An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1 *بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم* _Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._ ........Ƙarfe uku da mintuna ashirin da biyar jirgin daya taso daga birnin tarayyar Nigeria Abuja ya sauka a *_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT_* da ke a Kanon dabo. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikinsa suka fara fitowa. Vvip section ƙyaƙƴƙyawar budurwa dake cikin ado mai tsananin ɗaukar idanun duk wanda ya kalleta ta miƙe a hankali tana ɗan wani ɓata fuska tamkar mai jin warin mutane. Sanye take cikin wasu shegun wando da riga da sukai tsananin fidda cikakkiyar surarta musanman ma wandon jeans ɗin da ya kasance fari tas, an ɗan faffasashi daga cinyarta da gwiwa har ana iya ganin kalar fatarta. Siririn veil kalar pink mai haske da yay dai-dai da kalar rigar jikinta shima data ɗan yana a saman kanta ya matuƙar ƙawata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta, sai bag fara tas da adon stones pick and blue daga gani kasan mai tsada ce. Ga wani shegen takalmin mai tsananin tsini sai dai ya matuƙar ɗauki ƙafar tata musamman da wandon ya kasance baije ƙasa can sosai ba kuma yabi jikinta ya lafe luf sai ya bama siririyar sarƙar ƙafarta da taji adon stones pink and blue damar fitowa ɗar. Yanda ta rufe idanunta da eyeglasses blue ya ƙara saka fuskarta kwarjini da bayyana ƙyawunta mai sanyi, sam fuskarta babu alamar wata fara'a, sannan babu kwalliya ko ɗigo idan ka cire ɗan lipstick kalar pink mai shining data zizara ma laɓɓanta. A kallo ɗaya zaka ɗauka bata san minene ko murmushi ba, sannan zaka iya kiranta da ƙabilar kudancin ƙasar, dan babu ta inda tai kammani da Hausawa ko yankin arewacin ƙasar musamman inda addinin Muslunci keda ƙarfi irin su kano. A hankali taja ƙaramin tsaki dai-dai tana miƙewa da tura wayarta cikin aljihun wandonta, headphones ɗin kunnenta kalar pink ta gyarama zama, tare da gilashin idonta sannan ta ciro ledar chewing gum ta ɓare ta jefa a baki tana ballama saurayin dake ta bayanta kaɗan harara, tun ɗazun ya dameta da kallo dan jaraba har zuge labulen da ya rabasu yayi. Bag ɗinta ta fisga ta ɗora a kafaɗa ɗaya sannan ta ɗauka Apple laptop ɗin ta tana sake jan siririn tsaki ganin shima ya miƙe tai ficewarta cikin takunta na ƴammata marasa jin magana.. Yanda take taku tsinin takalmin nata na bada wani irin sautin jan magana, ga sautin madaidaicin akwatinta da take gungurawa tamkar a gajiye ya jawo hankalin mutane da yawa gareta. Caaaa idanu da yawa a kanta, wanda basu iya gani suyi shiru tuni sun fara tankawa, wasu ƴammatan kuwa kishine ya lulluɓesu, yayinda samari da yawa sukai mutuwar tsaye da ganin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta. Ita dai daka ganta kaga cikakkiyar baƙar fata haihuwar Africa sai dai ɗabi'u da shiga duka ba namu bane. Ga wani shegen ƙamshi da duk wanda ke a kusa da ita kaɗan dolene ya jisa saboda yanda ta bulbulashi kamar ba mace ba. A yanda take juya madaidaita lips ɗinta a taunar chewing gum ɗin bakinta kawai dole ya tada hankalin mai kallonta. Dan duk namiji mai tsantseni ya dubeta sau ɗaya bazai sake yarda yay na biyu ba kodan tsoron ALLAH... *_Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi_* kenan da akafi kira da suna _Lulu ƙamshi_ ƙyaƙyƙyawar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da huɗu a duniya. Itace ɗiya ta uku a gidansu. Mahaifinta sananne ne da kowa yafi sani da Engineer Isma'il l. Jiƙamshi. Babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin *_Jiƙamshi Motors_*. Mawaddat yarinya ce da batajin magana, gata masifaffiyar gaske ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu musamman wajen mahaifinsu Engineer Isma'il Ibrahim Jiƙamshi da Kawunta Yousuf Ibrahim Jiƙamshi. Gatan data samu da rayuwar turai data tashi a ciki ya sata zama fanɗararriyar gaske. Ga rashin kunyar tsiya. Dan kowace irin shiga Lulu ƙamshi zata iya fita da ita waje ko zama a cikin gida in har ba Uncle ɗin su Yusuf yana kusa ya tsawatar mata ba. Mawaddat ta samu wadataccen ilimin boko, dan a yanzu haka ita ɗin lawyer ce mai zaman kanta, duk da dai karatun ma da ƙyar ta iya kammalashi saboda rashin jinta, gaba ɗaya karatunta a ƙasar ƙetare ta yisa idan ka cire Nursery school datai a Nigeria. Sai dai a ɓangaren ilimin addini kam fanko ce, dan ko faatiha Lulu ƙamshi ba lallai ta kawo maka ita dai-dai ba. Sam bata son harkar talauci, ba kuma ta son talaka. Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shine kasancewa da namiji. Ko kai ɗan uban waye a kuɗi ko nasabar zuri'a baka ishi Lulu ƙamshi kallo ba, dan ko turawan sun buga sun barta kam, hannunka ma yace zai yi gigin zuwa jikinta komai shigar rashin mutuncin da tai zata sauke maka kwando-kwandon masifarta. Ta dai yarda ta shiga club aci uban rawa ayi nishaɗi tai gaba. Sai sirrintaccen harkar da takeyi da har yanzu babu wanda ya sani a gidansu, dan tana aikatawa ne cikin taka tsantsan da kula, shiyyasa har yanzu babu wanda ya ganota duk da an ɗan taɓa samun akasi tsakaninta da Uncle Yousuf dai ya kusa harbota ta kuɓuta da ƙyar. Wannan itace Mawaddat Isma'il Jiƙamshi (Lulu ƙamshi) a taƙaice. Saurayin nan da suke tare tun daga cikin jirgin sauri yake na son cin mata, duk da yanda take takun nata cike da yauƙi da yanga. Wannan ita kaɗai ce damar data rage masa, gashi kuma tana neman kufce masa. Tunanin hakan babbar asarace a garesa ya sashi ɗaga murya wajen faɗin, _"K! Sarauniyar mata. Son kowa ki dakata mana!!"._ Ɓuɗaɗɗiyar muryarsa da tsarin adon dake nuna shima ɗin wani shege ne ya saka mata da yawa tsayawa cak, sai kuma suka shiga juyawa suna kallonsa. Sai dai abin mamaki ita ko nuna lamar ma tasan yanai batai ba tafiyarta take. Ganin ya cigaba da ƙoƙarin cimmata ƴammatan da duk suka juya garesa suka shiga taɓe baki da yatsine fuska. Ko kallo basu ishesa ba sai ƙoƙarin cimmata da yake yi dai-dai tana ƙoƙarin isa ga inda motocin ɗaukar mutane keda hurumin tsayawa. Wani shegen kallo ta watsa masa fuskarta na sake tsukewa. Fuska ya marairaice yana mai haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo gareta, amma saita ja masa tsaki zata cigaba da tafiyarta. Sake shan gabanta yayi da faɗin, "Haba mana Babie ki saurareni koda akan abu ɗaya ne Please. Address ko phone number abeg you". Cike da yauƙi da yanga ta furta, "A matsayinka na wa?". Duk da yay mamakin jin hausa a bakinta sai ya shanye, cikin murmushi ya ce, "Neighbour naki a jirgi mana beauty!. Sunana MM Atik Kumo. Mahaifina M Atik Kumo sunane da duk wanda ya kwana ya tashi a Nigeria dama ƙasashen Africa ya sansh....." "Kai dalla can ka isheni da zance yannn-yannn!! kamar tsohuwar akorukura. Bani hanya kona wanke banzan face ɗin nan naka zubin alakoro da mari stupid". Ta faɗa cikin katsesa da yarfi ta bi gefensa ta wuce. Tamkar gunkin da aka sassaƙa domin tarihi haka yay tsaye ƙiƙam yana kallonta, hakama duk wanda ke kusa da su sai da yay mutuwar tsaye akan abinda tayi. Dan kowa dai yasan wanene sunan MM Atik Kumo, amma yarinyar nan mai zubin yahudawa tai masa wannan yarfin. Kuma ko'a jikinta kamar yanda shima babu alamar zai ɗauki wani mataki..... "Laahhh *_Uncle Smart_* ga Aunty Lulu ɗin nan". Wani ɗan ƙyaƙyƙyawan yaro dake saman jibgegiyar mota baƙa siɗik ya faɗa yana nunata. Wanda ya kira Uncle Smart dake gefensa tsaye kansa a ƙasa da keypad waya ƙirar Nokia a hanunsa ya ɗago a hankali tamkar mai ciwon wuya.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏 _* [7/18, 2:27 PM] Maman Aslam: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣ ........Ƙyakykyawan saurayi ne chocolate color mai cikar kamala da nutsuwa. Baida hayaniya a yanayinsa na zahiri bai kuma da fara'a sam akan fuska. A halittar jiki da cikar kamalar fuska mai nuna barazana ko maƙiyinsa dole ne ya yarda yaci wannan suna na *_Smart_*. Maimakon kallon wadda yaron yay nuni da kira Aunty Lulu sai ya ɗaga shi cak ya sauke ƙasa kawai tamkar ma baiji ba. Da gudu kuwa yaron ya nufeta cikin farin ciki da ihun kwakwazo yana mata oyoyo Aunty Lu. A hankali ta saki murmushi daya ƙara ƙawata ƙyawun fuskarta a karo na farko tana mai tsayawa cak har yaron ya ƙaraso gareta. Yana dab da zuwa gareta ta ajiye laptop ɗinta a saman akwatin dake ɗayan hanunta ta tarbi yaron. Dai-dai nan MM Atik Kumo da ya biyota ya ƙaraso wajen. A hankali murmushin dake a saman fuskarta ya fara ɓacewa, cikin ƙanƙanin lokaci fuskarta ta koma asalin yanda take. Cikin fushi da tsananin ɓacin rai ta watsa masa kallon nan nata na raini da wulaƙanci. A fusace ta furta, "Halan kai babu zuciya a ƙirjinka? Nifa a duniya na tsani wasu *_MAYUN MAZA_* wlhy". _(Mayun Maza!!!)_ Kalmar tai wani irin amsa kuwwar maimaita kanta a cikin kunnensa duk da bashi aka faɗawa ba. A hankali ya ɗago fararen idanunsa masu girma karan farko ya saukesu a kanta. Dai-dai nan itama cikin tsiwa ta nuna MM Atik Kumo da yatsanta mai ɗauke da farce data ƙara a duk farautan hannuwan nata biyu da ƙafafu. Ɗauke idanun nasa yay da sauri wani irin sukar baƙin ciki na tokare ƙirjinsa, a duniya ya tsani mace irinta da zata iya saka kowane irin kaya ta fita kamar yanda take, tun daga samanta har ƙasa babu suffar mace musilma bahaushiya a tare da ita. Siririn tsaki yaja yana sake tamke fuska sai dai kunnensa na garesu. Itako da bata san yanayi ba yi take kamar zata tsole ma MM Atik Kumo ido da yatsanta data nunashi da shi. A cikin kaushin murya take faɗin, "Wlhy! wlhy! idan ka sake gigin zuwa gabana a karo na uku saina wulaƙantaka a wajen nan, mafi munin wulaƙanci, na yaga maka rigar mutunci kuma, danni *_FURAR DANƘO CE, A SHEKARA ANA DAMU BA FARAU-FARAU!!._* Mtsowww ban san damuwa ok". Fuuuu ta figi hannun yaron da ya tsaya kawai yana kallonsu tare da lap-top ɗin ta tai gaba batare data ja akwatin ba. Babu alamar gargaɗin nata ya zafi MM Atik Kumo, dan wani murmushin ma ya saki da bin ƙugunta da kallo a ransa yana maimaita kalmar _(Furar danƙo a shekara ana damaki baki farau-farau)._ Wani shegen yawu ya haɗiye yana lumshe idanunsa da suka wani ƙanƙance tare da lashe lips ɗinsa. A gaban motar da Uncle Smart ya ke tsaye taja birki, cikin hucin takaici tai masa kallon sama da ƙasa fuska a yatsine. "Kai kuma malam haka ake aiki a garinku? Kana kallon mutane da kaya bazakaje ka amsa ba!!?". Idan motar nan ta motsa to shima da ke jingine a jikinta ya motsa. Wani irin baƙin cikine ya sake turniƙe mata zuciya, "Kai sakarai kai waye da har ina maka magana zaka ɗauke mun kai? kan bala'i.....!" Da sauri yaron ya katseta da faɗin, "Aunty Lu! Uncle Smart ne fa! Shi bai san ihu, muma idan zai kaimu school ca yake muyi shiru a mota, kuma Daddy ma baya masa ihu ki bari kem....." "Kai dalla yimun shiru. Shi ɗin waye da baza'a masa ihu ba. Shashasha da shi driver mai jiran wata tayi a bashi dubu goma". Ƙwal-ƙwal yaron yay da idanu kamar zai yi kuka. Ya kalleta ya kalli Uncle Smart ɗin da ya ɗauke kansa kamar ma bada shi take ba. Itako idanu rufe ta cigaba da zazzaga masa masifa kamar mai jiransa dama. Da yawan mutane hankalinsu ya fara dawowa kansu. A hankali ya raba jikinsa da jikin motar, batare da ya sake mata kallo na biyu ba bayan wanda ya mata sanda take gaban MM Atik ya buɗe motar ya shige abinsa, da wani irin ƙarfi ya fisgeta yay reverse ɗin daya saka taron fashewa ganin zai takasu, fuuuu ya ɓace da ga wajen yay hanyar fita airport ɗin baki ɗaya.. Tuni wasu da abin ya birgesu suka shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin hakan da yay ya musu dai-dai. Wasu ko mamakin ƙarfin halinsa sukeyi. Duk da dai tabbas guy ɗin ya haɗu iya haɗuwa, sai dai duk wanda ya kalli uniform ɗin dake jikinsa ya san kalmar driver data kirashi da shi kam gaskiya ne. Wasu ko dariya suka shiga kwasa da yaɓa mata baƙar magana musamman ganin wulaƙancin da taima MM Atik Kumo da har yanzu yana tsaye a wajen duk da body guard ɗinsa da sukazo suka zagayesa shima yana kallon komai. Lulu da gaba ɗaya ta koma butum butumi da wulaƙancin driver ɗin nata tuni jikinta ya fara tsuma. Numfashinta har wani irin fisga yake dan ɓacin rai, da sauri MM Atik ya matso gareta, yayinda security ɗinsa suka fara yima mutane nunin su tafi dan ALLAH. So yake yace wani abu amma wlhy shi tsoronta ma yake ji, bai taɓa ganin masifaffiyar yarinya irinta ba, ga azabar kwarjinin tsiya kamar wata babbar mace mai shekarun dattijantaka. Da ƙyar ya iya furta, "Please calm down Babie..." "Anƙi ai Calming down ɗin kai kuma!. Har ni sakarai irin wancan guy ɗin mai aikin tuƙi a gidanmu ƙarƙashin ikona zaima wannan walaƙancin? Mi yake taƙama da shi....?" Da sauri yaron nan yace, "To Aunty Lu bana faɗa miki Uncle Smart baya son ihu ba ki daina masa..." Hannu ta ɗaga zata fallama yaron mari MM Atik ya janyesa da faɗin, "Please Babie karki aikata haka". Idanu ta rumtse da masifar ƙarfi dan kuka ma take jin yana taso mata tsabar baƙin ciki da tuƙuƙin da zuciyarta ke mata duk da kasancewarta mutum mai shegen taurin kai akan abu.. Duk yanda MM Atik Kumo yay ƙoƙarin ganin ta shiga motarsa hakan ya gagara. Dole ya haƙura cikin bodyguard ɗin sa yay mata kiran ɗaya daga cikin taxi ɗin dake wajen da dama su aikinsu ɗaukar manyan mutanen. Nanma ƙin shiga taso yi, sai da ya dinga magiya da roƙonta sannan. Kuɗin dake a aljihunsa ya ciro batare daya irga ba ya ajiye masa kusan dubu goma. Godiya sosai mai taxi ya dingayi tare da tambayar ina zai kaita. Cikin ɗar-ɗar ya dubeta, sai ma yaji ya kasa cewa komai ganin yanda take uban huci.. mai taxi da ya fahimci shima bai sani ba ya dubeta ta mirror. "Hajiya ina zamuje...?" "Gidan ubanka!! Dilla malam kaja mota ban san shiga sharo ba shanu". "ALLAH ya baki haƙuri". Mai taxi ya faɗa yana kunna mota........✍️ *_Kai kai wannan yarinya ta cika jaraba. Anya zan iya kuwa😲😏? Bara dai muga ko zamu iya cigaba da bin al'amarinta😔🤔. Nasan dai Uncle Smart ya higa uku yau🥱._* _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇 +22799643131 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* [7/19, 6:34 PM] Maman Aslam: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣ ........Da sauri MM Atik ya nufi tasa motar yana sanarma bodyguard ɗin sa su bisu. Wani saurayi dake jingine jikin motarsa da ke kusa da su MM Atik ɗin ya dubesa. Komai a gabansa ya faru, dan haka yay murmushi da duban MM Atik ɗin. "Ranka ya daɗe Bama sai ka wahal da kanka ba indai sanin gidan su Lulu ƙamshi ce. Sai dai zan baka shawara karka wahal da kanka dan ba lallai ka samu yanda kake so ɗin ba. Kamarka ma ɗan manya daya fito a gidan mutunci ka wuce da ajin wadda ta gama zama gawurtacciyar karuwar turawa tun tana mitsitsiyarta". Ƙaramin murmushi MM Atik Kumo yayi, ya matso kusa da saurayin yana mai girgiza kansa. "Abokina karka damu da son nuna min abinda na gani da idona. Kai dai kawai faɗamin inda zan sametan tunda har ka mata irin wannan sanin haka". Cikin rashin damuwa saurayin ya faɗa masa cikakken adireshin gidan su Lulu ƙamshi. Sosai ya masa godiya ya shige motar da aka buɗe masa fuskarsa ƙawace da murmushi...... *_Manseer M Atik Kumo_* kenan. Ɗa na farko a wajen Hon. Mustapha Atik Kumo. Babban ɗan siyasar nan kuma tsohon gwamnan Kano da ya sauka, a yanzu haka kuma yana ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na wannan zangon da ake kan fara campaign. Sannan shi a karan kansa ma matashin ɗan kasuwa ne da kuɗi ke kaɗa masa gangar lokaci. MM Atik Kumo shegen kansa ne shima a wajen rashin jin magana. Dan duk wani mahaɗar marasa ji na ƴaƴan manyar ƙasar sune ɓoyayyun limamai. Manemin mata ne ƙwararren gaske, dan duk yanda mace takai da iya kame kanta sun san yanda zasu kutsa kai cikin mutuncinta har saita koma jin maganarsu fiye data iyayenta. Mahaifinsa mutumin kirki ne dattijon arziƙi abin alfahari, dan haka yake taka tsantsan akan iya shegensa ba ko'ina yake yarda ya nuna halinsa mara ƙyau ba, idan ma akace maka yana aikata wani abu makamancin hakan zaka iya ƙaryatawa dan ya iya takunsa sosai sosai.... Wannan kenan. ∆••••••∆ ★ ∆•••••∆ Tafkeken gida daya amsa sunansa gida a anguwar Nasarawa GRA drivern taxi ɗin yay horn kamar yanda ta umarcesa. Leƙowa maigadin yayi, ganin ba motar gidan bace ya wani yamutse fuska zai farama mai taxi ɗin wulaƙanci idonsa ya sauka a kanta. Wani irin rawa jikinsa ya fara da gudu ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Ko gama parking mai taxi ɗin baiyi da ƙyau ba ta ɓalle murfin motar ta fice cikin takun nan nata da ke motsa duk wata hallitar jikinta kamar tarwaɗa. Abinda zai baka mamaki ko rawa ƙafarta batayi a dalilin matsiyacin takalmin ƙafarta mai shegen tsini. Duk wani ma'aikaci dake gidan da ga kallo ɗaya baya sake mata na biyu zakaga ya nutsu cikin tashin hankalin ganinta. Dan halin masifarta da iya taka kowa a duk lokacin da taso buɗaɗɗen abune ga duk wani ma'aikaci na gidan. Duk tsufarka duk ƙanƙantarka zata iya gogeka tas idan ka kuskure mata koda a ƙanƙanin abu ne, tsiranka gareta kawai kada ka shiga shirginta, idan kuma ta saka ka abu yi ƙoƙarin mata a yanda ta buƙata babu kuskure. A duk lokacin da tai tafiya daɗi kowa keji a gidan, idan kuma ta dawo zakaga hankalin kowa a tashe. Satin ta biyu kenan da tafiya Abuja wajen ƙanin mahaifiyarta domin yin hutun aiki data samu acan, har addu'a suke ALLAH yasa karta dawo da wuri, sai dai kuma da alama addu'ar tasu bata amsu ba😂 dan gata ta dawo ɗin a bazata. Shigowarta a fusace katafaren falon gidan ya saka duk wanda ke ciki ɗagowa ya zuba mata idanu. A tsakkiyar falon ta tsaya tana harare-harare da cika da batsewa kamar wata kububuwa. "To aunty masifatu, lafiya kika shigo kina kumbura da ga dawowa kuma?". Ɗaya da ga cikin wanda ke a falon ya faɗa cikin taɓe baki. Kamar mai jira a taɓata a fusace ta ce, "Shi ɗan uban waye a ƙasar nan da aka aikashi ɗakkoni? Miyake taƙama da shi?..." Kusan a tare suka shiga kallon-kallo, sai dai kafin wani ya bata amsa Dattijo mutumin dake a kujerar zaman mutum ɗaya da jarida a hannu ya miƙa mata hannu, "Kinga zo ki zauna naji miya faru Baby na?". "Daddy babu maganar zama a fara faɗa min uban waye shi?, dan sai na wulaƙanta rayuwarsa a gidan nan wlhy, sai yayi dana sanin shigowa gidan nan yin aiki, idan kuma bazaku faɗamin ba ALLAH duk wani ma'aikaci da ke a gidan nan yau sai ya bar gidan...". Sun san zata iya aikatawa, kaɗan daga aikinta kuma babu abinda Daddy ɗin nasu zaiyi saboda makahon son da yake mata a gidan. Ƴar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha bakwai ce ta bata amsa da "Aunty Lu! Uncle Yousuf ne ya kawo shi, sabon driver ne ko sati biyu ma bai yiba fa, dan bayan wucewarki Abuja da kwana biyu ya kawo shi. Ni kaina baimin ba saboda naga yana da girman kan tsiya, ƙyawun fuskar tasa ne inaga ke ruɗarsa bayan baida ko sisi matsiyaci Mtsowww!!....." Ta ƙarasa maganar a hankali cikin ƴar sassarfar harshe saboda hararar da dattijuwar matar dake gefen Dattijon nan ta watso mata. Wanda yay maganar farko ne a shigiwarta ya ce, "Wai miya miki ne? Bai je ya ɗakkokin ba?". "Bamunje ba ta masa ihu. Shiko yay tahowarsa. Kuma na faɗa mata Uncle Smart baya san ihu amma tayi" yaron nan da suke tare ya shigo yanzu ya basu amsa yana tuttura baki shi a dole yaji haushin abinda tayi. Duka ta kaima yaron ya ruga da gudu, cikin zafin rai da masifarta tace, "An masa ihun waye shi. Daddy wlhy yau idan banci uban guy ɗin nan ba babu zaman lafiya a gidan nan!". Cikin sauri dattijon ya miƙe yana girgiza kansa, cike da damuwa ya iso gareta. Hannunta ya kama murya a tausashe yace "Kinga Baby yi haƙuri zauna kisha ruwa ki huta. Ni da kaina ma zan ɗauki matakin dan bazan taɓa zama da wanda zai saɓa miki ba a gidan nan ko wanene shi. Har mi akai akayi wani driver banza can da zai ɓata miki rai irin haka. Haba dai cool down my heartbeat ɗin Daddynta yanzu zan nema Yousef ɗin ma ya dakatar da shi". Yanzu kam babu musu ta yarda ta zauna ɗin, sauran yaran duk sai suka shiga taɓe baki. Hakama mamansu tsaki ta ɗan ja a hankali tama miƙe tabar falon. Shiko Daddy ko'a jikinsa ya shiga lallashinta da kalaman ban haƙuri masu sanyaya zuciya gareta tamkar itace uban shine ƴar. Ruwa ma da aka saka mai aiki kawowa da kansa ya tsiyaya a kofi ya bata a baki. Kaɗan tasha ta kauda kai tana faman huci. Sake matsota yay jikinsa ya kwantar mata da kai a kafaɗarsa yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa kamar wadda ta fito daga tarnaƙin yaƙin duniya, sai kuma zuwa can ta ɗan ɗago. "Daddy kar ka kira Uncle Yousuf ɗin ban san a sallemsa yanzu, sai na rama abinda yay min. Aikin sati biyu zai min ALLAH sai na wajiga rayuwarsa sannan na masa korar da kare ma sai ya fisa daraja". "Babyna in dai hakan zai sa ki huce ina tare da ke". "Thanks you sweet Papa.." Ta faɗa tana ɗan rungumesa da sumbatar hannunsa sannan ta miƙe, yatsu biyu ta ɗaya masa alamar bye ta nufi ɗakinta dake acan gefe part guda kamar wata mai aure, sai dai duk a cikin sashen iyayen ne. Murmushi yake da binta da kallo har ta ɓacema ganinsa. Bata zauna a ƙayatacen falonta da ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom kai tsaye. Ɗaki ne haɗaɗɗen gaske kuma ƙato. Dan bayan ƙaton gado da wardrobe kusan rabin bango da mirror akwai set na kujeru da aka shirya tsaf tamkar falo anan ma, sosai ɗakin ya haɗu tare da amsa sunansa ɗaki kamar na macen aure. Cikin yamutse fuska take bin dattijuwar dake ta saka turaren wuta a burners kusan kashi uku da harara, sai kuma cikin faɗa da masifarta ta daka mata tsawa. "Da uwar mi kike a ɗakin da baki gama min ba har na shigo....?" "A gafarce ni Aunty (Duk da zata iya haifarta ta kafama duk wani ma'aikaci dake gidan dokar kiranta aunty komai tsufarsa). Bayi na tsaya wankewa da ƙyau har jikin bangon da kikace". Kakkauran tsaki ta ƙara ja da ƙarasa shiga ɗakin, saman gadon da aka lailaye da bedsheet mai shegen ƙyau fari tas ta jefa wayarta, itama ta faɗa ta kwanta tana mai wargaza fillos ɗin da aka gama wahalar tsara mata yanda take so, har ta lumshe idanu ta buɗe, a gadarance ta ce, "Kimun farfesun kifi mai yaji da kunun tsamiya, biyar nayi ki haɗamin ruwan wanka. Idan kikai min kalar haukan wancan ranar wlhy bazaki gane kanki ba a hannuna fitar min anan banza ƙazamiya sai wani tsamin zufa kike"........✍️ *_Humm nama rasa abin cewa nikam😶😒._* _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇 +22799643131 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* [7/25, 5:41 AM] +234 803 931 9517: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣ ........Idanun dattijuwar cike da ƙwalla ta amsa mata da girmamawa. A haife ta haifeta, bama ita ba har wadda ta fita, amma sam bata ɗaga ƙafa wajen cimata zarafi. Wai a hakan ma itafa da sauƙi, dan a kaf masu aikin gidan ita kawai ta yarda ta shigo mata ɗaki ta gyara kota dafa mata abinda zata ci, hatta key ɗin ɗakin ita kaɗai ta bamawa amma ko momynsu bata da shi. Rigarta ta kama ta shinshina, babu abinda take sai ƙamshi amma ta ce mata tana warin zufa. "ALLAH ya shiryeki ƴarnan" ta faɗa cikin tausasawa tana ɗauke ƴar ƙwallar da suka cika mata ido. Dan duk da wulaƙancin da Lulu ke mata tana ƙyautata mata, zata iya cewa duk abinda ta samu na cigaba a aikin nan nata sanadin Lulu ne, ba ita kawai ba hatta ƴaƴanta dake ƙauye da ƴan jikokinta suna ci da ga alkairin Lulu, barta dai da shegen rashin mutunci, dan in har zakai lissafin masifaffun mutane a rayuwa to indai Lulu batazo ta farko ba tazo ana biyu. Bata da kirki sam, kuma bata ragama uban kowa sai Daddy da Uncle Yousuf, wani lokacin ma Uncle Yousuf ɗin ne ya ɗan fi cin nasararta, dan shi har faɗa yakan ɗan mata da nuna mata kuskure idan tayi, amma Daddy shi komai tayi ma dai-dai yake koda kuwa ba dai-dai ɗin bane ba.... Wannan kenan ∆•••••∆ ★ ∆•••••∆ Da ga airport babban kamfanin Jiƙamshi's ya nufa ransa a ɓace. Kai tsaye ofishin Uncle Yousuf yay ma tsinke, sai dai yayi rashin sa'ar samunsa da ga bakin sakatariyarsa. Bayajin zai iya ƙara minti biyar a wajen, dan haka ya ajiye key ɗin motar tare da amsar takarda a wajen sakatariyar yay ɗan rubutu ya haɗa da key ɗin. A takaice yace, "Ki bashi idan ya dawo". Da ga haka ya juya yay ficewarsa. Da kallo ta bisa tana tsarkake sunan ALLAH. Ga dai namiji har namiji sai dai aljihu babu ko sisi. A hankali taja ajiyar zuciya da ɗan taɓe baki... Shiko da bai san ma tanai ba tuni ya fice, a ƙofar Companyn ya samu napep. Tsaki ya dinga ja a ƙasan maƙoshi har yanzu zuciyarsa na masa ƙuna da kaikawon abinda ballagazar yarinyar can ta masa. Har abada shi *_Aliyu Haydar Mika'il Idris Mawashi_* baiga talaucin da zai sakashi zama ana ƙasƙantar da rayuwarsa irin haka ba. Zai iya jure kowace irin wahala da ƙarfin ƙwanjinsa amma ba ƙasƙanci ba. Shi ba kowa bane, amma har gaban abadan bazai iya zama a ƙarƙashin takalmin kowa ba. Da'ace wannan yarinyar namiji ce yau wlhy sai ya kakkarya mata ƙasusuwa ya zubar da ita a airport ɗin nan. Amma ta godema ALLAH data kasance ƴa mace..... "Ɗan uwa wane layi muka nufa?". Mai napep ya faɗa ganin har sun shigo cikin anguwar ta fage. Sauka kawai yay daga napep ɗin maimakon amsa, ya zaro ɗari biyu a cikin aljihunsa ya miƙa masa. Bai jira mai napep ɗin da ke faɗa masa baida canjin hamsin da zai bashi ba yay gaba abinsa.. *_Aliyu M Idris Mawashi_* kenan da akafi sani da _Smart Mawashi_ yara da matasa na ƙasa da shi kan kirasa Uncle Smart. Abokansa kance Mawashi ko Smart guy, dan sune suka saka masa sunan dama saboda mutum ne mai matuƙar nutsuwa da kuma himma akan komai ga kaifin basira. Ɗa na bakwai a gurin Malam Mika'il Idris Mawashi. Shekararsa talatin da huɗu a duniya. Yayi karatunsa na addini dana zamani har zuwa matakin masters. Bayan nan ma yayi wasu couses har biyu. Sai dai har yanzu aiki ya gagara garesa. Uncle Smart mutum ne mai matuƙar nutsuwa, sannan babban hubby nasa a duniya shine ƙwallon ƙafa. Ya iyata matuƙa dan tun yana a secondary yasha ciwoma makarantar su wassani, bayan kammala sakandire ɗinne ya samu nasarar shiga Kano pillars. Ya buga wasu manyan wassani da suka fara fiddo darajarsa da sunansa wa duniya, sai dai abin mamaki sai komai ya tsaya masa cak, ya zamto in har ya shiga fili domin buga ƙwallo sai ya yanke jiki ya faɗi sai an kamosa an maida gida kamar wanda ya mutu. Da yawan mutane sun fassara al'amarin da asiri, sai dai shi yaƙi ɗaukar hakan da muhimmanci. Daga baya ma sai ya tattara ƙwallon ya ajiye ya koma makaranta bisa shawarar mahaifiyarsa. Duk da haka yakan ɗan gwada yin ƙwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar ƙasa ma, ya fara neman aiki amma yaƙi samuwa duk da takardunsa sunyi ƙyau matuƙa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an ɗaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaƙanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya ɗaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da ƙwallon ƙafa ya ajiye gefe ya shiga ƙoƙarin sana'a, sai dai anan ɗin ma dai komai yaƙi zama. Gashi daya fara sai ALLAH ya sanya masa albarka amma abin mamaki sai komai ya tushe cikin ƙanƙanin lokaci al'amarin nasa dai kamar saka hannu. Yanayin rayuwar gidansu da ake ta kowa nasa ke son ya zama gwani ya sashi bai daina ƙoƙarin kamo can idan nan taƙi ba, a hakanne har takaisa ga samun aikin nan na driver a dalilin wani yayan abokinsa, badan yana so ba ya yarda zaiyi, sai dan tausayama mahaifinsu akan wahala da yay da su game da karatunsu amma a yanzu ƴan uwansa babu mai taimaka masa daga su sai matansu da iyayensu mata. Dan matan Malam Mika'il Idris Mawashi huɗu ne cif, hakama ƴaƴa su talatin da biyu ne maza da mata. A yanzu haka wasunsu sunyi aure a mazan da matan, akwai kuma samari da ƴammata da suka rage musu har ma da Zawrawa biyu.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09018600202 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇 +22799643131 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* [7/25, 5:41 AM] +234 803 931 9517: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨??𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣ _Free pages end_ .........Gidane irin ginin da amma kuma babbane sosai, sannan kuma ko'ina mulmule yake da suminti. BQ ɗin yaran gidan maza itace a farkon shiga, sai daga can ciki iyayensu mata, baya can ƙarshe sashen mahaifinsu Malam Mika'il Idris Mawashi. Sam baya buƙatar shiga cikin gidan balle ya tada hankalin mahaifiyarsa, dan haka ya shige nasu sashen na samari. Da ga can ciki ɗakinsa yake, kasancewarsa tuzurun da duk ya girma sauran ƙanensa da basuyi aure ba yasa shi kadai ke rayuwa a ɗakinsa. Dan a yanzu haka akwaima ƙanan nasa da sunyi auren wasu ma matansu har sun haihu, shiko bama ya kula ƴar kowa balle a saka ran zaiyi. Mahaifinsa yayi faɗan har ya gaji, hakama mahaifiyarsa har ƙwallar ɓacin rai take akan zaman nasa haka babu aure, babu aiki, babu wata ƙwaƙwƙwarar sana'a. Shi ba wani iskanci yake ba, ba shaye-shaye ba, ba ɗaukar magana ba. Amma sun rasa mi yake taɗe rayuwarsa haka. Duk inda ɗa nutsatstse mai nagarta yake Aliyu Hydar yakai har ma ya zarta, gashi mutum mai tausayin iyayensa da son tallafar rayuwarsu. Ga tarin ilimin addini dana zamani ALLAH ya bashi, ga addini. Barshi dai da shegen taurin kai ga saurin fusatar tsiya da shiru-shiru, dan ko'a cikin abokai idan ba yaso ba baya fira. Ɗakine ɗan babba mai ɗauke da kafet maroon color mai laushi, sai ƙatuwar katifa irin wadda ba'a sakawa a gadon nan. Wadrobe mai biyu sai kanta a gefenta cike da litattafan addini dama na bokon, an ɗan yi teburin karatu da kujerarsa. Ɗakin babu wani tarkace sannan fes yake ga ƙamshi kamar ba ɗakin namiji ba. Uniform ɗin da aka sharɗanta masa sakawa matsayin driver ya cire, a kujerar 2sitter dake ɗakin ƙwara ɗaya ya jefasu ya haye katifarsa da ga shi sai boxer da singlet yay kwanciyarsa yana furzar da tagwayen huci masu zafi da ɗaci, dan abinda yarinyar tai masa sam yaƙi barin ransa. Sai kuma shigar jikinta da tafi komai ƙona masa zuciya. Haka yake shi ya tsani mace haka. Kai koda atamfa ko lass yaga mace tama ɗinkin fidda surar jikinta baƙin ciki yake ji balle wannan da gaba ɗaya ta canja suffarta daga hausawan ta koma kamar wata jinin kafirai. Tsaki yaja mai ƙarfin gaske ya juya kwanciyarsa yana mai ingije tunanin a ransa. Sai dai duk yanda yaso hakan bai yiwu ba. Al'amurin ma yaƙi barinsa yin barcin da yake buƙatar yin ko zai samu sassaucin baƙin cikin dake sukar zuciyarsa.. Da ƙyar ya samu barcin ya ɗaukesa, baima yi na minti talatin ba akai kiran sallar la'asar. tashi yay da ƙyar yana faman yamutse fuska dan a barcin ma harda mafarkinta. siririn tsaki yaja ya miƙe ya shiga toilet ɗin ɗakin nasa, a gurguje yay wanka da alwala ya fito jin har za'a shiga salla. jallabiya kawai ya saka da turare ya fita kasancewar masallacin a kusan ƙofar gidansu yake, dan baifi gida huɗu ba ne tsakaninsu.... Ana idar da salla gidan ya dawo, sai dai maimakon ɗakinsa yanzu ciki ya shiga ɓangaren iyayensu. Gida ne da tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar na zaman mace huɗu ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a ƙalla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform na islamiyya wasu nacin abinci wasu kuma na ɗan kai kawon aiki. Tsit kake ji duk wani ihu da hayaniyar da gidan ya ɗauka ya tsagaita, yaran suka shiga gaidashi. Sau ɗaya ya amsa musu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa kai tsaye. Sun san ba wasa yake da su ba dan haka babu wanda ya damu da yanayin nashi, sai dai sauri-sauri da suka shiga yi na son kowa ya kammala abinda yake ya fice islamiyya kafin ya fito ya sake ganinsu.. Daga ɓangarensa kam da mamaki mahaifiyarsa ke kallonsa daga inda take zaune. A hankali ya kai zaune a ƙasan carpet ɗin da aka saka a gaba ɗaya falon kalar blue. Basu da kuɗi, amma mahaifiyarsa mace ce mai tsananin tsafta da cikar kamala, tanada haƙuri sosai, sai dai bata son raini ko kaɗan ita, dan kana shiga sabgarta zata tabbatar maka da ita ɗin jinin zazzagawa ce. "Ammah barka da yamma". Ya faɗa cikin muryarsa mai sauƙin amo da rashin son hayaniya. Maimakon amsa masa gaisuwar tambaya ta jeho masa cikin nutsuwarta da cikar kamala. Dan da yawan halayensa ya samosu da ga gareta ne, duk da ya ɗakko wasu da yawa ga mahaifinsu ma. "Baka da lafiya ne?". Gajeren murmushi yayi da ɗan girgiza kansa. "Lafiya lau nake Ammah, na ɗan yi barci ne". "Shima wannan aikin an samu matsala kenan? Ya rabba.." Ta ƙarashe faɗa a hankali cikin damuwa. Gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, murya a sarƙe ya ce, "Amma ba matsala aka samu ba karki saka damuwa a ranki. Na dawo da wuri ne dai". Shiru tai tana kallonsa, sai dai har cikin ranta bata gamsu da maganar tasa ba. Ta sanshi fiye da yunwar cikinta akan zurfin ciki, sannan kuma bai iya ƙarya ba, ko yaya ya kuskure takan saurin harbosa. Tunda ya fara aikin ko ƙarfe biyar na yamma baya dawowa balle yanzu da azhar, alamuma sun nuna tun ɗazun yake a gidan tunda gashi yace har barci ma yayi. Fitowar ƙannensa biyu ƴammata Maryam da Asma'u masu kama da shi sosai kamar mahaifiyarsu ya katse shirun falon. Ƴammata ne ƙyawawa masu tarin nutsuwa da rashin son hayaniya suma. Suma dai ɗan turus sukai na ganin nasa. Sai kuma cikin damuwa duk suka kalli mahaifiyar tasu. Ɗauke kanta tai, dan gaba ɗaya rauninsu da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu. "Yayamu ina yini" Suka haɗa baki wajen faɗa a sanyaye. Kansa ya jinjina da amsawa cike da kulawa, duk ba wani yana wasa dasu bane ko sakewa yana ƙaunar ƙanensa, sannan suna bashi tausayi da ya gagara tsayawa akan al'amuran su na yau da kullum a matsayinsa na babba namiji a ɗakinsu tunda mahaifinsu abubuwa sun masa yawa yanzu, ga shekaru ga rashin tausayinsa da ga ƴaƴan gidan da kowa ya samu ya tsallake da ga shi sai iyalansa sai uwarsa ne.. "Babu wata damuwa ko?". Kai suka jinjina masa alamar babu duk da sunada buƙatu, sai dai sun san koma sun faɗa tayar masa da hankali kawai zasuyi tunda bashi da shi. Abincin da akai gidan kason ɗakinsu da aka kawo suka zuba masa, tuwon shinkafa ne da miyar ganye dai-dai ƙarfin talaka mai rufin asiri. Ya jima yana kallon tuwon bayan fitar su Asma'u har sai da Ammah tai masa magana sannan ya fara ci dan yunwa yake ji sosai, yau baya jin ko karin kummalo ma yayi, sai ruwan shayi da ya zame masa jiki ko yaushe bai rabo da shi a flaks da ya sha...........✍️ *_Humm rikitata-rikitata kenan. Masu karatu ina faɗa muku Bama a fara komai na fa, dan ko shimfiɗar labarin bamu kammalaba balle shiga cikinsa. Littafin FURAR DANƘO...!! Labarine da yazo muku da nashi salon na musamman. Babban abinda ke addabar al'ummar mu a wannan lokaci a cikin gidajenmu da ma wajen gidajenmu da rayuwar ƴaƴanmu mata da maza dama na gidan aure duk ya taɓo fiye da inda kuke zato._* *_Ga dai Uncle Smart a matsayin drivern Lulu ƙamshi, yarinyar ƴar ƙwalisa mai tsananin wayewar rayuwa. Ƴar gata kuma ƴar hamshaƙan masu kuɗi. Uncle Smart matashin saurayi ɗan talakawa dake cikin jarabawar rayuwa kala-kala. Ya taso cikin gida mai yawan zuri'a da kowa kansa ya sani. Shin ta ina muke tunanin labarin waɗan nan mutane biyu zai kamanceceniya da juna?_* _Minene abinda Lulu ƙamshi ke ɓoyewa na rayuwarta?_ *Minene ke faruwa a rayuwar Aliyu Hydar (Uncle Smart) da ke taɗe rayuwarsa da ga cigabansa?* _Baku ba, hatta da ni kaina ina son sani. Dan haka ku garzayo domin kasancewa da ZAFAFA BIYAR ɗin nan naku abin alfaharinku. Ƴan amanarku, akoda yaushe labaransu masu gamsarwane a gareku._ *_Ki daure a matsayinki na mace mai kima da daraja, musulma da ta san muhimmancin hakki da son cigaban nata kasuwancin ko aiki kizo ki saya domin karanta halak ɗinki, karki bari ki ɗorama kanki nauyin da zaki iya yin kaico da sakacin ɗaukar watarana saboda ruɗi da ɗaukar komai a ba komai ba ƴar uwata._* _ALLAH ya ƙarama rayuwa albarka, duk wanda ya tsare domin ALLAH shima ALLAH ya tsare masa kasuwancinsa ko aikinsa. Alkairin ALLAH ya kai gareku a duk inda kuke a duniya masoya. Muna sonku irin trillions ɗin nan. Duk wanda ya somu domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka shi da zuri'arsa baki ɗaya. ALLAH ya gafartama iyayenmu da duk al'ummar musulmi baki ɗaya😭🙏😘😘❤️❤️❤️❤️😘_. Garzaya ki biya naki kar a baki labari gasu nan da ɗumi-ɗuminsu suke👇😀😘. _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09018600202 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇 +22799643131 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣ .......Shiru kawai yay yana kallon takarda da key ɗin motar da sakatariyarsa ta kawo masa na tsawon lokaci, kafin ya furzar da huci mai kauri ya tashi zaune sosai da ga kwanciyar da yay a kujerar office ɗin nasa. Wayarsa mai ƙyau da ɗaukar ido ya ɗauka. Har yay dailing number da akai saving da _Yaya Isma'il_ sai kuma ya katse yana ɗan girgiza kansa. Dan ya san halinsa, wani lokacin ba gane abubuwa yake ba birkitaccen mutum ne. Wata number ya sake lalubowa yay dialing, ring biyu aka ɗauka. "Uncle You.. Good Afternoon". Aka faɗa daga can, muryarsa a sauƙaƙe ya amsa da "Afternoon dear! How are you?". "Am good Uncle". "Haka ake so. Lulu ta dawo ne?". "Yes Uncle tun ma ɗazun. Sai dai tanata masifa wai Uncle Smart ya barta a airport. Amma Deen ya ce ta masa ihu ne a gaban mutane kuma bai mata komai ba kadai santa. Yanzu kuma Daddy ya goya da bayanta wai zata walaƙanta shi ta koreshi. Uncle ALLAH ni bana so sumasa haka, shi ɗin mutum ne nutsatstse". Wani ɗan murmushin takaici yayi da gyada kansa kamar yana a gabansa. "Karka damu Son! bazan bari su aikata hakan ba insha ALLAHU. Kuma zai dawo aikinsa". Sosai yaron ya shiga ihun murna daga can. Shi kuma ya katse wayar yana mai jin takaicin hali irin na ɗan uwansa. Yanda yake training rayuwar Mawaddat na ɓata masa rai. A rayuwa ko ɗa namiji ne bazakace komai ya nema sai ya samu ba duk arziƙinka da matsayinka. Balle mace da wataran aure zatayi ta koma ƙarƙashin ikon wani. Wanin da ba lallai shi ya iya ɗaukar waɗan nan ɗabi'un nata marasa ƙyau ba. Da wannan ɓacin ran yabar office ranar. Kai tsaye gidansa ya nufa dake anguwar ta Hotoro GRA shima. Sai dai ba street ɗin su ɗaya da gidan yayan nasa ba. Da gudu ƙyawawan yaransa guda uku masu kama da shi sukazo tarbarsa. Murmushi yayi cike da jin daɗi, gaba ɗaya ya haɗasu ya rungume a jikinsa bayan sun gaidashi. Yana ƙoƙarin miƙewa da ƙaramin Deen da sukaje ɗaukar Lulu airport mai wayon tsiya a hannunsa idonsa ya sauka akan matarsa. Ƙyakykyawar mace ƴar duma-duma. Murmushi ya sakar mata kamar yanda take masa itama, ya miƙa mata hannu alamar tazo itama. A hankali ta ƙaraso ta shige jikinsa, rungumeta yay da sumbatar goshinta kamar yanda ya saba. Ko'a jikin yaran dan sun saba ganin hakan ga iyayensu, basa aikata wani abu dazai lalata musu tarbiyyar yara, amma su tarbi juna yayin da wani yay ɗan nesa da gida kona yini guda ne sun nunama yaransu hakan ba komai bane face ƙauna, kuma ya halatta miji yayma matarsa, idan sunga hakan ko'a wani waje ba haramun bane ba. Shiyyasa suma yaran suke kallon hakan a normal ne. Da ƙyar ya samu ya gudarma Deen dake bashi labarin faɗan aunty Lulu a airport. Bayan yay wanka falon ya dawo ya zauna cikinsu yana shan fruit salad. Matarsa Saleeha da kowa ke kira da Aunty a family ɗin ta kallesa cikin damuwa da sauƙaƙa harshe. "Abul Mahsin kamar kana cikin damuwa? Wani abun ya sake faruwa ne a office ɗin?". Ƙaramin tsaki yaja da ɗan girgiza kansa. Kamar bazaice komai ba sai kuma ya numfasa. "Mawaddat! Halin yarinyar nan nacimun rai matuƙa Sweetheart. Kullum maimakon abubuwan su dinga sauƙi tana hankali amma sake jagulewa yake. Abinda yafi ɓatan rai Yaya. Shi sam nunawa yake kamar ma komai yana tafiya daidai ne a rayuwar yarinyar. Safiyya ina tsoron UBANGIJI ya tuhumemu akan amanar da baiwar ALLAHr nan ta tafi tabar mana fa..." "Tabbas hakane, to amma ya zakayi tunda Yaya yana sama da kai ne. Ita kuma ɗabi'un sun riga sun shigeta tankwarata abune mafi wahala duk da ma kana iya bakin ƙoƙarinka tun bata kai haka ba. Amma babu abinda ya canja". "A wannan karon ina son ya canja kota ƙarfi Saliha. Dan gaskiya na gaji da gani, bana son yarinyar nan ta kuma fi haka gagara..." "Tankwarawar ta ƙarfi kam akwai damuwa, dan shi icce tun yana ɗanye ake tankwarashi. Idan ya bushe akace za'ayi zai iya karyewa. Sai dai ni inada shawara. A yanda Deen ya bani labarin abinda ya faru tsakaninta da drivern nan nasan zasu ce zasu koresa ne, inaga karka bari hakan ta faru, inma da dama ya zama driver nata ita kaɗai, dan shi naga ba mutum ne mai wasa ba, ba kuma zai ɗauki halinta ba". A hankali ya sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya furta, "Nagode miki dan tunaninmu yazo ɗaya. Sai dai magana ta gaskiya bamma san yanda zan tunkari yaron ba. Kedai kin san a yanda na samosa ai, aikin nan kuma yana yinsa ne saboda tsare mutuncinsa bawai irin sauran drivers nada bane da take takawa yanda take so. Sannan Aliyu yanada zuciya fiye da yanda kike tsammani da hasashe bar ganinsa hak shiru-shiru baya son magana". "Duk ɗan halak dole ya kasance mai kishin kansa Abul Mahsin. Sannan wannan itace cikar kamalar duk wani ɗan adam na ƙwarai. Karka ƙasƙantar da kanka ga kowa ga komai saboda talauci, ka kasance mai tsaftatacciyar zuciya a baɗini da zahiri, ka kuma zama jarumi a neman na kanka koda duk jama'a na kallon hakan da faɗuwa. Ni nasan baka kawosa yay wannan aikin da ƙasƙanci ba, sai dan wani dalilinka da kuma kare mutuncinsa daga taɓarɓarewar abubuwan da ba'asan mafari ba a rayuwarsa. Kamar yanda kuka samu mahaifinsa a farko kai da Ahmad yanzu ma ku sake samunsa insha ALLAHU zai dawo ya cigaba har ALLAH shima ya kawo masa iyakar komai na jarabawarsa". "Shike nan in sha ALLAHU zan gwada nagani. Ita kuma zuwa anjima zanje gidan na sameta". "Hakan yayi, amma Please smile". Ta faɗa tana kwatantawa da hannunta a kan baki. Hararta yay yana sakin murmushin..... ∆••••∆ ★ ∆••••∆ Washe gari ma baiyi yunƙurin zuwa aiki ba, sai ma tunanin neman wata mafitar da ya tashi da shi. Kamar yanda ya saba bayan dawowa sallar asubahi ya shiga sashen mahaifinsu domin gaishesa duk da tare suka fita massalaci suka kuma dawo. Ƙyaƙyƙyawan dattijon mutum mai cike da tarin nutsuwa. Da ga gashin kansa har zuwa na gemu fari ne fat. Duk da tsufansa ya bayyana a kallo guda zaka tabbatar da zamanin ƙuruciya ansha ƙyau. Duk da ya ɗan ɗago ya dubesa a lokacin da yake shigowa bai ajiye littafin dake a hannunsa ba. Sai ma ɗan turɓune fuska da ya sake yi. Tsahon mintuna uku baida alamar kulashi, har sai da wasu samari biyu suka shigo, abin mamaki sai ga murmushi ya mamaye fuskar tashi, ya ajiye littafin cike da kulawa idonsa akan samarin dake gaishesa bayan sun ma Uncle Smart kallo ɗaya a gatsine sun ɗauke kai. Oho baima san sunai ba, dan basu isa masa a ido cikin ido ba. "Abba Barka da safiya". Suka faɗa kusan a tare. Cike da kulawa yake jinjina musu kansa. Ya amsa da "Har an shirya fita kasuwar? Ƴan albarka". "Eh Abba". Suka bashi amsa suna miƙewa. Albarka ya shiga saka musu, suko tunda suka amsa sau ɗaya ma basu sake ba. Har zasu fice ya dakatar da su. Cikin ƴar damuwa yake kallonsu. "Nabeel yau kam da ban takuraku ba da kun bama iyayenku kuɗin cefane. Na tashi banda ko nera a jikina gashi babu hanyar samuwarsu garan a yau". A turɓune wanda aka kira da Nabeel ke dubansa. Bakinsa a sama ya ce, "Abba kafa san abubuwan sai a hankali. Kuɗin cefanen gidan nan inba kaiba kuma wazai iya. Sannan jiya fa sai da kasa na baka dubu biyu". "Nima ai sai da na bashi dubu ɗaya". Ɗayan ya amshe da sauri shima rai ɓace. Ɗan murmushi Abban yayi, yayinda Uncle Smart kejin wani irin raɗaɗin zantukansu ga mahaifinsu akan abinda bai taka kara ya karya ba. Mahaifinsu jarumin ubane da ya tsaya a kansu da ƙare ƙarfinsa wajen gina rayuwarsu. Amma yau sun zama wani abu kowa najin ƙyashin taimaka masa. Ɗari biyar-biyar suka ajiye masa saɓanin abinda ya tambaya suka fice rai ɓace. Gaba ɗaya sai yaji jikinsa ya ƙara sanyi, cikin ƙarfin hali ya fara gaida Abban dake sake ƙoƙarin ɗaukar littafinsa bayan ya kwashe dubu ɗayan da suka ajiye masa. Maimakon amsa masa gaisuwar a zafafe ya ce, "Shima wannan aikin sun korekan?". Kasa amsawa yayi ya ƙara ƙasa da kansa zuciyarsa na ƙuna. Ba'a kan ƙaddararsa ba, ba kuma akan abinda mahaifinsa ke tuhumarsa ba, sai akan damuwa da halin da mahaifin nasu ke ciki.... "Wai halan bada Ali nake magana ba?!". Ya faɗa cikin fusata. "Kayi haƙuri Abba dama...." "Dama mi? Mi kake son faɗamin? To wlhy bari kaji a wannan karon bazan ɗauka iskancinka ba. Bari ma na faɗa maka gaskiya in har maganar banzarka ce da ka saba to a wannan karon ka shirya barmun gida, dan bazan iya cigaba da wahala da kai ba bayan wadda nayi kana yaro. Na ciyar da kai abinci, na tufatar da kai sutura, na sakaka a makaranta islamiyya data boko har matakin digiri na biyu sannan na cigaba da wahala da kai. Ga kanenka nan na bayan baya sun tsaya da ƙafafunsu harda masu aure amma kai ban daina cidaka abinci ba, wannan wace irin rayuwa ce. To ba asiri ba a wannan karon ko kukar bulukiya aka sauke a kanka bazan ɗauka ba na gaji da shashancin ka, tashi ka ficemin daga nan na baka zuwa dare wlhy ka tsara mai yuwuwa sakarai kawai cima zaune". Idanunsa da suka kaɗa sukai jazur ya ɗago kaɗan ya subesa. "Kayi haƙuri Abba ALLAH ya huci zuciyarka, dan ALLAH ka gafarce ni". Banza ya masa bai sake tankawa ba. Yasan minene shiru a wajen mahaifin nasu. Dan haka ya miƙe ransa a matuƙar ƙuntace ya fice. Har ya nufi hanyar sashensu na samari ya fasa. Ƙirjinsa zafi yake masa. Ji yake kamar ya saki kuka amma bazai iyaba saboda taurin zuciyar tsiyarsa. Sosai mutane ke kai kawo a cikin layin nasu. A halin da yake ciki baya buƙatar yin magana da kowa, dan haka yay ƙoƙarin juyawa zai koma ciki. Daga motar da tun fitowarsa idonsa ya sauka a kanta amma ya kauda kai aka danno masa horn. Ƙin juyawa yay har sai da aka sake na biyu da ambaton sunansa. Cak ya tsaya amma bai juyo ba har Uncle Yousuf da abokinsa Ahmad suka ƙaraso garesa. "Kayi haƙuri". Kalmar data tilastashi juyowa da ga bakin Uncle Yousuf..........✍️ _Alhmdullah, mungode da haƙurinku. Bari muga a fara ko kaɗan-kaɗan kafin na murmure. Mungode sosai da addu'oin ku🙏._ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇 +22799643131 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣ .........Hannu ya basu batare da ya yarda ya kallesu ba. Uncle Yousuf yay murmushi da amsar hannun sukai musabaha bayan ya gaisa da Ahamd dake ƴar dariya saboda harar da Uncle Smart ɗin ke masa ƙasa-ƙasa. "Idan ban takura da yawa ba ina son muyi magana Please Smart Mawashi". Karan farko ya ɗan ɗago idanunsa da har yanzu suke da damuwa ya dubi Uncle Yousuf mai maganar. Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru. Uncle Yousuf ya sake murmusawa da faɗin, "Please". Bashi da yanda ya iya dole ya amince masa, sai dai maimakon cikin motarsa da ya buƙata suje anan cikin soron gidansu suka zauna saman bench. Shiru na wasu mintuna kafin Uncle Yousuf ya nisa. "Jiya na dawo na samu takarda da key ɗin mota a hanun sakatariyata Aliyu, sai dai ban gamsu da bayanin dana gani a rubuce ba shiyyasa nace Ahmad ya rakoni nazo da kaina". Ya ƙare maganar idonsa a kansa alamar son jin amsa. "Na ajiye aikin ne kawai". Ya faɗa cikin dakewarsa. "Ko miyasa?". Ahmad ya tambaya cikin kafesa da idanu. Kansa ya jinjina yana ɗan furzar da iska, sai kuma ya dubu Uncle Yousuf maimakon Ahmad da yay tambayar. "Saboda bazan iya ba Alhaji. Ni mutum ne da ba komai zuciyata ke iya ɗauka ba duk da na kasance talaka mai nema." "Haka ake so duk mutum na ƙwarai ya kasance Aliyu Hydar. Amma har yanzu baka faɗa mana dalilin ba?". Murmushi ya saki mai ciwo a karo na farko. Ya ɗan dubi Uncle Yousuf ɗin sai kuma ya ɗauke kai. "Miye amfanin maimaita abinda bashi da muhimmanci koya wuce Alhaji. Kawai na ajiye shikenan ya wuce. Nasan insha ALLAHU zaku sami wanda ya fini, ni kuma zan tara gaba maybe abincina ba'a nan yake ba". "Nasan bazaka juraba kamar na baya da suka shuɗe domin Kanada banbanci da su. Sai dai irinka na jima ina fata ni kuma, dan kai kaɗaine zaka iya da ita har ma ka tankwarata. Har yanzu nasan baka san ni wanene ba Aliyu Hydar, sai dai ka sani ban nema kamin wannan aikin ba dan kana buƙatar aikin da kuɗi zai shigo maka. Tun randa na ganka wajen abokina yayan abokinka Ahmad naji a raina ka cancanta zama wani ɓangare da zai jagoranci haska wata fitila ta rayuwarta. Ita ɗin a fanɗare take, tabbas a haka ta tashi shiyyasa tanƙwarata yayma kowa wahala a cikinmu. Ada kallon komai muke a bigire na ƙuruciya da tunanin wata rana zata daina, sai dai ranar har yanzu taƙi tazo, bamu san kuma ranar da zata zo ba, ko kuma tazo ne ta wuce batare da mun farga ba oho?. Nasan kana da ƙanni mata maybe ma harda yayu, kasan irin zafin da nakeji a raina koda a kwatance ka kwatanta da ace sune, miyasa bazaka gane ba ne....?" Yanda ya ƙare maganar a raunane cikin sigar tambaya yasa Uncle Smart fesar da iska mai nauyi. A ɗan zafafe batare daya dubesu ba yace, "In dai har ku da kuka haifeta kun gagara tanƙwarata ni kuma taya kuke tunanin iyawa? Mahaifinta fa na raye, hakama mahaifiyarta, sannan gaku ku ƴan uwanta, Alhaji Please kayi haƙuri bazan iya ba fa. Bana son raini, bana iya jurarsa ga kowa. Bana son wulaƙanci ko ƙasƙanci duk da kasancewata talaka mai nema. Ina ganin kimarka dan ALLAH karka bari mu shiga wata hanya daba ita ta dace mukai ba dan alkairi ya haɗamu kuma bazan taɓa na manta da kai ba, dan kamun abinda mutane da yawa basu minba na alkairi ka gaida gida". Yana gama faɗa ya miƙe. Dakatar da shi Ahmad yayi, kamar bazai tsaya ba sai kuma ya dakata tare da juyowa. Miƙewa shima Uncle Yousuf ɗin yayi yana ɗan murmushi. Hannu ya kai ya dafa kafaɗarsa, "Shike nan na fahimceka kuma nagode sosai. Ina son mutum irinka mai tsayawa akan ra'ayinsa da riƙe mutuncinsa. Zan jima inajin raɗaɗin rabuwa da kai Aliyu. Amma dan ALLAH ina roƙon alfarmar kazo office ko zuwa gobe ne domin amsar hakkinka, kuma bana son kace da ni a'a". Baki ya buɗe zai yi magana Ahmad ya dakatar da shi. "Dan ALLAH karkace a'a Smart, ban sanka da musu ba karka fara akan Yaya Yousuf, sannan kayi nazari akan roƙon da yay maka, nasan kanada damar taimakons.....". Hararar da ya ɗan ballama Ahmad ɗin ce ta sashi yin ƙaramar dariya batare da ya ƙarasa ba. Ɗauke idanunsa yay da faɗin, "Shike nan insha ALLAHU idan na samu lokaci zanje, amma kai ma kasan kawai dai dan ta Yaya boss ne wlhy". "Na sani Mawashi. Yaya boss kuma na godiya da wannan karamci". Bai ce komai ba, sai murmushi da Uncle Yousuf dake saurarensu yayi. Har cikin rai ɗabi'un yaron birgesa sukeyi matuƙa. Yana son ganin mutum mai nutsuwa musamman matashi kamar haka. Ba irin matasan yanzu da shegen rawar kai yayma mafi yawansu katutu ba... Har mota ya musu rakiya. Bayan wucewarsu sai yaji ya kasa komawa cikin gidansu dan baisan da wane irin harshe zaima Ammah bayani akan sake rasa wannan aikin ba shima, duk da dai jikinsa yay ɗan sanyi da kalaman Ahmad na ƙarshe, amma dai bai yanke hukunci ba na sake amsar aikin har yanzu. Sai dai in ya tuno bayanin Abba ya kanji faɗuwar gaba. Tabbas yasan wanene Abbansu, sam baya magana biyu. Mutum ne tsayayye da idan yace e to e ɗinne da har ransa. Idan kuma yace a'a to a'a ɗin ce fa. Da ƙafa yabar cikin anguwar tasu, rashin abunyi da sanin ina zai dosa ya sashi miƙewa a titi yay ta tafiyarsa kawai. Yayi tafiya mai nisa da bai san ina yake jefa ƙafa da ɗaukewa ba ya fahimci kamar binsa akeyi a baya. Tsamm yayi na tsarguwa tare da tsayawa, sai dai abin mamaki babu alamar wani tare da shi a ƙafa, wanda ke a kan mashina ma da napep babu alama, hakama na mota. Dakewa yay ya cigaba da tafiyar, still dai ya sake jin tabbas akwai mai binsan. Yanzu kam bai juyo ba sai ya yanke titin ya shiga cikin wani layi, ya ɗan yi nisa da layin sosai ya samu rumfar wasu masu kayan kafinta ya ɗan dakata cikin dabara kamar mai gyara igiyar takalmi. Ta cikin mirror da aka jingine ya hango wasu samari biyu, sai dai suna ɗan waskewa cikin ɓadda kama. Hakan ya ɗan bashi mamaki, dan shi dai a rayuwa duk da yana da tsatstsauran ra'ayi bashi da abokin faɗa. Cigaba yay da tafiyar dan son gane iya gudun ruwansu badan yasan sirrikan layukan inda yake ba. Sai da sukaje ƙarshen layin sosai ya fahimci akwai matsala, ya ɗan ji wani abu a ransa amma sai ya dake, wata hanyar da yake ƙyautata zaton zata ɓillesa da titi ya bi, sai dai yana shan kwanar tsukin wajen suka sami nasarar rufesa ruf ata gaba da bayansa. Ɗaya bayan ɗaya ya bisu da kallo har ya sauke akan napep ɗin da aka faka a gabansa. Cikin dakewa da ambaton sunan ALLAH ya ce, "Ku kuma fa?". "Zaka sani amma ba'a nan ba". Ɗaya ya bashi amsa cikin gatse da nuna masa bindiga dake soke a ƙugunsa. Bindiga bata kasance abar wasa ga kowa ba. Duk ƙarfinka da taurin kai a duk inda mai ita ya kasance shike zama a saman ƙarfin ikon ka. Dan haka ya shiga napep ɗin zuciyarsa na saƙa masa abubuwa masu yawa game da mutanen. Biyun da suka dinga binsa ne kawai suka shiga gefe-da-gefensa, mai napep yaja suka fice daga layin, sai da suka fita gaba ɗaya wanda ke gefen haggunsa ya jefa masa wani ƙyalle a fuska, da sauri na kusa da shi ya kama ya ɗaure masa idanu yayinda wanda ya fara jefa ƙyallen ya ɗora masa bindiga a gefen ciki ta yanda bai isa musawa ba. Duk da ya sake firgita haka ya dake a zahirance, a baɗini kuwa yana mai ambaton sunan ALLAH...... Tofa, su kuma waɗan nan daga ina?. Wayyo Uncle Smart ɗinmu😫😢 ∆••••∆ ★ ∆••••∆ Tun daga main falour na gidan kana iya jiyo tashin sautin kiɗan dake fitowa da ga ɗakinta, duk da kiɗane mai taushi na mawaƙiya Shakira yanda ta ƙure voluen yasa ake iya jiyowa. Tun safe babu wanda zai ce ya ganta yau a gidan har zuwa yanzu da agogo ke nuna ƙarfe takwas da wasu mintuna. Mafi yawan yaran rai a ɓace suke fitowa daga ɗakunan su dan sautin kiɗan data saka ya takurasu da hanasu barcin safen. Hatta da ƙananun Suhaib da Imran da fita makaranta kan hakanasu barcin safen ji suke ta takura musu, musamman Imran dake son ƙarasa Assagment ɗinsa amma ya gagara fahimtar komai. Kaf ɗinsu sun gama hallara a dining, sai dai fuskar kowanne a turɓune da takaici. A haka Daddy da Mommy suka fito suka samesu, a kallo ɗaya zaka fahimci itama Momy ranta a ɓace yake, sai dai shi Daddy kam ko'a jikinsa. Yaran ma na gaidashi bai wani saurarensu ba hankalinsa nakan kiran Tabawa mai aiki. Da ɗan gudu-gudu ta fito a kitchen hannunta riƙe da ƙaramin ludayi da alama girki takeyi. "Babyna fa?". Ya faɗa kai tsaye yana nuna upstairs. Itama upstairs ɗin ta kalla, cikin sake rissinawa tace, "Barci takeyi Alhaji, tace zuwa ƙarfe tara da rabi na tadata". "Shi kuma wancan kiɗan da ga ina?". "Itace ta kunna". Nunin ta tafi kawai ya mata batare da ya sake cewa komai ba. Mommy da tai kicin-kicin da fuska ya kalla, sai kuma yabi sauran yaran nasa da kallo. Hafiz dake ƙoƙarin kai shayi bakinsa wanda a haihuwa shike bima Lulu ne ya ce, "Humm Daddy yanzu bazakace komai ba kenan?". "Akan me?". "Aunty Lu. Ai ko kafiri ba kowa ke iya saka kiɗa ya kwanta da shi ba. Kuma ina da tabbacin ko sallar asuba batayi b....." "Kai ban san shashanci da ƙazafin banza, wai Hafiz ita ɗin sa'arka ce? Kuma kai ubanwa yace maka batai sallar ba". "Ai ba sai wani ya faɗa masa ba abinda kowa ya sani ne. Ni ban san wane irin makahon so kakema Mawaddat ba a gidan nan, kuma ka sani wannan ba gata bane kashe mata rayuwa kakeyi matsayinta na mace. Da haka kowace yarinya ake rainonta a gidansu da baka gammu haka ka aura ba matsayin iyayensu Alhaji. Dan ALLAH ya kake so nayi da raina akan Mawaddat ne?". Wani banzan kallo ya galla mata ita da yaran baki ɗaya yana cika da batsewa, sanin yanzu zasuyi sama ya sata miƙewa tabar dining area ɗin zuciyarta na ƙuna da raɗaɗi. Ta rasa mike damun mijin nata akan babbar ƴarsu mace, yana nuna mata ƙazamar rayuwa a matsayin soyayya, iya bakin ƙoƙarinta tana yi akan Mawaddat amma abubuwa sake taɓarɓarewa sukeyi. A hankali hawaye masu raɗaɗi suka silalo mata saman kumatu.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* _* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣ ........A can falo kam tashin Mommy dai-dai da shigowar Uncle Yousuf, da murna yaran suka tarbesa. Sai dai ganinsa kamar rai ɓace yasa jikinsu sanyi. Abba da shima idonsa ke kansa ya baro dining ɗin ya nufosa. Kusa da shi ya zauna idanunsa a kansa ɗan uwansa, yana son ɗan ƙanin nasa namiji ɗaya tilo da ya rage masa a duniya. "Anya lafiya kake cika kana batsewa haka?". Ya faɗa cikin kulawa da dafa kafaɗarsa. A hankali yace, "Ba komai. Sai kuma ya kai dubansa ga sashen Lulu. "Wannan kiɗan fa?". Shima Daddyn kallon saman yayi, sai kuma yay ɗan murmushi da faɗin "Kaima ka sani sai dai ƴar gidanka ai". Komai Uncle Yousuf bai sake cewa ba, sai rumtse idanu da yay cikin takaicin yayan nasa. Kusan mintuna biyu kafin ya buɗe, "Yaya mika yanke akan yaron dana kawo?". Murmushi Daddy yay mai bayyana haƙwara. Ya ɗan bigi kafaɗarsa cikin sigar zolaya ya ce, "C-mon magajin baba saki fuskar mana, ni idan kana wannan cikar sai naga kamar baba ne ya dawo fa". Baki Uncle Yousuf ya tura masa kamar mai shirin yin shagwaɓe fuska. Sai kuma ya kauda kansa saboda murmushin da ke son kufce masa. Sam baya iya dogon fushi da ɗan uwan nasa. Shima Daddyn murmushi ya sake saki da faɗin, "Yauwa ko kai fa. Yanzu kamun bayani yanda zan gane. Wane yaro kake magana a kai?". A taƙaice ya ce, "Driver". "Okay ni babu abinda na yanke. Dan Babyn ka har yanzu tace tana buƙatarsa ai". "Shi kuma baya buƙatarmu dan ya ajiye aiki". "Wannan ra'ayinsa ne ai. Idan itama ta haƙura sai a nema mata wani ba damuwa bane". Wani shegen takaici ne ya sake kume Uncle Yousuf. Shi bai san wane irin mutum bane yayansa. Sam bai damu da damuwar kowa ba sai kansa da su ahalinsa. Kai kawai ya jinjina yana miƙewa. Daddy dake binsa da kallo ya ce, "Badai wucewa ba?". "Yaya to mizan zauna nayi kuma. Ina son dai ka sake tunani a wannan gaɓar. Domin duk a yanda muke kallon rayuwa da ɗaukarta yaya watarana sai ta tsere mana ta ɗakko wasunmu a madadinmu. Zata iya yuwuwa kuma ta ɗakko waɗanda muke kallo ba kowa ba su kasance a saman tamu damar". "Hakane Auta, sai dai ban san dalilin wannan gugar zanar ba". Murmushi Uncle Yousuf yay mai ciwo. "Nasan ka sani Yaya, duk da ni ba gugar zana nake maka ba. Sai dai akan Mawaddat kana rumtse idanunka da kunnuwanka domin ƙin amsar gaskiya". Daga haka ya nufi part ɗin nata. Yanda yake haɗa ɗan steps ɗin shiga sashen da bibbiyu zai baka tabbacin ransa a ɓace yake. Sai da ya rumtse ido lokacin daya ɗaura hannunsa kan handle ɗin ƙofar ɗakin nata. Batare da ya yarda ya kalla ɓangaren da gadonta yake ba ya nufi kayan kiɗan ya kashe. Kafin cikin daka tsawa ya ambaci sunanta. A firgice ta tashi tana mai yaye ƙaton lallausan bargon data jibgama kanta. Gaba ɗaya gashin kanta madaidaici a tsaho ya wani hargitse, sanye take da wando da riga na pyjamas farare tas masu santsi da ƙyalli. Kasancewar sun mata bujin-bujin yasa basu bayyana mata surar jiki ba. Ya ɗan samu nutsuwar ganinta da kayan mutunci, dan haka ya kalleta cikin ido babu wasa a tattare da shi ya ce, "Kinyi sallah?". Tana son Uncle Yousuf matuƙa dan shima yana sonta da mata gata. Sai dai kuma baya wasa akan tarbiyyarta da gyara lamarinta shiyyasa take tsoronsa idan ya birkice, dan yasha kwasa mata mari mai gigitarwa. Akwai wani lokaci da ƙawaye suka yaudareta suka sakata dawowa gida a wani yanayi da ga club da ya ɗauketa da wani mahaukacin mari sai da ta yini jinta bai dawo ba. Tuni kuma ta watsakke daga makuwar da tayi..... "I say kinyi salla?!!". Ya sake maimaitawa a tsawace fiye da farko. Daburcewa tai ta ɗaga masa kai ta kuma girgiza. Sai kuma ta sauka da gudu a gadon kamar wata ƙaramar yarinya ta nufi toilet ɗin ta. A cikin mintunan da basu gaza biyu ba ta fito fuska da ƙafafu jiƙe da ruwa wai tayi alwala. Abin salla da Tabawa ke faman ajiya a ma'ajiyarsa kamar na ado dan ba sallar take ba sai randa taso ta ɗauka ta shimfiɗa. Akan kayan barcin ta zumbula hijjabin da shima dai baida banbanci da kayan decorations na gida gareta. Uncle Yousuf na daga inda yake tsaye har yanzu cikin ƙunar rai. Fara sallar da bata da fasali balle makama da gamata ba'a ƙulla mintuna biyu cikakku ba. Hankalin Uncle Yousuf ya ƙara tashi. Dan yau ne karan farko da ya fahimci Mawaddat bata iya ko salla a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un" ya shiga maimaitawa jikinsa na tsuma. Baima san sanda ya kai zaune jagwab cikin kujerar kusa da shi ba. Yanzu nan kamar Mawaddat mai shekara ɗai-ɗai har ashirin da huɗu tana cikin ta biyar, mai karatun matsayin cikakkiyar lauya da duk wanda ta tsayama a shari'a zai iya alfahari da itace babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninta da UBANGIJINTA a ɓangaren bauta masa irin haka. Wane irin sakaci sukan sukai da shagala akan al'amarin yarinyar nan har haka?..... "Uncle You! please kayi haƙuri kar kai fushi da ni". Kalamanta cikin damuwa suka katse masa tunani. Tuni ta rarrafo gabansa ma hijjab ɗin na harɗeta batare da ya sani ba. Idanu kawai ya zuba mata dan shi kam tausayi ma take bashi wlhy. Shi mutum ne mai zafi amma kuma yana da saurin sauka da kuma sauƙin kai shiyyasa yaran ɗan uwan nasa ke sonsa, dan ya taso ne kamar duk shi ya raine su. A hankali ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Muryarshi a rissine bakamar ɗazun ba ya ce, "Mawaddatan-wa'rahmah!". A hankali ta ce, "Yes Uncle". "Mi kikayi haka?". "Uncle salla mana da kace". "Bani nace ba ALLAH ne yace ayi kuma ba haka akeyi ba. Mawaddat wannan ranar ita nake gudun zuwa gareki shiyyasa nake zaneki idan kikaƙi zama Islamiyya a shekarun baya kafin abar ƙasar nan da ke, shiyyasa kuma na dage a nema miki malamin da zai koyar da ke addini bayan Yaya ya maidaki can. Yanzu ace kamarki, ɗiyan musulmi hausawa ƴar ƙasar Nigeria a arewa amma baki iya salla ba? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Mawaddat da duk mi kike yi ke kuwa a duniyar nan haka? Mi kikaima kanki tanadi na tunkarar UBANGIJI da har kikejin ƙwarin gwiwar baje kolinki a duniya da abinda ke cikinta kawai? Anya kin yarda zaki mutu kuwa? Za ki kuma kwanta kabari? Za kuma a tasheki? Za'a kuma miki hisabi sannan ki ƙarɓi sakamakon makomarki?. Makomar da gida biyune kacal dole kuma ka tsinta kanka a ɗaya wuta ko aljanna........." "Uncle Please kabar zancen mutuwan nan mana. Badai sallan bane kuma nayi. Kaga inama da zuwa court zuwa ten ga shi har nine na neman wucewa." "Wato shi zancen sallan baida muhimmanci ko?". "Noo Uncle You! Bance ba fa. Kawai dai ni....." Sai kuma tai shiru. Kansa kawai ya girgiza dan y fahimci ba irin wannan zaman na kai tsaye Mawaddat ke buƙata ba. Yana buƙatar yin nazari akan al'amurinta kafin ya nemo mafita mai ɓullewa. Da hannu yay mata nunin ta tashi da faɗin, "Okay jeki shirya". "Yawwa Sweet Papa na!!!". Ta faɗa da ihu tana miƙewa. Kansa kawai ya girgiza yana mai karanto mata addu'ar shiriya wajen UBANGIJI kamar yanda ya saba akoda yaushe ya tashi ya fice dan bata damar yin shirin.... ∆•••∆ ★ ∆•••∆ Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da sukai masa tsananin nauyi ya fara bin inda yake da kallo. Falo ne babba mai ɗauke da kaya na alfarma. Sai garadan samari guda biyu dake tsaye a kansa da alama sune suka ajiyesa a wajen. Akan mutumin dake zaune cikin kujera mai zaman mutum ɗaya ya tsaida idanun nasa. Shima kallonsa yake yi. Fuska ya ƙara tsukewa tare da kauda kansa, babu alamar tsoro tattare da shi ya ce, "Su waye ku? Mi nakeyi anan?". A karo na farko mutumin yay murmushi har ana iya jin sautinsa. Kansa ya jinjina da faɗin, "Abinda duk aka faɗamin game da kai naga fiye ma da hakan. Sanin ni wanene gareka baida amfani. Abinda ya kawoka nan kuwa shine aiki. Idan kaso zaka iya ɗaukarsa a business ɗin da zaka ƙaru kaima, idan kuma kai tunanin bijirewa ko cigaba da wannan zafin kan naka to komai zai iya faruwa. Sunanka shine *_Aliyu M. Idris Mawashi._* Mata huɗu ne a gidanku ƴaƴa talatin da biyu. Mahaifiyarka itace ta farko a wajen babanka, ku biyar ta haifa ɗaya ya rasu. Kai kaɗaine namiji biyu sunyi aure kanada kanne mata biyu yanzu haka Maryam da Asma'u. Yanzu haka suna a ajin karshe a sakadire, islamiyya suna ajin hadda. Babbar yayarka na auren Alhaji Abubakar Azare itace amaryarsa. Bata sonshi mahaifinku ya haɗasu, yaranta biyu duk maza. Kanwarka dake bimaka tana auren abokinka Sa'id Ibrahim, yarinyarta ɗaya da ciki. Kana cikin matsanancin rayuwa sosai akan al'amuranka daba sai nayi zaman lissafasu ba ka sansu kaima". "Daka sanni har kamar haka, amfanin mi zai maka?". Uncle Smart ya faɗa cikin zafin rai. Ƙaramar dariya mutumin yayi yana wani ɗage kafaɗa. "Amfani masu yawa kuwa, ciki harda abinda zuciyarka bata kawo maka ba. Dan duk wanda na buƙaci alaƙa da shi dole ne ya amince min. Inba haka ba zai fuskanci abinda babu shi a lissafin rayuwarsa. Idan kuma ya amince lafiya zamuyi mu gama cikin mutunta juna na ƙaru ya ƙaru". "Sai kuma gashi ni ba'aimun barazana?". "Ba barazana nake makaba nima. Ina faɗa maka abinda zan iya yine koda a yanzu ne da kake gabana. Aliyu Mawashi! Ko nace Smart Mawashi ni bana faɗar abinda bazan yi ba. Idan na faɗa maka zanyi to na gama shirya yanda zanyi ɗin ne. Ka kwantar da hankalinka aikin da zakamun bamai wahala bane ba, sannan kaima zaka fita a ƙangin damuwar rashin abunyi da kake a ciki, maybe ma ka tsallake ƙasar nan insha ALLAHU a wannan karon ka samu cikar burinka. Mahaifiyarka ta samu kwanciyar hankali da samun salamar hantara daga kishiyoyi da miji, rayuwar ƙannenka ta inganta kamar yanda kake fata. Mahaifinka ya cire zargin da yake maka da fifita ƴan uwanka a samanka duk da bawata tsiya suma suke tsinana masa ba....." "Waye kai?".........✍️ *_Ku ƙara haƙuri dani dan ALLAH. Idan na ɓalle typing har sai kunce ya isa haka in sha ALLAHU🙏😩_* _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 9️⃣ ........Dariya sosai Alhajin ya kwashe da shi. "Karka damu da sanin ni wanene saboda nasan kai waye? Sanin aikin da zakai min kawai ne yafi muhimmanci. Dan na sanka fiye da yanda na faɗa maka a yanzu. Kaɗan na tsinkulo a sanin danai maka kawai. Gidan daka ajiye aiki nake so ka koma ka cigaba da min aiki. Duk wata zan baka albashin naira dubu hamsin bayan albashin da su suke baka dubu ashirin". Ya ajiye masa wani envelope gabansa da cigaba da faɗin, "Wannan shine kundin ayyukan da zakamin a gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi. Zan iya baka dama ta kwana ɗaya kaje kayi tunani, sai dai ka sani ko'a cikin ɗakinka idanuna a kanka suke, dan haka da zuciyarka kawai nake buƙatar kayi nazari. A duk sanda nake buƙatar magana da kai zan nemeka tanan" ya ajiye masa waya akan envelope ɗin daya ajiye gabansa. "A yanzu bana buƙatar cewarka anan, kaje kayi nazarin na barka lafiya. Ku maidashi". Ya ƙare maganar da duban yaransa cikin bada umarni Da wani irin kallo mai nuna tsananin zafin zuciya Uncle Smart ya bisa. Sai dai da alama ran ƴan maza ya ɓaci dan ya kasa furata komai..... Kamar yanda Alhajin ya bada umarni sun maidoshi har kan titin anguwarsu. Kasancewar magrib yayi a gurguje ya ƙarasa gida domin watsama jikinsa da yay nauyi ruwa. Ya samu wasu daga cikin samarin ƙannensa sun dawo gidan. Wanda ya samu a waje suka gaishesa. Da hannu ya amsa musu kawai ya shige ɗakinsa. Shi mutum ne mai tsafta sosai da ƙwanƙonin tsiya, dan haka ganin ɗakin a yanda ya barsa ya sashi jan tsuki yana ɗan dafe kansa dake masa ciwo. Har yanzu abinda suka shaƙa masa bai gama sakin masa jiki ba. A karan farko ya laluba aljihunsa neman wayarsa, cikin sa'a ya jita. Ƙanwarsa Maryam ya kira, suna zaune a falo suna karatun Alkur'ani kiran ya shigo, cike da zumuɗi Asma'u da wayar ke'a gefenta ta ce, "Lah Yaya ne". Kallonta Ammi da Maryam ɗin duk sukayi, ita kuma ta ɗaga da sallama. A hankali ya amsa mata cikin muryarshin nan a dake da wasu ke fassarawa da girman kai da suke kallonsa da shi saboda shiru-shirunsa, batare daya bata damar cewa wani abu ba ya cigaba da faɗin, "Zan samu ruwan zafi a wajenku?". "Eh Yaya". Ta amsa masa cike da girmamawa. Tana ajiye wayar Maryam tace, "Ya dawo ne?". Kai ta ɗaga mata da faɗin, "Ya dawo, cayay na kai masa ruwan zafi, inaga wanka zaiyi". A hankali Ammi ta sauke ajiyar zuciya, sai dai batace da su komai ba ta cigaba da laziminta. Tun safe hankalinsu ke'a tashe, dan bai shiga gidan gaishesu ba kamar yanda ya saba. Da farko Ammi tayi zaton koya fita wani uziri ne, sai da ta shiga gaida Abba ya yanka mata baƙar magana son ransa, kamar yanda ta saba yin shiru akan ƴaƴanta idan yana faɗa haka yanzu ma ta haɗiye, sai da ya gama ta bashi haƙuri, sai dai furucinsa akan zai bar masa gida ya matuƙar tayar mata hankali, har ta aika Maryam kira mata shi ko yana ɗaki amma suka samu baya nan ɗakin ma a buɗe, neman number sa ta shiga yi amma sai ba'a ɗaga ba, daga ƙarshe ma ta daina samunsa. Da wannan damuwar ta yini yau ita dasu Asma'un. Koda Asma'u takai masa ruwan zafin sai da ta gyaro masa toilet sannan ya shiga, ɗakin ta shiga kimtsa masa shima. Kafin ya fito harta kammala ta fice. Kasancewar anyi sallar magriba yay tashi a ɗaki sannan ya fice massalaci yin isha'i. Bayan an idar gidan ya sake komawa. Abba bai shigoba, dan haka ya wuce cikin gidan. Kamar yanda ya saba sai da yabi duk ɗakunan matan gidan ya gaidasu. Da ɗakin Aunty Amarya ya fara. Mace ce mai yawan fara'a da son mutane, sai dai kuma bata da yawan magana itama. Duk da zai iya sa'anni da ita hakan bai hanashi girmamata saboda yanda take girmama Ammi a gidan itama kamar ba kishiya ba. Ya gaidata cikin mutuntawa, ta amsa masa da kulawa. Yaranta dake sabgogin gabansu a falon tun shigowarsa duk suka nutsu dama. Duk sun gaidashi, yayinda ƙaramar tazo jikinsa tana kawo masa ƙarar ɗan uwanta dake bima babbar ɗakin nasu cewar ya karya mata pencil ɗinta tana homework. Da sauri yaron mai suna Abbas ya ce, "Yayanmu ƙarya take ita ta karya abunta a makaranta suna faɗa da Ameer. Kuka ta saka itama tana faɗin, "Ƙaryane Yaya shine". Hannu ya ɗaga musu duk sukai shiru. Aunty Amarya tace, "Ai inba ubansu kaci ba Yayansu ba barin kunnen mutane ya huta zasuyi ba. Tun ɗazu suke rikicin nan ni harna gaji ma da magana". Faɗa yama yaran cikin sigar nasiha, yace da safe kafin su wuce makaranta Anisan tazo ɗakinsa ta amshi sabon pencil. Da ga haka ya fito zuwa ɗakin Umma. Itace ta biyu a gidan, amma itace mai manyan ƴaƴa a sakamakon rashin samun haihuwa da Ammah bataiba da wuri, kusan duk sunyi aure kuma. Sai dai tanada sauran ƴammata biyu a yanzu haka da samari biyu da basuyi aure ba. Ta amsa masa a ɗan fisge, bai damuba dan hakan ba sabon abu bane a garesa. Nusaiba autarta dake gefenta zaune tana cin abinci ta gaidashi itama. Amsa mata yayi yana miƙewa. Dakatar da shi Umman tayi da faɗin, "Yau lafiya kuwa bamu ganka da safe ba?". Ɗan murmushin ƙarfin hali yay mata da faɗin. "Ba komai Umma na fitane da safe sosai wani uziri". "Uhhm to yayi". Ta faɗa a taƙaice. Iska ya ɗan furzar da ga bakinsa kawai ya miƙe yana ficewa. Ɗakin Mama ya nufa, mace ta uku a gidan, sai dai ya samu tana sashen Abba dan itace da girki yau. Mansur ƙaninsa ɗanta na huɗu kawai ya samu a falon da yarinyar ƙanwarsu (jikar gidan) tana barci a kujera. Gaishesa Mansur ɗin yayi yana wani nannoƙe kai na rashin kunya, sai dai babu damar yi dan suna tsoronsa a gidan ba kamar sauran yayunsu maza da suke iyama rashin kunya ba. Amsa masa yayi yana kallon askin kansa na rashin tarbiyya. "Idan na wayi gari na ganka da wannan askin bisa kai kayi kuka da kanka". Daga haka ya fice. Baki Mansur ya tura gaba yana ƙunƙuni da yarfa hannuwa. Sai dai babu damar yi da ƙarfi. Ammah na zaune su Maryam a gefensa suna cin abinci da kallo film ya shiga da sallama. A tare suka amsa masa da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana kaiwa zaune. Ammah ya gaida da bata haƙurin rashin shigowarsa da safe. Dai-dai nan Maryam ta ajiye masa abinci da fure weter. Ɗakinsu suka shige da abincin dan sun san akwai magana a bakin Ammah. Suna shigewa kuwa ta dubesa da ɗauke kai ta ce, "Lafiya ka fita tunda safe?". Samun kansa yay da faɗin, "Lafiya lau Ammah naje wajen aiki ne". A hankali ta sauke numfashi. "Nasan ba son aikin nan kake ba Hydar. Sai dai mai haƙuri yakan dafa dutse har yasha romonsa. Kafi kowa sanin yanda gidan nan ya koma yanzu, miyasa bazaka sakama kanka haƙuri da mutane ba ka karɓi rayuwa a duk yanda tazo maka. Kowane bawa daka gani akwai irin tashi ƙaddarar, amsarta da haƙuri kuma shine mizanin imani. Zuwa yanzu yakamata ace kun bar mahaifinku ya huta dako ciyar da kune, shekarunsa yaja yana buƙatar hutu na rayuwa dana jiki. Yasha matuƙar ɗawainiya da ku tun kuna ƙanana har girmanku, bai tauye kowannenku ga ilimi ba da ci da sha da kula da lafiyarku har girmanku. A yanzu kune ya kamata ace kun rungumesa shima tare da ƙannenku da suka rage a gabanmu, dan wataran kune zaku maye gurbinmu garesu a yayin da ƙasa ta rufe idanunmu". Gaba ɗaya jikinsa ya ƙarayin sanyi da nasihar mahaifiyar tasa. Idanunsa sun kada sunyi ja, cikin gyaɗa kai da tausasa harshe ya ce, "Inasha ALLAHU Ammah zaki sameni fiye da yanda kike buƙata. Kuyita haƙuri damu kuma kuci gaba da mana addu'a". "Addu'a kullum cikin yimuku muke babu fashi". Sun cigaba da hira da mahaifiyarsa da ƙanensa da suka fito ya nuna musu assagment har zuwa ƙarfe tara da kusan rabi sannan ya fito. Ɗakinsa ya koma dan yasan yanzu Abba ya riga ya kwanta. Sai da yay shafa'i da wutiri ya samu kwantawa, abinda ya faru a yinin ya shiga dawo masa dalla-dalla. Envelope ɗin nan ya ɗakko ya fara dubawa. Takarda ce kawai a cikinsa ɗauke da rubutu mai ɗan tsaho, abubuwan da aka rubuta ɗin ya matuƙar bashi mamaki harma ya rasa wane kalar tunani zaiyi a kai. Shi dai har yanzu babu abinda zai iya ƙaraswa akan Jiƙamshi family na ƙwarai ko akasinsa. In ma akwai abinda zai iya faɗa to maybe akan wannan ballagazar yarinyar ne ta jiya, siririn tsaki yaja saboda tunota da yayi. Takardar ya yasar gefe ya kwanta yana mai lumshe idanunsa dake cike da barci...... _______________________★ Washe gari da abubuwa da yawa ya tashi a cikin rai. Mafi girman jagorantar ƙarfin gwiwar sa nasihar Ammah, sai kuma wani dalili nasa akan mutumin jiya da son sanin manufarsa ta haƙiƙa, dan yasan in ma bai amshi aikin ba zai iya saka wani yay masa, shiko duk da bai gama sanin suwaye Uncle Yousuf ɗin ba sai yaji bazai iya sakacin barin ƙofar da za'a cuta musu ba har sai yasan gaskiya a kansu. ƙarfe bakwai da kwata a gidan Uncle Yousuf ɗin yay masa. Yana zaune a gate wajen maigadinsu suna ƴar hira kasancewar mutumin Dattijo ne nutsatstse mai aikinsu ta kawo breakfast. Cikin girmamawa ta gaidashi shi da maigadin. Hannu kawai ya ɗaga mata ya ɗauke kansa. Harta juya zata koma maigadi ya tsayar da ita da tambayar Alhaji ya fito ne?. "A'a nadai ji aunty na batun tadoshi an kirata a waya wannan masifaffiyar aunty Lu suke kiranta ko ta gidan Alhaji Babba bata da lafiy....." Bata gama rufe baki ba sai gashi ya fito kamar a ɗan rikice. Tun daga nesa ya ƙwalama maigadi kiran ya buɗe masa gate. Miƙewa maigadin yay da hanzarinsa, hakan yasa Uncle Smart ɗin shima miƙewar ya nufesa. Ganin yanda ya daburce yama kasa tantance motar da ya ɗakkoma key yay masa sallama. Juyowa yay ya ɗan kallesa, har ya ɗauke kai sai kuma ya sake jiyowa. "Alhamdullah" ya faɗa yana miƙo masa key ɗin batare daya tuna cewa yanzu fa ba ƙarƙashin su yake ba. Babu musu ya amsa key ɗin, dannawa yay motar tai ƙara, dan haka ya nufeta. Sai da ya dai-daita ta sannan, yana batun fitowa ya buɗe masa yaga ya buɗe gaban motar ya shiga yana faɗin, "Yi sauri Please da alama abun babbane, dan duk ciwon Mawaddat da zai iya saka Aunty Kareema ruɗewa irin haka ba ƙarami bane ba". Gudu kawai ya ƙara batare da yace komai ba dan ba fahimtar akan wa ake maganar yay ba shi dai. Bawani nisane tsakaninsu ba, dan layinne kawai ba ɗaya ba.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 🔟 ........Ko parking bai gama yi da ƙyau ba Uncle Yousuf ɗin ya fice, ba'a rufe mintuna biyar cikakku ba sai gashi ya fito ɗauke da Lulu yaran gidan biye da shi cikin tashin hankali. Shi ya buɗe masa motar, sai lokacin ma yasan itace. Wani iri yaji a ransa musamman tuna abinda akace game da ita a takardar jiya da Alhajin nan ya bashi. Da wannan tunanin yaja motar suka fice a gidan. Kai tsaye wani babban p-hospital mai suna *_SHIRA'S HOSPITAL_* suka nufa. Yanda aka tarbesu zai tabbatar maka da an san da su. Har yay zamansa a mota sai kuma ya fita yabi bayansu, dai-dai nan suma ƴan gidansu da suka biyo bayan su motarsu ta iso cikin asibitin. Duk wani kai kawo da ake a kanta shi dai nashi ido ne. Yayinda acan ƙasan zuciyarsa yaketa tufƙa da warwara akan abubuwa da dama. Musamman akan abinda ya dawo da shi aiki cikin wannan family ɗin a karo na biyu. Tabbas ya amshi aiki, sai dai kuma bada manufar wanda ya bashi aikin ba. Dan ko kaɗan baiji wani kurari daga gargaɗinsa sun tsoratashi ba. Hasalima shi wanda ya bashi aikin da yasan shi ɗin wanene maybe dabai bashi ɗin ba. Amma zaiyi, dan in bai amsa ba zai bama wani da zai iya masa yanda yake so... Ringing ɗin wayarsa ne ya katse masa tunani, ya ciro wayar daga aljihu yana miƙewa ya fito. Sallama yay bayan yakai wayar kunnensa, daga haka bai sake magana ba sai saurare. Bayan ya katse kiran ya cire wayar a kunnensa yana furzar da iska kaɗan. Cike da iya nazari yake bin farfajiyar asibitin da kallo a kaikaice, can idonsa ya sauka akan abinda yake nema. Basarwa yay ya share na wasu mintuna, kafin ya nufi fita gate ɗin a nutse. Dai-dai inda almajirai ke zaman bara ya dakata, naira ɗari biyu dake aljihunsa ya ciro ya saka a kwanon barar wani gurgun almajiri dake kan katako mai tayu, almajirin ya shiga jera masa addu'a. Yana ƙoƙarin juyawa matashin saurayin dake gefensa kaɗan yazo ta gefensa suka bangaji juna, kallon juna sukai kamar cikin jin haushi. Sai dai shi saurayin yay saurin faɗin, "Yi haƙuri abokina ban lura bane ba". Kai kawai ya kaɗa masa yabar wajen batare daya tanka ba. Maimakon komawa cikin asibitin sai ya samu waje a harabar ya zauna abinsa, can kusan mintuna uku yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu sai yaji takardar da saurayin nan ya saƙala masa a aljihu sanda sukai karo batare da ya lura ba. Zarota yay ya warware cike da mamaki, sai kuma ya shiga ɗan waige-waige amma babu alamar saurayin ko wani da zai ce hankalinsa a kansa yake. _"Ni kamar iska nake, a duk lokacin data kaɗa sai anji sautinta a dukkan ƙofofin gashi na jiki. Idan kuma nai shirin zuwa waje matsayin guguwa tarwatsa komai da kowa na gari nake hatta ruwan kogi baya tsira da ga mamayata. Ka kula, in ba hakaba ni na ƙulleka a cikin ƙullina Aliyu Hydar Mawashi"_. Wani irin tashi tsigar jikinsa ta farayi na ɓacin rai. A take zuciyarsa ta fara kaikawo da sauri-sauri cikin ƙirjinsa. Takardar ya ninke ya maida aljihu, yana batun tashi waya ta sake yin ringing a jikinsa. Wayar dai da Alhaji nan ne ya bashi jiya, yana kuma ƙyautata zaton takardar nan ma da ga garesa take duk da ya kirashi ne ɗazun a wayarsa. Shi sam yama manta da wayar. Cirota yayi daga aljihun, kamar bazai ɗaga ba sai kuma miya tuna ya ɗaga tana gab da tsinkewa ya kai kunne. Baiyi magana ba daga can ma akai shiru, ganin ana neman shafe minti guda ya katse shirun da faɗin, "Inada abinyi fa Malam". Ƙaramar dariya akai daga can tare da faɗin, "Wannan girman kan naka da gizago kesani ƙara jin ka dace da buƙatar aikina Smart Mawashi. Mutanena sun sanar min ka koma aiki, weldone daka kasance mai biyayya irin haka da saurin gane abu...." "Na koma ne badan kurarinka ko farfagandarka ba! Ko a tunaninka sakawa ana bibiyata da kawomin wasu banzayen saƙwanni a takarda ko kiran wayata zaisa nayi abinda kake so?". Ya faɗa cikin katseshi murya a dake. Dariya akayi da ga can, Alhaji ya ce, "Muɗauka haka ɗinne to. Sai dai ka sani ni samaniya ne mai rufe rufin kowanne gida da daji. Abinda kaga ya faru har ya kawoku asibiti yau ka ɗauka shine signing na contract ɗinmu da kai. Ya rage naka ka fara aiwatar da ayyukanka yanda ya dace ko kai kuskuren nunamin zafin kai na cigaba da nuna maka sauran kalolina. Dan a duk inda Jiƙamshi family suke ni nan da kake ji da gani zagaye nake da su har a cikin ɗakin kwanansu, har ma da kai kanka a yanzu...." Baki ya buɗe zai yi magana ƙittt aka yanke wayar, da sauri ya cirota daga kunnensa, ƙoƙarin kiran layin ya shigayi sai dai yaƙi shiga, ya koma wajen massage danya tura sai ya gama babu app na massage a wayar kwata-kwata. Cikin tsarguwa ya ɗan fara dube-dube, sai dai babu alamar wani da hankalinsa ke a kansa a eriya ɗin wajen gaba ɗaya. Wayarsa ya ciro ya kwashe number da zummar yin kira sai dai kuma taƙi shiga, wadda aka kirashi a farko ya gwada kira itama taƙi shiga. Yay ɗan shiru ransa a dagule, tunanin kiran wani abokinsa yay da zummar masa tracing layukan sai kuma ya fasa saboda tuna maganar mutumin. (A duk inda kake idanuna a kanka suke koda a cikin ɗakin barcinka ne). Fasawa yay ya maida wayar aljihu yana jin zuciyarsa ta masa nauyi da tunani kala daban-daban. Gaba ɗaya wannan yinin haka ahalin Jiƙamshi gaba ɗaya suka yisa a asibitin tare da shi. Bai yi yinƙurin komai akan son sanin abinda ke damunta ba. Yana dai biye da motsin kowa har zuwa azhar da Uncle Yousuf ya buƙaci ya kaishi gida zai ɗan watsa ruwa. Sai da suka hau hanya yake tambayarsa ya mai jiki. Cikin damuwa Uncle Yousuf ya ɗan furzar da nannauyar ajiyar zuciya tare da dafe kansa ya ce, "Da sauƙi za'ace, dan tunda muka zo sai yanzu ne aka samu kanta har barci ya ɗauketa. Shiyyasa nake son a yau mubar ƙasar nan dan ban taɓa ganin Muwaddat a cikin halin ciwo mai tsananin irin wannan ba. Ban san mi yarinyar ke son maida kanta ba, ban taɓa tunanin rashin jinta ya kai haka ba sai yau, yanzu doctor ya ɗan fara min bayanin wai shaye-shaye ne ke son jawo mata matsala, ban san wane irin rayuwa yarinyar nan take son kai kantaba kuma. Amma duk laifin Yaya ne da ke nuna mata ƙazamin gatan da shi a gurinshi yake ɗauka so ne..." yaja tsaki mai nuna tsananin ƙunar da zuciyarsa ke masa. Da gani kasan yana jin zafi ne a ransa har yake furta abinda bai kamata ya furta a gaban driver kamarsa ba. Sai dai shi kansa ya matuƙar girgiza dajin kalaman Uncle Yousuf ɗin. A ransa faɗi yake (No wander idanunta sam babu kunya da mutunci a cikinsu ashe ƴar shaye-shaye ce) wani irin tsanarta yaji ta sake ɗarsuwa a ransa, ashe bayan ballagazanci harda shaye-shaye. Da ƙyar ya iya furta ma Uncle Yousuf cewar "ALLAH dai ya bata lafiya Alhaji. Sai dai addu'a, a wannan zamanin yara mata da yawa suna cikin wannan mummunar ɗabi'ar ta shaye-shaye, wasu samari ke ɗorasu wasu ƙawaye, wasu matsin rayuwa maimakon suyi tawakkali da haƙuri su maida al'amarin su ga UBANGIJI sai su zaɓi wannan hanyar mara ɓillewa. Wasu ko tsabar gata ne da jin daɗin duniya ke kwasarsu. Sai dai fatan ALLAH ya shiryesu ya kare wanda kuma basu fara ba dan abin tashin hankalin harda matan aure ma yanzu". Cikin tsananin damuwa Uncle Yousuf yace, "ALLAH ka shiryar mana da su. Kayi mana maganin duk wasu azzalumai dake safarar mugayen abubuwan nan zuwa ƙasashenmu suna ɓata mana yara". "Amin ya rabbi". Ya amsa masa dai-dai yana shiga layin gidan Uncle Yousuf ɗin..... ★A ranar bai samu damar zaman yin magana da Uncle Yousuf kan batun dawowarsa aiki ba. Dan yana shiga yay wanka sake fitowa yay suka koma asibitin. Zuwa yanzu kam ta samu barci kamar yanda yaji ƴan uwan na faɗama Uncle Yousuf. Sai a lokacin ya samu damar gaisawa da Daddy daya iso yanzu da ga Abuja da Mommy ya jajanta musu. Cikin ƙarfin hali Daddy ya ce, "Kamar yaron nan daka kawo ne kace kuma ya ajiye aiki jiya Yousuf?". Kai tsaye Uncle Yousuf ɗin ya ce, "Shine Yaya. Sai dai banyi magana da shi ba dai bayan wadda nace maka nayi, amma inaga ya dawo aikinsa ne". Daddy ya ɗan ja numfashi da faɗin, "Dama Baby batace bata buƙatarsa ba ai. Amma mu jira har ALLAH ya bata lafiya sai muji ta bakinta dai". "Uhum" Kawai Uncle Yousuf yace. Mommy ma dai dake jinsu batace komai ba sai ma ɗauke kanta tai gefe dan haushin mijin nata akan ƴarsu da zata iya rantsuwa da ƙazamar soyayyar da yake matane duk ya zama silar komai na halin da take ciki a yanzu. Duk da dai basu ji komai da ga bayanin likita ba amma yanzu zasuje garesa suji ɗin. Su duka ukun suka nufi office ɗin Doctor Khalil Shira.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* [𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣1️⃣ ........Nagartaccen likita nutsatstse da ya san makamar aikinsa. Cikin girmamawa ya gaida Mommy da Daddy, Uncle Yousuf kuma ya bashi hannu sukai musabaha dan zasu iya zama sa'anni. Kusan mintuna uku ya nisa yana mai gyara gilashin idanunsa da ɗagowa ya ɗan kallesu. "A ɗazun mun ɗan fara magana da Yousuf wani hanzari ya katseni, shiyyasa na buƙaci ganinku ku duka saboda muhimmancin abinda zan faɗa game da lafiyar Muwaddat". "Doctor ALLAH dai yasa ba wani mummunan ciwo bane, idan kasan akwai matsala dan ALLAH ka barmu mu wuce da ita ƙetare kar sai al'amarin ya ƙwace azo ana wallahi tallahi zuciyarmu bazata iya ɗauka ba". "Ka kwantar da hankalinka Alhaji, bawai matsalar zamanta anan ko fitar da ita zuwa ƙasar waje ne damuwar ba. Sanadin abinda ya haddasa mata ciwon nake son ku sani domin a ɗauki mataki...." "Minene likita?". Daddy ya sake faɗa a zabure cikin katse Dr Khalifa Shira. "Kwantar da hankalinka Alhaji". Khalifa ya faɗa yana sake gyara zama. Cigaba yay da faɗin, "Ina son ku fahimci maganata da idon basira duk da ban sani ba ko kun san halin da take ciki kafin yau ɗin. Bincikemu ya nuna mana ba komai ya haddasa mata matsalar da take ciki ba yanzu sai Shaye-shaye.." "What?!!". Daddy ya faɗa yana miƙewa zumbur. Jikinsa har rawa yake wajen nuna Dr Khalil Shira. "Yarinyar tawa zakaima sharri, miya haɗa wata Muwaddat da shaye-shaye? Yarinyar da bata san komai ba sai karatunta. Amma kai dai wlhy anyi......." "Yaya Please ka bari ya faɗa mana abinda ke faruwa mana. A wannan zamanin har wani gardama ko shaidar yaranmu za'ai akan hakan". Uncle Yousuf ya faɗa cikin damuwa da takaicin Daddy. Mommy ma kallonsa take cikin tashin hankali da ɓacin rai, duk da ba itace ta haifi Muwaddat da cikinta ba bazata so ace yarinyar ta lalace kamar haka ba. Tasha wahala a hannun mijinta akan mahaifiyar Muwaddat matuƙa, bayan rasuwarta kuma tabar baya da ƙura dan Daddy wani sabon shafin wulaƙanci ya buɗe akan al'amarin Muwaddat gareta.... Bayanin da likita ya fara ne ya katse mata tunaninta. Dr Khalifa Shira ya cigaba da faɗin, "Alhaji a wannan zamanin da muke ciki wannan ba abin mamaki bane. Yara mata da yawa sun shiga wannan mummunar aƙidar abin tashin hankali harda matan aure ma. Iya gaskiyata na faɗa muku Muwaddat na shaye-shaye, kuma da alama ta jima a cikin wannan al'amarin dan gashi har ya fara taɓa mata lafiyarta. Idan kuma har bata dainaba komai zai iya faruwa ciki harda rasata. Ya dace kusa ido akanta da duk wani motsinta na rayuwa, idan da dama ma a nisantata da komai cikin hikima, sannan a rabata da duk abokan mu'amalarta akan hakan harma da inda take zuwa ta shawo dan alamu sun nunamin baku san tanayi ba. Iyaye da yawa sunfi maida hankali da damuwa akan kar ƴaƴansu mata su lalace wajen zubar da mutuncinsu akan huɗubar maza (zina), a tunaninsu wannan itace kawai matsalar dake iya tauye mace ko fanɗarar da tarbiyyarta. Shiyyasa sai yaran har suyi nisa a lalacewar da basu jawoma kansu tunaninta ba misali irin wannan ta shaye-shaye daketa ƙara yawaita a cikin al'ummar mu a yau. Hakama mazaje da yawa sakacinsu da son zuciya ya haifarma matansu da yawa shiga irin wannan halin batare da sun fargaba. Yayinda wasu ɓangare na matan kan jefa kansu ne ga ɗabi'ar shaye-shayen saboda son zuciya ko zama da abokai ko ƙawaye ko samari dakan koya musu. Ya kamata ku binciki silar faɗawarta wannan yanayin kuyi kuma gaggawar maganceta duk da abin ya rigada ya mata nisa sosai sai addu'a gaskiya. ALLAH ya bata lafiya ya kuma shiryar damu da zuri'armu baki ɗaya akan tafarki na gaskiya". Uncle Yousuf da Mommy ne suka iya amsawa da Amin. Daddy kam da alama ma hankalinsa sam baya jikinsa. Dr Khalifa Shira ya ɗan ƙara musu da shawarwarin yanda zasu fuskanci rayuwar Muwaddat ɗin. Kafin ya sallamesu. Har lokacin Daddy bai iya sake furta komai ba. Dan da zasu tafi ma sai da Uncle Yousuf ya taɓashi, sai dai yana yunƙurawa zai tashi juwa ta kwasheshi ya tafi zai zube ƙasa sai da suka taro shi. Hankali tashe shima aka bashi gado. Nanfa Jiƙamshi family suka sake shiga maɗaukakin tashin hankali mara misali. Haka suka yini ranar zubir a asibitin. Shi kansa bai samu kansa ba sai wajen goma na dare bayan ya maida Aunty Saliha matar Uncle Yousuf gida da yaransa yace ya dawo masa da motar ya wuce kawai shi dole zai kwana anan saboda Daddy shima dole an bashi gado. Dr Khalifa kuma yace bazasu sallamesa ba har sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da rai. Godiya yay masa da hakan dan harga ALLAH ya matuƙar gajiya dama ga yunwa dake cin hanjinsa kasancewar bai wani samu abincin kirki yaci a yinin ba sai wata ƴar gurasa. Sai dai babu yanda zai yi tunda hanyar neman abincinsa ce. Koda ya shiga gidan bai nema kowa ba ya shige ɗakinsa. Sai da ya kammala komai na al'adar rayuwarsa sannan yay zaman cin indomie ɗin daya saya wajen Haladu mai shayi. Tare da shayinsa daya sabarma kansa sha yaci, dan ya samu an dafa masa sabo a flaks. Yasan aikin ƙannensa ne dan basa gajiya da hidimarsa. Hatta ɗakinsa ƙal yake da gyara, dan ko kayansa ƙananu basa ƙyashin zama su wanke masa fes su goge, manyan kayanne dai irinsu shadda sai dai ya kai wanki. Badan kuma bazasu iyaba yake kaiwar, sai dan rage musu aiki ne. Ya jima baiyi barcin ba yana ƙullawa da kwancewa akan al'amuran rayuwa da suka haye masa badan ya tsara su a cikin rayuwarsa ba. Tun yana yaro a kullum burinsa shine buga ƙwallon ƙafa da yin kasuwanci, sai gashi yau ya tsinta kansa a wani matsayin ɓoyayyen aiki da ya zame masa haye. Dan lamarin wannan ɗan taran da bai san miye manufarsa ba yana sake kutso rayuwarsa cikin rayuwar mutanen da har yanzu ya kasa samun amsa ko dalilin dangantakar da ALLAH ya ƙulla a tsakaninsa da su batare da su sun san ma'anar hakan ba suma na cimasa rai. Su dai kawai kallon driver a ƙarƙashinsu suke masa kamar yanda Uncle Yousuf ɗin ya ɗakkosa tun farko yi. Sai kusan ɗaya da wani abu ya samu barcin ya ɗauke sa mai cike da mafarkai marasa daɗi da suka shafi Jiƙamshi family, kodan ya kwanta da tunanunsu ne a rai oho. Ai ko sai gashi ya kusa makara da asuba. Da ƙyar ya iya tashi yay alwala ya wuce massalaci... Sashen Abba ya fara shiga kamar yanda ya saba a kowace safiya duk da sunga juna a massalaci. Gaishesa yayi cikin girmamawa da ƙanƙan da kai tare da masa bayanin komawarsa aiki jiya. Karan farko Abba yay ɗan murmushi irin na manya. Tare da faɗin, "Naji daɗin haka sosai, ina kuma maka addu'ar fatan alkairin ALLAH ya baka ikon jurewa. Aliy ba sonka bane banayi da kaga ina maka faɗa. Zaman nan naka ne bana so a hakan. Kai ba aiki ba, ba aure ba, ba wani sana'a ƙwaƙwƙwara ba. Ka duba ƙannen bayanka kusan huɗu sunyi aure har ma ana batun yima wasu ukun. Ba maganar mata nake ba dan su dama dan hakan ta faru ba komai bane ba ai tunda matane". "Kayi haƙuri Abba in sha ALLAHU zaku cigaba da samuna a yanda kuke fata. Ku gafarceni da duk ɓata muku da nake yi". "ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, amma ka dage dai ka nema matar aure zamanka ya isheni haka, kaima ina son ganin jininka kafin ƙasa ta rufe idanuna". Ɗan murmushi kawai yayi kansa a ƙasa. Yau ya ɗan jima a wajen Abban har wasu a cikin ƙanensa suka ɗan shigo gaida Abban. Bayan barinsa nan cikin gida ya shiga. Kowane ɗaki sai da ya leƙa suka gaisa, a ɗakin Ammah ya ɗan sha shayi a tsaitsaye yay mata sallama ya fito ganin yana neman makara. Wanka yayi a gurguje yay shirinsa cikin uniform ɗin aikinsa ya fice a gidan.... ★ Yau ma dai gidan Uncle Yousuf ya nufa kai tsaye, saɓanin jiya ya sameshi a compound zaune tare da baƙo. Bai zauna wajen maigadi ba ya nufesu. Uncle Yousuf dake dubansa da murmushi ya ce, "Uncle Smart na yara". Murmushi yayi da ɗan shafa kansa suka gaisa cikin girmamawa. Baƙon nasa ma suka gaisa. Yana ƙoƙarin barin wajen Uncle Yousuf ya tsaida shi tare da nuna masa wajen zama. "Kaga zauna muyi magana shima ɗan gida ne. Dama kuma akan abinda ya shafi aikinka muke maganar. Sunansa Tajuddeen, surukina ne kuma ɗan uwana. Yaso Muwaddat da muka kai asibiti jiya kuma yana akan sonta dan har ranar aure an saka musu shekaru uku da suka gabata, sai dai taƙi yarda ai bikin. Abinda yasa nace maka zaman ya shafeka saboda taimakon da muke son kai mana ne tare da sake roƙonka kan ajiye aiki da kai niyyar yi. Aliyu a haɗuwarku ɗaya da Muwaddat kawai na fahimci zaka iya bamu taimako akanta, dan kafin kai mun saka drivers da yawa tun dawowarta ƙasar nan amma tsoronta sukeji saboda azababbiyar yarinya ce da kake ganinta, gashi bata shakkar kowa. Shiyyasa basa iya yin komai kan al'amarin ta. Akan Muwaddat kam nasan aikine mai wahalar gaske zamu baka amma dan ALLAH ka taimakemu kaine kawai hope ɗinmu a yanzu game da yanayin da take ciki." Ganin yanda yakai ƙarshen maganar kamar a yanayin son jin ta bakinsa ya sashi nisawa. Cikin dakewar nan tasa ya ce, "Alhaji zan iya taimaka muku, sai dai fa akwai matsala dan zamanmu inuwa ɗaya da ita bazai yiyu ba. Kayi hakuri bazan iya ɗaukar ƙasƙanci ba, idan tace zata wulaƙantani bana zaton kallonta matsayin wadda nakema aiki zan ɗauki mataki kanta ako ina ne kuma". "Na baka wannan damar, dan hakan nafi buƙata nima". "Shikenan, wane irin taimako kuke buƙata da ga gareni?". "Sanya mana ido akan al'amuranta, ƙawayenta, abokan mu'amalarta, inda take zuwa bayan wajen aiki. Kai hatta waya da zatayi idan san samune musan dawa take yi. Bayan ka gama sanin waɗan nan sai muje mataki na gaba". "Indai wannan ne babu damuwa in sha ALLAHU". Godiya sukai masa, tare da tabbatar masa zai fara aiki da ita da zarar an sallamota asibiti. Sun kuma ninka masa albashinsa..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* [8/22, 7:41 AM] Maman Aslam: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣2️⃣ ____________________ https://youtu.be/y6YMU120RZI Please subscribe to Rukayyat khalid YouTube channel fisabilillah. I only uploads videos na karatun Qur'an a tashar Please help me reach 1k subs soon insha Allah *RUKAYYAT KHALID* *Assalamualaikum warahmatullah* *Yar uwa shin mene amfanin wayar hannunki da bazaki koyi sana a da ita ba?* *Kullum kina yawo a social media irin su Facebook, WhatsApp, tiktok,Instagram, twitter da ma sauransu.* *Kina asarar data a banza kina zuba adashinda babu ranar dauka* *bakya chas bakya as? Se chart kika iya 🤔* *kin damu mijinki da BANI BANI?? Kizo nan ni* *~Graphics by Rukayyat~* *zan koya miki sanaar Graphics design wanda zaki samu abin dog dogaro da kai. Kina zaune daga gida kina sanaarki.* *Ga mai bukata a masa design ko wani iri, munayi insha Allah* SERVICES PROVIDED 🌹Logos 🌹Flyers 🌹data flyers 🌹Pos banner 🌹Book cover 🌹 Invitation Card 🌹 Business Card 🌹 Banner 🌹 Save The Date 🌹 Bank Sticker 🌹 Video Invitation card 🌹 Birthday Videos 🌹Business logo 🌹graduation poster 🌹e t c Muna kowani design a farashi mai kyau idan training kikeso ma munayi shima a farashi mai kyau insha Allah kedai kimin magana ta wannan number 👇?? *DM FOR ANY ENQUIRY* 07084515410 _____________________ ........A ranar dai bai yi aikin komai ba sai zama tare da maigadi suka sha hirarsu, abinci ma daga cikin gidan aka kawo harda nashi. Yaso ƙin ci dan shi irin mutanen nan ne masu tsantsenin tsiya. Abu indai ba nasu ba kona gidansu sukan iya hana kansu koda suna buƙatarsa. A hakan ma kaɗan yaci ya cire hannu. Sai bayan sallar la'asar ya tafi kai Aunty Saliha asibiti tare da su Deen. Kasancewar da kayan abinci ta tafi ya taimaka mata wajen shiga da su ciki. Anan ne ya samu damar ganinta. Kwance take rai-rai a kan gado Mommy na zaune ta jingina da jikinta, a kallo ɗaya zaka tabbatar da taji jiki, dan kwana ɗaya kacal harta faɗa da ƙarayin wani fayau da ita. Bayan ya gaisa da su Mommy ya gaisheta da jiki itama a taƙaice. Kaɗan ta ɗago idanunta dake nuna yanayin halin da take ciki na ciwo ta dubesa. Maimakon amsa masa sai ta watsa masa wani kallon rashin mutunci ta ɗauke kai a yatsine. Mommy ce ta dubeta cikin ɗan faɗa-faɗa. Sai dai kafin tai magana Deen ya ce, "Aunty Lu Uncle Smart fa na gaisheki da jiki baki amsa masa ba kuma kina masa harara". Harara ta zubama yaron, muryarta a ɗashe irin na mai ciwo tace, "To maganatu naƙi na amsa ɗin, an kuma hararesan. Yaro sai sa idon tsiya. Ko dokace kowane trash idan ya gaisheni sai na amsa". Baki ya tura mata da matsawa jikin uwarsa yana ɗan ƙunƙuni. Zata sake magana Mommy ta tareta. "Wai nikam yaushe ne zakiyi hankali Muwaddat? Yanzu kina a gadon asibitin ma bazaki bar masifa ba. Jiya i yanzu fa kina nan keba matatta ba keba mai rai ba hankalin kowa a tashe. Haba ayi mutum babu haƙuri sam sai baƙin tujaran tsiya kamar mara mafaɗi". Sosai ranta ya sosu ganin yanda Mommy ke mata faɗa a gabansa. Badai ta tanka ba amma tayi alƙawarin koya masa hankali tunda har akai mata haka a kansa. Bata sake magana ba ta gyara kwanciyarta ta juya musu baya, dan koyaya tana shakkar Mommy ɗin kasancewar bata yarda ta bata fuskar rainata ba duk da abinda Daddy kemata akanta tun tana a showal. Shima ficewa yay daga waje abinsa yana sake jinjina halin yarinyar mai ido a tsakar kai... *_BAYAN KWANA UKU_* Kwanakinta uku a asibitin aka sallamosu, dama shi Daddy tun washe gari aka sallamesa sai dai Dr Khalipa ya bashi shawarar ɗan yin nisa da asibitin har ya samu nutsuwa. Shiyyasa bai sake zuwa ba akan tsayawar Uncle Yousuf amma duk da haka kullum sai yazo da dare ya dubata. Alhmdllh jikin nata da sauƙi sosai. Sai dai har sannan batajin ƙarfinsa. Ga buƙatar kayan shaye-shayenta da take matuƙar yi sai dai babu damar shansu. Shine ya ɗakkota tare da Mommy. Yanda kowa ke tattalinta na bashi mamaki kamar wata ƙaramar yarinya. Musamman ma Daddy dake yi kamar zai maidata cikinsa. Ko yaya ta motsa sai ya tambayi ba'asi. Idan ko tace wash yaringa jera mata sannu kenan kaji har muryarsa na zuga dan damuwa. Kasancewar sallamar dare akai musu yana ajiyesu ya wuce gida. Da ƙyar ya samu napep saboda yanayin anguwar tasu. Ana sallar isha'i ya shiga gida. Wanka ya farayi sannan ya shiga gaida su Ammah. Yau kam ya samu Umma da Mama na rikici akan yara, duk da abune da bai cika faruwa ba a gidan irin haka kaga suna faɗa a zahiri sai da yaji ransa ya sosu. Aunty Amarya ce tamai bayanin tushen faɗan wai Mubarak ne ya daki Sakina saboda ya aiketa taƙi zuwa har ya jimata ciwo a gefen ido fuskarta ta kumbura. Ita kuma Mama tai magana akan ita bata hanashi dukansu idan sun masa ba dai-dai ba. Amma yasan inda zai daka saboda gudun nakasa mutum. Umma kuma dake kamar a jirace ta amshe faɗan shine fa suka rikice haka. Daga inda yake ya ƙwalama Sakinar kira, fitowa tai da ga ɗakinsu da taimakon Yayarta Khadijah. Hankalinsa ya tashi shima da ganin yanda kusan rabin fuskar yarinyar ya kumbura, gashi ciwon kamar ma akan idon ne ba gefe ba. "Kawo mata Hijjab" kawai yace yana kallon Khadijan. Da to ta amsa masa. Su Umma dai nata sa'insar su Ammah na basu haƙuri. Shikam wayarsa ya cigaba da dannawa kamar ma bai san mi ake a gidan ba har Khadijah ta dawo. Mayafi ta kawo mata dan hijjab ɗin zai takura mata, baice komai ba yay gaba Sakina ta bisa a baya. A rukunin ɗakunsu na samari ya tsaya, kira ya dannama Mubarak dake ɗaki zaune shiru alamar akwai damuwar abinda ya aikata tattare da shi shima, dan tunda abin ya faru baya cikin nutsuwarsa yayi dana sani babu adadi, jin hayaniyar su Umma ta sake ɗaga masa hankali shine ya koma ɗaki ya rakuɓe. "Fito nan ina son ganin ka". Bai gama ajiye wayar ba Mubarak ya fito dan suna shakkarsa sosai a gidan. Gaba yay suka bisa baya su duka biyun, kasancewar akan titi layin gidansu yake a ƙofar gida suka samu napep, shi da Sakina suka shiga baya, Mubarak kuma kusa da driver. Wani babban canix na anguwar tasu dake can ƙasa sukaje, yanda suka tarbesa da alama sun sanshi sosai. Dan babu ɓata lokaci aka hau duba Sakinar. Bayan an rufe ciwon da bandeg mai camix ɗin ya basu shawarar kaita asibiti da safe gudun kar idonta ya taɓu. Godiya ya musu ya biya kuɗin suka fito. Dama Uncle Yousuf ne ya bashi su da safe dubu biyar. Sun sami gidan yanzu tsit, dan Umma da Mama na gaban Abba da ya gama musu tijara yace kuma su sameshi. Suna shigowa Sadiq yace suje Abba na kira. Su kaɗai suka shiga shi kuma yay shigewarsa ciki, ya zauna sun fara gaisawa da Amma Sadiq ya shigo shima yace yazo Abba na kiransa. Miƙewa yay yabi bayansa. Ya samu Abban nata zagin Mubarak, shi kuma kansa a ƙasa kamar ma yana kuka. Koda ya zauna yana kallon yanda Umma ke hararsa. Bai damu ba ya fuskanci Abban dake cigaba da zagin Mubarak. "Abba ayi haƙuri haka nan, yayi kuskure kuma dama nima zan hukuntashi akan laifinsa duk dai ya amsa laifinsa kuma ya bada haƙuri da yin nadama. Itama kuma tace ta yafe masa, amma duk da haka so nake taji sauƙi sai na zauna da su..." "Ikon ALLAH ƙarfin hali, ni kana bani mamaki a gidan nan Hydar. Ka dinga wani ɗaukar gabara kamar kaine ubansu. To ko Salim dake yayanku gaba ɗaya yana wannan aikin ne? Ko sai kai sarkin iya zartar da hukunci..." Tsawa Abba ya daka mata har sai da ta zabura. "Ke Usaiba ki kiyayeni a gidan nan. Da kike faɗin kamar ubansu ai uban nasu ne shi tunda babba yake garesu. Shi Salim ɗin dake babba miya amfanama kansa ma balle wani, shiko da kike ganin bai miki dai-dai ɗin ba tsaye yake akan tarbiyyar har ƴaƴanki. Badan Aliyn ba a gidan nan sai ƴaƴan ɗakinki sunfi kowa zamemun fanɗararru saboda banzan halinki nason ƴaƴan tsiya. Wlhy sonai ma ya masa dukan mutuwa shima ya fasa masa ido kamar yanda ya fasa mata..." "Saboda ita ƴar sonka ce da uwarsa. To wlhy ya dakesa ai gashi nan yaga in ban rama masa ba. Har yau ne yabo ya tashi a kansa gareka. Da kake kiran Salim mara amfani wlhy sai dai in shine mara amfanin. Dan koba komai yarona nada iyalinsa da gida da motar hawa ga aiki bashi dake yawon gal-gal ba babu makama sai watsewa a gari. Auren ma da zai ajiye iyali ya gagara sai bin ƴaƴan mutane ana lalubewa a sorayen iyayensu, da yake tsoron uwarsa kakeji ka kasa magana..." Sosai ya rumtse idanunsa dan jin zafin maganganun Ummar garesa. Cikin dakewar nan tasa da sanyaya harshe ya ce, "Dan ALLAH Abba kuyi haƙuri abar maganar. In dai Mubarak da Sakina ne zan hukuntasu akan laifinsu." Mama da tun ɗazun batace komai bace ta karɓe zancen da faɗin, "ALLAH yay maka albarka ɗan halak, wannan shine girma na gaskiya ga babba Hydar, ba ɗagawa da alfahari akan abinda ALLAH shine mai badawa ba. Koda yake iyakar mutum ma alfaharin kawai tunda bai isa tanƙwara ɗan ya masa yanda yake so ba sai dai yaga yanama iyalansa". A take falon ya nema sake rikicewa tsakanin Umma da Mama ɗan kai tsaye dai akan Salim ɗin da Umman ta gama kurantawa ne Mama ta yaɓa mata magana. Wata gigitacciyar tsawa Abba yay musu data sakasu nutsuwar dole su duka. Dan dama shi kam a yanzu ne kura tai lafiya saboda girman shekaru da yau da kullum. Amma tsayayyen mutum ne a gidansa kusan ma halayensa ne Uncle Smart ɗin ya ɗakko a gidan. Masifa sosai ya musu tare da wankesu tas. Shi dai bai sake magana ba har Abban ya gama ya sallamesu. Koda suka shigo gidan Umma nata cigaba da ƙananun maganarta kamarma zata maida faɗan kan Amma ne. Ammah nunawa ma tai bata san da ita take ba. Duk da ita mutum ce mai zafi da rashin ɗaukar raini, mace ce mai kawaici musamman akan al'amurin yaranta. Dole Ummar dai tagaji tai shiru dan kanta. Koda Uncle Smart kuma ya koma wajenta bai mata maganar abinda ya farun ba, ba kuma ta tambayesa ba, ya ɗan tsakuri abinci ya ƙarama su Asma'u karatun Alkur'ani da suke jiransa. Koda ya koma ɗaki ya jima maganganun Umma na masa kai kawo a zuciya da ruhi, yana jin matuƙar ciwo da zafi a duk sanda aka zagesa da ƙaddararsa a gidan musamman akan aiki. Dan shi akan aure bawani yana gabansa bane har yanzu. Zaima iya rantsewa bayan Kubrah ɗiyar ƙanwar Ammah da suka haɗasu daga ƙarshe iyayenta suka wargaza abun wai akan baida aikinyi bai taɓa tsayawa da ƴar wani da sunan soyayya ba. Ko ita ɗin da farko ko kallo bata ishesa ba, sai da Ammah ta zaunar da shi ta masa nasiha kasancewar gwaggon tasu ce ta buƙaci haka da kanta saboda son da yarinyar ke masifar masa. Har ranar aure an saka musu kafin abubuwa su rikice iyayen suga mai kuɗi suka canja shawara. Ko a yanzu haka da yarinyar ke'a gidan aure tana masifar son sa, dan a duk sanda ALLAH zai haɗasu sai tayi kuka dan ma baya nuna ya fahimci mitake ciki ne........✍️ ____________________ https://youtu.be/y6YMU120RZI Please subscribe to Rukayyat khalid YouTube channel fisabilillah. I only uploads videos na karatun Qur'an a tashar Please help me reach 1k subs soon insha Allah *RUKAYYAT KHALID* *Assalamualaikum warahmatullah* *Yar uwa shin mene amfanin wayar hannunki da bazaki koyi sana a da ita ba?* *Kullum kina yawo a social media irin su Facebook, WhatsApp, tiktok,Instagram, twitter da ma sauransu.* *Kina asarar data a banza kina zuba adashinda babu ranar dauka* *bakya chas bakya as? Se chart kika iya 🤔* *kin damu mijinki da BANI BANI?? Kizo nan ni* *~Graphics by Rukayyat~* *zan koya miki sanaar Graphics design wanda zaki samu abin dog dogaro da kai. Kina zaune daga gida kina sanaarki.* *Ga mai bukata a masa design ko wani iri, munayi insha Allah* SERVICES PROVIDED 🌹Logos 🌹Flyers 🌹data flyers 🌹Pos banner 🌹Book cover 🌹 Invitation Card 🌹 Business Card 🌹 Banner 🌹 Save The Date 🌹 Bank Sticker 🌹 Video Invitation card 🌹 Birthday Videos 🌹Business logo 🌹graduation poster 🌹e t c Muna kowani design a farashi mai kyau idan training kikeso ma munayi shima a farashi mai kyau insha Allah kedai kimin magana ta wannan number 👇🏻 *DM FOR ANY ENQUIRY* 07084515410 ______________________ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* [8/22, 9:46 PM] Maman Aslam: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣3️⃣ ______________________________ *_Wai wai wai_* _wani kaya sai amale,don raqumi bazai iya dauka ba_ *MAAB LUXURY* _GIDAN ADO DA KECE RAINI_ *MAAB LUXURY* _DUNIYAR QAWATATTUN KAYAYYAKI_ *MAAB LUXURY* _TUNQAHON GIDA DA GININ GIDAN GABA DAYA_ _IDAN NACE ZAN LISSAFO BAZAN GAMA BA A NAN KUSA,DON SUN CANCANCI KOWANNE IRIN SUNA_ *DAME DAME SUKE SIYARWA NE?*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 _SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI... KWASHA KWASHA_ _SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI... INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_ _KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_ _KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_ _KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM: @Maabluxuryhome_ _FACEBOOK:@maabluxuryhome_ _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_ _A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_ _MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED... JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_ _08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_ _______________________ ........Washe gari da ranakun da suka biyo baya babu wani ƙwaƙwƙwaran aiki da yayi kasancewar wadda aka ɗaukesa aikin a yanzu da ita bata fita. Sai dai yaje ya zauna wajen masu gadi har lokacin tashi yayi ya koma gida. Ganin hakan yasa yau bai fita da wuri ba yabi su Maryam makaranta kamar yanda yakan yi lakaci zuwa lokaci batare da sun sani ba. Yakan ɗan binciki halin da suke ciki da yanayin karatunsu. Sai goma yabar makarantar. Lokacin da ya iso gidan aikin nasa sha ɗaya saura kaɗan. Tunda ya turo gate ɗin ya shiga akanta ya fara sauke idanunsa. Tsaye take a can jikin wata farar mota da ke ƙaton compound ɗin nasu. Kallo ɗaya da yay mata bai sake marmarin ƙarawa ba saboda shegun kayan da ke jikinta. Skert ne blue da ya kamata ɗam-ɗam ya fidda mata halittar jikinta da ƙyau, sai ƴar riga mai santsi kalar gwaiduwar ƙwai. Babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta sai wani ƙaton glasses data toshe idanunta da shi, kanta da hula irin ta zamani da ake yayi. Dan ƙyau kam tayi ƙyau, sai dai ga ɗabi'a da tarbiyyar ɗiyan musulmi bahaushen arewacin Najeriya babu abinda shigar tata ke nufi ga duk wanda zai kalleta sai ƙarancin tarbiyya da wayewar banza. Ga wayayyu kuma irinta hakan normal ne. Tsaki ya ɗan ja a ƙasan maƙoshi yana ƙara tsuke fuska. Su maigadi dake zaune kamar a tsorace duk ya bama hannu suka gaisa. Yanda suke kamar a noƙe ya bashi mamaki. Sai dai yana niyyar kaiwa zaune mai wanki ke faɗin, "Ɗan uwa Hajiya Muwaddat fa kai take jira. Tsaiwar da kaga tayi can tun ɗazun take zuba tijara har mu ma nan sai da muka samu rabonmu na zagi, kasan ita sanda aka raba mutunci tana cikin bargo ƙudindine shiyyasa bata samu ba". Shiru kamar bazai amsa ba. Sai kuma zuwa can a dake ya ce, "Tunda kun maida kanku sakarkaru gareta ba". Da ga haka yaja bakinsa ya tsuke tare da ciro wayarsa da ga aljihu zai fara sana'ar danne-dannen nasa. Wata irin gigitacciyar tsawa Lulu data gama kaiwa wuya da takaicinsa ta daka masa. Sai dai ko gezau wai an tsikari kakkausa. Cikin takun nan nata na izza da yanga ta ƙaraso gate ɗin. Ashariya ta mulmulo tare da faɗin, "Wai kai ɗan uban wanene? Mi kake taƙama da shi ne, tsabar kai cikakken mara mutunci ne kazo a makare ina tsaye tun 8:30 ina jiranka amma kazo ka zauna anan irin ma kai baka gannin nan ba. Na rasa mi Daddy da Uncle Yousuf suka gani gareka suka takura da sai kai ne zaka zama driver na a gidan nan illiterate irinka.." A hankali ya rumtse idanunsa sai kuma ya buɗesu a kanta. Wani irin yankawa zuciyarta ta shigayi da sauri-sauri, dan wani irin kwarjini mai cika idanu yay mata. Amma saboda tsabar ƙarfin halinta da taurin zuciya sai ta cigaba da masifar kamar zata cinyesa ɗanye. Harda cewa sai tayi maganin rawar kansa a gidan. Sosai su maigadi ke'a rikice. Shiko yanda ya dake sai ma ka ɗauka ba dashi takeyi ba. Dan tuni ya maida hankalinsa ga wayarsa... "Wai ya akayi ne?". Mommy da hayaniyar Lulu ke zuwa mata cikin kunne sama-sama tun ɗazun ta fito dan ganema idonta ta faɗa tana ƙarasowa. Cikin masifar nan tata ta juya tana faɗama Mommyn abinda yay mata. Dai-dai nan shima Daddy ya fito da alama ma wanka ya fito dan bathrobe ce a jikinsa. Mommy ta juya ga Uncle Smart, sai dai kafin tace masa komai ya shiga gaidasu ita da Daddyn da sai yanzu Mommy da Mawaddat suka lura da shi cike da girmamawa kamar bashine ya watsar da al'amarin Lulu ba tun ɗazun. Cikin kulawa suka amsa masa, Daddy ya dubesa cikin alamar sanyin yanayin daya riskesa a kwanaki biyun nan akan halin da Lulu ke ciki tare da faɗin, "Ya akai ka makara haka Aliyu Hydar?". Bai iya ƙarya ba ko kwana-kwana. Sak yake shi akan komai. Dan haka kai tsaye ya ce, "Alhaji na ɗan biya ta school ɗin ƙannena ne dan sanin halin da suke ciki akan karatunsu tunda naga kwana biyu ba wani waje nake zuwa ba". Lulu zatai magana a hargitse Daddy ya katseta cikin lallashi. "To kiyi haƙuri haka tunda dai kinji uzirinsa ai ko Babyna. Kuje ya kaiki haka nan rana na ƙarayi wannan gyaran jikin naki dake ɗaukar lokaci kamar za'a sauyaki". Takaici kamar ya kashe Mommy da ke kallon mijin nata. Sai dai batace komai ba. Lulu dake wani cika da batsewa ta ce, "Amma Daddy kana ganin kofa haƙuri bai bani ba. Tsabar wulaƙanci kallo ma ban ishesa ba balle gaisuwa sai da Mommy ta fito ma ya taso da ga inda yake zaune tsabar shi mashahurin mara mutunci ne". "Oh oh". Daddy ya faɗa yana dafe kansa. Sai kuma ya dubesa da faɗin, "Kaga dan ALLAH bata haƙurin nan a rabu lafiya kaji Aliyu". A harzuƙe ta ce, "Bana buƙatar haƙurin nasa Dady, sai da aka roƙa min. Ka barsa zanyi maganinsa tare da sauke masa girman kansa, banza mutum ba kowan kowa ba sai ɗaukar kai wata tsiya kana driver. Shiyyasa na tsani irin jahilan nan da ko primary basu yi ba sai ji da kai motsoww!!". Maganganun ta sun masa zafi, amma sai ya miƙe kodan darajar Daddy da Mommy. Key ɗin jikinsa ya ciro yana nufar motar. Tsawa tai masa tare da wurga masa wani key ɗin. "Ba ita nake so ba stupid Men! illiterate kawai". Key ɗin data jefa masan yabi da kallo na kusan minti ɗaya, kafin ya ɗago ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana mai cije lips ɗin sa ya ɗauka batare da yace komai ba nan ma. Daddy ya ɗan girgiza kansa da faɗin "ALLAH ya shiryeki Muwaddatan-warahamah. Koda ya gyara motar zuwa gabanta ƙin shiga tayi. Daddy da ke tsaye zaman jiran ganin sun fita lafiya yay masa nunin ya fito ya buɗe mata. Bai musa ba ya fito fuskarsa na karayin wani kicin-kicin. Batare daya kalleta ba ya buɗe mata ƙofar. Sai da taja tsaki da faɗin, "Motsoww! baƙauye kawai da ko aikinsa bai sani ba" sannan ta shiga. Maidawa yay ya rufe suka fice a gidan. Karan farko Mommy ta saki murmushi, dan tabbas tasan a wannan haɗin akwai ƙura. Lulu masifa da izza. Aliyu jan girma da rashin ɗaukar raini. Taga dai yanda wasan zai cigaba da kasancewa tsakanin ɓera da mage. Karaf murmushin Mommyn a idon Daddy da ya juya zai koma ciki. Ya wani ɗaure fuska da faɗin, "Aniyarki ta biki idan ma wani abu kike ƙullawa akan yarinyata". Sarai Mommy ta jisa amma sai bata tanka ba, dan ta fahimci masifa yake nema da ita akan Muwaddat ɗin tunda suka dawo asibiti. Itako taƙi bashi kowacce irin damar cimata mutunci dan a yanzu kam bazata ɗauki abinda ta ɗauka a baya ba kan Mahaifiyar Muwaddat ɗin da ita kanta yarinyar. Suna shiga ciki tai wucewarta ɗakinta bata bisa ba duk da ƙananun maganar daya cigaba da faɗa masu ƙona zuciya. Har da cewa ƙilama itace taima Muwaddat ɗinsa asiri take shaye-shaye saboda tana baƙin ciki da ita a gidan. Tana shiga ɗaki ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Sai da tai mai isarta ta share hawayenta, dan duk yaran sun wuce makaranta da ga ita sai masu aiki. Duk yanda take jurewa da dakewa akan al'amurin mijin nata game da ƴarsa a yanzu hakan yana neman fin ƙarfinta. Dan al'amarin akwai ciwo sosai matuƙa gaya. Cikin ƙanƙanin lokaci tai ninƙaya a tunanin shekaru ashirin da shida da suka shuɗe kafin yau.... *_SHEKARA ASHIRIN DA SHIDA DA SUKA SHUƊE_* Malam Ibrahim Jiƙamshi shine sunan mahaifin su Isma'il (Daddy), yayinda Malam Salisu Ibrahim Jiƙamshi ya kasance ƙaninsa ɗaya tilo da iyayensu suka haifa (Mahaifinta). Sun rasa iyayensu tun suna ƙananun yara, dan haka suka tashi da tsananin ƙaunar juna da shaƙuwa a hannun kakarsu Iyan Jiƙamshi. Iyan Jiƙamshi kakarsu itace har taga aurensu su duka biyun, dan ALLAH yay mata rasuwa ne bayan haihuwar Isma'il da ita Kareema. Duk da bawani wayone da su sanda ta rasu ba bazasu iya manta wasu ƴan abubuwa da suka shafeta ba. Iyan Jiƙamshi ita tabarma Ibrahim da Salisu wasiyyar haɗasu aure idan sun girma, ba komai yasa haka ba sai ganin yanda Isma'il (Daddy) ke yawan kaffa-kaffa da ita tun tana jinjira kasancewar ta ita ɗaya ƙanwarsa da yake gani. Bayan rasuwar Iyan Jiƙamshi da shekara biyu ALLAH yayma mahaifinta Salisu rasuwa shima. Wannan mutuwa ta matuƙar girgiza Ibrahim matuƙa da har takaisa da baro garin Jiƙamshi gaba ɗaya ya dawo cikin Kano tare da ita Kareema daya amshe wajen mahaifiyarta dan bayan ta kammala takaba anta bashi shawaran aurenta ciki harda mahaifiyar su Isma'il (Daddy) amma yace bazai iya ba. Bazai taɓa iya auren matar ƙaninsa Salisu ba. Wannan daliline yasa iyayenta cewa ta bashi ƴarsu tazo gida ta samu miji. Ba rabuwar daɗi akayi ba, dan mahaifiyarta ta tafine ta barta tana kuka mai tsanani, haka ma Ibrahim da matarsa da Isma'il. Riƙonta ya koma hannun iyayen Isma'il (Daddy), inda suke tattalinta da kulawa matuƙa su da ɗan su Isma'il. Dawowarsu Kano da shekaru uku aka haifi Yousuf, inda ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa itama a wajen haihuwarsa. Abubuwa sun sake rikicewa, inda mutuwar ta sake taɓa rayuwar Ibrahim matuƙa har sai da ta zama sanadin kamuwarsa da ciwon ajali shima. Yayi jinya sosai ta kusan shekara takwas, yayinda ita da Isma'il suka raini Yousuf tamkar uwa da uba a garesa..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣4️⃣ ______________________________ *_Wai wai wai_* _wani kaya sai amale,don raqumi bazai iya dauka ba_ *MAAB LUXURY* _GIDAN ADO DA KECE RAINI_ *MAAB LUXURY* _DUNIYAR QAWATATTUN KAYAYYAKI_ *MAAB LUXURY* _TUNQAHON GIDA DA GININ GIDAN GABA DAYA_ _IDAN NACE ZAN LISSAFO BAZAN GAMA BA A NAN KUSA,DON SUN CANCANCI KOWANNE IRIN SUNA_ *DAME DAME SUKE SIYARWA NE?*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 _SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI... KWASHA KWASHA_ _SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI... INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_ _KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_ _KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_ _KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM: @Maabluxuryhome_ _FACEBOOK:@maabluxuryhome_ _SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_ _A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_ _MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED... JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_ _08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_ ______________________ ........Wannan haɗin kan nasu da ƙaunar juna ya ɗan dinga ragema Malam Ibrahim raɗaɗin ciwo, dan duk da yana kwance a duk sanda suke tattalin Yousuf a tare kamar wasu mata da miji duk da ƙarancin shekarunsu sai yaji farin ciki har fuskarsa kan nuna hakan. Gashi shima suna kulawa da shi matuƙa sai kace wasu manya. Yana da shekara biyar kwance ya yanke shawarar ɗaura musu aure saboda halin rayuwa, a lokacin shekarar Isma'il goma sha tara a duniya. Itako nada goma sha huɗu. Maƙwafcinsu ne ya jagoranci komai, ranar wata juma'a sun dawo makaranta Isma'il ya gama jarabawar ƙarshe ta kammala sakandire, ita kuma jsce suka iske an ɗaura musu aure. Ita bata wani ɗauki abin da muhimmanci ba, kasancewar da sauran ƙuruciya a tare da ita. Sai ma biyema Yousuf dake da shekara biyar a duniya tai suna murnarsu. Yayinda Isma'il ya shiga yanayin damuwa, dan shi harga ALLAH kallon ƙanwa yake mata uwa ɗaya uba ɗaya bawai matar dazai iya aure ba. Lura da hakan da Malam Ibrahim yayi ne ya sashi zaunar da shi yay masa nasiha mai ratsa jiki data saka jikinsa yin sanyi, tun kuma da ga wannan lokacin ya fara koyama kansa sonta ita Kareema (Mommy) tunda dama akwai ƙauna ta jini da shaƙuwar zaman waje ɗaya a tsakaninmu. Karatu muka cigaba da yi abinmu batare da anyi maganar tarewa ba, haka shima Yousuf an sakashi makaranta, gefe kuma muna cigaba da jiyyar babanmu malam Ibrahim. Isma'il na shekara ta uku a jami'a, ni kuma shekarar ƙarshe a sakandire jikin Baba ya sake rikicewa, ganin haka yasa maƙwafcinmu da muka zama tamkar ƴan uwan jini a yanzu shirya bikinmu ni da Isma'il dan yana fatan gani kafin yabar duniya. Haka ɗin kuwa akayi, aka gyara gidan tare da kawo abubuwan da suka dace da amarya sati ɗaya da kammala jarabawata ta ƙarshe akasha biki. Anan dai gidan muka tare, inda kwanaki goma sha ɗaya da tarewar tamu ALLAH yayma Baba rasuwa shima. Mun shiga ruɗani da tashin hankali matuƙa irin wanda bazai misalu ba. Dan da ƙyar al'amura suka daidaita mana bayan wani lokaci. Mun cigaba da rayuwa cikin shaƙuwa da soyayya mai ban mamaki, ga ɗan ƙaninmu Yousuf da muke tattali matuƙa, inda wanda bai sani ba zai iya ɗaukama ɗan mu ne sai idan ka kalleni ne zaka san ban kai haihuwarsa ba. Alhamdullah Isma'il ya kammala jami'a bayan rasuwar Baba da shekara biyu, ya kuma samu result mai ƙyau. Haka shima Yousuf ya shiga fimare 4. Burina a kullum shine na koma makaranta na cigaba da karatu nima, sai dai Isma'il na lallaɓani akan na bari ya samu aiki abubuwa su sake warware masa. Banyi musu ba nayi haƙurin, cikin ikon ALLAH kuwa sai ga aiki ya samu cikin sauƙi kasancewar a wancan lokacin ma neman masu irin kwalinsa ake ido rufe suna yanga dan aiki saima sun zaɓa. Wannan samuwar aiki shine mafarin komai, dan daga lokacin abubuwa suka fara canja salo a saɓanin yanda nake kallonsu ko na tashi na sansu. *_Alhaji Sufi Ado Garko_* shine ya kasance ogan Isma'il a wajen aiki, mutum ne mai tarin dukiya da mutunci. Bashi da mugunta da ƙeta, dan ba aikin gwamnati kawai ya dogara da shi ba ɗan kasuwane babba da akeji da shi sosai a lokacin. Ƙwazo da amanar Isma'il ta fara janyo masa soyayya a wajen Alhaji Sufi ya fara jansa a jikinsa tare da ɗorashi akan wasu harkokinsa na kasuwanci a bayan fagen aikinsu na gwamnati. Alhamdullah wannan al'amari ya fara canja mana rayuwa, dan kuɗi sun fara shigowa Isma'il fiye da farkon samun aikinsa. Inda ya cika alƙawarin maidani makaranta, shima Yousuf ya shiga Sakandire. Shekarata ɗaya da komawa makaranta sai ga ciki. Isma'il da Yousuf da ni ɗin kaina mun shiga matuƙar farin ciki da baida misali. Na haihu lafiya bayan ciki yakai haihuwa, inda ALLAH ya bani ɗa Namiji wanda yaci suna Ibrahim muna kiransa da Abba. Na cigaba da rainon Abba koma nace Yousuf ya cigaba da rainonsa, dan tattalin yaron yake tamkar ƙwai a cokali. Sai dai ALLAH baiyi mai zama bane yanada shekara ɗaya da wata uku ya rasu. Yousuf ya sha kuka sai mune muka koma lallashinsa. Sai dai me ashe a lokacin ma ina maƙale ne da ciki batare da mun sani ba. Sai bayan rasuwar Abba ne ya bayyana. Munyi murnar hakan na cigaba da rainon ciki da karatu, yayinda ALLAH keta ƙara ɗaukaka Isma'il ta silar Alhaji Sufi Garko. Bayan isar cikin jikina haihuwa shima na haifesa, sai dai wannan karon ƴan biyu ne duk maza. Wayyo murna zo kaga farin ciki a wajen Yousuf da Isma'il dama ni kaina. Yara sun sake cin sunan Ibrahim da Salisu iyayenmu. Ana kiransu da Hassan da Hussaini ɗinsu. Bayan haihuwar ƴan biyu da shekara biyu na kammala karatuna, sai dai Isma'il yace bazanyi aiki ba sai da naita roƙonsa ni da Yousuf harda kukanmu sannan ya amince. Shine ya amshi takarduna da kansa domin nemamin aiki kamar yanda ya sanar min mai-gidansa Alhaji Sufi Garko yace ya kawo zai sama min gurbin a kamfaninsa insha ALLAHU. Kasancewar yace ya kai masa takardun gida a cikin weekend ya sakashi shiryawa ranar wata asabar. Wannan shine karo na farko a rayuwarsa da zai je gidan ogan nasa. Tare da Yousuf suka tafi, inda akai musu tarba ta mutuntawa, gidane katafaren gaske da ya basu mamaki, dan a ranar suka sake tabbatar da lallai Alhaji Sufi Garko mai kuɗi ne sosai. Suna zaune a falon Alhaji Sufi da aka saukesu saboda karamci saɓanin falon baƙi ƴarsa ƙyaƙyƙyawar budurwa data dawo daga karatu da ga ƙasar larabawa ta shigo falon amsar saƙo wajen mahaifinta. Tunda ta ɗora ido akan Isma'il ta kasa ɗaukewa, dan Isma'il ƙyaƙyƙyawan mutum ne ɗan gaye sosai, ina faɗa muku zancen gaskiya ne badan yana mijina ba. Ba Isma'il kawai ba hatta Alhaji Sufi ya lura da irin kallon da ƴar tasa kema yaronsa na ƙurilla. Yayinda Yousuf shi kuma abin ya bashi haushi saboda kishina ni ƴar uwarsa. Wasa-wasa Muwaddat ta kasa barin falon tana manne da su har suka bar gidan duk da bayan gaisuwar shi Isma'il bai sake kulata ba ma. Aiki dai an ɗaukeni ta silar Alhaji Sufi, sai dai tunda Yousuf ya bani labarin ƴarsa da abinda ya faru naji komai ya fitamin arai. Ban dai yima Isma'il maganar ba, amma kullum cikin kasa kunne nake naji abinda zai biyo baya. Shiru-shiru banji komai ba har na shiga wata shida da fara aiki ga kuma ciki ya sake samuwa. Abinda ya bani mamaki a wannan karon Isma'il bai wani nuna murnarsa sosai akan cikin ba kamar nasu ƴan biyu da Abba. Sai dai banyi magana ba. Bayan haka al'amuransa da yawa sun ɗan fara canjawa a yanda na sansu. Zai fita aiki da sassafe batare daya karyaba yanzu, bai dawowa kuma sai goma na dare. Wani lokacin ya tsakuri abinci, wataran ma baya ci sai yace min ya ƙoshi a gajiye yake. Tun bana ɗaukar al'amarin wani abu har ya fara damuna naima Yousuf maganar. Shima da yake yaro ne mai hankali da lura ashe ya fahimta yay shirune kawai. Kuɗi na sake shigoma Isma'il abubuwa na ƙara rikicewa a tsakaninmu da ban san kansu ba, dan haka Yousuf dake ƙoƙarin kammala sakandire ya lallasheni akan zai bincika. Yaron nan shine yay ƙoƙarin binciko mana komai, inda ya gano ashe Isma'il soyayya suke da Muwaddat ta bugawa a jarida, saboda shi ma yanzu haka ta koma aiki ma'aikatarsu. Hankalina ya tashi da gani har Yousuf, inda duk yanda naso danne abun a raina na kasa Isma'il na dawowa na taresa da maganar. Da farko naga shock a fuskarsa, amma da yake halin maza sai ya dake ya shiga borin kunya akan wane munafuki ne yay masa sharrin nan. Ƙin faɗa masa nayi, amma duk da haka yace yasan Yousuf ne. A daren ya tado Yousuf da ga ɗakinsa ya zagesa tas. Hakan da yay ya sake ɓata min rai muka kwasa da shi sosai abinda bai taɓa faruwa ba har ya kaisa ga marina, ya kuma tabbatar min nama shirya aure shi da Muwaddat babu fashi sai dai mu mutu ni da Yousuf ɗin. Kamar yanda ya faɗa kuwa ya cika, dan baifi sati biyu dayin rigimar tamu ba aka tsaida bikinsu shi da Muwaddat. Wannan tashin hankalin dana sakama kaina saboda yanda ya sake birkicemana a gidan ni da yaran da Yousuf yasa cikin jikina ya ɓare. Bai nuna ya damu ba ya cigaba da shirye-shirye aurensa. Inda Alhaji Sufi Garko ya ce ƴarsa fa tace bazata zauna a gidan da muke ba. Dan haka ya bashi mukullin ƙaton gida da dalleliyar motar hawa, nima mota da kayan faɗar kishiya kai kace ma nice amaryar kuma wai da ga gidan iyayenta. Shima Yousuf da ƴan biyu da nasu hidimar. Wannan abu ya sake ɗagamun hankali dan a ganina Isma'il dai auren jari ma yake shirin yi. Taruwa mukai muka tada masa hankali ni da Yousuf amma yace ko zamu mutu auren Muwaddat babu fashi wlhy. Hakan kuwa akayi, dan wata ɗaya kacal da komawarmu sabon gidan da ya zama dole garemu akai bikinsa shi da Muwaddat........✍️ *_Karku rikice wannan Mawaddat ɗin mahaifiyar Lulu ƙamshi ce ba Lulun muke nufi ba😂_* _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu??🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣5️⃣ ____________________ 🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥 *HOHOHO WANI KAYA SAI AMALE, DON JAKI BAZAI 'DAUKA BA, INA MATA MASU BUK'ATAR 'DAGA DARAJARSU A WAJAN MAZAJENSU INA MATAN DAKE SHAN WULAK'ANCIN MIJI KO NA KISHIYA ,INA MATAN DAKESON ZAMOWA MOWA AGIDAJEN AURENSU TO ALBISHINRU MAMAN ZARAH YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GABATAR MAKU DA ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI WANDA BASUDA ALGUS ACIKI , AKWAI MAGANI DANAYI BINCIKE AKANSU DAN FARIN CIKIN MA'AURATA NAMU BA IRIN NASU BANE KAYAN MU NA DABAN NE NA ASALIN SAKKWATAWAN SHEHU MASU ABUN MAMAKI* 07034251528 kayanmu masu inganci ne masu ladaftar da kowane irin namiji Kad'an daga cikin abubuwan da muke dasu Ingantaccen maganin nono , Wanda zai gyara maki nononki donmin dawo da martaban nononki acikin kankanin lokaci komai lalacewarshi kuwa sauran bayani sai mun had'u pc +234 703 425 1528 Maganin hips (hips up) Wanda zai ciko maki da hips dinki su cika suyi bul bul ga laushi dasu k'ara suyi dass abun sha'awar kowane namiji Maganin infection Sha yanzu magani yanzu Yana fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci magani ne na maza da Mata insha Allah kowane irin sanyi gareki kikayi amfani dasu anwuce wajan Ingantacce Kuma sahihin maganin k'iba Wanda Zaki ciko acik kankanin lokaci zakiyi kibar ki Yar dai dai misali ki huta Zama da Rama Baki rasa ci ba Baki rasa sha ba amma kullum Ana kallon cewa kinada matsala agidan aurenki saboda wannan ramar , Rama batayi ba Sam Yar uwa Sabulun wanka Kalolin sabulun tsarki Turaren tsugunno Turaren al'ajab Hatsabibin turare Da sauransu 07034251528 Kalolin gumba Gumbar Dabino Gumbar gero Gumbar madara Gumbar matsi Gumbar ukku bala'i Gumbar tada zaune tsaye Gumbar sabon budurci Gumbar sa buzu kuwa Gumbar aya da kwakwa Gumbar ridi Gumbar mazari Sarauniyar gumba 3in1 Da sauran kalolin da bansamu fadi ba, Kalolin gari Garin mallaka Garin hutar da malaminki dakan jaraba Dakan Amare Dakan Ni'ima Dakan kishiya in bakiyi bani waje Garin sa buzu kuwa Garin buje.sharkaf Garin Dan la'asar Yayan hadiya mai suna dan la'asar Original Dan goshi Original Dan goshi (sabon salo) Original man damo Original man ayu Kitsen damo Sirrin tafin kafa Sirrin farinjini na uwargida da amarya harma da yan mata Kwallin idonka idona Muna hada set na sirrin mallaka hajiya ba boka ba Mallam sai tarin sirrika kema kizama kowa agidan surenki Akwai hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar d'a namiji da izinin Allah akayi maki wannan hadin to an wuce wajan sauaran bayani sai mun had'u pc Kalolin tsumi Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin madarar ni'ima Tsumin tabaje Tsumin Amare Tsumin sabon budurci Tsumin nono rakumi Matan gaske Ruwan jaraba, Da sauran kalolin da ban fada ba Kalolin matsi da basuda illa ajikin mace sai dai ma sukara maki lafiyar Matsin Dan mannau Matsin mallaka Dan la'asar Sabon budurci Mak'alemata Mashahurin matsi Ukku bala'i Matsin uban budurwa Akwai gumba ta matsi wadda Shanta akeyi ga matan da basa son yin matsi Muna hada set ga wadda Allah ya jaranfa da matsalar fyade har yarasa budurcinta , muna hada mata kaya ingantattun don dawo da martabar ta, Hohohohoho in ana dara fidda uwa ake *Kyallen al'ajabi* babban sirrin mallaka mai abun al'ajabi mallaki naki don samun damar shiga cikin jerin mata masu fada aji a gidan mazajensu , KARKU manta da sunan maman zarah sokoto sayen nagari maida kudi gida 07034251528 ina maraba daku sayen daya ko sari ina Sokoto sannan ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah Ga Wanda suke bukatar ganin kalolin kayana to suyi sarving number na suyimun magana nayi sarving number ku zaku dinga ganin kalolin kayana a status ngd sosai 07034251528 Maman zarah mabera SOKOTO ________________ ........Anyi shagalin biki kam na nunama tsara, dan har a gidan tv na ƙasa da jiha an nuna. Kuɗi sunyi kuka abin sai wanda ya gani. Mudai namu ido ni da Yousuf dan ko shagali ɗaya bamu halarta ba Isma'il ya hanamu wai baƙin ciki muke masa. Amarya ta tare ita da abubuwan ban mamakinta. Dan kuwa dai Mawaddat ta shigo gidan ne a tsaitsaye da tarin gadararta irin na ɗiyan wasu masu arziƙin. Dan sai da takai hatta kwanakin girkina wani lokacin Mawaddat cemin take wai ta saya tazo ta diremin kuɗi a gaban Isma'il baya cewa komai kuma. Akwai lokacin da sai da nai wata guda babu miji, dan kuɗi maƙudai tazo ta diremin wai ta sayi kwanakin girkina na wata ɗaya dan tana buƙatar hutawa da mijinta yanda ya kamata. Nayi kuka nayi kuka har na rasa hawayen zubarwa a wannan lokaci, sai Yousuf ne ke lallashina shima idan ya koma gefe yasha kukansa dan yanzu tsakaninsa da ɗan uwansa da ga faɗa sai ƙyara. Wannan damuwar tasa yana kammala sakandare da Mawaddat tace ta samar masa gurbin karatu a ƙasar ƙetare bai wani ja zancen ba ya amince ya tafi dan gara ya bar musu gidan. Tafiyar Yousuf ta sake sakani a cikin ƙuncin rayuwa dan abubuwa sun sake rikicewa sosai tsakanina da Isma'il. Takai yanzu sai dai su shirya su tafi yawon shakatawarsu ƙasashe daban-daban su huta sannan su dawo. Ɗan fita aikin da nakeyi ne yake ɗan ragemun nauyin zuciya, amma sai rana tsaka Isma'il ya hanani fita aiki wai ya dakatar dani. Ban taɓa shiga damuwa ba irin wannan lokacin, dan takai ko kuka ma na daina iya yi sai na zuci kawai. Dole kuma nabar aikin na cigaba da fuskantar matsalolin gidan masu ƙona zuciya. Ashe wasa farin girki, dan kuwa ba'ai komai ba sai da ciki ya bayyana a jikin Mawaddat, naga abu iri-iri wasu ma bazasu faɗu ba. A haka na cigaba da haƙuri sai dai na rungumi ɗiyana nai kuka na share hawaye har ALLAH ya kai wannan ciki watan haihuwa lafiya suka fara shirin tafiya ƙasar waje wai haihuwa. Sai dai kuma suna nasu ne ALLAH yana nashi, dan suna saura kwana biyu su wuce Mawaddat ta tashi da naƙuda, ga shi lokacin Isma'il ya fita gidan. Naso shareta dan ihun kuka sosai ta dingayi har part ɗina ina jinta, sai dai kuma na kasa saboda hakkin maƙwaftaka da daraja irin ta ɗan adam. Karan farko dana shiga sashenta, haɗuwa kam ya haɗu iya haɗuwa, dan ma ban iya masa kallon tsaf ba saboda halin da take ciki. Ni ɗin dai maƙiyyarta ni na taimaketa, ganin yanda take murƙususun kuka da ihun naƙuda gashi inata kiran Isma'il yaƙi ya ɗagamin ya sani samo ruwa nai mata addu'a a ciki, ina ƙoƙarin bata dai-dai nan ya shigo gidan, da wata irin sassarfa yay kammu, babu wani tunani ko bin ba'asi yasa hannu ya kaɓe ruwan, sai dai harta rigada tasha. Sosai ya balbaleni da masifa yana tabbatar min da duk abinda ya samu matarsa bazai barni ba. Kuka na fashe da shi ina masa bayani amma bai sauraren ba ya ɗauketa sukai asibiti tana kukan faɗin na yafe mata dan ALLAH. Tausayi ta bani, dan haka na bisu har harabar gidan ina faɗin, "Na yafe miki Mawaddat, ALLAH ya saukeki lafiya, nima ki yafemin". Da ƙyar ta iya furta "baki mun komaiba sai alheri" dai-dai yana sakata a motar. Dazai barni dana bisu, amma rashin ganin fuska da ga garesa ya sani haƙura na bisu da addu'a zuciyata duk babu daɗi, ga jikina yay matuƙar sanyi da ganin yanayin nata. Kafin su isa asibiti ta haihu a mota dan haihuwar tarigada tazo, gaba ɗaya ya rikice yama rasa miya kamata yayi, ga holdup da suka samu a hanya da ƙyar suka fita, kafin su isa asibiti Mawaddat ta zubda jini sosai har jikinta ya saki. Ko taɓata likitocin basu kai dayi ba UBANGIJI ya amshi abarsa, sai jaririya da aka samu gyarawa. Bayyana muku irin tashin hankalin da Isma'il ya shiga da wanda na fuskanta a garesa ma ɓata lokaci ne. Dan duk da bayanin da likitoci sukai masa akan dalilin rasa ranta cayay sam bai yardaba nice na kasheta, dan ya samu ina bata abu. Wasa-wasa rigima tai girman da har sai da hukuma suka shiga ciki, ALLAH ya soni mahaifinta mutum ne da yasan abinda ya kamata, shine ya balbale Isma'il ɗin da masifa tare da bani kariya har ALLAH yasa zancen ya mutu. Sai dai fa Isma'il ya koma mana kamar wani zautacce, jaririya kuwa tana manne da shi ya hana kowa ɗaukarta har iyayen Mawaddat. Duk kuma yanda sukai masa kurari da jan ido bai basu ɗin ba dole suka barshi da kayarsa. Randa akai addu'ar bakwai mahaifin Mawaddat Alhaji Sufi Garko ya raɗama yarinya sunan mahaifiyarta Mawaddat. A taƙaice dai Isma'il shine ya koma rainon Mawaddat da hanunsa, yayinda soyayyar mahaifiyarta kacokan ta koma kanta, tare da tausayinta. Komai shine kema yarinyar, a saboda ita ya ajiye aikinsa ya koma rainonta. Ko motsi idan tana barci babu wanda ya isa yayi. Idan kuma akayi kosu ƴan biyu ne ya kamasu yay musu dukan mutuwa. Nasha shan mari a wajensa saboda Mawaddat. A haka yarinyar ta taso a taɓare babu kwaɓa komai sai wanda take so za'ayi. Lokacin data isa shiga makaranta ya sakata a mafi tsada dake cikin garin na Kano, Islamiyya ce dai dole ya barta atasu ƴan biyu saboda tsayawar Yousuf da ya kammala karatunsa ya dawo, sai dai bai yarda ba sai da ya kafama malaman sharaɗi akanta. Sabbin matsaloli sun fara akan zuwan Mawaddat Islamiyya, dan bata karatun sai jibgar ƴaƴan jama'a, idan malami yay mata faɗa koya daketa koda akan karatu ne saita faɗama mahaifinsu, shiko ba kunya zai ɗebo ƴan sanda su kama malamin su rufe, wani lokacin ma har marin malaman yake da kansa. Yousuf ne da ya fahimci al'amarin na neman zama wani abu daban ya fara tsayawa akan tarbiyyar Mawaddat, dan ni ko kallon yarinyar na cikayi yanzu zaice itama ina son kashetane kamar uwarta. Dole duk yanda nake kwaɗayin janta jikina kodan maraicin mahaifiyarta da bata sani ba na haƙura na zuba ido dan a zauna lafiya. Dai-daita rayuwar yarinyar da Yousuf ke son yi ce yasa Isma'il ganin ɗan uwan nasa na takura mata. Dan haka ya tattarata ya ɗauke bayan gama Nursery school ɗinta ya maida ƙasar Garmany da zama. Ya ɗauka mata Nanny acan ƙasar aka sakata makaranta. Shima dai wasu harkokin kasuwanci da mahaifin Mawaddat ya sake ɗirasa akai ne yasa zamansa yafi ƙarfi a Garmany ɗin, ga kuma ƴar sonsa da ya maida can. Tafiyar Mawaddat babu jimawa na sake haihuwar yarona Namiji da yaci sunan Mubeen, bayan shi na sake ƴan biyu duk mata da gabonsu Suhaib sai auta Nazeer. Tunda aka ɗauke Mawaddat daga Nigeria bamu sake ganinta ba sai Yousuf dake zuwa akai-akai ganinta, dan shima Isma'il ya tsindumasa akan harkar kasuwancin kawo motocin da yake kanyi a yanzu, duk da dai kuma yana aikinsa anan ƙasar Nigeria saboda shine hubby nasa. Rayuwa ta shuɗa Isma'il ya sake bunƙasa haka ma Yousuf da yay aurensa, ya auri yarinyar kirki mai tarbiyya da sanin yakamata Saliha ɗiyar maƙwafcin nan namu da ya jagoranci bikina da Isma'il. Dan muna zaune lafiya kuma tana matuƙar girmamani. Mawaddat dai bata dawo ba, ko hutu bata taɓa zuwa ba har sai da ta kammala sakandare ɗinta a can sannan tazo mana. A halayen banzanta babu abinda ya canja sai ma ƙaruwa da yayi, dan yarinyar gaba ɗaya a fanɗare take babu wanda ya isa ya sakata ko ya hanata. Ko kallon banza kamata sai ta maida maka murtani, Yousuf ne kawai ke iya tsawatar mata ta nutsu. Hankalina ya tashi matuƙa, dan koba komai Mawaddat ɗiyar Isma'il ce, ita ɗin jininace ai koba aure tsakanina da shi. Dan haka na duƙufa da addu'a akanta kamar yanda nakema nawa yaran. Tawani ɓangaren kuma ina ɗan janta a jikina cikin hikima sai dai ban bata wata ƙofar da zata kawomin raini ba ko kaɗan. Kusan watanta shidda ta sake barin ƙasar zuwa London karatun ta na University, daga haka bata sake zuwa ba sai da ta kammala ta zama cikakkiyar lawyer. Da ƙyar daya ALLAHU Yousuf ya tilastata dawowa gida Nigeria, amma shi Daddynsu ko'a jikinsa. Dawowar tata kuma baisa abubuwa sun canja a yanda suke ba kanta a can baya tsakanina da Isma'il, dan ƙiri-ƙiri yake nuna bambanci tsakanin yarana da Mawaddat, idan nai magana yace arziƙin uwarta da Kakanta muke ci, dole na tattara na watsar da al'amarinsu, dan dama da ƙyar ya biyama su ƴan biyu kuɗin karatu zuwa Saudiyya, a yanzu haka kuma sun dawo suna aikinsu sai dai ba'a nan cikin Kano ba, shiyyasa sai Lokaci-lokaci suke zuwa mana weekend. Mubeen ne kawai tare damu sai ƴanmatana da da Suhaib da auta..... Wannan kenan. ∆••••∆ ★∆••••∆ A ɓangaren su Uncle Smart da Lulu ƙamshi sun bar anguwar gaba ɗaya amma taƙi ta faɗa masa inda suka nufa. Shi kuma ya shareta ya cigaba da tafiyarsa a nutse. Yanda yake juya steering motar a nutse ya sata ɗan tsira masa ido a kaikaice. Sai dai ga duk wanda zai iya kallonta zai ɗauka hankalinta nakan tab ɗinta ne. Kamar wadda ta tuna wani abu kuma sai ta yamutse fuska da jan siririn tsaki ta maida hankalinta ga tab ɗin. Sunyi nisa sosai da anguwar dai-dai wasu gungun masu sai da kayan fruit ta ce, "Malam dakata min". Yanda tai maganar a gadarance ya sashi ɗan cizar lips ɗinsa. Ƙoƙarin wucewa yake ta sake maimaitawa cikin daka tsawa. Ƙin tsayawa yay sai da ya gota sosai ya gangara gefen titin ya kashe motar. Jitai wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ya turniƙe mata zuciya har ta kasa yin magana ma. Sai huci take lips ɗinta na motsi amma ta kasa furta komai. Shiko ko'a kwalar rigarsa wayama ya ɗauka yana dannawa batare da ko kallonta sau ɗaya yayi ba. "Amma kai babban illiterate ne!!". Ta faɗa cikin matsanancin ɓacin rai. Idan motar ta motsa to shima ya motsa ballema ya nuna mata yasan da shi take. Zata sake magana akai knocking glass ɗin motar, nan ɗin ma bai motsa ba, bai kuma sauke gilashin ba sai itace ta buɗe motar ta fita zuciyarta na mata wani irin tuƙuƙi, ji take bata taɓa tsanar wani mutum a duniya ba kamar wannan guy ɗin, dolene ma ta ɗauki mummunan mataki a kansa ta yanda ko ƙarar takalminta da warwarayen hanunta yaji sai hanjin cikinsa sun kaɗu.........✍️ *_Ina bayanki ta wajenmu, karki bari ya raina ki😏, mutum sai ɗaukar kan tsiya aljihu babu manda🥱 gidan sanyi ma shiru ne. Bari nayi nan dan yau nasan namana ɗanye ga ƴan Smart team🚴😜🤪_* _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣6️⃣ .........Wanda yay knocking glass ɗin ya gaisheta cikin girmamawa. Hannu kawai ta ɗaga masa. Bai damuba dan yasan halinta. Cikin yarensu na gayu ya ce, "Mi hajjaju ke buƙata?. Kankana, lemon zaƙi, abarba ko tuffa?". "Wanne gareku a ƙasa". "Duk akwai hajjaju, akwai ma sabon ɗiba daga lambu kuma sabon icce ne nata tsumayenki ko zaki shigo amma shiru". Karan farko hankalinsa ya ɗan fara komawa garesu. Kaɗan ya ƙara sauke gilashin motar yana kallonsu ta mirror. Muska taɗan yamutse da faɗin, "Daga wane garden aka kawoshi?, miye kuma tsaftarsa da ɗanɗanonsa?". "Hajjaju akwai sirri a ɗanɗano kam, gashi ya nuna luguf amma dai zan iya haɗa miki da shi kije kiga samfur". "Okay" kawai ta faɗa da miƙa masa kuɗi masu yawa da zasu iya kai naira dubu hamsin. Da sauri ya juya ita kuma ta buɗe motar ta zauna batare data rufeba ƙafafunta a waje. Shiko Smart cikin hikima ya cigaba da bin saurayin da kallo ta mirror da ya saita har yana iya hango wajen masu fruit ɗin. Yanda saurayin ya ɗanyi diri-diri zuwa ƙasan teburinsa kafin ya ɗago ya fara zuba fruit a ledan hanunsa ya sashi sake maida hankali garesa. Bai wani jimaba ya dawo da leda shaƙe da fruit. Ta ɗayan gefen ya zagaya ya ajiye gefenta, ita kuma ta shiga ta maida motar ta rufe. Ƙin taɗa motar yay har kusan minti ɗaya. Badai tace masa komai ba sai ma ƙoƙarin kai waya take a kunnenta. "Kina shago ne?". Yaji ta faɗa batare da tayi sallama ba. Bai kuma san mi'akace mata da ga can ba ta dai katse wayar. Batare data kallesa ba ta faɗa masa inda zasu a taƙaice. Shima komai baice ba ya harba motar saman titi zuciyarsa na faman kai kawo. Lokaci zuwa lokacin yakan kalla ledar fruit ɗin ta cikin mirror. Sun ɗan samu huldup a hanya dan haka suka ɗan ɓata lokaci kafin suzo. Tun daga waje zaka san wajen saloon ɗin babba ne kuma na manyan mata masuji da manda a gidan sanyi. Ƙin fita tai ita a dole sai ya fito ya buɗe mata. Shiko ya shareta kamar bai fahimta ba. Aiki ta cika tai fam, dama ƙulle take da shi ta fara zazzaga masa masifa har mai saloon ɗin data kasance ƙawarta ta iso. Ita ta buɗe mata cike da murna tana faɗin, "Oyoyo my Lulu ƙamshi gawa taƙi rami" tai maganar tana jawo ganunta dole ta fito suka rungume juna. Suna niyyar barin wajen ta balla masa harara da jan tsaki tana faɗin, "Ka kuma jirani harna gama villager kawai Mtsowww". Idanu ƙawar tata ta wani tsira masa dan sai yanzu ta lura da shi. A hankali ta furta "Woow vary handsome fa, my Lulu Ina kika samo sa?". Harara ta balla mata da jan tsaki ta fisgi hanunta suka bar wajen. Itako sai ƙara waigowa take dan ba ƙaramin tafiya da imaninta Uncle Smart ɗin da tun kallo ɗaya da yay mata ta mirror ya ɗauke kai bai sake ba dan itama dai irin Lulu ɗin ce. Sanye take cikin skert da riga na atamfa sun masifar matsata kamar tai nishi su yage. Ga uban attachment kan yasha da zaro-zaro na farce da gashin idanu kamar ɗiyar aljanu. A dire take kuma ƙyaƙyƙyawace amma hakan baisa yaji ta ishesa kallo ba. Yanda take tafiya da waigensa yasa Lulu cikin takaici faɗin, "Wai ke Deeyah wace irin banzar yarinyace ban san kayan zubar da mutunci fa kema kin sani". "Wayyo my Lulu bazaki ganeba wlhy, Guy ɗin nan yay masifa-masifar haɗuwa dan ALLAH ina kika samosa?". "Mtowww! Ban sani ba banza kawai". Ta faɗa dai-dai suna shigewa cikin shagon saloon ɗin. Tuni yaran Nadeeya suka fara zubewa gaisheta dan sun san halin masifarta. Ko kallo basu isheta ba takai zaune a ɗaya daga kujerun saloon ɗin. Babu kowa a wajen sai Nadeeyar dama da yaran, dan duk randa Lulu zatazo gyara dokar da take sakawa kenan kar a amshi kowa bata buƙatar hayaniya da gwamutsen numfashi. Duk da hakan na tauye Nadeeyar haka take haƙuri tabi yanda take so dan a zauna lafiya. Amma kuma tana biyanta kuɗi sosai da yafi na aikin duk da itama Nadeeyar da ga babban gida ta fito, sai dai ko kama ƙafar kuɗin gidan su Lulu basuyi ba, su Lulun ma zasu iya kallonsu a faƙirai. Nadeeya fa ta damu da son sanin wanene. Yayinda Lulu ta mata banza. Batai zuciya ba tama cikin yaranta sginal da ido. Fahimtar abinda take nufi da yarinyar tayi ya sata kaɗa mata kai. Cikin fakar idon Lulu ta ɗauka drinks da ruwa ta fita. Har yanzu yana zaune a motar ko buɗewa bai yiba, sai dai ya sauke gilashin tare da kwantar da kujerar yanda zaiji daɗi. Ita kanta yarinyar sai da taji wani iri datai tozali da shi. Dan Uncle Smart ƙyaƙyƙyawan mutum ne kuma nutsatstse ɗan gaye ga masifar tsafta, irin mutanen nan ne masu shegen tsaftar shiya da a wajen wasu suke ɗaukar harma tai yawa, duk da baida kuɗi bai kuma tashi cikin dukiya ba ALLAH ya bashi lafiyayyen fata mai ɗaukar idon mai kallonsa ga kamala da cikar haiba. Rashin yawan walwalarsa da shiru-shiru na zame masa adon kwarjini ga duk wanda zai dubesa ko zama da shi. Cikin ɗan daburcewar harshe ta gaishesa. Hannu kawai ya ɗan ɗaga mata dan tunda yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Cikin ɗan in'ina ta ce, "Dama Aunty tace a kawo maka wannan". Kamar zai share sai kuma yay magana cikin deep voice ɗin nan nashi mai rikita marasa jin magana musamman ƙannensa, mai kuma saka ƴammata da yawa mutuwa a kansa, "Waye aunty?". Cikin motsa lips ɗinsa a hankali. (Masha ALLAH kaji wani dakakkiyar murya mai ratsa zuciya) ta faɗa a zuciya. A zahiri kam tai saurin faɗin, "Madam ɗinmu ƙawar aunty Lulu ƙamshi, Aunty Nadiy....." "Ba buƙata". Ya katseta cikin ɗauke kansa da lumshe idanu yamayi sama da gilashin gaba ɗaya. Tsaye tai sororo kamar kayan ado, sai kuma tabar wajen jiki a sanyaye. A cikin shago har an fara kwance ma Lulu kalbar kanta da wanke mata ƙafafu, yayinda suke hira da Nadeeya ƙasa-ƙasa. Sai dai hankalin Nadeeyar gaba ɗaya na kan ƙofa ne. Da mamaki tabi yarinyarta data dawo da abinda ta fita a hannu. Sai dai batace komai ba gudun kar Lulu ta ganota. Kusan mintuna biyar da barin yarinyar wajen ya buɗe idanunsa. Haka kawai zuciyarsa ke masa kaikawo akan ledar fruit ɗin nan. Duk da wani gefe na kwaɓarsa ya kasa hana kansa dubawa. Ɗakkota yay, ɗaya bayan ɗaya ya fara fidda fruit ɗin da aka loda a sama. Kamar yanda zuciyarsa ke raya masa acan ƙasa wasu abubuwa ne daban, fiddosu yay baki ɗayansu ya maida fruit ɗin ciki tare da ajiye ledar a inda ya ɗauka. Wani irin dokawa ƙirjinsa keyi da sauri-sauri ganin mugayen ƙwayoyin dake a ƙasan, kasancewar shi ba ma'abocin shaye-shayen bane babu abinda ya fahimta a tare da su, sai dai yasan dole ƙwayoyin zasu zama na shaye-shayen ne. Sake naɗesu yay da ƙyau ya adana acan ƙasa inda ƙafafunsa suke, da ga haka ya sake buɗe motar ya fiddo ƙafafunsa dan yasha iska. Awani kusan huɗu Lulu ta kwashe a wajen gyaran jikin nan. Dan sai wajen 3 ta fito. Kallo ɗaya da yay mata sai da gabansa ya faɗi, yay saurin ɗaukewa yana jan siririn tsaki. Oho ita bama ta lura da shi ba. Dan yana da ga can gefe a bench na wani mai sai da ƙwa-ƙwa da aya da dabino dake ɗan jikin symbol ɗin shigowa harabar plaza ɗin. Tana da ga tsaye tana hararar motar da tunanin ko yana ciki amma shiru, a fusace ta fara knocking glass ɗin nan ma babu alamar za'a buɗe. Ashar ta mulmulo cikin ƙufula da faɗin, "Mi wannan illiterate ɗin ke nufi da nine wai? Barin wajen yay ko mi?". "Kai haba shi ya fara wannan ganganci kamar bai san wacece Lulu ƙamshi ba ne". Nadiya ta faɗa cikin ƙara fasa mata kai. "Ai da alama har yanzu ban sanar da shi ɗin ba. Guy ɗin nan fa mara mutuncine da kike ganinsa. Na barshi ne ban koreshi ba tun a ranar farko saboda sai na gama wulaƙanta rayuwarsa sannan da nuna masa banbancin da ƙasa da sama ke da shi". Cikin ƴar dariya Nadiya ta sake faɗin, "Ai wannan karon drivern naki ne sam bai kama da driver ba wlhy. Irin wannan haɗuwa haka, da gani kuma akwai girman kai fa, koda yake ya kai yayi ne dan ya haɗu ba kary....." "Mtsowww kema shashasha ta biyu da har kika zauna masa kallo haka. Ina wani abin haɗuwa mutum na warin talauci da jahilci. Ƙaton banzar bana zaton (A) kota kai girman garinsu ya sani". Cikin dariya Nadeeya ta ce, "Kai Lulu harda sherinki, wannan ɗan ƙwalisar ne za'ace bai san miye A ba?. Da gani yayi karatu wlhy danni kamar ma na taɓa sanin fuskarsa a cikin ƴan ƙwallon Kano pillars sai dai nasan da wuya ace wancan ne". Tsaki Lulu ta sake ja cikin gatse ta ce, "Sai dai ƴan ƙwallon kwashe gotta ɗin anguwarsu. Dalla malama ni kin isheni". Nadeeya zata sake magana ya iso wajen, dan duk da ba jin mi suke faɗa yake ba da ga inda yake haka kawai zuciyarsa ke raya masa maganarsa suke, maganar kuma da bazata wuce zagi ya sha ba a wajen ƴar balaja'un tsagerar yarinyar nan. Wani banzan kallo Lulu ta watsa masa. Sai dai batace komai ba. Shima ɗin bai nuna yasan tana yi ba ya buɗe mata motar batare daya jira shigarta ba shi ya shige nasa mazauni.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣7️⃣ ........Sai da ta zagesa ciki-ciki da kalmar illiterate sannan ta shiga motar Nadeeya ta rufe da faɗin, "Sai mun haɗu anjima. Dan yau dole ne a warware gajiya Lulu ƙamshinmu ta samu lafiya. Barama na nemo Ɗan-takife ya haɗa mana kayan aiki yau network na gasken-gaske zamu hau". Yatsu biyu ta ɗaga mata tana murmushi, shi kuma yaja motar batare da bari ta faɗi abinda tai niyyar faɗa ba. Dama tun a kallo ɗaya da yayma Nadeeya ya fahimci itama tana shaye-shayen. Dan ita har jikinta ma ya fara nuna kansa saboda har taba tana sha. Masifar da batai masaba a farko ita ta fara zazzaga masa yanzu akan dan mi yasa zaija mota bata bashi iznini ba. Ko sau ɗaya bai nuna yasan ma tanai ba balle ya tanka. Hakan kuma na ƙara fusatata da cimata rai akan al'amarin sa, dan a duniya ta tsani tayi ma mutum abu ya mata shiru, amma shi kulatama bayayi balle ya bata haƙuri kamar yanda sauran masu aiki ƙarƙashinsu ke mata. Suna isa gida tun bai gama tsayawa ba ta fice a motar, cikin gargaɗi ta ce, "Sai nayi maganin wannan zafin kan naka baƙauye kawai". Da kallo kawai ya ɗan bita, sai kuma ya janye idanunsa yana ambaton auziyya saboda yanda skert ɗin yay mata ɗam illahirin surarta na juya kansu. Bayan ya kashe motar ya ɗan ja kusan mintuna biyu zaune shiru abubuwa da yawa na masa kai kawo, ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana mai cigaba da ambaton ALLAH tare da buɗe idanunsa dake lumshe har kalarsu ta canja. Ledar nan daya cire a fruit ɗinta ya ɗauka ya fito a motar, kai tsaye ya nufi wajen su maigadi. Suna cikin gaisawa Nazeer autan gidan ya fito. Sai da ya gaishesu dan sukam Mommy tsaye take akan tarbiyyarsu, bata yarda sun raina kowane ma'aikaci ba a gidan duk da wani lokacin su Hussaina kan so ɗaukar hallayar Lulu suce zasu taka ma'aikatan a bayan idonta. Duk kuma randa ALLAH yasa kunnenta yaji ko idonta yaji bata musu da wasa, shiyyasa ma suke shakkar aikatawar. Cikin ladabi Suhaib daya maida hankalinsa garesa ya ce, "Uncle Smart Aunty Lu ce tace na ɗauka leda a mota. Ta kuma ce wai karkaje ko ina yau har sai idan itace tace". Karan farko da al'amarinta ya so fara bashi dariya. Amma sai bai nuna ba ko'a fuska. Miƙewa kawai yay yaje ya Bama yaron ledar data aiko a ɗauka. Wadda ganin bai biyota da ita bane yasa ta fara masifa, da farko ma catai Suhaib ɗin ya kira mata shi, Mommy ce ta hana tace ya amso kayan kawai. Duk rashin mutuncinta tana jin shakkar Mommyn, dan haka ta cema Suhaib ɗin to ya faɗa masa yau kar yabar gidan nan sai da izinin ta. Kai kawai Mommy ta girgiza, a zuciyarta tana tausayin hallayar Mawaddat ɗin, dan tsaurin idonta da izza na bata tsoro. Koba komai ɗiya mace take, komai daɗewa ƙarƙashin ikon wani zata koma. Wanin ma da bata san shi kuma tashi kalar tsagerancin ba. Koda Suhaib ya kai mata ledar fruit ɗin sama-sama kawai ta cire ta ajiye musu ta shige da sauran ɗakinta. Babu wanda yayi magana sai binta da sukai da kallo kawai. Duk da tana buƙatar wanka hankalinta ba'a can yake ba. Kayan shaye-shayenta kawai take buƙatar ɗan ɗorawa, dan kwana biyun nan da bata sha ba jinta take kamar mara laka a jiki, kuma kamar ana mata susa a brain. Tsaf ta gama zazzage kayan fruit ɗin a ƙasa batare data damu da yanda aka gyara ɗakin ƙal-ƙal ba. Duk da ba wani a cinkushe suke ba haka ta shiga tonawa da mamakin rashin ganin waccan ledar. Da gaske dai babu alamar ledar, dan haka ta miƙe zumbur, bataima kowa magana a falon ba ta fice. Har yanzu yana zaune a wajen su maigadi da sauran masu aikin gidan. Hira suke suna kwasar dariya shiko yana zaune shiru sai waya da yake dannawa, wani lokacin yakan ɗanyi murmushi da hirar tasu musamman idan sun sakosa a ciki. Cikin jan tsaki a zuciyarta ta ce, (Baƙauyen banza sai jin kan tsiya ko ubanwa zaima) dai-dai wajen motar da suka dawo ɗin ta dogare tana faɗin, "Kai!!". Dukansu juyawa sukai suna kallonta. Shikam ko motsi ma baiyiba balle ya nuna yasan da zuwanta. Baƙin ciki, takaici kamar zasu kashe Lulu. Cikin takaici da izza tace, "Wai kai banzan nan bada kai nake ba". Yanzun ma shiru bai ɗago ba. Sai dai mai-wanki ya zunguresa da faɗin, "Aliyu da kaifa take inaga". Nan ma shiru yay yaƙi nuna yaji. Dan haka ta nufo wajen a fusace. "Wai kai mika ɗauki kanka? Waye ubanka a ƙasar nan?!!". Idanunsa ya ɗan rufe sai kuma ya buɗesu a hankali. Karan farko ya ɗagosu a buɗe gaba ɗaya ya zuba mata su. Wani irin motsawa zuciyarta tayi, dan wani irin kwarjini da shakkarsa ce ta daki ƙirjinta har zuciyarta na sukur-sukur a cikin jiki. Cikin ƙarfin hali ta watsa masa harara da faɗin, "Dalla malam daina kallona da wannan shegunayen idanun naka uwa na macizai". Bai janye idanun ba, haka kuma bai tanka mata ba dai, sai ma sake tsatstsareta yay da idanun duk da masifar da hakan ke haifar masa shi kansa. Neman daburcewa take, dan tama kasa cigaba da masifar da ke ta mata tuƙuƙi a zuciya. Fahimtar hakan da yay ya sashi motsa laɓɓansa karo na farko da nufin yin magana. Cikin deep voice ɗin nan tasa dake fita da dakewar da nutsuwar fitar da lafazi ya furta, "Duk macen data cika mace mai suturtawace akan kanta koda ga muharramanta ne, hakan kansa ko bata kira daraja gareta ba, darajar kanzo ta risina mata a gaban wanda ya fita ma balle wanda ke a ƙarƙashin ikonta. Wannan gata da musulunci yayma mace har a lafazinta ana so ta zama mai ƙyautatawa akan harshe". Yana gama faɗa ya miƙe tare da miƙa ma mai-wanki dake kusa da shi key ɗin motar. "Mu kwana lafiya" ya faɗa cikin miƙa masu hannu ɗaya bayan ɗaya sannan ya nufi hanyar gate batare da ya sake ko kallon inda take tsaye ba. Babu abinda ta fahimta a kalamansa, sai dai abin mamaki ta kasa koda motsa yatsanta garesa balle maida masa murtani ko yin masifa kamar yanda ta saba har ya fice gidan abin sai kace wani siddabaru. "Aunty wani abu za'a ɗakko a motar?". Mai-wanki ya dawo da ita hayyacinta. Kamar wadda aka farkar a barci a zabure ta ce, "Ubanka zaka ɗakko min wawa kawai" ta juya zata bar wajen. Sai kuma ta dawo ta shiga nuna maigadi da yatsa. "Idan har kabar wancan ɗan iskan ya shigo gidannan a gobe a bakin aikinka kaima. Shima kuma ba ƙyalesa nayi ba, sai naga waye ubansa a garin nan, mi kuma yake taƙama da shi? Dan wlhy sai na wulaƙanta rayuwarsa ta yanda ko sunana yaji sai ya saki fitsari a wandonsa". (Ko kuma ke ki saki ba) mai-wanki ya faɗa ƙasa-ƙasa yana danne dariya. A zahiri kam kawunansu a ƙasa babu wanda ya motsa harta isa motar da suka dawo ta buɗe, ko'ina sai da ta leƙa amma babu alamar abinda take nema. Rai ɓace ta nufi komawa dan a zuciyarta ta fara bata *_Ƙwaro_* bai saka mata abubuwan nan bane. Dai-dai tana shigewa motar Uncle Yousuf nayin horn. Da sauri maigadi ya tashi ya buɗe gate ɗin. Fitowar Uncle Yousuf ɗin a motar shi da Smart ya sakasu sakin ajiyar zuciya a tare, a hankali mai-wanki ya saki dariyar da yake ta riƙewa tun ɗazun ganin Uncle Yousuf ya dawo da Uncle Smart ɗin tun ba'aje ko'ina ba. Hakan yasa mai bayin fulawoyi tayasa shima. Sai da sukai mai isarsu sannan mai-wanki ya ce, "Yau fa gamai maganin fitsararriyar nan. Ga kuma Alhaji ƙarami ya dawo da shi tun minti biyar basu cika ba, maga yaya wasan zai kaya. Dan wlhy ya mugun burgeni guy ɗin nan. Ga shi da alama ta tsorata da shi. Ai ban taɓa tunanin anan kusa za'a samu mai maganin masifaffiyar matar nan ba, sai gashi kuwa a cikin waɗanda tafi rainawa da cima zarafi wato mu ma'aikata, dan kawai muna neman guminmu a ƙarƙashin dukiyar gidansu sai take jin mune ƙasar takawarta a duniya". Nisawa maigadi dake kaiwa zaune yayi yana sakin wani ɗan murmushin manya. "Ai ni tun randa yaron nan ya fara zuwa nasan ba kanwar lasa bane ba, dan a cikin idanunsa zaka fahimci shima taƙadarin kansa ne". "Shine dai-dai da ita ai. Wulaƙancin yarinyar nan wanene bamu gani ba. Sau biyu fa tana marina". Mai-wanki ya faɗa cikin ƙunar rai alamar har yanzu yana jin raɗaɗin marin a zuciyarsa, sai dai babu yanda zai yi... Kafaɗarsa mai bayin fulawoyi ya dafa shima cikin ƙunar rai dan ya taɓa shan marin Lulun, "Ai ga mai rama mana nan yazo da ikon ALLAH. Fatanmu dai ALLAH yasa Alhaji Yousuf ya tsaya kan hanata korarsan da tace". "Ai insha ALLAHU bazata taɓa samun wannan damar ba ma. Dan randa ta dawo ashe shi aka aika ɗakkota tai masa halin nata yay tahowarsa ya barta acan, kamar dai yau ɗin nan da ya manna mata hauka, amma Alhaji Yousuf ɗin yaje ya dawo da shi aiki matsayin ma drivern ta, kaga ko da ace dane ai tun ranar zata koresa bayan taci masa zarafi kamar yanda takema na baya ko, kuma ya koru ɗin kenan. Nima a wajen Mubeen naji yana labartama yayansu Husain ta waya jiya". "Ai Alhaji ƙarami yana birgeni wlhy". Cewar maigadi. Haka suka cigaba da gulmar Lulu da a gabanta to tari basu iyawa bare satar kallonta..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣8️⃣ .........A ɓangaren Lulu kam sosai ta haukacema ƙwaro ta waya da masifa shiko ya dinga rantsuwar ya saka mata. Har abokinsa da yay komai a gabansa ya bama wayar ya zame masa sheda amma taƙi yarda. Sai ma katse kiran tai da tabbatar masa sai ya san ita ya cuta wlhy... Gado ta faɗa zuciyarta na mata wani irin tafasa, babu abinda ke mata kai kawo a rai irin maganganun drivern ta, haka kawai zuciyarta ke ingizata akan son sanin ma'anarsu. Wayarta data yasar gefe ta jawo. Nadeeya ta kira, ana ɗagawa daga can Nadiya ta fara da faɗin, "Bastie dama fa yanzu zan kiraki, dan gama wayata da Gajere kenan yace za'a samu kaya a wajen ogansa kona mil. ake s....." "Kinga ni ba wannan ba..." Ta faɗa cikin katse Nadeeyar. "Oh to ina saurarenki, na jiki kamarma cikin ɓacin rai, miya faru kuma? Badai driver ɗin ba kuma?". "Komai ma ya faru, har ma abinda banyi zaton faruwarsa ba ya faru. Wani Hausa nake son ki fassara min". "Tofa! Wane Hausa kuma?". Batasan ta haddace abinda ya faɗa matan ba sai da ta zayyanosu tsaf a yanda ya faɗesu babu ko gargada. _"Duk macen data cika mace mai suturtawace akan kanta har akan muharramanta, hakan kansa ko bata kira daraja gareta ba, darajar kanzo ta risina mata a gaban wanda ya fita ma balle wanda ke a ƙarƙashin ikonta. Wannan gata da musulunci yayma mace har a lafazinta ana so ta zama mai ƙyautatawa akan harshe"._ "Woow Madam irin wannan kalamai haka kamar wata mai tsara baitikan waƙe, dan ALLAH waya shiryasu haka...." "Mtsoww malam dilla fassararsu nake buƙata nace". "Oh sorry, tab wlhy fa kalaman sunyi tsauri, ni kaina ban san yanda zan fassarasu ki gane ba dan hausan ba gama isata yay ba. Amma ina zuwa bari na tambaya". Tana ƙoƙarin ajiye wayar cikin jan tsaki Suhaib na mata knocking. "Uwar miye?". Ta faɗa cikin masifa. Cikin tunzura baki Suhaib da ke da ga ƙofa dan bai shiga ba ma ya ce, "Uncle Yousuf ne yazo, ya ce kizo" da ga haka yay wucewarsa. Tana son Uncle Yousuf matuƙa, tana kuma girmamashi saboda wasu dalilai nata na kanta. Dan haka tace ma Nadiya tana zuwa ta yanke wayar. Da mamaki mai nuna ɓacin rai take duban Smart da ke zaune a ƙayataccen falon nasu kusa da Uncle Yousuf. "Mi wannan abun yazo yimana nan Uncle You?". Ta faɗa tana nuna Smart da ke zaune babu alamar ɗari-ɗarin nan irin na ma'aikaci da iyayen gidansa a tare da shi. "Ni na kirawoshi" Uncle Yousuf ya bata amsa cikin ɗaure fuska. "Uncle nifa bana buƙatar sake ganinsa" ta faɗa itama a harzuƙe. "Da yay miki mi?". Baki ta tura gaba cikin kumbura fuska ta ce, "Wlhy na tsanesa, har ni wannan mutumin zai zaga. Korar ma da nai masa yanzu ba'ita kenan ba Uncle, ya jira hukuncin da zai biyo bayanta. Har ni zaima banza ina masa magana, sannan ya biyoni da baƙaƙen maganganu a gaban su maigadi, har shi waye? Mi yake jin kansa? Ɗan u......" Hannu Uncle Yousuf ya ɗaga mata, "Ya isa haka. Mawaddat wai yaushe zakiyi hankali ne dan ALLAH. Yanzu abinda kike yi ko su Suhaib ƙannenki zasu aikata ne? Ke kullum cikin korar mutane. Yanzu dai ina son ki nutsu ki kwantar min da hankalinki, dan shiyyasa ma na dawo da shi gidan a yanzu dan na haɗu da shi a hanya ne. Ban kawo Aliyu gidan nan dan ki koresa ba, zan ƙara jaddada miki a yanzu shi ɗin zai dinga kaiki duk inda kike so dan saboda ke kaɗai ma na ɗaukesa aiki. Zai zo ƙarfe bakwai da rabi saboda takwas kike fita aiki, zai dawo da ke ƙarfe biyar da rabi kamar yanda kike dawowa shike nan ya tashi sai kuma washe gari period na gama magana." "Amma Uncle...." Hannu ya ɗaga mata alamar baya buƙatar ta sake cewa komai, rai ɓace tabar wajen kamar zata fashe dan haushi. Da ga haka ya juya ga Smart da ke zaunensa a yanda ta shigo ta samesa batare da yabi takanta ba. "Wannan shine lokacin zuwanka aiki da tashin ka. Amma weekend zaka iya zuwa da ga goma zuwa huɗu sai ka tashi. Zan baka duka tsare-tsaren fitarta a rubuce, sai kuma idan zuwa wani waje ya kamata kasan aikinsu yana sakasu ɗan yinan-yinan koba shiri. Dan ALLAH ka ƙara hakuri, al'amarin Mawaddat sai addu'a, ga yanayin da take ciki na ƙara kangarar da ita. Kai tsakaninku ma akwai cigaba, dan naga alamar tana shakkar ka sosai". Karan farko ya saki ɗan murmushi da shafa kansa. "Alhaji wane tsoro kullum ana zageni da kirana illiterate ko villager. Kawai dai zanyi haƙuri domin mutuncinku da ceto rayuwarta, dan koba komai nima inada ƙanne mata, ina son kuma ALLAH ya karemin su a duk inda suka shiga." "Gaskiya ne wannan Aliyu. Ina godiya matuƙa a gareka da sake baka haƙurin di. Yanda ALLAH ya haɗa wannan zuminci a tsakaninmu ALLAH yasa muci moriyarsa har a gidan aljanna. Amma ina son naji wannan kalamai da aka faɗama yarinyata haka har suka harmutsa min ita, duk da nasan abu kaɗan ma fusata Mawaddat yake". Murmushi Smart ya sake yi a karo na biyu da faɗin, "A Alhaji ai ba'ayi haka ba. Tunda ya wuce a barsa kawai sai na gaba idan ALLAH yasa za'ayi a gabanka, duk da ina tsoron kuma karta kwaɗa min mari dan yau ma dai da ƙyar na sha shiyyasa ma na gudu". Dariya sosai Uncle Yousuf yake kwasa da faɗin, "A lallai ka tsira da ƙyar, dan a ma'aikatan gidan nan ɗai-ɗai ne basu sha marin Lulu ƙamshi ba kam". "To kaji ko Alhaji. Bara nayi nan kafin ta sake fusatowa ma, nasan yanzu bai zama lallai na sha ba". Dariya Uncle Yousuf ɗin ya sake kwashewa da shi, shi kuma ya fice yana ɗan murmushinsa mai sanyi, har ga ALLAH yana ganin mutunci da kimar Uncle Yousuf, yaji kuma zai iya haƙuri da yarinyar kodan shi ɗin. Mutum ne da yasan daraja da kimar mutane, duk yanda kake baya wulaƙantaka ko nuna maka ɗagawar shi ɗin wani ne. Ya iske har lokacin su maigadi na gulmar Lulu, ganinsa baisa kuma sun daina ba sai ma kwarzantashi da suka shigayi akan abinda yaymata. Komai baice musu ba sai kansa da ya ɗan girgiza kawai ya ciro wayarsa ya fara sana'ar tasa, ba kuma wani abu yake a ciki ba face game ɗin ball. Bayan kamar awa ɗaya Uncle Yousuf ya fito zai wuce gida, Lulu ce tai masa rakkiya har wajen motarsa, aiko ta dinga antayama Smart da bai san tanayi ba harara. Dariya Uncle Yousuf ya dingayi ƙasa-ƙasa, dan sarai ya lura da ita, sai dai baice komai ba yayma su maigadi alheri kamar yanda ya saba. Godiya da addu'a suka shiga kwararo masa. Murmushi ya dinga musu kawai, dan harga ALLAH yana jin matuƙar daɗin addu'oi nan nasu. Duban Lulu da keta faman yamutse fuska yay, cikin tsokana ya ce, "To Daughter kin bani aron drivern naki ko na tafi da shi". Fuska ta sake kwaɓewa da faɗin, ni nama bar maka Uncle You, Dan bana buƙatarsa sai shegen girman kan tsiya". Dariya yayi, yana mai kiran Smart dake zaune kansa ke ƙasa. "Shiga muje" kawai yace masa. Bai musa ba ya raɓa ta gaban Lulu dake faman binsa da kallon banza, ciki-ciki ta furta, "An samu motocin banza sai hawa ake". "Ko ke kika zama mota hawa zanyi". Ya faɗa shima a ƙasa-ƙasa lokacin da yake shigewa cikin motar. "Kai ɗin banza! Shashasha!" Ta faɗa a zafafe har tana zaburowa. Wani shegen murmushi ya sakar mata a karon farko yana ɗan ƙara gimtse fuskarsa kamar bashi ya furta ba ya shige motar abinsa. Wayyo ba'a taɓa Lulu ba ma ya aka ƙare balle. Dariya sosai Uncle Yousuf yake yi, dan ya fahimci akwai abinda ya faru duk da Smart ɗin ya fuske abinsa kamar bai aikata komai ba. Har yaja motar suka fice bata bar masifar ba. "Na kula dai kai kake fara kunna min yarinya ka noƙe". Uncle Yousuf dake dariyarsa har yanzu ya faɗa dai-dai yana harba motar saman lafiyayyen titin anguwar. Kaɗan Smart ya shafo kansa yana ɗan murmushi batare da yace komai ba. Sai da sukai ɗan nisa ya zaro ledar da ya cire a cikin kayan fruit ɗin Lulu. Buɗeta yay, tarin ƙwayoyi kala-kala suka bayyana. Motar neman ƙwacema Uncle Yousuf ɗin tayi, da sauri ya gangara gefen titi cikin rawar harshe ya furta, "Wannan fa Aliyu?". Cikin damuwa da ɓacin rai shima ya bashi amsa da, "Fitar da mukai ɗazun abinda muka fara tsayawa akai order kenan a wajen wasu masu fruits kafin mu ƙarasa inda tace zataje". Sosai jikin Uncle Yousuf ke rawa, dan har ga ALLAH shikam bawai bai yarda da maganar Doctor Khalifa bane, kawai dai rashin ganin al'amarin a zahirinsa ya sa bai kai masa ƙololuwa a rai ba, shiyyasa ma ya ɗora Smart ɗin dan ya samu tabbaci. Kamar wanda ya shiga ɗimuwa ya sake furta, "Aliyu Hydar! Ka tabbata a jikinta ka samu waɗan nan ƙwayoyin?". Cikin salon dakewar nan tasa da rashin son magana ya ɗan ɗage kafaɗunsa da faɗin, "Yaah! A gabana ma aka saya". "Dolene na saka a kama yaron nan dake sayar mata, bara ma na kira CP...." Da sauri Smart ya dakatar da shi. "Niko a nawa shawaran Alhaji kamar kama yaron ba shine mafita ba tun a yanzu. Domin inaji a jikina ba dashi kaɗai take huɗɗa ba. Dan ka saka an kamashi kamar ka fargar da itane ta sake sabon salo ita da abokan mu'amalarta. Kaga kenan ba hanyar da zamu rabata da al'amarin muka ɗakko ba kenan, dan yanzu aka fara wasan kamar". Sosai maganarsa ta shigi Uncle Yousuf ɗin, dan haka ya ɗan dakata da ga ƙoƙarin kiran cp da yake shirin farawa, sai dai idanunsa sun kaɗa jazur harda ƴar guntuwar ƙwalla a cikinsu. Shiru babu wanda ya sake magana a motar har kusan mintuna huɗu, kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa.. Shine ya kashe shirun nasu da furzar da iska mai zafi. "Alhaji ni zan wuce, dan yamma nayi gashi ina son na isa gida da wuri". Cikin damuwa ya gyaɗa masa kai batare da ya iya furta komai ba har sai da ya fita yana ƙoƙarin rufe ƙofar motar ya kira shi a hankali. Ɗan duƙowa yay yana amsawa, Uncle Yousuf ya miƙa masa kuɗi masu yawa. Kansa ya girgiza da faɗin, "Kayi haƙuri Alhaji, tun farko na faɗa maka kada irin haka ya dinga shiga tsakaninmu. Hakkina kawai nake buƙata a kowane ƙarshen wata kamar yanda mukai alkawari. Na barka lafiya". Ajiyar zuciya mai ƙarfi Uncle Yousuf ya sauke ta re da sakin ɗan murmushi yana mai binsa da kallo. Tabbas a girme yasan zai iya bama Aliyun shekara bakwai. Amma dattako da kamunkan yaron na sakashi jin ya cika masa ido tamkar wani babba garesa. Wata irin kima da kwarjini yake masa a zuciya da cikin udanu. Yana matuƙar son ganin mutumin da yasan ciwon kansa a rayuwa da riƙe mutuncinsa. Ya yarda ya nema halak ɗinsa koda za'a kallesa a mai riƙe da sana'a mai ƙasƙanci, amma bai yarda ya ƙasƙantar da kansa ba wajen a bashi ya amsa balle zuciyarsa ta mutu. Insha ALLAHU zai taimaki rayuwarsa.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣9️⃣ ........Smart kam tuni ya shanye titin layin zuwa babban titi, da ƙyar ya samu napep. Tafiyar da bata wuce mintuna talatin ba ta kawosa anguwarsu. Kasancewar da sauran hasken gari koda ya shiga sai ya ɗan watsa ruwa tare da zuwa ya gaida Abba da su Ammah, sai dai ya iske Ammah ma ta fita ita da aunty Amarya Barkan ƙanwar Aunty Amaryar da ta haihu a can Gadon ƙaya tun la'asar, sai su Maryam kawai da suka dawo islamiyya. Dan haka bai zauna ba suna gama gaishesa ya fito ya koma ɗakinsa. Ba wasu abokai ne da shi ba shi dama sai Ahmad kuma ba anguwar yake ba. Dan Mutum ne mai ƙarancin kwaramniya. Idan kaga abokinsa da har zasu iya zaman doguwar hira to sai dai abokan karatunsa, amma na cikin anguwa sai gaisuwar mutunci kawai, duk da dai a da anyi abotar yarinta, sai dai kasancewar sa mara sakewa da mutane suke masa kallon mai girman kai duk suka janye jikinsu da shi, shi kuma bai nuna ya damu ba. Abokan karatun kuwa akan jima ma ba'a haɗu ba sai ta waya ko wani taro mai muhimmanci ya haɗa. Shiru ya kwanta kamar mai barci, da gani kasan duniyar tunani ya faɗa, dan babu abinda yake sai furzar da huci akai-akai da ga bakinsa, hakan kamar ɗabi'a ce data zame masa jiki in dai yana cikin damuwa.. Abubuwa ne masu yawa ke ci masa rai, ciki harda batun bauɗaɗɗiyar yarinyar can, shi mutum ne da baya shiga sabgar da ba tashi ba koda kuwa a cikin gidansu ne sai idan yaso, amma sai yake ji zuciyarsa na ingizashi akan taimakon ubangidan nasa da yarinyar, badan komai ba sai dan ƙannensa mata da bazai taɓa fatan su tsinta kansu a irin wannan rayuwar ba. Yasan idan har ya tsamota da ga wannan musifar yayi jihadi, sai dai bai san ta ina zai farama taro wannan al'amari nata ba. Karan farko yaja sirrin tsaki, sai kuma ya tashi zaune yana ɗan furzar da huci tare da kai hannunsa saman goshinsa yana ɗan murzawa. Ganin yaƙi samun nutsuwar hutawar da yake buƙata ya sashi tashi ya fito a ɗakin, nan ƙofar gidansu ya zauna yana ɗan gaisawa da mutane masu wucewa har akai kiran sallar magrib. Bai fito da ga massalacin ba sai da akai isha'i, yana kwaɗayin shiga gidan suyi hira da Ammah dan wannan ɗan lokacin kawai yake da damar haka gareta, amma zuciyarsa nata masa tuni akan Lulu da abinda yaji suna magana ita da ƙawarta zasuyi a daren na yau da sunan wai murnar samun lafiyarta. duk yanda yaso yaƙar zuciyarsa abin ya gagara, saboda yana ji a ransa ba alkairi za'a shuka ba wajen, dan haka ya fito da ga layinsu ya samu Napep zuwa hotoro gra. bai damu da kuɗin da suka tsuga masa ba. Ɗan nesa da gidan ya sauka, amma ya tsayar da mai napep ɗin, ya samu jikin wata bishiyar dabino kusa da katangarsu ya tsaya, ya kai mintuna talatin da wani abu a wajen yaji motsin an buɗe gate ɗin gidan, ido ya zuba na son ganin wanda zai fito. Ilai kuwa Lulu ce, dan a kanta idanunsa suka sauka saboda haske dake tako ina a street ɗin, gashi ta sauke glass ɗin motar sosai har kana iya hango kalar kayan da take sanye da su. Tayi ƙyau matuƙa ga uban ƙamshinta na isowa har inda yake tsaye saboda yanda ta gumbuɗashi kamar ba mace ba. A ɗan kasancewarsu na kwanaki ya fahimci sam bata tausayawa ƙamshi, haka kawai sai yaji tanan ɓangaren ta ɗan samu sassauci a garesa, duk da tana saka nata ƙamshi ne ba bisa ƙa'idar da ya kamata ace mace ta saka ba. Da sauri ya ƙarasa ga mai napep da ke zaman jiransa. "Kabi wannan motar Please, amma karka bari ta fahimci muna biye da ita". Ya faɗa yana nuna ma mai napep ɗin motar Lulu da ke tafiya a hankali kamar bata son tuƙin yau. Yanda take tafiyar ya bama mai napep ɗin damar binta cikin hikima har zuwa wata sabuwar anguwa, dai-dai wani gida da alamu suka nuna shima ba'a daɗe da kammalashi ba ta tsaya, da ga inda suke yana hangen yanda ta kai waya a kunnenta alamar kira take ko an kirata, tana ajiye wayar ana buɗe gate ɗin gidan. Da sauri ya fita tare da miƙama mai napep kuɗi yana faɗin, "Abokina nagode ko". Bai jira amsarsa ba ya nufi gidan, kasancewar akwai ƙarancin haske a anguwar dan kamar ma basu da wuta sai ƙarar gen... Ɗin gidan data shiga yake jiyowa ya samu damar bin motar tata ta gefe suka shiga tare batare da mai-gadin ya lura ba. Motoci ne kusan bakwai a gidan duk an parker a babban compound ɗin kamar wasu masu biki, tun kafin ta fito a motar ƙawayen nata suka baibayeta da ihun faɗin, "Sai Lu ɗin mu!!!, sai ƙamshin mu!!!". Fuskarta ƙawace da wani shegen murmushi ta fito. Wani shegen gown ne a jikin nata ta lafe mata kamar babyn roba. Da sauri ya kauda idanunsa yana mai jan sirrin tsaki da taune lips ɗinsa da ƙarfi. Bai sake kallon inda suke ba har suka shige ƙofar da yake ƙyautata zaton ta cikin gidan ce. Huci mai zafin gaske ya furzar tare da gyara tsaiwarsa. A ɓangaren su Lulu kam suna can cikin ƙaton falon gidan da ya sha kayan alatu. Abinda zai baka mamaki bawai iyakar su kaɗai bane ƴammatan ashe, akwai dattijan maza a shekaru bawai a cikar kamala ba har su huɗu, tun shigowar su Lulu kusan su duka suka zubo mata idanu fuska a washe, yayinda ita kuma nata murmushin ya ɗauke ta wani yamutse fuska tana kallon Nadiya, sai kuma ta juya ta fito a fusace. Da sauri Nadiya tabi bayanta tana faɗin, "Please Lu ki saurare ni." "Anƙi a saurareki ɗin, Nadiya kin san dai na tsani irin wannan ko...?" "Na sani, amma bamu da wani zaɓi ne wlhy Lu.., dan ALLAH ki fahimce ni, kin san dai bazanyi abinda zai ɓata miki rai da gangan ba...." "In ba kinyi da gangan ɗin ba miya kawo waɗan nan tsoffin banzar nan? Ni ban hanaki huɗɗa da su ba, amma ki sani duk randa suka zubar da ke bayan gama lalata miki ƙuruciya kiyi kukanki ke kaɗai kar ki tunkareni. Amma ki daina sakamin su a sabgogin rayuwata". Ɗan murmushi Nadiya tayi cikin rashin ɗaukar zancen na Lulu da muhimmanci ta ce, "Naji, ni dai yanzu kiyi haƙuri mu koma ciki dan ALLAH. Dan wannan fa zaman naki ne, dan ke akayisa, mun riga mun gama tara mutane, su Shony fa tun daga ktn suka taho a yammacin nan domin wannan shagali kawai. Abinda yasa ki ka ga su Alh. Baita anan ma saboda su Shony ne, dan sun riga sun kirasu cewar zasu shigo Kano, amma wlhy badan ke bane ba". A hankali ta furzar da iska, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. "Shike nan amma ki kiyaye gaba, dan in har kika sake sakamin sabgar waɗan nan mutanen a tawa wlhy sai mun rabu. Suma su Shonyn idan suna buƙatar haɗuwa da su ne suje can su haɗu bai shafeni ba". "Naji na yarda baza'a sake ba. Suma kuma zan musu bayani yanda zasu gane Muje to dan ALLAH suna jiranmu". "Bani details ɗin mai kayan nan na tura masa kuɗinsa karna shiga wata sabgar. Sannan wannan gidan na waye uwar kwashe-kwashe kika kawo mu kuma?". Gidan Nadiya ta kalla tana ƴar dariya tare da faɗin, "Gidan wanda ya sayar mana da kayan ne, wlhy Guy ɗin akwai kirki gashi so handsome kuma, ya bamu shawara ne muzo nan musha shagalinmu dan zaifi mana sirri kasancewar kinga dare ne, ke kuma ba cika son shiga clubs na nan Kano kikai ba kin ce ƴan hayaniya da ƴan iska sun cika yawa". Cikin rashin damuwa ta ɗage kafaɗa kawai, batare da ta sake tofa komai ba ta bar wajen. Binta Nadiya tai suka shige tare.... Gaba ɗaya zuciyar Smart ta sake jagulewa da takaici, dan duk abinda Lulu da Nadiya ke tattaunawa yana jinsu batare da su sun lura da shi ba. Shigarsu da kusan mintuna uku sautin kiɗa ya fara tashi kaɗan-kaɗan saboda rufe windows da sukai duk dan kar kiɗan ya fita wa mutanen anguwa. Kansa ya ɗan dafe yana mai ambaton sunan ALLAH, gaba ɗaya ma ya rasa miya kamata yayi, duk da yazo nan ɗinne da burin ganin abokan sheɗanar tata da kuma hanata shan komai. To amma ta ina zai fara ma?. Ya kwashe kusan mintuna ashirin yana ƙullawa da kwance ta yanda zai shiga wajen.... Ƙarar hayaniya da ta fara tasowa kaɗan-kaɗan da ga cikin falon ta maidosa da ga dogon tunanin mafita da ya tafi, ajiyar zuciya yaja kamar wanda aka farkar da ga barci tare da tsurawa ƙofar idanu. Wasa-wasa hayaniyar ta daɗa karfi har yana iya shaida muryar Lulu saboda tsayawar ƙarar sautin kiɗan da ke tashi, da alama sun kashe ne ko wata matsala ta faru. Falon ya nufa da sauri batare da tunanin komai ba ko neman izinin ya tura ƙofar ya shige, yanda ya gansu a yamutse ga Lulu na ɗurama wani hamshaƙin Alhaji zagi har tanayi kamar zata tsole masa ido da ɗan yatsa ya sashi yin turus, mamaki ne ko takaici oho baima sani ba, kayan shaye-shayene da na ciye-ciye ko'ina a barbaje, yayinda alhazan nan guda huɗu da ya shaida fuskar biyu a cikinsu kasancewarsu wasu manyan ƙusoshin attajirai kuma ƴan siyasa masu faɗa aji a garin na kano ɗaya ke tsaye cikin fusata kamar zai daki Lulu, sauran ukun na zaune sun zuba mata ido harda wanda take zagin da shi fuskarsa ma ƙawace take da murmushi kamar bashi akema tujarar ba. Kalaman Lulu ne na ƙarshe-ƙarshe da kukan da ta fashe da shi ya dawo da shi hayyacinsa.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣0️⃣ ........Cikin kuka da dafe kanta tana ɗan layi alamar ta fara shiga maye ta ke faɗin, "Wlhy! Idan baka fita sabgata ba sai na keta maka rigar mutuncin tufafi da mutanen gari ke kallonka da shi, dan dama shi kaɗai ya saura gareka. Nace banayi! Banayi wai na minene wannan takura duk inda na saka ƙafa kana biye dani, shine yau harda bani wine saboda kai tsinanne ne, ka taɓa ganin na sha wine ne duk rashin ji na azzalumi!! Shin wai ku kuna ɗaukar duk macen da ke shan wannan abubuwan dan bama kanta farin ciki ita ɗin ƴar iska ce ko me? Manyan banza manyan kawai, ku gama hura hanci ga al'umma ku dawo bayan fage kuna lalata musu tarbiyyar yaransu. Ka sani har gaban abada bazaka taɓa samun wannan jikin ba, bama kai ba duk wani maye sai gani sai hange dan ni ba mazinaciya bace, bar ganin ina wannan rashin jin nasan ciwon kai na wawa kawai da ƙi ƙ....." ta kasa ƙara sawa saboda shuuu da tai zata faɗi. Da sauri Nadiya ta tarota. Fisge jikinta tai tare da ɗagowa gaba ɗayanta kan ƙafafunta ta ɗauke fuskar Nadiya da mari haggu da dama.. A fusace Alhajin nan da ke tsaye tun ɗazun cikin ɓacin ran zagin da Lulu kema abokin nasa yayo kanta. Hannu ya ɗaga zai kwasheta da mari shima, sai dai cak ya tsaya jin an riƙe masa hannu ta baya. A karo na farko duk wanda ke'a falon ya farga da shi. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Alhajin da ke faman huci. Idanu ya lumshe cikin girgiza kansa da faɗin, "Haba kai kuwa ai babba babba ne, ba'asan namiji kuma da faɗa da mace ba. Bakaga abokinka yanda ya nuna mazantaka ba? Tunda kun gama zubar da kimarku garesu banga abin tada jijiyar wuya ba idan irin haka ta taso a tsakaninku ai......" "Kai kuma a matsayinka na ubanwa anan?". Maimakon amsa sai ya ƙara tsaresa da idanunsan nan masu kwarjini da suka gama ƙwarewa a kallo mai girgiza zuciya cikin nuna gargaɗi (Na macizai inji Lulu😂). Sakin hannun Alhajin yayi, kafin cikin yanayin nan nasa a daƙile da kowa ke ɗauka girman kai ya ɗage kafaɗunsa da ɗan taɓe lips ɗinsa. "Sanin ɗan waye ni bazai maka amfani ba, idan dani kake son sani sai na baka amsa da cewar drivern ta ne". "What?! Driver fa?!!. Ubanwa to ya baka damar shigo mana nan har da tsoma baki a cikin abinda bai shafeka ba?". Shi ba mai yawan magana bane, dan haka maimakon amsa masa a yanzun ma sai kawai ya zuba masa ido. Hon. HD Nakowa sai ya sake fusata. Magana zai sakeyi cikin fusata Alhaji Ɗan-kande Baita ya dakatar da shi. "Kaga HD please it's ok mana. Kai ɗan saurayi jeka kawai waje ka jirata nan ba huruminka bane ba". Wani banzan kallo Smart ya watsa musu su dukan, sai dai baice komai ba ya juya ga Lulu da ke zaune a kujera sharɓe tanata surutai da zagi har yanzu. Hanunta kawai ya fisga ta miƙe, batare da wani binta a hankali ba ya jata tana turjewa sukai waje. Da ƙyar ya iya kaita har motarta, dan haka ta maido da zagin da take ma Hon. Babale Misau kansa. Hakan bai damesa ba, sai ma rufeta da yay a motar ya koma falon ɗaukar handbag ɗin ta dan key ɗin motar na ciki.... "Ban yarda da wannan yaron driver bane ba, dan haka ina son a binciko min ɗan uban wanene shi a faɗin garin nan na kano". Hon. HD Nakowa ne ke faɗa dai-dai Smart na sake shigowa falon ɗaukar tarkacen Lulu. Nunawa yay kamar baiji mi Hon. Nakowan ya faɗa ba, ya nufi handbag ɗin da ya gani ɗazun a hanunta da takalmanta masu azabar tsini ya kwashe ya sake juyawa ya bar falon ko kallo basu ishesa ba..... Gotawarsu kaɗan da gidan wata dalleliyar mota ta iso ƙofar ita kuma. Horn yay aka buɗe masa. Yanda sautin kiɗa ke tashi a cikin motar zai baka tabbacin yana cikin nishaɗi matuƙa. Duk da yasan taro ake a gidan nasa hakan bai hanashi jin mamakin ganin wasu manya-manyan motoci guda uku ba, bawai ƴammatan bazasu iya zuwa da motocin bane, a'a kawai dai yasan sun musu girman da bazai yiwu ace sune suke hawansu ba. Cikin kai-kawo zuciya ya fito yana ƙara ƙarema motocin kallo, cikin ɗan basarwa irin na masu akwai ya ɗage kafaɗu da ɗan taɓe baki yay ciki abinsa ransa fal nishaɗi yau zai haɗu da mafarkinsa. Yayi alƙawarin sai ya ɗanɗani yarinyar nan dan ta tsare masa ko'ina na zuciya tun a randa ya ganta. Da wani irin sauri yaja birki ya tsaya yana ƙarema falon nasa da ya hargitse kallo, bawai na tarkacen da suka zube bane kawai dan yasan wannan ne ya kawosu ai. Iya shegen da ake aikatawa a falon duk da shima yasan yana aikatawa ya sashi zama turus, dan shi dai Nadiya batace masa zasu gayyato namiji ko ɗaya ba. Amma sai ga har mutum huɗu manyan mutane sa'ar Daddynsa, kai abinma tashin hankalin shine harda abokan Daddyn nasa ma da suka sanshi ya sansu. Da baya-baya ya koma ganin hankalinsu su bai kai kansa ba saboda shagala a ɓarnar da suke aikatawa da yaran mutane. Duk cikinsu baiga Lulu ba, gashi kuma an tabbatar masa da tazo wajen awa biyu baya da suka shuɗe. Waya ya ciro yay kiran Nadiya, an jima ba'a ɗauka ba dan har tana batun tsinkewa sannan aka ɗauka. Cikin wata irin murya ta ce, "Ranka ya daɗe barka da dare". Sai da ya ɗan cije leɓen haushi kafin ya amsa mata da "Ta iso ne?". Cikin muryar nan na wadda ta gama buguwa da shiga yanayin masha'a ta amsa masa da "Tazo amma shegen driver ɗin nan nata ya kwasheta sun tafi". "What!!" MM Atik Kumo ya faɗa da ƴar tsawa. Bai jira cewar Nadiya ba ya yanke wayar ransa a ɓace. Mota ya shige ya zauna tare da kwantar da kansa kan steering. A karo na biyu ya rasa damarsa akanta, tunda yake wata mace bata taɓa shiga ransa irin haka kamar yanda Lulu ƙamshi ta shiga ba. Da gaske sonta yake, yana kuma tsananin buƙatar mallakarta. Bai damu ace sai da aure ba, dan shi a halin yanzu babu maganar aure ma a gabansa duk da kullum faɗan momynsa kenan shine yay aure. Sai dai da to kawai yake amsa mata a duk sanda ta titsiyesa. Tun randa suka haɗu da Lulu a airport ya kasa hutawa da tunanin surar yarinyar da tsiwarta, burinsa kawai ya gusar da ƙishinsa gareta dan kowace mace tama daina birgesa a dalilinta yanzu. Sake kaiwa steering duka yay tare da tashi zaune yayma motar key a fusace ya bar gidan...... ★★ Driving ɗin yake cikin ɓacin rai da takaici, yayinda ita kuma ta keta faman surutai da zaginsa akan ya maidata sai ta koyama Hon. Babale Misau da Nadiya da suka haɗa baki hankali. Faɗi take ita ba ƴar iska bace, duk wanda yace zai mata iskanci sai ta wulaƙanta shi..... Wani irin baƙin ciki ne ya sake turniƙe zuciyar Smart dan surutanta sun ishesa, sake tunzura fushinsa suke zuciyarsa na ƙuna. Wani shegen birki ya taka a harzuƙe har sai da tai gaba ta bugu da kujerar gabanta ta sake buguwa da jikin ƙofa sannan ta koma ta zauna daɓar. Dafe kanta tai dan azaba kamar zata fasa kuka, sai kuma ta harzuƙo cikin fushi da masifa ga rashin kasancewa a hayyaci da ya ƙara hauhawar masifar tata ta ce, "Kai wai miyasa baƙauye ne akoda yaushe? Mugu so kake ka kasheni ka gudu da motan ko? Illiterate kawai, ba abinda ya iya sai shashashanci baƙauye". Idan motar nan ta motsa Smart to shima ya motsa, yakai matuƙar wuya so yake ya mata masifa dan maƙogwaronsa sai kaikawo ya ke a wuya amma yanata ƙoƙarin hana kansa, sai ma wayarsa da ya ɗauka ya fara danne-danne abinsa. Hakan ya sake fusata Lulu, da ma yaya lafiyar kura balle ta tsinke. Tana ƙalau ma yaya aka ƙare da jaraba balle yanzu da ya haɗa da maye. Sosai ta cigaba da zazzaga masa masifa ko haɗiyar yawu ma batayi, ganin badai zai kulata ba ta kama murfin ƙofar zata buɗe ta fita amma sai taji yayi lucking motar. Wayyo azabatun azaba. Yau dai kam yaga masifar ƙare dangi, dan bakinta baiyi shiru ba har sai da barci ya fara rinjayar mata idanu. Da wahala kaga Lulu tasha abu ya sakata barci, shiyyasa ko cikin abokanta ake ji da ita da kwarzanta ƙarfin kanta, amma yau da yake wani mugun haɗine MM Atik yay mata batare da ko Nadiya ta sani ba yasa abinda yafi ƙarfin kanta kala-kala wani ma bata taɓa shansa ba. Tun randa suka haɗu a airport bai huta ba, biye yake da ita yana ninƙaya cikin al'amurranta har sai da ya gama sanin ita ɗin wacece. Dan haka ya jawo Nadiya a jikinsa ya dinga jiƙata da kuɗaɗe harta amince da shi bawai yazo dan ya cutar da aminiyar tata bane son gaskiya yake mata. Ita da shi suka haɗa plan ɗin wannan phaty na samun lafiyarta, ya kuma saya musu duk kayan shaye-shayen tare da basu gidan hutawarsa da ya gama ginawa kwanan nan, shi yayi hakane dan ya rutsa Lulu a can, yayi imanin in har ya sameta sau ɗaya da kanta zata cigaba da nemansa kamar sauran ƴammatansa tana kawo masa kanta. Sai dai kuma kash, bayan ya gama wahalar haɗa dukkan plan ɗinsa wani shegen driver ɗinta ya zo ya rusa masa komai.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣1️⃣ ........Wayar da yake faman daƙila ya ajiye, dan dama yana dannawar ne kawai badan yana fahimtar komai ba da yake yi. Ta cikin mirror yake kallonta, sai kuma kamar wanda aka tsikara ya janye yana jan tsuki. Da sauri ya furzar da iska zuciyarsa tana masa kai-kawon tunanin ina ya dace ya dosa da ita. Gidansu ko gidan Uncle Yousuf?. A gidansu tana da ƙanne, kuma basu san halin da take ciki ba bayan iyayensu, ganinta a haka garesu zai ƙarasa zubar mata da mutunci ne a idonsu har ma da ma'aikatan gidan nasu da take takawa kamar ƙasa a duk sanda taso. Gidan Uncle Yousuf kam yaransa basu da wayo sosai kasancewarsu ƙanana, zai ma iya yiwuwa yanzu sunyi barci, ajiyar zuciya ya ɗan sake ja da kallonta ta mirrorn sai kuma ya janye idanunsa a lokaci ɗaya. Har ya ɗauki waya da nufin kiran Uncle Yousuf ɗin sai ya fasa, key yayma motar kawai ya cigaba da tafiya. Kaɗan-kaɗan sai ya dubeta ta mirror har suka iso gidan. Horn yay maigadi ya buɗe ƙofa ya fito, dan ba'ace masa wani zaizo gidan ba a irin wannan lokacin dan ƙarfe sha ɗaya saura. Ƙarasowa yay jikin motar sosai, Smart dake kallonsa shima yay ɗan murmushi da faɗin "Baba Barka da dare yaya aikin?". Murmushi shima maigadi yayi, dan ya ganesa. Cike da kulawa ya ce, "Mazan fama kaine yanzu da dare haka?". "Eh baba na kawo wannan ne". Yay maganar yana nuna baya, ɗan leƙawa baba maigadin yayi, ganin Lulu kwance a bayan ya sashi ɗan yin baya yana dafe baki dan shi a zatonsa ko barcin isa ne take yi. Da sauri ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Har gaban ƙofar shiga falon gidan Smart yay parking. Sai da ya kashe motar ya fito sannan ya ɗaga waya ya kira Uncle Yousuf. Ba'a jima ba aka ɗauka. Shi ya fara gaidashi dan a girme dai ya girmesa. Uncle Yousuf ya amsa da ƴar fargaba, sai yay saurin tambayarsa badai wani abu ya sake haɗasa da Mawaddat ba?. "A'a Alhaji komai bai faru ba. Itace dai na kawo nan ɗin gamu a ƙofar falo". Da mamaki Uncle Yousuf ya miƙe zumbur, Jallabiyarsa ya ɗauka ya zura dan har sun kwanta ma. Ko amsa tambayar lafiya da Aunty Saliha ke masa baiyi ba ya fice cikin sassarfa yana faɗin, "Ina zuwa". Shi da kansa ya buɗe motar ya leƙa, ƙirjinsa yay matuƙar bugawa, ɗagowa yay yana kallon Smart kallo na neman ƙarin bayani. Fahimtar hakan shi kuma ya sashi furzar da iska kaɗan. "Bayan tafiyata ta fita, jin hirarsu da ƙawarta a ɗazun ya sani sake dawowa, sai na samu zata fita shine na bita". "Ya Arrahaman harma ta sha kenan?". Uncle Yousuf ya faɗa cikin matsanancin damuwa. Tausayi sosai ya bama Smart, ya ɗan cije lips da faɗin, tana buƙatar saka ido sosai dan koba wannan halayyar bai dace ace mace kamarta tana fitar dare ba haka Alhaji". "Gaskiya ka faɗa Aliyu, na kuma gode sosai da ƙoƙarinka, duk laifin na yaya ne da bazai iya tsawata mata ba a duk sanda yaga zatai fitar, amma inasha ALLAH zan ɗauki mataki ni da kaina. Sai dai abin damuwar nima ɗin wani lokacin bana nan tunda ina tafiye-tafiye, da zaka min alfarmar dawowa kusa da mu da naso haka Aliyu, wlhy na yarda da kai, ina jinka tamkar ɗan uwana na jini, zan iya bar maka amanar Mawaddat batare da jin ko ɗar ba a zuciyata...." "Nagode sosai da wannan karamci Alhaji. Sai dai maganar dawowa nan kam abun ne mai wahala gareni, dan Abba ma bazai yarda ba balle kuma Ammah. Sannan nima inada ƙanne, kuma suna buƙatar saka ido duk da dai ba wayona ke tsaremin su ba ko jajircewa. ALLAH ne gafurin rahimun". Duk da Uncle Yousuf ya gamsu da bayanin nasa amma bai so hakan ba. Dan yana matuƙar buƙatarsa tare da su. Yaron nada wata nagarta mai matuƙar ƙayatarwa. Ga nutsuwa da cikar kamala tamkar ba talaka ba. Godiya yay masa tare da fiddo Lulu da ke sharɓan tana ɗan surutanta jefi-jefi a cikin barcin, wanda ba komai bane sai zagin Hon. Baita. Shi dai sallama yay masa zai wuce. Dakatar da shi yay da faɗin, "Kaga dare yayi yanzun. Kaje da motar gida dan abin hawa zai iya maka wahala". Kamar zai ce a'a sai kuma ya tuna maganar Uncle Yousuf ɗin gaskiya ce. Dan haka ya gyaɗa kansa tare da godiya. Saida ya ga ya shige ciki sannan shima ya shiga motar ya tayar ya bar gidan. Mubarak kawai ya samu a waje alamar dai shi ake jira, cikin washe baki Mubarak ɗin ya taso yana masa sannu da zuwa da shafa motar har ya kasheta ya fito yana lucking. "Yaya ka sayi mota ne?". Mubarak ɗin ya faɗa cikin zumuɗi. Karan farko yayma yaron ɗan murmushi. Cikin deep voice ɗin nan tashi da ta gaurayu da gajiyar son yin barci ya ce, "Daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi Mubarak? Ta mutane ce". Kamar an zarema Mubarak lakar jiki ya ɗan rausayar masa da kai gefe kawai. Daga haka suka shige ciki gidan shiru alamar duk anyi barci, sai wasu a ƴammatan dake waya da samarinsu, idan ka cire Asma'u da Maryam dako wayar Yayansu yama hanasu riƙewa sai ta Ammah suke ɗan ɗauka. Ɗaki kawai ya shige dan kwanciya yake matuƙar buƙata....... ★★★ ∆∆ ★★★ Da asuba Uncle Yousuf da kansa ya shiga ɗakin aunty Saliha da ya kai Lulu dan ita a ɗakinsa ta kwana ya tadata yin salla. Sam bata da nauyin barci, damma yau akwai na maye tare da ita, da alama kuma ya bugar da ita da yawa, dan ma tana da jini mai ƙarfi, da ace tana da saurin buguwa ma abubuwan da MM Atik Kumo ya harmutsa mata zata iya ƙara shanye yinin yau bata san inda kanta yake ba. Amma sai gashi Alhamdullah ita da sauƙi ya saketa. Zata fara masa gardama ya daka mata tsawa. A firgice ta tashi zaune zumbur jin Muryar Uncle Yousuf tana mazurai. Sosai take zazzaro idanun mamaki, shiko ya watsa mata harara da faɗin, "Karna dawo Massalaci na tadda baki tashi kinyi salla ba, zan matuƙar ɓata miki rai". Kai kawai ta gyaɗa masa mamaki fal ranta akan ganinta nan ɗin. Sai kuma abinda ya faru a daren jiya ya shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya. Cikin wani irin takaici da jin ƙuna a rai ta dafe kanta tana jan tsaki. A fili ta furta, "Sai nayi maganinka wlhy, illiterate kawai ko wa yace ya kawoni nan? To wai ubanwa ma ya nuna masa can ɗin da har ya bini?" Anya mutumin nan baida iskoki bisa kai ko? To inba mai iskoki ba itako mizata kirashi? A jiya dai tasan ya tashi a aiki ai da wuri ma. Amma kuma sai gashi ta gansa a inda babu wani mahaluki da yasan zataje. Kai wannan lamari da mamaki, dole ne tasan yanda ma akai ya bita can, kuma sai ta koya masa hankali akan shiga abinda bai shafesa ba. Nadiya ma sai ta shuka mata rashin mutuncin da bazata taɓa mantawa da shi ba da ga ita har su Hon. Baita ɗin. Jin ana neman idar da salla ya sata sauka a gadon dan tasan Uncle Yousuf babu wasa ne, ba ruwansa rufe ido zaiyi yaci mata uwa babu ruwansa da shirin da sukeyi. Wanka ta farayi sannan ta ɗauro towel Dan tana so ta sake wattsakewa. Batako zaman jiran tsanewar jikinta ba ta zura abayar Aunty Saliha. Sallar tai babu wani nutsuwar a cikinta, tana zaune a inda ta idar tana kulla mai fishseta Uncle Yousuf ya leƙo, gaidashi tayi, sama-sama ya amsa mata duk da yaga yanda ta koma kalar tausayi. Ba yanzu ya shirya mata magana ba dan haka yay ficewarsa. Ji Lulu tai gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi, sam bata ƙaunar fushin Uncle You a rayuwarta, har gara ma Daddy yay fushi da ita dan shi tasan abu ɗaya zata masa ya rikice ya dawo lallaɓata. Kuka take so tayi, sai dai ita mai juriya ce da shegen taurin kai, ba a komai take iya kuka ba komai ƙololuwar ɓacin rai ko tashin hankali da zata tsinta kanta a ciki. A karan farko taji kunyar haɗuwa da mutanen gidan, tashi tai jikinta duk babu ƙarfi, bata ko nemi jakarta da takalminta ba ta fice cikin sanɗa, taji daɗin rashin samun kowa kuwa, da sauri tabi ta ƙofar kitchen ta baya. Tunda ta fito bayin fulawoyi ke mata kallon mamaki da ga nesa, dan shi dai bai san sanda tazo gidan ba kam, ƴar tsawar da tai masa ta sakashi dawowa a hayyacinsa. "Wawa mi kake kallo ne? Dilla buɗe min ƙofa!!". Jikinsa har kakkarwa yake duk da kuwa a girme ma zai iya girmarta shima, kuma ba aikinsa bane, ta watsa masa harara lokacin da take ficewa tare da jan tsaki. Yasan laifinsa dan haka ma baiji haushi ba. Mawaddat ta tsani taga ana kallonta, gashi kuma yau shi ta kamasa dumu-dumu. Ya san dai bala'i bai ƙare ba, dan duk randa ta dawo gidan zai sha masifa. Ƙila ma harda zagin ƙare dangi za'a haɗa masa. Da ƙafa ta isa gida, kasancewar garin da sauran duhu ga ɗan sanyi-sanyin da aka fara na lokacinsa. Acan ma sai da maigadinsu ya samu rabonsa na zagi. Dan shima dai galala yay yana mata kallon mamaki. Amma tunda ta fara danna masa na maguzawa sai ya nutsu ya koma gaisheta a daburce. Bata amsa ba tai shigewarta tana jan tsaki..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 ??𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣2️⃣ ........Anan kam tasan basa barin ƙofa a buɗe, dan haka ta zagaya ta window ɗin ɗakin Iya Tabawa. Tana kuwa zaune tana addu'oi tun bayan idar da salla. Ba yau Lulu ta fara mata haka ba, shiyyasa koda ta kirata bata firgita ba. Sai ma miƙewa da tai a ɗan ɗarare. A kausashe Lulun ta ce, "Dalla Malama ki buɗen ƙofa kin wani tsaya kallo na". Haƙuri Iya Tabawa ta bata ranta fal wasi-wasi. Zuciyarta ta fara raya mata ko dai yawon banza Lulu ke fita ne, tunda ba taɓa ganinta cikin maye tai ba. A ƙasar Hausa kam mafi yawan al'umma sukan fassara yawon dare na ɗiya mace da tazubar ne kawai, da wahala hasashensu ya wuce haka har su hango wasu abubuwa masu illa a rayuwar ƴaƴanmu mata bawai zina kawai ba. Sun manta a rashin ji duk abinda namiji yasa kansa iyawa wasu matan kan kwatantashi ba wai sai iskanci kawai ba. (Ya rabbi ka shiryar damu da zuri'armu baki ɗaya). Tana shiga ɗakinta a saman katafaren gadonta ta zube tana mai sauke numfashi, lamo tai cikin lallausan bedsheet da duvet ɗin gadon masu ltaushin tsiya da ƙamshi. Tunanin matakin da zata ɗauka akan tsageran driver ɗinta takeyi, da su Hon. Nakowa, sai dai kuma barcin da bai gama fita idonta ba ne yaci ƙarfinta...... ★Kasancewar alerm data saita ƙarfe takwas ta farka badan barcin ya isheta ba. Sai dan tana da shari'a mai zafi a yau ɗin da zata gudanar wadda a yau ɗin take fatan alƙali ya yanke hukuncinta. Cikin rashin kuzari ta tashi ta faɗa toilet, sai da ta gamsu da gyara jikin nata a fannin wanka sannan ta fito. Shiri tayi tsaf da ita cikin suit na mata kalar baby pink, rigar cikinta fara. Dan ƙyau kam tayi ƙyau, ga shegun takalmanta masu dogayen dudduge ɗin nan da tsabar ƙwarewa a sakasu yasa ko gargada batayi a tafiya da su. Yau dai anyi abun arziƙin saka ƙaramin baby hijab fari da yay mata ƙyau sosai, sai dai iyakarsa kafaɗarta dan ƙaramine. Ƙamshin nata na fitar hankali ta bulbula a jiki har ita da kanta tanajin ƙamshin na hawa mata kai, sai dai haka take buƙatarsa. Cikin takun nan nata na isa da gadara ta fito, illahirin jikin nan na motsa kansa kamar wata tarwaɗa a ruwa. Mubeen kawai da Daddy ta samu a dining suna breakfast, sai Mommy tana tsaye a tsakkiyarsu da alama abincin take haɗa musu. "Good morning Daddy & Mommy!". Ta faɗa kanta tsaye babu wani alamar respect gareta matsayinsu na iyayenta. Musamman ma Daddy dake amsa sunan mahaifi. Kowa dai yasan yanda ƴaƴa ke shakkar iyayensu maza fiye da mata a ƙasar hausa. Mommy dai kallonta kawai tai ta girgiza kanta. Shiko Daddy fuskarsa a washe da murmushi, duk da dai kamar alamunsa na nuna yana cikin damuwa ne yake dannewa. "Morning sweet heart. Kin tashi lafiya? Yaya ƙarfin jiki". "Komai normal Daddy". Ta faɗa tana ɗaukar shayin gabansa da yake sha ta kurɓa da ga tsayen da take. Da kallo ya bita har yanzu da murmushi a fuskarsa. "Babyna zauna mana kisha ba ƙyau shan abu da ga tsaye ai". "No Daddy, hakan ma it's ok for me. Ina sauri ne 9:30 inada Shari'a". "Allah yay miki albarka, ya kare munke ga duk wani sharrin maƙiya na gida dana waje". "Amin sweet Papa na". Sarai Mommy ta fahimci harda ita a addu'ar tasu. Hakama Mubeen. Dan tuni sun gane abinda mahaifin nasu kema Mommy akan ƴar uwarsu. Sai dai ko sunce zasu ɗauki mataki hanasu yin hakan Mommyn take yi. Babu yanda suka iya dole suke haƙura. Amma badan jajircewarta a kansu ba ba ƙaramar tsanar Lulu sukeji ba a rai. Wani lokacin ma hatta shi Daddy ɗin takaici yake basu shiyyasa su ƴan biyu sam basu son zaman gidan. Harta ɗan sha shayin na Daddy kusan sau bakwai ta ajiye Mubeen bai mata magana ba itama batai masan ba. Batama nuna tasan da zamansa a wajen ba kamar yanda shima ya nuna. Tana shirin sauka a ɗan steps ɗin hawa dining ɗin Daddy ya dakawa Mubeen ɗin tsawa. "Kai dan uwarka ita ɗin sa'arka ce da bazaka gaishe ta ba?!". Kallon Daddy ɗin Mubeen keyi zuciyarsa a bushe, sai kuma yaja numfashi mai nuna zuciyarsa na yunƙurowa, sai dai kallon gargaɗi da Mommy ke masa ya hanashi cewa komai da ga tarin abubuwan faɗar da ke cikin bakinsa game da mahaifin nasu. A hankali ya furta "Daddy kayi haƙuri" kawai yaja bakinsa ya tsuke. Tsaki daddy yaja dai-dai Lulu na ficewa a falon gaba ɗaya. Bata jira jin abinda Daddyn ke shirin faɗa ba. Karo na farko a rayuwarta taji kamar babu daɗi akan abinda Daddy ɗin kema ƴan uwanta saboda ita. Har ga ALLAH tana ƙaunar ƴan uwanta, hasalima bata haɗa son su da komai ba. Hatta su Yaya Hassan batajin daɗin rayuwar doya da manjan da ke a tsakaninsu. Dan ko gidan su ƴan biyun sukazo basa kulata bata kulasu, saboda sun riƙe abubuwan da mahaifiyarsu ta fuskanta da ga mahaifinsu dalilin mahaifiyarta da ita kanta. Goshinta da yay mata nauyi saboda abinda ta sha jiya bai gama sakinta da ƙyau ba ta ɗan shafo tana furzar da iska. Ba ƴan uwanta kaɗai ba hatta Mommy tana jin ƙaunarta, dan kallon uwa take mata a zahiri da baɗinin rayuwa. Ta sani duk wanda yasan gidansu ma ya sani Mommy bata taɓa cutar da rayuwarta ba koda da harara, idan dai tayi laifi yanda take ma yaranta faɗa itama haka take mata. Shiyyasa duk rashin mutuncinta har abada bazata taɓa kwatantashi ga Mommy ɗin ba. Musamman ma idan ta tuna nasihar da Kakanta Alh. Sufi Garko kanyi mata a duk sanda taje garesa game da Mommy ɗin da halaccinta ga zamantakewarta da mahaifiyarta. Duk da dai itafa har yanzu bata taba jin labarin ainahin zaman da Mamanta tayi da Mommy ɗin ba...... Gaisuwar da ma'aikatan gidan ke mata ce ta katse mata tunani, batare data kalli ko guda a cikinsu ba take wucewarta kawai da takun nan nata na yauƙi da isa. Tana gab da isa motar da take buƙatar hawa idanunta suka sauka akan Smart da ke zaune wajen maigadi kamar kullum hankalinsa a waya yana buga game ɗin ball da yake matuƙar bege. Sake tamke fuska tai da ɗauke kanta, abinda ya faru jiya ne ya shiga mata kaikawo cikin kai. Sosai taji ɓacin rai ya sake baibayeta da takaicin su Nadiya da suke son jamata rainin nan wajen wannan shashashan, ta jima tana shaye-shaye, amma duk wanda yay mata sani na haƙiƙa bai san wannan halayyar tata ba, a koda yaushe cikin ƙoƙarin binne sirrinta take, amma sai gashi a haɗuwarta da mutumin da tafi tsana fiye da kowa a duniya shi ya ganta a yanayin. Ƙwafa tai da balla masa harara, cikin borin kunya ta cilla masa key da sake jan tsaki. Idanunsa da ke nuna alamun barci bai ishesa ba ya ɗan lumshe ya sake buɗewa, batare da ya kalleta ba ya miƙe zuwa gaban Motar data ɗakkoma key ya buɗe mata bayan, sai da ta shiga ya maida ya rufe sannan ya koma mazaunin driver, motace mai tsadar gaske da ɗaukar hankali, kasancewarta ƴar gatan gidan hatta Daddy tafi yawan motoci. Dan motarta biyar kuma duk ƙosassu, sai ƙarama ɗaya da sha'awa kawai ya sata matsawa Uncle ɗinta Khamil ɗan uwan mahaifiyarta dake Abuja saya mata ita. Dai-dai suna barin kan titin layin nasu ya miƙa mata handbag ɗinta ta jiya da key ɗin mota, a hankali ta ɗago da ga duba takardun da takeyi ta ɗan sake hararsa sannan ta kalla kayan a yamutse. Murya a dake sai dai acan ƙasan maƙoshi ta furta, "Waya gayyaceka inda nake jiya?". Sarai ya jita, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita ya haura kan babban titin bayan motar da ya dakatama ta shige layin da ya fito. "Malam da kai nake yi". Ta sake faɗa cikin zafin rai da borin kunya. Karan farko ya ɗan ɗago idanu ta cikin mirror ya dubeta. Ido suka haɗa, tai saurin kauda nata zuziyarta na tsirgawa. Itafa komi za'ai ayi amma kar ya kalleta da wannan shegun idanun na macizai (kamar yanda ta raɗa musu😂🥱). Yanda tai ɗin sai ya so bashi dariya, amma sai baiyi ba ya ɗan saki murmushin gefen baki da maida hankalinsa ga titi cikin salon lumshe idanun nasa kamar yasan suke razanata, babu alamar zai bata amsar da take buƙatar son ji. Ba ƙaramin takaicinsa bane ya kume Lulu, ga wayarta ta isheta da ruri. Nadiya ce keta faman kiranta tun ɗazun, sai dai taƙi ɗagawa dan tai alƙawarin sai ta koyama ƙawar tata mafi kusanci hankali. Tsaki taja a karo na babu adadi, ta fisgi wayar da ke kan rigarta ta lauyoyi ta kashe tare da sake cillar da ita kan rigar da ke a gefenta. Haushin Nadiyar dana sharetan da yay ta tattaro gaba ɗaya ta nufesa da shi. "Wai kai mika ɗauki kanka ne da har ina maka magana kana wani cika da batsewa?". Yanda tai maganar muryarta har tana zuga kamar wadda kuka ke son yunƙuromawa sai dai ƙarfin halinta na dannesa ya sashi sake dubanta a karo na biyu ta cikin mirrorn. Sake maida kansa yay ga titin sai kuma ya ɗan muskuta zamansa da furzar da iska. Ƙasa-ƙasa na rashin kuzarin da kasala irin na wanda barcin bai ishesa ba cikin deep voice ɗin nan ta shi ya ce, "Mi kike son sani?". Wata irin kasala muryar tasa ta nema saukar mata saboda yanda yay maganar cikin sanyi da tausasa lafazi, sai dai cikin yaƙi da kai da nuna juriya irin ta masifaffun mutane ta watsa masa kallon banza da yin ƙwafa tana maida kanta ga takardun da take dubawar. Kamar bazata ce komai ba sai kuma bayan kusan minti ɗaya ta ce.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣3️⃣ ........."Waya aike ka inda ka sameni jiya? Miye ma dalilinka na bina?". Idanu ya lumshe tare da buɗewa a lokaci guda. Kamar yanda yay magana ɗazun a tausashe yanzu ma haka yayi. "Baki so asan kina aikata abinda na gano ɗin ne?". "Kai ɗin banza da zanji ina son ɓoye maka abu. Shiga abinda ban saka ka bane ya sa nake neman ba'asi dan bana son shiga sharo. Idan kuma kace zaka cigaba da shiga min hanci wlhy zan saka ka dana sani kai da duk wanda ma yake maka kallon arziki. Tsabar kai ɗan haɗin masifa ne ka ɗauke ni ka kai gidan Uncle you.., wlhy kasan mima zaka faɗa masa, in ba haka ba sai naje har gidanku kaima na maka ƙullin da har gaban abada baka isa ka kwancesa ba ɗan sa ido kawai. Idan kuma kaji ƙarya mu zuba ni da kai mai shishshigin tsiya, kai a dole sai ka shiga jikin iyayena dan maular tsiya irin ta talaka". (Maula! Talaka!) Zuciyarsa ta maimaita cikin jin ƙunar kalmomin. Kamar zai yi magana sai kuma ya haɗiye abinsa dan ya fahimci al'amarinta na buƙatar sai da uzuri, idan yace zai biye mata sai ma su zama ɗaya. Yanda bata sake magana ba tana ta faman duba takardun nata shima bai sake kallon inda take ba, sai dai ƙamshin turaren data bulbula ya addabesa har yana hawar masa kai kamar yanda itama nashi ke cizon can ƙasan zuciyarta. A cikin tsare-tsaren da Uncle Yousuf ya bashi nata ya sashi sanin inda zasu je a yanzu ɗin, dan haka kai tsaye babbar kotun da muke kira da (kotun ALLAH ya isa) dake a jiha ya nufa. Tamkar ba safiya ba harabar court ɗin cike da mutane, hancin motar na kunna kai cikin gate ɗin wasu gungun ƴan jarida suka yomusu caa, isowar securitys da ke son hana ƴan jaridar isowa garesu ya ɗan maido hankalin mutane kan motar suma. Kafin ya gama kashe motar har an buɗe mata. Fuska a yamutse da ɗan jan tsoki ta kalla harabar court ɗin. Wanda ya buɗe matan ta miƙama tarkacen hanunta tare da rigarsu ta lauyoyi. Ita kuma ta ɗauki handbag ɗinta bayan ta toshe fuska da wani shegen gilashi mai tsananin ƙyau ta haɗa da hular, dai-dai tana ficewa ta balla masa harara da faɗin, "Saura nan ma kace zaka biyoni kaga yanda zan baka mamaki". Da kallo kawai ya bita, sai kuma ya ɗan furzar da iska ransa fal mamakin yanda bata gajiya da masifa. Da ga can ƙasan ransa kuma yanda ake ta bata wani girma da kariya da ga security ɗin da zallon da ƴan jarida ke faman yi na son isowa gareta ya ƙara ɗaure masa kai da jin takaicin da sun san wacece a zahirinta da ko kallon mutuntawa bata cancanta a garesu ba. Bai iya ɗauke idanunsa garesu ba dan takaici har suka shige wata ƙofa ba ainahin ta Court ɗin ba. A take ya ga gurin ya sake ribcaɓewa, mutane sai faman ɗura kai suke cikin court ɗin. Maganar wasu samari da ke wuce motar cikin ƙaucin shiga kotun ta ɗan ja hankalinsa. Na farko mai riƙe da camara ke faɗin, "Yaufa akwai ƙura, dan na tabbatar barrister Mawaddat Jiƙamshi ba ƙaramin sabon shiri tayo ba duba da yanda Barrister Marafa ya nema zubar da ita a wancan zaman. Kasan fa ita bata taɓa bari a kaita ƙasa musamman a kan irin wannan case ɗin na fyaɗe, ga shi tasan aikinta lawyers ƴan uwanta da yawa har tsoron karawa suke da ita, dan ita ko waye ma ubanka akan fyaɗe sai tayi kutu-kutun turaka jail dan haka kullum ita bata kare mai laifi sai wanda aka zalunta musamman ƴan uwanta mat......." Bai ƙarasa jin abinda saurayin ke son faɗa ba dan sun masa nisa. Da farko baiyi niyyar shiga wajen ba, sai dai saboda gargaɗinta ya ƙudiri shigar dan yaga mizata iya masan. Ƙoƙarin fitowa yay a motar kira ya shigo wayarsa. Kamar zai share sai kuma ya cirota da ga aljihu. Ƙanwarsa ce mai bimasa Hawwah dake auren abokinsa. Ɗagawa yay, sai dai yana kaiwa kunnesa yay saurin janye wayar yana mai lumshe idanunsa. Buɗesu yay a hankali zuciyarsa na wani irin zallo. Cikin motar ya koma tare da sake kiranta. Ringing ɗaya ta ɗauka. Cikin matsanancin kuka ta ke faɗin, "Yaya dan ALLAH ka barni na taho gida. Wlhy na gaji da wannan rayuwar bazan iya ba. Inko ba haka ba wataran sai mahaifiyar Abban Nasreen ta kasheni a gidan nan...." Iska ya ɗan furzar mai ɗaci, tare da faɗin, "Miya kuma faruwa?". Sake fashe masa tai da kuka, da ƙyar ta iya faɗin, "Mai fa da nake suya airish ma Nasreen da zata wuce school ta kusa kwaramin yau a jiki Yaya. Ban san wane irin rashin ƙauna matar nan take min ba. Wlhy bazata taɓa canja halinta ba nima na gaji da haƙuri da ita." "Shi ina Sa'id ɗin yake?". "Yaya yana fa a gidan, gashi can ya jata wai yana bata haƙuri saboda ni ba'a san ciwona ba. Yanzu Yaya data sameni da man nan haka zai tsallakeni ya bita ke nan...." "Kinga ya isa. Ki jirani gani nan zuwa gidan yanzu". Da ga haka ya yanke wayar batare da ya jira abinda zata ce ba. Fitowa yay a motar ya kulle. Da ƙafa ya fita a habar court ɗin da ta yi tsittt alamar an fara shari'ar ko za'a fara. Yana fitowa a gate ɗin ya samu napep zuwa Daurawa anguwar da gidan ƙanwar tasa take. Kasancewar safiya ce basu wani samu matsala ba, dan haka suka iso da wuri. Bayan ya biya mai napep ɗin maimakon shiga gidan kai tsaye ko yin knocking sai ya ɗaga waya yay kiran abokin nasa Sa'id Ibrahim da sukai karatu a jami'a tare. Yanda Sa'id ɗin ya ɗaga wayar ta isa tabbatar da a rikice yake. Dan duk ya daburce sallamar ma da in ina yayi ta. Sai kuma ya shiga kame-kamen gaisuwa. Katsesa Smart ɗin yay da faɗin, "Gani a ƙofar gidanka ka turo min Hawwah zamu wuce gida". "G...g...gida kuma Mawashi? Miya faru ka...k...kake wannan maganar haka? Ko itace ta kira ka ta faɗ......" "Sa'id!!". Ya dakatar da shi a harzuƙe. Sake tsurewa Sa'id ɗin yayi dan yasan halin abokin nasa sarai. Bai da yawan magana ko hayaniya, dan bai taɓa ji ko ganin abokin faɗan Smart Mawashi ba a rayuwa. Amma shi kaifi ɗaya ne akan komai da kowa. Duk yanda yake da kai bai yarda ka latsashi ba ko gasu abokai. Yanda ya rikice ɗin sai ya harzuƙa ran mahaifiyarsa da ta hanashi fita duba matarsa. Dan ta rantse ko bakin ƙofa yaje domin Hawwah ɗin sai ta tsine masa. Cikin masifa ta wafce wayar, kunnenta ta kai da faɗin, "To ɗan mulkin mallaka wai shin nikam ko kai ne ka haifa min Sa'id ne ban sani ba? To bazai zo ɗin ba, nace bazai zo ba idan ka isa kai duk abinda kake jin zaka iyayi, ko ita ƙanwar taka autar mata ce da in ya rabu da ita zai kasa cigaba da rayuwa har ya auro wasu huɗun. Aikin wofi kawai anga kuɗi an nanema yaro na". Har tayi ta gama bai ce uffan ba, sai da yaji tayi shiru ya yanke kiran. Yanda yake huci zai baka tabbacin sanin ran ƴan maza ya kai ƙololuwar ɓaci. Number Hawwah yay kira, bugu ɗaya ta ɗaga. Kafin tace komai ya ce, "Ɗakko mayafinki ki sameni waje". Ya yanke kiran. Minti shida kuwa bata gama cika ba sai ga Hawwah da ƙaton akwati da Nasreen ƴar shekara huɗu biye da ita. Tana ganinsa ta cilla da gudu garesa tana faɗin, "Oyoyo Uncle". Kaɗan ya saki murmushi, tare da duƙawa ya ɗauketa ita da school bag ɗin da ke goye a bayanta alamar an gama mata shirin makaranta ne. Sau ɗaya ya kalla ƙanwar tasa ya kauda kansa. Batare da yace komai ba ya amshi akwatin hanunta yay gaba tabi bayansa. Napep ya tare musu suka shiga, Nasreen nata zuba masa surutu dan yarinyar ko akku haka ta ganta ta bari kamar ƴar ƙwa-ƙwa akwai wayon jaraba. Dan bakinta ya girmi shekarunta. Sai da ya kaisu har gida sai dai bai shiga ba yace taje ta jirasa zai je ya dawo. Bata musa ba ta fita, shi kuma yace ma mai napep ya juya da shi babban kotun dake jaha. Ya samu har an fito da ga shari'ar, yanda harabar kotun ke'a harmutse da ƙayataccen murmushin da ya hango a fuskar Lulu ya sashi tsira mata idanunsa. Tsaye take a tsakkiyar lauyoyi ƴan uwanta wanda da alama duk ƴan ɓangare ɗaya ne a shari'ar, dan yanda fuskokinsu ke a washe kamar ita saɓanin waɗanda ke gefensu kaɗan zai baka tabbacin hakan. Ƴan jaridar da suka zagayesu ya sashi daina iya hangota, ɗauke kansa yay tare da buɗe motar ya shiga, a kallo ɗaya zaka fahimci damuwar dake zagaye da fuskarsa, dan babu abinda ke faman masa kai kawo sai batun ƙanwarsa Hawwah, shi shaida ne Sa'id na matuƙar son Hawwah, sai dai matsalar mahaifiyarsa da tun farko ta nuna bata son auren saboda ƴar ƙanwarta da taso ya aura shi kuma yaƙi tsayawar mahaifinsa ta sa ta janye ta amince ya auri Hawwah, sai dai tunda take gidan mahaifiyar tasa ke nuna mata hantara da ƙyara musamman idan Alh. Ibrahim mahaifin Sa'id ɗin baya gari. Tasha marin Hawwah ɗin dayi mata abubuwa masu cin zuciya shi yana zuwa ya sasanta bada sanin iyayensu ba. Sai dai a wannan karon ya fahimci dole ne fa a tauna tsakkuwa dan aya taji tsoro. Dan tsohuwar na buƙatar sanin Hawwah nada gatan iyaye da dangi itama, sannan dukiya ba itace rayuwa ba kawai akwai muhimman abubuwa da suka fita a zamantakewar rayuwa. Kai dai kai fatan kawai ALLAH ya rufa maka asiri kafi ƙarfin yau da gobenka. Idan kuma ya azurtaka da dukiyar ka bida ita ta hanyar da kai a karan kanka zakai alfahari da kanka watarana da zaka amsa tambaya akan dukiyar kwabo bayan kwabo........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨??𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣4️⃣ .........Gigitaccen knocking ɗin da akai ma glass ɗin motar ne ya sashi dawowa hayyacinsa. A hankali ya buɗe idanunsa da sukai mugun kaɗawar ɓacin rai ya sauke a kanta. Harara ta balla masa da juyayyun idanun nan nata da shaye-shaye ya gama canjawa yanayin kallo. "Kai anya kuwa ka taɓa shiga ajin makaranta? Dan na fahimci baka san aikin ka ba, malalacin banza kawai ka zauna kanama mutane tunanin iska a mota, ko an gaya maka a banza ake mallakar irin motar har ai zaman tunani a cikinta Mtsowww!! Baƙauye". Ta buɗe motar a fusace ta shige tare da rufe murfin da ƙarfi. Fitowar da yay niyyar yi buɗe mata ya fasa, batare da ya tanka mata ba kamar yanda ya saba yayma motar key. Bata sake bi takansa ba ta maida hankalinta a lap-top itama, yayinda shi kuma yake tafiya a nutsensa. Sunyi nisa sosai batare da ko sau ɗaya ta ɗago taga ina suke nufa ba, dan ita duk zatonta hanyar office ɗinta ya nufa da ita tunda Uncle Yousuf yace mata ya bashi komai nata a rubuce. Jinfa tafiya na neman ƙin ƙarewa ya sata ɗagowa. Da sauri ta ƙara ware Lulu ayes ɗinta tana kallon inda zata iya rantsewa bata taɓa sani ba ma, dan ita dai kusan yawonta wajen Kano a jirgi ne. Gabanta ne ya faɗi, zuciyarta ta shiga mata kai-kawon ko yayi kidnapping ɗinta ne? Amma sai ta dake a masife ta ce, "Kai malam mi kake ƙullawa ne? ina ne kake shirin kaini nan?". Shiru kamar bazai tanka mata ba, dan har ya kunnata ta ƙara ƙarfin hucinta. Sai kuma cike da rainin wayo ya bata amsa cikin halin ko'in kula da cewa "Asibiti ganin likitan ƙwaƙwalwa". dai-dai yana ƙoƙarin shiga ƙaton gate ɗin asibitin na dawanau. "What?! Wai nice ka kawo duba masu taɓin ƙwaƙwalwa kake nufi ko mi?". Tana sake ware idanunta kan rubutun saman ƙaton ginin inda yay parking. Bai tanka mata ba har sai da ya kammala dai-daita motar a gaban wajen. Kasheta yay gaba ɗaya tare da kai idanunsa kanta ta cikin mirror. Kallon nasa kuwa take itama dan tsabar takaici ya hanata iya sake cemasa komai amsar dalilin zuwansu kawai take buƙata da ga garesa. "Kinada kati anan ne ko yau za'a fara yankar miki? Dan naga kamar ƙwayar da kika sha jiyan bata kammala sakinki ba". Ya faɗa a dakensa. "Kai! Wai dama ni kake nufin inada taɓin ƙwaƙwalwar ma kenan?". Idanunsa da take kira na macizai ya wara mata cike da salon sake tura mata takaici. Sai kawai taji ƙwalla na neman cika mata idanu. Tunda take a duniya bata ko tuna an taɓa wulaƙantata makamancin yau ba, ba zuciyarta ba hatta numfashinta fita yake da sassarfa. Wai ita wannan ya kawo asibiti, asibitin ma na masu taɓin hankali. Babu abinda take ji a ranta kamar ta haɗama ƙyaƙyƙyawar fuskarsa jini da majina da maruka fiye da yanda ya yagata, ta dunƙule hannunta amma hannun ya gagara ɗaguwar aikatawa. Maimakon ma hakan kanta kawai ta dafe dan jin zuciyarta na barazanar tsagewa biyu. Batajin idan ta sake kai mintina sama da uku a motar nan bata shaƙe mutumin nan ya bar duniya ba. A wani irin harzuƙe ta bankaɗe murfin motar ta fita, inda yake zaune mazaunin driver ta buɗe. Shi kansa bai taɓa ganin ɓacin rai tattare da ita irin yau ba, dan tsabar masifa fuskarta har jaja takeyi.... "Fitar min a mota!!". Ta faɗa da ƙyar muryarta har rawa takeyi. Cikin deep voice ɗin nan tasa da sake dakewa ya ce, "Maizasa na fita bayan akan aikina nak....." "Wlhy zan kashe fuskarka da mari idan baka fitar min a mota ba tunda ban haɗa kuɗi da kai na saya ba!!". Ta sake faɗa a wani yanayin da muryarta ke fita da cracking. Ya gama sanin ta kai ƙololuwar fusatar da yake buƙata, dan haka cikin taɓe baki ya fice yana wani murmushin da ke sake tafasa mata ruhinta shiko yana sake ƙayatar da kwarjininsa. "Ka rubuta ka ajiye sai na wulaƙanta rayuwarka a mizanin mafi munin wulaƙanci". Ta faɗa dai-dai tana fisgar murfin motar bammm! Ta rufe. Kamar yanda ta saba a guje ta fice a asibitin, dan Lulu akwai iya tuƙin ganganci da wauta balle yau da ya zama an kunnata ne, shiyyasa Daddy yafi son driver ya jata a mota. Da gaske tuƙi take irin na wauta da isa, har takai wasu drivers ɗin na zaginta idan tai wani abun cike da gadara. Tana kan round about ɗin da zata ɗauki titin office ɗinsu ta kusa haɗa accident sakamakon neman shallakewar ƙin tsayama traffic light data nema yi. A fusace drivern data dakarma mota ya fito, itako babu alamar ko ɗar a tare da ita ta ƙara sautin kiɗan wakar Shakira da ke tashi a motar, dan tana matuƙar son waƙoƙin mawakiyar, shiyyasa bata da wakar data bama amanna kamar waƙoƙinta musamman idan tana cikin ɓacin rai irin haka. "Ke ƴar uban wacece da zaki da kar min mota ki cigaba da zama a ciki kamar bakiyi ko mai b........" ya gagara ƙarasawa saboda tozali da abinda baiyi zato ko tsammanin gani ba. "Ni ƴar gidan ubanka ce!!". Lulu da dama take a harzuƙe jira take a taɓata ta fashe ta bashi amsa a fusace itama. Kansa ya ɗan dafe da wani irin salo yana juya jikinsa kaɗan, sai kuma ya sake jiyowa gareta da ɗan kuzari ya ranƙwafo a motar. "Oh Baby dama ke ce? Please am so sorry". Harara ta balla masa tare da jan sirrin tsaki ta ɗauke kanta. Zai sake magana ta ɗaga masa hannu, tare da ɗakko bandir na sabbin dubu ta jefa masa a harzuƙe. "Ko basu kake buƙata ba dama?". Siririyar dariya ya saki mai ƙayatarwa. "Mai sunan gwaggo kenan, ni bance ina buƙata ba, sai dai idan kin bani ƙyauta ne zanso haka. Koba komai ƙyauta da ga masoyiya zuwa masoyi ai abin alfahari ne ko". "Tajuddeen bani hanya na wuce kafin kaja na sauke maka abinda ke kaina wlhy!! Dan inada abunyi". "Zan iya ɗaukar ko miye da ga kanki ko mi nauyinsa, sannan nima inada abunyi dan haka ma kika ganni da farar safiyar nan akan titi, duk da dai naci ribar fitar kodan ganinki da nayi". Maimakon amsa masa sai taja tsaki, tare da yin sama da glass ɗin motar. Da sauri yaja da baya dan neman takashi take yi. Cikin murmushi da cizar lips ya duƙa ya ɗauki kuɗin nan data jefesa da su a ƙasa yana kaisu hancinsa dan tuni ƙamshin turarenta mai ƙarfi ya mamaye su. Duk abinda ke faruwa akan idanun Smart ne da ke cikin napep kamar sauran mutane, dan tana baro asibitin yay murmushi, sai dai da sauri shima ya fito saboda ganin yanda ta fisgi motar cike da ganganci ya kuma san bata san hanya ba sosai, baya fata wani abu ya sameta a dalilinsa, cikin sa'a ya samu napep, dan haka yace masa su bita, sai dai tuni ta musu fintinkau saboda gudun da take zubawa dan har ta ɓace musu, sai gashi kuma sun haɗu a traffic light ɗin. Ƴar hayaniyace ta fara tashi, wasu na zagin Lulu wasu najin haushin Tajuddeen da ya taso gigigi ya kuma koma yay sakwat, daka gansa dai shima kasan akwai nerar balle ace saboda kuɗin data watso masa ne. Sai dai wasu sun fahimci ma dai kamar sun san juna ne shiyyasa, amma hakan bai hana ƙananun maganganun ba dai. Sirrin tsakin da bai shirya bane ya fita a bakinsa a karo na farko. Yana ƙoƙarin ɗauke kansa da yima mai napep maganar su juya titin anguwarsu dan ya fasa bin bayanta da yay niyya idon Tajuddeen ya sauka a kansa. Murmushi ya sakar masa da ɗaga masa hannu, hakan yasa shi dole fitowa fuskarsa a ɗan sake shima ya miƙa masa hannu suka gaisa. "Ya naga yau tafiyar taku daban-daban? Koda yake da alama yau ogar taka fitina take ji". Tajuddeen ya faɗa da alamar ƴar damuwa, dan harga ALLAH yana matuƙar son Lulu. A karo na farko Smart ya ɗan saki murmushi mai sanyi. Cikin nutsuwar nan tasa, sai dai a can ƙasan maƙoshi ya furta "Ita dama kullum a cikin rigimar take ai. Tunda ta tsere mana ma zan juya gida ne kawai". "A'a ba'ayi haka ba. Bari mu ƙarasa dan office ɗin nasu kusa yake damu". Badan Smart yaso ba Tajuddeen ya biya mai napep da ya ɗakkosa, shi kuma suka shiga motarsa a tare. Tunda suka bar wajen Tajuddeen ɗin ke jansa da hira. Shi dai nashi murmushi ne kawai bai iya cewa komai. Tajuddeen ya fahimci Smart bamai yawan magana bane, sai dai sam baza'a taɓa kiransa miskili ba. Kawai dai shiru-shiru ne shi bai cika hayaniya bane. Tafiya kaɗan ta kawosu, guri ne mai ƙyawun gaske da ɗan girma dan gaskiya ya tsaru. Tajuddeen yaso su shiga tare da Smart amma yaƙi ya ce ya barsa anan wajen, badan yaso hakan ba ya barsa nan jikin motar shi kuma ya shige. Ya ɗan gaisa da tsirarun ma'aikatan da suke kai kawo saboda sun sanshi dan lokaci zuwa lokaci yakan ɗan zo wajen Lulun, da ga haka ya nufi lifter zuwa 3floor. Offices ne kusan goma a wajen, a office na kusan bakwai, a hankali idanusa suka sauka kan rubutun saman da aka rubuta. *_Barrister Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi_*. Kai tsaye Tajuddeen ya shige babu wani neman excuse, ƙaramin falo ne dan table ɗin sakatariyarta ne kawai sai kujeru uku 3sitter da 1sitters guda biyu da table a tsakkiyarsu. Da ga ɗan gefe kaɗan water dispenser ce mai ƙyau sai tv da ke maƙale acan sama. Glass ne ya raba wajen da office ɗin ta, dan haka ya iya hango yanda take ma wata dake tsaye gaban table ɗin ta masifa, duk da bajin mi take faɗa yake ba yanayin yanda take karkaɗa hannu ya bashi tabbacin hakan. Da sauri Tajuddeen ya tura ƙofar ya shiga, a tare Lulu da sakatariyarta da ke shan masifa dan a kanta ta hau juye takaicin Smart suka juyo........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣5️⃣ ........Fuska Lulun ta sake tsukewa, yayinda sakatariyar ta risina tana gaishesa dan tasan ko wanene tunda ba yau ya fara zuwa ba. "Jeki abunki". Ya cema sakatiyar yana kaiwa zaune. Sakatariyar ta ɗan kalli Lulu a tsorace, sai kuma ta dubesa cikin girgiza kai kamar zatai kuka. Shima Lulun da ke faman haɗa takardun gabanta ya kalla, sai kuma yay ɗan murmushi. "Madam please taje?". Harara ta ɗago ta balla masa, ta sake maida kanta ga abinda take yi. Ƴar ƙaramar dariya ya ƙarayi mai fidda haƙora, tare da yima sakatariyar nuni da hannu alamar taje. Da sauri ta fice har tana neman cin tuntuɓe. Idanunsa da ke ma sakatariyar kallon ƙasa-ƙasa ya janye ya maida ga Lulu... "Miyasa ka biyoni?". Ta katse maganar da yay yinƙurin mata. "Idan masoyi ya biyo masoyiyarsa laifi ne Mawaddat. Please ki daina wahal damu haka mana, ko so kike sai na kai ƙasa ne?". "Bani da matsala da kaiwarka ƙasa Tajuddeen, matsalata ɗaya shigarmin rayuwa da kake yi. Ka bar wahal da kanka dan bazaka taɓa samuna ba. Ko'a baya na amince ma batun su Daddy ne saboda Grandpa kaima ka sani. Amma ban taɓa jin sonka ba, kai bama kai ba, duk wani namiji ban taɓa jin sonshi da sunan soyayya ba a rayuwata. Idan ka cire Daddy na, Grandpa, da Uncle you. Ina baka shawarar ka daina bibiyata dan ina ɗaga maka ƙafa ne saboda zumincin da ke tsakaninmu, idan kuma ka cigaba zan iya fyatoka ta duk inda yay mun bawai hancina kawai ba". Daga haka ta miƙe hannunta ɗauke da takardun data tattara. Cikin takun nan nata na yauƙi. Tamkar wanda ta danne bakinsa da dannau ya kasa iya furta komai sai binta da kallo da yay cikin tashin hankalin kalamanta. Ya jima da fahimtar bata ra'ayinsa a yanzu, amma bai taɓa tunanin tun farko ma bata taɓa sonshi ba alfarmar Grandpa ɗin su yaci ba. Hannunsa ya kai saman goshinsa ya shiga murzawa, dai-dai nan sakatariyar Lulu ta shigo. Ɗagowa yay yana kallonta, ta ɗan rissina da girmamawa ta ce, "Sorry sir ta ce na rufe mata office ɗin". Idanu ya ɗan lumshe ya sake buɗewa akan matashiyar yarinyar mai tarin nutsuwa. Sai kuma ya saki murmushi da jinjina mata kansa ya miƙe kawai. "Sorry sir" ta sake faɗa dai-dai yana fita. Hannu kawai ya ɗaga mata batare da ya juyo ba ya fice abinsa zuciyarsa fal damuwa. Koda ya fito ƙurar motarta kawai ya samu alamar ta fice. Ya kalla Smart da ke jigine jikin motarsa da waya a kunne alamar magana yake. Tsaiwar jiransa yay har ya kammala. Bayan ya kammala wayar ya juyo idonsa akan Tajuddeen da fuskarsa ta nuna alamun ɓacin rai da damuwa, kai tsaye ya furta, "Inaga zan wuce gida dan wani uziri ya taso min". Cikin damuwar dake shimfiɗe a fuskarsa ya gyaɗa masa kai da ɗan ɗage kafaɗa. "Ba damuwa ai itama ta sake tafiyarta". Sam shi Smart bai ga fitar Lulu ba, dan haka ya kallesa cikin son ƙarin bayani. "Ina magana ne akan ogarka bakaga fitar ta ba?". Smart ya kai dubansa ga inda ya ga motarta tun shigowarsu, wayam babu ita. Sai kawai ya dawo da dubansa akan Tajuddeen ɗin yana mai girgiza kansa da ɗan furzar ya huci. A taƙaice ya ce, "Bara na wuce". Ba yanda Tajuddeen ɗin baiyi ba akan ya bari ya kaisa amma yaƙi. Dole sukai sallama ya fito domin samun napep..... ★★★ Sosai ran Tajuddeen yake a dagule, dan haka maimakon office da yay niyyar zuwa sai ya nufi companyn mahaifinsa da yake da tabbacin yana can. Koda ya isa gaisuwar ma'aikatan wajen ma bai iya amsawa da ƙyau, hannu kawai yake iya ɗaga musu. Sun sha mamaki dan sun san shi mutum ne mai saukin kai sosai ga fara'a. Sam baida wulaƙanci, wani lokacin ma idan yana jin barkwancinsa ya shigo Companyn bazaka taɓa cewa ɗan oga bane ba. Kai tsaye office ɗin mahaifin nasa ya nufa batare da jiran sakataransa yay masa iso ba. Alhaji Sulaiman Sufi Garko da ke tsaka da tattaunawa da babban yaronsa da ba'a jin sirrinsu a tare suka zuba ma Tajuddeen ɗin ido har ya ƙaraso inda suke. Hannu ya Bama yaron mahaifin nasa mai suna Isyaku, sai dai ana kiransa da Malami. Malami ya gaida Tajuddeen ɗin da girmamawa duk da kuwa zasu iya sa'anni, to amma ai baba ma da babansa. Alhaji Sulaiman dai kallon ɗan nasa yake kawai bai dai tanka ba, sai wani inkiya da yayma Malami da ido. Kai ya gyaɗa masa dan babu wani yaren jiki na Alhaji da bai haddace ba. Ko tari yayi yasan mi yake nufi. Fita yay ya bama ɗa da mahaifin waje... "Auta wani abu ya faru ne na ganka a haka?". Alhaji Sulaiman ya faɗa cike da kulawa ga tilon ɗan nasa namiji kuma auta a cikin ƴaƴansa. Cike da damuwa Tajuddeen ya sake tsuke fuska, sai kuma ya kalla mahaifin na sa da idanunsa da suka kaɗa sosai. "Abba Please ina son zancen aure na da Mawaddat ya motsa mana. Wlhy bazan iya daina sonta ba, dan na gwada hakan amma na kasa". Murmushin manya Alhaji Sulaiman yayi tare da ajiye pen ɗin hannunsa idonsa ƙyar akan Tajuddeen kamar yana son tabbatar da gaskiyar furucinsa... "Abba Please say something mana". Tajuddeen ya faɗa kamar zai saki kuka. Alhaji Sulaiman ya furzar da huci yana mai haɗiye sauran murmushin fuskar tasa da ya rage. "Tajjudeen in ce maganar nan ta wuce ai ko?". "Abba bata wuce ba wlhy, dan nikam ina sonta kuma zan zauna da ita a duk yanda take. Dan ALLAH kayi haƙuri ku sasanta da Uncle Isma'il ni dai a auramin ita. Kaga zuwa jibi Grandpa zai dawo da ga Umra ɗinsa, ni dai zan samesa da zancen a karo na biyu tunda har yanzu bawai ta tsaida wani mijin bane. Nima kuma na kasa kallon kowacce mace da sunan soyayya dan ita kaɗai nake so tun ina yarona". "Humm Tajuddeen sasantawa tsakanina da Isma'il abune mai matuƙar wahala. Kuma nasan zai iya wulaƙantani fiye da da saboda ƴarsa. Amma zan iya komai a kanka kamar yanda shima yake jin zai iya komai akan tasa ƴar. kuma kafin ma Baba ya dawo jibin yau zan fara masa zancen a waya". Sosai farin ciki ya baibaye zuciyar Tajuddeen. Miƙewa yay yaje ya rungume mahaifin nasa. Shima fuskarsa da murmushi ya amshesa hannu biyu. Kusan mintuna biyu Tajuddeen ya ɗago. Cikin komawa serious ya ce, "Abba wai dan ALLAH miye ya haɗaku kai da Uncle Isma'il? Nasan dai sanda ina yaro ba haka kuke ba. Kuna ƙaunar juna kamar ƴan uwa na jini, kuna mutunta juna matsayin surukai. Amma abin mamaki sai ga mijin ƙanwarka uwa ɗaya uba ɗaya ya juye ya zama maƙiyika! Abba Please ka sanar min miya haɗaku ko zan iya wani abu mana". "Tajuddeen wannan ba huruminka bane, kai dai ba kana son auren Mawaddat bane? To ka saka a ranka kamar ka samu dan koba komai ita ɗin ɗiyar ƙanwata ce Isma'il bai isa canja wannan tarihin ba. Dan haka jeka ka cigaba da harkokinka Mawaddat ta zama matarka nan da sati biyu kacal". Sosai maganar farko ta tsaya masa a rai, sai dai ta ƙarshe ta masa matuƙar daɗi da sakashi a farin ciki dan haka bai musa ba yay masa sallama ya fita cike da ƙwarin gwiwar ya kusa mallakar Mawaddat. Ni dai nace hummmm😵‍💫. Kufa masu karatu ya kuka gani🤷?. ★★★....★★★ Kallon mamaki yake ma matar tasa akan furucinta. Fahimtar hakan ya saka Aunty Saliha sake faɗin, "Wlhy da gaske nake Sweetheart bata nan fa. Alamu ma ya nuna ta jima da barin gidan nan kamar". Sosai ran Uncle Yousuf ya sake dugunzuma. Dan haka ya cije lips ɗinsa da ƙarfi batare da yace komai ba. Ture shayin gabansa yay tare da miƙewa ya fice a falon. Cike da tausayin mijin nata ta bisa da kallo. Baba maigadi ya gaishesa da girmamawa duk da ganin yau fuskar ubangidan nasa babu walwala. Hannu kawai ya iya ɗaga masa. Sai kuma ya furta "Baba ko akwai wanda ya fita a gidan nan ne bayan yara da suka wuce school?". Baba maigadi da ya ɗan daburce ya shiga in-ina da inda-inda. "Baba tambayarkafa nake? Bana son kwane-kwane ka faɗa min". Uncle Yousuf ya faɗa da ɗan jin haushi a muryarsa. "Kayi haƙuri Alhaji, abunne dai kamar da ruɗewar kai. Hajiya Muwaddat dai ta fita kam tunda duku-duku kafimma yara su wuce, sai dai abinda ya ɗauremun kai da hargitsani ni banga shigowarta bane shiyyasa na fara tunanin ko junnu ne ke son buɗe min idanu n...." Takaici ya saka Uncle Yousuf yin gaba batare da tsayawa jin ƙarashen labarin da yayma kallon na soki burutsu ba. Sai dai harga ALLAH shi baba maigadi iya gaskiyarsa da yake faɗa. Sosai hankalin Uncle Yousuf ɗin ke'a tashe, dan zuciyarsa ta fara masa wasi-wasin karfa taƙi zuwa gida. Yana shiga key ɗin motarsa da ke a dining kawai ya bama aunty Saliha umarnin bashi, bai ma ko saurareta akan magiyar yazo ya ƙarasa break fast ɗinsa baiyi ba ya sake ficewa abinsa. Sai ƙarar buɗe gate da fitar motarsa kawai tajiyo. Addu'ar isa lafiya kawai tai masa dan bata da yanda ta iya tunda tasan ƙaunar da yakema ahalinsa dabance a rayuwa. Bai haɗa son su da komai ba. Ita hakan bai taɓa zame mata matsala ba dan itama suna nuna mata ƙauna a cikinsu. Basu taɓa wareta ba ko nuna mata bambancin kasancewarta bare garesu. Hasalima suna ɗaukar mahaifinta matsayin uba garesu a yanzu fiye da kowa har danginsu na Jiƙamshi. Dan haka bazataima ALLAH butulci ba sai dai ma ta tayashi son danginsa itama tare da musu fatan alkairi musamman akan Mawaddat data zame musu tamkar zakka.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅??𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣6️⃣ ........Cikin ƙanƙanin lokaci Uncle Yousuf ya isa gidan ɗan uwan nasa. Anan ma sama-sama ya gaisa da su maigadi. Su ya farama tambayar Lulu tazo gida. Sun bashi amsar da ta sakashi sakin ajiyar zuciya mai kauri. Sai kuma ya samu ƙwarin gwiwar ƙarasawa ciki duk da sun tabbatar masa ta fita aiki tunma ɗazu tare da drivern ta. Kusan karo suka ci da Daddy dake ƙoƙarin fitowa har lokacin yana ƙananun magana wa Mommy akan Mubeen bai gaida Lulu ba. Sai dai duk wanda ya sanshi yaga yanda yake faɗan yasan yana yinsa ne kawai amma akwai abinda ke damunsa mai raɗadi ba abinda Mubeen ɗin yayi bane, shi kamar ya taka sahun ɓarawo ne. Ita dai Mommy bata tanka ba sai ma maida hankalinta tai akan cin abincinta da shi Daddy ɗin ya fasa ci saboda Lulu bataci ba. Mubeen ma na zaune cikin ɓacin ran yanda faɗansa ya koma kan Mommy kamar dai dama Daddyn nasu dama da biyu ya ƙirƙiri faɗan dan ya maidasa kanta ne. Gaishesa Uncle Yousuf ɗin yayi, sai kuma ya leƙa ya gaida Mommy da ga inda yake tsaye, acewarsa yana sauri ne dama ya biyo ne yaga Yaya. Mommy tai ɗan murmushi da masa addu'a. Tare suka fito da Daddyn da ya bar faɗan tun ganin Uncle Yousuf, dan yasan yana ji zai fara kare Mommy koma shi ya maida faɗan a kansa. "Yaya magana ce da ni mai muhimmanci". Ya faɗa cikin rashin walwala. Tsai daddy yay yana kallonsa. Sai kuma ya kamo hanunsa da faɗin, "To muje office ɗina ko naka sai muyi a can ko auta". "A'a Yaya, anan gida ya cancanta muyita dan zatafi dacewa". Komai Daddy bai sake cewa ba sai hannun ƙanin nasa da ya sake ja suka nufi falon baƙi da ke can ta wajen garden. Tsaf falon yake dan kullum sai an gyarashi da saka masa turaren wuta. Bayan sun zauna cikin kulawa da san danne damuwa Daddy ya ce, "Ina jinka mike faruwa Auta? Danni duk ka ɗaga min hankali da wannan yanayin naka wlhy." Numfashi mai ɗaci Uncle Yousuf yaja da gyara zamansa. Kai tsaye ya ce, "Akan Mawaddat ne." "Kuma dai Yousuf? To mi ta sake yi?". Da ga jin a yanda Daddy yay tambayar kasan ransa a jagule yake. Amma sai Uncle Yousuf ɗin yay biris ya cigaba da faɗin, "Gaskiyar da muke buƙatar gani da ido ce na gani jiya a zahirance. Dan an maido min Mawaddat gida a buge tana warin kayan maye kamar ma harda giya". Tsurru Daddy yay yana kallon Uncle Yousuf, sai kuma cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka ya ce, "Yousuf dan ALLAH ka gayamin gaskiya, dan in har wani yazo ya faɗa maka nasan za'a iyama Mawaddat sharri kasanta da magauta. Na rasa mi yarinyar nan ta tsarema wani a rayuwa. Gashi ita bata damu da kowa ba amma ita an dam........" Dakatar da shi Uncle Yousuf yay da faɗin, "Yaya! Kasan dai bazan ma Mawaddat ƙarya ba dan naci riba ko? Kuma ni babu wanda yazo ya faɗa min ni na gani da idanuna. Kuma gashi misawarka tasa na fahimci kai kanka baka san Mawaddat bata kwana gida ba ma. Hakan na nufin dama ba yau ta fara fitar dare ba batare da ka sani ba kuma baka taɓa maida hankali ko damuwa ba akan tabbatar da kowa na gida kafin ka kwanta. Yaya bansan yashe ka koma haka ba, shin dan ALLAH miya canjaka? Anya kuwa son Mawaddat kakeyi da gaske har cikin ranka? Wace irin bahaguwar rayuwace wannan mara fasali. Iyayenmu sun baku tarbiyya gwargwadon iyawarsu kai da Aunty Kareema. Sannan kuma kun bani dan gashi a yanzu ina cin ribarta matsayin nagartaccen mutum da ke banbance fari da baƙi koda a cikin rufewar idanu ne. Sannan sauran yaran ma suna samun irin tarbiyyar dana samu da ga gareku. Shin miyasa komai ya canja akan Mawaddat ne? Miyasa makahon so ya lulluɓe zuciyarka kake ɗorata akan abinda zata iya kaico da kai wataran da tunanin soyayya ce. Ban ce karka sota ba, amma ka dinga dubayya mana. Shin dole ne sai ka nuna mata ƙazamar soyayya zamu san kaso mahaifiyarta kamar haka itama? Ko sai ka mata makahon so zai sanarma duniya ita ɗin ƴar sonka ce da ta fito da ga jikin matar son ka?. Anya yaya ba alhakin Aunty Kareema bane kuwa ke bibiyarku akan Mawaddat kai da mahaifiyarta? Anya ba farkawa ya kamata kayi da ga nannauyan barcinka ba a wannan gaɓar kafin komai ya ƙarasa taɓarɓarewa mu rasa Mawaddat gaba ɗayanta". Sosai jikin Daddy ya ƙara yin sanyi, dan dama harga ALLAH ƙarfin hali kawai yake na son musawa uncle Yousuf ɗin tunda shima ya ga shigowarta gidan a ɗazun da safen batare da ita ko wani ya sani ba. Wannan damuwar ce ya tashi da ita, sai dai ya rasa ta yanda zai tunkari Mawaddat ɗin shine ya huce haushin akan Mubeen da Mommy. A hankali ya damƙo hanun Uncle Yousuf cikin nasa ya ƙanƙame da ƙarfi, so yake ko sau ɗaya yayi kuka akan wannan damuwar ta halin rayuwar da Mawaddat ta jefa kanta a ciki amma ya kasa. Sai dai idanunsa sunyi wani masifar kaɗawa da ja. Cikin rawar murya ya ce, "Nagode ɗan uwana. Nagode da ka kasance mai faɗa min gaskiya komai ɗacinta. Wlhy auta al'amarin Mawaddat shine mafi zama ƙololiwar damuwata a yanzu fiye da komai, dan hanani barci yake yi. Zan faɗa maka gaskiya ko jiya nasan fitar ta a gidan nan, kuma nabi bayanta, sai kuma na samu yaron nan driver da ka kawo shima ɗin yabi bayanta. Dan haka na laɓe a kangwon kusa da gidan data shiga a wajen har kunama ta harbeni jiyan. Ban damu da azabar kunamarba, ni dai burina yaron nan ya fito da ita a gidan lafiya. Cikin amincin UBANGIJI kuwa sai gashi ya fito da ita a mota, na fito zan sake biyosu duk da azabar harbin kunamar da nake ciki idona ya ganemin ɗan gidan tsohon gwamna M Atik Kumo zai shiga gidan shima. Na shiga tashin hankali matuƙa, sai dai ban tsayaba na biyo motar tata dan naga ina yaron nan zai kawota sai naga gidanka ya nufa da ita. Nutsuwar hakan dana samu ce ta sani komawa da baya can gidan ɗin dai na sake tsayawa a mota, abinda ya sake tadamin hankali Yousuf su Alhaji Baita na gani sun fito a gidan nan dai da Mawaddat ta shiga kusan ƙarfe ukun dare. Wlhy tsabar ruɗani bamma san kunamata ta sauka ba. Da ƙyar na iya sake maido kaina gida shine fa ko rintsawa banyi ba har akai sallar asuba, bayan na dawo massalaci naga shigowarta gidan nan". Ya ƙare maganar hawayen da yaketa son su zubo na sauka a yanzu masu zafi. Sosai shima Uncle Yousuf ya shiga ruɗani da tashin hankali. Dan jin sunayen manyan mutane da duk wanda ka tambaya zai tabbatar maka ɗunbin ganin mutuncinsu da yake a cikin wannan labari na yayansa...... Daddy ne ya katsesa da faɗin, "Yousuf kaina ya kulle gaba ɗaya akan al'amurin nan, ka kawo mafita inba hakaba ina gab da kaiwa ƙasa akan lamarin Mawaddat". "Yaya mafita ɗaya muke da ita shine yi mata aure...." "Aure Yousuf? To da wa? Kasan dai Mawaddat bata kula kowa. Kana dai ganin duk kurari da jan idon Baba (Alhaji Sufi Garko) yayi ya barta akan sanya ranarta da yaron Sulaiman data bijirewa. Har gargaɗin duk randa wani ya sake zuwa garesa domin santa zai aura masa ita koba amincewar ta da mu kammu yay mata amma bata ɗauki hakan da muhimmanci ba saboda bushewar zuciya. Yousuf na rasa da ga ina na kuskure akan Mawaddat. Shin nuna mata soyayya na nufin ba dai-dai ba kenan?". "Humm Yaya wannan harda laifinka kaima ka sani, ba'a hana iyaye su nunama ƴaƴansu soyayya ba, sai dai ba ƙazamar soyayya irin wadda kaima Mawaddat ba da har tazama jagoran hanata fahimtar minene addininta. Yaya kofa salla nagartacciya Mawaddat bata iya ba a wannan shekarun nata balle azo ga sauran al'amuran addini, hakan kuma duk kuskurenka ne da kasa barinta ta samu tarbiyya irinta uwa a wajen Aunty Kareema saboda son zuciyarka..... Amma dai mu ajiye abinda ya wuce mu kalla na yanzu. Yanzu dai bayan tabbatar da aure ne mafitarmu akan lamarin Mawaddat bani da wani idea kuma. Amma dai ka bani lokaci nayi nazari tukunna. Sannan dan ALLAH ka kwantar da hankalinka. Dan lamarin Mawaddat an baro shiri ne tun rani. Amma insha ALLAHU tsayayyen miji a gareta zai jagoranceta da sabuwar tarbiyyarsa irin wadda tun farko ya kamata ace ta samu da ga garemu. Addu'a ya kamata mu duƙufa mata musamman ma kai ɗin nan. Sannan mu dage da sadaka ALLAH ya shiryar mana da ita, ya kuma kawo mana mafita cikin sauƙi. Sannan ka ajiye batun su Alh. Baita ni da kaina zanyi bincike a kansu insha ALLAHU zan gano alaƙarta da su". "Shike nan Yousuf ALLAH yay maka albarka." "Amin yaya". Daddy ya sake nisawa a hankali da faɗin, "Sai dai kabi a hankali a duk wani bincikenka dan a wannan gaɓar da gaske inajin ƙanina, tsoro na gaske nakeji wlhy a wannan gaɓar. Miya kawo su Alh. Baita cikin rayuwar Mawaddat?". "Bana tunanin wani abu saɓanin wanda zuciyata ke kallo yaya. Kasan dai da yawan wasu manyan ƙasar nan sunata taka wata rawa cikin rayuwar lalacewar yaranmu batare da mun farga ba". "Nafika sanin hakan Yousuf. Sai dai al'amarin ya wuce a yanda kai kake kallonsa da hasashensa. Kai dai kamar yanda na faɗa maka inajin tsoro da gaske a yanzu tsoro nake ji irin wanda a baya babu shi a zuciyata....." "Yaya na kasa fahimtar mi kake nufi ka ruɗar dani fa, Miye ke baka tsiro ne wai?". Murmushi Daddy yayi mai nuna tsantsar damuwa a bayyane. Maimakon amsa sai ya dafa kafaɗar Uncle Yousuf tare da ɗan bubbugawa ya miƙe. "Tashi kaje office auta karka makara". Kallo Uncle Yousuf ya bisa da shi mai tsayawa a rai, sai zuciyarsa ke wani irin rawa dan shi kaɗai yasan mi yake iya hangowa game da ɗan uwan nasa, sai kawai shima yaji kamar ya fara jin tsoron. Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari wanda ya kamata ace ya sani amma ta yaya? (Bincike akan alaƙar Mawaddat da su Hon. Babale Nakowa) kansa ya jinjina cikin gamsuwa da shawarar zuciyarsa. Dan haka shima ya miƙa ya fice. Da kallo yabi motar Yayansa dake ƙoƙarin ficewa a gidan. Numfashi ya sauke da ƙyar tare da nufar tashi motar shima. ★★★ ∆ ★★★ Smart kam tattara al'amarin Lulu yay ya wancalakar gefe domin fuskantar tasa mai muhimmanci. Gida ya nufa kai tsaye saboda kiran da Abba yay masa. Ya samu gidan da ƴar hayaniyar kasancewar zuwan Sa'id da wasu kawunansa uku. Cikin girmamawa ya gaishesu batare da ya kalla inda Sa'id ya ke gurfane ba kamar mai kuka. Ya maida hankalinsa ga Abba da Hawwah ke a kusa da ƙafafunsa kamar tana kuka itama. "Abba gani". Ya faɗa cikin dakewarsa. Nisawa Abba yay da nuna Hawwah ya ce, "Kaine ka ɗakko Hauwa'u a gidanta?". "Eh tabbas nine Abba". "Me yasa?". Shiru ya ɗan yi kafin ya nisa. "Abba saboda ta kirani akan ga mahaifiyar mijinta na neman ƙonata da mangyaɗa. Banje gidan da nufin ɗakkota ba sai jin ba'asi na kuma sasanta kamar na baya da akai batare da kun sani ba. Sai dai na samu abin ya wuce yanda nake zatonsa shiyyasa na ɗakkota kafin a cutar da ita tunda mu bawai mun daina sonta bane ba. Ba kuma mun bashi bane dan mun gaji da ita a gidan nan kota gundiremu. Abba abubuwa da yawa sun faru akan auren Hawwah amma ina sasantawa a iya can batare da kai ko Ammah kun taɓa sani ba. Bama ku ba hatta da Aunty Bilkisu ban taɓa sanarmawa ba, kuma na gargaɗi Hawwah sanar ma kowa. Shiyyasa wannan karon na ɗakkota kuma bazata sake koma musu gida ba. Yaje ya auri wadda mahaifiyarsa ke son zama da ita haka nan dan ALLAH kowa ya huta."........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣7️⃣ ........Cikin ɓacin rai ƙanin mahaifin Sa'id ya ce, "Ai ba ita kaɗai ce keda iko da shi ba. Sannan kuma ni banga laifinka anan ba yaro. Hasalima abinda kai sai ka birgeni dan kayi abinda ya kamata ace ƴan uwa na ƙwarai suyi akan ƙannensu. Wannan shine girman kuma shine darajtawar." "Tabbas abinda yay yayi dai-dai. Kuma tunda hakane muma kan zamu fidda kammu a wannan zancen ku ɗauki duk matakin da kuke gani shine dai-dai dan halin Rafi'a sam bashi da burgewa. Narasa mitake son maida kanta a rayuwa ita ba ƙaramar yarinya ba amma kullum aita abu guda kamar cin ƙwan makauniya, yanzu da tsautsayi yasa ta samu yarinyar nan da mangyaɗan yaya kenan? Wace amsa take da shi na kare kanta. Dama tausayin yaron nan ya samu tasowa mu biyosa da wuri kafin abin yay zurfi. Amma tunda hakane zamuje muma har sai kun yanke hukunci kafin sannan shima Yaya Ibrahim ɗin ya dawo da ga tafiyar da yayi". Kuka mai tsuma rai Sa'id ya saki, dan harga ALLAH yana matuƙar ƙaunar matarsa Hauwa'u da ƴar ɗiyarsu Nasreen da taci sunan mahaifiyar tasa. Amma hukuncin da iyayen nasa suka yanke yasa bazai iya jayayya da su ba. Babu yanda zai yi ya bisu yana kallon Hawwah da kanta ke ƙasa tun shigiwarta batako kalla sashen da yake ba ma...... Ajiyar zuciya Abba ya saki a hankali, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. A taƙaice ya ce, "Kuje ciki zamuyi maganar a nutse". Daga Hawwah har Smart miƙewa sukai suka fice. Babu kowa a tsakar gidan sai Umma da ke kai kawon girkin rana. Yanda bata tanka musu ba suma basu tanka mata ba. Sai dai murmushin data saki akan idon Smart. Shi ba ma'abocin maida hankali bane akan irin waɗan nan abubuwan dan haka yay shigewarsa, sai dai murmushin ya sosa masa zuciya da tsaya masa a rai. Ammah dake zaune a falo Nasreen a cinyarta tana shan kunu kallo ɗaya tai musu ta maida hankalinta ga Nasreen ɗin. Zama yay kamar yanda Hawwah da ke sharar hawaye itama ta zauna. Idanu ya ɗan zuba mata tare da furzar da huci kaɗan. "Shi wannan kukan babu amfanin da zai miki, bakuma zai gyara abinda yake faruwar ba. Kisama ranki haƙuri da nutsuwa, dan bazaki koma wannan gidan ba har sai tasan darajarki. Idan kuma kina ganin ba'ai miki gata ba a hakan dan naga k da mijin naki duk shashashu ne ga hanya nan zaki iya binsu" Daga haka ya miƙe. "Kayi haƙuri Yaya ni banga laifinka ba, kuma nagode da ƙoƙarinka a kaina". Komai baice mata ba, sai duban Ammah da tai kamar bata ɗakin da yay. "Ammah ni zan koma". "ALLAH ya tsare ya bada sa'a". Tace masa batare data ɗago ba. Da Amin ya amsa yana ɗan lakatar kumatun Nasreen da itama tai masa a dawo lafiyar. Da ga haka ya fice abinsa badan yasan ina ya kamata ya dosa ba tunda boss ɗin tasa ta korosa yau. Sai da ya fito gaba ɗaya da ga layin nasu zuciyarsa ta kwaɗaita masa zuwa ma ya duba trainers ɗinsu. Dan kwana biyu basuga juna ba. Waya ya ciro tare da ɗan ƙura mata ido kamar mai tunani, sai kuma ya ɗan ɗage kafaɗa tare da kai wayar kunnensa bayan yay dailing number daya lalubo. Bugu uku aka ɗaga, yay ƙaramin murmushi da faɗin, "Barka da hantsi sir". Amsar da aka bashi da ga can ta sakashi sakin murmushi. Sai kuma ya ɗan shafo kansa alamar jin kunya tamkar yana gabansa. "Am sorry Sir na ɗauka laifina. Yanzu ma ina son zuwa gaishekanne shiyyasa nace bara naji inda kake". Ya ɗan yi shiru alamar saurare. Sai kuma ya amsa da "Okay gani nan zuwa in sha ALLAHU". Tafiyar mintuna ƙalilan da bai wuce ashirin ba ta kaisa babban stadium ɗin da coach ɗin nasa yace masa yana acan. Wajen ya ƙayatu matuƙa. Babu yawan hayaniyar mutane sai isu-isu ƴan wasa da ke ta tsalle-tsalle alamar training sukeyi saboda wasan sada zumunci da suke shirin zuwa kudancin ƙasar. Tunda ya shigo wajen ɗaya da ga cikinsu da ya fara ganinsa ya saki wani irin fito daya jawo hankalin sauran suma. *_"Capten!! Carpten!!"_* suka shiga faɗa cikin ihun da ke nuna tsantsar farin cikin ganinsa. Murmushin Smart ne ya sake faɗaɗa, shima ya shiga ɗaga musu hannayensa duka biyu har ya ƙarasa gaban Trainers ɗin nasu da ke kallonsa shima da murmushi. Har cikin rai yana matuƙar son yaron, ya kuma ci buri a kansa dan Smart ya iya gara ƙwallo mai suna ƙwallo ta gaske, dan ma mun kasance a ƙasa irin ta Nigeria da mai alfarma yafi ma'iyi da tuni wani labarin ake akansa ba wannan ba. Amma duk da haka shima ya damu wasu dama na barin ƙasar ƙaddara ta toshe su. Sai dai ALLAH mai hikima duk da tarin damammakin da yaron ya samu tun yana da shekara goma sha takwas komai yaƙi motsa kansa a inda yake. Hannunsa ya kamo da ga hanashi risininawar da yay niyyar yi, "Yarona irin wannan ƙiba haka anya kuwa kana motsa jiki?". A yanda coach ɗin yay maganar ya saka Smart yin ƙaramar dariya da shafa kai yana ɗan dudduƙar da kansa da faɗin. "Sir ina nan a yanda ka sanni girman rigane kawai". "Bari nace to. Amma badan na yarda ba. Ykk to ya kwana biyu? Tunda ka samu aikin nan ka ɓuya gaba ɗaya ko?". Ya ƙare maganar yana jan hanunsa suka ƙarasa kan wasu kujeru da ke gefe kaɗan. Smart da har yanzu bai bar murmushi ba ya ce, "Sir aikinne bai barin motsin kirki. Amma kuna raina sosai". "To Alhamdullah babu dai wata matsala kuma ko?". "Da sauƙi dai Sir". "A cigaba da haƙuri, komai yay farko zaiyi ƙarshe. Fatanmu dai ALLAH ya warware mana abinda bamu da ilimin sani akansa". "Amin Sir". Ya faɗa cikin damuwa idanunsa akan teammate ɗinsa da ke ta tsalle-tsalle su har yanzu. Hira suka cigaba da yi da oga wani kaso na hankalinsa na ga teammate ɗin nasa dai. Kiran wayar coach da akai ta sakashi miƙewa ya ɗan matsa a wajen. Dai-dai nan ɗaya daga cikin ball ɗin da suke training ɗin da ita ta gangaro wajen filin har inda Smart ke zaune. Kamar wanda aka tsikara ya miƙe da alamar tsumin ya motsa. Cikin wani irin salo da iya ƙwarewa a harkar ya buga ball ɗin tamkar abin almara bata sauka ko ina ba sai cikin raga. A take wajen ya ruɗe da ihunsa, kamar waɗanda ake juyawa da remote suka raba kansu yanda ƴan ƙwallo kanyi a cikin fili yayin wasa. Ƙarasa shigewa cikin filin yay shima cikin zafin nama da jin shauƙi a ransa, dan da gaske ball itace hubby na Smart. Tana sakashi karsashi da nishaɗi maƙurar ƙurewa. Juyowar coach da ya kammala waya ya sashi waro idanunsa waje sosai na ganin abinda ke faruwa. Sosai ya rikice dan yasan da wahala a wanye lafiya... Ilai kuwa kafin ya kai ƙarshen tunaninsa da yay dai-dai da sake saka ƙwallo ta biyu a raga da Smart yayi ya wani ƙwalla ƙara hannayensa duka biyu dafe da kansa. Kafin su isa kansa ya zube ƙasa a sassanƙame. Hankalin coach idan yay dubu ya tashi, haka ma sauran teammate ɗin nasa duk sun rikice. Babu ɓata lokaci suka fiddashi a filin coach na musu faɗan miyasa suka barshi ya shiga tunda sun san matsalarsa. Su dai basu da tacewa dan mai afkuwa ta riga da ta afku kuma. Sai fatan a kiyaye na gaba dai. Duk wani kalan taimakon da sukan masa idan matsalar ta samesa ita Hameed yay masa, sai dai kamar yanda aka saba babu alamar za'a samu kansa a yau ɗin. Sosai ya sake shiga damuwa, ina daɗi da ga zuwansa gaishesa a rarraɓesa a kaima iyayensa shi a haka. Dole yay kiran ƙaninsa Ahmad aboki ga Smart ɗin kenan akan yazo suje gidan su Smart ɗin. Da mamaki Ahmad ke tambayar yayan nasa ko wani abu ne ya faru? Bai wani tsaya kwana-kwana ba ta sanar masa. Hankalin Ahmad ya tashi, babu shiri ya baro office ya nufo stadium ɗin. Yana ajiye wayar kiran babban amininsa Yousuf Ibrahim Jiƙamshi na shigo masa a waya (Uncle Yousuf) kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga ɗin dan sunyi da shi zasu haɗu shi shaf ma ya manta sai da yaga kiran. Furucin Uncle Yousuf da ke faɗin, "To baban ƴan tamaula ALLAH yasa dai ka gama da yaran naka dan bana son zuwa nai zaman jiranka zan koma office saboda baƙi da nake tsumaye bayan azhar". Cikin damuwa coach ya ce, "Wlhy ni nama manta da da batun zuwan naka ina nan a rikice". "A rikice kuma a kan mi?" Uncle Yousuf ta faɗa cikin mamakin aminin nasa. Shima amsa ya bashi da faɗin, "Wlhy Aliyu ne yazo mu gaisa fa na ɗan tashi amsa waya ban san yaya akai ba ya shiga cikin fili ka gansa nan sharɓan babu alamar rai tare da shi". "Ya Arrahaman! Aliyu dai Aliyu nawa Smart Mawashi?". Sai yanzu ma shi coach ya tuna ashe Aliyu a ƙarƙashin abokin nasa yake a yanzu. Dan haka ya bashi amsa da cewar, "Yess! Yes! Shifa wlhy". "Ya Salam gani nan a hanya". Kusan a tare Uncle Yousuf da Ahmad suka iso wajen. Kowanne ya fito a motarsa da sassarfa zuwa inda suke zagaye da Smart da ke kwance a ƙasa kansa bisa jikin coach da ke faman shafa masa ruwa yana fatan ya farfaɗo, dan bai son su kai shi gida a wannan yanayin musamman daya tuno irin tashin hankalin da Ammah ta shiga last da abin ya faru da shi. Har rige-rige ake tsakanin Uncle Yousuf da Ahmad, sai dai kowanne ya samu nasarar kai hannunsa jikinsa. Ganin yanda aketa faman saka masa ruwa babu alamar zai farfaɗo Uncle Yousuf ya cema coach "Hameed muje asibiti kawai dan banga alamar zai farfaɗo ba a hakan nan". Cikin damuwa coach ya dubesa shima da bashi amsa da "Yousuf zuwa asibitin nan babu abinda zai canja. Dan mun gwada yin hakan a baya sai dai mu gama zaman banza dan su amsa ɗaya ma suke bamu zuciyarsa ta tsaya da aiki. Al'amarin nasa ne fa kamar abin sihiri gashi nan dai. Gida kawai ya kamata mu kaisa duk da gaskiya hakan na sakani fargaba dan tayarwa iyayensa hankali kawai zamuyi". "Gaskiya kar a kaishi can Brother" Ahmad ya faɗa cikin damuwa. Bai jira cewar kowa ba ya cigaba da faɗin, "Mizai hana muje wajen mutumin nan da ya taɓa bashi magani sanda abun ya takura masa". "Shawara mai ƙyau Ahmad, da ni duk nama rikice wlhy hakan bai zo min a rai ba. Kunga ku kamashi kusa a mota". A bayan motar Uncle Yousuf aka saka shi kamar yanda ya buƙata, shi da coach suka shiga gaba Ahmad a baya ya riƙe Smart. Kai tsaye ƙofar ruwa suka nufa, gudun da coach keyi ya sakasu isa cikin ƙanƙanin lokaci. Gidane irin na talaka mai ƙaramin ƙarfi, sai dai da ga waje shafe yake da siminti tsaf da shi da milk ɗin fenti. Da ga gaban gidan kaɗan islamiyya ce ta ƙanan yara da keta karatu kasancewar akwai ta safe zuwa ƙarfe ɗaya. Tsaiwar motar ta saka wani saurayi da ke tsaye da ga jikin barandar Islamiyyar matsowa garesu yana musu sannu. Basu wani tsaya jan maganar ba suka buƙaci ganin Malam. Kafin ya basu amsa sai ga malam ɗin ya fito da ga gida..........✍️ _Yau dai Smart ɗin ku ya ɗan bani tausayi🥲_ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣8️⃣ _Ya rabbi ka gafartama *Sheikh Abubakar Giro Arugungun*. Ka yafe masa kurakuransa, alkairan da ya isar garemu na wa'azantarwa da koyarwa kasa ya amfanar da mu duniya da lahira. ALLAH ya albarkaci zuri'arsa. Suma iyayenmu ALLAH ka gafarta musu, damu baki ɗaya 😭✍️_. ........Wata nannauyar ajiyar zuciya Smart ya saki mai ƙarfin gaske lokacin da malam ya shafa masa ruwan addu'oi da yayi tofi a ciki, sautin karatun suratul Naazi'aat da ɗaliban malam ce ta fara shiga cikin kunnensa da wani irin ƙarfi tamkar a iya cikin kunnen nasa akeyi. Ya sake sakin ajiyar zuciya sai kuma ya kai hannunsa ya dafe goshinsa dan kansa wani irin ciwo yake kamar zai tarwatse. Uncle Yousuf ne ya fara ambatar sunansa, dan haka ya sake yunƙurin buɗe idonsa a karo na biyu sai dai ya kasa. A rikice duk suka dubi malam. Ya karkaɗa musu kansa da faɗin, "Kamar yanda na faɗa muku tun wancan karon ku sake jajircewa wajen addu'a da sadaka akansa, dan al'amarin nasa akwai ruɗani kamar na sihiri mai ƙarfi. Sai dai ban tabbatar ba dan UBANGIJI shine kawai masanin gaibu. Amma gaskiya al'amarin nasa yana nuna kamar bugewar junnu ne. Na fara baku ruwan addu'oi a wancan karon amma sai aka daina zuwa a karɓa kwata-kwata, dama ba komai bane face addu'oin karya sihiri wanda ya kamata ma ace duk musulmi kan dingayi a gidansa domin shi da iyalinsa koda lafiya lau ake dan rayuwa kake baka san mike biye da al'amarin ka ba. Koba sirihi akwai baki (kambun baka) da yafi sihiri kaifi a wasu lokutan. Koda ma bazaku juri zuwa nan ɗin a karɓa ba to ku dage da yi masa a gida dan ALLAH". A tare suka amsa da "In sha ALLAH malam" sai kuma suka ɗora da godiya. Ganin yanda Smart keta faman jujjuya kansa malam ya ƙara masa addu'a tare da basu umarnin kaisa asibiti mafi kusa. Godiya sukai masa dan a wancan karon ma haka yay musu. Suka ajiye masa sadaka shi kuma ya basu ganyen magarya da ayoyin da zasu karanta da ga cikin Alkur'ani mai girma. Kai tsaye asibitin suka nufa kuwa, inda aka bashi gado dan a kallo ɗaya idan kai masa dole ne ya baka tausayi, kai kace ba a yanzu kaɗai ya kasance a kwance ba yanda yay sharɓan. Sun bashi taimakon gaggawa har sai da ya samu barci suka ɗan samu nutsuwa. Sun yanke shawarar sanar da gidansu amma sai coach ya ce adai ɗan dakata idan basu sallamesa zuwa yamma bane sai a sanar musun. Hakan ya musu, dan haka sukai yunƙurin fitowa aka barsa da Ahmad ya zauna da shi kafin suje su dawo..... ★★★★★ Duk yanda taso cigaba da gudanar da al'amuran gabanta na wannan yinin hakan sai ya nema gagararta. Ba ƙaramin tsaya mata a rai abinda drivern nata yay mata yayi ba. Dole ta hakura da tattara bayanan case ɗin da zata fara tunkara a safiyar litinin kan dukiyar wasu marayu da wan mahaifiyarsu ke ƙoƙarin handamewa dan zuciyarta a cinkushe take matuƙa. Steering da take murzawa ta kaima duka a karo na babu adadi. Ta cije lips da masifar ƙarfi da faɗin, "Sai na koya maka hankali!". Kalmace data ambatata yafi sau shurin masaƙi. Ga takaicin daren jiya da ma na cigaba da ci mata rai dan a duniya tai masifar tsanar wani namiji ya raɓeta da sunan taɓata ko soyayya. Shiyyasa shima Tajuddeen lissafinsa ya shiga cikin jerin lissafin abubuwa masu ƙuna da ajiyewa a kudin tarihinta na wannan yinin da take ganin yazo mata a birkice. Office ta koma, inda ta tarar da baƙi kashi-kashi na jiranta. Tabbas batajin magana, sai dai a ɓangaren aikinta ita ɗin jajirtacciya ce, dan ma ɗabi'arta ta shaye-shaye na matuƙar maidata baya a lokuta da dama, dan badan wata hikima ta UBANGIJI ba da Lulu ta jima da daina zuwa wajen aikin ma gaba ɗaya ne. Mummunar hallayya mafi muni tattare da Mawaddat shine sakaci da addini, sam babu abinda ta sani akan addininta sai abinda ba'a rasa ba sakamakon karatun ta na lawyer. Bata san a kira salla ta tashi tayita akan lokacinta ba, to idan ma tayin babu maganar yinta a yanda MANZON ALLAH ya koyar damu. (Kuyi haƙuri ba Lulu kaɗaice a wannan matsalar ba. Wlhy da yawan mutane sunayin salla ne ba'a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. Dan bawai fa muna nufin Lulu bata san salla ba, a'a itama ta tashi ne a yanayin yanda akeyi kawai nakeyi batare da samun ilimin yinta ba kamar yanda da yawa mutane suka kasance. Mafi yawanmu idan da zaman tsayawa akan ibadarmu ta salla za'ai tun daga tsaiwarta ma zamu fara samun gyara. Please Dan ALLAH a wannan gaɓar kowanmu ya nutsu ya kalla sallarsa da kuma bincike akan yaya ake salla kamar yanda MANZON ALLAH S.A.W ya koyar mu gani ko zamu ribantu da gyarawa). Sanda ta gadama take salla, tana kuma yin tane a yanda kawai taga anayi kasancewar karatun addinin ma gatan mahaifinta ya zame mata cutarwar da bata samesa ba. Masifarta kam wannan halitta ce, wani mai haƙuri wani saɓani haka. Sai ɗabi'ar shaye-shayen data jima tana binnewa wanda har yanzu bamu san tushen farawarta ba ko dalilinsa. Wulaƙanta mutane da takasu a duk yanda taso kuskuren mahaifinta ne da ya ɗorata a turbar komai take so zata samu. A duk sanda ka nunama yaro komai yake so zai samu tofa kansa zai ƙara girmane da tunanin yafi kowa daraja da power a rayuwa, sannan akan komai shine sama da kowa. (Iyaye sai mu kula hakan ba soyayya bace).... Yanda ta zube wayoyinta da zama jagwab cikin lallausar kujerar office ɗin nata ya sake bayyanar da ɓacin ranta akan fuska. Hand bag dinta ta jawo tare da fiddo key ɗin drower ɗin jikin decks ɗinta da bata yarda kowa ya taɓa saboda abinda take ajiyewa a ciki ta lalubo. Tana ƙoƙarin buɗe drower ɗin sakatariyarta ya shigo office ɗin da sallama. Wani takaici ya sata ɗago idanunta da suka kaɗe da gajiya. Sai dai gaba ɗaya tama kasa mata masifar da ta saba yi mata a duk sanda tai mata kuskure. Da sauri sakatariyar ta ce, "Please am sorry maa. Wlhy abinda matar can tazo da shi ne yay matuƙar tayarmin da hankali. Jiya ma tazo nace mata ta dawo yau dan kina up 2days sai yau ne zakiyi res....." Hannu Lulu ta ɗaga mata alamar gajiya da saurarenta. Murya a shaƙe ta ce, "Zainab ba wanda zan iya saurare a yau koma minene akazo da shi. Ki sake bama duk wanda ya dace sabon appointment banda yau da gobe. Duk case ɗin da kuma kika sani bani da buƙatarsa a teburina karma mai shi ya shigomin office ok". Zainab da damuwa ta bayyana ma a fuska ƙarara ta gyaɗa kanta da ke ƙasa. Sai kuma cikin rawar murya dan har ta fara hawaye ta furta, "Aunty matar can fa mijinta ne yayma yarinyarta da taje agolanci da ita gidansa fyaɗe. Kuma yarinyar shekararta tara kwata-kwata. Sunje asibiti da yarinyar amma anƙi karɓarsu tun jiyan wai sai da ƴan sanda. Taje police station ɗin kuma ƴan sandan nata mata yawo da hankali. Wlhy bakiga a yanda sukazo da yarinyar ba a jiya da yamma abin babu ƙyan gani...." Wani irin matse idanu da damƙe kujera Lulu da jikinta ya fara tsumar mazari tayi. (Mawaddat calm down. Mawaddat calm down. Mawaddat calm down). Wani sashe na zuciyarta ke ta ambata mata. Sannu-sannu ta fara sassauta damƙe kujerar da rumtse idanun nata da tai, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya sunyi jajur matuƙa kamar wadda tasha wani abu a lokacin. "Shigomin da ita". Ta faɗa ƙirjinta na ƙara ƙarfin sukar da yake mata. Ga jikinta bai daina tsumar da yake ba. Da ace tanada ilimin addini da addu'a tafi cancanta da harshenta a irin yanayin. Amma sai aka samu akasin hakan a gareta. Da sauri sakatariyar ta ta fice cikin matuƙar sassarfa. Minti biyu basu rufaba sai gasu sun shigo. Matar dai da ka ganta kaga wadda ke'a cikin mawuyacin hali, sai dai da zata samu kulawa ƙyaƙyawar mace ce dirarriya. A lamarin Lulu da talaka a teburin aikinta kawai suke iya shan inuwa ɗaya, shima akan abinda ya shafi aikintane kawai babu ruwanta da rayuwarka. Har ƙasa matar ta kai ga alamun ciki da ya turo a jikinta zata gaida Lulu. Bata hanata durƙusawar ba amma dukkan hankalinta na gareta, sai kuma katseta da ga gaisuwar data fara da tai... "Kinga wannan gaisuwar baida amfani faɗamin ina yarinyar take?". Cikin gyaɗa kai da share hawaye matar ta ce, "Tana gidan ƴar uwata da ta rakoni nan jiya, saboda yanda jikin nata yake ne ƴar uwar tawa tace na dawo yau ita ta kula min da ita". "Wane police station kukaje domin kai ƙarar?". "Na nan unguwarmu ne sai kuma da mukazo nan wajen ƴar uwar tawa itama ta kaimu na nan ɗin. Sai dai shima basu ɗauki abin da muhimmanci ba shiyyasa ta ce zata rakoni nan inda take da tabbacin za'a share mana hawaye. Hajiya dan ALLAH ki taimakeni kamar yanda ALLAH ya taimakeki. Yarinyar nan marainiya ce mutuwar mahaifinta ta sani auren wannan tsinannen da tunda na aure shi ban sake farin ciki a rayuwata ba......" Cikin jan tsaki da takaici Lulu ta katseta da faɗin, "Kika zauna da shi kuma har ya miki ciki. Malama ni ba rayuwar aurenki nake buƙatar ji ba. Ki tashi kuje zan haɗaki yanzu da wanda zaku sameni a asibiti". Ta ƙare maganar tana miƙewa cikin matsanancin ɓacin rai. Waya takai kunnenta, da ga can aka ɗaga. Kirari aka fara mata ta katse da faɗin, "Musa ka sameni a office yanzu kai da Shu'aibu Please inada emergency case." "An gama ranki ya daɗe". Musa ya faɗa ransa fes dan yasan yau aljihunsu zai kasance a cike. Dan aiki da Lulu yafi masa zaman cikin station aita kayan hamma balle tsaiwar kan titi amsar na goro. Ɗan rubutu tai a takardar data yago ta miƙama sakatariyar ta dake tsaye har yanzu. "Idan sun zo ki basu wannan, suje da ita sai su sameni a wannan asibitin dana rubuta. Kibasu 5k da zasu saka mai a mota". Daga haka ta fisgi hand bag dinta da ɗayar wayarta da key tai waje... Batako kalli sauran mutanen da ke zaune a inda table ɗin sakatariyarta ya ke ba ta fice. Taja ƙaramin tsaki lokacin da take dana unlock ɗin motar tunkan ta ƙarasa gareta. Bazata iya jure wannan zirga-zirgar tuƙin ba fa gaskiya. Dan tun farko ita dama ba gwanar sonyi driving bace. Cikin ƙara jan tsaki lokacin da take ficewa a gate ɗin ta dannama Uncle Yousuf kira. Sai da ta shiga ta tuna abinda ya faru jiya da wasan ɓuyan data ƙudiri aniyar farayi da shi. Da sauri ta rarumi wayar zata katse sai dai harya ɗaga. Babu alamar wasa a muryarsa ya ce, "Lafiya?". Kamar ta fasa ihu haka taji, amma sai ta dake cikin pretending da ƴar shagwaɓa ta ce, "Uncle Barka da safiya. Dama no ɗin mutumin nan zaka turamin koka kiramin shi Please ya sameni a Shira's hospital". Ɗan jimmm yay kamar bazai amsa mata ba sai kuma cikin dakewar da takan bata tsoro a Duk sanda yayita ya ce, "Wane mutumin?". Yanzu kam sai da taji bugawar zuciya. Da ɗan rawar harshe ta ce, "Driver fa my papa". Har zaiyi yi mata tambayar yaya akai bashi ya kaita office ba sai kuma ya fasa saboda tare ya ke da abokinsa Hameed. "K kina ina yanzu?". Ya faɗa cikin goce tunaninsa. "Ina hanyar Shira's hospital ɗinne ". "Sai kin ƙaraso". Ya faɗa kawai yana yanke kiran.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣9️⃣ ........Kaɗan ya rage ta bugama motar gabanta. Tai saurin take birkin da ƙarfi. Ganin yanda mai motar ya dakata shima da alama fitowa zaiyi ya sata sake mata key tabar wajen da saurin dan ba wannan ne a gabanta ba yanzu. Tana hango zagin da mai motar ke mata cikin daƙuwa da wanda wasu ke mata na gefen titi. Oho basu bane a gabanta. Furucin Uncle Yousuf ne ke mata kai da kawo. Ji take kamar ta koma su canja asibiti sai dai ta riga kuma tace su Sha'aibu su sameta a can. Sannan yanda uwar ke nuna yarinyar na cikin mawuyacin hali maganar sakaci daga gare ta ma bata taso ba, dan a yanzu al'amarin su drivern ta ya shafe a zuciyarta yanda zata yaga rayuwar mijin matar nan kawai take ƙullawa. A wannan fanin ba'a gayyacesu ba ma taka rawa suke balle sune da bikin. Ai rawa sai kalar wadda sukaso takawa wlhy..... "Da gaske dai Uncle You na asibitin nan? To mi ha kawoshi?". Ta faɗa a fili tana parking idanota akan motar Uncle Yousuf dan babu ta yanda za'ai motocin gidansu su ɓace mata. Cikin rashin sanin abinda take buƙatar sani ta fito a motar. Sai da ta leƙa motar Uncle Yousuf ta tabbatar babu kowa a ciki sannan ta bar wajen zuwa cikin asibitin. A reseption kuwa suka haɗu da Uncle Yousuf ɗin. Karan farko a rayuwa taji bazata iya haɗa ido da shi ba, tsoron ma haɗuwar tasu take yi. Musamman kuma yanda ya zuba mata idanun nasa duk sai ta nema daburcewa. Shi ya fara ɗauke idanunsa da ga kanta yana kai wayarsa da aka kira kan kunne. Hakan ya bata damar nufar inda ake yankar kati, sai dai kuma fa ko sunan yarinyar bata sani ba ma fa ashe. Cikin ɗan yarfar da hannu da juyawa gaba ɗayanta tai facing ƙofa ta ke faɗin "Ouhhh! Saurin banza ma ashe nake". Dai-dai nan motar ƴan sanda mai ɗauke da matar nan da yayarta da yarinyar suka iso. Shigowar Musa ya sata sauke ajiyar zuciya, shi ya sanar da nurses cewar akwai mara lafiya a waje kafin ya ƙaraso gareta. Kallo ɗaya da Lulu taima yarinyar ya sata rumtse idanunta takalminta har yana gullewa sai da ta dafe kantar reseption ɗin....... "★"★ ∆ ★"★" "Ranka ya daɗe yaron nan fa daka tada hankalinka kansa ba wani ɗan kowa bane face wani mutum da ake kira Malam Mika'il Idris Mawashi a anguwar fagge. Shi kansa mahaifin nasa a iya layin nasu kawai aka sanshi balle shi. Kuma da gaske drivern yarinyar ne kwata-kwata bai ƙulla sati huɗu da fara aiki gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi b....." "Kace Alhaji wa?!!". Alh. Baita yay saurin tarar numfashin yaronsa da suke kira Goga a kamar razane da jin sunan Alhaji Isma'il Jiƙamshin. Bashi kawai ba hatta Hon. Nakowa da ke tare da shi dan tunda suka baro gidan MM Atik Kumo da ya basu aro anan gidan hutawar Alh. Baitan suka ƙarasa kwanan nasu. Shine tun da farar safiya kuma suka nemi babban yaronsu na bangar siyasa Goga suka sakashi binciko wanene Smart ta hanyar ɗan bayanai da suka samu ga Nadiya wadda itama ta samune ga Lulu randa taje saloon shagonta.... "Alhaji Isma'il Jiƙamshi nace ƙwarai da gaske oga. Dan shine mahaifin ita yarinyar ma ai." "Babbar magana ƴarsa ta cikinsa?". Hon. Nakowa ya faɗa wani irin abu mai ma'anoni da yawa na tsirga masa tun daga saman kai har tsakkiyar ƙafafunsa. Cikin tabbatarwa Goga ya gyaɗa masa kai. Tare da masa ƙarin bayanin da zai gaskata hakan duk da shi bai san dalilinsu na jinjina sunan ba tunda shi dai a ɗazun yaga hankalinsu akan yaron yake ba ita yarinyar ba. "Kaga jeka". Honorable Babale ya faɗa cikin katse masa tunani. Dai-dai Goga na miƙewa ya sake faɗin ka jiramu a waje nan zamu nemeka." shi dai da to ya amsa musu ya fice kamar yanda suka buƙata. Yana kuwa fita Hon. Nakowa ya firta, "Tabɗi jan inji mata. Dama ƴar iskar yarinyar nan ɗiyar Isma'il Jiƙamshi ce? Haba shiyyasa bata zubar a banza ba." sai kuma ya wani ƙyalkyale da dariya alamar hakan ya masa daɗi ƙwarai da gaske. Shima Alh. Baita dariyar ya fara. Sai kuma ya buga ƙafa da faɗin, "In kere na yawo zabo na yawo tabbas faɗar masu iya magana watarana za'a gamu. Honorable Please kira mana Hon. Misau mana. Dolene ai wannan shagalin da shi". "Ƙwarai ma kuwa". Cewar Hon. Nakowa yana wani bula-bula da babbar riga wajen laluben wayarsa. Cirota yay tare da yin danne-danne ya kai kunnensa...... Tofa masu karatu wata sabuwa kenan. Mi'a haɗin Daddy kuma da su Honorables?🤔. ∆★∆★∆★∆ Tun bayan wucewar ɗan nasa yake ta faman kai kawo a lafiyayyen office ɗin nasa. Abubuwa da yawa ne ke masa sukur-sukur a brain game da buƙatar autan nasa a karo na biyu. Tabbas zai fi kowa farin ciki da ƙulluwar wannan auren dan koba komai dai Mawaddat ɗiyar ƴar uwarsa ce Mawaddat. Ƙanwarsa mafi soyuwa garesa a duk cikin ƙannensa. Wadda yasha bama sirrin al'amuransa batare da tunani ko jin ɗar ba har ALLAH ya ɗauki ranta. Zai kasance mai yin farin cikin ganin jininsa da nata sun zama abu ɗaya. Sai dai kuma matsalar itace Isma'il. Isma'il shine babban bakangizo mai razani da ya gitta a tsakkiyar wannan ƙaunar zumunta mai cike da ababen burgewa ga duk wanda zai iya jin asalinta da wanzuwar ta. Dan tarihin ratsawar Isma'il a cikin labarinsa dana ƴar uwarsa uwa ɗaya uba ɗaya ya juya akalar waccan ƙayataccen labarin zuwa ɗimautacce mara armashi a yanzu. Ata wani fanin kuma kamar zai zo da sabon armashin kansa da kansa dan labarin zai canja ne da ga na shi da ƴar uwarsa zuwa na shi da Isma'il Ibrahim Jiƙamshi mijin ƴar uwarsa da ƴarsa. Ƴarsa da yasan yana matuƙar ƙauna fiye da komai a rayuwa. Kafin yau da faruwar matsalar farko na tusguɗewar aure tsakanin Mawaddat da Tajuddeen labarin ba a haka ya tsarashi ba, sai dai yana ganin wata dama ce da zai masa editing dan ya zauna dai-dai da zamanin nan na 2023 a ajiye wancan ƙarnin dan ya koma tsohon yayi. Ya wani lumshe idanu da dunƙule hannunsa ya ce, "Yess!! Sulaiman Sufi Ado Garko kai mai nasara ne akoda yaushe. Isma'il Jiƙamshi sabon game, sabbin players and sabon stadium ka zama cikin shiri". Wata sabuwar kuma dai🤔. ★★★★★ Duk da a yanda take jin matuƙar gajiya bata huta ba har sai da doctors suka rufu akan yarinyar nan da lamarinta ya taɓa duk wanda ya ganta a cikin asibitin. Dan hatta Uncle Yousuf tuni ya ajiye batun takaicin Lulu gefe da shi akai komai na ganin likitoci sun tsaya a kanta. Abin tausayi ita uwar ma zuciyar ta bushe ko kukan zahiri ta kasa sai na zuci. Ganin komai ya natsa dan ana neman uku na rana ma Uncle Yousuf ya kai dubansa ga Lulu da alamunta suka nuna gajiyarta matuƙa. Dan sai faman yamutse fuska take. Tausayi ta bashi, dan haka ya cigaba da kallonta a kaikaice cikin tausasawa da mata addu'ar shiriya akan halayenta marasa ƙyau. Isowar Ahmad wajen ta sakashi maida hankali garesa. Fuskarsa da murmushi yay ma Lulu magana, amma sai ta amsa masa a ɗan ɗage. Bai damu ba dan ya santa ya san halinta. Hasalima ya taɓa nuna sonta amma ta taka masa burki lokacin tana farkon dawowarta da ga Uk. Uncle Yousuf da yanda tai masa ɗin ya bashi takaici ya harareta, sai kuma ya maida hankalinsa ga Ahmad ɗin da ke faɗin, "Yaya ya farka, doctor ɗin ma ya sallamemu dan ya matsa zaije gida. Kasan Mawashi fa sam bai son asibiti." Murmushin Uncle Yousuf yay, cikin yanayin tsokana ya ce, "Kai haba kamar wani yaro ko mace". Dariya Ahmad yayi, dai-dai nan Smart ya fito a wani ɗaki da ke kusa da inda suke. Coach riƙe da hanunsa kamar wani ƙaramin yaro sai ɓata fuska yake. Dan da gasken fa bai son asibiti shi sam a rayuwarsa. Kuma bai san allura. Yanzu ma ba ƙaramar badaƙala akasha ba kafin ai masa shine ma Ahmad yay fushi ya fito. Ilai kuwa hararar Ahmad ɗin yayi tare da ɗauke kansa duk a lokaci guda, cikin rashin sa'a ya saukesu akan Lulu da tai kicin-kicin da fuska saboda kasancewar Ahamd a wajen, ita ala dole kar a kawo mata raini, dan duk wanda ya taɓa furta cewa yana sonta ko ya nuna basa ƙara shan inuwa ɗaya kuma. Ƙoƙarin janyewa yake sai kuma yay dai-dai da ɗagowarta cikin shirin miƙewa tabar wajen. Ta wani yamutse fuska fiye da yanda take sai kace wadda taga kashi. Shima ƙara tsuke tashi fuskar ya ɗanyi tare da ɗauke kansa gaba ɗaya irin bai ganta ɗin nan ba ma.... "Ga Aliyu nan babu lafiya sai ki masa sannu. Dama ina son ki gama da wannan kai kawon ne muje ki dubashi ashe ma zasu sallamesa yanzu". Uncle Yousuf ne yay maganar cikin katse hanzarin Lulu dake niyyar barin wajen abubuwa masu yawa na mata kai da kawo musamman ganin drivern nata a nan. Dakatawar tai, sai dai ta kasa cewa komai sai ɗan hararsa da take ƙasa-ƙasa. "Wai nikam bada Mawaddat nake ba?!". Uncle Yousuf ya faɗa cikin ɗan kaushin murya dan ya san taurin kanta na tsiya da gadara. Sosai taji haushin hakan, amma babu yanda zatai dan Uncle Yousuf ne. Ta ɗan sake ɗagowa ta kallesa, a taƙaice ta furta, "ALLAH ya bada lafiya". Coach ne ya amsa da "Amin". Cikin murmushi. Shi kam a zuciya ya amsa mata. A zahiri kam ya ɗauke kansa gefe kamar bai san da shi take ba. Sosai ta sake tunzura da salon rainin nasa. Tana mai tabbatar ma kanta a zuciya sai ta koya masa hankali da sauke masa wannan girman kan nasa. Batare da ta sake kallon kowa ba ta ce, "Uncle You ni na koma Office. Uncle Hameed ka gaidamin Aunty Rukayya sai nazo gaisheta". Coach yay ɗan murmushi da faɗin, "Zan sanar mata idan da gaske kike Daughter. Dan na sanki ke da sabgoginki marasa ƙarewa." karan farko da ta saki sassanyan murmushinta da kan ƙawata ƙyawun fuskarta, sai dai batayinsa sai ta gadama. Kai Ahmad da zuciyarsa tai wani irin tsargawa ya ɗauke gefe. Dan Lulu cikakkiyar mace ce da kan iya jan hankalin mafi yawan maza musamman irin matasanmu na yanzu masu fifita ƙyale-ƙyale ga mace fiye da nagarta. Sai kuma ka kwasa ka kai gida ka samu fanko ce ko addininta bata sani ba sai duniyar kawai aka saka a gaba da son birge al'ummar cikinta.... Suma a tare suka fito su huɗun, Coach da Ahmad da Smart suka shiga motar Ahmad da ya koma ya ɗakko. Uncle Yousuf kuma ya shiga tasa motar dan Lulu kafin su fito ma har ta bar asibitin. Babu wanda ya sake bi takanta. Godiya Smart yay ma Uncle Yousuf sosai tare da su coach ɗin ma gaba ɗaya. Da ga haka kowa yaja motarsa. Har gida suka kaisa. Ahmad yay masa rakkiya har cikin ɗakunan kasancewar ba baƙonsa bane ɗakin dama. Bai wani zauna ba saboda Yayansa dake jiransa a mota. Yay masa ALLAH ya ƙara lafiya ya tafi.......✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣0️⃣ .......Bayan yay sallar la'asar barci ya sake sha har kusa da magrib batare da kowa yasan yana a gidan ba. Dan sanda su Ahmad suka maidosa basu ga kowa a ƙofar gida ba. Wanka yay da alwalar magrib ya fito. Yanayin yanda yake jin jikinsa babu ƙarfi ya sashi yin sallarsa a ɗaki. Bayan ya idar ya fita zuwa cikin gidan. A kallo ɗaya zaka iya fahimtar baida lafiya ƙarfin hali ne kawai. Sai dai hakan bai hanashi leƙa duk ɗakunan gidan ya gaida su Mama ba. A ɗakin Umma ya samu babban yayansu Salim yazo gidan shima. Sama-sama suka gaisa Salim ɗin na wani cika da batsewa shi adole mai naira a gida. Ko'a jikin Smart dan shi ba wannan shirmen ne a gabansa ba. Yana juya baya zai fita Salim ɗin da Umma suka raka bayansa da harara. Oho baima san sunai ba shi dai. A falo ya samu ƙannen nasa duka. Sai Nasreen dake ta faman tsalle-tsalle ita da autar Aunty Amarya. Gaisheshi suka shigayi, ya amsa yana zama tare da ɗan dafe kansa da har yanzu bai gama saki ba. Ammah da tun shigowarsa take kallonsa ta ajiye littafin addu'oin da ke a hanunta da faɗin, "Baka da lafiya ne Hydar?". Hannun ya janye da ga goshinsa ya ɗan furzar da iska. "Kaina ne ke ɗan ciwo kaɗan kawai Ammah, na kuma sha magani ma. Ina yini". Maimakon amsawa sai ta cigaba da kallonsa cike da nazari. Ganin yanda ta kafesa da ido ya sashi duban Hawwah cikin son kauda hankalin Ammah ɗin ya ce, "K babu wata damuwa dai ko?". Kanta ta jinjina masa itama da ɗan damuwar ganin yanayin nasa. "Ba komai Yaya Hydar. Sai dai kamar ba ciwon kan bane kawai ke damunka. Ka wani zabge a lokaci ɗaya kamar wanda ya kwanta ciwo." Baiyi mamakin jin furuci nata ba. Dan a duk lokacin da ciwon ya bugesa ba ƙaramar fyaɗa yake masa ba. Ya ɗan sake furzar da iska yana tashi zaune da ƙyau da kamo hannayen su Nasreen. "Ciwon kai ne kawai kin san bai min da wasa". Badan sun gamsu ba dai suka yarda da hakan. Maryam ce ta kawo masa abinci da faɗin, "Ko sai kayi sallar isha'i". Nan ma iskar ya ɗan furzar da duban kular abincin. Yasan dai shinkafa ce dan ya ga Salim na ci a wajen Umma. Shi kuma sam shinkafa bata da farin jini a wajensa sai dai kawai ya cita dan yunwa. "Ai banama jin zanci abincin nan ɗauke kawai. Ko kuna da ƙullin kamu ki ɗan dama min kaɗan". "Eh akwai. Dama na kunun gyaɗa da Ammah tasa aka markaɗo ɗazun ko shi za'a dama makan". "Yauwa dama min shi ɗin kawai bara naje massalaci na dawo"... Ana idar da sallar isha'i ya sake dawowa. Anan yasha kunun gyaɗar da Maryam ɗin ta dama masa Ammah harda badawa a sayo masa ɗanyar awara dan tasan yana so sosai, kasancewar bata da yawa duk kafin ya dawo har an soya. Kusan ma tare suka cinye awarar da Nasreen da ke ta faman zuba masa surutu. Murmushi kawai yake mata cikin ƙarfin hali. Ammah dai da ke ɗan kallon tv duk tana lure da shi. Cikar agogo ƙarfe tara yasa Amma maida channel zuwa NTA, su Maryam ba wani son kallon labaran suke ba sai dai dole. Musamman ma Asma'u. Tashi yay ƙoƙarin yi shima sai dai kanun labaran suka ja hankalinsa. Inda rahoton farko ya kasance akan yanda shari'ar matashin nan Emanuel da aka kama a anguwar Yakasai akan lalata yara ƙanana maza da ya ɗauki tsawon shekaru uku yanayi. Kusan wata huɗu kenan ana tafka shari'ar sai a yau ne aka yanke masa hukuncin bisa jajircewar lawyer ɗin da ke tsaye akan bibiyar hakkin yaran da al'amarin ya shafa. Har tsakkiyar kansa yaji saukar muryarta tamkar a gabansa take kamar ko yaushe. Yanda take magana cikin nuna takaici da kuma jin daɗin samun nasara a shari'ar ya sashi kasa ɗauke idonsa ga tvn. Tambayar da ɗan jaridar yay mata akan miyasa a duk irin waɗan nan cases ɗin in dai tana a cikinsa da wahala bata samu nasara ba, anya ba tana saye bakin alƙalan bane ba ta bayan fage. Ƙaramin murmushi da ke sake fidda loɓawar kumatunta duka biyu ta saki tare da yamutse fuska kamar yanda ya santa musamman idan tanajin masifa. Cikin izzar nan tata ta bama ɗan jaridar amsa da faɗin, "Mi zaisa sai na sayi alƙali akan abinda yake gaskiya. Ashe ma karatun da nai akan harkar shari'a da wahalhaluna sun zama a banza kenan in har sai na sayi alƙali akan gaskiya ta. Nasarata itace gaskiyata. Dan bana tsayawa mutum sai na tabbatar da gaskiyarsa. Na kumayi alkawarin cigaba da yaga mutunci da rayuwar duk wanda ya kasance bunsuru mai halayen dabbobi akan mutuncin yaran mutane. Dan ni duk wanda zai iya ƙwatar mutuncin yarinya ta ƙarfi ballema wadda take ƙanƙanuwa bashi da wani suna a gareni face Dabba alade. Yanzu shi wannan da na kai ƙasa ma ai yafi matsayin alade a gareni bamma san mizan kirashi ba. Shege ya baro yankinsa yazo yana ɓarna a namu yankin saboda suna ganin muna haihuwar yara mu saki a titi kamar bamu san ciwonsu ba. Indai akan harkar fyaɗe ne nai alƙawarin ni Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi sai na hana waɗannan aladun shan ruwa da numfashi cikin salama. Dan nan gaba kaɗan abinda suke lalata yaron mutanen da shi zan koma datsewa da almakashi ƴan ƙaniya. Idan aure kuke so uwarmi kuke jira da bazakuje kuyi ba ko ku tafi gidajen karuwai Mtsowww!!". Ɗan jaridar ya ce, "Turƙashi. Da alama dai Barrister Mawaddat Jiƙamshi ta fusata a wannan karon, masu halin binsiraye sai ku kama kawunanku, inba haka ba za'a sake maimaita gilli da girma bayan wanda akasha da ƙanƙanta. Sai dai a yayin da wannan zantuka na Barrister wasu ke nuna goyon bayanta wasu ƙalubalantarta suke musamman akan zance gilli da zata fara da kanta. Dan haka a yinin yau zantukan barrister suka ɗauki ɗumi da zagaye kafafen yaɗa labarai harma dana yanar gizo aketa tafka mahawara. Ballema da wasu ƙungiyoyin mata masu yaƙi da wannan ɗabi'a ta fyaɗe suka fito muraran da cewar sumafa suna bayanta. Dan zasu sayi nasu almakasan su fara sakawa a jakuna dumin tayata aikin gillin. To ALLAH dai ya ƙyauta, kowa rai yayma daɗi ai baran mai shi ne. Shi dai wannan gashi zai ƙare shekaru talatin cif a gidan kaso bisa tasa mummunar aƙidar mai muni, tare da biyan maƙudan kuɗin da za'a fuskanci lafiyar yaran da ya ɓatama rayuwa". "ALLAH yay ma wannan yarinya albarka da iyayen ma da suka kawo ta duniya". Furucin Ammah a bazata ya maidosa hankalinsa. A tare Hawwah da su Asma'u suka amsa da amin. Har Asma'u na faɗin, "Ammah nima in sha ALLAHU lauya zan zama. Wlhy tun randa na fara ganin matar nan kan case ɗin nan nake jin ƙaunarta da sha'awar nima na zama kamarta....." (Ba Amin ba a ɓoyayyar halayyarta) ya faɗa a zuciyarsa yana miƙewa batare da ya ƙarasa jin zancen Asma'un ba. Sallama yay musu ya fito acewarsa zai sha maganin ciwon kai ne ya kwanta. Sun masa addu'ar samun lafiya, yayinda Ammah ta dakatar da shi da faɗin yazo ta kama masa kan. Gabanta ya dawo ya zauna. Ta kai hannun nata saman goshinsa da ke da ɗumi har yanzu. A hankali ya sauke ajiyar zuciya da har ta iya jiyosa, sai dai batace komai ba dan tun ɗazun zuciyarta ke bata kodai lamarin nasa ne ya motsa bai son faɗa, ko kuma yana son ya motsa ɗin. Sosai tai masa addu'a yanata faman sauke ajiyar zuciya kafin ya miƙe yana jin wata nutsuwa ta musamman na ratsa masa jini da ɓargo. Koda ya koma ɗakin ma magungunan da malam ya bashi ya shashsha sannan ya kwanta. Maimakon barcin sai abinda ya gani a tv ya shiga dawo masa tiryan-tiryan. Shi yama rasa a mizai fassara wannan yarinya. Ita dai gata nan rabi mutum rabi muna mutum. Sai dai kalaman nata na yau sun matuƙar tasiri garesa har yana haɗasu da na jiya data dinga faɗa cikin shirmen buguwar ita ba ƴar iska bace. Bawai ya gamsu da hakan bane. Dan babu ta yanda za'ai irinta mai ƙwalewa da kayen maye ta iya furta ita ƙillatacciya ce ya yarda. A yanzu hakan ma wani sashe na zuciyarsa na kallon kalamanta na ɗazunne kawai a gurbin fuska biyu irin na halayyar ɗan adam na yanzu. Ya ɓoye zahirinsa na mutumin banza, ya shiga gaba-gaba wajen bayyanama duniya shi na kirki ne na ALLAH. Guntun tsoki yaja da lumshe idanunsa yana fatan barci ya ɗauke sa..... ★★★ ★.★.★★ Tabbas a daren jiya yanda yaga rana haka yaga dare dan ko sau ɗaya bai rintsa ba. Sai faman bulbulama cikinsa hayaƙin cigarette da yay tayi dana shisha. Baya taɓa neman abu ya rasashi, haka ma bai taɓa harar mace sau biyu ba ta zille masa sai a kanta. Duk da ɓacin ran da ya tsinta kansa dalilin rasata a jiya bai ji ko ɗigon sha'awarta ya ragu masa a rai ba. Sai ma ƙaruwa yay yana sake azalzakarsa da sake tunzura buƙatarsa. Neman hanya ta uku ya tsunduma a tunani, sai dai zuciyarsa ta rabu gida biyu. Ɗaya na tabbatar masa ya nema aurenta kawai itace hanya mafi sauƙi. Ɗaya na tabbatar masa bazata amince ba, dan haka kota halin ƙaƙa kawai ya kore ƙishirwarsa, kai koda sakawa a sace masa itane. Ganin ya rasa makamar riƙewa sai kawai ya yanke shawarar neman shawarar abokinsa. Gabanin asuba yay kiransa, bugu biyu kuwa aka ɗaya dan shima a lokacin yana cikin club ne a Abuja..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣1️⃣ ........."Mtsoww! Kaifa baka da aiki sai gantali, a ina kuma kake haka irin wannan lokacin?". "Kai mai maganar a ina kake? Kujimin sa ido. Kodan kaje Kano kai ka koma ɗan gargajiya". Ƙaramin tsaki Mm atik yay da faɗin, "Ɗan iska banda time ɗinka. Nifa magana mai muhimmanci na kira muyi, ka ɗan fita gefe Please nasan kana nan nane da cingam gal ɗin nan taka". "Naji, na matsa ɗan shiga sharo, ina saurarenka". Ɗan tsaki MM Atik yayi, dan harga ALLAH ya tsani budurwar abokin nasa da tabi ta kanainayesa ta hanashi rawar gaban hantsi. Cikin ture batunta ya ce, "Akan yarinyar nan ce dana faɗa maka. Plan ɗin mu na jiya fa ya rushe bata shiga tarkon ba". "Whart! Wai kana nufin ka aiwatar?". "Eh mana yau ɗin nan ma, amma sai....." ya zayyane masa komai da ya faru. Da ga can Arman yay ƴar dariya da faɗin, "Wai driver? To ko dai shima yana hutawar ne?". "Mtoww bana jin hakan gaskiya. Dan randa na fara haɗuwa da ita na gansa. Yanda ta yarfashi ma sai ya baka tausayi. Kawai dai irin mutanen nan ne masu shegen shishshigin tsiya. Nidai yanzu manta bani mafita". "Ni dai mafita ɗaya na hango maka nasan kai kuma baka buƙatarta". "Waccece? Please tell me!". "Aure!". "Mtsoww auren ƙaniya. Nima ina tunanin haka, sai dai banda shiri gaskiya na zama da mace yanzu, ban san takura kai ma ka sani...." "Ka tsaya nakai ƙarshe mana". "Oh sorry ina jinka". "Abinda nake nufi bawai auren nata zakai ba. Tunda ka riga ka ƙwallafa ranka ka zama cingam boy kuma ita bazata samu ta sauƙi ba kawai kasa su Dad gaba aje maka neman aurenta....." "Baka da hankali! Dad fa? Kasan waye Dad kuwa?!". "Calm dawn mana my man. Lamarin fa duk lissafine. Yanda Dad keda alfarma na tabbatar sun san juna da babanta tunda kace itama ƴar manya ce. So da zarar magana ta shiga kai kuma sai kaita jan ra'ayinta harka samu cikar burinka. Daga haka mu ƙirƙirar mata laifin da shi Dad ɗin da kansa zai ce bazaka aurenta ba". "Woow! Woow woow my dear wannan salon yayi kuma zai ƙayatar. Sannan ita kanta zan firgita lissafinta tasan ba irinmu ake ja a ƙasa ba. A safiyar yau ɗin nan zan zauna da Dad, nasan zai matuƙar ɗaukar abin da muhimmanci tunda dama burinsa kenan shi da Mom. Kai dai ALLAH ya barka da cingom gal taita ƙarar maka da ruwan kai bye". Ya yanke wayar yana wani jin matuƙar farin ciki tamkar ya samu Lulu ƙamshi ɗin ya gama ne. Ni ko na ce, "Hummm!" ★★★ Kamar yanda Alh. Baita da Hon. Nakowa suka girgiza da jin Mawaddat ɗiya ce ga Alhaji Isma'il Jiƙamshi haka shima Hon. Misau yay matuƙar girgiza da batun. Dan abune da ko'a lissafin hasashe basu taɓa kawowa ransu ba. A take suka zauna teburin shawara. Dan kuwa tabbas wata dama ce a yanzu tazo hannunsu akan Alhaji Isma'il Jiƙamshin. Kuma lokaci ne na ɗaukar fansa da zai goge tarihin baya labarin yazo da salon alƙalamin da sune zasu zama masu rubuta shi. Tsaf suka kammala tsara komai a yanda suke buƙata. Fatansu kawai nasara da kuma sake sabon bincike dan ƙara riƙe hujjoji masu ƙarfi musamman akan Alhaji Sufi Garko da suka yanke shawarar tunkara a farko. Dan tabbas babban ɗaurin huhun goro suka shirya yima uban da ƴar gaba ɗaya dan su kasance gaba ɗaya a tafin hannunsu. Basu sa wasa ba tun a ranar suka nema appointment ɗin ganawa da babban ɗan kasuwar, kuma ƙusa a ɓangaren siyasar arewacin kasar musamman ma Kanon ta dabo Alhaji Sufi Ado Garko. Tsoho da kuɗi kenan abokin tafiyar yara, manyan kuwa baba suke kiransa dan ya kere ya kuma zarce koda a tsaransa. An tabbatar musu yaje Umrah sai dai nan da kwanaki biyu idan ya dawo washe gari su shigo. Sun samu wannan damar ne dalilin shaƙama babban yaronsa kuɗaɗe masu kauri, sai kuma mulki da Hon. Nakowa da Hon. Misau ke riƙe da shi wannan ma babban makami ne..... ★★★.... Ga Alhaji Sulaiman Sufi Garko ma ya gama shiryawa tsaf domin tunkarar mahaifin nasa game da auren Tajuddeen da Mawaddat. Dan a wannan karon ya ɗau aniyar koda yardarta, ko babu sai wanan auren ya ƙullun. Dan ya gama tanadar kalaman da zai tsara mahaifin nasa da su tsaf komai ya tafi dai-dai. Tajuddeen ya samu cikar burin shima ya samu nashi..... ★★★.... A ɓangaren Lulu ƙamshi da bata san mi suke ba gaba ɗaya hankalinta na kan case ɗin yarinya da akaima fyaɗe ne. Dan anata neman mijin matar amma an rasashi wai ya gudu yabar gari tun a randa yay abun. Wannan takaicin ne ya taru yay mata yawa ta tada hankalin su Sha'aibu ɗan sanda dama na duk wanda ke mata aiki idan irin wannan case ɗin ya taso. Hatta Daddy bata barsa ya huta ba. Ga takaicin Smart yaƙi dawowa aiki itako ta gaji da tuƙi dan sunata zirga-zirga. Shiko Uncle Yousuf ne yace ya zauna gida ya huta har sai jikinsa yay masa ƙarfi. A washe garin kwana na biyu da take saka ran dawowar Grandpa ɗinta da ga umra duk da tarin ayyukanta haka tai wancakali da su ta shiga tawagar ƴan tarbarsa a airport dan ya kwana biyu baya Nigeria, saboda daga uk ganin doctor ɗinsa ya wuce Saudiya Umrah. Tana kewarsa dan tana matuƙar so da ƙaunar kakan nata daya haifi mahaifiyarta da bata sani ba sai a hoto. Shi takema kallon uwa ga shi kuma shine kaɗai ya rage mata a kakanninta dama. Shima kuma a karan kansa yana nuna mata tsagwaron soyayya kasancewar ta ɗiya ga Mawaddat dinsa da ya rasa dan ita kaɗai ya taɓa rasawa a cikin ƴaƴansa shiyyasa yake matuƙar tausayin Lulu. Ƙarfe kusan sha biyu jirginsu ya sauka. Duk da hango ƴan uwanta jikokin Alh. Sufi Garko da tai su Tajuddeen da sukazo tarbarsa suma ƙin fitowa tai tana daga motar har sai da taji ance jirgin da ya taso da ga Saudiyan ya sauka sannan ta fita. Sanye take cikin gawn ta material mai taushi da santsi da sukai matuƙar mata ƙyau da fidda mata ƙyaƙyƙyawar surarta kamar wata ƴar tsanar roba. Ɗaurin kanta da Amrah (Hussaina) tai mata yayi ƙyau ya kuma rufe mata gashi, sai ta gaba kaɗan da aka zamashi ake iya ganinsa baƙi siɗik a kwance, Kasancewar a ɗaure yake da ribbon sai yay tilluwa a cikin ɗankwalin da aka rufesa da shi ruf. Siririn mayafi kalar material ɗin ta ɗora a kafaɗa babu zancen yafawa. Sai dogon takalmi kamar koyaushe duk da kuwa ita ɗin doguwa ce amma bacan ba tsaka tsaki. Ƙaramar handbag ɗin hanunta ta sake gyarawa da gilashin idonta da ya sake ƙawata kwalliyar tata duk da kuwa a fuskarta babu ko ɗigon kwalliya bayan hoda dan itafa bata kwalliya, sai lips glose data saka a lips ɗinta kaɗan. Yanda take taku kamar wata tarwaɗa da sautin da takalmanta ke badawa ga ƙamshin turarenta data bulbula ya sata janyo hankulan mutane gareta musamman na kusa da ita. Sosai numfashin Tajuddeen ya dinga kaikawo a ƙirji har ta ƙaraso garesu. Ya haɗiye busashen yawun da ya kasa wuce masa a maƙoshi yana ɗan sakin murmushi. Ɗauke kanta tai kamar bata gansa ba, sai ma yatsu biyu data ɗaga musu a taƙaice tare da faɗin, "Hy girls and boys". Duk wanda yasan Lulu a family ɗin yasan ba kanwar lasa bace, ba kuma wani take ragawa ba. Duk da mafi yawansu sunada labarin tushen asalin arzikin mahaifin nata da ga kakansune wani bai isa furtawa ba tai masa wankin babban bargo ita babu ruwanta. Yanda tai musu gaisuwar cike da raini ya zafi wasu musamman ma matan amma babu wanda ya nuna, to ita bama ta tsaya sauraren amsawar tasu ba tuni tai gaba, dan a dai-dai nan Alhaji Sufi Garko ke fitowa da ga jirgi gefensa p.a ɗinsa ne da shima zai iya kai sa'annin su Daddy. Lallai ya tsufa kam, damma harka irin ta masu hannu da shuni mai wahalar sha'ani. Amma irin wannan tsoho ai kamata yay ace yana zaune gida jikoki zagaye da shi yana hutawa kawai. Cike da ɗoki da farin cikin murmushi mai bayyana haƙora da ke da tsada a fuskar Lulu dan kafin ka gansa ka yara ta nufi kakan nata ta rungume. Shima tashi fuskar ƙawace da murmushin ya tarbi abarsa yana mai farin ciki da jin kewarta har cikin ransa. Sai da ta gama nata farin cikin sannan sauran yaran suma suka matso garesa su Tajuddeen. Suma ya nuna jin daɗin ganinsu dan yana son ƴan jikokin nasa da a yanzu duk suka zama manya samari da ƴammata har ma da masu aure, dan su Lulu kusan sune ƙanana ma duk da dai suma akwai waɗanda suka girma. Da ga haka aka ɗunguma zuwa gida, inda Lulu ta tubure motarta zai shiga dole kuma akai hakan dan kowa yasan rigimarta original ce. Yanzu kam a hankali take tuƙin dan Alhaji Sufi yayi gargaɗi. Daga shi sai ita ne a motar, dan haka taketa masa hira shiko yan biye mata. Tausayinta yake ji fiye da kowa a cikin zuri'arsa saboda maraicinta, ga kuma ƙaunar da yakema mahaifiyarta itama ya shafeta. A gidan ma koda suka iso sai suka samu ƴaƴansa maza da mata da ke cike da gidan duk dai akan dawowar tasa. A duk sanda akai irin wannan taron da wahala kaga Lulu batai kuka ba koda a ɓoye ne saboda jin buƙatar mahaifiyarta itama. Yanzu ɗin ma da ƙyar take iya danne hawayenta, tama ƙi shiga gidan, tana ganin ƴaƴansa sun janyesa ta zame jikinta ta gudu. Tuƙi take tana hawaye da jin kewa mai tsanani, tasan Mommy uwa ce a gareta, amma da gaske tana buƙatar ɗumin mahaifiyarta koda sau ɗaya ne inda ace hakan zai yuwu, sai dai tasan har gaban abada bazai yiwun ba kuma. Gefen titi ta gangara a hankali ta kashe motar ma baki ɗaya ta lafe cikin kujerar idanunta lumshe tai shiru, so take tai kuka amma tana ƙoƙarin hana kanta hakan. Bata cika son shan komai da rana ba musamman a lokacin aiki, sai dai a yanzu babu abinda tafi buƙata kamar tasha ɗin. Duk yanda taso hana kanta taji shan kawai take buƙata. Cikin rawar jiki ta jawo handbag ɗinta, faudanta ta zaro tare da buɗeta acan ƙasa ta ciro wata takarda da'aka naɗa kamar ƙullin magani. Tana warwareta sai ga ƙwayoyi a ciki. Gaba ɗaya kusan fin biyar duk da ƙananu ne sosai ta afa batare da neman ruwa ba ta haɗe abinta tana wani sauke ajiyar zuciya. (Kamar wadda ta haɗu da uwar tata da take nema😔🤦. Ya rabbi ka shiryemu ka shirya mana zuri'a ka rabamu da mummunar ƙaddara😭🙏)...........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣2️⃣ ........Motar taima key ta cigaba da tafiya duk da ta fara jin kanta ya ɗauka. Da ƙyar ta iya kai kanta office saboda abinda tasha ɗin ya fara aikinsa. A yanda ta shiga duk da bawai tana layi bane yasa mutane da yawa ɗan binta da kallo. Office kawai ta faɗa tare da maidashi ta rufe harda saka key. Tai jifa da handbag ɗinta da key da takalma har ma da mayafi da ɗan kwali. Zama tai jikin kujera ta dunƙule jikinta waje guda tana mai tura kanta data dafe da duka hannu biyu tsakanin ƙafafunta. Surutai takeyi ƙasa-ƙasa irin wanda idan ba kusa da ita kake sosai ba bazaka taɓa iya fahimta ba... _(Kai jama'a shaye-shaye baiyi ba. Shaye-shaye kan zubar da mutuncinka kowane matsayi ka taka. Yana maidaka baya komai ƙarfin ikon ka. Yana ƙasƙantar da kai komai darajarka. Ga lafiyarka kaima da ɓarnar kuɗi. Miyasa ƴan uwa? Mike birgemu? Mike ruɗarmu?. Kuɗi? Ƙawaye? Abokai? Samari? Gata? Kokuwa son zuciya?. Idan duk sune mu tabbata masu ƙarewa ne kamar ba'ai ba. Masu zama labarine kamar basu zo ba. Shaye-shaye wafce mana dukkan muhimman damammaki yake na cigaban rayuwarmu ta duniya da lahira. Kuduba ku gani, duk shekaru irin na Mawaddat bama tasan minene addininta ba, duk da tarin damammakin rayuwa da ALLAH ya bata wannan illar ɗaya take ta shaye-shaye da ke tare da rayuwarta na ƙoƙarin maidata baya. Tun tana ganin tana kiyayewa akan aikinta gashi ta fara kuma a cikin lokacin aikin, mi kuke tunani? Wataran aikin ma sai ta gagara yinsa gaba ɗaya. Da ga sanda ta rasa wannan damar kuma shike nan ta ƙarasa rushewar baki ɗaya sai jiran ta fara bin bola kuma duk da gatan ta😭. ALLAH ka shiryemu ka shiryar mana da zuri'armu da duk masu wannan mummunar ɗabia)._ ★★..... Bayan sallar la'asar Daddy da Uncle Yousuf suma suka shiga jerin ƴan sannu da zuwa ga Alhaji Sufi Garko. Ya nuna farin cikin ganinsu. Dan mutum ne da ya san mutuntawa. Kallo yake musu suma irin na ƴaƴa tun kan aurattayya ta shiga tsakanin ɗiyarsa da Daddy balle yanzu ga Mawaddat ta ratsa duk da babu ɗiyar tasa data zama sanadi a duniya. A hirarsu ne ma suke jin cewar Mawaddat ce ta ɗakkosa da ga airport, yana ƙyautata zaton ma har yanzu tana a gidan tare da ƴan uwanta. Daddy yaji daɗin hakan har Uncle Yousuf ma kansa. Basu nemeta bata suka cigaba da hirarsu hankali kwance. Shigowar Alhaji Sulaiman (mahaifin Tajuddeen) ce ta saka Daddy yin shiru, sai kuma ya dubi Alh. Sufi Garko da suke kira da Baba cikin girmamawa ya ce, "Baba inaga bara mu wuce ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne". Alh. Sufi ya tsatstsare Daddy da idanu batare da ya amsa ba, sai kuma ya maida dubansa ga ɗansa Alh. Sulaiman da ya koma can gefe zai zauna. Cikin bada umarni ya ce, "Isma'il koma ka zauna". Babu musu Daddy ya koma ya zauna ɗin. Ya maida dubansa ga Alh. Sulaiman da faɗin, "Kaima zonan". Gaba ɗayansu a gabansa sukaje suka zauna kowa na hararar ɗan uwansa kamar wasu ƙananan yara. "Ku yanzu kuna ganin wannan rayuwar bazaku ajiyeta ba. Ko a tinaninku har yanzu ku yarane? Ku duba gashin kawunanku furfura duk ta gitta a ciki. Tunda kun gagara faɗamin matsalarku a tsahon shekarun nan ni bazan cigaba da damuwa da sai na sani ba. Sai dai ku sani idan har abinda ya shafeku kuka bari ya shafi zuri'arku bazan yafe ba. Ku shaida hakan ko bayan ƙasa ta rufe idanuna ne". (Anzo wajen) cewar Alh. Sulaiman a zuciya. Dan haka ya gyara zama cike da makirci ya sake raunana muryarsa. "Baba ni ba laifina bane, tunda kowa shaidane na biyo hanyar da zamu sasanta da shi a shekarun baya amma ya koma bayan fage ya zuge yarinya komai ya sake rushewa. Shine ya sakama ransa ni maƙiyinsa ne kawai. Shiyyasa naso haɗin auren Tajuddeen da Mawaddat dan ya tabbatar ba hakan bane ba. Kuma ko a yanzu in har zai amince ya cire komai a ransa ni a shirye nake komai ya zama labari. Mu kuma dunƙule ƴaƴanmu waje guda matsayin ma'aurata dan ƙara danƙon zumincinmu". Wani irin kallon ɓacin rai Daddy ke masa. Sai dai baice komai ba. Alh. Sulaiman da ke masa kallon ƙasa-ƙasa ya saki wani irin makirin murmushi da kashe masa ido ɗaya. Ƙara tunzura zuciyar Daddy tai amma sai ya danne dan jin Baba ya fara faɗin, "Ni kaina zanso wannan haɗin zumincin, zan kuma so ya zama sanadin canja wannan gabar taku. Sai dai kuma bazan so ya rikiɗe daga manufarmu ya koma abinda bashi muke fata ba zumincin ya taɓarɓare ma fiye da yanzu...." "Amma Baba ai yaran suna matuƙar son junansu. Dama tun farko matsalarmu ce ta tilastasu haƙura a wancan karon ma". Alh. Sulaiman ya faɗa yana sake sakin makirin murmushi. Baba da ba ganin abinda ke faruwa yake ba ya kai dubansa ga Daddy da baice komai ba. "Isma'il bakace komai ba. Abinda ɗan uwanka ke faɗa gaskiya ne?". Murmushin mugunta Daddy dake ƙulla murtanin da zai maida ga Alh. Sulaiman ya saki. Cike da sake girmamawa ga surukin nasa kuma ogansa ya jinjina kansa. "Baba duk ina saurarensa. Sai dai na tafi wani tunani ne, kenan Mawaddat ƙarya tamun ko kuwa rashin jin nata ne ya sata kawo min wani a matsayin miji alhalin suna tare da Tajuddeen har yanzu..." "Miji?". Alh. Sulaiman ya faɗa kamar a ɗan razane. Shiko Baba murmushi yayi da faɗin "Miji Mawaddat ɗin ta fitar?". "Eh Baba. Dan dama dawowarka muke zaman jira muzo maka da batun. Saboda yanata ma damuwar turo magabatansa amma ina dakatarwa da cewar har sai ka dawo tukunna". "Wlhy ƙarya kake Isma'il! Wannan makirci ne ka ƙulla dan kar Mawaddat ta auri Tajuddeen, an gaya maka tsoronka nakeji wai ne da na gagara ɗaukar mataki a kanka tun a baya". Alh. Sulaiman ya faɗa yana miƙewa zumbur. Gaba ɗaya falon suka zuba masa ido. Sai kuma duk ya daburce dan fahimtar yana neman yin ɓaran ɓarama fa. "Ka ɗauki mataki a kansa! A wane dalili Sulaiman?". Baba ya katse shirun. Kame-kame Alh. Sulaiman ya fara, hakan ya bama Daddy damar sakin murmushin mugunta. Sai kuma ya dubi Baba. "Baba ƙyalesa kawai shirmensa ne. Kasan shi Sulaiman idan ya fusata akan abu baida fahimta. Sannan ya iya sakin duk maganar da tazo masa a baki koda ba hakan bane a ransa. Ni dai ba ƙin haɗin auren Mawaddat da Tajuddeen nake ba. Kawai shashancin da tayi ne na kawo min wani matsayin miji da har na sanar da nawa dangin dama jiranka kawai muke ka dawo a tsaida biki alhalin tana tare da Tajuddeen kuma ne yasa ma harna faɗa. Amma ayi haƙuri ni zanje ga babanta Yousuf mu sameta a nutse na mata tambayoyi dan nasan halinta bajin magana take ba. Kaga idan Tajuddeen take so ni bazan hana ba, sai nasan dabarar yi wancan ya janye a rabu lafiya mutuncin kowa bai zube ba...." "Mizai hana w kirata yanzu ayita ta ƙare". Cewar Alh. Sulaiman. Shiru kamar Baba bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da faɗin, "Ku dukanku kunzo da shawara mai ƙyau kuma duk na gamsu da maganarku. Sai dai muyi haƙurin goben sai a zauna a nutse kan maganar. Amma yanzu ina son a kiramin Mawaddat da Tajuddeen". Sosai hankalin Daddy ya tashi, amma ya danne a ransa yana mai addu'ar ALLAH yasa kada Mawaddat ta watsa masa ƙasa a ido. Dan shifa bazai taɓa yarda ya haɗa zuri'a da Sulaiman ba. Shi kansa Uncle Yousuf zancen Yayan nasa ya sakashi a ruɗani. Duk da yasan akwai ƴar tsamar da har yanzu bai san tushen ta ba tsakanin ɗan uwan nasa da Alh. Sulaiman bai san dalilinsa na ambaton wani ba matsayin Mawaddat ta kawo bayan yasan ba hakan bane ba. Kusan a tare suka saki ajiyar zuciya shi da Daddy lokacin da ɗan aiken ya dawo ya tabbatar musu ai Mawaddat ance ta tafi tunma ɗazun. Alh. Sulaiman kuwa bai so haka ba. Amma baice komai ba, sai dai a ransa yana ƙudurta duk Daddy yayi ya gama a wannan karon sai Mawaddat ta zama matar Tajuddeen..... 😂Anayi muna cin tuwon masara miyar kuka🤪. ★★..★★ Yau gaba ɗaya a gida ya yini saboda tun daren jiya Uncle Yousuf ya ce masa karfa ya fito aiki yau ɗin ya bari har sai yaji ƙarfin jikinsa. Hakan ya saka shi yin zamansa tunda dama sunyi faɗa da ogar tasa. Ɓoye kansa yay a ɗaki ya sha barci, hakan yasa babu wanda yasan yana gidan ballema ya tuhumesa tunda bai sanar musu abinda ya samesa ba. Bayan sallar la'asar gaba ɗaya kuma sai zaman gidan ya gunduresa. Hakan ya sashi miƙewa ya kimtsa. Yayi ƙyau cikin ƙanan kayan duk da shi bawai ya saka don kwalliya bane ba. Ƙamshin turarensa yake mai sanyi da sakama zuciya nutsuwa. Sai da ya fito ya fara tunanin inama ya dace ya nufa? Duk da har yanzu yana jin jikinsa babu kuzari sosai. Rashin mafitar ina ya kamata ya nufa ya sashi kallon agogo, yasan yanzu bata tashi aiki ba, bara ya gwada zuwa idan ta huce sai ya maidata gida kawai, yafi ya tafi yawo mara dalili. Napep ya tare ya shiga. Zuwa yanzu gaba ɗaya yanayinta ya sake birkucewa, ta zame ribbon ɗin data ɗaure dogon gashinta da ya sauka har kafaɗarta. Sosai idanunta sunyi jazur haɗe da kumburowa. Surutai take ita kaɗai da gaba ɗayansu na bege ne ga mahaifiyarta. Sai kuma zagin mijin matar nan da yay fyaɗe tare da ɗaukawa kanta alƙawarin koya masa hankali da duk ire-irensa. Hawaye take da murmushi a lokaci ɗaya, yayinda ta ƙurama hoton mahaifiyarta da ta ɗakko saman decks ɗinta dake a cikin wani ɗan ƙyaƙyƙyawan fram ita da Daddynta, hoton anyisa ne bayan aurensu a ƙasar Mexico lokacin sunje honeymoon. Su dukansu suna sanye ne a cikin ƙanan kaya suna kallon juna da murmushi mai nuna tsantsar soyayya da sukema juna. Hannunta ta kai ta shafa fuskokinsu, sai kuma ta rungume hoton tana mai komawa kwance rigingine ta ƙurama p.o.p ɗin office ɗin ido. Ƙwayar tata ce ta fara gaya mata shirme ga mahaifiyarta a wajen cikin farin tufafi tana mata kallo mai kama da tausayi.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣ .......Bai san ainahin Office ɗin nata ba, sai dai ganin motarta a harabar wajen ya sake tabbatar masa da tananan bata wuce ba. Tunanin zaman jiran fitowarta yayi, hakan ya sashi samun wajen zama a gurin securitys. Bayan gaisuwa a tsakaninsu bai sake kula kowa ba ya shiga sana'ar tasa ta game ɗin ball a waya. Biyar dai-dai babu alamar zata fito, tun yana ɗan ɗagowa ko zai hangota har ya fara sarewa ganin biyar da rabi har ta gota ma. Ga mafi yawan ma'aikata sun wuce dan motarta da wasu biyu ne kawai suka rage a harabar wajen. Ɗaya da ga cikin security ɗin ne ya dubesa tare da faɗin, "Abokina wanda kake jira har yanzu bai ƙaraso bane? Dan shida dai-dai ake rufe wajen nan fa". Wayar ya ajiye tare da ɗagowa ya dubi security ɗin fuskarsa a ɗan sake, sai dai ba murmushi yake ba. "Wadda nake jira tana ciki dan ga motarta nan, nima ina tunanin ko lafiya har iyanzu bata fito ba". "Kana nufin Madam Mawaddat Jiƙamshi?". Kai ya jinjina masa alamar ita. Shima security ɗin cikin nuna jimami ya ce, "Inaga dai yau aiki ne yay mata yawa gaskiya, dan a kullum zakaga idan bata zama ta farkon tashi ba to zata zama ta biyu. Nima kaina nayi mamakin rashin fitowar tata yau duk da dai naga wani aiki tasa a gaba kwana biyun nan mai muhimmanci. Amma bari na duba maka maybe bata san kana zaman jiranta bane". Kafin Smart ya samu damar cewa wani abu security ɗin yay gaba. Minti kusan uku sai gashi ya dawo. "Abokina inagafa kamar akwai matsala". "Matsala kuma? Tami fa?". Smart ya faɗa ƙirjinsa na bugawa da sauri-sauri. Amma sai ya dake abinsa kamar babu komai. Security ɗin ya cigaba da faɗin, "Bawai matsalar bace a zahirance, na samu sakatariyarta ce kawai zaune cikin damuwar wai tun ɗazun data fita ta dawo ta shige office ta rufe kanta har yanzu bata fito ba. Ta mata knocking kuma yafi sau ashirin batako ji motsinta ba sai yanzu babu jimawa taji maganarta kamar cikin surutai". Ƙirjinsa ne yaji ya ƙara bugawa, ya kai yatsunsa biyu saman goshi ya ɗan murza. Basai ya nema ƙarin bayani ba yasan wani abu tasha. Sai dai bai taɓa tunanin har a wajen aikinta ma tana shan abubuwan nan ba. Ɗagowa yay idanunsa har sun kaɗa da ɓacin rai. "Kozan iya shiga office ɗin nata?". Ya tambayi security ɗin. "Ah eh mana mizai hana. Ai gara a je a duba mike faruwa ko?". Miƙewa kawai yay, security ɗin yay masa jagora har office ɗin. Sun samu sakatariyarta tsaye jikin ƙofar tana knocking da faman kiran "Aunty! Aunty Please ki buɗe ko kiyi magana dan ALLAH." "Kinga ƙyaleta idan da key bani". Ya faɗa cikin dakewa. Cikar kamala da kwarjininsa yasa Zainab jin bazata iya musa masa ba. Duk da kuwa yau ne karo na farko data taɓa ganinsa anan ɗin. Sai kuma ganin harda security ya ƙara mata ƙarfin gwiwa. Muryarta a sanyaye ta ce, "Sai dai na duba ko zanga extra keys dan ta shiga da key ɗin ciki". Kansa kawai ya jinjina mata, ta koma wajen table ɗinta domin bincikawa. Shi kuma ya jingina da bango tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya lumshe idanunsa. Kusan mintina huɗu tana ta binci-bincike har dai ta samo keys ɗin da ƙyar. Gabansa tazo ta miƙa masa cikin girmamawa. "Thanks" yace a hankali yana amsa. Koda ya buɗe ƙofar bai yarda ita da security ɗin sun biyosa ba sai da ya leƙa. Saurin rumtse idanunsa yay tare da yo baya, cikin ɗan furzar da huci ya gyara yanayin fuskarsa yanda zasu fahimcesa. "Inaga bata da lafiya ne, kun san halin ogar taku kuma maybe bata buƙatar kowa ya sani shiyyasa taya rufe kanta a ciki, ku barni da ita kar ku samu rabon faɗa kuma". A yanda yay maganar dole ne ka gamsu, dan haka security ɗin yay murmushi dan kuwa masifar Mawaddat kowa ya santa, idan sukai sanya wajen buɗe mata gate kota saka wani aikin kai mata wasa sai ta tsefeka tas. Balle ma Zainab da tafi kowa sanin wacece uwargijiyar tata. Sallama security yay ya fita, Zainab kuma ta koma mazauninta ta zauna duk da ya kamata ace ta tashi, amma dai tafi yarda taga sai Mawaddat ta fito lafiya sannan. Ƙofar ya sake turawa ya shiga ya maida ya rufe tare da jingina jikinta kansa a ƙasa bai yarda ya sake kalloba. Kamata yay ya kira Zainab, sai dai baya son ta ganta a yanayin. Har yanzu tana kwance a tsakkiyar sofas ɗin da aka shirya dan zama bayan ta zamanta da wanda ke a gaban table ɗin nata. Ta ture Centre table ɗin tsakkiyar kujerun tana kan carpet ɗin gashinta yaɗan barbaje. Har yanzu idanunta na kallon p.o.p ɗin office ɗin, hira take da mamanta da idanunta ke gani ko nace ƙwaya take siffanta mata. Hawaye share-share a fuskarta ga murmushi. Tsaiwarsa gurin shiru na wasu sakanni ya sashi ɗan jin soki burutsunta. A karo na farko ya ɗaga kansa ya dubi p.o.p ɗin shima jin tana faɗin, "Mammah karki sake tafiya ki barni kinji. Kiyi zamanki muyi hirarmu, inma bazaki min magana ba ni zan na miki murmushinki ya wadatar dani. Kar kiyi kuka a kaina bana son ganin hawayenki ki bari Please ki bari..." ta faɗa cikin wani irin sanyin murya sai kuma ta fashe da kuka. Da farko bai ɗauki surutun nata komai ba sai shirme irin na masu shaye-shaye, sai dai Mammah da take ambata ya tsaya masa a zuciya. Ganin yana ɓata lokaci ya sashi furzar da ƙaramin iska tare da cigaba da takawa cikin office ɗin, ƴan dube-dube yake yi duk da baiyi tsammanin zai iya dacewa da abinda yake neman ba. Dama baiyi tsammanin ganin ba ai. Fita yay inda sakatariyarta ta take, tana zaune dai har yanzu sai dai yanzu da waya a hannunta, dan tunda ta turama Uncle Yousuf text take tsammanin shigowar kiransa amma shiru kake ji. "Ko zamu samu Hijjab?". Firgigit ta dawo a hayyacinta dan jin saukar deep voice ɗin sa a bazata cikin kunnen ta. Sake maimaita mata yay ganin kamar bata jisa ba. Kanta ta gyaɗa masa da sauri tana nufar inda ta jiye hijjab ɗin sallarta ta ɗakko masa. Amsa yay kawai ya koma ciki. Yana ɗan sauke ajiyar zuciya, yanzun ma bai yarda ya kalletan ba ya warware hijjab ɗin tare da kaiwa duƙe gabanta. Karan farko na rayuwarsa ya ambaci "Mawaddat!" cikin ɗacin murya da tausasawa, sai dai acan ƙasan makoshinsa zaka iya fahimtar jin zafinta. Ƙarfin muryarsa da yanda yay kiran nata ya saka shigar sautin cikin kunnenta a bazata. Kamar wadda aka farkar a cikin barci ta juyo idanunta da suka sake girma da ɗan juyewa kansa. "What!" ta faɗa a zabure tana tashi zaune sosai. Sai kuma ta kalla sama da ɗaga hanunta. "Mammah ki jirani dan ALLAH". Kallonta yay jin abinda ta sake faɗa, hakan sai yay dai-dai da yanda ta zuba masa juyayyun idanunta fuska a yatsine tana wani ƙwaɓeta ta ce, "Who are you? Miya kawo ka nan?". Tsaki ya saki tare da ɗauke idanunsa ya yafa mata hijjab ɗin a jiki. Hannun da takai cikin yar kokawar ture hijjab ɗin ya buge. Da sauri ta janye tare da faɗin "ouch!" saboda zafin da taji. Baibi takanta ba ya ƙarasa saka mata hijjab ɗin batare da ya yarda ya taɓa mata jiki ba. Wata muguwar harara ta watsa masa ta ƙara kai hannu zata cire hijjab ɗin ya daka mata tsawa. "Idan kika cireshi na rantse sai na canja ma fuskarki kammani da mari!!" Sosai tsawar tasa ta ratsata. Gaba ɗaya sai ya sake juye mata a cikin idanu kamar wani bahagon zaki. Kuka ta saki da duban p.o.p ɗin ta ce, "Mammah kinga yana min ihu ko. Bana son shi yanada girman kai". Bakinsa kawai ya taɓe da cigaba da tattare kayayyakinta data barbaza a office ɗin waje guda, a zuciyarsa yana faɗin (aike naki kan ƙarami ne). A dai-dai nan aka turo ƙofar aka shigo. Juyowa yay da ɗan sauri dan a tunaninsa sakatariyarta ce, amma sai ya ga Uncle Yousuf ne. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke dan gaskiya yaji daɗin zuwan nasa. Dama sai faman ƙullawa da kwancewar ta yanda zai fita da ita a office ɗin yake. "Barka da yamma Alhaji". Murmushin ƙarfin hali Uncle Yousuf ya saki yana jinjina kasa, sai kuma ya maida dubansa ga Lulu da har yanzu ke sambatunta irin na rashin kasancewa a hayyaci. Idanu ya ƙura mata da kamar wanda ya zurfafa kansa a tunani, maganar Smart ta sakashi yin firgigit. Cikin ƙoƙarin shanye abu mai ƙona zuciya ya sake dubansa da murmushi. "Aliyu ya jikin naka? Kai da nace yau karkazo aiki shine kuma ka fito?". "Naji sauƙi ai Alhaji. Kasan zaman gidan isar mutum yake yi shiyyasa na fito. Nafito ɗin kuma na rasa ina zan nufa shine kawai nace Bara na duba ko bata tashi aiki ba sai na maidata.." Uncle Yousuf da ke jin zuciyarsa babu daɗi ya kai zaune yana mai tallafo haɓarsa. Kusa da shi ya nunama Smart da ke kallonsa. Babu musu ya zauna sai dai a kujerar gefensa. Ya fahimci irin damuwar da Uncle Yousuf ɗin ya shiga, dan haka sai shi ya ɗan sassauta tasa cikin furzar da ƙaramin huci. "Alhaji damuwa bata zama maganin matsala ba, sai dai ta zama sanadin ƙirƙirar sabuwar matsala wa rayuwa....." "Hakane Aliyu. Amma ka duba fa kenan har a wajen aikinta ma tana sha? Hakan kuma na nufin duniya ta jima da sanin halin da Mawaddat ke a ciki amma mu bamu sani ba". "Banajin hakan gaskiya Alhaji". Idanu kawai Uncle Yousuf ya tsira masa, dan haka office ɗin yay shiru sai surutan Lulu kawai ke tashi cikin sambatun maye. Kiran da ya shigo a wayar Uncle Yousuf ɗin ce ta katse shirun nasu. Kamar zai share sai kuma dai ya cirota a aljihu. Daddy ne, yasan jiransa ya keyi dan sun zauna zasuyi magana ne Zainab ta tura masa saƙo shine ya taho hankali tashe. Wayar ya ɗaga tare da kaiwa kunnensa. Muryarsa a sanyaye ya ce, "Yaya!". Daddy da tun fitowar ƙanin nasa ya kasa zaune ya kasa tsaye ya ce, "Yousef miya faru da ita?". "Babu komai yaya ka kwantar da hankalinka dan ALLAH. Dan nama tadda Aliyu har yazo ma shi...." "Waye Aliyu? Ko drivern ta?". "Eh yaya." "Ka faɗa min gaskiya Yousuf abubuwan tasha ko?". "Yaya dan ALLAH k..." "Yousef please". Daddy ya faɗa cikin tare numfashin Uncle Yousuf ɗin. Cikin sakin ajiyar zuciya ya ce, "Hakane. Amma dan ALLAH ka kwantar da hankalinka, gamu nan tahowa gidan ma". Daga haka ya yanke wayar. Shi ya ɗauki Lulu kamar ranar, Smart kuma ya fita da kayayyakinta a hannu. Zainab da gaba ɗaya hankalinta ya tashi da ganin yanda aka fiddo auntyn tata ya kalla. "Ki rufe office ɗin ki sameni waje a maidaki gida". Daga haka yay ficewarsa. Kamar yanda ya bata umarni hakan tayi, lokacin data fito har Uncle Yousuf da ya saka Mawaddat a motarsa yana ƙoƙarin ficewa a gidan. Yayinda smart ke tsaye yana jiranta. Batare da yi mata magana ba ya shiga motar, itama sai ta buɗe ta shiga kusa da shi. Har gida ya kaita abisa kwatancen da tai masa, godiya taita masa cikin girmamawa, karan farko yay mata guntun murmushi cikin jinjina kai ya ja motar ya wuce........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 ??𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣4️⃣ .......Idanu kawai Daddy ya zubama Mawaddat hawaye na kwaranya saman dattijuwar fuskarsa. Itako sai surutai take musu. Sai ta kalla Daddy tayi ta kalla Uncle Yousuf shima tayi. "Yaya kukan nan fa bashi da wata ma'ana, addu'a itace kawai. Sannan bazan gaji da faɗa makaba ka bada kaso mafi yawa akan shiga wannan yanayin nata. Sai dai kawai muyi ƙoƙarin gyara kuskuren a yanzu. Ga kuma wannan matsalar data kutso kai, duk da dai ni da za'a bi ta tawa da kawai a aura ma Tajuddeen ɗin tunda mun san dai yaron nan bashi da wani aibu a rayuwarsa....." "Yousuf matsalar ba daga Tajuddeen take ba da ga mahaifinsa ne. Nasan abinda baka sani ba akan sulaiman sani na haƙiƙa. Kamar yanda na faɗa maka tun a wancan karon Tajuddeen an kwaɗaita masa son Mawaddat ne kawai da manufa, sai dai shi yaron ya afka batare da sanin manufar mahaifin nasa ba, ko kuma dama yana son nata shiyyasa Sulaiman yay amfani da wannan damar wajen sake jan zuciyarsa da tunanin hakan zai bashi nasara akaina." "To amma yaya ai shine zai zauna da ita ba Mahaifinsa ba. Indai har mun tabbatar da yana son nata kamar haka banga aibun aura masa ita ba. Na sani ka sani Mawaddat bata kula kowa, ta ina shi mijin daka ambata gaban Baba zamu samar da shi? Dan kasan dai in har babu wannan mijin to dolene Mawaddat ta auri Tajuddeen tunda baba da dangin mahaifiyarta duka sun ɗauki abin da muhimmanci bakuma zasu taɓa bijirema umarnin mahaifinsu ba kamar yanda suka saba". "Duk nasan da wannan Yousuf. Kuma nima damuwata a yanzu shine ta yanda zamu samar da mijin koda ace na wucin gadi ne kafin ƙura ta lafa." "Wucin gadi kuma?". "Yes wucin gadi, dan ba zan taɓa yima yaranmu ko ɗaya auren dole ba. Auren ma da jini irin na Sulaiman mai shirye da manufofi masu yawa da sai anyi auren ne sun fara bayyana zaka fara dana sani kai kanka". Shiru kawai Uncle Yousuf yay yana kallonsa, shi kam gaba ɗaya ma a wannan gaɓar ya shiga ruɗani zai ce. Ya kasa fahimtar ainahin abinda ke tsakanin yayan nasa da yayan matarsa da a shekarun baya suka kasance shaƙiƙan abokai da ko ƙuda baya iya jin sirrinsu. Anya kuwa yayansa baya ɓoye masa wani babban al'amari da ya kamata ace ya sani..... "Assalamu alaikum". Sallamar Smart a ƙofar falon ta katse tunaninsa. Daddy ne ya amsa tare da bada izinin shigowa dan ya shaida muryar yaron. Akan Lulu da ke kwance a ƙasa barci na neman rinjayar idanunta tana kokawar hanashi ya fara sauke idanunsa. Kaudasu yay duk da sanye take da hijjab ɗin da ya saka mata har yanzun. A nutsensa ya gaishe da Daddy, tare da ajiye key ɗin motar hannunsa. "Sannu da ƙoƙari fa, ALLAH ya saka maka da alkairi kaji". Daddy ya faɗa a karo na farko. Ɗan murmushi Smart yay cikin jinjina kai. "Babu damuwa ai Alhaji. Nima na gode. Bara na wuce gida". Godiya Daddyn ya sake masa, tare da zaro kuɗaɗe masu yawa da ga aljihunsa ya miƙa masa. Kallon kuɗin Smart yay da sake sakin murmushi mai ma'anoni da yawa sai kuma ya girgiza kansa. "A'a Alhaji nagode sosai. Amma bazan amsa ba, albashin da ake biyana ya wadatar dani ALLAH ya ƙara buɗi". Mamaki matuƙa Daddy ya shiga, dan haka ya kalla Uncle Yousuf da tun shigowar Smart ɗin baice komai ba. Kafaɗa ya ɗage masa alamar haka yake. Ai Daddy kasa ƙara cewa komai ma yayi har Smart ya sake musu sallama ya fice abinsa..... ★★ *_8:25pm_* ★★ Ƙarfe takwas da kusan rabi na dare tawagar Hon. Babale Nakowa da su Alhaji Baita suka isa gidan Alhaji Sufi Ado Garko kamar yanda suka tsara. Ziyara ce ta bazata, dan haka Alh. Sufi yay mamakin zuwan nasu duk da kuwa su dukansu sun kasance yaransa ne ta fannoni daban-daban kafin yau. Sai dai duk da kasancewar wannan zuwa nasu ya kasance na bazatan hakan bai hana su sami tarba ta mutuntawa ba. Bayan sun gaisa da Alh. Sufi cikin girmamawa a matsayinsa na _God Father_ nasu sai kuma hira ta ɓalle mafi ƙarfi akan kasuwanci da siyasa. Sun ɗan taɓa hira kafin Hon. Misau ya fara bayani akan abinda ya kawosu. "Ranka ya daɗe mufa zuwan nan namu kamar gaisuwa ce da roƙon iri. Munzo mu maka Barka da dawowa da kuma yaya jiki sai kuma babbar magana mai alaƙa da son ƙulla sabon zumincin da muka san kaima zakayi farin ciki da shi". Cikin mamaki da dattijantaka Baba yay murmushinsu na manya idonsa akan Alhaji Misau. "Jeka maganarka kai tsaye Ɗan kande! kasan ni a koda yaushe nafi buƙatar abu abuɗe fiye da rufa-rufa". "Hakane Baba". Cewar Hon.. Misau cikin murmushi da sake gyara zama. Sai da ya ƙara juya zancen a ransa ta yanda zai fito da armashi sannan ya cigaba da faɗin, "Akwai wata yarinya a cikin zuri'arka da Alhaji Haruna ya gani ya kuma ji ta kwanta masa matuƙa a rai saboda nutsuwarta da hankalinta. Da farko mun shirya tunkarar mahaifinta sai kuma mukai tunanin ai baba ma da babansa. Shiyyasa muka dakata har sai yau daka dawo mukazo da ɗumi-ɗumi dan a tabbatar bada wasa muke ba". Murmushin mai cike da jin daɗi Alhaji Sufi Garko ya saki tare da faɗin, "Kai kai Masha ALLAH. Masha ALLAH, naji daɗin hakan kuma zanayi matuƙar farin ciki saboda sani da naima Haruna a rayuwa da nagartarsa. Amma wace yarinya ce wanna haka?". Yanzu kama Hon. Baita ne ya nisa shima da murmushin shinshino nasara akan fuskarsa ya ce, "Baba sunanta Mawaddat. Ƴar wajen Alhaji Isma'il Jiƙamshi. Kaga a gareku ku jikace." "To to! Ko kaine dama yake faɗa mijin data fidda ɗin? Dan ɗazun dama muke magana akan ɗan wajen Sulaiman da aka taɓa son haɗa su sai abin bai yiwu ba da yake a lokacin ba matarsa bace." Kallon juna sukai kowanne zuciyarsa kamar zata ɓallo ƙirji ta fito, sai kuma suka haɗa baki wajen faɗin, "Aiko bazai wuce hakan ba kam". Duk da maganar ta ɗan yima Alhaji Sufi Garko gingirin a zuciya sai kuma hakan bai hanashi jin daɗi ba da nuna farin cikin sa. Dan haka babu wani kwalo-kwalo ko jan magana ya tabbatar musu suje gida insha ALLAHU zuwa gobe su dawo garesa da shirinsu bayan sallar azhar zasu samu amsa mai gamsarwa. Dan ya tabbatar musu duk da shi kaka ne ta ɓangaren mahaifiya yana da nasa ƙarfin ta wani fanin ma ubane shi ga mahaifin nata shima ai. Farin ciki iya farin ciki sun shiga, dan haka suka tafi da ƙwarin gwiwar samun nasara batare da sun sha wata wahala ba. Gefe ɗaya kuma suna dariyar muguntar kama Daddy a tafin hannunsa ta inda bai zato ba ko tsammani. Ko a mota hirar da suka dinga yi kenan cike da jin alfahari..... ★★ ...... Tun bayan wucewar Uncle Yousuf da ya maida Mawaddat ɗakinta batare da ko ɗaya a cikin ƙannenta ya ganta ba shima ya shige nasa ɗakin ya kulle kansa dan samun damar yin isasshen tunani. Ƙarar wayarsa ce ta katse masa dogon lissafin da zuciyarsa tai nisa a yi. Jawota yay cikin jan ƙaramin tsaki zai kashe yaci karo da sunan _Baba garko._ Tashi yay zaune sosai, sai dai bai ɗaga ba har sai da ta yanke shi yay kiransa. Dan haka dama yake masa. Cikin girmamawa ya gaida ogan nasa kuma surukinsa. Da kulawa Baba ya amsa. Ta re da faɗin, "Isma'il ko ka fara barci ne na tasheka amin afuwa. Na kasa haɗiye abin farin cikin nan ne shiyyasa na nemeka yanzu ɗin. Ashe baƙon da kake maganar ɗazun na gida ne....." "Baba baƙo kuma?". "Eh baƙo mana Isma'il. Mai auren Mawaddat mana. Dan yanzu nan suka wuce su sarakan zumuɗin ma sun kasa haƙuri har sun kawo kansu. Ko kuma ja'irar ƴar taka ce ta turosu ma dan kasanta da gaggawa". Sosai ƙirjin Daddy ke lugude. Duk da shi sam yama kasa fahimtar Baba ɗin yanda ya kamata. Kasa jurewa yay dai yace, "Baba kai min afuwa. Wlhy ban gane akan wa kake magana ba. Dan inada tabbacin Mawaddat bata turo kowa ba kasancewar ma ni bamu zauna magana ba dan na sameta kwance a gida ma kanta na ciwo tun bayan ɗakkoka airport". "Tofa wata sabuwa kenan? Su Alhaji Baita ne fa suka sameni a daren nan kan wai Hon. Haruna Dauda Nakowa na son Mawaddat har ma sun dai-daita kansu kaima kuma kasan maganar ma. A yanzu haka ma na basu damar dawowa a gobe idan ALLAH ya kaimu da shirins....." Cikin suɓutar baki Daddy ya furta, "What! Su Alh. Ɗan-kande Baita fa kace baba?". "Eh ƙwarai su ɗin fa na faɗa Isma'il. Shin akwai matsala ne?". Yawune ya nema sarƙe Daddy, da ƙyar ya iya figo glass cup ɗin ruwa dake a bed side drawer ya kwankwaɗa. "Baba ni wlhy bamma san akwai wata alaƙa tsakanin Mawaddat da su Alhaji Baita ba sam. Sannan kuma bana jin ita ɗince ma ta turosu. Dan yaron da take so ɗin wanine daban". "Ikon ALLAH to mi hakan ke nufi?". Cewar baba. Daddy da takaici da damuwa suka lulluɓe a lokaci guda ya ce, "Baba wlhy ban san manufa ko dalilinsu nayin duk hakan ba. Danni nasan Mawaddat bata da wani alaƙa da su". "Uhhmm to kaga ina ganin mu ajiye maganar nan to. Amma ka tabbatar gobe idan ALLAH ya kaimu a wajen taruwar meeting ɗin nan kazo min da Mawaddat, idan ma zai yiwu harda shi wanda take so ɗin". Godiya Daddy yay masa. Yayinda tuni yay jagaf da zufa. Kamar wanda ya fito a wanka. Gaba ɗaya lissafinsa ya rushe shi yanzu ma baya gane komai ma. Wayar ya ɗauka yay kiran Uncle Yousuf. Ba'a ɗaga ba sai da tai gab da tsinkewa. Ko sauraren tambayar da Uncle Yousuf ɗin ke masa bai yiba. Sai ma katsesa yay da faɗin, "Yousef akwai matsala. Tabbas akwai matsala. Amma ka jirani ina zuwa gidanka ɗin yanzu". "Haba-haba yaya da kanka. Inaga ka jirani kawai gani nan zuwa". "Karka damu Yousuf kai dai ka jirani kawai. Nan ɗin zaifi sirri ". Babu yanda Uncle Yousuf ya iya dole yabi umarnin nashi yay zaman jiransa. Mintinan da basu wace goma sha ba sai ga Daddy ya iso..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣5️⃣ .......A harabar gidan ya sami Uncle Yousuf ɗin tsaye da alama shi yake jira shima. Ciki suka shiga har falonsa. Tsaf daddy ya kwashe ya sanar masa da duk abinda surukinsa kuma ogansa ya kira shi yanzu nan. Karan farko shima Uncle Yousuf ya girgiza. Duk da sam bai gane ainahin manufar shiga Daddy a ruɗani ba. Kwantar masa da hankali Uncle Yousuf ya shiga ƙoƙarin yi, amma sai Daddy ya dakatar da faɗin, "Yousuf bamu da wani lokaci isashe. Minene mafita. Dan wlhy wlhy kaji na rantse maka. Suma da wata manufa sukaje ga baba, kuma lallai dole akwai wata a ƙasa ..." "A ƙasa kamar ya?. Nifa yaya ƙara dilmiyar dani kake wlhy akan al'amarin nan, sannan ka fara bani tsoro. Dan ALLAH ka bani abuɗe mana ko zanfi sanin makamar riƙewa ta ƙwarai". "Zan baka amma ba yanzu ba Yousuf. Yanzu hanyar kuɓutar da Mawaddat da mu kammu gaba ɗaya kawai ya kamata mu nema dan ALLAH. Idan ba haka ba komai zai canja da ga yanda muka sanshi zuwa a yanda bamuyi zato ko tsammaninsa ba. Miye mafita? Wa zamu kai matsayin miji ga Mawaddat? Dan fa dole ne mu samar da wannan mijin saboda Baba baya magana biyu. Sannan duk waɗan nan mutanen suna da tasirin da zai iya zartar da hukuncin basu Mawaddat ko ina so ko bana so musamman akan abinda ya faru a baya da kuma gargaɗi da sharaɗin daya shimfiɗa mata kan duk wanda yazo neman aurenta zai bashi kota yarda ko bata yarda ba". "Hakane yaya, sai dai yanzu mu a ina zamu iya samo miji? Sai nake ga ya kamata itama Mawaddat ɗin mu tuntuɓeta ko?". "Tuntuɓar tata yana da amfani, sai dai kuma zuciyata na raya min wani abu. Mizai hana mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne". "Okay yaya kamar ya kenan?". "Yauwa abinda nake nufi anan itama mu barta a rufen kawai mu samar da mijin amma na bogi dan fatana kawai mu nunasa ga Baba dan abar zancen, ita kuma mu nuna mata hukuncinta kenan akan wannan halayyar tata, sai ta gama wajiguwa matuƙa sannan mu faɗa mata gaskiya mu kuma bata damar fidda mijin da take so. Amma yaya ka gani kai?". Uncle Yousuf da shima ya gama tsara nasa tunanin tun fara maganar yayan nasa yay wani shegen murmushi da faɗin, "Tabbas hakan yayi, kuma ina ganin mutum ɗaya ne zai iya mana wannan aikin, sai dai maganar riƙe hakan matsayin hukunci gareta ko barazana bazai taɓa canja abinda muke fatan canjuwarsa ba da ga gareta. A halin da Mawaddat ke ciki canjata na nufin bin wasu matakai daki-daki dan tayi nisan da ƙyamatar ta ko mata hargagi bazai kasance hanyar gyarata ba". "Na yarda da kai auta, shiyyasa akoda yaushe nake kasancewa a farin ciki da ƙwarin gwiwa idan kana a kusa da ni. Amma wanene shi ɗin?". "Aliyu drivern ta Yaya". Da sauri Daddy ya ce, "Haba Yousuf driver fa? Ina mudai samar da wani mai darajar da tafi tashi ko cikin yaran abokaina haka ko a cikin ma abokanka". "Yaya kenan, amma karka manta fa cewa dai ba auren za'ai ba. Zamu samar da mijin ne kawai dan ai mata kurari sannan mu toshe waccan damuwar da aka kasa a teburin Baba. To indai hakane ai kuwa shi wannan da kake ganin bai kai ba ne dai-dai da wannan shirin namu. Amma waɗan can zasu iya zamar mana ƙarfen ƙafa, shi kaɗai ne makamin da zamu riƙe, inada yaƙinin zai taimake mu wajen yakin nan har muci nasara". "Eh kuma fa haka ne gaskiya Yousuf na fahimceka kuma. Yanzu minene mafita?". "Karka damu bar komai a hannuna. Kai dai ka zama cikin shiri kawai itama Mawaddat ɗin ka barni da ita, ka koma kawai gefe ka zama ɗan kallo". Sosai daddy yaji nutsuwa da kwanciyar hankali. Yanata jerama ɗan ƙanin nasa addu'a da fatan gamawa lafiya kafin su ɗan ƙara tattaunawa yay masa sallama ya tafi. Uncle Yousuf ɗin ne dai yay masa rakkiya kusan har gida. Dan sai da ya ga shigarsa sannan ya juya ya koma yanata sakin murmushinsa da shi jaɗai ya san dalilin kayansa sai kuma UBANGIJI da ke kallon dukkanin motsin zuciyarsa. Koda ya koma gidan maimakon kwanciya sai yay alwala ya nutsu wajen miƙa kukansa da buƙatar neman zaɓin alkairi ga abinda yake ƙudirtawar duk da ba yau ne dama ya fara irin wannan addu'a ɗin ba...... Tofa Uncle You mi kake ƙullawa haka kaima😂🥱?. ★....★ A washe gari data kasance safiyar alhamis a duka ɓangarorin huɗu kowa ya tashi da shirinsa game da abinda ya kwana da shi a rai. Ɓangaren su Hon. HD. Nakowa sun shirya tsaf da shirin zuwa neman auren Mawaddat a wajen Alhaji Sufi Ado Garko kamar yanda ya basu dama. Haka ma a ɓangaren Alh. Sulaiman da ɗansa sun gama tsara komai a daren jiya domin cikar burinsa da kuma burin ɗansa Tajuddeen da ke ƙaunar Mawaddat har cikin zuciyarsa. Ɓangare na uku shine MM Atik Kumo da shima ya tunkari iyayensa da maganar samo mata da yay, sai dai ya gagara tunkararta yana son iyayen nasa su fara zuwa masa neman izinin nemanta ga nata iyayen. Sosai mahaifinsa da Mom ɗinsa suka shiga matuƙar farin ciki, dan babban burinsu dai a rayuwa shine suga auren ɗan nasu daman. Sun samu wannan damar kam bazasuyi sakaci da itaba, musamman ma da sukaji yarinyar ta fito ne da ga zuri'ar Alhaji Sufi Ado Garko da duk wani ɗan siyasa a jihar Kano ke masa kallon uba. Hakama ƴan kasuwa domin a duk ɓangarorin biyu yana taka rawar gani da tarihi bazai iya mantawa da shi ba ko bayan ransa. Rukuni na gaba sune gidan allurar da kowa ke iyo cikin ƙaton kogin domin nema, wato _Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi_. Mawaddat da tun a daren jiya ta dawo cikin hayyacinta sam bata san duk wannan babban yaƙin basasa da ake shiri a ɓangarori uku domin ita kaɗai ba. Hasalima ita ta wayi gari ne da babban shiri akan mijin matar nan da yay ma yarinya fyaɗe. Har yanzu yarinyar na asibiti cikin mawuyacin hali. Da farko ta hana ƴan jarida yayata zancen har sai ta kama shegen, sai dai a yau wani tunani datai yasa zata bama ƴan jarida damar fitar da komai, tana ganin hakan zai taimaka musu wajen kamashin. Yau da wuri ta kammala shirinta cikin wandon jeans dark blue da milk color ɗin riga. Rigar nada ɗan tsaho musamman ta baya. Ƙaramin veil ta naɗa a kanta tare da bulbula ƙamshin nan nata. Cikin takunta na yanga da izza ta fito, babu alamar jama'ar gidan wani ya tashi, sai su Iya Tabawa dake ta aikin gyaran gidan. Gaisheta suka shigayi cikin girmamawa. Hannu ta ɗaga musu sau ɗaya tai ficewarta dan bata cikin mood ɗin yin magana yau. Karo suka kusan ci da Uncle Yousuf da ke ƙoƙarin shigowa a main falour. Tai saurin komawa baya da faɗin "Sorry Papa ban san ka taho ba". "Ina zaki haka?". Ya faɗa a dake maimakon amsa maganarta ta farko. Ɗan kallonsa tai da mamaki, sai dai ganin yanda shima ke kallonta babu alamar wasa a tattare da shi ya sata maida kanta ƙasa cikin tsarguwa, dan dama dauriya take kawai, amma tun a daren jiya take ƙullawa da kwancewar ta yanda zata iya haɗa ido da shi, da kuma yanda zata shukama drivern ta rashin mutunci a wannan karon tunda har ya sake bari Uncle Yousuf ɗin ya ganta a cikin wannan yanayin..... "Baki ji bane? Ina zaki je?". Ya sake faɗa cikin katse mata tunani. Firgigit ta dawo hankalinta. Cikin in ina ta ce, "Uncle You office, amma zan fara zuwa nai magana da ƴan jarida akan case ɗin yarinyar nan shiyyasa zan fita da wuri". "Shi kuma naki case ɗin kiyi yaya da shi?". Da sauri ta ɗago ta dubesa. "Uncle case ɗina kuma? Ni ai babu abinda ya faru da ni". "Zai farun ne ai. Biyoni". Kamar wadda aka bugama guduma a kai haka Lulu ta tsinta kanta a wannan lokacin. Sai dai bata da zaɓin da ya wuce bin bayan nasa kamar yanda ya bata umarni. Duk abinda ke faruwa Daddy na kallonsu da jinsu. Ya haɗiye hawayen da ke neman zubo masa. A daren jiya ko sau ɗaya baiyi barci ba, sosai jininsa ya hau har bugun zuciyarsa ya fara canjawa. Sai da Mommy ta bashi shawarar yin karatun Alkur'ani sannan ya samu ƴar nutsuwar ganin wayewar gari lafiya. Mommy dai bata san ainahin mike faruwa ba. Amma zuciyarta na bata akan Mawaddat ne, dan a yanzu babu wata damuwa da ke neman kai mijin nata ƙasa sama da al'amarin yarinyar, bayan kuma tun farko shine yay shukar datai tsirran da ya samar da ita a haka. A falon baƙi da ke a garden kam babu abinda zuciyar Lulu keyi sai bugawa da sauri-sauri. Ga Uncle Yousuf yay matuƙar ɗaure fuska ta yanda bata taɓa gani da ga garesa ba. Zama tai jiki babu ƙari da faɗin, "Uncle gani". "Na ganki ai". Ya bata amsa shima kai tsaye yana gyara zama. Tambayar da tai matuƙar girgiza mata zuciya ya jefa mata. Babu shiri ta ɗago a firgice ta dubesa. Sake maimaitawa yay babu alamar wasa a tare da shi. "Nace wanene Hon. Haruna Dauda Nakowa a gareki? Miye alaƙarku?". "B...b...bamu da wata alaƙa wlhy Uncle". Ta faɗa cikin in ina da firgici. "Amma yaje neman aurenki ga Baba a daren jiya". "What!! Uncle You aure fa? Ni kuma Mawaddat?!". Cikin sigar harara Uncle Yousuf ya bata amsa da "K ɗin fa, bayan shi kuma Tajuddeen ma ya dawo. Dan a jiya mahaifinsa a gabanmu ya sake gabatar da zancen ku ga Baba. Nasan kuma baki manta da alwashi Baba ba na cewar duk wanda yazo neman aurenki ko da amincewarki ko babu ko da tamu ko babu zai aura masa ke. Kinga hakan na nufin a cikin biyun nan dole ne ki zaɓi ɗaya". "Wlhy Uncle You bana son kowa a cikinsu. Kuma shi tsinanne Haruna ɗin nan ni ban taɓa magana da shi ba ma balle maganar aure na rantse maka Uncle". "Ni wannan ba matsalata bace Mawaddat. Dan a yanzu haka ma Baba nacan na zaman jiranmu ni da ke da Yaya akan wannan maganar dan haka ma na dakatar da ke daga fita. Idan kuma kina da wanda kike so sai ki faɗa mana yanzu mu nemosa aje da shi gaban Baba ki kuɓutar da kanki, dan hakanne kawai zai hana Baba bama ɗaya da ga cikin waɗan can ɗin aurenki kamar yanda kika san shi baya magana biyu".........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣6️⃣ ........"Na shiga uku Uncle, ni ban shirya yin aure ba wlhy. Dan ALLAH ka faɗa mini ya zanyi?". "To ni Mawaddat taya zan san ya zakiyi. Yanzun ma na faɗa miki ne dan bana son a miki abinda nasan baki so. Dan Baba bazai taɓa canja ra'ayinsa ba a wannan karon kin sani na sani. Ga kuma Yaya wajen ƙoƙarin ganin ya kare ki sai ya sake wata ɓaranɓaramar wai kina da wanda kike so". Fuska ta kuma kwaɓewa idanunta na cika da ƙwalla. "Uncle You wlhy guduwa zanyi". "Guduwa kuma? A ganinki itace mafita Mawaddat?. To ai ina ganin dan kin gudu kinyi a banza, dan in dai Baba ne zai aurar da ke ɗin babu fashi ya kuma saka mijin taddaki har inda kika je ɗin ko shi yaje da kansa ya dawo da ke ya danƙama mijin. Kinga anyi ba'aiba kenan ko. Ni dai ina ganin kawai mu ɗauki kariyar da Yaya ya baki muyi amfani da ita dan ki kuɓuta gaba ɗaya". "Uncle wacce kenan?". "Samo wani matsayin wanda kike so kuma zaki aura. Sai dai ni da ke ne kawai muka san ba haka bane, bayan ƙura ta lafa shike nan sai ki cigaba da sabgarki, idan Baba yayi magana muce iyayen yaron muke jira dan sunce a ɗan jinkirta musu zai ƙarasa gininsa ko dai mu samo wani abu da zai ɗauke hankalin Baba da ga kanki gaba ɗaya" "Hakan yayi, to amma Uncle kasan fa baba da shegen bin ƙwaƙwƙwafin abu idan kuma ya gano fa?. Sannan ma wa zamu iya samu ya mana wannan aikin batare da an samu wata matsala ba?". "Eh kuma fa kema kinzo da maganar dubawa gaskiya. Dan Baba kam zai ma iya sawa ai masa bincike. To amma ina ganin mizai hana shi wanda zamu samar ɗin kawai ki yarda kuyi auren contract da shi, komai mune zamu tsara masa ayi auren amma bayan wata ɗaya ya rabu da ke, sai dai da sharaɗin kada kowa ma yasan ya sake ki har sai bayan wasu shekaru." Shiru Lulu tai tana auna zancen Uncle ɗin nata. Sai dai da ace tana da ilimin addini da ya kamata tai hasashen yin hakan fa zai iya zama kamar ta zurma kanta ne. Amma a maimakon hakan ita wani tunani take da ban, dan tana ƙiyasta faruwar al'amarin ne cikin sauƙi kasancewar a inda ta girma cikin turawa wannan ba komai bane yin auren yarjejeniya.. ganin yanda tai nisa Uncle Yousuf ya katseta da faɗin, "Mawaddat bamu da wani isashen lokacin dogon tunani a yanzun fa". Firgigit ta dawo hankalinta, sai kuma ta langaɓe kai cikin shagwaɓa. "Uncle You ni gaba ɗaya ma kaina ya kulle ne, dan ban san inda zan samo wanda zamuyi hakan ba". "To mizai hana ki yarda da batun Tajuddeen kawai, yaron nan yanada hankali da nutsuwa ga ilimi. Yana aikinsa sannan yana matuƙar sonki". "Uncle wlhy ni bana son sa, na tabbatar kuma bazan taɓa son shi ba. ALLAH idan aka matsamin kan na auresa zan iya halakash...." "No! no! Kar na sake jin haka. Tunda har baki sonshi shike nan kawai abar maganarsa. Mu koma kan maganar mu kawai ta nemo wanda zai zame mana makamin kuɓuta da ga Baba." "Uncle bazan ɓoye maka ba wlhy na tsani duk wani abinda zai haɗa mu'mulata da wani namiji bayan ku, balle ma ace mu kasance wai ma'aurata. Impossible hakan ya kasance dan bazan taɓa aure ba." Har cikin rai kalmar (Bazan taɓa aure ba) ta daki Uncle Yousuf, dan a karo na farko zuciyarsa ta fara hasaso masa wani al'amari mai girma dangane da Mawaddat ɗin. Dolene akwai abinda ya kamata su sani da ke ɓoye a ƙasan zuciyarta, sanin kuma na nufin haƙurin bin matakan daya dace. Wannan tunanin ya sashi cigaba da faɗin, "Mizai hana muyi amfani da Aliyu, dan yaron nada nutsuwar da bazai taɓa iya bamu ciwon kai ba koda anan gaba". "Aliyu kuma? Waye shi?". *_"DRIVERN KI"_* Fitar kalmar da ga bakinsa da zaburowar zuciyarta tamkar ragabzane a tsakanin jirgi da jirgi a sararin samaniya. Badan Uncle You bane, da bayan zaburar da tai abinda zai biyo baya shine lailayo masa zagi mai kawuna bakwai ta dire masa shi a tsaye sannan ta tisa da wanke fuskarsa da marin da sai ya hango yanda yaƙin duniya na uku zai kasance tun kafin lokacin faruwarsa. Sai dai kash furucin ya fito da ga bakin da ko harara bazata iya binsa da ita ba balle ɗaukar mataki. Uncle Yousuf da ya zuba mata idanu, sai dai a ƙasan ransa dariya ce ke cinsa yana dannewa da ƙyar yay mata nuni da kujera, tare da faɗin, "Sit mana kika wani zabura kamar wadda na faɗama mummunar magana. Nifa ba nace dole bane, shawarace kawai dan neman mafita. Amma idan batai miki ba muje kawai dan lokaci ma ya cika gashi ana jirana a office. Kije ki zama cikin shiri da yin sabon tunani akan wani tunda naga baki aminta da zancen shi Aliyu ba". Bakin data tura gaba ta buɗe zatai magana sallamar Daddy ta dakatar da ita. Alamar zip Uncle Yousuf yay mata wai kar Daddy yaji. Daddy da gaba ɗaya ya gama jin tattaunawar tasu dan tun ɗazun a laɓe yake dama sai ya sake fuskewa cikin pretending ya ce, "Wai mi ake tattaunawa ne kuka shige haka shiru?". Cikin ɗan ɗage kafaɗa Uncle Yousuf ya bashi amsa da "Sirri ne tsakanin baba da ƴarsa yaya". Dariya Daddy yayi, sai kuma ya juya hanyar fita yana faɗin, "Oh to bari nayi nan tunda ba'a buƙatar naji". A karan farko Lulu tai dariya tana mai kamo hannun Daddyn nata cike da shagwaɓa. A haka suka fito suna ƴar dariya..... Fitowarsu tayi dai-dai da shigowarsa gidan. Kamar ko yaushe sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsar jikinsa. Ƴar ramar da yay ta ciwo ta sashi zama wani fayau da shi a idon mai kallo. Cikin girmama juna ya gaisa da su baba maigadi sannan ya ƙaraso inda suke tsaye. Anan ɗin ma da girmamawa ya gaisa da Daddy da Uncle Yousuf. Lulu da ke gefensu tana danna waya tai jiran jin ya gaisheta amma sai taji shiru. Karo na farko ta ɗago idanunta ta kallesa tana mai sake tsuke fuska. Ƙoƙarin barin ma wajen yake alamar ita bazai gaisheta ba kenan. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne da takaici ya shaƙure mata wuya har taji tama kasa yin magana, sai dai yanda take binsa da wani mugun kallo ya sa Daddy farga da ita. Ya kuma fahimci miya fusatata ɗin. "Aliyu!". Yay kiran sunan Smart da ke ƙoƙarin komawa inda su baba maigadi suke. Cikin girmamawa ya amsa yana mai juyowa garesu. Uncle Yousuf da ya sha jinjin jikinsa da tunanin ɓaranɓaramar da Yayan nasa ke shirin yine yay saurin faɗin "Am yaya inaga muje na ajiyekan tunda malam Zaidun bai dawo ba, in yaso daga can sai ya sameka Office ɗin. Aliyu zuwa 1:30 ku samemu a Nasarawa G.R.A please karku makara". "In sha ALLAH Alhaji". Smart ya faɗa cikin gyaɗa kai abubuwa da yawa na masa kai kawo a rai musamman da Uncle Yousuf ɗin ya ambaci Nasarawa G.R.A. Huci ya ɗan furzar kaɗan, a yanzun ma dai bai kalla inda taken ba ya nufi motar da mai wanki keta faman gogewa alamar ita zasu shiga. Baya ya buɗe mata, batare da ya jira tazo ta shiga ba ya koma mazaunin driver ya shiga yana karanto addu'ar shiga abin hawa. Harta ƙudiri aniyar ƙin shiga, sai kuma mita tuna oho mata ta tako cike da yauƙin nan nata da yanga ta shiga. Mai wanki ya maida motar ya rufe yana jera mata addu'ar dawowa lafiya. Motar yaja suka fice, zuciyarsa cike taf da abubuwan da suka faru jiya a waya tsakaninsa da Uncle Yousuf.... A daren jiya bayan ajiye motar Mawaddat da ya kai sakatariyarta Zainab gida shima gida ya koma abinsa. Kai tsaye wajen Abba ya nufa suka gaisa, sun ɗan taɓa hira da Abban sai dai hirar batai masa daɗi ba sosai kasancewar da ga maganar Hawwah ta juye maganar aurensa. Sosai Abba ya dinga zuba masa faɗa akan infa har bai nemo matar aure ba a cikin watannan tofa shi zai nemo masa da kansa duk da ba aƙidarsa bace yima ƴaƴansa auren dole. Haƙuri shi dai yayta bashi da tabbatar masa cewa in sha ALLAHU zai kawo matar auren nan kusa. Kamar Abba ya gamsu da hakan sai kuma shigowar Umma ta sake saka Abban hayewa sama. Dan kamar wadda dama take a laɓe tana saurarensu tana shigowa sai kawai ta shiga assasa wutar kan cewar shi dai baiyi niyyar yin auren bane kawai. Inba haka ba baga yarinyar maƙwaftansu ba nan Nazifa yarinyar na matuƙar sonshi amma yaƙi saurarenta. Kallonta yay da mamaki, dan kowa dai yasan wacece Nazifa a anguwar. Yarinya ce mara jin magana dan tsabar bleaching fuskarta har yellow takeyi. Tabbas Nazifa ta jima tana nuna masa soyayya, sai dai shi bai taɓa nuna yasan mi takeyi ba. Kai shi ko magana tai masa ma da ga gaisuwa bai sake kulata. Wannan halin watsar da ita ɗin da yake yi yasa tun tana juriyar bibiyarsa har tai fushi ta daina kulashi. Amma da har abubuwa take saye ta aikoma Ammah ko ta bama su Asma'u. Nan ɗin ma dai bata samu nasarar ba dan Ammah tace ita babu ruwanta, idan yaga zai aureta bazata hana ba, za kuma ta bisu da addu'a dan koba komai yayi jihadin raba Nazifa da rayuwar banza da kowa ya shaida tanayi. Yanajin Ammah ta bada goyon baya ya samu Nazifa yay mata gargaɗi na ƙarshen ƙarni ya kuma yima Yayanta magana akan ta fita sabgarsa, shi kuma Yayan yaji haushi ya gaggaya masa magana bai kulashi ba shi dai dan ya yanke magana. Da ga ranar bai san miya faru ba bai sake ganin Nazifa ba. Amma shine dan tsabar sharri Umma ke tisa zancen a yanzu bayan shekara kusan uku kenan da ajiyesa gefe. Tuni Abba ya ƙara tujaresa da faɗa amma baice komai ba akan Nazifa, hasalima ya fahimci kamar faɗan nasa na son zama zargi ne ko minene bai dai fahimta ba. Jiki a sanyaye ya baro wajen Abba, ɗakinsa ya nufa dan bai buƙatar zuwama Amma a wannan yanayin. Ya gama cire kayansa kenan zai shiga wanka kira ya shigo masa. Yayi mamakin ganin Uncle Yousuf, sai da ya kalli agogo ƙarfe kusan sha ɗaya da rabi fa. Haka dai ya daure ya ɗaga cikin taraddadi.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣7️⃣ ........"Alhaji badai wata matsala bace ba ko?". Ya faɗa maimakon sallama da Uncle Yousuf ɗin yay masa. Murmushi da ga can Uncle Yousuf ya saki tare da gyara zamansa a kujerar falon da ya fito. "Babu komai sai alkairi Aliyu. Wata magana ce mai muhimmanci tasa na kiraka. Ina dai fatan baka kwanta ba na tasheka ko?". "Ina dai shirin kwanciyar ne Alhaji. Amma dai lafiya?". "Eh lafiya kamar yanda na sanar makan". "To Alhamdullahi Alhaji, ina saurarenka". Ɗan jimmm Uncle Yousuf yay kafin ya furzar da huci kaɗan. "Aliyu shawara nake nema a wajen ka". Cike da mamaki ya amsa da, "Alhaji shawara? Sannan kuma ma a wajena?". "Eh Aliyu. Kuma ina fatan zaka bani wadda zata fiddani da ga ruɗanin da nake ciki" bai jira cewarsaba ba ya cigaba da faɗin. "Kasan na faɗa maka an taɓa sakama Mawaddat rana da Tajuddeen ai. Amma ALLAH baiyi auren nasu ba wasu matsaloli suka gitta, mafi yawansu da ga Mawaddat ne sai dai kuma akwai ɓoyayyen sirrin saɓani a tsakanin Yaya da mahaifin Tajuddeen da shima ya taka rawar gani. So an share maganar aure kowa ya haƙura, sai dai kakanta na ɓangaren mahaifiyarta Alhaji Sufi Ado Garko ya ɗauki alwashin duk randa wani yazo domin neman aurenta koda yardarta ko babu zai amince masa ya aurar da ita. Wauta ya sata amincewa. Bayan nan magana bata ƙara tashi ba sai a yau ɗin nan a gaban Alhaji Sufi ɗin, shi Alhaji Sulaiman ya sake kawo maganar, amma Yaya yayi saurin cewar ai Mawaddat nada wanda take so........." Tsaf ya kwashe komai ya sanar masa har zancen su Hon. HD Nakowa da Daddy ya sanar masa suma sunje bayan barowarsu. Hakan ya matuƙar bashi mamaki dan tuna abinda ya faru a tsakanin Mawaddat ɗin da su Hon. HD Nakowa. Cikin kasa daure abinda ke bakinsa ya ce, "To amma Alhaji naga kamar ita da shi Honorable ɗin sam basa shan inuwa ɗaya. Taya zaije yace yana sonta da aure?". "Muma shine abinda ya ɗaure mana kai Aliyu. Shiyyasa muka kasa zaune muka kasa tsaye akan al'amurin, dan Hon. Nakowa nada ƙarfi sosai a wajen Baba, saboda yaronsa ne, hasalima shine ya zame masa kamar wani ƙashin baya a harkar siyasa." "To amma Alhaji mizai hana ku sasanta shi Alhaji Babba da mahaifin shi Tajuddeen ku aura musu juna kawai a wuce wajen". "Hakan bazai yiwuba Aliyu. Dan ita Mawaddat sam bata son Tajuddeen, ta tabbatar min idan aka aura mata shi komai zai iya faruwa. Sannan abinda ke tsakanin yaya da mahaifin Tajuddeen abune babba bawai yanda kake zaton zai sasantu cikin sauƙi bane. Kaga ko maganin ayi zumunci ya wargatse ai Gara kar a fara ko". "Hakane kuma Alhaji". "To Miye mafita Aliyu? Dan Baba fa sam baya magana biyu. In har gobe idan ALLAH ya kaimu Mawaddat bataje da wanda take son aura ba babu fashi cikin biyu dole ayi ɗaya. Shiyyasa ma na kiraka domin neman taimako. Ina son idan ban shiga huruminka ba dan ALLAH Mawaddat ta nunaka a matsayin kai ne zaɓinta, da zaran Baba ya yarda a wajen shikenan. Ni kuma zanyi ƙoƙarin ganin ta fidda miji kafin Baba ya sake magana". "Ni kuma Alhaji?!!". "Eh dan ALLAH Aliyu ka taimakemu. A yanda rayuwar Mawaddat take yanzu muna buƙatar nutsuwa kafin sama mata mijin da zai saita mata rayuwa. Ni kaina bazan so ta auri Tajuddeen ba duk da nasan mutumin kirki ne amma bazai iya control ɗin ta yanda yake so ko ya kamata ba. Sannan Hon. HD Nakowa, kai ne shedar a inda ka gansu tare, maimakon gyaruwar Mawaddat aurenta da shi sai dai ya ƙarasa lalata ta kawai, shi kuma Baba duk bai san waɗan nan halayyar ba. Amma kaga idan muka kuɓutar da ita a wannan gaɓar sannu a hankali sai irin mijin da muke fata ya samu, kai kawai ta nunakan a gobe shine kawai dan Baba ya aminta ya bar waɗan can ɗin. Amma na baka damar kayi tunani, sai dai bamu da isashen lokaci daren yau ne kawai...... "Wai kai malam ba magana nake da kai ba! Tsabar baka san muhimmancin rayuwa ba kana driving kana ma mutane tunaninka na iska!!". Firgigit ya dawo hayyacinsa tamkar wanda aka tada a barci. Sam bai san tunanin nasa har yayi zurfi irin haka ba. Gefen titi ya gangara a hankali tare da kai hannunsa saman goshi ya dafe yana mai furzar da iska. Gaba ɗaya ma ba hanyar da ya kamata yabi da su yabi ɗin ba tsabar hankalinsa bama a tuƙin yake ba gaba ɗaya. Karan farko a rayuwarsa da tunda ya fara aiki matsayin driver ɗinta ya furta mata "Am sorry". Cikin tausasa harshe kuma. Cak numfashin Lulu ya nema tsayawa a ƙirjinta. Haka ma maganar bakinta kasa ƙarasa fita tai tsabar kalmar ban haƙurin tazo mata a matuƙar bazatar da bata taɓa tunanin hakan da ga bakinsa ba kasancewar kallon da take masa mai shegen girman kai. Har ya sake tada motar da juyawa bata iya sake yin ko tari ba kamar wadda aka ɗinke ma lips. A nashi ɓangaren bai kawo komai game da shirun nata ba, a tunaninsa maganar Uncle Yousuf ce ta jiya ke damunta kamar yanda shima da ya kasance ɗan karoro kawai a ciki take neman jefa shi a ɗimuwa. Har suka isa office babu wanda ya sake magana. Kafin kuma ya fita ya buɗe mata har ta buɗe ta fice. Kallo ya ɗan bita da shi, dan duk da yau ma dai irin kayan daya tsani gani a jikin mace tana yawo kan titi ne a jikinta ɗan zoɓawar rigar da ga baya ya taimaka wajen suturta wani ɓangare na jikin nata. Janyewa yay tare da furzar da huci. Dai-dai nan Zainab ta fito ɗaukar mata kaya dan babu abinda ta ɗauka tai shigewarta. Ganinsa ya saka Zainab yin murmushi, ta risina cikin girmamawa ta ce, "Yaya ina kwana". Kalmar yaya da ta kirashi da shi ce ta sakashi maida mata da murtanin murmushin nata itama. Cike da kulawa ya amsa mata kuma. Handbag ɗin Lulu da laptop da riga ta ɗauka sai wasu tarkacen takardu, shi kuma ya fito a motar tare da kulleta ya nufi security ɗin nan na jiya dan su gaisa..... Duk yanda Lulu ta so fuskantar aikin gabanta hakan ya gagara. Abubuwa ne da yawa ke cizon zuciyarta musamman shawarar Uncle You da yace ta nuna drivern ta matsayin wanda take so a gaban Grandpa ɗinta. Kai ina a gareta wannan ai ƙasƙanci ne ma, kenan ma ya samu hanyar cigaba da kawo mata raini fiye da wanda yake son gwada mata a yanzu, dan ma dai ita tsayayya ce yana shakkarta. Kai maganar gaskiya shawaran nan na Uncle You baiyi ba sam. To amma a yanda guri ya ƙure ɗin nan idan ba shi ba wa zasu samo yay musu aikin batare da an samu matsala ba?. Wannan tambayar ita ta shiga cizon zuciyarta tama kasa iya aiwatar da komai na gabanta. Tana buƙatar shawara, gashi ƙawarta kuma Nadiya ce kawai da har take iya faɗama damuwarta. Kai ina bazata kira Nadiya ba, dan sai ta koya mata hankali. Kai anya ma bada saninta wannan tsohon kwandon Hon. Nakowa yazo neman aurenta ba? Lallai akwai lauje cikin naɗi, dan zuwa yanzu ta fara shakkar al'amarin Nadiya, ita shiyyasa fa bata ƙawa musamman da ya zam ƙawaye sun taka rawar gani suma wajen bar mata wani tabo a zuciya da har yanzu gyambonsa ke kan yin ruwa da mata ciwo. Kodai Uncle Yousuf zata kira ne tace ta fasa a nema wani? Aminta da wannan shawarar ya sata kiransa. "Lafiya dai ko Daughter!". "Uncle you ba lafiya ba, shawaran nan ne yaƙi zama a zuciyata. Kodai mu nema wani can daban yay mana aikin nan, kasan fa bana son raini". Murmushi yay da ga can har tana iya jiyo sautinsa. "Mawaddatan'warahma!". A hankali ta amsa da "Da yes papa". Dan tana matuƙar son ya kirata hakan. "Ki kwantar da hankalinki Please, sannan ku tuna bamu da wani isashen lokaci, a yanzu haka fa awowi kaɗanne suka rage mana dan za'ai amfani da ɗan break na lokacin sallah ne wajen zaman meeting ɗin kafin kowa ya koma office. A tunaninki a irin wannan tsukun lokacin wa zamu samu mai amana da hankali kamar Aliyu da zai mana aikin nan batare da wata matsala ba? Ko kina son mu ɗakko wanda zai mana baragada har Baba ya gane ya zartar miki da hukuncin auren ɗaya da ga cikin waɗan da baƙya son?". "A'a Uncle You... ALLAH idan yace sai na auri wani a cikinsu zaku iya rasani dan na tsane su". "To mafita ɗaya ce ta kufce musu shine bin abinda muka tsara. Shin kin san da yaya ma shi Aliyun ya amince zai mana aikin? Da ƙyar fa na iya shawo kansa wlhy". A zuciyarta ta ce (kuji ɗan iya, dama ya samu aka sakashi zai wani kawowa mutane iyayi. Mtsowww banda ma dai wannan Grandpa ɗin da matsalarsa shi ko'a mafarki ya isa ma na kallesa balle wani kalman so can na wofi. Bari ana gama zaman nan korarsa zanyi dan karma ya ɗauka ya samu wata damar kawo min raini.....) "Hello Mawaddat! Kina jina kuwa?". Ajiyar zuciyar dawowar hayyaci ta saki, cikin shagwaɓa ta ce, "Shike nan Uncle sai mun haɗu". Dariya yay sosai daga can bayan ya katse kiran. Dan harga ALLAH dariya suke bashi. Dama yanzu ya gama waya da Smart ɗin shima. Haka kawai sun sakashi komawa lauyan dole. Ya tsara wannan ya tsara wannan. ALLAH dai ya bashi nasara burinsa ya cika akan abinda ke ransa game da su su duka biyun........✍️ 🥱Ba abun faɗa. _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣8️⃣ .......Ƙarfe ɗaya da minti biyar ta fito da ga office saboda kiran da Uncle Yousuf yay mata da gargaɗin karfa su makara. Kamar ko yaushe babu kwalliya a fuskar tata, sai dai an toshe idanu da glass. Tabbas glasses na mata matuƙar ƙyau shiyyasa da wahala ka ganta babu shi, gashi bata saka ƙarami sai in zatayi aiki. Duk irin manyan nan ne na manyan mata masu ji da gayu. Shima ɗin dai kiran Uncle Yousuf ɗin ne ya sashi dawowa, dan tun kusan sha biyu ya wuce gida. Yanzu kam ya canja kayansa zuwa shadda ash color da tai masa matuƙar ƙyawun da har ita sai da ta saci kallonsa irin wanda bata taɓa yi ba. Dan tunda ya fara tuƙata bata taɓa ganinsa da manyan kaya ba sai yau har da su hula. Gaba ɗaya sai ya sake mata wani kwarjini da cika waje, dan haka ta sake jan girma tai tamau da fuska tare da ɗauke kai sama kamar bata gansa ba. Ita a dole kar waccan maganar tasa ya kawo mata wargi tunda Uncle Yousuf ya tabbatar mata ya sanar masa. Shima ɗin dai tasa fuskar a ɗauren take, dan baya son ta taresa da wata maganar banza, ta wani ɓangaren kuma ransa ne a ɓace, dan zuwa gidan nan da yay ya samu Umma na tujara harda yima Ammah gori akan ƙaddararsa wai a bincike wannan ƙin auren nasa sai dai idan yana samun abinda auren ne kawai zai iya bashi a bayan fage. Kenan tana nufin shi ɗin mazinaci ne. Bai san miya kawo rikicin ba, bai kuma shiga gidan ba yaji ba'asi tunda muryar Umman kawai yake ji, dama kuma yasan Ammah bazata tanka mata ba. Ganin Lulu ta dogare tana wani huhhura hanci irin na ubangida da yaronsa ne sashi jan ƙaramin tsaki ciki-ciki, batare da yace komai ba ya buɗe mata ƙofar, shiga tai fuska a yamutse, shi dai baibi takanta ba ya maida ya rufe sannan ya koma mazaunin driver. A hankali yake murza steering Lokaci-lokaci yana ɗan furzar da iskar takaicin kalaman Umma da sukai masa kane-kane a zuciya. Yayi nadamar zuwa gidan nan ma.... Kusan lokaci guda suka iso da su Daddy, dan haka Uncle Yousuf ya dakatar da shi a gate, fita yay a tasu motar yazo inda suke. Lulu da keta ɓata fuskar shagwaɓa ya kalla. "Mawaddat ya haka kuma? Maza koma gaba karma wani ya ganki". Zatai magana yay mata nunin tai shiru kawai ta koma. Fitowa tai baki a sama ta koma gaban, kusan a tare ƙamshin turaren junansu ya daki hancinansu duk da dama tun ɗazun suke shaƙar. Shi dai baice komai ba, hakama Uncle Yousuf ya koma tasu motar shima, sun samu ƙaton compound ɗin gidan cike da motoci, ya dai samu gefe yay parking. Hango Uncle ɗinta Khamil na Abuja ya sata sakin murmushi, cike da zumuɗi ta buɗe motar ta fita.... Baki ya taɓe tare da ɗauke kansa. Sai ma ya lumshe idanunsa kamar mai shirin barci tare da kwantar da bayansa a jikin kujerar yay luf... Suna shiga aka fara taron dan kamar sune dama na ƙarshen zuwa. Ana tsaka da tattauna batun Tajuddeen ɗin da Lulu da aka kira amma ta botse musu akan ita fa bata son Tajuddeen, shi ko ya marairaice fuska kamar zai fashe da kuka yanata faman mata alamar roƙo amma tai kamar bata gansa ba. Takaici ya saka Alh. Sulaiman fara zagin Mawaddat ɗin, ana hakan saƙon isowar su Hon. Nakowa ya iso falon. Damar shigowa Baba ya basu. Su ukune kamar dai jiya. Shi mai gayya mai aikin Hon. HD Nakowa da aminansa Hon. Misau da Alh. Baita. Bayan anyi gaisuwar mutunci tsakaninsu da su duk da Alh. Sulaiman yayi mamakin ganinsu a gidan nasu Baba ya gabatar da su da dalilin zuwansu cikin meeting ɗin tare da buƙatarsu. Shiru falon yay kamar waɗanda ruwa ya cinye. Sai Lulu ce ke antayama Hon. Nakowa harara tamkar idanunta zasu zubo ƙasa. Cikin katseta Baba ya kirayi sunanta. Amsawa tai tana ƙoƙarin danne fushinta. Baba da ya gama lura da duk hararar da take antayama Hon. Nakowan ya cigaba da faɗin, "Bayan maganar Tajuddeen ga Hon. Haruna. Nasan shima dai kin sanshi tunda yace kece kika turosa wajenmu kamar yanda Mahaifinki ya tabbatar mana dama akwai wanda kike so". Da sauri Lulu ta kalla Hon. Nakowan, cikin fushin da ya fara fallasa kansa a maƙoshinta ta ce, "Baba ni bamma san wannan mutumin ba face a poster. Magana kuma bata taɓa haɗani da shi ba kota gaisuwa balle zancen soyayya. Ni bashi bane wanda nake so kuma shi yana a waje". Maganar ƙarshen ta fito a bakinta cikin suɓucewar harshe da ita kanta sai da ta gama faɗa ta tsinta kanta cikin matuƙar takaicin kan nata. Dan haka ta wani yatsine fuska, a zuciyarta tana faɗin (ALLAH ya kiyaye naso driver na can dai)... "Waye shi? Miye sunansa? Ɗan wanene kuma?". Jerarrun tambayoyi da ga bakin Alh. Sulaiman cikin makirci da shirin da ya kammala tsarawa tsaf tun a daren jiya, dan ya ɗauki alwashin ƙararma da Daddy man kai tsaf kasancewar yana ji a ransa shirine kawai, dan a bibiyar da yake ma Mawaddat ya tabbatar bata da wani saurayi, duk wanda ma ya raɓeta da batun soyayya yagashi takeyi. Uncle ɗin nata ta kalla a ɗan daburce, sai dai kafin tace wani abu Baba da hankalinsa ba'a kanta yake ba balle ya fahimci halin da take ciki ya furta "Jeki shigo da shi". Kamar wadda dama take jiran umarnin, zumbur kuwa ta miƙe ta fice. Har yanzu yana kwance a motar, sai dai saɓanin ɗazun yamzu karatun Alkur'ani yake saurare a wayarsa. Darajar waɗan da ke ɗan kai kawo da gudun kar wani ya ganta ya sata masa knocking a hankali. Tun fitowarta ya riga ya ganta, tsaiwarta a wajen da hararar data dallarama motar wadda yasan tasace kuma duk a kan idonsa ne. Amma sai yay buris har sai da ta ƙara na biyu cikin ɗan fara tunzura. Gilashi ya sauke ƙasa a hankali, babu zato idanunsu suka shige cikin na juna. Kusan a tare suka janye da sauri, ita tana jan tsaki da ƙarewa da kwafa. "Sai ka fito malam. Saura kuma idan ka shiga kaima mutane ƙauyancin da ka saba. ALLAH sai na koya maka hankali". (idan baki koyamin ba ni zan koya miki) ya faɗa a zuciya, a zahiri kam kansa ya gyaɗa mata kamar wani salihin gaske (😔🥱) itako sai taji kan nata ya ƙara girma. Matsa masa tai ya fito tana watsa masa hararar ƙasan ido. Shi dariya ma ta bashi, amma sai ya kanne, a ransa kam ya riga ya gama tsara haukan da zai manna mata a ciki, dan ya gama shirya kwance mata zani a kasuwa, ya san dai Uncle Yousuf zaiji ba daɗi, zai bashi haƙuri kawai a wuce wajen dan gaskiya shikam ba za'ai wannan aikin rashin gaskiyar da shi ba. Dan garama ya zame kan nasa kakan nata yay mata auren dolen da shi yafi dacewa da ita ma kodan tarbiyyarta da ke ƙara neman taɓarɓarewa. A jere suka tafi tana wani ɗan murmushin da iyakarsa lips. Shima kuma yana murmushin muguntar da ya gama shirya mata. A nutsensa yay sallama. Duk da yawan mutanen da ke a farlon baiji ko ɗar ba a ransa, sai ma gaishesu da yay a jimlace cikin cikar kamala. Da yawa ya burgesu, sun kumaji a aransu lallai Mawaddat ta iya zaɓe, ashe girman kan nata da izza bazai ƙare a banza ba irin wannan hot guy haka. Tajuddeen kam sumar zaune yay kansa a juye, haka suma su Hon. Nakowa idanu kawai suka zuba masa cike da ɗimuwar rashin makamar yin tunani. Baba ne yay murmushi bayan ya gama ƙarema masa kallo da ga sama har ƙasa cikin ƴan sakkani. Cike da dattakonsa ya nunama Smart gefensa da faɗin, "Ƙaraso nan ka zauna kaji my Grandson". Baiyi musu ba ya ƙarasa garesa, sai dai maimakon inda ya nuna masa sai ya zauna a ƙasa gaf da ƙafafunsa dan haka kawai tsohon yay masa wani irin masifaffen kwarjini. Murmushi mai ma'anoni da dama Baba ya sake saki, haka ma Uncle Yousuf. Cikin tsantseni da noƙewa ya sake gaishe da Baba da ya miƙo masa hannu alamar su sake gaisawa. Nan ma murmushin Baba ya sake yi da faɗin, "Shike nan tunda baka so mu samu ladan juna. Minene sunanka yaro na?". "Aliyu Hydar M. Idris Mawashi". Ya bama Baba amsa cikin girmamawa. Kai baba ya jinjina da faɗin, "Masha ALLAH suna mai daraja. ALLAH yasa kayi koyin ainahin mai sunan. Ali mazan fama, Ali gadanga ƙusar yaƙi. Ali zaki, Ali sadauki." Kirarin da Baban yay masa ya saka wasu da yawa sakin murmushi a afalon ciki harda shi kansa Smart ɗin. Baba ya cigaba da maganarsa kai tsaye. "Sadauki minene alaƙarka da jikata Mawaddat?!". Wani irin bugun ƙirjinsa tambayar tayi har acan ƙasan rai, amma sai ya dake cike da bama kai ƙwarin gwiwa ya ɗago kaɗan da nufin kallon Lulu cikin ido ya bama Baba amsa da (babu komai) amma aka samu akasi a bazata idanunsa suka sauka akan mutumin daya saka aka satoshi, ya kuma damƙa masa aiki akan Jiƙamshi family. Cikin ido suka kalla juna shi da Alhaji Sulaiman Sufi Ado Garko da shima ya kafeshi da idanu cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara. Matuƙar girgiza Smart ya shiga, sannan mamaki ya nema halaka shi, (wanene shi anan ɗin?) Zuciyarsa ta ayyana masa bayan ya janye idanunsa. Bashi da mai bashi amsa, sai dai yana da damar neman amsar ta dalilin amsar da zai bama Baba a yanzu. Dan haka kai tsaye ya furta, "Ranka ya daɗe alaƙar soyayya da muke fatan ta kaimu ga aure. Kuma harta yarjemin turo magabatana duk da kasancewar baka nan ya kawo tsaikon hakan".. "Masha ALLAH Alhamdullah, ai yanzu gani na dawo. Mawaddat! Ga Tajuddeen, ga Haruna, ga kuma Aliyu Hydar, wanene zaɓinki? Ina son ki faɗa ko nace ki sake faɗa a gaban kowa domin samun daidaito da rufe wannan babin mu fuskanci na gaba". Da ƙyar Lulu ta haɗiye yawun takaicin Smart da ya maƙure mata maƙoshi da cimata zuciya. Ta ɗan dubi inda Uncle Yousuf yake, cikin sa'a ta samu ita yake kallo sai ya gyaɗa mata kai a yanayin bata ƙwarin gwiwa. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye, tare da danne zafin da takeji da ƙyar ta gyaɗa kanta da faɗin, "Grandpa ni shi nake so". "Wa ɗin?" Sai da ta rumtse idanunta sannan ta furta "Hydar" a hankali kamar mai raɗa.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* ??𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣9️⃣ ........"Ƙarya kike yi munafukan yarinya". Alh. Sulaiman ya faɗa cikin suɓucewar baki. Yayinda Daddy da Uncle Yousuf suka saki wata irin ajiyar zuciya a ɓoye. Shiko Smart ƙirjinsa ne yay wata irin yankawa har sai da ya lumshe idanunsa yana mai ambaton sunan ALLAH. Furucin Alh. Sulaiman dana Tajuddeen da shima a zabure ya furta, "What! Drivern naki? Kai ina wlhy ƙarya kike Mawaddat akwai wani shiri a wannan zancen naki". Falon ne ya nema ruɗewa kowa na ƙoƙarin faɗin albarkacin bakinsa. Yayinda Smart ya dilmiya cikin kogin ninƙayar nazari. Dan abinda Alh. Sulaiman ɗin yayi ya sake zaburar da shi ne har wasu abubuwa masu girma da ya gama tsara gujemawa suka fara bijiro masa. Tsawatarwar Baba ta saka falon yin shiru. Hakan ya sake bama Smart da Alh. Sulaiman damar yin kallon kallo, kai tsaye Smart yake nazartar gargaɗi mai firgitarwa da ga idanunsa, dan haka ya sakar masa wani shegen murmushi da masa alamar 1-0 ya kashe ido ɗaya. Rawa jikin Alh. Sulaiman ya fara, sai dai ƙoƙarin ganin ya nutsar da kansa yake. Ganin fa hakan bazai faruba ya sashi miƙewa a zabure ya kama hannun Tajuddeen suka fice. Babu wanda ya hanasu. Ganin haka ma sai suma su Hon. Baita suka ce zasu wuce. Godiya Baba yay musu da basu haƙuri yana mai sake tabbatar musu bazai ma Mawaddat auren dole ba. Amma yana mai basu haƙuri tare da dama idan har akwai wata da Hon. Nakowa zai iya so a cikin zuri'arsa bayan Mawaddat ya bashi dama yazo ya sake gwada sa'arsa su dai-daita". Godiya sukai masa da tabbatar masa yin nazari akan maganar tasa, suka kuma yi fatan alkairi ga Mawaddat ɗin duk da dai ta ciki fa na ciki. Bayan wucewarsu Baba ma addu'a ya saka ayi ya sallami kowa, sai dai banda Daddy da Uncle Yousuf da Smart. Amma har Lulu yace taje. Koma ba'ace taje ɗin ba batai niyyar zama ba, dan in har ta cigaba da zama a falon zata iya aikata ɓaranɓaramar da komai zai tashi a wajen.... Tambayoyi na mutuntawa Alhaji Sufi Ado Garko ya sake yina Smart, shiko ya amsa masa cikin nutsuwa kuma kansa tsaye. Hakan ya saka Uncle Yousuf jin farin ciki, sai dai umarnin Baba na ƙarshe akan Smart na cewar ya je ya sanar ma iyayensa suzo a cikin satin nan ya girgiza Daddy matuƙa har ya ɗan waro ido sai da Uncle Yousuf ya zunguresa. Shi kansa Smart maganar ta girgiza shi, dan da ƙyar ya iya haɗiye yawu ya gyaɗa masa kai..... 🤣Wayaga cakwakiya mai taurari. Kai Smart ka ɗauka abin wasa ne kenan, ai gashi nan Baba yay maka ɗaurin huhun goro 🤪🚴. ★★★..... "Kai Yousuf bazai yiwu ba. Ina bazan taɓa yarda Mawaddat ta auri yaron nan ba gaskiya. Da ace nasan wannan shawarar ka yanke dana kwaɓeka tun farko. To gashi nan DAGA WASA KARAMAR MAGANA NA NEMAN ZAMA BABBA. Dama kai kana tunanin yin wasa da hankalin Baba ne?". Daddy ne mai wannan magana cikin tashin hankali da damuwa wa Uncle Yousuf da ke driving. Cikin dakewa da nuna alhini kamar gaske shima Uncle Yousuf ɗin ya ce, "Yaya sam ba haka nai tunanin kasancewar al'amarin ba fa. Banyi zaton zaice Aliyu ya turo magabanasa da wuri kamar haka ba. Shima fa yaron da ƙyar na shawo kansa ya yarda zai mana aikin. Ni yanzu ma gaba ɗaya kaina ya kulle na rasa mima ya kamata nayi". "Faɗama Baba gaskiya mana. Dan nasan Mawaddat bazata taɓa yarda ta auri drivern ta ba. Kai koni ma hakan bai min ba Yousuf. Ina impossible kamar yarinyata mai daraja irin Mawaddat ta ƙare da auren drivern ta, sai kace wani almara ma". Ɓacin raine sosai ya dunƙule zuciyar Uncle Yousuf, cikin matsanancin takaici yake duban Yayan nasa, sai dai baiyi magana ba ya sake maida kansa ga titi har suka isa gida. Shima Daddyn ya fahimci ran ƙanin nasa ne ya ɓaci, amma bai fahimci ainahin miya ɓata masa ran ba. Suna isa gida Uncle Yousuf baiko fita a motar ba yay shirin juyawa. Da mamaki Daddy da ke kallonsa ya furta, "Ya zaka koma kuma bamu gama magana ba Yousuf". Idanu Uncle Yousuf ɗin ya rumtse sai kuma ya buɗesu akan Daddy. "Yaya to wace magana kuma ta rage? Kace bazata auri driver ba, shike nan magana ta ƙare ai, dan ni kam iya abinda zanyi nayi k...." "Kaga sakko muje ciki wannan ba maganar mota bace." kamar zai ce a'a sai kuma dai yabi umarninsa ya fito. Falon baƙi suka nufa, dan in har zasu maganarsu ta sirri sunfi buƙatar zuwa can kasancewar babu wanda zai iya jinsu. Suna shiga Daddy ya ce, "Yousuf ka fahimceni mana. Ni fa ba ina nufin bakai ƙoƙarinka bane ba. Amma Please ka duba mana. Yaron nan fa driver ɗinta ne...." "Shi driver ba mutum bane? Ko kuwa shi dama mai arziƙi ALLAH ya tabbatar masa shine mafifici ga kowa a duniya da da lahira?. Gaskiya yaya ka fara bani tsoro, matuƙar tsoro ma kuwa. Wai kai kuwa wani irin so mara fasali kake ma Mawaddat? Ko kai ne zaka aure ta...." "You'r vary stupid Yousuf! Wane irin banzan magana ne wannan?". "Dolene na faɗi hakan ai Yaya. Dan al'amarin naka ya fara wuce makaɗi da rawa kuma. Idan ka manta shekarun Mawaddat ashirin da huɗu har da watanni balle kace bata isa aure ba. Tun tana shekara ashirin aka saka mata ranar aure ka goya da bayanta al'amarin ya wargatse. Idan kace wancan yana da wani aibu shi wannan minene aibunsa? Dan kawai ya kasance driver mai neman halaliyarsa? To wlhy bakai ya kamata kace Mawaddat tafi ƙarfin Aliyu ba. Aliyu ne ya kamata yace yafi ƙarfin Mawaddat kodan halin da take a ciki wanda kai ne gaba-gaba wajen zama silarsa. Kai ne ya cancanta kai ƙoƙarin ganin ka gyara ko neman hanyar da zata gyaru ta zama cikakkiyar mutum kafin kowa amma baka ƙoƙarin yin hakan sai sake bata damar ma da zatafi yanzu lalacewa kake yi. Ina ji maka tsoron ranar da Baba zai fahimci halin da Mawaddat take a ciki, in dai maganar Aliyu ce kuma na bari....." Da sauri Daddy da jikinsa yay sanyi ya riƙoshi. "Kaga kayi haƙuri auta." Batare da Uncle Yousuf ya yarda ya juyo ba ya ce, "Kai zan bama haƙuri ai Yaya. Dan na shiga hurumin daba nawa ba. Na manta Mawaddat ƴarka ce kai ɗay...." "Shiiii! Ni ba haka nake nufi ba auta. Amma tunda zuciyarka ta kaika ga hakan amin afuwa. Ni kaina wani lokacin yanda nake ɗaukar al'amarin Mawaddat na bani tsoro. Amma dan ALLAH ka tayani da addu'a. Sannan kayi haƙuri ka cigaba da duk yanda kake ganin shine dai-dai. Ba Mawaddat ba ko ni ka isa dani ai ko. Wlhy a duk sanda kake faɗamin gaskiya akan lamarin Mawaddat fuskar Mahaifinmu nake gani akan fuskarka, yayinda muryarka kan juye min tamkar ta mahaifiyarmu. ALLAH yay maka albarka auta. Ina alfahari da kai a matsayin ɗan uwana da ga kai har Kareema. Wlhy itama fahimtata ne kawai batayi tun farko, amma tana da wata daraja da kima mai girma a gareni". Tsira masa idanu kawai Uncle Yousuf yay kalaman nasa na bashi mamaki da al'ajabi. Anya kuwa Yayan nasa bashi da Alhaju? Dole ne yace haka, dan yau wai bakin Yayansa ne ke yabon Aunty Kareema. Kai anya kuwa dai..... Kamar Daddy ya fahimci abinda ke a ran ɗan uwan nasa ya saki murmushi mai ciwo. "Mamaki kake ko auta? Kana mamakin yabon Kareema a baki na. Humm bazaku gane bane, dan tun farko bakubi hanyar da zaku gane ɗin bane shiyyasa kuke min kallo irin wanda bashi ya kamata kumin ba. Kaje kawai abinka. Na kuma maka alƙawarin bazan sake saka baki ba akan al'amurin auren Mawaddat dan kai ne ubansu dama ni ɗan kallo ne. Sai dai a wannan gaɓar ina tunatar da kai suma su ƴan biyu ya kamata ka sakasu suyi aure fa. Kaje ALLAH ya huta gajiya". Da ga haka Daddyn ya fice idanunsa taf da ƙwalla. Da kallo kawai Uncle Yousuf ya bisa zuciyarsa na kaikawo a ƙirji. Dan ba ƙaramin ratsa masa zuciya kalaman ɗan uwan nasa sukai ba yau...... ★★.... A ɓangaren Lulu da bata san hukuncin da Baba ya yanke ba suna fitowa a street ɗin gidan Baba a gadarance ta cema Smart "Malam tsaya da motar nan". Kamar zai shareta sai kuma ya gangara dan yanzu ba shirmenta bane a gabansa. Abubuwa ne masu yawa ke masa kaikawo a zuciya. Fita tai ta koma baya, bai ce komai ba ya sake tada motar suka cigaba da tafiya. Sun ɗan ƙara nisa motar shiru babu mai magana, shi hankalinsa ya rabu biyu, wani a tuƙi wani a tunanin al'amarin da ya faru yanzun nan. Ita kuma hankalinta nakan tab... Ɗinta ne tana aiki har suka iso. Ita ta buɗe da kanta dan hankalinta nakan abinda takeyi, sai da ta zura ƙafarta ɗaya waje zata fita sannan tai magana batare data kallesa ba. "Malam ina fatan baka ɗauki abinda ya faru a gidan Grandpa wani abu ba. Idan kuma ma ka ɗauka ɗin to ka ajiyeshi a motar nan karma ka koma gidanku da shi dan zai zame maka dakon wahala ne, dan ba Mawaddat ba ko mai aikin gidanmu tafi ƙarfin nunaka matsayin abin sonta balle ni, ka cigaba da zama matayinka na yarona kana amsar albashinka hankali kwance a samu na koko da ƙosai". Ta ƙare maganar da balla masa uwar harara da jan tsakin tabbatar da gargaɗinta ganin yanda ya wani tsareta da idanu ta cikin mirror. Kansa ya ɗan girgiza bayan ficewar tata, sai kuma ya saki wani shegen murmushi da cije lips ɗinsa yana mai kai hannu ya shafa tattausar sumar ƙasumbarsa. A hankali ya furta, "Kema lokaci yayi da zaki fara cin koko da ƙosan ai ƴar gidan madara". Ya ƙara cije lips ɗinsa da kashe ido ɗaya.... (Makiri Smart. Mi kake shirya mana ne🥱😨). ______________________ "Dad! Wlhy wannan abun ƙarya ne shiri ne kawai. Amma babu wata soyayya a tsakanin Mawaddat da shi. Drivern ta ne fa, hasalima Alhaji Yousuf dani muka zauna muka roƙesa akan ya tuƙata saboda muna son ya bibiyar mana al'amarinta akan s....." Sai kuma yay shiru tuna ɓaranɓaramar da yake neman yi ga kallon da mahaifin nasa ya kafesa da shi. "Ya ka dakata? Ƙarasa mana akan mi?". "No Dad share. Wannan bashi bane mai muhimmanci, musan gaskiyar zancen da tabbatar ma Grandpa shine nafi buƙata a yanzu. Idan ba hakaba wlhy sai na tada hankalin kowa a family ɗin nan dan Mawaddat kaɗai nake so, da ita kawai nake buƙatar zaman aure". "Tajudden ka kwantar da hankalinka, in dai Mawaddat ce babu fashi kai ne mijinta. Yaron nan kuma nima na tabbatar sakashi akai ko kuma shine ya sa kansa. Amma barni da shi, zan tabbatar masa wanene ni dan naga yana son yin wasa da wuta ne a tafin hannunsa batare da ya sani ba. Kaje ka cigaba da shirye-shiryen aurenka nan da kwanaki takwas". "Amma miyasa ba gobe ba Dad? Ni gobe nake so Friday a ɗaura. Next Friday ai shagalin biki na nunawa Sa'a ta tare a gidana." "Ka ɗauka yanda ka tsara labarin, haka za'a bugashi a jaridu da mujallu a yammacin gobe cewa Tajuddeen Sulaiman Sufi Garko ya zama angon Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi". "Thanks You Dad". Tajuddeen ya faɗa cike da zumuɗi yana mai rungume mahaifin nasa, dan yasan baya magana bai tabbatar da ita ba...... Gaba ɗaya tattaunawar ɗa da mahaifin acikin kunnenta ne, dan tun farawarsu ta iso ƙofar falon bisa umarnin auntynta da ta aikota. Da sauri ta tallafe tray ɗin dake hanunta mai ɗauke da kayan motsa baki jin zai suɓuce mata. Juyawa tai da sauri zuwa apartment ɗin yayarta cikin sassarfa kamar zata faɗi ga idanunta na kwarar da hawaye masu zafin gaske........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣0️⃣ ......."K! K! Lafiya kuwa naga kin dawo min da shi haka kamar ma wadda take a firgice?". Ƙasa ta dangwarar da tray ɗin tare da faɗawa jikinta ta sake fashewa da kuka. "Aunty Abasiyya wannan karon ma zan rasashi. Dama ashe abinda ake ƙullawa a gidan nan kenan amma baki faɗamin ba kika barni inata shirme na?" ta ƙara fashewa da kuka. "Mtsoww! Wai nikam Ramlah yaushe ne zaki hankali? Kimin bayani danni ba fahimtarki nake ba. Kinga tashi zaune". Babu musu Ramlah ta tashi, ƙyaƙyƙyawar yarinya kuma ƴar gaye. Bata damu da share hawayen da suka gagara tsaya mata ba, ta ce, "Aunty Abasiyya zaki cemin baki san shirye-shiryen auren Tajuddeen ake ba a gidan nan kuma da mayyar yarinyar can dai". "What! Auren Tajuddeen fa? A gidan nan kuma ban sani ba? Lallai Alhaji ya sake zama abinda ya zama. Wlhy Ramlah sam ban san da zancen ba, sai dai tabbas naga anata wani ƙus-ƙus tsakaninsa da matarsa na munafunci tun jiya, yau kuma ya ɗauketa suka fita sai dai ban san ina sukaje ba". "To Aunty babban gida sukaje, dan inaga Baba ya dawo....." Ta kwashe kaf abinda taji Tajuddeen da babansa na tattaunawa ta sanar mata. Tare da faɗin, "Aunty dan ALLAH ki taimake ni, wlhy idan na ƙara rasa Tajuddeen a wannan karon zan iya rasa rayuwataa gaba ɗaya ina sonsa matuƙa fiye da yanda nake son kaina". "Hummm Ramlah kenan, badan nasan minene zafin soyayya ba da nace baƙya kishina. Ina matsayin yayarki uwa ɗaya uba ɗaya amma kina son ɗan kishiyata da bata taɓa ƙaunata ba a gidan nan, da ace ma tanada dama da tuni ta kawar dani a duniya. Gaskiya wannan soyayyar taki bataimin adalci ba. Sai dai bazanƙi taimakonki ba, dan nima hakan zai taimakeni wajen ƙuntata rayuwar Hajiya Turai. Dan haka ki kwantar da hankalinki, yanzun nan zan warware musu ƙullin nasu ta inda basu taɓa zato ko tsammani ba." Cike da ɗoki Ramlah ta ce, "Aunty mi zakiyi?". "Jira ki gani". Ta faɗa tana janyo wayarta. Daddanawa tai takai kunne tare da miƙewa ta shige ciki tana faɗin, "Baba barka da rana......." iya abinda Ramlah taji kenan..... ★ Alhaji Sulaiman kam da basu san Ramlah ƙanwar amaryarsa da take riƙo taji tattaunawar tasu ba tuni Tajuddeen ya fice da waya a kunne yana waya da telansa kan ya jirashi a shago yanzu zai zo da ɗinkin ujila... Da kallo Alh. Sulaiman ya bisa yana wani murmushin mugunta. Shima ya kai wayarsa kunne. Bugu ɗaya Malami ya amsa da ga can. Batare da ya amsa gaisuwar Malamin ba cikin bada umarni ya furta, "Yaron dake mana aiki a gidan Isma'il Jiƙamshi ina buƙatarsa". "Angama ranka ya daɗe". Malami ya faɗa cikin tsantsar girmamawa tamkar yana a gaban ubangidan nashi ne..... ★★...... Alhaji Sufi Ado Garko da ke zaune a falonsa na baƙi har yanzun, dan bayan fitowa sallar la'asar ya sake wasu baƙin da suka sake rikita masa lissafi. Ba kowa bane face tsohon gwamna sannan babban ɗan kasuwa M Atik Kumo mahaifin MM Atik Kumo da tawagar abokansa uku neman izini wa ɗan nasa fara neman soyayyar Mawaddat. Sun gama masa bayanin kenan ya tabbatar musu da abinda ya faru game da kawo wanda Mawaddat ke so a yau har ma sun basa damar turo magabatansa suka masa godiya da bada haƙuri dan mahaifin MM Atik mutumin kirki ne. Ya fahimci bayanin Baba ya kuma gamsu suka rabu cikin girmama juna dan Baba ya kasance tamkar uba ga duk wani ɗan siyasa to. Bayan fitarsu ne yana ƙoƙarin tashi ya shiga ciki dan ya huta da hayaniyar da ya sha kiran matar ɗansa Alh. Sulaiman ya shigo masa. Bai kawo komai a ransa ba dan shi surukansa tamkar ƴaƴa suke garesa. Bayan sun gaisa tai masa barka da sauka da yaya jiki tare da bada haƙurin rashin zuwa tarbarsa saboda batajin daɗi ne. Ya gamsu da abinda ta faɗa tunda tabbas bai ganta ba a cikin gidan dan haka ya saka mata albarka. Ɗan jimm da tai ya sakashi fahimtar akwai wani abu, dan haka ya tambayeta. Sai da ta sake kwantar da murya cike da kissa ta zayyano masa dukkan abinda ƙanwarta ta tabbatar tajiyo, sai dai tace itace taji ba ƙanwar tata ba. Ta kuma kira ta faɗa ne dan kar abinda zasuyi ɗin ya taɓa kimar Baba da Family ɗin. Amma dan ALLAH bata son kowa yasan ita ta faɗa gudun abinda zaije ya dawo. Murmushi Baba ya saki irin na manya. Ya sake saka mata albarka sannan sukai sallama. Yasan Sulaiman zai aikata abinda ma yafi hakan, kuma shima yayi tunanin wani abun zai iya ɓullowa game da hukuncin nasa. Sai dai abinda ya bashi mamaki mi yake faruwane haka maneman Mawaddat ɗin keta karakaina a wannan gaɓar? Ko dai rawar data taka ne game da shari'ar mutumin nan ta kwanan nan data ɗauki hankalin mutane da yawa ce? Dan duk da baya ƙasar kunnensa da idanunsa na a Nigeria ɗin. Yafi zaton hakan shiyyasa bai ɓata lokaci wajen zurfafa tunani ba. Sai ma ya dannama Uncle Yousuf kira dan ya gama tsara kafin Sulaiman ya ƙulla abinda yake tsarawa shi zai tabbatar masa wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi...... ★★..... Sosai mamaki ya dabaibaye Uncle Yousuf da ke sauraren Baba. Dan ya masa bayani ne akan zuwan su M Atik Kumo kafin hukuncin da ya yanke a yanzu-yanzu saboda labarin da ya samu na shirin ɗansa da jikansa. Cikin girmamawa da godiya Uncle Yousuf ya tabbatar masa yanzu nan zai tura a isar da saƙon in sha ALLAHU. Suna yanke wayar kuwa yay kiran abokinsa Coach ɗin su Smart Abdull-Hameed, wanda ta sanadinsa ya fara sanin Smart ɗin dama. Tun yana waya da Hameed ɗin kiran Yayansa (Daddy) ke shigowa, bai ɗaga ba har sai da ya kammala da Hameed ɗin. Wani kiran ne ya sake shigo masa, ya ɗaga yana kaiwa kunne da faɗin, "Yaya irin wannan kira lafiya dai ko?". "Inafa lafiya Yousuf! Wai kaji suma su M Atik Kumo sunzo nemawa ɗansu izinin neman Mawaddat. Anya abunnan na lafiya ne? Ni bama wannan ya damen ba, dan M Atik mutumin kirki ne, ɗan nasa ne kawai sai a hankali, dan wlhy da ace ya kasance mutumin kirki kamar mahaifinsa da hankalina zaifi kwanciya da aura masa Mawaddat fiye da yaron nan daka kawo...." Cikin gatse Uncle Yousuf ya ce, "To kodai a bama ɗan M Atik ɗin dama kawai, tunda shi dai ai ba wani abu ya taɓa aikata mana ba. Sannan a a bayyane ban taɓa jin ance ga aibun yaron ba..." "No no no Yousuf bar wannan maganar kai dai. Dan wlhy ina gama waya da Baba yanzu na ɗan fara bincike kan yaron wajen wani aminina al'amarin babu daɗin ji, dan akuyace lulluɓe da fatar kura bai gado uban nasa ba. Kayi haƙuri bakwai kushe yaron nan Aliyu nake ba. A'a kawai ina tunanin taya zai iya riƙemun yarinya bashi da aikin yi, danni ban ɗauki direbanci wani abunyi ba face hanyar maƙalewa domin rage matsaloli..." "Humm Yaya kenan. Nifa ban tsawwala ba, idan akwai wani da kake ganin hankalinka ya kwanta da shi game da Mawaddat ƙofa a buɗe take ka kawosa mu canjashi da Aliyu dan shi dama bawai ya ɗauki abun da girma bane tunda auren wata ɗaya kacal ne zai saketa, ni kuma na gaji da maimaita magana ɗaya". "Ina ai zancen wani ma bai taso ba auta. Yanzu fa Baba ke sanar min kuma munafukin can abinda yake ƙullawa akan ɗansa. Kaga ko ai bamu da wani isashen lokaci. Mu ƙarasa da Aliyun kawai sai dai zamuyi komai a rubuce da ƙa'idoji dan karma da ga baya wani abu saɓanin wanda akai a rubuce ya biyo baya tunda mun samu Mawaddat ɗin ta amince babu rigima. Sannan zan basu gidan da zasu zauna a kuma canja masa aiki". Sosai takaici yake neman shaƙure wuyan Uncle Yousuf. Amma sai ya danne ya ce, "Nima munyi waya da baban yanzu. Yanda kuma kake so haka za'ayi. Zan cema Aliyun ya tsaya idan ya kawota sai muyi maganar, idan kuma zamu bari ne sai zuwa weekend zaifi a nutse". "Eh weekend ɗin yayi kawai ALLAH ya kaimu". Sallama Uncle Yousuf yay masa tare da kashe wayar gaba ɗaya ma. Takaici yakeji na ɗan uwan nasa da halayyar da yake nunawa akan al'amurin Mawaddat mara fasali. Ya rasa wane irin soyayya yakemata irin haka. Ya kamata ace yayi nadama da neman hanyar gyara. Sai dai kash, nadamar tasa alokacin da ya ganta cikin wani hali ne kawai yake yinta..... ★★.....★ Duk wannan cakwakiya da ƙura da take cigaba da tashi a wannan yini da ga mai gayya da aiki kam normal ne. Dan tuni ta tattara komai ta watsar ta tattara hankalinta akan case ɗin yarinyar nan da akaima fyaɗe dake neman caza mata kai. Tun bayan isarsu office bata wani zauna ba ta fito suka sake fita. Kasancewar hankalinta ga a inda yake ya sa yau tsakaninta da drivern nata babu masifa. Sun ɗanyi yawace-yawace har kusan bayan sallar la'asar sannan suka koma office. A hanyar komawar ne ya fahimci ana binsu a baya. Da farko bai kawo komai a ransa ba sai da ya ga bayan ta shiga office tai zaman kusan mintina talatin ta fito zai maidata gida a hanya ya sake ganin motar ɗazun ɗin nan dai da napep a biye da su. Yaji a ransa cikin biyu dole ai ɗaya. Kodai su Honorables, ko kuma Alhajin nan da ya sa aka sace shi wancan karan a yau kuma ya ganshi a gidan Baba. Yafi buƙatar ya kaita gida lafiya daga nan koma mizai farun ya faru, dan haka ya take motar ya tsere musu cikin salon canja titi gaba ɗaya..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣ .......Mawaddat da ke da burin amsar saƙo ta kallesa fuska babu wasa. "Malam miye na canja hanyar? Dalla ka koma tacan ina buƙatar amsar saƙo". Shiru kamar bazai tanka mata ba sai kuma ya bata amsa a taƙaice. "Akwai holdup ta canne, ga shi lokacin sallah ya kusa bana buƙatar rasa jam'i". "To ɗan iya wannan kuma matsalarka ce. Bai kuma damen ba. Ka koma ta inda nace bana buƙatar sharhi". Hanyar ya canja batare da ya sake cemata komai ba, amma kuma ba wadda dai take son abi ɗin ba dai ce. Dan zuciyarsa ta bashi kayan shaye-shayen nata ne zata amsa. Takaici ya turniƙe Lulu. Dama ga gajiya na nuƙurkusarta, ai tuni ta balbale sa da masifa amma yay biris da ita kamar yanda ya saba, bai ƙara tari ba har suka iso gida. Buɗe motar tai a fusace ta fito, dai-dai da shima yana fitowar da nufin buɗe matan. Ta zabga masa uwar harara da wani banzan kallo. Nunashi tai da ɗan yatsa tare da tattaro dukan ƙarfinta na zazzage masa abinda ke a ranta amma ko kalma guda ta gagara fita mata a harshe saboda yanda ya wani tsareta da idanunsa data raɗama suna irin na macizai. Sai lips ɗin ta ne kawai ke rawa kamar wanda ya ɗaureta da idanun nasa. "Kaje na koreka, da ga yau bana buƙatar sake ganin wannan shashashar fuskar taka illiterate velleger...!" A hankali ya lumshe idanun nasa sai kuma ya sakar mata wani shegen murmushi da ya kusa fisge mata numfashi gaba ɗaya. Jitai kamar zata zube a wajan tsabar wani ƙudu dun takaici da murmushin sa ya haifar mata. Dan bata fassarashi a komai ba face na rainin wayo. Fahimtar ya samu nasarar ƙular da itan da yake buƙata ya sashi matsota a hankali, cikin ƙasa da murya da wani maidata can ƙasan maƙoshi ya furta, "Oh! Kin fison sake ganin angon naki kawai a ɗakin barcinmu ke nan AMARYA, ba damuwa a bani albashina dan da shi zan biya sadaki". "What!!!" ta faɗa da ƙarfi tare da kai ma fuskarsa mari da gaba ɗaya ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata a jiki. Baya yay cikin wani salon da ta samu iska shuuu, ya ɗago yana murmushi tare da kashe mata ido ɗaya, sai kuma ya nuna fuskar tasa da yatsa yana ɗan sake matsota harda ranƙwafowa kaɗan. "Duk randa wannan hannun ya sauka kan wannan fuskar da sunan mari to kisa a ranki MAZA sun faɗi, faɗuwa irin ta MUTUWA. dan itace kawai damar da ƘYANWA zata iya samun yin birgima a gaban ZAKI yanda take so". Ya ƙara kashe mata ido ɗaya yana ɗaga mata yatsu biyu da faɗin, "Bye *MATAR ILLITERATE*". Yay gaba abinsa. Yuuuuu!! Lulu ta dinga jin hajijiya na neman kwasarta, wato itace ma ƙyanwar yake nufi. Dariya sosai Uncle Yousuf da ke cikin motar dake a kusa da su batare da sun san akwai mutum a ciki ba ke tuntsurawa harda ƙwalla. Ashe zaton da yakema yaron nan ya wuce nan. Kai jama'a har ya fara tausayin ƴar tasa gaskiya. Dan tabbas akwai babban wasa a wannan tafiya yanzu ne kuma za'a fara. Ganin yanda ta wuce tana haɗa hanya ga hawaye sun wanke mata fuska ya sashi daina dariyar ya buɗe motar ya fito, sai dai duk yanda yake son binta ya haƙura dan lokacin sallah yayi. Ya kai dubansa ga su Smart da ke alwala sai kawai ya nufesu yana gyara yanayinsa kamar bashi ya gama kwasar dariya ba a mota... Bayan an idar da salla kusan a tare suka fito. Uncle Yousuf ya dakatar da Smart da ke sallama da su maigadi akan ya jira su wuce tare. Kamar zai ce a'a sai kuma dai yay shiru dan kiran da Abba yay masa suna ƙoƙarin shiga massalaci akan idan ya dawo gida ya sameshi falonsa yanzun nan. Yasan maganace da Abban, shi kuma da yayi niyyar bama masu bin san nan a baya dama dan ya tabbatar ba haƙura sukai ba su kamashi dan yana son yin magana da koma waye ya turosun. Babu yanda ya iya dole yabi Uncle Yousuf ɗin, shiko ya ƙaunaci ALLAH ya kaisa har gida yau. Tunda suka fito kuma yaga motar nan sai dai ba napep ɗin yanzu, motar dai ce ke cigaba da binsu yanzu ma. Suna isowa titin anguwarsu yaga sun dakata cikin takaici direban motar na kaina sitiyari duka alamar ba haka sukaso ba. Sai dai kuma abinda bai sani ba shima Uncle Yousuf ya san da su shiyyasa ma ya ɗakkosa ya kawo har gidan. "Alhaji yau na saka ka aiki, Nagode sosai". Murmushi Uncle Yousuf da idonsa ke kan mirror yana kallon mutanen nan ya saki, tare da faɗin, "Har yanzu dai ina a Alhaji na? A tunani na na zama Uncle yanzu tunda ƴa zan bayar duk da auren wucin gadi ne". Yanda Uncle Yousuf ɗin ya ƙare maganar ne ya saka Smart kallonsa, sai kuma ya ɗauke kansa yana sakin murmushi ya ce, "To ayi haƙuri Uncle". "Shike nan na haƙura, dan dama ba'a san iyaye da fushi da ƴaƴansu ba. Ina fatan zaka samu Abba da maganar yau ko?". "Da wuri haka?". Smart ya faɗa da mamaki yana kallon Uncle Yousuf ɗin. "Dole ne muyi da wurin, dan ɗazun Baba ya sake kirana akan zuwan M Atik Kumo shima yana nemawa ɗansa aurenta, sannan Alhaji Sulaiman da ɗansa sun gama ƙulla matakin da zasu ɗauka a gobe idan ALLAH ya kaimu....." tsaf ya zayyane masa komai shima. Mamaki ne ya sake lulluɓe Smart, yayinda a ƙasan zuciyarsa yake ta lissafi akan yanda zai canja salon wasan a yanzu tsakaninsa da Alh. Sulaiman. Kafin yanzu shi bai wani ɗauki zancen da muhimmanci ba, dan har ya gama ƙulla yanda zai kuɓuce wa al'amarin, sai dai a yanzun nan ya canja sabuwar shawara. Duk da bai san minene dalilin Alh. Sulaiman ɗin ba ya kamata ace ya nuna masa shima tsageran kansa ne a wannan gaɓar. Bai damu da zancen MM Atik Kumo ba..... "Aliyu kayi shiru!" Uncle Yousuf ya katse masa tunani. Iska ya ɗan furzar kaɗan sai kuma ya fuskanci Uncle Yousuf ɗin. Cikin sake furzar da wata iskar ya ce, " Please Uncle kozan iya sanin yaya kuke da shi Alh. Sulaiman ɗin?". "Yerh babu damuwa Aliyu. Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko ɗane ga Alhaji Sufi Ado Garko. Sannan Yaya ga mahaifiyar Mawaddat uwa ɗaya uba ɗaya. A shekarun baya ɗan uwana mahaifin Mawaddat abokai ne da Alh. Sulaiman na ƙut-da-ƙut, dan sun haɗu ne tunkan ya auri mahaifiyar Mawaddat ɗin adalilin shi Baba da ya ja Yayana jikinsa. Sai dai a yanzu ba haka bane, dan bamu san minene ya shiga tsakanin wannan amintaka ba abokan biyu suka zama maƙiyan juna ta yanda ko inuwa ɗaya basa sha. Iya tambaya na yima Yaya amma yaƙi faɗa min komai. Shi iyakarsa fita harkar Sulaiman, amma shi Sulaiman a bayyane yake nuna tsanarsa garesa da mu ma ahalinsa gaba ɗaya shiyyasa Yayana yay ruwa yay tsaki wajen hana aure tsakanin Tajuddeen da Mawaddat dan yace akwai manufa. Wannan shine iya abinda na sani gaskiya". Kai Smart yake jinjina wa cike da gamsuwa. Sai da Uncle Yousuf yay shiru sannan shima ya bashi labarin kamasan da Alh. Sulaiman ɗin yayi a randa yazo shi da Ahmad suka roƙesa ya koma aiki, ya kuma sanar masa aikin da yace ya koma yay masa tare da nuna masa motar yaran Alh. Sulaiman da ke tsaye a bakin layinsu kasancewar suna iya hango su da ga nan ƙofar gidan su Smart ɗin da ke a bakin titin." Sosai al'amarin ya girgiza Uncle Yousuf ɗin, ya kuma tabbatar masa da shima dalilinsa na kawoshi gida yanzun. Dan tunda suka kammala waya da Baba yaji a ranasa Alh. Sulaiman zai iya ɗaukar mataki kowane iri ne akan Smart shine ya saka wani ɗan sanda zuwa office ɗin Lulu ya saka masa ido, ɗan sandan ne ma a Napep ashe, sai ko gashi bayan tahowarsu gida ɗan sandan ya tabbatar masa ana binsu... "Wato Aliyu idan na fahimta tun fara aikinka da mu Alh. Sulaiman na biye da lamarinka kenan? Kuma bana raba ɗayan biyu a wajen Tajuddeen ya sani. Lallai ya kamata musan dalilinsa danni zuwa yanzu har Tajuddeen ɗin ma na saka masa alamar tambaya". "Sanin dalilinsa abunne mai sauƙi Alhaji, yanzu dai barshi na fara masa duka a ciki, bayan cikin ya ƙulle zai amayar da duk abinda ke a ransa da kansa. Sannan Tajuddeen bai zama lallai yasan komai ba, zata iya yiwuwa amfani uban keyi da shi batare da shi ma ya sani ba". Murmushi Uncle Yousuf yayi tare da bubbuga kafaɗar Smart, dan tsaf ya fahimci inda zaurancen nasa ya nufa game da duka a ciki. Murmushi shima Uncle Smart ɗin yayi tare da buɗe motar yay masa godiya ya shige gida, shi kuma yaja motar yana ƙara jin ƙaunar yaron har tsakkiyar ransa. A rayuwa yana matuƙar ƙauna da son jarumin mutum. Musamman ma matashi irin Smart mai tsayyar zuciya. Wannan nagartar tasa ya fara hanga a filin ƙwallo ya shige masa zuciya, faruwar ƙaddarar data nema dakushesa da ga cikar burinsa ta fara sakashi jin tausayinsa da laluben hanyar da zai iya taimaka masa. Bayan yin dogon nazari ya yanke shawarar kusantosa gefensa domin ƙara tabbatar da halayensa kafin ya ja hannunsa hanyar da ya gama shiryawa domin kaisa ga cikar burin nasa. Sai kuma ga al'amarin ƴar ɗan uwansa ya gitta a cikin labarin tamkar bakangizo a tsakiyyar gagarumin hadarin da ke gab da zubda ruwa. Fatansa kawai ta kasance bakangizo mai amayar da ruwan da ta shanye bamai haɗiyewa ba har abada.........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣2️⃣ .......Bai samu ganawa da Abba ba sai bayan sallar isha'i ya samesa a falonsa. Bayan sun gaisa cikin dakewa Abban ya ce, "Aliy!". Ya amsa da "Na'am Abba". "Aliy!" Ya sake ambata. Shima sake amsa masan yayi kamar farko. Malam Mika'il bai gajiya ba ya sake kiransa a karo na uku shi kuma ya amsa masan dai kamar yanda yay na farko da na biyu. "Na kiraka sau uku ko?". Kai ya gyaɗa masa alamar eh. "Na kiraka badan tisa maka sunan da ni na saka maka ba ne, na kiraka ne domin a yau zan tabbatar maka da magana ta ƙarshe ne akan aurenka. Dan duk maganganun da Yahanasu ta faɗa ɗazun akanka sun sosama mahaifiyar ka da nima kaina zuciya. Kuma mun ɗauki alƙawarin bazaka sake rufa wata anan gidan babu matar aure ba. Dan haka a yanzu ina son jin ta bakinka, idan kana da wadda kake so sai ka faɗeta, idan kuma babu mahaifiyarka ta maka mata, nima kuma na maka sai ka zaɓi guda a ciki." Sai da ya ɗan rumtse idanunsa da jan numfashi, sannan ya ɗago a hankali ya kalli mahaifin nasa. Sai kuma ya sake maida kansa ya duƙar. "Kuyi haƙuri Abba duk ni ne na ja muku, amma insha ALLAH komai yazo ƙarshe, ba sai kun nemomin mata ba ni da kaina ma na samota". Wata irin ajiyar zuciya Abba ya sauke a hankali, sai dai cikin dakewar san nan ya ce, "Wacece? Ƴar wanene? A ina kuma ta ke?". Duk da yawan tambayoyin bai gazaba wajen amsasu ga mahaifin nasa. Ya ce, "Yarinyar da nake aiki gidansu. Ɗiya ga Alhaji Isma'il Jiƙamshi. A yau suma kuma suka buƙaci na turo iyayena dama in har na shirya". "Alhamdullahi. Aliyu Hydar ka daɗe baka faranta min rai irin yau ba. ALLAH yay maka albarka. Ya yaye maka dukkan damuwarka. Ya ɗauraka akan maƙiyanka. Ya kawo maka mafita ga al'amuranka. Na amshi zaɓinka badan ta kasance ɗiyar Alhaji Isma'il Jiƙamshi ba, ko dan yana da kuɗi, sai dai dan nasan kai nagartaccen mutum ne da bazai taba yin zaɓen tumun dare ba." (Abba ka gafarceni wannan dai kam zaɓen tumun asubace ma ƙarewar dare) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam murmushi kawai yayi da faɗin, "Nagode Abba. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Ku gafarceni akan dukkan abinda nai muku ba dai-dai ba kuma insha ALLAHU zan cigaba da zama a fiye da yanda kuke buƙata". Sosai Abba yay murmushin jin daɗi, Aliyu na cikin ƴaƴan da yafi ƙauna a cikin ƴaƴansa, sai dai shi kansa a wasu lokutan bai san mike danne soyayyar ba yayta kyararsa da hantararsa a dalilin ƙaddarar da wani bai isa ya canjata ba. Albarka sosai ya saka masa sannan ya sallamesa. Koda yabar wajen Abba cikin gida ya shiga, sai dai kai tsaye ɗakin Ammah ya shige yau bai gaida kowa ba a matan gidan. Ya samu tana shirin fitowa kaima Abba abinci dan yau itace da shi. Ya fahimci tana cikin damuwar da ya san babu makawa akan abinda ya faru ɗazune tsakaninta da Umma. Ƙannensa kansu yau basa cikin walwala. Suna gama gaisawa Ammah ta fice, annan ne Hawwah ke bashi labarin faɗan da akai sosai ne ai yau ɗin kuma duk a sanadinta ne. Da ga ƙarshe aka ƙare da musu goron halin da yake a ciki. Sosai ya ƙara jin zuciyarsa ta Zafafa. Sai dai komai bai ce ba yay musu sallama ya tafi makwancinsa...... *_WASHE GARI_* Washe gari batare da sanin kowa ba Abba da tawagarsa suka nufi gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi nemawa Aliyu Hydar auren Mawaddat Isma'il Jiƙamshi. Sun sami tarba ta mutunci dan har Baba ma yazo gidan shima. Abinda zai birgeka babu ƙyama ko hantara irin ta mai kuɗi ga talakawansa. Abin farin ciki da mamaki ashema Alh. Sufi Ado Garko school mate ɗin Abba ne ma a secondary school. A take hira ta kaure a tsakaninsu har zuwa kan abinda ya tarasu. Sai dai kuma bayanin da shi Baba yazo da shi ya girgiza su a wajen. Dan a ganinsu babu wani shiri ai tare da su game da haka. Baba ya kwantar musu da hankali tare da tabbatar musu da dalilansa masu ƙwarin gaske ta yanda su duka suka gamsu da hakan. Sun ɗan ƙara tattaunawa sannan sukai musu sallama cike da jin daɗin karramawar da suka samu suka suka taho akan sai anjima idan sun haɗu ɗin.... ★★...... Sam Smart bai san mima ake ciki ba. Dan hatta zuwan nasu Abba bai san da shi ba saboda yau bai ma fita aiki ba. Tunda ita tace ta koresa da kanta a ganinsa babu amfanin ya koma su sake raba hali. Dan haka ya zaɓi yin kwanciyarsa a ɗaki yayta buga game ɗinsa hankali kwance har lokacin sallar juma'a ya gabato. Yana shirin shiga wanka Ahmad yazo gidan. Zuwan Ahmad gidan ba sabon abu bane garesa dan haka bai damu ba. Haka koda ya bashi shadda sabuwa fil yace ita zai saka bai kawo komai a ransa ba dan Ahmad ɗin ya sha musu ɗinki irin hakan, haka shima kansa yasha yi musu ɗinki a taren. Bai wani ɓata lokaci ba ya fito a wankan, Ahmad na zaune har ya kammala shirinsa. Yayi ƙyau matuƙa kamar ka sacesa ka gudu. Ahmad ya wani shiga masa ruwan turare. Warce turaren Smart yay yana hararsa da faɗin, "Kaifa a duniya kamar baka san wahalar kayan duniyar nan ba. Anata wannan yanayin zaka ƙaramin turare haka dan neman hanyar talautani". Dariya kawai Ahmad yay masa da kashe ido ɗaya ya furta "Am sorry Zakin zaki". Shima dariyar yay a karo na farko. Dan duk sanda ya kira shi da Zakin zaki yana nufin shi ɗin na Coach Hameed kenan yayansa. Cikin nishaɗi da farin cikin tsokanar juna da suke na kiran tuzurai suka fita. Jan Ahmad yay suka shiga ciki gaida Ammah. Ta saka masu albarka tare da addu'a data so tsayama Smart a rai. Amma sai ya danne ta a ƙasan rai da tunanin Ammah tayi addu'ar ne kawai domin gabansa. Daga haka suka taso suka fita acewarsu zasuje sallar juma'a su dawo nan suci biranuskon da Amma keyi matsayin abincin rana... "Wai wane massalaci zaka akaimu haka ne?". Cewar Smart yana kallon Ahmad dake drivering a nutse. Murmushi Ahmad yay masa idonsa a titi ya bashi amsa da "Mi kakeci na baka na zuba? Zaka gani ai". Baki Smart ya ɗan taɓe da cigaba da game ɗinsa a waya. A haka suka cigaba da ƴar hirarsu har suka iso massalacin juma'ar. Zamansu babu jimawa aka fara khuɗuba, dan haka suka nutsu wajen saurare har aka kammala. Ana ƙoƙarin tada salla ya hango Uncle Yousuf da Coach da ke isowa yanzu, da alama sun makara ne. Baice komai ba ya gyara tsaiwarsa aka tada salla. Kasancewar bayan idar da sallar juma'a yin ɗaure-ɗauren aure a massalacin normal ne yasa bai kawo komai a ransa ba. Sai dai haka kawai yake jin sa wani iri yau kamar wani abu na shirin faruwa da shi. Ga kansa da ke ciwo ƙasa-ƙasa amma dai sai ya daure tunda bawai ya matsa masa da yawa bane. Wani irin harbawa da dokawar ƙirji ce ta samesa a lokaci guda a dalilin jin sunansa matsayin angon da aka ɗaurama aure da amarya mai suna Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi. Shi al'ajabi ne ma ko ruɗani yama rasa ganewa. Ya dubi Ahmad da ke kallonsa yana dariya, "Kai nifa ban ganeba wlhy, wai waye haka mai irin sunana komai da komai fa". Sake tuntsirewa da dariya Ahmad yayi har da riƙe ciki. Sai da yaga Smart ya turɓune fuska har yana harararsa sannan ya ɗan sassauta. Sai dai maimakon amsa masa sai ya miƙe dan yau dama ɗaurin auren biyu ne kawai ma, bayan an ɗaura na farko da ya kasance Smart da Lulu na biyun kuma aka fahimci shima dai da amaryar farko ne da wani angon, dan kuwa dai Alh. Sulaiman ne ya ƙulla, abin mamaki kuma babu shi a massalacin sai Tajuddeen kawai da gayyar abokansa. Yana jin kuma an ɗaura auren Lulu da Smart ya yanke jiki a wajen ya faɗi. Su dai mutane basu fahimci minene matsalar ba, haka ma su Abba magabatan Smart dan sai da aka tashi idonsa ya gane masa mahaifin nasa da tawagar dattijan anguwarsu. Sagade kawai yay yana kallonsu kamar television. Abba da ke kallonsa da murmushi ya ce, "Ɗan nema daina kallona ni, ko duk murnar ce ta saka sumar tsaye". Dariya dattijan suka sanya har da Baba. Uncle Yousuf da ke jin ALLAH ya gama masa komai a yau ya matso ya kama hannun Smart cikin nasa ya jasa ya rungume. "FATAN ALKAIRI SURUKINA". ya faɗa cikin kunnensa. Kamar wanda aka farkar a barci Smart ya ja nannauyar ajiyar zuciya. Cikin marairaice fuska alamar yaya haka.. yake kallon Uncle Yousuf. Shiko ya sake faɗaɗa dariyarsa da ɗan ɗage kafaɗa alamar nima ban sani ba. Coach ma rungumesa yayi yana mai jera masa addu'oi. Shi gaba ɗaya ma ya kasa iya furta komai. Sai da Ahmad yaja hannunsa gaban su Baba sannan ya motsa gaɓɓansa da ƙyar. Rissinawa sukai suka gaida Baba da ke zagaye da manyan mutane ciki harda gwamna. Abin zai baka mamakin yanda har aka iya haɗa mutanen bayan auren babu wani shiri a cikinsa. Koda yake ba abin mamaki bane idan akai dubi da girman Alh. Sufi Garko ɗin da ƙarfin ikon da yake da shi wajen manyan jihar. Sosai manyan mutanen nan suka dinga saka masa albarka kowa na jansa jiki ganin yanda Baba ya damƙe hannunsa cikin nashi shima. Daddy ma sun gaisa yana ƴar fara'arsa dai. Daga haka suka ringuɗa zuwa government house. Dan sakamako gwamna ne ya bada auren Mawaddat matsayin waliyyi yasa shi shirya liyafar cin abinci bayan ɗaurin auren. Smart dai ya zama kamar wani butun butumi. Komai ɗaukarsa yake kamar a mafarki. Ga kansa dake ƙara nauyi matuƙa har idanunsa na ɗan rinjayar ganinsa. Amma dai yanata dakewa kodan fidda mahaifinsa kunya. Dan duk da Malam Mika'il Idris Mawashi ba mai tarin dukiya bane. Dattijo ne nagartacce mai cikar kamalar da masu kuɗun dole suga girmansa da jin shakkar kawo masa raini. Shi da kansa ya biyama ɗansa sadaki naira dubu ɗari biyu. Sai dai Baba ya ce ɗari kawai zasu amsa ALLAH ya sanya albarka. Hakan ya ƙara sakama Abba jin kimar mutanen. Dan shi mutum ne mai girmama mutumtaka fiye da dukiya. A Government house mutanen da suka taru har sunfi na massalacin yawa saboda wasu sun iso a makare sai dai walimar zasu samu kasancewar sakon gayyatar ɗaurin auren yazo musu a ƙurarren lokaci dan a jiya jiyan nan da dare duk Baba yasa aka watsa shi a waya ta hanyar contacts ɗinsa dana Uncle Yousuf da na Daddy. Amma da ace shirine na musamman ai sai ma an rasa masaka tsinke. Sai dai hakan ma Alhamdullah, dan basuyi zaton taruwar mutanen kamar hakan ba amma sai gashi kamar wasa a kaso uku da suka gayyata kaso kusan biyu sun halarta bayan wanda sukaje massalacin salla kawai. Anci ansha anyi asuwaki da kaji yanda ya kamata, sai dai ango ya gagara cin komai. Ga abokansa ko nace teammate ɗinsa na ball zagaye da shi sunata masa shaƙiyanci da masa ciwon bakin jin auren a ƙurarren lokaci da sukai. Haka dai yayta daurewa har aka kammala cin abinci aka shiga hotuna. Nanma dauriyar yay tayi kasancewar duk wanda zai ɗauki hoto sai an jajubosa musamman ma manyan mutanen nan da ke nanuƙe da Alh. Sufi Garko. Shigowar lokacin sallar la'asar ne yay belinsa. Da ga salla kuma kowa zai kama gabansa..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣3️⃣ ......Sam Lulu bata san wace waina ake toyawa ba. Dan yau ma dai tashi tai da ciwon kai har da zazzaɓi sakamakon mura da ta mata ɗaurin kazar kuku. Da ƙyar ta iya tashi kusan 12 da Mommy ta tasheta akan tai wanka. A sannan ne ma suka san bata da lafiyar. Bayan ta ɗan samu tai wankan ne ta sha tea da Mommy ta haɗa mata da kanta mai kayan ƙamshi sosai. Wani irin faɗuwar gaba takeji ga rashin lafiyar da ta kadata. Da ƙyar ta samu ta ɗanyi waya da Zainab dan jin yaya ake ciki a office, sai kuma Sha'aibu ɗan sanda da yay kiranta yay mata albishir ɗin cafke mijin matar nan da suka sami nasarar yi. Hakan ya ɗan faranta mata rai da jin zazzaɓin nata ma ya sauka har ta fito falo. Anan taci karo da yayunsu su Twins sun zo. Sama-sama sukai gaisuwa ita da su dan sam babu jituwa tsakaninsu. Fasa zaman falon tai ta juya ta koma ciki ranta na ƙara dagulewa. Ta rasa mitai ma ƴan uwan nata suke jin zafinta irin haka. Hira da ta samu sunayi da sauran ƙannensu har da dariya, amma ita tana fita duk suka gimtse fuska sai Suhaib da Nazeer ne suka gaisheta, sai kuma Amrah da tai mata yaya jiki. Wannan abun ya jima yana damunta, sai dai rashin riƙe abu a rai kansa ta watsar ta cigaba da al'amarin ta musamman idan tasha wani abu haka. Gadonta ta koma ta kwanta dan da jikinta yay mugun zafin zazzaɓi, barci ne mai nauyi ya ɗauketa batare data shirya hakan ba. Hakan yasa har su Abba suka fita massalaci tare da yayunta da Mubeen da su Suhaib bata sani ba. Ba kuma ta farka ba har bayan la'asar da ƴar hayaniyar da gidan ya ɗauka ya farkar da ita da ga barcin da take mai cike da mafarkin mahaifiyarta da take matuƙar bege, sai drivern ta da bata san daga ina kuma mafarkin nata ya yayo mata shi ba dan ita dai bata kwanta da tunanin ko mai kama da shi ba balle ace. A hankali ta ɗan ja tsaki da murza goshinta da yay mata nauyi. Zazzaɓin nata ya sauka, sai dai nauyin da kan nata yay mata da rashin jin ƙwarin jiki. Landline phone da ke saman bed side drawer ɗinta ta ɗauka tai kiran sashen masu aikin gidan. Batare da jiran jin waye ya ɗauka ba balle amsa sallamarsa tai umarnin ganin Iya Tabawa ta yanke wayar ta ajiye. Cikin mintuna kaɗan kuwa sai ga iya Tabawa na faman washare baki. Kallo ɗaya tai mata ta ɗauke kanta cikin bada umarni kamar yanda ta saba ta ce ta haɗa mata ruwan wanka. "An gama ranki ya daɗe". Iya Tabawa ta faɗa tana nufar bathroom cike da farin cikin abinda su Daddy suka shigo da shi gidan cewar an ɗaurama Lulu aure. Harga ALLAH da gasken gaske son yarinyar take da ƙaunarta. Duk halayyar Lulu a gidan ta taka ma'aikata baisa taji ƙinta ba. Dan duk wulaƙancin da take musu hakan bai hanata ƙyautata musu randa ta so ba kuma musamman ma ita. Ba kuma komai ya ƙara girmama farin cikin ta ba sai jin wanda Lulun ta aura, dan ita sam bataga hakan komai ba duk da sauran ma'aikatan gidan na can na dariya da gulmar wai alhakinsu ne ya kamata ta ƙare da auren drivern ta. Dan su sosai abin yay musu suga da kallon cewar Lulu tayi faɗuwar baƙar tasa. Tana ƙoƙarin shiga wankan ta bama Iya Tabawan umarnin haɗa mata farfesun kifi mai yaji sosai dan Lulu na matuƙar son kifi a rayuwarta. Harta nufi ƙofar fita Lulun ta dakatar da ita. "Wai lafiya ne a gidan aka ishi mutane da hayaniya? Kema naga sai wani washare baki kike". Iya Tabawa da murmushi ya kasa barin fuskar tata ta ce, "Muma dai bamu san mike faruwa ba Aunty, munga dai su Alhaji ƙarami (Uncle Yousuf) nata farin ciki inagama aure dai ya ƙara". "What?! Uncle You ɗin ne ya ƙara aure ki kike nufi?". "Bani da tabbacin hakan Aunty, hasashen dai kawai nake". Tsaki Lulu taja cikin taɓe baki ta nufi bathroom ɗin cikin ƙunƙuni take faɗin, "Kai wannan tsohuwa da neman masifa kike. Haka kawai da ranar nan tsaka ace amma Aunty Saliha kishiya ai akwai ƙura. Dan koni nan na korar mata shegiya". Daga haka ta shige. Ta fito a wankan tana cikin shiryawa da kaya marasa nauyi na wando da riga akai mata knocking ƙofa. "Waye?" ta faɗa tana fesa turarrukanta. Uncle Yousuf ya amsa mata da cewar shine. Ƙofar ta nufa da sauri tana faɗin, "Uncle You!". Amsa mata yay yana turo ƙofar ya shigo, dan haka suka kusa cin karo. Baya taja da sauri tana mai zuba masa ido. Cikin kasa danne abinda ke bakinta ta ɗan waro manyan idanunta ta da faɗin, "Oh god wai da gaske ne kenan?". "Da gaske mi?". Ya faɗa idonsa a kanta. Fuska ta ƙwaɓe da wani yamutseta. "Kishiyar kaima aunty Salihar mu Uncle?". Yanda tai tambayar da wani tsuke masa fuska taso bashi dariya. Amma sai ya dake ya ce, "Eh haramunne?". "Kutt! Wai da gaske ne ma?". Kasa jurewa yay yanzu kam sai da ya dara. Dan a masifaffiyarta ta sake tambayar. Ya ce, "Kinga maida wuƙar Daughter ba haka bane. Ai auntynku ita da kishiya sai a aljanna". "Oh har na samu relief". Ƴar dariya yayi yana kaiwa zaune a kan sofa. Ya nuna mata wajen zama itama. "Kinga zauna bani da lokaci magana nazo muyi.". ganin yanda yaci serious ya sata kaiwa zaunen cikin bashi dukkan attention nata. Shima sake gyara yanayinsa yay da nutsuwarsa ya ce, "Mawaddat!". "Yes Papa". Ta amsa cikin sake nutsuwa. Cigaba yay da faɗin, "Kin san daga ina muke?". "Massallaci". Murmushi yayi da jin jina mata kai. "Yes daga massalaci muke, sai dai bayan yin sallar juma'a an ɗaura aure. Auren kuma bana kowa bane sai naki". Wani shegen dariya ta saki a lalace. Tace, "Uncle You ALLAH ka iya tsokana, sai kace wata babyn roba ". Murmushinsa ya sake faɗaɗawa da gyara zamansa. "Mawaddat ba wasa nake ba. Kema kuma kin san bana miki kalar wannan wasar ai". A take fara"ar fuskarta ta ɓace ɓat gaba ɗaya. Ta tsirama Uncle Yousuf ɗin ido kamar wadda tai suman wucin gadi. Fahimtar yanayin data shigan ne ya sakasa riƙo hanunta a cikin nashi yana girgiza mata kansa. "Kinga calm down sweet heart. Wannan aure ya tafi ne kamar yanda muka tsara da ke. Abinda yasa kuma akayisa yanzu ba tare da saninki ba kema shine a jiya da yamma......" ya kwashe komai game da ƙudirin su Tajuddeen da mahaifinsa ya sanar mata. Ya ɗora da hukunci baba dama abinda ya faru yau a massalaci yanzu haka ma Tajuddeen na asibiti an kwasheshi." A hankali ta lumshe idanunta. Sai kuma ta koma jikin kujera ta lafe dan ƙirjinta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Da'ace ta iya addu'a ita ya kamata ace ta karanto a wannan halin, sai dai kash hakan bai samu ba. Taja wasu mintuna a haka kafin Uncle Yousuf ya dawo da ita a hankalinta. "Mawaddat Please relax. A yanzu haka fa tare muke da Baba a gidan nan. Kuma son ganinki sukeyi. Ina so. Ki nutsu kisa hankalinki waje ɗaya dan kar kije ki canja abinda muka tsara kuma ta ƙwaɓe, dan idan Baba ya fahimci shirinmu bake ba hatta ni da Yaya da bai san komai ba sai ranmu ya ɓaci. Ki dake zuciyarki ki nuna jin daɗinki ga hukuncinsa ta haka ne kawai zai kauda kai akan ki mu samu cikar burinmu dan zuwa dare zan nemo Aliyu yazo ayi komai a rubuce ma". "Uncle karfa ya bamu matsala. Wlhy guy ɗin nan yanada taurin kan masifa fiye da yanda kake tsammaninsa". "Karki damu insha ALLAHU babu abinda zai faru. Komai bazai canja ba da ga yanda muka tsara in har kin yi abinda ya dace yanzu a gaban Baba ta yanda bazai fahimci komai ba". Kanta ta jinjina masa muryarta a shaƙe ta ce, "Shikenan zanyi yanda kace. Amma Please bana son ganinsa yau sam". Murmushi Uncle Yousuf yayi yana miƙewa. "Baki da matsala da hakan tashi kisa mayafi muje. Koma dai ki canja kayan nan zuwa atamfa haka ki lass ok". Badan taso hakan ba ta gyaɗa masa kai kawai. Ya fita yana sake jadadda mata ta kiyaye dai ta kuma kula kar wanda ya fahimci halin da suke a ciki...... ★..... A ɓangaren Smart kam tunda suka bar government house hannunsa riƙe yake da kansa. Tun su Ahmad na masa shaƙiyanci da wasu a cikin teammate ɗinsa da suka biyosu a motar Ahmad ɗin har suka fahimci shirun nashi bana lafiya bane. Dan duk da dama shi bamai yawan magana bane koyaya ne zai musu murmushi ko yace wani abu koda sau ɗaya ne, balle wannan ranar a gareshi ta musamman ce, tunda su dai basu san komai game da auren ba. "Mawashi lafiya dai?". Cewar Ahmad yana gangarawa layin anguwar su Smart ɗin. Kansa ya nuna masa da hannu kawai. "Subahanallahi ciwo yake maka kan?". Kan ya sake gyaɗa masa. Shiru motar tai na ɗan lokaci duk suna kallonsa, sai kuma suka shiga jera masa. Kusan tare motar tasu ta tsaya da ta su Abba suma. Dan haka suka firfito a tare, dole ya sake daurewa dan a cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar gidan shima ya fara tara mutane ƴan taya murna, dan al'amarin kamar busa usur zancen auren ya dinga shiga kunnuwan mutane, dama gashi juma'a ce yawancin mutane duk sun dawo gida..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲 🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗 𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻 𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣4️⃣ ........Gayyar yayunsa da ƙanne su Salim da sai da sukaje wajen ɗaurin aure suka san dawa aka ɗaura kusan ransu duk a ɓace yake, dan gani suke kamar Abban ya rufe zancen ne dan yafi son Hydar ɗin a gidan kamar yanda iyayensu kan faɗa. Komai ya sake tsaya musu a rai jin ƴar wanda ya aura da kuma Gwamna da yay waliccin auren. Zuwa walimar cin abincin ma a gidan gwamnati sai da Abba ya nuna ma wasun su ɓacin rai sukaje. Su dai su Mubarak ƙanana ko'a jikinsu, sai ma farin ciki suke ballema yau gasu a cikin government house. Sune suka fara isa gida da labarin wannan aure na bazata, dan sun riga su Abban tahowa, sune kuma suka baza batun auren a anguwar.. Smart yayi dauriyar tsayawa amsa gaisuwar mutane da taya murna kafin su shiga ciki. Sun tadda gidan a ɗan harmutse, dan kamar kowa jiran shigowar Abba yake. Shiko Abba da yasan da hakan a tsumensa ya shigo, dan haka dole kowa ta kama kanta sai dai ƴar ƙus-ƙus a ɗaki tare da yaransu dan har na ma'auri matan yau suna gida kasancewar hakan kamar ɗabi'ar yaran gidan ce duk juma'ar ƙarshen wata anan suke yini su da gayyar ƴaƴansu.. Umarni Abba ya bama Smart ya biyoshi falonsa. Ya kuma aika Musaddiq tattaro sauran jama'ar gidan suma. Cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya hallara har falon na neman musu kaɗan. Dan kuwa dai ALLAH ya azurta malam Mika'il Idris Mawashi da baiwar ƴaƴa. Matan ne suka shiga gaisheshi da sannu da dawowa dan sanda wasunsu suka iso shi ya fita. Ya amsa musu da tambayarsu mazajensu dama yaran duk da yasan sukam duk suna tare da su anan. Zakuma su zo gaisheshi. Duk da ran wasun su a dagule yake haka suka dinga amsawa mahaifin nasu kamar yanda suka saba. Shima ya lura da yanayin wasun su ɗin, amma sai bai damuba dan yasan iyayensu mata ne suka gama kunnosu, ya kuma san bai wuce akan wannan aure na Hydar da ya sirrinta ba. Yayi gyaran murya da sake tsare gida yana maida kallonsa ga matan nashi duka huɗu. "Zan fara da ku matsayinku na iyaye. Alhamdullah da farko zan fara da sanar muku yau dai ALLAH yayi an ɗaurama Aliy aure. Nasan abin zai iya zama abin mamaki a gareku har ma da ka-ce-na-ce. To bazan hana hakan ba, sai dai zan fahimtar da ku muma a haka al'amarin yazo mana. Ga mahaifiyar sa nan ita kanta sai a safiyar yau na sanar mata cewar zamu kai kuɗin auren Aliy domin iyayen yarinyar da yake so ɗin sun buƙaci haka sakamakon ɗan rikici da abokan neman auren nasa suke son kawo wa a ciki. Ni kaina kuma a yau ɗin munje ne da batun kai kuɗin aure sai suka buƙaci kawai a ɗaura domin hakan ya zama masalaha ya kuma bama kowa kwanciyar hankali. Sosai hakan yamun daɗi, dan ganin auren Aliy a yanzu yana ɗaya da ga cikin abinda ke damuna, bayan mun dawo naso zaunar da ku na muku bayanin halin da ake ciki sai ya zam guri ya ƙure, dan haka nace bari mu bari har sai mun dawo. To Alhamdullah yanzu dai ta ƙare, shima Aliy ya shiga sahun ƴan uwansa, sai muyi masa fatan alkairi da zaman lafiya da zuri'a mai albarka kamar saura, an ɗaura aure ne kawai sai zuwa wani satin insha ALLAHU za'ai biki duk da mu hakan dai yazo mana a ƙure amma ALLAH muka riƙe mun san kuma bazai bamu kunya ba...." "Tofa bazawara ce kenan?". Cewar Umma a gatsine. Murmushi Abba yay da kafeta da idanu, sai kuma ya janye yana jinjina kansa. "Yarinya ce budurwa ba bazawara ba, ɗiya ce ga Alhaji Isma'il Ibrahim Jiƙamshi, sannan jika ga Alhaji Sufi Ado Garko". Kusan duk falon musamman matan babu wanda bai zabura da jin sunayen guda biyu ba. Dan daga Alhaji Isma'il Jiƙamshi har Alhaji Sufi Garko babu sunan da bai zama mai shura ba a cikin Kano da wajenta musamman ma shi Alhaji Sufi Garko ɗin. Ƙwarai da gaske sun girgiza har mazan a yanzu dan suma dai basu san kuma amaryar tanada alaƙa da Alhaji Sufi Garko ɗin ba sai yanzu. No wander dole gwamna yay walicci kam ashe. Ƙus-ƙus ɗin da falon ya ɗauka ne ya saka Abba yin gyaran murya, a take duk sukai tsit. Abba ya cigaba da faɗin, "Kamar yanda na faɗa muku sati mai zuwa za'ai biki amarya ta tare, sai kowa yaje kamar yanda tsarin wannan gida yeke kowa ya kawo gudunmawarsa, a kuma kasance cikin shirin biki." "To amma yanzu Abbansu a sati guda ɗin nan har wane shiri za'ayi? Bayan kowa yasan Hydar bai ajeba bai ba ma wani ajiya ba. Gashi ya kinkimo ƴar babban gida da su komai sunfi buƙatar ganin dozin". Mama ce da wannan magana itama dai da alama ranta a jagule yake, dan fa jin Smart ya samo ƴar babban gida ransu fal kishi da hassadar ba ƴaƴansu bane. Caraf Umma ta amshe da faɗin, "Kema kike ta wannan ai ga zancen gudunmawa da yaywa yaran nan. Maganar gaskiya ba'ace gudunmawa ba kuma a irin wannan ƙurarren lokacin Abban su. Yanda abubuwa sukaima mutane yawa kowa na fama da kansa da iyalinsa, shi Hydar ɗin yasan bai shirya ma auren ba ya kinkimo ƴar masu hannu da shuni shi ba sana'a ba ba komai ba. inba dai sune zasu masa komai ba dan da'alama ma sadakin sune suka biya masa ko?". Kallonsu kawai Abba yake yi, su kansu kuma a cikin yaran duk sai sukaji kunyar abinda iyayen nasu keyi kamar wasu ƙananun yara sun kasa ɓoye baƙin cikinsu. Abba ya maida kallonsa ga Ammah da tunda ta shigo kanta a ƙasa yake baiwar ALLAH. Ajiyar zuciya ya sauke da sake maida idonsa kansu Mama ɗin. "Yalwati da Yahanasu nasan dai kun san da Aliy da yaran nan duk nawa ne ko? Kuma ni ne na bada umarnin haɗo gudunmawa kamar yanda nake basu akan kowacce hidima anan gidan tunda ba yau na fara ba. A kaf ɗinsu kuma ba gori ba babu wanda Aliy bai taka rawar gani a hidimar aurensa ba a bashi da aikin yin dai. Maganar kuma sati guda yay kaɗan ba'a shirya ba wannan komai na ALLAH ne babu ruwanku. Sannan sadaki ga ƴaƴanku nan ku tambayesu a duka aurensu ni ne na biya musu sadaki, ko akan Aliy ne zan canja abinda nake tun farko?. Ƴar babban gida kuma data tsole muku ido ALLAH ne ya bashi kasancewarsa mai ƙyaƙyƙyawar zuciya da nagarta, fatanmu ALLAH ya taya shi riƙo dan shi bai auri ƴarsu dan kuɗinsu ko sunansu ba". Sosai murtanin Abban ya hana kowa sake yin motsin kirki. Sai ma a cikin yaran ne maza jikin wasu yay sanyi suka shiga bama Abban haƙuri, tare da masa alƙawarin yin zaman meeting na musamman akan bikin. Albarka ya saka musu tare da sallamar kowa. Smart ne kusan ƙarshen fita, dan haka Abba yace masa bayan sallar isha'i ya samesa. Kai kawai ya jinjina masa ya ƙarasa ficewa cikin dauriya.. Fitowar tasa ta bama wasu da ga cikin ƴan uwan nasa damar tayashi murnar da suka gagara yi a ɗazun. Murmushin kawai yake musu da amsawa cikin dauriya, da ga haka ya wuce ɗakin Ammah. Ya samu Aunty Bilkisu da ƙanwar Ammah da tazo gidan babu jimawa suna tattauna abinda su Ummar sukai yanzu a gaban Abba. Yayinda su Asma'u ke ta faman murnarsu sukam finally Yayansu yayi aure shima gorin Umma ya ƙare. Gaban Ammah yaje ya zauna, yayinda Gwaggo Sa'adah ƙamwar Ammahn ta muƙe tana masa ghuɗa da kirari kasancewar sunan mahaifinsu ne ya ci, dan duk ƴan gidan su Ammah Babangida suke kiranshi ko suce Hydar, shiyyasa ma ko'anan gidan nasu Hydar ɗin ta bisa, Abba ne kan kirashi da Aliy shima wani lokacin yakance masa Baba. Idanunsa ya rumtse da sauri dan har cikin tsakkiyar ƙwalwar kansa ghuɗar nan ke ratsashi. A take kansa ya fara juyawa ya ringa ganin kamar ɗakin na juya masa shima. Ɗayan hannunsa ya kai ya ƙara dafe kan da hannu biyu. Hawwah ce ta lura da hakan, da sauri ta ce, "Yaya Hydar lafiya kuwa?". Yanda tai maganar cikin zaburowa ya sa Gwaggo Sa'adah dakatawa, Ammah ma ta haɗiye murmushin fuskarta ta maida dubanta garesa. Aunty Bilkisu ma da ke ta faman turama dangi saƙo ta wayar Ammah ta miƙe zumbur. Ammah da ke kusa da shi ce ta samu nasarar taroshi jikinta, dan gaba ɗayansa ya tafi zai zube damma a zaune yake...... ________________★ Ƙololuwar ɓacin rai Alh. Sulaiman ya shiga sakamakon kiransa da akai masa cewar ga Tajuddeen a asibiti sakamako auren Lulu da mahaifinsa ya ɗaura yau da shegen tsageran yaron nan da yakema kallon abin alhaki. Abu mafi ɗaure masa kai shine ta yaya Baban yasan da shirinsa har yaje ya ɓata masa shiri haka? Ya san dai da ga shi sai Tajuddeen suka ƙulla hakan. Dan ko mahaifiyar Tajuddeen ɗin bata san komai ba akai. To kodai cikin waɗanda ya aika sumasa waliccin auren ne? Kai bayajin hakan zata kasance ai. Dan Kawu Laminu mutum ne makwaɗaici yasan kuɗin da ya shaƙa masa bazai barsa buɗe baki ya faɗama wani ba. To ko Tajuddeen ɗinne yay ɓaranɓarama a gaban wani? Shima dai hakan bai kama hankali ba gaskiya dan yasan yanda Tajuddeen ke son auren nan bazai taɓa bari wani ya samu ƙofar rusa masa shi ba. Tattare komai yay ya ajiye gefe yabar maɓoyar tasa zuwa asibiti. Dan yazo nan ɗin ne ya ɓoye saboda Baba har sai ƙura ta lafa zuwa gobe kamar yanda ya tsara idan an ɗaura aure da Tajuddeen. Lokacin da ya isa ya samu Tajuddeen ko farfaɗowa baiyi ba ma. Ga shi labari yazo masa su baba na government house ana liyafar cin abinci bayan a gabansu Jikansa ya faɗi amma ya shure saboda bai ƙaunarsa shi da ɗansa. Sosai zuciyarsa ke ƙara tafasa, yayinda yake saƙa abubuwan alkaba'i da zai rusa rayuwar Smart da duk wanda ke tare da shi. Dan a ganinsa duk shine ya ruguza masa shirinsa, sai yanzu ma yake nadamar bayyana masa fuskarsa a waccan ranar... Farfaɗowar Tajuddeen babu jimawa mahaifiyarsa ta iso, sai dai daga zuri'arsu kaf babu wanda ya leƙo asibitin dan Baba ya hana. Ya kuma tabbatar musu duk wanda yaje sai ya ɓata masa rai fiye da yanda yake zato ko tsammani..........✍️ _LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* FURAR DANKO Billyn Abdul -ZAFIN KAI Mamuhgee -TABARMAR 'KASHI Safiyya Huguma -BAKON MUNAFIKI Miss xoxo Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Pay at👇 1487616276 Access Bank Bilkisa Ibrahim Musa Sai katura shedar biyanka anan👇 09032345899 Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇 09033181070 VIP🔥💯 Zafin kai 3k Furar danko 3k Tabarmar kashi 3k Bakon munafuki 3k *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* *THANKS FOR CHOOSING US*🥰 Zafafa🫶🔥 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels