abba ina kwana? Ummu Ina kwana?”.     Imam ya faɗa yana mai kaiwa duƙe. Hannu Uncle Nasiru ya miƙa masa alamar suyi musabaha yana murmurshi, yayinda Hajiya Zuwairah ta amsa masa da kulawa. Fuskar Imam da murmurshi ya bama Abban hannu kamar yanda yake masa kullum. Dai-dai lokacin Sadiyya da Bintu ke fitowa suma dan ɗakinsu ɗaya.        Abba ya ce, “Abdul-Rasheed kaifa abokina ne ba suruki ba”. Murmurshi Imam yayi kamar yanda ya saba a duk sanda Abban nasu ya faɗi haka. Hakama Hajiya Zuwairah na tayashi. Imam na kaiwa zaune a kujera shima su Bintu suka ƙaraso dining ɗin, cikin girmamawa suka gaida Abban sannan Ummu da Yaya Imam. Duk sun amsa musu da kulawa, Ummu ta kalli Sadiyya tana faɗin, “Halimatu taso min su Adam suzo suyi kari, dan yanzu haka ma basu tashi ba balle batun tafiya Tahafiz, ni narasa miyasa kukafi ɗaukar tafiya boko da muhimmanci a rayuwarku fiye da islamiyya”.       Sadiyya data zama budurwa sosai tai ƴar dariya da faɗin, “Ummu itama islamiyya muna so ALLAH, baga Yaya Imam nan ba har jami'a fannin Islamic ya zaɓa”.        “To ai shi dama yana son karatun addini ba irinku ba. Dan magajin mai sunan nashi ne da Haysam.”     Hajiya Zuwairah ta bata amsa. Murmurshi Uncle Nasiru yayi, zuciyarsa na tuno masa amininsa kuma ɗan uwa Abdul-rasheed, tare da jin raunin zuciya na gagara taka kowacce irin rawa akan al'amarin babban ɗa na ƙwarai irin Haysam. KIƊA A RUWA 2 22 .........“Wlhy Abba zasu aika kada ka amince da daɗin bakinta. Idan ba haka ba nima sai dai a maida ni makarantar su Asma'u ai ƙawaye basu ƙawaye ba”. Caraf Adam yace, “Muma haka Abba”. Dariya kowa ya sanya. Abba ya shafa kan Adam da Sadiq. “Kenan dai na gane a gidan nan kowa yana jealous da Mamana kawai”. “A da alama kam”. Cewar Ummu tana murmushi. Itako Bintu tayi kicin-kicin da fuska alamar jin haushi. Sai da Ummu ta lallasheta sannan ta yarda ta zuba abinci. Daga haka suka nutsu suka fara karyawa babu mai magana. Sai da suka kammala kowa ya miƙe dan zuwa yay shirin Tahafiz har Imam. A lokacin ne Uncle Nasiru ya sake kallon Hajiya Zuwairah dake gyara gurin duk da su Bintu duk sun kwashe kwanikan sun kai kitchen. “Zamu iya magana yanzu?”. Kallonsa ta ɗanyi, sai kuma ta tura baki kama ƴar yarinya. Dariya yayi yana haɗe hannayensa da faɗin, “To ni dai duk ma laifin da nayi ayi haƙuri ai min afuwa. Amma dan ALLAH a sanar min damuwa kada zuciyata ta sake kumbura.” Kanta ta sunkuyar kawai batare da tayi murmushi data saba yi ba a duk sanda yay irin wannan maganar, sai kuma ta ɗan sauke numfashi cike da nutsuwa ta ce, “Abban Jiddah akan maganar jiya da kaƙi sauraren Jiddah akai ne. Bayan kuma ni da kai duk munji abinda Ismat ta faɗa fa. Yanzu dan ALLAH sai ka bari ɓacin rai ya rinjayeka barin yaran nan a cikin tarkon musiba? Kana jin fa abinda ke faruwa; a tunaninka watarana mahaifiyarsu bazata ci galaba akansu ba musamman ma Nabeeha dake ɗauke da igiyoyin aure a kanta! Nasan Nabeeha mai laifi ce a gareka, dan babu izninka babu na mijinta ta koma wata ƙasa da zama bayan ana cikin damuwa da halin da mijinta ke ciki, amma abinda zamu kalla ko tana da laifi wani kaso ne a ciki Hajiya Hasiba nada wani, saboda tana da tasiri ƙwarai da gaske akan al'amarin yarannan idan ka cire Jiddah da ALLAH yay saurin fargarwa...” Cikin ɗacin murya da sauyawar idanun da ɓacewar murmushin kan fuskarsa ya ce, “Ya kike so nayi Juwairiyya? Shin basu ne suka zaɓi irin rayuwar ba shiyyasa suke ciki? Ai su duka ba yara bane har Ismat ɗin da ake ganin batai aure ba, amma suke biyewa gafalar uwarsu da son duniya ta rufema idanu ko”. “Hakane, amma abinda zamu duba har yanzu su yara ne akanmu. Sannan mata ne. Mufa mata a kowace sigar rayuwa a karkacen nan muke tamkar haƙarƙari. Shekaru basa saka mu canja ko ilimi. Sai wanda UBANGIJI yaso ya gane kawai daga cikinmu. Mu godema ALLAH da yarannan basu tasirantu da huɗubarta ba ma har suka fahimta illar al'amarin. Dan wlhy UBANGIJI ne kawai ke riƙe da igiyoyin auren Nabeeha saboda Haysam mutumin kirki ne, in sha ALLAHU ALLAH bazai haɗa masa zafi biyu a lokaci guda ba. Dan ALLAH kayi wani abu kodan Haysam, saboda koba komai da saka hannunka ya auri Nabeeha, sannan yana sonta”. “Hummm Juwairiyya....” “Dan ALLAH karka ce A'a Abban Jiddah”. Tai maganar cikin katse masa hanzari. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kawai. Tare da faɗin, “Shike nan zan duba. Amma ki sani Adeel yaro ne mai dauɗar duniya a hannu, sannan ya fito daga babbar zuri'ar da yake da ƙarfin aji ako ina a duniya musamman ma ƙasashenmu na Afirika. Barowarsu ƙasar nan zai zama babban al'amari. Amma zan gwada wata hanya idan za'a dace.” “ALLAH yasa a dace, dan duk ƙarfinsa bai kai na UBANGIJI ba ai. Darajar auren dake kan Nabeeha ALLAH zai hanashi dukkan nasara. Itama ALLAH ya shiryar da ita ta gane halakar da take neman jefa yarannan da kanta.” “HUmmm”. Kawai Uncle Nasiru yace, itama sai ta saki zancen ta ɗakko na batun zuwa sake duba Aunty Mimi mai haihuwa duk da kuwa randa ta haihu taje. Amma a matsayinta na kamar uwa koda Mammah na nan dama ita ya kamata ta yi abinda uwa zatayin, saboda ita da Mammah suna jin kansu kamar ya da ƙanwa uwa ɗaya uba ɗaya. Kamar yanda Uncle Nasiru ke ɗaukar Mammah ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗayan. Bai hanata ba, shima ya miƙe yana faɗin zai shirya dan yau yana da ganawa da sanata Yusuf Shu'aibu Tafida tsohon janar. ƘIDA A RUWA 2 23 .........A wannan rana ƙarfe sha biyu na rana jirgin su Mammah ya sauka, tare take da Ammar ɗinta sai ƙaninta Tasi'u da Ammar ke kira Uncle. A tsakkiya suka sakata har inda motoci suke. Aiko cikin sa'a sukai arba da tagwaye biyu Yaya Ma'aruff da Ja'afar da suka zo ɗaukarsu da kansu. Sai dai me suna yunƙurowa a tare suka koma suka ƙame kamar gunkinaye idanunsu akan Uncle Tasi'un. Dan duk da suma suna yara sosai ya aikata abinda ya aikata hakan bai sa sun mance wannan fuskar tasa ba. Dan bayan mahaifin Biebah shine mutum na biyu daya bar musu tabo a zuciya na zahiri. Abinda dangin mahaifinsu suka aikata duk a labari suka sanshi, a labarin ma ba komai ba daga bakin Mammah ko Dadansu. Gwaggo Alawiyya ce ta gaya musu komai. Ganin yanda sukai ɗin ya saka Mammah cikin dakewa furta, “Oh bakwa farin ciki da ni na koma kenan ko?”. Jikinsu ne yay sanyi, cikin dauriya da danne zukata suka nufota, batare da ko kallon Uncle ɗin nasu sun sake yi ba suka rungumeta ita da Ammar suka manta da shi. Ammar daya tsargu da abinda ya farun da ƙyar ya iya dannewa yana murmurshi. Haka suka kama Mammah a tsakkiya har mota. Sai da ta shiga suma suka shiga Ammar ya shiga, ganin Uncle Tasi'un bai shigo ba Mammah tace su masa magana ya shigo. Kallonta sukai kamar zasu fasa kuka. Amma kallon da itama tai musu na gargaɗi ya sasu risinar da kawuna Ja'afar ya fita yay masa magana. Sum-sum kamar munafuki ya shiga kusa da ita suka sakata a tsakiya shi da Ammar...... Sun iso gida da yake shiru kasancewar basawan cikinsu duk ana makaranta. Masu aiki ne kawai sai Aunty Shariffa da Aunty Lailah da yay basu je gidan haihuwa ba saboda dawowar Mammah. Hasalima da kansu suka shiga kicin yi mata abincin da suka san tafi so da ƙauna. Masu aiki da suma ke farin ciki da dawowarta na tayasu da ƙananun ayyuka. Daga Aunty Shariffa har Aunty Lailah kowace fama take da ƙaramin ciki, dan cikin ikon ALLAH kamar yanda sukai haihuwar su Abees a tare da tasu Afrah da Ayyan haka wannan cikin ma basu da nisa a samu. Sai dai Aunty Lailah ce ta fara samu kafin Shariffa. Dan haka nata yafi fitowa sosai har ana iya gani. Mu'azz ya fita akan batun karatunsa dan Imam ne yazo har gida suka fita a mashin ɗinsa. Wannan ya ƙara haifar ma da gidan shiru. Motar su Mammah na gama tsayawa Lailah da Shariffa suka fito cike da ɗoki da farin ciki dan Mammah uwa ce a garesu ba uwar miji ba. Itama fuskata ƙawace da murmushi ta fito da taimakon Ammar. A tare ta kamosu jikinta ta rungume tana mai jin farin cikin ganinsu da sanya musu albarka. Yayinda suma suka zame suka zube cike da girmamawa suna mata barka da dawowa. Ta amsa musu da kulawa tana kamasu ta miƙar. Cike da tsokana Ammar ya ce, “Wato kunga Mamanku ni in ma na ɓata a can babu ruwanku ko Auntys?”. Yanda yay maganar yana cika baki da iska har su Ma'aruff dake faman haɗe fuska saboda Uncle Tasi'u Sai da suka dara. Suma cike da tsokana sukace, “Mu mun isa muso kawun yara ya ɓata. Ai sai suyi mana bore suma Yaya Ammar”. “Ato naga ba'a wani ji dani ne sai Mammah kawai”. “To ayi haƙuri, kasan rashin ta ya maida mu kamar marayu a gidan cike muke da ƙaguwar son ganinta. Kaima bari kaga ƴaƴanka su dawo duk kanka zasuyi”. “Ai shiyyasa ma ban damun ba. Dan da kaina zanje na ɗakkosu a schools”. Duk hirar da suke zugawa Uncle Tasi'u na kallonsu ne kawai cikin damuwar kallon banzar da su Ja'afar ke masa a kaikaice. Su ko su Lailah basu lura da shi ba sai daga baya. Kamaninsa da Mammah dake a bayyane ya sakasu kasa jurewa suka bishi da kallon sakanni. Sai kuma suka duƙar da kawuna cikin ƙaulani da rashin tabbaci suka shiga masa barka da zuwa. A karo na farko yaɗan sauke ajiyar zuciya. Dan koba komai girmamawar tasu ta ɗan sakashi jin sanyi a ransa. Ya amsa musu da kulawa shima. Mammah ta katse su da faɗin, “Kumuje ciki kun san fa ni bana jurar tsaiwa”. Da to suka amsa mata suna sakata a tsakkiya, dai-dai nan kuma maigadi da sabon driver suka iso wajen cike da girmamawa suka duƙa har ƙasa suna gaida Mammah. Tabbas Mammah zata iya haihuwarsu idan muka musalta da yanayin auren da na ƙarancin shekaru musamman ma itama da akai mata tana ƴar 14. Dan driver dai zai iya zama sa'an Dada, maigadi ko bai wuce sa'an su Yaya Ja'afar ba, idan ma Dada zai girme ma sabon driver ɗin kaɗan ne, sai dai yanayin jin daɗi ba ɗaya ba, duk da a yanzu basu san yaya Dadan yake ba amma ya fishi ƙyawun jiki da ƙuruciyar zahiri. Dan shi wannan ma har furfura ta cika masa gemu duk da dai kansa akwai hula tashi da ƙwaƙwa baƙa data ɓoye gashin kan nasa, sai na iya fuskar zaka shaida zuwa gemu dan yana da saje... “A'a bawan ALLAH tashi-tashi kaji, mun sameku lafiya ko Almu. Ka yi baƙo ne?”. Maigadi ya bata amsa da mata bayanin ba baƙonshi bane su Yaya Ma'aruff ne suka kawo shi. Kafin tace wani abu sabon driver wanda shima a karo na biyu fuskarsa da murmurshi ya amsa mata, kafin ya miƙe yana sake mata barka da dawowa da sannu da jiki. Sannan ya juya yana gaida Uncle Tasi'u da Ammar. Ma'aruff ne ya juyo yana kallon Mammah ya ce, “Sabon driver ne daya maye gurbin Baba Ari. Sunansa Buba kwana uku da tafiyarku ya fara aiki”. Fuskar Mammah da fara'a sosai ta ce, “Masha ALLAH. Sannu da zuwa Malam Buba. ALLAH yasa zamanmu tare ya zama alkairin da zamu shiga aljanna gaba ɗaya. Ina dai fatan babu wani damuwa a zamanka tare da mu ɗin?”. “Amin Hajiya. Amin Amin. Babu wata damuwa sai godiya tsakanina da ku. Dan kuwa kwanakin da nai kawai na shaida alkairin mutanen wannan gida.” “To Alhamdullahi ALLAH yasa mu dace. Bari naje na huta munsha zaman jirgi zuwa anjima ka shigo mu ƙara gaisawa?”. “To to shike nan Hajiya, ALLAH ya huta gajiya nagode sosai.” Fuskar Mammah da murmushi ta amsa da amin Kafin su Shariffa su kamata har zuwa ciki. Shi dai Uncle Tasi'u na biye da su sum-sum kamar munafuki, sai dai harga ALLAH yayi matuƙar girgiza da ganin irin wannan katafaren gida mai kama da wani ƙaramin estate wai duk mallakin Adda A'isha ne da zuri'arta. Addarsa fa dake wujiga-wijiga akan marayun ƴaƴanta dana gayyar soɗi na kishiya data kama ta riƙe ita mai son miji. Addar nan tasa dai daya damfara gida ya gudu ya batta da sanin bata ga tsuntsu bata ga tarko a lokacin, amma a yanzu sai gasu a wannan ƙosashen gidan a babban birnin tarayyar ƙasa da dukkan alamu suka nuna nasu ne, kai shifa tun a motar dasu Ja'afar ɗin suka ɗakkosu dama zuciyarsa ke bugawa, yanzu kuma da suka shigo gidan ma sai yaga motocin da sukafi wadda suke ciki, sannan ba ɗaya ba a ƙalla motoci sun kai bakwai a gidan harda wadda suka dawo ta takwas. Bai ji zuciyarsa na tsitstsinkewa ba sai da suka shiga cikin katafaren sashen Mammah ita ɗaya, dan dama sashenta dana Dada sunfi kowanne girma a gidan. Kafin kace mi kuma ƴan aiki har uku sun zagayeta suma da tasu gaisuwar girma. Ga waɗan nan tsala-tsalan matan daya fahimci matan su Ja'afar ne sai rawar jiki suke akanta kamar wata uwarsu mahaifiya... .....★DUBAI★..... “Inaga a wannan gaɓar zan saka a kashe mijin nata, dan hakan ne kawai zai saka ta yarda ta saduda ta mallaka min kanta”. A wani irin firgice Hajiya Hasiba ta ɗago tana kallon Adeel mai maganar. Mamawo kuwa abincin da suke ci ne ya nema ƙwareta. Sai da ta ɗauki ruwa tasha da sauri. Shi ko ko'a jikinsa, dan tamkar ma bai ga halin da suke ciki ba ya cigaba da maganarsa. “A karo na farko ina son sanin wanene shi mijin nata? Miya taka a ƙasar taku? Ɗan wace zuri'a ce? Miye ƙarfin ikon sa?”. Su duka biyun rasa mai bashi amsa akayi, dan dama daga su sai shi ne a dining room ɗin. Su Ismat sunbi Nabeeha sun fice a gidan tun da sukaji zancen zuwansa. Ɗan dukan table ɗin yayi ta yanda suka dawo hayyacinsu firgigit. Da ƴar tsawa da raini da wulaƙanci ya ce, “Ko kuma kuna bin bayan wulaƙanta ni da take ne....?” “A'a wlhy bama bin bayanta. Da muna da iko da zuciyarta ma da tuni kun jima da zama ma'aurata maybe ma kun haihu. Mijinta ba kowa bane, ba ɗan kowa ba, baya da komai, baya taƙama da komai. Kawai soja ne a ƙasar mu, kamar yanda muka sanar maka tun farko kuma yana prison yanzu haka, shekaru ashirin da biyar kuma aka yanke masa a can”. “What! Shine kuma take tunanin zaman jiransa?”. “Shirmenta ne kawai Prince, amma tun kan ya shiga prison ma ita ta bar masa gidan sakamakon auren yarinya ƴar shekara 7 da yayi saboda ya ɗakota a wajen yaƙi. Daga ƙarshe ma mukaji ashe shine ya kashe mata iyaye dan ya aureta, da alama wani laƙanin asirin aka bashi dan dama yanda yake juya sojojin da wani gadararsa har manyan suna tsoronsa kai ka san ba haka kawai bane, dole akwai aikin asiri a ciki”. “Woow naji daɗin wannan labarin ƙwari da gaske. Yanzu ita yarinyar tana ina ne?”. “Tana a gidansu tare da ahalinsa. Sai dai a yanzu takai kusan 15years da wasu watanni”. Komai bai sake cewa ba ya miƙe kawai, da kallo suka bishi yana tafiya cike da ƙasaita da gadara, sai da yaje gab da fita a dinning room ɗin sannan ya juyo yana kallonsu. “Zamuje ƙasarku tare da ɗaya a cikinku”. Daga haka ya fice abinsa batare da jiran amsarsu ba.........✍️ KIƊA A RUWA 2 24 ..........Shiru sukai kowa ya gagara iya cewa komai. Sai zuwa can Mamawo ta ja numfashi mai ƙarfi ta furzar. Sai kuma ta ajiye spoon ɗin hannunta ta rabga tagumi da hannu biyu. “Anya Aunty mutumin nan bada wata manufa yake son Nabeeha ba?. Wlhy nikam al'amarin nan fa ya fara bani tsoro gaskiya. Duk matan ƙasar nan ko a cikin nan Dubai irin sa, da masu shigowa baƙi kullum, dana ƙasashen da yake yawo ace ya rasa matar aure sai Nabeeha da aka jima da sanar masa tana da miji. Abin mamaki duk cin kashin da take masa bai taɓa nuna koda damuwa a fuska ba balle zuciyarsa. Kai wannan batu yana buƙatar dubawa fa. Kalla gidan nan daya mallaka miki halak mallak, ga motar hawa, mu dukanmu yasa akai mana katin zama ƴan ƙasa. Yanda suke da ƴanci a ƙasar nan haka fa muma muke da ƴancin shiga duk inda muke so a lokacin da muke so..” “Ni kaina a wannan gaɓar na fara tsorata Mamawo. Balle ma maganar kashe Haysam da yayi, bawai bana son ya kashe san ba. Nasan wannan kuma abu ne mai sauƙi a wajensa aikata hakan. Babbar damuwar wataran Nabeeha tasan yanda komai ya faru wlhy bazata rufa mana asiri ba. Dan tsaff zata ce damu aka haɗa kai akayi. Shi yana da kuɗi da mulkin da zai cire kansa, muko mune a ruwa..” “Tabbas zancenki na kan hanya Aunty, sai dai ai zamu iya roƙonsa karya sanar mata, sannan zuwan da zai yi ma duk yanda zamuyi kawai muyi kada ta sani. Dan na tabbatar ya samu Nabeeha duk abinda muke so a duniyar nan zamu sameshi a wajensa, ni dai kawai babbar damuwa ta mu fara sanin wai minene ma manufarsa akan son nata”. “To ta yaya zamu sani kuwa Mamawo? Tunda ba zuciyar tasa zamu tsaga mu duba ba”. “Ai bata wannan ake gane sirrin zuciya ba Aunty, shiryawa zakiyi wuff muje India wajen mai mun aiki, koma minene shirinsa sai ya sanar mana shi”. Shiru Hajiya Hasiba ta kasa magana. Bawai bata bin bokaye bane, sai dai mafi yawa irin wannan leƙe-leƙen bata yinsu a karan kanta first lady ce ke aikenta, kuma tunda suka sauka a mulki ta ɗan rage yi sai na kan kasuwanci da takan je mata, wani lokacin kuma suje tare..... “Aunty kinyi shiru?”. “Ba shiru nayi ba Mamawo, ina auna yanda tafiyar tamu zata kasance ne, balle kinji shi yace zai tafi da wata a cikinmu. Kinga bamu da tabbacin yaushe ne ko?”. “Haba aunty mu sai kace ba mata ba. Zaki iya bagarar da shi akan tafiyar gaggawa ta taso miki wani business ɗinki haka. Kinga sai muyi mu gama da wuri mu dawo. Dan haka ya kamata ma ace cikin watan nan mu tafi”. “To bari muga zanyi tunani”. Daga haka ta miƙe tabar haɗaɗɗen dinning room ɗin da aka cika kayan abincin alatu duk saboda Adeel. Sai gashi ko cikakken lauma uku baiyi ba ya tashi ya barsu da kayansu..... <%><<<%>>><%> Mintuna talatin da isowar Mammah da Ammar su Aunty Ummi suka shigo gidan ita da Aunty Mommy. Cikin matuƙar farin ciki suka rungume Mammah dan yanayin ta kaɗai ya tabbatar musu da lafiya ta ƙara samuwa Alhamdullah. Suma dai hankalinsu bai kai ga Uncle Tasi'un ba sai da suka gama gaishe-gaishen su. Turus sukayi suna kallonsa. Ba kallon sani ko tuna waye shi ba. Kallon mamakin kamaninsa da Mammansu kawai. Dan suma sanda wancan abin ya faru basu da wayon tuna komai gara ma Ma'aruff da Ja'afar ɗin. To balle ma Mimi ƴar ƙarshe ita da Ammar da lokacin basu wuce shekaru shuda ba. Biebah kuwa na jaririyar wata baifi biyu ba. Maida kallonsu sukai ga Mammah, kafin ma suce wani abu ta basu amsa da, “Kawunku ne”. “Kawunmu Mammah? Na ina to? Mudai a sananinmu ƙannenki duk sun rasu, gashi kuma yana kama da ke”. Sai da ta ɗan girgiza kanta da murmurshi kawai sannan ta ce, “A'a Bashir ne dama ALLAH yay ma rasuwa, Tasi'u kam ƙaddara ce ta nisanta mu”. A take murmushin fuskokinsu ya ƙarasa ɓacewa. Dan duk da bata taɓa basu labarin abinda Uncle Tasi'un ya aikata mata ba duniya ta jima da sanar musu. Koma suce cikin danginta. A taƙaice sukace, “ALLAH sarki”. Tare da gaisheshi sama-sama suka bar wajen. Cikin sake raunanuwar zuciya Uncle Tasi'u ya bisu da kallo. Mammah da duk take jin babu daɗi da yanayin tarbar da ɗan uwan nata ke samu wajen ƴaƴanta cikin sanyin murya ta ce, “Sai kayi haƙuri da abinda zaka gani a wajensu. ALLAH ne shaida ban taɓa sanar musu koda kuskuren dangin mahaifinsu ba balle naka a gareni, sai dai yau da gobe ta wuce wasa duniya da dangin sun gama sanar musu batare dana sani ba. Amma ka bani lokaci ƙanƙani, in sha ALLAHU zan zauna da su ni da Yaya Nasiru zasu fahimta”. Murmurshin ƙarfin hali yayi cikin girgiza kai. “Ba komai Adda, kuma ki sani ni banga laifinsu ba sam. Kawai ina jin tsoron isowar yaran nan da kullum zancen su danginsu danginsu kuma su fuskanci abinda bashi nake fata ba daga dangin. Nine nai laifi basu ba, dan haka dan ALLAH ko sunzo suyi haƙuru su su amshesu koda ni bazasu ashe ni ba”. “Kaima zasu amshe kan in sha ALLAHU. Kadai bani lokacin. Bismilah muci abinci sai ka samu kaje ka watsa ruwa lokacin Azhar na gabatowa. Yanzu kuma gidan zai sake rikicewa dan masu shi na gab da dawowa daga makaranta”. Murmurshi kawai yayi. Ya gyara zama ya fara cin abincin da aka shirya musu a tsakkiyar falon.... ★★★ “Tab ɗi, wai yaya mi hakan ke nufi? Miya kawo wannan mutumin rayuwarmu a wannan gaɓar? A ina ma su Mammah suka samo shi wai shin?”. Ya ƙare maganar tana kallon Ammar. Ammar cikin sake ɓata fuska ya ce, “Aunty acan muka haɗu da shi cikin asibiti fa. Ni kaina nayi mamaki da Mammah ta bashi damar wai ya biyomu, nazata kawai zata barshi ya koma inda ya fito ne”. Hawaye Aunty Momy ta share, muryarta na rawa ta ce, “Sun manta damu a lokacin da muke buƙatar tainakonsu da ƙarfinsu. A yanzu zasu fara dawowa rayuwarmu kenan a lokacin da ƙarfinsu ya ƙare mu mukai ƙarfin. Ni tsorona ma kada ya sake zuwa yaye dukiyar tamu ne ya gudu”. “Shi ɗin banza”. Cewar Ja'afar a hasale. Ya cigaba da faɗin, “Ai ko a wancan karon dan Dada baya nan ne ya samu nasara, kuma yana da hakki a wancan amma a wannan fa. Ko a yanzu da babu Dada akwai halifofinsa a kusa. Idan da rabon yazo yayi ta ransa ne bismilah”. Cikin furzar da iska Ma'aruff ya ce, “Wlhy ni nama rasa tacewa sam. Amma al'amarin ɗan adam bai taɓa bani ƙarshen mamaki ba irin yau. Wai dama Uncle Tasi'u har yana da ƙarfin zuciyar iya sake tunkarar Mammah?”. “Ai baida kunya Yaya Ma'aruff gashi kuwa yayi ka gani. Wlhy ina matuƙar jin kewar Dada. Ya ALLAH ka saka mana ka tarwatsa farin cikin duk wani azzalumi dake da hannu a kama mana shi. Wlhy wani cin kashin ma da yana nan da bazasu kwatanta mana shi ba. Dan na tabbatar duk tsawon shekarun can saboda shakkarsa yasa ko ƴan Bauchi kasa sake tunkarar inda muke. An kama shi dan kar su zo mu nema taimakon sun suka sake ja baya damu. Yanzu kuwa tunda sunga ALLAH ya rufa mana asiri zasu fara kawo kansu...” “Ai ko zasu fuskanci wulaƙanci da tozarci a garemu. Dan mu mun jima da sallama dangi a duniyar mu. Mune dangin kammu mahaifiyarmu da Dada sun ishemu uwa uba a duniya. Azzalumai kawai masu matacciyar zuciyar watsar da marayu”. Ammar ne ke maganar yana kuka. Rungumeshi Ja'afar yayi yana shafa bayansa. Haka ma Aunty Momy hawaye take ta sharcewa ita da aunty Ummi. Kasancewar a sashen Yaya Ja'afar suke zaune sai suka ƙi komawa sashen Mammah har sai da yara suka dawo school. Basa son su fahimci komai dan haka suka dawo sashen Mammah ɗin. Inda suka sameta zagaye da yaran cike da farin ciki kowa ji yake kamar ya koma cikinta. Ita ko bakinta ya kasa rufuwa. Abinci ma ita ta dinga basu abaki tun daga kan Nimrah, Ruƙayya, Abees, Aheel, Afrah da Ayyan ƙarami. A haka shima Mu'azz da Imam suka shigo gidan suka samesu. Suma daɗi ya kamasu da ganin Mammah ta dawo. Ai tuni suma sunyi zaman dirshan suna amsar abincin. Wannan farin cikin ya saka su Aunty Ummi mantawa da damuwarsu. Dan Mammah na kammala bama yaran abinci suka dawo wajen Uncle Ammar shima kowa na tambayar tsarabarsa. Musamman Nimrah da Ruky da suka bada sakwanni na musamman...... <•><•><•><•><•> Kusan lokaci ɗaya Uncle Nasiru da Daddy Imran suka shigo gidan. Dan dukansu daga wajen aiki suke. Sabon Driver dake zaune tare da maigadi ya bisu da kallo su duka. Dan yau kwanakinsa shida a gidan bai taɓa ganin Uncle Nasirun na, sai Imran sau 1 shima. To Daddy Imran ɗin kuma yayi ƴar tafiya bayan wucewar Mammah da yazo sau ɗayan daya gansa, kwanansa huɗu ya dawo. A randa ya dawo yazo gidan lokacin shi kuma yaje ɗakko yara daga Islamiyya. Motarsa na fita shi kuma ya dawo da su. Tun ranar kuma bai sake zuwan ba sai yau. Uncle Nasiru kuwa dama tunda Mammah tai tafiya bai leƙo gidan ba saboda ayyuka sun masa yawa, ya kuma san yaran duk ba zama suke ba sai matan su Ja'afar kawai. Suna tsaka da gaisawa Maigadi ya gama rufe gate ya nufesu, dole shima driver ya bishi suka iso inda suke. Rissinawa sukai suna gaishesu duk da kusan sa'an Imran yake shi sabon driver, koma ya iya girmarsa kaɗan duk da shi Imran akwai jin daɗin rayuwa da kulawa da lafiyar jiki irin ta soja a tattare da shi. Uncle Nasiru yana tsokanar su. Shi ko Imran sai ya ɗan zuba ma sabon driver idanu. Har sai da Uncle Nasiru ya ce, “Imrana yaya dai? Ko ka san shi ne?”. Cikin ɗan murmushi Imran ya girgiza kai da faɗin, “A'a Uncle. Kawai na tafi wani tunanin ne daban”. Bai jira amsawar Uncle Nasiru ba ya juya ga drivern ya amsa masa gaisuwarsa. Daga haka suka bar wajen driver na binsu da ido. A zuciyarsa kam dake bugawa ayyanawa yake (lallai akwai matsala. Shegen nan ko bai gane ni ba ya tsargu da ni. Lallai dole na canja takuna kenan. Dan banzo nan dan na tafi batare da na kammala abinda ya kawoni ba) a zahiri kam miƙewa yay ya koma gate ya zauna a kujera. Sai kuma ya zaro wayarsa ƙaramar nokia ya shiga danne-danne kafin ya kai kunnensa.....KIƊA A RUWA 2 25 ..........★A falo kam daga Imran har Uncle Nasiru sunji matuƙar daɗin ganin yanda jikin Mammah ya ƙara ƙyau. Da alama ta samu maganin da yafi wanda take samu anan gida. Dan wannan ne karon farko da suka fita Egypt ɗin dama. Kasancewar su Nimrah duk sun wuce islamiyya da ƙyar gidan shiru, dan ca sukai bazasu ba yau suna murnar dawowar Mammah. Sai da Yaya Ma'aruff ya fatattakesu sannan kowa ya wuce baki a sama. Sai Biebah kawai itama bata jima da dawowa daga school ba. Mu'azz yabi Imam gida. Mammah ta kalla Biebah dake laƙai-laƙai ɗin cin abinci saboda bata jin daɗi yau da ciwon kai ta dawo makaranta ganin Mammah ɗin ne ma ya ɗan watsakkar da ita. Sai dai ganin baƙon dake gidan ya tsaya mata a zuciya kamar sauran ƴan uwanta. Dan yanzu haka ma Aunty Momy da Aunty Ummi da Ammar na ɗakinta suna sake tattaunawa. “Biebah tashi kira Uncle ɗin ku”. Idanu Biebah ta ɗago tana kallon Mammah, sai kuma ta amsa da to cikin sanyi tana tashi. “Kina lafiya kuwa Biebah?”. Cewar Imran. Idanunta na cika da ƙwalla ta ce, “Yaya kaina ke ciwo”. “Ayya Auta stress ne sannu. Jeki dawo kizo kisha magani kije ki ɗan kwanta kafin akkunayen gidan su dawo su hanaki”. Kai ta jinjina masa. Shima Uncle Nasiru yay mata sannu. Nan ma amsawa tai ta wuce aikar Mammah... Babu jimawa ta dawo tace yace gashi nan zuwa. Bata zauna cigaba da cin abincin ba ta ɗauka plate ɗin takai kitchen. Koda ta dawo da ruwa a hannunta ƙoƙarin wucewa tai ɗaki. Dai-dai nan Uncle Tasi'u ya shigo falon da sallama. Duk amsawa sukai suna kallonsa. Sai dai zaram Uncle Nasiru ya miƙe yana kallonsa. Shi ko Imran bai san shi ba a zahiri sai labari a sanda wancan abin ya faru, dan haka babu wani alamun mamaki ko damuwa a tare da shi. Sai ma sannu da zuwa da yake jera masa. Sai dai ya gagara amsawa dan hankalinsa shima gaba ɗaya yana kan Uncle Nasiru ɗin ne. “Tasi'u!”. Uncle Nasiru ya faɗa cikin matsanancin mamaki da al'ajabi. Karo na farko Tasi'u yay ƙasa da kansa, idanunsa na cika da ƙwalla. Fin sakan biyar kafin ya sake ɗagowa tare da takowa inda Uncle Nasiru yake ƙafafunsa nayi kamar suna rawa. Yana zuwa gaban Uncle Nasirun kawai sai ya zube akan gwiyawunsa. Imran ya zaro idanu waje sosai yana miƙewa, dan zuwa yanzu kam ya fahimci lallai akwai matsala, sannan baƙon yana tare da wani babban al'amari, yo dukda ba yaro bane babba da shi ya durƙusama Uncle Nasiru. Mammah ya kalla, ya ga ta duƙar da ƙai itama kamar mai kuka. Sai shima ya girgiza kansa. Muryarsa a raunane ya ce, “Mammah waye shi dan ALLAH? Naga kuna kama ba ɗan uwa bane ba shin?”. Ɗagowa Mammah tayi ta kalla Imran tana ƙoƙarin maida hawayen da suka cika mata idanunta. Fuskarta da ɗan murmushi. Babu wani ko ɗar ta amsama Imran tambayarsa. Dan har cikin ranta kallon Imran take dai-dai da su Haysam. Jinsa take tamkar ɗan data ɗauki cikinsa ta haifa. “Imran Tasi'u ƙanina ne uwa ɗaya uba ɗaya. Baka san shi bane saboda wasu abubuwa da suka faru a baya. Amma sun riga sun wuce na yafe masa. Mun haɗu da shi a asibiti nd kwana huɗu kenan.” Gaba ɗaya Imran sai yaji kamar ma yayi mutuwar tsaye. Ga kukan Uncle Tasi'u daya cika falon. Dan kuwa ya riƙe ƙafafun Uncle Nasiru ne yana raira kuka da kalmomin ban haƙuri kamar wani yaro. Yayin da shi Uncle Nasirun ya gagara sake iya cewa komai yana tsaye kawai shima idanun nasa sun kaɗe jazur. Kukan Uncle Tasi'u ne ya sakko da su Aunty Ummi. Ko muce Biebah taje ta kirasu dan komai dake faruwa tana kallo daga inda take laɓe. Ammar daya gama kaiwa wuya cikin fushi ya ce, “Ni wlhy wannan drama ɗin ta isheni haka nan.” Duk juyawa su Mammah sukai suna kallonsu, dan basu san da sakkowar tasu ba. Sai dai kan wani yay magana Aunty Ummi ta ce, “Ba kai kaɗai drama ɗin nan ta isa ba Ammar harda mu ma. Shiyyasa ma su Yaya Ja'afar suka bar gidan, dama kuma jiran zuwan Uncle Nasiru kawai mukeyi muma. Idan Mammah nada zuciyar kawaici da haƙuri mu bamu san wannan ba, babu yanda za'ai maciji ya saremu a bakin rami mu sake maida ƙafarmu da tunanin bazai sake na biyu ba. Ai ko hausawa sunce sanin hali yafi sanin kama. Dan haka Uncle! Yaya kodai ku bashi shawarar ya koma inda ya fito, ko kuma ya nema masauki a wajen wannan gidan magana ta gaskiya”. Tana gama faɗar haka ta juya zata bar falon tana hawaye. Take mata baya su Ammar sukai suma. Mammah zata dakatar da su Uncle Nasiru ya girgiza mata kai alamar ta barsu.... Dole Mammah tai shiru, shi kuma ya miƙe yana sake faɗin, “Tasi'u tashi muje can gidana, mu basu lokaci nan da kwana biyu.” Daga shi har Mammah ɗin babu wanda yay jayayya, dan Uncle Nasiru yaya suke kallonsa uwa ɗaya uba ɗaya. Bayan wucewarsu shima Imran bai jima ba ya wuce gida abubuwa da yawa na masa kai-kawo a rai da zuciya...... (((★)))(((★)))(((★))) ★PRISON★ Yana komawa ɗakinsa ya zauna a gefen gadon sa yana kallon sojojin dake ƙoƙarin ɗaura tvn da suka kammala haɗawa a jikin bangon ɗakin. Baiyi musu magana ba, dan ko gaisuwar da sukai masa bai amsa ba a sanda ya shigo hannu kawai ya ɗaga musu. Suna kammalawa suka fice daga ɗakin tare da maida ƙofar suka rufe masa. Shima sai ya rufe idanu kamar yana barci amma ƙwaƙwalwarsa ce ta shiga aikin aunawa da lissafin abinda ya faru. “Facemask Analysis. Camara jikin agogo”. Ya furta a saman lips yana wani ɗan gajeren murmushi har lokacin idanunsa a rufe. A zuciya ya cigaba da ayyana suffar mutumin dalla-dalla da irin ƙwaƙwalwar ma'aikacin daya san aikinsa. (Fuskar bogi, agogo, tsayayyun idanu na masu busashiyyar zuciya da shekarun girma na tantance gwagwarmayar rayuwa na tsawon lokaci. Yanayin motsin ƙwayoyin cikinsu na ƙwararren operatives. Hakan na nufin wani daga cikin manyansu ne. Ba sabon shiga ba. Barazanar da ya faɗa. Sun ce suna sarrafa shugabanni… hakan na nufin akwai infiltration a cikin gwamnati. Wannan na iya zama sashin da ke kai rahoton Board of Inquiry. Ya ambaci makusanta. Hakan na nufin da damar su Imran ya zo wurina shekaru biyar da suka wuce. Yanzu kuma sune suka saka aka dakatar da shi. In dai haka ne to akwai idanu dake zagaye da Imran cikin rundunar soji ko wajenta, lallai Imran zai iya shiga haɗari akoda yaushe dan ko zai mutu bazai bisu fuska da fuska ba. Ya furzar da iska mai nauyi yana runtse idanu, dan Imran wani sashe ne na jikinsa da taɓashi tamkar ruguza jarumtarsa ne. Abu na uku tambayar su (Me yasa suka barni da rai har yanzu? Nima wannan tambayar ta jima a raina. Tabbas da nine a matsayinsu, zan kashe wanda nake tsoro musamman in haɗarinsa zai zama babbar barazana ga ƙasata bawai a karan kaina ba. Amma su suna bukata na a raye. Me yasa?) yay shiru na tsawon lokaci, sai kuma ya tashi zaune da ƙyau ya ɗauki pen da takarda ya rubuta wannan tambayar. _“They need me?. For what? To watch me? To use me? Or to fear me?”_ Pen ɗin ya kai saman lips ɗinsa da suka ɗan bushe dan yau yana azumi. Abu na huɗu (Wasan da suke cewa ya fara… hakan yana nufin wani babban shiri da suke da shi a wannan tsakanin kenan? Wani sabon hari ne?. Ko wata rawar juyin siyasa?. To amma ai basa buƙatar mutum kamar ni wajen gane kosu su waye?, ko ina matsalar?. Wannan kuskurensu ne ko ni ne ban fahimta dai-dai ba?) ya sake yin shiru alamar dogon nazari. Tsohon lokaci yana kai kawo da tunaninsa, sai kuma ya kai dubansa kan television ɗin da aka saka a ɗakin. Karo na farko ya miƙe yana ajiye littafin hannunsa da pen ɗin, gaban tvn ya isa, sai da ya gama duba ko ina na jikinta ya tabbatar babu camara sannan ya ɗauka remote ya fara searching channels, tashoshin dake cikin decoder ɗin da aka haɗata da ita duk zaɓaɓɓune. Domin guda uku ne kacal ba'a komai a cikinsu kuma sai abinda ya shafi labarai. Labaran ma ba kowane labari ba. Dan a yanzu dai kusan harkokin siyasa ne da campaign da aka fara kusan wata uku kenan. Idanun ya janye a hankali cikin salon yin luuu da su ya maida gefe da sakin murmurshin nan nasa na ƙeta. Sai kuma ya maida remote ɗin ya ajiye inda ya ɗauka ya koma bakin gadon ta sake zama.. Gaɓar da tafi tsaya masa ce ta sake maimaita kanta a brain ɗinsa. (Sun ce suna sarrafa zuciyar manyan. Idan haka ne, bayanan da Imran ya kawo min game da janar mai ritaya… dole sai na sake nazari. Domin kuwa wani daga ciki yana iya zama mai sarrafa Janar a gefe, da wannan damar kuma kaɗai za'a iya cimma Imran. Dan tabbas tunda har suka faɗa ya fahimci cewa ziyara ta farko da ta biyu na Imran sun haifar da damuwa a ɓangaren kungiyar shaiɗanun nan, shiyyasa ma suka hana shi cigaba da zuwa. Ya ɗan murmusa kaɗan, dan ya fahimci abu mafi mahimmanci har yanzu suna tsoronsa. Shiyyasa suka hana a ziyarcesa, suka hana yay communication da kowa, suka saka aka killaceshi inda baya ganin kowa sai masu tsaronsa dake kawo abinci dama duk abinda yake buƙata. Ya jima da gane a jikin masu tsaronsa akwai camara dake isar da saƙon shigarsu da fitarsu wajensa. Zuwan baƙon nan ma ba saƙon da yazo faɗa bane kawai maƙasudin zuwansa nan, suna son suga ko ya raunata a zuciya zuwa yanzu. Suna son su gane ko ya ragargaje da raunin kaɗaici. Suna son su tabbatar ko har yanzu yana da ƙarfi daga irin ƙarfin da suke tsoro. Gaba ɗaya ma sai yaji ya sake raina wayonsu. Dan da da gaske, suna da ƙarfin ikon da suke faɗa, ba zasu zo su gaya min ba. Babu mai saƙon barazana da ikon cikakke sai wanda yake jin tsoron wanda aka aika wa saƙo. Yay ƙwafa, saboda wannan tunanin ya ƙara masa ƙarfin gwiwa, da fushi, da nunin ya sake tashi tsaye da shirye-shiryesa. Dole kuma ya aikama Imran saƙo batare da jinkiri ba...........✍️KIƊA A RUWA 2 26 ..........KWANA UKU da dawowar Mammah suka karɓi baƙuncin ƴan Bauchi da sukazo sunan Aunty Mommy. Gwaggo Khadijah, Gwaggo Alawiyya, da Gwaggo Nanah. Sai matar Uncle Jamilu da wannan ne karonta na farko da tazo. Dan tun abinda taima su Mammah ɗin a wancan shekarun take jin matsanancin kunyar zuwa inda suke. Sai dai har cikin ranta taji nadama. Musamman da ayanzu su Mammah ɗin ne riƙe da rayuwarsu tunda su Ja'afar ne suka buɗema Uncle Jamilu babban shago kayan sakawa a can Bauchin ƙyauta, da shi suke ci suke sha. Sannan kuma suka ɗauki nauyin karatun yaransu a makaranta mai ƙyau. Gwaggo Nanah kam ta fita zakka a cikin ƴaƴan Inna, tana iya ƙoƙarinta dama tun ma suna cikin wahalar rayuwa kamar yanda Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya keyi. Sai dai tsoron ƴan uwanta su Yaya Babba ke hanata zuwa inda su Mammah suke. Wannan karon kuwa itama sun mata halin nasu, dan mijinta ya gudu ba'a san inda yake ba shekara biyu kenan duk sun ƙi taimaka mata, ga wahala tana ciki ita da yara. Babu mai taimaka mata sai Uncle Jamilu da su Gwaggo Khadijah ɗin. Shiyyasa ta yanke shawarar zuwa sunan nan danta sanar ma Mammah halin da take ciki ko zata samu wani taimako. Kuɗin mota ma Uncle Jamilu ne ya biya mata. Ba ƙaramin daɗi Mammah taji da ganinsu ba. Musamman Gwaggo Nanah da matar Uncle Jamilu Badiyya da suketa ɗari-ɗari suna jinjina hukuncin UBANGIJI da ganin gidan da Mammah ke ciki a yau da zuri'arta. Lallai duniya budurwar wawa, wanda yace shine kuwa ba shi ɗin bane ba. Tuni Mammah ta saka su Kulu masu aiki suka gyaro musu ɗakunan baƙi, dan sunyi isowar wuri lokacin sha ɗaya na safe, sunce tafiyar asuba sukayi dan mota suka ɗakko kai tsaye. Mammah dake ta farin ciki ta ce, “Ku fara yin wanka da ruwa mai zafi sai kuzo ku karya. Bara kiga nasa a kakkaɓo min yaran nan duk suna gado jiya sun raba dare ne suna shargallen su”. Gwaggo Khadijah tai ƴar dariya da faɗin, “Aike da gayyar nan taki Maman Ma'aruff sai ALLAH. Kinga barsu suyi barcinsu, muda ba yau zamu koma ba. Anjima ma wata hidimar ce ta bikin suna a kansu”. “Kamar ko kin san harda fati suka shirya wai. Biebah ce kawai ta iya bin su Lailah gidan maijegon, yanzu babu jimawa suka fice suma dan jiya sai goma suka dawo”. Yanzu kam Gwaggo Alawiyya ce ta ce, “Kai waɗan nan yara ALLAH dai ya saka musu da alkairi. Wlhy samun surukai irinsu sai an tona Addah.” “Ai su Shariffa sun wuce surukai ƴaƴane Alawiyya. Babu abinda zan cigaba da musu sai addu'a da fatan suma ALLAH ya basu masu yi musu”. Gwaggo Nanah dake jinjina kai ta ce, “Wlhy ki musu ki ƙara muma muyi musu, ga gidan Yaya Babba can su Haire su da surukai ba arziƙi. Jiya matar Haƙilu kamar zatai dambe da Haire akan ɗanta, ke bakiji wannan tujara ba abin kaico”. Murmurshi Mammah tayi, saboda a saki zancen ta ce, “ALLAH ya ƙyauta to, ai zamanin ne ya zama abin tsoro sai addu'a kawai. Kunga kuyi wankan kuzo ku karya hirar tafi armashi”. Godiya suka yi ta juya ta fita. Dukan su suna jin ƙaunarta a ransu, Badiyya kam kunyarta take ji sosai shiyyasa tunda suka gaisa tai shiru kanta a ƙasa. Sarai Mammah ta fahimceta, dan haka ta ƙuduri aniyar cire mata abinda ke ranta gaba ɗaya, dan ita babban fatanta ta haɗe kan zuri'ar Abdul-rasheed ba rabuwar kansu ba.... ★ Sai sha biyu su Nimrah suka tashi da ƙyar, shima sai da Mammah tazo da kanta ta tashesu. Dan suna yin sallar asuba suka koma gado. Aiko sai shagwaɓa suke mata wai ta barsu sai ƙarfe ɗaya sannan. “Shike nan kun fasa zuwa gidan sunan kenan? Ai da nasan haka ne sai na tadaku kun wuce Tahafiz. Ga ƴan Bauchi can tun sha ɗaya suka iso ku kuna nan kuna barci”. Tuni duk suka watsakke, cike da farin cikin jin zuwan ƴan Bauchi. Zasu nufi ƙofa a guje Mammah ta dakatar da su. “Kai kuji min ƙazaman banza. Haka zakuje musu da kayan barci? Ba brush kamar wasu ƙazamai. Maza ku koma ku gyara jikinku, wata taje ɗakin Biebah yanda zakuyi sauri”. Cike da farin ciki sukace to. Mammah ta fito tana murmurshi. Koda ta dawo falon wajen su Gwaggo Alawiyya ta samu su Ma'aruff sun iso gidan. Dan tun ɗazun ta sanar musu sukace zasu zo yanzu. Sai ko gasu da ledoji niƙi-niƙi na kayan ciye-ciye. Fuskokinsu washe da murmushin ganin gwagwgwannin nasu. Badiyya na sinƙe-sinƙen kai ganin yanda suma basu nuna mata komai ba kamar Mammah sai ta ware aka fara gaisuwa da tambayar yara. Yaya Ja'afar ya ce, “Haba Gwaggo, kwa taho ku kaɗai duk babu yara? Bayan kun san ba ganin juna ake ba tsahon lokaci sai irin haka ta faru”. “Makaranta tasa haka Ja'afar, amma in sha ALLAHU idan anyi hutu sai su zo. Tunda kudai kun tattaramu kun watsar, yaushe rabonku da Bauchi balle Maiduguri?”. “Dama idan sunje Bauchin ba ganinsu muke ba Adda Khadijah, iyakarsu gidan Yaya Jamilu da Adda Alawiyya. Dan nidai sau biyu suka taɓa zuwa min lokacin rasuwar Inno surukata, da ciwon Ahmadi”. “Munyi laifi Gwaggo Nanah, amma kiyi haƙuri zamu gyara in sha ALLAHU. Wani lokacin abubuwan ne ke yawa. Mafi yawan lokuta kuma zuwa Bauchin kasuwa ke kaimu. Ki tambayi Aunty Badiyya sau da yawa shima Uncle Jamilu a kasuwa muke samunsa ba gida muke zuwa ba. Itama Gwaggo Alawiyya takan jima bata gammu ba. Maiduguri ne dai kam ma zamuce muna shiga dan ziyara kai tsaye”. “To na gamsu, amma dan ALLAH a gyara, mun san mu masu kuskurene a gareku, amma kuyi mana afuwa kunji, Yaya Abdul-rasheed mutum ne mai son zumunci da Adda A'isha da Adda Yakura, na tabbatar kuma akwai wanan jinin alkairin nasu a tare daku, kar ku biyema aikin son zuciyar wasunmu ku watsar damu gaba ɗaya. Suma lokaci zai yi da zasu yi nadamar abinda suka shuka. Dan har ma wasu sun fara, Yaya Babba a tsakanin nan babu abinda yake sai tafka asarori kala-kala, ga yara cike da gida, mata har huɗu. Yaya Haruna ne ma za'ace da ɗan sauran damshi-damshi. Shi ko Yaya Garzali ma yaje ya tare saudia aikatau ƙiri-ƙiri ko takan matan baya bi sai ya gadama.” Sosai zancen ya girgiza su. Sai dai basu ce komai ba face ALLAH ya ƙyauta. A haka Ammar ya shigo shima da Mu'azz. Nan fa falon ya sake lacamewa da farin ciki. Sai kuma gasu Nimrah na fitowa cikin kwalliya tsaff suna baza ƙamshin turaren da suka satarma Aunty Biebah na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Cike da farin ciki suka rungume Gwaggo Alawiyya da Gwaggo Khadijah dan su suka sani sukam. Abin birgewa bazaka taɓa cewa ba jininsu bane su. Sun gaida su Gwaggo Nanah suma. Suka amsa musu da kulawa duk da basu san alaƙarsu da gidan ba. Garama Fiddo ƴar Aunty Mommy data kwana a gidan itama, tunda sun jajje Bauchin ita. Gwaggo Khadijah ta ce, “Oh ni Dije Maman Ma'aruff ƴan matan nawa duk sun miƙe. Kaga yara kamar wasa sun ƙosa. A wannan sai aure”. Caraf Mu'azz ya ce, “Tab ɗin wazai kwasa Granny? Wannan gayyar ciwon kan da basu iya komai ba sai dambe da neman masifa da ƴaƴan mutane”. Baki duk suka tura gaba. Gwaggo Khadijah ta ce, “Kunga ƙyaleshi ƴan uku Ko nace ƴan huɗu dan banbu Bintu ne. Ai ana yin auren duk zaku daina ko. Kuma dai ai kowa da ƙuruciyarsa, shima idan za'a faɗi abinda yayi ai sai kowa ya gudu”. Dariya suka shiga yima Mu'azz suna masa gwalo, shiko yana hararsu da musu alamar zai kama su. Su Yaya Ma'aruff dai na murmurshi ne, Yaya Ammar kam dining ya nufa yana faɗin shifa yunwa yake ji, mi aka dafa ne?. Miƙewa su Nimrah sukai suma suna faɗin yunwar suke ji. Daga haka suka koma kan dinning ɗin harda su Mu'azz aka bar su Yaya Ja'afar suna hira da su Gwaggo Khadijah..... <<%>><<%>><<%>> Da yamma shagalin suna aka sha sosai a gidan Aunty Mimi, duk da kuwa haihuwa ce ta huɗu tayi. Babu ƙarya su Nimrah sun cashe da rawa iya iyawarsu. Kasancewar hall aka kama iyakar kuma mata ne kawai a wajen dan ko su Mu'azz basu shiga ba sai abin ya ƙayatar. Ƙarfe shida aka tashi saboda sallar magriba. Nan fa motoci suka fara ɗibar mutane zuwa gidajensu. Su Nimrah dai yau a gidan Aunty Mimi zasu kwana. Dan haka sukabi ƙanin mijinta da yazo kwasar yaranta dana family ɗin mijinta. Duk da dai da farko ca sukai su bazasu shiga cikin yaran ba, sai da Aunty Shariffa ta fara musu faɗa da tabbatar musu zako ta kaɗa kansu zuwa gida sannan suka nutsu saboda suna son zuwa can ɗin su ƙarasa weekend ɗin su. Ga Bintu kuma ta ƙaru sun zama su huɗu yanzu. Haneef dake matuƙar son Ruƙayya na sharewa yana faman murmushi yace su jira shi ya kai yaran ya dawo to. Feedo ce ta amsa masa da “To Uncle”. Su Ruky kam aka wani ɗauke kai gefe. Murmurshin shaƙiyanci Nimrah tayi, tare da ɗagama Bintu gira ɗaya cike da gulma. Aiko suka kwashe da dariya. Ruky da tasan da ita suke ta balla musu harara da jan tsaki zata bar wajen Nimrah ta riƙota........✍️ KIƊA A RUWA 2 27 .........“Sorry Trouble Buddy na. ALLAH ke ɗin ce kin cika wulaƙanci, Uncle Haneef fa ya haɗu ALLAH. Amma kiyita wani shan ƙamshi. Dan ALLAH ko kaɗan ki dinga kulashi mana, ALLAH idan ya ganki zakiga duk bakinsa yaƙi rufuwa”. “Ai shiyyasa bazan kulashin ba. Ni fa bana son susun namiji haba. Mutum babu wani jan aji. Kuma ni an faɗa masa za'a min aure ne yanzu mtsoww!!”. Bintu dake dariya ta ce, “Baby ai kece zaki saita shi yanda kike so. Amma kina wani yayyarfashi, jifa da salla yanda ya mana siyayya”. “Mayya dama ke ai kwaɗayi ne zai kashe ki ke da Ninah”. “Ya kashe mu dai, tunda tare muke”. Cewar Nimrah tana hararta. Ramawa tai itama, sai dai dai-dai nan Haneef ke dawowa dan haka hirar tasu ta tsaya. Fitowa yay da kansa ya buɗema Ruky gaba, zata zille ta shiga baya inda su Nimrah ke shirin shiga suka turata suna ƙumshe dariya. Juyawa Haneef yay ya kallesu da musu jinjina yana murmurshi. Daga haka ya rufe mata ƙofar ya zagaya dan suma har sun rufe. Yana fara tafiya a titi ya ɗan kalla Ruky, cike da son birgeta ya ce, “Muje shan Ice-cream ne Baby?”. Kai ta girgiza masa alamar a'a. Sai ya ɗan marairaice fuska, tare da maida lallonsa kan su Nimrah dake baya ta mirror. “Yaran Uncle muje mu sha ice-cream ne?”. Cike da iyayi Feedo ta ce, “Yes Uncle”. Nimrah zatai magana Bintu ta rufe mata baki, dan sun san bakinta ɗaya da Ruky. Ganin zata fisge itama Feedo ta ɗaura nata hannun akan na Bintu suka haɗu suka danne Nimrah. Sai da ta sakar musu wasu shegun mintsini masu zafi suka saketa kowanne na sosa wajen. Badan Nimrah da Ruky sun so ba akaje wajen shan wannan ice-cream dai. Haka ya jasu har ciki kowacce ta zaɓi flavor ɗin da take so. Ya ƙara musu da snaks. Duk yanda suka so ya maida su gida ƙi yay, haka ya janye ra'ayinsu suka zauna a wajen. Sai dai rashin sabo ya sasu kasa sakin jiki su dukansu. Dan abu ne da su dukansu ba tarbiyyarsu bace. Shi ko yanata tsiyaya musu zance da ɗaukarsu hoto da wayarsa iPhone. Ganin fa an fara sallar isha'i hankalin Nimrah ya tashi. Dan in har ka gansu a waje irin wannan lokacin tabbas da wani a cikin Uncles nasu ne ko Ya Mu'azz ko Aunty Biebah ko kuma sun raka su Aunty Lailah anguwa ko Ammie. Amma basu kaɗai ba balle wannan da saurayi ma wai. “Nimrah ya naga kin miƙe?”. Haneef ya faɗa yana kallonta. “Uncle Haneef kayi haƙuri ka maidamu gida. Wlhy idan Mammah taji zatai mana faɗa, balle Daddy ko su Uncle's”. “Haba-haba ai in sun san nine babu wani faɗa da zasuyi”. Miƙewa itama Ruky tayi, hakan yasa suma su Feedo duk suka miƙe. Kafin ma Nimrah ta bashi amsa Feedo ta ce, “Wlhy Uncle koni Abbana ya sani ubana zai ci. Muje ɗin kawai ma ƙarasa a gida”. Babu yanda ya iya dole ya miƙe, ya tayasu tattare kayan suka fito. Kamar ɗazu yanzu ma dole Ruky gaba ta shiga. Cikin ƙankanin lokaci ya iso gidan Aunty Mimi da su. Yay horn maigadi ya buɗe masa gate ya shige. Suna fitowa a motar maigadi ya iso inda suke. Kai tsaye gaban Nimrah ya isa yana miƙa mata ledar hannunsa da faɗin, “Hajiya gashi wani yace a baki. Yata jiran dawowar ku amma yaji shiru yanzu babu jimawa yabar wajen nan.” Ba ita ba hatta su Ruƙayya da mamaki suke kallonsa. Cikin kasa daurewa Nimrah tace, “Kuma ni Nimrah yace a bamawa?”. “Tabbas ke yace, yace sunansa Kamal malaminku na islamiyya”. Ruky ce ta amshi ledar tana faɗin, “Wato shima Sayyadi Kamal ɗin nan ɗan naci ne fa na lura”. Daga haka tabar wajen fuuu. Tsaff su Nimrah sun fahimci fushin Haneef tai amfani da shi akan Kamal. Dan haka suka wayance da masa godiya suka shige cikin gida. Sun sami sauran dangin mijin Aunty Mimi da basu kai ga wucewa ba. Suka gaishe su suka wuce ɗakin da suke sauka in har sunzo gidan. Dama can suka kai kayansu da daddare. Ƙaton gado ne da zai iya isarsu koda su shida ne a ɗakin, sai wadrobe da mirror, sai ƙofar bayi. Kayan hannunsu duk suka ajiye suna zubewa a gadon kowa na faɗin wash, dai-dai nan Ruky data rigasu shigowa ta fito daga bayin alamar har tayi alwysSuma duk miƙewa sukai, dan rashin yin sallar akan lokaci na tsaye a ran kowannensu. Bintu ce kawai ke period dan haka taja ledar snaks ɗinsu ta fara ci tana faɗin, “Bari muga mi Sayyadin ya aiko mana da shi shi kuma”. Tsaki Nimrah tayi a karo na farko tana shigewa bayi abinta. Fiddo ta sanya dariya dan Ruky ma harta kabbara salla. Dariyar su Bintu data cika ɗakin ya saka Nimrah fitowa da sauri, itama Ruky dai-dai tana idar da sallar ta juyo tana kallonsu. Litattafai ne a ledar saƙon Sayyidi Kamal suka nuna musu. Feedo ta ce, “Wannan fa shine auren ustaz ɗin, kaga wata lukutar jaraba wai saƙon littafai. Ninah kina cikin yanayi gaskiya”. Nan ma dariya suka sanya harda Ruky yanzu kam. Dan haka Nimrah ta watsa musu harara ta kabbar sallarta itama. Koda ta idar sun gama mata shaƙiyancin nasu, dan haka bata sake tada zancen ba ta haye gadon ta kwanta wai kanta ke ciwo. Da ƙyar suka lallaɓata ta zauna suka ƙarasa shan Ice-cream ɗinsu da snaks ɗin bayan Feedo ta idar da salla itama. Dan haka koda Aunty Mimi tai kiransu suzo su ɗeba abinci sukace mata sun ƙoshi. Bata takurasu ba dan taga abinda suka shigo da shi, ta kuma san aikin Haneef ne...... <<<<<<(⁠✷⁠‿⁠✷⁠)>>>>> ★CAMPAIGN★ Kwanaki 100 na campaign suna gab da cika, dan kuwa ana satin ƙarshe na kammala taron kowane kamfen. Dan haka amsa kuwwar cikar kwanakin tamburan siyasa na gab da cika, tako ina ƙasa ta kara hargitsewa dan kowa burinsa satin ƙarshen nan ya tumfayesa da zuciyar yan kasar. Baka iya jin komai sai sautinkan waƙoƙin da aka rairana ƴan siyasa. Yayinda hankalin matasa kacokan ya koma can. Wasu ma sun ajiye harkokinsu da sana'o'in su ne kacokam. Kamar dai yanda aka saba alƙawuran nasu guda huɗu ne ga al'ummar ƙasa a lokacin da suke kan munbarin campaign. Zamu gyara muku harkar karatun, zamu inganta wutar lantarki, zamu wadata ku da ruwa, zamu gyara asibitoci. Cikin rashin lissafi da auna abubuwa a yanda ya dace, da taro da kwabon da ake raba mana mu talakawan ƙasa da ɗan sabulai da zannuwan ɗaurawa mai hoton ƴan siyasar a jiki sai kaji mun sallama muna bada kai bori ya hau. Babu ruwanmu da tantance wane shugaban ya dace damu? Mi muke so a ƙasar da kawunanmu bayan waɗan can lissafin huɗu da ko a karatu sukazo ya kamata ace mun haddace su tsaff zuwa yanzu daga daɗin bakinsu mu nemo cigabansu. Amma ina babu batun tantancewa, a wasu wajajan ma siyasar ta haɗa rigima ne tsakanin ƴan uwan juna saboda ni ina son wannan wane ɗan uwana yana son wancan ba jam'iyyar mu ɗaya ba. Wasu har gaba zakaga ta ƙullu mai girma a tsakaninsu. Yayinda su ƴan siyasar da sukeyi domin su suna can tare suke shan shayi, tare suke ƙulla mai fishshesu musamman akan abinda zasu ribantu da shi game da kuɗaɗen da suka kashe wajen jawo ra'ayinku idan sun haye. Wanda ma bai haye ba akwai hanyoyin da za'a bi dan maida masa wahalarsa ta bayan fage kune a ruwa... Alhamdullahi duk da irin tasu tafiyar bata banbanta data Janar Yusuf ba a yau kasancewar a ƙarƙashin damarsu ya ke shima a siyasar kamar saura abinda shekarun baya suka zo da shi wajen campaign shima dai shine a yau yake zuwa da shi. Kuma Alhamdullah zamu ce akwai nasara a al'amarin dan yana da magoya baya sosai a cikin jam'iyya da al'ummar gari. Abinka da soja, a kwanakin kai-kawon duk da wahala da jigatar rashin barci dana hutu zuciyar maza a tsaye take da ƙyaƙyƙyawan fata. Tun ana farkon satin nan da sukai zama da Imran ya kuma gana da Uncle Nasiru basu sake haɗuwa ba. Dan a zahiri Imran baida alaƙa da siyasar Janar. Gara-gara ma Uncle Nasiru har campaign ya rakashi sau biyu. Duk wani abinda ya dace su tattauna sun kammala sun ajiye kundin shirinsu gefe har sai ta ALLAH ta kasance. Wato aci zaɓe ko a faɗi... Tsahon kwanaki sun cika cir, awanni 48 ya rage a fara jefa kuri'a, dan haka batun campaign komai ya lafa a koma jiran ranar jefa kuri'a da gwamnati ta riga ta fitar kuma kwanaki 2 ne kacal, dan yau alhamis.... ★_______★ ★RANA BATA ƘARYA Yau safiyar asabar. Safiyar zaɓen shugaban ƙasa. Duk wani masoyi na yan takara a kowane ɓangare jikinsa na'a farce ne. Ba yan takara kaɗai ba da zuri'ar su yan kasa kansu kowa hankalinsa nakan fata ga wanda yake so. Dan haka kasar ta wayi gari a yanayin sai addu'a kawai. Wasu cike da fata, wasu cike da tsoro duk da tako ina jami'an tsaro na aikinsu ne. A ka'ida daga shekara sha takwas ne za'a iya saɓe zuwa sama. Dan haka su Nimrah basa cikin masu jefa ƙuri'a. Amma ganin su Mu'azz zasu suka maƙale zasu je. Mammah kam Daddy Imran da kansa yazo ya ɗauketa ita da Hajjo ya kaisu suka jefa kuri'arsu da wuri sosai tare da Janar Yusuf Shu'aibu Tafida da iyalansa. Duk da dai ba kai tsaye Daddy Imran ya fito a tawagar janar din ba saboda bada ƙafa. Amma janar na jefawa da iyalansa suna a rukuni na biyu da suka jefa suma. Daga can Mammah tabi Hajjo suka wuce can gidan dan suma su Gwaggo Khadijah zasuje gaida Abba, amma su basuje jefa kuri'a ba daga gida za'a kaisu can tunda Mammah ce ta riƙesu tace sai an gama zaɓe zasu koma gida, kuma acan suke da mazaɓa.........✍️KIƊA A RUWA 2 28 ..........A ƙafa zuri'ar Mammah suka fita domin zuwa jefa kuri'a dan anan cikin street ɗinsu ne mazaɓar tasu take, dan babu wanda aka bari a gidan har su Afrah. Kasancewar anguwa ce ta ƴan gayu babu hayaniyar mutane, wasu ma duk sun koma state ɗinsu jefa kuri'a a can yasa anan ɗin babu yawan jama'a babu hayaniya balle damuwa. A nutse su Uncle Ma'aruff da su Aunty Shariffa suka jefa har zuwa kan Mu'azz karamin gidan. Kuma alhamdullahi dukansu Janar Yusuf suka dangwalawa. Suna kammalawa suka juya zuwa gida abinsu. Nimrah da Ruky ne a gaba, suna tafiya da baya-baya Mu'azz na musu video dan Nimrah harda Teddy ɗinta ta fito. Dan haka su Abees keta binta dan suna son taɓa teddyn magen. Daga ita har Ruky abaya ce a jikinsu, su duka sun musu ƙyau, tare da fidda tsayinsu masha ALLAH... ★WASHE GARI aka tashi da batun sakamakon zaɓe. Hankalin su Nimrah ba'anan yake ba. Bama kuma su fahimci miye damuwar ƴan gidan da batun sakamakon zaɓen ba da suketa bibiya tun jiya. Dan kamar wasa ranar ma a gaban television suka yini. Har kuma akai sallar magriba babu wani bayani, sai da aka dawo sallar isha'i suna cikin cin abinci aka sanar..... A wannan daren ba gidan Mammah kawai ba ake jiran jin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba, kusan ƙasar gaba ɗaya a kowanne gida hakan take, dan yau Daddy Imran salla kawai ke sakashi matsawa a gaban television amma ko abinci sai Anmie ta matsa masa ma yake cinsa, shima laumomi ne kawai. Ga Asma'u da Khalifa nane da shi suma. Zuciyarsa kam cike take da tsoro da fargaba. A wasu gidajen kuwa irin namu na talakawa an kunna fitilu ƴan uwa da abokai sun taru a gaban rediyoyi suna jiran murya ɗaya tak ta shugaban zaɓe, murya ce da zata faɗa musu ko tarihin ƙasar za’a sake rubutawa ko zai sake maimaita kansa ne da wanda ba zaɓinsu ba. ★★★ Ko'a gidan tsohon Janar Yusuf Tafida ya ɗauki wani irin shiru mai nauyi. Yana zaune a kan kujerarsa mai laushi, hannunsa riƙe da remote, television ɗin a kunne amma zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. Matarshi, Hajiya Zainab, tana zaune a gefensa, hakama kaf yaransa har mazan dake da mata na a falon zaune zagaye dasu kowa zuciya na rawa da addu’a, dan sun san yanda mahaifinsu ya ƙwallafa rai akan shugabancin nan yana buƙatar sanda za'a sanar da wa ya samu ace suna kusa da shi. Hakan zai bashi ƙarfin gwiwar amsa daga abinda ƙaddara zatazo da shi. Tunda shugaban zaɓe ya fara magana kusan a lokaci guda numfashin biliyoyin al'ammar ƙasar ya tsaya cak. _“A bisa sakamakon da aka tattara, ɗan takarar AGS Party, Honourable Yusuf Shu’aibu Tafida… ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.”_ “Ya arrahim!”. Hajiya Zainab ta faɗa tana mai fashewa da kukan farin ciki tare da miƙewa ta rungume Janar da ke kusa da ita kamar yayi sumar zaune. Sai da ta sake furta, “Alhamdulillah Daddyn Deen! Alhamdullahi!. ALLAH ya baka, ALLAH ya cika maka burinka, ALLAH ya baka wannan ne don ka gyara gaskiya!”. A hankali Janar ɗin ya lumshe ido, zuciyarsa cike da wani nauyi mai girman gaske, nauyin da yake jin tamkar ya ɗauka daga yanzu nan har zuwa shekaru da yawa. Lokacin da ya buɗe ido sai kawai ya zame yay sujida, ganin haka itama ta bishi, hakama yaran da gaba ɗaya suka kacame da ambaton Alhmdllh duk sai suka bisu.... ★★★ A gidan Mammah ma lokaci guda falon yay wani irin shiru na sakan, kafin su Yaya Ma'aruff su kacame da ambaton kalmar Alhamdullah. Sai da suka ga Mammah ta tafi sujida sannan suma duk suka bita har su Ruky. Mammah ta jima bata ɗago ba saboda hawayen da suke zubar mata. Koba komai tana ji a ranta nesa tazo kusa in sha ALLAHU. Sai da ta goge hawayen tas sannan ta ɗago tana murmurshi. Su dai su Yaya Ja'afar na mamakin yanda Mammah ke son janar ya samu kujerar nan, amma basu taɓa tambaya ba, yanzu ma kuma basu tambayar ba. Kawai suna ganin da Yaya Imran na son shi ne dai. Kuma Dada ma sanda yana nan yana girmama al'amarinsa matsayin ogansa...... <<%>><★><<%>> Shima dai a ɓangaren Daddy Imran tamkar Janar ana sanarwa yi yay tamkar ha suma a zaune. Duk ihun da Khalifa da Asma'u keyi baima jisu ba sai da Ammie data zuba masa ido tana murmushi ta kama hannunsa ta matsa a cikin nata. Wani nannauyan numfashi ya kawo hawaye na cika masa ido. Ya kalli Ammie dake lallonsa cikin ido tana murmushi, dan duk da bai taɓa fitowa ya sanar mata shirinsa tsakaninsa da Janar ba tana tsintar wasu abubuwan nasu ta waya idan suna yi. Yau kam ko kunyar yara baiji ba ya jawota jikinsa ya rungumeta, a haka cikin dabara ya share hawayen da suka cika masa ido. Kafin ya saketa ya tafi sujida shima. Sai suma duk suka bishi, yana ɗagowa yayma su Asma'u alamar suzo gareshi, suma su biyun ya haɗasu ya rungume dan auta barci yake. Sai da ya sake su suna masa congratulations yana gyaɗa musu kai da ɗaukar waya dan bakinsa ma ji yay ya masa nauyi. Kai tsaye layin janar ya kira duk da baida tabbacin samu, dan yasan a yanzu duk wani masoyinsa abinda yake ƙoƙarin yi kenan... Tabbas hasashen Daddy Imran akan Janar haka ne, dan wayoyine keta rige-rigen shigowa wayar sa a dai-dai wannan lokacin, sai dai ta yayansa kawai ya ɗaga sai ga ta Imran ma. Sunan da ya gani yasa zuciyarsa ta tsaya na ɗan daƙiƙai. (Imran....) Sai yaga sunan na koma masa bibbiyu tamkar haɗe da sunan Haysam. Sai da ya lumshe idanu ya sake buɗewa sannan ya ɗaga yana kaiwa kunnensa. Daga sallama abu na biyu da Daddy Imran ya furta shine, “Sir… mun yi nasara Alhamdullah. Subahanal-lah. Allahu-akbar. ALLAH ya tabbatar da alkairi, mulki jarabawa ce mai girma, ina roƙon UBANGIJI ya dubi tsarkin zuciyarka, da ƙyaƙyƙyawan fatanmu da ƙyaƙyƙyawan zaton da muke maka yay riƙo da hannayenka wajen baka damar sauke nauyin al'ummar wannan ƙasa gwargwadon iko. Duk wanda zai kasance da kai a cikin wannan sha'anin mulkin in har bazarana ne shi ga sauke hakkokin mutane koda wanene ALLAH ya tauyeshi ta inda zai rasa ƙarfin iya yin komai. UBANGIJI ya zama gatanka, bangon jinginarka, mafakarka, damu baki ɗaya. Once again, Congratulations, Sir.” “Thanks you Imran. Amin ya rabbi Jazakallahu khairan. Imran ka san wannan nasara ba tawa ba ce. Tawa da taka ce. Ta Haysam ce. Ta gaskiya ce.” Hawaye ne suka cika idanun Daddy Imran daga can, muryarsa na rawa ya ce, “Na gode, Sir… na gode da bama wannan YAƘIN daraja da kake yi.” “Yaƙin Haysam yaƙinmu ne ƙasa gaba ɗaya, wanda bai sani bane ko bai fahimta bane kawai keja da baya. Ka shirya, dan tun gobe idan ALLAH ya kaimu nake so ka fara haɗa min duk bayanan shari’ar Haysam tun daga farkon ranar da aka fara har ƙarshe. Ba zan shiga gidan gwamnati ba tare da na duba gaskiya ba. Lokaci ya yi da za mu dawo masa da mutuncinsa tare da namu muma Imran. Dan haka kwana ɗaya kawai zanyi da shiga gidan gwamnati Haysam ya fito in sha ALLAHU”. Daddy Imran ya gyaɗa kai, hawayen da yake ta riƙewa tun ɗazun na sauka masa. Muryarsa ta shaƙe a cikin maƙoshinsa dake kai-kawo da nauyin shekaru takwas na zafi ya furta, “Sir! Sai nake jin kamar ina mafarki ne irin wanda na sabayi. Dan ALLAH idan barci nake kada ku tada ni”. “Ba barci kake ba Imrana. Gaskiya bata da lokacin jira. Dole tun a yau mu tunawa kammu akwai wani mutum da ba zamu bari ya cigaba da kwana cikin duhu ba bayan ALLAH ya bamu wannan AMANAR, maza kaje, jeka ka fara shirin fitowar gwarzon haziƙin jarumin soja mai gaskiya da kwatanta gaskiya akan kowace gaskiya duk ƙarfinta.” “Thanks you Sir! Thanks yo...” Daddy Imran ya kasa ƙarasawa saboda yanayin da yake ciki misaltashi sai UBANGIJI. Ji yake tamkar zai faɗi sai da ma Ammie ta riƙeshi suka zauna ta miƙa mashi ruwa. Dama ta kora su Asma'u suje suci abincin dan kaf ɗinsu yau babu wani abincin kirki a cikinsu saboda uban gayya bai ci ba hankalinsa nakan television yini guda. Tambayar da Ammie ta jefa masa a karo na farko game da al'amarin yasa Daddy Imran kallonta cikin ido. Wani sassanyan murmushi ya sakar mata, batare da ya buɗe mata ba a dunƙule ya furta, “Akwai wani mutum guda dake bina bashi Hafsat, bashin adalci, bashin ƙauna, bashin zuminci. Kuma lokaci ya yi da zan biyashi koda da kwatantawa ne.” “ALLAH ya cika maka wannan buri Daddyn Khalifa”. “UBANGIJINA ya cika min sai dai tabbatarwa”. Ya faɗa cikin salon raɗa da rungumeta a jikinsa..... ============= ★PRISON★ A kwanakin farko na kawo television ɗin ɗakinsa bai maida hankali akan zaman kallonta ba, dan lissafinsa nakan haɗa kalaman vistor ɗinsa da musu fashin baƙi a farashin mutane masu hangen nesa da basu raina bincike irinsa. Abu uku kawai da aka turke tvn da ita ne ya fara tasirin jan hankalinsa gareta dole. Sun saka mata security ta yanda bata kasuwa, bai iya rage volum, bai canja tasha daga ukun nan kacal duk da kuwa akwai remote. Duk da basu sakata da ƙara mai takura ba kasancewar sa mutum mara san damuwa da hayaniya sai da ta fakurashi a kwanakin farkon. Sai daga baya daya fahimci an kawota ne garesa dan tai masa irin wannan takurar ai sai ya dake ya ajiye komai gefe har a kwana na huɗu ya maida hankali a kallon fashin baƙin masana akan taron campaign ɗin da aka rufe, a bazata yaci karo da na Janar Yusuf Shu'aibu Tafida ne a gaba. Duk da bawai akan Janar ɗin masu fashin baƙin ke tattaunawar ba, suna tattaunawa ne akan mabiyan ɗan takara, inda daga ƙarshe suke faɗin alƙaluma na sake nuna tsohon Janar dake gaba wajen tara masoya a duk jahar da yaje. Wannan shine karo na farko daya fara bama tvn hankalinsa, daga ranar kuma ya cigaba da bibiyar komai daki-daki, har hakan ya bashi damar fara tantance kowace fuska dake tare da Janar Yusuf dama sauran ƴan takara tun daga na shugaban ƙasa har zuwa shugabannin jihohi. A haka aka gangaro har ranar zaɓe, duk yanda abubuwan ke gudana nan ma yana biye, sai ta kai har ƙirga ƙuri'u ya bibiya. Sai dai a yau da aka tashi da jiran faɗar sakamako ya yini da ciwon kai saboda matsawa kansa da ayyukan ƙwaƙwalwa da yay a cikin satin nan gaba ɗaya. Dan haka bai wani maida hankali ba sosai ga television ɗin, bayan ma ya idar da sallar isha'i yay zaman fara karatun Alkur'ani ne, kasancewar tvn ba kasuwa take ba, ba rage ƙara take ba a bazata bayanin shigaban hukumar zaɓe ya shiga cikin kunnensa. Cak harshensa ya tsaya dai-dai da bugun zuciya na sakanni, kafin ya iya ɗago manyan idanunsa zuwa kan tvn ya saukesu akan fuskar ɗan jaridar dake maimaita kalmar.........✍️ KIƊA A RUWA 2 29 ..........“Wow! Congratulations, Her Excellency General Yusuf Tafida.” Dada bai motsa ba. Bai yi murmushi ba. Bai yi mamaki ba. Sai dai zuciyarsa ta furta abu guda ɗaya dai-dai da lumshewar idanunsa a hankali (Wata rana gaskiya za ta dawo da kanta. In dai har zuciya bata manta da UBANGIJI da masu gaskiyar ba) sai kuma a hankali ya ajiye Alkur'anin ya zame zuwa sujuda. Ya jima kafin ya ɗago ya sake ɗaga hannu yana ambaton, “Subahanal-lah! Allahu-akbar!”. Akan tausasan laɓɓansa Bai ce ya damu da samuwar shugabancin Janar Tafida domin ya fita anan ba, amma tabbas ya damu da addu'ar ƙasar nan tasamu mai kishin ƙasa kamar Janar da yakema ƙyaƙyƙyawan fata akowane motsinsa, ta samu shugaba mafi alkairi, yana ji kuma a ransa ogansa kuma yaya koma uba shine zaɓin ALLAHn da suke fata da roƙa in sha ALLAHU. Sake juyawa yay yana kallon tvn a karo na biyu, dan duk da sanarwar dare ce wasu wajajen har al'umma sun fara bikin murna, sauke numfashi mai nauyi yayi, zuciyarsa tana ƙonewa irin ƙonawar da MAZAN FAMA kawai ke iya fuskanta a lokacin da suke iya hango HASKEN MASU GASKIYA...... ÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ ★ONE WEEK LATER★ Sati guda kenan da bayyana sakamakon zaɓe. Janar da ubannin gidansa dama talakawan ƙasa da suka zaɓesa sun sha shagulgulan biki tako wane ɓangare. Idan ka cire sauran mabiya sauran jam'iyyu dake cikin takaici da baƙin cikin rashin samun nasara. Sai dai abinda mu talakawa da muke a wannan yanayin basu fahimta ba. Su waɗan can manyan da suke so tuni sun ƙulle da Janar ɗin anata farin cikin samun nasara. Sai a kafafen media ne kawai suke suka da nuna rashin jin daɗi. Duk da kuwa da yawansu har cikin zuciyarsu suna jin rashin daɗin, amma suna shanyewa saboda a hakan ma dai da ai dasu za'aci gwamnatin tunda dama duk tafiyar ɗaya ce a baɗini, a zahiri ne ake daban-daban. A lokacin da nan ake faman bidirin farin ciki ga sabon shugaban ƙasa janar Yusuf ba haka bane ba. Duk da bai kai ga tarewa a gidan Gwamnati ba aikin suke ta ƙarƙashin ƙasa shi da Daddy Imran da Haydar Galadima (Faro). Dan a yanzu haka a yau Janar Tafida ya gama ganawa da kwamitin miƙa mulki da sukai zaman meeting da tunda aka ci zaɓen nan shi suketa zamanyi saboda tsare-tsare musamman ƴan jam'iyya da kowa ke ganin lokacin fanshe wahalarsa tayi za'a bashi muƙamin da yake buƙata. Suna fitowa daga meeting ɗin aka ɗaukeshi zuwa gida. Tun ma kan ya ƙarasa shigewa falon sashensa ta baya kasancewar gidan bashi cike yake da dangi sati guda kenan ya ciro wayarsa a aljihu ya fara neman layin Daddy Imran. Bugu biyu Imran ya ɗaga, dan a lokacin shima suna tare da Faro ne a wani guesthouse ɗinsa da in har zasuyi magana akan Dada can suke zuwa. A nutse Daddy Imran yay sallama tare da gaishe da Janar. Daga nan ya amsa masa sai dai Daddy Imran baya jinsa sosai sakamakon matsalar rashin network da kowa ya sani ƙasar na fuskanta. Hakan ne yasa Janar ɗin faɗin, “Ka na ji Imran?”. “I’m here, Sir.” “Yauwa ina fatan kun kammala dukkan abinda muke buƙata?”. “Yes sir! Yanzu haka ma ina tare da Haydar anan guesthouse ɗina. Ga komai daya dace a hannunmu ko abu guda bana tunanin mun bari yayi saura. Hatta da sabbin bayanai akan Ojo Dabo ya zo da su a daren jiya, sune kawai nake ganin zanyi ƙoƙarin tabbatarwa dan nima akwai wasu a hannuna”. “Babu lokaci Imran, inaga ku ajiye sabbin bayanan Ojo yanzu a hannunku, muyi amfani da tsoffin dake wajenka zasu wadatar. Dan wannan aikin shine farko da nake son na gabatar a ƙarƙashin mulkina a ranar dana taka ƙafata a gidan gwamnati in sha ALLAHU washe gari sake nazarin shari’ar Haysam Abdul-rasheed Shehu zai tabbata. Babu wani aiki da zan gabatar na tabbatar da godiyata ga ALLAH sai in fara da wannan. Dan haka ku kasance cikin shiri kawai”. Daga can Daddy Imran ya runtse ido yana sakin wani wadataccen murmushi mai faɗi da armashi, dan yana jin kamar an buɗe wata ƙofa da ta rufe a zuciyarsa da ƙwaƙwalwa a shekaru takwas da suka gabata, ƙofar dawowa, ƙofar adalci, ƙofar fansa. Cike da wata irin muryar shauƙi ya furta, “Sir! Umarninka kawai muke jira a wannan gaɓar”. Murmushi mai faɗi shima Janar ya saki, tare da faɗin, “Imran… ka shirya abinda na tambaye ka?”. “Na shirya Ranka ya daɗe. Na dawo da kowace takarda, kowace sanarwa, kwafe-kwafen shari’a, rahotanni, bincike, duk wani abu na shekaru takwas ya kammala a cikin kundi guda ɗaya. Kundin da saka hannunka kawai yake buƙata da umarni yayewar baƙin labulen daya rufe min gani da jin Zak-Shadow. KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DODONNI.” “Good Imran. Lokaci ya yi da zan sa hannu wajen dawo da gaskiya. Lokaci yayi da The two shadows zasu sake bayyana a inuwa ɗaya. Amma…” ya ɗan yi shiru, sai kuma ya cigaba da faɗin “......ba za mu je tare da kararrawa ba.” Daddy Imran ya fahimta. Aikin da aka basu ba na kan titi ba ne. Yana cikin inuwa, cikin sirri kamar yadda azzalumai ke yin wasan su. Tamkar yana a gaban Janar ya ƙame jikinsa waje guda irin aƙidar sojoji da girmamawarsu, sannan ya sara masa da Salute na girmamawa mai harsuna da yawa har Janar na iya jin ƙarar bugawar ƙafafunsu shi da Faro da shima ya miƙe ya ƙame. A tare suka furta, “Yes, Sir. I'll handle it quietly”. Daga can shima Salute ɗinsu Janar yayi yana wani shegen murmushi mai matuƙar bayyana tsantsar makamancin farin cikin da yake a cikin zuciyarsa. Daga haka ya yanke wayar. Ba ajiyeta yayi ba, sake lalubo wata number yayi. Lambobi ne da ba kowa ke da su ba, lambobin da suka tsaya tsayin shekaru biyu babu wanda ya kira shi da su. Badan bai isa ba, sai dan shiri irin na masu makirci dake da dama a hannu. Sai dai yau shi zai kira, kiran da dole a ɗauka masa kuma a risina masa, dan wannan kiran ya zama dole ga masu amsawar.. A bazata kiran tsohon Janar ya shiga wayar babban hafsan tsaro da zai hau aiki tare da shi a sabuwar gwamnatinsa. Kiran daya saka General a ƙaulani, firgici, ruɗani duk da bai san takamaiman dalilin sa ba. Amma shi ya san jiya ba yau bace, ko giyar waye yasha bai isa hana kansa amsa wannan kiran ba a yanzu. Cike da rawar jiki kuwa ya amsa, cike da girmamawa da risinawa da ƙanƙan da murya ya fara gaishe da tsohon Janar ogansa a gun aiki, sabon shugaban kasar sa mai jiran gado kuma a yanzu. Janar Yusuf Shu'aibu Tafida yay wani murmushi mai ma'anoni da yawa yana mai jinjina kai. Lallai ƙasa ta lalace, lalacewar da mutane sun koma girmama kujerun iko sama da girman daraja da kimar ɗan adamtaka da UBANGIJI yayi ma bayinsa. Bai ja tunaninsa da nisa ba ya fara magana ba daɗi, ba sirri mai nauyi, amma da umarni. “Ina bukatar sashin ku ya fara nazarin batun jami’in SOJA da aka jefa cikin gidan maza shekaru takwas da suka wuce. Ba tare da hayaniya ba.” Cikin matuƙar bugawar zuciya Genaral ya furta, “Sir! Zak-Shadow?”. “Eh. Na san akwai ɗan hazo. Ina so ku share min hanyar ganin shi cikin sirri kafin na shiga ofis.” Yawu mai matuƙar kauri Genaral ya haɗiya jininsa na tsitstsinkewa, a take zufa ta jiƙe jikinsa sharaf. Ya kasa magana har sai da Janar Yusuf yay gyaran murya irin ta manyan da umarni kawai suke badawa sau ɗaya tak. Kamar wanda aka farkar a suma General ya amsa da sauri har harshensa na sarƙewa. “Za’a yi, Ranka ya daɗe. Amma wannan… zai bugi wasu mutane.” “Ai dama so nake ya buge sun da bulala mai zafi da dafi. Dan lokaci yayi da zasu ji su kuma sani. Gaskiya ba ta tsorata da MAKIRCI ko ƘARFIN IKO. Gaskiya ce take tsoron TUGGU koda MAKIRCI yayi nasarar ƁOYETA.” General ya kaɗa kai kamar tsohon ƙadangare dan ya kasa magana ma. Sai sake wanke masa jiki zufa take dan tabbas a wannan gaɓar yana a tsaka mai wuya ne..... <<%>>★<<%>> PRISON *8:30pm* aka samu baƙuncin jami’an tsaro na musamman, dole a kirasu jami'an dana musamman, domin ko sun iso ba tare da hayaniya ba balle yanayin rububi. A nutsensu suke cikin Uniform. Kai tsaye kuma sun nema ganin shugaban prison ɗin ne ta hanyar bama securitys ɗin dake kula da shiga da fitar kowa takarda. KIƊA A RUWA 2 30 .........Isowarsu ɓangaren da Dada yake ya tabbatar min da lallai ba wannan jami'an bane ainahin vistors ɗin, dan a ƙofar wajen suka samu wanda akaima rakkiyar. Bayan sun ƙame tare da salute ɗinsa ɗaya ya matsa yana sanar da ogan nasu cikin magana ƙasa-ƙasa. Kansa kawai ya jinjina batare da yin magana ba, kuma ba'a ganin fuskarsa dan ya saka norse mask ga eyeglass, sannan kansa da hula p-cap data sake ɓoye ainahinsa. Yana sanye cikin ƙananun kaya daga sama har ƙasa baƙaƙe. Har cikin ainahin ɗakin ganawar securitys ɗin sukai masa rakkiya, dan shi kaɗai ya shiga banda jami'an sa. Koda suka nuna masa kujerar zama bai zauna ba, yana daga tsaye kawai a cikin dakin yana jiran shigowar wanda zuciyarsa ke bugawa saboda tsoron abin da zai gani, tsawon shekaru biyar har da wattani huɗu a kai bai ga Zak-Shadow koda daga nesa ba. Mintina kaɗan da suka kasance masu nauyi na cika wanda yake begen gani da ƙagauta ya iso. Cak numfashinsa yaso tsayawa sakamakon bayyanar mazan fama, sosai ya rame fiye da wancan ganin da yay masa na shekarun baya. Duk da lokaci-lokaci ana masa aski hakan bai hana gashin saje taruwa a farar fuskarsa ba da kansa. Fata kam tayi haske da kwanciya saboda zaman waje guda. Sai dai baza'ace akwai laushi na jin daɗi ba. Yanda yake kallonsa haka shima Dada ke kallon nasa, dan duk da ya rufe fuska a kallo ɗaya ya gane wanene, dan ko cikin rububi manta wannan halittar ta gabansa sai dai ɗimuwa a lokacin magagin mutuwa amma ba a cikin hayyaci ba. A karo na farko baƙon ya ɗan murmusa da ƙoƙarin danne abinda ke yunƙuro masa. Sai kuma ya kai hannu a hankali ya zare glasses ɗin idanunsa. A tare idanuwa nasu suka haɗu a cikin na juna. Imran ya kasa motsi. Haka shima Dadan bai motsa ba, dan kai tsaye zuciyarsa yake kallo a zahiri. Fin sakan talatin suna a haka kafin Dada ya saki wani ɗan murmushi da lumshe idanu ya buɗesu a lokaci guda, a hankali ya cigaba da takowa har inda Imran yake. Har yanzu nutsatstsiyar fuskar nan tasa da murmushin nan nashi na ƙasaita, ya motsa lips kamar mai son raɗa ya furta, “Ranka ya daɗe, soja… har yanzu baka daina kuka da ido ba?”. Kauda kai Daddy Imran yayi yana haɗiye hawayen da basu ƙaraso cikin idanunsa ba, amma da yake Zak-Shadow ɗin nasa Zak-Shadow ne shi har ya karantosu daga ƙirjinsa. Wata ƴar ƙaramar dariya Dada ya saki da kaiwa zaune, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya hannayensa da yau babu handcuffs harɗe a ƙirjinsa ya sake faɗin, “Sit mana my Boss”. Yanzu kam shima murmushi Daddy Imran yayi, sai kuma ya gyara kujera ya zauna irin zaman Dadan suna kallon juna tamkar wani saurayi da budurwa. “Na yi missing naka sosai, Zak...” kalma mafi nauyi da girma dake riƙe da zuciyar Imran ta fito daga bakinsa. Sai kuma hawaye suka cika masa idanu. “Idan ka cigaba da wannan kukan, how many missions za ka gama?. Kalleni da ƙyau ina raye, kuma ina cikin ƙoshin lafiya mi kake buƙata bayan hakan daga UBANGIJI? Ko sai na tashi mun gwada ƙarfi ne?”. Dariya sosai Daddy Imran keyi cikin hawaye, dan ya fahimci yau raha Zak.. ɗinsa ke ji. Kai tsaye ya ce, “Kai dai ba zaka canza ba.” “Zama da kai ne Imran, kwana biyu sai nake jin matsanancin kewar ka. Ashe kana gab da ni ne shiyyasa.” “Duk randa muka zama a nesa da juna lallai ƙasa ta bizne idanun wani a cikinmu ne ko mu duka. Sai dai ni nafi fatan fara tafiya na barka dan nasan bazan iya ɗauka ba idan kai ne ka barni”. Idanu sosai Dada ya zuba masa. Dan haka shiru ya biyo baya, irin shirun nan mai cike da abubuwan da bazasu faɗu ba. Tsohon lokaci kafin Daddy Imran ya katse yanayin nasu ta hanyar miƙa masa briefcase daya shigo da ita. “New President Yusuf Tafida… ya buƙaci nazarin shari’arka tun daga farko har ƙarshe. Sai dai ba yau za mu faɗi komai ba. Amma daga yau ɗin game ya fara dawowa.” Cak numfashin Dada ya tsaya ba ƴan sakanni, ya kuma zuba ma Imran ido tamkar zai haɗiyo shi da su, “Sabon shugaban ƙasa, zai iya zama yana da alaƙar huɗɗa da waɗanda suka karyar da ni fa Imran, sai dai maybe shima bai sani ba.” “Miyasa kai wannan tunanin? Dama ce fa tazo mana daga UBANGIJI. Kafa san wanene Janar”. “Tabbas nasan Janar, sani na nagarta da mazantaka. Ba kuma bana farin ciki da damar bane, ina ganin kamar yazo da gaggawa ne, gaggawar da zasu iya kaishi ƙasa da ita a kaina, dan yazo musu da bazatar abinda ba shi suke hasashe ba a kansa. Dole ya zama mai zaɓi biyu a lokacin da ya bayyana musu ainahin fuskarsa a kaina. Saboda a tsarinsu babu wani shugaban ƙasa da zai kasance baya abota da su. Koda sun ɓoye masa waccan fuskar tasu a yanzu inada tabbacin zasu bayyana masa ita ya sansu ya san aikinsu. Matsalar kuma idan har yana son gaskiya, to sai ya tabbatar min da hakan da aikin shi. Ba da kalamai ba. Dan kar ya kasance na amince na fita ya zama yana cikinsu bazan ƙyalesa ba koda shine Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi”. Daddy Imran ya fahimci hangen Dada, dan haka ya sauke numfashi mai nauyi yana jinjina kansa da faɗin, “Haysam na yarda da ku kai da Janar da Faro. In sha ALLAHU Janar bazai bamu kunya ba, yanda muka fara da shi zamu ƙare a tare koda sai bayan babu ran mu ne NASARA zata bayyana. Na tabbatar shima kamar mu ya ke, idan gaskiya tana gona, zai haƙo ƙasa ya nemota da kansa.” Dada yayi murmushin mai zafi fiye da bala’in da yake hangowa da ƙurar da zata tashi. “Shike nan Imran! ka gaya masa, idan yana neman gaskiya, kada ya zo da haske. Duk wanda yake neman ƙasar nan, sai dai ya biyo duhun dare. Ni zan fara jiranku daga yau. Ku dinga tuna kuma zan dawo da gudunmawata. Game on.... again.” yay furucin ƙarshe da wani salo yana kashema Imran ido ɗaya da yin alamar harba bindiga da yatsu biyu. Dariya Imran ya kece da ita, irin dariyar da shi kansa yasan ya jima baiyi ta ba. Kai koda kwatance baya kawota a zuciyarsa balle ma fuskarsa. Shima Dadan kallonsa yake yana wani shegen murmushi mai bayyana haƙwara, kai daka gansu kasan ƙara'in farin ciki ne na tsahon shekaru ke fidda kansa tun daga ƙasan zuciya har zuwa fuskokinsu. Sai dai Imran yasan minene ma'anar murmushi irin wannan a fuskar Zak-Shadow ɗinsa. Ya tabbatar zafin daya jure cikin wannan duhu na tsawon shekaru takwas da wata huɗu, sakamakon wannan murmushin idan ya fito ƙasa za ta sake girgiza...... <%><%><%><%> “Malam Almu maganar ciwo ai ta wuce wasa, kuma ta kori komai a rayuwa. Dan haka babu batun neman alfarma zuwa gida daga garemu. Ka shirya kawai abinka ga kuɗin mota. Wannan kuma sai kai amfani da shi wajen kaita asibiti, ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne. Zaka wuce yau ne ko sai zuwa gobe? Dan muma zamuje airport ne ɗaukar Bilal yau zai dawo”. “Kai kai Masha ALLAH. Yau Alhaji Bilal zai dawo ashe? To bari na jira ya dawo tukkuna ai kamar zai fi”. Kai tsaye Mammah dake saurarensu ta ce “A'a Malama Almu ban goya bayan haka ba, kaje dai tunda zaka dawo ai. Itama Innarka na buƙatar ka, kuma tana buƙatar a kaita asibiti. Ina ga ma idan kaga jikin babu daɗi sosai kawai ka ɗakkota zuwa goben ku taho nan a kaita asibiti zai fi”. Godiya maigadi yake jerama Mammah dasu Yaya Ja'afar har hawaye na cika masa idanu. Yana tausayi da mamakin alkairan bayin ALLAHn nan, shiyyasa a lokuta da dama idan ya tuna dalilinsa na zaman gidan nan tare da su sai yaji zuciyarsa na karaya akan ƙudirinsa. Haka ya miƙe yana shartar hawayen da shi kaɗai yasan dalilinsu ya fita... A gurguje maigadi ya shirya tare da damƙa gate a hannun sabon driver kamar yanda su Ja'afar suka ce masa. Ya wuce ya tafi yana ayyana wa a ransa ai bazai wuce jibi ba, idan har zuwa kwana uku bai dawo ba to bazai wuce safiyar kwana na huɗu ba in sha ALLAHU. Dan babu wani ciwo da Innarsa keyi kamar yanda ya faɗa, ogansa ne ya bashi umarnin zuwa ya sameshi da gaggawa a yau. Saboda shi Innarsa ma ta jima da rasuwa, a hannun kishiyar uwa ya tashi, azabar data bashi da wahala ta maida shi yanda yake a yau, sai dai a gidan Mammah sanin mutum cikakke sukai masa mai nagarta sakamakon ɓoye ainahin wanene shi da yayi a garesu.... Tofa, wata sabuwa maigadi🤔🤐🏃🏼‍♀️. ÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ ★DUBAI★ Duk yanda su Hajiya Hasiba suka so tafiya India bincike akan Adeel bai yiwu ba. Dan kuwa randa ta samesa da dabarun zuwa India business a ranar yace mata ya kammala shirin tafiyarsu. Ta jira har su dawo sai taje. Kota sanar masa business ɗin da kamfanin da zasuyi koma miye a kawo mata shi. Jin haka yasa ta saurin cewa ba damuwa suje ɗin kawai su dawo tayi nata uzirin daga bayan. Shirin nashi bai bata tsoro ba sai da ya tabbatar mata harda su Nabeeha za'a. Ta tambayesa ba'asi yace hankalinsa zaifi kwanciya idan tana acan tare da shi. Dan karma ya barta anan wani abu ya faru. Duk da kuwa yana da ƙarfin ikon sakawa a bibiyar masa ita duk inda ta shiga a cikin ƙasar. Amma baya buƙatar hakan, dan bayan abokinsa ɗaya jal babu wanda yasan yana bibiya ko son auren Nabeeha. Abinka da sai yanda akai da kai, dole suka hau shirin tahowa. Sai dai ran Nabeeha da Ismat fal farin ciki. Hakama Mamawo, dan koba komai itama akwai nata shirin data barma tata zuciyar game da Adeel ɗin, tana ganin kuma zuwansu ƙasar tasu ce zai iya cika cikin sauƙi saɓanin anan da wasu dalilai zasu iya hanata. Amima da Raihana ko basu so wannan tafiya ba. Dan harga ALLAH su daɗin zaman Dubai suke ji, har basa son tuna zuwa ƙasar haihuwarsu. Shiyyasa ma suke matuƙar jin haushin Nabeeha da taƙi bada haɗin kai bori ya hau. Dan wlhy da a cikinsu Adeel ya nuna yana son wata hohoho da wani labarin ake ba wannan ba ma..........✍️ 31 ........Sun iso cikin dare. Kasancewar a babban birnin suka sauka yay bucking hamshaƙin hotel na gani na faɗa da yafi kowane hotel tsari da ƙayatarwa. Su kuwa gidan Hajiya Hasiba suka sauka. Dan tun a can ya nuna musu baya son asan tafiyarsu ɗaya da shi har ya kammala aikin nasa su koma.             Ba laifi gidan babba ne sai dai ba ƙato ba. Six bedrooms ne. Sai faluka guda uku. Akwai na baƙi da bedroom ɗaya, sai falon ƙasa shima da bedrooms 2, sai upstairs da falo da 3 bedrooms shi kuma. Akwai kitchen a ƙasa. Sai can gate akwai ɗakin maigadi. Shi kaɗaine kuma a gidan da matarsa da yaransu biyu. Kasancewar idan suna nan itace ke musu aiki. Dan haka tun suna can ta sanarma maigadin zuwansu. Haka matar ta yini yau tana ƙalƙale gidan, da yamma mai musu abinci tazo tai musu, sai da ta shirya komai a dinning sannan ta wuce dan dama ba'a nan take kwana ba.        Tun kan Hajiya Hasiba ta shiga siyasa tana da kuɗi, dan kuwa tako wace hanya nemansu akeyi. Alaƙarta da manyan ƙasar musamman first lady ya sake armasa dukiyarta da sanin manyan mutane da ake harkokin da basai ance komai ba (🥱🤭🤫), ko wannan gidan ƙyautarsa aka bata sukutum kamar juye alalar gwangwani a plate 🥱🤣. A yanzu kuma ga Adeel ya ida jiƙeta.          Duk da ba wata gajiya ce a tare da su ba kowa sai wayyo-wayyo yake yi. Duk suka zube a falon ƙasa suna sauke numfashi, maigadi da matarsa nata kai-kawon shiga musu da kaya da jera musu sannu. Da ƙyar suka iya tashi bayan wani lokaci suka haye sama su duka. Dan duk can suke da ɗakunan barci har Mamawo ɗin ma daba wani zama take sosai a ƙasar ba. Wanka suka fara gabatarwa sannan suka nema abinci. Suna kammala ci kowa ya nema makwanci. Basu tashi farkawa ba a washe garin ma sai ƙarfe kusan sha biyu. Haka sukai wanka suka sakko ƙasa neman abinci. Sunko samu Joy ta kammala komai har na rana, aiko suka far masa da ci sai da kowa yay ƙat.       Wajen ƙarfe uku Nabeeha tace tana son zuwa gidanta ɗakko wani abu. Aiko daga Mamawo har Momyn tasu suka hayayyaƙo mata da masifa. Da farko shiru tai musu, sai daga baya ta saka musu kuka. Jikinsu ne kuma yay sanyi, dan haka Momyn tata tace ta shirya amma su Ismat ne zasu rakata su dawo tare, amma yau yamma tayi ta bari sai gobe. Bata musa ba tace ta yarda....... <<%>><<%>><<%>>            Kamar kullum yau ma a dai-dai lokacin da aka saba tashinsu islamiyya aka tashe su. Kasancewar Yaya Mu'azz ne ya kawosu sun tabbatar bazai zauna zaman jiransu ba kamar driver har zuwa yanzu. Sai dai zai dawo ya ɗauke su. Su duka zukatansu cike suke da zumuɗin komawa gida saboda Uncle Bilal, dan ba ƙaramar kewarsa sukai a watannin nan da baya nan ba. Sune farko fitowa a aji, ajin nasu kuwa daga shi sai na ƴan sauka, duk da suma dai gab suke da kaiwa sittin ɗin in sha ALLAHU.      Hayaniyar dake tashi a ajin ƴan saukar ne ya daki kunnuwan su Nimrah da suka fara fitowa, kallon juna sukai ita da Ruky, sai kuma suka nufi ajin da sauri dan ganewa idanunsu abinda ke faruwa. Gaba ɗaya ajin ya hargitse da ɗaliban ƴammata da samarin cikinsa, dan kuwa sun girmi su Nimrah su zasu iya kaiwa sha bakwai ne. Yanda suka dunƙule waje guda suna jefe-jefen takalmansu yasa Nimrah data kutso kai cikinsu kallon abinda suke jifar. Abin takaici abin mamaki ba komai bane sai mage. Wata baƙar mage ce da jariran ƴaƴanta biyu, ɗaya fari tas ɗaya baƙi da kwalliyar golden a jikinsa. Mai kwalliyar golden ɗin na kwance kansa da jini alamar wani ne ya jefesa, farin kuwa ya maƙale jikin uwar da itama har an jimata ciwo sai wani irin nishin kuka take. Ai bama tasan ta zabura inda magen take ba jikinta na rawa.        Ihu ƴan ajin suka fara mata da kiran karta je ba mage bace aljana ce ko wata mayyar ta rikiɗa tunda ance mayu na zama mage, amma kota kansu batabi ba ta ƙarasa. Hannu ta saka ta ɗauki magen ta rungume, tare da ɗaukar farar itama dake jaririya abin sha'awa, tana kai hannu zata taɓa golden ɗin dake kwance a ƙasa kawai cikin ƴan ajin wani ya wulwulo dutsina har biyu. Ai ko ɗayan ya sauka akan magen babba ɗaya akan Nimrah. Juyowa Imam yay yana hararar Ruky da tai maganar. Kafin yace wani abu cikin sake lanjarewa Nimrah ta ce, “Dan ALLAH Yaya. ALLAH su Afry ma naso ko?”. Ta juya tana kallon su Aheel. Magiya suma suka fara. Sai lokacin Mu'azz daya ɗan juyo ya hararesu ya sake maida kansa ga titi sannan yay magana. “Ku yaran nan kun cika nemarwa mutane hanyar kashe kuɗi. Ga asarar salla a jam'i da kuka jawo mana. Wai kun manta yau Uncle Bilal zai dawo ne”     Su dai basu kula faɗansa ba suka cigaba da maguyarsu duk da ransu cike yake da farin cikin batun dawowar Uncle Bilal da zaiyi a daren nan. Sai da yay ƙwafa sannan ya rage gudun motar. Canja hanya yay zuwa inda yasan ana saya musu ice-cream ɗin da suke so. Basu wani jima ba suka iso. Har zasu fito ya hararesu yana faɗin, “Ina zaku bimu da uniform a jiki ace satoku mukayi, ke kuma ga rauni a kai”.       “Abinda ba'a ganin ciwon na rufe da hijjab. Dan ALLAH ka barmu muje”. Nimrah ce mai maganar cikin tura baki. Mu'azz zai ƙara magana Imam ya ce, “Barsu dan ALLAH Bro. Muje, muna sake tauye lokacin salla ne kawai a wannan surutun”.     Ba yanda Mu'azz ya iya yayi gaba suka bishi, Ruky harda masa gwalo. Su Imam na gaba riƙe da hannayen su Abees, su kuma suna biye da su, suna gab da shigewa Ruky ta riƙe hannun Nimrah ta tsayar da ita, batare da tayi magana ba takai hannu tana gyara mata hijjab ɗinta ganin bandage ɗin kanta ya fito. Hakan yasa suka rigasu shigewa. Dai-dai suma suna ƙoƙarin shigewa suna gulmar su Mu'azz ɗin ƙasa-ƙasa suka kusa cin karo da mutanen dake ƙoƙarin fitowa. Da sauri Ruky tai baya tana jan hannun Nimrah, sai dai cikin rashin sa'a ta tafi zata faɗi, a cikin waɗan can ɗin ɗaya yakai hannu zai riƙota.      Cike da tsiwa ta ce, “Malam miye haka, karka taɓani”.      Duk da da hausa tayi, bai ji mita faɗa ɗin ba saboda ba yarensa bane yanda sautin muryarta mai cike da tsiwa ta daki kunnensa sai ya tsaya cak, tare da ɗago manyan idanunsa ya kalleta. Sai akai sa'a kuwa dai-dai itama ta balla masa harara...........✍️ 32 .........Ba ƙaramin motsawa zuciyar Adeel tayi ba, batare da ya shirya ba ya saki murmurshi mai faɗi yana ƙare mata kallo. Sake balla masa harara Nimrah tayi tana bin Ruky dake jan hannunta sukai ciki.         Yako lumshe idanu ya sake buɗewa a kansu. Zai iya rantsuwa tunda yake bai taɓa ganin baƙar fatar data gama tafiya da duniyarsa lokaci guda irin yarinyar nan ba. Gata dai ba wata ƙatuwar budurwa ba, hasalima a ƙasarsu bata wuce babyn raino ba, amma tayi masifar tafiya da dukkan zuciyarsa. Abin mamaki kuma ba irin son da yake jin yanama matan baya bane na sha'awa, wannan wani baƙon al'amari ne mai girman gaske a gareshi da ban mamaki...        “Oga ya dai?”.    Wanda suke tare ya faɗa yana taɓa shi. Juyowa yay ya kallesa, sai kuma ya ɗan sake murmusawa da faɗin, “Mi ta faɗa ɗazun?”.       Murmurshi wacan ɗin yayi, duk da bai san wanene Adeel ba a matsayi na rayuwa balle ma ƙasar da ya fito. Dan kuwa daga hotel ɗin daya sauka ne ya buƙaci ɗan rakiya zaga gari shine aka bashi ma'aikacinsu ɗaya da mota, har sun wuce wajen nan ya ɗauki hankalinsa yace su shigo dan ya ga harda kilishi ake saidawa. Cikin harshen turanci ya sanar masa abinda Nimrah ta faɗa. Kawai sai ya sanya dariya. A ransa yana raya (Wato ita tana jinta wata mace ce karna taɓa ta). A zahiri kam waje ya ƙarasa fita, sai dai ya tsaya a jikin motar su ne ya zubama hanyar shiga da fitar idanunsa....        Babu jimawa kuwa su Nimrah suka fito su Mu'azz biye da su. A gaban idanunsu duk suka shiga mota, sai da yaga Imam daya amsa tuƙin yanzu ya tada mota sannan shima ya shiga tasu yana faɗama abokin tafiyar tasa su bisu. Bai kuwa musa ba tunda aikin kuɗi yake. Haka ya dinga binsu a baya ta yanda bazasu gane ba har gida. Daga can ɗan nesa kaɗan suka dakata, har motar ta shige aka maida gate ɗin aka rufe.         Kai tsaye Adeel ya ce, “Ya sunan Street ɗin? Sannan kasan gidan waye?”.      Kai ma'aikacin hotel ɗin ya girgiza masa da faɗin, “Ban san gidan waye ba gaskiya. Amma sunan nan ɗin KOBI STREET.”      Sunan Kobi Street ɗin ya maimaita da karyayyen harshensa, kafin yace, “Okay zaka iya sake kawoni gobe?”.        “In sha ALLAHU Sir!”.      Fuskarsa da murmushi yace, “Muje inda zan samu layin ƙasar nan da waya”.      “Okay Sir”.    Daga haka suka bar wajen.  ____       A cikin gida kuwa tunda su Nimrah suka fito a mota sabon driver malam Buba dake tsare da gate a yau ya zuba mata ido. Duk yanda yaso daurewa sai ya kasa, sai da ya iso inda suke yana tambayar lafiya kuwa yaga bandeji a goshin Nimrah ɗin. Imam ne ya bashi amsa a taƙaice da cewar “Ciwo taji a islamiyya”. Itako da tunda tai masa kallo ɗaya tsigar jikin nata ta fara tashi ta kauda kanta. A taƙaice ta gaisheshi kamar kowa sukai gaba ita da Ruky. Haka ya bisu da kallo yana jin kamar ya bisu ciki. Sai dai ya danne zuciyarsa da ƙar, amma can ƙasan rai ayyanawa yake (Lokaci yayi da zai fitoma Nimrah ɗin a mutum tasan shi ɗin waye).      A ciki ma hankalin Mammah da su Aunty Shariffa ba ƙaramin tashi yayi ba. Dan su Yaya Ja'afar sun tafi Airport ɗaukar Yaya Bilal dake gab da sauka, tuni sun cire mata hijjab suna duba wajen. Sai ita ke magana cikin shagwaɓa da son kwantar musu da hankali tana faɗin, “Babu fa zafi. Tunda aka min allura ya daina ciwo”.       Faɗa Aunty Biebah ta fara akan cewa bazasu yarda ba, gobe sai taje islamiyyar da kanta dole yaron nan a hukunta shi. Sai da Mammah tai maganar “Baza'a kai ga nan ba. Tunda ance kuskure ne to a barshi a hakan ALLAH ya kiyaye gaba.”     Badan sun so ba suka haƙuran. Amma Mu'azz dama ya ayyana a ransa sai yaci uban yaron tunda shima islamiyyar yay sauka, yanzu kuma weekend kawai suke zuwa Tahafiz shi da Aunty Biebahn. Ɗaki suka wuce yin salla. Mammah tace Biebah ta bisu tasa towel a ruwan zafi ta gasa mata goshin da fuskarta. Da to ta amsa tana bin bayan nasu... <<<<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>>>       ★RANTSUWA★   A yau sati uku da fadar da tabbatar da Janar matsayin shugaban ƙasa ta cika, a yau kuma ake shirye-shiryen rantsar da shi da shiga gidan gwamnati da aka kammala gyarawa tsaf. Tuni a cikin sati ukun nan ya kammala komai akan fiddo Dada, office kawai yake fatan shiga ya zartar da hukunci. Yanda kuma suke komai a sirrance daga shi sai Imran, da Haydar yasa zai mamayi mutane da yawa akan wannan kyakkyawan ƙudiri nasa.        Kamar yanda aka tsara an gabatar da rantsuwa tako wane fanni a ƙasar, sabbin shugabanni da wanda suka sake komawa tenure ta biyu duk sun shiga gidan gwamnati a wannan rana ta litinin tare da sabbin ofisoshin su. Sai dai mu cigaba da musu fatan alkairi da nasarar yin adalci ba satar kuɗaɗenmu ba😝🏃🏼‍♀️.      (Mai son soyayya da ɗan shugaban ƙasa tamun magana mu sasanta ta biya cin hanci na haɗasu🥱💃. In baki da ko sisi karma kizo😏🙄🤭🏃🏼‍♀️.)        ★A yau daren farko na sabon shugaban ƙasa Janar Yusuf Shu'aibu Tafida cikin gidan gwamnati. Tsaye yake cikin ƙayataccen falon daya kasance na ƙarshe sai bedroom ɗin barcinsa, tunda ya shigo gida bisa rakkiya bai buƙaci ganin ko ɗaya daga iyalansa ba, sakamakon son fara zartar da babban birinsa. Komai kashe yake a falon in ka cire ac kawai shima ba'a wani sakashi da ƙarfi ba, an sauƙaƙa hasken fitilu gaba ɗaya dan falon na cikin ɗan duhu-duhu, zaune yake shi kaɗai kamar yanda yafi buƙata, tunaninsa gaba ɗaya ya tsaya ne akan mutum guda ɗaya, mutumin da yake ma kallo mafi muhimmanci na farko da zai shimfiɗa wannan mulkin mai cike da cakwakiya da ƙalubale kashi-kashi da shi, dan tun a yau ɗaya da fara shigarsa office ya fahimci hakan. Saboda haka bazaiyi ƙasa a gwiwa ba ko sakaci, yana buƙatar Haysam Abdul-rasheed Shehu a cikin wannan tafiyar tasa tamkar yanda ƴan ƙasa ke buƙatarsa koda basu san muhimmancin sa a garesu ba.         Ƴar ƙarar buguwar agogon dake bango falon ya katse tunaninsa, numfashi ya sauke a hankali, dan ƙarar ta bugane tamkar da bugawar umarnin zuciyarsa dake ambaton (lokaci ya cika, ka fitar da takardar zartarwa kawai, rikicin da kake kallo da ƙalubalen bai fi nauyin burin nan naka ɗaya ba, cikashi tun a wannan daren masalaha ce ta zuciya da kwanciyar hankali ka, fitar Zak-Shadow daga dunkulallen makircin da aka garkame shi cikin kurkuku tsawon shekaru takwas itace zai tabbatar ma masu shirin mamayeka kai ba kurar wasansu bane, aiki kazo yi ga ƙasa da al'ummar ƙasa ba aikin aljihunansu ba).        Cike da gamsuwar shawarar zuciyarsa ya sauke numfashi, cikin nutsuwa ya ɗauki wani file da takarda a cikinsa mai tambarin ofishin shugaban ƙasa (Presidential Seal). Wannan shi ne takardar ikon afuwa da zai miƙa wa Ministan Tsaro, wanda zai tafi kai tsaye zuwa hannun Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa. Duk da yasan aikin bamai sauƙi bane a garesu; dan akwai al’amuran cikin gida da ya sani zasu taso, munafukan dake da hannu akan lamarin Haysam, waɗanda ba a san ainihinsu ba har yanzu, amma yasan zasu bayyana ne da wuri akan wannan fitar ta Haysam, dan dole suna da tasiri a cikin gwamnati harda tasa kamar yanda Haysam ɗin ya faɗa. Shi kansa daya samu wannan mulkin cikin sauƙi duk da yasan komai hukuncine daga UBANGIJIN, amma sanin wacece wannan ƙasar tasu akwai tambayoyi a ransa: Su wanene ainihi? Kuma me yasa Zak-Shadow ya zama barazanar da suka ƙuduri aniyar kawar da ita? Miyasa kowa Haysam dai Haysam dai?.         (Fitar tasa ce zata baka hasken samun wannan amsar) Zuciyarsa ta ayyana masa. Murmurshi ya saki mai ƙayatarwa cike da gamsuwa ya ɗauki wayarsa dake gefe. Kai tsaye number Imran yay kira.....         ★A yau gaba ɗaya Imran ya kasa barin office har zuwa wannan lokacin, zaman jiran kiran mutum ɗaya tak yake, kuma bazai ƙosa da wannan jiran ba daga nan har wayewar gari in sha ALLAHU. A dai-dai wannan lokacin da Shugaban kasa ke neman layinsa yana tsaye jikin windown ofishin sa yana kallon titin da ke cike da motocin jami’an tsaro. Rabonsa da cikakken barci tun dare shekaran jiya, gaba ɗaya barci ya gushe masa a cikin idanu tun bayan samun saƙon shugaban ƙasa ta text message bayan kammala rantsuwa. Dan haka ya ƙare wannan yinin gaba ɗaya da ƙagautar jira, jiran kiran Janar da a yanzu ya shigo wayar tasa a bazata. Jikinsa har tsuma yake wajen kai hannu ya ɗaga.          “Assalamu alaikum Your Excellency…” ya faɗa cikin ladabi da kuma farin ciki da bai iya ɓoyewa ba.     Janar daya fahimci ƙagautar Imran a bayyane ya saki murmurshi, batare da jan rai ba ya furta “Imran, lokaci yayi. Takardar afuwa ta kammala.” Ya ɗan yi shiru, irin shiru mai nauyin tasiri, kafin ya cigaba da faɗin, “Ina so ka shirya tawaga mai tsabta. Ba na son hayaniya, ba na son labari ya fito. Ka tabbatar da babu wanda idonsa ke buɗe a kanku”.      Da wata irin sauke ajiyar zuciya mai masifar nauyi Imran ya lumshe ido cikin jin daɗin kalmar da ya dade yana jira kamar mafarki. Muryarsa na rawa ya furta, “Za’a yi sir. Da izinin ALLAH Zak-Shadow zai fito gobe ƙarfe tara na safe.”      “Good. Kai nake son ka jagoranta Imran. Na san kai kaɗai zaka iya tsallake duk wata inuwa daga ƙalubalensu. Zaku wuce inda na tanada dan duba lafiyarsa da saituwar al'amarinsa. Ka tsare shi da ranki. Har sai ya koma randa zai dawo ƙasa ya zama barazana, dan Zak-Shadow nake son a gani ba firsinan shekara takwas ba”.        Daddy Imran ya murmusa, murmushin jarumi wanda ya dace da mai ɗauke da nauyi mai girma na tsakanin soja da dangi. Sai da ya ƙame tare da salute sannan ya furta, “Na rantse da ALLAH za’a yi fiye da umarninka Sir. Ba zan bari koda iska tai barazanar kaɗa nauyin daya rage masa ba kafin ka gan shi duniya ta ganshi zuri'armu su ganshi.”        “I'm proud of you, Soldier”.      “Thank you, Sir. I'm proud of you too”...      Daga haka suka katse kiran, amma zuciyar Imran kamar zatayi tsallen kwaɗon sojoji dan farin ciki. Sai da yay sujidar shukur sannan ya miƙe bakinsa ya kasa rufuwa dan murmushi, ji yake kamar UBANGIJI ya sauke masa wani babban nauyi daya toshe bugun zuciyarsa a tsawon shekaru. Wayar ya ɗauka ya tura sako ga ɗaya daga manyan abokan amana da zai jagoranci motar sirri zuwa prison wato Haydar Galadima (Faro)........✍️ 33 ..........Fuskar former First Lady ɗauke da murmushin ƙasaita take kallon Hajiya Hasiba, sai kuma ta girgiza kai da faɗin, “Hummm.. Adeel! Adeel. Yanzu kina nufin tare da shi kuka zo ƙasar nan?”.      “Sosai kuwa ranki ya daɗe. Dan yanzu haka ma yana masauki. Kuma abinda na sanar miki ya ambata ne ya kawo shi, wato kashe Haysam. Sai dai bamu san ta wace hanya zaibi ya tabbatar ba”.       “Yana da daman bin kowace hanya, dan yana da ƙarfin ikon dukiya da sunan zuri'ar gidansu. Sai dai abinda ke ban mamaki wace manufa yake da ita akan Nabeeha har haka? Dan nasan Adeel matuƙar sani, nasan al'amarinsa akan mata. Tabbas idan yana a giyar kwaɗayin tarayya da mace komai yana iya aikatawa, da zarar ya cika burinsa kuma shike nan.”        “Amma yana iƙirarin auren Nabeeha zai yi ai. Shiyyasa ma ya iya juriyar shekaru kusan tara kenan a kanta.”       Murmurshi mai haɗe da ƴar dariya First Lady tayi. “Bazan ce miki ƙarya yake kai tsaye ba Hajiya Hasiba, sai dai zan iya miki yaƙinin ba haka bane ainahin abinda ke ransa. Duk wannan iskancin da kike ganin Adeel nayi yana matuƙar tsoro da bin dokokin ahalinsa. Ba Nabeeha ba, ko ƴar shugaban ƙasar wannan ƙasar tamu zuri'arsa bazasu bari ya aura ba. Maybe da a yankin turawa ne su barshi yay hakan, dan sunfi ɗaukarsu da kima da daraja fiye da al'ummar yankin Afirika da suke amsa sunan baƙaƙen fata. Mu a wajensu bayi ne kawai, bayin da zasu musu bauta a gidaje da masana'antu, sannan bayin da zasu gusar da kishirwarsu cike da wulaƙantarwa da izgili. Ƙalilan ne a cikinsu masu mana kallon mutane, bari na miki ƙaramin misali mana, Kinga dai ance musulmi ɗan uwan musulmi ne, amma ko a saudia idan kinje ibada baki taɓa lura da yanda in kika haɗa sahun salla da mai jan kunne ke ƙoƙarin hana gangar jikinsa raɓar taki ba?”.         “Tabbas nasha ganin hakan ranki ya daɗe”.     “Good. Idan har basu so baƙin fata a sahun bautama UBANGIJIN daya tabbatar musu su da mu babu banbanci ba sai wanda yaji tsoronsa ta yaya zasu zo mu a haɗaka ta mu'amula mai girma irin wannan? Dan haka zan sake tabbatar miki ƙarya Adeel yake yana da manufa akan bibiyar Nabeeha, akwai burin da yake son cimmawa kuma bana jin na sha'awa ne”.           “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kai biri yayi kama da mutum gaskiya. Bazan ɓoye miki ba kullum cikin yima kaina irin tambayar nan nake. Sai dai ganin yanda take masa rashin kunya da nuna halin ko'in kula balle nuna jin haushi kan shafe min tantama ta. Yanzu ranki ya daɗe minene mafita? Kin san mutumin nan nada ƙarfi, kota wace hanya zaibi dan cimma manufarsa a kammu”.      “Tabbas zai bi, dan shafe babin rayuwar ɗan adam ƙaramin aiki ne daga tarin ƙananun ayyukansa. Sannan kunyi gangancin sanar masa mijin Nabeeha na rufe ne, duk da nasan idan yaso sanin hakan zai yi koda bata hanyar ku ba. Yanzu kije gida ki bani lokaci zanyi tunani, abinda na yanke zan kiraki mu haɗu ko nazo gidan na sameki, shima kuma zan je har masaukin nashi duk da banda isasshen lokaci, saboda gobe zamuje gidan gwamnati domin ganawa da sabuwar First Lady. Kin san ɗan takarar CSP candidate ɗin Excellancy ne. Dama nayi niyyar nemoki a satin nan kizo ƙasar saboda rantsuwa da akai, sai kuma gaki ALLAH ya kawo ki ma duk da an riga an gama dai”.        “Ranki ya daɗe duk abinda kuke so zamuyi, ni dai a taimaka na fara maganin wannan matsalar dan samun nutsuwa”.      “Karki damu Hasiba. Idan ta kama Excellancy ya shiga wannan maganar zai shiga. Zan saka ya nema Adeel da kansa koya gayyato shi nan gidan idan ALLAH ya ɗaura mu akansa dan abune mai wahala yazo ɗin. Amma zamu gwada sa'ar mu”.           “Nagode sosai ranki ya daɗe. ALLAH ya bar zuminci. Ya tabbatar da nasarar ku daga nan har ƙarshen rayuwa”.      “To amin Hasiba”. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨       ★★..10/9/2021..★★            🔥8:55 AM🔥      Duk da kasancewar hantsi ya ɗaga kurkukun ya yi shiru yau fiye da kowanne rana. Tun 8 aka kammala basu abincin safe kamar yanda komai yake a tsari aka saka kowa komawa ciki saboda baƙin sirri da zasu shigo. Sai irin su Dada da ba'a bari su fito sai da ƙwaƙwƙwaran dalili dan haka kai musu akeyi su har ɗakunansu. Received at 12:27        A bakin ƙofar gate 8:55am motocin sojoji ne masu duhun glass guda biyu suka tsaya kamar taurari a cikin duhun dare. A motar farko kawai aka sauke gilashi ƙasa tare da miƙama securitys ɗin ƙofar takarda. Suna duba abinda ke ciki suka ƙame jikinsu tare da salute ɗin motocin. Kafin da hanzari a wangale musu ƙofar suka shige a jere. Basu tsaya ko'ina ba sai a ƙofar sashen da Dada yake. Inda shugaban prison ɗin da kansa ke tsaye tare da jami'an soji na gidan guda uku alamar jiransu suke dama.        Sai da sojojin ɗayar motar suka gama fitowa da hanzari suka zagaye wajen kafin a buɗe ta ƙarshen. Col. Imran Abbas ne a ciki, cikin farin kaya na musamman bana soja ba, sai Brig. Haydar Usman Galadima (Faro). Cikin nutsuwar girma irin na masu kamewa suka fito a hankali, a take sojojin da suke tare da su harda na cikin prison dake tare da shugaban su suka ƙame tare da sara musu.      Suna ajiye hannu shugaban prison ya ƙaraso shima gabansu, ƙame jiki yay shima tare da salute nasu irin na girmamawa, suma sai suka ƙame ɗin sukai salute ɗinsa na girmamawa. Hakan na nufin kowa ya girmama girman kowanne, dan su duka ukun kowanne nada matsayin girmama ɗan uwansa a dokance. A karo na biyu sukai musabaha, kowanne fuska da murmushin mutunta juna. Kafin Colonel Imran Abbas ya miƙa takardar Presidential Pardon ga shugaban prison.       Sai da ya ƙame a karo na biyu yay salute ɗin Imran sannan ya amsa takardar. Shima sai Imran ɗin ya sake salute nashi a karo na biyu idanuwansa sun yi kaifi tamkar yana hango duk wani inuwa da zata takura masa a cikin idanun shugaban prison, sai dai babu dama, babu dalilin bijirewa.        A karo na farko, kai tsaye Brig. Haydar Usman Galadima ya furta, “Muna so a fito mana da Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu yanzu.”       Duk da shugaban prison yasan abinda ya kawosu kenan sai da numfashinsa ya tsaya cak na wucin gadi, jikinsa yay wani yamm kamar an jefasa da dusar kankara. Amma bashi da zaɓin daya wuce bin umarni na zahiri da gaskiya. Gudun kada yaransa dake zagaye da shi, da yake da tabbacin akwai idanun ɓoyayyun mutanen da suka kawosa wannan gidan suka ɗora a wannan kujerar yasa ya ɗanyi jarumtar son cizawa. Murya a takure ya furta,       “Sir… zuwa yanzu babu wani…”    Cikin zafi Imran daya gama fahimtarsa ya katsesa da faɗin, “Shi kawai muke buƙata a gabanmu. Wannan umarnin shugaban ƙasa ne. Ko akwai wani daga cikinku da zai ce bai san ma’anar wannan tambarin ba?”.         “I'm sorry, Sir!”.      Shugaban prison ya faɗa yana ƙara ƙamewa. Kafin ya juya yayma yaransa umarni da idanu. Duk da mamaki na neman kashe da yawansu saboda fahimtar abinda ke shirin faruwa basu da zaɓin daya wuce bin umarnin suma. Dole da sauri suka shige domin zartar da abinda aka saka su.....        ★A dai-dai lokacin da suke ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin, Dada na zaune ne ya idar da sallar walha yana karatun Alqur'ani. Motsin buɗe ƙofar da shigowarsu bai saka ya dakata ba balle kallonsu. Dan haka suma suka tsaya tsamm alamar jira. Sai da ya kwashe mintina biyar cir da shigowar tasu sannan ya rufe Alkur'anin yana mai ɗagowa ya kallesu. A tare suka nuna girmamawar soja, kafin suyi gaisuwa da sanar masa umarnin da aka basu.      Maimakon amsawa idanu ya lumshe a hankali, sai kuma ya kife zuwa sujuda. Minti biyu cir kafin ya ɗago. Ya ɗauki Alkur'anin sa ya maida inda yake. Sai kuma a dai-dai nan jami'ai  biyu dake tare da su Imran suka shigo. Suma sunyi gaisuwar sannan suka fara tattara kayansa na buƙata masu muhimmanci. Komai baice ba, sai bin ɗakin da yay da kallo, kallo irin na bankwana da tuna abinda ya shuɗe, kafin ya juya a hankali ya nufi ƙofa jami'an farko suka take masa baya.....       A hankali ƙofar corridor ɗin ta buɗe. Sai kowa ya sake nutsuwa da zubama ƙofar ido musamman Imran, Faro, shugaban prison. Yaran sojojin uku da suka rage a wajen kawunansu a ƙasa na girmamawa. Sakan goma tsakani jarumin jarumai ya bayyana, bayyanar data saka gaba ɗaya sojojin wajen harda su Imran ƙamewa a tare suka sara masa.Sai da ya lumshe idanunsa ya buɗe a kansu, sannan shima ya dunƙule hannaye duka yana ɗan miƙasu gaba alamar amsar girmamawar su. A karo na biyu, shugaban prison, Imran, Faro suka sake ƙamewa da sarawa irin ta girma da girma. A yanzu kam shima sai ya ƙame ya sara musu su ukun murmushin mai nauyi ya bayyana a fuskarsa. Kai tsaye ya saka idanunsa cikin na Faro da shima ke murmushi, ido ɗaya Faro ya kashe masa da sake yin wani salute na abokantaka da amintaka.       Dada ya girgiza kansa yana murmusawa da yima Faro alamar (bazaka taɓa canjawa ba) da idanunsa. Sai kuma ya janyesu a slowly ya maida kan Imran da ya tsaya cak kawai yana kallon sa shima. Idanusu ne suka haɗu cikin juna, shekaru takwas na ɓacin rai, rashin adalci, fushi da raɗaɗi duk suka bayyana cikin wannan idanuwa huɗun tamka a film ɗin da aka dannama pause.       Zak-Shadow ya sakarma Imran murmushi cikin nauyin zuciyar da ya saba ɓoyewa.      “…Imran Abbas?”.    Dada ya faɗa a karo na farko da wani irin salo na jini yaga jini.       Imran ya saki murmurshi tare da matsawa kusa da shi gab, sai kawai ya rungumeshi.          “Shagwaɓaɓɓena”.      Dada ya faɗa cikin kunnen Imran jin saukar hawayensa akan kafaɗarsa. Share hawayen yayi sannan ya ɗago yana murmurshi.        “Alƙawarin ALLAH ya cika. Rubutacciyar ƙaddara daga littafi na gaskiya ta taƙaita. UBANGIJI ya tabbatar mana zai jarabcemu, sai dai da jarabawar nan zai ɗaga darajojinmu a sama idan mun kasance masu haƙurin cinyeta. Ƙasarka ta jira dawowarka. Zuri'a bata manta da kai ba. Rundunar soji na kwatance da sunanka. Bararka da zuwa mai son a gina gaskiya a zartar da ita koda zata ƙona kai da kai. ALLAH ya cigaba da amintar da wannan RUHIN bisa kyakkyawan gini na gaskiya. A yau zan buɗe muryar data disashe saboda kukan kewa na faɗama duniya cewar Haysam Abdul-rasheed Shehu is back again”.         Murmurshi Dada ya saki mai nauyi, zuciyarsa ta rikice da son fitar da abinda ke zagaye da ita na kewa tsahon shekaru, ba dan prison ba, ba don wahala ba, sai dan kalaman Imran dasuka ratsata har cikin jini da jijiya dama ƙashi. Amma da yake mazan maza ne sai suka rikiɗe da ƙarfafa kai bayyananne. Da nayin kamewa da nutsuwa ya furta,        “Imran! You are my destiny. I am proud of you........✍️ 34 ..........“Almu na maka kiran gaggawa ne saboda ƙarin abokin aiki da zaka samu”.     Cikin tashin hankali maigadi ya ɗago yana kallon mutumin dake zaune cikin lallausar kujerar ƙayataccen falon. Sai kuma ya sake maida kan nasa ƙasa da sauri. Zuciyarsa na bugawa da yin rawa a cikin ƙirjinsa ya furta, “Ranka ya daɗe nawa aikin baya tafiya dai-dai ne?”.         Sai da mutumin yaja fin sakan uku kafin ya amsa cike da isa. “Aikin ka na tafiya dai-dai Almu, anzo gaɓar da shima wannan ɗin dole sai ya shiga gidan ne”.      “Shike nan ranka ya daɗe, yanda kace haka za'ai. Ni dai ALLAH ina sake roƙon arziƙi kada a cutar min da ƴar uwa. Kaima ka sani mu marayu ne, bamu da kowa a wannan duniyar sai kammu mu biyun nan rak.”           “Bijirema umarni na ne kawai zai iya sakawa ta cutu. Idan ka kiyaye ta kiyaye lokaci kaɗan ya rage muku ku samu freedom.”       “Zamuyi duk abinda kake buƙata in sha ALLAHU ranka ya daɗe. Amma dan ALLAH zan iya ganinta?”.      Wani banzan kallo daya saka maigadi sake nutsuwa mutumin ya watsa masa. Sai kuma yaja tsaki yana ɗaukar wayarsa dake gefe yay danne-danne. Kunnensa ya kai, sai dai a taƙaice ya furta, “Zaka iya fitowa”. Daga haka ya ajiye wayar. Shiru falon ya ɗauka, sai ƙarar tv dake fita ƙasa-ƙasa dana ac. Cikin abinda bai gaza mintuna biyar ba wani ya fito. A ƙalla dai bazai wuce shekara talatin da shida ba. Shima cike da tashi izzar yay ma Almu kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Sai da ya zauna a kujera sannan wancan mutumin dake kallonsa fuska da murmurshin da tun da Almu ya shigo bai gani a fuskarsa ba.       Almu ya nuna yana gyara zama. “Wannan shine mutumin da nake gaya makan. Yana aikin gadi a gidan kusan shekara huɗu ke nan, bayan mun tsige wancan ganin bazai iya mana komai ba.”       “Shi wannan yana yin abinda ake so kenan?”. Saurayin yay magana a karo na farko.     “Tabbas yana yi, dan tunda ya fara aiki babu wani kuskure da zance mara daɗi. Sunansa Almu.”       “Okay”.   Ya faɗa a taƙaice. Mutumin bai nuna ya damu ba ya cigaba da faɗin, “Zaka shirya ne ku wuce tare? Ko zaka bishi daga baya?”.       “Kawai mu wuce taren, ai da zafi-zafi ake dukan ƙarfe. Sai dai ya kamata nasan wane aiki zan iya samu a gidan?”.       Yanzu kam mutumin baice komai ba, illa juyawa da yay shima ya kalla Almu. Da sauri Almu yace, “Ranka ya daɗe sai dai in munje can ɗin, amma a yanzu gaskiya a gidan nan babu wani aiki. Dama a wata biyu daya wuce ne driver ɗinsu ya samu hatsari to da an samu sai ya maye gurbinsa. Amma yanzu ma inada tunani guda, akwai mai sharar tsakar gidan kullum da bama filawoyi ruwa. Yakan zo da safe yayi ya dawo da yamma. Sunyi-sunyi ya dinga zama nan koma kwana yaƙi, acewarsa yana wasu ayyukan ne idan ya kammala da nan. To ko shi zamu tunɓuke ta hanyar maƙarƙashiya sai shi ya maye shi?”.         “Eh wannan ma kazo da zance mai ƙyau. Amma miyasa ban san da labarin driver ba? Bayan kuma na sanar maka ko sabuwar kaza akai a wannan gidan nasan da ita. Ko cokali ya faɗi nasan da sautin ƙarar faɗuwarsa....”      “Ka gafarceni ranka ya daɗe, na nemeka amma ban samu ba, idan baka manta ba jiya daka turo min saƙon kana son ganina na tura maka amsa da dama inada wata magana. To dama maganar kenan”.       Maimakon amsa zancen sai cayay, “Kaje waje ka jira shi zai fito”.       Idanun Almu cike da ƙwalla ya jinjina kai. Yayi kamar zai miƙe sai kuma ya sake komawa ya duƙa. “Ranka ya daɗe dan ALLAH ko zan iya ganin ƴar uwata ɗin?”.          “No!”.    Ya bashi amsa a ɗan tsawace. Da sauri maigadi ya miƙe jikinsa na rawa ya fice a falon. Idanunsa kuwa tuni sun cika da ruwan hawaye. Zuciyarsa kam raɗaɗi take masa. Tabbas badan da ƴar uwarsa da mutanen nan suke amfani wajen juyashi yanda suke so ba sun san basu isa ba. Shine fa Almu, Almu na babba ƙarfe bashi ratsa jininka. Guduma mai fasa kan tantiri.... Ƙwafa yayi yana mai cije laɓɓansa, daga haka ya samu waje a bakin baranda ya zauna...... °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°      A gidan Mammah rashin barcin wuri saboda murnar dawowar Uncle Bilal yasa yau kusan kowa sai da ya makara. Gasu Nimrah zasu je makaranta tunda an koma hutu. Ganin yanda lokaci yaja suka so lanjarewa akan bazasu je ba, gashi yau monday fa. Amma Uncle Ammar ya buɗe musu wuta dole suka shirya suna faman ɗaga baki. Uncle Bilal dake biye musu kuwa suna fitowa ya fara lallashinsu, ƙarshe yace shine ma zai kaisu school ɗin da kansa. A take bakunansu suka washe da farin ciki, dan suna matuƙar ƙaunar Uncle Bilal.       Breakfast ɗinsu aka shirya musu a lunch box Mammah tace suci a mota. Sun fito Mu'azz na tsokanarsu wai sun zama su Abees ƴan Nursery, Uncle Bilal ne yace karsu kulashi, dan haka harara kawai suka zuba masa suka shige mota. Tunda suka ɗauki hanyar school suna karyawa suna ma Uncle Bilal hira, duk da kuwa jiya babu kalar labarin da bai sha ba da ƙyar suka barshi ya kwanta. Su Aheel ya fara saukewa a tasu school ɗin, su Rukyn suka taimaka masa ya raka su har ajinsu yay magana da class masters ɗinsu. Dan Aheel da Abees ajinsu ɗaya. Afrah da Ayyan ma haka. Basu ɓata lokaci ba suka fito suka koma mota.      Suma har aji Uncle Bilal ya raka su, sunyi sa'a Teacher Khalil ne a ciki. Ya gaisa da Uncle Bilal cikin mutunci kasancewar sun san juna. Sannan ya bada hakuri akan makarar ƴaƴan Mammah. Fuskar Teacher Khalil da murmurshi ya ce, “Ba komai Uncle ai yau da gobe sai ALLAH. Sai nazo gida cin tsarabar turai.”       Ƙaramar dariya Bilal yayi da faɗin, “Sai kazo ina nan ina jiran ka.” daga haka yayma su Nimrah bye ya wuce. Ƴan ajin kam da yawansu sun ƙyasa, yo sunga handsome masha ALLAH. Cike da neman magana Nimrah taja tsaki da taɓe baki tana magana cikin ƙunƙuni. “Mudai kar a cinye mana uba, naga mayu sunyi yawa a ajin nan haba irin wannan kallo haka kamar sabbin kwartaye”.      Dariya Ruky ta sanya, sai kuma tai saurin toshe baki saboda tunawa akwai Teacher Khalil a ciki. Kuma sarai yaji mi Nimrah ɗin ta faɗa da dariyar Rukyn. Dan kai tsaye ya juyo daga rubutun da yake akan allo. Sai dai baiyi magana ba, suma duk sun wayance sun ɗauka books kamar basu suka aikata ba. Yayinda mafi yawan ƴan ajin suka shaƙa da baƙar maganar Nimrah, sai dai sun san ba damar maida murtani Zakanya da Damisa su daki banza. Hibba dai tunda taci duka a wajensu take neman shishshige musu ayi ƙawance. Amma wulaƙanci irin na Ruky da Nimrah sai yarfata suke..... ★★★    “Wai Mammah ko duk farin cikin dawowar Bilal ne. Tunda na shigo gidan nan na fahimci farin cikin ki a bayyane yake”.          Murmurshi Mammah ta sake yi tana kallon Aunty Ummi mai maganar, ganin suma su Shariffa da su Mimi sun zuba mata ido sai ta sake sakin murmurshin da faɗin, “Inaga dawowar Bilal ɗin ce, dan yau kam wani farin ciki mai girma da ni kaina na gagara misaltashi ne zagaye da zuciyata. Dan haka na saka su Kulu suyi abinci mai yawa a fitar sadaka.”        Addu'a suka shiga jero mata da fatan ALLAH ya ƙara mata farin ciki da nisan kwana masu albarka. Ta amsa musu da amin tana shafa kan Mimi data kama hannunta ta sumbata. Dai-dai nan Bilal daya dawo daga kai su Nimrah school ya shigo falon. Ture Aunty Mommy abokiyar karawar tasa yay daga kusa da Mammah ya zauna yana faɗin, “Mi ake tattaunawa auntys.”       Aunty Mommy dake harararsa ta ce, “Anƙi a faɗa ɗin. Kawai dan neman faɗa kazo ka wani ture ni, da kama samu nazo ganinka tuzuru kawai”.           Cikin dariya Bilal dake amsar Babyn Aunty Mimi a hannun Aunty Lailah ya ce, “Humm kwantar da hankalinki yarinyar nan, kwanan nan kalmar nan ta tuzuru zaki bar faɗarta ne.”      Cike da zumuɗi Aunty Mimi ta taso ta dawo kusa da shi. “Dan ALLAH da gaske Yaya Bilalu? Dan ALLAH guntsa min wacece?”.         “Uwar gulma kenan”.    Cewar Bilal. Dariya gaba ɗaya suka sanya. Aunty Shariffa ta ce, “Wlhy dama nasan sai ka faɗa haka. Dan ALLAH a bamu musha Yaya Bilal. Dama gidan shiru kwana biyu babu shagali dan ma mun ɗan rage da sunan Baby Nawal ne”.    “Aunty Shariffa karki damu, lokaci ne zaku sani, amma shagalin biki sai Dada na nan in sha ALLAHU”.      A take falon yay tsitt, Dan shima yayi maganar ne muryarsa na ɗan rawa. Mammah ce tai gyaran murya, dan tasan yanzu zasu fara mata koke-koke. Cikin canja hirar ta ce, “Mudai yanzu tashi ka ɗakko mana tsarabar mu nan duk ita mukai zaman jira”.         Cikin dariya Bilal ya ce, “Kai Mammah harda ke? To kowa yay haƙuri baza'a buɗe tsarabar nan ba sai yarana sun dawo school gaskiya. Dan sune zasu buɗe ta”.        “Yau muna ganin jalala, har sai su kafi auta sun dawo za'a bamu tsarabar?”.        Yanda Aunty Lailah tai maganar yasa kowa fashewa da dariya........✍️ 35 .......... ★PRISON★        9:30am dai-dai motocin sojojin biyu suka fice daga cikin prison ɗin cikin tsaro mai cikakken sirri, yayin da hukuncin UBANGIJI da ƙarfin ikonsa suka tabbata a daidai wannan lokacin wani razani ya gitta a zukatan wasu mutane daga ɓangaren Ƙungiyar duhu, a ƙasan rayukansu suka dinga jin cewa abu mafi hatsari ya faru. Sai dai daga ina? Daga wane yanki? Akan mi? A dalilin mi? Duk UBANGIJI ya toshe wannan amsoshin daga garesu, koda ata hanyar yaransu dake cikin prison ɗin babu wani labari da suka samu saboda gargaɗin shugaban ƙasa...... ★A ɓangaren su CSP Alpha shugaban prison bayan fitar motocin su Imran biyu sai wajen ya sake nutsuwa takar an ɗora dutse a zukatansu, ga iskar da suke shaƙa ji suke kamar ta rikice da wani irin nauyin da babu mai iya fassara shi. CSP Alpha bai iya ya motsa daga tsayen da yake ba har bayan an kulle ƙofar gate ɗin. Jikinsa ya ƙara sanyi, numfashinsa na fita a cure, zuciyarsa ta kumbura cikin ƙirjinsa. Jin tamkar hajijiya na neman zubar da shi babu shiri ya jingina da bango kaɗan, hannunsa na riƙe da takardar Presidential Pardon da yake jinta da uban nauyin da yafi na takarda a hannunsa, ta koma mata tamkar nauyin dutse ne.        Dai-dai nan wani sojan da ke tare da shi ya matsa kaɗan yana son yin magana, amma CSP Alpha ya kaɗa masa ido cikin gargaɗin tsoro da rashin tabbas....        “Ka tafi! Ku tafi ku duka…!” Muryarsa ta fita da ɗan kauri cike da bada umarni irin na manya. Kai tsaye sojojin suka bar wajen, sai dai zukatansu nata tsalle-tsalle, tsallen da suka tabbatar da in ya wuce zuciya yace zai zo kan harshe zasuyi nadama ne ta har abadan. Dan haka kowa ya ajiye abinda yaji ya kuma gani anan dan wata shirun tafi alkairi. Musamman ma daya kasance an musu gargaɗi na haƙiƙa dan tamkar an zaɓesu ne akan al'amarin...       Sai a lokacin shima CSP Alpha ya tuna da maganar da shugaban ƙasa janar Yusuf ya yi masa kwanaki biyu da suka gabata a cikin waya…       “Ka kiyaye sirri fiye da kiyaye rayuwarka. Idan ka yi kuskure, ba zan iya kare ka daga hukumar tsaro ko daga mutanen dake a waje suna jiran Zak-Shadow ba. Kuma wlhy duk wanda ya san wannan al’amari kafin lokacin da ya dace, to kai kanka ka yi masa jagora zuwa lahirarsa”.       Wannan kalamai ne da har cikin jinin CSP Alpha suke da tasiri mai saka razani da ƙaulanin zuciya har yanzu. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, goshinsa ya cika da zufa. Hannu ya kai ya sharce gumin, kafin ya furta da ƙasa-ƙasa kamar mai roƙon iska. “Ya ALLAH an sakani a tsakiya?. Wane irin mutum ne wannan Zak-Shadow ɗin da shugaban ƙasa ya zo kan al'amarinsa haka da gaggawa?”.       Bashi da amsa, babu kuma mai bashi ita a yanzu. Dan haka bai yiwa kansa dogon tambaya ba ya haƙura. Tsoron da yake ji game da maƙudan mutanen da ke bayan fage ya fi ƙarfin neman amsoshin tambayoyin nan dake danƙare a zuciyarsa....... <<<%>>><★><<<%>>>        Tunda suka baro cikin prison ɗin shiru ya ratsa motar, sai sautin AC da numfashin su dake fita iyakar motsin ƙirazansu. Baradan jaruman haziƙan sojojin uku Imran, Faro, Zak-Shadow. Ba wanda ya ce komai. Kowa da abin da yake tattaunawa da zuciyarsa.       Sai rufaffen gilashin motar da ke nuna hasken rana daya fara zafi, launin duhun sa ya bayyana fuskokinsu dake da sanyin annuri.       Daddy Imran yana kallon Dada akai-akai tamkar idan ya ɗauke idanun nasa zai ɓace masa ne, ko yana son tabbatarwa wannan ba mafarki ba ne. Faro dai sai murmushi yake yi irin wanda yake nuni da cewa (Na gaya maku wataran ƙaddara da ƙarfin ikon wanda ya fiku iko zai dawo da shi a duniyar ku).       Amma shi Dada ya rufe idanunsa cikin nutsuwa, yana fitar da numfashi a hankali da shaƙar mai tsabta fiye da duk wanda ya shaƙa a cikin shekaru takwas. Yawan jin idanu a kansa dan in har ana kallonsa sai yaji a jikinsa, balle wannan kallon yana jin ƙarfin idanun mai su a cikin ƙirjinsa. Ya kuma tabbatar da Imran ne ke da wannan tasirin. A hankali ya buɗe idanuwan nasa, sai ko suka sauka kai tsaye akan Imran ɗin da yay hasashe. Hararasa ya ɗanyi, tare da ɗage masa gira ɗaya, da murya ƙasa-ƙasa amma cikin zurfi ya furta, “Kallon fa?”. Ƙaramar dariya Imran yayi da faɗin, “Ina tsoron karka sake ɓace min ne”. Kauda fuska Dada yay kaɗan da sakin ƙaramin murmushi, batare daya tanka batun Imran ɗin ba ya sake jeho masa sabuwar tambaya. “Motar nan ina take son kai mu?” Daddy Imran ya ɗan taɓe baki da matsawa kaɗan ya jingina da kujera. Shima cikin salon raɗa ya ce, “Wurin da ba wanda zai same ka. Wurin da babu ƙungiya, babu siyasa, babu duhu. Wurin da zaka samu iska ta ƴanci bayan shekara takwas daka rasa”.        Dada ya girgiza kai a hankali tare da lumshe idanu ya buɗe a lokaci guda. “Na gode muku Imran, Faro, na gode sosai.”      Kafin Imran yace wani abu Faro ya katse su cikin siririyar dariya mai armashi da jin daɗi. “Zaki wlhy idan ka sake irin wannan sakon godiyar, zan fara tunanin da gaske zaka canja halinka.”     Dada ya kalle shi yana murmushin ƙasaita sai kuma ya maida kansa ya kwantar a jikin kujera ya lumshe idanunsa har lokacin da murmushi a kan fuskarsa. Sai a lokacin ya furta, “Ga shi kai baka da ranar canzawar da wannan sa idon naka”.        Dariya Imran da Faro suka sanya, cikin irin dariyar da ta bayyana ƙyallin ruwan hawaye daga idanun Imran da ya kasa ɓoyewa....        Dada dake murmushi zuciyarsa ta tafi sabon tunani. (Shugaban ƙasa da kansa ya yanke wannan hukuncin da gaggawa? Mi yasa? Mi ya faru da ƙasata cikin wannan lokacin? Mi ake shirin bani? Mi ake buƙata daga gare ni?). Kafin ya samo amsoshin waɗan nan tambayoyi masu nauyi Imran ya katse shi da faɗin, “Muna da tsaro mai ƙarfi, babu wanda zai kusance ka har sai ka shirya. Koda likitoci sun gama duba ka zaka cigaba da zama a ɓoye. Babu wani abu da zai kusanto ka. Sai mun kammala gyara rashin adalcin da aka yi mana, dan ƙasa tana buƙatar komawar ka a Zak-Shadow ɗin data sani ne. Mammah zatafi farin ciki idan ta ganka a Haysam ɗinta itama. Balle kuma ƴaƴan Dada”.      Dada ya ɗan furzar da numfashi da buɗe idanunsa dake a rufe, zuciyarsa cike da wani nauyin da bai gama wargajewa ba. Tabbas a yanzu ba wanda ya fi buƙatar son fara gani kamar Mammah da ƙannensa, amma zai daure ya jure dan yasan duk yawan kwanakin da suke so yayi anan bazasu kai yawan wanda yayi a baya ba. Shima zai fi son Mammah ta gansa cikin ƙyaƙyƙyawan kamanni ba wannan kamannin da yake a yanzu ba da zasu iya raunana zuciyarta har ta gagara mantawa da su. Numfashi ya sauke a hankali, a yanayinsa na Zak-Shadow da suka sani ya furta, “Imran kun tabbatar babu wanda ya san dawowa ta?”.      “Ai ko motar nan ta bari wasu suka ji Zak-Shadow ya dawo, ta riga ta mutu.” Imran ya ƙare maganar yana dariya mai taushi. Faro ma hannu ya ɗaga yana dariya da faɗin, “Duniya zata san dawowar ka ne lokacin da ka yanke hukunci, ba lokacin da kowa yake jin yanada ƴancin faɗar abinda ya gani ba koda Imran da Faro da shugaban ƙasa ne.”          “ALLAH ya shiryeku, yau kuma kun zama ƴan comedy”. Cewar Dada yana ɗaukar takardar dake gefensa. Yanzun ma dariya suka sanya, dan har ƙarƙashin zukatansu suke jin wannan nishaɗin mara misali. Shi kansa Dada yana jin fiye da nasu, kawai dai ya fisu kamewa ne, sannan halayyar su dama can ba ɗaya bace, su sunada faran-faran da magana, sabanin shi da ko wasa bai iya ba, dama dai da Imran ne wani lokacin idan ya matsa masa, sai shima Faro ɗin idan ya gallabesa wasu lokutan yakan maida musu murtani.....       ⭐ 10:43am dai-dai Motocin biyu suka isa secret medical base wuri na musamman mai tsafta, nutsuwa, da ƙa’ida. A yanda gurin yake a killace zaka ɗauka Shugaban ƙasa yasa an tsara shi ne tamkar dan ɓoye Dada ɗin ne anan. Dan tuni har likitoci suna jiran su, likitoci kam na musamman ne aka tanada dan duba lafiyarsa, saboda duk ƙarfin halin da Dada ke nunawa su sun san abu na farko da yake buƙata shine duba lafiyar tasa.        Sun masa tarba ta girmamawa suma, dan duk da halin da yake ciki kwarjinin yawan ibada da UBANGIJI ya bashi yana nan a tare da shi sai ma ƙaruwa da yayi da sake ɗaga darajarsa ga duk mai kallonsa. Received at     Shi ɗin DODO ne a kowane irin yanayi, dan haka a nutse yake bin komai da aka shirya da nazari irin na masu nutsuwa: Kayan aiki, ma’aikata, da tsaro mai ƙarfi. Sai da Idanunsa suka gama tantance kowanne daga cikinsu, kamar yadda yake nazarin duk wanda zai shiga cikin binciken sa.       Imran dake lure da shi ya saki murmurshi ya juya kansa zuwa ga Faro. “Faro, ka tabbata babu wanda zai san dawowar sa.”      Faro daya fahimci saƙon da Imran ke son isarwa ya ɗaga hannu tare da kashe masa ido ɗaya ya ce, “Babu wanda zai sani, har sai lokacin da Zak-Shadow ya yanke hukunci.”        “Kayi ƙyan kai Faro. Lokaci zai bayyana komai da kansa. Duk wanda ya ga fitowarsa ba a shirye ba kuwa zai zama....” Imran yay alamar mutuwa.       Su suke maganar, amma Dada nazartar likiticin daya tabbatar su su Imran kema wannan zaurancen yake. Ganin yanda suka duƙar da kawuna yasa shi fahimtar suna fahimtar komai suma. Baiyi magana ba yay gaba kai kace yasan wajen ne. Da sauri likiticin suka zabura dan masa jagora, Imran da Faro suka sake kallon juna da murmurshi, sai suma sukabi bayansu..........✍️ 36 ........Ciwon kai sosai ya gallabi Nimrah a makaranta saboda raunin kanta da bai gama warkewa ba. Babu shiri wajen sha biyu aka maidata gida bayan an kaita clinic ɗin cikin makaranta sun dubata. Ba ƙaramin tashi hankalin su Mammah da su Aunty Ummi dake gidan yayi ba. Dan duk ciwon da zakaga ya kwantar da Nimrah haka ba ƙaramin jinsa take ba. Ga jikinta zafi zau da zazzaɓi. Mammah ɗakinta ta Kaita ta kwantar bayan kowa ya gama jera mata sannu da addu'a. Da kanta ta zame mata uniform ɗin jikinta ta barta da vest da shot kawai, ita ta goge mata jiki da ruwan sanyi tasa aunty Mimi ta ɗakko mata riga mara nauyi a ɗakinsu. Aunty Shariffa ta kawo mata kunun madara, da ƙyar aka lallaɓata tasha tana hawaye dan ji take kamar kan zai rabe mata biyu, kaɗan tasha kunun tasha magani Mammah ta kwantar da ita tana tofa mata addu'a har barci ya ɗauketa...... <<<<<★★★★>>>>>              “Sir na bincika kamar yanda kace. Gidan nan gidan wani soja ne, akwai mahaifiyarsa a ciki da ƙanensa, amma shi yana ɗaure shekaru takwas kenan. Ita kuma yarinyar ban sani ba ko ƙanwarsa ce ko ƴa gaskiya. Dan ban samu wani cikakken bayani a kanta ba, a dai gidan take, kuma ƴar gidan ce”.      Gaba ɗaya ma'aikacin hotel ɗin yayima Adeel bayanin ne da harshen turanci, dan da shi suke magana kasancewar shi baya jin yarensa shima baya ji, amma dukansu sunyi tarayya akan yaren turanci. Ajiyar zuciya Adeel dake saurarensa ya shiga saukewa. Dan tun marecan jiya da yaga Nimrah bai sake jin cikkiyar nutsuwa ba a zuciyarsa. Yau ɗin nan yana da zama da tsohon shugaban ƙasa, amma bai iya yaje ba saboda ba waccan damuwar bace yanzu gabansa ta yarinyar da ko sunanta bai sani ba ce. Hatta su Nabeeha bai sake bi takansu ba. Ko wanda yasa yana bibiyarsu da yazo da safen nan masa bayani kamar yanda ya bashi umarni cayay yaje kawai yana buƙatar hutu.      Da turancin ya ce, “Miye sunanta?”.         “Nimrah!”.     Sai da ya wani lumshe manyan fararen idanunsa ya buɗe sannan ya saki murmurshi. Dan kuwa sunan ya dace da ita. Dan a cikin sakannin da suka haɗu ya tabbatar da ita ɗin zakayyarce, zuciyarsa ta shiga wassafo masa ɗan mitsitsin bakinta na tsiwa mai ɗauke da kyawawan lips pink da baƙi. Yanda ta zazzaro masa dara-daran idanunta farare tas masu suffar ƙwai da masa gargaɗin kada ya taɓata da yaren da bai gane komai ba. Ya saki ƴar dariya da sake hango idanunta da suka watsa masa harara.      Galala ma'aikacin hotel ɗin yay hana kallonsa, dan lallai ya yarda wannan guy ɗin ya faɗa da yawa. Koda yake baiga laifinsa ba. Dan yaran fa sun haɗu, su duka biyun wanke hannu ka taɓa ne. Daga gani kasan ƴan hutu ne kuma ƴan gata ƴaƴan manyan ƙasa. Duk da basu wani gama cika manyan ƴammata ba ko a haka za'aje da su, damma a cikin hijjab suke ba komai nasu ake gani ba face fuskoki.....       “Ka samo number wayan ta?”.   Adeel ya katse masa tunani. Kansa ya girgiza da faɗin, “A'a Sir, bayan waɗan nan bayanan babu abinda na samu gaskiya. Dan gidan nan ba ƙaramin gida bane da samun information ɗinsu zai mun sauƙi. Wannan ma sa'a akaci na ga wanda na sani a street ɗin, shima kuma bai wani jima da kama haya ba.”       “Good kaje ka zomin da shi”.   Kai ya jinjina masa a ransa yana mamakin irin wannan haukacewa haka daga ganin yarinya? To amma ina ruwansa, aikin kuɗi yake yi, ya tabbatar kuma idan Adeel ya samu abinda yake so shima zai ja kaya. Dan Vvip ɗin da ya kama kawai ya isa ya sanar dakai mugu-mugun mai kuɗi ne shi. Balle manyan agogo da designers kayansa zuwa takalmi, kai wayar hannunsa kanta kai kasan lallai akwai manda. Dan zai iya rantsuwar bai taɓa ganin irinta ba balle kamfanin da ake yinta. (😜Ƙaryar marubutan ta motsa anan. Ya kuka iya🤣 ku karanta kawai🥱. Amma in gaskiya za'abi ai akwai masu kuɗin nan dai ko🥱😎).     Hannu Adeel ya ɗaga masa, ya ɗan risina na girmamawa sannan ya fice.....    >>>>>>>%<<<<<<<        Kamal na ƴar dariya da shafa kai ya ce, “To kusan haka baba, amma ai da sauran lokaci tunda nasan baza'a mata aure yanzu ba nima kuma haka”.      “Kai! A wannan shekarun naka?”. “Baba tsahon ƙafa ne kawai, amma ba wasu shekaru bane dan ashirin da biyar ne kacal”.         “To ai sune dai-dai auren ɗana. Mutum ya more yanda yake so ba auren bariki ba sai an gama tsofewa a ɗakin soro. Mu kaga iyayenmu sun mana gata a sha tara ma suka mana auren”.      “Baba sha tara fa?”.   “Sosai. Ba gashi mun mora auren yanda ya kamata ba. Itama kuma ai in a ƙauye ne yanzu ta isa haihuwa ma ta biyu ko ya yaye na farko tana da cikin na biyu. Shekara sha biyar fa tana cikin ta sha shida koba haka ba?”..           “Tabbas haka ne Baba”.     “To ka gani, ai karka wani damu kanka, ka fara yaɗa manufa kawai muma zamu tayaka”.     “To baba ALLAH ya tabbatar mana da alkairi”.      “Yawwa haka nake so naji ka faɗa”. Cewar Malam Buba yana miƙewa. Ya cigaba da faɗin, “Kaga jirani bara na kirata, dan naga kwana biyu ma bata zuwa makaranta sunce bata da lafiya. Kwana kusan biyar kenan taji ciwo a islamiyyar su ne...”      Cike da jimami Kalam ya amsa masa da, “Haka ne Baba, wlhy a islamiyya ne fa.....”    Ya kwashe labari tsaff ya sanar masa. Malam Buba dake saurarensa cike da nazari yay wani murmushi mai ma'anoni da yawa. Dan kuwa tabbas yau ya samu hanya mai sauƙi da yake nema da fata. Tabbas Kamal shine zai kasance makamin amfaninsa akan cimma burinsa kan Nimrah. Labarin nan kuwa yay masa matuƙar daɗi da ɗaukar hankalinsa. Tuni ya nufi cikin gida kiran Nimrah.........✍️ .........Imran ya miƙe kenan zai wuce Malam Buba yay sallama. Amsa masa suka yi shi da Mammah, kafin Mammah ta bashi izinin shigowa. Koda wasa bai kalla sashen da Imran yake ba, dan haka kawai yake jin tsarguwa idan Imran ɗin na kallonsa. Daga bakin ƙofar ya rissina ya gaishesu, sannan ya isar da saƙon Nimrah tayi baƙo.       Cike da mamaki a tare Mammah da Imran suka furta, “Baƙo kuma?”. Har yanda sukai ɗin ya bama Malam Buba mamaki. Amma sai ya shanye mamakin nasa yay ƙarin bayani da, “Yace malamin su ne na islamiyya, mage ce ya kawo mata, yace kuma itace da kanta ta buƙaci haka.”      Mammah tasan labarin mage, dan har Nimrah a kwanakin tana mitar batun kawota da malaminsu baiyi ba. Kusan yanzu ma take jiyosu daga kitchen Nimrah na batun da tasan number sayyadinsu data kira a wayar Biebah ta tuna masa batun magenta. Sunan Nimrah ɗin ta kira, ta amsa tana fitowa daga kitchen ɗin hannunta da kofin tea, ganin sabon driver ɗin su da ko sunansa bata riƙe ba har yanzu ya sata ɗan tsayawa turus, sai kuma ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ƙaraso wajen Mammah.       Hannu Mammah tasa ta amshi kofin shayin hannun nata tana faɗin, “Saka hijjab kije ga malamin ku yazo kawo miki magen taki”.       Washewa fuskar Nimrah tayi da murmushi, cike da farin ciki ta ce, “To Mammah. Ta ɗauki hijjab a inda suke ajiyewa ta saka. Malam Buba na gaba tana biye, haka kawai ta samu kanta da zubawa bayansa ido duk da zuciyarta dake bugawa. Imran na daga ciki sallama yay ma Mammah ya fito dan kiran Faro nata shigo masa a waya, yasan kuma zai iya yiwuwa Dada ne, shi kuma baya son ɗagawa a gaban Mammah dan ko a fuska bai nuna mata fitowar Dadan ba. Dai-dai Nimrah na kaiwa gate, cikin ɗan risinawa ta gaida Sayyadi Kamal daya zuba mata ido. Ita kam kanta a ƙasa batama san yana yi ba.         Idanu sosai Imran ya zubama Kamal ɗin daga inda yake tsaye cike da nazari, yayinda shi kuma hankalin Malam Buba yake kan Imran a kaikaice shima yana nazarin kallon da yake ma Kamal ɗin. Nimrah kam bata ɓata lokaci ba ta miƙa hannu amsar kwalin magen. Kamal na murmushi da kallonta ya miƙa mata tare da miƙewa, kaɗan ya matsota yana magana ƙasa-ƙasa. Nimrah ta yamutsa fuska da ɗan jan jikinta baya, yayinda fara'ar fuskarta ke raguwa alamar maganar daya gaya mata ce batai mata ba. Dan kamar wadda take a ƙage ma yana sakar mata kwalin ta baro wajen tana masa sallama da tafiya duk a lokaci guda. A haka ta ƙaraso inda Imran yake tsaye yana kallon Kamal dai dake binta da kallo..        “Daddy kaga mage na”.    Nimrah ta faɗa dai-dai tana isowa gabansa, murmushi ya saki yana ciro hannunsa daga aljihu ya amshi kwalin cike da kulawa. Da kansa ya kwance ɗaurin zaren da akaima kwalin yasa hannu ya ciro kyakkyawar magen fara tas ƴar ƙarama.        “Masha ALLAH Babyn daughter ta iso gida lafiya. ALLAH ya rayata ta haifa mana yara da yawa duk a raba mana”.      “Amin Daddy”. Nimrah ta faɗa cike da farin ciki. Maida mata ita yay a kwalin. “To ya sunanta?”.       “Uhmm Daddy sai Ruky ta dawo zamu saka mata suna”.      “Oh na manta, Ussaina bata yanke hukunci sai Hassanarta na nan. Bari na wuce idan an saka sunan maji a waya”.           Nimrah na dariya ta ce, “Daddy ALLAH ya tsare hanya. Ka gaida Ammie da su Aunty Ma'u gobe zamuzo daga nan muje gaida Grandpa tunda Grandma taƙi dawowa daga ƙauye. Sai mu wuce mu gaida Ummu da Grandpa suma ko”.       “Tunani mai ƙyau Daughter, ALLAH ya kaimu. Amma ki kwantar da hankalinki ma su Asma'u suna hanyar zuwa nan gaida Mammah suma.”      Wani irin farin ciki ya sake kamata. Tai ciki tana murna da faɗin zataje tai ƙwaɓa fulawa nayin ɗanwake da kalallaɓa”.      Fuskarsa da murmurshi ya bita da kallo harta shige. Kasa riƙe abinda yake ayyanawa a zuciyarsa yayi sai da ya ambata, “My Zaki ɗiyata ta zama macen nan da kake tunanin za'a jima bata kai ba, Abu na farko kenan da zai fara baka mamaki idan ka taka ƙafarka a gidan nan”. Sai kuma ya sake sakin murmushi yana girgiza kai saboda hasaso cakwakiyar dake gaba. Har yanzu Nimrah bata san akwai aure a kanta ba, shiyyasa suke kaffa-kaffa da al'amarinta ko nan da can ba'a barinsu zuwa su kaɗai sai da driver ko Mu'azz.. dai-dai yana isowa wajen motarsa, kallon da yaron nan da akace malaminsu ne ya faɗo masa a rai. Juyawa yay ya kalli gate ɗin, sai yaga sabon drivern nan daya sakama alamar tambaya ne kawai a wajen yaron baya nan alamar ya wuce. Lallai dolene yay saurin tsaida wannan alaƙar, dan ya lura akwai wani abu mai girma a idanun yaron game da Nimrah. Mota ya buɗe ya shiga, bayan an buɗe masa gate ya fice yana mai kallon agogon motar dan yana son daga massalaci ya ziyarci Janar ne su tattauna batun ƙarasowar Zak-Shadow gida tunda likitoci sunce bawani damuwa, sai dai sakamakon gwaji ɗaya da ake jira kawai yau ya fito suji...... >>>>>>%<<<<<<               Bayan sakkowa massalacin juma'a gidan Mammah ya kacame da hayaniya. Tuni su Ruky sun dawo gida, ga yaran gidan Uncle Nasiru da matarsa Hajiya Zuwairah da kowa ke kira (Ummu). Yaya Imam, Aunty Halimatu, sai ƙawa aminiyar su Ruky Bintu, da autoci Sadiq da Adam. Hakama daga gidan Daddy Imran akwai Babban Yaya Haysam da suke kira Khalifa, sai Asma'u dake bimasa suna kiranta Aunty Ma'u, Ruƙayya ke bima Asma'u, sai Auta Marwan suna kiransa (Lolo). Yaran Aunty Ummi huɗu suma sun iso, Firdausi itace ke bima Mu'azz, itama sa'anni suke da su Nimrah, sauran uku duk maza ne. Abdul-rasheed suna kiransa Dady, sai Harun, da auta Saddam. Sai na Aunty Mimi itama uku. Ita kam duk maza ne da ita jinjirarta ce kawai nace a yanzu, Fu'ad, Salman, Ishaq. Sai na Aunty Momy huɗu itama. Maza biyu mata biyu. Kasancewar mazan sune manya matan sai suka kasance ƙanen su Nimrah. Itama tana da Na'eem, dan sunan surukinta yaci suke kiransa Na'eem, sai Sauban. Matan Nusaiba, da Khairat.        Tunda aka kammala kaya-kayar cin abinci kowa yaja sa'anninsa suka dasa hirarsu. Halimatu da Asma'u suna tare da Aunty Biebah duk da dai ta girmesu, sai dai da yake suma sun gama cika ƴammata sunfi su o'e ƙwailoli iyayen kankanba da rashin ji nustuwa😂. Sai Imam, Mu'azz, Khalifa suma suna ɗakin Mu'azz abinsu matasan samari kenan ƴan shiga jami'ar bana. Suma sauran na ƙasan kowa yaja tashi da irar sai ƙananun sosai su Afrah dake manne da Mammah da Ummu.       Ƙawayen juna masu ji da tashen farkon balaga ma dai suna can sun kulle kansu a ɗaki ana cafta. Nimrah, Ruky, Bintu, Feedo. Kai da kaji yanda suke hirar kasan basa ɗaukar kansu fa ƙwailoli sai manyan ƴammata. Dan Feedo ke basu labarin saurayi da tai cousin ɗinsu daya dawo daga karatu Saudiyya shine fa aka baje kolinsu cike da iyayi ana cafkewa......          ++++++++++++++        Da ƙyar abokin ma'aikacin hotel ɗin nan ya yarda ya biyoshi kiran Adeel, sai da yazo yaga kuma mai kiran nashi duk ya rikice. Dan duk da bai san waye Adeel ɗin ba a zahiri abubuwan dake zagaye da shi ya tabbatar masa wani shegen duniya ne.        Cike da gadara kuwa Adeel ya ajiye masa rafofin kuɗi masu kauri yana sanar masa buƙatarsa akan gidan da yake zaune yake son ya bashi wajen zama a ciki. Sannan ya masa bayani akan gidan su Nimrah. Gaye yaga kuɗi duk ya gigice, yo dala wasa ce. Jiki na rawa ya tabbatar masa da ya amince yazo su zauna. Batun gidan su Nimrah kuwa yace shi ba komai ya sani game da su ba gaskiya, amma yana gaisawa jefi-jefi da wani yaron gidan da safe idan ya fito zaije jugging shima zai je.          Fuska a ɗan yamutse Adeel ya ce, “Ba damuwa wannan alaƙar ɗin ta wadatar. Zamu iya wucewa gidan naka yanzu, dan bana son ɓata lokaci. Miye sunan ka?”.      Da ɗan rawar baki yana kallon abokinsa ma'aikacin hotel ɗin ya ce, “Yohana!”.           “Okay yayi, zamu iya tafiya”.      Duk da zuciyarsa na rawa haka ya amince, dan shi da abokin nasa ma suka ɗauki ƙaramin traveling bag ɗin Adeel ɗin daya kasance ƙaramin troly ne zuwa harabar hotel ɗin. Sai dai yabar wasu ɗan abubuwan sa a ɗakin hotel ɗin dan haka da card ɗin buɗe ƙofar ma ya wuce. Kusan ƙarfe takwas suka iso anguwar, ko'ina da haske fes ga anguwar shiru babu hayaniya sai securitys kawai dake kai kawo. Ta gaban gidan su Nimrah suka wuce. Sai Adeel yaji kamar ya sauka anan ya shiga ya ganta. Sai dai babu dama. Tsakanin gidan Yohan da gidan su Nimrah bai wuce gidan huɗu ba. Kuma su suna ɗayan hannun ne ta yanda daga gidajen su Yohan ɗin ma kana iya ganin gate ɗin su Nimrah tsaf musamman idan kana upstairs ne. Can ma gate aka buɗe musu suka shiga, da yake wani ɗan ƙaramin estate ne yake, mai ɗauke da apartment da basu wuce goma ba gaba ɗaya.........✍️ ..........“Tofa, gyaran gidan nan aka sake yi haka Aunty Nabeeha?”.         Ɗago kai Nabeeha da hankalinta ke kan wayarta tai ta kalla gidan a karo na farko. Ba ƙaramin ƙyau gidan yayi ba kam dan tun daga waje zaka shaida hakan, flowers ɗin da suka ƙawata katangar gidan ta wajen kawai abin kallo ne, ƙamshinsu ya cika wajen sosai kuma. Balle baƙin gate ɗin. Ajiyar zuciya Nabeeha ta saki a hankali batare da tace komai ba. Ismat da Raihana kuwa suka cigaba da santin su har Malam Buba ya leƙo sakamakon horn da Ismat ɗin tayi dan itace ke jan motar.      Malam Buba bai sansu ba, dan haka ya fito sosai yana tambayar “Su waye ku?”.      Sai da duk sukai masa kallon sama da ƙasa, a yamutse Amima uwar rashin kunya ta ce, “Matar gidan ce da ƙanen ta”.         “Kiyi haƙuri Hajiya kumin bayani yanda zan gane, ni baƙone anan, dan dole zan fara sanar da masu gidan kafin na barku ku shiga”.      Sai a lokacin Nabeeha da taja tsaki ta kallesa a wulaƙance. “Kai sha-sha-sha ka buɗe mana gate mu wuce. Shi gidan ya zama na shugaban ƙasa ne yanzu da ba'a shigarsa sai da doka komi?”.         “Ba haka bane Hajiya, ina kan aiki na ne”.     A fusace Amima ta buɗe ƙofa ya fito, hakan kuma yay dai-dai da isowar taxi wajen. Ba kowa bane a ciki sai ainahin maigadi da baƙonsa. Malam Buba ya maida hankalinsa kansa yana ɗan murmurshi da faɗin, “Alhamdulillahi Malam Almu sannu da zuwa?”.       “Yauwa Malam Buba, mun sameku lafiya? Ya na ganka a waje haka kai da su way....”       Ya haɗiye sauran maganar saboda ganin Amima. “A'a Hajiya ashe kune, sannunku da zuwa. Malam Buba buɗe musu ƙofa ai ƴan gida ne”.       Amsa masa Malam Buba yay yana juyawa, Amima kuwa taja tsaki tana komawa cikin motar dan ta fito ne da shirin wanke fuskar mutumin nan da mari. Sai da motar tasu ta shige Malam Almu ya kalli abokin tafiyarsa da ya ce, “Su kuma su wanene su?”.     Cikin ɗan sauke ajiyar numfashi Malam Almu ya amsa masa da, “Matar Baban yayansu ɗin nan da nake gaya maka sunce yana ƙasar waje ce, sauran ƙanenta ne. Ba zama take a gidan ba sai lokaci-lokaci take zuwa tana iskance-iskancenta. Nama fi shekara uku banga ta sake zuwa ba sai yau”.      Kai kawai ya jinjina masa batare da yace komai ba, daga haka suka shige ciki suma. Malam Buba nata jera musu sannu, ya kawo musu ruwa sannan ya zauna suka gaisa yana tambayar mai jiki. Malam Almu ya ce, “Da sauƙi sosai, ɗan uwana dake Niger yazo ya tafi da ita can a nema mata magani, shiyyasa ƙanina ma ya biyo ni nan dan kar a barshi shi kaɗai. Sunansa Sanda”.         “Kai masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Malam Sanda sannu da zuwa kaji”. Yay maganar yana bama Sanda hannu suyi musabaha. Hannun shima Sanda ya bashi suka gaisa.. Dai-dai nan Rayhana ta ƙaraso wajen cike da tsawa da gadara ta ce, “Kai wani yaje can sashen ya amso mana key ɗin ɓangaren mu”.     Su duka kallonta sukayi, Malam Buba zai yi magana Malam Almu ya katsesa da faɗin, “Hajiya ai ɓangaren nan babu komai a cikinsa tunda aka kammala aikin gidan nan. Ina ga zaifi ƙyautuwa ku shiga wajen hajiyar da kanku dan tana nan. Ko ta fita ne Malam Buba?”. Yanda yay maganar ƙarshe yana kallon Malam Buba da sigar tambaya ya sashi amsa masa da, “A'a tana nan bata fita ko ina ba. Dan yau ma gidan cike yake da baƙi kamar jikokin gidan ne duk suka zo. Sai dai naga matan su Ja'afar sun fita su kam”.       “To kinji Hajiya, ku shiga kawai zai fi”.     Harara Rayhana ta zuba musu su duka, batare da tace komai ba ta juya ta koma inda su Nabeeha ke tsaye a ƙofar sashen nata suna jiranta. Abinda ta sanar musu ya saka Nabeeha jan tsaki. Cike da takaici ta ce, “Nifa ban son iyayi, to ina suka kaima mutane kayansu?”.         “Muje dai wajen Mammah ɗin sai muji kamar zaifi”. Ismat ta faɗa tana binsu da kallo....        ★Gaba ɗaya falon ya cika da hayaniyar su Aheel dake wasan guje-guje, sunma falon kaca-kaca da tarkacensu. Amma hakan bai hana Mammah dake zaune yin hirarsu ita da Ummu (Hajiya Zuwairah matar Uncle Nasiru) hirarsu ba. Sun juyama ƙofa baya, hakan yasa har su Nabeeha suka shigo falon basu sani ba. Babu tabbacin sunyi sallama ko a'a, sai wani kallon yaran suke a yamutse kamar sunga wasu abin ƙyama. Yaran da suma shigowarsu bai hanasu wasan su ba duk da wasu sun gansu wasu basu lura da su ba, Abees dake bin Ishaq da bindiga da aka zuba ruwa ciki yana fesa masa suka iso inda suke. Ishaq ya shige tsakkiyarsu yana ɓoyema Abees suna dariya, shiko Abees ya cigaba da fesa ruwa har a jikinsu. Cikin wani irin takaici Rayhana ta kwaɗe Abees da marin daya saka yaron sakin gigitacciyar ƙarar data saka su Mammah juyowa da sauri. Dai-dai Nabeeha ta finciko Ishaq dake bayanta ta hankaɗashi kan Abees itama. Wannan al'amari na mari da hankaɗewa yayi dai-dai ne da fitowar Nimrah daga lungun ɗakinsu ɗauke da magenta zata haɗo mata madara. Magen ta dire saman stairscase tayo wajen ranta a ɓace.      Miƙewa Mammah da Ummu duk sukai suna kallonsu, haka sauran yaran tuni sunyi tsit kamar anyi ruwa an ɗauke. Sai khairat ce mai ɗan wayo ta ƙaraso inda su Abees suke da sauri. Isowar Khairat dai-dai da ƙarasowar Nimrah da babu ma wanda ya lura da ita a kaf falon sai yanzu. Kafin Mammah data buɗe baki zatai mata magana tayi kawai sukaji saukar mari mai ƙara a fuskar Rayhana, ba kuma kowa yayi mata shi ba sai Nimrah. Kafin ma Rayhana ta dawo cikin hayyacinta ta watsama su Amima da suka wani yunƙuro kanta a fusace manyan idanunta.      Babu tsoro babu shakka duk da sun fita girman jiki da tsayi, dan ma itama ɗin dai doguwar ce, amma kasancewar sun girmeta nesa ba kusa ba sun fita tsayin. Amma tsabar bushewar idanu ko'a jikinta. Sai ma cike da gargaɗi da kaushin murya ta ce, “Oh zaku rama mata ne?”.       Cikin matsanancin baƙin ciki Amima ta ce, “Ai ba rama mata mari kawai ba duka zaki ci”.          “To bari kema na baki rabonki sai ku rama mata ɗin”. A bazata ta sake sauke wani marin a fuskar Amima. Rayhana ta yunƙuro zata cakumeta tasa ƙafa ta taɗeta sai gata a ƙasa wanwar. Ai ko yaran suka saka ihun dariya suna tafi da tsalle da faɗin, “Aunty Ninah! Aunty Ninah!”.      Inda suke yanzu kam Mammah ta iso, dan Nabeeha ma ta yunƙuro kan Nimrah zata cakumota, sai dai Nimrah ta riƙe hannun nata tana mata kallo mai cike da rashin kunya da tsiwa. Yayinda Amima ta cakumi rigar Nimrah ɗin ta baya, Ismat da hankalinta ya tashi dan ita bata fatan ayi wani abu mara ƙyau ita dake fatan samun fada ta shiga janye Amima tana faɗin, “Wai miye haka dan ALLAH.”         “Nimrah! Sake ta”.    Mammah data iso wajen ta faɗa idonta akan Nimrah. Tashin hankali, duk fa wannan abu dake faruwa su Nabeeha basu gane Nimrah ba, haka ma Nimrah bata gane su ba, dan sanin datai musu na ƙuruciya ne, zuwan da sukeyi jefi-jefi kuwa basu taɓa haɗuwa ba tana makaranta, idan ma sun kwana kasancewar randa suka shigo kawai suke zuwa gaida Mammah harsu wuce bata ganinsu. Suma kuma rabonsu da ita tun tana ƙaramar, tsabar yanda suka tsaneta basu taɓa sha'awar idan sun zo gidan su ganta ba musamman Nabeeha. Sai gashi a yau yarinyar da suka sani mitsila ta zama budurwa, ga hasashen ƙyawu da sukama yarinyar a baya ya tabbata. Dan kuwa Nimrah akwai dogon hanci da ɗan bakinta dai-dai ita, ga manyan idanu farare tas da suka ƙawata baƙar doguwar fuskarta mai cike da tsiwa da rashin tsoro. A tsaye yarinya ce doguwa, duk da ƙirjinta ba wani cike yake taf na wuce misali ba komai dai ya bayyana na yammatanci, dan doguwar rigar jikinta ta fitar da komai, tun daga tudunsu har zuwa shafaffen cikinta da kugunta mai faɗi kaɗan dake tabbatar da nan gaba shekaru suka ƙaru zai sake buɗewa sosai, dan ko a yanzu ka kalleta kasan akwaisu har sunfi na Amima da Ismat ɗin ma dake kusan 27years a duniya. Baƙar fatarta kuwa sai wani sheƙi take da ɗaukar idanun mai kallonta, da gani kasan zatai laushi da sulɓi dan babu ɗigon ƙurji balle tabonsa a fuskata. Kanta ba ɗankwali, hakan ya bayyana gashinta mai yawa duk da kitsone a kanta shiku yama ɗan tsufa.       Maganar da Mammah tai ya sakata sakin Hannun Nabeeha datai sumar tsaye, dan ambaton sunan Nimrah da Mammah tayi sai da taji kamar an kwaɗa mata guduma a saman kai ne, ta wani kafe yarinyar da ido ko ƙyaftawa batayi. Hatta su Ismat sunyi wani irin kasare suna kallon Nimrah, dan harta doke hannun Amima data riƙe mata riga ta baya da alama itama tayi sumar tsaye ne. Dan da gaske fa ƴar yarinyar da bata kai ko sha shida ba ta fisu jikin mata, sai dai su nuna mata shekaru kawai da farar fata. To zama a iya jera masu farin nasu gaban maza ɗari su tsallakesu su zaɓi Nimrah ɗin dake baƙa, dan mazan sun gama zige mata da kalmar fara ko mayyace duk sunbi sun kwaile jikinsu yanzu sun dawo baƙaƙen suke kwashewa sukai gidan aure. (Yo ko mijinki kika biyema da kankare can, tada can, ALLAH sai kin gama wahala da kashe kuɗin da ɗorama kanki ciwuka ƙarshe ya auro wadda bata kaiki komai ba ya sota ya tiritata🤣. Kai mata ku dawo habkalinku, babu biyayya ga abokin halitta akan saɓon UBANGIJI. Wanda ya halicceki ya fiki sanin abinda ya dace dake. Kici abinci mai ƙyau da nagarta kiga yanda zakiyi ƙyau, ba shafe-shafe man gyaran fata da ƙarin haske, ko saka gashi da farce, kankare gira shan supplement na ƙarin baya da gaba, ƙarin girar ido kankare haƙori ke saka mace ƙyau ba. Kiyi ibada, kici abinci mai ƙyau, ki kwantar da hankalinki kiga ƙyau hajjaju, wlhy kyau na asali UBANGIJI kawai ke bada shi ba shirme da sabon ALLAH ba. A duk sanda kika damu da yin ƙyau dan burge mutanen duniya sune zasu taru su zageki da tsine miki kafin zuwa gaban UBANGIJI da kika saɓamawa kika nuna bai iya ba sai ke ƴar iya😏🙄).........✍️ KIƊA A RUWA 2 39 ........Mammah data fahimci halin da suka shiga da yanda suke kallon Nimrah ɗin sai ta ɗan murmusa, batare da ta sake magana akan abinda ya farun ba ta kama hannun Nimrah tana barin wajen da faɗin, “Bismillah ku ƙaraso ku zauna”. Sai da suka kalla juna, kafin su bi bayanta jiki a saɓule. Karasowar su falon dai-dai Nimrah da Mammah ke miƙama ruwa alamar tasha na faɗin, “Mammah su waye su?”. “Sha ruwa”. Mammah ta faɗa batare data bata amsa ba. Sai da ta tura baki gaba sannan ta amshi ruwan tasha. Ismat dake fatan al'amarin ya tsaya iya haka ta zamo a kujera tana gaishe da Mammah da Ummu da taƙi cewa komai sai mamakin ma ganinsu Ismat ɗin daya cika zuciyarta. Saboda tuna kusan wata ɗaya kenan da kiran Jiddah da sukai akan an hanasu baro Dubai. Da mamaki Nabeeha da su Amima ke kallon Ismat, itako ta fuske dan tasan abinda tai shine dai-dai. Mi Nabeeha ɗin ta gani oho mata, itama sai ta daure ta gaida Mammah kaɗai banda Ummu. Mammah ta amsa mata da kulawa tamkar komai bai faru ba, harda tambayarsu mahaifiyarsu. Nabeeha ta ce, “Tana lafiya. Mammah dama zamu amshi key ne”. Ɗan murmushi Mammah tayi da kallon Nabeeha da ƙyau. Ta ƙara ƙyau sosai da ƙiba alamar tana cikin kwanciyar hankali da ƙoshin lafiya. Cike da dattako ta bata amsa da, “Aiko akwai matsala Nabeeha, dan sashen nan naku babu komai a ciki. Tunda za'ai gyara aka fidda komai, abubuwanku masu muhimmanci ne kawai aka bari suna cikin nan sashen ma, amma funichars duk an bada su kuma ba'akai ga zuba wasu ba ganin ba kowa ke zama ba kar aita asara”. “Amma Mammah da an gaya min kafin a kwashe ɗin, musamman kayan bedroom ɗina dana kitchen dan duk ina buƙatarsu. Gashi na ajiye abubuwa masu muhimmanci da sirrina ne da ya dace ace ni da kaina na ɗaga su a wajen ba wani ba”. Zuwa yanzu Nimrah ta fahimci wacece a gabata, wato matar Dada data taɓa yankata a cinya, har yanzu tabon na nan kuma. Yanda takema Mammah magana cike da rashin taunawa da girmamawa, yasa zuciyar Nimrah sake zuwa wuya. Hakama Biebah da duk suka fito zuwa yanzu ranta a ɓace ta ƙaraso wajen. Sai dai da ido Mammah tai musu gargaɗi su duka akan kada suce komai. Dan kusan lokaci guda Nimrah da Biebah ɗin suka yunƙuro zasu bata amsa. Babu yanda zasuyi, dan Mammah tafi ƙarfin basu umarni su tsallake. A karo na farko Ummu tai magana tana kallon su Nabeeha ɗin. “Amma wannan maganar taki babu tarbiyya a ciki, dan ko Adda A'isha bata haifa miki Haysam ba matsayin ƙanwar mahaifinku take Nabeeha. Kayan da kike magana basu suka taɓa miki ba ai Jiddah ce tai komai da ƴan uwanki su Halimatu”. Rai ɓace Nabeeha ke kallon Ummu, sai dai kafin ta fara maganar da take tattarowa a zuciyarta Ja'afar da suke shigowa shi da Yaya Ma'aruff, Bilal da Ammar ya katseta. “Ummu daina ɓata lokacinki wajen yi mata bayani. Ke Nabeeha kike ko wa? Tashi ki tattara waɗanan tarkacen ku wuce anan.” Wani mugun kallo Nabeeha ta zuba masa. Ya ɗage gira sama cike da rashin mutunci. Tasan waye Ja'afar dan karonsu babu daɗi. Shi da Ma'aruff shegen zuciya ne da su mai zafi fiye data Dada, kawai dai su suna da barkwanci ne da hira ba kamar shi da baida yawan magana ba. Sannan shi akan jima ba'aga fushinsa ba saboda ya iya shanyewa... “Malama kina kallona ko akwai magana ne? Nace ku tashi ku bar mana gida..” “Ni kuma twiny na ƙara mata da gargaɗi na ƙarshe. Kada na sake ganinki a wannan gidan namu, dan baki da sauran hurumin zamansa sai in har Dada ne ya dawo yace ki dawo da kansa. Yanda kika saka ƙafa kika fita da kanki, ki cigaba da zama acan bama buƙatarki a cikinmu. Idan kuma taurin kai yasa kika cigaba da zuwa kina nunama mahaifiyarmu rashin tarbiyyarki, wlhy Ninah da Ruky kaɗai zamu barki da su sai sun saitaki a layi”. Ma'aruff ya ƙare maganar yana nuna mata Nimrah da Ruƙayyan. Aiko ƴar wulaƙancin suka wani tuntsure da dariya Nimrah na faɗin, “Yess Uncle, wlhy ni kaɗai na ishesu su duka ma koba Buddy na. Idan mutum shi ɗan daba ne mai yankan mutane da wuƙa, ni Zakanyar Mammah ce mai kai manyan namun dawa ƙasa harma da ƙananu. Darje baki nake cikin ƙasa, na cikashi da ƙasar taf ta yanda zai iya yima manya magana”. Ihu Ruky da Bintu da Fiddo suka saka cike da ƙarin haushi suna faɗin, “Naja bomb! Naja bomb! Sai dake Zakanya, Trouble Queen”. “Mai bombing ɗin ƙananun tantirai ba”. Nimrah ta basu amsa cike da salon iyayi tana wani juya manyan idanunta. Yanzu kam dariya harda su Yaya Ja'afar ɗin, Mammah ta kai mata rankwashi. Tashi tai da gudu tana dariya taje bayan Aunty Biebah ta maƙale. Ummu dake murmushi itama ta ce, “ALLAH ya shirya ku yaran nan. Nimrah dai kin zama Gang leader? Ga mabiya nan irinki kin tara yayunku kuma na ɗaure muku ƙugu. Bari Abban Jiddah yazo aure zance ai muku”. “Aure Ummu?”. Suka faɗa a tare suna waro idanu. Asma'u dake dariya tace, “Wlhy Ummu da kin taimake mu, dan yaran nan jinsu suke kamar muma sun girmemu ma”. Amshewa Halimatu tai da, “Ashe angunan zasu sha shirme da rashin kunya”. Cike da shagwaɓa suka kalla su Uncle Ma'aruff a tare sukace, “Uncles kun gansu ko? Ai dama sun saka mana ido”. “Ku barsu sune za'aima aure ba kuba”. Cewar Bilal yana kallon Asma'u ƙasa-ƙasa. Cike da farin ciki suka dawo inda yake suna ma su Asma'u gwalo. Su Nabeeha sun fahimci fa an ma manta da su a falon gaba ɗaya, yayinda Ismat ta shagala a kallon Ja'afar idanunta cike da ƙwalla. Shi ko ko kallon inda take ma baiyi ba. Bare ma da taga su Aheel sunzo inda suke sai taji wani kishi ya cika mata ƙirji, tana jin inama itace ta haifi su Aheel ɗin..... _____★ Tunda Adeel ya dawo gidan Yohan baida aiki sai zaman balcony dake facing gate ɗin su Nimrah. Ga alaƙa ta ƙullu tsakaninsa da Ammar a dalilin fita morning jugging. Dan a washe gari saka Yohan yay suka jira har Ammar ya fito a gida, kasancewar sun saba gaisawa normal Ammar ya bama Yohan hannu suka gaisa, sannan ya bama Adeel shima. Daga haka suka fara abinda ya fito da su, suna gudu kaɗan-kaɗan Yohan ke gabatar da Adeel ga Ammar matsayin abokinsa. Hannu biyu Ammar ya amshesa, haka sukaje suka dawo tare, su suka shiga gida shima ya wuce. Tun daga ranar kuma sai hakan ta cigaba da faruwa, kamar wasa bayan kwana biyu suka haɗu a massalacin anguwar nan ma, tun Ammar baya wani sakin jiki da Adeel bayan gaisuwa harya fara suna ɗan yin hira kaɗan-kaɗan. Yau ma kamar yanda ya saba yana a balcony ɗin tsaye, gaba ɗaya kuma hankalinsa akan gate ɗin gidan yake. Kunensa da headphone mai shegen ƙyau, sai dai babu tabbacin waƙa yake ji ko wani abun daban. Ganin an buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ya sa ya ƙara nutsuwa da maida hankalinsa da ƙyau, cikin wata irin bazatar mamaki Nabeeha dake fitowa ta bayyana cikin idanunsa. Da sauri ya cire headphone ɗin daga kunnensa dan tsabar mamaki, ya ciro wayarsa ya shiga camara. Zooming ɗinta yay ta ciki dan gani yake kamar idanunsa ne ke faɗa masa hauka. Itace ɗin kuwa idanunsa ba ƙarya sukai masa ba, dan dai-dai nan Ismat ta fito itama tana waige-waige alamar nemanta take. Ganinta a gefe ta dafe kai da hannu ya sata ƙarasawa inda take da sauri, sai dai baya jin mi take ce mata har aka wangale gate ɗin duka mota ta fito. Dai-dai inda su Nabeeha suke Rayhana tai parking, buɗe motar da fitowar da sukai ita da Amima suma suka nufi su Nabeehan ya sake cire masa tantama. Sai ma ya rasa abin cewa shi kam. Yana anan tsaye tamkar wani gunki Yohan daya fito ya kai dubansa inda yake kallo, bai san su waye matan ba, dan haka ya juyo ya kallesa tare da faɗin, “Sir ka sansu ne?”. Shiru kamar Adeel bazai tanka ba sai kuma ya ce, “Ba saninsu bane mai muhimmanci, sanin alaƙarsu da wannan gidan. Zaka iya bincika min”. Received at 4:37 PM “Nima irin wannan tunanin naki na zomin a rai. Musamman dana fahimci ba tayi wani serious bane kan batun sai ma zancen ƙulla auren da suke sonyi tsakanin ƴar su da ɗan shugaban kasa. Duk da yaron ya nuna ba sonta yake ba sun nace.” “Kinji ba! Ai halin ɗan Adam sai shi wlhy.” Da wannan zantukan suka fice a gidan batare da sunma yaran nasu sallama ba. Sai fitar motarsu sukaji a gidan. Da wannan damar Ismat tai amfani ta fito itama tabar gidan da kaya niƙi-niƙi. Sai dai maigadi ta saka ya tare mata taxi a waje bata ɗauki motar kowa ba. Dan dama dai Mamansu da Aunty Mamawo da Nabeeha keda mota kawai a gida. Su basu da ita...... ================ Anan gidan Mammah bayan tafiyar su Nabeeha Malam Almu ya kawo ƙaninsa ciki dan su gaishe da Mammah su mata barka da dawowa. Da fara'a kuwa ta tarbe su. Tare da amsa musu gaisuwa da kulawa tana tambayar Malam Almu mai jiki. Kamar yanda yay ma malam Buba bayani itama haka yay mata duk su Yaya Ma'aruff na jinsa. Ya kuma nuna ƙaninsa Sanda ya musu bayani a kansa da aiki da ya fito nema idan ya samu. Sai dai bai nuna anan gidan ba kamar yanda suka shirya. Cikin sa'a kuwa Mammah ta ce, “To ai bai kamata yay nesa da kai ba ko Malam Almu. Sai a bincika anan idan da wani aikin sai ya dinga yi, kaga sai kuyi zamanku ka samu abokin hirar dare tunda shi driver ba kwana yake ba yana tafiya gida da yamma”. “Nagode Hajiya Mama, ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Sanda kayi godiya mana”. Godiyar Sanda ya fara shima kamar yanda yaga malam Almu nayi, suka juya suna sake godiya gasu Yaya Ma'aruff suma. Sai da Mammah tace ya isa sannan sukai shiru. Daga haka ta ɗan yima Sanda tambayoyi yana bata amsa. Kai ta dinga jininawa cike da nazarin al'amarinsa, kafin ta sallamesu su koma bakin aikinsu... Suna fita Yaya Ammar ya ce, “Mammah wai baƙya jin tsoron ɗauke-ɗauken nan kada wataran mu ɗauki abinda zai dame mu. Yanzu fa akan al'amarin Dada kowa zai iya shigowa jikinmu dan ya cutar damu. Shiyyasa kikaga ma Yaya Imran kullum yana kaffa-kaffa”. “Hummm Ammar kenan, banda abinka bawa na iya gujema ƙaddararsa daman? Duk abinda kaga ya faru hukuncine na UBANGIJI. Jarabawa ba tawaya bace. Ba kuma faɗuwa bace ga bayi, sau tari kankarewar zunubi ce ko tsanin nasara daga wata ɗaukaka da UBANGIJI zai kai bawa kanta. Kar ku damu da makircin masu makirci, idan duk wanda ke zagaye da kai mugune mai fuska biyu, in har ka tsaida gaskiya, kai ka zauna da shi da kyakkyawar zuciya bisa umarnin ALLAH, wlhy ko shine ibilis akan sheɗanci da mugunta sai dai yayi ya barka. Dan shi bai isa canja komai daga ƙaddararka ba koda murmushi fuskarka ne, sai dai yayta wahalar banza da ɓata lokacinsa akan ka amma ko badaɗe ko ba jima saika cimma wannan nasarar. Ƙilama UBANGIJI yay masa tsahon ran da zai koma neman taimakon ka. Kudai kuyi addu'a kawai, idan ma da manufa mutum yazo mana, ALLAH zai hanashi nasarar cutar damu. Shima da yake can ALLAH zai kuɓutar da shi idan lokaci yayi, dan bana yanke ƙauna da rahamar UBANGIJI akan Muhammad zai fito ya dawo garemu. Ban taɓa jin na sare akan wannan fatan ba, duk da ina jin tsoron kar su cutar mana da shi. Amma ALLAH na tare ta shi, addu'a ta da taku na tare da shi. In sha ALLAHU indai gaskiyarsa ce ta kaisa wancan wajen komai tsahon lokaci zata ƙwatoshi daga hannun azzaluman makirai...” “In sha ALLAHU Mammah”. Suka faɗa a raunane, Biebah da Ammar kuwa sai da suka share hawaye. Su Ja'afar dai idanun sun canja launi amma babu hawayen. Su Nimrah dake laɓe suna sauraren su suma dai duk jikinsu yayi sanyi. Cikin Zuciya Nimrah ke jin tana son sanin inda Dadan yake? Miya faru da shi? Mi ake ɓoye musu game da shi?. A zahiri kam batace komai ba ta nufi komawa ɗakinsu, sauran duk suka bita dan dama tun shigowar maigadi Mammah tace su koma ɗaki abinsu. Shine suka laɓe, da farko dariyar shigar ƙanin Maigadi suka maƙe sukeyi, dan yayi wani shigar gayun ƙauye irin masu iyayin nan ne abin dariya...... •••••••••••••••••••••••••••••• ★ONE WEEK LATER★ ★10:15 AM★ SECRET MEDICAL BASE “Colonel Imran… mun kammala dukkan gwaje-gwajen da muka yi masa.” Dr. Idris Ali, ya faɗa yana ɗan gyara gilashinsa. Imran bai ce komai ba. Ɗaga masa kai yay alamar ya ci gaba. Doctor ya jinjina kansa, kafin ya buɗe baki ya cigaba da faɗin, “Mu godema ALLAH jikinsa ya nuna ƙarfin juriya mai ban mamaki. Idan ba haka ba, da gubar da aka saka masa ta riga ta yi mummunan tasiri a lafiyarsa zuwa yanzu.” Cikin wani irin bugawar kai Faro ya ɗan matsa gaba, murya ƙasa-ƙasa da alamar tashin hankali a ciki ya furta, “Guba kuma Doctor?”. Dr. Idris ya ɗan numfasa, kamar yana neman kalmar da zai musu bayani da ita da bazata ɗaga musu hankali ba fiye da kima. “Eh. Poisoning ne… dan abinda sakamakon bincikenmu ya nuna mana kwanaki uku kenan shiyyasa ma muka sake masa sabon gwaje-gwaje akan hakan, kusan wannan dalilin ne ya hanamu faɗa muku komai a ranar wednesday data gabata mukace ku saurare mu. Sai dai ku kwantar da hankalinku poising ɗin bai jima da fara shigarsa ba, da dai ya jima a inda yake ne zai cigaba da shiga kamar yanda koma su waye suka tsara, sanan zai dinga tasiri a jikin nasa ne a hankali har sai ya gama yima jikinsa illa ne zai bayyana. Dan haka ko a yanzu babu wani damuwa mai girma. Sai dai idan aka bar shi haka a jikinsa, akwai haɗari sosai anan gaba”. Imran da gaba ɗaya yake jin jinin jikinsa na tsiyayewa tamkar an ɓula ledar ruwa da tsinin allura ya rumtse idanu yana matse hannunsa.........✍️ KIƊA A RUWA 2 40 .........Gaba ɗaya ran Hajiya Hasiba a dagule yake. Koda su Nabeeha suka koma gida da nasu ɓacin ran sun sameta tana faman kai-kawo a falo. Aunty Mamawo zaune itama ta rabga tagumi. Ismat ce kawai tai ƙarfin halin tambayar su ko lafiya? Amima da Rayhana kam da ƙorafin abinda ya faru suka fara. Nabeeha dai ranta a ɓace yake, dan haka bata tankama kowa ba ta wuce upstairs abinta. Dan a wannan gaɓar ta gama yarda dole ta nemawa kanta mafita. Mafitar kuma ɗaya ce jal shine komawa gidan su Haysam. Dan a can ne kawai zata samu damar maganin wannan shegiyar mayyar yarinyar da ganinta ya gama birkita mata dukkan lissafinta, sannan ta samu mafakar gujema Adeel da bata san manufarsa ta biyosu ƙasar nan ba. Tsakanin Aunty Mamawo da Hajiya Hasiba babu wanda ya kula tambayar Ismat, sai ma umarnin su wuce ciki da Mamawo ta basu. Hakan ya sake tabbatar musu babu lafiya. Wucewar sukai, dan sun san halinta da masifarta bata musu ta wasa. Shiyyasa ma suka fi son Hajiya Hasiba dan tafita sauƙin kai. Koda suka hauro saman ma kowa inda yafi masa ya nufa, dan kowa da abinda ke ransa da zuciyarsa. Ismat dai a wannan gaɓar ta gama yanke shawarar komawa gidan mahaifinsu. Dan tayi alƙawarin bazata sake komawa Dubai zama ba sai inda ziyara itama tare da mijinta Yaya Ja'afar in sha ALLAHU. Dan a wannan karon yaƙi zatai ɗan gaske babu gudu babu ja da baya. Ta share ƙananun hawayen da suka cika mata ido, wani irin wutar sonsa na sake ruruwa mata a zuciya, saboda ganinsa ba ƙaramin tayar mata hankali yayi ba. Ya ƙara ƙyau da cikar jiki da buɗewa irin ta magidantan dake samun dukkan gata a wajen iyalansu. Tunda yay auren nan bata yarda taga matarsa ba saboda bata buƙatar hakan, amma a yau tana jin kwaɗayin ganin Shariffa ɗin duk da ta santa dama can. Akwatin kayan da tazo dasu daga Dubai ta buɗe, kasancewar ƙaton gaske ne dama kuma ta haɗo komai nata mai muhimmanci daga can sai ta sake tattare na nan gidan ma ta loda a ciki, ganin ya cika da yawa ta sake ɗaukar wani ƙarami ta zuba sauran abinda ya rage ta rufesu. Bakin gado takai zaune ta ɗauki wayarta ta fara kiran Aunty Jiddah. Gidanta take son fara zuwa, dan tai mata rakkiya gidan Abban. Da mamaki Aunty Jiddah data ɗaga wayar ta ce, “Yaushe ke kuma a gari haka?”. “Aunty mun jima da zuwa. Kina gida ne dan ALLAH?”. “A'a ina gidan Aunty Fateema, zata aurar da ƴarta Aminatu muna shirye-shirye dan za'a fara gobe idan ALLAH ya kaimu.” “ALLAH ya sanya alkairi, yaushe zaki koma?”. “Amin ya rabbi. Lafiya kuwa?”. “Aunty zan zo ne, ni dai yaushe zaki koma?”. “Ki tafi kawai ai yara na nan, Shafa'atu ƙanwarsa ma na gidan tazo weekend”. “Okay tom. Ki gaida Aunty Fateeman, in sha ALLAHU dani za'ai kamun gobe”. Daga haka ta yanke wayar tabar Jiddah da mamakinta.... ★ Anan falo kam bayan wucewarsu Aunty Mamawo ta furzar da iska mai zafi tana kallon Hajiya Hasiba. Ta ce, “Aunty tunani ko damuwa bazata kaimu ko ina ba. Kawai muje wajen wani mutimina, shima yana ƙoƙari ya iya aiki, da rafanai yake aiki na tabbata zai mana nasa ƙoƙari kafin muje India ɗin. Dan dole gaskiya muyi wani motsi a wannan gaɓar, dan ina ji a jikina shirun Adeel bazai zama alkairi ba”. “Kina ganin zamu samu mafita kuma?”. “Tabbas Aunty, dan na yarda da aikin Malam Ƙolo sosai”. “To shike nan muje ai kawai mi zamu jira. Dan mutumin nan na tabbatar shima yana can ya bazama hanyar samun damar ganin Haysam, dan gaskiyarki kam shirunsa bazai zama alkairi ba.” “Wlhy ni wannan bai dameni ba Aunty, idan ma ya saka an kashe shi matsalarsu ce. Miye amfanin wani Haysam a rayuwar Nabeeha, banda soyayyar wahala da take masa ma. Garama ya kashesa ta samu wanda ya fisa koda ace zata bar Adeel ne, idan ma babu wata illar da ita First lady ɗin ta ambata ba shike nan ba. Dan ni ban yarda ma da matar ba kin san dai mutane da baƙar hassadar tsiya a wannan zamanin. Kowa yafi son ace shi shine kai kana ƙasanshi kana masa bauta bare ma manyan ƙasar nan”. “Mizai hana nayi hakan”. “Yanzu yanzu fa. Ko zaka kira abokinka ne Ammar?”. “Kodai kayi haƙuri zuwa anjima, kuma ba Ammar ya kamata a tambaya ba dan kar ya zargi wani abun tunda mun samu ya fara sakin jiki damu.” Ji Adeel yay kamar yace bai yarda ba, amma sai ya daure dan baya son Yohan yaga zalamarsa a fili da yawa, har ya kawo masa raini dan har yanzu bai san shi ɗin waye ba. Kuma baya son ya sani har ya gama abinda ya kawo shi ya bar ƙasar nan. Duk da yau da safe yaga saƙon Ummu ɗinsa ta Email akan tana son ganinsa da gaggawa, ya tabbatar koma miye take nemansa a kansa ba na wasa bane. Kuma dole ya amsa wannan kiran dan baya tsallake maganar iyayensa..... Bai sake magana ba sai ma barin wajen da yayi ya koma kan kujerar da take a balcony ɗin ya zauna zuciyarsa fal abubuwa. Dan gaba ɗaya yarinyar can ta rikita masa lissafi ko zancen abinda ya kawo shi ƙasar nan bai sake waiwaye ba. Kai su kansu su Hajiya Hasiba ɗin tunda suka iso bai bi takansu ba, sai ma da yaga Nabeeha yanzu ya tuna da al'amarinsu........... 41 ........Da ƙyar Daddy Imran ya iya fisgo kalma ɗaya wajen furta, “Wace irin guba ce?”.    “Slow-acting toxin. An tsara ta ne don ta lalata jiki a hankali ba kashewa nan take ba. Hakan na nuna wanda ya aikata ya so yaga yana rayuwa cikin rauni ne.”        Shiru ɗakin yay dan kowa da kalar da raɗaɗin da zuciyarsa ke masa akan jin wannan baƙon al'amari mai rikita lissafi. Suna cikin farin cikin babu wani damuwa a tare da Dada a kwaje-kwajen farko, ashe tashin hankalin na gaba. Da ƙyar Faro ya yanke shirun nasu.        “Doctor yanzu minene mafita? Tana da makari ne?”.     Doctor ya ɗan gyaɗa kansa. “Tabbas za'a iya samun makarinta, abin da ya rage mana shi ne inda zamu same sa, musamman a ƙasar nan tamu kuma da bana jin zamu samu ɗin kai tsaye, idan ma mun samu hankalinmu bazai kwanta ba ga duk wanda zai bamun. Dan duk wanda ya samar da gubar dama dole shine mai makarinta. A yanzu kuma mu kowa ba abin yarda bane a wajenmu. Musamman tunda bamu san wanda ya aikata masa haka ba. Sai dai mubi wata hanyar sirri da cikakken tsaron da zamu fitar da ita gaba ɗaya.”     Imran ya ɗago kansa ya zuba masa idanunsa da suka juye jazur. Kai tsaye ya furta, “Waje ke nan?”       “Tabbad Sir! Asibiti na musamman a waje ya kamata mu kaishi. Zaman wata ɗaya zuwa biyu. Idan aka yi hakan da wuri zamu tsare rayuwarsa da cikakkiyar lafiya.”        Komai Imran bai sake cewa ba, sai ma ya tashi tsaye a hankali, sai dai nauyin abin da yake ji ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa da kuzarin jikinsa. Ɗan juyowa yay ya kalla Doctor ɗin, cike da gargaɗi ya furta, “Babu wanda zai san wannan bayan mu ukun nan.”      Dr. Idris ya gyaɗa kai da girmamawa. “Mun riga mun ɗauki rantsuwar sirri ai Sir.”      Imran ya juyo ga Faro, idanuwansu suka haɗu a waje guda. “Zan sanar da shugaban ƙasa yanzu.”     Faro ya ɗan murmusa da gyaɗa kansa, sai dai murmushin da ke ɓoye fushi. “Ka sanar da shi. Amma ka faɗa masa gaskiya ɗaya: Zak-Shadow bai fito daga prison don ya mutu a asibiti ba.”      Imran ya gyaɗa kansa yana ɗaukar wayarsa, harya fara tafiya ya tsaya a ƙofar ɗakin, a taƙaice ya furta “Ba zai mutu ba in sha ALLAHU.” daga haka ya fice ya bar Faro da Doctor Idris na cigaba da tattaunawa.        Dada da basu san duk ya gama jin abinda basa son yajin ba ya bar jikin ƙofar yana murmurshi. Drip da ake faman saka masa a kwanakin nan dama doctor ɗin ya saka masa bayan sallar isha'i, shine ya saka shi barci har su Imran ɗin suka shigo gidan bai sani ba. Yanzu ma ya farka ne sai yaga ruwan ya ƙare ya cire da kansa, ruwa da yake buƙata na sha daya duba babu a ɗakin ya saka shi ƙoƙarin fitowa duba Dr Idris ɗin, dan koda yaushe Doctor na tare da shi a gidan. Barin wajen yay ya koma ya zauna a bakin gado. A zuciyarsa yana faman maimaita kalmar poising ɗin, sai dai fuskarsa da murmurshi, dan ya jima da fahimtar hakan a tare da shi, musamman a watannin nan da suka gabata. Har ma yana tunanin yaushe hakan ta faru? Tun yana a prison ɗin, dolene a ɗayan biyu gubar ta shigesa. Mafi ƙarfi a zuciyarsa shine television da aka kawo ɗakinsa watannin da suka wuce, ko kuma ta hanyar securitys ɗinsa...... %★%★%★%★%         A ɓangaren su Hajiya Hasiba kam abinda suka jiyo ga bokan Mamawo ya matukar rikitasu, amma sai Hajiya Hasiba tace ita dai su sake zuwa wajen wani mana. Ko suje India ɗin kona kwana biyu ne.       Mamawo ta yarda da shawarar, amma tace su fara fuskantar Adeel. Itama Hajiya Hasiba bata musa batun ba, sai dai sun nema ganin Adeel ɗin shi kuma ya toshe hakan. Dan yama ɓoyema ganinsu gaba ɗaya dan haka dole sukai hakuri dan zuciyarsu na kitsa musu ko wani abu yake shiryawa. Ga First lady ta takurama Hajiya Hasiba akan harkokin bikin ƴarta, dole ta haƙura da batun India ɗin ta maida hankali a kanta. Har takai ma bata fahimci Ismat bata gida ba sai bayan kwana biyu. Sai dai tana taɓota tace tana gidan Aunty Jiddah zatai kwana biyu sai ta saki batun ta. Dan bata kawo a ranta wani abu Ismat ɗin ke shiryawa na komawa gidan babansu ba.     Shiru kaɗan ya biyo baya Imran ya gagara magana saboda abinda ya toshe masa maƙoshi. Shima sai Shugaban ƙasa bai iya yace komai ba yana dai saurarensa cikin shiru, irin shiru na masu fahimtar juna ba tare da doguwar magana ba. Tsohon minti guda Janar ya katse shi da faɗin,       “Ka samu abin da ka je nema ne Imran?”    Imran ya sauke numfashi karo na farko a hankali. Muryarsa da ɗaci ya furta, “Eh, ranka ya daɗe. Amma abin ya fi yadda muke zato nauyi.”        “Faɗa min kawai”.    “Akwai guba a jikinsa. Ba ta gaggawa ba, amma an tsara ta ne don ta lalata shi a hankali. Likitoci sun tabbatar da cewa a nan ba za a iya magance ta gaba ɗaya ba, koda akwai makarinta zai iya kasancewa a hannun wanda sukai aikin yake ko suna da alaƙa da wanda suka yin, dan dole mai makarin shike da gubar. Fitar mu nemata zai basu ƙofar sanin sirrinmu”.       Shiru ne ya sake biyo bayan bayanin Imran ɗin. Dan Janar ya kasa koda motsin kirki tsabar yanda zancen ya buge shi shima. Imran ya san wannan shirun na Janar shiru ne na mutum da ke ƙoƙarin riƙe fushinsa  shima, dan dole Janar zai ji kamar yanda suka ji a lokacin da Doctor ke sanar musu.       “A wajen akwai maganin? ta hanyar da muke buƙata?”.     Janar ya faɗa cikin wata irin murya mai bayyana ɗaci da zafi.       Amsa Imran ya bashi, “Akwai, ranka ya daɗe. Amma zai iya ɗaukar wata ɗaya zuwa biyu inji Doctor.”        Muryar Janar ta sauya kaɗan zuwa matsayin shugaban ƙasa, cikin nauyin umarni ya furta. “Amincewar UBANGIJI kawai muke nema. Amma babu wanda zai ji wannan har Haysam.”      “Mun riga mun kulle komai Sir.” “Zan zo yanzu. Ina son na gansa.” Imran bai yi mamaki ba, dan haka kai tsaye ya ce. “Muna maraba da zuwanka ranka ya daɗe.”       “Uhhm”.    Janar ya faɗa yana yanke kiran.........✍️ ........Bayan la'asar su Nimrah suna a garden suna basket ball su duka huɗu sai Yaya Khalifa, Yaya Mu'azz da Yaya Imam da suka zo gidan babu jimawa, sai Auta Lolo. An raba team ɗin biyu, amma Nimrah da Ruky sunƙi yarda a rabasu, dan haka sai ƙwange sukema su Mu'azz da rinto.         A yanzu ma ana tsaka da gardama Nimrah da Ruky sun dage kuma akan rinto ne Khalifa ya hararesu da faɗin, “Kufa matsalar ku rinton jaraba, shiyyasa sam bana son haɗa sabga da Ninah da Ruky munafukan yara ne ALLAH”.         “Ashe ka gane Broth, wlhy haka suke”. Cewar Mu'azz shima yana hararsu. Baki Ruky da Nimrah suka taɓe, Nimrah zatai magana sallamar maigadi ta dakatar da su. Imam ne ya amsa masa duk suka juyawa suna kallonsa. Kai tsaye inda Nimrah take ya isa, ya miƙa mata ƙaramar ledar hannunsa yana faɗin, “Saƙo ne wani ya kawo wai a baki. Yace malamin ku ne na islamiyya Kamal”.      Tsit wajen yay ana kallan kallo, sai Bintu ce da tai dariya da faɗin, “Humm guy ɗin nan fa ya dage wlhy”.        Kafin wani ya bata amsa Lolo ya amshi ledar, maigadi ya juya abinda yabar wajen. Dai-dai Lolo na fiddo littatafan cikin ledar. Yanzu kam dariya Feedo, Ruky, Bintu suka kwashe da shi. Yayinda Nimrah taja tsaki. Aunty Asma'u kuma ta tambayesu waye ya kawo?. Labari su Feedo suka bata, har su Mu'azz duk na saurarensu, sai dai abin mamaki duk fuskokinsu sun canja, dan cikin faɗa Khalifa ya ce, “Zamu ci uwar guy ɗin nan kuwa, ƙannenmu da aka tura makaranta ne abin bibiyarsu da soyayya? Dan ubansa aure akace za'ai musu?”.       Cikin ɓacin rai Imam ya ce, “Dolene muje har makaranta muja masa gargaɗi kam, wannan ai rashin hankali ne”.      Mu'azz kam daya kume bai iya ya tanka ba, dan fuuu yabar garden ɗin ma. Khalifa da Imam suka take masa baya. Daga haka wasan ya watse. Ammie dake falo sai ganinsu tai suna shigowa ɗai-ɗai. Bata ce da su komai ba dan tana waya da Daddy Imran ne....        Washe gari daga Nimrah har ƙawayenta babu wanda ya sake bin batun litattafan Sayyadi Kamal kamar wancan karo da suka ma barsu a gidan Aunty Mimi. Dan tunda suka tashi ma suka taya masu aiki gyaran gidan da haɗa breakfast. Bayan sun karya kuma sukai shiri wucewa gidan Baffa dan Hajiyar Daddy Imran ta dawo daga ƙauye jiya da yamma. Tunda Aunty Asma'u ta sanar musu sukace yau can zasu yini. Duk da Ammie na son su zauna babu yanda ta iya. Dole ta haɗa lafiyyayen farfesu da kunun aya da kunun gyaɗa tace su kaima Baffah da Hajiyar (Iyayen Imran kenan). Nimrah ce ƙarshen fitowa a ɗakin. Ta kammala rolling veil ɗin abayarta kalar maroon da adon milk da taji stone tana maida kayan kwalliyarsu a make-up kit ɗinsu idanunta suka sauka akan books ɗin Sayyidi Kamal dake zube a side drawer inda tun jiya Bintu ta zube su. Samun kanta tai da ƙarasawa inda suke ta ɗaukesu su duka uku yau dai tana kallo. Zuuu taɗan buɗesu a tare, sai ga wata ƴar ƙaramar takarda ta faɗo a ɗaya daga cikinsu. Takardar tabi da kallo, ganin rubutun jikinta ta kai duƙe ta ɗauka.        _Ba litattafan bane muhimmanci a gareki yau kamar saƙon farko, ainahin saƙon yana a littafi mai jan bango shafi na hamsin da uku da shafi na tamanin, ki tabbatar ke kaɗai kikaga abinda ke ciki batare da kowa ba har aminiyarki, saboda muhimmancin abinda ke ciki da zai amfaneki ke kaɗai. Idan kuma kika bari wani ya gani bayan ke to tabbas zai mutu._      Takardar ta ɗan jujjuya cike da mamaki zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri saboda kalaman ƙarshe, dai-dai nan akai knocking ƙofar ana kiran sunanta. Dan haka ta maida takardar kawai cikin littafin farko tana amsawa da haɗiye abinda ke shirin hargitsa mata brain, sai kuma ta buɗe handbag ɗinta ta saka duka books ɗin a ciki dan basu da wani girma sosai. Haka ta fito zuciyarta na kai-kawo akan abinda ta karanta. Amma da yake tana da wayo sai ta danne ta yanda kowa bazai fahimta ba. Received at 2:38     Yau kam Yaya Khalifa ne ya kwashe su zuwa can gidan Baffan. Cike da farin ciki suka zagaye nutsatstsiyar tsohuwar mai cike da kwarjinin ibada da lafiyar data haɗu da jin daɗin rayuwa. Hajjo tsohuwa mai ran ƙarfe kenan, mahaifiya gasu Imran da a yanzu ta zama uwa harga su Mammah, sannan kaka gasu Nimrah. Dan dattakonta yasa itama bata san raba ɗaya biyu ba, ta zama ginshiƙin dunƙule familyn nan uku da basu da alaƙar jini a yanzu sunfi ma waɗanda keda alaƙar jinin gina ƙyaƙyƙyawan zuminci...          “Oh ni Bilkisu, yaran nan ina zakuje da girman jiki? Ba'a kauda uwarku Biebah ba balle yayunku amma neman dannesu kuke da girman jikin ku, anya bazance a haɗeku rana ɗaya da Habibah da su Asma'u ba”.      A tare suka gwalalo mata idanu, cike da shagwaɓa har suna haɗa baki wajen faɗin a'a gaskiya su auren su sai sannan da shekara goma.       “Shekara goma? Kuji min shaƙiyan yara, sannan kuma in sha ALLAHU ai sai dai lissafin auren ƴaƴanku. Ni yanzu kunga tunda gaku ku duka huɗun yau ba lalaci da surutu zaku yimin ba. Tashi zakuyi kumin kwalemar ɗaki a fitar da komai a canja min jere na, dama su Asma'u zance suzo suyi, amma tunda gaku shike nan sun huta”.        A tare suka amsa mata da to. Sai kuma Nimrah da duk bata da kuzari ta ce, “Granny ina Baffa wai?”.       “Naja'atu sun fita shi da baban ku Ammar, dan kamar ma suna can gidan kakanku Nasiru. Amma nasan anjima kaɗan zasu dawo”.             Kai Nimrah ta jinjina, har sun miƙe Hajjo dake binta da kallo ta kira sunanta, juyowa tai, sai kuma ta tako inda Hajjon take. Sai da ta kama hannunta ta zaunar kusa da ita sannan taima su Fiddo da suka tsaya suna kallonsu alamar suje su. Basuyi musu ba suka wuce hanyar bedroom ɗinta. Ita kuma ta maida hankalinta ga Nimrah.        “Naja'atu mike damun ki? Ko baki da lafiya ne?”.     Sai da gaban Nimrah ya faɗi, dan bata taɓa zaton wani zai gane halin da take ciki ba. Amma sai tai ma Hajjo murmushi da girgiza kanta. “Ba komai Granny, mi kika gani?”.         Hajjo dake kallonta cike da nazari ta ce, “Ban yarda ba Naja'atu, nafa san halin kowa a cikinku, ko yaya kuka canja kuma ina ganewa.”       Har Nimrah ta buɗe baki zatai mata bayanin abinda ta gani a takardar nan sai kuma ta tuna kalaman ƙarshe na cewar duk wanda ta bari ya sani zai mutu, da sauri ta canja zancen tana kwantar da kanta jikin Hajjo ɗin. “Granny da gaske ba komai. Kawai dai yau na tashi ne duk zuciyata wani iri ba daɗi, kuma gabana nata faɗuwa”.      Ajiyar zuciya Hajjo ta saki a hankali, sai kuma ta shafa kan Nimrah ɗin cike da lallashi da so da ƙauna ta ce, “Ki yawaita ambaton Hasbunalahu wani'imal wakil da talatin ANNABI kinji. In sha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi. Barsu ma suyi aikin muyi hirar mu”.        “Granny zan taya su ina son nima nayi. Amma kin zo mana da farar mu?”.     “Buhu guda ma kuwa, tana nan a store dama in baku zo yau ba zan bayar a kai muku, damma na manta ne da A'isha tazo ɗazun ita da Bilalu ban basu ba”.     Farin ciki sosai ya bayyana a fuskar Nimrah, sai kawai ta nufi ɗakin Hajjo tana ƙwalama su Ruky kira. Da kallo Hajjo ta bita tana murmushi, dan har cikin ranta take ƙauna da tausayin Nimrah....... <•><•><•><•><•><•><•> ★ SECRET MEDICAL BASE ★              Yanda Imran yake a ruɗe ko damuwa da kallon lokaci baiyi ba ya dannama shugaban ƙasa kira. Cikin sa'a kuwa ba a jima ba aka amsa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin yay sallama. Daga can shugaban ƙasa da alamu ya nuna barci yake ya amsa, duk da dai a cikin murya mai nutsuwa ne.         “Imran.”      “Ranka ya daɗe ka gafarce ni na tashe ka a barci bazan iya haƙuri bane shiyyasa ko lokaci ban damu da dubawa ba na kira ka.”        “Karka damu Imran nima barcin ya ɗauke ni ne kawai batare da na shirya masa ba. Nima ina son kiran naka a daren nan ai. Amma minene ya tada maka hankali haka?”. Dada bai nuna mamaki ba, sai ma murmurshi da ya saki da ɗan taɓe baki kaɗan ya ce, “Na fahimta tun kafin likitoci su faɗa.”      Shugaban ƙasa ya ɗan zuba masa ido da jinjina baiwar da ALLAH yay masa, irin su Haysam wata ajiyar ALLAH ce a cikin al'umma da sai mai hankali ke fahimta, kaɗan ya ɗan murmusa shima cikin baƙin ciki da ɗacin murya ya furta. “Har yanzu kai ne Zak-Shadow ɗin da na sani Haysam. ALLAH ya cigaba da ɗaga darajarka da baka kariya, UBANGIJI ya cigaba da ɗora nasararka akan maƙiyanka?”. Ya ɗan yi shiru na sakan biyu har Dada ya samu damar motsa lips ɗinsa kaɗan wajen amsawa da amin.         “Ba zan iya barinka a nan ba. Za ka tafi waje. A ɓoye. Ba suna, ba matsayi, ba labari kamar yanda muka fara ka ƙarasa jiyyarka a can”.       Dada ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya furta, “Zan je. Amma ba dan tsirana kawai ba. Sai dai ina kewar Mammah da son ganin su”.      “Na sani Haysam. Amma kayi haƙuri bana son kowa naka ya ganka a cikin wannan halin, in sha ALLAHU wata biyu tamkar gobe ne indai da rayuwa. Mammanka zatafi farin ciki da son ganin Haysam. Saɓanin hakan raunana mata zuciya zaiyi daga ita har ƴan uwanka. Ka duba halin da Imran ke ciki a yanzu haka kawai ya isa misali”.       Cike da gamsuwa Dada ya jinjinama shugaban ƙasa kai. Kafin cikin ɗan furzar da iska ya furta, “Zan dawo in sha ALLAHU. Ba a matsayin wanda aka yima afuwa kawai ba. A matsayin wanda ya dawo ya gyara abin da ya samu karaya daga BURINSA.”       Da ƙarfi Shugaban ƙasa ya sauke ajiyar zuciya yana miƙa masa hannu. Kama hannun nasa Dada yayi sukai musabaha irin ta amintattun sojoji masu kishin ƙasa da tsayayyar zuciya, musabaha ta tarihi, ta alƙawari da cikakkaiyar JARUMTA.       Janar dake murmurshi ya furta, “Ina ji a jikina Haysam, da izinin UBANGIJI a ranar da ka dawo ƙasar nan zata fara canjawa da canji irin na masu son a shinfiɗa gaskiya. Da taku irin na masu girgiza zukatan ɓoyayyun munafukai. Daren gobe in sha ALLAHU zaku wuce”.        “ALLAH ya kaimu”.    Dada ya faɗa...... ================= Ranar Lahadi su Nimrah suka dawo gida da yamma. A kuma ranar Daddy Imran da tunda suka je gidan bai kwana ba dan Ammie ta faɗa musu yana wajen aiki yazo gidan da safe, sun nuna farin cikin ganinsa shima kuma yaji daɗin ganinsu. Dan haka suka zagayeshi da uban surutunsu yana biye musu. A ƙasan ransa kam ji yake badan yau ne tafiyar nan tasu ba daya shiryata da Nimrah a ciki. Amma lokaci ya riga ya ƙure, dan yau ne jirginsu zai tashi ƙarfe goma na dare shi da Haysam. Tunanin ya ture gefe ya cigaba da biye musu, dan sunata masa shagwaɓa wai zasuyi missing ɗinsa saboda ya sanar musu zai yi tafiya, kuma zai jima dan wata ɗaya zai yi ko sama da haka. Da yammar ma da kyar suka yarda suka bi Yaya Khalifa da zai maidasu gida. Shi Daddy Imran yace sai anyi isha'i zai shigo yayi ma Mammah sallama... Da yamma Mu'azz yazo ɗaukar su shima, sai kawai Khalifa yay zamansa dan dama yana da uzirin aikin makaranta. Ammie ta haɗa musu kayan kwalliya da kayan ƙamshi na musamman na turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Duk da kuwa Aunty Biebah ta saya musu kwanaki. Yanzu ɗin ma harda na Biebah Ammie ta bada, sannan taima Mammah gasashen nama mai ɗan karen daɗi itama a kai mata. Suka wuce Asma'u na musu tsiyar yau zatai barci mai daɗi. Lolo kuwa yana islamiyya ma suka wuce da ansha rigima duk da shima fa ya zama ɗan saurayi tunda 2years kawai Rukyn ta bashi. Gasu yanzu suna shekara sha biyar da watanni. Sai da suka fara sauke Fedoo a gidansu, sannan Bintu. Dan gobe in sha ALLAHU Monday ba batun tafiya gidan Mammah a cigaba da shargalle. Su kuma su biyu Mu'azz ya wuce da su gida cike da jin kewar ƴan uwansu da aka rabu.     Duk abinda suke Ammie na jinsu, itama kuma hirar tasu ta fara kai hankalinta akan al'amarin Asma'u ɗin da Bilal, dan kwan biyun nan ta fahimci ko yaushe Asma'u na maƙale da waya, idan ta tambayeta sai tace wai assignment take yi. Ashe ita ta maida assignment ɗin. Kai yaran yanzu sai a barsu dai kawai. Tai murmushi mai yalwa, dan har cikin ranta wannan haɗin ya mata. Wlhy idan duk ƴaƴan data haifa zasu kasance matane ace yaran gidan Mammah suka auresu zatafi kowa farin ciki, dan jinin Mammah jinin alkairi ne. Abotar Imran da Haysam babban rahama ce kuma alkairi ga zuri'arsu guda biyu. Addu'ar fatan alkaici tayi ta cigaba da sabgarta.........✍️ 43 ........Shima Imran lumshe idanu kawai yayi a wajen yana jingina da kujera. Ya san wannan ganawa ba ta siyasa ba ce, ganawa ce ta gaskiya, ta amana, ta zumunci, ta yarda da bashi na tarihi. Ciki ya koma ya sanar ma Faro, dan haka suka nufi ɗakin da Dada yake duk da su a zatonsu har yanzu barci yake.....     ★2:42am★           Shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida suka iso cikin base ɗin. Fita ce ta sirri dan a cikin ɓadda kama ma yake. Dan haka daga shi sai dogarinsa ne a motar. Su Imran dake faman zaman jiran tsammani na zaune a falo dan tunda suka leƙa ɗakin Dada suka samu yana barci har lokacin basu zauna ba suka sake dawowa falon. Sai dai abinda basu sani ba likimo Dadan yay musu yana jin motsin shigiwarsu a lokacin, baya son su san yasan abinda suke ɓoyewar, dan haka yay likimo ɗin.        Shigiwar Shugaban ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida ba tare da hayaniya ba ya sakasu miƙewa tsaye a tare. Basuyi mamakin ganinsa a shigar ɓadda kamar ba, kuma ba tare da yan rakiya ba sai dogarinsa kaɗai. Sai da ya zauna, dogarin nasa ya juya ya fita a falon sannan yay musu nunin su zauna suma.       Kawuna suka jinjina cikin girmamawa, sannan suka zauna suna gaishe shi. Da kai kawai ya iya amsa musu. Daga haka shiru ya biyo baya na tsawon sakanni kaɗan, babu wanda ya yi magana kowa da abinda ke a ransa.. Janar ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Yana ina?”.      Ƙofar ɗakin da Dada yake Faro ya nuna masa. “Ranka ya daɗe yana ciki yana barci”.      “Muje in gansa”. Ya faɗa yana miƙewa. Suma duk miƙewar sukai. Imran a gaba Janar a tsakkiya sai faro ƙarshe. A mamakinsu suna shiga da sallama suka samu Dada a zaune ya jingina da gadon idanunsa a lumshe. Da ɗan sassarfa Imran da Faro suka ƙarasa garesa har suna haɗa baki wajen tambayar, “Ka tashi?”. Idanun sa dake lumshe ya buɗe a hankali ya sauke a kansu. Sai kuma ya jinjina kansa yana maida dubansa kan Janar. Yanda Janar ɗin ke kallonsa ko ƙyaftawa babu ya saka Dada sakin ƙaramin murmushi a karo na farko, sai kuma ya fara ƙoƙarin yaye blanket ɗin da yake ciki cikin nutsuwar sa. Karo na farko shugaban ƙasa ya matso gaban gafon, tsayawa yay a gabansa sosai yana mai dafe hannunsa da girgiza kai alamar kar ya sauka. Nan ma murmurshi ƙarami Dada yayi. Sai kawai Imran ya gyarama janar kujera a gaban gadon suka fice shi da Faro a ɗakin tare da rufe musu ƙofa...        Janar yakai zaune, har lokacin hannunsa na riƙe dana Dada tamkar mai gudun ya ɓace masa, murya ƙasa amma da nauyin fitar sauti ya furta, “Na yi maka laifi. Haysam”.         Dada ya ɗan murmusa, murmurshi irin na dattako da kamewar nutsuwa, sai kwarjininsa ya sake bayyana da cikar kamala. Kaɗan ya motsa lips ɗinsa ya furta, “Ranka ya daɗe, bazaka taɓa zama mai laifi ba a wajena. Duk abinda ka gani a rayuwar bawa ƙaddararsa ce, sai dai idan tazo a mummunar ƙaddarar saɓama UBANGIJI wannan kam daga mu ne da jagorancin shaiɗan. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, ina kuma tayaka murnar tare da addu'ar baka ikon sauke nauyi da haƙƙokin al'umma. ALLAH yasa baka cikin shugabannin da zasuyi dana sanin samuwar mulki a garesu a ranar rarrabe ayyuka”.       “Amin ya rabbi Haysam na gode sosai. Sai dai ka sani shi gudanar da wannan mulkin namu ne a tare, dan kana da muhimmanci a cikinsa wajen sauke nauyin haƙƙin al'ummar ƙasar nan. Shiyyasa nake jin kaicon kaina na kasa kare ka da nayi a shekarun baya.”      Dada ya sauke numfashi, kafin cikin nutsuwa irin tasa ya furta, “ALLAH ya fi kowa iko. Shi ne Alƙali mafi adalci. Wannan rubutacciyar ƙaddara ce tun daga alkalamin farko. Sir ka daina damun kanka”        Kai Janar ya jinjina yana sauke numfashi mai nauyi, tabbas ya yarda ilimin addini duniya ne, wanda ya samu wannan ilimin yay kuma aiki da shi ya more, dan kasancewar Haysam a yau ya tabbatar masa da hakan. Sake duban Dada yayi cikin katsewar tunani ya cigaba da faɗin, “Na zo ne ba a matsayin shugaban ƙasa kawai ba. Na zo a matsayin soja… a matsayin mutumin kuma da ke bin ka bashi.”. Ya ɗan dakata, yana kallon idanuwan Dada kai tsaye. “Akwai guba a jikinka Haysam.” Maigadi ya buɗe musu gate, Mu'azz ya shige da motar yana samun waje yay parking. Sun fito suna gulmar ƙanin maigadi Sanda dan gayene, akwai son yin gayu sai dai irin namu na ƙauye.       Har zasu wuce ciki sabon driver ya iso wajen yana kiran sunan Nimrah. Kusan lokaci guda Nimrah, Ruky, Mu'azz suka juyo da mamaki. Nimrah da ƙirjinta yay mummunar bugawa da ƙyar ta iya daurewa ta amsa masa. Sai dai ta kasa motsawa taje inda yake sai shine ya ƙaraso. Ledar hannunsa ya miƙa mata yana faɗin, “Yaron nan daya kawo mage ranar ne yace a baki. Yace a gaishe ku ke da yar uwarki”.        Ji Nimrah take kamar jikinta na rawa. Ta dai daure ta amsa tana gyaɗa masa kai dan ta kasa magana. Shi kuma bai damu ba ya juya ya bar wajen. Sai ma Ruky ce dake ƴar dariya cikin tsokana ta ce,.........✍️ Jininta na tsinkewa ta ciroshi, haka ta shiga buɗeshi zuciyarta na rawa. Kamar Ranar kuwa sai ga takarda ƙarama a ciki, ɗauka tai ta buɗe.         _Da alama baki duba saƙon ranar ba ko? To ki sani, cigaba da sakacinki na nufin yin dana sani. Duk da kuwa a cikin dana sanin kike shekaru da dama. Idan kuma bakiyi gaggawar dubawa ba zaki dawwama a dana sanin har karshen rayuwarki musamman idan kika fara cin karo da gawar wani a cikin gidank....._     Batama iya ta ƙarasa ba saboda wani yuuuu data risketa na hajijiya. Ta miƙe zambar tana nufar inda suke ajiye handbags ɗinsu. Laluben ta wadda tai amfani da ita a ranar ta shiga yi dan ko books ɗin batama cireba a ciki. Haka ta zazzageta litattafan suka zubo ƙasa. Tsabar ta rikice tama manta littafin da ka rubuta saƙon yake a ciki a ranar, dan haka dukansu ta shiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya sai ana ƙarshe taga takardar, ɗauka tai ta sake karantawa, jin book mai jan bango yasa ta ɗaukesa ta fara buɗo shafukan ƙarshe tana duba lamba harta samu wanda akace. Data buɗe shafin bataga komai ba, sai da ta maida zata rufe ta farga da memory card da aka tura ciki sosai kaɗan ake ganinsa. Tana jawo shi ta wani sauke ajiyar zuciya mai nauyi, sai da ta zuba masa ido ranta fal tambayoyin da basu da amsa. Dai-dai nan aka fara buga ƙofa dan haka ta miƙe tana tattare books ɗin da sauri ta maida a bag ɗin, memoryn ta saka a cikin bra dan dole ta nema waya yanzun nan.       Koda taje ta buɗe ƙofar sai taga Afrah ce. Da ƙyar ta daure ta ce, “My Afry ya akayi?”.        “Aunty yunwa nake ji, kuma ke nake so kimin noodles”.      Kai ta iya jinjina mata kawai ta kama hannunta suka fita...... <%><<%>><%>        A yau Adeel ya sake dawowa ƙasar bayan tafiyar kwanaki da yayi amsa kiran mahaifiyarsa. Sai dai masaukinsa na hotel ɗin can ya fara sauka, dan kwana biyu kawai yake ganin zai yi ya sake komawa sai ya kammala uzirin daya taso masa sai ya dawo sannan yayi shirin da yake so. A bazata Hajiya Hasiba da suka samu labarin yaje gida batare da gaya musu ba a bakin First Lady taga kiran nasa a yau. Sai da gabanta ya faɗi, ta daure da ƙyar dai ta ɗaga dan voice call ne na WhatsApp yay mata. Tashi tai a falon dan duk suna zaune ne idan ka cire Mamawo da bata ƙasar ma. Nabeeha na charting da ƙawayenta ne. Su Amima na kallon Film, sai dai hankalin Nabeeha ya rabu ne gida biyu da tunanin hukuncin data gama yanke ma kanta na komawa gidan Abbansu itama kamar Ismat. Dan haka koda taji Momyn tana gaisuwa da yanayin girmamawa taji a ranta Adeel ne, dan duk da tana tare da manyan mutane girman da take bama Adeel da banne dana kowa. Kuma zata iya girme masa, sai dai bazata haifeshi ba a kwatance duk da tayi karatu kafin aure, ita ba'ai mata auren ƙarancin shekaru ba kamar yanda take basu labari........ ((%))★((%))★((%))       Har washe gari duk yanda Nimrah taso samun waya ta saka memoryn nan hakan ya gagara, ba kuma samun wayar ne mai wuya ba, keɓewa gefe ne ta gagara samu. Dan kowa yau na gida su Mammah ce ma ta ɗan fita tare da Uncle Bilal kuma zuwa sha biyu suka dawo. Gashi tana fashin salla. Ruky ce kawai ke shiga yi balle ta fake da wannan. Da dare kuma suna tare da Ruky, bata son fito mata da abinda ke faruwa saboda ance wani zai mutu. Koda Rukyn ta tambayeta ma littafan da Sayyid ya kawo kawai ta nuna mata cewar ta kaisu cikin littatafan su dake shirye a ƴar kanta, wajen yana a ƙasan hannun bene ne matsayin study table ɗinsu.. Ita kuma tana bata labarin yanda sukayi da su Uncle's jiya.        Nimrah bata samu yanda take so ba sai da kowa ya tafi sallar magriba , ta tabbatar sai isha'i kuma. tana ganin Ruky ma ta kabbara salla ta zare jikinta tabar bedroom ɗin zuwa sama da wayar Mammah a hannu, dan tasan itace zata jima bata fargaba fiye da sauran. A sama a kwai ɗakin kusan ƙarshe da ƙofarsa ta ɗan juya ma nasu Yaya Ammar, shi ta shige. Babu kowa a ɗakin babu ma wanda ya taɓa zama cikinsa. Amma akwai kaya da aka ajiye sai dai komai na a leda a jingine kawai.44 ..........“Da alama fa Sayyadi Kamal ya buɗe wuta Sisi, kwanaki a gidan Aunty Mimi books, kwana biyu da suka wuce ma haka, yau kuma mi muka samu?”.      Har Nimrah ta sakar mata ledar sai kuma ta amshe da sauri saboda tuna takardar cikin wancan saƙon. Dai-dai Mu'azz na ƙarasowa yana tambayar, “Sayyadi Kamal ɗin dai again yau ma?”.        “Ai kuwa dai Yaya Mu'azz, halan bakuyi masa maganar da kuka ce ba?”.    Ruky ta bashi amsa cike da shaƙiyanci. Sai dai kafin yay magana Nimrah tabar gurin da sauri, ga kuma su Yaya Ma'aruff sun shigo suma gidan da alama daga wani waje suke dan a ƙafa suke, sai ya zam hankalinsu Ruky ya rabu har su Yaya Ammar ɗin suka tambayesu lafiya ganin yanda Nimrah ta wuce ciki kamar da sassarfa. Cikin takaici Mu'azz ke sanar musu wai saƙo sayyadinsu na islamiyya ya aikoma Nimrah.        “Saƙon mi?”.     Yaya Ma'aruff ya tambaya. Kallon Ruky Mu'azz yayi da faɗin, “Wlhy Uncle ban sani ba nima. Ruky ce tasan komai duk da dai ranar muna gidan Daddy ya aiko mata books nan ma”.      Hankalinsu duk suka maida akan Rukyn, sai duk taji tsoro ya kamata. Da sauri ta ce, “ALLAH ba komai fa Uncle, kawai dai ina ga litattafai ne.”       Yanda tayi yasa duk suka fahimci akwai abinda ya dace su sani bayan hakan. Dan haka Yaya Ammar ya ce, “Kinga zo nan”.           “Uncle nace fa ba komai ALLAH”.      “Nima ai bance da komai ba Ruky, canai kawai kizo naji.”      Ita tsoronta kar suji son Nimrah yake a musu faɗa, amma babu yanda ta iya ta ƙarasa inda suke. Wani lokacin Yaya Bilal ya fisu sauƙi su ukun nan har Dadan ma. Amma yau sai ga Yaya Ja'afar cikin lallashi yana tambayarta ta faɗa musu bazasu musu faɗa ba. Minene tsakanin Nimrah da Sayyadin nasu?.         “Idan kuma bazaki faɗa ba zan sanar da Yaya.”      Tasan Daddynsu ake nufi, dan haka ta shiga girgiza kai, “A'a Uncle dan ALLAH karka faɗa masa. Dama kawai shi Sayyadin yana son Ninah ne. Amma wlhy bata kulashi, kuma ka tambaya ma kaji”.          “In bata kulashi miyasa yasan gidan ku?”.       Yaya Ma'aruff ne yay magana yanzu. Da sauri Rukyn ta ce, “Randa ya kawo mage ne, sai kuma ranar sunan Baby Nawal ya kai saƙo gidan Mah-mah na books, kuma can gidan ma muka mantasu. Shekaran jiya ma a gidan Daddy haka”         Ammar zai yi magana Yaya Ja'afar ya hanashi ta hanyar riƙe masa hannu, ƙofa ya nunama Rukyn da faɗin, “Shike nan shige ciki”.      Aiko da gudu ta wuce. Koda ta shiga falo ba taga Nimrah ba sai su Aunty Biebah, sai kawai ta rungume Biebah ɗin, kafin ta saketa ta koma kan su Aunty Lailah tana tambayar ina Mammah?. Bedroom suka nuna mata inda Nimrah dama tana ciki, dan itama tana shigowa ta gansu sai ta shanye tashin hankalinta tayi kamar yanda Ruƙayya tayi sannan ta shige bedroom ɗin Mammah. Tana rungume da ita itama Rukyn ta shigo, sai kawai itama ta rungume Mammah ɗin dan kewarta suke ji mai girman gaske...... ==============      Da daddare kamar yanda Daddy Imran ya faɗa yazo yay ma Mammah sallama akan zaije wani aiki. Amma zai jima dan zai iya ɗaukar wata ɗaya ma. Mammah ta jimanta sosai, amma tai masa addu'a ranta duk babu daɗi. Ganin Imran na rage mata kewa Dada sosai a zuciyarta. Shiyyasa bata cika son taga shima zaiyi nesa da su ba. Sai dai babu yanda suka iya tunda aikinsu ne.         Su kansu su Yaya Ma'aruff sunji babu daɗi, dan kamar dai Mammah ɗince Imran na ɗauke musu kewar Dada. Amma da yake su maza ne sai suka danne suka bishi da addu'a suma. Daga nan suka taɓa hira Ruky da Nimrah na jera masa tsarabar da suke so idan zai dawo harda wayoyi. Duk da dai Nimrah dauriya kawai take yi tun ɗazun hankalinta nakan saƙon Sayyidi Kamal da bata samu ta duba ba. Ƙarfe tara dai-dai Imran yabar gidan, daga nan kuma airport zai wuce dan a can zasu haɗu da Dada kawai...       Bayan wucewarsa Nimrah ta faki idonsu ta wuce ɗaki ganin hankalin Ruky ya koma wajen yima su Abees homework ita da Mu'azz. Gabanta sai faɗuwa yake, tana shiga ta maida ƙofar ta rufe harda mirza key dan jikinta ma rawa yake. A haka ta buɗe ledar ta leƙa, a mamakinta yau ma books ne kamar koyau she. Sai dai yau guda ɗaya ne kawai, hisnul muslim ne kuma ƙarami. Received at 4:00 PMƘaramin table ta jawo duk da akwai ƴar ƙura haka ta zauna ta saka wayar Mammah a plane mood dan karma a kira, ta zare memory ɗin ciki ta saka wanda tun jiya ke maƙale a jikinta. Tana tabbatar da ya hau ta wuce wajen videos kawai. Videos uku ne kacal a ciki, jikinka har rawa yake ta shiga na farko tai playing...........✍️        KIƊA A RUWA45 .........Babu abinda kallon videos ɗin nan suka zamewa Nimrah face rikicewar tunani da ruɗanin zuciya. Sakamakon abu uku masu tsayawa a zuciya. Na farko kamammin matar dake kama da ita matuƙa. Matar da ƙwaƙwalwarta ke son hasaso mata abubuwa da yawa game da ita da tuna mata sunanta na uwa mahaifiya da take kira da UMMA a wani ƙarni da ba komai take iya tunawa da ƙyau ba sakamakon ƙaracin shekaru. Sai dai wayonta da kaifin basira na hasko mata abubuwa daban-daban, dan wani ɓangare na brain ɗinta na ƙoƙarin hasko mata kamanin Umman tata da rashin ganin ko hotonta bayan rabuwarsu yasa suka fara disashewa kaɗan, amma dai bata manta da ita ba. Abu na biyu dattijon tsoho shima dake kammani da Umman tata dai, duk da furfurar sajen gemunsa ya lulluɓe kaso mafi yawa a zahiri, abin tsoro da ruɗani shima dai tamkar waccan fuskar ta Ummanta an harbesa da bindiga hannunsa da aka juyar a bayansa da handcuffs tamkar wani dabba. Abin sake rikita lissafin mutum ɗaya ne duk yay harbin, mutum ɗaya tak da taga hotonsa a wannan gidan kuma ake kira da suna DADA, Dada dai da kowa ke girmama sunan matsayin uba jigo na wannan gidan. Shi ɗin nan dai ɗaya tak ya ɗaga bindiga fuskarsa da murmurshin rashin tausayi, rashin imani ya harbi mutane biyun nan dai da take jin tabbacin muhimmancinsu a gare ta mai matuƙar girma ne. Girma mara misali balle iyakar hasashe. Abu na huɗu harbe yara ƙanana da sojoji sukayi, yaran da fuskokinsu ke mata kai-kawo na tabbacin ta sansu fa.         Ba zuciyar Nimrah ba, hatta ƙwaƙwalwata bugawa take tamkar zasu tarwatse a tare da rawar jikinta daya jiƙe sharkaf da zufa kai kace an watsa mata ruwa ne, ruwan ma na zafi dake saurin bayyana gumi.. Shekarunta sunyi ƙanƙanta sosai a wancan lokacin da har ta gagara iya tuna abubuwa da yawa. Sai dai ko bazata iya tuna komai ba wannan fuskar guda ɗaya tak mai kama da tata bazata mantu a cikin zuciya da ƙwaƙwalwarta ba. Fuskar Ummanta, tabbas Ummanta, Ummanta dai Ummanta da sukai wata rayuwa a baya a wani wajen daba wannan da take ba a yanzu da ba komai zata iya tunawa ba. Sai fuska ta biyu, fuskar sojan daya harbi Ummanta, Dadan nan dai da itama ta sanshi amma ba komai zata iya tunawa a kansa ba. Fuska ta biyu da itama dai Soja kuma Dada ya harba da kansa dake ɗaure cikin sarƙar handcuffs, fuskar tsohon dattijo mai kammani da fuskar Ummanta da tata, wanda tunaninta ya fara dawo mata da matsayinsa na kaka da suke zuwa gaidawa ita da Ummanta, sai dai ba komai take iya tunawa game da shi ba shima. Shima dai wannan soja Dada ne ya harbesa ya faɗi ya mutu, mutuwa fa dai da kowa ya sani kuma yake tsoro. Kai wlhy ita kam zata haukace, lallai tana buƙatar fashin baƙi, fashin baƙi a wajen wanda ya aiko mata da wannan rikitaccen video mai sabauta tunani da ƙwaƙwalwa. Kuma da gaggawa take buƙatar hakan, kai in zai yiwu ma a daren nan maybe hakan yasa ta fahimci abinda ake nufi da a yanzu ta gagara fahimta.       Sai dai a daren nan dai da tasan bazai yiwu mata ba. Karo na farko da taji zafin rashin waya da riƙe number kowa a rayuwarta, dan data san koda number ɗaya ce tak ta Sayyadi Kamal data nemeshi a yanzun batare da ko zaman yin wannan tunanin mai son tarwatsa mata kanta dake sarawa ba. Kamar an bata umarnin shiga videon ƙarshe da bata kalla ba ta ɗauka wayar da sauri ta koma ciki tai playing. Cikin sa'a kuwa sai ga wata fuska ta bayyana. Fuskar wani mutumi da bata taɓa sani ba. Yana zaune ne kawai tamkar suna video call yana ganinta tana ganinsa. Dan kai tsaye idanunsa akan screen ɗin suke. Kalmar farko daya fara ambatawa ta sakata sake nutsuwa a kallonsa.         “Naja'atu Nimrah! Na tabbatar idan har kin iso kan wannan videon nawa yanzu tom kin kalla bidiyon baya kenan. Bani da isasshen lokacin janki da nisa. Amma zan baki dama da albishir guda ɗaya da zai fiddaki daga ruɗanin da ko tantama banayi dole ne sai kin shiga a lokacin da kika kalla waɗan can bidiyon guda biyu kafin wannan. Da farko dai sunana Dagger, nine na aiko miki da waɗan nan saƙwanin guda biyu ba Sayyidi Kamal Ba kamar yanda kika ji, na saka sunansa ne dan ki amshi saƙon da muhimmanci tunda shi kin sanshi. Nimrah kina buƙata ta a wannan gaɓar fiye da kowa a rayuwarki, dan kuwa nine kawai zan iya banbance miki tsakanin aya da tsakuwa ta ainahin RAYUWARKI. Ni ne kawai zan miki fashin baƙi akan abinda kika gani a videos ɗin can. Nine kawai zan kaiki inda UMMANKI take. Ba ruɗani zan saka miki a zuciya ba, amma ni ne kawai zan sanar dake gaskiya akan mutanen da kike rayuwa da su a yanzu. Idan kuma baki yarda dani ba na baki ɗan lokaci ki bincika ina wanda kuke kira DADA anan gidan yake? Da gaske yana wata ƙasa ne ko yana prison saboda abinda ya aikata a wannan videos ɗin dana nuna miki. Idan kika samu wannan amsar tayi kama da abinda na kawo miki zaki iya nemana ta wannan number ɗin ni kuma zan sanar miki inda nake na miki dukkan bayanin da kike buƙata. Sai dai da sharaɗi guda biyu tak, wanda in har kina buƙatar duk wannan dole kiyi abu biyun nan. Na farko ki rufe wanan zancen daga UBANGIJI sai ke, idan kikace zaki bari wani ya sani zaki iya rasa Ruƙayya dan akwai masu son kasheta. Abu na biyu na ƙarshe. A duk inda kika ɓuya yanzu dan ganin wannan video ɗin ki tashi ki saita kanki tamkar komai bai faru ba ki koma harkokinki karki sake ki bari wani ya fahimci halin da kike ciki koda Ruƙayya ɗin ce. Idan ba haka ba zan sake maimaita miki wasu zasu kashe ta. Kar kiyi tunanin kirana da wayar da kika kalla video ɗin nan, idan kina son kirana ki samu wayar wani daban ba ɗan gidan ba. Na barki lafiya. Ki kasance cikin aminci ƴar albarka”.      Ƙitt videon ya ƙare, ya kuma ƙare ne tare da tsayawar duniyar Nimrah a lokaci guda....... <<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>       Wauta da ƙuruciya suka haɗu sukai tasiri mai ƙarfi ga al'amarin Nimrah da abinda take ta ƙoƙarin hana bayyanarsa a fuskarta da zuciya. Kamar wasa a daren wannan ranar ko sau ɗaya bata rintsa ba, da Ruky ta dameta da tambaya ma sai ta gaya mata baƙar maganar da ta saka sukai faɗa Rukyn tai zuciya itama ta watsar da ita. Ƙarshe ma ta bar mata ɗakin ta koma ɗakin Biebah ta kwanta. Hakan ba sabon abu bane ga Biebah, dan lokaci-lokaci Nimrah da Ruƙayya kanyi faɗa, wanda yafi shaƙa sai ya dawo ɗakinta ya kwanta ko ɗakin Mammah, hakan kuma baya hana gari na wayewa kaga sun shirya, dan sukan jima ma basuyi faɗan ba. Shiyyasa koda Ruky ta dawo ɗakinta a wannan daren batace mata komai ba ba kuma ya hanata kwanciyar ba. Dan ta tabbatar itama Nimrah ɗin da wuya ta kwana a ɗakin nasu zata wuce ɗakin Mammah ne.       Sai dai hasashen Biebah bai tabbata ba, dan kuwa a yau Nimrah bama ta iya motsawa a gadon da take kwance ba balle fita a ɗakin duk da taji sanda Ruky ta fice ta bar mata ɗakin. Hasali ma sai lokacin ta samu damar fashewa da kuka saboda nauyin da ƙirjinta yay mata. Daga wannan kukan ne zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeta, dama gashi tana period. Haka ta kwana tana rawar sanyi tama kasa tashi ta kashe acn ɗakin, kai ko jan bargo ta rufa ta kasa yi ma. A haka sanyin asuba ya sake bayyana ya kuma mata rijif. Lokacin da Ruky ta shigo ɗaukar rigar sallarta da nishinta ta fara cin karo. Tuni ta manta da wani batun faɗan su ta zabura kanta jiki na rawa. Ai tana taɓa jikinta taji matsanancin zafin da yayi sai ta sake rikicewa, tama fita a guje tana ƙwala kiran Small Mom.      Zambar Biebah data idar da rakata'ainul fijir ta miƙe tayi ƙofa. Hannunta kawai Ruky ta kama suka juya tana maimaita sunan “Ninah! Ninah batare data iya mata cikakken bayani ba. Sai da suka shiga ɗakin itama hankalinta ya tashi da ganin halin da Nimrah ɗin ke ciki..... Ana idar da sallar asuba doctor ɗinsu da aka kira ya iso gidan. Kasancewar an maidota ɗakin Mammah har nan aka kaisa ya dubata da mata ƴan tambayoyi. Da ƙyar take bashi amsa wasu ma sai Mammah ke bashi. Ya gama ƴan rubuce-rubucen sa yace yana ganin malaria ce ta saka mata zazzaɓi. Sai ƴar damuwa da kukan da tayi.       Ba ƙaramin mamaki Mammah tayi ba da jin batun damuwa dana kuka. Amma sai batace komai ba tabar doctor yay aikinsa. Allurori yayi cikin drip ya saka mata, kasancewar akwai masu saka barci a take barcin yay galaba a kanta. Mammah bata sanarma kowa abinda likita ya faɗa mata ba, ta bar komai a hannunta zata saka ido kan Nimrah ɗin harta fahimci damuwar tata..........✍️46 .........Kwana biyu Nimrah na jiyyar zuciya da jiki ko muce sunayi ita da Hassanar tata Ruƙayya, dan itama dai duk ta zama sukuku da ita. Sannan komai Nimrah tace tana so zata tashi tai mata cike da kulawa. Ita Biebah har dariya ma suke bata kamar ba waɗanda suka gama shan faɗa ba a daren ciwon Nimrah ɗin. Uncle's ɗinsu kam da su Aunty Shariffa kowa ƙoƙarin tattalinta yake, bare kuma Mammah da suka dawo ɗakinta ma kwana tare da ita, dan tace har Nimrah ɗin ta samu sauƙi sannan.      To Alhamdullah sauƙi ya samu, dan yau juma'a ma har cewa tai zata makaranta Mammah ce ta hanata tace dai Monday, amma taso zuwa kodan ta samu hanyar samun wayar da zatai kiran number ɗin can da aka faɗa mata a video ɗin. Dan duk yanda take yaƙin ture abun a ranta da hakan kanta yin abinda suka ce ta kasa. Kamar wadda ake mintsini da azalzalarta haka take ji. Dan ma bata samun sukunin yin tunani saboda Mammah bata barinta koda yaushe tana tare da ita musamman idan du su Ruky sun tafi makaranta. Amma yau da Mammah ta hana tabi su Ruky makarantar ta gama yankema kanta shawarar koma ta yaya sai ta samu tayi magana da mutumin nan a cikin weekend ɗin nan su haɗu a tahfiz. Da wannan tunanin ta kasance har su Ruƙayya suka dawo daga makaranta. Mazan gidan sukai shirin massalaci suka fita..        ★Ammar ya fito a mota zaije massalacin juma'a shi da su Abees da Mu'azz sai ga Adeel a hanya shima zai je a ƙasa, sai kawai Ammar ya tsaya suka ɗaukeshi. Mu'azz dake gaba ya koma baya Adeel ya shiga. Haka sukaje Central mosque ɗin tare, bayan idar da salla a ƙa'ida sukan wuce gaishe da Baffan su Imran da Hajjo, dan haka tare da Adeel sukaje, acan kuma suka samu su Yaya Ja'afar da Ma'aruff. Ammar ya gabatar da Adeel matsayin abokinsa makwafcinsu. Su mutanene masu daraja ƴan adam, babu wanda ya nuna komai akan Adeel sai mutuntawa, sukaci abinci a gidan akasha hira duk da shi Adeel baya jin Hausa sai turanci, dan haka hirar duk sai ta koma da yaren nasara.      Sai da a gaɓar da Baffa ke ma su Yaya Ma'aruff nasiha akan batun Uncle ɗinsu Tasi'u daya koma Lagos akan su manta da komai suyi hakuri su karɓesa kamar yanda Mammah ta hakura ne ya koma Hausa. Ya kara musu nasiha sosai duk da kuwa randa su Nimrah suka zo gidan suka samu Uncle Ammar ya fita da shi sun haɗu ne a gidan Uncle Nasiru dama sun musu faɗa akan batun Uncle Tasi'u ɗin. A ranar dai sun ce komai ya wuce, amma basuce sun yafe masa ba. Shine ya koma Lagos ɗin da nufin zai kawo yaransa gidan Mammah ɗin, washe gari ya tafi. Shine yanzu Baffan ya sake musu nasiha shi da hajjo. Daga haka suka koma batun kasuwanci. Dan shima Baffa ɗan kasuwa ne da sukaci zamani a lokacin ƙuruciya....      ★★★★★ A kusan dai-dai wannan lokacin Nimrah ce ta faki idon su Mammah datai baƙi Ruky kuma na barci ta nufo gate. Ƙanin Baba maigadi kawai ta samu zaune yana latsa ƴar wayarsa rakani kashi harda ƙyauro a jikinta. Sallamar da tai masa ya saka shi ɗagowa yana kallonta, dan tunda yazo gidan magana bata taɓa haɗasu ba daga ita har Ruky. Saboda kallon marasa ji da rashin kunya yake musu ma shiyyasa bai taɓa fatan wani abu ya haɗasu ba.       Amma mi, a mamakinsa sai ta masa sallama, baima san lips ɗinsa ya fara rawa wajen amsawa ba. Bata damu ba ta ɗora da gaishesa. Nan ma mamaki ya kama shi. Cikin kasa haƙuri ya ce, “Hajiya kina son wani abu ne?”.         Nimrah ta ɗan sauke numfashi da waigawa ta kalla hanyar cikin gida, har yanzu babu alamar kowa kamar yanda tai fata, sai sabon driver data hango can wajen mota yana fitowa daga ciki alamar wani abun yake yi wanda ta san bai wuce goge motar ba dan ɗazun taga suna wankewa shi da Sanda ɗin. Kauda kanta tai daga kallonsu dan bazai yiwu yaji maganarsu ba daga inda suke, kuma taga hankalinsa gaba ɗaya baya a kansu ma.         “Waya zaka ara min”.     Tai furucin idonta akan wayarsa. Shima da mamaki ya kalla wayar sannan ya sake ɗagowa ya kalleta. “Hajiya waya dai? Kalli fa wayar tawa yanda take.”         “Karka damu ba wani abu zanyi da ita ba.”     A zuciyarsa ya furta (wannan yarinyar kuwa anya ba zargina take ba, dan na fahimci shegen wayo ne da ita. Ko kuma wani ne dai ya turota gareni a cikin gidan...)       “Malam Sanda”.   Nimrah ta katse masa tunani. Firgigit ya dawo hayyacinsa. Ganin yanda ta tsatstsare shi da manyan fararen idannunta baima san ya miƙa mata wayar ba.      “Na gode”.   Ta faɗa a hankali tana barin wajen. Da kallo ya bita, kamar yanda Malam Buba driver ke binta da kallon gefen ido, dan tun ɗazun dama hankalinsa a kansu yake duk da baya iya juyo abinda suke faɗa. Ganin ta amshi wayar Sanda ya sashi fahimtar mi take shirin yi, da sauri ya koma cikin motar kamar bai gama abinda yake ba, ya zaro tashi ƙaramar wayar ya shiga neman layin Dagger daya san zai iya samunsa da gaggawa. Aiko babu wani jimawa ya ɗaga shima daga can, dan kwanakin nan gaba ɗaya cikin ƙaguwar jiran kiran Nimrah yake yi, amma shiru kake ji, sai da ma Molen ke sanar masa bata da lafiya ne kwana biyu sannan. Ko gaisuwa basu yi ba Mole ya fara sanar masa, “Oga ka kasance cikin shiri na tabbatar kai zata kira. Dan gata can ta amshi wayar Sanda ta nufi bayan ɗakin janareton su.”      Sai da Dagger ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya sannan ya ce, “Mole waye Sanda kuma?”.        Cikin ƙaguwa Mole ya ce, “Wannan ƙanin Almu ɗin fa da nake gaya maka sunzo ranar daya dawo tare”.       “Oh-oh na tuna, bara na ɗaga inaga gata tana kira.....”     Bai jira amsar Mole ɗin ba ya katse kiran.....       A ɓangaren Nimrah data zagaya bayan ɗakin Gen... Ɗin gidan kuwa da sauri ta fara loda number wayar data kwafe a jikin ƙaramar takarda, sai da ta danna kira ta tabbatar ya shiga sannan ta nema waje ta zauna dan ta tabbatar babu mai zuwa nan a cikin ƴan gidan balle yay tunanin tana nan. Sai dai ma'aikatan gidan irin su maigadi, kuma sai da ta leƙa ta tabbatar babu kowa a ɗakin dan dama maigadi ne bata gani ba acan waje, shiko ƙaninsa Sanda da Malam Buba tunda sun ganta tasan baza su zo b......        Sallamar da akayi ce ta katse mata tunaninta. Duk da yanda muryar mai maganar ke a buɗe ba daɗin ji dai ta daure ta amsa. Daga can Dagger ya sake matse murya shi a dole yau yana waya da masoyiya, dan jikinsa har tsuma-tsuma yake yana dannewa da ƙyar. Saboda yanda muryar Nimrah ɗin ta dakesa ji yay kamar zai shiɗe....        “Kana magana da Naja'atu Nimrah ne? Dan ALLAH waye kai?”.      Da ƙyar Dagger ya iya dannewa ya daidaita yanayin sa ya bata amsa da, “Sani na a yanzu ba shi bane mai muhimmanci, ina ya kamata mu haɗu ya dace ki nema kawai. Dan lokacin da kike da shi a gareni bashi da wani yawa, zan iya ɓace miki a kowane lokaci.”        Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tare da faɗin, “Shi ke nan a ina zamu haɗun? Yau she kuma? Amma ka sani ina son ganin ka da gaggawa”.      “Baki da matsala indai ni ne. Kamar yanda nai niyyar sanar miki gaskiya ba zan guje miki ba. Na baki damar ki faɗi a indai zai miki sauƙin mu haɗun batare da ko ƴar uwarki ta sani ba, saboda gudun kar a cutar miki da ita”.       Ba tsoro Nimrah ke ji ba, tsoronta kawai kada a taɓa mata lafiyar kowa a ahalinta ne. Dan haka ta ce, “Ni bani da inda na sani bayan gidan mu, kuma ba'a barina fita ni kaɗai”.        “Okay na gane, makaranta fa?”.    “Makarantar bokon mu ma baza'a bari na fita ba, sai dai mu haɗu a tahfiz gobe, shima lokacin da ake kawo ma ɗalibai abinci”.        “Ta yaya kenan?”.    “Zan ma drivern gidanmu magana”. “Amma nace miki bana son kowa ya sani ko? Shi drivern baƙya tsoron ya bamu matsala?”.      “To ni ban san yaya zan yi ba, wannan hanyar gareni kaɗai gaskiya. In dai ba ita ba sai dai a haƙura....”      Da sauri Dagger daya fahimci zata ƙwaɓa masa aiki ya ce, “Karki damu bar komai a hannuna zan san yanda zanyi. Goben kawai ki saurare ni”.      Kanta ta gyaɗa tana ɗan juyawa jin kamar motsi, sai kuma ta sauke wayar a kunnenta. Ganin babu komai ta sauke ajiyar zuciya tare da goge number ɗin daga cikin wayar ta muƙe zata bar wajen. Da sauri Sanda dake laɓe jikin window ɗin bayinsu dake ta wajen ya duƙe dan duk yana jinta.47 ..........★Anan kam su Ammar sai da akai la'asar suka baro gidan Baffa, daga nan gidan Uncle Nasiru suka je shima gaishesa, kuma nan ma Adeel ya bisu bakuma suce masa komai ba. Dan a ganinsu ma ya ɗanyi yawon buɗe ido tunda ya sanar musu abinda yazo yi kasar kenan a gidan Baffa. Sun samu Uncle Nasiru bai kai ga shigowa gidan ba saboda sune dai keta gwagwarmaya akan kafa gwamnatin Janar Yusuf kowa ya sani. Amma Ummy ta musu tarbar girma kamar yanda ta saba. Yaran duk sun zo sun gaishesu, anan ne ma Mu'azz ke takalar Bintu da cewar ƙawayenta nacan zasu yawon juma'a tazo su tafi da ita. Shine take dariya da bashi amsar ai Mammah ta hana su fita. Tace Ninah harda kuka.        Su duka dariya sukai, sunan Nimrah da Imam ya ambata ya saka Adeel jin zuciyarsa na motsi, da kyar ya iya dannewa baice wani abu akan sunan ba, dan ya tabbar Nimrah ɗinsa ake nufi. Suna nan Uncle Nasiru ya shigo gidan, haka sukai zaman hira da shi shima har gab da magriba, shima kuma bai ce komai akan Adeel ba bayan bayanin da sukai masa da alaƙarsa da Ammar.      Sun dawo anguwarsu anan sukai magriba, Mu'azz ne kawai ya shiga da su Aheel gida saboda sun gaji ansha gantali. Bayan an idar sai Adeel yaji kunyar binsu gida, da kyar ya daure yace zaije gida shima ya huta ya gaji, koda sukai masa tayin shiga sai ya kanne yace karsu damu watarana zai shiga yanzu dai su masa afuwa ai sun sha yawo. Dole suka barsa suka shige shi kuma ya shige yana danne ransa da kyar, amma tunda dai aka fara samun wannan damar yasan nan gaba za'a samu wadda ta fita ma. Damma zai ƙara tafiya ne kan uziririnsa, amma yasan yanzu kam ya ƙulla da wannan ƙasar kenan. Batun mijin Nabeeha kan tuni ya ajiye sa gefe bai ko sake tunashi a cikin manyan ayyukansa ba, ba kuma hakan na nufin ya ƙyale Nabeeha ɗin bane ba, yana son ya ƙarasa abinda ke gabansa ne kawai kafin ya sake waiwayenta.....          <<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>          Washe gari asabar duk da Mammah ta hana Nimrah zuwa tahfiz ta dage da shagwaɓa da magiya, har sai da Bilal yasa baki yace ta barta. Babu yanda Mammah ta iya ta ƙyaleta sukai shiri suka fita harda su Ayyan driver na jiransu. Kamar yanda suka saba Mu'azz na gaba da su Aheel, su kuma da Aunty Biebah suka shiga baya. Malam Buba na saukesu suka nufi shiga gate, tsayawa Nimrah tai tare da juyawa da baya tana faɗin, “Kai nayi mantuwa a mota. Kuje bari na amso kada ya tafi”.     Babu wanda ya kawo komai a ransa suka shige, dan Ruky na riƙe da Afrah ne a hannu. Nimrah ta iso Malam Buba na ƙoƙarin barin wajen, duk da dai shima hankalinsa na kanta dan yanda suka tattauna da Dagger a jiya ya sanar masa yanda sukayi ya tabbatar zataso yin magana da shi. Ilai kuwa sai gata. Glass tai masa knocking, ya sauke shi ƙasa. Suna gaɗa ido tai saurin janye nata saboda yanda tsikar jikinta ta tashi. Cikin dauriya ta ce, “Baba dan ALLAH wayarka zaka ara min”.       Kalmar Baban nan ba ƙaramin dukan ƙirjinsa yayi ba, ya danne da ƙyar yana gyaɗa mata kai, wayar ya miƙa mata har hannunsa na ɗan rawa kaɗan. Da yake hankalinta ba'a nan yake ba ma bata lura ba ta amshi wayar ta saka number ɗin jiya. Kamar jiranta ake bugu ɗaya aka ɗaga. Kai tsaye bayan sallama ta sanar masa Nimrah ce, ta cigaba da faɗin, “Number ɗin drivern gidanmu ce, idan ka tashi sai ka kirashi nan da ƙarfe sha biyu”.       Daga can Dagger ya ce, “Okay bashi wayar naji yanda zamuyi da shi. Ke kawai ki shige ciki”.      “Okay”.   Ta faɗa kawai tana bama Malam Buba wayar. “Baba kayi magana da shi baƙona ne, zuwa anjima in zaka kawo abinci ka bada sunana zan fito amsa”.        Kasa magana Mole yay sai jinjina kai. Ita kuma ta wuce kawai abinta....     Da kallo ya bita har sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya ce, “Kana jina?”.      Daga can Dagger yace, “Eh.......”     <<%>><<%>><<%>>            “Ka bani tsoro fa, miya faru kake so mu haɗu da gaggawa haka?”.   “Wani abu ne ya rikita min lissafi, shiyyasa nake son ganinka da gaggawa. Ko Almu bai san zan zo nan ɗin ba, dan nace masa ne kawai zanje sayo kati ne”.        “Miya faru?”.    “Cikin yaran nan biyu dake gidan ƴammata akwai alamar tambaya akan ɗaya daga cikinsu fa”.      “Wacce a ciki?”. “Baƙar. Kamar ita naji suna kira Nimrah. Jiya tazo ta amshi aron waya a hannuna, ta koma can baya domin yi, sai kawai naji na tsargu da tunanin ko zargina take zatai wani bincike ko kuma wani ne ya sata.”        “Ka bata wayar?”.     “Na bata, amma na bita a baya ta cikin toilet sai naji tana maganar kamar zata haɗu da wani ne a makaranta”.       “Wani?”.    “Tabbas”. “Number data kira ɗin tana wayarka?”. “Tana bani wayar ita na fara dubawa, sai dai ta goge ta, kasan yarinyar nada wayo matuƙa.”        “Kai mi kake tunani?”.     “Ɓoyayyar alaƙa da saurayi, ko wani abu akan mutanen gidan”. “Nafi yarda dana farko”. “Zamu iya sakankancewa ya zama na biyu kuma”.      Shiru wancan yayi alamar tasirantuwar maganar Sanda ɗin. Kusan mintina biyu ya furzar da iska kaɗan yana jinjina kansa. “Kaima kazo da magana. Amma dole muyi abu ɗaya a yanzu, kaje ka saka mana ido a kanta sosai, idan munga zatai mana amfani sai mu jawota muma. Dama tsintacciyar mage ce ai a gidan” .          “Ban gane hausar ba fa”.     Dariya wancan yayi da taɓe baki, sai kuma yace, “Tunda ba yarenka bane taya zaka gane.”       “Kai kullum gorin yare, naga nima dai ina da yaren, kuma yanzu ba iya yaren naku ai”.      Ƴar dariya waccan yayi da faɗin, “Haka ne, gashi ma harka zama Sanda”.     Dariya suka bushe da ita a tare.....               •••••••••••••••••••••     ★TAHFIZ★              Gaba ɗaya yau Nimrah bata wani nutsu a karatun da akai ba duka. Sai ma yawan duba agogo data dinga yi har Ruƙayya ta gaji ta jefa mata tambaya. Sai ce mata tai kawai ba komai. Haushi Ruky taji sai kawai ta shareta. Dan kwana biyun nan abubuwa da yawa ta fahimci Nimrah bata son ta sani idan tanayi, tun ma bata maida hankali har ta fara ranta na sosuwa a kai. Sai dai bata taɓa mata magana ba ko damuwa da bibiyar son sanin abinda take ɓoyewar ma.      Ƙarfe sha biyu da ashirin Nimrah ta miƙe, inda malamin dake koya musu karatu a yanzu haka yake ta nufa, sanar masa tai zata bayi. Bai hanata ba dan hakan ba wani abu bane. Koda ta fita bayin ta fara zuwa, bata ko shiga ba aka kaɗa ƙararrawa, alamar lokacin amsar abinci yayi an kuma tashi yara daga ƴan aji ɗaya zuwa uku. Da sauri Nimrah ta fito ta nufi gate. Cikin sa'a ta faki idon securitys ɗin gate ɗin dake ƙoƙarin amsar sunan wanda zasu amshi abinci, ɗayan kuma zai fara fida yara da aka tasa.      Waige-waige ta fara na neman motar gidansu....      “Hajiya gamu ta nan”. Taji muryar malam Buba a bayanta. Da sauri ta juya inda yake, yana tsaye a jikin motar, duk da yanda taji faɗuwar gaba sai ta fuske. Shima bai sake magana ba ya nuna mata motar kusa da shi. Motar ta kalla kamar mai nazari ko tsoron shiga, sai da ya maimaita mata, “Baƙon naki ne a ciki Hajiya” sannan ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. Dai-dai nan kuma aka buɗe mata gaban motar, sai kawai tai addu'a sannan ta shiga ƙirjinta na dukan ɗari-ɗari na rashin sabo. Sai dai abinda take buƙata ya danne wannan a zuciyarta.      Tana gama zama Malam Buba ya rufe motar, sannan ya buɗe ta gidansu ya fara kwasar abinci. Ɗauke ido Nimrah tai daga kallon malam Buba a karo na farko ta kalla wanda ke cikin motar da suke dan har yayi reverse zai bar wajen. Ido suka haɗa da Dagger, sai taji tsigar jikinta na tashi har sai da ta karanto addu'a. Gashi dai cikin shigar mutunci dan manyan kaya ne a jikinsa. Shadda fara harda hula, sai dai fuskarsa da jajayen idanunsa zuwa lips ɗinsa dake baƙi sosai alamar shaye-shaye sai wankan ya banbanta da kalar tasa. Shi ko wani shegen daɗi yake ji yau gashi ha kyakkyawarsa Nimrah, duk yanda yaso kamewa ya kasa sai sakin murmurshi yake.... Received at 5:07 PM        Kallon juna Ruƙayya da suma nasu jikin ke rawa a yanzu sukai. Tuni hawaye sun wanke fuskar Ruƙayya, ta rungume Nimrah da gaba ɗaya ita kukan yaƙi zuwa mata. Dan kuwa a wannan gaɓar hankalinta ya rabu gida biyu ne. Ba komai yasa hakan ba sai zancen mutumin can da tun randa suka haɗu bata sake bi takan al'amarinsa ba balle binciken da yace tayi, kenan da gaske yake Dada na prison ne ba ƙasar waje ba kamar yanda suka ji ƴan gidan na faɗa?. Tabbas a yau ta zama cikin ruɗani na kasa banbance waye mai gaskiya tsakanin shi da ƴan gidan to. Shin kukan murna zatai itama kamar kowa? Kona baƙin cikin sakin wanda bata da tabbacin shine ya kashe ahalinta ɗin ko ba shi bane?.        Bata da mai bata amsa, hasalima hawayen sun gama wanke mata fuska batare data farga ba. Dan a duniya kukan Mammah yana jerin farko na karya lagonta. Matuƙar so takema tsohuwar nan a cikin jininta da ɓargon jiki. Bata jin kuma koda ta tabbata mutumin nan shine ya kashe mata iyaye hakan zai shafi soyayyar da take ma Mammah duk da mahaifiyarsa ce. Ta saka a ranta shi da laifinsa daban, alaƙarta da Mammah daban. Yanda laifinsa bazai hana alaƙarsu ba, soyayyar Mammah bazata hanata hukuntashi ba in har ta tabbata shi ɗin ne ya kashe mata zuri'a.        Tuni ita da Ruƙayya da Biebah ma sunje sun rungume Mammah dake kuka sosai saboda karanto mata abinda suka karanta da Mu'azz yayi. Bayan tayi sujidar shukur ta ɗago harda Uncle's nasu suma. Hakama su Shariffa da suka shigo, sun haɗu sun zagayeta kowa na kukan farin ciki mara misalin ƙididdiga.........✍️           “Ba gaisuwa ƴammata”.    Ya katse mata tunani. Maimakon ta gaishesan sai ta ɗan yamutsa fuska. Dan duk da turaren daya bulbula a jikinsa ita jitai kawai kamar dai bata shaƙar iska mai nagarta. “Bana son yin nisa samu waje anan”.       Maimakon yaji haushi sai yay murmurshi, kai tsaye ya furta, “Yanda kike so haka za'ayi ginbiya”.     Nan ma bata tanka masa ba, ya samu ƙasan wata bishiya yay parking, gefensu kaɗan da shaguna na saida abubuwa kala-kala. Hakan sai ya ɗan bata nutsuwa. Cike da son birgewa Dagger aka wani gyara zama yana kallonta, ita ko ta sake haɗe rai, cike da nuna halin tsiwa da rashin kunyar tata ta ce, “Kaga nifa bana son kallo wlhy. In dai kana son mu shirya kaja girmanka naja ƙanƙantata”.       Ƙaramar dariya yayi anan ma, yana jin tana wani bala'in sake burgesa. Ya ce, “Okay duk yanda kike so haka za'ayi. Nasan kina buƙatar na fara miki bayanin waye ni, sai dai ba zanyi hakan ba saboda rashin lokaci, dan ina son ki koma kafin ƴar uwarki ta farga da rashi ki. Yanzu dai duk videos kin gansu ai ko?”.        “Eh na gani”.    “Kimin duk tambayar dake ranki zan baki amsa”.        Kai ta jinjina masa tana gyara zama sosai. Bata son kollonsa, amma bata da zaɓi a wannan gaɓar, dan haka kai tsaye ta kallesan da faɗin, “Ni wacece?”.       Kallonta yay da ƙyau shima yana jinjina shegen wayonta da basira. Amma sai ya shanye kai tsaye ya bata amsa da, “Naja'atu Nimrah mana”.        “Nasan wannan ai. Ina nufin asalina. Sannan minene alaƙata da su Mammah?”..        Ba wannan tambayar yake buƙatar tai masa ba, dan bashi da amsarta kai tsaye sai nan gaba. Dan haka yace,........✍️ ........“Zaki san wacece ke nan gaba kaɗan Naja. Su kuma mutanen nan baki da wata alaƙa da su face riƙo”.        “Riƙo!?”.     “Tabbas riƙo. Shi sojan nan da kikaga ya kashe mahaifiyarki nan da tsohon nan Kakanki ya kuma bada umarnin a kashe yaran nan a kuma tayar da bomb a cikin gidan shine ya kawoki gidan. Bari na fito miki a mutum. Sunansa Haysam Abdul-rasheed Shehu, soja ne mai muƙamin Lieutenant Colonel a lokacin da waɗan nan abubuwan suka faru shekara takwas kenan.......”       Tsaff ya kwashe labarin komai ya bata shekaru takwas da suka wuce. Sai dai labarin ya bata shi ne a yanda suka tsara ba'a yanda yake gaskiya ba. Daga ƙarshe ya ɗora da faɗin, “A dalilin wannan kisan gillar da yay ma nahaifin Ummanki da Ummanki da danginku da mahaifinki ne aka kamashi aka rufe a prison. Shine har yanzu yake can a ɗaure....”      Cikin matsanancin ruɗani Nimrah ta furta, “Taya zan yarda da kai. Bayan su sunce su yana ƙasar waje? Mutanen nan fa sunmin komai a rayuwa, fiye da yanda wasu iyayen na kema ƴaƴan da suka haifa. Ban kuma taɓa jin an faɗi wani mugun hali na Dada a gidan ba sai alkairansa”.        “Babu wani ƙasar waje Naja, suna ɓoye gaskiya ne saboda ke. Amma daga shi har Imran akan haka aka rufesu. Daga baya shi Imran saboda babansa mai kuɗi ne ya shiga ya fita aka fiddoshi a shekara uku. Kada kuma kiyi mamaki dan sun miki gata ai, saboda abinda ya tsara suyi miki kenan dan a binne miki wannan gaskiyar da nake faɗa miki a yau. Zak-Shadow ya wuce duk yanda kike tunani, kuma komai tsanani mutanen gidan nan har mahaifiyarsa da Imran bazasu yi abinda ba umarnin Zak-Shadow ɗin ba. Amma na baki dama kije kiyi bincike a hankali daga nan har wata ɗaya. Nasan zaki sake nemana da kanki, duk da nasan zasu iya canja miki labarin saboda su ɓoye miki gaskiya akan kashe miki iyaye da yayi. Amma maimakon su ki tambayesu tunda ke ƴar makaranta ce kiyi binciken miya faru a yankin Bankaura a 2013 zaki samu dukkan amsoshin ki. Duk randa kika buƙaci sake gani na number ɗin nan dai zaki nema, koda wani abu ne ya shige miki a bincikenki ki kirani kawai zan baki haske akan ko miye. Ga wannan idan kin samu nutsuwa ki duba su...”        Da ƙyar Nimrah data amshi ledar daya batan ga zuciyarta tai nauyi ta furta, “Har yanzu bai zama lallai na yarda da kai ba, amma kuma bazan ƙaryataka ba, dan zuciyata na matuƙar rawa da abinda na gani a videos ɗin can. Amma na barma UBANGIJI komai ya bayyana min gaskiya batare da ya barni da wayona ko dabarata ba. Idan kuma ta tabbata hakan ta faru Daddy Imran.....” ta kasa ƙarasawa saboda hawayen da suka ziraro mata. Sharesu tayi da cigaba da faɗin, “Kai ma ya kamata nasan waye kai?”.       “Naja'atu ba yanzu ba. Amma na miki alƙawarin nan gaba kaɗan zaki sani. Amsa ɗaya zan baki dan rage damuwa akai na. Ni ɗaya daga cikin ahalinki ne, wata rana kuma zaki tabbatar da ni dake jini zai zama ɗaya”.      Bata wani fahimci kalamansa na ƙarshe ba. Ba kuma ta nema son sani ba dan basu ne masu muhimmanci a gare ta ba. Shima sai bai sake magana ba, dan ya fahimci a yanzu shiru take buƙata. Motar kawai ya tayar ya koma makaranta. Cikin sa'a ya samu an fito break, sauka tayi batare da masa magana ba balle sallama, ya bita da kallo yana murmurshi, sai dai ita ko waiwayensa batai ba ta ƙarasa gaban gate inda securitys suke. Bai san mita gaya musu ba suka barta ta shige.. shima sai ya tada motar yabar wajen ransa cike da nishaɗi yau gashi ga Nimrah har sunyi magana. Ji yake kamar ya warware speakers yay ta rawa a hanya. Amma ko baiyi a yanzu ba zuwa dare dole yay party.....       ★       “Ke kuwa daga ina kike haka?”. Ruky ta faɗa tana kallon Nimrah cike da tuhuma.    “Ina baya ne zaune kawai”. Itama Nimrah ɗin ta bata amsa batare data kalleta ba.      Gaba ɗaya sai Ruky taji wani abu mai nauyi ya tsaya mata a maƙoshi. Sai kawai ta ɗauke kanta bata sake mata magana ba. Sai ma kular abincinsu data tura mata.    “Kinci ne?”.    “Uhmm”. Ruky ta bata amsa a daƙile tana tashi tabar wajen. Sai kuma duk Nimrah taji babu daɗi. Riƙo hannun Ruky ɗin tai kawai da sauri ta rungumeta. Ruky zata kwace Nimrah tai saurin faɗin, “I am sorry my luv.”        “Wace luv ɗin. Kima daina yaudarar kanki Nimrah. Amma zan baki shawara ɗaya, koma mi kike ɓoyewa a kwanakin nan ki tabbatar ba abinda zai ƙona ki ko ruguza rayuwarki bane. Komi zakiyi ki dinga tunawa da UBANGIJI mai jinki mai ganinki. Bana zarginki da aikata komai mara ƙyau kona rashin ɗa'a, amma zuciyata na rawa da hangen-hangen abubuwa masu yawa.”         “Nagode da kikai min kyakkyawan zato, kuma ki cigaba da min, dan in sha ALLAHU har abada bazan taɓa aikata wani abu na saɓama UBANGIJI ba. Abinda kuma kike tunanin ina ɓoyewar ma nan gaba kaɗan zaki sani ba mummuna bane. Amma Please ki bar fushi dani. Fushi da juna na nufin sheɗan yaci galaba a kanmu, mun kuma yima kammu alƙawarin babu shaiɗan a tsakkiyarmu har abada duk tsanani”.      Sai da Ruky ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan ta ce, “Haka ne ki yafe min” daga haka ta rungume Nimrah, itama rungumeta tai suka shirya....... >>>>>>>>✷⁠‿⁠✷<<<<<<<<<    ★BAYAN WATA BIYU★        7:00am          “Mammah!!”      “Mammah!!!”. Muryar Bilal ya karaɗe gidan cikin sauti mai tada hankali yana sakkowa daga upstairs da steps bibbiyu. Ba Mammah kaɗai ba hatta su Ruky da gudu suka fito daga ɗakinsu, dan Nimrah ma daga bayi ta fito wanka, ALLAH ma ya sota bathrobe ce ba towel ba. Biebah ma wandon kayan barci ne kawai a jikinta sai best, sai dai ta yayimo hijjabin salla a hannu batare data saka ba.     ALLAH sarki Mammah ita kam tana cikin ruturarta, dan har tayi wanka kasancewar ta mai wankan wuri. Dan tana idar da sallar asuba tai azkar wanka take fara yi kafin ta fito. A yanzu ma kammala shirinta kenan tana son fitowa tama su Nimrah magana su shirya su rakata gaishe da Baffa wannan kiran na Bilal yay mata amsa kuwwa. Jikinta har rawa yake wajen ƙoƙarin fitowa a ɗakin saboda tsabar jin tashin hankali. A ƙofa sukai karo da Bilal ɗin da waya a hannu. Rungumeta kawai ya fashe da kuka yana faɗin,      “Mammah Dada! Dada Mammah shugaban ƙasa....” ya kasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙesa. Dai-dai nan kuma Ja'afar da Ma'aruff ma suka shigo suma a kiɗime. Sai ga Ammar da Mu'azz suma daga sama. Kuma kowa da waya a hannu Mammah kawai suke ƙwalama kira.     Rikicewa Biebah da su Nimrah sukai, sai kawai Biebah ta koma ɗaki da ɗan gudu ta ɗakko wayarta. Yayinda Nimrah da Ruƙayya suka nufi Mu'azz suna tambayar abinda ke faruwa. Dan su Uncle Ma'aruff gaba ɗayansu sun rungume Mammah ne suma suna kuka. Hawaye Mu'azz ya share yana miƙa musu wayarsa, a tare suka amsa, rubutu kawai suka gani a X, kafin ma su sake tambaya cikin kuka Mu'azz ya ce, “Ku karanta”. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida (RTD) ya fitar da sanarwa a shafinsa na X kamar haka.         ★★Bayan cikakken nazari da sake duba shari’ar da ta shafi Haysam Abdul-Rasheed Shehu, wanda aka fi sani da Zak-Shadow, Gwamnatin Tarayya ta fahimci cewa an samu kura-kuran shari’a da suka shafi yadda aka gudanar da bincike da hukunci a wancan lokaci. Bisa ga ikon da Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar ƙasa ya bai wa Shugaban Ƙasa, tare da shawarwarin hukumomin shari’a da na tsaro, Shugaban Ƙasa ya amince da ba da cikakkiyar afuwa ga Haysam Abdul-Rasheed Shehu. Wannan mataki ba wai hujja ba ce ta cewa an warware dukkan tambayoyi da ke tattare da shari’ar, sai dai wani yunƙuri ne na tabbatar da adalci, kwanciyar hankali, da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam★★.       A ƙarshe Gwamnatin Tarayya na kira ga al’ummar ƙasa da su zauna lafiya, su guji yaɗa jita-jita ko ɗaukar doka a hannu, yayin da hukumomi ke ci gaba da aikin su bisa doka da ƙa’ida. Wannan ƙasa ce mai doka da zaman lafiya, kuma babu wanda yafi ƙarfin doka. 49 .........Ba gidan Mammah kawai ba a wannan safiya ƙasar ce gaba ɗaya data wayi gari da wannan batu ke neman rikicewa. Ya rabbi, kwatanta muku irin yanda ƙasar ta ɗauki al'amari bazatar nan da shugaban ƙasa yay ma kowa ɓata lokaci ne. Domin kuwa ƙura uku ce ta tashi a lokaci guda.         Masoya masu farin ciki da godema UBANGIJI. Manyan azzalumai da hankalinsu ya tashi dan Janar ya mamaye su. Yara matasa irin su Nimrah da basu san miya faru ba. Dan haka suka fara neman bayanai akan dalilin rufe wannan gwarzon haziƙin soja da aka tashi a wannan safiya da zancensa tako wace manhajar social media. Dan gaba ɗaya media tamkar zata fashe ne da wannan batu da hotunan Zak-Shadow da aka rasa ma daga ina mutane ke samo su. Kafofin sada zumunta, gidajen rediyo, gidajen tv. Jama'ar gari, zaka rantse fitowar tasa ce kawai abu mafi muhimmanci a wannan satin a ƙasar...      Babbar tsiyar da shugaban ƙasa ya tafka musu kuma ana fitar da sanarwar aka kuma sanar da barinsa ƙasar wani babban taro zuwa ƙasar waje da zai halarta na kwana uku. Wayyo ya rabbi, ai sai wutar ta ƙara sama. Saman data nema girgiza ƙasar gaba ɗaya. Musamman da aka samu bayanan shi kansa Zak-Shadow akwai ƙishin-ƙishin ɗin baya cikin prison. Gashi gidan gwamnati sunƙi sake cewa komai daga waccan sanarwar har zuwa yanzu da dare ya ratsa. Abu na ƙarshe zuba wani masifaffen tsaro daya bama kowa mamaki a anguwar su Mammah musamman ƙofar gidansu. Dan ko awa ɗaya ba'ai da sanarwar ba aka kawo sojoji anguwar suka zagaye gidansu. Hatta masu alaƙa da su irin su Uncle Nasiru da zasu shiga gidan sai da aka bincike su tsaf. Ko su Aunty Mommy da suka iso suma sai da akai musu hakan. Hakan ya sake tabbatar ma kowa abin da babbane, musamman ƴan media da tuni suka yoma anguwar tsinke na rediyo dana television harma dana social media dan son bin ƙwaƙwaf. Sai dai yanda suka samu gidan dole suka haƙura, sai kuma suka fara juya maganar akan Zak-Shadow baida isashiyar lafiya ne shiyyasa aka kaishi gida aka zuba tsaro kuma dan kar a ga halin da yake ciki.      Wannan batu ya sake tada sabuwar magana. Ƴan ƙasa da ƴan siyasa da masu fashin baƙi suka fara kai-kawo da ka-ce-na-ce. Wasu suna sukar shugaban ƙasa, wasu suna yaba ma abinda yayi. Yan bani na iya na haɗa hotunan karya da videos a social media a zuwan Zak-Shadow ne aka fitar a prison magashiyan cikin raunuka da galabaita. Kai wani fa idan ya tsara maka batun ga abinda ya faru sai ka rantse a gabanshi akai komai ma......    ÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷      ★JAMUS★          Yanayi ne mai armashi da ni'ima dake kaɗawa a irin wannan lokacin na yammaci a ko'ina ma kake a duniya. Koda lokaci ya banbanta ƙasashe irin wannan yanin a kowacce ƙasa yana da tasiri sosai saboda yakan zama abin so ga kowa, musamman mutane masu nutsuwa da rashin son hayaniya.               Zaune a balcony ɗin ɗakin hotel ɗin nutsatstsen matashin dattijo ne cikin yanayi na ƙasaita da nutsuwa. Yanda ƙafafunsa ke harɗe a zama irin na izza zai tabbatar maka da kasancewarsa cikakken mutum. Sanye yake cikin ƙananan kaya da sukai masa ƙyau sosai kalar ruwan madara marasa nauyi. Hakan ya bayyana cikakken jikinsa dake a buɗe musamman daga sama, sam ba siriri bane, ba kuma yi da ƙiba mai yawa dan har yanzu ainahin jikinsa bai gama dawowa ba. Sai dai ko a haka ƙarfinsa a bayyane yake na ma'abota lafiya da cikar kamala. Gaba ɗaya hankalinsa yana akan littafin hannunsa ne da yake nazari, da ganin littafin kasan mai matuƙar amfani ne. Sosai hasken fatarsa ya sake washewa, ƙasumbar daya tara tun a prison na nan bai kwashe ta duka ba daga fuskarsa, sai dai yanda take kwance luff da style ɗin gyara na musamman zai baka tabbacin yana samun kulawa, dan harda wasu ƴan tsilli-tsillin gashi da sukai fari alamar furfura ta baiwar matsawar shekaru na cikar kamalar girma. Yanda siririn farin gilashin daya sanya ya zauna masa a kan nutsatstsiyar fuskar tasa ko kaine hasidin iza hasada dole ka furta masha ALLAH. Balle ga wani ƙamshinsa mai natsuwa daya cika wajen.     Gefensa kaɗan ƙaramin coffee table ne da mug daketa turiri alamar coffee ɗin ne a cikinsa. A hankali yakai hannunsa da ƙumbar ke fes-fes batare da ya ɗauke idonsa daga kan book ɗin ba ya ɗauki kofin. Kan lips ɗinsa dake dai-dai da taswirar fuskarsa ya kaishi yana mai kurɓar coffee ɗin da alamu suka nuna dole zai yi zafi. Dai-dai nan aka buɗe ƙofar glass ɗin wajen data kasance mai bango guda. Duk da yaji an buɗe ɗin bai kalli wajen ba, bai kuma dakatar da kansa daga abinda yake ba har mai buɗe ƙofar ya bayyana.        Ba kowa bane face Daddy Imran, shima dai sanye yake cikin ƙananun kayan tamkar Dadan. Hannunsa riƙe da tab... Da shima hankalinsa ke a kanta gaba ɗaya. A haka ya gyara kujerar gefen sa ya zauna yana faɗin, “Hummm wai kasan mike faruwa kuwa yau a gida Zak...?”.                A karo na farko Dada ya ɗan ɗaga ido ya kallesa, sai kuma ya maida kan book ɗinsa yana buɗe shafi na gaba. Sai a lokacin ne cikin golden voice ɗinsa dake fita a nutse ya furta, “Miyasa baka son hutar da kanka”.      Murmurshi Daddy Imran yayi da faɗin, “Ai ba abinda kake tunani bane. Takardar yi maka afuwa ce ta fita daga fadar shubagaban ƙasa a yau. Daga bakin mai magana da yawunsa a shafinsa na X.”       A yanzu kam sosai Dada ke kallonsa. Hakan yasa Imran miƙa masa tab... Ɗin. “Duba ka gani, dan ƙura ta tashi fa. Yanzun nan Faro ma yay kirana ya ƙara min bayani”.        Tab... Ɗin Dada ya amsa bayan ya kife book ɗinsa a saman cinyarsa, ya kai hannu ya ɗan gyara gilashin idonsa. Shi ke karatun amma Daddy Imran ke faman murmurshi, zuciyarsa na ƙara cika da jin ƙaunar Janar Yusuf Shu'aibu Tafida. A hankali Dada ya furzar da iska daga bakinsa yana ajiye tab... Ɗin a coffee table ɗin tsakkiyarsu. Sai kuma ya jingina bayansa da kujerar ta lumshe idanunsa yana sake furzar da iskar. Fin sakanni talatin yana a hakan Imran dai bai ce masa komai ba dan yasan akwai abinda yake nazari. Har sai da ya ɗago dan kansa yana mai sauke birkitattun idanunsa a kansa....       “Akwai matsala ne?”.   Imran ya katse shirun nasa da kallon da yake masa. Anan ma sai da yaja kamar minti ɗaya kafin ya girgiza kansa, sai kuma ya motsa lips kaɗan ya furta, “Imran, da nasan Janar zai yi hakan da na bashi shawarar kar yayi”.          “Mi yasa?”.      “Fitar da wannan afuwar tamkar zaburar da su ne a kansa.”     “Ni kuma sai nafi tsoron bats tashi zasuyi ba ta kai zasuyi. Dan Faro ya sanar min yanzu haka gidan soji ya ɗauki zafi da ƙananun magana. Suma ƴan siyasa nayin nasu”.             “Wannan dole zata faru ai, baka fahimceni bane. Shima Janar ya manta yanzu shi ɗan siyasa ne ba soja mai iya bada umarnin da za'abi ba koda ba'a so kuma dole ai shiru. Amma a siyasa koda a zahiri akwai shiru to a baɗini za'a samu matsin lamba ta cikin gida”.         Kai Imran ya shiga jinjinawa, dan ya fahimci abinda Dadan ke hangowa. Cikin sauke ajiyar zuciya ya ce, “Na fahimceka yanzu kam. To yanzu minene mafita? Dan shima ana sanar da afuwar yana barin ƙasar fa”.        Karo na farko Dada ya saki ƙaramin murmushi, sai kuma ya taɓe baki kaɗan yana shan coffee ɗinsa da kallon Imran. “Imran dole zamu koma gida a satin nan....”          “Amma Janar yana so ka huta da ƙyau, idan son samu ne ma kamar wata biyar”.      “Bamu da wannan isasshen lokacin. Idan kuma mukai wannan sakacin za'a mamayemu a gaɓar daya kamata ace mune mukai mamaya. Ka kirashi yanzu....” daga haka ya miƙe. Imran ya bisa da kallo har ya ɓace masa. Kafin ya sauke ajiyar zuciya da furzar da iska mai nauyi yana zaro wayarsa a aljihu. Sai da ya fara nazartar time ɗin ƙasar da shugaban ƙasa yake a yanzu kafin ya rubuta text message ya tura masa. Daga haka ya miƙe shima yana ɗaukar tab... Ɗinsa da kofin coffee ɗin da Dada bai sha ko rabi ba ya koma ciki dan lokacin sallar magrib yayi.....                    <<<<<<•>>>>>>>   Duk wani masoyi na gaskiya yau Mammah ta amsa wayarsa. Har sai da takai ta ma fara gajiya da amsa wayoyin su Aunty Ummi suka koma tayata. Wasu ma ko gane su basayi. Kai da ka ga mutanen gidan a yau kasan farin cikinsu ya canja matuƙa, canji kuma mai girman gaske. Dan bakin kowa yaƙi rufuwa. Mammah kam ta yini ne da tasbihi a baki na nuna godiya ga UBANGIJI, duk da hakan sabone a rayuwarta mace ce mai yawan ibada.      Tuni Ja'afar da Ma'aruff sun fita gidajen abinci sunata saya suce a rabawa mutane. Sun kuma turama Uncle Jamilu kuɗi masu yawa sukace acan ma ayi dan mabuƙata sunfi tacan. Duk inda sukaje a fitarsu tare da sojoji ne, dan yau kowaye a cikinsu ya fita a gidan nan sai ya kasance da rakkiyar sojoji. Hatta su Nimrah da zasu tahfiz duk da ma sai da Uncle Nasiru ya korasu dan da sunce bazasu je ba suma dai sojoji suka musu rakiya, hasalima cikin sojojin ɗaya yay driving.       Tsabar kuma yanda zaka fahimci shirin fa bana wasan yara bane har a ƙofar ajinsu sai da soja biyu suka tsaya, hakama ajin su Abees da su Afry. A wannan gaɓar Nimrah fa tana a cikin ruɗani ne. Amma tayi jarumtar shanyewa da danne komai a ƙasan zuciyarta ta barma isowar mutumin da duk ake wannan kai-kawo a kansa zuwa gida. Dan har yanzu dai basu ji komai akan batun zai zo gidan ba.      Ba Nimrah ce kawai a ruɗani ba a wannan lokacin harda su Malam Buba driver, da Nabeeha dake can gidansu cikin matsanancin farin ciki, dan al'amarin yazo musu a matuƙar bazata kamar yanda yazo ma shugabanninsu. Gashi sai samun kira Malam Buba yake daga su Dagger, suna son jin ko Dada ya iso gida ne.........✍️ 50 ........A lokacin da zuriar alkairi ke farin ciki anan a ƙungiyar duhu dama wasu munafukan bayan fage cikin soji irinsu Garba a hargitse suke da tashin hankali. Dan shugaban ƙasa kam ya musu mamaya irin wadda ko'a mafarki basu taɓa kawoma zuciyarsu za'ayi ba.         Tuni oga Jush yay kiranyen meeting na gaggawa, duk da shi bama ya ƙasar ya koma inda ya fito tunda dama lokaci-lokaci yake shigowa. Amma sai ya kira ta video call da akai connecting da ƙaton tvn meeting room ɗin nasu. Yau kam a zafafe yake, dan kai tsaye ya ƙalubalanci Mr Scythe dake matsayin ogan Janar, dan shine ya kawo sunansa matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa. Ya kuma nuna musu jawo Janar ɗin a jiki zai taimaka musu wajen sanin sirrin gidan soja fiye da sanin da suke da shi a yanzu. Sannan zasu sake karya zuciyar Zak-Shadow dan Janar ogansa ne. Su kuma ganin yanda Janar ke faman kwantar da kai da biyayya ga Scythe dama duk wani ɗan siyasa sai suka yarda da shi, batare da barinsa yasha wata wahala ba suka shiga suka fita ya samu kujerar ɗan majalisar tarayya, tenure ɗaya ya sake nuna musu sha'awar zama shugaban ƙasa, nan ma suka sake dagewa ya samu da babban shirin zasuyi amfani da shi wajen dawo da abubuwan da suka daina yi a baya dan ace da gaske da hannun Zak-Shadow a ciki tunda Janar ogansa ne. Sai kuma gashi tun kan aje ko ina reshe zai juye da mujiya. A satin da shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida ke ƙoƙarin cika kwanaki ɗari da samun mulki ya fitar da babban barazanarsu daga kurkuku. Lallai Janar bai nema zaman lafiya ba.        Yau gaba ɗaya meeting ɗin bana daɗin rai bane ba. Dan haka baiyi wani armashi sosai ba suka watse akan kowa zaije yayi tunanin mafita daga nan zuwa sati ɗaya. Dan dole su bincika inda Zak-Shadow yake dan sun sami tabbacin asibiti aka wuce da shi ba gida ba. Dole ne su bincika asibitin kawai su kashe shi tun daga can sai dai gawarsa ta bayyana ma duniya. Shugaban ƙasa kuwa sai sun shayar da shi mamaki na gaske da sai ya gwammace shima kashe shi sukai. Kai hatta da ahalin Zak-Shadow a wannan karon bazasu tsira ba. Dole ne su shirya wasa na gaske mai sunan wasa a wannan gaɓar......    >>>>>>>>>>%<<<<<<<<<          ★3-DAY LATER★      Kwanaki uku kenan al'amarin fitar afuwar shugaban ƙasa ga Dada na cigaba da trending a cikin ƙasar. Mutane ko gajiya ma basayi, sai ma wasu ƙungiyoyin matasa dake zanga-zangar lumana akan sufa ko sau ɗaya ne suna buƙatar ganin Zak-Shadow dan su samu kwanciyar hankalin yarda yana cikin ƙoshin lafiya kuma afuwar da akai masan ta gaske ce ba yaudarar ƴan siyasa ba. Dan ɓoyesa na saka musu jin kamar baya cikin ƙoshin lafiya ne ko wani abu ake son shiryawa da batun.       A yanzu ma gwamnati batace uffan ba, sai ma batun dawowar shugaban ƙasa akeyi a yau ɗin daga taron kwanaki biyar da yaje. Dan washe gari yake cika kwanaki ɗari da samun mulki. Ga batun naɗe-naɗen mukamai da har yanzu yaƙi yi sai tsiraru da aka bamawa. Dan haka ita kanta jam'iyyar a wuya take da shugaban ƙasa, suna ganin raina musu hankali yake shirin yi da nuna mulkin mallaka irin na gidan soja daya saba a baya... ✨✨✨✨✨✨✨       .★JAMUS★.    A wannan lokacin daga ƙasar Jamus ma su Daddy Imran sun kammala shiri tsaff na isowa ƙasarsu ta haihuwa. Sai dai su akwai saɓani sai gobe idan ALLAH ya kaimu ne. Dan haka a karo na biyu Imran yay waya da Mammah. Dan randa aka sanar da takardar afuwar Dada sunyi waya suna taya juna murna, sai dai bai gaya mata yana tare da Dada ba ko'a lokacin. Ya dai tabbatar mata da yana nan dawowa gida a satin nan.      Dan haka yanzu ma daya kira sunyi gaisuwa yanda suka saba irin ta mahaifiya da ɗa. Daga nan yake sanar mata a gyara ɗakin da babu kowa anan ɓangarenta. Yayi magana da wani kamfanin funichars za'azo a saka. Ɗan jimmm Mammah tayi na alamar tambaya, sai dai fahimtar kamar Imran bai son buɗe zancen yasa bata tambayi mi za'ai da ɗakin ba tace to kawai. Daga ƙarshe take sanar masa ya kira su Ma'aruff yay musu magana dan Uncle Tasi'u na son zuwa da yaransa yau da daddare amma tasan halinsu da shegen taurin kai. Bata son a samu matsala kuma, fatanta suyi haƙuri su barsa da halinsa su yafe masa komai ya wuce a cigaba da zumunci. A cewarta duka ma rayuwar nawa take. Murmurshi Imran yayi yana sake jinjina ƙyawawan hali irin na Mammah. Cikin lallashi yace mata karta damu, in sha ALLAHU zai musu magana. Daga haka sukai sallama.        Duk wannan wayar da Daddy Imran keyi Dada na zaune a wajen. Sai dai hankalinsa na'a kan laptop zaka rantse baima san mi Imran ɗin keyi ba. Sai dai sarai yana fahimtar komai, dan ji yayi kamar ya kwaci wayar yayi magana da Mammah ɗin. Amma ya danne baiyi magana ba koda Imran ɗin ya kammala wayar ma. Sai ma wani zancen ya ɗakko masa akan aikin da yake yi a laptop ɗin.      Kusa da shi Imran ya dawo ya zauna shima yana maida hankalinsa ga screen ɗin laptop ɗin......      <<<<<<<★>>>>>>>           Washe gari a gidan Mammah bisa umarnin Daddy Imran abubuwa biyu suka faru. Na farko isowar Companyn da zasu shirya ɗakin daya buƙata. Ba kuma wani ɗaki bane daban, ɗakin da Nimrah ta shiga ne tai kallon video kwanaki. Dama tun safe su Ammar suka fidda komai na cikinsa su Kulu suka sharo suka wanke bayin da ba'a taɓa amfani da shi ba. Lokacin da masu zuba kayan suka zo aikinsu kawai suka fara cike da ƙwarewa.      Abu na biyu isowar Uncle Tasi'u gidan a karo na biyu, sai dai a wannan gaɓar harda yaransa uku. Biyu maza, ɗaya mace. Kamar kowa sai da sojojin nan suka musu bincike ciki da bai aka kuma tabbatar da sanin masu gidan suka zo kafin a barsu su shigo. A lokacin su Nimrah basa nan, suna makaranta iyayen gidan ne kawai sai su Aunty Ummi da kullum yanzu suna gidan sai dare suke komawa nasu gidajen. Shariffa ce kawai babu a falon dan yau ta tashi bata jin daɗi sosai kasancewar cikinta yafi na Lailah tsufa.       Babban ɗansa yana kamanni da shi sosai da Mammah. Sai dai ko Ammar zai iya girmarsa da kusan shekara biyu. Sai mace itama budurwa, daka ganta kaga wayayya, gata fingai-fingai kamar kazar mayu. Itama dai Biebah zata iya girme mata kaɗan, dan bazai fi irin shekara ɗayan nan ba ta bata. Sai Auta namiji, shi kam zasu iya dai-dai da Mu'azz. Kai da ka gansu kasan rainon ƴan gayu ne, sai dai kuma da ganin inda suka zo ɗin yama fi gidansu komai suka kama kansu. Ga Mammah ta musu tarba ta mutuntawa da soyayya kamar zata haɗiyesu. Su Aunty Mimi ne ma dai sama-sama suka amshesu dan ma gargaɗin Yaya Imran ne. A haka su Nimrah suka dawo gidan suka samu baƙi, duk da dama a kwanakin nan kullum gidan bai rabo da baƙin. A gidan nan babu wanda yakai Nimrah da Ruky wulaƙanci idan mutum bai musu ba.        Sun gaida Uncle Tasi'u da girmamawa matsayinsa na uba. Amma ƴaƴansa kallo ɗaya sukai musu suka watsar da su kamar sun ga kashi. Sun kuma yi musu haka ne saboda ganin yanda suketa wani jijji da kansu su a dole ga rainon turai. Kota kansu kuwa basu sake bi ba suka shige ɗakinsu, bakuma su sake fitowa ba ko abinci sakawa sukai masu aiki suka kai musu dan yau alhamis ne babu Islamiyya. Sai da Mu'azz ne ma ya dawo gidan yazo ya jajibesu suka haura sama ganin ɗakin da aka zubama kaya. Anan suka lalace sunata santi da hotuna da wayar Mu'azz ɗin. Dan ɗakin yayi ƙyau matuƙa. Haka suka fito suna damun Mammah da tambayar wazai zauna a ɗakin. Tace bata sani ba itama Daddynsu ne kawai yace a gyara.... ★RANA BATA ƘARYA......★   Tabbas wannan batu haka yake. Dan kuwa washe garin juma'a kamar jiya yau ma Daddy Imran ya kira Mammah a waya yace su shirya za'azo a ɗaukesu bayan sallar juma'a zuwa wani waje. Kan Mammah ya fara ɗaurewa, amma sai nan ma bata tambaya ba saboda halin girma da dattako irin nata tace kawai to. Su Bilal ne ma data sanar mawa suka fara shan jinin jikinsu. Jiya an gyara ɗaki, yau ance su shirya anya kuwa?..      Kasancewar baƙin ido a gidan yasa basu ja maganar da nisa ba. Bayan sunyi shirin massalaci sun fita harda ƴaƴan Uncle Tasi'u Dayyan da Afeef, suma su Mammah dake gida suka hau shiri. Sai ga su Aunty Ummi sun fara isowa da tasu tawagar suma. Dan yaran basu sami sukunin zuwa gidan ba sai yau saboda makaranta. Shiyyasa yau juma'a kowa da ɗansa yazo. Nan fa aka sake kacamewa har wani baya jin zancen wani.          Banda yara za'ai fitar, dan haka su Nimrah a gida akai shirin barinsu da yara amma suka shiga magiya da roƙon Mammah dole tace su shirya. Kasancewar harda Aunty Biebah da su Aunty Lailah su Nimrah sune ƙanana. Su yaran ma murna sukai da tafiyar tasu, dan a sanin da sukai musu basa ɗaukar raini, idan aka barsu da su dole su daku. Dan kaɗan daga aikin Damisa da Zakanya yaro yaci duka kafin uwarsa ta dawo....       Ba ƙaramin ƙyau sukai ba kuwa da kwalliyar tasu. Nimrah skirt da riga ne na atamfa da tai mugun zama mata a jiki, sanin ba barinta ake fita da ƙaramin gyale ba idan ta saka irin waɗan nan kayan yasa ta ɗora after dress a sama, ba ƙaramin ƙyau tayi ba ga fuska tsaff da kwalliya mai nutsuwa. Hakama aminiyar tata tana sanye da irin kayan nata sai dai ita kam gyale ta saka. Suka kawo turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. suka saka, gashi dama sunyi kabasa da shi a kaya..      Suna fitowa Ya Mu'azz ya fara tsokanarsu wai kamar ranar auren su. Ba raga masa suke ba, dan haka suka shiga ramawa ana dariya. Daga haka suka fito harabar gidan kowa ya shiga mota. Ninah da Ruky na tare da Mammah, Uncle Bilal ke tuƙi sai Mu'azz a gefensa. Ana buɗe gate suka fito motocin sojoji biyu dake jiransu suka take musu baya. Ɗaya a gaba ɗaya a baya. Wannan matakan tsaro na ba kowa mamaki a cikinsu, dan ko yanzu su Nimrah sai da sukai magana. Dan har a makaranta ma yanzu tare suke zuwa da sojojin da a yanzu suka zamewa kowa dogari a gidan batare da sun san dalilin yin hakan ba. Abinda kawai sojojin suka sanar musu tun a ranar farko da aka kawosu shine umarni suma kawai suke bi........✍️ KIƊA A RUWA 2 51 .........★AIRPORT★ Ba ƙaramin mamaki su Mammah sukai da ganin inda aka kawosu ba. Airport fa, sukam wa garesu da zai dawo daga wata ƙasa. Imran ne kawai yay tafiya, basa jin kuma dan zai dawo zai musu irin wannan tattarowar iya su kaɗai. Kowa da magana a bakinsa sai dai sunyi dauriyar dannewa. Ba a kai su Mammah da iyalanta cikin waiting hall na jama’a ba. Sai ma wani mamakin da aka sake basu, dan kuwa Jami’an tsaro masu bakaken kaya suka sake tarbarsu anan ɗin sannan suka jagorance su zuwa wani ɓangare na musamman a airport ɗin da zasu iya rantsuwar basu taɓa sanin akwai shi ba. (VIP lounge) wurine da ya sha bamban da hayaniyar waiting hall. Ga tsaro ko’ina. Iska mai sanyi ga ƙamshi mai saka nutsuwa. Ga kujeru masu taushi da ƙawa kai kace wani shiryayyen falon hutawar shugaban ƙasa ne. Koda yake ko ba'a faɗa ba kai kasan wannan wajen sai dai tanadin zaman shugaban ƙasar. Sai da Mammah ta zauna sannan kowa ya zauna ana kallon kallo. Su Nimrah kam kasa haƙuri sukai cikin raɗa-raɗa sukace Ya Mu'azz dake kusa da su yay musu hoto. Bai ko yi musu ba ya fara ɗaukarsu, daga ƙarshe ya koma yima kowa video sai da Mammah ta masa daƙuwa. Cikin dariya ya ce, “Mammah yi haƙuri, ALLAH wajen ne ya haɗu. Idan bamuyi hoto ba ai ansha damu. Wai dama a waiting hall na airport akwai vip room irin wannan?”. Kowa murmurshi yake da zancen Mu'azz. Uncle Ja'afar ya bashi amsa da, “Ai dole ne ya zama akwai irin wannan ɗin Mu'azz kodan shugabanni ko”. Cikin gamsuwa Mu'azz ya ce, “Haka ne kuma Uncle. Tunda dama kasarmu komai yana da banbanci dana talaka dana masu mulkin”. Basuyi ko zama mintun goma ba jirgin da ake tsumayen zai sauka ya sauka ɗin. Sai dai da yake a ɓangaren ɗaya suke na masu jira basu san wainar da ake toyawa ba har matafiyan da suka fito a jirgin suka fara fitowa. Tun suna tsumayen ganin fuskar wanda suka sani ya shigo vip lounge ɗin har suka haƙura. Dan kusan sai da sukai zaman fin mintuna talatin zuwa lokacin har ruwa an kawo musu da lemo, bayan nan kusan wasu mintina uku security ɗin dake ƙofar ta waje ya buɗeta. Duk ƙofar kuwa suka zubama idanu dan a ƙage suke su kam. A bazata Daddy Imran dake gaba ya bayyana a idanunsu. Kusan a tare duk suka miƙe, idan ka cire Mammah da bata motsa ba ta dai zuba masa idannunta na girma kawai. Yayinda zuciyarta ke wani irin bugawa da bugu mai girman gaske a cikin ƙirjinta. Hakama Nimrah dake kwance a jikinta tana game da wayarta, kasancewar hankalinta na kan game ɗin bata san mike faruwa ba ita kam. “Oh kona koma ne?”. Daddy Imran ya faɗa yana ɗan wara idanunsa akan su Ammar dake tsaye kawai sun zuba masa idanu abubuwa na musu yawo a zuciya da ƙwaƙwalwa. Murmurshi suka saki a tare, kafin su ɗaga ƙafafunsu da sukai musu nauyi na rashin dalili su nufesa a jere, zaratan mazajen Mammah kenan guda huɗu, masu kamanni ɗaya, dan su duka huɗu da mahaifinsu suke kama, Dada ne kawai ya ɗakko hasken fatarta amma shima kamaninsa irin nasu ne. Dai-dai lokacin itama Nimrah ta ɗago saboda zaburar Ruky da uhununta na ambaton Daddy!... Sai dai ta yunƙura zata tashi itama ta tsaya cak, kamar yanda suma Uncle's nasu suka tsaya ɗin. Dan takunsu bai gaza biyar ba suka iso inda Imran ya ke, sai dai kamar jira yake su iso ɗin suna ajiye ƙafafunsu a takun ƙarshe shi kuma ya matsa gefe tamkar mai shirin basu hanyar wucewa, hannunsa ɗaya riƙe dana Ruƙayya, ɗaya kuma ya nuna musu ƙofa. Dai-dai nan ƙofar wajen da suka zubama idanu su duka ta shiga buɗewa, buɗewar data kasance tamkar tare da zukatansu dake rufe ne tsawon shekaru takwas da wata shida.... Ɗasss! Ɗassss! Ɗasss!! Sautin takunsa ya fara bayyana a cikin shirun su mai nauyin gaske, dan a wannan gaɓar ko numfashi mai ƙarfi babu mai yi idan ka cire Imran da fuskarsa ke cike da wani irin murmushi mai nauyi da armashin gaske. Kafin bayyanarsa cikin kwarjini da kamalar masu natsuwa ta wanzu cikin idanunsu. Shi ɗin ne dai, shi ɗin da suke zaman jira tsahon shekaru da hawaye da bugawar zukata a kowace daƙiƙa ta kwanakin da suka shuɗe da abubuwan da bazasu lissafu ba. Duk da basa ganin ainahin fuskarsa, sannan ba wasu kaya bane na alfarma a jikinsa. Hasalima sanye yake da ƙananun kaya da suka kasance baƙaƙe daga sama har ƙasa. Baƙin wando da riga t-shirt mai gajeren hannu data bayyana murɗaɗen damtsen hannunsa duk da kuwa jikinsa bai gama dawowa ba kamar da, sai dai ya ciko fiye da sanda ya fita a prison. Fuskarsa da norse mask daya ɓoye bakinsa da hanci, sai ƙwayoyin birkitattun idanunsa da ko yana a cikin kwanciyar hankali basa zama tas-tas, daga sama da hula p-cap itama baƙa. Hannunsa ɗaya a aljihu, ɗaya rataye da jacket ɗinsa da itama ta kasance baƙa. Sassanyan ƙamshin turarensa da duk suka sanshi da shi kuwa ya cika wajen... Kamar yanda suka tsaya cak suna kallonsa haka shima ya tsaya cak yana musu kallo mai matuƙar nauyi da tsawa a zuciya. Dan kuwa Imran ya matuƙar yi masa bazata. Sam bai sanar masa da zuwansu tarbarshi ba, kasancewar dama saukar tasu sauka ce ta sirri kamar yanda ya buƙata. Da wani irin slow motion ya janye idanunsa daga kallonsu ya maida su kan Mammah dake zaune a inda take, sai dai kamar wadda ta suma dan babu inda ke motsi a jikinta sai idanunta dake tsaye a kansa cak... Nimrah kwance a kafaɗarta itama dai ta zuba masa ido ne kamar yanda kowa ke kallon nasa. A bazata idanunsa daya janye slowly daga kan Mammah suka shige cikin nata. Shigewar data saka mummunar faɗuwar gaba riskarta. Dan ji tai tamkar an matse zuciyarta da hannu ne har sai da ta kumburo kamar zata fashe sannan aka saki. Kasa jurewa tayi, a hankali ta fara lumshe idanun nata dake cika da hawaye na rashin dalili. Hakan kuma yay dai-dai da cigaba da takowar Dada inda suke kai tsaye dan burinsa kawai ya iso gaban Mammah... Karo na biya ya fara motsawa a hankali, yanda ɗakin yay musu shiru tamkar an tsaida duk wani motsi na ƙasar da mutanen cikinta yasa sautin takalmin nasa cigaba da bada sauti kamar ɗazun. Sautin daya cigaba da bugawa da bugun zukatansu har ya ƙarasa inda Mammah da Nimrah suke ya tsaya cak. Kafin a hankali ya tura ƙafarsa ɗaya baya, ya sauke gwiwar ɗayar ƙafar itama a ƙasa tamkar mai shirin bama budurwa zoben baiko. Hannunsa ya kai ya zare p-cap ɗin ya ajiye a ƙasa, ya sake maidawa ya zare norse mask ɗin shima. Duk dai Mammah na kallonsa tamkar sumammiya, dan idannunta ne kawai dake yawo a kansa ke motsawa... A ɓangaren su Ja'afar da su Aunty Ummi, Lailah, Mimi, Mommy, Shariffa da Biebah kam idan akace maka suma sun suma ɗin ne tamkar Mammah kada ka musa. Dan yanda duk suka kasance a tsaye ƙyam babu motsi babu ƙyafta ido ya isa shaida ga mai kallonsu. Dai-dai yana gama sauke norse mask ɗin cikin tamkar fisgar numfashi Mimi ta furta kalma mai nauyi da girgiza zuciya a karo na farko, kalmar data zama tamkar ta yayyafa musu ruwan sanyi ne daya farkar da su a suman nasu... “D..a...da!!”. Sai kawai ta tafi luuuu zata zube ƙasa saboda yanda jikinta ya ɗauki rawa. Da sauri suka zabura kanta dan taro ta, sai dai kuma hankalinsu ya rabu biyu. Dan a dai-dai wannan lokacin itama Mammah da sunan Dadan ya daketa sakamakon fitarsa a bakin Mimi jikinta ya hau rawar, duk da ƙoƙarin da take na riƙe kanta hakan ya gagara. Hannunta ta motsa a hankali tare da kai shi kan fuskar da ta shafa kumatunsa dake ɗauke da kwantaccen gashin saje mai adon farin gashi tsilli-tsilli. Da wani irin gudu hawayen da take riƙewa suka zubo a saman fuskarta, lips ɗinta dake rawa suka motsa a hankali ta furta, “Muhammad!”. Sai kawai ta tafi itama luuuuu ɗin kamar Mimi, sai dai ita da alama suna ma tayi. Ƙarar firgita Nimrah ta fasa tana cukuykuye Mammah jikinta na rawa, hakan yasa shi kuma Dada tarosu su biyun duka a jikinsa ya rungume.... Ƙarar Nimrah ce ta kasance tamkar zaburarwa garesu duka. A tare sukai kansu suma. Wata irin runguma Ammar daya fara isowa yay ma Dada tare da fashewa da kuka mai matuƙar dukan zuciya, dan a wannan gaɓar wlhy ya manta da kansa a matsayin namiji. Tamkar yanda Ammar yayi suma su Ma'aruff rungumesan kawai sukai suna hawaye.. A hankali Dada ya lumshe idanunsa da suka juye lokaci guda, cikin wani kalar sanyin jiki da tsinkewar jini ya shiga ƙoƙarin shanye hawayen da yake jin tamkar suna neman ciko masa idanu shima. Da ƙyar Imran daya ƙaraso inda suke da ruwa a hannu ya shiga ɗagasu ɗaya bayan ɗaya. Nimrah dake jikin Dada male-male batare data fahimta ba ya fara kallo, janyewa yay kawai yana murmurshi a zuciyarsa da ƙoƙarin shafama Mammah dake jikinsu su biyun ruwa. Cikin sa'a kuwa ta kawo nannauyan numfashi.......✍️ KIƊA A RUWA 2 52 ........“Mammah are alright?”. Nimrah ta faɗa tana shafa fuskarta ga hawaye na gudu suna ɗiga har kan fuskar Mammah ɗin. Mammah ta buɗe idanu a hankali tana kallonta, sai kuma tai ƙaramin murmushi da kai nata hannun kan fuskar Nimrah ta shafa da jinjina kai. Sake lumshe su tai kafin ta sake buɗewa kai tsaye akan Dada. Shima dai ita yake kallo, cikin wani irin yanayi mai zafi da kamilalliyar fuskarsa ta kasa iya shanyewa. Dan in mai kallonsa bai ƙarya ba ma ƙyallin hawaye idanun nasa keyi. Mammah kam ta kasa jarumtar riƙe nata hawayen tamkar shi, a take ta sake su suka fara kwarara tamkar an buɗe fanfon ruwa. Hannun nata dai data shafa fuskar Nimrah shima takai kan fuskarsa ta sake shafa fuskar a karo na biyu, ɗayan hannun kuma takai kan Imran. “ALLAH yay muku albarka”. Ta faɗa hawaye na sake zubo mata. A tare suka amsa da amin. Imran da a wannan gaɓar zuciyarsa ta matuƙar raunana da tausayin wannan ahali ya haɗiye abinda ya toshe masa maƙoshi da ƙyar, dan baima san kuka yake ba shima sai da yaji saukar ɗumin hawaye akan tashi fuskar. Da ƙyar ya iya dauriyar dai-daita kansa ya fara lallashinsu. Sai lokacin Nimrah ta farga da jikin wanda take. Mutumin da ko gama tantance wanene shi batai ba. Sai suna biyu da taji Mammah da Mamy sun ambace sa da shi kacal a yanzu. (Dada! da Muhammad). Yanda take mutsu-mutsu yasa shi shima farga da abinda ke faruwa. ALLAH ya soshi dai-dai Mammah na ƙoƙarin tashi ne, Daddy Imran ya kamata ya zaunar da ƙyau. Har neman faɗuwa Nimrah take wajen barin jikinsa, sai da Aunty Ummi ta riƙeta. Shima Dada sai ya basar kawai tare da maida hankalinsa kansu Mimi, hannu ya miƙa musu, da sauri kuwa suma suka nufoshi suka rungume sa suna kuka. Hannunsa ya ɗaura a bayan Biebah da Mu'azz yana ɗan bugawa alamar lallashi, sannan ya shafa kan Ruƙayya itama. Kafin a hankali ya furta, “It's okay”. A tare suka shiga jinjina kawuna suna ɗagowa da share hawayensu. Yayinda su Bilal suka kasa daina kallonsa, dan bayyanar fuskar tasa a garesu ta ƙara zama wani abu mai girma da kimantawa. Dadan ne dai da suka sani, sai dai sajen dake kan fuskarsa da basu taɓa gani a baya ba ya canja shi kaɗan. Shima ganin yanda suka zuba masa idanun gaba ɗaya ga falon yayi shiru tamkar an musu tsawa sai ya motsa tausasan laɓɓansa kaɗan ya furta, “Kallon fa?”. Cikin yanayin ɗage gira kaɗan akan su Ma'aruff. Tamkar waɗanda ya farkar a barci duk sai su Ja'afar suka fara sakin murmushi, kafin su Ammar su sake rungumesa kamar wanda suka ji kunya. Ya ɗan murmusa kaɗan shima a karo na farko, yana shafa bayansu. Cikin golden voice ɗin nan tasa data iya shanye abubuwa da yawa ya sake furta, “Shi dai wannan kukan bazai ƙare ba halan. Imran kama ƙannenka magana su daina min kuka”. Murmurshi Imran yayi yana kallonsu, yayinda su Bilal da suka ɗago a jikinsa ke goge hawayen suna murmushi. Cike da lallashi Daddy Imran ya ce, “Gaskiya Haysam ya faɗa, yanzu ba lokacin kuka bane lokacin farin ciki ne. UBANGIJI ya nuna mana wannan ranar batare da mun biyasa ko sisi ba, hasalima ba muyi zato ko tsammani ba. Dan haka a maimakon kuka sai muyita jera masa godiya da kirari zaifi mana alkairi da ƙarin farin ciki a zukata”. Cikin gamsuwa suka shiga jinjina masa kai suna ƙara share hawayensu. Dai-dai nan cikin kasa haƙuri Ruky ta rage murya da faɗin, “Mammah dan ALLAH waye?..” Mammah da idanunta ke jajur na kukan da tasha ta ɗaga tana kallon Dada dake zaune a kujerar kusa da ita hannunsa riƙe da nata, murmushi tayi mai cike da abubuwa da yawa, kafin ta janye ta maida kansu dan Nimrah da Rukyn na zaune ne ɗayan gefenta, sai dai daga ƙasan carpet ganin haka su Biebah sukayi, duk sun ƙagu ta basu amsa... Zatai magana caraf Uncle Bilal ya ce, “Mammah karki faɗa dan ALLAH, sai sun bada goron albishir sannan”. Murmurshi Mammah ta sake saki mai faɗi tana share hawayen da suka sake silalo mata. Yayinda shima Bilal ɗin hawaye yake sharewa tamkar su Biebah da nasu suka gagara tsayawa. Sanyi jikin su Nimrah ya sake yi, tamkar zasu saki kuka suma suka sake maida kallonsu ga Daddy Imran. Hannu ya ɗaga musu alamar shima babu ruwansa, dan haka akai ƴar dariya mai zuwa batare da an shirya mata ba. Dan shi kansa Dadan sai da ya ɗan yi gajeren murmushi yana kallonsu su duka biyun ƙasa-ƙasa. Sai kuma karo na farko ya miƙa musu hannu alamar su zo garesa... Ruƙayya dai babu musu ta rarrafa inda yake, Nimrah kam ɗan shiru tayi kamar mai tunani, sai da Mammah ta kamo hannunta tare da mata nunin taje da ido sannan. Itama matsawar tai, amma sai ta zauna kusa da Ruky idannunta a ƙasa dan gaba ɗaya jinta take kamar a cikin matsa-tsi, ba kamar sanda suka shigo ba da take sakayau. Ba ta san dalilin rawar jikinta ba. Ba ta san dalilin bugun zuciyarta ba. Ta san sunan Dada kawai, sunan da take ji a bakin kowa na gidan, suna mai nauyi da daraja a cikin gidansu, sunan da ake furtawa da girmamawa da bege. A karo na farko hoton bidiyon nan ya ratsa cikin tunaninta. Sunansa na ainahi yay mata amsa kuwwa acan ƙasan ƙirji matsayin wanda akace ya kashe mata Ummanta, (Aka ce ko kika gani da idon ki) wani sashe na zuciyarta ya tuna mata, samun kanta tai da matse yatsun hannunta cikin juna, ta sake sunkuyar da kai, dan ji take tunaninta na neman hargitsewa da rabuwa kashi-kashi a kwakwalwar ta. A lokacin suma su Shariffa suka ƙaraso. Cike da matuƙar girmamawa suka shiga gaisheshi. Idanunsa dake karantar yanayin Nimrah da babu wanda zai iya fahimta ya ɗauke. Kallo ɗaya yay musu suma ya janye idanunsa, su ɗin ƙanne suke a garesa koba auren ƴan uwansa a kansu, sai kuma ga alaƙar auren ya ƙarama matsayin ƙarfi. Cikin kamewarsa da cikar kamala ta uba kuma babban wa ya shiga amsa musu, tare da musu fatan alkairi a cikin aurensu. Sosai suka sake shiga cikin yanayin kunya, girmansa ya sake mamaye musu waje ko kallonsa sun gagara yi, dan koba shekaru shi ne uba ga mazajensu, sannan shi ne garkuwa, shi ne ginshiƙi. Babu wacce ta iya amsawa a cikinsu sai ma sake sunkiyar da kawuna da sukayi. Sai su Mammah ne suka amsa addu'ar tasa da amin. Sai da suka miƙe suka koma wajen zamansu sannan Ruky da Nimrah suka fara gaishe shi. Suma ya amsa musu da tambayarsu karatu. Suka amsa da Alhamdullah har yanzu kan Nimrah a ƙasa tana cuɗa yatsunta cikin juna. Yatsun nata ya ɗan sake zubama idanu a fakaice tare da janyewa duk a lokaci ɗaya dan cikin sakanni harya gama karantar akwai abinda ke damunta bayan kasancewarsa baƙon ido a cikin waɗanda ta sani, sai dai babu wanda zai ce kallon nata yake, sai ma maida hankalinsa da yay kan Mammah can ƙasan ransa kam mamakin girmansu yake ita da Ruky da Mu'azz fiye da kowa. Ƙasa-ƙasa yay maganar da babu wanda zaice ya ji abinda ya faɗa mata. Sai murmushin ta kawai da kowa ya gani a bayyane.... Shigowar Daddy Imran daya fita ta katse Mammah daga maganar datai niyyar yi, ya dubi su Ma'aruff yana faɗin Su tashi suje gida kafin mutane su farga da abinda ke faruwa. Dan tabbas ana gama sanin Zak-Shadow ne a airport ɗin ba ƴan media da jama'ar gari ba hatta munafukai bazasu barshi ba, dan dama ce mai sauƙi a garesu duk da zagaye suke da jami'an tsaro da suka fara fargar da mutane akwai wani babba dake airport ɗin, saboda a fitar nan tashi ya fahimci hakan ta hanyar ƙananun maganar da ya fara jin na tashi, da ƙyar su Ma'aruff suka miƙe, dan sun san gaskiya Yaya Imran ɗin ya faɗa. Dada ne ƙarshen miƙewa riƙe da Mammah da har yanzu hawaye sun gagara barinta. Ya kuma maida facemask ɗinsa. A yanda suka fito cikin tsari da nutsuwa duk da kuwa ta hanyar sirri ce yaja hankalin tsirarun mutane dake ta wajen kansu. Dan tamkar ƙyaftawar ido sojojin da suka zo da su da jami'an tsaron da suka tarar na farin kaya a airport ɗin suka zagaye su, suma an ajiye su ne a sirrance batare da sanin su Imran ɗin ba. Wannan kuma duk aikin shugaban ƙasa ne. Mutane da son ɗauke-ɗauke a waya kam har sun fara batare da sun farga da sanin su wanene ba. Sai dai yanda jami'an tsaro sukama mutanen zobe yasa kowa fahimtar koma su waye su lallai masu muhimmanci ne a ƙasar. A haka suka shiga motoci babu ɓata lokaci aka bar wajen. Sai dai mi, kafin ma su isa gida guntayen videos ɗin da wasu suka ɗauka da ƙananun magana da ake a airport ɗin har ya fara yawo a media, sai dai anata canki-in-canka ne na rashin sanin wanene. Mike faruwa?. Yayinda ƴan bin ƙwaf nacan sun fara bibiyar al'amarin dan sunyi ma kansu alƙawarin kafin dare sai sun gano su wanene ɗin.........✍️ 53 .........3:21pm      Jerarrun motocin masu baƙin gilashi suka fice daga filin jirgin cikin tsari mai ɗaukar hankali. Babu jiniya ko wani babban motsi da zai saka ace wani babban ƙusar ƙasa ne, amma tsaron dake zagaye da motocin ya isa ya sanar da kowa ba tafiya bace irin ta yau da kullum, sannan koma su waye sunada wani girma da muhimmanci.        A motar tsakiya da Daddy Imran ya ƙarɓi tuƙin Dada ne a gefensa. A baya Mammah da ƴan gatanta Ruky da Nimrah sun sakata a tsakkiya. A binda zai baka mamaki kamar basu ba bakin surutun nan ya mutu murus. Dan har Daddy Imran ya kasa haƙuri sai da yay magana..           “Mammah wai yau bakunan kafi autanki sun mutu ne? Na jisu tsitt kamar basa a motar nan”.      Murmurshi Mammah tayi da ɗan kallon Nimrah da Ruƙayyan da suka lafe a jikinta. Dan gara ma Ruky wayar Mu'azz ce a hannunta tana kallon hotunan da sukai a airport ɗin. Nimrah kam idanunta a rufe suke da alama tayi zurfi a tunani. Ba kuma tunanin kowa bane face na wannan baƙo nasu da Uncle Ammar ya faɗa musu shine Dadan da suke ji ana faɗa tun tasowarsu. Duk da fuskarsa ta canja daga waccan fuskar data gani a video. Waccan fuskar da babu gashin saje sam, sai dai kuma sajen ne kawai ya bambanta ta da wannan fuskar ta yanzu da itama babu yawan murmushi, babu sakewa, babu filin kai wargi. Sai tsabar kwarjini, kamala, hasken ibada, kamewa da tarin cikar haiba irin ta masu tantsar riƙe girma. Tabbas a wannan gaɓar ta shiga ruɗani mai tsanani akan wannan fuskar da zuciyarta ta kasa yankema hukuncin daya dace. Jitai hotunan bidiyon na son dawowa. Sautin muryoyin da ke zargi na so sake yi mata amsa kuwwa.....      Tunaninta ne ya katse saboda girgizatan da Mammah tayi. “Nimrah mi kike tunani haka?”.     Mammah ta faɗa tana kafeta da idanu. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki tana girgizama Mammah kai da faɗin, “Mammah ba komai”.         “Karya take yi wlhy Mammah, gaba ɗaya yanzu haka ta koma, haka kawai sai kiga ta shiga tunani bare ma idan muna ɗaki mu kaɗai, a gaban ku ne batayi”. Ruky ce mai maganar tana hararar Nimrah. Itama ramawa tayi, sai dai batace komai ba. Sai Daddy Imran ne ya ce, “Nima dai naso lura da haka, duk tayi sanyi babu kuzari. Daughter mike faruwa? Ko baki da lafiya ne?”.       Idanun Nimrah suka ɗan ciki da hawaye, muryarta na ɗan shigewa ciki ta ce, “ALLAH ba komai Daddy sharri take mun. Kuma lafiyata ƙalau” sai ga hawaye sharr. Mammah da taji hankalinta ya tashi ta kamota jikinta, dan ita kanta a tsakanin nan tana lura da Nimrah ta ɗan rage kauɗi, sai take tunanin ko exam ɗin da suka fara ce a makaranta. Itama dai Ruky idonta har ya tara ƙwalla. Ta riƙo hannun Nimrah cikin nata tana faɗin, “Dan nace haka kike kuka, to kiyi haƙuri bazan ƙara ba”.        Cikin ɗan tura baki Nimrah dake kwance jikin Mammah ta ce, “Nifa ba dan kinyi magana bane ba, kawai kaina ke ciwo”.       Sannu Mammah da Ruky suka shiga jera mata. Daddy Imran kam ya saki murmushi da faɗin, “Mammah kina fama.”        Duk abinda suke Dada na jinsu. Amma ko motsawa daga yanda yake zaune bayansa kwance jikin kujera ya lumshe idanunsa baiyi ba. Zama ka rantse barci yake a hakan...      Dai-dai nan jerarrun motocin dake tafe da tawagar jami'an tsaro suka iso cikin anguwar. Tsakiyar KOBI STREET. Dai-dai gate ɗin gidan zuri'ar Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi da yasa mutane fara farga da abinda ke faruwa. Dan kuwa duk da akwai jami'an tsaro a tare da su hakan bai hana wasu biyosu ba tun daga airport dan samun labari duk da su ɗin ba ƴan jarida bane, amma ganin Imran da yaso fargar da masu wayo yasa suka tsargu shiyyasa suka biyo su dan tabbatarwa, da alama kuma zasu samu abinda suke so ɗin musamman ganin inda motocin suke ƙoƙarin shiga.        Maigadi kansa ya girgiza da abinda ya gani, balle su Malam Buba dan su Mammah basu fita da driver ko ɗaya ba daga gida duk su Ammar ne suka ja motocin sanda zasu fita. Yanzu kam wasu motocin ma sai sojojin nan ne suka dawo da su dan har suka iso gida hawaye wasun su sun kasa tsayawa. Sai da gaba ɗaya motocin suka gama shigowa kafin kowa ya fara ƙoƙarin fita. Su maigadi dai sunyi tsuru-tsuru suna kallon ikon ALLAH. Kusan motar su Mammah ce ƙarshen buɗewa, Nimrah da Ruky suka fara fita, kafin itama Mammah ta fito hankalinta duk akan Nimrah datai mata wani kalar tausayi. Riƙota tai tana kai hannu a goshinta,         “Ciwon kan ne?”.    Nimrah ta ɗan girgiza kai tana Kama hannun Ruky da itama ta zagayo inda suke cike da damuwar yanayin twiny ɗinta. Dai-dai nan aka buɗe ƙofor ɓangaren da Dada yake, a nutse ya fara sauke ƙafafunsa dake sanye cikin baƙin takalmi Boot mai ɗan tsaho. Kafin bayyanar baƙin wandonsa zuwa shafaffen cikinsa dake kwance cikin bakar t-shirt ɗin jikinsa kasancewar yayi zanzaro ne. Daga maigadi har Driver suka ɗan zuba masa ido daga can inda suke tsaye tamkar an basu aikin yin hakan ne. Har sai da ya kammala tsayawa cak akan ƙafafunsa sannan suka ɗaga idanun nasu a hankali zuwa kan fuskarsa dake sakaye cikin norse mask da p-cap.        Shi kam da bai san sunayi ba, sai ma a bazata juyayyun idanunsa suka sauka akan Nimrah da Mammah kema magana ƙasa-ƙasa tana tattaɓa mata kai, anyi sa'a itama ta ɗago nata zata harari Mu'azz daya ƙaraso wajen yana tsokanarta wai tana ma Mammah shagwaɓa, ai ko sai idanun Dada cikin natan. cikin sauri ta janye dan har tsakkiyar ƙwalwa taji kaifinsu da tasirinsu ya riski tsakiyar zuciyarta.      Shi kam baima nuna yasan mi akai ba ya maida idanun nasa ga kallon gidan cike da mazewa.......        °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°                   ★Gaba ɗaya tambayoyin zuciya sun gagara ƙarewa a zukatan su Maigadi dama jami'an sojan da aka bari gidan, dan suma dai har yanzu basu san wanene ba balle abinda ke faruwa. Sai dai duk sun sha jinin jikinsu. Amma a ɓangaren mutane biyu da suka san Dada tun a baya sun shaida tabbas shi ne ba saƙo ba ba kuma mafarki ba duk da yaƙi buɗe fuska. Dan haka suka kasance a firgice fiye da sauran. Saboda ɗimuwa ce ta gaske ta samesu da ruɗani na bazata. Tambayar kawunansu kawai suke ta yaya hakan zata kasance? Dan tabbas wanda akace an fitar a prison kwanaki biyar kacal da suka shuɗe ba zaiyi kama da hakan ba sam a idanun mai kallo. Yafi kama da jarumin dake rayuwa a ni'imtaccen muhalli da kwanciyar hankali da nutsuwar rayuwa. Da alama ana raina musu hankali ne ko wani abu daban gaskiya...... <<%>><<%>><<%>>              Gab da magriba Daddy Imran ya bar gidan. Su Aunty Ummi kam har akai isha'i suna nan abinsu suna hidima da Dada. Dan abubuwan da aka shirya masa harma ya rasa mizai ci a ciki.        Abin zai baka mamaki yanda gidan ya nutsu babu hayaniya duk da yaran dake cike da shi. Amma kowa ya nutsu waje guda alamar wargi ma waje yake samu. Duk da kuwa baƙon idon daya saka su nutsuwar ko harara baima kowa ba. Hasalima cike da so da ƙauna ya dinga rungumesu lokacin da ake gabatar masa da kowa da sunayensu. Dan Mammah bata rage kowa ba hatta ƴaƴan Uncle Tasi'u ya masa bayanin su a taƙaice, sai dai komai baice akan su ba. Ga shi macen ta mugu-mugun jin mutuwa akansa. Dan a cewarta bata taɓa ganin namijin daya daki zuciyarta a kallon farko irin Dadan ba, wanda ita kanta ta tabbatar ko cikakken kallo ɗaya bai mata ba. Lokacin da akai masa rakiya ɗakinsa da aka zubama kaya jiya jitai tamkar tayi tsuntsuwa ta bishi, sai dai babu dama...       Duk wannan bidirin da ake babu Nimrah a falon, dan tunda suka shigo tai wucewarta ɗakinsu. Kayan jikinta da gaba ɗaya ƙamshin turaren Dada ya gauraye ta cire, jin ƙamshin yaƙi barin har jikinta dole tai wanka kafin al'awalar la'adar. Koda ta fito tai sallar sai ta haye gado ta kwanta dan wani ma ɗan zazzaɓi take ji. Lokacin da za'aci abinci bayan dawowar mazan sallar la'asar Mammah taga babu ita ta fara jajenta. Dan haka ta aika a duba mata ita. Nusaiba da tazo kiranta ta sameta kwance, sai tai tunanin barci take, dan haka ta koma tace tana barci. Mammah datai tunanin ko ciwon kan ne tace a barta tayi barcin... Nimrah da sarai tana jin sanda Nusaiba ta shigo tun tana juye-jiye da tunane-tunane har barcin gaskiya ya ɗauketa, daga nan kuma zazzaɓin na gaske ya rufeta. Gab da magriba Mammah ta shigo ɗakin da kanta, anan taji jikin nata da zafi. Babu ɓata lokaci ta saka Biebah ta haɗo mata abinci da magani, tashinta Mammah tayi, da ƙyar kuwa ta yarda taci abincin kaɗan tasha maganin, sai ga amai. Aman ne ya sata galabaita dole aka kira doctor ya dubata. Tunda ya dubata yay mata allura ta sake komawa barci shine bata farka ba sai kusan tara saura.        Lokacin su Aunty Mommy da Mammah ta kora gida akan dole duk suka shigo suka sake dubata suka wuce. Sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, dan Mammah ta tabbatar weekend ɗin nan kaf a gidan zasu yi shi. Yo sukai yawo mara dalili ma balle wannan mai dalili ya samu. Ruky na ɗakin Nimrah ta farka, cike da farin ciki tai kanta, dan tun da Nimrah tai amai aka kira doctor itama ta koma kalar tausayi, abokiyar rayuwa ba lafiya ba nutsuwa. Ita ta shiga hidima da ita sai kuma ga Biebah ta samesu, dan ta baro ɗakinta ne tana mitar takura mata da zaman Hanoon yayi, yarinyar ta cika iyayi da feleƙe, ko jiya dauriya kawai tayi da ƴar kunyar baƙunta ga Hanoon ɗin, amma harga ALLAH yau ji take bazata iya ba. Itama ganin Nimrah ta farka sai ta sakin batun Hanoon ta nufesu da farin ciki tana mata sannu..........✍️ 54 .......Afalo kam su Kulu ne ke faman tsaftacesa, dan harsu Ja'afar Mammah ta kora sashensu. Tace kowa yaje ya huta a barma gobe kuma idan ALLAH ya kaimu. Kodan su Lailah dake fama da kansu, musamman ma Shariffa data tsufa da yawa. Badan sun so ba suka wuce, dan Dadan ma tuni yana ɗakinsa dan ya samu ya huta da wannan hayaniyar.       Tamkar ba dare ba su Kulu suka gama gyaran ko'ina suka saka ƙamshi. Sai falon ya ƙara zama cikin nutsuwa.  Shayin Mammah na ƙa'ida Kulu ta ɗauka takai mata ɗaki, ta sameta zaune tana karatun Alkur'ani, dan haka ta ajiye sannan tai mata sallama dan zasu wuce suma su kwanta yau sun sha aiki, dan ma su Aunty Mimi basu barsu su kaɗai ba sun tayasu. Kai kawai Mammah ta ɗaga mata, ta cigaba da karatunta. Itama sai ta fice tana jin ƙaunar wannan baiwa har ƙasan zuciyarta. Duk da basu san miya faru da Dada ba, yanda ƴan gidan basa gajiya da hirarsa sun san yau suna cikin matsanancin farin ciki da dawowar tasa. Dan ko su yau da ganinsu na farko da shi sun tabbatar lallai shine zakin gidan, sannan garkuwa mai ɗaukar matsayin uba...       ✨✨✨✨✨✨✨     Tunda ya shigo ɗakin da komai na cikinsa ya tabbatar sabo ne ya tsaya shiru yana kallon komai daki-daki. An shirya komai fiye da yanda yake buƙata. Ga ƙamshi mai ƙarama zuciya butsuwa na tashi. A hankali ya kai zaune cikin sofar ɗakin, cikin yanayin zamansa na ƙasaita da girma ya kwantar da kansa tare da lumshe idanunsa dake nuna matuƙar gajiya. A karo na farko tunanin da yaketa dannewa ya shiga dawo masa cikin kai. Yaga kowa daga zuri'arsa harma da wanda aka haifa baya nan amma babu Nabeeha. Ina ta shiga? Tunda yabar gidan ne itama bata nan? Ko tayi tafiya ne tunda babu wanda yasan da dawowar sa. Maimakon samun waɗan nan amsoshin sabuwar hoton fuska ya gitta masa a brain, ba kowa bace sai Nimrah. Yarinyar da ya bari tana shekara bakwai… yanzu ta zama mace, cikin tsabta, nutsuwa, da wani yanayi mai ban mamaki. Damuwar da ya karanta a tattare da ita tazo masa a tsakkiyar tunani, sai kuma sanda yake magana da Imran Bilal ya shigo da wani, wanin da yaji sun kira doctor wai zai dubata bata da lafiya. Baiyi magana ba a lokacin sai Imran ma ya tashi yabi Bilal ɗin, yana gurin kuma har Imran ɗin ya dawo, shi kuma bai tambayi abinda ya faru ba, Imran ɗin kuma yaƙi faɗa masa komai suka cigaba da maganarsu. Ji yake acan wani sashe na zuciyarsa kamar ya kamata yasan mike damunta. Koba komai ita ɗin AMANARSA ce ai...       Idanunsa ya buɗe tare da ture tunane-tunanen ya miƙe. Kai tsaye ƙofar da yake tsammanin ta bathroom ce ya nufa, dan gwara yaje yay wanka ko zai samu nutsuwa daga waɗan nan shirmen tunanin nasa...        Ƙarfe goma dai-dai ya kammala kimtsawa cikin kaya marasa nauyi daga akwatin kayan da sukazo da shi daga Germany. Ya saka turare kaɗan. Maimakon kwanciya sai ya nufi hanyar fita, dan yaji hira da Mammah kawai yake buƙatar yi. Bai san suwaye da waye a upstairs ɗin ba. Bai kuma yi tunanin leƙa kowane ɗaki ba ya sauka ƙasa. Tunkan ya gama sauka a stairscase ɗin ya fahimci babu kowa a falon. Dan hatta fitilu sa ma an kashe. Ƙaramin murmushi iya lips ya kufce masa, dan yasan aikin Mammah ne wannan, in ba haka ba yaran nan zasu iya kwana suna hira basu gaji ba balle tunawa da gidajen auren su.                    Ƙofofi huɗu na corridor ɗin daya tabbatar bedroom ɗin Mammah na cikinsu ya zubama ido, bai san wanne ne ɗakin ba, amma yana ƙyautata zaton na farko ne. Duk da haka sai da yay kusan sakan biyu kafin yay knocking ƙofar.      Daga ciki Mammah dake ƙoƙarin rufe Alkur'ani ta juya tana kallon ƙofar, sai kuma ta furta, “Waye? Shigo”.         “Uhhmm”.    Ya faɗa cikin maƙoshi tare da   murza handle ɗin ƙofar. Cikin takunsa na nutsuwa da ƙasaita ya tura ƙofar ya shiga da sallama mai cike da girmamawa.. A jiyar zuciya mai nauyi Mammah ta sauke da jin muryarsa, kafin fuskarta ta washe da murmushi mai sanyi tana mai zuba masa raunanan idannunta. Sai da ya kai zaune kusa da ita, sannan ya furta, “My Sweet Mammah”.          Murmurshi Mammah ya ƙara ƙawatuwa, jin komai take tamkar a mafarkin data saba. Cike da jin nutsuwar zuciya na tuna zahiri ne ba mafarki ba ta furta, “Na zata yanzu kamayi nisa a barci Muhammad”.        “Mammah na kasa barcin ne, shiyyasa na taho kawai muyi hirarmu mu more, hira ta zahiri ba wadda nake gani a mafarkina ba. Ina yaran naki? Naji gidan shiru tun 10”.           “Duk na kora kowa makwanci, su kuma iyayen dabar gida, dan in aka biye musu nan zasuce zasu kwana ma”.       Ya ɗan murmusa. “Har yanzu basu canja hali ba kenan?”.         “Cabjawar tasu ɗin nan ai babu rana, ƙila to in kun fara aurar da ƴaƴa.”      Yanzun ma murmushin ya sake yi. Itama Mammah shayin data zuba masa ta ajiye gabansa tana nata murmushin. Daga haka suka cigaba da hira cike da shauƙi da kewa. Gaba ɗaya hirar ta ta'allaƙa ne akan abubuwan da suka faru a lokacin da baya nan. Musamman gyaran gidan nan, albarkar kasuwancin su daya sake haɓaka, auren su Ma'aruff da akasha kicimmili, da yanzu su Bilal da suka dage akan sai randa ya dawo zasuyi nasu. Ganin bai tambayi ina Nabeeha ba ita ta ɗakko masa batunta akan zuwa da safe zata kira Hajiya Hasiba ta sanar musu tunda basu san da dawowar tasa ba.      Shiru yay kamar bazai ce komai ba akan batun, sai zuwa can har ma ta ɗakko wani sai kuma ya furta,           “Ba gidan take zaune ba kenan?”.      Mammah ta ɗanyi murmushi da girgiza kai. “Yanzu dai ya kamata ta dawo ɗin, tunda gaka sai ka bata haƙuri akan laifin da take gani ka mata, in sha ALLAHU a satin nan za'a zuba kaya a sashen naku.”          Yanzu ma maimakon amsa batun zai bada haƙurin ko zuba kaya a sashen nasu sai kawai cayay, “Zan huta anan sashen dai tukunna Mammah. Yaran can uku kuma kukace yaran Uncle waye?...”          Mammah tasan sarai ya fahimci wa ake nufi tun a ɗazun, kawai yana son sake ji ne a bakinta. Murmurshi tayi da jinjina halin Muhammad ɗinta da bazai canja ba. Kai tsaye ta maimaita masa sunan Uncle Tasi'u ɗin, ta kuma ɗora da labarin duk yanda suka haɗu a Egypt har kicimillin da aka sha da ƙannensa a watannin baya da yasa Uncle Tasi'un haƙura ya koma kan aikinsa sai jiya kuma yazo da yaran. Ta lissafa masa sunansu. “Babban shine Dayyan, sunan mahaifinku ya saka masa, sai macen Hanoon, ƙaramin Afeef. Nasan halinka Muhammad, sannan nasan halin ƙannenka, in har baka amshi tuban Tasi'u ba suma zasu sake birkicewa ne. Nasan shi mai laifi ne a garemu, amma sanda ya aikata yaransa basu sani ba ma. Sannan shima daya aikata ɗin bai ragemu da komai ba da UBANGIJI ya ƙaddara zamu samu, sai ma ɗaukaka da sanadin hakan ya jawo mana. Tunda gamu a yau cikin rufin asirin ALLAH da yalwarsa da har shima yazo ya raɓemu da zuriarsa zai ci. Dan ALLAH da kaina ina roƙon komai ya wuce kaji”.         Dada daya zubama Mammah idanu ya ɗan murmusa. Sosai yake jin wannan baiwar ALLAH a zuciyarsa, yana mata wata irin ƙaun mara misali, kyawawan halayyar nan tata ita ke sakashi yin sanyi a wasu lokutan koda ya ɗauki zafi damuwa ta mamayesa. Tabbas wanda ya samu mahaifiya irin Mmamansa ya more, dan uwa ɗaya ce tamkar da dubu. Flaks ɗin shayinta ya ɗauka ya ƙara kawai, batare daya sake cewa komai akan zancen ba. Itama bata sake cewar ba, sai ma ta ɗakko wani batun.      Sun cigaba da hirarsu har sha ɗaya da wani abu, agogo ta kalla da faɗin ya kamata yaje ya kwanta. Sai ya kalla gadonta dake gyare tsaff yana murmurshi. “Anya Mammah ba gadonki zaki bani na kwana ba, maybe hakan yasa na sake yarda ba mafarki nake ba fa ina tare dake a yau ɗina.”         Cikin ƴar dariya Mammah dake kallon gadon itama ta ce, “In dai gado ne gashi nan Muhammad kayi kwanciyarka akai”.           “To Mammah ke fa?”.      “Ga ɗaki nan ba kowa, dama ɗazu su Mimi sun saka a gyara musu shi na kora su.”     “A'a Mammah kiyi kwanciyarki a ɗakin ki, zan koma sama na kwanta”.       “Ai ni nace ka kwanta abinka ko. Bari ma kaga na duba Nimrah ko zazzaɓin nata ya sauka. Dan duk ciwon da kaga ya kwantar da Nimrah da Ruƙayya ba ƙarami bane ba.”              A karo na farko kan al'amarinta ya furta, “Kina shagwaɓa su ne da yawa Mammah shiyyasa.”       “Toba dole ba Muhammad, ku yanzu duk kun girma, idan nace wayyo kafin naga wani a cikinku na gansu su huɗun nan. Ga Biebah kam tunda ka dawo gida na tabbatar ta fara mana bankwana kuma.”             “Ai gara ta tafi nata ɗakin itama haka nan Mammah. Yanzu fa kusan 26 take nema. Damma bata da girman jiki tunda har su Ruƙƙayya na neman taddota naga”.        “Ruƙayya da Nimrah kam tubarkalla, dan nan da wata shekarar tsaff zasu danne uwar tasu kam. A hakama wai tattalin jiki suke basa son suyi ƙiba.”       Guntun murmushi Dada yayi da ɗan taɓe baki. Itama Mammah data kammala haɗa duk abinda take buƙata tai masa sallama ta fice. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali. Sai kuma ya miƙe ya hau gadon da bismilah, wani irin sanyi na ratsa masa zuciya da ɓargon jiki. Shifa yanda yake jin kewar Mammah bai ƙi ace ma ya kwanta a kusa da ita ba ko zai samu sassauci....        Koda Mammah ta fita sai da ta share guntayen hawaye tana murmurshi, kayan nata takai ɗakin kusa da natan sannan ya nufi ɗakin su Nimrah. Har sun kashe fitila alamar sun kwanta, dan haka ta haska da fitilar wayarta tana ƙarasawa. Ganin Biebah a ɗakin ya bata mamaki, sai dai batace komai ba ta tattaɓa jikin Nimrah dake barci, jin zazzaɓin ya sauka yasa ta sauke ajiyar zuciya. Addu'a ta sake musu su duka sannan ta fice. Koda ta koma ɗakin ba kwanciya tayi ba, alwala ma ta ɗauro ta kabbara salla....       Kusan 12:30 Nimrah ta farka. Bayi ta shiga tayi fitsari, koda ta fito ta koma gadon sai ta kasa barci. Tunane-tunane marasa daɗi suka cika ƙwaƙwalwata. Tun tana turesu da fatan barci ya sake ɗaukarta harta fahimci bafa ɗaukar tata zaiyi ba. Ga kanta har ya fara mata ciwo. Bargon ta yaye tare da sakkowa a gadon ta saka bedroom slippers ɗinta ta fito a ɗakin gaba ɗaya. Gara ta koma ɗakin Mammah ƙila gurɓataccen tunanin nan nata ya barta karma zazzaɓin daya sauka mata ya sake dawowa. A hankali ta murɗa ƙofar ta shiga dan tasan Mammah ta kwanta yanzu, dan tana barcin wuri saboda tashi sallar dare da bata wuceta. Bata damu da ganin ɗakin da duhu ba, dan Mammah bata son kwana da haske koda na lamp ne, shiyyasa suma suka koya. Da lalube ta isa gadon, hankali kwance ta haye, jin mutum data san Mammah ce yasa ta matsa sosai ta shige jikinta tare da gyara bargo da ƙyau........✍️         Yau fa akeyinta, ke madam Ninah ya da haka?🤣. Gaskiya Dada kana cikin alheri yau ɗin nan🤭, ga tsuntsu daga sama gasashe😂 koya kukace mutane na🥱😜. 55 ...........“Baka ganin kayi gaggawa akan fitar da yaron nan kuwa Genaral? Kasan fa ita siyasa shegiyar aba ce a zahirinta da baɗinin ta.”        Murmushi shugaban ƙasa yayi mai ƙayatarwa, cike da girmamawa irin wadda ake bama oga, duk da ba wani girmarsa yayi sosai ba, amma a siyasa ubangida zai kira shi. “Ranka ya daɗe a zahiri wasu zasu iya kallon al'amarin a haka. Sai dai idan mukai dubi da gaskiya abinda ya dace ace nayi kenan akan Haysam. Duk wanda yasan shari'ar Haysam a shekara takwas data gabata ya san Shari'a ce ta gaba gaɗi akayi. Dan kuwa an ɓoye muhimman hujjoji da yawa shiyyasa shari'ar ta taƙaita aka rufesa. A yanzu kuma fito da shi zai taka rawar gani mai yawa dana tabbatar kowa zai ji daɗinta.”         “Hakane, ni ka cire tani na fahimceka, kuma ina goyon bayanka akan duk abinda zaka yi. Sai dai lokaci yayi da zaka duba ƴan jam'iyya suma. Kayi baɗe-naɗen bada muƙamai a fara gudanar da mulki. Sannan shi Haysam ɗin wane shiri kake da shi a kansa? Dan bayan takardar afuwa baka sake cewa komai ba game da fitarsa a prison ɗin. Ya kamata kayi abinda ya dace kafin masu hannu a rufesa su suyi wani motsi. Dan na tabbatar ba zasu kwanta barci ba awannan gaɓar”.         Ba saurare kawai ba, tasiri sosai maganganun ogan keyi a kwakwalwar Janar. Amma sai ya murmusa cike da dattako ya furta, “In sha ALLAHU duka za'a duba ayi kuma abinda ya dace. Sai dai ƴan jam'iyya zamu iya samun matsala da su akan batun 60-40 na muƙamai”.          “Saboda mi?”.      “Saboda gwamnatin mu ta zama ta kowa da kowa ce ba ƴan jam'iyya da suke ganin sunyi wahala dan jiran waɗan nan sakamakon ba. Idan ma har za'ai 60-40 ya kama ace itama jam'iyya tayi 30-30 ita da sauran al'ummar wajen jam'iyar. Hakan zai ƙara kimantamu a fahimci canjin mu daga na jiya zuwa yau. Bawai akoda yaushe ƴan ƙasa suyita ganin fuskokin da tun haihuwarsu sune ke mulkar su ba. Abar matasa da shaye-shayen ƙwaya kawai da bangar siyasa. Mutum ɗaya kaga yayi kansila, yayi Chairman, yayi Dan majalisar jiha, yayi gwamna, ya koma ɗan majalisar tarayya, wani shugaban jam'iyya, gobe minister, jibi takarar shugaban ƙasa why? A ƙasar mu kawai ake wannan kwamacalar, ai ko a gidanka kullum ake maka abinci kala ɗaya zaka gaji, kuma duk yanda za'aso canja kalar miyyar zakaji ɗanɗanon ɗaya ne dai tunda hannu ɗaya ya girka. Oga mu kalla komai da idon basira mana”.        Sosai oga ke jinjina kai da yima kalaman Janar fashin baƙi dalla-dalla, lallai gaskiyar Oga Jush janar Yusuf da shirinsa ya shigo. Ya kwantar musu da kai ne kawai dan samun nasarar kai da kai. Hakan kuma na nufin dole ya ɗanɗana kuɗarsa. A zahiri kam murmurshi yayi mai ƙayatarwa. Cike da makirci ya furta, “Tabbas zancenka nakan gaskiya. Kuma na gamsu kwarai da gaske. Sai dai kuma ta ina ya kamata mu fara? Menene shirin ka kai a yanzu? Musamman ma akan Haysam da kake gani zai iya taka mana wata rawa a mulkin nan?”.       Shirye-shirye kam nada yawa oga, bani kuma da hurumin zartar da su sai an zauna tebirin shawara. Akan Haysam kam bani da wani shiri bayan fitar da shi gaskiya. Hasalima bana jin Haysam zai yarda ya koma gidan soja, dan likitoci sun tabbatar bashi da isashiyar lafiya, yana buƙatar dogon hutu a gida ko asibiti. Kaga kuwa bai kamata mu tunkare shi da wani batun aikin gwamnati ba yanzu tukunna. Sai in har ya buƙaci hakan ne da kansa”.     Harga ALLAH a wannan gaɓar sai da Oga yaji ajiyar zuciya mai ƙarfi na neman kufce masa. Ya dai danne da ƙyar......        🤣🤣Na lura da Janar ya fara zama makiri hwa shima🤭🏃. >>>>>>>★<<<<<<<<        Jin ƙamshin daba na Mammah ba bai sa Nimrah ta fahimci inda ta kawo kanta ba. Dan turaren, turare ne da bata san kowa da shi a gidan ba, sannan ba irin shi Dadan yake ba a ɗazun. A maimakon ma fahimta ko tunanin wani abu kasala irin ta mai son yin barci ta risketa. Cike da shagwaɓa muryarta a ɗan ɗashe irin na wadda ta tashi a ciwo da muryar raɗa ta furta, “My Mammah goodnight, ki min addu'a idan kin tashi salla”. Daga haka ta rufe idannunta tana sake naɗe jikinta a jikin da zuciyarta ke bata na Mammah ne saboda rashin man kai...           Tun daga buɗe ƙofar ɗakin, shigowarta zuwa hawowa gadon duk a cikin kunensa. Amma da yake mazan maza ne koda ta shige masa a jiki bai motsa ba, baima da niyyar yin hakan face mamakinta daya cika masa zuciya. Idan banda rashin man kai da wautar yarinyar nan taya zata kasa bambance jikin Mammah da nasa. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya daga cikin ƙirjinsa, shi ba abin ya motsa ba ko sanar mata ba Mammah da take tunani bace girma yay tangal-tangal. To mima ya kaishi wannan gangancin, ai gara ya barta kawai yanda ƙafarta ta kawota ta fitar da ita, ko shi zuwa anjima idan tayi barci ya sulale yabar mata ɗakin. Dan da yasan ma suna shigowa kwana irin haka da bai kawo kansa ba shi kam... Tunaninsa ya tsaya cak, saboda yanda ta juyo gaba ɗayanta yana fuskantar sa. Yanda ta sake ƙanƙamesa dole ya lumshe idanunsa dake cike da son yin barci yana ɗan cizar lips. Sai da ta gama mutsu-mutsunta dan kanta ta nutsu tana sake mamuƙeshi sannan ya saki numfashin daya riƙe a cikin ƙirjinsa. A haka ya fara jin saukar ɗumin numfashinta a hankali cikin jikinsa. Tun yana saurarenta har shima barcin yay awon gaba da shi batare da ya farga ba, dan ya gaji matuƙa, ga magunguna da yake sha na saka shi barci dama. Ga hayaniyar daya sha yau tasu da yawan magana da aka saka shi.....       Ƙarfe uku dai-dai ya farka, sabo da tashi sallar dare yasa komai nauyin barcin da yake ciki idan lokacin yayi sai ya farka. Idanunsa ya buɗe a hankali, tare da karanto addu'ar tashi barci a saman lips ɗinsa. Ya motsa hannunsa da nufin kunna lamp yaji ya masa nauyi, ya ɗan laluba da ɗayan sai yaji mutum. Abinda ya faru a farkon dare ne ya faɗo masa. Ya ɗan cije lips ɗinsa kaɗan yana kai hannun ƙasan pillow, ALLAH ya taimake sa ya samo wayarsa. Dannata yay screen ɗin ya kawo haske, kai tsaye hasken ya faɗa kan kyakkyawar black beauty face ɗinta. Cikakkiyar girar ido da eyelashes da suka dace da girman idanunta, hancinta dake zaune ɗaram a fuskar tata da madaidaicin bakin tsiwa mai pink da baƙi. Cike da kame kai irin na manyan jarumai da nutsuwa ya janye idanun kai kace baiga komai ba ma. Sai ma zameta ya shiga yi a hankali daga jikinsa data kanainaye dan gaba ɗayanta a rabin jikin nasa take, yanda har ya gyara mata kwanciya ya ja bargon ya rufa mata bata ko motsa ba sai ma filon daya saka mata a madadinsa ta sake kanainayewa ya sashi fahimtar tana da nauyin barci, sannan ta saba da wannan rungume filon shiyyasa shima ta masa ɗaurin goro batare data fahimci shi ba filon nata bane ba.         Bedroom slippers ɗinsa ya saka ya fice a ɗakin dan gwara salin alin ya bar mata ɗakin ya koma inda ya baro ya ƙarasa daren kada a tafka abin kunya. Ko'a mafarki bazai so ta buɗe ido ta ganshi ba balle tasan abinda ya faru.....      ★Itama saboda da tashi sallar asuba ya saka ta farkawa a kiran sallar farko. Duk da suma Mammah ta horesu da tashi sallar dare tun basu kai hakan ba. Yau ma dan alluran da doctor yay mata ne sukai tasiri wajen ƙara nauyin barcinta yasa har bata farka ba a lokacin da sukan tashin. Cikin lalube take kiran sunan Mammah, sai dai jin shiru da jin gadon empty sai ita kadai yasa ta buɗe idon. Dama tasan da wuya Mammah takai yanzu a gado bata sauka ba, dan ita in har ta tashi sallar ta ta dare bata sake komawa gado kuma sai in barcin rana.      Nimrah na buɗe ido ta maida ta rufe saboda ganin duhu. “Mammah baki kunna fitila ba? Wayyo duhu ba ƙyau”. Tayi maganar ne da mirginawa gefen gadon cikin lalube ta taɓa makunnar lamp. A take kuwa ɗakin ya gauraye da haske, sannan ta buɗe idanun. Ɗaki dai shiru babu alamar Mammah a ciki, dan haka ta shiga waige-waige, sai kuma ta zubama inda alamun kwanciyar mutum ta nuna idanu. Ta ɗauke ta maida toilet, sai dai tsin babu alamar motsin ruwa a nan ma, dan haka ta sauka a gadon gaba ɗaya. Kamar yanda suka saba gyara gado da sun farka yasa ta janye blanket ɗin da filos tahau ƙoƙarin gyarawa. Ta kammala tana maida filoluwan idannunta suka sauka akan baƙin agogon dake a side drawer, mai ƙyau da tsada da tambarin sunan mawaad Company. Daga gani kasan an saye shi da kuɗi masu nauyi. Bata kawo komai a ranta ba ta ɗauke idanun nata ta ƙarasa aikinta. Tunanin Mammah na bayin yasa ta fice abinta zuwa ɗakinsu.       Ta samu suma su Biebah duk sun tashi, dan daga ita har Ruƙayya akan sallaya ma suke. Ruky na Sallah Biebah na karatun Alkur'ani. Sai ita ma ta wuce bayi abinta. Da yake sheɗan sheɗan ne sai da ta kabbara salla ya tuna mata a hannun data ga agogon nan da rana. Sai ko da ƙirjinta ya buga, da ƙyar ta iya ture tunanin a ranta ta cigaba da sallarta. Suna idarwa kuma suka hau tilawar Alkur'ani dan yau akwai tahfiz akwai kuma amsar hadda. Wannan ya sake mantar da ita batun agogo na wucin gadi.........✍️ 56 ..........8:30am suka fito cikin shirin tahfiz, Mammah ce kawai a falon zaune tana shan shayi. Su Kulu sun gyara ko'ina tsaff sai ƙamshi ke tashi kamar me, dan zuwa yanzu ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Sun gama kama gidan tako ina.  yanda Nimrah da Ruky ke faman tuttura baki gaba yasa Mammah faɗin, “Oh oh mi akama Autaras ɗin Mammah? Kuzo naji”.       Inda take duk suka nufa, yayinda Biebah ke faɗin, “Yo Mammah miza'ai musu, halin ne ya motsa makarantar ce basa son zuwa”.          Rungumesu Mammah tayi tana faɗin, “Su dai basu ce ba Biebah, zasuje makarantar su ko?”. Tai maganar tana taɓa wuyan Nimrah. “Kinga babu ma zazzaɓin”.        Sake langaɓe mata sukai suna shagwaɓar su, dai-dai nan Mu'azz da Ammar da suka fara sakkowa daga stairscase, cike da neman tsokana Mu'azz ya kalli su Nimrah da suka tashi daga jikin Mammah zasu je dinning ke faɗin. “Tunda kaga Zakanya da Damisa na kumbura yau akwai ɗaukar magana a makaranta kenan.”      Ammar dake dariya ya ce, “Kada ka musu sharri”.         “Hummm ALLAH Uncle baku fahimce su bane, duk randa yaran nan basa son zuwa makaranta ka kula sai sun ɗakko magana. Kuma zaka ce nina faɗa maka. Kai dai kabar wayarka a kusa da kai kawai, dan nasan za'a kiraka, bare ma kwana biyu basu tafka ta'asar ba”.        Hararasa kawai su Nimrah sukai basu ce komai ba, Mammah dake hararar Mu'azz itama ta ce, “Kar ku kulashi kunji ƴan albarka. Maza kuje ku karya kar ku makara.”        Gwalo suka masa suna matsawa suka gaida Uncle Ammar dake musu dariya. Dai-dai nan suma su Ayyan suka shigo da gudu cikin nasu shirin. Afrah ta faɗa jikin Nimrah. Sosai bakin Nimrah ya washe da farin ciki, ta ɗauketa suka wuce Dinning dan Biebah da Mu'azz har sun ƙarasa. Yanda suka cika falon da uban surutun su sai ka ɗauka wata gayya ce guda. Mammah da Ammar na daga falo suna tasu hirar. A haka su Yaya Ja'afar suka shigo falon tare da su Shariffa. Cikin girmamawa duk suka gaida Mammah, ta amsa musu da kulawa tana tambayar ya jiki-jiki. Su duka kunya ta hana su amsawa sai murmushi da sukai suna duƙar da kawuna. Sai ga Bilal shima ya sakko, yanda yake ɓata fuska yasa Yaya Ma'aruff tambayarsa lafiya?. Sashen Dining ya harara da faɗin,          “Wlhy yaran nan sun hana ni barci Yaya”.       Shima su Nimrah dake kwasar dariyar abinda Ayyan yake yi ya kalla. Sai kuma ya dawo da kallonsa kan Bilal ɗin yana faɗin, “Ai kai ke ɗaure musu ƙugu dama idan sana wani abun. Sai ka bari su tafi ka koma? Dada fa?”.           “Inaga yana barci shi ma, tunda muka dawo massalaci ya sake shigewa. Yauwa Mammah yaran nan fa kwana biyun nan basa fita sallar asuba wlhy. Dan yanzu haka Dayyan baiyi ko salla ba”.      Tsaki Ammar yayi, cikin takaici ya ce, “Shiyyasa na baro masa ɗakin, nafa tada shi yafi sau uku amma yaƙi tashi. Sai kace wanda yasha wani abu. Ni dai Mammah yau kisa a gyara musu ɗakin baƙi su koma gaskiya”.       Caraf Biebah dake isowa wajen ta ce, “ALLAH nima ƙorafina kenan Yaya. Ita waccan sai latse-latsen wayar banza, ta dameni da charting da dare da dariya.”        Ja'afar da sai yanzu yay magana cikin takaici ya kalla Mammah shima. “To wai tunda sun gaishe mu su koma gida mana? Idan shi Babban ya gama makaranta su kananun fa?”.          Rasa ma abin cewa Mammah tayi, dan gani take taron dangi suke neman yi mata ita kam. Cikin sa'a takun sakkowar Dada ta saka wani bai sake magana ba, sai ma maida hankali sukayi ga stairscase ɗin. Su ko su Nimrah da hankalinsu ba nan ma yake ba sun cigaba da surutun su ne. Dan kusan yana step ɗin ƙarshe Ruky ta taso da gudu da abu a hannu, Nimrah na binta alamar koma miye nata ne Rukyn ta ɗauka. Tsabar kuma basu da man kai ta wajen stairscase ɗin suka yi. Ai ko kaɗan ya rage Ruky taci karo da shi, yay gyaran muryar data ratsa kunnuwansu. Ai ko cak ta tsaya tana zaro idanu, haka ma Nimrah dake bayanta sai da taji zuciyarta ta buga. Lokaci ɗaya falon yin tsitt, dan har su Abees sai da suka nutsu..... Sosai ya zuba musu idanunsa da suka saka su duƙar da kawuna ƙasa. Cikin ƙarfin hali Ruky ta ce, “Dada mun tuba, ALLAH bamu san ka taho ba ne”.       Maimakon tankawa kallonsu kawai yake. Duk sai suka sake firgicewa, Nimrah ta sake ɓoyewa a bayan Ruky kamar wata munafuka. Sai da yaja fin minti ɗaya idanunsa na ladabtar da su kafin ya furta, “Dama ya dace mata suna guje-guje?”.      Kawuna suka shiga girgizawa da sauri. Yanda suke yi ɗin ya bama kowa dariya, sai dai babu mai zarrar yinta a fili inba Mammah ba. Ita kuma murmushi kawai tayi ta ɗauke kanta. Ƙasa-ƙasa Ammar ya furta, “Aiki gamai ƙareka. A kallo kawai Ninah da Ruky sun nutsu dole nayi sadaka idan na fita”.        Mintsininsa Bilal yayi, ya rufe baki yana buge masa hannu. Ya Ma'aruff kam gefe ya kauda ido yana murmurshi bayan sun kalla juna da Twinyn sa Ja'afar.      Shima bai sake ce musu komai ba ya ƙaraso falon, hakan ya saka su Lailah sake nutsuwa kawunansu a ƙasa na girmamawa. Zaune ya kai a kujerar kusa data Mammah, sai kuma ya kalla su Aheel da sukai tsuru-tsuru, to iyayen daba sun nutsu bare su. Hannu ya miƙa musu, babu musu kuwa suka nufe shi su duka ukun. A mamakin kowa kansu ya shiga shafawa fuskarsa na sassautawa duk da ba murmurshi yake ba. Suma yaran sai suka fara gaida shi, duk da ganin jiya kawai sukai masa da alama kamaninsa da iyayensu da yake ya tasirantu a zukatansu.       Ya gaisa da su Ma'aruff duka bayan sun dawo sallar asuba. Amma hakan bai hana su sake gaishes hi ba a yanzu. Suma su Shariffa suka gaishe shi da Biebah. Sai lokacin su Nimrah suka ƙaraso suma suka gaida shi. Biebah yay ma umarnin kawo masa coffee, ta amsa tana nufar kitchen. Bata wani jima ba ta dawo, table taja gabansa tana ajiye masa ƙaramin tray ɗin data ɗora cup ɗin, dai-dai su Nimrah sun kammala tattare kwanikan dining suma. Sun dawo falon da nufin ficewa Mammah ta dawo da batun da su sun ma manta sun fara, dan tasan halinsu zasu iya zagayewa su gayama Dadan nasu.           “Ina roƙonku ku bisu a hankali, kuyi haƙuri kuma da su, kofa ba komai ƴan uwanku ne, da wannan ƙorafin ai inaga kuyi jihadin gyara musu ɗabi'un nasu na banza cikin hikima zai fi ko”.     Kamar Biebah zatai kuka ta ce, “Wlhy Mammah ko mazan zasu canja banda macen. Bata da mutunci fa, da nai mata magana jiya da daddare zatai live da kayan barci catai min wai bata son takura naji da matsalolin gaba na. Shiyyasa na bar mata ɗakin na koma ɗakin su Ninah na kwana”.     Caraf Nimrah ta ce, “Lah Small Mom dama kece? Nifa na zata ita finga fiyau ɗin ce ta shigo mana. ALLAH kaɗan ya rage ban faɗo da ke ba a gadon, kuma da har na ayyana haka a raina naga ban gama fita daga kamun UBANGIJI ba ina zazzaɓi sai na wuce ɗakin Mammah abina acan na kwana nima.”        Dariya su Bilal sukayi saboda (Finga fiyau data kira Hanoon). Yayinda Dada ya kusa ƙone lips da coffee jin taɓargazar da tsuntsuwar yarinyar nan ke neman yi masa, tunda in kowa bai san a ɗakin Mammah ya kwana ba ai ita Mammah ta sani. Sarai Mammah taji mi Nimrah ta faɗa, amma ta basar dan koda ta ɗan kalli Dada ta gefen ido ta lura sai da ya ɗago nasa idanun ya kalla Nimrah ɗin, kafin itama ya saci kallonta.     Ke Biebah da baki san miya faru ba ta amshe zancen Nimrah da faɗin, “Haba naso inyi magana da kika shigo da asuba kina ƙanshin turaren daban sani ba, sai kuma na tuna sanda muka tashi baƙya nan. Kice kaɗan ya rage nasha ƙasa. Ina arziƙi an jeho uwa, dole na fara kwana da fitila indai na shiga ɗakin ku kuwa”.            Ammar da Mu'azz da su Lailah na dariya ƙasa-ƙasa, Dada na ayyana dole ya sallama turaren daya saka a daren jiya kuwa a gidan nan. To Biebah taji ƙamshi ai bashi ba sake saka wannan turare balle ta fahimci daga shi yake.      Ja'afar ne ya katse zancen da faɗin, “Mammah a bar zancen sai an jima. Ku kuma kuwuce kada ku makara”.          Mammah ma ta fahimci dole zancen ya tsaya iya nan kada a kama wani layin, sai dai a ranta tana jinjina hukun UBANGIJI, dan ikonsa ne ya haɗa waccan haɗuwar ta daren jiya a ɗakinta..........✍️ Gaskiya ya kamata a ƙara gasama Nimrah baki karta ɓaro aiki wataran da shegen surutun nan nata😂         Yanda suka kallesa suka watsar ya saka shi jin zafi, amma dan kar abokansa daya tabbatar suna kallonsu su fahimta sai ya sake faɗin, “Bai kamata ace kyawawa kamarku wayayyu suna wannan halin ba. Baƙyau wulaƙanci fa”.         Kallonsa Ruky tai cike da harara da taɓe baki ta ce, “Ka bari sai ka koyi sallama tukunna ka mana wa'azi”.             “Oh sorry! Nayi kuskure. Assalamu alaikum ƙyawawa”.       Yanzun ma Ruky ce kawai ta amsa masa. Nimrah kam ko kallonsa bata sake yi ba dama. Shi su duka birgeshi suke, dan harga ALLAH baya iya tantance wama yake so. Sai dai yanda Nimrah ta watsar da lamarinsa ya sashi zuba mata idanu da faɗin, “I really like your style Baby. Kiyi komai ba komai kin isa ne.”       Karon farko taja tsoki, batare data tanka masan ba dai ta miƙe tana Kama hannun Ruky da itama ta watsa masa harara. Shi ko ɗan iskan sama, sai kawai ya riƙo hannun nasu dake cikin na juna yana neman rungumesu su duka. Hummm babbar bala'i kenan, ai kawai saukar yatsun hannun Ruky biyar yaji akan kyakkyawar farar fuskarsa, bai gama dawowa a hayyacinsa ba Nimrah ta saka gwiwar ƙafarta ta daki gabansa...         Wata irin gigitacciyar ƙara data amsa wajen gaba ɗaya ya fasa yana sakin fuskarsa ya damƙe gaban wandonsa. Ƙafin ma sauran ɗaliban dake wajen suzo kansu ya zube a wajen a sume. Ko'a kwalar rigar su Ruky, dan saima nuna shi da Nimrah tai da yatsa tana faɗin, “Sha-sha-shan banza bunsuru ka ɗauka mu ƴan gidan gala ne. Wannan kaɗan ne daga tunatar dakai tarbiyyar daka rasa. Shege, halan gidanku ba mata ne, miyyasa bakaje ka rungumi gyatunarka ba ai itama mace ce zaka samu biyan buƙatar abinda kake nema......”         “Shike nan kun kashe shi”.      Cewar ɗaya daga cikin abokansa da yay jarumtar taɓa hancinsa da yatsa, da kai kunne ƙirjinsa ya tabbatar zuciyarsa bata bugawa. Maimakon yaran nan su razana kai tsaye Ruky ta ce, “Ai an rage mugun iri”. Taja hannun Nimrah suka bar wajen hankali kwance.        Tuni wajen ya kacame da hayaniyar ɗalibai, wasu kuma suka garzaya sanarma malamai dan abin ya tayar musu da hankali bana wasa ba......       ★✨★✨★✨★✨★     A dai-dai wannan lokacin da waccan cakwakiyar ke faruwa a makaranta anan Daddy Imran ne bisa hanya sun dawo daga wani waje shi da Dada. Shi da kansa yake driving, ta gefensa Dada na zaune ya baza takardu a jikinsa da laptop yana aiki. Yanda motar tai shiru zaka fahimci aikin mai muhimmanci ne. Dan shima Imran ya maida hankalinsa ne kawai ga tuƙinsa, lokaci-lokaci yakan kalla Dadan ya maida kansa ga titin. Sai dai a yanzu koda ya kallesan sai ya ɗauke kansa da faɗin, “Kana buƙatar hutu fa haka nan, dan ka samu nutsuwar fuskantar tattaunawar anjima da shugaban ƙasa. Ga su Dabo sun matsu su ganka suma”.          Ɗan mitsilin murmushin gefen baki ya saki, batare daya daina abinda yake ba ya bama Imran ɗin amsa bayan shuɗewar minti ɗaya.       “Basu san na tsufa ba suke zumuɗin gani na”.      Dariya Imran yayi har yana ɗan dukan streeng. Sai da yay mai isarsa sannan ya ce, “Kaga ko bazan bama tsoho ɗiyata ba, ka lallaɓa matarka ta dawo ka huta wannan shaye-shayen shayi da lomon shamin da kanwa kullum.”           Dada bai bashi amsa ba yanzu kam, sai kai da ya ɗan girgiza kawai. Shima Imran ɗin zai sake magana wayarsa ta hau vibration. Dole ya haɗiye yana kallon wayar. Ganin mai kiran nashi ya sashi faɗin, “ALLAH yasa ba wata magana yaran nan suka ɗakko ba, dan in har naga kiran mutumin nan baya wuce hakan”.         Ɗan ɗagowa Dada yay ya kallesa, hakan yayi dai-dai da amsa wayar. Kasancewar a hansfree yasa har Dadan yana ji, sai ya maida kansa ga aikinsa kawai yana sauraren gaisuwar da Imran keyi da mutumin. Daga can bayan sun kammala gaisawa vice principal ya cigaba da faɗin, “Kayi haƙuri ranka ya daɗe, muna buƙatar ganinka ne da gaggawa anan idan babu damuwa. Dan mun kira ƙaninka Bilal bai ɗauka waya ba maybe baya kusa”. 57 .........“Aunty! Aunty Nabeeha! Aunty please ki tashi”.        Da ƙyar Nabeeha ta iya buɗe idanunta da sukai mata nauyi saboda barci. Dan ko sallar asuba da ƙyar ta tashi tayi ta wajen ƙarfe shida ta sake komawa gado. Yanzu kuma ga Ismat tazo tana tashinta. Akan Ismat ɗin ta sauke su, sai kuma ta sake lumshewa da buɗewar dai.         “K kuma daga ina da safiyar nan?”.      “Daga gida mana. Ina su Momy naji gidan shiru”.      Cikin yamutse fuska Nabeeha tai hamma tana tashi zaune da ƙyar, sai da taja wayarta ta duba agogo. Ganin goma harta wuce ta maida ta ajiye tana bama Ismat amsa. “Momy tayi tafiya, suna Chaina ita da Aunty Amo.”          “Uhmm ita Momy ai bata gajiya da yawo a jirgi kamar ƴar sama jannati. Taita biye ma matar nan, sun sauka a mulkin ma bazata ƙyaleta ta huta ba. Su Amima fa?”.        Baki Nabeeha ta taɓe alamar amsa zancen farko kenan, kafin ta amsa na ƙarshe da faɗin, “A club suka kwana. Ina ƙyautata zaton kuma yau Momy zata dawo ma. Ke dai da gaske kin bar gidan nan ko? Ko takaicin zama da wannan shegiyar matar ta Daddy baƙya yi”.            “Hummm wlhy Aunty Ummu nada kirki, kawai dai bamu fahimceta bane. Yanzu fa ki duba, badan tayi tsayin daka ba Daddy bazai barni na zauna a gidan nan ba, amma wlhy har faɗa saida sukayi a kaina saboda ƙin sauraren Aunty Jiddah da yayi a farko. Ni bama wannan ba, labari na kawo miki mai daɗi, sai dai ban tabbatar da ingancinsa ba.”         Koƙarin sauka Nabeeha tayi a gadon cikin halin ko'in kula tana faɗin, “Labarin mi? Uwar kwashe-kwashe”.       “Hummm Aunty Nabeeha wannan kwasha-kwashan fa indai ya tabbata gaskiya wlhy har ƙyauta zaki bani. Wani ƙishin-ƙishin fa naji a wajen Imam kamar Dada ya dawo gida”.         Cak Nabeeha dake ƙoƙarin shiga bayi ta tsaya, sai kuma ta juyo da sauri tana kallon Ismat dake murmushi. Gira ta ɗaga mata da faɗin, “Bani fa da tabbas, shiyyasa nazo sanar miki ma dan ki bincika. Nayi tunanin su Imam zasuje gidan ne ma sai naga sun wuce tahfiz, Ummu kuma banga tana wani shirin fita ba balle nace zan bita na sami tabbaci. Dan abinda ma ya faru waccan ranar yasa wlhy tsoron zuwa nake ji. Nimrah ɗin nan ba kunya ce da ita ba ita da Ruƙayya”         Nabeeha daba wani saurarenta take ba a yanzu tuni ta dawo bakin gadon ta zauna. Kamar wadda ta ruɗe ta kalli Ismat ɗin da faɗin, “Ismat kar ki saka naji kamar zan haukace dan ALLAH da gaske?”.           “Aunty shiyyasa nace miki ban tabbatar ba ai. Amma mu bincika dai”......     <<<<<<<<%>>>>>>>>              A gidan Mammah kusan ƙarfe uku na rana Daddy Imran ya iso gidan. Su aunty Ummi duk suna nan, dan su Ja'afar ma yau basu je kasuwa ba. Dama su Bilal ma'aikata ne yau ranar hutu. Suna zagaye da Mammah da Dadansu cike da nishaɗi mara misali. Ga Uncle Nasiru yazo gidan shima kusan tare suka yini. Uncle Jamilu ma da su Gwaggo Khadijah sun tabbatar da suna tafe in sha ALLAHU. Dan yau ɗin ma duk sunyi magana da Dadan ta waya. Itama dai Ammie matar Daddy Imran tun ɗazun tana gidan, sai dai ita kaɗaice yara sun wuce islamiyya. Rashin yaran ya saka gidan zama babu hayaniya dan baby Nawal ce kawai data kasance ana goyo.      Duk da Dada bamai jimirin hira bane bai ji ya ƙosa da wannan zaman ba. Dan ma su Lailah sun kasa sakewa saboda kunyarsa, shiyyasa ko hirar basa iya saka baki sosai sai jefi-jefi. Sai da ma suka ɗan shiga yin girki kitchen da su aunty Mommy sannan. Sanda suke kammalawa su Dadan suka tafi sallar azhar. Wannan fita salla ita ta saka Dada da su maigadi yin kiciɓus na farko, dan da asuba dukansu kaucewa sukayi dan ma shi Malam Buba ba gidan yake kwana ba.  Yanzu kam babu wannan damar. Koda yake sun fito ne a bazata daga sashen Mammah ɗin, shi Malam Buba daya fara hangoshi har ya miƙe zai gudu cikin bayi sai akai rashin sa'a Ammar ya tsaida shi ta hanyar ƙwala masa kira. So yake ya bashi aikar amso masa saƙo wajen wani abokinsa. Daburcewa Malam Buba yayi, sai dai ganin da sun riga sun ƙure masa ya aro jarumtar dole. Haka ya iso inda suke da sassarfa yana kaucema idanun Dada, dan yasan a waccan haɗuwar tasu ta shekarun baya babu daɗi.       Shi Dada ma hankalinsa ba kansu yake ba, waya yake yi da Imran ne daya kira shi. Har yayi kamar zai wuce su dan Ammar daya tsaya na bama Malam Buba saƙon ne. Sai dai me, kamar gilmawar inuwa a cikin ƙwaƙwalwa ya lura da malam Buba dake cikin yanayi na tsarguwa. Karo na farko ya ɗan zuba masa ido, dai-dai Malam Buba na gaishesu su duka. Sai akai sa'a kuma a lokacin Bilal ya furta, “Kun shigo kun gaida baƙo kaida su Malam Almu kuwa?”.          Malam Buba da ya runtse ido irin na naga takaina ɗin nan yay murmurshin ƙarafafa kai da faɗin, “A'a Alhaji, ai bamu san akwai wani baƙo ba, mun zata Alhaji Imrana ne ya dawo daga tafiya. A gafarce mu. Alhaji barka da zuwa ina yini”.           Dada dake kallonsa cike da nazari hannu kawai ya ɗaga masa. Sai kuma yay wucewarsa yana cigaba da wayarsa hankali kwance kai kace babu wani abu daya ma lura da shi. Dada mutum ne mai taku. Shiyyasa ko a gidan soja suke faɗin suna tsoron shirunsa. Dan ko kai waye baka isa a tashi guda ya maka magana ko nuna maka wani yanayi akan wani abu naka ba. Idan ma kana da ƙaracin tunani saika ɗauka bai san dakai ba a waje, a wannan silen yanayin nasa yake ma mutane da yawa illa batare da sun farga ba. Dan shi yanda kasan iskar dake gurɓata yanayin ƙasa haka yake shiga jiki a hankali batare da an ɗauki al'amarin da girma ba a zahiri..      Ganin abinda Dadan yayi ya bama Malam Buba nutsuwa da tunanin ai bai ganeshi bane, to taya ma zai gane shi a wannan yanayin ɓadda kamar tasa. Amma duk da haka dole ne yaje wajen Malaminsa ai masa aiki akan mutumin nan, dan lokaci yayi da za'ai wasa mai ƙyau da shima yake ganin zai zama wani abu a wajen manyansu, ba wai cigaba da zama ƙarƙashin Dagger ba kullum yana sammusu daga uwar dukiyar da ake basu. Ya tabbatar Dagger ya jima yana cutar su, kawai dai suna ƙyalesa ne tunda shine yasan manyan arnan, ta hannunsa suke samun umarninsu.      Bayan sun dawo sallar ya sake iske Malam Buba ya ɗakko su Afrah daga makaranta, ya kaima su Nimrah abinci kuma. Anan ma ta gefen ido ya gama ƙare masa kallo dan ya kawo saƙon Ammar ne daya amso. Falon suka sake zama aka cigaba da ƴar hira, duk da dai shi ba wani magana yake mai tsaho ba ko da yawa. Hasali ma ya gaji da surutun amma bazai iya tashi ba saboda farin cikin ƴan uwansa dake zagaye da shi da yake ciki. Balle ga su Ayyan da aka ɗakko daga Islamiyya sun zagaye shi da labarinsu da a magana ɗaya biyu sai ance Aunty Ninah, aunty Ruky. Tun baya fahimtar wacece suke kira Ninah ɗin har ya gane. Dan tun jiya yake jin sunan a bakunan ƴan gidan bai tantance dawa ake ba sai yanzu. Kusan 2:30 ya tashi ya haura sama.              ★Mintuna kusan talatin da shigowar tasa yana zaune kawai a sofa da laptop akan ƙafafunsa daya miƙe saman table, aiki sosai yake, sun fara shiri da yawa, shiyyasa yake jin bashi da wani lokacin hutu. Dan a nan kusa yake son ganawa da su Faro da sukai waya ɗazun ya sanar masa baya babban birni yaje wata jiha aikin gaggawa. Goran ruwa ne daya sha fin rabi a kusa da ƙafafun nasa, sai takardu daya baza a kusa da shi saman sofa ɗin da jikinsa. Koda akai knocking ƙofar bai ɗago ba balle dakatawa da abinda yake yi a haka ya bada iznin shigowa...          Daddy Imran ya turo akwatin hannunsa Ammar da Bilal na biye da shi da wasu akwatinan suman. Sallamarsu da ƙarar tayoyin akwatinan ya saka Dadan a karo na farko ya ɗan kallesu. Sannu da aiki Bilal da Ammar sukai masa, ya jinjina musu kai kawai idonsa dai akan akwatinan da suke ajiye wa. Sai da suka juya zasu fita ya jefa musu tambayar da ta sakasu dakatawa...        “Ma'aikata nawa ne a gidan nan?”.      Batare da tunanin komai ba Ammar ya ce, “Su biyar ne Dada, sai mata biyu dake aikin cikin gida. Kulu da Asabe, maigadi Malam Almu. Sai driver malam Buba. Akwai mai sharar tsakar gida da bama flowers ruwa sunansa Sanda ƙanin Malam Almu ne mai gadi. Sai kuma can ɓangaren su Yaya Ma'aruff, akwai maigadi ta gate ɗin can ma, da mai kula da flowers”.         Dada dake ɗan jinjina kai ya lumshe idanu yana sake buɗe su. Da hannu kawai yay musu alamar suje kafin ya maida idanunsa ga laptop ɗin. Sai da suka tura ƙofar batare da ya ɗago ba ya furta,              “Malam ka dameni da kallo”.        Murmushi Daddy Imran dake tsaye ya riƙe ƙugu yayi, sai kuma ya zauna a bakin gadon yana faɗin, “Ba dole na kalleka ba. Kwana ɗaya ko gama hutawa bakai ba ka fara tambayar ma'aikatan gida. Anya kuwa Zak... Baka da aljanu?”.         “Tsamiya ce da kuka ba aljanu ba”. Fashewa da dariya Imran yayi sosai.........✍️ 58 ........“Daga ina ka fito da wannan kayan, kamar mai shirin kai lefen aure?”. Dada ya katse dariyar tasa.      Cikin shanye dariyar Daddy Imran ya ce, “Kayan lefen Nimrah ne dan gara ta tar......”     Ai bai ma kai ƙarshe ba Dada yay wata kalar ɗagowa ya watso masa firgitattun idanunsa. Ai ko Imran ya sake fashewa da dariya harda kwanciya. Sai da yay mai isarsa ya tsaigata da faɗin, “Haba Zaki irin wannan kallon ai saika gigita ni, maida wuƙar wasa nake maka. Nima ba kare ya cizan ba da zan baka yarinyata tun yanzu ka halaka min ita yanda ka shekara takwas ɗin nan kana mafarke-mafarke.”      Kai kawai Dada ya girgiza batare da ya tanka zancen ba... Imran yasan iyakar amsar kenan. Shima sai ya saki zancen dan dama tsokanarsa yake ya fara masa bayani akan kayan cewar nasa ne da aka ɗinka. Sai takalma da dai duk wani abin buƙatarsa daya saba na yau da kullum....       Dada yasan wannan kaɗan daga aikin Imran ɗinsa ne, sai kawai ya zuba masa ido yama kasa magana. Cikin ƴar Harara shima Imran ya ce, “Malam nima daina kallo na.”         Dada ya ɗan murmusa kawai yana maida idonsa ga screen ɗin laptop ɗin sa...... ★←★→★←★→★       “Mole miyasa kake nemana da gaggawa haka?”.      “Oga akwai matsala ne, duk yanda nai tunanin ajiyewa har na san gaskiya hakan ya gagara. Akwai fa baƙo da akayi a gidan nan shekaran jiya, kuma sam zuciyata ta kasa nutsuwa da shi saboda tare da Imran suka zo”.            “Baƙo! Tare da Imran?”.        Dagger ya faɗa yana tsatstsare Mole da idanu.      “Tabbas, yanda kuma ƴan gidan suke masa ya saka na ɗora ayar tambaya a kansa”.        “Mole ina buƙatar ganin Nimrah yanzun nan”. Yanzu kam sosai Mole ke kallonsa kafin ya girgiza kai”.       “A yanzu haka kaima kasan bazai yiwu ba, duk da makaranta zani ɗaukarsu, amma kasan ba ita kaɗai bace. Ga yarinyar nan murɗaɗɗiyar kanta ce, idan ba ita taso abu ba akwai daru.”      Iska mai zafi Dagger ya furzar yana kaina sitiyari duka, dan yasan gaskiya Mole ya faɗa akan Nimrah. Duba da tunda suka haɗu sau ɗayan nan yarinyar nan bata sake nemansa ba. A duk videon da masu bibiyarta kuma ke kawo masa babu ko ɗaya daya ganta a damuwa. Ya rasa wace irin sheɗaniyar yarinya ce ita. Cikin ɗan zafi-zafi ya kalla Mole da faɗin, “Amma ai kasan Zak-Shadow, taya zaka gagara ganesa a yanzu?”.         “Oga! Idan na gagara ganesa fa banyi laifi ba. Karka manta sanin da nai masa wancan karon sani ne na sama-sama. Yanzu kuma wannan baƙon harda ƙasumba a fuskarsa”.        “Mtsoww! Mole dolene naga Nimrah, dan na fara fahimtar kai wawa ne a wasu lokutan. Kayi duk yanda ma zakayi gobe mu haɗu.” ya ƙare maganar yana jawo jotter da pen a cikin drower ɗin motar, rubutu yayi mara tsayi ya miƙa masa. “Ka bata wannan yau, a yanzu kuma”.         Komai Mole bai sake ce masa ba ya amsa takardar, dan kalmar Wawa daya kira shi da ita ta ƙona masa rai, dama ga Mole da shegen zuciyar tsiya. Shima Dagger cikin takaici ya sake faɗin, “Fita min a mota”.        Kallonsa Mole ya juyo yayi cikin ido, sai dai nan ma baice komai ba ya buɗe motar ya fita. Ta gidan su Nimrah da zai je ɗaukarsu ya koma. Sai da ya bar wajen sannan ya buɗe takardar da Dagger ya bashi....         (Ki gaggauta haɗuwarmu daga gobe zuwa jibi, dan akwai magana mai muhimmanci. Jinkirin ki zai iya zame miki dana sani da kukan rashin Ruƙayya ko Mamanku).       Laɓɓa Mole ya cije tare da yin ƙwafa. Saboda irin wannan dama ya nutsu ya koya karatu da rubutu a wajen Dagger ɗin, gashi kuwa amfanisa ya fara zuwa masa a gaɓar data dace. A baki ya saka takardar ya taune ta, sai da ya tabbatar ta narke ya tofar a titi ya cigaba da tafiyarsa zuwa makarantar tahfiz ɗin su Nimrah......         ★Idanu sosai Malam Buba ya zubama Nimrah da suke fitowa ita da Ruky, yanda suke dariya zaka tabbatar wata hirar farin cikin suke yi. Mu'azz ya ƙaraso inda suke yana miƙa musu leda, hannunsa da ince na leda yana sha alamar shine a ledar da suma ya basu. Wani murmushi ya saki a karo na farko. Zuciyarsa na ayyana masa lokaci fa yayi da shima zai ci arziƙin wannan wahalar tasa. Dole ne yay ma Dagger juyin mulki ko su zama sarakuna biyu a fada guda. A yanzu fa ƴar nan tasa itace IGIYAR FITO da kowa zai buƙata wajen samun nasarar kaiwa GAƁAR ruwan kodan ceton rai ba DUKIYAR da aketa kai-kawo a kanta kawai ba. Domin kuwa shi shaida ne, mutumin nan da gaske shi ne DODON mutanen nan duk ƙarfin su da damar da suke da ita a hannu. Gashi kuma a salon daya dawo zai iya zame musu KIƊA A RUWA... kenan washi dama ce a yanzu da zai murza kambunsa fiye da kowa, ta yanda gaba ɗaya manyan ƙungiyar ma zasu koma tafin hannunsa sai abinda ya faɗa musu, dan yana da abubuwa fiye da Dagger da suke ganin shi kaɗai ne shegen su. Kai-kai shi kam yau sai yaji ma yana alfahari da abinda Hassatu tai masa na bada Nimrah ga Zak-Shadow... Karo na farko a rayuwarsa ya ayyana (ALLAH ya jiƙan ki Hassu na. Kin haifa min ƴar gudalliya ta zame min alkairin tsanin yin kuɗi da zan fantama a rayuwa ni da ita.....)      Isowar su Nimrah ya katse masa tunani, duk suka gaisheshi kamar ya da suka saba sannan suka shiga mota. Mu'azz na gaba suna baya. Duk sun cika motar da hirar su har suka iso gida....       °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°       “Wai nikam yau lafiya? Sai nake ga kamar kanata ɓoye-ɓoye. Musamman idan ka kimanci lokacin fita massalaci. Sai yanzu kuma nake ganin kamar kana yin haka ne saboda baƙon nan na jiya.”       Wata shegiyar harara Sanda ya zabgama Malam Almu da faɗin, “Oh ido ka saka min kenan ban sani ba?”.      “A'a wlhy taya zan saka maka ido ni kuwa. Kawai dai ina ganin ya kamata idan da wani abu ne ka sanar min nima sai na kiyaye gudun kwaɓa aiki. Bana son nayi wani kuskure da ƴar uwata zata cutu a dalilin sakaci na shiyyasa. Saboda ni kaina dai da jiya kawai na fara ganin baƙon nan sai na jini kamar a tsorace. Dan daga ganinsa kaga BARDEN NAMIJI da baya buƙatar wargi. Irin waɗan nan kuma yana da ƙyau kasan su wanene su kodan ka kiyaye musu”.         “Mtsowww! Malam Almu tashi ka bani waje kafin na canja maka kamanni, ka cika min kunne da shegen surutunka fa mara amfani”.      “ALLAH ya baka haƙuri, ya huci zuciyar ka. In dai nine kaga tafiya ta”. Maigadi ya faɗa yana fita a ɗakin yabar Sanda dake binsa da kallon harara. Fitar tasa ce kuma tai dai-dai da isowar Malam Buba ɗauke da su Nimrah. Dan haka ya buɗe masa gate al'amarin Sanda na cigaba da masa kai-kawo....... ______★         Matuƙar farin ciki su Nimrah sukai da samun su Aunty Mimi yau ma a gidan. Duk da su kaɗai ne babu yara ko ɗaya sai Baby Nawal dake ɗakin Mammah tana barci. Bayan sun gama rungume Mammah da mata shagwaɓa suka gaida iyayen nasu.      Dai-dai suna cire hijjabai Ruky ta makama Dayyan daya zuba musu ido kamar tsohon maye harara. Maimakon yaji haushi sai ya sakar mata murmushi. Ita Nimrah bata lura ba, hankalinta nakan magenta dake matuƙar shan gata a gidan kamar ƴar mutum. Tayi girma abinta tayi ƙyau kai kace magen turawa ce. Ta ɗaga ta tana mata kiss da rawa Ruky ta ƙaraso inda take. Dai-dai nan kuma Daddy Imran ke sakkowa daga upstairs Dada a bayansa. Sai dai da yake Daddy Imran ɗin ne a farko shi suka fara gani, sai dai shima sai da yay magana tsabar yanda su duka hankalinsu ke kan magen da suke kira da suna Mishi. Wani lokacin kuma suce Peppy.        “Halan yaran nan yau basu ganni bane”.      Muryar Daddy Imran ta shiga cikin kunnuwansu a bazata. A tare suka juya inda yake, sai kuma Ruky ta zabura ta rungumeshi. Sai dai Nimrah batai hakan ba, dan tun suna ƙanana ma sosai ko tazo rungumesa kamar Ruky cikin wayo yake hanata yin hakan, tun bata fahimta harta fahimta, bayan sun ƙara girma a islamiyya ta fahimci kuma dalilinsa na yin hakan, shiyyasa bata taɓa damuwa ba sai ma kima da daraja daya ƙara a idonta. Kusa da shi ta matso tana masa sannu da zuwa itama, sai kuma ta juya a hankali jin motsin kamar mutum a kusa da su. Da sauri ta janye saboda saukar idanun nata akan Dada dake ƙoƙarin ɗaura agogo. Sai dai kuma tamkar walƙiya hoton agogon ya gilma mata a brain, da sauri ta kuma ɗagowa ta kalla hannun nashi. (Wlhy agogon ne fa na ɗakin Mammah) Wani sashi na zuciyarta ya ayyana mata. Sai dai gaisuwar da Ruƙayya kema Dadan ta katse mata lissafi. Cikin satar kallon agogon ƙasa-ƙasa itama ta gaishe shi.      Kamar yanda ya amsa ma Ruƙayya a taƙaice itama a taƙaicen ya amsa mata. Daddy Imran dake kallonsu ya ce, “Halan yanzu ma kuka shigo gidan?”.        “Eh Daddy ko ɗaki ma bamu shiga ba.” Nimrah tai maganar cike da shagwaɓa tana ma magenta wasa. Ƴar dariya Daddy yayi da faɗin, “To aje ai wanka a huta, ALLAH dai ya bada ilimi mai albarka. Mishi ina gaisuwa”. Ya ƙare maganar da taɓa kan magen.      A tare suka amsa da amin. Suna nufar hanyar ɗakinsu. Ta ƙasan ido Dada ya bisu da kallo, can ƙasan zuciyarsa yana nazarin kallon da yaga Nimrah nama agogonsa a sace. Sai dai bai kawo komai a ransa ba tunda bai san ta gansa a ɗakin Mammah ɗin ba suka ƙarasa cikin falon. Dan zasu ɗan fita ne zaga gari kamar yanda Dadan ya buƙata. Duk da Imran yaso ƙi Dadan ya nuna masa sai fa sunje, tunda a mota ne wazai wani ganshi tunda yasan abinda suke gudun dai kenan. Shi kuma a yanda yake jin ransa ma bashi da dalilin wani hutu aiki kawai yake son fuskanta..........✍️ 59 ..........“Waye ya tura wannan saƙon?”.     “Baban yarinyar nan ne da Dagger ya kawo mana hotunanta kwanaki”.     “Shi ba a ƙarƙashin Dagger ya ke ba?”.    “Tabbas a ƙarƙashinsa yake, shiyyasa nima nayi mamakin saƙon. Dan haka na kawo maka ma ka gani, dan zancen sa ya ɗauki hankalina kuma ba abin wasa bane ba”.        “Kayi ƙyan kai, kuma tabbas muna buƙatar mu sanshi a zahiri. Kwanaki nama Dagger umarnin ya kawo min shi amma shiru, ban san mi yake nufi ba. Ga Scythe shima shiru bayan yasan shi muke jira da bayanai”.        “Oga na tabbatar zuwa anjima zamu iya ganin Mr Scythe, dan a daren jiya na samu tabbacin ganawarsa da Tafidan. Na wannan ne abin dubawa. Dan ya kamata musan wane saƙo yake son isar mana da baya son Dagger ya sani harya zagayo ta bayan fage”.        “Haka ne, ka masa reply da muna son ganinsa. Sai kayi ƙoƙarin yanda za'a yazo nan ɗin daga yanzu zuwa sati guda bayan ka gama karantar al'amarinsa da bincike sosai akansa.”.      “An gama oga. Ka daɗe kayi ƙarko”.... ===================    ★1-WEEK LATER★         Satin Dada ɗaya kenan da dawowa gida. Abubuwa sun faru sosai a cikin satin. Ta kowane ɓangare komai yayi tsauri da yin zafi. Sai dai har yanzu maƙiya sun kasa samun tabbacin dawowar Dada cikin zuri'ar sa. Ƙarshe ma sun ɓige ne da binciken asibitin da suke zargin yana jiyya ne.         Shi ko Malam Buba sai yawo yake ma Dagger da hankali, acewarsa ya rasa hanyar da zai bama Nimrah wannan takarda kullum tana tare da Ruƙayya. Tun Dagger na yarda har ransa ya fara ɓaci, zuwa yanzu ya fara tunanin bin sabuwar hanyar samun Nimrah ɗin batare da sanin Malam Buba ba. Shi ko Malam Buba bai taɓa tunanin Dagger zai nemi wata hanya ba, hankalinsa ma gaba ɗaya nakan jiran shubaninsu da suka bashi sati guda akan ganawa da shi fuska da fuska, dan haka a ƙagare yake da hakan, dan ya tabbatar da in har ya samu wannan damar Dagger bai isa cigaba da juya shi ba, shima ya zama ogan kansa sai dai a raba yaran da Dagger ke jagoranta biyu a bashi rabi.          ★SCHOOL★          Kamar yanda suka saba idan anyi break zaka samesu group-group ne kowa na sha'aninsa. Wasu hira ce ta ƙawaye, wasu da samarinsu kasancewar makarantar haɗe take maza da mata. Wasu kam samarin ne zalla ke sabgarsu suma. Da yawan ƴammatan kan so haɗa ƙawance da su Nimrah, sai dai sanin halinsu kesa suji shakkar raɓarsu. Hakama samarin suna son suyi mu'amula da su, sai dai sanin kaɗan daga aikinsu su maka zagin ƙare dangi kesa su kama kansu.      A yanzu ma suna gefe su biyu zaune, note Nimrah ke ƙwafa a littafin Ruky dan ita ɗazun ƙinyi tai, duk da ba wani note ɗin kirki bane kasancewar kowane subjects ɗinsu suna da textbooks ɗinsa. Ruƙayya na gefenta tana cin cin-cin, hirar Hanoon suke suna dariya, dan wani rashin mutunci suka mata yau da safe kafin su taho school. Nimrah ta ɗiba cin-cin ɗin tana faɗin, “ALLAH yasa mu tarar Dada baya gidan, yanda in ta tambaya muci uwarta da armashi, shegen fuska tasha mayukan bleaching kamar an silala carrot”.       Sake tuntsurewa da dariya Ruky tai tana faɗin, “Sai da ke Trouble Queen. Hot pepper! Naj... Naj... Naja bombs”.         Ƙulli Nimrah tai mata a baya da faɗin, “Muguwa irin jera min wannan suna haka, so kike sai na mutu naji ana Naja bomb yau zaki sha bamai-bamai...”           Dariya sosai yanzu kam Ruky keyi, itama Nimrah na tayata....       “Hy beauty Barbies”.    Wani yaro mai sanye da irin uniform ɗinsu ya faɗa. Tsagaitawa sukai da dariya suna masa kallon daga sama har ƙas. Ya girmesu sosai, dan kuwa ɗan ss3 ne. Hasalima shine headboy ɗin ƴan ss. Yaron baya ji a makarantar, dan ya tara ƴammata yanata haɗasu faɗa. Kasancewar sa ɗan tsohon president yasa ko ƙararsa makaranta bata taɓa kaiwa ba gidan su, dan tun yana js yake tsula tsiyarsa. Ya jima da sanin su Nimrah sai dai bai taɓa shiga sabgarsu ba duk da suna birgesa, amma fahimtar da yay yaran basu da kunya ya sa ya kama kansa. Yau dai yana zaune cikin group ɗin dake haɗe maza da mata ana shafta amma hankalinsa duk yana kan su Nimrah, ji yay ya kasa haƙuri ya taso ya samesu. Shine maimakon sallama ya ce musu wai (Hy Beauty Barbies).         “Lafiya dai ko?”.     “Eh to da sauƙi gaskiya. Mutanen naka ne dai suka aikata abinda suka saba, ga kuma wanda suka buge ɗin nan kwance baya numfashi ma. Kuma yaron tsohon shugaban ƙasa ne”.          “Bugewa kuma? Sai kace wasu ƴan fashi...”      “Wlhy ranka ya daɗe abin babba ne fa. Kuma suma can gidansu har mun kira su. Kaga kafin suzo wani abu kuma ya faru gara ku ku fara zuwa. Dan yaran nan gasu nan ko'a jikinsu kamar ma basu aikata komai ba.”          Iska Daddy Imran ya ɗan furzar da faɗin, “Okay ba damuwa. Gani nan akan hanya”. Daga haka ya yanke kiran. Dada ya ɗan kalla da faɗin, “Inaga zamu wuce makarantar su Ninah akwai matsala, wlhy yaran nan nakan rasa mike damun kawunansu. Anya ba aljanu ne da su ba na faɗa. Da wahala ga Ruƙayya da Nimrah su cinye sati biyu ba'ace sunyi faɗa a makaranta ba, daga Islamiyya har boko. Idan anyi magana suce yaran ne basu da tarbiyya, shike nan su sun zama malaman koya tarbiyya kai jama'a”.           Ko uhumm Dada baice ba, ta aikinsa ma yake hankali kwance. Shima Daddy Imran bai sake magana ba har suka iso makarantar tasu. Sai da ya samu waje yay parking sannan Dada ya bi makarantar da kallo. Imran dake ƙoƙarin fita ya ce, “Ina zuwa”. Daga haka ya maida murfin ya rufe yana barin wajen..........✍️            60 ..........★Ko sakan ashirin Daddy Imran baiyi da barin wajen ba motar ƴan sandan farin kaya ta iso. Ta ɓangaren da yake sukai parking. Dan haka kunensa ya jiye masa abinda ɗaya daga cikinsu dake waya yake faɗa. Da kallo ya ɗan bisu har suka bar wajen, kamar zai share ya cigaba da aikinsa sai kuma ya dakata, ƙofar da Imran ya shiga suma ƴan sandan suka shiga ya kalla, tare da ɗaukar waya dake gefensa. Ɗauke idonsa yay yana ƙoƙarin kiran layin Imran, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka.         “Mike faruwa?”.     Banji mi Imran ɗin ya sanar masa daga can ba, naga dai kawai ya yanke kiran yana sauke laptop ɗin tsakkiyar kujerun, hakama takardun ya tattare su ya riƙe a hannu har sai da ya fita ya ajiye su a kujerar daya tashi. Motar ya kulle gaba ɗaya, ya saka norse mask daya cira a gaban motar, dan a sati gudan nan in har suka fito idan ba'a mota ba zaka ganshi da facemask ne.....        A dai-dai lokacin a office ɗin vice principal jami'an farin kayan nan ke magana cikin gadara. Acewarsu dole su tafi da su kansu hukumar makarantar kamar yanda aka tafi da su Nimrah. Dan har yanzu yaron mai suna Zahir bai farfaɗo ba, duk da an wuce da shi asibiti ne tare da su principal tun ɗazun, su kuma suka tafi da su Nimrah. Amma koda shi tsohon shugaban ƙasa ya isa asibitin da matarsa sukaga halin da ɗansu ke ciki sai ya bada umarnin komawa a kama suma hukumar makarantar bayan suma nan su principal an tattare su dukansu an wuce da su station ɗin.         Dada na tsaye jami'an suka fito da vice principal dake faɗin ai ga mahaifin yaran nan sai shima a haɗa da shi. Yana maganar ne yana nuna Daddy Imran cikin ɓacin rai. Sai dai su kuma basu saurareshi ba, dan umarni suke bi kawai, kuma shi akace su kamo ai na mahaifin yara ba, tunda yaran na hannunsu ai dole iyayensu sukai kansu da kansu. Sai da suka wuce Imran ya ƙaraso, ganin kallon da Dada ke masa ya ɗan furzar da iska yana faɗin, “Sun kaisu station, yaron kuma naji kamar suna batun asibiti ma wai bai farfaɗo ba. Ban san mi sukai masa haka da zafi ba. Ina ga mu bisu dan musan ina suka kai mana su”.      Komai Dada bai ce ba, suka bar wajen zuwa inda motarsu take. Haka suka dinga bin motar jami'an tsaron a baya har station ɗin su. Ta hakan ne suka fahimci wane irin jami'ai ne ma. Da farko hanasu shiga station ɗin akayi, sai da Daddy Imran ya nuna id card ɗinsa sannan.           A yanzun ma Daddy Imran ne kawai ya shiga, Dada yay zamansa a mota. Da farko hana shi ganin su Nimrah akayi, sai da ya nuna id ɗinsa anan ma sannan, a hakan ma wani a cikinsu ne yay kiran ogansu ya sanar masa, shine yay magana kan a bar Daddy Imran ya gansun, dan sauran idanunsu ya rufe umarnin da aka basu kawai suke iya kallo da girman wanda ya basun, duk da baya kan mulki a yanzu. Sai dai tunda ƙasar tamu in dai wane na amsa suna wane dole abu umarninsa shike nan.         Idanu ya zubama Ruky da Nimrah ganin su hankalinsu ma kwance. Dan suna ganinsa ma suka nufoshi fuska da murmushi suna faɗin, “Daddy kai ne?”.       “A'a aljanun ku  ne”.   Ya basu amsa yana hararsu. Bakuna suka rufe da hannaye alamar dariya ma suke son yi, sai ya girgiza kai kawai da cewa, “ALLAH dai ya shirya min ku”.          “Amin Daddy. Kuma wlhy a shirye ma muke. Kawai idan aljanun suka motsa ne al'amarin namu ba daɗi”.         Cikin ɓacin rai jam'in daya fito da su ke hararar su da faɗin, “Yaran nan kanku rawa yake na lura, aljanu ko? Zamu sauke muku su kuwa. Dan yanzu zaku koma cikin call ai marasa kunyar ƙarya”.       Daddy Imran ya fara nuna musu hakan bazai yiwu ba, sai dai a jira daga nan har wasu awanni aji daga asibitin dole. Amma sunƙi saurararsa sai wani gadara suke masa dan a farin kaya yake ba uniform ba. Har wani maimaita masa minti goma suka bashi a maida su suke. Sosai zuciyar Nimrah takai wuya, cike da tsiwa da takaici ta ce, “Daddy ka barsu, dan ALLAH ba cell ba su kaimu cikin kabari, daga ni har Ruky ba tsoron su muke ji ba. Shi daya aikata rashin ɗa'a ba'ace za'a kalleshi ba ma sai mu? Kuma wlhy shi da ire-irensa yanzu ma muka fara musu haka, tunda su bunsuraye ne. Ai duk wanda uwarsa tace masa JEKA KA GANI idan har ya yarda ya fito ɗin MU ZAI GANI. Duk an saki yara ba tarbiyya kamar ɗiyan aladu a ƙasa. Tunda shi yace ɗan iska ne miyyasa bazai je ya rungumi uwarsa ko yayarsa ba. Sai mu tunda iyayenmu basu taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙasa ba, balle kuji tsoron su ko?.”        Caraf Ruky ta amshe da faɗin, “Barsu Ninah. Ɗan shegiya ni wlhy yanzu ma da zaku kaimu mu gansa sai mun danne masa kai da pillow ta yanda ko ya farfaɗo ɗin zai sake komawa mutuwar gaskiya......”       Sai kawai suka cafke ita da Nimrah suna dariya.          “Eh lallai yaran nan baku da mutunci da kunya. Anya kunsan gaban wanda kuke kuwa? Hukuma ce fa”.      Wani ya faɗa a cikin jami'an farin kayan yana latsa waya da kaita kunensa. Baki kuwa Nimrah ta taɓe irin na kai ka sani ɗin nan ƙasa-ƙasa tace, “Ko gaban gwalando muke miya shallemu, mu ubanmu soja ne ma baban ɗan sanda”.        “Mi kika ce?”.   Ɗan sandan ta tambaya dan baiji mita faɗa ba. Kanta ta ɗauke kamar bata jishi ba itama. Sai Ruky dake dariya ƙasa-ƙasa.       Daddy Imran daya rasa abin faɗa sai ya girgiza kai kawai shima. Ya ɗauki waya zai kira lawyer ɗinsa. Nimrah kuwa na hararar jami'in nan da suka fahimci kamar yafi kowa nuna gadara da tsanarsu kamar ɗansa sukama abinda suka yin.          “K! Ni kike harara?”.     Nimrah ta yamutse fuska zatai magana Dada ya shigo office ɗin a bazata.....       Ɓamm ta ɓame bakinta batare data bari kalmar dake ƙoƙarin fitar ta ƙarasa fita ba. Dan a cikin tsakiyar idanunta nasa idanun suka shiga, duk da fuskarsa akwai norse mask hakan bai hanasu gane shi ba. Shi ko ɗan sandan ya hasalo ne kamar zai mareta kiran daya shigo wayarsa ya katse shi. Sai ya ƙare da balla mata harara shima yana kai wayar kunnensa yana fita a wajen. Hakan yasa ɗakin komawa daga su sai su.          ★Daga can wani office na station ɗin wani ɗan sanda ne dake tabbatar da oga ne a wajen, zaune yana kallon duk abinda ke faruwa ta computer dake desk ɗinsa. Sakamakon ɗakin da su Nimrah suke akwai cctv. Babu abinda yake saki sai murmushi, dan ba ƙaramar dariya yaran nan ke neman saka shi ba. Ganin ma suna neman hasala ɗan sandan da ke tare da su ɗin ne ya sashi kiranshi a waya. Dai-dai nan ya shigo office ɗin, sai da yay salute ɗinsa sannan ya ce, “Gani Sir!”.         Ogan daya kafe Dada da idanun ta desktop ɗinsa bai maji shigowar yaron nasa ba balle abinda yace, sai da ya sake maimaitawa sannan ya kawo ajiyar zuciya yana kallonsa.     Cike da mamaki yaron ya ce, “Sir! Akwai matsala ne?”.     Kai ya girgiza masa, tare da faɗin, “Waye ya shiga wajen yanzu?”.        “Ban sanshi ba Sir, amma da alama tare suke da shi. Dan yana shigowa naga sun nutsu alamar suna shakkar sa.”      Oga ya sake kallon Dada da ƙyau, sai kuma ya furta, “Koma inda suke, amma kasan maganar da zata fita a bakinka, baka gani yara ne”.      Cike da girmamawa ya amsa yana fita. Mamakin ogan nasu fal ransa. Badan yasan halinsa ba daya zargi wani abu, sai dai yasan ba hakan bane ba....      ★Anan kuwa. Maƙalewa Ruky tai bayan Nimrah ganin yanda Dada ya zuba musu zafafan idanunsa da suka gagara fassara abinda ke cikinsu. Itama Nimrah kanta a ƙasa tana faman cuɗa yatsunta cikin juna. Murmurshi Imran yayi a ransa yana raya, (Marasa ji ashe ni kuka raina da su Ma'aruff). A zahiri kam sai ya mike abinsa yana faɗin, “Bari na shigo da lawyer”. Bai jira amsawarsa ba ya fice abinsa.        Kusan mintina biyu da fitar Imran sannan yaja kujera ya zauna. A take suka ƙara jin ya cike musu waje. Duk girman wajen kamar an sake matse su. Ruky ta fara gaishe shi da rawa baki, kafin itama Nimrahn ta gaishe sa. Duk ɗin su babu wadda ya amsawa, sai ma bayan wasu sakanni ya jeho musu tambaya idanunsa akan wayarsa daya fiddo daga gaban aljihu.          “Mi kuka aikata?”.     Kalmomi uku ne kacal, amma sai da suka jisu suna maimaita kansu a cikin kunnuwansu sau sittin. Ruky da Idanunta suka cika da hawaye ta fara faɗin, “Wlhy Dada shine yaja duk abinda mukai masa, maganar banza yazo yana mana shine kawai muka....”      Ta kasa ƙarasawa. Shiru ɗakin yayi na sakanni, sai kuma yanda ya ɗago yana kallon su yasa Nimrah fara magana itama hawaye na ciko mata ido. Muryarta na nuna ɗaci ta fara bayani tun daga farko ba kamar yanda Ruƙayyan tayi a taƙaice ba.........✍️ 61 ........Tana kaiwa ƙarshen inda ta dakesa bayan marin da Ruky tai masa ta ƙara tura baki gaba cike da shagwaɓar da suka saba yina Mammah da Imran da Uncles ɗinsu. “Mu bamu san zai suma ba, kawai mun dakesa a wajen ne dan yasan mace abar martabawa ce ba iskar dake kaɗawa bace da kowa zai iya shaƙa a arha. Kuma wlhy Dada kowa yasan shi ɗan iska ne, kwanaki har wata yarinya ƴar js 1 sukama fyaɗe shi da abokinsa akace ƙarya ne faɗuwa tai taji rauni, kuma wlhy ba haka bane kawai dan yarinyar ƴar masu aiki ce iyayen gidanta suka sakata a makarantar shine aka ƙi yin komai ko Buddy?....”       Yanda take kuka yanzu kam Ruky na tayata da jinjina mata kai alamar anyi hakan ya sashi zuba musu ido su duka kawai. Ba shi kaɗai ba hatta Lawyer da Imran da jam'in nan har ma da wasu biyu dake ƙoƙarin shigowa da Ogansu dake kallon komai ya office ɗinsa duk sun tsaya cak suna sauraren Nimrah da kallonta. Daga ƙarshe ma yanda suka rungume juna ita da Rukyn suna kukan sosai ya saka Dada lumshe idanunsa a slowly yana furzar da iska mai nauyi ta cikin norse mask ɗin sa.           Matuƙar sanyi jikin ƴan sandan nan yayi, su duka har mai zaƙewar nan. Dan haka duk a saɓule suka ƙarasa shigowa. Cikin lallashi Imran daya ƙarasa inda suke ya ce, “Ya isa haka kukan to. Oya ku zauna”.      Sakin juna sukayi kuwa, zasu zauna a ƙasa ɗaya daga cikin jami'an ya nuna musu kujera. Dan wajen dogon table ne da kujeru kusan goma sha biyar saboda waiting room ne na visitors. Cikin bada umarni ogansu daya kira waya yace aje a fito da su principal ma. Dan suma masu makarantar yanzu suka kira su a waya sun kuma tabbatar da turo lawyers ɗin su.      Har su principal suka shigo su uku Dada bai buɗe ido ba yana zaunen sa kawai. Suma wajen zama aka basu, vice principal daya shaƙa sosai sai hararar su Nimrah yake. A zuciyarsa kam fadi yake kodai da gaske yaran nan aljanu ne da su? A fili kuwa da yake cikin takaici yake sai ya furta, “Haka muke fama da su fa ranka ya daɗe, ga bakinsu baya mutuwa, wani lokacin ma gara ita wannan kan nuna risina amma kaga wannan sai addu'a wlhy, ga su da taurin kan masifa.”          Baki Nimrah ta sake buɗewa zatai magana Daddy Imran ya harareta, dole tai shiru tana sake tura baki daga ita har Rukyn. Karo na farko jam'in nan yay guntun murmushi, sai kuma ya tsuke fuska yana kallon vice principal da faɗin, “Ai halinsu abin ku gode ne, dan na fahimci makarantar taku ta kasa yin abinda su suke yi daya dace. Wai dama haka makarantun kuɗi sukeyi na bama kowa freedom ɗin aikata abin da duk ya birgesa? Ko kuwa dan wannan ta ƴaƴan manyan ƙasar ce shiyyasa?”.         Principal ya sauke numfashi a karo na farko yana girgiza ma vice ɗinsa dake ƙoƙarin ƙara yin magana kai. “Ranka ya daɗe ka fahimta mu ma'aikata ne, yanda kuma wannan makaranta ta tsara mu bamu da wani hurumin yima yara hukunci. Ko laifi suka yi sai dai mu kira iyayensu a zauna a sasanta ko a basu suspension. Gaskiya Vice ɗina ya faɗa su Ruƙayya basa jin magana, dan zan iya rantsuwa daga farkon kafa makarantar nan zuwa yanzu sunfi kowane ɗalibi takardar laifi da samun suspension. Dan ba'a ƙulla sati biyu wani bai reporting ɗinsu ba. Idan kuma an tuhumesu suce aljanun su ne”.          “Zaka iya lissafa mana duka laifukan da ake reporting ɗin nasu a kai?”.       Golden voice ɗinsa mai cike da izzar abinda yake ƙoƙarin dannewa na fushi ta daki kunnuwansu a bazata. Kaf ɗin su sai da suka kalla inda yaken, dan su su principal ma da tunda suka shigo idanunsa ke rufe wlhy sun ɗauka kurma ne ko makaho. Dan haka yanzu suka ji mugun tsarguwa da yanda ya zuba musu su. Gaba ɗayan su sun kasa cewa komai sai rawar lips suke yi. Imran dake kallonsu cikin taɓe baki ya ce, “Ku muke saurare. Dan muma dole mu shigar da ƙara akan bayanin da yaran sukayi. Wace irin makaranta ce haka da har ɗalibi zaima ƴar uwarsa ɗaliba fyaɗe amma a rufe zancen. Kenan mu muna can cikin jin amincin yaranmu na makaranta mai inganci suna karatu ashe saɓanin haka ne”.        Cikin su principal babu wanda bai rikice ba. Sai ƴar kallon juna suke tsakaninsu, sai dai an rasa mai fara magana. Sai da ƙyar Discipline master ya furta, “Fyaɗe kuma yallaɓai? Ku fyaɗe yace zai muku yaron?”. Ya ƙare tambayar ƙarshe yana kallon su Nimrah.             Cike da tsiwa Nimrah ta ce, “Halinsa ne ai kowa ya sani. Kuma baƙwa son ku faɗa saboda babansa nada hannun jari a makarantar......”         “Naja'atu Muhammad! Are you Madd?!!”.      Vice principal ya faɗa cikin daka tsawa har jikinsa na rawa. Dan wlhy baiyi zaton abinda yaran nan zasu faɗa ba kenan. Ai ko shima tsawar Daddy Imran da jami'in tsaron nan suka daka masa a tare. ALLAH sarki principal mutum ne mai sauƙin kai, gashi yana son su Nimrah a rayuwar sa, sai yaji duk ya sake rikicewa. Ƙura na neman tashi Dada ya miƙe abinsa. Idonsa akan jami'an tsaron ya furta, “Ku miƙa maganar kotun”. Daga haka ya nufi ƙofar fita hankalinsa kwance.     Miƙewar Daddy Imran yayi shima cikin tabbatarwa ya ce, “Ga lawyer ɗin yaran nan zaku iya ƙarasawa da shi. Ku tashi muje”..       Ai kafin ma ya rufe baki Nimrah da Ruƙayya sun miƙe abinsu. Tsabar iya shege sai kallon vice principal suke da Discipline master suna murmurshin iskanci. Dan dama haushin su suke ji sun saka musu idanu da yawa. Da sunyi laifi sun dinga gaya musu baƙaƙen magana da kiransu Shaiɗanu. Ai ko sosai suka sake jin sun kai wuya da iskancin su Ruky ɗin, dole ma suyi duk yanda zasuyi a kora yaran nan a wannan gaɓar daga makarantar. Dan nan gaba har abinda basuyi tunani ba sai sun bankaɗo musu......        Sai da ku ƴaƴan Mammah🤭, walle aikin ku na ƙyau Zakanya da Damisa 🤣🏃. .__.          A can office ɗin ogan nan kuwa tunda Dada yay magana kai tsaye ya furta. “Zak-Shadow!. Babbar magana, mike shirin faruwa haka? Wanda aka ce an fitar a prison sati guda kenan har ma yana asibiti yana jiyya ne kuma anan?”.          Lallai akwai Magana. Ya tuna kwanan wayarsa nawa a kashe bai samu wani information daga gidan su Nimrah ba. Ya tabbatar kuma zata nemesa. Miƙewa yay yana ji a ransa dole ne yau ɗin nan shi da kansa ya nemeta kuwa....        🤔To kai kuma daga ina ɗan sanda?.      ••••••••••••••••••••      Yanda suke kuka kamar ransu zai fita bai saka Hajiya Hasiba taji ko gezau ba balle suyi tunanin samun abinda suke roƙo. Yau sati guda kenan da zuwan Ismat gidan ta kawo ma Nabeeha gulma. Kwatsam suna cikin tattaunawar nan a bedroom ɗin Nabeeha ɗin su Amima da suka kwana a club suka dawo gidan suka jisu. Amima uwar gulma jiki na rawa ta ɗaga waya tai kiran Hajiya Hasiba ta sanar mata komai da suka ji da zuwan Ismat da tunda ta gudu a gidan bata zo ba sai yau.     Ai ko Hajiya Hasiba tace ta kulle mata su ta baya a ɗakin. Kai kace dama wannan umarnin Amima ke jira, wuff ta shiga ɗakin babu ko sallama. Nabeeha data fito daga bayi ta kalleta, hakama Ismat dake kwance a gado. Cike da farin cikin ganinta Ismat ta ce, “Ƴan ƙasa.” sai dai maimakon Amima ta bata amsa sai kawai ta zare keys ɗin ƙofar tana ficewa garam ta rufesu, ta dannama ƙofa key. Duk bugun da Nabeeha keyi da kiran sunanta harda zagi da barazanar duka bata buɗe ba. Sai ma cemusu tai ai Momy ce ta sakata tayi musu hakan, abinci ma za'a dinga ziro musu ta window ɗin ɗakin.      Tun suna ɗaukar lamarin wasa har suka fahimci gaske ne. Dan kuwa a wannan yinin ta window ɗin su Amima suka dinga ziro musu abinci, tsabar wulaƙanci kuma a leda suke sakawa bama ko ɗan roba ba. Acewarsu ta leda ɗin ne kawai zai shigo ai. Sai da sukai kwanaki uku a wannan hali, ga network ya ɗauke gaba ɗaya, sun kuma fahimci na gidan ne aka tsayar saboda su. Ga su Amimah ba zaman gidan suke ba. A randa suka cika kwana ukun ne Hajiya Hasiba ta dawo gidan, amma ko kula su batai ba sai washe gari. Shima ta window ta leƙa su, suna fara magana tabar wajen. Basu sake ganinta ba sai yau data buɗe ƙofar ta shigo musu.      Duk tashi sukai daga kwancen da suke, su duka biyun sun rame kamar wanda sukai wani babban ciwo. Ismat ta fara sauka a ƙasa ƙan gwiyawunta tana hawaye da bama Momyn tasu haƙuri akan idan wani laifi sukai mata ta yafe musu. Ganin haka itama Nabeeha sai ta sauka tayi kamar Ismat ɗin. Amma sai Hajiya Hasiba tama taɓe baki tana kauda kanta gefe da faɗin,..........✍️ 62 .........“Ai ku ke da haƙuri masu uba. Yanzu ku ku ɗin nan dana gama ƙare rayuwa a wahalar yi muku gata har kuke shirya yanda zaku barni kamar Jiddah. Koda yake ke Ismat ma ai kin barni ɗin, to halan da kika koma gidan uban naku gwal aka maidaki? Har waye Nasiru? Mi yake da shi? Wane gata ya baku a rayuwa matsayin uba da zaku bijire min ku zaɓe shi sama dani?”.          “Momy kiyi haƙuri ku duka kuna da muhimmanci a garemu kuma darajar ku ɗaya ce. Dan tare kuka haife mu har duniya ke iya kallon mu da daraja irin ta ƴaƴa masu iyaye guda biyu da aka haifa da aure. Momy ba damuwar mu dukiyar da kuka tara ko gatan da kuke mana ba. Abinda ke tsakanin ki da Daddy daban haka muma, ke matsayin mata kike kuma ƴar uwar sa, muko sunan mahaifi yake amsawa, albarkar ku da addu'ar ku kawai muke buƙata a cikin rayuwar mu, sai mu zauna lafiya. Sannan koda bakwa tare zaman mu a tare da shi zaifi bamu daraja musamman ga masu iya zuwa neman auren m.....”       Tauuuu!!! Kake jin saukar mari mai ƙara a fuskar Ismat da sai da kanta ya bigi gado. Jikin Nabeeha na rawa ta riƙota. Zuciyar Hajiya Hasiba na tafarfasa da hanƙoro a cikin ƙirji ta miƙe tana nuna su su duka biyun da yatsa. “Ku baku isa ba wlhy, ban haifi ɗan dazai bijire min ba. Ko Jiddah da kuke ganin na ƙyaleta na barta ne zuwa lokacin dazan waiwayeta. Kuma zaku san kunyi da ƴar halak. Idan ma uban baku ne ya aikoki ki faɗa min waɗan nan zantukan ina dai-dai da shi. Zan je kuma na sameshi har gidan nashi wlhy”.      Daga haka ta fice fuuuu tare da rufe ƙofar bummm ta sake murza mata key...... >>>>>>>%<<<<<<<          Gaba ɗaya a ƙage Malam Buba yake da son ganin dare yayi, dan yau jinsa yake tamkar an masa albishir da mukullin shiga aljanna. Saƙo fa ya samu daga shugaban nin su cewar yau suna son ganinsa da daddare. Shi ko mizai ce da wannan ranar albarka. Lokaci yayi da zasu goga kafaɗa da Dagger, lokaci yayi da shima zai jiƙe da kuɗi masu suna kuɗi ba kuɗin cefane da Dagger ke sammusu ba.      Yayi zurfi a wannan tunanin nasa har Daddy Imran yay horn maigadi ya tashi ya buɗe gate bayan ya leƙa yaga wanene. Sai da maigadi ya gama maida gate ɗin ya rufe ya dawo ya zauna ya taɓashi sannan yay firgigit, sai kuma akai sa'a idanunsa suka sauka akan su Nimrah dake fitowa daga motar. Agogon hannunsa na ƙarfe da ya gama cin duniyar sa a tsufa ya kalla, dan yana aiki lafiya lau, ko ya samu matsala badawa take a gyara masa saboda yana son agogon sosai. Ganin lokacin tashin su da saura mamakinsa ya kasa ɓoyuwa, sai kuma maigadi ma ya riga shi da faɗin,        “Da alama yau masu gidan sun ɗakko maganar da suka saba a makaranta. Dan in ka gansu a gida ba lokacin tashi ba akwai wata a ƙasa. Kai waɗan nan yara ban taɓa ganin ibilisai irinsu ba. Anya basu da aljanun faɗa kuwa?.”        “To waya sani ko su gare su”.    Cewar Malam Buba da duk hankalinsa ke kansu. Dan ji yake tamkar ya zama ƙuda yaje ya tambayi Nimrah miye damuwarta. A kwanakin nan ji yake ƙaunarta na sake mamaye masa zuciya da ɓargon jiki. Idan ya ɗau wani lokaci bai ganta ba ji yake kamar yay tsuntsuwa ya shiga gidan. Sai yata dannewa da ƙyar yake samun kansa. Maigadi bai lura da halin da Malam Buba ke ciki ba dan fitowar Sanda da tunda ya buɗe gate yay wuff ya shige ɗakinsu ta sashi maida hankali a kansa. Harararsa Sanda ɗin yayi tun kan yace komai, dole ya haɗiye abinda yaso faɗar kuwa koda tunawa da malam Buba a wajen.....       ★A ciki kuwa tunda su Nimrah suka shigo falon Mammah dake zaune tana cin apple su Shariffa na mata hira, sai Dayyan dake kallon Film, Hanoon na daga gefensa tana latse-latsen waya da bata gajiya tasan akwai matsala.      Dan Dada ne ya fara shiga, hakan yasa su Lailah sukai tsitt daga hirar da suke yi suka sake nutsuwa saboda girmamawa suna masa sannu. Dayyan ma da sauri ya gyara zamansa dan har cikin rai yake jin tsoron Dadan nan dako harkarsu baya shiga a gidan, kai ko kallo basu ishe shi ba. Ɗan zungurin Hanoon dake murmushi idonta a waya yayi, ta ɗago zata watsa masa harara a bazata taga Dada. Ai da sauri itama ta gyara yanayin ta, sai dai ita bana tsoro bane kawai harda na soyayya.     Mammah kawai ya gaisar, yana amsa gaisuwar su Shariffa ya nufi hanyar upstairs. Dan haka Mammah ta maida idanunta kan Imran cike da neman amsar tambayarta akan su Ruky. Zama yay ya gaida Mammah, shima su Lailah suka gaishe shi. Su Dayyan dama gaisuwarsu sai sun so, amma da yake shima Imran ɗin shakkarsa suke ji kasancewar ba wasa ya taɓa yi da su ba sai suka gaishe shi. Amsa musu yay suma da maida hankalinsa akan Mammah data kasa haƙuri ta jefa ma su Nimrah tambaya.       “Yanzu ina farin cikin kwana biyu kun nutsu ashe lumbu-lumbu kuka min. Yau kuma mi kuka aikata?”.        “Hummm! Ɗan tsohon shugaban ƙasa suka sumar Mammah”.     Ba Mammah ba hatta su Dayyan sai da suka ƙwalalo idanu waje. Lailah da Shariffa kam na haɗa baki wajen faɗin, “Ɗan tsohon shugaban ƙasa fa Yaya!”.       “To waɗan nan yaran kuma ai inaga shi kansa shugaban ƙasar dake kan kujerar mulki idan tsayawa zai yi bazar da shi zasuyi. Ina ga aikin soja kawai zan kaisu dan al'amarin nasu zaifi armashi a can”.         “Oh ni A'ishatu ALLAH kana gani, to miyay musu da zafi har takai da sumarwa? Sannan ma wai yaro ne kamar su ko yaya?”.        “Mammah ina fa sa'ansu, ajin ƙarshe fa yake a makarantar tasu. Kinga ko ai kusan sa'an Mu'azz kenan ake batu”.       Salati Mammah ta sake sakawa tana zabga tagumi, yayinda su kuma suke cika baki da iska suna hararar Dayyan da Hanoon dake dariya, dan su abin dariya ya basu harga ALLAH. Yara kamar jinin Chaines jama'a.         “Kun bar wajen ko sai na tashi kan ku”. Daddy Imran ya faɗa yana harararsu gani abinda suke ma su Dayyan. Ɗaki suka nufa sunama su Dayyan ɗin alamar zasu haɗe. Imran ya girgiza kai kawai yana danne dariyarsa, shi wlhy bai san yaya zai yi da yaran nan ba. Jifa ba'a gama kashe wani case ɗin ba suna ma wasu gargaɗi a cikin gida, dole ne a wannan gaɓar itama Ruƙayya a mata aure kawai zai fi samun nutsuwa. Sai da suka gama shigewa ya zayyanema Mammah komai da bayanin da sukayi har Dada yace akai zancen court, sai dai shima bai san dalilinsa na yin hakan ba. Amma yafi ƙyautata zaton kawai yayi hakan ne dan barazana tunda abinda su yaran suka faɗa dole su iyayen yaron zasu so case ɗin ya tsaya iya inda yake a yanzu. Mammah ta gamsu, tare da jera musu addu'ar shiriya. Daga haka shima Imran ya miƙa yay musu sallama dan yace zaije gida ne anjima zai dawo.....         ★★★★    Tsoron haɗuwa da Dada ya hana su Nimrah fitowa. Sai da yunwa ta ishesu Nimrah tai ƙundun balar zuwa ga ɗiba musu abinci ta koma. Da yake yau babu islamiyya haka suka cigaba da maƙalewa a ɗakin har akai magriba. Sai bayan sallar isha'i sannan suka fito bayan sun gama leƙowa sun tabbatar da Dada ya wuce sama baya falon, dan idan ya dawo sallar isha'i wani lokacin babu mai sake ganinsa. Su aunty Lailah ma suna sashensu basu kai da zuwa hirar dare ba. Hanoon ce kawai da Afeef yanzu zaune. Mammah ma tunda tai salla bata fito ba. Nimrah na rungume da magenta da in tana gida haka take manne da ita kamar ɗa, ta zube a kujera Ruky kuma ta nufi kitchen ɗiba musu abinci. Afeef da yafi tsanarsu saboda abinda suke musu dan shima fitinanne ne irinsu yaja tsaki yana miƙawa yabar falon. Sarai Nimrah ta jisa, dan haka ta bishi da kallo cikin rai kuwa tana ayyana (shege mai suffar tsaka. Ka rubuta ka ajiye yau da kumburarren baki zaka kwana a gidan kuwa) a fili kam sai tayi ƙwafar data saka Hanoon kallonta, harara ta wurga mata tana zazzare mata manyan idanunta sai kace Hanoon ɗin bata girmesu ba. Dole Hanoon ɗin ta ɗauke kai dan ita tana da tsoro Ba kamar Afeef ba.      Dai-dai nan Biebah ta shigo falon. Daga gidan Aunty Mimi take tun safe. Da gudu Nimrah taje ta rungumeta. Hakama Ruky data fito plate ɗin abincin ta ajiye tazo ta rungumeta. Har cikin ransu suke ƙaunar Biebah, dan itama tana son su matuƙa. Dai-dai nan Mammah itama ke fitowa a ɗaki. Kamar an saita sai gasu Aunty Lailah da yara duka. Nan fa falon ya kacame aka zagaye Small Mom Biebah dake raba musu tsarabar chocolate da tayo musu.......... ✍️ 63 .........Mu'azz ya shigo a gajiye, dan daga makaranta yake mashin ɗinsa ya samu matsala a hanya sai da Ammar ya biya ya ɗakkosa, dan haka sukai dare. Sun maida hankali a kansu suna musu sannu da jajanta abinda ya faru Dada ya fara sakkowa daga sama. Dan kafin ma ya bayyana ƙamshinsa ya fara isowa hancinan wasun su da takunsa. Tamkar an saita shima Afeef ya fito daga kitchen ɗauke da tea zai sha. Dan su abinci sai sun zaɓa. Nimrah da hankalinta ke kan kwance ma Afrah kai sam bata ji batun sakkowar Dada ba. Sai hankalinta ya koma kan Afeef. Alƙawarin datai ma kanta na yau sai ya kwana da kumburarren baki ta tuna. Ta kalla dole sai Afeef ya bi ta gabanta sannan zai wuce sai ta saki murmurshin da ALLAH ya tabbatar ma Dada ganinsa sakamakon idanunsa da suka sauka a kanta daga stairscase ɗin da yake sakkowa. Har zai kauda kai sai ya fahimci kallon da take ma ƙafafun yaron nan da ko sunansa bai sani ba. Sam bai kawo tunaninsa akan abinda take shirin yi ba, dan kamar ƙyaftawar ido kawai ta sakama Afeef ƙafa sai gashi kifff a ƙasa shi da kofin shayin nasa. Azaba ta saka shi fasa gigitacciyar ƙarar data saka kowa zabura a falon. Ita ko mai gayya da aiki tuni ta maida ƙafarta ta naɗe yanda take baka isa cewa itace ta aikata ba.... ###########         Tunda fa yau Malam Buba ya buɗe ido ya gansa a gaban shugabannin kungiyar duhu yaji yana neman susucewa, dan kuwa wannan shine karonsa na farko a tsawon fara aikinsa da su shekara takwas. A haka ma iya shugabannin ƙungiyar ne su biyar ba kowa da kowa ba sauran members.      Daga sama har ƙasa oga Jush ya gama ƙare masa kallo da nazartarsa. Kafin ya fara magana cike da gadarar taƙadaran masu mulki.          “Miyasa kai ƙoƙarin isar da wannan saƙon kai tsaye garemu bayan akwai Dagger dake jagorantar ka kafin yau?. Duk wani aiki shike baka umarnin sa. Ko akwai wani kuskure ne daka gani a tare da shi da ka ji rashin yarda?”.        Kasancewar Mole ba jin yaren Oga Jush yake ba Black Spider ya fassara masa. Mole ya sake risinar da kai cike da tsantsar girmamawa yana kuma girgizawa. Shima da yarensa daya iya yay magana black Spider tafinta. Ya tabbatar idan yana son kama kurwar mutanen nan sai ya bisu mataki-mataki, domin kuwa mugu shi yasan makwantar mugu ai.        “Ranka ya daɗe babu wata matsala shakanina da oga Dagger sai alkairi. Shi mutum ne mai amana kuma yasan aikinsa. Kwana biyu ban samesa bane ga kuma abinda na gani na cimin rai. Na kuma tabbatar kuna buƙatar wannan bayanin da gaggawa saboda matuƙar muhimmancin sa.”        Koda Black Spider yay ma oga bayani sai oga Jush ya zubama Mole idanu yana sake nazartar sa. Cikin gamsuwa ya ce, “Naji daɗin hakan ƙwarai da gaske. Dan yabon Dagger da kayi ya tabbatar mana kaima mutum ne mai amana. Da kaci amanarsa muma mun san zaka iya cin tamu. Zaka iya bayanin ka yanzu kam”.        Sosai Mole yaji daɗin wannan yabo, dama kuma irinsa yake son ji. Cikin ƙara kwantar da kai ya fara bayani dalla-dalla akan dawowar Dada. Babu wanda a cikinsu bai rikice ba kam. Dan oga Jush ma har miƙewa yayi tsaye tsabar firgici. Cikin tsawa-tsawa Viper ya ce, “Kasan abinda kake faɗa kuwa? Kai ya akai kasan shi?”.          “Babu tantama ko kokwanto a maganata oga, duk da a yanzu ya canja kamannin fuska ya ajiye gashin saje bazai layance min ba ai. Sannan taya zan manta da wanda gudan jini na take a hannunsa. Sai da na sake tabbatar da dukkan abinda zan kawo muku sannan na yarda nazo nan. Kuma na baku damar bincikawa kuma, dan kullum suna fita da Imran ɗin nan, sai dai ban san ina suke zuwa ba. Da farko nayi tunanin zai gane ni, sai kuma naga shekara takwas da rabi ba kwana takwas bace ba. Oga ku taimakeni yarinyata ta dawo hannuna nima, dan sun mata asiri bata ko tuna tanada uba. Mun bata video ɗin nan da kuka bada amma babu wani motsi daya nuna alamar ma saƙon da muke ƙoƙarin isarwa ya mata tasiri”.         Komai babu wanda ya iya sake ce masa a cikinsu. Dan halin da suke ciki a yanzu yafi nashi......      ★+++++++++++++++★          Ƙarar da Afeef ya fasa ta daki falon gaba ɗaya. Kowa ya zabura kamar an harba bindiga. Kofin shayin ya watse, ruwan ya zuba a kafet ɗin tsakkiyar falon, shi kuma yana mirgina a ƙasa yana riƙe ƙafarsa yana nishi.        “Wayyo ALLAHA! Wayyo kaina, ƙafata”.        “Subhanallah!”    “Innalillahi!” Muryoyin su Aunty Shariffa suka gauraye falon. Mammah ta miƙe da sauri tana nufarsa, Aunty Lailah ma ta biyo bayanta. Hakama Biebah da Ruky da har zata nufi kitchen ta dawo. Hanoon da Dayyan sun miƙe tsaye suma a firgice, hakama Mu’azz da sauran yaran su Aheel na tsaye kowa na kallon abin kamar fim.       Dada ma ya tsaya cak, sai dai baiyi magana ba. Sai idanuwansa da suka sauka a wajen. Kallon farko ya tsaya ne kan Afeef dake kwance yana nishi. Kafin ya maida kan kafar daya riƙe da hannu biyu yana magowa alamar tana masa raɗaɗi. Slowly ya maida kan Nimrah ƙasa-ƙasa ta yanda babu wanda zai ce ita yake kallon.           Tsaye take. Hannunta biyu riƙe da ƙugu. Fuskarta a haɗe, kamar bata fahimci me ya faru ba, ta wani zuba masa idanu kamar kowa. Idanun kuma darr babu alamar na mai laifi data firgita sakamakon ganin abinda ta aikata. Dada ya ɗan lumshe ido, ya sake buɗe su a hankali, ya maida kallonsa kan Afeef. Sai dai yanzun ma bai da alamar cewa komai.       “Subahanallahi kaji ciwo ko ruwan zafin ne ya ƙona ka?” Mammah ta faɗa tana durƙusawa kusa da shi da kamo sa jikinta.         “Zafi nake ji!. Kafa ta…”     Afeef ya faɗa hawaye na ziraro masa a fuska.       Biebah ta kalli shayin da ya zube. Cikin nuna mamaki ta ce, “Wai yaya ma haka ta faru? Naga babu komai a hanyar nan dai amma kamar wanda yaci tuntuɓe irin wannan muguwar faɗuwa haka”.       Afeef ya ɗaga kai, idanunsa na sauka kan Nimrah kai tsaye ya ce, “Ita ce. Ita ta saka min ƙafa.”       Falon ya ɗauke shiru na daƙiƙa ɗaya. Kafin Nimrah data zazzaro masa idanu ta ce, “Ni?!” ta faɗa cikin kamar ma mai mamaki irin na karya. Sai kuma ta shiga tafa hannaye “Kai! Amma kai mugun maƙaryaci ne. Ta ina zan iya kada ƙaton nan kamar ka to?!”.      Hanoon da ranta ya ɓaci sosai ta watsa mata harara, sai dai batace komai bata. Ruky data gama sanin wacece Trouble Queen ɗinta ta haɗiye dariyar dake son bayyana a fuskarta saboda Dada. Mu'azz ya taɓe baki yana ƙoƙarin danne dariya shima, dan tsaff ya gane aikin Ninah ɗin ne, haba shekara nawa ana haɗakar tsiyataku a tare.        Aunty Lailah da Shariffa kam kallon su biyun kawai suke kamar ba su san dawa zasu yarda ba.       “Nimrah… Mi ya faru?”.   Mammah ta kira sunanta a hankali, sai dai ta kafeta da idanu.          Shagwaɓe fuska Nimrah tayi, kafin ya ce, “Ni Mammah sharri kawai yake mun. Kowa ai yana ganin tsifa nake ma Afrah. Yanzu nida ke can, yana nan ƙafar barewa ce da ni balle na iya zunguro shi?. Ƙilama ƙafafun nasa ne basu da kwari, dan gasu nan tsulai-tsulai kamar na talo-talo wlhy”.         Kafin kowa yace komai Afeef ya harare ta. “Wallahi ke kika saka min ƙafa!”.        Caraf Ruky ta ce, “Karya kake! Dan ina tsaye ta kusa da ku ni ban gani ba”      A hasale Hanoon dake hararar Ruky ta karɓe da, “K dama ai bazaki faɗi gaskiya ba bakin ku ɗaya munafuka fitinannun yara! Kawai”.       “Ke ma fitinanniya! Dan ni da Buddy na albarka kullum Mammah ke saka mana da iyayenmu”. Nimrah ta faɗa tana murguɗa ma Hanoon baki da nuna su Shariffa.        Hanoon zata sake magana Mammah ta dakatar da su.       “Ya isa haka. Mu'azz bani first aid kit” Mammah ta faɗa tana kama ƙafar Afeef da cigaba da faɗin. “Bari mu fara ganin kafar yafi wannan gardamar taku.”         Sai lokacin ta juya ta kalli Dada da tamkar baya ma a falon kamar tana neman taimako. Amma sai gani tayi hankalinsa ma akan wayarsa yake gaba ɗaya. Dole ta haƙura ta maida idanuwan nata ga Afeef.       Abinda Mammah bata sani ba sarai Dada na lure da kallon datai masan, amma ya fiske. Sai ma mamaki da jinjina ƙarfin halin yarinyar nan da yake a ransa. Dan tsaff ta koma inda ta tashi abinta hankali kwance ta cigaba da ma Afrah tsifarta babu alamar tausayin yaron ko ɗigo. Murmurshi ne yay kamar zai kufce masa amma ya matse. Sai ma ya nufi ƙofa abinsa yana faɗin, “Mammah sai na dawo”.         Maganarsa ta saka hankalin su Shariffa dawowa kansa. Sai lokacin suka tuna ko gaishe shi basuyi ba. Aiko cikin sauri suka fara gaishe shin, dole ya dakata yana amsawa.        Nimrah dake jin idanu masu kaifi a kanta tun ɗazun sai dai ta rasa wake kallon nata ta ɗan motsa kaɗan, zuciyarta na bugawa, amma fuska a tsuke kamar ba ruwanta. Nata idanun ta ɗan ɗago a karo na farko ta saci kallon Dada da kowa ke gaidawa. Cikin sa'a kuwa sai idanun nata suka faɗa cikin nasan. Cikin sauri ta janyesu ta sauke kanta ƙasa ƙirjinta na sake bugawa..         Dada da shima ya janye nasa cike da basarwa yana sake ɗaure fuska ya ɗan ja numfashi a hankali. Sannan ba tare da ya ɗaga murya ba ya furta “Sai na dawo”.        Muryar sa ba tai ƙarfi ba. Amma amonta da tasirinta ya ratsa kowa dake falon, musamman Nimrah. Dan kallon da ya sake yi mata kafin ya juya, ya sa zuciyarta ta buga sau biyu. Domin ta fahimci abu ɗaya. Dada ya gani. Kawai bai faɗa ba ne. Sannan bai nuna alamun yama san abinda akai ba. Bai ce Nimrah ba. Bai ce Afeef ba. Bai yi hukunci ba. Sai dai taji tasirin kallonsa na ƙarshe ɗin nan da idonta ya gani, dan bazata iya tantance na baya da bata san wanene ke mata shi ba.........✍️ 64 ..........Babu wanda ya sake furta komai a ɗakin sai babbar jakar dake gefen oga Jush yay ma Mr Specter nuni da idanu. Mr Specter ya jinjina kai da tura jakar da ƙafa gaban Mole. “Ga wannan kaje da ita zamu nemeka idan buƙatar hakan tashi.”      Wani irin daɗi ne mai barazanar fasa zuciya ya daki zuciyar Mole. Duk da yaji damuwa da shirunsu bayan maganarsa ta ƙarshe, dan yaso ace sun tattauna fiye da haka domin su ƙara yarda da shi fiye da yanzu. Amma ko hakan ma ai tafiya tayi riba, dan ya tabbatar maƙudan kuɗi ne irin wanda aka saba bama Dagger yana tsakura musu yanda yaso, shima yau gasu an bashi matsayin nashi. Lokacin gina sabuwar rayuwa yayi, dan yana son sanda Nimrah zata dawo hannunsa tasan shi cikakken uba ne da zai mata gata....           Bayan sun sallami Mole ƙofar ɗakin ta maida kanta ta rufe. ɗakin ya sake komawa wani irin yanayi na shiru. Ba hayaniya. Ba motsi. Sai na ac. Shirun da kan gitta tamkar mutuwa ta ziyarci waje. Shirun da yake sa zuciya ta dinga tambaya kafin harshe.       Oga Jush ne na farko da ya motsa. Ya gyara zama a kujerarsa a hankali, kamar wanda ke sauke nauyin wani tunani mai tsanani. Bai dubi kowa ba. Sai teburin dake gabansa.         “Zak-Shadow…”     Ya faɗa sunan cikin murya ƙasa-ƙasa. Black Spider ya ɗaga kai kaɗan ya kallesa, sai dai bai ce komai ba.         “Na zata an gama da shi.”    Oga Jush ya ƙara faɗa, wannan karon muryarsa cike da ɗaci da zafin rai daya kasa dannewa.          Iska mai kauri Viper ya furzar. Cikin nashi yanayin ɗacin ya furta, “Oga dama mutane irinsa nada taurin rai saboda taurin kansu. Gadararsu ta banza da wofi kansa su dinga jin ba su gama ba. Su kan ɓace ne kawai da maimaita kalmar zasu dawo koda da cika baki ne.”          Ƙwafa mai ƙarfi oga yayi, ƙwafar dake nuna babban ƙudirin dake tafasa zuciyarsa a wannan gaɓar. Sai kuma shiru ya sake ratsa ɗakin, kowa da irin tunanin da yake yi. Dan su sun ma fi oga Jush shiga cikin razani.       Oga Jush ya sake katse shirun nasu. “Tambaya ya kamata muyi ma kammu yanzu, ba dawowarsa kawai ba.” Ya ɗaga kai ya dubi kowan nen su a jere. Kafin ya cigaba da faɗin, “Tambayar ita ce… me ya dawo domin yi?”        Tamkar ya dakesu a zukata ne da wannan kalma, dan babu wanda baiyi motsi irin na mai cizon cinnaka ba. Black Spider da ya jingina da bango, muryar sa na shaƙewa a naƙoshi ya amsa da, “Idan har ya sake kafa gida, to yana nufin yana da abin karewa.”        Viper ya ɗan yi murmushi mara daɗi. “Ko kuma ita ribar ƙafar ba, dan ina ji a raina riƙonta a garesa da manufa. Karfa ku manta yana da wayo, yana da target.”      Oga Jush ya lumshe ido na daƙiƙa kaɗan. Kafin a hankali ya ce, “Tabbas maganarka gaskiya ce. Musamman idan muka kalla Mole. Tana kusa da shi. Kuma ba ta san komai ba a kansa.”         Black Spider ya ɗan jinjina kai da furzar da numfashi mai nauyi. “Wannan ne mafi haɗari. Ku duba, mun bata video ɗin nan, amma babu wani motsi…”         Shiru ya sake mamaye ɗakin kamar an kashe iska. Kowa ya nutsu cikin tunani, ba don rashin amsa ba, sai don girman barazanar da ke gabansu.        Viper ya gyara zamansa da faɗin, “Idan har yarinya ta iya jure irin wannan barazanar, to tabbas tana da ƙarfin zuciya da dole sai mun sake nazartar ta… ko kuma tana cikin shakka da wasi-wasi. Kuma dole mu gaggauta......”        Oga Jush ya ɗaga hannu da alamar yarda da zancen Viper ɗin.     “Yarinyar ba matsala bace,” Oga Jush ya furta yana zuƙar sigari, sai da ya fesar da hayaƙin da sake gyara zaman ƙasaitarsa yana kakkaɓe tokar sannan ya cigaba da faɗin, “Matsalar ita ce wanda ke kusa da ita. Ku sani Zak-Shadow bai dawo domin zama ba. Idan har ya sake takun zahiriyya, to lallai ya dawo ne domin ya gama abin da bai kammala ba a baɗini.”         “Kenan oga hakan na nufin idan yarinyar bata motsa ba, zamu tilasta mata ta motsa dole?.”     “A’a. Ba da gaggawa ba.”   Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya saki wani murmushin mugunta mai armashi da ban tsoro. Sai kuma ya haɗe fuska da ƙarasawa da,     “Amma daga yau… ta zama hanyar shiga.”        A tare suka bubbuga tebirin gabansu alama na amincewa. Babu dariya. Babu tambaya. Babu jayayya. Shirun da ya biyo bayan maganar ya fi kowace hukunci nauyi. Wannan shirun ya fi kowace tsawa firgita..... >>>>>>>%<<<<<<<        Fitowarsa ya saya Imran dake tsaye jikin mota yana duba wayarsa kamar wanda ke jiran lokaci ɗagowa yana kallonsa. Shima kallon nasa yake, koda suka haɗa ido sai ya ɗauke nasa, kai kace baiga Imran ɗin ba ma. Dan kai tsaye gaban motar ya buɗe ta gefen mai zaman banza ya shiga abinsa. Imran dake binsa da kallo yay murmushi yana ɗan taɓe baki, kafin shima ya zagaya gefen driver ya shiga ya zauna..        Sai da ya tada motar ya ɗan kallesa da faɗin, “Ni harna fara tunanin binka ciki ma, jin shiru bayan kace gaka nan fitowa”.       Dada bai amsa ba. Ya daidaita zamansa ne kawai, ya jingina da kujerar, yana mai lumshe idanunsa. Sai da suka fice gaba ɗaya a gidan sannan Dada ya ɗan saki numfashi, tare da motsa lips kaɗan, cikin murya ƙasa-ƙasa ya furta,      “Hmm.. yaranka basa ji.” Imran ya ɗan juya kai ya kallesa, sai kuma ya saki murmushi da maida hankalinsa a titi sosai.        “Oh, su ne suka tsaidaka kenan? Mi ya faru?”     A nan ma shiru yay kamar bazaiyi magana ba. Irin shirun nan na manya, wanda baya nufin babu abin cewa, sai dai ana tattara abin faɗar ne saboda ɗabi'ar rashin son magana. Imran yasan halin kayansa, dan in kaji doguwar magana a bakin Zak... Ɗinsa ɗayan biyu ne. Kodai akan aiki, ko yana tare da Mammah ko da shi randa yaso hirar. Sun riga sun fice daga unguwar, har sun shiga babban titi, Imran na kallon hanya cike da natsuwa.       “Wai bazaka gaya min ba, sai na sauke ka a hanyar nan?”.     Idanu Dada ya ɗan buɗe yana harararsa, Sai ya kauda kai gefe, kamar yana kallon wani abu a waje, ya ɗan taɓe baki, murmushi yana ƙoƙarin kufce masa amma ya haɗiye kayansa.       “Kana son bani ciwon kai ne kawai kai da su Imran. Tsabar mugunta yaron nan kawai ta sama ƙafa ya kife a ƙasa shi da kofin tea. Ta kuma fiske abinta baka isa cewa ita ta aikata ba, harda kiransa mai ƙafar talo-talo”.       “ALLAH ya shirya min Ninah” Imran ya faɗa yana ƴar dariya. Dada ya juyo ya watsa masa harara.      “Oh abin ma sugar yay maka kenan? Idan taji masa ciwo kuma fa?”.      “In banyi dariya ba kuka kake son nayi. Indai su Nimrah ne kaɗan daga aikin su ka gani.”            Shiru ya sake ratsa motar. Amma wannan karon shiru ne mai ɗauke da dariya a ciki. Dan Dada gintsewa kawai yake, amma yanda ta saka ƙafar yaron ya kife kifff kawai ke dawo masa cikin rai. Yana buɗe file ɗin daya ɗauka a gaban motar ya sake furta, “Na shaida hakan yau kam, dan ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta bata kariya bayan yaron ya tabbatar ita ce ta kada shi, Mammah kuma ko faɗa bata musu ba fa.”        Imran ya saki dariya sosai har yana ɗan dukan sitiyari. Sai da yay mai isarsa, Dada da ya kallesa ya girgiza kai kawai.         “To wai wanene aka kada? Nasan dai ba zasu ma Mu'azz ba”.     Dada ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Cikin yaran mutum nan ne. Dama na fahimci ƴar tsama suke da su”.        “Kaji fitina, yaron da a tsaye ya fisu sau biyu!” Imran ya furta yana dariya.            “Ba ku kuke ɗaure musu ƙugu ba, ba Mammah ɗin ba, ba kai ba balle Uncle's da Auntys ɗin nasu. Abinda suka aikato a school yau banji wani yace musu dan mi ba, ƙarshe ma Mammah na gayama su Ma'aruff dariya na jiyo sunayi Bilal harda musu kirari”.      Imran ya sake kallonsa, wannan karon da nishaɗi sosai. “Ba wani ɗaure musu ƙugu da muke. Dole akwai abinda ya aikata musu shima, dan duk ƙiriniyarsu basa faɗan rashin gaskiya. Ɗazu ma lawyer ɗin nasu ya kirani yana min bayani wai yaron ya farfaɗo, amma iyayen sun kawo lawyer suma, da farko da sun dage sai an sake maido su station ƴan sandan suka nuna masa basu cika 18years ba, basu da hurumin riƙesu anan.”     “A’a. Ba da gaggawa ba.”   Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya saki wani murmushin mugunta mai armashi da ban tsoro. Sai kuma ya haɗe fuska da ƙarasawa da,     “Amma daga yau… ta zama hanyar shiga.”        A tare suka bubbuga tebirin gabansu alama na amincewa. Babu dariya. Babu tambaya. Babu jayayya. Shirun da ya biyo bayan maganar ya fi kowace hukunci nauyi. Wannan shirun ya fi kowace tsawa firgita..... >>>>>>>%<<<<<<<        Fitowarsa ya saya Imran dake tsaye jikin mota yana duba wayarsa kamar wanda ke jiran lokaci ɗagowa yana kallonsa. Shima kallon nasa yake, koda suka haɗa ido sai ya ɗauke nasa, kai kace baiga Imran ɗin ba ma. Dan kai tsaye gaban motar ya buɗe ta gefen mai zaman banza ya shiga abinsa. Imran dake binsa da kallo yay murmushi yana ɗan taɓe baki, kafin shima ya zagaya gefen driver ya shiga ya zauna..        Sai da ya tada motar ya ɗan kallesa da faɗin, “Ni harna fara tunanin binka ciki ma, jin shiru bayan kace gaka nan fitowa”.       Dada bai amsa ba. Ya daidaita zamansa ne kawai, ya jingina da kujerar, yana mai lumshe idanunsa. Sai da suka fice gaba ɗaya a gidan sannan Dada ya ɗan saki numfashi, tare da motsa lips kaɗan, cikin murya ƙasa-ƙasa ya furta,      “Hmm.. yaranka basa ji.” Imran ya ɗan juya kai ya kallesa, sai kuma ya saki murmushi da maida hankalinsa a titi sosai.        “Oh, su ne suka tsaidaka kenan? Mi ya faru?”     A nan ma shiru yay kamar bazaiyi magana ba. Irin shirun nan na manya, wanda baya nufin babu abin cewa, sai dai ana tattara abin faɗar ne saboda ɗabi'ar rashin son magana. Imran yasan halin kayansa, dan in kaji doguwar magana a bakin Zak... Ɗinsa ɗayan biyu ne. Kodai akan aiki, ko yana tare da Mammah ko da shi randa yaso hirar. Sun riga sun fice daga unguwar, har sun shiga babban titi, Imran na kallon hanya cike da natsuwa.       “Wai bazaka gaya min ba, sai na sauke ka a hanyar nan?”.     Idanu Dada ya ɗan buɗe yana harararsa, Sai ya kauda kai gefe, kamar yana kallon wani abu a waje, ya ɗan taɓe baki, murmushi yana ƙoƙarin kufce masa amma ya haɗiye kayansa.       “Kana son bani ciwon kai ne kawai kai da su Imran. Tsabar mugunta yaron nan kawai ta sama ƙafa ya kife a ƙasa shi da kofin tea. Ta kuma fiske abinta baka isa cewa ita ta aikata ba, harda kiransa mai ƙafar talo-talo”.       “ALLAH ya shirya min Ninah” Imran ya faɗa yana ƴar dariya. Dada ya juyo ya watsa masa harara.      “Oh abin ma sugar yay maka kenan? Idan taji masa ciwo kuma fa?”.      “In banyi dariya ba kuka kake son nayi. Indai su Nimrah ne kaɗan daga aikin su ka gani.”            Shiru ya sake ratsa motar. Amma wannan karon shiru ne mai ɗauke da dariya a ciki. Dan Dada gintsewa kawai yake, amma yanda ta saka ƙafar yaron ya kife kifff kawai ke dawo masa cikin rai. Yana buɗe file ɗin daya ɗauka a gaban motar ya sake furta, “Na shaida hakan yau kam, dan ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta bata kariya bayan yaron ya tabbatar ita ce ta kada shi, Mammah kuma ko faɗa bata musu ba fa.”        Imran ya saki dariya sosai har yana ɗan dukan sitiyari. Sai da yay mai isarsa, Dada da ya kallesa ya girgiza kai kawai.         “To wai wanene aka kada? Nasan dai ba zasu ma Mu'azz ba”.     Dada ya lumshe ido na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Cikin yaran mutum nan ne. Dama na fahimci ƴar tsama suke da su”.        “Kaji fitina, yaron da a tsaye ya fisu sau biyu!” Imran ya furta yana dariya.            “Ba ku kuke ɗaure musu ƙugu ba, ba Mammah ɗin ba, ba kai ba balle Uncle's da Auntys ɗin nasu. Abinda suka aikato a school yau banji wani yace musu dan mi ba, ƙarshe ma Mammah na gayama su Ma'aruff dariya na jiyo sunayi Bilal harda musu kirari”.      Imran ya sake kallonsa, wannan karon da nishaɗi sosai. “Ba wani ɗaure musu ƙugu da muke. Dole akwai abinda ya aikata musu shima, dan duk ƙiriniyarsu basa faɗan rashin gaskiya. Ɗazu ma lawyer ɗin nasu ya kirani yana min bayani wai yaron ya farfaɗo, amma iyayen sun kawo lawyer suma, da farko da sun dage sai an sake maido su station ƴan sandan suka nuna masa basu cika 18years ba, basu da hurumin riƙesu anan.”         Dada ya ɗan yi ƙwafa kaɗan, murmushi na neman kufce masa. Ya dai juyo gefe yana ƙoƙarin ɓoye abinsa. Kamar baya so ya furta,       “Yara ne. Amma ba ƙanana bane tunda har suna da wayon banbance abubuwa. Dan itama Ruƙayya aure zan mata”       Cike da neman magana Daddy Imran ya ce cikin raha,       “Hmm… yanzu ka fara ganewa kenan?”       Dada ya kallesa. “Gane mi?”    Imran ya ɗaga masa gira cike da tsokana da son ganin ya ƙure shi.       “Cewa ɗiyata Nimrah ta girma.” Nan ne Dada ya kasa danne kansa. Ya saki ɗan murmushi mai nauyi, ya kauda kai gaba ɗaya yana girgiza kai a hankali.           “Kar ka fara”. Ya faɗa cikin gimtsewa. Dariya Daddy Imran ya saki.    “Wlhy dole in fara. Saboda kallon da ka mata yau a station… ai na san wannan kallo.”        Dada ya ɗaga kai yana harararsa da sake ɗaure fuska, sai dai murmushin dake makale a fuskarsa ya neman fallasa shi.      “Imran!” Ya faɗa da gargaɗi. “Yi haƙuri Babban Yaya, wannan idanun bana son suna hararata.”       Sake hararar tasa kuwa Dadan yayi yana ɗauke kai. Imran ya murmusa da cigaba da faɗin, “Amma kai ka fi kowa sanin damuwar ka. Ka ƙi kace komai akan dawowar Nabeeha. Zak.. shekara takwas fa ba wata takwas bane. Lemon tsami, kanwa, azumin nan duk basa hana komai, kwantarwa ne kawai na lokaci. Ya kamata kayi abinda ya dace, bance Nimrah ba, dan tabbas tayi ƙanƙanta a shekaru, amma da wayonta. Sannan Nabeeha ba sakinta kai ba balle kace. Komai ya dai-daita, sai dai ka sani aiki bazai samu dukkan ƙarfinka ba, sai kaima ka Dai-daita. Wannan danne damuwar ta tsiya-tsiya bazata haifar da ɗa mai ido ba”.          Dada da ya ce, “Hummm” kawai ya yi shiru. Sai dai wannan shiru ba na ɓacin rai bane. Na tunani ne… da ɗan murmushi a zuciya. Dai-dai nan suka iso inda suka nufo. Ɓoyayyen guesthouse dan haɗuwar ta sirri ce da shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida...........✍️ 65 ........A gidan Mammah kam bayan komai ya lafa, aka taimaka wa Afeef aka kai shi sama, ƴan uwansa Hanoon da Dayyan na tare da shi. Dan wata irin tsanar Nimrah da Ruƙayya suke ji na ƙara tasiri a zukatansu. Hatta ƴan gidan kowa ya basu haushi yau, yanda ko sau ɗaya ba'ama Nimrah faɗa ba balle cigaba da tuhumar gaskiya. Dan koda su Ma'aruff suka shigo kasancewar basa gidan su duka huɗun sunje duba wani makwafcinsu ne da baida lafiya da aka basu labari ko nuna zargin ma Nimrah basuyi ba su. Ƙarshe ma hira suka koma abinsu kamar komai bai faru ba.       Hanoon ta kira Abbansu ta sanar masa komai, baya ƙasar dan tunda ya kawo su gidan yay tafiya. Shima ransa ya ɓaci har yana faɗin sai yayi maganin Nimrah idan ya dawo. Tunda yaga tsoronta suke ji a gidan. Shi yama rasa dangantakar su Adda A'isha da yaran duk da dai adadin jikokinta kawai ta sanar masa batai masa bayani ba bayan hakan. Shiyyasa yake tunanin jikokinta ne. Wayar yace a bama Afeef, ya lallasheshi da tabbatar masa zai dawo a cikin satin nan. Idan kuma zasu koma gida Lagos ne to ya saya musu ticket. Caraf Afeef yace shi bai yarda ba, yafi son Nan ɗin, dan wlhy bazai tafi ba sai ya rama..      Sallama yay musu da faɗin sai ya zo to. Daga haka aka yanke wayar Hanoon na cigaba da faɗin, sai ta koyama su Nimrah hankali a gidan nan. Shi ko Dayyan ƙudirinsa daban a cikin rai. Dan tunda yazo gidan hakanlinsa akan yaran nan biyu yake. Rashin mutuncin su ya saka shi haɗiye kwaɗayinsa.      Sun jima a ɗakin kafin su fice su bar Afeef, dan abokin kwanan nashi Mu'azz bai shigo ba.      A daren Afeef ya jima bai yi bacci ba yana ƙulla abinda zai ma Nimrah. Dan can cikin dare ma zaune ya tashi a kan gado kafarsa na masa masifar zogi, fuska a haɗe kamar ya ci lemon tsami. Waya ya ɗauka yana danne-danne, amma tunaninsa na kan ƙulle-ƙullensa.     (Wallahi ba zan bari ba) Ya tuna murmurshin da Nimrah ta masa da gwalo bayan fitar Dada. Da yanda suka kalla juna da Ruky da munafukin nan Mu'azz sukai wani salo da yatsu suna gimtse dariya. Itama Ruƙayyan yana ganin yanda take kallonsa tana murmurshi. Harda gwada masa yanda shugaban ƴan iska ta saka masa ƙafa. Hakan na nufin itama ta gani amma da yake mufuka ce bakinsu ɗaya ne ta musanta harda bata kariya.      “Yar iska… zanyi maganinki ta yanda ko takuna kika ji sai kin firgita ” ya faɗa ƙasa-ƙasa. Sai kuma yay ƙwafa da sake faɗin, “Ba kince kina da wayo ba.” Ya saki murmushi yana cizar lips da ƙara faɗin, “Zan tabbatar muku na fiku zama tantiri. Zaku san ni cikakken rainon yahudawa ne. Idan ba yau ba, gobe. Idan ba a falon ba, a wani wuri.”      Ya saki wata shegiyar dariyar data farkar da Mu'azz a barci. A fili ya sake faɗin, “Sai kin gane baku kaɗai bane jiƙaƙƙun tantiran ƴan iska a gidan nan”.      Sarai Mu'azz yaji furucin Afeef na ƙarshe. Sai dai bai ce komai ba, baima nuna masa ya farka ba. Amma ya fahimci akwai abinda yake shiryawa kuma akan Nimrah. Ji yay tausayin Afeef ɗin ma ya kama shi, dan wlhy ya tabbatar yace zai cigaba da shiga sabgar Ninah da Ruky a gidan nan to da wahala ba'a fita da shi a ambulance zuwa asibiti ba wataran. Dan yafi kowa sanin yaran nan, zaman lafiyarka da su kawai kada ka shiga sabgarsu. Anan kam zaka ga biyya, amma saɓanin hakan ALLAH ne kawai mai ƙwatarka saboda hanyoyin mugunta iri-iri sun santa kamar goyon iblis. Bari ya barsu da shi jikinsa zai gaya masa....                ★A ɓangaren Nimrah tuni tama manta da wani batun Afeef. Dan koda suka shiga ɗakin su tsara yanda zasuyi yawo a weekend ɗin nan suke yi, suna fatan ALLAH ya ɗorasu akan Mammah kada ta hana su duk da suna hutun tahfiz ne. Sun jima kafin su kwanta sanin gobe akwai makaranta, duk da dai basu san ya zata kaya ba tunda sun bazar da ɗan shugaban ƙasa mai sauka a ƙasa. Nimrah ta kwanta amma bacci ya ƙi zuwa. Ruky ko tuni ta yi bacci tana sauke numfashi a hankali. Ita kam… ido biyu a rufe amma zuciya a buɗe. Haka kawai abinda ya faru ɗazu a falo kuma ya shiga dawo mata a rai. Ba kuma akan kowa ba sai kallon Dada ne yake dawowa mata a kai. Ba tsawa. Ba magana. Sai shiru da kallonsa mai kaɗa hanjin ciki..          Dai-dai lokacin dogarinsa ya kammala zuba coffee a kofuna masu shegen ƙyau na zallar farin gilashi mai garai-garai daga haɗaɗɗen coffee maker dake saman Centre table ɗin. Gaban kowa ya kai ya ajiye. Kafin cikin girmamawa ya nema izinin tafiya. Kai Janar ya jinjina masa alamar bashi dama. Sai ya sake risinawa sannan ya fice ya maida ƙofar ya rufe musu, bayan ya ƙara rage hasken falon ya bar blue ɗin wuta mara ƙarfi kamar waɗanda ke cikin club.........✍️ 66 .........Shiru falon ya ɗan ɗauka na mintuna. Shiru irin na manya kowa na nazartar ɗan uwansa. Kafin Shugaban ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida ya katse yanayin. Bada murmushi mai yawa ba, amma da girmamawa ta gaskiya kuma ta musamman da amana ya furta,      “Zak-Shadow”.          Kai daga jin yanda sunan ya fito daga bakinsa kamar sirri da aka daɗe ana ɓoyewa kasan yana cikin farin ciki mara misali ne.        Dada ya wani ɗan lumshe idanun sannan ya buɗe su. A nutsensa ya amsa da.       “Ranka ya daɗe, Your Excellency.” Shugaban ƙasa ya ɗan yi murmushi. Hakama Imran dake kai coffee bakinsa sai da ya murmusa.      “Anan… babu ‘Your Excellency’. A yau, ni da kai ne da Imran kawai. Ba matsayin shugaban ƙasa ba, matsayin abokin aiki a gidan soja kawai. Idan kun so zaku iya ƙarawa da wani abinda kuke ganin ya dace ku ambace ni. Amma ba bigiren siyasa ko shugabancin ƙasa ba”.       Yanzu kam ba Daddy Imran kawai ba, har Dadan sai da ya saki wani guntun murmushin gefen baki yana sake gyara zamansa na ƙasaita.        Shiru ne ya sake ratsa ɗakin, shiru mai nauyi, irin wanda ke gwada ƙarfin zuciya da girmamawa. Shugaban ƙasa ya cigaba da faɗin,       “Na jira sati guda. Ba don rashin gaggawa ba… sai don na tabbatar kana lafiya. Sannan ka huta, ka gana da Mammah da ƴan uwa da iyalai yanda ya dace.”        Dada ya ɗan jinjina kai, kafin ya furta, “Na gode ranka ya daɗe. Dama ni ba na son gaggawa. Nafi son tabbaci.”       Shugaban ƙasa ya jinjina kai. “Wannan dalilin ne yasa ka dawo.” Dada bai yi mamaki ba. Sai dai ya ɗan murmusa, sai kuma ya ɗan harari Imran.        Ƙaramar dariya Imran da Janar sukayi a tare. Janar ya sake faɗin, “Ba Imran bane ai. Na sani tun kafin ka taka ƙasar nan. Kuma na sani cewa dawowar ka ba ta nufin hutu. Hakan ya mun daɗi, dan na sake gaskata har yanzu wannan ƙasar tana cikin zuciyar Zak-Shadow, kuma itace gaba a cikin manyan burukan sa na rayuwa.”       Dada ya ɗan jingina da kujerar yana furzar da iska mai nauyi, sai kuma ya zuba kaifafan idanunsa cikin na Janar. Ba wargi, amma ba wasa. Cike da dakiyar sa matsayin soja da bai san tsoron tunkarar matsala ba ya ce,        “Idan haka ne… me yasa kuka kira ni nan?”.     Shugaban ƙasa ya ɗan yi shiru yana kauda idanunsa, sannan ya ce cikin murya mai kauri:        “Domin wasan ya sake farawa Haysam. Dan a yanda na ilimantu cikin siyasar ƙasar nan babban yaƙi ne a gabanmu ba murƙushe ƙunya kawai ba”.       Idanuwan Dada suka yi kaifi akan Janar. Cikin wani yanayi ya furta, “Kana tsoron Ƙungiyar duhu bazata iya mutuwa bane cikin sauƙi?”.           “Ba haka nake nufi ba Haysam, ai tunda kafiran baya masu taurin kai da izgili irin su Abu Lahabi suka ƙare a doron ƙasa, daular musulunci ta kafu a cikin idanunsu, a cikin ƙasar da suke alfahari da ita, a hannun marayan nan da suke iƙirarin an haifa a gabansu, sadauki uban sadaukai, masoyin ALLAH ɗan gatansa, mai faɗa da cikawa kyakkyawan balarabe ɗan dangi. To waɗan nan dauɗar duniyar ba komai bane ba. Idan ma mu mun shuɗe a cikin yaƙin, wasu da zasu ƙarasa mana ZASU TASO NE. Kawai ina son ka fahimta, a yanzu ƙungiyar duhu ta ɓoye. Ta canja fuska. Ta sake yin mamaya ta mutane da dukiya. Amma tana nan kuma tana motsi da motsin ƙarfin ikon ƙasa da masu shugabancin ƴan ƙasar. Amma bana son hakan yasa kaji tsoro, dan tsoro shine matakin farko na rauni da tarwatsewar ƙarfin iko, sannan shi ke bama marasa ƙarfi ƙarfi akan masu rinjaye. Shike bama masu taka baza da bazar ƙarfin masu ƙarfi gadara da ɗauka sune a sama dole a bisu. Shi ke sawa suji kamar zasu iya juya duniyar bayan talakawan ƙasar da suke amsa suna ƙasar tasu”          Murmurshin da Dada ya saki a yanzu har sai da ya bayyana fararen haƙwaransa a cikin idanun shugaban ƙasa da Imran. Sai kuma ya ɗan taɓe baki. “Na riga na ji motsinta tun ina sakaye. Sai dai ranka ya daɗe ka sani bazamu ce mu bama jin tsoro ba, saboda mutane ne tamkar kowa. Muna da rauni, muna da ruhin mutuwa tamkar kowa. Muna son rayuwa, dan wannan ɗan adam taka ce irin na kowane rai. Sai dai hakan bazai hana mu sadaukarwa ba, saboda addininmu addinin jarumta ne. Mun san kammu, mun san makomar mu da darajar rahamar da mahalicci mu yayi mana. Yanda sahabban MANZON ALLAH suka ƙare rayuwarsu wajen bama MASOYINMU kariya da kafa daular da har a yanzu muke ci daga arziƙinta, muma na baya da bamu ganshi ba, amma soyayyarsa bata da iyaka a jininmu bazamu bari wasu munafukan cikinmu da azzalumai suka mamaye da ƙyale-ƙyalen duniya ba su saida mu a hannaye marasa daraja. Zamuyi da basirar mu, da ƙarfin mu, da lokacin da UBANGIJI ya bamu, randa umarninsa na gushewarmu ya tabbata sai mu kwanta mu barma na baya sauran aikin, dama mun san duniya kasuwa ce, sanda wani ke kammala cin tashi sannan wani ma ke shirin shigowa tashi sayayyar. Dan haka ba ruwana da ƙarfinsu, dukiyarsu, mamayarsu, dan koda da Imran da su Ma'aruff suka mamaya zamu haɗa duka mu zubar da su da ƙarfin ikon ALLAH”.        Shugaban ƙasa ya ɗan yi murmushi yana jinjina ƙudirar UBANGIJI mai bada ƙarfin iko ga wasu zukata. Sannan ya gina tsokokin jikinsu da ƙarfi mai bayyana a idanu. Ya rage naka ka zama irin Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi wajen nuna godiyarka ka gina kyakkyawan aiki, ko ka zaɓi butulce masa wajen lalata wannan baiwar a neman duniya da burge mutanen ciki dan kawai a kiraka wane a riga ko dukiya ko suna. Imran da yasan duk abinda zai fito daga bakin Zakin sa tun daga ƙarƙashin zuciya ne bawai cika baki ko gadara irin ta wawayen mutane ba, sai ya lumshe idanu yana ɗan sakin ajiyar zuciya.          Shugaban ƙasa ya sake katse shirun da faɗin, “UBANGIJI yayi ma rayuwa albarka, ya ƙara mana ƙarfin zukata da jajircewa. Ya ɗora nasararmu akan masu zalunci. Duk mai son kaimu ƙasa ya Rabbi ka kaishi a lokacin da muke barci batare dama mun sanshi ba. Haysam ka godema ALLAH kaji, dan ya baka abubuwa da yawa da bai baima da yawan mutane ba. Irin ku kai da Imran kaɗanne a cikin wannan haɗamammiyar al'ummar tamu da basu da burin komai sai na son tara dukiya da suna cikin haɗama da babakere. Burin kowa ace shi ɗin shi ne dai, yana mantawa da ranar tafiya babu ko zoben ƙarfe a ɗan yatsa, sai farin ƙyalle da a kwana uku zai fara ruɓewa ma, sai wannan halayen dai da in ka gagara ginawa akan gaskiya, amana, imani, tsoron ALLAH. Kowa gani yake kawai daya mutu ya huta. Bai hango kwanciyar shekaru da za'ai a cikin kabari balle ranar rarrabe ayyuka, kowa dai sai yace aljanna ta mai rabo ce. To aljannar an faɗa maka layin rabon kunu ce balle kace idan kaga idon sani a wajen zai ƙara maka kofi ɗaya akan kasonka naka ya ƙara yawa. Iya nauyin sikelinka, iya matakin da zaka taka daga falala ko uƙuba. Ya rabbi kasa mu cika da imani”.         “Amin ya rabbi”.    Dada da Imran suka amsa a tare.         Karan farko Imran ya saka baki a tattaunawar tasu. “Ranka ya daɗe nima ƙarfinsu bashi yafi damuna ba ko nake kallo a barazanar wannan yaƙin. Zak.. ka san abin da ya fi haɗari?”       Dada ya girgiza kai. “Ba kai bane”. Imran ya cigaba da faɗa.           “Ban gane ba”.      Cewar Dada yana tsare Imran da idanu. Sai dai maimakon Imran ɗin ya bashi amsa sai shugaban ƙasa ya amsa masa da.        “Gaskiya Imran ya faɗa, ba kai ne haɗarin ba a yanzu. Abin da ke kusa da kai ne. Shiyyasa dole a fara wannan aikin a rufe, dan zuwa yanzu koda sun sami labarin dawowarka zasu fara maida hankali a binciken tabbatarwa ne kafin shiri”.         Shiru ya ratsa falon kamar hukunci. Dada bai tambaya ba. Bai kuma ƙaryata ba, sai ma nazartar maganganun yake dalla-dalla a ƙasan zuciya.. Fin minti biyu kafin ya kallesu su duka. Kai tsaye ya furta, “Minene shirin yanzu?”.         Shugaban ƙasa ya ɗaga gira kaɗan. “Ajiye aikin soja a zahiri. Sannan sabon muƙami a ɓoye. Ba muƙami na takarda ba. Ba wanda zai gani. Ba wanda zai sani. Ba wanda zai ji, sai mu ukun nan kacal”.          Shiru kawai Dada yayi yana kallonsu. Sai Imran ne cikin dunƙule hannu ya furta, “Yes ranka ya daɗe. Wannan itace power ta gaskiya, power ta ruɗani. Power ta mamaya, sannan ta ƙarfin iko”.       Ƙaramar dariya shugaban ƙasa yayi, dan yanda Imran ɗin yayi dole kai dariya. Shi kansa uban gayyar duk da ya fuske sai da ya murmusa a zuciyarsa.        Janar ya buɗe drawer jikin center table ɗin ya zaro wata takarda, Imran ya miƙawa yana faɗin, “Ba takardar aiki ba. Umurni ne. Jagorancin sashen tsaro na musamman”. Ya maida idanunsa kan Dada. “Kai kaɗai zaka ba da rahoto kai tsaye gare ni. Kana da damar haɗa ɓoyayyar rundunar aiki, a cikin kowanne jami'an tsaro na ƙasar nan ko farar hula. Sai dai ka sani zan saka ɓoyayyen tsaro a bayanka, dan kai ma tsaron lafiyarka zai koma ƙarƙashin ikona ne daga yau a gida da waje. ALLAH ya bamu fiye da nasarar da muke fata da buƙa”.         “Amin ya rabbi ranka ya daɗe”. Cewar Imran cike da farin ciki. Dada ma ya ɗan yi murmushi kaɗan. Sai kuma cikin ɗan taɓe lips ya furta.      “Sir! A ɓoye baiyi ƙarfi ba? Karfa ka manta akwai soji biyu tare da ni.” ya ƙare maganar da kallon Imran...........✍️ 67 .......“Hakan shine yafi dacewa”. Shugaban ƙasa ya amsa yana kallon Imran ɗin shima, sai kuma ya cigaba da faɗin, “Domin idan aka bayyana, za su motsa. Idan aka ɓoye… za mu gan su suna motsi. Dole Imran zai koma ɓoyayyen ma'aikaci a wajenka daga shi har Haydar, dan karka manta akwai kaki a jikinsu, kuma suna da ƙarfin iko a waccan bishiyar ma. Dole kuma su cigaba da zama dan inuwarsu zata mana amfani cikin wannan ɓoyayyar tafiyar, ta haka ne zasu banbance ganyen daya bushe akan bishiyar da suke”.        Cikin gamsuwa da jinjina kai Dada ya miƙa hannu ya ɗauki takardar a karo na farko, bai kalle ta ba. Sai dai kai tsaye ya furta,        “Yaushe aiki zai fara?”    “Ba a wannan daren ba. Amma daga yau… ka riga ka fara.”       Dada ya ɗauki kofin sabon shayinsa da Imran ya sake zuba masa, dan sun shanye coffee ɗin farko tuni, ya kai bakinsa. Sai da yasha ya ajiye sannan ya furta.       “Idan haka ne, ku shirya kawai.” daga haka ya miƙe. Shugaban ƙasa ya miƙe shima, hakama Imran da ya furta kalmar;        “Da me?”   Dada ya kallesa, idanuwansa sun yi sanyi amma murya ta yi kaifi. Kai tsaye ya bashi amsa da.        “Da komai ma. Domin wannan karon… ba zan tsaya tsaka-tsaki ba. Zan yi aiki kunne a toshe, ido a makance. Ba uba, ba ɗa, ba ƙani, ba aboki, ba mata koda tsautsayi ya gitta”.          Shugaban ƙasa ya kalleshi na ɗan lokaci yana siririyar dariya, sannan ya ce, “In sha ALLAHU ma baza'a kai ga nan ba ZAKIN IMRAN”. Ya ƙare maganar yana miƙa musu hannu alamar su yi musabaha. Sai da suka ɗan dara a tare, kafin musabahar dake nunin abubuwa masu yawa.       Ba murmushi. Ba alkawari mai yawa akan ɗagama kowa ƙafa. Sai dai akwai fahimta. Sannan akwai tabbatarwar a waje ƙungiyar duhu na jira. A gida, zuri'a da iyalai na kusa. A ɓoye munafukai na motsi.....         >>>>>>>%<<<<<<<       WASHE GARI JUMA'ATU babbar rana. Ranar da kan biɗa ka samu da izinin UBANGIJI mai taskar da bata girgiza balle ƙarewa. Babu wanda yasan lokacin da Dada ya dawo gidan a daren jiya. Wayar gari kawai sukai suka ganshi. Ganin nasa ma su Uncle Ja'afar ne kawai a wajen fita massalaci sallar asubahi. Su Nimrah kuwa har suka kammala shirin makaranta suka fito basu san ma mi gidan yake ciki ba. Sai da suka fito kai tsaye Mammah tace bazasu makaranta ba sun mance abinda suka aikato jiya. Dole su jira sai anji halin da yaron ke ciki gudun abinda zai iya zuwa ya dawo.         Ko'a jikinsu dan daɗi ma suka ji, tuni suka koma ɗaki suna tsallen murna suka cire uniform. Hankali kwance suka sake hayewa gidajensu suka duƙun ƙune a barguna bayan sun kashe fitilu sun saki labulale da ƙara gudun ac. Babu kuwa wanda ya sake jin labarinsu bare motsin su har sha biyun rana. Koda Mammah ta saka Kulu ta tado mata su suzo suyi breakfast samu tai sun kulle ƙofa ma. Bugun duniya kuma babu ƙo motsinsu sai kawai ta ƙyalesu.         Kaf mazan gidan yau suna gida. Dama su Ma'aruff basa fita kasuwa juma'a, Bilal da Ammar ne kawai sukaje aiki. Kuma sun taso da wuri saboda tafiya massalaci. Dada kam babu wanda ya gansa a safiyar har yanzu. Yana ɗakinsa. Da yake ya sanar ma Mammah zai yi barci ne sanda ya shiga suka gaisa da asuba, dan shi yama ce ta hana su Nimrah zuwa makaranta shiyyasa bata damu da rashin fitowar tasa ba balle tayi jajensa...         Sai misalin ƙarfe sha biyu da kwata duk suna falo ana hira sai gashi ya sakko. Ƙamshinsa shi ya fara ratsa hancinansu kafin bayyanarsa. Babu wanda baiyi tasbihi a ransa ba ga UBANGIJIN halittar wannan bawa. Dada ko yaya sutura take idan ya saka tana masa kyau matuƙa, koda ba mai daraja bace. Sai dai fa manyan kaya sukan zama na musamman dake ƙara masa kamala da cikar haiba tamkar uniform ɗin aiki. Dan a shekarun baya Imran yasha tsokanarsa da kalmar (bai taɓa ganin wanda uniform kema ƙyau a jiki irinsa ba). Ko a lokacin baya ce masa komai, wani lokacin ma sai dai ya samu tukuycin harara.           Shi ya fara gaishe da Mammah kafin su ma duk su gaishe shi. Koda Mammah ta masa maganar abinci ce mata yay sai sun dawo massalaci.     “Zama da yunwa ko Muhammad? Bafa ka karya ba”.      Murmurshi yay mata. “Mammah nasha Coffee”.         “Coffee ba abinci bane ai, yanzu dai ko milk tea a haɗa maka”.     Bai ce komai ba, dan yasan in ma bai sha ba hankalinta bazai kwanta ba. Kafin Mammah tai magana Biebah ta miƙe kusan lokaci guda da Lailah. Mammah tace Lailah ta koma ta zauna ita dake fama da kanta. Dan yau Shariffa ma gaida Mammah kawai tazo tayi ta koma sashenta alamar ɗan baba nata harama. Dan har asibiti ma Yaya Ja'afar ɗin yaso su wuce taƙi, acewarta a ɗan dai saurara tunda ba wani ciwo take ji mai tsanani ba, kawai dai jikin ne baya mata daɗi. Biebah ce taje tai mata komai a sashenta, su Abees kam sai Lailah ta haɗasu tai musu shirin makaranta dan su sunje.       Yana kammala sha suka wuce massalaci. Bayan wucewar tasu Mammah da kanta taje ya tada su Nimrah. Da ƙyar suka zo suka buɗe mata ƙofar kuwa. Korasu tai suje suyi wanka, ita kuma ta fice nata ɗakin. Koda suka fito fes da su, duk da ba wasu kaya masu nauyi suka saka ba amma da yake yaran Mammah masha ALLAH sai suka fito darr. Hanoon kawai suka samu a falon tana kallo, ko kallon inda take basuyi ba suka wuce kitchen, dan tsabar neman magana ma hanci Ruky ta rufe, sai kuma ta ɗauki turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ta saka bonner. Mi Nimrah zatai inba dariya ba. Harda wani faɗin, “Sai dake Trouble Buddy na”.        Ruky kam ta fuske kamar bata aikata komai ba. Hanoon ta shaƙa sosai, sai dai batayi magana ba. Haka suka zauna suka fara cin abinci suna hira da dariya data saka Hanoon daina fahimtar Film ɗin ma gaba ɗaya. Fitowar Biebah ya taimaki Hanoon. Dan Biebah data fahimci abinda ke faruwa sai ta ɗauke musu hankali da labarin ƙawarta Chef Yakudima, tace su tambayi su Yaya Ma'aruff su biya musu su shiga makarantar koyon girke-girken ta tunda gashi za'a shiga hutu.       Ruky na bala'in son harkar girke-girke, Nimrah ce ma sai a hankali tanan ɓangaren, dan ma Ruky na jan ra'ayinta shine ma take ɗan taɓawa. Suna tsaka da wannan hirar ne Mammah ta fito. Koda taji batun da suke sai itama ta gamsu da shawarar Biebah ɗin, tace ta binciko ya tsarin yake. Cike da farin ciki Ruky ta rungume Mammah. Dariya suka saka mata harda su Kulu da suka fito, dan kowa yasan yanda take son harkar. Daga nan aka fara hirar girki. Nimrah da yake ba so take ba taƙi saka baki, Hanoon ma sai wani yatsine-yatsinen fuska take yi.      Mammah datai tunanin ya kamata a gyaro ɗakin Dada duk da baiyi magana ba tace Nimrah taje ta gyaro tunda ba hirar take ba. Nimrah bata son aiki, dan haka kamar zatai kuka ta fara roƙon Ruky ta rakata suyi, ita ko Ruky hankalinta nakan kallon videos ɗin Chef Yakudima a YouTube channel tace bazata ba. Nimrah taji haushi kuwa ta wuce fuuuu. Sai kawai Hanoon ta saka mata dariya. Ta juyo zatai magana Ruky ta ƙyafta mata ido alamar karta kulata. Bako ta tanka ɗin ba ta wuce, itama Rukyn ta cigaba da kalle-kallen ta kamar ba'ai komai ba. Biebah data fahimci abinda sukayi sai taji tausayin Hanoon tayi kamata, dan wlhy tasan wata tsiyar zasu ƙulla mata ne, ga dai Afeef nan ya koma ɗangyasa ƙafa yau, baki yayi tumm na kumbura abin tausayi.        ★Tunda ta buɗe ƙofar ta shigo, wani ƙamshi mai ratsa zuciya ya daki hancinta, kasa haƙuri tai sai da ta wani lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Harga ALLAH tana son ƙamshi, dan ƙamshi duniya ne. Ɗakin ta fara bi da kallo bayan ta zube kayan sharar, babu wani tarkace sannan babu datti, sai saman gadon ne ma dake barbaje da takardu, sai laptop. Sannan daga study table ɗin da basu san sanda aka shirya shi ba an saka wani babban board fari, an mammana hotuna a jikinsa. Ba iya gane hotunan take ba, saboda an saka board ɗin sama sosai, hotunan kuma kanana ne kamar na passport.      Baki ta ɗan taɓe kawai zuciyarta cike da ƙananan tunani. Bayi ta fara shiga dan gyarawa, shima babu wani datti sosai, amma haka ta nutsu ta fara gyara komai yanda ya kamata. Dan-danan ya ƙara ƙyau da ƙamshi. Fitowa tai tana duba kayan ɗakin suma da tunanin ta ina zata fara, sake saukar idanunta a study table ɗinsa yasa ta nufi can ta fara, ƙananun abubuwa ta fara tattarewa, musamman su pens da flash drive masu yawa dake a saman study table ɗin. Ganin basu da wajen ajiya ta fita, ɗakinsu taje ta ɗakko wasu ƙyawawan baskets ƴan mitsi-mitsi na kaba da suka taɓa saya ita da Ruky. Sai kawai ta zuba masa flash drive ɗin a cikin ɗaya, hakama pens, makers suma, da pins, komai dai ta ajiye shi a tsare da ƴan uwansa ta jerasu a table ɗin bayan ta ɗaga ta goge komai na wajen har desktop ɗin. Ta koma kan mirror ɗinsa nan ma ta gyara turarrukan wajen tsaf da mayuka, harma da abubuwan da bata san amfani su ba. Tsabar son ganin ƙwaƙwaf sai ta buɗe wadrobe ɗinsa. Yanda kayan suke komai a tsare da muhallinsa sai abin ya birgeta, ta tuno tasu wadrobe ɗin ita da Buddy ɗinta dake a up side down kullum sai ta sheƙe da dariya. A fili ta ce, “Buddy na ALLAH ya ƙara mana hankali, muma mu dinga gyara wadrobe ɗinmu kamar haka”.       Gado ta dawo ta fara tattare takardun, kamar abin almara ta ma gama tattare su tas ta ɗora saman laptop ɗin data rufe tana shirin sauka a gadon dan hayewa tai ɗare-ɗare, kawai taja Duvet zata sauka da shi sai taga wani file ɗin a wajen. Ta ɗaga file ɗin batare data fahimci ta riƙe gefe ne ba sai kawai abubuwan dake ciki suka tarwatse mata a jiki. Harda hotuna.........✍️ 68 .........Cikin ɗan jin takaici ta furta, “Wayyo ji salon ƙara min aiki” Ta furta a hankali, tana ƙoƙarin fara tattaresu. A bazata taci karo da hoton Umman ta da shima ya faɗo daga cikin file ɗin. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, ta ƙurama hoton ido zuciyarta na hanƙoro, “Miya kawo hoton Ummana wajensa?” ta sake faɗa a fili tana fara ɗaukar sauran hotunan da suka kife tana birkitosu. Hotunan farko guda uku sojoji ne bata san su waye ba, sai dai a baya an rubuta sunan (Captain Musa, Ojo.... Da sauransu) sai a hoto na huɗu Kakanta ne cikin jini ga handcuffs a hannu kamar dai a video ɗin can data gani, banbancin kawai anan hoto ne. Koda tazo hoton bayansa jitai kanta na neman tarwatsewa, nan ma hoton Ummanta ne a cikin jini Daddy Imran tallafe da kanta shi kuma Dadan na tsaye da bindiga a hannu gefe ga wani mutum kwance da bindiga shima sai dai da jini jikinsa alamar an kashe shi ne. Hawaye masu zafi ne ke kwaranya a idanunta, ta ajiye hotunan ta fara buɗe file ɗin, bayan hotunan da bayanai masu yawa. Sunan ƙauyensu, sunan mamanta, sunanta harda hotonta tana yarinya, ɗayan hoton kuma tana ɗauke a hannunsa jikinta kaca-kaca da jini kamar tana barci ne  ma oho. Gaba ɗaya tai masifar birkicewa, musamman da taga har ma wasu hotuna da bayanai game da wani wai shi Dagger da abubuwan da suka shafi sunan wata ƙungiyar duhu. Bayanan sun mata tsauri da yawa, ba komai take iya ganewa ba, amma duk da haka bata ajiye ba ta cigaba da dubawa......          A bazata aka buɗe ƙofar ɗakin data sakata razana. Yanda ta zabura da sakin file ɗin, komai na ciki ya ƙarasa tarwatsewa a gadon. Ya saka Dada da bai san da ita a ɗakin ba tsayawa cak. Dan dawowarsu kenan daga massalaci shi ko zama a falon baiyi ba ya hauro sama. Koda yaga Ruky ita kaɗai a jikin Mammah sai da ya tambayi zuciyarsa ko ina twin ɗin tata, ashe tana nan ɗakinsa tana abinda bai san mizai kira shi ba.      Nimrah da gaba ɗaya ta gama birkicewa da ganinsa a bazata ga abinda ta gani takardun ta fara tattarewa da hotunan tana turawa cikin file ɗin kawai, ga hawaye sun kasa tsaya mata sai dai tana ta ƙoƙarin sharesu dan kar ya gani. Dada daya zuba mata ido takowa ya fara yi cikin ɗakin sosai batare da yayi magana ba har lokacin, wanda suka zubo ƙasa ya ɗauke, ya matsa da nufin ɗauke laptop ɗinsa da take neman hayewa ta firgita. Wani irin wantsalowa tai a gadon tare da wurgar da file ɗin a saman gadon ta nufi ƙofa. Sai dai yanda ta birkice ƙofar toilet ta nufa saɓanin ta fita. Nan ɗin ma dai da kallo kawai ya bita, shi yama rasa wane tunani zai yi akan yanayin nata. Ganinsa ne? Ko kuwa abinda ke cikin file ɗin ne?...       Tunaninsa ne ya katse sakamakon sake fitowa da tai a bayin alamar ta fahimci ba hanyar da take nema bace. Ta nufi ƙofar a yanzu. Sai dai anan ma ta gagara buɗewa tanata kici-kici da key kamar sabuwar marainiya. Kansa ya girgiza kaɗan, tare da ajiye hotunan hannunsa da takardu daya kwashe a ƙasa ya shiga takawa wajen ƙofar, tsayuwarsa a bayanta ya ƙara harmutsata, kici-kicin ta ya ƙaru, har tana neman buga kai da bango. Dan ta tafi gaba ɗayanta da nufin kifewa a jikin bangon ko zata samu sassaucin halin da take ciki.          A hankali ya lumshe idanun da suke neman juyewa ya sake buɗesu a kanta, kafin ya kai hannunsa jikin bangon dai-dai saitin inda ya tabbatar goshinta zai sauka, dan ya tabbatar yanda ta tafi gaba ɗayanta in har goshinta ya bugu bangon nan sai ya fashe. Nimrah ma ta gama sadaƙarwa harta runtse idanunta da ƙarfi, sai taji saɓanin saukar goshinta a bango ya sauka kan tattausan abu. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ce ta kufce mata, ta sake runtse idanun da ƙarfi. Yayinda can wani gefe na zuciyarta ke faɗa mata (Nimrah relax, wai mi kike yi haka? Bai kamata ki haukata kanki ba harya fahimta, ki tuna da zantukan mutumin daya baki videos ɗin nan mana).       Tasirin maganganun zuciyarta ya sakata fara sauke ajiyar zuciyar nutsuwa, ta shiga maimaita kalmar: ”لاَ إِلَهَ إِلاَّ الله“ “La ilaha illal-lah”. A hankali nutsuwa ta fara riskarta, numfashinta ya daidaita, ta haɗiye hawayenta tare da kai hannu ta share wanda suka jiƙa mata fuska. Jinta a takure tamkar an mata rumfa ya sata jan jikinta baya a hankali tana ɗagowa, abinda ya bama goshinta kariya ta fara kalla, zuciyarta ta harba da ƙarfi ganin hannun Dada, gashi kamar ta jingina da abu ta bayanta kuma, ai bama ta san sanda ta juyo da sauri ba, sai da kanta ya bugi ƙirjinsa kuwa saboda a yanda yake tsaye. Ta waro idanu sosai tana mannewa da bango, tare da duƙar da kanta tana ambaton ALLAH a zuciyarta.           Duk abinda take Dada bai motsa ba daga yanda yake tsayen tamkar ya mata runfa ma, ga hannunsa har yanzu yana a bangon bai cire ba. Sai dai ya zuba mata idanunsa masu kaifi. Kusan mintuna biyu suna a haka, Nimrah ji take kamar ta saki fitsari, dan yanda yake ɗin, gasu gab da juna, fuska a haɗe sai kace yana filin yaƙi. Rasa abin yi ya sata buɗe baki a karo na farko ta furta,         “Dan ALLAH Dada kayi haƙuri”.      Bashi da alamar zai tanka mata har shuɗewar wasu sakanni, kafin a bazata ya jefa mata tambayar data sakata ɗagowa ta kallesa da manyan idanunta da sukai ja saboda kukan da tayi da halin da take ciki, duk da tana ƙoƙarin shanyewa.         “Kinyi laifi ne?”.     Maimakon samun salama da kalmomin nasa guda uku ita wlhy sake hargitsata sukai. Sai kawai ta hau jinjina kai, kamar kuma wadda ta fahimci mi tayi, sai ta girgiza alamar a'a.         “Uhhm! Mi kike yi anan?”.     “Mammah!... Mammah ce tace nazo nayi maka gyara”.         Tai maganar idanunta na sake cikowa da hawaye, dan a yanda suke tsayen ta takura, da ace wani ne ba shiba da tuni ta hankaɗe shi ta wuce, kota kirashi da ɗan iska, ƙilama ta ƙara da zagin tsamar nama. Amma ina, shi wargi ma waje yake samu. Sannan ko kura tasan gidan mai babbar sanda....          “An saki aiki, amma kina min bincike?”.     Ba ƙaramin dukan ranta furucin nasa yayi ba yanzu ma. Sai kawai ta fashe masa da kuka da faɗin, “ALLAH Dada ni banyi maka binciken komai ba. A gadon fa na gansu zan ɗauke suka faɗi, shine nake kwashe wa”.        “Hy Kiddo! Nayi ƙarya kenan?”.    Nan ma kai ta shiga girgiza masa tana tura baki. Ga hawaye share-share da ke neman sakashi murmurshi yana dannewa da ƙyar. Handkachiff ya fiddo ya miƙa mata, ɗagowa tai ta kallesa da yanayin kamar mai mamaki.          “Na maida abuna ne?”.      Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. Sai ta samu kanta da tura baki, caraf kuma ta riƙo handkachiff ɗin da yake ƙoƙarin maidawa aljihu. Ƙin sakar mata yayi, cikin sake ƙasa da murya ya furta, “Ai na fasa, dama aro ne”.            Cikin shagwaɓa tana sake sakar masa hawayen da take maƙalewa ta ce, “Dan ALLAH”.       Lips ɗin data tura ga hawaye na shatata ya zubama idanunsa da sukai matuƙar shigewa ciki, ga launinsu ya canja matuƙa. A bazata taji saukar yatsansa a tsinin hancinta ya ɗan ɗalle shi.       Daburcewa ta nema yi, shi ko ya sake tsuke fuska yana wara mata idanunsa da faɗin, “Ni kike ma wannan shagwaɓan?”.         Itama sai ta waro masa nata idanun da faɗin, “Da... dahh!”.        “Uhumm Kid.... doo”.     Ya amsa mata da yanayin da tayi kiran sunansa. Ai da gudu kawai ta saki masa handkachiff ɗinsa ta juya baya ƙirjinta na wani irin motsi, dan gaba ɗaya ya juye mata kamar ba Dadan ba. Sai ta dinga jin ma anya ba mafarki take ba. Shi ma bai sake ce mata komai ba ya janye jikinsa a wajen. Sai ko data saki wata wawiyar ajiyar zuciyar data saka ɗan mitsilin murmushi kufce masa. ALLAH ya so shi ma ya riga ya juya ne bata gani ba, duk da koda kallonsa take ba lallai ma ta fahimci yayin ba. Sai da ya zauna akan sofa yana ciro wayarsa a aljihu, kallonta ya ɗanyi, tana a inda ya bartan tana faman cuɗa yatsu cikin juna, ya fara karantar wannan dabi'a tata ta cuɗa yatsu da har in tanayi akwai abinda ke damunta ko bata jin kanta free a inda take.      “Zo ki ƙarasa aikin ki”. Ya faɗa yana cire hular kansa da kwantar da bayansa da kan jikin kujerar ya lumshe idanunsa kawai. Simi-simi Nimrah ta tako bayan ta saci kallonsa, a yanayin da take ciki da ace ba shi bane ALLAH bazata iya ƙarasa aikin nan ba, dan kaɗaici tafi buƙata a yanzu. Tunanin take son yi, so take tai nazari akan abubuwa masu yawa. Tana ganin a yau kuma dole ta yi ƙoƙarin kiran mutumin nan, amma sai ta duba saƙon ƙarshen nan daya bata a randa sukai haɗuwar farko kuma ta ƙarshe da shi kafin taga idan ya dace suyi wayar. Tambayoyi take son yi masa, wanda da ace zata iya Dadan zata yima su, sai dai yi masan tamkar ganganci ne. To taya zata bama kura ajiyar nama, daga shi har Daddy Imran a yanzu zuciyarta rawa take a kansu. Idan ba rami miya kawo rami to?...........✍️ 69 .......Duk tana aikin tattare takardun data watsar da kanta ne tana wannan tunanin, yayinda take jin idanu a kanta, idan ta saci kallonsa kuma sai taga idonsa a rufe suke shi kam. Haka ta daure da ƙyar ta kammala har gyaran gadon. Ta kalli tsintsiyin shara ta kalla inda yake, a mamakinta sai taga ya maida ƙafafunsa saman table. To kenan yana kallonta, tunda har ya fahimci yanayin ta. Nan ma sai taji ta sake daburcewa, ta dai danne da ƙyar ta fara sharar dan gara tayi-tayi tabar ɗakin nan kafin zuciyarta ta fita waje.       Sauri-sauri ta kammala ta hau mopping, turaren wutar data shigo da shi na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ta zuba a bonner ta kunna socket. Cikin sanɗa ta nufi ƙofar zata fita a tunaninta ko yanzu barcin gaskiya yake yi, duk da tana ji a jikinta ana kallonta, amma ita shari'a ko'a gaban alƙali ai sai da hujja, a yanda yake ido a rufe ita kam bata da hujjar cewa shine kenan.         “Zonan”.     Cak ta tsaya tana mai runtse idanunta da ƙarfi. A zuciyarta ta furta (Na shiga uku na). Yanda bai sake maimaitawa ba, ya sata juyowa dole....          °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°   “Wai halan zaka je wani wajene? Naga kanata sauri Abban Jiddah”.          “Juwairiyya da neman magana kike, kina duba lokaci kuwa? Nafa gaya miki zan raka Baffa ɗaurin aure, kuma da'an sakko massalaci ne dai-dai. Kalla agogo yanzu ƙarfe nawa? Gashi ko wanka banyi ba. Kuma da ƴar tafiya ba'anan cikin gari bane?”.        “Yi haƙuri na shafa'a ne gaba ɗaya, tunda dana tasheka ai tun ɗazun. Dan ko yara da zasu wuce makaranta sai da sukai cigiyarka.”         “Karsu damu idan na dawo ma gaisa. Ita wannan bata dawo gidan ba har yanzu?”.             “Wlhy kuwa, ni hankalina yama fara tashi”.      “Miye abin wani tashin hankali tunda kin san ina ta tafi. Dama kece ai kika dage, amma ni nasan yaran nan bazasu taɓa canjawa ba, uwarsu ta riga da ta ɗorasu akan wani layi da yayi tasiri a tare da su”.           “Kayi musu addu'a, kuma yau zan bincika dai duk da na kira wayarta yafi sau nawa bata shiga. Zan kira Jiddah taje gidan maman nasu ta bincika.”      Baki kawai Uncle Nasiru ya taɓe yana miƙewa abinsa. Itama sai bata sake masa magana ba tabi bayansa dan haɗa masa ruwan wanka. Ta kammala ta sake fitowa tattare kwanikan da yaci ɗumamen tuwon a dinning ta tadda baƙuwar bazata. Ba kowa bace face Hajiya Hasiba. Tayi wani zaman ƙasaita ɗan ƙwali agaban goshi. Duk da Ummu taji bugawar zuciya da wannan ziyara ta bazata sai ta hau ambaton ALLAH kafin ta ƙaraso falon. ALLAH ma yaso ta cikin kwalliyarta take fes Masha ALLAH. Ga ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Na tashi, dan shine tun daga kabasa har cikin gidan dama su khumra data saka. Ba Ummu ba itama kanta Hajiya Hasiba sai da gabanta ya faɗi, dan Ummu ta fita yarinta, ga nutsuwar zaman gidan aure bashi dai-dai da mata irinsu gantalallu da ba'a nan ba'a can kullum. Shi kansa ƙamshin nan ba ƙaramin rikita mata lissafi yay ba. Ta dai daure ta haɗiye tana wani yamutse-yamutse.        Murmurshi Ummu ta saki da faɗin, “Oh manyan baƙi ne damu haka a gidan? Barka da zuwa”.      Wani kallon banza Hajiya Hasiba tai mata ta watsar, sai kawai Ummu tai murmurshi da komawa sabgar gabanta, dan irin mutanen nan ne ita marasa ɗaukar wulaƙanci, zata baka girma fa dan girma, dan wani lokacin ma sai ka ɗauka kamar bata san ciwon kanta ba, amma data fahimci daga wane jinsin hali ka fito tofa zata nuna maka ta fika iya kalar hali naka. Aiko bata sake bi takan Hajiya Hasiba ba ba harta kammala sabgarta. Koda ta kintaci lokacin fitowar mijinta wanka yayi sai ta koma ɗakinsa.      Bata faɗa masa yayi baƙuwa ba ta hau taimaka masa ya shirya suna hirarsu cike da nishaɗi. Zuwa can sai gasu sun fito suna dariyarsu Hajiya Hasiba ta gama cika, ai ko sai dariyar tasu ta sake kunnata matuƙa. Shi Uncle Nasirun ma bai lura da ita ba sai da taja tsaki sannan ya waiwaya inda take. Nan ma ido ya ɗan zuba mata kamar wani makaho. Kafin ya juya yana kallon Ummu da faɗin, “Wai wacece haka zaune kuma Juwairiyya?”. ★✨★✨★✨★✨★ Sum-sum Nimrah ta koma kamar munafuka ta ƙaraso inda yake, cikin ƴar bada tazara a tsakaninsu ta kai zaune saman tattausan milk carpet dake gaban sofa ɗin da yake zaunen. Sai dai bata yarda ta kallesan ba dai. Shima bai gyara zamansa ba, a yanda yaken kuma a haka ya cigaba da kallonta, har ita da kanta taji kallon ya mata yawa ta ɗago a hankali ta saci kallonsa. A mamakinta yana a yanda yake idanun a rufe kamar yanda ta gani, bata san ta ƙasa-ƙasa yake kallon ba musamman saboda kansa kwance yake a jikin kujerar. Samun kanta tai da shagala a kallonsa. Kallo irin wanda bata taɓa kwatanta masa ba. To inama taga fuskar yin hakan.      Dada yana da ƙyau, irin ƙyawun da aka san baƙaƙen fata ƴan ƙasar nan tamu kuma yankin mu da shi. Sosai ta fahimci kamaninsa da Ammar da Aunty Ummi, kawai dai yafi su Ammar hasken fata ne sosai, duk da suma dai sauran yana kama dasu amma yafi yi da Ammar ɗin da Mamy ɗin gaskiya. Gashi dai duk ance ya girma kowa a gidan, amma jikinsa mai ƙyau ne, dan irin ƴan gayun matasan dattijan nan ne masu matuƙar kula da jiki da son gyara....        Ta matuƙar shagala a kallonsa har bata san ya motsa ya gyara zamansa ba ma. Sai da yay gyaran murya tai firgigit ta dawo hayyacinta, sai kuma ta kama sosa wuya na borin kunya. Basarwa yay kamar bai fahimci halin da take ciki ba, sai ma tambaya daya jeho mata.           “Ta ya kuka san yaron yama wata fyaɗe?”.       Ɗiff ta ɗanyi na sakanni, kafin ta saki numfashi da ɗagowa tana kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba ta sake maida kanta tana ɗan tura baki. Sai kuma ta ce, “Dada!”.         “Uhumm”.     Ya amsa mata yana danna waya. “Ni da Ruky mun san abubuwa da yawa a makarantar nan kawai bama faɗa ne.”         Biye mata yay ya ce, “Uhmm-umm manyan yara ne ku kenan? Ta ya kuke sani?”.      Ajiyar zuciya ta sauke duk da ɓoyayyar damuwarta a kansa na nan a ranta bata gushe ba, to amma ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi ne. Dan haka ta fara jera masa zance.          “Wanda ke son ƙawance da mu ne ke faɗa mana. Wani kuma mun sani ne dan muna gani. Suma fa malaman inaga dan suna jin tsoron students ƴaƴan masu ƙuɗi ne, kada a daina biyan kuɗin school fees ɗin su halan. Amma makarantar nan freedom yayi yawa, shiyyasa kaga mun zama jan wuya, dan mun gane ƙarfin, shike ƙwatarka kawai. Duk wanda ya mana sai mun masa. Shi shegen yaron nan ya jima yana abubuwa, dan dasu aka buɗe makarantar wai, gashi da ƴammata da yawa, haka zaita haɗasu faɗa wai shi namiji, ko ina mazan suke?....”        Yanzu kam kaɗan ya rage dariya ta kufcema Dada ya dai daure, jifa wai ƴar yarinyar nan har ta wani san maza da wanda ba maza ba. Kai jama'a ƴar amana ta girma...     Ita ko da bata san tunanin da yake ba ta cigaba da baza masa zance hankali kwance, har ma da abinda bai tambaya ba, shi ko yana recording. Tun yana basarwa har ya zuba mata idanunsa da sukai wani kalar laushi da ƙyalli-ƙyalli kamar ruwan kogi mai irin light blue ɗin nan na motsi. Kamar an kaɗa mata ƙararrawa ta farga da yanda ya zuba mata ido, sai ta tura baki cikin suɓutar baki da manta a gaban wanda take ta ce, “Dada banda kallo”.       Samun kansa yay da faɗin, “Mi yasa?”.           “Babu ƙyau ne ana ganin munin mutum”.     A zuciya ya furta, (childish) a fili kam sai ya samu kansa da furta, “Ke mummuna ce?”.        Hannu takai ta shafa fuskarta, sai kuma ta taɓe baki da girgiza kai alamar a'a. Sannan ta ce, “Hummm ai mutane suna cewa farare sunfi baƙaƙe ƙyau. Wasu fa har zagi suke da kalmar baƙar banza, ko irin dai hakan, wasu kuma da shafe-shafe ne, idan zaka bayyana tasu halittar sai ka gudu dan muni. Amma idan muna ganin ƴan comments na media a wayar Small Mom zakaga masu aibanta halittar mutane kamar ALLAH abokin wasan su ne. Ai naga shine dai yayi halittarsa, kuma mutum ko cinnaka babansa ma bazai iya yi ba balle shi. Amma jahilci da daƙiƙanci na damunsu. Idan kuma kace musu jahilai sai suce suba jahilai bane. Shifa jahilcin mai karatu yafi na jahili muni. Dan ILIMI DABAN, KARATU DABAN.”         A wani kalar slowly ya lumshe idanunsa dake neman fallasa sirrin zuciya. Ya haɗiye wani busashshen yawu daya saka maƙoshinsa yin sama ya dawo da sauri. A ƙasan zuciyarsa kam ayyanawa yake (Idan na biye abar nan ba gajiya zatai da zance ba) a zahiri kam buɗe idanun yayi a kanta, tsabar rashin man kai yasa ɗiyar ga bata gane komai da yanayinsa ba, koda yake banga laifinta ba, dan fuskar dai a tsume take kamar yanda suke ganinta kullum, sannan a zaunen ma a kamenwar sa yake cike da ƙasaita, launin idanun ne kawai suka sauya kamar abinda ke cikinsu zai amayo kansa. Haka ma muryarsa ta shaƙe tamkar mai mura. Dan ko kalmar ƙarshe daya furta da ƙyar ya iya fisgota.         “Kiddo tashi kije.”     Dama a takure take, kawai dai surutun ne baki ya riga ya saba. Ko'a wane hali sai an furta. Yanda ta nufi ƙofa da sassarfa ya tabbatar masa dama hanyar fitar take nema. Sai kawai ya runtse idanunsa yana ambaton ALLAH dan shine kawai mafita..... Itama data fito yanda ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tana kallon ƙofar ɗakin ya saka Imran dake haurowa hannunsa da kaya tsayawa kallonta. Kusan mintuna biyu kafin ta juyo da nufin barin wajen suka haɗa idanu. Da sauri ta haɗiye yanayin nata tace, “Daddy sannu da zuwa”.        Shima haɗiye nasa mamakin yayi ya amsa mata da, “Yauwa Daughter dama kina nan?”.         Sai da ta ɗan tura baki gaba da shagwaɓa ta ce, “Mammah ce tace nazo nayi shara”.      Murmurshi yayi da faɗin, “To ALLAH ya bada lada. Dadan naku fa?”.         “Yana ciki”........✍️              70 ........Shigowar Imran baisa ya buɗe ido ba, dan tunda Nimrah ta fita yana a yanda yake bai motsa ba. Sai dai ya zubama ƙofar data maida ta rufe idanu, shiyyasa a kan idonsa Imran ya shigo. Ganin haka yasa Imran nufin tsokanarsa.         “Ikon ALLAH ashe kana ciki! Shiyyasa naga yarinyata ta fita a birkice. Alhajin ALLAH mi kai mata ne?”.       A mamakinsa yau kam murtani ya samu, dan cike da gatse Dada daya buɗe idanun sa da suka canja launi yana harararsa ya ce, “Abinda zuciyarka take tunani”.       Dariya Imran ya fashe da ita yana kaiwa zaune da faɗin, “Naga tabbacin a idanunka kam haƙun. Haba Suger Daddy ai ka bari na baka ita tukunna”.           “Kai dai ALLAH ya kimtsa wannan gurɓataccen tunanin naka”.     Dada ya faɗa yana sauke ƙafafunsa ƙasa da miƙewa ya shige bathroom. Shi dai Imran dariyarsa yake da cigaba da tsokanarsa. A haka bayan wasu mintina kusa goma sha ya dawo ya zauna inda ya tashi batare daya tanka masa ba....       ★A ƙasa Nimrah na sakkowa Mammah tace mata ta ɗauki abincin Dadan ta kai masa gashi nan an haɗa. Da lafiya-lafiya ne sai ta shagwaɓe fuska. Amma yanzu sai kawai ta jinjina ma Mammah ɗin kai bayan ta gaida Uncles ɗin nasu da surutunsu ya cika falon. Babu Ruky babu Small Mom da Mamy ma. Hakan yasa ta ɗauka abincin salin alin ta juya ta koma saman, har Mu'azz na gulmarta da faɗin, “Oh yau su Ninah anyi hankali”.       Dariya su Ammar sukayi, Bilal ya ce, “Daina yabon ɗan kuturu, dan dai aikin Dada ne kawai, amma Ninah da son jikin tsiya. Ruky ta fita son aiki”.       “Itama in bata jin tsiyarta ba”.    Cewar Ammar. Nan ma dariyar sukayi. Dayyan da Afeef dai basu tanka ba. Dan har yanzu cike suke da Nimrah da Ruky a rai...       __     Nimrah data dawo sama kuwa ta ɗan tsaya kamar mai nazari kafin ta ƙarasa gaban ƙofar, nan ma sai da ɗan yi shiru na sakanni sannan ta kai hannu zatai knocking. Amma sai ta tsaya cak sakamakon furucin Daddy Imran.        “Kana nufin taga komai dake file ɗin Zak...?”      Sai da wasu sakanni suka shuɗe kafin ta jiyo Dadan ya bashi amsa da, “Ta gani, dan baje-baje na taddata da su a gadon nan, nasan kuma a haɗe na barsu cikin file ɗin daka kawo su. Naga tana kuka, sai dai ban fahimci dalilin yinsa ba, saboda bana jin akwai abinda zata fahimta”.          “Hakane, babu dalilin ta na fahimta, sai dai ina tsoron karta gane hoton Mamanta da Babanta dana tsohon nan da nata ma. Dan kasan a shekarun baya ta taɓa ma Mammah tambayar data saka ta sanar mata Mamanta ta rasu da babanta, na tabbatar wayonta bazai sa ta manta da hakan ba kuma, kuma bazata manta da fuskar mamanta ba. Ya rabbi, ALLAH yasa bata fahimci komai ba ɗin dai. Dan bana son a yanzu Nimrah tasan abinda ya faru a baya har sai mun kammala project ɗin nan, shiyyasa ma ko batun aurenka dake kanta muka ɓoye mata”.           Ƙirjin Nimrah yay wani bala'in bugawa, har bata san ta furta kalmar,  “Aure?!”. a lips ɗinta ba. Yayinda kalaman Daddy Imran ke mata wani kalar amsa kuwwa a cikin kunne da ƙwaƙwalwa. (Basa son ta san komai har sai sun kammala project ɗin nan? Ke nan ta tabbatar Dada nada alaƙa da mutuwar Ummanta ko mi? Idan ba haka ba miyasa zasu so karta sani to? Wane project ne haka? Sannan waye ma keda aure? Wa kuma ake aure?).      Babbar bala'i, wannan wace irin rana ce a gareta? Mike shirin faruwa?. Wlhy ta gagara gane komai fa....          “Imran ina son zan sai gida a anguwa mai ƙyau, dan aikin nan bazai yiwu anan ba. Yaran nan basa ji, na tabbatar kuma zasu cigaba da shigowa ɗakin nan musamman ita, idan na adana wani abun wani zan iya mantawa na bari ta cigaba da gani”.      Furucin Dada ya katse mata tunani. Amsar da Imran ke bashi yasa ta ƙara kanga kunne.         “Nima nayi tunanin hakan gaskiya, ya kamata ace kana da wani privete place kodan ma yanayi tsaro, kaima hakan zai baka damar yin aikin batare da damuwar komai ba. Sai dai yanzu sayen gida zai iya jan hankalin masu biye da lamarinmu”.        “To ya kake so ayi?”.     “Gashi ka duba cikin waɗan nan gidajen namu ko akwai wanda yay maka”. Imran yay maganar yana miƙa masa wayarsa.       Maimakon Dada ya amsa wayar sai ya zuba masa idanu. Cikin ɗan waro idanu Imran ya ce, “Wai kallon fa?”.         Kauda kai Dada yayi, sai kuma ya amshi wayar da faɗin, “Kana nufin har yanzu kana wannan business ɗin?”.          Cikin ƴar dariya Imran ya ce, “Zak.. nawa, to mi za'a fasa. So nake ma ka ƙara nutsuwa na maka bayani akan yanda abubuwa suka ƙara bunƙasa, dan cikin watannan zamu fara fitar da ayyukan gine-gine kai tsaye daga kamfanin SAMRAN in sha ALLAHU.”        Dada ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, yana kallon hotunan gidaje tunaninsa na komawa baya, lokacin da Imran ya matsa su haɗa kuɗi su fara sayen filaye suna sayarwa, a lokacin gidan nan ɗaki biyu ne zagaye da langa-langa, ga albashinsu bai taka kara ta karya ba, ga biyan kuɗin makarantar su Ma'aruff, ga halin baƙin ciki da Mammah ke ciki akan abinda ƙaninta Tasi'u ya aikata mata da mahaifin Biebah. Yay gajeran murmurshi daya saka Imran ma murmusawa. Dai-dai nan Nimrah tai knocking ƙofar jin basu cigaba da zancen ba. Ga ƙafafunta sun fara nauyin gagara ɗaukarta, sai ta yanke shawarar kawai basu abincin ta fita ko zata samu filin yin tunanin abinda ke faruwa da rayuwarta itama. Dan tana ji a ranta addu'ar data dage da yi ce yau UBANGIJI ya fara warware mata gaskiya...      Buɗe ƙofar da Imran yayi ya sata dawowa hayyacinta, tai murmurshin yaƙe da faɗin, “Daddy abinci ne in ji Mammah”.       Murmurshin ya mata shima da bata hanya alamar ta shigo. Kallo ɗaya taima Dada daya canja rigar shaddarsa zuwa baƙar t-shirt data kama jikinsa sosai ta kauda kai, duk da wandon shaddar na nan shi bai cire ba. Shi ko ko sau ɗaya baima kalla inda take ba, hankalinsa nakan waya gaba ɗaya. Ita dai tana ajiyewa ta fito abinta... >>>>>>>%<<<<<<<         Dariya taso kufcewa Ummu, amma dai ta daure ta gimtse, sai itama ta ce, “A ina kenan?”.          “Oh kema baki san da mutum ba ma ashe?”.     Uncle Nasiru ya faɗa da iya gaskiyarsa. Zaram Hajiya Hasiba da ke jin kamar zuciyarta zata kama da wuta ta ce, “Aikin banza aikin wofi, to sai me daga hakan? Shi daya ajiye ki bai isa bama balle ke sha-sha-sha kawai. Kai kuma Nasiru nazo maka gargaɗine akan saƙon daka aika Ismat ta isar min, ta isar da shi dalla-dalla, sai dai ka sani idan kace zakai wannan wasan da ni zaka faɗi ne ƙasa wanwar wlhy. Ai na faɗa maka ka manta ka taɓa haihuwar wasu yara a baya ko? Idan ba haka ba kuwa zakai kuka da idanunka. Idan ba jaraba da masifa ba yara sunce uwarsu suke so amma sai bibiyar su kake yi. Ka aurar da biyu an sakani na ƙyaleka shine itama Ismat kake yaudararta kai mata yanda kai musu. Ita kuma Nabeeha ka maidata gidan waɗan can faƙirin faƙara'u ɗin da basu ajiye ba basu ba wani ajiya ba jinin talauci da gallafiri. To wlhy ahir ɗinka, aniyar moɗa tabi randa. Dan Nabeeha tabar Haysam har abada kenan, yaje ya zauna da tsintacciyar magen daya kawo. In ce dai shike nan ai ko?. Kuma......”         Cikin katseta Uncle Nasiru ya girgiza kai kawai yana kallon matarsa da faɗin, “Juwairiyya kinga nikam nayi nan. Ga kiran Baffa nan na shigowa. Ai min dambu fa kar a manta, yaji gyaɗa sosai da man kyaɗa da zogale. Sannan ayi abincin dare da Haysam dan yace zai shigo, ban sani ba ko shi kaɗai ko da su Ja'afar ne”.         “Ba damuwa duk za'ayi Abban Jiddah, ALLAH ya tsare ya kiyaye hanya. A gaida Hajjo da Baffan”.     “Zasu ji, a gaida yara idan sun dawo, Imam ya ɗauka motar nan ya kaita service yau kar yace min ya manta”.         “In sha ALLAHU”.    Ummu ta faɗa tana masa murmushi. Da alama tun fara maganar tasu Hajiya Hasiba tai kamar wadda tai sumar tsaye, ganin sun manna mata hauka. Har Uncle Nasiru ya fice bata farfaɗo ba, sai da ya maida ƙofa ya rufe. Ai wata ashariya data mulmulo Ummu bata san dariya ma ta kufce mata ba, ta dai samu ta shige cikin bedroom abinta ta sake mannawa Hajiya Hasiba hauka. Ai ko ta haukace ɗin, dan zage-nage ta dinga jerawa kamar wata ƴar tasha, lamarin sam babu aji a ciki dai zattakaici. Nan kuma da za'a taɓata sai tace ita mace ce mai aji manyan mata, ke ko ta kusa da matar tsohon shugaban ƙasa ai ba'a magana. Surukar Adeel ɗan Larabawa jinin masarauta, ga kuɗi.........✍️ Gaskiya ya kamata mu fara girmama Hajiya Hasiba, ita kuma Ummu ta fita sabgar ƙawar Zainabu ehe.😜🤭🥱... 71 .........Nimrah kam maimakon komawa falo ɗakin su ta shige, ta dannama ƙofar key tana sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin Ruky bata ciki. Kai tsaye wadrobe ɗinsu ta nufa, can wani lungun wadrobe ɗin data san hankalin Ruky zai daɗe bai je ba ta zaro abinda Dagger ya bata watanni biyu da suka shuɗe. Ƙasa ta zauna share-share ta zazzage. Hotuna suka faɗo. Hoton farko data fara cin karo da shi shine hotonta, kuma abin mamaki exactly irin wanda ta gani a ɗakin Dada yanzu. Sai dai na nan ma biyu ne, ɗaya tana a cikin kwalla, ɗaya tana a hannun Dadan jikinta duk jini. Hoto na biyu Ummanta durƙushe tana kuka a gaban Dada, akwai sojoji kusan biyar tare da shi. Ɗayan sojan shima taga hoton shi a ɗakin Dadan, an rubuta Captain Musa, sai wanda ke gefen haggunsa yana miƙa masa bindiga shi kuma Ojo taga ansa a nashi hoton acan ɗakin Dadan dai. Sauran hotunan ta cigaba da bi ɗaya bayan ɗaya, mabanbanta fuskoki, yara da manya, harda Iya kakarta. Wasu kuma sai ta jima tana kallonsu ma dan ta manta suna, amma kuma duk a hankali take ta faman tuna su wanene. Dan duk da akwai ƙuruciya a tare da ita bazata manta ƴan gidansu ba, musamman Iya da Kawu Tanimun ta, da abokan wasan ƙasa su Lawwali.       Ai bama tasan ta fashe da kuka ba, dan abubuwa ne ɗai-ɗai ke dawo mata a rayuwarta da Kawu Tanimu a ƙauyen su. Ta jima a wannan yanayi na kuka kafin ta share hawayenta, zuciyarta na tabbatar mata yanzu ba lokacin kuka bane, lokacin nutsuwa da bincika gaskiya ne, lokacin daya kamata tasan ainahin wacece ita ne? Lokacin gane waye Dada waye Daddy Imran ne? Lokacin sanin kalmar nan da tafi kowace kalma mata girma ne, wato kalmar data fita a bakin Daddy Imran. (Aure) Ta kasa fahimta sam, auren waye? Sai da taji kamar Daddy Imran yace ita da Dada. (kai ina bataji daidai ba ne) Wani sashi na zuciyarta ya faɗa. Sai taji ta gamsu da hakan.      Miƙewa tai ta tattare komai ta maida inda yake. Duk da fargabar dake manne da zuciyarta. Amma ta fara tunanin yadda zata sarrafa sirrin da ta tsinta yau a zuciyarta, ta fara fahimtar cewa mahaifiyarta ta kasance cikin wani babban labari, kuma akwai haɗari da zai shafi rayuwarta. Akwai ɓoyayyen al'amari daga zuriarta da tushenta da ake ɓoye mata kuma ya kamata ta sanshi. Sai ta ɗan yi murmushi mai ciwo, tana tunanin yadda Mammah zata ji idan ta san ta tsinci wannan. “Yanzu ya kamata in fara tunani… amma yadda zan yi, ba komai ba ne.” ta faɗa a zahiri hankalinta na sake komawa akan hotuna da videos ɗin baya masu gogayya da juna. Tabbas duk abin da ta gani, yana haifar mata da tunanin cewa lokaci ya yi da zata fara fahimtar gaskiya da kuma ɗaukar mataki. Sannan dole tai amfani da wayonta akan Dada, ta cusa kanta jikinsa cikin hikima ko hakan zai sa taga fiye da abinda ta gani a yau, sannan tasan ainahin waye shi, ainahi fuskar da yake ɓoyewa da ƴan uwansa basu sani ba. Daga yanzu WASAN YA FARA......        Da wannan ta shiga bayi ta wanke fuskarta tayo alwalar la'asar da ake kira. Koda ta fito gaban mirror taje ta canja kwalliya sannan ta shimfiɗa abin salla. Dai-dai nan Ruky tai knocking ƙofar, buɗe mata tayi. Ruky na shigowa ta rungumeta cike da farin ciki tana faɗin, “Albishirin ki Ninah?”.      Cikin dauriya Nimrah dake murmurshi ta ce, “Goro”.            “Ammy haihuwa zatai”.      Idanu sosai Nimrah ta waro waje da faɗin, “Haba dai?”.     “Wlhy, gata can ma zasu tafi asibiti. Tun ɗazun na ƙagara ki gama gyara ɗakin Dada ki sakko ai. Mammah ma bata sani ba sai yanzu. Ni da Small Mom da Mamy kawai muka sani dan muna sashen tun ɗazun.”      Duk da damuwar da Nimrah ke ciki hakan bai hanata nuna farin cikinta ba. Salla sukai suka fito. Zuwa lokacin mazan gidan ma sun san halin da ake ciki. Dan har an wuce da Shariffa asibiti.        Da wannan damar Nimrah tai amfani wajen zare jiki ta nufi gate, cikin sa'a ta samu Sanda kawai zaune maigadi ma salla yake, da alama sallar la'asar ce baiyi ba duk da ba'a jima da kammalawa ba.      ALLAH ya sota, tana amsar wayar ta zagaya baya Dada da Imran da suka dawo salla na shigowa gidan, wuff Sanda ya shige bayinsu yana danne ƙirjin sha da ƙyar, dan yau kam ALLAH ne ya yabawa aya zaƙinta da sai anyi kaciɓus tsakaninsa da Dadan, duk da ba Dada kawai ba shi fa har Imran wasan ɓuya yake da shi daman. Shi kuma baima san Imran bai taɓa wani maida hankali a kansa ba.       Number ɗin nan ta saka na wancan karon dan ta kasa mantawa da su. Sai dai har wayar ta tsinke ba'a ɗaga ba. Addu'a ta fara yi a ranta tana sake kira. Yanzu ma sai da ta kusa tsinkewa a ka ɗaga. Jin waccan muryar dai da bazata layance mata ba ta sata sauke ajiyar zuciya. Duk da Dagger a ƙage yake da wannan kira na Nimrah tsahon wattani biyu hakan bai hanashi yi mata na ƴan duniya ba. Dan maimakon amsa gaisuwar ta bayan ta sanar masa ita ce sai cayay,           “Lafiya kika kirani?”.        Duk da taji haushi sai ta danne, maimakon masa rashin kuwa sai ta furta, “Kayi haƙuri, sai yanzu lokacin dazan iya kiran naka yayi. Ina son mu haɗu da gaggawa dan ALLAH”.        “Bani da wannan lokacin, dama na gaya miki zan iya ɓace miki ai. Yanzu ma sa'a kika ci na ɗaga wayar ki. Kuma yanzu zan kashe.”       “Dan ALLAH kada ka kashe. Sannan karka manta kai ka ɗora ni a wannan hanyar daban san da ita ba, bai kamata kai walagigi dani a lokacin da nake son sanin sirrin ta ba da taimakon ka. Ni mai rauni ce a yanzu, sannan makauniya dake buƙatar koda sandar jagora ce. Na maka alƙawarin bazan sake wasa da damar da zaka bani ba”.        “Shike nan naji, zanyi haka ne kuma kawai dan Ummanki data bani amanar faɗa miki gaskiya a duk lokacin da kika kai minzalin girman ki. Sannan ta bani wasu sirrika na baki. Ban baki da farko bane, sabo da ina son auna hankalinki da yardarki gareni. Yanzu sai ki faɗi ina zamu haɗu”.       “Na gode sosai. Sai dai kamar yanda na faɗa maka a baya ba'a barina fita ni kaɗai, sannan a yanzu gidanmu zagaye yake da jami'an tsaro saboda dawowar mutumin dake cikin video ɗin nan. Idan suka ganka zasu zarge ka ko kazo cutar da shi ne, dan saboda shi aka ajiye su......”         Wani mugun girgiza zuciyar Dagger tayi, kaɗan ya rage yawun bakinsa ya biyo masa ta hanci tsabar yanda kalmar Nimrah ta dake sa. Da rawar lips ya maimaita, “D...awo wa...?”.       Ɗan jimmm Nimrah tayi, sai kuma tace, “Eh mana, ba shugaban ƙasa ya masa afuwa ba? An fiddo shi ko ka manta ne?”.         “Haka ne! Haka ne! Na manta ne sam, kin san abubuwan yawa suke”.     Duk da yanda yayi ɗin ya ɗan sake taɓa zuciyar Nimrah da bata mamaki sai ta share kawai. Ta ce, “Ka bani nan da mintuna goma, akwai mamanmu zata haihu suna asibiti, idan an yarda muzo zan kiraka da wannan layin, dan zan riƙe wayar a wajena sai mu haɗu a cikin asibitin”.        “Shike nan ba damuwa, sai na jiki”.     Ya faɗa daga can wasu jerarrun zufa na yanko masa ta ƙofofin gashin jikinsa gaba ɗaya. Ita ko da bata san yanayi ba wayar ta yanke tana barin wajen. Koda ta fito maimakon zuwa gate ta bama Sanda wayarsa sai ta wuce ciki kawai.... +++++++++++++      “Tabbas gaskiya mutumin nan ya faɗa Oga, Zak-Shadow na cikin ƙasar nan, a cikin gidansu. Kuma a ƙalla sati guda kenan yake cikawa. Kaga kenan kwanaki huɗu kacal tsakani da sanar da afuwar shugaban kasa. Wato mutumin nan lallai ya masifar raina hankalinmu. Dan a majiya mai ƙarfi na samu tabbacin Zak-Shadow yafi wata biyu da barin prison, a ƙalla satin da ya fara shiga office ya fitar da shi.”       Gaba ɗaya Oga Jush yama gagara iya cewa komai saboda yanda zancen yay masa dukan tasar ruwa a kai. Shin Yusuf Tafida ne ya raina musu hankali? Ko yaran da suka zagaye ko'ina a ma'aikatun ƙasar ne suka maidasu wawaye jahilai?. To lallai lokaci yayi da sabon wasa zai tashi, badai sai sun bari ayi mulkin lafiya ba. Daga shi Tafidan har Zak-Shadow ɗin zasu ɗanɗana kuɗarsu ne. Batare daya tofa komai ba akan batun ya bama Iron Fang umarnin sanar da meeting, ko ina kake kuma dole ka dawo ayi wannan zaman dakai, ba'a buƙatar kowa ya kiran waya ko video call. A zo kawai..        Iron Fang yasan oga ya ɗau zafi, sai kuma abinda ALLAH yayi, dan dole itama ƙasa ta ɗauki zafi a wannan gaɓar, zafin daya tabbatar muninsa sai yafi na baya girgiza kowa. Bai musa ko ja da nisa ba ya rubuta text message ya turama kowane member na ƙungiya. Shima ya kaɗa kansa ya tafi tashi sabgar sa........✍️       72 .........Gaba ɗaya gidan Mammah ya hargitse da farin cikin saukar Shariffa lafiya. Bakin Uncle J kam har kunne. Suka rungume juna shida Twinyn sa. Bilal da Ammar ma suka haɗasu suka rungume. Dole suyi farin ciki zuri'arsu nata ƙara yawa da faɗi. A take sukai kiran Mammah suka sanar mata, dan tana gida bata bisu asibiti ba, sai ma su Nimrah ne dake ta damunta suje-suje?.       Da farko ta hana su ne, dan bata son su tafi su barta ita kaɗai a gidan, dan Dada da Imran sun fita. Su Kulu kuma yau juma'a sun tafi gida su gaisa da mutane kamar yanda sukeyi duk bayan sati biyu. Su Dayyan kam sai a hankali, dan zatace ma tun bayan dawowa massalaci ta sake ganinsu ba. Garama Hanoon uwar son kallo da tana maƙale da tv kafin ta tashi itama ta shige.          Hankalin Nimrah a rabe yake, ga farin cikin samun ƙaruwa da sukai ga lamarin son haɗuwa da Dagger. Ta tabbatar idan su Ammyn suka dawo gida ba lallai ta samu wata dama ba kuma balle suna hutun tahfiz ma gobe babu, dan cikin satin sama za'ai bikin saukar ƴan ajin sauka su su maye gurbinsu. Duk da suma dai saura ƙiris ne fa. Kawai dan makarantar nada ƙa'idar bin komai daki daki ne.     Ganin yanda suka dage Mammah tace su duba idan driver na nan, idan baya nan sai dai su haƙura kam, tunda yanzu suma zasu dawo kasancewar an haihu lafiya asibiti bazasu riƙesu ba.      Nimrah tafi kowa zumuɗi, kasancewar tata fitar da manufa biyu ne. Koda Ruky taje ta duba sai gata ta dawo baki a sama. Wai Malam Buba ya fita. Kaɗan ya hana Nimrah ta saki kuka, ta dai daure dan kar Mammah ta fahimci halin da take ciki. Suna cikin hakan ma sai ga ƴan asibitin sun dawo da kyakkyawan Jariri mai kama da Uncle Ja'afar Masha ALLAH.       Sam ba haka Nimrah taso ba, dan ba ƙaramin ƙwallafa rai tayi da son haɗuwa da mutumin nan tai ba a yau. Sai dai ta san wannan damar kuma ta suɓuce mata. Dole ta saki jiki aka cigaba da murnar jariri, dan tabi ta katantane ta hana kowa ɗauka saboda Nimrah akwai son yara matuƙa. Kusan ma ganin jinjirin ne ya kwashe kaso mafi yawa na damuwar tata ta ɓuya daga fuskar ta, duk da sai da Mammah ta tambayeta ganin idonta ya canja tace abu ne ya faɗa mata..... ================        Hajiya Hasiba ta baro gidan Uncle Nasiru rai mace kiran Fomer First Lady ya sake harziƙa mata zuciya. Dan ko gaisuwa bata bari sunyi ba cikin bada umarni tace tazo tana nemanta duk inda take. Daga haka kuma ta yanke kiran batare data bari tayi magana ba. Tsabar takaici kamar zuciyarta zatai bindiga haka taji, kuma dole taje kasancewar da bazar First Lady ɗin take rawa. Akalar motar ta canja tana jan tagwayen tsaki. Mintuna kaɗan ya kawota gidan saboda gudu tai sosai.      Securitys ɗin gidan sun riga sun san wacece ita a wajen masu gidan, tunma suna gidan gwamnati bata da shamaki. Dan haka kai tsaye suka buɗe mata gate ta shige. Tun a compound ta fara gamo da abin takaici, wasu matan ƴan siyasa dake zaman jiran son ganawa da First Lady ɗin sukai mata caaa. Sama-sama ta amsa su da cewar su jirata shiga tukunna, daga haka ta shige. Yanda bata tsaya falo na farko ba balle na biyu zai baka tabbacin lallai ita ɗin ƴar gida ce. Dan kaitsaye upstairs ta haura abinta. Ga masu aiki nata miƙa mata gaisuwa cike da girmamawa.       A falon saman ta samu First Lady harda tsohon shugaban ƙasa, sai Zahir dake kwance a kujera zuru-zuru alamar baida isashen lafiya. Idonta akan Zahir ɗin ta gaida shugaban ƙasa da take kira Daddy, sannan ta gaida First Lady. Cikin ƙasa haƙuri ta furta, “Zahir lafiya kuwa?”.        Kai tsaye First Lady ta amsa mata da, “Inafa lafiya Hasiba, wasu shegun yara ne a makaranta suka nema illatashi. Shiyyasa ma Excellency yace na kiraki, dan binciken mu ya nuna yaran nada alaƙa dake”.        “Alaƙa dani kuma ranki ya daɗe? Nida yarana sun kammala har University su duka balle secondary. Sannan banda yaro namiji da har zai iya faɗa da Zahir”.      “Ba alaƙar jini ake nufi ba. Sannan ba maza bane yaran mata ne”.         “Mata fa! Suka masa wannan abun?. Amma ina fatan ba'a barsu ba ko Daddy?”.        Daga First Lady har Fomer President cikin takaici sukai ƙwafa a tare. First Lady ta ce, “Yanzu ne dai zamu ɗau mataki, dan mun saka ƴan sanda sun kama su amma sun sake su wai basu cika shekara 18 ba. Sai dai sukai maganar kotu.”         “Ai gwara aje kotun, kaji ƴan iskan yara kamar wasu ƴan daba. To wai ƴaƴan ma uban waye a ƙasar nan?”.       “Wannan shine dalilin da yasa muka kira ki. Dan muna son musan ƴaƴan waye ɗin. Dan a bincike na naga abokin mijin Nabeeha ne yaje ya cire yaran daga station, ya kuma kai lawyer. Sannan sunje da wani gadararren mutum daya ɓoye fuskarsa shine ma yace aje kotun Saboda yaran sun faɗi wata magana. Yanzu haka sun shigar da makarantar ƙara gaba ɗaya. Shi kansa alƙalin Excellency ya kirashi kan ya kora ƙarar yace case ɗin yafi ƙarfinsa”.         “Abokin Haysam! Imran kenan? Indai kuma haka ne zata kasance ƴaƴansa ne shi Imran ɗin. To amma waye suka je taren?”.       “Wannan shine amsar da muke nema muma. Yaran kuma ɗaya tabbas ƴarsa ce, dan da sunan sa take amfani, suna ma kama. Ɗaya kuma Muhammad”.          “Miye sunanta?”.      “Naja'atu Muhammad”. “Mom anfi kiranta da Nimrah, a register kawai ake kiranta da Naja'atu ”. Zahir yay magana da ƙyar a karo na farko.          “Nimrah, eh lallai wannan yarinya sheɗaniyar yarinya ce. To ai itace nake gaya miki shi Haysam ɗin ya tsinto a ƙauye shekarun baya wai an kashe iyayenta. Nabeeha tace bata yarda ƴarsa bace shine ya aureta. Mafari kenna na samu Nabeeha ta baro gidan”. Salati First Lady ta fara, shiko tsohon shugaban ƙasa da bai fahimci zancen ba ya nema ƙarin bayani. Nan fa sukai masa. A kuma lokacin ne tunanin Hajiya Hasiba ya dawo baya. Ta ce, “To kodai zancen Ismat gaskiya ne. Kusan sati guda kenan muna Chaina ni dake ba Amima ta kirani ba take min bayanin.....”       “Tabbas anyi haka”.    Cewar First Lady. Hajiya Hasiba ta ce, “To shine fa ni kuma na kullesu a ɗaki har yanzu na hana su fita, yanzu haka ma daga yima Uban nasu gargaɗi nake dan na zata shine ya shiryo makircin dan itama Nabeeha ya janye hankalinta. To lallai bana raba ɗayan biyu Haysam ne. Dan babu mai wannan ɗabi'ar gadarar irin tasa. To amma yaya haka? Duka yaushe shugaban ƙasa yace ya masa afuwa? Kodai makirci ne abun dama ba'a prison ɗin yake ba?”.          Gaba ɗaya tsohon shugaban ƙasa ya ma kasa magana, sai first lady ce ta furta, “A lallai biri yayi kama da mutum. Kuma yanzu na yarda gargaɗi mai razani akama alƙalin nan. To ai inaga Hajiya Hasiba kawai ki bar Nabeeha ta koma gidan, ta haka ne zamu san gaskiya. Dan tabbas bazamu bar wannan abin ya tafi a banza ba, dole ne yaran nan sai sun ɗanɗan kuɗarsu. Bazasu illata min yaro a banza ba, dan yanzu haka likitoci sunce sai an fiddashi waje, in ba haka ba nan gaba ya samu matsala a privete part ɗin”.        “Kai jama'a wann shaggun yara. Banƙi ta taki ba ranki ya daɗe, kanku komai kuma zan iya yi. Amma baƙya tsoron sharrin Adeel. Jiya jiyan nan nake ganin saƙonshi wai na shirya zai sake sauka a ƙasar nan, kuma wannan karon komai yake so ayi a gama”.        “Karki wani damu, ki barmu dashi. Yanzu kawai kije ama Nabeeha gyara kona kwana uku ne ta koma a cikin satin nan. Zan tura miki kuɗi, zan kuma kira ƴar Kamaru ta sameku gida”.           “An gama raki ya daɗe. ALLAH ya ƙara girma”.....       ×==×===×==×===×==×          Sai dare Dada ya dawo gidan, lokacin kusan tara. An kawo masa jinjiri domin ya gani. Nimrah dake maƙale da shi ce kuma ta kawo. Dan har faɗa sukai da Ruky babu jimawa da taƙi bata shi shine tai zuciya taje tai kwanciyarta. Itako ko alamar barci bata ji, ga yunwa na cinta taƙi cin abinci, Mammah da Ammie dake gidan sunyi faɗa har sun gaji.       Tunda ta shigo falon ya zuba mata ido. Dan yanda ta rungume jaririn famm abinta sai tai masa ƙyau. Kai tsaye ta nufo inda yake tunda shi akace ta kawo mawa. Cikin tsokana Ammar yace, “To ALLAH yasa dai shi Dada a bashi kona minti biyar ne, dan mu minti bibbiyu aka bamu”.      Dariya Mammah tayi, “Ai ku kun samu minti biyun ma, Mu'azz sai a hannunta ya gani. Ruƙayya kam yanzu ba jimawa ta shige tayi fushi”.         Dariya Bilal da su Ma'aruff suka sanya, Mu'azz ya dalla mata harara da faɗin, “Ai wlhy sai na rama”.         “Sai dai kuwa ka rame”.    Cewar Nimrah tana murguɗa baki. Kasancewar Dada a falon kuma ya sa ta tsaya iya hakan. Takawa tai ta ƙarasa inda Dadan yake, dan shima Mu'azz ya mata shiru saboda Dadan na nan. Maimakon ta bashi sai ta durƙusa a gabansa tana faɗin, “Dada gashi ka gani a haka. Idan aka tattaɓashi da yawa zai yi ciwon jiki”...........✍️ 🤣🤣ASHE Dadan ma bazai tsiraba Ninah😂🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️. 73 .......... “Bala'i”.    Cewar Ammar suna fashewa da dariya shi da Bilal. Ja'afar ya ce, “Haba Ninah harda Dadan kuma?”.      Baki ta tura cike da shagwaɓa ta ce, “To Uncle dan ALLAH kace masa minti uku kawai ya bani. Ko kuma na saka masa a ƙafafu daga hannuna ya gani.”        Dariya Ja'afar da Ma'aruff suka gimtse suma, karo na farko Mammah ta ce, “Adai yi haƙuri a bashi Auta. Kinga kafin ya gama gani sai kije ki dafa Noodle kizo kici dan abinci ma ya huce yanzu, ni kuma bazan bari ki kwanta da yunwa ba”.        Mammahn ta kalla kamar zatai kuka. “Mammah ALLAH bana jin yunwa nifa”.     Kafin Mammah ta bata amsa kawai taji za'a ɗauke mata jaririnta. Ai firgigita ta juyo. Suka kuwa haɗa ido da mai shirin ɗaukar. Ba kowa bane kuma face Dada. Dan shi kam ya gaji da jan ran da ake masa. Kannewa kawai yake. Amma ya ƙagara shima jaririn yazo hannunsa. Rabonsa da ɗaukar jariri kamar haka har ya manta. Idanunta da suka tara ƙwalla ta risinar, dan bazata iya jurar kallon nasa ba. Sai dai fa tsabar ƙarfin hali taƙi sakin yaron, ƙarshe ma tashi tai akan gwiyawunta tai kneeling a haka ta saka masa jinjirin saman cinya, hannayenta nakan cinyar tasa itama, dan ita sam a wannan yanayin bafa ta gane ma dawa take tare balle abinda tayi.       Babu wanda bai gimtse dariya ba a falon nan. Dan hatta Mammah kauda kai kawai tayi tana murmurshi.         “Tashi min anan?”.    Dada ya faɗa cikin law voice ta yanda ita kaɗai taji shi. Maimakon tashin sai ta saki hawaye sharr. A matuƙar shagwaɓe tace, “Dada dan ALLAH ka bani to, ai ka gani”.        Shi kam yau yaga lukutar jaraba. Yarinyar nan bata san a ina suke ba ne.          “Kina son duka?”.     Ya sake faɗa ciki-ciki. Kafaɗa ta maƙe masa tana tura baki. Bai sake ce mata komai ba, yasa hannu ya zare hannayenta duk biyu. Zatai magana ya wulla mata kallon daya sakata duƙar dakai ƙasa. Babu alamar wasa ya sake furta, “Tashi ki wuce ki dafa Noodle ki dawo sai ki amsa”.          “Dada kayi alƙawari?”.     Yanda ya zuba mata ido ya kasa magana ma yasa kowa ɓoye fuska yana danne dariya. Dan duk sunji mita faɗa ɗin. Shi ko ganin yanda ta tsatstsare shi da idanu babu alamar tsoro balle shakka yasa shi jinjina mata kai kawai. Tashi tai da sauri ta nufi kitchen ɗin, sai dai tana tafiyar tana waigen babyn. Kaɗan ya rage taci karo da kujera. Mu'azz ya fashe da dariya. Sai dai hararar da Dada ya watso masa ta sashi saurin danne bakin. Nimrah data hararesa itama tai ƙwafa tana shigewa kicin ɗin.         Bilal ya ce, “Kai jama'a, anya duk randa Ninah ta haihu zata bari a ɗauka ɗan kuwa?”.      “Gaskiya kam da kamar wuya”.    Ja'afar ya bashi amsa. Mammah dake murmurshi ta ce, “Hummm ina wannan tunanin nima kam, dan kwanaki fa da suka rakani barka tunda ta amshe yarinyar mutane ta hana, duk wanda yazo sai dai ya gani a hannunta. Babyn ta fara kuka akace ta bada ita maman ta shayar da ita taƙi, wai sai-dai maman ta saka nn a fida ita zata bata.”       Dariya suka sanya sosai. Shi kansa Dada da hankalinsa ke kan Baby yana masa addu'a duk da yayi kamar baya jinsu sai da yay ɗan murmurshi. Mammah ta cigaba da basu labarin kicimillin da akasha ranar. Ta ce, “In dai fa akai haihuwa a gidan nan Nimrah da Ruƙayya basa ƙara shiri, kullum cikin faɗa suke saboda ƙarfa-ƙarfar Nimrah akan Baby. Shiyyasa yaran nan duk suka shaƙu da ita, dan rainon datai musu ko iyayen iyaka kenan”.         Motsawar Babyn ya saka Dada cema Mu'azz yazo ya kaishi dare yayi a kwantar da shi haka nan kada sanyi ya kamashi. Tasowa Mu'azz ɗin yay ya amshesa. Ya fita kenan shima Dada ya miƙe zai haura sama dan hutawa ihun Nimrah ya ratsa kunnuwansu.         “Wayyoooo yaji wayyo idona?”. Gaba ɗaya suka kalla hanyar kitchen ɗin, Dada ya tsaya cak. Kafin wani ya miƙe Nimrah ta fito tana laluben hanya da faɗin, “Wayyo Mammah ki cire min zan haukace idona. Zafi-zafi na shiga uku Mammah zan mutu....”       Mammah da duk ta rikice itama har zata miƙe dan kamo Nimrah ɗin, duk da ga Dada a kusa da inda take amma taga bashi da niyyar hakan sai kuma Nimrah ɗin data iso gab da Dada tana lalube ta taɓa shi. Ai tana jin mutum bama ta tsaya son sanin waye ba kawai ta damƙeshi tana cusa fuskarta a jikinsa, dan wani irin tashin hankali take ji da raɗaɗi har tsakiyar ƙwaƙwalwa, sakamakon yajin ya shiga mata sasai cikin idon. Gata dama koda hannu ta taɓa kayan miya sai su yini suna mata zogin yaji shiyyasa ta ƙara tsanar girki.         Dada bashi da zaɓin daya wuce riƙeta, dan duk wanda ya kalleta yasan a gigice take, kuma dole ka tausaya mata. Gashi iyayen nata duk sun miƙe suma fuska cike da tashin hankali kamar zasu tayata kuka. Ya tabbatar yayi sake zasu iya cewa ma baya ƙaunar ƴar tasu ko ya mata mugunta.          A nutsensa ya furta, “Ki nutsu”.     Ina ita ba saurarensa take ba, dan ita tasan mitake ji. Shima ya fahimci hakan, dan haka ya kamata kawai yana komawa zaune a kujerar daya tashi, ita ko da yake tana a jikin nasa sai kawai ta zauna a cinyarsa. A nan ɗin ma Dada bashi da mafita, baiyi magana ba kawai ya hau ƙoƙarin buɗe mata idon, ita kuma ta ƙanƙame masa hannu tana faman tirje-tirjen da kuka da kiran Mammah-Mammah.       Matsowa Mammah tayi ta kama hannun nata cike da lallashi tana faɗin, “Kinga ya isa nutsu a cire miki. Da ya fita zaki ji zafin ya daina.”          “To Mammah dan ALLAH ki cire. Wlhy ji nake kamar zan haukace.”        Bilal ya kawo tissue, riƙe mata hannun da Mammahn tayi yasa Dada samu ya buɗe idon nata. Sai ko ga ƙaton yaji a ciki harda ɗiya. Idon kuwa yayi wata masifar rinewa jazurr kamar garwashin wuta. Tissue ɗin hannun Bilal ya amsa, yana saka mata taji zafin yafi nada, sai kawai ta sake ƙanƙameshi tana son ƙwace kanta. Sai dai riƙon na manya ne, dan haka ya matseta da ƙyau sai da ya cire shi gaba ɗaya.     Babu wanda baiji tausayinta ba da ganin yajin babba da shi. Ita ko ta kife kanta tana sauke numfashin wahala da sauran azabar da take ji akan ƙirjinsa. Dada da ya san wannan yanayin haɗari zai zama mai girma da shiga cakwakiya sai kawai ya miƙe a hankali da ita a jikin nasa ya nufi doguwar kujera ya kwantar da ita. Yana ɗagowa zai bar wajen suka haɗa ido da su Ma'aruff dake murmushi. Da sauri suka gimtse shi da Ja'afar. Shima sai ya ɗauke idanun nasa cike da basarwa kamar bai gansu ba ya bar falon gaba ɗaya. Sai da suka tabbatar ya gama haurawa staircase ɗin suka fashe da dariyar. Kallonsu Mammah tayi itama, da sauri suka sake gimtsewa.      Ammar, Bilal da Mu'azz daya dawo yanzu basu fahimci inda dariyar Yaya Ma'aruff da Yaya Ja'afar ta nufa ba sam. Itama Mammah da farko ba fahimta tai ba, sai da taga suna satar kallon upstairs suna ƙus-ƙus sannan ya harbo jirgin su. Kanta kawai ta girgiza tana maida hankalinta ga Mu'azz tace yaje ya ƙarasa dafama Nimrah indomie ɗin taci taje ta kwanta....... ^^^^^^^^^^^^^^^^            A wannan daren ƙungiyar duhu sukai meeting na sirri. Meeting ɗin da gaba ɗayansa ƙulle-ƙullen masifu ne na tashin hankali ga ƙasa dama shugabanta Janar. Dan abinda yay musu sun tabbatar da babu bashi sai sun hukuntashi. Sai Dada, gaba ɗaya shirinsu a kan Dada kuwa ya ta'allaƙa ne akan yin amfani da Nimrah. Sun fahimci dole su canja taku, takun da zasu haifar da rauni mai raɗaɗi da ƙuna a zuciyar sa. Wannan kuma raɗaɗi da ƙunar ba zasu iya samar da shi ba sai ta hanyar taɓa zuri'arsa. Ta ko ina kuma sun fahimci dole sai da wani na jikinsa zasu iya hakan, musamman da a yanzu tsaro yayi yawa a gidan, dan Mole ya zama mai kawo musu bayanai sosai akan gidan yanzu fiye da Dagger. Hatta haihuwar Shariffa ta yau ɗin nan tazo kunensu, shima Dagger ya sanar musu kiran da Nimrah tai masa da buƙatar su haɗu da tayi sai dai hakan bai faru ba sakamakon rashin fitowar ta. Ta haka ne ma suka sake samun tabbacin Zak-Shadow ɗin ne dai a gida Mole baiyi ƙarya ba.         Sai da suka gama tsare-tsaren su iya su manyan Sannan aka sake wani sabon meeting da saura members duk a daren dai. Hukuncin da suka yanke da tsarin da suka kammala yi yasa shima Dagger suka buƙaci ganinsa zuwa safiya. Dan yanzu kam aiki ne zai tashi ba wasan yara ba. Sannan zasu bama Mole dama irin ta Dagger, sai dai ba'a kan Nimrah ba. Nimrah Dagger zai cigaba da aiki kanta kamar yanda ya fara tunda ta riga tasan fuskarsa. Canjawa zai saka ta iya zargin wani abu daban tunda sun fahimci tana da wayo............✍️ Idanunsa dake lumshe shima ya buɗe yana sauke ƙaramar ajiyar zuciya, kafin ya ɗagota a hankali zai maidata ya kwantar ta sake ƙanƙamesa cikin ƙunƙunan barci name magagi tace, “Uhmm-uhmm Mammah, ni zan kwanta ana....”        Batare data ƙarasa ba ta cigaba da barcinta. Wani ɗan murmushi mai fidda sauti cikin ƙirji kawai ya saki. A ransa yace (Trouble maker, idan kin kwanta anan ni kuma twin ɗinki ta farka ta ganni fa?). A zahiri kam kwantar da ita ɗin yayi a hankali, sannan ya haska mata fuska da waya. Idon da gefensa har ya kumbura, yakai hannu ya ɗan shafa wajen kaɗan, sai kuma ya ɗan furzar da iska yana zame hannunsa data riƙe gam a ƙirjinta. Sake ƙoƙarin cafkowa tayi, kawai ya saka mata bargo a ciki. Sai ko ta damƙe tana juya kwanciya ta matse bargon har abin yaso bashi dariya ma, ya dai gimtse ya tashi abinsa da ledar maganin ya fita, dan yasan idan ya bari da safe sai sunta shelar neman waya ajiye a gidan, ba man kai ne da su ba.                °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°        °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°            Washe gari gidan Mammah ya cika da ƴan barka. Musamman sashen su Lailah. Danginsu sai zuwa sukeyi. Sai dai duk wanda ya shigo sai yazo ya gaida Mammah. Kuma duk wanda zai shigo securitys ɗin nan sai sun masa ƙwaƙwaf.       Yanayin da Nimrah ta tashi akan idonta ya taƙaita al'amarin tana nanuƙe da Mammah. Ruƙayya kam duk ta damu kamar zatai kuka. Kaɗan-kaɗan saita ce, “Ninah ba zafi?”.      Tun Nimrah nace mata eh, harta koma tsokanarta idan ta tambaya sai tace akwai, sai taga ta damu sai ta saka dariya. Mu'azz ya tasa su gaba da tsokana sai da Mammah ta Koresa a falon. Hakama Afeef ko sau ɗaya bai nuna tausayin Nimrah ba balle Hanoon. Biebah kam har ɗan gasa mata idon tayi da ruwan zafi dan fuskarta ya ɗanyi fushi, a haka ma dan Dada ya saka mata magani ne ai da ba'a san yanda zata tashi ba.      Har kusan sha biyu Dada bai sakko ba. Dan haka Mammah tace Nimrah dake zaune Ruky tayi filo da ƙafarta tana barci ta tashi ta kai masa abincin breakfast. Saboda ta kirashi a waya yace aiki yake shiyyasa. Kuma yaga yau gidan nasu hayaniya tayi yawa. Mammah tace shike nan bari tasa a kawo masa. Shine ta yanke wayar tace Nimrah ɗin ta tashi.         Cike da shagwaɓa Nimrah ta ce, “Mammah banda lafiya fa”.             “Haba auta, to wa kike son ya kai? Bakiga Ruƙayya barci take ba? Mamanku kuma tana aiki a kitchen”.     Caraf Hanoon ta ce, “Mammah kawo naje”.     Kafin ma Mammah ta bata amsa Nimrah data watsa mata harara ta miƙe. Ta sake watsama Hanoon kallon banza tana nufar tray ɗin da kulu ta kawo da faɗin, “Dama mutum ya kama kanshi. Mu uban mu bazai auri finga-fiyau ba. Mace sai kace taɓaryar gwari ba sama ba ƙasa.” dariya kamar zata kashe Kulu, da ƙyar ta iya matsawa ta shige kitchen. Hanoon kam da kallo tabi Nimrah dan ba komai ta gama ganewa ba. Mammah ta girgiza kai tana murmushi, a zuciyarta addu'a take ALLAH ya shirya mata Nimrah da Ruƙayya ita kam. Yara baƙar magana a bakinsu kamar dangin mahauta. Muhammad ne yay tashen baƙar magana yana yaro, ba yawan surutu amma idan ya yaɓa maka mai zafi kamar ka mutu. To ga magada nan ya samu har suna neman zartashi.         Koda Nimrah tazo kofar ɗakin sai abinda ya faru jiya ya shiga dawo mata. Bana tattaunawarta kawai da shi ba, harda na abinda ta gani, har yanzu take neman mafitar fita amma ta gagara samu. Tafi minti ɗaya a tsaye kafin tai sallama dan babu daman knocking hannunta da tray. Sarai ya jita amma yaƙi tasowa ya buɗe mata balle amsawa. Yau ƴan sarautar ne aka. Itama jin shiru babu motsin kowa tayi kuma har sau kusan huɗu sai kawai ta rungume tray ɗin da hannu ɗaya, cikin dabara ta saka ɗayan ta buɗe. Koda taci karo da shi a zaune sai da taji shock. Ta ɗanyi diri-diri sai kuma ta nutsu jin tana neman yin ɓari.       Yi yay kamar baima jita ba. Nan ko ya gama kalleta ta gefen ido. Amma sai ka rantse hankalin nasa akan rubuce-rubucen da yake yi yake. Ƙananan kaya ne a jikinsa, yanda rigar ya kamashi sosai gashi ƙaramin hannu yasa kallo ɗaya datai masa bata sake gigin yin na biyu ba. Sai kuma ta tafi tunani mara dalili daya sakata shagala a wajen ta kasa ƙarasawa ta ajiye abincin..          “Idan kikai ɓarin abincin nan sai kin cinye shi”.      A bazata furicinsa ya shiga kunnenta. Da sauri ta dawo hayyacinta. Saman table ɗin gaban sofa taje ta ajiye tray ɗin. Dan shi yana a study chair ne zaune. Desktop ɗin sa a kunne gefe yana rubuce-rubuce. Ta bayansa kaɗan ta risina ta ce, “Dada ina kwana”.         “Haɗa min abincin”.     Ya faɗa batare daya amsa gaisuwarta ba. Baki ta zumɓura dan taji haushin ƙin amsa matan da yayi.........✍️ 75 ..........Harta gama zuba komai dai-dai misali ta zuba shayin lemon tsami da na'a-na'a dake ta ƙamshi bakinta na a sama. Inda yake ta nufo, ya matsar da takardunsa kafin ta kife masa abincin a kansu. Shiru bata ajiye ba, hakan ya sashi ɗagowa dole ya kalleta. Suna haɗa ido ta risinar da nata, shima sai ya kauda kansa ya cigaba da aikinsa. Kusan sakan biyar sannan ya furta,         “Fishin mi kike yi?”.     Bakin ta ƙara turawa taƙi magana. Yay ɗan jimm na mamaki, sai kuma ya ɗago ya sake kallonta.        “Abincin naku ne baƙya son naci?”.       Yanzu ma kai ta girgiza.   Ya dai sake daurewa ya ce, “Idon ne?”.        Sai kawai ta sakar masa kuka. Mamakin duniya ya gama mamaye shi, kaji yarinya fa dan ALLAH kamar wata mai aljanu. Bai sake magana ba ya zuba mata idanu kawai. Ganin kukan ma daɗi yake mata sai ya amshi abincinsa da kansa ya ajiye. Kafin ya furta, “Tunda bazaki  yi magana ba wuce ki tafi”.          Gurin tai ƙoƙarin bari tana sake fashewa da kukan da ita kanta bata san dalilin yinsa ba, kawai jitai tana son yi masa kukan ko a cikin drama ɗinta ne, duk da da gaske taji haushin bai amsa gaisuwar datai masa ba. Jiyay bazai iya barinta ta tafi tana kukan ba, ko wani abu akai mata. Sai ya riƙo hannunta ya dawo da ita inda take da. Bai saki mata hannun ba ya cigaba da kallonta har kusan mintuna biyu.           “Kina son na zane ki?”.     Kanta ta girgiza masa. Cikin sake tsuke fuska ya ce, “Bana son wannan kukan. Faɗa min mike damun ki? Wani ne ya miki wani abu?”.      Hawayen ta fara sharewa da faɗin, “A'a. Kai ne”.        “Kiddo ni kuma?”.     Kanta ta jinjina tana tura baki. “Ikon rabbu, to mi nayi?”. “Na gaishe ka baka amsa ba. Sai naga kamar kana fushi da ni”.          Sagale kawai yay yana kallon ta, mamakin duniya ya gama mamaye shi. A ransa yace (Ƙuruci dangin hauka. Kaji yarinya fa) a fili kam baima san ya furta, “Ni kuma yau a hannun ƴan sari na tashi kenan!. To sake gaisheni sai na amsa ba shike nan ba”.        “To ba fushi kake ba?”.     Tai maganar cikin yanayin ɗan waro masa idanu. Sai kawai ya girgiza mata kansa yana ƙoƙarin danne murmushin dake neman bayyana a tsukakkiyar fuskarsa. Ajiyar zuciya kuwa ta saki, sannan ta sake gaishe shi. Ɓoyayyar ajiyar zuciya shima ya saki ya amsa yanda take son, harda ɗorawa da, “Yaya idon ki?”.          “Da sauƙi, amma yana zafi kaɗan”.       “Tunda kina kukan da babu dalili ba dole yay zafi ba. Ɗauka min leda gashi can a mirror na sa miki magani”.         Ya kai ƙarshen maganar yana sakar mata hannu. Inda ya aiketan ta tafi, ya bita da kallo yana girgiza kai kawai. Tabbas yana da son yara, bai sani ba kodan baida su. Duk da Nimrah da Ruƙayya sun girma a yanzu, ganinsu yake ƴan 7years ɗin nan daya tafi ya bari... Dawowarta da ledar ya saka tunaninsa katsewa. Amsa yay ya buɗe, ya ciro maganin sannan ya kalleta, kamar ta fahimci mi yake nufi ta tsugunna kawai tana mai dafa hannun kujerar. Kanta ya dafa da hannu ɗaya, tare da buɗe idon sosai da babban yatsansa ya zuba mata maganin.....          “Wayyo Dada zafiiiiii”.      “Shiiiii!”.   Ya faɗa yana riƙe da kan nata, dan ya hanata ɗagowa kar maganin ya fita. Sai da ya tabbatar ya shiga sannan ya barta. Har zata miƙe ya ce, “Ɗauka wannan abinci ko canja ya huce. Kije ki kira min Ruƙayya itama”.        Cike da tsantseni ta amsa, dan duk wannan biye matan da yake shakkarsa na nan damar a zuciyarta. Musamman da fuskar na tsukenta ne babu ko murmurshi. Sai dai son cikar burinta da shirinta a kansa yasa take danne zuciyarta da bama kanta ƙwarin gwiwa. Alhamdullahi kuma taga tasirin hanyar data biyo masa. Bayan ta ajiye wani sabon abincin dan ALLAH yaso ba plate ɗaya Kulu ta saka ba, haka ma kofi. Tana kammalawa ta fita a ɗakin.      A ƙasan ransa ya furta (Kiddo kina bani ciwon kai)...      Babu jimawa suka dawo ita da Ruƙayyan, dan ta iske ta tashi barcin. Yanda yay ma Nimrah tambayoyi jiya cikin wayo da dabara akan makarantarsu haka ya dinga musu a tare yau, suka dinga bashi labarai kala-kala, har kansa ya fara ciwo sai da ya gaji ya korosu. Oho ko'a jikinsu, dan daɗi ma suka dinga ji Dada yayi hira da su, koda suka dawo wajen Mammah sai suka dinga yi ma Mu'azz wulaƙanci. Har sai da yaji haushi ya haura saman yace shima ya tafi ɗakin Dadan. Mammah dai murmurshi take kawai da jinjina shiriritarsu. Sauran Uncles ɗin nasu ma duk wanda ya shigo sai an bashi labari yau sunyi hira da Dada. Congratulations suka dinga ce musu suna dariya..       Wannan hira ta bama Dada haske sosai akan makarantar su Ruky. Koda suka tattauna da Daddy Imran yayi mamakin wayon yaran. Dan abune ma da shi kam bai taɓa kawoma ransa ba... ))))★(((((★))))))★((((            A bangaren Hajiya Hasiba kamar yanda First Lady tace tayi hakan tayi, ta buɗe su Nabeeha. Ta kira likitanta ya fara duba su saboda damuwar da suka sakama kansu duk sun rame. Ya tabbatar mata da basa tare da wata matsala sai damuwar kawai. Amma ya basu shawarwari sosai da suka fahimcesa. Bayan tafiyarsa itama ta zauna da su. Ta nuna musu ta haƙura, amma su kiyaye gaba. Sannan tace Nabeeha ta fara shirin komawa gidan mijinta.       Ba Nabeeha ba hatta Ismat ta shiga matsanancin mamaki. Dan har sai da ta furta, “Momy da gaske kike yi?”.        “Oh na saba miki ƙarya ne Ismat?”.     “A'a Momy kiyi haƙuri. Wlhy mamaki ne kawai abin ya bani”.       “Humm to sai ya daina baki. Kawai shawara likitan nan ya bani akan na barta ta koma kada ta kamu da wani ciwo. Dan haka na amince ta koma. Kema kuma na baki nan da wata uku ki kawo mijin aure, idan ba haka ba ni inada wanda zan bama ke. Masu gyaran jiki zasu zo gobe idan ALLAH ya kaimu sai ki shirya”.     Tai maganar ƙarshe tana kallon Nabeeha. Kai kawai Nabeeha ta jinjina mata, dan al'amarin Momyn tasu a wannan gaɓar ya razanata fiye da ko yaushe. Tana sonta sosai, amma maganar gaskiya ta fara jin tsoron ta mai girma.         Tun daga ranar suka fara ganin canjin abinci masu ƙyau, saɓanin wanda ake basu a kwanakin nan da suke a kulle. Sannan ta dawo musu da wayoyinsu. An kuma dawo da network ɗin gidan. Sukan fita falo su zauna, har ma tayi hira da su. Ƴar Kamaru tazo ta fara aikinta na gyaran jiki wa Nabeeha. Dan maƙudan kuɗaɗe First Lady ta biya kamar bata san ciwon kuɗi ba. Koda yake bata san ciwon nasu ba tunda an tara musu, ta yanda ko jikokinsu bazasu yi talauci ba idan ba wata jarabawar UBANGIJI ba kuma....     <•••><••••><••••><•••>          A lokacin da can ake gyara Nabeeha anan Dada da Imran sun matuƙar maida hankali wajen haɗa runduna ne akan aikin da zasu fara. Dan kamar yanda shugaban ƙasa ya bama Dada damar samar da masu taya shi aiki cikin kowanne jami'an tsaro dama farar hula haka yaketa tattarasu. Sai dai fa dukansu kowa bai san da zama ɗan uwansa ba. Hasali ma su Dabo aka saka suke yi basu san waye shugaban tawagar ba.        Har yanzu suma su Dabo basu ga Dada da idanunsu ba, sai dai su duka yayi waya da su ta hannun Imran. Duk abinda zasuyi Faro ke basu umarni. Sai yau ne ma yake tunanin zama da su. Dan akwai tsofaffin bayanan da yake so a hannunsu. Sannan yana son jin bayani akan duk wanda suka ɗakko a cikin tafiyar dan tantance ko zai iya aiki da shi ko bazai iya ba.           Kwanaki biyar kenan da haihuwar Shariffa, tunda kuma akai haihuwar kullum su Aunty Ummi na gidan nan. Hakama ɓangaren dangin su Imran tunda abu ne duk na gida. Shiyyasa sam Dada baya zaman gidan. Bama zai iya cewa yasan wace waina ake toyawa ba. Suma sun maida hankalinsu akan wancan gidan da suke shirin maidawa na sirri.  Tabbas, wannan gida a zahiri Dada da Imran sun maida shi tamkar gida na yau da kullum, amma a gaskiya UNIT ZERO ne, cibiyar sirri da aka gina domin yaƙin da ba a sakawa suna ba a fili. An sauya duk wani abu mai ƙarancin tsaro zuwa mafi girman matakan tsaro. Tun daga ƙofar shiga, komai ya sauya. Ba ƙofa ce da ake buɗewa da hannu kawai ba. Ana amfani da multi-layer authentication: lambar sirri, na’urar biometric, da kuma time-based access. Ko su da kansu, idan lokacin bai dace ba, ƙofar ba za ta buɗe ba.        Tagogi kuwa an maida su bullet-resistant glass harbi ba zai iya ratsa su ba. An saka ɓoyayyun cameras ko’ina. An kuma tanadi ɗaki guda na musamman domin ajiye ayyukan sirri, ɗakin da Dada shi kaɗai ke shiga, sai Imran da Faro. Smart perimeter sensors sun zagaye gidan gaba ɗaya ba wai don mutane kawai ba, har da motsin iska, ƙasa, ko duk wani abu da bai dace ba. Akwai silent alarm system: babu ƙara, babu haske, amma UNIT ZERO ya riga ya zama ido da kunne na komai. Thermal cameras suna iya gano mutum ko da cikin duhu ko ta bayan bango. Ƙofofi kuwa EMP-resistant ne ko an katse wuta, ko an yi hacking, ba za su buɗe musu ba..........✍️ 76 .........Cameras marasa gani da ido, ba su da haske, ba su da amo. Wasu an saka su a cikin bango, wasu ma a cikin furanni. An tanadi blind-spot tracking a inda babu camera, akwai sensor. Duk motsi ana adana shi ne a local encrypted server, ba tare da haɗin internet ba. A wasu sassa ma babu wata waya da ke kama signal, musamman a EMI shielded rooms.       Hatta talabijin da ke nuna dukkan motsin gidan ta hanyar cameras suna cikin ɗakin kula da tsaro. Akwai na'urorin aiki na musamman da shugaban ƙasa ya samar, irin waɗanda manyan ƙasashe ke amfani da su a duniya. Manyan monitors suna nuna duk motsin gidan, sarrafa cameras, da ajiye bayanan sirri. Babu waya, babu recorder, babu wani motsi da zai faru ba tare da sun sani ba, ko da basa cikin gidan. Abin da aka faɗa a nan, ya mutu a nan. Ko hoto ma ba ya ɗaukuwa a gidan, balle a ɗakin sirri.        A tsararren ɗakin sirri, dukkan takardu suna cikin classified physical files da aka kulle da code da fingerprint. Wasu bayanai ba su da suna, sai lambobi kawai. Wasu hotuna da bayanai ana ajiye su ne a dead vault, ba a buɗewa sai an cika sharaɗi guda uku. Ana amfani da dead-drop system wajen musayar bayanai, ba tare da haɗuwa kai tsaye ba.       Akwai makamai iri-iri makaman da ba a rubuta su a kowanne rijista ba. Na'urorin sauraro, bin sawu, da ɓoye fuska. Haka kuma akwai kayan fitar gaggawa idan aka kai hari, da wuraren ɓoye ainihin jami'an sirri masu kai ɗauki. Da zarar ka shiga wannan ɗakin, zaka fahimci cewa an shirya yaƙi ne yaƙi na gaske, ba wasan yara ba.      Ba kayan aiki kaɗai aka tsaya ba. An tanadi hanyoyin fitar sirri ta ƙasa, waɗanda kai tsaye ke haɗuwa da manyan magudanan ruwan unguwar. Hanyoyin ƙasa da aka ɓoye cikin tsarin gine-gine. Ba hanya ɗaya ba fiye da uku. Wasu suna kaiwa wurare daban-daban a unguwar, wuraren da ba za ka taɓa tunanin suna da alaƙa da gidan ba.           Tabbas shugaban ƙasa yayi ƙoƙari wajen zuba kuɗi akan wannan aiki, duk da dai ba'a fitar da su daga asusun gwamnati kai tsaye da wannan manufar ba, an laɓe bayan wani aiki ne da aka bada kwangilarsa kai tsaye, a bayan fage kuma akai wannan aikin. Kowa da zaiyi aiki da UNIT ZERO bai san ainihin shugaban tawagar ba. Umarnin aiki zai dinga zuwa ne ta code name. Idan aka kama mutum, babu abin da zai iya faɗa da zai rushe tsarin gaba ɗaya. UNIT ZERO ba gida ba ne kamar na shirin Film kawai, babbar FADAR YAƘI ce a ƙarƙashin umarnin ZAK-SHADOW. Wani gawurtaccen station blinding ne da zai ruguza duk wani mai tsautsayi da zai iya shiga tarkon ZAKI. Dan duk wani shiri an kammala shi yanzu kam hatta filin saka mazare rawa da sarƙa a kafa. Shi kansa uban gayyar ya furta “YANZU NE AIKIN ƘARSHE ZAI FARA. A kashe ko ya kashe, wannan shine ƙarshen BURI......”         “Alhamdullahi komai ya kamala, lokacin fara aiki yayi. Yanzu minene shiri na farko?”.         Iska Dada ya ɗan furzar yana ajiye takardun hannunsa ya gyara zama da kallon Imran mai maganar. Cikin sake maimaita godiyar ga UBANGIJIN shima ya bashi amsa da, “Inaga zan gana da su dabo a daren yau. Kai ma lokaci yayi da zaka koma aiki sosai kafin su fara tsarguwa da rashin zamanka office.”       “Nima nayi wannan tunanin. In sha ALLAHU kuma zan koma wannan Monday ɗin. Yaya batun karatun yaranka, ya kamata su koma makaranta fa. Dan in ka biye musu su wannan zaman shiriritar daɗi yake musu, musamman daya zam babu islamiyya. Ammien su tace a zaman jegon nan babu abinda suke sai rashin ji, kawai dan baka yini gida ne kai ma. Dan jiya ALLAH ya kiyaye suda yarinyar nan Hanoon da anyi babu daɗi.”          Murmushi kawai Dada yayi. Daddy Imran ya hararesa. “Kace mune ke ɗaure musu ƙugu, amma ka fimu. Nazata dawowarka zata saka su nutsu amma shirun da kake musu yayi yawa, ya kamata ko sau ɗaya kaci ƙaniyarsu.”       “Basuyi abinda zanci ƙaniyar tasu bane shiyyasa. Makaranta kuma zasu koma. Dan baza'a canja musu ba akwai shirin da nakeyi kafin su koma ɗin, da kaina zan maida su”.       “Hakan yayi ALLAH ya kaimu. Sai mutuminka ya dameni akan batun Auta. Wai kunyarka yake ji shiyyasa ya kasa magana. Kar kaga kamar yayi gaggawa.”     Nan ma murmushi Dada yayi da faɗin, “Ai yayi ƙoƙari, ya kamata ka duba masa. Sai ka haɗa da Bilal da Ammar. Dan suma bana son zamansu haka. Ya kamata duk su ajiye iyali”.         “Eh wannan shawara ce mai ƙyau. Amma ban taɓa ganin Ammar da budurwa ba. Gara Bilal”.      “Na tambaye shi nima yanata min ƙunshe-ƙunshe. Shine nace masa yaje ya tura min saƙo to. Sai jiya yake tura min wai ai bata girma ba, kuma tana a gidan tare damu. Amma bai taɓa nuna mata ba sai ta kammala Secondary”.         “Tofa ji ja'iri, wacece haka?”.      “Bai faɗa ba, amma ni na fahimci Ruƙayya yake nufi”.    “Kai amma Ammar mashiririci ne. Yarasa mata sai wannan kayan shirme da shiriritar. Kuma a haka kake cewa a haɗa da shi, ciwon kai kawai ka nemar masa”.         “Ko?”.     Dada ya faɗa yana ɗan ɗage gira sama. Baki Daddy Imran ya taɓe. “Kaima ka san yarinyar nan taka sai a hankali”.        “Ba komai zata bari wataran. Ai dama na gaya maka aure zan mata”.      “To ALLAH ya taimaka. Sai kai kuma uban gayyar. Dan ALLAH kayi haƙiri muje bikon Nabeeha. Dan ina cikin mamakin yanda har yanzu bataji ko labarin dawowarka ba. Ko har yanzu tana fushi ne”.       “Dawa zaka je ɗin?”.    “A! Dakai mana. Zakina dan ALLAH ka rage taurin kan nan. Sufa mata ba'ai musu haka. Lallaɓasu ake, a riritasu. Ayi haƙuri da halayensu marasa ƙyau. Tunda har akace mana tun daga tushe a karkace suke, tsaurin mu bazai sa su miƙe ba fa. Idan ma muka tsananta zasu karye ne.”          “Ni babu inda zanje, ƙafarta data fiddata idan ta gaji da zaman ta dawo da ita”.       “Kai kuma halin da kake ciki fa?”.    “Ni na gaya maka ina cikin wani hali ne?”.     “Kasan na sanka fiye da kowa. Ai ba sai ka faɗa min ba. Koda kake ganin dama can kana azumin ka ai na yanzu yasha banban. Sannan yanzu fa kake faɗar su Bilal su ajiye iyali saboda shine cikar kamala. Amma kai kana bijirewa. Kai ne fa uba, ko Mammah na tabbatar ta maka shiru ne taga iya gudun ruwanka. Idan kai bazaka je ba, ni ka barni naje to”.       “Wlhy bazaka ba”.    “Harda rantsuwa? To shike nan Nimrah ta tare”.     “Amma baka da hankali”.   Dariya Imran yayi sosai, ya ce, “Naji banda shi. Miye a ciki to. Naga yaran ƙauye ana musu aure ƙasa da shekarunta. Balle su suna cin abinci mai ƙyau kuma ALLAH ya kawo girman da wuri. Kadai duba al'amarin nan. Bar ganinsu haka sun san abubuwa da yawa tunda suna zuwa islamiyya. Idan ba hakaba kana nan wasu zasu fara koya mata abinda kai kake ganin bata sanshi ba. Dan kwanaki sai da naci ƙaniyar wani malamin islamiyyar su wai shi Kamal. Daga baya ma na bincika wai yabar makarantar, amma da ya dage shi son Nimrah yake yi. Har ya fara zuwa gidan fa”.        Wani mugun kallo Dada kema Imran kai kace shine Kamal ɗin. Aiko mi Imran zai yi inba dariya ba. Sai kawai Dada ya miƙe abinsa daga nan hirar ta watse ma. Har ya kawo shi gida bai sake kulashi ba. Haka ya sauke shi shima ya kama hanyar gida yana kwasar dariya. Dan shi kaɗai yaga bala'in daya hango a idanun zakinsa. Ai ko a fagen fama albarka.       Ƙasa daurewa yay sai da ya bama Ammie labari. Itama taita dariya. Daga ƙarshe tace, “Ni kaina nayi tunanin fara shiri sai naga bakuce komai ba, amma share masa ɗaki a sashen Mammah. Amma magana ta gaskiya bana son Nabeeha ta dawo gidan nan Yarinyata bata tare ɗakinta ba.”          “Ai kunji matsalarsu iyayen zamani, zaku fara koya mata kishin banza ko”.      “Ba wani koya kishi Daddyn Khalifa magana ce ta gaskiya. Tunda ita bata da hankali dan mijin ya ƙara aure kin ɗauki ƙafa kin tafi gida. Ya shiga wani hali ki dawo ɗakin ki ki zauna kuyi jimami, kuyi kuka tare da ƴan uwansa da Mahaifiyarsa amma kin biyema taki uwar sai yawon gantali. Yanzu duk randa yasan wannan zaman Dubai ɗin da taje tayi mi kake tunani dan ALLAH. Zargi ma bazai shigo ciki ba”.         “Ai babu ma wanda zai gaya masa. Yanzu dai mubar maganar, gyara kuma kiyi tayi, sai ki haɗa da Biebah da Asma'u harma da Ruƙayya”.      Idanu sosai ta waro na mamaki. “Ruƙayya fa?”.         “Eh, ubanta yace aure zai mata, yama mata miji. Gara ma yayi hakan, dan zanfi samun dama a kansa nima game da tarewar Nimrah ɗin”.       Ammie da abin ma ya bata dariya ta ce, “To ALLAH ya sanya alkairi, yasa ayi damu, amma dai wannan miji zai kwasa.”        Dariya Daddy Imran yayi itama tana taya shi. Ya ce, “Kamar kina wajen abinda na faɗa kenan nima. Amma tunda mai abu da abunsa sai ka tayashi da sambarka.”        “Haka ne kam, ALLAH yasa ayi da rammu to”.      “Amin ya rabbi”.........✍️ 77 ........Ana gobe suna su Gwaggon Alawiyya suka iso. Ai fa gida ya kacame. Su Nimrah amarori. Dan ma ita damuwa ta raba mata hankali biyu, dan ta gama shirya a cikin rarumar sunan nan zata haɗu da Dagger. Shiyyasa ma tai luff abinta a kwanakin da suka gabata kamar komai baya damunta. Amma da yake ita Ruƙayya na tare da ita tsaff ta gane damuwar kwanaki tana neman dawo mata. Koda ta dameta da tambaya sai tace rashin zuwa makarantar su ne ke damunta. Har tana bada shawarar idan anyi suna su sami Dada da maganar, dan gani suke kamar Mammah ce bata son su koma tana tsoron a musu wani abu. Ruƙayya ta gamsu da hakan shiyyasa ta saki maganar. Itama kuma Nimrah sai ta sake canja takunta. Dan yarinya ce mai shegen wayo da iya rikiɗa kamar hawainiya.     Cikar gidan kuma ta sake maidata busy, dan ranar su aunty Ummi ma duk anan suka kwana. Dada ne dai basu gashi a gidan ba kwata-kwata tun safe. Babu ma wanda zaice ga sanda ya fita..... <>%<>%<>%<> A ɓangaren Malam Buba jinsa yake sharr, dan kuwa shugabannin ƙungiya sun sake zama na biyu da shi. A cikin satin nan ma akwai babban aikin da zasu fitar. Ya samu cikar burinsa an bashi shugabanci harda yara a ƙarƙashin sa, sai dai ba yaran Dagger aka raba aka bashi ba kamar yanda yaso. Sabbin yara ne waɗan nan da baima san dasu ba. An basu horo mai suna horo. Sai yaji ya sake tsoro da shakkar al'amarin ƙungiyar duhu. Dan hatsabibancinsu na gaske ne ƙwarai da gaske. Sannan sun wuce dukkan inda ake zato da tsammani. Duk iya hasashenka baka isa iya ƙare musu gudu ba. Suna da ɓoyayyun abubuwa da sai UBANGIJI ne kawai ya sansu sai su.      Abinda dai ya tayar masa da hankali shine sun tabbatar masa dole ne yabar gidann su Nimrah. Dan zamansa bazai yiwu ba dan yau da gobe zata iya kwaɓewa kasancewar sun san waye Zak-Shadow, sun karanceshi sun kumayi imani da mutumin ne mai shegen wayo. Na biyu ɓoye fuskarsa da nisantar Nimrah zai bashi damar cimma burin dawo da ita cikin rayuwarsa. Duk kuma randa zata san shi waye a gareta zata ji martaba da girmansa matsayin uba.       Ya gamsu, duk da hakan ya saka shi a damuwa. Amma sun bashi shawarar ziyartar gidan lokaci-lokaci koda da nufin gaisuwa ne, hakan zai sa ya dinga ganin nata...     Na biyu Sanda. Sanda har yanzu yana wasan ɓuya da Dada, bai taɓa bari Dada ya ganshi ba. Yaƙi kuma sanarma maigadin komai. Tun yana tambayarsa harma ya daina. Nimrah kuwa dakan ari wayarsa bai taɓa hanata ba. Gashi Sarkin wayon data gama take goge number ɗin. Sai dai yana nan ya shirya. Dan yana son yasan abinda take ɓoyewar. Tunda duk da akwai camaras a gidan ta iya kaucewa hakan ta ɓuya a inda babu tayi wayarta. Ya saka mata ido sosai batare data sani ba. Dan ita tana ɗaukarsa ne a garan ƙauye da baya gane komai....       ••••••••••••••             ••••••••••••••        RANAR SUNA..... RANAR DA ABUBUWA UKU MASU MUHIMMANCI SUKA FARU A CIKINTA.   NA FARKO....       Yau take suna a gidan Mammah, tun daga sallar asuba aka raɗa sunan yaro da yaci Uncle Nasiru. Wato Naseer. Dada ne kuma ya zaɓa masa wannan suna bai kuma sanarma kowa ba sai a yau ɗin. Kowa yayi farin ciki da abinda yayi, musamman Mammah dake ta saka musu albarka. Tun kafin tara tayi su Nimrah suka cika gidan da hayaniya.          Dan party suka shirya ita da Ruky, Bintu, Feedo. Babu wanda kuma yasan sun shirya abinsu sai Mammah. Sai Uncle Bilal da suka tasa a gaba ya basu kuɗi. Sunyo gayyar ƙawaye sai dai ba wani da yawa ba, yawancin su ma ƙawayen Feedo da Bintu ne, dan masifar Ruky da Nimrah tasa ko ƙawaye basa iya zama da su. Su biyun nan sun ishi kansu suke cewa, sai su Bintu. Girkinsu suka ƙirƙira daban, duk da an biya kuɗi za'ai na suna su sunce zasuyi nasu a gida, saboda ba abinci sukai ba duk kayan kwaɗayi ne da shiririta. Hakan yasa su wannan sammakon tashi suketa cacai-cacai.          Dada da suka isa da hayaniyarsu, dan tun daga sama yana jiyo su, ga kiɗa sun kunna ya tashi kawai yay shirinsa. Dan gara yabar musu gidan shi kam. Zai je kawai ya gaida Baffa suyi hira tunda ya dawo dama bai nutsu sunyi hira ba sai dai yaje ya gaishe su shi da Hajjo sama-sama. Lokacin da yake sakkowa sam su Nimrah basu sani ba, dan sun dage suna shan rawa abinsu bil haƙƙi. Biebah na musu video ita da Mu'azz. Kansa kawai ya girgiza ya wuce abinsa batare da kowa ya lura da shi ba sai Aunty Mommy, da ido kuma yay mata alamar kar tai magana. Dole tai shiru tana murmurshi, shi kuma ya fice.       NA BIYU    Fitar Dada babu jimawa labari da ɗumi-ɗuminsa ya iso sashen Mammah. Wai ga wasu mutane sunzo sashen Dada da babu kowa a ciki tare da Nabeeha da ƙannenta. Falon yay tsitt, kafin kowa ya iya magana sai ga Hajiya Hasiba ta shigo Amima biye da ita. Sai da ta gama bin falon da kallo sannan tai murmurshi tana ƙarasawa inda Mammah take da su Gwaggo Khadijah. A ranta kam faɗi take (Ni Hasiba yaushe mutanen nan sukai kuɗi haka? Ya akai Banda labari) a zahiri kuma da murmushi nan na fuskarta takai zaune a kujerar da Aunty Badiyya matar Uncle Jamilu ta bata tana faɗin, “Hajiya A'isha ashe suna ake gidan haka bamu da labari”.          Mammah a duk yanda kake ta iya da kai, sai itama ta saki murmurshi. “To ayi haƙuri munyi laifi. Wani lokacin abubuwan nauyi suke a kai sai ka manta da wasu”.       “Haka ne kam, ALLAH yasa mu dace. Dama ɗiyarki ce zata dawo ɗakinta, shine muka zo da kamfanin da zasu saka kaya a sashen nasu, kinga ba'a maida waccan ba ai”.      Nan ma murmurshi Mammah tayi, ga falon yayi tsitt kowa na jiran yaji amsar da Hajiya Hasiba zata samu. Musamman su Aunty Mimi da wani tarnaƙin baƙin ciki ya lulluɓesu. A bazata suka ji Mammah ta ce, “Keys ɗin suna hannun Muhammad ai, ta kira shi nasan zai kawo muku. Dan babu ma jimawar nan ya fita”..            Dariya Biebah ta ƙumshe, haka ma Aunty Mimi. Su dai su Nimrah basu fahimci komai ba. Hankalinsu ma nakan ƙulla kayan da zasu raba dan Mammah ta saka sun kashe kiɗan dan kunensu ya huta. Maimakon Hajiya Hasiba ta nuna jin haushi, sai sukaga tayi murmushi kawai da faɗin, “A to shike nan ai ba damuwa. Bari naje sai ta kira shin”. Tai maganar tana watsama Ummu kallon banza, ita bama tasan tanayi ba, dan tunda ta shigo ko kallonta ma batayi ba.      Tana fita su Aunty Ummi suka saka dariya. Aunty Mommy tace, “Kai Mammah kin iya bada amsa, ALLAH yau sai naga kamar bake ba. Dan na gama shirya zanyi rashin mutunci fa”.         Mammah ta harareta da faɗin, “Ku kuna son bala'i yay barci ne? Shiyyasa ga yaranku nan sun nuna sun fiku iyawa ai.” ta ƙare maganar da kallon su Ruky dake ta hidimarsa. Dariya manyan suka sanya, daga haka hirar ta koma kan su Nimrah ɗin ko tada zancen Hajiya Hasiba babu wanda ya sake yi. Sai bayan kusan mintina arba'in har Mammah ma ta manta da zuwanta sai ga Mu'azz ya shigo wai yaga ana shiga da kaya sashen. Mamaki ya kama kowa, su Aunty Ummi zasu fita Mammah ta hana su.        “Haba Mammah ya zaki ce a barsu, kenan fa ɓalla kofar sukayi?”.      Gwaggo Khadijah ce tai magana yanzu kam. “Suma ɓalla ginin, kar wanda yace musu komai. Itafa shari'a idan zakayi ta yana da ƙyau kayita da hujja. Kuda kuka tara mutane kuna hidima ina zaku biye ai tashin hankali da ku. Ai amsar da Maman Ma'aruff ta basu ya wadatar, abinda kuma suka aikata sai ku jira Haysam ɗin, ai sun san ba kanwar lasa bane ba. Dan wannan karon na roƙeku kada wanda ya shiga wannan maganar a gidan nan, Maman Ma'aruff kema dan ALLAH ki bar Haysam yayi yanda yake so”.         Murmurshi Mammah tayi. “In sha ALLAHU bazan tauye shi ba Addah Khadijah. Dama na saka a raina su ƙarata.”         Daɗi ne sosai ya kama su Mimi. Dan dama sun san Mammah ce matsalar Dada. Idan kuma ta cire hannunta komai zai tafi yanda suke so. Ai koda akace kada suyi magana wlhy sai sun gasama Nabeeha aya a tsakiyar tafin hannu. Suda suke da babban makami a hannu yanzu Nimrah. Ai zama zasuyi su zuge su Gwaggo Khadijah Nimrah ta tare itama idan son samu ne ma kafin su koma ɗin nan. Dama tunda Dada ya dawo suke wannan ƙulle-ƙullen. Yanzu haka ana gama sunan nan su Ja'afar zasu wuce kawo kaya daga nan zasu haɗo kayan Nimrah dana Biebah. Iya su suke ƙulle-ƙullen su sunƙi bari Mammah ta sani balle Dada ko uwar gayyar Nimrah da bata ma san da auren ba........✍️ 78 .......★A ɓangaren Hajiya Hasiba tana komawa wajen su Nabeeha tai kiran wani yaronta mai yin ƙofifi. Babu jimawa kuwa yazo. Bata gayama su Nabeeha abinda ya faru ba. Ta kuma gargaɗi Amima. Yaron nata ne yay dabarar kwance injin key ɗin ƙofar gaba ɗaya, sai dai kuma ya kasa maidawa dan ya lalata shi. Bata damu ba tace ya ajiye musu, idan sunga zasu gyara sa gyara. Ko su cire ƙofar su canja.      Matuƙar haɗuwa fa sashen ya haɗu. Sai dai yanda tsarin ƙasa yake ya tabbatar da na zaman mace biyu ne, kasancewar ƙofofin duk a buɗe suke suka shiga ko'ina. 2 bedrooms ne, da falo ɗaya babba sosai, sai ƙarami, sai kicin, store. A kwai bayi a babban falon sannan akwai a bedrooms ɗin. Acan sama ma ƙaton falo ne guda ɗaya sai bedrooms biyu, sukam ma duk suna a kulle ne.         Cikin kuka Nabeeha ta ce, “Momy mi hakan ke nufi? Haysam na nufin harda waccan yarinyar.....?”.      “Haysam ko munafukar uwarsa da ƴan uwansa da wannan shegen Imran ɗin. Shi da baya nan sukai gini miye nashi”.      Nabeeha zata sake magana Ismat ta riƙe mata hannu. Ƙasa-ƙasa ta ce, “Aunty wlhy kada kima kanki ganganci, duk da baki san manufar Momy akan dawowar ki gidan nan ba koba komai kin tsira. Ya kamata ki sani fa yaƙin gidanki a hannunki yake, ke ya kamata kiyi. Kuma yanzu duk da bata faɗi abinda ya faru ba da taje can sashen yanda aka ɓalla ƙofar nan ya isa ki fahimci bada yardar mutanen gidan nan bane, sun hana keys ɗin kenan. Ina baki shawara kada kiyi abinda zaki rasa Dada gaba ɗaya a wannan karon, dan ba ƴan uwansa kawai ba har Mammah a wannan gaɓar ta shirya hakan”.        Sosai zantukan Ismat sun shigi Nabeeha. Dan kasa cewa komai tai sai bin Ismat ɗin da idanu. Hajiya Hasiba ta zaɓa sashen da za'aima Nabeeha jere da kanta, kamfani sukai gwaje-gwajen su, kasancewar dama sun riga sun zaɓi kayan da suke so.       Ƴan suna na shagalinsu ɓangaren Nabeeha ana zafga jere. Hajiya Hasiba da su Ismat na tsaye kan komai suna nuna inda za'a gyara, da kuma abinda za'a ƙara. Kowa na tunanin Dada na gab da dawowa gida kenan daga asibiti da aketa ƙishin ɗin yana jiyya ne. Sai dai yanda a ɓangaren masu gidan babu wanda yace komai babu kuma wanda ya nuna yama san mi su Hajiya Hasiba ɗin keyi yasa ƙananun maganar basuyi tasiri ba. Har suka kammala komai zuwa bayan azhar kamfanin da Hajiya Hasiba suka wuce, su kuma yaran suka hau shara da goge....       ★••★•••★••★        A dai-dai wannan lokacin kuma Nimrah data tabbatar kowa ya gama shagala da bikin suna ta gama shirinta tsaf na silalewa domin ganawa da Dagger. Yayinda Sanda yay mugun saka mata ido kamar yanda ya saba a kwanakin nan.          Sai dai abinda bai fahimta ba Nimrah nada shegen wayo. ALLAH ya bata basirar iya tsara abubuwa duk da ƙarancin shekarunta. Hatta wannan fatin ita ta ƙirƙiresa ta sakama Ruky son ayi a zuciya dan kawai ta samu damar. Dan ta tabbatar koda hidima ta ɗauke hankalin su Mammah a kanta banda Ruky. Amma yin wannan fatin zata samu hankalin itama Rukyn ya koma can ɗin.       Lallai dabarar tata kuwa tayi, dan kamar yanda suka tsara anayin sallar azhar suka fita can bayan sashen Dada da babu yawan mutane da hayaniya suka fara shirya kujeru, wajen an gyara shi ne da green carpet da flowers masu ƙyau. Duk da ba zaman sashen ake ba sanda na ƙoƙarin tsaftacesa bisa umarnin su Ammar. Dan wani lokacin sukanje can suma su ɗan huta.....      Lokacin da suka fara aikin su kuma su Nabeeha hankalinsu nakan nasu aikin, shiyyasa babu wanda ya maida hankali akan wani, musamman daya kasance bata wannan bangon ɓangaren Nabeeha ɗin yake ba. Sun kammala suka koma sashen Mammah yin shiri, dan sabon ɗinkuna su Uncle Ja'afar suka musu har kala uku-uku na suna. Afrah na maƙale da Nimrah, dan haka ta fara shiryata ta mata wayon aikata wajen Mammah. Daga haka itama tahau shiri, su ma su Ruky nayin nasu. Sauri-sauri ta kammala nata shirin, ta idar da sallar la'asar sai ga wasu ƙawayen Bintu sun kira akan basu gane Street ɗin ba. Caraf Nimrah tace ta bata wayar tunda ita ta shirya zataje ta tarbosu. Basu kawo komai a ransu ba ta amshi wayar Bintu ta fito, dan suna da waya daga ita har Feedo.         Lokacin da Nimrah ke fita a gate Sanda na cikin bayi, sai baba maigadi kawai. Shi kuma bai kawo komai a ransa ba jin tana waya tana yin kwatance alamar wasu zata tarbo. Hakama securitys ɗin dake waje, yanda ta tsaya tana waige-waige ga waya tanayi yasa suma basu maida hankali ba, gashi ma abinci da aka kawo musu suke ƙoƙarin fara ci. A wannan lokacin da gaske Nimrah ta fito ne da niyyar tarar baƙin Bintu, amma daga nan tana son tayi waya da Dagger ta sanar masa da anyi magriba ya fito su haɗu. Amma sai mi ta ɗan bar gate ɗinsu kaɗan sai ga su Adeel da Yohan da yake gidansa zaune. Nimrah bata san shi ba, kai ko Yohan ɗin bata sani ba, dan haka ko kallo ma basu isheta ba ta cigaba da tafiyarta tana tunkaro su.         Cak Adeel ya tsaya kansa na wani irin tsuwwa da ganin Nimrah a bazata. Dan yau kwanansa biyu kenan da dawowa ƙasar amma ko mai kama da ita bai taɓa gani ba. Kai koda Ammar ma basu haɗu ba. Ganin kallon da yake mata Yohan ya fahimci akan ta ne kenan Adeel yazo anguwar ya tare, shi kansa yaran biyu suna birgeshi dan yana shan ganinsu idan za'a wuce dasu makaranta haka a mota. Ita dai Nimrah tazo ta gittasu a taƙaice tace musu “Good Afternoon”. kawai, dan gaishe da na gaba da su koda basu sanshi ba wannan tarbiyyarsu ce. Da ƙyar Adeel ya iya controling kansa baibi bayanta ba, sai dai yace da Yohan su dakata a ƙofar gate ɗin su kira Ammar idan yana nan, dan yau bazai iya haƙuri ba sai ya shiga gidan nan duk da yaga anata shiga da fita alamar wata hidima sukeyi.       Nimrah data gotasu kaɗan tana ƙoƙarin sake kiran su Teemerh dan har yanzu bataga wata alamarsu ba kuma ta fara gajiya gashi tayo nesa da gida kawai wata farar mota ta tsaya mata. Ganin motar ba wata babba bace sosai tayi tunanin su Teemerh ɗin ne, dan haka tabi ta da kallo tana ƙoƙarin kai wayar kunnenta kawai taji an fesa mata abu a fuska. A kiɗime ta ɗago numfashinta na fisga zatai magana kawai ta tafi gaba ɗaya, duhu ya mamaye mata cikin idanu, sautin motsin anguwar da ba wani mai yawa ba yay nesa da kunnenta. Daga haka bata sake sanin abinda ke faruwa ba...      Wani mai gadi dake ƙofar gate ɗin wani gida da yay facing inda Nimrah ta tsaya, sai dai motar tai blocking ɗinta dan har yana jin haushi saboda tunda Nimrah ta ɓullo suka zuba mata ido shi da abokin zamansa suna magana kawai sukaga motar tabar wajen a guje. Koda suka duba inda sukaga Nimrah kafin zuwan motar sai sukaga wayam babu komai.         “Anya lafiya kuwa Zailani? Kalli fa yanda motar can ta bar wajen kuma babu yarinyar fa”.       Wanda aka kira Zailani ya miƙe cikin mamaki yana faɗin, “Ai ni nazata ko wanda ta sani ne. Amma gaskiyarka fa wannan gudun marasa gaskiya ne”.     Da wannan surutun suka tsallako titin zuwa inda Nimrah ta tsaya, sai ko ga wayar Bintu yashe a ƙasa, harda abin hannunta da mayafi alamar fita sukai. Wayar su Zailani suka ɗauka, dai-dai nan kira ya shigo. Bintu ce ta kira da wayar Feedo jin Nimrah shiru bata koma ba. Zailani na amsa wayar kafin ma yayi magana daga can Bintu ta ce, “Ninah wai har yanzu baki gansu ba ne?”.        Zailani yaja numfashi ya fesar, sannan cikin son fahimtar da ita yace, “Ba ita bace ba.”           “Kai! Waye to? Ina mai wayar? Ya akai tazo hannunka?”.      Kai tsaye ya bata amsa da, “Akwai fa matsala. Yanzu wata mota ta ɗauki mai wayar suka gudu da ita, shine suka yadda wayar, sai kiyi ƙoƙarin faɗa a gida azo a amshi wayar da mayafinta kuma....”      Wani kalar razannanen ihu Bintu ta saka. Ihun daya dawo da hankalin kowa dake falon ɗakinsu Nimrah ɗin. Suma su Ruky dake ɗauri a gaban mirror tuni sunyi kan Bintu a hargitse. Dan sai kwarara ihu take tana faɗin, “Ninah! Ninah! Ninah”.        Ruƙayya ta fashe da kuka tana faɗin, “Ki gaya min miya samu Ninah ɗin dan ALLAH Bintu, wlhy zuciyata zata buga”. Itama ta fashe da kuka jikinta na rawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin ya cika, kowa Bintu yake tambaya dan ita keta faɗin, sunan Nimrah. Sai da Ummu tai mata tsawa da faɗin ta nutsu tai musu bayani sannan ya faɗa abinda wanda suka kira ya faɗa. Wayar Feedo aka amsa daga hannunta akai kiran layinta, kai tsaye nan ma Zailani ya amsa. Irin bayanin da yayma Bintu kuma yay musu. Hankali ya ƙara tashi, akace ya faɗi inda yake. Babu kwana-kwana ya sanar musu. Tsabar rikicewa wasu ma ko gyale babu akansu suka fito,........✍️ 79 ........Mammah ma sai da aka biyota da takalma. Securitys ɗin wajen gate najin abinda ya faru suka watsar da plates ɗin abinci. Su Adeel sun bar wajen dan sun kira Ammar yace musu baya nan, kuma a gaban securitys ɗin nan akayi, ɗan sanin da sukaima Yohan dakan fito daga gida kullum motsa jiki ko idan zai wuce wajen aiki sukan gaisa yasa basu kawo komai a ransu ba. Kafin kace mi gayyar mutane sun zagaye su Zailani. Kamar yanda sukai bayani a waya haka suka maimaita.         Jikin Mammah rawa yake sosai, dama tunda ta tashi yau gabanta ke faman faɗuwa. Sai ta barshi akan wannan taron ne maybe, da su Hajiya Hasiba sukazo kuma sai take ganin ko sunzo da wata fitina ne dan su ɓata mata taro, shiyyasa ta kwaɓi al'amarinsu cikin sauƙi tanata addu'a, ashe ga abinda ke shirin faruwa nan...     <<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>          A dai-dai wannan lokacin Imran da Dada na gidan Baffa ne. Tare da shi sukai sallar la'asar sukaci abincin rana. Sun sake dasa sabuwar hira da gaba ɗayanta akan al'amarin ƙasar ne sai ga Uncle Nasiru. Wannan ya ƙarama hirar armashi har lokacin la'asar da suka fita massalaci. Bayan sun dawo salla suna shirin daga nan suyi sallama da Hajjo da Baffah, sai dai da yake Baffa akwai son hira abinka da tsufa sai ya ƙara riƙesu da labarinsa. Da ƙyar ya sakesu suka fito suka barshi da Uncle Nasiru.      Kai tsaye gidan nan na sirri da suka sakama suna UNIT ZERO suka nufa. A yanzu gida ne bana kai tsaye ba. Komai a cikinsa da tsari da tsaro. Suma kansu sai sunbi tsarin suke shigarsa musamman security na ƙofa da baya buɗewa sai da password. Kuma su biyu kacal suka sani. Imran ya saka Password ɗin ƙofar ta shige. Sun shiga kenan sun zauna Imran na ƙoƙarin buɗe laptop da faɗin, “Dabo ya tura min saƙo yanzu nan, idan ka basu izinin zasu ƙaraso shi da Yusuf”.        Kafin Dada ya bashi amsa motsin da wayarsa tayi ƙirar Samsung a karo na kusan uku kenan yasa shi jan ɗan siririn tsaki. Ajiye haɗaɗɗen pen ɗin hannunsa daya ɗauka shima saman takardar da zai yi rubutu yayi, sannan ya ɗago yana mai ɗaukar wayar. Ganin sunan Mu'azz ga miss calls ya jera masa kuma ya cigaba da kira ya sashi ɗaga wayar ya kai kunnensa a nutse, kafin ya motsa lips ɗinsa cikin dakakkiyar muryarsa dake a buɗe irin ta ainahin jaruman maza ya furta, “Kai ka iya damun mutane suna aiki ko?”.       Cike da girmamawa daga can muryar Mu'azz na rawa ya furta, “Dada. Dama Ninah ce ta fita wai tarar ƙawayen Bintu a waje wai wata mota ya ɗauket.....” kuka ya sarƙe shi ya kasa ƙarasa faɗa.       Wani irin duka zuciyar Dada keyi a cikin ƙirji. Ya dai daure cike da dakiya ya ce, “Ita kaɗai ta fita a gidan?”.        “Eh ita kaɗaice sai wayar Bintu.......” nan ya bashi labarin duk yanda su Ruky sukai bayani akan fitar tata da abinda kuma masu gadin nan suka sanar musu.     Kasa cewa komai yay, sai ya katse kiran gaba ɗaya yana furzar da iska mai nauyi.        “Lafiya dai?”.    Imran daya maida hankali a kansa ya tambaya.       Sai da ya ajiye file ɗin hannun nasa kafin ya furta, “Muje gida akwai matsala.........” a taƙaice yay ma Imran bayani. Cikin ƙanƙanin lokaci Imran ya rikice. Tuni shima ya miƙe yana kashe laptop ɗin. Dada ma miƙewa yay yana sake kiran Mu'azz da saka wayar a hans free ya ajiyeta saman center table ɗin yana fara tattare takardun daya gama bazawa yanzu nan, sai dai kunnensa nakan wayar.        “Dada naji ka katse ne!”.     “Kai kaɗai ne a gida?”.     “Eh, amma an kira su Uncle Ja'afar suma gasu nan tafe. Kaima tun ɗazun su Mammah ke gwada kiranka yaƙi shiga, shiyyasa hankalinmu ya ƙara tashi sosai.”      “Gani nan zuwa gidan”.   Ya faɗa yana nufar ƙofar fita. Imran yabi bayansa. Hankalisa a natuƙar tashe ya kallesa, “Haysam kodai a sanarma jami'ai ne?”.         “Imran karka ruɗa kanka, ko su wanene suna da dalili....” Ya faɗa dai-dai yana ƙoƙarin ficewa, dan haka shima Imran ya zabura. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan. Gaba ɗaya a compound suka same su, idan ka cire Mammah dake falo da su Ja'afar da suka ƙaraso. Amma sauran mutane da yawa ƴan suna duk suna compound, a hakama kasancewar yamma tayi mutane sun ragu sosai sai iya na jiki-jiki.      Yanda ya ɓalle murfin motar ya fito. Ya isa ya sanar maka lallai kam shi ɗin tsayayyen mutum ne kuma jarumin sadaukin gaske da ko'a cikin sojojin ya isa a kirashi BARDE. Ga dai shekaru sun ja amma da alama har yanzu jinin jikin da ƙarfinsa yake gudana. Dan yanda yake taku ma kawai ya isa ka shaida asalin ZAKI ne, kuma tabbas a ƙuruciya an baza capacity iya capacity na manyan BARADA. Daga shi har Imran ɗin nasa a tsayensu suke.       Badan da yawan wanda ke wajen sun san shi waye ba da sai suce kamar babu damuwa a tare da shi ma. Amma shi Imran yasan waye Zakinsa. Tarnaƙi baya bayyana kai a fuska sai a cikin zuciya da kwanji.       Suna isowa wajen cike da girmamawa aka fara gaishe su, Imran ne kawai ke amsawa. Shi kam hannu kawai ya ɗaga musu ya wuce hanyar falo Agogon hannunsa ƙirar Maawad Company ya kalla, ganin lokacin sallah na sake matsowa. Tura ƙofar da shigarsa ya saka duk wanda ke a falon juyowa, sai kuma duk suka miƙe a kusan tare, banda Mammah da Gwaggo Khadijah.      Kai tsaye Ja'afar da Ma'aruff suka nufosu suna musu sannu shi da Imran, shima idonsa a kansu dan haka ya jinjina musu kai. Ruƙayya dake jikin Mammah tana kuka ta taso da gudu ta shige jikinsa tana sake fashewa da kuka.           “Dada Ninah ɗita, zasu cutar min da ita, dan ALLAH kuje kaida Daddy ku dawo da ita...”        “Ya isa haka. Ki mata addu'a ALLAH zai kareta a duk inda take”.      Kai Ruky ke jinjina masa amma hawaye sun gagara tsayawa. Kama hannunta yay suka ƙarasa cikin falon sosai.       Cike da girmamawa su Ammie dake falon suka shiga gaishe shi. Dan har sun gaisa da Imran ya zauna shi. Amsa musu yay batare da ya kallesu ba, sai kuma ya nufi inda Mammah take. Har ƙasa ya rissina yana gaisheta, ta amsa da kulawa da tsantsar damuwar dake shimfiɗe a fuskarta. Tashi yay ya koma a kujerar kusa da ita ya zauna, tare da riƙo hannunta cikin nashi, dai-dai nan Ammar da Bilal suma suka ƙaraso. Suma gaishe su suka yi. Imran ya amsa musu da kulawa, shi ko hankalinsa nakan Mammah yana mata magana ƙasa-ƙasa. Hawaye Mammah ta share tana jinjina masa kai.       Imran ya katse shirun da faɗin, “Ya akai ta fita ita kaɗai?”.        Aunty Ummi ta share hawaye tana bama Imran ɗin amsa da, “Babu wanda yasan ta fita wlhy Yaya, gaba ɗayansu suke hidimar su can bayan sashen Dada, sai da aka kira la'asar suka shigo sukai wanka, dan ita tama sakko ta kawo Afrah wajen Mammah ta sake komawa, ni wlhy hankalina ya fara tashi, mi Ninah zataima wani da har zai yi kidnapping ɗinta, dole yana cikin gidan nan tun ɗazu tare da mu. Kuma ni gaskiya ina zargin.......” Kallon Da Mammah ta mata ya hanata ƙarasawa.      Imran daya lura da abinda Mammah tayi sai shima bai nema ƙarin bayani ba. Kallonsa ya maida kan Ruƙayya, cikin bada umarni ya ce, “Tashi zaune”.       Tashi tayi sosai ta zauna. Kafin ma ya tambayeta ta faɗa masa komai daya faru. Aka kira Bintu da Feedo suma. Wayar Bintu ɗin ya amsa. Yay ƴan bincike-bincikensa ya miƙa mata. Ya maida hankalin sa ga Dada dake kwance jikin kujera idanu a lumshe Mammah tai magana muryarta na nuna damuwa sosai, “Ni nama rasa wane irin tunani zanyi. Dan koma su waye suka aikata idanunsu na kanta ne shiyyasa har suka san fitar tata kamar yanda Ummi ta faɗa. Idan suka cutar min da yarinya bazan yafe musu ba, Imran kuje ku nemomin yarinyata kar ku barta ta kwana a wani waje dan ALLAH.”       Dada ya ƙara damƙe hannunta dake cikin nashi, sai kuma ya buɗe idanunsa dake rufe amma duk abinda ake yana saurarensu, cike da lallashi da kulawa, murya a tausashe ya ce, “Please Mammah calm down, in sha ALLAHU babu abinda zai faru...”       “Muhamamd ta ina hankalina zai kwanta kuwa, kasan mi ake nufi da rashin budurwar yarinya kuwa?. Dan ALLAH kuje ku nemo min yarinyata”.     “In sha ALLAHU Mammah, bari muje muyi salla gata can ana kira. Kuma kuyi, kuyi mata addu'a ita tafi buƙata a yanzu kamar yanda Haysam ya faɗa”.     Kanta ta jinjina ma Daddy Imran mai maganar tana share hawayen da suka cika mata ido da hijjabin jikinta. Miƙewa su Ja'afar sukayi. Imran ya kalla Dada da bai motsa ba. Idan ka kallesa sai ka rantse bashi da wata damuwa, amma ya fisu jin tashin hankali, musamman ma furucin Mammah, kawai dai mazan maza ne shiyyasa ya shanye komai yanata nazarin abubuwa ne. Tare suka fita da ƙannen nasa da Imran masallaci.........✍️                 80 .......An idar da salla, koda suka fito a massalaci wajen su Zailani Mu'azz yay musu rakiya. Sun sameshi yana salla a ƙofar gate daga ciki, koda ya idar tasowa yay, dan yana ƙyautata zaton ƴan gidan su yarinyar nan ne da aketa masa zirga-zirga tun ɗazun, shiko bai gajiya da bada duk amsar tambayar da akai masa.         Nutsuwa ya sake yi ganin masu zuwan yanzu. Ya rissina yana gaishe su dan bazai wuce sa'ar Ammar ba shi kam. Tambayoyi Imran yay masa, ya amsa kamar yanda yake amsawa kowa. Har suka gama Dada baice komai ba, sai daga ƙarshe ya tambayi kalar motar, sai kuma number ɗinta ko zai iya tunawa.         “Wlhy ranka ya daɗe bazan iya cewa ga lambar jikin motar ba. Amma dai Camry ce fara mai baƙin gilashi. Da alama kuma wani abun suka hura mata ko shaƙa mata shiyyasa ko ihunta bamu ji ba sai da suka wuce, dan babu wani motsi da sukai da za'a iya zarginsu.”       “Ya isa”. Ya faɗa a hankali yana kama hannun Mu'azz. Gida suka koma, Imran ya balbale sojojin dake gate da faɗa irin wanda basu taɓa sanin ya iya ba. Dan shi kansa Dada idanun kawai ya zuba masa, daka ƙarshe ma murmurshi ya nema suɓuce masa sai da ya zo ya kama hannunsa suka koma cikin compound. Cike da lallashi ya ce, “Relax Imran. Ko su waye irin wannan fusatar suke son gani daga garemu har mu kasa tunanin abinda ya dace. Gaskiyar Mammah kosu waye sunga fitar ta, sannan ba ɗaukarta ya kawosu ba, basu samu abinda suka shigo yi bane sai suka samu ita ta fita, shine sukai amfani da damar....” yay ɗan shiru, sai kuma ya maida hankali kan Imran daya zurfafa tunani.        Iska ya ɗan furzar kaɗan. Cikin dakakkiyar muryarsa ya cigaba da faɗin, “Ina son ganin Dabo yanzun nan.”      Iska Imran ya ɗan furzar shima cike da gamsuwa da zantukan Dada, ya ce, “Amma mi Ummi ke son faɗa Mammah ta hana ta?”. “Ina sane da batunta karka damu”. Kai Imran ya jinjina, zai yi magana wayarsa ta fara vibration, dan haka yay shiru, sai kuma ya ciro wayar a aljihu yana ɗagawa ya kai kunnensa. Baiyi magana ba, dan ko tsayawa kallon lambar baiyi ba tsabar hankalinsa da tunaninsa basa jikinsa,  a maimakon sallama da dariya ya fara cin karo. Hakan ya sashi janye wayar a kunensa ya danna recording sannan ya saka a hansfree har Dada yana saurare. Sai da aka gama dariyar cike da iskanci kafin a fara magana.         “Imran Abbas!... Ko nace Yaron Zak-Shadow. Nasan kana kusa da shi a halin yanzu, dan haka ga saƙo zan isar kai tsaye a gareshi. Ashe shi matsoraci ne ban sani ba, irin wannan zubda girma haka, miye na ɓoye kai? TSORO NE?. Koda yake mubar ma wannan batun, awanni uku kacal da fara wasan har kun fara kai-kawo kuna cikama mutane kunne da ihu yannn!! Yannnn!!. Uhhmm! Koda yake banga laifinsa ba, dolene duk wani lafiyayyen namiji ya ruɗe akan wannan ƴar shilar matar tasa. Ƙyau iya ƙyau, ga jikin nata kuwa yay mata ɗas tamkar an zanata a takarda, kasan irin waɗan nan ƴan shilar da daɗi na musamm.....”       A tsawace Imran ya katse shi da faɗin, “Kai tsinanne, ka kiyayi wasa da GOBARAR JEJI, domin idan ta tashi zatai maka mummunar ƙuna ne da ko suffarka ta mutum mai halayyar dabbobi baza'a shaida ba!”.         Tamkar Imran ya karanta abinda ke zuciyar Dada ne dake jingine jikin mota ya wani lumshe idanunsa. Sai wani kalar kaɗa yatsun hannunsa na dama yake. Hakan kuma na nufin zuciyar mazan fama tana a maƙoshi...        Shi kansa mutumin sai da yaji razani daga muryar Imran dama kalaman kansu, dan bai taɓa tunanin Imran nada zafi haka ba. Amma sai ya danne cike da raunin wayo ya ce, “Oh oh! Nayi shiru! Nayi shiru! Kawai nima naga ya dace ne na yaba halittar UBANGIJI ne. Amma shike nan! Shike nan chapter closed. To amma shi ubangidan naka tsoron magana yake ji daya kasa magana sai kai? Koda yake nasan ya zama ɗan wasan ɓuya ne, to ga saƙo a faɗa masa. Nasan yana son ganin GUDAN JININSA daya ɗauki tsawon shekaru yana nema ido rufe, na tabbatar kuma akan ƴar shilar tasa ya ɗora samun cikar wannan burin ko? Kaga ko zai so ta dawo garesa hankali kwance cikin ƙoshin lafiya. To komai mai sauƙi ne, buƙata ce ɗaya rak muke da ita sai mu samar da hakan mu kuma a gareku. Ka janye yaranka dake ƙofar yamma na awa ashirin da huɗu kacal. Mu da kammu zamu maido maku matar ubangidanka a inda muka ɗauketa.....”        “Kai ɗin banza...”     Babu wanda bai zabura ba a wajen dan su Ma'aruff ma sun fito babu jimawa. Yanda ya faɗi (Kai ɗin banza...) ɗin da doka glass ɗin motar dake gefensu har sai da glass ɗin ya tsage. Da sauri Imran ya ajiye wayar ya riƙe hannun nasa da jini ya wanke yatsun alamar yaji ciwo.        Daga ta cikin wayar da suka zata Imran ne yay maganar aka furta, “Okay! Ashe kuwa taurin kanka zai sake maimaita maka tarihin daya shuɗe a baya, tare da tukuycin rasa matar oganka da ƴarka dan itama gab take da zuwa hannun mu. Na kuma dawo naima waɗan nan zaratan samarin ƙannen nasa tsinci ɗai-ɗaya, na rufe tarihinku da waɗanan tsoffin guda huɗu. Awa ashirin da huɗu!!”.      Ya faɗa yana yanke wayar gaba ɗaya yana dariyar iskanci. Hannun Imran kawai Dada ya rimtse a cikin hannunsa da masifar ƙarfi, hakama idanunsa a rufe suke ruff. Sai da Imran ya dinga faɗin, “Haysam calm down, relax, relax please”.         <<%>><<%>><<%>>          Da baya-da-baya Malam Buba ya dinga barin inda yake laɓe. Dan yau ya maƙale a gidan har akai magriba bai wuce ba. Duk da dai dama yakan kai hakan wani lokacin. Yau ɗin kuma rarumar rashin Nimrah ta zaunar da shi. Da farko hankalinsa a kwance yake da tunanin aikin Dagger ne. Sai dai yanzu kiran da akaima Imran ya sashi shan jinin jikinsa. Duk hatsabibancin Dagger yasan bazai kira Imran a waya ba. Musamman yasan Zak-Shadow na nan. Tashi wayar ya ciro bayan ya shiga bayin su yay kiran Dagger. Kamar yanda ya saba ya amsa masa, sai dai ko gaisuwa bai bari ma sunyi ba ya ce, “Oga Uwa na hannunka ne?”.          Dagger dake faman busa sigari saboda haushin Nimrah data raina masa hankali tun ɗazun yake jiran kiranta shiru yaja tsaki. “Mtsoww! Yaushe ma na ganta da har zata kasance a hannuna. Yarinyar nan fa ƴar rainin hankali ce, na fahimci akwai abinda take ƙullawa....”        Cikin matuƙar kiɗimewa Mole yace, “Ban gane ba, oga anfa ɗauke uwa ɗazun da la'asar yanzu haka hankalin ƴan gidan duk a tashe yake. Nayi zaton kaine ka ɗauketa ma shiyyasa naketa nemanka wayar bai shiga ba. Sai yanzu da aka kira Imran naji mai maganar ba muryarka ba dan a amsa kuwwa suka saka, ni kuma ina laɓe a bayan mota. Sannan kalmar MATARSA da suka kira uwa da ita ya sake tabbatar min bakai ɗin bane, na kuma sake shiga ruɗani......”         “MATARSA?!!”.      “Tabbas haka naji mai kiran wayar ya faɗa.”      Wata shegiyar ashariya Dagger ya lailayo ya dire yana miƙewa. “Eh lallai wannan mutumin mutuwa yake so da gaske. Shi tsohon nan ne zai ce Nimrah matarsa?”.          “Bafa shi ya faɗa ba, wanda ya kira waya ne ya faɗa.....”      “To shi ya musa zancen ne?”. “A'a gaskiya, ni yanzu ba wannan kaɗai bane tashin hankalina. Sanin waye ya ɗauki min Uwa. Oga wlhy Naja'atu itace rayuwata.”         “Nima itace rayuwar tawa ai!!....”    Dagger ya faɗa cikin ƙarajin da dole Malam Buba ya yanke wayar. Gaba ɗaya ji yake duniya na juya masa ma, kansa kuwa kamar ana buga masa ƙusoshi a ciki..... ★★★            Ba Malam Buba ne a ƙaulani kawai ba. Shima Sanda a cikin irin wannan yanayin yake. Dan shima dai kamar yanda Malam Buba yaji komai tunda a compound suke shima yaji. Jiki na rawa ya nufi bayan ɗakinsu jikin ɗakin Gen... Da Nimrah ke maƙalewa idan zatai waya shima ya shiga neman ogansa. Yana ɗagawa ya zayyane masa abinda ke faruwa. Kafin shima cikin tuhuma ya ce, “Ko kai ne ka ɗauke ta?”.        “Kamar ya ni? Wace magana kake haka? Ni a kanta nake wasana ko akan Haysam. Sannan ma wannan ƴar yarinyar ce MATARSA? Ina waccan to?”.          “Nima batun matar tasa da aka ce ya bani mamaki. Matarsa kuma naga ta dawo gidan yau, banama tunanin ya sani, ko kuma wannan al'amari ne ya kiɗima shi. Dan gaba ɗaya fa hankalin gidan a tashe yake. Kasan da yarinyar da Ruƙayyan nan sune zuciyar gidan. Kodai wanda take yawan waya da shi ne ya sace ta?”.       “Tabɗi jan yau naji abinda yafi ƙarfin kaina, amma sai na ci uban Almu kuwa. Ya akai bai taɓa kawo min wannan labarin ba? Wannan fa shine tirƙa-tirƙa”.         “Ta gasken gaske kuwa. Yanzu miye abinyi?.......” ★★★         Acan bayan sashen su Bilal da babu kowa a ciki wata ce cikin irin wannan ruɗanin. Ita tana ta faman neman layin nata ogan amma yaƙi shiga. Ga labari tana son isar masa na abinda ke faruwa. Amma fin kira ɗari wayarsa na saka mata busy, daga ƙarshe dai ta yanke shawarar rubuta text message ta tura masa, a ranta tana addu'a da fatan ALLAH yasa ya gani da wuri. Dan wannan al'amari ya matuƙar rikita lissafinta. Musamman batun kasancewar Nimrah matar Dada. Bata taɓa jin maganar datai mata bazata ba a tsahon rayuwarta irin yau ɗin nan. Dan mutanen gidan basu taɓa yin zancen ba.....✍️ ALHAMDULLAHI. BOOK 3 LOADING....... ƘARSHEN WASA. ƘARSHEN YAƘI. TUSHEN SOYAYYA. Su waye da wannan aika-aikar? Dan a wannan gaɓar kowa abin zargi ne. Kungiyar duhu? First Lady da mijita?. Nabeeha da uwarta? Mole? Sanda? Shugaban dan sandan farin kaya? Shugabannin makaranta? Kai harma da wanda ban lissafo ba. Ga Nabeeha ta dawo. Dada zai amsheta kuwa? Batun aure ya fasu. Kokwanton Nimrah ya ƙare. Karna cikaku da zance. BOOK 3 ya haɗa komai da kuke buƙata, harma fiye da... Dan anan komai zai baje kansa-da-kansa...🥰🥰🥰❤️🔥🤸. Kumuje zuwa kawai ba wasa🥱🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️      Kwana biyu ido ya sani gaba shiyyasa kuka jini shiru.🥲      bilyn Abdull ce🥰🥰 C-27/12/2025. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels