An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Magana Jari Ce Littafi Na Farko Magana Jari Ce 1 Yaro Ba Da Kudi A Gaya Maka! Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E., C.O.N. -Kámfanin Littafai Na Nijeriya Ta Arewa ZARIA. Mallaka (M Kamfanin Gaskiya Zaria 1945 Ba a yarda a kwafi wannan Littafi ba, dukkansa ko sashinsa don bugawa ko sa wa a kowace irin na'ura, sai an samu izini a rubuce. An Fara Bugawa 1937, An sake Bugawa Sau 17, daga 1954 - 1985. Gyaran Farko 1993, 1997. 1998 An Shirya a Kamfanin Littafai Na Nijeriya Ta Arewa Lambar Gidan Waya 412, Kamfanin Gaskiya, Zaria. ISBN: 978-169-057-7 An Buga Shi a Kamfanin Gaskiya, Zaria Labarun Da Ke Ciki Gabatarwa Shafi Labarin Sahoro Da Sahorama Magana Jari Ce Labarin Wani Bororo Da Dan Zaki Banza Ta Kori Wofi Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku Taho Tare Labarin Auta Dan Sarkin Noma Da Naman Jeji Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yan Birni 1 13 18 22 26 29 32 Labarin Wani Aku Da Matar Ubangidansa 37 Labarin Sarkin Zairana Da Sarkin Bokaye Gara Labarin Kyanwa Da Bera 40 44 Labarin Wani Jaki Da Sa 49 Yadda Muka Yi Da Ubangijina Ojo 53 In Ajali Ya Yi Kira, Ko Babu Ciwo A Je 57 Labarin Wadansu Abokai Su Uku 61 Munafuncin Dodo, Yakan Ci Mai Shi 65 Abin Da Mutum Ya Shuka Shi Zai Girba, In Hairan Hairan, In Sharran Sharran 68 Fara Koyon Mulki Da Baki, Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu 71 Babban Mugun Abu Gun Da Ya Yi Hushi Da Iyayensa 75 Banza Girman Mahaukaci, Karamin Mai Wayo Ya Fi Shi 79 Labarin Sarkin Busa 62 Kowa Ya Yi Kokarin Ya Sami Fiye Da Abin Da Allah Ya Nufe Shi Da Shi, Ya Ja Wa Kansa Lalacewa Labarin Annabi Sulaimanu Ba Wahalalle Sai Mai Kwadayi Saurin Fushi Shi Ke Kawo Da Na Sani Raina Kama Ka Ga Gayya Labarin Shaihu Mujaddadi Dan Hodiyo Da Umaru Mu'Alkamu Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Madugu Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Wani Malami Sauri Ya Haifi Nawa 88 94 96 99 103 107 110 113 116 GABATARWA Wannan littafi, Magana Jari Ce, 1, yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin zaßo shi kuwa ya rubuta wadannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa ta rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'. An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin Kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta 'Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen kaga labari mai ma'ana ya sa Dr. R. M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya. Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko ta Arewa. Shi ne ma ya rada mata suna 'Gaskiya Ta Fi Kwabo' aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939. Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin 'Yakin Duniya Na Biyu' watau 'Yakin Hitila' da ya ba suna 'Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da labarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa ta Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943. Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne 'Tarihin Annabi da na Halifofi' wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin nan yana shugaban Hukumar Daukar Ma'aikata ta Nijeriya ta Arewa. Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nadawa Kwamishinan Jin Kararakin Jama'a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana kiranta Arewa ta Tsakiya. Ya rasu yana da shekara 70 a duniya ranar Juma'a 19 ga watan Yuni, 1981. Alhaji Abubakar Imam ya rika cewa wannan aiki da ya yi, na talifin 'Magana Jari Ce' ya yi masa amfani ainun. Ya kan ce wannan aiki shi ne ya ba shi damar zama tare da mashahurin Baturen nan na talifin Hausa, Dr. R. M. East, O.B.E. Ya ce daga gare shi. ne ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi. Abin mamaki, shi kuma wannan Bature, Dr. East O.B.E., a wajen 'Mukaddamar' da ya yi da Turanci tun farkon buga 'Magana Jari Ce', ga abin da ya ce: 'Muna godiya ga En'e ta Katsina, saboda taimakonsu, da hangen nesa da suka yi, har suka yarda, suka ba mu aron Malam Abubakar Imam. Suka yarda, ya bar aikinsa, na koyad da Turanci a Midil ta Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadannan littattafai a cikin harshensa. 'Iyakar abin da mu ma'aikatan wannan ofis muka yi, na game da talifin wadannan littattafai, shi ne aiki irin na ofis, na shirya al'amuran, yadda suka kai har aka buga su. Ban da wannan sai kuma taimakonsa da muka yi na tattara masa littattafai iri iri, don ko zai kwaikwayi wani samfur. Sai fa,kuma wajen shiryawa bayan da ya rubuta. 'Kai, in dai'har muna da wani abin da za mu yi kirari mun yi, game da talifin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu kawai, shi ne yadda muka yi har muka binciko wannan malamin talifi'. 1982 N.N.P.C. Magana Jari Ce A wani gari a kasashen gabas an yi wani babban Sarki wanda a ke kira Abdurrahman dan Alhaji. Rabonka da samun ko labarin mai arziki irinsa tun Dankaruna, mutum ko gidansa ya shiga ya ga yadda aka kawata shi, ya ga kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya rike baki kawai, don abin ya fi gaban mamaki. Zaurukan gidan nan kuwa-kai! In ma mutum ya ce zai tsaya ya bayyana arzikin Sarki Abdurrahman ga wadanda ba su san abin da a ke kira duniya ba, sai su yi tsammani shara ta yake yi. Amma duk yawan arzikin Sarkin nan sai ya zama na banza, don ba shi da 'ya'ya, ba shi da kane, ba shi da wa. 'Ya daya kadai gare shi, an ko yi mata aure, Saboda haka Sarkin nan ya zama ba wani wanda zai gani ransa ya yi fari cikin fadan nan tasa duka. Ya ga in ya mutu duk dukiyan nan sai a raba a ba matarsa da 'yarsa kadai, abin da ya rage a sa baitulmali. Kuma sarautarsa sai wanda Allah ya ba ya ci. In ya tuna da wannan, duk sai ni'imomin duniyan nan da Allah ya ba shi su yi masa baki kirin. Ana nan ran nan sai 'yan nan tasa ta haifi da namiji, aka yi shagali, aka sa wa yaron Maiımudu. To, amma ko da ya ke Sarki ya yi murna kwarai da ya sami jika, duk da haka murnarsa ragaggiya ce domin dan mace ba ya gado, balle har a ce ya yi sarautaа. Yana nan cikin wannan bakin ciki, sai ran nan wani shaihun malami ya zo ya ce masa, "Na yi mafarki jiya, an gaya mini da za ka tara malamai arba'in su yi ta yi maka addu'a har kwana arba'in, in Allah ya so za ka haihu." Sarki ya yi murna da wannan mafarki, ya dauko kudi da riguna zai ba malamin nan. Malamin ya ce shi ba kuďi suka kawo shi ba, ya zo ne ya isad da umurni, ya yi sallàma, ya tafi. Ranar ba ta sake juyowa ba sai da Sarki ya sa aka tara masa 1 manyan malamai guda arba'in na kasarsa, ya gaya musu abin da ya ke so. Suka ce, "To, Allah ya karbi rokonmu!" Mutane suka ce amin. Suka yi shiri, suka shiga masallaci, suka duka. Ubangiji ya nufe su da katari, ya karbi rokonsu. Kwanan nan arba'in ba su cika ba sai da matar Sarki ta sami ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji, wanda kyaunsa ba shi da iyaka. Shagalin da aka yi cikin kasan nan, da farin cikin Sarki bisa ga wannan al'amari, ku da kanku kun san ba shi yiwuwa a bayyana shi cikin wannan dan karamin littafi. Aka dai, rada wa yaron nan suna Musa. Watau tsakaninsu da jikan Sarki abin bai ko yi shekara ba. Sarki kuwa ya dauki ransa ya kallafa bisa kan yaron nan. A ma tsaya a kwantanta son da Sarki ke wa dan nan nasa, abin ya zama kauyanci ke nan. Kwanci tashi, bayan shekara biyu aka yaye yaron. Sarki kuma ya aika aka kawo jikan nan nasa Mahmudu, aka yaye su gaba daya, don su rika wasa tare. Suka tashi sai ka ce tagwaye, ba abin da ke raba su. Da duk abin nan burin Waziri, tun da Sarkin nan ba shi da da namiji, in ya mutu shi ya ci sarauta. Yana alla-alla Sarki ya mutu bai haihu ba, sai Allah ya kaddara haihuwar wannan yaro. Tun ran da Waziri ya ji gudar haihuwar Musa, zuciyarsa ta yi baki kirin, daga ran nan ya zama ko mai suna Musa ba ya so ya gani, ya shiga kulle-kulle kullum na yadda zai yi ya kashe Musa, ko kuwa ya sa ya bi uwa duniya, abin ya gagara. Har yara suka yi kamar shekara goma sha biyar biyar, ko ina Sarkin nan za shi da su ya ke zuwa. Ana nan ran nan, ina ya Allah babu ya Allah sai Waziri ya sami wata dabara, ya ce a ransa, 'Alhamdu lillahi, ko-da-ya-ke ba yadda za a yi in sami Musa wani wuri shi kadai ba tare da Sarki ba, balle in san abin da zan yi masa, ai in na yi kokarin da na raba Musa da Mahmudu, kome ya yi kyau. Domin yadda suka shaku haka, lalle in aka raba su hankalin Musa zai tashi, ta wannan hanya zan san yadda 2 zan yi in sa shi ya sulale da dare ya bi dan'uwansa." Sai ya yi dariya, ya buga kafa a kasa. Kashegari, ko da ya tafi wajen fadanci aka fara 'yan tade-taden duniya, sai ya takalo maganar yaki, ya ce, "Mu dai mun saki jiki da duniya yanzu, ba mu shirin kome." Sarki ya ce, "Me ya kawo wannan magana, Waziri? Muna cikin sulhu haka, me ruwammu da wani shirin mayaka?" Waziri ya ce, "Ai ka san ba a san abin da sauran kasashe ke ciki ba. Gwamma ko mu zauna da shiri, don ba a fafa gora ranar tafiya." Sarki ya ce, "Wane shiri ya fi wanda mu ke da shi yanzu? Ga Sarkin Yaki, ga Barde, ga Madawaki, cikinsu kowane ya yi kukan kura sai a ba shi hanya." Waziri ya ce, "Wadannan ai duk sun tsufa, ga Sarkin Yaki yanzu a kalla ya ba saba'in baya. Wanda ya ke haka, tun da Allah ya nufe shi da samun magaji, ya kamata ya huta. Dabarata sai Mahmudu ya koma gidansu, ubansa ya rika koya masa al'amuran yaki." Musa da ke nan sai ya tsolma baki ya ce, "In dai don a dauke Mahmudu ne, a bar ni ni kadai, ni ban yarda ba, sai dai mu je a koya mana tare." Waziri ya kau da kai ya kuta, ya ce, "Ina ruwanka da koyon yaki, kai da za ka sa a je a yi maka?" Musa ya ce, "Ni dai ban yarda mu rabu ba." Sarki ya ce, "Tun da Musa bai yarda ba, dabararka ba ta yi ba ke nan, Waziri." Waziri ya bata fuska, zai fara wata magana sai ga wani ya zo ya fadi gaban Sarki, ya ce, "Ga Wazirin Sarkin Sinari ya zo da wadansu manyan garinsu, ya ce a yi masa iso." Sarki ya ce ya shigo. Da ya shigo ya yi gaisuwa, ya mika masa takarda. Magatakarda ya karba ya buda, sai ya ga an rubuta: 3 "Takarda ta fito daga Sarkin Muminai, Sarkin Sinari, Abdul'azizi, dan Shaihu Muhtar, zuwa ga masoyinsa amininsa Sarki Abdurrahman, gaisuwa mai yawa, da so, da yarda, da aminci. Amma bayan haka ina so in karfafa zumuntan nan da ke tsakanimmu, saboda haka na ba dana Musu 'yarka Sinaratu, in sun kara girma a yi biki. Sai mu shirya a gama su tun muna da rai. Haza wasalamu.” Da Sarki ya ji abin da takardan nan ke ciki sai ya tashi da fada, ya fizge takarda daga hannun Magatakarda ya kyakke ta. Ya tashi ya kama gemun Wazirin Sinari, ya jefad da shi gefe guda. Sarakunansa suka shiga tsakani, suna "Hucewa mai duniya! Rashin hankali ne na yara." Sarki ya сe, "Ko Musa ya lalace ya auri Sinaratu? Me aka yi aka yi Sarkin Sinari, balle 'yarsa Sinaratu?" Ya dubi mutanensa, ya ce, "Ku yi ta dukansu sai sun bar kasata! Wazirin Sinari ya ruga, ya haye dokinsa, mutanensa suka dafi bayansa. 'Yam birni suka bi su eho, eho. Fada duk ta rude, fadawa suka yi ta duban juna. Liman ya ce, "Allah ya ba ka nasara, abin nan da aka yi, a aika lafiya dai?" Sarki ya ce, "Me ya firgita ka? Don dai mai garin Sinari ko cewa na yi a mare shi, ya yi magana?" Barde ya ce, "Ai Sarkin Sinari yanzu ganin kansa ya ke daidai da kowa. Ban yi tsammanin abin nan da aka yi masa zai kyale ba." Sarki ya ce, "Kai ma ka karai ne, kamar Liman?" Waziri ya ce, "Ba karaya ba ce, ai gaskiya c abin da na ke fadi yanzu na kan ba mu da shirin kome." Mutane suka ce, "Gaskiyarka, Wazir, ga Sarkin Yaki yau 4 kwanansa kamar ashirin ke nan sai a kwantar a tayar, ba shi ko da magaji." Sarki ya kara fusata, ya ce, "Ba shi da magaji? Watau kun shiga maganar tsohon banzan nan? In dai maganar Mahmudu ku ke wa mita, na dauki alkawari, ko bai iya kome ba, duk yakin da ya fara tashi nan gaba, shi zai zama jagaba." Aka gama fadanci aka vatse, suka tafi suna zunden Waziri. Waziri ya koma gida da fushi, ya kama shawarwarin abin da zai yi wa Sarki ya huce haushinsa. Daren nan ya kasa barci, ya kulla wannan ya kwance, har asuba. Da gari ya waye sai ya rubuta takarda zuwa wajen Sarkin Sinari, ya ce, "Kada wani bu ya ba ka tsoro da Sarki Abdurrahman, shirim ne ba inuwa. Muddin ka dauki alkawarin za ka naďa ni Sarkin garin nan, ni ko na san yadda zan yi in taimake ka ka ci kasar. Domin duk mutanen kasar sai abin da na ce musu. Da farko sai ku dauri niyya maza ku zo kafin su shirya. Ku biyo ta kadarkon Kimba, don ta wannan hanyar har ka shigo birni kowa bai sani ba. Ku taho tare da wannan yaro ya nuna muku hanya, domin ko ban da shi nan kasar ba wanda ya san wannan hanya." Sai ya ba wani amintaccen bawansa, wai shi Barakai, ya gaya masa yadda zai yi, ya sallame shi. Sarki Abdurrahman kuwa bai sake komawa ta kan Sarkin Sinari ba. Ana nan ran nan ya sa aka daura wa dawaki sirada, ya hau tare da yaran nan suka tafi shan iska, har suka kai wata fadama, suka sauka suna hutawa, sai ga wani Balarabe dauke da aku cikin keji. Ko da Musa ya daga ido ya gan shi sai ya ce, "Alo, alo, ga aku a saya mana!" Nan da nan wani bawan Sarki da aka je da shi ya kira Balaraben nan, ya tambaye shi kuďin akun. Balarabe ya ce, "In ba jaka guda ba, ba na sayad da shi." Da bawan nan ya ji haka sai ya ce, "A'a! Da Sarkin za ka yi ba'a? Kana tsammani Sarki ya tambaye ka karin magana ce?" Da bawan nan ya fusata Sarki haka, sai ya cika ya ce a kama Balaraben nan. Bayin da aka zo da su suka tasam masa kamar za su cinye shi danye, da shi da tsuntsunsa duka. Da dai tsuntsun nan ya ga haka, sai ya kada fifike, ya се, "Allah ya ba ka nasara, kada ka yi hushi bisa ga gaskiyar ubangijina. Ni ma a jaka gudan nan da ya fadi a ganina ya karya mini daraja ne. Kamata ai bai kamata a sallama ni jaka guda kadai ba." Sai sarki ya ce wa bayi su tsaya. Ya dubi dan tsuntsu, ya ce, "Kai kuwa dan tsuntsun nan mene ne dalilinka na wannan cika baki haka?" 5 Sai aku ya dukad da kai, ya ce, "Akwai kuwa, Allah ya ja zamaninka, takamar da na ke yi ba don saboda kyaun jikina kaďai na ke yi ba, ba ko don saboda dadin bakin nan da Allah ya ba ni ba, amma saboda baiwa wadda Ubangijimmu ya yi mini ta wajen iya duba. Har yanzu ta kai ni fagen ina iya ba da labarin abin da za a yi nan gaba, balle ma a tambaye ni wanda aka yi ya wuce. Kuma a cikin bokanci, sanin da Allah ya ba ni ba shi da iyaka. In kuma labaruruka ka ke son ji, ko na aljannu, ko na barayi, ko na Sarakuna, in ka saye ni in ya so ma kada ka sake batad da kuďinka a banza garin sayen Alfulaila, ko wadansu littattafai na Turawa wadanda ba su da wani labari daga na tafiye-tafiyen gano kasashe, sai fa na tarihe-tarihe da na lissafelissafe, da na kiwace-kiwacen lafiya, masu gundurad da mutane. In kuma karuwa ka ke nema wurin arziki, in ka saye ni bukata ta biya." Sarki ya ce, "Ta wajen suruntun naka na wofi?" Aku ya ce, "Surutu ba abin rainawa ba ne. Magana ai jari ce." Da yaran nan suka ji ya iya ba da labarai, da ma abin da su ke so ke nan, sai suka yi ta tsalle-tsalle suna murna. Sarki ya rike baki yana mamakin wannan tsuntsu. Sarki ya ce wa aku, "Tsaya mene ne na wannan irin fafarniya? Yabon kai jahilci. In kana da hikima, gaya mini yau shekarun Musa nawa?" Sauran mutanen da suka zo tare da Sarki suka fashe da dariya, suka ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, ka ko kashe mana bakinsa! Ya fadi mu ji, kan ba karya ba." Aku ya dubi Musa, ya ce, "Yau shekarunsa goma sha hudu da wata biyar da kwana uku." Mutane suka ce, "A'a! Ai ko, Allah ya ba ka nasara, gaskiyarsa!" Sarki ya ce, "Kai, ji ya yi wajen wadansu ana fadi. Labarin Musa yanzu ina ne bai kai ba?" Ya sake ce wa aku, "To, mun ji ka rike wannan da ka ji mutane ke fadfi, amma wace rana ce aka haife shi?" Aku ya sake duban Musa, ya ce, "Ranar Jumma'a da la'asar." Sarki ya ce, "A'a! Ai ko gaskiyarsa." Ya dubi aku, ya ce, "Da ya ke kana da hikima, sai ka gaya mini me za: fara aukuwa gare shi?" Aku ya ce, "Ba za ka so ka ji wannan al'amari ba, don zai bata maka rai kwarai. Ya fi kyau a bar kaza cikin gashinta." Sarki dai ya nace sai ya gaya masa, in ya ki kuwa yanzu ya sa a hura wuta a babbaka shi da rai. Da aku ya ga Sarki ya fusata sai ya ce, "a yi mini gafara bisa ga abin nan da zan fadi. Musa zai zama snad.n cuce-cuce, da 6 raunuka, kai har da halakar rayukan mutane kamar dubu na kasan nan. Wannan al'amari kuwa ba da daďewa ba zai auku. Da ma kana ganewa, ka sake shiri tun da wuri." Da Sarki ya ji haka sai ya hasala, don aku ya ce dansa zai zama sanadin mace-mace. Ya dauki kejin ya jefar. Ya tashi zai je ya take dan tsuntsun nan ya mutu. Bayi kuma suka zaburam ma Balarabe, duk wurin ya harmutse. Sai kwaram suka ji kuwwa. Su waiga haka, sai ga wani mai doki sukwane, ya zo ba ko sirdi, duk jikinsa jina-jina, abin ba kyaun gani. Ya fadi gaban Sarki, ya ce, "Wayyo Allah! Wayyo Allah! Ka yi mana agaji! Ai ga Sarkin Sinari can ya shigo kasarka da yaki, 'yan garuruwammu na nan kan iyakar arewa duk sun zama toka. Na rantse har da girmanka, ni kadai na tsere!" Sarki da mutanensa duk suka yi sako, kowa na duban dan'uwansa. Sai kawai daga bayansu suka ji wani abu, ha ha ha! Duk suka waiga firgigi, sai suka ji daga cikin keji an ce, "Ai ga ta nan. Da ma na gaya maka, ka tashi kashe ni, kai ne ba ka sani ba, ba irin magana kamar tamu a ke rainawa ba." Sarki bai sami ta cewa ba. Aku ya ce, "Ko yanzu in ka bi shawarata allah ya kyauta, ba wani abin da zai bata maka rai. Sarki ya dubi aku da fushi, ya ce, "Ka rufa mana baki nan! Wata shawara gare ka?" Musa ya sa baki ya ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, matambayi ai ba ya bata, ya fadi mu ji." Sarki ya ce, 'To, fadi, in ko shawarar taka ba ta fita ba, ina murde maka wuya, kowa ya huta." Aku ya ce, "Yanzu Sarkin Sinari ya kusa kawowa kadarkon Kimba, nufinsa ya biyo ta tsakanin dutsen Kimba da na 7 Ubandawaki ya kewayo ta gabas ya fada wa birni ta inda ba a tsammaninsa." Sarki ya ce, "Cikin 'yan gari ma akwai wani mahalukin da ya san wannan hanya, balle Sarkin Sinari?" Aku ya ce, "Kai dai ka ji abin da zan gaya maka. Yanzu maza ka koma gida ka aika da 'yan kwarbai su tsare makurdin nan da ke tsakanin dutsen Kimba da na Ubandawaki. Kome yawan rundunarsa, ko mutum goma masu karfin zuciya sa iya mai da shi baya a wannan wuri, kafin ya kewayo ma ka shirya uwar yaki." Sarki ya yi tsaki. Musa ya ce, "Dan akun nan ya san abin da ba mu sani ba, sai a bi shawararsa mu gani." Ko-da-ya-ke abin nan da aku ya fadi Sarki na jinsa kamar tatsuniya ce, duk da haka tun da Musa ya sa baki sai ya hau, suka koma gida, ya zabi 'yan kwarbai guda dari ya aika da su inda aku ya misalta masa. Ya kuma ta da manzanni ya aika da su kudu da arewa, gabas da yamma, a gaya wa mutane su yiwo harama su zo maza da shirin yaki. Makera kuma suka shiga gyara makamai. Ana nan bayan kamar kwana biyar sai ga wani daga cikin 'yan kwarban da Sarki ya aika ya zo a sukwane da bushara, ya ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, ai wannan dabara da ka yi ta fita. Shekaranjiya da hantsi muna nan mun yi kwanto inda ka ce mana, sai muka hangi kura ta toshe sama, sai tsinin masu kawai ka ke gani suna wal wal wal. Ga masu dawaki da dakarai bilahaddin, muka hanga har iyakar ganimmu, ba mu ga karshensu ba. Muna nan dai sai da muka bari goshin yaki ya kawo dab da mu, sa'an nan muka yi ta sako musu kibau kamar ruwan sama. Na gaba suka juya da baya suka gamu da wadanda ke biye, abin ya cude, ga 'yar hanya karama, dawaki suka yi ta zallo suna fada wa junansu. Mu ko dai sai zuba musu kibau mu ke, na bisa na ta sullubowa kasa, dawaki na tattake su. Cikin na gaban nan sai dai dai suka sami komawa wajen uwar yaki. Jim kadan kuma sai ga wadansu suka taso wai za su yi mana sukuwar salla. Ba dama, don hanyar ta cika matsatsi tsakanin duwatsu. Muka yi musu yadda muka yi wa na farko. Aka yi ta aiko wadansu, muna yi musu hakanan, har la'asar ta yi. Da suka ga ba dama suka koma, suka bar gawawwakin 'yan'uwansu nan, abin sai wanda ya gani!" Ko da Sarki ya ji haka, sai ya yi kamar ya ce kaka don murna. Ya shiga ya gaya wa aku, ya yi ta gode masa, ya yi kamar ya dauke shi ya hadiye shi. Nan take ya dauko jaka biyu ya ba Balarabe, kuďin aku. Ya kawo ingarma taka hau ya ba shi, ya kara masa da bayi bakwai, ya ba shi kyankyandi goma sha biyu na tufafi, ya sallame shi ya tafi. 8 Cikin daren nan sai ga Barakai ya komo ya gaya wa Waziri abin da ya faru, ya ce, "Mu ke kan gaba, sai kawai muka ga ana ta zubo mana kibau, har aka sami dokina ban sani ba, sai na ga kawai mun zube. Ni ko da na ga haka sai na kwanta karkashinsa kamar na mutu. Na yini nan ba motsi, ana ta yaki bisa kaina. Da dare ya yi tsaka, na ji sun yi shiru, sai na sulale na dawo." Waziri ya yi masa barka, ya ce, "In ji ba a gane kai ne ba?" Barakai ya ce, "Na tabbata ba wanda ya gane ni." Waziri ya се, "То, madalla. Amma ina mamakin yadda Sarki ya gane ta nan za su bullo." Barakai ya ce, "Ni ma hakanan. Bakina dai ban yi da kowa ba." Waziri ya ce, "Lalle mutanen Sinari akwai munafukai. Amma ba kome, gobe ma rana ce." Bayan kamar kwana uku gayyar yaki ta taru, gari ya cika da dawaki da dakaru har ya amaye, kauyukan rabe da birni ba wanda bai cika ba. Da Sarki ya ga duk an hallara, tun da sassafe sai ya kira Waziri ya bar shi tsaron gari. 9 Waziri ya duka, ya ce, "Na ko karbi amanan nan taka da hannun dama." Yana 'yan koke-koken munafunci. Sarki ya tashi ya shiga gida, ya kira wadansu bayinsa amintattu guda goma sha biyar, ya bar su tsaron gidan, ya ce su lura kada su Musa su fita waje sai sa'ad da Allah ya dawo da su lafiya. Ya kuma tafi ya kira su Musa wajen aku, ya ce musu, "In kun kuskura kuka fita wajen gidan nan bayan ba ni nan, ban yarda muku ba. Kuma kome za ku yi ban yarda muku ku yi shi ba, sai kun zo kun shawarci akun nan. Abin da ya ce muku kuwa, ko da kuna tsammani kan kuskure ne, kada ku ketare shi." Yara suka fashe da kuka suna cewa, "Baba, mun ji abin da ka ce duka, ma ko bi." Sarki ya juya wajen aku, ya ce, "Kai kuma, ga amana nan, in ka ci amanata, to, Allah ya isa." Aku ya ce, "Hakanan ne, ranka ya dade. In Allah ya so kuwa, ka tarad da abin da ka ke so." Sarki ya ce, "To, madalla." Zai tashi ya ce, "Af, jiya kuwa na ga wani da wata macen aku, na saya don in gama ku tare, ta rika debe maka kewa." Ya aika aka kawo ta, aka gama su. Aku ya yi godiya, suka yi sallama da Sarki. Walaha na yi, aka buga tamburan tafiya. Sarki ya taka ya hau, sai Waziri ya zo ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ko ka sha'afa ne? Ka yi alkawari duk yakin da ya fara aukuwa da Mahmudu za a." Sarki ya kawo iya wuya, ga bakin cikin rabuwa da iyali, ga kuma wata maganar banza. Sai ya sa baki ya kira Mahmudu ya ce, "Ga doki nan, hau mu tafi, da kai za a." Mahmudu ya dare doki. Musa ya ce, "Ni ma zan tafi!" Sarki ya ce. "Ba na zuwa da kai." Musa ya fashe da kuka, ya cę ba ya rabuwa da Mahmudu. Sarki ya daka masa tsawa ya koma gida, ya kira Sarkin gida da bayin nan da aka bari tsaro, ya ce, "Ku lura kada ku bar Musa ya ko leko waje, in wani abu ya same shi ina yanka ku!" Suka shiga da shi. Runduna ta dunguma, aka taryi inda Sarkin Sinari zai fito. Da Waziri ya ga an raba Musa da Mahmudu, ga shi kuma Sarki ba ya nan, sai ya tafi gida ya yi ta murna, yana tsalle-tsalle. Ya shiga tunane-tunanen abin da zai yi ya halaka Musa kafin Sarki ya dawo. Domin in ya samu ya kashe Musa, kome ya faru wurin yaki shi ke bisa. In Sarkin Sinari ya ci nasara, bukata ta biya, in ko Sarki Abdurrahman ma ya ci, duk daya, don ko ba jima ko ba dade shi ne zai gaje shi. Da ya ga kurar yaki ta bace, sai ya kira wadansu katti hudu cikin bayinsa wadanda ya amince da su, ya ce yana da wata 10 bukata, wanda duk ya biya masa ita zai 'yanta shi. Bayin nan suka dauka gaba daya, "Fadi, yanzu ka ga aiki da cikawa!" Waziri ya ce, "Ina so ku kashe mini Musa. Yana nan cikin gidan Sarki an kulle shi, an sa duk bayin gidan su tsare shi." Bayin nan suka ce, "Af, in haka ne yaya za mu yi mu kashe shi?" Waziri ya ce, "In dai kun kasa kunne kwa ji, aiki a ke so ba surutu ba. Yanzu duk hankalinsa yana ga Mahmudu dan'uwansa. Na san lalle in kafa ta dauke, yadda aka yi duk saı ya yi kokarin da ya fito don ya bi shi. Sai ku nemi buhu, in dare ya yi ku tafi kofar gidan Sarki, ku sami wuri ku make. Da kun gan shi ku kama shi, ku rufe bakinsa, ku tura shi cikin buhu ku daure, ku je da shi kogi ku jefa." Bayi suka ce, "An gama." Musa ya yini ran nan sukuku. Mutane suna tsammani uban ya ke tunawa, saboda haka ba su koma ta kansa ba. Da magariba ta yi Sarkin Gida ya kulle kofofi duka, ya miko wa Musa mabudi ta taga, yadda Sarki ya ce ya rika yi kullum. Ya koma zaure wajen bayin nan da aka bari, suka yi ta hira har kusan asuba, sa'an nan barci ya kwashe su. Duk abin nan kuwa Musa bai yi barci ba, yana jira bayin nan su yi, ya je ya gaya wa aku ya bar shi ya fita ya bi su Mahmudu. Da ya ji sun yi barci, sai ya shirya, ya dauki mabudan nan, ya shiga damaru, ya dauki garkuwa da mashi, ya nufi wurin aku. Sai ya tarad da aku namijin, watau wanda aka fara saye mai sihiri, yana barci. Sai ya ce, "Af, tun da wannan ke barci bari in tambayi matar, da Bako da Tukura ai duk Umbutawa ne." Ya tsaya gaban macen aku, ya ce, "Na zo in gaya muku ne don ku sani, za ni bin Mahmudu, duk abin da zai same shi ya same mu tare." Da akun nan ta ji haka sai ta girgiza kai ta ce, "A! Wannan ko kusa ba shi yiwuwa. Yaya Sarki zai bar mana amanarka, sa'an nan mu saba?" Ko da Musa ya ji haka sai duk ransa ya baci, ya harari aku ya ce, "Har ke dan tsugunin nan naki kin isa ki hana ni zuwa wurin dan'uwana? Karyarki ta sha karya!" Sai ya kama ta, ya murde kan, ya yar. Yana jefad da ita sai mijin ya farka. Musa ya juya wajensa, ya ce, "Kai kuma me ka ce? Na zo in gaya muku ne zan bi Mahmudu yanzu.' Da akun nan ya ji haka, sai ya dubi matar, ya ga abin da ya auku gare ta. To, ga shi Sarki ya bar masa amanar yaro, in ya bari ya fita, lalle ya ci amanar Sarki. Ya ga kuma in ya hana yaron nan 11 tafiya, lalle abin da ya auku ga matarsa zai auku gare shi. Yana nan yana tunanin wadda za ta fisshe shi, sai Musa ya сe, "Ban ji ka ce kome ba, ko kuma kai hana nin za ka yi, yadda matarka ta tashi hana ni?" Aku ya daga fiffike, ya duka, ya ce, "Mamakin abin da ya sa ka ba mace shawara na ke yi. Ai magana irin wannan sai mu tsakanimmu maza. In ba rashin hankalin mata ba, ina mutum zai ce za shi ga dan'uwansa, sa'an nan a hana shi? Yi maza ka tafi, kada ka ji tsoron kome. Ba shakka dai ka cika dan kirki, tun da ba ka saba abin da tsohonka ya hore ka da shi ba, da ya ce kome za ka yi ka shawarce ni. Ga shi ka san ni ba kome ba ne, amma don ka cika umurnin ubanka ka zo. Da ma abin da a ke so ke nan kawai ga dan kirki ya bi maganar iyayensa da malumansa. Dan zaki da ya bi halin 'ya'yayen zamani, ya ki bin maganar magabatansa, ai ka ga yadda ya kare." Musa ya ce, "Dan zaki? Wace magana ya ki bi? Su ma dabbobi suna wata magana ne?" Aku ya ce, "A! Suna yin irin tasu mana. Bari ka ji yadda suka yi." 12 Labarin Wani Bororo Da Dan Zaki Wata rana namun daji suka taru suna shawarar ta kofar da ya kamata su rika fitowa 'yan Adam, don su kubuta daga tarkokinsu. Kowa na kawo tasa ana kushewa, sai dila ya ce, "Ва abin da ya fi, sai a yi makaranta nan dawa, mu da muka sha gwagwarmaya da mutane, muka gane makircinsu, mu rika koya wa na baya irin dabarummu." Sauran dabbobi suka yarda da wannan magana. Daga nan sai kura ta ce, "To, wa za a sa? Ai ka san wannan aikin sai mu." Zaki ya ce, "To, gaya mana irin dabarun da ki kan yi ki kubuta daga mutane, sa'an nan mu gani in hanyoyinki na da amfani ga sauran su bi." Kura ta ce, "Ai ba wata dabara da ta ke raba ka da mutum, sai idan wuri ya kure maka ka bude hakora ka tasam masa. In ko akwai 'yar tazara, ka sanke ka yi ta kanka." Zomo ya ce, "Allah wadan wannan dabara taki. In ke kina da karfin tasam musu, mu muna da shi ne?" Ya dubi zaki, ya ce, "Allah ya ba Sarki nasara, mafitarmu daya ce, idan kowa ya yi rami a kasa, ya yi masa kofa kamar goma duk nesa da juna. Ka ga in an rutsa ka nan sai ka bulle nan, in an datse nan sai ka bullo nan." Bauna ta dubi zomo, ta yi murmushi, ta ce "Kadai, yaro dai yaro ne. Kana maganar a gina rami, ni ina ka ga ramin da zan iya shiga?" Dila ya ce, "Ce ma kya iya shiga, to, in kun gamu a wajen kiwo fa? Ko kuwa don tsoro sai a bar neman abinci?"" Zomo ya ce, "Ai wannan sauki gare shi. Da kum gamu ya sa karnukansa suka biyo ka, sai ka yi gaba kamar ka wuce, ka ta da kura ka komo baya, ka sami gidan gara ka make gindinsa, sai ka saje da shi." Wannan magana ta zomo ta ba kowa haushi, har giwa ta tashi take shi, ba ta sani ba. Ta harare shi ta ce, "Kai sakarai, in kai kana iya makewa a suri, mu fa? Kai karnuka suka dame ka, me 13 aka yi aka yi karnuka? Cikin abubuwan ba tsoro har a gama da karę? Wannan ba dan'uwammu ba ne, kwadayi ya kai shi cikin mutane har ya yarda suna wulakanta shi kamar ba dan halas ba? Kai ma zomo, ba ka san maganar da ka ke yi ba." Kowa ya yi ta kawo dabararsa, don a sa shi malamin dawa, amma in saura suka bincika, sai su ga shi kadai ta ke wa amfani. Can an rasa wanda za a zaba, sai dila ya yi tsalle ya fado gaban manyan dawa, ya ce, "Allah ya kiyashe ka daga sharrin mutane, ni za a ba malanta, domin duk makircin mutane ba wanda ban sani ba." Kura ta ce, "Ba a tambaye ka yawan magana ba. Ka fadi dabarun da ka ke yi kana tserad da kanka mu ji, in mun yarda." Dila ya dubi zaki, ya ce, "Allah ya daukake ka, na san kuka na cikin abubuwan da ke tona mu ga mutane, saboda haka in na yi kuka gabas sai in ruga in koma yamma, in na yi a yamma sai in koma kudu. Ban taba tsayawa inda aka ji na yi kuka ba, balle a biyo." Zaki ya girgiza kai, ya ce, "Lalle kana da dabara a wannan wuri, amma in ka yi barci fa? Ko kuwa kullum ba ka yi, sai ka yi ta gudu ka je nan, ka je nan?" Dila ya ce, "Allah ya ba manyan dawa nasara, ai ni ba na barci sai tsakiyar ganyayen doka. In da ko fara ta fadi na ji kyamas sai in farka, in na ga ta tsaya in tsaya, in zuciyata ba ta ba ni ba in ruga." Zaki ya ce, "Lalle kana da dabara." Kura ta ce, "Manyan dawa, ai ko wajen shan ruwa mutane na cutarmu. In ya ce yana da dabara a fili ta wajen shan ruwa fa?" Dila ya ce, "Ai ni ba na shan ruwa yadda ku ke yi. In na ji kishirwa sai in tafi rafi, in tsoma wutsiyata cikin ruwa, in fito waje in tsotse, in koma in sake tsomawa. Haka na kan yi ta yi har in koshi, amma ban gane wa in dukad da kaina ba. Irin wannan shan ruwa da ku ke yi, ai ita ce baya ba zane. In wani ya lababo daga baya, ai barna ta auku." Damisa ta ji haka sai ta ce, "Mhm, ai ba nan mutane su ke sha da arna ba, sai wajen yin tarko. Babban abin da ba mu san kansa ba ke nan." Dila ya ce, "Ni dai abin da na tsare, shi ne duk inda na ga itace ya sarke, ba alamar ganye, ba alamar saiwa a gindinsa sai in sake hanya. Na san lalle itatuwa ba su tsira sai da saiwa da ko ganyaye, ko sun bushe a ga alamar inda su ke. In ko ina tafiya, na ga wani abincina a inda ba safai ya kamata a same shi nan ba, sai in hade kwadayina, in kewaya in wuce shi." Zaki da sauran dabbobi suka ce, "Lalle, dila, mun yarda kai ne 14 malamin dawa." Suka tara 'ya'yansu a makaranta, dila ya yi ta koya musu wayo iri iri. Kullum in darasi ya fado a kan dabarun da ya kamata su yi su kubuta daga mutane, sai dan zaki ya tashi, ya ce don mutum, wannan dan karamin alhaki, shi ba ya bata lokacinsa ga jin labarin makircinsa ba. In dila yana rarrashinsa ya tsaya ya karu, sai ya ce, "Ni dai don mutum Allah ya kawo ranar da za mu gamu da shi, ran nan yá kwashe kashinsa a hannu. In same shi in keta cikin, in karairaya kasusuwansa, in cinye namansa, in sha jininsa in more!" A kwana a tashi, ran nan dan zakin nan na yawo, da shi da dan rakumin dawa, sai suka hangi wani Bararo tafe da kayan tsabgu da igiyoyin dangwali mai yawa, sun yiwo tashi, ya bar 'yan'uwansa a baya, yana sauri ya riga su isa mashekari, ya fara zaben wuri ya yi bukka. Yana tafe yana 'yan wake-wakensa da Fillanci, yana kirari shi kadai kamar mahaukaci. Ko da rakumin dawa ya hango shi, sai ya ga bayanin da dila ke yi musu na mutum lalle wannan ya zama shi ne, saboda haka ya gudu ya shiga daji. Dan zaki kuwa ya tsaya, yana kallon wata irin halitta dabam da wadda bai saba gani ba. Da Bororon nan ya yiwo kusa, sai dan zaki ya ce masa, "Kai, tsaya! Cikin namun daji, kai ne wa? Tun da na tashi ban taba ganinka ba. Kai ko gaisuwa fada ba ka zuwa?" Bororo ya ajiye kayansa, ya fadi gaban zaki ya ce, "Ni ne Kuzajje. Abin da ya sa ba ka ganina fada, kunya na ke ji, ga kowa da kafa hudu, ni ko sai biyu, ga kowa da wutsiya, ni ko fimfirin. Dubi gashinku layalaya, ni ko tik da ni, kamar na fito daga wuta." Dan zaki ya ce, "To, ina za ka da wadannan itatuwa?" Bororo ya ce, "Kura ta kira ni in je in yi mata gida, don tana tsoron mutum." Dan zaki ya ce, "Shin don Allah ina zan bi in gamu da mutum yanzu? Shi na ke nema ruwa a jallo, kwana da kwanaki ban gan shi ba." Bororo ya durkusa, ya ce, "Yau da gobe dai ai ka gan shi, yallabai. Amma ai tsoron karo da irinku ya ke yi. M, kada ka tsai da ni, ina sauri in je in yi wa kura aikinta, ko ba don tsoron mutum ba ma, ga rana ta fara zafi. Ba abin da ya fi gida dadi." Dan zaki ya ce, "tsaya ka yi mini gidan tukuna in ji, sa'an nan ka wuce wajen na kura." Bororo ya ce, "A'a, yallabai ai ba ni da dama tun da muka yi alkawari da ita, da ba ya magana biyu. In dai na yiwo mata na dawo, na yi maka don amfanina ke nan kawai wajenku." Dan zaki ya ce, "Zancen banza. Mece ce kura, har ka ce sai ka 15 yi mata gida za ka yi mini?" Ya taso wa Bororo, ya sa dagi ya keta masa dan warki. Bororo ya dubi warkinsa sabo ful, an yi masa karantsaye, sai ya kume, ya dai hade bacin ransa, ya ce, "Tun da ka ce kana so, manyan dawa, ai sai a tsaya a yi maka tukun." Dan zaki ya ce, "Dole. Ashe ana tsoron Inna, in ji 'ya'yan mayya." Bororo ya tsuguna ya shirya tsabgunan, ya yi tsaikon daki mai karfi tsakar wadansu itatuwa. Ya bi tsaikon nan ya daure tam da itatuwan nan, sa'an nan ya samo ciyawa himi guda ya tara, ya samo kirare tuli ya tsiba gefe daya, kamar mai shirin gashin tukwane. Da ya tara su duk, ya yi ta diba, yana jitawa bisa tsaikon nan. Ya bar'yar kofa wadda za ta isa dan zaki ya shiga. Da ya gama aminta shi, ya durkusa gaban dan zaki, ya ce, "Shiga mu gani in ya yi daidai da kai." Dan zal:i ya shiga cikin bukka, nan da nan Bororo ya mai da itatuwa, ya kulle, ya buga kyastu, ya kewaye bukka da wuta. Da hayaki ya murtuke, dan zaki ya kasa numfashi, sai ya yi neman fitowa, ya kasa. Da ya ji ya matsu, sai ya yi kara ya сe, "Kai Kuzajje, wannan daki naka ya faye kunci, kuma iskar ciki ba ta shakuwa. Fid da ni." Bororo ya ce, "Haba, me ka ce? Kara fadi in ji? Ka makara. Ni ne mutum wanda ka ke fartar kasa ka ke cewa sai kun gamu. Kafin ka fara shan alwashi, da ya kamata ka tambayi iyayenka, ka ji yadda mu ke murtuku da su." Da dan zaki ya ji wuta ta kama ba ba ba, ya ce, "Na tuba, don Allah ka fid da ni!?" Bororo ya ce, "Haba, da ma ka dangana. Alkalami ya bushe." Dan zaki ya cinye wuta kurmus. Bororo ya kama hanyarsa ya yi gaba. Wanda ya raina maganar na gaba gare shi, ya yi abin da ya ga dama, kome ya same shi babu kaito. Musa ya ce, "Me na ke ji haka kamar kiran salla?" Aku ya saurara, ya ce, "Kiran salla ne kuwa! Kai, wannan ladani ya yi sauri. Har asalatu ta yi?" Musa ya tashi ya shige, bai ce masa kome ba, don ya ga ba damar fita, duk mutane sun farka. Musa ya yini ran nan yana ta cizon hannu, bai sami fita ba har dare ya yi. Ya zauna yana allaalla bayin nan su yi barci, suka ki, sai can asuba. Da ya ji sun yi. 16 barci suna minshari, sai ya tashi ya taho wurin aku neman iznin tafiya. Aku ya ce, "Yallabai, ina ni ina hana ka abin da ka ke so? Alhali ko ma abin da a ke so ne ga dukan dam Musulmi, zumunci. Sai ka yi hanzari, ka ga alfijir ya keto." Musa ya juya zai fita, aku ya ce, "Yallabai, sai ka dauki fitila. Jiya na ji an koro wadansu barayi daga gidan Kakaki, na ji 'Yan Gadi na cewa kowa suka gani ba fitila sa kama shi." Musa ya ce, "Yaya aka yi ban ji ko kuwwa ba, ga shi kuwa ban runtsa ba?" Aku ya ce, "Hankalinka ne ba ya nan, da ka sha dariya. Wani barawo ne ya shiga taskar Kakaki, ya shinfida bargo yana shirin daure kayayyakin da ya sata, sai wani barawon kuma ya fado dakin, bai san wannan gudan ya riga shi ba. Yana sawo kafa ciki, sai wannan barawon da ya fara zuwa ya yi tsammani Kakaki ne mai gidan. Saboda haka ya yiwo kofa da gudu. Shi kuma wannan da ya zo yanzu, da ya ji an nufo inda ya ke, sai ya yi tsammanin shi aka biyo, shi kuma ya yi baya ya zura a guje. Banza ta kori wofi, yadda 'Yan Gadi suka yi da suka kori barayi daga gonar Madaki." Musa ya ce, "Jiya har sata biyu aka yi? Sun ga Sarki ba ya nan!" Aku ya ce, "A'a, nasu dabam ne." 17 Banza Ta Kori Wofi Wata shekara aka yi tsananin yunwa a wani gari, har abinci ya zama ba mai ganinsa sai mai dalili. Talakawa da matsiyata ba su da wani abinci sai rogo, rogon ma bai wadata ba. Saboda haka wadanda ba su da ko dalilin samun rogon sai suka rika zuwa gonakin rogo da tsakad dare suna satowa. Ana nan cikin wannan hali, sai wadansu mutum uku suka yi shawarar su tafi gonar Madaki su sato rogo. Suka dauki kwanduna, da dare ya raba suka nufi can. Daya daga cikinsu ana kiransa Kodago-a-taka-a-kare, guda kuma ana ce masa Kadanmai-ban-haushi, daya kuwa sunansa Kazunzumi-a-gan-ka-аraina. Da shigarsu sai suka yi wa juna rada suka ce ya fi kyau su ci tukun, sai sun koshi sa'an nan su diba, gobe su kai kasuwa su sayar. Saboda haka suka debo, suka sami wuri suka zauna suna ci. Kodago ya dubi saura, ya ce, "Kai, ai ko rogon mutumin nan duk zako ne." Kadan ya ce, "Haba, ai zakin ba magana a ke yi ba, in ka sa baki sai ka ji kamar sukar." Kazunzumi ya ce, "Ai Allah ya buda mana kofar arziki." Tun suna raďa har dadi ya sa suka koma magana sosai, kamar suna cikin gidajensu. Da suka koshi suka yi ta tuga suna cika kwanduna. Ka san dare in ya yi tsaka, da an yi 'yar magana ko da sannu sannu ce, sai ka ji ta da nisa. Saboda haka waďansu 'Yan Gadi suka jiyo su, suka lababo, suka tasam musu suna cewa, "Kada su kai! Biyo nan, harbar su! Kowa ka gani, kashe shi!" Sai suka yi ta bara da ka, suna harba kibiya cul cul. Wadannan 'Yan Gadin wadansu sakarkarun kauyawa ne, sabon shiga. Da jin yadda suka tasam ma barayin nan da hauka haka, ka san gaulaye ne, tashin kauye. Ka san in da 'Yan Gadi ne na sosai, Allah ya ba ka nasara, sai su lababa da ya ke ana duhu, su kama su a hannu ba su sani ba. To, ka ga yadda suka bata al'amarin. Ko da barayin nan suka ji haka fa, sai suka kwashe 'yan 18 kayansu suka runtuma da gudu. 'Yan Gadi kuma suka dafo su suna cewa, "Kada su kai!" Ko da ya ke ana duhu, har ba mai ganin kowa, duk da haka 'Yan Gadin nan na ta kurari, suna bin motsin barayin. Barayin nan suka yi ta gudu kamar ransu zai fita. Suna cikin gudu dai, sai Kodago ya yi wa saura rada ya ce, "Kai, ni fa na gaji, ya kamata mu yar da kwandunan rogon nan, mu yi ta kammu."" Kadan ya ce, "Ni ma da abin da na ke shiri in gaya muku ke nan." Da Kazunzumi ya ji haka, sai ya ce, "Kada ku yi saurin karaya. Ku dai dan jure kadan, ku ga tawa dabarar." Sai ya fadi rica, ya ce, "Wayyo Allah, ya kashe ni! Ashe, harbin nan da na ce an yi mini, sai yanzu dafin ya narke. Ku ji kaina, 'yan'uwa, ku yi mini rai." Ya rada wa sauran abin da za su ce. Sai suka ce, "Tashi don Allah, mu isa gida, watakila ka sami makari, in ka sha ka amaye shi." Kazunzumi ya ce, "Ni tawa ta kare. Ina maganar tashi?" Kodago ya ce, "Lallabo dai, in fa ka mutu ai lalle mu je Gidan Sarki da su, su gaya masa dalilin da ya sa suka kashe ka, don mun debi saiwar rogo za mu ci, kada mu mutu da yunwa." Kazunzumi ya marairaice ya ce, "To, mu tafi in gani, in na iya." Ko da barayin nan suka ji wannan makircin, sai suka kara mai. Da 'Yan Gadin nan suka ji haka, sai guda ya dubi dan'uwan, ya ce, "Ka ji abin da suka fadi?" Dan'uwan ya ce, "Ai na ji." Shi kuma ya dubi na ukun, ya се, "Kai ka ji abin da suka.ce?" Na ukun kuma ya ce, "Na ji mana, ai kome ya same su halas ne. Mu matsa, ko sun yar da abin da suka sato, mu gani." Suka dai yi ta bin su. Da Kazunzumi ya ji suna tafe sai ya sake faduwa, ya ce, "Wayyo, ni kaina! Da dai na ce ko zan kokarta in kai gida, don in sami inda za a lura da ni, kada in kumbura kafin safe. Amma na ji dafin ya ci karfina. Ku ku yi ta kanku, ku kyale ni, ashe da ma kasa ke kirana. In kun isa ku ba mata da iyalina hakuri, su tuna dukan mai rai mamaci ne."" Da'Yan Gadi suka ji haka, sai suka cirje, suna saurare. Ya sake cewa, "Ku lura da wasicin da zan yi. Ku shaida na ce a ba da sadakar sule talatin daga cikin kudina da na bari. Kuma ku na ba ku amanar 'ya'yana, ku lura da su da kyau, kada su sangarce. Ni tawa ta kare." Ya yi kalmar shahada. Da'Yan Gadin nan suka ji haka sai wannan ya dubi wannan, wannan ya dubi wannan. Kodago da Kadan kuwa sai suka yi ta tafa hannu, suna 19 sallallami, suna cewa, "Kada ka gakamar ka yi mutuwar kare, ka ji. Yadda aka kashe ka duk wanda ya yiwo harbin nan ta same ka shi ma sai Sarki ya sa an tsire shi, in gari ya waye. Ai cewa aka yi su kama barayi, ba a ce musu su kashe ba. Duk mu tsaya, in ya so in za su kashe mu ne su kashe mu duka, tun da dai suka raba mu da dan'uwammu. In ko suka kashe mu, ai lalle sur ma a kashe su, don mu ma Musulmi ne, ba kafirai ba." Da 'Yan Gadin nan suka ji haka fa, sai suka yi tsammani sun kashe mutumin nan ne. Saboda haka suka fara shawarar su gudu, kada a gan su. Suna cikin shawarar inda za su bi, sai suka ji barawon nan na kwance, ya fara kakarin mutuwa, yana shakuwa kikaf kikaf. Can sai ya ja wani kakari mai karfi, ya yi shiru. Sauran barayin suka buga salati baki daya, suka ce, "Ya cika." Ko da 'Yan Gadi suka ji haka, ba su tsaya su gama shawarwarinsu ba, sai kowa ya ce in ba ka yi ba ni wuri. Kazunzumi da jin tif tif tif na 'Yan Gadi suna gudu, sai ya tashi ya shiga gaba, sauran na biye har gida. Da zuwa suka sami ruwa mai sanyi, suka kyankyama. Ka san na gaya maka kafin su debi rogon nan sai da suka ci daya daga cikinsu tukuna. Abinka da kayan zalunci, ko da suka sha ruwan nan sai danyen rogon nan da suka ci ya taso, ya murde su, kowane ya yi ta murde-murde abinsa, yana nishi. Kafin asalatu cikunansu suka haye tim, sai amai sai zawo, gari bai waye ba, sai da duka suka hauri arewa. Da safe da aka tarad da su kowane cikin nan ya kumbura kamar salka. Ga su kace-kace cikin amai da zawo. Rogo na fita har ta hanci. Aka duba sako aka ga kwanduna cike da danyen rogo, sai aka hakikance danyen rogo suka yi wa cin yunwa, ya halaka su. Aka yi 'yan koke-koke, aka yi musu jana'iza, aka kare. 20 Garin nan ya faye yawa, 'Yan Gadin nan ba su san wannan abin ya auku ba. Da suka gamu da hantsi sai guda ya ce, "Shin wa ku ke tsammani ya harbi mutumin nan ne na jiya? Ni dai na tabbata ba ni ba ne." Na biyu ya ce, "Balle fa ni da na ke biye da ku daga baya." Na uku ya dubi na fari, ya ce, "Amma ko da ku ke neman ku maka mini laifi, ai ku kuka ce in harba." Na fari ya ce, "I, gaskiya ne, amma ai kai ka san abin da na ke nufi. Ka harba ta ketare kansa, ba ka same shi ba." Na uku ya ce, "Ni ma tsammani na ke koli na harba ta. Ina mamakin yadda ta same shi. Kaddara dai ce ta tarad da ajali kusa." Sauran suka ce, "Gaskiya ne, sai dai mu yi kurum, kada mu tona kammu." Daga'ran nan duk sa'ad da biyu daga cikinsu suka gamu sai su ta da taďin, su rika kokari su lika wa wanda ba ya nan laifin. Suka zauna kan hakanan dari dari har iyakar ransu, suna tsammani a gane su yau, a gane su gobe, ba su ji magana ba. Suna son su tambaya, suna jin tsoron kada son iyawa ta tona su. Musa ya ce, "Wadannan 'Yan Gadi sun kuwa isa sakarkaru." Aku ya ce, "Su ma ai suna da hankali bisa ga wani Bahaushe wanda ya tafi fatauci cikin kasar Yarbawa." Musa ya ce, "Har ya fi wadannan sakarci? Haba, wanda ya fi wadannan sakarci, ai sai yanka." Aku ya ce, "Bari ka ji gogan naka, ka san ko cikin Hausawa akwai Yausawa." 21 Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku Taho Tare Wata rana wani Bahaushe wai shi Wawa za shi fatauci, sai ya bi ta kasar Yarbawa, Wawa ba ya jin Yarbanci, mutanen da ya tarar a wannan gari su kuma ba su jin Hausa. Amma duk da wannan Wawa bai lura ba. Yana cikin tafiya, ya kawo kofar gari, sai ya ga wani katon garken shanu fari fat suna kiwo. Wawa ya yi mamakin wanda ke da wadannan shanu masu yawa haka, sai ya tambayi wani mutum nan kofa ya gaya masa ko shanun wane ne wadannan. Mutumin ya amsa da Yarbanci, ya ce, "Ni baı ji ba." Wawa da ya ji haka tsammani ya ke "Ni ban ji ba" shi ne mutumin da ke da shanun. Don haka ya ce, "Ni-ban-ji-ba lalle yana da sukuni." Ya wuce ya shiga gari, sai ya kai ga wani babban gida. Ya daga kai, ya ga lalle gidan nan ya amsa sunansa, sai ya ce wa wani yaro da ke nan kofar zidar, "Don Allah, samari, wa ke da wannan babban gida haka?" 22 Yaron ba ya jin Hausa, shi kuma sai ya ce a cikin harshensa "Ni ban ji ba." Da Wawa ya ji haka, sai ya ce, "Kai, ba shakka Ni-ban-ji-ba ba wanda ya fi shi sule garin nan. Wannan irin gida sai ka ce na Sarki. Da ganin wannan ai ko ba a gaya maka ba ka san wurin nan sule ya zauna da gindinsa." Ya haura takalmansa ya wuce faram, faram, faram, faram, har bakin kogin garin. Yana zuwa sai ya tarad da wani jirgi ya zo, ana ta fid da kaya daga cikinsa. Wawa ya dubi kaya, ya ce, "Oi! Wannan jirgi ya yiwo kaya!" Ya dubi wani nan kusa gare shi, ya ce, "Dan'uwa, duk ko kayan nan na mutum guda ne?" Shi Bayarabe bai ji abin da ya ce ba, sai ya dube shi, ya ce, "Ni ban ji ba." Da Wawa ya ji haka sai ya rike baki, ya ce, "Masu gari! Hakika Ni-ban-ji-ba ya huce haushinsa. Ina ma Allah zai sa in gamu da wannan mutum, ko wajen adonsa ma in more ma idona!" Sai ya zauna ya huta, ya debi ruwa ya sha, ya kama hanya zai wuce. Ya kai kofar gari ke nan, sai ya ga wani matacce an dauko shi, za a kai shi a rufe, wadansu na ta kuka. Wawa ya tsaya yana dubansu. Tausayi ya kama shi, ya matsa wajen wata tsohuwa, ya ce mata, "Wane ne wannan ya riga mu gidan gaskiya?" Tsohuwa ba ta ji Hausa ba, sai ta dube shi, ta ce, "Ni ban ji ba."" Wawa da ya ji haka sai ya dafe kai, ya ce, "Allah mai girma! Ka san kowa samun nan na duniya ya ruda, ya shiga uku. Don Allah dubi abin da Ni-ban-ji-ba ya tara. Ga shi yanzu ya zama sai labari, kamar dadai duniya ba a halicce shi ba! Cikin duk abin nan da ya tara, dubi dan kyallen da za a kai shi da shi. Tun da ya ke al'amarin nan haka ya ke, to, ni yanzu me ya ruda ni har da na rabo da gida don rashin wadar zuci? Ga shi Allah bai hana mini abin da zan ci ba. Watau ba dai abin da ya fid da ni gida sai in sami abin alfahari in kara sabo. Mhm, Allah ya kiyashe mu da aikin Shaidan! Na gode Allah da ya kawo ni nan na sami gargadi daga al'amarin Ni-ban-ji-ba. Ba sauran abin da ya fi, sai in koma garimmu, in dangana da abin da Allah ke ba ni wajen 'yar gonata. Da ma an ce, "Gani ga wani ya isa tsoron Allah." Musa ya tashi, har ya bude zauren farko, sai ya ji bayi sun farka. Sai ya kuta, ya koma. Da Waziri ya ga kwana biyu sun wuce, kowace safiya bayin 23 nan da ya sa suka dawo sai su ce ba wanda ya ko leko zauren, har abin ya dame shi, ya ce, "A'a! Da ko na yi tsammanin zai fito, yaya haka! Amma ba kome, kada ku fasa aikinku, na san dabara." Ya kira wata tsohuwar baiwarsa, ya bayyana mata abin da ya ke so duka game da Musa, ya ce mata in ta yi kokarin ta taimake shi har ta sa Musa ya fito waje, zai ba ta fam goma, ya kuma 'yanta ta. Ya kawo sule goma, ya fara ba ta ta lasa. Tsohuwa ta ce, "Ta kwana gidan Sauki." Magariba na yi, sai ta shiga gidan Sarki da kayan talla, ta kaikaici idon mutane ta yahuto Musa waje guda, ta ce, "Mahmudu ya aiko ni, ya ce a gaya maka wai kai haka za ka yarda ka lalace cikin mata? Ya ce a gaya maka fa duniya ba ta auren raggo." Musa ya matsa kusa da tsohuwa, ya ce, "Don Allah iya, yana can yana ta yaki ko?" Tsohuwa ta ce, "Haba! Yanzu sansanimmu akwai wanda a ke magana irin Mahmudu? Ni ma fa can na ke sansani, mu ke yi musu abinci. Mahmudu ya shaku da ni, ya aiko ni gare ka." Musa ya ce, "Koma maza ki gaya masa, gobe in Allah ya so ya gan ni." Tsohuwa ta koma. Da dare ya yi, Musa ya saurara ya ji barci ya kwashe bayin nan, sai ya shigo damaru, ya zo wurin aku, ya ce, "Ka ji Mahmudu na can sansani yana ta abin kirki, ni za ka sa in lalace nan cikin mata." Aku ya ce, "Yallabai, ina ruwana? Ni ban hana ka ba. Yaya barde kamarka zai ce za shi wurin yaki a hana shi? Tun da ya ke niyyarka ka yi abin da zai faranta wa tsohonka rai ne, ai kowane 24 hadari ka shiga Allah ya fisshe ka, yadda ya fid da Auta dan Sarkin noma daga namun jeji." Musa ya ce, "Wane rigima ta kai shi ga fadawa hannun namun jeji?" Aku ya karba: 25 Labarin Auta Dan Sarkin Noma Da Namun Jeji Wata rana wani manomi ya ce wa dansa Auta kullum ya san yadda zai yi ya harbo musu abin da za su yi miya. Auta yа сe. "To." Kowace rana sai ya je daji, yau in ya harbo zomo, gobe ya harbo batsiya ko gada. Kullum haka har ran nan bai samo ba, uban ya yi ta yi masa fada har ya ba shi kashi. Yana cikin haka, ran nan har namomin daji suka gaji da kisa, suka kai kara gun zaki, Sarkinsu. Zaki ya ce, "To, yaya za mu yi? Kun sani fa Allah abin tsoro ne, mutum ma abin tsoro ne." Sai kura ta ce, "Ai, ranka ya dade, babu wata dabara sai mu yi kokari mu kawo maka yaron nan, kai kuwa ka yi abin da ka ga dama da shi." Sauran dabbobi suka ce, "Ai kuwa haka ne, abin da kura ta ce shi ne gaskiya." Suka sallami Sarki, suka watse. Ran nan yaron yana yawon harbi sai ya ci karo da dila ya ja baka zai harbe shi, sai dila ya ce, "Tsaya! Na ce ko abinci ka ke so? Zo in kai ka inda za ka hųta da wahala." Auta yana tsammani gaskiya ne. Ya bi shi, suka mika har wani katon kogo inda zakin nan ya ke mulki. Da shigarsu dila ya ce ya ajiye bakansa daga waje don kada a ce shi maharbi ne. Suka shiga, sai dila ya komo da baya ya boye bakan yaron. Suka tarad da zaki a zaune, duk ga namomin daji sun kewaye shi, ana fadanci. Dila ya fadi, ya yi gaisuwa. Kura ta dubi yaron nan, ta ce, "Kai, ba ka gai da Sarki?" Auta ya ce, "Ke, me ya sha miki kai? Ke kika aiko ni?" Ya duka ya yi gaisuwa. Da suka zauna, zaki ya dubi dila, ya се, "Shi ne wannan da ya dame ku?" Kura ta amshe ta ce, "Shi ne, ranka ya dade. Kuzajje mai kaі kamar kodago!" Zaki ya ce ma Auta, "Kai samari, me ya sa ka ke kashe mana 'yan'uwa?"" Kafin ya amsa tambayar Sarki sai kura ta ce, "Ranka ya dade, raina mu dai ya yi, dubi jikinsa, dan nema, jemamme!" Auta ya durkusa, ya ce, "Ranka ya dade, shin kai ne Sarki, ko kuwa kura?" 26 Da zaki ya ji hàka, sai ya yi fushi da kura, ya ce. "Kada in sake jin kin yi magana a nan. Faďi jawabinka, samari." Auta ya sake durkusawa, ya ce, "Dattijan garimmu suka ce in zo in rika kashe ku, don mu ga idan abubuwan da kura ke fadi na labarinka gaskiya ne." Zaki ya ce, "Me kura ke faďi na labarina?" Auta ya ce, "Mu da nufimmu mu fid da Sarkimmu na mutane, don ba shi da hakuri, mu nada ka, ka yi mulkin dabbobi kuk da mutane baki daya, mu gama kammu mu bi ka, duk abin da ka ce mu yi, mu yi, abin da ba ka so mu bari. To, muna cikin wannan shawara sai ran nan kura ta shigo gari ta ce ka aiko ta, wai ba abin da ke tsakanimmu da kai sai kisa. Muka sake tambayarta, ta ce duk Sarakunan duniyan nan babu azzalumi irinka. Wai da an yi maka dan laifi kadan sai ka ce a kashe mutum. Saboda haka aka ce in rika kashe ku, mu gani ko ka sa a kashe ni. In ka sa an kashe ni, lalle maganar kura gaskiya ce. In kuwa ka yafe ni, kura ta zama makaryaciya." Zaki ya dubi kura, ya buga mata tsawa ya ce, "Wa ya aike ki ga mutane?" 27 Ta zabura, zawo na fita, ta ce, "Karya ya ke yi, ban taba shiga gari ba." Auta ya ce, "Wa ke maki karyar, zaki da kansa? Kin manta har muka ba ki kujera kika zauna, don girmamawar Sarki da kika се ya aiko ki?" Za ta yi magana zaki ya zabura, ya sa gaba ya banke ta, duk namun daji suka hau mata, mai yaga na yi, mai cizo na yi, har suka kashe ta. Zaki ya sallami yaron nan. Ya ba shi kaya mai yawa irin wanda su ke kwacewa daga fatake. Yaro ya yi godiya, ya ce zai je ya gaya wa mutanen gari abin da ya auku. Wannan shi ya sa ko yaushe in ka ga zaki a daji ka durkusa, ka ce, "Ranka ya dade," ba zai cuce ka ba. Musa ya duba haka, sai ya ga gari ya waye. Bai ko tsaya ba ya ji ko labarin ya kare, ko bai kare ba, sai ya yi tsaki, ya juya ya shiga gida. Yinin ran nan duk ya ki ko zuwa wurin aku, har magariba ta yi. Bayin Sarki suka ci abinci suka zauna hira, sai can barci ya kwashe su. Da Musa ya ji alamar bayi sun yi barci sai ya tasam ma wajen aku. Da hango shi sai aku ya bushe da dariya. Musa ya dube shi, ya ce,'Me ka ke wa dariya haka, kai kadai kamar mahaukaci?" Aku ya ce, "Ai ba ka san abin da aka yi ba jiya da dare. Shigarka ke da wuya, sai na ji bayin can naka na babban zaure suna hira, Sarkin Gida na yi musa tatsuniya. Da na ga ba na jin barci, ni kuma na tafi in taya su. Da Sarkin Gida ya kare tatsuniyoyinsa, ni kuma na ba su labarin. wani bakauye da wadansu 'yam birni." Musa ya ce, "Ashe Sarkin Gida tsofai-tsofai da shi nan, har ya iya tatsuniyoyi?" Labarin me ka tarar yana yi musu?" Aku ya ce, "Ba wani labari mai dadi ba ne, tun ina yaro na san shi. Kokawa da aka yi cikin labarin ne, in na tuna ta ke ba ni dariya." Musa ya ce, "Yaya suka yi?" Aku ya ce: 28 Labarin Sahoro Da Sahorama Wai akwai wani saurayi ne wanda a ke kira Sahoro. Kullum bá ya tabuka wani aiki sai ya kora akuyarsa, ya kai ta bakin rafi ta yi kiwo, da maraice ya kwanto ta. Nonon akuyan nan shi ne abincinsa, ko ya sayar ya sayi wani abu, ko ya sha hakanan. In akuyar ta yaye kuwa, sai ya sayar da ita, ya sayi wata mai da. To, ba abin da ya miskile shi sai kiwon akuyan nan. Kullum ya dawo gida sai ya ce, "Wash, ba shakka kiwon akuya ba aikin da ya sha kansa kan wahala! Haba, lokacin nan yanzu akwai abin da ya fi mutum ya sami inuwa mai sanyi, ya kishingida, ya yi ta barci? Amma ba dama, dole ne mutum ya bi ta, in ko ya ki, ta fada wata gona ta shirga barna a ci mutum tara, ko kuwa ta ki dawowa kura ta sami kalaci. Kai, ya kamata dai in tuna yadda zan sanyaya wa raina daga wannan azaba. Rai fa an ce dangin goro ne, ban iska ya ke so." Yana nan kullum yana zulumin wahalar kiwo, sai ran nan ya ce, "Ah! Na san dabara, ba abin da ya fi sai in auri Sahorama. Ga ta da akuya daya ita kuma tana kiwo, ka ga in na aure ta sai ta rika gamawa da tawa, ni ko in samu in rika taba dan kailula." Sai ya nemi Sahorama aure. Iyayenta suka ce, "Am ba ka. Dа ma da Tukura da Bako duk Umbutawa ne." Aka yi aure, ta tare, ta shiga hidimar kiwon awakinsu biyu. Don ba su da wani abinci sai wanda suka samu daga gare su. Sahoro ya yi ta shara barci a natse. Ba a dade ba kuma Sahoroma ta ce wa Sahoro, "Maigida, ni fa na gaji da wannan irin wahala, kudaje na cizona, ina tuntube. Don Allah, dubi jikina. Da na zo nan gidanka ina sheki, duk yanzu na fara kirci don cizon kudaje. Kai, ba na yarda in tsofad da kaina tun ina gabar kuruciya, sai mu sake dabara." Sahoro ya ce, "Wannan batu naki ba makankara. Ni ma fa na ga kin fara baki, ni ko dubi yadda na fara ajiye taiba. To, yaya zan yi da su?" Sahorama ta ce, "Sai mu ba Dabo, ya ba mu amiya guda, mu ajiye a bayan gida, in zuma ta shiga ta yi saka, mu rika diba muna 29 samun abinci. Ka ga ba ruwammu da kiwonsu, balle mu wahala." Sahoro ya ce, "Kai, ai ko kin samo dabara, ga shi kuma ko ba a faďi ba zuma ta fi nono dadi." Sai ya sa matar ta je ta yi magana da Dabo. Ya yarda da musayar, don ya ga da riba. Ya ba su amiya guda, suka yi ta samun zuma daga ciki suna sha. Suka sami wani gora suka cika, suka rataye. Sahoro dai in ya kwanta tun da dare, ba ya tashi sai rana ta take. Ya kan ce wai tashi da wuri shi kan hana gira tofo, kuma ya kan sa dundumi. Ran nan ya farka daga barci da rana tsaka, sai ya ga matarsa ta dauko goran zuman nan, za ta diba ta yi musu gari su sha. Sai haushi ya kama shi, ya ce, "Ku fa mata barnarku ta fi ku! Dubi goran zuman nan har ya kusa karewa. Watau zuman nan ta kare ne, har za ki fara dibar ta gora? Abin da na ga ya fi sai mu sayar da goran zuman nan mu sayi kaji da zakaru, su rika yi mana kwai suna kyankyashewa." Sahorama ta ce, "In ko haka ne sai mu sami wani yaro wanda zai rika zuba musu ruwa da hatsi. Ni dai ba na iya wannan jidali kullum kwanan duniya." Sahoro ya ce, "Lalle kiwon kaji wahala ne ja wur. Yaran yanzu kuwa kowa ya san su a kan ragwanci. Yanzu ko, ko mun yayo wani yaro don ya rika lura da kajin, in mun saya sai ki ga wasa ya dauke masa hankali, ba ya wani abin kirki." Sahorama ta ce, "Ko wane yaro muka dauko in ya ki yin aiki sai in dauki sandan nan" (ta sa hannu ta dauki wani guntun itace), "in sheme shi, tau a kai!" Sai ta kwantara wa gora ice, Gora ya fashe, 'yar zumar da su ke takama da ita ta tsiyaye. Sahoro ya ce, "Shi ke nan, ta faru ta kare, an yi wa mai dami 30 daya sata! Da kajin da za mu saya, da yaron da za mu dauko, duk ga su nan sun malale a kasa. Amma dai na isa barka, da sakainan nan da ta yi tsalle ba ta fada mini a kafa ba." Ya dubi matar, ya ce, "Sa hannu, kwashe wannan da ke gudu kasa kafin kasa ta shanye, don mu sami na farawa, kada yunwa ta sa in gintse barcina tun ban koshi da shi ba." Sahorama ta shiga sa hannu tana kwashe zuma, tana zuba dan abin da ta samu cikin wata kwarya, tana lashe rabi tana ba mijin labari tana cewa, "Abin nan fa da na yi yanzu amfanimmu zai yi nan gaba. Don na taba jin wata rana an gayyaci kunkuru wajen aure, don rashin saurinsa da ya tashi bai kai gidan ba sai bayan watanni. Da ya isa ya tarar ana sunan dan amaryar da ya zo bikinta ta haifa. Da aka gaya masa ya ce, "Ba kome, sauri shi ke haihuwar nawa!" Sahoro na kwance bisa gado yana kallonta, tana ta shan zuma da wayo, tana zuba masa surutun banza. Sai haushi ya kama shi, ya ce mata, "Wane labarin banza ki ke ba ni haka, ba kai ba gindi? Wayon a ci an kori kare daga gindin kanya! Ga shi ragwancinki ya jawo mini asara, wai ba ki iya kiwon kaji biyu sai kin nemi yaro. Mutuniyar banza, sullutuwa!" Sahorama ta ce, "Kai ne mutumin banza, wanda in ya kwanta da magariba ba ya tashi sai gari ya waye da rana tsaka!" Sahoro yana dai daga kwance ya ce, "Wa ki ke zagi, Sahorama? Ka ga lalatacciyar banza, Kafira!" Sahorama ta ce, "An je an zage ka, kai dai ne Kafiri, ba ni ba. In kai da ne, ba shege ba, ka gina rami ka tsattsage ni!" Sai zuciya ta turnuke Sahoro, ya tashi daga kwance ya sauko, ya tarad da matar, sai kokawa kici kici, kica kica. Can Sahoro ya gaji, ya ga bai ka da matar ba, sai ita ke neman tandara shi da kasa. Sai ya ce mata, "To, sakan ni, kin kayar. Na ce ko iyakarta ke nan?" Sahorama ta ce, "Af! To, in sake ka, ni in fadi?" Musa ya ce. "Lalle ne wannan kokawa tana da ban dariya. To, kai gogan da ka je, wane labari ka ce ka ba su na bakauye da wadansu 'yam birni?" Aku ya ce, "Wannan shi ma yana da ban dariya." 31 Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yam Birni Wata rana wadansu 'yam birni na zaune, sai ga wani bakauye tafe, yana janye da jakinsa zai kai kasuwa ya sayar. A gaban bakauyen nan kuwa akwai wani dan hoto, shi kuma za shi kasuwar ya yi wasa. Ana tafe ana yi masa kidi, yana jefa garma yana cafewa. Da 'yam birnin nan suka lura da bakauye, sai suka ga ya bude baki yana ta kallon dan hoto, bai kula da ko jakin da ya ke ja ba. Daga nan sai wani daga cikinsu ya ce, "Yanzu fa ba ku sani ba, karbe wa muzin nan jakinsa bai sayi wuri ba, in ina so." Saura suka ce, "In ba kurarinka ba yanzu, yaya za ka yi? А buge dai ba ka iya buge shi ka karba, yanzu ko ba dare ba, balle ka ce ka sace." Sai dan birnin nan ya tashi ya bi bayan bakauye, saura na biye da shi sululu. Ya matsa, ya kwance igiyar da ke wuyan jaki ya daura wuyansa, ya mika wa 'yan'uwansa jakin, suka koro. Gagon naka tun da dai ya ke jin tsauri-tsauri a hannunsa, sai ya yi ta tafiya baki bude, yana kallon dan hoto. 32 daya sata! Da kajin da za mu saya, da yaron da za mu dauko, duk ga su nan sun malale a kasa. Amma dai na isa barka, da sakainan nan da ta yi tsalle ba ta fada mini a kafa ba." Ya dubi matar, ya ce, "Sa hannu, kwashe wannan da ke gudu kasa kafin kasa ta shanye, don mu sami na farawa, kada yunwa ta sa in gintse barcina tun ban koshi da shi ba." Sahorama ta shiga sa hannu tana kwashe zuma, tana zuba dan abin da ta samu cikin wata kwarya, tana lashe rabi tana ba mijin labari tana cewa, "Abin nan fa da na yi yanzu amfanimmu zai yi nan gaba. Don na taba jin wata rana an gayyaci kunkuru wajen aure, don rashin saurinsa da ya tashi bai kai gidan ba sai bayan watanni. Da ya isa ya tarar ana sunan dan amaryar da ya zo bikinta ta haifa. Da aka gaya masa ya ce, "Ba kome, sauri shi ke haihuwar nawa!" Sahoro na kwance bisa gado yana kallonta, tana ta shan zuma da wayo, tana zuba masa surutun banza. Sai haushi ya kama shi, ya ce mata, "Wane labarin banza ki ke ba ni haka, ba kai ba gindi? Wayon a ci an kori kare daga gindin kanya! Ga shi ragwancinki ya jawo mini asara, wai ba ki iya kiwon kaji biyu sai kin nemi yaro. Mutuniyar banza, sullutuwa!" Sahorama ta ce, "Kai ne mutumin banza, wanda in ya kwanta da magariba ba ya tashi sai gari ya waye da rana tsaka!" Sahoro yana dai daga kwance ya ce, "Wa ki ke zagi, Sahorama? Ka ga lalatacciyar banza, Kafira!" Sahorama ta ce, "An je an zage ka, kai dai ne Kafiri, ba ni ba. In kai da ne, ba shege ba, ka gina rami ka tsattsage ni!" Sai zuciya ta turnuke Sahoro, ya tashi daga kwance ya sauko, ya tarad da matar, sai kokawa kici kici, kica kica. Can Sahoro ya gaji, ya ga bai ka da matar ba, sai ita ke neman tandara shi da kasa. Sai ya ce mata, "To, sakan ni, kin kayar. Na ce ko iyakarta ke.nan?" Sahorama ta ce, "Af! To, in sake ka, ni in fadi?" Musa ya ce. "Lalle ne wannan kokawa tana da ban dariya. То, kai gogan da ka je, wane labari ka ce ka ba su na bakauye da wadansu 'yam birni?" Aku ya ce, "Wannan shi ma yana da ban dariya." 31 Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yam Birni Wata rana wadansu 'yam birni na zaune, sai ga wani bakauye tafe, yana janye da jakinsa zai kai kasuwa ya sayar. A gaban bakauyen nan kuwa akwai wani dan hoto, shi kuma za shi kasuwar ya yi wasa. Ana tafe ana yi masa kidi, yana jefa garma yana cafewa. Da 'yam birnin nan suka lura da bakauye, sai suka ga ya bude baki yana ta kallon dan hoto, bai kula da ko jakin da ya ke ja ba. Daga nan sai wani daga cikinsu ya ce, "Yanzu fa ba ku sani ba, karbe wa muzin nan jakinsa bai sayi wuri ba, in ina so." Saura suka ce, "In ba kurarinka ba yanzu, yaya za ka yi? А buge dai ba ka iya buge shi ka karba, yanzu ko ba dare ba, balle ka ce ka sace." Sai dan birnin nan ya tashi ya bi bayan bakauye, saura na biye da shi sululu. Ya matsa, ya kwance igiyar da ke wuyan jaki ya daura wuyansa, ya mika wa 'yan'uwansa jakin, suka koro. Gagon naka tun da dai ya ke jin tsauri-tsauri a hannunsa, sai ya yi ta tafiya baki bude, yana kallon dan hoto. 32 Can da dan birnin nan ya ga 'yan'uwansa sun bace da jaki, sai ya ja ya cirje. Bakauye ya ja ya ja, yana has has has! Amma bai waiwaiya ba, yana jin kada ya dauke kansa dan hoto ya yi wani abin mamakin da bai gani ba. Da ya ja dai ya ji jakin bai biyo ba, sai ya waiwaya don ya buge shi su tafi. Dubawan nan da ya yi sai ya ga mutum maimakon jakinsa. Abin ya ba shi mamaki, ya ce, "Kai, me ya faru haka?" Dan birni ya ce, "Ni ne jakinka, tsaya ka ji labarina, domin abin na da ban mamaki. Tun asali ni da ma ba jaki ba ne, mutum ne dan'uwanka. Ina zaune da tsohuwata, sai ran nan kuruciya ta debe ni, na sha giya. Sai na zo gida, ba ta san abin da ya faru ba. Ta yi mini 'yar magana kadan, ba ma ta tashin hankali ba. Ka san wańda ya yi sha bai san inda kansa ya ke ba, sai na zage ta. Ta dafe kai ta dube ni, ta ce, 'Ni ka ke zagi? Ashe har Allah ya kawo mu lokacin da 'ya'ya ke zagin iyaye?' Ka san mai maye sai na ce, 'Na zage ki! Ke wace ce da ba za a zage ki ba?' Sai ta sa hannu kai, ta yi ta kuka, ta roki Allah ya mai da ni jaki. Tun ran nan na ke jaki har Allah ya sa na zo hannunka. Yau ina ga ta gafarta mini ne, ka ga na koma mutum." Bakauye ko da jin haka sai tausayi ya kama shi, ya kura masa ido, ya ce, "Don Allah ka rika bin maganar iyayenka, kada ka yarda kuruciya ta debe ka, ka yi kyalkyalin tsada. Ga ka kyakkyawan saurayi, amma zuciyarka ta munana." Dam birni ya yi sako, yana jin wa'azi, kamar wani mummuni. Da bakauye ya kare ba shi wa'azi ya ce, "To, na ko bi wa'azin nan da ka yi mini." Ya faki idon bakauye, ya yi masa gwalo. Bakauye ya kwance masa igiya ya tafi, ya nufi wajen 33 'yan'uwansa. Suka kai jaki wani gida suka daure, kafin ranar kasuwa su kama shi su kai su sayar. Bakauye ko daga nan bai isa kasuwa ba, sai ya koma gida ya gaya wa matarsa duk abin nan da ya faru. Suka yi ta jin tausayin dam birni, domin wulakantad da shi da suka yi suna tsammani jaki ne, ba dan Adam ba ne. Ran nan bayan kamar kwana uku, ranar kasuwa 'yam birnin nan suka kai jaki su sayar, su sami abin zaman gari. Sai aka yi muwafaka bakauyen nan kuma ya tafi neman jaka. Da ma don ya sami mace shi ya sa ya so ya sayad da nasa namijin. Ko da ya isa ya duba haka sai ga jakinsa na da, sai ya matsa kusa da shi, ya dube shi, ya yi tsaki mts, ya ce, "Allah wadanka! Duk wa'azin nan da na yi maka ba ka lura ba? Mai hali ba ya barin halinsa. Haka ku ke shaye-shayenku, kuna sa mutane asara a wofi. Dubi duk wahalar da ka sha wajena, buga wannan kasuwa, dauki itace kai wannan kasuwa, duk ba ka daddara ba, sai da ka sake yin sha. Ni dai na gane ka. Sai ku yi can da wanda tsautsayi ke bibiya, mu dai muna tudun mun tsira." Ya hauri jaki ya wuce. Dan Sarki ya ce, "Ai ko wannan lalle ya isa bakauye!" Aku ya ce, "Ina ka san ya isa muzi tukun? Ai da sauran labari." Da ya duba bai samu wani jakin saye ba, sai ya komo gida yana kunne da dam birnin nan. Can zuwa maraice, 'yam birnin nan suka karyar da jaki, suka karbi awalaja. Da wata kasuwa ta kewayo, sai bakauye ya samo kuďinsa ya komo kasuwa neman jaka. Yana zuwa kusa da kofar gidan mai gari, sai ga fam birnin nan da ya ce shi ne ya rikide jaki, bakauye ya saya. Ya yi sitati za shi kasuwa, kayan nan sun dauki zargina tsar. Ko da bakauye ya gan shi sai ya gane shi, haushi kuwa ya kama shi, ya ce a ransa, "Kai, ba na dai yarda in yi asara a wofi don lalataccen nan!" Sai ya dubi dam birni, ya ce, "Ashe ka koma mutum kuma?" Dam birni ya yi biris da shi. Sai bakauye ya tasam masa ya kama shi, ya sa masa akumari, ya ce wai zai hau ya tafi da shi ya yi kwarami. Dam birni da yana tsammani da wasa ya ke, sai ya ga ya yi wuf ya haye kafadarsa. Ga shi ya fi dam birnin karfi, ya kuma fi shi iya kokawa, ya yi ya yi ya ka da shi, ya kasa. Mutane suka cika wuri su ga.ikon Allah. Bakauye ko bai kula da su ba, sai df1, dl, d'l, ya ke yi, yana has! kur! wai shi ya hau jaki, yana ta ba shi dudduge a ciki, yana duka. 34 Da dam birni ya ji ba dama, sai ya kwanta. Bakauye ya haye cikinsa yana duka, wai ya tashi su tafi, yana cewa, "Ai fa ko a janye sai na kai ka gida, ka daukam mini taki, ba na yarda in yi asara. Ka sha ka zagi uwarka, ta mai da kai jaki, na saya ban sani ba, ta koma ta gafarta maka ka koma mutum, na dauki asara, na sake ka. Ranar Talata kuma, da na zo cin kasuwa, na tarar ka sake yin wani abu ta mai da kai kuma jaki, wani ya saya. Ga shi yau kuma ina ga ta gafarta maka, ka koma mutum. Ka sa kuma wancan mutumin da ya saye ka ya yi asara kamata." Ya dubi mutanen da ke kewaye, ya ce, "Don Allah, jama'a, gaskiya fa kun ga wannan na yiwuwa? Kura da shan bugu, gardi da karbe kaya? Ai ka san ba abin da zai hana ni yin kwarami da shi, ko kuwa ya fanshi kansa:" Sai ya sake hau masa da bugu, wai ya tashi su tafi dai kauyensu. Suna cikin haka sai ga wani Dogari, ya kwashe su ya kai ga Alkali. Alkali ya tambayi bakauye yadda aka yi, duk ya kwashe ya fadi, bai rage kome ba. Da mutane suka ji haka, suka ce me za su yi ba dariya ba? Alkali ya tambayi dam birni in hakanan ne. Dam birni ya ce faufau shi bai ko taba ganin bakauyen ba, sai yau. Alkali da ma ya san halin irin mutanen nasa sa aika. Sai ya sa Dogarai su tambaye shi sai ya faďi gaskiya. Da masu fushi da fushin wani suka same shi, ya ji zafi, sai ya ce, "Wayyo Allah, ku tsaya, ku tsaya!" Suka dakata. Ya kwashe maganar bakauye, ya ce duk hakanan ne, mutane suka yi ta al'ajibi. Alkali ya sa ya biya bakauye kuďin jakinsa sule goma sha daya da taro, yadda bakauye ya ce ya saya. Ka san abu hannun barawo, shi fa dam birnin nan sule shida da sisi ya sayar da shi wannan kasuwar da ta wuce. Alkali ya sa aka daure dan birni. Bakauye ko aka ba shi kudinsa, ya tafi. Bakauye dai bakauye ne. Duk abin nan gogan naka har ya tafi bai san wayo ba dam birnin nan ya yi masa ya sace jakinsa. Shi har yanzu tsammani ya ke dai rikida ya yi. Musa ya yunkura zai fita, sai ya ji magana a babban zaure, wadansu daga cikin bayin sauro ya dame su, sun kasa barci. Suka farka suka yi ta taďi har gari ya waye. Musa ya koma gida yana jin haushi. Da shigarsa gida ka san ba abin da ke cikin idonsa sai barci, don duk cikin 'yan kwanakin nan bai runtsa ba. Ko da ya kwanta bai farka ba sai can zuwa la'asar, ya tashi ya yi salla, yana nan har 35 magariba ta yi, aka ci abinci. Bayi suka duka hira. Da Musa ya ji bayi sun yi barci, ya tashi ya shigo damaru, ya ce wa aku, "Don Allah yau kada ka tsai da ni, sallame ni in tafi. Kai, Allah ya kiyashe mu! Ban taba ganin tsuntsu mai surutunka ba." Aku ya tuma nan ya tuma nan, ya ce, "Ba kai kadai ba, Allah ya ba ka nasara, kowa na ganin surutummu, amma in kun lura da mu ba mu surutu a banza. Ko dai mu ba da gargadi, ko kuwa don rashin munafuncimmu mu bayyana asirin da muka gani ana kullawa za a cuci jama'ar Annabi. Don haka yanzu duk inda muka fi rashin fada shi ne wurin mata. Tsaya ma ka ji yadda wani aku ya yi da wata mace, don ka san dai al'amarimmu muna yi don Allah ne, ba don mutane su yaba ba." 36 Labarin Wani Aku Da Matar Ubangidansa Wata rana wani tajiri za shi fatauci, sai ya bar matarsa a gida. Yana kuma da wani aku. Suna nan tare, sai matar ta rika fita yawo, don ta ga mijin ba ya nan. Barorin gida da suka ga abin ya dame su, ba su da damar su yi magana, kada matan nan ta sare su wajen mai gidan in ya komo. Saboda haka suka zura mata ido. Ana nan ran nan sai mai gida ya dawo. Ka san al'amarin duniya ba shi boyuwa, sai wani ya tsegunta masa abin da matarsa ta yi ta aikatawa bayan ba shi nan. Da mai gidan nan ya ji haka, sai ya kira matar, ya same ta ya yi ta zagi. Ya dauki sanda kuma ya ba ta kashi. Da matan nan ta ga haka sai ta yi yaji, aka komo da ita. Ta ce a ranta, "Ba wanda ya fadi abin nan sai aku." Ka san mu, Allah ya ba ka nasara, bakin jini gare mu kwarai, tun ba game da mata ba. Suna cewa mun faye tsegumi. Saboda haka, ta bari mai gida ya tafi kasuwa, sai ta kama aku, ta fige shi da rai, ta wurga shi waje ta taga, ta ce, "Daga gare ni ka bar tsegumi!" Allah ya sa aku bai mutu ba, ya tsallaka har ya kai wani hurumi ya sami kabari ya shige, ya yi ta jiyya. Da mai gidan nan ko ya dawo, sai matar ta ce wai bayan fitarsa kadan kyanwa ta cinye aku. Ko da ya ji haka sai ya san karya ta ke yi, kashe shi ta yi, don tana tsammani shi ya gaya masa tana fita da ba shi nan. Saboda haka ya fusata kwarai da gaske, .ya same ta da duka kamar ba zai bar ta da rai ba. Ya kore ta daga gidan, ta tafi wajen hurumin nan tana kuka. Ashe aku na nan kusa da ita cikin wani kabari, yana ji. Sai ya ce mata. "Yi shiru, bari kuka, in Allah ya so kya koma dakinki. Amma akwai sharadi guda, sai ki je ki aske kanki sarai, sa'an nan ki dawo nan, gobe zan taimake ki ki koma." Matan nan ta duba, ba ta ga kowa ba. Abinka da mace, sai ta yi tsammanin, wani matacce ne ke yi mata magana. Nan da nan ta tafi gidan iyayenta, ta sa aka aske mata kai kwal. Da gari ya waye, maraice ya yi ta nuho wajen hurumi, kai na kalli sai ka ce na namiji. 37 Da isowarta sai ta tafi wajen kabarin. Abinka da jahila, ta durkusa, ta ce, "Na asko." Sai aku ya ce, "To, kin san dalilin da ya sa na ce ki aske kanki, domin kin zalunci wani dan tsuntsu, kika targe shi a kan abin da bai ji ba bai gani ba, har kika fige shi da ransa, kika wurgo shi bayan gida. A wannan na yi miki sauki, na ce ki aske gashin kanki kawai, amma in kin kuskura kika sake yi wa wani tsuntsu haka, ki kuka da kanki. Amma akun nan da kika kashe zai komo duniya, yadda zan mai da ke dakinki, shi kuma zan mai da shi gare ki. To, ki lura da shi da kyau, ki sa mijinki ya ajiye yaro guda mai hankali wanda zai rika lura da shi, a rika ba shi ruwa da sukari. Kuma ki tsawata wa yara su bar kiransa aku kuturu." Matan nan ta kara dukawa, ta ce, "Na ji." Da za ta tashi sai aku ya ce, "Da saura. Yau kin ga sha biyu ga watan Safar. To, ko wace shekara sha biyu ga watan Safar ki aske kanki, don ya rika tuna miki aku dai da ki ke ganinsa banzabanza ba banza ba ne. Amanar Allah ce ya sa a hannunku 'yan Adam, ya fi kyau kuwa ku lura da ita da kyau. Watan duk da ya zo ba ki aske kanki ba, yadda na gaya miki yanzu, ki tabbata ba ki shekara. Shi ke nan, gobe kya koma in sha Allahu. Tafi gida abinki. Amma ki kiyaye gargadin nan da na yi miki, ki kuwa yi kirki, ki bi mijinki sau da hannu. Allah ya gama mu da alheri & Darassalamu!" Mace ta koma gidansu. Aku ya tashi yana tsalle, har ya kai gidan tajirin nan, ya ce masa, "Ka san ni?" Tajirin ya dubi aku ba gashi, ya ce, "Yaya zan yi in san ka, ban taba ganinka ba?" Aku ya ce, "Ba ka taba ganina ba? Ai ni ne akunka wanda kyanwa ta cinye." Tajiri ya ce, "Tun da kyanwa ta cinye ka, yaya kuma aka fara har ka yi rai? Da ma dai ba kyanwa ta ci ka ba akwai yadda aka yi." Aku ya ce, "Daga cikin kyanwar aka nufa in fito, don in shaida maka duk abin da matarka ta fadi na batun kyanwa ta cinye ni gaskiya ne. Kada ka zarge ta. Amma in kana sona, zan kara dakatawa kuma wurinka, in yi gashi in koma kamar da, har Allah ya kari kwanana gaba daya. Amma sai ka mai da matarka, ka yafe mata, ku yi zaman lafiya." Mai gida ya ce, "To." Ya aika matar ta dawo, ya gafarta mata, suka sake zamansu. Daga ran nan ta zama mazar kirki, duk gari ba wadda a ke so sai ita a kan kirki. Musa ya tashi zai fita, aku ya dube shi, a ce, "Wallahi, yallabai, ba ka ga yadda ka rame ba. Maza ka ta i kada zulumi ya 38 halaka mana kai a banza, yadda ya tashi halaka Sarkin Zairana." Musa ya waigo, ya ce, "Ina ne Zairana kuma? Zulumin mene ne haka ya sami Sarkin, har ya tashi halaka?" Aku ya ce, "Yallabai, me ka mai da zulumi ne?" 39 Labarin Sarkin Zairana Da Sarkin Bokaye Gara Akwai wani Sarki a Zairana wanda Allah ya nufa da kiba, abin har ba iyaka. Idan ka gan shi sai ka ce giwa, in ya zauna ba yadda zai yi ya ga cibiyarsa, dokin duniyan nan duk ba mai iya daukarsa. In ya tashi daga zauren gidansa zai shiga, mutum ya yi tafiyar loko biyu Sarkin nan bai isa ba. Sarki fa duk abin duniya ya dame shi bisa ga wannan kiba, shi kuwa ba abin ya ki cin abinci ba ya mutu. Saboda haka ya tara bokayen kasarsa, ya ce su yi kokari su samam masa maganin da zai sha ya rage kiba. Bokayen suka shiga aikinsu. Kowa sai ya sassako wannan itace, ya gino wannan sauya, ya kai wa Sarki. Ya yi ta sha, amma a banza. Maimakon ya ragu sai karuwa ya ke kullum safe, sai ka ce ma maganin ya kara kiba su ke ba shi. Da Sarki ya ga haka sai ransa ya kara baci, ya yi kamar ya kashe kansa don haushi. Ga duniya Allah ya ba shi, kiba ta hana shi jin dadin cinta. Yana nan haka sai ya ji labarin wani boka wanda a ke kira Gara Mai Aburkuma. Sarki ya aika aka kira shi, ya bayyana masa bakin cikinsa. Ya ce in ya warkad da shi kuwa zai yi masa kyauta har ya kasa godiya. Gara ya се, "Tо, Allah ya taimake mu. Amma in ka yarda,. ranka ya dade, ina so a ba ni kwana uku in je in shawarci Aburkuma, Inna uwa ma ba da mama, abin da muka yi da ita duka zan zo in gaya maka." Sarki ya ce, "To, je ka, na ba ka iznin kwana uku, amma kada ka wuce haka." Gara ya yi ban kwana, ya tafi. Ya yi ta tunanin inda zai fito wa Sarki ya yaudare shi. Ya san dai, in ba wautar Sarki ba, wane boka ne zai iya ta da hukuncin Allah? Bayan kwana uku sai Gara ya komo wajen Sarki, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, na dawo." Sarki ya ce, "To, ina labari?" Gara ya ce, "Allah ya daukake ka, ai sai a bar kaza cikin gashinta, al'amarin ya tayar mini da hankali."" 40 Sarki ya ce, "Me ka gani, na ce. Fada mini mana in ji." Gara ya ce, "Allah ya ja zamaninka, ai ba na iya fadin abin da Inna ta gaya mini. Saboda bakin cikin al'amarin, jiya, na rantse har da rawaninka, ban yi barci ba. Abin da na gani ya fi sai a bar wata wahalar neman magani, a tasam ma istingifari." Sarki ya fusata, ya ce, "Yau ga zancen banza. Na ce ka gaya mini abin da ka gani, ka tsaya kana kewaye-kewaye." Gara ya ce, "Allah ya yi wa Sarki rahama, Inna ta ce saura kwana arba'in ka riga mu gidan gaskiya." Sarki ya fusata, ya ce a kama shi a daure. Dogarawa suka cafe shi. Gara ya ce, "Da ma abin da na ke gudu ke nan da gaya maka gaskiya." Aka dai iza keyarsa zuwa gidan kurkuku. Sarki ya shiga zulumin abin nan da Gara ya fadi, ya ce, "Na san Gara fa shahararre ne bisa ga al'amari da aljannu. Ba abin da ya fi dai sai a rika kidaya kwanakina da ya fadi. In sun cika arba'in na ga ban mutu ba, na san Gara karya ya ke yi. In kuwa na ga bayan kwana talatin da takwas, ko talatin da tara, na fara 'yar mashasshara na san ni tawa ta kare."" Wannan zulumin da ke ran Sarki fa ya sa ya tsunke. Ko abinci ba ya iya cin abin kirki, balle ma ya faranta ransa da wadansu kawace-kawacen duniya. Saboda haka kullum sai ramewa ya ke don zulumi. Duk mutane suka rasa kansa suka rasa gindinsa. Bayan kwana talatin da wannan magana sai tashin hankalin nan ya yi masa yawa, har ya sa kansa ya rika ciwo. Rana ta talatin da tara da ya ji ciwon kan na karuwa, sai ya kira dansa ya danka masa mabuďin taskoki, ya yi ta yi masa wasiya, yana gargadinsa yana cewa su tasu ta kare. Yaro bai san abin da ya ke nufi ba, tsammani ya ke don ya fara tsufa ne ya ke so ya nuna masa al'amuran mulki. Ana nan dai kwana arba'in suka cika, Sarki na jiran mutuwa, bai ga ya mutu ba. Kwanaki dai suka kai kwana arba'in da biyar, Sarki bai ga ya mutu ba. Sai ya áika aka zo da Gara daga gidan sarka, ya се, "Ка сеe bayan kwana arba'in zan mutu, ga shi yau kwana arba'in da biyar da maganar, ban mutu ba." Gara ya ce, "Da ma maganin ka rage kiba ka tambaye ni, to, karyan nan da na yi na ce'saura kwana arba'in ka mutu ita ce maganin. Ka tambayi kowa nan garin ka ji in ba ka rage kiba ba."" Da Sarki ya ji haka, sai hankalinsa ya kwanta, ya bushe da dariya, mutane suka yi kyakkewa baki daya, suka ce, "Lalle Gara ya isa dan duniya." Gara ya ce wa Sarki, "Ba abin dariya ba ne, sai ka ba ni abin da ka alkawarta." 41 Sarki ya sa aka yi ta kawo masa riguna da zannuwa da wanduna, ya kuma ce duk mai kaunarsa ya yi wa Gara kyauta. Mutane suka yi ta zuba masa kudi, tun yana godiya har ya fashe da kuka don murna. Sarki ya sallame shi, ya kwashe kayan da aka ba shi duk, ya tafi. Kullum in an ta da labari, sai Sarki ya yi ta yi wa kansa dariya in ya tuna abin da ya yi daren da kwanan nan arba'in za su cika, da ya yi ta yawo tsakar gida shi kadai, ya kai gwauro ya kai mari, yana ta salati ga Fiyayyen talikai. Aku na kare wannan labari, sai Musa ya ji zakara na ta cara, gari ya waye. Ya rasa abin da zai ce wa aku ya huce, sai ya shiga gida, ya yini ran nan bai ce wa kowa kome ba. Magariba na yi, sai ga 'yar tsohuwan nan ta dawo, Waziri ya aiko ta da takarda wai daga Mahmudu, ta kawo wa Musa. Musa ya karba ya karanta, ya cе, "Allah wadan dan abin nan da ke hana ni fita." Tsohuwa ta ce, "Yanzu haka, yallabai, duk karkaran nan da mace da namiji ba ka jin wani abu sai Mahmudu. 'Yam mata ma yanzu ba su da wata waka sai ta Mahmudu." Musa ya ce, "Har waka 'yam mata suka yi masa? Don Allah, in kin iya, rera mu ji." 'Yar tsohuwa ta karkace kai, don iya kissa ta fara wakan nan, ba da ko ta taba jinta ba: Jama'a ku zo ga kallon Mahmudu, Wanda ya wuce wargi. Ya fi karfin sai gobe, Ya wuce mai wargi. Shi ne ya kori Sinarawa, Har ya kashe musu Sarki. Ya fi karfin sai gobeе, Ya wuce mai wargi. Mahmudu wa ga Musa, mazaje, Da sunka kawo karfi. Ya ki wargi dattijo, Ba ya son mai wargi. Zaman gida na raggo, Sai dan da ke gudun mai karfi. Dan Sarkin da ke cikin mata, 42 Shi da su ana nan daidai. Ya fi wargi, Mahmudu, Ba ya son mai wargi. Da Musa ya ji wannan waka sai idandunansa suka jujjuye. Tsohuwa ta tashi, ta tafi wurin Waziri ta gaya masa. Waziri ya yi mata kyauta. Da asubahin farko, Musa ya yi damara, ya dauki wata babarbara, ya tafi wajen aku, ya ce, "Zan tafi, ko ka yardá, k ba ka yarda ba." Aku ya duka, ya ce, "Yallabai, ina da ikon hana ka? In dai ka fita, ka sami dan kwabo ka yi sadaka. Allah ya ba da sa'a!" Musa ya ce, "To." Ya juya zai fita, aku ya ce, "Af, yallabai, ko za ka dakata kadan in fita ta taga in samo maka wani maganin karfe da na gada daga kakana? Ka san fa mazaje ba a tasam musu ba shiri." Musa ya ce, "Gaskiyarka. Yi maza ka debo, amma kada ka tsaya." Aku ya fita ta taga, ya sami wata itaciya ya haye, ya yi zamansa. Can da ya ga asalatu ta kusa, ya debo ganyen itaciyar, bai san ma ko wace irin itaciya ba ce. Ya taso fir ya kawo wa Musa. Musa ya karba, ya се, "Amma kuwa ka tsai da ni."" Aku ya ce, "Ba ka san iyakar inda na tafi ba ne, da ba ka zarge ni kan dadewa ba. Ka sa a dafa maka, ka yi wanka da shi, ba dai karfe ba, sai wani abu." Musa ya ce, "Ka ji asalatu ta yi." Aku ya cе, "Bа kome ka tafi gobe, zuwa da wuri ai ya fi zuwa da wuri wuri. Kafin a kare kiran salla bari in gaya maka wani dan labari guntu." 43 Labarin Kyanwa Da Bera Akwai wata itaciyar kuka a bayan wani gari. A gindin itaciyan nan akwai wani bera, a cikin kogonta kuma ashe akwai wani muzuru na kwana. Kukar kuwa cikin gonar wani mutum ta ke. Kullum dare sai muzurun ya fito ya je ya yi ta wa mutumin nan barna. Da mutumin ya ga haka, sai ya samo wata raga ya yi tarko, don ya kama kome ke shiga ke yi masa barna. Allah ko ya ba shi sa'a. Da asalatu ran nan muzurun ya ga beran, ya zabura zai kashe, sai ya fada cikin tarkon, ya yi ya yi ya fita, ya kasa. Bera kuwa da ya waiga ya ga tarko ya kame muzurun, sai ya yi rawa yana murna. Yana nan yana murna, ya duba haka cikin kara kusa da raminsa, sai ga wani maciji nan yana jira ya rabo da muzuru ya hadiye shi. Ya duba sama don ya hau, sai ya ga shirwa na kewaya, tana jira ya motsa ta fyauce shi. Bera ya tsaya, ya rasa inda za shi. Abu ya zama masa gaba siyaki baya damisa. Yana nan sai ya tuna wata dabara, ya ce, "Na san dai da maciji da shirwa ba mai iya zuwa kusa da muzuru. Yanzu ba abin da ya fi sai in je wajen muzuru, in ce ya rantse ba zai sake cutata ba, ni ko in cinye igiyar ragan nan in sake shi."" Sai ya tafi ya tambaye shi. Muzuru ya ce, "Ina za a fara wannan aiki? Ka fid da ni daga halaka, sa'an nan in cuce ka? Ai ka kubutad da ni, mun zama abokai ke nan har abada." Bera ya ce, "Bari in jarraba alkawarin nan naka in gani, in gaskiya ne. Zan kurda tsakanin kafafunka in gani in ba ka cuce ni ba. Amma fa ka sani in ka halaka ni, ka halaka kanka ke nan." Muzuru ya ce, "Ai ni ba na magana in tayar." Bera ya kurda ko'ina, muzuru bai motsa ba. Da maciji ya ga haka sai ya sulale, kada muzuru ya sami kubuta ya gama masa aiki. Shirwa ita kuma ta yi nata wuri, don tana tsoron muzuru. Muzuru ya ce wa bera, "Aboki, yi maza ka cinye igiyoyin nan, ko na tsira. Ko yaushe na motsa sai in ji sun kara daure ni." Bera ya ce, "Yi hakuri dai kadan, igiyoyin ke da karfi." Don wayo sai ya takarkare, kamar yana cin igiyar da karfi, amma sannu ya ke yi, yana cewa a ransa, "In na yi maza na kwance shi, AA ban yi tsammani zai bar ni ba. Amma in na ja aiki sannu sannu har mai gona ya zo, sa'an nan in yi da sauri in na hange shi, da ya kubuta sa'an nan sai ya kama gabansa, ba zai nufe ni ba." Muzuru ya rika duban bera, yana cewa, "Don Allah yi maza, gari ya waye, yanzu mai gona ya zo ya ga abin da ya faru. Kasan ko, in ya same ni nan, na lalace." Bera ya ce, "Gabanka ya bar faduwa, iyakar kokarina na ke yi. Ban da ni ba beran da zai yarda da kai ya taimake ka." Ya ci gaba da tauna sannu sannu, yana barin wadansu. Can sai suka hangi mai noma tafe, yana sabe da bota. Muzuru ya ce wa bera, "Ga shi can tafe, ga shi can tafe, don Allah yi maza."" 45 Bera ya kama aiki da karfi. Manomi ya kusa kawowa, ya tsunke raga duka. Muzuru ya gudu ya fada daji. Bera ya ruga ya shiga raminsa. Manomi ya rika tafa hannu yana cewa, "Kash! Ya cinye ragar, amma bari, gobe na sake dabara." Ya kwashe, ya koma gida. Da gari ya waye kashegari muzuru ya zo bakin ramin bera, ya ce, "Abokina, abokina, fito mu yi tadin abota." Bera ya yi dariya da ya ji wannan zance na muzuru, ya ce, Wane aboki? Ai muddin kana nan ba ka ganina na leko. Da ma kaddara ta sa mu aminci, ba wata abota ce mai dorewa ba, ta fatar baki ce, tun daga jiya kuwa muka babe. Yadda ruwa ke abokin gabar wuta, haka na ke abokin gabarka. Da ma ka dangana. Wannan hadari mun haye shi, sai wata rana." Da muzuru ya ji haka sai ya tsuguna nan, ya yi ta rantse-rantse, ya kalallame shi da baki, yana cewa, "Fito, mu sami wurin zama, ni ba zan cuce ka ba. Kuma da ya ke ni na fi ka karfi, ko wane abu na ga zai cuce ka na yi kokarin in tsare maka shi." Ya dai sami dan beran nan, har ya yarda da maganarsa, ya fito. Ya kewaya, bai ga ya yi masa kome ba, sai ya ce, "I, ashe dai gaskiyarka, ko cikin kyanwoyi akwai 'yan halas da yawa." Muzuru ya ce ya kwashe kayayyakinsa da ya tara, su koma cikin kogon kuka inda ya ke, don can ya fi yalwa. Bera ya yi ta kwaso kayayyaki masu yawa wadanda ya ke tarawa, domin lokacin dari ya yi kwanciyarsa cikin rami, ba ya fitowa, balle ya sha dari. Da muzuru ya ga kayan da bera ya tara, ga su daddawa, ga mai, ga nama, ga fura, ga cuku, ga kayayyaki barkatai, sai kunya ta kama shi, don ba shi da wani abu gidansa. Ya tambayi bera inda ya samo wadannan kaya cikin daji. Bera ya ce, "Wajen mai gonan nan da ya kama ka. Kullum matarsa ta kawo masa a nan gona, kafin ya kai kunyar da ya fara ya zo ya ci, ni ko sai in yi ta diba, ina kawowa gida da gudu, ina komawa. Wadansu ko ma ta wajen ubana na gaje su." Muzuru ya ce, "Sai haka." Shi kuma ya shiga nasa kokari, bera kuma ya sake ta da himma, suka kara bisa ga abin da ya zo da shi. Da suka tara, sai suka tsaya shawarar inda za su boye. Muzuru ya ce, "Ba inda ya fi nå masallacin can na bakin kofa." Suka dauki kaya, suka sami wani wuri can suka boye suka komo gida suka shiga hidimar ci da kawunansu kullum. Suna nan zuane, ran nan muzuru ya ji kasala ta kama shi, ga shi kuwa yana jin yunwa, dari kuwa bai kama ba, balle a duba ajiya. Sai ya tafi wurin bera, ya ce, "An aiko mini daga cikin gari 46 wai wata kanwata ta haihu, yau kuwa ne suna. Ina so in tafi yanzu, kai sai ka zauna ka share gida, don ba za mu tare ba, gama halin 'yan Adam ba iri daya ba ne. Abin da wani yə gani ya kyale, in wani ya gani, ba ya kyalewa." Bera ya ce, "Hakanan ne, amma fa kada ka manta da ni cikin kayan suna." Muzuru ya ce, "Haba, in na manta da kai, in tuna da wa?" Ya nufi gari. Da ma karya ya ke yi, ba wanda ya gayyace shi suna, wajen ajiyarsu ya ke so ya je ya ci. Da ya ci ya koshi, sai ya sami wuri ya kwanta yana lasar gashi, yana gurnani. Can da rana ta yi, sai ya komo gida. Ko da bera ya hango shi, sai ya tarye shi da murna, yana tsammani ya rago masa wani abu, ya fara cewa, "Me aka samu?" Muzuru ya ce, "Namiji." Bera ya ce, "Me aka sa masa?" Muzuru ya ce, "Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba." Bera ya ce, "Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba? Ai ko wannan suna yana da ban mamaki. Haka sunayen-zuriyarku su ke?" Muzuru ya ce, "Mene ne abin mamaki ciki, ku da ku ke sa wa naku 'ya'yan Damburuntu fa?" Bera da ya ga kamar ya yi fushi, sai ya kyale. Da aka kwana biyu kuma, muzuru ya ce an sake haihuwa a gidansu, za shi wajen suna. Bera ya ce, "To, amma don Allah yau kada ka manta da ni, ka san ran nan ba ka rago mini kome ba." Muzuru ya ce, "Yawa aka yi a wurin, amma yau na yi kokari in samo maka ko da 'yar tsokar nama biyar." Ya fita, bai zame ba sai masallaci, ya shige, ya sami ajiyar ya ci ya koshi, ya komo waje ya kwanta. Da rana ta yi, ya tashi ya koma. Bera ya tambaye shi ya ce, "Ina tawa ragowar dina, ko kuma yau an yi yawa ne?" Muzuru ya yi biris da shi. Sai kuma ya bar wannan tambaya, ya ce, "Ina sunan da aka sa wa jaririn kuma yau?" Muzuru ya ce, "Yau-da-gobe-ba-ta-bar-kome-ba." Bera ya ce, "Yau-da-gobe-ba-ta-bar-kome-ba? Mts, wadannan irin sunaye naku ban taba jinsu cikin littattafammu ba." Muzuru bai sake ce masa ci kanka ba. Ran nan kuma ya ce an gayyace shi, ya tafi yà cinye sauran ajiyar da ta rage, ya dawo. Bera ya tambaye shi sunan yaro, ya ce, "Ta-faru-ta-kare." Don gudun zuciyar muzuru, bera bai ce kome ba, sai suka shiga sha'aninsu. Daga ran nan ba a sake kiran muzuru zuwa wajen suna ba, 'yan'uwansa suka rabu da haihuwa. A kwana a tashi dari ya tsananta, sai bera ya ce wa muzuru, 47 "Lokacin duba ajiya fa ya yi." Muzuru ya ce, "Tun kwanan baya na so in gaya maka na yi gudun kada ka ga karayata." Suka tashi suka nufi masallaci, muzuru na tafe na yi wa bera gwalo a kaikaice. Da suka isa, bera ya duba, bai ga ko burbudi ba. Ya yi shiru, ya dubi muzuru, ya ce, "To, haka ka yi mini? Na dai gane abin da ya faru. Ashe nan ka ke zuwa, kana cewa wai wani an gayyace ka gun suna. Ran da ka fara ci ka ce wai sunan yaro 'Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba.' Da ka koma ka ce, 'Yau-dagobe-ba-ta-bar kome-ba.' Da ka zo na karshe ka cinye saura ka се wai sunan jariri..." Muzuru ya fusata, ya сe, "Ka rufe baki tun da girma! In na sake jin ka ce M, nan yanzu ina gama maka aiki." Dam beran nan na shiri ya ce, "Ta faru ta kare," muzuru ya kwabe shi. Saboda haka kafin ya yi shiru sai ga 'T', ta fita ta bakinsa. Ko da muzuru ya ji 'T', bai tsaya jiran wani abu ba, sai ya fada wa bera ya lakwame shi. Allah ya ba ka nasara, ka ji cutar shigege. Abin da zan kare ka da shi, in kai basarake ne, kome za ka yi nemi Sarakuna, malami ya nemi maluma, talaka ya nemi talakawa. Kowa ya ki bin abin nan da na fadi, in ya daka ta wadansu, shi ko ya rasa turmin daka tasa. Musa ya tashi ya shiga gida, ya ba da magani aka dafa masa, ya yini ran nan yana ta wanka da shi, yadda aku ya ce. Da rana ta fadi, aka yi salla. Musa ya kama wuridi, har can da asuba bayin Sarki suka yi barci. Sa'an nan ya yiwo shiri, ya taho wajen Aku, ya ce, "Zan tafi!" Aku ya ce, "Kai, ai ko wannan kintsawa da ka yi, ka fita fagen fama ba abin da za a so da kallo irinka! Ba shakka kowa ka gani nan duniya da irin dawainiyar da Allah ya aza masa. Malami ta neman ilmi, boka ta neman asiri, dan Sarki ta neman mulki. Duk ko fa, Allah ya ba ka nasara, wanda ya dami kansa a cikin wannan al'amarin da Allah ya dora masa don kyashin na. wadansu, ya ko sa kansa uku." Musa ya ce, "In ba rashin hankali ba, da ma me zai sa wani ya kula da wani a cikin wannan? Ga shi kowa ya sani Allah ya halicci mutane, ya buda musu kofofi dabam daban wadanda za su bi su sami abinci." Aku ya ce, "Ai ka san halitta kowa da irin ra'ayin da Allah ya yi mata. Hala ba ka taba jin labarin wani jaki da sa ba ne?" Musa ya ce "A'a." Aku ya ce, "Haba, sai haka! Bari ka ji." 48 Labarin Wani Jaki Da Sa Wata rana an yi wani mutum wai shi Sale, wanda Allah ya yi wa arziki kwarai. Kullum dare mutumin nan sai ya yi ta addu'a, yana rokon Allah ya ba shi ilmin fahintar maganar dabbobi. Duk inda ya ji duriyar wani shaihun malami, sai ya aika masa da kudi, ya yi masa roko Allah ya biya masa wannan bukata. Ana nan, a kwana a tashi, Ubangiji maji kan bawa ya karbi rokonsa. Ran nan Sale na barci, ko da ya farka da asalatu sał ya ji wani zakaransa ya ce, "Kikiriki!" Sai wata kaza ta ce wa zakaran, "Kai, maigida kana da murya! Yanzu caran nan taka duk garin nan ba inda ba a ji ta ba." Zakaran ya kada fiffike, ya ce, "Don ma ina mura yanzu ba na iya yi da karfi. Da sa'ad da na ke lafiya ne, in na yi ai duk kasan nan a ji. Sale ya bingire da dariya, har ya rasa abin da ya ke ciki. Ya yi godiya ga Allah bisa ga amsa rokonsa da ya yi. Ya tashi ya yi alwala, ya yi salla, ya fita zaure wajen yaransa, aka yi ta tadin duniya, kowa na fad'in albarkacin bakinsa. Da rana ta yi zafi, sai Sale ya shiga gida, don ya kwanta kafin azahar. Da ya hau gado ya kwanta, sai ya ji ya kasa barci, ya dauko buzu ya fito gindin dabi a barga, ya kishingida. A cikin dabin nan kuwa da ya ke akwai sansa na noma da jakinsa na hawa, suna daure kusa da kusa. Yana nan kishingide, sai ya ji san nan ya ce wa jakin, "Kai dai ka ji dadi. Barorin gidan nan ko yaushe hankalinsu na wajenka. Dubi har wanka su ke yi maka, su ba ka abinci irin wanda ka ke so. Ni kuwa ga ni kullum sai a daura mini kaltibeta, a sa maketacin bawan nan ya tafi da ni gona, in yi ta aiki tun daga fitowar rana har ya zuwa faduwarta. Ba wannan ma ke ba ni haushi ba, sai dukana da ya ke yi in na dan tsaya in sarara. Don Allah dubi wuyana ka gani, duk ya kuje domin wahala. In mun dawo gida kuma ba wani abinci mai dadi ba za a ba ni in ci. Shin wanda ya ke haka don ya ga kyashin wadansu, ai bai kamata ba a ga wautarsa." Da jaki ya ji haka sai ya ce, "Af, ai wannan duk sakarcinka ya sa su ke raina ka haka. Tun da su ke zuwa daura maka kaltibeta, ka taba tunkuyin wani daga cikinsu? Ko ba ka tunkuye su ba ma, in kana tasam musu kamar za ka danne su, ka ga sun fara rage maka azaba. Ga shi Allah ya ba ka karfin da za ka neman ma kanka girma da shi, amma wautarka ta hana. Kuma ai ko ba ka fito musu ta haka ba, ka ce su kan kawo maka rubabbiyar dusa, to, in sun kawo kada ka ci, in ka sunsuna ka kau da kanka. Wallahi in ka bi wannan dabara tawa, ka ga al'amarin ya yi maka dadi har ka gode mini." Sa ya kama abin nan da jaki ya gaya masa, ya yi masa godiya bisa ga nasiharsa. Sale dai na kishingide, yana jinsu. Da gari ya waye sai bawan nan ya dauko kaltibeta ya daura wa sa, ya tafi da shi gona: Suka yi aiki, suka komo. Da dare, ko da bawan nan ya zo ya daure shi, sai ya ga ya tasam masa kamar zai halaka shi, ya ruga ya dawo, sa ya yi gunji, ya rasa yadda zai yi ya daure shi, sai ya rufe dabin, ya bar shi a sake. Ya'kawc dusa da kaikayi ya tura masa, yana cewa, "Yau san nan lafiya ya haukace? Ko kuwa yana jin kishiruwa ne?" Ya tafi rijiya ya jawo ruwa, ya tura masa, sa ya ki ko dubansu. Da gari ya waye bawa ya dawo ya ga kwanan sa, sai ya tarad da shi kwance, ya mimmike kafafunsa, yana nishi, ya dubi kwandon dusa da na kaikayi, ya gan su yadda ya ajiye, sa bai ko taba ba. Ga ruwan kuma da ya kawo, ba abin da ya taba shi. Da ganin wannan bawan ya ce, "Haba, na san a yi haka, haukacewar da san nan ya yi jiya ba banza ba. Ashe yana da gaskiya, shi kadai ya san abin da ya ke ji. Yau dai bai kamata a je da shi gona ba." Ya ruga ya gaya wa Sale haka. 50 Da Sale ya ji, sai ya lura watau san'nan ya bi shawarar da jaki ya yi masa ne. Saboda haka ya ce wa bawan nan ya je ya kama jakin, ya tafi da shi gona. Ya ce ya daura masa kaltibeta, ya yi noma da shi maimakon sa, kada kuwa ya ji tausayinsa ko kadan. Bawan ya tafi ya kama jaki, ya kai shi gona, ya daura masa kaltibeta, ya yi ta aiki da shi, in ya dan dakata don rashin sabo, sai bawan ya aza masa kulki tim, jaki ya kara mai. Suka yi ta yin haka tun da sanyin safe har rana ta koma ga Ubangiji, sa'an nan bawan ya koro shi zuwa gida, ya kawo shajaran majaran. Sale na kofar gida zaune, ya ga sun dawo. Ya dubi jaki, ya ga lalle kamarsa ta sake. Ya tambayi bawan yadda suka yi da jaki, ya gaya masa duka. Sale ya'ce a ransa. "Bari in bi jakin in ji yau kuma me zai ce wa sa." "Daure jakin ke da wuya sai ya fadi yana nishi, ya dubi sa, ya ce, "Kai, yau in an kawo maka abinci, me ka kulla kuma za ka yi?" Sa ya ce, "A'a! Har da wata dabara ce da ta fi wannan da ka gaya mini? Ga shi yau duk ranan nan da aka yi sai kwance na ke cikin inuwa ina hura hanci. Ai ni wannan makwabtaka da kai ta yi mini amfani." Jaki ya harare shi, ya ce, "Kai sakarai, kana nan kwance ba ka san abin da a ke kullawa a yi maka ba. Yanzun nan da zan shigo na ji ubangijimmu na cewa bawan nan nasa, tun da ya ke ba ka iya cin abinci, balle ka yi wani aiki, gobe sai ya je ya kira Sarkin Fawa, ya zo a yanka ka a yi rarraba. Da kamar in kyale ka, sai na ga dai yadda ka yarda da ni haka, har ka ba ni shawara, bai kamata ba in ci amanarka. Don an ce kowa ya ci amanar wani, ko ba jima ko ba dade, ya ga sakayyar Allah. Abin da na ga ya fi yanzu, in sun kawo maka abinci ka sa hankalinka ka yi ta ci, sai ka koshi. Wallahi in ba haka ka yi ba, in gaya maka gaskiya, gobe war haka kai kuma sai labari. Wannan magana fa ta kama sa, nan take ya kama kiwo ba ji ba gani. Yana ta godiya bisa ga wannan nasiha da jaki ya sake yi masa. Sale ya kura wa sa ido, yana dariya da ya ga ya takarkare ba ya ko daga kai, in ya ci dusa ya juya ga kaikayi, sai cika bakinsa ya ke yi kamar mahaukaci. Sale ya yi ta mamaki, yana cewa a ransa, "Ashe duk abin nan da mu ke yi wa dabbobi sun sani, Allah dai ne bai ba su bakin da za su furta mana ba. Yadda Allah ya hore mana su haka, ba don karfimmu ba, ba abin da ya fi sai mu rika sawwake musu wahala matsananciya. Mu tuna duk abin da mu ke ji, su ma suna ji, mu lura da su yadda za mu lura da kammu, kada mu gode wa Allah da mugun aiki." 51 Ya tashi, ya kira bayinsa, ya hore su da rika lura da dabbobinsa da kyau, kada su sa su abin da za su wahala fiye da kima. Musa ya се, "А! Ashe har mutane na iya jin maganar dabbobi ko? Wannan abu da ban mamaki!"" Aku ya çe, "Ai ko ni na taba ba wani ubangijina maganin jin, sa'ad da ya auro wata karuwa da ta matsa mana lamba. Ta wannan hanya na raba su. Af! Kai, kada in tsai da kai da labarin, sai ka yi shiri ka fita kafin gari ya waye." Ya yi shirin fita sai aka yi asalatu. Ba dama ya leka ko waje, tun da ya ke kowa ya farka. Ya koma gida, tun safiyan nan har magariba yana ta tunanin dabarar da zai yi wa aku ya samu ya fita, ba da ya tsai da shi ba. Zuwa asubahin fari, da ya ji bayi sun yi baci, sai ya zo ga aku, ya ce, "Yau ba na son wani labari. Abin da na ke so sai ka gaya mini yadda kuka yi da ubangijin nan naka, da ka ba shi maganin jin maganar dabbobi, in tafi. Shí kaďai na ke so, ba kome ba." Aku ya ce, "Ka ko yi tambaya ga dan gida." Ya tsirgo, ya soma. 52 Yadda Muka Yi Da Ubangijina Ojo Kafin in zo wajen Balaraben nan da Sarki Abdurrahmani ya sayo ni a gunsa, da wajen wani Bayarbe na ke wai shi Ojo. A cikin garin nan da ya ke duk ba wanda ya kama ko kafarsa wajen arziki. Amma duk da haka abin ya ba ka mamaki in ka ji na се matarsa daya ce tal. Da yana da uku, sai ya auro wata hatsabibiyar karuwa, suka yi su huďu. Ko da karuwan nan ta shiga gidansa, sai ta tasam ma shiga bokaye da 'yam bori, don ta sami maganin da za ta kori sauran matan. Kwanci tashi, ta ko samu. Ojo kuwa da ma ba ya ganin kowa da gashi, ban da karuwan nan. Don tsananin son da ya ke mata shi ya sa ya aure ta. Da ta sami maganin da za ta yi ta raba Ojo da sauran matansa, sai ta ce, "Kome ya yi kyau. Amma ai fa an ce kau da bara ba ta ci sai an gama da gociya." Saboda haka fa ta soma kulla makirci, tana gama Ojo da matansa dai dai. Yau ta sa ya kori wannan, gobe ya kori waccán har ya zama gidan ba wata sai ita. Ga mijin kuma Allah ya ba ta a hannu. In kara ta gifta masa ba shi da ikon ketarewa, sai ka ce ba mai arżiki ba. Mulkin nata ya wuce bisa kan mijin, har yaran gida ba mai ikon tari in tana nan. Da wani, ya yi mata dan tashin kai, sai ta sa a kore shi. Kai, bari ta şu mutane, har ni ma da na ke dan tsuntsu shakkarta na ke yi. Ga mijin mutumin kirki, yana son yin wani abu, amma yana shakkar kada ta yi hushi ta ce za ta fita ta bar shi. Da na ga dai abin nan ya rude haka, sai na ce, "Abin nan ya kamata mu sa hannu." Na yi kwana uku ina shawarar hanyar da zan bullo wa wannan al'amari, yadda karuwan nan ba za ta ji ba, balle ta halaka ni, yadda kuma Ojo ba zai gane nufina sosai ba balle shi kuma ya tsane mi. Don ka san an ce, "So hana ganin laifi." Da na sami wata dabara, sai na kyale. Ran nan muna tare da Ojo, sai na ga yana sauraron wata 'yar tsuntsuwa da ke kuka nan bisa taga. Na dube shi na ce, "Da kana jin abin da 'yar tsuntsuwar nan, ke cewa, ashe da ban san abin da za ka yi ba don murna." Ojo ya ce, "Haba, yadda na ke da arziki haka, ya zama kuma 53 ina jin abin da dabbobi da tsauntsaye ke fadi, ai da ba haka ba." A raina sai na ce, "Wannan ya samu." Na dube shi, na ce, "Akwai maganin da a ke yi a ji, amma da sharadi guda mai wuya, shi ya sa ba shi da amfani sosai, ba don haka ba, ko ni ma da sai in ba ka. Ba wanda ya san wannan asiri ko cikin tsuntsaye, sai zuriyar gidammu kadai." Ojo ya ce, "Don Allah ka ba ni. Gaya mini sharadin kome wuyarsa na iya." Na yi dan musun karya, ya matsa ni. Sai na tafi, na samo maganin na ba shi, na ce ya sa a dandaka, a rika zuba masa ruwa cikin kunne kullum, da dare. Ya tambaye ni bayan kwana nawa za a bari. Na ce masa in lokacin bari ya yi, ba sai an gaya masa ba, zai ji abin da ya ke so ya samu. Yana doki zai shiga gida ya bayar a dandaka, sai na се masa, "Ai ba ka ji sharadin ba." Ya dakata. Na ce, "Sharaď'insa shi ne duk wanda Allah ya yi wa wannan baiwa kada ya bi shawarar mata, kome mace ta gaya masa, ko 'yar wane ne, ko da abin da ta fadi gaskiya ne. Ran da kuwa ya kuskura ya bi shawarar mata ko sau daya, ran nan fa shi kuma sai labari. Wannan, ma in an faďi ba a kwana, ni na kara shi." Da ya ji haka sai ya harare ni, ya ce, "Da ma don dan wannan sharadi ne ka ke cewa ba na iyawa? Me ka mai da ni ne?" Na ce, "Iyakarsa ke nan. Da ma batun mutuwan nan kadai na ke tsoro gare ka." Sai ya yi tsaki ya shiga gida ya dandaka maganin da hannunsa, ya kwaba, ya zuba ruwa cikin wata 'yar kwalaba. Kullum da dare sai karuwan nan ta zuba masa cikin kunne sa'ad da zai kwanta barci. In ta tambaye shi dalilin da ya sa ana yi masa haka, sai ya ce mata kunnensa ke ciwo, aka ba shi magani. A kwana a tashi, ran nan da ya farka barci, sai ya ji wani dan bera yã ce wa gudan, "Shin Damburuntu, me ya sa kyanwoyi ke cimmu ne? Su ba su da wani abinci sai mu? Da haka a ke zaman duniya, wanda ya fi wani karfi ya cinye shi, ai da yanzu ba kowa!" Damburuntu ya ce, "Haba, raina mu dai suka yi. Babban munafikin kuwa mai gidan nan. Shi ba Sarki ba, ba Waziri ba, har da ajiye kyanwoyi uku! Don Allah dubi yadda ya kwanta ya bude ciki, sai ka ce taiki!" Ojo murna ta cika shi, ya yi kamar zai yi dariya, sai ya kanne, don kada ya yi su gudu. Yana nan shiru, sai ya ji wancan na fari ya ce, "Damburuntu, kewaya can, ni in kewaya nan, mu ciji kunnuwansa, ko nan ma mu more.'" Da jin haka sai Ojo ya yi wuf ya tashi. Beraye suka watse. Ya bushe da dariya, yana godiya ga samun wann an babbar baiwa. 54 Yana nan kwance, ya kasa barci don murna, har aka yi kiran asalatu. Ya tashi matarsa ta kawo masa ruwan alwalla, ta ajiye ta tafi. Ya fito ya fara alwalla. Ya kusa gamawa, sai ga wani burtu nasa da ya ke kiwo ya nufi wajen wata kaza, ya ce "Ni dai, kaji, kuna ba ni mamaki wajen butulcin nan naku da cin amana." Kaza ta ce, "Me ka gani ne, ka ke tsinammu haka?" Burtu ya ce, "Dubi alherin da mutane ke yi muku. Da rana su ba ku hatsi da ruwa, ku sha a huce. Da dare su sa ku cikin daki su rufe, su yi ta saurare don kada muzuru ko maciji ko wani naman jeji ya je ya cuce ku. In kun haihu' su sa 'ya'yanku daki, su yi ta ba su abinci har su yi girma, don kada su fito tun suna kanana, shirwa ko shaho su raba ku da su. Hasali ma dai, zaune ku ke kawai, ba abin da kuka rasa. Amma kuwa ran da suka ce za su kama daya daga cikinku, duk ku gama gari da kuka, ku tashi ku fada bisa wannan shigifa, ku yi tsalle bisa wannan zaure. To, wannan ba butulci ba ne, mene ne? Hala irin godiyarku ke nan?" Kaza ta yi masa wata irin duba haka yakine, ta ce, "To, kai da ya ke ba butulu ba ne, gaya mini ta inda ka fi mu godiya ga mutane."" Burtu ya ce, "Ni a dawa Allah ya halicce ni, ba kamarki ba, amma duk da haka in mutane suka kama ni suka kawo gida, sai in dangana, ko da ya ke ban saba ba, in yi ta yi musu duk abubuwan da su ke so suna dariya. In sun kira ni, sai in taho. In na ga ubangidana sai in bi shi, in rika hawan buzunsa ina wasa. In ya jefa wani abu in bi in rida, don ya yi dariya. To, wannan ba rashin butulci ba ne, mene ne?" Kaza ta ce, "I, gaskiya ne, ya kamata kuwa ka yi alfahari bisa ga godiyan nan taka. Amma da ka taba ganin mutane sun kama 'yan'uwanka sun yanka, sun fige suna soyawa, yadda na ke ganin kullum suna yi wa dangina, da ran da suka tashi kama ka, bari ta gudu kana fadawa shigifu, in ka balle daga nan ka shiga daji, ko labarin inda ka ke ba a sake ji." Burtu ya yi shiru, ya rasa abin da zai ce wa kaza bisa wannan magana tata. Kaza ta harare shi, ta juya, ta ce, "In za ku yi magana, ku rika tsayawa tukun kuna lura, kuna auna ta tukun kafin ta fito bakinku har wadansu su ji. Ga irin abin da a ke gudu ke nan, mutum ya fadi maganar da bai san kanta ba, bai san gindinta ba, ta zo ta dame shi daga baya. Kai, Allah wadan zaman daji!" Da Ojo ya ji haka ya bushe da dariya, har ya haure ruwan alwallarsa bai sani ba. Da ya gama dariya, ya kare alwalla, ya shiga daki ya yi salla. Da ya gama, sai karuwan nan ta zo ta ce masa, "Maigida, yau ni marmarin shinkafa na ke ji, ita zan dafa, sai a sayo tozo." 55 Zai ce to, sai ya tuna da maganar aku, yana tsammani da ya yarda zai mutu, ga shi kuma ba ya son bata wa matar zuciya, sai ya tuna ba abin da ya fi ransa dadi. Ya san yanzu da ya mutu sai ta fita ta auri wani, shi ta manta da shi. Sai ya ce mata, "An ki, ni yau tuwon dawa za a yi mini, miyar shuwaka." Ta dube shi haka yatsine, ta watsar, ta yi tsaki, ta ce, "In wani ke min da hannun, ba sai ya sa in yi na dawa ba? Ni na shinkafa zan yi, in kama kazarka a yanka in ka ki sawo mini tozo. In ya so, in na yi, ko ka ci, ko kada ka ci, ni ba abin da ya dada ni da kasa." Sai ta tashi ta nufi wajen buhun shinkafa, za ta diba. Ojo ya ga in ya bar ta ta yi abin da ta ke'so, watau shi zai mutu ke nan. Sai ya tafi ya kama ta. Sai kokawa ta kaure kiki kiki. Ojo ya tuna shi namiji ne, ya dauke ta ya kantara da kasa, ya yi ta bugu. Da mutane suka ji kuwwarta tana cewa, "Wayyo Allah, na tuba! Ba na kara yi maka musu, ka ji kaina!" Sai suka rugo, aka zo, aka kwace ta da kyar. Ta yi yaji. Bayan kwana uku Ojo ya bi ta, aka yi rarrashin duniyan nan ta dawo, ta ce in ta koma gidan nan ya zama kabarinta. Ta tashi za ta yi masa halinsu na karuwai, ta tona masa asiri cikin jama'a ya ce ya sake ta. Abinka da mai sule, kafin kwana bakwai ya nemi 'yam mata uku 'yan gaske, aka ba shi. Da ya mila, sai ya ce a sà su lalle gaba daya. Aka sa su, aka yi biki, aka gama. Muka yi zamammu lafiya lau da matan nan nasa, ba sauran mai kuka da wani. Da aku ya kawo nan, ya ga gari bai waye ba, sai ya dubi Musa, ya ce, "Don Allah ka yi kokari ka yiwo abin da kowa zai yaba. Kа tabbata wata dabara taka, da wani tsoro, duk ba su hana makaа mutuwa, domin duk ran da ajali ya yi kira, ko babu ciwo a je. Gama Sarkin Yaki yana zaune lafiyarsa lau, amma ran da ajalinsa yà sauka, sai da ya sayo wa kansa halaka." Musa ya ce, "Ai Sarkin Yaki ya sami lafiya har ya tafi tare da Sarki." Aku ya ce, "Ba Sarkin Yakinku na nan gari na ke magana ba, ina zancen Sarkin Yakin Niraini ne." Musa ya ce, "Ina ne Niraini? Ban taba jih sunan wannan gari ba, balle Sarkin Yakinsu. Me ya sa ya saya wa kansa halaka?" Aku ya ce, "Yanzu kuwa ka ji." 56 In Ajali Ya Yi Kira, Ko Babu Ciwo A Je Wata shekara mutąnen kasar Suraida suka kai yaki kasar Niraini. Mutanen Suraida suka kori na Niraini suka kashe musu jama'a mai yawa. Suna murna za su shiga garin, ashe Sarkin Yakin Niraini ya shirya wadansu dakarai, suka biyo jama'ar Suraida suka yi musu zobe, suka hana su gaba, suka hana su baya. Da wani dakaren Suraida, wai shi Barde, ya ga za a halaka su nan tsaye da yunwa ma kadai, sai ya ce wa 'yan'uwansa, "Ya kamata mu yi kunar bakin wake. Kada mu mutu nan, mu bar wa na baya abin fadi." Suka yarda, suka tasam ma mutanen Niraini. Barde ya fara kaiwa, ya soki wani dan saurayi, ya mace. Mutanen Niraini suka kashe yawancin mutanen Suraida, aka kama Barde, har an fara sassare shi za a kashe, Sarkin Yaki ya ce a kyale shi. Ya sa aka dauke shi aka kai shi gidansa, ya yi ta jiyyarsa ba dare ba rana, kamar dansa. Kullum safe, da ya fara iya magana, sai ya zo ya tambaye shi yaya ya kara ji. Shi kuwa sai ya amsa masa, "Na gode Allah." Yana nan gidansa, ba ya iya tashi har wata guda, sa'an nan ya fara tashi da sanda yana doddogarawa. Sarkin Yaki na binsa, yana-tare shi kada jiri ya kwashe shi ya faďi. Bayan 'yan kwanaki, ya fara tafiya ba sanda. Ran nan yana tattakawa, ya dube shi, ya ce, "Yi tsalle mu gani, in ka iya." Barde ya yunkura kamar zai yi tsalle, sai ya ji ba ya iyawa. Ya dubi Sarkin Yaki, ya ce, "Baba, ai ba na iyawa sai dai an.kara kwana biyu." Bayan kamar kwana bakwai, da Sarkin Yaki ya ga lalle Barde ya warke, sai ya ce ya yi tsalle ya gani. Ya yunkura, ya yi tsalle, ya buga kafa, ya dube shi, ya durkusa ya ce, "Allah ya taimake ka yadda ka taimake ni." Sarkin Yaki ya ce, "Alhamdu lillahi, tun da ka warke!" Sai ya nufi cikin gida, ya dauko masu guda biyu, ya fito da su wajen Barde, ya ce, "Mu je bayan gari yawo, mu shawo iska." Barde ya се, "То." Ya karbi masu ya rike, har suka isa bayan gari. Da isarsu sai Sarkin Yaki ya ce masa, "Zabi daya." Barde ya ce, "Me za mu yi da su?" 57 Sarkin Yaki ya ce, "Kai dai zabi daya, na ce." Ya zabi guda gajere, ya mika masa dogon. Ko da ya karba, sąj ya ce masa ya tsaya nan, shi ya ja da baya kadan su yi yaki. Yaki ko na sosai, ba wasa ba, kowa ya sami dan'uwansa ya kashe. Da Barde ya ji haka, sai ya yar da nasa mashin, ya ja da baya, ya ce, "Subuhana lillahi, Allah ya sawwaka in yi yaki da kai!" Sarkin Yaki ya ce, "Ko kana kasa kana dabo, sai ka yi. Cikin yakin da muka yi da ku watan jiya ina da da, kai ka sa mashi ka tsire shi. Na neme ka kasa da bisa lokacin nan, na rasa, sai daga baya har an yi maka raunuka za a kashe, na gan ka, na ga in na kashe ka sa'an nan ban huce ba, don lokacin nan kusa da matacce ka ke. Saboda haka na ce a kyale ka, na jiyyace ka, sai yanzu da na ga ka warware, ka iya jin zafin da dana ya ji, na ke so in rama masa, ko da ya ke ba shi da rai. Yana kan kokarinsa ka kashe shi, saboda haka ni kuma na ke so in kashe ka bisa kokarinka, ba sa'ad da ka ke ba wąni makami a hannunka ba. Yanzu ko kana so, ko ba ka so, sai ka dauki mashin nan ka taso mini, sa'an nan ni ko in tsire ka." Barde ya yi tubar duniyan nan, ya ki ji, sai ya ce a ransa, "Da ma ni kusan cikin matattų na ke, shi ya kubutad da ni, to, tun da Allah ya nufa, don in kara shan ruwan wata guda ne kadai, aka nufe ni da tsira da fari, ai sai in yi godiya." Ya dauki mashi ya rike. Ko da Sarkin Yaki ya ga ya rika, sai ya zaburo zai tsire shi, yana tsaye yana Kalmar Shahada. Allah mai aikata abin da ya ke so, wallahi, yallabai, kafin ya kawo gare shi, sai kafarsa ta fada cikin wani ramin kurege, mashinsa ya kafe daga baya. Yunkurawan nan da ya ke yi da fushi, sai ya fadi da baya bisa 58 mashin. Nan take ya tsire kansa, bai ko motsa ba. Da Barde ya ga haka, sai ya rungume shi yana kuka. Ya sa hannu a kai, ya shiga gari ya gaya wa Sarki yadda duk aka yi. Aka zo aka iske shi, aka yi ta mamaki, aka rufe shi. To, tun daga ran nan Barde ya dauki alkawari yana kawo wa iyalin Sarkin Yaki abin da za su ci, har ya kan kawo musu awaki su sayar su sayi hatsi, duk dai wai saboda alherin da Sarkin Yaki ya yi masa. Musa ya ce, "Wallahi in ni ne ko kasa ba na bada musu, tun da ya ke ba da niyyar gari ya yi mini alherin ba." Aku ya ce, "Ai ba kai kadai ba, kowa ma ya ji wannan labari haka zai ce." Musa ya yunkura zai tashi, sai ya ji an yi asalatu, ba damar ya fita, kowa ya farka. Da azahar tayi, Waziri ya ga ba zai sami Musa ba, ta ya rude shi da Mahmudu na can na abin kirki, sai ya sake dabara ya rubuto takarda kamar daga Mahmudu, ya aiko tsohuwan nan ta kawo wa Musa. Da ya karanta sai ya ga an ce, "Daga Mahmudu zuwa ga dan'uwana Musa, rabin ransa. Gaisuwa mai yawa da so da yarda. Bayan haka, Musa, yanzu kana da rai har ka yarda aka raba mu ko? To, ga shi jiya na fada wani barde cikin mutanen Sinari, ya yi mini raunuka abin ba ko masaka tsinke. Ga alamar da na ke ji a jikina, ni da ganinka kuma sai Darassalam. Tun da har ka manta da ni, ba ka iya kokarin da za ka zo mu nemi juna gafara ba, to, shi ke nan, ba kome, ni na roke ka gafara. Mutuwa dai ai kowa ka gani za shi ne. Musa! Musa! Tuna zumunci, Musa! Haza wassalam." Da Musa ya karanta wannan takarda $ai hawaye. Tsohuwan nan kuma ta tsuguna ta yi ta yanka maså karya, wai a gidansu (a ke jiyyar Mahmudu). Wannam takardar wai shi ya ba ta hannunsa da nata. Musa duk ya dimauta, mutanen gida suka rasa kansa, suka rasa gindinsa. Da asubar fari, tun bayin nan ba su yi barci ba, sai ya kintsa, ya tafi wajen aku yana kuka, ya nuna masa takardan nan da tsohuwa ta kawo. Aku ya sa tabarau, ya karanta, sai shi kuma ya fashe da kukan karya, ko da ya ke ya 59 san takardar ba Mahmudu ya yiwo ta ba, makirci ne. Sai ya ce wa Musa, "Sai ka yi shiri ka tafi." Musa ya ce, "Ina fa ka ga taflya yanzu, ga bayi can ba su yi barci ba? Da ma abin da ya sa ka ga na zo tun da wuri haka, don in kawo maka takardan nan ne ka gani. In kuma kana da wani labari wanda zai dan faranta mini rai, ka gaya mini tun yanzu, ko na ji dan sanyi-sanyi a zuciya, kada in taho an jima in sun yi barci ka ce za ka tsai da ni, har in zo in makara." Aku ya ce, "Haba, ranka ya dade, in tsai da kai bayan na karanta wannan takarda, mahaukaci ne ni? Tun da dai ka ce kana son in gaya maka wani dan labari wanda zai sa bakin cikinka ya ragu, wannan shi ya fi kome sauki gare ni. Ga kujera nan, zauna, don tsayuwa ba ta da amfani." Musa ya haye kujera ya zauna zugudum. Aku ya yi kaki, ya tofad da yawu, ya fara: 60 Labarin Wadansu Abokai Su Uku Wata rana wadansu samari su uku, abokan juna suka tashi daga garinsu za su wani gari neman aure. Kowane ya yi wankin kayansa, suka yi ado, suka kama hanya. Suna cikin tafiya, sai karamin ya ce, "Ku ci gaba, na iske ku ni zan ratse. Suka wuce, shi kuwa ya ratse, ya rabu da hanya kadan sai ya tarad da wani dan akwati, barayi sun sato ya fadi. Ya duba gabas, ya duba yamma, bai ga kowa ba, ya duka ya dauki akwatin, ya ji da nauyi, ya nemo wani dutse ya fasa. Da fashewarsa sai ya ga kuďi ciki cunkus, sulalla. Ya durkusa, ya sa hannun rigarsa ya kunshe, ya fito da gudu ya bi 'yan'uwansa yana kira. Da suka ji kira, suka tsaya. Ya ce, "Albishirinku!" Suka ce, "Goro." Ya ce, "Kun ga abin da na tsinta." Kowane da ya kyalla ido ya ga kuďi, duk suka yi ta murna, suka koma gefen hanya suka kidaya, suka ga fam ashirin da hudu ne da sisi. Wanda ya tsinto kuďin na kirki ne, saboda haka ya ce, "Sai a raba, kowa ya sami fam takwas takwas, sisin nan kuwa mu sayi abinci da shi mu ci." Da babbansu ya ji haka sai ya сe, "To, madalla, mun gode, Allah ya bar mu tare! Amma abin da ya fi, sai ka tafi gari maza ka sawo mana tuwo da tsire da sisin nan namu. Mu kuwa mu ajiye kuďin, in ka dawo sa'an nan mu raba." Yaron da ya tsinci kudin ya tashi, ya nufi gari da gudu. Da bacewarsa sai babban ya ce, "Abin da ya fi sai mu yi dabara mu karbe kudin nan, mu raba mu biyu, watau fam goma sha biyu biyu ke nan." Daya abokinsa ya ce, "Lalle gaskiyarka. To, yaya za mu yi ke nan?" Babban ya ce, "Ina da dabara. Ga wani maharbi can, mu kirawo shi mu ce ya shiga kogon itacen nan, in an yi magana ya rika amsawa." Suka kira maharbi, suka gaya masa duk abin da su ke so ya yi musu, da abin da su ke so su karbe wa dan'uwansu, har suka ce sa ba shi lada. Da maharbi ya ji batun kudi haka ya yarda. Ya shiga 61 kogon ke nan sai yaron ya komo. Da hango shi, sai suka fara kuka. Ya ce, "Lafiya?" Suka ce, "Ina fa lafiya, itacen nan ya kwace kudi duka!" Yaron ya dubi itace, ya ce, "A'a karya ne, itace da ba ya magana ma, ina ya kai ga sata? Ku dai ku sake shawara." Daga nan sai mutumin da ke cikin itace ya ce, "Wace shawara za a sake? Ni na dauke. Kuma in kana tsammani kai ka fi 'yan'uwanka jaruntaka, to, zo karbi. Matsiyata 'ya'yan zamani, wadanda ko iyayensu ma ba su san girmansu ba, balle wani!" Ko da yaro ya ii haka sai ya garzaya, bai zame ba sai gidan Sarki. Ya gaya masa duk abin daya faru tun daga farko har karshe. Sarki ya ce, "An tasam ma munafunci. Yaya za a ce itaciya ta yi magana? Ina 'yan'uwanka?"" Yaro ya ce, "Suna can gindin itaciya." Waziri ya dubi Sarki, ya ce, "Ranka ya dade, ai sai ka sa ni in tafi in ji in gaskiya ne. Ka san ikon Allah ya fi da haka. Sarki ya ce, "To, sai ka tafi ka gani." Yaro ya shige gaba har gindin itaciyan nan, suka tarad da 'yan'uwansa can suna 'yan koke-koke kamar da gaske. Da ganin Waziri suka ce, "Alhamdu lillahi!" Suka faďi suka yi gaisuwa. Waziri ya dube su, ya ce, "Ku ne itaciya ta kwace muku kuďi?" Suka ce, "1, mu ne, ranka ya dade. Daga mun zauna nan gindinta muna kidayawa, sai muka ga guguwa ta tashi ta murtuke wurin, duk kura ta buce mu, muka rasa inda mu ke. Can an jima sai ta natsa, muka duba kudin da ke gabammu, suka ce dauke mu. Muka shiga tonon kasa, don muna tsammani kura ce ta rufe su, ba mu ga ko kwabo ba. Muka tashi za mu yi fada da juna, don kowa na tsammani dan'uwansa ne ya boye kudin, sa'ad da mu ke ta kammu yayin da guguwa ta buce mu. Da muka fara zage-zage, sai muka ji kamar daga sama an ce, "Kada ku zargi junanku, ni na dauki kuďin. In kuwa kuna jin wata-wata ne ku zo ku kwata. Muka duba babu kowa, sai dai magana mu ke ji na fitowa daga itaciyan nan." Da maharbin nan na cikin itace ya ji haka, sai ya nisa, ya се, "M, wannan dahir ne." Waziri ya dube su, ya ce, "A'a! Ai kuwa ashe da gaske ne." Itaciya ta ce, "Af, da kana tsammani karya ne? Sai ka zo ka kwatam musu."" Ko da Waziri ya ji haka sai ya rike baki, ya ce, "Ki yi mini gafara, ni ba ruwana, aiko ni aka yi." Nan da nan sai ya aika aka fada wa Sarki ya zo da kansa ya gani, domin an ce gani ya kori ji. Can an jima ya tinkaro duk da 62 mutanensa. Da isowarsa Waziri ya ce, "Ranka ya dade, ka ga 'yar itaciyar da a ke markabu kanta." Da maharbi ya ji haka sai ya ce, "Wai, wai, wai, ni ce 'yar itaciya! Kai ne wa tukun da ka ce mini 'yar itaciya? Har dan tsugunin nan naka ka isa zagina? Daga yau ba ka sake duban kamata ka ce mata 'yar itaciya ba!" Da jin haka fa, sai hantar Waziri ta kada, ya fadi ya yi sujada yana ta ahi, yana rokon gafara. Sarki ya tsaya tsayin daka, ya dubi kogon itaciyan nan, ya ga lalle mutum na iya shiga. Ya lura da gindinta kuma ya ga sawun mutum kamar ya hau ta, ya dubi takon nan ya ga dai bai yi daidai da na ko daya daga cikin samarin nan masu kudi ba. Ya tuna tun da ya ke bai taba jin ma wanda ya ji maganar aljannu haka a fili ba. Kai, karewa ma dai tun da Annabi ya kaura aka bar jin irin wannan al'amari. Ko da ya lura da haka sai ya hakikance makirci dai aka kulla, don a cuci yaron nan da ya tsinci kudi. Sai ya dubi Waziri da ke ahi, ya ce, "Kai, tashi! Kwaure ka ke wa sujada?" Ya juya wa itaciyar, ya ce, "Yanzu dai ko ki ba su kudinsu tun da girma da arziki, ko kuwa in sa a kone ki. Da mutum da aljani ni duk wanda ya tasam ma zalunci cikin kasata sai na ga iyakarsa!" Sai itaciyar ta ce, "Kai dai tsaya kan mutane. In ka fada aljannu sai kai a ga iyakarka." Sarki ya dubi mutanen da ke nan, ya ce, "Duk ku saro kirare." Suka ruga nan da nan suka cika gindin itaciyan nan da itatuwa da kirare. Ya ce, "A kawo ashana." Aka mika masa. Ya tasam ma itaciyar zai kunna mata wuta, duk kowa ya rike baki. Maharbi ya ga dai in ya kyale minti biyu, lalle zai halaka. Sai ya yi kara ya се, "Don Allah, ranka ya dade, kada ka sa wutan nan. Ni ba kowa ba ne, mutum ne. Bari in sauko don Allah!"" Nan da nan sai mutum ya tsirgo daga kogo, da kudin rike a hannunsa. Ya fadi ya gai da Sarki, ya tsuguna nan, ya fede masa biri har wutsiya. Sarki da mutanensa suka yi mamakin wannan al'amari. Mutane suka yi ta cewa, "Lalle Sarki shi ma aljani ne." Nan take Sarki ya sa aka yi wa yaran nan biyu azzalumai, da maharbi, bulala hamsin hamsin, ya sa aka kai su gidan kurkuku su yi wata shida shida, ran da za su fito kuma a kewaya da su gari, kowa ya gan su. Ya dauki kudin duka ya ba yaron abinsa. Yaro ya fadi ya yi gaisuwa, ya tashi ya koma gidansu. Sarki kuma ya koma gida. Kullum in an ta da tadi, in ya dubi Waziri, ya tuna da yadda ya yi goho da katon bujensa, sai ya yi ta dariya. Musa ya yi murmushi ya ce, "Ai ba Sarkin nan kadai ba, kowa 63 ya ji wannan labari ya yi dariya. Munafunci dai ba shi da amfani." Aku ya ce, "Ina ka san munafunci ba shi da amfani, tun da ba ka ji labarin Kado ba, da wadansu 'yam fashi guda uku?" Musa ya ce, "Har ya fi wannan daďi? Ban yi tsammani bа. То, yaya suka yi? Fada mini mu ji." Aku ya ce, "Wannan d'in me? Kasa kunne ka ji." 64 Munafuncin Dodo, Ya Kan Ci Mai Shi Wata rana wani bakauye wai shi Kado ya dauki gatarinsa, ya shiga daji zai yiwo itace. Dawan nan kuwa da 'yam fashi, mutanen dan kauyen nan duk sun san da su. Can bakauyen nan ya yi nisa cikin daji, sai ya hango wani abu tsibe yana daukar ido, ya matsa ya ga ko mene ne, sai ya tarad da sulalla ne tsibe. Ya waiwaya baya, ya waiwaya gaba, bai ga kowa ba. Sai ya duka, ya cika aljihun taguwarsa fal, ya saba gatarinsa, ya sheka da gudu ya nufi gida. Ya rabu da wajen da ya debi kudin nan ke nan, sai ya gamu da 'yam fashi su uku. Suka ce masa, "Kai, tsaya! Me ya koro ka?" Kado ya tirje yana kaduwa, yana tsammani kudin nan da ya debo nasu ne. Sai ya ce, "Iye! Ni? Na'am. Mutuwa ce na gani a fili, shi ya sa na ke gudu." 'Yam fashin nan suka yi dariya, suka ce, "Mutuwar da kanta ka gani, ko kuwa maciji dai?" Kado ya ce, "Iye! Ni wallahi mutuwar ce da kanta na gani a can tsibe, shi ya sa ban ko tsaya wurin ba, don kada a ce na gan ta, na sheko da gudu." Da 'yam fashi suka ga lalle ya tsorata da su, sai suka ce masa, "To, mu je, ka kai mu mu gan ta mu ma." Kado ya wuce gaba suna biye, har wajen da kudin nan su ke. Ya ce, "Ga ta! Na rantse da Allah kuwa ban diba ba, kada ku ce ko na ďiba ne." Yana boye-boyen aljihu yana tsammani ajiyarsu ce, shi ya sa ya kara rudewa haka. Da Allah ya sa ba su dubi aljihunsa ba sai suka ce, "To, tafi. In ka fadi kuwa, muna zuwa da dare mu yanka ka." Ko da Kado ya ji haka sai ya ranta cikin na kare, bai zame ba sai gida. Ya kai yana haki, kamar ransa zai fita. Ya boye kud insa, ya kama bakinsa ya tsuke. Da 'yam fashin nan suka ga ya wuce, sai suka yi ta mamakin kudin nan, suka ce, "Watakila wadansu barayi ne suka sato, da suka ga sun yi musu yawa suka zubad da sashi nan. Allah Sarki! " Bakauyen nan fa tsammani ya ke, namu ne. 65 Babbansu ya ce, "Kai, ai ko ya firgita. Yanzu fa ya dade da kaiwa gida." Sauran suka ce, "Haba, tuni. Sa'ad da ya garzayan nan, ai ko mota ba ta kamo shi." Suka bushe da dariya. Sai babban ya dauki sule guda ya ba karamin, ya ce, "Ruga maza kasuwa ka sawo mana abinci mu ci tukun, idanummu su bude, sa'an nan mu san yadda za mu yi kasafin wannan kudi." Karamin ya karba, ya sa riga kamar ba barawo ba, ya yi nadi, ya tafi kasuwa, ya nufi wajen mai tuwo, ya sayo, ya kuma biya mahauta, ya sayo musu tsire ya dora kan tuwon, ya dauko ya nufo daji. Yana kulle-kullen abin da zai aikata da kuďin nan, da nasa ne shi kaďai. Sai ya ga itacen tinya, ya ajiye kayansu, ya ce, "Alhamdu lillahi! Bari in debi ruwan tinya in zuba wa abincin nan, in kai musu. Ni kuwa ko sun ce in ci, sai in ce na ciwo daga kasuwa. Ka ga da sur ci duk sai su mace, ni kuwa in kwashe karfena, in shiga gari in yi ta kece raini." Ya karya tinya ya zuba. Shi kuma ashe kafin ya dawo 'yan'uwansa sun yi shawara da ya zo su kashe shi, su kwashe kudi, su raba su kadai. Suka ce ai haka abin ya fi auki. Can sai wannan karamin ya iso da kayan abinci. Ko da ajewarsa sai suka hau masa da bugu, bai san hawa ba, bai san sauka ba, suka kashe shi. Suka fada abinci da ci, in sun gama sa'an nan su kwashe kudi su san inda suka nufa. Da gama cinye abinci, sai kowanensu ya fara kaduwa, yana faduwa yana tashi, kafin kiftawa da bismilla duk suka kai takarda. Can bayan kamar kwana bakwai sai Kado ya ce a ransa, "Bari in koma wurin nan, in na tarar suna kwashe kudinsu in tsuguna in yi kala, ko Allah ya ba ni dan taro. In kuwa na tarad da su sai in ce na zo ne in gaya musu Sarki zai aiko da dogarai a kama su gobe, abin da ya fi kowa ya yi ta kansa. In ce kuma abin da ya sa na gaya musu don haka, sun ji kaina ne ran nan. Ka ga watakila ma sa ba ni dan sule. Kuďin dai ga su nan tsibe kamar ba su so, ba su da alamar karewa." Da isarsa wurin sai ya tarad da su duk sun mutu. Ya yi juyayin abin da ya kashe su, ya rasa. Da ya lura har kuraye sun ci su, sai ya yi zaton su ne suka kashe su. Ya rasa abin da zai yi don murna. Ya shimfida gwadonsa, ya kwasa. Ya yi 'yan kirare ya dora, don kada a gane, ya kai gida, ya gina rami ya binne. Magariba na yi kuma ya kira dansa, suka tafi suka kwashe saura. Ya zauna ya yi ta cin kudinsa sannu kan hankali, da shi da dansa, ba wanda ya gane. Musa ya bingire da dariya, ya ce, "Allah mai girma! In rabo ya rantse, sai mai shi!" 66 Ya Saurara haka sai ya ji kiran salla, ya ce wa aku, "Wancan kiran sallan fa, na fari ne, ko na biyu?" Aku ya ce, "Sai dai na fari. Amma bari mu ji." Sun yi shiru suna saurare, sai suka ji ladani ya ce, "Assalatu!" Musa ya ce, "Subuhana lillahi, ashe har gari ya waye ba mu sani ba!" Sai ya tashi fuu ya shiga cikin gida. Tun safiyan nan kar magariba bai sa ko loma bakinsa ba don bakin ciki. Ko da wata ya fadi, tun ba a ko yi kiran sallar asuba ba sai ga Musa ya shiryo. Ya zo ya ce wa aku, "Sai na dawo." Aku ya ce, "Ka dawo lafiya." Ya sake duban Musa, ya ce,"А! Kam ba Waziri ba, a dubi kakkarfan dan Sarki kamarka a ce za a hana shi zuwa yaki? Shin halin Waziri wane iri ne?" Musa ya ce, "Rabu da shi tsohon wofi! Ko da ya hana, ai ga shi yanzu za ni yana gani." Aku ya ce, "Tafi abinka, rabu da shi! Kome mutum ke aikatawa dai ai, kul ba jima, kul ba dade, ya ga sakayya. Da Allah ya sa ya ji labarin Hafaru da dansa, da ya rage wadansu abubuwa." Musa ya ce, "Wane labari ne na Hafaru da dansa? Gaya mini, ko ni ma in karu.'" Aku ya cе: 67 Abin Da Mutum YaShuka Shi Zai Girba, In Hairan Hairan, In Sharran Sharran Wata rana an yi wani mutum wanda ba shi da da, ba shi da jika. Ya yi maganin duniyan nan don ya sami da, Allah bai nufa ba, y gaji ya dangana. Ran nan yana zaune a kofar gidansa, sai ya ga wani ya kama dansa yana ta duka, ba ji ba gani, sai ya ce, "M, Allah mai girma! Dubi wani Allah ya ba shi har yana bugu, ni kuwa ga shi ina nema ruwa a jallo, Allah bai nufe ni da samu ba. In da ni Allah ya ba wannan, kome rashin jin kansa, me zai sa in buge shi? Da da ya yi jin kai, da kada ya yi, ai duk uwarsu daya, in ba dai don batan basirar mutane ba." A kwana a tashi, ran nan sai Allah ya ba matar mutumin nan ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji. Aka yi suna, aka sa wa yaron nan Hafaru. Yaron ya girma a sangarce, kome ya yi uban ba ya ce masa kanzil. Ta kai dai fagen yaron nan ba ya jin kan uban, balle ya taimake shi. Don son da uban nan ke yi wa dan har abinci ma tare su ke ci, har ya kai ga aure ba su raba kwarya da ubansa ba. Da ubansa ya fara tsufa sai Hafaru ya rika kyamar cin abinci da shi. In suna ci sai ya hana uban ya taba gabansa, yana cewa wai uban ya faye kazanta, duk yana-barin majina a hanci, wai kuma ga shi da yawan tari, yana zuba musu yawu a ciki. Uban dai bai ce masa kome ba. Ana nan dai har ya kai ga fagen yana ci hannu na rawa, na baka na fadowa cikin kwarya. Sai dan ya buga masa tsawa, ya janye kwanon abincin, ya ce sai ya ci kana ya ba uban. Suna nan haka, sai ran nan Hafaru ya ce wai uban ba ya sude kwarya, kullum sai ya bar kwano cakal, duk ya bata shi da yawu. Saboda haka sai ya samar wau uban akushi, aka rika zuba masa nasa abincin dabam. Ran nan yana ci garin makyarkyata sai ya tuntsurad da dan akushin, tuwon ya zuba. Hafaru ya zo ya yi ta yi masa fada, wai ya faye gidi-gidi. Saboda haka sai ya tafi kasuwa ya sawo kwami irin na ban ruwan shanu, ya kawo gida ya rika zuba wa uban abinci a ciki, ya ce, "Ture wannan kuma, mu gani!" 68 Uban dai bai ce kome ba, sai in abin ya dame shi ya yi ta kuka yana. cewa, "Wannan dai duk laifina ne da na ki kwabonsa tun yana karami. Amma ba kome, Allah ya ba da mai rama mini." A kwana a tashi, sai ran nan Allah ya ba matar Hafaru ciki, ta haifi da namiji, aka sa masa suna Ishiye. Da ya kai shekara hudu ya yi wayo, sai ya zama ba shi da wajen wasa sai tare da kakansa, ko abinci ma tare su ke ci. Uban ya yi ya yi ya hana shi cin abinci da kakan, yaro ya ki. Saboda yaron nan har aka rika sa wa abincin tsohon mai da nama. Kome yaron nan ma ya samo sai ya nufo kakansa. Ana nan har Ishiye ya kai shekara shida, ran nan suka tafi gona da uban, yana rike masa da goran ruwa. Da suka isa uban ya yi ta noma, har rana ta yi tsaka, sai ga matarsa, uwar yaron, ta kawo masa abinci, ya kakkabe hauyarsa, ya zo ya zauna yana ci, matar kuwa ta zauna kusa da shi. Sai yaron ya dauki wani dan guntun gatari da ke nan, ya shiga gona ya fara saran wata 'yar itaciya da ke ciki, kwas, kwas, kwas. Da uban ya hanga ya gan shi, sai ya се, "Kai me ka ke yi nan? Ajiye wannan abin banza, ka zo ka ci abinci. Haka ku ke yi har ku sare 'yar kafarku, ku bar mutane da jiyya." Da yaron nan ya ji haka, sai ya ce wa uban, 'Ci naka, ka bar mini nawa nan. Ni ina nan sai na sare itacen nan tukuna, ina so in gyara rassan ne in yi maka dan kwami da shi, in kai gida in ajiye, don in ka tsufa in rika zuba maka abinci a ciki!"" Da iyayen yaron nan suka ji haka, sai suka yi nadama, suka rike baki suka ce, "Ashe gaskiya ne abin da mutane ke fadi, kome ka shuka shi ka kan girba." Daga nan Hafaru bai sake dukawa noma ba, sai ya tashi, suka kwashi 'yan hauyoyinsu, suka iza keyar yaron nan har gida. Da isarsu gida Hafaru ya kama' hannun dansa har wajen kakan.a durkusa, ya gaya wa tsohon abin da yaro ya ce a gona, ya kuma sake durkusawa ya roki tsohonsa gafara, yana ahi da kuka bisa ga abubuwan da ya yi masa. Yaro na kallo, bai san abin da a ke yi ba. Tsohon nan ya ce, "Mhm. Ai duk abin nan da aka yi, ni na ja. Je ká, na gafarta maka duniya da lahira." Hafaru ya tashi yana murna. Daga ran nan bai sake, tozarta ubansa ba, har Allah ya nufa ya cika a hannunsa, suka rabu da alheri. Kullum in Hafaru ya ga dan nan nasa, in ya tuna da maganar da ya yi, sai ya rike baki ya ce, "Ya'yan zamani, saninku ba sanin halinku ba!" Da Musa ya ji aku ya kai karshen wannan labari, ya cе, "Wannan labari naka gargadi ne mai amfani ga wanda ya ji shi." Aku ya се, "Ва wannan kadai ba, duk labarin da na ke 69 bayarwa, in ka lura, ka ga haka ya ke. Ai ba muni ga mutum da ya fi ya kai muddin mutane bai iya bakinsa ba. Ga wani karamin misali nan na kunkuru da gauraki: 70 Fara Koyon Mulki Da Baki, Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu Wata rana wadansu gauraki guda biyu suka gane wani itacen baure a bakin wani rafi. Kullum suka tashi sai su nufi can su hau, su yi ta ci. Gindin bauren nan kuwa ashe akwai wani kunkuru. Kullum idan gaurakin na cin baure, wadansu 'ya'yan su kan kucce musu su fado kasa, Da kunkuru ya ga suna fado masa yana ci, sai ya yi tsammani gaurakin nan ke ba shi kyauta, don suna sonsa. Saboda haka, da ya ga alherin ya yi yawa, ran nan sai ya daga kansa ya dubi gauraki, ya ce, "Kai 'yan'uwana, na gode! Kullum dai na kan ga 'ya'yan bauren da ku ke sako mini. Abin naku ya yi yawa, wallahi har kunyar godiya na ke yi. Allah dai ya saka da alheri!" Da gauraki suka ji haka, suka duba suka gan shi, sai suka gane abin da ke aukuwa. Da har babbar za ta ce masa su ba a kan sonsu bauren ke zuwa gare shi ba, sai karamar ta hana ta. Ta dubi kunkuru ta ce, "Don mun ga kai ba ka iya hawowa, shi ya sa mu da Allah ya ba fiffike mu ke taimakonka. Don dan wannan abu kada ka sa wa kanka wani jin kunya ciki. Allah dai ya bar zumunci." Kunkuru ya ce, "Amin! Na ko yi godiya." Suka zauna kan haka. Da abu kamar wasa, har ya zama aminci na gaskiya. Gaurakin nan da sun zo da safe, ba abin da su ke fara yi sai sun tambayi kwanan kunkuru tukun. Suka zauna, ba su son abin da ya taba shi, shi kuma ba ya son abin da ya taba su. Ana nan, bayan kamar wata guda baure ya kare, gauraki suka koma neman kwadi da tana. Bayan kamar wata biyu kuma dan sauran ruwan rafin ya kafe. Wurin ya koma sai ka ce dadai duniya ruwa bai taba zama nan ba. Da gauraki suka ga haka, sai suka yi šhawarar su tashi su sake wuri, don ba su iya zama sai inda ke da danshi-danshi. Ran nan har za su wuce, sai karamar ta ce, "Ya kamata mu je mu sallami kunkuru, kada ya ga shiru hankalinsa ya tashi, ya yi zaton wani abu ne ya same mu." Suka tashi, suka tafi wajen kunkuru, suka gaya masa za su yi kaura. 71 Da kunkuru ya ji haka, sai ya ce, "Af, to, ai ba ku barina, sai mu tafi tare. Abin da ya yi Goje, ai shi ya yi Kaura. Ni ina na ke iya zama inda babu laima?" Da gauraki suka ji haka, sai suka ce, "Yaya za ka yi ka bi mu, alhali kuwa kai ba ka da fiffike?" Kunkuru ya ce, "Sai ku dauke ni, in kun ga kwa iya kokarin hakanan." Babbar gaurakar ta ce, "Wa ka ke zato cikimmu zai iya daukar kato kamarka? To, ce ma muna iyawa, ina za a kama, ga ka jiki duk kwarya?"" Karamar ta ce, "Bar shi, mu ji tasa, watakila yana da dabara, Kin san an ce mai rai ba ya rasa kokari." Kunkuru ya ce, "I, ina kuwa da wata 'yar gurguwar dabara, in kwa iya. Sai mu sami kara mai karfi kamar zira'i biyu, ni in cije tsakiyar, ku kuma kowace ta kama gefe guda dá baki. Kun ga da haka sai ku tashi da ni har inda za ku." Babbar ta ce, "Wannan dabarar ban ga za ta yiwu ba ga kamarka, mai surutu." Karamar ta ce, "A'a, in ya ce dai ya iya kyalewa, ai sai mu 72 daúke shi." Ta tashi, ta tafi ta samo karan dawa mai karfi, ta dauko, ta zo ta ajiye gaban kunkuru. Ta dube shi, ta ce, "To, don Allah in ka kama, ban da yawan magana." Kunkuru ya ce, "Haba, wannan ma sai an dankwafe ni kansa, sai ka ce yaro? in yi surutu mana, in ina so!" Gauraki suka ce, "To, madalla!" Suka kama kara suka tashi da kunkuru yana cije. Suna cikin tafiya, sai hanya ta daukè su ta bisan kasuwa. Suna kaiwa tsakiyar, sai mutane suka daga kai suka hange su, suka ce "Eho, eho, ku zo ku ga inda gauraki ke daukar kunkuru! Kai jama'a, abin mamaki ba ya karewa nan duniya!" Da kunkuru ya ji haka, sai ya fusata ya ce, "Kai, Allah ya tsine idandunan nan naku mutane, da ba su iya ganin abu su kyale." Bai gama fadin abin da ya ke nufi ba, sai da ya kawo ķasa kum. Duk da karfin kokon san nan, ya haure, bai ko motsa ba. Gauraki suka wuce abinsu suna bakin ciki, suna cewa "Wanda duk bai iya mulki da bakinsa ba, lalle yana tare da halaka." Musa ya saurara haka, sai ya ji wani daga cikin bayin nan na ta da 'yan'uwansa, gari ya waye. Ya bata fuska. Aku ya ce, "Ai ko yau ba ka yi zaman banza ba, don na yi maka gargaďi." Musa ya çe, "Gargado!" Aku ya shiga shashatad da shi, har ya 'ciwo kansa. Suka yini nan suna 'yan tade-tade. Da rana ta fadi, lokacin fitar Musa ta yi, sai ya taho ya ce wa aku, "Yau, don Allah ba ka kyale ni in wuce baki alaikum?" Aku ya ce, "Sai ka dawo." Musa ya ce, "Kai, yau wace rana ka kyale ni ba ka yi min wani surutu ba!" Ya sa mabudi ya bude zaure na farko ya taka zai shiga ya buda na biyu, aku ya biyo shi, ya ce "Yanzu wani babban abu ya fado mini a rai. Kwanaki na bä ka maganin karfe, na manta ban ba ka kau da bara ba. Ko kuwa ba ka so ka iya gociya?" Musa ya ce, "Ban iya gociya ba, in kau da baran na kusa ka kawo mini. Ba wanda ya ki taimako." Aku ya ce, "Wani kauci ne nan kusa, bari in fita in kawo maka." Ya fita fir ta taga. Musa ya ce, "In kana wa Allah, ka yi sauri!" Aku ya ce, "Shi babba." Ya tafi ya sami wani lambu, ya yi ta satar baure yana ci. Da ya koshi, ya ga kamar asalatu ta yi, ashe farin wata ne, ya debo ganyen bauren ya taho, ya ce wa Musa, 73 "Ga shi, ka sami saki ka dfinke shi da shi, ka gama cikin damarunka, ko ana ruwan kibau, ka tabbata ba dayar da za ta same ka. Amma da sharadi guda, ya kamata ka koyi gociya, domin kau da bara duk ba ta ci sai ana gamawa da 'yan zukezuke." Musa ya ce, "To, madalla." Ya bude zaure na biyu, aku ya dubi gabas yà gani ko asalatu ya yi, ya ga ashe bai yi ba, farin wata ne ya rudo shi ya dawo da wuri. Sai ya tashi da 'yan tsalletsalle yana bin Musa, ya tarad da shi har ya bude zaure na uku, ya ce, "Bari in gaya maka wani labari mai daďi. Wata rana akwai دو wadansu 'yam makaranta Musa ya ce, "Kai, tafi ka ba ni wuri! Ni na gaji da labarun nan naka." Ya bude zaure na hudu. Aku ya yi tsalle ya bi shi, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni dai wallahi kana kayatad da ni, tun da ba ka wuce maganar iyayenka ba. Dubi abin da Sarki ya gargade ka da ni, ka ga har Allah ya kawo mu rana wa ta jiya kana nan rike da abin nan da ya се." Musa ya waiwayo ya ce, "Rana wa ta jiya kadai, ranar yau fa?" Aku ya ce, "Ai kullum kana rike, da ma dai ai-." 74 Babban Mugun Abu Gun Da, Ya Yi Fushi Da Iyayensa Ina tsammani ban taba gaya maka ba, wata rana aka yi wa wadansu 'yam makaranta jarrabawa. Daga cikinsu akwai dan limamin garin, ana kiransa Ilu. Ba ya kula da aiki ko kaďan. Kullum in ana koya musu aiki, shi sai ya yi ta wasa. Saboda haka da aka yi jarrabawan nan bai ci kome ba. Sai ya sami sifiri. Malaminsa ya yi fushi kwarai da ya ga haka, ga yaro dam manyan mutane ya lalace. Saboda haka ya je ya gaya wa liman abin da dansa ke ciki, don kada nan gaba a kore shi, uban ya bata rai. Da aka gaya wa uban, sai ya kira shi wai ya yi masa fada ya kara kokari. Ya zazzage shi yana cewa in bai yi kokari ya yi karatu ba, ba shi da wani amfani, sai fa ya je ya yi tallan tsire. Yaro ya tashi yana ta hushi, wai uban ya ce in bai yi kokari ba, zai ba da shi ga mahauta ya je ya yi tallan tsire. Ya koma karamin zauren gidan, ya zauna. Yana nan yana ciccika, lokacin cin abinci ya yi, kanensa Ibrahim ya zo ya kira shi su je su ci. Sai Ilu ya dube shi da hushi, ya ce, "Je ka, ci! Ni ban ci." Ibrahim ya bushe da dariya, ya ce, "Kana tsammani wani ya kula don ba ka ci abinci ba? Je ka, huta." Ya tafi ya gaya wa iyayen. Liman ya ce, "Fushi ya ke yi, don na yi masa fada? To, kyale shi! Don cikinsa." Matar ta ce, "Ya da ta ki auren Sarkin Noma ba?" Ko da ya ke uwar ta ce haka, duk da wannan hankalinta na Wajen Ilu. Та kaikaici idon liman, ta tafi wajensa tana rarrashi, ya ki cin abinci. Ta yi ta yi, sai ya dube ta, ya ce, "Ina ruwanku da ni, ni da kuka ce ba ni da amfani sai ga masu tsire? Ina kokarina, don malam ya ki jinina ya zo ya ce ba na kokari. Na ko san duk ajin nan ba a samun yaro goma gabana." Sai uwar ta tashi, ta ce, "Bari mu je mu ajiye maka." "Me za ku ajiye mini? Ni ko kun ajiye, ba na ci. Me za ku yi da mai tallan tsire?" Da liman ya duba, bai ga matar ba, sai ya yi tsammani tana 75 wurin Ilu ne, saboda haka ya sa baki ya kira Ilu, ya ce, "taso ka ci abinci, kada ka yi sakarci." Ilu ya ce, "Ba sakarci na ke yi ba, karatu na ke yi. Kuma ni mai tallan tsire, yaya zan ci abinci da ku?" Liman ya ce, "Ho lalatacce, d'an banza, mai taurin kai! Allah wadan yaron zamani!" Ilu ya ce, "Na kuma zama dan banza, lalatacce, bayan da fari ga ni bawan mahauta?" Ibrahim ya dubi uban, ya ce, "Ya yi fushi ne, baba." Ashe Ilu ya ji, sai ya ce, "Kai kuma me ya sa bakinka ciki? Cin danko har da kaza?" Sai kuma fushi ya koma kan Ibrahim, ka san da ma an ce zomo ba ya fushi da makashinsa sai maratayi. Ya ce, "Wa ya tambaye shi ma ne, da ya sa bakinsa? Ka san Ibrahim ya raina ni." Sai ya tashi, ya shiga dakinsu na kwana. Da zuwa sai ya tarad da wandon Ibrahim bisa gadonsa, sai ya jeho shi waje, ya ce, "Raini ke nan ya sa kazamin wandonsa bisa gadona, ya sa mini kyaya." Ya haye gadonsa ya kwanta, yunwa kuwa ta fara dafa shi. Yana nan kwance, wai don ya fito sai Ibrahim ya zo ya ce masa, "Ka yi bako." Ilu ya harare shi, ya ce, "Fita, ba ni wuri!" Ibrahim ya yi murmushi, ya ce, "Abokinka ne ya zo." Ilu ya ce, "Na gaya maka ka tafi ka ba ni wuri tun da girma, ko?" Ibrahim ya wuce, yana cewa, "Na san dai yunwa ta sa ka wannan hushi, ba kome ba." Ashe fa gaskiyar Ibrahim. Ilu ya tashi ya rasa inda zai sa kansa don yunwa. Ya yi shawara ya koma ya ce a ba shi abincin da aka ajiye masa, ya ga in ya yi karaya haka a yi masa dariya. Saboda haka ya jure dai. Can zuwa la'asar ya ji abin ba dama, sai ya dauki wandonsa, ya sulale zai kai kasuwa, sai ya ji motsin ubansa a zaure. Ya ga in ya gane zai ba shi kashi. Saboda haka ya komo ya kurda ta kofar damfami, ya fita. Ya nufi kasuwa wajen 'yan tsumma. Ya tarad da wani mai dinkin mashimfidi, ya ce masa "Kana sayen wandona?" Madinki ya karba ya duba, ya ce, "Kai, karbi abinka" kyallen ai namuzu ne. Tir! Ko Ingila ba sayenka a ke ba, sai Turawa su watsar sadaka. Amma to, nawa za ka sayar mini don in rika kara wa jakina wajen laheru?" Ilu ya ce, "Nawa za ka biya?" Madinki ya ce, "Kwabo hudu. Ko ma na zura jiki ne?" Ilu ya ce, "An ce in bai yi kwabo takwas ba, kada in bari." Madinki ya bude baki kamar zai yi hamma, ya mika wa Ilu 76 wando, ya ce, "Lalle in ka kewaya a sami mai sayensa sule ma. Duba shi, ai sabo ne." Ilu ya lura ba'a ya ke yi masa, sai ya mika masa wando, ya ce, "Kawo kuďi." Aka mika masa awalaja, ya runtse a hannu, ya shiga kasuwa neman abin da zai ci, Magariba ta kusa, kowa ya watse, bai sami kome ba. Sai ya nufi tukubar tsire ya tsuguna, ya sa aka zare masa wajiya ta kwabo huďu, ya ci ya ci har ya koshi. Ya nemi ruwa ya sha. Ya tasam ma gida yana cewa, "Tun da aka zazzage ni, sai na sayad da kayana duka na ci abinci. Ba na sake cin abincinsu sai sun zo sun rarrashe ni." Yana zuwa gida, sai ya tarad da fura mai zuma uwar ta kai masa dakinsa. Ya bude, ya duba, ya diba kadan da ludayi ya kurba, sai ya ji ta coin. Ya ce, "Yau ga ni ina son furan nan, amma in na sha lalle a yi mini dariya." Amma bari in kurba luddayi uku, na san dai ba a ganewa. Ya tsuguna ya sha. Ya gama ke nan, sai ga kanen ya shigo, ya ce, "Ina ka tafi, ga Inna ta ce in kawo maka fura?"" Ilu ya ce, "Ina ruwanka da in da na tafi? Me ka ba ni ajiya? Dauki furarku, ba na sha. Ni sakarai, dan banza, me ruwanku da ni? In je in mutu mana." Ibrahim ya fita ke nan da fura, sai wajiya ta yi ta taso wa Ilu, sai amaí. Nan da nan ciki ya murde shi, ya yi ta murde-murde bisa gado yana kugi, Da uwar ta ji, ta kira Ibrahim suka rugo su ga ko mene ne. Suka tarad da shi sai amai ya ke yi, duk idanduna sun jujjuye, suka tambaye shi abin da ya ci. Yà če, "Na-na-nama." Nan da nan uban ya се a пеmo tsamiya. Uwar ta ruga. Ilu sai kuka ya ke yi yana murde-murde, ya kasa kwance ya kasa tsaye. Nan da nan uwar ta kawo, aka jika, aka dura masa ya sha. Sai ya barke da zawo. Kafin lisha ya sami sauki. Gari na wayewa ya warke sarai. Sai ya tafi wajen iyayen, ya roke su gafara, ya сe daga yau ba ya sake yi musu musu. Aikin makaranta kuwa, su saurari abin da zai faru in an sake yi musu jarrabawa. Daga ran nan ya koma dan kirki, duk ajinsu aka rasa kamarsa. In ka ki jin horon iyayenka, ka ji na Mahaliccinka. Musa ýa duba, ya ga har rana ta kunno, sai ya ce wa aku, "Ка ga dai da zan yi tafiya, ka tsai da ni a wofi, ga shi ka sa na makara." Ya koma ciki da hushi. Duk yinin nan ya hana a kawo wa aku wani abinci sabo. רר Da rana ta fadi, asuba ta yi, aku ya kura ido hanyar da Musa ke fitowa. Ko da ya hango shi tafe da takobi tsirara, sai ya ce, "Daukan ni mu tafi tare." Musa ya harare shi, ya ce, "Ka yi mini amfanin me wurin yaki, dan tsurut da kai haka? An ce maka labari a ke so?"" Aku ya ce, "Ko ba don labari ba, dabara aì ita ce yaki, ba karfi ba. Ina zaton ba ka taba jin labarin yadda bunsuru ya yi dabara har ya kori kura ya gaje gidanta ba ne?" 78 Banza Girman Mahaukaci, Karamin Mai Wayo Ya Fi Shi A cikin wani daji akwai wata kura wadda ke da gidanta mai kyau kwarai da gaske a wani kogo, ta kawata shi da kyau, babu abin da babu a ciki. Sai kuran nan ta sami wani biri, ta sa shi ya rika tsaron gidan nan kullum in ba ta nan, don kada wani abu ya fasa in ba kowa, ko kuwa a zo a yi mata sata. Kullum birin nan ba ya rabuwa da gidan. Ran nan yana zaune sai wani bunsuru da mata tasa da 'ya'yansu uku suka fado nan gidan. Dalilin zuwansu kuwa, kiwo suka tafi har dare ya yi musu, suka rasa hanyar komawa gari, suna kuwa tsoron kada su gamu da zaki ko kura. Da biri ya gan su, sai ya ce, "Kai daga ina? Su wane ne ku? Nan fa gidan kura ne, ku rufa wa kanku asiri ku koma, in ba haka ba kuwa, in je yanzu in gaya mata ta zo ta hau doronku dai dai." Akuya ta dubi bunsuru, ta ce, "Maigida, yau fa abin da mu ke gudu ya auku, mun kawo kammu ga halaka. Da ma mun sani mu dangana da ciyawar da ubangijimmu ya ke zuba mana kullum dare! Ga shi kwadayin son danya ya sa mun kawo kammu a mahalaka." Biri ya dubi bunsuru, ya ce, "Ni fa na gaya muku ku gudu, in ba haka ba, yanzu in tafi in gaya mata." Bunsuru ya harari biri, ya ce, "Mutumin banza, wannan gidan tun daga kakan kakana, Sarkin Masu, na gaje shi. Ba wanda zai kwace shi daga gare ni duk fadin duniyan nan. Je ka, gaya mata mana, ina nan ina jiranta." Biri ya zabura, ya tafi wurin kura. Bayan ya tafi akuya ta ce wa bunsuru, "Mu yi ta kammu, kafin kura ta zo!" Bunsuru ya ce, "Ke ar, mara hankali! Ai yanzu idan muka nuna alamar mun ji tsoro mun kade, ba mu da wurin tsira ko mun gudu. Idan mun ga kura tafe, sai ki ce wa 'ya'yammu su yi kuka gaba daya, in na tambaye ki dalilin kukansu, ki ce suna jin yunwa ne, wai suna son naman kura su ci, ba su cin na jiya, ya rube." Akuya ta amsa ta ce, "To, amma dai ni ban sa wannan za ta fid da mu bа." 79 Da biri ya isa wajen kura ya ce mata, "Ga wani abu nan da iyalinsa, ya zo ya ce wai gidan nan ba naki ba ne, wai na kakan kakansa ne, Sarkin Masu. Na ce ya gudu, kada ki zo ki cinye su. Ya ce ke din me? Ba irin zagin da bai yi miki ba." Kura ta ce, "Ka san shi?" Biri ya ce, "A'a. Amma barewa ta ce wai bunsuru ne." Kura ta ce, "Ko da ban gan shi ba, lalle ba bunsuru ba ne. Bunsuru ba yadda zai yi wannan aiki. Yaya kamarsa ta ke? Ya kai girmana?" Biri ya ce, "Ko kusa, ni ma kadan ya fi ni. Wani irin launi gare shi ja ja, da gasusuwa zaro-zaro, da 'yan kofatai kamar na barewa." Kura ta ce, "In ka tabbata bai fi ni karfi ba, mu je mu gan su. Shin su nawa ne?" Biri ya ce, "Har da 'ya'yansu su biyar ne.duka." Kura ta ce, "Nawa? Biyar! Ko ba su da karfi fa akwai yawa. Sarkin Yawa kuwa ya fi Sarkin Karfi!" Biri ya ce, "Ai duk kanana ne, babban ma da tsawon kafa kadai ya fi ni. Kuma a nan duniya ai babu naman dajin da ya fi ki karfi, in ba zaki da giwa ba." Kura ta ce, "Kai, yi mini shiru! Namun dajin da suka fi ni karfi nan duniya wa ya san iyakarsu? Kai dai mu tafi mu gani, in da riba mu fafata, in kuwa babu mu yi ta kammu." Ko da bunsuru ya hango su sai ya ce wa matarsa, "Tura 'ya'yanki cikin kogo, in sun shige kuma su yi ta kuka baki daya." Da suka shige duk suka barke da kuka baki daya, Ba-a-a-a-a-aa-a! Bunsuru ya ce, "Kai, me ya sami yaran nan?" Akuya ta ce, "Wai sun ce duk cikin naman da ke gidan nan ba su cin naman kowa sai na kura kadai, wai ya fi dadi." Bunsuru уa се, "То, a ba su sauran na kuran nan da na kashe jiya mana su karasa." Akuya ta ce, "Na ba su, sun ce ba su cin naman da ya fara bashi, wai sai sabo su ke so." Bunsuru уa сe, "Tоo, su hakura kadan su bar motsi, don na ji biri ya ce wai kura yau tana tafe, za mu yi fada, in Allah ya kawo mana ita ai kin ga yau sa wadata in dai don nama ne, don na ji an ce ta yi mai kwarai." Kura ta dubi biri, ta ce, "Ka ji ko, gaskiyata ce da na ce lalle abin nan ya fi ni karfi, ka ji jiya ma sai da ya kashe wani kura. Na san lalle bunsuru ba ya iya daurewa ya yi mini haka ba, ko daji ma ba ya yarda ya fito ba, wanda kullum yana can boye cikin gari. Ni zan koma tun bai rigaya ya gan ni ba!" Biri ya ce, "Kada ki lura da zancensa, fankama kawai ya ke yi 80 miki da karairayi, na gan shi dan karamin abu ne, kuma da ganin tafiyarsa ka ga raggo. Da kura ta ji haka zuciyarta ta yi dan karfi, ta ce, "To, mu tafi." Ko da bunsuru ya hango ta, sai ya tura 'ya'yansa a cikin kogon kura, suka soma kuka gaba daya. Ya ce wa akuya, "Don Allah gaya musu su yi shiru, biri ya yi mini alwashin zai yi dabara ya kawo mini kura har nan gidana, in sun yi hayaniya yaya za ta yarda ta iso, balle mu samu mu kashe ta mu sami abin kalacin? Kun gani fa yau saboda ita ba mu yi tanajin kome ba, a gare ta muka dogara." Da kura ta ji haka sai ta kama biri, ta ce, "Ashe da munafunci aka kulla da kai, don ka sa a kashe ni a banza? To, Allah ya tona asirinka, dan banza!" Zai yi magana ta sa kafa ta taka shi, ta kashe. Ita kuwa ta yi baya da gudu tana zawo. Da bunsuru ya ga sun sami sa'a haka sai suka kwashe duk kayan da ke gidan suka kama hanya suka koma gari gidansu. Aku ya dubi Musa, ya ce, "To, mu tafi, kyaun dan halas duk abin da ya yi niyya ya cika. Abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa, in ka ji ai sai ka yi kurum." Musa ya ce, "Me ke faruwa ga mai saba alkawari? Don mutum ya yi niyyar abu, ya koma ya fasa, sai wani abu ya same shi?" Aku ya ce, "Babban mugun abu kuwa zai same shi." 81 Labarin Sarkin Busa Abin da ya sa na ce haka, a wani gari can ketaren Bahar Maliya a cikin kasar Jamus, tun shekaru da yawa da suka wuce, Allah ya saukar musu da wani babbar bala'i. Aka saukar musu da beraye ko'ina cikin garin. Berayen nan suka yi ta karuwa, har mutane suka rasa abin da su ke ciki, duk inda mutum-ya duba garin ba ya ganin kome sai beraye. Ko wajen barci mutum in ya zo sai ya tarad da kamar ashirin tuku-tuku suna kwance. In hula ka ajiye, ko riga, kafin da safe sai ka tarar aljihun cike da beraye. In takaice maka labari, yawansu ba su kidayuwa. In da za ka kidaya su, ka kidaya kudajen da ke garin, sai ka ga sun fi yawan kudajen nan kamar sau dari. Gari dai ba wajen sa kafa, duk beraye ne. Abinci kuwa mutum ko ya fi Aula dabara, ba yadda zai yi ya ajiye shi. Kome za a dafa sai a yi daidai da yadda za a iya cinyewa, don ko cikin akwati ka sa abinci ka kulle, sa san yadda za su yi wa akwatin nan huda, su shiga su cinye. Duk wani abu da ka sani ana yi da fata sun cinye. Ba ka ganin mai takalmi, ko matashin kai, ko gafaka, ko buzu a garin. In ko sun kai ga abin da ba su ci, sai su yi masa hudoji, su bata shi. Ta ishe ka ma ko jariri suka tarar yana barci, sai su tasam masa da cizo za su cinye. Sai in ya yi kuka iyayen su kwace shi. In dare ya yi kuma su kan hana mutane barci da kuka da gujeguje. In sun ga jikin mutum waje, sai su kama da cizo, wai za su cinye shi. To, kada ka zargi mutanen garin, ka ga kamar sakarci ya hana su kashe su. Bala'i sai sa'ad da Mai abu ya sawwake abinsa. Da sun ga kare sai su tasam masa, su nuna masa Sarkin Yawa ya fi Sarkin Karfi. Don kyanwa kuwa, wannan karamar alhaki, ba su kula da ita ba. Abin mamaki, mutane kuma in sun tasam ma kashe su, sai ka ga kamar kara su su ke yi. Don a sa tarko kuwa, ko a sa dafi cikin abinci a ajiye, duk wannan ba ya rudinsu. Da sun gani sai su kewaye, kamar gaya musu a ke yi. Duk mutanen gari suka rasa yadda za su yi, sai suka tasam ma mai garin, suna cewa shi ne ke da gashin tsiya, don tun da aka 82 halicci duniya ba su taba jin irin wannan ba, sai cikin wannan zamani da ya ke sarauta. Suka ce ko dai ya san yadda zai yi da berayen nan, ko kuwa su fitad da shi, su kore shi daga kasar. Sarkin ya rasa inda zai sa kansa. Mutanen gari kuwa sai kara matsa masa lamba su ke yi. Ran nan yana zaune zugum, wadannan dattijai su zö su zazzage shi su wuce, wadannan su zo su zunzungure shí su wuce. Sai ga wani dan tsoho bako ya zo, ya duka ya gai da Sarki. Sarki ya dube shi, ya gan shi wani iri, sai ya ce, "Malam, daga ina? Wace sana'a ka ke yi?" Tsoho ya ce, "Ga ni dai. Inda na fito da nisa, amma sana'ata busa, har mutane na kirana Sarkin Busa." Sarki ya ce, "To, sai ka je ka sauka, in kana iya sauka nan, mu ba ta busa mu ke yi ba yanzu, ta kawunammu mu ke yi da wannan bala'i." Sarkin Busa ya ce, "Ai ni ma ba busar banza na ke yi ba, wani asiri Allah ya ba ni wanda in na yi busa duk ko wane abu mai rai ya biyo ni. Da kwadi, da macizai, da beraye, da dukan naman ruwa da na tudu, da tsuntsaye, har da masu tafiya da kafa biyu, duk wanda ya ji na yi busa, ba sauran zama, sai ya yi ta bi na. Don wadannan 'yan berayen da suka dame ku, in ka iya ba ni abin da na ce, yanzu sai in raba ku da su." Sarkin ya ce, "Don Allah ka taimake mu! Kome ka ke so nan duniya na ba ka. Tambayi, mu ji." Sarkin Busa ya ce, "Ka ba ni sule dari, in na raba ku da su?" Sarkin ya dube shi, ya ce, "Yau ga abin mamaki, mene ne sule dari kuma! Sule dubu goma ma, in kana so sai in ba ka. Kai dai mu rabu da wannan bala'i." Sarkin Busa ya ce, To, madalla." Ya sa wata irin mabusa bakinsa, ya yi ta-busa, yana yawo cikin gari rariya rariya. Sai berayen nan suka yi ta fitowa ko ta ina, suna binsa tururururu, wadansu manya, wadansu kanana, wadansu tultul, wadansu kyamas-kyamas. Ga wadansu ja wur, wadansu fari fat, abin har da shudda da rawaya. Ka ga wadansu ruku-ruku da ciki wadansu kuwa ga 'ya'ya kanana ke biye da su. Sai tsalle-tsalle su ke yi, suna 'yan kuka tsui tsui, kamar suna fara'a da wata bushara. Da ya kwashe duk, sai ya nufi kogi yana busa, suna biye, mutane na kallo na murna. Da isarsa bakin kogi sai ya fada cikin ruwa yana busa, beraye kuma ba su san sa'ad da suka bi shi ba, duk suka mutu cikin ruwa, sai daya kadai ya tsere. Mutane suka yi ta yi wa juna barka. A tsaya ma a fadi farin cikin da mutanen garin nan su ke yi da rabuwa. da wannan bala'i, ya zama kauyanci. 83 Da Sarki ya hangi Sarkin Busa na dawowa, sai ya ce wa mutane kowa ya koma gidansa, su kwaba kasa su lillike ramummukan da berayen nan süka giggina. Da Sarkin Busa ya iso, Sarki ya yi masa godiya kwarai. Sarkin Busa ya ce, "To, madalla, sai ka cika alkawarinka ko? Allah ya ba ka nasara." Sarki ya bata fuska, ya ce a ransa, "To; yanzu in na ba shi sule dai dai har dari, to, ni yaushe zan tara kudi in ina haka? Beraye dai ne ganin idon kowa sun mace, ba su ko komowa. In ma ba zarinsa ba dan tsoho da shi tukuf haka, me zai yi da sule dari?" Ya dubi Sarkin Busa, ya ce, "Ai da wasa na ke yi maka da na ce zan ba ka sule dari. Ashe kai ba ka san wasa ba? Ga dai sule sha biyar sun ishe ka. Me za ka yi da kudi da yawa ga shi ka tsufa?". Sarkin Busa ya harari Sarki, ya ce, "Zancen banza. Kai din ba ka tsufa ba da ka ke alkawari ba ka cikawa? Yi maza ka ba ni in kana ba ni, in ci gaba. Ba a kanku na fara ba!" Sarki ya ce, "In ba rashin hankalinka ba, yanzu yanzu da isowarka har ka yi aikin sule dari? Ko sha biyar din da na ce ai don dad'in girmana ne. In an bi kididdiga ne, ni ke uku da sisi ba ka ci ba. Dubi fa tun da safe har la'asar mutum ke aiki a ba shi sisi, balle kai yanzu yanzu!". Sarkin Busa ya ce, "In fa ba ka ba ni abin da ka yi alkawari ba, yanzu na sake mabusa, ka ga kuma abin da zai faru." Sarki ya yi fushi, ya ce, "Sake mana! Mu-ze a ci da burga, sai ka ce ba mutanen birni ba? Wanda ya mutu ban da Allah wa ke iya rayad da shi?" &4 Sarkin Busa ya ce, "Ko ni ban ce ina iyawa ba, amma ka ga abin da zai faru." Sai ya dauko wata mabusa ya fara busa, ya shiga gari titi titi yana busawa. Sai yaran gari duk mai iya tafiya, tun daga mai shekara uku har goma, suka yi ta fitowa suna binsa da gudu, suna tafa hannu suna rawa. Wani yaro mai dan dama daga cikin 'ya'yan Sarki ya rika ba da waka, saura na amsawa baki daya. In ya fadi ta farko, su kuma su fadi ta biyu, suna cewa: Ku zo ga daula wa zai ki, Alo alo, mu ci daďi! Kowa ya bari ta gota shi, Alo alo, mu ci daďi! Tuwo, nama, sai mun koshi, Alo alo, mu ci daďi! Nono da zuma ba mai zari, Alo alo, mu ci daďi! Siliki ran Salla ba datti, Alo alo, mu ci daďi! Zagi, mari, mun huta shi, Alo alo, mu ci daďi! Aikin wahala duk ba ma yi, Alo alo, mu ci daďi! Alo alo, mu ci daďi! Alo alo, mu ci daďi! Mutane ba su san abin da suka yi da Sarki ba, suna tsammani wasa Sarkin Busa ke yi da 'ya'yansu, sai suka tsaya suna daáriya, su ga ikon Allah. Amma da suka ga ya nufi kogi duk sai ransu ya baci, suna tsammani zai fada ne. Da Sarkin Busa ya fita bayan gari, sai ya tasam ma wani tsauni nan kusa da gari. Sarki da mutanensa na tsaye na kallonsu. Sarki ya ce a ransa, "Na san dai yaran nan ba su iya hawa wannan tsauni, na ga yadda zai yi da su." Ko da Sarkin Busa ya isa gindin tsaunin, sai mutane suka ga tsauni ya bude. Sarkin Busa ya kutsa ciki, duk yaran nan suka duru bayansa. Da suka shige duka, saura daya da aka bari can baya yana d'ingishi, sai tsauni ya rufe. Mutane suka yi ta kuka saboda batan 'ya'yansu. A cikin yaran nan akwai 'ya'yan Sarki su hudu, su ko ke nan gare shi, duk suka bace. 85 Inda Allah ya kyauta wa Sarki da ya ke mutane ba su san rashin tsaida maganarsa ta sa wannan abu ya faru gare su ba. Da sun sani nan take su ke halaka shi duk da zuriyarsa. To, ga shi kuma duk nasa sun bace, balle a ce wani makirci aka kulla da shi. Da uban yaron nan mai dingishi ya ga abin da ya faru, sai ya ruga ya jawo dansa, yana murna. Aka tambayi yaro me ya sa su ke bin mutumin nan? Yaro ya ce, "Ai mun ji yana cewa mu biyo shi, duk abin dadi na duniya ya ba mu. Ya ce akwai tabkin zuma, da nono, mu yi ta sha. Ga nama soyayye da dafaffe, wai inda zai nuna mana shinkafa ba a maganarta. Ni yanzu, duk bakin ciki na ke yi da aka bar ni baya. Yanzu suna can suna cin dadinsu, ni ina nan." Beran nan guda kuwa da ya haye, sai ya tafi ya iske wadansu beraye can, ba irin wadannan na bala'i ba. Ya rika ba su labari, yana cewa, "Ba ku sani ba, na yi daron cin dadi. A can ketaren rafi wani mai busa ya tara mu zai nuna mana inda daddawa ta ke banza, ga nama, ga mai, ga abinci iri iri, ba mai hana ka ci. Ya ce wajen nan da zai nuna mana ba a taba sanin akwai wani abu wai shi kare ba balle kyanwa, karamar alhaki. Zan isa, saura kadan, sai na ji na fada cikin ruwa. Yanzu 'yan'uwana na can sun yi kiba ni rashin sa'a ya sa ni na tabe!" Saura suka yi ta cewa, "Allah ya sa wata rana mai busan nan ya zo nan kasar, ya tafi da mu mu ma!" Sarki ya baza mutane cikin duniya, ko a sami labarin ya bulla wani wuri da 'ya'yansu. Aka yi nema, ko labari. Suka gaji suka dangana. Manyan gari suka ce, "Kai, ba ku sani ba fa, Sarkin nan ke da duk wannan gashin tsiya. Tun da aka halicci duniya kun taba ko jin inda irin wadannan al'amura suka faru?"" Saura suka ce, "A'a, lalle in ba tasam masa muka yi ba, har mu kuma zai sa a halaka mu." Sai suka taru suka tafi gidan, suka kunna masa wuta. Mai gari ya fito da gudu, suka bi shi da jifa, suka kore shi garin, ya fita tsirara. Iyalinsa kuwa suka fid da su, kowace ta nufi gidansu. Suka kwashe dukiyar da ya tara, da akwatunan kudi da ya jibge. Suka kona gidan, don kada sabon Sarkin da za su yi ya kwashi ciwon wancan na tsiya. Ka ji abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa. Musa ya duba ya ga wuri ya yi haske, ashe har rana ta fito ba su sani ba. Sai ya ce wa aku, "Na ji abin da ke aukuwa ga mai alkawari ba ya cikawa. To, me 86 ke faruwa ga irinku masu hana a cika alkawari? Bai tsaya garin jiran amsa ba, sai ya shiga gida a fusace. Da azahar ta yi Waziri ya kira tsohuwan nán ya yi mata kwando goma na zagi, don har yanzu ta kasa dabarar da za ta yi tfito da Musa. Tsohuwan nan ta ce, "Kullum ina kokari, wani dan aku gare shi mai tsai da shi da labaru ko yaushe har gari ya waye." Waziri ya tashi ya mangare ta, ya ce, "Tun da ba ki da wata dabarar da za ki wayace dan tsuntsu, tafi, yau na sa wani." Sai ya kira bawansa Barakai, wannan da ya aika wajen Sarkin Sinari kwanan baya, ya gaya masa abin da ya ke so, da kuma yadda aku ke hana Musa zuwa da labaru. Barakai ya yi shiri irin na mata, ya tafi gidan Sarki, ya tarad da Musa inda tsohuwan nan ta yi masa kwatanci. Ya yi masa maganar Mahmudu na can rai ga Allah, ya ce wai Mahmudu ya сe a gaya masa, tun da ba ya kaurfar zuwa su gana, shi ma ko lahira kada Allah ya gama su. Musa ya fashe da kúka, ya ce, "Kullum ina so in tafi, dan akun-nan ke tsaishe ni da labari. Ga ko Sarki ya ce in na yi wani abu ba da na shawarce shi ba, bai yarda mini ba duniya da lahira." Barakai ya ce, "Don dai wannan dan tsuntsu, yau ka tafi. Nan zan kwana, da mun ji bayin nan sun yi barci mu je tare ka sallami akun, in hana shi ya tsai da kai." Musa ya ce, "Da kin kyauta.". (Don yana tsammani mace ce.) Suka zauna nan, har barci ya share bayin da ke zaure. Suka tashi suka nufi wajen aku. Ko da aku ya hango su tafe su biyu, sai ya gane Barakai namiji ne, ba mace ba ce. Saboda haka, kafin su iso su yi masa wata magana, ya riga su ya ce, "Don Allah, yallabai, yau ka tafi. Ni ba na iya ba ka wani labari. Duk inda ka ke son zuwa, ka tafi." Barakai ya dubi aku, ya ce, "Ko ba ka ce ba, da ma yau ba mu son wani labari naka." Aku ya langabe kai kurum, sai tausayi ya kama Musa, ya ce masa, "Me ya same ka yau?" Aku ya ce, "Tunani na ke yi." Da ya ke Musa ba ya son ya yi wa akun nan abin da zai motsa masa rai, sai ya tambaye shi tunanin da ya ke yi. Aku ya ce, "Ina tunanin abin da ya faru ga wani masassaki ne, wanda ya yi kokari ya tara fiye da abin da Allah ya ba shi." Musa ya ce, "Wannan masassaki ýa ja wa kansa halaka." Aku ya ce, "Da. ma ka ji abin da ya same shi, ai da ka san lalaçewar ba ta da iyaka." Bai tsaya a ko ce ya fadi ba, sai ya fara: 87 Kowa Ya Yi Kokarin Ya Sami Fiye Da Abin Da Allah Ya Nufe Shi Da Shi, Ya Ja Wa Kansa Lalacewa Domin wai akwai wani masassaki a Katako, yana da 'yarsa mai shekara biyar da haihuwa, sunanta Halima. Ko da ya ke an sanyaro a kan son tambayar kome ya ji ko ya gani, duk da haka son tambaye-tambayen Halima sun wuce kima. Wata rana da safe uban na zaune na sassakar wata kujera, sai Halima ta shigo, ta ce masa, "Baba, inna ta ga mussa ta ce mata kyanwa, ashe ba ta san sunanta ba, ko ta sani ke nan?" Kafin uban ya bayyana mata da mussa da kyanwa duk daya ne, sai ta sake masa wata tambaya, ta ce, "Baba, kawu ya ce wai akwai giwa na yawo nan sama, ita ce ke yin fitsari da damina muna cewa ruwan sama, gaskiya ne?" Uban ya fashe da dariya, zai bayyana mata ba gaskiya ba ne, sai ta ce, "Baba, wai kai ma inna ce ta haife ka?" Uban ya ga za ta hana shi aiki da surutu, sai ya ce mata, "Fita waje can, ki yi wasa da yara, sai in na kare ki dawo." Sai ta tashi ta ruga. Tana fita, sai ta ji yara na bin wani wada, suna cewa, "Malam Dogo, Malam Dogo! Halima kuwa ko wane karambani ya ja ta, da ganinsa sai ta tsaya daga kofar zaurensu, ta ce, "Malam Dogo, Malam Dogo, ka zo, baba na kira." Malam Dogo da ya ji haka sai ya nufo zauren. Halima ko ta ruga zaure wajen ubanta, ta rungume shi tana kuka. Tsammaninta wani dan sanho da wadan ke rataye a bayansa duk ba kome ciki sai 'yan yara kamarta. Malam Dogo ya zo, ya durkusa gaban masassaki, ya ce, "Ga ni, 'yar matan nan tawa ta ce kana kirana."" Masassaki ya kawo sadakar abinci da goro da kwabo, ya ba shi, ya ce, "Tun da Halima ta kira ka, ai lalle in sallame ka." Malam Dogo ya yi godiya, ya bude sanho ya fitad da wata 'yar nakiya da aka ba shi sadaka, ya mika mata, ta ki karba, don ita ce gamuwarsu ta fari. Daga ran nan kullum kuma in zai wuce sai yar biyo ta zauren -gidan, in ya ga Halima a waje ya ba ta dan wani abin da ya samo sadaka. Tun tana gudu, yau da gobe har ta saba da shi, ta rika tsayawa tana karba. Da ya gan ta dai sai ya zauna, ta hau bisa kafarsa suna wasa. In ta fara irin 'yan tambayoyin nan nata na yara, sai shi kuma ya rika ba ta amsa irin yadda ya kamata. In ta tambaye shi, "Me ke cikin sanhonka?" Sai ya amsa mata, "Tuwo da nama da sukar." In ta ce, "Ina innarka?" Sai ya nuna ungulu ko shirwa, ya ce, "Ga ta nan tana tashi." Sai su bushe da dariya. Duk sa'ad da yarinyan nan ta ga ungulu ko shirwa sai ta ce, "A! Ga innar Malam Dogo." Ta dubi uwarta, ta ce, "Inna, ke ba ki iya tashi kamar innar Malam Dogo?" Uwar ba ta ko kulawa da ita in ta fara tambayarta. Suna nan haka, ashe wadan nan wani mai sihiri ne, ba a sani ba. Ran nan sai ya zo wurin masassaki dauke da 'yan kayansa duka, ya ce, "Na yi niyya yau zan koma kasarmu. Amma in Halima ta tambaye ka inda na ke, ka ce ni ma na yi fiffike na tashi kamar innata, don kada ta yi kuka. Kullum ku ce mata zan dawo gobe." Masassaki ya yi bakin ciki, don 'yarsa ta rasa abokin wasa. Ya shiga gida ya dauko wata tsumman riga, ya ba Halima ya ce ta kawo wa Malam Dogo a zaure. Yarinya ta jawo riga da gudu, ta kawo masa. Ta fada jikinsa tana murna. Malam Dogo ya dube ta, duk idonsa suka cika da hawaye domin sabo. Ya zauna nan har magariba. Da suka yi salla, ya ci abinci, sai ya kira masassaki, suka fita bayan gari, suka yi tafiyar kamar loko guda cikin daji, sai suka kai ga wani dutse. Da suka isa, wada ya dubi masassaki, ya ce, "Ka san an ce soyayya gamon jini ce, ko ba haka ba?" Masassaki ya ce, "Hakanan ne." Wada ya ce, "To, tun da na zo garin nan, ban ga wanda jinina ya hadu da shi kamar 'yarka ba, Halima. Tun da tana tsorona, har ka ga yanzu ba wanda ta ke so da gani irina. Kome ta ci ta rage mini. Kai kuma kana yi mini alheri iyakar gwargwado. Saboda haka ni kuma zan saka maka. Ko da ya ke kana ganina haka a wulakance, don in jarrabi mutane shi ya sa na wulakanta kaina. Nan kasar duk kafin ka sami wanda ya ke al'amari da aljanu kamata, ka dade." Ya tsuguna ya tara 'yan hakukkuwa, ya debi ganyayen kan dutse, ya yi turare. Masassaki ya rike baki ya ga al'ajibi. Da hayaki ya tashi, sai Malam Dogo ya dubi dutse, ya ce, "Fayau, bude dutsen kudi!" Nan da nan sai dutse ya bude. Da budewarsa sai Malam Dogo ya dauki wata 'yar fitila nan rataye cikin dutsen, ya kunna. Másassaki ya duba cikin kogon dutsen nan, ba abin da ke ciki sai 89 karfe ja wur cikin wata katuwar randa. Ya bude baki yana mamaki. Malam Dogo ya ce, "Na ba ka abin da ke cikin dutsen nan duka, amma da sharadi guda. Duk sa'ad da ka zo, kada ka debi abin da ya fi fam guda kowane zuwa. Na san fam guda dai ya ishe ka kashewa yini guda. Daga nan har ka mutu ba ka ganin kudin nan na raguwa. Ka lura in Halima ta isa aure ka yi mata kaya masu kyau, ga dai gudummuwata nan na bayar." Masassaki ya fadi yana godiya, yana rokon Malam Dogo gafara in ya yi masa wani laifi da. Suka gafarta wa juna. Malam Dogo ya ce, "Ko da rana ka zo sai ka diba, in dai ba ka gudun kada mutane su gan ka. In ko da dare za ka zo, in ka fita, ka yi turare da ganyen nan, ka tabbata ba wani abin firgita da zai dame ka. In ko ka zo, ka ga abin da na yi ba wani abu ba ne mai wuya. Sai ka debi ganyen nan na bisa dutse, ka yi turare da shi a gindin dutsen, ka ce, 'Fayau, bude dutsen kudfi.' In ka shigo, ga fitila ka kunna, in da dare ka zo. In da rana ne ko, ba ruwanka da ita. Ka kuma amince, ba kayan aljannu ne ka ke sata ba, balle ma ka ce za ka ji tsoro. Kai dai ban da dibar abin da ya fi fam guda kullum." Ya dubi masassaki ya ce, "Fara daga yau." Masassaki ya duka ya kidaya fam guda, suka fito. Malam Dogo ya ce, "Garam, kulle dutsen kudi!" Dutse ya koma ya rufe. Malam Dogo ya dubi masassaki ya ce, "To, sai mu yi ban kwana, ni zan wuce." Suka yi sallama. Malam Dogo ya wuce, masassaki ya komo gida yana tsalle-tsalle don murna. Ya kwashe duk labari ya gaya wa matar, amma bai gaya mata abin da za a се da dutsen ya bude ba. Suka yi ta murna. Gari na wayewa, ko da magariba ta yi sai ya koma ya debo fam guda. Ya yi ta yin haka kullum. Nan da nan kafin wata takwas ya sa aka debe dannin gidansa, aka gina masa na kasa. Aka yi zauruka kamar goma sha biyu kafin a shiga gidan. Aka ta da soraye. Ya kwashi kayan sassaka duk ya kona. Cikin mako guda ya auri 'yam mata uku, ya gama da matarsa, suka yi hudu. Duniya ta komo sabuwa, sai katta ke ta kaiwa suna komowa cikin gida. Aka manta da kiransa Maikujera, sai aka lakaba masa Maigida. Da ya yi magana sai a zabura a gama abin da ya ce, kome ya faďi sai ka ji barori na cewa, "Allah ya kyauta yin maigida." Bai cika shekara ba sai da ya daure doki goma sha biyu a bargarsa suna harbin iska. Da ya hau sai a bi shi tii, kamar Sarki. Mutane suka yi ta al'ajibin yadda ya yi arziki haka. Suka ga ko ba ya saye ba ya sayarwa, amma kullum abin nasa gaba gaba ya ke 90 ci. Da mai garin da wadansu sun fara hassadar abin, suna kushewa. Amma daga baya, da suka ga hassadarsu ta zama taki, sai suka saki, suka mika kai neman abin sutura. Da ba ya girman kai da wannan abu, amma daga bisani mutane da makada da maroka suka kumbura shi, har ya fara hura hanci yana alfahari, tun ba in ya je dutsen kudi ya ga abin kamar ba alamar karewa. Ran nan yana zaune bisa kujera, sai ya ce a ransa, "Kai, ni fa wahalar zuwa dutsen kudin nan kullum ta dame ni. Kullum, gemai-gemai da ni, a ga na nufi daji saboda fam guda. To, ni ba abin in ki zuwa ba, don ina so in kwashe kudin duka inda yana yiwuwa. Gobe dai fam biyu zan debo gaba daya in gani. Watakila dai Malam Dogo ya ki barina ne, don kada in huta wa raina. Amma fa ina amfanin a ga kamata ya tashi ya shiga daji don fam guda?" Ko da magariba ta yi, sai ya tafi dutsen kudi, ya debo fam biyu, ya fito. Sai ya ce, "Haba, na sanı da ma abin nan na Malam Dogo ya rufe ni ne. Tun da ya ke dai nawa ne, mene ne na yi mini haka?" Ya yi kamar wata guda yana diban fam biyu biyu kullum. Sai wata rana ya ce, "Shin me ya sa ne zan rika wahala da kaina don 'yam fam biyu tak? An ce ba sata na ke yi ba. To, ba na kawo abina gida, kowa ya huta, ni ma ko in sami hankalina ya kwanta in yi kiba, da wannan wahalar shiga daji kullum, sai ka ce talaka?" Sai ya sami buhunan gishiri ya ajiye, ya ce, "Gobe da wadannan za ni, in rika cika su ina kawowa gida har in kwashe sarai, in huta da shan dari kullum magariba." Gari na wayewa, ko da magariba ta yi sai ya kwashi buhunan ya nufi dutşen, yana takawa sai ka ce namijin agwagwa, don cikin 'yar shekan nan guda da rabi ya zama sai ka ce taiki don kiba. Ni'ima da din dadi duk sun sa har furfurarsa ta koma baka. Ya yi tsar, shuni ya huda shi, jikinsa sai kalli ya ke yi. Da ya isa sai ya zauna ya huta, yana kulla abin da zai yi a ransa in ya kwashe kudin nan duka. Yana cewa lalle ya buge gidansa ya sake wani. Matansa kuma duk ya kamata ya sake su, don tun da suka kai ga shekara guda da rabi a dakunansu ai sun tsufa. Da ya gama kulle-kullen abin da zai yi, ya tashi ya shiga kogo da buhuna. Ya ajiye su gefe guda, ya dauki daya don ya cika yadda ya ke iya dauka, ya kai gida ya dawo. To, ko da ya duka ya sa hannu zai diba, sai ya ga randar kudin ta yi kasa, ta bace. Dutsen kuma ko kasa ko bisa, sai aka bar Usuman jikan Usuman nan tsugune yana sallallami, yana da na sani sa'ad da ba ta da 91 amfani. Ya kwashe 'yam buhunansa, ya nufi gida yana bakin ciki. Da ma ai irin bukatarsa ka san ba tari ya ke yi ba. Kafin wata uku dan abin hannunsa duk ya kare, ya sayad da dawakinsa, barorinsa da suka ga abin na lalacewa suka watse. Da wadannan kudi na dawaki suka kare, ya karyar wa mai garin da gidansa araha, ya yi awo da kuďin. Kafin shekara wannan dan hatsin ya kare, sai matan nan yara suka fita, suka bar shi da tsohuwar matarsa. Da ma an ce tsohon doki sai mai shi. In gajarce maka labari dai, na rantse har da rawaninka, Allah ya ba ka nasara, ba a yi shekara biyu ba, sai da ungulu ta koma gidanta na tsamiya. Ka ji aikin zari. Kowa ya yi kokarin wai ya sami fiye da abin da Allah ya ba shi, ya lalace. Kafin aku ya kare ba da labarin nan gari ya waye. Musa ya dubi Barakai, ya ce, "Kin ga irin halin nasa ba?" Barakai ya ce, "A'a! Ashe kana da gaskiya, ka ji abu kamar na magani! Wallahi ko da ya fara labarin sai na ji na manta abin da ya kawo ni. Amma ba kome, na dawo da magariba." Ya fita ya koma gida, ya gaya wa Waziri yadda aka yi. Waziri ya fusata, ya ce, "Har kai ma watau tatsuniyoyinsa sun rude ka ko? To, gobe ka fito ba da shi ba, ka ga abin da zai same ka." Da magariba ta yi sai ga Barakai ya yiwo shiri ya dawo, ya се wa Musa, "Zan sake kwana nan gunka, yau lalle mu fita. Suka zauna suka yi ta hira. Da suka ji bayin nan sun yi shiru suka iske aku, Musa ya ce, "Zan tafi, ga shi har na sami 'yar rakiya kuma."" Aku ya duba ta taga sai ya ga hadari ya taso, yaşce wa Musa, "Haba, ko kuna hauka kwa fita yanzu cikin wannan ruwa?" Barakai ya ce, "Ai ba a fara ruwa ba, ma tafi hakanan." Aku ya yi ta jansu da 'yan tade-tade, har ruwa ya goce. Suka zauna suna jira a dauke. Aku ya dube su, ya ce, "Da zaman banza bari in gaya maku dan labari." Musa ya dubi Barakai, ya ce, "Ai ko kin san gaskiyarsa, ya fada mana dan gajere." 'Barakai ya сe, "Kуale shi, ba mu so. Kullum sai ka rika tsai da shi a kan surutun wofi, kai ba hadisi ka ke masa ba, kai ba labaran Annabawa ka ke gaya masa ba, balle a san kara shi ka ke yi." 92 Aku ya ce, "Abin da ya sa ba na ba da labaran Annabawa, tsoron jahilai na ke. Kun san yanzu akwai mutane da yawa wadanda su ba malamai ba na sosai, amma da sun ji mutum ya yi wata 'yar magana game da irin wadannan, sai ka ga suna neman daukar kafarsa, wai ya yi sabo. Amma fa im ba don gudun haka ba, labarin Annabawa, tun daga Annabi Adamu-tsira da aminci su tabbata a gare shi-har zuwa ga Shugaban Ma'aika, akwai wanda ban sani ba?" Musa ya ce, "To, in haka ne fara gaya mana labarin Annabi Sulaimanu, wanda aka ce ya mallaki mutane da aljannu har da tsuntsaye." Aku ya ce, "Wannan ai sananne ne har yanzu ba ka ji shi ba?" Musa ya ce, "I, na ji cikin dukan mutanen duniya babu wanda ya fi shi arziki." Aku ya ce, "Ai wannan daga baya ne. Domin sa'ad da aka nufe shi da annabci aka ce ya zabi dukan abin da ya kę so a ba shi. Shi ko ya ce tun da ya ke an ba shi mulkin jama'ar Allah, shi ba abin da ya fi so sai hikima, don ya san yadda zai rike su a kan adalci. To, tun da ya zabi wannan bai zabi dukiya ba, ko tsawon rai, ko girman duniya, Ubangiji ya ba shi hikima fiye da dukan sauran mutanen zamaninsa, ya kuma kara masa har da abubuwan nan da bai roka ba." Musa ya ce, "Haba, tun da na ke ban taba samun wanda ya bayyana mini asalin wannan al'amari ba, sai fa kai yau." Aku ya ce, "Ko labarin yadda ya yi hukunci tsakanin wadansu mata biyu ba ka taba ji ba?" Musa ya ce, "Wallahi ban taba ji ba. Wane irin hukunci ya yi?" Aku ya matso kusa da Musa, ya kishingida a bisa hannun rigarsa, ya fara: 93 Labarin Annabi Sulaimanu Wata rana Annabi Sulaimanu-tsira da aminci su tabbata gare shi-yana zaune, sai wadansu mata su biyu suka zo suka kawo kara a gabansa. Guda ta ce, "Ya Annabin Allah, da ni da wannan mace gida daya mu ke zaune. Na haifi da. Ana nan, bayan na haihu da kwana uku wannan mace kuma ta haihu. To, duk gidan ba kowa sai mu biyu kadai. Ran nan cikin dare ta kwanta bisa danta ba ta sani ba, har ya mutu. Sai ta tashi da tsakad daren, ta dauki dana ta mayar wajenta, ta dauko danta mataccen ta kawo gabana, ni ko duk ban sani ba. Sa'ad da na tashi da safe garin in ba dana mama sai na gan shi matacce. Da na duba da kyau, sai na ga ashe ba dana ba ne. Na gaya mata haka, ta ce karya na ke yi, maiaccen ne dana. Muka yi ta gardama. Da muka ga abin zai kaї ga barna, muka zo gare ka ka raba mana gardama, ya Shugaba." Waccan kuma ta ce, "A'a, karya ta ke yi, ya Shugabammu. Ni na riga ta haihuwa da kwana biyu, ran nan da dare ta taka nata ya muťu, ta zo ta musanya shi da nawa." Jama'ar da ke nan suka ce, "Kai, wannan shari'a ai ba ta warwaruwa, sai gobe ga Allah." Da Annabi Sulaimanu ya ji maganar matan nan sai ya sa aka dauko takobi aka zare, ya ce, "Tun da ya ke abin ya rikice haka, abu daya kadai za a yi a raba gardaman nan. Zan raba dan nan biyu ko wacenku ta dauki rabi, kowa ya huta, ku dangana har Allah ya sake ba ku wadansu." Da mace daya ta ji haka sai ta ce, "Don Allah kada a kashe shi. A ba ta, na yarda mata." Amma waccan ta ce, "A'a, daidai ne, ya Annabi. A dai raba shi, kowa ya huta." Da Annabi Sulaimanu ya ji haka sai ya ce, "Ku mika dan nan mai rai ga waccan da ta ce kada a kashe shi. Danta ne, ita ta haife shi."" Da Musa ya ji aku ya yi shiru sai ya ce, "A'a! Yaya aka san wannan ke da da?" Aku ya ce, "Haba, ba ka ga abin da a ke nufi ba? In da waccan ta haife shi ta ce a kashe shi tana kallo kiri-kiri?" Bai'tsaya su 94 Musa su sami damar fadin wani abu ba, sai ya ce, "Kafin ku kare tunanin wannan, tsaya ku ji yadda wani Sarki ya yi nasa hukuncin." 95 Ba Wahalalle Sai Mai Kwadayi Da aka yi wani Sarki mai son nishaďi. Ana nan wata rana zuciyarsa ta yi baki kirin, har ya kasa barci. Ya kira yaronsa ya ce masa, "Maza ka tafi wurin Waziri, ka ce ina kiransa." Yaro ya tafi ya gaya wa Waziri, suka zo tare, suka shiga wurin Sarki. Da suka shiga Sarki ya ce wa Waziri, "Yau zuciyata ta baci, har barci ya gagare ni. Ina so mu tafi mu zaga rafi, ko zuciyata ta yi sanyi." Waziri ya ce, "To, shi ya fi, ranka ya dade." Da fad'in haka sai yaron ya yi dariya. Sarki ya ce, "A'a! Mene ne? Ni ka ke wa dariya ko Waziri?" Ya ce, "Ranka ya dade, wane ni in yi maka dariya? Wani abu ne ya fado mini a rai wanda na gani jiya, shi na ke dariya." Sarki ya ce, "Wane irin abu ne?" Yaro ya се, "Ranka ya dade, jiya ina yawo a bakin kogi sai na iske wani mutum, mutane sun kewaye shi, yana ta ba su dariya." Sarki ya ce, "Maza ka tafi ka kirawo shi, ya zo ya yi mini abin da zai ba ni dariya, ko na samu zuciyata ta huce." Yaro ya tafi wurin mutumin, ya ce, "Sarki yana nemanka." Sai mutumin ya ce, "To, da kyau. Me ya sa Sarki ya ke kirana?"" Yaron ya ce, "Yau Sarki yana bakin ciki, yana so ka zo ka ba shi dariya, don zuciyarsa ta yi fari." Sai mutumin ya ce, "Mu je." Yaro ya ce, "To, sai mu yi sharadi, abin da Sarki ya ba ka duka a kasa shi uku, kai ka kwashi kashi daya, ni in kwashi kashi biyu. In ka yarda da haka zan kai ka, in ba ka yarda ba, yi zamanka, ni kuwa in koma in ce ba:ı gan ka ba." Sai ya ce, "To, shi ke nan, na yarda. Mu tafi." Yaro ya kai shi wurin Sarki, ya fita. Sarki ya ce wa mutumin, "Ina so ka yi mini abin da zai sa in yi dariya. In na yi, in yi maka kyauta, in ban yi ba in yi maka bulala." Mutumin ya yi ta yin abubuwa masu ban dariya, da labaru iri iri, har ya gaji. Sarki bai yi dariya ba. 96 Sarki ya ce, "Shi ke nan, ko akwai saura?" Mutumin ya ce, "Shi ke nan." Sarki ya ce, "Ga shi ban yi dariya ba. Kwanta in yi maka bulala." Mutumin ya matso, ya kwanta. Sarki ya tsala masa bulala da karfi. Sai ya yi ta kururuwa, ya ce, "Tsaya, ranka ya dade! Na karbi rabona, saura na yaronka. Domin mun sharada kome na samu in dauki kashi daya, shi kuwa biyu." Sarki ya kira yaronsa, ya ce, "Na ba wannan mutum rabonsa, sauran naka, matso kusa ka karba." Yaro ya matso kusa, yana tsammani zai sami kudi. Sarki ya tsala masa bulala da iyakacin karfinsa. Yaro ya kwala ihu. Sarki ya ce, "Tukuna, ai kashi daya kadai ka samu, saura daya." Yaro ya ce, "Ranka ya dade, kashi dayan nan ma ya ishe ni, na bar maka dayan." Da Sarki ya ji haka sai ya fashe da dariya, bakin cikinsa ya yaye. Ya kawo kyauta ya ba su, ya sallame su. Kafin aku ya kare wannan labari gari ya waye Barakai ya koma yana cizon hannu, yana neman hujjar da zai fada wa ubangidansa. Da zuwansa Waziri ya harare shi, ya ce, "Ban ji an gama aikin ba. Ina dalili?" Barakai ya ce, "Ruwa!" Waziri ya ce, "Ruwa? Wane iri? Ruwa da aka yi aka dauke tun kafin a yi kiran sallar fari?"" Barakai ya ce, "Watakila nan wajen gidanka aka dauke da wuri, wajen fada har rana ta fito ana ruwa." Waziri ya cika, ya kawo iya wuya, ya zabura ya danne shi ya shake, ya ce, "Fada mini gaskiya, in ba haka ba ko yanzu in kashe ka, mutumin banza, munafuki! Lalle kai ne ka tona asirin da muka kulla da Sarkin Sinari. Da ma ina shakkar haka." Da Barakai ya ji haka sai jikinsa ya dauki rawa, ya ce, "Na tuba Allah ya ba ka nasara, gaskiya zan gaya maka yanzu. Akun nan sihiri gare shi, in ya fara ba da labari, sai duk hankalin mutum ya rude, ya rasa abin da ya je yi. Muddin akun nan na numfashi ba yadda za a yi a fid da Musa daga gidan nan, ko kai ka je da kanka." Waziri ya ce, "Rufa mana baki nan da karyar banza!" Ya dauki bulala ya tsala masa har ya gudu. Waziri ya koma ya zauna, yana ciccika shi kadai, yana cewa, 97 "Ina Wazirin kasan nan duk tsawonta da fadinta, ga shi dan abu kadan ya rage da zan yi in zama Sarki, dan tsuntsu ya ce zai hana! To, bar ni da shi." Sai ya aika wajen Musa ya ce yana son aku ya zo yau ya debe masa kewa da labaru. Ya ba da igiya, ya ce in Musa ya yarda a dauro shi a zo da shi. Da aka gaya wa Musa, bai san abin da a ke nufi ba ya ce shi ya yarda, zai tambayi akun kuma ya ji in ya yarda. Ya tafi ya tambayi aku, aku ya ce, "Yallabai, tun da ka ce in tafi, ai sai in tafi." Yaron da aka aiko ya jawo igiya zai daure aku ya kai shi. Aku ya ce, "Mene ne na dauri? Ban saci kayan kowa ba. Ba cewa aka yi ana sona don nishadi ba? Wuce, in hau bisa kanka mu tafi." Suka tafi har gidan Waziri, suka tarad da shi a kofar gida. Aku ya sauka, ya tsaya nesa kadan. Waziri ya sallami mutane. Da shi niyyarsa, yana da wata katuwar sanda a boye ya kashe aku, kowa ya huta. Da aku ya lura da sandan sunne cikin rigar Waziri, sai ya kara ja da baya. Waziri ya ce, "Matso mana." Aku ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ina ni ina zuwa kusa da kai?" Waziri ya ce, "Ina so ka ba ni labari, kowane iri ka ke iyawa, in na ji da dadi in yi maka kyauta." Aku ya ce, "To, sai ka zauna in fara." Waziri ya zauna, aku ya fara: 98 Saurin Fushi Shi Ke Kawo Da Na Sani Wata rana Sarki yana kilisa, sai ya tarad da wani dan kwikwiyo yana kwance, duk kiyashi sun cika bakinsa nishi ya ke yi dai dai, zai mutu don yunwa, Ga shi ya faye kankanta, har ba ya iya ci da kansa. Ko yaya aka yi ya rabu da uwarsa, Allah kadai ya sani. Da Sarki ya dube shi sai tausayi ya kama shi, ya ja linzami ya tsaya, ya dubi mutanen da ke biye da shi, ya ce, "A kakkabe wa dan kwikwiyon nan kiyashi a dauke shi a kai mini gida. A ba Sarkin Babanni ya lura da shi da kyau yana ba shi abinci, in yana da sauran kwana gaba ya tashi." Nan da nan, kafin Sarki ya rufe baki, bayi sun dira sun kama karen, sun shafe masa baki da hannayen rigunansu. Wani ya sa shi kan kwacciya, ya tafi da shi gida ya kai wa Sarkin Babanni, ya gaya masa abin da Sarki ya ce. Ya saki hammadanci ya tarad da Sarki. Da rana ta yi sanyi suka komo. Bayan kamar kwana uku sai dan kare ya farfade, har ya fara tafiya, Da ya sami kamar wata biyu sai ya zama kamar ba shi ba. Ya yi bulbul, duk inda Sarki za shi yana biye. Da ya girma sai kullum dare in Sarki ya shiga barci, shi kuwa sai ya zo kofar turakar ya kwanta. Ba mai ikon gifta wurin sai gari ya waye. Saboda haka Sarki ya rika sonsa kwarai da gaske. Ba mai ikon ya buge shi, ko ya yi masa wata katuwar tsawa, don tsoron Sarki. Ana nan, ran nan safiyar Salla Sarki ya yi shiri zai fito ya hau zuwa idi, sai karen nan ya biyo. Sarki ya waiwaya ya gan shi, ya buga masa tsawa, ya koma daki ya kwanta, don ya san haka a kan yi masa in ba a son ya bi. Yana nan kwance dakin Sarki, can an kusa saukowa daga idi, sai aka kare toye-toyen Salla. Wata sadaka ta fara dauko kwano guda ta kawo cikin dakin nan ta ajiye. Amma maimakon ta rufe abincin yadda ya kamata sai ta bar shi a bude, don ta san ko da zai rube karen nan ba shi tabawa. Karen nan yana kwance, sai ya ga wani kumurci ya biyo matakin soro, ya sauko daga kan azara, ya sa baki cikin abincin yana ci. Kare ya fita waje yana haushi don mutane su zo. Ba 99 wanda ya kula da shi. Da mata suka ji ya dame su da haushi, sai suka dauki dutse suna jifarsa, don sun ga Sarki ba ya nan. Da karen nan ya ga ba su gane abin da ya ke nufi ba, sai ya kyale ya shiga daki ya kwanta. Maciji kuma da ya ga ya koshi, sai ya sulale ya koma cikin azara abinsa ya shige. Can an jima Sarki ya dawo. Da shigowarsa iyali suka yi masa barka da sauka. Bayan sun tashi, ya nufi wajen abincin nan zai ci. Kare ya bi shi yana kada wutsiya kamar ya ce, "Kada ka ci, maciji ya zuba dafi a ciki." Allah bai ba shi ikon magana ba. Sarki ya wanke hannu ya sa cikin abinci,ya yanko. Kare kuwa sai ya kai nan ya kai nan, Sarki na tsammanin son abinci ya ke yi. Ya jefa masa ya ki ci, sai haushi ya ke yi wa Sarki. Sarki ya bude baki zai sa wannan lomar sa'an nan ya dauki sanda ya kore shi, sai karen ya yi farat ya buge hannun Sarki, loma ta fadi kasa. Sarki ya dunkula hannu ya shiga dimar kare, amma kare sai gurnani ya ke, bai kula ba. Ya sa baki ya cinye loman nan da ta fadi daga hannun Sarki, ya kuma hau wa sauran abincin duk ya cinye sarai. Tun Sarki na dukansa, har haushi ya kama shi, ya gaji ya bari. Ya tsaya kuru ya ga ikon Allah. Ko da kare ya cinye abincin nan, sai ya koma gefe guda ya kwanta. Kafin Sarki ya kare ciccika, kare ya ınimmike nan ya mutu. Ganin wannan abu fa ya kara ta da hankalin Sarki, ya се, "Lalle akwai wani abu game da abincin nan. Watakila sadakar da ta kawo ta yi mini sammu ne in ci in mutu." Sai Sarki ya fito ya kira ta, ya tambaye ta, ta rarise da abin da zai kashe ta ba ta sa kome ba ciki. Ya tanta mba:ta ko ta bari 100 gaban sauran kishiyoyin, ta ce a'a, da karewa sai ta zuba cikin wannan kwano ta kawo. Sarki ya ce, "To, da kika fita ba wadda ta shigo bayanki?" Sadaka ta ce, "Mts, bayana ba wadda ta shigo. Ba na daukan alhakin wani, ni kadai na dawo na bude, don ya sha iska da na ji kuna tafe." Sarki ya yi shiru, ya ce, "Lalle karya ku ke yi. Munafincinku na mata wane ne bai san shi ba? Ba shakka ki gaya mini abin da kuka zuba, in ba haka ba kuwa in sa a yanka ki." Sadaka ta fadi tana ahi, tana rantse-rantse tana cewa ba ta sa kome ba ciki. Ya dube ta, ya ce, "Ke ar, munafuka!" Ya aika a kira bayi su zo su yanka ta. Nan da nan suka shigo, aka cafe ta tana kuka, aka yi waje da ita. Sarki ya yi zugun cikin daki, yana mamakin abin da ya yi wa sadakan nan har da ta ke so ta kashe shi, ya rasa. Can sai ya ji dakin ya gume da wani wari kamar na gwano. Ya tashi ya duba inda ya ke zaune, bai ga gwano ba. Yana kakkabe rigarsa ko ya shiga ciki, sai ya ji ka-ka-ka-ka-ka a bisa rufin daki. Ko da ya daga kansa sai ya ga wani katon kumurci a cikin azara. Da ya gan shi sai ya san lalle barin abincin nan da ta yi a bude ne, macijin nan ya zo ya ci. Saboda haka ya tashi da sauri,ya tafi inda bayin nan za su yanka sadakar. Ya tarda su har sun kayad da ita, sun dandanne za su yanka, sai kuka ta ke tana salati. Sai ya ce, “Kai, ku tsaya, ku tsaya!" Bayi suka tsaya suna kaduwa, suna tsammani Sarki ya raina saurinsu ne. Sarki ya ce a sake ta. Ya kira bayin, ya tafi da su turakarsa, ya nuna musu kumurcin. Ya gaya musu kuma da abin da zai sa a yanka sadakan nan. Ya sa bayi nan da nan aka fyado kumurcin kasa, aka fid da shi waje aka yar. Sarki ya tara dukan iyalinsa, ya gaya musu wannan al'amari, ya kuma gargade su kada su sake barin abinci a bude. Nan gabansu kuma ya gafarta wa sadakan nan, suka koma sha'aninsu. Ya sa aka fita da karen nan zaure, ya gaya wa fadawa da Sarakunansa abin da ya auku cikin gida duka. Ya sa aka gina dan daki a kofar gidansa, aka yi wa karen nan kabari a ciki aka sa shi. Ya yi bakin ciki kwarai saboda mutuwar karen nan. Ya kuma gargadi mutanensa da abu biyu. Na daya, ya ce kada su rika saurin fushi, kowane al'amari ya auku, kafin su zartad da hukunci su tsaya sai sun bi cikin al'amarin. Ya ce domin da bayin nan sun yi saurin cika umurnin da ya bayar a yanka sadakan nan da ya yi da na sani daga baya. Na biyu, ya ce su kyautata tausayi da jin kai ga dabbobi da tsuntsaye, ko da ba su da dabara 101 kamarmu, ba a san inda rana za ta fadi ba. Kowa ku ka gani a duniya, yana da ranarsa. Ko ba don wannan ma ba, ai an ce aikata alheri ga kowa, sakayyarka tana wurin Allah. Da Waziri ya ji haka sai ya ce a ransa, "A'a! Me ya ke nufi da wannan labari? Dan tsuntsun nan fa rigima gare shi! Yana tsammani ni yaro ne, balle ya ce ya yi mini wa'azi?" Sai ya hadiye fushinsa, ya yi murushi, ya ce, "Wannan labari naka iyaka ne. Bari in yi maka kyauta." Sai ya zaro wani zobe na zinariya ya rike a hannun hagu, ya nufo aku wai zai ba shi, hannunsa na dama ko na cikin riga. Aku ya rika tsalle yana ja da baya, Waziri na binsa yana cewa, "Tsaya mana ka karba!" Aku na ja da baya dai yana cewa, "Ai sadaka na yi maka labarin, ba don ka biya ba." Da Waziri ya lura aku ya gane shi, sai ya zabura gaba daya ya kai masa bugu, aku ya goce, buje ya tadiye Waziri ya fadi, ya daushe baki har hakorinsa guda ya fita. Ya tashi ja wur cikin jini, nan da nan baki ya haye. Da aku ya ga haka sai ya haye cediyar kofar gidan, ya kaikaici idon Waziri ya yi ta dariya. Da ya ga Waziri ya dubo, sai ya kanne, ya ce "Sannu bawan Allah! Ba ka sani ba, Waziri, ni kuwa ban ji zafin ba. Da ka taba jin labarin yautai da wani mai keke, da ba ka kulla wannan niyya ba game da ni. Kana so in kare ka da shi?" Waziri dai bai ce uffan ba, yana can yana fama da abin da ya same shi. Aku ya faki idonsa ya yi masa gwalo, ya ce, "Ko ba ka so ina gaya maka, ai mu abimmu muna yi don Allah ne. Sai ya soma: 102 Raina Kama Ka Ga Gayya Wata rana yautai yana kiwo a bayan gari sai tarko ya kama shi. Ya yi ya yi ya kubuce, ya kasa. Yana nan yana kuci-kuci sai ga wani tsohon kare ya zo. Da yautan nan ya gan shi sai ya ce masa, "Don Allah, wannan kare, ka dubi zumunci, ka ji kaina, ka sake ni, kai kuma Allah ya taimake ka." Kare ya tsaya kamar ya ki, ko kuwa ya dan cinye shi ne ya wuce. Ya ga dai kamar ko ya ci shi, ba zai san inda ya nufa ba. Sai ya tafi kusa da shi, ya sa baki ya tattaune tarkon nan, yautai ya kubuta. Da yautai ya ga an kubutad da shi sai ya yi wa kare godiya, ya tambaye shi inda za shi. Ya ce za shi neman abinci ne. Shi kuwa kafin ya zo nan a kama shi a tarko, ashe ya ga inda wata 'yar akuya ta mutu, aka kai gindin wata itaciya aka yar. Saboda haka ya ce wa kare ya zo ya kai shi, kafin dare ya yi kuraye su cinye. Ya tashi, kare yana bin inuwarsa har suka isa wurin. Kare ya tsaya, ya sa hakori ya barke cikin akuya, ya ci ya ci, har ya koshi. Yautai ya ce masa, "Da ya ke ka koshi sai mu tafi ka ga shekata, kullum in ka matsu da son abinci ka zo, ni kuwa in tashi in kewaya gari, inda na ga wani abin da za ka iya ci in zo in kira ka mu tafi." Ya ce, "To, madalla! Mu tafi in gani." Da suka fara tafiya suka kai kan titi, sai ya ce, "Wallahi naman nan da na ci ya kusa ya kware ni, da za ka dan dakata mini in kwanta nan in huta kadan, da na so." Yautai ya ce, "Ai gaskiyarka. Kwanta ka huta, in kana son barci ma yi, ni kuwa zan hau nan in tsaya in na ga yara zan gaya maka ka tashi, don kada su buge ka." Kare ya ce, "To, madalla!" Kwantawarsa ke da wuya sai barci ya share shi. Can an jima kadan sai ga wani tafe da keken shanu, yana dauke da buhunan gero. Da yautai ya hango shi sai ya ce masa, "Kai mai keke, kai mai keke, yi kwana, don kada ka take mini dan'uwa, ga shi nan yana barci. Mai keke ya harare shi da fushi, ya ce, "Wane ne dan'uwanka da ka ke tsai da ni dominsa?" 103 Ya nuna masa kare da ke barci, ya ce, "Ga shi nan." Mai keke ya dubi kare, ya yi tsaki, ya ce, "Da ma don saboda kare ka tsai da ni? Karen me? Kai ar, Allah wadanka!" Sai ya kora shanunsa suka bi ta bisa karen. Bai ko shura ba, ya mutu, hanji waje. Yautai ya tashi ya bi shi yana kuka, yana cewa, "Wayyo ni, kaico kaina, ka kashe mini dan'uwa, bai ci ba bai sha ba. Na yi maka magana ka lura, ka ki, don ka raina ni. To, yadda ka sa na zubad da hawayena yau, kai kuma sai na sa ka zubad da naka. A bar ma ta batun hawaye, yadda ka sa dan'uwana ya bar duniya yau, kai ma kana barinta, in Allah ya so." Mai keke ya yi dariya, ya ce, "Har kai nan dan tsuntsu, yadda ka ke za ka ce ka iya sa ni kuka? Duban ni da kyau fa ka gani." Yautai ya ce, "To, shi ke nan. Raina kama ka ga gayya!" Mai keken nan kuwa a gaba ya ke zaune, buhunansa na baya. Da yautai ya ga ya kora, sai ya yi gaba kamar ya wuce shi, sai ya 'dawo ya sauka bisa buhunan gero, mutumin nan bai sani ba. Ya yi ta yi musu huda, gero na tsiyayewa, mutumin nan bai sani ba. In ya ga kamar zai waiwayo sai ya boye tsakanin buhu. Zuwa can gero ya tsiyaye, sai ya ji keke na gwaram gwaram, kamar ba kaya. Ya tsai da shanu, ya sauka ya duba kaya, ya yi salati. Yautai ya tashi, ya ce, "Kadan ke nan. Ai ban gaya maka ba, raina kama ka ga gayya?" Ya tashi ya sauka bisa idon sa guda, ya yi ta tsatsagewa, sa na tsalle-tsalle. Mai keke ya gan shi, ya dauki wani gatari nasa zai kwantara masa, sai ya tashi, ya sami kan san. Sa ya fadi nan take ya mimmike. Mai keke ya ce, "Wash!" Yautai ya ce, "Tukuna. Ai na gaya maka, raina kama ka ga gayya." Mai keke ya ciji baki, ya sauka ya daura wa daya san keke, ya hau ya kora, ya nufi gida. Yautai ya komo ya sauka bisa idon sa dayan, ya fara tsattsaga, shi kuma ya yi ta tsalle-tsalle, yana harbe-harbe. Mai keke ya dube shi, ya ce, "Lalataccen nan ya dawo." Ya dauki gatari, ya tsaya tsai, wai ya dube shi daidai ya sare sai ya tashi, ya sami kan san. Sai ya fadi, nan ya shure. Ya sauka ya rasa abin da zai yi, sai ya saba gatarinsa, ya nufi gida yana cizon yatsa. Yautai ya ce, "Mu tafi gidan, ai na gaya maka, raina kama ka ga gayya." Da matarsa ta gan shi ya shigo yana zage-zage sai ta ce masa, "Lafiya, babba da kai kana wannan irin mugun baki?" •Ya ce, "Ina fa lafiya, wani dan tsuntsu duk ya sa na kashe shanuna, wai don na taka wani kare a hanya?" Ya waiwaya sai ya ga yautai bisa tukwanensu, ya ce. "Kin gan shi ma ya biyo ni, lalatacce!" Matarsa ta ce. 'Kai ar, sululun wofi, yaya dan tsuntsu 104 kamar wannan, wanda bai fi a hadiye ba, zai ruďa ka haka?" Sai ta fizge gatarin da fushi, ta wurgi yautai da shi. Yautai ya tashi, ta sami tukwanensu, duk suka fashe. Yautai ya koma cikin dankin matar ya sauka, ya ce, "Raina kama ka ga gayya!" Da matar ta waiwaya ta gan shi, sai ta sake daukar gatarin ta wurge shi da shi, ta sami korenta, duk suka fashe. Kai, in gajarce maka labari dai, suka yi ta yin haka har ta fasa kayan dakinta duka. Yautai ya dube su, ya ce, "Tukuna dai. Raina kama ka ga gayya!" Daga nan mijin ya tuna da wata dabara, ya matsa wurin matarsa, ya rada mata ya ce, "Rufe taga maza, ni kuwa in rufe kofa, mu rutsa shi, mu kama, mu yi masa irin kisan da mu ke so." Suka zabura waje gaba daya, suka rurrufe. Suka koma ciki, tarya nan tarya nan, har suka kama shi a hannu, Suka bude kofa da taga, suka fa tsaya gardamar yadda za su kashe shi. Mijin ya ce, "Hura wuta za ki yi ki jefa shi."" Matar ta ce, "A'a, ba haka za mu yi ba. Fige shi za ka yi yanzu, ni kuwa in nika tosshi in kwaba shi, in tsoma shi ciki. Ko kuwa ma ba haka za mu yi ba, in mun fige shi in sa wuka in kwakule idandunansa yau, gobe in yanke kafa guda, jibi in yanke fiffike guda, mu bi shi da yanka haka gaba gaba har ya mutu, dan lalatacce!" Da yautai ya ji haka sai ya ce, "Ta Allah ba taku ba. Raina kama ka ga gayya!" Ko da suka ji haka duk sai suka fusata, matar ta zaro wani takobin mai gidan da ke nan, ta çe, "Bari in sare shi."" Mijin ya ga nawar ya bar matar ta sare shi, sai ya duka wai ya take shi, sai matar kuwa idonta duk ya rufe don fushi, ta kai wa yautai sara daidai da sa'ad da mijin ke dukawa ya take shi, sai ta sare kan mijin. Ya fadi, ya mutu. Yautai ya tashi ya fita, ya ce, "Alhamdu lillahi! Da ma hakin da ka raina shi ke tsone ma ido." Ganin wannan al'amari ya sa matar ta haukace, ta dauki gatari ta shiga jeji. Kowane tsuntsu ta gani sai ta kai masa jifa tana cewa, "Raina kama ka ga gayya!" Da aku ya gama ba da wannan labari sai ya tashi fir ya koma fada. Da Musa ya gan shi ya tambaye shi labarin da ya gaya wa Waziri, aku ya ki gaya masa hakikanin abin da aka yi sai ya ce, "Na gaya masa labarin Umaru Mu'alkamu ne da Shaihu dan Fodiyo ya nuna masa karama." Musa ya ce, "Wace karama ce Shaihu Mujaddadi ya nuna wa Umaru Mu'alkamu, wadda ban tuna da ita ba? Alhali kuwa 105 labarun Shaihu da mu'ujizarsa sai mu gaya wa wani ba wani ya gaya mana ba. Aku ya ce, "Ranka ya dade, ai ka san sani wuyar al'amari gare shi, kome abin mutum in ya san wani abu bai san wani ba." Musa ya ce, "To, fada mini wannan labari in ji, ko na tuna da shi." 106 Labarin Shaihu Mujaddadi Dan Hodiyo Da Umaru Mu'alkamu Wata rana, sa'ad da Shaihu dan Hodiyo na Sifawa, sahabbansa suka taru ana tadi, daga nan sai wani daga cikin sahabban Shaihu wanda a ke kira Umaru Mu'alkamu, ya dubi mutane, ya ce, "Kai, ina ko son goro, ko akwai wani mai dan tsalli ya ba ni in ciza?" Mutane suka ce duk ba mai saura. Shaihu na kallonsu, ya yi kamar bai ji ba, sai can, har an saki wannan magana, ya dubi Umaru Mu'alkamu, ya ce, "Tashi mu je shan iska bayan gari." Umaru Mu'alkamu ya ce, "To." Ya tashi, suka tafi, Shaihu na gaba, yana biye. A lokacin nan ko la'asar ta yi sakaliya. Da fitarsu kofar gari, sun dan taba tafiya kadan sai suka kai ga wani dan rafi, suka sa kafa suka tsallake, sai suka isa wani daji, Umaru Mu'alkamu ya duba, bai ga kome ba sai itatuwan goro ko'ina. Shaihu ya dube shi, ya ce, "Ka ce kana kawar goro, to, ga su nan, debi iyakar abin da ke isarka." Umaru Mu'alkamu ya shiga diba yana mamaki, ashe akwai dawan goro kusa da Sifawa ba a sani ba? Ya cika aljihunsa, ya се wa Shaihu dan Hodiyo, "Ai wannan ya ishe ni, Allah ya gafarta malam." Nan da nan suka tsallako dan rafin nan suka komo gida. Ana nan, bayan 'yan kwanaki kadan goron da Umaru Mu'alkamu ya debo tare da Shaihu ya kare. Da ya ga dai dawan goron nan ba nisa gare shi ba, sai ya tashi shi kadai ya kama hanyar da suka bi da Shaihu, yana sauri ya je ya debo kafin hantsi ya yi zafi. Ya yi ta tafiya, ya yi ta tafiya har rana ta take tsaka cur bai ga ko alamar ya kusa da wurin ba. Sai ya yanke kauna, ya juyo. Kafin kuma ya iso sai da la'asar ta yi sansanya. Da isowarsa bai zame ba sai wajen Shaihu. Suka gaisa, ya dubi Shaihu, ya ce, "Kai, yau na ga tasku!" Shaihu ya ce, "Me ya same ka haka, har ka ke yaba wahalar da ka sha?" Umaru Mu'alkamu ya ce, "Ai tashi na yi tun da safe, wai in tafi dawan nan na goro da muka je da kai shan iska kwanan baya 107 na debo, in sake karowa. Na yi tafiya har Allah ya gajishe ni, ban ga na kai ko dan rafin nan ba. Da na ga rana ta yi tsaka dai, sai na rufa wa kaina asiri na dawo. Ka ga tun sa'an nan isowata ke nan, ko ruwa ban biya gida na sha ba." Shaihu dan Hodiyo ya dube shi, ya yi murmushi ya ce, "Da ka san inda muka tafi fitarmu ran nan, da ba ka ce za ka bi ba. Ai cikin dawan Gwanja na kai ka ka samo goron." Umaru Mu'alkamu ya rike baki. Shaihu ya ce, "Ka ga dan rafin nan da muka sa kafa muka tsallake kafin mu shiga dawan goron?" Umaru Mu'alkamu ya ce, "Na gani." Shaihu ya ce, "Wannan ai kogin Kwara ne ka ga ya tsulance hakanan." Umaru Mu'alkamu bai sami ta cewa ba, sai ya kada kai kawai, ya ce, "Allah ya ba mu albarkacinku!" Da Musa ya ji haka sai ya ce, "Af, wannan ai ina tsammani ma shi na fara ji cikin mu'ujizozin Shaihu dan Hodiyo. In dai za ka ba ni wani labari, na yarda ka ba ni, amma na Shaihu wannan namu ne, sai mu ba wani, muddin dai an yi shi. Gama ko labarin jihadin da ya yi, da biranen da ya gina, da wadanda ya ba tutoci, duk a kaina su ke." Aku ya gyara fiffike, ya ce, "Ai ni ma hakanan, Allah ya ba ka nasara, ko da na ke tsuntsu sai dai in ba wani labarin Shaihu đan Hodiyo, ba wani ya ba ni ba." Da Musa ya ga aku ya tsunke da surutai yana yabon kansa, sai ya ce, "Tsaya! Mene ne na yabon kai? Yabon kai jahilci. Ni ba wani surutu na ja ka ba, balle ka cika mini kunne haka. Cikin labarin mu'ujizozin Shaihu dan Hodiyo yanzu zan gaya maka wanda ba ka sani ba, in kure ka. Ba na ma takalo labarin jihadi ko labarin asalinsa balle ka ce na yi zurfi shi ya sa ka kasa. Shiga kidaya,.sai na gaya maka uku wadanda ba ka sani ba, sa'an nan in shiga in yi azahar, na ji an yi kira." Aku ya ce, "To, ba sai ka fara ba mu ji? In dai lalle an yi shi, ai sai na gani." Musa ya ce, "Da fari ma ba ka san wannan ba. Wata rana, sa'an nan Shaihu dan Hodiyo na yaro, suna zaune a Dagel da shi da ubansa Hodiyo. Ran nan Hodiyo ya shiga ya yi alwala su yi azahar, sai ya kira Shaihu ya ce, "Zo in aike ka Murnona--" Aku ya yi farat ya karbe ya ce, "Wanda Shaihu ya tafi ya dauko littafi har ya dawo uban bai gama alwala ba? Shaihu ya yi alwala ya bi shi aka yi sallar da shi? Alhali kuwa daga Dagel zuwa Murnona zango guda ne ga mai kaya?" Musa ya ce, "Me ka ke faranniya haka don ka gane na fari? In ka san wani ka san wani ne?"" 108 Aku ya ce, "To, fadi mana mu ji, Allah ya ba ka nasara." Musa ya ce, "Wata rana Sarkin Gobir Wuro Nafata ya aika a kira Shaihu dan Hodiyo kamar abin girma-" Aku ya karbe ya ce, "-ashe ko nan ya sa an gina rami mai zurfi, ya kafa wukake da masu ciki, ya sa an rufe ramin da tabarma, don in Shaihu ya zo ya ce ya zauna nan ya faďa ciki ko? Shaihu kuwa ya zo ya zauna, bai fada ba. Sarkin Gobir ya daga wata bindiga da ke gare shi nan boye zai harbi Shaihu, bindigar ta fashe. Sarkin Gobir duk ya kokkone. In ko ba wannan mu'ujizar ba, wata ka ke nufi ka fadi mu ji, Allah ya ba ka nasara." Musa ya ce, "A'a! Ashe dan tsuntsun nan a yi da shi. Ya dubi aku, ya ce, "Ka san labarin Shaihu da madugu?" Aku ya ce, "Shaihu da madugu? Wane labari ne kuwa na Shaihu da madugu wanda ban sani ba? An ko yi shi? Allah ya ba ka nasara, sai ka faďi mu ji." Musa ya се: 109 Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Madugu Wata rana wani madugu yana dawowa daga Gwanja, ya iso Kwara ya shiga jirgi. Suna kan tafiya cikin jirgin nan, sai igiyoyin Kwara suka murda, jirgin ya yi nan tangan tangan, ya birkice. Sai madugun ya kama, "Shaihu dan Hodiyo, ka taimake mu! Shaihu dan Hodiyo, ka yi agaji! Ni dai kam wallahi in na kubuta daga wannan halaka, in na je Sakkwato sai na kai maka sadakar goro kwarya goma:" Yana fadin haka sai ya ga wani ya zo ya kama shi, ya fid da shi duk da kayansa. Ya duba ya ga kowane ne, sai ya ga ba kowa. To, a cikin wannan lokaci kuwa Shaihu Mujaddadi dan Hodiyo yana Sakkwato, yana ba da karatu, kuma yana wa'azi ga jama'a. Sai aka ga ya yi shiru. Can sai aka ga yana matsa hannun rigarsa, ruwa na zuba tsurururu. Jama'ar da ke nan suka nemi bayanin wannan al'amari daga gare shi. Shaihu ya ce, "Wani bawan Allah ne ya nemi taimakommu a Kwara da jirginsa ya kife. Allah ya nufa muka je muka taimake shi." Jama'a suka rike baki suna cewa, "Allah ya sa mu cikin ceton Annabinsa, ya ko ba mu albarkacinku, Mujaddadai!" Bayan an yi kusan wata biyu, ran nan sai ga madugun ya zo Sakkwato, ya debi goro kwarya uku ya tafi wajen Shaihu ya kai masa don ya cika alkawari, ya kuma nemi albarka. Bayan ya gaishe shi, ya gaya masa abin da ya faru duka ga jirginsu sa'ad da suna tsakiyar Kwara, da kuma yadda ya roke shi, ya zo ga taimakonsa, ya ga kamar wani ya zo ya fid da shi, amma da ya duba bai ga kowa ba. Shaihu dan Hodiyo ya tambaye shi wace rana ce wannan hadarin ya auku, kuma nawa ga wane wata ne. Madugu ya fadi ranar da watan, ya lissafa kuma ya fadi kwanan watan sa'ad da wannan al'amari ya auku. Da almajiran Shaihu su kuma suka lissafa, sai suka ga ya kama daidai da ranar da Shaihu Mujaddadi ya yi shiru cikin wa'azi yana matsar hannun rigarsa. Abin ya kara ba da mamaki. Madugu ya fitad da goro ya mika wa Shaihu, ya ce, "Ga abin 110 da na yi alkawari zam ba ka in Allah ya nufa na kubuta." Allah ya nufa na kubuta." Shaihu dan Hodiyo ya yi godiya, ya karba ya ajiye, ya yi murmushi ya dubi madugun, ya ce, "Ai ko ba ka cika alkawari sosai ba. Kwarya goma ka ce, ga shi ka kawo uku." Madugu ya rasa abin da zai ce don kunya, yatai gida ya ciko kwarya bakwai ya kawo wa Shaihu, ya fadi ya yi godiya, Shaihu ya karba, ya raba wa mutanen da ke nan sadaka. Musa ya dubi aku, ya ce, "Ka ji labari daya da ba ka sani ba cikin mu'ujizozin Shaihu Mujaddadi dan Hodiyo. Yanzu kana daya. In dai ga labarun Shaihu ne, in na fara na iya gaya maka goma ba ka sami wanda ka sani ba." Aku ya tuma nan ya tuma can, ya karkata kai, ya ce"Allah Sarki! Ai wannan labari na Shaihu ko na goye ya san shi, amma ka ga duk da haka sai da ka yi babban kuskure cikinsa. Shi ya sa ka ruda ni, na ji kamar ban sani ba." Musa ya сe, "To, ka fara ba? Kai dai wani ba ya yin abin kirki in ba kai ba. Wannan labari na ji shi ya fi sau kam, amma duk ban taba jin inda suka saba ba." Aku ya ce, "Saurara, Allah ya ba ka nasara, abin da na gaya maka duk na labarin Shaihu dan Hodiyo sai ka yarda, Madugu da ka ce ba madugu ba ne, farke ne. Ai ka ji batan da ka yi." Musa ya ce, "Wasalam! Ka ji ka ba? To, me ya raba dambe da fada?" Aku ya yi dariya, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, zage-zage." Sai Musa ya yi dariya, ya yi tsaki, ya ce, "Kai dai ba ka gajiya da surkulle. Ko mutum ya tashi yin hushi da kai sai ka ba shi dariya. Allah ya kai mu dare, kai ka gaya mini naka wanda ba mutum duka ya sani ba. In na bi taka yanzu, har lokaci ya wuce ban yi salla ba."" Aku ya kada fiffike, ya ce, "Allah ya kai mu. Amma ina da fatawa. Don Allah, Shugabana, shi sai mutum ya sa da me da me a jikinsa za a san lalle ya yi ado, ba abin kushewa?" Musa ya ce, "Kai fa na san ka, wadansu tambayoyinka duk na ba'a ne. Kai ba ka kan gani da kanka ba? Ai ko tsuntsu ya san ba abin da ke kambama mutum irin ya sa wando mai zina, da jabba, da riga aska takwas a bisanta, kana ya sami-." Aku ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ai ma ado ya kare. Kada in tsai da kai, sai da dare." Musa ya ce, "Allah ya kai mu da alheri." Da dare ya yi, barci ya share Musa, sai can da asuba ya farka, ya tashi, ya shiga damaru, ya dauko mashi ya zo wajen aku, ya cе, "Madalla, ai kowa ya yi karyar dare gari ya waye! Ka ce labarin 111. Shaihu da na bayar jiya ko na goye ya san shi. To, ina son in ji naka wanda ba a sani ba." Aku ya kada fiffike, ya dukad da kai, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, yanzu ko ka ji." 112 Labarin Shaihu Dan Hodiyo da Wani Malami Wata rana wani malami daga gabas da ya ji labarin Shaihu sai ya yiwo wa Sakkwato tsinke, ya zo ya ga abin da a ke fadi da idanunsa, domin an ce gani ya kau da ji. Da ya kusa da Sakkwato ya yi shiri irin na alhazai, ya shiga kokuwa, ya tafi wajen Shaihu Mujaddadi, ya ce, "Ina da fatawa, ya Shugabana." Shaihu dan Hodiyo ya amsa, "Allah ya sanasshe mu!" Mutumin nan ya ce, "Ya Shugabana,. da me a ke miya a nan kasarku?" Shaihu ya ce, "Da kuka, da gishiri, da tosshi, da daddawa." Mutumin nan ya се, "То, ashe sun sha bamban da na kasarmu." Ya yi ban kwana da Shaihu, ya fita. Shaihu ya ci gaba da sha'anin da ya ke ciki na jihadi. Aka ci kasashe, aka ba wadansu tutoci, sai can bayan shekara biyu har an manta da wannan mutum da ya yi tambaya, sai mutumin nan ya dawo, ya sami irin kayan Hausawa, ya yi shiri yadda ba mai ganewa shi ya zo bara waccan. Ya tafi wajen Shaihu ya gaishe shi, ya ce, "Da me kuma?"" Da ya ke Shaihu dan Hodiyo al'amarin nasa ya yi nisa, ya tuna tambayar bara. Ya dubi mutumin nan, ya ce, "Idan da wadata a kan sa nama." Ko da bakon nan ya ji haka, sai ya fadi ya nemi Shaihu dan Hodiyo gafara, ya sallame shi ya koma garinsu. "Tsakaninka da Allah, Allah ya ba ka nasara, ka taba jin wannan irin labari na Shaihu Mujaddadi in ba yau ba?" Musa ya ce, "Gaskiya dai, ban taba ji ba. Shin don Allah ko kai ka kaga shi yanzu?" Aku ya kada kai, ya ce, "Haba, Allah ya ba ka nasara, wallahi ba yanzu na kera ta ba, ni ma haka na ji shi. Ko mutum na hauka, irin karairayin nan da a ke wa tatsuniyoyi a yi wa tarihi kamar na Shaihu Mujaddi dan Hodiyo? Haba, ai wargi wuri ya ke yi." Musa ya ce, "To, ko da ya ke haka, kana tsammani wannan ya fi wanda na gaya maka jiya ban mamaki?" Aku ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ai ba gardama na ke ja da 113 kai ba. Wadannan al'amura ne na waliyyai, idan aka yi zurfi ciki, sai a tasam ma yin sabo. Ba mu da wata ta cewa, sai Allah ya ba mu albarkacinsu, amin, amin, amin!" Musa ya ce, "Gaskiya ne, Allah dai ya kiyashe mu azabobin Jumma'ar da ba ta da Asabar, domin alfarmar Shugaban talikai!" Ya juya zai tafi. Aku ya ce, "Af, Allah ya ba ka nasara, kana ya sami me?" Musa ya waiwayo, ya ce, "Kana ya sami me fa?" Aku ya cе, "Tambaya na ke. Kana ya sami me?" Musa ya ce, "Me ka ke nufi da 'Kana ya sami ne?' Wa ka ke maganarsa? Wane abu zai samu? In kana tambayar wani abu ne ka faďi mu ji. Kai ba abin da ke dibarka sai samartaka. To, ni na aske." Aku ya duka, ya ce, "Allah ya huci zuciyarka, yallabai. Sauran tambayar da na yi maka jiya, da na so in gani in ka iya iyad da jawabin da ka fara ba ni, don ka ce tarihin da na bayar yanzu na Shaihu Mujaddadi ba shi da bam mamaki kamar wanda ka bayar jiya." Musa ya ce, "Wane tambaya ka yi mini jiya?" Aku ya bushe da dariya, ya ce, "Jiya-jiya har ka manta, ranka ya dade? Na tambaye ka shin sai mutum ya sa me da me a jikinsa za a san lalle ya yi ado, ba kushewa. To, ina ga wannan da aka yi da shekara biyu?" Musa ya dubi aku ya ce, "Hо dan nema! Kai dai ba ka barin ko ta kwana, duk inda mutum ya fito maka kana make kana kallonsa." Ya duba haka sai ya ga gari ya waye, ya harari aku, ya ce, "In don mugunta ka ke mini wannan abu, ba kome, Allah ya isa." Ya shige gida. Azahar na yi sai ga Sarki Abdurrahman ya aiko da dan bushara an ci nasara, gobe kuwa tun da safe ga shi nan tafe. Musa ya tambaya. "Ina Mahmudu? Ya warke? Dan busharan nan ya cе, "Ai da ma ba abin da ya same shi, gobe ka gan shi." Kafin Musa ya sami damar tambayarsa sai ya hau ya koma, don an ce kada ya zauna. Duk gari ya rude da gude-gude, ana ta murna, Waziri ko sai ka ce an yi masa mutuwa. Magariba na yi sai ya kira wadansu samari hudu daga cikin yaransa, ya gaya musu abin da a ke ciki duka, ya yi alkawari in 114 sun yi kokarin da suka kashe Musa daren nan na yau, ko da su murde wuyansa ne, shi ko ya ba su fam ashirin ashirin. Bayin nan suka ce, "Don wannan har wani aiki ne?" Suka shiga neman kayan ado irin na mata suna sawa. Aku kuwa da ya ke ya san haka zai faru, magariba na yi sai ya ce wa Musa, "Yallabai, yau bai kamata a yi barci ba, sai mu koma babban zaure, mu gamu da bayin nan a yi ta hira." Musa ya ce, "Ai ko hakanan ne," Aka kai kujera, Musa ya tafi ya kame bisa, bayi suka kewaye shi. Jimawa kadan aku ya biyo, ya duba ya ga bayin nan ba mai wani makami kusa da shi, sai ya ce, "Ashe ku duka mata ne, yaya za a bar ku kumu ku rika zama ba mai ko sanda? Halal kun manta da duniya." Bayi suka ga gaskiyarsa, kowa ya dauko takobinsa ya zare ya ajiye a gabansa, aka shiga hira. Can lisha sai ga bayin nan na Waziri su biyar, har da Barakai, suka shige gida sai ka ce mata, aku kadai ya gane maza ne. Suka sami wani zaure suka make, su ba su cikin gida, su kuwa ba su waje. Suna nan suna jiran Musa ya shigo, don su tarye shi nan su halaka shi, hira ta ki karewa. In aku ya ga za su dan dakata sai ya yi musu wani abin dariya. Suka yi ta yin haka har asuba ta yi. Da aku ya ga sun gaji da hira, wadannan sun fara gyangyadi, sai ya ce, "Bari in yi muku wani labari mai daďi." Musa ya ce, "Ai ko hakanan ne, ku tsaya ku ji fasaha wurin dan tsuntsun nan nawa." Wadanda ke jin barci suka murje idanunsu. Aku ya sami ruwa ya kora, ya yi kaki ya zubad da yawu, ya fara: 115 Sauri Ya Haifi Nawa An yi wani Sarki nan arewa wanda ke da dan auta da ba a taba ganin kyakkyawa irinsa ba. Da fari dai ga shi, shi bai cika kyamushewa ba, shi kuwa ba kakkaura ba hakanan. Wuyan nan nasa sai ka ce goran nono, idanunsa ko fari fat sai ka ce madara. Gashin kansa ma abin kallo ne, don sai ka ce mai ya ke shafa masa. In ko har ya yi dariya ka ga hakoran nan, wayyo Allah! Kafafunsa kuwaMusa ya ce wa aku, "Kai don Allah in za ka ba mu labari ka ba mu mu sha, in ko ba ka ba mu, ka kyale mu kowa ya san abin da ya kama." Aku ya ce, "A'aha! A bar ni in gyara labarina yadda zai yi daďi." Wata rana Sarkin nan ya hau duk da mutanensa, don ya kewaya kasarsa ya buga musu haraji. Suna cikin tafiya sai autansa ya janye wani baransa, suka rika ja da baya. Suna son a wuce su kama labarin duniya. Ko da suka ga rundunar Sarki ta bace, sai suka yi ta tadinsa suna kakkawa suna tafawa. Suna cikin haka sai suka isa wani dan kauye wanda Sarki ya wuce tuni. Da suka ga azahar ta yi sai suka sauka, don su yi salla. Baran nan ya tafi gidan mai garin ya gaya masa ga dan Sarki nan zai yi salla a garinsa. Da bayin nan na Waziri suka ga ga shi har asuba ta yi Musa bai ko motsa ba, balle su sami damar gama masa aiki, sai suka sake shawara, wani daga cikinsu ya zo ya durkusa gaban Musa kamar mace, ya ce, "Ana kira ciki." Musa na tsammani baiwarsa ce, sai ya ce, "Je ki, ina tafe," ya koma, Aku ya ci gaba da labarin da ya ke bayarwa, ya yi ta jansa, don kada ya kare gari bai waye ba Musa ya ce zai tashi. Da baran ya wuce, sai ga wata yarinya kamar 'yar Larabawa ta fito daga wani gida kusa da masallaci. Tana leko kai sai duk wurin ya haske, in ka dube ta sai ka yi tsammani ba ta cin abinci don ba alamar ciki. Jikin nan nata kuwa na rantse har da girmanka, yallabai, kamar in ka duba za ka ga bargo. Hancirta 116 ko sai ka ce ita ta yi wa kanta. In da ka dubi idanunta sai ka rantse da Allah ba ta kifitawa, Gashi koMusa ya ce, "Kai, ya isa hakanan. Ci gaba da labari, ka ji ana kirana gida." Aku ya ce, "Ina zuwa." Ya yi ta tsawaita shi: Dan Sarkin nan ya ta da kai, ya dube ta tun daga kasa har sama, sai ya ce a ransa, "An ce dan Adam duk bai cika goma ba, to, yau ga wadda ta kai goma sha biyu." Ya kara dubanta ya ce, "Yam mata, daga ina?" Ta ce, "Daga Waila Fadama. Mun zo biki ne nan jiya, yanzu kuwa da azaharin nan za mu koma." Dan Sarki ya yi mamaki, ya ce, "A Waila Fadama? Wane gida ki ke kuwa har ban sani ba?" Ta ce, "Nan gidan mai garin. Ai ni ce babbar 'yarsa. Ba na fita ne, daga biki sai salla, shi ya sa ba ka san ni ba. Amma ka ga, ni kuwa na san ka. Ko kai ma ba ka rasa jin labarin Nana Yauki ta Waila Fadama ba." Dan Sarki ya yi shiru, ya ce, "Wallahi kuwa, na ji ana labarinta." Та се, "To, ai ni ce." Da dan Sarkin ya ji haka sai ya takale ta da maganar aure, ya ga alamar lalle tana sonsa. Wancan mijin da za a ba ta wai dattijo ne mai gemu, ita kuwa ta ce ba ta auren mai gemu. Bayan sun shirya da ita a nan sai ta tafi. Ya dauki buta a masallaci ya yi alwala, ya shiga ya yi salla. Da yai sallama, ya yi addu'a ga Fiyayyen taliki ya nufa Allah ya sa ya auri wannan yarinya. Don dokin bukatar auren yarinyan nan har ya yi subul da baka ya ce wai in Allah ya nufa ya aure ta ya kashe kansa don murna. Bayan ya fito daga masallaci sai ya tarad da mai garin ya kawo masa sauka. Suka gaisa, ya hau, suka mika da baransa. Suka bi Sarki har suka iske su. Yana tafe yana ba baran nan labarin yarinyar. Da aka kare kewayar kasa aka koma gida. Sai dan Sarkin nan ya gaya wa Wazari yana son su neman masa 'yar Sarkin Waila Fadama da aure. Waziri ya gaya wa Sarki. Aka neman masa, aka ba shi. Aka yi biki aka kare. Bayan sun yi kamar shekara uku da auren, sai ran nan Nana ca ce tana son mijin ya raka ta ta gano gida. Dan Sarki ya gaya wa ubansa, uban ya yarda. Ya sa wani babban bawansa ya raka su, aka yi musu shiri, suka hau rakuma suka tafi. Suna cikin tafiya har suka kai garin da dan Sarkin ya fara ganin Nana, suka yi zancen aure, suka tsaya kusa da masallacin, don ya 117 yi alwala ya yi sallar azahar. Ko da ya shiga ya gama salla zai fara tasbaha, sai ya ji kamar daga bisa an ce masa, "Ina alkawarin da ka dauka, da ka ce in Allah ya nufa ka auri Nana za ka kashe kanka don murna da godiya ga Ubangiji?" Da dan Sarki ya ji haka, sai ya tuna da alkawarin nan da ya yi. Ya duba gabas, ya duba yamma, bai ga mai magana da shi ba, sai jikinša ya dauki rawa, ya yi salati, ya ce, "Lalle baki shi kan yanka wuya!" Sai ya zare takobi, nan ya fille kansa. Ya fadi ya mutu. Da aku ya kawo nan sai suka ji assalatu. Wani daga cikin bayin Waziri ya yi maza ya sake zuwa ya durkusa gaban Musa, ya ce, "Ana kiranka maza maza ciki." Musa ya ce, "Haba, su sai su dami mutum da kira. Ina kika ga zan iya tashi ban ji karshen wannan labari mai dadi ba? In wani abu a ke so, Sarkin Gida, je ka ka gani." Da bawan nan ya ga Sarkin Gida zai biyo shi sai ya ce, "A'a zauna abinka, Sarkin Gida, shi a ke nema. In ba ya zuwa, bari in je in gaya musu." Sai ya koma ya gaya wa 'yan'uwansa, suka yi waje da sauri, suna wa juna barka da Sarkin Gida bai biyo ba, da yau sun bakunci lahira. Suka tafi suka gaya wa Waziri abin da ya faru. Waziri ya ce ku koma su sake kokari, zai kara musu fam goma goma. Suka sake shiga irin ta maza, suka komo. Duk gari an tashi, har rana ta kunno, aku kuwa sai jan labarinsa, ya ke yi: Da Nana ta ga ya dade bai fito ba, sai ta ce wa bawan nan ya shiga ya gani wane irin dogon wurdi ya kama, har yanzu bai gama ba. Da shigarsa sai ya tarad da shi kwance male-male cikin jini, ba kai, ga tokobi can gefe yashe. Ya dafe kai, ya yi salati, ya се, "Yanzu in na fita na fadi abin da ya faru, lalle za a ce ni na kashe shi, Ban ga wata hanya ba sai in kashe kaina nan tare da shi, in an ga haka a san lalle sai da na yi kokarina har na kasa, abin ya faru haka." Sai ya dauki takobin nan ya fille kansa. Ya fadi gefe daya ya mutu. Nana tana waje tana jira. Shiru shiru, ba ta ga wani ya fito ba, ta ce, "Kai, yau fa ga inda na yi ma'aikin kibiya. Abin nan lafiya dai?" Ta kara hakuri dai har la'asar ta yi sakaliya, sa'an nan ta cе, "Ko da mata ba sa shiga masallaci, lalle ni in je in ga abin da ya auku." Sai ta sauka, ta kutsa kai cikin masallaci. Da shigarta sai ta ga mijinta da bawansa duk ba kawuna. Ta ja da baya, ta yi nan ta yi 118 nan, ta fadi ta yi ta kuka. Da ta ga dai kuka ba ya magani, sai ta dauki takobi, ta ce, "Bari ni ma dai in kashe kaina, in huta da wannan bakin ciki, raina dai ba shi da amfani gare ni muddin mijin nan nawa ba ya numfashi." Ta cira takobi za ta sare kanta, sai ta ji an ce, "Tsaya. Dauki kawunansu ki lillika musu, duk sai su tashi." Ta duba gabas, ta duba yamma, ba ta ga wanda ya yi mata magana ba. Sai ta tashi da rawar jiki, ta dauki kawunan ta lillika jikunansu. Ashe cikin dokin ta ga mijinta ya tashi har ta kidima ta dauki kan dan Sarki ta lika wa jikin bawan, ta dauki kan bawa ta lika wa jikin dan Sarki. Sai suka tashi, dan Sarki da kan bawa, bawa da kan dan Sarki! Kowane da mikewarsa sai ya rungume ta, ya ce matarsa ce. To, jama'a, wa kuka gani ke da mata? Bayi suka tashi da gardama haya haya, haya haya, wadansu na 119 cewa mata ta kan dan Sarki ce, wadansu na cewa a'a, mata ta gangar jiki ce. Suna cikin gardamar, ga bayin Waziri tsaye bakin zaure, ba wanda ya san abin da su ke jira sai aku. Sai aka ji tambura Sarki ya tinkaro. Kafin a yi haka, kofar fada ta fara daukar 'yam bushara. Bayin Waziri da suka ga ba dama, suka koma suka gaya wa Waziri, ya yi ta cizon hannu don bakin ciki. Jim kadan Sarki ya kawo, Mahmudu na gaba maroka sun daho shi, sai kirari a ke masa, ana yi masa waka. Mahmudu, jimre ka dau himma, Sai an gwada za a san babba. Zama ga daki na raggo ne. Wan Musa, taso mu je gaba. Mai son fada, duk ya zo nana, Gun Mahmudu, yanzu ya bar wasa. Sinari bana sun tabo wahala, Wan Musa Allah ya jaya ma! Sakaci da tsoro ka yashe su, Duniyag ga ba tai mai wauta. Sinari sun tuba, sun bi ka, Sarkinsu ya zo, ka gafarta. Kyaun saurayi duk ya dau mashi, Don shi da mata a bambanta. Ayyururui! Mutane, mu dau guda, Mahmudu da mai kamar baba. Allah ka dube mu kai rahama,. Allah ka dube mu kai rahama. Allah ka dube mu kai rahama, Ka ji kan mahaifa, mu ce amin! Da suka iso duk gari aka dauki alo alo. Musa ya tafi ya taryi Mahmudu a kofar gida, ya rungume shi, suka yi ta murna. Ya tambaye shi kwana nawa ya yi yana jiyya, ya ce shi ko kaya ba ta taba sukarsa ba tun fitarsa, balle ya yi jiyya. Musa ya yi ta mamaki. Ya tambaye shi batun takardar da ya sha yiwowa, ya се shi bai aiko kowa ba. Musa ya tafi dauko takarda, ya tarar ba ko daya, ashe duk aku ya kwashe su ya boye. Waziri ya zo yana 'yan dararraku, wai shi yana murna. Da aka natsa, aku ya ce wa Musa, "Na ji kana neman takardun da Mahmudu ya aiko maka sa'ad da su ke wajen yaki, ai suna nan na ajiye maka." Ya tafi ya dauko ya kawo musu, suka yi ta karantawa suna tu'ajjibi, suka boye takardun suka kyale. Da gari ya waye, sai suka dauki takardun nan suka kai wa 120 Sarki. Ya duba, ya ce, "Wańnan ai hannun Waziri ne." Mahmudu ya ce, "Hannun Waziri! Karanta ta ka ji." Sarki ya karanta takarda, sai ya rike baki, ya ce, "Me ya ke nufi da wadannan?" Ya juya ga Musa ya tambaye shi yadda aka fara, har aka aiko masa da wadannan takardu. Musa ya ce shi bai san abin da a ke ciki ba, tsammani ya ke Mahmudu ke aiko da su. Ya kwashe abin da aka fara aikowa, da dukan abubuwan da suka auku, da yadda aku ya yi ta rudinsa da labaru har bai sami fita ba, duk ya fada wa Sarki. Da Sarki ya ji haka, ya ce, "Ba shakka akwai magana. A kira aku." Nan da nan aka zo da shi, Sarki ya tambaye shi. Aku ya zauna ya kwashe yadda aka yi duka har da abin da suka yi da Waziri sa'ad da ya aiko a je da shi, da labarin bayin nan da a ke aikowa suna yiwo shirin mata suna zuwa, da abin da ya faru daren da Sarki zai dawo, har ya są suka komo cikin bayin da aka bari tsaro ya rika ba su labari don kada su yi barci, da yadda ya yi ta fama da Musa don kada ya fita, duk ya fadi. Da Sarki ya ji wannan abu, sai hawaye suka zubo masa don tausayin aku, ya dauke shi ya rungume, yana cewa, Yaya za mu yi mu fito wa wannan al'amari?" Aku ya ce, "Duk wadanda a ke aikowa, ko ina suka shiga, in na gan su na gane su. Bari in kewaya wajen gidan Waziri in na ga daya daga cikinsu a kira shi ya zo, in an matsa masa ya fadi abin da suka yi niyya. Da zan sami ganin wata tsohuwa da ta fara zuwa, da ta fi bayyana abin sosai." Sai wani bawa ya sa shi a wuya, suka yi ta yawo unguwar Waziri, da wadansu katta uku kuma suna biye. Suna kawowa kofar wata 'yar rusasshiyar bukka, sai aku ya leka cikin bukkar, ya ce, "Ga ta!" Kattan nan da ke biye suka kutsa kai ciki, suka jawo ta, suka iza keyarta har gaban Sarki. Da Musa ya gan ta ya ce, "I, lalle ko ita ce, wannan aku abin nasa sai a yi shiru." Sarki ya tambaye ta abin da Waziri ya tashi kullawa game da Musa. Tsohuwa ta gigice, ta ce, "Iye, na'am! Allah ya ba ka nasara, wallahi tilasta ni ya yi." Mahmudu ya mike, ya dube ta ya kashe ta da mari, ya cе, "Sarki ke tambayarki, ki gaya masa abin da aka tilasta ki yi." Tsohuwa ta durkusa, ta fede wa Sarki biri har wutsiya. Da Sarki ya ji haka sai ya aika duk dogarawansa suka zo ya ce, "Ku jeku kamo mini Waziri!" Dogarawa suka ruga. To, ashe tun sa'ad da aka kama tsohuwań nan wani ya tafi wurin Waziri, ya ce, "Ranka ya dade, na ga wadansu bayin Sarki guda uku da wani aku sun zo sun kama tsohuwar baiwarka ta nan bayan gida, ko lafiya?" 121 Da Waziri ya ji haka, sai ya ce, "Lafiya mana." Bai sake wata magana ba, sai ya shiga gida, ya sa aka daura masa sirdi, ko rawani bai tsaya nema ba, balle bara. Sai ya hau, ya sulale ta bayan gida ya fita gari, ba wanda ya gan shi. Da dogarwa suka zo, suka fada cikin gida suka tarad da Jakadiya, suka ce, "Ina Waziri?" Jakadiya ta ce, "Lafiya, har cikin gida ba sallama?" Dogarawa suka iza ta, suka ce, "Je ki, ki yi mana iso." Jakadiya ta shiga cikin gida. Jim kadan ta fito, ta ce, "Ai ba ya nan." Dogarawa suna tsammani karya ta ke yi suka bazu cikin gida, wadansu suka tsare kofar zaure. Da suka yi nema ba su same shi ba, suka kama duk bayin gidan suka kai wa Sarki, suka ce ba su ga Waziri ba. Sarki ya ce, "Ya gudu ne." Ya sa 'Yan Doka su hau su bazu ko'ina, duk inda suka same shi su kamo shi. Aku ya dubi bayin nan na Waziri da aka zo da su, ya се, "Ranka ya dade, ga ko shaidu da suka san abin da aka yi." Sarki ya ce, "Ka san su?" Aku ya ce, "Na san bakwai daga cikinsu, har ma ga wanda aka aika gun Sarkin Sinari." Sarki ya ce, "To, nuna mini su." Aku ya tashi ya ce wa wani dogari, "Da wannan da wannan, kai su nan. Wadannan, ku ku komo nan. Kai, wancan da ke noke kai, komo cikin wadannan." Ya dubi Sarki, ya ce, "Ga su. Wadannan, su aka ce su boye nan kofar gida in Musa ya fito su kashe shi. Wadannan, su suka wo shirin mata suka zo shekaranjiya, daren da za ka dawo. Wannan ko," (ya nuna Barakai) "shi ne babban munafukin, shi aka fara aika wurin. Sarkin Sinari ya nuna musu hanya. Shi kuma ne ya, shigo cikin gida bayan tsohuwan nan." Da bayin nan suka ji haka sai suka dauka. "Wallahi, karya ya ke yi. Allah ya ba ka nasara, mun rantse har da rawaninka ba mu taba shigowa nan ba." Sarki ya dubi dogarawa, ya ce, "Ku tambaye su." Dogarawa suka same su da duka, suna ihu. Sai Barakai ya се, "Ni zan fadi gaskiya, na sai da raina don ubangijina ya yaba, ban sami kome ba sai duka, nan kuma in zo haka?" Sai ya kwashe duk al'amarin ya gaya wa Sarki. Sauran da suka ga ba dama, su ma suka faďi gaskiya. Sarki ya sa aka daure su cikin gidansa. Aka kwana biyu, rana ta uku da azahar sai ga 'Yan Doka sun zo da Waziri, sun kamo shi can kan iyaka, ya kusa ketare kasa, ya nufi Sinari. Da aka zaunad da shi gaban Sarki, sai ya bata fuska, ya tashi da fada ya dubi Sarki yana cewa, "Na mene ne za a aika 122 'Yan Doka su kama ni, ban ci kayan kowa ba?" Sarki ya tashi da mamaki, yana tafa hannu yana cewa, "A'a! Ashe kamo ka suka yi?" Waziri ya harari 'Yan Doka, ya ce, "Kamo ni suka yi mana." Sarki ya ce, "Ni ban ce su kamo ka ba, cewa na yi su kira ka, in ji ko lafiya, don tun shekaranjiya waccan rabona da ganinka. Da Waziri ya ji maganar lumana sai ya ce a ransa, "A'a! Ashe da ma asirina bai tonu ba na ke son tona kaina a wofi. Da ma na san Sarkin nan gabo ne, ba ya gane kome. Kuma ko ma ba wawa ba ne, irin makircina ai ba mutum duka zai gane shi ba." Sai ya ce, "Af, ashe Shamakina bai gaya maka ba?" Ai na tafi ganin wata goggona ce da aka aiko mini ba ta lafiya. Amma dai, Allah ya ba ka nasara, 'Yan Dokan nan sun karya mini irli." Sarki ya ce, "Sai ka yi hakuri da su. Da ma ina gaya maka sakarkaru ne, kai ke cewa suna da kirki." Waziri ya harari 'Yan Doka, ya ce, "Na rantse har da girmanka, ba na iya yafe musu, tun da suka ci zarafina haka. Su duk sai a daure su yanzu. Ko mahaukaci ai ya san abin da ya kamata. Sarki ya ce, "Ai kai ne da mulki, sai ka yi abin da ka ga dama da su. Amma bari in tambaye ka abin da ya sa na kira ka tukun. Tun da na dawo ban sami damar tambayarka wani abu ba game da gidana da na bar maka amana." Waziri ya ce a ransa. "A'a! Ka ji tsohon banza da wata irin tambaya." Sai ya dube shi, ya ce, "Ka tarad da wani abin tashin hankali ne? Ai ni ban yi wasa da gidan nan ba, da kaina na ke fitowa da tsakad dare in kewaya." Sarki ya ce, "Na san haka. Amma wadansu takardu ne aku ya nuna mini wadanda ban gane kansu ba." Ya dubi aku, ya се, "Je ka, kawo su." Aku ya tashi ya kawo su, ya zube gaban Sarki. Da Waziri ya ga takardun nan, sai cikinsa ya ba da kulululu. Ya dauke su yana budawa, yana dariya, yana cewa, "Wani ne ke kwaikwayon hannuna. In ka bibiya ma shegen akun nan ne. Amma, Allah ya ba ka nasara, ya kamata a tsawata masa, in zai yi wasa, ya rika yi da tsarar-rakinsa su ungulu da jemage!" Ya fashe da dariya, wai shi gwanin ba'a. Ya daga kai ya dubi Sarki, ya ga shi bai yi dariya ba. Ya dubi Musa, ya ga shi ma hakanan. Ya juya ga Mahmudu, ya ga kowa kinne. Aku ko ma, sai wasansa ya ke yi da kwayar gyada, kamar bai ko ji abin da a ke fadi ba. Sai idonsa ya raina fata. Sarki ya dubi Sarkin Dogarai, ya ce, "A zo da mutanen nan." Dogarawa suka duru da gudu cikin gidan Sarki, suka fito da 123 bayin nan na Waziri, kowanensu an bankare shi. Da Waziri ya gan su sai gabansa ya fadi. Ya gyara zama, ya duba gabas ya duba yamma, ya ga kowa ya kura masa ido. Sarki ya dube shi, ya ce, "Ka san wadannan?" Waziri ya ce, "Allah ya ba ka nasara, na tuba, na bi Allah, na bi ka!" Sarki ya ce, "Me ka yi mini na tuba? Cewa na yi ka san su?" Waziri ya ce, "Ka ji kaina, ka yafe ni, ba don halina ba!" Mutanen gari da aka tara suka yi ta duban Waziri, ba su san abin da a ke ciki ba. Mahmudu ya tashi, ya kashe Waziri da mari, ya ce, "Sarki ke tambayarka, ka san su, ka dame shi da magiyar banza!" Waziri ya dubi Barakai, ya ce, "Kai ne amintaccen bawana, don Allah bayyana musu sosai, su san ba ni da laifi cikin wannan al'amarin." Barakai уa сe, "A'a! Ba ka da laifi? To, wa ke da shi?" Makirin banza!" Ya gusa gaba, ya daga murya ya fadi duk makirce-makircen da Waziri ya kulla game da Sarkin Sinari, da game da Musa, bai rage kome ba. Da mutane suka ji haka sai suka yi salati, suka taso wa Waziri gaba daya kamar za su cinye shi danye, sai da dogarawa suka shiga tsakani. Sarki ya ce musu, "Ku dakata tukuna, ai ba a kare ba." Shi kuma ya kwashe labarin yadda aku ne ya yi ta kokari ya kubutad da su daga zama bayin Sarkin Sinari. Ya kuma gaya musu yadda ya hana Musa ya fita waje, don ya gane abin da Waziri ke kullawa. Da mutane suka ji haka sai ya ga kowanensu ya yi ta tafa hannu, suka dubi aku, suka dubi Waziri. Sai suka fara dibar kura za su yi masa ature, sai da Sarki ya tsawata. Da suka dakata ya sake dubansu, ya ce, "To, jama'a, ku dubi laifin nan na Waziri. Wanda ya aikata haka me ya kamata a yi masa?"" Jama'a suka dauka gaba daya, "Sai a tsire shi! Da shi ai halaka mu ya tashi yi, don Allah ya ki nufinsa. Da ma ba mai kaunarsa garin, don mugun halinsa." Sarki ya ce, "Na ji tasa. To, wadannan mutanen ko fa?" Jama'a suka ce, "Su ma sai a tsire su, abin da ya ci Doma ai ba ya barin Awai." Musa ya ce, "A'a, tun da dai Allah ya ki aniyarsu, ya gama fuskokimmu da Mahmudu lafiya, ga shi kuma Sarki ya ciwo nasara, sai a yafe su." Sarki ya ce, "Gaskiya ne, Musa. A kwance su." Aka sake su, suka zo suka fadi gaban Sarki suka yi godiya, don da sun tabbata 124 za a kashe su. Mutane suka yi mamakin Sarki a kan wannan nasiha. Sa'an nan Sarki ya tashi tsaye, ya ce wa jama'a, "To, mun ga inda wadannan tasu ta kwashe. Amma ina tambaya, shin don me a ke yin Waziri?" Jama'a suka ce, "Don ya rika taimakon Sarkin gari shawarа, yana kwabe abin da zai cuci jama'a, ba kamar wannan ja'iri ba. Allah ya kiyashe mu da halinka!" Sarki ya ce, "In don haka ne, na nada wannan aku Wazarina. Da shi zan rika shawara." Ya dubi mutane, ya ce, "Ko kuwa kun ga bai isa a yi shawara da shi ba, don yana tsuntsu?" Jama'a suka ce, "Wane irin isa? Wanda ya yi wadannan abubuwa a ce bai isa ba? Wannan tsuntsu ai baiwa ce Ubangiji ya nufe mu da ita, wa ke da ikon jayayya da nufin Allah? Mu dai wallahi mun so, mun so." a Sarki ya dubi dogarai ya ce, "A kama Waziri, a daure shi cikin jaka da ya bayar a sa Musa, a tafi da shi a jefa cikin kogi, yadda ya yi niyyar yi wa Musa. Ku kuwa Sarakunana da makada, a tafi kai Waziri Aku gidan Waziri, a fid da matansa na aure, sauran ko duk abin da ke gidan an ba shi." Sarki ya tashi ya shiga gida. Duk fada ta yamutse, wadansu suka nufi wajen da za a kashe Waziri, wadansu suka bi sabon Waziri, ana ta goce ganguna da kakaki. Aku kuwa yana bisa wata karaga ta zinariya, an sa laima, katta na dauke da shi. Sai makada ke ta binsa suna waka: Haba jama'amu, ku zo mu yi caffa, Gunsa Waziri, mazajen aiki. Masu rabo da yawa mai ba mu! Sannu da sirdi, tsuntsun kirki! Da ba don shi ba, masu fasaha, Da yanzu da muna Sinari. Ga wani sauna, don sakarci, Ya yi butulci, ya bashe shi. Ikon Allah wa zai ki shi? Kowas saba yai jahilci. Ka sai mana doki, baba Waziri, Muje mu gwada wa mutan Sinari. In ba donka ba, mai cika aiki, Da wani mun ga irin bautanshi. Masu fasaha, masu basira, Mai tauhidi, Sarkin ilmi! Ga ni a durkushe, na roke ka, Ya Allahu ka gafarce ni. 125 Aka kai aku gidan Waziri, ya debi dawaki uku daga cikin wadanda ya samu gidan Waziri, ya ba makada da suka rako shi. Ya sa bayi su yi ta gadinsa. Aka yi ta shagalin sarauta har kwana bakwai. Da aka natsa, Sarki ya sami matan aku guda hudu ya sai wa sabon Waziri. Duk inda Sarki ya ji wani na da aku, in mace ce, sai ya sayo ya kawo wa Wazirinsa, watau kwarakwarai. Ana nan, bayan 'yan kwanaki daya daga cikin matan nan na Waziri Aku ta yi kwai. Bayan kamar kwana ashirin ta kyankyashe wani dan aku namiji. Ya sa masa suna Fasih, ya sa wani bawa ya yi ta kiwonsa. Waziri Aku ya yi zamansa, yana tą muskakar sarauta. Ba уа shan ruwa sai da sukar, shinkafa ko ba ya cinta sai an dafa an sa gishiri da mai: 126 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels